[4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/L3FON3yJGYpBg3fVdxikGe *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 1 Kwance take a jikin sa ta yi lifet tamkar mage, bacci suke mai cike da farin ciki Saddiqa da Aminu kenan ango da amaryar da suka tare a daren jiya. Cikin baccin nata ta ji wani uban wari ya baibaye hancin ta, kasa jurewa ta yi ta ɗan fara juye-juye jim kaɗan dai ta ji warin ya ƙaru tamkar an saka hancin ta a ɗakin da mushe yake a ciki. A ɗan gigice ta tashi zaune ita gabaɗaya yanayin warin ma ya sa ta manta cewa ita fa amaya ce kuma tare da ango suke kwance. Da yake bata wartsake ba sai ta yi zaton a gidan su ne da yake a gidan su katifa ɗaya suke kwana da ƙanwar ta Noor hannu ta kai ta ɗakawa angon duka a baya duk tunanin ta Noor ce, tana ɗaga dukan ta buɗe bargon da sauri ta fito cikin sauri ta sakko daga kan gadon ta fito daga ɗakin don gabaɗaya warin ya hautsina mata ciki har wani ɗaci take ji a maƙoshin ta. Ƙololon amai take yi don a lokacin da ta sakko da ta buɗe bargon ta ankara da a she fa a gidan ta take kusa da ango, kunyar dukan angon nata ce ta kamata sai dai yadda warin ya cika ɗakin ba za ta iya tsayawa ba, don lokacin da ta kai dukan ma sai da ya saki wata tusar. Ango kuwa cikin bacci ya ji an ɗaɗa masa duka a baya, sakin tusar da ya yi ya yi daidai da tashin sa zaune sai dai da yake amarya tana buɗe bargon ta fita sai ya zamana shi kaɗai ne a cikin bargon, shi ma jin warin da ya cika cikin bargon sai ya buɗe ya fito yana shaƙar gurɓatacciyar iskar ɗakin don gabaɗaya ma ɗakin ya haɗe da warin. Saddiqa tana gama ƙolon aman duk da bata amayo komai ba haka ta dawo falon ta zauna a kujera tana mamakin warin tusar nan don ta kasa komawa bedroom ɗin. Tana zaune sai ga Aminu ya fito daga ɗakin da yake tun fitowar ta ta kunna fitilar falon yana fitowa ya yi tsaye a tsakiyar falon hannu biyu ya ɗaga sama yana miƙa bakin nan hangame yana hamma cikin hamma yana salati. "Baby!" Ta kira shi tana kallon sa. Kiran da ta masa shi ya katse masa hammar ya juyo kawai sai ta ji ya ce "Haba Saddiqa sau nawa kike so na maimaita miki cewa na tsani sunan nan haba tun kafin mu yi aure na ce miki ni fa ba na sha'awar wannan sunayen yahudawan ina dalili ga sunan da aka yanka mini rago amma ake wani kira ni Baby kamar yaron goye" Ya faɗa yana dawowa kusa da ita ya zauna. Bai jira ta ce wani abu ba ya miƙo hannu zai rungumo ta ta ɗan moƙe. "Haba Saddiqa sai ka ce wani ba mijin ki ba za ki kauce daga rungumar da na kawo miki?" Ya tambaya yana kallon ta da ɗan mamaki. "Wai yanzu Bab.... "Wai ba na ce ba na son sunan ba na yahudawa ba za ki daina faɗa ba, uhmm ke mai sunana na Aminu ya miki ne da ba za kike faɗa ba" Ya faɗa yana ɗan kallon ta irin na lallashin nan. "Yanzu don ina kiran ka da sunan soyayya shi ne yahudanci? Yanzu daga tarewa ta a gidan ka jiya har za ka fara ɓata mini rai ashe abin da ake faɗa na cewa zaman haƙuri ake yi ashe haka ɗin ne? Sai in ji ana cewa wuyar ta a yi auren daga an yi auren shikenan, wasu ma su ce auren ya yi ƙarko bai fi ya yi wata biyu ba za a fara ƙunsa maka baƙin ciki shi ne ni tun daga kwana ɗaya abubuwan da nake jin su ya wai za su fara bayyana a nawa zaman auren" Ta ƙarasa faɗa tamkar za ta yi kuka. Kallon ta ya yi sai kuma ya ɗan sasauta murya ba kamar yadda ya yi magana ɗazu ba ya ce. "Ni fa ba wani abu ba na ce kawai sunan nan ne na ce bana so kuma kin san tun kan mu yi aure ina faɗa miki ba na son iri-iren waɗannan sunayen. "Tashi mu je mu kwanta, muna baccin mu mai daɗi kika fito kika bar ni har da dukana a baya ko bakya so na yi baccin irin na angwaye?" Ya tambaya yana kallon ta. Murmushin yaƙe ta saki tana tunanin shin bai san mai ya yi ba har ta tashe sa ɗin. "Wallahi Bab..." Shiru ta yi ta fasa faɗar sunan Baby da ya hana ta, ba don tana so ba don ita mace ce mai son soyayya da nuna kulawa ga masoyi. "Wani wari ne fa ya tashe ni, na ji duka ɗakin ya ɗumame da wari" Ta faɗa cikin wayincewa don bata so ƙiri-ƙiri ta nuna masa cewa tusa ya yi. "Ko dai ɓera ne ya mutu?" Ya yi furucin yana kallon ta. Kai ta girgiza alamar a'a. "Ina ga fa nine na samu sacewar iska(Tusa) Ina cikin bacci ba tare sa na sani ba" Ya faɗa yana ƴar dariya don ya gano ta gane tusar ya yi tun da ga shi da ya ce ɓera ne ta girgiza kai. Idanu ta ɗaga tana kallon cikin idanun sa. "Jiya ne a gida suka yi faten wake shi ne na cika cikina da shi kin san ina son faten wake" Ya faɗa. Idanun ta ta rufe tare da buɗe su a kansa ta ce "Ango da cin faten wake a ranar ɗaurin auren sa" Ta faɗa tana murmushi. "Kin san an ce zuciya da abin da take so" "Haka ne" Hannun ta ya kama a cikin nasa tana jin wani son sa a ranta tabbas tana matuƙar ƙaunar Aminu hakan ne ya sa ya yi fice tare da yin zarra ga sauran maneman ta. Tashi suka yi ya kashe fitilar falon tare da riƙo ta suka nufi ɗakin, zuwa lokacin warin ɗakin ya fita sai dai ɗan abin da ba a rasa ba. Komawa suka yi suka kwanta cikin ɗorawa da cin amarcin su. Da asuba suka shiga bayin cikin ɗakin wanka suka yi, tana yin alwala sai ta ga zai fita daga bayin. "Ya na ga za ka fita baka yi alwalar ba?" Ta jefa masa tambayar don dama ko jiya ma da za su yi wanka da daren ita ce ta ga bai ɗaura alwala ba zai yi wankan tsarki don kai ya fara wankewa sai da ta tambaya ya wayince yana ɗaura alwala kamar yadda ake alwalar sallah sai da ta ce masa kai da za ka yi ɗai-ɗai ma'ana kowace gaɓa sau ɗaya za ka wanke a maimakon alwalar da ake ta yin sallah wacce ake wanke kowace gaɓa sau uku. Haa dai ya ce wai mantawa ya yi saboda kansa yana ciwo na taron ɗaurin auren da aka yi shi ya sa ya sha'afa. Duk da wankan ma bai wanke ɓangaren dama da ban na hagu da ban ba, duka jikin ya shiga wankewa sai da ta nuna masa ya ce wai duk mantawa ya yi amma dai yanzu ta ga ya yi wankan tsarkin daidai. "Au da fa wai sai na je na shirya in zan yi sallar sai na dawo na yi alwalar" "Kawai ka yi kayan ka" Da to ya amsa mata ya dawo ya yi alwalar suka fito kayan sa na jiya da ya zo da shi wacce ta ga ita ce shaddar da ya saka da yamma da suka je da abokan sa aka yi hotuna. Bata tanka masa ba ta ɗakko doguwar rigar ta saka ta shimfiɗa sallaya tare da ɗakko qur'ani ta ajiye a kan sallayar daga gefe. "Ya kika shimfiɗa sallayar ɗaya?" Da mamaki ta ɗago tana kallon sa. "Nawa zan shimfiɗa?" Ta tamabaye shi. "Ni kuma fa? Kin san dai ai mace da namiji ba sa sallah a jere a sallaya ɗaya tun da dai nine zan mana limanci" "Wai kana nufin a gida za ka yi sallah?" "A ina zan yi to?" "Haba dai!. Kana namiji mai zai haɗa ka da sallah a gida kuma, ga shi can ana shirin shiga masallaci, don na ji an buɗe ƙofar gida ɗazu ma wataƙila ƴan uwanka ne suka fita( Da yake gidan ɓangare uku ne, nasu sai na Yayan sa Shafi'u wanda yake zaune da matar sa Sumayya da ƴarsa Ruma, sai kuma ɗaya Yayan nasa Sule da matar sa Amina, suna da yara biyu Yusuf, da Albani). "Yo ni ba ango ba ne" "Shi ango ba zai yi sallah a jam'i ba saboda kana ango sai ka yi asarar sallah a jam'i?" Ransa ne ya ɓaci ya ga alama in bai zage dantse ba Saddiqa za take juya shi a cikin gidan, amma ya bar wannan ɗin a farkon amarci amma da sannu zai fara nuna mata kudu ba arewa ba ce. Bai ce uffan ba ya juya a ƙufule ya fita sani ne bata yi ba shi addinin kansa ma bai damu da shi ba bata san ƙasurgumin ƙazami ne kuma jahili wanda bai damu da ibada ba. Tana idar da sallah tana zaune za ta fara karatu ta ji shigowar sa ko sallama bai yi ba, da alama ma ana sallamewa ya taso ko azkar bai yi ba don ta ji shi ne farkon dawowa don bata ji ƙaran shigowar sauran ba. Ɗagowa ta yi ta kalle shi shi kuwa bai ma lura da kallon da take masa ba gadon ya haye da yake a bedroom ne take. Shame-shame ya yi a kan gadon ya ja bargo ya rufe iya jikin sa ban da kansa cikin wata murya ya ce "Amarya ta ango to a taho a fara aikin lada" Bata tanka masa ba ta ɗauki qur'ani da yake irin mai izu goma-goma ne mai guda shida a ciki. Tasowa ta yi ta miƙa masa. Da mamaki yake kallon ta cikin ɗan diriricewa ya kalle ta don yana fatan dai ba ɗori za ta ce ya mata ba don idan haka ne ta ɗakko dala ba gammo. "Ka karɓa ka karanta ko izu biyu ne" Amon muryar ta ya katse shi. Idanu ya kafe ta da su yana kallon ta ya ce "Wai karatun ma sai kin saka ni Saddiqa? Lokacin muna yara muna zuwa islamiya in ban manta ba a hadisi na ɗaya da ake mana ana cewa dukkan ayyukan ibada basa iyuwa sai da niyya" Ganin ya hayyayƙo mata sai ta juya jiki sanyi ƙalau ta koma kan sallayar ta zauna tare sa yin bismillah ta fara karatun suratul yasin a bayyane. Aminu da ya koma ya kwanta ya ja bargo ya ji karatun nata zai hana shi bacci ya ɗago ya ce "Wai kike yi a zuciyar ki mana" Ko juyowa bata yi ba ta fara karatun a hankali don ta ga abin nasa ya fara wuce gona da iri a ce mutum hatta sautin qur'ani ba ya so. "Ki rufe qur'anin nan ki zo mu kwanta" Maganar sa ta katse ta HAJIYA BAKI DA LABARIN HAJIYA MEERAH ME KAYAN MATA KUMA LIKITAR MATA? IN KINA DA ZAN ƘARA MIKI SANI IN KUMA BAKI DA ZAN SANAR DA KE. BAKI TAƁA GANI ANA TALLAR KAYANMU A AREWA 24, KO TAURARUWA KO HIJRA BA? KAYANMU BABU INDA BASA ZAGAYAWA A FAƊIN DUNIYA MUNA AIKAWA KO INA SAYEN ƊAYA KO SARI HAUSAWA SUKA CE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA🤗 GA LIST ƊIN KAYANMU KAWAI IN KINA SO KI MINI MAGANA SANNAN AKWAI GRP DA MUKE TURA KAYAN GA MASU SON SHIGA DON SU GA HOTUNAN KAYAYYAKIN MU👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* MAMAN AFRAH 09013181851 [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/L3FON3yJGYpBg3fVdxikGe *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 2 Babu yadda ta iya haka ta yi addu'a ta naɗe sallayar ta mayar da qur,anin ta je wajen nashi. Gari yana fara haske ta shiga ƙoƙarin raba jikin ta da nashi, amma ya riƙe ta ya hana ta yinƙurin hakan. Jin bata daina kiciniyar ƙwatar kan nata ba a hankali ya buɗe ido ya ce "Ina za ki je?" "Wanka zan yi in yi gyaran ɗaki sai na dafa abinci" Galala yake kallon ta. "Don wankan tsarki dai da ba wani wahala gare shi ba Saddiqa sai ki bari kya yi anjima, kuma yanzu ɗakunan nan sabbi ina suke buƙatae shara, kuma abincin sai mu ci kaza da lemon jiya in kuma bakya son ci ko waina sai na siyo " "Ai har wankan sabulu zan yi ni dama daga gari ya waye nake wanka, don ni a ƙalla sai na yi wanka sau huɗu watarana har biyar ma" Cike da mamaki yake kallon ta can dai ya yi ƙarfin halin cewa "Wai a wata kike wankan sau biyar ko a shekara?" "Wata? Shekara?" "To ai na san dai ko a sati ba a yi wanka sau biyar ba" "To a rana nake nufi" Sai da ya ɗan ɗago yana kallon ta sosai. "Wankan ne kike sau biyar kamar baki da aikin yi" "Rashin aikin yi ne? Tsafta ce fa" Bata ƙara magana ba ta shige bayi ta yi wankan tsarki ta ɗore wankan sabulu, yana ta jin tana ta dirzar jikin ta tamkar wacce ta yi wata jikin ta bai ga ruwa ba. Sai da ta gama ta fito. "Wai amma sabulu a gidan ku ba ya wata ko Saddiq" "To ajiyar sa za a yi dama ba don a yi wankan aka siya ba" Shiru ya yi bai ce komai ba shiryawa ta yi ta saka doguwar rigar atamfa ta sha ɗauri sai bulbula ƙamshi take. A bakin gadon ta zauna tana ɗan jifan sa da kallon soyayya. "Wai Bab... Bata ƙarasa ba ta tuno ya hana ta kiran sa da Baby. Sai da ya tashi yana shiga bayin ta yi saurin gyara kan gadon ta ɗakko tsintsiya ta shiga sharewa kafin ya fito ta share ɗakin ta dawo falo tana sharewa sai ta ji ya fito kamar yadda ta zata hakan ce ta faru domin kuwa iya wankan tsarki ya yi. Tana son cewa mai ya sa bai yi wankan sabulun ba amma tana jin kunya. "Tun jiya nake wanka wannan ne na uku ita ƙazantar da kanta ta san bata isa tsayawa a jikina ba, ba sai na sanya sabulu ba" Ya faɗa tamkar ya san tunanin da take. Ita dai tana ɗan mamakin a ranta amma sai take tunanin ko sai daga baya zai yi, kaya ya saka bayan ta gama gyaran ɗakin ta ɗakko sauran kazar jiya ta je ta ɗumama musu, tana ta ƙarewa gidan kallo, tana hango ɓangarorin facalolin nata. Da yake dama ta taɓa zuwa gidan sau ɗaya amma sai dai da daddare ne da ya kawo ta ta yi musu sannnu da shan ruwa a ramadan, to ta shiga ɓangaren kowacce sun gaisa sannan da za ta tafi sun rako ta, wannan ne sanin junan da suka yi. Haka suka yi ta hirar su sai wajen sha biyu ya fita zuwa gidan su. Bayan fitar sa ne tana zaune rana ɗan danna waya Sumayya ta shigo da sallama amsa mata ta yi suka zauna suna ɗan taɓa hira, cikin hirar tasu ne kamar an ce ta kalli kafaɗar Sumayya abin da ta gani ne ya bata mamaki, hannun bireziyar Sumayya da ya leƙo ne baƙiƙƙirin da shi daga gani kuma fara ce bireziyar amma tsabar datti duk ta dafe. 'Ikon Allah, ita kuwa wannan mai ya sa take saka abu da datti haka?' Saddiqa ta faɗa a zuciyar ta tana jin wani iri don ita a duniya ta tsani ƙazan ta, abin bai tsaya a nan ba tana sauke idanu a ƙasan zanin ta ga shi ma ya ci uban datti da alama ma an yi ta saka a atamfar. Mamaki take da tunanun ita kuwa bata jin kunya mijin ta ya ga hannun bireziyar ta ko ƙasan zanin. "Amarya an kwana a baƙon waje" Muryar Sumayya ta katse mata tunani. Murmushi ta yi ta ce "Wallahi kuwa, ni ina Ruma?" Ta tambayi ƴarta. "Ruma bacci take ne" "Amina fa?" "Ban ji motsin ta ba tana ɓangaren ta" Haka suka cigaba da taɓa hira daga ƙarshe ta tafi. Da yamma ta yi ta yin baƙi maƙota da ƴan uwa masu zuwa ganin gidan amarya, da yake shi ma angon tun da ya zo ya ci abincin rana ya fita ganin tana ta yin baƙi. Sai bayan sallar isha'i ya dawo gidan. *BAYAN KWANA BIYU* Da yamma tana zaune tana yankan farce sai Ruma ƴar gidan Sumayya, da Yusuf da Albani ƴaƴan Amina suna wasa. Kallon yaran Amina ta yi tastas da su gwanin sha'awa amma Ruma hancin ta maji duk ta bushe ga kan nata duk kalbar da aka mata ta tsufa wandon ta kuwa sai zarnin fitsari yake, kwata-kwata ƙazantar jikin yarinya ta yi yawa ba don kar a ga baƙin ta ba da ta kora yarinyar wajen uwar ta don ita ba mutum ba ce da take son ƙazami ya raɓe ta, don ko tana gida in dai yaran maƙota suka shigo to kuwa indai kai ƙazami ne gidan ku take kora ka. Da sallama ya shigo ta amsa, don dama danta masa maganar ya ɗan huta ko sati guda ne sai ya cigaba da zuwa kasuwar cewa ya yi babu wani hutun amarci da zai ɗauka ai maza ƴan su fita su nemo a ci ne. Jikinsa buɗuɗu da fulawa, da yake sana'ar sa aunar da filawa ce, a can kasuwa gaban wasu shaguna yake buɗe buhun filawa yana aunarwa, idan ya ƙare sai ya sake buɗe wani. Sannu da zuwa ta masa ta karɓi ledar hannun sa, sai kallon ta yake yadda ta masa kyau ta yi kwalliyar ta cikin baƙar abaya sai ƙamshi take bakin nan nata yana sheƙin lipstic. Kicin ta nufa da ledar ta ware kayan miya ta saka a kwando ɗaya ledar kuma kayan marmari ne sai ta saka a frige, ta wanko wasu ta yanko a plate ta zo ta ba yaran, suna karɓa da murna suka fice. Kayan abincin ta ɗakko ta ajiye masa a falon tare da ruwa sai ta nufi bedroom ɗin, kwance ta same shi a kan gadon. Ta ji babu daɗi ganin jikin sa babu yadda yake duk filawa amma ta hau kan gadon danne abin da ta ji a ranta ta yi, bayi ta nufi tana shirin shiga maganar sa ta katse ta. "Baki yi sallah ba ne?" "Sallah kuma?" "Eh na ga kin nufi bayi" Ya faɗa yana kallon ta shi tana birge shi yadda take ƴar gayu. "Ruwan wanka zan haɗa maka" Shiru ya ɗan yi sai kuma ya ce "Wane irin wanka da la'asar ɗin nan, bakya ganin sanyi ake ai sai mura ta kama mutum" Da mamaki take kallon sa kawar da kai ya yi gefe ya kuwa maje. "Yanzu haka za ka zauna kalli jikin ka fa, jiya ma fa da na haɗa maka ruwan cewa ka yi la'asar ta yi ba za ka yi ba, kuma fa akwai ruwan ɗumi ba na sanyo ba ne" "Haɗa" Ya ce a taƙaice. Juyawa ta yi ta shiga ta zuba ruwan ta fito ta ɗakko na zafi ta haɗa masa, brush ɗin sa da ta goga masa makilin da safe ta gani bai yi ba ta wanke brush ɗin ta sake tatsa masa makilin ɗin ta fito. "Na haɗa maka" Da to ya amsa da kamar ba zai tashi ba sai kuma ya tashi ya tuɓe kayan jikin sa daga shi sai gajeran wando ya shiga bayin ya rufo. Ya ɗan jima da shiga amma bata ji alamar kwara ruwa ba jim kaɗan ta fara jin alamar taɓa ruwa, can sai ga shi ya fito amma abin mamaki fuska, hannaye sai ƙafafun sa ne kaɗai suka san ya taɓa ruwa da alama wankin jiki ya yi ba wanka ba. Wani takaici ta ji a ranta ta rasa mai ya sa Aminu ba ya son yin wanka ta lura ko kaɗan ya ƙi jinin zuba ruwa a jikin sa. Ita kuma tana ɗan jin kunyar sa shi ya sa ba ta iya faɗa masa hakan yana damun ta. Shi kuwa yana fitowa ya wani haɗe rai yadda ba za ta ga fuska ba bare ta ce wani abu mai ya ɗauka ya shafa abin sa ya ɗauki singlet ɗin da ya cire ya mayar ya ɗakko wata jallabiya ya saka. "Mu je ki zuba mini abincin" Ya ce bai jira cewar ta ba ya fita falon, shiru ta yi tana zaune a wajen, ita da a gida idan Noor bata yi wanka ba in za ta kwanta ta ringa mata bala'i a kan ba za ta kwana shimfiɗa ɗaya da ita ba sai ga shi jiya ta kwana da wanda bai yi wanka ko sau ɗaya da sabulu ba a rana, yau ma kuma da alama tarihin jiyan zai maimaita kansa. Kamar wacce aka tsikara haka ta tashi bayin ta nufa ta leƙa brush ɗin sa yana nan kamar yadda ta ajiye wai don ma kar ya ce bai gani ba a kan buta ta ɗora masa kusa da kwandon wankan amma bai yi ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin babu daɗi. "Saddiqa" Ta jiyo muryar sa yana kiran ta. Amsawa ta yi ta nufo falon tana ƙirƙirar murmushin yaƙe. "Amarya, amarya" Ya ce yana kallon ta. Bata ce komai ba ta zuba abincin ta tura masa, ya fara ci ruwa ta ɗakko ta zuba masa ta koma gefe tana ɗan tunani, ita yanzu damuwar ta bai wuce rashin wankan sa ba. A daddafe ya gama ana magriba har ya miƙe a falon sai da ta masa maganar sallah sannan ya tashi yana ɗan jin kunya ya shiga bayi zai yi alwalar ita kuma ta fito da kayan zuwa cikin. Shafi'u ta gani ya fito daga part ɗin su ya zo da fita da alama masallaci zai je don a kallo ɗaya da ta masa ta ga alamar ruwa hakan yana nuni da alwala ya yi. Farin yadin da yake jikin sa wanda a kallo ɗaya ta gama tantance wanke yake tas ga karin guga, wani ƙamshin turare da ya buɗaɗe hancin ta mai sanyin ƙamshi ya sa ta ji a ranta ina ma Aminu mijin ta ne yake gyara kansa haka. Tun zuwan ta gidan bata taɓa jin wani nau'i na ƙamshi daga jikin sa ba, ko da a ce ta ɗakko turaren ta ta ce ya shafa ko kuma ta yi ƙoƙarin shafa masa in zai fita wajen sana'a sai ya ce shi ba ya son asarar abu, wanda zai je ya sha rana wajen sana'a ina shi ina wani turare, haka idan za su kwanta tana ƙoƙarin ya shafa sai ya ƙi ko ya ce wai turaren juya masa kai yake ko kuma ya kawo mata wata hujja marar madogara. "Yaya Shafi'u ina wuni" Ta gaishe da shi. Shafi'u kuwa tun da ya fito ya hango fitowar ta ya ƙura mata idanu haka kawai ya ji ta birge shi ganin ta cikin tsafta da kwalliya. Amsawa ya yi ta yi gaba tana jin yadda idanun sa yake yawo a jikin ta. Ko da ta dawo shi ma ya fito ɗaure da alwala. Kayan da ya dawo da su daga kasuwar su ya mayar sai dai yanzu ta ga babu farin fulawar a jiki sosai da alama ya karkaɗe ne. Murmushi ya sakar mata, bata ankara ba sai ji ta yi ya zo ya kawo mata wata wawar sumbata a kunci kusa da bakin ta, idanu ta ɗan runtse jin wani gumus ɗin bakin sa da ta shaƙa. Bakin sa ya janye yana ƴar dariya ya ce "Kin ƙi sakin jiki da ni sai kike jin kunya, ina mijin ki mene ne na runtse idanu. Murmushin yaƙe ta ƙaƙaro ya juya da sauri jin an fara sallar, ɗaki ta shiga ta yi alwalar ta gabatar da tata sallar. Haka da dare ma ya zo mata tashin wani hamamin gumi don ban da warin rana babu abin da yake tashi daga jikin sa, haka ya zo neman haƙƙin sa ita kuma tana ƙamshi ta tsaftace jikin ta da bakin ta, rungumar da ya mata kanta a wajen hamatar sa sai da ta ji har wani juyawa kanta yake saboda wari, da ya haɗe bakin su kuwa gabaɗaya numfashi ma sai da ya gagare ta tamkar an saka hancin ta a wurin kashi haka ta ji tabbas warin baki babu daɗi ga shi Aminu yana da rami a haƙorin sa irin abin nan da ake kira da kogon haƙori wanda wasu suke cewa tsutsar haƙori ce take cinye wajen. Abincin yana shiga wurin idan har mutum ba ya wanke baki tare da fitar da abincin da ya maƙale to kuwa warin da bakin sa zai yi sai dai Allah KAYAYYAKIN MU NA KAMFANIN MEERAH B HERBS 👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* MAMAN AFRAH 09013181851 [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 3 *SUMAYYA* Zaune take a falo ta yi zaman dirshan sanye take da zanin falle ɗaure a jikin ta sai wata riga t-shirt , Ruma tana waje zaune a foo tana kashi, shigowar Ya Shafi'u falon sai da ransa ya yi mugun ɓaci ganin falon duk datti ga wata takarda da leda nan duk ya yaga ƙanana da alama Ruma ce ta yayyaga, gefe ɗaya ga farantin abincin da Rumar ta ci, ita ma kuma Sumayyar da nata kwanon a gabanta da alama abincin ta gama ci ko hannu bata tashi ta wanke ba. "Ummi na gama" Ruma ta ce tana daga wajen. Wata uwar gyatsa ta saki ta ce "Ki zauna zan zo in wanke miki" "Wai mai ya sa Sumayya kullum lamuran ki gaba suke ba baya ba? Kin ga yadda ƙuda yake bin yarinyar nan kuwa, maimakon ki je ki raba ta da kashin shi ne... "Dakata malam wai kai kullum a ganin laifina kake, komai na yi ban iya ba, shi wankin kashin ibada ne da za a ce lallai daga faɗa na tashi na wanke mata " Ta katse shi a zafafe, kallon ta yake da takaici falon duk ya haɗe da warin gumin ƙazanta in ba mantawa ya yi ba rabon da ta yi wankan yau kusan kwana uku kenan haka ma bata wa Ruma ba. "Ya kamata ki wa kan ki faɗa duk abin da kike yi idan yaran ki suka taso su ma shi za su yi, yanzu ki dubi ƴaƴan Amina gwanin sha'awa tas da su kullum amma ke ƴarki sai ta kwana uku jikin ta bai ga ruwa ba daga ta zo kusa da mutuk sai zarnin fitsari, idanun ta kwantsa bakya wanke mata baki haba wannan wace irin ƙazanta ce Sumayya?" ,Wani uban tsaki ta ja, ta tashi tare da saka ƙafa ta ture kwanon gabanta da ta ci abinci bata bi ta kansa ba ta shige ɗaki ko hannu bata wanke ba ta je ta hau gado ta kwanta take danna waya. Rumar ya ɗakko ya je ya wanke mata kashin ya yi floshin, hatta banɗakin sai tashin zarni yake duk bango da ƙasan tiles ɗin sun dafe. "Ɗakko wandon ki a falo in saka miki" Ta ce wa Ruma hankalin ta a kan waya. Wandon ta ɗakko ta kawo mata, ta saka mata, shi kan sa zarnin yake duk ga wamdunan yarinyar nan babu wanki ga kayan wanki kamar su yi magana, ta gwammace ta zazzaga musu mai datti su saka idan ta ga banu hali sai ta tsakuri kaɗan ta wanke. Falon ya dawo ya haɗa plate ɗin Rumar da kwanon Sumayyar ya fita ya je kicin kayan wanke-wanke tari guda ƙuda yana bi abin tsantsani tsayawa ya yi ya kama tsantsa. Gabaɗaya shi dai ya yi da na sanin auren Sumayya saboda muguwar ƙazantar ta, ya rasa dalilin da ya sa bai fahimci hakan ba lokacin da yana neman auren ta ko don tana kwalliya tsaf-tsaf idan zai je zance, sai da suka yi aure abu da kaɗan-kaɗan yake bayyana har ta kai tun tana ɗan ɓoyewa yanzu abubuwa sun kai har bata ma jin kunyar ƙazanta. Da dare tana zaune babu ɗanwakwali shi ma yana zaune yana danna waya lokaci zuwa lokaci yana ɗan satar kallon ta ganin yadda kitson kanta ya yi tsofa sosai har ba a ganin tsagar ko kaɗan duk ya cushe sai wani susa take. "Sumayya" Ya kira ta da murya mai kamar lallashi, amsa masa ta yi ba tare da ta kalle shi ba. "Yanzu Sumayya rayuwa ta yiwu a hakan anya? A ce wanke-wanke sai kwanuka su ƙare a kwando kin gwammace in xa ki yi amfani da kwano ki ɗauka ki wanke, haka tukunya ma? Wankin kayan ki da na Ruma har sai kun rasa na sakawa za ki tsakura ki wanke, yarinyar nan bata samun kulawa ta tsafta kullum ka ganta da ƙazanta don Allah ki gyara tun da dai dai gwargwado ina kawo komai kuma duk abin da kike buƙata ina miki" Ya ce cikin rausayar da kai amma ko arziƙin kallo bai samu ba. "Magana fa nake miki ko?" "Wai don Allah Shafi'u mene ne matsalar ka da ni ne da za kake takurawa rayuwata? Ni fa babu dalilin da zai saka kullum in ke wahalar da kaina, in ke wanki bai taru ba ko wanke-wanke ko in ƙare bauta a kan ƴa ɗaya ƙwallin ƙwal, haba ita mace bata da lokacin hutu sai na bauta a gidan miji idan abin da nake bai gamshe ka ba za ka iya ɗauko mai aiki take maka duk abubuwan da ba na yi" "Haka mw za ki ce mai ya sa ke har kullum in dai hanya ta masalaha ce aka ce za a bi amma ke bakya yarda da ita? Ke ko kaɗan bakya son a miki gyara? Yanzu daga ni sai ke sai Ruma har sai na zauna ɗaukan mai aiki" "To tun da har ba za ka ɗauki mai aikin ba, sai ka ɗauki na annabawa don ni ba zan ƙare a wahala ba wallahi" Tana gama faɗar hakan ta tashi fuuuu ta shige ɗaki, wani gumus ya shai warin kayan jikin ta da suke warin dauɗa da kuma warin gumi don ya san wannan maimaicin bai san na nawa ba ne, haka take ta maimaita kaya. Sai da ya kammala da abin da yake a wayar ya tashi zuciyar sa duk a cunkushe, don dama ba komai yake gani a wayar ba illa hotunan ƴan mata yana ganin haɗaɗɗun mata da suka yi kwalliya hakan yake sawa yana jin shauƙi yana ji dama a ce Sumayyar sa ce take haka da babu ruwan sa fa kalle-kalle ya shiga ɗakin kayan jikin sa ya ɗan rage ya shiga ya yi wanka ya fito ya shafa turare, yana hawa gadon ya shaƙi warin jikin ta ga bakin nan da ta hangame tana bacci sai wari yake fitowa daga bakin, warin rashin wankin bakin don ita Sumayya abin ya mata yawa wai shege da hauka. A haka ya yi ta maza ya matsa kusa da ita don a buƙace yake sosai sai sai abin da yake shaƙa daga jikin ta ya sa ya ji tamkar ya toshe hancin ya biya buƙatar a haka don ya san ko mai za a yi ba za ta yarda ta watsa ruwa a jikin ta ba bare ɗan warin gumin da take yi ya kau. Hannu ya kai ya ɗan taɓa ta, da yake ita Ruma shimfiɗar ta da ban, cikin bacci ta sanya hannu ta buge hannun, ɗan matsawa ya yi kusa da ita duk da yana jin hamamin yana damunsa ya kai bakin sa kusa da kunnen ta ya ce "Sumy baby" Kiran da ya mata ya sa ta ɗan buɗe idanu tare da ƙanƙance su ta sauke a kan sa ta sauran hasken farin watan da ya haske ɗakin. Wartsakewa ta yi tare da tashi zaune ta zauna daram, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ce "Haba don Allah wannan ai ɗaukan alhaki ne ya ina baccina mai daɗi za ka zo ka tashe ni kana mini wata raɗa a kunne" Ta faɗa tana haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba. Shafi'u ji ya yi kamar ya yi amai da ya shaƙi iskar da ta fito daga bakin ta wani irin wari, amma da yake a buƙace yake sai ya ji zai jure ko da kuwa yana kawar da kai ne ya samu ya kauda buƙatar sa. Sai dai inda gizo yake saƙar bai san ma ko za ta amince ba. "Ki ɗan saki fuskar mana kin ji baby nah... "Eh mana dama yanzu za ka kalailame ni da zaƙin baki, saboda kana buƙatata ai ɗazu ka rufe ido ka faɗa mini baƙar magana ka ga ai baka zo wajen ƙazama ba" Ta ce cikin hargowa. Ɗan marairaice fuska ya yi ya ce "Ki yi haƙuri kin ji Sumy na daina" "Wallahi yanzu bacci zan yi babu abin da zai sa na ɓata lokaci na ban yi bacci ba kaina yake ciwo, kai da in ka fara abu baka san ka tsagaita ba" Ta ce tana juya baya ta kwanta. "Don Allah ki taimaka yau kwana nawa ina fama da ke ko so kike in faɗa halaka haba ke kuwa" "Ka daɗe baka faɗa halaka ba, kuma babu wata halaka sai dai ka ce son zuciya in ba son zuciya ba mene ne kuma ko ma dai mene ne kabarin ka da ban nawa da ban" Ta ce tana jan abun rufa ta rufa ta bar shi, da ya kama bargon ma zai shiga ta daddanne ta hana shi ya shiga. Jikin allon gadon ya koma ya jingina, ransa yana ƙuna ya gaji da abin da Sumayya take masa ban da ƙazantar ta har da hana shi haƙƙin sa. Bai yi fushi ba ya ƙara kai mata raruma ta kuwa balbale shi da masifa tana mai tashi fuuu ta suri bargon ta koma falo ta kwanta a doguwar kujera. Iska ya furzar daga bakin sa yana jin yadda buƙata take bijiro masa. Filo ya ja ya runguma yana jin tamkar ya saki kukan takaici da haka bacci ya yi awon gaba da shi. *SULE* Zaune yake a falo yana sha tea yana duba news Amina tana daga gefe tama danna wayar ta, ɗago kai ya yi kalle ta cike da kulawa da nuna soyayya ya ce "Annurin zuciyata, son ki ya daɗe da yon nutso a birnin zuciyata duk ranar da aka ce babu ke a wannan duniyar to ba na jin zan iya ƙara wasu kwanaki ina cikin hayyacina in ma dai ba mu yi mutuwar kasko ba" Kallon sa ta yi sheƙeƙe tana jinjinawa rainin wayo da ƙaryar tashi ta ce "Abban Yusuf wai me ya sa kai ka zaɓi kullum kake faɗar abin da ba haka ba ne? Yanzu mene ne amfanin wannan tsarana ɗin da kake?" "Tsarawa" "Eh mana in ba tsari ba mene ne" "Soyayyar ce tsari Amina yanzu ina matsayin mijin ki amma don na miki kalaman soyayya shi ne tsari?" Ya faɗa yana jon takaicin abin da take masa ita kullum magana ɗaya ce shi ne soyayya tsara zance ne ita kuma bata yarda da kalaman soyayya ba ya rasa gane wace irin mace ce ita "To kai ma Abban Yusuf ka san dai an ce amfanin soyayya aure to mun yi aure a kan me za mu ke wahalar da kan mu yin wata soyayya da kalaman soyayya sai ka ce wasu farin shiga?" Ta jefa masa tambayar hankalin ta a kan wayar ta. Shiru ya yi don ya rasa ma bakin magana. "Haka kawai ni ba budurwa ba ni ba amarya ba a ishe ni da wata kalamar ina son ki haba!. Ai na daɗe da sanin cewar kana sona ko sai ka yi ta maimaitawa kamar karatu, ƴaƴa biyu mai kuma ake nema a wata soyayya?" Ta ƙara faɗa har lokacin bai ce mata ko uffan ba don in da sabo ya saba, shi mutum ne ɗan soyayya yana son kulawa da nuna soyaya sai dai kash!. Bai dace da mata ba wasu matan suna son kulawar miji da nuna soyayya amma sai ka ga daga an yi auren an gama cin amarci shikenan sai namiji ya ajiye soyayya a gefe sai dai kuma a fara zaman kurame ko zaman haƙuri amma ba na soyayya ba. Ita ga shi ta samu amma tana wofantarwa shi ya sa sai ya ringa jin babu daɗi kwata-kwata ya rasa ya zai shawo kan lamarin ga ta kuma da shegen masifaffan kishin tsiya amma bata iya kula da miji ba bata iya nuna masa kulawa ba ita ma in an nuna mata kulawar bata damuwa da hakan. *SADDIQA* Bayan sati uku abubuwa sun fara cunkushe mata, don babban abin da ta ƙara fahimta daga Aminu shi ne ba ya son yin aski daga askin matse matsi har aske kansa kuwa. Gashin hanatar sa ya taru haka na marar sa sannan uwa uba gemu da gashin kansa babu gyara duk sun cunkushe. Gashin Hammatar har wani tsatsa-tsatsa yake idan ya fita wajen sana'ar sa ya kwaso rana ya dawo tamkar ta yi irin yadda warin ana yake bugun ta daga jikin sa. Haka zai dawo hajaran majaran busu-busu da fulawa amma a hakan zai turmusu a gadon ta wanda take gyarawa ta ɗame shimfiɗar gadon, kusamman wani farin zanin gadon ta duk ya dafe sai yanzu take tunawa a ranar da ta tare a gidan hatta jakar kayan sawar sa da ta zo shirya masa kayan a drower duk kayan basu da wankin masu wankin kaɗan ne duk sun dafe sai tashin warin dauɗa suke, tun a lokacin ta yi mamaki a ce sabon ango da zai tare a gidan amarya amma kuma ya zo da kayan marar sa wankin tun a sannan ta fara ɗora masa alamar tambayar anya ba ƘAZAMIN MIJI ta aura ba , sai ga shi da kaɗan-kaɗan abubuwa suna bayyana halayen suna fitowa. "Ranka ya daɗe!. Na ce ka bani dama in maka aski" Ta ce tana ɗan murmushi hannun ta riƙe da sabuwar sheba ta aski wacce ta zo da ita tun daga gida dama siyen su take yi ta ajiye don ita bata yarda da barin gashi ko yaya a jikin ta ba. Wani kallon rashin fahimta ya mata yana mayar da kallon nasa kan shebar da takr riƙe da ita ya ce "Wane irin aski?" Na marar da na hammata mana, sannan ko gashin fuskar ka yana buƙatar ka ɗan rage shi" "Lallai Saddiqa kin ga makwancina da yawa wallahi, ni ne ma za ki yi wa aski sai ka ce wani ɗanki?" "Haba mene ne na ɗaukan zafi ni fa matarka ce mene ne don na maka askin" "To ban ga dama ba lokacin da na ga dama zan aske tun da ba a jikin ki yake ba" Ya ce yana haɗe rai. Ta ce " Don Allah ka yi haƙuri ni ba da wata manufa na faɗa ba a ganina miji ɗan gata shi ne mace take ba kulawa har ma ta buƙaci masa wani abun don ta faranta ransa... "To ni na yafe wanann kulawar, gashin da yake hammata da wanda yake mara da ba ganin su ake yi ba ina ruwan ki da su daga ka saka kaya zancen su ya ƙare ko ma ana gani ai wanda ya raina tsayuwar wata hawa yake ya gyara" Ya faɗa hankali kwance. KAYAN GYARANMU NA MEERA B HERBS SUNA DA INGANCI *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* A MINI MAGANA A PC 09013181851 [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 4 Tun daga wannan rana da ya ƙi maganar askin nan sai tattara lamuran sa ta yi ta ajiye saboda ko kaɗan ta lura ba shi da ra'ayin yin hakan. Abin da yake bata mamaki bai wuce yadda daga ta toshe waccan kafar sai wata ta kawo kai ba, shi kullum da kalar ƙazantar da zai fito da ita, da abin ya dame ta ne wata rana ƙanwar sa Fatima ta zo take faɗa mata wasu daga cikon halayen masa da yake sun shaƙu da Fatimar tana son ta, a nan ne ta ji abin mamaki cewa wai ashe Aminu dama haka yake don dik gidan su shi ne ƙazami na ajin ƙarshe. Ta ce mata yana gida ma sai ya yi sati bai yi wanka ba bare wanki kuwa kaya sai ya maimaita shi ya fi sau huɗu, ɗakin sa kuwa dama a gidan su taron yuyuyu ake cewa saboda tarkace da kuma kayan wanki in ka shiga ɗakin sa ko ina kaya ne a zube, haka zai tattara su gefe guda idan zai kwanta, saboda ba zai gyara ba. A nan ne ma Fatimar take ce mata, da suka fara soyayya ne ma ya fara ɗan yin wanki da ɗan gyara jikin sa, shi ma sai ranar da zai je hirar ne zai ɗauki kala ɗaya ya wanke. Sannan ta ce mata akwai lokacin da suna junior secondry school ma wani malamin su a gaban asambili ya fito da shi lokacin ana fito da ƙazaman makaranta, ta ce a gaban kowa aka tuɓe masa riga prefect suka masa wanka da soson buhu saboda rashin tsafta, amma hakan bai sa ya saduda ba. Saddiqa tun da ta ji wannan batu sai jikin ta ya ƙara sanyi kasancewar ta mai tsafta amma kuma ga shi cikin jarabawar ubangiji ta auri ƙazami lamba ɗaya. "Ni fa Fatima ba wannan ne damuwata ba, shi fa ko kayan na wanke sai ya ga dama zai saka, ga wankekken kaya amma sai ya ce in zai tafi wakem sana'ar sa ba zai saka ba saboda in ya saka ma asarar wanki ne tun da awon fulawa zai yi da su ɓaci za su yi, to in ya dawo kuwa hallaw ba zai cire wanda ya je aikin ba ya saka wasu sai ya ƙara zaman sa da su sai ya ce wai tun da la'asar ma ta yi ba zai canja kayan ba saboda ɓata kaya ne a ce rayuwa kai ba za ka ga mijin ka cikin tsafta ba ka ji daɗi a ranka?" "Ai fa Aunty Saddiqa sai dai ki yi haƙuri amma Yaya Aminu kam lamba ɗaya ne a ƴan ƙazanta" Furucin Fatima ya sa ta ƙara ɗaura ɗamara don magance wannan matsala tata don ba zai yiwu a ce su cigaba da rayuwa a haka ba. *BAYAN WATA BIYU* Yanzu kam abin na Aminu ya daina bata mamaki da al'ajabi ya koma bata tsoro domin yanzu gabaɗaya halayen sa na ƙazanta ya bayyana tun tana ganin za ta iya magance matsalar da kanta har ta kai ta fara tunanin shigo da manya cikin lamuran. Hakan ya sa ta fara tunanin wanda za ta tunkara da maganar da farko ta so zuwa gidan su ta kai ƙaran sa amma kuma sai ta fara tunanin kar hakan ya zama matsala don yanzu a iya wannan watannin ta lura yana da zafin kai ga shi yana da girman kai yanzu ya rufe duk wata kafa da za ta masa maganar gyara jikin sa ko tsaftacewa yanzu ya zamar mata kamar dodo ma don sai yake nuna mata abin da take masa tamkar raini ne ta raina sa ne shi ya sa har take ganin za take masa irin abin da take masa, ko kaɗan ba ya ganin tana yin hakan ne don kawo masalaha a zamantakewar auren su saboda tana cutuwa da ƙazantar sa. 'Saddiqa yadda Aminu yake da taurin kai kin san dai kowace uwa za ta yi ƙoƙarin ganin ta tsaftace ƴaƴanta ko kuma basu tarbiya da nusar da su tsaftace jikin su da nisantar ƙazan ta duk da wasu iyayen su ne mafarin farko na koyawa ƴaƴan nasu ƙazantar misali kamar Sumyya yadda take ƙazanta ba ta tsaftace jikin ta da na ƴarta da kuma muhallin ta wannan kaɗai zai sanya Ruma ta koya tun da yara sun fi koyar abin da idanun su suke gani. Wasu iyayen kuma sun iya bakin ƙoƙarin su na ganin sun koyawa yaran amma daga sun kai munzalin da za su yi komai da kan su sai hakan ya fasakara ake ta fama da su wani sai dai ka gaji ka ƙyale shi, kamar Aminu dai kin ga Fatima ta faɗa miki shi kaɗai ne ya fita zakka a gidan su kuma an yi fama da shi amma ƙazantar har ta zaune masa, dama Fatinar ta ce mata mahaifiyar su ta ce matar Aminu ta shiga uku da ƙazantar sa ashe kuwa hakan ne. Idan kika je gidan su kika faɗa hakan zai haifar da matsala tsakanin ku tun da yana ganin kin raina sa amma ko ki samu Yayan sa ki faɗa masa ko Allah zai sa a samu maslaha'Ta ƙare maganar a zuciyar ta tana jin hakan ya kwanra mata a zuciyar ta. Da safe bayan ya shirya ya fita wajen kasuwancin sa ganin Yaya Sule bai fita ba sai ta shiga jiran fitowar sa daga sashen su, don bata so matar sa ta san abin da yake wakana, duk da ta san ba lallai su kasa sanin hakan ba amma sai dai in su lura da iya ƙazantar jikin sa tun da zama gida ɗaya ba wasa ba amma dai ba za su san abubuwan da suke a ɓoye ba wanda iya ita da take matsayin matar sa ne ta san da hakan. Saboda ita mutum ce mai riƙe sirri bata yarda da yaɗa sirrin mijin ta ba musamman ma irin wannan sirrin da wani in ya ji sai ya maka dariya a bayan idanun ka ko kuma ya je yana faɗawa wasu. Shi ya sa ma sai Fatima ta faɗawa kaɗan daga cikin matsalar ita ma don ta ga ƙanwar sa ce sannan kuma ta san Fatimar ba za ta kasa sanin hakan ba tun da ƙazantar ba ta wasa ba ce. Ƙaran ƙofar falon su Aminar ne ya dawo da ita daga ɗan guntun tunanin da ta tafi, da sauri ta taso ta ɗan ɗaga labule ta leƙo ai kuwa ta hango Yaya Sule ya fito da alama fita zai yi. Da yake part ɗin su Saddiqa ne a wajen hanyar fita, sai sa ta bari ya zo zai yi hanyar wajen ta taso tana sanye da hijabi ta leƙo. "YAya ina kwana" Muryar Saddiqa ta katse masa tafiyar da yake don har ya bada baya. "Lafiya ƙalau amarya" Ya ce cike da sakin fuska. "Yaya dama, uhm, d "Akwai wani abu ne Saddiqa?" Ya katse mata maganar ganin tana ta inda -inda ta kasa faɗar komai tana wasa da yatsun ta. "Eh, dama akwai maganar da nake so mu yi" Ta faɗa tana ɗan jin nauyin sa sannan gaban ta yana faɗuwa. "To ba damuwa mu je" Ya ce yana mata nuni da hannu alamar su shiga daga falon don ya lura kamar bata son yin maganar a wajen. Ta ji daɗin maganar sa hakan ya sa ta juya suka shiga falon nata ya zauna sai ya ce "Ina sauraron ki" "Yaya dama a kan maganar Aminu ne" "Mai ya samu Aminun?" "Dama dai ba ya son tsaftace jikin sa ne, ni kuma abin yana damuna wallahi, na yi ƙoƙarin nusar da shi amma abin ya ci tura!." Iska ya furzar daga bakin sa yana kallon ta da tausayawa shi ya ga ƙoƙarin ta ma da har ta iya kai wa wannan lokacin bata nemi maslahar faɗawa kowa ba, saboda ya san in ba mai matuƙar haƙuri ba babu mai iya zama da ɗan uwan nasa, sai dai kuma ko ƙazama kamar shi. "Saddiqa abin da nake so ki gane Aminu ya wallahi mutum ne da yake da taurin kai, dama na san wataran wannan zai iya biyu baya saboda babu macen da za ta iya jure zama da shi ko da tsawon kwana sati uku ne, kin yi haƙuri da jarumta da kika iya kai wa har wata biyu ba tare da kin yi ƙorafi ba" Ya faɗa cikin tausayawa da tausasawa. Idanun ta ne suka tara ƙwalla tana tuno irin warin da bakin sa yake wanda idan ta shaƙa sai ta ji har wani juyawa kanta yake, tabbas!. Babu abin da ya fi ciwo a nata ganin sama da auren ƙazamin miji, duk da kowace mace akwai tata matsalar da take fuskanta a gidan aure amma dai kowane mai ɗako shi ya san inda yake masa yoyo. "Na masa magana shi ne ya yi biris da maganata na rasa yadda zan yi ne amma don Allah Yaya in za ka masa magana kar ka ce ni na faɗa maka" "Haba Saddiqa magana fa ake ta gyaran aure ai tun da ke ce iyalin sa kuma ke kika fi buƙar ya gyara dole a faɗa masa, sannan idan har kina ganin zai ji babu daɗi in kin faɗa mini to ki cire wannan a ranki domin kuwa Aminu wannan ba wani baƙon abu ba ne a wajen sa sannan ba abin kunya ba ne, abu ne da ya saba ko da za a yi bikin mun zauna an masa faɗa sosai kuma ya nuna ya ɗauki hakan amma dai dama na san da wuya wai gurguwa da auren nesa "Amma Yaya abin ya yi yawa" "Ki yi haƙuri zan same shi" Da to ta amsa ya mata sallama ya fito yana ɗan waiga ɓangaren su kar sarkin ƴan kishin nan ta hango shi cibi ya zama ƙari. Tun da ta faɗawa Yaya Sule maganar sai ta ji wani daɗi da sanyi a ranta ji take tamkar ta sauke wani nauyi. Ɗakin ta koma ta cire bedsheet ɗin kan gadon ganin duk ya dafe da ƙafar sa da ya kwanta jiya, wani wankakke ta ɗauko ta shimfiɗa. Bayan ta gama komai ta ɗakko freshner mai ƙamshi ya feshe ko ina tuni ɗakunan suka buɗaɗe da ƙamshi sai ta ɗakko qur'ani tana tilawa cikin kwanciyar hankali. Da yamma ta ƙara shiga ta yi wanka ta sanya kaya marar sa nauyi ta zauna tana jiran dawowar ogan nata, duk tana jin babu daɗi a ranta don ta san daga ya dawo yanzu ɗakin zai sauya daga ƙamshi zuwa wari, don duk ƙamshin nan daga Aminu ya dawo ɗakunan za su yi wani gumus. "Assalamu alaikum amarya ya ango" Ta tsinkayi muryar Sumayya a falo. Tana daga cikin bedroom ɗin ta amsa mata kafin ta fito zuwa falon tana ɗan sakin dariyar yaƙe. Ƙarasowa ta yi za ta zauna a kujerar mai daf da Sumyyar amma wani warin gumi da ta shaƙa a jikin ta sai ta ɗan wayinci ta koma ɗayar saboda ba za ta juri shaƙar wannan warin ba, duk da tana ganin mijin ta ma ƙazami ne amma ai shi namiji ne duk da mazan ma akwai masu tsafta amma mace an santa da gayu da tsafta koman ta tsaf-tsaf. "Saddiqa amaryar Aminu wato wannan kwalliyar yamma ce aka yi wa ango?" Ta tambaya tana kallon ta tare da washe baki kamar gonar auduga. Kallo ɗaya Saddiqa ta yi wa haƙoran Sumayya da ta washe yadda duk suka dafe ta ce "Eh mana yo ina da wanda zan yi wa kwalliya da ya wuce shi" Ta ce tana ƴar dariya. "Gaskiya babu, ai na farko-farko ne duk amare ai suna wannan gayun a farkon aure amma daga baya sai ki ga komai ya zama tarihi" "A kan me zai zama tarihi" "Dainawa sume yi" "Ni ka in Allah ya aramin tsawon rai har tsufana" "Muna nan da keSaddiqa duk za ki watsar" "Ina Hajiya Ruma" Ta tambaya don kawar da maganar ,"Tana can tana bacci' "Baccin la'asar?" "Eh" "Ai kuwa babu kyau" Saddiqa ta ce tana jingina da jikin kujera Shiru ne ya ɗan biyo baya, sai suka ji sallamar Aminu gaishe da shi da shi Sumayya ta yi ya amsa suna ɗan wasa irin na ƙanin miji. Sallama ta yi wa Saddiqa ta fita. Bai shigo da komai ba yau don haka yana shiga ɗakin ya hau gado ya kwanta, shiga ta yi tana masa sannu da zuwa ya amsa dakyar. "Bari na kawo maka abinci" "Na ƙoshi" Ya furta tare da juya mata baya ya kwanta ga jikin sa dirnis da farin filawa. "Ƙoshi kuma?" Ta tamabaye shi jin wani sabon abu don bai taɓa cewa ya ƙoshi da abinci ba. Danne abin da ta ji ta matsa kuda da shi ta zauna daga gefe ta ce "Ko baka da lafiya ne?" "Lafiyata ƙalau kawai dai ba na ra'ayin ci ne" Ya ce yana zaro wayar sa a aljinu ya shiga latsawa. Shiru ta yi tana mamakin kalaman sa ganin yana amsa mata dakyar kamar wanda ya sha magani mai ɗaci, tonowa ta yi da yanzu suka gama gaidawa shi da Sumayya yana faram-faram da washe baki har da wani washe baki yana zolayar ta. Bai ƙara mata magana ba tana ta satar kallon sa yadda ya mayar da hankalin sa kan waya, sai wani sakin murmushi yake wanda wannan murmushi yana da alaƙa da abin da yake a wayar. Ranta ne yake ƙuna ganin duk lokacin da ta ɓata wajen gyara da kwalliyar da ta masa ko kallo bata ishe shi ba, amma yana zuwa ya washewa ƙazama haƙora sannan yanzu yana yi waya murmushi ita ta zama kamar wani hoto a wajen. Ganin bai san tana kallon sa ba sai ta ɗan yi dogon wuya kaɗan tana hango mai yake yi a wayar gabanta ne ya faɗi ganin ya yi zoomin na hoton wata mace da take murmushi kanta ɗauke da kitson atach ko ɗankwali babu a kanta. Da sauri ta kawar da idanun ta daga fuskar wayar ta mayar fuskar sa har lokacin dai wannan murmushin yana kwance a saman fuskar sa. 'Ikon Allah dama abin da yake a waya kenan, ni ina zaune basho ashe ba ta ni yake ba?' Ta jefawa kanta tambayar a zuciyar ta. "Aminu" Ta kira shi da kausashshiyar muryar ra da take cike da jin kishin abin da ta gani. "Ina jin ki" Ya ce ba tare da ya amsa ba kuma ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba. "Me kake kallo a waya kake dariya?" "Wani abu ne na abin dariya nake karantawa shi ne ya bani dariya" Kallon sa take tana jinjina ƙaryar sa amma sai ta ce "Gaskiya ne" Falo ta koma ta bar masa ɗakin don ta lura yau kwata-kwata ba ya son zaman ta kusa da shi. Sai da aka kira sallah ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta fito ta yi sallaha. Amma shi ko gizau bai yi ba, ita kuma bata masa magana ba don yanzu daga ta masa maganar yin sallah sai ya ce mata kabarin su ɗaya?. Har aka kira sallar isha'i amma Aminu bai tashi ya yi sallah ba, ranta in ya yi dubu ya ɓaci. Bayan ta idar da sallar ta fita tw zubo abincin ta zauna tana cikin ci sai fa shi ya fito falon. "Ni sai na roƙi abincin za ki bani?" Bata ce komai ba ta fita ta kawo masa, yana ci yana danna waya duk ta kasa sukuni ganin yanzu ya fi ba wayar sa muhimmanci a kanta. Yana gamawa ta kawar da kayan, jin almajiri yana bara ta fita ta karɓi kwanon sa ta juye masa sauran abincin. Bedroom ta koma ta kwanta tana tunanin ko akwai wani laifi da ta masa amma iya tunanin ta bata tuno komai ba. "Sallamar Yaya Sule da Yaya shafi'u ta jiyo a sashen nasu, wani irin bugawa ƙirjin ta ya yi da ƙarfi, don bata taɓa tunanin zuwan su ba, sai ta fara jin da na sanin sanar da shi ta da so ta yi ya masa magana kamar dai hannun ka mai sanda ashe dai har wani zai gayyato tabbas!. Suna shirin ɗora mata jakar tsaba kaji su bi ta. ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA? KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST? BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYATAN FATA MUNA DA AKWAI👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI MAMAN AFRAH 09013181851 [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/DHHvkSDbSKeFqXeWD4p37a *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* BOOK 1 PAGE 5 Ɗif ta yi kamar ruwa ya ci ta gabanta yana tsananta bugu, tana fatan Allah ya sa wani abu ne da ban ya kawo su ba waccan maganar ba. Tana jin sa ya amsa musu ciki-ciki shigowa suka yi, tashi ta yi ta lallaɓo take ɗan leƙowa ta tsakanin labule. Kwance yake reran ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Bai bar danna wayar ba kuma bai tashi zaune ba har suka zauna dama sun san hali duk gidan su bashi da kunya ba ya girmama mutane. "Baka ga mun shigo ba? Kana kwance kenan shigowar tamu ɓangaren ka bashi da wani amfani tun da ga shi ka nuna da shigowar mu da rashin ta duk ɗaya" Yaya Shafi'u da ya ƙulu ya ce yana kallon sa. Ɗan dim ya yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma dai ya tashi ya zauna ya ajiye wayar yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. "Akwai maganar da ta kawo mu shi ya sa ma ka ganmu a tare don haka kawai ba za mu zo ɓangaren ka ba" Yaya Sule ya ce "To" Kawai ya ce a taƙaice. "Kai yanzu Aminu ka yi aure ma ba za ka sauya ɗabi'un ka ba? Mutum yana da iyali amma in kana yin wani abu tamkar dai ƙaramin yaro wani abun ma da kake ƙaramin yaro ba zai yi ba" Yaya Sule ya faɗa. "To in ban da ma ɓacewar basira ba, kai ma fa yanzu watarana uba ne kana so ƴaƴan ka su taso suke... "Haba don Allah wai ya za ku zo kuke mini magana a rufe ai gwara ku faɗa mini asalin mai yake tafe da ku amma kuna magana a ƙudundune ina zan gane manufar ku" Ya katse Yaya Shafi'u Saddiqa da take laɓe tana ganin abin da yake wakana gabanta yana dukan uku-uku, duk mamaki ya cika ta saboda ita sun saba girmama na gaba da su ko yaya mutum in ya girme ka to fa ko da baka san shi ba kana daraja shi amma shi ga shi yayunsa na jini ma tamkar dai shi ne gaba da su ta jinjinawa lamarin ƙurr ta musu da idanu tana jira me zai biyo baya. "Maganar rashin sallah da baka fita, ko da asuba dukanmu sai mu je masallaci amma kai kaɗai ne baka zuwa" Yaya Shafi'u ya ce "Kuma batun ƙazantarka dai ashe baka sauya ba sai abin da ya cigaba? Duk faɗan da aka maka ashe bai shige ka ba ta bayan kunnenka ya bi ya wuce.. "Allah na gode maka, yanzu a ce mutum ba zai makara sallaha ba har sai an tuhume sa? Ƙazantar me kuma?" Wannan tambayar da ya yi yana wani kallon jikin sa ita ce ta saka hanjin Saddiqa hautsinawa, tana addu'a Allah sa kar su ce ita ce ta faɗa don yanayin yadda ta ga yana musu magana kamar wasu sa'annin sa ta san ba ma lallai ya ɗauki maganar su ba bare har ya yi aiki da ita. "Ƙarya za a maka ne, na ce ƙarya za a maka to matarka ce ta kawo ƙaranka a kan a maka maganar kake tsafta ka ga kuwa dole a faɗa maka don ba za a zuba maka ido ka cutar da ƴar mutane ba saboda ƙazanta ai cutar da abokin zama ne" Yaya Shafi'u ya faɗa cikin hargowa. 'Subhanallah! Shikenan sun saka ni a maganar' Saddiqa ta faɗa a zuciyar ta. "Saddiqa?" Ya tambaya mamaki kwance saman fuskar sa. "Eh ko kana da wata matar bayan ita?" Yaya Sule ya tambaya yana kallon sa. "To ko da a ce matarsa bata kawo ƙaransa ba ai ko yanzu komai ya aka kalla wataƙila rabonka da sallaha tun ta asuba ko ma a ce tun ta safe tun da baka je masallacin asuba ba, amma yanzu bari a kira ta waƙa a bakin mai ita ta fi daɗin ji" Cewar Yaya dama in za a yi sulhu mutum biyu ake haɗawa a ji ta bakin kowa abin da ya sa ma muka maka maganar kai kaɗai saboda wannan sulhun ba ya buƙatar ma sai an ji ta bakin wani don abu ne a bayya ne" Cewar Yaya Shafi'u. "Wai ni baku san yanzu da kuma da ba ɗaya ba ne? Ni ma yanzu na yi aure don haka a daina biyo ni ana mini wani faɗa don na girmi faɗa, sallah kuma ai Allah ake yi wa ba mutum ba batun tsafta kuma ita Saddiqar za ta faɗa mini sauran bayanan" Ya faɗa a ƙufule yana komawa yadda yake tun farko wato ya kwanta ya ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tare da fara latsa wayar sa. Lamarin Aminu ya fara basu tsoro ganin haka suka bambame shi da faɗa kamar za su ari baki don yadda ta musu ma in suka kira matar tasa wataƙila su ji kunya don ba ƙaramin aikinsa ba ne ya tsinkasu a gabanta duk da sun san tana ji tun da dai sun san tana cikin ɗaki, basu ƙara ma kallon inda yake ba suka tashi suka fita Saddiqa da gumi ya gama wankewa tsabar tsoro ta juya da sauri ta koma bakin gado ta zauna, kamar jiran tafiyarsu yake sai ga shi ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. "Ashe baki da hankali?" Ya faɗa tamkar zai kai mata duka. Furucin nasa ya bata mamaki duk da ta tsammaci wasu abubuwan amma bata zaci har zai iya alaƙantata da rashin hankali ba. "Aminu ni kake ce... "An faɗa miki na ga alama baki san wa kika aura ba, har ni za ki je ki haɗa da ƴan uwana? Har kin kai ki fara bibiyar ƴan uwana kina kai musu maganganu ?Yaushe aka yi daren da har gari zai waye? Yaushe aka yi auren ma, tabbas hakan ya nuna mini ke ba matar rufin asiri ba ce kuma baki da riƙe sirri, tun da har kin kasa jure abubuwan nan tun tafita bata yi nisa ba" Ya tari numfashin ta yana magana kamar zai kai mata duka. "Aminu ni ce ba matar rufin asiri ba?" Ta tamabaya ranta yana ƙuna tare da nuna kanta da yatsa. "To matar rufin asirin ce? Har ni za ki je ki samu ƴan uwana ki musu maganar banza kina son ki shiga tsakanin mu ki haɗa mu dama ana cewa wasu matan idan suka auri miji burin su bai wuce su raba shi da kowa nashi shi ya dawo mallakin su su kaɗai. To ki sani ba dai ni Aminu ba har yau baki fahimci wa kike aure ba kuma ina so ki sani tun da har ni kika yi wa haka ƙazanta yanzu na fara babu sauyi ba irin mu ake yi wa abu ta ƙarfi ba" Tun da ya fara maganganun ranta yake ƙuna ji take tamkar dai ta buɗe ido ta ga mafarki take, wai Aminun ta wanda yake lallaɓata tamkar ƙwai wanda yake son ta shi ne yau yake jifanta da munanan kalamai wai ita ce take son ta raba shi da ƴan uwan sa. 'Ashe dama gyara kayanka yana zama sauke mu raba?' Ta tambayi kanta a zuciyar ta idon ta har ƙwalla ya ciko ta takaicin maganganun sa. Zuciya ce ta ɗauke ta don ta ga lamarin ya yi tsamarin da sai ta turbuɗawa idanunta toka, idan ta bari abun a haka zai ƙara girma ne ya bunƙasa tun da shi bai ɗauki ma abin da yake yi a matsayin kuskure ba. "Aminu bari ka ji ni ban auri kafiri ba musulmi na aura don haka dole ka cigaba da amsa sunanka na musulmi ta hanyar kiyaye sallah da kuma tsafta ce jikin ka, shiru-shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne kana ganin har akwai matar da za ta jure wannna halayyar? A ce mutum ba zai tsafta ce jikinsa ba wanka wannan ba za ka yi ba bare wankin baki kayanka in wanke maka amma ba za ka saka ba na gaji da maka alkunya dole in fito maka a mutum... "Kin gaji? To in har kina gani za ki ƙwaci abin da kike so ta ƙarfi ga fili ga mai doki, ko an faɗa miki ana haɗa gudu da susar ɗuwawu ne? Babu gyara haka na ga dama sai lokacin da na ga dama zan yi wanka sannan sallah ina yi kiyaye lokacinta kuma wannan tsakanina ne da wanda ya yi umarnin a yi sallah shi kuma yana gafara amma dai ki sani ba gudu ba ja da baya... "Wallahi ba zan yarda ba don ƴaƴana ba za su taso su ga wannan rayuwar marar kai da ƙafa... Fuuu ya juya ya bar mata ɗakin, ji take ranta yana ƙuna wai ita ya ce ba matar rufin asiri ba ce, wannan maganar ta fi ƙona mara rai da kuma yadda ya tabbatar mata ba zai canja ba. Tana jin fitar sa har ƙaran rufe ƙofar da ya yi ta ƙofar gidan hakan ya nuna ficewa ma ya yi daga gidan. Komawa kan gadon ta yi ta kwanta bata san lokacin da wani kuka ya ƙwace mata ba, dama al'adar ta ce matsawar ranta ya ɓaci wani lokacin sai ta yi kuka in ba haka ba bata samun sassauci a zuciyar ta. Ta jima tana kukan sai da ta ji zuciyarta fess sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya. Tun tana saka ran dawowar sa amma shiru babu shi har ƙarfe goma ta gota amma bai dawo ba. Har sha ɗaya saura idon ta biyu, daga nan bata san lokacin da bacci ya ɗauke ta ba. Can cikin bacci ta yi juyi ta falka sai kuwa abin da ya faru ya faɗo mata da sauri ta tashi tana ƙarewa wajen da Aminu yake kwance kallo ganin babu shi babu alamar sa. Mamaki ne ya ɗarsu a zuciyar ta tana tunanin shin bai dawo ba ko dai bayi ya shiga?. Sakkowa ta yi daga gadon bayan ta duba wayar ta ta ga ƙarfe uku da kwata, wutar ɗakin dama a kunne ta bar ta don haka bayin ta nufa ta ɗan ƙwanƙwasa jin shiru ta tura ƙofar amma sai ta ga wayam tsoro da mamaki suka ƙara rufe ta ko ƙofar bata rufe ba ta juya da sauri nufi wayar ta lambar sa ta kamo ta shiga kiran sa don kawai sai ta ji hankalin ta ya tashi don tuni ta manta da abin da ya mata, wataƙila ko son da take masa ne ya danne laifin nasa ko dai ruɗun da take ciki ne ya mantar da ita komai. Sai da ta kira sau uku wayar tana shiga amma ba a ɗauka ba. Har ta yanke shawarar ta daina kira tun da ba a ɗauka ba sai ta ji ba za ta iya ba hakan ya sanya ta sake kira sai da ta yi sau biyu nan ma babu amsa. Bata yi tunanin kiran ɗaya daga cikin yayun nasa a waya ta sanar da su ba sai kawai ta yanke hukuncin ta je part ɗin ɗaya daga cikin su ta sanar da shi kar wani abu ya biyo baya a ce da gangan ne bata faɗa ba cewa bai dawo gida ba. Tana fitowa falon da yake a kunne ta bar wutar falon amma sai ta ga a kashe don ko ta ɗakin bata kashe ba lokacin da za ta kwanta tun da ta san bai dawo ba, ganin ta falon a kashe sai ta yi mamaki matuƙa. Kunnawa ta yi haske ya gauraye falon kamar an ce ta waiwaya sai kuwa ta gan shi kwance saman doguwar kujera yana bacci hankalin sa kwance. Baki sake take kallon sa ganin ya shigo da wani sabon salo wai kiran sallah da usur. Bata tashe sa ba sai kawai ta kashe fitilar ta koma ɗakin har za ta kwanta sai ta yi alwala ta yi sallah raka'a biyu ta yi addu'a ta koma ta kwanta a ranta tana mamakin wannan sauyin da ya shigo rayuwar su tun da tsawon lokacin nan basu taɓa raba makwanci da shi ba, amma yau ga shi ya raba musu makwanci. Da asuba ta tashi ta yi alwala ta tafi falon ta shiga tashinsa ita ma da bata gajiya. "Mai zan miki ne wai da kike katse mini bacci?" Ya tamabaya a ƙufule. "Sallah aka kira" "Za a saka mu kabari ɗaya da ke ne? Ba kin ne kin faɗawa su Yaya Sule ba na sallah ba to yanzu ma sai ki je ki ce gani nan kwance ban yi sallah ba sai su zo da bulala ko?" "A'a" Ta ce cikin sanyi murya tana jinjina irin yadda yake mata magana cikin hargagi kamar dai ba wannan Aminun da yake son ta ba yake nuna babu mai raba su sai mutuwa babu wanda zai shiga tsakanin su, yana faɗa mata idan sun yi aure za su huta ba za su taɓa yin faɗa ba ba zai taɓa ɓata mata rai ba ba zai taɓa mata kishiya ba da ita kaɗai zai rayu. Amma ga shi tun ba a je ko ina ba ayyukansa suna ƙaryata maganar sa, na farko dai ya ce ba zai mata kishiya ba sai ga shi tun auren bai je ko ina ba ta kama shi yana kallon hoton mace, sannan ga shi a jiya ya shuka mata kalmomin rashin mutunci tare da gasa mata baƙaƙen maganganu. "Tun da kowa kabarin sa da ban ki je ki ji da naki kabarin" Maganar sa ta katse mata tunani, yana gama faɗar hakan ya juya mata baya ya kwanta. Jiki babu ƙwari ta juya ta koma bedroom ɗin tana tunanin wane irin miji ta aura? Shin jiya da ya fita ya yi sallar magriba da isha'in ne ko kuwa haka ya gama bulayi ya dawo ya kwanta? In kuwa haka ne ai da sake ta yaya za take zaune da miji ba ya sallah ga baƙar ƙazanta. Tun da ta yi sujada take addu'ar Allah ya kawo mata mafita a cikin lamarin tun da ta ga abu kamar wasa amma ƙaramar magana tana shirin zama babba. Sai da ta gama karatu gari ya ɗan yi haske sannan ta kwanta. Bacci ya yi awon gaba da ita. Sai wajen ƙarfe tara ta tashi. Ta yi mamakin baccin da ta yi tana hamma ta sakko daga gadon amma tana zuwa falo ta ga Aminu kwance wannan karon ba bacci yake ba idanun sa biyu amma yana danna waya. Ƙafarsa ta kalla ta ga babu alamar an saka ruwa alamar an yi sallah. Tsabar takaici bata masa magana ba ta koma ta shiga bayi ta yi brush ta wanke fuskar ta tana kallon brush ɗin Aminu har ya fara ƴar ƙura alamar ma ko ta kansa ba a bi. Kicin ta shiga ta kwaɓa fulawa ta shiga soya musu waina. Sai da ta kammala ta tafasa ruwan shayi ta ɗakko ta taho. ta ajiye abin mamaki sai ta ji ƙaran zubar ruwa a bayi alamar ana wanka. Matsawa ta yi gaban bayin ta ƙara kunne ta ji da gaske wankan yake, hannu ta ɗaga sama tana yi wa Allah godiya, tana tunanin an samu sauyi tun da ga shi ana wanka don ta ji ƙaran dirza soso. Falo ta dawo ta zauna tana jin daɗi a ranta tana fatan Allah sa maganganun da aka faɗa masa ne suka shige shi. Wayar sa da take kan kujera ce ta fara haske leƙawa ta yi sai kuwa ta ga kira ne yake shigowa da alama wayar a silent take shi ya sa ba a jin ƙaran. "Ƴar aljanna" Sunan da ta gani yana yawo kenan a saman wayar, hannun ta har karkarwa yake tana mamakin a iya wannan ɗan lokacin da aka ɗauka da yin auren su wace ce wata ƴar aljanna wato saboda matsayin ta har an kira ta ƴar aljanna. Kallon hanyar bedroom ɗin ta yi sannan ta kasa kunne tana jiyo ƙaran ruwan. Tana shirin ɗaukan wayar ta gudu kicin ta ci mutuncin ta a kan tana kiran mijin ta a cikin gida sai kawai kiran ya katse bata gama dawowa daga mamaki ba sai message ta ga ya shigo hannun ta har karkarwa yake ta buɗe. "Ya ina kiranka ka ƙi ɗauka, kai da ka ce mini ƙarfe goma za ka zo yau ko wajen sana'a ba za ka je ba" Ganin wannan saƙon ya mugun ɗaga mata hankali tana cikin wanann yanayin ta ji ƙaran buɗe ƙofar bayi alamar ya fito daga banɗakin, message ɗin ta goge. Da sauri ta tashi daga kujerar ta koma gaban kayan abincin da ta ajiye musu. 'Kenan wannan dalilin ne ya sa ya yi wanka wato wajen wata zai je?' Ta faɗa a zuciyarta. Shi kuma dama kamar an ce masa ga abun da yake wakana a falon ya taho yana zuwa ya ɗauki wayar ko kallon inda take bai yi ba da harara ta bi shi a ranta tana cewa 'Aikin banza bata san ƙazami bane kai da bata ɓatawa kanta lokaci ba' Ta ce a zuciyar ta. Jim kaɗan zuciyarta ta ce ta leƙe ɗakin ko dai chatting suke tana zuwa ta same shi yana sallah, wai sai lokacin wannan yake sallar asuba. Falo ta dawo can sai ga shi ya fito sanye da wata shaddar sa da ta wanke masa ta goge, da a ce bata san inda zai je ba da ta ce ya birge ta, yau amma tuno da abin da ƴar aljanna ta ce sai ta ji tana jin haushinsa. "Ina kwana "Ta gaishe shi ciki-ciki. "Lafiya" Ya amsa a taƙaice. Ganin ya nufi ƙofa da alamar fita zai yi ta buɗe baki ta ce "Ya na ga ka kama hanyar fita ina jiranka mu karya?" "Ki karya kawai ni na makara a wajen sana'a ta" Ya ce ba tare da ya kalle ta ba kafin ta ce wani abu har ya fita. Tasowa ta yi ta biyo bayansa ta ce "Wannan ne shirin zuwa wajen sana'a?" "Kamar ya?" Ya furta yana haɗe rai. "Na ga ai ka yi kwalliya kuma ba haka ka saba ba in za ka je wajen kasuwa ba ko dai wani waje za ka je da ban? Kai da ka ce wajen sana'a ba wajen saka kaya wankakke ba ne amma yau har gogagge ka sanya" "Tuhuma ta kike yi ne? Ni da kayana sai ana tambayata don na saka ba ke kike damuna kullum a kan in ke saka kaya ba" "Amma da nake cewa ka saka ai baka taɓa sakawa ba sai yau?" "Haka na ga dama'" Ya ce yana juyawa ya bar ta tsaye da tuƙuƙin baƙin ciki. ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE? KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST? BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE? KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI MAMAN AFRAH 09013181851 Akwai lesuna shaddodi atamfofi, frames, kayan yara, zannuwan gado, takalman yara da manya, mayafai, tuntu na kwalliyar ɗaki labulaye ga mai son siyen ɗaya ko sari. 09013181851 [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/IbZ6N1f4kuwLodHvKgrO78 *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* BOOK 1 PAGE 7 Saddiqa tun da ya hau gadon sai ta kasa ma zaman ɗakin, don yanzu sai ta ji ma kwata-kwata haushinsa ba zai bari ta zauna inuwa ɗaya da shi ba, saboda duk wata kafa da za ta samu farin ciki Aminu ya toshe wannan dalilin ya sa ta ji gabaɗaya auren ma ya fita a ranta. Falo ta dawo ta zauna ta jingina bayanta da jikin kujerar, tunani ne barkatai suka cunkushe mata, babu abin da take nema illa mafita, tun da ga shi wannan mafitar da ta bi hanyar bata ɓulle ba, tun da ga shi dai Aminun tamkar wanda aka kaɗawa ganga ya nuna ma ba ta ita yake yi ba. Bata tashi daga wajen ba sai sallah kawai take tashin ta, shi kuma yana kan gadon ya hakimce sai aikin latsar waya yake, ko kallo bai ishe ta ba don yanzu mugun haushinsa take ji.Tana jin sa sai da aka yi isha'i sannan ya tashi ya shiga bayi tana jin motsin ruwa da alama alwala ya yi, bayan ya fito ta ji ɗif bata jin motsinsa hakan ya alamanta mata cewa wataƙila sallolin yake jerowa tun da shi kiyaye lokutan sallah ba ya cikin ɗabi'arsa. Tana nan zaune sai ga shi ya fito, wuri ya zauna cikin dakkakiyar muryarsa wacce ya fara amfani da ita a kwanannan, ya ce "Ki tashi ki je ki sama mini abin da zan ci" Ya faɗa yana haɗe rai. A ƙufule ta ɗago ta sauke idanunta a kan fuskarsa ta masa kallo ɗaya ta kawar da kanta gefe ba tare da ta furta komai ba, sannan kuma bata yi ko gezau ba bare har ya saka ran za ta tashi ta aikata abin da ya saka ta yi masa. Sai da ya ɗauki kamar minti biyu bai ce komai ba, yana jiran tsammani daga gare ta ganin bata da alamar motsawa ya sake cewa. "Saddiqa ba da ke nake magana ba?" Banza ta masa bata ce komai ba. Ya sake cewa "Kurma ce ke ne?" Ganin bata ce komai ba, sai ya ga ta raina masa hankali a fusace ya tashi ya zo gaban kujerar da take zaune, tsaya mata ya yi a kanta tamkar yana jiran ta masa musu ya hukuntata. Ya ce "Saddiqa idan har ba za kike jin maganata ba ban ga dalilin aurenki ba, ina mijinki ina miki magana amma kin mayar da ni tamkar mahaukaci?" Ya kai ƙarshen maganar yana wani huci tamkar zaki. Cikin halin ko in kula ta ɗago kai ta kalle shi a raine ta ƙara kawar da kai. Hannu ya kai ya dunguri kafaɗarta, kamar jira take ta zabura ta miƙe tsaye, hannu biyu ta saka ta riƙe ƙugu da yake ma kusa da kusa suke sai ya zama tamkar jikinsu zai gogi juna saboda kusancin. Saddiqa ta ce "Wai ya za ka zo kana mini magana cikin ɗaga murya? Magana kaɗan sai kake cewa ko ba zaman aure na zo ba? Wanann tambayar ai ba sai ka tambaye ni ba, kai kanka kana da amsarta in auren nazo in akasin haka" Ta faɗa cikin tsiwa. Baki sake yake binta da kallo kuma sai ya ji yana shayinta amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama sai ya kalleta cikin dakiya ya ce "Ni kike wa magana haka gatsal kamar wani sa'anki Saddiqa?" Bata ce komai ba sai wani yatsina fuska take. "Ki wuce ki dafa mini abinci" "Ai tun da na dafa maka abinci da safe ka ƙi ci, ka fita ka tafi wajen wata banza ca... Kafin ta kai ƙarshen maganar hannun da Aminu ya kawo sai wanke kyakkyawar fuskarta da mari shi ya dakatar da ita daga maganar, cikin sauri ta durƙushe hannun nasa ya mari iska ɗagowa ta yi tana mai ƙanƙance ido ranta fal mamaki. Aminu kuwa hannun ya mayar bayansa da sauri, gabansa yana faɗuwa ganin kuskuren da ya kusa yi, wanda hakan ba tare da saninsa ya yi ba zuciya ce ta ɗauke shi jin an kira masoyiyarsa da banza, wacce yake so da ƙauna kuma ba ya son duk wani abu da zai taɓa ta. Son da yake mata ne ya sa yake kiranta da ƴar aljanna, sannan abin da Saddiqa bata sani ba shi ne, a rashin uwa aka yi uwar ɗaki, ma'ana Aminu ba ita ya so ya aura ba sanadin budurwarsa Khady an ce karatu za ta yi a gidansu, wannan dalilin ya sa ya auri Saddiqa duk da ita ma soyayya suka yi amma ya yi wa Khady alƙawarin tana kammala karatu za su yi aure don ita ma Aminun ne zaɓinta. "Aminu ni za ka mara?" Ta faɗa a ƙufule tana nuna kanta da yatsa, har lokacin tana cike da ɗinbin mamaki don bata taɓa zato ko a mafarki zai tarki kai hannunsa jikinta ba. "Ba da niyya na yi ba" Ya faɗa yana ɗan wayincewa don ya san bai kyauta ba. "Hmmm!" Ta ce tare da yin ƙwafa ranta yana mata ƙuna. Ta ce "Wannan ya zama na farko sannan karo na ƙarshe da za ka yi tunanin kai hannunka jikina, babu wajen duka a jikina ko da kuwa ɗan yatsana ne bari fuska, wacce take cike da daraja" Ta ce tana kallon yadda duk ya diririce bata wani jira cewarsa ba ta raɓa jikinsa ta shige ɗaki, don bata jin akwai wani abu da ya yi saura wanda za ta saurara daga gare shi. Tana shigewa ɗakin ya sauke wata ajiyar zuciya, zamewa ya yi ya zauna a kan kujerar yana jin rashin kyautawar da ya yi daɗin da ya ji ma shi ne da Allah ya sa hannun nasa bai samu fuskarta ba. Saddiqa kuwa tana shiga ɗaki sai ta zauna a kan gadon ranta yana mata ƙuna, hannu ta kai ta shafo fuskarta mai laushi da santsi wacce a baya take ganin duk namijin da ya aure ta laushin fatarta kaɗai ma ya isa ya girmamata amma sai ga shi yau an kusa sauke mata yatsu biyar a fuskar. A zuciyarta ta ce 'Mai hakan yake nufi ne, kenan Aminu banda ƙazanta, rashin kula da ibada hallaw namiji ne mai dukan mace?' Akiyar zuciya ta sauke a fili ta sake rayawa a zuciyarta ta ce 'Ba zan taɓa lamuntar hakan ba, dole da sake ni ba matar duka ba ce don ba zan zauna ina gani ba ya kashe ni da raina, da yarintata amma ya tsufar da ni da ƙazantarsa' Filo ta ja ta ɗan kishingiɗa zuciyarta tana tunano mata irin soyayya da ƙaunar da suke wa juna ita da Aminu wacce ta kai su har ga turbar aure. Juyi ta yi tana ƙara tafiya duniyar tunano wace ce ni. Sunana Saddiqa ni ce ƴa ta farko a gidanmu sai ƙanwata Asiya muna kiranta da Noor. Mun taso cikin gata da tarbiya duk da iyayenmu ba wasu masu ƙarfi bane, amma dai suna da rufin asiri daidai gwargwado. Iyayanmu sun tsaya kai da fata wajen bamu ilimin boko da na arabiya. Mahaifiyarmu da muke kira da Mamy, mace ce mai haƙuri da sanya idanu a kan ƴaƴanta duk abin da muka yi na kuskure sai ta nuna mana, idan kuma muka yi abin kirki tana yaba mana fiye da abin da muka yi wannan abin yake sanyawa, mu sake ɗaure ɗamarar yin wani abun kirkin. Mamy mace ce mai tsafta, tsaftar jiki da ta muhalli zan iya cewa ni ce na biyo ta don ni tawa tsaftar har ta so ta yi yawa don bana ƙaunar ƙazanta ko wanda ya haɗa hanya da ƙazanta. Hakan ne ya sa, ƙanwata Noor take kirana da sarkin tsaftar gidanmu, duk da ita ma tana da tsafta daidai gwargwado amma ni na dame ta na shanye. Tin kafin in gama secondry school muka yi saukar qur'ani a islamiya, duk da Mamy ita ce makarantar farko da take koya mana karatu, saboda haka ma ko a makaranta za a karɓa harda sai a ji na fi kowa iyawa ita ma Noor a nasu ajin haka ne. Ƙawata ɗaya Mubina, da yake ni ban cika son tara ƙawaye barkatai ba, ina kammala secondry school Abba ya saya mini waya sannan ya bami damar in kula samari sai dai ya gargaɗe ni cewa bai yarda in tara samari ba, duk da ya san ni ma ba abu ne da zan yi ba sai dai ya yi hakan nr don fita haƙƙina. Saurayina na farko sunansa Kabiru na haɗu da shi ne wataran Mamy ta aike ni gidan ƙawarta, tun da muka haɗu muka ƙulla alaƙar soyayya duk da ban ji ya kwanta mini ba, amma ganin yana ƙaunata sai na kasa bayyana masa, sai dai yana da aure da ɗansa guda ɗaya. Muna waya sannan yana zuwa gidanmu zance, mun yi wajen wata huɗu da shi muna tare, don har yana shirin aiko da mayansa su yi magana da Abba, kwatsam mummunan labari ya riske ni daga abokinsa Hamidan Kabiru ya samu mummunan hatsari inda motar d yake ciki ta kama da wuta, sanadin buguwa da wata motar homa wacce ita ma ta ƙone ɗin. Labarin nan ya gigita ni, ya hautsina mini tunani, inda na ji komai na duniya ya daina mini daɗi dama ai ɗan adam ba komai bane, sai nake tuna lokacin da ya mini waya yana faɗa mini tafiya ta same shi ashe dai ajali ne ya yi kira, tafiya ba ta dawowa ba ce. Tun bayan mutuwar Kabiru sai na daina kula kowane namiji, sai in ke ganin kamar shi ma sai na saba da shi zai mutu ya bar ni, sai da Mamy ta dage sosai da mini nasiha sannan na fara kula wasu. A watarana da ba zan taɓa mantawa ba, ranar juma'a da yamma na je gidansu ƙawata Khady Mamarta da bata da lafiya, a hanyata ta dawowa na rasa napep ina tafiya ina son isa gida kafin magriba, wata daddaɗar murya ta mini sallama a bayana, da farko ban tsaya ba kuma ban juya ba. Jin mamallakin muryar bai daina bina ba don ina iya jin takun tafiyarsa sannan sautin muryarsa ina ji yana matsowa dab da ni, wannan alama ce ta cewa yana biye da ni. Ganin dai abin nasa ba na ƙare ba ne, da yake kuma layin ma babu mutane sai jefi-jefi suna giftawa, dakatawa na yi amma ban juyo ba. Sai ji na yi ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga wannan halitta, alkairi da albarka su lulluɓe ki ke da ahalinki baki ɗaya" ,Na ji sautin muryar yana shiga kunnuwana a hankali. A karo na biyu ya ce "Ina neman afuwa na yin laifin tsayar da kamilar mace a hanya, ina neman yarda da amincewa domin a bani mintina biyu zuwa uku na bayyana abin da yake tafe da ni, ina fatan hakan ba zai sa a gajiya ba sannan ba zan shiga rayuwar gimbiya ba" Daɗin muryarsa da iya tsara kalamansa su suka sanyaya zuciyata har na ji ko da a ce abin da ya yi laifi ne to tabbas! Na yafe masa. Ya sake faɗin "Ba don idan kika kuɓuce ban san ina zan sake ganinki ba, to da babu yadda za a yi in tsayar da kyakkyawar mace mai cike da kamala da haiba a hanya" Ji na yi idanuwana suna son yin arba da wannan bawan Allahn, a hankali na shiga juyowa har sai da na juyo duka na, a kan fuskarsa na yi wa idanuna masauki inda na ga idanunsa a rufe sannan hannayensa biyu a haɗe waje ɗaya alamar roƙo. Ban san ya aka yi ba sai na ji magana ta fito daga bakina kamar an fisgota na ce. "Kai ma amincin Allah ya tabbata a gare ka" Na faɗa cikin sassanyar muryata. Idanunsa na ga ya buɗe a hankali wanda hakan ya sa ni kuma na sunkuyar da nawa idanun, saboda sai na ji nauyinsa da kunyarsa sun lulluɓe ni. Sai ji na yi ya ce "Sunana Aminu don Alah ina neman alfarma idan ba damuwa ki bani lambar wayarki, sannan ki faɗa mini sunan unguwarku" Kasa masa musu na yi, saboda ni ma sai na ji ya kwanta mini a rai. Lambar wwayar na bashi tare da faɗa masa sunan unguwarmu, godiya ya hau yi kamar zai ari baki. Murmushi kawai na masa tare da juyawa na cigaba da tafiya amma dai shi na ga ko gizau bai yi ba, a tsaye na bar shi a wajen kamar gunki na san kuwa ni yake kallo. Tun da muka rabu bai kira ni ba, har aka yi kwana biyu ga shi zuciya da bata da ƙashi sai nake ta tunaninsa, ko kirana aka yi a waya sai in zaci shi ne, sai a rana ta ukun bayan magriba ya kira ni tun da ya yi sallama a wayar na gane shi ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Mun daɗe muna hira tamkar mun saba da juna daga ƙarshe muka yi sallama ya ce gobe zai kawo mini ziyara. Wannan shi ne farkon alaƙata da Aminu, shi ne mafarin soyayar da har ta kai mu ga aure, duk da bayan mun yi nisa a son juna ya sha faɗa mini wai ba ya son sunayen soyayya mace take kiransa da su da farko na ɗauka ma wasa yake sai ga shi a ranar da na tare a gidansa ma matsayin amarya ya maimaita mini kalmar. Ƙaran wayar Aminu da ya karaɗe falon shi ya dawo da ni daga nisan kiwon da na tsunduma cikin tunani, kwanciya na gyara ina jin duk jikina ya mutu don lamarin Aminu abin ya yi tsamarin da sai dai in ce Allah mini maganin matsalata. Tun da wayar ta fara ƙara ba a ɗauka ba saboda ina jin ƙaran bata daina ba, juyi na yi haɗe da jan ƙaramin tsaki a zuciyata. Wani kiran ne ya shigo a karo na biyu wannan lokacin ƙaran bai wani ɗauki lokaci yana yi ba, sai na ji ɗif. Bayan kamar minti uku sai na yanke shawarar zuwa kicin in haɗa shayi in sha, fitowa na yi amma abin mamaki falon wayam babu Aminu babu alamarsa, baki ta taɓe ta fito ta saka takalmi ta nufi kicin ɗin sai dai tana dab da shiga kicin ɗin ta jiyo dirin muryar Aminu yana magana da alama waya yake, mamaki ne ya baibaye ta sai dai ba wannan ne ma abin dubawar ba kalaman da ta ji yana faɗa a wayar ne ya matuƙar razanata, ji ta yi tamkar an buga mata guduma a kanta nan take wani abu ya mata tsaye ya tokareta a maƙoshi, jikinta ya ɗauki karkarwa... MAMAN AFRAH 09013181851 *TALLA !TALLA!!!* ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE? KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST? BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE? KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI MAMAN AFRAH 09013181851 [4/17, 9:29 AM] MAMY SHEHU: https://chat.whatsapp.com/DHHvkSDbSKeFqXeWD4p37a *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 6 Tun da ya fice ta juyo jiki babu ƙarfi ta dawo falo ko kallon kayan abincin bata yi ba wani kishi ya tokare mata maƙoshi, kan kujera ta faɗa ta kwanta tare da kifa kanta ta fashe da wani kuka. Sai yanzu take tuna irin yadda ake labarin irin yadda maza suke wujijjiga mata a gidan aure, sai ta ji ana cewa wuyarta a yi auren shikenan namiji zai juya maka baya. Ga shi dai yanzu ba a je ko ina ba abubuwa sun fara cunkushewa, wai duk irin yadda Aminu ya nuna mata soyayya da kulawa amma yanzu daga yin auren a ce har ya sake wata budurwar wai har yana saving lambar ta da ƴar aljanna. Kenan me yake nufi da hakan? Ita ƴar ina ce tun da yana da ƴar aljanna. 'To kika sani ma ko tun kafin ya aure ki yake tare da ita, ai kaɗan daga aikin namiji kawai ki kalli namiji, don namiji karatun sa ba zai taɓa ƙarewa ba, ai namiji halayensa littafi ne guda mai ɗauke da tarin takardu da kuma dogayen shafukan da ba a ƙare karatunsa bare a gama fahimtarsa' Wani ɓangare na zuciyar ta ya bata amsa. Sosai ta shiga damuwa ganin ita tana ta fama da shi ya sauya halayyarsa ta ƙazanta da tsakaninsa da ubangiji, amma bai ji maganar ta ba ko don haƙƙinta, sannan yanzu ya ɗauki kayan da ita ta sha wahalar wanke su da goge su duk don ta faranta masa, amma a ƙarshe sakayyar da zai mata da ya saka su wajen mace zai je, tun da gashi nan tas kamar dai ba wannan Aminun da yake zaune da ƙazanta ba yana warin dauɗa. Tana nan tana ta saƙa da warwara ta kasa jurewa don sai zuciyar ta take ta raya mata cewar yanzu fa yana can tare da wata, wataƙila ma yana ta mata murmushi. Waya ta ɗaga ta shiga kiransa amma har ta tsinke ba a ɗauka ba, bata daddara ba dai ta shiga kira a karo na biyu amma amsar ɗaya ce no answer. Tana riƙe da wayar bacci ya yi awon gaba da ita bata tashi ba sai sha biyu, ta yi mamakin irin baccin da ta yi. Haka ta tashi zuciyar ta duk ba daɗi, kayan abincin nan ta kwashe ta mayar kicin don yadda take jin zuciyar ta ba za ta iya cin wani abu ba. Dawowa ta yi da nufin ta gyara ɗakin, tun da yau babu abin da ta tsinana, bedroom ta shiga tana shiga ta ji wani irin wari ya haɗe ɗakin. Fuska ta yatsina tana ɗaɗɗaga hanci tana son gano daga inda warin yake amma ta kasa ganewa sai take ma tunanin ko ɓera ne ya mutu. Ganin gajeran wandon Aminu da ya cire da singlet da alama wasu ya saka, sai da zuciyar ta ta tashi ganin farar singlet ɗin ta yi wani irin datti har ta zama milk ta ƙarfi da yaji. Da tsantsani ta ɗauke su ta ta kai hancin ta wai ko warin su ne ya haɗe ɗakin amma sai ta shaƙi warin dauɗa da na gumi da sauri ta kawar daga wajen hancin ta. Kayan wanki ta jefa su ta dawo tana duba inda warin yake. Sai da ta duba har bayan drower da ƙasan gado, ta yi ta duba ɓera amma ta sha binciken ta bata ga ɓeran ba. Dakyar ta iya share ɗakin saboda yadda warin yake damun ta ta rasa daga ina ne kuma. Da ta gama gyaran sai ta cire kaya za ta shiga wanka, tana buɗe banɗakin wani irin wari ya bugi hancin ta. Sai yanzu ta gane daga inda warin yake sai dai ta yi mamakin jin wari a banɗakin domin kuwa bata barin banɗakin da datti, dama yanzu ma nufin ta idan ta shiga ta wanke banɗakin sai ta yi wanka. Sai da ta toshe hancin ta ta iya shiga bayin tana tunanin a banɗakin ne dama ɓeran ya mutu. Duk ta duba babu ɓera babu alamar sa, ganin an rufe toilet (Shadda) Da murfin sai ta buɗe. Abin da ta gani ne ya ɗaure mata kai. Kashi ne Aminu ya yi bai yi floshing ba. Da sauri ta danna wajen floshing ɗin kashin ya tafi da ɗan gudu ta fito daga bayin, bata tsaya a bedroom ɗin ba sai falo ta taho saboda yadda ta ji warin duk ya ɗumame ɗakin. Idanun ta har ƙwalla suka kawo tana tunanin wannan wace irin rayuwa ce a ce mijin ka bashi da aiki sai ƙazanta, har ta kai a ce mutum ya yi kashi amma ba zai zuba ruwa ba ya tashi ya bar shaddar a haka, to wa kenan yake son ya yi floshing ɗin?. Ta jima a nan sai da ta tabbatar zuwa lokacin warin ya fita sannan ta je ta wanke bayin ta yi wanka. Bayan ta shirya ta fito sai ta nufi kicin ta dafa indomie ta dawo ta zauna ta ci, don ta lura in ta ce saka damuwar ɗa namiji a ranta ne zai sa ta daina cin abinci to tabbas!. Tana dab da komawa kamar tsinke don rama ko dai ulcer ta kama ta,. Ana kiran sallah ta ɗaura alwala ta gabatar da sallah, don ita bata wasa da sallah ko kaɗan, lokaci yana yi take yi bata yarda ta saɓa lokacin sallah ba. Har aka yi la'asar Aminu bai dawo ba, ganin zaman ya gundure ta kuma tana ta saƙa da warwara sai ta ɗauki hijabi ta saka ta nufi part ɗin Amina don ita Sumayya yau ta tafi gidan su wuni. Da sallama ta shiga Amina tana zaune tana cin jallof na shinkafa wanda ya sha alayyahu. "Inyee yau amarya ce da kanta" Ta ce tana dariya. "Ni har wani kai gare ni" Ta faɗa tana zaunawa fuskar ta ɗauke da murmushi. Sun shiga yin hira inda take tambayar ta Yusuf da Albani ta ce mata da Baban su zai fita ya tafi da su ya miƙa su gidan su. Suna ɗan tattaunawa Saddiqa sai ta ji Amina ta ce "Kai gaskiya Saddiqa kina ƙoƙari" "Ƙoƙarin me?" Ta tambaya cike da rashin fahimta. ,"Zama da Aminu mana" "Ban gane ba?" "To miji ƙazami ai sai ka jinjina zama da shi, don dai ni ina son ƘAZAMIN MIJI, saboda babu ruwanki da ciwon kai wato duk namiji mai ado da kwalliya ɗan ƙwalisa ƴan mata kullum suna kai masa farmaki" Bakin Saddiqa buɗe yake wayam tsabar mamaki ta rasa mai za ta ce. "Ni yanzu da nake tare da wannan mijin nawa mai shegen tsaftar jaraba, koyaushe cikin ado da kwalliya kin ga kowace mace ta gan shi dole ta ƙyasa wallahi shi ya sa wani lokacin sai in ce duk macen da ta auri ƘAZAMIN MIJI ta huta" 'Ikon Allah wato dai ita magana sai ka barta iya kai kaɗai ne take sirri? Daga ka fitar ka faɗawa wani shikenan ba sunan ta sirri ba za ka iya tsintar ta a ko ina ma' Saddiqa ta faɗa a zuciyarta tana mamakin ashe dai Yaya Sule ya kwashe maganar da ta faɗa masa ya faɗawa matarsa, saboda ita dai ta san bata taɓa wannan maganar da ita ba, sannan duk da suna zaune a gida ɗaya ko da za a ce ita Aminar ta ga wasu alamomi a jikin Aminu wanda ya danganci ƙazanta ai ba za ta tunkare ta da maganar ba. Shi ya sa ake cewa kowa da abokin zancen sa, idan ka faɗawa wani sirrinka ko da ka ce kar ya faɗawa kowa shi ma in ya tashi faɗawa wani sai ya ce masa kar ya faɗa, shi ɗin ma idan ya ba wani labari sai ya ce kar ya faɗa, a haka maganar za ta yaɗu baka ankara ba sai ka ji ta je inda baka yi zato ba ko da bata dawo kunnen ka ba to wanda suka sani za suke kallon ka da abun. "Ai ni tun da ya ce wai kin kawo ƙaran Aminu a kan rashin tsafta na ce masa dama ni ce" Maganar Amina ta katse mata zancen zucin. Murmushin yaƙe Saddiqa ta yi ta ce "Haka ne kam kowa ai da ra'ayinsa kuma ai da aka masa maganar ma ya ce zai gyara" "Amma kuma ya ce mini baram-baram suka rabu bai Aminun bai amsa laifinsa bama?" 'Wato dai sai da ya kwashe komai ya faɗa mata?' Saddiqa ta ce a zuciyar ta. "Bari in je kar ya dawo na ga lokacin dawowar sa ya yi" Saddiqa ta ce cikin sanyin murya ta mata sallama ta baro sashen ranta cike da haushin abin da Yaya Sule ya yi, dama an ce wasu mazan sai sun kwashe komai sun faɗawa miji, su ma wasu matan haka suke kwashe zance su faɗawa miji ko da kuwa sirrin gidansu ne shi ma mijin haka ne, amma bata zaci Yaya Sule zai faɗi sirrinta ba gashi facala ce watarana za ta iya yi mata gori. Ta fito sai ga Sumayya ta shigo gidan. "Amarya mai daɗin tuwo" "Ni dai na rasa ranar da sunan nan zai canja zuwa asalin sunana" Ta ce tana ƴar dariya. "Ina!. Ai sunan nan in kin ga an daina faɗa miki, sai ranar da Aminu ya rambaɗo miki amarya wato ya miki kishiya, sannan ne sunan ki zai tashi daga amarya ya koma uwar gida ita kuma ta zama amaryar" Sumayya ta faɗa cikin wasa. Dammm!. Ƙirjin Saddiqa ya buga jin wannan furucin na kishiya, a take sunan ƴar aljanna da ta kira Aminu kuma ta turo masa saƙo ya faɗo mata, lokaci guda ta ji komai ya tsaya mata kishi kumallon mata. "Gaskiya haka ne fa" Ta faɗa tana yin murmushin yaƙe. "Ruma ƴan mata" Ta ce tana kallon Ruma da take cin biskit. Ta faɗi hakan ne don ganin ta kawar da waccan maganar. "Gata nan!. Bari mu shiga mu fatsar don a ƙafa muka taho" Sumayya ta ce tana yin gaba. Ita ma nata ɓangaren ta nufa tana jin yau tamkar bata fito a sa'a ba don duk maganganun facalolin nata basu mata daɗi ba. Yanzu ta fara tunanin Allah sa dai shi ma Yaya Shafi'u bai faɗa wa Sumayyar ba, duk da ita ma ƙazamar ce. Ta shiga kenan jim kaɗan sai ya shigo da sallama, da sauri ta fito falon amma abin da ya bata mamaki ganin duk fulawa a jikin sa. Tambayar kanta ta shiga yi kenan dama kasuwa ya tafi? Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da ta yi tunanin ko dai bai je wajen ƴar aljannar ba. 'Ko dai sai da ya je can ya tafi kasuwa?,' Wani sashen na zuciyarta ya faɗi hakan. "Sannu da zuwa" Ta faɗa ganin ya zauna a kujera yana ambaton wash!. Alamar gajiya. "Yawwa" Ya amsa a taƙaice. "Kawo mini abinci" Ya furta fuskarsa babu walwala don ta lura tun da ya shigo sai wani cin magani yake. "Ban dafa ba" "Kamar ya?" Ya ce yana wani yatsina fuska. "Kamar yadda ka ji mana, da safe da na dafa abincin ka ci? ",Don banci ba sai a ƙi dafa mini wani abincin, wa yake nemo mini?" Kalaman nasa sun daki zuciyarta kuma ta san ba ita take nemowa ba, amma da yake ita ma dama a cike take da shi sai cewa ta yi "Ni ba baiwa ba ce da zan ke girka abincin da ba ci za a yi ba, idan na girka an ci zan sake wani in kuma ba a ci ba to ba zan sake yin wani ba" ,Kallon ta yake yana mamakin furucin ta. "Saddiqa yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?" Kai ta ɗauke gefe ba tare da ta ce masa komai ba. "Ni nake auren ki ba ke kike aure na ba, don haka abin da na shimfiɗa a cikin gidana shi za a yi" "Ai ni tunanina inda ka tafi an baka abincin a can" Shiru ya yi yana nazarin kalaman ta. "Kenan dama ke ce mai rawar kan da ta goge saƙon da aka turo mini a wayata? Har kina da damar taɓa mini waya da goge abin da aka turo?" Ya ce yana jifanta da wani kallon rainin hankali da ta ji tamkar ta wanka masa mari. "Ashe dai an turo ɗin, ai na gani kuma na goge" Ta ce tana wani ƙanƙance ido don ta lura in tana ɗaga masa ƙafa kowane datti ya kwaso a kanta zai juye. "Ina so ki sani babu wata mace da za ta juya ni, don haka in zaman aure kika zo yi ki yi abin da ya kawo ki, in kuma ba shiya kawo ki ba to sai ki yi sa idon, amma ki sani saka idanun ki ba zai taɓa amfanar da ke komai ba sai wahala da ɓacin rai, don saka idonki babu abin da zai sa kuma babu abin da zai hana" Yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe ya nufi hanyar ɗaki. Sosai ranta yake zugi, take tunanin mai ya sa yanzu Aminu yake fito da wasu sabbin halaye wanda bata taɓa kawo yana da su ba? Shin daman da ake cewa sai zama ya haɗa ake gama sanin halayen juna hakan ne?. Fuuu ta bi bayan sa cikin ɗakin ta ce "In ba zaman aure na zo ba to me na zo yi? Mai ya sa za ka ɗauki tsauraran kalamai kake jifana da su? Ko dai har ka fara gajiya da zama da ni... "Ba na son maganar banza ni ina da aikin yi, sannan daga yau sai yau babu ke babu faɗawa ƴan uwana zancena kin saka sun je gida sun faɗa an mini faɗa, to ke baki isa ki raba ni da ƴan uwa da iyayena ba, abu na gaba babu ke babu taɓa wayata don ban miki lamuni ba!." Idanun ta ne suka ciko da ƙwallah amma ta maje, ta ce "Ban ga wanda ya isa ya hana ni taɓa wayar ba, kuma laifi in ka ga ba a faɗa ba to ka tabbatar da cewa baka yi abin faɗar bane" Ta faɗa rai a ɓace don furucin sa na cewa babu ita babu wayar sa ya bala'in ɓata mata rai gani take ya hana ta taɓa wayar ne don yake cin karensa babu babbaka, wato yake ajiye hotunan ƴan mata yana waya da su, sannan suna aiko masa da message ita tana nan ya kasa gyara alaƙarsa da ita. "To ga wurin nan za ki gane shayi ruwa ne" "Kuma wallahi daga yau kar ka ƙara bar mini kashi a banɗaki don ni ba baiwarka ba ce" Ta faɗa cikin hargowa. Banza ya mata ya hau gado ya kwanta wani haushi da takaicin sa yana cika mata zuciya. Musamman na rashin yin sallah ga shi kuma ya shigo da batun kula ƴan mata bayan ita kanta da take cikin gidan. Ba daɗinsa take ji ba a karo na ba adadi ta yi da na sanin auren Aminu don auren namini ƘAZAMI kuma marar addini ba ƙaramin abu bane. ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE? KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST? BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE? KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI MAMAN AFRAH 09013181851 [4/17, 9:33 AM] +234 806 438 0669: *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* BOOK 1 PAGE 8 Gabanta yana mugun faɗuwa ta ji yana cewa "Haba ƴar aljannata ke kin san aure tsakanina da ke babu fashi, duk wata mace a doron duniya ai sawu take take miki domin kuwa bayanki take bi ke kin sani ina son ki!" Dam ƙirjin Saddiqa ya cigaba da bugawa, lokaci guda ruwan hawaye suka ciko a idanunta ta fara tunanin kenan har an ci moriyar ganga za a yada korenta. A zuciyartw a ta ce 'Yanzu Aminu har ya fara tunanin yi mini kishiya daga yin auren namu da watanni? Wato duk wata mace bayanta take kenan har ita da take matsayin matarsa wata can banzar bazara ta fi ta?' Ta jefawa zuciyarta tambayar. Ta ƙara jiyo muryarsa yana faɗin "To ya kike so in yi yanzu ma fa ina kicin na laɓe saboda kawai in yi waya da ke, don tun da na dawo take masifa in taƙaice miki ko abinci bata dafa ba saboda baƙin kishinki da take yi, wai saboda ta karanta saƙon ki da safe" Jin sa ya cigaba da faɗin "Ai ni ban san haka take da masifa ba, rabu da ita an ce mata namiji mijin mace ɗaya ne? Ai duk abin da za ta yi ihu ne bayan hari" Bayanta ta jingina a jikin bango tana jin ciwon tononon sililin da yake mata a wajen budurwarsa duk da har da ƙari ya yi, amma a nata ganin bai kamata yake bankaɗawa budurwarsa sirrin gidansa ba. Jin yana ta lallaɓa budurwar tasa sai ta ji ba za ta iya jurewa ba, hakan ya sa ta durfafi cikin kicin ɗin. Ganinsa ta yi ya juya baya yana can ƙarshen kicin ɗin ya saka kansa daga lungun tsakanin loka da bango. Aminu da ya sha'afa yake hira abinsa don bai taɓa sanin za ta zo kicin ɗin a wannan lokacin ba. Jin motsin shigowar mutum kicin ɗin tsabar yadda gabansa ya buga sai da wayar ta suɓuce, don kaɗan ya rage ta faɗi amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama sai ya yi saurin wayincewa yana cewa. "Ina jinka inusa dama idan na dafa ruwan zafin zan gasa wajen, tun da ina ga ƙashin wajen ne ya yi sanyi" Ya dage yana faɗa tare da juyowa ya kashe wayar ma. Kallon Saddiqa yake wacce ta baiwa bango ajiyarsa tea flacks ta ɗauka da kofi ta zuba suga da lifton ta ɗauka, tana daf da fita daga kicin Aminu da ya fara ƙoƙarin haɗa haruffa daƙyar ya yi ƙarfin halin cewa. "Dama hannuna ne yake ciwo to sai na tambayi Inuwa shi ne ya ce in gasa wajen da ruwan dumi da ɗan gishiri" Ko kallo bai ishe ta ba don gani take ma ɓata lokacinta za ta yi, ko kuma idan ta buɗe bakinta bata san mene ne zai fito ba kai ta saka za ta fice daga kicin ɗin. Aminu da yake ganin kamar tana masa kallon tuhuma, duk da a ransa bai kawo cewa ta ji abin da ya ce ba don a nasa ganin in har da ta ji abin da yake cewa ya san da sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci. Ƙaran da wayar ta ɗauka ne ya sa Aminu saurin danne makunnar kiran ya katse, ita kuwa ko kallonsa bata sake yi ba ta bar masa kicin ɗin. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana jin har lokacin gabansa bai bar faɗuwa ba, don shi abu ɗaya ne ma ya ƙara tsorata shi ne ganin a kicin yake kar ta ɗauki wuƙa ta burma masa saboda ya sha jin labarin matan da suke kashe maza saboda kishi. Lallaɓowa ya yi sai da ya leƙo kansa a hankali, ya ga bata nan, sannan ya koma kicin ɗin, ganin kiran yana ƙara shigowa da sauri ya ɗauka, yana karawa a kunnensa ya ji ta ce "Sannu ɗan aljanna yanzu ni ce ma Inuwan?" Cikin son lallashinta ya ce "Haba ƴar aljannata wa ya ce miki haka, wallahi Saddiqa ce ta yi wa kicin ɗin dirar mikiya kawai sai ganinta na yi kamar an jefo ta" Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa don ya ƙosa su yi sallama kar Saddiqar ta sake dawowa, saboda tun yadda ta sauya ɗazu da ya kusa kai hannunsa jikinta sai yake ɗan shayinta. Sai ji ya yi ta ce"Ikon Allah na kwance ya faɗi, yanzu kai kuma mijin ta ce za ka zama ko mene ne wannan ɗin, kai da kake da tsarin mace biyu amma kake tsoro to wallahi tun wuri ma in bacci kake ka falka amma tabbas akwai aiki ja a gabanka" Cikin ƙarfin hali ya ce "Ba fa tsoronta nake yi ba ai ni daga ganina kin san cikakken namiji ne mai kwarjini da haiba, na fi ƙarfin mace ta juya ni" Ƙwafa ta yi sannan ta ce "To a dai juri zuwa rafi don watarana tulu zai fashe" Bai biya ta ba don burinsa yanzu su yi sallama saboda ya koma ɗakin, kar Saddiqa ta yi tunanin wani abu da ban saboda sai da ya ji dama fita waje ya yi idan ya gama wayar ya dawo. Wani ƙaramin ƙyalle da ya gani ya ɗauka tare da wata ƙaramar roba, fitowa ya yi ya dawo falon, zaune ya same ta tana kurɓar shayin da take jin tamkar maɗaci ne take sha, gabaɗaya ranta a cunkushe yake ta kasa gane wane irin zaman aure take yi lallai ta yarda maza su ba ƙwarya ba ne bare a ƙwanƙwasa a ji. A yadda take kallon Aminunta bata ɗauka za ta samu wata kasawa ko gazawa daga gare shi ba, amma sai ga shi hakan ta faru a kwana kusa. Ji ta yi ya ce "Bari na tsiyayi ruwan nan" Ya faɗa yana ɗaukan flacks ɗin, a gefe ɗaya yana satar kallonta ta wutsiyar ido amma sai ya ga kamar dai bata ki mai yake faɗa ba, duk da dai yanayinta bai nuna masa ta nuna wata alama da za ta alamta masa ta ji wayar da yake yi ba, amma dai ya fi zargin abin da ya faru tsakaminsu ɗazu ne yake kai kawo a birnin zuciyarta. Ɗan gefe ya matsa ya zauna ya shiga tsoma ƙyallan nan yana matsewa sai ya ɗora a hannunsa, kallon gefen ido ta masa tare da taɓe baki don ta fahimci babu wani ciwo a tare da shi. Tana gama shanye shayin ta ɗauki kofin da flacka ɗin ta mayar kicin. Ɗaki ta koma ta cire kayan jikinta ta ɗaura towel ta shiga bayi ta yi brush tare da yin wanka, fitowa ta yi ta ɗauki wata rigar bacci iya gwiwa ta sanya. Jikinta ta feshi da turare ta ɗauki wayarta da take kan madubi, har za ta hau gadon kawai sai ta ga duk dattin ƙafar Aminu da kuma farin fulawa ya ɓata zanin gadon ƙyanƙyami irin nata sai ta ji ba za ta iya kwantawa ba, cirewa ta yi ta ɗakko wani ta shimfiɗa ta ɗauki freshner ɗinta da ta ji ta kusa ƙarewa ta fesa ta hau ka ta kwanta. Wayar ta cigaba da dannawa ta hau whatsapp, gani saƙon ƙawarta Khady ta buɗe ta fara karantawa kamar haka. "Gobe zan dawo" Tana daga kwancen sai da ta tashi zaune, sosai ta ji daɗin maganar dawowae ƙawar tata wacce bata gari aka yi bikinta ma tana can Niger dangin Babanta. Amsa ta bata da cewa "Da gaske kike ko wasa?" Ita ma amsar ta maido mata don lokacin tana online. "Wallahi da gaske" Cike da zumuɗi ta ce "Allah kawo ki lafiya" Sallama suka yi ta ajiye wayar ta ja bargo ta yi addu'a ta shafa bacci ya yi awon gaba da ita, don bata san shi Aminun yau ma ko kwanan falon zai yi ba, in ma a ina zai kwana shi ya sani saboda yanzu ta daina saka damuwarsa a ranta kar ta je ta cutu a banza tun da shi ba ta ita yake yi ba, wata ce a gabansa ba ta tata yake yi ba. A ɓangaren Aminu kuwa tana shigewa ɗaki ya sauke wata ajiyar zuciya, bai san mai ya sa ba tun da ya yi yunƙurin marinta ya ga ɓacin rai ɓaro-ɓaro a fuskarta sai ya ji yana shayinta kaɗan. A zuciyarsa ya ce 'Oh duniya mai juyi-juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi yau ni Aminu ne nake jin fargaba a kan mace, sai ka ce wanda bakin uwa ya kama' Hannu ya sa ya ture robar da ya zuba ruwan zafin ya ajiye ƙyallan ya koma ya jingina da kujera, wayarsa ya fiddo ya yi shige-shige ya gama ya mayar da roba da ƙyallan. Sai da ya mayar da wayar silent sannan ya je ya buɗe drower ɗinsa ya saka wayar saboda tsaro ba don tsoro ba, ya san ƴar aljannarsa za ta iya ƙara kiransa, duk da yana jin saukar numfashin Saddiqa alamar bacci ya yi awon gaba da ita. Bayi ya shiga ya hau toilet ya rage nauyin cikinsa, bayan ya yi tsarki ya tashi ya mayar da murfin ya rufe ba tare da ya yi floshing ba. Tunowa da ya yi da abin da Saddiqa ta ce a kan bar mata kashi bai kora ba, sai ya yi floshin ɗin don yau so yake ya lallaɓa ya sauke buƙatarsa a kanta tun da dai jiya ma a falo a kujera ya kwana kamar wani gauro. Yana fitowa ya haura gadon yanayin ƙamshin turaren da Saddiqa ta shafa da na freshner ya haɗe kan gadon, hanci ya ƙara buɗewa yana shaƙa, sai da ya kwanta ma ya ji ƙamshin duk ashe a jikin zanin gadon ma. Bargon ya ja ya shige ya rarumo Saddiqa da take cikin tsafta tana bacci cikin kwanciyae hankali. Cikin baccin ta tsinkayi muryarsa yana cewa "Saddiqa ba dai har kin yi nisan zango ba" Wani irin hamami da ya ziyarci hancin ta daga warin bakinsa dai da kanta ya sara, a take zuciyarta ta tashi ta ji wani amai ya tasho mata, janye jikinta ta shiga yi shi kuma sai ƙara maƙalƙaleta yake kamar ƙadangare ya samu bango. Fisge -fisge ta shiga yi don babu abin da ta fi buƙata yanzu sama da ta ganta a bayi, kokawa ce ta kaure a tsakanin ma'auratan biyu ita tana son ta je ta amayar da abin da ya taho mata, shi kuma duk tunaninsa gudunsa za ta yi saboda abin da ya faru tsakanin su, tana cikin kiciniyar ƙwatar kanta sai ya sake buɗe bakinsa ya ce "Haba Saddiqa, ke yanzu saboda saɓani ya gifta tsakanimu sai ki hanani haƙƙina? Ko so kike mala'iku su tsine miki?" Kai kawai take jijjigawa alamar a'a don bata son ta buɗe bakinta amai ya zubo saboda maganar da yake ƙara hautsina cikinta warin bakin nasa yake, bata san adadin kwanakin da ya yi bai wanke bakin ba ga warin hammatar gumin jikinsa kaɗai ma ta sai tabbas ƘAZAMIN MIJI take aure. Tana ta ture shi ta samu ta kuɓuta sau ya ce "Na ga dai ban yi marin ba, kuma kowa yana kuskure ki tausaya mini a buƙace nake wallahi" Ya faɗa yana rungume ta. Ganin shi bai fahimci komai ba ta dage ƙarfinta ta tura shi baya, da sauri ta tashi tsaye a kan gadon tana shirin ta dira, sai ji ta yi ya saka hannu ya riƙo ƙasan rigar baccin nata. Hannu ɗaya ta saka ta toshe bakinta gudun kar aman ya zubo, ɗaya hannun kuma ta yi amfani da shi wajen yi masa zancen kurame alamar tana zuwa, sai sannan ya gane banɗaki take son shiga don ya ga tana masa nuni da jikinta hakan ya sa ya washe rinannun haƙoransa. Har neman tuntuɓe take wajen yin gudu, takalmin ma a juye ta saka tana sauri tana shiga bayin ta shiga kelaya amai tamkar ƴaƴan hanjinta za su fito. Sai da ta gama ta wanke fuskarta tana cikin yin brush sai ganin mutum ta yi tsaye a bakin ƙofa yana kallonta kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai, bata ankara ba sai ji ta yi ya ce "Haba Saddiqa wai ke kama sau nawa kike wanke baki a rana ne, a ce mutum ko fashin wanke baki ba ya yi kullum sai ya wanke, wankewar ma ba sau ɗaya ba sau biyu ba?" Ya faɗa yana riƙe da ƙugu. Bata ce komai ba sai da ta gama brush ɗin don so take ta daina jin abin ƙarnin aman a bakinta, tana shirin ajiye brush ɗin ta ji ya ce "Ina miki magana kin watsa yina Saddiqa, mace dai an santa da tattali da cancana abu amma ke baki iya komai ba sai almubazzaranci, ni bakin nan sai in kwana uku huɗu ban wanke ba, kuma ko da na tashi tatsar makilin ɗin ɗan kaɗan nake matsa, amma ke sai kin cika kan brush ɗinki da makilin gaskiya ya kamata ki iya tattali saboda rayuwa" Ajiyar zuciya ta sauke ta taho ta raɓa shi ta wuce ya biyo bayanta, tana zuwa ta zauna a bakin gado, zuwa ya yi ya tsaya a kanta yana hucin jin haushin ƙyaleshi ɗin da ta yi yana bambami, ita warin da take shaƙa daga jikinsa kaɗai aka barta da shi ba ƙaramin cutuwa take yi ba ta rasa sai yaushe zai fahimci cewa ƘAZANTA ba ƙaramin cutar da abokin tarayya take yi ba, amma haka ta danne zuciyarta ta ce "Yanzu shi wankin bakin ma sai an tuhumi mutum? Kai yanzu tsakani da Allah daɗi ta maka kake ikirarin kwana huɗu biyar baka wanke baki ba? Har kake cewa wai tattali ne hakan?" Hannunsa ya mayar baya jin tamkar ya kwaɗe ta sannan ya ce "Yanzu daga magana sai cibi ya zama ƙari Saddiqa kike neman faɗa mini baƙar magana, su baki dai mene ne don ka yi fashin wankewa?" Tsabar takaici sai da ta kai zuciyarta nesa ta bashi amsa da faɗin "Babu komai" Ganin kamar dai ranta a ɓace kuma ya lura kamar ma tana ɗan kauda kai sai ya sassauta murya ya ce "Yanzu dai ya wuce amma in zaki saka makilin ɗin kike lakutar kaɗan, ni ma duk ranar da na samu damar yin wankin bakin sai in lakuci kaɗan ɗin, ko kuma in lakuta mai ƴar dama kin ga na yi ƙara'i kenan har na sauran ranakun da ban yi ba" Ya faɗa yana ɗan ranƙwafowa ya miƙa hannu ya dafo kafaɗarta. Kai kawai ta iya gyaɗa masa ta tashi ta haye gadon shi ma ya hau, ji ta yi tamkar ta saki kuka saboda yadda ta ji ya gundure ta da tashin warin rana. Daga haka ya matsa ya shiga neman haƙƙin nasa babu wani nuna soyayya hannu ta kai ta riƙe masa hannu, cikin sanyin murya mai kamar son lallashi ta ce "Ba don ni ba don Allah ka zuba ruwa a jikinka" Kallon kin raina mini hankali ya jefeta da shi kafin ya ce "Saddiqa idan haƙƙin nawa ne ba zai samu ba ki faɗa mini mana sai wani jan rai kike mini, kar fa ki manta sadaki na biya amma kina shimfiɗa mini wami sharaɗi din za ki bani halaliyata" Murya ta sassauta cikin raɗa, don ita in ma mai zai ce gwara ta lallaɓa shi ya raba jikinsa da ƙazantar nan kar a je ta cutu. Sai da aka kai ruwa rana ta nuna ta yi fushi sa yake yana son biyan buƙata, a haka ya tashi ya shiga bayin wanda ya ga shigarsa shi ya ga fitowarsa, sai sheƙin rashin fitar wankan yake don kana gani ka san dai ruwa ya sheƙa bai saka sabulu ba. Idanu ta lumshi tana jin yadda ranta yake ƙuna, shi kuma fitilar ya kashe musu yana wani washe baki ya hau gadon yana cewa "Na yi belin kaina dai na yi wankan nan da ake ta faman cewa in yi" Wani gumus ɗin warin gajeran wandonsa dabya cire, garin ajiyewa ya jefo saman fuskarta abin da ta shaƙa sai da ta gwammace kiɗa da karatu, da sauri ta ɗauki wandon ta cilla shi gefen gado. Kamar dai wanda ya taso da dattin haka ce ta kasance, amma dai da dama-dama wai kibiya a ido, haka dai aka shiga ƙoƙarin aiwatar da sunna, ga shi da ƘAZANTAR rashin wankin baki amma sai masifar son yin sumbata tamkar ba,indiye aiki ya yi nisa ita dai babu wata nutsuwa, don aiwatar da sunna ma ya fi idan kowa a tsaftace yake. Hannu ya kai yake saka mata yatsa a jikinta, wani kartar ta da ya yi da zaƙo-zaƙon farcen da ba ya yankewa shi ne ya sa ta zaro ido tare da saurin runtse idon, duk ya bi ya karce ta, a haka ya gabatar da sunnar sai wani uban gashi da bai aske ba da take ji tana goga a jikinsa. Lokacin da komai ya lafa sai ya ɓingire da bacci, ko jikinsa bai suturta ba sai bargon ta ja ta rufe masa jiki, ita kuma ta je ta yi wankan tsarki ta dawo ta kwanta don ta san idan ta ce ya yi wankan ma ba zai yi ba, baya ta juya masa ta ja rigar baccinta ta kai hancinta tana shaƙar ƙamshin turaren har bacci ya ɗauke ta. 09013181851 TALLA TALLA TALLA ƳAR UWA SANYI NE YA DAME KI, MAI FITAR RUWA KO MAI SANYA ƘAIƘAYI KO KUWA ZAFI KIKE JI YAYIN SADUWA KO KURAJE YA FESO MIKI KINA SUSA KINA JIN DAƊI DAGA KIN GAMA ZAFI YA BIYO BAYA DUK SU ƘWAILE? KINA DA NANKAREWA NE? KO MIJI GARE KI MAI NEMAN MATA KE YA WOFANTAR DA KE? MATSI NE MATSALAR KI KO ZUBEWAR BREAST? BUSHEWA KIKE BAKI DA NI,IMA KO MIJINKI YANA DA HANNUN JARIRI WATO BAI IYA BAKI KYAUTAR KUƊI BA, KINA DA MIJI MAI BIN MATAN WAJE BA YA KULAKI SAI MA WULAƘANCI YAKE MIKI TUN DA YANA SAMUN BIYAN BUƘATARSA WAJEN MATAN WAJE? KO MATSALARKI HIPS NE IDAN KIKA SAKA KAYA KIKE YAWO CIKI KAMAR MUCIYA? BREAST NE TAKI DAMUWAR KINA KUNYAR MIJINKI MA YA GANSU? KO BRA KIKA SAKA TUDUNSU BA YA HAYOWA? AMARYA CE KE KO ME JEGO DUK MUNA DA KAYAN GYARANKU, MASU BUƊEWAR HQ AKWAI WANDA ZAKIYI BANKWANA DA BUƊEWARSA. WASU ABUBUWAN BA SAI NA LISSAFA BA A KAMFANIN MU NA MEERA B HERBS MUNA DA FIYE DA ABUBUWAN DA BAKI BA ZAI IYA LISSAFAWA BA DON HAR KAYAN GYARAN FATA MUNA DA AKWAI👇 *Shu,umar humra, maganin breast, maganin ƙara ƙiba, maganin tumbi,maganin hips, bujenki shakaf, sa kurma surutu, hatsabibim ruwa, tsumin lahaula, sabulun farinjini, turaren farinjini,maganin ulser, baƙar mallaka, hatsabibiyar mallaka,ƙarin kunama, mallakar gado, mallaka me sirinji, me kwaɗo da allura, sirrin gado 13, mallakar tafin ƙafa, kaska, sirrinki, mallakar kunkuru, raƙumi da akala, mutukaraba, maganin sanyi big& small, nurfan, maganin nankarwa, turaren kasuwa* . *Tarko, mutu ka raba, mb hair treatment,mb original black soap, vip whitening soap,mb syrup,mb face cream,mb lotion,mb cream, mb oil mb set,ƙarshen martaba, dakan amare, maganin basir, zobe me hayaƙi, zoben tazarar haihuwa, maganin haihuwa, mai tula tula syrup, sabon budurci na aure, sabon budurci na ƴanmata, zinaren haɗi, ATM me cingam, ATM na lasa da zuma, maganin sliming, karab da lebo, maganin sanyi, maganin sanyi na maza, man power, haɗin amarya, haɗin me jego, kazar amarya, shu,umin daka, tsumin sharp sharp, hatsabibin daka, garin emergency, zoben mallaka.* KI TUNTUƁE NI DOMIN SAMUN MAFITAR MATSALAR KI MAMAN AFRAH 09013181851 [4/17, 9:33 AM] +234 806 438 0669: https://chat.whatsapp.com/C2hdHP2TbYy0gjsyNpCN6j *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* BOOK 1 PAGE 9 Daƙyar ta tashi da asuba don gabaɗaya jikinta ciwo yake mata, tana zaro ƙafafunta ta sauke a kan gajeran wandonsa da ta cillar tsakanin gado jiya, wani irin yamm jikinta ya ɗauka duk ƙyanƙyami ya kamata tunowa da ta yi da yadda ta shaƙi warin jikin wandon jiya da ya sauka a fuskarta. Sunkuyawa ta yi za ta ɗauke wandon amma sai ta kasa taɓawa don hatta zuciyarta sai ta ji tana tashi, ga wani yawu da ta ji ya taru a bakinta. Fitilar ta kunna haske ya gauraye ɗakin, a kan Aminu ta sauke idanunta da yake bacci duk ya cika ɗakin da munshari, wani kallon tausayin kanta ta masa ganin wannan shi ne matsayin mijinta, a ce mutum ya samu janaba amma bai iya tsarkake kansa ba ya kwanta a haka, ko ba zai yi wanka ba ai ya je ya yi tsarki ya wanke najasar jikinsa. Bayi ta shiga ta ɗauro alwala ta fito ɗan guntun ruwan hannunta ta fatsa masa a fuska, ammma ko gezau bai yi ba sai sharara munshari yake kamar an danne wuyan rago. Ƙafarsa ta fara bugawa daƙyar ya buɗe idanunsa da suka masa nauyi saboda baccin ya sauke a kanta, yana hangota duru-duru don baccin bai wartsake a idanunsa ba. Kallon takaici ta masa ta ce "Ka tashi lokacin sallah ya yi, yanzu duk na yi ƙaran buɗe ƙofar gida da alama ƴan uwanka ne suka tafi masallaci" Wani irin yatsina fuska ya yi yana jin kamar ya mangare ta don ya ji haushi matuƙa da ta katse masa baccinsa mai daɗi, cikin haɗe girar sama da ƙasa ya ce "Sai aka yi yaya? Ko ni an ce idan na falka ba zan yi sallar ba, wai sau nawa zan ce miki kabarinki da ban nawa daban Saddiqa amma sai kike shige mini hanci da ƙudundune kar fa ki manta mijinki nake ba ɗanki ba, ni ya dace na baki umarni" Ya kai ƙarshen maganar kamar zai fasa mata kunne da ƙaran maganarsa ganin yadda ya hayayyaƙo mata. Cikin jin takaicinsa ta danne abin da ta ji ta ce "Haba don Allah yanzu mene ne na tada jijiyoyin wuya da asubar fari, ka san dai gidan nan ba iya mu kaɗai bane, amma a ce da asuba ana jiyo hayaniya ai sai cibi ya zama ƙari, sannan ni ba umarnina bane yin sallar umarnin Allah ne ai" Kallonta yake mamaki yana bayyana a fuskarsa da alama mamakin kalamanta yake a zuciyarsa ya ce 'Kannan yarinyar tana shiga shirgin da babu ruwanta, ai wani lokacin ma auren mace uztaziya ko mai riƙe addini da alama matsala ne in ba haka ba yarinya kamar ƴar gidan malam Kabiru Gombe duk ta bi ta addabi mutane da magana ɗaya' A fili kuma sai ya ce "To tun da umarnin Allah ne ba naki ba, ki sakar mini mara na yi fitsari" Yana kaiwa nan a maganarsa ya ja bargon ya rufa har kansa. Galala take kallonsa rufe cikin bargon tana tuna ko jikinsa fa bar suturta ba tsirara yake, ita ce ma ta sakaya jikinsa da bargon. 'Wane irin miji na aura ne na kasa ganewa, haka zan rayu ni da ƴaƴana ƙarƙashin wanda bai damu da addini ba a ce sallah sai mace tana fama da miji zai yi in ba haka ba sai lokacin da ya shirya a shelaƙe zai yi, shin mene ne fa'ida ko ribar auren namiji irin wannan ga muni ga cin zanzana wato ga ƙazanta ga jahilci' Ta faɗa a zuciyarta tana ta tunanin ina ma akwai yadda za ta yi ta sauya masa halayensa, da ta yi saboda tana ƙaunarsa kuma shi ma dai ta san haka ne ta ɓangarensa amma bata taɓa zaton za ta same shi da wannan halayen wanda ba na ƙwarai ba. Juyawa ta yi ta koma ta saka kaya a jikinta ta saka hijabi ta shimfiɗa sallaya, raka'atainil fajr ta gabatar, bayan ta yi addu'o'in ta a cikin sujada ciki kuwa har da addu,ar Allah ya dawo da mijinta kan hanya madaidaiciya wato yake kiyaye salloli da kuma zama mai tsafta don su samu rayuwar mai ɗorewa haɗe da farinciki don watarana ƴaƴansu su yi alfahri da su matsayin iyayensu, domin ta fahimci in har zai ɗore a haka to tabbas babu wani yaro da zai taso ya ji daɗin ganin mahaifinsa yana wasa da sallah. Miƙewa ta yi za ta gabatar da sallar asubar sai kawai ta ji wani haushinsa ya cika mata rai, tana tunanin a ce su uku a gidan kowacce mijinta ya tafi masallaci amma nata a kwance, shi ba da zuwa masallacin ba kuma bai yi a gida ba. A zuciye ta nufe shi tana zuwa ta cire masa bargon da ya ƙudunduna, can gefe ta warɓar da bargon sai ga shi ya bayyana tsirara, ita kuma sai ta kama ƙugu ta fara jijjiga jiki don ta ga alama sai ta yi da gaske gwara ma tun kan ta fara haihuwa ta yi wa tufkar hanci, kafin yara su zo su ga halin da ake ciki. A ƙufule ya buɗe idon jin iskar da ta fara shiga jikinsa suuuu ya gane buɗe masa rufar ta yi, zaune ya tashi ya shiga ƙarewa kansa kallo ganinsa tsirara cikin dakakkiyar murya ya ce "Wai ni Saddiqa sa'anki ne ni, ko don kinnga makwancina ne raini ya shiga tsakaninmu? Sabosa kina matata kin saba ganina babu kaya har hakan ya zama raini? Ina rufe ki zo don ƙarfin hali ɓarawo da sallama ki buɗeni tsirara ki tsaya a kaina?" Ya faɗa yana wani huci kamar kumurcin zaki. Ganin haka ita ma ta maje ta ce "Mene ne na rainin a ciki? Ni ban ga wani abin rainaka ba, tun da wane dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, da kake cewa na buɗe ka tsirara shin dama ba haka ka kwanta ba? Ai ni ce dama na suturta maka jikin naka amma dama hakan ka kwanta ai" Wani kallo ya jefe ta da shi ya ce "Don kin rufa mini bargo shi ne kika buɗe, ai da kin barni na kwana a haka tun da ba roƙar ki na yi ki rufe ni ba" Ya faɗa yana waige-waige, bata san mai yake dubawa ba sai ta ga ya leƙa can gefen gado, sai kuma ya shiga ɗaga filillikan bata ankara ba sai ji ta yi ya ce "Ina kika kai mini gajeran wandona?" Ji ta yi kamar ta yi kuka amma sai ta ce "Tun da baka bani ajiya ba a kan mai za ka tambaye ni" Kai ya jijjjiga alamar lallai wuyanta ya isa yanka tun da suka fara musayar yawu da ita, ɗaya gefen gadon ya leƙa inda wandon yake sai kuwa ya hango shi yamushe a ƙasa, ɗakkowa ya yi ko karkaɗewa bai yi ba ya saka kayansa ya koma ya kwanta yana mai gargaɗinta da cewa "Wallahi kika kuskura kika ƙara tashina sai kin raina kanki" Yana faɗa ya kwanta. Hannu ta kai ta ja babban yatsan ƙafarsa, yadda ya tashi a fusace ya sa ta yi saurin ja da baya ganin ya miƙe tsaye a kan tsakiyar gadon. Tsalle ɗaya ya yi ya dira a gabanta, da baya ta ja don ta fara tunanin kar ya wanka mata mari, da hanzari ta ƙara matsawa har sai da ta jingina da bango sai da ya je dab da ita ya tura ƙirjinsa ya tokare ta idanunta ta ɗaga ta sauke a fuskarsa kasancewar ya fita tsawo. Baki ya buɗe ya fara magana cikin gargaɗi ya ce "Saddiqa kar ki fara bari in ke sauke fushina a kanki, ina so ki sani ni rashin mutunci gaba na bashi ba baya ba in har kika ce ni za ki shigewa hanci da ƙudundune to za mu saka ƙafar wando ɗaya da ke ne,na lur har yau baki san wa kika aura ba to ina so ki sani a cikin halaye na ko kashi ɗaya baki sani ba a cikin ɗari gwara ki lallaɓa amma in har kina so mu shiga zaman doya da manja ga fili ga mai doki" Tun da ya fara maganar gabanta yake faɗuwa da sauri da sauri don ita tsoronta ɗaya kar ya kai mata hannu, kawai kallon fuskarsa take mai ɗauke da farin abin yawun bacci da ya bushe sawun yawun baccin har haɓarsa, ga bakinsa da ya buɗe yana mata magana sai ta ji ta ƙosa ya bar kusa da ita. Cikin dauriya ta buɗe nata bakin ta ce "Ka yi haƙuri" Ta faɗi hakan ne don ya janye jikinsa daga gare ta, don bata ƙaunar warin da take shaƙa daga gare sa" Hannu ya ɗaga ya kaɗa mata yatsunsa a saitin fuskarta ya ce "Wannan ne karo na ƙarshe" Kai kawai ta iya gyaɗawa. Ƙwafa ya yi haɗe da jan wani gajeran tsaki ya juya ya shiga bayi ya banko ƙofar da ƙarfi. Wata ajiyar zuciya ta sauke, kasancewarta mutum marar son tashin hankali ita in ba bango aka kaita ba bata son yin faɗa ma sai dai in raina mata wayo aka yi. Tana jin ƙaran ruwa a bayin ta juya ta hau sallaya ta shiga gabatar da sallarta, a raka'arta ta biyun tana sujjadar ƙarshe ya buɗe banɗakin ya fito dama wankan tsarkin ya yi ta ɗauro alwala, bayan ta gama addu'a za ta fara karatu ya ce "Fita falo ki yi, zan yi sallah a sallayar" Bata ce komai ba siyam-siyam ta busawa rigarta iska. Yana saka jallabiyarsa ya kabbara sallah yana idarwa ya koma ya kwanta don daga sallama ko azkar bai yi ba ya tashi. Tana karatun amma duk ta damu da halayen da Aminu yake yi, saboda karatun da ta yi ne ma zuciyarta ta yi sanyi da ta gama ta je ta ajiye ta dawo falon ta kwanta a kan kujera tunani barkatai yana adabar zuciyarta. Ko da gari ya waye haka ta tashi suƙuƙu, ɗanwake ta kwaɓa ta yi don shi ta ji tana son ci haka ta musu ta soya manja ta ci da shi, shi kuma sai ta soya masa farin mai. Bayan fitarsa ta gyara ko ina ta shiga yin goge -goge sai da ta gama tas sannan ta shiga ta wanke bayin za ta yi wanka, amma yadda ƙasanta yake raɗaɗin karcenta ɗin da ya yi da farce jiya sai ta ji tana buƙatar shiga ruwan zafi ta gasa jikinta, ruwan ɗumin ta shiga sai kuma ta yi wankan saboda shi gogan kaya kawai ya saka saboda wannan wankan da ya yi ta wadatar a wajensa, ko ta kan brush ɗinsa bata bi ba domin ta san idan ta duba ma ranta ne zai yi ƙuna saboda ta san da wuya in ya wanke bakin. Don ta ga ya sauya mata fuska ma duk da ta san hakan ba ya rasa nasaba da abin da ya faru a tsakaninsu. Wajen shida na yamma tana zaune falo wayarta ta yi ƙara tana ɗakkowa ta ga Khady ce, cewa ta yi "Assalama alaikum ƙawata ta kaina" Daga ɗaya ɓangaren Khady ta ce "Ni na yi fushi, da alama angon nan ya sauya mini ke kin san na ce yau zan taho amma maimakon ki kira ki ji ko na taho shi ne baki kira ba" Ta faɗa cikin sigar zolaya, dariya ta yi don ta san da alama rigima take nema sai ta ce "Yi haƙuri ta hannun damana ni na isa, kawai dai abubuwa ne suka sha kaina" Baki ta taɓe kamar Saddiqae tana ganinta ta ce "To shikenan gani a gida na dawo" Cike da murna Saddiqa ta ce "Don Allah da gaske ko wasa" Dariya mai sauti Khadyn ta yi jin duk Saddiqar ta ruɗe da murna ta ce "Wallahi da gaske nake don ɗazun nan na dawo" "Amma na ji daɗi, ji nake kamar na zama tsuntsuwa in zo in ganki My Khady" Dariya ta fashe da ita ta ce. "Haba amarsu ta ango ai ni zan kawo miki ziyara, in sha Allah gobe a gidanki zan wuni, mu sha hira in zo in ga soyayyar nan taku ke da Babynki Aminu ko na yi kwas nima" Ta faɗa cikin tsokana don ta san irin so da ƙaunar da suka shuka a neman auren. Dimm gabanta ya buga jin wai za ta zo ta ga soyayyarsu, bata san tun tuni komai yana neman ya zama tarihi ko ma ya zama. Sai ta yi arfin halin cewa "Sai kin zo kuwa" Haka dai suka yi sallama suna ta tsokanar juna. Tun bayan da suka yi sallama sai ta shiga taraddadin zuwan Khady tana fatan Allah daidaita tsakaninsu kar ta zo ta gansu, ba ma wannan ba tana addu'a da fatan Allah ya sa har ta zo ta tafi kar su haɗu da Aminu, don wannan tsaf sai ya ja mata raini wannan ƙazantar a yadfa take ƴar ƙwalisa a ce wannan ƙazamin ne mijinta daga ya gifta sai warin rana daga ya buɗe baki kamar ana kwasar kwata ai abin kunya ne wallahi. Ko da suka zo kwanciya ma kadaran kadahan, domin baya ma ya juya mata. So take ta sanar masa za ta yi baƙuwa amma tana tsoro sai dai ta yi ƙarfin cewa "Aminu gobe fa Khady ta ce wunin gidan nan za ta yi" Ta ƙarasa faɗa cikin sanyin murya. Banza ya mata har ta cire ran zai yi magana sai kuma ya ce "Allah kawo ta" Haka kawai ya ce bai ƙara magana ba amin kawai ta ce ita ma bata bu ta kansa ba ta kwanta. Ko da safe da ya tashi jugum ya yi ba dariya ba murmushi ba magana, duk sai ta ji ta rasa ya za ta yi, ko da ta kawo masa abinci ma sai cewa ya yi a ƙoshe yake haka dai da zai fita ta ce masa kayan miya ya ƙare babu a frige buɗar bakinsa sai ya ce "Ki yi wake da shinkafa da mai da yaji" Shiru ta ɗan yi sai ta ce "Amma ka san na ce maka zan yi baƙuwa ai da an kawo na mata wani abu amma kuma babu abu mai ɗan daɗi sai a ce wake da shinkafa" Kallo baki da hankali ya mata sai ya ce "Shi ba abinci ba ne?" Bata ma samu damar bashi amsa ba, da yake dama yau bai fita da wuri ba lokacin ma wajen ƙarfe sha ɗaya da wani abu. Yana dab da bakin ƙofa ta tsinkayi muryar Khady tana sallama, kallonsa ta yi ta ɗan langaɓar da kai alamar ya saki fuskarsa kar a gano wani abu a tsakani, banza ya mata ya juya don yau da yake basu gabatar da sunna da dare ba ankan baƙin ruwan ma bai yi ba kaya kawai ya saka taimakonta ɗaya kayan a wanke, duk da cewa idan har aka ɗora kaya a kan dauɗa to duk ɗaya ne an ce wa makaho ga ido. Fitowa ta yi tana amsa mata, shi ma sai ga shi ya fito abin mamaki sai ya washe jajayen haƙoransa suka gaisa da Khady tana ta musu tsiya wai sun yi aure sun manta da ita. Yana dariya yake tsokanarta kafin ya musu sallama ya tafi su kuma suka shige falo suna ta murnar ganin juna. Zaunawa Khadyn ta yi Saddiqa ta zauna a kusa da ita suna ta hirar yaushe gamo, cewa ta yi bari ta ɗakko mata ruwa ta fita zuwa kicin. Khady fitar Saddiqa ke da wuya ta shiga ƙarewa falon kallo ganin yadda ya sha gyara ko ina sai ƙamshi yake sai dai abin da yake bata mamaki wani ɗan hamami da take ji yana tashi daban da ƙamshin. Ɗan hura hanci ta yi amma sai ta ji warin har yana ɗan shigar mata maƙoshi, kamar an ce ta duba bayanta daga saman kujerar da take zaune ta yi ido huɗu da wani talallan gajeran wando wanda ya gaji da tsufa har ta fara tauyewa daga ƙugu, ya haɗa uban datti waiwayawar da ta yi ne ta ji warin har wani dumm ya sa ta ji a kanta da sauri ta tashi ta bar kujerar ta koma wacce take ɗan nesa da ɗayar. Mamaki take mai ya kawo wannan wandon haka amma jin takun Saddiqa sai ta kawar da wannan tunanin. Saddiqa da ta shigo bata kawo komai ba da ta ga Khady ta sauya wajen zama ruwan ta akiye mata har da fruit da ta yanko mai sanyi. Hira suka shiga yi tana cin fruit ɗin can ta ce "Wai ƙawata kin ganku kuwa kamar ba amarya ba, maimakon in zo in ga kin yi ƙiba kin yi jawur dake amma sai in ga kin rame kin yi baƙi kamar wacce aka yi wa auren dole, ni gani nake babu abin da zai sa in yi rama in har masoyina yana kusa da ni" Ta ce tana kallon Saddiqa. 'Allah sarki Khady baki san mene ne zaman aure ba, a haka muje ganin gidan aure kamar babu matsaloli amma kowane gidan aure cike yake da matsaloli da ƙalubale birjik sai dai na wani ya fi na wani, babu sabon aure babu daɗɗe' Saddiqa ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi dariya ta ce. "Kin jiki da wani abu, rashin lafiya fa nake fama" Idanu Khady ta zaro ta ce "Don Alla da gaske? Ki ce an samu ɗan baba" Dammm ƙirjinta ya buga don sai yanzu ma ita ta tuna cewa wannan watan bata yi priod ba, kallon yanayin da ta shiga Khadyn ta yi ta ce "Ya dai" Murmushi ta yi ta ce "Babu komai" Suna nan suna hira bayan ta ɗora abincin, lokaci zuwa lokaci tana fita kicin ta dubo, amma dai ta ɗan ji ɗan bashi-bashi a falon sai dai bata kawo komai ba, dama sai ta fita ne idan ta dawo sai ta ji falon ya sauya. Bayan an kira sallah Khady ta fita banɗakin tsakar gidan za ta yi alwala, ɗaki ta shiga ta ɗakko sallaya ta zo ta shimfiɗa mata kamar an ce ta ɗaga kanta saman kujerar da Khady ta fara zama ta tashi, aikuwa ta yi arba da gajeran wandon Aminu daƙyal-daƙyal da shi gabanta ne ya faɗi shiru ta yi tana ɗan nazari a nan ne ta ƙiyasta a zuciyarta cewa wannan wandon ne ya saka Khady tashi daga kujerar. Wani takaici ne ya saka ta danne leɓen bakinta tana jin haushi da takaicin ajiye mata wandon da ya yi bata san ma ya ajiye ba. Jin takun Khadyn ya sa ta yi saurin ɗaukan wandon ta shige ɗaki tsabar haushi cilli ta yi da shi wajen drower Aminu, wandon kamar an nuna masa wajen zama sai kuwa ya maƙale a jikin hannun drower yake reto yana ta lilo. Ƴar guntuwar freshner tata da ta rage ta ɗakko ta feshe a falon, ita ma Khadyn tana shigowa ta sauke idanunta a wajen gurbin wandon sai ta ga wayam hakan ya nuna cewa Saddiqa ta kawar da shi. Sun idar da sallar ta zubo musu abinci har da sauran kabeji da albasa ta yanka musu, za su fara ci kenan kamar daga sama ta jiyo muryar Aminu yana rafka sallama, hatta Khady sai da ta lura da sauyin da fuskarta ta nuna, shigowa ya yi yana washe baki firi-firi da shi da fari fulawa yana shigowa falon ƙamshin freshner ɗin ya sauya zuwa wani abun daban saboda ya kwaso rana, kuma abin haushin yana zuwa ya yi wa kansa masauki a falon. Murmushin ƙarfin hali Saddiqa ta yi ta ce "Sannu da zuwa" Amsa mata ya yi ita ma Khadyn ta masa ya amsa sai ya ce "Ai yau na ce tun da muna da baƙuwa gwara na dawo da wuri ni ma asha hirar da ni kar a yi babu ni kawo mini abincin nima" Ya ce yana dariya. Tashi ta yi tana sakin murmushin yaƙe ta fita kicin, tsayuwa ta yi tana jin kamar ta nutse don kunya ya dawo daga kasuwa amma bai san ya je ya tsaftace jikinsa ba, zai zo ya saka su a gaba. Abincin ta zubo masa ta dawo. Suna gefe guda suna ci shi ma ya cin nasa, ana haka sai kuwa ya yi wani kaki, ya kako majina sai kuwa ya tashi su duka da kallo suka bishi ƙofar ɗaki ya nufa yana zuwa ya ɗaga labule ya tofar a ƙofar ɗakin, don daga inda suke ma suna hango inda ya tofar da majinar, yana sakin labulen kuwa da yake labulen har ƙasa yake aikuwa iska ta ja labulen ya tsunduma cikin kakin majinar da ya tofar! TIRƘASHI!!! 09013181851 Kina neman zannuwan gado? Ko kuwa labulaye, kina son siyen frames, ko takalma, kina son siyan mayafai masu beat work ko leshi da atamfa kike so? Ina da kamfala sannan har da laffaya. Hijabai kike so ko kuwa sarƙa da ɗankunne agogo ko warwaro, ina siyar da magungunan mata masu inganci har da na sanyi da basir babu abin da bana siyarwa har da wanda ban zana ba ki dai tuntuɓi MAMAN AFRAH 09013181851 *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09013181851* PAGE 10 Aminu dawowa wajensa ya yi ya zauna hankali kwance ya cigaba da cin abincinsa, Khady kuwa zuciyarta ce take ta tashi ganin abin da ya yi domin tun da ya tofar da yawun nan bata kai ko da loma ɗaya ba bakinta sai jujjuya cokalin take, Saddiqa kuwa kunyar duniyar nan ce ta ishe ta duk da ita ma abincin ya fice mata rai amma kuma tana jin kunya da nauyin abin da ya yi a gaban ƙawarta. Ganin duk sun yi jugum-jugum bakinsa da abinci ya kalle su da mamaki ya ce "Ƙawayen juna ya kuka dakata da cin abincin, ai ni wallahi Saddiqa yau kin biyani da wake da shinkafar nan, ya yi daɗi sosai" Ya faɗa yana ƙara cika cokali ya kai bakinsa, Saddiqa bata ce komai ba sai Khady ce ta yi ƙarfin cewa "Ai kam ya yi daɗi ni da yake dama ban cika cin abinci sosai ba, yanzu ma ƙoshi na yi ba don abincin ya isheni ba" Ta faɗa tana sakin dariyar yaƙe. Bai sake magana ba sai da ya cinye abincin nan tas, lokacin Saddiqa ta haɗa kwanukan ta fita da su tsintsiya da klin haɗe da ruwa ta ɗakko ta wanke ƙofar ɗakin ta ɗakko wani labulen ta cire wancan ta saka ta kai bayi ta saka a bokiti ta wanke ta fito ta je ta shanya. Kiran sallar la'asar ne ya saka Khady cewa bari ta je ta yi alwala, tana fita Saddiqa ta kalle shi jin yana sakin gatsa haɗe da miƙe ƙafa a kan kujera bashi ma da niyyar tashi yin sallah ta ce "Yanzu Aminu kai sai ka ce ƙaramin yaro a ce a ƙofar ɗaki za ka tofar da yawu? K...Tun kafin ta kai ƙarshen maganar ya katse ta da faɗin "To sai aka yi yaya wai ku mutane mai ya sa ba a iya muku ne? Yanzu yawu ma don na tofar sai an tuhume ni? Idan ba a ƙofar ɗaki ba a ɗakin kike so in tofar hallaw cibi ya zama ƙari? To ni da gidana babi wanda zai mini wani iyayi wai ke sarkin ƴan tsafta" Idanu ta runtse tana jin takaicin maganarsa amma sai ta danne ta buɗe idanun da tuni sun yi jajur saboda takaici, ta ce "Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah tun da mu ma sallah za mu yi" Shiru ya yi bai ce komai ba sai kuma ya ce "Ko dai in yi alwalar in zo in ja ku jam'i?" Wani haushi ta ji ita da take so ya fita a falon ko sa samu damar shaƙar iska mai daɗi amma wai zai ja su jam'i ɗan rausayar da kai gefe ta yi ta ce "Kamar na ga baka yi azzahar ba fa, kuma ta yaya za ka ja mu sallar la'asar" Shiru ya yi don tabbas ya san bai yi ɗin ba sai kuma ya ce "Na rama ta daga baya" Kallonsa ta yi tana jinjina jahilci irin nasa ta ce "A'a azzahar ai ita ya dace a fara yi sannan la'asar, wai ni kuwa anya Aminu ka yi islamiya?... Tun kafin bakinta ya rufu ya hayyyaƙo mata tamkar zai kai mata duka ya ce "Ban yi ba Saddiqa tun da ke kika koya mini karatun sallar da nake yi, tun da abin ya zo da cin fuska ba zan yi sallar ba idan ke ake yi wa in na yi ki watso mini" Wannan maganar da ya faɗa a zafafe ya yi daidai da tahowar Khady don haka a kan kunnuwanta ya faɗa gabanta sai da ya buga jin hargowar da yake yi, a bakin ƙofar ta tsaya da yake labule ya shiga tsakaninsu. Shi kuwa yana kaiwa nan ya tashi fuuuu ya shige ɗaki, jin sallar Khady sai ta yi saurin kawar da kai gefe ta amsa mata tana danne kukan da yake son ƙwace mata. Ɗaki ta shiga da sauri a kan gadon ta gan shi ko kallo bai ishe ta ba, bayi ta shiga ta ɗauro alwala a can ta yi ɗan kukan takaici kasancewar ta mai zurfin ciki bata son Khady ta fahimci abin da yake faruwa, bata san cewa Khadyn ta ji abin da ya ce na ƙarshe kuma ko ba komai ai ta gama fahimtar Saddiqar tana cikin damuwa. Bayan sun idar da sallar Khady ta dafa kafaɗar Saddiqa cikin ƙasa da murya ta ce "Ƙawata na san kina da zurfin ciki, kuma duk da baki faɗa mini ba na san kina da damuwa, amma matsayinki da kuma kusancina da ke ba zai sa in kasa faɗa miki wani abu ba ina so ki yi watsi da zurfin cikin da kike da shi ma'ana ya zama kina faɗawa wani damuwarki saboda kar kike barin damuwa a zuciyarki hakan zai haifar miki da matsala" Wasu hawaye ne masu zafi suka ƙwace mata, ita kanta Khady idanunta cike suke da ƙwalla domin tana jin Saddiqa tamkar ƴar uwarta ta jini ganin Saddiqar bata ce komai ba sai ta ɗora da faɗin "Ban ce kike fitar da sirrinki ba, amma a ƙalla kike fitar da damuwarki ba a son ake tarawa zuciya damuwa saboda gudun matsala, sannan addu'a ita ce takobin mumini ki dage da ita sosai duk da na san baki da sakincin yinta abu na ƙarshe, kar kike bari namiji ya rainaki ko ya raina wani naki ke dai ki zama mai biyayya amma kar ki yarda ake miki cin kashi, domin shi itace tun yana ɗanye ake tanƙwasa shi abin da nake nufi idan har kina bari kpwace shara namiji ya watsa miki to za a wayi gari har girman ƴaƴanki a gabansu zai ci zarafinki, kuma ko da ya auri wata nan gaba ita in ta nuna ba za ta ɗauka ba sai ya zamana ke kalai ce jujin zuba shararsa, duk da bani da aure amma na san abubuwa da dama a kan aure" Saddiqa sai ta ji tamkar Khady ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi a take hawaye suke sintiri a kumatunta kuma daga hakan ta gane cewa kuka wani ma ya lallashe ka rahma ne, sai da hawayen ya tsagaita ta ce "Na gode ƙawata kuma duk abin da kika faɗa haka ne, zan kiyaye kuma zan yi duk iya ƙoƙarina" Ta faɗa ita ma cikin raɗar don ta san Aminu zai iya kasa kunne, kuma ta ƙara gane cewa yanzu da yake tare da wata budurwar kenan in tana danne komai in ya auro wata ita ta zaɓa bola. Ta jima tana lallashinta har dai ta ga ta saki ranta daga nan ta mata sallama ta raka ta ta tafi. Khady tana tafiya ta tsaya a falo ta share hawayenta tas, tana shiga ɗakin ta gan shi yana sallah idanu ta sauke a kan gajeran wandon nan nashi na jikin drower bakin gado ta zauna har ya sallame sallar. Dama yana gama sallama yake barin kan sallaya saboda ba azkar yake yi ba. Kallonsa ta yi yana danna waya ta ce "Aminu shin mai ya kai wandonka falo saman kujera?" Tambayar ta zo masa a bazata duk da ta yi kama da tambayar rainin hankali amma sai ya maje ya ce "Kamar ya?" A ƙufule ta ce "Ya ina tambayarka kana tambayata?" "Ra'ayi riga" Ya faɗa hankali kwance. Ƙwafa ta yi cike da ɓacin rai ta tashi za ta bar ɗakin ƙiiii ta ji ya janyota ta dawo waiwayowa ta yi ta ga ya haɗw fuska babu zato ba tsammani ya ce "Daga yau da rana mai kamar ta yau kar ki ƙara gogin yi mini ƙwafa ni ba sa'anki bane" Yana kai wa nan ya saki hijabin nata da ya kama, bata ce masa komai ba ta juya ta bar ɗakin. Sai da ya ga la'asar lis ya ƙwama uwar hula ya zo wuce ta tana zaune a falo ya ce "Sai na dawo" Da banza ta yi da shi sai kuma ta ce "A dawo lafiya" Ta faɗa ba tare da ta kalle shi ba tun da ta ga har zai iya fita haka yana warin rana shi abin ma ba ya damunsa ita kuwa har mamakinsa take yi. Bai dawo ba sai bayan isha'i, lokacin ta shirya tsad cikin fararen kayan bacci, tana kwance tana game a waya, ganin yana washe baki yana wani nan -nan da ita ta san wani abu zai buƙata ita kiwa ta ƙudurce a ranta cewa, duk runtsi yau ba za su haɗa jiki ba har sai ya tsafta ce jikinsa ko dai ya haƙura. Kamar abin kirki ya zauna yana ta zuba kamar kanya, zuwa can ya ce "Amarsu ta ango daga ke babu ƙari" Kallon maƙaryacin banza ta masa kafin ta buɗe baki ta ce "Namiji ai ba mijin mace ɗaya bane" Dammm ƙirjinsa ya buga, a take ƙwaƙwakwarsa ta shiga tariyo masa furucin da ya yi wa ƴar aljanna lokacin suna waya a kicin, tunani ya fara ko dai ta ji wayar da ya yi ranar sai kuma ya kawar da maganar ta hanyar cewa "Wani namijin ba" Wani murmushin rainin hankali ta yi ta ce "Uhm in ji mai ciwon haƙuri" Daga haka ta mayar da hankali kan game ɗin pop game da take yi. Shi kuma jin yana tsuma yana son kawar da abin da yake ji, sai ya ɗan matsa tare da miƙa hannu ya shafo kafaɗarta da yake wuyan rigar sleeping dress ɗin irin wanda yake da kafaɗa a buɗe ne. Laushi da santsin fatarta ya sa ya saki wani murmushin jin daɗi, ita kuma a nata ɓangaren ba haka bane domin kuwa garin shafo kafaɗarta ya karce ta da farce. Bata nuna masa komai ba tana jiran har ya ida nufinsa ta gabatar da tata buƙatar wacce take ganinta a matsayin sharaɗin da za ta gindaya masa na kwanciya da ita. Ɗan matsawa ya yi yana sosa ƙeya ya ce "To wai ni a ajiye wayar mana tun da ango ya zo kusa, ni fa saboda ɗokin kasancewa da ke yau ko abincin dare ba zan ci ba" Wani murmushi ta saki wanda ya bayyana kyawawan jerarrun haƙoranta wanda suke a jere kamar masara, suna sheƙi kamar bayan kwanon silba. Ganin kyan da ta yi ya ƙara fusgarsa zuwa gare ta ya matsa kusa, ganin tarkonta ya kama tsuntsu sai ta yi yunƙurin sauka daga gadon, cikin rashin fahimta ya ce "Ina kuma zaki bayan buƙace nake" Idanu ta farfara tare da langaɓar da kai ta ce "Ai ba wani waje zan je ba abu ne zan ɗakko maka" A ransa sai ya fara tunanin ko dai Saddiqa ta fara wayewa ne maganin ƙarfin maza za ta bashi, wannan tunanin ya sanya shi ya ƙara jin kansa ya masa gingirin gim. A hankali ta tafi kan madubi cikin takunta na mace mai aji da nutsuwa, da kallo ya bita yana ɗan lashe baki kamar tsohon maye. Baƙar ledar da ta miƙo ya karɓa, tana tsaye ya buɗe ledar ya leƙa abih da ya gani ciki ne ya sanya fuskarsa sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗako kai yana kallonta mamaki shimfiɗe a fuskarsa ya ce "Mene ne wannan?" Ɗan murmushi ta yi ta ce "Sheba da ake shebin da reza da ake yankan farce, Aminu idan ka ga yau ka kusanci ne to sai in har ka aske gashin hammatarka da na mararka sannan ka zauna ka yanke farcenka, abu na ƙarshe sai ka yi wanka soso da sabulu sannan sai mu yi abin da za mu yi babu cuta babu cutar... "Wannan labarin ƙanzon kurege ne, ki ƙaddara tatsuniya kike mini" Ya faɗa rai a mugun ɓace don zuciyarsa har ta raya masa cewa, Saddiqa bata son bashi haƙƙinsa ne shi ya sa ta ɓullo ta wannan hanyar. Daga nan inda yake ya yi jifa da ledar kan madubin. Kallon abin da ya yi ta yi tana jin takaici ta ce "Tun da haka ka ce za ka ga labarin ƙanzon kurege" Tsaye ya miƙe tamkar zai kai mata duka ya ce "Indai har kina ganin kin kai ki saka doka ko sharaɗi in bi, to ki sani baki isa ba kin yi kaɗan kin yi tsarara kamar ruwan shayi, in dai har wannan abun naki kike taƙamar sai na yi aski da yankan farce haɗe da wanka to ki jiƙa ki sha ba a so, sannan ina so idan kin manta in miki tuni ni mijin mace huɗu ne idan kin hana zan iya kawo wacce za ta bani sannan ta tarairaye ni ba tare da ta yi la'akari da ƙazantatar da kike ikirari ba" Yana kaiwa nan ya juya zai yi wajen drower raina sai ƙuna yake ta shiga bayi ta ɗakko ruwa a hannunta tana zuwa ta kama hannunsa bai yi musu ba duk da ransa a ɓace yana son ganin gudun ruwanta. A hannunsa ta zuba ruwan tare da nannaɗe hannun rigar ta shiga murzawa, aikuwa datti yake fitowa kamar wanda bai taɓa wanka ba, dirzawa take datti yana fitowa da sauri ya janye hannunsa cikin hargowa ya ce "Wannan rainin naki ya yi yawa har ni kike yi wa titsiye kina son fito mini da dattin da ya ɓuya a jikina, ke baki san akwai dattin da yake zama kariya a jikin fata ba" Kallon raini ta jefe shi da shi ta ce "Ba wani nan dauɗar rashin wanka ce wanann" Tsaki ya daka ya ƙara juyawa taku ɗaya biyu ya yi maganar da ta fara kamar haka ita ta katse masa tafiyar. "Idan dai har kana ganin akwai macen da za ta juri zama da kai a wannan halin da kake ciki, to ga fili ga mai doki" Ko kallo bata ishe shi ba ya juya da nufin zuwa ya ɗauki gajeran wandonsa, saboda yana so ya saka sai ya kwanta tun da ya ga alamar haƙƙin nasa ba zai samu ba, kayan jikinsa ya cire duka don gajeran wandon zai saka ya kwanta. Saddiqa da take jiran ganin abin da zai yi idanunta suka sauka a kan gajeran wandon da ya nufa zai ɗauka, cikin zafin nama ta ɗare kan gado ta dira sai gata ta riga shi zuwa wajen suka miƙa hannu kusan a tare za su ɗauka cikin rashin sa'a Aminu ya riga ta ɗauka, baki ta damƙe da haƙori ganin ya yi wa wandon riƙon sakainar kashi ta yi saurin tankwaɓe hannun wandon ya faɗi, duk da bai san dalilinta na son ɗaukan wandon ba amma dai ba ya so ta ɗauka. Tana ɗauka yana tsaye sai gani ya yi ta ɗan sunkuya ƙasa, bai ankara ba sai ta bi ta tsakanin ƙafafunsa, cikin jin haushi ya ce "Wai mai za ki yi da wandon nan" Ya ƙarasa faɗa rai a ɓace. Cikin hakin da take na cin nasarar zuwan wandon hannunta ta ce "Aminu tun da wannan wandon ba shi kaɗai ne gajeran wandonka ba, daga yau ka rasa shi" Jin furucinta sai da gabansa ya faɗi, don shi babu wandon da yake so a duniya sama da wannan wandon nasa da ya mallaka tun kafin ya yi aure Cikin tsantsar mamaki ya ce "Sakawa za kike?" Ya tambaya don shi a ganinsa in ba sakawa za ta yi ba mene ne na cewa ya rasa shi" Ko uffan bata ce ba sai ta juya ai kuwa ya take mata baya yana faɗin "Wallahi kika sake wani abu... Bai ƙarasa ba ganin ta zura da gudu shi ma ya bi bayanta da gudun, har falo suka fito ganin ta nufi hanyar ƙofa sai lokacin ma ya lura tsirara yake, ga shi gida ba su kaɗai ba. Da gudu ya juya ɗaki ya sako rigarsa jallabiya ya fito da sasaarfa, yana fitowa tsakar gidan ya hange ta ta yi hanyar kicin Sumayya da take hangensu daga windown tsabar tsegumi har ɗaɗɗage take. Kafin ya cim mata har ta shige kicin, Saddiqa kuwa tana shiga kicin ta shiga neman ashana da yake a rikice take sai ta rasa ina take jin takun gudu-gudu sauri-saurinsa ya sa ta shiga waige sai sannan ta hangi ashanar a saman loka. Da sauri ta ɗauka ta fito daga kicin ɗin, yana shirin shiga ya ga ta fito tamkar an jefo ta, har bangaje shi ta yi, can ta yi wajen haryar bayin tsakar gidan ta jefar da wandon ta ƙyasta ashana t jefa masa a take ya kama da wuta. Aminu da sai lokacin ya fahimci abin da ta yi idanu ya zaro a guje ya ƙarasa ya saka ƙafa ya taka wandon wutar ta mutu da wata uwar harara ya bita ya nufi ɗaki saboda ba ya so ya fara mata a tsakar gidan. Yana zuwa falo ya ɗaga wandon nan ya ga saitin mazaunai ne daga baya ya ƙone, sai ya fito ƙunar har gaban wandon kamar ya yi kuka ya ji saboda soyayyarsa da wandon nan, ɗaki ya shiga ya saka wandon ya cire jallabiyar ta mudubi ya juya ya hangi yagar mazaunan ya ga ana ganinsa, ya duba gaban ya ga mafitsararsa ta fito daga yagar. Wani takaici ne ya turnuƙe shi amma bai ji zai iya cire wandon ba, yana nan tsaye sai ga Saddiqa ta shigo da mamaki ta kalli wandon a jikinsa ita kuwabta ƙiyasta ba zai sake saka wandon nan ba. Baki ya buɗe zai mata masifa ai kuwa bai kai ga magana ba ya ji ta saka hannu ƙiiii ta fisgi wandon da yake ba wani ƙwari gare shi ba ya tsufa ga dauɗa ta kashe masa ƙarfi kullum shi yake sakawa kamar rai, cikin yahar ta saka hannu ɓetttt yana ja tana ja saida gabaɗaya ta yaga shi shammatarsa ta yi ta fice da wanda ta riƙe ta bar shi sanye da wajen ƙafar wandon ɗaya wacce ta zamo wajen cinyarsa. Tana fita ta ƙyasta ashanar sai da ya ƙone ƙurmus, Sumayya da take ganin komai sai dariyar mugunta take dukmda bata gane mene ne aka ƙona ba amma dai ta fahimci rigima suke. Tun da ta dawo ɗakin yake masifa kamar zai cinye ta ɗanya, bango ta ba ajiyarsa ta hau gadon ta kwanta, shi kuma yana tsaye tsirara wai ba zai saka wani wandon ba sai ta maido masa da wanda ta ƙona, cikin bala'i ya ce "In na saka wani wandon shege nake wallahi ki tashi tun dare bai miki ba ki dawo mini da wandona" Kallonsa ta yi ta ce "Sai ka ɗaura zani in ba za ka saka wandon ba" Ta ce tana kallon yadda yake tsaye babu kaya kamar wani ƙaramin yaro. Tun da ta bashi baya bata bi ta kansa ba, yake ta masifa ƙarshe bata san yaya ya ƙare ba don bai kwana a gadon ba a ƙasa ya ajiye katifa ya kwanta. Tun da ta ƙona gajeran wando kamar ta ƙona ɗan mutum sai ya zamana ya ɗauki wata muguwar gaba da ita, sannan kuma wandunan nasa ba ya amfani da su tun da ya nuna bata isa saka shi abin da bai yi niyya ba. Gidansu ya koma a ɗakinsa wani bakko da ya ajiye wasu kaya ya sake ɗakko wasu wandonan biyu wanda sun fi wanda ta ƙona tsufa, ya kawo su gidan yake sakawa sai idanu ta zuba masa. *BAYAN SATI BIYU* Jinya take zazaaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani, ga bata cin abinci sai abubuwan kwaɗayi yawan tashin zuciyar da take shi ya fi damunta dole sai lemon tsami take ajiyewa tana lasa, hakan yake kwantar mata da tashin zuciyar. Aminu ganin haka sai ya tsiri takura mata sannan magana ɗaya ce a kan cewa ba dai ciki ta yi ba, wannan kalmar tana ƙona mata rai sai ka ce ita ta yi wa kanta cikin da zai ke faɗin ba dai ciki ta yi ba. Dakyar ya bata kuɗin zuwa asibiti yana cewa ya san ma ba ciki bane, don haihuwa ba yanzu ba shi a shekara biyar ma babu tsarin haihuwa a tsarinsa. Wannan dalilin nasa ya sanyata fargabar sakamakon asibitin tun da ta san dai bata ganin proid ɗinta, sakamakon farko da ya fito ya nuna cikin wata biyu kwance a mararta . Bayan ta dawo gida gabanta yana tsananta bugu ta miƙa masa takardar sai da ya taɓe baki bai karɓi takardar ba ya ce "Ba panadol bane aka rubuta miki idan na fita zan sayo, ko ba shi kaɗai bane aka rubuta?" Ya faɗa yana maida hankalinsa kan wayar da yake charting da ƴar aljanna. Wani ƙululun baƙinciki ne ya tokare ta ta kalles shi ta ce "An ce ina ɗauke da cikin wata biyu" A kiɗime ya tashi tsaye har wayar tana faɗuwa ƙasa ya kalle ta da mamaki cikin ɓacin rai ya ce "Wane irin ciki wai? Ko dai suna nufin kina da fama da ciwon ciki" Wani kallo ta masa na takaici kafin ta ce "Ba ciwon ciki ba ina da ciki na haihuwa... Tun kafin ta rufe bakinta ya dakatar da ita ta hanyar cewa "Wanann wasa ne ma, sannan idan har gaske ne ina so ki sani zan sayo miki magani ki sha cikin ya zube don ni haihuwa bata cikin tsarina a yanzu" Da tsananin tashin hankali shimfiɗe a koɗaɗɗiyar fuskarta irin ta marar lafiya ta ce "Zubarwa? Cikin sunnar? To ni wallahi ban shirya yi kisan kai ba, kuma wannan cikin sai na haife shi, ka san baka shirya haihuwa ba ka aure ni? Ko ka san baka shirya haihuwa ba ka neme ni ka biya buƙatarka shin baka san cewa cikin zai shiga ba dama? To wallahi ko mai zai faru sai dai ya faru amma ba zan taɓa zubar da ciki ba ko da na shege ne bare ɗan sunna" Cike da takaicin shigar masa hanci da ƙudundu ne da take ya kalle ta ya ce "Ki shirya zama cikun uƙuba kuwa a gidan nan" Kallonsa ta yi tana jin haushin kasancewarsa mijinta kuma uban ƴaƴanta ga ƙazanta ga jahilci ga rashin tsoron Allah, duk da bata da ikon tare ƙaddararta amma ta yi da na sanin auren Aminu!. Tun daga wannan rana kamar yadda ya faɗa hakan ce ta faru kwata-kwata bata jin daɗin zaman gidan, duk wani abu da take so na kwaɗayi sai dai ta nemawa kanta taimakonta ɗaya idan ta je gidansu Abbanta yana bata kuɗi tun da ba wata sana'a take yi ba, da wannan kuɗin take samu ta sayi abu in tana sha'awa. Bayan wannan siraɗin sai kuma wasu abubuwa suka fara fitowa lokacin cikinta yana da wata biyar ya fito amma ba sosai ba kasancewar cikin fara bai fiya girma ba. Ƙazanta dai sai abin da ya cigaba saboda shi dai mai hali ba ya canjawa. Yanzu abin da ya tsiro da shi, ba ya siyan sabulun wanka tun da shi dama ba damuwa ya yi da sabulu ba wankan farin ruwa ma sai lokaci zuwa lokaci, sabulun wanki ba ya siya mata bare a zo ga turaren shafawa ko freshner makilin kuwa ba a ma batunsa duk waɗannan kayan ita take saya amma kuma in ta saya shi kuma zai yi amfani da su idan amfanin hakan ya taso. Ganin hakan sai take ɓoyewa tun da shi ma da haƙƙin hakan yake kansa bai siya ba, babu dalilin da zai sa ta sarawa jaki ciyawa. Abin da ta lura kawai ya tsane ta ne saboda cikin da take ɗauke da shi wanda ya so a zubat tun yana ƙarami ta ƙi. Da yammacin wata ranar laraba tana zaune tana yanke farce a ƙafafun ta da suke kumbure, wayarsa ce ta yi ƙara ganin sunan ƴar aljanna sai ya washe haƙora, da tashi zai yi daga wajen sai kuma don ya ƙona mata rai ya ɗaga wayar a gabanta ya ce "Hello ƴar aljannata" Daga ɗaya ɓangaren Zulaiha ta ce "Na'am ɗan aljanna albishirinka" Ta faɗa cike da ɗokin sanar da shi. Baki a washe ya ce "Goro fari ƙal" Cikin murna ta ce "Babana ya ce ya amince a yi bikina, wai na cigaba da karatun a ɗakin mijina shi ne ya ce in faɗa maka ka turo manyanka" *INA SANAR DA KU CEWA WHATSAPP SUN KULLE MINI WANNN ACCONT ƊIN 09013181851 YANZU DA WANNN NUMBER NAKE CHARTING 09025576222* *DUK MAI BUƘATAR MAGANA DA NI YA MINI TA WANCAN ƊIN KAFIN SU BUƊE MINI ƊAYA, MAI SON LITTAFI KO KAYAN MATA NA KAMFANINMU NA MEERAH B HERBS KO KAYANA NA ZANNUWAN GADO TAKALMA ATAMFOFI DA SAURANSU YA TUNTUƁENI* *MAMAN AFRAH 09025576222* [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 11 Gaban Aminu ne ya buga da ƙarfi, jin wani ɗan jijjiɓin tashin hankalin kuma, a zuciyarsa ya ce 'Ana wata ga wata hallaw, ni da nake ta fama da matar ɗaya ma abu yana neman gagara, ita ma tana zaune da ciki turtsitsi ke ma ki zo da wanga batu' A fili kuma sai ya haɗiye wani yawu muduk, yana mai mayar da kallonsa kan Saddiqa da take yankan farcenta hankali kwance a zuciyarsa ya ƙara faɗin 'Saddiqa wannan abu ba ke kaɗai ya samu ba har da ni, mata biyu ni Aminu ta ina zan fara ɗawainiya da su' Ya faɗa yana jin tamkar ya kurma ihu. Saddiqa kuwa ganin ya tsare ta da ido sai ta ce "Lafiya dai?" Ta faɗa tana kallonsa, yaƙe ya saki yana wani ciccira ido tamkar kwarton da aka kama a ɗakin amayar ya ce "Babu komai Saddiqa cigaba da yankan farcen naki, ni ma kya aramin rezar in yanke" Ya ce bayan ya ɗan kawar da wayar saga kunnensa yana sakin wani yaƙen a karo na biyu. Saddiqa kuwa mamaki ne ya kamata ganin mutumin da ko kaɗan ba ya son ya raɓi tsafta, amma yau har yana batun zai yanke farce, duk da haka bata yarda da maganarsa ba don ta ga rashin gaskiya ƙiri-ƙiri a tare da shi ga wani uban gumi da yake wanke masa fuska da wuya, tamkar wanda ya yi wa sarki ƙarya. Daga ɗaya ɓangaren Zulaiha ƴar aljanna ta katse shi da faɗin "Wai ɗan aljannata ya na ji ka yi shiru? Ko baka yi murna da jin wannan kyakkyawan albishir ɗin ba" Jin abin da ta ce sai ya tattaro jarumta ya tashi ya fita daga falon, Takalmi ya saka ya fice daga gidan, yana zuwa ƙofar gida ya buɗe baki ya ce "Kai amma Baba ya kyauta" Wannan kalmar kaɗai ya yi ƙarfin halin faɗa, don shi gabaɗaya sai ya ji an rikita masa lissafi ai shi tun da aka ce sai ta gama karatu ya ɗauka shekaru ne a nan gaba. Zulaiha jin amsar ta yi banbarakwai don ta ɗauka ɗoki da murnarsa ya wuce haka, cikin jin haushi ta ce "Ni ban gane maka ba, yanzu in zo maka da wannan albishir amma ka ce wai Baba ya kyauta, sai wani kame -kame kake anya kana da gaskiya kuwa? Ko dai tsoron matarka kake?" Jin ta harbo jirginsa tana cewa yana kame-kame kamar dai bai yi murna da jin maganar ba sai ya saki wata dariya yana mai bayyana farinciki ya ce "A haba ita ɗin banza, yo har akwai wata mace da za ta sa in ji tsoronta saboda ke, ai kawai i cewa Baban zan aiko kawai ya shirya watannin aure in ma shekara zai saka to, in kuma yana ganin ma har kya gama karatun ai duk ana kan hanya... Jin furucinsa sai ranta ya ɓaci cikin harzuƙa ta ce "In ce maka ya janye batun karatun kake cewa wai in har na gama karatun, kuma da kake cewa watanni ko shekara shi cewa ya yi wata ɗaya zai saka" Ta ce ranta yana ƙuna, gabansa ne ya faɗi wai wata ɗaya, dakyar ya shawo kanta yana lallaɓa ta bata san gabaɗaya shi ta saka shi a matsala ba, ba wai ba ya sonta ba amma riƙon matan biyun ne ya sare. Washe gari da daddare ya nufi gidansu, da Fatima ƙanwarsa ya fara cin karo don ita ta amsa masa sallama, bayan ya shigo ta ce "Yaya barka da dare" Hannu ya ɗaga mata bai amsa ba, saboda ya lura yarinyar nan ta ga makwancinsa don ko ranar da ya zo ɗaukan gajerinan wanduna sai da ta leƙa ɗakin nasa, tana tambayar ina zai kai wannan tsumman ko ƙonawa za a yi ya bata ta ƙona a murhu. Ita ma ta faɗi hakan ne saboda ta san wataƙila gidansa zai tafi da su saboda ta san mai hali ba ya canja halinsa, amma wata uwar harara da ya jefe ta da ita, hakan ya sa ta bar wajen ba shiri. Falon Babansu ya wuce a can ya same su shi da Umma suna ɗan taɓa hira, bayan ya gaishe su Umma take tambayarsa Saddiqa ya ce tana lafiya. Kai ya sunkuyar yana son faɗar maganar gidansu Zulaiha Umma ce ta ce "Aminu lafiya kuwa? Ko dai Saddiqar ce babu lafiya?" Murmushi ya saki yana mai sosa ƙeya ya ce "Lafiyarta ƙalau, kawai dai ina tafe da wani batu ne" Kallon tsaf Umma ta masa tana jin bata yarda da batun nasa ba amma sai ta ji Babansa ya ce "Mene ne Aminu" Jin abin da Baban ya faɗa ya shiga zayyana abin da yake tafe da shi cikin ɗari-ɗari. Wani salati da Umma ta kwasa, shi ya sanya shi ɗagowa yana kallonta, tana dire salatin ta shiga faɗin "Aminu ashe baka da hankali? Yanzu yarinyar nan mai ladabi da biyayya, tana ɗauke da ciki za ka je mata da batun ƙarin aure, kai yanzu ko wani ya ce ka yi aure ai ka ce ba yanzu ba am... Maganar da Baba ya yi ce, yana mai ɗaga mata hannu ita ta dakatar da ita daga faɗa da ta fara masa ya ce "Yanzu ke mene ne na tada jijiyoyin wuya, kawai don ya ce zai ƙara aure, sunnar ma'aikin kamar dai ya ce zai yi saɓon Allah" Wani murmushi Aminu ya yi yana mai sunkuyar da kai, jin Baba ya goyi bayansa ji yake kamar ya tashi ya taka rawa. Kallon Baba Umma ta yi za ta ce wani abu amma ya ƙata dakatar da ita da faɗin "Ku mata dama ai bakwa ƙaunar kishiya, kin ga idan kika yi amfani da kalmar bahaushe da yake cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ba za ki so a mata kishiya ba" Jin furucinsa sai Umma ta buɗe baki wannan karon bai dakatar da ita ba, ta ce "Yarinyar nan ba ƙaramin haƙuri take da Aminu ba, amma kuma maimakon ya bari ma ta haihu duka yaushe aka yi auren?" Murmushi Baba ya yi tare da faɗin "A rana ɗaya ma ana iya ɗaurawa namiji aure, da mace sama da ɗaya, kin ga kenan ƙara aure bayan watanni ba zai zama laifi ba, sannan a zaman aure ai kowa haƙuri ake da juna ba wai mutum ɗaya ne mai haƙurin ba" Bata ce komai ba don ta san ko kwana za a yi ba zai sakar mata ba, kallon Aminu ta yi ta ce "Ka faɗa mata?" Cikin sanyin murya ya ce "A'a so nake sai abu ya kankama" Tana mai jin takaicin furucinsa ta ce "Allah tabbatar da alkairi" Baba ne ya ce amin don shi Aminu ya sunkuyar da kai" Gyara zama Baba ya yi ya ce "Zan sanar da kai lokacin da za mu je sai ka faɗa mata, ita kuma sai ta sanar a gidan nasu, Allah baka ikon yin adalci" Daga haka ya shiga yi wa Baba godiya ya musu sallama ya fita. Yana fita Baba ya kalli Umma ya ce "Ki godewa Allah, da har aure ne a ransa ba wai neman mata ba, nawa suna da auren amma suna neman matan waje , kawai ki masa addu'a Allah bashi wuyan ɗauka tun da dai har yana sana'arsa" Kai kawai ta gyara don takaici ma ya hana ta magana, tana tuna Saddiqa da irin haƙurin zama da shi da take, fa shegiyar ƙazantarsa. Aminu yana fitowa suka yi kiciɓis da Fatima, ta zo wucewa ta wajen falon Baba kallon tsaf ya mata kawai sai ya ji bai yarda da ita ba, cikin kakkausar murya ya ce "Ke zo nan" Tahowa ta yi sai da ta zo cikin girmamawa ta ce "Gani Yaya" Yana aika mata harara ya ce "Ba ke uwar ƴan rawar kai ba, mai shegen surutu idan kika sake ƙaiƙaiyin bakin ki ya sa, kika faɗawa Saddiqa wata magana ni da ke ne" Kallon rashin fahimta ta masa ta ce "Wace magana kuma Yaya?" Bai faɗa mata komai ba ya sake cewa "Gargaɗi nake miki dai" Yana kaiwa nan, ya tafi ya barta tsaye tana ta mamaki wace magana ce wannan da yake ta faman faɗin kar Saddiqar ta sani. *BAYAN KWANA UKU* Su Baba sun je nema masa aure, sun bayar da kuɗin gaisuwa sannan a wajen aka tsayar da rana da yake har kayan sa ranar Baban Zulaiha ya ce su kai kawai a yi zama ɗaya. Fatima ta ji ciwon auren nan da Yayanta zai yi amma dai sai ta yi addu'ar Allah sa ta kirkice kuma mai tsafta kamar Aunty Saddiqa. Bayan kwana biyu, yana zaune a falo tana shan garin kwaki da suga da madara, sai gyaɗar da ta saka a ciki. Aminu ne ya zo ya zauna a kan kujera da yake ita a ƙasa take a zaune ta miƙe ƙafa ɗaya, ɗayar kuma ta lanƙwasa ta. Cikin izza ya dube ta yana wani shan ƙamshi ya ce "Saddiqa ina son sanar da ke wata magana, gabanta ne ya faɗi bata san dalili ba, amma hakan ba ya rasa nasaba da rashin sabo a ce Aminu ya zauna ya ce za su yi magana, cikin nutsuwa haka. Kofin ta ajiye ta saka cokali ta bashi hankalin ta, yana wani ɗaɗɗaga kai irin na rawar kan da ango yake idan zai yi ƙara aure ya ce "Dama ba wata magana ba ce, ina so abin da zan faɗa ki ɗauke shi ƙaddara, idan kuma baki ɗauka ƙaddara ba, za ki iya ɗaukansa duk yadda kika ga dama" Kallon mamaki ta masa haɗe da na rashin fahimta kafin ta furta komai ya ce "Aurena nan da sati huɗu" Gabanta ne ya buga da ƙarfi, amma sai ta danne ta ƙura masa ido tana mamaki, hanzarin katse ta ya yi da faɗin "Za ki zaɓi guda ɗaya, ina nufin ko bedroom ko falo, don ɗaya za ki haɗe kayanki ɗaya ita ma ta zauna" Dummm kunnuwanta suka yi, ta ji zafin maganar amma sai ta mayar da komai ba komai ba, saboda ita yanzu ta rasa a wajen Aminu mene ne za ta yi alfahri da shi a tare da shi ɗin? Wanda har zai sanya ta ji kishinsa, duk wani abu ya toshe hanyar sai dai abin da ba a rasa ba. "Kai ma sha Allah, amma na ji daɗi, kuma na taya ka murna matuƙa Allah sa abokiyar arziƙi ce" Ta faɗa hankali kwance tana mai ɗaukan kofin ta cigaba da shan garin, duk da tana jin garin a yanzu tamkar maɗaci take sha. Tsaye ya tashi da sauri sai kuma ya koma ya zauna, baki sake yake kallonta yana son gano maganarta da gaske take ko kuma ƙarfin hali ne, saboda abokinsa ya ce masa yau babu zaman lafiya wataƙila ma Saddiqar ta shaƙe masa wuya. Ransa ne ya ɓaci ganin bai gano komai ba a fuskarta sai kwanciyar hankali alamar dai maganar bata ɗaɗata da ƙasa ba, cikin ɓaci rai ya fara magana yana cewa "Saddiqa anya son Allah da annabi kike mini? Ya za a yi bayan an ce kishi kumallon mata amma ke in zo miki da maganar kishiya ki mini addu'a, sona ne bakya yi ko kuwa? Don duk inda so yake akwai kishi" Daƙyar ta ci nasarar danne dariyar da take taho mata, ganin ya haƙiƙance yana faɗa da tada jijiyoyin wuya amma sai ta kalle shi ta yi fari da ido haɗe da murmushin fatar baki ta ce "Kamar ya? Tambaya kake ko neman sani? " Wannan yanayin da ta yi furucin ya sake harzuƙa shi ya ce "Cewa na yi anya kina sona?" Wannan karon dariyar da ta yi sai da kyawawan haƙoranta suka bayyana ta ce "Shafa ka ji" Tsaye ya ƙara tashi ganin ita ma ta miƙe, yana huci ya ce "In shafa ina? Ai so a zuciya yake ke ya kamata ki faɗa mini" Kallon sheƙeƙe ta masa ta ce "Ni ma ban sani ba, abu ɗaya dai na sani ni matarka ce, sanna kai mene ne damuwarka da ina sonka ko ba na sonka, kai da za ka kawo sabuwar amarya? Abu na gaba ka kira amaryar ka tambaye ta tsakanin falo da bedroom wanne take so, duk wanda ta zaɓa sai ka faɗa mini na ɗauki wanda bata zaɓa ɗin ba" Tana gama faɗar haka ta fice daga falon ta tafi kicin za ta kai kofin da ta sha garin. Tsaye ya yi yana riƙe da ƙugu da hannu biyu, ransa ƙuna yake shi da ya zo ya ɓata mata rai, amma ido ya juye da mujiya tun da ga shi, shi ne yake tsaye ransa yana ɓaci. Kallon jikinsa ya yi yana rayawa a ransa to shi kuwa bai kai a yi kishinsa ba ko me? Shi da ake bashi labarin yanzu zai zama kamar ƙwai a wajen matan nasa, kowacce tana ririta shi, kowacce za take son shi ana rububinsa amma tun ba a je ko ina ba Saddiqa ta nuna shi bata kishinsa?. Yana cikin wannan halin wayarsa ta fara ƙara, ɗakkowa ya yi ya ga sunan abokinsa, a ƙufule ya ɗaga daga ɗaya ɓangaren abokin ya ce "Ango ka sha ƙamshi, ango ɗan gatan amarya da uwar gida" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare masa wuya, tsabsr haushi kasa cewa komai ya yi ya katse wayar, don ya san yanzu yana faɗa masa yadda suka kwashe da Saddiqa da ya sanar da ita auren, shikenan ya samu abin tsokana. Saddiqa kuwa tana zuwa kicin ta ajiye kofin, wani irin ɓacin rai ne yake dabaibayar zuciyarta, ita ganin yaushe ma aka yi aurenta, yaushe ma ta ji daɗin zaman gidan mijin da har za a kawo mata wata abokiyar zama?. Ta jima tsaye a kicin ɗin har sai da ta ji ta samu nutsuwa ta hanyar yin addu'a sannan ta dawo falon, bata same shi ba baki ta taɓe tana ƙarewa falon kallo, bedroom ɗin ta ƙarasa tana ƙare masa kallo ta tabbatar duka biyu babu wanda zai iya ɗaukan kujeru set da kayan gado, dole sai dai an rage kujerun. Bakin gado ta je ta zauna, ta ɗauki wayarta ta kira, Mamyn ta, bayan sun gaisa ta shiga labarta mata abin da Aminun ya sanar da ita, sosai Mamy ta kwantar mata da hankali, duk da ta ji ciwon abun kuma ta lura tun ba yau ba Saddiqar tana cikin damuwa amma dai babu yadda za a yi da abin da Allah ya tsara. Noor ƙanwarta ma da ta karɓi wayar, sai da ta kusa kuka jin za a yi wa Auntyn ta kishiya, gabaɗaya ma ita sai ta ji aure ya fita ranta, tun da dai tana ganin soyayyar da take tsakanin Aunty Saddiqa da Yaya Aminu amma tun ba a je ko ina ba zai mata kishiya. Bayan sun gama ta kira Khady take faɗa mata, haushi ne ya turnuƙe Khady ta ce "Ai gwara ma ya yi auren, kya samu salama ta wani fannin, ki yi haƙuri ƙawata mahaƙurci mawadaci, in dai aure ne ga wurin nan in kika yi haƙuri kwana nawa ne, maye ya yi amarya ya cinye kayarsa da sannu watarana za ki gan su a rana ke dai ki kame kanki ban da ɗaukan cin fuska ko raini" Sosai Khadyn ta kwantar mata da hankali hakan ya sa ta ji ƴar salama a ranta. Ummar Aminu har gida ta zo ta lallashe ta, tare da bata haƙuri sosai Saddiqa ta ji daɗin kulawarta, ko ba komai ta ƙara kima da daraja a idanunta. Aminu tun daga ranar ya shiga muzurai, shi a dole Saddiqa bata son shi, hakan ya sanya duk abin da zai yi da gayya yake don ranta ya ɓaci, amma ita sai ta yi kamar bata san yana yi ba. Da yake Zulaiha ya tambaya ta zaɓi bedroom, hakan ya sa Saddiqa aka mayar mata kujerarta guda ɗaya gida, da yake bata samu waje a falon ba, ƙofar bedroom ɗin kuma ya rufe ta, aka fasa wata daga waje aka fara aikin amarya haiƙan duk da yana jin ciwon fitar da kuɗin amma ina ya tuna gwangwajewa zai yi da amarya, sai ya da dama-dama kibiya a ido. Wani sabon salon wai kiran sallah da usur, Zulaiha ta ce ita ba za ta zauna a ɗaki mai siminti ba, dole sai an saka mata tiles har jikin bango, haka Aminu ya yi ƙuri ya saya aka gwangwaje ɗakin amarya uwar gida kwa ko oho. Kasancewar bayin a bedroom yake sai ya zamana ya zama a ɓangaren Zulaiha hakan ya sa aka yi wa Saddiqa wani bayin a waje, tun da wanda yake tsakar gidan na kowa da kowa ne. Saddiqa duk da ta ga yadda yake kashe kuɗi ana aiki amma bata ɗaga hankalinta ba. Sumayya da Amina suna gefe suna mata dariyar ƙetar za a mata kishiya, lamarin sosai ya tsorata Amina ganin Aminu zai yi aure, ita da take sha'awar miji ƙazami saboda tsabar kishinta amma sai ga shi ƙazamin zai yi aure. Tun da bikin ya ƙarato yawancin kullum yana gidan su Zulaiha ƴar aljanna, ɗakin amarya kullum in zai fita ya garƙame da mukulli, sai dai ba a raba musu kicin ba don wannan guda ɗayan ne hakan ya sa Saddiqa ta tattara kayan kicin ɗin ta saka a lokokin kicin ɗin ta bar wanda za take amfani da su kawai. Ganin bikin ya zo, sai Aminu ya fara ɗaga mata wani kai, yana jijji da kansa ki gidan ya dawo sai ya buɗe ɗakin amarya da aka gama ya shiga, wani lokacin ma sai dai in ta je kicin ta ga ya zuba abincinsa ya je ɗakin amarya ya ci, wai tun kafin amaryar ma ta tare. Tun saura kwana biyu ɗaurin aure aka zo aka yi jere a ɗakin amayar, ango sai giggiwa yake yana bada faɗi shi ala dole mai amarya. A ɓangaren amarya Zulaiha babu ya ita, don magungunan matan MEERAH B HERBS masu kyau da inganci, da farko maganin sanyi Mamarta ta saya mata na kamfanin MEERAH B HERBS, saboda duk wani abu da ya shafi maganinmata ba ya aiki, in har akwai sanyi a jikin mace. Magungunan mata da na hips, duk na MEERAH B ne suka saya a wajen Maman Afrah ga number ta mai buƙata ya tuntuɓe ta 09025576222, don kama daga set na kayan uwar gida, set na amarya, set na mai jego babu abin da basa siyarwa. Zannuwan gado da labulaye, tumtum da frame, duk a wajen Maman Afrah akansiyawa ƴar aljanna, jin yadda magungunan suka fara saukar mata da ni'ima ya sa ta gane tabbas magungunan kamfanin MEERAH B HERBS suna da kyau. Yau ya akama asabar a yau aka ɗaura auren Aminu da amaryarsa Zulaiha. Saddiqa bata yi wata gayyata ba, daga Khady ƙawarta sai Noor ƙanwarta sai kuma Fatima ƙanwar Aminu, sai Amina da kuma Sumayya. Leshi ta ɗauka na lefenta aka mata doguwar riga buba, wacce ta karɓe ta don gabaɗaya sai ya ƙara mata kyau, kasancewar cikin girmab jiki ya ƙara mata, ta ƙarw cikowa ta yi kyau, ga ƙirjin nan nata da duk ya cika bra, kamar ita ce amarya in ba wanda ya lura ba babu mai cewa tana da cikin wata shida. Bayan an kawo amarya, kowa ya watse bayan wata Auntyn Saddiqa da suka zo, su ne suka mata nasiha haɗe da bata baki. Bayan kowa ya tafi tana zaune a kan kujera, tana jin shigowar Aminu da abokansa amma babu wanda ya shigo ɗakinta a cikinsu, tana jin suka wuce ɗakin amarya, duk da faɗan da su Yaya Sule da Yaya Shafi'u suka masa amma bata ga alamar zai saduda ko ya sakko ba, don yanzu a yadda ta lura da ita da rashinta uwar ubansu ɗaya a wajensa. Ɓangaren amarya da ango kuwa, tun da abokansa suka tafi, ya shiga rawar ƙafa a wajen amarya, haka suka sha amarcida amarya duk da cewar wannan ne karo na farko da namiji ya kusance ta, amma dai sai ta ga kamar akwai gyara a lamarin angon nata. A nashi ɓangaren sai ya ji ƴar aljanna, bata kai Saddiqa a komai ba na ɓangaren ƴa mace. Abin da ya bashi mamaki bai wuce yadda ya yi buzigir babu wankan tsarki ba ita ma haka ta kwanta ko a jikinta, haka ma da asuba babu wanda ya tashi yin sallah, da gari ya waye tangararai ya yunƙura ya tashi da yake ta saka pant da suka gama sunna, idanunsa ƙirrrr a jikin pant ɗin tun da bacci take, yadda ya ga datti a jikin pant ɗin ne ya bashi mamaki ganin pant ɗin ba sabo bane kuma akwai dauɗa a jiki. Tambayar da ya yi wa kansa ta farko ita ce, ina panties ɗin da ya saka a kayan lefe har dozin biyu? Kanta ya kalla wanda babu kitso da alama shamfo aka yi don ya ga ribom ɗin kanta shi da ban gashin da ban saboda kan nata da alama dakyar ya yi parkin. Da wannan ɗan al'ajabin ya sauka daga gadon ya nufi bayi karon farko da ya ji Saddiqa ta faɗo masa, wacce bata kwanciya sai ta tsarkake jikinta sannan har shi take yi wa faɗan kawar da najasa, amma yau ga shi ita wannan sai bacci take hankali kwance. Wankan tsarki ya yi ya fito bayan ya yi alwala, da yake ma ko sabulun wanka bai gani a bayin ba, yana fitowa ya ɗan taɓa Zulaiha ganin har takwas ta gota. Idanu ta ɗan buɗe tana yatsina haɗe da doka tsaki ta ce "Haba Aminu ya za ka tashe ni, ka san ni ko a gida in ana son ganin ɓacin raina to a tashe ni daga bacci" Kasake ya yi yana kallonta, ya fara tunanin to wa ta yi wa tsakin? Sannan ina ɗan aljannan da take kiransa. Dannewa ya yi ya ce "Ki tashi ki yi wanka da sallah mana" Ko gizau bata yi ba sai kuma dai ta ce "Goma ta yi?" Da mamaki ya kalle ta ya ce "Goma kuma?" Kallonsa ta yi tana daga kwancen ta ce "To a gidanmu sai tara nake sallah, yanzu kuma nan gidan mijina ne ka ga sai goma ta yi na yi" Bakinsa ne ya ƙi rufuwa a zuciyarsa ya ce 'Yasin wannan ta fi ni jahilci da wasa da sallah, duk tsiya bana kaiwa goma ban yi sallaha ba, yanzu wannan ya kwaso a matsayin mata turƙashi' Dakyar ya lallashe ta, ta shiga bayi ko minti uku bata rufa ba sai gata ta fito, kallonta ya yi tana ɗaure da tawul, fatarta sai sheƙin rashin fitar wanka take ya saba da ganin fatar Saddiqa ko tsayawa ruwa ba ya yi saboda fita a wanka ya ce "Babu sabulu a banaɗakin ko?" Ya faɗa yana fargabar amsar da za ta bashi, don ba ya so ya gano wani abu na cewa ƙazama ce don ya ga alamomi sun fara bayyana. Fuska ta ɗan yatsina ta ce "Sabulu kuma, kar ka damu kanka ni ba baƙuwar zafi ba ce, don a gidanmu kowa da sabulunsa, na kowa sai ya ƙare nawa yana nan" Wani yawu ya haɗiye ya ce "Mai ya sa?" "Wallahi sai in yi sati ban yi wanka da sabulu ba, ni a na yi amfanu da sabulu watarana na goga sau ɗaya a hannuna na wanke fuska, uban jiki kuwa idan na kwara baƙin ruwa ya wadatar, ai ni dama ina cewa mijina ya huta da siyan sabulu" Shi kaɗai ya san yanayin da ya shiga da ta furta kalmar baƙin ruwa ya wadatar, ashe dai ko kai ƙazami ne baka son ƙazamar mace? Wannan yake ta saƙawa a ransa sai dai ya dake ya ce "Wai ni kuwa ina panties da aka saka a lefe, na ga na jikinki kamar ba wanda aka saka ba ne? " Tana saka riga ta ce "Na rabar da dozin ɗaya, dozin ɗayar yana nan cikin akwatin, tun da ina da wanda nake amfani da su a gida ai ba sai na ɓata wani ba, shi wando da a ciki yake a rufe ba gani za a yi ba" Tana faɗar haka ta hau sallaya hankali kwance ta kabbara sallah, ba tare da ta sake cewa komai ba, shi kuma ta ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa saboda ya ga yanzu ma wandon jiyan ne ta mayar ta saka riga bata sauya wani ba. Tun da ya ja tasa sallayar ya kabbara sallah, har ya idar bashi da nutsuwa sosai yana ta tunanin dama Zulaiha kura ce da fatar akuya ko yaya?. Ko da ta idar kwanciya ta yi tana danna waya, shi kuma ya shiga tunanin ranar farkon aurensu da Saddiqa gyaran ɗaki ta shiga yi washe gari har yana hanata. Wai ita amarya ba za ta shiga kicin ba, haka ta saka shi zuwa ya dafa shayi ya ɗumama kazar ya kawo musu, ta hanƙare ciki tana ci tana korawa da shayi. Inda suka gama break fast ɗin, a nan ta bar kayan, shi ma bai ɗauke ba yana son ganin gudun ruwanta. Wajen sha ɗaya ta ce ya siyo mata kati, haka ya fita ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Saddiqa yana ta waiwaye, don da ya zo giftawa ma sai da ya shaƙo ƙamshin turaren wuta. Zulaiha kuwa yana fita garin tashi za ta shiga banɗaki, ta tuntsurar da kofin da ta sha shayin ya zube, ko ta kanta bata bi ba ta shiga bayin. Aminu da ya dawo daga siyen kati, yana shigowa bai lura da shayin ba ya ɗora ƙafarsa, ji kake suuuuu santsin sabon tiles da na shayi ya kwashe shi, sai da ya yi gaba-gaba ya yi baya, yana ta baza hannu inda zai dafa wani abu amma sai da ya je ƙasa, zaman ƴan bori ya yi yana jan salati. Zulaiha jin faɗuwar abu ta fito daga bayin, ganin Aminu yashe yana riƙe da ƙudu sai kuwa ta fashe da dariya ta ce "Ango garin yaya?" Wani haushinta da takaicin ƙazantar ta ya tsaya masa a maƙoshi, yana ganin ban da ƙazanta da ta goge ai da bai faɗi ba, tsabar takaici bai san ya yi suɓutar baki ba ya ce "Saddiqa!!!" *INA SANAR DA KU WTSAPP SUN RUFE MINI LAYINA 09013181851 YANZU DUK MAI NEMANA ZAI MINI MAGANA TA 09025576222* [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 12 *AMINA* Tun daga ranar da ta faɗawa Saddiqa cewar ta kai ƙaran Aminu, wurin su Yaya Sule a kan ƙazanta, shikenan ta ƙara ɗaura ɗamara a ranta cewa dama a ce ƙazami ta aura da babu ruwanta da fargabat ƴanmata. Amma yanzu gashi nan wannan mijin nata mai shegen muguwar tsafta da gayu ta san dole yake birge ƴan mata suna son shi, duk yana cika bakin cewa shi babu shi babu wata ƴa mace amma dai bata yarda da hakan ba don ta san namiji baka raba shi da ƴan mata. Bayan an yi hakan da kwana biyu, da daddare suna zaune kowa ya duƙufa yana danna waya, wayar Yaya Sule ce ta yi ƙara, idanu ya shiga ciccicirawa gabansa yana faɗuwa, ta wutsiyar idanu ya kalli Amina da take latsa waya ya ga hankalinta bai kai kan wayar da ake masa ba. Da sauri ya kai hannu ya katse kiran, yana shirin mayar da wayar silent wani kiran ya shigo a karo na biyu, a wannan lokacin ne hankalinta ya kai kan wayar da ake masa, barin abin da take ta yi ta maida kallonsa gare shi ta ce "Baka ji ana ta maka waya ba?" Alamomin rashin gaskiya ne suka bayyana a fuskarsa, duk da ya yi ƙoƙarin danne hakan amma sai da ta fahimta, ganin za ta harbo jirginsa ya yi saurin faɗin "Wani abokina ne ya dame ni da kira, wai rancen kuɗi yake so ni kuma bana so in bashi saboda taurin bashi gare shi" Ya faɗa yana fatan ta yarda da maganarsa saboda ba zai iya da wannan ɗan banzan kishin nata ba, domin kuwa ya san muddin ta gane budurwa ce ya yi sai ya fi naman cikin oven gasuwa. Kallon rashin yarda ta bishi da shi, don lokacin kiran ya cigaba da shigowa a karo na uku, wayar kuma tana hannunsa abin da ya ƙara bayyana mata cewar ba gaskiya yake faɗa ba yadda hannunsa yake karkarwa. Wayarta ta ajiye a kan kujerar da take zaune, ta ce "Yanzu abokin naka ne zai rinƙa kiranka sai ka ce wanda ya baka ajiya? Rance ka ce yake nema fa, to a kan mai zai ke maka kira a jere- a jere kamar dai ya baka ajiya ko kuma shi ne yake binka bashin?" Ta faɗa don har ranta ya fara ƙuna don ta san ƙarya yake, addu'a ya fara a zuciyarsa yana cewa 'Allah ka fitar da ni, Allah ka rufa mini asiri kar wannan masifafiyar ta gano ni... Bai gama addu'ar ba ganin ta ƙaraso gabansa kamar an jefo ta sai ya ɗago kai yana kallon yadda take huci kamar wacce ta yi tseran gudu ya ce "Ai ni blocking ɗin lambarsa ma zan yi in goge ta, yo ina dalili zai ke damuwa ina gida da iyalai na" Tana tsaye a kansa kiran ya sake shigowa MAMUDA shi ne abin da ta ga an rubuta da manyan baƙi, ajiyar zuciya ta sauke ganin sunan namiji har ta ji salama a ranta sai dai hanzari ba gudu ba yadda ƙwaƙwalwarta ta kai mata cewa kaf cikin abokansa bata san wani MAMUDA ba. Kallon tuhuma ta masa ta ce "Daga kira ko ɗagawa baka yi ba, sai ka ce wani blockin da goge lamba anya kana da gaskiya kuwa?" Wannan tambayar da ta masa shi ya sa shi saurin cewa "Bari na ɗaga na faɗa masa bani da kuɗin" Wani ɗan sanyi ta ji a ranta, don har ta yarda da shi ta ce "Yawwa ɗauki amma ka saka a handsfree" Kallon ta ya yi ya ce "Haka kawai kina matar aure sai na kunna miki muryar gardi ki ji" Ya faɗa yana muzurai da son nuna mata kishinta yake yi, ɗan kallonsa ta yi tana mai nazartarsa ta ce "Ikon Allah, in ce dai muryar mace ce take haramun namiji ya ji, kenan yaushe muryar namiji ma ta zama al'aura?" Ta faɗa tana kaiwa wayar hannunsa farmaki, janyewa ya yi yana sakin yaƙe tare da wayincewa ya ce "Yo ai ni bana son kike jin muryar wani ƙato sai tawa" Wani daɗi ta ji don ita dai maganar soyayya ce rashin aikin yi da ɓata lokaci amma dai in dai fagen kishi ne to ita ce lamba ɗaya. Sai da ya gama saƙa abin da zai ce sannan ya ɗaga wayar gabansa yana faɗuwa, don ya san ko kiran nan da Salaha budurwarsa ce da suke shan soyayya, ya san yanzu ta ƙufula tun da har katse kiran ya yi, sannan tana ta kira bai ɗauka ba, sannan babban abin ma bai taɓa faɗa mata yana da aure ba saboda ita ɗin ma ya lura tana da mugun kishi, shi kuma wannan ce ƙaddararsa wato mata masu kishin jaraba wanda ya wuce hankali. Yana tuna irin rikicin da zai shiga a wajen Salaha, in ya kira ta da MAMUDA amma haka ya daure don da wata masifar gwara wata, da ya shiga tashin hankalin Amina ta san budurwarsa ce take kiransa gwara Salahar duk bala'i dai a waya za ta masa ko in ya je wajenta zance, yana ɗagawa idanunsa a kan Amina da ta kasa ta tsare, taimakonsa da Allah ya yi volume ɗin wayar ba a ƙure yake ba, bare ta ji muryar mai magana. Yana kai wayar kunnensa Salaha cikin shagwaɓaɓɓiyar muryarta mai kashe masa jiki da saka shi yin nutso a kogin ƙauna ta ce "Hello haba babynah tun... Ya san dai bai wuce ƙorafi bane za ta masa a kan ƙin ɗaga wayar da wuri amma haka ya yi ƙundunbala ya ce "Haba MAMUDA in ce dai mun gama magaa da kai, na ce maka bani da kuɗi amma ka dage kana ta kirana, shin a inanka taɓa gani an bada babu?" Salaha da sauri ta cire wayar a kunneta tana ƙara duba sunan wanda ta kira, duk da ta ji tabbas! Muryar Sule saurayinta ne amma kuma yadda ya amsa mata yana kiranta da sunan namiji wai MAMUDA bayan kuma ita ta fara yin magana, da a ce shi ya kira ta sai ta ce ko bai san ya kira ba. Amina kuwa jin abin da ya ce, sai ta ji ta ƙara yarda da shi, tana sakin wani murmushi sai kallonsa take ya cigaba da faɗin. "Don Allah ka nema a wani wajen" Salaha kuka ne kawai bata saki ba amma ranta ya yi mugun ɓaci, ta buɗe baki za ta fara zazzaga masa rashin mutunci ta ji ƙit ya kashe kiran, shi kuma da ya katse kiran bai ɗauke yatsansa ba sai da ya tabbatar ya kashe wayar gabaɗaya, don Amina tana ganin ya sauke wayar daga kunnensa ta koma mazauninta don haka bata ma lura cewa ya kashe wayar ba. Salaha kuwa a zuciye ta ƙara kiransa, don ta sauke masa kwandon rashin mutunci, amma sai ta ji wayar ma a kashe. Wurgi ta yi da wayar a kan gadonta da take kwance, zuciyarta tana ƙuna don ita ta fara tunanin ko dai Sule wata budurwar ya sake shi ne yana gaban waccen ɗin ita ya maida ta MAMUDA. Sule kuwa tun da ya kashe wayar nan, hankalinsa bai kwanta ba gabaɗaya hankalinsa, yana wajen Salaharsa, yanzu kuma bai san ya zai yi ya fita su yi waya ya kwantar mata da hankali ba, ya mata bayani hakan ya sa ya ɗan kalli Amina ya ce "Ni yaran nan duka sun yi bacci?" Bata ɗago ta kalle shi ba ta ce "Eh duka sun yi bacci, kaima ka san da basu yi bacci ba da tuni suna nan" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ɗan haɗa mini ruwan shayi mai zafi sosai" Ɗan yatsina fuska ta yi don bata son tashi sai kuma ta tuna lipton ta ƙare cikin zaƙuwa ta ce masa "Babu lipton fa" Wani murmushin gefen baki ya saki, don dama abin da yake hasashe kenan, shi ya sa ma ya ce a haɗa shayin, wani ƙaramin tsaki ya saki irin na kamar ba ya son ya fita sai ya ce "Bana son fita, ga shi kuma ina son shan shayin" Kallonsa ta yi ta ce "To ka fita shagon ƙofar gida ka siyo mana" Wani daɗi ne ya cika ransa ya tashi kamar ba ya so, yana riƙe da wayarsa ɗaya hannun kuma yana taɓa aljihu ya ce "Bari na karɓo" Ya bata baya ya nufi ƙofar fita, sai murmushi yake matar sauti kamar daga sama sai ya ji ta ce "Ɗan aramin wayarka, zan yi wani abu, ntwrk ɗina yana ɗaukewa, kafin ka dawo" Idanu ya zaro duk da bata gani, yana jin ta ruguza masa gabaɗaya shirin fita ya lallashi Salaha, ba a nan gizo yake saƙar ba ma, idan ta ga wayar a kashe sai ta tuhume shi dalilin hakan, wannan zai sanya ta zargi cewa da walakin goro a miya, ida kuwa hakan ta faru ya san tana buɗe wayar abu na farko da za ta fara yi shi ne kiran lambar nan mai ɗauke da sunan MAMUDA, cakwakiyar da zai shiga Allah ne kaɗai ya sani, don idan ta kira lambar MAMUDA Salaha za ta ɗauka, kowacce za ta ji muryar ƴar uwarta, da wane baki zai warware wannan badaƙalar, sannan ya san ma bai isa ya hana ta aron wayar ba, saboda hanawar ma wani sabon zargin ne. Salaha bata san yana da mata ba har da yara biyu, ga shi ta ƙwallafa rai a kansa tana son aurensa, shi ma a nashi ɓangaren haka ne yana son ta da aure, amma yadda ya lura tana da tsananin kishi shi ya sa bai sanar da ita ba, ya bari sai abu ya zo dab amma gashi yau Amina za ta warware masa ƙullin da ya ƙulla. Sannan ita ma Amina bata san ma yana da wata budurwa da yake soyayya da ita ba, ita da kullin burinta ya dawwama da ita kaɗai a rayuwarsa bs tare da kishiya ba, kuma sai yake ɗora ta a kan cewa daga ita babu ƙari kuma duk da mugun kishinta amma yau da alama asirinsa yana dab da tonuwa, wannan shi ake kira rana zafi inuwa ƙuna. *SUMAYYA* Zaune take a bakin gado, tana ɗaure da zani ɗaurin ƙirji, Yaya Shafi'u ne ya shigo yana kallonta wani ɓacin rai ya turnuƙe shi, haka ya danne ya ce "Ranke daɗe Hajia Sumayya" Wani kallon sheƙeƙe ta masa, don ta san wannan maganar da biyu ya faɗa ta ce "Faɗi da ihu ka ƙara da wayyo, na san dai duk ranar da Allah ya kira ni babu wanda zai hana, don haka sai dai in ce Allah sa ka faɗa da bakin mala'iku" Kallonsa ya mayar kan Ruma da ta taso ta nufo shi za ta kama shi, da sauri ya riƙe hannun yarinyar don kar ta daƙuma masa kayansa ya ce "Sumayya don Allah kalli yarinyar nan, wallahi wannan ko ƙauye aka je sai an bincika za a samu wanda zai bar ƴarsa a haka dagaje-dagaje da ƙazanta, kalli kwantsa a idanunsa, hanci duk majina, hannunta ta ci abinci duk manja ba a wanke mata ba, sannan shi kansa kayan jikinta babu tsaftacewa. Yanzu a haka kike ganin in ta girma ita ta tsafta ce jikinta bayan uwar da ta haife ta bata tsafta mata ba, duk abin da ake wa yaro shi yake kowa, kalli wandonta Allah kaɗai ya san adadin maimaicin da aka masa" Ya kai ƙarshen maganar yana ɗagowa ya kalleta jin bata ce komai ba, ganin ta zuba masa ido tana wani jijjiga jiki ya san kalamansa basu samu shiga ba, bare su samu matsugunni. Kallon ɗaya saura kwata ta masa ta ce "Ka gama? Na ce ka gama? Sau nawa kake so na maimata maka cewar duk wanda ya raina tsayuwar wata hawa yake ya gyara ba, kullum magana ɗaya kamar karatu yanyanyanyan tun da ba ɗauka zan yi ba ya kamata ka haƙura ya shafa mini lafiya" Ta kai ƙarshen maganar taba sakin wata gyatsa, da alama ta yi over feeding saboda shegen ci kamar gara. Hannun Ruma ya kama ya fita da ita, wanka mata hannun ya yi ya dawo da ita ɗakin ya cire mata kaya, banɗaki ya shiga zai mata wanka, pant ɗin Sumayya ya gani rataye babu wanki abin haushin ma jinin period ne a jiki amma saboda tsabagen ƙazanta ba za ta wanke ba ta rataye a haka. Ji ya yi tamkar ya yi kuka, yawu ya tofar a daddafe ya yi wa Ruma wanka suka fito, lokacin Sumayya ta tashi tsaye, priod ɗin ya gani ya ɓata mata zani daga baya sannan har inda ta tashi ma gashi nan ya taɓa bedshet ɗin, kallon bedsheet ɗin ya yi yana jin wani haushi zanin gadon da ya yi oder wajen Maman Afrah ne yadi mai kyau da inganci ba ya tashi bare koɗewa amma saboda tsabar rashin gyara da ba ya samu duk ya fita hayyacinsa. Ita ko a jikinta ma, kayan wanki ta birkita ta kwaso panties ɗin ta masu yawa, duk babu wani mai wanki sun yi duƙun-duƙun wasu da priod a jiki, zazzagawa ta shiga yi ta ɗauki wani ta mayar da sauran, baya ta juya ta saka pant ɗin tare da ɗaukan wata doguwar rigar bacci marar wanki ta saka ta cire zanin gadon ta haɗa da zanin da ta cire da pant ɗin, ta tuƙunƙuna ta tura su kayan wanki. Wayarta ta ɗauka a kan madubi ta koma bakin gadon ta zauna. Shafi'u sai da ya shirya Ruma dakyar ya samo wankakkiyar riga ya saka mata, ya ɗakko turare ya fesa mata, tuni ta shiga murna don yaro ma yana son gayu amma ita bata samu saboda ƙazantar uwarta. Drower Sumayya ya buɗe ya ga yadda ta jera pad(Always) Kowacce yadda ya siyo ko buɗewa bata yi ba, idan wani watan ya yi sai ya ƙasa siyowa amma saboda rashin tsafta shi ne take tarawa kamar wanda za ta siyar. Kamar zai yi kuka ya ce "Sumayya ƙazantarki ta ishe ni wallahi, yanzu a matsayinki na mace bakya jin ƙarni ma a ce kina priod amma babu pad a jikinki kin gwammace jini yake ɓata miki jiki, bakya ma kunyar kike shiga cikin mutane babu wanka babu tsafta ce jikin ki matsayin na mai haila? Maimakon daga pad ɗin ta jiƙe ki sauya amma ke sakawa ne na bakya yi" Jin yana ta zuba cikin ƙufula ta ce "Faɗawa kunne ƙeya ta baka amsa" Tana gama faɗar haka ta juya masa ƙeya. Kallonta ya yi ya ce "Haka kika ce ko?" Yatsina fuska ta yi ta ce "Ni wallahi na kasa gane maka, anya ba haushina kake ji ba saboda ina mace Allah ya ɗaga mini yin sallah idan ina priod, ai ina lura da kai ko a watan azumi idan ina fashin azumi saboda priod sai in ga kana ta ɓata rai, da alama baƙinciki kake saboda ku maza bakwa fashin yin sallah" Wani takaici ne ya cika shi, ganin ana ga yaƙi tana ga ƙura, bata san cewa shi tsabar ƙarnin da take yi in tana priod ne ba ta so ba saboda bata gyara jikinta. Ruma ya kama zai fita da ita falo, sai ji ya yi Sumayya ta ce "Bari dai in je in watsa ruwan nan, kar a jima a ga bana nan na ɓace" Juyowa ya yi don ya san da shi take ya ce "Tun da ga maye ba, mai zai hana a rasa ki" Baki ta taɓe ta ce "Ni dai ban ce ba" Tana faɗar hakan ta faɗa banɗakin, Ruma ya ce ta je wajen Aunty wato Saddiqa tana fita ya koma ɗakin, ganin vata rufo bayin ba karowa ta yi ya ƙarasa bakin ƙofar bayin ya tsaya yana kallonta da yake ta bashi baya ne yana gani ta ɗauki sabulu wankan ta goga a pant ɗinta, ta wanke pant ɗin ba wani fita ya yi ba ta matse ta rataye ta fara watsa ruwa ko sabulun bata saka a wankan ba bare a yi zancen soso. Tana gama sheƙa ruwanta ta janyo pant ɗin da ta wanke da lema ta saka, ta ja zaninta ta ɗauro, da sauri ya matsa daga bakin ƙofar, tana fitowa ya ji wani ƙarni ga fatar nan tata sai sheƙi take alamar an tado dauɗa. Yana ƙare mata kallo a fusace ya ciro belt ɗin jikinsa, idanu ta zaro ganin ya ɗaga fuskarsa a murtuke babu alamar wasa ya ce "Ko ki koma ki yi wankan kirki, ko wallahi na zazzabga miki" Ganin ransa ɓace sosai ta ga babu wasa ta juya tana gungune, yana tsaye ta yi wankan ya koma ya kwaso panties ɗinta guda goma sha biyar na Ruma goma, ya watsa mata banɗakin, ya ɗauko klin ya jefa mata ya koma gefe ya kama ƙugu, tuni ta shiga wankewa tana sake saɓawa har sai da suka fita ta ɗauraye sannan ta shanya ya bar wajen, da yake tana da abin shanyar panties a banɗakin. Ɗaya daga cikin wasu sabbin panties da ya shigo da su jiya ya ajiye a drowersa ya ɗakko, always ya buɗe ya ɗakko ɗaya ya buɗe ya manna a jikin pant ɗin, bayan ya goga miski a jiki. Miƙa mata pant ɗin ya yi sannan ya gogo muskin ya shafa mata a mara ya ce ta saka pant ɗin. Tana sakawa ta shafa mai, ya bata rigar abaya a drower sa saboda ƙazantar ta, yanzu ko ya sayo kaya ba ya son ya bata don duk dafe su za ta yi da dauɗa. Sai da ta saka sannan ya ji wani sanyi a ransa ya kalle ta ya ce "Ina sonki Sumayya halayenki ne ba na so" Murmushi ta saki, ya ce ta kwaso kayan wankin nasu su je ya taya ta ta wanke, bata yi gardama ba saboda yau ta ga ya sauya kamar dai ba Yaya Shafi,un da ta sani ba. Washe gari ya yi wanke-wanke ya lallaɓata ta musu abinci ta ce shinkafa da miya za ta yi ya je ya iyo markaɗe ya siyo salad, ya dawo ya ji ɗuriyarta a kicin can ya je hakan ya yi daidai da sheƙa shinkafa da ta yi a cikin tukunyar kan wuta. Da mamaki take kallonsa ganin ya tsaya bakinsa a buɗe yana binta da kallo, ta yi ƙarfin halin faɗin "Lafiya dai?" Kamar zai yi kuka ya ce "Haba Sumayya shinkafar na ga kin zuba a haka fa" Cike da mamaki take kallonsa ta ce "To ba ita za a dafa ba dama?" Wai baki ga abin da kika yi ba" Ta ce "Ni ban ga komai ba" Ledar hannunsa ya ajiye yana faɗin "Shinkafar fa kika zuba ba tare da kin wanke ba" Kasaƙe ta tsaya tana kallonsa ta ce "Ikon Allah na kwance ya faɗi, amma kai ban da abinka har a nunawa na ringingine farin wata, ina mace za ka nuna mini aikina wannan fa shinkafar gwamnati ce wacce ake kira daga buhu sai tukunya, ko a cikin sunan da ake kiranta ka ji an ce daga buhu sai ruwa sai tukunya?" Jin bai ce komai ba ta ɗora da faɗin "Shinkafar gwamnati ba a wanke ta, shinkafar hausa wacce ake tsince tsakuwa da datti ita ce ta dace da wanki" Tsabar takaici ya rasa bakin magana sai komawa ya yi ya jingina da bango. *AMINU* Dariyar da Zulaiha take yi ce ta dakata da yi, jin ya ambato mata sunan kishiyarta a ɗakinta tana aika masa harara ta ce "Me ka ce, Saddiqa ka ambata Aminu" Idanunsa ya buɗe warai sai yanzu ya gane suɓutar baki da kuma katoɓarar da ya yi, ya san dai zafin faɗuwar da ya yi ne da kuma kewar Saddiqa da ya ji tana masa dabaibayi yau ɗaya. "Ba ce wa ka kira a tsakar ɗakina" Kallonta ya yi sai yanzu ma ya ga ashe babu kaya a jikinta a ransa yana fatan Allah sa dai wankan sabulu za ta yi, ganin tana tsare shi da ido a ransa ya ce 'Gaba da gabanta aljani ya taka wuta, wato baba ma da babansa kenan'" A fili kuma sai ya ce "Cewa zan yi fa Saddiqa ta fara zama tarihi a gidan nan tun da kika bayyana, to ke kuma baki bari na ƙarasa ba" Shiru ta yi tana nazarin maganarsa sannan ta juya ta koma ta rufo bayin, yana nan yana naƙudar tashi saboda yadda kwakwason sa yake ji tamkar kakkaryawa ake yi sai gata ta fito, tana cewa "Yo ni mantawa na yi amarya tana shiga ruwan ɗumi, shi ne ma yanzu nake ɗan jin raɗaɗi sannan kuma ina jin tafiyata tana sauyawa shi ne na juye ruwan flaks ɗin na shiga" Kai kawai ya gyaɗa mata jin bata ce ta yi wankan sabulu ba. Haka ta karɓi katin ta koma ta zauna, ko taimaka masa bata yi ya tashi ba, ta loda kati a waya ta shiga kiran ƙawaye da ƴan uwa tana faman cewa su taho gidan amarya mana a zo a dafa a ci a sha. Aminu fa sarewa ji ya yi kamar ya ce kar kowa ya zo masa gida amma dai babu yadda ya iya, haka suka rinƙa zuwa kamar mai suna taruwa wasan mai kuwa da suka ringa soye-soye duk sun yi wa man gara lahani. *BAYAN SATI GUDA* Sannu -sannu halayen Zulaiha sun bayyana, ƙazama ce fitik ta ajin ƙarshe wannan ya sanya Aminu yi da na sanin aurenta don ya lura ta dame shi ta shanye a ƙazanta. Yanzu duk abin da ya ga Zulaiha ta ɓata sai ya tuna yadda Saddiqa take gyarawa. Abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya yanzu bai wuce yadda bata iya girki ba kwata-kwata, kuma baban tashin hankali da ƙalubalen da yake gabansa shi ne, zuwan abokansa gidansa jibi, akwai abokinsa Kabiru, Lawan da kuma Bukhari wanda yake aikin soja, ba a garin yake ba don haka ko lokacin da ya auri Saddiqa ba ya nan sai yanzu ya ce tun da ya zo gobe za su zo da sauran abokanan nasa guda biyu Kabiru da Lawan. Da yake Kabiru da Lawan su a gari suke, kuma sun zo lokacin amarcin Saddiqa ta musu abinci na gani na faɗa, ko ina a gyara ko ina yana ƙamshi. Abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya shi ne, tun saura kwana huɗu ɗaurin aurensa, ya samu Saddiqa ya ce mata idan amarya ta tare sai ta yi sati biyu tana girki, duk da Saddiqa ta ji haushi amma sai ta ce ta amince tun da dama ita har murna take za ta samu salama da kwana da Aminu a gado ɗaya. Yau kuma da ya ji gobe zai yi baƙi sai yake da na sani, tun da, da a ce bai cewa Saddiqa Zulaiha sati biyu za ta yi ba, da tau tun da Zulaiha ta cika sati ɗaya da Saddiqa ce za ta karɓi girki, kuma baƙinsa za su zo a girkin Saddiqa ne ya fita kunya, sai dai su je su gaisa da Zulaiha. Amma ganin abin yana damunsa, kuma ba ya so ya kunyata a gaban abokai a je ana masa dariya ana gulmarsa, tun da shi ma ana haɗuw da shi a yi ta wasu, amma shi da yake Saddiqa ta fitar da shi kunya shi ya sa wancan karon bai kunyata ba, don haka yanzu ma ya ce a ransa zai je ya lallaɓa Saddiqa ta shiryawa baƙi girki su sauka a wurinta yana fatan Allah ɗora shi a kanta. Zaune take a kan kujera tana duba hadisin bulugul maram, ya shigo da sallama, amsawa ta yi tana shaƙar wani dummm daga jikinsa, sai ta ji duk warin yana neman hargitsa mata ciki amma a haka ta dake tare da danne mamakinta na ganinsa yana washe mata jajayen haƙoransa da basa samun wanki, tana ta tunanin ko ya amarya take yi? Bata san cewa duk kanwar ja bace, da shi da amaryar zani ce ta tarar da mu je mu. Ɗan murmushi ta saki ta ce "Barka da yamma" Ƙurr ya mata da ido sai ya ga kamar an ƙara mata kyau, haƙoranta ya kafe da ido yadda suke tas a wanke gasu nan a jere kamar masara, ƙamshin da yake tashi a jikinta da kuma ɗakin sai ya ji har wata hamma ta fara suɓuce masa, yana kallonta kamar yau ya fara ganinta ko dai hakan bai rasa nasa ba da kwana biyu da bai ganta ba wai shi mai sabuwar amarya ya ce "Barka dai Hajia Saddiqa mutanen gayu da tsafta" Wata dariya ce mau sauti ta kuɓuce mata jin sunan da ya kira ta da kuma kirarin da ya mata ta ce "Yau ɗin kuma" Ta faɗa a ranta tana mamakin ashe dai tsafta tana da rana, tun da shi ya tsani tsaftar da take komai ta yi bata iya ba amma yau ga shi yana yabawa, kawar da tunanin ta yi da sake faɗin "Ko dai ɓatan hanya ka yi, nan fa ba ɗakin amaryarka ba ne" Maganar da ta faɗa ta gane kamar ta ɗan sosa ransa don har a fuskarsa sai da ta fuskanci hakan, amma ta nuna kamar bata gani ba. Shi kuma kawar da maganar tata ya yi ya ce "Don Allah alfarma na zo nema wajenki" Da mamaki take kallonsa wai ita Saddiqa ce Aminu zai nemi alfarma a wajenta, saurin kawar da tunanin dalilin hakan ta yi ta ce "Allah sa zan iya" Cikin sanyin murya ya ce "Dama baƙi ne zan yi, kin gane Bulhari abokina soja?" Ta ce "Eh na gane shi" Sai ya ce" Shi ne ya zo gari, to gobe zai zo shi da Kabiru da Lawan shi ne za ki musu abinci" Wata ƴar dariyar rainin hankali ta yi ta ce "Ni ɗin? Gaskiya bani da lokaci" cike da mamakin kalamanta ya ce "Baki da lokaci, ni mijinki kike faɗawa haka Saddiqa? Kin manta zamana kike?" Tsaye ta miƙe daga zaunen da take, kafe ta ya yi da ido ganin body hug ɗin jikinta ta kama ta ga ɗan cikin nan da ba a gani sosai ya zauna ɗas kamar a wajen yake tun asali. Taku ɗaya biyu ta yi ta sauya wajen zama don hamamin hammatarsa ya dame ta, sai da ta koma ɗan nesa da shi ta zauna cikin haɗe fuska ta ce "Ka manta ba bakina bane? Kai fa ka ce amarya sai ta ci amarcin sati biyu, don haka wallahi ko ruwan zafi babu wanda zan dafawa" Tana kaiwa nan ta hau gado ta naɗe ƙafa ta shiga latsa waya, ɗiff ya yi ya kasa cewa komai don ji yake ya shiga tara ba ma uku ba, din abin ya fi ƙarfin uku sai dai uku sai uku. Siyam-siyam ya tashi ya fita, da harara ta bi bayansa tana ƙarewa rigar jikinsa kallo, duk saitin hamatar gumi ne daga ganin rigar ma babu wanki. Yana dawowa ɗakin Zulaiha, ya ganta, zaune tsakiyar gado da ɓawon lemon fata a kan gadon, lemo uku ta yanka da ayaba biyu ta cinye amma ɓawon a kan gado. Wani ɓacin rai ya ji ya linku da wanda Saddiqa ta masa amma ganin so yake ya lallaɓata ta wa baƙi abinci sai ya danne ɓacin ran ya zauna ya ce "Amaryata, bakya laifi" Kallonsa ta yi tana mai kai hannu tsakiyar kanta da babu kitso ta sosa, garin susar ribom ɗin ya faɗo ai kuwa ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da susa, tana mai cewa ina jinka "Baƙi zan yi gobe abokaina" Ta ce "Sai aka yi yaya" Danne takaicin da ya ji na maganarta ya yi ya ce "Dama sun ƙosa su zo su ganki" Ta ce "To baka nuna musu hotona, ai ba sai sun ba kansu wahala ba" Shiru ya yi ya ce "Don Allah ki taimaka abinci suka ce za su ci a nan fa" Ya faɗa yana son ya ce ta taimaka ta musu mai daɗi don ya san babu abin da ta iya dafawa ko jiya sai da ta yi ɗanwake ya narke a ruwa, haka ya dawo sai wani ɗanmalili wanda ake yi da masa a ci da manja da yaji ta yi suka ci ai kuwa ya ɓarke da gudawa, yana tuna abincin Saddiqa baiwar Allah, da ba ya gode mata. "Allah kawo su lafiya" Ta faɗa tana saka hannu a bireziya ta ringa susa, kallo ɗaya ya mata ya san ba komai bane yake mata ƙaiƙaiyi sai ƙazantar rashin wanka, yau sati guda da zuwanta gidan amma bata taɓa wanka da sabulu ba, wai wankan baƙin ruwa ya wadatar, sai ta ce fatar da za a mayar da ita cikin ƙasar kabari mene ne na wanke ta da sabulu. Nan dai ya lallaɓa ta, ta ce za ta musu tuwon shinkafa miyar kuka, sai ya ce zai siyo zabuwa ta musu farfesu. Da wanann suka bar maganar. Washe gari da safe tun da suka yi wankan tsarki, suka yi sallah, ta koma gado ta kwanta, tsintsiya ya ɗauka ya shiga share ɗakin saboda ya san dai a nan baƙin za su sauka, ita kuma ba gyarawa take ba, tana baccin ya shiga share ɗakin, ya sunkuya yana sharo ƙasan gado sai ya hango wani plate da mamaki ya janyo ya ga abinci aka ci aka suɗe kuma aka tura ƙasan gado saboda tsabar ƙazanta, da ganda ba za a fita da shi waje ba. Kai ya girgiza yana jin ya gamu da gamonsa, fita ya yi da shi ya dawo ya cigaba da sharo ƙasan gadon, abin mamaki sai ya sharo pad, wacce aka yi amfani da ita, ko a leda ba a saka ba, jinin jiki har ya yi wani baƙi-baƙi kore-kore. Da tsintsiya ya janyo pad ɗin har tsakiyar farin tiles ɗin da ya ci uban datti kasancewarsa fari, tamkar ba sati ɗaya ta yi a ɗakin ba, a ƙufule ya shiga faɗin "Yar aljanna, ƴar aljanna, Zulaiha ke" Idanu ta runtse da ƙarfi jin kitan har tsakar kanta ta tashi a zuciya tana cewa "Ni fa a kan wasu banzayen abokanka, ba za ka damu rayuwata ba, wallahi in ka taɓo ni sai na fasa mutu tuwon" Ɗif ya yi jin za ta shuka masa salalan tsiya, idan ta ƙi karɓar abokan nan ai ta jaza masa raini da dariya a cikin abokai. Kai ya karkata gefe kamar maraya ya sassauta murya ya ce "Ba wannan maganar ba ce, haba Zulaiha leƙo ƙasa ki ga abin da na gani nake kiranki" Fuska ta yatsina tana cewa "Ka san bana so ake tashina " Ta faɗa tana leƙowa, ya ɗauka za ta nuna wani yanayi in ta ga pad ɗin amma cikin halin ko in kula ta ce "Lah wai wannan abar ce dama, ai ranar nan ina kwance na ji ta ishe ni, kuma dai na ji kamar jinin ya bar zuba, shi ne na fisgo shegiya na jefa ƙasan gado, na cigaba da baccina" Tana kaiwa nan ta koma ta kwanta ta cigaba da bacci abin ta. Sakaka yake kallon pad ɗin yana kallonta ita ma, a ransa yana raya cewa ya gamu da gamonsa, tabbas ya auro wacce ta dame shi ta shanye a ƙazanta. Pad ɗin ya ɗauka a makwashin shara, fita ya yi ya jefa a shara, ya dawo ya cigaba da share ɗakin, dama rabar da ta yi kwana biyu ne priod ɗin ya zo kuma kwana uku ta yi, sai ta yi wanka. Mopping ya yi ya yi goge -goge, ya kunna turaren tsinke ya saka a kusurwa-kusurwa. Banɗaki ya shiga, wanka yake so ya yi don ya ga yanzu goma ma ta yi, babu sabulu don tsawon satin nan daga shi gar amarya babu wanda ya yi wanka da sabulu, fitowa ya yi ya zo ya ɗan taɓa ƙafarta yana tsoron ta tashi ta ce an tashe ta, sa'arsa ɗaya bata yi ƙorafi ba ya sasaauta murya ya ce "Don Allah ina sabulun wankan nan na cikin lefe" Sai da ta tashi ta zauna ta ce "Sabulun wanka kuma? Dama kana wanka da sabulu ne" Ya ce "Kin san baƙin nan za su zo shi ya sa gwara na yi wanka, don Allah ke ma ki taso yau ɗaya dai ki yi wanka da sabulu, kar su zo ni wari ke wari abin zai yi yawa shege da hauka" Ya faɗa yana ɗan lallaɓa ta. Ta ce" To tun dare bai maka ba, ka tafi shago ka siyo, sabulun kayan lefen ne zan fitar ka suɗe shi ai na lefe na amarya ne, saboda adani shi ya sa tsawon sati ban ɗakko ko goga na yi na wanke fuska ba, wannan ajiyewa zan yi har ɗan da zan haifa a wanke shi da sabulun kayan auren ubansa, kuma ni ma dai in ina jego ai sai na ɗan wanka ko banza na wanke ƙarnin jego" Har sai da idanunsa suka kawo ƙwalla wai sabulun ne saboda adani za a ajiye har sai an haihu an yi wa ɗa wanka da shi, ko cikin ma babu kai jama'a. Magiya ya shiga yi mata, a kan cewa zai mayar mata da haka ta ɗakko guda ɗaya ta bashi, tana cewa sai da ta danne zuciyarta. Lallaɓata ya yi suka yi wankan tare don sai da ya dirza mata bayanta, suka fito suna ɗan ƙamshin sabulu. Bayan ta shafa mai ta buɗe drower ta ɗakko atamfarta, wacce tun tana gida dama ta kwaso wasu daga cikin kayanta don ta ce va yanzu za ta fara ɗinka na lefe ba, saboda adani. Kallon atamfar ya yi duk ta sha jiki, ta koɗe ya ce "Mu da za mu yi baƙi" Daƙayar ta yarda ya ɗakko mata wani leshi daga cikin kayan fitar biki, tana ta mitar ita da ba wani waje za ta je ba, zai sa ta saka sabon kaya. A nan ma sai da Saddiqa ta faɗo masa wacce kullum cikin ado da kwalliya take. Bayan sun shirya shi ma ya saka wankakken kaya, ta shiga kicin ta fara ɗora ruwan tuwo, tun kan ruwan ya yi zafi bare a yi zancen tafasa, ta kwaso shinkafar tuwon ta zuba. Ta rufe ka ruwa bai ishi shinkafar ba, ta rufe ta koma ɗaki bayan ta haɗa kayan miyar ta tsayar da ruwan miyar. Jimawa can ta dawo, tana buɗe tuwo ta ga har ya fara ƙauri, ga shi shinkafar ta jiƙa babu batun dahuwa, wani wajen ma ɗanye ne haka ta sauke ta tuƙa ta mulmule. Miyar ta kaɗa da yake da bushashen kifi ta yi tana saukewa ta zuba a food flaks ta ajiye. A daidai nan Saddiqa ta shigo kicin ɗin ɗaukan kofi, ganin Zulaiha a ciki sai ta shigo da sallama, amma Zulaiha bata amsa ba, sai ma ta tsiri ƴar waƙa tana faɗawa Saddiqa magana ko ta kanta Saddiqa bata bi ba sai ta ba bango ajiyarta, ta ɗauki abin da ya kawo ta ta fita don gabaɗaya ƙaurin kicin ɗin ma tada mata zuciya yake. Bayan fitar ta suka ci karo da Aminu, ya dawo riƙe da ledar zabuwa, ko kallonta bai yi ba, tana gaishe ya yi banza, don haushinta yake ji bata wa baƙinsa abinci ba ga shi kuma dai ashe amarya za ta share masa hawaye. Yana shiga kicin ganin sabbin flaks a kan tire wani daɗi ya cika shi, gar da saka mata albarka ya rungume ta, yana aika mata da sumbata, ita kuma sai ta ji kanta ya yi wani gingirim ita ala dole ta birge miji. Nan ya fita sayen lemuka ya barta tana dahuwar nama, tana gamawa ta kai ɗaki ta jera. A ɓangaren Aminu yana ƙofar shagon lemuka wayar Bukari ta shigo, yana ɗagawa suke sanar masa suna hanyar gidan nasa, nan ya faɗa musu inda yake suka je suka taho da shi. Yana gaba suna binsa a baya suka shigo gidan, tun daga nesa ya hango Zulaiha a ƙofar ɗakinta tana zaune a baranda, abin da ya gani ne ya mugun ɓata masa rai, shikenan ya san ta wargaza masa mutuncin da yake tattali a wajen abokan nasa, gashi su duka sun ganta.... ME TA YI? MAI YA GANI? AKWAI CAKWAKIYA FA MU HAƊU A PAGE 13 DON JIN AMSAR DA YADDA BAƘI ZA SU SAMU KANSU A ƊAKIB AMARYA *GABAƊAƳA ZAN BAKU BOOK 1 DAGA FARKO HAR ƘARSHENSA A FREE, IDAN MUKA GAMA BOOK 1 GA WANDA YAKE DA HALI KUMA YAKE BUƘATA ZAI IYA BIYAN KUƊIN BOOK 2* *INA SANAR DA KU CEWA WHATSAPP SUN KULLE MINI LAYINA 09013181851 YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI 09025576222* ~NA GODE MAMAN AFRAH~ [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BxScHoTf7PzDHEWZgZCnnf *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 13 *YAYA SULE* Da sauri ya danne makunnar wayarsa, sai kuwa waya ta kunnu, duk da gabansa yana tsananta bugu amma dai da dama -dama a kan a ce ta ga wayar a kashe domin, a take za ta ɗora masa alamar tambaya haɗe da tuhuma. Hannu Amina ta miƙa masa a lokacin da ta tako zuwa gabanta, jikinsa babu ƙarfin tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Addu'a yake karatowa a zuciyarsa, ƙaran shigowar kira wayar wanda mai kiran tamkar jira yake a kunna wayar ya kira dama. Kaɗan ne ya rage Yaya Sule ƙwalla ƙara, saboda ya san kashinsa ya bushe, Amina kuwa har ta ƙagara ta ga mai kiran don har ta fara tunanin wannan anya kuwa MAMUDAN ne?. Yaya Sule cike da fargaba ya duba fuskar wayar, amma cikin iko da hikimar ubangiji sai ya ga sunan Babansa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da sakin murmushin jin daɗin kuɓuta, cikin ƴar inda-inda ya ce "Baba ne yake kirana" Ajiyar zuciya Amina ta sauke a fili, hatta Yaya Sule sai da ya ji saukar ajiyar zuciyar a zuciyarsa ya ce 'Yadda kike sauke ajiyar zuciya haka nake saukewa, bambancinmu kawai ni ɓoyayya na sauke ke kuma bayyananniya' Ya ce a zuciyarsa ita ma a zuciyarta ta ce 'Allah na gode maka, ashe dai Baba ne ya kira shi, har gabana ya faɗi ai bana so in ke ɗora zargi a kan mijina, duk da na san ba zai taɓa raɓar wata ƴa mace da sunan so ba, kawai dai sheɗan ne yake saka mini wasi-wasi saboda ba ya so a zauna lafiya' Wayar tana dab da tsinkewa ya ɗaga ya kara a kunne, bayan ya zauna ya ce "Assalamu alaikum, barka da dare Baba" Daga ɗaya ɓangaren Baba ya amsa sallamarsa, bayan sun gaisa ya tambaye shi su Albani yake cewa sun yi bacci, nan ya shiga cewa "Sule ni kuwa kun yi magana da Aminu, baka ji gidan su tsohuwar budurwarsa sun ce ya aika ba" Cike da mamaki Sule ya amsa da cewa Aminun bai tunkare shi da maganar ba, nan Baba ya kwashe komai ya faɗa masa, cikin sanyin murya ya ce "Amma Baba da baka goyi bayansa ba, yanzu yaushe ma aka yi aurensa da Saddiqa, yarinyar nan tana ta fama da ƙazantarsa amma yanzu tun ba a je ko ina ba a ce zai mata kishiya" Amina da tun da ta fahimci bakin zaren zancen, ta saki wani murmushin jin daɗi da farinciki, a hankali ta ajiye wayarta, tasowa ta yi ta je kusa da Sulen ta zauna don ta ji ƙwal uwar daka. Baba ne ya ce masa "Shi fa zai zauna da matarsa, ka ga bai kamata a tauye masa haƙƙinsa ba" Cike da tausayin Saddiqa Sule ya ce "Wallahi Baba da ka ce masa ya haƙura ba... Hannun da Amina ta sakawa Sule a bakinsa, shi ya masa shamaki da ƙarasa maganar da yake son yi, kallonta ya yi take masa alamar ya daina cewa a hana Aminun, Baba kuma jin Sule bai ƙarasa maganar ba ya ce "Ni dai na amince, kai ma ka amsa fatan alkairi, da a ce mutum yana bin mata gwara a ce yana da yawan aure-aure ka ga sai dai mutane su ce mutum yana aure ɗanɗane amma ba wai zina ba" Jin furucin nan na Baba, sai Sule ya buɗe baki don lokacin Amina ta ɗauke hannunta daga bakinsa ganin maganar kuramen da take masa ta yi tasiri, ya ce "Haka ne Baba, to Allah tabbatar da alkairi" Wannan maganar da ya yi sosai farinciki da annashuwa ya bayyana a fuskar Amina. Son haka yana cire wayar daga kunnensa ta ce "Haba kai kuwa, ya za a yi ka hana sunnar ma'aiki" Ta faɗa tana dariyar farinciki, kallonta ya yi ya ce "Ina ga fa Amina baki gane inda maganar ta dosa ba, magana fa Baba yake a kan Aminu ya je masa da maganar zai yi wa Saddiqa kishiya" Hannu ta tafa, tare da kai hannun ɗaya haɓarta ta ti tagumin mamaki ta ce "To kuma mene ne, abin da mutum babu ruwansa ai daɗin kallo gare shi" Kallonra ya yi yana tuna irin yadda ta tsani kishiya, amma kuma ga shi tana so a yi wa wani, shi ya sa dama ake cewa mata su ne matsalar kansu da kansu, ya ce "Amma Amina ya za a yi abin da bakya son a miki, kike so a yi wa wata? Kar ki manta fa yarinyar nan ba a daɗe da aurenta ba, amma yanzu a bijiro da maganar kishiya ai da damuwa" Tsaye ta tashi tana kama ƙugu ta ce "To ai shi wasa ma waje yake samu, abin da zai iyu ma shi ake yi, ka san dai ai ni bani da abokiyar zama har abada!. Ita kuma in ita ce ƙaddararta waye zai hana a mata?" Iska ya hurar daga bakinsa ya ce "Allah bata haƙuri da dangana" Harara ta aika masa ta ce "Dangana sai ka ce wacce uwarta ta mutu, ni sai wani tausayinta kake" Ɗan shiru ya yi ya ce "Ba haka bane kin san yarinya ce kuma shi Amina zama da shi sai haƙuri" Baki ta taɓe ta ce "Kowa ma zaman haƙuri yake da nashi mijin" Tana gama faɗar haka ta koma wajen wayarta, kawai sai ya ji tana voice tana cewa "Eh mana Aminu ƙanin mijina, wanda ya yi aure kwanannan" Mamaki ne ya rufe shi, daga haka ya zame ya fita siyan lipton ɗin, saboda ko ta kan karɓar wayar bata yi ba hankalinta yana ga bada labari. Yana fita ya kamo sunan MAMUDA ya doka kira, wajen sau uku wayar tana shiga amma ba a ɗauka ba, ba ya raba ɗayan biyu ya san fushi take da shi. Kiranta ya cigaba da yi a ransa yana cewa 'Mata biyu da alama zama da su zai yi wahala, ga shi dai kowacce bata san da zaman ɗaya ba amma a hakan suna haɗa mini zafi, ina ga na haɗa su waje ɗaya a matsayin matana, lallai akwai badaƙala, ni kuwa yanzu ba zan iya rabuwa da Salaha ba, kin ga Amina kenan taki kishiyar tana tafe kema, tun da har kina yin murna za a yi wa wata, shi dama ramin mugunta gajere ake ginawa' Yana wanann zancen zucin ya ji ta ɗauka, amma bata ce komai ba, cikin ɗan karya murya ya ce "Baby nah, fushi da ni?" Nana ma shirun ne, amma tana jinsa, ya cigaba da faɗin "Amma ai gimbiyar tawa ta bani dama, na kare kaina ko? Amma in aka ƙyale ni sai abin ya mini yawa wai shege da hauka" Dariya ce ta ƙwace mata jin karin maganar da ya yi, wani sanyi ya ji a ransa jin ta yi dariya ya san tana dab da sakkowa. Sai da ta tsagaita dariyar ta ce "Dama ka iya karin magana amma baka mini?" Wani murmushi ya saki cikin zaƙuwa ya ce "Ni in kullum ma kike so zan ke miki" Shiru ta yi sai kuma ta ce "Yanzu ni za ka kira da MAMUDA? Bayan kiran da na maka ka ƙi ɗagawa, har da wanda ka katse" Dimmm gabansa ya faɗi, nan ya shiga haɗa kalaman ban baki yana cewa "Kin san ya aka yi?" Bai jira ta amsa ba ya ɗora da faɗin "Lokacin da kika kira da farko ba na kusa, da na zo kuma garin in ɗauka na katse, sannan kuma lokacin da na ɗauka, kiran MAMUDA ne ya shigo, ni kuma duk tunanina shi ne kuɗi ne da yake so in ara masa, sai bayan na gama magana na gane katoɓarar da na yi, sanin za ki yi fushi sai na kashe wayar ma baki ɗaya, na ce bari in bari sai kin ɗan huce in zo bada haƙuri, kar in zo ranki a ɓace ki ƙara tunzura" Shiru ta yi tana jinsa, tana kuma nazarin maganarsa. Ajiyar zuciya ta sauke da har sai da ya jiyo sautin ta wayar, sa kuma ta ce "Allah sarki, ashe duk gudun ɓacin raina ne ya sa ka kashe wayar ma, ba komai na fahimce ka" Daɗi ya ji sosai a ransa, nan suka shiga hirar soyayya, sun daɗe suna magana cikin so da ƙaunar juna, kafin daga bisani suka yi sallama suna masu yin kewar junansu. Sai da ya ƙarasa shago ya siyo lipton ɗin, sannan ya dawo gida, Amina ko a jikinta da ta ga ya daɗe don bata kawo komai ba, hankalinta yana waya tana gulmar za a a yi wa facalarta kishiya. Tun da aka yi haka shi ne fa Aminar, take yi wa Saddiqa wani gani-gani tamkar dai ita ce ta jawa kanta kishiyar, shi ya sa ko ranar auren Aminun ma ta rinƙa shiga ta alfarma tana fita, don murna take a ranta tana rayawa saura Sumayya ma, amma ita ta san ita da kishiya sun yi hannun riga. *AMINU* Kunya ce ta rufe shi gabaɗaya, yana jin tamkar dai ya je ɗakin Saddiqa ya ɗakko ta ta zo ta maye masa gurbin Zulaiha, ta karɓi baƙin nasa in ya so idan suka tafi ita Zulaihar ta zo. Amma sai dai bakin alƙamai ya bashe, bai san ledar lemukan hannunsa ta suɓuce ba sai da ya ji Kabiru yana faɗin "Aminu lafiya dai" Ya lura basu gane abin da yake gani ba, don ya san babu wanda zai yarda cewa Zulaiha matarsa ce, duba da cewa babu wata amarya da za a gani a yanayin da take yanzu. Sanye take da wani zanin atamfa roba, wanda ya ci uban datti tamkar na mai siyar da mai da ƙuli, don yadda ta zo da shi dama babu wani wanki zaninta ne tun tana gida, ita kanta t shirt ɗin da ta daka duk maiƙo ne a jiki ita ma babu wankin kan nan ,nata bucai da shi babu kitso amma ribom ɗin yana jikin gashin, wanda reto ribom ɗin yake kamar zai faɗi saboda gashin ba ya haɗuwa ya yi parking. Tun da ta zo dama bata yi kitso ba, ga kuma uban ruwa da kan yake sha na wankan tsarki. Wainar fulawa ce a farantin take ci, ta wani barbaje. Haƙori ya saka ya danne leɓansa na ƙasa, yana ƙoƙarij saisaita nutsuwarsa, Lawan ne ya ɗauki ledar da ta faɗin ya riƙe. Aminu kuwa tunani yake, mai ya sa ta cire les ɗin da ya saka ta saka a jikinta. Ki yake kamar ya je ya yi ta dukanta ko ya huce amma babu dama haka suka ƙaraso shi da abokan nasa yana dariyar yaƙe wacce ta fi kuka ciwo. Ita kuma ganin suna dab da zuwa, sai ta haɗa tafukan hannayenta ta murza tamkar mai shafa mai, bata nufi ko ina da hannun ba sai kanta, ta shafe maiƙon a jikin gashin kan nata, sai kuma ta mulke ragowar maiƙon a jikin zanin nata ta janyo wata hularta da take gabanta ta saka a kan nata, sai dai wani daga cikin gashin kan nata ya fito daga gefe ɗaya a gaban hular, sai ya yi tamkar doron zabuwa. Kuka ne kawai Aminu bai saki ba, shu damuwarsa ma Bukari don ya lura Bukarin bai gane cewa wannan matarsa ba ce amaryar da yake ta musu kurin za su je su gani ya yi babban dace, kuma ya yi babban kamu don ya auri muradinsa wacce ƙaddara ta sako Saddiqa a matsayin matar farko kafin ita. Zulaiha kuwa tana gama saka hular ta miƙe tsaye, tana washe baki tana musu sannu da zuwa, don lokacin har sun zo barandar. Kallonta Aminu ya yi yana jin wani takaicin ganinta da abokansa suka yi a shiga marar kyan gani shiga ta ƙazanta wata irin kunya ta rufe shi yana jin dama bai kawo su ba. Sai a sannan ya lula tunanin ranar da Khady ƙawar Saddiqa ta zo, yana rayawa a ransa kenan haka Saddiqa ta ji kunya da ƙawarta tw gan shi a haka? Lallai ya yarda cewa baka gane abu har sai an maka shi, amma dai ba za ka gane ciwonsa ba sai in kai aka yi wa. Sai sannan ya ji ashe bai yi wa Saddiqa adalci ba. Maganar Bukari ne ya katse masa tunani da faɗin "Wai ina amaryar ne" Kallon kallo aka shiga tsakanin Lawan da Kabiru, don su sun gane cewa wannan ta tsaye a gabansu ita ce amaryar. "Gani kuwa" Zulaiha ta faɗa tana ƴar dariya irin ta amare, har da wani ɗan kauda kai irin tana jin kunya. Washe baki Aminu ya yi cikin wayancewa yana ƴar dariya ya ce "Eh mana, ita ce, ai ka ji ma ta baka amsa, dama masu magana sun ce waƙa a bakin mai ita tafi daɗin ji" Bukari kallonta ya yi yana ɗan jinjina abin a zuciyarsa ya ce "Sannu amarya" Ta ce "Yawwa" Aminu kuwa ya ga alamar suna son su raina masa hankali, don sun ga amaryarsa cikin shiga marar kyau, ga kuma abin da ta yi na goge maiƙo a tsakiyar kanta da jikin zaninta, shi ya ma rasa mai ya sa ƙazanta ta zaunawa Zulaiha. Ya ɗauka yadda ta cigaba da karatun nan, zai samu wayewa da tsafta ta fitar hankali, amma dai sai ya ga tana abu kamar dai bata shiga ajin ma kwata-kwata ba. Ya ƙagara su shiga cikin ɗakin, don su gane ita fa ta rasa giɓi ne ta wani ɓangaren, amma ta fannin girki za su gane yau kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Gaba ya yi yana cewa "Bismillanku" Suka take masa baya, ita kuma Zulaiha sai ta koma gefe suka wuce. Suna shiga ɗakin suka zazzauna a ƙasa inda ta shimfiɗa table mart ta jera abinci, Aminu sai washe baki yake yana so ya mantar da su abin da suka gani, dai da suka zazzzauna kamar an ce ya kalli gefe kusa da Bukari ya hangi breziyar Zulaiha yashe a wajen, gata ta ci uban dauɗa, hannun breziyar daƙwa-daƙwa kamar mai tallar kalwa, ganin hakan Aminu ya shiga faɗar hakan a zuciyarsa 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakil, kin kashe ni Zulaiha' Babu wanda ya lura da breziyar, shi ya sa yake fatan ya samu nasarar kawar da ita daga wajen, ba tare da idanun ɗaya daga cikinsu ba ya gani. Amma dai ya san da wuya hakan ta kasance, sai a sannan ya tuna ranar da Saddiqa ta ce ya bar mata gajeran wando a falo, amma ya nuna ko a jikinsa ashe dai ko da kai ƙazami ne akwai abin da baka so a gani, bai ankara ba ya ji Lawan ya ce "Abokina wai ya duk ka yi shiru ne?" Yaƙe ya yi yana sosa ƙeya, amma hankalinsa yana kan breziyar nan ta Zulaiha, kamar an ce ya ɗaga kai ya hangi kan gadon ma duk ta cukurkuɗa shimfiɗar, ga kayan da ta cire nan yashe a kan gadon. Sai ya ji dama dai ko durƙusawa Saddiqa ne ya yi ya roƙe ta a kan ta karɓi baƙin nan a wajenta, ya san ko ledar pure water ba za ta jefae a ɗakinta ba, bare kuma wata breziya, a zuciyarsa ya ce 'Allah na tuba breziya ko wankakkiya ce matarka ta jefar abokanka suka gani ai da kunya, bare kuma wannan daƙalƙalar ta ci datti ta more' Cikin kawar musu da tunanin ya ce "Lah ba komai fa, da yake yau na tashi da ciwon kai" Ya faɗa yana ƴar dariya, tare da kallon Bukari yadda ya ga duk ya yi kamar dai a takure yake, da alama dai ganin Zulaiha ko ya sa ya ji ƙyanƙyami kasancewarsa mai tsantsani. Zulaiha kuwa da suka shige ta koma ta zauna, har ta zauna ta tuna ba ta kai plate da cokula ba, tashi ta yi ta tafi kicin ɗin amma plate ɗin wainar fulawa yana nan da ɗan guntun yaji a kan farantin. Riƙe ta taho da plate ɗin da colula a ka, sai kuma kofuna a kan wani plate ɗin, da sallama ta shigo tun da ta shigo wani haushi ne ya turnuƙe Aminu yana aika wa zanin jikinta harara ƙasa-ƙasa, sai lokacin ya ƙure ƙirjinta da kallo ya ga ashe dai breziyar da ya gani cirewa ta yi babu wata a jikinta. "Barkan ku da rana ina wuninku" Ta faɗa tana daga durƙushen da ta yi, ganin Aminu ya yi fuska sai muzurai yake, ana haka Bukari ya ɗaga hannunsa bai masa masauki a ko ina ba sai a kan breziyar Zulaiha, ya juya zai kalli wajen da sauri Aminu ya ce "Ni Bukari baka bamu labarin wajen aiki ba" Wannan maganar ce ta ɗaukewa Bukari hankali, bai ga breziya ba, shi kuma Aminu sai tunanin yadda zai yi ya kawar da ita ba tare da sun ankara ba. Zulaiha kuwa bayan ta gaishe su, ta ɗauki zanin less ɗinta a kan gado ta yafa a kanta kamar mayafi don sai lokacin ma ta tuna suturcr jikinta tun da a gaban abokansa ne. Aminu kuwa sai signa yake mata, a kan ta gyara gaban goshinta, wato hular nan inda gashi ya fito, don ganinta yake kamar bararoji. Tana fita aka Lawan ya matso da plates ɗin yana faɗin "Ya kamata mu fara cin abincin nan" Kowa da to ya amsa suka ma manta da batun Zulaiha, sai Aminu da yake kallon breziya lokaci zuwa lokaci yana fatan Allah sa kar su gani, shi ya manta yadda Khady ta ga gajeran wandonsa, Kabiru ne ya ce "Ni fa a rayuwata ina son cin girkin amare, ban san mai ya sa girkin amarya ya fita da ban ba, shi ya sa ina son abokina ya gayyace ni cin abincin amarya" Gabaɗaya suka kwashe da dariya, aka shiga buɗe flaks. Lawan ne ya buɗe flaks ɗin tuwon, ganin tuwon bai mulmulu ba, alamar dai ruwa bai ishi shinkafar ba, sannan ina iya ganin shinkafar raɗo-raɗo alamar rashin tuƙuwa, lura ne ma basu yi ba da sun ga yadda wata take fari tas alamar tana ɗanyarta. Lawan sakawa kowa tuwo guda ɗaya, a plate ɗinsa, Kabiru har ya ce "Wannan ai zubin rowa ne, ni na fi son malmala biyu" Sai suka fashe da dariya, irin ta abokai, nan kowa ma ya ce biyu za a zuba masa, amma saboda tsokana sai Lawan ya ce "Kai ango guda ɗaya za a bar maka, tun da kai kullum kana cin abincin amarya" Dariya ya yi, Kabiru ya buɗe flaks ɗin miya ta yi kauri kirtif saboda yadda aka kaɗa kukar da yawa, ga ɗan ƙarnin kifin da ta saka a miyar yana tashi, kasancewar bata saka corry da sauran kayan ƙamshin da zai kashe ƙarnin ba. A haka dai aka zubawa kowa miya, basu damu da ƙarnin ba ko yadda miyar take koriya tsarrr tun da wani abincin a ido ne bashi da kyan gani amma a baki sai ka ji yana da ɗanɗano. Kabiru ne ya gyara zama ya ja nasa farantin gabansa, da yake table mart ɗin tana da girma ya ce "Gwara na jingina da kujera, kar na fara ci na yi santi ku ce a saka mini waigi" Ya faɗa yana haɗiye yawu. Lawan ne ya yi dariya ya ce "Yo dama santi ai sai dai in baka fara ci ba" Bukari ya ce "Ni dai na san da wuya in koma gida da kunnena, wataƙila a cin abincin zan cire kunne ɗaya" Gabaɗaya suka kwashe da dariya, Aminu ya ce "Idan kuka fiye yabawa ƴar aljannata abincin ta, ba zan ƙara kawo ku cin abincin ba" Aminu ya faɗa don yadda suke ta zuzuta abincin sai ya ji tamkar dai sun ci ne, a ransa ya san dai yau in suka ci za su kusa tsinke yatsa, Kabiru ya ce "Kishi ne ya motsa Aminu, baka so a yabawa amaryar taka" Bukari ya ce "Surutun ya isa haka, a ci abinci" Kowa cokali ya ajiye wai ba za su ci tuwo da cokali ba. Aminu ne number one wajen gutsurar tuwo ya haɗo da miya, kafin kowa ya kai nasa ne ya fara isa bakinsa, wani irin ɗaci ne ya ziyarci bakinsa gabaɗaya bakin ya game da ɗaci tamkar ya tauna magani filajin, idanu ya ƙwalalo yana kallon abokan nasa a fakaice yana addu'ar Allah sa wani abu wanda zia dakatar da su daga saka tuwon nan a bakinsu ya bayyana, ko da a ce a waje ne za a yi ihun gobara a kawo ɗauki tabbas zai yi yadda zai yi ya sa su tafi taimako amma dai ba ya fatan su ci. Haka ya daure yake mumulmumultu da tuwon a bakinsa, tamkar tsohon da babu haƙori a bakinsa, yana cikin wannan halin ya ga Lawan ya ɗago idanu ya kalle shi yana riƙe da tasa lomar tuwon da ya yi wa wanka da miya, da sauri Aminu ya yi yaƙi da zuciyarsa wajen sauya akalar fuskarsa, daga yamutsewar jin ɗaci zuwa walwala, muduk ya haɗiye tuwon babu shiri, gabaɗaya ɗacin har maƙogwaronsa. Maganar Lawan da Kabiru ce ta dawo da shi daga suman ɗacin da ya yi jin sun haɗa baki wajen faɗin "Bismillah" Kafin wani yunƙuri sun kai lomar a kusan tare, Bukari ne na ƙarshe, yana sakawa ya yi fosta da lomar tuwo a bakinsa, shi bai haɗiye ba shi bai tofar ba. Wani tari ne ya ƙwacewa Lawan bakinsa da tuwon da sauri ya ce "Kabiru lalumo ledar lemon can ka miƙo mini kashina" Kabiru kamar jira yake ya warto ledar ya ɗakko lemon, maimakon ya miƙawa Lawan sai ya buɗe robar ya kafa kai dakyar ya samu ya kora tuwon nan da lemo, yana zare idanunsa da suka yi jawur saboda tsabar wahalar ɗaci. Kafin Kabiru ya gama shan lemon Lawan da yake ganin ba zai iya jumurin buɗe wata robar ba, ya warce sauran ya shiga kwankwaɗa, sai da ya ji faɗawar nashi tuwon bidik sannan ya shiga dawowa hayyacinsa, bai ankara ba Bukari soja ya karɓe saura lemon don shi ya fi kowa shiga tashin hankali saboda ya tsani abu mai ɗaci ko yaya, bare wannan ɗacin mai ɗaga hankali, Aminu kuwa shi a dole sai wayincewa ya yi da faɗin "Kai gayu kuna yarfa ni fa, so kuke amarya ta shigo in ji kunya, ga lemuka nan kala-kala amma kun zauna kuna fasin-fasin da guda ɗaya kamar kun samu ƙwallon ball" Ya faɗa yana daurewa ya suri wata lomar amma wannan karon ƙarama ya ɗauka, su duka ukun kallon inda zai kai lomar suke, suna mamakin to ko shi bai ji abin da suka ji ba, haka Aminu ya yi shahadar aika lomar nan bakinsa, wani amai yana neman tahowa, haka ya daure ya haɗiye. Abin ya haɗe goma da ashirin, tuwo ɗanye duk ɗanyar shnkafa a ciki, ga miya ƙarni ga kuma wani ɗaci mai shiga harshe. Dakyar ya samu lomar ta shige cikin, a take cikinsa ya ji yana murɗawa. Yana ankare da sauran babu wanda ya sake gigin kai wata lomar bakinsa, sai juya hannu suke a farantin to shi ma da aka bashi malmala ɗaya da yaya, bare su kuma masu malmala bibbiyu. Ya san tabbas kara ce suke masa, basa so su nuna wani aibi daga tuwon shi ya sa kuma don kar ya ji babu daɗi suka ƙi ajiyewa. Cikin wayincewa ya ce "Gayu dama fa basu son tuwo, gwara mu fara da zabuwar can da ta dha dahuwar amare, kuma dai na ɗan ji kamar hannun amarya ya ɗan goce a miyar nan wataƙila miyar ta ɗan kama ne, shi ya sa take ɗan ɗaci" Ya faɗa yana ture plate ɗinsa gefe, su duka ukun kamar jira suke suka turo nasu, fita ya yi zai ɗakko musu ruwan wankin hannu, don ba ya ƙaunar ƴar aljanna ta sake dawowa ɗakin, bare da ya ga ta ɗauki wani uban zanin leshi ta sha lulluɓi da shi. Yana fitowa ko inda take bai kalla ba, kicin ya je ya ɗakko ruwa a wata roba mai ɗan faɗi, da ya dawo fuskar nan tasa a haɗe yana dab da shigewa ɗakin ta ce "Ɗan aljannata, ya kuka ji tuwon? Amma fa don Allah kar ku cinye duka wallahi ban ɗauki nawa ba" Wani takaici ne ya sa ya kasa magana, kaɗa kansa ya yi a zuciyarsa yana cewa 'Indai wannan tuwon naki ne, mai kama da maɗaci ga shi nan an bar miki har na ɗumamen safe ma kya samu' Ya faɗa a zuciyarsa yana shigowa falon, da ya ji suna zance ƙusƙuƙus amma yana zuwa sai aka yi ɗif, kunya dai yau ya san ya kunyata daɗinsa ɗata ma sa ci naman ba sa zauna da yunwa ba, ko dai su zo basu ci komai ba. Kowa hannunsa ya wanke suka ɗan fatsar, farantin da ta ɗoro kofuna ya sauke ya jirkice musu naman a ciki, sai turiri yake tuni kowa ya ɗan murmusa, suna jin daɗi an raba su da alaƙaƙai wato miyar maɗaci, don wanna sunann ne ya dace da miyar duk da babu wanda ya san dalilin da ya sa miyar ta yi ɗaci, wannan amsar sai Hajiya ƴar aljanna. Wani ya ɗau cinya, wani haƙarƙari, wani kwankwaso, kowa dai da abin da ya ɗauka, a baki suka luntuma a tare, kowa ya shiga kokawa da naman da sai an yi yaƙi zai gutsuru saboda tauri, idanunsu ya ƙanƙance jin wani ɗanɗanon da ya bambanta da na miyar tuwo, ɗanɗanon da duk cikinsu su huɗun basu taɓa cin karo da shi a cikin nama ba, ba a nan gizo yake saƙar ba jikin haƙarƙarin hannun Kabiru wata ƙatuwar ƙusa ce wacce romon naman da ya baibaye ta, bai hana a ga tsatsar da ta yi ba. A wannan halin ne Bukari da ya ɗora ɗaya hannunsa a kan breziya bai, ɗanɗanon naman ya sa ya ɗago hannun ashe hannun breziyar ya maƙale a jikin links ɗin hannun rigarsa, sai ga breziya tana reto a hannun soja, su duka ukun da kallo suka bi hannun soja, banda Aminu da ya yi saurin sadda kai ƙasa, a zuciyarsa yana cewa "Subhanallahi wa bihamdihi, subhanallahilmazim" *ZAN BAKU BOOK 1 A FREE BOOK 2 GA MAI HALI YAKE DA BUƘATA ZAI BIYA 500 ZAKU IYA FARA PAYMENT DAGA YANZU ZUWA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222* *INA SANAR DA KU WTSAPP SUN KULLE MINI WANNAN NO 09013181851 YANZU DA WANNAN NAKE AMFANI 09025576222* *AKWAI MAGUNGUNAN MATA, NA KAMFANIN MEERAH B HERBS,AKWAI NA GYARAN BREST AKWAI NA SANYI AKWAINSET NA AMARYA HAƊIN ME JEGO MALLAKOKI, LABULAYE ZANNUWAN GADO LESUNA, ATAMFOFI, LAFFAYA TAKALMA MAYAFAI MASU BEAD WORK DA NA SHAGO KAYAN YARA DA SAURANSU MAI SO YA MINI MAGANA TA 09025576222* [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BkaHPj3RyI1JJmiwfXfnAA *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su *09025576222* BOOK 1 PAGE 14 Bakin Bukari kamar ƙofar gari haka ya buɗe tsabar mamaki, tamkar wanda aka ratayawa igiyar kashi hake yake ganin breziyar tana reto a hannunsa, ga wani tsantsani da ya hana rai da zuciyarsa sukuni. Kabiru shi har wani idanu yake zarewa don son tabbatar da cewa breziyar ce a hannun soja, ganin duk sun raja'a a kallon breziyar hakan ya sa Kabaru fahimtar babu wanda ya lura da nasa gamon da ya yi. Hannunsa ɗayan ya sanya ya fincikon ƙusar daga jikin haƙarƙarin nan da ta yi nutso cikin tsoka, tana cake jiki kamar an buga ta a katako duk da har a wani lanƙwashe take. Kabiru yana zaro ƙusar ya ɗagata sama, har lokacin Aminu kansa yana sunkuye a ƙasa ya kasa ɗagowa, Lawan salati ya kwasa ganin ƙusar da aka zaro daga jikin nama, shi Buƙari ya rasa bakin magani ji yake tamkar ya shaƙo Aminu ya yi ta duka saboda takaici. Aminu kuwa jin an ɗauki salati duk sai ya ɗauka har lokacin, suna jimamin breziyar ne hakan ya sanya ya ƙara sunkuyar da kai ƙasa, idanunsa kafe da cinyar zabuwar da take riƙe a hannunsa, ga cinya har cinya saboda girma amma ɗanɗano da rashin dahuwa ya hana ya ci naman cikin kwanciyar hankali, uwa uba ga wannan tashin hankalin abin kunyar da Zulaiha ta jaza masa. A ƙufule Kabiru ya ce "Aminu dama kawo mu gidanka ka yi don a kashe mu?" Wanann tambayar ta ba Aminu mamaki don ya zaci a kan breziya ake magana, kunya ta hana shi ɗagowa amma dai duk da haka bai zaci har za a ɗauki abin da zafi a sako maganar kisan kai. Bai ɗago ba kuma bai ce komai ba, sai cewa yake a zuciyarsa. 'Allah ka ji tausayina, ka sa breziyar nan ta ɓace, sai in ce dama aljannu ne suka kawo' Lawan ne ya ce "Alamomi da dama sun nuna hakan, miya ɗaci firit ga kuma baƙar breziya a ajiye kusa da mu, sannan yanzu ga guba an tsinta a cikin nama" Dummm gaban Aminu ya buga, don dama da aka ce baƙar breziya har sai da ya runtse ido, yanzu kuma jin an ce guba sai gabansa ya tsannata bugu yana tunanin hallaw wace masifa ce Zulaiha ta jaza masa, da za a ce guba a nama, shi da ya san zai haɗu da wannan ƙaddarar a baƙar ranar nan da bai kawo su gidan ba. "Aminu magana ake maka fa" Kabiru ya ce yana wani huce kamar zai kai masa duka. A hankali ya ɗago kansa, gumi ya gama jiƙa shi, a kan zarɓeɓiyar ƙusar ya sauke idanunsa, kafin ya mayar da akalar ganin nasa zuwa hannun Bukari da yake rataye da breziyar, basu ankara ba sai suka ga Aminu ya fara gwala idanu yana cewa "Jama'a duhu nake gani, bana ganin komai fa, jama'a a kawo ɗauki ko dai baƙar iska ake yi yau" Ya faɗa yana baza hannuwa kamar mai zancen kurame, sannan sai gwale idanu yake yana runtsewa ya buɗu. Su duka da kallon rashin fahimta suka bi shi, shi kuma ya yi wannan dibarar ne saboda ya tsira daga jin kunya. Tun da dai ya san in ya ce ba ya gani dole su masa uzuri ko ma hankalinsu ya tashi, dole su manta da batun ƙusa da breziya tun da ya ga alamar babu sauƙi wai ciwon arne. "Lawan ne ya karkata kai ya ƙare masa kallo, cikin hargagi ya ce "Wallahi ƙarya kake mu za ka rainawa hankali, a'a ka manta ba baƙar iska ba ce ta taso, guguwa ce mai haɗe da ƙasa" Ɗif Aminu ya yi a ransa yana tunanin kar dai sun hango lagwansa. Hannayen ya fara miƙawa saitin Bukari wansa yake a ƙufule, ya cika fam kamar zai fashe, yana miƙa hannun yana gwale idanun, yatsunsa ne masu zato-zaton farce da hannun yake riƙe da cinyar kaza ya kusa nutsawa Bukari a ido. Lawan ne ya ce "Kabiru nutsa masa ƙusar nan a idon da yake gwalewa, wataƙila idanun su washe ya daina ganin duhu" Da sauri Aminu ya ja baya, da jan mazaunai ya koma daga can gefe yana cewa "Haba ku tausaya mini ga cutar makanta ga ta ƙusa ai sai ku tsiyayar mini da idanun" Bukari cikin kakkausar murya mai cike da takaici idanunsa sun kaɗa sun yi jajur yana jin amai yana yunƙuro masa in ya kalli breziyar hannunsa ya ce "Aminu wallahi ka buɗe idanunka ka ɗauke mini wannan abar daga hannuna, in ba haka ba to wallahi zan manta matsayina na Bukari abokinka, in koma Bukari soja in lakaɗa maka na jaki, hatta ita matar taka ba zan barta ba" Ƙwuitttt wata ƙaramar tusa marar ƙara ta suɓucewa Aminu, don shi fa a duniya yana tsoron soja, dama abin da ya sa yake sakin jiki da Bukari ma saboda ya san abokinsa ne, kuma dai ba da unifoarm yake ganinsa ba, don ganin idanun Bukari sun yi ja sai ya fara tunanin ko allurarsa ce ta soja ta motsa, jin wannan batu sai ya saki wata ƴar dariya mai ɗan sauti ya ce "Wallahi idanun nawa ma sun washe, yanzu kam ina gani raɗau-ɗau, subhanallahi wannan abar fa? "Ya ce yana kallin breziyar. Bai jira cewar kowa ba ya ce "Wannan da gani aljannu ne suka mana ajiya, wataƙila ma yanzu suna zaune a ɗakin nan, donn wannan breziyar ko kusa ba ta amarya ba ce, kuma ko ƙusar cikin naman bata rasa nasaba da aljannu" Kallon ka raina mana wayo suke yi masa, kunya yake ji har lokacin, bai taɓa zaton zai kunyata haka ba, tun da suka shigo gidan ake cin karo da abubuwan al'ajabi da bashi kunya ba zai gaji da faɗin Zulaiha ta tozarta shi yau ba. Bukari yana jefa masa wani kallo ya ce "Ka ɗauke mini ita daga jikina, don wannan kayan nawa ma na gama saka su har abada" Ya faɗa yana wani irin yatsina fuska. Ana cikin wannan yanayin ne, amarya Zulaiha ta shigo, har lokacin zanin leshinta yana yafe a jikinta sai dai wannan lokacin iya wuyanta ta yafe bata rufa har kai ba. Wata ƙaramar roba ce a hannunta mai ɗauke da yajin daddawa, dama tun daga gida aka niƙo mata shi, to sai ta manta bata kawo ba hakan ya sa ta shigo da sallama tana mai cewa "Ga yajin daddawa, duk da na san ai yanzu tuwon ma kun ci ƙarfinsa, an ji miyar amarya zaƙwaiƙwai" Ta faɗa ba tare da ta lura da yanayin da suke ciki ba, da yake tana ɗan sunkuyar da kai ne, ta sunkuya ta ɗago kenan ta yi arba da naman kowa a hannu, sannan ga tuwo nan duk ba a ci ba, cike da ɗan mamaki ta buɗe baki ta ce "Haba abokan ango abin har da zari kuma, wato bakwa bari ku gama cin tuwon ba ku ci naman, shi ne ake hannu baka hannu ƙwarya" Ta faɗa cikin sigar wasa irin na matar abokinsu. Bukari cije leɓe ya yi yana jin wani haushinta, a ɓangaren Aminu ma hakan ce ta kasance amma babu wanda ya bi ta kan Zulaiha, Aminu ne ya miƙa hannu ya ciro breziyar hannun Bukari wacce warin gumi da na dauɗa yake tashi daga jikinta. Karaf idanun Zulaiha suka sauka a kan breziyar, cike da ɗan jin kunya tana ƴar dariya ta miƙawa Aminu hannu tana cewa "Lah faɗowa ta yi, wallahi da na cire tare da kayan nan na ɗora ta a kan gado" Aminu da ya yi fosta jin ta ƙara tona masa asiri, shi da yake wayincewa yana cewa ta aljannu ce, amma ta gama faɗar komai. Har ta karɓi breziyar Aminu bai samu bakin magana ba, tana karɓa ta ɗauki rigar leshin da ta cire ta saka breziyar a ciki ta tuƙunƙune, ta ajiye tana cewa "Ga yajin naku nan, ni bari na fita, sai ku ce gaba da gashi" Har ta juya Kabiru ya ce "Amarya ni sai na samu ƙusa a cikin nawa kashin nama" Juyowa ta yi tana dariya irin ko a jikin nan nata ta ce "Ayyo, wallahi kasan zabuwa da wahalar dahuwa, shi ne aka ce ana saka ƙarfe ko cokali, to shi ne na saka tsohuwar ƙusar nan don ta yi saurin dahuwa" Idanu Lawan ya ƙanƙance jin amsar da ta ba Kabaru, Kabiru kuwa zuciyarsa ce ta tashi saboda har ya fara hango inda aka samo ƙusar zai iya kasancewa waje ne marar tsafta. Ganin hankalinta kwance za ta fita, Lawan ya ce "Naman ma zaƙi cai" Shiru ta ɗan yi tana nazari, jin an ce zaƙi, sai sannan ta tuna waje ɗaya ta ajiye robar suga da ta gishiri kuma robobin iri ɗaya ne, sannan gishirin ma ba mai laushi sosai ba ne. A zuciyarta ta ce 'Cakwakiya lallai kuna cin daɗi' A fili kuma sai ta yi dubarar faɗin "Haba Lawan, to ni ina amarya ya zan yi in muki girkin ƴan ƙasarku baƙaƙen fata, ai ni da kake gani na yi girkin ƙasashe da ban da ban" Su duka ukun sai suka bi ta da kallo ban da Bukari da yake jin kamar ya shaƙo mata wuya, Lawan cikin son jin girkin ƙasar da aka musu ya ce "Yanzu dahuwar naman nan ba na Nigeri'a ba ne" Murmushi ta yi jin tarkonta ya kama tsuntsu ta ce "Kaima da wani abu, ai dahuwar naman nan na ƙasar indiya ne, ka san su da suga suke amfani ba gishiri ba, shi ya sa na ce wataƙila baku taɓa ci ba, shi ya sa na gwangwaje ku da shi" Kallon rainin wayo Kabiru ya mata ya ce "Shi kuma tuwon nan mai miyar ɗaci na wace ƙasa ne" A zuciyarta ta ce. 'Na shiga uku, ɗaci?' A fili ta ce "Miyar ƙasar Marocco ne" Kafin wani ya ƙara jefo mata tambaya ta fita daga ɗakin da sauri, kicin ta nufa tana zuwa ta ɗakko robar kuka ta duba, tana dangwala ta ɗanɗana sai kuwa ta ji ɗaci, a take ta tuno cewa daga gidan an ce mata ƙullin kayan miyar nan na baƙaƙen leda ɗaya kuka ce ɗayan kuma lalle, sai yanzu ta gane ashe lallan ta juye a robar ba kuka ba don haka shi ta kaɗa musu miya da shi. "Ni Zulaiha yau na kunyata, waɗannan ƴan rainin wayon abokan Aminun sun zo suna wani damuna da mini tambaya ƴar ƙure, dole sai sun ƙure ni, to an yi ma da wane shegen ya kawo su ƙwalama" Ta faɗi hakan a fili tana fitowa daga kicin ɗin ko a jikinta A can cikin ɗaki kuwa, kowa naman hannunsa ya ajiye Kabiru yana tsokanar Aminu da cewa "Yo kai abokina ka ce girki sai na ƙasar da ka zaɓa za kake ci, ka auri ƴar Nigeri'a amma tamkar ka auri mata ne na mabambanta ƙasashe" Aminu bai yi magana ba, don gani yake ma da gangan Kabiru ya faɗa masa magana. Hannu suka saka suka wanke a ruwan robar nan, cikin ɗan ƙarfin hali Aminu ya ce "Masallaci za mu je?" Harara Bukari ya aika masa ya ce "Ni dai tafiya zan yi, sai dai su ku je masallacin tare da su don yunwa nake ji gida zan je" Cikin sauri Aminu ya ce "Haba kai kuwa ga abinci an shirya saboda da ku" Lawan da Kabiru suka kwashe da dariyar irin ta abokai. Banza Aminu ya musu, nan suka miƙe su duka suna masa godiya hatta lemon babu wanda suka ƙara sha. Suna fitowa suka farawa Zulaiha sallama, cikin sigar wasa ta ce "Har an fito kenan" Amsa mata suka yi Lawan ne mai ƙarfin halin cewa "To amarya mun gode Allah ƙara zaƙin hannu" Wani daɗi ne ya baibaye ra don tunaninta bayan fitarta sun ci abincin, tun da ta faɗa musu ba abincin ƙasar nan ba ne, ta ce "Ba komai ai baƙon ka annabinka" Har za su tafi Lawan ya zaro dubu biyar ya bata, godiya take ta musu, Aminu kuwa yana gefe bai ce komai ba sai harara yake galla mata, ko kallonsa bata yi ba ta ce "To godiya nake, sai kun ƙara dawowa, ranar kuwa girkin larabawa zan muku" Ta faɗa cike da wasa, Bukari kuwa fuuuu ya yi gaba don in ya tuna breziyar da ya gani a maƙale a jikin hannunsa zuciyarsa tashi take. Suna fita ta shiga ɗakin, naman ta fara ɗauka ta ɗanɗana wani rin zaƙi kauuu, da sauri ta fito waje ta tofar da yawu ta wuce kicin ta ɗakko ruwa a wani kwano ta dawo, haɗe da maggi mai tauraro. Zaunawa ta yi ta wanke naman tas ta barbaɗa maggi take ci, tana cikin ci sai ga Aminu ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi. Yana kallonta ya ji wani ɓacin rai, da sauri ya ɗakko rigar leshin nan yana zazzagawa sai ga breziya ta faɗo, ɗagawa ya yi cikin ɓacin rai ya ce "Zulai wane irin rashin mutumci ne wannan, saboda tsabar rainin wayo za ki ajiyewa mutane wannan abar daƙalƙal da datti, har abokaina su gani" Tsaye ta tashi ta yi wurgi da hular kanta ta kalle shi ido cikin ido ta ce "Aminu ni kake cewa Zulai? Idan ka daina kirana ƴar aljannar ne ai sai ka kirani da Zulaiha, sunan da aka yanka rago aka raɗa mini, ba wai Zulai ba sai ka ce wata tayar keke" A ƙufule ya kalleta idanunsa suna hasko lokacin da breziyar take maƙale a hannun Bukari ya ce "An faɗa Zulai" Kallon kai aka bari da yawo da zance ta masa tana komawa ta zauna tare da ɗaukan wata cinyar zabuwa, ta shiga yaga dakyar kasancewar rashin dahuwa. Kallon takaici ya mata yana ganin yadda farantan suke cike da tuwon da babu abij da abokan nasa suka ci a ransa yana tunanin da Sadsiqa ce ba za a a samu wannan matsalar ba. Tsabar takaici ficewa ya yi daga gidan, ya zo zai wuce ta gaban kicin ya ji wani ƙamshi tana tashi, a take yunwar cikinsa ta motsa, ya san Saddiqa ce take girki, amma tunowa da ya yi ko maggi ba ya siya mata sai ya kaɗa kansa, yana dab da fita daga gidan sai ga Sumayya ta fito ta ce "Ango ka sha ƙamshi na Sumayya bada kanka a sare" Ta faɗa cikin sigar wasan ƙanin miji. Ransa ne ya ƙara ɓaci jin wai saboda Sumayya zai bada kansa a sare, ya ce "Ina Ruma" Haka kawai ya faɗa kafin ta bashi amsa ya juya ya fice kamar zai tashi sama, baki ta taɓe a fili ta ce "Ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Tun da ya fita bai dawo ba sai yamma, yana shigowa ya ganta tana bacci a kan gado, kwanukan nan suna inda suke babu wanda ta ɗauke, tuwon ma duk ya sha iska har ya fara ɗan bushewa. Kai ya dafe ya kafe farantin da ta ci naman duk ta ɗaye tsokar sai ƙasusuwan kwanukan ya shiga kwashewa. Yana shiga kicin ɗin ya ajiye su, ganin tukunyar Saddiqa a rufe ya buɗe sauran jallof na shinkafa da wake ne a ciki, bai fi ka ba yaro ƙarami ɗan yaye ba, amma haka Aminu ya shiga cin abincin da hannu a tukunyar, yana jin wani daɗi yana ratsa shi a fili ya ce "Yanzu da abokaina wannan suka samu, ai da babu ni babu jin kunya, amma har zabuwa na saya aka kasa fitar da ni kunya" Ya faɗa yana jin daɗin girkin har tsakiyar kansa. Saddiqa wacce ta taho za ta ajiye plate a kicin ɗin, kawai sai ganin mutum ta yi kamar almajiri yana ƙanƙare ƙanzon tukunya, Aminu jin motsi ya juyo da sauri sai kuwa ya yi arba da Saddiqa, ga shi dai ta ganshi amma kuma sai ƙoƙarin wayincewa yake, yi ta yi kamar babu wata halitta a wajen, sai dai idanunta sun sauka a kan tuwon da aka yi wa abokan Aminu da aka ajiye farantan a kicin, tana gani ta gane abincin ne ya kasa ciyuwa, don ta fahimci kenan dalilin rashin iya girkin amarya ne ya sa, ya je mata da batun ta yi wa abokan nasa girki saboda bata san ciwon kanta ba. Ta ajiye plate ɗin za ta fita, sai kuwa ya matso don ƙamshin turarenta ya gama haɗe kicin ɗin, cikin ƴar murya ya ce "Saddiqa" Wannan furucin ya yi daidai da zuwan Zulaiha ƙofar kicin ɗin, hakan ya sa Aminu dakatawa yana ciccira ido kamar an kama kwarto a gidan amarya. Saddiqa kuwa tuni ta fahimci tsoron matarsa yake, baki ta taɓe ta raɓa ta gefen Zulaiha da ta tsaya ƙiƙam tana musu kallon tuhuma, ita Saddiqa warin jikin Zulaiha da ta shaƙa ne da kuma kayan jikin Zulaihar suka saka ta a zuciyarta ta ce 'Cakwakiya lallai zani ce ta tarar da muje mu' Zulaiha kuwa bayan wucewar Saddiqa ta kalli Aminu, rai a ɓace ta ce "Wato amanata za ku ci, ranar girkina ka zo kun laɓe kuna ƙusƙus a kicin, saboda ka zubar mini da mutunci ka zo kana cin abincinta, bayan ga tuwon da na muku nan kun bar mini" Tsabar takaici ma ya rasa mai zai ce hannu ya wanke ya fice ya bar ta tsaye a wajen. Fuuuu ta bi shi ɗakin tana zuwa cikin tsiwa ta ce "Kar ka ƙara mata magana ranar girkina, tun da kai ka cw sati biyu zan yi, don haka babu kai babu ita sai ranar girkinnta" Galala yake kallonta a ƙufule ya ce "Zulai baki fahimci wa kika aura ba har yau ko? Saboda ban fito na nuna miki asalina na Aminu ba... Kiranta da Zulai ya ƙara dagula lissafin hakan ya sa ta ce "Wallahi ka daina ɓata mini suna, kuma da kake cewa ban sanka ba kana da wani suna ne da ya wuce Aminu ƘAZAMI... Rai ɓace ya yi wajenta zai kai mata duka ta kama ƙugu ta ce "Ba irinmu bane matan da ake duka, wallahi yadda kake ji da tsagiranci haka nake tantiriya" Kallonta ya yi ya ɗauke ka, yana ji da kansa yana ganin, kamar dai shi Aminu za ta rainawa wayo, shi da Yayunsa ma bai ƙyale ba tabbas bata so zama lafiya ba a gidansa. Jin zuciyarsa tana masa zafi ya fice daga gidan. La'asar lis Saddiqa ta shiga kicin za ta wanke ƴan kwanukan da ta ɓata, tana cikin wanke-wanke Zulaiha ta shigo kicin ɗin, ganin kwanukanta a gefe ta ce "Malama ya za ki ware mini kaya a gefe, nufinki waye zai wanke" Bango Saddiqa ta ba ajiyar Zulaiha, don ta lura irin matan nan ne masu shegen kishi, ita kuma yanzu gani take Aminu ba ya cikin mazan da za ta yi kishin su. Haushi ya sa Zulaiha ta ƙara cewa "Ba da ke nake magana ba?" Ganin Saddiqa bata tanka ba, sai Zulaiha ta fara jidar kayan tana kaiwa wurin Saddiqa. Juyowa Saddiqa ta yi cikin muryarta mai sanyi ta ce "Na miki kama da mai aikin wanke-wanke?" Zulaiha ta ce "To da wa kike kama? Ni fa ba na ɗaukan ki matsayin kishiyata, baki ga ko da na zo gidan nan mijina Aminu bai haɗa mu waje guda ya nuna ki a matsayin matarsa uwar gidansa ba, wannan dalilin ya sa na ga baki da maraba da mai wanke-wanken, kuma ga shi dai cikin kwananki ya ƙara mini sati guda, kin ga kenan baki da wani muhimmanci" Tun da ta fara faɗar baƙaƙen maganganu, abin ya yi wa Saddiqa ciwo amma kuma sai ta raina Zulaihar don haka take ganin ɓata lokaci ne da rashin girmama kai ta tsaya sa'insa da ita, amma sai ta yanke shawarar faɗa mata magana ɗaya zuwa biyu hakan ya sa ta ce "Ni fa in na raina kasuwa ne ko sautu ba na bayarwa, kuma ina so ki sani kayan da suke samun wanki da guga ana tsafta ce su koyaushe, su ne kayan da mutum yake jin yana so ya sanya a jikinsa, amma in har kaya basa samun abubuwan da na lissafa to koyaushe mutum zai ji ba ya ma son au raɓe shi" Tana kaiwa nan a maganarta, ta juya ta cigaba da aikin gabanta. Zulaiha kuwa saboda tsabar toshewar basira, bata fahimci kurman baƙin da Saddiqa ta karanta mata ba, bare ta gane magana Saddiqa ta faɗa a kan cewar Amunun da take kishi tun da ƘAZAMI ne ita bata ma sha'awar ya kusanci inda take. Buguzum-buguzum ta juya ta bar kicin ɗin. *BAYAN KWANA BIYU* Aminu ne bayan ya dawo daga kasuwa, suka rinƙa bala'i shi da Zulaiha, hakan ya sa ya fito ya bar mata ɗakin, don ya ga ko kaɗan bata raga masa. Ɗakin Saddiqa ya nufa, ƙamshin turaren wuta ya cika ɗakin, tana zaune sanye cikin fararen riga da wando, gaban rigar an yi pink ɗin flower. Da sallama ya shigo tun da ta amsa masa ta maida hankali ga cin gaɗar da take. Zaunawa ya yiannu ya miƙa ya tsakura ya kai bakinsa. Tun da ya zauna ta tsaya cak da cin gyaɗar, saboda warin rana da yake tashi daga jikinsa, amma haka ta daure, wani kallo ya yi mata mai cike da shauƙi sai ƙare mata kallo yake, cikin ƴar murya ya ce "Saddiqa manyan mata, ana nan ana caɓa ado da kwalliya, kin yi kyau ɗakinki ƙamshi ko ina" Ya faɗa yana baza hanci, tare da tuno yadda ya baro ɗakin amarya da rabon ɗakin da shara, tun shekaran jiya da ya share da zai yi baƙi. Kallonsa ta yi ta ce "Anya kuwa, ni ɗin ko dai ɓatan kai ka yi" Yana kafe ɗan ƙaramin bakinta da yake sheƙin lipstic ya ce "Da ke nake mana" Duk kallonta da yake sai ya ji yana buƙatarta. Ƴar dariya ta yi ta ce "Na gode" Yana wani ɗan kashe mata ido ya miƙa hannunsa zai kai jikinta, da sauri ta ɗan ja baya, cike da mamaki ya ce "Kamar zan aikata haram" Ta ce "Ni dai ban ce ba, amma dai a iya sani na, sai nan da kwana huɗu ne kwanakin amarya za su ƙare" Kamar ta ambaci sunan maƙiyarsa ya ce "Wace amarya kuma" Banza ta masa. Nan ya zauna yana ta ƙoƙarin kai hannunsa jikinta, amma ta ƙi bashi amsa, da ta gaji ma sai ta fito ta bar shi a ɗakin don duk ya haɗe ɗakin da warin rana. Lokacin da ta dawo, don dama ɓangaren Sumayya ta tafi, sai ta tarar da shi ba ya nan, baki ta taɓe ta ƙasa saka turaren wuta, ita tunaninta ma in sati biyun ya ƙare yadda za su dawo su yi rayuwa da shi. Misalin ƙarfe biyu na dare, Aminu ya kasa bacci tun da ya ga shigar Saddiqa ya saka a ransa yau a ɗakinta zai kwana, sai dai Zulaiha uwar ƴan kishi yake tsoro, hakan ya sa ya yi bakam kamar mai bacci. Yanzu jin tana ta munshari ya lallaɓa ya sauka daga gadon, a hankali ya buɗe ɗakin ya fito ya mayar da ƙofar ya rufe. Ɗakin Saddiqa ya je cikin sanɗa ya tura ƙofar ya shige, cike da farin cikin zai biya buƙatarsa a waje mai tsafta ya hau kan gadon. Saddiqa tana cikin bacci ta ji hayowar mutum kan gadon, kafin ta yi yunƙuri ta ji warin jikinsa ya sanar da ita wane ne. Tana shirin magana ya rungumota. Zulaiha cikin bacci ta miƙa hannu don taɓo ango amma ta ji babu shi babu dalilinsa. Matsawa ta yi don duk tunaninta ko ya bata tazara ne, duk da ta san a kusa da juna suke kwana. Tana mirginawa ta ji wayam, idanu ta buɗe don duk abin da take idanunta a rufe suke, kaf kan gadon ita kaɗai ce. Cike da mamaki ta tashi ta kunna fitila, ɗakin ta shiga ƙarewa kallo babu Aminu babu alamarsa, ko kan gadom sai wata singiletinsa da ta ci wani uban datti. Bayi ta nufa amma Aminu ba ya ciki, cike da mamaki take tunanin ina zai je a cikin daren nan, don ta duba agogo ta ga ƙarfe biyu har ta gota. Idanunta ta sauke a kan ƙofar ɗaki, ai kuwa ta ga alamar an buɗe ɗakin don ƙofar bata rufu sosai ba, a zuciyarta ta ce 'Ina Aminu yake? Wallahi yau za a yi bala'i idan har zargina ya zama gaskia' Ta faɗa a zuciyarta tana buɗe ƙofar ta fito.... ƘAZAMIN MIJI BOOK 1 FREE ne BOOK 2 NA KUƊI 500 MAI BUƘATA ZAI BIYA TA ASUSUN Faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta 09025576222 [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 15 *YAYA SULE* Soyayya mai ƙarfi ta ƙara kankama tsakaninsa da Salaha inda yake ƙara iya takunsa ga duka matan guda biyu, wato Salaha mai shirin shigowa gidansa sai kuma ita mai gayya mai aiki Amina, ta hakan yake cin karensa babu babbaka. A inda Amina, har yanzu tunaninta yake ƙara tabbatar mata da cewa ita kaɗai ce mamallakiyar Sule kuma ita kaɗai za ta rayu da shi, daga ita sai ƴaƴanta wannan ya sanya take cin duniyarta da tsinken tsire, tana huce hanci kanta yana fashewa ita a nata ganin ita ce mace ɗaya tamkar dubu a wajen mijinta. Hakan ya sanya idan zama ya haɗa su da Saddiqa take jefar mata da magana a fakaice, duba da yanzu Saddiqa bata fiya zuwa ɓangarensu ba, sai take cewa Saddiqa baƙin kishi ne yake nuƙurƙusarta shi ya sa bata son shiga cikin mutane, ta gwammace ra zauna a ɗaki ita kaɗai, idan ta faɗawa Saddiqa hakan sai dai ta yi dariya, don ita Saddiqa ta sani bata wani jin kishin Aminu, duk da dai idan ta ce bata son sa ta yi ƙarya tun da auren soyayya suka yi, amma kuma a duk sanda ta tuna ƙazantarsa da kuma irin mugayen halayensa da ya mata, na watsar da wasu daga cikin buƙatunta da Allah ya ɗora masa, sannan a gefe ɗaya ba ya son cikin jikinta haɗe da wulaƙanci in har ta tuna hakan tana jin son sa ya ragu da kaso mafi yawa daga cikin wanda take masa. Amina ce zaune a bakin gadonta tana daddanna waya, hira suke da ƙawarta a akan zancen za a yi wa qata ƙawarsu kishiya, shi ne Amina take ta cika baki, tana cewa macen da ta isa ba a mata kishiya, tun da ga shi nan ita ko alama Sule ba ya ma sha'awar kula mace. Murmushi ƙawar tata ta turo mata kafin ta mata rubutu kamar haka ta ce "Amina, ki kiyayi namiji fa, shi namiji ɗan kunama ne baka gane zafin dafin jikinsa sai lokacin da ya harbeka, amma fa son mata da kuma ƙarin aure a ran kowane namiji yake, sai dai idan bashi da halin yi ko kuma lokacinsa bai yi ba, ko kuma dai bashi da rabon ƙarin auren har ya bar duniya" Amina tana gama karantawa ta mata replaya da cewa "Ba za ki gane irin ɗinbin son da Sule take mini bane, ba na jin akwai wata ƴa mace da zai kalla da sunan soyayya bare har ya ji yana son aurenta, ni shaida ce babu abin da yake ɓoye mini" Ƙawar tata ta ce "To ke in zai yi auren ko in yana kula ƴan matan faɗa miki zai yi, bayan ya san bakya so kuma dai ya san yadda yake koɗa ki, ai akwai mazan dansuke baka komai a rufe" Amina ta ce "Ki daian faɗa mini hakan Fauziyya, mijina nawa ne na ni kaɗai, sannan mijina yana cikin mazan da basu da rabon ƙara aure har su koma ga Allah, don haka mu yi wata hirar ba wannan ba, duk wacce kika ji za a yi wa kishiya a cikin ƙawayenmu ki faɗa mini, ni kuma ki ba a gayyace ni ba ,an je dannar ƙirji!" Suna cikin chart ɗin ne wayar Sule da take a kan madubi ta shiga yin vibration, har ta share bata je ta duba ba, har kiran ya katse tun da shi yana wanka. Jin kiran ya ƙara shigowa a karo na biyu sai ta ajiye wayarta ta je kan madubin ta leƙa wayar, MAMUDA sunan da ta gani kenan yana yawo a kan screen ɗin wayar, mamaki al'ajabi haɗe da faɗuwar gaba suka dirar mata lokaci guda, tana tuna cewa jiya da dare ma har sun kwanta sai da ta ga MAMAUDAN nan ya kira shi, ƙarshe ya ce mata zai fita ya siyo panadol jikinsa yana masa zafi, da haka ta manta da maganar kiran tun da tun kiran farko ba a sake kira ba. Ita kuma jin ya ce jikinsa yana zafi sai tausayinsa ya kamata, ta manta batun kiran MAMUDA. Yanzu ma sai ta fara tunanin dalilin da ya sa shi MAMAUDA zai ke kiransa koyaushe, duk da MAMAUDA ba suna mace bane amma dai ta ɗan shiga shakku da taraddadi. Hannunta ne ya fara karkarwa jin zuciyarta tana ɗarsa mata wani zargi, duk da ta ƙaryata zuciyarta amma dai sai ta ji tana son sanin dalilin kiran da MAMUDAN yake yi wa mijin nata. Tana ɗaga kiran sai wayar ta mutu, da ta duba sai ta ga cajin ne ya ɗauke gabaɗaya. Jin ƙaran sheƙa ruwan Sule a banɗaki da alama ya gama wankan ma, sai ta ajiye wayar, tana shirin barin gaban madubin sai ga shi ya fito daga bayin, abin da ya ɗaure mata kai shi ne yadda ta ga alamomin razana a tare da shi, wannan ya sanya ta ji hankalinta ya tashi, tana tambayar zuciyarta shin idan har babu wani abu da yake ɓoyewa a wayar mai ya sa da ya ganta a kusa da wayar zai razana. Kafe shi ta yi da idanu tana son gano gaskiyar lamarin, shi ma Sule a nasa ɓangaren tsorata ya yi, don tunaninsa ko ta masa bincike a wayar tasa amma kuma tunowa da ya yi cewa yau da safe ya canja passward na buɗe wayar sai ya ji daɗi a ransa, hakan ya sanya ya yi saurin kawar da tsoro daga fuskarsa, matsowa ya yi yana zuwa sai ya riƙo ta tare sa rungumota jikinsa ya sanya lemar hannunsa ya shafe mata fuska tare da juyo da ita suke fuskantar juna, ita kuma da bata gama dawowa daga nisan kiwon tunanin son sanin alaƙarsa ta yawan kira da MAMUDA yake yi ba, sannan uwa uba dama ita ta tsani soyayya sai kishin tsiya ne kawai da ita amma mijinta ba ya samun kulawarta, ko soyayarta wanda hakan ya sa shi kuma yake cutuwa, har ya sa ya fara tunanin mafita wato ya auro wata macen ko ya samu yadda yake so. Hannunta ta fincike saga riƙon da ya mata ta ce "Na sha faɗa maka ni ba ma'abociyar soyayya bace, amfanin soyayya aure ne, kuma mun yi aure to mene ne saura?" Da kallo ya bita duk da ya saba jin kalamanta masu tsauri irin wannan, amma bai san mai ya sa yau suka masa zafi fiye da kullum, kafin ya ce wani abu har ta ɗora da faɗin "Shin waye MAMAUDA?" Tambayar ta zo masa a bazata, tunanin ya fara kan cewa ko dai ta samu damar buɗe passward ɗin wayar ne, har take tuhumarsa kuma ba a kan kowa tuhumar ba sai a kan Salaha(MAMAUDA) Idanunta ya kalla yana son tantance tambayarta domin ya san irin amsar sa ya kamata ya bata, yana cikin wannan halin ta katse shi da faɗin "Magana nake maka fa, waye MAMUDAN nan wai yanzun nan ma na ga yana kiranka" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ya san dama sai dai in kiran ta gani amma da bincike ta masa a wayar ta gano abubuwa da dama na soyayyar da suke zubawa da Salaha ai ya san ya kaɗe har ganyensa kuwa, don irin musayar zantukan soyayyar da suke masu tsayawa a zuciya ya san da wataƙila ta suma in da gani. Jarumta ya aro ya ce "Kai Amina, wallahi ni na ɗauka ma wani abu ne ya faru, yanzu a kan MAMUDA ya kira ni kika tsare ni da tambaya haka, kamar dai wata macen... Wani kallo ta aika masa kafin ta katse shi da cewa "Kar ka ma fara, don ba a haifi macen da za ta kira ka ba, kuma har abada ba za a haifeta ba, kai nawa ne" Murmushi ya yi yana jinjina kishi irin nata ya ce "Maganarki dutse, ai ni kaina na san babu wacce za ta kira miki ni, kisha kuruminki amanarki ta riƙu, MAMUDA dai ni ban san me ya sa yake damuna ba, shi bashi da aiki sai neman rancen kuɗi... Katse shi ta yi da faɗin "Amma ranar nan cewa ka yi za ka yi blocking ɗinsa" Dakyar ya samu dabarar faɗin "To ai bayan na yi blocking ɗin da wata lambar ya kirani yana cewa, ya gode da na rufe hanyar da zai sameni, don na ga bashi da kuɗi, wannan dalilin ne ya sa na sake saved sabuwar lambarsa" Shiru ta yi tana nazari shi kuka ganin maganar ta yi tasiri ya sake cewa "Babu daɗi din baka da shi a gujeka" Ajiyar zuciya ta sauke mau ƙarfi ta ce "Haka ne kuma, amma dai kiran koyaushe bashi da wani amfani, ni sai in ke jin faɗuwar gaba" Ya ce "Ki kwantar da hankalinki ni naki ne har abada, ko ana ruwa ana iska, ana ruwa da ƙanƙara daga ke babu daɗi na kulle ƙofa tuf da mukulli" Wata dariya ta saki mai sauti, don ta ji daɗin yaudararrun kalaman da ya tsarata da su bata san cewa rami ya mata ta faɗa ba don MAMAUDA ba kowa bane sai matar da yake son aura, yana ta tunanin wannan cakwakiya ta yaya zai sanar da amarya cewa akwai uwar gidanta har suna da yara biyu, sannan ita mai gayya mai aikin sarkin ƴan kishi Amina ta wacce hanya zai faɗa mata yana neman aure, ya san duk ranar da ƙwan nan ya fashe tabbas akwai ɗan jijjiɓin rikici, shi ya sa ma ya iya takatsantsan, sannan ya iya takunsa don ko da a ce zai sanar da su, su duka biyun to sai aski ya zo gaban goshi, wanda bahaushe yake cewa aski in ya je gaban goshi ya fi zafi. Tun da ya fahimci Amina ta gama gane yawan kiran da MAMUDA yake yawan yi masa, gashi shi kuma ba zai iya sanar da Salaha cewa ba koyaushe za take kiransa ba, tun da bata san yana da iyali ba duk da wasu ƴan matan ko sun san namiji yana da mata basa fasa kiran wayarsa koyaushe, domin wata a lokacin da ta san namiji yana da mata a sannan ne za ta buɗe ƙofofin rashin mutunci ba za ta tsiri kiransa ba sai yana gidansa don haɗa fitina da husuma. Idan aka samu uwar gidan mai ƙarfin zafin kishi shikenan sai a rinƙa bala'i da miji wata daga wanann har saki a gifta tsakaninta da mijin, don abu guda da mata basa ganewa shi ne, duk lokacin da namiji yake neman aure idanunsa rufewa suke ba ya ji ba ya gani, ko a mutu ko a yi rai. Goge sunan MAMUDA ya yi ya maryar da shi MARAINIYA, bayan an yi hakan da sati biyu, wayarsa tana caji ya jona, sai kuwa ta fara ƙara, ya tashi da ɗan hanzari zai ɗakko Amina ta ce "Bari in yi aikin lada in miƙo maka, ba sai ka tashi ba" Murmushin yaƙe ya saki yana komawa ya zauna gabansa yana faɗuwa, Amina tana ɗaukan waya ta ga sunan MARAINIYA da manyan baƙi yana yawo a kan screen ɗin waya. A ɓangaren Sule kuwa yana ta addu'ar Allah sa wani ne daban yake kiransa ba Salaha ba, yana wannan halin sai ta ji Amina ta ce "Sule wace ce kuma MARAINIYA" Gabansa ne ya faɗi, shi a nashi ɓangaren ya saka sunan ne don yana ganin ba lalai hakan ya ɗauki hankalinta ba, amma ganin hannunta har karkarwa yake wayar tana neman suɓucewa cikin dakiya ya ce "Wai dama MARAINIYA na saka?" Ta ce "Ban sani ba, kai za a tambaya" Sai ya ce "Kai amma fa typin error sai ya haɗa maka ɗan jijjiɓin faɗa, MARAYA fa zan rubuta, wani abokinmu ne tun muna primary babansu ya rasu to shi ne fa kullum aka masa abu sai yake cewa, don mun san shi maraya ne, shikenan daga nan sunan maraya ya bi shi" Yana kai wa nan ya kafe ta da ido, idanu ya ga ta runtse, tana jin yadda ƙirjinta yake bugawa, sai kuma ta buɗe a hankali tana shirin miƙa masa wayar wani kiran ya shigo, wayar ta kafe da ido har sai da ta ji ta gamsu da maganarsa, ta miƙa masa tana faɗin "Wallahi na tsani abin da za a ke saka mini shakku" Karɓa ya yi yana cewa na sha faɗa miki ki kwantar da hankalinki" Komawa ta yi ta zauna tana faɗin "Ba dole gabana ya faɗi ba, na ga an sanya MARAINIYA. Idanunta ya faka ya danne wayar ta mutu gabaɗaya, sai ya kara a kunne yana cewa "Babu MARAYA sai rago" Yana faɗar hakan ya ɗan yi shiru alamar kamar amsa ake bashi daga ɗaya ɓangaren. Sai kuma ya ce "Allah sarki kowa lpia" Daga haka ya shiga yin ƴar hira yana dariya, tamkar da wani yake yi, yana gamawa ya tashi ya mayar da wayar caji. Daga haka suka ɗan shiga hira da ita, yana ƙara faɗa mata babu ita babu kishiya a gidan duniya, tashi ta yi daga jinginen da take ta ce "Mene ne nufinka? Kenan a lahira ba da ni kaɗai za ka zauna ba?" Tambayar ta so bashi dariya, amma ganin haka sai ya dake ya ce "Baki san akwai matan aljanna ba?... Tun kafin ya kai ƙarshen maganar ta ce "Ni a aljannar ma ni kaɗaice " Dariya ya yi ya ce "To Aminatu sarkin ƴan kishi, wato har da matan aljanna ma" Ita ma dariyar ta yi ta ce "Yo su ma ai mata ne" Bai ce komai ba ya ɗan yi murmushi a zuciyarsa yana cewa 'Iska tana yawo da mai kayan kara, ni da nake son mace ƴar soyayya wacce za ta shagwaɓani ta tarairaye ni, in ɗanɗani zumar soyayya da ta lobayya, ni ma in nuna mata tawa kulawa da soyayyar, amma ke kin zo kin mini dikim, in an yi batun soyayya ki ce ba haka ba, amma batun kishi ke ce a gaba, baki san ya za ki ɗauke hankalin mijinki ya dawo kanki ba' Ya faɗa a zuciyarsa yana yi wa Yusuf magana ganin yana ɓarna. Yana fita daga gidan ya sauya sunan Salaha daga MARAINIYA zuwa, ABOKINA washe gari kuma sai ya sha kwalliya tare da fesa turare ya cewa Amina zai je wajen walima da abokinsa ya shirya musu saboda yana ƙara aure, Amina jin haka ta washe baki don ita a rayuwarta tana so ta ji an ce za a yi wa wata mace kishiya amma ban da ita. Hakan ya sa bata hana shi ba, kuma bata nuna damuwar kwalliyar da ya ci ba, har da ɗakko wani turare da ta saya mai bala'in ƙamshi ta fesa masa sosai, wai bata son ya je wajen abokai a raina shi. Yana fita ya dokawa Salaha waya ya ce yana hanya. Suna cikin hira da Salaha tana ta yaba ƙamshin turaren, zuwa can sai ta ce ya ara mata wayarsa za ta tura wata waƙa da ta ji ranar nan ana kiransa da ita, hankali kwance ya miƙa mata, tana cikin danne -danne sai wayar ta ɗauki ƙar gani ya yi Salaha ta zaro idanu sai ta ce "Me zan gani wane suna ne wannan?" Ta tambaya tana tashi tsaye, gabansa ne ya buga da ƙarfi yana jin wani tashin hankali don ya san ba zai rasa nasa ba da kiran Amina ba ne ya shigo wanda ya yj saved na sunan da MY WIFE, cikin karkarwa hannu ya miƙa hannun yana cewa "Wane suna kuma? Bani in gani, tana aika masa wani kallon tuhuma ta miƙa masa wayar, sunan da ya gani ne ya sa hankalinsa tashi, ya fara tunanin amsar da zai bata... *ZULAIHA* Ɗakin ta koma ta ɗauko fitila, ko tsoro bata ji ta fito daga ɗakin ta shiga baza idanu amma babu kowa, ƙwafa ta yi ta kama hanyar ɗakin Saddiqa duk da bata taɓa shiga ɗakin ba wannan ne karon farko amma yau ya zame mata dole ta je tun da a nata ganin ai neman kadararta za ta je, wato mijinta. Tana zuwa ƙofar ɗakin ta ganta a rufe, amma tun daga hanyar take duba sawun Aminu, ko takalmi babu, kuma ta ga sawun nasa ya yanke ne daga lokacin da ta zo ƙofar ɗakin Saddiqa sai ta nemi sawun ta rasa. A can cikin ɗakin kuwa Saddiqa, jin Aminu ya rungume ta, ta shiga kiciniyar ƙwace kanta daga gare shi, saboda yadda warin jikinsa ya gama cika mata hanci ba abin da ta fi buƙata illa ya sake ta, ko ta shaƙi wata iskar mai daɗi wacce ba gurɓatacciya ba irin ta jikinsa. Shi kuma jin tana son raba jikinta da nasa, sai ya bada ƙaimi wajen yi mata wani irin riƙo, cikin murya raɗa-raɗa ya buɗe bakinsa mai warin da ya sa ta fara jin kanta ya fara juyawa ya ce "Saddiqa ni ne Aminunki fa, ki saki jikinki yau na zo na share miki hawayenki na kewata, na san tabbas! Kin yi kewar mijinki da ɗumin jikinsa" Yana faɗar hakan ta ji amai ya taho mata jin aman yana barazanar zubowa sai ta shiga girgiza masa kai. Bai damu da yanayin da take nunawa ba, shi dai buƙatar maje hajji sallah wato ya samu biyan buƙatarsa. Rigar baccin jikinta ya shiga ƙoƙarin raba ta da ita. A daidai wannan lokacin ne a halin da suke ciki, suka ji an banko ƙofar ɗakin ba Saddiqa ba hatta Aminu dai da ya razana da bugo ƙofar, kafin su yi wani yunƙuri an dalle su da wata fitila mai haske. Zulaiha kuwa ganinsu a manne da juna ya mugun ɗaga mata hankali, ga wani tuƙuƙin baƙin cikin da ya tokare mata maƙoshi a take ta fara jin wani jiri yana juyata, da sauri ta juya ta je kicin a guje ta ɗakko taɓarya dawowa ta yi ta shiga cewa "Ihu mutanen gida, kwarto, kwarto a kawo ɗauki ihu kwarto" Aminu duk tunaninsa bayan fitowarsa ne kwarto ya kaiwa Zulaiha farmaki, ashe bai san iya shege ne ba da shi take. A ɓangaren Sule jin ihun kwarto sai ya fito daga ɓangarensa ɗauke da wata ƙatuwar sanda, haka Yaya Shafi'u ma ya fito ɗauke da wata zarɓeɓiyar wuƙw da take cikin gidanta. A gigice suka iso wajenta, don sun gane amaryar gidan ce amma ganinta a ƙofar ɗakin Saddiqa sai suka fara tunanin ko ɗakin Saddiqa kwarton ya shiga, shi ya sa ta tsaya a wajen, suna zuwa a kusan tare suka ce "Yana ina ko ya fice" Cikin muyarta wacce tamkar kuka zai fito ta ce "Yana ɗakin wannan" Ta faɗa tana musu nuni da ɗakin Saddiqa, su kuma sai suka jinjina mata, ganinta ɗauke da taɓarya sannan kuma tana gadin ɗakin da kwaton yake. Aminu kuwa jin muryoyin Yayunsa bai sanya ya yi girgizu ba, Saddiqa ce ma jin ya sakar mata jiki sai ta fara ƙoƙarin sauka daga kan gadon. Tana sakkowa su duka ukun suka kawowa ɗakin farmaki, Yaya Sule, Yaya Shafi'u da kuma Zulaiha kowanne ɗauke da makami. Yaya Shafi'u ganin Saddiqa cikin kayan bacci, da yake suna shigowa Yaya Sule ya kunna fitilar ɗakin, ga kuma hasken fitilar hannun Zulaiha. Jikinta kawai Shafi'u yake bi da kallo don ba ƙaramib kyau ta masa ba cikin rigar baccin, duk da doguwa ce amma dai ta bayyana asalin suffarta. Zulaiha kuwa ta shagaltu da kallon ɗakin ne, tana wani taɓe baki jin yadda ƙamshi ya zauna a ɗakin tamkar yanzu aka saka turaren wuta. Yaya Sule kuma ganin Aminu zaune dirshan a kan gado yana sanye da gajeran wandonsa, sai abin ya ɗaure masa kai, shi ma Yaya Shafi'u da ya mayar da ganinsa wajen mamakin ne ya dirar masa. Cikin Kakkausar murya Yaya Sule ya katse Zulaiha da faɗin "Ke Zulaiha mene ne wannan ɗin, Aminun ne kwarto, haka kawai muna bacci kin zo kin ɗagawa mutane hankali" Yana kaiwa aya Yaya Shafi'u ya ɗora da faɗin "To wai mai hakan yake nufi?" Jin kalamansu cikin tsiwa ta ce "To amma haka za ku ce ko tambayata za ku yi dalilina na yin hakan?" Da hanzari Yaya Sule da ya fi jin zafin ɗaga musu hankalin da ta yi ya ce "Mai za a tambaye ki a nan to, bamu ga kowa ba sai Aminu kuma kin ce kwarto yana ɗakin" Ita ma cikin fitsara da rashin girmama na gaba ta ce "Ai ba kowa bane ƙasurgumin kwarton illa Aminu" Su duka da kallo suka bita ganin ko a jikinta. Yaya Sule a zuciyarsa ya ce 'Taɓ lallai Aminu ya auro mace daidai shi' A fili kuma ya ce "A ina ya yi kwartancin" Shi kuma Aminu ya rasa ma bakin magana, ba komai ne ya bashi haushi ba illa yadda aka katse masa wani yanayi mai ban al'ajabi wanda ya san a wajen kaɗai ne yake samun wannan yanayin, bai tantance haka ba sai da ya auri Zulaiha ya gane Saddiqa ta keta Zulaiha da tazara mai nisan gaske. Yaya Shafi'u ne ya ce "Kin san me kike faɗa?" Cikin harzuƙa ta ce wai ku haka ake alƙalanci, ba za ku tambaye ni dalili ba sai kawai kuke yanke hukunci, to bari ku ji abin da baku sani ba, Aminu tun kafin in tare a gidan nan ya mini alƙawarin sati biyu zan yi ina amarci, amma yau saura kwana huɗu shi ne zai yi satar hanya ya mini satar kwana" Ta faɗa tana aikawa Aminu harara. Su duka mamaki suke inda Saddiqa ta sunkuyar da kai. Yaya Sule ne ya ce "Wai haka ne Aminu?" Aminu yana jin kamar su duka ya rufe su da duka, ganin sun hana shi rawar gaban hantsi ya ce "Haka ne" Kai Zulaiha ta kaɗa irin ai kun ji da kunnenku. Yaya Sule cikin ɓacin rai ya fara magana "Kai yanzu Aminu ka kyauta kenan, ka yi wa Saddiqa adalci a ce ka ɗauki kwananta ka haɗawa amaryarka, muna gidan nan amma bamu san wannan cakwakiyar da ka haɗa ba" Aminu ya buɗe baki zai yi magama Saddiqa ta yi saurin faɗin "Yaya da sanina kuma da yardata aka yi hakan, yanzu ma na ƙara masa sati biyu ka ga wata ɗaya kenan" Ta faɗa don ita zuwansa yau da ta ji warin da ta shaƙa sai ta ji ta ƙara son nesanta kanta da shi. Da sauri Aminu ya diro daga gadon cikin ɗaga murya ya ce "Wallahi baki isa ba, daga kwana goman nan dole ki karɓi girki" Zulaiha jin haka ta sakin taɓaryar hannunta ta ce "Idan akwai shegen da ya isa ya yanke wannan hukunci shegiya nake" Yaya Sule kai ya sunkuyar yana danne dariyarsa ganin ƙanin nasa ya samu daidai da shi in ba don sakayya da Allah ya yi wa Saddiqa ba, ya za a yi a ce amaryar kwana goma tana wannan masifa. Sosai hargitsi ya kaure na faɗi in faɗa, tsakanin Aminu da Zulaiha, dakyar Yaya Sule ya sasanta amma abin ya ci tura!. A ƙarshe dai Aminu ya yi wa su Yaya Sule rashin kunya saboda suna masa faɗan rashin kyautawar da ya yi wa Saddiqa, hakan ya sa kowa ya kama gabanshi suka bar Zulaiha da su Aminun a ɗakin Saddiqa. Zulaiha ta ce "Wallahi ina ɗakin nan babu inda zan je" Ta faɗa tana samun kan kujera ta zauna tana riƙe da taɓarya, ta ce Aminu idan ya yi gigin taɓa ta kai za ta ɓare masa, don sosai kishi yake nuƙurƙusarta musamman da ta ga Saddiqa rigar jikinta ta mata kyau, sannan har lokacin bata daina hango hotonsu a idanun zuciyarta ba, yadda ta same shi rungume da Saddiqar hakan ya sa take jin tamkar ta same su da taɓaryar ta yi ta duka ko ta samu rangwamen abin da take ji. Aminu yana tsakiyar gado a zaune, ya kifa tagumi don yau ya ga abin da ya turewa buzu naɗi, Saddiqa kuwa wuri ta samu ta zauna tana kallon ikon Allah, amma yadda amarya da ango suka ɗumama ɗakin da warin dauɗa kaɗai ya isheta. Zulaiha har aka kira assalatu tana zaune a wajen, ita kuwa Saddiqa ta fito ta barsu a ɗakin, bayinta ta buɗe da yake kullewa take da mukulli ta je ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin ta ɗauki sallaya da hijabi ta fita waje ta kabbara sallah. Shi kuwa Aminu lokacin har ya fara gyangyaɗi jin sanyin asuba yana ratsa shi, hakan ya sa sai yana cikin gyangyaɗin Zulaiha ta ce "Wallahi Aminu ka tashi, don ba zan bar ɗakin nan ba sai tare da kai" Ganin ta kaɗe masa hankali jin an shiga sallah ya fito daga ɗakin ya barta a ciki, banɗakin Saddiqa ya nufa amma cikin rashin sa'a ya same shi a kulle, dawowa ya yi lokacin ta idar da raka'atainil fajr ya ce "Saddiqa ina mukullin banɗakin?" Cikin rashin fahimta ta ce "Mai za ka yi da mukullin banɗakina" Ya ce "Shiga zan yi mana" Ta ɗan yi jim sai ta ce "Ai ba a bakina ba kake, don haka ka je ka shiga banɗakin amaryarka, kuma ina ƙara maka tuni sai nan da sati huɗu da kwana uku ne za ka dawo kwana ɗakina" Tana faɗar hakan ta tashi ta kabbara sallah, hakan ya yi daidai da fitowar Zulaiha, yana ganinta haushinta ya cika shi, ya juya ya nufi ɗakin Zulaihar ransa yana ƙuna ita kuma Zulaiha ta mara masa baya. Tun da ta shiga ɗakin take balbala masa masifa, wai ya ci amanarta ya satar mara kwana, dakyar ya yi sallah tana masa masifa ita kuma ko sallar bata yi ba, da ya idar ya kalle ta ya ce "Ke yanzu Zulai... "Wallahi ka daina faɗa mini Zulai na faɗa maka" Sai ya sake cewa "Yanzu Zulaiha abin da kika yi kin kyauta, waɗannan fa yayuna ne amma kika faɗa musu magana son ranki ko kunya bakya ji" Kallonsa take sheƙeƙe ta ce "Kunya? Wace irin kunya, ai ni abin kunya gaba na bashi ba baya ba, kuma da kake kiransu yayunka ai ba iyayenka bane, sannan ni ko daga wajenka ban ga kana girmama su ba, ni ma don ban yi ba ai ba za ka zargeni ba, sannan ina so ka sani batun karatun da na ce zan cigaba da yi a gidanka na fasa dama tun a gida na sanar cewa babu batun karatu kuma an amince mini, don ba zai yiwu in zo ina tafiya makaranta kuna keɓewa da kai da wancan matar taka kuna cin amanata" Tun da fara yake kallonta ganin ba saurarawa za ta yi ba ya ce "Zulaiha takun da kika shigo gidan nan da shi kinwatsar, saboda ba zan ɗauka ba, sannan ina so ki sani ni nan Aminu bani da mutunci nima don ko matata Saddiqa tsorona take ita da ta shafe watanni ma a gidan bare ke da ko sati biyu baki haura ba" Kallon sakarai ta masa ta ce "Saddiqa ka ce ni kuma Zulaiha nake, tsakanin harafin sunana da sunanta akwai tazarar haruffa bakwai, don haka ka sani babu gudu babu ja da baya" Banza ya yi da ita ya ce "Ki je ki yi ta yi amma ki sani za ku zuba ne ɗan halak ka fasa" Ta yatsina fuska ta ce "To shikenan, ina ƙara maka gargadi da cewa muddin ka ce za ka koma wajen waccana matar taka a cikin kwanakina da ka mallaka mini to ka sani za a yi faɗuwar baƙat tasa, za a yi haihuwar guzuma don wallahi babu wanda ya isa ya taka Zulaiha" Ganin da gaske take faɗan har jijiyoyin wuyanta suna tashi sai ya ƙyaleta a kan cewa zai je gidansu ya sanar da Umma halin da ake ciki, don shi ya fara takura da rashin Saddiqa. Har wajen tara sannan ya fita, ko wanka bai yi ba wani farin yadinsa da ya koma milik ya saka, don ko abin karyawa bata yi ba tana zaune sai uban soshe -soshe take. Gidansu ya wuce yana so daga can sai ya wuce kasuwa wajen sana'arsa. Umma ya samu tana zubawa tattabaru abincin, da sallama ya shiga ta amsa, ganinsa sanyi ƙalau sai ta ji duk babu daɗi don dama ta san duk namijin da ya ce zai haɗa mace sama da ɗaya to tabbas ba zai rabu da damuwa ba, duk da ta san Saddiqa tana da haƙuri amma dai ba za a rasa kishi ba. Bayan ya gaishe ta, ta kalleshi ta ce " Aminu lafiya dai?" Hannu ya kai ya sosai gashin kansa da ya taru ba ya samun aski ya shiga zayyane mata halin da gidan nasa yake ciki. Kallonsa Umma ta yi ta ce "Hmmm! Dama ai duk wanda ya saya rariya ya san za ta zubda ruwa, yanzu kai saboda rashin adalci da kuma rashin tsoron Allah, ka ƙwacewa Saddiqa kwanan sati guda, anya Aminu kana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Rarinyar nan ko shekara bata yi ba da aurenka ka mata kishiya, sannan baka tsaya a nan ba don ka musguna mata za ka ba kishiyarta bakin kwananta?" Tunda ta fara magana ya sunkuyar da kai, lokaci zuwa lokaci yana sosa kansa da yake ta masa ƙaiƙayi, ya ce "Umma ni fa ba don musguna mata na ce hakan ba, ai gani na yi ita Zulaiha amarya ce" Umma ta ce "Wato amarya sai a bata kwananta wata? Yanzu don Allah kalli kayan jikinka, ko wanki babu baka ji yadda warin dauɗa yake tashi ba Aminu, yanzu a ce wannan kayan mai datti a jikin magidanci mai mata biyu, shin sai yaushe za ka gyara wanann ƙazantar da kake fama da ita, ai wallahi mace mai zama da kai sai ta kai zuciya nesa, kuma dole ka siyawa kanka raini wajen mace shi ya sa ma Zulaihar ta rainaka" Da sauri ya ce "Umma dama fa Zulaiha ita ƙazama ce, wallahi da na yi baƙi ranar nan baki ga kwamacalar da ta haɗa musu ba, wai ta kaɗa lalle a matsayin kuka, ta dafa zabuwa da suga Umma wai girkin indiya da na marocco ta musu... Dariyar da Umma ta fara shi ya katse masa maganar ya ɗago yana kallonta. Sai da dariyar ta tsagaitawa Umma sannan ta ce "Kuma sun ci girkin ƴan indiar ko na maroccon suka ci" Ta tambaya cike da gatse. Aminu da bai fahimci magana Umma ta faɗa masa ba sai ya ɗora da faɗin "Wallai basu ci ba Umma, hasali ma ƙusa ta saka wai don naman ya yi saurin dahuwa amma bata cire ƙusar ba ta zuba musu a ciki, ranar na kunyata Umma, abin haushin har rigar nono ta je... Kafin ya kai aya Umma ta dakatar da shi don duk ta fahimci inda ya dosa ta ce "Babu ruwana da duk wani ƙorafinka Aminu, yanzu wannan maganar da ka zo danita a kan maganar kwana shi ma zan je in kashe case ɗin ne saboda Saddiqa, tun da haƙƙinta ne amma sauran sai dai ka faɗawa Babanka tun da ni baka ji shawarata ba lokacin da ka ƙara aure" Kai ya shiga sosawa hannu biyu ya ce "Umma ita fa Saddiqar da bakinta yau ta ce, sai dai in ƙara sati biyu a kan wanda na ɗaukawa amarya, wai ya zama wata guda, kuma wallahi amaryar nan bata son gyara kanta Umma wanka ma wai ba za ta yi da sabulu ba wai ɓarna ce gwara a cancanta" Baki Umma ta cije ta ce "Ka ce tuwona maina aka yi kai da Zulaiha, wato zani ce ta tarar sa muje mu, ita ƙazanta kai ƙazanta dama ai gwano ba ya jin warin jikinsa, ita kuma Saddiqa haushin abin da ka mata ne ya sanya ta faɗi hakan amma zan je in lallasheta" Kai ya kaɗa yana sosa kai da hannu ɗaya, ɗaya hannun yana sosa wuyansa, kallonsa Umma ta yi ta ce "Wai ni Aminu susar nan kuwa ta lafiya ce kake yi?" Yana susar ya ce "Umma kaina ne yake wani mugun ƙaiƙai wallahi, kuma sai in ke jin kamar wani abu yana yawo a cikin kan, har sai na sosa, kuma wallahi ko a cikin mutane haka nake fama Umma" Mamaki ta yi tana ta kallonsa ta ce "Inda miƙo mini kan naka in gani" Kan ya miƙa mata, tana jin warin gashij da gumi da ya cakuɗe, ga warin jikinsa na rashin wanka, haka ta shiga buɗe cikin gashin don ganin mene ne, cike da mamaki a maganarta ta ce "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Aminu ka san mene ne a cikin gashinka? Ka san mene ne cunkus a gashin?" Da mamaki ya ɗago yana son jin mene ne wannan wanda ya sanya Umma faɗin haka ya ce "Mene ne a ciki Umma?" Umma da ta ga abin da ta gani, har guda ɗaya ya gangaro wuyansa yana yawo a jikin farin kayansa.... *MUNA GAB DA GAMA BOOK 1* *GA MASU BUƘATAR BOOK 2 NA ƘAZAMIN MIJI ZA SU BIYA 500 KACAL DOMIN JIN LABARIN HAR ƘARSHE, AKWAI CAKWAKIYA, SARƘAƘIYA, TURKA-TURKA, ZAN IYA CEWA A GABA ZA MU NUTSA CIKIN LABARIN* *ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY* *SHAIDAR BIYA TA 09025576222* *INA SAYAR DAMAGUNGUNAN MATA MASU INGANCI NA KAMFANIN MEERAH B HERBS, AKWAI MAGANIN MATA, AKWAI NA RAGE TUNBI AKWAI NA RAGE ƘIBA, AKWAI NA GYARAN NONO, AKWAI NA ƘARA ƘIBA, AKWAI MAGANIN CIRE NANKARWA, DA SAURANSU* *AKWAI ZANNUWAN GADO, LABULAYE, FRAMES MAYAFAI MASU BEAD WORK, MAYAFAI NA SHAGO, KAYAN YARA, TAKALMA, LESUNA, ATAMFOFI* *DA* *SAURANSU* *MAI BUƘATA YA MINI MAGANA 09025576222* [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 16 Mamaki fal a fuskar Aminu ya ce "Ba dai kiyashi ne a shigar mini kai ba kwana da kwanakin nan da nake fama?" Ya faɗa yana kafe Umma da har lokacin ta ras bakin magana, rai a ɓace da haushin maganarsa jin wai yana batun kiyashi cikin masa gatse ta ce "Tururuwa ce (Ant) Ta yi gida a cikin gashin naka" Aminu da bai fahimci gatse Umma ta masa ba cikin mamaki yana mai sosai kan tare da nutsa yasunsa cikin gashin ya ce "Tururuwa Umma? Amma abar nan ta cuce ni wallahi, baki ga yadda nake ta fama ba amm dama Umma tururuwa tana shigarwa mutum kai, ko dai ba ta lafiya ba ce?" Haushi ma dakyar ya bari Umma ta ce "Aminu to ƙwarƙwata ce a cikin kanka cunkus, gata nan har wata ta zo wuyanka daga cikin kan kuma ta ganganro" Da sauri Aminu ya cire hannuwansa daga kan nasa yana mai miƙewa tsaye a kiɗime, don maganar da dake shi matuƙa ya ce "Kwarkwata Umma? Dama kwarkwata tana fitowa maza na shiga uku" Ya faɗa har lokacin yan tsaye hankalinsa a tashe. Cikin halin ko in kula Umma ta ce "To mene ne na kiɗimewar? Abin mamaki ne don an samu shazumamu a wajen da aka zubar da suga? Ai ba zai zama abin mamaki ba, tun da in dai an ga zara za a ga wata, in har an zubar da suga ko abu mai zaƙi dole shazumamu ya baibaye wajen, to haka ma tun da kwarkwara ƙazanta ce take kawota ka ga babu ruwanta da kan mace ko kan namiji, duk inda ta samu ƙazanta ta samu mafaka kenan" Umma tana mas wannan jawabin shi kuma ya tafi tunani kamar wanda ya tuno wani abu ya ce "Wallahi Umma wannan kwasa mini aka yi, tun da Zulaiha ta tare take soshe-soshe a kanta da jikinta, wallahi sai dai in ita ta kwasa mini"Sheƙeƙe Umma ta kalle shi ta taɓe baki ta ce "Abubya haɗu dai guda biyu, dama can kwarkwatar ta samu mafaka ne saboda tsabar taka ƙazantar" Komawa ya yi ya zauna ransa yana ƙuna, yana hango yadda za su kwashe da Zulaiha don sosai ya ƙara tunzura. Umma ta ɗora fa faɗin "Yanzu Aminu kana magidanci da mata har biyu, ɗaya tana da ciki amma a ce wai an samu kwarkwata a cikin gashinka? Shin ya kake so in yi da kai? Ka mallaki hankalinka ma sai ina maka faɗan ka gyara jikinka, ko so kake in ke binka gidan naka ina maka wanka ina saka ka gyara jikinka, don Allah dubi kanka kamar tukufar tsire, babu aski babu gyara wari jir ko yanzu baka ji wurin nan yadda yake tashin wari ba, ina amfanin baɗi babu rai, yanzu wa ya san tsawon lokacin da ka kai baka yi aski ba, kuma wa ya san lokacin da ka kwashe baka yi wanka ba... "Jiya da abokaina za su zo na yi wanka wallahi Umma, ni fa kawai gani nake wankan nan don a ji sanyi da iska ake yi, kuma tun da Allah ya kawo mu, lokacin sanyi ba sai mutum ya huta ba" Tsabar takaici ma sai ta rasa bakin magana, ganin bata ce komai ba ya ɗora da faɗin "Maganar aski kuwa Umma yanzu ai zamani ya sauya, ba a wani aske gashi, duk mai askewa ma kallon kidahumi ake masa wanda bai waye ba" Baki kawai ta saki tana kallonsa jin bata ce wani abu ba ya ɗora da faɗin cewa "Ko kuma a yi wa lan wani gyara ki ga kamar kalba, duk ya dunƙule waje-waje haka ake yi... A tsawace ta ce "Wayewa ko ƙazanta, ai gashin da ake bari wanke shi ake tas a shafa masa mai a taje, amma ba naka ba kai da baka yi wanka ba ma za ka wanke kai? Yanzu a haka ma gashinka ya samu kwarkwata bare aka maka gyaran curi-curi ai ina ga har ƙudan cizo sai an samu a cikin kanka" Yana kallonta yana susa hannu bibbiyu. Ta cigaba da faɗin "Ka gyara halinka, ƙazantarka kaɗai za ta sa mace ta rainaka, yanzu a ce miji ba zai yi wanka ya saka kaya a wanke ba, kalli haƙoranki har wani iri suka yi kamar mai cin goro, don Allah wace mace ce za ta ji daɗin ganinka a matsayin mijinta?" Shiru ya yi yana wani harhaɗa rai ya ce "Ni fa Umma babu wata mace da ta isa ta ja da ni, ko ta kawo mini raini a cikin gidana, in kuwa ta ce haka za ta yi wallahi Umma sai ta gwammace kiɗa da karatu... Katse shi Umma ta yi da faɗin "Dalla rufewa mutane baki, shi ya sa ai na ga yanzu ma matsalar gidan naka ce ka kawo, kuma shi ya sa na ga tsabar isarka ce gashi nan matarka a gidanka ta bika har ɗakin matarka ta maka ihun kwarto" Shiru ya yi yana tuna yadda ya so yau ya kwashe ganima a wajen Saddiqa da jikin nan nata tsaftatacce mai daɗin ƙamshi amma kuma Zulaiha ta katse masa hanzari har yanzu in ya tuna ji yake kamar ya je ya yi ta bugunta har sai ya ladabtar da ita, amma duk da haka yana nan a kan bakarsa na ba zai yarda da raini a gidansa ba, dole duk wacce ta so ta taka shi ya taka ta son ransa. Jin ya yi shiru Umma ta cigaba da faɗin, ban maka baki ba Aminu amma na tabbata ba za ka taɓa samun mai hankali da nutsuwa haɗe da haƙuri da juriya kamar Saddiqa ba, amma yanzu kai wannan kwarkwatar ma ina za ka je da ita, cunkus a kanka wace mace ce za ta yarda ka raɓe... Shigowar Fatima ce ta katse maganar da Umma take, gabaɗaya Fatima ta ji abin da Umma ta ce, hakan ya sanya ta zaro idanu haɗe da toshe baki ta ce "Umma kwarkwata kuma a kan Yayan? Na shiga uku wayyo Aunty Saddiqa kin gamu da jarab... Hararar da Umma ta bita da ita ce ta sanya ta haɗiye sauran maganar. Aminu kuwa jin furucin ta sai ya tashi tsaye a ƙufule yana nuna ta da yatsa ɗaya ɗayan kuma yana susa ya ce "To magulmaciya, wallahi kika sake wannan maganar ta fita sai na sauya miki kamanni, don wallahi dukan tsiya zan miki" Fatima da sauri ta koma bayan Umma ta raɓe tana cewa "Umma ni fa ba wani na ce zan faɗawa b... Katse ta Aminu ya yi da faɗin "Ki faɗa mana, uwar shgen shishshigi" Umma ganin yana kumfar baki ta ce "Fatima fita ki ba mutane wuri" Fita ta yi tana kallonsa ƙasa-ƙasa da sakin dariya a ɓoye, da sauri ya bita zai kai mata duka Umma ta ce "Dawo nan, wai kai yaushe za ka nutsu yanzu ƙarya aka maka kalli yadda kake sosa kai, ai abin kunyar ya yi yawa ni takaicin ma kamar in yi kuka nake ji na rasa ya zan yi da kai Aminu, tun kana ƙarami nake fama da kai, amma har yanzu ka kasa gyara rayuwarka da tsafta, komai ƙazanta bakya jon kunya, ko kaɗan" Jin tana faɗa ya koma ya zauna yana ɗan sunkuyar da kai amma fa har zuciyarsa shi bai ga abin da ya yi wanda za a ke masa wannan maganganun ba tun da gani yake a kan daidai yake. Suna nan tana ta masa faɗa, har ta koma masa nasiha don abin ya fi ƙarfin faɗa, da a ce Aminu yana jin faɗa da an wuce wannan wajen, shi kaɗai ne Allah ya bata ƙarami a cikin ƴaƴanta kuma marar jin magana, ga taurin kai tun yana ƙarami yake bata wahala, amma har yanzu ana fama da rashin tsaftarsa ta ɗauka idan ya yi aure abij zai yi sauƙi amma ga shi abu yana cakuɗewa har kai da kwarkwata. Ranta duk a ɓace ta shiga tunanin tun yana ƙarami, kowa zai yi brush amma shi ba zai yi ba, in har zai yi wata da watanni bai wanke baki ba to bab ruwansa sai dai an ce ya wanke, wani lokacin ma sai Umma ce za ta saka masa makilin a brush ɗin, amma in ya faki idanunta sai ya saka ruwa ya wanke makilin ɗin daga jikin brush ɗin a ajiye. Ta sha fama amma a banza, mai ya fi takaici a ce mutum da iyali amma kana masa faɗan wanka. Ɗagowa ta yi idanunta sun i ja ta ce "Yanzu Aminu kalli farcenka, zaƙo-zaƙo kai baka san cewa farce inuwar shaiɗan bace? A jikinka kai to mene ne kake gyarawa? A haka za ka ji daɗin gabatar da ibada anya kuwa?" Shigowar Baba da sallama shi ya katse maganar da suke yi. Waje ya samu ya zauna, yana kallonsu Aminu yana ta faman susa, Aminun ne ya gaishe da shi ya amsa, yana kallon yadda yake sosa kai, duk da Aminu yana ƙoƙarin danne ƙaiƙayin kar ya yi susar amma abin ya ci tura. Kafin Baba ya fara magana Umma ta ce "Gashi nan ya kawo ƙaran matansa" Nan ta kwashe komai ta faɗawa Baba, buɗar bakin Baba sai cewa ya yi "Aminu da yardar Saddiqa ka ƙarawa amaryarka kwanaki?" Ƙoƙarin saita kansa ya yi ya ce "Eh, eh, eh Baba" Shiru Baba ya yi Umma kuma ta shiga aikawa Aminu harara yana sadda kai ta ce "Ƙarya yake" Nan Umma ta shiga faɗawa Baba dalla-dalla. Baba ya rufe shi da faɗa ya ce ba ya son rashin adalci in rashin adalci zai yi to gwara ya sawwaqewa ɗaya, jin haka sai Aminu ya yi zuruf ya ce "Amma Baba banda Saddiqa ko? Sai dai Zulai... Katse shi Baba ya yi da cewa "Aminu gatse na maka fa, ni yanzu kana ganin zan iya saka ka saki matarka babu wani dalili? To ka buɗe kunneka ka jini, tun da ka aure su su duka mutuwa ce za ta rabaku, sannan ina so ka sani duk rashin adalcin da ka yi musu ko ka dannewa wata haƙƙinta Allah ba zai barka ba" Kai ya sunkuyar Baba ya masa tas ya ce da Yamma Umma ta je gidan ta sasanta matsalar. Umma ta faɗawa Baba maganar kwarkwatar Baba kaɗan bai kai masa duka ba saboda haushi. Nan ya ƙara masa gargaɗi a kan tsafta ya ce ya kama hanya ya tafi kasuwa, haka ya musu sallama ya fita Umma tana cewa idan ya je kasuwa ya saya maganin kwarkwatar ya kai wa ita Zulaihar sannan shi ma ya yi wanka kuma ya wanke kan nan tas ya saka magani, da to ya amsa ya fito. Yana cikin tafiya a tsakar gidan Fatima ta leƙo tana danne dariyarta ta ce "Yaya Aminu in ɗakko maka shantos idan ka je gida ka fesa a kanka" Da sauri ya juya ta tahonda gudu ta saka sakata a ɗakin, ya tsaya yana ta masifa yana cewa kar ta kuskura su haɗa hanya, ya rasa mai ya sa Fatima take masa haka ko do ta ga ita take binsa daga shi sai ita. Kasuwa ya wuce. Da yamma Umma ta shirya ta biya ta gidan ƙawarta suka wuce gidan Aminun. Sun shiga ɗakin Saddiqa inda ta gaishe su cikin mutunci, ta kawo musu ruwa mai sanyi sai dai waina ta yi kuma ta cinye babu hakan ya sa bata kawo musu abinci ba. Bayan sun gaisa Umma suka shiga tambayarta ba'asin abin da ya faru, kai Saddiqa ta sunkuyar tana jin wani ɗaci a zuciyarta ji take tamkar ta roƙi Umma cewa ta sanya Aminu ya sawwaqe mata, saboda ta lura Aminu ba mijin aure bane, indai za su cigaba da zama a haka tabbas za take cutuwa, duba da yadda yake ƙazamin nan, dama ita yanzu daɗin da take ji bai wuce cewa komawa ɗakin amaryarsa ba ƙaramin daɗi ta ji ba saboda haɗa makwanci da Aminu akwai damuwa. Umma ce ta ce "Saddiqa da amincewar ki Aminu ya ɗauki kwanaki ya ba Zulaiha? Bayan nata kwanakin bakwai sun ƙare matsayinta na amarya kuma budurwa" Shiru Saddiqa ta yi don ta tasa abin cewa saboda na farko dai kwanan nan umarni ne aka bata ba a shawarce ta ba, ta wani ɓangaren kuma za ta iya cewa taimakonta aka yj don ita da, da hali ma da ta ƙauracewa Aminu har abada!. To mai ma za ta ce? Mutumin da ya yi amarya ko ya haɗa su ya gabatar da ita a wajen amaryar ba matsayinta na uwar gidansa ba, sai a kicin ta ga amaryar, sannan ya yi watsi da duk wasu buƙatunta hatta abin cikinta ya nuna bai shirya haifarsa yanzu, to ita wace irin magana za ta yi a kan Aminu? Ta ce mai, ita yanzu kishin Aminun ma bata ji sai wanda ba a rasa ba ga matarsa marar kamun kai duba da yadda jiya ta zo ɗakinta ta yi wa Aminu ihun kwarto a cikin gidansa a ɗakinta, kawai saboda tana ganin satar kwana ya mata. Ƙawar Umma ce ta kalle Saddiqa da tausayawa ta ce "Saddiqa ana tambayarki amma kin kasa bada amsa?" Ta faɗa tana kallon yadda fuskar Saddiqar ta bayyana asirin zuciyarta, amma duk da haka sai suka tsaya sauraron jin ta bakinta, cikin muryarta mai sanyi cike da ladabi ta ce "Umma da amincewa ta ya ƙara mata kwanan, shi ya sa jiyan ma na ce na ƙara musu sati biyu" Ta faɗa idanunta suna kawo ruwa amma ta danne bata basu damar zubowa ba, tana tuna irin so da ƙaunar da zuciyarta ta yi wa Aminu amma yanzu ya dishashe komai, da a ce bata zo gidansa ta samu halayen da bata yi zaton samunsa da su, da babu yadda za a yi ta bari a nisanta da shi, duk yadda za ta yi sai ta ƙwato mijinta amma ita yanzu neman kai ma take da shi, so take a barta ta ji da cikin jikinta da take ɗawainiya da shi. Kallonta Umma ta yi ta ce "Saddiqa kowa ya kalli fuskarki ya san ƙarya kike, a yadda hasashena ya nuna Aminu ya ba amaryar kwanakin naki ne ba da amincewarki ba kuma wannan tozarci ne a ce namiji ya karɓi kwananaka ya ba kishiyarka" Ƙawar Ummar ce ta ce "Alamomi masu yawa sun yi nuni da hakan, amma Aminu bai kyauta ba" Umma ta ce "Zai zo ya same ni sai an rama miki kwanakin ki da aka ƙwace, ma'ana idan kika karɓi girki gobe sai kin yi kwanakin da ta yi a cikin naki sannan miji zai koma bakinta" Da sauri Saddiqa ta ɗago kai tana kallon Umma ta ce "Umma wallahi na bar mata ba sai na rama ba, idan suka yi wata gudan sai mu fara rabon kwan... Umma ce ta y saurin katse ta da cewa "Saddiqa me kike ƙoƙarin yi ne? Mijinki kamar kina neman kai da shi? Ya za a yi mace ta barwa kishiyarta har sati uku kamar wani shirin wasan kwaikwayo ko littafin hausa? Hakan fa tozarci ne da jan raini a wajen kishiya, za ta ga baki isa a gidan mijinki ba" Wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata ba tare da ya shirya zubowarsu ba ta ce "Umma ni alfarmar da nake nema a wajenki, don Allah Umma ki faɗawa Aminu yake yin tsafta" Ta faɗa tana mai jin nauyin furucin sai dai babu yadda za ta yi hakan ya zama dole ne domin yanzu mafita take nema a kan ƙazantar Aminu, ta tsani warin jikinsa ta duniya tana baƙin cikin shaƙar warin bakinsa, mai za a yi da ƘAZAMIN MIJI babu wanda zai gane halin da take ciki sai matar da ita ma mijinta ya kasance ƘAZAMIN MIJI. Shiru Umma ta yi don ta rasa bakin magana, sai ta ji tana jin nauyin Saddiqa, tana tuno yadda ta ga kwarkwata a cikin kansa da yadda jikinsa yake tashin wari, ita ce mahaifiyar Aminu ita ce za ta bayar da shaidar cewa Aminu ƘAZAMI ne na ajin ƙarshe. Cikin lallashi ta kalli Saddiqa ta ce "Saddiqa na san kina haƙuri sai dai in ce ki ƙara haƙuri a kan haƙuri, sannan ko yau da Aminu ya je na kwashe tsowon lokaci ina masa faɗa da nasiha a kan ya gyara halayensa, amma yanzu ma zan ƙara nannaga masa, na san akwai damuwa amma ki yi haƙuri watarana sai labari, amma ina roƙon ki arziƙi ki yi haƙuri mijinki ya dawo ɗakin ki yau" Ba za ta iya cewa Umma a'a hakan ya sa ta ce "To Umma babu komai na amince" Ta faɗa tana sadda kai. Ƙawar Umma ta ce "Allah miki albarka, ya sa hanyar shigarki aljanna ne auran, Allah ƙara miki haƙuri, domin haƙuri shi ne matakin cimma nasara a rayuwa" Da amin Umma da Saddiqa suka amsa kafin suka mata sallama suka fita, ɓangaren Sumayya suka shiga, tana zaune da ɗaurin ƙirji tana shan take, Ruma ma tana shan raken ruwan raken duk sai zuba yake ya gama ɓata mata gaban rigar, duk ta ɓata ɗakin dama daga gani babu shara ga kayayyaki nan zube a ƙasa da kan kujera. Shigowar su Umma ne ta ɗakko hijabi a kan kujerar wani da ya gama shan uban datti, kana iya ganin datti a fuskar hijabin. Zaunawa ta yi ta shiga gaishe da su, ɗakin sai tashin warin jikin Sumayyar yake. Bayan sun ɗan taɓa hira, Umma ta ba Ruma biskit da alewar da ta kawo mata, haka suka wuce ɓangaren Amina ma suka gaisa suka ba su Albani nasu biskit da alewar, suna fitowa suka nufi ɗakin Zulaiha. Zaune take a tsakiyar ɗaki, jikinta da rigar buba ta yadi kanta babu ɗankwaki, duk ta cukurkuɗa shi duk ya tashi tsaye da alama ma susa take yi. Bayan sun zauna ta gaishe da su, Umma tana lura da ita yadda bayan ta saka hule a kan mata amma ta cigaba da susa, sai sosawa take a kai- a kai, Umma kallon tsaf ta mata a zuciyarta ta ce 'Tsakanin ke da Aminun a samu wanda ya kwasawa wani kwarkwatar don ita ma alamomi sun nuna hakan. Umma ce ta yi gyara murya ta ce "Zulaiha Aminu ya faɗa minj saɓanin da aka samu a gidan nan, shi ne na ce bari in zo in bincika in ji" Tun kafin Umma ta rufe bakinta Zulaiha ta ce "Umma shi ne bashi da gaskiya, bayan ya bani sati biyu amma na kama shi yau ya munafurce mi Umma turmi da taɓarya na tarar da shi da matarsa" Ta faɗa babu jin nauyin Umma ko wani ladabi Umma ta ce "Amma ai kwanan Saddiqa ne, ita mun je min mata magana kuma komai ya wuce, don haka yanzu ki bari yau Aminu ya koma can idan ta yi kwana biyu sai ya dawo bakin ki" Kallonsu take tarrr da wankakkun idanunta ta ce "Haba dai Umma abin har da zaɓunta, ai maganar fari ita sarki yake karɓa, kuma ko jiya ita matar tasa da bakinta ta ce ta ƙara masa sati biyu, don haka yanzu kuwa sai na yi ƙarasa kwana ukun sannan na ƙarasa sati biyun, ai baki shi yake yanka wuya" Baki sakkak suke kallonta saj da ƙawar Umma ta ce "Haba ke kuwa ana yin sulhu kuma kya ke wannan maganar, ko ba komai wannan ai surukarki ce" Shiru ta yi tana haɗe gira alamar maganar bata shige ta ba, tashi ta yi ta je kicin ta ɗakko jallof ɗin wake da shinkafa a plate ta rufe da wani plate ɗin sai cokula biyu da pure watar biyu, ta kawo. Bayaj fitar ta sun jinjina rashin ta ido irin na Zulaiha, don kar ta zargi wani abu suka buɗe abincin, tana gefe tana danna waya, su duka suka yi cokali ɗaya, guntse da abincin suke a bakinsu, don waken bai dahu ba, ita ma shinkafar kamar ta jiƙu ga wani gashiri, kallon juna suka yi dakyar suka haɗiye, Umma tana ƙara ɗakko cokali na biyu sai ga gashi dogo a ciki. Da sauri Umma ta ajiye tana ɗaukan plate ɗin ta rufe tare da ɗaukan pure water ta shiga sha, ita ma ƙawar Ummar ruwan ta sha, Zulaiha ta ɗago tana kallon plate ɗin da suka rufe ta ce "A ƙaro muku ne Umma?" Da sauri ƙawar Umma ta ce "Ah Alhamdulillahi, ai da yake kafin mu fito mun ci abinci" Ba ta taɓe a ɓoye ta tashi ta kinkimi plate ɗin ta ajiye a kicin sai gata ta dawo, daidai nan Aminu ya shigo da sallama. Jir da warin gumi ga jikin nan butu-butu da fulawa. Gaishe da su Umma ya yi, nan Umma suka ƙara musu nasiha da kuma tabbatar da cewa Saddiqa ce za ta karɓi girki, Aminu sai washe baki yake yana tuno yau zai yi kwanan wuri mai tsafta ga kuma tsaftatacciya Saddiqa a gefe, tabbas ya yi kewar ɗumin jikinta da fatarta mai laushi da santsi tamkat kifi tarwaɗa. Sallama suka musu suka tafi, suna fita suka shiga suka yi wa Saddiqa sallama suka tafi. A can ɗakin Zulaiha kuwa su Umma suna fita ta tashi tsaye ta buga cinya ta ce "Babu wanda ya isa in ba da kwanakin nan sai na cike sati biyun nan da ka ambata, ai baki shi yake karya wuya, wato saboda an fi son Saddiqar ni za a nuna mini wariyar launin fata" Shi ma a ƙufule ya miƙe tana jin haushin cikas ɗin da take kawo masa na hana shi zuwa kwana ɗakin Saddiqa ya ce "Yanzu ke uwata ta taso tun daga gidanmu, ta zo ta yi sulhun amma ki ce ba zai iyu ba?" Kallon sheƙeƙe ta masa tana riƙe da ƙugu ta ce "To in ma ita ce ta zo ɗin, tun da ba adalci ta mini ba ai dole na ɗauki hukunci a hannuna" Yana wani zaro ido ya ce "Wallahi baki isa ba, wai ke a ce ko sati biyu baki cika a gidan nan ba, kina matsayin amarya amma mu zauna muna sa'insa ke irin ɓoye halin nan na farkon aure ma ba za ki yi ba" Dariya ta sheƙe irin ta rainin hankali ta ce "Ai yanzu shiru -shiru ƙauyanc ne, kuma ɓoye halayya munafurci ne, na lura kamar ka gaji da ni, ne shi ya sa kake kwaɗayin komawa wajen matarka kuna ko sama da ƙasa za ta haɗe baka isa ba" Cike da haushi ya kalleta ya ce. "Idan na je sai ki je ki janyo ni ki maido da ni" Yana kaiwa nan a maganarsa, ya juya ya shige banɗaki, jikinsa ya wanke, ya fito ya je kicin ya zazzago klin a hannunsa ya ɗauki mataji(Kumb) Ya shiga bayin ya zuba klin ɗin a kan ya zuba ruwa yana tajewa yana wankewa, kwarkwata tana ta zubowa, sai da ya gamsu cewar ya wanku kan tas, amma maimakon ya saka sabulu ya yi wanka sai ya saka baƙin ruwa ya shashsheƙa, ya fito yana aikawa Zulaiha harara tana sosa kanta ya ce "Zulai" A ƙufule ta ɗago ta kalle shi don ta tsani Zulan nan da ya tsiri faɗa mata, ya daina kiranta ƴar aljanna yanzu ta ce "Zulaiha ne sunana, in ba za ka kirani ƴar aljanna ba ka daina mayar mini suna kamar wata tsohuwa" Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai ya ce "Ƴar aljanna ai mace mai jin maganar miji ce" Ƙaramin tsaki ta ja ta ce "Indai a kan maganar rabon kwanane sai daj ka kaini ko ina in ba za ka kaini aljannar ba" Yana binciko kayansa na wanki ya samu wata riga jallabiya yana cikin karkaɗewa ya ce "Yanzu ke ba abin kunya bane, a ce kin kwasawa miji kwarkwata" Cikin halin ko in kula ta kalle shi ta ce "Haba ni na ji ƙaiƙayin kaina ya dawo, duk tunanina ba kwarkwatar bace" Baki sake ya juyo yana kallonta da jallabiyar da ya saka a wuyansa bai ƙarasa sakawa ba ya ce "Wai dama kin san kina da ita?" Ta ce "Eh mana, ai da za a yi bikin nan aka saka mini relaxer a wajen gyaran kai aka ce za ta fita, ashe dai likimo ta yi" Kamar zai yi kuka ya ce "To wallahi kin kwasa mini" Dariya ta yi mai sauti ta ce "Yo ladan amarci ne ka kwasa" Harara ya aika mata, ganin ko shi namiji ya ji ciwon kwarkwatar ita amma hankalinta a kwance ko don ta saba ya ce "Daga yau idan na dawo ɗakin nan, da kwana sai dai muke kai da ƙafa, don ba za ki ki kashe mini kasuwa ba, in je ina awon fulawa ina susa waye zai siya ina susar kwarkwata" Miƙe ƙafa ta yi bata ƙara masa magana ba ya ƙari mitarsa ya fita. Da daddare tana kallonsa yana haɗa kayansa wanda ciki babu wani mai wanki, haka ya kwasa niƙi-niƙi ya fita ta taɓe baki tana yin ƙwafa. Wajen ƙarfe takwas da rabi ta ga shiru bai dawo ba, haushi da kishi ya ishe ta don ta san ɗakin matarsa ya tafi, kishi duk ya turnuƙeta tana tuna irin rigar baccin da ta gani a jikin Saddiqa da ta je ɗakin, da irin ƙamshin da ɗakin yake, wannan dalilin ya sa wani kishi ya tokare mata maƙoshi, ta rinƙa juyi tana jin takaici. Har wajen ƙarfe goma saura amma shiru bai dawo ba bizigir ta sakko daga kan gadon ta fito, ɗakin Saddiqa ta nufa ranta yana ƙuna, tana zuwa da ƙafa ta hangaza ƙofar, yana zaune a bakin gado Saddiqar tana tsaye, magana suke kamar dai jayayya amma dai bata ji abin da suke faɗa ba, idanu ta kafe Saddiqa da shi ganin tana sanye da wani riga da wando na bacci masu laushi, daga wajen ƙirjin rigar gabaɗaya net ne kana iya hangar har bra ɗin Saddiqar wacce dare bai hana ka gane fara ce bra ɗin tas ba. Kallo ne ya koma kan Zulaiha, ran Aminu in ya yi dubu ya ɓaci, sanye yake da gajeran wando, da singileti don shi tun da ya ga ya ɗauki kayansa a gabanta bata ce komai, kuma ya tafi kusan awa biyu amma bata zo ba sai ya cire rai da zuwanta, tun da ya zo yana ta fama da Saddiqa , sai danya shawo kanta ta amince da shi suna shirin keɓewanya kwashi ganima a wajen aiwatar da sunna, shi ne ta kawo masa cikas. Saddiqa ita ɓacin ranta yadda Zulaihar take halayya kamar dabbobi, ka bankowa mutum ɗaki babu sallama babu neman izini kenan haka za take mata, abu babu kamun kai, da a wani halin ma suke haka za ta shigo hakan ya sa Aminu cewa "Wai lafiyarki kuwa Zulaiha" Tana wani taɓe baki tana ƙare musu kallo ta ce "Lafiyar ce ta kawo haka, na faɗa maka cewa baki shi yake yanka wuya, da ka san kana son zuwa wajen matar taka amma ka ce ka bata dubu biyu ta bar maka sati gudan, yanzu kuma ka dawo sati biyu bai cika ba, in haka ne ai sai ta kawo dubu ɗayar a bar mata kwana ukun" Zulaiha ta sako maganar dubu biyun ne saboda ta ci wa Saddiqa fuska. Cike da jin haushi Aminu ya ce "Ni na ce miki na bata dubu biyu ta siyar mini da kwananta na sati guda?" Ya faɗa jin ta ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa. Kafin Zulaiha ta ce wani abu Saddiqa ta taka zuwa wajen Zulaiha ta miƙa hannu ta dafa kafarɗata ta ce "Zaliha kike ko Zulaiha, nan ba ɗakin ki bane, kuma ba ba filin ƙwallo bane, da za ki shiga a lokacin da kika zo, ina miki kashedi daga yau da rana irin ta yau karki ƙara taka mini ƙafafunki a ɗakina, ki tsaya a waje har shi wanda ya ajiye ki ɗin ya fito, sannan batun dubu biyu da kike magana ni na fi ƙarfin in siyarwa wata ƴa mace kwanana a kuɗaɗe ƙalilin marar daraja, ni sai dai ɗa namiji ya bibiye ni kin ga kuwa ai ba zan sayar da kwana ba, yanzu ga ki ga shi nanki tambaye shi tun zuwansa yake fama da ni sai na yarje masa" Saddiqa tana kaiwa nan a maganarta ta ɗan tunkuɗa kafaɗar Zulaiha ta juya ta koma kan kujera ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Haushi takaici ɓacin rai, su ne suka turnuƙe Zulaiha, jin cin fuskar da aka mata, babu abin da ya fi tsaya mata a rai irin yadda wai Aminun yake bin kan Saddiqa wato ita ce bata kai ya bibiyeta ba ita ce take binsa ɗakin matarsa, idanunta ne suka tara ƙwalla, Aminu ya tako ya zo gabanta ya ce "Ki je ɗakinki kin ga ta ce kar ki ƙara zuwa mata ɗaki" Juyawa ta yi ƙafafunta tamkar ba za su ɗauke ta ba, bin bayanta ya yi zai rufo ƙofar amma sai dai me? Suna zuwa ƙofar ɗaki Aminu bai ankara ba, sai ji ya yi ta kama hantsar gajeran wandonsa, ta shiga jansa ƙiiiii za ta mayar da shi ɗakinta ta ƙarfi da yaji, don ta rantse da Allah ba za ta bar shi ya kwana a ɗakin Saddiqa ba.... MUNA DAB DA GAMA BOOK 1 BOOK 2 500 KACAL GA MAI SON JIN BADAƘALAR DA ZA TA CIGABA DA FARUWA A WANNAN LITTAFIN ZA A BIYA TA ASUSIN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 09025576222 NA GODE MUTANENA😍🤝 [5/5, 6:25 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/J171xDTqqkq4e6hp9PBZU7 *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 17 *AMINU* Idanu ya shiga zarewa, jin ɗanyan aikin da Zulaihar take ƙoƙarin yi masa, cikin inda-inda don gabaɗaya hankalinsa ya tashi, cike da faɗuwar gaba ya ce "Zulaiha, Zulaiha, ki mini rai kar ki nakasta mini rayuwa" Ya faɗa a kiɗime jin ta damƙo jikinsa da daidai inda ta haɗa da hantsar wandon. Ko sauraronsa bata yi ba saboda yanzu da hannu biyu ta damƙi wajen, shi kuma yana tsoron ya shiga ƙwatar kansa da ƙarfi a je a samu matsala don in akwai inda Aminu yake tattalawa bai wuce wannan wajen ba. Kamar wani raƙumi da akala haka ya zama, gani yake Zulaiha tun da ta damƙi makasarsa to sai yadda hali ya yi, musamman da ya tuna cewa ya ce mata Saddiqa ta ce kar ta sake zuwa mata ɗaki. A daidai bakin ƙofar ya kama jikin ƙofar da hannu biyu yana ɗan waiwayen bayansa, a kan Saddiqa ya sauke idanunsa wacce take zaune hankali kwance ta ba bango ajiyarsu daga shi har Zulaihar, cikin ɗan ɗaga murya ya ce "Saddiqa ki taso ki kawo mini ɗauki, in kuma abu ya gagare ki ki tafi ɓangaren su Yaya Shafi'u su kawo agaji kar ta lahantani a banza, domin gabaɗaya ni na san riƙon da ta yi wa wajen nan mai daraja yadda kika san ta damƙo wuyan tinkiya" Wani ɓoyayyan tsaki Saddiqa ta saki don yanzu daga Aminu har Zulaiha haushi suke bata, kwata-kwata lamarinsu babu jan aji tamkar basu taɓa zaunawa aji da sunan ɗaukan karatu ba. Zulaiha kuwa jin yana cewa a kira ƴan uwansa, sai ta ƙara ƙaimi wajen jansa, saboda so take sai ya jigata kafin ta ƙyaleshi in ya so daga yau zai daina raina mata hankali. Aminu kuwa jiran amsar Saddiqa yake jin bata ce komai ba ya fara magana da cewa "Shikenan dama an ce na shiga ban ɗauka ba, bata fidda ɓarawo, shikenan ni kuma sai yadda hali ya yi ɓarawo a hannun mata" Zulaiha ɗan sunkuyawa ta yi kamar mai jan abin da ya fi ƙarfinta, Aminu jin za ta lahanta shi ya shiga roƙonta, ko ta kansa bata bi ba ta fisge shi sai kuwa ya daina ja baya son ya ga za ta masa lahani a zuciyarsa ya ce 'Ɗakin Saddiqar nan dai ko ɗakin gwal ne, gwara in haƙura da kwanan yau, in ba haka ba sai dai a zo ana mini jaje, ko dai ta mayar da ni mata maza ko ta cisge mini mafitsarae ma ta sa in shiga uku, sai dai in ga ana aure ni kuwa da nake da niyyar sai na rufe ƙofa, wato mata huɗu' Ya faɗana ransa yana daina togewa daga jan da take masa, a haka suka fita bar ƙofar ɗakin Saddiqa, suna tafiya Zulaiha tana jaye da hantsar wandon, yana ji yana gani sai waiwayen ɗakin Saddiqa yake bayan ya san ya gama shawo kanta ta amince da shi amma Zulaiha ta kawo cikas. Suna dab da ƙarasawa ɗakin Zulaiha wata dibara ta faɗowa Aminu, tunani ya yi a kan ya damƙi gashin Zulaiha tun da ya san tsawon lokacin nan bata yi kitso ba kuma ba mai take shafawa ta taje ta gyara ba, ya san kuwa dole ta ji ciwo, Zulaiha ta juya tana jansa hankali kwance a ranta tana jin daɗin ta raba shi da ɗakin Saddiqa tana ƙudurtar yanzu ta fara yin hakan, duk da gargaɗin da Saddiqa ta mata ya ɗan razanata, amma dai a nata ganin ta samu lagon Aminu da za ta ƙwace shi ya koma hannunta, Saddiqa ta zama ƴar kallo. Tana murmushin jin daɗin a ranta sai ta ji kamar daga sama an damƙi gashinta, wani ƙara ta saki don sosai ya damƙa yadda za ta ji a jikinta, zafin da ya ziyarce ta sai ta manta da riƙon da ta yi wa Aminu don tuni ta sake shi, bai saka mata ba sai da ya bari ta sakankance ya saki. Hannunta duka biyu ta kai ta dafe kan nata, kafin ƙiftawar ido Aminu ya fita da gudu, zai koma ɗakin Saddiqa don yau kawai hango shi yake ya kasance da ita. Sai lokacin Zulaihanta lura da abin da ya yi ta kuwa take masa baya, Aminu yana dab da faɗawa ɗakin Saddiqa a nufinsa yana shigewa zai saka sakata, sai dai mai kusan ƙarasowarsa ya yi daidai da tashin Saddiqa wacce ta burmawa ƙofar ɗakinta sakatar sama da ƙasa. Don haka Aminu gwaram ya bugu da jikin ƙofa, wanda hakan ya yi daidai da zuwan ƴar aljanna tana zuwa a maimakon ta damƙi hantsar sai ta kamo tsantsar wandon wato ƙugun ƙiiiii ta shiga jansa da baya, sai rafka salati yake jin tana jansa da ƙarfi kuma sai taka duwatsun tsakar gidan yake, tana zuwa ta tura shi cikin ɗakin ta garƙama sakata, daga shi har ita suka shiga mayar da numfashi kowa yana aikawa ɗan uwansa harara kamar idanunsa za su faɗo. Banza ta masa ta zauna bakin gado tana ɗan taɓa kanta, don yanzu gabaɗaya kanta ma ciwo yake sanadin gashin da Aminu ya ja mata. Shi kuwa a tsakar ɗakin ya zauna yana buga tagumi hannu bibbiyu, Zulaiha kallo ɗaya ta masa ta taɓe baki ta ce "Ai ko zinariya ce wannan matar taka, dole ka haƙura sai kwanaki bakina ya ƙare sannan" Tamkar ya saki kuka haka ya ji, yana ciro hannu ɗaya daga tagumin da ya buga ya kai hantsar wandon nasa ya taɓo jikinsa, yana son tabbatar da cewa Zulaiha bata yi masa illa ba, yana ɗauke hannun daga wajen ya kai ƙugun wandon wanda Zulaiha ya janyo shi baya ta saka hantsar kasancewar wandon ya ci uban tsufan shi ya sa jan da ta yi masa ya taɓe don yanzu har zamewa yake yi ma ba ya zama a jikinsa. Idanu ya runtse yana jin daman bai auro Zulaiha ba don ta sanya shi a rijiyar matsala mai gaba dubu. Jin tafiya a cikin gashin kansa gabansa ya faɗi, don duk a tunaninsa yadda ya wanke kansa da klin ya taje to kwarkwatar ta fita amma wani ƙaiƙayi da ya ziyarce shi ya hau susa da hannu biyu. Kallon Zulaiha ya yi wacce take susa tun ƙarfi kamar zai yi kuka ya ce "Wallahi Zulai kin cuceni," Bata daina susar na ta masa kallon sheƙeƙe ta ce "Da na maka me?" A ƙufule yana susa ya ce "Da kika kwasa mini kwarkwata mana" Baki ta taɓe ta sosa tsakiyar kan nata, tare da dunƙule hannun ta ranƙwashi kan nata inda ta ji ƙaiƙan ya fi yawa ta ce "Muka kwasawa juna dai, ni fa ba na jin ma cikin gashin nan naka za a rasa kyankyasai, don na san tsabar datti da wari kyankyaso zai ɗauka masai ne ya shige maka kai... Tsaye ya miƙe yana muzurai ya ce "Wallahi Zulai kin ga makwancina da yawa, amma tun da kin rainanj zan fara banbance miki aya da tsakuwa don bana ɗaukan raini, Saddiqa sai yadda na yi da ita sai abin da na ce mata, kuma bata taɓa faɗa miki magana a kan ƙazanta don ta tozartani ko ci mini mutunci ba, amma ke kin zo da sabon salo kiran sallah da usur, ke irin kawaicin nan ma na farkon zuwa da amare suke yi baki yi ba... Dariyar da ta kwashe da ita ne ya dakatar da Aminu daga banbamin faɗan da ya ɗauka, sai da dariyar ta tsagaita mata ta ce "Saddiqa ka ce, an faɗa maka kowace mace ce mai haƙuri ko kawar da kai, da can baka san abin da take maka ba sai da ka rufe ido ka rambaɗo mata kishiya, sai yanzu ne ka san halaccin da ta maka, ku dama maza ai bakwa gane halaccin mace a wajenku, to ni ba zan ɗauki duk wani soki burutsu ba, kuma da kkae batun bata maka cin fuska a kan ƙazanta wannan ita ta ga dama, kuma wallahi Aminu aurenka kaɗai ma sai dai in ce Allah ya sa kaffara ne" Ta faɗa tana tafa cinya. Bai ji zai ita furta komai ba shi yanzu lamarin Zulaiha ya fara wuce masa makaɗi da rawa, yanzu tunaninsa ma ɗaya yadda ta je ta janyo shi, ba don Allah ya sa cikin dare bane gida ba su kaɗai ba ai da ta gama kunce masa zani a kasuwa. Yana ji tana ta nasifar ya fara gudunta tun ba a cinye amarci ba, don munafurci yana ƙulafucin uwar gidansa. Zuwa ya yi zai canja wandon tun da ta taɓa ƙugun wandon nasa, amma sai ya tarar ashe duka ya kwashe kayan ya mayar ɗakin Saddiqa. Can gefe ya raɓe ya kwanta, zuwa can ita ma ta shiga zabga doguwar hamma, hakan ya sa ta kwanta a kusa da shi, da ya ƙyalla ido ya bucan kanta wanda babu hula bare ɗankwali a kusa da nasa kan, sai da ya bari bacci ya sure ta ya lallaɓa ya maida kansa wajen ƙafarta wato suka yi kai da ƙafa. Ashe ba nisan bacci ba ta yi, sai ji tashinta ya yi hakan ya sanyabya fara sakin munsharin ƙarya, bata bj ta kan munsharinsa ba sai ji ya yi ƙiii ta ja ƙafafunsa duka biyu, ta juya shi kamar wata waina a tanda, ta mayar masa da kansa inda ya ɗauke wato suka koma ga kanta ga nashi, kowa hannu a ka yana susa a haka bacci ya sure su. A haka sai da Aminu ya ƙarasa ragowar kwanaki ukun nan na sari biyun Zulaiha, don addabarsa ta yi da masifa, zuwa wannan kwanakin kwanukan Zulaiha duk suna baje a kicin kaca-kaca don har ranar ko kwanunkan da baƙin Aminu suka ci abinci bata wanke ba. Abin da ya fara ci wa Saddiqa tuwo a ƙwarya kenan, ita gashi bata ƙaunar ƙazanta sai kuma ta haɗu da miji ƙazami kishiyar ma ƙazama. Har bata son zuwa kicin saboda yadda ƙudaje suke safa da marwa a kan kwanukan Zulaiha, farantina food flaks cokula tukwane babu wanda babu ta lodosu abinta, idan za ta yi amfani da kwano, saboda baƙar ganda da ƙazanta ba za ta ɗauka cikin mararsa wankin ta wanke, sai dai ta ƙara buɗe wani sabo fil ta yi amfani da shi. Ga rashin iya girkin da bata yi ba sai ta yi abincin wajen sau nawa, wani lokacin sai ta dafa shinkafa kusan sau uku kafin ta samu wacce za ta ci wata ta ƙone wata ta yi ɗanya-ɗanya wata kuma gata nan dai to ta hakan yake ɓata kwanuka masu yawa, ko mai za ta soya sai ya ƙone duk kayan garar da aka kawo musu ta ci ƙarfinsu. Ranar da ta cika sarin biyu ne, Saddiqa ta shiga kicin za ta dafa ruwan zafi, abin mamaki sai ta ga Zulaiha ta ɗauki tukunyarta ta dafa indomie, da alama girkih da dare ta yi, cike da mamaki ta ga har fork da plate ɗin duk nata ne, sannan kuma da ta gama amfani sai ta kwasa cikin jibgin kayan wanke-wanken ta. Amma haka Saddiqa ta ware su ta wanke ba tare da ta ce komai ba. Da yamma kuma ta shiga kicin ɗin za ta ɗakko plate da wuƙa za ta yanka mangwaro tana shiga ta samu Zulaiha ta yi ɗanwake a tukunyarta, ta kwashe a robarta sannan tana zubawa a plate ɗinta sannan fork da spoon ɗin ma na kai duk nata ne. Mamaki al'ajabi suka saka kanta ya ɗaure, ta ma rasa ta ina za ta fara magana, tana tunanin cewa wani abu amma sai ta ga ita Zulaiha ko a jikinta hasalima ta nufi wajen robobin Saddiqa wanda take zuba yaji da su maggi ta buɗe robar jan yaji ta saka cokali ta ɗakko za ta zuba a ɗanwaken da Saddiqar take yi kallon ɗanye, saboda kana kallonsa za ka gane bai dahu ba. Har Zulaiha ta zuba yajin ta ɗakko plate ɗin ta zo za ta gota Saddiqa, cikin dakakkiyar murya Saddiqa ta ce "Wai ni malama mai yake faruwa a wannan kicin ɗin ne? " Yatsina fuska Zulaiha ta yi cikin rashin sanin manufar Saddiqa ta ce "Ban gane ba mai kike tambaya" Zulaiha ta faɗa tana ƙarewa Saddiqa kallo ga wani sihirtaccen ƙamshi da yake tashi daga jikin Saddiqar wanda ƙamshin ya haɗe wajen, saɓanin jikin Zulaiha da yake bada wani nau'in warin dauɗa da ban. Saddiqa ta ce "Shin bakya bambance tsakanin fari da baƙi ne?" Cike da wani kishin Saddiqa da ya tokare Zulaiha cikin zafin zuciya ta ce "Wai mai kike nufi ne, ya za ki tare ni kina mini wani bayani marar kai da ƙafafu?Idan za ki tambayi abu ki yi da hausar da zan gane" Ɗan ƙanƙance ido Saddiqa ta yi ta ce "Ina nufin ke bakya gane kayanku da kayan da ba naki ba? Ina nufin kwanuka, ya za kike ɗaukar mini kwanuka kina ɓatawa, sannan abin bai tsaya a nan ba har kike buɗe mini robar yaji kina ɗauk... Tun kafin Saddiqa ta kai ƙarshen maganar Zulaiha ta katse ta da faɗin "Sai mai to? Idan ba a so kowa ya taɓa kayan kowa a kicin ake warewa, ke kuma naki mijin saboda tsiya ya haɗamu a kicin ɗaya kamar wasu sakarkaru, kwanukan da na ɗauka kuma wanda na gani a wanke ne, shi kuma yaji na ji daka da ɗanɗanonsa ya mini kin ga babu buƙatar sai matar gida ta san mini tun da ba almajiranci na zo gidan ba, gidan mijina ne, sannan kwanukan nan da suka taru na wanke-wanke za ki iya haɗawa da naki ki wanke, don ni wanke-wanke da shara basa ma cikin tsarina" Saddiqa ta ce "Sannu zaƙaƙura wannan sai dai ki faɗawa wanda ya ajiye ki, ko shi yake wankewa ko ya ɗauka miki mai yi, don ni na fi ƙarfin bautawa kishiyar da za ta yi gadara da ni, batun yaji kuma wanda kike taƙamar da shi ba shi ya saya ba, ba shi ya daka ba don haka karki ƙara gigin taɓawa don sai na saka kin gwammace kiɗa da karatu" Tsaki Zulaiha ta ja, ta ce "Ke banza ce sakar... Tun kafin Zulaiha ta ƙarasa sai ji ta yi ƙiii Saddiqa ta warce farantin hannunta wajen kwanukan nan mararsa wanki ta nufa ta ɗauki wani faranti a wajen ta ɗaga ɗanwaken za ta juye, da sauri Zulaiha ta ce "Kar ki kuskura don wallahi ba zan yar... Kafin ta ƙarasa Saddiqs ta juye a kan farantin marar wanki ta nuna Zulaiha da yatsa cikin kalami na wanda ya san abin da yake faɗi ta ce "Idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, domin babban goro sai magogin ƙarfe, iya gani iya ƙalewa ki sani duk nisan jifa ƙasa zai faɗo, ni na fi ƙarfin ki kirani sakarya, ina so ki sani wanda ya rigaka da kwana ya rigaka da tashi, domin wanda zai je sama ya taka dutse haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya" Saddiqa tana kaiwa nan ta wuce ta ɗauki plate da ƙaramar wuƙar cokula ta juya za ta tafi, har ta kusa fita ta koma ta haɗa kayanta da Zulaiha ta ɓata a waje guda. Ran Zulaiha ƙuna yake tana ji kamar ta shaƙe Saddiqa ta mata dukan tsiya. Tana juyawa ta hangi ɗanwakenta a faranti marar wanki, bayan ta shirya cin ɗanwaken, Saddiqa tana zuwa za ta wuce sai ta ji Zulaiha ta ja rigarta ƙiii ta dawo da ita baya saitinta. Rai ta haɗe tana aikawa Zulaiha wani kallo ta ce "Daga yau kar ki ƙara kai hannunki jikina" Zulaiha tana jin wani tuƙuƙin ɓacin rai ta ce "Mai ya sa kika zuba mini ɗanwakena a kwano marar wanki?" Cikin halin ko in kula Saddiqa ta ce "Saboda shi wancan marar wankin shi ne mallakiinki kuma halaliyarki, kuma ai hausawa sun ce guntun gatarinka ya fi sari ka bani, sannan idan har tsafta da daɗi ka ga abu mai kyau ya baka sha'awa, to ya zamana dole ka koyi kintsa naka da tattala naka, ba wai ka mayar da kayan wani naka ba" Saddiqa tana kaiwa nan ta juya ta fito daga kicin ɗin, hakan ya yi daidai da shigowar Aminu gidan, wanda yau yake cike da murnar komawa ɗakin Saddiqa da kwana. Wani ƙaramin kukan kissa Zulaiha ta rushe da shi, wacce ko sannu da zuwa bata masa ba ta shiga faɗin "Ɗan aljannata, ka ga matarka tana mini wani irin cin kashi" Aminu da yanzu kawai dama cike yake da ita, jin ta kirashi da ɗan aljanna sai ya ce "Ni fa bana son tashin hankali, ya tun da sanyin safiya na fita neman abin rufawa kaina asiri amma daga zuwana zan tarar da wani makararran faɗanki?" Bai jira cewarta ba ya juya zai tafi ɗakin Saddiqa rai cike da haushi Zulaiha ta bi bayansa da harara. Saddiqa ma baya ta take masa tana jin wani abu yana yunƙuro mata don zuwansa wajen ya sauya iskar da take kaɗawa. Zulaiha ɗakinta ta nufa ranta yana ƙuna, ta ɗauka a matsayinta na amarya Aminu zai ƙuntatawa uwar gidansa saboda ita amma ta zo ta ga saɓanin yadda ƙawaye suke zugata sai dai bata gane cewa ko dai ita ce bata kai matsayin da za a ƙuntatawa wata dalilinta ba, don yanzu ta lura Aminu kamar an sauya mata shi. A ɗakin Saddiqa kuwa Aminu ransa fari ƙal ya shiga, jin wani ni'imtaccen ƙamshi ya mamaye ɗakin, wani yadi ne ruwan toka a jikinsa saboda yadin bai cika nuna datti ba sai ya maimaita shi ya fi a ƙirga don shi dama bai damu da haske ko dauɗar abu ba. Yadda ya sha rana a kasuwa ya sanya bayansa jiƙewa hakan ya sa rigar har mannewa take yi. Yana ƙarewa ɗakin kallo ya ƙarasa bakin gadon ya zauna. Saddiqa da tun da ya doshi ɗakinta annaurin zuciyarta ya sauya ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Tamkar ya ari baki haka ya shiga amsa mata cike da ɗokin ganinta yana faɗin "Saddiqa amaryar kuma uwar gida" Bata amsa masa ba ta ƙarasa ta zauna a ƙasa tana janyo wankakken mangwaron da za ta yanka, ranta yana ƙuna don ganin Aminu ya zauna a kan gadonta ta san zanin gadonta fari ya tashi daga aiki, don ko shigowarta ɗakin kaɗai ta san akwai wanda datti ya yi wa kanta a ɗakib nata. Bai damu da yanayin fuskarta ba ya ce "Saddiqa ina mukullin banɗakin ki" Wani daɗi ta ji a ranta duk da tana taraddadin shigarsa banɗakin nata, amma dai duk tunaninta wanka zai ce zai yi bata san cewa har yau Aminu yana nan yana taka matsayinsa na Aminu kuma yana amsa sunansa ya ƘAZAMI ba, tana cikin tunanin hakan ya ce "Ina son zan tsugunna" Dimmm ta yi jin wai kashi zai yi, ta fara tuno yadda banɗakin yake a wanke tass, yadda take amfani da kayanta ita kaɗai. Kallonsa ta yi tana tuna yadda ba ya ploshing wani lokacin da yadda yake ɓata shaddat kanta in ya tsubunna kamar wani ƙaramin yaro, ita dai ba don ba don ba da ta ce ta yafe Aminu a matsayin miji, sai dai ƙalubalen da take ganin za ta fuskanta akan hakan cikin jikinta yana taka muhimmiyar rawa, duk da hausawa suna faɗin da babbar budurwa a gida gwara ƙaramar bazawara sai dai yanzu ta fara taraddadin komawa gida zawarci da ƙaramin ciki, har ta haife ta raine shi, sannan ta yaye in ma ta samu mai aurenta shin ya makomar rayuwar abin da za ta haifa zai kasance. Mukullin ta miƙa masa, yana ta ƙoƙarin son ganin fuskarta amma ta ƙi bashi dama, fita ya yi yana rawar ƙafa ya nufi bayin. Zulaiha tana hangoshi ya shige bayin bayan ya buɗe, tana jin wani kishinsa yana taso mata. Ya daɗe a bayin kafin ya fito bayan ya yi wankin jiki haɗe da yin alwala ya rufe banɗakin ya fito. Ko kallon inda Zulaiha take bai yi ba, yana ganin lokacin da ta tashi ta nufi ɓangaren Sumayya. Saddiqa tana zaune tana shan mangwaron ya dawo ɗakin, a ranta tana ta addu'ar Allah sa wanka yake da ta ga ya daɗe, sai dai yana shigowa ta gane jikinsa bai san da zaman wani abu ruwan ba, a ranta tana ƙiyasta mai hali ba ya sauya halinsa. Kabbara ya yi tana gani ya yi azahar da la'asar, tana hango a ce wannan uban ƴaƴanka ne shin mene ne wanda yaran za su koya a bayyane daga mahaifinsu, ƙazanta ko rashin kiyaye sallah a kan lokacinta, ko uwa uba rashin kula da addinin kansa, babu wani abin koyi daga Aminu, sai dai abin Allah wadai. Ko da dare haka ya kwaɓe kaya ya hau mata gado tiƙiƙi, yana son haɗa jikinsa mai dauɗa da nata tsaftattacen jikin, wannan ya sanya ra ji duk ta tsani kanta, amma babu yadda za ta yi ta hana shi kanta saboda gujewa tsinuwar mala'iku, haka ya kusanceta damuwarta ma soshe-soshe musamman cikin kansa wanda duk tunaninta dauɗa ce bata san cewa kwarkwata bace. A wannan daren mutane biyu ne suke cike da ɓacin rai kasancewar wannan daren da Aminu da Saddiqa suka raya, Zulaiha wacce kishi ya hana bacci tana ta saƙe-saƙen abubuwan da su Saddiqar suke gabatarwa, sai kuma Yaya Shafi:u wanda tun lokacin da ya yi arba da rigar baccin jikin Saddiqa ranar da Zulaiha ta yi wa Aminu ihun kwarto ya ji ya kamu da son kasancewa da ita, wani irin shauƙi da shaiɗan yake ƙiyasta masa a kan matar ƙanin nasa, hakan ya sa yake jin zafi da zugi a ransa don ya san yau Aminu ya koma ɓangaren Zulaiha. Yana rayawa a ransa cewa an ce idan ka ga wata mace ta birge ka ka koma ga matarka ta gida, to sai dai a nasa ɓangaren abin ba haka yake ba, domin kuwa a halin da yake ciki yanzu da yake jin tunanin wata ya hana shi sukuni, watan ma matar auren, matar auren ma matar ƙaninsa, amma a sannan ne idan ya juya ga tasa matar da take kwance shame-shame a kusa da shi sai ya ji wani ɗoyin rashin tsafta da warin hammata yana tashi daga jikinta. Bakinta da ta buɗe wayam tana bacci wani warin baki ne yake fita, hakan ya sa daga ya doso gare ta sai ya juya can ƙarshe gadon da sauri yana mayar da numfashi tare da yin da na sanin a kan kasancewar Sumayya matsayin mata gare shi. Tun daga wannan rana ya zamana rabon kwana ya koma kwana bibbiyu, wanda Zulaiha babu abin da ya yi saura a lamuran ƙazantarta sai abin da ya yi gaba, musamman da ya kasance ɓollowar ciki a jikinta, wanda ya dagulawa Aminu lissafi don shi dama cikin Saddiqa ma ba so yake ba bare kuma yanzu abu ya haɗe masa biyu. Ƙazantar Saddiqa ta yi tsamari da tunbatsar da komai ta cunkushe saboda laulayin ciki, hakan ya sanya Saddiqa ta sallama mata kicin, ta biya kuɗi aka mata kicin na langa-langa ta kwashe kayanta ta mayar can, saboda ba za ta iya cigaba da cuɗanya w kicin ɗaya da Zulaiha ba. A ɓangare ɗaya nata cikin yana girma, inda har ya kai matakin haihuwa, lokacin na Zulaiha kuma watansa uku. Allah ya sauki Saddiqa lafiya inda ta haifa ƴarta mace, Babansu Aminu ne ya ce a saka mata Fatima sunan autarsu inda suke kiranta da Nihal. Tun da Saddiqa ta haihu aka kawi mata mai zaman wanka sai gabaɗaya Aminu ya ƙwaura ɓangaren Zulaiha, duk da ba haka ya so ba, amma hakan ya zama dole a gare shi, ga kuma tasa ƙazantar da babu abin da ya yi saura sai dai cigaba. Bayan Saddiqa ta yi arba'in sai ta nuna masa dole sai ya canja halayya don ita ba za ta juri zaman wannan da shi a haka ba, ga kuma ƴarta kar ta taso a haka tana koyi da shi, lamarin da ya kawo musayar yawu da tashin hankali don sai Aminu ya nuna ita bata isa ta sauya masa ra,ayinsa ba ki ta sanya shi dole, dama tun da ta haihu yake jin haushinsa saboda yana ganin ta ƙara ɗora masa nauyi ne, ga kuma Zulaiha ita ma da nata guzurin cikin. Hakan ya sa Aminu ya buɗe wuta, yake taka duk wanda ya so kuma yana nuna babu wanda zai saka shi ko ya hana shi daga Zulaiha har Saddiqa. Ita Saddiqa yanzu sau ta yi sati bata ga Aminu ya saka kaya mai wanki ba, duk ya yi baƙi haƙoransa sun yi yellow tamkar mai cin goro, ƙafafunsa faso babu kyan gani, hammatarsa kuwa tamkar za a yi kitso saboda tsawon gashi, hatta mararsa biyuyu da gashi, sannan tun lokacin da Saddiqa ta gane yana da kwarkwata, a washe garin ranar da ta karɓi girki da safe, tana gyaran gado ta ga kwarkwatar a kan filo guda biyu a kan zanin gadon kasancewar zanin gadon fari ne, ta shiga tashin hankalin da har sai da ta zubar da hawayen baƙincikin auren ƘAZAMI irin Aminu. Ta nemi magani har sai da ta ga kwarkwatar ta mutu, amma da yake a kan Zulaiha ya kwasa yanzu ma ya sake kwaso wata kwarkwatar ita kuwa Saddiqa duk ranar da yake ɗakinta sai ta yi shimfiɗa a ƙasa ta kwanta, tun da ta ga yanzu da ta haihu ma kansa rawa yake, kamar dai wanda yake kula ƴanmata. Hakan ya sa yake mata wulaƙanci, bai san cewa ita ta fi kowa baƙincikin zama da shi ba, ga yayansa da yake mata kallo mai ma'anoni da dama hakan ya sa ta ji duk gidan ya gundure ta. Watan ta biyu da haihuwa lokacin cikin Zulaiha yana da wata biyar, a sannan ne Aminu yake ganiyar neman macen aure wacce za ta maye masa gurbi, saboda yana ganin Saddiqa ta haihu yana mata ganin budurcinta ya kau, duk da wata budurwar ma ba za ta faɗa mata matsi ba, kasancewarta mace mai kula da kanta amma da yake hankalinsa ya yi gaba sai yake hangen wasu, tun da ita dama Zulaiha ma ba ya saka ta a layi don a ganinsa ita ta gaza ta fannoni da dama, tun ba a je ga haihuwa ba. Aminu yanzu idanunsa da suka shiga yawon neman matar aure basu yi masauki a ko ina ba sai a gidan yarbawan unguwarsu, gidan gidan haya ne inda wani bahaushe ya gina yake bada haya shekara da shekaru. Maman iyabo sun dawo arewa ne daga kudu inda mijinta ya kama musu haya, suke zaune, asalinsu ba musulmi bane amma zaman su a cikin musulmi da yake Allah ya saka suna da rabo sai suka musulunta. Maman iyabo da baban iyabo ƴaƴansu biyu iyabo wacce ta rasu tun tana ƙarama sai kuma Aisha wacce bayan sun musulunta suka haife ta. Aminu ya san gidansu kuma ya san Aisha, tun tana budurwa take gasa masara mamanta kuma ƙosai take yi. Aisha ta auri wani bahaushe inda auren bai je ko ina ba ya mutu, duk da shi Aminu bai san mene ne silar mutuwar auren ba. Aisha irin manyan matan nan ne masu ƙiba da cikar haiba, amma baƙa ce tana da manyan gaɓɓai tamkar namiji haka yanayin jikinta yake. Aminu tun da ya ganta ya ji duk duniya bashi da wani buri da ya wuce auren wannan matar inda ya shiga mata hidima, yana ƴar tsafta da kwaskwarima don ya samawa kansa matsugunni a zuciyarta saboda aurenta yake son yi da gaske. Bai sanarwa da su Saddiqa yana neman aure ba, duk da abubuwa da dama sun nunawa Saddiqa haka, don in har mijin mace yana neman aure duk takatsantsan ɗinsa na kar ta sani tana iya ganewa sai dai ba lallai ta fahimci hakan ba Bai faɗawa Umma ba don ya san ita tamkar adawa take da aurensa, kullum maganarta ɗaya ita ce ya tsaya ya samawa iyalansa nutsuwa da shi kansa. Baba jin inda Aminu ya ɗakko dala babu gammo sai ma ya ji ya fi Aminun farinciki tun da mahaifin yarinya yana da kamala kuma kowa ya yaba da tarbiyar yarinyar kasancewar ana zaune waje ɗaya shekara da shekaru. Baba ya amince inda Umma faɗa tamkar ta ari baki, sai dai babu yadda za ta yi tun da ita ma ƙarƙashin Baba take umarni yake bata, shi Baba yana kafa hujjar cewar indai yaro aure zai yi ba zai hana shi ba da a ce yana zina gwara auren. Ita kuma tana hangen na gidan ma da ya suka ƙare, bare kuma yanzu ya je zai auri wacce yarensu ba hausa ba, amma dai ta san kowa ya shiga rayuwar wani akwai darasin da yake ɗauke da shi, tana fatan Aisha ta shiga gidan Aminu da darasi mai ƙarfi wanda za ta zama silar warkewar ciwukannda zukata suke fama da shi a dalilinsa. Gida ya kama haya, ɓangare uku ne a gidan kowanne ciki da falo da bayi, kicin ne guda ɗaya, sai kuma ɓangaren Aminu wanda ɗaki ɗaya ne babu bayi a ciki. Kasancewarta bazawara aka yanke aure wata guda, yau da ya rage saura sari uku biki shi ne Aminu ya kirawo Zulaiha da Saddiqa domin faɗa musu auren da zai yi, saboda Umma ya roƙe ta faɗa musu ta ce babu ruwanta ya je ya yi abin da ya ga ya dace. Zaune suke a falon Saddiqa don dakyar Zulaiha ta zo shi ma sai da Aminu ya mata muzurai, sanye take da zanin falle da riga tshrt wacce faɗin ya mata yawa amma saboda yadda take jin daɗin saka kayan a haka take sakawa. Ita Zulaiha ta ɗauka sulhu ne zai yi, a kan rashin mutuncin da yake zai nemi yafiyarsu, shi ya sa take ta wani shan ƙamshi, saɓanin Saddiqa da dama tana lura da takunsa, ta san dai yana waya kuma tana ganin ana kiransa, amma bata san har yana da burin yin aure a kwana kusa ba wanda ya rage sati uku! Gyaran murya ya yi hannunsa ɗaya a kansa yana susa ya fara magana kamar haka... *MUN ZO GANGARA A BOOK 1 SAURA SHAFI ƊAYA MU KAMMALA WASU TUNI SUN BIYA KUƊINSU BOOK 2 SUNA ZAUNE A PAID GROUP DA ZARAR MUN DATSE ZA SU CIGABA DA SAMUN LITTAFIN HAR ƘARSHE. IDAN KEMA KINA SO ZA KI IYA BIYAN 500 KACAL DON JIN TIRKA-TIKRA DA CAKWAKIYAR DA ZA MU NUTSA A WANNAN LITTAFI NA ƘAZAMIN MIJI,* *BAN CE NA IYA BA, BAN CE NA ƘWARE BA, NI DAI TAKEN ALƘALAMINA KAƊAI NA SANI WATO ALƘALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME* *ZA A BIYA TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222* [5/5, 6:39 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/J171xDTqqkq4e6hp9PBZU7 *KAZAMIN MIJI* NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Bonono rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK 1 PAGE 18 *END OF BOOK 1* *YAYA SULE* Saurin saita kansa ya yi daga duniyar rashin gaskiyar da ya bayyana daga gare shi, ɓaro-ɓaro yana sakin wani murmushi ya ce "Kai typin error ma bai yj ba, wai fa Abokiyata zan rubuta, shi ne na rubuta abokina" Ya faɗa yana kafe Salaha da idanu don ganin yadda za ta ɗauki maganar. Shiru ta ɗan yi tana nazartar maganar kafin ta ce "Kai dama abokiya kake son saka mini, dama wani saurayin ƙawata ne suna hira sai ta karɓi wayarsa ta kira shi da wayarta, a take sunan GARZALI ya bayyana ɓaro-ɓaro, to da ta bani labari shi ne ni ma na ce zan gwada shi ne na ga ni kuma ABOKINA aka yi saving" Ƙoƙarin saita kansa ya yi ya ce "Haba Baby ni ya za a yi ma in yi saving numberki da wani suna da ban wataƙila shi ma wancan saurayin ƙawar taki ko yana da aure ne, ba ya so matarsa ta gani... Tun kan ya kai ƙarshen maganar ta yi saurin katse shi da faɗin "Kenan maza masu aure ne suke yin haka?" Da sauri ya ce "Ba haka bane yawanci dai an fi samun hakan" Baki ta taɓe ta ce "Ni fa shi ya sa kwata-kwata namiji mai mata ba ya birgeni" Wani yawu ya haɗiye sannan ya ce "Ai dama ku mata bakwa son kishiya" Kallonsa ta yi ta ce "Yo mai za a yi da auren mijin wata?" Yana ƙoƙarin danne abin da ya ji ya ce "Kenan za ki iya bari a auri naki mijin? Na wata ne ba za ki bari ki aura ba... Ranta a ɓace ta ce "Ka ga Sule ni fa ba na son irin wannan wasan, idan na shiga gidanka babu wacce za ta shigo" Galala yake kallonta a zuciyarsa ya ce 'Akwai cakwakiya, tabbas iska tana yawo da mai kayan kara, wannan ai shi ake nufi da rana zafi inuwa ƙuna' A fili kuma ya ce "Ai babu ma wacce ta isa ta shigo" Daga haka suka cigaba da hirar soyayyarsu. Soyayya ta cigaba da wakana babu kama hannun yaro, a inda Amina duk inda ta ji wata ƙawa ko da a ce ƙawar-ƙawarta ce mijin zai ƙara aure sai ta je ta ga ƙwaƙwaf, shi kuma Yaya Sule sai ya iya takunsa yanzu duk lokacin da zai shigo gidan sai ya sanya wayarsa airplane mode domin ya gwammace kar kiran kowa ya shigo wayarsa a kan rigimar Amina. Ai kuwa hakan da ya yi ba ƙaramin shakku ya cire mata ba, saboda yanzu ganin babu wani mai suna namiji da yake kiransa sai abin ya daina ɗarsa mata zarginsa, a inda shi kuma yake cin karensa babu babbaka. A ɓangaren Salaha kuwa ko da ta masa ƙorafin ta nemi wayarsa bata samu ba, sai ya ce yanzu bai san mai ya sa idan ba waje ya fito ba, sai network ɗin wayarsa yake ɗaukewa, da hakan ya kuɓuta daga nata ƙotafi. A ranar da ya samu Baba da maganar cewa, yana son ya ƙara aure, Baban farinciki ya yi, tun da shi al'adar Baba babu ruwansa da hana ɗansa ƙarin aure matsawar ɗan yana da halin riƙe matan nasa, domin a ganinsa hana ɗa ƙara aure tamar tauye masa haƙƙi ne, kuma bayan hakan halal ne kuma dai a nasa ganin hana hanzari a kan ƙara auren zai iya jefa yaron a halaka, sai dai abu ɗaya ne zai sanar da kai shi ne ka yi adalci. Umma da ta ji hakan ba ƙaramin ranta ne ya ɓaci ba, a nata ganin ita indai namiji ya samu mace ta gari suna zaune lafiya ai ba a bar shi ya ƙara aure ba, tun da wani auren ƙarinsa fitina zai zama tun da duk namijin da ya haɗa mace sama da ɗaya to tabbas dole ya fuskanci ƙalubale, idan kuwa ya haɗu da mata mararsa imani da tsoron Allah, a nan kowacce saboda kishi za ta baje hajarta gaban malamai da bokaye shikenan fa, sai ka ga ya koma wani sha ka tafi, kowacce tana ƙoƙarin ta maido da hankalinsa kanta ta zama ita ce tauraruwa kuma ta sha gaban abokiyar zamanta a wajen miji, daga haka sai ya koma kamar wani zararre saboda an rikita masa ƙwaƙwalwa. Baba ne ya dakatar da Umma a kan maganar, kamar yadda ya taka mata birki lokacin da Aminu ya zo da nasa batun ƙara auren, har yana nuna mata cewa Aminu ma shi ne ƙarami kuma bai daɗe da yin auren fari ba ya ƙara aure, sannan yanzu zai yi ta uku, bare kuma Sule da dake shi ne babba kuma har yana da yara biyu, don shi a tsarin Baba ko rana ɗaya ka ce za ka auri mace biyu ba zai hanaka ba. Addu'a Umma ta yi da fatan zaman lafiya, wannan ya sanya Baba ya ce "Haka ya dace iyaye su dawwama wajen yi wa ƴaƴansu fatan alkairi, a duk abin da suka sanya gaba su basu ƙwarin gwiwa, matsawar bai saɓawa Allah ba, duk abin da Allah ya halatta bai kamata a tauyewa wani ba" Ya faɗa yana kallonta, nuna masa ta yi ta gamsu da hakan, saboda ta lura Baba gani yake kamar don tana mace ne kishi ne yake sakawa take nuna rashin amincewarta idan yaran za su ƙara aure. A nan Baba ya ya ce za su je nema masa auren, bayan ya gabatar musu da iyayen da unguwar su yarinya, sai Baban ya ce da zarar ya gama bincika wace ce yarinyar da nagartarta da ta iyayenta za su nema masa aurenta. Cikin wasa ma Baban ya kalli Yaya Sule ya ce "Saura Malam Shafi'u kuma, tun da na san matsawar ya ƙyalla ido ya ganku da matan shi ma zai ce zai ƙara" Gabaɗaya suka yi dariya har Umma daga nan ya musu sallama ya tafi, bayan ya bayyanawa Umma a kan cewa yana son komai ya kasance a ɓoye, da ta tuhume shi ma a kan dalilin da zai ɓoyewa matarsa zai ƙara auren, sai ya fito mata da manufa da halayyar Aminar a kan kishiya, jin hujjojinsa ya sanya iyayen suka amince tun da Baba ya ce ita fitina kwantar da ita ake yi, musamman ma da Yaya Sulen ya sanar da su ba a gida ɗaya zai haɗa su ba, haya zai kamawa Salahar kafin Allah ya hore masa in yana da halin gina babban gida sai su tare. Sun gansu kuma sun amince. Tun da Baba ya yi bincike ya gano gidan su Salaha ƴan mutunci ne da dattako ga tarbiya, sai ya yi farinciki a inda aka je neman auren Yaya Sulen aka sanya daidai da ranar na Aminu, kasancewar ɓangaren amarya sun gama shirye -shirye. Kwanaki suka shuɗe, suka rikiɗe suka zama satika, inda satika suka zama watanni, har ya rage saura sati biyu a ɗaura auren Yaya Sule, a inda har lokacin Amina bata da labari, don ko Sumayya bata faɗa mata ba, tun da Yaya Shafi'u ya gargaɗe ta a kan cewa ba a so ta sani, ita ma kuwa sai ta ja nata bakin ta yi shiru, idan Amina ta je wani bikin dannar ƙirji ta dawo tana ɗaga kai tana murna da nuna jin daɗin na yadda ta ga uwar gidan da ta je dannar ƙirjin cikin damuwa, sai ta zo tana bada labari tana dariya, Sumayya a zuciyarta ta ce 'Ke ma taki tana tafe, wannan shi ake kira rashin sani ya fi dare duhu' Gidan da Yaya Sule ya kama ciki da falo ne, sai ɗaki ɗaya da bayi a ciki akwai wani a waje sai kuma kicin, irin gidan da ake yi wa laƙabi da gidan mace ɗaya. Salaha har yau Sule bai sanar da ita yana da mata ba, daga ya yi yunƙurin faɗa mata, sai ya fahimci za ta iya fasa aurensa, su kuma su Baba sun ɗauka ya sanar da ita shinya sa ma ko da suka je neman auren basu faɗa musu ba. Tun da a nasu ganin duk inda aka yi soyyayya har ta kai ga an amincewa juna za a yi aure haƙiƙa an sanar da komai har hakan ya sanya yarda da amincewa na ƙulla auratayyar. Ana saura sati ɗaya biki, lokacin har su Saddiqa sun tashi daga gidan, Yaya Sule ya shigo da wasu manyan shaddodi da ya ɗinka, set biyar ne, dama a satin Amina ta faɗa masa za ta je wani bikin dannar ƙirjin wata ƙawar, ƙawarta, tana faɗa masa ma bikin na yi ne don su Yusuf ma da Albani gjdansu za ta kai su, wannan dalilin ne ya sanya ya haɗu da wasu shaddodi guda biyu ɗinkakku da less ɗinkakke, duk shi ya bada aka ɗinka, Yusuf kala biyu Albani ma kala biyu. Lokacin da ya shigo bai san mai ya sa ba, da ta amsa masa sallamar sai ya ji gabansa ya faɗi kawai sai yake ganin kamar za ta hango jirginsa, amma duba da yadda ya gama tsara maganar da zai faɗa mata sai ya ji ɗan dama-dama. "To fa yau kuma Abban Yusuf ledoji riƙi-riƙe haka mai muka samu" Ta ce tana linke kayan yaran da ta kwaso daga shanya. Ƴar dariyar ƙarfin hali ya yi gabansa don faɗuwa yake amma haka ya dake ya ce "Ke dai bari cikin wasu kuɗaɗe da na samu, na mana ɗinkuna, kin san satin nan muna da bikin abokinmu, ga kuma ɗaurin auren Aminu, kuma ke ma na ji kin ce za ku yi bikin dannar ƙirji" Ya faɗa lokacin da ya samu waje ya zauna don tun kan ya zauna ne suke wannan maganar. Kayan ta ajiye ta fasa linkin ta ce "Inyeee lallai shagali wan duna, gaskiya ka faranta mini, don dama ina son yin shigar kece raini yadda zan nunawa duk masu kishiya ni matar mijin mace ɗaya ce" Ta ce tana matsowa wajenta. Yadda ya ga tana rawar kai sai da dariya ta kusa kufce masa don har ya hango dirama da bidirin da za ta yi in ta ji shi ma auren zai yi, ya san tabbas har ƙaramar hauka sai ta yi. Cewa ya yi "Ai dama na san za ki yi farinciki, ni ma yadda za mu yi ta shige sa fice shi ya sa na yi ɗinkunan" Tana ɗaya leshin ta ce "Kai amma leshin nan ya tafi da ni wallahi, amma mai ɗinkina ka ba ya ɗinka mini ko?" Amsa mata ya yi da eh kafin ya ta ce "Kai amma naka ma sun yi kyau, na yaran ma haka, bari na zaɓa maka wanda za ka saka ranar dinner da kuma ɗaurin aure" Ta faɗa tana duba kyan kayan har ta hango yadda za su masa kyau ta ce "Dan Allah Abban Yusuf kar ka kalli kowacce mace a wajen bikin nan, kuma kar ka shiga hoton abokai in dai da mata a ciki, ban amince ba, sannan kake sunkuyar da kai in ka ga mata za su wuce" Cikin zolaya ya ce "Ke kuma da za ki je naki bikin ƙawayen waye ya saka miki dokar kallon maza?" Ƴar dariya ta yi ta ce "Ai ni duk mata ne" Dariyar shi ma ya yi ya ce "Mu ma duk mazan ne" Su duka suka yi dariya, haka ta zauna ta ware kayan nasa tana ta yabawa da kyawun su, ta ɗauki nata da na yaran shi ma ya ɗauki nasa, har wata ajiyar zuciya ya sauke ganin bata zargi komai ba. Ranar alhamis haka ya saci jiki ya je wajen ƙauyawan da su Salaha suka shirya, har aka je ka yi hotuna aka tashi ya dawo bata fahimci komai ba, tun da ya ce mata suna hidimar bikin abokin ne ita kuma da yake dama shirme ne da kishin kawai a ranta bata damu da mijin ba, hakan ya sa bata zargi wani abu ba. Ranar juma'a da ya kasance ranar kamu, tun wajen ƙarfe goma ta shirya ta ɗauki yaran a cewarta, wai gidansu za ta kai yaran, sai a lokacin ma take ce masa ta je za a yi wa wata ƙawarsu kishiya, gidan su Saddiqa kuma sai ranar ɗaurin aure za ta je musu, tana son ta je ta jajanta mata in ta fita, kuma daga gidansu za su wuce gidan wacce za a yi wa kishiyar saboda aikin abin da za a raba gobe ɗaurin aure. Shi ma da yake dama haka yake so ta kama gabanta sai ya amince har da bata kuɗi masu kauri, duk da wani ɓangaren yana jin tausayinta a ransa amma in ya yi duba da cewa, laifinta ne zai saka shi ƙara aure, yadda ya rasa wasu abubuwan da ya faɗa halaka gwara ya yi aurensa, sannan yana ganin ma hakan izna ne a gare ta, da bata da aiki sai bibiyar gidan wanda za a yi wa kishiya ko da basu da wata makusanciyar alaka, kawai don ta je ta kashe ƙwarƙwatar idonta. Da yamma lokacin da ya yi wanka ya shirya, abokansa suna ta kiransa a kan cewa suna jiransa domin tafiya wajen kamu, ga amarya ma tana ta doka masa kira a kan cewa su zo a tafi wajen kamun don tuni mutane sun kun ƙagu a tafi saboda wajen kamu ya gama kankama, jere kuwa dama tun ranar laraba suka je suka yi. Fitowar da ya yi yana cikin rufe ƙofa ya ji, an saki wata uwar guɗa, gabansa ne ya yanke ya faɗi yana tunanin waye kuma zai saka shi a matsala, duk da ya san Amina bata nan amma dai guɗa ta hautsina masa ciki yana waiwayowa ya ga Sumayya ce sanye cikin wani koran leshi mai jajayen fulawoyi an sha uban jambaki, tana riƙe da hannun Ruma. Sai danya ɗan waiwaya ya ga babu kowa. "Irin wannan guɗa haka kamar za ki cire hanci" Ya faɗa cikin wasa. Dariya ta yi ta ce "Ango ka sha ƙamshi, mijin mace biyu ka fi mai mace ɗaya, mai mace ɗaya ya fi gwauro" Ta ce tana dariya. Shi ma dariyar ya yi yana sauri ya juya ya fita tana cewa a gaishe mata da amarya. Sumayya ta shiga tunano ranar da za su je gidan Ummar Aminu su gaishe ta, da ta biyawa Zulaiha don kafin su bar gidan ƙawance ya ɗinke a tsakaninsu, lura da ta yi ita Saddiqa bata iya gulma ba kuma dai ta ga kamar Saddiqar bata son take shigar mata ɗaki, kuma ita ma Saddiqar ba zuwa ɓangaren Sumayyar take yi ba sai da dalili, abin da ta fahimta kamar dai Saddiqa tana gudunta ne saboda tsantsanin ƙazantarta hakan ya sa yanzu sai suka haɗe kai da Zulaiha amma ba wai ta daina kulata ne bane kwata-kwata. ta tuno lokacin da ta shiga ɗakin Zulaiha ta nufa ta shiga da sallama, aka amsa mata, tana shiga ɗakin Zulaiha ta tashi da sauri bakin nan fal cike da yawun da ya taru a bakin, dama a hakan ta ɗaga bakin dama gudun kar yawun ya zubo ta amsa sallamar. Banɗakin ta shiga ta tofar ta dawo tana ɗan kiran sunan Ruma ta koma ta zauna, Sumayya ta kalle ta ta ce "To ke baki shirya ba mu wuce gidan Ummar" Ɗan yatsina fuska ta yi ta ce "Yanzu zan saka kayana" Kallon ƙafarta Sumayya ta yi ta ga furu-furu kamar ta yi tsere a sahara ta ce "Yau ɗaya dai ki mulke ƙafar nan da mai kar mu je ake mana kallon ɗaya saura kwata" Kallonta ta yi ta ce "Shiga zan yi ai in wanke ƙafafu da fuska da hannuna, sai na shafa mai ai dama ni ina ni ina watsawa jikina ruwa, taɓ ni na yi sati ma ban yi wani abu wanka ba, in kinga ruwa ya taɓa jikina to alwalar sallah ce, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, dama can bana ƙaunar wanka kuma yanzu sai abin ya haɗu da cikin nan da na samu sai in ji babu abin da yake saka ni sai ƙyamar wanka" Dariya Sumayya ta yi ta ce "Dama fa wahala da rai ne wanka, ni yau kwanana tara ban yi ba wallahi Shafi'u har ya gaji da mita ya zuba mini ido yo dama wankan dai na tsarki ne aka fiya yi, yanzu kuwa ya tsiri wani hali in zai kusance ni sai ya ce sai na yi wanka na wanke baki in na ƙi sai ya haƙura har falo ya ƙaura saboda ba ya son haɗa makwanci da ni, ni kuwa na ce ta fi nono fari gaba ta kaini gobarar titi, bare yanzu da nake fashin sallah ma kin ga ba zai wani zo neman buƙtarsa ba" Baki ta taɓe Zulaiha ta yi tsaki ta ce "Rabu da gulmammu shi ma wannan sarkin ƴan rainin wayon Aminu, sai yake cewa wai in watsa ruwa ko ba zan saka sabulu ba ., ni kuwa in ce ya daɗe bai ga wanka ba, don ko sabulan kayan lefe na na saka na datse da mukulli na ɓoye mukullin, sai rai ya kai in na sauka lafiya, nake mulkawa in rabu da ƙarnin jego" Tana faɗar haka suka kwashe da dariya, ta shiga bayin ta yi wankin jiki, tana cikin wankewa ta ji wani hamami daga bakinta wanda ita kanta sai da ta ɗan runtse ido, hakan ya sanya ta lakuci makilin a yatsanta ta ɗan goga ta kurkure bakin ta fito, mai ta shafa ta saka atamfa riga da zani ta yafa mayafi suka fito. Da wannan tunanin ta bar gidan. A ɓangaren Amina tun da ta shirya da yamna ta nufi gidan ƙawar tata, wacce ake yi wa ƙawar kishiya, haka suka wuce don uwar gidan tana ta musu waya a kan su iyi sauri saboda hall ɗin da ake kamun amaryar mijin za su je, don za su je su rawa su yi liƙi su nuna ko a kwalar rigarsu, dama kuma da sanin mijin uwar gidan za ta je. Shi ma gudun fitina ya amince kuma da yake lallaɓata yake a rabu lafiya. Mota biyu suka cika da ƙawayensu, suna ta hira da zage-zage suna tsinewa maza wata ta ce "Ai mazan ƴan buhun uba ne, sai sun hango wata za su aura su isheka da cewa ƙaddara ce" Wata kuma ta ce "Ai ba za ki gane namiji munafuki ne ba sai ya ɗirka miki kishiya, shikenan fa sai ya shiga raina miki wayo, a wajenki ya nuna ke ce a gaba ita ma a nata wajen hakan ce za ta faru ai maza munafukan mata ne" Buɗar bakin Amian cikin cika baki ta ce "Ai ni Allah ya taimake ni, kuma na taimaki kaina, na nunawa mijina babu ni babu zama da wata, shi ma kuma ya amince da hakan, yanzu ko sha'war kallon mace na ya yi bare a kai ga soyayya" Wacce ake yi wa kishiyar ce ta ce "Raba kanki da namiji wallahi duk ƙarya ce, kawai suna raina mana wayo ne, nima nawan ba da haka ya fara ba, ban san da maganar auren ba sai da aka saka rana, shi ma auren ya rage sati uku" Kallonta Amina ta yi ta ce "Naki mijin da ban nawa da ban, yo ni aka mini haka kuma ai sai gawata!" Uwar gidan ta ce "Ko mushe za ki yi namiji babu ruwansa, in ma bai haɗa miki da saki ba in ya ga za ki tada masa hankali... Katse ta Amina ta yi da faɗin "Ya isa wasa ya yi wasa ban da, tsikarin uwar miji"Da haka suka ƙaraso wajen da za a yi kamun, wurin guda biyi ne a jere kuma dama sun lura ana ta shiga kowanne kuma ba a buƙatar kowane get pass. Da suka rasa wanne ne nasun, sai suka fito suka bi ayarin wasu ƴan mata, suna shiga ashe wajen kamun su Yaya Sule ne amma ango da amarya basu riga da sun iso ba, wajen dai an shriya komai gwanin sha,awa. Ana cikin wanna halin wayar uwar gidan ta yi ƙara, mijin ne yake sanar mata cewa ga sunan wajen idan sun zo, nan suka gane ba inda suma shiga bane suka fito domin zuwa ɗayan. A daidai nan ne motoci suka zo reras, da alama motocin amarya da ango ne da kuma ayarinsu, amma dai mamallakan hall ɗin da su Amina suka shiga. Tun da a daidai wajen suka tsaya. Amin tana riƙe da hannun ƙawarta, kamar an ce ta kalli cikin ɗaya daga cikin jerarrun motocin amarya da angon da suka tsaya a abin da ta gani ne ya hautsina hanjin cikinta, wanda ya so zautar da ita, jikinta ya kama rawa tamkar mazari cikin karkarwa baki ta shiga ƙoƙarin haɗa wasu haruffa.... *AMINU* Ya yi gyara murya yana ƙara dakewa don kar su gane yana ɗan fargabar gabatar musu da ƙudurinsa, ya fara magana yana cewa "Dama na tara ku ne domin in sanar da ku cewa, na kama mana wani gidan haya, kafin in samu in yi ginina in koma gidan kaina" Wani shu'umin murmushi ne ya suɓucewa Zulaiha jin za a sauya musu gida tana fatan dai can ba ɗaki ɗai-ɗai bane kamar wannan, don dama tana tunanin yin taron suna a gidan idan ta haihu, to yanzu faɗuwa ta zo daidai da zama. Saddiqa kuma bata ji komai ba a kan maganarsa don ta san ruwa dai ba ya tsami banza. Bai jira ta cewarsu ba ya ɗora da faɗin "Ɓangare uku ne a gidan, kowacce tana da ciki da falo fa banɗaki, sannan abu na gaba ina sanar da ku cewa zan ƙara aure nan da sati uku... Dididimmm gabansu ya faɗi amma dai Zulaiha ta fi shiga ruɗani don Saddiqa dannewa ta yi tare da majewa duk da abin ya ɗaure mata kai. Zulaiha bata san lokacin da ta ganta a tsaye ba ranta yana mata ƙuna, Saddiqa kuwa wani shu'umin murmushi ta saki irin na an zo wajen, cikin hargagi Zulaiha ta shiga faɗin "Au me? Aure fa ka ce, mafarki kake ko a falke kake, to idan bacci kake ka falka daga nannauyan baccin da kake don bani da kishiya" Ta faɗa tana tada jijiyoyin wuya kamar za ta kai masa masa duka. Kallon baki da hankali ya mata ya ce "Kar ki nemi ki mini rashin kunya, dama mun yi da ke ba zan auri wata ba bayan ke? To idan mun yi ma na janye bare kuma ni babu wacce na taɓa yi wa alƙawarin ba zan mata kishiya ba, don haka ki shirya kishi da ƙabila ma kuwa" Saddiqa jin ya ce ƙabila sai da ta ƙanƙance ido tana mamakin wani sabon salo, Zulaiha kuwa kuka ta fashe tana mai yin kukan kura ta yi kan Aminu, wanda ganin haka ya miƙe tsaye yana taka mata birki da faɗin "Kar ki fara haukar kishi fa, don in aika ki gida zuwa wani lokaci ba abin mamaki bane a wajena" Cike da jin haushinsa ta ce "Wannan ai wulaƙanci ne wato an ci moriyar ganga za a yada korenta, daga yin auren har za a fara taryata da kishiya bayan wacce na tarar a gidan" Ta faɗa tana huci. Kallon sakarya ya mata ya ce "Ita wacce kika tarar ba mutum bace, ko ita bata yi magana ba sai ke, ko ke kaɗai ce matata, to aure babu fashi ki yi duk abin da za ki yi" Kallonsu Saddiqa ta yi ta taɓe baki ita su duka ma tsantsaninsu take ji, ta rasa ma mai ya sa Zulaihar take wannan tsantsar kishin, iya wani lokacin idan ta tsaya ta ƙarewa Aminu kallo sai ta rasa abin so a jikinsa ko abin kishi, don yanzu ta fi karkatar da lamarin aurenta da shi a matsayin ƙaddara. Sai dai ita Zulaiha kishinsa take haiƙan, ko don ita ɗin ma ƙazamar ce oho, ita yanzu ai sallama musu Aminu za ta yi su jiƙa su sha ita yanzu hankalinta ya fi karkata ga yadda za ta ba ƴarta tarbiya. Zulaiha ce ta ce "Ai ita don ba ita za a yi wa kishiya ba, ni za a yi wa ai ita ni ce kishiyar ta wacce za a auro yanzu kuma kishiyata ce" Tsaki ya ja ya ce "Ke kika sani, in ma mene ne ita ma haka ta jure, ke ma ba zai gagare ki ba ita da har kwana bakwai na ƙara miki daga cikin kwanakin bakinta, ashe babu daɗi... Jin hakan sai Zulaiha ta harzuƙa tana faɗin "In ka isa ka ƙarawa amaryar da za ka auro kwanakina shegiya uwata ta haifeni, na rantse da Allah uban kuturu ma ya yi kaɗan bare na makaho... Saddiqa ganin abin nasu yana neman wuce makaɗi da rawa ta kalli Aminun cikin sanyin murya ta ce "Ni dai ina maka fatan alkairi, Allah sa a yi a sa'a amma don Allah ku ita mini daga ɗaki na gaji da jin wannan hayaniyar" Zulaiha jin wannan furucin ranta ya ƙara ɓaci ta harzuƙa ta ce "Wato ga dabbobi suna faɗa ko, dama ai gajiya za ki yi da hayaniya tun da daɗi kike ji ba ke za a ƙarowa ba" Ko kallo Zulaiha bata ishi Saddiqa ba, ta koma kujera ta zauna ta harɗe ƙafafu, wannan abin ya yi wa Zulaiha ciwo, don ta so Saddiqa ta biya ta ta sauke fushinta a kanta, amma Aminu daɗi ya ji don haka sai ya fara bubbuɗawa ya fara tafiya da niyyar barin ɗakin, Zulaiha taku ɗaya biyu ta yi ta damƙo wuyan rigarsa ta shaƙe shi, yana ta faman ta saka amma ta ƙi dakawa wai sai ya fasa aure ai kuwa ya ɗaga hannu ya kwashe ta da wani gigitaccen marin da ta sakar masa wuyan da ta shaƙe babu shiri, tana sakinsa ya gyara rigarsa ya fita daga ɗakin, ita kuma ta buɗe baki tana sheƙa kuka, tamkar wacce aka yi wa mutuwa har da su Allah ya isa take ta faman yi. Saddiqa ganin abin babu tsari, sai ta kama hannunta za ta fitar da ita daga ɗakin don hamamin da suka sanyawa ɗakin ya haifar mata da ciwon kai, wani irin cisge hannunta Zulaiha ta yi tana aikawa Saddiqa mugun kallo. Dariya ma abin ya ba Saddiqa ta kalle ta ta ce "Shi fa rashin mutunci da kike gani biki ne, idan aka maka ramawa kake, amma ni bani da lokacin ramawa sai dai in ce ki je ki sha ruwan sanyi, amma ki saka a ranki auren Aminu babu fashi gwara ki kwantar da hankalinki ko don abin cikin ki" Harara ta aika mata ta ce "An ƙi a kwantar ɗin, kuma da kika ce zai ƙara a bakinki" Tana kaiwa nan fuuuuu ta fice daga ɗakin ta nufi ɗakinta, nan ta tarar ashe Aminu ficewa ma ya yi daga gidan. Ta ɗaga hankalinta amma bata sauya zani ba, don sai abin da ya cigaba, Sumayya ta ji babu daɗi jin za a yi wa Zulaiha kishiya don dama yanzu ita ce abokiyarta dama an ce abokin damo guza. Amina kuwa daɗi ta ji musamman ma da ya kasance an ce za su tashi daga gidan da zama. Shafi'u ya ji babu daɗi jin Saddiqa za si bar gidan, ɗan kwallin ganinta da yake yana jin shauƙi sai ya ji zai yi kewa, amma ya saka a ransa cewa duk runtsi zai ke zuwa gidan da sunan ziyara. Ana saura kwana goma bikin suka kwashe kayansu suka koma gidan da ya kama haya, Zulaiha har lokacin bata huce ba tana ta hancini tana kuma mugun jin haushin Aminu. Da yake ɗakinsa da ban yanzu bashi da burin da ya wuce Aisha amarya ta tare domin hankalinsa ya yi kanta yana ganin da wuya a samu wata mace da za ta kaita ko ta fi ta don yana ganin ta mallaki komai, duk da ƙiba da kuma faɗin mazaunanta yana ɗan bashi fargaba sai dai ya sanya a ransa shi ba zai ɓata mata rai bama bare wani faɗa ya haɗa su, don ya lura tana da faɗa, gashi abu kaɗan ta hayayyaƙo shi tun kan a je gidan amma dai ya saka a ransa cewa wuyarta ta shigo gidan ne dole zai gyara mata zama kamar yadda ya ladabtar da sauran. Yau ya kama asabar aka ɗaura auren Aminu da Aisha. Rawar kai wajen Aminu ko kallo su Saddiqa basu ishe shi ba, saboda yana cikin maza masu mayar da macen gida ba kowan kowa ba a lokacin da suka samu wata matar. A yau ne za ta tare gabaɗaya ɓangaren amarya ya sha jere kasancewar suna neman na kansu daga ita har mahaifiyarta sai aka mata kaya na kece raini tamkar aurenta na fara, kujeru farare, kayan gado farare, labulayen Aisha ma farare ne. Kasancewarta mace mai son farin abu. Da yake Aminu yana da ɗakinsa amma saboda tsantsani irin na Aisha tun daga gida ta faɗa masa cewa ita fa ba za take kwana a ɗakinsa a kan katifar da yake kwana da matansa ba, saboda tana da ƙyamar ƙazanta hakan ya sa take ganin kawai sharing ɗin katifar ba za ta iya ba, wannan lamari ba ƙaramin daɗaɗawa Aminu rai ya yi ba, don dama wani uban shirgin kayansa ne mararsa wanki da ya tare da tarkacen tsuffin takalmansa wasu ma tun nasa ne na gida, don tun da ya gabya samu turakarsa ya je ɗakinsa na gidansu ya kwaso sauran kayansa, duk ya libge daɗin dabya ji kuwa ba ya so Aisha ta fahimci halayyarsa ta ƙazanta tun da wuri don ya lura irin masu tsaftar nan ne ta innanaha. Bayan kowa ya watse tana zaune a ɗakinta da ya sha turaren wuta, farar laffaya ce a jikinta mai flower golding, ɗakin fanka tana kaɗa ko ina. Bayan Aminu ya shigo ta ga yana ta ƙoƙarin rufe ƙofa nan take sanar da shi ya bata ga ya haɗasu da sauran matansa ya gabatar da ita ba, Aminu kuwa da ya san Zulaiha tana tamfa sai ya ce wai sai zuwa gobe. Haka dai ta ƙyaleshi Bayan sun ɗan ci kayan maƙulashe, ta tashi ta buɗe wata jaka ta ɗakko sabon brush tana mai cewa "Na hutar da kai siyan brush na taho da kayana, saboda ni bana son brush mai laushi na fi son mai tauri" Dariya ya yi abinsa, yana ganinta shiga bayi ta fito sai kawai ta tarar da shi ya yi mata saƙamƙam a kan gado, da mamaki take kallonsa don ita ta saba indai ta ci abu sai ta wanke baki amma shi ta ga ko bakin bai kuskure ba bare ya wanke da brush. Kuma yau da take ganin za a yi amarci dole za a buƙaci yin wani abu, kenan tsaftace ko ina ya zama dole saboda kar ɗaya ya cutar da ɗaya. Cikin ɗan jin nauyi ta muskuta mazaunanta, Aminu yana bin mazaunan da kallo ta ce "Al'amin ya baka wanke baki ba" Dimmm gaban Aminu ya faɗi jin wata sabuwa da sauri ya shiga dariyar yaƙe yana cewa "Ai na wanke da safe" Ya faɗa rashin gaskiya yana bayyana a tare da shi, don shi ko brush ma bashi da shi, a halin da ake ciki ma ba zai ce ga ranar da rabonsa da ya wanke baki ba. Bidik ya sauko daga gadon yana cewa "Bari ki ga in je in yi, saɓi biyar zan yi, ina yi ina maimaitawa" Ya faɗa yana ƴar dariya gabansa yana faɗuwa, ita kuma Aisha tun da ya ce ya wanke da safe sai ta masa ayar tambaya tana ta mamaki. Yana fita daga ɗakin, ya kama hanyar ɗakin Saddiqa sai dai ta rufe ƙofa amma haka ya buga ta buɗe, tana kallonsa ta ce "Ango ka sha ƙamshi" Bai amsa ba ya ce "Brush za ki aramin" Wata dariya ce ta so ƙwace mata amma sai ta dake ta ce "Brush kuma? Dama ana aron brush?" A ƙufule ya ce "Idan ba za ki aramin ba shikenan" Tana danne dariyarta a ranta ta ce 'To ni na ara maka brush kuma ai na sallama shi' A fili kuma ta ce "Akwai wani sabo bana amfani da shi, bari na baka" Cike da murna ya washe baki, tana miƙo masa har da maikilin ya shiga saka mata albarka, ita dai bata ce komai ba kawai dai tana son ganin diramar auren ƙabila da Aminu. Buta ya je ya cika ya tafi bayin tsakar gidan, sai da ya cika kan brush ɗin taf da makikilin, ya shiga wankewa, jini bakin ya ringa yi kasancewar bakin ba ya samun wanki. Sai da ya wanke sau biyar don har ya fara jin duk ya karce dadashi duk don ya birge amarya. Da ya koma ɗakin ya same ta ta sanya kayan bacci, cikin ganin ta ruɗa shi ya ce "Amarya ta ango" Yar dariya ta yi don har lokacin tana cike da tambayar dalilin da ya sanya tun da ya wanke baki da safe bai sake ba. Ta ce "Na'am angona na biyu, ni ai na san daga kai na rufe wani namijin, dama can mijina na farko wanka yake yi sau ɗaya a rana, wannan ne babban dalilin da ya sanya muka rabu, ni duk inda ƙazanta take bana son in raɓe ta" Suuuttt wata tusa marar ƙara ta kufcewa Aminu lokaci guda ya haɗa zufa, murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce "Amma wannan an yi ƙazami" Yana tuna shi da sai ya rufa sati jikinsa bai ga ruwa ba, ko jikin nasa ya ga ruwa to ba za a samu sabulu ba, to an rabu da mai wanka sau ɗaya ina ga shi, dariya ta ce "Kai ma ka faɗa" Daga haka sai suka lula duniyar ma'aurata, tun daga fara ɗan wasanni kafin a je ga mai ɗungurugum, hannun amarya na dama ya sauka a tsakiyar hamnatar Aminu, inda ta ji lallausar fatarta ta sauka a cikin wani cumus ɗin gashi mai gaushi, idanu ta zaro shi kuwa gogan bai san mai ake yi ba, kafin ta gama mamaki sai ta ji mararsa ta gogu da jikjnta inda nan ma ta ji wani gashi, biyubiyu. Hankalinta tashe ta shiga damuwa, tana mamakin yaushe mutum zai bar gashi haka a jikinsa, ita tun da ta kai munzalin gashi ya fito mata bata taɓa bari gashi ya kai ko rabin na jikin Aminu da ta ji ba. Ana sunna tana kukan zuci, zuciyarta tana ƙuna, ta shiga tashin hankali amma dai tana son tabbatar da zarginta. Da asuba bayan sun yi wanka sun yi alwala, Aminu da yake ƙoƙarin saka wando sai kare jikinsa yake kar amarya ta ga gashin nan, ai kuwa sai gani ya yi amarya tana kallonsa wajen ƙasa-ƙasa a ransa ya ce 'Ai indai baka yin abu ka ce za ka tarka to kuwa sai an samu matsala' Ya faɗa a ransa don yana ta zuci-zucin ya yi aski saboda amarya amma zumuɗi ya mantar da shi. Amarya kuwa ta shiga kokwanto a kan ango, ta ɗora masa ayar tambaya. Haka suka yi nafila, don ma kar ya ƙara wani laifin sai ya saƙala takalmansa ya ce ya tafi masallaci, don ya lura Aisha ma tana da riƙon addini kamar Saddiqa. Tana masa a dawo lafiya ya tafi, bayan tun da suka tare a gidan ma bai taɓa zuwa masallacin asuba ba. Ko da ya dawo dai ya lura da sauyi a fuskarta sai ya kasa sukuni, idanu ta ɗaga ta sauke a kan gashinsa wanda tun da fake zuwa wajenta yake ƙaƙaba hula, sai yanzu ta lura gashin ba ya samun gyara. Ganin gari ya ɗan waye suka koma bacci, bayan sun tashi suka sake yin wankan sabulu, wannan karon Aminu bai yi ha'ince ba ya yi wanka saboda yana son cirewa amarya kokwanto don ya lura kamar tana zarginsa ne. Tun da ta kalli ƙafar Aminu ta ga wani ɓaskara-ɓaskaran faso tamkar ƙazangare zai samu mafaka a ciki, sai ta hau salatina ranta, don ta lura da Aminu bai taɓa zuwa wajenta da normal takalmi ba kullum da kambas yake zuwa, sai ya ce mata wai yana jin daɗin sakawa ashe faso yake ɓoyewa, don ƙafar kamar ta tsoho ko baƙauyen mutum marar gyara haka ta koma. Bayan sun karya sai ya fita, ta shiga gyara ɗakin, ita abin da ta lura kayan da ya cire na jiya su ya mayar da ya yi wankan, abin da bata sani ba kayan wankinsa suna nan tare banda kayan jikinsa babu wankakke, dama duk masu dama-damar na fitar bikinta ne kuma duk ya saka. Dama ta kai ƙyallyen da suka yi amfani da su banɗaki ta wanke ta shanya, yanzu kuma tana son sauya zanin gadon ne, tana shirin cirewa sai ta ga ƙwaro ƙarami yana tafiya, da ta zuba ido da kyau ta gane kwarkwata ce, mamaki ruɗeni suka rufe ta, tana tunanin yadda aka yi kwarkwata ta zo kan gadon tun da ta san bata da ita. Tsantsani ya sa ta cukurkuɗa zanin gadon da rigunan filon da ta cire don kwarkwata uku ta gani raɗo-raɗo sun ƙoshi da jini. Jikinta har karkarwa yake lokacin da ta fito tsakar gidan, hango Zulaiha tana harararta bai hana ta gaishe da ita ba amma ta ɗauke kai, ganin Saddiqa za ta shiga ɗakinta ta ƙarasa tana gaishe da ita, ta amsa mata cikin sakin fuska, tana ɗan jin nauyi ta ce "Don Allah in ba damuwa ina son tambayarki, amma mu shiga daga ciki" Dama Saddiqa ta bata suka ɗhiga ɗakin, ta ɗauki Nihal tana mata waya zuwa can cikin muryarta da kake gane ba asalin bahaushiya bace ta ce "Don Allah ke ce uwar gidan Aminu" Kai Saddiqa ta gyara alamar eh. Cikin sanyin murya ta ce "Ina son sanin waye mijinki" Da mamaki Saddiqa ta kalleta nan ta shiga faɗawa Saddiqa abin da ta gani a kan gadonta, murmushi Saddiqa ta yi jin tana haɗata da Allah ta faɗa mata gaskiya, Saddiqa kuwa ganin matarsa ce sai bata ɓoye mata komai ba. Tsabar karkarwa da hannun Aisha yake sai da Saddiqa ta karɓi Nihal, idanunta yana kawo ruwa ta ce "Wallahi ba zan juri wannan abin ba, ai ni ba zan ma iya shan ruwa a inda Aminu yake ba, don haka a yau ba sai gobe ba zai sawwaqe mini" Ta faɗa tana share hawaye. Haƙuri Saddiqa ta bata, sai Aisha ta ce "Ba ina kukan komai bane ina kukan yaudarata da ya yi matsayinsa na ƙazami, amma na miki alƙawarin sai na gyarawa Aminu zama, sai na saita Aminu, sai na zamewa Aminu dodo a gidan nan" Murmushin gefen baki Saddiqa ta yi ta ce "Aisha kenan, ba za ki iya da Aminu ba, Aminu a ƙazamai ma shi dole a bashi mulki ko sarauta" Baki Aisha ta damƙe da haƙori, fitowa ta yi ta je, ɗakinsa ganin halin da ɗakin yake ciki ya ƙara tada mata hankali, ɗakinta ta ɗau waya ta kira shi. Dama wajen su Kabiru ya je, don ya ɗan bata waje saboda baƙi, ganin kiranta sai ya ɗauka ko har ta yi kewarsa ne, sai dai jin tana batun zuwa duba mamanrta babu lafiya kuma ta ce kar ya zo yanzu za ta dawo, hakan ya sany Aminu ya mata izini. Wayarta ta saka a jaka ta ɗauki kuɗi ta saka a jakar. Napep ta hau ta nufi kasuwa, wajen masu siyar da soson ƙarfe na wanke bayan tukunya irin manyan nan ta je, guda uku ta saya ta kaɓata a waje guda. Ta wuce wajen masu siyar da klin viva manyan nan ta siyo guda huɗu, wajen da ake siyar da aska irin ta wanzamai da suke aski ta wuce ta saya wata mai kaifi ta, ta je wajen masu gugar kaushi ta siyo magogin kaushi, ta hau napep ta koma gida. Tana shiga ta ajiye ledar a ɗakinta, ɗakinsa ta shiga bayan ta saka safar hannu, kayan Aminu karkaf mararsa wankin nan ta kwaso ta tare su libgi guda a tsakar gidan. Wani ƙaton baho ta ɗakko sabo, ta cika da ruwa ta buɗe klin viva ta zazzage kusan rabi a ciki, ta kaɗa kumfar, duka kayayyakin da ta siyo ta fito da su ta ajiye a gaban bahon, aska, dutsin gugar kaushi, soson ƙarfe, sai kuma sheba da ta ɗakko a ɗakinta. Saddiqa ce ta zo ta kalle ta da mamaki ta ce "Ba dai ke kaɗai za ki wanke wannan kayan wankin ba?" Ta faɗa tana kallonta, yatsina fuska Aisha ta yi cikin hasusarta da bata fita ta ce "Waye bawansa, ni? Allah sawaƙe, kin ga wannan klin ɗin Aminu ne zai zo yau sai ya wanje kayan nan duka tasss, ya ɗauraye ya shanya, wannan askar kuma wallahi yau sai na tattale wannan gashin kan nasa mai kwarkwata, na mayar da shi tanƙwal (Ƙwal uwar kwabo) Sannan sheba ɗin nan sai na aske masa wannan gashin hammatar da na mararsa, soson ƙarfen nan da shi zan saɓa jikin Aminu sau goma, don yadda yake sati ko fiye da hakan babu wanka na tabbata dauɗa tana nan nannage a fatarsa, sannan ya wanke kaushin wannan na ƙafarsa" Ta faɗa tana riƙe da ƙugu. Tsabar mamaki Saddiqa ta rasa abin cewa, hatta Zulaiha mamakin ƙarfin halin amaryar take don tana window tana ganin komai. Bata jira Saddiqa ta ce wani abu ba ta ɗora da faɗin "Sai na zamewa Aminu ciwon ido a gidan nan, zai san ya auro gamonsa wallahi, sai na saka Aminu ya ƙyamaci ƙazanta da kansa ba don son ransa ba sai don dole uwar naƙi, Zulaiha ganin abin ba na wasa bane sai ta fito tsakar gida tana son ganin yadda wasan zai fara. Ɗaki amarya ta koma, wata vest ta sako da wani shegen burgujejen wando tiri kwata, wanda ya bayyana asalin ƙibarta, da wayarta ta fito ta dokawa Aminu kira, Aminu yana surutu ya ga kiran amarya ya ɗauka sai ya tsinci maganarta cikin bada umarni tana cewa "Ka zo gidan nan yanzun nan ina son ganinka" Zulaiha da Saddiqa suna jin yadda ya dirirce a wayar yana ta ambaton gashin nan zuwa. Ba a jima ba sai suka ji ƙaran buɗe ƙofa, buguzum-buguzum Aisha ta wuce shi ya bi ta da kallo, kafin ya gama tunanin inda za ta je sai ya ji ta bankama sakata a ƙofar gida sakatar sama da ƙasa. Kamar an ce ya juya ya yi wa idanunsa masauki a kan gabaɗaya kayan da ta ajiye a tsakar gidan, don ganinsu ya bayyana masa dukkan aikin kayan saboda ya fahimta, idanu ya shiga gwalewa ya ɗaga kai ya sauke a kan fuskar Zulaiha wacce da alama dariyar ƙeta ce shimfiɗe a fuskarta, da sauri ya mayar da akalar ganinsa zuwa kan fuskar Saddiqa wacce hatta haƙoranta sun bayyana a dariyarta marar sauti, tun da ta baro Nihal tana bacci, yanzu kallon wasan da za a buga ya rage su ne masu gani. Ƙaran takun dawowar Aisha shi ya sanya Aminu waigawa, gabansa yana dukan uku-uku. *A NAN MUKA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 WANDA NA BAKU A FREE, KU NUNA KULAWARKU DA SOYAYYARKU GA MARUBUCIYARKU MAMAN AFRAH, WAJEN SAYAN WANNAN LITTAFIN BOOK 2* *DA NAIRA 500 KACAL ZA KI MORE KARATUN ƘAZAMIN MIJI HAR ƘARSHE, DON JIN YA ZA TA KAYA, ANYA AMINU ZAI YARDA A YI WANKAN NAN, A WANKE ƘAFA A ASKI MASA GASHIN DA TAKE JI DA SHI, A SANYA SHI YIN WANKIN DOLE, SHIN AISHA BATA ƊAKKO DA ZAFI BA* *YA CAKWAKIYA ZA TA KASANCE TSAKANIN AMINA DA YAYA SULE GA KUMA SALAHA A GEFE, SHIN GASHI DAI SALAHA BATA SAN YANA DA MATA BA HAKA ITA MA AMINA BATA SAN DA AUREN SALAHA BA* *ZA A BIYA KUƊIN KARATU 500 TA ASUSUN FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222*