[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR1FT5* __________________________________ A lokacin da na buɗe idanuwana cikin tsanani da raɗaɗin ciwo akan fuskar da ban taɓa sani ba na sauke su wato fuskar SJ wanda yay min rumfa a ƙoƙarinsa na taimako ga likita da ya buƙata na a rirriƙe ni. Kuma wannan shine mafarin shigowar rayuwar Sadiƙ Abubakar Jadda gare ni, kamar yanda silar siyan rake ya zama mafarin haɗuwata da Nazifi Bala Mai Kalwa. Na sha jinya a sanadiyar hatsarin da nayi kamar ba zan rayuwa ba don har sai da aka yi tunanin fitar da ni ƙasar waje domin a duba ƙwaƙwalwata a cewar likitoci ba ƙaramin buguwa nayi ba, hankalin ahalina ya tashi, natsuwa tayi ƙaura daga garesu domin ba su da kuɗin da za su fidda ni ba su da dalilin su, tsananin damuwar ne ma silar kamuwa da hawan jinin mahaifina domin shi a lokacin ce yay kawai a bari ubangiji yay ikonsa, shi kam ya cire rai da ni, duk da Amb Jadda ya ce ba su da damuwa su ne za su yi komai tun da sune sanadi, kuma kan ka ce mene wannan SJ da ke matuƙar ba ni kulawa har ya tattara bayanan komai zuwa ƙasar da za'a fitar da ni, sai ga shi kuma cikin hukuncin ubangiji a irin adu'oin da iyayena ke ta min da faɗi tashin ɗawainiyar asibiti da iyalan Amb Jadda ke ƙara yi akaina sai komai ya zo da sauƙi cikin ikon ubanji kuma na sami lafiya. Ahalin Amb Jadda mutanene ma su tsananin mutunci da karramawa da sanin darajar ɗan Adam, Dr Hassana Abubakar Jadda macece ta gari wadda ta fita daban a cikin mutane, akwai ta da tsananin tausayi gami da kyautatawa, haka shima mijinta Amb Jadda mutum ne me tausayin talaka da son taimaka masa shi dai illarsa ɗaya shan sigari da har aka ce tayi masa illa ta taɓa lafiyarsa amma duk da hakan bai daina sha ba sai ma ƙari, wanda shan sigarinsa shi ne sanadin rashin jituwa tsakaninsa da Ɗansa SJ da ko magana bata haɗa su. Idan har magana wa junansu ta zama dole to suna isar da ita ta rubutun takarda ko kuma a waya, idan kuma a gida ne Maamee ita ce me aika saƙo a tsakanin uba ga ɗan, amma Amb Jadda in har zaka faɗa masa gaskiya akan shan sigari to zaku ƙulla gaba ne da shi. Ko bayan sallamata a asibiti da aka yi Maamee bata watsar da mu ba, ta kan zo gidanmu ta gaishe da mahaifana nima kuma ta duba ni tana me ƙara bada haƙuri akan afkuwar hatsarin. Wanda a kowanne lokaci Ummani da Abbaa ke nuna mata babu komai hakan tsararran lamari ne da ubangiji ya shirya faruwarsa ko da bata sanadinta ba. Silar hakan kuma sai ya zama zumunci ya ƙullu tsakaninmu da ahalin Amb Jadda musamman ma ta ɓangarensu, don ana mu ɓangaren mu kan ja da baya da su duba da cewa ba tsararmu ba ne su, suna da kuɗin da ko da kaf zuriyarmu aka siyar ba za'a haɗa kaso biyu na daga dukiyar da Allah ya ba su ba, kuma su ɗin manyan mutanene da duniya ma ta san da zaman su. Ta ɓangaren Nazifi me rake shima mutum ne me tsananin kirki na gaban kwatance, rashin zuwa makarantar da na ke yi ya tambayi su Safiyya dalili suka faɗa masa, a ranar ya zo duba ni da ledar kayan dubiyansa daidai ƙarfin talaka, sai ka rantse wani ɗan uwa ne na kusa. Kuma ba'a cika sati ba sai ga shi sun zo da ƙannensa maza da mata, suma zuwan na su da kayan dubiyarsu suka zo, haka aka dafo min miya da kaji da kayan marmari a leda. Kusan kullum sai ya zo duba ni, kuma ba ya zuwa haka kawai sai da kayan dubiya. Daga nan kuma shikenan sai zumunci ya ƙullu a tsakaninmu domin kuwa bayan an sallame ni daga asibiti hatta Yayar Nazifi da Mahaifiyarsa sai da suka zo har gida duba jikina, da yake mahaifiyarsa macece mai faran faran yini ɗaya sai suka zama tamkar dama can an san juna ita da Ummani har Abbaa ke musu tsiya, ita dai tana ba su labarin ai Nazifin kan yi mata hirarmu ni da su Safiyya akan yabon hankalinmu da tarbiyarmu. Tun daga wannan ranar kuma ko abincin gargajiya Iyam tayi sai ta aiko an kawowa Ummani duk da nisan da ke tsakaninmu da unguwarsu, aiken alkhairi duk ita ce, idan ta tashi haka zata ciko ƙaton kwano da daddawa ta ce a kawowa Ummani. Itama Ummani haka duk sanda ta samu abun arziƙi ta bani in kaiwa Iyam, idan na je gidan yini na ke sai Yayan Shago ya dawo ko Yaya Nazifi tukunna Iyam tasa a rakoni gida. Tafiya tayi tafiya wata rana na dawo daga islamiya, na tarar da sabuwar mota kar a ƙofar gidanmu, zuciyata cike da mamakin su waye baƙin da muka yi, sai da na shiga gida na tarar da Maamee ita da Marfu'a da Madam waɗanda zuwansu babu jimawa kenan. Bayan gaisawarmu na wuce ɗan tsukukun ɗakina domin cire uniform, ina ciki Ummani ta ƙwala min kira nayi saurin ƙarasawa na fito da hanzari, a kicin na sameta ta dube ni tana cewa. "Sanyo gyalenki ki kaiwa me suke ce masa ruwa yana waje". Nayi ɗan jim sai can na ce,"ohh Bayya ko?". Ta gyaɗa kanta,"ehh shi, yaƙi shigowa gidan kin san bai da sakewa kamarsu". Na koma ɗaki na sanyo ƙaramin gyalena na zo na karɓi ɗan ƙaramin farantin robar hannunta, wanda aka sanya pure water masu sanyi guda biyu akai, fita nayi inda na tarar motar bata ƙofar gidanmu kamar ɗazu, nayi leƙe leƙena ban ganta ba hakan yasa na juya domin komawa sai kuma sai naji anyi fakin, na waigo naga motar ce ta dawo. ƴan sakanni kana na taka na ƙarasa ɓangaren mazaunin direba na ƙwanƙwasa gilashin. A hankali aka zuge gilashin, tsammanina ma Bayya ne ashe Na-Madam ne sarkin tsokana. Yana kallona da murmushi ya kira ni da sunnan da kaf gidan na su ke faɗa min. "Dimple". Murmushi nayi inda malotsan gefen bakina suka lume ciki, na rissinar da kaina ƙasa ina cewa da shi. "Ina wuni". Ya amsa min da fara'arsa,"lafiya lau Dimple, ya su Ummani da Abbaa". "Lafiya ƙalau. Ga ruwa ta ce in kawo maka". Ya kalli farantin hannuna wanda har naji wani iri saboda na roba ne kuma duk yasha jiki. Ya miƙo hannu ya ɗauka ruwan cikin tare da faɗin an gode. Sallama na masa zan wuce nan yake ce min,"ba ku gaisa da Bayya ba". Sai sannan ma idona ya kai cikin motar in da na hango shi zaune idonsa zagaye da baƙin gilashin da bai rabo da shi, da ƙananun kaya a jikinsa kamar ko da yaushe don ni dai ban taɓa ganinsa da manya ba, yay kyau sosai p-cap na ɗaukar fuskarsa, shi irin masu kyan da ake kallo ne aji kamar a sace a gudu. haka ɗaya sai naji gabana yay mugun faɗuwa nayi saurin ɗauke ido daga barin kallonsa, a hankali kuma na ce,"Ina wuni Bayya". A kaikaice ya dube ni ta cikin gilashin, kamar ba zai amsa ba saboda yanda yaja lokaci can kuma sai ya ce,"lafiya lau, ya kike ya mutanen gida?". Yay maganar cikin birkitacciyar hausarsa da bankinsa bai gama ƙwarewa da ita ba, don ba ya dogon zance ba tare da ya saka faransanci a ciki ba, har sha'awar hakan na ke ni kam, sai naji ina ma ni ce na iya wani yaren bayan hausa. Ina gyara gyalena da ke neman zamewa na ce masa,"duk suna lafiya ƙalau, Ummani ta ce a gaishe ka". Kansa ya gyaɗa wajen amsa min. Na-Madam cikin zolaya ya ce da ni,"Hajiya Dimple sanyi ƙalau, ke dai sam ba ki son magana, yanzu idan na ce ki tayani hira fa sai ya zamar miki jan aiki. To ai shikenan ki gaida mutan gidan". Ina murmushi na wuce, ina gab da sanya ƙafata cikin soro maganar SJ ta dakatar da ni, haka kawai kuma sai naji kiran sunan nawa da yay a karo na farko ya amsa a gaba ɗaya ilahirin jikina, haka kuma naji tamkar sunan a bakinsa aka raɗa shi tun usuli duk da cewar kana jin yanda ya faɗi Sa'ida ba muryar bahaushe ba ne. Ni kam ban san dalili ba amma tabbas na kan tsinci kaina cikin wani yanayi da na ke kasa fassara shi balle gane masa in har na ga SJ ko naji ƙamshinsa, don hatta ƙafafuna kan yi rawa a irin wannan lokacin hakazalika in rasa natsuwata. A hankali na juyo hannayena na karkarwa riƙe da farantin na kai ƙwayar idona kansa, ya cire gilashin idanuwansa, idanun a ƙanƙance kamar basa gani da kyau, ganin na tsaya yay min alama da kansa na in zo. Na tafi sannu a hankali ina jin kamar zan faɗi ba tare da sanin dalilin wanzuwar hakan ba. "Ya wuyan na ki?". Idona a ƙasa na haɗiye yawu kafin na iya cewa,"Da sauƙi". "Es-tu sûr?". Ɗago ido nayi na dube shi, ganin na tsare shi da ido sai ya kulle ido ya kaɗa kansa kaɗan kafin ya ƙara buɗe baki da ƙyar ya ce min,"kin tabbata?". Na ɗaga kai da cewar,"Ehh yay sauƙi ba kamar da ba". "Zan iya gani?". Gyalena na ɗaga ina yaye wajen tare da nuna masa, ina ga ganin sacewar kumburin wuyan yasa ya kai hannu ya taɓa babu shiri na wani zabura ina ja da baya saboda yanda zafin ciwon gun ya ratsani da kuma jin hannunsa kamar shokin na wutar lantarki. Ƙwayar idonsa akaina bayan wucewar ƴan sakanni ya ƙara cewa,"kina iya zuwa school?". Na sauke numfashi tare da cewa,"Ehh yanzu ma daga islamiya na dawo". Kallona ya tsaya yana yi, wucewar minti ɗaya yay min alama da hannu na in matso kusa, na matso kusa da ƙofar motar da ya buɗe ya ziro ƙafafunsa waje. Ya kai hannu ya ware idanuwana yana duddubawa irin yanda likita yake min, sai da ya gama bincikensa matsayinsa na likitan da ya ajiye aiki saboda saɓanin da ke tsakaninsa da mahaifinsa kana ya ce min. "Jinin ya ɗauke gaba ɗaya, kar kina wasa da magani please". Sai kuma yay shiru kafin ya ƙarasa maganar,"Ki yi haƙuri kin ji". Kai na sunkuyar ƙasa, ni kam wannan kalmar ta ban haƙuri da ke fitowa daga bakinsa ko da yaushe da ace tana tsiro da tayi a jikina. Haƙurin nasa duk yana bayarwa ne saboda mahaifiyarsa, Marfu'a ta taɓa ce mana in ace Mahaifinsa ne ya buge ni da mota to SJ zai iya tayamu shigar da ƙara kotu, kuma ba zai tsaya akaina ba don ganin na sami lafiya kamar yanda ya ke a yanzu, hasalima zai ce ina ruwansa shi shan sigarin mahaifin nasa ne ya janyo masa ba wani ba, ai anyi anyi ya daina shan sigari yaƙi ji. Muryana kamar an shaƙeni na kalle shi ina jin gabana na tsananta faɗuwa saboda kwarjininsa na ce,"Bayya ka daina ba ni haƙuri don Allah...". Ban ƙarasa ba ya ɗaga min hannu alamar in dakata, sai kuma ya ce da ni,"SJ not Bayya". Bayan ya huta da wannan ɗan guntun furucin ya ƙara cewa,"Su ƙannena ke kuma wata ce daban, just call me with me my name Sadeeq or SJ". Kai na gyaɗa a hankali don tuni na fahimci bai son wancan sunan kam yafi so a kirasa da SJ ko Sadeeq, ƙannensa ma da suke faɗin Bayya ba so yake ba, shi a kirasa da zallar sunansa kawai, su kuma ƙannensa na ganin idan suka kira sunansa gatsal tamkar aikata zunubi ne, nima kuma gaskiya a irin yanda na taso da tarbiyar gidanmu ba zan iya faɗar sunansa ba domin ya girme min nesa ba kusa ba. "Ƙafan na ki yana takuwa sosai yanzu?". Ina ɗaga kai na ce,"Ehhh, ta daina ciwon". Ya gyaɗa kansa sau biyu, bai kuma ƙara cewa da ni komai ba ya mayar da ƙafafunsa cikin motar ya rufe ƙofar, ni dai ina tsaye kawai kamar me neman gafara duk a tsorace na ke ina jin jikina na kyarma, sai satar kallonsa na ke ina jin wani abu na motsawa a tare da ni. Ji nayi suna magana da Na-Madam cikin yarensu wanda ban san me suka ce ba, sai kuma naji Na-Madam ya ce da ni. "Idan kin shiga ki ce da Maamee su fito mu tafi". "To". Na amsa a hankali ina barin wajen da sauri. Yanda na shiga gidan kamar wadda taga wani mugun abun, na faɗa ɗakina ina haki tare da dafe ƙirjina da ke ta bugawa. Sai da na natsu kana na fito na shiga ɗakin Ummani, daga gefe na tsuguna na sanarwa da su Maamee saƙon su SJ na cewar su fito. Ni dai tun daga wannan ranar wani sabon Al'amari ya sauka akaina, gaba ɗaya na rasa me ke damuna mene kuma dalili, domin kuwa tunanin SJ ya samu muhalli a cikin raina, komai na ke yi duk abun da na ke yi da tunanin SJ, haka idona a kowanne bugawar sakan da minti sai na tsinci haskawar hoton surarsa, bini bini kunnena ya jiye min sautin muryarsa, gaba ɗaya sai na rasa gane kan dalilin hakan, abu ɗaya kawai da na sani tunda na taso nayi hankali ban taɓa jin wani abu irin haka ba, kuma ban taɓa jin namiji ya burge ni ba har ina son wani abu nasa sai akan SJ. Yawaitar faɗuwar gaban da na ke a duk lokacin da na ayyana kamar bayyanarsa a inda na ke sai na fara ramewa, ramar har tayi min yawa saboda rashin sake ganinsa da banyi ba tun wancan zuwan da suka yi gidanmu, sai wata rana ne ma Ummani ke ce min taje gidan zuwa yi musu godiyar ƙara turo kuɗin magunguna da suka yi da aiken da akayowa Abbaa na kayan abinci. Ranar ji nayi tamkar na fashe da kuka domin ko babu komai da taje da ni zanga SJ mutumin da na rasa dalilin tsaya min a rai da yay. Ban taɓa sanarwa da kowa halin da na ke ciki ba hatta Safiyya da ta gallazeni da tambaya ganin duk na sauya. Bayan wucewar kwanaki masu tsayi ina daɗa girma da wayo da hankali na farga da cewar na kamu da son SJ, so kuwa me tsanani tun da har yana wahalar da ni duk da ƙarancin shekaruna, du da cewa so ba shekaru ba ne, don in ace a ƙauye muke tuni an min aure ba kuma zan kawo ya wannan shekarun ba ma ban fara tsayawa da saurayi ba, sa'annina kowacce da yaronta. Kuma tun daga lokacin da na fahimci na kamu matuƙa da soyayyar SJ na yiwa kaina faɗa akan dole na yakice tunaninsa da sonsa a raina domin SJ ba tsarana ba ne ba ajin aurena ba ne, shi mai kyau ne, mai ilimi, mai kuɗi, mai ji da kansa, ɗan manyan mutane, to ina gamin haɗi tsakanina da shi daddawa a kunu? Shi kam ai sai manyan mata da suka amsa sunansu, masu ilimi ƴaƴan masu kuɗi ba irina ƴar Malam Salman me teburi a kasuwar rimi ba, wadda bata da komai ɗin da namiji kamar SJ me aji zai gani yace yana so, sai dai tabbas da ace zan samu wata dama da zan isar da saƙon zuciyata ga SJ lallai da nayi hakan, to amma ban san hakan me zai iya haifarwa a gare ni ba, ba na son wulaƙanci haka ba na son abin da zai haifar da matsala tsakanina da iyayena, amma tabbas ina son SJ kuma zan so rayuwar aure da shi. Ganin fa ni kaɗai na ke kiɗa da rawata akan soyayya, tuni na miƙe da adu'a, na duƙufa akai babu dare babu rana akan Allah ya cire min son SJ ya kuma ƙara nisanta tsakanina da shi ta yanda ba zan gansa ba balle ya zame min famin ciwo, sai na fara samun salama domin kuwa babu abin da yafi ƙarfin adu'a, a hankali a hankali yawan tunaninsa da jin motsawarsa a zuciyata duk ya tafi sai jefi jefi, nayi hamdala na gode Allah don hakan ba ƙaramin alkhairi ba ne a gare ni na sani, tunda ba taɓa samun SJ zan yi ba, ba zai taɓa zuwa yace yana sona balle har ya furta zai aure ni. Tambayar ma da na kewa kaina har kullum garin ma ya akai na kamu da sonsa? Shi son dama haka ya ke babu shawara babu neman izini? Sau tari na kan yi murmushi takaicina idan na tuna kwanciyata a asibiti, wato lokacin a haukar tunanin da nake yi irin rawar jikin bani kulawa da tsananin nuna damuwa gami da tausayi akaina da SJ yay sai na tsammaci ko sona yake yi, tun ma da naga yanda ƴan gidansu kowa ke haba haba da ni kamar wata shaƙiƙiyarsu ba tsintuwar hatsarin titi ba, ashe duk ina cin alfarmar mahaifiyarsa ne da kuma kyan zuciyarsa ta masu imani, ba yanda na ɗauka na soyayya hakan yake a ɓangarensa da ɓangaren ƴan uwansa ba, hasalima yana da matar da zai aura wacca ba'a ƙasar nan take ba, naji hakan ne a bakin Ummani, wadda itama na san hira ce tayi hira tsakaninta da Maamee har ta san hakan, ranar kuma na ga rashin hankalina don kwana nayi ina kuka, har ina ayyana ina ma ace SJ ya fasa auren kowacce mace ya dawo gare ni, sai dai babu yanda zan yi haƙura da shi ya zama dole, silar ciwo ya haɗamu da su kuma samun waraka ya rabamu da su, don tun da na gama wartsakewa likita ya tabbatar musu da bani da wata matsala ta ko'ina muka bar jin ɗuriyarsu haka suma suka daina jin tamu ɗuriyar. Sai ma in wataran ana zaune ne haka Abbaa ya tuna su ana faɗin kirkinsu. ____________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR02FT5* *Advert!* _Ina masu son koyan kalolin abincin ƙasashen waje? Kamar irin su mandi rice, Chinese rice, chicken biryani, Afghani rice, eggs rice, chicken kabab, chicken biryani da sauran abincin labarawa da indiyawa masu daɗi da kwantar da hankali tun daga jin ƙamshin su. akwai kalolin salad irin su patoosh salad, normal salad, macaroni salad da sauran su. Baku da labarin Leemars_mandi zatayi class don ta taimakawa mata ta koya musu kalolin abincin ƙasashen waje wanda mu bamu san da su ba...?. Ta ƙware indai a wannan b'angaren ne shiyasa ake mata take da "Home of delicious and Arabian foods." ni na shaida Leemars_mandi ta ƙware a wajan sarrafa d'anye ya koma dafaffe. Ka da ku sake ayi babu ku class d'in zai zo muku nan bada jimawa ba akan naira 7k kacal, akwai ragi mai auki ga wad'anda suka fara biyan kud'in su. Domin neman ƙarin bayani nemeta akan wannan number 09030398006, ko DM a Instagram @Leemars_mandi._ __________________________________ A gefe guda kuwa Allah ya haɗa jinina da Nazifi Bala Mai Kalwa, nagartar Yaya Nazifi ita ta sanya muka yi shaƙuwa ta ban mamaki, ya zama tamkar ɗan gidanmu, kuma yanda ake zumunci da gidanmu da gidansu in ba sani kayi ba zaka ce ko dama can ƴan uwan juna ne mu. Kowa nawa ya san shi, ba shi da shamaki da ko'ina a cikin gidanmu, abota me ƙarfi ta ƙullu tsakaninsa da Yayyuna, ƙwarai shi kam mutum ne me shiga rai saboda kyawun halinsa da ɗabi'unsa ga uwa uba kuma addini, yayi haddar ƙur'ani har sau uku banda manyan littafan addini da ya haddace, duk wani mutum na ƙwarai zai so ace yay mu'amala da Yaya Nazifi, kai ba ma shi kaɗai ba zuri'ar Malam Bala Mai Kalwa kaf babu na yarwa, ko kwatance ake a unguwarsu na matasa na gari za'a sako sunan Yaya Nazifi a farko haka za'a sako maka sunayen samarin gidan Malam Bala Mai Kalwa. Tun da har Abbaa na ya yarda da mu'amalarmu da Yaya Nazifi na san kuwa lallai ya samu lambar yabon shaidawa, ya iya mu'amalantar mutane ga kyautatawa da son taimakawa, haka bai da abokin faɗa, shiga shirgin abokai ma bai dameshi ba, indai ba fita neman na kansa ba to yana gida tare da mahaifiyarsa ko kuma yana wajen mahaifinsa ɗaukar karatu. Abbaa da kansa ya yarje min mu'amala da Yaya Nazifi domin yay masa duk wasu jarabawowi sannan kuma ya karance shi sosai, duk da baka ba wa mutum dukkan yardarka kamar yanda ba'a barin ƴa mace sakin jiki da namiji, amma ko da yaushe cikin masiha da ankarar da ni ake. Abbaa har roƙarsa yay da ya ke zuwa gida yana min karatu duk sanda ya samu lokaci, ya damƙa masa amanata domin ya yarda da shi bai da haufi akansa. Tsakanina da Yaya Nazifi mutunci da girmama juna ne, bama ɓoyewa juna komai, duk wata shawara da ta shafi rayuwarmu da juna mu ke yi, yana matuƙar bani gudunmawa wajen ganin rayuwata ta inganta, bayan mahaifana shine mutum na farko da zan ce yana ɗora ni akan daidaitacciyar hanya, wanda kai tsaye kuma zai faɗa min gaskiya komin ɗacinta, ya kuma tsawatar min da bin hanyar da take ba daidai ba. Lokaci guda sai ya zamana in har zaka zauna da ni to ba zamu rabu ba sai ka san Yaya Nazifi a bakina, shima ta ɓangarensa duk wanda ya ke tare da shi ya san sunana a bakinsa, haka har ta fara kaiwa ga mutanen da ke kewaye da mu sun fara zargin ko soyayya muke yi, sai dai ko kaɗan babu hakan daga zuciyar kowannemu, ni dai matsayi ɗaya ne a zucciyata Yaya na ɗaukesa kuma aboki, tamkar yanda shima ya ɗauke ni matsayin ƙanwa kuma abokiya, Yaya Nazifi sam ba ya banbanta ni da ƙannensa, ko abun faɗa na yi da gyara zai fito min a matsayin wa na gari yay min faɗa sosai, ina basa girmansa matsayinsa na wanda ya girme min sosai. Sai dai fa ko kusa an ƙi yarda da cewar babu soyayya a tsakaninmu, tun daga kan ƙawayena har shi kansa ƴan gidansu kan tsokane ni wataran su ce budurwar Yaya Ƙarami ta sirri. Iyam kuwa sau tari idan yana mata hirata sai tace uhmm lokaci dai, Hatta mahaifiyata sai da ta taɓa tambayata anya babu wata alaƙa ta daban tsakaninmu, na tabbatar mata da babu wannan kamar yanda su ke tunani, ta kuma yarda da ni domin ta san bana mata ƙarya bana mata ɓoye ɓoye kuma ta sanya ido akan hakan sosai taga saɓanin zarginta, wasu da basa iya tantance soyayya da mutuntaka ne dai suka kasa gasgata yanda muka ɗauki junanmu. Lokacin da muka zo term ɗin ƙarshe a SS2 lokacin manema aurena su ka fara fitowa kamar dama jiran lokacin su ke, caaaa wannan ya zo wancan ya zo, daga yamma tayi an fara sintiri kenan a soron gidanmu wai ana sallama da Sa'ida, kuma manyan mutane ba ƙananu ba, duk da ba fita na ke ba idan aka zo amma na kan yi mamakin inda har suka ganni ma suka biyo sawu, haka kuma mafi yawancin masu zuwan sai in tuƙe maƙura a mamakin me suka gani tattare da ni da kamar su masu kuɗi zasu zo neman auren ƴar talaka kamata, yau ace me mota kaza, gobe ace kalar mota kaza, anjima ace wani babban mutum da mota kaza shine babba a wuri kaza, ni ranar da aka ce ma wani ya zo da kaki sai da nayi mugun tsorata ce nake laifi na yi. Lamarin ya fara bawa Abbaa haushi, da ka ji Abbaa na tsaki to akan hakan ne, har gargaɗina yay akan ya soke min ko zuwa unguwa da Ummani, daga makaranta sai gida. Shi kam so ya ke ko zai aurar da ni sai nayi nisa a karatun jami'a kamar yanda ya ke fata, don haka duk wanda ya zo da maganar aurena Abbaa zai saita masa hanya da cewar ba yanzu zai aurar da ƴarsa ba domin karatun likita zanyi ba ya so a gurɓata min tunani da soyayya. Ta ɓangaren mahaifiyata ma hakan take don sosai take sanyani gaba da faɗa akan kar na sake in faɗawa tarkon namiji, in tsaya na natsu na tsayar da hankalina wuri guda in yi karatu shine burinsu, kuma shine babban gatan da zasu tafi su barni da shi, wannan ita ce babbar damata in moreta tun da ƙuruciyata kafin girma ya riskeni al'amuran duniya ma su sha kaina. Na kuma yi masu alƙawarin hakan domin nima banda ra'ayin soyayya ko kaɗan, ko da ina da shi zan ajiye saboda farin cikin iyayena da cikar burinsu, ko son SJ da nayi a baya da ace zuciyata tayi shawara da ni da hakan ba zata soma faruwa ba, to godiyar da na yiwa ubangiji ma har nayi yayin son nasa na gama babu wanda ya sani hatta shi kansa, a yanzu kuma da na ƙara hankali da wayo sai na gane bama sonsa na ke ba burge ni kawai ya ke yi, abin da mutane da dama basa ganewa kenan banbanci tsakanin so da burgewa. Wata ranar juma'a bayan la'asar muna zaune a tsakar gida ni da Ummani ina tayata tsinkar zogale, muna ta hirarmu ta ƴa da uwa, aka yi sallama daga soro, jin muryar kuma ya saka ni sauke sanyayyen murmushi ina kafe hanyar shigowa da ido, Ummani kuma ta warware ɗaurin ɗan kwalinta ta yafa kafin sannan ta ce,"To shigo mana Nazifi ka tsaya daga nan, gidan ai ba baƙonka ba ne ko". Har ya sanyo ƙafarsa tsakar gida ban ɗauke idona ba akan hanyar shigowa, shima ɗin shigowar tasa ƙwayar idonsa akaina ta sauka, ya murguɗa min baki da hararar wasa ni kuma sa'adda da na ɗauke kaina zuwa gefe ina murmushi me faɗi don sosai ya bani dariya, yanda mu ke abu da shi kamar ƙawa da ƙawa. Yau kam yayi kyau sosai cikin farin yadinsa me sauƙin kuɗi, ga shi sai ƙamshi ya ke yi me daɗi, suna gaisawa da Ummani take ce masa. "Yanzu mu ke maganarka na ce kyan miyar zogalen nan da zan yi ace ka samu kaci. Mutuniyar taka sai ce tayi ai ka daina shan miyar zogale, tuwan ma ka daina ci wai ka zama ɗan gayu". Yana murmushi sosai yace,"Ai Ummani yarinyar nan ƴar adawata ce, buƙulu ne irin nata kawai kuma ko me zata yi sai na ci tunda ba cefanenta ba ne". Duk sai muka yi dariya ina gaida shi, bai amsa gaisuwar ba yace,"Ke da kike buƙulun na ci tuwo nayi dumurmur kamarki, to alqur'an duk baƙin cikin tanda sai mun ci waina, Yarinya ko za ki bindiga sai nayi ƙibar nan da kike baƙin cikin na yi". Dariya muka ƙara yi gaba dayanmu ina cewa,"Wallah Yaya kai dai ka min biyayya kawai, don sai abin da na ce da Ummani ka dai sani". Ummani tace,"Ke asuwa ɗan wake a hotel, wacece ke?". "Autar Ummani mana". Tace,"Su Autar Ummani manja, to ko da kike Auta ai ba ki samu kwatan son da nake masa ba". Haƙoransa suka washe yana cewa,"Ahh tou, Auta daban wanda ake so daban, Yarinya ki kumbura ki fashe ni kam nasha gabanki". Ɓata fuska nayi ina murguɗa baki kaɗan kaɗan yanda na saba yi masa. Ummani ta dube shi tace masa,"To ko ƙafa zaka sa ka hankaɗata gefe ta baka wajen zama". Tashi nayi ina ƴar dariya na ba shi wurin zama akan tabarmar, sai faman dai hararata yake da alama nayi laifin da ban sani ba. Ledar da ya zo da ita ya miƙawa Ummani, haka yake duk lokacin da zai zo sai ya taho mana da wani abun sai in bai da kuɗi kam. haka kuma sai ya zo da alawa duk ranar juma'a ya rabawa yaran gidan da na maƙota, yaran har dakon zuwansa suke ranar juma'a, yanzu ma tuni suka baibaye shi kowa na Yaya Nazifi ba'a bani ba. Hayaniyarsu duk ta cika ni nayi miƙewar da ban shirya ba, lokacin da na dawo ɗauke da lemu da ruwa har ya sallami yaran, na aje masa farantin a gabansa ina kai hannu cikin tsokana zan ɗauke lemun yay saurin ɗaukewa. Lemun ya fara buɗewa ya sha, daɗin ya ratsa shi har da su rufe ido. Sai da ya sauke yake cewa,"Ummani wai har kin fara lemun?". Tace,"Au bafa ka zo ba tunda aka fara ko, ai lemu dai in faɗa maka gashi nan yanata jan kasuwa Alhamdulillah, wannan ɗin ma Allah ne yay da rabonka, don dai ta riga ta ɗauko maka ne amma na ƙawata ne a ajiye mata zaka tafi mata da shi". Suka shiga hirarsu shi da Ummani, nan yake shaida mata ta taya shi murna kuma ta faɗawa Abbaa wani maƙocinsu ya ɗauke shi yaron shago zai ke zama a shagon kullum tun safe har dare, babban shago ne su uku aka saka a ciki amma shine oga don mutumin ya damƙa masa ragamar komai. Cikin nuna jin daɗi Ummani ta ce,"Amma kuwa naji daɗi Nazifi, kai masha Allah da wannan albishir a ranar juma'a babbar rana, ubangiji yasa hanyar arziƙi ce ya bada sa'a ya shige muku gaba. Wallahi na tayaka murna sosai, Allah kauda fitina da idon maƙiya". Shima cikin nuna jin daɗin adu'ar tata yake ta amsawa da amin. Yana daɗa gaya mata yanda tsarin shagon nasu yake, kayan kwalliya ne da kayan jarirai a ciki. A ɓangarena kuwa bayan farin ciki har da tausayinsa naji ya kama ni, don kusan wata uku kenan yana fafutukar neman abun yi don tuni jarinsa ya karye, yanzu babu sana'ar da yake, yana gida kullum sai dai ya fita ya sha iskar gari. okacin da Abbaa ya siyowa Yaya Al'amin ice har da shi ya raba musu, amma shima yanzu babu, idan yana bani tarihin rayuwarsa a irin gwagwarmayar da ya sha har ƙwalla na ke yi masa saboda tausayi, namiji ne shi mai ƙokarin neman na kansa sai dai ubangiji bai saka masa nasibi a nemansa ba, yana da jajircewar neman amma kuma da ya fara sai abu ya lalace masa, in jari ya zuba sai ya karye, haka idan kasuwa ya fara zuwa sai wani abun ya gifta kasuwancin ya lalace, idan tafiye tafiye ya soma zuwa garuruwa itama sai tafiyar ta tsaya masa, sau tari wani aikin shine silar nema musu shi da ƴan uwansa amma kowannensu sai ya samu ci gaba shi kuma sai dai koma baya a kullum, kai a taƙaice ma idan yasa hannu a kasuwancin da ba nasa ba sai kasuwancin mutum ya lalace, shiyasa yafi gane duk abin da zai yi ya kasance nasa ne na kansa, har ya kan ce ina ma ace yayi karatun boko ko da iya sakandire ne wataƙila da ya rage zafi, to amma a hakan ma Alhamdulillah tun da a ɓangaren addinin da zai je lahira da shi babu ta inda aka barsa, kuma ya san komai lokaci ne yana adu'a haka iyaye suna masa. Bayan sun gama magana da Ummani ta miƙe tana ce masa,"Bara in yi na kammala girkin nan ka tafiwa da Ƙawata tuwon nan kaima kuma ka samu ka ci". Har ta nufi kicin kuma sai ta dakata tana ce masa,"Kaga kuwa ma yau idan ka ci gyaranta a karatu wallahi ka zaneta don jiya yawo ta kaɗa suka tafi da ƴan islamiyarsu, taja min faɗa a wurin Abbaanku". Da sigar tsokana na ce,"Ai Yaya da har zamu biyo maka ma sai Safiyya tace muna zuwa zaka fara mana wa'azi". Sai naga yanayinsa ba kamar yanda muka saba da shi ba, banda haka da yanda nayi maganar nan ai ya bani amsa daidai da maganata, haka yake shikam wajen zaro maida martani, ka faɗi ɗaya ya faɗa maka talatin, ga iya baƙar magana me saka cikin mutum ya ƙulle saboda dariya. Gyara zama nayi na fuskance shi sosai, domin kuwa idan har na gansa a irin wannan yanayin to akwai matsala, domin shi ɗin mutum ne me raha, in har ka gansa saɓanin walwala to tabbas akwai damuwa babba, imma ciwon ƙafar Iyam, imma kuma a gida babu abin da za'a ci sai idan kuma ya fita yay buga bugarsa ya rasa abin yi. Kallonsa na ke sosai da nazarin son fahimtarsa, na san babu ɗaya daga cikin abubuwan da na ke tunani, idan Iyam ce jikinta ya tashi shigowarsa za su yi maganar da Ummani, aikin yi kuma yanzu yake murna da mana albishir ɗin ya samu wajen sana'a. To mene matsalar? Hannu na saka na firfita idonsa ya ƙirfta daga kafe wuri ɗaya da yay. "Yaya lafiya dai?". Yasa hannu ya shafi fuskarsa yana cewa,"Lafiya lau, ɗauko kayan karatun na ki da sauri ina da uzuri". Kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya juyo yana kallona, fuskarsa babu wani annuri ya ce,"ba ki ji ba ne?". "Naji Yaya, kawai na damu ne da canjawar yanayinka cikin ƙalilan ɗin mintuna, kuma sai zuciyata yau duk bata yarda da lafiya ɗin da ka ce ba". "Yanzu dai ɗauko littafan muyi abin da ya kamata". Na miƙe jiki a sanyaye na wuce ɗaki, na dawo da jakar littafaina sanye kuma da hijabina. Dardumar da na zo da ita na shimfiɗa nayi zaman karatu ina mai fuskantarsa. Bismillah ya fara muka shiga karatun, ina jin daɗin karatunsa sosai, duk daƙiƙancin mutum ya ɗauki darasi a wajensa sai ya iya kuma sai ya zauna a kansa, bai yi min wani ƙari me yawa ba naji yana rufewa da adu'ar tashi, nayi saurin cewa. "Yaya ko rabi fa bamu yi ba, kuma yau littafi ɗaya za'ai?". "Ehh gwara muyi kaɗan ba zan so shiga lokacin wani". Sai kuma ya kalli agogon ƙurƙurar wayarsa da nake tsokanarsa da ita, ba tare da ya dube ni ba ya ce,"Ƙarfe Biyar da rabi yanzu, duk inda ya ke yana kan hanya sai ki shirya". Furucin nasa yasa na ware ido ina kallonsa da kyau, sai duk naji zuciyata babu daɗi sam, na san yana yi min tuni ne, domin tuntuni yace na ɗaukar masa alƙawarin ba zan tsaya ina bawa wani namiji fuska ba, ba zan tsaya kule kulen samari ba, kuma ba zan tsaya zance da duk wanda ya zo wajena ba. Kuma waccan shekaranjiyan kawai sai ya zo ƙofar gida ya taradda ni da baƙo, dama tun a lokacin da naga yanayin yanda suka gaisa da baƙon na san bai ji daɗin ganinmu tare ba, nima kuma bai san ba'a son raina ne har na ke tsaye da baƙon ba. Hasalima ranar ne na fara ganinsa kuma bisa umarnin Kaka, shi ɗin Yaya ne a wurin Safiyya don ɗan Yayar Ummansu ne, Saurayi ne ba wani babba ba, Air force ne yanzu haka yana cross river can yake aiki sai lokaci zuwa lokaci yake leƙowa ganin iyaye, Wai ya ganni ranar mun je gidan su Safiyya, shine maimakon ya fara tuntuɓata kawai sai ya tafi wurin su Kaka kai tsaye, kuma zuwan ma ba shi kaɗai ba har da manyansa, Abbaa ya gaya masa cewar yay haƙuri ya sanar da su gaskiya akan ba yanzu zai aurar da ni ba, amma sai ce yaji ya amince zai jira zuwa duk lokacin da aka ɗiba masa, shima dama ko da auren aka yi yanzu zai barni nayi karatuna ba zai hanani ba ko da ace aiki ne ma, Kaka yace to shikenan sun ba shi, amma da sharaɗin babu waya babu zuwa zance har sai lokacin da aka ba shi izini amma ya san da cewa kam sun basa Sa'ida, Ya ce ya yarda ya amince, Wan mahaifinsa ya dage akan za su bada kuɗin aure, dole haka aka karɓa naira dubu ɗari ba don son ran Abbaana ba sai don amincewar Kaka. Shine ranar ya zo gida wai na gansa, Safiyya sai wani faman koɗa min shi take wai na yarda ai auren ana yi sai ƙasar da na zaɓa, kuma mahaukacin kuɗi ne da shi, yay bala'in iya soyaya, waye waye ɗinta dai, ni har ta ban haushi ma na ce ita me ya hana ta aure shi, sai ce tayi ai don bai ce yana sonta ba ne, da yace yana sonta da naga yanda ake auren miji na kece raini. Ni dai ranar da kukana na fita, fuska babu yabo babu fallasa muka gaisa da shi, tashin farko kuma tambayar da yay min wai in faɗa masa yayi min zan iya aurensa? Idan ba zan iya aurensa shi ba zai shiga hakkina ba zai haƙura yabawa wasu dama, ko da naga ya fara magana da iyaye saboda hakan shine mutuncinsa, amma ko kuɗin aure da aka bayar dama an bada ne bisa sharaɗin idan nace bana sonsa za'a mayar masa da kayansa. Ni dai kai na ɗaga masa na amincewa kawai, don ko fuskarsa ma ni ban tsaya ƙare mata kallo ba, abu daya zan iya cewa fari ne me matsakaicin tsayi, muka gama gaisawa sama sama yana ta faman gabatar min da kansa da tarihinsa, yana aikin min tambayoyi. Ni da ina ta jinsa kawai zuciyata a matse babu daɗi, to amma ya zanyi! ni ko da naji waye shi na kuma gansa a gabana ko kaɗan ban ji bana sonsa ba, haka ban ji ina sonsa ba, ni dai kawai na san da cewa ina ƙaunar zaɓin Abbaana, kuma zan koyawa zuciyata son zaɓin Abbaana ko da ace zan cutu, ko da zan mutu ta silar hakan. wannan alƙawari ne da na ɗaukarwa kaina ba tun yanzu ba, na shirya zama da duk wanda Abbaana ya zaɓa min matsayin mijin aure ko da ace ina da wani wanda na ke mutuwar so a gefe, to balle ma yanzun babu kowa da na ke so a zuciyata, babu wani da na ke hasashen aure, don haka na san da sannu zuciyata zata amshi soyayyar lieutenant Salim Sadiq Oluwa. Idanuwana suka yi nayi narai narai na shiga wallacewa Yaya Nazifi,"Allah Yaya ko ranar da ka zo ka taradda mu ni ban san da zuwansa ba, ina zaune ne fa kawai Kaka ya ce naje waje ina da baƙo, ina jin nauyin faɗa maka ne shiyasa amma na san Ya Imam zai maka maganar". Kansa ya gyaɗa alamun yaji, bai ƙara cewa da ni komai ba nima nayi shiru ina jin kamar zan saka kuka. Sai bayan wucewar kusan minti goma kana ya kalle ni ta gefen ido yana sosa gemunsa ya ce,"Ki yiwa Ummani magana zan wuce?". Na maƙe kafaɗa ina cewa,"To Yaya ai kana fushi da ni". "Fushi kuma akan me". "To Yaya idan ba fushi ba, ɓacin ran saman fuskarka na menene?". "Kar ki damu Ƙanwata, kawai dai banda muhimmanci ne yanzu a wurinki, matsayina kuma ya canja tun da kin samu abokin rayuwa...". Ji nayi kamar in kai hannu na toshe masa baki, amma babu damar hakan. "Kayi haƙuri don Allah Yaya, kai fa Yayana ne muna tare har abada, kai me aurar da ni ne, kuma ni wallahi Allah matsayinka bai canja ba a wurina...". "Ya kike wallacewa bayan ga zahiri, idan da ne ai duk yanda ake ciki kafin ki fita wajensa ma sai kin kira ni kin faɗa min, karo na farko da ba ki nemi shawarata ba, ai shikenan na gode". "Kayi haƙuri Yaya don Allah, ba ni da wani zaɓi ne. Amma ai kace kai zaka tayani zaɓar mijin aure, idan bai yi ba shikenan". Murmushi yay wanda bai kai har ƙasan ransa ba ya ce,"Yayi mana Ƙanwata, ai yana da kuɗi kuma yana da ƙwaƙwƙwaran aikin yi, yana da wurin ajiye ki, zai iya riƙe mace kuma ko yanzu aka ce ya fito zai kawo lefe kuma a shirya biki cikin kwanaki ƙalilan, babban ma'aikaci irin wannan ba abun yarwa ba ne". Na ɗan juya idanuna ina daɗa jin wani iri cikin raina. Na dakatar da shi da cewa,"Yaya ni duk ba wannan ba. miji me nagarta na ke so, me ilimin addini, tarin kuɗinsa bai dame ni ba, ni dai ya so ni kawai da dukkan zuciyarsa, in dai akwai rufin asirin da zamu ci musha mu zauna a kowanne irin muhalli ya ishe ni. Kuma kaga shi fa ban san ya halinsa yake ba, ban san ɗabi'unsa ba, addininsa ya yake? Nagartarsa ya take? kuma su irinsu ka san matansu basa samun lokacinsu saboda irin aikinsu, ni kuma mijina lokacinsa, soyayyarsa, yardarsa da kulawarsa na ke biɗa. Ni Yaya miji irinka kawai na ke so kayi min adu'a Allah yasa shima haka yake". Shirunsa yasa na ɗago ina kallon, na ce"Yaya". Sai kuma na rasa abun faɗa, ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yace,"Kin san me?". Na girgiza masa kaina alamar a'a. "Ina tsoron rabuwa da ke ne Ƙanwata saboda nayi sabo da ke fiye da tunanin me tunani". Na karayar da kaina na ce,"To me zai rabamu kuma? Aure fa kawai zan yi". "Au aure ne ma kawai? Tunaninki mijinki zai yarda da alaƙarmu ne? A irin wannan shaƙuwar tamu? Ko ni ina tsananin kishinki balle mijin da za ki aura, Miji ma irin wannan mutumin, daga lokacin da kika yi aure Sa'ida duk wata alaƙa da ke tsakanina da ke ta rushe babu ita". Tsorata nayi naja da baya saboda yanda yay furucin cikin huci. Yanayin kuma da ban taɓa ganinsa a ciki ba, kawai sai hawaye ya fara sakko min nasa hannu ina gogewa ina ce masa. "Yaya indai baka sonsa zan haƙura da shi, ni bana son abin da zai rabamu". "Ban zauna da shi ban san waye ba amma daga yanayin da na gansa ni kaina zan iya zaɓa miki shi, to amma bai yi min ba, idan na ce bana son aurenki da shi Ya za ki da su Abbaa?". "Nima ban sani ba amma ba zan iya bijirewa zaɓinsu ba, zan faɗa masa ya ce musu ya janye. Yaya zan fasa aure in har alaƙarmu da kai zata taɓu". Na faɗi hakan ina kuka sosai, kuma kawai sai gani nayi ya miƙe ya zura takalmansa ya fice. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR04FT5* _Not Edited, Plss avoid error mistakes._ ________________________ Cikin sati biyu kamar yanda Abbaa ya yanke hukunci aka kawo lefena akwatu biyu maƙil da kaya, sai shinkafa kwano bakwai da dardumar sallah da ƙur'ani da littafan addini. ba ƙaramin ƙoƙarin Yaya Nazifi na gani ba, kuma sosai naji daɗi tunma da naji yanda ake ta santin kayan da ya zuba da yaba masa a irin ƙoƙarin da yay, a lokacin atamfa mai mugun tsada dubu biyu da ɗari biyar ce zuwa uku, kusan duk kayan da aka ɗaga sai Umma ta faɗi tsadarsu da ke ƴar kasuwa ce ita. Don haka murna ba ni ɗaya ba har da Ummani domin kuwa an bawa maƙiya kunya don kaf ƴaƴan Baba Tijjani da aka aurar ba wadda ta sami kaya kamar nawa. To tun fa daga nan hidima sai ta ɓalle a gidanmu aka shiga shirye shiryen biki, shi Abbaa bai taɓa tsammanin Yaya Nazifi zai iya kawo lefe a ɗan ƙanƙanin lokacin da yanke masa ba, ya tauna tsakuwa ne domin aya taji tsoro, sai ga shi kuma yaga saɓanin tunaninsa, don haka a maimakon ya matse Yaya Nazifi sai ya zamana kansa ya ɗanawa tarko, domin kuwa dai a wannan lokacin ana cikin rufin asiri ne amma cikin jin jiki ake, sam bai da wasu kuɗin aurar da ni, na abincin gida ma da ƙaƙa ake samu, sai Ummani tayi cinikin lemo ake yin cefane da siyan abubuwan buƙata, ga lokacin jikin Kaka sai a hankali don haka duk wasu ƴan kuɗi da suka samo akan magungunansa suke tafiya, kuma kullum ana hanyar asibiti, don hatta kuɗin jarabawata na waec sai bashi Abbaa yaci ya biya acewarsa gwara na haɗa jarabawa duka biyun. Ni dai sai ya zama gaba ɗaya bana cikin farin ciki, kamar ma ba wata amarya ba, na yi mugun shiga damuwa da ganin yanda iyayena duk suka takura, babu wani me walwala a cikinsu, ko da yaushe suna jugum sai walwalar ƙarfin hali da suke kawai. na shiga damuwa sosai hankalina ya ƙara tashi na rame domin kuwa Abbaa sam a lokacin banda gaisuwata da yake amsawa ba wani magana da ke ƙara haɗa ni da shi, Ummani ce ke ta tausarsa a hakan ma. Ana saura kwanaki goma biki Yaya Nazifi ya zo, na saka masa kuka akan a ɗaga biki ni kam, yaga na tashi hankalina sosai to da yake shima yana da buƙatar ɗaga ƙafa sai yace zai yi magana da Malam sai su zo a sami Abbaa. Ni dai na san da kamar wuya domin mahaifina kaifi ɗaya ne, ba ya sauka akan maganarsa, shi ya yanke don haka ba zai taɓa janyewa ba na sani, amma wataƙila a wannan karan ya sauko, kuma abin da ya ɗaga min hankali naje gaishe shi da safe naji suna maganar shi da Ummani akan ko kuɗin katifa ma babu balle sauran kayan ɗaki da ake buƙata, gwara ita Ummani ma tun da jimawa an taɓa kawo mata tallan tukwane tayi dabarar siya bayan su itama bata ajiye komai na kicin ba domin duk basu tsammaci zuwan lokacin aurena yanzu ba, yanda suke kaishi da nisa ashe ba haka Allah ya shirya lamarinsa ba, aure ƙanin mutuwa ne idan ya zo babu yacca za'ai. Malam suka zo suka sami Abbaa da batun a ɗaga aure yace sam ai shi magana ɗaya yake yi, shi dai zuwa ranar asabar zai ɗaura min aure babu ruwansa da inda Nazifi zai ajiye ni, yayi min abin da na ke so ya kuma fita hakkina. Abin da ya rage tsakaninsa da Nazifi riƙe masa ni amana da kuma cika alƙawarin da ya ɗauka na barina in yi karatu a gidansa, shima kuma ta ɓangarensa zai cika alƙawarin da ya ɗauka na ba zai bar Yaya Nazifi da ɗaukar nauyin karatuna ba shi zai ci gaba da ɗauka matsayinsa na mahaifina da hakkin hakan yake akansa, duk abin da ya shafi katatuna a gidan Nazifi shi a mahaifina shi ke da hidimarsa. To haka dai da karime karimen abubuwa a ɗau wancan a siyar a ɗauka wancan a siyar, Yayyuna su kawo ɗan abin da suka fita suka samo da haka aka haɗa aka min kayan ɗaki, Ummani kuwa kusan duk wasu kayanta masu daraja sai da ta ɗaga ta siyar aka siya min kayan kicin. Ranar lahadi aka ɗaura aure, ɗaurin auren da ya tara mutane da yawa. Ranar kam nayi kuka sosai na kuma yi mugun danasanin ɗaga hankalin iyayena da nayi akan auren nan, haka naji ina ma ban san Nazifi ba a rayuwata, domin ranar sai bashin kayan abinci aka karɓo aka yi abincin biki. Daren ranar aka kaini gidana bayan tarin nasihohin da na sha daga wajen mahaifina masu ratsa jiki, irin nasihar da yake ta min akan zaman aure sai naji ina ma ace a warware wannan auren. hatta shi kansa sai da yay kukan rabuwa da ni, Ummani kam da ƙyar aka ɓanɓare ni daga jikinta, abin da ya ƙara sakani kuka a lokacin yanda Abbaana ya dinƙa bani haƙuri akan ƴan kayan da suka yi ƙoƙari wajen siya min, yana faɗa min don Allah kar nayi fushi in sha Allahu bayan aure da ya samu kuɗi zai sauya min komai ya siya min sababbi masu kyau da ƙarko, kuma za su ƙaro min kaya da yawa indai kuɗi suka zo hannunsa, ya san waɗannan sai dai nayi maleji, kuma yasan za'a iya min dariya idan aka gani tunda tsofaffi ne aka siya amma kar na damu sa duk wanda yay min dariya, wata rana zai saka ni dariyar in Allah ya yarda, kuma fushin da yay da ni akan lamarin auren nayi haƙuri, sannan da zarar naji an fara biyan kuɗin jamb na faɗa masa ya tura min kuɗin registration, haka aka fita da ni daga gidanmu kamar zan shiɗe saboda kewar iyayena da zan yi. Yashaik ne ya aro motar gidan da yake direba aka kaini a ciki saboda shi Yaya Nazifi ba abokai ne da shi ba, Hamisu ne shi kuma adaidata yake ja don haka shine ma yay ƙoƙarin tattaro tawagar masu adaidaita sahu aka dinga ɗiban ƴan kai amarya. To a rayuwar gidan aurenmu babu abin da zance da ubangiji sai godiya gare shi da ya mallaka min Yaya Nazifi matsayin mijina, domin kuwa nayi dacen samun miji na gari da ya san darajar mace, wata iriyar rayuwa muke shimfiɗawa me cike da zallar soyayya da ba zamu taɓa mancewa da ita ba a tarihin rayuwarmu, Yanda Yaya yake ji da ni tamkar zai haɗiye ni da soyayyarsa, zazzafar ƙauna yake nuna min ta kowanne ɓangare, bai taɓa bari na koka ba, motsi kaɗan ya tambaye ni me nake so, me zai yi min, duk wani abu da ya san ina so sai yay ƙoƙarin samar min shi, haka idan ya fita ya tashi dawowa da ɗan namansa ko kifi ko kayan marmari, a gida ma mu girki me kyau da rai da lafiya ko gidan wasu masu kuɗin sai haka, haka idan ya fita aiki shine baro shago da rana ya zo ya duba ni sannan ya koma, kullum faɗamin yake son da yake min baida adadi, domin samun macen aure ta gari irina da wuyar samu, don haka yay min alƙawarin mutuwa ce kawai zata rabamu, kuma yay min alƙwarin zai inganta rayuwata da dukkan ƙarfinsa da ikonsa. Ta ɓangaren ƴan uwansa ma haka, nuna min so suke tamkar zasu haɗiye ni, komai suka samo a rakito akawo min, abinci wannan sai naga damar girkawa don da wuri ake gama abinci acan a kawo min, kuma da yake bamu da nisa sosai kusan kullum ina gidan don Iyam bata da wani batu a bakinta sai na Sa'idata, Nazifi turo Sa'ida ta zauna kusa da ni idan ka dawo daga aiki sai ka zo ku tafi tare. Irin ƙaunar da sirikata ke nuna min sai nake jin kamar mahaifiyata, komai Iyam taci sai ta bani, duk wani sirri ko shawara ko damuwarta ni ɗin nan dai nice, sai ta faɗa min ma abin da ya shafeta bata faɗawa ɗanta ba, har shima yake tsokana da cewa gaskiya zai yi ƙarata wurin alƙali na ƙwace masa mahaifiya. To haka ma babbar Yayarsu Yaya Maijidda, matar nan yanda ta ɗauke ni ko yanda ta ɗauki Nazifi da suke ciki ɗaya albarka, itama komai matar ƙaninta Ƙarami, har facalolina suka fara jin haushin hakan, bini bini ta kira waya ta tambaya ya muke, ban da wata matsala ko, kuma Ƙarami ba ya min komai ko? Idan yana min wani abu kar na ɓoye na kira na faɗa mata. To ni kuwa ƙarar me zan kai mata akan mijin da ya tattara dukkan soyayyarsa da ƙaunarsa, kulawarsa da hidimtarwasa ya ɗora akaina? Ai ni babu abin da zance da Nazifi a rayuwa. Kamar yanda Abbaa ya faɗa min shekara guda da aurena ya canja min kayan ɗaki sababbi masu kyau, kuma ba'a kwashe tsofaffin ba yace duk na haɗa, nayi murna sosai da farin ciki tare da adu'a wa mahaifina. Dama ɗakuna biyu ne don haka sai na mayar da tsofaffin ƙaramin ɗakin, da yake kujera ɗaya ce dama duk sai ya ɗauke ɗakin bai cunkushe ba, wancan ɗakin kuma da yafi girma can na bar sababbin kujeruna har uku na bar shi a matsayin ɗakin Hubbi, don har labulaye Abbaa ya canja min, dama waɗancan wasu ajiyayyu ne na Ummani da bata saka su aka fito min da su. Jarabawar waec da neco ɗinmu ta fito a lokacin kuma sai ban ci ba duk biyun, a waec bani da english da biology, neco kuma bani da english da maths, haka na sha kukana Abbaa yay ta lallashina yace in bari idan za'a kuma yin wata sai na ƙara zanawa, to ita kuma lokacin da ya zo sai ya zamana babu kuɗi har aka rufe biya, amma haka Abbaa yay ta ban haƙuri da cewa in jira lokaci Yashaik yace masa ana zana wata da ake biyan kuɗi masu yawa a ci, to idan za'a yi indai da kuɗi zai biya min na kwantar da hankalina. Cikin shekaru biyu da aurenmu al'amura suka fara taɓarɓarewa Hubbi, rana ɗaya megidansa yace ya saida shagonsa, ya sallami su Hubbi da dubu tamanin tamanin yana basu haƙuri. Wannan rasa shago da Hubbi yay shine mafarin ƙalubalen da muka fara fuskanta, kuɗin sallamar da aka ba shi da su ya samu ya buɗe tireda a ƙofar gida yake siyar da provision. Sauran kuɗin da yay saura kuma ya siyo kayan abinci na ɗan lokaci ya ajiye, sai ƴar dubu huɗu da ya bani yace na ɓoye ko da wata buƙatar ta ujila zata ta so. To yau da gobe kayan abinci duk suka ƙare, tireda kuma sai dai ace an gode Allah domin tuni itama kayan ciki suka ƙare kuma ya rasa ta ina kuɗi suka tafi, abun dai ba'a cewa komai lokaci guda komai ya tsaya masa cak. Kullum zai fita amma haka zai je ya dawo babu wani ƙwarin jiki, ya buga duk ta inda zai buga ya rasa wata sana'a da zai kama, sai dai ya fita haka yaje wajen su Yayan Shago inda suke leburanci ya zauna wajensu ya ɗan taya su wani abun, su kuma a kuɗin sallamar da ake basu a ciki suke sammasa, to ɗan kuɗin ba wani me yawa ba ne idan yazo da su basa kaiwa ko'ina, iyaka abin da za'aci na lokaci ɗaya ne kawai ake samu, to don ma Allah yasa babu yara da damuwar da zamu shiga sai tafi haka. Rayuwa taci gaba da tafiya har aka zo gaɓar da kullum sai dai ya fita haka ya dawo babu komai, ɗan na garin kwakin ma da ake siyowa aci yanzu ba ya samuwa, ƙanzon da muka shanya duk ya ƙare, muka koma sai dai wata rana muci watarana kuma haka zamu yini mu kwana da yunwa, ruwa kawai muke sha. Wannan hali da muka shiga na tsananin babu ita tasa na koma yin waya gida ina yin dabara na ce ni abincin gida nake so ci idan anyi a aiko min da shi, har aka fara zargin ko ciki ne da ni, to fa da wannan ne ma muke samu muci rana da dare, dama na safe ba'a batunsa, wataran kuma idan na tashi sai in je can gidansu na yini to acan zanci na rana idan dare yay kuma a zubo mana mu taho da shi, kuma duk wannan hali da muke ciki babu wanda ya sani domin kuwa muna da wadatar zuciyar da babu wanda zai ganmu ko ya zo gidan ya gane halin da muke ciki, fes fes zaka ganmu cikin annuri da walwala, gidanmu ɗasɗas babu wani alamar tsanani. To abu fa yaci tura babu wani sauƙi sai tsanani, talauci yay mana ƙatutu, ko lalura muke sai dai mu roƙi Allah ya bamu lafiya magani kau biyar ɗin siya ma babu. Da haka dai na bawa Hubbi shawarar ko in nemi sana'a ko da aikatau ne nake yi, yace bai amince ba sam, zai ci gaba da jajircewa wajen neman abun yi. Kullum cikin hawayen tausayin halin da muke ciki na ke, ga mijina me tsananin tawakkali wanda ko bacci cikakke baya iya yi haka yake kwana yana gayawa Allah ya kawo masa ɗauki da mafita. Watarana kawai na yanke shawara ni ɗaya domin ba zai yiwu muci gaba da zama a haka ba, ba tare da sanin Hubbi ba na nemo dillaliya ta siya kayan ɗaya ɗakina da sabuwar kujerata guda ɗaya. Hubbi ya dawo da daddare na damƙa masa naira dubu talatin a hannunsa. Ya kalle ni yana tambayar Habibity ina kika samo damin kuɗi haka sannan ne nake sanar da shi yanda aka yi. Tsabar farin ciki har da ƙwallarsa, ya rungume ni jikinsa yana saka min albarka da godiya. A washegari kuwa yaje kasuwa ya siyo buhun garin masara da shinkafar hausa, yasa kuma aka yiwa tiredarsa ƴan gyare gyare, ya fara aunar da garin masara da shinkafa dama babu irin masu awo a cikin layin sai anje titi, ai ko kan kace me wannan ƴan unguwa an ganewa wajen, ni kuma cikin gida sai na ke sana'ar wanki da guga, haka zanyi wanki me uban yawa, idan dare yayi Hubbi ya tayani guga, kuma ɗan abin da za'a samu bai kai ya kawo ba amma a hakan dai babu laifi, haka muka haɗu da taimakon juna muna rufawa kanmu asiri. Muna cikin wannan rayuwar dai Allah ya kuma kawo mana jarabawa, shima awon da Hubbi ke yi aka zo aka sace tiredar, rana ta farko da na taɓa ganin hawayen mijina wanda yay matuƙar ɗaga hankalina ranar har ban yi bacci ba. Tun daga nan kuma Hubbi ya sare yace shi ya gaji, ta kai ta kawo idan ma ya fita da anga ya dosa waje za'a fara ƙusƙus ana maula ta kawo shi, masu shago kuwa duk sun sauya masa fuska saboda basa son ba shi bashin kayan abinci don ba'a samun damar biya da wuri. Duk ƙarfin hali irin na Hubbi haka zuciyarsa ta mutu yace kawai ubangiji yay ikonsa akanmu, har ta kai ga ya kusa yin saɓo sai da na rufe masa baki. Tsaka da wannan tashin hankalin da muke ciki na kwashi kujeruna duka naje na siyar, kayan kicin ɗina ma haka duk na tattara masu kyan na siyar da sitturuna masu kyau, don har ga Allah na gaji da ganin mijina na zaman jugum yana hawaye, na gaji kuma da jin yana fita mutane na gulmarsa suna gudunsa. Don haka kuɗin da na haɗa dubu arba'in da biyar na kaiwa maƙocinmu na ce don Allah ya nema mana aron adaidaita sahu ga wani abu zamu rage, a hankali kuma sai a dinƙa cikawa, amma don Allah kar ya bari mijina ya san nice na zo da zancen kawai yace shine ya taimaka masa. Mutumin da ke yana da mutunci a washe gari kuwa sai ga shi ya kira Hubbi, suka je can wurin karɓar babur ɗin aka saka hannu da komai tare da yarjejeniyar cikin shekara guda zai gama biyan kuɗin babur ya zama na shi, ya dawo yana ta farin ciki yana shaida min yanda akai, ni dai ko kusa ban nuna masa ma ina da sa hannu a lamarin ba, haka muka kwana cikin farin ciki da adu'ar Allah sa zuwan ƙarshen komai kenan. To a ranar farko da Hubbi ya fara fita da babur ɗin yay hatsari babba don babur ɗin sai da yay raga raga, shi kuma ya samu karaya har biyu a cinya. Ya sha wuya ba kaɗan ba, a wannan lokacin ne kuma aka fara fuskantar halin da muke ciki bayan dawowarmu daga asibiti, Ummani taga bata ga kujeruna ba ko da ta tambaye ni nace mata ai ina so a sauya min su ne mun kai wajen gyara. Hubbi na tsaka da ciwo jikin Iyam ma ya tsananta, ciwon nono da sikari ya tsananta mata sosai, har ana tunanin sai an yake nono ɗaya, tashin hankalin da muka shiga a wannan lokacin Allah kaɗai ya bamu ƙarfin tawakkalin sake karɓar jarabawar a karo na barkatai. Sama da wata uku Iyam na kwance a asibiti anata fama, nan gida ma haka karayar Hubbi da ake ta fama sai tayi sauƙi sai ciwo ya koma gidan jiya, ni da shi duk muka fita a hayyacinmu muka rame kamar kuɗin guzuri. Ni dai a hakan na ci gaba da jajircewa a wanki da guga wajen tallafa masa, ban taɓa nuna masa na gaji ba, haka ban taɓa nuna bana tare da shi ba. kullum ma ni ce me tausarsa da kwantar masa da hankali, ƙarfen da yake dogarawa da shi ya lalace magungunansa suka ƙare, muka rasa ya zamu yi, ga can ana fama da Iyam wadda itama cukucuku ake tayi wajen neman kuɗi nata magungunan. Ana haka Abbaa ya turo min dubu saba'in yace in je nayi rijistireshon na jamb da na waec, abun da yay saura kuma na adana su da kyau idan jarabawar ta fito na ci sai na biya kuɗin makaranta da su, ya san ba zasu isa ba amma zai ke turo min wani abu ana tarawa a hankali a hankali. To da yake ba'a ma fara registration ɗin ba da saura kusan wata biyu, Hubbi yace to na ɗauko kuɗin mu siyo kayan abinci, a siya maganin Iyam shima a siya nasa, kafin lokacin in sha Allahu za'a mayar da kuɗin. Hakan kuwa aka yi cikin ikon ubangiji kuma sauƙi ya samu, sai dai ba ya wani iya fita kullum yana gida. Iyama jikinta yay sauƙi sosai don dubu talatin da ake nema duka muka ware aka kai asibitin. To da haka muka ci gaba da rayuwarmu cikin rufin asirin Allah, idan nayi wanki shi zai guga, ya fara karɓo mana kalwa ma a gida ina siyarwa. Watarana da rana muna zaune a tsakar gida muna sauraron rediyo muka ji labarin wani attajiri da ke taimakawa talakawa, aka faɗi sunansa da adireshinsa. Na kalli Hubbi naga kamar ma bai ji abin da aka ce ba, da daddare muna cin abinci na taso da maganar, ya girgiza kansa yace ba zai je ba shi yanzu yana tsoron zuwa neman taimakon wani. Nayi ta tausarsa sam yaƙi amincewa yace shi fa ba zai je ba, haka muka kwanta zuciyata fal da saƙe saƙe. Ana kiran farko na tashi nayi alwala na shirya, na ɗauki takarda da biro nayi rubutu na ajiye kusa da Hubbi, a ciki na faɗa masa cewar zanje can wajen mutumin ko Allah zai sa a dace, idan ya farka yaga zai iya biyo ni to. Yana ta barci bai ma sani ba na tsallake na fita cikin mamakon ruwan saman da ake ta zugawa tun bayan isha'i, ga ban da kuɗin mota amma ban karaya ba sam haka na taka tun daga Yakasai har Nasarawa GRA, tun ƙarfe huɗu da rabi na dare ba ni na isa ba sai ƙarfe shida da rabi saura, ba tare da naji tsoron gamuwa da komai ba hasalima ban tunanin wani abun cutarwa ba, ni dai ina cikin adu'a da zullumin fatan Allah sa zuwan nawa ya zama alkhairi. Ni ce ta uku a layin mata kuwa, Alhaji Isma'il Fari bai sami fitowa ba sai ƙarfe takwas, ban ma san layi ya zo kaina ba saboda ina can ina gyangyaɗi, sai da wata ta zungure ni kafin nan na miƙe da ƙyar saboda ciwon jiki da kuma yacca nake jin cikina a ɗaure. A kallon farko da na yiwa mutumin a raina naji in sha Allahu za'a dace, haka na zauna ina faɗa masa matsalar da muke ciki, tun ina hawaye a hankali har na koma kuka sosai, matarsa tana kusa da shi itama ta tausaya min, ya jinjina kansa yana faɗa min cewa in sha Allahu zai yi mana abin da zai iya. Ya kalli matarsa ya ce ta lissafo dubu ɗari biyar ta ba shi, ni dai kaina na ƙasa zuciyata na ta bugawa, tausayin kanmu na ƙara lulluɓe ni. tunanin da na ke ya katse lokacin da naji Alhaji Fari na cewa,_"Iyakar abin da na ke iya taimakawa da shi matsayin jari dubu ɗari da hamsin ne, to amma tsakani da Allah duk a cikin masu zuwa neman taimako matsalarku tafi taɓa ni, don haka ga wannan dubu ɗari biyar na muku domin Allah"._ Yay furucin a daidai lokacin da Hubbi ya shigo ciki wanda aka yi masa iso, tsananin farin ciki ban san lokacin da na miƙe daga gaban Alhaji Fari ba riƙe da kuɗin a hannuna ina ta karkarwa jiki naje gaban Hubbi ina nuna masa. Na kama hannunsa na damƙa masa ina faɗin,"Hubbi ga shi na ka ne halak malak, Allah ya amsa adu'armu Hubbi yaji kukanmu, Allah yasa ƙarshen wahalarka kenan yasa kuma silar ɗumbin arziƙinka ne mara yankewa". Kuma maganar da Alhaji Fari ya ƙara yi ita tasa na juya gare shi ina jin furucin da yake kamar a mafarki, faɗa yake wai ya bawa Hubbi shago ɗaya kyauta a ɗaga daga cikin plazar da yake da ita a janbulo. Don haka yasa rana zai sa ayi masa iso zuwa shagon, abun da ya rage masa kawai ya zuba kaya. Tsabagen farin ciki sai muka rasa da wanne kalami ma zamu yiwa Alhaji Fari godiya, ga kayan abinci ma da yasa aka haɗo mu da shi, buhun shinkafa biyu, katan na taliya biyu, sai galan ɗin manja da man gyaɗa, haka muka dawo gida da murna sosai mara misaltuwa, Hubbi ya dinƙa min godiya dasa min albarka. Kuma a wannan ranar ne da muka je duba Iyam Hubbi ke labarta mata duk abubuwan da suka faru tun daga farko har wa yau, Iyam taji na ƙara shiga ranta, ta kasa ɓoyewa sai da ta sanar da Malam da Yaya, waɗanda suma suka dinga min godiya da irin halaccin da na nunawa ɗansu, wanda in ace wata ce tuni ta rabu da shi amma ni haka na rayu da shi cikin tsanani da wahala, ba tare da na taɓa fallasa sirrin matsalar mu ba. Allah alqawiyu ashe wannan shine silar arziƙin Hubbi, domin kuwa cikin ƙanƙanin lokaci da zuba kaya da yay a shagon Allah yasa masa nasibi shagon ya bunƙasa, dama shaddodi yake siyarwa nan da nan sai ga shi yana rufa riba da wasu ɗaruruwan kuɗaɗe, kuma kafin kace me wannan Hubbi ya zama Alhaji, da yana sawa a shigo masa da kaya daga baya kuma sai ya koma fita da kansa yana shigo da su. Tashin farko ya ƙerawa iyayensa sabon gida na gani na faɗa, bayan ya gama da su muma ya tamfatsa mana namu anan ɗorayi salanta link 3, gida na haɗuwa, gata iya gata na gani domin kuwa gwalagwalai ya dinƙa siya min, Yayyuna na roƙe shi duk ya bisu da jarin naira miliyan ɗai ɗai. Da nayi masa maganar ci gaba da karatuna ya nuna shi kamar ma bai san da zancen ba, ga Abbaa na ta min magana akan naje nayi registration yaji an fara, shi kuma da na masa zancen sai ya ɓata rai har ma yace min kar na ƙara tambayarsa wani kuɗin makaranta, wannan kuma shine ƙalubale na farko da na fara fuskanta daga gare shi bayan canjin rayuwar da muka samu, kafin ƙalubalen rashin haihuwa ya biyo baya daga ta ɓangarensa da ƴan uwansa har kawo lokacin yanzu da ya ƙaro aure. *DAWOWA LABARI.* _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR03FT5* Ummani ta fito ta sameni durƙushe ina kuka, ta shiga tambayana dalilin kukan, ni dai ko da na ɗago ido na zube akanta sai na rasa amsar bata, domin ni kaina ban san dalilin kukan nawa ba, na dai san kawai zuciyata babu daɗi. Ta matsa min da tambaya ban san lokacin da na ce mata,"Yaya ne yaƙi min ƙari saboda yaci gyarana a karatu". "To ai maganinki, Sa'ida jiya kaf ba ki duba karatunki ba, ba na so ki fara saka wasa a karatu wallahi. Kuma ai da gaskiyarsa idan kin iya ya ƙara miki. Yanzu yana ina?". "Wai yaje ya dawo". Na faɗa ina goge hawayen fuskata. "To ga abincin idan ya zo sai ya tafi da shi. Nasa yana cikin ƙaramin flask naga magriba tayi ba lallai ya tsaya ci anan ba, babbar kular kuma ya kaiwa Iyam. Ni zan shiga daga ciki zan yi lazimi". Tana gama faɗin hakan ta wuce ɗakinta. Nafi ƙarfin minti goma sha zaune ni ɗaya ina ta jira in ga ko zai dawo amma shiru. Tashi nayi na ɗauka ledar kayan abincin na shiga ɗakina, na je ɗakin Ummani na ɗauko wayarta na dawo na zauna na kira tasa wayar har sau uku bai ɗaga ba. Daga ƙarshe na yanke shawarar tura masa message, sai ya dawo min da reply ɗin cewa zai aiko Adamu ya karɓar masa yanzu yay nisa. Da magriba kuwa Adamu ya zo ya karɓa dama ina ta gudun kar Ummani ta shigo ɗakin ta gani. Tun daga wannan ranar kuma shikenan sai Yaya Nazifi ya ɗauke ƙafa daga gidanmu, zuwa gaida Kaka ma da ya saba duk ya daina, kowa kuma sai cigiyarsa yake yi a gidanmu, da an tashi sai a tambaye ni, nima sai na rasa amsar da zan ke ba su. Abbaa yake cewa ƙila ko yanayin kasuwar tasu ne don ranar nan yaje can wajensa sun gaisa, Wata rana ma sai Yaya Al'amin ya ce mana ai sun haɗu can shagon yake ya faɗa masa yanzu ba ya samun lokaci shiyasa bai leƙowa, amma ya gaidar masa da kowa. Ni dai duk sai na takura kullum cikin tunani, kawai abin da zuciyata ta gama yankewa shine zan sanarwa da su Abbaa a mayarwa da Salim kuɗinsa, domin a kaf nazarin da na zauna nayi Salim shine zai yanke alaƙata da Yaya Nazifi, ni kuma ko kusa bana son abunda zai raba zumuncinmu domin kallo ɗaya na ke masa da yayyena maza waɗanda muka fito ciki ɗaya, don haka zan sanarwa da Salim tun wuri Yaya Nazifi, idan yaga zai iya ɗaukar alaƙarmu da shi ko bayan aure shikenan, idan bai iyawa to ni bai isa ya raba ni da shi ba. Bayan watanni sai ga Salim ya zo gidanmu, ranar da ƙyar Abbaa ya amince na fita wajensa domin cewa yay ai ba haka aka yi da shi ba, yanda aka yi ko da zai fara zuwa muna gaisawa sai nayi candy tukunna, Abbaa yay ta faɗa sosai yana cewa shi baya son irin haka dalilin da yasa yaƙi karɓar kuɗinsa kenan amma Kaka ya matsa. Ranar kuwa na sami damar nunawa Salim duk wata shaidar da zai fahimci ba na sonsa ko kaɗan balle sha'awar zaman aure da shi, ban fito da baki na faɗa masa cewa bana sonsa ba, amma in dai shi me hankali ne zai gane inda na dosa, haka ya zo da manyan ledojinsa na sahad store guda biyu amma naƙi karɓa. Kuma ban san ya akai ba bayan kwana biyu da zuwan nasa sai Ummani ke ce min Iyayen Salim sun zo sun karɓi kuɗinsu, wai shi yana so yay aure yanzu don haka idan ni matarsa ce komin daɗewa zai mallake ni amma a yanzu ya samu wata yarinyar da iyayenta suka shirya aurar da ita. Ranar kamar nayi me don farin ciki, dama ni har ga Allah ko ba don Yaya ba zan aure shi ne kawai saboda zaɓin mahaifina. Washe gari da muka je makaranta Safiyya ƙememe taƙi kula ni, na damu da fushinta sosai, kuma ko da na takura da roƙonta akan me na mata sai tace bata yi zaton zanƙi wani ɗan uwanta ba, na ce ai ba ƙinsa nayi ba shi yace ya sami wata matar, tace ƙarya ne dama akan me ba zai ce haka ba tunda na nuna masa bana ƙaunarsa. haka dai tayi ta maganganun rashin jin daɗin abin da nayi, tace kuma ta san ba kowa ne sila ba sai Yaya Nazifi don haka wallahi ta tsane shi, ba don ya shigo rayuwata ba tana da tabbacin babu dalilin da zai sa in ƙi Yayanta ko don amintar da ke tsakaninmu, ta san zan so shi ko saboda ita. Ni dai nayi ta bata haƙuri da ƙoƙarin fahimtar da ita amma taƙi saurare na sam, har da cewa ni munafuka ce dama can son Nazifin na ke yi kuma ba zan burgeta ba sai na aure shi. Sai ma ta bani dariya, ni dai abin da na sani tsakanina da Allah bayan son ƴan uwantaka da nake masa bana masa irin son da suke tunani, amma kowa ya gagara fahimtata, sun kasa ganewa cewa Allah ne ya haɗa jinina da shi, ranar ko da aka tashi makaranta ƙin tsaya ni tayi tai tafiyarta, ni kuma tafiyar nata ma sai yay min daɗi domin kuwa ina son zuwa shagon Yaya Nazifi sai dai in har da ita ban san ya zan yi na je ba. Na hau adaidaita sahu ya kai ni Jakara kasuwa, da tambaya na je har Shagon Yaya, lokacin yana alwalar azahar na isa ƙofar shagon, tun kallo ɗaya da yay min bai ƙara ba ya ci gaba da alwalarsa, sai dai na san ko bai faɗa ba yay mamakin zuwan nawa domin naga hakan a ƙwayar idonsa a kallon farko da yay min. Ina tsaye gabansa har ya kammala alwalar, ya miƙe ya shiga ciki ya bar ni tsaye, ina jiyosa yana cewa da yaran shagon da suke tare su ɗan ba shi aron wajen yay baƙuwa, sai da suka fito dukansu kana yay min wani duba da cewa. "Bismillah". Na taka a hankali zuwa ciki, yay min nuni da wata kujerar katako na zauna, yana warware hannun rigarsa da ya naɗe ya ce,"Zan je masallaci ina dawowa". Ina ta kallonsa dai ban ce komai ba ya fita ya turo ƙofan shagon, sai naga duk ya faɗa idanunsa sun yi loko kamar ma yay jinya. Ina zaune shiru ni ɗaya ina ta kallon kayayyakin shagon, ma sha Allah akwai kaya sosai kuma shagon babba ne da alama ana ciniki ba kaɗan ba. Bayan wasu mintuna ya dawo hanunsa da leda baƙa, ya aje kan glass ɗin gabana yana cewa. "Ga lemu. Akwai pure water a ciki ko za ki alwala". Ya faɗa yana miƙo min wani botiki gabana, a ciki nayi alwalar ya shimfiɗa min sallaya daga ciki nayi sallar, sai yace na zauna anan ba sai na dawo bakin ƙofa ba saboda masu wucewa. Ni dai duk bana jin daɗi saboda rashin sakin fuskarsa, ya kuma nuna bai murna da zuwan nawa. Nayi shiru shi kuma yana ta karatun ƙur'aninsa, yana cikin yi kuma wata mata ta shigo siyan kaya, bayan ya sallameta ne murya can ƙasan maƙoshi na kira sunansa. Ido ya ɗora akaina ba tare da ya amsa ba, idona ya kawo ruwa ina cewa,"Yaya laifin me na maka?". Sai ya bagarar da zancen nawa da cewa,"Bamu gaisa ba ma". "Na gaidaka ai amma sai ka nuna kamar baka ji ba". "Ki yi haƙuri ban ji ba. Ya su Ummani?". "Suna lafiya. Ya kasuwa?". "Kasuwa Alhamdulillah, ga shago nan yau kin gani, sai ai mana adu'a". "Allah ya bada sa'a Yayana". "Amin na gode ƙanwata. daga makaranta kika biyo nan?". Na ɗaga masa kai ya ce,"To me yasa?". "Kawai na zo na ganka ne, ka daina zuwa gidanmu gaba ɗaya". Sai ya shafo gashinsa yana cewa,"gaba ɗaya babu wani lokaci ne yanzu amma in sha Allahu ina nan tafe, zan samu wannan lahadin ma in zo ki faɗawa Ummani". Nayi shiru ban ce komai ba. Sai kuma ya ce,"Ƙanwata akwai damuwa ne? Na ga yanayin na ki wani iri". "Kaima Yaya naga duk ka rame, rashin lafiya ka yi?". Fuskarsa ta murmusa yana kallona sosai kafin ya ce,"To ƙila ko don kin jima ba ki ganni ba ne, amma ni da na ke jina ma kamar zan fashe saboda ƙiba, yanzu hankali ya kwanta an sami sana'ar yi, mutane basa ta surutun kana zaman banza ba, haka gida ma kullum ana samun wadatuwa da abinci". Murmushi nayi da sautinsa ya fita kaɗan na ce,"Alhamdulillah Allah ƙara rufa asiri. Ai dama Yaya na faɗa maka komai zai wuce ya zama kamar ba'ai ba. Kuma Yaya kace kayi ƙiba, kalla fa wuyanka yanda ya ƙara zugewa, wannan sai dai karyewa ba fashewa ba kam". Hularsa ya cillo min yana faɗin,"Za ki fara tsokanar tawa ko". Kawai sai na tsinci jin daɗi a raina saboda yanda naga fuskarsa ta washe da dariya, ya miƙe yana cewa,"Tashi to na raka ki kar aga kin jima, ko za ki faɗawa Ummanin kin zo?". Nayi shiru sai ya ƙara cewa,"akwai me wainar fulawa a baya na siyo miki?". Girgiza masa kai nayi alamun a'a, ji na ke kamar kar na tafi amma haka dole na tashi ina jin kewarsa tana cika ni. Leda ya ɗauko me layi layi shaƙe da kaya ya miƙo min, na karɓa na duba sai naga kayan kwalliya ne a ciki masu yawa da su man shafawa da under skirt, na dube shi cikin jin daɗi ina cewa,"Yaya na waye?". "Na ki ne, tuntuni na ke ta cewa zan bawa Al'amin ya kawo miki kuma sai bai fiya biyowa ta nan ba. Akwai wata baƙar ledar a ciki wannan na Ummani ne. Wannan kuma ki bawa yaran gidan". Ya ƙarashe da miƙo min ledar biscuite. Ganin nayi shiru ina kallonsa ya hure min ido da iskar baki. Nayi murmushi ina ta miƙa masa godiya, sai da ya fara fita ya tarar min adaidaita sahu kana ya dawo yace na fito, kuma sai bayan na shiga motar ne yake ce min. "Ki gaida sirikina, kice inji wani Yayanki na kalen dangi". Ina murmushi me faɗi kamar dama jiran maganar na ke na ce,"Wanne sirikin? Yaya Al'amin bai faɗa maka maganar ta rushe ba? Yaya babu maganar aurena akan kowa yanzu". Sai naga ya waro ido yana kallona da mamaki sosai bayyane a fuskarsa, haka rashin jin daɗin furucin a ƙwayar idonsa, kafin kuma ya sauke numfashi yace min. "Ki gaida gida". Yana faɗin hakan ya juya ya koma shagonsu ina kallonsa. Bayan kwana biyu na dawo daga makarantar magriba zan shiga gida kawai naji an dakatar da ni, da mamakina kuma Hamisu ne abokin Yaya Nazifi, muka gaisa da shi yana ce min wurina ya zo zamu yi magana amma in shiga gida in fara sanarwa tukunna. Na shiga gida na sanar da Ummani, tace to nayi sauri kar Abbaa ya dawo ya tarar da ni naja mata faɗa. Batun da Hamisu ya zo min da shi yay matuƙar girgiza ni har na kasa tantance ma wanne irin abu naji a tare da ni, wai faɗa min yake Yaya Nazifi yana sona kuma har jinya yay akaina, ya rasa ta yanda zai faɗa min ne tuntuni har wani yayi masa shigar sauri. Har dalilin janyewar da yay min duk sai da ya faɗa min wai saboda kar ya zama ya haddasa fitina don ya lura akansa zan iya cewa na haƙura da auren wancan iyayena kuma ba za su ji daɗi ba, shima kuma ba zai juri ganina da wani ba, amma tabbas yana tsananin sona kuma da gaske aurena zai yi duk da bai san ya zan karɓi maganar ba, amma idan na amincewa soyayyarsa yana roƙon da na basa damar gabatar da soyayyarsa kafin wani ya ƙara riga shi. Lokacin da Hamisu ya gama isar min da duk saƙon Nazifi ban iya cewa da shi komai ba na koma gida. Har raina ban ji daɗin batun da ya zo min da shi ba, ban kuma taɓa tsammanin wannan maganar daga bakin Nazifi ba, hasali ni ban taɓa hasaso shi matsayin wanda zamu yi soyayya ba balle aure. Kawai sai naji ina jin haushinsa sosai, amma wataƙila yana so ya yanke alaƙarmu ne kwatakwata shiyasa ya ɓullo da maganar soyayya tsakaninmu, ni soyayyar Yaya da Ƙanwa na ke masa kuma ita zan ci gaba da masa, ba irin wadda yake nema a yanzu ba soyayyar saurayi da budurwa. Sai dai me duk yanda na so na ƙyamaci wannan batun da Yaya Nazifi ya zo min da shi abun sai ya faskara, Saboda yanda Yaya Nazifi ya nace ya dage wajen cusa min soyayyarsa, ya koma kusanta kansa da ni fiye da baya, shine rakani makaranta da ɗauko ni, kullum yana ƙofar gidanmu, a da idan ina farin ciki da ganinsa a gidanmu yanzu duk ba na yi, ina ta kaucewa faɗawa tarkon soyayyarsa amma sai da ya san yacca yay ram da ni a tarkon soyayyarsa domin yau da gobe tafi gaban wasa. Ba zan ce ba, kuma ban san taya ba, lokaci ɗaya, rana ɗaya cikin lokaci ba mai tsayi ba na aminta da soyayyarsa, Soyayya me ƙarfin gaske ta ƙullu tsakaninmu, Wani irin soyayya yake muna min tsaftatattciya, Kulawarsa, ɗawainiyarsa da gudunmawarsa akaina suka ƙara ninkuwa, ya maida ni ƴar gata a cikin ƴan mata, soyayya mukewa juna me tsanani da har muke ganin ba zamu iya rayuwa ba tare da juna ba. Kuma ba tare da ɓata lokaci ba iyaye suka shiga maganarmu don Yaya kasa haƙuri yay yace gwara yay magana a sabon matsayinsa kafin wani ya ƙara zuwa da neman aurena, don yana tsoron sharrin samarin da ke ta kawo min hari. Ranar da ƙyar na iya sanarwa da Umman su Hindatu ta faɗawa Ummani Yaya Nazifi na so ya turo iyayensa ayi maganar aurenmu. Ranar kuwa ji nayi tamkar na buɗe ƙasa na shige ciki saboda yanda suka hau tsokanata, wai dama can ai sun san soyayya muke yi muke ta ƙaryata kanmu, Ummani ma tayi ta min tsiya kunya duk ta kamani na kulle kaina a ɗaki. Ranar Asabar Malam wato mahaifin Yaya Nazifi da ƴan uwansa suka zo suka nema masa aurena. Kamar yanda Abbaa yaywa magaban Salim bayani haka suma yay musu bayani kan cewar karatu shine burinsu akaina a yanzu, don haka ba zasu ce ba zasu bawa Nazifi ƴarsu ba amma sai dai ba yanzu za su aurar da ni ba, idan zai iya jiran lokaci to, da yake da Yaya Nazifin aka zo ya amsa da cewar ya amince shima dama ba maganar aure yake yanzu ba tunda akwai tsare tsaren abubuwa da yake yi, sai dai yana so Abbaa yay masa alfarma ya bada kuɗin aure yanzu saboda wasu ƴan dalilai. Lamari na babbar magana su Abbaa suka fahimci nufinsa suma suka ga dacewar bayar da kuɗin auren, don haka cikin sati guda kuwa Yaya Nazifi ya kawo kuɗin aure naira dubu ashirin. Tsakanin Ummani da Abbaa ban san wanda yafi wani farin ciki da batun auren ba, domin na faɗa muku babu wasu iyaye da za su kasa yiwa ƴarsu kwaɗayin Nazifi Bala Mai Kalwa a matsayin mijin aure ba, haka babu wata budurwa da ba zata so ta mallake shi ba in har ba burin auren me kuɗi ne kawai a ranta ba. Tafiya tayi tafiya soyayyarmu na ƙara ƙarfi, ina jin duk duniya babu wanda zai iya min irin wannan soyayyar tasa, haka ina ganin na gama dacewa da samun mijin aure. muna gabanin fara zana jarabawar neco sai Yaya ya fara matsamin lamba akan zancen shi gaskiya muyi aure, shi kawai zai fi samun kwanciyar hankali da natsuwa idan ina gidansa, shi yana buƙatar aure yanzu kam nan ba da daɗewa ba, karatu ne dai yay min alƙawarin ba zai tauyeni ba zai barni har in ga ƙarshen biro da takarda. Raina ya ɓaci da wannan maganar tasa, domin ba haka suka yi da iyayena ba, an faɗa masa an jadda masa sai na kusa kammala karatun jami'a a ƙalla nan da shekara biyar masu zuwa, ya kuma ce ya amince shima yafi so sai ya mallaki wurin zama, amma shine yanzu ko shekara ba'a gama rufawa da magana ba zai fara wannan zancen saboda yaga da kuɗin aurensa akaina. Dalilin hakan ya janyo saɓani mai girma tsakaninmu, muka dinƙa rigima da shi rigimar da bamu taɓa yi ba, na nuna masa fushina da bai taɓa sanina da shi ba tsawon tarayyarmu, haka shima naga fushinsa da ban taɓa ganinsa da shi ba a sanin da na masa. Ni dai na tsaya masa akan bakana na cewan ba zan taɓa iya tunkarar iyayena da maganar aure yanzu ba, nima ina so in faranta musu in saka musu da irin ɗawainiyar da suka yi da ni a rayuwa, kuma karatun da zan yi na likita ba ƙaramin karatu ba ne don haka damata yanzu ce, yanzu ne na ke da damar natsuwa in mayar da hankali da ban da ɗawainiyar kowa akaina, don haka yay haƙuri kawai zuwa lokacin da aka ɗiba, yama rufe maganar aure ba yanzu ba kam, shekara biyar ne kamar yanzu zai ga lokacin ya zo, kafin nan in sha Allahu ya mallaki gidan kansa ma. Amma yanzu idan yace aure ƙarshen shekara ina zai kai batun neman gidan zama da haɗa lefe da sauran hidindimu, ɗawainiyar gida bayan aure da tunanin kuɗin gidan haya da ta yara. Duk yanda na so in fahimtar da shi sam yaƙi fahimtata, yaƙi jin shawarar da na ke ta ba shi akan ko da fili ne ya fara mallaka tukunna, amma ina sai yay min mummunar fahimta ma, yake ganin kamar na daina sonsa ne, har yake cewa Safiyya ce take neman hure min kunne saboda ɗan uwanta me kuɗi yana sona, shi kuma bai da kuɗi kuma shi ɗan talakawa ne, ya kama maganganun ashe na raina nemansa, duk irin jajircewar da yake akan sana'arsa shine na ke ganin ba zai iya riƙe ni ba, shi ariziƙi ai na Allah ne, kuma shi dama fatansa Allah ya rufa masa asiri yafi ƙarfin ci da sha, kuma idan har akan ina ganin ba zai iya riƙe ni ba ne to naci amanar soyayyarmu. Haka muka ta fafatawa da shi tsawon lokaci, kullum cikin rigima muke da shi akan fa sai an saka rana ƙarshen shekara. da yaga na cije na kafe sai ya koma sauke murya yana lallashina, ya dinƙa roƙona yana min daɗin baki, ƙarshe kuma sai ya fara faɗa min shi yana da matsala ne, yana gudun kar ya faɗa wani halin, kaza da kaza dai, da wannan ya shawo kaina har na yarda na amince don nima a gaskiya ina jin idan ba shi ba ba zan iya rayuwar aure da wani ba. Ranar da najewa Ummani da maganar Yaya Nazifi yace yana so a saka rana nan da ƙarshen shekara, kasa cewa da ni komai tayi sai da Abbaa ya dawo ta faɗa masa, ai kuwa raina yay mugun ɓaci, na sha kuka iya kuka saboda irin faɗan da Abbaa ya dinƙa min, yana cewa wato soyayya har tayi tasirin da zata sa karon farko in fara tirjiya da maganarsu, to idan yaga dama sai ya mayar musu da kuɗin na su auren Nazifin ma ba zan ba. Sosai Abbaa ya ɗauki fushi da ni kamar yanda ya ɗauki mugun zafi da maganar. hankalina ya tashi, shi kuma Yaya Nazifi idan naje masa da batun halin da ake ciki shima sai ya ƙara dagula min lissafi, na rasa ina zan saka raina, haka har sai da yasa na tada hankali a gida akan ni dai nan da ƙarshen shekara na ke so ai aurena, har ma na kai ƙarar Abbaa wurin Baba Tijjani lokacin kuwa ba ya gari. Da wannan Abbaa ya fusata kuma don ya ƙure Yaya Nazifi sai ya ce shi kuma ya tsayar da auren nan da wata guda, idan har ya wuce haka to ba zai kaffara ba ya fasa bawa Nazifi ƴarsa, don haka nan da sati biyu ciff ya kawo kayan lefe. Wannan hukuncin na Abbaa duk ya ɗaga hankalinmu, musamman ma daga ni domin na san shikenan na rasa Yaya Nazifi, don kuwa a halin da ake ciki yanzu Yaya Nazifi bai da wasu kuɗi da ya aje da zai iya haɗa lefe balle akai ga tanadin wurin zama duk cikin wata guda. Ana haka kuwa yazo min da zancen mahaifiyarsa ta ba shi aron gidanta da ta zuba ƴan haya a ciki, sai dai akwai gyare gyare a gidan sosai don ko masai sai an ƙara haƙansa, ban da gyaransa rufin kwano da su simintin ƙasa da duk ya farfashe. Amma yanzu dai zai yi iya duk ƙoƙarinsa yaga ya haɗa lefen kafin sati biyun da Abbaa ya yanke, in ya so ko wurin Hamisu ne sai ya ari kuɗin, Ranar yay ta bani haƙuri da lallashina akan in kwantar da hankalina komai zai zo cikin sauƙi, kuma in sha Allahu ko don hallacin da na masa ba zai bani kunya ba.... _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR05FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ Tun daga ranar da Nazifi ya buƙaci da na siyar masa da kwanana ya ɗauke ƙafarsa daga gare ni daga inda na ke, rawar ƙafa kawai yake a wurin amaryarsa, sai shan soyayyarsu suke hankali kwance, wani abun ma na lura da gayya yake min shi, yanda yake faman rawan kai ka rantse aurensa na farko kenan. Sam ba ya ko waiwayena balle tunanin sauke hakkina, bai damu da ya lafiyata take ba haka bai damu da dukkan wata buƙata tawa ba, ya barni kawai da ɗawainiyar gidansa, yaransa da ɗawainiyar mahaifiyarsa da ke mini kallon baiwa, wacca kowanne kalar kashi ta kwaso ni take watsawa, gaba ɗayansu basu ko tunawa da hakkin cutar da ni da suke yi. Haka har aka cika wata guda ɗin da na ɗibar masa amma mutumin nan bai yi aiki da hankali da tunanin ba, bama za'a sa ilimi ba don yanzu ni bana saka shi sahun masu ilimi kam, ranar da naje ɗaki na same shi ya na ta faman ɓata rai da cin magani saboda ya baro ɓangaren Amaryarsa, abincin ma da na kai sai ce yayi ai ya ƙoshi, ni dai ina ta bin hanyar da zata sa ba zamu samu saɓani ba amma shi neman hanyar ayi tsiya kawai yake, ni kuma ganin hakan kawai na bar masa ɗakinsa na koma nawa, tun sannan na fita sabgarsa na ce idan anyi duniya don manzon Allah bani ƙara zuwa inda yake sai idan ya neme ni, ashe shi hakan ma yake so don bai ko nuna bi ta kaina ba, ganin na fita harkarsa ya tattara ya koma wurin amaryarsa gaba ɗaya, maganar dole idan ta kama zai aiko min message ne kawai, ni kuma idan ina buƙatar abu mahaifiyarsa na ke faɗawa wanda kafin a bani ma ko a faɗa masa sai na sha jiki. Wannan abubuwa suka ƙara gwada min da gaske Nazifi ba ya buƙatata a rayuwarsa sam, zaman dole kawai yake da ni, wanda kuma na ke ta nazari da tunanin dolen da ta gagare shi fitowa fili yace da ni ya sallama auranmu, domin kuwa yanda ya gaji da zama da ni haka nima na fishi gajiya da zama da shi. Gaba ɗaya ya mayarshe ni wata banza shara a cikin gidan, ya gama tsinka darajata da mutuncina a wurin matarsa, Munafukin miji wama ya san me ya gaggaya mata akaina, tun da ta kai ta kawo yanzu tsakanina da ita ma kallon banza ne musamman idan ta fita aiki ta dawo, da zarar ta ganni sai kallon raini da ƙasƙanci saboda mijinta ya nuna mata ni ɗin ba komai ba ce a gare shi, don haka take wani nuna isa da gadara matsayinta na wadda miji yake so yake bawa kulawarsa, yake kuma ji da ita. Ni dai basa ko gabana tuni na ɗauke ido akan su, harkokin gabana kawai na ke yi. Abinci ne zan girki iya cikina da na mahaifiyarsa da yara, shi da ita kuwa dama takeaway yake musu ne oho ni dai ya min text yace na bar girki da su. Kuma tuni na yiwa kaina karatun tanatsu, na kira Ummani muka tattauna akan shawarar da na yanke, ya kamata na kama sana'a wacce nasan in har Allah ya saka min albarka da ganin ina samu ma kaɗai Nazifi ya rage wulaƙanta ni, yanzun ma ai har da ganin cewa shi yake min komai shiyasa, kuma duk abin da na ke buƙata sai na jira shi dole kuwa inga walaƙanci kala daban daban. Saboda haka na tattara duk gwala gwalaina guda uku muka je kasuwa aka auna aka siyar da tsada sosai, ina batun saro kaya irin su atamfofi da danginsu Maman Yasmin tace a'a tunda kuɗin har za su kai a siya fili to gwara a siya min filin na ajiye shi zuwa wani lokaci sai a ɗaga a siyar tunda ba kuɗin gini gare ni balle na gina, amma wannan zan ta iya juyawa da ribar ma sai in dinga ƙara siyan ƙasa ina ajewa, amma idan nace kasuwancin cikin gida zan yi to Nazifi zai iya min muguntar da zai dakusar min da shi, wannan kuwa bai ji bai gani ba kuma kar ɗokin soyayya wataran tasa nayi suɓutar bakin faɗa masa. Ai kuwa da wannan shawarartata ne Ummani tasa Yaya Al'amin ya samo dillali aka siya min wani fili can unguwar rimin auzinawa, da yake can akwai arhar filaye, tace da shi ko Abbaa kar ya bari ya sani zata faɗa masa idan lokacin hakan yayi, nima kuma naja bakina nayi shiru ko da wasa kar Nazifi ya san da zancen siyar da gwala gwalai balle siyan fili, takardun filin kuma zata ajiye min su a wajenta. Ranar da farin cikina na dawo gida, ko babu komai yanzu ina da kadara a ƙasa, karatuna kuma da ya tauyen hakkin ci gaba, ya kuma hana ni kuɗaɗen da mahaifina ya bani domin biyan kuɗin makaranta yaje don kansa Allah ai ba azzalumin bawansa ba ne. Sai dai na samu ajin online da ake koyar da turanci da kuma ajin biology, nayi register na shiga domin hakan zai fiye min alfanu, gwara na nemi ilim ta waya akan ya zama kullum sai dai na saka data na hau nayi chart da kalle kallen tictok a banza a wofi ni ban ƙaru da komai ba, ga shi kuma koyawar da ake babu mugunta darasi ake sosai in har ka natsu ka mayar da hankali ba zaka ce a online ne ka ke karatu ba, jinka zaka yi tamkar a cikin makaranta zaune a aji gaban Malami. Yau ina ɗaki da yamma zaune ni da Rumana, yanzu kam ta zama ƴar ɗakina, Atika kuma ta zama ƴar ɗakin Zahra'u. Ganin lokaci na miƙe na fita don zuwa haɗa abun shan ruwa, ina sakkowa Nazifi na hayowa shima wanda ya dawo daga kasuwa. Nayi kamar ban gansa ba don tuni na ƙuduri aniyar zai sha mamakina, tabbas ko magana ce idan ba shi yay min ba ba zan masa ba, gaisuwa ma bana so ta haɗamu. Hanya na ba shi don ya wuce sai na ga ya tsaya, ganin bai da niyyar wucewa naci gaba da takawa ina sauka ya dakatar da ni. "Me ke damunki ne Sa'ida? Za ki ce ba ki ganni ba ne da sannu da dawowa zata gagara fitowa daga bakin ki, kina nuna tamkar ni ba mijinki ba ne". "To Nazifi sannu da zuwana zata ƙare ka da wani abu ne da ka damu da ita? Ko ba'a faɗa maka ne a inda ka nufa". "Ni kike faɗawa haka?". Ya faɗa yana ɗaga murya sama, ni ko ganin zai min hargowa nayi masa banza na wuce na barshi anan. Bai san ni baƙin cikin ganinsa ma nayi ba da har yake kiran nayi masa sannu da zuwa, ni kuwa yanzu ina yaga wannan darajar a idona, ai ana zaman jinginar aure ne kawai tsakanina da shi, kuma ban fidda ran zuwan lokacin da zai ce ya raba aurenmu ba. Har na shiga kitchen ina jin yacca yake bina da kallo, dama kunu na sakko na dama saboda ina azumi, kuma ma sai naji ina sha'awar awara don haka na koma sama na ɗauko kuɗi na dawo na bawa ƴar aikin Zahra'u ta siyo min ɗanyar awara a waje. Har aka sha ruwa ina kitchen ina aiki sai sauri na ke yi. Motsin shigowa naji na ɗago na waiga kaina ina kallon in da Zahra'u ke tsaye, har zan ɗauke kai sai kuma naga tana lalube, ban san me take nema ba, ban ma san me ya shigo da ita kitchen ɗin nawa ba, tunda tuni aka raba mana kitchen tun sanda ta nuna bata so mu haɗa girki, wai ita ba girkin kowa take ci ba, kuma in aka ce za'a haɗa girki ita zata takura da yawa. Sai ya zauna ya sauya tsari yace kowacce ta dinga girkinta amma nauyin ciyar da duk wanda yake zaune a gidan da duk wani ɗan uwansa da zai zo ya rataya a wuyana ne. Ba tashin hankali na ke nema ba kuma ba abu ne da zan soma shi sabo ba na amince ba tare da nuna masa ko rashin jin daɗin hakan ba, lokaci ne dai yana nan tafe da zai gane gaskiya kuma Allah ya saka min. "kina neman wani abu ne?". Na tambayeta a mutunce, shiru tayi ta ci gaba da binciken durowa, na bita da kallon mamaki ina ajiye kofin hannuna da na ɗaga zan sha lemo. Kaf dai kitchen ɗin idan ba shi ya faɗa mata cewa duk kayan ciki nasa ba ne to banga wani abu da yake mallakinta a ciki ba da har ta zo nemansa tana min bincike haka. Na buɗe baki na ƙara cewa da ita,"Ina magana kin yi banza da ni. Ko kin mance ba ki da hurumi da nan ɗin?". "Ba sai kin tuna min ba ai na sani, Idan ban da mallaki anan ɗin ai ba zaki ganni a ciki ba, ko kin manta kafin sama min nawa da yafi wannan girma da ƙawatuwa kayan kitchen ɗina sun haɗu da naki, so ina son bincikar abin da aka iya ɓoyewa ne". Juyawa nayi ban saurareta ba don na fahimci neman tashin hankali take da ni, ni kuma bata isa ba tayi kaɗan, ko kusa ba zan taɓa sauraron rigimarta ba. Da farko ta nuna kamar zamu zauna lafiya da ita, tun da har hira muke zama muyi a falo, ayi wasa da dariya cikin mutunci da girmama juna, har ma a lokacin take cewa taga ina fama da halin Fati saboda haka zata gyara mana zamanta don ita gaskiya bata da haƙuri da shiru irina, ni a lokacin murmushi kawai nayi ban ce mata komai ba. Idan gari ya waye taji shiru ban fito ba da kanta take leƙowa ɗakina mu gaisa, to amma lokaci ɗaya sai naga ta fara sauyawa, muna ƴar hy hy da ita kafin kuma ta sauya gaba ɗaya wanda magana ma idan nayi mata bata ɗaga kai ta kalle ni, bar ta dai da min kallon wulaƙanci. Na kammala duk abin da zan yi na fita na barta a kitchen ɗin. Bayan na idar da sallar magriba ina biyawa Rumana karatu sai naji an murɗa ƙofa, da tsananin mamaki na ke kallon Nazifi da ke shigowa, kallo ɗaya na masa na ɗauke kai akansa, rabonsa da sanyo ƙafa cikin ɗakina har na mance wallahi. Rumana ta yi masa sannu da zuwa tare da gaida shi, nima kuma yaci darajar yarinyar na buɗi baki nace masa. "An dawo lafiya?". Bai amsa min ba sai ce yay da Rumana,"Je ki ɗakin ku zan yi magana da Antynki". Kallona ta tsaya yi don yarinyar tuni ta fara tausayina a gidan, gyaɗa mata kai nayi kana ta miƙe ta fita tana ta waigena, da alama dai tana ji a jikinta ba mutunci ya kawo uban ruƙon nata ba. Tsaye yay min aka hannaye zube cikin aljihu, jirana yake na masa magana oho dai, ni ko na ci gaba da abin da na ke nayi kamar ma ban san yana cikin ɗakin ba, sai can ya nemi wuri ya zauna yana kiran sunana. Ɗago ido kawai nayi na dube shi ban amsa ba, ya numfasa kana yace,"Wai ke me yake damun ki ne?". "Me ko yake damuna, lafiyata ƙalau ni kam. Yanzu dai me ke tafe da kai?". Kallon mamaki yay min kafin ya ce,"Tambayata kike hakan?". Sai kuma ya kama ɗaga murya yana faɗin,"Sa'ida so kike sai na fito na miki bayanin irin wulaƙancin da kike min ne? Ina matsayin mijinki wanda aljannarki ke tafin ƙafarsa amma ba ki ganina da daraja balle ki mutunta ni, sai in wuce ki wuce ba zaki buɗi baki kiyi min magana ba, yaushe rabonki da zuwa ɗakina? Yaushe rabonki da shiga ki gyara min makwanci? Yaushe rabon da ki dafa abinci ki ba ni? Yaushe rabonki da bani hakkina? Yaushe rabonki da gaishe da ni? Yaushe rabon da na fita na dawo kiyi min sannu da zuwa? Kina abu kamar wadda ke zaman kanta a cikin gidan, ko kina so ki faɗa min ke kika auro ni?". Ya kai aya ya kalle ni muka haɗa ido, muryarsa ta ƙara fitowa da ɓacin rai wajen cewa,"Ina magana kin kafe ni da ido, to na gaji da wannan halin rashin mutuncin da kika tsira, idan kuma hakan kika zaɓarwa kan ki ni ban da matsala ban da damuwa tunda ba ke kaɗai na ke aure ba, a yanzu ina da wadda ta fiki komai, wacca tayi miki tseren da ba za ki taɓa iya taddota ba, Zahra'u ta fiki wayewa, ta fika iya kwalliya, ta fiki sanin yanda zata tarairayi miji da ba shi kulawa, ta fiki iya soyayya, ta fiki iya gado haka kuma ta fiki ɗanɗano, saboda haka Sa'ida kar kiyi tunanin wannan girman kan da kika ɗorawa kan ki zai dame ni domin da ke da babu ɗaya a wurina". Rasa abin ce masa nayi, kallonsa na ke babu ko ƙifce, haka kawai sai na fashe da kukan da na jima ban yi ba, kuka na ke sosai kafin na fara ce masa. "Nazifi ni kake faɗawa waɗannan maganganun?". Na miƙe jikina na karkarwa na ke cewa,"Ban san me na maka ba ka tsane ni? Amma kuskurena ne da na rusa farin cikin iyayena na zaɓeka, ban da haka da baka aje ni cikin gidanka kana gana mun azaba ba, da baka kalle ni kana gaggaya min magana irin haka ba, haba! me na maka a rayuwar nan Nazifi? Me nayi maka da na ke fuskantar tozarci irin haka daga gare ka?...Kuma ma idan har da gaske ni da babu ɗaya ne a wurinka menene na zuwa kayi ƙorafi akan hanyar da na zaɓa wadda na ke jin sanyi cikin raina, Mene damuwarka da rashin kulaka da na ke yi ɗin ehh Nazifi? Mene damuwarka na ce?...". Ni gaba ɗaya ma sai na rasa me zan ci gaba da cewa, nema na ke kawai na rikice, banɗaki na nufa zan shige ciki domin Allah ya gani bana son ganinsa a gabana, ruƙo hannuna yayi ya janyo ni na dawo gabansa yana zuba idanunsa akan fuskata, ƙasa da murya yace,"Kin san me ya kawo ni wajen ki?". Hawaye ne kawai na ke ban iya ce masa komai ba, sai ya ƙara cewa,"Idan kina tunanin na zo karɓar wata tsiya daga jikinki ne to kinyi kuskure. So idan kin gama kukan Zahra'u na so taci awara da kunu". Ban san lokacin da nayi masa wani kallo na baka da hankali ba kafin na ce,"Me ya shafe ni da abun da zata ci to?". Kai tsaye ya maimaita min,"Kunu da Awarar da kika dafa za ki zo ki zubawa Zahra'u tana son ci". Na ƙwace hannuna daga ruƙon da yay min, ina goge hawaye na ce,"Saboda ita ta dafa? Ko kuma saboda kai me karɓa mata ɗin ina tsoronka?". Buɗar bakinsa zai magana aka turo ƙofar ɗakin, muka waiga a tare, Iyam ce ta shigo da kwano tana ce min. "Ke ƴar nan ina kunu da awara da kika dafa? Zubo maza anan Amarya zata ci". Wani murmushi nayi a ƙasan raina, duk ɗin su na gane inda suka dosa, suna so su faɗa min cewar sun samu ƙaruwa ne wanda na fahimci hakan tuntuni. Zazzafan hawaye ya ƙara sakko min nasa hannu ina gogewa, ta dube ni tana min kallon sama da ƙasa ta ƙara cewa,"Ki bar zagina cikin ranki ki bani abun da na ke tambayarki". Na ce,"Ai ba da ita na dafa ba Iyam, azumi nayi na dafa iyaka cikina kuma na cinye". "Iyeee lallai Sa'ida, Dama har za ki dafa abinci a gidan nan ni ba ki bani ba?". Na saki baki ina kallonta ganin zata min sharri gaban ɗanta na ce,"Akwai wata rana da na hanaki abinci ne Iyam? Wannan awara da kunu ne nayi na shan ruwa kuma azumin nan ni kaɗai nayi". "Ohh ni ban yi ba kenan ban isa ki dafa komai da ɗana ya siyo ya ajiye ki iya zubawa ki bani ba, da kyau. To yanzu dai ko me za kiyi ki zubo akaiwa Amarya don babu in da za'a je samun na siyarwa yanzu, idan kuma kin cinye ɗin ki fito yanzu kije ki dafa mata wani". Nayi murmushi na ce,"Kiyi haƙuri Iyam, amma ko akwai wallahi ba zan bayar ba, haka ko da babu wallahi ba zan dafa saboda ita ba. Jikin aiki na fita? Ko kuma iya dafawar ne bata yi ba da ita ba zata girkawa kanta ba? Ita har mene ma na sha'awar abun hannun kishiya da zata taro jama'a su zo su ƙwatar mata? To kunu da awara ne nayi nawa ne babu kuma wanda zan bawa a cikin gidan nan wallahi...". Maganata ta katse ganin Nazifi ya ɗaga hannu zai sauke min mari, Iyam tayi saurin dakatar da shi da cewa,"A'a ƙyaleta Shalele, ai ba komai take ba sai baƙin cikin Amarya ta samu ciki ita ta nan sai ci da kasayarwa, daga yarinya ta samu ciki kuma sai ki hau baƙin ciki da hassada". Ina hawaye na ƙunar zuciya sosai na ce,"Ni kuwa akan me zan yi baƙin ciki da abun da Allah ne ke bayarwa, ina da ilimi kuma ina aiki da shi don haka wallahi ko kusa don wata ta zo a bayana ta samu ciki ba zai dame ni ba...Kiyi hakuri ba da ke nake ba amma baƙin ciki ai sai wurin wanda bai san alƙur'ani da hadisi ba, ni kuwa na san kamar yanda Allah ya bawa wasu ariziƙi a dare ɗaya haka nima ciki idan ina da rabo zai ba ni, Allah kaɗai ya san me tsara min a rayuwata". Shigowar Atika yasa nayi shiru, ta dubi Iyam tana ce mata,"Anty Amarya na kuka wai cikinta". Iyam ta fita da sauri tana cewa,"Innalillahi, wato mace dai idan ba taɓa samun ciki tayi ba bata da imanin tausayawa me laulayi, to Allah ne ma ya san manufar jaki da bai ba shi ƙaho ba". Ta na fita na wurgawa Nazifi banzan kallo na ce,"Kaima ka samu damar fice min daga ɗaki". Yatsa ya daga yana nuna ni da shi ya ce,"Na san ba komai ya ba ki lasisin iya buɗe baki ki farfaɗi abin da kika ga dama ba illa wannan munafukar ƙawar taki da ke baki shawara. To daga yau zan yanke alaƙar ki da ita". Ina kallonsa kai tsaye na ce,"Safiyya ce tare ka ganmu, haka kuma zaka buga ka barmu, da na rabu da Safiyya gara na rabu da kai Nazifi, domin kuwa ita ba butulu ba ce, Safiyya tafi min kai sau dubun dubata Nazifi Mai Kalwa...Kuma dai ka sani duk lalacewar goma tafi biyar, kafin wancan ni ɗin dai mara ilimin ni ka sama kuma ni ɗin dai silar matsayin da kake fariya da shi a yau". Yana fita naje na sakawa ƙofar maƙulli, a gefen gado na zube ina fashewa da kuka soai, na jima a haka kafin na kai hannu na ɗauko wayata, yau kam gani na ke gwara na kira Abbaa na faɗa masa dukkan halin da nake ciki, sannan na faɗa masa suyi min haƙuri da uzurin nemarwa kaina mafita, ba zan iya ba, ba zan iya jurar sabon wulaƙanci akan cikin da Zahra'u ta samu ba. Lambar Abbaa na danna sai bayan da ta fara ringing kuma na shiga tsoron abin da zance masa. Kamar yanda ya saba bai ɗaga kirana sai ta katse kana ya biyo baya. Yanzun ma sai bayan ta yanke kana ya kira. Na saita natsuwata ina ɓoye yanayina a natse nayi sallama, maimakon jin muryan Abbaa sai naji Ummani ta amsa. Kuma jin muryan mahaifiyartawa idona suka ciko da ruwan hawaye. Ta kira sunana jin nayi shiru, na amsa ina ta ƙoƙarin danne kukan da ke son ƙwace min, saboda ko kusa ba na so ta gane a halin da nake ciki ta shiga damuwa, ni yanzu ɓoye mata komai na ke yi saboda yanda duk taƙi kwantar da hankalinta, kullum tunaninta na inda na ke da halin da nake ciki, har ta kai yanzu sai dai ta sanya abinci a gaba ta kasa ci. Duk yanda na so ɓoye kukan abun yaci tura, kawai na fashe da kuka saboda na san hakanne kawai zai sa na samu salama, in yisa a kunnen da za'a lallashe ni da kalamai tausasa. "Ya su hanallah Sa'ida lafiya?". "Ummani ba komai". "Wanne irin ba komai, haka kawai za kiyi kuka don kiji daɗi, ana haka dama? Ko wani abun farin cikin ne ya same ki?". Cikin kuka sosai na ke ce mata,"Ummani ni kawai na gaji da zama da Nazifi ne, na gaji Ummani so na ke ya rabu da ni, umarninku na ke nema in ce ya bani takardar sakina". "Kul kar na ƙara jin wannan furucin a bakinki, idan na ƙara jin kin faɗi haka sai nayi mugun saɓa miki Sa'ida. Ba na ce miki kici gaba da adu'a ba Allah yana sane da ke kuma zai kawo miki mafita". "Ina ta Adu'a Ummani, ina yi amma kullum babu sauƙi, babu sauyi, Ummani wani sabon shafin ci min mutunci ne ya buɗe saboda Zahra'u na da ciki. Yanzu shikenan da gaske banda rabon haihuwa, matsalar daga ni ne ba zan taɓa haihuwa ba Ummani, shekara takwas da ɗoriya ban taɓa ɓarin wata ba amma ita wata huɗu ta dauki ciki...Ummani ki bar ni na roƙi Nazifi ya sakeni don Allah don Annabi". _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR07FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ "Kwantar da hankalinka babu abin da zai same su kaji. Yanzu shiga ɗakina ka ɗakko wata jarka yaluwa ka kawo min, jiya ne Adamu bai sami kawo rubutun da wuri ba sai bayan ta rufe ƙofa". Kaina na jingina da bango ina hawaye, ina jiyo su duk tashin hankali yasa ma sun rasa me ya kamata suyi, ita kuma sai kuka take yi sosai, sai can kuma saboda baƙin munafurci da iya kirsa ta shiga cewa da shi. "Derling ban san matsalar cikin nan ba, ni da akwai hali da an ciro Baby haka, in ya takura min ni kaɗai ba damuwa ba ne Derling, ko kuma idan kana wajena duk ba matsala ba ne, amma kar Sa'ida taga kaman da gangan na ke shiga hakkinta, ban san ya zan yi ba Honey". Tsintar kaina nayi da share hawaye na fita zuciyata na tafarfasa, ina zuwa na kamo hannunsa ina cewa. "Wuce mu je". Iyam ta tsaya galala tana bin kayan jikina da kallo tace,"Wacce irin fitsara ce wannan zaki fito a haka? Ko kin manta da cewa ina cikin gidan". Ban bi ta kanta ba na ƙara cewa da shi,"Hubbi magana na ke maka. Ai ciwon nata ya lafa yanzu tun da har ta iya gane tana shiga hakkin wata. So lets go ina so zan koma bacci". Zai magana na kai hannu na rufe bakinsa, ina kallon yanda ta rumtse ido alamun abun ya bata takaici sai ta kama cewa. "Ke kam kiyi haƙuri Sa'ida ba laifina ba ne, ban da cikin nan haka kawai ai ba zan hana kaina bacci a irin lokacin nan ba, to Babyn ne har ya san Daddynsa tun yana ciki, idan bai kusa duk sai naji yana karkartata ya hana ni sakat". Wani kallo na watsa mata ina cewa,"Kinga dakata ban nemi jin wani ba'asi daga bakin ki ba. Ciwo ke ya dama, abun da na sani miji a wajena yake kuma ba zai yiwu sai muna tsaka da jin daɗin rayuwarmu ba wani can da bai riga ya zo duniyar ba ya dinga shiga lokacina...". Wa ni kallon fusata Nazifi yay min yake faɗin,"Keeee ya isheki haka, kar ki ce za ki banzar kishinki akan ɗana, a hakan da kike ganin bai zo duniyar ba to ni yafi min ke, kuma zan fi ba shi lokacina fiye da ke ɗin, idan baccin kike ji akwai wanda ya hana ki ne ki wuce kiyi kayanki mana". Nima cikin fusata na ce da shi,"Kai ne ake rainawa hankali amma wannan abun da take ƙarya ne wallahi, kai kuma saboda son ɗa ya rufe maka ido ka gagara ka gane...amma ka sani wallahi ba zai yiwu muna tare a dinga zuwa ana katse min bacci ba, ba zai yiwu ta dinga shiga lokacina ba, don haka ka zaɓa ko ka dawwama a wajenta har sanda zata haife maka ɗan naka ko kuma duk lokacin da kake wurina babu ita babu shiga huruminka". Gigitacciyar ƙara ta sake saki tana dafe mara. Duk su biyun suka yi kanta ita kuma ƴar aikin ta tsaya gefe tana jera mata sannu, can kuma sai ga Innarta da Ƙannenta sun sauko suma suka rufa kanta sai sannu suke jera mata. Iyam ta dube shi tana faɗin,"Kaga ɗauko maƙullin mota mu wuce asibiti kawai, ai bamu ga ta zama ba, shi dama ciki in ya shiga wata bakwai ai ana iya haifarsa. Bamu san ko Allah ne ya kawo haihuwar yanzu ba. wannan susutacciyar matar taka ma kaɗai ta isa tasa a haihu babu shiri. Ban da rashin imani ma na juya ana zancen ciwo kina ke ina ruwanki, da ike bata san zafin ɗaukar cikin da rainonsa ba. Allah ne ma ya san manufar jaki da bai ba shi ƙaho ba, Allah ya baka matar da zata cika maka gida da iyali tana baƙin ciki da hassada saboda ita bata haihuwar wata ba zata haihu ba, to aniyarki ta koma miki duk baƙin cikinki sai naga jikina jinin Shalele". A wannan furucin na Iyam kam tuni idanuna suka ƙara tara ruwan hawayen baƙin ciki, wani rauni ya baibaye ni, raina ya kai ƙololuwar ɓaci har na kasa haƙuri sai da na tanka. "Ni ba na baƙin ciki da abin da Allah ne ke bawa bawansa, cutar hassada kuma ban ɗorawa kaina ba don Allah kar ki ƙara alaƙanta ni da ita. Kuma idan hakan da kuke ke da ɗanki kuna ganin daidai ne kuci gaba da zaluntata, Allah yana ji yana gani zai saka min". Tass naji saukar mari a fuskata, na dafe wurin cikin jin raɗaɗin zafin, Nazifi na nuna ni da yatsa ya ce,"Idan mahaifiyata na magana kina yi sai na yi fatali da ke, ƙarya aka yi akan ki ke ba juyar ba ce, idan kin ji haushi ki ɗauki cikin mana ki haife kiga idan ba'a so ki ba, karo na uku da zan ƙara faɗa miki wallahi da na san ba ki haihuwa Sa'ida ba zan taɓa aurenki ba, juyar banza da wofi kawai". Ƙurii na masa da ido ina kallonsa, da yanda yake maganganunsa cikin kwanciyar hankali, a duk kalaman da yake faɗa min a baya ba su ƙona min rai ba kamar yanda wannan yay min ba, a maimakon zubar hawaye sai na tsinci murmushin da ban shirya masa ba a fuskata, ban ƙara cewa komai ba na juya na koma ɗaki, da shigowar tawa shima ya shigo ya saka jallabiyarsa tare da ɗaukar maƙullan mota ya fita. Yana fita na saki marayan kukan da nayi dauriyar riƙewa, jikina rawa kawai yake yi, Allah ya sani yau na ƙara jin na daɗa gajiya da zaman auren Nazifi, tabbas aka ci gaba da tafiya a haka zaciyata zata iya bugawa, wanda a yanzu haka yanda na ke jin jinina yay zafi kamar zan shiɗe haka na ke jina. Wallahi ban da mahaifina ban ga abin da zai hanani tattarawa na bar gidan Nazifi ba a gobe da safe, kuma bari na har abada, ai ban haifa ba balle na tafi da tunani da damuwar barin ƴaƴana, aure ne dama yama fita gaba ɗaya akaina ba iyaka aurensa ba kawai. Tun daga wannan ranar lamari ya ƙara sauyawa, hankalin Nazifi ya tattara gaba ɗaya ya koma kan Zahra'u da abin da ke cikinta, wai ai likita ya ce tana da buƙatar a kula da ita sosai, don haka ko fita yay bini bini ya dawo, haka idan muna tare bini bini ya tashi ya tafi wajenta ya dubata, kuma da ke muguwa ce ta ƙarshe sai ta koma cewa ita abincina kawai take iya ci ta zauna lafiya, don haka dole na koma girkawa ina bata tana ci, idan naƙi girki kuwa ta dinƙi ciwon ƙarya kuma duk abin da aka bata taci sai tayi amansa, sai taci nawa ne kawai take zama lafiya, a hakan ma duk bai mata ba sai abun da take so na ke dafawa, idan ma na ce zan yi son raina to fa idan raina yayi dubu sai ya ɓaci. Nazifi har da min kashedin kar hakan ya bani lasisin zuba wani abu a abinci da zai cutar masa da mata da yaro, in bar ganin matarsa ce ni yin shari'a da ni abu ne me sauƙi a wurinsa. Kusan kullum ba ni da aiki sai kiran mahaifiyata ina shaida mata abubuwan da ke faruwa, nayi ta mata kuka ina shaida mata na gaji, banda burin da ya wuce na ganni kusa da ita a ƙalla ko da a kafaɗarta ne na zubar da hawanyen kuma nayi hira da ita naji sanyi, haka zata lallashe ni ta turo min su Hindatu da Ƴaƴan wurin Yashaik su ɗebe min kewa, ita kuma ko da yaushe sai dai tayi ta ƙara jaddada min muhimmancin haƙuri, juriya da ƙara dagewa akan adu'a. Ga shi har yanzu ban ƙara zuwa gida ba tun wannan case ɗin da akai na su Atika, don ko da Kaka yasha jinya Abbaa ce yay na zo masa gida bai yafe ba. To daɗin ma da nake ta ji dai wata guda ya rage a cika shekara. Amma tabbas ina da buƙatar duk san da na shiga damuwa irin haka naje gidanmu wurin mahaifiyata, don ma dai Allah yasa yanzu makarantar koyon turanci ta online da na shiga karatunta duk ke ɗebe min kewa, haka kuma zan ta ganin Safiyya na live vedio a IG akan harkar lafiya wannan ma duk sai yake sawa ina jin daɗi. Kar ku so kuga irin kuɗin da Nazifi ke kashewa wajen siyayyar kayan jariri, duk wasu kayan haihuwa ya siya ɗakinsa yay maƙil da akwatuna kamar me haɗa lefe, ko zama muka yi sai ya kama tambayata me zai ƙara siya, ba ɗakinsa kawai ba ita kanta can ɗakinta ya cikata da kaya nata da na jariri, Haka ba dama suyi waya da wani cikin mutanensa da yaji mutum yace bai ƙasar zai ce a taho masa da kayan jarirai masu tsada, gidan kuwa har yasa ana gyaransa wasu wuraren ana sabunta su. Ana haka Iyam tayi tafiya ƙauye, tana tafiya kuwa na samu damar sararawa, don kwanciya nayi ciwon ƙarya ko motsawa ban yi, ni kam na gaji da bautawa matarsa na ciyar da ita da kula da ita, saboda haka gidanmu nima aka turo min Saudatu ƴar wurin Baba Tijjani wacca da ƙyar uwarta ta barta, itama kuma Zahra'un sai ga shi an turo mata ƙannenta har biyu da wata tsohuwa. Ƙaton cikin Zahra'u a gaba ya fito turtsetse haihuwa yau ko gobe, a kitchen take tana kaiwa da kacaniya da tukunya, kunnenta sanye da earpod tana magana da alama waya take yi. Ƙanwarta Mubina da ke can gefe tana yanka salad ta dube ta tana faɗin,"Yaya shi kawai za'a yanka?". Kai ta ɗaga mata alamar ehh kana a hankali tace mata,"Je ki sanya turare a ɗakin Honey, kuma ki haɗa salad ɗin kisa a friedge ɗin ɗakina". Mubina ta fita ita kuma taci gaba da maganar da take yi. "Ki bari ke dai wani abun ma sai Unborn ya sauka anan zan ƙara ƙwace shi ya zama nawa ni ɗaya". Sai kuma tayi dariya sosai kafin ta ce,"Kai ƙawata! To ai na faɗa miki nima sai da na gama shishshigewa jikinta na gane sakarya ce sanyinta yay yawa kana na ce to bari in karkata in san yanda nayi na dawo da shi tafin hannuna gaba ɗaya. Kin san ina faɗa miki yarinya ce gaba ɗaya bata da wayewa, da ke ma naga yanzu ta fara baki in anyi tana iya mayarwa, amma tana abu komai irin na ƴan da, kuma like tayi rayuwan ƙauye ne i think so, kin san wani abu ma? Idan fa muna gado sumbatun da yake min haka za kiji yana ta faɗin shi a wajena kawai yake jin daɗi, can ba'a masa komai, bata iya salon komai ba salam takee". Ta ƙara yin dariya bayan gajeran shirun da tayi tace,"A'a ni ba zan koreta daga gidan ba, ai so nake ta zauna tayi min rainon yara ni kuma naji da aikina. Kin san tana da addini da kuma tarbiyya dan ba ki ga yaran da suke wajenmu ba yanda ɗayar ke da karatun ƙur'ani a baki da ibada". "Hhhh Allah ko ƙawata to ya kamata dai ki dawo ɗin gaskiya don kam dai ɗanku ya kusa fitowa, a yanzu haka ji na ke kamar zan haihu ƙarfi hali kawai na ke. Kin san na gama wancan wasan na ƙyaleta ta huta kar ɓakin cikina ya kasheta a rubuta min zunubi, amma dai kam har yanzu bana barinta runtsawa idan ya koma wajenta". Nazifi ya shigo kitchen ɗin a lokacin, daga bakin ƙofa ya tsaya tare da harɗe hannayensa yana ta kallonta, jinta yake har can ƙuryar zuciyarsa, yana mata wani irin so ne da shi kansa bai sani ba, a duk lokacin da yake tare da ita sai ya ciji yatsar rashin samunta tun da daɗewa, ban da zanen ƙaddara ma da me zai kai shi haɗa layi da auren Sa'ida? Sai dai wani ɓari na zuciyarsa kan faɗa masa cewar ko da a wancan lokacin ya samu Zahra'u ba lallai ta aure shi a irin matsayin da yake ba, don a yanzu wataran yana ganin ɓacin ranta idan ƴan gidansu na masa magana da turanci yana kasa mayarwa, ranar nan har magana ta yaɓa masa ya kuma ji zafin maganar amma haka ya shanye saboda yana mutuwar sonta. Zahra'u kuwa ƙamshinsa tuni ya sanar da ita zuwansa, don haka a hankali tace da ƙawarta ta kashe wayar, sai taci gaba da aikinta tana ta murmushi kamar bata san yazo ba. tana son Nazifi sosai shiyasa take so ta ƙwace shi gaba ɗaya babu boka babu Malam, kuma bata so ta kori Sa'ida tafi so ta zauna ta zamar mata ƴar aiki. Amma Allah ya gani duk ranar da Nazifi bai wajenta ji take tamkar tayi hauka saboda bala'in kishinsa da take yi. Da sanyayyan muryata ta kira sunansa cikin salo na jan hankali. "Derling". Ta faɗa ba tare da ta juyo ba. Shi kuma ya tako ya iskota yana me rungumeta ta baya tare da ɗora haɓarsa bisa kafaɗunta. "Derling lafiya dai ka dawo da wuri haka?". Lumshe ido yay yana shaƙar ƙamshin da ke fita daga jikinta yace,"Na kasa samun natsuwar yin komai ne Swty, hankalina duk yana kanki ke da Unborn". Ya faɗi hakan yana ɗora hannayensa saman cikinta ya shiga shafawa. Tana murmushi ta janyo towel ta goge hannayenta tare da juyowa ta fuskance shi, in da hannayensa suka koma kan ƙugunta. "Sannu da dawowa". Kafin yay magana ta ƙara cewa,"Amma Derling anya ayi haka kuwa, shikenan kuma sai ka dinƙa baro office ba zaka zauna kayi aiki ba, yanzu idan Babyn ya zo ya ke nan?". Ta ƙarasa maganar a shagwaɓance wanda hakan ke ƙara narkar da zuciyarsa akan sonta don shi bai ganin hakan akan Sa'ida, idan ma tana yi to bai masa kyau kaman na Amaryarsa. "Hmm Swty kin san yanda na ke azabtuwa da rashinki kusa da ni kuwa. Kinga da ban san in fita aiki nayi ta zumuɗin dawowa gida ba sai yanzu da na sameki. Balle kuma da tunanina ya yawaita akan ajiyata, ke dai madallah da ƙoƙarin samar min abin da aka kasa samar min shekaru da shekaru". Shafo fuskarsa tayi tana cewa,"Ina sonka ne da yawa shiyasa nayi iyaka ƙoƙarina wajen ganin na sama maka farin ciki, kuma in sha Allahu ba tare da gajiyawa ba zan ta haifa maka yara har sai kace Swty sun isa haka". "Godiya na ke Allah yayi miki albarka". Ya faɗa yana ƙara janyota jikinsa da cewa,"Ina son wannan kwalliyar. Kin san Unborn yasa kwalliyar na ƙara yi miki kyau sosai". Tayi murmushi me sauti da cewa,"Wato ma ɗanka ne ke sawa nayi kyau?". Hannunsa na shafa cikinta yace,"Tukunna ma wai me ya kawo ki kitchen?". "Ina ƙoƙarin ƙarasa girki ne na bada akai maka office ashe ma kana hanya. Ban ji daɗi ba da ka dawo ban gama ba, kuma kaga Sa'ida ma...". Ya ɗan ɓata fuska cikin nuna rashin jin daɗi ya ce,"Haka zamu yi da ke idan na fita ki ke satar baro ɗaki kina shigowa aiki? Ko kin manta likita yace ki huta ne, Swty ke da Unborn Baby kuna da buƙatar hutuwa, don Allah ki daina takura kanki, ga ƴan aiki nan da za su dinƙa miki duk me kike so, bacin nan ga Babaa Zulai da su Mubina, Sa'ida kuma ai ƙanwarta tana wajenta akan me za ki damu kan ki da ita. Ki daina don Allah kinga ko wanka ba na bari kiyi da kan ki so ban lamunce da shigowa kitchen ba daga nan har ki haifa min farin cikina". "Derling ni gaskiya bana so ne kake cin girkin ƴan aiki, ko su Mubina kishi na ke da su akanka. Ka bar ni na samu lada tunda na sami lafiya ai, yanzu bana jin wani ciwo sosai, haihuwan ma a sauƙi zata zo in sha Allah". "Ni dai ki huta, idan ba kya so naci abincin ƴan aiki zan kira gida idan sun yi abinci suke aiko mana, idan kuma Sa'ida taji sauƙi shikenan". "A'a Honey ya kamata fa mu bar Sa'ida ta huta haka da ɗawainiyarmu. Kaga babu daɗi kar ta zo ta ƙulla ce ni ka jawo min baƙin jini a wurinta". Bai sake cewa komai ba ya kama hannunta ya riƙe suka fita a kitchen ɗin, tana ta roƙonsa akan ya barta ta ƙarasa ta kusa gamawa amma bai saurareta ba. A falo ya tsaya yana ƙwala kiran Marawiyya ƴar aiki, wacca ta zo da saurinta tana duƙawa gabansa. Yana kallonta da faman kanainaye jiki a mayafinta yace,"Ki ƙarasa aikin da ke kitchen, Idan kika ƙara bari naga matata a kitchen tabbas zan sallameki ne". "Kayi haƙuri Alhaji hakan ba zai ƙara fauwa ba". Kamar zai duƙa ya ɗauki Zahrau sai ya fa tuna ba Sa'ida ba ce da yake rarumarta farat ɗaya, wannan da nauyinta sosai da har ƙirjinsa ke ciwo idan ya ɗauketa. Suna shiga ɗaki ya zaunar da ita kan gado. Ya wuce ya ɗauko magungunanta ya kawo ya bata da kansa kafin ya shiga mammatsa mata jiki wai alallai tayi aiki ta gaji. Ita kuwa tana yi masa wani irin kallo ta kwanta kan gado tana janyo shi jikinta. "I am missing you Derling". Ta faɗi hakan wanda tuni jikinta ya fara tsuma domin sun jima ba'a je ga majiyar daɗi ba, tun satikan baya da jini ya ɓalle mata har akai tunanin ma ko ɓari ne amma da suka je asibiti sai likita yace da Nazifi ya ɗan barta ta huta, to tun sannan duk son Nazifi da ayi harka itama duk sonta sai dai su haƙura, dama ita ta fishi naci da ƙulafucin abun, gwara shi ma yana samu a wurin Sa'ida wanda hakan ke sosa ranta. Cikin wani salo na kashe jiki tace da shi,"Honey wasa kawai, ina kewarka da yawa". Lokaci guda kuma ta sauya labarin yanayin na su, ta birkita Nazifi ya rikice, shifa baƙaramin godiya yake ga Allah ba da ya ba shi Zahrau matsayin matarsa, Nazifi yana matuƙar bala'in son kasancewa da ita ko da yaushe. Yana iya rantsewa bai san daɗin aure ba sai da ya sameta, domin duk wasu wasanni na tarwatsa ƙwaƙwalwa da jin kamar zai mutu sai da ya mallaketa ya san su, ita ce kawai take masa irin yanda yake buƙata, amma ita Sa'ida ko da yaushe a cikin jin kunya take da rashin sanin irin abubuwan da zata masa wanda za su fasa kwakwalwarsa, har ta barsa da tunani idan ya fita office ya kasa sakat sai ya dawo gareta. Sai yanzu ya daina ganin laifin wata Malama da ke lecture tana cewa mata namiji yana tsananin son mace me kunya, ki zama me kunya da zarar an zo ga abin nana ki nuna masa ba ki san wata aba kunya ba, ki zama fitsararriya a wajensa idan aka zo harka, yauwa ina nufin karuwar gidan Oga. Kuma tun da ta gama yi masa wasannin sai ɓacin rai ya maye gurbin baƙin cikinsa,saboda tunawa da yay yau zai koma wajen Sa'ida. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR06FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ "Ke dakata!". Ummani ta tsawartar min da maganar da na ruɗe ina yi. Kafin a hankali kuma ta shiga faɗa min kalaman kwantar da hankali kaman yanda ta saba a ko da yaushe, tare da ƙara faɗa min cewa na dage da adu'a komai me wucewa ne. Sai da ƙyar na samu na iya tsayar da kukana, muna gama wayar na kwanta kan gado saboda yanda naji kaina na bala'in sara min, baccin ma sai ya gagara zuwa kamar yanda na ke so ta ƙarfi da yaji ya ɗauke ni. Ina cikin juyi cikin tunane tunane wayata tayi ringing, ganin lambar Safiyya nayi saurin ɗagawa, tana jin yacca nayi sallama a sanyaye ta danna ashar da cewar,"Wato sun kuma guma miki ko?". Na ce,"Hmm Safiyya lamarin nan fa kwata kwata babu sauƙi". Nan na kwashe duk abin da ya faru a ɗazu na faɗa mata, ta dingi zage zagenta da cewa,"Wai ke ba zaki iya nunawa Nazifi ƴar daba ba ce ke, ki nemi abu ki ce zaki sassara shi idan bai sawwaƙe miki ba, haba wannan bala'i na kullum yaƙi ci yaƙi cinyewa, haihuwa ke za ki bawa kan ki ne. To wallahi ki nunawa Nazifi ke mahaukaciya ce, kuma har mahaifiyar tasa ki bar ɗaga mata ƙafa yanzu idan ya so ko mai zai faru ya faru kin dai ji me na faɗa miki ko, mata ƴar bala'i da miji a raye tazo gidan ɗa ta tare saboda dai ta hana ki sakat". Nayi shiru ina jin sabbin hawaye na sakkowa ta gefen idona. "Ni dai shawara na ke ba ki Beb, ki nemarwa kanki mafita tun wuri wallahi, ba zai yiwu kici gaba da zaman wannan ƙasƙantacciyar rayuwar ba, haba Miji yay maka, Uwarsa ta maka da ƴan uwansa, yanzu ta kai ta kawo ma lamarin ya haɗa har da kishiya. To wallahi gwara tun wuri ki zama mahaukaciya a cikin gidan nan, kiyi haukan da za ki hana kowa kwanciyar hankali, rashin mutunci waye bai iya shi ba, idan ma baka iya ba a wannan zamakin koyarsa kake, don haka ki daina barin miji yana taka ki son ransa Beb". "Hmmm ba za ki gane ba ne Safiyya, ni fa duk faruwar wannan lamuran ba na so igiyar aurena ta girgiza, Safiyya idan Nazifi ya rabu da ni wa kike tunanin zai auri macen da bata haihuwa? Shima fa rashin haihuwar ne yasa ya juya min baya har yake ganina banza a wofi, yau idan ace na aje masa ɗa zai kalle ni ne yace ni da babu ɗaya a wurinsa? bayan haka Safiyya ba ki ganin irin rayuwar da zaurawa ke yi ne? Irin tarin ƙalubalen da suke fuskanta ba daga waje ba har da cikin gidan iyaye, a wannan ƙananun shekarun nawa ina zan kai zaman zawarci ni da na ke ɗorawa kaina damuwa da surutun mutane. Na gaya miki fa Kaka ya rantse aurena ya mutu zamana a gidanmu sai in faɗi yay ya mutu. Ko kaɗan mutuwar aure ba ta da daɗi Safiyya, yayin da zuciyarmu ke tafasa ne kawai muke ganin gwara rabuwa da ci gaba da zama, ke dai kawai ki tayani da adu'a ubangiji ya saita dukkan al'amura, ya kawo min sauƙi cikin wannan musibar". Muryan Safiyya a sanyaye tace da ni,"To Allah ya kawo sauƙi ya saita tsakaninku. Amma lamarin kam sai dai ke ɗin uwar haƙuri, idan ni ce sai dai Baba ya kore ni a gidansa amma sai na kashe auren billahillazi, kuma ba zan bar gidan ba sai na fasa ƙoƙon kan mijin yasin, da irin rayuwar gidanki ai gwara yawon zawarcin ina tafe ana zagina, ina ce dai ba fitowa zai ajikina ba...". Dafe goshi nayi ina girgiza kai nace,"Safiyya ya isa haka mana. Don Allah kike adu'a Allah ya sanyaya miki zuciya. Anyway yanzu dai ya ake ciki, kiran nan da kika min har naji sanyi a raina". Numfasawa tayi kana tace,"Dama zan faɗa miki ne wannan ƙwararriyar chef ɗin zata fara classes na girki amma online zata yi, kinga kin samu dama sai kiyi joining ko? Gwara kema ki koyi girke girken zamanin nan da ake na larabawa kike girkawa kanki ke ɗaya kina ci kina barin ƴan iska da shaƙar ƙamshi da tsinkewar yawu". "Uhmm to Safiyya ni kam don wa zan koyi girkin idan ba don shi ba, ai gwara na iya yaci na wuce gori. Amma nawa ne kuɗin da ake biya?". "7k ne kuma kar ki damu da wannan zan biya miki, dama i want hear from you ne if kina so kar nayi azarɓaɓin biya miki ki gwanya ni". Ina murmusa kunci na ce,"Alright na gode sosai ƙawar arziƙi, Allah barmu tare ya baki miji na gari. Sai batun spices na abinci da kika ce shima za ki haɗa ni da wacca zan ke siya a wurinta". "Amin ya Allah na gode da adu'a. Ehhh spices kar ki damu akwai Mrs Arab zan haɗaku, ba lambarta ne a wannan wayar da sai na ba ki yanzu...Ai in sha Allah kwanan Nazifi zai raina kansa, sai yay danasanin duk abubuwan da yake miki, ke dai kike riƙe duk tips ɗin da na ke ba ki, ƙananun kayan ma zan sako su a mota jibi a taho miki da su, saura idan an kawo kike ƙin sakawa kin ji, wallahi Beb kayan da na siya miki kika saka kika gimla ta kusa da Nazifi na rantse miki da kansa zai kawo kansa ɗakinki, bar shege da mu yake zancen, itama matar tasa zata ci uwarta ne". "Ƙawata ta kaina, shikenan to ina godiya kuma in sha Allah duk shawarwarinki gare ni zan ke amfani da su. Naji kin ce za ki yi aiki bara na barki haka sai da safe". "Ok Beb bye bye take care. Allah kuma ya saka miki nan kusa. Zan tura miki lambar chef ɗin sai kiyi mata magana tayi adding naki group". Ta kashe wayar ni kuma na tashi naje na ɗauro alwala nayi sallar isha'i da ban yi ba. Ƙarar wayata na shigowar text na ɗauka ina duba lambar da Safiyya ta tura mini, 09030398006. Take ko nayi saving na shiga whatsapp na aje mata saƙo. Cikin kwanaki biyun da suka biyo baya abubuwa sai ƙara faruwa suke, ƴan uwan Zahra'u kuwa sai shige da fice suke a gidan ana zuwa dubata da jiki, yanda suke ta nan da ita sai abun ya burgeni da bani sha'awa, ina jin ina ma ace ni ce, wato ashe haka me ciki ke zama ƴar gata ta kowanne ɓangare. Nazifi da ƴan uwansa kuwa sun maida ita kamar ɗanyan ƙwai sai riritata suke yi, ni dai ina ta ganin abubuwan da yanzu ko kusa basa damuna ma sai dai nayi murmushi na girgiza kai, haka za suyi ta yada habaici idan suka zo, to ni kalmar juyan ma yanzu jinta na ke kamar iska bata taɓa zuciyata. Shi kuwa da gayya sai ya shigo min ɗaki yana tambayata wai ina da abu kaza Baby ta kasa cin komai, ai na nake ganin za'a samu abu kaza, haka dai ni kam ban bi ta kansa ya gama surutunsa ya fice. Ranar ma da yana wajena sai ce yay in taimaka duk sanda nayi tuwo in ke zuba mata na ce ba zan iya ba, shine ya hau fushi wai a tunaninsa zan fishi farin ciki da samun cikin nan amma sai yaga akasin haka, bai taɓa tsammanin hakan daga gare ni ba kuma yayi mamaki sosai, amma na sani yaron da za'a haifa shine farin cikinsa sama da komai a duniya, saboda haka gwara na koyawa zuciyata sonsa tun kafin yazo duniya idan ba haka ba kuma zaman mu da shi zai fi na baya muni. Cikin ikon Allah da na ƙara dagewa akan adu'a sai na ɗan fara samun kan Nazifi, yanzu zai zauna da ni har mu ɗan yi magana, kuma ko ban je ɗakinsa ba zai neme ni, duk da ahakan ba gane masa na ke ba. Kuma wani abun mamaki hakan sai yasa Zahra'u ta tsiro da wata tsirfa ta makirci ganin cikinta ya fito sosai, wato duk ranar da Nazifi ya dawo wajena ba zata bar ni da shi ba, sai mun kwanta sai kiranta ya shigo waya tana yi masa kuka ita cikinta, Small Baby yana takura mata, amai take tayi ta kasa bacci, zata ci abu kaza, tana ga haihuwa zata yi, abubuwa dai iri daban daban da ba ya iya haƙura shi kuma sai ya farka yaje wajenta, haka zai zauna ba zata barsa ya dawo ba sai asuba. Lamarin tun bai damuna sosai har ya zo ya dame ni, na kira Ummani na faɗa mata sai ta shiga bani haƙuri kamar kullum tana faɗa min dama a irin wannan gaɓar akwai wahala, sai dai na ƙara haƙuri da kawar da kai, aduar nan dai kawai naci gaba kar na fasa. Da dai naga abin ya ishe ni muka yi waya da Safiyya na ke faɗa mata, sai ce tayi nima in fara yi masa ƙaryar ciwo wala yana wurina wala bai wurina, ita zama ta haɗa ni da likitan da zaa ce ciki ne da ni, cikin ƙarya ai ba akaina aka fara ba. Ban dai ɗauki wannan shawarar ba kawai na yanke abin da na ke ganin yafi min, dama da ya kwanta gado sai bacci shine kawai sai na samu na saka wayar a silent, haka kafin nayi bacci zan ta ganin kiranta na shigowa, asuba nayi kuma zan riga shi farkawa na cireta a silent, sai da safe idan yaga kiran sai ya kama tambayata wai kwana biyu wanne irin bacci muke yi ne, sai in masa shiru bana tanka masa. Yauma muna kwance mun ma yi nisa a bacci, kamar a mafarki naji ana ƙwanƙwansa ƙofa. Na kasa motsawa daga kwancen da na ke saboda mamakin da ya kama ni haka kuma kaina ya ɗaure, na tafi tunanin wa ye da bugu a daidai wannan lokacin haka? mirginawa nayi na ɗauko wayarsa don duba lokaci sai naga kiran Zahra'u na shigowa, ikon Allah kawai sai na kasa aje wayar na tsaya kallo har kiran ya katse, ƙarfe biyu lokacin. Tsaki nayi na aje wayar na koma na kwanta, can kuma sai aka ƙara ƙarfin bugu ka ce an biyo sahun karɓar bashi. Ina kallonsa ya tashi zaune yana ɗaukar wayarsa ya duba, sai kuma naji yana magana shi ɗaya. "Allah yasa lafiya". Ya faɗa yana sauka akan gadon ya tafi ƙofa yana tambayar waye. Wallahi tsammanina duk Iyam ce ko kuma ita Zahra'un, amma sai naji muryar ƴar aikinta na cewa. "Alhaji Anty ce bata da lafiya". Ai lokaci guda baccin ya bar idonsa da sauri ya buɗe ƙofar, yana niyyar fita na kasa haƙurin cewa da shi,"Ina zaka je kuma?". Ya juye ya kalle ni fuska duk ta gama bayyana da damuwa yace,"Ba ki ji ba Amarya ce babu lafiya, ko za ki taso muje ki ɗan taimaka mata". Iya shaƙa na shaƙa har naji kamar na miƙe na wanke shi da mari. A yau kam bana tunanin zan musu uzuri, na gaji da cutarwar da ake min, Na ɓata rai ban miƙe daga kwancen da nake ba na ce,"Amma dai kasan hakan shiga hakki ne ko? Ita ciwonta ba ya tashi kullum sai taga kana wajena, a wajen nawa ma sai muna tsaka da bacci, wato kiran wayar ma da ta saba duk bai mata ba sai ta koma haɗawa da buga ƙofa? Wannan ai zalunci ne, mutum yay magana kuma ace yana baƙin ciki da hassada". Wani kallo ya shiga yi min wanda na kasa fassara shi. Sakkowa nayi a gadon na isa bakin ƙofa zan mayar da ƙofar na rufe na ke cewa da ƴar aiki,"Ki koma kiyi jinyartata ko ki faɗa mata tasha magani". Kafin na kai ga rufe ƙofar sai jiyo ihunta muka yi a falo, tana kiran,"Wayyo cikina, wayyo marata, Derling ka zo ka taimaka min don Allah, Derling mutuwa zan yi". Ai kafin na ƙifta ido Nazifi ya fice, idona ya ciko da ruwan hawaye, ina tsaye naji Iyam na faɗin. "Ki yi haƙuri Amarya ciki dama ya gaji haka amma ki daina kiran za ki mutu, mutuwa ba yanzu ba in sha Allahu. Zafin ciwo ne kawai sannu kin ji, ai kina ma ƙoƙari wallahi Allah ya ba ki da sauƙi". Shi kuma hankalinsa a tashe yake cewa da Iyam,"Yanzu me zamu yi mata? Ko asibiti zamu tafi? Iyam ba na son abin da zai taɓa min yaro, ba na son abin da zai taɓa Zahra'u, ina son su dukansu sune rayuwata". [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR09FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ Washegari ban farka ba sai ƙarfe tara. Hakanma da ƙyar na iya tashi saboda zazzaɓi da ciwon kan da na kwan da shi. Ga ɓarin zuciyata da ya dinƙa min ciwo don ko da asuba da nayi sallah haka nayi ta nishi ina jin zuciyata kamar ana soya min ita, shi kansa farko yay banza da ni yana ji ina ta faman kiran sunan Allah cikin wahala, ashe zuciyar tasa da sauran tausayina sai ya tashi ya samo min pain relieve wurin Matarsa, naƙi karɓa na sha a ganina akan me zai karɓo min magani wurin kishiya, kuɗin siyo min me bai da shi? Asibiti kuwa dama bana saka rai don rabon da nayi ciwo yace naje asibiti har na mance, idan na buƙaci zuwa sai ya kama ƙorafin na fiya ciwo da raki, in nemi paracetamol na sha asibitinma ko naje shi zasu ba ni. Duk sanda yay furucin nan sai dai na girgiza kaina, Namiji ne shi Ƙayar Ruwa, amma ban da rashin adalci irin nasa ko da muna zaman lafiya sarai yasan irin ƙarfin hali na ciwona, sai nayi ciwo ma na gama ban bari ya gane ba. Kuma idan shine ke ciwo mura wannan ya dinƙa kwakwazo, sannan a hakan Zahra'un da ta zo kafin ta samu cikin ma kusan duk sati suna hanyar asibiti bata da lafiya, amma bai taɓa ƙorafi ba. Ai har sai da na ga ciwo na neman kashe ni kana na karɓa maganin na sha baƙin ciki na daɗa tokare min zuciyata, danasani da nadamar ƙin tsayawa nayi karatuna na baibaiyeni, don duk da wannan tarin baƙin cikin ban fuskance shi ba, a ƙalla da ina aiki ko ba'a biyana da yawa nafi dai ƙarfin na ce da Nazifi ya siya min magani balle har ya ƙuntata mini. Ni dai maganin ma da na sha sai naji tamkar ana ƙaramin zafin ciwon, haka nayi ta malelekuwa a ƙasa ina hawaye, ga zafin ciwo ga fargabar tunanin Allah sa ba ciwon zuciya ne ya kama ni ba, shima dai abun sai ya ba shi tsoro ya shiga binciken paracetamol ya kawo min, ƙarshe dai sai ruwan zamzam ya tsiyaya ya tofa min bismilla ƙafa sha tara ya ban na sha tukunna na samu sukuni na koma bacci. Agogo na kalla naga har goma saura, rashin ganin Nazifi a ɗakin banji wani mamaki ba, don na san dama yau ba lallai ya bi ta kaina ba idan zai fita, kuma ba saboda tausayin ciwon da nake ba, sai saboda na faɗa masa Allah ya saka min katse min baccin da yay akan biyan buƙatar wata can da alhakin ci da ita ba akaina yake ba, har ina faɗin ba zan yafe ba shine yace kar na yafe na ce dama ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne ko ban ce ya saka min ba zai saka min ne. Shine har ya na ƙara faɗa min shi fa bai ƙaunar duk wanda ba zai so ƴaƴansa da uwar ƴaƴansa ba, kuma akan hakan yana iya ɓatawa da kowa. Na sakko a gado cikin ƙarfin hali, ɗakin na gyara anan nayi wanka kana na koma ɗakina na shirya. Saudatu na kallona tace,"Yaya Sa'ida ba ki da lafiya ne?". Na ce da ita,"Lafiyata lau". "Naga idonki yay jawur". Ta faɗa tana taɓa jikina sai ta ƙara cewa,"Kuma kin ji jikinki ma zafi". Bance mata komai ba na buɗe wadrobe ina kwaso kayan wanki, sai sannan idona ya kai kan Rumana da ke bacci. Na kalli Saudatu ina cewa,"Lafiyar ƴar nan bata je school ba?". Saudatu tace,"Nima ina bacci ta ƙwanƙwasa ta shigo naga tana hawaye". Rigar da ke hannuna na ajiye, na yaye bargon da ta rufa da shi ina taɓa jikinta, babu wani zazzabi don haka na shiga tashinta. Ta buɗe ido tana miƙa ganina kuma tayi firgigi ta miƙe zaune tana micimici da idanu. Ina mata kallon shiga taitayinki da ni na ce,"Rashin lafiyar ƙarya saboda kar kije makaranta ko? A haka kike so mu shirya da ke? Salon ki jawo min zagi da cin mutunci ace ni nake hana ki saboda ina baƙin cikin ban haifa ba, koma me za'a gaggaya min ai kin sani dai tun da gaban idonki ake komai. Ina ce har alƙawari kika min akan ba za ki ƙara yin abin da zai jawo min faɗa ba. To saukar min a gado ki ficen kije can, kuma kar na sake naji kin ambaci sunana a bakinki". Ƙasa tayi da kanta kafin ta sauka ta fita jiki a sanyaye. Na ci gaba da haɗa kayan Saudatu sai magana take min akan na kwanta na huta kuma akwai kuɗi a wurinta ko taje ta siyo min magani nace mata a'a. Haka na gama na shiga banɗaki ina wankewa tana tayani ɗauraya, babu yanda bata yi da ni ba akan na barta tayi ita ɗaya, ni kuma bana so ne ciwon da nake ji ya kwantar da ni shiyasa gwara na motsa jikin nawa. Yau ɗin dai haka na ke jina sukuku babu wani daɗi, Da ace akwai injin wanki ne sai na ƙyale mata, to tun zuwan Iyam ƴan uwansa suka lalata shi, kowacce ta tashi zuwa sai ta yayibo uban kayan wanki, dama ni ba damuwa nayi da amfani da shi ba dan ko da na ke wankin Iyam ma ban taɓa yi da shi ba. Mun fita shanya kawai na ga Rumana durƙushe gefen ɗaki ta kifa kai sai shashshekar kuka take yi a hankali a hankali. Ban saurareta ba nayi gaba, sai kuma duk naji zuciyata ba zata iya watsi da yarinyar ba na barwa Saudatu shanyar na dawo. Kanta na tsaya na kira sunanta ta ɗago tana kyarmar jiki. "Don Allah Anty kiyi haƙuri". Harara na galla mata nace,"Rufe min baki ni, ba damar ayi miki faɗa sai ki kama kuka, idan kinje makarantar zan miki faɗan ne? Ke ba ki san ni kike bari na kwana a ciki ba, ni kike jawa maganganun ɓacin rai". Ta saka kuka tana rungume ni tace,"Anty ai ba ƙin zuwa nayi ba, yau ba ki zo kin tashemu ba kuma da Atika ta tashi bata tasheni ba. Sai da ta gama shiryawa na farka, kafin na shirya an tafi kaita shine Anty Amarya tace zata aiki direba na haƙura da zuwa ko na karɓo kuɗin mota ko na tafi a ƙasa". Tausayi naji ta bani, duk sanda na kalleta sai na tuna wahalar da suka bani, haka sai na tuna wulaƙancin da iyayensu suka yi min, da wanda ake kan yi har yanzu, don na kasa mantawa da dukan da Uwayensu suka min, haka na kasa mantawa da a dalilin sharrinsu watana goma sha ɗaya cif ban taka gidan ubana ba. To amma ita yanzu duk ta maƙale min, ko shareta nake ta dinga kuka kenan tana bani haƙuri, kuma wai saboda ta daina wancan mugun halin Iyam sai take tsangwamarta, itama ƴar uwartata da ta samu ɗaurin gindi sai ta daina kulata, shi kansa gogan saboda Rumanan a wajena take bai fiya lura da lamarinta ba, Atikar dai ita ce ƴar gata a wurinsa tunda tana wurin amaryarsa, ni Rumanan ma har tausayi take bani nayi nayi ta koma can wajen Zahra'un taƙi ita tafi son wajena. Na ce,"To kin yi breakfast?". Kaɗa min kai tayi alamar a'a. Muka sauka naje na dafa mata indomie don ni ban jin ma zan iya cin wani abu kam, Saudatu kuwa tana azumi da yake alhamis da alhamis bai wuceta. Da rana muna falo muna kallo sai ga su Ummaa sun zo. Da fara'ata na miƙe ina musu sannu da zuwa, fuska babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata, ina cewa ga wurin zama sai ce tayi. "A'a ai ba wurinki muka zo ba, ba ki ga kayan hannun mu ba ne, me ciki muka zo dubawa da kayan barka kafin a haihu mu ƙaro wasu". Nayi murmushi na ce,"Allah sarki to an gode. An zo lafiya ya Malam?". Tana jefa min banzan kallo irin wanda Iyam ke min tace,"Malam na lafiya". Suka wuce ina bin su da kallo, irin set ɗin robar kayan wankan jarirai ne sai ƙatuwar baƙar leda da na san ba zai wuce kayan yaro ba. Abin na ta dai ba na Allah ba ne don ta ƙara samun shiga wajen Iyam ne da shi kansa Nazifin. Dama ai ita da Iyam ɗin kansu a haɗe yake sun ware Amarya a gefe baiwar Allah da babu ruwanta, ita kam zuciyarta fess babu datti. Sama suka nufa, kuma nayi musu shiru ban shaida musu cewar tana ƙasa ba, tun da ba wurina suka zo ba ina na ke da hurumin faɗa musu kuwa, gwara nayi shiru kafin a ƙara faɗa min magana, ile sai ga su sun sakko suna raba idanu. "Sa'ida ai babu kowa a wurin nata". "Ta nan ƙasa ai". Ta bini da kallo wanda ke shaida taji haushi, ta kama faɗin,"To da ba sai ki shaida mana ba amma kika barmu muka hau. Ko don na ce ba wurinki na zo ba, to me zan zo nayi a wurinki ke da ba ƴaƴa ba balle na ce na zo ganin ƴaƴan Nazifi". Ta gama maganganunta suka wuce, nan ma dai haka ta gama bin ɗakunan ƙasan ta dawo tana ce min. "Ina ne wajen nata ne, wannan ƙasan naku masu surƙuƙun waje duk a kasa gane masa". Kamar na ce,"ki kira wayarta ki tambayeta". Sai naga hakan kuma ai zama da rashin girmamawa, ko ba komai matsayin uwa take, ni kuma ban da halin rashin kunya wa manyana. Na kalli Rumana zan ce ta tashi ta raka su sai naga ta ɓata fuska tana kaɗa min kai a hankali alamar bata son zuwa, kawai sai nayi musu nuni da hanyar dama ta jikin lungun tsakanin ɗakina da nasa ne. Saudatu tace,"Wallahi Yaya Sa'ida idan da nice ba zan faɗa mata ba. Mtswww mutanen nan ba su da kirki ko kaɗan". Nayi guntun murmushi bance komai ba. Ni dai hankalina duk bai ga kallon da muke yi, domin kuwa lokaci ɗaya naji gabana na ta faɗuwa kamar ƙirjina zai faɗo, na shiga adu'a amma inaa. Tuni kuma sai na fara tunanin can gida, kwana uku kenan bamu yi waya da Ummani ba saboda wayarta ta lalace, wanda rashin jin nata ya haifar min da rashin kwanciyar hankali duk abin da nake ina daurewa ne kawai. Jiya ma sai Yashaik na kira yace idan ya shiga gidan zai haɗamu, Yaya Al'amin kuma haushi naji don ko a shekaranjiyan sau huɗu ina kira ina cewa ya haɗa ni da ita sai yace in kashe zai je ya kai mata amma sai inji shiru, ni kuma nayi zuciya na ce ba zan ƙara kiransa ba. Kasa haƙuri nayi na kira Maman Yasmin, muka gama gaisawa muka yi ƴar hira sannan nace ko zata taimaka ta bayar akaiwa Ummani wayar. Tace min to bara ta duba ko zata sami yara don yanzu duk sun tafi Islamiya. Shiru shiru bata kira ni ba har na ƙara kira tace bara kawai taje ta kai da kanta, na ce a'a ta bari ko su Yasmin suka dawo ta basu, ni dai kawai don Allah ta haɗamu. Bayan gama wayar tamu na kwanta, a raina ina jin ina ma ina da kuɗi in siyawa mahaifiyata sabuwar waya, da haka bacci ya ɗauke ni. Ban jima da soma baccin ba na farka a tsorace ina salati, wani mummunan mafarki nayi wai ƙofar gidanmu cike da mutane an kafa rumfar tanfol, kuma na shiga gidan sai na tadda su Yashaik sunata kuka, na tsallake mutane na faɗa ɗakin Ummani da gudu, ina shiga na ganta itama tana kukan, na faɗa jikinta ina tambayarta me ya faru sai ta kasa ce min komai. Daga tsakar gida sai naji ana Allah yasa ya huta yasa Annabi ya san da zuwansa, ban san lokacin da na fita ba ina tsallaka mutanen tsakargidan nayi ɗakin Kaka, shima a can na sameshi shi da ƴan uwansa da su Baba Tijjani, na bi kowa da ido Abbaana ne kawai babu, ban gansa ba haka kuma fuskokin duk ɗinsu da jimami. Sai naji kafafuna sunyi sanyi na fito a gigice nayi ɗakin Abbaa, ina zuwa naga an saka kwaɗo abin da ba'a taɓa ba, wai sai naji muryar Hajjo na ce min kiyi haƙuri Sa'ida ita mutuwa dole ce, Abbaanki ya amsa kiran mahallicinsa. Ai ban san lokacin da na ƙwalla razananniyar ƙara ba na zube a wajen ina ihu ina kiran sunan Abbaa, aka taru akaina Ya Imam shi kuma na min ihun na rufewa mutane baki. Ina hankalina zai kwanta da wannan mugun mafarkin, ai tuni na miƙe ina cewa da Saudatu,"Tashi ke ki shirya". Itama yanda taga na fita a hayyacina ta kama tambayana, ban tsaya sauraronta ba na haye sama suka biyo ni suna ta me ya faru. Ko da na shiga ɗaki sai na rasa abun ɗauka, duk na ruɗe na riki ce. Ta zo ta kamani ta zaunar, Tuni kuma hawaye ya fara sauka a fuskata kamar an kunna famfano, ina ta juya kai na kasa cewa komai duk da cewar magana na ke so nayi, mafarkin ne yake ta haska min a ido. Yawu naji tana tofa min wanda na fahimci adu'a ne take yi, ita kuma Rumana ta ƙanƙame jikina ganin ina kukan itama sai ta sa kuka. Sama sama naji Saudatu na faɗin,"Kema da saka abu kike a rai, na san rashin jin Ummanin ya sa kika yi mummunar mafarki, dama shaiɗan me jiran kaɗan ɗin saƙa maka mummunan abu. bara a ƙara gwada lambar Ya Hindatun ko zata shiga". Murya na rawa na ce,"Ba ita za ki kira min ba, kira me gidan nan ki faɗa masa zan tafi gida". Ganin bata da niyyar kiran na ƙwaci wayar, ruwan da ya taru a idona yaƙi barina ganin screen ɗin wayar, sai itan dai na miƙawa nace ta taimaka ta kira shi. Ta kira har sau uku bai ɗaga ba, nima na karɓa na dinga kira amma bai ɗaga ba, duk da ba yau ne karon farko na rashin ɗaga min waya da yake amma na yau ɗin sai na fi jin na damu da shi, hankalina ya ƙara tashi, to kar dai mafarkin nan ya zama gaskiya Abbaa ya mutu, Ina zan sa kaina idan na rasa Abbaana a wannan gaɓar? Yaushe rabon da na gansa? kuma ya mutu yana fushi da ni? Bana so ya mutu duk da mutuwa dole ce, haka ba na so ya mutu sai ya san gaskiyar lamarin da ya faru akan case ɗina da Nazifi da yaransa. Tunani nake akan na tafi kawai in yaso ko na ƙarasa gidan na faɗa masa, sai dai har kullum ina tsoron fita babu izinin miji duk da lalura ce ta kama a yanzun, to amma ai bani da tabbas. Zuciyata ta yanke shawarar na tashi na shirya kawai, kuma sai bayan mun shirya har mun sakko falo na tuna da kuɗin mota, naira ɗari ce da ni hagu da dama, na kalli Saudatu nace,"Nawa ne kuɗin hannunki?". "Ɗari ce". Shiru nayi ina tunanin yanzu wa zai ɗaukemu ya kai har makwarari a ɗari biyu? ga shi kwanakin nan na fahimci can gida ma a matse suke don haka ba na ce in munje can ma karɓa ba. Kiran wayar Nazifi na ci gaba da yi, nayi sa'a ya ɗaga a wannan karon, ko sallamarsa ban amsa ba nace,"Don Allah zan je gida". A daƙile yace min,"wanne rainin hankali ne hakan baki san da tambayar ba sai bayan na fita, kuma tun tashinki sai yanzu za ki kira ki tambaya, to babu in da zaki je". Roƙonsa na shiga yi, yanda yaji ina masa magiya ya daka min tsawa da cewa,"Ke ya isa, ina tsaka da aiki kin addabe ni da kira kamar me bina bashi, na kira kuma kina min kuka da faman magiya, ke wacce kalar macece ne mara natsuwa da rashin sanin yacca ake magana da miji. Me ake a gidan naku dama?". "Kayi haƙuri, zan je naga Abbaa ne". Hmmm zuciyata ta matse jin yana tambayata,"Waye Abbaa?". Ya faɗa kafin na bashi amsa kuma sai ji nayi yana faɗin,"Hasbunallahu ai na manta ma gaba ɗaya". Kamar an kulle masa baki sai yay shiru. Na daɗa ruɗewa ina tambayarsa,"Me ka manta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un don Allah ka faɗa min wani abu na faruwa ne da aka ɓoye min?". Ƙaramin tsaki yaja kafin yace"Ki shirya kije ɗin". Na ce,"To don Allah ko zaka turo min da kuɗin mota, ɗari biyu ce da ni ba zata kaimu ba". Sai ya ƙara cewa,"To wai dole ne zuwa gidan, ko kin manta har yanzu wa'adin da Baban naki ya ɗauka miki na rashin zuwa gidansa bai ƙare ba ne. Ko kiranki suka yi?". A sanyaye na ce,"A'a hankalina ne yaƙi kwanciya don Allah kayi haƙuri ka taimaka min da kuɗin motar". "Ki aika Saudatu ta karɓo miki dubu ɗaya wajen Amarya". Na rumtse ido nace,"Amma...". Ya katse ni da cewa,"Kinga idan ba za ki aika ba ki haƙura ko ki tafi a ƙasa. Ni dai kar ki ƙara kirana kina katse min abu me muhimmanci". Daga haka ya katse wayarsa, ina jinsa kafin ya katse yana faɗin,"Hamisu kaga na manta ina cewa zaka raka ni gidan su Sa'ida, wanne asibiti ma Al'amin yace mana?". Sai naji hawaye ya ƙara zubo min, zuciya da jiki na rawa na miƙe. Tabbas akwai abin da ake ɓoye min, kuma mafarkin nan yana haska min ne, haka nayi watsi da takaicin karɓo kuɗi wurin Zahra'u. Ban da yanda zan yi haka dole na tura Rumana ta karɓo, sai da ta jima aka gama jan lokaci sannan aka bata dubu biyu wai ya kirata yace ta ƙara mana dubu ɗaya. Rumana tana kuka akan zata bi mu na ce tayi haƙuri saboda makarantarta ba zai yiwu mu tafi tare ba. Muna isa gida muka tarar jikin Abbaa ba yanda yake, Yayyuna suna gefensa sai firfita suke masa, Ummani tayi jugum a gefe ɗaya ta zabga tagumi tana kallonsa, kana kallon fuskarta kaga na wacca ta sha kuka ta gode Allah. Wai ashe kwanansa huɗu yau a kwance, saboda kar na san da ciwon aka ce min wayar Ummani ta lalace, Su Yashaik suka amshe don kar zuciyarta tayi rauni ta faɗa min, hatta Abbayoma ya zo shi da yake can garin damaturu amma ni da nake nan aka gagara sanar da ni rashin lafiyar mahaifinmu saboda kar a ɗaga min hankali, a ganina ba'a min adalci ba sam. Haka na isa gefen kan mahaifin nawa na zauna ina kamo hannunsa na riƙe, bai gane ni ba kwatata kwatata, ga dai shi idonsa akaina yake ashe ba ya gani yau ne ma idon ya ɗan buɗe masa amma jiya da shekaranjiya duk ba ya gani. cikin kuka na ke jera masa sannu ina cewa Abbaa ka yafe min don Allah. Sai da yaji muryata ya gane wacece, duk da a tsananin ciwo yake amma sai ce yay,"Me yasa kika zo alhalin wa'adin lokacin da na ɗauka maki bai cika ba, karo na biyu da kika take maganata Sa'ida". Yay maganar a wahalce. Ni dai kuka kawai na ke yi, shi kuma cikin zafin ciwo faɗi yake na tashi na tafi gidana. Sai da Kaka yay magana kana yay shiru ya haƙura. Har bayan isha'i muna kan Abbaa, ciwo babu wani sauƙi har cewa yake a ƙyale shi ko yanzu ya tafi ai ya mori duniyar kuma dama kullum cikin jiran cikar lokaci yake, muyi masa fatan dacewa da rahmar ubangiji kawai, sannan mu haɗa kanmu Yayyuna su kula da ni, kuma mu riƙe mahaifiyarmu da kyau. Wannan furucin nasa ya daɗa tsinkar da zuciyoyinmu, mazan ne kawai suka yi ƙarfin halin riƙe hawayensu a hakan ma ban da Abbayo, ni da shi kuka muke haiƙan. Sai wajen tara na dare ciwo ya lafa masa har bacci ma ya ɗauke shi. A ɗaki Ummani ke faɗa min ai tunma a ranar da ya fara ciwon aka kira Nazifi, aka ce kar ya bani aron wayarsa ma na kira gida, mamakin da tayi da har yanzu bai zo ba kuma waya ma bai kira ba, don ɗazu ma da ana neman kuɗin da za'a yi masa scanning na hanta Yashaik yake cewa ko shi zai kira ya tambaya aron kuɗi sai ta hana. Ko kirana bai yi ba yaji daga gare ni, ban san dalilin ma dana sa a raina cewa zai kira ni ɗin ba. Washe gari da safe sai gashi ya zo, yana bawa su Yashaik haƙuri wai ayyuka ne suka sha gabansa shiyasa, duk yanda ya so ya yakice ba yanda zai yi. Da zai tafi ya ajiye musu kuɗi Ummani tace ba za'a karɓa ba tasa Abbayo ya ɗauka zai mayar masa, ni kuwa na karɓa nace ba za'a mayar ba tunda dama cikin buƙatar kuɗin ake, Don yanzu haka wata allura aka rubuta dubu goma Yashaik da Yaya Imam na can sun fita nemo kuɗi. Ranar cikin dare a lokacin ƙarfe uku, ina tsakiyar sallah wayata ta shiga ƙara, bayan na idar kuma ina jan carbi ta ƙara yin ƙara na kai hannu zan kashe zatona alerm ne, ashe kira ne na ɗaga ma ina tunanin kashe alerm ɗin nayi, sai daga nesa nesa na ke jin kamar ana kiran Sa'ida, wayar na ɗauka da zummar kunna fitila na haska na fita ko Ummani ce ke kira, sai naga ashe a wayar ne kira ke tafiya. Tsaki nayi na kashe kiran na koma kan sallayar, kiran ya ƙara shigowa raina a ɓace naja tsaki na ɗaga,"Ina jinka lafiya kira ya wannan lokacin kamar wanda ke bina bashi". Muryarsa na shaida tsananin damuwar da yake ciki yace,"Muna asibiti ne Zahrau ce ke naƙuda, kin ganmu tun tara amma har yanzu shiru. Shine na kiraki don Allah ki sakata cikin aduarki, na san sallah kike yanzu. To don Allah kiyi mata adu'a sosai kin ji bana so wani abu ya sameta ita da yaran". Nayi shiru zan sauke wayar a kunne yace,"Don Allah Habibty, kinga shekara cikin ta goma da aure sai yanzu Allah zai bani haihuwar nan, ko ba don ita ba kiyi saboda mijinki, nima kar kiyi don ni kiyi saboda Allah Habibty". Ido na rufe ina jin wani abu na tasowa a ƙirjina, a hankali na ce,"Tom zan yi saboda jalla wa'azza, Allah ya sauketa lafiya. Ka kwantar da hankalinka kaima ka natsu kayi mata adu'ar". A sanyaye ya amsa da,"To nagode. Na so ma ace kina nan, ya jikin Baban na ku da sauƙi ko?". Ban amsa shi ba na kashe wayar na ci gaba da ibadata ina roƙawa mahaifina lafiya da kawo mana sauƙi cikin halin babun da ake, Haka kuma na haɗa har da ita me haihuwar nayi musu adu'a. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR08FT5* _Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._ __________________________________ Baccin yammar da bai saba kwatata shi ya ɗebe shi bayan sun gama gurzar soyayyarsu, da ƙyar Zahra'u ta raba jikinta da nasa ta tashi tana jin jikinta duk ciwo, nan ta fita ta barsa ko motsi bai yi. kuma ba shi ya farka ba tun bayan la'ar sai da aka fara kiran magriba Zahra'u ta zo ta tashe shi. A da sabon sa ne bai baro masallaci sai anyi isha'i amma tun da ya auri Zahra'u ba ya izama, ana idar da magriba zai dawo idan anyi isha'i ya ƙara komawa, lazimi da sauran karatunka da ya saba yi duk ya watsar. Yanzu ma ko da ya dawo daga masallacin a ƙa'ida ɓangaren Sa'ida zai wuce, tun da dama shigar lokacin kowacce bayan magriba ne, amma sai yay tsaki fuskarsa na nuna ɓacin rai, sam bai son komawa can, shi da zata taimaka ma ta amince da ya jingine aurensa da ita, zai bata maƙuden kudaɗe, bacin haka ma yana duba abu ɗaya ne shiyasa yake zaune da ita har kawo yanzu, amma shi ganinta ma bai son yi kuma a wajensa batta da amfanin komai tun da har ta gaza samar masa da ɗa, yana ta faman tsaki ƙasa ƙasa ya ƙara komawa ɓangaren Zahra'u. Ko da ya shiga ɗakinta bai sameta ba don haka ya fito ya nufi falonta, can ya iske su ita da su Inna Zulai da Iftihal, Inna Zulai ta sakata gaba da cewar sai ta tattaka yawan zaman da take yi ya isa haka kam, ya kamata take motsa jiki ko dan ta samu sauƙi wurin haihuwa. Ganinsa ɗin ita kuma ta shagwaɓe fuska tana yin narai narai da idanu, Innar ya gaida su Iftihal ma suka gaida shi kana ya juya ya koma, cikin ransa yana ta adu'ar Allah yasa kar Inna ta hana Zahra'un fitowa tun da tasan yau ya fita a wajenta. Yana tsaye ya tsurawa ƙofa ido sai gata ta shigo, ya saki ajiyar zuciya yana tafiya wajenta cikin nuna jin daɗi da ɗoki kamar wanda ya shekara bai ganta ba, rungumeta yay yana kai hannu cikinta, idonsa a rufe yake cewa. "Ina tsananin son ku, kune farin cikina, kune rayuwata, kune komaina, Allah yay miki albarka Swty, Na gode Na gode da ƙoƙarinki na samar min cikar muradina, Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya kula min da ke da abin da za ki haifa min". Sai ya zameta ajikinsa yana tallafo fuskarta yana ƙarema kyawunta kallo. "Nayi miki alƙawarin rabin dukkan abin da na mallaka, sauran kuma na abin da za ki haifa min ne, ni bana da buƙatarsu, babban buƙatata haihuwa kuma na sameki kin sama min ita a lokacin da na fidda tsammanin samu, don haka kin gama samuna da ni da dukkan wani abu da yake mallakina. Ina sonki so mai girma". Ya faɗa yana sumbatarta a gefen baki, tayi murmushi kawai tana kallonsa, ya kamo hannunta suka isa bakin gado ya zaunar da ita, har ta zauna sai kuma tayi saurin dafa shi ta miƙe jin kamar an tsikareta, nan ta kama yi masa ƙorafin irin ciwon da take ji a jikinta, shi kuma sai faman lallashinta yake kamar zai ciro cikin ya mayar jikinsa. Hankalinsa ya tashi ganin ta kasa zama, ya fita a ruɗe ya kira Inna wadda tana zuwa ta dubi Zahra'u tace da shi,"Ka kwantar da hankalinka kai kam, ba haihuwar ba ce kawai dai alamominta ne na ana kan hanya. Itama dai don raguwa ce". Innar ta ƙarasa maganar da zolaya, Zahra'u tace,"Ai ko dai Inna a irin wahalar da Babyn nan ke bani Allah ni ba ƙaramar jaruma ba ce". Innar ta fita tana murmushi, shi kuma ya riƙe hannunta sunata kaiwa da komowa a ɗakin da yake ƙato ne gari guda, kaf ɗakunan gidan albarka, a hankali kuma sai ta fara jin daɗi har da kanta ta buƙaci zama. Ta zauna tana sauke numfarfashi, shi kuma ya duƙa a gabanta yana ta shafa cikin yana kallon fuskarta. "Sannu Sweety". Hararar masoya tayi masa, ya kama hannunta ya ruƙo cikin nasa sai zuba yake mata. Idonsa ƙyam kan cikin yake cewa,"Yanzu Sweety da gaske ƴaƴa biyu ne a nan?". "Ummm kuma duk masu kama da kai ba". "A'a ai dole a samu ɗaya me kama da ke, ni nafi so ma suyo kamanninki, amma dai shi abokina kar yay gajarta irin taki". Dariya tayi tana faɗin,"Ohh ji son kai, kana jin irin zagin da ƴan gidanmu ke min akan rashin tsayi kuma shine zaka so princess ta biyo ni. Aa itama gwara tayi tsayi kaman naka kasan fa ance doguwar mace rabin kyau. Kuma sannan ma ina so tayo irin idonka kaga ai ka fini manyan ido naka sexy eyes ne suna da kyau a wurin mace". Dogon numfashi ya sauke yace,"Sweety kinga ni ban samu nayi karatun boko ba, wanda kuma hakan ke damuna. Sam ba zan yi saken da za'a ce Muhammad bai yi karatun boko ba, dama na addini wannan kam gidan suka tarar zan ɗora shi akai Sweety, zai gaje ni in sha Allahu, sai dai ina roƙonki da ki taimaka min wajen tsayawa akansa kiga boko ta kafu akansa". "Honey son kai? Komai sai kace shi baka saka Pricess". "Ai har da ita na ke nufi. Kinga tun yanzu ma ya kamata muga irin makarantar da ta dace a sa su". Wayarsa ya zaro a aljihu ya bata yana cewa,"Shiga goggle ki dudduba mana tsadaddun makaratun ƙasar nan, amma wanda ake karatu haiƙan. Ɗazu na gwada yi to ban san me zan rubuta ba, ko ana rubutawa da hausa?". "Hmm Honey turancin nan fa babu wahala. Ka dai ƙara dagewa akan Jammaje Academy ɗin nan zaka gani har sai kazo ka fini, turanci ai yare ne kana sa kanka zaka koya. Kuma Honey batun school na su ai da ka bari sun zo duniyar tukunna ko". Fuskarsa ya shafo yana cewa,"Kin san wani abu ma. Ki binciko ƙasar da kike so na kaiki ki sami hutu kamar na shekara guda, kina buƙatar hutawa Sweety saboda ɗaukar cikin yara biyu ba wasa ba ne". Haka fa suka zauna suna ta lissafi da tsarawa akan rayuwarsu da yaran da za'a haifa, shaf ya mance yana da wata matar ma a gefe, wadda ko tunanin ma Allah ya iya kawo mata haihuwar bai yi, idan ta haifa ɗin kuma bai da wani abu da zai ɗaga yace ya bawa yaran wajenta don komai ya tattara ya baiwa Zahra'u, har ATM ya ɗauko ya bata yace ta ajiye a wajenta na Muhammad ne, duk wata zai dinga saka masa kuɗaɗe a ciki, ba ya so ɗansa yay irin rayuwar wahalar da yay a baya. Ita dai sai dai tace to, sai ita ta ankare da tafiyar lokaci ma tace da shi lokacin sallar isha'i yayi, ya fita kamar ba zai fitan ba, lokacin da ya dawo ya sameta tana waya da Iyam. Dama da zai wuce masallaci ta kira shi ya haɗata da ita sai yace mata yaje masallaci, shine ita kuma ta kasa haƙurin jiran ya dawo ta ciyo bashin kamfani ta kirata, don ko iya jiran a zo a saka mata kati ma ba zata iya ba, tunda ta kira take ta tambayarta jikin nata tana faɗa mata ai ta kusa dawowa cikin satin nan ma kuwa saboda ta karɓi haihuwar jikanta. A ƙasan zuciyar Zahra'u tace mahaukaciya ce ta haifan zan yi irin haihuwarku ta marasa ilimi, ke har tunanin ma zan haihu a gida kike da kika fara lissafin za ki karɓi haihuwata, ai wallahi ko da wasa. Dawowarki ma ni bana so don dama ba son zamanki na ke a gidan ba, lokaci ma na ke jira ki koma matsuguninki. Bayan gama wayar tasu ta ankarar da Nazifi tafiyar lokaci, ɗan tsaki yay ɓacin rai na ƙara wanzuwa a fuskarsa ya ce,"Sweety ba na son matsawa daga kusa da ke. Ko na tafi ma gangar jikina ce kawai acan, Ko in kira Sa'ida in tambayeta ta bar mana kwananta? Kinga tana da sauƙin kai zata amince". Ta ware ido tana kallonsa, cikin ranta ta ayyano idan ita Nazifi kewa wannan ɗibar albarka ai tuni ta zagwanyar masa da fatar jiki. Ko ranar da ya mari Sa'ida a gabanta sai da taji lamarin har ƙasan zuciyarta don sosai ta bata tausayi, Sai dai a nata ganin Sa'idan ce tayi saken da har yake mata abubuwan da yaga dama, da ace tun fari tana taka masa burki wataƙila ya raga mata, wai ma har yana faɗin zai iya tunkararta ya tambayeta ta bar masa kwana akan kishiya? To ba rashin haihuwa ba ko rashin me take yi ya isa ya gwada mata haka in bata masa ɗanyan kai ba. Hure mata iska a ido yay da ƙara cewa,"Ko kin fi so na tafi ɗin? Amma dai ki sani farin cikina da duk jin daɗina anan yake, can wallahi takura kawai na ke yi. Ni dai kima bari na kirata na nemi izininta za kiji da tace da ni to". Tayi saurin dakatar da shi da danna kiran da yake shirin yi a waya tace,"Amma Honey zamu yi hurting ɗinta ai, kayi haƙuri kaje kar mu ke shiga hakkinta. In dai Babynka ne idan ya zo ma sai kake tafiya da shi can, nima don babu yanda zan yi ne da na maƙale a jikinka mun tafi tare domin bana son rashin jin daɗin da kake yi. Kaga yanzu ita sai ta ƙullace ni take zaton ni ce na ke hanaka zuwa wajenta, kuma zuciya bata da ƙashi sai ta iya ɗarsa mata ta cutar da ni kuma ga Twins tare da ni". Ta faɗa da nuna damuwa sosai, ai ko ya shiga jijjiga kai yana faɗin,"Ta cutar da ku? Ai kuwa da zaman duniyar nan ya gagareta wallahi, akanki da Ƴaƴana?". Sai da ƙyar dai Nazifi ya iya tashi ya tafi ransa duk a dagule. Har sai da yaje ya faɗawa Inna kome ake ciki ayi gaggawar kiransa komin dare. Zaune muke ni da Saudatu da Rumana muna ta hira, sosai zamanta kam ke ɗebe min kewa har bana son ma lokacin komawarta yayi, shiyasa idan aka kira ni daga gida sai na ƙara narkar da murya don su shaida sauƙi fa babu shi, don haka suma bar kiran ta dawo. Agogo na kalla naga har ƙarfe goma, na jijjiga kaina haɗe da yin murmushin takaici. sai ga kiransa ya shigo, haushi yasa nayi biris da kiran naƙi ɗagawa, ban da ya raina min hankali sai yanzu ƙarfe goma tukunna zai baro wajenta, ko da akai magriba naje ɗakin nasa ban gansa ba tsammanina ya tsaya masallaci ne , haka nayi ta zaryan hawa da sauka wai sai can dawowan da zanyi na jiyo muryarsa acan ɗakin nata yana faɗa mata shi fa yana ganin za'a ƙara yawan kwana domin gaskiya kwana biyu nayi masa kaɗan a wajen kasancewa tare da ita, ita kuma me ta faɗa masa Allah masani sai jinsa nayi yana ƙara cewa to ai ita akwai yaronsa tare da ita zama da ita yafi zaman wajena muhimmanci. Irin wulaƙantanin da yake da nuna mata rashin darajata a wurinta sai dai Allah ya saka min kawai. Don ko satin baya sai da ta yaɓa min magana kan ai yanzu ita ce matar so a gidan, miji bai taɓa ɗaga mata murya ba balle yasa hannu ya mareta ko yay mata gorin haihuwa, idan ina taƙama da Uwar gida ai suna ne kawai domin yanzu ita ce da gida, ranar maganganunta sun ƙona min rai sosai sai dai ban bi ta kanta ba, Saboda banga laifinta ba kome ta gaya min shi yaja min, shi ya bata ƙofa. Rumana tana dubana tace,"Abba yana kiran waya". Ban amsa mata ba na miƙe na shiga banɗaki, lokacin da na fito sai ga shi ya turo ƙofa ya shigo yana kiran sunana, ban amsa ba rai a haɗe kamar hadari. Saudatu ta gaida shi ya amsa yana tambayarta ina ina, ta kallo ni sannan ta kallesa tace,"Dama ta shiga banɗaki ne amma gata nan ta fito". Niko na tako kamar ban san da zuwan nasa ba ina goge ruwan fuskata na nufi wadrobe, Cikin muryar ɓacin rai yace,"Ba ki lura da ni ba ne?". Ciki ciki na ce,"Na ganka mana". Hakan sai ya ƙara ƙona ransa ya hau bambami, zuciyata ta sosu na ɗora idona kansa, na lura yanzu idan zai yi min faɗa yaci mutuncina idan bai ɗaga muryar da matarsa zata ji ba hakan sam bai masa daɗi ba, ko kuma yayi a gabanta shine kwanciyar hankalinsa. Ko bama ita ba aganina ba dacewa ba ne ya ke min faɗa gaban Saudatu. Sauri sauri nayi wajen zarar kaya, jikina har rawa yake ban ma iya rufe murfin ba na tafi da sauri na fice a ɗakin na barsa nayi ɗakinsa, duk da cewar ba'a son raina ba don da niyyata idan ya neme ni zan faɗa masa ya koma can inda ya baro zai fi masa dan acan aka damu da shi ni bai gabana. Ina cikin saka kaya sai ga shi ya shigo ɗakin har lokacin faɗan yake yi. "Ban san me kika taka ba Sa'ida da rashin mutunciki na raina ni ya hauhawa, har ina miki magana za ki banza da ni alhalin kina jina, kuma saboda tsabar rashin sanin darajar miji da rashin ilimi ina miki faɗa zaki fito ki barni wato ga kare na haushi ko, kin yi laifi ba zaki iya bada haƙuri ba saboda girman kai". "Ka gane finka sanin ya kamata nayi da aiki da ilimin shiyasa na baro cikin yara, kai a ganinka kana faɗa gabansu hakan na maka daɗi ba burgewa da cinyewa ba ne, domin kuwa zasu daina ganin girman da kake da shi a idonsu ko da ace ɗan da ka haifa da cikinka ne, hakan ma ba tarbiyya ba ne, ƴaƴa mata aka baka kuma wataran aurar da su zaka yi ka kai wa wani...kuma kana ƙara daga murya ne saboda matarka taji, ai gani a ɗakin da gani sai kai kana iya kiranta tazo nan ɗin ba sai ta tsaya iya ji ba, gani da ido ai ya kori ji. Sannan kar ka ƙara alaƙanta ni da kalmar girman kai don ni ƴar Aljanna ce kaima ka sani". Wai ƴar wannan maganar da nayi sai ta zama ciwo, har yana nuna ni da yatsa yana cewa,"Wato kin yi bakin da ba zan faɗa ba sai kin faɗa kema, to na rantse da Allah zan koya miki hankali, zan baki mamaki dan na lura har yanzu ba ki gama sanina ba". Nace,"Ina kuwa zan gama saninka Nazifi, ai har yanzu ma ban sanka ba domin kasha gaban tunanina. Kuma duk wannan Bala'in dai da kake akan ka baro wajenta ne, to ka koma mana ai ban riƙe ka ba, ƙarƙarina nayi kallo ranar ƙiyama, wanda ya shiga kwanan wata ai ya san makomarsa Nazifi Mai Kalwa". Hankaɗa ƙofar yay ya rufe har sai da na tsorata, ya wuce ni fuuu zuwa banɗaki. Na taɓe baki na zauna kan kafet, ai yanzu kam sam bana tsoronsa bana shakkarsa, na daina masa shiru ina ƙyale shi yay duk bala'insa da zai yi, barazana ce kawai na ke jira ya fara kafin itama ya aiwatar. na ɗauko wayata na kunna data, kai tsaye group na ajin koyar da english na shiga don ni yanzu ya fiye min komai da ke cikin gidan nan. Hasalima ina mancewa da ɓacin rai muddin na shiga ina karatuna. Sai bayan ya fito a wanka yay shigar bacci kana ya zauna yana ce min,"Abincina fa?". Kamar ba zan tanka shi ba can kuma na ce,"Ina naga lafiyar da zan iya wani girki". "Kamar ya? Ba kin ji sauƙi ba". "Da na ji sauƙin ban gama hutawa ba ne shiyasa". "Duk ba abin da ku ka ci kenan?". "Mun ci mana". "Kuma sai wanda za'a dafa min ya gagara ba? Da ban kawo na ajiye ba kuma a kira ni da azzalumin miji". Wani kallo na masa sai kawai na aje wayata na miƙe na fita, ba jimawa na dawo riƙe da ɗan ƙaramin flask na miya da cokali duk a hannu, kan teburin da ke gabansa na ajiye na ce,"Ga sauran da muka rage". Na faɗa yayin da na ke buɗe masa flask ɗin, wata ƴar guntuwar shinkafa ce bata fi cokali huɗu ba, ko ƙaramin yaro yaci ba ƙoshi zai yi ba, ta ƙandashe sanyi ƙalau, Saudatu ce da ƙiwa yau tayi jallof babu cikakken mai da kayan miya, su kaɗai suka ci abinsu don ko ni sai indomie na dafa. Miƙewa yay bayan yaja tsaki ya fice a ɗakin, nayi guntuwar dariya ina rufe murfin. Sai kusan minti biyar ya dawo da ƙatuwar leda hannunsa, Biredi ne ya fita ya siyo babu shiri, in banda haka sai da sassafe yake aikawa gidan biredi a siyo sabon yi me zafi, ina kallonsa ya buɗe friedge ya ɗauko lemu. Kallona yay nayi saurin ɗauke ido don na san saboda yaji babu sanyi ne, kamar ba zai magana ba sai kuma ce min yay,"Me ya samu firij ɗin?". Ya faɗa yana duba socket. Ni kuwa ina sane na kashe yau da safe, ai na rantse sai na guma masa a kwanaki biyun nan da zai yi, abinci sai dai ya siyo na waje amma na bar yi masa girki ko yaje can ya karɓo a wajenta. Duk da naga kamar bai jin daɗin girkinta, don ranar nan tana min baƙaƙen maganganu wai idan ma asiri nayi akan ya daina jin daɗin girkinta to nayi kaɗan na rabata da shi. Ni dai ban kulata ba don nafi ga na bawa banza ajiyarta, wayewartata da ake ta faɗa a banza a iska tunda har tana iya faɗa da kishiya, a wannan zamanin wa ke wannan shirmen? Bokon nata ma ai na banza da wofi ne. Shi kuma sai ya tsiri cewa irin girkin ranar kaza zan yi, don kam dai Alhamdulillah naji daɗin koyon girkin Leemars Mandi, kuma koyon yay min rana sosai. Waya naji yana yi yana cewa da me gadi ya siyo masa leku me sanyi, shi kuma yace masa ai masu shaguna duk sun rufe yanzu. Haka nan bai iya shan lemun ba don ba ya iya shan abu mara sanyi. Naga ya buɗe wadrobe ya ɗauko jakar takardunsa ya zo ya bajesu yana dube dube, nan dai na barsa har na kwanta ma. Sai can cikin barcina naji ya tashe ni, ina farkawa na dube shi da tausayin yanayin fuskarsa na ce,"lafiya?". Yay ɗan jim kafin yace,"Ko za ki taimaka ki soya min wainar ƙwai don Allah". Agogo na kalla naga ƙarfe uku da rabi, sai naji ya ban tausayi don duk me imani dai ya san illar yunwa balle shi da ba ya jure mata. Na sauka na fita naje babu daɗewa na dawo da soyayyar wainar ƙwai ƙatuwa har da ɗauko masa lemu me sanyi a ɗakina. Amma saboda mutumin nan baida imani babu Allah a ransa ashe Zahra'u ce ta kirasa a lokacin wai tana son cin wainar ƙwai, ina kallo ya ɗauka ya fita cikin rawar jiki da sassarfa, ji nayi kamar na tashi na iske shi na kifar da wainar ayi duk bala'in da za'ai, amma sai ɗayan ɓarin zuciyata ya hane ni da cewa,"Kauda kai lokaci ne". Haka nan na kwanta riƙe da gefen zuciyata ina hana kaina kukan da ke son ƙwace min. Ban san san da ɓarawon bacci ya ɗauke ni ba kuma. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR10FT5* Tsawon kwanaki muna ta fama da jikin Abbaa, Asibitin Aminu Kano suka bamu gado da taimakon Baba Tijjani da wani mutum da ke siyan kaya wurin Abbaa aka samu na biyan gado da sauran abubuwan da likitoci suka nema. Abinci kuwa na kullum Ummansu Hindatu ita ke dafowa ana kawo mana na safe, Maman Yasmin tayi na rana, Anty Khairi tayo na dare, ni da Ummani da Abbayo mu ke kwana a asibitin, ba kullum muke zuwa gida ba saboda yanayin kuɗin mota. Idan ba Yaya Imam ko Yashaik ba ne suke da kuɗi a hannu sosai shine zasu ce muje muyi wanka sai mu dawo. Ba Abbaa kaɗai da yake ciwon ba hatta mu da muke jinyarsa duk mun rame mun fita a hayyacinmu, don abun biyu ya haɗe mana, shima Kaka jikinsa ya tsananta sosai duk da shi nasa ciwo na tsufa ne. Su Yaya Imam na ta in koma gida abun zai zama da hauka har kwana shida, gwara in ke zuwa ko bayan kwana ɗaya ne, Babanmu ya ce ai tun da mijin ya barni su ƙyale ni, cacar kuɗin mota ma aiki ne. Sannan idan ina gida zan fi damuwa har wani ciwon yazo ya iya kamani. Ba su san ma ni rashin dama ce dama tasa na ke zaune acan ɗin ba, a hakan dai da hankali ba a kwance yake ba nafi jin daɗin zaman akan na koma wancan kurkukun. Ni dai ban iya cewa da su komai, don na san idan suka yanke magana akaina ko Ummani ba ta iya cewa ba haka ba. Nazifi ya zo sau biyu ya duba Abbaa da jiki, haka wani sa'in da daddare zai kira ya tambaye ni ya me jiki yana magana kamar na tursasa shi. Uhmm sai yanzu ai na ƙara yarda da ake cewa idan iyayenki basu da kuɗi miji ba ya musu kallon daraja musamman in ace shi bana arziƙi ba ne, ga dai shi na gani kan Nazifi yana ganin bamu da komai, wanda kamata yay ace ko bai zo kullum ba ya ke kirana kullum yaji yanda jikin mahaifin nawa yake, haka ma ya taimaka mana da ko na magani ne tun da ai yasan halin da muke ciki, amma duk ba ɗaya tun zuwan dai da yay a gida ya bada dubu goma ɗin nan bai ƙara zuwa ma ko da ruwa ba yace ga shi. Ranar ƙarshe da ya zo yana faɗa min itama Zahra'un sun koma gida wai haihuwar ba yanzu ba sai nan da sati ɗaya, idan bata haihu da kanta ba zasu yi mata aiki. Iyam ma naji ta dawo amma bata ko kira ni balle zuwa dubiya, gidansu Nazifin ma dai kaf babu wanda yazo min sai jiya ne Lubabatu da Yayan Shago da Amarya suka zo, naji daɗin zuwan na su sosai da kayan dubiyarsu da zasu tafi har dubu biyu Yayan Shago ya bawa Ummani. Da muka yi waya da Safiyya Babansu ya haɗamu da wani babban likita a asibitin, ita ma Ummar tasu ta turawa Ummani dubu biyar tace basa Nigeria da sun zo dubiya. Yau da muka tashi jikin Abbaan da sauƙi, haka yana ɗan magana yace ayi masa kaza, ko kuma yana son kasa. Har ma da yaji maganata yake cewa har yanzu ban tafi gida ba, Ummani ranta a dagule tace,"Kai dai kaji da ciwon da ke damunka". Ummani kam yanzu haushin Nazifi take yi sosai, haushin da na san ba lallai ta taɓa daina ganinsa da abubuwan da yake min ba, don ita tana da ruƙo, na faɗa muku a baya tana da tsananin haƙuri amma idan ta ƙullaci mutum akan abin da yaywa ƴaƴanta tofa sai ta Allah. Balle yanzu da ya ƙara nuna mata su ɗin ba komai ba ne du da suna iyayen matarsa. Yau ɗin da Abbaa yaji daɗin jikinsa sai ga ƴan dubiya nata zuwa, wannan ya shigo wannan ya fita, kowanne ya zo da ɗan alherinsa. Dama ciwon nasa na damuwa ne kwana biyu kasuwa shiru idan ya fita haka yake dawowa, shi kuma ba ya iya fitowa yace da ƴaƴansa su taimaka masa ko ya faɗa musu ga halin da yake ciki, a bikina kawai aka yi hakan, amma Ummani ce min tayi sun sha yini da yunwa sai idan Maman Yasmin ta kawo abincin rana da ke kullum sai ta aika, to shine suke tattala shi aci har dare. Dukanmu ba ƙaramin daɗi muka ji ba da har yace a tayar da shi ya zauna, na saka masa pillow a baya ya jingina da shi. Ya buƙaci na zuba masa tuwon masara da miyar kuɓewa ɗanya da Anty Khairi ta zo da shi. Da kaina na ba shi yana ci ya kuma ci sosai dan ƴar kaɗan ya rage malmalar, yasa Abbayo ya kama shi ya taimaka masa zuwa banɗaki yayo alwala, haka yazo a lokacin nan yay ta ramakon sallolin da ke kansa, bai tsagaita ba sai da ya rama sallolin kwana shidan da yay a kwance. Ummani dai sai ta kalle shi in ga ta kaɗa kai ta faki idonmu tasa hannu ta share ƙwallarta, cuta ba mutuwa ba amma ni kaina har na sallama da Abbaa, don ko yanzu irin abubuwan da yake tamkar mai yi mana bankwana. A hankali na ke sa gefen hijabina na goge hawayena. Abbaan da kansa yake jan mu da magana har dai muka saki jikinmu saboda yacca yaga duk mun ƙara damuwa jikkunanmu sun yi laƙwas. Da zolaya yake cewa da Ummani,"Hajiyar Salman ana tsoron zaman takaba ne". Tace da shi,"Kaga ni dai rabani da wannan zancen. Naga alamun ma ka samu lafiya bara na yiwa likita magana ya zo ya bamu takardar sallama". "Ehh fa dai kirawo shi ɗin su bar cin kuɗin Ƴaƴana haka. Amma kafin nan kunto kuɗaɗen da ke bakin zaninki". "Ehh lallai kaji sauƙi tun da har ka iya saka ido. Mutum duk ya ɗagawa mutane hankali, ga ƴarka nan duk ka ramar da ita, ko da yaushe a kuka take abinci bata iya ci". Abbaa ya zuba idanuwansa akaina ko ƙiftawa bai yi, ni kuma ina ta ƙoƙarin gusar da tsantsar damuwar saman fuskata ta dole, don bana so ya hangi abin da zai ɗaga hankalinsa tun da gaskiya rabon da nace na zauna irin haka gabansa yay min kallon ƙurilla da fahimta irin wanda yake min yanzu anfi shekara uku, kuma don dai yaji daɗi sai na ɗago ido ina kallonsa da murmushi na ce,"Sannu Abbaana Allah ya ƙara maka lafiya". Ya amsa da amin yana saka min albarka gaba ɗayanmu da su Anty Khairi. Ya kalli Ummani yana ce mata,"Kinga da Sa'ida ta zama likita irin wahalhalun asibitin da muka sha da duk mun samu sauƙi, to Allah bai nufa ba". Ummani tace,"Umm Kana naka Allah na nasa, bai rubuta faruwan hakan a kundinta ba ne". Nasa hannu na goge hawayen da ya zubo min. A hankali naji Abbaa na cewa,"Shi fa gidan aure gida ne na yaƙin neman Aljanna, sai mace ta yi haƙuri bana wasa ba kana take iya jin daɗinsa har ta iya samun Aljannarta. Na jima ban miki kallo irin wannan ba Sa'ida, sai dai yau ɗin fuskarki ta shaida min kina cikin wani hali a matsuguninki, wannan ramar taki ba ta sauƙi ba ce, na tsorata da ita ƙwarai, ina ga ba kiga yanda kika ƙare ba ne ko? Na san mahaifiyarki na sane da duk irin halin da kike ciki, nima kuma daga baya duk na fuskanta, na san kin san waye mahaifinki a ɓangaren iya takun yin bincike. To kamar yanda na ke faɗa miki ko da yaushe a baya yanzun ma zan ƙara nanata miki. Ki ƙara haƙuri akan wanda na san kina yi, kiyi haƙuri kiyi adu'a sune kawai jin daɗinki, haƙuri ba ya yawa ba ya janyo danasani da nadama, haka adu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza, Sa'ida babu wanda ya yake nasara ba tare da yay haƙuri da juriya ba, don haka ki zama me tawakkali da duk halin da kika tsinci kanki kin ji. Sauƙi a wurin ubangiji ya ke, tsanani da akasinsa basa dawwama, da sannu labarin zai canja komai ya shuɗe". Ina hawaye sosai na ce,"To Abbaa ka yafe min, don Allah ka yafe min akan...". "Ni ai tuni na yafe miki. Amma a dinga kulawa, a dinga kai zuciya nesa, a daina ɗaukar huɗubar shaiɗan, in ka cutar kaima za'a cuceka. Allah yay miki albarka, Allah yay miki albarka ya lulluɓe dukkan rayuwaki da farin ciki mara yankewa". Na ce,"Tom Abba, na gode Allah ƙara lafiya yaja kwana". Shiru na ɗan sakanni ya ƙara cewa,"Ya wajen abokiyar zaman na ki, kuna dai zaune lafiya ko?". Na kasa riƙe kukan da ke maƙale, ina fitar da shi na ce,"lafiya muke Abbaa". Sai naga ya ɗan murmusa yana jijjaga kai kafin yace,"Ma sha Allah, sai aci gaba da zama lafiya kin ji". Da magriba sai ga Nazifi ya zo duba Abbaa, ni na fita na shigo da shi. Ummani dai babu sakin fuska ta amsa gaisuwarsa sama sama, Abba yace da shi ya zauna. Yanda yake yi dai irin a gurguje yake don ina lure da shi, tun da yake zuwa bai taɓa zaman minti biyar ba, da ya zo an gaisa yace ya me jiki aka ce da sauƙi zai ce to ya tafi. Abbaa ya shiga tambayarsa akan zancen plazarsa yace ai Alhamdulillahi adu'arsu ta amsu komai yanzu ya daidaita, Abbaa na nuna jin daɗinsa yake ta jero masa adu'a da fatan alkhairi. Yana daɗa dubansa yace da shi,"Amma dai baka samun wata hatsaniya daga wurinta ko? Yanzu ba ita kaɗai ba ce kuma nasan lamarin ƴaƴanmu a zama irin haka". Kansa a ƙasa yana juya muƙullin hannunsa, wani abu yake so yace da dukkan alama, to ƙila sharrin ne bai gama haɗuwa a ran nasa ba shiyasa yay murmushi kawai bai ce komai ba. Abba ya ƙara cewa,"Hakan ya shaida min akwai matsalar kenan, dama na san dai kana haƙuri ne, to ai na faɗa maka duk san da tayi maka laifi ka zo ka sameni hakan umarni ne ba ƙararta ka kawo ba, idan tana ganin tafi ƙarfinka ai mu bata fi ƙarfinmu ba. Allah yay maka albarka, haƙurin da ake Allah ya bada lada, sannan ayi ƙoƙarin kwatanta adalci nauyin da ke kanka yanzu yafi na baya, tsakiyar mata biyu kake don haka sai kayi da gaskiya saboda lahirarka". Kansa na ƙasa yake cewa da Abbaa zai wuce. Ba dan idon Abbaa ba da bai isa na bi bayansa da kallo ba, ba da son raina ba ha na miƙe na fita raka shi, ko ƙofar ward ban ƙarasa ba na juyowata dama yana gaba ne ina bayansa kuma da nisan tazara tsakaninmu. Ina komowa Abbaa yace da ni,"Ba tare zaku wuce ba?". Maƙot na haɗiye dunƙulen yawu na ce,"A'a Abbaa, ai da yake gidan ma babu kowa itama an kwantar da ita a asibiti zata haihu". Ashe tsautsayi ne ya ɗebe ni nayi wannan maganar, Ummani nata min sigina ban lura ba. Sai ce yay to ai wannan rashin hankali ne ace abokiyar zamana na asibiti zata haihu ban je na dubata ba kwata kwata, ban da abuna ma ai sai ace baƙin ciki na ke da haihuwartata. Saboda haka na tattara abin da zan tattara na bi bayan mijina shi kam ya yafe zaman kula da shi ai yaji sauƙi. Idona ya cika da tarin hawaye, babu abin da zan ɗauka dama, Ummani na kallona da tausayawa tace,"Abbansu da ka barta sai ta tafi da safe. Ko abinci ma bata ci ba". Ai fa nan Abbaa ya hauta da faɗa sosai akan me yasa ita bata san abun da ya dace ba, dama su iyaye mata sune ke ɗaurewa ƴaƴa gindin yin abin da suka ga dama a gidan aure, kuma sai auren ya mutu su zo suna kuka ana ganin laifin miji. Faɗa fa kamar ba majinyacin da ke kan gadon asibiti ba. Ni dai ina ta kuka na ce,"Ummani sai an bani kuɗin mota na san yanzu ya rigada tafiya. Kuma ma ban san asibitin da suke ba wayata babu kuɗin da zan kira shi na tambaye shi". Ana haka Abbayo ya shigo, Abbaa ya kalle shi yace,"Kai da kuɗi a hannunka?". Yace,"Ehh akwai". Ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ɗebo kuɗi. Abbaan yace da shi,"Nawa ne?". Ya shiga ƙirgawa kafin ya ce,"Dubu ɗaya da ɗari uku ne". Abbaa yace,"To ara min ka bawa wannan yarinyar. In wayarka da kuɗi kira mata mijinta". Abbayo yace,"Ai da zan shigo na gansa bakin motarsa, ina ce ma ko ita yake jira". "Ehh kira mata shi ɗin dai". Abbayo ya miƙo min wayarsa na saka lambar na kira, kamar me jiran kiran kuwa bugu ɗaya ya ɗauka duk da na san baida lambar, ya ɗaga yana sallama, na amsa ina cewa da shi,"Ka tafi ne?". Jin muryata munafuki sai ce yay,"Ya za'ai na tafi kema ai kin san jiranki na ke yi. Kin san an kusa shiga da ita ɗakin tiyatar ya kamata muje da sauri". Ƙit na kashe wayar kafin ya ƙara karanto abin da zai haɗa ni da mahaifina, na miƙawa Abbayo wayar hannuna na karkarwa ganin kallon da Abbaa ke watso mini. Nayi msu sallama zan wuce ina maidawa da Abbayo kuɗinsa sai Abbaa ce yay. "Rike kije da shi. Kuma kar da ki tafi ki ɗorawa kanki damuwa, ni na warke gobe ma a gida za ki jini". Ummani ta rako ni har waje ranta duk babu daɗi, tana ta bani haƙuri da ƙara yi min nasiha. A bakin mota na same shi yana ganina ya murmusa da cewa,"Ai dama ma san Abbaa zai ce ki biyo ni. To ki ga hakan ai yafi, rashin zuwanki ɗin sai a fara ƙananun maganganu kin san halinku na mata, yanzu ace kina baƙin cikin haihuwar ne". Na ce,"Ai ba su kaɗai ba kaima kana iya faɗa, yanzun ma ai shaguɓe kayi". Sai yaji haushi akan me zan faɗi hakan. Tun da muka shiga motar ban ce da shi ƙala ba, duk da yana ta jana da magana yana ta faɗa min irin wuyar da Zahra'un ke sha. Wai ai har sai da aka haɗa da saukar ƙur'ani saboda an ce asiri aka yi mata akan karta haihu ana so a kwantar da cikin, yana faɗar hakan na ɗago na kalle shi, ban iya yin magana ba yaci gaba da bayani wai so ake ma a raba auren asirin dai da ake tayi babba ne. Ni kuwa kamar na tambaye shi sai kawai nayi shiru. Sai da muka ɓata wajen awa ɗaya akan siyesiye da yake tsayawa yi, ya saya wancan ya siya wancan, ni ko bana ganin laifinsa dole yayi ɗoki tun da ya jima bai samu haihuwar ba, Ya tambaye ni ko ya siya min abinci nace a'a na ƙoshi. Wani babban asibitin kuɗi ne a nasarawa GRA, haɗuwar asibitin kaɗai zai shaida maka asibiti ne na masu hannu da shuni, haka yake faɗa min kwanciyar duk kwana ɗaya dubu ɗari yake biya. Na ce to Allah ya ƙara horewa yace amin. Su Iyam muka fara gani a ƙofar ɗakin tsaye da alama ma sun dawo daga rakiya ne, sai da suka gama gaisawa da ɗan nata kana nima na gaisheta ina cewa sun dawo lafiya, fuska babu annuri ta amsa kamar nayi mata dole. "Sai yau kika ga damar zuwa kenan". Banyi mamaki da furucinta ba, sai na tsareta da idanuwana cikin wani yanayin da na san ta girgiza da shi, na rasa me zan ce ma, tabbas da na san zata yi min wannan furucin ko gaisheta ba zan yi ba wallahi. Sai shine yace da ita,"Ina ga kin sha'afa na faɗa miki an kwantar da Babansu a asibiti". Ni kuwa idan yana Babanku ko mahaifina mamaki yake ba ni, da yanda na ke kiran mahaifina haka shima yake kiransa, Abbaa sama Abbaa ƙasa. Tahowar nan tamu da suka yi waya da Baban Zahra'un tamkar zai yi masa sujjada, amma ni da yaje wajen mahaifina gaisuwar ma ina ga so yay Abbaan ya gaida shi. Iyam tayi min wani kallo tace,"Oh anyi haka yo na mance ne, Allah shi sawwaƙe. Amma ai da ko sau ɗaya kya leƙo ki duba ita me naƙudar ba wai ki nemi wuri ki zamanki ba". Ina murmushi me ciwo na ce,"Da yake abin da ya shafeka shi ya dameka". Yaya na tsaye ita dama ban ma yi karambanin gaida ita ba, muna shigowa da ta ganmu da shi ta ɗauke kai. To me zata ba ni? Don haka ban ce mata komai ba, haka ko ya mai jiki itama bata iya ce min ba duk da taji ana zancen. Ya bani leda yace na shiga ɗakin na kai musu ƴan uwan Zahra'un na ciki, na shiga na samesu da yawa sunata hira da dukkan alama ma sun mance a halin da ƴar tasu take ciki. Muka gaisa suka amsa min kadaran kadahan, na ajiye musu ledar nace in jishi sannan na juyo na fito don ba zan juri irin kallon banzan da suke yi min ba, haka na zauna can gefe kan wata kujera ni ɗaya, idan ka ganni sai kayi zaton marainiya ce gaba da baya. Shi kuma yana ta kai komo zuwa ofishin likita, hankalinsa duk yaƙi kwanciya, daga baya kuma sai ga shi ya dawo ya zauna wajena yana ta roƙona in ke yiwa Zahra'u adu'a. ƙarfe goma da rabi ana shirye shiryen shiga da ita ɗakin tiyata sai ga wata Nos ta zo wajenmu, ganinta muka miƙe a tare da shi ita kuma tana tambayar,"Kune ƴan uwan Zahra'u Abdullahi?". Da sauri ya ɗaga kansa da cewa,"Ehh mune, an shiga da ita tiyatar ne?". Kafin tayi wata magana tuni su Iyam suka ƙaraso wajen, ban san me ta gani ba ta dafa kafaɗata tana murmushi tace,"Ta haihu an samu ƙaruwar ƴaƴa biyu duka mata, ina taya ku murna". Ai ji nayi kamar ni aka ce na haihu, don ban san lokacin da na kama murna ba, haƙorana talatin da biyu du a waje. Su Iyam aka yi hamdala su Yaya ma sai murna aka tafi sanar da ƴan uwanta don su suna cikin ɗakin ba su san wainar da ake toyawa ba. Shi kuma yana ƙara tambayar Nos ɗin,"Babu namiji duka mata ne?". Ta ce,"Ehh duka mata. Ba da jimawa ba za'a fito muku da yaran ana gyara su ne". A iya zamana da Nazifi ban taɓa ganinsa a cikin tsananin farin ciki ba kamar yanzu, don zubewa yay kawai ya miƙa sujudu shukur. Bayan ya ɗago kuma sai ya dube ni yana,"Kinga lamarin Allah ko, mahaƙurci mawadaci, da nayi haƙurin kinga lokaci guda ya bani har guda biyu, nan gaba kuma na san zai bani abokin me taimaka min in sha Allahu. Ki tayamu murna Sa'ida". Ina murmushin jin daɗi dan na mance ma ni da wata damuwa na ce,"Ina tayaka murna Allah ya raya mana, yay musu albarka". Kowa dai a wajen murna yake, sai dai duk ana ce musu babu namiji sai naga jikinsu yay la'asar, haka ma Iyam tun da aka ce duk mata ne fuskarta ta sauya alamun ba hakan ta so ba. Ba'a jima ba sai ga Nos biyu tare da yaran, ya tafi da sauri ya karɓe su, bakinsa yaƙi rufuwa yanda ka san gonar auduga, wato Allah ɗaya yasan farin cikin mutum ke riskar kana a ciki idan ya sami haihuwa, haka ga wanda Allah bai ba shi ba Allah ɗaya yasan irin abin da yake ji a tare da shi, da taimakon Nos ɗin ɗaukan yaran ya daidaita a hannunsa. Likita yazo yace da shi,"Zasu nuna muku ɗakin da aka sauya mata, sai dai a yanzu mutum ɗaya ne zai iya ganinta sai nan da wani lokaci kowa ya iya shiga". Muka ɗunguma duk muka bi bayan Nos ɗin da ke mana jagora zuwa ɗakin, Shi dai ya kasa ma bawa kowa yaran duk suna hannunsa, bayan ya gama yi musu kiran sallah ne yay musu huɗuba tsautsayi yaja ni na miƙa hannu zan karɓi ɗaya sai ce yay min,"Yi haƙuri bari su fara jin ɗumin jikin mahaifiyarsu tukunna". Ya faɗi hakan yana shigewa ciki, Na jiyo Iyam na faɗin,"To ai ko saboda ma ta tofe yaranta da adu'a gudun masu cutarwa wani ba ya ɗauke su ba ita bata ɗauka ba". Sai lokacin na dawo cikin hayyacina na shiga hankalina na daina ɓarin jiki, don haka na koma gefe na rakuɓe. Ta glass ɗin tagar ɗakin na ke hango yanda Nazifi ya haɗa yaran da uwarsu ya rugume yanata sumbatarta. Sai bayan awa guda kana muka shiga ciki, aka baibayeta kowa na mata barka. Ta kalle ni muka haɗa ido da ita, murmushi na sakar mata ita kuma lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya daga farin cikin da take. Sai da ƙyar aka bani yaran na ɗauka, don nunawa ma suka yi basu san ina wajen ba, sai da Innarta ta karɓeta su ta miƙo min tukunna. Kallon yaran kawai nake yi ina jin kamar kar wani ya karɓe su, na yi adu'a sosai na tofa musu, haka kawai naji soyayyarsu ta rufe ni, ma sha Allah kyawawa da su farare tass, ga hanci har baka irin na mahaifinsu, dukansu kamar su ɗaya da mahaifinsu ni dai ban ga ta inda ma suka yi kama da Babarsu ba banda haskenta da suka ɗauko. Na shagala a kallonsu Yaya ta zo ta karɓe su daga hannuna tana faɗin ai daga haihuwar yaran ba'a dinga jagwalgwala su ba. Haka ina ji ana ta yada min magana, wata cikinsu na cewa da Zahra'un tayi mamaki da taga duka mata, da aka yi scanning ai mace da namiji aka ce. Sai wata da bata jima da zuwa ba kamar ma Yayarta naji suna cewa, tace,"To kin manta kishiya ce da ita, kishiyar ma juya, ai dole za'ai ƙulla ƙullar ganin an hana haihuwar namijin. Irin basu da imani, basa zama kullum a tafe suke cikin jeji, kuma fa tun da ta samu cikin nan nake cewa da ita ta dage da adu'a kar tayi sakaci don yanzu kishiyar zata iya hanata haihuwar ma, kinga dai irin baƙar wuyar da ta sha ai kwana kusan goma ana naƙuda, nayi imani asiri tayi mata ta so kwantar da cikin, to sai Allah yasa mu ƴan uwanta ba zaune muke ba tafe muke muma". Maganar ta soki raina, nayi ƙasa da kaina ina ambaton Allah. Ina jiyo ana kwaɓarta da cewa tayi shiru gani can zaune, sai ta kallo ni tana cewa,"Au wai ita ce ma kishiyartata? Ni wallahi ce nake wata cikin ƴan aikin gidan ne. Tabɗijam". Iyam ma ta kawo ruwan rubutu tana cewa a bawa Yaran wai saboda mahassada kar su cutar da su, tun da ba kowa ke murna da zuwan na su ba. Gaba ɗaya sai naji na tsani kaina, kamar na tashi na fita to amma me amfanin fitar? gwarama na zauna tun da magangunsu dai ba fito min a jiki zasu yi ba. fatana ɗaya kar Nazifi yace anan zai barni na kwana don ban san ya zan yi ba. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR12FT5* Wuri na samar mana can gefe da su Fati muka zauna kan wata kujera. Zamanmu Rumana ta takura akan muci gaba a game ɗin, ni kuma gaba ɗaya raina a dagule yake, sai ji nayi Anty Aisha da su Basira na faɗin,"Yo dama juya ai bata da wani daraja a wurin miji". Na ɗago ido na kalli ɓangaren da suke, ban san wacece ɗayar ba amma dai naga har da ƴan uwan Zahra'u su uku da na sani. Suka ɗora da maganar da Anty Aisha ta dire. "To ai kinga ita yanzu duk wata dukiya da aka mallaka tata ce. Me haihuwa da mara haihuwa darajar ai ba ɗaya ba ne, ita fa me haihuwa gaje gida take yi, ta mallake miji da komai nasa, soyayyarsa ta zama tata gaba ɗaya, kuma a dangin miji za ki ga ita ce ƴar lele, kinga dai ita Zahra'un ai ko mutuwa yay ƴaƴanta sun mallaki komai ɗinsa, kuma ko a yanzu dai kinga ƙiri ƙiri ai ya na nuna yafi damuwa da ita akan uwar gidan". Ni kam jin su kawai nake yi zuciyata nata min ba daɗi, A wannan lokacin na samu kaina cikin tsananin son haihuwa. Sai dai a gefe ɗaya cike na ke da tsoron duniya da mamakin halin ɗan adam, wato shi yana maraicin rashin ƴaƴa, yanzun kuma da Allah ya ba shi amma har an fara maganar mutuwarsa da gadonsa, ba ma ƴan uwan matar ba kawai har da nasa ƴan uwan, lallai duniya. Sai dare Nazifi yazo muka tafi, haihuwan da kwana uku aka sallamo su, cikin wannan kwanakin kam na aikatu, abincin safe rana dare duk nice, jama'ar Iyam a ƴan barka duk ni ke ɗawainiya da su. Ban taɓa nuna ɓacin rai ko gajiyawa ba, ni ina yi ne ma ina roƙon Allah da nima ya dube ni ya bani ko da ɗaya ne. Sai bayan dawowan na su na samu ɗan sararawa hakan ma ban wani hutawa kawai dai aikin ya ragu, tun da suka dawo kuwa ban ɗauki yaran nan ba duk sona da na ɗauke su, tsakanina da su kallo ne daga nesa, ko kusa da su na tunkara Kakarsu ta ɗaga min murya, sau ɗaya ne ma na shiga ɓangaren Zahra'un sai ce tayi yanzu suka gama shan nono suka kwanta, kuma ba'a ɗaukarsu idan sun sha nono saboda tumbuɗi suke yi. Kullum da anyi musu wanka ake miƙa su wurin Kakarsu, ita kuma ko Uban ne ya dawo sai tace ya ɗauke su iya nan ɗakinta kar yaje can wani waje da su a cutar mata da jikoki, to yanzuma in ya dawo har sai nayi bacci bai shigo ɗakin ba, abinci ma can ɗakin Iyam ɗin yace na ke ajiye masa, tun da ba ya rabuwa da yaran sai kusan sha biyu ƙarfe ɗaya yake kaiwa uwar su. Ummani da Maman Yasmin da Anty Khairi suka zo barka, a wajenta kuwa an musu tarbar mutunci don wata Yayar Mamarta da Inna suka yi ta godiya da kayan barka, riguna ne set biyu sai turmin atamfa guda biyu amma kace akwatun kaya guda aka kai musu. Da muka je wajen Iyam kuwa haka ta nuna tamkar bata san Ummani ba, kamar ba Iyam ɗin da shekara goma baya ba ta laƙabawa Ummani Ƙawata ƙawata, ta ɓata fuska tana faman amsa musu gaisuwarsu a wani daddaƙile kamar waɗanda suka zo neman taimako wurinta, sosai zuciyata ta sosu, na tabbata da ace jariran ma suna wurinta ba lallai ne ta basu ba, har wani cewa take da Fati tayi sauri ta kunna hayaƙi saboda masu zuwa ba'a san da irin manufar da suka zo ba, Maman Yasmin tsabar ɓacin rai sai da ta so ta gaggaya mata magana Ummani ta hanata. Ranar suna kuwa wani shagalin taro aka haɗa zan iya rantsewa tsayin rayuwata ban taɓa ji anyi shi ba da dai sunan wai taron haihuwa, duk kuwa irin kuɗin masu kuɗi, duk irin tarukan sunan da nake jin labarin ana yi. Waterfall event center aka kama da naji ana batun miliyoyin kuɗi aka saka a iya kama wajen kawai ban da kuɗin abinci da sauransu, ni ban ma san da cewa ba'a gida za su yi taron ba sai da azahar na shiryo na fito naga suna tafiya, sai kuma ga Rumana tana ce min na bata sabon kaya wai za su tafi wurin suna. Kuma sai da na shiga IG ne ma na ke ganin vedio har ya fara trending, abun ya ƙayatar da ni matuƙa da ke zuciyata babu baƙin ciki, ga shigar da aka yiwa yaran ma sha Allah kamar ka sace ka gudu, ni dai sai naji na ƙara jin sonsu a raina, jama'a a hall ɗin kuwa tamkar kaji an cika maƙil, shi da matar shigar kaya kala ɗaya suka yi, kowanne fuskarsa da annuri yana riƙe da ɗaya itama tana riƙe da ɗaya, shi ya saka shadda dakakkiya ita kuma ta sanya wani arnan less da shi ɗaya ya isa ɗaukan ido a wajen, ina kallon bidiyon ina murmushi ina hawaye. Ina sama sai na sakko ƙasa saboda gidan ni kaɗai ce, sai da na sakko ne ma naga ashe su Marawiyya sun dawo, na samesu suna faɗin irin watsi da nerar da uban ya dinƙa yiwa yaran da uwarsu, kyauta kuwa da aka dinga bawa yaran ba'a magana, shi kansa sai da ya bada atamfofin chiganvy aka rarraba. Har yaywa mahaifiyar yaran kyautar mota dalleliya. Haka kawai naji ba zan iya ci gaba da zama ina jin labarin na su ba, na wuce ɗakina na ƙasa ina jin kamar ina so nayi kuka, ina shiga na kashe wayata kawai na kwanta ina ta tasbihi cikin raina saboda kawar da abin da shaiɗan ke neman dasa min. Basu fara dawowa ba sai bayan isha'i, lokaci ɗaya gidan ya kacame da hayaniya. suna kan hanyar dawowa ya kira ni yace na shirya zamu je akaiwa Malam yaran, nace masa to. Bai ma shigo gidan ba ya turo aka kira ni, na isa motar na sameta hakimce a gaba, sai naga ai cin fuska ne ace ni na zauna a baya, don haka na tsaya daga bakin motar har ya dawo daga sallamar wasu ƴan ƙauyensu, Iyam ta aiko masa a basu kuɗin mota. Ya dube ni yana hararata yace,"Ba ki je wurin suna ba motar ma ba za ki shiga ba?". Nayi guntun murmushi na ce,"Ina da muhimmancin da za'a ce naje suna ne? Ko ina da arziƙin da za'a faɗa min abin da aka shirya? Rashin zuwan nawa ai bai hana kun yi yanda kuke so ba. Ita kuma kayi mata magana ta dawo baya". Ganin zai ɗaga min murya yaci mutuncina gabanta gaban mutanen unguwa na ɗaga masa hannu kawai na buɗe bayan na shiga. Da muka je gidansu ashe can mutanen ƴan uwan Iyam gayya guda ta gayyato, Ah to kuwa Nazifi ya shekara goma da aure bai haihu ba ai dole ayi shagali ban ga laifin su ba. Ni na ɗauki Noor me sunan Iyam da ubanta ya miƙo min ita da muka shigo, Iman ɗin kuma tana hannunta, abin sha'awa idan ka kallemu sai naji inama ace kanmu haɗe yake kamar ya da ƙanwa. Wurin Gwaggoje muka fara shiga muka gaida ita, sannan muka je ɗakin Amarya kai matar nan da mutunci yana yawa zancen kirkinta yay yawa. Ummaa kuwa dama a falo muka sameta ita ce ma taje ta isawar da Malam cewa mun zo, da ke ita ke da girki, ni tun da na gaida itama bata ƙara bi ta kaina ba sai karɓar Noor ɗin tayi tana cewa ga yanda ake ɗaukar yaro hakan da nayi ai sai wuyan yarinyar yay ciwo, kuji haɗin masifa don Allah. Ana haka kuwa Yayan Shago ya iso wurin, cikin barkwancin nan nasa da zolaya yake cewa Hassana da Hussaina matan Alhaji Ƙarami uwayen Hassana da Hussaina. Ni dai murmushi na ke muka gaisa da shi, ita kuwa ta haɗe rai da ƙyar ma suka gaisa. Bata san shi ɗan ba ruwansa ba ne yana tsokanarta ya ce,"Amma dai Amarya kin bawa Yayar taki ɗaya ko?". Kanta a gefe tana ƙara haɗe gira sama da ƙasa tace,"Wace Yayar tawa? Kuma akan me zan ba da abin da ba'a tayani naƙuda ba, ita ma macece ai ta haifi nata mana". Da yake shi ba baƙon zafi ba ne yay ƴar dariya yana ce mata,"Maida wuƙar Amarya, Allah ya raya mana sai an kawo min kwanon nama na". Yana barin waje na ce da ita,"Kiyi haƙuri fa shi haka yake da wasa". Bata tanka min ba sai faman kallon ƴarta da ke hannuna take. Sosai Malam yayi murnar ganin yaran, ya tofe su da adu'oi kafin ya miƙo mana su, bayan mun gama gaisawa ne sai muka ji ya fara faɗa, ya tasa Nazifi a gaba kamar zai cinye shi ɗanye, wallahi ni ban taɓa tsammanin ba zai yi masa mugun duka ba, dama shi mutum ne me zafi, Ƴaƴan duk tsoronsa suke yi, bana mantawa da ko hira ake aka ji sallamarsa sai kowa yay ɗif, gyaran muryar Malam kawai zaa ji a natsu, shi kansa Nazifin tun kan aurenmu yasha faɗa min da ka aikata laifi Malam ya sani gwara baka ma fara aikatawa ba, ga fadansa ba ya wucewa. Kuma yana da sakin jiki da ƴaƴansa kawai dai yana da faɗa. Ni Iyam ce dai da ta fanɗare masa yanzu, amma ko ita da ai mugun tsoronsa take ji, kuma duk rashin lafiyar nan da yay ne yay sanyi dan ni dai nayi mamaki ace Malam ya iya barinta zama a gidanmu. Haka yay ta faɗa jikina har rawa yake, yana cewa ashe zaluncin da ya ke bugawa a cikin gidansa babba ne, to an same shi an zayyana masa from A-Z. Yana nuna shi yace,"To Nazifi idan shiryawa tashi ranar ƙiyama da shanyewar ɓarin jiki kayi to kaci gaba da duk abubuwan da kake yiwa matarka. Ita kuma uwar taka da taje can ta tare ta zama fitina a tare da ku, zata zo har inda na ke ta same ni, wallahi Nazifi ka sani sai na mugun saɓawa mahaifiyarka, ka dai san sarai waye ni". Muka haɗa ido da shi, ko bai ce ba na san tunaninsa ni na kai ƙararsa, gabana naji yana ta faɗuwa don ni har ga Allah ba'a taɓa faɗa irin haka a gabana ba, kuma ban taɓa ganin ana yiwa babba kamar Nazifi faɗa ba don haka duk sai nake jin tsoro. Malam ɗin ya kira sunana yana cewa,"Ke kuma Sa'ida me yasa ba ki taɓa zuwa kin faɗa min abubuwan da yake miki ba? Da ba sai ki bar masa gidansa ba don ubansa tun da shi ɗin me rama alkhairi da sharri ne. To daga yau duk abin da Nazifi yay miki na rashin kyautawa na sahale miki kai tsaye ki kirani a waya, zan tabbatar masa da ni Bala Mai Kalwa ubansa ne kuma mijin uwarsa". Ya ƙara komawa kan Nazifin da cewa,"Ina iliminka Nazifi? Kaf ƴaƴana babu wanda na ke alfahari da shi irinka ashe zaka bani kunya, ashe kayi watsi da addininka, har abun duniya ya iya rufe idanuwanka, ita uwar taka idan tayi tsufan da ya ɗebe tunanin yakamatanta ba sai ka nusar da ita daidai ba. To wallahi kaji na rantse idan baka saita zaman gidanka ba ka zama adali tsakanin matanka ba zaka sha mamakina, domin ina mai tabbatar maka da akan yarinyar nan Sa'ida zan iya yafe ka. Ai ni ban mancewa da halacci". Kuka na saka kaina a ƙasa na ce,"Don Allah kayi haƙuri Malam, duk ba haka ba ne, ba yanda aka faɗa maka ba...". Katseni yay da ɗaga murya,"Rufe min baki, saboda kina da tsananin haƙuri shine za ki kare shi, ki zauna suna cutar da ke". Ni ban ma san yanda zan kwatanta maku irin faɗan da Malam ke yi ba. Nazifin ya hargitse sai haƙuri yake ba shi, da ƙyar ya sassauto ya shiga yi mana nasiha mai matuƙar ratsa gaɓaɓan jiki, wanda ni dai irin yacca wa'azinsa ke shigata hawaye kawai na ke yi, shi kansa Nazifin muryarsa tayi rauni, ga irin ayoyi da hadisan da yake janyowa sai da na mugun jin tausayin Nazifi, take kuma naji a zuciyata na yafe masa duk abubuwan da yay min, to nawa rayuwar take ma? Allah kawai ya yafe mana gaba ɗaya. Malam ma nunawa yay kamar bai san wata Zahra'u ba, muka baro gidan ran kowa babu daɗi, ta karɓe yarinyarta a hannuna tana yi masa kuka wai ana so a shiga tsakaninta da mahaifinsa, shi kuma ya ƙara rikicewa da kukan nata yana faɗin tayi masa shiru don Allah da wanne take so yaji. Tace ita dai koma waye yaje ya ɓatata wurin Malam bata yafe masa ba, sarai na san shaguɓe ta min, ni kuwa har muka isa gida ban kulawa lamarinsu ba, shi ɗin ne ma dai da muka shiga wajen rabuwa zan yi ɗakina yace wallahi matsawar ya bincika yaga da sawar hannuna wajen kai ƙararsa gun mahaifinsa to aurena na yiwa, tun da nake rayuwa da Nazifi a irin uƙubar nan bai taɓa yin furucin da ya dake ni ba irin wannan, wai aurena na yiwa! Kenan zai rabu da ni! Washe gari ƴan taron suna duk suka watse, gida ya dawo yanda muke da, sai Innarta dai tana nan wacca aka bari zata dinƙa yi mata wanka. Daga baya Mamanta ta zo itama tana da kirki gaskiya domin uwa ce ta gari, tasa aka kira ni tayi mana nasiha, tace kuma ƴaƴan da aka haifa bana Zahrau ba ne kawai nima na ɗauka nawa ne, don duk macen ƙwarai tana ɗaukar ƴaƴan miji matsayin nata ne, don Allah mu haɗa kanmu mu zauna lafiya fitina ba wata abar so ba ce kar mu biyewa sharrin zuciya. To ni dai zatona samun yaran nan zai kawo canjin zama me daɗi, sai dai ina ashe ba haka ba ne. Zahra'u da Iyam sun mayar da ni muguwa abar tsoro, ban da ikon tunkarar in da yaran suke za su farga suna maganganun marasa daɗi, har cewa suke suna gudu ne kar na lashe kurwar yaran, kullum in har zanga Zahra'u sai tayi min gorin haihuwa, sai ta nuna min ita ke da gida da miji yanzu, ni kuma haka kawai Allah ya ɗora min tsananin ƙaunar yaranta, ko wa naga ya ɗauke su sai na ce zan karɓe su in dai ba hannun Iyam suke ko kuma uwarsu ba. Da naga abun yana yawa sai na haƙura kawai na kame kaina daga yaran, na kama kaina sosai ko ubansu ne ya ɗauko su bana sha'awar ma na kallesu balle ɗauka. Hakan kuma sai ya janyo wata sabuwar maganar a wajensa shima, wai nasa baƙin ciki a raina shiyasa duk na lalace ina ta ƙarewa, to koma dai me na ke nufi na ke kuma ƙullawa Allah ya fini, yana yiwa ƴaƴansa adu'a kuma yana yiwa mahaifiyarsu, nan da lokaci kaɗan ma zan ƙara ganin ta samu wani cikin. Ni kuwa ina kallonsa a nutse na ce Allah ya bada masu albarka bana baƙin ciki. Wata ɗaya bayan nan ina zaune ina haɗa kayan wankinsa ya shigo, yana goye da Noor Iman kuma tana hannunsa. Ya zo ya kwantar da su kan gadon, tun da na kalle shi sau ɗaya na ɗauke kai naci gaba da abin da nake yi. Can sai jinsa nayi yana faɗin,"Sa'ida me yasa ba kya son ɗaukan yaran nan?". Na kalle shi hankalinsa na kan yiwa yaran wasa, ni mamakin ma maganar tasa nayi, yo idan ya zo da su ba ya ji ba ya gani, idan zan masa magana dubu da wuya ya amsa min ɗaya, dama zaman namu da shi gashi nan ne dai wai ai ance masa asiri na ke neman yi akan yaran. Jin nayi shiru ya ɗago ido ya kalle ni, sai ce yay,"Zan shiga wanka ki tafasa min shayi kafin na fito. Anjima kuma zan yi baƙi ki san me za ki tanadar musu". Na ce masa to amma ya karɓo lemu wajen Iyam da kansa. Fita yay ya barni da yaran, naci gaba da aikina ina jin Noor tana kuka amma ban juya kai na kalleta ba, ya shigo ya ganni ina abin da nake sai ya kama faɗa akan rashin ɗaukar yarinyar na lallasheta. Nace,"To so kake na ɗauketa Iyam ko Uwarta su zo su ganta hannuna su ce nayi mata wani abun". Harara ya watsa min yana faɗin na ƙware a kimtsa magana, ya ɗauki yarinyar ya kaita aka bata nono ya dawo da ita har tayi bacci ma, dama ita Iman ɗin bata fiya kuka sosai ba barta da bacci. Shigarsa wanka ba daɗewa Noor ɗin ta farka da sabon kuka, na kalleta kamar zan ɗauketa kuma sai na ƙyaleta. Ya buɗe ƙofar banɗakin ya leƙo yana cewa,"Yanzu tsakani da Allah kina ɗakin saboda rashin imani kina jin yarinya na wannan kukan ba za ki iya ɗaukarta ba. Dilla Malama ɗauketa ki rarrashta, banza me baƙar zuciya kawai". Kallonsa nayi kawai na girgiza kai bayan na ce na gode da zagi. kukan yarinyar ne ya taɓa ni naje da sauri na ɗauketa ina jijjigata, haka kawai sai naji kamar tawaz da naga taƙi yin shiru na ɗau ruwan fida na bata tasha, kukan nata ya tsagaita na goyata a bayana har ta koma bacci. Ina aiki a kicin yarinyar ta fara mutsutsu a bayana, da alama dai nono take so sai na sakkota, na fito zan kaiwa Babarta sai wata zuciyar tace da ni kul don haka nayi ɗaki in bawa ubanta shi da ya ɗaukota. Sai da na shiga na lura da Idanun yarinyar sun juye, jikinta kuma ya saki, haka nan naji zuciyata ta amsa. Sai na nemi wuri gefen gado na zauna ina jin sanyi na ratsa ƙafafuna, a hankali na shiga bubbuga bayanta ina jijjiagata duk sai naga bata motsi, hankalina ya tashi na ɗaga ido na dubi bakin ƙofar banɗakin. Na ambaci innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe da ƙarfi na faɗa ma ban sani ba, ai kuwa sai ga shi ya fito daga banɗakin a guje yana tambayar lafiya. A ruɗe na ke nuna masa ita ina cewa,"Kaga idanunta naga sun juye". Karɓarta yay yana kallonta kafin yasa yatsansa a hancinta. "Ya naji bata numfashi?". Ya faɗa yana ɗora hannu saman ƙirjinta, sai kuma yasa tafin hannu ya rufe mata idanu. A kiɗime ya ɗago ya kalle ni yana daka min wata razananniyar murya da cewa,"Me kika yi mata Sa'ida?". Ido na zuba masa ina kallonsa cikin kaɗuwa, da ƙyar na iya buɗa bakina na ce masa,"Me kuwa zan yi mata Hubbi, wallahi babu abin da nayi mata, goyata nayi kawai har ma tayi bacci sai take ta mutsu mutsu a bayana, na sakkota zan kaiwa Zahra'u na ce bara na bari ka kaita da kanka. Kawota na bata ruwa muga...". Fizgewa yay ya fice fuuu, na bi bayansa da sauri, ɗakin Zahra'un na bi shi na kasa haƙuri na cusa kaina ciki, ya duƙa gabanta ya kama nono yana ta sakawa ƴar a baki bakinta a datse taƙi kamawa, na tsaya daga gefe ƙirjina sai lugude yake, uwar tuni ta fara hawaye tana ƙwala kiran Inna Zulai, sai gata itama ta zo da gudunta, tana zuwa ta karɓi ƴar ta jujjuyata a hannunta, ina kallon yanda ta bimu da kallo dukanmu kafin a sanyaye tace,"Wannan ƴar ai ta koma". "Kamar ya ta koma Inna?". Na faɗa cikin rawar baki ina kai hannu na taɓa yarinyar. Innar ta maimaita,"Haƙuri za'ai Allahn da ya bayar ya karɓa, ina Iman ɗin?". "Kina nufin ta mutu Inna?"... Ƙarar da Zahra'u ta ƙwala ita ta katse sauran maganata, ni kuma a kiɗime na durƙushe a ƙasa ina ɗora hannaye saman kaina, Tsautsayi! a hankali cikin harɗewar harshe na ke faɗin innalillahi, jikina sai rawa yake yi, idona cikin na Nazifi da ke kallona da wani kalar ƙwayar idon da ban taɓa saninsa da ita ba. Sai girgiza masa kai na ke kafin na shiga ranse masa da cewa ban yi mata komai ba. "Kin kashe min Ƴa Sa'ida, sai da kika san yanda kika rabani da ƴata, duka biyun kika kashe?". Kuka na fashe da shi ina cewa,"Akan me zan kashe maka ƴa, akan wanne dalili, wallahil azim ban mata komai ba, ka yarda da ni wallahi banyi mata komai ba". Inna da ke kan Zahra'u tana yi mata firfita tace,"A'a kai kuwa me ya kawo magana irin haka". Takowa yay wanda ban taɓa tsammanin ba takeni zai yi ba saboda yanayinsa, ya wuce ya fita a ɗakin. Ya bar ni da kuka ina jin wani bala'in tiriri na fitowa ta ko'ina a jikina. Bango na dafa na miƙe da ƙyar, bana iya gani da kyau na ke laluba hanya, kaina na ke jin yana bala'in sarawa, wannan wacce iriyar ƙaddara ce? Daga ɗaukan yarinya sai mutuwa! A yau kam nasan zamana ya ƙare a gidan nan, ni da wannan halin da na ke shiga wancan zuwa wannan a irin rayuwar nan tawa gwara ace na faɗi na mutu, gwara na mutu da wannan bala'in, yanzu wa zai yarda ba ni na kasheta ba? Ko kotu aka je sai akai har busa ƙaho ba'a gama shari'ar ba tun da bani da shaida. _____________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR11FT5* Haka suka yi ta yada min magana me zafi, na nuna kamar ma ban jin su duk da kowanne harafi na maganarsu sai ta taɓa zuciyata, ita kuma sai zugata suke yi akan kar tayi saken wata ta nemi tayi mata rainon ƴaƴa, daga haka me ake raba uwa da ƴaƴanta. Iyam kuwa sai albarka take saka mata tana ta faɗa mata wai duk abin da take so zata yi mata shi ai tunda har ta bawa Shalelenta ƴaƴa. Sai ƙarfe ɗaya Nazifi ya dawo ɗakin, ce nake ma ko ya tafi gida ganin dare ya tsala haka, ashe yana can wurin likita yana ƙarasa biyan bill. kowa ya tashi ya fita aka barmu daga ni sai shi sai Zahra'u. Kujera yaja ya zauna gaban gadon, ita kuma tana daga kwance yaran na kusa da ita. Ya shiga yima yaran wasa yana cewa da ita,"Sannu uwar ƴaƴana, fatan babu in da yake miki ciwo ko?". Ta ce,"Ciwo akwai shi kam uban ƴaƴana, Kaima kuma sannu domin tare muka sha wahalar naƙudar nan, Babies sun wahalar da mu Honey". Ya shafo fuskarta yana cewa,"Ke dai sannu da ƙoƙari. Kinga scanning ɗin sai bai zama gaskiya ba". Ya faɗa da sanyin murya daga ji ba yanda zai yi ne amma ya so shima ace da namiji aka haifa. Hannunsa ta riƙe tana cewa,"Kar ka damu da wannan Daddyn Twins, cikin da ya baka mata biyu shi zai ƙara baka maza ko nawa kake so in sha Allahu. Ni ai farin cikinka na ke so don haka zan cika maka gida da yara har sai ka ce sun isheka, ni ba zan hanaka haihuwa ba Honey". Cikin nuna jin daɗi ya ce,"Na gode Sweety Allah yayi miki albarka. Nayi musu huɗuba da sunan Iyam da Momi, Salamatu da Shema'u". Take annurin fuskarta ya canja. "Haba Honey kuma don Allah sun zo a zamani sai ka saka musu sunan tsofaffi. Ni kam gaskiya ba za su ke amfani da wannan sunayen ba". Tayi maganar muryata na nuna rashin jin daɗi sosai, shima turus ɗin da yay na bai ji daɗin abin da ta faɗa ba, amma sai ya kaudar yana cewa,"Kin gane su kuwa? Wacece Babba wacce ƙarama?" A kumbure tace,"ina zan sani abu iri ɗaya ba banbanci". Sai ya murmusa kuncinsa yana nuna mata wacce ke kan hannunta ya ce,"Ita ce Hassana Salamatu, wannan kuma Hussaina Shema'u...kin san ta yanda za ki gane su kinga wuyan Hussaina akwai tawadar Allah". Ina ga bata san lokacin da ta saki guntun tsaki ba wanda har shi kansa sai da yayi mata duba na ransa ya sosu, ta ɗauke kai gefe tace,"Za'a dinga ce musu Noor da Iman". Ya kaɗa kansa da cewa,"Duk yanda kike so amma dai ai ba za'a ɓoye musu suna duka ba dole a makaranta za su ke amfani da asalin sunayensu, kuma ban da abinki Salamatu fa Ummu Salma ne ƙauye ne suka ɓata shi da Salamatu". Ranta dai babu daɗi tace,"Ni dai da kayi shawara da ni, ai ba lallai sai munyi musu takwara ba. Tsakani da Allah duk irin sunaye masu daɗi da ake sakawa yara yanzu zaka tashi ka sakawa yarana irin sunayen ƴan gidan ku". Ko ni kaina furucinta ya ban haushi, ai ko ba komai sunan mahaifiyarsa ne ya saka to ya zata yi? To da Jummai ɗin da ake ce mata yasa fa? Ko da yake ai har da na uwarta ta nuna bai mata ba. Ransa kuwa ya ɓaci yana gaya mata cewa saboda yay mata kara ma ya saka har da sunan tata mahaifiyar shine zata dinga faɗa masa magana, nan da ya hau sama, ganin abin nasu na neman zama babbar rigima sai na tashi zan fita na basu waje, don ina ga ma ta manta ina wajen ne amma ko don kirsa bata bari hakan ta faru ba. Waigowa yay yana dubana yace,"Zan bar ki anan ne ko tare zamu tafi?". Nace,"A'a tare zamu wuce". "Ba za ki zauna tare da Yaran ba?". Na ɗanyi murmushi na ce,"Ai muna tare da su". Sannan na kalleta na ce,"To Maman Ƴan Biyu Allah ya ƙara lafiya, Allah kuma yaywa yaranmu albarka, ya raya su da imani". Bata da niyyar amsa mini sai ma nono da ta fito da shi tana faɗin ya tayata sakawa Yarinyar da take kuka a baki, wai idan ta motsa tana jin zafi sosai. Ƙafafuna suka kama rawa na nufi ƙofa da sauri zan fita naji yana cewa da ita,"Kin yi mata ya me jiki kuwa? Har yanzu Babanta yana asibiti". A daƙile tace,"Ya me jiki, Allah ya ba shi lafiya". Na amsa da,"Amin, na gode". Kana na fita na bar su. Ina fita ban tsaya ba ganin ana min kallon wulaƙanci kawai na zaɓi da na wuce waje na jirasa. Sai da na gaji da tsayuwa har ina tunanin ma ko mun fasa tafiyar ne zamuyi kwanan asibiti, don biyu na dare ne ke kawo kai, ina ƙoƙarin tsugunawa kana sai ga shi ya fito, ya buɗe motar zan shiga gaba sai ce yay,"Koma baya da su Iyam zamu tafi". Iyam na gaba ni da Yaya muna baya. Sai da muna kan hanya Iyam ta tambaye shi ko ya faɗawa Malam yace a'a yana jin nauyi ne. Faɗa ta kama yi masa da cewa Allah ya baka arziƙi babba kace kana jin nauyin faɗawa mahaifinka, ko don kaga har yanzu yana jin haushin ƙarin auran naka, to shi ya zai yi da abun da Allah ya tsara?. Sai tace ya tura mata kati a wayarta, tura mata yayi ta miƙowa Yaya wayar ta danna mata lambar Malam ta kira tana shaida masa haihuwar, sai kuma naji tana faɗin ita fa ya ƙyaleta ya rabu da ita da maganar dawowa gida, banda abinsa ai gidan ɗanta take zaune ba baƙon waje ba. A daren nan haka muka kai Yaya har gidanta can Ƙwalli tukunna muka wuce, ai kuwa ƴan sanda sun tare mu yafi sau uku, duk inda muka tsaya sai dai ya basu cin hanci sannan su barmu mu tafi. A daren nan zan iya cewa Nazifi bai runtsa ba, ni a rayuwata ma ban taɓa ganin wanda aka ma haihuwa yake tsananin farin ciki haka ba, kai ni ban ma taɓa ganin mutum da farin cikin nasa ba, motsi kaɗan sai yace Alhamdulillah, motsi kaɗan sai ya kira wayarta yace suna dai lafiya ko?. Da asuba bayan na idar da sallah har na koma saboda bacci ne fal a idona, ya zo ya tashe ni yace ga naman kai can an kawo na dafawa me jego, sannan naje wajen Iyam na karɓo garin kunun kanwa za'a dama a tafi mata da shi, kuma sai me nake ganin za'a ƙara musu? Na ce da shi,"Ni da ban haihu ba ina na san abubuwan da me jego ke so". Kana na gyara kwanciyata ina cewa,"Bari na ɗan matse idona kaina ciwo yake wallahi". Faɗa ya kama yi yana cewa,"Haba ke kuwa, naman kai fa na ce miki idan ba ki ɗora tun yanzu ba sai da rana kike so a kai mata? Ta shi don Allah kiyi abin da ya kamata in kin kammala kya huta gaba ɗaya, ga paracetamol can ɗauki ki sha sai kan ya daina ciwo". Tashi nayi kawai don bana son biye masa raina ya fi haka ɓaci. Ya ƙara cewa,"Naga masu jego ana so suci nama mai ruwa ruwa ko? To ko za kiyi mata irin wanda kika yi kwanakin baya, yay daɗi sosai ina ta so ma na ce ki ƙara yi". Wani kallo na watsa masa da cewa,"Da alama ka manta ni mutum ce ba inji ba. Haba kace wannan kace wancan, kana tunanin banda darajar ƴaƴanka ne ma zan amsa da cewa zan yi". Sai ya sauke murya yana faɗin,"To shikenan dafa iya wannan ɗin. Ni ba kya ɓatan rai ba ina tsaka sa farin cikina. Allah yay min babbar kyauta kema ka ci albarkacin hakan". Ina fita na tarar Iyam ta fito tana cewa,"Ya faɗa miki aikin da zaki yi ko, to kinga naman kai ba ace za'a dafa shi kan gas ba za'a ɓata lokaci, sai dai kisa itace ko gawayi ga Adamu nan nasa ya kawo babbar tukunya. Don Allah sai kiyi da jiki na ga sai faman lanƙwashe lanƙwashe kike yi, idan ba kiyi ba wane zai yi ummm? dama amfanin naki kenan aikin". Ni ban ma ko gaisheta ba na amsa da to kawai na wuce sama. idona har ba ya buɗewa da kyau saboda baccin da ke cikinsa, amma haka dole na yaƙe shi na fito na kama aikin. Ko kusa ban ji ina ɓacin rai dan zan yi aikin ba, hasalima annashuwa na ke ji a tare da ni, banda ma yanayi na gajiya da ramakon bacci dama ina da niyyar in gari ya waye na tambaye shi me zan dafa da za'a kai musu. Shiga ɗakinsa ɗari fita ɗari sai na same shi yana waya da abokai da mutanen arziƙi yana gaya musu an masa haihuwa. Tun asubar nan bai koma bacci ba kiraye kiraye kawai yake yi, wasu kuma yana tura musu saƙo ta message. Ya kira Malam ma yace masa za'a kawo Sa a yanka ayi sadaƙa sannan kuma ayi sauƙar ƙur'ani wa yaran. Naci wahala sosai wajen dafa naman kan saboda itacen ɗanye ne, da dukkan alama da gayya Iyam tasa aka kawo shi haka, ga Naman kan gari guda kan shanu manya huɗu. Iyam sai azalzata take yi akan nayi sauri kar rana tayi, shima ɗin kuma da nasa ƙwazzafar yana faɗin to na dama kunun in dafa shayi a fara kai musu, duk sai na bi na rikice aikin ma yaƙi yin sauri, ga ba damar ƴar aikin Zahra'u ta taya ni saboda tana ta gyaran wajensu, haka dole na rabu da naman na dawo kitchen na ɗora shayin sannan na dama kunun. Atika ta shigo kitchen ɗin tana ce min,"Abba yace kije da sauri". Hmm yarinyar nan idan ta girma ban san ya zamu kwashe da ita ba, ko gaishe ni bata yi, magana ma idan tana min kamar wacca ta isa da ni ko kuma sa'arta. Sharewa kawai na ke saboda dai a zauna lafiya amma ko ranar nan ita da ƴar uwaratata sai da suka yi faɗa, ita Rumanan na ce mata kar ta ƙara yiwa Antynta rashin kunya in ba haka ba zata faɗa a islamiya a zaneta, ita kuma tace ai dai ta faɗawa Anty Amarya a cireta daga islamiyar a sauya mata wata. Biredin da nake soyawa a cikin ƙwai na tsame na kashe gas na fita. Samunsa nayi ya shirya sai baza ƙamshi yake kamar sabon ango, don kayan ma da ya saka sababbi ne, bakinsa yaƙi rufuwa fuskarsa sai fitar da murmushi take yi, kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka san a tsananin farin ciki yake. waya ce kare a kunnensa yana cewa,"Ehh dama na ce ƙila baka tashi daga bacci ba ne, sai na maka text ta whatsapp". "Ehh wallahi Ƴaƴa biyu ne duka mata, sai ayi musu adu'a don Allah". "A'a Amaryar ce ba uwar gidan ba. Ameen na gode sosai a gaida iyalin, sai anjima". Ya aje wayar yana dubana da cewa,"Wai har yanzu ba ki gama ba? Kinga fa har na shirya zan tafi can, ƙarfe nawa yanzu tara fa, ace kuma har yanzu me shayarwa bata ci komai ba, kin san fa ƴaƴan za su sha nono duk su zuƙeta itama ta buƙaci abinci". Numfashi na sauke na ce,"Kafin ka fito na gama, amma Nama ba zai samu yanzu ba ka turo a ɗauka anjima. Kuma sai ka ɗauko kula a wajenta da zan zuba biredin a ciki". Na faɗa ina juyawa na fita. Can sai ga shi ya shigo kitchen ɗin, barinsa nayi da zuba soyayyan bireɗin ni kuma na ɗauko kwando ina saka kwanukan kayan abincin. Ya ɗauki wasu yay gaba da su nima ina biye da shi da ɗaya kwandon. Shi a shirin nasa ma tare zamu tafi, sai Iyam tace ina fa zai yiwu tafiya da ni, idan naje can me zanwa me jegon me zanwa yaran? Kawai na zauna na dafa abincin rana akai musu, kuma wataƙila ayi baƙi ƴan barka basa zo gida babu kowa ba, roƙonta na tari mutane da girmamawa kar su zo na nuna musu mugun halina dan dangin Zahra'u mutane ne masu mutunci, in kula kar jakin kishina da baƙin cin haihuwa yasa na ɓatawa miji girman da yake da shi a wajensu. Babu yanda Rumana bata yi ba akan zata bisu Iyam ta hana, wai ai tunda ta iya munafurci yanzu to ta jira ni mu tafi tare, ita Atika ai uwar wajenta ce shiyasa zasu tafi da ita, Yarinyar ta ban tausayi sosai, tana tashi ta tambayeni akan ta shirya nace to ai makaranta tace Atika ma bata je ba Abbansu yace zasu je gano jarirai, nace to itama ta shirya ɗin, na dai fahimci duk wani da zai raɓe ni ya soni Iyam bata ƙaunarsa ko da jininta ne. Sai kusan sha ɗaya na sauke naman kan, na zuba a kulolin tsakiya har biyu irin na taron biki, sannan na dafa shankafa da miya da coslow itama kwano ɗaya yace a dafa, ya turo Adamu ya ɗauka kai musu, ni kuma yace na shirya da yamma na je. Na gaji sosai ina so na kwantar da haƙarƙarina, na ce masa naje gobe kawai sai ya kama faɗan shi ba ya son musu, kuma kar na ɓata masa rai, ko na manta ƴaƴansa zan je gani da na ke faɗin ba zanje ba. Nace masa ni fa idan yana tunanin ina jin haushin haihuwar yaran nan yama daina, domin kuwa ni zuciyata tas take babu tsatsa, idan kuma ba zai cire zargin hakan a ransa ba to yaci gaba da ɗaukar alhakina. Da Yamma na shirya muka tafi Asibitin ni da Rumana, na tarar an ƙara cika wanda ke shaida dai ita ɗin yar gata ce, don har wata likita ma naji tana cewa amma wacca ta haihu nan ta gaban goshi ce. suma kusan ƴan uwan Nazifi duk suna nan, asibitin dai sun mayar da shi kamar wajen taro su kawai ake gani. A waje na tsaya muka gaggaisa da ƙannnen nasa da Yayyensa, kana na shiga ɗakin. Sallamar da nayi babu wanda ya amsa sai nayi musu uzuri da hayaniyar da ake tayi hakan yasa basu jini ba, sai bayan na shiga ne na ajiye kayan abincin tukunna Innarta ta lura da ni tace,"A'a Sa'ida sannu da zuwa, tun ɗazu kuwa na ke ta zuba idon ganinki". Na amsa da yauwa ina tambayarta ya jarirai suka kwana. Tayi min nuni da wajen zama tana ce min ƴaƴan nawa an fita da su Kakansu ya zo, nace mata tom ga dai abincin dare can na zo da shi. Tayi min sannu tare da godiya sosai tana ta faɗin an barni da ɗawainiya, sannan ta juya garesu tana gabatar musu da ni, na kula kusan duk ɗinsu ba waɗanda muka bari jiya ba ne. Haka suka bini da wani irin kallo na raini da ƙasƙanci, ai suna ganin na saka hijabi har ƙasa ga niƙab da safa ga ni duk a koje, haka kuma suna jinjina ni ce kishiyar Zahra'u. Babu me niyyar min magana, ni kuma girmansu yasa na gaishe su sai dai babu wanda ya amsa min sai ɗauke kai da suka yi, ina ji suna ƙusƙus Allah masanin me suke cewa a zuciyata ni kuma ina nanata "Wallahulmusta'anu ala ma tasifun, hasbunallahu wani'imal wakil, la'ila ha'illa anta subhanaka inni kunta minazzalumin". Me jegon ma haka na daure nayi mata magana to ni ban sani ba ta amsa ko bata amsa ba, ci kanki dai bata ce min ba kamar ma bata san ina wurin ba. Rumana ta dame ni da cewa Anty ina jariran na doka mata tsawa akan ta ƙyale ni ai tana ji aka ce an fita da su, Atika ta zo wajen tana ce mata jariran Antynta masu kyau, ita kuma ance Antynta ba zata haihu ba. Rumanan ta ɗago ta kalle ni, tabbas yarinyar yanzu tana sona bilhaƙƙi da gaskiya, sai in kuma shaiɗan ya kuma buga mata ganga, don yanzu ko wani ya ɓatan rai to sai tayi kuka musamman ma idan taga Nazifi yana min faɗa, sai tace ita bata so Abbansu na yi min faɗa. A sanyaye tace da ƴar uwartata,"Nima Antyna zata haihu ai in sha Allahu". Tana faɗar hakan na girgiza kaina ina murmushi me ciwo, na ce da ita ta tashi su fita daga waje sai ta girgiza min kai, haka na tilastata ta fice tana matsar ƙwalla, ni kuma bana son ƙara jin bakin Atikar ne saboda zuciya zata iya ɗibana na daki bakin yarinyar. Kiran Ummani ya shigo wayata, bayan mun gaisa na ke ƙara tambayarta jikin Abbaa tace wallahi yaji sauƙi sosai in kwantar da hankalina, gobe ma ake sa ran basu sallama. Ban dai yarda ba sai da naji muryan Abbaan tukunna, saboda na kira da safe ce min tayi bacci yake yi ni kuma sai nake tunanin ko jikin nasa ne ya dawo, tun da ko a jiyan kana ganinsa ka san ƙarfin hali yake yi, don niyyata ma da zan fito can zan wuce Yashaik yace kar na je. Ummani tace na bawa Zahrau wayar na ce ko ta bari kawai idan ta koma gida sa zo mata barka, tace a'a na bata ɗin dai kafin ta zo. Na miƙe na isa gaban gadon na miƙa mata wayar, ta bi hannuna da kallo na ce mata,"Babarmu ce zata yi magana da ke". Karɓa tayi babu sakin fuska, kuma da mamakina sai naji tana magana da Ummani cikin ladabi da girmamawa, har tana tambayar jikin Abbaa, sai naji daɗi da hakan don nayi tsammanin zata wulaƙanta min uwa ne yanzu mu kwashi ƴan kallo, ban san me Ummanin tace mata ba naga tayi murmushi tace,"To Mama ai sai su zo har gida ma su gaishe ki". Sannan kuma naji tana jero in sha Allahu Mama, kafin ta koma jera to to, da haka na san aduo'i ne Ummani ke bata don na san wacece mahaifiyata, bayan gama wayar tasu har godiya nayi mata ko ba komai ta darajarta min Uwa. Ina nan zaune zaman asibitin duk ya gundure ni, ba don yace lallai na tsaya sai ya zo tukunna mu tafi tare ba, niyyata muna gama gaisawa naga yaran sai na juya. Ba abin na fita daga wajen ɗakin ba duk ƙannen Nazifi ne da Yayyansa, ni kam da na zauna tare da su gwara na zauna nan ɗin suyi ta min habaicin, don nafi jin zafin cin mutuncin ƴan uwan Nazifi akan na ƴan uwan Zahra'un. game ɗin ludo na saka mana a wayata muke yi ni da Rumana, hankalina ya bar kan kowa sai dai kunnuwana ba su fasa jiye min yacca ake ta aikin yada min baƙaƙen maganganu ba ana aibata ni, zuciyata taji ba zata jura ba kawai na miƙe na kama hannun Rumana muka fice. [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR13FT5* Maman Yasmin da Maman Khairi da Yaya Nusaiba wato Yayar Safiyya suna ta hirarsu, ni dai ina daga gefe ina jin su sama sama, nayi wanka lokacin na shirya cikin wasu kaya marasa nauyi da Maa ta bayar aka kawo min, hankalina duk ba ya jikina, zuciya da gangar jiki sun cika da kewar Salim, babu abinda na ke son ji a yanzu sama da muryarsa, don na san ba zan samu ganinsa ba ko da ace yana cikin gidan. Idona na rufe Safiyya ta shigo tana faɗin,"Ke to ga ƴarki nan ta addabi mutane a kaita wurin New Mommy". Nayi saurin buɗe ido ina kallon Rofi'at ɗin da murmushi, zaune na tashi na buɗa mata ta taho da gudunta ta shige jikina, Allah ya gani tun ba'a je ko ina ba na kamu da soyayyarsu, muna can muna magana ashe yarinya har tayi bacci, gyara mata kwanciyarta nayi a jikina. "Safiyya hanya dai lafiya ai babu matsala ko?". Ta baro hirar da suke ta waigo tana kallona tace,"To banda abinki ba tare da security suke ba, ki kwantar da hankalinki nan da ƙarfe uku na dare za ki gansu". "To Allah ya kawo su lafiya". Na faɗa ina kwantar da kaina kan filo, sai da muka yi dai wayar da su Mama A'i suka ce min wallahi lafiya lau suke gasu ana ta fafara gudu da su akan hanya, zuwa ƙarfe ɗaya ma za su iya zuwa. "To Allah ya kawo ku lafiya Mama A'i". Cikin baccin da ya fara fizgata naji yo ƙarar wayata, da sauri na farka na ɗaga ina sawa a kunne ko numbern ban duba ba, can naji muryan mace cikin turanci na ce min,"Ba dai har kin yi bacci ba". "Umm wa ke magana?". Muryarta ya bayyana irin rashin jin daɗin nan da cewa,"Kudrat ce". Fuskata a yatsine na ce,"Ayyah barka da dare". Haƙuri ta shiga ba ni kan kiran da ta min nayi bacci, na ce mata,"babu komai ai". Sai ta sake cewa,"Shi ne ba ku biyo ta nan ba kun barni ni ɗaya a gida shiru". Na kyaɓe baki ina cewa,"Kema ai sai kika ƙi zuwa nan ɗin". Murmushinta tayi wanda ke bayyana bata da damuwan komai tace,"Ki yi haƙuri shi ne yace ba sai na zo ba, yaran kawai za'a kai, amma ɗazu Maa tace gobe da safe nima na taho tunda akwai party da za'ai". Murya a daƙile na ce,"Allah ya kaimu". Tana son jana da hira ina ga ko kaɗaicin gidan ne ya dameta, da kuma mijin nata da basu samu yin waya ba don alamun hakan ya nuna, tana ta ce min fatan dai Yarana ba su dame ni ba ko, na ce mata ga Rofi'at ma kusa da ni har tayi bacci, ni dai na nuna mata bacci na ke ji, muka yi sallama nayi cilli da wayar gefe tare da jan dogon tsaki wanda har sai da Yaya Nusaiba ta tambaye ni lafiya, kawai nayi saurin kulle idona da zummar a cikin bacci nayi, nan kuwa haushi da takaicin kiran Kudrat ne, aikin banza ita ko kishi ma bata yi zata wani kira ni da ƙatuwan muryanta ita lallai ga ta me kirki, ta bar ni inji da damuwan rashin jin Salim ɗina ma, shegen iyayi da neman suna da makirci irin na su na ƙabila, ƙwafa nayi ina janye Rofi'at a jikina na juya mata baya. Ni fa banga ta bacci ba yau sai ta Allah kuma, babu nutsuwa sam tare da ni, kowa ya shigo yaga yanda na takure kaina sai kallo da ido sai ace baƙunta ce, Safiyya ma haka ta zo ta gama zuba min surutunta sai da ido kawai na ke kallonta, ita ce ma ta fahimci yanayin da na ke ciki tace bari dai taje ta jiyo min labarin mijin nawa wurin Sir, na zama ƴar soyayya zan mace musu tun basu kai ni ɗaki ba. bayan fitarta duk na zaƙu ta dawo ta sanar min halin da mijina ke ciki, na ɗaga waya zan kirata sai naga ashe ta bar wayan nata anan, ni dai nayi ta faman juyi akan gadon duk na rasa me ke min daɗi, su Maman Khairi ma da suka lura da ni sai suka shiga min shaƙiyanci irin na su wanda har sai da naji kunya, tun kuwa da nasa filo na rufe fuskata ban ƙara buɗewa ba. Sai ƙarfe biyu da rabi Umman Batula suka iso, da aka tashe ni ma ce na ke gari ne ya waye jin hayaniya da hasken fitilun gidan da ba zaka taɓa cewa dare ba ne, naji daɗin ƙarasowarsu lafiya kuma ina ganin hakan na rarumi wayata na kuma kiran Salim shiru kiran bai tafiya. Hankalina sai ya tashi idona ya cika da ƙwalla, rabona da shi fa tun safe, shima magana muka yi a tsaitsaye, jiya kam dama totally banji muryansa ba, ni kuwa wanne irin horo wannan aikin na su yake min, dama haka aikin na su ya ke da barin mutum cikin fargaba da tashin hankali? Kuma babban abin da ya ɗaga min hankali da yace jirginsu ne zai kewaye a can wani ƙurgummin daji. rumtse ido nayi jin hawaye na neman sakko min na rungumo Rofi'at jikina gabana na ta faɗuwa, haka bacci ya sace ni ina ta adu'an Allah yasa dai lafiya, ya kula min da mijina a duk inda yake. Da asuba ma da muka yi sallah ban iya komawa bacci ba, ina kallon su Mama A'i da Maman Khairi aka yi sallah aka koma bacci, kowanne to a gajiye yake sai faman miƙa suke yi, ga shi sun samu gado wawakeke da katifa me bala'in taushi. Har gari ya fara wayewa kaina na bisa gefen gado duk na kasa sukuni, zuciyata matse da taraddadi, idona kuwa na kasa ɗauke shi akan wayata ƙiris na ke jira in ga kiran Salim ya shigo. Duk yanda na so na daure na kasa sai da na kira Ummani, ko da ta ɗaga yanda taji muryana sai ta shiga tambayana lafiya, kwana nayi ina kuka?". Nace mata,"A'a tun jiya ne bayan ɗaurin aure har yanzu bamu ƙara magana da Salim a waya ba, ko message idan na masa ba reply kuma ni har yanzu ban ji wani yace sun yi magana da shi ba". Na faɗa da muryana tamkar zan yi kuka. Sai naji ta sauke numfashi tana tayani adu'a Allah yasa lafiya. "In Allah ya yarda lafiya, kin san yanayin aikinsu da kurɗa kurɗan shiga daji wataƙila suna wurin da babu network ne". Haka ta ɗan kwantar min da hankali, sai da ta haɗa ni da Abbaa muka yi waya shima yana tambayana ya kwanan baƙunta nace masa babu daɗi duk nayi kewarsu, shima kuma yace in kyautata zato a raina in Allah ya yarda lafiya lau Salim yake koma a'ina ne. Wajen takwas aka turo ƙofan ɗakin, idona karaf akai kaman zan ga Salim, baccin gajiya ne fal cikin ƙwayar idona amma har ga Allah ba zan iya ba, duk wanda ya ganni ya san hankalina ba kwance yake ba, abinci ne aka kawo mana kala kala na break fast, bayan tea da soyayyan bread da ƙwai, akwai ferfesun ganda da snacks da soyayyan kaza, sai kunun tamba da ƙosai, kowanne ya bani sha'awa amma ba zan iya ci ba, ko jiya ina ganin teba da miyan kuɓewa yawuna kaman zai dalala amma na kasa ci, to da wanne teste ɗin bayan wanda ke da ɗanɗanon bakin ya tafi da shi. Haka su Maman Yasmin suka zage suka ci abincinsu ni kuwa ban iya ko kai hannu kwanon ba, ina zan iya cin abinci ban san a wanne hali Salim yake ciki ba, ai ko ruwa ba zan iya sha ba, ba yanda ba'a yi da ni ba na ce ni na ƙoshi, har da ƙaryan amai ma na ke ji, Safiyya na min iskancin wai da an kai ni na faɗi haka sai ta ce Salim ya iya aiki, su kuma duk tsammaninsu ƙulafucin gida ne babu wanda ya kawo a ransa cewa rashin jin mijina ya jefa ni a halin ƙaramar rashin lafiya. Safiyya ta zo muka fita tare da ita Maa ce ke kirana, a ɗakinta muka sameta cikin shiga na alfarma, tana ganina fuskanta ya washe da annuri, cike da kunya na isa kusa da ita inda take min nuni da na zauna, muka daɗa gaisawa da ita don tun sassafen da aka kai mana abinci muka fito gaba ɗayanmu muka same su a main falo ita da Mommi muka gaida su, kuma babu ɗagawa Maa da Mommi ɗin su ne suka je da kansu har ɗakin da aka sauke su Mama A'i suka gaishe su, ashe can ma haka aka kai musu tulun uban abinci, ko ina za su kai shi oho. Tana kwanto ni jikinta take ce min,"Kin ci kin ƙoshi?". Na ɗaga mata kai alaman ehh, sai tace min to nayi wanka anan na shirya, can sai na barwa sauran suma su sami kimtsawa. Kaya ta ɗebo min a wadrobe ɗinta riga da skirt na atamfar ankara, ta aje min duk wasu kayan shiryawa, ni dai duk a kunyace na ke na so ace ta bar ni na shirya a can cikin ƴan uwana, da taga itama alaman hakan tana murmushi take dafa kafaɗana tace,"Ni fa Mamanki ce babu batun jin kunya tsakaninmu, ki saki jikin ki da ni kinji daughter nah". Nayi murmushi kaina a ƙasa, tace min akwai towel a toilet ɗin sabo ta ajiye min, dama da ƙaton hijabi a jikina haka na shiga da shi sai a banɗakin ma na cire kayana. Har na fito still tana zaune bakin gado inda na barta, tayi min nuni da dressing mirror tace ga stool nan na zauna na gyara jikina, ga turaruka nan duakkansu na fesa. Ina shafa man ina ji suna waya da Kudrat tana ce mata tom sai ta ƙaraso. Ban san me yasa na ke jin zuciyata kamar bata son Kudrat ba, ko duk cikin kishi ne, ko ambatar sunanta aka yi sai naji zuciyata tayi bala'in motsawa da haushi, har mamakin kaina na ke yi, adu'ana ɗaya kar wannan kishin yay min illa. Na shirya cikin kayan da Maa ta bani nayi kyau sosai, lokacin ne take ce min,"Kun samu magana da Onochie?". Kamar ta san Alla allan da nake kenan tayi maganarsa, na rasa wa zan tambaya shi to, ai kuwa ban san lokacin da na amsa da sauri ba nace"A'a ina ta kiran wayarsa ba ya tafiya tun jiya". Na faɗi hakan da muryan damuwa. Sai bayan nayi maganar ne kuma kunya ta lulluɓe ni, itama murmushi tayi da sautinsa ya fito sosai tace,"Yana lafiya kwantar da hankalin ki, za ki saba ne a hankali". To ni kowa sai yace min in kwantar da hankalina, ta ya kenan alhalin su kansu ba su ji daga gare shi ba. Muna zaune tana ɗan jana da hira wanda duk tambayoyi ne take min game da rayuwana, har tana tambayana mun dai gama magana da Salim akan asibitin da zai nema min ko na ce mata ehh, tace sai ranar da zan je ganin gida zamu tafi har da ita su gaisa da iyayena. Wani dogon saurayi me kama da ita ya shigo ɗakin, ba zai wuce 20years ba. Da fara'arsa muka gaisa suna kama da Maa ɗin sai dai shima ingarman jikin Sir yayi, over over ya miƙa mata yace Brother ne yake magana yace a bawa matarsa. Idona akan abar ina mamaki wai ta nan ake magana mutum kuma yaji, abar da nake gani a film sai gata gaban idona har zan taɓa kuma zan yi magana da wanda na sani ta ciki, ina wannan tunani kuwa na jiyo muryansa na faɗin,"Nnọọ(Hello)". Ita kuma tace masa,"Ibolachi(Good morning)". Dama iya abinda na sani kenan a yaren shima kwanaki ne da muna chart da shi ya ɗan koya min, yo wa ya san ma ko zan iya ni da na zo rayuwar dindin a cikinsu, yaren da na ke jinsa da wahala. Sai da suka gama magana da Maa kafin ta miƙo min, na karɓa kaina a ƙasa, fita tayi sai naji daɗin hakan ko don na samu sakewar magana da shi. Na riƙe a bar a hannuna ina zuba mata ido, a baki zan sa ko kuwa a kunne? Don lokacin da Maa ke maganar da shi ban lura da yanda tayi ba, muryansa nan da ke kashe min jiki naji yace,"Ola’m (My Diamond)". Wani yanayin daɗi naji ya ratsa ilahirin ɓargona, idanuwana a lumshe ina sauke ajiyan zuciya, wallahi na azabtu da rashin jinsa Allah ma ya sani, ashe haka na ke mugun sonsa ban sani ba. "Myyy are you there?". Kawai sai naji na fashe masa da kukan gaske, kuka har ina jan numfashi. Hankalinsa ya tashi ya shiga jero min tambayan mene? Me ya faru?, cikin shagwaɓan da ban taɓa sanin na iyata ba a duniyana na ce,"Tun jiya ban ji muryanka ba, ina ta kira bana samu, ban san wanne hali kake ciki ba, zuciyana nata min zafi, hankalina duk ya tashi". With low voice da ke fita da amon damuwa da tsantsan kulawa yace,"Am so sorry Ola’m, banda yanda zan yi ne, duk abinda na ke hankalina na kanki, kowa sai da ya gane bana cikin natsuwata, har kwaɓa nayi a confrence meeting, ni kaina zuciyana bai samu salama ba sai yanzun da naji muryanki, amma kuma hankalina ya fi da tashi dalilin jin kukanki, kiyi haƙuri kin ji ina nan lafiya, ki daina kukan please bana son zubar hawayenki masu tsada, kukan yana taɓa min zuciya kar kisa ta samu matsala". Na ɗan ja numfashi nace,"To yaushe za ka dawo?". A hankali yace da ni,"Muna Abuja right now amma na gama shiryawa tahowa kawai zan yi, ba zan iya ƙara yini ba tare da na jini tare da ke ba. Kin yi breakfast?". Kaman ina gabansa na girgiza kai da cewan,"Na kasa cin komai tun jiya, kai kawai na ke son gani". Ya furzar da iska wanda na tabbata sai da ya shafi goshi kamin yace,"Ki yi haƙuri kin ji, zan iso gareki nan ba da jimawa ba, amma ki daure ki ci abincin ko kaɗan ne idan na zo sai na ƙara ba ki". Na ƙara shagwaɓe masa da faɗin,"Ni ba zan iya cin komai ba sai na ganka, baki duk babu ɗanɗano kuma kasan kai ne ɗanɗanon bakin nawa". Haka yay ta lallashina da soyayyarsa, na amsa masa da to zan ci abincin amma ba da yawa ba. Ya tambaye ni ya naji yanayin nan ɗin, banda wata matsala ko? Sun min tarba me kyau? Ya makwancina? Na takura? Garin da daɗi?". A hankali na ce masa,"Naji daɗi sosai da yanda aka karɓe mu hannu bibbiyu, abinci har sai da muka bar shi, wurin kwana kuwa ai ƴan gida muka zama ba baƙi ba, garin kuma akwai daɗi duk da babu inda na fita". Duk na ba shi labarin abun da ya wakana daga jiya zuwa yau, sai naji yayi farin ciki musamman da na ce masa family ɗinka suna da kirki kuma naji daɗin kasancewana cikinku, su Maman Khairi ma kowa yaji daɗi yanda ba su nuna mu ɗin ba nasu ba ne suka rungume mu da soyayya, Ina basa labarin irin adu'an da Sir ya dinƙa min sai naji kaman na tsoma shi cikin kogon nishaɗi. "Myy dama na fada miki ai, Family na ba za su nuna miki banbanci ba, kowa zai so ki, nima suna sona sosai kuma suna son duk abinda na zo musu da shi, wani gatan ma tukunna dai, wataran Maa sai ta kusa goya ki saboda soyayya, za ki ga gata iya gata a wajen family na, an kai ki wurin Granny?". Na ce masa,"Ehh mun je, Mommi ma duk ta raka ni na gaida su Uncles". "Ohh wan nan tsohuwa sai da ta ja min ke yawo kenan ta wahalar min da ƙafan mata, ita bata zama da anyi baƙo ta dinƙi kaisa wuri tana aikin masa bayanin mutane, kema haka ta miki ko?". Ina ƴar ƙaramar dariya na ce masa,"Ehh amma tana da shiga rai babu ruwanta". Kaman ina gabansa na ji sanda ya ke jijjiga kai da cewan,"Uhmm da kike ganinta masifaffa ce, ke ma ɗokin ganinki ne na sabunta, ita ko wasan jika da Kaka bata yi, kowa a gidan shakkarta yake, amma idan kika iya zama da ita bata da damuwa sam, ta dungure miki kai?". Nayi murmushin da ya zarce har zuciyata da ce masa a'a. Mun jima muna magana da shi kaman ba zamu rabu ba, haka kamar ma ba zuwa zai yi ya ɗauki kayarsa ba. Wallahi sai naji ma ashe idan ina tare da shi nafi missing ɗinsa, kaman na bisa ta cikin abar haka na ji, haka na ɗauka waya na masa text me daɗin gaske, kai wani hanin ga Allah ma dai baiwa ne. Ina zaune ina ta juya over over ɗin a hannuna Maa ta dawo, tace to naje can wurin ƴan uwan nawa nan da ƙarfe biyu dai za'a fara taro. Nace mata to na tashi na fita tana ta cewa na yi kyau sosai a shigan kayan. Da ƙarfe sha biyu ina kwance ni ɗaya a ɗakin da aka sauke mu, wayata ce a hannuna ina ta kallon hotunan ɗaurin auren da Yashaik ya saka a status, bana kallon kowa da kyau sai mijina, nayi nisa cikin kallon wani hotonsa naji an faɗo kaina, na razana zan kurma ihu sai aka toshe min baki, ido warwaje na ke kallonsa, yaushe ya shigo ban ji motsi ba? Mutsu mustu na shiga yi zan ture shi ina tsoron kar wani ya shigo ya ganmu, sai naji yace,"Nasa key a ƙofan fa". Mirgina ni yay na zamana a samansa, yay min peck a goshi kafin ya shiga bawa fuskartawa kiss ta ko'ina, ina ta kakkaucewa ina ce masa ya bari wani zai iya shigowa ni ya ƙyale ni bana so. Sai kawai yay min wata runguma da har sai da ƙashin bayana ya amsa. "Myyy kin san yanda na ƙagu na mallake ki kuwa? Halalina ce fa ke yanzu ko waye ma ya shigo ya ganmu a haka babu abin da zai ce, wuri ma za'a bamu kuma mutum shi zai ji kunya". Sai ya kulle ido yana cika bakinsa da iska ya hure min a fuska, na lumshe ido shi kuma ya buɗe nasa yana ta kallona kaman zai cinye ni. "I missed you so much matar Soja, kaman zan mutu fa haka naji". Ina haɗiye yawu da ƙyar na ce,"Plss ka daina zancen mutuwa, yaushe ku ka dawo?". "Yanzun muka shigo, wurinki na yo direct, kowa sai kallona yake don na tambayi ina amaryana suka ga na taho kai tsaye, laifi nayi hakan?". "Ko wurin Maa baka je ba?". Yay wani killer smile ya ce,"Na leƙa ɗakinta naga ba ki nan, na san kuma ta ganni don naji sautin fitar murmushinta". Ɗan marin wasa nayi masa ina kwantar da kaina a ƙirjinsa na ce,"Salim ka ba ni kunya". Yana nutsa yatsunsa cikin gashina yace,"Har an ɗaura aure ma ba ki daina faɗin sunana ba gatsal ko, oookkk na ma gane so kike sai anyi abin kana ki sama min suna". Ni dai da ace da hausa yake magana sai na fi jin kunya, fuskata na ɓoye a ƙirjinsa. "Ka san yanda ka tashi hankalina kuwa? Da sai dai ai kaji labari a media ana wata matar soja taje neman mijinta fadar shugaban ƙasa, don shi zan je na tsare da tuhumar ina ya kai min abin ƙaunata". Dariya sosai yayi wadda ta bayyana haƙoransa dukka a waje, dariyar da sautinta yay min mugun daɗi, ya daɗa rungume ni yana cewa,"Sai ki ce masa me idan kika je?". "Na ce mijina da ka aika a jirgi can wani waje na zo ka bani abina mu tafi, don na fiku buƙatarsa". Na faɗi hakan ina murmushi ina kai hannu na taɓa sumar kansa, fuskansa ya shiga gogawa da nawa muka yi shiru ni da shi sai fitar numfashinmu kawai da kake ji. Da wani kasalalliyan muryasa yake ce min,"Myyy wannan Ƙamshin na ki, ko naje na faɗawa Maa a fasa taron mu wuce kawai? Ni ba zan iya ƙara jiran lokaci ba". Lumsassun idanuna na buɗe ina kallonsa, sai dai ni kaina a yanda na ke jina jikinsa ko maganan ba zan iya ba, ni fa gaba ɗaya a yacca na ke jin soyayyarsa da feelings ɗinsa tamkar ban taɓa sanin komai ba a game da soyayya da aure. shi yay ƙarfin halin da ya raba jikinmu yana sauka akan gadon yace,"Myy ba zan yarda ki ƙara kwana ba, zan faɗa musu yau zamu wuce kin ji". Knooding kaina kawai na masa, ya fita yana faman shafa kansa, na bi bayansa da ido har lokacin ina jin rungumar da yay min wadda naji kamar muna manne ne still. Babu jimawa sai ga shi ya dawo da tray na abinci, ya zauna yana cewa da ni na sakko, na dube shi na ce,"Wai kai Salim baka jin nauyin mutanen da ke kallonka ne?". Shiru yay min sai da ya gama zuba faten doya kana ya dube ni yace,"Kina cin Teba?". Gyaɗa masa kai na yi nace,"Jiya da aka kawo ya bani sha'awa". "Oya to sakko". Na zamo akan gadon yace alalle sai dai na zauna saman cinyarsa, naƙi babu yanda bai da ni ba, yace ya ɗaga min ƙafa ne kawai saboda ba gidanmu ba ne, ina masa dariya na kai hannu zan fara ci ya riƙe hannun nawa, da kansa ya ke bani na tambaye shi miyan menene yace min sunanta Ogbono soup, yana sonta sosai na dage na iya zan mallake shi da ita. Sai da ya tabbatar na ƙoshi kafin ya bar ɗakin har yana zolayana,"Da ga cin teba sau ɗaya har kin zama ƙatuwa". Na ce masa ko dai daga ci har gari ya tsotse ni. Yay dariya yana ƙwafa wadda na san ma'arta. Karfe biyu wata budurwa ta shigo ɗakin sa'ilin muna magana da Safiyya, wadda ke ta bani tips na kula da miji, tana ce min ko da naji ana matan ƙabila na ƙwace miji ba da asiri ba ne ba kuma makirci ba ne, kawai tsantsan iya kula da buƙatunsa ne da iya tattalinsa su mayar da shi kamar jariri, babu batun kuma an girma an aje ƴaƴa shikenan batun soyayya ya tashi, riƙe abinsu suke da ladabi da biyayya jin kai duk a aje a gefe ayi ta gurzar lamura, har tana faɗin banda dai aure rubutaccen al'amari ne da ita dai bata ga me zai sa Salim ya ƙara aure ba, domin Kudrat kat ce wajen sanin zamantakewar aure, naji haushin maganar ma Safiyya har zuciyata na ɗarsa min ko kishi take taya Kudrat ɗin, to nima dai za su ga salon nawa mallakar mijin ne babu boka babu Malam. Budurwan da ta shigo tace Maa ta turota ta shirya amarya, lokacin bamu jima da gama cin wani abincin ba, duk da cikina a cike yake da wanda Salim ya bani, to saboda kar Hajjo ta tsare ni da tambayan inda na ci na ƙoshi dole haka nasa hannu, ni kam har na gaji da ganin abinci ma. Duk wanda muka zo tare sai da aka basa kayan shigan partyn ya saka, ni kuwa ban san ta yanda zan faɗa muku haɗuwar da nayi cikin shigar da aka min ba, Safiyya ta ƙwala wani ihu tana tafi da tsalle tana cewa,"Ke kam ai zam igbo ɗin, wallah wanda bai san ki ba zai rantse ba bahaushiya ba ce". shigan blue akan min ni kai na da na kalla madubi sai da naji na burge kaina, ku kuwa dama sai dai na barku da haskowa idanunku kawai. Lokacin da aka fito da ni Mommi ta riƙe ni ta tsayar da ni gefen Salim, wanda kaɗan ya rage ban sume ba saboda yacca ya tafi da ni a kyan da yay cikin shigarsu. Ga wata sanda ta ƙarfe ta ya riƙe, kai ba ka ce sojana ba, fuskarsa sai annuri take fiddawa. Ranƙwafo kansa yay saitin kunne na yana cewa,"Baby kyan da kika yi kaman a sace a gudu, to Allah ya so ma ni zan ɗauke kayata ba kuma me hana ni, nan gani nan bari ɗumamen maya". Na waro ido ina ce masa,"Har da su karin magana ka iya, lallai ne Onochie". Ƙuguna ya matsa yana murmushi. Tab lallai arziƙi na inda yake, haka talauci ma na can inda ake kukan babu, ashe duk girman compaound ɗin nan akwai inda ya fishi, ta can ciki wani wawakeken fili ne anan suke shagulan bikinsu babu ruwansu da kama event center, an ƙawata wajen ka rantse wani mashahurin event center ɗin aka kama, plate na abinci ne kawai ke haske maka ido da drinks. ni dai kaina na ƙasa amma ba ƙarya kowa a wurin abun kyau da burgewa ne, Musamma yaransa da aka yi musu shiga iri ɗaya suna zaune a gabanmu kan kujeran da muka zauna, suma kamar ni hannayensu duk da ƙananan mafitai me gashi. Hoto kawai ake ta ɗasa mana, sai naji ina ma acan gida ne nayi hoto da mahaifiyata da ƴan uwana, ba shakka Yaya Imam ma zai kyau cikin irin shigar nan, sai dai na san ko me za'a masa ba zai saka murjani a wuya ba. Taro yay taro, duk ba wasu mutane ne da aka yi gayya ba iya Family ne kawai, Safiyya ce ta gabatar da ni ta faɗi tarihina tun daga haihuwa har kan matakin aikina, Kudrat ma ta zo masha Allah wallahi da na ganta sai da na raina kaina, ashe kyan da na gani jikin ƴaƴanta da wanda ake faɗa min ba komai ba ne. Nayi ta mamakin me ya kai salim ƙara aure shi kuwa yana da wanga zuƙeƙiyar mata. Babu ruwanta sakaraftunta kawai takeyi cikin farin ciki kamar ba wadda miji kewa kishiya ba, ni da ka aka kawo ma na fita kishin miji, har da su zuwa tayi mana liƙi, haka ta zo tana ta yaƙe min haƙora hoto kuwa mun yi da ita yafi a ƙirga, tun ban sakin jikina da fuska da ita sai da na rissina, kowa na ta rawa ni dai na kasa saboda kunya, Salim kuwa ya zage yana ta abarsa shi da ƴaƴansa da matarsa, Kudrat ɗin ce ma ta kamo hannuna ta shigo da ni tsakiyar su tana rawar tana aikin watsa mana kuɗi dukkan mu. Ba'a watse a wajen ba sai ƙarfe bakwai Granny ya aiko a kashe kiɗa aje ayi ibada, sai lokacin naga Salim ya murmusa, don tunda ya gama rawarsa yaci magani sai zungurana yake wai ana ta ɓata lokaci salon aja masa ƙin tafiya da ni yau, ni dai dariya kawai nake ƙasa ƙasa, kunya na ke ji na biye masa yanda idon kowa ke a kanmu. Fakar ido yay ya fige ni muka shige wani ɓangare, yace min da na koma ciki kawai in cire wannan kayan hayaniyar na shiryo na fito, nace masa ni kam ban iya rashin kunya ba, sai ya matse bakina na samu dai na zilla masa ganin abinda yake ƙoƙarin aikatawa. Ai kuwa ana can ana nemana duk sai naji kunya, ina jin wata mata ina ga inlaw ce a gidan tana faɗin a bawa Onochie matarsa su wuce yau, Kudrat ma ta hango ni ta taho da hanzarinta tana ce min a yau fa zamu tafi gaskiya ba za'a kuma barinta kwana a gida ita ɗaya ba tunda dai mijina ba barinta kwana anan zai yi ba. Nace da ita,"Tafiya da wannan daren?". Ranta fess tace,"Mene dare? Shi bai faɗa miki babu nisa ba, 2hours ne fa kawai zuwan". A hankali na ce mata,"Da dai mu bari sai goben ma tafi da safe". Hannuna kawai ta kama muka yi ciki sai ɗakin Maa. Ita ta kira shi a waya tana faɗa masa wai ya shigo ya shirya ni mu tafi, ni duk sai ta bani mamaki sosai, kamar ba kishiya aka mata ba, to ko ba auren soyayya suka yi ba ne? Ko kuwa dai dama matan arewa ne kawai ma su kishi?. shi kuwa sai ce mata yayi to idan ni ban son tafiyan ta kwaso masa yaransa su tafi yana jiransu a waje idan ya so gobe ni na kai musu kaina. Yanda yay maganar sai da nayi dariya don a fusace yayi ta. Can ɗakin da muka sauka na koma, Umman su Safiyya ita ta shirya ni, tayi min shigarmu ta hausawa kamar dai jiya swizz less ne na saka blue sai faran lafaya, haƙƙun nayi kyau ko a faɗa ko kar a faɗa, duk wanda yace ban ba to ɗan hassadata ne. Yo idan ka ganni ma ina zaka taɓa cewa Sa'ida ta taɓa aure? Ina zaka taɓa cewa ba tsaleliyar budurwa ba ce a gabanka? Rantsuwa kuwa idan za'a kwana ana maka da labarin irin rayuwar da nayi a baya ba zaka taɓa yarda ba, to ina ma wani alama da zai nuna na fuskanci ƙabulace me raɗaɗi a rayuwata, canjin rayuwar fa ba ƙaramin canji na samu ba sai dai godiya ga me sama kawai, shiyasa aka ce haƙuri ba yawa, me haƙuri ba ya tawaya, haka kuma me haƙuri shi ke dafa dutse har ya sha romonsa, ga matakin nasarar da haƙurin ya kawo ni nan. Sai da naga dai an gama shirya ni da gaske tafiya zamu yi sai kuka kamar daga cikin gidanmu za'a ɗauke ni, Nasihan da Hajjo ke ƙara min ita ta sake karyar min da zuciya, hatta Maman Khairi da Maman Yasmin sai da suka yi hawaye, na ce a bani waya na kira Abbaa, kaman kuwa yana jiran kiran nawa shima don bugu ɗaya ya ɗaga, na ce masa gani yanzu za'a wuce da ni can gidana, nan yay ta min adu'a yana ƙara jaddada min nasiharsa gare ni, muka yi sallama da shi sabon kuka na ƙara zuwar mini. Sai da su Gwaggo Abula suka fara fita kafin Umman su Safiyya ta fito da ni kaina na ƙasa. Falon Sir aka kai ni, a can na tarar da Salim ɗin shi da Kudrat, dukkanmu Sir ya haɗe yay mana faɗa da nasiha, nasiha me tsuma zuciya. Daga nan aka kai ni can wajen Maa wannan karon kuma da gani sai shi ne, Itama tayi mana nata adu'oin irin na kowacce mahaifiya ta ƙwarai, musamman shi da take faɗa masa ya zama me adalci tsakaninmu, kar ya taɓa bari wani abu da zai haddasa ƙabilanci a tsakaninmu ya afku. Har Maa aka rako mu compound tana riƙe da hannuna ita ta saka ni cikin mota, su Hajjo na ta yi musu godiya da irin karramawar da aka yi mana. A motan da na ke Mama A'i ne da Hajjo sai Gwaggo Abula da Safiyya, ɗaya kuma su Maman Yasmin ne a ciki, ɗayar kuma Salim da iyalansa. To a motar ma tun ina kuka har na gaji na daina, na biyewa hirar da ake, yo tafiyar ba ta minti goma zuwa talatin ba ce, awa uku ne babu kaɗan, zuwa sha ɗaya na dare dai mun isa, Kamar dole Salim da rigima dai da yay haƙurin. Naji ƙaran shigowar message a wayana, ina dubawa na ga lambar Lubabatu ne, mamaki ya mamaye ni ita kuma message da wannan daren haka? Me zan mata? Ni fa bana ƙaunar wani iri na Nazifi Bala Mai Kalwa ya ƙara gifatawa a rayuwata, Tun ban buɗe ba kuwa nayi regretting bata lambar tawa, sai dai ko da na duba saƙon magana yake akan. _"Don Allah ki yafe min Sa'ida, hakkinki ba zai bar ni ba, ban da idon da zan zo gaban ki na fuskanceki na nemi yafiyarki, don Allah ki ce kin yafe min, na gode sai naji daga gareki, ba ni da waya ne a hannu"._ Tsaki nayi na goge message ɗin, can kuma sai zuciyana tace na mayar masa da amsa tunda shi bai da hankali bai san menene aure ba, kar ya zo ya ƙara turo min saƙo mijina ya gani ya rikita min zama ya tashi hankalin farin cikina. _"Idan ba so kake ka ƙare rayuwanka a gidan yari ba to kar ka ƙara turo min saƙo, domin kuwa mijina ba zai ƙyale ka ba. Yafiyata ka jira mu haɗu a kotun Allah gaban alƙalin da ba ya zalunci"._ Mun isa Delta State lafiya, na shiga gidana da ƙafar dama, wata faɗuwar gaba da ban ji ta ba tun ranar ɗaurin aure sai yanzu ta ziyar ce ni, jiki a sanyaye fuskana na rufe haka na tako cikin falona, Umman Batula na faɗin shiga da Bismillah, suna biyo min ayoyin da zan karanta, kai yanda ake tayi da ni fa kamar auren budurwa b abazawara ba. Suna kai ni cikin ɗakina duk suka watse aka bar ni daga ni sai Safiyya. Ganin har lokacin ina hawaye ta daki kafaɗata tace,"Beb wannan hawayen ya isa sai kace wacce ta auri wanda bata so? Bafa auren farko bane na biyu ne balle kice min kina tunanin first night, haba mun fa girma Beb". Ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya ta shakiyanci. Sai kuma ta tsuke fuska taja tsaki tace,"Allah ya isa da mai kalwa ya same ki a banza, ina ma ɗan uwana ne ya aureki tun farkon farko ba mai kalwa ba shege matsiyaci". Sai ta sake sakin fuska tace,"To ya za'ayi da ƙaddara ce Allah ya riga ya rubuta. Ke ki kwantar da hankalinki ki kwashi soyayya, wallahi Salim ba shi da matsala na san kin sani, ki cire batun fargaban zai sameki wani ya riga shi shiga hanyar, yo dama ai a yanda ya ganki ya ce yaji ya gani har sai da ya amso ki hankalinsa ya kwanta. Anty Kudrat kuwa zan ta nanata miki sauƙin kanta ya wuce tunaninki, matar nan dabance, don ni ko yau aka ce an samu matsala to wallahi Beb ke zan fara ɗorawa ayar tambaya". Ni dai kallonta kawai na ke yi, cikin raina tunani kawai na ke yi akan sabuwar rayuwar auren da zan fara a karo na biyu, shin ya zama zai gudana tsakanina da Salim? A yanzu ni dai ba za'a kira ni mara ilimi da rashin wayewa ba, haka ba za'a kalli kayan da iyayena suka zube min a cikin gidan ba a goranta min da ɗiyar talakawa, fatana na samu ɗorewar farin ciki, sai dai a ko da yaushe ina hangen wani nakasu da na ke tare da shi, nakasun rashin haihuwa wanda shi ne maƙasudin lalacewar zaman aurena, ban sani ba, ban kuma san ta ya wa'annan ahalin za su karɓi lamarin ba, shin za su nuna min banbanci ne ɓaroro da matar gidan da ta riga ta ƙyanƙyashen ƙwai ba ɗaya ba ba biyu ba? Ko kuwa za su zama masu goranta min ne da hantarata kamar waɗancan?, duk ba wannan ba shi wanda ya ɗakko ni ya aje ya rayuwar tamu zata tafi da shi idan muka haura wasu shekaru ban samar masa da haihuwa ba, ko kuma zai mayar da ni bora ne soyayyarsa, mutuntawarsa da darajartawarsa na ga uwar ƴaƴansa? Ban san ya ubangiji ya tsara rayuwata ba, wataƙila ina ɗaya ne daga cikin bayinsa da ya jinkirtawa haihuwa ne, ko kuma ina daga cikin waɗanda bai rubuta suna da rabon samun haihuwar ba har su koma gare shi. Safiyya ta kalla agogo sai ta miƙe ta ɗauki mayafinta da jakarta tana ce min,"Sai ki yi ta aikin tunani da hawaye kin ji, ke da ba ki jin shawara, ni dai zan wuce sai da safe, wajen Anty Kudrat zan tafi, babu ke ba zan iya kwana cikin su Hajjo ba". Na gyaɗa mata kai kawai, ai dai tare zamu kwana da ita a cikin gidan na matuƙar jin daɗin hakan. Har ta nufa hanyan fita sai ta dawo ta sake zama kusa da ni tace,"In yazo yaga kina wannan kukan ba zai ji daɗi ba fa, zuciyansa zai so su duk ki saka shi a damuwa, dan Allah ki daina ki saki jikinki komai zai tafi dai dai da izinin Allah". Sai kuma ta dungure min kai tana faɗin,"Munafuka me kukan gulma, nan da anjima sai dai in jiyo na tashi, to earpiece zan saka ba zan kawo ɗauki ba". [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR15FT5* Cikin dare ciwo ya tasar min, tun ina dauriya ni ɗaya abu har yaci tura, gurnani na ke ina nishi ina wani irin miƙa, da kwance na ke kan benci haka har na faɗo ƙasa ban sani ba, malelekuwa kawai nake yi har ta kai ga na fara mawahalcin kakari kamar zan yi amai. Ɗan sanda da ke tsare da ni ya leƙo yana buga min tsawa tare da faɗin na ishe su na kiyaye na natsu. Ina kuka cikin ƙarfin hali na ce masa"Ka taimaka min da ruwa". Sai ya ƙara doka min tsawa yana cewa,"Ba za'a bayar ba". Kaina na jinginar da bango ina ta sauke numfashi wanda ma sai na matse hancina na buɗe baki kafin nan na samu na shaƙi iska. Juya kaina nayi ga bakin ƙofar, idanuna a rufe ina ta so na buɗe su amma sunƙi buɗuwa, murya na fita da ƙyar na ce,"Ka taimaka min don girman Allah, ina da ruwa a cikin nan ka yiwa darajan Allah ka hasko min fitila na duba". Ni ban sani ba ashe ya hasko ɗin, sai ji nayi yana masifa cikin ɗagawar murya yana cewa,"Ba za ki ɗauka ba ne na kashe fitila ta". A rikice na ce,"Yi haƙuri ban san ka kunna ba, idona bana gani don Allahu ku taimaka min". Na faɗa cikin ruɗewa ina lalube da hannu. Hasko fuskarta yay, ya tsaya na ƴan sakanni yana kallonta kafin yasa maƙulli ya buɗe ƙofar ya shigo. Naji shigowar tasa amma ban san ta ina yake ba, sai jinsa nayi yana cewa,"Me ya sami idon na ki?". Na dinƙa ɗaga murfin idona yaƙi buɗuwa sam, tsoro da tashin hankalin da na ke ciki suka ninku, take na fara tari babu ƙaƙƙautawa, sai ji nayi ina tofar da wani abu mara daɗin ɗanɗano a harshe. Naji ɗan sandan ya furta,"Subhanallah, ba ki da lafiya dama ba kiyi bayani ba tun ɗazu". Ba zan iya magana ba a halin da nake kam, ni dai taimako kawai na ke buƙata a lokacin, a bani maganin da zan sha zuciyata ta bar zafin da take yi, haka kuma a buɗe min idanuwana da suka kasa buɗuwa, sannan a bani in sha ruwa, fitarsa naji, take na shiga ambaton Allah ina kuka ina roƙonsa da ya buɗa min idanuwana, kafin na koma kiran sunan Abbaana. Can sama sama naji mutane akaina ana magana amma ban san me suke faɗa ba, kafin naji kuma an kinkime ni can nesa nesa naji ana batun asibiti. *Ƙarfe Bakwai na Safe.* Abbaa ya fito daga ɗakinsa yana kiran sunan Ummani, ta fito daga kitchen da sauri ta iso gabansa da leda baƙa a hannu. Miƙa masa tayi cikin sanyin yanayi tace,"Don Allah ko na sako mayafina na bika, ina so naje naga ya ta kwana". Abbaa yaja numfashi ya sauke, hannu yasa a aljihu ya ɗauko kuɗi. Tsohuwar ɗari biyu ce ya nuna mata yana cewa,"Ki yi haƙuri naje ni ɗaya, kinga ko ni ɗaya wannan ba zata kai ni ba balle har mu biyu, dole nima sai dai nayi rabi tafiyar ƙafa rabi ta mota". "To ko aikawa zan yi a taso Yashaik?". "A'a don Allah mu bar yaran nan su huta haka nan, tun da ni zanje ai ba sai kin damu ba. Kuma dama sun ce yau ɗin zasu bayar da ita in sha Allahu". "To ubangiji Allah yasa, Allah ya amince saboda sirrin la'ila ha'illallahu. ga shi nan ma na saka mata sauran awarar jiya da bamu ci ba naji bata yi yami ba. Don Allah kasa taci abincin kaga tana da ulcer". "In sha Allahu. Bari na wuce". "Tom aje lafiya a dawo lafiya, amma idan anyi cinikin lemo zaka ganni na taho". Kai kawai ya gyaɗa mata ya fita. Kana duban idonsa ka san ido biyu ya kwana, haka kana ganin yanayinsa kaga na me ƙarfin hali, dauriya kawai yake yi, dauriya saboda ƴarsa da iyalansa. Haka yake tafiya da ƙyar, bai jima a bakin titi ba ya samu me napep ɗin da ya ɗauke shi da taimako har ƙofar na'isa a naira ɗari. Zone 1 shine headquater ɗin dama da case ɗin yake, ko da yaje dakatar da shi aka yi daga waje aka ce ya jira zuwa ƙarfe goma, babu irin roƙon da bai yi musu ba akan su taimaka ko abinci ne su barsa ya bata amma suka ƙi sai karɓa suka yi, sai bayan ya shafe awa guda har da rabi sannan ɗan sandan da ya shiga kai mata abincin ya dawo yana faɗa masa ai ya manta ma anje da ita asibiti babu lafiya tun daren jiya. Ai jin wannan furuci Abbaa ya nemi yanke jiki ya faɗi, su kuma ƴan sandan babu tausayi bare imani don haka babu wanda yabi ta kansa, da taimakon ubangiji ya samu kansa, tunaninsa ɗaya me ya sami Sa'ida kuma wanne hali take ciki? duk yanda ya so su faɗa masa asibitin da aka kaita suka ƙi, har sai sha biyu na rana lokacin AIG ya shigo, sannan ne insifecta Usman wato Yayan Zahra'u ya kira shi ofishinsa. Lokacin su Ummani da Yayyun Sa'ida kaf sun zo har da Kaka, sai da aka jira zuwan su Nazifi sannan Insifecta yake shaida musu da cewa an tura case ɗin na su gaba zuwa Fagge Shari'a Court, kuma zasu fara zama a sati na gaba in Allah ya kaimu, saboda haka sai su nemi lauyan da zai tsaya musu. Nazifi yace babu matsala suna da lauya a hannu, su Abbaa dai basu iya cewa komai ba illa ma dukkaninsu tunanin ta in da zasu fara nema lauyan da kuɗaɗen da za'a fitar suke, ga babban tashin hankalinsu an ce basu da damar ganin Sa'ida, Ummani tun tana kuka da hawaye har ma ya daina zuba sai dai ka jita tana fizgar numfashi, Abbaa ma duk ƙarfin halinsa da dauriyarsa sai da ya karaya, Ƴaƴansu ne kawai masu ƙarfin gwiwa da suke tausar su. Malam mahaifin Nazifi zai yi maganar cewa ko za'a iya basu lauyan da zai tsayawa Sa'idan, zuwan Safiyya ya katse maganar tasa wadda ta zo ita da Antynta da kuma lauya, wacca ta gabatar da kanta wa Insifecta. Ta kuma karɓi bayanai da date ɗin fara zama, daga nan ta buƙaci a kaita wurin Sa'ida nan aka shaida mata cewa tana asibiti, haka aka haɗata da ɗan sanda wanda suka tafi da shi can asibitin. *23-Nove-2023, Fagge Shari'a Court, Muhammad Murtala Way, 10:30am.* Kotun bata cika sosai ba iya ƴan uwa ne na jiki wanda suka san da case ɗin sai baƙin fuska ƙalilan wanda sha'awar sauraron shari'a ya saka suka zauna. Bayan shigowar Alƙali rajistara ya tashi tsaye yace,"A yau juma'a sha bakwai ga watan nuwanban shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, wanda yayi daidai da uku ga watan jumada auwal shekara ta dubu ɗaya da ɗari huɗu da arba'in da biyar A.H. zamu saurari ƙarar Zahra'u Abdullahi wacce take ƙarar kishiyarta akan kashe mata yarinyarta da tayi har lahira". Ya faɗa yana tattara file ɗin ya miƙawa Alƙali ya karɓa yana dubawa. Shiru kotun tayi na wani lokaci kafin Alƙali ya kalle su yace,"In lauyoyi masu kariya suna kusa su gabatar da kansu." Wani dogon namiji baƙi mara tsaho sosai ya miƙe ya ce,"Ya mai girma mai shari'a sunana Barr Mu'azzam Ibrahim ni ne Lauyan mai ƙara". Ya faɗa yana zama. Wata Mace doguwa mara jiki ta miƙe itama tace,"Sunana Barr Zaliha Muhammad, ni ce lauyan wacce ake ƙara". Ta faɗa tana zama itama. Alƙali ya fara rubutu a kan file na wani lokaci kafin ya ɗago yana kallon su. "Lauyan wanda yake ƙara ko yana da abin faɗa?". Alƙali ya faɗa yana kallon su. Miƙewa yayi yace,"Ya mai girma mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai alfarma da ta bani dama domin yiwa wacce ake zargi tambayoyi". "Kotu ta baka dama". "Na gode ya Mai Shari'a". Ya faɗa yana fitowa ya ƙarasa inda Sa'ida take tsaye yana kallonta. "Malama Sa'ida ko za ki iya yiwa kotu bayanin yarinyar da aka rasa wacece a wajan ki?". Sa'ida ta haɗiye yawu ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce,"Ƴar mijina ce". Ya kalleta da kyau ya ce,"Ƴar kishiyarki ce kenan ko?". Sa'ida ta ɗaga kai alamun eh. ya girgiza kai ya ce,"Ke ina naki ƴaƴan?". Tambayar tashi ta motsa zuciyata, na ɗago ido ina kallonsa kafin na ce,"Bani da su". Ya girgiza kai sannan yace,"Kenan dan ba ki da su shiyasa kika kashe ƴar kishiyar ki?". Da mugun faɗuwar gaba na sake kallonsa jin yana neman ƙara ɗaure ni. "Ina da ja Ya mai girma mai shari'a!" Barr Zulaiha ta faɗa tana miƙewa tace,"Bai kamata lauyan mai ƙara ya fara yiwa wacce ake zargi tambaya akan abin da ya shafi rayuwar ta ba. Rashin yara abu ne da ya shafi rayuwarta bai shafi case ɗin da muke magana a nan ba". Mai shari'a yace,"Barr Mu'azzam a kiyaye". Yace,"Na gode ya mai shari'a". Ya kalle ni yaci gaba da cewa,"Ƴar mijinki ƴarki ce Malama Sa'ida amma meyasa kika kashe ta?". Na kalle shi nace,"Wallahi bani na kashe ta ba". "To waye kasheta?". Na share hawayen idanuna na ce,"Kawai ta rasu ne amma bani na kashe ta ba". "Me ye silar rasuwar tata shi za ki faɗa". A hankali nace,"ban sani ba nima". Ya sake kallona yace,"Kenan da gaske ne ke kika kashe ta?". "Wai sau nawa zan maimaita ban kashe ta ba?". "Ki daina ɗaga mana murya". "To ya ku ke so nayi, iyaka gaskiyata na ke ta faɗa muku amma kun ƙi yarda". Na faɗa ina jin tamkar zan shiɗe. Barr Mu'azzam ya kalli mai shari'a yace,"Ya mai shari'a, ina roƙon wannan kotu mai adalci da tayi duba akan bayanan Sa'ida sannan tayi duba akan itace ƙarshen ɗaukar yarinyar da ta mutu, yarinyar da lokacin tana hannun mahaifiyarta lafiya lau take, amma da Sa'ida ta ɗauketa sai ta mutu alhalin bata ɗaukar yaran, To babu wuta me ya kawo hayaƙi? Saboda haka Ya mai girma mai shari'a ina so a duba halayen mata akan kishi, tabbas Sa'ida zata iya kashe yarinyar kishiyarta ko don ganin cewa ita bata da su. Don haka na ke roƙon kotu ta hukunta Sa'ida akan laifin kisan da ta aikata kamar yanda mahaifin yarinyar da mahaifiyarta ke roƙon a ƙwatar musu hakkinsu. Na gode ya mai shari'a". Ya faɗa yana dawowa ya zauna. "Ko lauyan wacce ake ƙara tana da abin faɗa?". Cewar Alƙali. Ta miƙe tsaye tace,"Ina da shi ya mai shari'a. Ina roƙon wannan kotu da ta bani dama na kira Zahra'u Abdullahi mahaifiyar ita yarintar da aka rasa". Wani a cikin kotun ya miƙe yace,"Malama Zahra'u Abdullahi in kina kusa ki fito". Tasowa tayi with confidence. Barr Zaliha ta matso kusa da ita tace,"Malama Zahra'u ya ƙarin haƙuri?". "Haƙuri da godiya, Na gode". Barr ta numfasa sannan tace,"Malama Zahra'u ko za ki faɗa mana hujjarki da zata tabbatar mana da Sa'ida ce ta kashe miki yarinya?". Ta gyara tsayuwarta tana kallona, wanda ƙwayar idanuwanta ke nuna tsantsar tsanata a ciki tace,"Saboda itace ƙarshen ɗaukarta kuma goye a bayanta ta rasu". Barr ta girgiza kai tana murmushi tace,"Wannan ita ce kawai hujjar ki?". Ta ɗaga kai bayan ɗauke idonta akaina tace,"Zata iya kasheta saboda tana baƙin ciki ita bata haihu ba, shiyasa da ta goyata tayi mata wani abun har ta mutu". "Kafin wannan lokacin Sa'ida ta taɓa yunƙurin kashe yarinyar?". Ta girgiza kai tace,"Bata taɓa ba". Barr ta jijjiga kai,"Ok amma ta taɓa ƙoƙarin shaƙeta ko bata wani abun da zai iya zama silar barinta duniya?". "A'a bata taɓa ba". "Kenan akwai kyawun alaƙa ta nuna kulawarta akan yarinyar kafin ta rasu?". Wannan tambayar da Barr tayi mata sai na saddaƙar, domin dai na san daga ita har Nazifi da Iyam babu wanda zai amsa wannan tambayar da gaskiya. Sai dai kuma mamaki ya kamani da amsar da ta bayar wanda na ke da tabbacin ubangiji ne ya matsi bakinta ta faɗi hakan. "Ehh to gaskiya tana son yaran, farkon haihuwarsu tana nuna kulawarta akan su, hasalima ni na shiga tsakani na nuna mata bana so tana raɓar min yara, na hanata ɗaukarsu kwatakwata, to da yake tana da sanyin hali da haƙuri sai kawai ta janye jikinta da su saboda a zauna lafiya". Barr tayi murmushi tace,"To amma kuma duk wannan kyakykyawar shaidar da ta samu daga bakinki me yasa kuke zargin ita ta kashe miki ƴa?". Ta kalli Barr tace,"Saboa itace ƙarshen ɗaukarta, kuma a bayanta ta mutu". "A bayanta ta mutu? Kenan kin ganta da idon ki lokacin da ta kasheta?". Ta girgiza kai alamun a'a. Barr tace,"Magana za kiyi". Ta ce,"Ban ganta ba". Ta faɗi hakan jiki a sanyaye. Barr ta juya ta kalli Alƙali tace,"Ya Mai girma mai shari'a ina so ayi duba a bayanan mai ƙara, ayi Nazari za'a tabbatar da babu hujjar da zata gamsar da kotu cewa Sa'ida ita ta kashe yarinyar, ko don duba da yadda ita uwar yarinyar ta faɗa na cewa Sa'ida mutuniyar kirki ce. Idan mai shari'a ya bani dama zan gabatar da insifecta Usman Abdullahi wanda shine ɗan sandan da ya isa da gaggawa gidan a lokacin da abun ya faru". "Kotu ta ba ki dama". Kamar ɗazu wani ya tashi ya buƙaci shigowar Insifecta Usman. Shima bayan ya zo Barr ta kalle shi ta ce,"Insifecta lokacin da kuka isa gidan Alhaji Nazifi Mai Kalwa, wanne makami ku ka samu da Sa'ida tayi amfani da shi ta hanyar kashe ƴar kishiyarta?". "Babu". "Kace Babu? Kenan da me ta kasheta?". Numfashi ya sauke yace,"To a iyaka duk binciken da muka yi gaskiya babu wani shaida da ke nuni da cewa kashe yarinyar aka yi, don ko hoton sawun hannaye duk mun ɗauka na inda ita Sa'ida ta tattaɓa, kuma binciken likitoci ma babu rahoton nuna cewa kashe yarinyar aka yi". "Ok kenan har likita ma yay nasa bincike akan rasuwar?". "Ehh ƙwarai kuwa, likitoci har uku ma". "Da kyau, kun zo da rahoton?". "Ehh mun zo da shi". "Ko zaka iya bamu?". File ɗin da ke hannunsa ya bata, ta karɓa tana faɗin,"Na gode, kana iya komawa". Daga haka ta miƙa file ɗin wurin Alƙali. Alƙali yay rubuce rubucesa, sannan Barr Zaliha ta ce da shi,"Idan mai shari'a ya bani dama ina so na gayyato likitan da ya duba yarinyar domin yayi mana bayani yadda zamu fahimta". Alƙali ya sake yin rubutu yace,"An ba ki dama". Aka nemi ganin likita ya ƙaraso ya tsaya, ta ƙarasa kusa da shi tace,"Dr ko zaka iya faɗa mana sunan ka?". "Sunana Dr Bashir Adam ƙwararre a fannin likitan ƙananun yara." Ta jijjiga kai tace,"Me ya kawo ka zaman wannan kotun?". "Domin bayar da rahoto akan binciken lafiyar wacce ta rasu". "Wa ya buƙaci da kayi binciken?". "Insifecta Usman". "To ko zaka iya mana bayanin rahoton rasuwar Salma Nazifi Mai Kalwa wato Noor, jaririya me kimanin kwana talatin da ƴan kai, wacce ka tabbatar da hukumar ƴan sanda sun baka damar yin bincike akanta?". "Ehh zan iya domin da kaina na dubata lokacin da Insifecta Usman ya buƙaci na tabbatar musu da ta rasu ko tana raye". Barr tace,"A yayin da kake dubata akwai shatin shaƙa ko guba a jininta wanda zai tabbatar mana da kasheta akayi?". Likita ya girgiza kai yace,"Babu ko ɗaya a ciki, domin kuwa ta silar ciwo ta rasu ba silar guba ko shaƙa ba". Barr Zaliha tace,"Ciwo dai?". "Ƙwarai ciwo". "To wanne irin ciwo kenan, ko zaka iya yi mana bayaninsa da kuma adadin kwanakin da ya ɗauka a jikinta". "Jaundice shi ne ciwon da ke tare da yarinyar, wanda kuma ya kai kimanin kwana talatin da biyar a jikinta, shaidar cewa da shi aka haifeta, kuma symptom ɗinsa a bayyana yake ba'a ɓoye ba, za'a samu fatar jariri tayi yelo da idanuwansa, yelo sosai, to shi wannan ciwo dama idan ya zama chronic har yay yawa ya hau ka shi ne yake leading to death, so yawanci iyaye idan suka haifi yaro a haka tunaninsu ba ya basu ga cewar ya kamata suga likita, sai su tafi akan an haifi yaro da rana ko shawara, in da kuma sai su tsaya a iya maganin gida, wasu iyayenma suna ganin hakan amma sai suyi ignoring su zuba ido har azo a rasa jariri". Barr tace,"Wato Dr idan na fahimceka wannan ciwon da kayi mana bayani shi ne silar barinta duniya ba dalilin hannu ko wani abu da aka bata ba?". Ya jijjiga kai cikin tabbatarwa yace,"Ƙwarai da gaske shi ne silar rasuwarta, bayan shi gaskiya babu wani abu". Tayi murmushi tace,"Na gode likita, zaka iya komawa ka zauna". Ya juya ya koma itama kuma ta kalli alƙali tace,"Ya mai shari'a ina so ayi duba ga bayanan Likita da bayanai akan ciwon da ya kashe yarinyar a tabbatarwa da jama'a Sa'ida ba ita ta kashe yarinyar ba, Allah ya nuna a bayanta zata rasu ne amma bawai dan ta kashe ta ba. Haka ma idan aka ƙara duba bayanan mahaifiyar yarinya, Da wannan na ke so kotu tayi watsi da wannan ƙara domin babu komai a cikinta sai zallar ƙazafi da son cutar da Sa'ida, sannan ina nemawa Sa'ida hakkinta akan sharrin da akayi mata. Na gode". Ta faɗa tana komawa ta zauna. Alƙali yayi rubutu kafin yace,"Shin lauyan da yake ƙara ko yana da abin fad'a?". Barr Mu'azzam ya tashi yace,"Babu ya mai shari'a". Mai shari'a yayi rubutu na wani lokaci, kotun tayi shiru ana jiran hukunci kafin ya ɗago yace,"Duba da rashin hujja gamsashshiya da ba'a samu daga ɓangaren masu ƙara ba, da kuma bayanai da hukumar ƴan sanda ta bayar, da rahoton likita da ya bayar zai tabbatar mana da abin da ake zargin Sa'ida da shi bata aikata ba". Ya sake yin shiru yana rubutu kafin ya sake cewa,"Wannan Kotu mai adalci ta wanke Sa'ida Salman Madobi daga zarginta da ake yi akan laifin kisa, bata da hannu kuma bata aikata ba, duk wasu bayanai da hujjoji sun tabbatar da hakan. Sannan kotu zata ci tarar Zahra'u Abdullahi da Nazifi Bala Mai Kalwa akan ɓatawa wadda suke ƙara lokaci, da wahalarwa, da kuma ɓata mata suna da tayi, ta ɓatawa shari'a lokaci, bisa hakan kotu taci tararsu naira miliyan ɗaya da rabi. Sannan Kotu na gargaɗin Nazifi Bala Mai Kalwa da Zahra'u Abdullahi akan ko dan gaba yana da kyau su san gaban alƙali ba wajan wasan yara bane, su samu hujja mai ƙarfi kafin su shigar da ƙara in ba haka ba nan gaba kotu zata hukunta su". Da haka alƙali ya buga teburi ko ya tashi da faɗin koootuuu. Ahalina da dukkan magoya bayana muryoyinsu da ke fitar da kalmar Alhamdulillah ita ta karaɗe cikin kotun gaba ɗaya. Ta ɓangarena kuwa zan iya cewa babu wani abu da naji a tattare da ni na farin ciki ko na murna, haka babu akasinsa domin kuwa cikin kwanakin nan da nayi a cel jina na ke tamkar wadda babu zuciya a ƙirjinta. Safiyya ta zo da saurinta ta rungume ni tana kukan farin ciki, Ummani ma haka, ina kallon yanda mahaifina ke share ƙwalla wadda na san bata komai ba ce illa tsananin farin ciki da murna. Yaya Imam da Yashaik na can gefe suna tattaunawa da wani insifecta. A wannan lokacin ƙyam na ke a tsaye, ƙwayar idona ta gama wurgawa kan kowa da komai, kafin a hankali ta shiga haska min hoton fuskar Nazifi. Na sani babu kalma mafi ɗaci da ciwo gami da firgici a rayuwar kowacce ɗiya mace irin kalmar ZAWARCI, to amma a yau nafi buƙata da kwaɗaituwar nayi zaman Zawarci fiye da zaman gidan miji. a yau na tsani kalmar miji, bana son auren, na kuma sha alwashin ni da aure har mutuwa, tabbas a yau ba sai gobe ko jibi ba sai in Nazifi ba ya raye amma sai ya sake ni, sai ya sakeni ko ta wanne hali. [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR16FT5* Farantin hannuna ya suɓuce ya sauka akan tiles ya bada sautin rikitacciyar ƙara, ƙarar da taja jaririyar da ke kwance razana ta farka daga baccin da take, nan kuwa ta tsanyara uban kuka wanda lokaci ɗaya gidan ya ɗauka da sautin kukanta, kan kace me wannan uwarta ta sakko daga sama, ta bangaje ni daga ƙofar ɗakin Iyam ta faɗa ciki tana ɗora hannu aka da faɗin ta shiga uku. "Ni Jummai me ya faru da yarinyar nan take tsala uban kuka haka?". Cikin kuka tana dudduba jikin yarinyar take cewa,"ban san me tayi mata ba Iyam, shikenan ta ƙara kashe min yarinya, na rantse da Allah a wannan karan ba zan yarda ba". Ai kan ƙiftawar ido sai tsintar Iyam nayi a gabana, tasa hannu ta ɗauke fuskata da mari tana zazzaga ruwan bala'i. "Wanne irin rashin imani ne danƙare a zuciyarki?, Mayya ɗiyar mayu kin dawo ki kashe kowa kenan, ke ninfa ko da haihuwa kika yi ba ƙaunarki zan yi ba, kuma ko rubuce yake sai na saka Shalele ya rabu da take". Kamar kar in tanka sai kuma na sauƙaƙa zuciyata, ko ba komai bayani na da daɗi duk da ba amfani zai yi ba, kuma ni rigima da tashin hankali ne ban so, Idona akan uwar da ƴarta na ce,"wallahi tallahi Iyam babu abin da na mata, kawai fa na ajiye miki abinciki ne na zo fita tsautsayi farantin ya suɓuce a hannuna, to ƙarar ita ta firgitata". Rufe bakina ba wuya Iyam ta ɗau waya ta kira uban yarinyar, da kwakwazo take faɗa masa ai na zo na ƙarasa kashe masa yarinya yay gaggawar zuwa wannan karan kotun ƙoli ce zata raba mu. gabana ya faɗi jin ƙaryayyakin da take gilla masa, ga jaririyar kamar haɗin baki sai ƙara tsanyara kuka take yi kace ɗaukarta nayi na buga da ƙasa, ba'a ɗebi wasu mintuna masu yawa ba sai ga shi ya dawo, lokacin ina tsaye a parlo na kasa zama saboda fargabar abin da zai faru. Ganinsa a furgice ba ƙaramin razana ni yay ba, kallona ya tsaya yi a fusace sai ga Uwar ta sakko tana jijjiga ƴar itama sai kuka take yi, ya tafi da sauri ya karɓi yarinyar yana duddubata, ita kuma uwar faɗa masa take yi wai asibiti zata kaita saboda kunnenta ya toshe, kuma bata san me aka tusa mata a baki ba dai maƙogoronta ya cushe ko nono ta kasa sha. Ni dai tsabagen mamakin sharrin daskarewa nayi a tsaye, to wai uban me ma ya dawo da ni gidan?, aikuwa ban yi aune ba naji saukar duka a jikina ta ko'ina, Nazifi ne ya shiga ɗaki ya zaro belt ya ke dukana kamar an aiko shi, garin in ƙwaci kaina in guje masa goshina ya bugu ajikin ƙarfen matakalar bene, tsananin azaba yasa na kurma uban ihu ina kiran sunan Allah. jini ya fara malala, ya koma saka ƙafa yana tattakeni yana faɗin sai ya kashe ni akan lahanta masa yarinya da nayi. ba Nazifi ya ƙyaleni ba sai da ya haɗa min jini da majina, fuskata duk ta kumbura idona ɗaya har bana ganin komai da shi. "Wannan dukan ba komai na yi miki ba, ki jira yi dawowata, ba aai burinki raba ni da farin ciki ba, to Sa'ida daga ranar yau na dinƙa dukanki kenan a cikin gidan nan har mutuwarki, sakin ki ba zan yi ba, ba zan taɓa sakin ki ba, yanda kika ƙuntata min kika kashe min yarinya wallahi nima sai na kashe ki da irin salon wuyar da zan dinga gana miki a cikin gidan nan daga ranar yau, za ki ƙwammaci ba ki taɓa sanina ba a rayuwarki". "Wayyooooo". Na kurma wata gigitacciyar ƙara ina saurin miƙewa daga kan katifar da na ke kwance. Ƙirjina bugawa yake yana dukan uku uku, zufa kuwa tuni ta wanke min jiki, jiki na rawa nayi ƙofa ina girgiza kaina. Sai ga Ummani da saurinta tana tambayata,"Ke lafiyarki". Numfashi kawai na ke saukewa kamar wadda ta sheƙa mugun gudu, na faɗa jikinta ina faɗin,"Ba zan koma ba Ummani, don Allah ku ƙyale ni ba zan koma ba, wallahi na koma kashe ni za su yi". Bayana take shafawa tana faɗin,"Ke me kike faɗi ne haka? Ko mafarki kika yi ne?". Shiru nayi ina haɗiye yawu a busashshen maƙogorona, a hankali na ke sauke ajiyar zuciya, na janye a jikinta sannan na bi ɗakina da kallo, kafin na ɗaga labule ina kallon tsakar gidanmu. Sai kuma na fara tunanin ashe fa daga kotu gida muka yo ba gidan Nazifi na koma ba, na hasko lokacin da muka fito daga cikin kotun Kaka yake maganar to ya za'ai da ni, Abbaa yay saurin cewa da shi ai gida zamu wuce da ita. Kuma muna dawowa gidan Ummani ta ɗora min ruwan zafi nayi wanka, ta bani abinci da kanta na ci na ƙoshi, ta mulke min jikina da maganin ciwon jiki, Abbaa ya fita chemist ya siyo maganin ciwon jiki ya ɓallo ya bani na sha, da kansa yace na shiga ɗaki na kwanta nayi bacci sosai, a lokacin kallonsu kawai na ke tayi a raina ina ayyana ko me ke zuciyoyinsu? Shin abin da ke raina shi yake ransu na game da zaman gidan Nazifi? Ko kuwa akasin hakan ne? Sai da Ummani ta zungureni ta kama min faɗan bata son ina nisan tunani irin haka, kafin nan na miƙe na shigo ɗaki na kwanta, ina kwanciyar sai bacci, baccin da ya haddasa min mummunan mafarkin ina maimaita rayuwa a cikin gidan Nazifi. Numfashi na ja na sauke na ce da Ummani,"Mafarki nayi ne". "To mafarki da zaka yi adu'a sai ka ƙwala ihu haka, kin ji yanda ƙararki ta bani tsoro kuwa. Kai haba Sa'ida ban san ki da haka ba, To me kika gani a mafarkin?". Ido na ɗaga ina kallonta sai nayi ƙasa da kaina ban ce komai ba. "Ko ganinki kika yi a can bursun ɗin? To ya kamata ki cire tunanin hakan a ranki, Allah ba zai kuma kawo miki ƙaddarar hakan ba, ki yi ƙoƙarin mantawa ma gaba ɗaya tun da dai har Allah ya fidda ke, Ko kuwa me kika gani dama?". Na girgiza kai ban ce komai ba. "A'a fa baki za ki buɗe ki min bayani". "Ummani a gidan Nazifi na ganni, wai na koma can". "A'a to kuma shi ne sai aka yi me? Mene da can ɗin?". Ba shiri na ware idanuna akanta ina cewa,"Ummani sai na soma komawa to?". "Banda ta cewa sai abin da Kakanki da Abbaanku suka yanke. Amma dai ki zama cikin shiri kin san duk dare suna iya cewa ki tafi. Mafarki kuma daga yau kar ki ƙara ihu irin haka adu'oi ne iri daban daban akanki kin san su, irin haka ba sai ki janyowa kanki matsala ba idan ma wani sharrin ake nufarki da shi ya sameki". Tana gama faɗin hakan ta fita ta barni. Ai a wurin na silale na zauna ina hawaye, wai komin dare zan koma gidan Nazifi? Ba ni na miƙe ba sai da aka yi kiran magriba tukunna naji muryan Ummani na faɗin,"Ki fito kiyi alwala ga ruwan ɗumi nan na zuba miki kar ya huce". Tashi nayi cikin mutuwar jiki na fita, ina alwala ina lissafi, matsawar aka ce na koma gidan Nazifi to wallahi sai dai ko na tsaya a titi mota ta bige ni, ko kuma nayi tafiyata ƙauye, ai ni da Nazifi kuma har abada, mun gama zama da shi haka kuma na gama ganinsa, ko a lahira bana fatan ƙara ganin ko da inuwarsa, a yanzu haka na san ba zai taɓa waiwayata da sunan cewa na koma gidansa ba, to nima haka ba zai taɓa jin motsina ba, idan naga take taken su Abbaa na in koma ne to zan nemi wani wajan, shi kuma duk sanda ya gaji ya aiko min takarda ta. Muna zaune ne tsakar gida muna cin abinci Abbaa ya dawo, muka yi masa sannu da zuwa ya zauna. Walida ta taho da gudunta ta faɗa jikinsa tana faɗin,"Abbaa sannu da dawowa, an dawo lafiya?". "Na dawo lafiya lau ƴar albarka, me kika ci haka duk kika ɓata bakin ki?". Kunnensa ta kama ta raɗa masa magana, Sai kuma ta ɗora yatsa a leɓenta tana cewa,"Amma fa kar kayi magana ta ji". Dariya nayi Abbaa ma yay dariya. Ummani ta fito daga kitchen tana cewa,"Babanki zai shigo gidan ne ai biyana kayana zai yi. Yarinyar nema kike ki ɓalla min jari ta ƙarfi da yaji". "To ai Abbaa yace shi ya ba ki jarin". Ta faɗa tana ƙara maƙalewa jikin Abbaa. Shi kuma yana tayata Ummani dai na mita akan shanye mata alawar yaran da take siyarwa, ta sauya wajen ajiya yafi sau nawa amma sai Walida ta bi ta ɗauko. Bayan gama cin abincin Abbaa ya dube ni yace,"Ke ya jikin na ki?". Fitar amon muryarsa kamar na me fushi da ni hakan yasa na ɗaga ido na ɗan dube shi kafin na ce,"Da sauƙi Abbaa". "Babu wani waje da kike jin ciwo?". "Ehh Abbaa". Na faɗa kawai amma ba wai don hakan ba ne, a zahiri cikin ƙashina ciwo na ke ji sosai. Muna nan dai zaune ita jiran naji Abbaa yay min maganar Nazifi ko maganar tafiya amma naji shiru bai yi ba. sai na ɗan fara jin tsoro don ban san ko yana so ya gwada hankalin yakamata na ba ne. Ummani ma da muke tare muna magana jefi jefi saboda shirin da take ji a radiyo itama ban ji tayi min wani zance ba. Da Kaka ya kira ni kuwa ba ƙaramin kaɗawa ƴaƴan hanjina suka yi ba, na yi hanzarin miƙewa ƙafafu a sanyaye nayi ɗakinsa, ya gama cin abinci lokacin na raɓe daga can gefe ina ce masa gani. "Ya jikin ki ɗin". Ya tambaya ba tare da ya dubi in da na ke ba. "Da sauƙi". Na faɗa a hankali. "Allah ya sauƙe, an siyo miki magungunan?". "Ehh Abaa ya kawo min tun da rana". "To shikenan tashi kije. Ko akwai wata matsala?". "A'a babu Kaka". "To Allah yay albarka". "Amin Kaka sai da safe, Allah ya ƙara lafiya". Na faɗa ina tashi na fita. Da Abbaa ya dawo ya shigo ɗakin Ummani, ina kwance kan gadonta na miƙe ina masa sannu da dawowa, ya amsa yana cewa,"Ungo maganin sauro, ko an samu net ɗin?". "Ehh an samu amma ya ɓuɓɓule Anty Khairi tace zata aiko a kawo wani to ban sani ba ko sai zuwa anjima idan Yaya Imam zai shigo". "Imam ai ba zai zo ba ƙarfe tara yanzu, saka maganin dai ɗayan ai zai isa har gari ya waye ko?". "Ehh Abba, an gode". Na karɓa ina miƙewa na fita na basu wuri duk da Ummanin sallah take. Ɗakina nayi na kaɗo sauro waje, na manta ma ɗazu da suka kawo wuta na bawa Hindatu wayata ta saka min caji, ko da yake ban gama dawowa hayyacina ba balle hankalin ya kai ga wata waya, sai yanzu da daren yay kuma na ke tunanin haske ga basa kawo wuta cikin dare. Ummani ce ta miƙo min ashana da ƴar ƙaramar toci, muka yi sallamar sai da safe kafin nan na rufe ƙofa na kwanta. Washe gari da safe duk yanda na so na taya Ummani aiki ta hana ni, sai ce tayi tun da naci abinci na dai yi wanka na kwanta ba cikakkar lafiya garen ba. Sai bayan ta gama aikinta tas sannan ta zo ta zauna, ina ta jera mata sannu ina cewa ban ji daɗi da bata barni nayi aikin ba. Abbayo yana zaune a ɗakin yake maimaitawa Ummani irin wulaƙancin da suke sha idan suka je ganina a bursun, iya ƴan kwanaki bakwan da nayi a ciki wulaƙancin da suka sha yafi miliyan, yace sau tari sai sun taho sai yaga Abbaa yana share ƙwalla. Ni dai duk abinda yake faɗa ina jinsu, wani na yi yaƙe wani kuma na buɗe haƙora kamar mai yin dariya amma a zahiri ban san ina yi ba, kawai dai na san ko da yafiyata ce kawai zata ragewa Nazifi ya shiga aljanna bana jin zan yafe masa, a silarsa naga hawayen mahaifina, a silarsa naga hawayen mahaifiyata, a silarsa ya hana kowa nawa kwanciyat hankali. Kaɗan kaɗan na ke jin ciwo haka, sai na ɗora hannu a kan ƙirjina saboda yadda naji kamar zuciyata zata faɗo ƙasa. Ummani ta lura da ni tayi saurin tasowa tana cewa da Abbayo,"Buɗe sif ɗin can ka miƙo magungunta, da yake ba sanin ciwon kanta tayi ba bata sha ba ni kuma ina ta zuci zucin nayi mata magana". "Ta ma ci abinci ne?". "Eii taci, ai sai da Abbaanku ya sata gaba ta sha shayin da aka kawo daga gidan Yashaik tukunna ya fita, ka santa da gardamar cin abinci". Sai bayan ya miƙo mata maganin tukunna ta dubi fuskar Sa'ida taga idanunta a rufe. "Au bacci kika yi saboda kar ki sha maganin, to tashi". Kaka da ke isowa ƙofar ɗakin ya ɗaga labule, yake tambayar Ummani jikin Sa'idan yaga bata leƙa wajensa ba, tace,"Da sauƙi jikin nata yanzu ne ma naga tana ɗan dafe ƙirjin, maganin zata sha kuma sai bacci ya ɗauketa". "Barta tayi baccin ko ya ya ne zata ji sauƙi a jikinta tunda ta jima bata samu yin ba, idan ta tashi sai ta sha amma ta bar wasa da shansa akan lokaci ai taji bayanin likitan ko". "Eiii ai ko da muka dawo ma sai da na ƙara gaya mata". "To Allah ya sawwaƙe, Kai zo ka saka min kujera a ƙofar gida". Har dai na kwana biyar a gida babu wanda yay min zancen tafiya, ni yanda ma suke nuna min kamar ko na dawo gidan ne, zancen ma bana jin suna yi ko kaɗan, sau tari idan naji kiran Abbaa ko Kaka sai na tsammaci zancen zasu yi min sai kuma naji lafiyata ce dai za'a tambaye ni sai kuma ace ban da wata matsala? Aikin gida kuwa ƙememe Ummani bata barina nayi sai tace ina buƙatar na huta, ai kuwa ina hutawar don bacci na ke sha abuna a hakan ma don ban samu tabbacin yanda na ke so ba. Yau ina zaune ɗaki mun gama waya da Safiyya, wacca itama ke tambaya ta ko su Abbaa sun min maganar komawa na ke bata labarin komai, mun jima muna hira kafin muyi sallama wanda na ke mata godiya akan taimakonta gare ni, har ta haɗa ni da Baba ma a waya. Bayan gama wayarmu na ɗakko reza ina yanke farce ina bin suratul Yusuf da na kunna. Muftahu ne ɗan wajen Baba Tijjani ya leƙo ɗakin nawa yana ce min naje Abbaanmu na kirana. Da hanzari na aje rezar na saka hijabina. suna zaune shi da Ummani na shiga, zama nayi daga gefe kaina a ƙasa, gabana sai faɗuwa yake saboda sanin cewa kiran muhimmi ne daga yanayin yanda na samesu. sai dai tsorona da fargabata bai wuce ayi min zancen Nazifi ba da komawa gidansa. Bayan Abbaa ya numfasa ne yace da ni,"Kun yi waya da mijinki?". "A'a Abba". "Bai neme ki ba tun ranar?". Na ɗaga kai,"Ehh Abbaa". Sai ya kalli Ummani yace da ita,"Akwai wanda ya zo cikin yaran nan?". "Anya kuwa, na dai ji kamar maganar Yashaik da safe a ɗakin Al'amin". Sai Abbaa ya sake dubana yace,"Me yasa ba ki taɓa karanta min irin zaman da ku ke yi ke da mijinki ba?". Nayi shiru na kasa cewa komai har sai da ya ƙara min magana kana na ce,"Abbaa ban san ta in da zan fara bayani ba ne, sai kawai na bar komai a matsayin me wucewa. Ban taɓa tsammani zata kaimu ga lamarin da ya faru ba". Na faɗa ina jin tahowar kukan da na kwan biyu ban yi ba. "To za ki koma gidan nasa?". Da sauri na kaɗa kai ina cewa,"A'a Abba ba na so na koma". "To ai koma kin ce za ki koma ba komawar za ki ba, don ranar da mahaifiyarki ta faɗa min dukka halin da kike ciki na yanke hukuncin cewar zamanki da shi ya ƙare. ni duk ban san haka al'amarin yake ba, tunanina irin ƴan matsaltsalu ne dai na gidan aure da aka saba fuskanta shiyasa ko da yaushe na ke cewa kiyi haƙuri, ashe abun yay ƙamarin da muka shiga hakkinki tunda bamu taɓa ba ki damar yi mana bayani ba, kuma da sai ki rubuto min ko a takarda ne tun inda baki ne katse ki na ke yi, amma kiyi haƙuri". Wayarsa ya ɗauko a aljihu, yana ƙoƙarin kiran Yashaik sai ga shi ya shigo, ya gaida su nima na gaida shi tukunna ya nemi waje ya zauna. Zamansa ba wuya Yaya Imam ma ya shigo, shima bacin sun gaisa ya zauna yana tambayata ya sauƙin jikina na ce masa naji sauƙi. Abbaa ya dubi Yashaik ya ce,"Ina ka nufa yanzu?". "Ehh to daga nan dai zan je makarantar su Yasmin zan biya kuɗin makarantarta". "Kai fa Imam?". "Ba ni da wajen zuwa Abbaa". Ya faɗa wanda na san ba hakan ba ne, haka yake a ko da yaushe idan iyayensa suka tambaye shi me zai yi ko ina zai je sai yace babu saboda biyan tasu buƙatar. "Yauwa to kasa kunne da kyau ka jini. Ka kira Nazifi kace masa ya aiko da takardar sakin Sa'ida, ya aiko da takardar sakin Sa'ida a yau ba sai wani lokaci ba, kar ya aiko min da takarda me ɗauke da saki ɗaya ko biyu, saki uku na ke so ya aiko min da shi, ka faɗa masa ya gama zama da ita har abada". Yaya Imam ya ɗauki wayarsa yana cewa,"Yanzu kuwa Abbaa, ai don kar nayi gaban kaina ne dama amma tun ranar da kotu ta sallame mu na so ya rubuta takarda a lokacin ya bayar, to da naji kayi shiru yasa na dakata don ban san me ka shirya ba". Ni na karanto masa lambar wayar, ashe shi tuni ma ya goge lambobinsa, kiran farko ya katse na biyu da na uku ma haka duk ba'a ɗaga ba, sai da ya ƙara na biyar ɗin kana aka ɗaga, muryarsa daga can a daƙile yay sallama, Yaya Imam ya amsa masa da cewa,"Saboda amsata wajibi ne ban da haka baka isa na amsa maka ba, nama yi mamaki da har ka san ya kamatan sallama, ai ce na ke ka manta da addinin gaba ɗaya. Anyway ka kore watsatstsen tunanin da ke ranka akan kirana, ba kiran da aka saba yi da ba ne, lafiya shiru har wannan lokacin baka aiko da takardar sakin Sa'ida ba?". Wani makirin murmushi yay irin na marasa mutuncin nan yace,"Mun yi da ita zan saketa ne? Idan ma tunanin hakan ne akanta to ta cire shi domin ni ba zan saketa ba, kuma ka faɗa mata ko ta gama zaman gidan ko ba ta gama ba ta tattaro ta dawo yau, dama ba bisa izinina ta tafi ba, kuma zata dawo ta same ni". "Kaga dakata, magana na ke maka ta dole zaka saketa, ka rubuta takarda a yau ka aiko mana da ita". "Imam ka ke ko? Ba zan taɓa yin abinda kuke so ba, Sa'ida sai dai ta ci gaba da rayuwa a gidan naku haka amma ba zan saketa ba, kuma ni da ku mu zuba mu gani". Ƙit ya kashe wayarsa kuwa. Abbaa ya fara magana cikin kakkausar murya, kana jin yadda amon ta yake fita hakan zai tabbatar maka da yana cikin tsananin ɓacin rai,"Babu wani mahaluƙi Wanda ya taɓa tozarta mu kamar wannan yaron! Babu Wanda ya taɓa wulaƙanta zuri'a ta irin wannan yaron, me yake jin kansa? Yaushe ya taka matsayin da zai ci mutuncinmu haka? saboda yana taƙamar yana da kuɗi...". "Taƙamar dai yana da tsiya da iskanci, kuɗinsa ɗin banza da wofi, mu ba irin talakawan da zamu bari mu wulaƙanta ba ne, ba ƴan tsiya ba ne mu amma tabbas zan nuna masa ƙaryar iskanci yake, zan nuna masa mun shallake gaban tunaninsa". Cewar Yaya Imam. Sautin kukana ne kawai yake fita a hankali, kaina bisa cinyar Ummani, sai faman goge min hawaye take yi, jikina ya yi zafi rau kamar wuta. Idanu na kawai na rufe gam saboda da zarar na buɗe su sai su riƙa haskomin abubuwa barkatai. Muryar Ya Imam na tsinta a cikin tunanin da nake yi yana faɗin,"Abba kayi shiru ka daina ɗaga muryarka akan wanda bai gaji arziƙi ba, ka bar lamarin komai a hannunmu, duk yanda zai yi sai ya bata takardar saki ko shi ya fi kowa taurin kai a duniya, nasa kaɗan ne zan nuna masa ƙaramin mara mutunci yake, ni ubansa ne a taurin kai, zan gwada masa wallahil azim Sa’ida tana da Yayye masu tsaya mata kuma ƴar gata ce, na baya ma da yay rashin sani ne shiyasa har ruwa ta sha". Yashaik ya ce,"Ki bar kuka ke kuma, ai kuka ya ƙare maki, kar ki ji komi ki kwantar da hankalinki zama da Nazifi ne kin gama shi... Ko ya ba da takarda ko kuma daga nan har kotun ƙoli wallahi". Yaya Imam yace,"Kotu zaka kai shi? Ka shirya ɓatawa kanka lokaci kenan, ai yanda Abbaa ya buƙaci takarda a yau tabbas a yau ba sai an kwana ba zai rubutata ko da yana rubutu jini na zuba a hannunsa, zan je har inda yake karɓowa, idan yay min garda wallahi zan raunata shi ne kuma na tilasta masa ɗaukan takarda da biro ya rubuta abin da muke so". Yana faɗin hakan ya miƙe yana saka wayarsa cikin aljihu, kafin ya nufa ƙofa Ummani ta dakatar da shi tana cewa,"Imam dawo, dawo kar ka tafi a zuciye ina tsoron zuciyarka Imam, gwara ayi abun nan cikin maslaha idan bai bayar ba sai muje gaban alƙali, amma kaga yana ji da kuɗinsa kar abu ya kwaɓe mana". "Je ka Imam, karɓo takarda sakin ƙanwarka a hannun Nazifi shi zai tabbatar min da kai jinina ne na gaske". __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR17FT5* "Kai kuma kaje ka gama da makarantar Yasmin ɗin". Abbaa yace da Yashaik wanda ke tsaye shima jikinsa na tsuma saboda fushi da ɓacin rai. Ummani tace,"Abbaa na faɗa maka idan yaran nan suna cikin yanayin ɓacin rai ka daina saka su aiwatar da ɗaukan mataki, kaga ba'a san me zai je ya dawo ba. Yanzu dai da ka dakatar da Imam ɗin ka san halinsa kar ya zo yay masa dukan illah mu kwana a ciki". "To ke kina zaton ko dukan mutuwa Imam zai yi masa zan ji daɗi ne? Ai a duniyar nan babu wani hukunci da za'ai wa Nazifi na ji sanyi a raina. Sakar min ƴa shi ne kawai zai ɗan ragen raɗaɗi, amma batun hukunci wannan sai mun haɗu a kotun Allah, ban da lokacin ɓatawa na yin shari'a da shi a duniyar nan". Sai ya dube ni yace,"Ke me kikewa kukan to". Cikin sabon kukan da ke zuwar min na ce,"Abbaa ba na son komawa gidansa, Abbaa Nazifi ya zalunce ni da yawa, tun da na aure shi ban huta ba Abbaa, ina jin tsoro kar yaƙi bani takardata". Yanda amon muryan Abbaa ya fita ni kaina sai da na tsorata musamman da naji furucin da bai taɓa yunƙurin yi ba. "Malama daina kuka ki share hawayenki, ki kuma kwantar da hankalinki, saki ne kamar yayi shi ya gama, ko da zan yanke hannun Nazifi ne sai na yanke ya rubutu sakin ki...". "Subhanallah". Ummani tayi saurin katse shi. "Abbaansu don Allah ka sanyayawa zuciyarka ruwan sanyi, ai duk ba sai ta kai ga an fusata irin haka ba, shi kansa ai ya gaji da ita ko ba'a tursasa shi ba dolensa ne ma zai bata takardarta, amma ka daina batu irin haka". Kansa kawai ya jijjiga yana ƙurawa waje ɗaya ido ba tare da yace da ita komai ba. Ummani ta zame kaina a bisa cinyarta ta miƙe tana faɗin,"Bara naje na ɗora girki, Me za'a dafa?". "Kar ki girka da ni sai naga yanda hali ya yiwu". "To Allah ya kyauta". Fita tayi, ni kuma ina nan zaune hankalina duk yaƙi kwanciya, tsorona Allah tsorona Nazifi yaƙi sakina, Abbaa yace na tashi na tafi kuma in ban daina kukan ba sai ya saɓa min ya mayar da ni can gidan da kansa tunda ya lura kukan na ke so, to gwara na koma inda zan ke yi kullum da hujja. Ko da Ummani ta sauke abincin rana kasa ci nayi, babu yanda bata yi da ni ba na ce mata na ƙoshi, Abbaa kuwa yanda ta aje kwanonta bai kalli inda yake ba, sallar azhar kawai naga ya fita, tunda ya dawo kuma ya zauna ban da jijjiga kai da girgiza ƙafa ba abin da yake yi. Sun yi waya da Yaya Imam yafi sau ƙirgen yatsu, shi kuma yana can office ɗin Nazifin wai ba ya nan amma ya tsaya jiransa ya dawo, Abbaa dai yace to karka dawo min gida sai da takardar sakin ƙanwarka. Ana haka Yashaik ya dawo shima ya ce ai yaje har can gidansa bai same shi ba, Abbaa bai ce komai ba sai Kaka ne ma yace,"Lallai yaron nan ya wuce tunaninmu a rashin mutunci, ƙila sai mun ɗauka hukuma mun masa shigar dare". Ni dai ina kallon fuskar Abbaa yay wani irin murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa. Ganin yanda na takura kaina Ummani ta ce,"Ke zo ki kitse min kaina". Tare muka fita da ita daga ɗakin Abbaan, muna kitson tana faɗa min na kwantar da hankali na saki raina nayi walwalata, na riga na san waye mahaifina tunda har ya furta yau to sai in ba ya numfashi ne abin da ya faɗa ba zai aiwatu ba, kuma na san su waye Yayyena su kan yi duk iya ƙoƙarinsu akaina wajen ganin sun nema min ƴan ci sun kuma faranta min. Ta shiga bani labarin ai lokacin da na kirata na shaida masu abin da ke faruwa ta zayyanewa Abbaa komai, shi ne ya fusata yace yana raye bai ga wanda zai wulaƙanta masa ƴa ba sai Nazifi ya sake ni kuma sai ya kai ƙararsa kotu an bi min hakkina, kuma in sha Allah Nazifi na raye zai ga ƴaƴana da ɗaukakata. Gama kitsonmu kenan yaro yay sallama yace ana kiran Sa'ida a waje, da mamaki ni da Ummani muka maimaida abin da ya faɗa, sai Ummani tace da shi,"Kaje ka ce waye". Yaron ya koma sai ga shi ya dawo yana faɗin wai mijinta ne ya zo, ta shiryo za su tafi. Kusan tare da Ummani muka girgiza kai a raina ina faɗin lallai Nazifi ya raina ni ya raina gidanmu. Ummani bata ce komai ba ni kuwa na miƙe na fita, ɗakina na shiga na yafo mayafina na nufi hanyar fita sai Abbaa ya fito yana cewa da ni,"Ina za ki?". Kaina ƙasa Ummani ta fito tana ce masa,"Wai Nazifi ne ya zo ya ce taje su tafi". Abbaa yace,"Madallah da ɗan marasa kunya, to kije ki same shi ki karanta masa duk wasu shiƙa shiƙan cin mutunci da ke cikin kanki sannan ki juyo ki dawo, ki tabbatar kin gusar da ɓacin ran saman fuskarki da maganganu masu zafi da tsayawa a rai". Ina fita na same shi daga cikin mota ya hakimce, yana ganina yay biris yana jiran na ƙarasa, minti ɗaya, biyu kawai sai na juya zan koma cikin gida sai ji nayi yana,"Malama dakata". Amon muryarsa ya fito tamau. Na waigo lokacin da yake isowa inda na ke. Yana faman haɗe rai yace,"Ɗan aiken bai faɗa miki saƙon cewa ki fito tafiya zamu yi ba". "Shi ne ai na fito naga wanne mara zuciyar ne, ashe kai ne Nazifi, me ya kawo ka ƙofar gidanmu?". Bai expecting furucin hakan daga gareni ba don haka ya tsaya kallona kafin ya ce,"Saboda ba ki da hankali kin baro gidan aurenki kin zo kin nemi wuri kin zauna, tukunna ma bisa izinin wa kika taho nan ɗin?". "Bisa izinin waɗanda suka isa da ni, ka san ai ni ban gama watsewa ba ina jin maganar mahaifina. rashin hankali kuma ai yana wajen wanda babu zuciya a ƙirjinsa. Kai Nazifi ban da ma baka da kunya har ka iya tako ƙafa ka zo ƙofar gidanmu kace na koma gidanka, gidan da babu arziƙi babu mutanen arziƙi a cikinsa, gidan butulu rainon butulu, To bari kaji na faɗa maka sai dai wata Sa'idan a gidanka amma ba dai ni ba, babu abin da zai maida ni gidan mutumin da bai tsotsi arziƙi ba sai tsiya, mun rabu rabuwa ta har gaban abada, sai ka jira haɗuwarmu a kotun Allah. Yanzu miƙo min takardata da ka kawo min sannan ka juya ka bar mana ƙofar gida bana son sake ganinka idan ba haka ba sai nasa yara sun maka cin kashin da kare ba zai shinshina ba". Wani kallo yake min da ke nuna tsantsar ɓacin ransa da takaici. "Ni kike faɗawa magana haka?". "An faɗa maka, an faɗa maka shayinka na ke yi, ai ko a ba ya darajar biyayya wa iyayena yasa na rangwanta maka, ban da haka abin da zan maka dabba aka nuna maka aka ce ka wulaƙantata Nazifi ba zaka soma ba. Kuma gidanka ne na baro shi kenan ko ba tsayawar ahalina, sakina ya zamar maka dole balle kuma sun tsaya min, zaka bani takardata ko kuwa zaka nuna min kare ya cinye zuciyarka?". Duk maganar da na ke yi ina yi ne cikin rawar murya da taruwar hawaye a idona wanda ban san na menene ba, sai dai sam na hana bayyana duk wata faka da zata nuna rauni a tare da ni. Yana jijjiga kai kaman ƙadangare yace,"Ko za ki mutu ba zan sake ki ba Sa'ida". "Haka nima ko zaka hauka ce ka bi bola Nazifi sai ka sake ni, ai ba ma sai na rantse ba don ayau zaka san an isa da kai a gidan da ka raina mutanan cikinsa. Ban da ma ƙaddara da jarabawa ina ni ina zama matar illiterate irinka, talaka irinka da ko ubangijinsa da yay masa ni'ima bai iya gode masa ba balle ya godewa wacca da kuɗin gumin mahaifinta aka samu ceto rayuwar uwarsa, a lokacin da ƴaƴan da ta haifa su kasa yi mata komai...Ai kin banza ƙwaƙwalwa babu komai sai tarin jahilci, yo jahilci mana tun da an karanta ba'a anfani da shi, matacce mai matacciyar zuciya, babu komai a tare da kai sai tsiya, wallahi na godewa ubangijina da bai sa na haɗa zuri'a da ƙaramin mutum irinka ba, kuma dama ubangiji ba azzalumin bawansa ba ne shiyasa ya hana ni haihuwa tare da mutum mara daraja irinka, don abin jaje ne ga duk ɗan da zai nuna Nazifi Bala Mai Kalwa a matsayin uba, haka abun kunya ne ga macen da zata nuna Nazifi a matsayin miji, ni kuwa yanzu tsakanina da kai tamkar nisan sama da ƙasa ne...". A zafafe ya kawo hannu zai wanke ni da mari yay rashin sa'a tawa zuciyar tafi tasa kusa, aikuwa bai farga ba na damƙe hannunsa na ɗauke shi da marin da sai da ya kifa ƙasa. Na ƙyasata yatsu ina nu na shi na ce,"Somin taɓi na maka, idan ka ƙara kuskuren ɗaga hannunka a gabana wallahi sai na maka wanda yafi wannan muni...kuma ka bani takardata na ce kafin na ƙarasa yaga maka rigar mutunci". Yana dafe da kuncinsa Yashaik ya iso wajen. ya duben yace,"Me ya fito da ke wajensa?". "Zan faɗa masa ne ya kwashe ƙazaman ƙafafunsa masu dattin zunubi ya bar mana ƙofar gida, wadda ya ke tunanin zata koma masa ba ƙaramar mutum ba ce ita kamar shi ƙasƙantacce kuma wulaƙantacce mara ilimi". "Shiga cikin gida". Yashaik yace da ni. Na watsawa Nazifi wata muguwar harara naja dogon tsaki da cewar,"Ka jira lokacin da zaka yi ƙuncin da yafi na saman fuskarka a yanzu, ka kuma jirayi lokacin da zaka burkice da nemana akan na yafe maka, itama ta gida ka faɗa mata hakkina ba zai barta ba gwara ta zo tunda wuri ta duƙa ta nemi yafiyata kafin duniya ta fara ƙwallo da kai da ita da magoya bayanku". Na shiga cikin gida ina jin Yashaik na ce masa ya ba da takarda kawai ya tafi babu wanda ke son ganinsa takarda kawai su ke so, ba su da lokacin ɓatawa da shi. Murmushi Nazifi yay me kama da na yaƙe yana sosa gemu, yaywa Yashaik kallon wulaƙanci kana yace,"Kuna ta in saketa in saketa, ban ga fa wanda ya isa ya tilasta min ba, yin kaina na ke babu me saka ni yin abin da ban niyya ba, idan kuma kuna da karfin ƙwata sai ku ƙwata...kuma ka shiga ka faɗa mata ta fito mu tafi don ban gama wahalar da rayuwarta ba". Yashaik ya girgiza kai yace,"To shikenan kar ka bayar, idan mu ka je gaban Alƙali ka maimaita hakan, zamu haɗu a kotu a karo na biyu". "Hhhh to shikenan muje zuwa, in dai kuna da kuɗin yin shari'a ku buga da ni". Ana haka Imam ya ƙaraso, da ƙyar ya iya tsayawa ya kashe machine ɗinsa saboda tafarfasar da zuciyarsa take yi musamman na ganin Nazifi a ƙofar gida, ƙofar gidan ma har yana kai yatsa ƙirjin Yashaik ya nuna shi. Ko maƙulli bai tsaya cirewa ba ya tafi da sassarfa yana zuwa ya damƙi hannun Nazifi da ke nuni da Yashaik, ya barƙala shi yana faɗin,"Wallahil azim ko Sa'ida ka nuna da yatsa a gaban idona sai na karya ƙasusuwan hannunka...Ka zo da abin da muka umarceka ko kuwa sai na sassaɓa maka kamanni tukunna ka shiga hankalinka ka bi umarninmu". Maganar yake gaba ɗaya ma ya mance da ya barƙale hannun Nazifi, sai da Yashaik ya taɓa shi tukunna ya sakar masa yana dukan ƙirjinsa tare da tankaɗa shi baya. Hayaniyarsu ta fito da Abbaa wanda ya leƙo cikin dattakunsa yace,"Sa'id kaga ku shigo daga ciki saboda maƙota da jama'ar unguwa". Imam na kallon Abbaa yace masa,"Mu shigo da shi ciki?". Abbaa yace,"A'a ku barsa dolensa ma zai shigo da ƙafafunsa, ai da sauran tunani akansa da har ya gane ya zo da ƙafafunsa na marasa mutunci". Abbaa da Yashaik suka shiga ciki, yayin da Imam yake ma Nazifi wani mugun kallo da cewar,"Ka ci sa'a da kaga yanda zan maka ɗaukan saman ka, kuma ka shigo mana gida a gadarance sai kaga yanda zan kwarfe ƙafafunka ka baje a ƙasa". Ya faɗa yana shige ciki ya barsa tsaye sanƙanƙan. Zuciyar Nazifi na jin wani ƙullutun baƙin ciki, shi babu babban takaici ma a wurinsa sama da irin yanda suke masa magana da nuna isa. Yay murmushin leɓe ƙasan ransa yana maimaita furucin Abbaa _,"Zai shigo da ƙafafunsa"._ shikenan zai gani shi da su waye a sama, itama kuma Sa'idan zata ƙwammaci kiɗa da karatu akan maganganun da ta faɗa masa, ba dai zata same shi gida ba ne. Juyawar da zai yi sai ganin Malam yay ya sauka a daidaita sahu, ido waje yake kallon mahaifin nasa da son sanin manufar zuwansa. Har Malam ya ƙaraso ƙofar gidan bai ɗauke ido akansa ba haka bai iya cewa komai ba, mamaki ya ƙamar da shi cike da tsoron abin da ya kawo mahaifin nasa. Sai da Malam ya shiga soron gidan kana ya ɗago murya da ce masa,"Ban kai ka ganni ka biyo bayana ba ne mara mutunci da bai gaji arziƙi ba, ni dai nayi danasanin haifarka". Ya haɗiye yawu yana rissinar da kai tare da bawa Malam ɗin haƙuri. Ashe da dalilin Abbaa na cewa zai shigo da ƙafafunsa, amma kuwa Malam bai kyauta masa ba domin ya so ya nunawa Abbaa cewa bai isa ba yayi kaɗan. Ba don ya so ba ya taka ƙafafunsa cikin soron cike da baƙin ciki da takaici. Ina kaɗa miya a kitchen na jiyo sallamar Malam ɗin na taso da sauri na fito, ƙasa na duƙa ina masa sannu da zuwa, ya amsa gaisuwata yana saka min albarka tare da adu'a wadda naji daɗinta sosai har cikin raina. Nayi masa iso ga ɗakin Kaka na ce,"Bismillah ka shiga". Sannan na wuce Nazifi wanda nayi tamkar ma ban taɓa sanin me zubin halittarsa ba, na tofa masa yawun bakina a ƙafafu ya san da cewar ƙyamatar ma ganinsa na ke. Kitchen na koma na ci gaba da aiki, bayan kusan minti goma sha Yaya Imam ya shigo ɗakin Ummani ya same mu da cewa,"Tashi ki je ana nemanki". Na miƙe gabana na faɗuwa na saka hijabina na bi bayansa. Na shiga da sallama na nemi waje na zauna da girmamawa a gare su, Nazifi na tsakiya Malam sai zazzaga masa masifa yake yana zaginsa. "Dilla Malami tashi kaje ka ɗauko abun rubutu, kuma ka haura mintuna biyu za ka sha mamakina". Yana ƙunci haka ya fita, Malam yana ta bani haƙurin abubuwan da suka faru, yana faɗin shima ba zai taɓa yarda da komawata gidan Nazifi ba, kuma ban kyauta masa ba da na kasa yi masa kallon mahaifi wanda ba zan iya kai masa kukana ba. Nazifi ya dawo da takarda da biro ya zauna gefe da ni, kamar an watsan wuta haka nayi saurin ja baya da shi don ko kusa ba na son ganinsa ma balle jinsa kusa da ni. Abbaa yana dubansa yace,"Kaga darajar mahaifinka fa kaci har ka ɗauka mintuna masu tsayi haka a cikin gidana. Ban da haka niyyata kana shigowa su Imam su saka rubutun da baka so kuma su fitar da kai cikin ƙalilan ɗin mintuna". Kansa ya ɗago ya kalli Abbaa yace,"Abbaa ba na son sakinta, zai fi kyau a sulhunta mu...". Yaya Imam yace,"Ka san Allah ka bar ganin Malam a zaune anan idan ka kuma musu da abin da mahaifinmu yace zan jaka waje na farfashe bakinka, na lura yanda ka raina naka iyayen haka ka ke ganin zaka raina na kowa". Yay maganar yana tasowa daga inda yake zaune yay tsaye akansa, ni dai ban kallesa ba ban kalli inda yake ba, amma ina da tabbacin yanda na tsorata da amon muryan Yaya Imam ɗin haka shima ya tsorata wanda shine dalilin fara rubutunsa akan takardar babu shiri. Yana gama rubutawa ya kallo inda na ke ya kira sunana da muryar da tayi kama da masu neman taimako. Ƙin ɗagowa nayi tamkar ban ji kiran ba, sai da Malam yace,"Sa'ida karɓi". Na ɗago ina bin takardar da yake miƙo min da kallo, kafin na kai hannu na karɓa. Kuma wai saboda bai da cikakkiyar kunya har yana faɗa min,"Ba da son raina na sake ki ba, ki sani zan iya maida ke a kowanne lokaci". Ni dai idona na kan farar takardar da ke ɗauke da rubutun cewa _"Ni Nazifi Bala Mai Kalwa na saki Sa'ida Salman saki biyu"._ "Na sake ki saki biyu, da sauran igiyar aurena akanki". Ya ƙara faɗa min da baki yana miƙewa zai fita Yashaik yace masa,"Butulu kawai wanda bai san mutunci ba mutunci bai raine shi ba balle halacci. Tun kana tsummanka baka da komai ka addabi rayuwar yarinya sai da ka aureta hankalinka ya kwanta, kuma kai ne yau ka wanko ƙazaman ƙafafunka a gaban idanun mutumin da ya dinga tallafar rayuwarka da jarin sana'a ka sakar masa ƴa, kai a ganin ka kaine da riba ko?, to bari kaji Sa'ida itace da riba domin tun farko daman taimaka maka tayi ta aureka ba don kun dace ba, kuma da sannu zaka girbi abin da ka shuka don Allah ba zai barka haka ba sai ya saka mata". Fuskarsa ta nuna yaji zafin maganar, ya tsaya yana duban Yashaik yana sauke numfashi. Abbaa ya doka masa tsawa da cewa,"Dalla can fice ka bar min gida kafin nasa a fitar da kai". "Ta zo ta kwashi kayanta da wuri". Ina saurin buɗar baki nayi magana Kaka ya riga ni da cewa,"Kai ne matsiyaci kai kayanta suka dama, ba ta biɗar ko tsinke a wannan tsiyataccen gidan naka, ka adana su domin amfanin wataran...maza ɓace mana da gani". Yana fita Malam ya shiga bawa su Abbaa haƙuri, Abbaa yana babu komai, shima yana cewa fatan wannan abu mara daɗi ba zai shafi zumuncinsu ba, Abbaa yace zumunci ai sai tsakanina da kai Malam Bala, amma babu matarka babu matata, haka babu ƴaƴanka babu ƴaƴana. Kuma ka jawa ɗanka kunne ko da wasa kar yay gigin sake bibiyar ƴata idan ba haka lallai ba zai ji daɗina ba. Kaka yana kallona yace,"Tashi kije". Na fita ƙafafuna a matuƙar sanyaye, da gudu na shiga ɗakin Ummani na faɗa jikinta, kawai sai na fashe da kuka sosai, kukan da na rasa na farin ciki ne ko kuma akasinsa. Ummani ta karɓi takardar hannuna ta karanta a hankali ta furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kafin ka shiga lallashina tana cewa,"Daina kuka, in sha Allah wannan rabuwar taku alkhairi ce gare ki mara misaltuwa, in sha Allahu ba za kiyi kukan zawarci ba sai dai ma ganin ranarsa tun da har gidan aurenki ya tauye miki abubuwa da dama". Ni dai kuka kawai na ke yi, cikin idona babu wani abu da ke haska min face dukkanin rayuwar da na shafe tare da Nazifi tun daga ranar farkona na siyan rake a wajensa har zuwa wannan rana da ya miƙo min takardar sakina a gaban mahaifina. A hankali na furta,"Allah na roƙeka kasa ƙarshen jarabawar kenan". __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR18FT5* Tun daga wannan rana da na karɓi sakina a hannun Nazifi na shiga wani sabon babin rayuwa. Ni kam sai dai nace Alhamdulillahi don bana wani fuskantar ƙalubale da zan ce gwara zaman uƙubar gidan aure akan zaman zawarcin da nake yi a gidanmu, duk da a baya naji tsoro sosai duba da yanda na ke jin mutane na kambaba tashin hankali da musibar da ke cikin zawarci. Ko kusa ba na fuskantar kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, ba ya ga sabuwar soyayya da tsantsar kulawa ma da iyayena da Yayyuna ke ba ni, ko da yaushe cikin nuna damuwarsu gare ni suke na me na ke da buƙata, motsi kaɗan me na ke so, hatta mahaifiyata ba ta so ma na ke aikace aikace. Umma da yaranta ne ma suka so su saka ni gaba da habaici da yada magana wai na kaso aurena saboda ina so nayi yawon zawarci irin na ƴan iskan mata, wani sa'ilin kuma su ce rashin haihuwa yasa aka sako ni, ni dai bana taɓa daga kai na dube su haka ban taɓa nuna na san suna yi ba, Ummani ma bata taɓa bi ta kan Umman ba duk da irin maganar da take yada mata me zafi wai ai da ban kaso aurena na fito ba saboda yanzu dai babu wanda zai aure ni sai dai na ƙare a haka tunda bana haihuwa, kuma ga shi ma ban da karatun boko mazan yanzu kuwa wayayyiyar mace suke aure, saboda haka ya kamata ta saka ido akaina saboda kar na fara yawace yawacen banza don ranar nan ma taji wajen masu shayi ana faɗin daga mutuwar aurena ko gama idda ban yi ba na fara yawon iskanci. Aikuwa ran Ummani ya ɓaci da maganarta, suka kama hayaniya har sai da Kaka ya fito ya tsawatar musu, Ummani tace to lallai fa yaywa Umma tsakani da ni babu ruwansu da zaman da na ke yi a gidan, su ɗauke ido akan ƴarta idan ba haka duk abin da tayi mutum shi ya siya da uwar kuɗinsa, a daren ranar kuwa Kaka ya tara dukka gidan Iyaye da Ƴaƴa ya jawa kowa kunne, yace duk wanda ya kuma ɗaga ido ma ya kalle ni ya furta kalaman bazawara sai ya bar gidan, Abbaa ma yace duk wanda bai ɗauke idonsa akan ƴarsa ba lallai zasu yi rigima ta ban mamaki, to tun sannan fa na samu salama a wajensu, babu ruwansu da ni nima babu ruwana da su, Umma ko magana ma bata min idan na gaida ita sai ta min banza, saboda haka kwata kwata ma na daina ko zuwa ɓangarenta, iyakata wajen Umman au Hindatu. Hankalina ya kwanta bani da wata damuwa, daga na ci sai na kwanta sai hira da mahaifiyata, wanda hakan ke ƙara kawar min da duk wani tunani da zai iya fama ciwon da ke a zuciyata, hatta Safiyya da suka zo ita da Hassana Tijjani sai da suka min tsiyar wai har na fara kumatu, kuma wanne man bleaching na ke shafawa, wanda kuwa duk ya san batun mutuwar auren sai yace Allah ya saka min, da can bai san bana haihuwar ba sai yanzu da yay kuɗi shi ne zai juya min baya. Abbaa kuwa watana ɗaya ya fara bani ƴan kuɗaɗe ina ajiyewa duk sanda ya fita ya dawo, yace da zarar na kammala iddah sai na koma makaranta na ci gaba da karatuna kafin Allah ya kawo mijin aure, ni kuwa a zuciyata babu wani lissafi na aure, ai tuni na gama faɗawa zuciyata na gama yin aure kuma, buri na bai wuce rayuwata ta inganta ba, na koma makaranta nayi karatu sosai na samu gogewa nima na zama cikakkiyar mace ƴar zamani mai ji da kanta, sannan na samu aikin yi me gwaɓi wanda zan tallafawa mahaifana da su kan su Yayyuna da sauran al'ummar musulmai. Wata rana muna zaune Yaya Al'amin ya zo yana faɗawa Abbaa cewa akwai scholership na school of nursing jigawa, abokinsa ne suke bayarwa yay masa magana yace zai yi magana a gida idan an yarda sai ya karɓawa ƙanwarsa, Abbaa dai yay shiru bai ce komai ba ni kuwa ina ta murna, bayan kwana biyu da maganar hakan sai Abbaa ke cewa a'a ba ya so nayi nisa, in ace dai nan school of nursing ne ta kano kusa kusa sai ya bar ni na tafi, amma shi ba ya son in da zanje na zauna ba zai samu kwanciyar hankali ba. Makaranta dai kowacce iri ce indai a kano ce to za'a sama min na je, wacca zan ke zuwa ina dawowa amma ba ta kwana da zan yi nesa da su ba. Ranar da na fita a iddah Yaya Imam ya zo da zancen cewa ya tambaya min wata makarantar islamiya anan farkon layinmu zan ke zuwa ina koyarwa kafin na koma makaranta, nayi murna sosai da sosai nayi ta masa godiya, a washegarin ranar kuwa na fara zuwa. Da ɗan kuɗin albashin da suke biya muka ja jarin kunun aya ni da Ummani, Abbaa ne ma yaje har makarantar almajirai ya samo almajiri bisa izinin Malaminsu, idan aka taso su ƙarfe goma zai zo ya ɗauka kular ya fita titi kafin ƙarfe ɗaya ya ƙare har ya dawo, kuma Alhamdulillahi sosai ake ciniki Allah kuma ya saka mana albarka, da kuɗin sau tari ma ake cefane idan Abbaa bai da kuɗi. ****Yaran duk sun fita hayyacinsu tamkar wasu marayu marasa galihu, yanda ka san basu da uwa ba su da uba a raye, zaune suke a falo sun yi jungum jungum, kana ganinsu kasan muguwar yunwa ce ke ƙwaƙularsu kuma ba su da yanda za su yi, kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu ba za su yi bala'in baka tausayi, rabon su da abinci tun guntun biredin da suka samu suka ci da safe, shima Abbansu ne ya rage ya kira su suka ɗauka ba don bai san ba su ci ba sai don ƙara musu. Iyam ta fito a ɗakinta ta samesu tana cewa,"Kun duba kitchen ɗin babu sauran garin kwaki?". Atika ta buɗe ido ta kalleta a wahalce tace,"Babu fa na faɗa miki, tunda Anty Sa'ida ta tafi kinga an kuma kai wani abu cikinsa ne, idan kina da kuɗi ki aika a siyo mana indomie kawai, ai akwai sauran gawayi a baya, kuma gaskiya ki faɗawa Abbaa kawai Anty Amarya ta cire girki da mu tun da bata son bamu, sai muke yi da kanmu ko Anty Faty ta dawo nan". Ta faɗi hakan tana matsar ƙwalla tare da dafe cikinta. Rumana dai na gefe bata iya cewa komai ba sai kallo da ido, ko da yaushe haka take bata da bakin magana, yarinyar ta rame sosai duk tayi ƙashin wuya tayi baƙi saboda wahala. Iyam ta zauna kan hannun kujera ta rafka tagumi, can kuma ta miƙe tayi ɗakinta tana cewa,"Bara mu gani". Ɗakinta ta wuce tana faman laluben kuɗi, duk kuwa da cewa ta san ba ta da ko da sile, amma tausayin yaran yasa duk ta kiɗi me, ita ba ma ta kanta yunwa kam har ta saba zama da ita, Nazifi bai damu da bata kuɗi ba yanzu saɓanin da kullu yaumin naira dubu biyu zuwa uku sai ya ɗauka ya bata duk sanda zai fita, idan ma ya mance bata mantawa Sa'ida kan bi shi ta karɓo ta bata duk da a lokacin tana tsaka da tsangwamarta, to in ace da kuɗin da sai suke samu suna siyo wani abin suna ci da rana. Wata huɗu kenan da tun bayan sakin Sa'ida al'amura suka canja a cikin gidan, ga ɓangaren masu son zuciya ba za su faɗi gaskiya ba amma tabbas shi kansa gidan da yana magana zai faɗi cewa anyi rashin nagartacciyar mace. Zahra'u irin rayuwar hutun da ta taso a gidansu ita take yi a cikin gidan, bata son yin duk wani abu da zai wahalar da ita, girki kuwa dama ita ko a gida ba yinsa take ba sai ma da za'ai aurenta ne Yayar Mamanta ta takura akan sai ta shiga catering school, a babu yanda zata yi shi ne taje ta koyi girki, kuma ita babu wani abu da take ƙiwan yi sama da girki, balle da taga tana da uwar kuɗinta miji ma ya sakar mata ATM saboda haka kashewa cikinta kawai take da ciye ciyen order, hatta shi kansa tafi yi masa ordern abinci ta juye a flask a zuwan ita tayi, dama tana da chef ɗinta a hannu duk ranar da ta tashi zata ce da ita ga abincin da za'a mata zuwa yamma a kawo mata. Tafiyar Sa'ida babu jimawa ƴan aiki suka yi tafiya ƙauye kuma har yau ba su dawo ba, ita kuma ganin akwai su Atika yasa bata damu kanta ba don dama bata shiri da yin shara da sauran ayyuka. Ita abin da ta sani taci ta kwanta ta danna waya, ranar da take da fita aiki ta fita, yarinya tayi kuka ta bata nono ta sha, idan goyo ya kama ta sauka ta miƙawa Kakarta ita, share share da wanke wanke da goge goge kai duk wani aiki na cikin gidan ta tattara shi ta barwa Rumana da Atika, yaran basa hutawa sam domin kuwa duty ta raba musu, da zaran Nazifi ya fita idan weekend ne zata tsawatar musu akan su yi aikinsu da gaggawa kafin ya dawo daga masallaci, idan kuma working days ne nan ma ba zata taɓa ko tsinke ba har sai yaran sun dawo a makaranta suyi aiki, idan ranar zata fita aiki zata ce musu idan ta dawo ta tarar ba su gyara wuri ba sai ta sumar da yaro. Batun abinci kuwa dama ba'a magana, ba ko da yaushe suke samun ci ba har na safe kuwa, gwarama na dare wannan ta kan basu kullum shima kuma saboda Nazifi yana gidan ne, amma da safe in suka shirya za su wuce makaranta zata kaɗa musu worning da cewa kar su kuskura su nunawa uban ruƙonsu basu yi breakfast ba, dama ta faɗa musu ba ubansu ba ne uban ruƙonsu ne dan haka ko Abbaa da suke ce masa kar ta ƙara jin sun kira shi da haka, suke faɗa masa irin sunan da sauran suke kiransa Baba Ƙarami, idan nasa yaran sun tashi za su ke ce masa Daddy. Duk wannan abun ba su kaɗai ba hatta Iyam bata ragwantawa ba, yanda ba zata bawa yaran abinci ba haka itama ba zata bata ba sai na daren dai, kira idan Iyam zata yi mata sau dubu miliyan ta amsa mata guda ɗaya tayi mutunci, kuma Iyam bata isa ta sakata aiki ba, kai tsaye zata faɗa mata ɗanki na ke aure ba ke ba, idan ma har ta samu arziƙin ta tanka mata kenan, don tafi gane ma taja mata tsaki ta wuce ta barta. Yanayin yanda ta ke takunta ba ƙaramin shakkarta suke ba, ita kanta Iyam tsoron Zahra'u take ji ba kaɗan ba kamar wadda ta asirce, gidan kuwa tsakani da Allahnta ya isheta ta gaji da zaman gidan Nazifi, don ko kaɗan Zahra'u bata mutuntata bata ganinta da daraja, magana ma idan zata yi mamta murya a sama kamar da sa'arta take, ga babu damar komawa gida don tun ranar da aka yi sakin Sa'ida Malam ya kira ya faɗa mata cewar kar ta sake ta ƙara ko da zuwar masa gida ne, tunanin dawowar shi kuwa ma kar ta soma a lokacin da sha'awar hakan ya taso mata, sai san da yaga dama yace ta dawo tukunna. Duk lamarin da ke faruwa babu masaniyar Nazifi tun da ba zaman gidan yake ba, duk da dai ya lura da canjin wasu abubuwan amma sai ya ɗauke ido bai maida hankali akai, hakan ma kuma saboda kar yay magana ne Zahra'u tayi fushi don ko kusa ba ya son yin abin da zai ɓata mata rai a cewarsa ita Uwar Ƴaƴansa ce, ba ta cancanci ɓacin rai a wurinsa ba tunda ta basa abin da ya shekara da shekaru bai samu ba. Tana kan gado kwance tana bawa Iman nono, gefe ɗaya kuma waya ce a hannunta take dannawa, tayi ƙiba ta ƙara fresh, kaɗan kaɗan take murmushi. aka turo ƙofan ɗakin aka shigo, kasancewar tayi nisa akan danna wayar sai sam bata ji alamun shigowa ba. Atika ta maƙale daga bakin ƙofa tsoro duk ya cikata, shayin yin magana take yi don ko magana ce suka yi zama tashin hankali ne, tace suna cika mata kunne idan ba Kakarsu ko uban ruƙon su zasu wa magana ba to ita su daina mata magana suna saka mata ciwon kai. Shiyasa ko da yaushe idan suka zo wurinta sai su raɓe a bakin ƙofa tana musu kallo ɗaya za su fice da sauri kafin ta sakko ta faffale yarinya da mari. "Anty". Ta kuma kiran sunan a karo na uku tun shigowarta. tana shirin juyawa ta fita sai taga Zahra'un ta miƙe zaune tana gyarawa Iman kwanciyarta. Aje wayarta tayi a gefenta sannan ta ɗaga kai ta kalli Atika tace,"Zo nan". Yarinyar ta tafi a hankali cikin sanyin jiki gami da bala'in tsoro, tana zuwa Zahra'u ta cafkota tare da ɗauke fuskarta da mari, cikin wata gigitacciyar tsawa da ta amsakuwa a ɗakin tace,"Don ubanki ban hana ki shigo min ɗaki ba, ban ce kome ne ba ku jira ni na fito, uban me zan miki da kika zo kina damuna da kira?". Cikin rawar jiki Atika da tuni hawaye suka wanke mata fuska saboda zafin mari tace,"Anty kiyi haƙuri don Allah". Zahra'u ta kama kunnenta ta murɗe sosai har sai da yarinyar ta fashe da kuka. "Durƙusa ƙasa da ubanki, na kira ki kin zo kin min tsaye saboda ba ki da ɗa'a". "Don Allah kiyi haƙuri ba zan ƙara ba". "Idan kika kuma shigo min ɗaki me zan miki?". "Ki yi min duka". "Ba duka zan miki ba kakkarya ki zan yi, me ya kawo ki yanzu?". "Dama yunwa muke ji, cikina ciwo yake yi". Ai tana rufe baki ta fara jin saukar duka a jikinta. "Shegiya munafuka masu kashe aure, wato so kike ya dawo yace bana baku abinci ko, ina guntuwan taliyan daren jiya da na baku, ko Kakar taku cinyewa tayi bata rage muku ba?". Maganar take tana tsutsula mata wayar caja. "Ba magana na ke miki ba, na ba ku abinci ko ban ba ku ba?". "Kin bamu Anty, mun ci mun ƙoshi kiyi haƙuri don Allah ba zan kuma zuwa na ce miki ina jin yunwa ba, don Allah kiyi haƙuri wayyo Allah na, Anty na daina dama Iyam ce tace na zo na roƙe ki". "Kina ban haƙuri kina min kuka, to idan kinga na bar dukanki kin rufe min baki, kuma kije kice mata ba zan bayar da abincin ba idan so take ku ci ta fito ta dafa muku, zaman ɗanta na ke yi ba zamanta ba, kin ji me na faɗa miki ko kuwa?". Ai kuwa babu shiri Atika tasa hannu ta toshe bakinta tana faman susar jiki, da ike da ɗan haskenta jijiyar goshinta ta fito tayi raɗau, idonta yay jawur duk ga shatin wayar nan ya fito a jikinta. "Sai na ce ki tashi ki fita sannan za ki tashi, in ci gaba da dukan na ki kenan, shegiya makira me kama da ƴaƴan aljanu, wai yunwa ku ke ji, don uwarki da ta kasa riƙe ki sauran taliyar da na ba ku da safe ubanki ne ya cinye, to wallahi ko za ku mutu cikin gidan nan ba ku isa nayi girki akanku ba sai dan son raina, shima kuma sai naga dama zan ba ku...kin fice min ko sai na tashi na take ki dangin tsiya da jaraba". Da sauri kuwa ta miƙe har tana kifawa ta ƙwala goshi akan gadon ta fice da gudu. Sai da ta fita ta buɗe baki ta saki kukanta, tana zuwa ɗakin Iyam ta faɗi a ƙasa tana burgima. Yaya wacce ta zo babu jimawa ta miƙe da sauri tana cewa,"Ke lafiyar ki?". Yarinyar cikin kuka mai ban tausayi take cewa,"Anty ce ta zane ni". "Duka? Me kika yi mata tayi miki wannan mugun dukan haka? Ji fa yacca fatarki ta farfashe, kutumar bala'i anya Zahra'u ta taki hanyar zama lafiya da mu kuwa". Yaya ta faɗa tana waigawa ta kalli Iyam wadda tayi shiru cikin damuwar abun, tace da ita. "Iyam kin ga fa yacca Zahra'u ta daki yarinyar nan". Iyam tace,"Uhmm ai ki bari kawai, Zahra'u ta zama abin da ta zama, yanzu bata da kirki sam, gaba ɗaya ta sauya daga Zahra'un da kika sani a baya, ni kaina ban isa ba yanda kika san ba uwar mijinta ba, ranar nan ma kusan kawo min hannu tayi saboda na ɗaga mata murya na ce ta gyara ko nasa ɗana ya koya mata hankali". Nan ta kwashe komai take faɗawa Yayan, wacce ɓacin rai yasata cewa,"Ba ta ba ku abinci? Shi kuma Nazifin yana ina?". Iyam ta haɗa hannaye alamun bata sani ba kafin tace,"To ina na ke ganinsa ma balle na masa bayani, yanzu fa idan ya shigo ya gaida ni da safe shikenan sai wata safiyar, dawowarsa ma bana sani don ba ya shigowa yace min ya dawo, idan na aika yara su kira shi sai dai yay ta cewa gashi nan ga shi, ita kuma.ta ƙware a makirci duk wannan iya shegen da take yi a gabansa bata yi mana, ke idan ya wuni a gidan ma sai tayi tamkar zata cinye ni". Yaya ta waiga ta kalli ƴarta Rumana da ke kwance kan gadon Iyam ta dafe ciki, idonta a rumtse tana cije fuska. miƙewa tayi ta fita a ɗakin Iyam na ta kiranta akan ta dawo ta dawo, bene ta nufa sai ga Zahra'u na sakkowa. "Ke ashe ba ki da mutunci, ba ƴar arziƙi ba ce, saboda ba ki darajarta uwarki shine za ki dinga wulaƙanta tamu uwar, kuma tsabar ba ki da imani har kike bar mana uwa da yara da yunwa, so kike ciwon yunwa ya kama su, ko ke kika kawo abincin da har kike da ikon hana su, banza mara mutunci". Tayi maganar cikin faɗa sosai. Zahra'u tayi mata duba na rashin mutunci tace,"Kin san wani abu? Na ɗaga miki ƙafa iyaka yau amma ko don gaba ki kiyaye ɗaga min murya ko kuma ki kwantata lamari da mahaifiyata, sannan kar ki ƙara zagina ni ba banza ba ce, idan kika yi kuskuren hakan za ki gane banbancin aya da tsakuwa. Sannan da kike maganar na wulaƙanta muku uwa ta dai wulaƙanta kanta, ban da wulaƙanta kai da aurenki da gidanki, mijinki da ransa da lafiyarsa ki kwaso ƙafafu ki taho ki tare a gidan ɗa...abinci kuma ba su suka aje ni ba, don haka girki zan yi shi me kawai na bawa wanda ya aje ni a gidan, idan sun ga basu iyawa su tattara su koma gidan ubansu tunda su ba shegu ba ne, idan kuma shegu ku ka haifa sai naji bayani don haka kawai ba za ku ɗebi ƴaƴa ku lalaƙa masa ba, ke koma shegun ne a yau ki tattara garanku ki wuce da su domin ban shirya ruƙon ɗan kowa ba, aikin wofi kawai ba ki da aiki ke kenan kina kan hanyar gidan ƙani sai jace wata tsohuwar bazawara". Hannu Yaya ta kawo zata mareta aikuwa Zahra'u tayi saurin riƙeta tana yin wurgi da hannun nata, ta ɗaga yatsa tana nunata da cewa. "Ko wannan tsohuwar ta gefenki bata isa ta ɗaga hannu ta mareni ba bare ke karan kaɗa miya Yayar miji". __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR20FT5* Nazifi na isowa gida ya tarar da Yaran Yaya har su shida, Maza huɗu mata biyu wai sun zo ramawa uwarsu dukan da aka mata. A falo ya tarar da su sun kafa sun tsare a bakin matakalar bene, Maimu da Zuwaira sai danna uwar ashariya suke me muni suna faɗin idan Zahra'u ta cika ƴar tasha ta sakko taga idan basu nakastata ba yau. Yau sai sun ga wanda ya tsaya mata ba kaki ba ko ubanta ne shugaban sojojin Najeriya sai sun mata lahani kuma sun zauna lafiya. Mazan kuma suna tare da mahaifiyarsu akan kujera ta na ƙara kora musu jawabai, jawaban da ke daɗa fusata su anci mutuncin uwarsu. Idon Labahani ne ya fara kaiwa kan Nazifi da ke tsaye bakin ƙofa yana kallon su Maimu, da sauri ya zunguri mahaifiyar tasu da sauran ƴan uwansa, da yake suna bala'in shakkarsa duk sai suka natsu Garzali na kiran sunan Maimu da yi musu alama. Yaya ta miƙe tana faman galla masa harara da cewa,"Ka dawo kenan, to ban tafi ba ina nan mara kunya mara mutunci, wato akan mace yau idonka ya rufe ka manta wacece ni a wajenka ko". Ko kallonta bai yi ba ya nufi hanyar sama, da sauri su Zuwaira suka matsa masa suna faɗin,"Baba Ƙarami sannu da zuwa". Babu wanda ya saurara cikinsu ya haye, ya daɗe yana faman kiran Zahra'u akan ta zo ta buɗe masa ƙofa taƙi, sai can tunanin sa spare key ya zo masa. Ƙasa ya sakko ya shiga ɗakinsa, durowan kusa da gado ya buɗa yana bincika maƙullan, sai dai iyaka dubansa babu, kuma nan take Sa'ida ta faɗo masa a rai, saurin kawar da tunaninta yay ya koma wadrobe yana ci gaba da bincikawa nan ma duk babu. Tsaye yay ya kama ƙugu, Allah ɗaya ya san irin girman ɓacin ran da ke tare da shi, har yanzu kuma ya rasa ma wanne mataki zai ɗauka akan Yaya da Ƴaƴanta. _"Na'am Hubbi, Ohhh na canja musu wuri suna ɗakinka na sama cikin durowan kusa da madubi"._ Rumtse ido yay gam tare da sauke ajiyar zuciya, bai san ta yanda aka yi maganar Sa'ida ta faɗo masa ba a halin yanzu. ya fito ya koma ɗakinsa na sama, yana buɗe durowan ya kwaso maƙullan dukka gidan yana ƙara tunawa da ranar ƙarshe da Sa'ida taje ƙauye ya kirata yana tambayar maƙulli. Ko da ya buɗe ɗakin ya tarar da Zahra'u akan gado ta kifa kai da gwiwo, tura ƙofar yay ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗauki Iman da ke kusa da ita, duban jikin yarinyar yake kamar wanda aka ce masa taji jiwo. Sai da ya tabbatar babu wani ƙwarzanan rauni a jikinta tukunna hankalinsa ya sassauto har yana sauke doguwar ajiyar zuciya. Shifa a rayuwarsa ta yanzu yarinyar nan ce, idan da ita akwai shi idan babu ita to tabbas babu shi. Ya kai hannunsa saman kafaɗar Zahra'u cikin kwantar da murya yace,"Kiyi haƙuri don Allah". Ture hannunsa tayi tana fashewa da sabon kukan munafurci. Nan fa kuma sai ya ruɗe ya shiga lallashinta yana ta aikin bata haƙuri har da sakkowa ya duƙa gabanta, ita kuwa faɗi take tana sake maimaita masa sai ta tafi gida. "Na faɗa maka Daddyn Iman ba zan ƙara kwana ba ka sallame ni kawai, ba zan iya da wannan cin mutunci da wulaƙancin na ƴan uwanka ba, kowa ya raina ni basa gani na da girma, Yayyunka su min Ƙannenka su min yanzu kuma tsabar cin fuska har ta kai ga Ƴaƴansu ma, kuma kowa ya tashi buɗar baki sai ya yaɓa min magana yace ba don kana sona ka auro ni ba, ni matar shige ce kuma matar shige bata daraja, tsakani da Allah kayi min adalci kenan idan ka san da haka me yasa baka faɗa min ba na cirewa kaina soyayarka tun da wuri". Tayi maganar tare da fashewa da kuka sosai a wannan karan kuma na gaske ne, ta goge hawayen tana kallonsa,"To ka bani takardata kawai tunda ka samu dalilin da yasa ka aure ni ɗin, idan ya so sai kaje ka dawo da Uwar gidanka ka bata ƴar taka ni na yafe, Allah ya haɗa ni da mafi alkhairin...". Saurin kai hannunsa yay bakinta ya rufe,"Haba Zahra'u, wai ke har akwai wanda zai faɗa miki cewa bana sonki ki yarda. Ke da kan ki ya kamata ki ƙaryata hakan ai, kin sani babu wanda na ke so bayan iyayena sama da ke da Iman, na sha faɗa miki zanen ƙaddara shi yasa na fara auran wata kafin ke, kuma ban san wata soyayya ba sai da na aure ki, in ace ni ke da kundin littafin rayuwata da babu wata mace da zan yi tarayya da ita in ba ke ba, ke ɗin nan kin fiya min kowa da komai, kar ki ƙara min zancen wacca muka rabu tarihinta ya riga ya shuɗe a wajena, ni ke kawai na ke kallo a matata ta farko kuma ta ƙarshe, Don Allah don Annabi na roƙe ki ki bar batun za ki tafi, in dai abin da suka miki ne zan ɗauka mataki akai ki bar ni da su, babu wanda ya isa ya taɓa min ke na ƙyale shi". Kukanta taci gaba, ya hargitse duk ya gigice ya burkice, yafi tsawon awa guda yana famana lallashi kafin tayi shiru tace masa ta haƙura amma ya takawa Yayarsa burki. Ya shiga mata rantse rantsen zai ɗau mataki amma ta bar kukan idan ba haka ba zai sami wata natsuwa ba, shi kukan nata ne ke ɗaga hankalinsa. Fita yay a ɗakin da Iman saɓe a kafaɗarsa, yana fita tayi wata dariya tana tafa hannu, ranta ƙal ta cimma target ɗin farko sai na gaba kuma, ai ta sha alwashin babu boka babu Malam sai ta raba Nazifi da kowa ya zama nata ita kaɗai, shi da duk wani abu da ya mallaka. Yana sakkowa ya dubi Yaran Yaya da ke zaune a falo, waɗanda ganin nasa yasa suka fara rawar jiki suna raba idanu, ya dube su yace,"Wato a gidana ku ka zo kuna juye rashin tarbiyar da aka ba ku ko? Matata sa'arku ce don ubanku?". Zuwaira ce tayi dakiyar cewa,"Baba Ƙarami ai ita ce ta fara cin mutuncin mahaifiyarmu, mu kuma babu wanda zai taɓa mana uwa mu ƙyale shi". Tasss ya ɗauke fuskarta da mari. "Nayi ball da ke a wurin nan, ita Uwar taku idan ta kama girmanta har a tsinka shi? To wallahi duk wadda ta ƙara zuwar min gida tayi ɗiban albarka irin haka sai taga yanda zamu kwashe da ita, banzaye marasa ɗa'a, Kun fita kun bar min gida ko sai na juye muku dukka ɓacin raina". Ya kalli mazan yace,"Minti ɗaya ku ka ƙara a cikin gidana sai dai yau ku kwana a bayan kanta, kuma ina mai tabbatar muku ba ku da me tsaya muku wajen karɓo ku". Ɗaya bayan ɗaya suka yi gaggawan ficewa, matan kuma suka ɗauki mayafansu Maimu tayi saurin saɓa ɗanta a baya suka fice da hanzari ba tare da ko sun tsaya sallama da uwarsu ba. Suna fita ya shiga ɗakin Iyam, yana shiga suka yi karo da Yaya da ke niyyar fitowa don ta jiyo shi da yaran. Kamar bai ganta ba don ko arziƙin gaisuwa bata samu ba a wajensa, ya zauna kan kujera murya ƙasa ƙasa dai kana ji kasan a ƴan ƙunci ake yace da ita,"Sannu da gida". Itama da irin nasa yanayin ta amsa masa,"Yauwa, ka dawo kenan". "Na dawo". "To sannu, Allah yay albarka". "Amin, Allah ƙara girma da lafiya". Sai kuma ya kalleta yace,"Amma Iyam kina da masaniyar fitinar da Yaya ta zo ta tayar min a cikin gida? Fisabilillahi abin da tayi ya dace a matsayinta na babba wacce take uwa a gare mu? Tsakani da Allah ina ita na yin faɗa da matata? Ko da sa'arta ce ai babu daraja sam tayi rigima da ita matsayinta na Yayar miji balle ma ba sa'arta ba ce, kin kusa yin ƴa da ita amma ki zauna ki kama dambe har kina faɗa mata maganganu irin na ƙananun yara marasa lissafi, to gaskiya ni banji daɗi ba, don wallahi tallahi ban da ita ɗin ce kafin zuwana na turo hukuma sun tafi da ita, to taci darajar wata darajar ne kawai, ko ba komai ciki ɗaya yafi gaban wasa. Amma duk da haka zan ɗauki mataki, domin ba zan zuba ido tana haddasa min fitina a cikin gida ba, kawai tun da bata son matata to kar ta ƙara zuwar min gida gaskiya, ta tsaya can iya gidanta idan gaisawa ne na ke zuwa muna yi, kuma ai ga waya idan ma wani abun take buƙata tayi min text don ko yawan kirana ma da take yi ya kamata ta barni haka, kuma ta fita a harkar iyalina ko kallo banza kar ta ƙara yi mata". Ya maida kallonsa ga Yayar da ke kallonsa da sakakken baki cikin mamaki. "Kuma Yaya yaranku kawai ki ɗauke su ki tafi da su, dama rashin haihuwa yasa na karɓe su kuma yanzu Allah ya azurtani da nawa, na samu matar da zata ke haifa min ƴaƴa don haka na gode da taimakonku da nuna kulawarku. Ba zan ce ban ji daɗi ba haka ba zan ce ba kuyi min adalci ba, kawai dai kije da su suci gaba da rayuwa a gabanku nima kuma sai na ji da nawa da Allah ya bani, In yaso kuɗin da kika karɓa a wurinta sai a bawa yaran". "Kuɗi kuma?, wanne kuɗi kenan?". Suka tambaya a tare ita da Iyam. Ya kalli Iyam yace,"Da safe da zan fita na bawa Zahra'u dubu ɗari huɗu akan zata yiwa yaran nan siyayyar sabbin kaya da duk abubuwan buƙatunsu, don har uniform ma tace ya kamata a canja musu, to da ta zo wai sai ta ƙwace kuɗin har tana faɗin ai satar min kuɗin tayi. To tunda bata ganin irin ƙoƙarin da take yi akan ƴaƴansu da ni kaina ɗin da bana banbanta cewa bani na haife su ba, to su ɗauki yaransu kawai dama bani nace a bani ba, ra'ayin kansu ne. Kuma na rantse da Allah Iyam ban da darajar ke da Malam da kuke raye wallahi akan danganta min mata da ɓarauniya da tayi sai nayi ƙararta gaban alƙali, don sai ta faɗi lokacin da ta kamata tana ɗaukar min kuɗi, bana son ƙazafi na tsani mutum me yiwa wani ƙazafi, amma a hakan ma taje ita da Allah don ta ɓatawa iyalina suna, kuma idan ta sake tabbas zan datse alaƙar da ke tsakanimu". "Ehh lallai Yarinyar nan ta cika makirar mace, wato ƙarayayyakin da ta shirya maka kenan, kai kuma saboda shashasha ne sakatare soloɓiyon namiji an shanyeka har ka hau ka zauna akan tsararriyar magana ta matarka. Banza uban wa yay sanadin auran na ku idan ba ni ba? Kai inda hankali da tunani akanka ma har ka zo kana waɗannan maganganun, wanne gata ne ban maka ba a duniyar nan Nazifi? Ina ce auranka na farko ni na maka lefe, amma shi ne yau akan mace zaka rufe ido kaci mutuncina, to bari kaji baka isa ka hana ni zuwa gidanka ba tun da har mahaifiyarmu na ciki, yara kuma da ta zugaka akan ka mayar da su yanda ta zo ta same su haka zata bar su". Kaɗa kansa yay yana miƙewa tsaye. "Shikenan kar ki fasa zuwar min gida, Allah Iyam duk abin da nayi mata ita tajawa kanta kuma zan je na sami Malam na faɗa masa abin da ta zo tayi min a gida. Yaran kuma idan ma ba ki tafi da su ba zan kira ubayensu su zo su ɗauke su, tun da na samu nawa babu ɗan wanda zan ci gaba da riƙewa". Yana gama faɗin hakan ya fice. A daren ranar ya kasa haƙuri sai da yaje har can gida ya samu Malam ya karanta masa duk abubuwan da suka faru, Malam ya kira Yaya ta waya yaci mutuncinta iya gwargwado, ya kuma tsawatar mata akan kar ta ƙara taka ƙafarta gidan Nazifi in ba haka shi da kansa zai ɗauki mataki. Wannan faɗa da Malam yay mata shi ya janyo jin cewa ta rabu da Nazifi ita da shi kuma sai ta Allah, ko mutuwa yay ba zata dubi in da iyalansa suke ba. Bayan wani lokaci da faruwan hakan Iyam na ɗaki tana ta ƙwala kiran Zahra'u, wacca take falon ƙasa tana kallo kuma tana jin kiran amma taƙi amsawa tayi biris kamar bata ji ba. Tun ranar da akai case ɗin Yaya na zuwa suyi dambe da Zahra'u Iyam ke fama da ciwon ƙafa, farko ba su tsammaci abun babba ba ne ashe ciwon ƙafarta ne ya dawo, dama ƙashin gwiwarta jona mata shi aka yi to shi ne ya daɗa gurɗewa yanzu. Cikin wata guda da ɗoriya har ta rame saboda tsananin ciwo, kullum ita da Nazifi suna kan hanyar asibiti zuwa gashi da karɓar magunguna. Wanda in ya dawo sai ya barta da Zahra'u a tsammaninsa zata bawa mahaifiyarsa kulawar da ya kamata, nan kuwa bata bi ta kanta in dai ba yana gidan ba taga idonsa, magani ma idan taga dama tana shiga ɗakin zata ɓalla taje tayi floshing ɗin su ba zata bata ba. Shiyasa Iyam ke shan wuya sosai, bata iya yin komai da kanta sai an taimaka mata, dama sau tari sai dai ta faɗo akan gadon ta rarrafa da jan ɗuwawu tayi abubuwan da zata yi, to garin wannan kifowar da take yi ne ta samu gocewar ƙashin kafaɗa. Tana ta so ta koma can gida Malam yace shi fa bai san zancen dawowarta ba ai bata ma fara gajiya da gidan Nazifi ba tukunna, Ita kuma Zahra'u har da kukanta akan a taimaka a bar mata Iyam zata dinga kula da ita ba zata bari iya ƴaƴanta su kwashe ladan su kaɗai ba, ai itama uwa ce a wurinta, kuma in suka ɗauketa kamar ba su yarda da ita ba ne, dama ga Nazifi ya rantse ya kuma ya rantse duk wacca ta zo masa gida a cikin Yayyunsa da Ƙannensa sai kotu ta raba su, to kuma haka dole ya haƙura duk sati biyu sai suke zuwa dubata sau ɗaya kuma in suka zo za su samu ranar Zahra'u ta gyareta babu ta in da zasu faɗi wani abu na cewa Iyam bata samu kyakykyawar kulawa a gidan Nazifi har a yarda da su. Yanzun ma banɗaki take ta so ta shiga zata yi kashi ta kasa lallaɓawa ta sakko, shi ne take ta faman kiran Zahra'u amma taƙi zuwa, duk ƙoƙarin da take na riƙe kashin abun ya faskare sai sakinsa tayi a wajen. Ai fa kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani irin ciwo a zuciyarta, yanzu har ita matar ɗan da ta haifa zata ke wulaƙantata haka? Kuma ta rasa dalilin da yasa ta kasa ɗaukar wani mataki, duk yunƙurin da tayi na ganin ta nunawa Zahra'u iyakarta sai taji tamkar an danneta, haka ta rasa ta ina tsoron Zahra'u da shakkarta ya samu muhalli a zuciyarta, Surukarta fa! Isan ba ta isa da ita ba ai ta isa da ɗanta ko? Har dare tana zaune cikin kashi, ga wani azababben ciwon ƙafa da ke damunta, ga uban yunwa don tun shayin da Nazifi ya kawo mata bata ƙara sa komai a cikinta ba, ta rasa yanda zata yi gaba ɗaya. Bayan dawowar Nazifi ɗakin mahaifiyar tasa ya fara shiga domin dubata, sai dai me? shima tun daga falo ɗoyin kashi ya bugi hancinsa, sai dai bai kawo cewar uwar tasa ce tayi ba. Daga kwance ya sameta ya kunna fitila yana kallonta kwance kamar mara rai, ya tafi da sauri gareta yana kiran sunanta. Sai da yaje bakin inda take ya ankare da dama dama ɗin da tayi cikin kashi. Ya furta,"Subhanallah Iyam ya aka yi haka?". Kamar zata yi kuka cikin murya mai ban tausayi tace,"Wallahi Nazifi matsuwa nayi ne". "To amma me yasa ba ki ƙwalawa Zahra'u kira ba, ina wayarki saboda irin haka fa na ce kike barinta kusa da ke ko da zaki kirata bata nan ƙasa sai ki kira wayarta, kuma ita ya akai yau ban sameta anan ɗin ba?". Iyam tayi wani murmushi me ciwo da cewar,"Wayar ce Nazifi ban an in da na wurgata ba, yau ko ƙararta ma banji ba". Da matuƙar tausayin mahaifiyar tasa yace,"Bari na kirata ta wanke miki, sannu in sha Allahu kin kusa samun lafiya, likita yaje kawai a fita da ke ƙasar Germany". Ya faɗa yana ƙoƙarin fita ta tsayar da shi. "Ƙyale Zahra'u Nazifi, kai dai Allah maka albarka da ɗawainiyar da kake yi akaina, yanzu dai kai taimaka min ka raka ni banɗakin sai na gyara jikina". Kawai a ɗan wannan furucin nata sai ya fahimci da akwai wani abu, don kamar ma muryarta da alamun tsoro a ciki, anya kuwa Zahra'u na kula da ita? Anya tana cika alƙawarin da ta ɗaukar masa kuwa? Baki ya buɗe zai yi magana ta girgiza masa da cewa,"Nazifi bana so na shiga tsakaninka da matarka ka rabu da sha'aninta kawai, amma dai dole ka haƙura Faty ko Lubabatu wani ya dawo nan wurina da zama don gaskiya ni ɗaya na san a halin da na ke ciki. Matar babu abin da take min a bayan idonka, duk wani rawar jiki daka ga tana yi akaina wajen nuna min so da kulawa to a gaban idonka ne, makira ce ta ƙarshen ƙarshe, Zahra'u idan kasa ƙafa ka fice ko waiwayowa ɗakin nan bata yi, Nazifi matarka halin da nake ciki ma bata duba ta bani abinci ba haka nake yini na kwana da yunwata, kuma banga laifinta ba wannan ɗawainiyar ba kowa zai iya ba sai wanda ka haifa ɗin". Ran Nazifi ya ɓaci zuciyarsa na tafarfasa ya fita ya bar ɗakin. Ƙwala kiran Zahra'u kawai yake cikin amon tsanin ɓacin rai tun daga ƙasa har ya hau sama. Garam ya banka ƙofar ɗakinta wadda ta firgita ta juyo tana dubansa da cewa,"Innalillahi Honey lafiya?". "Ashe ba ki da mutunci, ke ɗin dama ba ƴar arziƙi ba ce? Ashe wulaƙanta min mahaifiya kike yi, mahaifiyata Zahra'u za ki ke hanawa abinci? Sannan bata da lafiya ki kasa sauka wurinta kike kulawa da ita kina taimaka mata? Dama ashe ganin idona yasa kike mata abubuwan da ba zan zargi kina cutarta ba, kin san a halin da na zo na sameta kuwa yanzu? Uzurin bayan gida ne fa ya kamata kuma tace ta kira ki kina jinta kika ƙi zuwa gareta, Zahra'u mahaifiyar tawa kika ma wannan wulaƙancin?". Juya idanu tayi ta ɗauke kai, lokaci guda ta sha mur kafin ta jiyo cikin ɗaga murya ta katse shi da faɗan da yake faman mata. "Kaga Nazifi Dakata! To ni ɗin dama bautar mahaifiyarka na zo yi ne, gaskiya ni ba zan iya wahalar nan ba, haba komai sai dai ayi mata hatta wanka wannan sai an taimaka mata to ni ba zan iya ba, ka ɗaukar mata masu aiki ko ka maida ita gidan mahaifinka ni kam ba zan kashe kaina da bauta ba, kuma wallahi in har ka ɗauko wata cikin ƙannenka da sunan su dawo nan da zama su kula da ita wallahi sai dai in ka sallame ni". Ta faɗi hakan ta raɓa shi ta fita a ɗakin, barin Nazifi tayi da sakakken baki wanda ya bi bayanta da kallo da maɗaukakin mamaki, gaba ɗaya sai yaji abun wani gingirin gin domin tun da yake zaman aure matarsa bata taɓa ɗaga masa murya ba, haka bai taɓa umartata da ta yiwa mahaifiyarsa abu taƙi yi ba. Amma yau yaga zahirin wacece Zahra'u a cikin kalamanta da ƙwayar idonsa da sonta ya rufe ganin duk wani kuskurenta. Ficewa yay ya sauka ƙasa da sauri ya koma ɗakin Iyam jikinsa sai rawa yake yi, Yana son mahaifiyarsa so yake ya rabu da ita lafiya. Yana shiga da kansa ya kamata ya shiga da ita toilet yay mata duk abin da ya dace sannan ya fito da ita. Abincinsa ya ɗauko ya zauna gabanta yana bata tana ci, haka tana ci tana zubar hawaye shi kuma jikinsa duk yay bala'in sanyi ya mutu, a zahiri ma ba zai ce ga tunanin abin da yake cikin ransa ba amma tabbas yana jin wani ɗaci a ƙasan ransa. __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR22FT5* "Kai ɗago fuskarka ka kalle ni". Ya ɗago yana duban Malam ɗin wanda ke jifansa da mugun kallo. "Ka san dai ni ba shashasha ba ne, kuma ba sakarai ba ne mara tunani irinka, da hankalina kuma ni ba mutumin banza ba ne kamarka, don haka kar ka ƙara zuwa gabana da maganar wani wai kana so ka mayar da tsohuwar matarka...kai ban da ɗan banza ne baka da ta ido mutanen da ka nunawa rashin mutuncinka kace a koma a ƙara nema maka auren ƴarsu, to wallahi ko ji nayi za su sake baka ƴar su sai na hana...". "Don Allah Malam ayi haƙuri...". "Dilla gafara rufe min baki bana son jin komai, ka tashi ka bani wuri idan ka san abun da ya kawoka kenan, idan kuwa ka ƙara yunƙurin min magana irin wannan Allah sai ka ga yanda zamu kwashe da kai". Malam yay ta masa faɗa, shi dai a zuciyarsa bai san haƙiƙanin abin da yake ji ba, amma tabbas da Malam ɗin zai san a halin da yake ciki la shakka zai ji kukansa kuma ya karɓi roƙonsa. Sallama yaywa Malam ɗin ya fita cikin sanyin jiki, wajen Amarya ya shiga suka gaisa, ta kawo masa abinci ya zauna yaci, ita ma nan yay ta faman roƙo da magiya tace ita fa sam ba da ita ba wannan lamarin, yaje ya samu Ummaa suyi maganar. Yinin ranar dai gaba ɗaya haka ya wuni sukuku kamar wani mara lafiya. Bai koma gida ba sai sha biyu na dare ya bar asibiti wajen Iyam, lokacin da ya koma Zahra'u ta rufe ko'ina babu yacca bai yi ba akan ta buɗe ƙofar ta ƙi, kuma ba bacci take yi ba idonta biyu, zai kira ta ɗaga sai tace masa ya koma in da ya fito, ransa ya daɗa dagulewa, ga azababbiyar yunwa kamar bai ci abincin rana ba, kuma da zai taho ba yanda Anty Aisha bata yi da shi ya tsaya ya ci abinci ba yace ya ƙoshi domin idan ya zo a ƙoshe wani tashin hankalin ne na daban tsakaninsa da Zahra'u. Haka dole ya koma mota ba shi da yanda zai yi, ya buɗe baya yay kwanciyarsa. Ko da Asuba ma bata sakko ta buɗe ƙofar ba sai da safe wajen ƙarfe takwas kana, lokacin zata fita wurin aiki ta fito ko kallon wurin da yake bata yi ba, sai da ta shiga mota ta zo daidai wurin tasa kana ta zuge glass tace masa,"Ai yanda ka ɓarar min da aji kasa na hayo motar haya to ka dinƙi kurɓan baƙin ciki a gidan nan, yauma idan kaga dama kar ka dawo da wuri ka kuma zama a can". Tana ganin ya buɗe motam zai fito tayi sauri bawa motar wuta ta fice. A ciki ya samu ta kuma barin Iman yauma sai tsala uban kuka take, ba yanda bai da ita ba akan take tafiya da yarinyar in yaso ta samu me raino tace sam ita aiki kawai taje yi can ba zata dinga ɗaukan yarinya tana tafiya da ita ba, tama kusa yayeta na gaji da wahalar shayarwa. Ko wanka bai iya tsayawa yayi ba kitchen ya shiga ya dafa abin da zai ci, kamar ya san bata ajiye masa ba kuwa, bayan ya gama ya ɗora wanda zai tafiwa da su Iyam asibiti, matan ƴan uwansa kowacce ka ganta da coolern abinci amma shi ban da tasa. Bayan ya fito a wanka ya gama shiryawa ya sanya haƙarƙarinsa akan gado, idonsa na kallon sama kana gani ka san cikin harbawar sakan yay zurfi cikin tunani wanda har sai a iya zuwa ma ayi sata a ɗakin bai sani ba. Ya jima a haka kafin ya fita falo ya karɓo Iman wadda ke hannun Marawiyya tana ta faman lallashinta, ya zo ya zauna yana mata wasa tuni tayi shiru, can kuma sai tayi bacci ya ɗauketa ya kwantar da ita a ƙirjinsa, cikin shirun da yay sai ya tsinci gimlawar tunanin kiran lambar Sa'ida. Wayarsa ya ɗauko yay dialling numbern, tun ranar da ya saketa dama ya goge duk lambobinta da hotunanta, ashe akwai ranar da riƙe lambartata zata yi masa rana. Haka yay ta gwada kiran lambar bata shiga, sai can a koma ce masa a kashe take, ya jijjiga kai kar dai da gaske kamar yanda aka faɗa masa ta sauya layi ne, aje wayar yay a gefe bayan yanke shawarar zuwa yamma zai je gidan na su, ya san Sa'ida mai haƙuri ce da sauƙin kai, tabbas idan ta gansa zata ji tausayinsa kuma zata yi haƙuri ta dawo gidansa, wanda zai matuƙar son hakan ba don komai ba sai saboda Iyam, domin ya san in ace Sa'ida na nan babu dare babu rana tana kan zaryar asibiti babu gajiyawa babu ƙosawa, kuma cikin bawa mahaifiyarsa kulawa da kyautatawa, kuma atleast zai samu sauƙin damuwar da yake ciki a yanzu na wasu al'amura da ke neman cakuɗe masa, saɓanin Zahra'u da bai ma san ta yanda zai fara sanar da ita ba don babu ta yanda zata fahimce shi, batun sake aure ma kuwa tunanin hakan na zuwa kansa ya ke kaudar da shi amma Allah ya gani ya gaji da halin Zahra'u. ****Muna zaune ne a cikin staff room ɗin makarantar islamiyar da na ke koyarwa. Daga gefe na ke ina bitar littafin muwaɗɗa, ku san awa guda su Malama Mastura na aikin hira akan rayuwar zawarci, dama kusan duk Malamai matan mutum uku ne masu aure amma mu shida duk zaurawa ne, duk san da aka zauna ana hira sai naji suna ta faɗin ƙalubalen da suke fuskanta akan zaman zawarci, cikin gidan iyayensu ba sauƙi haka waje ma babu sauƙi, wasu cikinsu ma faɗi suke har gwara su zauna a gidan auren miji yay ta gallaza musu akan dai zaman gidan da suke yi ana tsangwamar su, ranar da Malama Alawiyya ke bamu labari har ƙwalla sai da nayi wai cikin gidansu kullum mahaifinta sai ya kyareta kuma sai ya goranta mata akan ta kashe aure ta dawo gida ta zauna, haka mahaifiyarta ma bata barta ba tayi ta faɗa mata magana komai nata ta hanata taɓawa har ce mata take tana lalata mata carpet saboda kwanciya, basu san buƙatunta ba komai ita kewa kanta da ƴar ƙaramar yarinyarta da ke hannunta, abinci kawai ake bata shima duk sanda za'a bata sai an mata mita, saboda haka ne ta nemi aikin koyarwar to shima mutane nata surutun yawon ta zubar take yi, Babansu kuma na faɗa mata ai ko aikin me zata yi bata dai da daraja a idon duniya. Hakan sai yay ta bani mamaki kuma sai naji fargaba ta kama ni, a raina sai na ce to ko dan ni mutuwar auren nawa ban jima ba ne shiyasa hakan bata fara faruwa da ni ba, ni ban san wani abu kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, gaskiya idan na buɗi baki na ce nafi jin daɗin gidan aurena akan zaman zawarcina to sai Allah ya kama ni, ƴan unguwa ne ma dai ke ta gulmace gulmacensu, wataran ma idan na dawo haka daga makaranta har na kanji ana ƙusƙus, Abbaa ma ina jinsa ranar suna hira da Ummani yana faɗa mata an fara surutu akaina ƴan unguwa don haka wataƙila zai yarda ne na tafi can school of nursing jigawan tun da ba a samu ta nan kano ɗin ba. Gaba ɗaya sai na saka damuwa sosai a raina don tunani bai wuce akan masu magana akaina ba, da kuma a zo nan ba da jimawa ba iyayena su fara min maganar aure don wataƙila ganin ban daɗe a gabansu ba ne, amma kuma sai ya kasance ko da yaushe Abbaa nasiha yake min da kwantar da hankali ta yanda damuwa bata da ikon samun muhalli a zuciyata, kuma da hakan na samu natsuwar ruhi da zuciya matuƙa ganin iyayena na tare da ni, Allah har mancewa na ke da wani suna bazawara ji na ke tamkar ban taɓa auren ba. Yayyuna kuwa babu abin da zan ce da su sai Allah ya saka musu da gidan Aljannah ya ƙara musu buɗi, gata dai iya gata da nuna tsantsar kulawa bayin Allahn nan na yi min, duk san da suka shigo gida sa tambaye ni ban dai da wata matsala ko na ce musu ehhh. Yashaik da kansa ya biya min kuɗin koyon ɗinki tun watarana da ya zo ya samu muna hirar da Ummani, wallahi ba ai sati ba sai kawai ganinsa nayi da form yace na cike anjima na kai gidan Maman Binta, ranar har kukan farin ciki nayi, to yanzu ɗinkuna na ke tayi kuma Allah yasa min nasibi a kaasuwancin. Duk wata kuwa idan aka bani dubu takwas ɗita a islamiyar da na ke koyarwa ba na riƙe ko sisi tawa yaran Yashaik da Yaya Imam na ke wa siyayya, sauran kuma in siyo omo da sabulun wanka da na wanki na aje mana a gida, Abbaa yay ta faɗa wai na ke rike kuɗina ina adanawa ko na ke siyawa kaina abu, ni kuwa banga amfanin kuɗin ba in har ban musu ba, to me ma na ke da buƙata wacca basa min? Ranar da na taɓa faɗawa su Malama Alawiyya na taɓa aure ƙaryata ni suka yi wai wallahi kwata kwata ban kama da wacca tayi aure ba, kar nayi wasa da damata na amincewa Malam Isah kawai tunda shi ba ƙaramin yaro ba ne da gaske aurena zai yi babu wasa a maganarsa, ni dai kawai nayi murmushi ban ce musu komai ba saboda Allah ɗaya ya san me na aje a zuciyata dangane da aure wanda ya fita gaba ɗaya a raina, ana hakan kuwa watarana sai Malama Aisha ke cewa ashe da gaske ne ni bazawara ce taji a staff room ɗin Malamai maza ana maganar wai Malam Isah yaje neman aurena ance masa na taɓa aure to yanzu ya janye maganarsa don bai san mene dalilin fitowar tawa ba, shi ne har Malam Amiru ke cewa dama baka shaidar mutum ta fuska, amma ƙila ganin ina da ƙuruciya ne yasa na kaso auren na fito ba zai wuce talaka na ke aure ba abun duniya kuma ya rufe min ido. Maganar ta tsaya min a rai, da na faɗawa Ummani tace ai sai na toshe kunnena akan maganganun mutane. Yau na dawo daga makarantar na samu wata Kakarmu ta zo, ban ma san da zuwan nata ba don har sai da nayi sallar magriba na fito zan ɗauko abincin rana a kitchen Ummani ke ce min idan na gama cin abincin na shiga ɓangaren Baba Tijjani na gaida Gwaggo Marka. Aje abincin na yi na ce bari na fara zuwa mu gaisa, ina zuwa kuwa na sameta cikin jikoki ana ta hira, da murnarta ta tarbe ni muka gaisa, take min jajen mutuwar aurena wanda sai da ta zo yaune ma take ji. Sai kuma ta shiga bani baki da shawara akan da na samu manemi nayi aurena kar dalilin mutuwar wannan in ce ba zan kuma aure ba, Umma ta sako baki tana faɗa mata ai ni da iyayena mun ci buri ba lallai na ƙara yin wani auren ba, don ko yanzu haka anata zuwa wajena ma bana fita Abbaa kuma ya ɗaure min gindi da kansa yake fita ma ya sallami mutum. Ai fa sai Gwaggo Marka ta kama faɗa sosai akan abin da Abbaa yake yi sam bai dace ba, idan shi bai sani ba ai ni suke zubarwa da mutunci, ni dai tana farawa hawaye tuni ya fara suntiri bisa kumatuna wanda na jima ban yi ba, tace na tashi muje can taji daga bakin iyayen nawa mene dalilin hakan kuma mene ribar hakan? Muka tafi da ita muna zuwa ta komar da faɗan kan Ummani wai wannan ba dacewa ba ne, ashe auren nawa ma sune suka shiga suka fita suka tilastawa mijin nawa ya sake ni. Sai da ƙyar Ummani ta fahimtar da ita shi ne fa ta sassauta murya kuma ta dafa kafaɗata ta shiga lallashina. Na ce mata ni ai ba zan ƙara yin wani aure ba zan zauna ne tare da iyayena, ina aiki ina sana'ata ya fiye min wani aure, tuni na cire sha'awar aure a raina da tunani duk wani ɗa namiji. Sai ta kama ce min ai zancen hakan ma bai taso ba domin akwai lokacin da zan zo da kaina ma ina buƙatar in yi auren, don haka gwara nayi abuna tun da ƙuruciyata ba sai lokaci ya ƙure min ba, amma ita zata fi so ma ace na komawa tsohon mijina idan an sasanta akan na kuma wani auren daban, a cewarta gwara na komawa wanda na riga na saba da shi na san halinsa, na ce Gwaggo Marka ba za ki gane rayuwar da nayi a gidan Nazifi ba ne shiyasa kike batun sasanci. Ni dai haka na baro ɗakin Ummani ina ta faman hawaye, ban ji daɗin fama min ciwon da Gwaggo Marka tayi ba, tuntuni na haƙa rami na binne Nazifi da duk wani abu da ya dangace shi amma shi ne yanzu take min maganar wani wai na koma masa, ai abun da ma ba zai yiwu ba kenan da waninsa ma ballanta shi. To a ƴan kwanakin da Gwaggo Marka tayi a gidan sai naji duk gidan ya ishe ni na gaji, ba don komai ba sai don takurawar da tayi min akan maganar aure yanda kasan auren nawa ya shekara dubu da mutuwa, na rasa irin wasu mutanen da kambaba abu, ta matsawa Abbaa ma akan lallai sai ya ƙyale ni na fara sauraron zaurawan da ke ta suntirin zuwa gurina, shi kuwa yace ai zaɓin a wurina yake idan ina so ai zan sanar da su da hankalina kuma na san inda ke min ciwo, sai ce tayi a'a ai har yanzu ni yarinya ce da ƙuruciyata dudu shekaruna nawa suke, kuma kar ya manta mace ma sai ta shekara arba'in take fara tunani irin na ɗan shekara bakwai. Duk haushinta ya tuƙe ni na ƙosa ta tafi ta bar mana gida, ga shi kome tace sai Kaka ya ara ya yafa dama ƙanwarsa ce, ranar ina jin Abbaa na yiwa Ummani ƙorafin shima ya fara gajiya da maganarta sai kace ita ke ciyar da ni ko kuma ina zaune ne akanta, Ummani tace yay haƙuri kwana nawa ne ma ya rage ta tafi ana gama bikin Hindatu ne. Ni kuwa dalilin haka sai na tattara kayana na tafi gidan Yashaik, tun da ba dama ayi sallama ace Sa'ida tazo zata ce da yaro jeka kace tana zuwa, kuma ba yanda na iya dole sai na je. Sai da daddare ne Yashaik na ta zuba idon yaga na fito na tafi Maman Yasmin take faɗa masa dalili yace to shikenan ai babu komai, har yake tsokanata yana cewa shima dai akwai wani ogansu a wajen aiki yace zai zo mu sasanta amma tsoho ne don zai yi shekara 70 sai dai akwai dukiya. Maman Yasmin ta kama cewa,"Allah ya kiyaye ya suttura can yaje wani wajen". "To ya idan ita kuma tana so fa?". Nayi saurin cewa,"Bana so ma Yashaik". Yaro ne yay sallama da cewa wai Sa'ida ta zo a waje, kaina na ƙasa na kama mamaki tunda dai ai Ummani ce kawai ta san ina nan, Abbaa kuwa wai ba zai zo yace masa yazo nan ba, to ko Gwaggo Marka ga sani ne? Yashaik ya dube ni yaga ban kai hankalina wurin ba tamkar ba sunana aka shigo aka ambata ba. Ya lura dai da gaske na ƙi jinin Maza yanzu. Sai naji yana cewa da ni,"Kun yi da wani zai zo wurinki ne?". Na girgiza masa kai da cewa,"A'a". Hannunsa ya tsame a cikin kwanon abincin da yake ci. Maman Yasmin ta zuba masa ruwa ya wanke hannu yasa hularsa ya fita. Daga ya leƙa yaga waye kuma shiru bai dawo ba har aka yi isha'i, muka yi sallah muka wuce ɗaki. Maman Yasmin ta shigo tana cewa da ni,"Sa'ida kin ga Abban Yasmin shiru tun fitar da yay". Na ɗago kai ina barin linke kayan yaran da na ke yi na ce,"To ko kiran wayarsa za ki yi". Tace,"Ai kinga wayar tasa nan ya barta, ko kuma can gida ya wuce, Amma dai da can ɗin ya tafi sai ya fara shigowa ya faɗa min, kinga ba sabonsa ba ne kaiwa haka a waje". Tashi nayi na sanya hijabina na ce,"Bara na leƙa mu gani". Ina fita ƙofar gida naga ba ya nan, sai na tsallaka wajen masu kankanar ƙofar gidan ina tambayarsu ko sunga wucewasa sai yake shaida min yaga sun fita shi da wani a machine. Ban koma ba na wuce gida, naje ma Ummani ta kama min faɗan na fito da daddare, na ce to ya zanyi naje gidan mata mijinta ya fita a dalilina muma shiru bai dawo ba, tace to shi ɗin yaro ne da za'a kama wani cigiyarsa. Sai tace ba zan koma na lallamata ta bar ni na fice Abbaa ma bai san naje ba. Na koma na faɗawa Maman Yasmin ɗin tana dai falo ta kasa zaune, kawai sai na tuna nima haka na ke fa idan ya fiata ya jima bai dawo ba, kai na girgiza na koma ɗaki na barta anan a raina ina cewa duk inda yake ma ai zai dawo. Shiru shiru kuma har sha ɗaya da kusan rabi Yashaik bai dawo ba, munyi jugum jugum lokacin don sinitin Maman Yasmin ya hana ni bacci har sai da naji inama ban zo gidan ba. Can muka ji ƙarar adaidata sahu a ƙofar gida, haka muka yi rige rigen fita ni da ita, yacca ya ganmu hankula tashe sai ya kama dariya yana cewa muyi haƙuri, to yanayin da muka gansa cikin farin ciki sai hankalinmu ya kwanta amma duk mun ƙosa muji ina yaje. Nan na bar su shi da Maman Yasmin na shiga ɗaki. Washe gari da safe na gama shiryawa zan wuce makaranta sai Yashaik ya kira ni, na zauna gabansa yake faɗa min jiya ai Nazifi ne ya zo wajensa. Gabana ba ƙaramin faɗuwa yay ba na ɗago ido ina kallonsa da jiran jin ƙarashen zancensa. Kuma lokaci ɗaya na tafi tunanin kwana biyu kenan da muka haɗu da Nazifi ina kan hanyar dawowata daga kasuwar rimi naje na siyowa Ummani kayan zoɓo. Ni na fara ganinsa a cikin mota na zo tsallakowa titin layinmu ashe shima ya ganni, ya fito daga motarsa ya biyo ni ta cikin layin da na shigo ina ta sauri ƙafata har harɗewa take yi kamar zan faɗi. Ya sha gabana yanda naga idanuwansa sai na rikice a raina haka kawai naji ko shaye shaye ya fara yi, ni dai tsoro duk ya cika ni na ture shi daga gabana ina cewa ya bani hanya, sai ya ruƙo hijabina yana faɗin na tsaya na saurare shi ba abin da na ke tunani ba ne ya kawo shi wurina. Ni dai duk a hargiste na ke ban san me yasa ganin nasa ya ɗaga hankalina ba na ke jin kamar irin ƴan iskan mazan nan ne suka biyo ni, haka na tsaya ina ta sauke numfashi ya kawo hannu zai taɓa fuskata na bige hannun nasa ina faɗa masa cewar kar ya soma wannan gangancin idan ba haka ba zan masa ihu na tara masa jama'a. Na faɗa masa hakan ina faman huci wanda shi kansa sai da yay mamakin yanayin nawa. Nace ya bani hanya na wuce sai ya kama faɗin wai dama zai gaya min ne Iyam tana asibiti watanta guda a kwance babu yanda take, yanzu haka ma anata cuku cukun fitar da ita ne za'a yi mata aiki wai ƙashin kwankwasonta ne ya samu matsala. Kaina a ƙasa na ce,"To ni mene nawa a ciki?". "Ba za kije ki dubata ba?". "Bisa wacca alaƙar da ke tsakani?". "Tsohuwar matar ɗanta mana, kuma surukarta". Na galla masa harara zan wuce shi don magana da shi ma ɓata lokaci ne a wajena na lura bai da hankali. Sai kawai ya kama cewa,"Sa'ida na zazzo gida Babanki yaƙi saurarena, kuma ya hana ni na ganki, dama so na ke mu zauna ni da ke muyi magana ki sanar musu cewa kina so a mayar da aurenmu, ina so ki dawo gidana ko saboda Iyam Sa'ida, na miki alƙawarin babu abin da zai ke haɗa ni da ke kiyi rayuwarki irin wadda kike so, ba zan takura miki ba, ba zan ci zarafinki ba, kawai ni dai ina so ne ki bawa Iyam irin kulawarki". "Amma dai baka da hankali da isassan tunani ko, kai wanne irin daƙiƙi ne da ka kasa lissafin rayuwa tsakanina da kai ta ƙare". Nayi maganar cikin doka tsawa ina zare idanu kamar wadda ta fita hayyacinta. Sai ya shiga takowa zai matso gabana na kuma waro manyan idanuwana ina dakatar da shi da faɗin,"Na rantse da Allah inci ɗaya ka ƙara tsakaninmu sai na ɗauke fuskarka da gigitaccen mari, kuma ka fita a rayuwata kar ka ƙara nuna ka sanni ko tsautsayi ya kawo ka ƙofar gidanmu". Haka kawai kuma a lokacin sai na samu kaina da fashewa da kuka wanda na rasa dalilinsa. Shi kuma sai ya samu damar faɗin,"kin gani ko, kema kina so ki dawo gare ni amma taurin kai ba zai barki ba, ki faɗa min yanzu idan ba ki yarda na dawo da ke gidana ba waye zai aure ki". Take na katse shi da cewa,"Wanda yake sona, ko an faɗa maka kowa irinka ne butulu ƙasƙantacce, haihuwar rashin arziƙi". Sai yay ƙasa da murya yana faɗin,"Haba Sa'ida ban sanki da halin rashin kyautawa ba, ki taimaka ki dawo gidana ina da buƙatarki". Na kalle shi da jajayen idanuna na ce,"Da dukkan alama a make kake, ko kuma ƙwaƙwalwarka ta samu matsala, ni zan dawo gidanka? Ka manta ni ce wannan mara wayewar, wadda bata jin turanci, wadda bata zuwa office, wadda bata iya soyayya ba kuma ƴar talakawa me satifiket ɗin sakandire, daɗin daɗawa Juya wacca bata haihuwa, Nazifi Bala Mai Kalwa mene amfanin mace irin wannan a gidanka? Menene abun buƙatar dawowarta gidanka?". Sai kawai na fashe da kuka sosai da yin maganar tawa, na duƙa ƙasa na ɗebi duwatsu ina jifansa da su na zama kamar wata mahaukaciya, kuma ganin zan masa rauni yasa ya bar ni ya tafi yana faɗin in sake tunani. Ranar haka na koma gida duk a firgice babu irin tambayar da Ummani bata yi min ba na kasa bata amsa har yau. Numfashi na sauke ƙirjina na bugawa sosai na ce da Yashaik,"Me ya zo yi?". Na faɗa da rawar murya. Sai yay murmushi yace,"Kwantar da hankalinki, wai ya zo ne akan maganar yana so ya mayar da ke, na faɗa masa har abada to muna haka ne sai ga Imam ya zo, shi kuma kin sansa zuciya a wuya kawai ya rufe shi da duka, yay masa jina jina a fuska har ta kai dai ga mun tafi station, don da ace kuna tsakar gida zaku ji yo hayaniya a waje". Idona ya cika da ƙwalla na ce,"Ku yi haƙuri Yashaik duk ni naja muku...". Ya katse ni,"Kinga duk manta da wannan karɓi wannan". Na sa hannu na karɓa envelop ɗin da ya miƙo min, ina ƙoƙarin buɗewa yace,"Bayan mun dawo Abbaa ya kira ni, wai anyi sallama da ke ya fita sai ya tarar da wani akan machine, yace masa aiko shi aka yi ya bawa Sa'ida. To gasu nan dai duka biyun takardar admission ne ɗauke da sunanki, duk Scholership ne da aka ɗauke miki ɗawainiyar komai tsawon shekarun da za kiyi karatunki ki gama, ɗaya University of Targu Mures ƙasar Germany, sun ba ki nursing studies, ɗayan kuma Scool of health ce Emirate za ki karanci Community Health..Ba'a san wanda ya kawo takardun nan ba Sa'ida amma kuma akwai phone number a jikin envelop ɗin na kira sai muka yi magana da shi Director na makarantar Emirate ɗin, yace Allah ne kawai ya kai sunanki wajensu kar muji komai idan zaki karatu to ki fara shirye shirye, babu wani abu da za kiyi komai an gama miki ko screening ba zaki yi ba...To mun yi magana da Abbaa shima yace Allah ne ya kawo miki, naji ta bakinki idan kina so shikenan, idan ba kya so shikenan". Tun fara maganar tasa kallonsa kawai na ke yi na kasa rufe bakina haka na kasa ƙifta idanu, ba zan iya tantance yanayin da na ke jina ba amma tarin tunanine fal a cikin kaina. Ta ina zan soma?.... [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR21FT5* Cikin kwanaki jikin Iyam ya tsananta ta zama babu yanda take, kullum suna kan hanyar asibiti, ta koma gidan jiya bata iya komai sai dai ayi mata, daga kwanciya sai kishingiɗe, dama ga jikin tsufa idan ka ganta sai ta mugun baka tausayi, ƴaƴanta ma da suka shiga damuwa duk sun rame musamman Nazifi don ko a baya ma da bai da kuɗi shi ne komai akan ciwon nata, wannan dalilin yasa dole Malam ya haƙura ta koma gidansa. A hakan ma saboda irin magiyar da Nazifi ya dinga masa da ba shi haƙuri, har da haɗa shi da wani amininsa da Malam ke jin nauyinsa, du dai sai da akayi ta fama da shi don sai da ƴan uwa suka shiga maganar, yace shi idan suka takura shi ma sai ya sallameta, lokacin da ta tafi ta tare a gidan ɗan nata ai nuna masa tayi bai isa da ita ba, ta mayar da shi kamar babu aurenta akansa, har faɗa masa take ita ya ƙyaleta, don haka in har zata dawo cikin gidan to shi zai tattara sauran iyalansa su sauya matsuguni tunda dama ba shi ya gina gidan ba, da hakan dai aka ta basa haƙuri ana faman lallashi sai da ƙyar ya sakko ya yarda aka mayar da ita can. Barinta gidan Nazifin kuma ba ƙaramin daɗi ya yiwa Zahra'u ba, dama sam bata son zamanta a gidan tun ma Sa'ida na gidan, lokacin kawai kirsa ce irin tata don ta samu fada a wajen Nazifi shiyasa bata fito da ɓoyayyan halinta ba akan uwarsa da ƴan uwansa. Yanzu gidan ya zama daga ita sai ƴan uwanta, ƴan uwan Nazifi duk basa tunkarar gidan, waɗanda ba su san meke faruwa ba ma idan suka je basa marmarin ƙara komawa domin ba a yi musu tarba ta mutunci, duk wanda yaje sai ta wulaƙanta shi, yanzu haka kaf dangi baki ya ɗauka Nazifi bai yi sa'ar matar aure ba, babu wanda bai zaginta a cikin danginsa, ko hidima ce ta tashi bata zuwa, in ba yay mata da gaske ba a hakan ma idan taje to a tsaitsaye kallon raini da wulaƙanci zata je ta dawo, wai ƙyanƙyaminsu take bata son shiga cikin ƴan ƙauye. Gaba ɗaya yanzu Nazifi jinsa yake wani empty, ba shi da natsuwa kwata kwata, ko wurin aiki ya fita hankalinsa na kan mahaifiyarsa, idan ya dawo wurin aiki ma can gidan yake tafiya ba ya dawowa gida sai wajen sha ɗaya, dalilin hakan kusan kullum sai sun yi rigima da Zahra'u waccca ke ƙorafin yana tauye mata hakkinta, ai itama tana da hakkin lokacinsa ba wai ya tattara duka lokacinsa wa mahaifiyarsa kaɗai ba, ga ƴarsa nan har ta fara yi masa ƙiwa. Wani sa'ilin har fargabar dawowa gida yake yi, ba don komai ba sai saboda masifarta da fitinarta, nema take ta hana shi kwanciyar hankali sam. Kuma ba ya bi ta kan fitinartata domin abin da ya ishe shi shine ya ishe shi, shi kaɗai yasan a halin da yake ciki, idan yana biye mata zata kai su ga haifar ɗa mara ido, a hakan ma don ya tsaya a tsaye ne ya zama namiji a gidansa, yana tsawatar mata kuma tana ɗan shakkarsa idan ya rikiɗe mata, da rainasa ɗin da zata yi tamkar yaronta haka zata mayar da shi. Yanzu ba damar ya zauna waje ɗaya sai ya fara tunanin shi fa da Zahra'u akwai ƙauna me ƙarfi da fahimtar juna tsakaninsu, sai dai bai san me ya lalata alaƙar soyayyarsu ta mata da miji ba, ko kafin aurensu irin yanda take kautatawa ƴan uwansa Allah ne kawai zai biyata, amma yanzu ya rasa me ya canjata lokaci ɗaya, daga ina haka canjin hali da ɗabi'a? Nuna masa take tamkar ita ke aurensa, hakama can gidan su gani suke yi tamkar ai alfarma suka masa suka ba shi ƴarsu, tun da ko ranar da ta kaiwa mahaifinta ƙararsa sai da ubanta yaci masa mutuncin da kare ba zai shinshina ba, har wai yana faɗin ai ƴarsa tana da freedom don haka ya barta tayi duk abin da taga dama a cikin gidan aurenta, kuma dama lokacin da zai aureta ba su yi yarjejeniyar zata yi zaman bautawa mahaifiyarsa ba, saboda haka kar ya ɗorawa ƴarsa wahalar da ba zata iya ba. Uzuri yay musu domin kuwa zuri'arsu na da ƙarancin ilmin addini, kwata kwata basa martaba aure sai suke nunawa ƴaƴansu ai mijinsu ma bai isa da su ba, kuma ubansu ne jagoran nuna musu yin rashin mutuncin da suka ga dama a gidan aure, shi sai dai ƴarsa ta mulki gidanta ba mijinta ba, da ƴarsa ta ɗan yi complain sai ya kira mijinta ya kama cin mutuncinsa yana faɗa masa bai kai ba, bai kuma isa ba, idan zai iya zama da ƴarsa a yacca ta tsara zaman rayuwar gidanta to ya zauna da ita, kuma babu me sakar masa yarinya ta zama bazawara in har ka auri ƴaƴansa ka aura kenan. To balle dama ita Zahra'u a gidan na su duk ita ce ilimin addini bai wadace ta ba sam, tafi ƙarfi a boko da koyarwar arna rabin rayuwarta duk a ƙasar turai tayi. Fitowarsa kenan a wanka, bakin madubi ya ƙarasa yana goge sumar kansa da towel, ta cikin madubi yana bin ɗakin da ido, ɗakin kaca kaca babu gyara, kan kujera ma wankin kayansa ne na kwana huɗu da ya cire bata ɗauke su ba kuma ta da niyyar ɗaukewar. Zuciyarsa ta ƙuntata sosai, zai iya rantsewa ɗakinsa yafi sati bai ga tsintsiya ba, ƙamshi kuwa idan ba na jikinsa ba ko na jikinta to ba zai iya tuna rabon da ayi ma ɗakin turare ba, shi abun ma ɗaure kansa yake yi, bai taɓa tunanin mace na sauyawa har haka ba, abun Zahra'u yay yawa kuma ya fara isar sa. Ransa duk a dagule ya gama shirinsa cikin sky blue ɗin boyel, zagewa yay da kansa ya gyara ɗakin yay fes fes, abun sai ya masa bambarakwai namiji da suna hajara, wai shi ne da da gyara ɗaki yau, rabonsa da hakan tun samartaka. Yana gamawa ya kulle ya fita zuwa ɗakinta, kwance ya sameta tana baccin asarar da ta saba da yake yau weekend babu aiki, ya kai hannu yana tashinta, ta jisa ba wai bata jisa ba ya sani, amma idan zai awa guda yana tashin nata ba fa zata motsa ba balle ta buɗe ido ta san yana yi. Yau kam bata isa yay mata yanda ya saba ba na zaman jiranta har lokacin da ta ga damar tashi, don haka ya buɗe toilet ya ɗebo ruwa yana zuwa ya fetsa mata a fuska, ta tashi a firgice tana faɗi,"Mene haka? Akan me zaka watsa min ruwa? Idan na tashi ɗin me zan baka ne?". Ta faɗa cikin masifa da hargagi. "Amma ai na faɗa miki tun da sassafe ki shirya zamu tafi asibiti, shi ne za ki zo ki nemi wuri ki kwanta ke da bacci ba ya taɓa isarki, dun kin bi kin zama malalaciya ɗakin mijinki ma ba zaki iya tsaftace shi ba". Wani kallo ta watsa masa tare da cewa,"Na dai fi ƙarfin ka ce min ƙazama, ɗakinka kuma ba ce kayi baka so ƴan aiki suke gyara maka ba, ni kuwa na faɗa maka ba zan iya stressing kaina da aiki ba, da wanne zan ji ga aikin office ga na gida, kai ko tausaywa mutum baka yi, idan kaga ba zaka iya zama da ɗakin naka a haka ma ka gyara da kanka mana". Ta faɗi hakan tana neman komawa ta kwanta ya dakatar da ita,"Ke dalla malama mene hakan wai, zaman jiranki zan ta yi sai lokacin da kika ga damar shiryawa tukunna". "To wai Nazifi idan na sakko nayi maka mene don Allah, me zai kaimu asibiti alhalin lafiyata ƙalau kaima lafiyarka ƙalau haka ma ƴarmu lafiyarta ƙalau". "Amma ai na faɗa miki cewar yau da asuba an kwantar da Iyam ko, ke kwata kwata ba ki san abin da ya dace ba, me yasa kika zama mara mutunci ne, na ki iyayen kawai ke da daraja da ƙima a wurinki nawa kuma kin raina su kin mayar da su mutanen banza". "Ni dai kar ka ce zaka zagi mahaifana, kuma kar ka ƙara ce min ban da mutunci, asibiti ne ba zanje ba a yanzu kayi tafiyarka kawai, idan na tashi na biyo bayanka, ni kenan kullum ina kan hanyar asibiti zaman jinyar suruka". Tayi maganar tana komawa ta kwanta. "Ke ba fa zai yiwu ba, na rantse da Allah Zahra'u idan ba ki sakko kin shirya mun tafi ba in ranki yay dubu sai ya ɓaci, Me kika mayar da ni ne, sakaran miji shashasha wanda sai yadda matarsa tayi da shi, to wallahi ba zan ci gaba da ɗaukar halin iskancinkin nan ba, ni ke aurenki saboda haka dole ki bi umarni na kuma ya zamar miki dole ki girmama min iyaye, yanda sauran matan ƴan uwana ke zuwa su zauna a asibiti tare da mahaifiyarmu haka kema, ki sakko ki shirya mu tafi" Yay maganar cikin tsawa da ɗaga murya na gaske, wanda har sai da ita kanta ta tsorata da yanayin da ya ke neman rikiɗe mata. Tana ƙunƙuni ta sakko a gadon ta shiga toilet wai sai ta sake yin wanka du dai don ta ɓata masa lokaci. Shi kuma ya fita yana ɗaga kiran waya. Bayan kusan minti goma sha biyar ya leƙo tsammaninsa ta gama shiryawa sai gani yay a sannan ne ma take wa Iman wanka, gajeran tsaki yay na takaici kafin yace da ita,"Kuma na ce ki bani ATM ko". Tayi kamar bata jisa ba sai da ya ƙara yin magana tukunna tace,"Wai wanne ATM?". "Ban sani ba, ke dalla na gaji da rainin hankalinki, zan tambaye ki ATM ɗinki ne uban me zan a shi". "Amma ai na faɗa maka babu ko sisi a ciki ko, duk na kwashe kuɗin na siya mata kadarori, dama kaima ai ba naka ba ne na ƴaƴana ne to mene kuma abin zuwa ka dinga takura min da cewa na baka. To ni duk na siya musu kadarori don babu amfanin aje kuɗin kawai ana zuba musu ido, kuma ni ATM ɗin ma tuni ya ɓata nayi duban duk ban gansa ba, sai blocking nayi". "To me ya hana kiyi shawara da ni kafin yanke hukuncin hakan, ko ƴar taki ce ke ɗaya". Shiru tayi masa taƙi cewa komai. Sai da ta gama shiryawa tukunna ya sake ce mata. "To ki tura min kuɗin da na saka a ciki jiya don da sune za'ai amfanin asibitin Iyam". Ta buɗe baki da cewa,"Amma to Daddyn Iman baka faɗa min ba tun lokacin da ka tura, ai ni suna shigowa na turawa Mami su nace a siyawa Iman zoben gwal, naga ba account ɗinka ba ne ban tsammaci kuɗinka ka saka ba". Kallon ba ki da hankali yay mata kamin yace,"Zoben gwal? Da duka miliyan ɗayan? Zahra'u wai me yasa ba ki san ciwon kuɗi ba ne, ba fa zuwa na ke na tsinko kuɗin nan ba, ko tsinkowar na ke ai da wahala, akan wanne dalili za ki siyawa ƙaramar yarinya zoben gwal mene fa'idar hakan, anya kina da hankali kuwa, kuma ban faɗa miki cewa na samu matsalar account ba sai naje nayi babban gyara". Ta ɓata fuska tana mitar. "Ni don Allah Daddyn Iman ka daina yawan min faɗa akan irin haka, mecece miliyan ɗaya a wurinka Allah na tuba, cikin dukiyarka aka taɓa miliyan ɗaya me aka cira, amma a kwanakin nan sai wasu abubuwa ka ke yi akan kuɗi kamar wanda bai da su". Ƙugu ya kama da hannu ɗaya yana jijjiga ƙafa, ya fara zirga zirga ya rasa me ke masa daɗi. Ita dai tsayawa tayi tana kallonsa kafin tace,"Wai lafiya?". Nunfashi ya sauke me nauyi yace,"Wuce muje". Gaba tayi yana biye da ita a baya, har suka shiga mota bai daina mita ba akan kuɗin da ta taɓa, da yacca take ɓarnatar masa da dukiya saboda bata san zafin nemansu ba. Earpice tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da faɗan da yake ta mata tunda suka taho, kuma ba zata iya ci gaba da jin maganarsa da yake na zata basa takardun filayen da duk tace ta siya ai ba hauka ake a iya waɗanda ya mallaka musu ma ya ishe su, ko kuma ta basa na Noor tun da ita ta mutu. Har dai suka je asibitin bata ƙara ce masa kanzil ba tun bayan ce masa da tayi Daddyn Iman ka koyi son kuɗi yanzu ko baka da shi sai haka. Zuwansu aka fara bari a shiga ɗakin da Iyam ke kwance, Zahra'u ya bari ya tafi can office ɗin likita shi da Yaya Babba da Yayan Shago. Su Yaya duk suna nan zaune bakin ƙofa an zabga tagumi, Zahra'u ta miƙe ta shiga ciki, babu wanda ta kula a cikinsu tun da ta zo, Jamila matar Yaya Babba ma da tayi mata magana shareta tayi. "Ina wuni". Iyam na kallonta cikin wahalar ciwo tace,"Lafiya lau Zahra'u, kuna nan lafiya". "Lafiya lau, sannu Allah sawwaƙe". "Amin na gode Allah yayi muku albarka". Tana maganar ne tana kallon Iman da Zahra'u kewa wasa tana ta ɓaɓɓaka dariya. Nazifi ya shigo bayan sun gaisa ya shiga tambayarta yanayin yanda take jin jikin, yana kuma faɗa mata yanda suka yi da likitocin akan wataƙila sai an fita da ita waje acan za'a yi mata aikin ƙashin kwankwasonta, bai dai san yanda zai mata bayanin kuɗin da ake nema ba don duk wanda zai faɗawa cewa bai da adadin kuɗin da aka nema sai an ƙaryata shi. Sai yay jugum da ka gansa dai ka san yana da tarin damuwa a tare da shi wadda ke neman fin ƙarfinsa, Iyam ta lura da hakan ta tambaye shi ko wata matsalar ce yace ciwon nata ne kawai damuwarsa. Sam Zahra'u ƙin zama tayi a asibitin, shi kuma yace wallahi bata isa ta bisa ba tunda bata da mutuncin da zata iya zama a asibiti wurin mahaifiyarsa, saboda haka yana fita itama ta fito yana bakin titi yaga ta tari napep ta hau. Abun duniya duk ya ishe shi, jikinsa har wani ɗumi yay kamar me zazzaɓi. Ya rasa dalilin da yasa cikin ƴan kwanakin nan zuciyarsa ta addabe shi da tuna masa irin azabar da ubangiji ya tanadarwa wanda bai kwatanta adalci ba tsakanin matansa, ya sani ba wai bai sani ba ubangiji ba ya barin mijin da duk ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, jiya har da mummunar mafarki yay da har yau ya kasa gane ma'anarsa balle yasan in da ya dosa da musababbin yinsa. Kai tsaye gida ya wuce, yana zuwa ɓangaren Malam ya nufa. Sai da ya jima zaune yana jiran Malam ɗin kafin ya fito, bayan sun gaisa ne kansa ƙasa ya rasa ta inda zai fara magana. Malam dai kallonsa kawai yake yay guntun murmushi irin na su na manya yace da shi,"Ka zo ka saka ni gaba, da wani abu ne? Ko jikin mahaifiyar taku ne". Ƙeya ya ɗan sosa kan yace,"Dama Malam akan waccan maganar da na maka ne kwanakin baya". Yay maganar cikin kame kame. Malam yace,"Wacce magana kenan, abubuwan da yawa bana iya tunawa ba". Sai ya ɗago ya kalli mahaifin nasa kaɗan kafin ya kuma sadda kai ƙasa, shi kansa nauyin maganar yake ji to amma babu yanda ya iya haka dole yace,"Amm Amm akan maganar Sa'ida, na maka magana tun kafin ta fita idda sai baka ce komai ba, to yanzu ina so ne na shiga sahun manema aurenta don Allah a shige min gaba". Malam yay masa wani duba na baka da hankali, so yake ya mayar da shi mutumin banza, tun ba'ai wata biyu da rabuwan auren ba yake ta masa zarya, haka yay ta damunsa da kira shi lallai yana so zai dawo da matarsa. Malam kuwa bai basa fuska ba sam hasalima ranar farko da ya fara yi masa maganar sai da yay masa tatas to da yake ɗan yau ne baka haifi halinsa ba saboda rashin kunya bai fasa masa maganar ba, shi kuwa ko gani yay iyayen Sa'ida ma za su kuma basa ƴarsu ai sai ya hana. Har da zuwansa wajen Amarya itama zai kama ƙafa da ita ta taya shi shawo kan mahaifin nasa da ike idan tasa baki a magana Malam kan yarda, dan ko cikin matansa ma yafi shawara da ita. To itama dama sam bata ji daɗin rabuwar auren ba, don a lokacin ji tayi da ace ita ta haifi Nazifi babu abin da zai hana bata masa duka ba don bai wuce duka a wurinta ba. Shi yasa ko da yaje mata da zancen komen yana magiyan akan ta roƙa masa Malam tace masa,"Babu ruwana Nazifi ba za ka haɗa ni faɗa da shi ba kuma kaja mahaifiyarka ta zo tana jin haushina, kana dai ganin a irin yanda ku ka rabu da yarinyar nan ni ban ma zaton zaka iya cewa zaka mayar da ita ba, wallahi ce na ke ka shafeta a babin rayuwarka". Sau biyu yana zuwar mata da ƙoƙon bararsa taga kamar dai duk hankalinsa a tashe yake, sai ta basa shawaran cewa yaje gidan su Sa'idan ya samu mahaifanta ko ita ya nemeta ya bata haƙuri idan ta haƙura shikenan sai su sasanta kansu amma ita ba zata iya saka baki a sha'anin ba, babu ruwanta kar ta zo tayi baƙin jini kuma ya janyo mata faɗan kullum a wurin Malam. Lokacin jinsa yay tamkar zai hauka, bai san dalilin da yasa tunanin Sa'ida da al'amarinta da shi ba ya addabesa, tun da ya rabu da ita bai yi danasani ba balle nadama, imfact ji ma yake kamar ya rabu da wata ƙaya ne, kuma dama bai san ma shi ba sonta yake ba sai da ya auri Zahra'u, to a yanzu ma da suka rabu ba wai don yana sonta ne zai mayar da ita ba, ba don tausayi ko don ya wulaƙantata ba kamar yanda ya sha alwashi lokacin da aka tilasta masa sakinta, a'a haka kawai zuciyarsa ke faɗa masa cewa ya dawo da ita kamar hakan na da amfani a gare shi, kamar yana da buƙatarta musamman ma idan yaga halin ciwon da mahaifiyarsa ke ciki. Har magana yay da abokinsa Hamisu shima yace bai da shawarar da zai basa ta wannan ɓangaren, bai kuma isa ya tunkari Iyam da zancen ba, su Yaya ma duk ba zasu goyi da bayan hakan ba shiyasa ma babu wacca ya tunkara da maganar a cikin Yayyun nasa, balle yanzu ma da basa wata hulɗa da Yaya gaba suke a tsakaninsu. Sai daga baya yay amfani da shawaran Amarya yaje gidan su Sa'idan har sau biyu sai dai ya rasa ta yanda zai aika a kirawo masa ita, idan ma ta fito bai san me zai ce mata ya kawo shi wurinta ba. zuwansa na uku ne kuma suka haɗu da Abbaa ya dawo daga masallaci, lokacin Abbaa har ya shiga soro sai ya dawo ganin baƙuwar mota a ƙofar gidan, bai ma san Nazifin ba ne don har ya fito a motar ya durƙusa a gabansa suka gaisa bai ɗauka muryarsa ba. Kuma hakan sai yasa du ya diririce, Abbaa ma yay zaton ko cikin zawaran da ke zuwa wurin Sa'ida ne sai da yace masa shi ne tukunna Abbaa yace,"Ohh to lafiya, me ya kawo ka gidana?". Babu kunya kuma yake faɗawa Abbaan abun da ya kawosa wai so yake a basa dama ya shiga cikin manema auren Sa'ida. Abbaa ya dakatar da shi cikin ɗaga murya,"Hala sai da ka maku kafin ka zo ko? Manta irin rashin mutuncin da ka shuka mana kayi ne? Ko saboda wancan lokacin ban ce da kai komai ba shi ne ka samu zarafin dawo min gida saboda baka da ta ido...Ai Kai dai ba zan taɓa mancewa da butulu ba irinka, Nazifi lokacin da ka shigo rayuwar ƴata cikin gata da jin daɗi ka sameta, duk da burin da na ke da shi akanta haka na haƙura lokacin da ka nemi auranta na aura maka ita saboda ina maka kallon ɗana wanda zai kula da rayuwar ƴata ya ingatata, ashe ashe kai ɗin baƙin mijici ne ban sani ba, na baka amanarta ka ɓige da cin zarafinta da wulaƙantata saboda kayi kuɗi, har sai da ta kai ta kawo ka mata ƙazafin kisa ka ɓatata a idon duniya, kuma tsabar ka isa ka zo har gabana ka sakar min ita, sannan yazu saboda kai fitsararre ne ka sake ɗebo ƙafafun rashin kunyarka ka zo wurina kana roƙon na baka damar ka mayar da ita, ai ko a baya abin da ka aikata mata rashin sanar da ni ne da wallahi sai nayi shari'a da kai...Ka saki ƴata kuma kun rabu, ba zan lamunci raini da iskancinka ba wai zaka sake aurenta, to bara na faɗa maka in dai batun mayar da aurenku ne ka bar tunaninsa domin lamari ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, ni ba sakaran uba ba ne da zan ƙara yarda ƴata ta komawa wanda bai san darajarta ba...don haka kayi gaggawar tashi ka bar min ƙofar gida kafin na kira Imam ya fito yay maka dukan saɓa kamanni, ina ga rashin dakuwar shi ya baka lasisin dawowar mara kunyar banza da wofi". Ya faɗa yana kallonsa cikin fusata. A lokacin gaba ɗaya kasa yin wata magana yay haka ya kasa ɗagowa ya dubi Abbaan, kansa a sunkuye ya miƙe yana jin ƙafafunsa a sanyaye ya koma mota ya bar wajen, duka abin da Abbaa ya faɗa masa bai ji zafi ba kuma bai ji haushinsa ba, sai dai duk yanda zai yi zai yi wajen ganin ya dawo da Sa'ida gidansa. Malam ya katse tunaninsa da cewa,".... __________________________________ *Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.* *KWANTAN ƁAUNA* Nana Haleema *ƘAYAR RUWA* Halimahz *LOKACI NE* Oum Mumtaz *FARGAR JAJI* Aisha Yabo *WASA DA RAI* Fadila Yakubu Ɗaya ₦500 Biyu ₦800 Uku ₦900 Huɗu ₦1000 Biyar ₦1200 *Biyan Kuɗi Ta*👇🏻 6314170140 Fidelity Bank Sa'adiyya Zakariyya Haruna *Shaidar biya ta👇🏻* 09061794195 *Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰* #TeamFitattuBiyar [2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR22FT5* "Kai ɗago fuskarka ka kalle ni". Ya ɗago yana duban Malam ɗin wanda ke jifansa da mugun kallo. "Ka san dai ni ba shashasha ba ne, kuma ba sakarai ba ne mara tunani irinka, da hankalina kuma ni ba mutumin banza ba ne kamarka, don haka kar ka ƙara zuwa gabana da maganar wani wai kana so ka mayar da tsohuwar matarka...kai ban da ɗan banza ne baka da ta ido mutanen da ka nunawa rashin mutuncinka kace a koma a ƙara nema maka auren ƴarsu, to wallahi ko ji nayi za su sake baka ƴar su sai na hana...". "Don Allah Malam ayi haƙuri...". "Dilla gafara rufe min baki bana son jin komai, ka tashi ka bani wuri idan ka san abun da ya kawoka kenan, idan kuwa ka ƙara yunƙurin min magana irin wannan Allah sai ka ga yanda zamu kwashe da kai". Malam yay ta masa faɗa, shi dai a zuciyarsa bai san haƙiƙanin abin da yake ji ba, amma tabbas da Malam ɗin zai san a halin da yake ciki la shakka zai ji kukansa kuma ya karɓi roƙonsa. Sallama yaywa Malam ɗin ya fita cikin sanyin jiki, wajen Amarya ya shiga suka gaisa, ta kawo masa abinci ya zauna yaci, ita ma nan yay ta faman roƙo da magiya tace ita fa sam ba da ita ba wannan lamarin, yaje ya samu Ummaa suyi maganar. Yinin ranar dai gaba ɗaya haka ya wuni sukuku kamar wani mara lafiya. Bai koma gida ba sai sha biyu na dare ya bar asibiti wajen Iyam, lokacin da ya koma Zahra'u ta rufe ko'ina babu yacca bai yi ba akan ta buɗe ƙofar ta ƙi, kuma ba bacci take yi ba idonta biyu, zai kira ta ɗaga sai tace masa ya koma in da ya fito, ransa ya daɗa dagulewa, ga azababbiyar yunwa kamar bai ci abincin rana ba, kuma da zai taho ba yanda Anty Aisha bata yi da shi ya tsaya ya ci abinci ba yace ya ƙoshi domin idan ya zo a ƙoshe wani tashin hankalin ne na daban tsakaninsa da Zahra'u. Haka dole ya koma mota ba shi da yanda zai yi, ya buɗe baya yay kwanciyarsa. Ko da Asuba ma bata sakko ta buɗe ƙofar ba sai da safe wajen ƙarfe takwas kana, lokacin zata fita wurin aiki ta fito ko kallon wurin da yake bata yi ba, sai da ta shiga mota ta zo daidai wurin tasa kana ta zuge glass tace masa,"Ai yanda ka ɓarar min da aji kasa na hayo motar haya to ka dinƙi kurɓan baƙin ciki a gidan nan, yauma idan kaga dama kar ka dawo da wuri ka kuma zama a can". Tana ganin ya buɗe motam zai fito tayi sauri bawa motar wuta ta fice. A ciki ya samu ta kuma barin Iman yauma sai tsala uban kuka take, ba yanda bai da ita ba akan take tafiya da yarinyar in yaso ta samu me raino tace sam ita aiki kawai taje yi can ba zata dinga ɗaukan yarinya tana tafiya da ita ba, tama kusa yayeta na gaji da wahalar shayarwa. Ko wanka bai iya tsayawa yayi ba kitchen ya shiga ya dafa abin da zai ci, kamar ya san bata ajiye masa ba kuwa, bayan ya gama ya ɗora wanda zai tafiwa da su Iyam asibiti, matan ƴan uwansa kowacce ka ganta da coolern abinci amma shi ban da tasa. Bayan ya fito a wanka ya gama shiryawa ya sanya haƙarƙarinsa akan gado, idonsa na kallon sama kana gani ka san cikin harbawar sakan yay zurfi cikin tunani wanda har sai a iya zuwa ma ayi sata a ɗakin bai sani ba. Ya jima a haka kafin ya fita falo ya karɓo Iman wadda ke hannun Marawiyya tana ta faman lallashinta, ya zo ya zauna yana mata wasa tuni tayi shiru, can kuma sai tayi bacci ya ɗauketa ya kwantar da ita a ƙirjinsa, cikin shirun da yay sai ya tsinci gimlawar tunanin kiran lambar Sa'ida. Wayarsa ya ɗauko yay dialling numbern, tun ranar da ya saketa dama ya goge duk lambobinta da hotunanta, ashe akwai ranar da riƙe lambartata zata yi masa rana. Haka yay ta gwada kiran lambar bata shiga, sai can a koma ce masa a kashe take, ya jijjiga kai kar dai da gaske kamar yanda aka faɗa masa ta sauya layi ne, aje wayar yay a gefe bayan yanke shawarar zuwa yamma zai je gidan na su, ya san Sa'ida mai haƙuri ce da sauƙin kai, tabbas idan ta gansa zata ji tausayinsa kuma zata yi haƙuri ta dawo gidansa, wanda zai matuƙar son hakan ba don komai ba sai saboda Iyam, domin ya san in ace Sa'ida na nan babu dare babu rana tana kan zaryar asibiti babu gajiyawa babu ƙosawa, kuma cikin bawa mahaifiyarsa kulawa da kyautatawa, kuma atleast zai samu sauƙin damuwar da yake ciki a yanzu na wasu al'amura da ke neman cakuɗe masa, saɓanin Zahra'u da bai ma san ta yanda zai fara sanar da ita ba don babu ta yanda zata fahimce shi, batun sake aure ma kuwa tunanin hakan na zuwa kansa ya ke kaudar da shi amma Allah ya gani ya gaji da halin Zahra'u. ****Muna zaune ne a cikin staff room ɗin makarantar islamiyar da na ke koyarwa. Daga gefe na ke ina bitar littafin muwaɗɗa, ku san awa guda su Malama Mastura na aikin hira akan rayuwar zawarci, dama kusan duk Malamai matan mutum uku ne masu aure amma mu shida duk zaurawa ne, duk san da aka zauna ana hira sai naji suna ta faɗin ƙalubalen da suke fuskanta akan zaman zawarci, cikin gidan iyayensu ba sauƙi haka waje ma babu sauƙi, wasu cikinsu ma faɗi suke har gwara su zauna a gidan auren miji yay ta gallaza musu akan dai zaman gidan da suke yi ana tsangwamar su, ranar da Malama Alawiyya ke bamu labari har ƙwalla sai da nayi wai cikin gidansu kullum mahaifinta sai ya kyareta kuma sai ya goranta mata akan ta kashe aure ta dawo gida ta zauna, haka mahaifiyarta ma bata barta ba tayi ta faɗa mata magana komai nata ta hanata taɓawa har ce mata take tana lalata mata carpet saboda kwanciya, basu san buƙatunta ba komai ita kewa kanta da ƴar ƙaramar yarinyarta da ke hannunta, abinci kawai ake bata shima duk sanda za'a bata sai an mata mita, saboda haka ne ta nemi aikin koyarwar to shima mutane nata surutun yawon ta zubar take yi, Babansu kuma na faɗa mata ai ko aikin me zata yi bata dai da daraja a idon duniya. Hakan sai yay ta bani mamaki kuma sai naji fargaba ta kama ni, a raina sai na ce to ko dan ni mutuwar auren nawa ban jima ba ne shiyasa hakan bata fara faruwa da ni ba, ni ban san wani abu kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, gaskiya idan na buɗi baki na ce nafi jin daɗin gidan aurena akan zaman zawarcina to sai Allah ya kama ni, ƴan unguwa ne ma dai ke ta gulmace gulmacensu, wataran ma idan na dawo haka daga makaranta har na kanji ana ƙusƙus, Abbaa ma ina jinsa ranar suna hira da Ummani yana faɗa mata an fara surutu akaina ƴan unguwa don haka wataƙila zai yarda ne na tafi can school of nursing jigawan tun da ba a samu ta nan kano ɗin ba. Gaba ɗaya sai na saka damuwa sosai a raina don tunani bai wuce akan masu magana akaina ba, da kuma a zo nan ba da jimawa ba iyayena su fara min maganar aure don wataƙila ganin ban daɗe a gabansu ba ne, amma kuma sai ya kasance ko da yaushe Abbaa nasiha yake min da kwantar da hankali ta yanda damuwa bata da ikon samun muhalli a zuciyata, kuma da hakan na samu natsuwar ruhi da zuciya matuƙa ganin iyayena na tare da ni, Allah har mancewa na ke da wani suna bazawara ji na ke tamkar ban taɓa auren ba. Yayyuna kuwa babu abin da zan ce da su sai Allah ya saka musu da gidan Aljannah ya ƙara musu buɗi, gata dai iya gata da nuna tsantsar kulawa bayin Allahn nan na yi min, duk san da suka shigo gida sa tambaye ni ban dai da wata matsala ko na ce musu ehhh. Yashaik da kansa ya biya min kuɗin koyon ɗinki tun watarana da ya zo ya samu muna hirar da Ummani, wallahi ba ai sati ba sai kawai ganinsa nayi da form yace na cike anjima na kai gidan Maman Binta, ranar har kukan farin ciki nayi, to yanzu ɗinkuna na ke tayi kuma Allah yasa min nasibi a kaasuwancin. Duk wata kuwa idan aka bani dubu takwas ɗita a islamiyar da na ke koyarwa ba na riƙe ko sisi tawa yaran Yashaik da Yaya Imam na ke wa siyayya, sauran kuma in siyo omo da sabulun wanka da na wanki na aje mana a gida, Abbaa yay ta faɗa wai na ke rike kuɗina ina adanawa ko na ke siyawa kaina abu, ni kuwa banga amfanin kuɗin ba in har ban musu ba, to me ma na ke da buƙata wacca basa min? Ranar da na taɓa faɗawa su Malama Alawiyya na taɓa aure ƙaryata ni suka yi wai wallahi kwata kwata ban kama da wacca tayi aure ba, kar nayi wasa da damata na amincewa Malam Isah kawai tunda shi ba ƙaramin yaro ba ne da gaske aurena zai yi babu wasa a maganarsa, ni dai kawai nayi murmushi ban ce musu komai ba saboda Allah ɗaya ya san me na aje a zuciyata dangane da aure wanda ya fita gaba ɗaya a raina, ana hakan kuwa watarana sai Malama Aisha ke cewa ashe da gaske ne ni bazawara ce taji a staff room ɗin Malamai maza ana maganar wai Malam Isah yaje neman aurena ance masa na taɓa aure to yanzu ya janye maganarsa don bai san mene dalilin fitowar tawa ba, shi ne har Malam Amiru ke cewa dama baka shaidar mutum ta fuska, amma ƙila ganin ina da ƙuruciya ne yasa na kaso auren na fito ba zai wuce talaka na ke aure ba abun duniya kuma ya rufe min ido. Maganar ta tsaya min a rai, da na faɗawa Ummani tace ai sai na toshe kunnena akan maganganun mutane. Yau na dawo daga makarantar na samu wata Kakarmu ta zo, ban ma san da zuwan nata ba don har sai da nayi sallar magriba na fito zan ɗauko abincin rana a kitchen Ummani ke ce min idan na gama cin abincin na shiga ɓangaren Baba Tijjani na gaida Gwaggo Marka. Aje abincin na yi na ce bari na fara zuwa mu gaisa, ina zuwa kuwa na sameta cikin jikoki ana ta hira, da murnarta ta tarbe ni muka gaisa, take min jajen mutuwar aurena wanda sai da ta zo yaune ma take ji. Sai kuma ta shiga bani baki da shawara akan da na samu manemi nayi aurena kar dalilin mutuwar wannan in ce ba zan kuma aure ba, Umma ta sako baki tana faɗa mata ai ni da iyayena mun ci buri ba lallai na ƙara yin wani auren ba, don ko yanzu haka anata zuwa wajena ma bana fita Abbaa kuma ya ɗaure min gindi da kansa yake fita ma ya sallami mutum. Ai fa sai Gwaggo Marka ta kama faɗa sosai akan abin da Abbaa yake yi sam bai dace ba, idan shi bai sani ba ai ni suke zubarwa da mutunci, ni dai tana farawa hawaye tuni ya fara suntiri bisa kumatuna wanda na jima ban yi ba, tace na tashi muje can taji daga bakin iyayen nawa mene dalilin hakan kuma mene ribar hakan? Muka tafi da ita muna zuwa ta komar da faɗan kan Ummani wai wannan ba dacewa ba ne, ashe auren nawa ma sune suka shiga suka fita suka tilastawa mijin nawa ya sake ni. Sai da ƙyar Ummani ta fahimtar da ita shi ne fa ta sassauta murya kuma ta dafa kafaɗata ta shiga lallashina. Na ce mata ni ai ba zan ƙara yin wani aure ba zan zauna ne tare da iyayena, ina aiki ina sana'ata ya fiye min wani aure, tuni na cire sha'awar aure a raina da tunani duk wani ɗa namiji. Sai ta kama ce min ai zancen hakan ma bai taso ba domin akwai lokacin da zan zo da kaina ma ina buƙatar in yi auren, don haka gwara nayi abuna tun da ƙuruciyata ba sai lokaci ya ƙure min ba, amma ita zata fi so ma ace na komawa tsohon mijina idan an sasanta akan na kuma wani auren daban, a cewarta gwara na komawa wanda na riga na saba da shi na san halinsa, na ce Gwaggo Marka ba za ki gane rayuwar da nayi a gidan Nazifi ba ne shiyasa kike batun sasanci. Ni dai haka na baro ɗakin Ummani ina ta faman hawaye, ban ji daɗin fama min ciwon da Gwaggo Marka tayi ba, tuntuni na haƙa rami na binne Nazifi da duk wani abu da ya dangace shi amma shi ne yanzu take min maganar wani wai na koma masa, ai abun da ma ba zai yiwu ba kenan da waninsa ma ballanta shi. To a ƴan kwanakin da Gwaggo Marka tayi a gidan sai naji duk gidan ya ishe ni na gaji, ba don komai ba sai don takurawar da tayi min akan maganar aure yanda kasan auren nawa ya shekara dubu da mutuwa, na rasa irin wasu mutanen da kambaba abu, ta matsawa Abbaa ma akan lallai sai ya ƙyale ni na fara sauraron zaurawan da ke ta suntirin zuwa gurina, shi kuwa yace ai zaɓin a wurina yake idan ina so ai zan sanar da su da hankalina kuma na san inda ke min ciwo, sai ce tayi a'a ai har yanzu ni yarinya ce da ƙuruciyata dudu shekaruna nawa suke, kuma kar ya manta mace ma sai ta shekara arba'in take fara tunani irin na ɗan shekara bakwai. Duk haushinta ya tuƙe ni na ƙosa ta tafi ta bar mana gida, ga shi kome tace sai Kaka ya ara ya yafa dama ƙanwarsa ce, ranar ina jin Abbaa na yiwa Ummani ƙorafin shima ya fara gajiya da maganarta sai kace ita ke ciyar da ni ko kuma ina zaune ne akanta, Ummani tace yay haƙuri kwana nawa ne ma ya rage ta tafi ana gama bikin Hindatu ne. Ni kuwa dalilin haka sai na tattara kayana na tafi gidan Yashaik, tun da ba dama ayi sallama ace Sa'ida tazo zata ce da yaro jeka kace tana zuwa, kuma ba yanda na iya dole sai na je. Sai da daddare ne Yashaik na ta zuba idon yaga na fito na tafi Maman Yasmin take faɗa masa dalili yace to shikenan ai babu komai, har yake tsokanata yana cewa shima dai akwai wani ogansu a wajen aiki yace zai zo mu sasanta amma tsoho ne don zai yi shekara 70 sai dai akwai dukiya. Maman Yasmin ta kama cewa,"Allah ya kiyaye ya suttura can yaje wani wajen". "To ya idan ita kuma tana so fa?". Nayi saurin cewa,"Bana so ma Yashaik". Yaro ne yay sallama da cewa wai Sa'ida ta zo a waje, kaina na ƙasa na kama mamaki tunda dai ai Ummani ce kawai ta san ina nan, Abbaa kuwa wai ba zai zo yace masa yazo nan ba, to ko Gwaggo Marka ga sani ne? Yashaik ya dube ni yaga ban kai hankalina wurin ba tamkar ba sunana aka shigo aka ambata ba. Ya lura dai da gaske na ƙi jinin Maza yanzu. Sai naji yana cewa da ni,"Kun yi da wani zai zo wurinki ne?". Na girgiza masa kai da cewa,"A'a". Hannunsa ya tsame a cikin kwanon abincin da yake ci. Maman Yasmin ta zuba masa ruwa ya wanke hannu yasa hularsa ya fita. Daga ya leƙa yaga waye kuma shiru bai dawo ba har aka yi isha'i, muka yi sallah muka wuce ɗaki. Maman Yasmin ta shigo tana cewa da ni,"Sa'ida kin ga Abban Yasmin shiru tun fitar da yay". Na ɗago kai ina barin linke kayan yaran da na ke yi na ce,"To ko kiran wayarsa za ki yi". Tace,"Ai kinga wayar tasa nan ya barta, ko kuma can gida ya wuce, Amma dai da can ɗin ya tafi sai ya fara shigowa ya faɗa min, kinga ba sabonsa ba ne kaiwa haka a waje". Tashi nayi na sanya hijabina na ce,"Bara na leƙa mu gani". Ina fita ƙofar gida naga ba ya nan, sai na tsallaka wajen masu kankanar ƙofar gidan ina tambayarsu ko sunga wucewasa sai yake shaida min yaga sun fita shi da wani a machine. Ban koma ba na wuce gida, naje ma Ummani ta kama min faɗan na fito da daddare, na ce to ya zanyi naje gidan mata mijinta ya fita a dalilina muma shiru bai dawo ba, tace to shi ɗin yaro ne da za'a kama wani cigiyarsa. Sai tace ba zan koma na lallamata ta bar ni na fice Abbaa ma bai san naje ba. Na koma na faɗawa Maman Yasmin ɗin tana dai falo ta kasa zaune, kawai sai na tuna nima haka na ke fa idan ya fiata ya jima bai dawo ba, kai na girgiza na koma ɗaki na barta anan a raina ina cewa duk inda yake ma ai zai dawo. Shiru shiru kuma har sha ɗaya da kusan rabi Yashaik bai dawo ba, munyi jugum jugum lokacin don sinitin Maman Yasmin ya hana ni bacci har sai da naji inama ban zo gidan ba. Can muka ji ƙarar adaidata sahu a ƙofar gida, haka muka yi rige rigen fita ni da ita, yacca ya ganmu hankula tashe sai ya kama dariya yana cewa muyi haƙuri, to yanayin da muka gansa cikin farin ciki sai hankalinmu ya kwanta amma duk mun ƙosa muji ina yaje. Nan na bar su shi da Maman Yasmin na shiga ɗaki. Washe gari da safe na gama shiryawa zan wuce makaranta sai Yashaik ya kira ni, na zauna gabansa yake faɗa min jiya ai Nazifi ne ya zo wajensa. Gabana ba ƙaramin faɗuwa yay ba na ɗago ido ina kallonsa da jiran jin ƙarashen zancensa. Kuma lokaci ɗaya na tafi tunanin kwana biyu kenan da muka haɗu da Nazifi ina kan hanyar dawowata daga kasuwar rimi naje na siyowa Ummani kayan zoɓo. Ni na fara ganinsa a cikin mota na zo tsallakowa titin layinmu ashe shima ya ganni, ya fito daga motarsa ya biyo ni ta cikin layin da na shigo ina ta sauri ƙafata har harɗewa take yi kamar zan faɗi. Ya sha gabana yanda naga idanuwansa sai na rikice a raina haka kawai naji ko shaye shaye ya fara yi, ni dai tsoro duk ya cika ni na ture shi daga gabana ina cewa ya bani hanya, sai ya ruƙo hijabina yana faɗin na tsaya na saurare shi ba abin da na ke tunani ba ne ya kawo shi wurina. Ni dai duk a hargiste na ke ban san me yasa ganin nasa ya ɗaga hankalina ba na ke jin kamar irin ƴan iskan mazan nan ne suka biyo ni, haka na tsaya ina ta sauke numfashi ya kawo hannu zai taɓa fuskata na bige hannun nasa ina faɗa masa cewar kar ya soma wannan gangancin idan ba haka ba zan masa ihu na tara masa jama'a. Na faɗa masa hakan ina faman huci wanda shi kansa sai da yay mamakin yanayin nawa. Nace ya bani hanya na wuce sai ya kama faɗin wai dama zai gaya min ne Iyam tana asibiti watanta guda a kwance babu yanda take, yanzu haka ma anata cuku cukun fitar da ita ne za'a yi mata aiki wai ƙashin kwankwasonta ne ya samu matsala. Kaina a ƙasa na ce,"To ni mene nawa a ciki?". "Ba za kije ki dubata ba?". "Bisa wacca alaƙar da ke tsakani?". "Tsohuwar matar ɗanta mana, kuma surukarta". Na galla masa harara zan wuce shi don magana da shi ma ɓata lokaci ne a wajena na lura bai da hankali. Sai kawai ya kama cewa,"Sa'ida na zazzo gida Babanki yaƙi saurarena, kuma ya hana ni na ganki, dama so na ke mu zauna ni da ke muyi magana ki sanar musu cewa kina so a mayar da aurenmu, ina so ki dawo gidana ko saboda Iyam Sa'ida, na miki alƙawarin babu abin da zai ke haɗa ni da ke kiyi rayuwarki irin wadda kike so, ba zan takura miki ba, ba zan ci zarafinki ba, kawai ni dai ina so ne ki bawa Iyam irin kulawarki". "Amma dai baka da hankali da isassan tunani ko, kai wanne irin daƙiƙi ne da ka kasa lissafin rayuwa tsakanina da kai ta ƙare". Nayi maganar cikin doka tsawa ina zare idanu kamar wadda ta fita hayyacinta. Sai ya shiga takowa zai matso gabana na kuma waro manyan idanuwana ina dakatar da shi da faɗin,"Na rantse da Allah inci ɗaya ka ƙara tsakaninmu sai na ɗauke fuskarka da gigitaccen mari, kuma ka fita a rayuwata kar ka ƙara nuna ka sanni ko tsautsayi ya kawo ka ƙofar gidanmu". Haka kawai kuma a lokacin sai na samu kaina da fashewa da kuka wanda na rasa dalilinsa. Shi kuma sai ya samu damar faɗin,"kin gani ko, kema kina so ki dawo gare ni amma taurin kai ba zai barki ba, ki faɗa min yanzu idan ba ki yarda na dawo da ke gidana ba waye zai aure ki". Take na katse shi da cewa,"Wanda yake sona, ko an faɗa maka kowa irinka ne butulu ƙasƙantacce, haihuwar rashin arziƙi". Sai yay ƙasa da murya yana faɗin,"Haba Sa'ida ban sanki da halin rashin kyautawa ba, ki taimaka ki dawo gidana ina da buƙatarki". Na kalle shi da jajayen idanuna na ce,"Da dukkan alama a make kake, ko kuma ƙwaƙwalwarka ta samu matsala, ni zan dawo gidanka? Ka manta ni ce wannan mara wayewar, wadda bata jin turanci, wadda bata zuwa office, wadda bata iya soyayya ba kuma ƴar talakawa me satifiket ɗin sakandire, daɗin daɗawa Juya wacca bata haihuwa, Nazifi Bala Mai Kalwa mene amfanin mace irin wannan a gidanka? Menene abun buƙatar dawowarta gidanka?". Sai kawai na fashe da kuka sosai da yin maganar tawa, na duƙa ƙasa na ɗebi duwatsu ina jifansa da su na zama kamar wata mahaukaciya, kuma ganin zan masa rauni yasa ya bar ni ya tafi yana faɗin in sake tunani. Ranar haka na koma gida duk a firgice babu irin tambayar da Ummani bata yi min ba na kasa bata amsa har yau. Numfashi na sauke ƙirjina na bugawa sosai na ce da Yashaik,"Me ya zo yi?". Na faɗa da rawar murya. Sai yay murmushi yace,"Kwantar da hankalinki, wai ya zo ne akan maganar yana so ya mayar da ke, na faɗa masa har abada to muna haka ne sai ga Imam ya zo, shi kuma kin sansa zuciya a wuya kawai ya rufe shi da duka, yay masa jina jina a fuska har ta kai dai ga mun tafi station, don da ace kuna tsakar gida zaku ji yo hayaniya a waje". Idona ya cika da ƙwalla na ce,"Ku yi haƙuri Yashaik duk ni naja muku...". Ya katse ni,"Kinga duk manta da wannan karɓi wannan". Na sa hannu na karɓa envelop ɗin da ya miƙo min, ina ƙoƙarin buɗewa yace,"Bayan mun dawo Abbaa ya kira ni, wai anyi sallama da ke ya fita sai ya tarar da wani akan machine, yace masa aiko shi aka yi ya bawa Sa'ida. To gasu nan dai duka biyun takardar admission ne ɗauke da sunanki, duk Scholership ne da aka ɗauke miki ɗawainiyar komai tsawon shekarun da za kiyi karatunki ki gama, ɗaya University of Targu Mures ƙasar Germany, sun ba ki nursing studies, ɗayan kuma Scool of health ce Emirate za ki karanci Community Health..Ba'a san wanda ya kawo takardun nan ba Sa'ida amma kuma akwai phone number a jikin envelop ɗin na kira sai muka yi magana da shi Director na makarantar Emirate ɗin, yace Allah ne kawai ya kai sunanki wajensu kar muji komai idan zaki karatu to ki fara shirye shirye, babu wani abu da za kiyi komai an gama miki ko screening ba zaki yi ba...To mun yi magana da Abbaa shima yace Allah ne ya kawo miki, naji ta bakinki idan kina so shikenan, idan ba kya so shikenan". Tun fara maganar tasa kallonsa kawai na ke yi na kasa rufe bakina haka na kasa ƙifta idanu, ba zan iya tantance yanayin da na ke jina ba amma tarin tunanine fal a cikin kaina. Ta ina zan soma?.... *B2ƘR23FT5* Yashaik ya katse gajeran tunanin da na tafi akan wanda ya zama silar wannan babban tagomashin da na samu. Yes na yarda Allah ne ya ba ni to amma ta dalilin wa? Tun farko fara kalaminsa na cewa wani ne yaje gida ba a sansa ba Safiyya ce kawai ta faɗo raina, sai dai kuma anya Safiyya zata yi suprising ɗina ta haka? In har ita ce to lallai asubar fari zata kira ni don tana da wutar ciki, duk da suprise ne zata kasa haƙuri sai ta kira ni ta tona kanta. Maman Yasmin dai sai murna take yi baki yaƙi rufuwa, hannu ta ɗaga sama kawai tana godiya ga Allah, Yashaik yace,"Autarmu ba ki farin ciki ne?". Nayi figigit na ɗaga ido ina dubansa da fuskata wacca murmushi ya wanzuwa a samanta. "Ina farin ciki sosai Yashaik, kawai dai na rasa ta yanda zan kwatanta murnata, ban san yama zan yi ba, abun da ban taɓa tsammani ba ne Yashaik". Sai kawai hawaye ya sakko min bisa kuncina, hawayen farin ciki masu sanyi da sanyaya zuciya. "Yashaik amma ka faɗa min gaskiya wane yay min hanyar samun admission ɗin nan? Ni dai ku na ke kawowa a raina kai da Yaya Imam domin kune ku ka dage akan lamarin karatuna, wanda ko da yaushe cikin shige da ficen yanda za'ai na samu gurbin karatu kuke yi. Na kasa yarda da cewar dalilin wani daban da bamu da haɗi da shi na samu, ku ɗin ne dai Yashaik domin kune jigona". Ya murmusa da cewa,"Kin san idan mune kai tsaye ba zan tsaya ja miki rai ba zan faɗa miki gaskiya, amma na san idan kika ji daga bakin Abbaa za ki fi gasgatawa, yanzu dai ta shi ki wuce kar ki makara". Kai na girgiza cikin wani irin yanayi na nuna tsantsar farin ciki da jin daɗi na ce,"Yashaik makarantar yau kuma ai ta mutu, da ma voluntry ne saboda haka suyi haƙuri". Na faɗa ina miƙewa nayi ƙofa, Maman Yasmin tace,"Ehh lallai ne sannu hamshaƙiya, ki kwanar min a gida ba za ki min aiki ba za ki wuce, to dawo ki min wanke wanke, ni babu ruwana da wata Auta". Ta faɗa da sigar tsokana, ni dai ina dariya kawai na fice don Alla Alla na ke na ganni cikin gidanmu, don na tabbatar ba mafarki na ke yi ba. A soro na samu Abbaa ya fito zai wuce kasuwa shi da Yaya Imam wanda ke riƙe da ledar kayan Abbaa da yake fita da ita. Kawai a lokacin sai naji tamkar na rungume Abbana, amma duk da haka na kasa controlling kaina na faɗa jikin mahaifin nawa kunya tattare da ni, yayin da naji wani irin abu ya tsarga min a dukka ilahirin jikina, tabbas na sani ƙaunarsa ce, soyayyarsa ce, tausayinsa ne. Shima muryarsa na bayyana amon tsananin farin ciki naji ya ɗora hannunsa saman kaina yace,"Ko ranar ɗaurin aurenki ban ga farin ciki da murna irin haka a tare da ke ba Likitata". A kunyace na zame jikina ina durƙusawa na gaida shi. Ya amsa min as usual yana saka min albarka, Yaya Imam ma na gaida shi. Sai Abbaa yace,"Lafiya ba ki tafi makarantar ba?". "Abbaa ai ba zan iya zuwa ba ne yau, dama ina ta cewa Allah yasa baka fita kasuwa ba, Abbaa Yashaik ne yake faɗa min wata magana da na kasa gama yarda da ita sai naji daga bakinka duk da shima na san ba zai min wasa ba". Yace,"Yanzu muke zancen na ki ai da Babarki, dama ina ce sai kin dawo daga makarantar ne, muje to cikin, sai kika ga rabo daga Allah ko?". Yanda ƙarashen zancen nasa ya fita da wani irin emotion sai naji idona ya cika da ƙwalla, ni kuwa wanne irin rashin kyautawa na yiwa Abbaana, ashe haka na hana shi farin ciki, ƙwarai ba zan yafema kaina ba tun da har na zaɓi farin cikin Nazifi fiye da na Abbaana, kuma Allah ya isa tsakanina da shi da ya riƙe min hakkina na kuɗin makarantata da Abbaa ya bani ya hana ni, ai dama ba kyauta na ce na basa ba, idan da ya bani hakkina da yanzu wata maganar ake a karatuna, amma babu komai ga shi Allah yay min sauyi mafi alkhairi. Muna shiga ciki na samu Ummani na wanke wanke, tana ganina sai naga itama fuskarta cike da annurin da ya wadatu da farin cikin da ba zai misaltu ba. Na faɗa jikinta ina cewa,"Wai duk ya na ganku cikin farin ciki, kar dai da gaske ba mafarki na ke ba". Ta tsame hannunta cikin ruwan kumfa tana cewa,"Ai ko mafarkin ne yi adu'a ya zama tabbatace Sa'ida, wannan Al'amari ba zamu so ya tsaya iyaka mafarki ba, jiya ni da mahaifinki kasa runtsawa muka yi saboda farin ciki, wallahi ido biyu muka kwana muna ta adu'a don gani muke kamar mafarki ne ko kuma saƙe saƙen zuci ne da ba'a rabo da shi tun da an saka lamarin karatun na ki a rai". Buɗar bakina zan magana Yaya Imam ya zunguro ni ganin Zainab ƴar wajen Baba Tijjani ta taho. Muka yi shiru dukanmu ba don komai ba sai don dai ka san irin mutanen da kake tare da su dole ya yi takatsantsan. Muka shiga ɗakin Abbaa, ina maƙale jikin Ummani Abbaa ya kira sunana da cewa,"Sa'ida kinga lamarin ubangiji ko, wallahi yanda ake ta kai komo a karatun nan na ki shiru har na fidda rai na ce ƙila ba ki da rabo, ƙila Allah bai rubuta burina zai cika akan karatunki ba, ashe tuni Allah ya amsa adu'a, lokaci ne kawai zamu jira kuma ga shi ya zo, Allah Allah yasa alkhairi ne". Duka muka amsa da amin yayin da na ce,"To Abbaa wai shi wanda ya kawo takardun waye?". Abbaa yace,"Wallahi ban san shi ba Sa'ida, don kansa ma a ƙasa ni ba zan iya shaida shi ba, ga mahaifiyarki nan da na karɓo envelop ɗin na dawo wullar da shi nayi ce na ke irin shashashun samarin nan ne masu aiken wasiƙa, sai ta dage akan cewar a dai duba a gani, shi ne fa da Sa'id ya shigo na ce ya duba ya gani sai yake cewa ai wai takardun makarantarki ne. Na ce ina ai ba zai yiwu haka kawai bamu san mutum ba ya zo ya kawo takarda yace wai ya samar miki makaranta, mu ai ba iyayen banza da wofi ba ne, to sai kuma ga wani ɗan kati a jiki ya ɗauka ya kira lambar sai wanda ya ɗaga wayar yake cewa shi ko menene wani abu dai dareta ne ko?". Ni da Yaya Imam muna gajeriyar dariya muka ce,"Ehh Abbaa director". Yace,"Yauwa to dai shi, yay mana bayani yace wani bawan Allah ne da ya saba ɗaukar nauyin karatun ƴan makaranta sai aka haɗa da sunanki a list ɗin, shi Sa'id ma ce yay yana zargin wani mutum da suka taɓa haɗuwa acan makarantar da yaje dubo miki jarabawar intiro ɗin da kika yi...to dai ina ba ki labari shi dareta ɗin sai da muka kusa faɗa da shi saura kaɗan yay zuciya yace an cire sunanki saboda na takura shi da tambaya ina cewa ya faɗa min tsakani da Allah ba cutarmu za su yi ba". Abbaa yay maganar yana dariya, muma duk dariyar muka yi, yace,"Yo Allah kuwa magana ta tsakani da Allah, yanda duniyar nan ta zama babu gaskiya da amana sai a zo a yaudaremu a cucemu saboda anga abin da muke so kenan mun ƙwallafa rai akan samu, shiyasa ni kuwa nayi ta jefa masa tambayoyi ina yaji tsoron tsayuwa a gaban Allah, ke har da wa'azizzika na dinga masa ƙarshe shima sai ya sakko yana dariya, yace bai ga laifina ba duniyar ce ta lalace. To dai kinga ai sai muka samu fahimtar juna yay min bayanai sosai da na gamsu amma duk da hakan dai na sa Yayyunki su ƙara bincike akai". Na ce,"Abbaa ai ni da tunanina ma Suprise ɗin Safiyya ne, dama adu'a bata fi ƙarfin komai ba ina ta faɗawa Allah ya bani ta wata hanyar, sai ga shi ma Abbaa an ɗauke maka ɗawainiyar komai karatu kawai zan yi Abbaa". Haƙoran gabansa tass a waje yace,"To Sa'ida ko da ba'a ɗauke min ko sisi ba ai in har an ba ki gurbin karatun an gama yi min komai, ba ni da shi, ban tara ba, ban bawa wani ajiya ba, amma kuma Allah ne mai yi, ba zai hana ni ba, zai hore min na yi miki duk wata hidima da ta shafi karatunki Sa'ida, ni dai fatana Allah yasa ki fara a sa'a kema na ganki cikin kayan asibiti kina taimakon al'umma musamman talakawa, kuma ina roƙon Allah ya bani tsawon rai naga wannan lokaci, ke kuma yasa miki albarka a karatun. Sa'ida bana mancewa lokacin da za'a haifi Imam irin rashin rashin kirkin da malaman asibiti suka mana akan babu kuɗin magani da alluran da za'a siya, don Allah Sa'ida ki zama me taimakawa ba mai wulaƙantawa ba, kar kuɗi su rufe miki ido ki kasa taimakon al'ummar Annabi". Na sa hannu ina goge hawayena na ce,"In sha Allahu Abbaa, na maka alƙawari Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana, na gode na gode sosai Allah yay muku sakayya da gidan aljannah, ina son ku wallahi ina sonku Allah yasa kuci moriyar ɗawainiyar da ku ka yi akaina". Ummani tace,"To mora kuma na nawa Sa'ida, ai mu babu abin da zamu ce da ubangiji sai godiya da ya bamu ƴaƴa masu jin ƙan mu da tausayinmu, ke ma ƴar sana'ar da kike yi da ɗan albashin da ake baki ba ga shi nan ba yaushe rabon da mu sayi sabulu da omo da kuɗinmu, ai Alhamdulillahi Allah ya ƙara buɗa muku ya sawa nemanku albarka". Abbaa yace,"To yanzu ina kika zaɓa can ƙasar turawan ko kuwa nan dai in dai muka fi kauri". Kafin na ce wani abu Ummani ta riga ni da cewa,"A'a fa Abbaansu na faɗa maka ta dai yi karatunta anan, ni bana son wannan nisan, ina zamu turata ƙasar waje tana mace a'a tayi a gabanmu ta gama har Allah ya kawo mata mijin aure, ni dai ka ma cire batun bata wani zaɓi na in da take so". Abbaa yace,"To anji ta bakinki Hajiya Sa'a Babar Sa'ida". Sai ya maida dubansa garen yace,"Ina jinki ƴar albarka ina kike so? Baturiyar za ki koma ko kuwa dai kasar ki ta gado garin hausawa". Ina wasa da yatsun hannuna na ce,"Abbaa ni ai na bar muku zaɓin duk inda ku ka ce nan zan je, zaɓinku shi ne nawa". Sai Abbaa ya dubi Yaya Imam ya ce,"Imamu me ka ce? Kun san abin da kuka ce akan karatun nan shi ne, tunda kun fi mu sanin lamuran yanda suke, jiyan Sa'id yace aji ta bakinta tukunna". Yaya Imam yana kallon Ummani yace,"Ehh ya kira ni ai a daren jiyan muka yi magana, ni da ce nayi ai ba aure ba ne da za'a bata zaɓi, inda muka ga yafi a turata can ɗin kawai. to yanzu tunda ta baku zaɓi kawai ka yanke magana Abbaa, zaka fi mu hange da zurfin nazari". Abbaa yay shiru na ƴan daƙiƙa, ya numfasa kafin yace,"To da muka dawo daga masallacin asuba na yiwa ƴan uwana maganar, mun tattauna da su akai na faɗa musu duk yanda aka yi kun san sha'ani irin wannan abun da zai je ya dawo ake ji ba wani abu ba. To shi Babanku Tijjani yace idan za'a bi shawaransa a barta ta tafi can ƙasar wajen saboda samun ingancin karatun, namu da na su ba ɗaya ba ne. To Amma ya kuke gani Imam taje can ɗin ko nan ɗin?". Yaya Imam yace,"Ke ki faɗa da kan ki, can ɗin ko nan?". Nayi shiru, Abbaa ya numfasa kafin yace,"To ni dai har ga Allah sallar da nayi a jiya ta istikara zuciyata tafi samun natsuwa da fitar taki Sa'ida, kuma dama zaɓin Allah shi muke nema, ni na yarda da ke na kuma yarda da irin tarbiyar da na baki, sannan na yarda da Allah ne me kiyayewa da karewa, wayonmu ko dabararmu ba su zasu mana ba, adu'a ce muna miki kuma ba zamu fasa ba, Allah zai tsare mana ke sannan kema kuma ki tsare mutuncinki. Naga ƴaƴa mata da yawa da suka fita karatun nan suka yi lafiya suka gama lafiya, ni dai roƙona a gare ki kiyi abin da ya kai ki Sa'ida, ba yinmu ba ne yin Allah ne, kuma ya dubemu ne ya dubi kyakykyawar niyayyarmu ta manufarmu akan karatunki, ki taimaka min Sa'ida kar ki bani kunya, kin dai gani irin yanda ƴan uwanki suke ta fafutukar nema miki ta gwamnati ma ba'a samu ba, amma Allah da ikonsa sai ya ba ki rabo a inda bamu taɓa tunani da kai kanmu can ba don sun fi ƙarfinmu, ko ba ƙasar waje za ki fita ba Sa'ida ko anan za ki zauna nasihar dai duka ɗaya ce, idan kika kiyaye sai Allah ma ya kiyaye ki, kin dai sani kaf danginmu babu me ɗaukarki ya kai ki wannan makaranta me tsada ta ɗururuwan kuɗaɗe, to amma da ke abun na Allah ne muna zaune sai ga shi ya kawo miki. Allah yay miki albarka, Allah ya lulluɓe rayuwarki da kariyarsa, ya ba ki sa'a da nasara a karatun nan da za ki fara". Dukanmu muka amsa da amin, ni dai gaba ɗaya jikina ya mutu. Sai kuma Abbaa ya sake cewa,"Amma kar ki yi maganar da kowa tukunna ki bari sai tafiyar ta kankama, sha'anin rayuwar nan kake ji baka sanin zuciyar wamda kake tare da shi, wani yana nan bai son ci gabanka amma a fuska yana nuna maka ya fi kowa sonka, to ki bar abun da ke sai ahalinki duk wanda za ki faɗawa ki jira zuwa ranar tafiyarki sai ki kira waya kuyi sallama cikin aminci...nan da sati na sama naji ko?". Na buɗe takardun na miƙawa Yaya Imam ya duba yace,"Ehh litinin ta sama kenan ban da wannan me zuwan". "To yanzu me da me ya kamata a siya mata, kuma wanne shirye shirye zata yi?". Yaya Imam yace,"Ai ina ga abun da zata tafi da su ba zai wuce kayan sawarta ba, idan ma da wani abu dai in taje can ɗin ta kira waya ko kuɗi ne sai a tura mata". Kawai sai naji jikina yay sanyi, na fara tunain yanzu idan na tafi sai fa na shekara uku kamar yanda na ke gani rubuce a jikin takardar. Anya ba zan fasa tafiya can ɗin ba duk da nima dama nafi so ta fita ɗin, to amma ya zan yi Abbaa har istikara yayi zaɓin Allah kuma ya nema, Allah yasa zuwana can ɗin babban alheri ne. Yashaik ya zo Abbaa ya jaddada masa akan kar ya manta yaje can Emorate ɗin yaga Director ɗin ido da ido sannan yay bincike sosai akan lamarin. Ina komawa ɗaki na ɗauka wayana na kira Safiyya, bacci take yi a lokacin amma jin albashiri ɗin da na zo mata tuni ta warsteka tana cewa,"Ke ba na son wasa da feelings ena". Nace,"Wallahi Tallahi da gaske nake yi miki". Wani ihu tayi tana faɗin,"Wow what a great news Beb, admission a germany kuma nursing wow Beb am so happy for you wallahi, wanda yay miki silar nan ubangiji Allah ya haɗa shi da dukkan alkhairan duniya, ina ma zan gasa na masa kyauta. Yanzu yaushe ne ake batun za ku tafi don naji wata cousin ena ma na maganar tafiya can?". "Sati na sama Beb, amma dai za ki zo kafin na tafi ko?". Shiru ta ɗanyi kafin tace,"Da wuya na zo nigeria cikin week ɗin nan, kin ganmu muna Saudiya mun je Umrah jiya muka tafi, amma kar ki damu kina makaranta zan kawo miki visiting". "To ƙawar arziki Allah ya amince sai na ganki, ki faɗawa Umma ma kin ji". Da yake dai Safiyyar tawa sai a hankali sai ce ta min,"Ke wacce Umman mun yi faɗa da ita fa ba ma magana, ki kirawota da kan ki". Kai na girgiza na ce,"Allah ya shirya min ke wallahi, yanzu da Umman ku ka yi faɗa?". "ƙwarai aure ma zan zuga mijinta ya ƙara, ba dai ganin bata da kishiya ba ne yasa duk take takura min akan sai nayi aure ba, ki ji fa jiya tutsiye ni tayi wai lallai sai na bata lambar My ta kirawo shi ya zo anyi maganar aure". "To mene abin laifi a ciki Beb, ai da gaskiyanta ke fa da kanki kin faɗa min yanda kike ta shan surutu a family na ku akan kin ƙi aure, kuma kin ga idan ke ba kya damuwa ita Umma dole zata damu, burin kowanne fa iyaye ne su ga sun aurar da ƴarsu wallahi hankalinsu yafi kwanciya". Daga yanda naji tayi shiru na san jina kawai take, ma'ana in gama mu ɗora da wani zancen. "Kika min shiru". "Ina jin ki ai, ni an faɗa miki irinki ce da maganar mutane ke damuna, wanda ya fasa cewa nayi kwantai yaci uwatas, idan mutum shi ke ci da ni ko a makwamcinsa na ke kwana duk ya ƙwace...ni na faɗa mata ta toshe kunne daga duk abin da zata ji, aure lokaci ne idan ya zo duk ƙina da shi fa sai nayi kamar mutuwa yake, ni dai kawai a min adu'a don wallahi tun a kanki na ke tsoron maza Sa'ida, Nazifi ya girgiza duniyata, amma ɗan bantan uba ai very soon zan girbe abubuwan da ya shuka, Allah ubangiji ya kawosa gabanki yana kuka". Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Sai na kwantar da murya ina mata nasiha ina bata shawara akan dai ta tsaya ta fidda mijin auren shi yafi, tun da tana da masoya masu sonta tsakani da Allah, kuma tayi karatun nan har ma tana da aikin yi to me ya rage mata kuma? Fitar nan da take tayi a har business ɗinta sai surutu ake akai to baka san bakin wani ba. Mun daɗe muna wayar da ita kafin muka yi sallama bayan ta haɗa ni da Ummaa a confrence call, wallahi Safiyya ƙawar ƙwarai ce muna gama wayar sai ga alert ɗin 30 tayi min wai gudunmawarta na tafiya makaranta. To cikin satin gaba ɗaya sai na zama cikin shire shirye, Abbaa kuwa kace zai min sabon aure sai faman siyo min atamfofi yake da shadda yana cewa na ɗinka abina duk da ba masu tsada ba ne, sai yace wai dai idan naje can aga ƴarsa fes fes da ita. haka Yaya Imam ma da yake yanzu turaruka yake saidawa da kayan kwalliya ya kwaso min kaya ni duk sai na ke jina ma kamar nafi kowacce mace gata da samun dacewar family, Yashaik kuwa shi ne da siyo bandir ɗin littafai da biro da ɗinko min hijabai. Hajiya Ummani kuwa ina gefe ina mata dariya, ta jidi uban shinkafa kusan rabin buhu tasa aka yo taliya ƴar murji kwano biyar wai na tafiyata, har da su ɗauko tsohon risho da muka daina amfani da shi tun da kalanzir yay tsada, ta wanke shi tass ta saka a bakko leda. sai da Yaya Al'amin yace mata ai duk ba'a tafiya da su tun da ni cikin hostel zan zauna ba gida zan kama ba, ko su man abinci ma duk ba'a tafiya da su, yaji ne da maggi kawai, sai ta siyar da shinkafar dama da cuku cuku ta haɗa kuɗin ta siya, ta aika kuɗin ƙauye a auno mata barkono kwano goma za'ai farin yaji da na daddawa, ni dai dariya kawai na ke yi, a gefe guda kuma ina ta jin tausayin iyayen nawa, ba damar suji kuɗi hannunsu sai su ce na tambayo me ake tafiya da shi a siya min, Ummani da taji kuɗi hannu sai ta ban tace sauri je ki rimi su ba ki haɗin maggi, haka ta daka min maggi kusan toba biyar irin manyan nan na zuba spices. Ana saura kwana uku tafiyar tamu Abbaa yace na shirya naje ƙauye muyi sallama da ƴan uwa na can, tare da shi muka je muka yini acan sai dare muka dawo, wallahi ranar duk sai naji tamkar sallamar ƙarshe na ke da mutane. Ana gobe zan tafi na jajje gidan ƴan uwanmu na amana suma na musu sallama, maƙota ma duk na shishshigaa su duk tare ma muka shiga da Ummani, kowa muka je sai ya tayani murna yay min adu'a. Da daddare ina ɗaki kwance na gama haɗa komai nawa nayi lamo ina ta tunani daban daban, sai naji ƙwala kiran Yaya Imam, na fito na same shi ya miƙo min leda baƙa babba, na buɗe naga takalma ne masu kyau da ƙarko guda huɗu ya siyo min, na gwada duk suka min nayi ta masa godiya har da ƙwallata. Bayan sun yi sallama da su Ummani zai wuce gida yace min,"Goben kin ga ƙarfe bakwai suka je jirginku zai tashi, don Allah sai ki daure ki kammala koma daren yau da kin yi asuba ki fito da kayan ki, na yiwa wani me adaidaita maƙocinmu magana daga masallaci zamuyo nan ko gida ba zan shigo ba". Na ce,"To Yaya". "Kar fa sai mun zo ki dinƙa tsaye tsaye". Da haka ya fita. Ummani tace,"To tun da haka ne kinga shiga kiwa mutanen gidan sallama ba'a zo ana tashin su da sanyin asuba ba". Wucewa nayi ƙafafuna a matuƙar sanyaye, na fara shiga ɓangaren Baba Sabi'u na jima a can shi da Umman su Hindatu suna ta min nasiha, wacca ta ƙara sanyawa jikina ya mutu duk nayi la'asar, kafin na fito na tafi ɓangaren Baba Tijjani, nan dai Baban ne yay min faɗansa da nasihohinsa, Umma kuwa kyaɓe baki tayi kawai tace Allah sa ayi abin da aka je yi, ƴaƴanta kuwa babu wanda yace min ci kan ki, saɓanin ƴaƴan Baba Sabitu da naga ƙauna cikinsu har da masu kuka. Kaka ma a daren muka yi sallama da shi, daren dai ni ban wani runtsa ba, kamar yanda zan ce Abbaa da Ummani ma duk basu runtsa ba don ina jiyo sautin maganarsu cikin dare sanda na fita alwala. Da asuba ana idar da sallar asuba Abbaa ko shigowa gida bai ba sai ga adaidai na horn a ƙofar gida, cikin sauri kuwa na fita gudun mita irin ta Yaya Imam, Yaya Al'amin ya bani wani agogo yace amma idan na tashi dawowa na taho masa da na ƴan gayu nace an gama Yayana, lokacin Abbayo ya kira waya shima muka yi sallama da yake ya koma can Ibadan ɗin tuni. A ƙofar gida muka tsaya sai da muka jira Abbaa ya dawo wai ya tsaya ne ayi sadaƙa. Haka muka ɗunguma muka tafi airpot, Yaya Imam a adaidaitar da Kayana suke, ɗayar da Yashaik ya aro kuma shi ke tuƙa mu da ni da Ummani da Abbaa da Yaya Al'amin, Ummani dai tun da muka taho take ta matse hawaye, nima kuma kukan bai zo min ba sai da muka je aripot ɗin. Duk ƙin tafiya suka har aka gama clearing ɗinmu, lokacin da aka kiramu na tashi kenan sai naji wayata tayi ƙara ina dubawa naga an turo min saƙo ta gmail ɗina daga wani banki wai suna taya ni murnar buɗe doller account da su. na aje mamakina a gefe na tafi wurin ahalina muna sallama, nan kuka ya ƙwac e min sosai har da su majina, da ƙyar na iya juyawa na bar wajen shima sai da naji ana ta sanarwar nan da mintu biyu jirgi zai tashi, Abbaa yace,"Sa'ida je ki Allah yay miki albarka ya tsare hanya, kina sauka ki kiramu ɗin kin ji, Imam yay miki canjin kuɗi yace suna ƙaramar jakar da Babarki ta baki babu yawa dai duba ashirin ne daga baya in sha Allah za'a karo miki, Allah yasa ki dawo ina da tsawancin kwana". Ƙafafuna naji suna neman kasa ɗaukata su tafi da ni, saƙo ya kuma shigowa wayata, cikin gudu gudu saurin tafiyar da nake na duba sai naga saƙo daga wata lamba ta ƙasar waje, cikin harshen turanci da cewa. _"Safe flight, Allah ya tsare hanya, a maida hankali a karatu first class muke so, a kula don Allah, amanar kanki"._ Har na shiga cikin jirgi ina murmushi don na san bani da wani me min messge irin haka sama da ƙawata Safiyya, sosai na ƙara jin sonta da ƙara ƙudurin kyautata mata idan har Allah ya ida nufi burina ya cika. Awan mu shida zan ce keman a jirgi muka sauka a ƙasar Germany, lokacin da na fito daga jirgin na kalla garin na shaƙi iskar sai naji tamkar komai mafarki ne, Allah kenan, ko da wasa, ko a tunani ban taɓa haskowa kaina zuwa irin wajen nan ba. Hatta tsohon mijina da yay kuɗin bai taɓa lissafin cewa zai kai ni saudiya ba ma, dama ita kawai na ke da burin ace yau na hau jirgi na ziyarci ɗakin Allah na kuma kai ziyara ƙabarin manzona. Kawai sai naji sabbin hawaye sun sauka a kuncina, ba na baƙin ciki ba ne ko damuwa ko kewar ahalina, a'a kawai ji nayi nasa rai da rabon zuwa makkah, kuma ina ji a jikina nan kusa ubangiji zai kira ni. Muna zaune ka wasu kujeru mu da muka zazzo daga nigeria ƴan makarantar, sai ga wani farin mutum dogo gashinsa kamar na larabawa, ya duba ƙaramin katin hannunsa yana tambaya wacece Sa'ida Salman Madobi, sai na ce masa gani yace an ce ya zo ɗaukana ne, sai na dubi sauran ƴan uwan tafiyar tawa, na ce su taso mu tafi sai yace ai ni kaɗai ɗin dai. Kamar ba zan tafi ba duba da cewar ya za'ai mun zo tare kuma duk makaranta ɗaya can zamu nufa ya zaman ni kaɗai ace an zo ɗaukana, sai wani Saurayi cikinmu yake cewa naje kawai ai ba wata matsala ba ce. Nace to nan na nunawa mutumin kayana, ya kwasa sai rawar jiki yake yana kirana da Madam, yana saka kayan a both ɗin mota zai haɗa da wata green ɗin jaka sai nace masa ba tawa ba ce, sai yace min a'a tawa ce an ba shi ya taho min da ita, amma gata ma na riƙe a hannuna. Na karɓa na shiga motar da adu'ata, duk na ƙosa na samu sarari na siya sim na kira gida na sanar musu mun sauka, ai ko ina cikin wannan tunanin sai drivern ya juyo yana bani layin waya yace na saka, na karɓa na saka da murnata ina ta masa godiya kuwa, ni dai a tsammanina tun da ya bani ai ƙila kyauta ne ake rabawa ɗalibai. Ba'ai minti biyar ba da ɗora layin naga shigowar saƙo da cewar,_"Fatan an sauka lafiya, Allah ya bada abin da aka zo nema"._ Wani sanyayyan murmushi na yi a fili na furta,"Zan kira ki ƙawata, ina son ki Allah ya bar mu tare". Wayar na aje gefe na buɗe green ɗin jakar da na ke ta tantamar tawa ce, sai dai ina buɗewa mamaki ya kamani matuƙa da uban kuɗin da na gani a ciki wanda aka rubuta Euro a jiki, sai na ɗauko kai zan wa drivern magana na ce masa wannan ba tawa ba ce, sai maganar ta maƙale dalilin shigowar wani cikin motar wanda ya zauna a gaba, kansa da p-cap fara kansa a ƙasa ya kuma sanya face mask. Gabana naji ya yanke ya faɗi ba tare da sanin dalili ba, ina aikin zare ido naji an jefo min abu jikina, ɗaga idon da zan yi na duba sai naga face maske ce, Drivern kuma sai ya katse tunanin da na ke da cewa,"Madam kisa face mask saboda zamu tsaya ne a shopping mall makaranta ta ba da umarnin haka". Fuskata a ɗaure na ke duban drivern, so na ke nayi magana to amma ina tsoro tun da ba hausa zan yi masa ba, kar nayi turancin nayi kwaɓa, to amma haka dole na dage na tattaro guntun turancina na ce masa,"Shi baƙon da ka ɗauka bai san darajar ɗan Adam ba ne da zai wurgo min abu jiki, ko ba zai ba ni da hannu ba ai sai yace na ɗauka". Sai ya kama ba ni haƙuri, ni kuwa duk da haka naƙi ɗauka sai ma cilli da nayi da shi gefe, muka iso bakin wani babban mall motar tayi parking, motar ma bata gama tsayuwa ba na gaban ya fita cikin sauri ya shiga mall ɗin, ahi kuma drivern yace na fito na shiga ciki duk abin da na gani na ke na ɗauko makaranta ta riga ta biya kuɗin. Na fito ina jin ƙafafuna na harɗewa, haka na tsaya kusan minti biyu ina ƙarewa wajen haɗaɗɗan mall ɗin kallo kafin a hankali nayi bismillah na fara takawa. Ina hawa kan step na biyu na duba saƙon da ya shigo wayata wanda ke cewa _"Mace me daraja bata yawo a ƙasar sai da face mask, ki ke rufe fuskarki kin ji"._ Murmushi nayi kawai na juya motar na ɗauko face mask ɗin yayin da na ke bin bayan kiran lambar Safiyya. ____________________________ ₦500 07018098175. *B2ƘR24FT5* Nazifi ne zaune a ƙasa kan carpet, gefensa mug ne da ruwan tea a ciki wanda yaji haɗin kayan ƙamshin shayi yake kurɓa a hankali a hankali, yayin da laptop ke kan cinyarsa sai takardu a gafen hannun hagunsa duk a barbarje. Wayarsa da ta yi ƙara ya dakatar da danne dannen da yake cikin laptop ɗin, ya ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa yace. "Wallahi kuwa ka ganni na kusa minti ashirin akanta na dai kasa fahimta, amma kuma na yi ƙoƙarin shigar da wancan document ɗin na dukka bayanan kamfanin, na samu Madam tayi min aikinsa, shi wannan ɗin ne dai na ke so zuwa anjima idan na fito sai ka duba kuma ka koya min saboda gaba ko". Daga can ɓangaren aka yi magana kafin shi kuma ya ƙara cewa,"Oak oak tom shikenan babu matsala duk yanda ka gani ɗin dai zai yiwu, tun da ni ba sanin harkar na yi ba kuma na yarda da kai ɗari bisa ɗari, na san ba zaka jefa ni hanyar da zan cutu ba. Amma kamar nawa ka ke ganin zasu iya ba ni bashin?". Shiru na ƴan sakanni yace,"Biliyan ɗaya! amma Alhaji Sunusi kana ganin zan iya requesting hakan kuwa? Basu yi yawa ba? Ka san yanda sha'anin kasuwancin yake duk ya taɓarɓare kar azo in karɓi kuɗi masu uban yawa ba fata ba azo a samu matsala". Ya kuma yin shiru na kusan minti uku yana sauraron na cikin wayar kamin yace,"Ehh ai shi ne abun dubawar da na ke faɗa maka. Ka san girman Allah Alhaji Sunusi kwata kwata ba zan ce maka ga ta inda nayi asarar waɗancan kuɗin ba, duk buge bugen lissafi da bincike wallahi na rasa ina miliyan ɗari da hamsin ta shiga, to amma ka san kowanne bawa Allah na jarabtarsa, na bar hakan matsayin ƙaddara sai adu'an Allah ya mayar min da alkhairi, ƙila wani mugun abun ne ma yake shirin faruwa da ni sai Allah ya kare hakan lamarin ya sauka akan dukiyata". Ya ƙara yin shiru sannan yace,"Amin ya Hayyu ya Qayyum, kaga har yanzu wallahi cikin iyalina da iyayena babu wanda na faɗawa, bab na so su shiga damuwa, ni kaina haka dai ina rayuwa ne kawai, tunda ka san duk wata ɗawainiya ta ahalina akaina yake, ƙannena da kowa nawa da ni suka dogara, idan suka ji cewan na rasa komai nawa zasu shiga tashin hankali...Amma dai mahaifina zan sanar da shi a yau ɓoyewan bai da amfani, muna da su a raye dole mu buƙaci adu'arsu, ta hakan Allah zai ɓullo da mafita. Yanzu ka nemi waɗanda zaku yi maganar sayan waccan plazar ta Kabuga, ka san ita kaɗai ta rage min dama, a ciki na ke so na fitar da kuɗin da za'ai wa mahaifiyata aiki sauran kuma kaga sai a wari wani abun da ko shago ne a buɗe kafin su banki su bamu aron kuɗin sai a tayar da kamfanin shinkafar". "Yauwa na gode fa, ina godiya sosai da sosai Alhaji Sunusi, Allah ya bar zumunci. A gaida iyalin". Daga haka wayar tasa ta ƙare ya ajiyeta gefen gado, laptop ɗin ya kashe kana ya shiga tattara takardun gabansa yana shirya su. Sai bayan ya gama ne ya ɗauki wayarsa ya danna lambar Yaya, ta ɗaga yake tambayarta sauƙin jikin Iyam tace masa kamar dai kullum don yauma ko buɗe ido bata yi ba, yanzu ma take shirin ta kira shi sun jisa shiru yau bai leƙo ba. Da muryan bayyana tarin damuwa yace mata,"Na ɗa tashi ne da uzuri amma jimawa kaɗan zan leƙo, ko da Iyam ɗin zata farka ta tambaye ni kya ce mata lafiya lau ba wani matsala aiki ne ya ɗan tsare ni". Yayan tace,"To shikenan". "Jiyan da ta farka ta samu taci abinci kuwa?". Yaya da ke kusa da Iyam tace,"Wallahi bata ci ba, ta dai ce tana son ferfesun kifi to kuma kaga dare yayi a lokacin, ka ma fa san likita ɗazu da ya zo ce yay sai an saka mata robar abinci". Ya furta kalmar innalillahi yana jin wani gumi na tsatstafo masa, duniyar gaba ɗayanta yaji ta ƙara yi masa nauyi aka. a sanyaye yace,"Allah ubangiji ya kawo mata sauƙin da ba za'a kai ga hakan ba, yanzu bara na kira Lubabatu sai na tura mata kuɗi tayo cefane ayi mata ferfesun, ƙila idan ta farka ɗin ta samu ci, yanzu ma dai zan gaggauta na taho". Tace,"To shikenan. amma ya ku ke ciki da maganar iyayen Zahra'un?". Ya sauke numfashi kana yace,"Yaya lamarin na su dai sai haƙuri, amma ni na faɗa musu ina kan bakana babu wanda ya isa ya raba ni da abin da Allah ya bani". Itama ta numfasa murya a hankali tace,"To Allah ya kyauta, amma lamarin nasu akwai son zuciya da rashin addini, yanzu dai kai zaka ta iya bakin ƙoƙarin ka shawo kan matarka kasan mu mata akwai daru idan lamari irin haka ya tashi, sai an ta faman lallashi tukunna". Ya shafi kansa da cewa,"Ai Yaya Zahra'u ma gaba ɗaya bata jin wani rarrashi wallahi, shiyasa na faɗa mata idan ta gaji ne to ta faɗa min kawai na sawwaƙe mata, ni ba zan iya da wannan tashin hankalin ba, rabona da samun kwanciyar hankali a cikin gidan nan wallahi Yaya har na manta, idan na tuna ma abin da na miki kan sharrin da tayi miki kar kiji yanda raina ke sosuwa". Yaya tace,"Allah ya kyauta wancan kuma ai ya wuce, hannunka bai taɓa ruɓewa ka yar, ciki guda muka fito kuma na fika hankali da shekaru da sanin yakamata, kaga ni ba zan bari zumuncinmu ya taɓu ba.... Yauwa jiya muna magana ma cajin wayar tawa ya ƙare sai yanzu zancen ya faɗo min, Kai Nazifi me ya shiga cikin kanka har kake tunanin dawo da Sa'ida gidanka?". Yay shiru bai ce komai ba. Ta sake cewa,"Magana na ke maka, kai kace kana neman shawara ko ba haka ba". Ya murza goshinsa kuma haka kawai sai yaji wani abu ya motsa a ƙirjinsa kan yace,"Kawai dai Yaya na ji ne ina so na dawo da ita ba tare da sanin dalili ba". "To wallahi ka sauya tunani ka yiwa kanka faɗa, me ya kai ka? Allah ya rabaka da ƙaya kuma ka ke neman sake janyowa kanka masifa, yo masifa mana zama da wadda bata haihuwa duk da Allah ya baka me haifa maka yanzu, to ni dai in har na kai na baka shawara ka cire tunanin dawo da ita, in ba haka bayan kashe maka ƴa da tayi ta dawo wannan karan zata ƙarasa kashe maka mahaifiya ne kaima kuma ta kassaraka ta barka gaya, don ba zaka yi aune ba zata kwashe duka dukiyarka tun da dai bata haihu ba". "Tom shikenan Yaya, dama daɗin shawarar kenan, ni ban yi wannan tunanin ba. sai na shigo asibitin". Suna gama wayar ya kwantar da kansa jikin filo yana kallon saman ɗakin, zuciyarsa cunkushe take yana ta aikin tunanin yanda zai samu mafita, mafita akan abubuwa da yawa da suka tsaya masa yanzu ciki kuwa har da son dawo da Sa'ida, ita ɗin kuma hr yanzu ya kasa gane dalilinsa na so ya dawo da ita gidansa, duk da cewa da yaje yana faɗawa Yayan Shago cewa ya taimaka ya shige masa gaba kan shawo kan iyayen Sa'ida ta dawo gidansa, Kai taye Yayan Shago yace shi kam ba da shi ba, ai dama ba'a sanin darajar abu sai an rasa shi, ya kasa gane Sa'idan na da muhimmanci a wurinsa sai yanzu ne saboda bai da kunya bayan duk irin wulaƙancin da yay mata sannan zai ce zai dawo da ita. Iska ya furzar me zafi daga bakinsa ya sauka akan gadon, wadrobe ya buɗe ya shiga kwaso tsaffin kayansa da zai bayar, wadrobe ɗin duk tayi kaca kaca sai tashin tsamin jiki da na turare da ya haɗe wuri ɗaya, ya girgiza kana saboda takaici da ya maƙure shi, ko da wasa Sa'ida bata taɓa haɗa kayan da ya cire da wankakku, kuma idan kaya sun isa a ɗauka a bayar da kanta zata ɗauko tace Hubbi wannan sun isa a bayar kafin su ƙarasa mutuwa, amma zai iya cewa bai taɓa ganin hannun Zahra'u a cikin wadrobe ɗinsa ba da sunan gyara masa kaya ko ɗakkowa tun bayan da ta gama na marmarin amarci. Yana cikin haɗa kayan ne kuma ya tuna da kiran Lubabatu da zai yi, cikin hanzari ya ajiye kayan hannunsa ya ɗauko wayarsa ya kirata, ya sanar mata cewa zai tura mata dubu huɗu tayi sauri ta siyo kifi tayi ferfesunsa ta kai asibiti. Gama wayar tasu yay daidai da shigowan Zahra'u, yanda ta shigo fuska a haɗe shima kuma ya haɗe tasa fuskar zaka san ba a shiri da juna an samu saɓani. Ta zauna kan kujera tana kallonsa tace,"Wai yanzu da gaske ka ke ba zanje bikin nan ba?". Tayi maganar tana girgiza ƙafafu haka kuma tana faman jijjiga kai alamun dai ranta a matuƙar bace yake, sannan ta shiryawa rigimar da duk ya taka. Bai ko kalleta ba balle ta saka ran zai amsa, ya sunkuya ya ɗauki Iman da ta fara rarrafawa can zata tafi yo ta'adi, wasa ya shiga yi mata, ba zai taɓa iya musalta yanda yake matuƙar kaunar ƴarsa ba, yana son fiye da kowa da komai nasa, irin son da bai haɗa shi da komai ba, haka yana matuƙar godiya ga Allah da ya ba shi ita ya ke kuma kan ƙara basa wasu. "Daddyn Iman magana fa na ke maka kayi banza kamar baka jini ba". Ido ya ɗaga ya kalleta, sai yay murmushin da shi ɗaya yaji sautin kayansa kana yace,"Sai na rubuta a takarda na bi ko'ina a cikin gidan nan na manna tukunna za ki gane abin da na ke nufi kenan". Sai kawai ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya, kuka sosai irin na cin rai. "Me yasa za ka zaɓi hakan a matsayin hanyar ƙuntata mini, ko laifi na maka ai bai kamata ka huce akan hakan ba". Barin Iman yay ya miƙe ya yana tuɓe jallabiyarsa, bai da lokacin biye mata shikam, ya fi gane ya mayar da ita mahaukaciya tayi ta zuba a duk san da irin hakan ta motsa. faɗa suke yi sama da watanni, dama tuni yana ta fushi da ita yana jin haushinta akan nuna rashin sanin darajar iyayensa da muhimmancin su, kwata kwata bata nuna damuwarta da kulawarta akan rashin lafiyar mahaifiyarsa, ta mayar da shi wani ɗan iska sauna sai dai ta shirya tayi fitarta aiki, haka idan zuwa anguwa ne ya kama tana kan gaba wajen fita, amma ko da sau ɗaya bata taɓa dubansa ba tace zata je asibiti wajen Iyam, haka ko da tursasata yayi akan su tafi ranar sai sun yi tashin hankali tun daga kan tafiya zuwa dawowa. Ga shi yana buƙatar kuɗi ƙememe taƙi ta ba shi wani abu a cikin kuɗaɗen da ya riga ya mallakawa su Iman tun kafin haihuwarsu, a cewarta yanzu ai ba nasa ba ne ko auro ba zata ba shi ba balle yay iko da su ganin yana ubansu. Sannan ta zo ta Yaye Iman yarinyar na da wata goma wai ta gaji da bata nono ita ba zata bari nonota ya zube ba, ya rabu da ita a wannan ganin yarinyar bata kuka kuma tana shan madarar da aka basu a asibiti sosai da zai kama cikin yaro. Kuma kwatsam bayan nan saboda bata da hankali tana batun zubar masa da cikin da Allah ya ƙara basa tana faɗin ita ba zata iya haihuwar kwanika ba, bata shirya mata ba, ya za'ai ƴarta ko wata goma sha biyar bata yi ba ace ta samu wani cikin, ba hauka take ba yanda ta tsara sai bayan shekara bakwai kafin ta sake samun wata haihuwar, bata yi aure don ta saki jiki tayi ta zuba ƴaƴa ba kamar wata kaza, don haka ko me zai yi sai ta zubar da cikin. Wata huɗu kenan suna ta fama da shi, yace wallahi muddin ta zubar masa da ciki sai sun yi shari'a kuma sai ya saketa kuma ba zai bata Iman ba, to wannan furucin da yay shi ne ta ɗan sassauto amma ba wai don ta haƙura ba, tana nan akan bakanta na sai ta zubar da cikin. Shi ne kuwa ya tattarata gaba ɗaya da duk huruminta ya aje a gefe, ko abincinta ya daina ci, magana ya daina yi mata, ko abubuwan da yake siyowa ya aje cikin gidan duk ya daina, shimfiɗa ma ban da kar ya cuci kansa sai ya ƙaurace mata gaba ɗaya don so yake ya horata ta horu. Kuma sai Allah ya kawo masa hanyar da zai rama ɗin, za'ai bikin Ƙanwarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya daga ita sai ita, Mahaifiyarta ma zata je saudiya duk ya hana yace ba zata je ba, ya kuma rantse da hakan, shi ne ta kira mahaifinta ta kai masa ƙara, shi kuma ya kira Nazifin ya dinƙa zazzaga masa bala'i yana cewa kar fa ya zaƙe da yawa, ya daina ganin don ya isa ne ko ya kai ya ɗauki ƴarsa ya ba shi, alfarma yay masa saboda haka in yace zai zaɓi cuzgunawa ƴarsa to tabbas zai ji sammaci. Tun da mahaifinta ke shiga huruminsu yay bake bake akai bai taɓa buɗe baki ya maida masa martani ba, idan aka cire mahaifiyarta kowa a familyn na su taka shi yake son ransa musamman ma mahaifin nata, shi har yana faɗa masa banda ƙaddara ma dai ai bai cancanci ya ɗauki ƴarsa ya bawa mara ilimin boko ita ba, wanda ko rubutun kirki bai gama iya ba, ranar kuwa ya kada baki ya maida masa martanin cewa ilimin addini shi ke gaba da na bokon da suke alfahari da tutiya akai, kuma Alhamdulillahi ya samu ko yanzu ƙiyama ta tashi, ko yanzu zai kwanta ƙabari lafiya tun da bai fifita duniya akan lahirarsa ba. Da wannan su kai ta fafatawa da mahaifin Zahra'un wanda ta kai har yace to shikenan zai ɗauke ƴarsa, shi kuma yace to in har ta fita daga gidansa a bakin aurenta, haka kuma yaywa ƴarsa kashedi tare da jan kunne kar tayi kuskuren zubar masa da ciki idan ba haka ba za su yi shari'a da ita, shari'a irin ta gani kashe ni. Zahra'u ta sassauta murya tana dubansa tace,"Daddyn Iman kawa girman Allah da manzonsa kayi haƙuri idan laifi na maka, amma don Allah kar kace zaka hana ni zuwa bikin gidanmu ka taimaka min". Ya isa gaban madubi yana ɗaukan clipper yace,"Ashe shugabar sanin right ta iya bada haƙuri". Ta rufe ido ta buɗe. "Ni dai ko me zaka kace ka faɗa amma kayi haƙuri ka bar ni naje, ni wallahi na yarda idan naje na dawo ka ware watanni ka hana ni zuwa ko'ina bayan aikina". Yay wani murmushi kafin yace,"Aikin ma ai kina gab da daina zuwansa, ai yanda kika zaɓi ki baƙanta min haka nima na dinƙi ƙuntata miki kenan, da ni kike zancen wallahi muddin ni ke aurenki sai kin shekara guda ba ki je gidanku ba, za ki sha mamakina". Aikuwa sai ta miƙe ta baɗawa idonta ƙasa ta kama tafa hannu cikin masifa tana faɗin,"Ƙaryarka tasha ƙarya Nazifi, baka isa ka hana ni zuwa gidanmu ba, baka isa ka raba ni da aikina ba, ka yi kaɗan, idan kuwa kace hakan za'ai nima zaka sha mamakina wallahi wannan cikin na jikina sai na zubar da shi, ba kuma shi kaɗai ba kowanne ciki naka da zan samu sai na zubar da shi kaji ma na faɗa maka". "To ki ta zubarwa mana, wa kika yiwa in ba kan ki ba, ke ce za ki ƙare a wahala kina shan magani yana lalata miki mahaifa ƙarshe ki zo ki daina ɗaukar cikin, ni kuma daga nan na danƙaro wata matar". Wani kukan kura tayi tayo kansa zata cakumi kwalarsa tana faman hargagin cewa,"Na rantse da Allah baka isa ka ƙaro aure ba, ni ɗaya zan ci gaba da zama da kai, kuma kayi gangancin hakan ka gani ko wacece sai na kasheta sai naga bayanku kai da ita, kuma ban ga uban da zai hana ni zubar da cikin nan ba ko me za'a yi". Tana gama maganar ta fita kamar zararra, in few minutes sai gata ta dawo da goran wani magani na hausa da kuma ƙwaya a hannunta, zuba mata ido yay yana kallonta ya kasa hanata har ta ɗiɗɗiki maganin. Jarkan faro guda sai da ta shanye kana ta sauke sai sauke numfarfashi take yi,"Na sha kuma zai zube, na kashe ɗan naka kayi duk abin da zaka yi....". Cikin tsananin ɓacin rai da ƙunar zuciya yay kanta yana ɗaukar sachet ɗin maganin ya duba, take ya daga waya ya roƙi wani likita da cewa ya hau whatsapp yay masa wani taimako, ya ɗauki hoton maganin ya turawa likitan kai tsaye yace masa ai maganin zubar da ciki ne. Lokaci guda gashin jikinsa ya mimmiƙe, gumi ya keto masa, abun da ya ƙwallafa rai a kai ta zubar masa? Ɗansa na halal ɗan sunnah ba ɗan shege ba? Zuciya ta ɗebe shi ta kai shi ga nufar wadrobe ya buɗe tare da zaro belt ɗin wandonsa. Zahra'u da ke faman zazzaga masifa tana yayi abin da yake tunanin zai yi ba tayi aune ba ya shiga lafta mata belt ɗin ta ko'ina tamkar an aiko shi. Yaji belt ɗin ma ba zata masa yanda yake so ba kawai sai ya koma sa ƙafa yana bal da ita yana kai mata kutufo da hannu. "Wallahi ba ki isa kin kashe min ɗana ba, idan har cikina ya zube da gaske sai na nakasta ki, sai na barki da mummunan tabon da ba zai taɓa gogewa ba a jikin ki, ko ban kasheki ba sai na zama sanadin da za ki daina farin ciki har abada". Sai da yay mata mugun duka tukunna ya barta yana huci ba don ya gaji ba ko kuma hakan yay masa. Hankalinsa ne ya tattara ya kaɗa yay asibiti wurin Iyam. Ita kuma ta miƙe da ƙyar cikin wahala tana faɗin,"Kuma wallahi baka duki banza ba, sai ka san ni ka yiwa wannan dukan Nazifi, mugu azzalumi, Allah ya isana da ka cuce ni ka aure ni". "Dilla can rufe min ba ki, ni da ke wa ya kamata yay Allah ya isa, ban da ƙaddara me zai sa na aure ki, auren bagidajiya mara ilimin addini, kuma Allah ya isa da kika zama sanadiyar da na rasa matata, matar arziƙi...Tun da na aure ki ban huta ba, kullum cikin ganin masifu na ke iri iri, mene a cikin auren na ki banda tarin takaici da nadama, ai tuni na fahimci ba don Allah kika aure ni ba sai saboda dukiyata, kuma kije na sake ki saki ɗaya, kar kuma ki sake ki tafi da ko tsinke da na mallakawa yarinyata, ki aje min yarinya da duk abin da na mallaka mata". Ya faɗa yana hanzarin shiga banɗaki jikinsa sai rawa yake yi, haka zuciyarsa tamkar zata fito waje saboda ɓacin rai. "Allah ya isana tun da ka mayar da ni bazawara, wallahi ba zan yafe maka ba sai mahaifina ya ɗauka min fansa". Tana ta surutanta ya shiga bandaƙi, ko minti biyar bai yi ba cikakke ya fito, shi kansa ya san ba wanka kirki yay ba. Jallabiyar da ya cire ya mayar ya kwashi wayarsa da maƙullai ya fita falo. Can ya sameta tana aikin zage zage tana faɗawa Babanta wai Nazifi yay mata duka har sai da cikin jikinta ya zube, Daddy ayi ƙararsa kotu ba zan yarda ba sai alƙali yabi min hakkina. Iman tana hannunta ya fizge ƴarsa da ke ta kuka. Sai da yaje bakin ƙofa sannan ya tsaya ya juyo yana kallonta da cewa,"Idan kika bari na dawo gidan nan na same ki ban san illar da zan yi miki ba". Ya fice a fusace, yacca yake tuƙi kuwa kana gani kasan na cikin motar ba lafiya ƙalau ba akwai matsala ta tashin hankali, ga kukan Iman duk ya daɗa ɗaga hankalinsa wacca tuni ya fara tunanin wacca uwar zai nema mata? Wacece zata kula da yarinyarsa bisa ruƙo na gaskiya da amana? Wace zata bata ingantacciyar tarbiyar da yake fatan yaransa su samu? Wacece zata yi duk iyaka ƙoƙarin wajen ganin sun wadatu da ilimi ta kowanne fanni musamman na addini? Wayarsa tana ta ƙara yaƙi ɗagawa sai da yaji kiran yay yawa tukunna, ganin likitan Iyam ne sai ya ɗaga da sauri, likitan yace masa zai bar asibiti ne ga result ɗin gwajin da aka masa ya fito, kwanaki ne yay fama da wani azababben ciwon ciki da mara a haɗe har sai da ya saddaƙar mutuwa zai yi. Da ƙosawar yaji menene ya shiga tambayar likitan sakamakon, saboda ko a lokacin likitan yace masa kamar matsalar babba ce amma dai sai result ya fito za su tabbatar. Likitan yace masa ya ƙaraso ɗin dai tukunna amma ya zo da sauri don zai fita ya bar asibitin saboda akwai wani asibitin da zai je zai yi aikin tiyata yanzu. Kashe wayar yay ya ƙarawa motar gudu, yana shiga asibitin ya miƙawa Fati Iman yace ta goyata, duk ganin yanayinsa kamar ba shi ba a wani rikiɗe suka tafi ruuu suna tambayarsa lafiya. Kai tsaye yace da Yaya,"Zahra'u ta zubar min da ciki, na mata dukan fitar hayyaci na kuma saketa, Yaya ki kirata ki shaida matta kar na koma gidana na sameta idan ba haka ba wallahi ko ban kasheta ba sai na kusa kasheta". Yana faɗin hakan ya faɗa ofishin Doctor, Yaya ta kama salati tana sallallami, ce take mun shiga uku an ta sake saken aure kenan, Nazifi me yasa ka kasa sarrafa zuciyarka kai kuwa. Yanzu wanne hali Iyam zata shiga idan taji wannan zancen. Shi kuwa yana can gaban likita zaune ya fito da takardun cikin file ɗinsa yana yi masa bayanin cewa. "Akwai abin da muke kira da Disruptions in hormonal levels, ma'ana dai ka samu low testosterone, sperm production ya ragu sosai wanda dalilin hakan haihuwa ta ɗauke maka, baya ga haka ma still akwai Hormonal Imbalances wato rashin daidaituwar ƙwan halittarka...". Gaba ɗaya ma sai ya daina ji da gane bayanan da likitan ke masa, to me yay saura da zai ji? Duk sauran bayanin dai akan cutar ne, gundarin ciwon kuma an faɗa masa, kalma ɗaya ya riƙe haihuwa ta tsaya maka ba zaka kuma haihuwa ba! Wannan Kalmar me ɗacin ɗanɗano daga ina haka! Garin ma ya hakan zata faru da shi? Daga ƴar karamar cuta sai binkicensu na ƙarya ya bada sakamakon daina haihuwa? Bai san wanna tunani zai yi ba kuma bai san me zan iya cewa da danganta maganar likitan akai ba, abu ɗaya ya sani ya ɗaga hannu ya dakatar da likita daga bayanansa, sannan kuma hannunsa na rawa ya zaro wayarsa a aljihu ya danna kiran mahaifin Zahra'u yace masa,"Na mayar da aurenmu Daddy". Daga wannan maganar kuma sai ya dafe ƙirjinsa da yake jin zuciyarsa na barazanar fitowa waje, har ta kai ga ya faɗo a saman kujera bai sani ba, haka kuma ba tare da sanin nasa ba likita yaji yana ambaton,"Hasbunallahu wani'imal wakil, Astagfirullah ya Allah, tabbas na maka wani laifin da ban sa ni da na ke amsar hukunci ka yafe min Allah na". Sai ya koma cewa da likitan ya taimaka masa zuciyarsa zata fito. _________________ ₦500 07018098175 *B2ƘR25FT5* Likita ya taso da sauri yayo kansa, ya kama shi ya mayar da shi kan kujerar ya zauna.wani irin numfashi ya ke saukewa me wahala, likitan na ta jera masa tambayar,"Dama baka da lafiya baka min bayani ba, ai you should have let me know, me ka ke ji a ƙirjin naka?". Bai iya ce masa komai ba kuma ba zai iya cewa da shi komai ɗin ba, likitan yay ƙoƙarin ɗora Stethoscope ya dakatar da shi da cewa,"Bar ni likita bana buƙatan komai, na gode". Yana faɗin hakan ya kifa kansa kan table, shin me ya aikata a rayuwarsa ne haka da abubuwa marasa daɗi ke ta ƙwallo da shi? A tarihin rayuwarsa yau ita ce rana ta biyu da zai iya cewa ya shiga tashin hankalin da yake jin zai iya haɗiyar zuciya ya mutu ya huta. Kusan mintuna goma yana zaune a hakan yana ta biyo innalillahi a bakinsa, natsuwarsa ma da yake so ya samu ya kasa samunta, kansa yay masa bala'in nauyi wanda in da za'a cire masa tabbas zai so hakan matuƙa. Bayanin likita ne ke ta faman tariya a cikin kansa, yayin da hoton Zahra'u ke ta haskawa a cikin ƙwayar idonsa san da take shan maganin zubar da ciki, shikenan ta gama da shi, ta cuce shi, kuma ba zai taɓa yafe mata ba, yanzu shikenan kuma shi da wata haihuwar har mutuwa, kawai sai Noor ta faɗo masa, a hankali ya furta Allah ya isa tsakanina da ke Sa'ida da kika raba ni da yarinyata. Dafa kujerar yay ya miƙe da ƙyar, ya dubi likitan da ƙwayar idanuwansa masu nauyi waɗanda ɓacin rai, tashin hankali, da gangamin damuwa sukawa ƙawanya. Fita yay a office ɗin a daddafe, likita na ta ce masa ya tsaya ya karɓi takardunsa bai ko masa magana ba kawai ya buɗe ƙofa ya fice. Can ya iske su Yaya zazzaune, tana ganinsa ta shiga tambayarsa lafiya duba da yanayinsa da ya kasa ɓoye halin da yake ciki. "Iyam ta tashi?". Ya faɗa da ƙyar da amon muryar da ya zama tamkar ba nasa ba. "Bata tashi ba, wai wani abu ne ke faruwa? Me likitan yace maka?". Ya rumtse idonsa ya girgiza shi, sannan yasa hannu ya shafo kansa. "Ina Lubabatu?". "Basu jima da fita ba Iman taƙi shiru, taje siyo mata biscuite". Bai ce komai ba ya nufi ɗakin da Iyam take ya buɗa ya shiga, tana bacci har yanzu, babu wanda zai ga tsohuwar nan bai ji ƙwalla ta taru a idonsa ba, saboda yanda ta rame ta yamutse, ƙasusuwan jikinta na ko'ina ya fito tamkar zasu yi magana, ya ilahi wannan rayuwa Allah ka mana da sauƙi. Gaban gadon yaje ya zauna akan kujera, ya daɗe yana kallon fuskarta, ya kai yatsu ya kara a ƙasan hancinta saboda wani motsi da zuciyarsa tayi na tsoro gani yake kamar bata numfashi. Sai da yaji numfashinta na fita ya sauke doguwar ajiyar zuciya, ya kama hannunta ya ruƙo ya ɗora a saman kansa. "Na sani a ko da yaushe adu'arki na tare da ni, Allah ya ba ki lafiya ya tashi kafaɗunki". Da haka ya miƙe ya fita cikin matuƙar sanyin jiki, lissafinsa guda ɗaya ne kawai a yanzu wanda zuciyarsa ta yanke masa shawaran ya siyar da gidansa kawai ya biya kuɗin aikin mahaifiyarsa, wannan ɓata lokacin da jiran tsammanin da yake ko saboda shi sai Allah ya hukunta shi, tana ta shan wuya kullum, ga shi yanzu ma dubu sittin ɗin da suke ci a kullum nema take ta gagara don a yanzu bai da kuɗin na yau da zai tura, sai dai kuma ko me za'ai yau sai Zahra'u ta fito da duk wasu abubuwa da ya mallakawa ƴarsa. Yana fita Iman da ke hannun Lubabatu tana bata biscuite ta shiga miƙo masa hannu, sai yaji wani sanyi ya ɗan ratsa shi, a ƙalla ubangiji bai jarabce shi ba sai da ya bar masa guda ɗaya. Miƙa hannu yay ya karɓeta ya saɓa a kafaɗarsa, ƙwarai Zahra'u ta shiga hakkin yarinyar da ta yayeta da wuri, har yanzu ta kasa kama wani abinci da zai ke kama cikinta, yarinyar duk a motse kamar me wata cutar. A mota haka yay ta surutai wa yarinyar yana jin sabuwar ƙaunarta na ratsa shi. Suna komawa gida ya tarar Zahra'u tayi aika aika da haukan da ta ɗorawa kanta, duk wasu gilasai na falon ta farfashe su, ta hargitsa jeran kujerun. Ciki kawai ya wuce yana takawa a hankali gudun kar ya taka kwalba, yana shiga ɗakinsa ma ya tarar ta warwatso masa da dukka sutturunsa, takardunsa da komai na amfaninsa, yay saurin isa ga kan gado ya ɗakko laptop ɗin yana kunnawa yaga taci screen, ya ambaci ƙalu innalillahi da ƙarfi. Jiki na ɓari ya aje Iman da ke ta shaƙuwa, kuma kafin yay wani motsi sai gata ta shigo ɗakin tana cewa da shi,"Ashe ma kai ƙaramin ɗan iska ne, ai da baka mayar da ni ba, ai da ka sake ni gaba ɗaya shi ne zaka tabbatar da ka isa ka kai, kuma abin da ka zo ka tarar kaɗan ne, wallahi sai na tabbata ka ɗora hannu saman ka kayi danasanin aurena da hujja, ba dai ni ka duka ba, zaka sha mamaki". Har ta gama surutanta bai ce mata komai ba, sai da zata fita ne yace da ita,"Ki kwashi muhimman kayanki zamu koma gidanmu da zama, zan siyar da wannan a yau". Wata iriyar juyowa tayi tana ƙunduma ashariya. "Nazifi ka ce mene? Za mu tashi anan? Mu koma gidanku? Na zauna tare da ƙannenka da matan Babanka ka ke nufi? Nooo impossible, ba a kaina ba sai dai kan wata". "Ok to idan ba kya son faruwar hakan sai ki tattaro duk abin da mallakawa ƴata ki bani na nemawa mahaifiyata lafiya...". "Kai dakata du Allah! Wai zatonka ni shashasha ce, ka man ce wayayya ka aura ƴar boko me lissafi, to tun da ka bani wannan kadarori na juya komai da nawa sunan Nazifi, kuma kai da kanka ka sanya hannu akai shaidar komai da ka bayar ba naka ba ne ba na ƴarka ba ne nawa ne mallakina ne, baka da iko ba ka da wata hujja a yanzu da zasu karɓa maka, idan ma zaka bar tunaninsu da nemansu zai fiye maka, gida kuma ka siyar ina ruwana, ƙarƙari na koma gidanmu da zama don wallahi ba zan zauna a gidan surukai ba ka zubar min da aji da ƙima". Ya san dai duk yana jinta da kalamansa, to amma abin da ya kasa ganewa yaushe ya rattaba hannu jikin takardu? Take watarana ta haska masa a cikin ƙwayar idonsa, sun gama gurzar soyayya ko tashi ba suyi akan gadon ba ta miƙo masa takardun tana faɗin takardu ne na neman promotion a wurin aiki, kuma ana neman sanya hannun miji wanda ta hakanne zata iya samu su ƙara mata matsayin da take fata. Shi kuma da murnarsa da azarɓaɓinsa ya karɓa takardun guda biyar ya rattaba sa hannunsa akai mai kyau da aji. Yana ta shi mata albarka yana faɗin ɗaukakarta ai tasa ce. Tunaninsa ya tsaya cak jin ta wullo masa abu a jiki, ya kai idonsa kan ATM har guda biyu, ya ɗauka yana juya su kamin ya kalleta ya miƙe cikin hanzari da ƴar guntuwar murnarsa sai kuwa furucinta yay daga daga da guntuwar murnar da ta ziyar ce shi. "Babu ko sisi a ciki domin kuwa duk na tura su cikin asusuna, wacca hujja zaka nunawa banki na cewar ba kai ka tura ba? Kuma sannan da kake maganar zaka siyar da gida, ka manta da cewa har da shi ka sanya hannu a takardarsa na cewa ka mallakawa Noor? Motarka ita kawai ta maka saura Nazifi baka da wani sauran abu da zaka yi tunƙaho da shi, kuma ban yarda ba saki tsakanina da kai ma ya zama dole, domin kuwa na lura da cewa kamar babu ta kamaka, ni kuma ba zan iya zaman aure da talaka ba, ba kuma zan bar maka ƴata ba dole zan tafi da ita domin ba zan bari rayuwarta ta tagayyara ba a wurin wanda bai da kuɗin ɗawainiyar kansa ma balle ta ƴarsa, ingantacciyar rayuwa na ke sowa ƴata da zata tashi cikin gata da jin daɗi da rayuwar cikin daula kamar yanda na so ba yanda ubanta ya ta so ba, shiyasa na ƙwace komai na ka kafin ma tsautsayi yaja ka ga samun wasu ƴaƴan ba tare da ni ba ya zama an raba dukiyarka da ba da ƴaƴana kawai ba, kuma kamar yanda ka faɗa ne Kuɗinka shi yasa na aureka ban da haka kai kanka ka san idan ba shaye shaye nayi ba nayi rayuwar ƙasar waje da kwalin degree na me aji ace na ɓige da auren namijin da ko satifiket ɗin primary bai da shi". Kalaminta ya ƙona ransa,"Ki je duk wata cutarwa da kika yi min ke da Allah domin kuwa kin zalunce ni, mayaudariya azzaluma, sannan ki sani ko za ki mutu igiyar aurena ba zata sauka daga kanki ba, kina nan tare da ni, kin zubar da ciki ko? To ki sani ni kuma a yanzu ba zan ƙara haihuwa ba, haihuwa ta tsaya min". "Na shiga uku, kenan idan ina tare da kai ba zan ƙara haihuwa ba, ina burin haihuwan ɗa namijin da na ke da shi? Na rantse da Allah baka isa ba Nazifi sai ka rabu da ni sai ka sakeni, ba zan zauna da namijin da ba ya haihuwa ba, ga talauci ga rashin ƴaƴa inaaa". Ta faɗi hakan tayo kansa kamar mahaukaciya tana cewa lallai ko ya saketa ko tayi masa rauni, shima yay saurin tashi ya ɗaure Iman a bayansa tare da maketa ta faɗa gefe ya fita a ɗakin yasa makulli ya kulleta. *BAYAN SHEKARA HUƊU* *Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, Nigeria.* Ƙarar saukar jirgin da ya jiyo na shawagi a ƙasa yay sanadin lumshe idanuwansa, wanda hakan yay nasarar bayyanar da zara-zaran gashin idonsa da kuma motsawar laɓɓansa masu taushi, kaman wanda yay mugun gajiya haka ya sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, yay saurin mayar da p-cap ɗinsa haɗi da daidaita zaman baƙin gilashin fuskarsa, sai fuskan ya ƙara ɓoyuwa ta yanda ba zaka yi saurin shaida shi ba, kewayyan sajensa me haɗe da gemu kawai kake iya haskowa kaɗan. Bugawar sakan ɗaya, biyu, uku ya buɗe idanuwan nasa daga lumshen da suke tare da ɗan juyasu yana jin wani sanyayyan abu na biyowa ta babban yatsansa yana shiga jikinsa. Idonsa ya sauka akan agogon hannunsa, agogon ya buga ƙarfe huɗu da rabi daidai na yamma, kuma lokacin yay daidai da gama shawagin jirgin da ya taso daga ƙasar Germany zuwa ƙasarmu ta nigeria, kansa ya ɗaga ya mayar da dubansa ga inda jirgin ya sauka, idonsa na kalle masa mutanen da ke fitowa daga cikin jirgin sannu a hankali, kallonsu yake yi sosai ya kasa ko da ƙifta ido, duk ya ƙosa yaga fitowar halittar da idanunsa ke jira, haka kuma ya kasa ɗauke ganinsa daga wurin duk da irin yacca yake jin wani taraddadi na fizgarsa, zuciyarsa faɗa masa take kamar ba zaka samu ba ka haƙura kawai. Bayan fitowar passengers da dama, gabansa ne ya yanke ya faɗi, zuciyarsa ta harba fat fat a lokacin da ƙwayar idonsa ta sauka akan kyakykyawar halittar da ke sakkowa a yanzu, hasken jikinta kaman jini ya tsarto, kai ba ka ce ƴar nigeria ba, sakkowa take yi daga matattakalan a hankali kuma cikin natsuwa, doguwar fuskarta na bayyana baiwar fara'ar da Allah ya bata, fuskar da kana gani kasan babu wata damuwa a tare da ita illa zumuɗi da ƙosawar son kasancewa da mafi muhimmanci wasu mutane a rayuwarta. Tun fitowanta a jirgin kanta a ƙasa yake, riga da wando ne a jikinta na uniform ɗin nurses ɗin ƙasar germany blue colour, sun matuƙar mata kyau tubarakallah ma sha Allah, a gefe ɗaya kuma tana gyara zaman sarƙar hannunta. Ta ɗago fuskarta tana kanne ido alamun haske yay masu yawa duk da rana ta ɗanyi ƙasa a lokacin. Cikin takun tafiyar da take me ɗaukar hankali da burgewa trolly ɗin da take jaye da ita ta cije wanda hakan yasa ta gurɗewa tayi saurin duƙawa. Gurɗewan nata ya taɓa zuciyarsa ya miƙa hannu da sauri da niyyar tareta daga yunƙurin faɗuwar da take neman yi, sai kuma ya ankare da cewar tazarar da ke tsakaninsu me yawa ce, kuma hakan ya haifar da rashin jin daɗi a tare da shi, bai kamata hakan ta kasance ba, alƙawarinsa ne na gyara kuskurensa zai tsaya tare da ita kowanne yanayi da motsinta ba tare da ya bari wani abu ya sameta ba, katanga ya ke so ya zamar mata, katanga ta kariya, hakana zai zame mata madafar da zata kaance ko da yaushe tana dafawa ba tare da kuka ko baƙin ciki ba, nasa alƙawarin ne a wannan karon wanzuwar tabbataccen farin ciki a fuskarta da duniyarta har ranar da zai daina numfashi, ba zai bari wani abu ya taɓata ba, haka ba zai ƙara gangancin maimaita kuskuren da yay a baya ba. Iskar bakinsa me ɗumi ya furzar, kansa ya sunkuyar ya leƙa cikin motar da yake jingine a jiki, ƴarsa da ƙanwar ne zaune a ciki, sai ya kai ƙwayar idonsa yana duban fuskar ƙanwar tasa, da wani yanayi sirrantacce a saman fuskar tasa, a hankali yace da ita,"Kayan sun mata yawa". Sai yay shiru for seconds kana ya ƙarasa maganar da cewa,"zan taimaka mata". Da murmushi me burgewa a fuskarta da ke nuna nata jin daɗi da farin cikin da ke neman zarce nasa tayi knooding masa kanta kawai. "But be carefull Mr Man". Leɓbansa ne kawai suka motsa, alamu na son yay murmushi sai dai hakan bai samu ba, domin kuwa a yau ɗin karo na farko da yake jin wani abu me kama da tsoro na kama shi, wanda a matsayinsa da sanin waye shi ɗin bai kamata tsoro ya nemi ya masa farmaki ba. Ya miƙa hannunsa cikin motar ta miƙo masa face mask ya saka, ya ƙara gyara p-cap ɗinsa ya zuba hannayensa cikin aljihun rigar sanyin jikinsa, fuskarsa ta rufu ruf kamar mara gaskiya, ya sake leƙa kansa cikin motar yana duban Ƙanwar tasa da cewa,"Yayi?". Haƙoranta na gaba suka bayyana dalilin siririyar dariyar da tayi, ta ce,"Ko ni ba zan iya shaidaka ba, balle kuma ita, duk da wani connection ɗin yafi gaban tunanin mutum". Da dogon yatsansa ya lakuci kumatunta, sannu a hankali kuma ya fara takawa yana tafiya yana jin wani irin yanayi na shigarsa, farin cike yake, farin cikin da zai iya cewa ya girmi nata da duk wani masoyinta makusancinta. Hanzarin tafiyarsa ya ƙara na gient ɗin namiji kamarsa. "Excuse me". Ya faɗa da amon muryar da ya fito da ɓacin rai, haka ma ɓoyayyar fuskarsa na bayyana zallar kishi da jin haushin mutumin da ya isa gabanta da niyyar taimaka mata ya karɓi trolly ɗin so that taji da jakunkunan hannayenta. Mutumin yay saurin matsawa gefe yana ba shi haƙuri tsammaninsa ko me gidanta ne. shi kuma ya kai hannu ya kama hannun trolly ɗin, a hankali kuma a miskilance cikin harshen turanci yace,"Barka da dawowa". Ya faɗa ba tare da damuwar ta jisa ko bata jisa ba, shi dai ya amayar, fushinsa kawai akan me zata fito haka fuska a bayyane kowanne kare da doki ya ganta yajinta burge shi, and just imagine ta tsaya tsakiya idon kowa da ke wajen ya ƙare mata kallo kenan, babu ruwanta bata san marairaice fuskan da take yi ma ƙara fitar da kyawun halittarta yake ba. "Mtssswww". Guntun tsaki ya fita a ƙasan maƙoshinsa, yana jin kamar ya zaro abar da ke cikin aljihunsa ya daki kanta da ita ko ta san da cewa kan hanya take tsaye ba cikin ɗakinta ba. Ƙwayar idonsa ta manne a saman fuskarta da murmushin jin daɗi da farin ciki yaƙi ɗaukewa. Waya take yi da ahalinta tana faɗin,"Mun sauka yanzu amma ban hango kowa ba, kuna daga ina?". Tayi maganar kaman zata yi kuka, wanda sautin hakan ya tafi har can ƙasan zuciyarsa ta motsa. "To Abbaa sai ya ƙaraso Allah ya kawo shi lafiya". Nayi maganar cikin rashin jin daɗi, domin ba haka na so ba, yanda na so ace ina sauka idona yay kwalli da mahaifiyata ko mahaifina, to amma babu komai tunda Yaya Imam da Yaya Al'amin ɗin suna kan hanya, kuma na san duk yanda aka yi kuɗin mota ne ya hane su tahowa gaba ɗayan su. Na kai hannu ga trolly ɗita sai naji an ja, nayi saurin ɗago ido in sauke kan dogon mutumin da ya fara takawa, da sauri na dakatar da shi da cewa,"Malam jakata ce". Bai tsaya ba yaci gaba da tafiyarsa, ni kuma ina ta binsa cikin sauri ina ce masa jakata ce yay mistake ɗin ɗauka ne, sai dai ganin bai juyowa ba tunanina ya bani ko bai jin hausa ne tun da yanayinsa kamar ba na bahaushe ba, don haka cikin yaren turancin da ya samu ƙwarewa yanzu a kan harshena na ce masa,"Jakata ce fa kayi mantuwa". Nan ma dai kamar bai jini ba, sai na ce to ko kurma ne, don haka muna shigowa cikin wata ƴar rumfa nayi saurin shan gabansa da niyyata na masa alama da hannu ya gane nufina. Bisa tsautsayi ƙafata ta gurɗe har na kai ƙasa dalilin ɗan tudun da na buga, wayata ta faɗi na saddaƙar da tayi raga raga, yunƙurawa nayi na miƙe na zauna kan kujerun ƙasan rumfar ina danne wajen da na buge idona a rumtse. "Sorry please". Buɗe ido nayi na gansa sunkuye gabana kaman zai kai hannunsa kan ƙafata wurin da na dafe sai dai kuma bai yi hakan ba, ya dai ɗauko wayata ya miƙo min. Haka ɗaya naji ƙirjina ya buga sosai, irin bugawar nan da yake a lokacin da mutum ya shiga fargaba ko tsananin tashin hankali na saƙon mutuwa. Wani sanyayyan ƙamshi ne ke tashi daga jikinsa ya ziyarci hancina, ban san dalilin da hakan ya haifar mini da haɗiye dunƙulallen yawu tare da jin motsawar zuciyata, kuma lokaci guda naji jikina yay sanyi, hannu na miƙa na karɓi wayar ina faɗin,"Thank you". "Sannu". Ya sake furtawa muryansa can ƙasa. "Na gode. Dama jakan da ka ɗauka nawa ne ina ga baka lura ba ne". "Na sani, na taimaka miki ne". "Hope ba ki ji ciwo ba?". Ina duba wajen na ce,"Ban ji ba". "Sorry na taimaka miki ba tare da izininki ba". Sai yanzu ya ɗago kansa wanda na san ya kalle ni ne ta cikin baƙin gilashin da idanunsa ke rufe a ciki, babu ta yanda zan iya ganin fuskarsa domin kuwa face mask ya ɓoyeta. Me na ke ji ne? Tamkar na san muryarsa, anya kuwa! Ta ya hakan ma zata kasance? Tunanin da na ke ya yanke ganin ya miƙe yana barin wajen da sassarfa. Na bi bayansa da ido ina kallonsa, ban san me yasa na ke ganin kamar na taɓa ganin me tafiya irin tasa ba, ba ya ga nan ma ga muryarsa da na ke da tabbacin na taɓa jinta, haka ƙamshin ma kamar na san shi? Sai dai duk me yaja bugawar ƙirjina akan hakan? Waye shi ɗin? Tambayar ƙasan ran nawa ta haɗe da saukar ƙwayar idona akan bayan rigarsa da ke da tambarin S a jiki, ni dai har ya ɓacewa ganina ban ɗauke idona da tunanin wani abu akansa ba. Wayata na cire key na danna lambar Safiyya, tana ɗagawa tace,"Beb ina ta kiran wayanki ban samu". Na ce,"To ai sai da muka sauka na mayar da sim ɗina na nan". "Beb can't wait to see you, an dawo lafiya". "Lafiya lau, ina Daughter nah?". Sautin murmushinta ya fita da cewa,"Ga ta tana bacci, itama ai ta ƙosa taga Mum ɗinta, kina airpot ɗin ina ne yanzu? Kano ku ka sauka ko Abuja?". "Muna Abuja". Sai yanzu ta ankare da yanayin fitar sautin muryata tace,"Beb lafiya dai? Yaushe rabon da naji muryanki a irin haka, menene?". Na karyar da wuya ina ɓata fuska na ce,"Kinga fa basu zo ɗaukana ba, kuma tun jiya sai da na cewa Abbaa na tura musu kuɗi sai ce yay a'a akwai kuɗi, kuma yanzu mun yi waya ma yana ce min Yaya Imam ɗin na kan hanya bai ma ƙaraso ba, don Allah haka zan ta zama anan ni ɗaya babu wanda na sani, ga sauran nan duk ƴan gidansu sai ɗaukan su suke yi". Na ƙarashe maganar idanuna na cika da ruwan hawayen da ke neman zubowa, kawai sai jin ihun Safiyya nayi a gabana ta faɗo jikina ta maƙalƙale ni, nima kuwa ban san lokacin da nayi mata wata runguma ba ina cewa,"Me yasa haka Beb, ni ki daina suprising ɗina irin haka". Muka saki juna tana bina da kallo da cewar,"Sa'ida ke ce kuwa? Kin ga yanda kika koma na rantse da Allah kamar sake halittanki aka yi, wannan kumatun fa, naga ƙashin wuyanki ko yana nan". Ta faɗi hakan tana ɗaga jesy hijab ɗin jikina tana aikin taɓa wuyana. "Beb ƙashin ma ya koma, kuturu yarinyar nan anya kuwa karatu kika je kika yi. Ko da yake ai result ɗinki kaɗai ya nuna ba wasa kika je kika yi ba, kin san duk wani handle ena na social media sai da na sa vedion result ɗinki, weldone ƙwaruwata za great first class". Dariya na ke sosai cikin jin daɗi, ina dubanta na ce,"Amma ya akai kika zo nan?". "Na san za ki dawo zan ƙi zuwa Beb, haba zance ne ai, muna nan Abuja ma fa tun last week Daddyn Amal ya zo seminer, jiya kina ce min zaku dawo yau kwana ne kawai ban ba a wajen nan, amma ina nan jirgin ku ya sauka na ce bari sai kin kira ni tukunna". Ina dubanta na ce,"To mu tafi gidan ki idan Yaya Imam ɗin ya zo ya same ni acan, ido yay min yawa duk na kasa natsuwa, kuma wani iri na ke ji, wanne turare ne a jikinki?". Ta miƙe tana faɗin,"Turaren da kika ba ni lokacin da naje miki visiting...Ke bara dai na fara tofe ki da li'ilafi, Allah Beb gaba ɗaya kin wani sauya, wannan karan kam ai sai miji me tsadar gaske, mijin hawa jirgi sama duk watan duniya, mijin haskawa a tv mijin da ƙasa da duniya ta sansa in sha Allahu". Ɓata fuska nayi. "Abeg na ce miki ki bar min zance irin wannan, mu tafi ni. Ina ma kika baro Amal ɗin wai?". "Ke ni ban iya aikin dinƙa yawo da ita tana mota na barta". Na waro ido ina ce mata,"What! Ƙaraman yarinyar za ki bari a mota, Safiyya wai ke kam yaushe ne ranar hankalin ki, ce na ke da kika yi aure kin saitu". Na faɗa ina ƙara saurin tafiyata tare da tambayarta in da motar tasu take, dama na ƙosa naga Babyn nata don tun da aka haifeta ban ganta ba, sun dai je min ita mijinta lokacin tana fama da laulayi. Kuma can sai na hango Yaya Imam tsaye yana faman ɗaga kai shi da Yaya Al'amin, wani sabon farin ciki ya lulluɓe ni naji kamar na kwasa da gudu na ƙarasa wajensu. Amma duk da hakan ban fasa gudu gudu sauri sauri ba ina ƙwala masa kira, na bar Safiyya da faman ƙwala min kiran da take yi tana ga motar tasu can, ina ce mata ga Yaya Imam ɗin can ya zo bari na je nemana suke. Ni dai ina zuwa tsananin farin ciki na kasa dakatar da kaina kawai na faɗa jikinsa da matuƙar murna. "Ke dilla mene haka sakar ni mana, gaban mutane fa mu ke". Yaya Al'amin yace,"Ah tou ba kun kaita turai ba, ta manta ƴar nigeria ce anan ɗin ma bahaushiya". Kunya na ɗanji na rissina ina gaida Yaya Imam, kallonsa na ke ina cewa,"Yaya naga ka zama babban mutum". Hararata yay da cewa,"Malama ina kayan na ki, kar muyi dare a hanya". Tare muka nufi inda kayana suke, muka ɗauko muna tafe sai ga mota baƙa ta faka a gabanmu, Safiyya ta leƙo tana cewa,"Yaya Imam shigo mu tafi ku barta anan". Da mamakinsa yace,"A'a Ƙanwata ke da wa?". Tace,"Kawata na zo tara ai, da ba ku zo ba wallahi Yaya kun barta ta taho da kanta". Gaisawa suka shiga yi, ya karɓi Babyn hannunta, kusan miti biyar ana tsaye sai hira ake. Wata mota fara ta faka gabanmu, na ciki ya fito saurayi ne baƙi ya zo wajenmu, muka gaisa da shi, yana dubana yace,"Don Allah ku ne ƴan makarantar da ku ka dawo yau?". Na ɗaga masa da cewa ehh. Sai ya ce min,"Please ko kin san wata Sa'ida Salman?". Safiyya tayi saurin ce masa,"Ehh ai ita ce ma, lafiya dai ko?". Sai ya miƙo ticket yana cewa,"A'a dama wannan aka ce na bata". Ta karɓa tana duba kafin ta miƙawa Yaya Imam tace,"Laa Yaya kaga ma ashe har da kuɗin jirgin masu zuwa ɗaukan su an musu, bamu sani ba. Ke ba'a faɗa muku ba?". Ina kaɗa kai na ce,"A'a zai iya yiwuwa kuma an faɗa ɗin ina can sakaraftuna na murnar tahowa ban sani ba". "Ga shi ma yanzu jirgin na ku zai tashi, sai mu koma ciki ai". Safiyya na tare da mu bata tafi ba har sai da ta ga tashin jirginmu. Tun da muka shiga na ke tawa su Yaya Iman dariyar fama zare ido da suke a cikin jirgi, ba sa banba ɗan kauye yay abin hannu, shi kuma daɗi duk ya cika shi yana faɗin yau ata sanadina ya shiga abin da bai taɓa zato ba, ina ma ace har da Abbaa da Ummani suka taho, gaskiya wannan makarantar tamu sai dai Allah ya biya su kawai. Haka muke ta hiranmu ina ba su labarin can, du da na ƙosa naga mun sauka burina na ga Abbaa da Ummani kawai. Lokacin da muka sauka a airpot ɗin Malam Aminu Kano messge ya shigo wayata, ina dubawa naga an sa,_"Saura nan ma ki tsaya tsakiyar titin jirgi kina ƙauyanci...gaisuwana ga Abbaa da Ummani". Dariya na saki ina jinjina lamarin ƙawata, ni na mant ma na tambayeta ko kamfanin sim card ta buɗe ne da duk message ɗin duniya in zata min da sabo take yi, duk da ma first visiting da taje min tana ta rantsuwa ba ita tayi min messges ɗin nan ba ni kuwa na ƙaryatata, to idan ba ita ba waye? _________________________________ *Alhamdulillah! Ƙarshen littafi na jiyu kenan, Littafi na uku zai fara sauka a ranar ɗaya ga watan December insha Allahu, zan ɗan huta na kwana biyu, kuma littafi na uku shi ne ƙarshen littafi na labarin Ƙayar Ruwa, Nagode, Nagode da Soyayyarku, masu siya Allah ƙara buɗi da arziƙi, Allah ya bar zumunci, Ameen* _Kuma kafin mu ɗora zan so jin ra'ayoyin ku, Fitattu Biyar na maku fatan alkhairi.._ *28/11/2023* *Halimahz* 07018098175 *B3ƘR01FT5* *_Bana jin zan iya fara rubutun ba tare da na ambace ki a wannan fejin ba Takwarata Sadiya Rabi'u, Alkhairin Allah ya isa gare ki da ke da ahalinki, Ya kare ki da kariyarsa, taimakonsa, salamarsa, ya azurtaki da mafirin ciki madawwami. Na gode na gode sosai kuma ina kan yin godiya._* *_Haka dukka mabiya wannan littafi musamman waɗanda suka nuna min ƙauna wajen sanya kuɗinsu su mallaka Allah ya mayar muku da ninkin abin da ku ka kashe, ya azurta rayuwarku da albarka da kariya tare da farin ciki._* ________________________________ Tafiyata kawai na ke tun saukarmu, na bar Yaya Imam da Yaya Al'amin can baya da uban kayana a hannun su, zumuɗina da ƙosawata duk bai wuci na ganni a gida ba gaban Abbaa da Ummani. Adaidaita sahu na tsayar mana, na faɗa masa unguwar makwarari zai kai mu ya faɗi kuɗin da za'a ba shi ban tsaya ciniki ba na ce masa to, Allah ya sani bana son in tsaya ciniki ana kaza ina a'a kaza, musamman ma na kuɗin mota, ga dai shi ni ba ƴar wani ba kuma ba me kuɗi ba, amma a hakan iyayena da suka san halina a wannan fannin duk sanda za su ba ni kuɗin mota da duk iya ƙoƙarin su sai sun nema min wanda su ke ganin zai ishe ni. Da sauri na buɗe hand bag ɗin hannuna na ɗauko dubu ɗaya da ɗari biyar da yace na miƙa masa, ba na so Yaya Imam ya ƙaraso na ɗora masa nauyi, tun da akwai kuɗin a hannuna gwara na biya, bayin Allahn nan tun da na tafi suke ta ɗawainiya da ni, ban da abin biyan su sai dai adu'an Allah yay musu sakayya da gidan aljanna. Ina tsaye jiran isowar su sai na tuna ma ashe ba guda ɗaya zamu yi ba, dole sai dai biyu, na ƙara tare wani shima ya faɗi abin da wancan ya faɗa take na basa kuɗinsa na ce su ɗan yi haƙuri ga su nan ƙarasowa. Ni da Yaya Imam muka hau ɗaya, Yaya Al'amin da jakkunan kayana a ɗayar. Da yake Yaya Imam shi ba gwanin hayaniya ba ne shima irina ne, duk sai muka yi wani dunkum a motar, sai ma ni ɗin ce da duk na ke a cikin farin ciki na ke ɗan jan sa da hira, ina cewa Yaya sai naga garin ya sauya min, me adaidaitar da ya ke jiyo hirar tamu shi ma ya sako baki. Muna isa ƙofar gida yanda ku ka san an jefo ni haka na fito daga cikin adaidaitar, Abbaa na ƙofar gida zaune kan tabarma yana jan carbi, ya kafa ya tsare yana jiran dawowarmu, dama Yaya Al'amin sai da ya faɗa yace Abbaa fa ba zai wuce mu same shi ƙofar gida ba ko bakin layi. Kafin na karasa ga in da yake har ya miƙe cikin tsananin farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a gare shi, jikinsa har wani kyarma yake, na tafi da saurina ina duƙawa a gabansa, ƙafafunsa na kama na riƙe ina jin wani irin sabuwar ƙauna da jin ƙan mahaifana, hawaye ya cika kwarmin idona, ban san irin godiyar da zan yiwa mahallicina ba da ya bar min su a raye tsawon wannan lokacin, duk da cewa me tafiya dole tana nan zuwa, haka ban san irin godiyar da zan yi a gare shi da ya bani iyaye nagartattu waɗanda a ko ina ɗa ya shiga zai bugi ƙirji yace shi ɗan wanene ba tare da wani shayi ba, kuma jin hakan yasa a kalle ka da daraja da martaba duk kuwa da cewa su ɗin ba masu kuɗi ba ne. "Miƙe! Miƙe mu shiga daga ciki ƴar albarka, likita bokan turai madallah, sai godiya ga lillahi". Tuni ƙofar gidan mu ya ɗinke da jama'a ƴan kallo, yara da manya duk an yi curko curko ana faɗin ƙasar waje taje ta dawo, ta zama likita yanu, duk sai na rasa ma me na ke ji a tare da ni, kalmar Alhamdulillahi ce dai ba zan daina faɗinta ba har na kai ga kushewa. Maƙotanmu kuwa su Malam Sani da Malam Auwal duk suka zo wurin Abbaa suna masa murna nima suna min murna da sanya albarka gami da adu'a. Abbaa ya ciro ɗari biyar a aljihunsa ya kira Yaya Al'amin ya ce,"Kaga ba wa waccan me awarar ka ce ta rabawa yara sadaƙa". "Na nawa Abbaa?". "Sadaƙa ce Al'amin na dukka zaka ce, niyyar na tare da ni da ɗiyata". Ya karɓi kuɗin ya tafi, lokacin kuwa matar ke kwashe na cikin kasko, da yake duk magriba ana idar da sallah ta ke fitowa ta fara suya, kuma kafin ka ce wannan an siye ta tashi. Tuni har an gama kai kayana cikin gida, muna shiga daga soro na samu Ummani tsaye na doka tsalle na ɗafe jikinta, itama Allah sarki uwa sai na ji tayi ihun murna har da su guɗa wacca ban taɓa ji tayi ba tana faɗin Alhamdulillah, Allah mun gode maka, muna godiya gare ka da ka kai mana ƴar mu lafiya ka dawo da ita lafiya ka kuma bamu aron rai da lafiya ganin lokacin da bamu tsammaci zamu kai ba. Daga cikin gida muka shiga in da duk ƴan gidan mu suka firfito, suma carko carko a tsakar gidanmu, dama dai ɓangarenmu tsakar gidan hanya ce don kowa ta nan yake wucewa ya shige sauran ɓangarorin, kowa sai taya ni murnar dawowata yake, kuma kowa ya zo bai min kallo ɗaya sai ya ƙara ya kuma ƙarawa, bayan kallon kyau har da na burgewa ganina sanye da kayan ma'aikatan lafiya. Sai ga Umman su Hindatu ta taho da tafinta tana,"Lale lale oyoyo oyoyo da mutanen ƙasar wajen, ohh ni Haule Sa'ida ke ce kika koma haka, Allah azimun wallahi kamar an canja ki, sannu da dawowa sannu sannu, shikenan abin acas cas mun yi likita a gida". Ina ta murmushina bakina yaƙi rufuwa na rissina na gaida ita. Yaran ma duk ina murmushi muka gaggaisa da su ina musu godiya da yanda suka nuna min kulawa, sai yau na ke jin ina ma ina da ƙanne da muke ciki ɗaya. "Sai kika ji haihuwar ƴar uwarki, na ce da Sa'ida na nan ai ita zata karɓi haihuwa". Cewar Umman su Hindatu. Na ce,"Ai Umma ji nayi kamar nayi tsuntsuwa na taho wallahi, wai ace Hindatu ta haihu bana nan". "To ya za'ayi, ai kun yi ɗa shima sai yanzu zai ga Babarsa". Haka dai muka ɗan taɓa hira anan tsaye kafin taja yaranta suka koma sashen su, ina duban Ummani na ce,"Umma fa?". Tace,"Kema kin san hali, ai tun da kika tafi ta daina min magana, ko zata wuce ta tsakar gidan nan sau ɗari ƙala ba zata ce min ba, to ni dai da na fita ilimi bana fasa yi mata sallama, yanzu leƙa can wajen na ta kar dai ki jima balle ranki ya ɓaci, Aniyarta ta baƙin ciki ta tsaya iya kanta". Girgiza kai nayi ina faɗin,"Allah ya kyauta, ita Umma ana girma rayuwa na tafiya amma tana abu kaman yarinya ƙarama, wa ya san ranar rabuwar da babu dawowa, ni kam ban jin daɗin halin nan nata". Ashe Abbaa yana jiyo mu sai ga shi ya fito daga ɗaki yana cewa,"Kin ga rabu da ita kar ki je, idan Babanki ya dawo taci albarkacinsa. Shiga ɗakin Kakan ku ga shi can naji yana ƙwala kiran ki". Allah sarki Kaka, ai kuwa da hanzarina nayi ɗakinsa, ina shiga na same shi kishingiɗe yana firfita, ya ƙara tsufa bawan Allah, na isa gabansa kaina rissine a ƙasa muka gaisa, ashe bama ya gani sosai yanzu dama tun ina can ake ta ce min yana fama da jinya, to da yake dai cuta ba mutuwa ba ce. Na ɗan jima a wurinsa kafin na fito na koma ɗakin Abbaa, na same shi zaune shi da Ummani, an baje min kulolin abinci Ummani na cewa,"Da duk yanda aka yi a ƙoshe kike ko, na ga ba ki halin sabonki ba na ki diro gida ki ce akwai abinci". Gajeriyar dariya nayi ina cewa,"Kinga ai mun ci abinci a jirgi shiyasa, don ma dai na ce ba zan ci da yawa ba kar na cika cikina". Ummani tace,"Ohh banda Allah waye zai maka, wai yau ƴar mu ce ta hau jirgi ta keta hazo, to ubangiji yanda ya kira ki tafiya ƙasar turai karatu ya kira mu zuwa ƙasa me tsarki mu ziyar ɗakinsa mu ziyar ci ƙabarin masoyi fiyayyan halitta Annabi Muhammadu SAW". Dukkan mu muka yi salati ga manzon tsira, na zauna ina cewa,"In sha Allahu Ummani indai saudiya ne mun kusa muje, Allah ya bani arziƙin da zan kai ku, amma tabbas a jikina ina jin lokacin ya kusa". Ita da Abbaa suka haɗa baki wajen furta,"Ilahi ajib". Sannan muka shiga gaisawa da su, zuciyata sai motsawa take da so da ƙaunar mahaifana gami da tausayin su da jin ƙan su, rayuwa kenan duk sun ƙara girma musamman ma Abbaa kansa duk furfura ta fara yawa, da ka gansa dai ka san shekaru sun ja masa. Ummani tace,"Ai ni dawowarki ta min hajji da umara, ga shi nan tun shekara jiya Abbanki ya siyo ganda saboda ke". Tuni yawuna ya tsinke na matsa wajen kwanukan ina cewa,"Allah sarki Abbaana na gode Allah ya ƙara lafiya da wadata, fatan dai ba'a kwashe an rabar min ba". Ummani na girgiza kai tace,"Au wahalar dafuwar ma da nayi ban miki gwaninta ba kenan, to bara na ɗauka na ƙarasa rabarwar". Murmushi nayi da cewa,"Yi haƙuri Ummanin mu". Tuni na tasa kwano a gabana na fara kaiwa baka don ganda na ɗaya daga cikin naman da na ke so a rayuwata, ko da sallah ni ban fiya ma cin nama ba kamar yanda na ke cin ganda". Da yake ba wani yawa ne da ita ba dama dai ya siyota ne saboda ni ɗin, don haka tuni na ga bayanta Ummani har na tsokanata da kura kura. Bayan na gama ci ne nake cewa,"Wai yaushe su Maman Yasmin suka yi tafiyar?". Ummani tace,"Kwana uku da rasuwar kenan, shima Yashaik ɗin ai sai ɗazu da rana ya tafi da yace zai jira dawowarki". Nace,"Allah jiƙan rai, naji mutuwar iya kuwa". "Da safe sai ki kirata ki mata gaisuwa, kin san ita ta yayeta". Abbaa yace to naje nayi salloli na kafin yaje masallaci shima ya dawo, na fito sai yanzu na ke ƙarewa gidan namu kallo da yake sun kawo nepa yanzu yanzu, sai naga gidan yay min faɗi kamar ba shi ba, an dai yi masa kwaskwarima ba kamar yanda na tafi na barsa ba, duk jikin bango da ya farfashe anyi siminti, sai irin fasassun tiles ɗin nan iri ɗaya da aka lailaye tsarkar gidan da shi, yay kyau sosai wallahi, gyara yana da kyau a ƙalla ko baka sabunta ba yafi ka bar waje a lalace. Na idar da Alwala na ke cewa da Ummani wacca ke daga cikin ɗaki,"Ummani wa ya saka tiles ɗin nan?". Tace,"Al'amin ne wallahi, sun yi aikin gini a wani gida sai me gidan yace ma'aikatan su ɗauka su raba, shi ne bayan sun rarraba shi kuma ya ƙara siya, har fa ɗakina da na ki, ɗakin Abban ku ne kawai ba'a saka ba, yayi kyau ko?". "Kyau sosai ma Ummani, sai ya ƙara haska gidan". "To yi dai sallar tukunna kya gyaran da aka yi, ɗakinki kamar ba shi ba". Tsalle na ɗanyi ina murna na ce,"A'a su Yaya Al'amin anyi abin kai iyee, har da ɗakina". Ɗakin nawa kuwa yay kyau, an yi shafe irin dai ragowa yay aka ɗan gogga, dama tun asalinsa ba fenti siminti ne shima kuma ba ko'ina ba, hatta rufin ɗakin ma an mayar da silin wajen da suka ciccire in ana ruwa ya dinƙa zuba. Allah sarki uwata ta gyara min shi gwanin sha'awa sai ƙamshin turaren wuta yake yi, ƴar yaloluwar katifata ma ta lailaye min ita da wani tsohon bedsheet ɗinta, bani da filo amma har da filo ba zai wuce ko nata ko na Abbaa ta ɗauko min ba. Allah dai ya bani ikon kyautatawa musu, ya kuma basu tsawon rai da lafiyar da zasu ci moriyata. Bayan na idar da sallah ina ƙarasa karanta suratul yasin da iza waƙa da basu wuce ni duk dare, Ummani ta leƙo tana ce min. "Kinga da na zuba miki ruwan zafi kiyi wanka, ko ba sai kin yi ba?". Na kai ƙarshen suratul yasin ina cewa,"Zan yi Ummani, jikina duk gajiya". "To sai ki hanzarta kar ya huce, garwashin ya ƙare kuma bamu da wani gawayin a ajiye, gas kuwa yay tsada idan kin ganmu da shi albashi aka yiwa Yashaik". Na shafa adu'a na miƙe ina lalubo zani na ɗaura, ita kuma sannan ta shigo tana gyara min net ɗin da aka kafa a jikin taga saboda sauro. "Wallahi Ummani gyaran nan da aka yi yayi kyau, kinga anyi dabara sauro ya rage shigowa". "Al'amin yay dabarar, ba kiga har bakin ƙofar ya haɗa da net ba a jikin labulen, Abbanki yanzu sai yay kwanciyarsa ma babu net ba maganin sauro". "An huta ai da cacar siyan maganin sauro kuwa, Su Yaya Al'amin an yi abin arziƙi". Ta ɗan yi dariya da cewa,"Ke da shi idan ya shigo ya jiki, kyama yi masa Allah sanya alkhairi anje an tambayo masa aure". Na waro ido waje ina faɗin,"Da gaske Ummani! Tab wace wannan kuwa ta ɗaukarwa kanta halin nurƙufanci". Na ƙyalƙyale da dariya ina sake faɗin,"Tab Yaya Al'amin ni wallahi ban tsammaci ma yana kule kulen ƴan mata ba, dama shiru shirun nan ki kalle su kawai, aina ya samo matar Ummani?". "Kin ma santa ai, ina gidan Alhaji Saleh nan baya wajen gidan me markaɗe, to jikin gidan akwai gidan farare da ake cewa ana siyar da kunu da awara da safe". Nace,"Eh eh na gane gidan, da suna markaɗe ko?". "Ƙwarai nan kuwa, to ɓangaren da suke yin gurasa za kiji ana wajen Baaba tabawa, ai yarinyar jikarta ce ruƙonta take yi". Bakina buɗe nace,"Ko dai wata za kiga tana biyowa Sajida tafiya islamiya, doguwa fara me ɗan jiki haka, naji kamar ma buzuwa suke ce mata". "Ai kuwa dai ita ce, su Abbanki har wani daji acan ƙarshen katsina suka je bincike". Ina kaɗa kai na ce,"Abbaa kenan, hakan ai yana da kyau gudun samun matsala". Muna haka Yaya Al'amin ya leƙo ɗakin, guntuwar dariya saman fuskata na ce,"Su Yaya ashe an girma an kusa aure". Murmushi yay yana kawo min hannu yace,"Ki kiyaye ni, ke ai na ke jira ma ki zo ki kwance jaka ki fiddo min lefena dan nauyin akan ki yake yarinya". "Yaya baka da damuwa kai dai kayi adu'a Allah yasa na samu aiki, in dai aiki ya samu Yaya to lefe sai na maka akwatu biyu da izinin Allah, ai kafi ƙarfin haka ma a wurina, ko me nayi muku ban faɗi ba wallahi. Ga gyara nan ma kayi mana gida yay kyau mun zama ƴan gayu". Yace,"Kin ga ma gado da kwabarta nace a kaiwa Yahuza kafinta ya siya na cika ayi mata sababbi taƙi yarda". Ummani tayi karaf tace,"Kaga ni fa ka ƙyale ni da wani zancen sauya gado da kwaba, ka adana kuɗin akwai lokacin amfanin su, haka kawai na tsufa sai kace wata yarinya ace za'a sauyan kayan ɗaki". Na fita a ɗakin ina cewa,"Ƙyaleta Yaya Al'amin ka yiwa Abbaa gudunmawa idan ya tashi ƙaro aure, ai dama naji ƙishin ƙishin ɗin sun daidaita da Rabi dillaliya". Karaf naji saukar murfi akaina. Ina dariya sosai na shige banɗaki da gudu, bayan na fito a wanka na shirya tukunna na isa ɗakin Abbaa, ina shiga yace naje mu gaisa da Baba Sabi'u da Baba Tijjani duk sun dawo. Sai bayan na dawo daga wurin su ne na ci abinci na ƙoshi sannan kuma aka shiga hira, ina ta basu labarin can ƙasar da yanda akayi gwagwarmayar karatu. Sosai iyayen nawa suka ji daɗin yanda ban wani wahala ko na fuskanci ƙalubale mara daɗi ba, dama ƙalubalen dai farko farko ne da ban wani ƙware da iya turanci ba to sai nayi ta jin wahalar yin magana da mutane musamman Malamai, har dai kuma a hankali da Allah ya haɗa jinina da wata Joy Johnsun take cewa haka zan ke ta gwada ko da za'a min dariya, nobody is perfect duk wanda ba yaren uwarsa ba ne to koya yay, da hakan kuma sai ga shi ko a award ɗin speech na ƴan nigeria da aka bayar ina ɗaya daga cikin mutum biyar da aka bawa kyauta, ni ce ta uku sai wani mas'ud da tare muke karatu da shi aka basa na ɗaya. Na kunce jakata na ɗauko kuɗi na miƙawa Abbaa na ce ga shi ya riƙe, ganin yawan kuɗin sai ya saki baki yana kallona da ayar tambaya. A hankali na shiga masa bayanin cewa,"Abbaa da yake acan su kan bawa ɗalibai kuɗi duk ƙarshen wata mutum ya ɗan siya abubuwan buƙata na karatu da dai abin da mutum ba zai rasa ba, to a ciki Abbaa na ke ɗan cire wani abun ina ajiyewa har suka taru haka, don sai da wani course mate ɗina yazo nigeria na ce masa ya canja min su, da zai koma sai ya tafi min da su. Abbaa ya mayar da ƙwayar idonsa kan kuɗin yana dubansu da jinjinawa yace,"To Sa'ida nan nawa ne kenan? Tun da na ke a rayuwata ban taɓa riƙe kuɗi masu yawan haka ba, naji su da yawa har danne hannu suke yi". "Dubu Ɗari biyar ne Abbaa, dama na ce a ciki sai a bawa su Yaya wani abun sauran kuma ku riƙe kai da Ummani". Murmushi me faɗi naga ya bayyana saman fuskarsa, kafin a hankali kuma ya kai hannu ya goge ƙwallar farin ciki, sannu a hankali ya shiga jero min goiya da sanya albarka kamar zai ƙarar da yawun bakinsa. Ummani kuwa ta ɗaga hannu sama tana godiya ga rabbi, faɗi take yi,"Haihuwa me daɗi, haihuwa me rana, Allah yay miki albarka wannan yarinya ya kawo miki babban rabo, ya azurtaki da mijin marainiya". Abbaa ya miƙe ya fita zuwa ɗakin Kaka, bai jima sosai a can ba ya dawo ya zauna, bayan ya numfasa yay nisa tare da ce min. "To yanzu Sa'ida ya ake yi kuma wajen neman aiki? Ko kuwa kana zaune ake neman ka?". Nace,"Ehh to Abbaa zan fara rubuta CV daga nan sai in kakkai muga ko Allah zai sa a dace, sannan akwai hanya ma da ake bi idan Allah ya taimake ka ya haɗaka da mutane na gari sai kaga abin ya zo da sauƙi kuma cikin aminci". Abbaa yace,"To shi abin da kika faɗa ɗin ya ake yinsa?". "Bayanai na zan rubuta Abbaa, kuma kaga tun da Allah yasa ma da result ɗin a hannu kuma an samu me kyau ba za'a wahala ba in Allah ya yarda". Yay ɗan jim kafin yace,"To shikenan Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi, idan Yayunki sun zo sai muyi magana da su naji, amma ban amince ki nemi taimakon wani ko hanya ta wajen wani ba, wannan duk Yayyunki zasu miki insha Allahu, mutane yanzu babu amana ke ba ƙaramar yarinya ba ce yanzu kina da hankalin tunani, idan kika rubuta shi bayanan duk ranar da za ki je kaiwa wajen ɗaukar aikin sai kiyi min magana mu tafi tare, Allah ya taimaka ya ƙara tsare mana ke da mutuncinki". Na amsa da amin, mun jima muna ta hira da su don har sai ƙarfe sha ɗaya tukunna na baro ɗakin Abbaa, ina shiga ɗakina kuwa sai bacci, yau ko sallar dare ma ban samu damar yi ba sai da ana sallar asuba na farka shima da ƙyar, don har Abbaa ya tafi masallaci ban iya miƙewa ba, dama shi kafin ya tafi sai ya buga mana ƙofa ni da Yaya Al'amin har sai mun tashi mun buɗe kafin ya wuce. Kwanana huɗu da dawowa Abbaa yace na shirya muje can ƙauye, ni da shi muka je ƙauyen su da na su Ummani muka gaggaisa da ƴan uwa sai da muka kwana biyu muka dawo. Muna dawowa kuwa a washegari na dire a gidan Safiyya da yake itama anan Kano take Nasarawa GRA, mijinta me kuɗi ne ɗan siyasa Babba da ake damawa da shi a wannan gwamnatin. Shekarata biyu a germany aka yi bikin har kusan kuka nayi a lokacin, na so ace ina nan aka yi bikin Safiyya, lokacin nawa tarewa tayi a gidanmu itace akan komai nawa. Gidanta masha Allah kamar ba a kano ba, kuma Allah ya bata mijin marainiya, yana mugun sonta sosai, ko da ta haihu sunanta ya sakawa ƴar suke ce mata Ilham, to da ke ma dai ƙawarta sai a hankali halinta sai ita tsiya take tsula masa son ranta, Ummansu tana faɗa min tace in ke bata shawara ina yi mata faɗa don ita har ta fara gajiya da halinta. Na dai bata shawara matsayina na amiyar ƙwarai, sai take ce min ita wallahi ban da mahaifanta auren nan ba yinsa zata yi ba, ita soyayyar duk da yake mata ba wani yarda tayi da ita ba saboda tun abun da ya faru akaina take tsoron sharrin kowanne namiji, na ce mata to ai ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, tayi ta adu'a kawai Allah kar ya kawo abin da zai canja daɗin zamantakewar aurenta. Ranar yini nayi muna shafta ni da ita, don har magriba, zance daya sai ta kama min zancen fitar da mijin aure tunda na gama karatu, yanzu ko aure nayi karyar namiji yace zai wulaƙanta ni, haka nayi ta bagarar da zancenta har ta haƙura ta ƙyale ni, don ko a gida Ummani sai tayi ta cewa,"Karatu ya kammala, Allah kawo aikin yi da mijin marainiya". Yi na ke kamar ban jita ba idan ta faɗi hakan, Abbaa kuwa kamar zuciyarmu ɗaya, tun da na dawo banji ya ambata min kalmar miji ba, sha'anina kawai ya barni na ke yi babu wani takurawa, don sai in ce abinda na ke a yanzu ban yisa lokacin ƴan matancina ba. Ga shi dawowata zuwa ake ko da yaushe maneman aure ta ko'ina, ni kuwa nayi mirsisi naƙi fita ko idan Ummani ta lallaɓa ni naje soro na sha zamana tukunna in dawo, ni sam aure ya fita kaina bana fatan ma na sake maimaita shi, na ƙwammaci na mutu da na kara yin aure. Abbaa ba ya sauraron duk wanda ya zo wajensa, sai yace shi a bar masa ƴa ta sarara ai ba a gidan ruƙo take ba balle a ƙwazzafeta. Haka mu ke ta sana'armu ta siyar da zoɓo da kunun aya ni da mahaifiyata, ga awara ma da na ke yi ƴar order da mutane ke sawa, a rana sai nayi ta dubu biyar sama, masu siyan ma duk yawanci Safiyya ke haɗa ni da su, Maman Khairi zata siyar da firij ɗinta Yaya Imam yace to ya siyawa Ummani tunda ana samun wuta sosai, yafi ayi ta faman siyan kanƙara ko da yaushe. Sana'ar ɗinkina kuwa ba kama ƙafar yaro, gowns na ke ɗinkawa ina ɗorawa a jiji app da instgram, Allah yasa min nasibi a nemana ko da yaushe sai nayi ciniki, kafin na fara ɗora kayan sana'ata sai naja lahaula wala ƙuwwa ƙafa goma tukunna, wannan sirri ne da duk wanda ya riƙe a kasuwancinsa zai sha mamaki. A gefe ɗaya kuwa Abbaa yasa Yayyuna suna ta fafutukar nemar min aiki, Yashaik ya rabawa mutanensa takarduna sun fi biyar, Yaya Imam ma da nasa jama'ar, shi kansa Abbaa sai da yace na basa file guda biyu ko da wataran a kasuwa zai ji ana hira tun da akwai ƴan harkar siyasa da yawa kusa da teburin su. Ta ɓangarena dai ni babu wani motsi da na ke yi, kawai dai naga su sun tsaya akan lamarin da iyaka ƙoƙarin su sai na barshi na san inda rabo za'a dace. Ana haka wataran da daddare muna zaune a tsakar gida ni da su Abbaa, har da su Yaya Imam ma da yake duk dare idan suka dawo daga wurin aiki kafin su tafi gida sai sun zo nan sun ɗan jima a wajen iyayensu kana su tafi wurin iyalin su, ana hira Abbaa yana bamu labarin rayuwarsu ta da, ni kuma ina zancen idan na samu kuɗi shagon siyar da kaya zan buɗe, na nunawa Abbaa bidoyin whatsapp na irin yacca mata ke ta buɗe shago, aikuwa kowa ya ƙarfafa min gwiwa da tayani adu'a, Abbaa dai yace ba zai hana ni ba tunda neman halalina ne amma tare da Yaya Al'amin zamu ke zama a ciki, kamar kuma ya shiga zuciyata ya ga abin da ke ciki. Wayata ce tayi ƙara, na ɗauka ina duba saƙon da ya shigo, kasantuwar datana a buɗe yake sai nayi gaggawan shiga email ɗin na duba, abin da na gani shi yasa ni ƙara tare da dire wayar ina ɗaga hannu sama ina faɗin Alhamdulillah, sai duk hankalinsu yayo kaina nima na maida hankalina gare su ina Kallon Abbaa tare da miƙa masa wayar na ce. "Abbaa wani asibiti ne suke nemana naje interview jibi". Yashaik ya miƙo hannu yana faɗin,"Mu gani". Na basa suka shiga dubawa shi da Yaya Imam, lokacin kuma wani saƙon ke ƙara shigowa ta text message duka dai daga asibiti ɗaya. Ai fa kowa sai murna tare da adu'an Allah sa a dace, Kaka bawan Allah sai ga shi ya rarrafo daga ɗaki yana dogara sanda ya fito shima aka hau murna da shi. Bayan kwana biyu kuwa na shirya da wuri don ƙarfe takwas suka rubuta cewar naje, Daren ranar ban rumtsa ina ta gayawa Allah haka iyayena ma, ƙarfe shida da rabi muka bar gida ni da Abbaa wai gudun kar mu makara azo a samu asara, ni dai da muka je baki na saki ina kallo, to asibiti babba haka na masu kuɗi wa ya kawo ni?. Ina duban Abbaa na ce,"Anya kuwa nan ne?". Abbaa ma dai shima da kokonto cikin ransa yace,"Ɗauko takardar da kika curo". Na fito da ita na ba shi, yace,"To ai sai dai mu shiga tare mu tambaya kinga ba lallai suna jin hausa ba ko?". Da wannan dan wannan kam, muka shiga tare ya dakatar da wani dattijo yay masa sallama suka gaisa, hausar tasa dai bata fita sosai don haka da ni muka ƙarasa magana cikin harshen turanci. Ya tabbatar mana da nan ɗin ne yanzu haka ma ai an kusa fara interview ɗin nayi sauri na shiga kar layi yay yawa, Abbaa yace to idan ba rabo na ubangiji ba Sa'ida wannan asiti ai sai kallo daga nesa. Nan ya zauna daga waje yana jirana, suka zauna tare da wancan mutumin. EHA Clinics Kano sunan asibitin anan Lamiɗo Crescent yake. Tsawon kwana biyu na ɗauka ana min gwaji wani babban likita ne me zaman kansa kuma bature ne ma, yawancin Drs ɗin duk turawa ne, nurses ɗin kuwa ƙalilan ne waɗanda suka yi karatu a nageria suma kuma duk ƴan private school ne. cikin ikon Allah kuma duba da ƙwarewata da ƙwazona suka tabbar da cewar sun ɗauke ni aiki tare da su, duk wata za su ke biyana dubu ɗari da casa'in. Ni dai abun tamkar a mafarki haka naji jin salary amount ɗina, Cikin sati guda na fara zuwa aikin, Abbaa bai yarda da batun night duty ba don ce yay indai zan ke aikin dare to gwara a haƙura da aikin, ya saɓi ƙafa shi da Yaya Imam suka je har can suka ga managern wurin, ya roƙe shi yace masa suna son aikin amma in dai zan dinga aikin kwana to gwara na haƙura, amma idan sun yarda aiki ko ce suka yi na fito da asuba to shi zai rako ni ma kafin lokaci, ya yarda na yini acan ɗin amma shi ban da dare, da haka aka tsara roster ɗin morning and evening duty da ni banda night. Sai da na jera sati guda Abbaa na raka ni kullum kuma idan lokacin tashi yayi shi zai je mu taho tare, har sun saba ma da mutanen asibitin, hatta managern kansa idan yaga zuwan Abbaa sai yace ya shigo daga cikin office ɗinsa. Watan farko da na ɗauka albashina jiki na rawa na tafi na curo su, ɗari da casa'in cass kuma babu lissafin kuɗin mota da na abinci, suke bamu na mota duk sati abinci kuwa Ummani dafa min take na tafi da kayana. Naira dubu hamsin na cire na damƙawa mahaifiyata, na zare saba'in na damƙawa Abbaa, na kara cire arba'in na bawa Yaya Imam da Yashaik ashirin ashirin, Yaya Al'amin na ba shi goma sha biyar, na cire biyar na bawa Kaka shima, sauran goman kuwa na kaiwa Baba Tijjani da Baba Sabi'u, naira biyar ban sha'awar naci ba a ciki, don tun ranar da na samu aikin na gama kasafin kuɗin. Aikuwa tsabagen adu'a da albarkar da aka dinƙa sanya min a cikin gidan nan sai da nayi kukan farin ciki. Har da su Umma aka zo ana taya ni murna nayi ta mamaki, na ce wato idan kana da shi sai ayi da kai, idan baka da shi baka kai ba ɗan iska kawai kake. Ummansu Hindatu ma kanta sai da ta faɗa tace,"Ai ko bata so ki don Allah ba yanzu ta soki don abin hannunki, kiga dai tun da kika dawo fa bata saurareki ba". Ummani tace,"Allah dai ya kyauta kawai". ______________________________ *_Tambayar da zan yi muku, duba da irin rayuwar da Sa'ida ta fuskanta a gidan tsohon mijinta, mu ɗauki matsayin hakan a zahirin rayuwa, babu yanda ubangiji ba ya lamarinsa, shin kuna ganin ubangiji zai iya ƙadartawa ta komawa Nazifi? A bar shi wataƙila yay nadamar abubuwan da ya aikata, sannan yana cikin hali na a tausayawa masa duk da bamu da tabbacin hakan don yanzu bamu san wacce rayuwa yake ciki ba, ko kuma ace ma Allah ya barsa da dukiyarsa amma kuma yay danasani da nadama yana neman dawo da Sa'ida gidansa, kuma mu ƙaddara wataƙila yana da sa hannu a wancan ɗawainiya ta karatunta, haka itama ɓangaren Sa'idan ta zaɓi komawa gare shi...idan hakan ta kasance ya zamu ɗauki al'amarin dukkan mu? Ko ma dai a ganinmu kwata kwata lamari ne da ba zai fara somuwa ba? Kuma a tsumayinku da tunaninku wanne kalar miji Sa'ida zata ƙara aura tun da dai ba zamu so ta ƙare rayuwanta a zaman zawarci ba....ina jiran jin ra'ayoyin ku akan hakan_* [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR02FT5* Ƙaramin yaro ya shigo gidan yana cewa,"Salamu alaikum a bada zoɓo". Ummani da ke daga cikin ɗaki tace,"Ana zuwa". Ta fito daidai lokacin tana tambayarsa,"Na nawa?". "Na ɗari, wai don Allah a bada na roba me kyau". Tayi murmushi tana cewa,"Ai duk masu kyau ne". Tana saka masa cikin leda wani yaron ya kuma shigowa yace,"Akwai kunun aya?". Tace,"Babu sai gobe idan Allah ya kaimu". Ta sallami me zoɓo Kaka yace mata,"Me yasa ba ku yi kunun ayar ba bayan kun san anfi son sa". Tace,"Jiya ne Sa'ida ta dawo a gajiye bata samu damar yi ba". "To amma ke da ba sai kiyi ba". "Kaka hannun jikar taka sirri ne da shi, akwai zaƙin hannu idan tayi wallahi yafi nawa daɗi". Kitchen ta shiga ta ɗauko abinci a ƙaramin filas tace da Kaka,"A shigar maka da shi cikin ɗakin ko anan zaka ci?". Ya gyara zama daga kishingiɗen da yake yace,"Bar min anan cikin ɗakin zafi, nepa sun hana wuta yau". Ta ajiya masa ta ɗauko ruwa ta aje masa, shi kuma yana ta saka mata albarka don shi kansa kaf matan ƴaƴansa yafi son Ummani, a ko da yaushe yabonta yake yi domin ita ɗin macece ta ƙwarai, yanda take masa tamkar shi ya haifeta. Yashaik ya shigo gidan, a nan tabarmar da Kaka yake ya zauna suna gaisawa, kafin daga bisani ya miƙe ya shiga ciki wurin mahaifiyarsa. Samunta yay ta fito da kayan sif ɗinta dukka tana linkewa, daga gefe ya zauna yan agaishe da ita ta amsa tana tambayarsa ya iyali. "Me makon ki aika a kira miki Maman Yasmin, yanzu ina ke ina aikin ninkin kaya masu yawa haka". "Ku dai kun fi so kuyi ta gani na kwance sharaf wuri ɗaya bana aikin komai, haka kawai kuma yarinya na can gidanta tana aikinta sai na aika a tasota, a'a kayan nawa suke gaba ɗaya yanzu zan gama ai. Yau babu in da kaje kenan?". Ya sauke numfashi yace,"Ban leƙa ko ina ba, gani nayi gwara in ke hutawa lahadin jiki na buƙatar hutu". "Haka ne, Allah daɗa rufa asiri. Jiya naji ka ce zaku yi magana da Abbaan ku sai ban ga ka dawo ba shiru, ba dai wata matsalar ba ce ko?". Ya kai hannu yana shiga tayata linkin kayan yace,"Da na ƙyale ne kawai saboda na san ko naje masa da zancen ba karɓa zai yi ba, wataƙila ma raina ya iya ɓaci, sai dai ko ke za ki faɗa masa". Ummani ta mayar da hankalinta kansa sosai tace,"Menene fa?". Yace,"Ba fa matsala ba ce". Ya faɗa yanda yaga mahaifiyar tasa ta kafe shi da idanu. "Dama akan Sa'ida ne ban san me Abbaa ke hange ba da yaƙi bawa zaurawan nata dama, haka kuma gaba ɗaya bai son zancen auren nata ba, amma ni gani na ke bai kamata a biye mata ba, duk da cewar dole auren ya sire mata, amma ai ba zamu ɗauka cewa lallai abin da ya faru a farko shi zai kuma faruwa ba ko kuma yayta maimaituwa, kawai ta ɗauka hakan matsayin jarabawarta ba wai saboda dalilin hakan kuma tace ita ba zata ƙara yin wani auren ba. ita macece ko ai na take ko me take yi duk matsayin da take da shi da aurenta tafi daraja a idon duniya, kuma ku kan ku idan da aurenta hankalinki zai fi kwanciya, kuma sannan shekaru tafiya suke ta yi gaba ba dawo baya zasu yi ba, nan da wata shekarar magana ake ta zata shekara talatin idan da rai da kuma lafiya, to ta gama karatun ta samu aikin yi me za'a ƙara jira Ummani? Baka biyewa maganar mutane balle ta dameka amma ana gudun baki, wani bakin kaifi ne sune masu kambun baka, ni gaskiya na fi ga sha'awar tayi aurenta, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ta dage da adu'a kawai Allah kar ya maimaita mata irin mijin baya". Ummani ta numfasa tace,"Ni kaina da ka ganni wlh yanzu hankalina yafi ga tayi auren, Sa'id idan ta fita aikin wannan wallahi sam sam bana samun natsuwa har taje ta dawo hankalina ba'a kwance yake ba, amma lokaci ne duk dai Abbaan naku na daƙile damar hakan, Allah dai ya kawo mata na gari ya musanya mata da mafificin alkhairi". "To amin ya Allah. Kuma dama Nura ne yay min magana ɗazu da safe yace abokinsa Ya ganta yace idan ba'a tsayar da maganar wani akanta ba ya gani yana so". Ummani tayi murmushi me faɗi tace,"Allah sarki, ai na yake to?". "A can garejin ma su yake shima, kin sansa ma sai dai ba za ki gane shi ba, amma da sallah ƙarama tare suka zo da Nuran ai". Tace,"To madallah, ai ina ga sai kace masa ya tunkari Abbaan na ku da maganar ko, ya gwada tasa sa'ar ko a kansa dacen yake". "Ehh to dama ni abin da ma yasa ban masa maganar so na ke na fara bugar cikinta naji ko tana da ra'ayin auren me ƴaƴa". Ummani tayi gajeriyar dariya tace,"To ita wanne zaɓin saurayi ne da ita yanzu, sai dai kuma wani lamarin na Allah, fatan dai Allah bata wanda yafi wancan". Da haka suka ci gaba da hirarsu akan maganar Al'amin ma da za'a kai kuɗin aure cikin satin nan, har sai da suka ninke kayan dukka. Shi ya share mata ɗaki ya goge ko ina, yay mata sharar tsakar gida da kitchen suma duk sai da yay mopping, dama sun saba hakan shi da Imam duk sanda suka sameta tana aiki, don shi da yake kusa da suma da sassafe yake zuwa yay sharar soro da ƙofar gida. Bayan tafiyarsa yana zuwa gida kuwa ya aiko mata Yasmin wadda ta shigo tana ta ƙunci wai Kawu yace ta zo tayi wanke wanke. Da yamma yaro ya shigo tsakar gida yana ta doka sallama babu wanda ya amsa, Ummani na daga cikin ɗaki a kwance kamar a mafarki taji sallaman wajen ƙofan ɗakinta, tayi saurin tashi tana cewa,"waye ne?". Yaron yace,"Ai ko ni aka yi, wai ana sallama da me gidan". Labule ta ɗaga ta leƙo tana cewa da shi,"To masu gidan ai da yawa, kaje kace wa ake nema?". Ba jimawa ya dawo yana cewa,"Wai Malam Salman". Ummani tace,"Tooo wallahi ba ya nan, amma kace musu yana kan hanyarsa ta dawowa ko zasu jira shi, suna da yawa ne?". Yaron yace,"Ehh mota biyu ce har da sojoji". Gaban Ummani ya yanke ya faɗi ya bada rasss, tayi saurin dafe ƙirji tana faɗin,"Sojoji kuma ɗan nan? An ya ba makuwa ka yi ba kuwa, ko can ɗaya gidan aka aika ka kusa da me kayan miya". Yace,"A'a ni dai nan suka ce min". "To shikenan je ka kace musu bai dawo daga kasuwa ba sai dare". Yaron ya juya ya fita ita kuma ta dawo cikin ɗaki, ta kasa zaune tayi tsaye tana tunanin lafiya? Me zai kawo sojoji neman Abbaan su? Sai tayi maza ta ɗauki wayarta ta yiwa Sa'ida flashing, Sa'ida ta biyo bayan kiran, ta ɗaga tana ce mata,"Ke sako min kati zan kira Abban ku". Yanayin fitar muryan nata yasa Sa'ida cewa"Lafiya Ummani?". "Lafiya lau sauri sako min zan ba shi sallahu ne a kasuwa kar ya riga ya taho". Within one minutes sai ga shigowan katin ɗari biyar a wayar, ta lalubo sunan Abbaan Sa'id ta kira. Abbaa a lokacin na bakin titi ya ɗaga kiran wanda hayaniyar ƙarar ababen hawa bai barin sa yaji me take cewa itama ɗin kuma bata jinsa sosai, haka tayi ta faman kira ƙarshe sai haƙura tayi, ta fito tsakar gida ta zauna tayi jugum, har sai da ta leƙa ƙofar gidan taga tabbacin maganar yaron, soja ɗaya na tsaye bakin mota da bindiga a hannu, wannan fa yasa ta daɗa tsurewa ta kama safa da marwa a tsakar gida tana ta faɗin Allah sa lafiya. Bayan kusan rabin awa sai ga Abbaa ya shigo gidan a gaggauce yana ƙwala kiran,"Sa'a! Sa'a! miƙo min babbar tabarma maza maza". Irin yanda yake ƙwala kiran bana lafiya ba, Ummani ta fito daga ɗaki fuskar hijabi a juye jiki duk sai ɓari yake yi, ganin yanda Abbaan yake shima da ruɗani ta tsaya tambayan,"Abbaa lafiya? Kaga baƙin ƙofar gidan ne kaima?". Bai amsa mata ba yaci gaba da ɗauraye ƙafarsa da duk tayi ƙura tare da wanke fuskarsa ma. "Ni dai sauri miƙo min tabarmar tukunna, ni kaina ba na ce miki lafiya ko ba lafiya ba Sa'a, amma hankalina duk ya tashi". "Abbaa to kaje wurin su kuwa? Ko na aika a kira Yashaik yau yana gida bai fita ba". "A'a ƙyale su Sa'a, bara na fara jin me ke tafe da su sun ce sun jima waje, maza miƙo min tabarmar dai, kin san irin mutanen ba'a barin su da jira". Ganin ta tsaya kawai ya wuceta yay ɗakinsa ya buɗe ya yayibo tabarma ya fito yay waje da hanzari, duk ya rikice tafiyar tamkar zai kifa ƙasa. A soro ya baza ƙatuwar tabarmar, takalamansa ma a baibai ya saka ya leƙa yana ce musu,"Bismillah ku shigo daga ciki". Zatonsa iyaka waɗannan sojoji biyun na waje ne sai yaga an buɗe mota manyan mutane dattawan arziƙi suna fitowa, da kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka shaida duniya ta san su ta san da zaman su, matsayi kuma an same shi sai wanda ake kan rabawa, kuma masu faɗa ne aji a ƙasar da suke ciki. Sojojin na basu kariya har suka shigo soron wanda duk Abbaa ya daɗa hargitsewa yana duban tabarmar da duk ta ɗan sha jiki, da shi kansa soron gidan wanda yake ganin sun girmi su ko rakuɓe a cikinsa balle zama. Sai dai ga mamakinsa babu wani yanayi na ƙyama ko jin kai a tare da su, duk sai yake jin wani iri, bai taɓa yin baƙo yana jin ya ƙasƙantar da shi duba da irin muhallinsa ba sai waɗannan mutanen. "To ko kujera za a samo muku?". Ɗaya daga cikin su yace,"A'a babu komai Malam, ai nan ɗin ma Alhamdulillahi ya isa, ga shi duk mun zauna, muna godiya da karramawa". Sai da duk suka gama zama sannan ya zauna yana mai fuskantarsu, ya ranƙwafa kamar bafaden sarki, da firgicin da ke tare da shi ya shiga miƙa musu hannu wanda a farko sai da yaji shakkar hakan, sai kuma yaga saɓanin fa yanda yake tunaninsu ne domin da kansu suka miƙo masa nasu suna gaisawa da girmama junansu da kuma mutuntawa. Cikin wani yanayi Abbaa da bai taɓa shigansa ba yake kallon tsohon mutumin da ke cewa da shi,"Da ka natsu naga duk ka dabarbarce da ganin namu". Abbaa yace,"To ai ranka ya daɗe ganin mutane irinku dole mutum ya shiga irin wannan yanayin na ruɗani, ni dai fatana Allah yasa lafiya, Allah yasa lafiya don cikin gida ma kanta iyalina a tsaye take". Alhaji Sama'ila ya murmusa yana duban Abbaa da kyau yace,"Kar ka samu damuwa lafiya lau, Alkhairi ne ya kawo mu gare ka, saboda haka ka bar tunanin ko ba lafiya ba ne". Sai sannan Abbaan ya samu ya ɗan sauke ajiyar zuciya ta salama yace,"To masha Allahu, bara a miƙo muku ruwa". Ya yunƙura zai miƙe sai ga wani baƙon ya shigo, Abbaa ya kalle shi cikin faɗaɗa fara'ar fuskarsa yay saurin miƙewa yana miƙawa Baba hannu yace,"A'a Alhaji Babangida kai ne da kanka a gidan nawa, barka da zuwa". Baban su Safiyya shima cikin fara'ar da ke wadatuwa saman fuskarsa yake cewa da Abbaa,"Malam Salman ka ganni kwatsam ko, to ya za'ai zuwa ya zamar mana dole". "Wallahi fa, kar dai kace min tare ku ke da waɗannan bayin Allah'n?". Baban su Safiyya yace,"Tare muke da su, da yake ni uzuri ya ɗan riƙe ni a hanya ne shiyasa suka riga ni isowa, tafiyar ai tawa ce ma gaba ɗaya, na ke ce musu ai gida muka nufa su isa kafin na ƙaraso". Baban su Safiyya ya nemi waje ya zauna yana magana da jama'arsa, yayin da Abbaa ya shiga daga cikin gidan yana kiran sunan Ummani a hankali saboda ana iyo jiyo maganar tsakar gida daga soron. Ummani kuwa na kitchen a lokacin ta rafka tagumi tana jinsa ta taso da sauri tana buɗa masa hannu alamun ya ake ciki. "To bana ce ba amma dai sun ce lafiya lau alkhairi ya kawo su, don tafiyar ma har da Alhaji Babangida". "Alhaji Babangida dai?". "Baban yarinyar nan ƙawar Sa'ida, bani sunanta nan, yauwa Safiyya". Ummani ta sauke nauyayyan numfashi da cewar,"Ohhh har na samu Sa'ida amma da hankalina duk ya tashi ina ta tunanin me zai kawo mana sojoji wajenka, don wallahi har na fara zargin ko matsalar rumfar nan ce". Yanayin fuskan Abbaan dai gata nan yace,"Samu faranti ki zubo lemu da ruwa". Ummani ta koma kicin ta ɗauko farantai guda biyu, shi kuma Abbaa ya shiga ɗakin Sa'ida inda firiji ke ajiye ya kwaso kunun aya da ruwa. Yasmin ta shigo Abbaan ya bata faranti ɗaya yace ta kaiwa baƙin waje, Ummani kuma na cewa da shi,"To ai kai musu waɗancan kofunan robar kuwa? Da dai an bar musu a jarkunan? Ko na aika Yusra ta bada kofunan tangaran ɗinta". "Bar shi akai musu hakan ai sun san inda suka zo". "To shikenan Allah sa khairan ɗin da gaske". Ta faɗa tana bin bayan Abbaa da kallo har ya fice. Kafin ta shiga daga ɗaki tana cewa bari ta kira Sa'ida ta faɗa mata ko zata siyo kofunan ƴan gayu a hanya saboda zuwan manyan baƙi irin haka, ranar nan ma haka ta zo da ma'aikatan asibitinsu duk sai taji kunya saboda irin farantin da aka zuba musu abinci, to da yake dai baka kunya da matsayin da Allah ya aje ka. Abbaa ya zauna suna ƙara gaisawa da juna, bayan an taɓa ƴar hira tsakanin Abbaa da Baban su Safiyya sai Alhaji Surajo ke cewa,"Tom Babangida kayi masa bayanin me ke tafe da mu ko". Baban su Safiyya na jijjiga kai yace,"Ƙwarai haka ne, bama biyewa hirarmu da ba zata ƙare ba, zumunci yay ƙaranci wai don ma Allah ya haɗa kan ƴaƴan namu sunata na su zumuncin". Abbaa yace,"Wallahi fa Alhajin Allah, da sai a wuce shekaru masu yawan gaske ma ba'a gaisa ba ko ta wayar, zumuncin zamanin sai adu'a sai mutum yayi da gaske zai samu ladansa". Baban su Safiyya ya numfasa kana ya dubi Abbaa yana yi masa nuni da babban mutumin da ke tsakiya me cikar kamala da dattako, wanda Abbaa zai iya cewa dama tun zuwansu yaji mutumin ya cika wurin da haibarsa, kuma yana da tabbacin ƙamshinsa ne ya gauraye dukka wajen tun daga ƙofar gida har cikin gida. A hankali Baban su Safiyya yace,"Malam Salman wannan shi ne Major Sadiq Oluwa Ibrahim, Yayar Matata ne uwa ɗaya uba ɗaya domin a wurinsa ma na karɓi auren ƙanwarsa, na kusa da shi kuma kusan mahaifi ne a wurinmu sunansa Captain Adebisi Oluwa...waɗannan kuma duk da kake gani abokai ne sai wancan". Ya faɗa yana nuni ma Abbaa da na kusa da shi yace,"Shi ƙane ne a wajen Major, sunansa Alhaji Mukhtar Oluwa". Abbaa yana ƙara rissinar da kai yace,"To masha Allahu, madallah dukkanku ina ƙara yi muku maraba, ayi haƙuri dai da irin wajen da aka samu". Captain Adebisi yace,"A haba dai haba dai muma duk irin namu muhallin kenan". Baban su Safiyya ya ƙara cewa,"To Malam Salman abin da yake tafe da mu muhimmin abu ne, magana ce babba, kuma alkhairi ne ya kawo mu gareka, sai dai bamu san a yanda zaka karɓi al'amarin ba, duba da cewa mun sake dawowa ne a karo na biyu da buƙata iri ɗaya, amma a wannan karan muna fatan samun karɓuwar tayin mu saɓanin baya da bamu samu karɓuwa ba". Abbaa yace,"To Alhajin Allah a ɗan warware ni ko, an saka ni a duhu". Ya faɗu haƙoransa a waje fuskarsa washe da fara'a. Major Sadiq wato Sir kamar yanda ƴaƴansa ke kiransa yay nisa tare da numfasawa, yana daɗa kallon fuskar Abbaa da ke kama da ta Sa'ida sak wadda ya gani a cikin jirgi ranar da zasu kaita makaranta, kafin ya fara magana a cikin birkitacciyar hausarsa ta yarabawa yace,"Ammm Malam Salman mun zo wurinka ne a dalilin Yarona, wato dai mun zo nema masa auren ƴarka da ya gani yake so, idan ba'a rigada an tsayar mata da mijin aure ba shi yana da buƙatar aurenta, aure nan kusa ba tare da anja lokaci ba". Abbaa ya ɗaga kai a karo na biyu yaywa Major kallo na ƙurulla, sai kawai yaji kwarjinin mutumin ya dake shi, haka kuma nauyinsa ya kama shi, yay saurin ɗauke ƙwayar idonsa akansa yana me ƙara sunkuyar da kai ƙasa yace,"Ina sauraronka Ranka shi daɗe". Major yaci gaba da cewa,"My son Salim na ɗaya daga cikin manema auren ƴarka a shekarun baya masu yawa da suka wuce, to kuma sai ubangiji ya ƙadarta cewa ba zata zama matarsa ba a wancan lokacin, shi ne a wannan karon ya turo mu gare ku da ƙoƙon bararsa yace a taimaka masa idan har wani bai riga shi ba". Kan Abbaa ya ɗaure, kafin ya kalli Baban su Safiyya yace,"Alhajin Allah ni ai har yanzu na kasa shaida ɗan namu da kuke magana akai". Baban su Safiyya yace,"Ehh to da yake a wancan karan ba mune muka zo ba gaskiya, amma ai ba zaka mance yaron da ya kawo kuɗin aure daga baya kuma aka karɓa da cewar ba zai iya jiran yarinya ta kammala karatun da aka ce masa ba, wanda kuma hakan ta faru ne duk ba da son ran zuƙatan kowa ba musamman shi yaron". Abbaan yayi ƙayattacen murmushi da cewa,"Na tuna, na tuna hakan, to amma shi da yay wancan magana a lokacin baya ai ce na ke an wuce babin...". Sai yay shiru kamar yanda duk suma suka yi shiru suna kallonsa. Zuciyar Major cike da fargaba da zullumin kar su ƙi amsar tayin su, don shi kansa ya kwaɗaitu wa ɗansa auren Sa'ida. A lokacin ne kuma aka yi kiran sallar magriba, don haka duk suka miƙe Abbaa ya shiga gida Ummani ta zuba ruwa a buta guda biyu ta ba shi ya fita da ita, ta aika Yasmin wurin Umman su Hindatu ta ƙaro buta aka ƙara musu kafin Abbaan ya dawo ya karɓa masu sallaya, ita dai Ummani ganin yanayinsa na yanda yay sanyi kamar jikinsa ya mutu sai duk ta shiga damuwa da fargaba, tana tayi masa magana ma bai tsaya ya saurareta ba. Don haka da sauri ta ɗauka waya ta kira Yashaik tace idan yana gida yay sauri ya leƙo gidan. Ko a wajen sallah ma babu yanda Abbaa bai yi ba akan wani cikin su ya ja su sallar suka dage masa akan lallai shi ne zai ja su, haka yaja su sallar bayan sun idar kuma suka komo soron suka zauna, Abba ya amso fitila a cikin gida ya saka musu saboda soron yayi duhu a lokacin. Bayan zaman nasu Alhaji Mukhtar yace,"Malam Salman na san kana tunani ne akan abun da ya faru a baya ko, to idan wannn ne kar ka damu, wallahi tallahi ko a baya Salim ba ya janye maganar aurensa da ƴarku ba ne saboda dalilin da aka faɗa, hasalima danne zuciyarsa yay ya haƙura a babu yanda zai yi saboda nuna masa da tayi na bata sonsa, shi kuma bai zai iya auran macen da bata sonsa ba, yana ganin idan ya nace aka yi auren zaman ba zai yi musu daɗi ba, saboda wannan dalilin a lokacin ya zo ya same ni muka yi magana ya faɗa min duk yanda suka yi da yarinya har ma ya fahimci akwai wanda ita take so, amma bai karɓi kuɗinsa don yay wulaƙanci ko tozarci ba, kum ahatta maganar da akayi a lokacin na cewa ya samu wata matar wallahi a lokacin babu wannan zancen anyi hakan ne duk don samun mafita". Abbaa ya sake jinjina kai kafin yace,"To da wannan da wannan, don bayanin da ka min yanzu shi ne nake so na tambaya. Sai dai duk da haka akwai wani hanzari ba gudu ba, ƴata ba budurwa ba ce yanzu bazawara ce ita, wataƙila kuma bai san da hakan ba ne". Baban su Safiyya yace,"Ya sani Malam Salman, ya san komai, sannan shima ɗin ba wai saurayi ba ne da aurensa, bayan aure ma har da arziƙin yara uku...". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR03FT5* Abbaa yay shiru yana nazarin kalaman na su, ba zai ƙi tayinsu ba, domin shi kansa ko a wancan lokacin Salim ya kwanta masa a rai, yafi gamsuwa da shi fiye da duk waɗanda suka zo neman auren Sa'ida, shiyasa ko a lokacin ya yarda ya amince aka karɓi kuɗinsa bisa sharaɗin da ya gindaya na cewar sai ta kammala makaranta, kuma ko a sanda suka zo karɓar kuɗin su bai ji daɗi ba fiye da adadin kalmomin baki, ba wai rashin jin daɗi na sun wulaƙanta su ba kan karɓar kuɗin ba, a'a rashin jin daɗin Ƴarsa ta rasa yaron kirki, yaro me nagarta kamar Salim, yaga haƙiƙanin soyayyar ƴarsa a ƙwayar idon yaron, haka ya tsinci raunin rasata a muryarsa, kuma gamsu ɗari bisa ɗari da irin shaidun da mutane suka yi akansa, ba tare da sanin iyalinsa da kowa ba ya ɗauki ƙafa yaje har garin Anambra state domin yayi kyakykyawan bincike akan yaron da iyayensa kuma duk suka samu shaida mai kyau, dama tsoronsa ɗaya bawa ƙabila auren ɗiyarsa. To a lokacin da ace shi irin mahaifin da ke tilastawa ɗiyansa abin da yake so ne ko da basa so, to da lashakka Sa'ida bata isa ta auri wani miji bayan Salim ba, to sai dai babu yanda zai yi shi uba ne me son farin cikin ƴaƴansa kuma me son dukkan abin da suke so ko da shi ba ya so in har wannan abu bai kaucewa shari'ar musulunci ba. A yanzu tarin tambayoyi ne a ransa to amma zai bar su bincikensa ya ba shi amsa, akwai dai damuwa da fargaba a tare da shi. Major ya katse tunaninsa cikin magana me taushi irin ta dattijon arziƙi, yace,"Malam Salman Safiyya ita ta tabbatar mana da babu maganan wani akan ƴarka, bisa wannan dalili muma muka ga ya kamata muyi gaggawan zuwa kar mu makara. Kuma ni da kaina ina baka tabbacin insha Allahu my Son zai kula da ƴarka ba zai ci mutuncinta ba, yaƙini na ke baka akan hakan saboda na san waye yarona". Da irin waɗannan maganganun Major ya ƙarfafawa Abba gwiwa. Wanda har Abbaa ya dinga jin zuciyarsa na buɗewa da yarda gami da farinciki, sai dai ba zai zama me fatan lamarin ya kasance ba har sai yayi istikara ya kuma sa Sa'ida tayi istikara itama. Abba yay nisa sannu a hankali ya fara magana da cewa,"Tom ni babu abin da zance sai Allah ya zaɓa mafi alkhairi wa yaran namu. Sannan kamar yanda na faɗa muku ne Ƴata ba budurwa ba ce bazawara ce, saboda haka ni ban da hurumin da zan mata zaɓi kai tsaye domin kuwa shari'a ta bata damar yiwa kanta zaɓi". Alhaji Mukhtar ya jijjiga kai da cewan,"Wannan haka yake Malam Salman, magana ce me kyau kayi". Abbaa ya sake cewa,"To madallah, saboda haka ku faɗa masa cewa ya zo ya fara samuna domin ina da buƙatar na gana da shi kafin na basa damar ganawa da ita ƴar tawa su sasanta kansu". Major shi ya fara cewa,"Tom shikenan zai zo ɗin in Allah ya yarda, muna godiya". Gaba ɗayansu kuma sai suka shiga yima juna godiya kafin suyi sallama su miƙe zasu tafi, Abba ya shiga ciki ya karɓo leda wurin Ummani yazo ya kwashe kunun ayar da ruwan ya zuba musu a ciki ya raka su da shi har mota. Kamar yanda suka ji daɗi suke ta godiya da irin karramawar da Abbaa yayi musu haka shima ɗin yake ta godiya a gare su. Bayan tafiyar su ya wuce masallaci bai dawo cikin gida ba sai da yayi sallar isha'i. Ya shigo a lokacin Ummani na daga ciki tana lazimi, yay ɗakin nata ya zauna daga bakin gado, kuma zuwan nasa yasa Ummani idda lazimin nata tare da juyowa ta fuskance tana nazarin yanayin fuskarsa kafin tace,"Abbaa lafiya dai ko?". Abbaa na duban labulen ɗakin kamar me son karanta wani abu a jikinsa yace da ita,"Ehh to lafiyar zamu ce". Furucinsa nasa yasa gabanta faɗuwa, ta ɗaga hijabinta ta cire tana aje carbi ta tashi daga kan dardumar ta dawo kusa da shi ta zauna. "Wani abu ne ya faru? Shi Alhaji Babangidan me ya kawo shi kuma mene haɗinsa da su mutanen?". Ganin duk ta ruɗe Abbaa yay murmushi yana me ɗora ƙafarsa ɗaya akan gado ya fuskanceta, fuskarta ya shafo tare da cewa,"Kwantar da hankalinki matata ta kaina, Sa'adatun Salmanu ba komai ya kawo su ba face alkhairi". Ummani ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana karayar da kai kafin tace,"Yanzu naji batu, amma da hankalina gaba ɗaya a tashe yake, wallahi ka ganni tun da na zauna Allah na ke ta faɗawa, to ai Alhamdulillahi tunda ba wata matsala ba ce, amma me ya kawo su?". Abbaa yace"Zuwan na su akan Sa'ida ne". Cikin mamaki Ummani tace,"Sa'ida kuma? Na shiga duhu me ya faru da Sa'idan?". "Kinga samu nutsuwa don Allah, zuwa suka yi da batun aurenta...". Bai ƙarasa ba ta katse shi,"Kamar ya ban gane ba, shi Alhaji Babangidan ya zo maka da wannan zancen kuma ka tsaya sauraronsa? Ya manta mahaifin ƙawarta ne shi ko kuwa ya manta akwai aminta tsakanin matarsa da ni? To ban da ma mutuwar zuciya ina shi ina zuwa neman auren Sa'ida fisabilillahi, kuma kai bai ji kunyarka ba ma". Tayi maganar cikin Firgicin da ya bayyana a muryarta zuwa ƙwayar idonta da ta fito waje. Wannan yanayin nata da kuma maganar da tayi sai ya bawa Abbaa dariya. Aifa ran Ummani ɓace ta miƙe tana faɗin,"Dariya na baka kenan, to ba zai yiwu ba wallahi, yanda ya zo ya tafi ya tafi kenan babu wani aure tsakaninsa da Sa'ida, hauka ake yi?". Abbaa yace,"To idan Allah ya ƙadarta faruwan hakan fa? Kuma ina ga ai ba haramun ba ne don ya aureta". "Allah ma ba zai ƙadarta hakan ba ubangiji ai ya san daidai, kuma nima ai ban ce haramun ba ne sai dai ai akwai duba a lamarin, kuma ya ce ko ka faɗa masa babu wurin shigarsa?". Abbaa na yin wata dariyar ganin duk tayi kicin kicin yace,"A'a na dai ce masa ya dawo gobe ya ganta, tunda yace yana so a ba shi dama ya shiga jerin zaurawanta ya fara kafa gwamnatinsa da wuri". Ummani tayi wani lakato tana dubansa kafin tace,"Amma kuwa banda na san waye mijina wallahi sai in ce mutumin nan siyeka yayi da kuɗi, yanzu tsakani da Allah sai ka bar Babangida ya auri ƴarka? Kenan kaima a wannan shekarun naka tsofe tsofe zaka iya zuwa neman auren ƙaramar yarinya ƴar cikinka ta kusan nawa? Ko da ike zamu ce ta tadda muje". Abbaa ya buɗe ba ki da mamaki ƙarara yana dubanta yanda duk ta mayar da maganar gaske. "Ka saki baki kana kallona, to ni dai ba dani za'ai wannan zalunci ba, yarinyata da sauran ƙuruciyarta don tana bazawara ba zai yiwu a laƙaƙa mata auren tsoho ba, daga nan har hizba wallahi, mene wani Babangida daga ya ɗan taimaka mana sai ya wani kwaso ƙafafunsa na marasa kunya yace ya zo neman auren ƴar cikinsa". Abbaa yace,"Babangida kai tsaye ma babu Alhajin". "Yo wanne Alhaji bayan ya zubar da girmansa, neman aurar ƴar cikinsa fa yake yi kuma daɗin abin kunyar ma aminiyar ƴarsa". Ganin fa ta haƙiƙance har tana ɗaukan fushi da shi sai mita take yi yace,"Kinga ke ba ki tsaya kin gama jin bayanin da zan miki ba kawai kin hau kan wata maganar, Aure fa ɗan su suka zo nemawa ba kansa ba". Ƙyam Ummani ta tsaya ko ƙyafta ido babu. "Ɗansa?". Sai kuma ta dawo ta zauna tana cewa,"Kar dai kace min yaron nan Khalid me hankali, ka san ƴaƴansa maza biyu ɗayan kurma ɗayan kuma shi ne lafiyayye". Abbaa yace,"To ai bama a nasa ƴaƴan ba ne, ɗan Yayar matarsa ne yaron nan Salim da suka nemi aurenta tun tana budurwa". Ummani ta ware ido akansa ƙwaƙwalwarta na auna maganarsa kafin tace,"Wai kana nufin yaron da ya kawo kuɗi suka dawo suka karɓa?". Abbaa ya jinjina kai yana Faɗin,"Ƙwarai shi fa". "Abbaa sojan nan fa da kace min babba ne da gwamnatin tarayya yake aiki". "Shi dai Sa'a". Nan Abbaa ya shiga bata Labarin duk abunda ya faru tsakaninsa da su Baban Safiyya, Ummani bata jira ƙarashen zancen ba ma ta rangaɗa guɗa a hankali. Ta ɗaga hannu sama tana faɗin,"Allah gatan bawansa, Allah mun gode maka, Allah maji roƙon bawa". Bakin Abbaa buɗe yake kallonta, mamaki sosai ya kama shi, kar dai abin da ke ransa ne a nata ran itama? Kawai sai yaji tana ƙara faɗin,"Bayan wuya sai daɗi, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, Rabo daga sarkin da ba ya zalunci, bijahi rasulillahi wannan yaron alkhairin Sa'ida ne". Abbaa yace,"To ke wai kin san yaron nan ne da kike ta farin ciki haka". "Abbaa ya ba zan yi farin ciki ba, ɗan gidan manya mutane fa, to ni dai wallahi ba don kuɗi ko matsayi ba zaɓin Allah na ke ta nemawa yarinyar nan kuma ina da yaƙinin Salim shi ne Allah ya zaɓo mana, domin kuwa tunda ta fito zaurawa ke ta sintiri akanta ban ji ina farin ciki da zuwan wani ko naji sha'awar ta ƙara yin wani auren ba sai da wannan batu ya afku". Tayi maganar baki dukka a buɗe kamar zai yage saboda murna. "Yanzu a wacca matsaya ku ka kwana da su? Na san halinka Allah sa suma ba ce kayi su kama gabansu ba, don ni dai ban sani ba Abbaa ko kwaɗa Sa'ida zamu yi muci ba". Yay murmushi yana cewa,"Ba haka ba ne Sa'a, aurenta na baya ne har yanzu abinda ya faru bai gushe min ba, shiyasa na ke ta jin tsoro ban san da wa zan kuma haɗata ba". "To ya za'ai na faɗa maka ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, adu'a zamu ta mata ya bata wanda yafi wancan". "To yanzu dai na ce musu su turo yaron ya same ni zuwa jibi idan Allah ya kaimu saboda bana so a saka wasa a lamarin, sai dai ita ɗin bamu sani ba ko ta amince". "Kai rabu da ita yanzu ai ba shashasha bace da hankalinta ta san inda ke mata ciwo, a bayan ma ƙuruciya ce ta hanata gane wanda ya kamata ta aura". ****"Maman Nana ni zan wuce". Na faɗa a sa'ilin da na ke ɗaukan jakata ƴar ƙarama na riƙe a hannu. Maman Nana tace min,"To Sister Sa'ida sai Allah ya kaimu, ki gaida gida ki gaida su Ummani". Na amsa mata yayin da Khadija ke tsokanata da cewa,"Wai ke don Allah ko ki ɗan gwada soliderity watarana ki ce za ki kwana". Ina murmushi na ce,"To madam indai za ki bar min albashinki na watanni biyu ni kuma zan dinga haɗawa da aikin ki". "Ehh lallai da ya ke ni bani son kuɗin". Ina dariya kamar yanda kowa yay na ce,"A'a to ke fa kin je saudiya, ni kuma so na ke nayi nayi na kwashe iyayena na kaisu su sauke farali, kinga idan na samu ƴar 380 duk wata ai tuni zasu wuce umra". Maman Nana tace,"To Allah dai ya cika buri, ki yi maza kinga Ummani ta bani amanarki yau kin yi dare". Nace,"Wallahi fa kinga Yaya Imam ɗin ne ma har yanzu bai kira ni ba, ɗazu ya kira nace masa Dr yace in tsaya saboda waccan matar da akai wa operation to ina ga ko tunani yake bamu gama ba". "To ki kira shi mana". Na ɗan karayar da wuya ina cewa,"Wallahi Maman Nana bana son takura mi shi, komai yake yi yanzu hankalinsa na kaina, Abbaa ne ma yaƙi ya bari na ke komawata ni ɗaya ni banga wani abu a ciki ba". Suka haɗa baki wurin cewa,"Gata ne suka miki wallahi, mace yar tsaro ce sai da kulawa, ki gode Allah da ya ba ki iyayen da idon su yake akan ki". "To bari naje, ni na manta ma daga yau nayi off ni da shigowa sai laraba". Khadija da tsokana tace,"Dama kullum ana ba ki na goron albishir ai dole kike son zuwa aiki kullum". Sauran pure water ɗin da ke hannuna na jefa mata. Da haka na fito daga Nursing station ɗin, Metrom na zaune muka yi sallama da ita, har na fito compound ɗin asibitin sai gata ta biyo ni tana ƙwala min kira da cewa,"Kinga ajiyar ki kin mance nima zan manta kuma". "Sauri na ke ta yi kinga ƙarfe tara ta kawo kai, na gode". Wasu hulunan sanyi ne da safuna Sister Hauwa ke siyarwa daga turkey ake kawo mata, shi ne na siya mana ni da Ummani da Safiyya, da yake safunan ma har da na maza sai na siya har Abbaa da Kaka. Ina tafe zuciyata nata tunanin in kira Yaya Imam ko na ƙyale shi, har dai na fito bakin gate, tunda bai kira ni ba na tabbata wani babban uzurin ne ya riƙe shi, iyaka koƙari suna yi akaina, Abbaa zai rako ni kullum sai mun ci rabin hanya yake komawa, in dai kuma nayi evening to ya sakawa Yayyuna duty yau idan wannan ya ɗauko ni gobe wannan ne zai ɗauko ni. Ina tsaye bakin gate na buɗe jaka ina laluben wayata sai naji gate man na ce min na matsa za'a wuce. Nayi gefe ce na ke ma ko Dr ne zai tafi sai naga ba motarsa ba ce. Na ɗaga waya na kira Yaya Imam yace,"Kin ganni na taho mashin ɗin nawa ya samu matsala yanzu haka ina wurin masu gyara, kiyi haƙuri gani nan zuwa kin ji". Nace,"'To Yaya kana ta wajen ina? Na gaji ne wallahi yunwa ma na ke ji". Yace,"Zan taho yanzu yi haƙuri". Na kashe wayar ina sanyawa a jaka, na fara tafiyata ni ɗaya cikin tsoron da ya fara kama ni, kafin na gama fita a layin ne Allah ya taimake ni na samu me adaidaita sahu na kuwa yi saurin tsayar da shi, na faɗa masa inda zai kai ni yace na bayar da ɗari takwas. Na shiga ina faɗin Allah ya sauke mu lafiya, ban manta da adu'ar zama cikin mota ba, a koƙarinsa na tayar da babur ɗin motar da ke gefenmu tayi masa horn, na ɗan leƙa na kalla sai naga motar da ta fito daga asibiti ce ɗazu. Mutumin da ke cikin motar ya fito ya ƙaraso yana cewa me adaidaitar,"Ina kayi?". Yace masa,"Cikin gari nayi can wajen gidan sarki". Yace,"Ok to nima can ɗin nayi motana ne kaga ya samu matsala, samun bakaniken da zai zo ma yanzu aiki ne". Na ɗan saci ido na kalle shi jin yanda yake hausar gwari, kananun kaya ne jikinsa blue riga me dogon hannu da baƙin wando, yasa bakin gilashi da face mask da sam ba zaka gane fuskarsa ba, zubinsa ma ba na hausawa ba ne duk da fuskarsa a ɓoye take. Zan fito ya fara shiga sai naji yace,"Noo shige daga ciki". Na matsa ciki ya shigo, ƙamshin turarensa ya daki hancina sai naji zuciyata ta motsa, kuma ban aune ba na tsinci gabana da faɗuwa sosai, yatsun hannuna har ji nayi suna rawa, sai da muka yi nisa sosai a tafiya kana na kira Yaya Imam nace masa ba sai yaje ba nama taho, ya gama min faɗansa ya kashe wayar. Ni dai na yita mamakin mutumin ganin bai sauka ba duk da cewa bai faɗi inda za'a kai shi ba, muna tafen ma me adaidaitar ke daɗa tambayarsa yace masa no worry muje kawai idan anzo inda zan sauka zan faɗa maka. Me adadaitar yake ce masa,"Yallaɓai ko dai baƙo ne kai a garin". Na jiyo sautin karamin murmushin da yay kawai ba tare da yace komai ba. Muka iso unguwarmu ina ta ma me adaidaitar kwatance har muka zo ƙofar gida, idona ya hasko min Abbaa tsaye a ƙofar gida hannayensa sarƙe a baya, ban san lokacin da na furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shikenan na kaɗe". Mutumin ya juyo yana kallona me adaidaitar ma ya juyo, duk da banga ƙwayar idon da ke cikin gilashi ba na san dai ayar tambaya ce a cikinta dangane da furucin da nayi. Me adaidatar yace,"Hajiya akwai matsala ne?". Ai kuwa kafin na buɗe baki Abbaa ya doka min tsawa da cewa,"Ba za ki fito ba ne". Na haɗiye dunƙulallan yawu, mutumin ya fita nima na fito sai rawar jiki na ke yi, na ciro kuɗi na bawa me adaidaitar na wuce zan iya cewa ina jin yanda ƙwayar ido ta manne a jikina. Muryar Abbaa tuni ta cika kofar gidan da faɗansa akan tahowar da nayi ni kaɗai, ga layin yay tsit ƙarfe tara da arba'in a lokacin, faɗi yake da uban dare na kamo hanya na taho ina matsayin mace, da ba zan iya jiran Imam ɗin ba me yasa ban kira Yashaik ko Al'amin sun je sun taho da ni ba. Hannu ya kawo zai buge ni nayi saurin shigewa cikin gidan, Ummani ma na tsakar gida na shiga tace,"Ya za ki mana haka, ba dole ayi miki faɗa ba ga wayarki anata faman kira ba ki ɗaga ba". Idona a waje nace,"Wallahi banji kiran ba na sakata a silent". Abbaa ya shigo yana ci gaba da faɗin,"Idan kika kuma tahowa ke ɗaya sai ranki yayi mugun ɓaci, kuma faɗa min gidan uban wa kika tafi?". Jikina ya kama ɓari na shiga wallacewa ina faɗin,"Allah Abbaa babu inda na je". "Ƙarya kike yi in ba haka ba me ya hana ki ɗaga waya? Kin san Allah zan soke fita aikin nan? Ba dai kin yi karatun ba kin samu na tsira da mutunci, to aikin ba dole ba ne zan hana ki". Tuni na durƙusa ƙasa hawayen idona na neman sakkowa nace,"Wallahi Abbaa babu inda na je, kayi haƙuri don girman Allah". Uwa me tausayin ƴaƴanta tuni ta shiga bawa Abbaa haƙuri da tausarsa akan yay ƙasa da murya dare yayi, cikin gida ana jinsa haka maƙota ma duk suna ji. Ya watsa min wani mugun kallo da cewa,"Ba zan ɗauki sakarci irin haka ba, kike jira duk dare za'a zo a ɗauke ki, amma wallahi kika ƙara kuskuren tahowa ke ɗaya daga ranar kin gama aiki". Yana faɗa ya shige ciki, nima na miƙe na wuce ɗakina, Ummani na leƙowa tace,"Abincinki yana ɗakina". Ko takalmi ban iya cirewa ba na zauna ina goge hawayena tare da danasanin tahowar da nayi. Ko kayan ban cire ba na tashi na fita zuwa ɗakin Abbaa, sai da na tabbatar ya haƙura ya daina fushin kana nayi masa sallamar sai da safe na wuce ɗakin Ummani na ci abinci. Wajen sha ɗaya har na rufe ido naji wayata na ringing, da sauri na tashi na rarumota gudun kar Abbaa ya jiyo ƙararta, nifa mahaifina is very strict, bai ƙi ya zo ya ƙwace wayar ba, ban ɗaga ba sai da naga kiran yay yawa har sau uku sannan na ɗaga ana huɗun. Nayi sallama aka amsa, shiru for some seconds sai aka ce,"Nurse Sa'ida ce?". Na ce,"Ehh ita ce". Na faɗa ina jin muryan kaman na santa duk da cewan muryan namiji ne. Sai aka ƙara cewa,"Sorry don Allah na kira ki da daddare, ɗazu na zo asibiti ne Dr Samuel yake bani number na ki yace duk sanda na zo na dinga nemanki, domin ke ɗin ƙwararriya ce wacca ta san makamar aikinta". Babu shakka na san muryar sai dai ba zan ce ga inda na santa ba ko kuma ta wacece ba, a hankali yaci gaba da magana yana ce min yana fama da ciwon baya ne da ƙafa ko zan taimaka na recommending masa maganin da zai sha yanzu kafin zuwa da safe yaje asibiti. Na zage na buɗe murya ina ta kora masa bayani da tambayan ya yake ji, kusan minti goma haka sai naji ya katse ni da tambayan,"Babu dai wani damuwa ko?". Na ce masa,"A'a babu, duk sanda kake neman taimako irin haka zaka iya kira na". Sai ya sake cewa,"Thank you so much, but still ba ki cikin wani matsala dai ko?". With confusion na ce,"Babu komai, kawai na dawo daga aiki ne yanzu na gaji ina so zan yi bacci". Na faɗa ina sauke wayan daga kunnena na kashe bayan ya cika ni da godiya. Daga can ɓangaren Salim ya sauke ajiyan zuciya, sai yanzu ya samu relief jin muryanta ba cikin yanayi na damuwa ba kamar yanda ya tsammata, kenan babu wata matsala saboda sosai ya damu da yanayin da yaga Abbaa a ɗazu, ya san dole zata sha faɗa kam, don faɗan da Abbaa ya dinga mata a lokacin ji yay kaman ya fito ya ba da haƙuri, shi kansa ji yay ba zai iya barinta ta tafi ita ɗaya ba a wannan daren shiyasa ya aje motarsa ya shiga napep ɗin domin ya san idan yace ta zo ya rage mata hanya ba yarda zata yi ba. Ya sauke a jiyan zuciyayana aje wayarsa, tare da jingina kai a gadon ta gefen ƙwayar idonsa kuma yana kallon Kudrat da ke gefensa tana bacci. ******Bayan kwana biyu yau tun tashina Ummani tace da na gama komai na gyara ɗakin Al'amin akwai baƙin da za'a yi anjima. Ban tsaya tambayarta ba ni dai ina gama wanke wanke na shiga na gyara tass, na sanya turaran wuta me bala'in ƙamshi da nasa ordarsa daga meduguri. Gidan duka ya ɗauka har Ummansu Hindatu sai da ta leƙo tana faɗin kamar gidan haihuwa ko sabuwar amarya. Ummani tace na shirya zan rakata unguwa, nayi wanka na saka rigar bubu sai ce tayi lallai sai na sauya in ɗauko abayata da na siya kwanaki mana. Na ce an gama ranki ya daɗe, haka na ɗauko na saka na zauna zaman jiranta sai ƙorafi na ke ina Ummani ki zo mu tafi kin san ba wuri ɗaya kike zuwa ba, an ta shige shige kenan yanzu za ki ga yamma tayi. Tace kar na dameta in ban rakata Yasmin zata rakata. Ban ƙara magana ba na fito da keken ɗinkina tsakar gida na hau ɗinka kayan wasu da za'a kaiwa bauchi. Lokacin yaro ya shigo yana cewa ana sallama da Abbaa, na tashi na leƙa ɗakin na faɗa masa, babu jimawa ya fito ya fita, can ya kuma dawowa yace da ni na ɗauko masa tabarma. Da kaina na kai soro na shimfiɗa kana na dawo ciki. Abbaa ya leƙa daga waje, tsaye ya hangi Salim jingine da motarsa hannayensa harɗe saman ƙirji, cikin kamilalliyar shigarsa ta cofee ɗin yadi da ɗinkin irin na yare, shigarsa tayi masa bala'in kyau. Abbaa dai murmushi ya suɓuce masa, tun asubahin yau ko kuma yace tun a lokacin da yay sujjada ga ubangiji a cikin dare yana me neman zaɓinsa akan lamarin Salim da Ƴarsa yaji fargaba ya barsa yayin da ƙwarin gwiwan aurama Salim ƴarsa ya shige shi, kuma a yanzu da idanunsa ke kan yaron sai yake jin yana samun salama a cikin ransa dangane da lamarin. Yaywa Salim izinin shigowa, ya tako cikin tafiyarsa ta namiji me cikar zati da kamala ya shigo soron lokacin Abbaa har ya zauna akan tabarmar, ya cire takalma ya nemi waje ya zauna, zaman nasa ma har sai da Abbaa yace masa tukunna don da tsugunawa yayi cikin jin nauyin zama a inda surukinsa ke zaune. Ya gurfanar da kansa gaban Abbaa kamar me neman gafara, da girmamawa da ladabi ya sake gaida Abbaa a karo na biyu, Abbaa ya amsa ƙwayar idonsa ƙyam akansa tun a ɗazun. Abbaa yay nisa tare da sauke numfashi ya kira yi sunansa. "Salim ka ke ko?". "Ehhh Abaa". "To ya kake ya aiki?". "Alhamdulillahi Abbaa, fatan na same ku lafiya". "Lafiya lau, Salim ko za ki iya faɗa min dalilin zuwanka wurina?". Da wani ƙwarin gwiwa da jarumta irin tasa ta sojan gaske yace,"Abbaa na zo gare ka ne da ƙoƙon baran ka bani amanar rayuwar ƴarka Sa'ida...". Abbaa ya katse shi,"Amana dai Salim? Ka kuwa san amana?". "Na sani Abbaa, ni musulmi ne cikakke, kuma ina da yaƙinin zan riƙe amanar shiyasa na ce aba ni ita". "Salim amana tana da girma, wutar Allah na cin wanda bai riƙeta ba". "Bana fatan na kasance cikin sahun maciya amana Abbaa, ka yarda da ni zan riƙe amanar da zaka bani tsakani da Allah". Abbaa ya sake cewa,"Kai ka turo iyayenka kenan ko kuwa sun yi zuwan kan su ne?". "A'a Abbaa ni naje musu da maganar". "Amma me yasa baka fara zuwa da kan ka ba? Ko kuma kana ganin kawai don mahaifanka sun zo sai na ce musu na baka ƴata? Shin ka taɓa neman soyayyarta ne?". Ya ƙara yin ƙasa da kai kafin a hankali yace,"Bamu da ƙarfin ikon da zamu zo kai tsaye mu ce zamu ne abu a bamu ta yanda muke so, na fi so ne a duk sanda wani babban lamari ya shiga gabana na fara saka manyana a ciki, musamman sha'ani me girman gaske irin wannan. Sa'ida kuma ban taɓa tunkararta ba, kawai dai na san da cewa in har iyaye suka amince min na nemi soyayyarta da sannu...". Sai yay shiru bai iya ƙarasa faɗin abin da zai ce ba. Abbaa yace,"Da sannu me? Yi min bayani ina jinka". Ya sarƙe yatsunsa da ƙyar ya iya cewa,"In har ta bani dama na shiga sahun manema aurenta da sannu zan koyar da ita so...". Sai kuma ya canja kalamin da cewa,"Da sannu zata aminta da ni". Abbaa ya jinjina kai sannan yace,"To amma kai da kake da iyali mene naka na son ƙara aure Salim? Ba ku zaman lafiya ne ko kuwa dai lamarin wasu mazan na son wulaƙanta matayen su ne?". Abbaa yay maganar wajen bugun cikin Salim ɗin. A hankali kuma cikin natsuwa Salim yace,"Babu ko ɗaya Abbaa, ina dai da sha'awan ƙara aure ne domin ko addini ya bamu damar yin hakan, idan har muna da iko kuma zamu yi adalci zamu iya ƙara aure. Sannan zaman lafiya iyaka gwargwado akwai shi tsakanina da iyalina, bani da nufin na ƙara aure don na ci mutuncin iyalina, ba zan ƙara aure don na cutar da wani ɓangaren ba, lamarin aure abinda Allah ya nufa shi ke kasancewa". [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR04FT5* "Masha Allah! Abbaa ya faɗa yana jinjina kai. "Salim da gaske kake kana son ƴata tsakaninka da Allah ba domin wata manufa ba?". "Ƙwarai Abbaa ina son Sa'ida ba tun yanzu ba, ko a wancan lokacin na haƙura ne saboda ta nuna bata sona, kuma ko a yanzu ma zan iya haƙura idan har ta ce ba zata iya aurena ba, ba zan zamar mata dole ba kamar yanda ba zan so ayi mata dole ba, ni dai burina ne auren nagartacciyar mace kamar Sa'ida, idan kuma hakan bata Faru ba na san da cewa Allah ne ya rubuta cewar ba zan rayu da ita ba a inuwa guda matsayin ma'aurata, kuma zan karɓi hakan a madadin ƙaddara". Abbaa yay ɗan jim kafin ya sake cewa,"Ka san da cewa ita ba budurwa ba ce bazawara ce ƙaddara ya rabata da mijinta?". "Na san da hakan Abbaa". Abbaa ya ƙara mayar masa da cewa,"Fatan kowanne miji ne ya samu zuri'a tare da matar aurensa, Shekaran Sa'ida goma da aure bata taɓa haihuwa ba Salim". Ya sauke numfashi kana cikin tattausan lafazi irin nasa yace,"Abbaa komai yin Allah ne, Haihuwa da rashinta dukka lamarin ubangiji ne, wataƙila ubangiji ya jinkirta mata lokaci ne wataƙila kuma bata ɗaya daga cikin waɗanda ubangiji ya tsara za su samu rabon hakan, Allah shi ne masani kuma shi yasan daidai na yanda ya tsara rayuwarta, kuma yanda ya tsara mata ɗin shi ne mafi alkhairinta ba don baya sonta cikin bayinsa ba...Abbaa ni Sa'ida na ke so zan kuma zauna da ita a kowanne irin yanayi babu cuta babu tsangwama babu kyara face cikin nuna kalawa da soyayya". Abbaa ya murmusa, tun farkon fara maganarsu da Salim yaji yaron ya burgesa saboda irin lafuzansa da ke fita daga bakinsa a nutse, kalami na me kaifin tunani da sanin yakamata gami da hankali. Abunda ya sani lokacin da zai aurawa Sa'ida Nazifi bai ji zuciyarsa na ƙarfafa masa gwiwar hakan ba, haka bai ji aminci da salamar da yake ji a yanzu ba. "Salim na amince maka ka nemi soyayyar ƴata, ka shiga layin zauwaran da suke neman auranta, idan har tayi amanna da kai ni kuma zan aura maka ita, zan baka amanarta, ina son ƴata ya kamata kan da wannan, ka rubuta hakan a tafin hannunka saboda gaba...sai dai akwai sharaɗi game da auren, idan ka amince faƙat idan baka amince ba to sai dai kayi haƙuri". Salim da kansa ke ƙasa tun ɗazu yana murmushi me kyau saboda samun nasararsa ta amincewar da Abbaa yay masa, furucin Abbaan yasa shi ɗago kai ba tare da alamu na sarewa ko kuma karaya ba, domin kuwa yana da tabbacin zai iya bin kowanne sharaɗi ne muddin zai samu Sa'ida, sai dai sam ya kasa ko da kallon gefen da Abbaa ya ke kamar yanda yay niyya saboda girman kwarjinin da Abbaan yay masa. Abbaa yace,"Ka shirya jin sharaɗin nawa?". "Ehh Abbaa". "Yauwa! Sharaɗin shi ne ƴata tana aikin asibiti, da aikinta ka ganta saboda haka babu batun cewar idan ka aureta zaka dakatar da ita ma'ana zaka hanata zuwa aikinta, sannan tana burin ƙaro karatu anan gaba shima ba zaka hanata ba, bayan haka tana ƴan sana'ointa na hannu, ka yarda da wannan yarjejeniyar ko kuwa ya?". Yay murmushin da sautinsa ya fita a ƙasan ransa, leɓensa kuma ya tale, to taya Abbaa yake tunanin cewa zai dakusarwa da Sa'ida karatunta ko kuma ya dakatar da ita aikinta? Idan da haka why zai shiga ya fita wajen ganin ta kawo wannan matsayin? Abinda yay mata don Allah yayi, kuma alƙawarinsa ne ba zata taɓa sanin hakan daga gare shi ba sai in Safiyya ce tayi katoɓarar faɗa mata duk da itama tayi masa alƙawari har abada ba zata sanar da Sa'ida ba shi ya ɗauki ɗawainiyar karatunta har matakin aikinta ba. Kuma ba ya so kowa ya sani ɗin domin za'a ga kamar yayi ne domin ya mallaketa, kuma itama with that reason zata iya zama with no other option ta tilastawa kanta saboda rama halacci da halacci. "Abbaa na amince na karɓi sharuɗanka, ba zan zama me sauka daga kai ba, illa iyaka ma ni zan zama wanda zai ƙara tallafawa lamuran nata". Abbaa yace,"Shikenan duk san da ka shirya kana iya zuwa ku gana da ita, amma bana so a ɗauki tsawon lokaci ana abu guda". Wannan karan sai da Abbaa ya jiyo sautin sanyayyan murmushinsa na samun nasarar da yay. Yana kallon yacca ya gyara tankwashe ƙafarsa kafin ya shiga cewa,"Na gode sosai Abbaa, na gode da bani dama, kuma da yardar Allah ba zaka yi nadamar aura mini ƴarka ba, nayi maka alƙawarin riƙe amanar da ka bani da dukkan ƙarfin ikona, zan kula da ita bisa gaskiya da aldalci". Abba ya murmusa kafin yace"Ina fatan hakan ta kasance, Allah ya baka ikon tsayawa a tafarkin da yake daidai, Allah yay maka albarka". "Amin ya Allah Abbaa, Allah ya ƙara muku lafiya da tsawon cin kwana". Shiru ya gimla tunanin Abbaa sun gama da shi ko zai tafi ne, amma sai yaga ya gyara zama yana aikin jujjuya yatsunsa, Abbaa dai kallonsa yake tayi da murmushi tare da fatan Sa'ida ta amince. "Za ka wuce ne?". Salim na ƙara yin ƙasa da kai da ƙyar ya iya buɗe baki cikin jin nauyi yace,"Abbaa idan ba damuwa ko zan iya ganinta kafin na wuce?". Abbaa ya yunƙura ya miƙe yana cewa,"Babu matsala ka ɗan jira". Abbaa ya wuce cikin gida, kai tsaye ɗakin Ummani ya shiga, tana zaune ita da Walida tana tsefe mata kai ya same su. Ummani ta bisa da kallo tana faɗin,"To ya ake ciki?". Tayi tambayar da zaƙuwa. "Yana jiranta sai ki mata magana, amma kin san bani son tsayuwan ƙofar gida". Ummani ta saki kan Walida tana cewa,"Ahh ai dama tun da safe nasa ta kimtsa ɗakin Al'amin, ko kuwa su zauna a soron?". Yay ɗan jima kafin yace,"Shikenan su zauna can ɗin". "Ɗakin Al'amin ɗin?". "Ehh". "To bari na faɗa mata ta kimtsa ko". Ta faɗa tana fita a ɗakin shi kuma Abbaa na tsokanar Walida da ƙwaƙwido, ta miƙe tana taɓara ya kama hannunta suka wuce ɗakinsa. Ummani na fitowa ta ƙwala kiran Yasmin wacca ke can wurin Kaka, sai gata da sauri ta fito tana zuwa Ummani ta bata maƙulli tace,"Je ki soro za ki ga baƙo ku gaisa ki buɗe masa ɗakin Al'amin kice an ce ya shiga, idan ba ya nan ki duba shi a ƙofar gida". Yasmin ta karɓa maƙullin ta fita, a soron ta sameshi zaune yana karkaɗa maƙullan hannunsa, ta durƙusa tana gaida shi, bayan sun gaisa ne ta buɗe ɗakin kana ta dawo ta kuma durƙusawa gabansa tace,"Ummani tace ka shiga daga ciki". Yanayin ladabin yarinyar sai ya burge shi, yana mata murmushi yace,"Mene sunanki?". "Sa'adatu amma Yasmin ake ce min". Yace,"Umm nice name, kice ina gaida Ummani idan kin shiga". Ta amsa da to daga bisani shi kuma ya miƙe ya shiga daga cikin ɗakin. Zamansa ba daɗewa Yasmin ta kuma dawowa ɗauke da farantin tangaran da jug da ƙananun kofuna akai sai purewater guda uku. Ina zaune a ɗaki ina saka stones ɗin rigar dana gama ɗinkawa ɗazu, ban san me ya same ni ba tun a ɗazun dai na ke jina a cikin wani irin yanayi da na kasa gane masa. Abunda ban taɓa yi ba tun mutuwar aurena wai na zauna ina tunanin aure ko sha'awarsa, amma tunda na hau kan keke wani banzan tunani ke neman dagula min lissafi. Kuma rabon da inji a raina na tuna da tsohon mijina da irin rayuwar da nayi a gidansa wallahi tallahi har na manta, amma yau ni ce tunanin Nazifi ke zuwar min da jin cewa ina ma na haɗu da shi ya ganni yaga yanda na koma da kuma irin matakin da Allah ya kai ni, kuma har na ke sha'awar ina ma na samu mijin da zai goge min tabon da Nazifi ya bar min shi da ƴan uwansa. Ummani ta shigo ɗakin da sassarfa tana cewa da ni,"Ke tashi yi da sauri ki gyara jikin ki". To na san fita zamu yi dama, saboda haka na miƙe ina gyara fuskata, ina ta kallon Ummani da farin ciki a tare da ita nace,"Wai me ya faru Ummani naga sai murna kike". "Aa to ba ki so kiga ina farin ciki ne?". "Ina ni, ai burina ku kasance cikin farin ciki a ko da yaushe". Na faɗa ina sanya pin a jikin veil ɗin da na yafa na ke kallon Ummani da annurin fuskarta ke ƙaruwa na ce,"To Ummani ai ke ba ki shirya ba". Tana murmushi me faɗi tace"Ai mun fasa waccan fitar, wannan shirin na ki ne ke ɗaya, kin gama?". Nace,"Ehh to amma me yasa kika fasa? Allah yasa ba Abbaa ne ya hana ki ba kinga dai kar a kuma abin kunyar da aka yi aƙi zuwar Hajiya Tabawa gaisuwa". Tasa hannu cikin jakata tana ɗauko turare ta buɗe tana ƙara feshe ni da shi kamar wadda akewa kamun aure tace,"Bar batun can ko gobe ma je insha Allahu, kije ɗakin Al'amin akwai baƙo ku gaisa da shi". Da mamaki ƙarara na ke kallonta na ce,"Gaida baƙo kuma Ummani sai naje a haka, ina lefin hijabi ma". Ta ɓata fuska tana kama hannuna,"To matar liman, yau dai ɗaya mene laifi a ciki, ba ki ga kyan da kika yi a hakan ba ne, duk wanda ya kalle ki sai ya ƙara kallonki yanda kika san balarabiya". Murmushi nayi da har haƙorana dukka suka bayyana. "Allah kin yi kyau da gaske na ke faɗa miki, tsab sai kin daɗa sace zuciya". Sai naji kunya ta kama ni, tare da sabon mamaki wanda na kasa samun haske a inda Ummani ta dosa. Tare muka fito a ɗakin ina aikin ɓata fuska don tunda tace baƙo naji sam ban son zuwa gaisuwar balle kuma a cikin shigar da na ke. Zungurar kai nayi ina faman jan ƙafafu takalmi na sharaf sharaf Ummani ta figo ni,"Wai ke ƙaramar yarinya ce, ya za ki tafi a haka". Na rufe ido na buɗe ina karyar da kai na ce,"Ummani shin baƙon wajen wa ya zo ne?". "Wurin ki ya zo, don haka ki natsu ki yi tafiya a yangance irin ta mace me tsada kamar ki". Na ƙanƙance ido da cewa,"Baƙo ya zo wurina? Kuma Ummani kike ta murna? Ni ai na muka yi da wani zai zo wurina? Gaskiya ba inda zani idan ya gaji ya tafi". Na faɗi hakan da haƙiƙanin bɓacin rai a tare da ni ina nufin juyawa na koma ɗaki. Harara ta wurga min tana cewa,"Idan ke baku yi da shi zai zo ba ai yayi da Abbaanku, na faɗa masa kin ce ba za ki ba ko ƙaƙa?". Jin haka na turo baki gaba ina haɗe gira sama da ƙasa na nufi soro ba don son raina ba, sai dai me! da zuwana soron naji gabana yayi mugu mugun faɗuwar da sai da na kai hannu na dafa bango, haka kawai na tsinci ƙafafuna da yin karkarwa. Da ƙyar na dawo hayyacina daga fitar da nayi daga cikinsa na ɗan lokaci, domin kuwa ƙamshin turaren da ya gauraye dukka soron da kuma tsadaddan takalmin da idona ya sauka akai sai ya nemi ya burkita ni. Na haɗiyi yawu ina cire takalmana a kusa da wanda na ke gani, ƙafafuna suka ɗaga da kansu suka shigar da ni ciki, da yanayina na sanyi nayi sallama da ƴar ƙaramar muryar da zata ɗauki hankali ko ai'na ne, kamar wata sokuwa haka na maƙale a bakin ƙofa kaina a ƙasa na kasa sarrafa kaina saboda yacca na ke jin ido ya manne akaina da kallo. A karo na biyu na ƙara cewa,"Salamu alaikum". Ban sani ba ko an amsa a wannan lokacin domin kuwa kunnena a toshe yake dumm haka na ke ji a cikinsa tun ɗazu. Wucewar bugun zuciyata sau ɗaya, biyu, uku, huɗu naji kamar babu motsin halitta a ɗakin saboda haka na ɗago ido a tsorace, karaf ƙwayar idona ta sauka akansa da yay saurin sadda nasa kan ƙasa kamar ba daga kaina ya sauke kallonsa ba. Zaune yake a gefen katifa, ya miƙe ƙafafunsa da na gansu dogaye, hularsa da ya cire ta yare a gefensa, yana wasa da yatsun hannunsa, kallonsa na ke da son na fahimto wani abu sai ji nayi na mugun tsorata dalilin jin ance,"Ga wani abu nan wajen ƙafarki". Ƙara na ƙwalla, kuma maimakon in yi waje sai na faɗo cikin ɗakin ba tare da sanin yanda aka yi na dira a tsakiyar ɗakin ba, idona rumtse jikina sai kyarma yake, cikin bakina ina faɗin kalmar la'ila ha'illa anta a hankali, saboda tsananin tsoro da furgicin da na shiga har hawaye na sakko min. Na jima a haka na kasa buɗe idanuna, sai naji kamar an rufa min abu akaina wanda hakan yasa ni buɗe idanuna a hankali, sai naga mutum tsaye a gabana, faffaɗan ƙirjinsa yay min rumfar na zama kamar wata ɓeranya a gaban nasa ƴar firit, a hankali kunnuwana ke jiyo min sautin bugun zuciya wanda na tabbatar da haƙikanin ba nawa ba ne nasa ne, sai naji wani dunƙulallan abu ya wuce ta maƙoshina gabana na tsananta faɗuwa sosai, so na ke tayi na ɗaga ƙafata na matsa daga baya amma ina kamar akan tarko na maƙale sam na kasa motsa ƙafata ko guda ɗaya. Cikin wani irin yanayi da na ke jina a cikinsa kasantuwar kusancinmu, na yi saurin ɗauke idona daga kan ƙirjinsa da na ke mamakin faɗinsa ina kai wa saman kamilallar fuskar da ta ƙawatu da kewayayyen saje me haɗe da gemu. Kuma karaf ƙwayar idon mu ta sarƙe ata juna, lokaci guda naji jiri na neman ɗibana ya watsar, nayi saurin dunƙule hannu ina riƙe kaina a tsayen, irin murmushin da ake kira da killer smile ya saki wanda sautinsa yay sanadin girgizawar allon ƙirjina nayi saurin ɗauke ƙwayar idona daga cikin tasa, ban saba da irin wannan kusancin ba sam da wanda ba muharramina ba, don haka kaina na ƙasa ina rawan jiki na shiga ja da baya yayin da ya daɗa kiɗima ni da amon muryarsa da ya fito lokaci ɗaya da cewa,"Am sorry ban tsammaci za ki tsorata da yawa haka ba, nayi hakan ne domin ƙafafun da suka maƙale wuri ɗaya su samu takowa zuwa ciki". Ina micincina idanu na ce,"To baka san ko a addinan ce babu kyau tsorata musulmi ba". "Tuba na ke yi ba zan ƙara ba daga ranar yau, amma ki sani kina da me ba ki kariya kar wani abu ya ƙara tsorata ki". Ni dai ja nake da baya har na zube kan ƴar ƙaramar plastic chair ɗin ɗakin ƙirjina sai faman sama da ƙasa yake yi. So na ke na ɗaga ido na kalla fuskar da na yiwa kallo ɗaya saboda na tabbatar da zargina. Sai kuma ringtone ɗin iphone ya cika ɗakin, wanda da sauri naga ya matsa daga inda yake ya isa katifar ya ɗauka, sai jinsa nayi yana magana cikin wani irin yare kamar jagwalgwalo babu daɗin ji, duk sai naji maganar tana hawar min saman kai har ta kai ga na rufe ido ina gwame fuska. "Ina wuni". Da sauri na buɗe idona ina dawowa cikin duniyar da na bari jin murya a gaf da ni, na kalle shi muka haɗa ido sai na kasa ɗauke kallona a kansa gaba ɗaya kuma na diririce. Zuciyata ta amsa da sunansa,"Salim!". Mutumin da na sani shekaru goma sha da suka wuce, mutumin da watannin baya da suka wuce naga hotonsa a album ɗin bikin Safiyya. Naja numfashi inda na haɗe da ƙamshinsa da ke tsumani na zuƙe, sannu a hankali ƙamshin turarensa ya ɗebe ni ya kaini tunanin germany, sauka a airport, cikin napep. Ba tare da sani ba kawai na tsinci bakina da furta,"Kai ne?". Sai naga ya ɗaga gira dukka biyu yana kallona kawai, kafin yace,"Ai na?". Na tsuke gira ina tuna komai daki daki na ce,"A airpot ranar da na dawo, da kuma ranar ma a adaidaita". Sai ya lumshe ido yana girgiza min kai alamun a'a. Na ɗan duki ƙafa a ƙasa na ce,"A'a wannan ƙamshin ne". Ba zan ce ga da irin muryar da nayi magana ba don ba zan iya tantancewa ba, amma sai naji ya kwaikwayi muryan da cewa,"Ba wannan ba ne, irin wannan ɗin ne". Kawai sai kunya ta kama ni na kai hannu ina rufe fuska, har ga Allah nema na ke na kasa controlling kaina ba don komai ba sai saboda ƙamshinsa da shi kansa da cikar haibarsa tayi gama gama da ɗakin musamman da yake zaune a gabana. Dariya naji yayi ƴar ƙarama yana maimaita gaisuwar da yayi. Sai na ɗan saci kallonsa, ni ya kamata ace na gaida shi ai to amma ta ya zan samu sakewar hakan mutum babba na zaune a gabana kamar yarona? "Ba za ki amsa ba?". Sai na samu kaina da cewa,"Ai kana zaune a gabana kuma ni ya kamata na gaishe ka". "Ni dai a amsa mini domin kuwa cancantar Sarauniya ne da isarta a duƙa a gabanta a gaida ita, musamman ga mutumin da ya zo da ƙoƙon bara". Tsintar kalamin nasa nayi har ɓargo da jijiyoyin jikina, kuma kafin na ankare sai gani nayi ya haɗe hannayensa alaman roƙo gami da ɗan karayar da kai yana cewa,"Please a amsa min, domin a ƙage na ke da na miƙo ƙoƙon barana bani a karo na biyu". Baki na buɗe ganin yacca yay da fuska kaman ƙaramin yaron da ke shagwaɓar ayi masa abinda yake so. Sai ya miƙo hannunsa yay kamar zai zura yatsa cikin sakakkun laɓɓana nayi saurin kauda fuska gefe cike da kunyar da ta kama ni, domin kuwa surar fuskarsa ce ta ɗauki a hankali, kallon da ban samu damar yi masa a wancan lokacin ba, dama wannan kyan ne Safiyya take ta faɗa min? Amma kuwa idan haka ne Allah ya saka masa domin me hoto ma ya rage masa kyau sosai da sosai. Yunƙurawa nayi zan tashi yay saurin dakatar da ni,"Please koma ki zauna". Ya faɗi hakan yana gyara zaman tanƙwashe ƙafafunsa tare da mayar da yanayinsa na masu magana da gasken gaske. Sai na ce,"To don Allah ka tashi a gabana". Wani kallo yay min yana sosa gira sannan yace,"Ni fa ki ƙyale ni a yanda kika ganni, ki zauna kawai muyi magananmu, ba dafa ki zanyi na cinye ba, in ma zan yi hakan tukunna dai. Muhimmiyar magana ce ta sani na ke zaune haka a gabanki saboda haka koma ki zauna, idan kuma salon zaman ne bai ba sai na gyara". Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa ya dire gwiwoyi a ƙasa. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina cewa,"A'a du Allah". Komawa nayi na zauna kamar me koyon zaman, shi kuma ya shafo fuska yana girgiza kai kafin yace,"Zan iya sake gabatar da kaina?". Kai kawai na kaɗa masa alaman ehh. Da yanayin barkwanci yace,"Awwa Allah sa dai kar ki ce wannan ya fiya naci kamar in mammake shi". Furucin ya ban dariya na ɗan dara kafin kuma na haɗe rai. Kuma sai ji nayi yace,"Ki gama haɗe haɗen ranki indai za ki buɗen ƙofa shikenan. Anyway kamar yanda na faɗa miki a baya ne My name is Salim Sadiq Oluwa, ni ɗan ƙabilar igbo ne.....". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR02FT5* Ƙaramin yaro ya shigo gidan yana cewa,"Salamu alaikum a bada zoɓo". Ummani da ke daga cikin ɗaki tace,"Ana zuwa". Ta fito daidai lokacin tana tambayarsa,"Na nawa?". "Na ɗari, wai don Allah a bada na roba me kyau". Tayi murmushi tana cewa,"Ai duk masu kyau ne". Tana saka masa cikin leda wani yaron ya kuma shigowa yace,"Akwai kunun aya?". Tace,"Babu sai gobe idan Allah ya kaimu". Ta sallami me zoɓo Kaka yace mata,"Me yasa ba ku yi kunun ayar ba bayan kun san anfi son sa". Tace,"Jiya ne Sa'ida ta dawo a gajiye bata samu damar yi ba". "To amma ke da ba sai kiyi ba". "Kaka hannun jikar taka sirri ne da shi, akwai zaƙin hannu idan tayi wallahi yafi nawa daɗi". Kitchen ta shiga ta ɗauko abinci a ƙaramin filas tace da Kaka,"A shigar maka da shi cikin ɗakin ko anan zaka ci?". Ya gyara zama daga kishingiɗen da yake yace,"Bar min anan cikin ɗakin zafi, nepa sun hana wuta yau". Ta ajiya masa ta ɗauko ruwa ta aje masa, shi kuma yana ta saka mata albarka don shi kansa kaf matan ƴaƴansa yafi son Ummani, a ko da yaushe yabonta yake yi domin ita ɗin macece ta ƙwarai, yanda take masa tamkar shi ya haifeta. Yashaik ya shigo gidan, a nan tabarmar da Kaka yake ya zauna suna gaisawa, kafin daga bisani ya miƙe ya shiga ciki wurin mahaifiyarsa. Samunta yay ta fito da kayan sif ɗinta dukka tana linkewa, daga gefe ya zauna yan agaishe da ita ta amsa tana tambayarsa ya iyali. "Me makon ki aika a kira miki Maman Yasmin, yanzu ina ke ina aikin ninkin kaya masu yawa haka". "Ku dai kun fi so kuyi ta gani na kwance sharaf wuri ɗaya bana aikin komai, haka kawai kuma yarinya na can gidanta tana aikinta sai na aika a tasota, a'a kayan nawa suke gaba ɗaya yanzu zan gama ai. Yau babu in da kaje kenan?". Ya sauke numfashi yace,"Ban leƙa ko ina ba, gani nayi gwara in ke hutawa lahadin jiki na buƙatar hutu". "Haka ne, Allah daɗa rufa asiri. Jiya naji ka ce zaku yi magana da Abbaan ku sai ban ga ka dawo ba shiru, ba dai wata matsalar ba ce ko?". Ya kai hannu yana shiga tayata linkin kayan yace,"Da na ƙyale ne kawai saboda na san ko naje masa da zancen ba karɓa zai yi ba, wataƙila ma raina ya iya ɓaci, sai dai ko ke za ki faɗa masa". Ummani ta mayar da hankalinta kansa sosai tace,"Menene fa?". Yace,"Ba fa matsala ba ce". Ya faɗa yanda yaga mahaifiyar tasa ta kafe shi da idanu. "Dama akan Sa'ida ne ban san me Abbaa ke hange ba da yaƙi bawa zaurawan nata dama, haka kuma gaba ɗaya bai son zancen auren nata ba, amma ni gani na ke bai kamata a biye mata ba, duk da cewar dole auren ya sire mata, amma ai ba zamu ɗauka cewa lallai abin da ya faru a farko shi zai kuma faruwa ba ko kuma yayta maimaituwa, kawai ta ɗauka hakan matsayin jarabawarta ba wai saboda dalilin hakan kuma tace ita ba zata ƙara yin wani auren ba. ita macece ko ai na take ko me take yi duk matsayin da take da shi da aurenta tafi daraja a idon duniya, kuma ku kan ku idan da aurenta hankalinki zai fi kwanciya, kuma sannan shekaru tafiya suke ta yi gaba ba dawo baya zasu yi ba, nan da wata shekarar magana ake ta zata shekara talatin idan da rai da kuma lafiya, to ta gama karatun ta samu aikin yi me za'a ƙara jira Ummani? Baka biyewa maganar mutane balle ta dameka amma ana gudun baki, wani bakin kaifi ne sune masu kambun baka, ni gaskiya na fi ga sha'awar tayi aurenta, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ta dage da adu'a kawai Allah kar ya maimaita mata irin mijin baya". Ummani ta numfasa tace,"Ni kaina da ka ganni wlh yanzu hankalina yafi ga tayi auren, Sa'id idan ta fita aikin wannan wallahi sam sam bana samun natsuwa har taje ta dawo hankalina ba'a kwance yake ba, amma lokaci ne duk dai Abbaan naku na daƙile damar hakan, Allah dai ya kawo mata na gari ya musanya mata da mafificin alkhairi". "To amin ya Allah. Kuma dama Nura ne yay min magana ɗazu da safe yace abokinsa Ya ganta yace idan ba'a tsayar da maganar wani akanta ba ya gani yana so". Ummani tayi murmushi me faɗi tace,"Allah sarki, ai na yake to?". "A can garejin ma su yake shima, kin sansa ma sai dai ba za ki gane shi ba, amma da sallah ƙarama tare suka zo da Nuran ai". Tace,"To madallah, ai ina ga sai kace masa ya tunkari Abbaan na ku da maganar ko, ya gwada tasa sa'ar ko a kansa dacen yake". "Ehh to dama ni abin da ma yasa ban masa maganar so na ke na fara bugar cikinta naji ko tana da ra'ayin auren me ƴaƴa". Ummani tayi gajeriyar dariya tace,"To ita wanne zaɓin saurayi ne da ita yanzu, sai dai kuma wani lamarin na Allah, fatan dai Allah bata wanda yafi wancan". Da haka suka ci gaba da hirarsu akan maganar Al'amin ma da za'a kai kuɗin aure cikin satin nan, har sai da suka ninke kayan dukka. Shi ya share mata ɗaki ya goge ko ina, yay mata sharar tsakar gida da kitchen suma duk sai da yay mopping, dama sun saba hakan shi da Imam duk sanda suka sameta tana aiki, don shi da yake kusa da suma da sassafe yake zuwa yay sharar soro da ƙofar gida. Bayan tafiyarsa yana zuwa gida kuwa ya aiko mata Yasmin wadda ta shigo tana ta ƙunci wai Kawu yace ta zo tayi wanke wanke. Da yamma yaro ya shigo tsakar gida yana ta doka sallama babu wanda ya amsa, Ummani na daga cikin ɗaki a kwance kamar a mafarki taji sallaman wajen ƙofan ɗakinta, tayi saurin tashi tana cewa,"waye ne?". Yaron yace,"Ai ko ni aka yi, wai ana sallama da me gidan". Labule ta ɗaga ta leƙo tana cewa da shi,"To masu gidan ai da yawa, kaje kace wa ake nema?". Ba jimawa ya dawo yana cewa,"Wai Malam Salman". Ummani tace,"Tooo wallahi ba ya nan, amma kace musu yana kan hanyarsa ta dawowa ko zasu jira shi, suna da yawa ne?". Yaron yace,"Ehh mota biyu ce har da sojoji". Gaban Ummani ya yanke ya faɗi ya bada rasss, tayi saurin dafe ƙirji tana faɗin,"Sojoji kuma ɗan nan? An ya ba makuwa ka yi ba kuwa, ko can ɗaya gidan aka aika ka kusa da me kayan miya". Yace,"A'a ni dai nan suka ce min". "To shikenan je ka kace musu bai dawo daga kasuwa ba sai dare". Yaron ya juya ya fita ita kuma ta dawo cikin ɗaki, ta kasa zaune tayi tsaye tana tunanin lafiya? Me zai kawo sojoji neman Abbaan su? Sai tayi maza ta ɗauki wayarta ta yiwa Sa'ida flashing, Sa'ida ta biyo bayan kiran, ta ɗaga tana ce mata,"Ke sako min kati zan kira Abban ku". Yanayin fitar muryan nata yasa Sa'ida cewa"Lafiya Ummani?". "Lafiya lau sauri sako min zan ba shi sallahu ne a kasuwa kar ya riga ya taho". Within one minutes sai ga shigowan katin ɗari biyar a wayar, ta lalubo sunan Abbaan Sa'id ta kira. Abbaa a lokacin na bakin titi ya ɗaga kiran wanda hayaniyar ƙarar ababen hawa bai barin sa yaji me take cewa itama ɗin kuma bata jinsa sosai, haka tayi ta faman kira ƙarshe sai haƙura tayi, ta fito tsakar gida ta zauna tayi jugum, har sai da ta leƙa ƙofar gidan taga tabbacin maganar yaron, soja ɗaya na tsaye bakin mota da bindiga a hannu, wannan fa yasa ta daɗa tsurewa ta kama safa da marwa a tsakar gida tana ta faɗin Allah sa lafiya. Bayan kusan rabin awa sai ga Abbaa ya shigo gidan a gaggauce yana ƙwala kiran,"Sa'a! Sa'a! miƙo min babbar tabarma maza maza". Irin yanda yake ƙwala kiran bana lafiya ba, Ummani ta fito daga ɗaki fuskar hijabi a juye jiki duk sai ɓari yake yi, ganin yanda Abbaan yake shima da ruɗani ta tsaya tambayan,"Abbaa lafiya? Kaga baƙin ƙofar gidan ne kaima?". Bai amsa mata ba yaci gaba da ɗauraye ƙafarsa da duk tayi ƙura tare da wanke fuskarsa ma. "Ni dai sauri miƙo min tabarmar tukunna, ni kaina ba na ce miki lafiya ko ba lafiya ba Sa'a, amma hankalina duk ya tashi". "Abbaa to kaje wurin su kuwa? Ko na aika a kira Yashaik yau yana gida bai fita ba". "A'a ƙyale su Sa'a, bara na fara jin me ke tafe da su sun ce sun jima waje, maza miƙo min tabarmar dai, kin san irin mutanen ba'a barin su da jira". Ganin ta tsaya kawai ya wuceta yay ɗakinsa ya buɗe ya yayibo tabarma ya fito yay waje da hanzari, duk ya rikice tafiyar tamkar zai kifa ƙasa. A soro ya baza ƙatuwar tabarmar, takalamansa ma a baibai ya saka ya leƙa yana ce musu,"Bismillah ku shigo daga ciki". Zatonsa iyaka waɗannan sojoji biyun na waje ne sai yaga an buɗe mota manyan mutane dattawan arziƙi suna fitowa, da kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka shaida duniya ta san su ta san da zaman su, matsayi kuma an same shi sai wanda ake kan rabawa, kuma masu faɗa ne aji a ƙasar da suke ciki. Sojojin na basu kariya har suka shigo soron wanda duk Abbaa ya daɗa hargitsewa yana duban tabarmar da duk ta ɗan sha jiki, da shi kansa soron gidan wanda yake ganin sun girmi su ko rakuɓe a cikinsa balle zama. Sai dai ga mamakinsa babu wani yanayi na ƙyama ko jin kai a tare da su, duk sai yake jin wani iri, bai taɓa yin baƙo yana jin ya ƙasƙantar da shi duba da irin muhallinsa ba sai waɗannan mutanen. "To ko kujera za a samo muku?". Ɗaya daga cikin su yace,"A'a babu komai Malam, ai nan ɗin ma Alhamdulillahi ya isa, ga shi duk mun zauna, muna godiya da karramawa". Sai da duk suka gama zama sannan ya zauna yana mai fuskantarsu, ya ranƙwafa kamar bafaden sarki, da firgicin da ke tare da shi ya shiga miƙa musu hannu wanda a farko sai da yaji shakkar hakan, sai kuma yaga saɓanin fa yanda yake tunaninsu ne domin da kansu suka miƙo masa nasu suna gaisawa da girmama junansu da kuma mutuntawa. Cikin wani yanayi Abbaa da bai taɓa shigansa ba yake kallon tsohon mutumin da ke cewa da shi,"Da ka natsu naga duk ka dabarbarce da ganin namu". Abbaa yace,"To ai ranka ya daɗe ganin mutane irinku dole mutum ya shiga irin wannan yanayin na ruɗani, ni dai fatana Allah yasa lafiya, Allah yasa lafiya don cikin gida ma kanta iyalina a tsaye take". Alhaji Sama'ila ya murmusa yana duban Abbaa da kyau yace,"Kar ka samu damuwa lafiya lau, Alkhairi ne ya kawo mu gare ka, saboda haka ka bar tunanin ko ba lafiya ba ne". Sai sannan Abbaan ya samu ya ɗan sauke ajiyar zuciya ta salama yace,"To masha Allahu, bara a miƙo muku ruwa". Ya yunƙura zai miƙe sai ga wani baƙon ya shigo, Abbaa ya kalle shi cikin faɗaɗa fara'ar fuskarsa yay saurin miƙewa yana miƙawa Baba hannu yace,"A'a Alhaji Babangida kai ne da kanka a gidan nawa, barka da zuwa". Baban su Safiyya shima cikin fara'ar da ke wadatuwa saman fuskarsa yake cewa da Abbaa,"Malam Salman ka ganni kwatsam ko, to ya za'ai zuwa ya zamar mana dole". "Wallahi fa, kar dai kace min tare ku ke da waɗannan bayin Allah'n?". Baban su Safiyya yace,"Tare muke da su, da yake ni uzuri ya ɗan riƙe ni a hanya ne shiyasa suka riga ni isowa, tafiyar ai tawa ce ma gaba ɗaya, na ke ce musu ai gida muka nufa su isa kafin na ƙaraso". Baban su Safiyya ya nemi waje ya zauna yana magana da jama'arsa, yayin da Abbaa ya shiga daga cikin gidan yana kiran sunan Ummani a hankali saboda ana iyo jiyo maganar tsakar gida daga soron. Ummani kuwa na kitchen a lokacin ta rafka tagumi tana jinsa ta taso da sauri tana buɗa masa hannu alamun ya ake ciki. "To bana ce ba amma dai sun ce lafiya lau alkhairi ya kawo su, don tafiyar ma har da Alhaji Babangida". "Alhaji Babangida dai?". "Baban yarinyar nan ƙawar Sa'ida, bani sunanta nan, yauwa Safiyya". Ummani ta sauke nauyayyan numfashi da cewar,"Ohhh har na samu Sa'ida amma da hankalina duk ya tashi ina ta tunanin me zai kawo mana sojoji wajenka, don wallahi har na fara zargin ko matsalar rumfar nan ce". Yanayin fuskan Abbaan dai gata nan yace,"Samu faranti ki zubo lemu da ruwa". Ummani ta koma kicin ta ɗauko farantai guda biyu, shi kuma Abbaa ya shiga ɗakin Sa'ida inda firiji ke ajiye ya kwaso kunun aya da ruwa. Yasmin ta shigo Abbaan ya bata faranti ɗaya yace ta kaiwa baƙin waje, Ummani kuma na cewa da shi,"To ai kai musu waɗancan kofunan robar kuwa? Da dai an bar musu a jarkunan? Ko na aika Yusra ta bada kofunan tangaran ɗinta". "Bar shi akai musu hakan ai sun san inda suka zo". "To shikenan Allah sa khairan ɗin da gaske". Ta faɗa tana bin bayan Abbaa da kallo har ya fice. Kafin ta shiga daga ɗaki tana cewa bari ta kira Sa'ida ta faɗa mata ko zata siyo kofunan ƴan gayu a hanya saboda zuwan manyan baƙi irin haka, ranar nan ma haka ta zo da ma'aikatan asibitinsu duk sai taji kunya saboda irin farantin da aka zuba musu abinci, to da yake dai baka kunya da matsayin da Allah ya aje ka. Abbaa ya zauna suna ƙara gaisawa da juna, bayan an taɓa ƴar hira tsakanin Abbaa da Baban su Safiyya sai Alhaji Surajo ke cewa,"Tom Babangida kayi masa bayanin me ke tafe da mu ko". Baban su Safiyya na jijjiga kai yace,"Ƙwarai haka ne, bama biyewa hirarmu da ba zata ƙare ba, zumunci yay ƙaranci wai don ma Allah ya haɗa kan ƴaƴan namu sunata na su zumuncin". Abbaa yace,"Wallahi fa Alhajin Allah, da sai a wuce shekaru masu yawan gaske ma ba'a gaisa ba ko ta wayar, zumuncin zamanin sai adu'a sai mutum yayi da gaske zai samu ladansa". Baban su Safiyya ya numfasa kana ya dubi Abbaa yana yi masa nuni da babban mutumin da ke tsakiya me cikar kamala da dattako, wanda Abbaa zai iya cewa dama tun zuwansu yaji mutumin ya cika wurin da haibarsa, kuma yana da tabbacin ƙamshinsa ne ya gauraye dukka wajen tun daga ƙofar gida har cikin gida. A hankali Baban su Safiyya yace,"Malam Salman wannan shi ne Major Sadiq Oluwa Ibrahim, Yayar Matata ne uwa ɗaya uba ɗaya domin a wurinsa ma na karɓi auren ƙanwarsa, na kusa da shi kuma kusan mahaifi ne a wurinmu sunansa Captain Adebisi Oluwa...waɗannan kuma duk da kake gani abokai ne sai wancan". Ya faɗa yana nuni ma Abbaa da na kusa da shi yace,"Shi ƙane ne a wajen Major, sunansa Alhaji Mukhtar Oluwa". Abbaa yana ƙara rissinar da kai yace,"To masha Allahu, madallah dukkanku ina ƙara yi muku maraba, ayi haƙuri dai da irin wajen da aka samu". Captain Adebisi yace,"A haba dai haba dai muma duk irin namu muhallin kenan". Baban su Safiyya ya ƙara cewa,"To Malam Salman abin da yake tafe da mu muhimmin abu ne, magana ce babba, kuma alkhairi ne ya kawo mu gareka, sai dai bamu san a yanda zaka karɓi al'amarin ba, duba da cewa mun sake dawowa ne a karo na biyu da buƙata iri ɗaya, amma a wannan karan muna fatan samun karɓuwar tayin mu saɓanin baya da bamu samu karɓuwa ba". Abbaa yace,"To Alhajin Allah a ɗan warware ni ko, an saka ni a duhu". Ya faɗu haƙoransa a waje fuskarsa washe da fara'a. Major Sadiq wato Sir kamar yanda ƴaƴansa ke kiransa yay nisa tare da numfasawa, yana daɗa kallon fuskar Abbaa da ke kama da ta Sa'ida sak wadda ya gani a cikin jirgi ranar da zasu kaita makaranta, kafin ya fara magana a cikin birkitacciyar hausarsa ta yarabawa yace,"Ammm Malam Salman mun zo wurinka ne a dalilin Yarona, wato dai mun zo nema masa auren ƴarka da ya gani yake so, idan ba'a rigada an tsayar mata da mijin aure ba shi yana da buƙatar aurenta, aure nan kusa ba tare da anja lokaci ba". Abbaa ya ɗaga kai a karo na biyu yaywa Major kallo na ƙurulla, sai kawai yaji kwarjinin mutumin ya dake shi, haka kuma nauyinsa ya kama shi, yay saurin ɗauke ƙwayar idonsa akansa yana me ƙara sunkuyar da kai ƙasa yace,"Ina sauraronka Ranka shi daɗe". Major yaci gaba da cewa,"My son Salim na ɗaya daga cikin manema auren ƴarka a shekarun baya masu yawa da suka wuce, to kuma sai ubangiji ya ƙadarta cewa ba zata zama matarsa ba a wancan lokacin, shi ne a wannan karon ya turo mu gare ku da ƙoƙon bararsa yace a taimaka masa idan har wani bai riga shi ba". Kan Abbaa ya ɗaure, kafin ya kalli Baban su Safiyya yace,"Alhajin Allah ni ai har yanzu na kasa shaida ɗan namu da kuke magana akai". Baban su Safiyya yace,"Ehh to da yake a wancan karan ba mune muka zo ba gaskiya, amma ai ba zaka mance yaron da ya kawo kuɗin aure daga baya kuma aka karɓa da cewar ba zai iya jiran yarinya ta kammala karatun da aka ce masa ba, wanda kuma hakan ta faru ne duk ba da son ran zuƙatan kowa ba musamman shi yaron". Abbaan yayi ƙayattacen murmushi da cewa,"Na tuna, na tuna hakan, to amma shi da yay wancan magana a lokacin baya ai ce na ke an wuce babin...". Sai yay shiru kamar yanda duk suma suka yi shiru suna kallonsa. Zuciyar Major cike da fargaba da zullumin kar su ƙi amsar tayin su, don shi kansa ya kwaɗaitu wa ɗansa auren Sa'ida. A lokacin ne kuma aka yi kiran sallar magriba, don haka duk suka miƙe Abbaa ya shiga gida Ummani ta zuba ruwa a buta guda biyu ta ba shi ya fita da ita, ta aika Yasmin wurin Umman su Hindatu ta ƙaro buta aka ƙara musu kafin Abbaan ya dawo ya karɓa masu sallaya, ita dai Ummani ganin yanayinsa na yanda yay sanyi kamar jikinsa ya mutu sai duk ta shiga damuwa da fargaba, tana tayi masa magana ma bai tsaya ya saurareta ba. Don haka da sauri ta ɗauka waya ta kira Yashaik tace idan yana gida yay sauri ya leƙo gidan. Ko a wajen sallah ma babu yanda Abbaa bai yi ba akan wani cikin su ya ja su sallar suka dage masa akan lallai shi ne zai ja su, haka yaja su sallar bayan sun idar kuma suka komo soron suka zauna, Abba ya amso fitila a cikin gida ya saka musu saboda soron yayi duhu a lokacin. Bayan zaman nasu Alhaji Mukhtar yace,"Malam Salman na san kana tunani ne akan abun da ya faru a baya ko, to idan wannn ne kar ka damu, wallahi tallahi ko a baya Salim ba ya janye maganar aurensa da ƴarku ba ne saboda dalilin da aka faɗa, hasalima danne zuciyarsa yay ya haƙura a babu yanda zai yi saboda nuna masa da tayi na bata sonsa, shi kuma bai zai iya auran macen da bata sonsa ba, yana ganin idan ya nace aka yi auren zaman ba zai yi musu daɗi ba, saboda wannan dalilin a lokacin ya zo ya same ni muka yi magana ya faɗa min duk yanda suka yi da yarinya har ma ya fahimci akwai wanda ita take so, amma bai karɓi kuɗinsa don yay wulaƙanci ko tozarci ba, kum ahatta maganar da akayi a lokacin na cewa ya samu wata matar wallahi a lokacin babu wannan zancen anyi hakan ne duk don samun mafita". Abbaa ya sake jinjina kai kafin yace,"To da wannan da wannan, don bayanin da ka min yanzu shi ne nake so na tambaya. Sai dai duk da haka akwai wani hanzari ba gudu ba, ƴata ba budurwa ba ce yanzu bazawara ce ita, wataƙila kuma bai san da hakan ba ne". Baban su Safiyya yace,"Ya sani Malam Salman, ya san komai, sannan shima ɗin ba wai saurayi ba ne da aurensa, bayan aure ma har da arziƙin yara uku...". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR03FT5* Abbaa yay shiru yana nazarin kalaman na su, ba zai ƙi tayinsu ba, domin shi kansa ko a wancan lokacin Salim ya kwanta masa a rai, yafi gamsuwa da shi fiye da duk waɗanda suka zo neman auren Sa'ida, shiyasa ko a lokacin ya yarda ya amince aka karɓi kuɗinsa bisa sharaɗin da ya gindaya na cewar sai ta kammala makaranta, kuma ko a sanda suka zo karɓar kuɗin su bai ji daɗi ba fiye da adadin kalmomin baki, ba wai rashin jin daɗi na sun wulaƙanta su ba kan karɓar kuɗin ba, a'a rashin jin daɗin Ƴarsa ta rasa yaron kirki, yaro me nagarta kamar Salim, yaga haƙiƙanin soyayyar ƴarsa a ƙwayar idon yaron, haka ya tsinci raunin rasata a muryarsa, kuma gamsu ɗari bisa ɗari da irin shaidun da mutane suka yi akansa, ba tare da sanin iyalinsa da kowa ba ya ɗauki ƙafa yaje har garin Anambra state domin yayi kyakykyawan bincike akan yaron da iyayensa kuma duk suka samu shaida mai kyau, dama tsoronsa ɗaya bawa ƙabila auren ɗiyarsa. To a lokacin da ace shi irin mahaifin da ke tilastawa ɗiyansa abin da yake so ne ko da basa so, to da lashakka Sa'ida bata isa ta auri wani miji bayan Salim ba, to sai dai babu yanda zai yi shi uba ne me son farin cikin ƴaƴansa kuma me son dukkan abin da suke so ko da shi ba ya so in har wannan abu bai kaucewa shari'ar musulunci ba. A yanzu tarin tambayoyi ne a ransa to amma zai bar su bincikensa ya ba shi amsa, akwai dai damuwa da fargaba a tare da shi. Major ya katse tunaninsa cikin magana me taushi irin ta dattijon arziƙi, yace,"Malam Salman Safiyya ita ta tabbatar mana da babu maganan wani akan ƴarka, bisa wannan dalili muma muka ga ya kamata muyi gaggawan zuwa kar mu makara. Kuma ni da kaina ina baka tabbacin insha Allahu my Son zai kula da ƴarka ba zai ci mutuncinta ba, yaƙini na ke baka akan hakan saboda na san waye yarona". Da irin waɗannan maganganun Major ya ƙarfafawa Abba gwiwa. Wanda har Abbaa ya dinga jin zuciyarsa na buɗewa da yarda gami da farinciki, sai dai ba zai zama me fatan lamarin ya kasance ba har sai yayi istikara ya kuma sa Sa'ida tayi istikara itama. Abba yay nisa sannu a hankali ya fara magana da cewa,"Tom ni babu abin da zance sai Allah ya zaɓa mafi alkhairi wa yaran namu. Sannan kamar yanda na faɗa muku ne Ƴata ba budurwa ba ce bazawara ce, saboda haka ni ban da hurumin da zan mata zaɓi kai tsaye domin kuwa shari'a ta bata damar yiwa kanta zaɓi". Alhaji Mukhtar ya jijjiga kai da cewan,"Wannan haka yake Malam Salman, magana ce me kyau kayi". Abbaa ya sake cewa,"To madallah, saboda haka ku faɗa masa cewa ya zo ya fara samuna domin ina da buƙatar na gana da shi kafin na basa damar ganawa da ita ƴar tawa su sasanta kansu". Major shi ya fara cewa,"Tom shikenan zai zo ɗin in Allah ya yarda, muna godiya". Gaba ɗayansu kuma sai suka shiga yima juna godiya kafin suyi sallama su miƙe zasu tafi, Abba ya shiga ciki ya karɓo leda wurin Ummani yazo ya kwashe kunun ayar da ruwan ya zuba musu a ciki ya raka su da shi har mota. Kamar yanda suka ji daɗi suke ta godiya da irin karramawar da Abbaa yayi musu haka shima ɗin yake ta godiya a gare su. Bayan tafiyar su ya wuce masallaci bai dawo cikin gida ba sai da yayi sallar isha'i. Ya shigo a lokacin Ummani na daga ciki tana lazimi, yay ɗakin nata ya zauna daga bakin gado, kuma zuwan nasa yasa Ummani idda lazimin nata tare da juyowa ta fuskance tana nazarin yanayin fuskarsa kafin tace,"Abbaa lafiya dai ko?". Abbaa na duban labulen ɗakin kamar me son karanta wani abu a jikinsa yace da ita,"Ehh to lafiyar zamu ce". Furucinsa nasa yasa gabanta faɗuwa, ta ɗaga hijabinta ta cire tana aje carbi ta tashi daga kan dardumar ta dawo kusa da shi ta zauna. "Wani abu ne ya faru? Shi Alhaji Babangidan me ya kawo shi kuma mene haɗinsa da su mutanen?". Ganin duk ta ruɗe Abbaa yay murmushi yana me ɗora ƙafarsa ɗaya akan gado ya fuskanceta, fuskarta ya shafo tare da cewa,"Kwantar da hankalinki matata ta kaina, Sa'adatun Salmanu ba komai ya kawo su ba face alkhairi". Ummani ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana karayar da kai kafin tace,"Yanzu naji batu, amma da hankalina gaba ɗaya a tashe yake, wallahi ka ganni tun da na zauna Allah na ke ta faɗawa, to ai Alhamdulillahi tunda ba wata matsala ba ce, amma me ya kawo su?". Abbaa yace"Zuwan na su akan Sa'ida ne". Cikin mamaki Ummani tace,"Sa'ida kuma? Na shiga duhu me ya faru da Sa'idan?". "Kinga samu nutsuwa don Allah, zuwa suka yi da batun aurenta...". Bai ƙarasa ba ta katse shi,"Kamar ya ban gane ba, shi Alhaji Babangidan ya zo maka da wannan zancen kuma ka tsaya sauraronsa? Ya manta mahaifin ƙawarta ne shi ko kuwa ya manta akwai aminta tsakanin matarsa da ni? To ban da ma mutuwar zuciya ina shi ina zuwa neman auren Sa'ida fisabilillahi, kuma kai bai ji kunyarka ba ma". Tayi maganar cikin Firgicin da ya bayyana a muryarta zuwa ƙwayar idonta da ta fito waje. Wannan yanayin nata da kuma maganar da tayi sai ya bawa Abbaa dariya. Aifa ran Ummani ɓace ta miƙe tana faɗin,"Dariya na baka kenan, to ba zai yiwu ba wallahi, yanda ya zo ya tafi ya tafi kenan babu wani aure tsakaninsa da Sa'ida, hauka ake yi?". Abbaa yace,"To idan Allah ya ƙadarta faruwan hakan fa? Kuma ina ga ai ba haramun ba ne don ya aureta". "Allah ma ba zai ƙadarta hakan ba ubangiji ai ya san daidai, kuma nima ai ban ce haramun ba ne sai dai ai akwai duba a lamarin, kuma ya ce ko ka faɗa masa babu wurin shigarsa?". Abbaa na yin wata dariyar ganin duk tayi kicin kicin yace,"A'a na dai ce masa ya dawo gobe ya ganta, tunda yace yana so a ba shi dama ya shiga jerin zaurawanta ya fara kafa gwamnatinsa da wuri". Ummani tayi wani lakato tana dubansa kafin tace,"Amma kuwa banda na san waye mijina wallahi sai in ce mutumin nan siyeka yayi da kuɗi, yanzu tsakani da Allah sai ka bar Babangida ya auri ƴarka? Kenan kaima a wannan shekarun naka tsofe tsofe zaka iya zuwa neman auren ƙaramar yarinya ƴar cikinka ta kusan nawa? Ko da ike zamu ce ta tadda muje". Abbaa ya buɗe ba ki da mamaki ƙarara yana dubanta yanda duk ta mayar da maganar gaske. "Ka saki baki kana kallona, to ni dai ba dani za'ai wannan zalunci ba, yarinyata da sauran ƙuruciyarta don tana bazawara ba zai yiwu a laƙaƙa mata auren tsoho ba, daga nan har hizba wallahi, mene wani Babangida daga ya ɗan taimaka mana sai ya wani kwaso ƙafafunsa na marasa kunya yace ya zo neman auren ƴar cikinsa". Abbaa yace,"Babangida kai tsaye ma babu Alhajin". "Yo wanne Alhaji bayan ya zubar da girmansa, neman aurar ƴar cikinsa fa yake yi kuma daɗin abin kunyar ma aminiyar ƴarsa". Ganin fa ta haƙiƙance har tana ɗaukan fushi da shi sai mita take yi yace,"Kinga ke ba ki tsaya kin gama jin bayanin da zan miki ba kawai kin hau kan wata maganar, Aure fa ɗan su suka zo nemawa ba kansa ba". Ƙyam Ummani ta tsaya ko ƙyafta ido babu. "Ɗansa?". Sai kuma ta dawo ta zauna tana cewa,"Kar dai kace min yaron nan Khalid me hankali, ka san ƴaƴansa maza biyu ɗayan kurma ɗayan kuma shi ne lafiyayye". Abbaa yace,"To ai bama a nasa ƴaƴan ba ne, ɗan Yayar matarsa ne yaron nan Salim da suka nemi aurenta tun tana budurwa". Ummani ta ware ido akansa ƙwaƙwalwarta na auna maganarsa kafin tace,"Wai kana nufin yaron da ya kawo kuɗi suka dawo suka karɓa?". Abbaa ya jinjina kai yana Faɗin,"Ƙwarai shi fa". "Abbaa sojan nan fa da kace min babba ne da gwamnatin tarayya yake aiki". "Shi dai Sa'a". Nan Abbaa ya shiga bata Labarin duk abunda ya faru tsakaninsa da su Baban Safiyya, Ummani bata jira ƙarashen zancen ba ma ta rangaɗa guɗa a hankali. Ta ɗaga hannu sama tana faɗin,"Allah gatan bawansa, Allah mun gode maka, Allah maji roƙon bawa". Bakin Abbaa buɗe yake kallonta, mamaki sosai ya kama shi, kar dai abin da ke ransa ne a nata ran itama? Kawai sai yaji tana ƙara faɗin,"Bayan wuya sai daɗi, kuma wani hanin ga Allah baiwa ne, Rabo daga sarkin da ba ya zalunci, bijahi rasulillahi wannan yaron alkhairin Sa'ida ne". Abbaa yace,"To ke wai kin san yaron nan ne da kike ta farin ciki haka". "Abbaa ya ba zan yi farin ciki ba, ɗan gidan manya mutane fa, to ni dai wallahi ba don kuɗi ko matsayi ba zaɓin Allah na ke ta nemawa yarinyar nan kuma ina da yaƙinin Salim shi ne Allah ya zaɓo mana, domin kuwa tunda ta fito zaurawa ke ta sintiri akanta ban ji ina farin ciki da zuwan wani ko naji sha'awar ta ƙara yin wani auren ba sai da wannan batu ya afku". Tayi maganar baki dukka a buɗe kamar zai yage saboda murna. "Yanzu a wacca matsaya ku ka kwana da su? Na san halinka Allah sa suma ba ce kayi su kama gabansu ba, don ni dai ban sani ba Abbaa ko kwaɗa Sa'ida zamu yi muci ba". Yay murmushi yana cewa,"Ba haka ba ne Sa'a, aurenta na baya ne har yanzu abinda ya faru bai gushe min ba, shiyasa na ke ta jin tsoro ban san da wa zan kuma haɗata ba". "To ya za'ai na faɗa maka ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, adu'a zamu ta mata ya bata wanda yafi wancan". "To yanzu dai na ce musu su turo yaron ya same ni zuwa jibi idan Allah ya kaimu saboda bana so a saka wasa a lamarin, sai dai ita ɗin bamu sani ba ko ta amince". "Kai rabu da ita yanzu ai ba shashasha bace da hankalinta ta san inda ke mata ciwo, a bayan ma ƙuruciya ce ta hanata gane wanda ya kamata ta aura". ****"Maman Nana ni zan wuce". Na faɗa a sa'ilin da na ke ɗaukan jakata ƴar ƙarama na riƙe a hannu. Maman Nana tace min,"To Sister Sa'ida sai Allah ya kaimu, ki gaida gida ki gaida su Ummani". Na amsa mata yayin da Khadija ke tsokanata da cewa,"Wai ke don Allah ko ki ɗan gwada soliderity watarana ki ce za ki kwana". Ina murmushi na ce,"To madam indai za ki bar min albashinki na watanni biyu ni kuma zan dinga haɗawa da aikin ki". "Ehh lallai da ya ke ni bani son kuɗin". Ina dariya kamar yanda kowa yay na ce,"A'a to ke fa kin je saudiya, ni kuma so na ke nayi nayi na kwashe iyayena na kaisu su sauke farali, kinga idan na samu ƴar 380 duk wata ai tuni zasu wuce umra". Maman Nana tace,"To Allah dai ya cika buri, ki yi maza kinga Ummani ta bani amanarki yau kin yi dare". Nace,"Wallahi fa kinga Yaya Imam ɗin ne ma har yanzu bai kira ni ba, ɗazu ya kira nace masa Dr yace in tsaya saboda waccan matar da akai wa operation to ina ga ko tunani yake bamu gama ba". "To ki kira shi mana". Na ɗan karayar da wuya ina cewa,"Wallahi Maman Nana bana son takura mi shi, komai yake yi yanzu hankalinsa na kaina, Abbaa ne ma yaƙi ya bari na ke komawata ni ɗaya ni banga wani abu a ciki ba". Suka haɗa baki wurin cewa,"Gata ne suka miki wallahi, mace yar tsaro ce sai da kulawa, ki gode Allah da ya ba ki iyayen da idon su yake akan ki". "To bari naje, ni na manta ma daga yau nayi off ni da shigowa sai laraba". Khadija da tsokana tace,"Dama kullum ana ba ki na goron albishir ai dole kike son zuwa aiki kullum". Sauran pure water ɗin da ke hannuna na jefa mata. Da haka na fito daga Nursing station ɗin, Metrom na zaune muka yi sallama da ita, har na fito compound ɗin asibitin sai gata ta biyo ni tana ƙwala min kira da cewa,"Kinga ajiyar ki kin mance nima zan manta kuma". "Sauri na ke ta yi kinga ƙarfe tara ta kawo kai, na gode". Wasu hulunan sanyi ne da safuna Sister Hauwa ke siyarwa daga turkey ake kawo mata, shi ne na siya mana ni da Ummani da Safiyya, da yake safunan ma har da na maza sai na siya har Abbaa da Kaka. Ina tafe zuciyata nata tunanin in kira Yaya Imam ko na ƙyale shi, har dai na fito bakin gate, tunda bai kira ni ba na tabbata wani babban uzurin ne ya riƙe shi, iyaka koƙari suna yi akaina, Abbaa zai rako ni kullum sai mun ci rabin hanya yake komawa, in dai kuma nayi evening to ya sakawa Yayyuna duty yau idan wannan ya ɗauko ni gobe wannan ne zai ɗauko ni. Ina tsaye bakin gate na buɗe jaka ina laluben wayata sai naji gate man na ce min na matsa za'a wuce. Nayi gefe ce na ke ma ko Dr ne zai tafi sai naga ba motarsa ba ce. Na ɗaga waya na kira Yaya Imam yace,"Kin ganni na taho mashin ɗin nawa ya samu matsala yanzu haka ina wurin masu gyara, kiyi haƙuri gani nan zuwa kin ji". Nace,"'To Yaya kana ta wajen ina? Na gaji ne wallahi yunwa ma na ke ji". Yace,"Zan taho yanzu yi haƙuri". Na kashe wayar ina sanyawa a jaka, na fara tafiyata ni ɗaya cikin tsoron da ya fara kama ni, kafin na gama fita a layin ne Allah ya taimake ni na samu me adaidaita sahu na kuwa yi saurin tsayar da shi, na faɗa masa inda zai kai ni yace na bayar da ɗari takwas. Na shiga ina faɗin Allah ya sauke mu lafiya, ban manta da adu'ar zama cikin mota ba, a koƙarinsa na tayar da babur ɗin motar da ke gefenmu tayi masa horn, na ɗan leƙa na kalla sai naga motar da ta fito daga asibiti ce ɗazu. Mutumin da ke cikin motar ya fito ya ƙaraso yana cewa me adaidaitar,"Ina kayi?". Yace masa,"Cikin gari nayi can wajen gidan sarki". Yace,"Ok to nima can ɗin nayi motana ne kaga ya samu matsala, samun bakaniken da zai zo ma yanzu aiki ne". Na ɗan saci ido na kalle shi jin yanda yake hausar gwari, kananun kaya ne jikinsa blue riga me dogon hannu da baƙin wando, yasa bakin gilashi da face mask da sam ba zaka gane fuskarsa ba, zubinsa ma ba na hausawa ba ne duk da fuskarsa a ɓoye take. Zan fito ya fara shiga sai naji yace,"Noo shige daga ciki". Na matsa ciki ya shigo, ƙamshin turarensa ya daki hancina sai naji zuciyata ta motsa, kuma ban aune ba na tsinci gabana da faɗuwa sosai, yatsun hannuna har ji nayi suna rawa, sai da muka yi nisa sosai a tafiya kana na kira Yaya Imam nace masa ba sai yaje ba nama taho, ya gama min faɗansa ya kashe wayar. Ni dai na yita mamakin mutumin ganin bai sauka ba duk da cewa bai faɗi inda za'a kai shi ba, muna tafen ma me adaidaitar ke daɗa tambayarsa yace masa no worry muje kawai idan anzo inda zan sauka zan faɗa maka. Me adadaitar yake ce masa,"Yallaɓai ko dai baƙo ne kai a garin". Na jiyo sautin karamin murmushin da yay kawai ba tare da yace komai ba. Muka iso unguwarmu ina ta ma me adaidaitar kwatance har muka zo ƙofar gida, idona ya hasko min Abbaa tsaye a ƙofar gida hannayensa sarƙe a baya, ban san lokacin da na furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shikenan na kaɗe". Mutumin ya juyo yana kallona me adaidaitar ma ya juyo, duk da banga ƙwayar idon da ke cikin gilashi ba na san dai ayar tambaya ce a cikinta dangane da furucin da nayi. Me adaidatar yace,"Hajiya akwai matsala ne?". Ai kuwa kafin na buɗe baki Abbaa ya doka min tsawa da cewa,"Ba za ki fito ba ne". Na haɗiye dunƙulallan yawu, mutumin ya fita nima na fito sai rawar jiki na ke yi, na ciro kuɗi na bawa me adaidaitar na wuce zan iya cewa ina jin yanda ƙwayar ido ta manne a jikina. Muryar Abbaa tuni ta cika kofar gidan da faɗansa akan tahowar da nayi ni kaɗai, ga layin yay tsit ƙarfe tara da arba'in a lokacin, faɗi yake da uban dare na kamo hanya na taho ina matsayin mace, da ba zan iya jiran Imam ɗin ba me yasa ban kira Yashaik ko Al'amin sun je sun taho da ni ba. Hannu ya kawo zai buge ni nayi saurin shigewa cikin gidan, Ummani ma na tsakar gida na shiga tace,"Ya za ki mana haka, ba dole ayi miki faɗa ba ga wayarki anata faman kira ba ki ɗaga ba". Idona a waje nace,"Wallahi banji kiran ba na sakata a silent". Abbaa ya shigo yana ci gaba da faɗin,"Idan kika kuma tahowa ke ɗaya sai ranki yayi mugun ɓaci, kuma faɗa min gidan uban wa kika tafi?". Jikina ya kama ɓari na shiga wallacewa ina faɗin,"Allah Abbaa babu inda na je". "Ƙarya kike yi in ba haka ba me ya hana ki ɗaga waya? Kin san Allah zan soke fita aikin nan? Ba dai kin yi karatun ba kin samu na tsira da mutunci, to aikin ba dole ba ne zan hana ki". Tuni na durƙusa ƙasa hawayen idona na neman sakkowa nace,"Wallahi Abbaa babu inda na je, kayi haƙuri don girman Allah". Uwa me tausayin ƴaƴanta tuni ta shiga bawa Abbaa haƙuri da tausarsa akan yay ƙasa da murya dare yayi, cikin gida ana jinsa haka maƙota ma duk suna ji. Ya watsa min wani mugun kallo da cewa,"Ba zan ɗauki sakarci irin haka ba, kike jira duk dare za'a zo a ɗauke ki, amma wallahi kika ƙara kuskuren tahowa ke ɗaya daga ranar kin gama aiki". Yana faɗa ya shige ciki, nima na miƙe na wuce ɗakina, Ummani na leƙowa tace,"Abincinki yana ɗakina". Ko takalmi ban iya cirewa ba na zauna ina goge hawayena tare da danasanin tahowar da nayi. Ko kayan ban cire ba na tashi na fita zuwa ɗakin Abbaa, sai da na tabbatar ya haƙura ya daina fushin kana nayi masa sallamar sai da safe na wuce ɗakin Ummani na ci abinci. Wajen sha ɗaya har na rufe ido naji wayata na ringing, da sauri na tashi na rarumota gudun kar Abbaa ya jiyo ƙararta, nifa mahaifina is very strict, bai ƙi ya zo ya ƙwace wayar ba, ban ɗaga ba sai da naga kiran yay yawa har sau uku sannan na ɗaga ana huɗun. Nayi sallama aka amsa, shiru for some seconds sai aka ce,"Nurse Sa'ida ce?". Na ce,"Ehh ita ce". Na faɗa ina jin muryan kaman na santa duk da cewan muryan namiji ne. Sai aka ƙara cewa,"Sorry don Allah na kira ki da daddare, ɗazu na zo asibiti ne Dr Samuel yake bani number na ki yace duk sanda na zo na dinga nemanki, domin ke ɗin ƙwararriya ce wacca ta san makamar aikinta". Babu shakka na san muryar sai dai ba zan ce ga inda na santa ba ko kuma ta wacece ba, a hankali yaci gaba da magana yana ce min yana fama da ciwon baya ne da ƙafa ko zan taimaka na recommending masa maganin da zai sha yanzu kafin zuwa da safe yaje asibiti. Na zage na buɗe murya ina ta kora masa bayani da tambayan ya yake ji, kusan minti goma haka sai naji ya katse ni da tambayan,"Babu dai wani damuwa ko?". Na ce masa,"A'a babu, duk sanda kake neman taimako irin haka zaka iya kira na". Sai ya sake cewa,"Thank you so much, but still ba ki cikin wani matsala dai ko?". With confusion na ce,"Babu komai, kawai na dawo daga aiki ne yanzu na gaji ina so zan yi bacci". Na faɗa ina sauke wayan daga kunnena na kashe bayan ya cika ni da godiya. Daga can ɓangaren Salim ya sauke ajiyan zuciya, sai yanzu ya samu relief jin muryanta ba cikin yanayi na damuwa ba kamar yanda ya tsammata, kenan babu wata matsala saboda sosai ya damu da yanayin da yaga Abbaa a ɗazu, ya san dole zata sha faɗa kam, don faɗan da Abbaa ya dinga mata a lokacin ji yay kaman ya fito ya ba da haƙuri, shi kansa ji yay ba zai iya barinta ta tafi ita ɗaya ba a wannan daren shiyasa ya aje motarsa ya shiga napep ɗin domin ya san idan yace ta zo ya rage mata hanya ba yarda zata yi ba. Ya sauke a jiyan zuciyayana aje wayarsa, tare da jingina kai a gadon ta gefen ƙwayar idonsa kuma yana kallon Kudrat da ke gefensa tana bacci. ******Bayan kwana biyu yau tun tashina Ummani tace da na gama komai na gyara ɗakin Al'amin akwai baƙin da za'a yi anjima. Ban tsaya tambayarta ba ni dai ina gama wanke wanke na shiga na gyara tass, na sanya turaran wuta me bala'in ƙamshi da nasa ordarsa daga meduguri. Gidan duka ya ɗauka har Ummansu Hindatu sai da ta leƙo tana faɗin kamar gidan haihuwa ko sabuwar amarya. Ummani tace na shirya zan rakata unguwa, nayi wanka na saka rigar bubu sai ce tayi lallai sai na sauya in ɗauko abayata da na siya kwanaki mana. Na ce an gama ranki ya daɗe, haka na ɗauko na saka na zauna zaman jiranta sai ƙorafi na ke ina Ummani ki zo mu tafi kin san ba wuri ɗaya kike zuwa ba, an ta shige shige kenan yanzu za ki ga yamma tayi. Tace kar na dameta in ban rakata Yasmin zata rakata. Ban ƙara magana ba na fito da keken ɗinkina tsakar gida na hau ɗinka kayan wasu da za'a kaiwa bauchi. Lokacin yaro ya shigo yana cewa ana sallama da Abbaa, na tashi na leƙa ɗakin na faɗa masa, babu jimawa ya fito ya fita, can ya kuma dawowa yace da ni na ɗauko masa tabarma. Da kaina na kai soro na shimfiɗa kana na dawo ciki. Abbaa ya leƙa daga waje, tsaye ya hangi Salim jingine da motarsa hannayensa harɗe saman ƙirji, cikin kamilalliyar shigarsa ta cofee ɗin yadi da ɗinkin irin na yare, shigarsa tayi masa bala'in kyau. Abbaa dai murmushi ya suɓuce masa, tun asubahin yau ko kuma yace tun a lokacin da yay sujjada ga ubangiji a cikin dare yana me neman zaɓinsa akan lamarin Salim da Ƴarsa yaji fargaba ya barsa yayin da ƙwarin gwiwan aurama Salim ƴarsa ya shige shi, kuma a yanzu da idanunsa ke kan yaron sai yake jin yana samun salama a cikin ransa dangane da lamarin. Yaywa Salim izinin shigowa, ya tako cikin tafiyarsa ta namiji me cikar zati da kamala ya shigo soron lokacin Abbaa har ya zauna akan tabarmar, ya cire takalma ya nemi waje ya zauna, zaman nasa ma har sai da Abbaa yace masa tukunna don da tsugunawa yayi cikin jin nauyin zama a inda surukinsa ke zaune. Ya gurfanar da kansa gaban Abbaa kamar me neman gafara, da girmamawa da ladabi ya sake gaida Abbaa a karo na biyu, Abbaa ya amsa ƙwayar idonsa ƙyam akansa tun a ɗazun. Abbaa yay nisa tare da sauke numfashi ya kira yi sunansa. "Salim ka ke ko?". "Ehhh Abaa". "To ya kake ya aiki?". "Alhamdulillahi Abbaa, fatan na same ku lafiya". "Lafiya lau, Salim ko za ki iya faɗa min dalilin zuwanka wurina?". Da wani ƙwarin gwiwa da jarumta irin tasa ta sojan gaske yace,"Abbaa na zo gare ka ne da ƙoƙon baran ka bani amanar rayuwar ƴarka Sa'ida...". Abbaa ya katse shi,"Amana dai Salim? Ka kuwa san amana?". "Na sani Abbaa, ni musulmi ne cikakke, kuma ina da yaƙinin zan riƙe amanar shiyasa na ce aba ni ita". "Salim amana tana da girma, wutar Allah na cin wanda bai riƙeta ba". "Bana fatan na kasance cikin sahun maciya amana Abbaa, ka yarda da ni zan riƙe amanar da zaka bani tsakani da Allah". Abbaa ya sake cewa,"Kai ka turo iyayenka kenan ko kuwa sun yi zuwan kan su ne?". "A'a Abbaa ni naje musu da maganar". "Amma me yasa baka fara zuwa da kan ka ba? Ko kuma kana ganin kawai don mahaifanka sun zo sai na ce musu na baka ƴata? Shin ka taɓa neman soyayyarta ne?". Ya ƙara yin ƙasa da kai kafin a hankali yace,"Bamu da ƙarfin ikon da zamu zo kai tsaye mu ce zamu ne abu a bamu ta yanda muke so, na fi so ne a duk sanda wani babban lamari ya shiga gabana na fara saka manyana a ciki, musamman sha'ani me girman gaske irin wannan. Sa'ida kuma ban taɓa tunkararta ba, kawai dai na san da cewa in har iyaye suka amince min na nemi soyayyarta da sannu...". Sai yay shiru bai iya ƙarasa faɗin abin da zai ce ba. Abbaa yace,"Da sannu me? Yi min bayani ina jinka". Ya sarƙe yatsunsa da ƙyar ya iya cewa,"In har ta bani dama na shiga sahun manema aurenta da sannu zan koyar da ita so...". Sai kuma ya canja kalamin da cewa,"Da sannu zata aminta da ni". Abbaa ya jinjina kai sannan yace,"To amma kai da kake da iyali mene naka na son ƙara aure Salim? Ba ku zaman lafiya ne ko kuwa dai lamarin wasu mazan na son wulaƙanta matayen su ne?". Abbaa yay maganar wajen bugun cikin Salim ɗin. A hankali kuma cikin natsuwa Salim yace,"Babu ko ɗaya Abbaa, ina dai da sha'awan ƙara aure ne domin ko addini ya bamu damar yin hakan, idan har muna da iko kuma zamu yi adalci zamu iya ƙara aure. Sannan zaman lafiya iyaka gwargwado akwai shi tsakanina da iyalina, bani da nufin na ƙara aure don na ci mutuncin iyalina, ba zan ƙara aure don na cutar da wani ɓangaren ba, lamarin aure abinda Allah ya nufa shi ke kasancewa". [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR05FT5* Idona da ke kallon fuskarsa sai naga kamar ya haska min da ƴar ƙaramar damuwa, na tsinkaye shi da ci gaba da faɗin. "Kina son sanin tarihina tun daga tushe?". Bai damu da jiran na amsa mishi ba ya ɗora da faɗin,"Mahaifina haifaffen garin Anambra state ne ɗan ƙabilar Igbo, Asalin sunansa na yare Kaodinakachi, sunan mahaifinsa Chibuzo Ibrahim Ude, sunan matarsa Isioma Debare kuma ƙabilar su guda, sai dai ita kirista ce bayan ta aure shi ne ta musulunta. Mahaifina shi ne na uku a ƴaƴansu, kasuwanci ya kai shi garin Oyo, a can garin ya haɗu da mahaifiyata Kafayat Oluwa Sunmola, ita kuma yoruba ce, soyayya me ƙarfin gaske ta shiga tsakaninsu wanda har su ke tunanin rayuwa ba tare da junansu ba. All tribes have an issue with each other ba wai tsakanin Igbo da Yaruba ba ne kawai, ƙalubalen farko da suka fara fuskanta a soyayyarsu shi ne ta ya zasu tunkari iyayensu da batun aure, duba da irin yaƙin da ke tsakanin ƙabilu biyun musamman idan aka zo ga ɓangaren sha'ani na aure. domin galibin iyayen ƙabilar Igbo ba sa goyon bayan ƴaƴansu maza su auri mace a wajen ƙabilarsu, an sha gumurzu kafin iyayen mahaifina su yarda ya auri mahaifiyata, sai dai duk da hakan sai ya kasance mahaifiyata bata jin daɗin auren saboda tsangwamar da Kakata ke mata, su ƙabilar Igbo in basa son abu to basa so, idan kuma suna so babu wanda ya kai su so, ta kai ta kawo har iyayen suka yi fushi da mahaifina suka kore shi daga gida, sai Baban Mahaifiyata ne ya ba su wuri, shi yaci gaba da tallafar al'amuran mahaifina tamkar ɗan cikinsa har ta kai ga matakin da ya shiga ya fita ya samar masa aikin soja, dalilin wannan karamci da halacci mahaifina ya sakaya sunan sirikinsa a jikin sunansa, madadin Sadiq Chibuzo Ibrahim sai yake amfani da Sadiq Ibrahim Oluwa, duk wasu takardun aikinsa da wannan sunan yake a amfani kuma da shi duniya ta sansa, sai bayan an haife ni ne aka samu fahimtar juna tsakanin mahaifina da iyayensa har suka yarda ya koma garesu tare da matarsa, lokacin da suka koma Anambra state an yaye ni sai aka bar ni wurin Maman Mamata, suka tafi da Yayana Chibuzo me sunan Kakanmu. na taso cikin soyayya da kulawar Kakana shi yasa nima na ke amfani da Salim Sadiq Oluwa kamar mahaifina madadin Salim Sadiq Chibuzo, sunana na yare Onochie don ko a garinmu da wajen aiki duk haka ake kira na. Papa mutum me mutunci sosai da sosai, ba ya nuna banbancin ƙabila don ko lokacin da Baban su Safiyya yaje neman auren Mamanta wato ƙanwar Mahaifina shi yay conviecing Kakana amma da ba za su taɓa bawa bahaushe auren ƴarsu ba". Ya numfasa kafin yaci gaba,"Mahaifina babban soja ne, kuma nima soja ne aikina yafi kai ni cross river da Ebonyi, a baya da na zo gare ki da batun aure ne a matsayin saurayi, amma a yanzu ni ɗin me iyali ne, nayi aure da matana ɗaya Kudrat, tare da yarana uku Rofi'at, Isioma da kuma Foridat, ni da su dukka muna zaune a barrack ɗin Edo state". Sai yay shiru ya ɗago yana kallona, nima shi ɗin na ke kallo da tsantsar mamaki, so na ke na auna bayanan da yake min domin kuwa na kasa fahimtar dalilin yi min su, ina ce zuwa yay kawai mu gaisa? Then why this information all of a sudden? "Abbaa ya faɗa miki dalilin zuwana wajen ki?". Kamar doluwa nayi saurin girgiza kai. Numfashi ya sauke ya gyara zama sosai tare da cewa,"Ki yi haƙuri da irin ƙarfin halina, haka na ke ni duk wani babban lamari nawa bayan Allah nah to manyana na ke fara sanyawa a ciki, kar ki ce na zaƙe da yawa kawai ina turo iyaye su nema min aure ba tare da na fara fuskantarki ba na nemi soyayyarki. No kawai zan fi samun ƙwarin gwiwa ne da sakewa idan ya zama na tunkare ki da amincewar iyayenki...Kwana biyu da suka wuce iyayena sun zo sun yi magana da mahaifinki...A yau kuma Abbaa ya bani damar in nemi yardar ki, amincewarki ita ce amincewarsa, ni da ke yanzu dukka ba yara ba ne balle a tsaya ɓata lokaci, musamman ma dai ni da na doshi hamsin da ƴan kai....". Mamakin furucin ƙarshe ya doke wancan mamakin da tunani na, ban san lokacin da na waro ido waje kamar zasu faɗo ba ina kallonsa baki buɗe, a raina na maimaita hamsin fa! Ta gaske ko ta wasa?. Ashe a fili nayi furucin sai naga yay dariya yana tsefe gemunsa kamar wani saurayi ɗanye shagaf yace,"Kin ganni da jikin yara ko, shekaruna basa nunawa a jikina ne, shekarun tsufa fuskar yarinta, kuma hakan ai yafi ko?". Ya faɗa yana ɗaga min gira dukka biyu, ni dai na san wannan mutumin na gabana bai kai hamsin ba, to me ma abin so a shekarun da yake kai kansa inda bai kai ba? Na ɗauke kai a hankali kuma naji ya ambaci sunana da harafin jaaa, ƙofofin gashin jikina suka buɗe na lanƙwashe yatsun ƙafafuna. "Sa'idaaaa! Ina son ki, ina miki irin son da ba zan iya misaltawa ba, da ƙyar na haƙura a wancan karon, amma a wannan karon bana jin akwai wasu adadin kalmomi na ban haƙuri da zasu yi tasirin da zan iya barwa wani soyayyata, ki yarda da ni ina faɗa miki abinda ke ƙuryar zuciyata ne, na miki alƙawarin kulawa, soyayya da ƙauna a cikin gidana...please ki ɗago ki kalle ni". Ya faɗi hakan ni kuma sai na kasa wani motsi illa ma sadda kai ƙasa da na ƙara yi, sai ya miƙo hannu zai ɗago haɓata nayi saurin janyewa ina girgiza masa kai alamun kar ya fara. Sai ya sauke hannu yana faɗin,"Sorry! But please ki sanya idanunki cikin nawa domin ki yarda da abin da na ke faɗa miki ki kuma bani amsar tambayar da zan miki". Da ƙyar na tattaro courage na sanya ƙwayar idona cikin tasa da ta kashe min jiki a lokaci guda. Ina ƙoƙarin janyewa sai yay saurin haɗe hannaye yana faɗin,"Please". Sai na fasa, shi kuma yace,"Za ki iya auren ƙabila? Za ki iya auren me mata? Kar ki tunani ta yanda za ki fara rayuwa a cikin ƙabilar da ba taki ba, family na suna da sauƙin kai, suna da mutunci, za su karɓe ki kamar ta su, ba su da matsala kuma ina tabbatar miki da ba za ki samu wata matsala tare da su ba, babu ta wani ɓangare da za ki fuskanci ƙalubale na banbancin yare". Ganin na bada dukka attention ɗina sai ya gyaɗa min kai da cewa,"Uhmm ki ba ni amsa, ni ba zan tilasta miki ba, amma dai zan so ki bani dama, ki bani damar da zan kafa gwamnatin soyayyata a zuciyarki, ina da ƙwarin gwiwa ta wannan fannin". Idanuwana suka cika da ruwan hawaye sai dai ba su samu nasarar gangarowa ba, a sanyaye na ce,"Wataƙila baka san wacece a gabanka ba ne...". "Akwai wata Sa'ida bayan ke ne a cikin gidan nan?". Na girgiza masa kai da cewa,"Ba haka na ke nufi ba". "To ya kike nufi?". "Ni bazawara ce ba badurwa ba, kuma ina tunanin ka zo da zummar samun waccan Sa'idar ne ba wannan da yanzu ke a gabanka ba". Na faɗi hakan ina rumtse ido sosai tare da jin wani ciwo a ƙasan raina. Sautin murmushinsa ya fito sannan yace,"A alqur'ani ko hadisi faɗo min inda aka haramta auren bazawara, na san kina da ilimin hakan, ni kuma in har kika kawo aya ko hadisi zan tashi na bar gabanki kuma ba zan ƙara dawowa duniyarki ba". "Babu". "To kuma kike ce min ke bazawara ce, mene da hakan?". "Saboda maza basa son auren bazawara". "Saboda bazawara bata darajar da za'a aureta kenan? Ko kuma ita abar ƙyamace da bata cancanci a sota a aureta ba? Look Sa'ida na san da cewa ke bazawara ce, kuma a haka na ke son ki kuma a haka zan aure ki kuma zan zauna da ke a hakan, ke na ke so, ke ɗin dai, hasalima idanuwan Salim basa miki kallon bazawara so kar ki ƙara furta min wannan sunan". Sai kuma yay ƙasa da murya yana cewa,"Wallahi tallahi Sa'ida ina sonki ina ƙaunarki, ba da cuta ko yaudara ba, da gaske na ke miki aurenki zan yi don Allah ki ba ni dama". Kawai sai na fashe da kuka sosai har ina kifa kaina a saman cinyoyina, domin kuwa kalamansa sun faman ciwon da ke zuciyata, Ta ya zan yarda da irin kalaman da Nazifi yay min? Ta ya zan kuma gasgata wani namijin har na yi kuskuren aurensa? Sai kawai na mike ina jin wani ɗaci da ƙunci sun mamaye ni, gani na ke kamar da gangan ya zo yana min wannan maganar, kamar saboda yaci mutuncina ne, to ai ni kuma har abada na rufe babin aure. Kukan nawa sai ya rikita shi, inda shima yay saurin miƙewa yana ruƙo gefen rigata. A rikice yake tambayata,"Me ya saka ki kuka Sa'ida? Ni na faɗa miki wani abun mara daɗi ne? Don Allah ki yi haƙuri kin ji". Nayi ƙoƙarin fizge rigata ashe ruƙon da yay mata da kyau, don haka na ɗago cikin kukana me ban tausayi na ce,"Ka sakeni, kuma don Allah kar ka ƙara dawowa gare ni da maganar aure, tsammanina ka zo ne mu gaisa matsayinka na Yayan Safiyya, ashe na tafka babban kuskuren zama ina sauraronka". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ya ambata tamkar wanda ya haɗu da wani ibtila'in. "Ka sake ni ka matsa ka bani hanya". Na faɗa a tsawace ina sake fashewa da kuka. Salim ya shafo kansa yana furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas da ina da damar da zansa hannayena na tunkuɗe shi daga gabana babu abin da zai hana ni aikata hakan. Kawai sai na tsinci muryarsa a marairaice yana cewa,"Don darajan Allah kar ki min haka, ni ba zan iya yafewa kaina ba idan ya zama ni ne silar wannan hawayen na ki, idan na faɗi wata kalma ne mara daɗi a gareki ki haƙuri ki yafe min kuskure ne ban san na aikata ba". Kai na girgiza ina cewa,"Ni baka min komai ba, kawai dai ka rabu da ni kar ka ƙara min zancen aure". Sai kawai ya tsare ni da ido da murya me bala'in sanyi da ban tausayi yace,"To mene laifina da ba za ki so ni ki aure ni ba? Ko ina da wani aibu da ban sani ba? Idan ina da shi ki faɗa min nayi alƙawarin zan gyara, kuma ni ban tilasta miki sai kin aure ni ba idan ba ki da ra'ayina zan ƙyale ki, ba zan miki dole ba amma kar ki zubar da hawaye ta dalilina, ba zan yafewa kaina ba". Ajiyar zuciya ya sauke yana matsawa daga gabana, wayarsa da hularsa ya ɗauko ya dawo gabana yana cewa,"Ki yi haƙuri ki yafe min". Yana faɗin hakan ya juya zai fita, na bi bayansa da kallo, ba tare da sani ba sai na tsinci kaina da cewa,"Ni kawai auren ne bana so da maganarsa, ina jin haushin duqk wata fuska da zata tunkare ni da batun aurena, na rigada na yiwa kaina alƙawarin ba zan kuma yin aure ba...". Na faɗi hakan kuka na daɗa cin ƙarfina. Ban ankare ba naji ya kama hannuna wanda sai da naji tasirantuwar wani abu a jikina, ya jani ya zaunar da ni a bakin katifa. Ya durƙusa gabana yana dubana da kyau sannu a hankali ya fara cewa,"Bana so naji dalilin da yasa kika ɗau alwashin hakan, bana so naji ko kaɗan, sai dai hakan da kika ƙudurta ba mafita ba ce kuma ba hanya me kyau kika zaɓarwa kan ki ba, idan kika ce ba za ki kuma aure ba means ba ki son auren kenan and kar ki manta aure sunnar ma'aiki ne me ƙarfi, shi yace kuyi aure ku hayayyafa domin nayi alfari da ku. Ki manta da abubuwan da suka faru a baya ki fuskanci gaba domin shimfiɗa sabuwar rayuwa me kyau". Sai yay shiru bai ce komai ba. Ni kuma nace,"To lallai sai nayi aure ne zan yi farin ciki? Lallai sai nayi ne rayuwata zata inganta?". "Kina da amsar dukka tambayoyin ki a wajenki, sai dai ba za ki iya bawa kanki amsar hakan ba har sai kin sanyaya zuciyarki kin yi watsi da ƙudurin da kika ɗauka". Sai ya miƙa hannu ya tsiyaya kunun aya a kofi ya miƙo min. Na karɓa kawai na riƙe ba tare da na kafa baki ba. Hawaye ya silalo saman kumatuna nace,"Ko da ka aure ni ba zaka iya zama da ni ba, zaka tsane ni ne, danginka ma ba za su so ni ba, zan zama abar ƙi da hantara a cikin gidanka da danginka". "Saboda mune azzaluman farko?". Da sauri na girgiza masa kai,"A'a ba haka na ke nufi ba". Naga ya haɗe rai yana cewa,"To me kike nufi?". "Saboda bana haihuwa, kuma babu namijin da zai iya rayuwa da mace me irin lalurata...". Ya katse ni,"Wacce irin lalura kenan?". Na kalle shi,"Rashin haihuwa mana, ko kana sona yanzu daga baya zaka daina sona idan ban haifa maka yara ba, suma ƴan uwanka zan fuskanci ƙalubalen hakan daga gare su, kuma matarka ma zata dinga min gori". Ina faɗin hakan ya zauna daga tsugunen da yake. "Au haba! Ashe haka aka yi?". Ya tanƙwashe ƙafa ya amshe kofin hannuna ya kafa baki ya shanye kunun ayar. Ya sauke yana yin gyatsa kana ya kalle ni kaɗan yace,"Ina son kukun aya sosai, wannan yayi daɗi matuƙa, ki cewa Ummani ɗanta ya na godiya Allah ya ƙara mata lafiya, and i hope kema kin iya me daɗin hakan?". Ƙura masa ido nayi kafin na ɗan harare shi, sai shima naga ya galla min harar ido kamar zai zazzago ka rantse macece, kawai sai na tsinci kaina da yin dariya kafin na sha mur. "Ehh ai gwara ki sani ba ke ɗaya ke da ido ba, harara ce kowa ya iya ai". "Ina maka zancen serious kana ɗauka da wasa, kuma na san ko Abbaa ya faɗa maka bana haihuwa don haka kar ka dage akan sai ka aure ni ba zaka yi farin ciki ba". "Yau ba ki je aiki ba kenan? Ko duk zumuɗin zuwana ne da son ganina ya hana ki fita, to a albashinki ni babu ruwana, kar ki zo daga baya kina min ƙorafi an cire miki kuɗi". Yay maganar da son shashantar da wancan zancen. Na tsinkaye shi da ƙara cewa,"Yanzu dai yaushe su Baba za su dawo ayi maganar sa rana? Ba na so ayi taking long, a yanda na tsara cikin satin nan su dawo a bada kuɗin aure a tsayar da rana wata guda, shima don na san za kice sai kin yi ƙaƙalen shirye shirye ne, to kafin dai mu shiga january na ke so na mallakeki ki zama matar lieutenant Salim". Ɓata rai nayi ina masa wani kallo na ce,"To ni nace maka ina sonka ne da har kike lissafin ayi aure". "Manta da wani so me wuyar dama shi ne mu fahimci juna kuma mun fahimta". "Da yaushe ɗin muka fahimta?". "Ehhh kin fahimci ni mugu ne mara mutunci me wulaƙanta mace me tozaratata me cuzguna mata, ni kuma na fahimci ke ba kya haihuwa kuma an rubuta a goshinki ba za ki taɓa haihuwa ba, shikenan sai me ya rage kuma? Sai aure idan muka je can sai ayi ko wacce wacce". Yanda yake zaro magana kamar bahaushen gaske, kuma magana ta masu karfin hali da zaƙewa, Na kauda kai gefe ina jin haushin ma maganar tasa, bai damu ba yaci gaba. "Safiyya ce babbar ƙawarki zan je na tambayeta sizes ɗin kayanki, tare zamu je haɗa lefen ko na haɗa da kaina ko kuma kuɗin zan ba ki?". Na kuma yin shiru ina daɗa kallonsa da zaƙewarsa. Kai tsaye kuma yaci gaba,"Ba zan raba muku gida ba fa tare za ku zauna, yauwa bana son kan matana da yarana ya rabu, so na ke ko da yaushe inga iyalina a tare cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kuma kinga abokiyar zamanki bata da matsala tana da sauƙin kai kamar dai ke ɗin nan". A wani zabure na miƙe babu shiri ina neman hanyar fita. Ban san me yasa naji zuciyata ta motsa ba, sai ya kamo rigata ya maido ni na zauna, ina cin magani na ce,"Kar ka ƙara kama rigana". Sai ce yay,"Kuɗin jikina ba su da yawa da na bada sadaki yanzu". Baki na murguɗa kawai, ni duk ya ishe ni raina sai ƙara ɓaci yake. "Allah ba ki haƙuri, yanzu dai yaushe zan dawo? So na ke dai nayi zuwa biyu uku duk inda zan yi na huɗu sai dai ya zamana na zo ɗaukarki ne gaba ɗaya". Na ware ido. "Dama haka ake yi?". "To ni haka zan yi kuma na tabbata Abbaa zai yarje min, idan kuma kina da kuɗin biyan jirgi ko motar ƴan kai amarya ne shikenan sai ki yi zugar jama'a, ni dai ba me kuɗi ba ne da a kano zan zauna ne dai sai in iya cewa zan biya kuɗin mota". Na dakatar da shi,"Kaga please joke apart and let be serious". Zama ya gyara yana tallafe haɓa ya maida hankalinsa gare ni da kyau. Nayi ƙasa da kai yatsuna a sarƙe nace,"Ni da gaske na ke maka ban da ra'ayin aure, ba zan ƙara yin wani auren ba, saboda haka ka janye maganarka kawai don Allah ka tafi wani wajen". Kawai wai sai naga ya kifa kai yana kukan wasa, har da su shashsheƙa yana faɗin,"Yanzu ni wanne kalar zunubi na aikata da ban cancanci likita ta so ni ba". Nace,"To ai ni ban ce bana sonka ba". Ya ɗago ido ya duben, na kulle ido kafin na ce,"Kuma ban ce ina sonka ba". Shi kuma yace,"Kuma ko darajan Safiyya da Umma ba zan ci ba?". Nayi saurin cewa,"Za ka haɗa ni da ƙawata kenan". "Bari ma na kirata na shaida mata, ai ƙanwar tawa ƙawata ce". Da sauri nace masa,"Aa don Allah kar ka faɗa mata, Safiyya akwai taking abu so serious". "To ki ce kina sona kuma kin yarda za ki aure ni". Raina still a cukule na ce,"Ba yanzu ba". "To sai yaushe?". "Sai sanda na gama nazari da tunani". Ya ɗaga kafaɗa,"Tom shikenan na ba ki lokaci...yanzu zan wuce kar Abbaa yaga na jima". Nayi saurin miƙewa ina cewa,"Tom". Shima ya miƙe yana faɗin,"Ai dama na san kin gaji da ni, kina ta zagina ma a zuciyarki". Shiru nayi ban biye masa ba, haka dai ya tsaya kusa da ni yana shafa waya, ban yi masa sallama ba na fita a ɗakin na barsa, wa ma ya san nayi sallama ko ban yi ba haka na shiga gida, ina shiga ɗaki na faɗa kan katifa ina ta sauke numfarfashi, kaina a kife yake kan hannuna, ba tunani na ke ba haka ban san me yake cikin kaina da abinda ke haskawa a idona ba, amma dai cikin zuciyata ina jin zafi kamar an hura wuta. Na jima a haka can naji muryan Ummani na faɗin,"Masu karɓar ɗinki sun zo na ba su". Nayi saurin miƙewa zaune da sanyin jiki nace,"Ummani kika ba su kuma, ban fa gama sanya stones ba". "Su suka ce a ba su a haka wai yau za su saka, ina ce stones ɗin a ƙasa ne kawai ba ki saka ba?". Na ɗaga kai alamar ehh ba tare da nayi magana ba. Sai tace,"To na haɗa su da Yasmin su tafi tare ta saka musu acan kafin su gama shiryawa, bana so Abbanku yaji ne ya fito ya kama faɗan rashin gamawar". Nasa hannu ina goge hawayen da duk ya wanke min fuska, ina jin idonta akaina kafin tace,"Sai ki yi istikara ai ki nemi zaɓin Allah ba ra'ayin zuciyarki ba, shi kukan mene amfaninsa banda ɗorawa kai ciwo, kuma dai ai ba zuwa aka yi aka ce ana ƙin ki ba". Na waiga ina dubanta na ce,"Amma Ummani ni kawai...". Ba ta jira ƙarashen zancena ba tace,"A'a ba da ni aka yi maganar ba yana ɗaki kije ki sameshi, mene a ciki dan kin ce masa ba kya so, mu dai ai ba kwaɗaki zamu yi mu cinye ba, lokacin kuma da kika sakko akan ƙudurin na ki ai kinga kya auri sa'an Kakanki". Tana faɗin haka ta fita tana cewa,"Ki fito ki tankaɗe min gari, ki kuma ƙarasa haɗa miyar gata can na ɗora a wuta". Na koma na kwanta ina ta tunanin ta yanda zan yarda na komawa duniyar aure, Mazan ba duka suka zama ɗaya ba na sani, to amma zaƙin bakin namiji fa? Ni a ganina tunda har Nazifi ya canja to tabbas kowa ma zai iya sauyawa, kuma tunda har ya daina sona ya tsane ni akan rashin haihuwa to bana tunanin akwai wani Namiji da zai iya shimfiɗa rayuwar aurensa da ni a yanda na ke. Ringing ɗin wayata ya katsen tunani, na ɗauka na duba naga Safiyya ce, ban ɗaga ba saboda fushi na ke da ita don na san ta san komai game da zuwan Salim, sau uku tana kira ni kuwa nayi biris kamar ban gani ba, sai can ga message ɗinta ya shigo da cewa,_"Zancen gaskiya wannan karon kika ƙi ɗan uwana to zamu samu saɓani da ke, kuma Umma ma kanta tace zata san zaman da zata yi da ke in har kika guji ɗanta, ke dolenki ma ki so shi ki shirya zama amaryar ending month na gama magana"._ Ina gama karantawa na tura mata da reply ɗin,_"To Sa'adatu Abdurahman Madobi"._ wato uwata kenan. Har tsawon kwana huɗu ina ta tunanin matsaya, gaba ɗaya na kasa yanke shawara akan lamarin, har yanzu ban ji ina sha'awar sake yin aure ba, haka ban san ta inda zan fara kallon Safiyya na faɗa mata cewa ta sanar da ɗan uwanta ba zan aure shi ba, Abbaa dai bai min maganar ba tun ranar, shi kansa Salim ɗin tun ranar bai neme ni ba ko irin ɗan kiran nan bayan ya tafi, Ummani kuwa sai dai tayi ta jefa min magana cikin magana, bini bini tace yo Allah na tuba tsofaffi gasu nan da yawa a duniyar. Yau tunda na zo aiki duk na ke jina wani iri, sai dai wani ɓari na zuciyata nata karanta min ki yi istikara yau ki samu mafita ki huta. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR04FT5* "Masha Allah! Abbaa ya faɗa yana jinjina kai. "Salim da gaske kake kana son ƴata tsakaninka da Allah ba domin wata manufa ba?". "Ƙwarai Abbaa ina son Sa'ida ba tun yanzu ba, ko a wancan lokacin na haƙura ne saboda ta nuna bata sona, kuma ko a yanzu ma zan iya haƙura idan har ta ce ba zata iya aurena ba, ba zan zamar mata dole ba kamar yanda ba zan so ayi mata dole ba, ni dai burina ne auren nagartacciyar mace kamar Sa'ida, idan kuma hakan bata Faru ba na san da cewa Allah ne ya rubuta cewar ba zan rayu da ita ba a inuwa guda matsayin ma'aurata, kuma zan karɓi hakan a madadin ƙaddara". Abbaa yay ɗan jim kafin ya sake cewa,"Ka san da cewa ita ba budurwa ba ce bazawara ce ƙaddara ya rabata da mijinta?". "Na san da hakan Abbaa". Abbaa ya ƙara mayar masa da cewa,"Fatan kowanne miji ne ya samu zuri'a tare da matar aurensa, Shekaran Sa'ida goma da aure bata taɓa haihuwa ba Salim". Ya sauke numfashi kana cikin tattausan lafazi irin nasa yace,"Abbaa komai yin Allah ne, Haihuwa da rashinta dukka lamarin ubangiji ne, wataƙila ubangiji ya jinkirta mata lokaci ne wataƙila kuma bata ɗaya daga cikin waɗanda ubangiji ya tsara za su samu rabon hakan, Allah shi ne masani kuma shi yasan daidai na yanda ya tsara rayuwarta, kuma yanda ya tsara mata ɗin shi ne mafi alkhairinta ba don baya sonta cikin bayinsa ba...Abbaa ni Sa'ida na ke so zan kuma zauna da ita a kowanne irin yanayi babu cuta babu tsangwama babu kyara face cikin nuna kalawa da soyayya". Abbaa ya murmusa, tun farkon fara maganarsu da Salim yaji yaron ya burgesa saboda irin lafuzansa da ke fita daga bakinsa a nutse, kalami na me kaifin tunani da sanin yakamata gami da hankali. Abunda ya sani lokacin da zai aurawa Sa'ida Nazifi bai ji zuciyarsa na ƙarfafa masa gwiwar hakan ba, haka bai ji aminci da salamar da yake ji a yanzu ba. "Salim na amince maka ka nemi soyayyar ƴata, ka shiga layin zauwaran da suke neman auranta, idan har tayi amanna da kai ni kuma zan aura maka ita, zan baka amanarta, ina son ƴata ya kamata kan da wannan, ka rubuta hakan a tafin hannunka saboda gaba...sai dai akwai sharaɗi game da auren, idan ka amince faƙat idan baka amince ba to sai dai kayi haƙuri". Salim da kansa ke ƙasa tun ɗazu yana murmushi me kyau saboda samun nasararsa ta amincewar da Abbaa yay masa, furucin Abbaan yasa shi ɗago kai ba tare da alamu na sarewa ko kuma karaya ba, domin kuwa yana da tabbacin zai iya bin kowanne sharaɗi ne muddin zai samu Sa'ida, sai dai sam ya kasa ko da kallon gefen da Abbaa ya ke kamar yanda yay niyya saboda girman kwarjinin da Abbaan yay masa. Abbaa yace,"Ka shirya jin sharaɗin nawa?". "Ehh Abbaa". "Yauwa! Sharaɗin shi ne ƴata tana aikin asibiti, da aikinta ka ganta saboda haka babu batun cewar idan ka aureta zaka dakatar da ita ma'ana zaka hanata zuwa aikinta, sannan tana burin ƙaro karatu anan gaba shima ba zaka hanata ba, bayan haka tana ƴan sana'ointa na hannu, ka yarda da wannan yarjejeniyar ko kuwa ya?". Yay murmushin da sautinsa ya fita a ƙasan ransa, leɓensa kuma ya tale, to taya Abbaa yake tunanin cewa zai dakusarwa da Sa'ida karatunta ko kuma ya dakatar da ita aikinta? Idan da haka why zai shiga ya fita wajen ganin ta kawo wannan matsayin? Abinda yay mata don Allah yayi, kuma alƙawarinsa ne ba zata taɓa sanin hakan daga gare shi ba sai in Safiyya ce tayi katoɓarar faɗa mata duk da itama tayi masa alƙawari har abada ba zata sanar da Sa'ida ba shi ya ɗauki ɗawainiyar karatunta har matakin aikinta ba. Kuma ba ya so kowa ya sani ɗin domin za'a ga kamar yayi ne domin ya mallaketa, kuma itama with that reason zata iya zama with no other option ta tilastawa kanta saboda rama halacci da halacci. "Abbaa na amince na karɓi sharuɗanka, ba zan zama me sauka daga kai ba, illa iyaka ma ni zan zama wanda zai ƙara tallafawa lamuran nata". Abbaa yace,"Shikenan duk san da ka shirya kana iya zuwa ku gana da ita, amma bana so a ɗauki tsawon lokaci ana abu guda". Wannan karan sai da Abbaa ya jiyo sautin sanyayyan murmushinsa na samun nasarar da yay. Yana kallon yacca ya gyara tankwashe ƙafarsa kafin ya shiga cewa,"Na gode sosai Abbaa, na gode da bani dama, kuma da yardar Allah ba zaka yi nadamar aura mini ƴarka ba, nayi maka alƙawarin riƙe amanar da ka bani da dukkan ƙarfin ikona, zan kula da ita bisa gaskiya da aldalci". Abba ya murmusa kafin yace"Ina fatan hakan ta kasance, Allah ya baka ikon tsayawa a tafarkin da yake daidai, Allah yay maka albarka". "Amin ya Allah Abbaa, Allah ya ƙara muku lafiya da tsawon cin kwana". Shiru ya gimla tunanin Abbaa sun gama da shi ko zai tafi ne, amma sai yaga ya gyara zama yana aikin jujjuya yatsunsa, Abbaa dai kallonsa yake tayi da murmushi tare da fatan Sa'ida ta amince. "Za ka wuce ne?". Salim na ƙara yin ƙasa da kai da ƙyar ya iya buɗe baki cikin jin nauyi yace,"Abbaa idan ba damuwa ko zan iya ganinta kafin na wuce?". Abbaa ya yunƙura ya miƙe yana cewa,"Babu matsala ka ɗan jira". Abbaa ya wuce cikin gida, kai tsaye ɗakin Ummani ya shiga, tana zaune ita da Walida tana tsefe mata kai ya same su. Ummani ta bisa da kallo tana faɗin,"To ya ake ciki?". Tayi tambayar da zaƙuwa. "Yana jiranta sai ki mata magana, amma kin san bani son tsayuwan ƙofar gida". Ummani ta saki kan Walida tana cewa,"Ahh ai dama tun da safe nasa ta kimtsa ɗakin Al'amin, ko kuwa su zauna a soron?". Yay ɗan jima kafin yace,"Shikenan su zauna can ɗin". "Ɗakin Al'amin ɗin?". "Ehh". "To bari na faɗa mata ta kimtsa ko". Ta faɗa tana fita a ɗakin shi kuma Abbaa na tsokanar Walida da ƙwaƙwido, ta miƙe tana taɓara ya kama hannunta suka wuce ɗakinsa. Ummani na fitowa ta ƙwala kiran Yasmin wacca ke can wurin Kaka, sai gata da sauri ta fito tana zuwa Ummani ta bata maƙulli tace,"Je ki soro za ki ga baƙo ku gaisa ki buɗe masa ɗakin Al'amin kice an ce ya shiga, idan ba ya nan ki duba shi a ƙofar gida". Yasmin ta karɓa maƙullin ta fita, a soron ta sameshi zaune yana karkaɗa maƙullan hannunsa, ta durƙusa tana gaida shi, bayan sun gaisa ne ta buɗe ɗakin kana ta dawo ta kuma durƙusawa gabansa tace,"Ummani tace ka shiga daga ciki". Yanayin ladabin yarinyar sai ya burge shi, yana mata murmushi yace,"Mene sunanki?". "Sa'adatu amma Yasmin ake ce min". Yace,"Umm nice name, kice ina gaida Ummani idan kin shiga". Ta amsa da to daga bisani shi kuma ya miƙe ya shiga daga cikin ɗakin. Zamansa ba daɗewa Yasmin ta kuma dawowa ɗauke da farantin tangaran da jug da ƙananun kofuna akai sai purewater guda uku. Ina zaune a ɗaki ina saka stones ɗin rigar dana gama ɗinkawa ɗazu, ban san me ya same ni ba tun a ɗazun dai na ke jina a cikin wani irin yanayi da na kasa gane masa. Abunda ban taɓa yi ba tun mutuwar aurena wai na zauna ina tunanin aure ko sha'awarsa, amma tunda na hau kan keke wani banzan tunani ke neman dagula min lissafi. Kuma rabon da inji a raina na tuna da tsohon mijina da irin rayuwar da nayi a gidansa wallahi tallahi har na manta, amma yau ni ce tunanin Nazifi ke zuwar min da jin cewa ina ma na haɗu da shi ya ganni yaga yanda na koma da kuma irin matakin da Allah ya kai ni, kuma har na ke sha'awar ina ma na samu mijin da zai goge min tabon da Nazifi ya bar min shi da ƴan uwansa. Ummani ta shigo ɗakin da sassarfa tana cewa da ni,"Ke tashi yi da sauri ki gyara jikin ki". To na san fita zamu yi dama, saboda haka na miƙe ina gyara fuskata, ina ta kallon Ummani da farin ciki a tare da ita nace,"Wai me ya faru Ummani naga sai murna kike". "Aa to ba ki so kiga ina farin ciki ne?". "Ina ni, ai burina ku kasance cikin farin ciki a ko da yaushe". Na faɗa ina sanya pin a jikin veil ɗin da na yafa na ke kallon Ummani da annurin fuskarta ke ƙaruwa na ce,"To Ummani ai ke ba ki shirya ba". Tana murmushi me faɗi tace"Ai mun fasa waccan fitar, wannan shirin na ki ne ke ɗaya, kin gama?". Nace,"Ehh to amma me yasa kika fasa? Allah yasa ba Abbaa ne ya hana ki ba kinga dai kar a kuma abin kunyar da aka yi aƙi zuwar Hajiya Tabawa gaisuwa". Tasa hannu cikin jakata tana ɗauko turare ta buɗe tana ƙara feshe ni da shi kamar wadda akewa kamun aure tace,"Bar batun can ko gobe ma je insha Allahu, kije ɗakin Al'amin akwai baƙo ku gaisa da shi". Da mamaki ƙarara na ke kallonta na ce,"Gaida baƙo kuma Ummani sai naje a haka, ina lefin hijabi ma". Ta ɓata fuska tana kama hannuna,"To matar liman, yau dai ɗaya mene laifi a ciki, ba ki ga kyan da kika yi a hakan ba ne, duk wanda ya kalle ki sai ya ƙara kallonki yanda kika san balarabiya". Murmushi nayi da har haƙorana dukka suka bayyana. "Allah kin yi kyau da gaske na ke faɗa miki, tsab sai kin daɗa sace zuciya". Sai naji kunya ta kama ni, tare da sabon mamaki wanda na kasa samun haske a inda Ummani ta dosa. Tare muka fito a ɗakin ina aikin ɓata fuska don tunda tace baƙo naji sam ban son zuwa gaisuwar balle kuma a cikin shigar da na ke. Zungurar kai nayi ina faman jan ƙafafu takalmi na sharaf sharaf Ummani ta figo ni,"Wai ke ƙaramar yarinya ce, ya za ki tafi a haka". Na rufe ido na buɗe ina karyar da kai na ce,"Ummani shin baƙon wajen wa ya zo ne?". "Wurin ki ya zo, don haka ki natsu ki yi tafiya a yangance irin ta mace me tsada kamar ki". Na ƙanƙance ido da cewa,"Baƙo ya zo wurina? Kuma Ummani kike ta murna? Ni ai na muka yi da wani zai zo wurina? Gaskiya ba inda zani idan ya gaji ya tafi". Na faɗi hakan da haƙiƙanin bɓacin rai a tare da ni ina nufin juyawa na koma ɗaki. Harara ta wurga min tana cewa,"Idan ke baku yi da shi zai zo ba ai yayi da Abbaanku, na faɗa masa kin ce ba za ki ba ko ƙaƙa?". Jin haka na turo baki gaba ina haɗe gira sama da ƙasa na nufi soro ba don son raina ba, sai dai me! da zuwana soron naji gabana yayi mugu mugun faɗuwar da sai da na kai hannu na dafa bango, haka kawai na tsinci ƙafafuna da yin karkarwa. Da ƙyar na dawo hayyacina daga fitar da nayi daga cikinsa na ɗan lokaci, domin kuwa ƙamshin turaren da ya gauraye dukka soron da kuma tsadaddan takalmin da idona ya sauka akai sai ya nemi ya burkita ni. Na haɗiyi yawu ina cire takalmana a kusa da wanda na ke gani, ƙafafuna suka ɗaga da kansu suka shigar da ni ciki, da yanayina na sanyi nayi sallama da ƴar ƙaramar muryar da zata ɗauki hankali ko ai'na ne, kamar wata sokuwa haka na maƙale a bakin ƙofa kaina a ƙasa na kasa sarrafa kaina saboda yacca na ke jin ido ya manne akaina da kallo. A karo na biyu na ƙara cewa,"Salamu alaikum". Ban sani ba ko an amsa a wannan lokacin domin kuwa kunnena a toshe yake dumm haka na ke ji a cikinsa tun ɗazu. Wucewar bugun zuciyata sau ɗaya, biyu, uku, huɗu naji kamar babu motsin halitta a ɗakin saboda haka na ɗago ido a tsorace, karaf ƙwayar idona ta sauka akansa da yay saurin sadda nasa kan ƙasa kamar ba daga kaina ya sauke kallonsa ba. Zaune yake a gefen katifa, ya miƙe ƙafafunsa da na gansu dogaye, hularsa da ya cire ta yare a gefensa, yana wasa da yatsun hannunsa, kallonsa na ke da son na fahimto wani abu sai ji nayi na mugun tsorata dalilin jin ance,"Ga wani abu nan wajen ƙafarki". Ƙara na ƙwalla, kuma maimakon in yi waje sai na faɗo cikin ɗakin ba tare da sanin yanda aka yi na dira a tsakiyar ɗakin ba, idona rumtse jikina sai kyarma yake, cikin bakina ina faɗin kalmar la'ila ha'illa anta a hankali, saboda tsananin tsoro da furgicin da na shiga har hawaye na sakko min. Na jima a haka na kasa buɗe idanuna, sai naji kamar an rufa min abu akaina wanda hakan yasa ni buɗe idanuna a hankali, sai naga mutum tsaye a gabana, faffaɗan ƙirjinsa yay min rumfar na zama kamar wata ɓeranya a gaban nasa ƴar firit, a hankali kunnuwana ke jiyo min sautin bugun zuciya wanda na tabbatar da haƙikanin ba nawa ba ne nasa ne, sai naji wani dunƙulallan abu ya wuce ta maƙoshina gabana na tsananta faɗuwa sosai, so na ke tayi na ɗaga ƙafata na matsa daga baya amma ina kamar akan tarko na maƙale sam na kasa motsa ƙafata ko guda ɗaya. Cikin wani irin yanayi da na ke jina a cikinsa kasantuwar kusancinmu, na yi saurin ɗauke idona daga kan ƙirjinsa da na ke mamakin faɗinsa ina kai wa saman kamilallar fuskar da ta ƙawatu da kewayayyen saje me haɗe da gemu. Kuma karaf ƙwayar idon mu ta sarƙe ata juna, lokaci guda naji jiri na neman ɗibana ya watsar, nayi saurin dunƙule hannu ina riƙe kaina a tsayen, irin murmushin da ake kira da killer smile ya saki wanda sautinsa yay sanadin girgizawar allon ƙirjina nayi saurin ɗauke ƙwayar idona daga cikin tasa, ban saba da irin wannan kusancin ba sam da wanda ba muharramina ba, don haka kaina na ƙasa ina rawan jiki na shiga ja da baya yayin da ya daɗa kiɗima ni da amon muryarsa da ya fito lokaci ɗaya da cewa,"Am sorry ban tsammaci za ki tsorata da yawa haka ba, nayi hakan ne domin ƙafafun da suka maƙale wuri ɗaya su samu takowa zuwa ciki". Ina micincina idanu na ce,"To baka san ko a addinan ce babu kyau tsorata musulmi ba". "Tuba na ke yi ba zan ƙara ba daga ranar yau, amma ki sani kina da me ba ki kariya kar wani abu ya ƙara tsorata ki". Ni dai ja nake da baya har na zube kan ƴar ƙaramar plastic chair ɗin ɗakin ƙirjina sai faman sama da ƙasa yake yi. So na ke na ɗaga ido na kalla fuskar da na yiwa kallo ɗaya saboda na tabbatar da zargina. Sai kuma ringtone ɗin iphone ya cika ɗakin, wanda da sauri naga ya matsa daga inda yake ya isa katifar ya ɗauka, sai jinsa nayi yana magana cikin wani irin yare kamar jagwalgwalo babu daɗin ji, duk sai naji maganar tana hawar min saman kai har ta kai ga na rufe ido ina gwame fuska. "Ina wuni". Da sauri na buɗe idona ina dawowa cikin duniyar da na bari jin murya a gaf da ni, na kalle shi muka haɗa ido sai na kasa ɗauke kallona a kansa gaba ɗaya kuma na diririce. Zuciyata ta amsa da sunansa,"Salim!". Mutumin da na sani shekaru goma sha da suka wuce, mutumin da watannin baya da suka wuce naga hotonsa a album ɗin bikin Safiyya. Naja numfashi inda na haɗe da ƙamshinsa da ke tsumani na zuƙe, sannu a hankali ƙamshin turarensa ya ɗebe ni ya kaini tunanin germany, sauka a airport, cikin napep. Ba tare da sani ba kawai na tsinci bakina da furta,"Kai ne?". Sai naga ya ɗaga gira dukka biyu yana kallona kawai, kafin yace,"Ai na?". Na tsuke gira ina tuna komai daki daki na ce,"A airpot ranar da na dawo, da kuma ranar ma a adaidaita". Sai ya lumshe ido yana girgiza min kai alamun a'a. Na ɗan duki ƙafa a ƙasa na ce,"A'a wannan ƙamshin ne". Ba zan ce ga da irin muryar da nayi magana ba don ba zan iya tantancewa ba, amma sai naji ya kwaikwayi muryan da cewa,"Ba wannan ba ne, irin wannan ɗin ne". Kawai sai kunya ta kama ni na kai hannu ina rufe fuska, har ga Allah nema na ke na kasa controlling kaina ba don komai ba sai saboda ƙamshinsa da shi kansa da cikar haibarsa tayi gama gama da ɗakin musamman da yake zaune a gabana. Dariya naji yayi ƴar ƙarama yana maimaita gaisuwar da yayi. Sai na ɗan saci kallonsa, ni ya kamata ace na gaida shi ai to amma ta ya zan samu sakewar hakan mutum babba na zaune a gabana kamar yarona? "Ba za ki amsa ba?". Sai na samu kaina da cewa,"Ai kana zaune a gabana kuma ni ya kamata na gaishe ka". "Ni dai a amsa mini domin kuwa cancantar Sarauniya ne da isarta a duƙa a gabanta a gaida ita, musamman ga mutumin da ya zo da ƙoƙon bara". Tsintar kalamin nasa nayi har ɓargo da jijiyoyin jikina, kuma kafin na ankare sai gani nayi ya haɗe hannayensa alaman roƙo gami da ɗan karayar da kai yana cewa,"Please a amsa min, domin a ƙage na ke da na miƙo ƙoƙon barana bani a karo na biyu". Baki na buɗe ganin yacca yay da fuska kaman ƙaramin yaron da ke shagwaɓar ayi masa abinda yake so. Sai ya miƙo hannunsa yay kamar zai zura yatsa cikin sakakkun laɓɓana nayi saurin kauda fuska gefe cike da kunyar da ta kama ni, domin kuwa surar fuskarsa ce ta ɗauki a hankali, kallon da ban samu damar yi masa a wancan lokacin ba, dama wannan kyan ne Safiyya take ta faɗa min? Amma kuwa idan haka ne Allah ya saka masa domin me hoto ma ya rage masa kyau sosai da sosai. Yunƙurawa nayi zan tashi yay saurin dakatar da ni,"Please koma ki zauna". Ya faɗi hakan yana gyara zaman tanƙwashe ƙafafunsa tare da mayar da yanayinsa na masu magana da gasken gaske. Sai na ce,"To don Allah ka tashi a gabana". Wani kallo yay min yana sosa gira sannan yace,"Ni fa ki ƙyale ni a yanda kika ganni, ki zauna kawai muyi magananmu, ba dafa ki zanyi na cinye ba, in ma zan yi hakan tukunna dai. Muhimmiyar magana ce ta sani na ke zaune haka a gabanki saboda haka koma ki zauna, idan kuma salon zaman ne bai ba sai na gyara". Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa ya dire gwiwoyi a ƙasa. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina cewa,"A'a du Allah". Komawa nayi na zauna kamar me koyon zaman, shi kuma ya shafo fuska yana girgiza kai kafin yace,"Zan iya sake gabatar da kaina?". Kai kawai na kaɗa masa alaman ehh. Da yanayin barkwanci yace,"Awwa Allah sa dai kar ki ce wannan ya fiya naci kamar in mammake shi". Furucin ya ban dariya na ɗan dara kafin kuma na haɗe rai. Kuma sai ji nayi yace,"Ki gama haɗe haɗen ranki indai za ki buɗen ƙofa shikenan. Anyway kamar yanda na faɗa miki a baya ne My name is Salim Sadiq Oluwa, ni ɗan ƙabilar igbo ne.....". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR07FT5* Ina kallonsa ya miƙe tare da jan kujera baya ya bar wajen, haka na bi bayansa da ido kamar me shirin tashi ta bisa, har ya ɓacewa ganina ban ɗauke ido ba, sai daga baya na kulle idanuna ina kifa kai saman dining table ɗin, wannan ne irin son da yake faɗi? a haka zan yi auren ana min famin ciwo? A hakan ake cewa za'a mantar da ni baya? A haka za'a cika alƙawarin? Ji nayi na ƙoshi da abincin da na ke ta marmarin ci, me yasa ma zan damu da shareni ɗin da yay? Bayan hakan ban san me ya tsaya min a zuciya ba har na ke jin ƙunci da ɓacin rai. Tashi nayi na bar wajen, toilet na shiga na wanko fuskata nayo alwala jin ana yin kirayen sallar la'asar, ina idarwa na ɗebi kayana na bar gidan ba tare da na yiwa Safiyya sallama ba tana can sama, ni ba zan wani tsaya sauraronta ba balle ta ƙara ɓata min rai, haushinta ma na ke ji. A mota ina ta ganin kiranta na ƙi ɗagawa, nayi jugum kamar wata mara lafiya haka na koma, tsabar nayi nisa a tunani ma me adaidaitar na tambayana canji ne a hannuna amma ina ban san yana yi ba har sai da matar da ta sauka ta taɓo ni, nayi firgigit na buɗe jaka na miƙa masa, su biyun suka ce min ya kamata na rage tunani kar hakan ya zamar min illa, kai kawai na kaɗa musu, to ni ban san ma tunanin me na ke yi ba, na dai san kawai na bar hayyacina ne, amma na rasa dalilin da yasa Salim ya tsaya min a rai, akan me zai wulaƙanta ni? Kuma da ya ɗakko bindiga ya aje mene nufinsa? Barazana zai yi min ko kuwa shima zai min tuhumar da bani da laifi akai? Ba zan so shi ba tabbas, kuma ba zan taɓa auransa ba ko za'a tashi duniya, mene tunaninsa zan kuma bari wani ɗa namiji ya wulakanta ni ne? To shi ya san wani soja ni ban sansa ba, sai kawai na rumtse ido sosai ina jin kamar na buga kaina jikin ƙarfen motar ko na samu hotonsa ya bar haska min a cikin ido. Ba don me napep ɗin ɗan mutunci ba ne tsaf zai iya fusata yay gaba da ni, ko yanzu sai da yasa aka taɓo ni kafin na ɗago na basa amsar,"Cikin layi zamu shiga". A ƙofar gida na samu Yashaik zaune suna hira shi da su Anas ɗan wajen Baba Tijjani, na durƙusa na gaida su na wuce ciki. Hayaniya ce ta fara min maraba a tsakar gida, idona ya kai ƙofar ɗakin Ummani, naga dandazon takalma kamar ana biki, yau su Ummani ansha baƙi kenan, daɗin da naji ba kowa a tsakar gidan sai ƴan yara da ke wasan su can wajen barandar shiga ɓangaren Baba Saminu, ba na jin zan iya shiga in ta faman gaisuwa ana faman yi min tambaya kawai na tsallake na shige ɗakina. Jaka kawai na rataye amma ko kayan jikina ban cire ba na kwanta, ba wai don bacci ba sai don samun sassaucin abinda na ke ji yana taso min a ƙasan zuciya, a haka kuma har bacci ɓarawo ya sace ni sai can cikin bacci naji ana tashina, na farka a firgice gabana na mugun faɗuwa sai ambaton innalillahi na ke yi, dama illar baccin yamma kenan shiyasa duk abinda aka ce maka babu kyau a musulunce to kawai ka haƙura da shi. Jikina har wani rawa yake yi Maman Khairi ta ruƙoni tana,"Ke lafiya?". Na buɗe ido na kalleta ina haɗiye yawu me wahala na ce,"Maman Khairi na tsorata ne". "Kema ai kin san baccin yamma babu kyau, wallahi da irin baccin yammar nan wata mata bata farka da idanu a buɗe ba sanadiyar makancewarta kenan, baccin yamma har hauka yana sawa, sai kita innalillahi da la'ila ha illa anta". Miƙewa nayi na fita nayo alwala, duk na ruɗe ma ban san magribar bata ƙarasa ba, sai bayan na yo na dawo zan tayar da sallah take ce min,"To ai ba'ai ko kira ba". Na sauke gwauron numfashi kana na zauna muka shiga gaisawa da ita, sai naji tana wata magana ta daban da ban san ina ta nufa ba. "Ai bamu san kin dawo ba ke muke jira tun ɗazu da tuni mun wuce, to Allah ya sanya albarka ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma sa rabo ne duniya da lahira". Ta faɗa da murmushinta gami da nuna murna zuwa gare ni, baki na saki ina bin ta da kallo har ta miƙe tana gyara goyon Sufwan, tayi ƙofa zata fita tana ƙara cewa,"To matar soja mu mun tafi, wai sai yaushe za ki ɗinka min kayan Maama ne, ku fa telolin gida tsiyarku kenan". Ɗan guntun murmushi nayi na ce,"Kai Maman Khairi zan bawa Babanta ya kawo mata dai in huta da mita". Da haka ta fice, nima na miƙe na fita da mutuwar jiki raina duk a dagule, na shiga ɗakin Ummani ganina duk suka zubo min idanu, ashema ba wasu baƙi ba ne kamar yanda na zata, ƴan uwan Ummani ne yayyanta da ƙannenta, sai su Maman Yasmin ita Maman Khairi ta tafi, sai kuma wata ƙanwar su Abbaa da suke uba ɗaya Mama A'i ita yaushe rabona ma da ita. Hajjo da ke gefen Ummani tace,"A'a likita likita an dawo". Na shiga daga ciki ina duƙawa na gaida su, duk suka amsa min suna tambayana ya wurin aiki. Na yiwa Ummani sannu da gida ina ƙoƙarin miƙewa sai naji suma suna bina da kalmar Allah tabbatar da alkhairi, kaina ya ɗaure musamman da naji Mama A'i na faɗin,"Kun ga yanzu sai na tsokani duk wanda na ga dama a najeriya tunda dai muna da soja a hannu". Umman Batula tace,"Ai kuwa dai mijin ƴarki guda soja, ai ki taɓa dukka wanda kika ga dama da hujja". Suka yi maganan cikin raha ana dariya. Umman Batula ta ƙara cewa,"Yanzu ya kama watan gobe kenan?". Sai Ummani tace,"Ehh to su da ƙarshen watan nan suka zo, kinga ya kama sati uku, amma dai sun tsaya akan cewar zai yi musu magana daga nan zuwa gobe, yace ai ba gaggawa ake ba". Na rufe baki na buɗe yafi ƙarfin sau goma, yanda na ke kallon mahaifiyar tawa kuwa tamkar ban taɓa ganinta ba a duniya, me kalamanta suke nufi kenan? Sai kawai naga ta miƙe tana faɗin,"Kin ci abinci?". Na girgiza mata kai ina bin bayanta wajen ficewa a ɗakin, yanda na ke tafiya kamar wadda tayi kashin wando ko wadda ba laka a jikinta. A kitchen na sameta ita dai na kasa gane yanayinta amma da bayyanuwar farin ciki a tare da ita. "Ko ba ki da lafiya ne?". Maganarta ta dawo da ni daga gajeran tunanin da na tafi, kamar dai na gama fahimtar komai to amma ba hakan ba ne dole ina buƙatar ƙarin bayani, na kaɗa kai ina cewa,"Lafiyata ƙalau, tun ɗazu ma fa na dawo bacci nayi". "Kuma ki dawo ba ki leƙa kin ce min kin dawo ba, ko da wata matsalar ne?". Na sake girgiza mata kai alamun a'a amma a haƙikanin gaskiya tambaya ce fal a bakina. Ta miƙo min kwanon abincin tana cewa,"To ungo idan kuma ba za ki ci shinkafar ba akwai sauran gurasa da Umman Batula ta kawo gata can ɗaki ki ɗakko ki kwaɗanta ko ki ci da miya". Na ɗan kalleta na ce,"Gurasar zan ci, amma Ummani to naji kuna yin wata magana ne". Tayi min wani duba kafin tace,"Maganar me?". Sai nayi ƙasa da kai ina wasa da yatsu na ce,"Kaman maganar aure kuke yi". Ta ce,"Ehhh mana, da safe bayan tafiyarki Alhaji Babangida suka kawo kuɗin aure da sa rana, amma dai zai neme ki ai ki jira ya dawo kiji daga bakinsa". Sai naji maganartata tamkar saukar aradu, na ɗago ido wanda tuni ya cika da ruwan hawaye na kalleta na ce,"Ummani kawai sai ya kawo kuɗin aure bai ji ta bakina ba, Ummani tun fa ranar da ya zo bai ƙara nemana ba, kuma ni ban ce masa na amince ba, har yau ban ba shi amsa ba, bafa sona ma yake yi da gaske ba Ummani, ta ya Abbaa zai yarda ya karɓi kuɗinsa". "Yo shi Abbaanki da yaji ba ki tunkare shi da maganar ba ai zatonsa kunya kike ji, shi yasa ya ɗauki shirunki a matsayin ehh, idan ya dawo kya masa bayani ba zai ji daga bakina ba". Tana gama faɗin hakan ta wuce ta barni nan tsaye, hannu nasa na goge hawayena, wacca gurasa kuma zan iya ci bayan mugun soja na neman sakani a tsaka me wuya, Haka ake aure dama babu soyayya? Haka ake aure babu fahimtar juna da amincewar juna? Haka ake aure da nuna isa da gadara? Me ya taka kuma me yake shirin aikatawa? Ɗaki na wuce jiyo wayata na ringing, Hassana Tijjani ce yaushe rabona da ita, kamar ba zan ɗaga ba saboda kar taji yanayin muryata ta kama tambayata menene, sai daga baya kawai na ɗaga ɗin dai, bayan na amsa sallamarta sai ta kama ƙorafin amana bata ce haka ba, bata yi tunanin bare na ɗauketa ba, yanzu zan yi aure shi ne ban faɗa mata ba, to taga invitation a status ɗin Safiyya kuma ta gode, ba zata ɓoye min ba zancen gaskiya bata ji daɗi ba. Ba ta jira cewata ba kawai ta kashe wayarta, ni kuwa ina zan iya bin bayanta in bata haƙuri alhalin ni kaina ba cikin jin daɗin na ke ba, bata san nima rashin kyautawa aka min ba, sai kace wata ƙaramar yarinya za'a nemi ayi min auren dole. Tunawa da Safiyya raina ya ƙara tugunzuma na ɗauka wayar na danna mata kira, tana ɗagawa ban jira cewarta ba cikin masifa na ce mata. "Yanzu abinda ku ka yi min ke da Yayan na ki kun kyauta kenan? Ke tsabar zaƙewa ma har da su zuwa kina faɗawa duniya, yaushe nace masa na amince zan aure shi da har ya iya rawan jikin kawo kuɗin aure? to ni ba zan aure shi ba ki faɗa masa, ba zan auri wanda bai da kulawa ba, idan ma ya aure ni to ya tabbata gangar jikina zai aura ba zai samu soyayya daga gare ni ba kamar yanda nima ba zan yarda da soyayyar dole ba, kuma ina faɗa miki tsakani da Allah banji daɗin abinda kika min ba kuma ba ki kyauta min ba, wannan ai shiga rayuwata ne". Kawai kuma sai na fashe da kuka ina ce mata,"Ni fa ban ce masa ina sonsa ba Safiyya, har yau ban yanke decision ba, ni ban san me na ke ji game da shi ba, idan ina sonsa ma ba ke za ki fara sani ba, Safiyya tunanina matarsa taya zata yarda ta zauna da kishiya? Kishiyar ma bahaushiya, bayan naji ana cewa matan Ƙabila mugwaye ne, tarwatsa aure suke yi basa yarda su zauna da kishiya, kuma babu abunda suka iya sai mugun asiri da makirci, a hakan to kike so na aure shi? Ke da kike sona ya kike neman jefa mi cikin rana, me zan yi da auren ƙabila fisabilillahi, kuma ƙabilan ma me mata, Shikenan sai na ƙare a aure ina fitowa ina faman yawon zawarci". Ina yin shiru tace,"Madallah Na gode Sa'ida, na gode sosai da ci min fuska, ba laifinki ba ne laifina ne da na nace miki, kuma na ɗauke ki ƴar uwa har na ke so ki shigo cikinmu, to Alhamdulillahi duk da muke ƙabilar mu tamu zuciyar a wanke take fesss, ba ma nufar kowa da sharri balle mugunta sai alkhairi, kuma ita kanta Anty Kudrat ɗin da kike ma mummunan zato kin ɗauka hakkinta wallahi, kuma kar ki damu Brother Salim ne bai da matsala zan sanar masa da duk abinda kika faɗa, muma ai da zuciya a ƙirjinmu inda ake son mu nan muke zuwa, saduwar alkhairi...". Ƙit ta kashe wayanta, ni gaba ɗaya ma ban san nayi wancan katoɓaran zancen ba sai yanzu, na yi ta bin bayan kiranta taƙi ɗagawa. Haka dai na samu na tura mata saƙon ban haƙuri da shaida mata ba yanda ta zata ba na ke nufi. Maman Yasmin ta shigo ta sameni tana ce min za su tafi, yanayina yasa ta zauna tana tambayana meke faruwa, ni da ya kamata a ganni farin ciki kuma sai a ganni a akasin hakan. Ganin idan nayi shiru zan cuci kaina nace mata,"Maman Yasmin ni fa bana da buƙatar na sake yin aure, nafi so inyi zamana a haka, zaman gidan iyayena yafi min daɗi da kwanciyar hankali, in je aikina na dawo nayi sana'ata na fi farin ciki da hakan". Sai ta numfasa tana dafa kafaɗana da cewa,"Sa'ida ya kamata ace kin mance baya kin fuskanci gaba, ke ba ki ga sauyin da Allah yay miki ba ne? Kin taɓa tsammanin za ki taka wannan matakin ne? Ba fa iyayenki da na ki ba kawai hatta wasu mora suke daga jikinki, to ko wannan ba ya isa ki kyautatawa sabuwar rayuwar auren da za kiyi zato me kyau ba, kuma ki kalla fa wanda Allah ya aiko miki, wallahi Abbaan Yasmin ce yay da Abbaa ya tura su bincike kar kiji yabo da kyakykyawan shaidar da ake yi masa". Sai tayi shiru kafin ta sake cewa,"Kuma fa bacin haka kefa macece me lafiya, ina za ki iya riƙe kanki? Dole kina da buƙatar abokin rayuwa, wallahi wallahi zaman aure shi yakamace ki shine mutuncinki da ƙimarki da darajarki". Na goge hawaye na ce,"Na sani Maman Yasmin to amma ni ina gudun matsalolin rayuwar ne, kar lamura su zo su taɓarɓare min kamar wancan, kinga har faɗa masa nayi ina da matsalar rashin haihuwa amma bai ɗauki zancen nawa da muhimmanci ba". "Kinga yanzu dai magana duka ta ƙare, ba ki ɓoye masa komai ba kin sanar da shi kin fita hakkinsa, kuma magana ma har ta kai ga an saka rana, don haka kawai ki durfafi adu'a ki faɗawa Allah". Haka dai tayi ta ban shawara tare da kwantar min da hankali sannan daga bisani ta tashi suka tafi don Yashaik nata aikowa akan ta zo ta ba shi maƙulli idan anan zata kwana. Bayan fitarta naji ƙwala kiran Abbaa, na miƙe da azama na sanya hijabina na fita zuwa ɗakinsa, na sameshi ya gama cin abinci suna zaune suna magana shi da Ummani, daga gefe da su na zauna nayi masa sannu da zuwa, ya amsa yana kai hannu ya rage volume ɗin rediyon da yake ji. Ƙirjina sai bugawa yake yi kamar wadda ke jiran zartar da hukuncin laifin da ta aikata. Abbaa ya kalle ni yana cewa,"Kun yi magana da Babarki?". Na ce,"Tace min dai sai ka dawo". Ya jinjina kai kafin ya ce,"Ɗazu iyayen yaron can da ke neman aurenki sun zo, sun kawo kuɗin aurenki da na kayan sa rana da kuma kuɗin lefe wanda haka suke yi a al'adarsu, sun bada miliyan ɗaya da rabi na kuɗin kayan lefe, dubu ɗari biyar kuma kuɗin kayan sa rana da kuɗin aure, gaba ɗaya dai miliyan biyu suka bayar, to na so ma su rage don ba yanda ban yi da su ba suka ce a'a hakan za su bayar, to ga kuɗi nan dai na karɓa, sun kuma yi batun wata guda nace musu a'a muna buƙatar lokaci duba da yanayinmu, to kuma ɗazu Kakanku sai yace wata guda ɗin yayi, nama kira su na sanar musu". Duk sai naji jikina yay sanyi, da gaske Aure zan ƙara yi bayan alwashin da na sha na ni da aure har mutuwa, yanda na ke jina kamar dai ba ni ba, A hankali ruwan hawaye na kawowa idona nace,"Tom Abbaa Allah ya kaimu". "Kun yi magana da shi Salim ɗin?". Ina girgiza kai nace,"A'a". "To yanda ku ka yi sai ki faɗa min amma kar ya wuce zuwa gobe, ga kuɗinki nan zan bawa mahaifiyarki amana bana so a ci musu ko ƙwandala, yanda suka bayar da sunan abinda suka ce haka na ke so ayi amfani da shi, Allah ba zai hana yanda za'ai ayi miki sauran buƙatu ba, sai kuje wajen Saleh kafinta ki duba kayan ɗakin da kike so". Nace,"Tom Abbaa". Da haka na miƙe nayi musu sai da safe na wuce ɗaki. Ni dai tun bayan dawowana daga wurin Abbaa kuka na ke yi sosai tamkar wadda aka yiwa mutuwa ko wani abun alhini ya sameta, har Ummani ta shigo ta kore min sauro ta ɗauka abu a firij ta fita ban ɗago ba haka ina ji taja ƙofa ta rufe tana faɗin,"Idan kin gama aikin wahalar sai ki tashi ki saka sakata, ba kya son nasa kika ja baki kika yi shiru saboda gulma, yanzu da kika je ai da sai ki faɗa masa, kina neman ƙaryata kanki akan gaskiya, ni dai Allah ya bamu alkhairi". Ai kamar ta tunzura ni fa sai kuka, ni fa bana son Salim, kuma bana ganin laifina don naƙi aure, haka kowa ma kar yaga laifina, auren nan na yi banji daɗi ba, na shekara goma har da ƴan kai amma jin daɗi da farin cikin da na tsinta a cikinsa ba za su wuce ƙirgen yatsu ba, nayi bautan aure gwargwadon iko, na kasance irin macen da ake kwaɗayi da fatan samu a gidan aure, amma sai zaman auren nawa ya kasance da wulaƙanci da tozarci, to tsakani da Allah ta ya zan sake sha'awar komawa duniyarsa? Wallah ko da naji cewar ina so ko saboda mahaifiyata da naga ta damu, idan na tuna batun haihuwa duk sai in ji inaaa ta ina zan soma? Ba zan iya ba, wahalar da na sha a baya ma ta isa, ina ni ina kuma auren me kuɗi su ci mutuncina shi da danginsa, balle ma me mata har da ƴaƴa. Ban gaji da kuka ba har ƙarfe daya, in kukan in saƙe saƙe da babu warwara, a lokacin ne kuma na miƙe na fita na yo alwala na dawo na kulle ɗakin, tun a wancan ranar sai a yau Allah ya nufa zan yi sallar istikara, bayan na idar na jima hannuna sama ina hawaye ina roƙon Allah akan ya shiga lamarin auren nan, idan alkhairi ne ya tabbatar idan babu alkhairi ya kawo sassauƙar hanyar da za'a fasa shi ba tare da anyi nisa ba. Haka na raya daren da sallah da karatun ƙur'ani tare da tarin adu'oi, bayan nayi sallar asuba ne kuma bacci me daɗi ya zo min, Allah ya so ba morning duty gare ni ba evening ne da ban san ya zanyi da tarin baccin da na ɗauka ba. Cikin bacci naji ƙarar wayata, a firgice na buɗe ido ina saurin miƙewa zaune tare da kai hannu na rarumota. Na maida kai na kwanta a sa'ilin da kiran ke yankewa, kuma ina lumshe ido da zummar komawa kiran ya daɗa shigowa nayi azamar ɗauka na kai kunne. Da kasalalliyar muryana na masu bacci na sauke numfashi tare da yin sallama. Daga can ɓangaren ma naji an sauke numfashi kafin a amsa sallamar. "Na katse miki bacci, bari na ƙyale ki idan kin tashi ki kira ni". Kamar a mafarki haka naji muryan nasa cikin turancinsa me daɗi, kuma tuni na buɗe ido ina saurin dakatar da shi da cewa,"Ai na tashi ma, kai ne?". "A'a Sa'ida ne". Murmushi ya suɓuce min me sauti, haka kawai sai naji kamar daɗi na ratsa ni. Ina miƙa nace,"Ina kwana". "Ba zan amsa ba". "Saboda me?" "Ba ki san kin yi laifi ba kenan?". "Ni ban yi laifi ba, wa nayi wa?". "No shikenan ai, ban bin baya ni gaba na ke tunkara". Kawai sai na tsinci bakina da faɗin,"Kayi haƙuri". Yay shiru na sake cewa,"Kayi haƙuri don Allah". Sai yace,"Ya isa haka, zan zo gida anjima". Zuciyata naji ta motsa, sai nayi shiru bance komai ba. "Ba kiji ba ne". "Zan fita aiki ne by 3". "Tom shikenan ki shirya sai na zo na kai ki". "Kaii ai Abbaa ba zai bari ba". "Zai bari, zan faɗa masa". Na ƙarasa buɗe idanu babu shiri nace,"Kace masa me?". "Zan kai matata wurin aiki". Murmushi kawai nayi ban ce komai ba. Ya sake cewa,"Kin yi break fast?". "A'a yanzun ai ka tashe ni". "Har eleven kina bacci, kin kwana kina kuka ko?". Sai nayi ƙasa da murya da shagwaɓewa nace,"To ai kai ne baka yi shawara da ni ba". "Ai nayi shawara da zuciyarki shiyasa". Ya sauke numfashi kana ya ƙara cewa,"Ki tashi ki ci abinci haka, bana son zama da yunwa". Da haka muka yi sallama, ji nayi ina ma bai kashe wayan ba, sai dai yanda na jisa ɗin kaman da damuwa a tare da shi. Har zan koma baccin sai na tuna maganarsa, haka na miƙe ba yanda na iya na buɗe ƙofa, brush da macline na ɗauka na fita, haka na shiga banɗaki sai aikin murmushi na ke yi ni ɗaya ko me yasa oho, ina dai neman zama kamar wata zararra. Sanda na shiga ɗakin Ummani ne na ga da gaske ashe ƙarfe sha ɗaya, nayi mamaki sosai yauhe rabona da bacci irin haka, na kama yiwa Ummani ƙorafin rashin tashina tace,"Kaman zan karya ƙofan haka na dinƙa bugu, kina can sheme kamar sumamma ba ki san me ake ba". Nayi dariya ina cewa,"Yo ina na sani ma ni, wallahi banji ba ko kaɗan. Yanzu yau haka Abbaa ya fita ban gaida shi ba". Tace,"Yo shi ai tsoroma kika ba shi, sai da ya leƙa ta taga yaga kin jiya kwanciya hankalinsa ya kwanta". "Allah sarki Abbaana, bara na kira shi a waya". Na faɗa ina fita a ɗakin, wayata na ɗakko sai da na shiga kitchen na ɗauko abin kari kunu da awara tukunna na dawo na samu Ummani. Ina shan kunun ina jin idon Ummani akaina wanda na san tana kallona saboda nishaɗin da ta ganni a ciki, ni kaina na rasa dalilin murmushina da kasa ɓoye shi. "Ɗazu na ke gayawa Abbaanki kan zancen ba ki son auren nan, yace zai kira iyayen yaran ya faɗa musu zu so su karɓi kuɗinsu...". Ai bata ƙarasa na tsinci kaina da saurin bakin ce mata. "Ummani nayi istikara jiya". "Au tuntuni ke da ba ki nemi zaɓin Allahn ba". Kaina ƙasa na ce,"Ni dai yau ɗin naji zuciyata ta samu natsuwa da lamarin, kuma ma har naji kamar ina sonsa, ɗazu ya kira waya yace anjima zai zo ya kai ni wurin aiki, nace masa Abbaa ba zai bari ba yace zai faɗawa Abbaan, kuma Ummani sai ya iya faɗa masa ɗin ko?". Na ƙarashe zancen ina ɗagowa na dubeta, murmushi naga tana yi wanda yasa naji kunya. Bata ce min komai ba sai na sunkwi da kai ƙasa ina bata labarin ma yanda na yiwa Safiyya jiya, sai ta bani wayarta tace na kirata da ita ai ba zata ƙi ɗaga tata ba, ina ƙoƙarin kiran wayata tayi ƙara, ban san lambar don sai da na jinkirta kafin na ɗaga, ina ɗagawan naji muryansa na cewa,"Kin ci abincin?". Kasancewar Ummani a wurin sai na kasa yin magana, na yunƙura zan tashi tace,"Yi zamanki". A hankali nace masa,"Ina ci ne yanzu". Sai ya marairaice da cewan,"Ki aje min nawa idan na zo za ki bani da hannunki". Sai ya sake cewa,"Na faɗawa Abbaa yace babu matsala, amma ni da ke duk muji tsoron Allah, idan su basa ganinmu Allah na ganinmu". Nayi shiru ya katse ni. "Baby yanzu ni da ke sai mu iya aikata wani abun mara kyau? Me ma muka sani to? Ko ke kin sani?". Na cije harshe ina cewa,"Sai ka zo ɗin dai". Na faɗa ina saurin kashe wayar. [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR09FT5* Maman Khairi da Maman Yasmin haka suka miƙe tsaye wajen gyara ni ciki da waje, kayan mata kamar hauka Maman Yasmin tasa na tura uban kuɗi aka yo aike tun daga niger, ga Safiyya ma da nata tasa aka kawo min daga sokoto, sam ba'a son raina na ke amfani da magungunan ba, haka na ke shansu a dole wani da daɗi wani ba daɗi, wani ma sai na kusa amai ma na ke iya sha, haka zan ta yiwa Safiyya ƙorafi Maman Yasmin ma na yita mata nurƙufanci, don ni a nawa ganin wannan abubuwan duk ba su da amfani duba da irin rayuwan da nayi a baya, amfanin da na dinƙi yi da su a banza. Safiyya ce ma me cewa ai yanzu zan san amfaninsu tunda sai yanzu ne zan yi auren, in daina lissafin wancan buhun a sahun maza, in bari in zan maganar ƴan iska mahaukata sai na ke sako shi a ciki, amma na bar tuna na taɓa aure a baya tunda dai ban haifa na baro ba. Da Safiyya muke ta shige da ficen abubuwan da na ke siya ta ɓangarena, itama haka ta tura min 100k ta account a matsayin gudunmawa, naji daɗi sosai da kuɗin na bawa Yaya Imam nace ya siyo buhun shinkafa da fulawa sai ya bawa Abbaa. Shima yay ta min godiya har da ƙwallata don ce masa nayi sirri ne tsakanina da shi. Na siya shadda nayi mana anko iri ɗaya ni da Ummani da Abbaa, sannan na siya wani kalan daban na ɗinkawa yayyuna da matansu da ƴanƴansu har da budurwan Yaya Al'amin ma, shigar da na ke so muyi ranar ɗaurin aure kenan, Uwata kuwa kayanta sunan sai ana gobe ɗaurin aure zan ɗakko in bata, don so na ke farin cikin saman fuskarta ya ninku sau dubun dubata, danƙararen less ne na siya mata guda biyu mai shegen tsada kuma nasa aka yi mata ɗinki na zamani, atamfofi biyu kowanne da shigar takalmi da mayafinsa, Abbaa nah ba da kala ɗaya na barsa ba bayan shaddar ɗaurin aure har da set biyu na yi masa na boyel. Salim ya tura min dubu hamsin na kuɗin gyaran jiki da lalle da kitso, ranar kuwa Safiyya ta dinƙa masifa wai yaushe Brother ya koyi tsumulmula basu sani ba, zata kira shi na hanata sai ta kira Ummansu ta faɗa mata, Umman nasu ma ta kama faɗa wai ko bai da shi ai ba ya bani 50k a matsayin kuɗin gyaran jiki ba balle kuma yana da shi, itama tace zata kira shi taci mutuncinsa nayi ta roƙonta da ƙyar ta haƙura ta ƙyale, ko kusa bana sawa Salim ido musamman akan kuɗinsa, ni yanda yake nuna min bai da wani kuɗi, ko hira muke yi zai ce in koyi haƙurin zama da shi a yanda yake, shi ba mai kuɗi ba ne amma insha Allahu zai yi ƙoƙarin ganin ban nemi wani abu daga gare shi na rasa ba, ba zan yi kukan babu ba in Allah ya yarda, saɓanin yacca na san labarin kuɗinsa a wurin Safiyya, to nima dai a haka na ke binsa dama ni abun hannun namiji ba damuna yay ba, har ce yay min motan da yake zuwa da shi ma na ogansa ne, wannan dai na jisa ne kawai ban wani yarda ba, kawai dai na san kyauta a soyayya da daɗi musamman ma a wurin wanda zaka aura, to ni zan iya cewa bai taɓa kawo min wani abu da sunan kyauta ba, kuma ko da na faɗawa Ummani ma ce tayi kar in sa hakan a raina, ƙila tsarinsa ne a haka sai na shiga cikin gidansa tukunna zai buɗe min aljihunsa, kuma gwara ma hakan akan ya buɗa min a waje sai na shiga daga ciki kuma ya matse kayansa, idan kuwa na nuna masa ban damu ba babu ƙorafi babu tambaye tambamye balle sa ido sai nafi kima a idonsa, shi kansa sai yafi jin daɗin yi min, balle ma mene na damun kai tunda ina aikina ina samu sosai kuma ga kasuwancin da na ke na kawo min kuɗi. Yau dai ƴan uwa sun ƙara cika gidanmu, Hajiya Ummani an kasa zaune an kasa tsaye, ayi can ayi nan, gidan ya kacame da hayaniya, ni da ban son hayaniya duk sai kaina ya ɗauka yay nauyi, na ƙagu ma ayi a gama taron a watse, du da ina ta faman mita akan me ma za'a tsaya yin wani taro aure ba auren budurwa ba, Maman Yasmin ta danno min zagi tace in ci gaba da maida kaina baya hakan yana da kyau ai. Yau tun asuba da na tashi kasa komawa bacci nayi, Maman Khairi ma da ta ganni da duku dukun Safiya a gidan Maman Yasmin sai ta kama tsokanata wai ta lura na zaƙu dai a ɗaura auren nan, yau ni ce babu baccin asuba. Nayi dariya kawai na shige ciki ni bata san me nake wa ba, ai kuwa na sha tsiya a wurin su Adama da duk mutanenmu dai na ƙauye da suke kwana gidan Maman Yasmin, ni da naje na ƙarasa haɗa kayayyakina takurawarsu ta hana ni sai baro gidan nayi na dawo gidanmu. Ɗakin Kaka na shiga inda anan aka ajiye akwatunan lefena da aka haɗa guda sha biyu, ɗauke da kaya masu tsada da kaya na alfarma, da aka kawo su ni dai sai dana tofe abuna da adu'oi saboda baki, kaya kamar ɗiyan wata ƙusar, ko shi da na ɗauka hoto na tura masa sai da yace mun fitar da shi kunya, da shi aka ce ya haɗa ba zai haɗa masu kyan haka ba, har da ce min yanzu da su Granny ba su yi karo karo an haɗa masa ya kawo wannan kuɗin ba ya zai yi? Ni kuwa na ce ummm shine yay ƙwafa wai in koka da ranar haɗuwarmu. Akwatun da ke ɗauke da abayoyi na buɗa na ɗauko guda ɗaya, pink colour tasha ado, na ɗakko agogo da yari ma har da sabon takalmi. Umman Batula ta ƙwala min kira na fita da sauri ina ɓoye kayana cikin hijabina kar a gani a ishe ni da mita, ni kuwa yau ban ga me hanani cakarewa da kwalliya ba. "Kije ga ruwan can na kai miki banɗaki, akwai wani daban cikin koriyar robar nan ki zauna a ciki sai ya huce sai ki fito". To kawai nace mata na wuce ina ƙunƙuni, wai ba za'a kiraka gefe a faɗa maka abu a sirrance ba sai an gama yayataka a bainar nasi kowa yaji me zaka yi. Shiyasa tunda ta zo da naji kiranta ina fitowa na ke faɗawa banɗaki, sai ta ƙara wani ince gani ciki. Kamar dai wata zautacciya haka nayi wankan nan na fito sai aikin imagination na ke ina ta murmushi, yau ɗin dai kana ganina kasan cikin farin ciki na ke sosai, kamar ma ranar ɗaurin auren, annurin fuskata sam yaƙi ɗaukewa duk murnar zuwan Salim ne, kwanana tara kenan ban gansa ba, na riga na saba duk kwana uku yake zuwa, waya ma bama samun damar yi sosai, idan ya tasheni da safe sai zan kwanta zai ƙara kira, nan ma ba zamu jima ba 2-3mints ne zai ce naje na kwanta yana cikin aiki ne. Sun je taro ne can garin Ekiti, suna tare da shugaban ƙasa sun masa rakiya, kuma a can ɗin suna tattaunawa ne akan matsalar tsaro na ƙasar nan, to duk basu da wani isashshen lokaci, a hakan ma yau ɗin sato hanya zai yi ya taho, yace shima ya gaji da missing ɗina, ƙwayar idonsa kullum zafin rashin ganina take yi, kuma idan yay kuka duk bai da me lallashinsa. Ina zancen zuci sai ga kiransa ya shigo, naji ƙirjina yay duka, wani sanyayyan abu ya ratsa jikina, da azarɓaɓina kuwa na ɗaga. "Myyyy". Ya kira sunan da wani irin salo da ya saukar min da kasala. Na lumshe ido kana na amsa,"Na'am Salim". Sautin murmushinsa ya fito, yayi yayi na canja masa suna nace ni haka zan ke faɗi, da haka kuma sai ya koma cewa nafi kowa iya faɗin sunan, kamar ni na raɗa yafi daɗi a bakina. "My mun dawo fa, gani a ƙofar gida". Basarwa nayi irin ban damun nan ba na ce,"Ah dama yau zaku dawo, amma kun yi sauri, ai ce na ke sai kun yi good one month". Na tabbata sai da ya tsotsi leɓensa kafin yace da ni,"My abu ɗaya yasa na ke ɗaga miki ƙafa, ni za ki munafurta ki nuna min ba kiji daɗin dawowana ba, to fito da sauri kafin na kasa jurewa na shigo gidan da kaina". Idona a waje na ce,"Kuma sai ka iya?". "Kina mamaki? Ki ƙara five minutes kika ga ni sai dai ki tsince ni ina tsallake mutane, kuma a gaban kowa zan kamo hannunki na fito da ke". Dariya nayi sosai nace,"Yi haƙuri Sojansu kar ka bani kunya". Aje wayan nayi na leƙa na ƙwalawa Yasmin kira na ce taje ta buɗe masa ɗakin Yaya Al'amin. Na dawo daga ciki na shiga shiryawa, kamar wanda zata je gasar kyau, ba fa wani makeup na tsaya yi ba, powder kawai da kwalli sai lip bam shikenan amma kamar a sace ni a gudu, ni kaina ba ƙaramin kyau na yiwa kaina ba. Na fito ina wani takun ɗaiɗai, na leƙa ɗakin Ummani bata nan na bita ɓangaren Ummansu Hindatu, wanda bai sonka dai har a bada ba zai so ka ba, tunda aka fara hidiman bikin nan ƙala Umma bata ce da mu ba, kamar ma bata san da za'ai biki a gidan ba, ranar da aka buɗe lefe ma Sha'awanatu ƴarta ce kawai ta zo taga kayan, amma har yau Allah sanya alkhairi bata ce da Ummani ba, ni kuwa idan taga gimlawata sai da ta harare ni, nima kuwa na koyi shareta ko gaida ita bana yi, me zaka yi da mutumin da bai gamin mahaifiyarka da mutunci. "Ummani zan tafi". Suna awon masarar da za'a kai niƙa ayi tuwon dare na yau saboda baƙi, ta ɗago tana kallona tace,"Kika ce kin ɗau hutu". Umman su Hindatu tace,"A'a ƴata irin wannan kyau haka, ko dai sirikin nawa ne ya zo". Nayi murmushi ina cewa da Ummani,"Bana faɗa miki zan je karɓo sauran ɗinkuna ba". "Ohh haka ne, to ke da wa zaku tafi? Ko ta gidan Safiyya za ki biya". Na ɗan yi ƙasa da kaina ina sosa gira cike da kunya na ce,"Salim ya zo shi zai kai ni". Ta ɗan shiru kafin tace,"To sai kun dawo Allah ya kiyaye ya tsare hanya, kinga idan ki samu dama ki biya asibitin ki duba ƴar gidan Baaba mai ƙosai". "Ai kuwa gwara da kika tuna mini, wallahi na manta kuma fa ko jiya sai da ta kira ni tace ko da nurse ɗin da zan taimaka na haɗa su". "To inda hali sai ki ƙoƙarta musu, yarinyar naji ance sai an ƙara yi mata wankin ƙunar". Ina jinjina kai da tausayawa nace,"Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Bari na tafi". "To sai kun dawo Allah ya tsare, a kula don Allah Sa'ida". Ni wai sai kace wata ƙaramar yarinya, indai zan je wurin Salim ko zance zai ne Ummani ta dinƙa a kula a kula, balle kuma idan na ce zamu fita tare ai sai an ja kusan rabin awa ana min wa'azi da nasiha, yau ɗin ma don tana cikin hidiman aiki ne da tana nan tana min nasihar yau da kullum, ni duk idan tana haka sai nayi ta tsarguwa ina cewa ko bata yarda da ni ba ne. Umman su Hindatu tace,"Ƴar uwar taki dai sai gobe zata samu shigowa". "Ai ki rabu da ni da ita Umma, duk rashin mutuncin da zan mata kar kusa baki". Suna dariya duk ɗin su na wuce Umma na faɗin mun fi kusa, a tsakar gidanmu su Gwaggo Talatu na ta faman yabon kyan da nayi, wata Kakarmu ta ɓangaren su Ummani na zolayata da cewa ko dai gasar kyau zan tafi, wata ƙawar Ummani kuwa na faɗin gaskiya wadda tayi min gyaran jiki tayi mugun iyawa, fatata sai sheƙi take yi na zama kamar ƙwanduwar ƙwai, ko da madara da kankana ake wanke ni kullum ai sai haka, ga ƙamshi na tashin hankali tun daga nesa, su Juwairiyya gulmammu na tsokanata wai ai nan dai da jibi ne in kwantar da hankalina sunga ina ta rawan ƙafa, dama tunda suka ga mota a waje suka san shine ya zo, Mubaraka na bada labari wai ya zo da kakin soja ya fito duk ya tsorata ƴan unguwa, yara har da masu gudu. Zuwana soro ƙamshin turarensa ya dakeni na lumshe ido, har ga Allah ƙamshin nan shi ne ke rikitani na kasa sarrafa kaina a duk sanda na ke tare da shi. Ina tsaye Maman Khairi ta zo wucewa zasu kai buhun fulawa gidan da za'ai kayan gara, ta mintsine ni da cewa kar dai in kai kaina in yi haƙuri in bari su kaini, kunya ta rufe ni nayi saurin rufe fuska ina saurin shigewa ɗakin Yaya Al'amin. Yana zaune gefen katifar Yaya Al'amin, dama ya saba duk sanda ya zo anan yake zama, na ce me yasa bai son zama kan kujeran, sai ce yay gwara ya ke zama kan abu me taushi da ɗumi kar sanyi ya shige shi in zo ina cika shi da mita a shimfiɗa, haka ya saki baki yana ta zuba maganganun da suka sa har ya tafi ban ƙara kallonsa ba saboda mugun kunya, mamaki ya bani sosai sam ban san haka yake ba, hmmm dama namiji ka gansa kawai sai in bai samu wuri ba, duk da na san komai amma haka yasa naji kalaman suna neman su fi ƙarfin kaina. Ni dai ko da na shiga sai na kasa motsi, na maƙale a wuri ɗaya shauƙin ganinsa duk ya game min ilahirin tsoka da jinin jikina, har wani abu na ke ji yana tsikarina a yatsan ƙafa, ƙafafuwana suka yi bala'in sanyi saboda kallon da ya kafe ni da shi wanda ke neman kassara gaɓɓaina gaba ɗaya, ya lumshe ido yana sauke wani wawiyan ajiyan zuciya da yasa na ɗago babu shiri na ƙura masa ido. Yau ne ranar farko da na gansa cikin shigar uniform complete, ashe haka kayan suke masa bala'in kyau, har ga Allah sai da naji ina ma ya zama halalina in ƙarasa gare shi da sauri in rungume shi cikin shauƙin soyayyarsa da ƙaunarsa, ai ko kamar ya san me ke raina sai gani nayi ya buɗen hannaye wai in zo in hugging nasa, ina murmushi na maƙe kafaɗa ina a'a. Abin dariya kuma sai ya kama buga ƙafa a ƙasa sai kace yaro, na ware ido ina cewa,"Kayii". Sai kuwa ce yay,"Ai yaronki ne ni, nan gaba kaɗan ma breast feeding ɗina za ki ke yi". Ya faɗin hakan yana kashe min ido guda, nace,"Ban hanaka ba irin wannan maganan ba". Tasowa yay ya zo gaba daf da ni ya tsaya, nayi saurin sunkwi da kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna, idan na gansa gabana irin haka daf daf duk sai na nemi na ruɗe in kasa fassara irin yanda na ke ji a tare da ni. Ban ankara ba naji hannunsa cikin nawa, da sauri na nemi na zare ya hana hakan, nima kuma sai na tsinci kaina da hana ƙwacewar, sai dai murya can ƙasan maƙoshi nace da shi,"Kasan fa babu kyau, idan kayi haƙuri kwanaki kaɗan suka rage". Bagarar da maganar tawa yayi da cewa,"Baby ina kika je aka sauya min ke haka? Kinga kyan da kika yi kuwa, ga rigar tayi fitting ɗinki, Baby faɗa min sirrin me kika samu da a kwana tara kika ƙara fidda shape". Sai yay shiru yana cewa,"In faɗi wani abu?". Sai na masa wani kallo don idan yayi irin wannan muryan na tabbata zai min katoɓara ne, ile kuwa sai ce yay,"Naga twins ɗina ma sun ƙara cika, ko wani abu kika sa suka ɗago don ni dai ba a haka na tafi na bar su ba". Dukan wasa na kai masa yay saurin ja da baya yana dariya, ya tsare ni da tambayan lallai alalla sai na faɗa masa me na sha na daɗa cika gaba da baya, ƙwayar idona ma har haske ta ƙara yi. Ban iya cewa da shi komai ba kamar yanda na kasa wani ƙwaƙwkwaran motsi dalilin yanda na ke jin yana kewaya babban yatsansa akan tafin hannuna, sai naji ina neman fita a hayyacina na haɗiye yawu ina rumtse ido. Na ƙware wajen buɗe baki nace masa,"Salim ka bari". Ai ban ida rufe baki ba ya sauke min mintsine a weast ɗina. "Ya sunana?". Dariya na ƙyalƙyale da ita dalilin cakulkulin da ya sakar min, na manne jikin bango ina cewa,"Salim sunanka". Ganin yana neman yi min rumfa na rumtse ido da kyau ina marairaice murya da cewa,"Kayi haƙuri ba sunanka haka ba, sunanka Lieutenant Onochie, kuma fa kaga kar wani ya zo wucewa". "Ina ruwana ke za ki ji kunya ai, ni dama a ƙage na ke a bani abata na tafi, dama hotel ɗin da muka sauka idan za ki kwana kina ihu babu me kawo miki agaji". [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR06FT5* Agogo ya kaɗa ƙarfe biyu, na miƙe ina tattara takardu na saka cikin file ɗin da ke aje kan ɗan ƙaramin table ɗin cikin nursing station ɗin namu. Na saka wayata cikin aljihun rigata na uniform tare da cire after dress ɗin da ke jikina na saƙale ta jikin hanger, in ka dubeni gwanin ban sha'awa, kayan na mini kyau tun balle da kullum na ke wani ƙara yin fresh da ni, wanda bai sanni ba ma sai yace ƴar Daddy ce, hankali da natsuwa sun wadatu babu wata makusa a tare da ni, a ganni a kushe sai maƙiyi, don ko daga aiki na dawo da uniform ban ɗora hijabi ko after dress akai ba, ƴan anguwa an dinƙi bina da kallo kenan me cike da burgewa, masu gulma suyi masu adu'a su yi, to surutun ma bai damuna tunda dai ina da iyaye a raye nima kuma ban yar da adu'a ba. Na isa gaban firij na buɗe na ɗakko allurai a ciki. Ina jin Sister Maryam na faɗin,"Wai ni na rasa irin Sister Sa'ida, ki ta gume baki ba za kike magana ba, daga murmushi sai uhmm da ummm haba kamar kina jin haushin zama cikin mu, in haka ne to ayi maki office ɗinki mana don naga kina da ƙafa a asibitin". Na waigo ina murmushi da cewa,"Allah ba don ko wulaƙanci ba ki daina faɗin haka Sister Maryam, ni kawai magana ce bata dame ni ba, kinga ko zaman nan da muke ku yi ta hira ana hayaniya wallahi hawar min kai take yi, kowa kin san da yanda nature ɗinsa yake, ni na kasa sabawa surutu har yanzu ko a gidanmu haka na ke". Ta taɓe baki tana cewa,"Tab ai kuwa dai to ba hali ba ne wannan ɗabi'ar girman kai ce, ka yi magana kace zaka faɗi gaskiya ne aji haushinka". Ban ƙara tankawa maganarta ba, gudun kar mu zo muyi rigima, rigima ba halina ba ce, haka Ummani ma tana cewa da ni kar na taɓa biyewa kowa muyi rigima. To ni ban san dalilin da yasa take jin haushina ba, har ga Allah ta takura min, babu siɗi ba saɗaɗa ta ke ƴar tsama da ni, amma ina ga don ina kama kaina ne ban shiga sabgar kowa, ba zaka ji ana gulmace gulmace ko munafurcin wani da ni ba, hira ma idan ana yi jefi jefi zaka ji na saka baki, ko kuma don fifita yabona da Dr yake yawan yi akansu ne oho, da su kansu mutane idan suka zo asibitin, haka ko a cikin ma'aikata asibitin kowa ya tashi kaji yace Sa'ida Sa'ida, ta dai ga Allah yay min ɗaukaka hakan sai ya tsaya mata a rai, don ita ko da yaushe cikin sukana take yi, tayi ta faman habaici akan ina da girman kai tana gaggaya min magana mara daɗi, ko kyauta aka bani a asibitin bata iya ɓoye baƙin cikinta ƙarara take fitowa ta nuna, ni kuwa bana taɓa nuna mata na san ma tana yi, idan tayi wani abun ne Khadija da Maman Nana ke shigar min su caccaketa, sai sun gama da ita su dawo kaina suyi ta zazzaga min masifa akan rashin baki, ya kamata in koyi maida martani idan anyi min, haka kuma in daina barin ko ta kwana, ni dai to kawai na ke ce musu, me zan ce wanda ya wuci hakan? Na riƙe adu'a na riƙi azkar don haka na sha gaban kowanne mutum babu faɗa balle tashin hankali. Ina ƙara kallon agogon hannuna nace,"Maman Nana bari na je duba waccan patient ɗin". "Wadda tayi miscarrage ɗin nan?". Nace,"Ehh ita". "Oak tom sai kin dawo". Na fita a ɗakin cikin hanzari don ko kusa bana son yin latti wajen kula da majinyacin da ke ƙarƙashin kulawata. Na tura ƙofar ɗakin na shiga da sallamata, muka gaisa da patient relatives, suna girmama ni kamar yanda nima na ke girmama su, ga yabona da suke yi wanda har Dr sai da suka faɗawa irin ƙoƙarin da na ke yi akansu, har da cewa na iya mu'amala da mutane, mijin matar kuwa kusan ko da yaushe sai yay min ihsani saboda jin daɗin yanda na ke kula da iyalinsa cikin sauƙin kai. Wadda ke zaune gefen gadon kusa da mara lafiyar tayi saurin tashi daga wajen, Na aje file ɗin hannuna bisa loka na isa gaban mara lafiyar wanda yay daidai da ƙarewar drip ɗin da ke shiga jikinta. Ta buɗe idanuwa a lokacin tana kallona, na mata murmushi na ce,"Sannu, ya sauƙin jikin?". A hankali tace,"Da sauƙi, sannu da ɗawainiyarki na gode". Na amsa da faɗin,"Aikina ne ai, Allah ya ba ki lafiya". Cikin sanin makamar aikina da ƙwarewa na cire drip da ke jikinta tare da mata alluran da za'a yi a lokacin, bayan duk na gama kana na ke tambayarta ya take jin yanayin jikin nata duk ta min bayani. Na dubi ɗaya daga cikin ƴan uwan nata wacca ke tsaye daga bakin gadon, ni dariya ma ta so bani don kamar a tsorace take, ganin cewa dukka ƴan boko ne cikin ƙwarewar harshen turanci idona cikin ƙwayar idonta na ce,"Kun bata drugs ɗin ta?". Kamar bata gane me na ke nufi ba ne sai ta tsaya lakato kamar wadda ta samu kallo kallo, ta ɗan ban haushi na canja fuska ina mayar da dubana zuwa ga ɗayar wacca ta taso tana cewa,"Wallahi na sha'afa kin ce ƙarfe biyu za'a bata, kuma yau ɗin kawai aka yi kuskuren hakan". Faɗa na kama musu akan sakacin da suka yi na rashin bada maganin akan lokaci, kafin daga bisani na nusar da su muhimmancin bayarwar akan kari. Muna haka Sister Badiyya ta shigo, ai fa sai ta amshe ganin ina magana a sanyaye wai da sunan faɗa na ke yi, tunda ta fara musu faɗan suka shiga bata haƙuri saɓanin ni da shiru kawai suka yi sai wata dattijuwa ce ma tace za'a kiyaye gaba. "Yanzu sai wani abu ya faru da ita ba fata ake ba ku janyo mana ace rashin iya aikinmu ne". Dattijuwar ta taso daga inda take tana cewa,"Ayi haƙuri Nurses ba za'a kuma maimaita kuskuren ba". Sai da na lallaɓata kana tayi shiru, domin idan aka kaiwa Dr gulma zai iya zamar mana matsala ace mun zo kan patient muna ɗaga murya kamar bamu san ya nurse ya kamata yayi ba idan irin hakan ta taso, balle su da suke ganin kuɗi suka biya maƙudai ba kamar asibitin gwamnati ba. Barinta nayi tana musu bayanin jinin da Dr yace za'a saka mata. Ni kuma office ɗin Dr na shiga na basa file ɗin mara lafiyar tare da masa bayanin yanda tace min tana ji a jikinta, yay rubuce rubucen da zai yi da sake rubuta magunguna a ciki yace ga drugs ɗin da za su ƙara siya, sannan ya faɗawa Badiyya ta sanar musu da batun ƙarin jini leda ɗaya da za'a yi mata. Ina fitowa daga office ɗin sai ga Badiyya ta ƙaraso, ta dafa kafaɗana muka nufi recieption tana ce min. "Ke naji wata cikin ƴan uwan marasa lafiyar can na ƙusƙus akanki, saura kaɗan na daki bakinta to sai naji maganar da take yi kamar ta sanki, kar naje ko ƴar uwarku ce in abin kunya". Murmushi nayi da sautinsa ya fita sosai, ba sai na tsaya tambayarta wacce a cikinsu ba balle ta tsaya min dogon bayani, tuni na rigada na san wadda take nufi, ni kaina nayi mamakin yacca nayi fuska na ɗauke kai, wanda na san kuma hakan dole yaywa wanda ya san ka sanshi ciwo, nuna tamkar ban ganta ba da nuna tamkar ban santa ba dole zai sanya ta magantu, ba kuma nuna ko in kulawar ganinta ba ne zai daketa illa yanda ta ganni, dole tayi mamaki kuma dole ta girgiza. Muka gama abinda zamu yi a phermacy don mun ɗan jima tsaye da su Manager muna magana, a hakan ma banda na zame Badiyya da surutu ba tahowa zata yi mu tafi ba. Can ɗakin mara lafiyar muka koma, ina kallonsu ɗaya bayan ɗaya na ce,"To cikin ku wa zanyi wa bayani?". Suka yi min nuni da Dattijuwar ɗazu, nace,"Mama ga wannan total amount ɗin drugs ɗin da Dr ya sake rubutawa ne, ayi payment yanzu sai kuje can pharmacy already an haɗa magungunan karɓowa kawai zaku yi, amma don Allah Mama kar ayi wasa ƙarfe shida na yamma za'a dinga bata". Ta amsa da to. Ni kuma na ƙarasa gaban gadon domin ƙara yi mata allurar da Dr ya sake bayarwa, ina cikin mata ne wadda tun ɗazu ƙwayar idonta tamkar zata faɗo ƙasa don kallona tace,"Ni kuwa kamar na san fuskar nan". Nayi kamar ban jita ba har na gama aikina, har sai da zan fita ne ta sake maimaitawa tana tasowa da sauri ta dafa shoulder ɗina. Na waigo na mata kallon sama da ƙasa sai duk ta dabarbace, irin kallon da na watsa mata yasa ta ɗauke hannun nata da cewa,"Am so Sorry". Na ce,"Lafiya?". Ta ce,"Ce nayi kamar na sanki, ko ba Sa'ida ba ce?". Na kalleta kamar ba zanyi magana ba sai kuma nace,"Ehh sunana Nurse Sa'ida". Ta kaɗa kai,"Haba nifa in ce, Sa'ida tsohuwar matar Nazifi ko?". Na ɗaga gira da ke nuni na tooo ina kallonta tare da girgiza kai nace,"Anya kuwa? Ƙila na miki kama ne da wadda kike magana". Baki ta saki da al'ajabin da ya bayyana muraran a fuskarta ta sake cewa,"Tsohuwar matar Nazifi fa me kalwa na ke magana, ke ba ki gane ni ba ne?". Nayi saurin girgiza da cewa,"Ban gane ki ba, kuma ban san ma akan abinda kike magana". Ina faɗin haka nasa kai na fice ina murmushi. Maɗaukakin mamaki yasa Zahra'u kama ƙugu baki sake tana bin bayan Sa'ida da kallo, kafin tace,"Kutmar amma yarinyar nan ta mugun manna min hauka". Ƙanwar Babansu tace,"To ke kin santa ne? Ƙila kamannin kika gani". Ta juyo tana dubansu tace,"Wallahi ƙarya take yi ta san akan abinda na ke magana, rainin hankali ne kawai da son ci min fuska, amma ta sanni sarai, Kishiyata ce fa". Wata cikinsu ta waro ido waje,"Kishiyarki kuma? Kishiyarki ta gaske?". "Hmmm". Ta faɗa tana wucewa ta zauna kan kujera tana jijjiga kai. "Kun san Allah kishiyata ce ada, ba fa wulaƙancin da ta min ne ya damen ba, mamakina ɗaya matsayin da na ganta akai, yaushe Sa'ida tayi gogewar da har ta taka matakin zama ma'aikaciyar lafiya?". Ta kusa da ita tace,"Wai kina nufin kishiyarki ɗin nan da tayi sanadin mutuwar yarinyarki?". "Ita fa! Kin san ai tun lokacin shari'ar nan suka rabu bata dawo gidan ba, to yanzu ace cikin shekaru shidda ta zama haka? Ƴar talakawa ce fa ina taje tayi karatun da har ta zo babban asibiti irin wannan aiki? Ke fa lokacin da muke tare na rantse miki da huwallahu ko turancin kirki bata ji, yo ina ma ilimin bokon, batta dai akwai ilimin addini ni kaina ba ƙaramin burge ni take ba a ɓangaren nan, Samiha na rantse da Allah na girgiza, Samiha asibitin nan fa sai waɗanda suka yi karatu a ƙasar waje ko kuma a makarantun kuɗi na cikin ƙasar nan suma sai manya manyan makarantun, kuma ko hanya za'a maka sai ka biyo ta babbar hanya, Daddy kansa ba ya cin alfarmar asibitin nan kina kallo duk nacin Naja'atu haƙura tayi, Samiha ta ina ta shiga ta fita ta zo nan? Albashinta fa yaci uwar nawa Samiha". Wadda take kira da Samiha tayi dariya da cewa,"Yo ba bazawara ba ce, ke har kya yi mamaki, kika san manyan mutanen da ta ke bi". Zahra'u tasha mur tace,"Ban son iskanci wanna irin furuci ne wannan, ku babu dama mace taci gaba sai kuce ai bazawara ce ga yanda akayi ga yanda aka yi, lallai duka zaurawa ƴan iska ne?". Tayi maganar cike da jin haushi har da su tsaki. Samiha ta dafa kafaɗarta tace,"Maida wuƙar mene abin ɗaukan zafi, kema kin san dai tsakani da Allah akwai zaurawan da ke siyar da mutuncinsu ke majority ɗin su ma haka suke, kuma ina da tabbacin yarinyar nan na ɗaya daga ciki don haka ɗaya dai ƴar talakawa ba zata zo aiki wannan asibitin ba. To ke mene na ki a ciki don na faɗi haka? Ke ko iskancin ma kika yi ai ba za'a ce kin yi ba tunda ansan ƴar waye kuma dama tuni kina da aikin yi, cikin kuɗi kika taso cikinsa kike, to wa ya isa kuwa yace kina sahun zaurawa masu siyar da mutunci, ni ita ɗin dai na ke maganar shiga hotel da fitarsa ce ta kawota nan". Zahra'u ta sauke numfashi kafin ta tuntsire da dariya. Duk suka kama kallonta. "Wallahi Allah Nazifi na hango! Idan ba yaga Sa'ida sai ya yanke jiki ya faɗi ba, kun san yanda ya wulaƙanta yarinyar nan kuwa shi da ƴan uwansa, ranar farko da ya fara haɗuwa da ni cewa yake matarsa bagidajiya ce, bata da wayewa, babu boko kwata kwata, babu aikin yi, mummuna shi kawai yana zaman dole da ita ne". Sai ta ƙara sakin dariya da cewa,"Allah ka haɗa Nazifi da Sa'ida, shegen Ƙwallo yaga yanda rayuwarta ta sauya". Ƙanwar Babanta tace,"Du Allah ke rabamu da zancen nan, kamar fa muna cin namansu ne dukka. Kema kuma ya kamata ki yiwa kan ki faɗa ki koma gidan mijinki". Tuni tasha mur tana faɗin,"Allah ya kiyaye ya tsare, haba Anty Amina ko maƙiyina ai ba ya min fatan na koma gidan Nazifi ba, mutumin da bai da ko sisi ina zan iya zama da shi, me yaci me ya ban naci balle ƴaƴa?". "Yo ba da kuɗinsa kika auresa ba, me yasa ba za ki tawakkali ki zauna da shi cikin jarabawar da ubangiji ya aiko masa ba, ko don ƴaƴanki ma ai kya koma". Ta cuno baki ta ce,"Komawa to sai dai ko wata Zahra'un amma ba dai ni ba, ƴaƴa kuwa ai na rantse ba zan taɓa ba shi ba, alƙalin ma kansa ya rattaba hannu ba zan basa yara ba za suke zuwa dai su gansa jefi jefi shima don ba yanda na iya ne ubansu ne dole, amma ina yarana ina rayuwar karkara kuma cikin talauci Allah kiyaye". Ƙanwar Baban na su ta sake cewa,"To aikuwa dai ba ki kyauta ba". Zahra'u ta jingina kanta da bango abinda Sa'ida tayi mata na tsayawa a ranta, Idanuwanta suka rufe hoton shekaru biyu baya na haskawa cikin idonta bayan haihuwar Mardiyya da ta ƙara yi don lokacin da ta sha maganin zub da cikin nan Allah bai nufa ya zube ba. Kwayar idonta ta haska mata hoto tarrr lokacin da hukuma suka zo tafiya da Nazifi da sunan yaci bashin banki bai biya ba, tana tunawa haka ya tsuguna gabanta yana roƙonta Allah Annabi har da hawaye akan ta taimaka masa da takardun gida ya siyar ya rage wani abu, tayi mirsisi taƙi lamarin har kotu tsakaninta da shi aka je, tace ita babu wani abu nasa da ya mallakawa yara ƙarya yake mata, haka aka yi ta bincike aka duba aka ga kaf wasu kadarori da yake faɗa yana da su duk mallakin zahra'u ne ba nasa ba, dole haka aka tasa ƙeyarsa gidan ɗan kande sai da ya shafe watanni bakwai a prison kafin ya fito. Itama fitowar tasa ba don an biya kuɗin ba ne an dai rage wani abu a ciki, kuma tasirin adu'a ne ma yay ƙarfin da har aka bayar da shi, mahaifinsa ne ya siyar da gidan da suke zaune sai ya nema musu gidan ƙasa wanda gaba ɗaya bai wuce dubu ɗari ba, gidan ɗaki biyu ne jal amma haka duk suka ruguntsuma suka koma. Sannan itama Zahra'u tayi imani darajar Iman da kullum ke kuka tana kiran Daddy, shi ne ta yarda aka siyar da gidan da suke ciki miliyan tamanin da biyar ta bayar da miliyan hamsin, aka haɗa aka bayar da miliyan casa'in, da yarjejeniyar duk wata zai dinga ba da dubu hamsin. Ranar da ya fito kuwa daga kurku ta maka ƙararsa a kotu kan cewar ba zata iya ci gaba da zama da wanda bai haihuwa ba, kuma ba zata zauna da wanda bai da muhallin zama ba, bai da akin yi sannan bai da abin da zai ci da su don haka ya zama dole ya saketa, ta gama zama da shi har abada, haka akai ta daburwa tsakaninta da shi, duk taurin kan Nazifi kan ba zai saketa ba sai da ya sallama yay mata saki ukun da suka nema, domin shari'a da me kuɗi wahala ce, ya sha wulaƙanci kuwa a gun mahaifinta, kuma ko wata guda ba'ai da sakin ba sai ga sabon sammaci sun kuma kawo masa, sun kai ƙararsa gaban alƙali wai ya ce lallai sai ta ba shi yara alhalin ƙarya suka masa, tunda ta bar gidan bai waiwayeta ba duk da yana so yaga yaransa kuma wulaƙanci yasa yake danne zuciyarsa bai neme su ba, ga halin masifar da yake ciki na kai kuɗi da aka saka masa duk wata shi kuma babu sana'ar yi ko da ta ihu ce, haka dole ya rattaba hannu kan takardar da alƙali ya ba shi kan cewa Yara wurin mahaifiyarsu za su zauna ba za'a ba shi ba ko guda ɗaya. Ya damu amma damuwar da yake ciki tafi wannan, don lokacin yana tsaka da tashin hankali, fitowarsa a bursun da ya zo ya tarar da gidansu faɗuwa yay, matan Babansa uku ace ɗaki biyu jal a cikin gida? Ga uban yara? Wai sai da dare yayi yaga kawai Malam yayi shimfiɗa a tsakar gida da shi da yaran maza, ɗaki ɗaya ƴan matan ke kwana a ciki ɗayan kuma Iyam da Amarya, don ita Ummaa tuni ta tafi gidansu, manyan samarin kuwa duka a ƙofar gida suke kwana, a lokacin kawai sai ya kama hawaye ya rasa dalilin wannan masifar, a barsa ma da lalurar mahaifiyarsa na rashin ƙafa da na magani kaɗai ya isa yay hauka, amma sam Zahra'u bata tausaya masa ba haka tace lallai sai ya ke tura kuɗin abincin yara da kuɗin makarantar Iman rabi, to ita yanzu ma bata san a halin da yake ciki ba. ****Ƙarfe uku na tashi daga aiki, akan hanya na yanke shawaran wucewa gidan Safiyya, ban ma kirata na sanar mata da zuwan nawa ba, kwana biyu bamu yi ko chart ba balle waya, sai fushi take yi da ni shine yau zanje na lallashi abata mu shirya, duk da wanda ma take fushin da ni akansa na mance da shi da babinsa, rabona da shi tun zuwan da yay, ni kuma wannan rashin neman nawa ya tabbatar min da ba son gaskiya yake min ba dama yaudara ce tsantsa, to Allah yasa ban faɗawa tarkonsa ba, zaluncinsa ya ƙare masa. Falon Safiyya idan zaka kwana kana kwaɗa sallama babu me jinka, kuma ni na saba duk sanda na zo kaina tsaye na ke hayewa samanta, dama kuma bana zuwa ranar da mijinta yake gari, ba mazauni ba ne shi zaman kwana uku yake yi a sati. Na zare mayafina nayi cilli da shi saman kujera tare da jakata, kaina kansa ji nayi yay min mugun nauyi saboda haka na cire hular itama na jefar, na cire after dress ɗin ma, ribon ɗin ma na cire gashi ya baje a kafaɗa, Allah ya gani nayi mugun gajiya ga uwar yunwa da ke ƙwaƙwalar cikina. Kwanciya nayi akan kujerar sanyi Ac na dukana ta ko'ina, sai kuma na tashi, da yake akwai wani switch na ƙararrawa shi ake dannawa ya isar da zuwan baƙo, naje nayi ta dannawa don ba zai wuce tana can tana aikin baccin da bata gajiya da shi ba, ƴan aikin nata ma inaga basa nan. Sanin cewar mijinta bai gari na zaƙe kamar gidana, ban da shamaki da ko'ina a gidan Safiyya, kai tsaye na wuce kitchen ɗinta sai miƙa na ke, na duba babu abinci sai na buɗe firij na ɗauko maltina, sai da na kusa shanyewa na sauke robar, sannan ne na ɗanji dama dama na fito ina faɗin Allah ka rabamu da ƙishiryawa da yunwa. Da yake gaskiya abinci ba ya yankewa a gidan, in babu a kitchen to akwai a dining, saboda haka na nufi rumfar da dining table yake. Ina zuwa naja kujera zan zauna, a wani mugun tsorace naja da baya ganin mutum zaune kamar aljani, ina aikin zare idanu na ke kallon ko'ina musamman ma shi ɗin da na ke ganin kamar gizau, ƙaramar riga ce ta kaki a jikinsa kansa babu hula. Ko motsi bai yi ba abincinsa kawai yake ci hankali kwance kamar ma bai ji alamun mutum ba, duk sai na rikice naji kamar na saka ihu. Haka na daskare a tsaye kamar wata soja, na kasa gaba na kasa baya, idona a rumtse ina jin kamar nayi kuka, takaicina ɗaya yanda na ke, kai babu ɗankwali na saki gashi, ga rigar jikina ta kamani daga sama, dogon wuya duk a waje. Bugun zuciyata ya ƙaru, mintinan da ba su fi biyu ba suka wuce, na buɗe ido a tsammanina ya tashi ya bar wajen sai naga har yanzu yana nan, ya gama cin abinci ya ture plate ɗin gefe, ya kwantar da bayansa jikin kujerar yana shafa waya, na saci kallonsa naga taunar cingom ɗinsa kawai yake alamun bai da wata matsala, babu ko tunanin ya kamata ya tashi ya bar wajen. Nayi guntun tsaki a ƙasan raina ina cewa ƙabila ma dai sam ba su da kunya, ni na kasa barin wajen saboda yacca na ke amma shi bai da hankalin ya tashi ya bar min wajen tunda ya san ni ba muharramarsa ba ce, na ƙara jan tsaki wanda na san yaji don sai da naji saukar ido akaina. Na ɗaga ƙafa a hankali cikin jin kunyar kaina sai naji muryan Safiyya na cewa,"Me ya kawo aljana gidana? Me aka zo yi min? Saukar ƙur'ani ake min duk sati don haka aniya bil aniya tub tub, azo ayi waje bana neman ku". Kamar in je in hamɓareta saboda takaici, na ɗaga ido ina kallon inda take tsaye na ce,"Dilla Malama ni miƙo min hulana da rigana". Maimakon ta ɗauko tukunna ta taho wai sai da ta zo ta gama ƙare min kallo tana cewa ta ina na ke jiyo maganar jinnu, muka haɗa ido ta wani yatsine fuska irin nata na wulaƙanci kana ta dube shi tana masa magana cikin yare. Bai bata amsa ba ko da ido ya amsa mata oho ni ba kallon inda yake na ke ba, sai ta juya ta koma, sai da ta shafe kyawawan mintuna kana ta jefo min hular tana faɗin,"Kuma ban girka da mutum ba". Na sunkuya na ɗauka hulan na saka, kamar zan bar wajen sai naji har ga Allah ba zan iya ba, ko bai kallona ji zan yi kamar ni ɗin yake kallo, yanzu sai in tafi na juya masa baya mazaunai na rawa? Inaa ba zan iya ba, kawai sai na dake naja kujerar nayi zamana, na kai hannu na janyo flask na zuba abincin, da ƙyar na ke iya kai spoon ɗin baki ina tauna kamar ba zan ba saboda duk na tsargu, gani na ke kawai kallona yake yi. Dalilin haka sai na haɗe girar sama da ƙasa ina harare harare da murguɗa baki, karaf idona ya kai kan hannunsa ya fito da shi daga cikin aljihu ya aje bindiga a gabansa, gabana ya yanke ya faɗi, tuni na jefar da spoon ɗin ƙirjina sai bugawa yake yi, lokaci ɗaya zufa ta wanke min fuska, na kasa ɗauke ƙwayar idona akan bindigar, ba komai na ke haskowa ba sai lokacin da ƴan sanda suka ɗora min ita a goshi suna cewa na faɗa musu me na bawa Noor tasha ta mutu. Hawaye ya sakko min zirrr, na ɗago kai na sauke kallona akansa, sai naga shima ni ɗin yake kallo kuma haɗa idon da muka yi sai kawai ya ɗauke nasa ya basar irin ma bai san da ni a wajen ba. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR08FT5* Na aje wayar saman fuskata ina faman fitar da murmushi kamar sauna, sai daga bisani kuma naji raina ya ɓaci na kama jin haushin kaina, sai kace wata shashasha ma a soyayyar, ina neman zaƙewa daga ance ana sona sau ɗaya, to shi dama haka ma yake no text no call? Soyayyar ce bai iya ba ko kuma salon tasa kulawar kenan? Ko kuma ya gamata akan matarsa ta farko? Rashin nemana da bai yi ba fa tun zuwan farkonsa ya bani haushi sosai, don har ce nayi yana da girman kai, yana nufin kenan ma ba zan ja ajina ba tunda ni ba budurwa ba ce, sai yanzu da wani karkataccen bakinsa zai kira ni yana Baby, a'a Bebo. To ni ina son miji me raha da zamu zama abokai bana son me ɗagawa, in ma zai sauke abinda ke kansa ya sauke, idan ba zai sauke ba yaje can ya nemi ƴar uwarsa ƙabila ko wadda zata iya da halinsa, Numbernsa na ƙara kalla da kyau don ko ya kira ba zan ƙara ɗagawa ba ehe, kar yaga ya kira ina ta wani zumuɗi ya zaci sonsa na ke yi. Ummani tace,"To ke ya kike ganin za'ai da waɗannan kuɗin? Dukka lefen miliyan ɗaya da rabi za'a haɗa miki? Ni fa kawai nayi shiru ne gudun faɗan Abbaanku, shi yana batun gwara ayi miki kaya na gani na faɗa kar su ce sun bada kuɗi masu yawa an riƙe. amma ai kuɗin ne sun yi yawa, a dai haɗa ko na miliyan guda ne, ke ni miliyan ɗin ma a wajena tayi yawa wanne sutturu za'a siya har na miliyan, ba gwara a raba biyu sauran a haɗa da wancan a bawa Sale kafinta yay miki kaya masu kyau". "Kawai ma da zai dawo ya karɓi kuɗinsa da yafi". Na faɗa cikin muryar da ke shaida faɗa faɗa, ina ta gungunin masifa na ƙorafin yanda ma ya raina ni. Ta ce,"Uhmmm daga baya kenan, ni bana son gulma". Sai na sami kaina da ɗagowa in kalleta, na buɗi ba ki nace,"To Ummani sai ka kama auren wanda bai san kulawa ba balle haƙƙinta, kuma ba zai ke nuna maka da gaske yana sonka ba saboda yana ji da kansa". Harar da ta galla min yasa na sauke kai ƙasa ina ci gaba da masifata ƙasa ƙasa. Lokacin Maman Yasmin ta shigo tana tsokana na da,"Amarsu". Gaisheta kawai nayi ban ko ɗaga kai ba, Ummani tace,"Ƙyaleta". Suka shiga gaisawa Maman Yasmin ɗin na cewa,"Abban Yasmin yace min kina nema mana". Ummani tace,"Ehh dama ce nayi ke da Nafisa ku zo ku shiga kasuwa ku haɗo kayan lefen nan, kunga wata guda kamar yau ne gwara ayi abu a tsanaki, gata nan ita ɗin kuma idan zata biku to". Maman Yasmin tace da Ummani,"Tom shikenan, amma kinga ko za'a yiwa Mrs Arab magana a faɗa mata ga na iya adadin kuɗin da ake so ta haɗa, mu bar mata zaɓi nan da kwana uku za kiga ta haɗo su har akwatuna, kuma wallahi tayi masifar sanin makamar iya haɗa lefe, mayan bikin nan da ake duk ita ake bawa kwangila". Ummani tace,"To idan kin san dai babu wata matsala ai sai ayi mata maganar ko". "To shikenan bari a kirata ma yanzu, ke Sa'ida rubuta lambar wayata babu kuɗi, ai shegun kaya zata haɗa miki, da muka je bikin Surayya duk shegun less ɗin da kika ga tana sakawa ai ita ta haɗa lefen". A ƙasan raina na ce ehh fa shigar Amaryar tayi kyau babu ƙarya. Na ɗau wayata ina,"Karanto lambar". "Oak, 07037599677". Ina gama dialling nayi saving da Mrs Arab Kano. Kiran lambar ya tafi na miƙa mata ina tashi na fita, ruwan wanka na ɗora kana na koma ɗaki na ɗakko wani ɗinki da zan ƙarasa haɗawa, masu shi na ta kirana na gagara ƙarasa musu. Ƙarfe uku na fito a shirye don tafiya wurin aiki, tun uku saura na ke ta ganin kiran Salim na shigowa nayi biris naƙi ɗagawa, har aikowa yayi nayi saurin kora ɗan aiken kar ma Ummani taji. Na shiga ɗaki na yiwa Ummani sallama bayan ta min adu'a na fito, da zuwana soro kiran Maman Khairi ya shigo tana tambayana su siya min jugs ɗin tangaran yafi yawa ko kuwa? Nace ni na bar musu zaɓi kawai, tun ɗazu ta zo suka fita ita da Maman Yasmin yo siyayyan kayan kitchen lefen kuma kamar yadda ta faɗa ne sun gama magana da Mrs Arab zata haɗo komai ta kawo, ina jin Maman Yasmin na faɗin don Allah ta haɗa akwatu set uku, ni dai kam mun yi dacen sirikai don Matan Yayyuna kamar ciki guda muka fito, yanda Ummani ke yabon su haka suma suke yabonta ko ina suka shiga sai sun ce su kuwa babu abinda zasu ce da Allah sai godiya domin ya basu suruka ta ƙwarai wadda ta ɗauke su babu banbanci da abinda ta haifa, kuma babu takurawa sam a al'amuranta, to nima dai bana kukan rashin Yayyu mata don sun maye min gurbinsu, sai dai nayi kukan rashin ƙanne mata kawai. Ina fita ƙofar gida nayi kiciɓis da mutum tsaye bakin mota shi da Yaya Al'amin, yadi ne jikinsa baƙi yay masifar masa kyau, duk yanda na so nayi masa kallo ɗaya hakan ya faskara sai da na ƙara kallonsa, Allah masanin ta inda farinciki ya samu damar lulluɓe ni, a ƙasan raina nace yay kyau kamar ba ƙabila ba, har wani kishinsa naji ya lulluɓe ni ganin ƴan matan layinmu na ta wucewa islamiya. Na kalla screen ɗin wayata da kiransa ke ƙara shigowa a karo na babu adadi, sai na ɗaga ido na kalle shi naga ni yake kallo yana jijjiga kai, hakan yaso ba ni dariya amma na fusge, hankalinsa ma ya dawo kaina gaba ɗaya ya bar Yaya Al'amin can yana ta faman zuba shi ɗaya. Na sha murr na ɗauke kai kamar ban gansa ba, na ɗaga ƙafa zan tsallake na wuce a sumame kar Ya Al'amin ya ganni, aikuwa daidai nan naji yana cewa da ni,"Ke Sa'ida ba ki gan mu ba ne". "Yaya kaina na ƙasa ban kula da ku ba". Na faɗi sa'ilin da na ke ɗaga ido na kalle shi zan harare shi, sai kuwa na kasa aiwatar da hakan dalilin ƙayattacen murmushin da ya sakar min wanda ya samu shiga har cikin ɓargon jikina, ga wani munafukan dariya da ya danne a saman leɓe. Ina ta ciccin magani haka na shiga motar, wai wai tunda uwata ta haifeni ban taɓa shiga mota me haɗuwa da tsada irin wannan ba, sai na zama kamar ƴar ƙauye har wani taɓa kujerun na ke yi da ko cire su a leda ba'ai ba, duk yanda aka yi sabuwa ce fil ma. _"idan kika yi fushi da ni masoyiya hankali zaya tashi idanuwa su yi kuka, ki taimakawa soja kar ya zamo ragon namiji ai masa dariya"._ Haka ya shigo motan yana rera waƙar, da zummar in caccake shi da tsiwa amma ba shiri dariya ta ƙwace min har da sarƙewa, sai tari kwaf kwaf yay saurin miƙo min ruwa, na karɓa na sha idona har ya cika da ruwa tsabar dariya. Na miƙa masa goran ya galla min harara da cewan,"Kina wa me dariya?". Sauran dariyar na danne ina ɗauke idona a kansa idan ba haka ba tsaf zan ci gaba da dariya na zama kamar zararra. Ganin bai da niyyan tashin motan na karkata ina dubansa na ce,"Please kar na makara". Fuskansa a ɗaure yace,"Ba kina wa waƙana dariya ba". Nace,"Ayya sorry ba waƙanka na ke ma dariya ba". Sai ya jijjiga kai yace,"Akwai ranar ƙin dillanci, tara ki kawai na ke za ki shigo hannuna, har ni za kike ganin kirana ki ƙi picking, kuma ma tsawon sati guda ba za ki iya kirana ki ce kin yi missing ɗina ba kina sona". A hankali na ce,"Ai ba ni na fara zuwa nace ina sonka ba da zan ke bibiyanka". "Kika ce me?". "Ba komai". "Har na tausaya miki yarinya". Sai na kalle shi leɓena na daɗa talewa da murmushi nace,"Wacece yarinyar?". Da yatsansa guda ya lakuce min hanci yana faɗin,"Ke me dimple ɗaya da rabi". "Sa ido dai babu kyau, har ina kasan ɗaya dimple yafi ɗaya". Kawai sai ya saki wani murmushi irin nasa na shi kaɗai me tsada da ya kusa sumar da ni, murmushin da ya tsaya min a rai wanda tuni ƙwayar idona tayi capturing nasa, Rufewar ido da buɗewarsa shi kawai na ke gani. Cikin sati uku muka yi wani shaƙuwa na ban mamaki da Salim, shaƙuwan da zaka rantse mun fi shekara guda, ga wani fahimtan juna da muka samu a tsakani, sosai ya fahimce ni haka nima sosai na fahimce shi, zuwa lokacin na gane ashe nayi masa bahaguwan fahimta ne a farko, amma mutum ne shi mai sauƙin kai, ya iya mu'amala bai da damuwa sam sam, sai na ce kusan halin su guda da gidan su Safiyya a ɓangaren kirki da mutunta ɗan Adam, ba ɗagawa ba nuna shi wani ne ko ɗan wani ne, ga kyauta da son yin taimako abin hannunsa sam bai rufe masa ido ba, ina ganin hakan ne duk sanda ya kaini aiki ko ya ɗakko ni, ko idan ya zo gidanmu ya gamu da wani nawa, ko a hanya haka idan yaci karo da masu neman taimako, duk da ni bai fiya sakar min kuɗi ko bani abu ba, kyautansa bai wuce idan ya zo naje raka shi ya miƙo min sauran turarensa, sai wataran da ya cire agogonsa yay alwala na ɗauka na gwada sai yace ya bar min. Na saki jiki da shi sosai ya zama best friend ɗina, bamu fiya waya irin bini bini an yi kira ba, hakan bai dame shi ba sai aka yi dace nima kuma dama ba na son namiji me nacin kira, ko da yaushe a waya ko idan yazo cikin raha mu ke da farin ciki gami da annashuwa, har idan ina tare da shi na kan manta komai, bana jin asaran ɓata lokaci tare da shi domin kuma a duk wata hira tamu sai na ƙaru da shi ɓangaren ilimi ne ko ita kanta rayuwa. Yanzu ko da abu zan aiwatar shi na ke kira na nemi shawaransa, har Safiyya ke min ciwon bakin soyayya tasa na kware mata baya, nace ba za ki gane ba ne Beb, tace ni kuwa na gane tunda na san waye Yayana. Ya haɗa ni da Mahaifiyarsa mun yi waya da ita, ranar ji nayi kamar na nutse a ƙasa don kunya, matan free take na fahimci tana da kirki sosai, tayi ta jana da hira tun ban amsawa har na saki jiki naji ma kamar tare da Ummani na ke, tana tambayan yaushe zan zo in ganta, ban iya cewa komai ba sai ita ke cewa to zata zo da kanta taga ƴarta, Kakarsa ma wadda ta haifi Babansa har da aike ta yo min na wani atamfa ankara me shegen kyau. Har matarsa da yaransa duk mun gaisa da su, matar ma ita ne ta takura masa kan sai ya haɗa mu a waya, ni kishi yasa na ke ta zillewa ranar kuwa muna tare sai gata ta kira, muka gaisa da ita cikin mutunci da girmama juna, da farko ina magana a daddaƙile daga baya da na fahimci ita with all her heart take waya da ni sai na sake kawai, tace min ga yarana ma kafin su zo su ganni, ina ji yaran na tambayanta Maama waye take ce musu New Mommy ɗin su ce wadda Papa zai kawo ta haifo musu Baby Boy, ni dai nayi ta mamaki na ce to Allah yasa dai yanda ake faɗan bata da matsala hakan take, don ni har ga Allah idan na tuna da ita na kan ɗan ji fargaba haka, to amma shi kansa yana yawan faɗa min kamar yanda Ummansu Safiyya ke faɗa min Kudrat bata da problem zan ji daɗin zama da ita sosai, idan kishina ya motsa min zan ta cewa ya tafi wurin matarsa ya ƙyale ni, sai ya nuna min shi ba ya son hakan, yana son matarsa kuma nima yana sona kowacce da matsayinta a zuciyarsa, zai kuma yi ƙoƙarin ganin ya fita hakkin kowaccenmu. Haka Salim yay amfani da salon soyayyarsa yay raga raga da zuciyata a lokaci ƙanƙane, ashe ma ni ban san komai ba a soyayya, soyayya tana inda aka iya a wurin mutumin arziƙi, har tsokanata ake a gida da wurin aiki saboda nema na ke na zauce kamar farin shiga, alerm ɗin wayata duk sai da na cire, in ƙarfe biyu da rabi tayi shi zai tashe ni in yi sallar dare, haka idan asuba tayi, da safe kafin na farka yay min text da daɗaɗan kalamai da suke sawa naji ni a gajimare, har idan ban ji daga gare shi ba na ke takura, in koma kamar mara lafiya, Salim ya mantar da ni duk sauran guntun damuwan da na ke yi na famin ciwo, banda wata matsala ni kam na yarda Allah ya kashe ya ba ni, domin samun namiji kamarsa a wannan marrar sai dacen ubangiji kawai, wai kafin ma na shiga cikin gidan nasa kenan, shi kansa yana faɗa min Baby ba ki ga komai ba a soyayyan da na ke miki da kulawa sai kin shigo gidana tukunna, duk da wani sa'ilin ina cewa Allah yasa kar ya sauya daga baya, aurena na baya yasa na gasgata zancen Namiji bai da tabbas. Ya rage saura kwana uku biki, ana ta shirye shirye, ƴan ƙauyenmu duk sun zazzo wasu daga cikinsu, ni sai mamaki ma na ke ko a aurena na farko irin hidima da zumuɗin da ake a yanzu ba'ai a wancan lokacin ba, na farko kamar wani taron mutuwa haka aka yisa, ni ba'a farin ciki ɗari bisa ɗari ba haka suma iyayen nawa, amma a wannan kam farin ciki da zaƙuwar da na ke ciki sun kai kaso fiye da dubu, farin cikin Ummani har ba ya barinta rufe baki, ta kira wancan ta aikawa wancan, haka Abbaa na ma shi kansa kamar yanzu ne karon farko da zai aurar da ni. Kuma wannan auren sai ya zo da albarka, domin kuwa wani buɗi ubangiji ya kawowa Abbaa, yanzu haka babban teburi ya kama a kasuwa, cikin gida kuwa sai da ya aje botikan fenti huɗu aka shafe mana shi kamar za'a aurar da budurwa, na lura dai kowa yafi farin ciki da wannan auren hatta yayuna, idan nayi magana sai Ummani tace bazawarar ai me daraja ce, ni dai sai in murmushi kawai, idan na ɗauko kuɗi na bayar ayi amfani da su sai Abbaa yace a'a hakkinsa ne yay min komai, nauyinsa ne ba nauyina ne ba, in adana kuɗina za su min amfani nan gaba, amma yanzu na bari su zasu yi min komai, hatta kuɗin ɗunkuna duk shi ya bani yay min kashedin kar na sake na karɓi ko sisin Salim, Abbaa yace shi ba zai ƙarya ba amma zai iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da ƴarsa kunya, haka ya yankewa Yayyuna kuɗi suka haɗa dubu ɗari biyu su huɗu, aka haɗa da kuɗin aurena dubu ɗari biyar, sai kuɗin kayan lefena da aka rage Ummani ta kaiwa Sale dubu ɗari uku tace don Allah yay min furnitures masu na miliyan ɗaya irin wanda ake yayi. To da yake ma aiki ya mayar da shi Delta state satin baya aka yi masa ƙarin girma, Kudrat ma da ta kira ni a waya tana zolayana wai ni ƴar sa'a ce, dama sun gaji da zaman Edo ɗin, ba yanda ba su yi ba a tashi a gidan yaƙi sai ga shi dole tasa an tashi babu shiri, ita da yarana suna min godiya. Salim ɗin na cewa ba sai anyi min kayan ɗaki ba, nayi karaf kuwa nace sam bai isa ba, na wani hasala kamar wanda ya zage ni, na dinka fifiƙa ina masa masifar ai ba'a gidan babu ya tarar da ni ba, Abbaa ma ba zai yarda da zance ba, mahaifina zai yi min kayan ɗakina idan ma ya san ya siya ya aje ya kwashe abinsa ya fitar da su idan kuwa ba haka sai dai idan ba zan zauna a gidan nasa ba, ni kuwa ai ban manta gorin da Nazifi yay min ba sanda zai ƙara aure na cewan iyayen matarsa har kayan ɗaki sun mata ba irin iyayena ba da suka bar miji da ɗawainiyan komai. Saboda yanayin nisa zuwa can garin sai Sale yace zai ɗiba mutanensa suje Delta ɗin a haɗa kayan acan maimakon ace daga nan za'a a tafi, kuɗin mota ma kansa wani babban lamarin ne, hakan kuwa aka yi aka tafi da Yaya Al'amin da Abbayo, Salim ɗin yace akwai wurin zama a gidan nasa ba sai sun nemi hayan wajen kwana ba, Abbaa yace to gwara ayi tafiya ɗaya kawai tunda bikin ƴan kwanaki ya rage a tafi ayi jere gaba ɗaya, sanda ake fito da bahhunan kwanuka sai da nayi matuƙar mamaki, Ummani ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba har sai da na tambayeta ina ta samu kuɗi haka tace rufin asirin Allah ɗan abinda take tarawa ne, sai kuma gudumawar da ƙannenta da yayyunta suka aiko mata, kayan kitchen masu kyau da tsada ni har ce nayi ma ina zan kai su. Kwanansu biyar a can, ranar da suka dawo kuwa suna bawa Ummani labarin gidan, sai santinsa suke yi su maza ma kenan, Anty Shafa da su Anty Lubna da Maman Khairi duk sai lokacin suka ji rashin jin daɗin da Abbaa bai bari sun je tare ba, shi kuma yace ne da akwai ƴan uwa acan ne sai a tafi da su, to ba za'ai rashin hankali ba kawai aje a tarewa mutum a gida, matarsa ma ba zata ji daɗi ba. Abbayo na faɗin wallahi Matar Salim ɗin tana da matuƙar kirki, haka ta karrama su kamar ƴan uwanta, motsi kaɗan sai ta aiko yaranta su tambaye su ko suna da buƙatar wani abun, abinci kuwa har ci suka yi suka ture, yace kuma idan suka yi aiki suka gaji da kanta take zuwa tace musu ga babban falo can ta buɗe musu ko za su yi kallo, iya kwanakin da su kai sun mata shaida me kyau. Da daddare na samu Abbayo ina tambayansa ya fasalin gidan yake, yace min babban gida ne flat ba bene, ɓangarena bedroom uku ne kowanne da banɗaki a ciki, sai falo biyu da kitchen, amma fa kowanne ɗaki tafkeke ne, Yace babu laifi Sale yayi ƙoƙarin yin kaya masu kyau don duk zubin kayan turkey yayi sai kallon ƙurulla ne ma zai sai za a gane b kayan ƙasar waje ba ne, kuma bedroom biyu dukka an zuba kaya a ciki, dama yanda muka yi da su nace idan sunje sunga bedroom yafi ɗaya su kirani su faɗa min sai na tura kuɗi ayi min na ɗaya ɗakin ko ba mai tsada ba, hakan kuwa aka yi da ike ina dashi kuma ina adani na tura dubu ɗari biyar nace sai ɗakin ya zama shi ne nawa wancan kuma masu tsadar sai ya zama nasa. Abbayo har da tsokanata wai Kudrat ta fini kyau ita fara ce ƙal kamar ba ƴar ƙasar nan ba, mene mene ɗinsa dai, sai naji bala'in kishi da haushi ya kama ni har da guntuwar ƙwallana, ranar kuwa har fushi nayi da Salim yana ta kirana naƙi ɗagawa, yayo text nayi kamar ban gani ba. _________________________ _Kuyi haƙuri don Allah wallahi banji daɗin rashin post na jiya ba, tafiya nayi garin sakkowa a mota na faɗi na yi buguwan ƙashi a hannu, duk yanda na so na ƙoƙarta wallahi abin ya faskara, naga adu'oin ku na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi._ [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR09FT5* Maman Khairi da Maman Yasmin haka suka miƙe tsaye wajen gyara ni ciki da waje, kayan mata kamar hauka Maman Yasmin tasa na tura uban kuɗi aka yo aike tun daga niger, ga Safiyya ma da nata tasa aka kawo min daga sokoto, sam ba'a son raina na ke amfani da magungunan ba, haka na ke shansu a dole wani da daɗi wani ba daɗi, wani ma sai na kusa amai ma na ke iya sha, haka zan ta yiwa Safiyya ƙorafi Maman Yasmin ma na yita mata nurƙufanci, don ni a nawa ganin wannan abubuwan duk ba su da amfani duba da irin rayuwan da nayi a baya, amfanin da na dinƙi yi da su a banza. Safiyya ce ma me cewa ai yanzu zan san amfaninsu tunda sai yanzu ne zan yi auren, in daina lissafin wancan buhun a sahun maza, in bari in zan maganar ƴan iska mahaukata sai na ke sako shi a ciki, amma na bar tuna na taɓa aure a baya tunda dai ban haifa na baro ba. Da Safiyya muke ta shige da ficen abubuwan da na ke siya ta ɓangarena, itama haka ta tura min 100k ta account a matsayin gudunmawa, naji daɗi sosai da kuɗin na bawa Yaya Imam nace ya siyo buhun shinkafa da fulawa sai ya bawa Abbaa. Shima yay ta min godiya har da ƙwallata don ce masa nayi sirri ne tsakanina da shi. Na siya shadda nayi mana anko iri ɗaya ni da Ummani da Abbaa, sannan na siya wani kalan daban na ɗinkawa yayyuna da matansu da ƴanƴansu har da budurwan Yaya Al'amin ma, shigar da na ke so muyi ranar ɗaurin aure kenan, Uwata kuwa kayanta sunan sai ana gobe ɗaurin aure zan ɗakko in bata, don so na ke farin cikin saman fuskarta ya ninku sau dubun dubata, danƙararen less ne na siya mata guda biyu mai shegen tsada kuma nasa aka yi mata ɗinki na zamani, atamfofi biyu kowanne da shigar takalmi da mayafinsa, Abbaa nah ba da kala ɗaya na barsa ba bayan shaddar ɗaurin aure har da set biyu na yi masa na boyel. Salim ya tura min dubu hamsin na kuɗin gyaran jiki da lalle da kitso, ranar kuwa Safiyya ta dinƙa masifa wai yaushe Brother ya koyi tsumulmula basu sani ba, zata kira shi na hanata sai ta kira Ummansu ta faɗa mata, Umman nasu ma ta kama faɗa wai ko bai da shi ai ba ya bani 50k a matsayin kuɗin gyaran jiki ba balle kuma yana da shi, itama tace zata kira shi taci mutuncinsa nayi ta roƙonta da ƙyar ta haƙura ta ƙyale, ko kusa bana sawa Salim ido musamman akan kuɗinsa, ni yanda yake nuna min bai da wani kuɗi, ko hira muke yi zai ce in koyi haƙurin zama da shi a yanda yake, shi ba mai kuɗi ba ne amma insha Allahu zai yi ƙoƙarin ganin ban nemi wani abu daga gare shi na rasa ba, ba zan yi kukan babu ba in Allah ya yarda, saɓanin yacca na san labarin kuɗinsa a wurin Safiyya, to nima dai a haka na ke binsa dama ni abun hannun namiji ba damuna yay ba, har ce yay min motan da yake zuwa da shi ma na ogansa ne, wannan dai na jisa ne kawai ban wani yarda ba, kawai dai na san kyauta a soyayya da daɗi musamman ma a wurin wanda zaka aura, to ni zan iya cewa bai taɓa kawo min wani abu da sunan kyauta ba, kuma ko da na faɗawa Ummani ma ce tayi kar in sa hakan a raina, ƙila tsarinsa ne a haka sai na shiga cikin gidansa tukunna zai buɗe min aljihunsa, kuma gwara ma hakan akan ya buɗa min a waje sai na shiga daga ciki kuma ya matse kayansa, idan kuwa na nuna masa ban damu ba babu ƙorafi babu tambaye tambamye balle sa ido sai nafi kima a idonsa, shi kansa sai yafi jin daɗin yi min, balle ma mene na damun kai tunda ina aikina ina samu sosai kuma ga kasuwancin da na ke na kawo min kuɗi. Yau dai ƴan uwa sun ƙara cika gidanmu, Hajiya Ummani an kasa zaune an kasa tsaye, ayi can ayi nan, gidan ya kacame da hayaniya, ni da ban son hayaniya duk sai kaina ya ɗauka yay nauyi, na ƙagu ma ayi a gama taron a watse, du da ina ta faman mita akan me ma za'a tsaya yin wani taro aure ba auren budurwa ba, Maman Yasmin ta danno min zagi tace in ci gaba da maida kaina baya hakan yana da kyau ai. Yau tun asuba da na tashi kasa komawa bacci nayi, Maman Khairi ma da ta ganni da duku dukun Safiya a gidan Maman Yasmin sai ta kama tsokanata wai ta lura na zaƙu dai a ɗaura auren nan, yau ni ce babu baccin asuba. Nayi dariya kawai na shige ciki ni bata san me nake wa ba, ai kuwa na sha tsiya a wurin su Adama da duk mutanenmu dai na ƙauye da suke kwana gidan Maman Yasmin, ni da naje na ƙarasa haɗa kayayyakina takurawarsu ta hana ni sai baro gidan nayi na dawo gidanmu. Ɗakin Kaka na shiga inda anan aka ajiye akwatunan lefena da aka haɗa guda sha biyu, ɗauke da kaya masu tsada da kaya na alfarma, da aka kawo su ni dai sai dana tofe abuna da adu'oi saboda baki, kaya kamar ɗiyan wata ƙusar, ko shi da na ɗauka hoto na tura masa sai da yace mun fitar da shi kunya, da shi aka ce ya haɗa ba zai haɗa masu kyan haka ba, har da ce min yanzu da su Granny ba su yi karo karo an haɗa masa ya kawo wannan kuɗin ba ya zai yi? Ni kuwa na ce ummm shine yay ƙwafa wai in koka da ranar haɗuwarmu. Akwatun da ke ɗauke da abayoyi na buɗa na ɗauko guda ɗaya, pink colour tasha ado, na ɗakko agogo da yari ma har da sabon takalmi. Umman Batula ta ƙwala min kira na fita da sauri ina ɓoye kayana cikin hijabina kar a gani a ishe ni da mita, ni kuwa yau ban ga me hanani cakarewa da kwalliya ba. "Kije ga ruwan can na kai miki banɗaki, akwai wani daban cikin koriyar robar nan ki zauna a ciki sai ya huce sai ki fito". To kawai nace mata na wuce ina ƙunƙuni, wai ba za'a kiraka gefe a faɗa maka abu a sirrance ba sai an gama yayataka a bainar nasi kowa yaji me zaka yi. Shiyasa tunda ta zo da naji kiranta ina fitowa na ke faɗawa banɗaki, sai ta ƙara wani ince gani ciki. Kamar dai wata zautacciya haka nayi wankan nan na fito sai aikin imagination na ke ina ta murmushi, yau ɗin dai kana ganina kasan cikin farin ciki na ke sosai, kamar ma ranar ɗaurin auren, annurin fuskata sam yaƙi ɗaukewa duk murnar zuwan Salim ne, kwanana tara kenan ban gansa ba, na riga na saba duk kwana uku yake zuwa, waya ma bama samun damar yi sosai, idan ya tasheni da safe sai zan kwanta zai ƙara kira, nan ma ba zamu jima ba 2-3mints ne zai ce naje na kwanta yana cikin aiki ne. Sun je taro ne can garin Ekiti, suna tare da shugaban ƙasa sun masa rakiya, kuma a can ɗin suna tattaunawa ne akan matsalar tsaro na ƙasar nan, to duk basu da wani isashshen lokaci, a hakan ma yau ɗin sato hanya zai yi ya taho, yace shima ya gaji da missing ɗina, ƙwayar idonsa kullum zafin rashin ganina take yi, kuma idan yay kuka duk bai da me lallashinsa. Ina zancen zuci sai ga kiransa ya shigo, naji ƙirjina yay duka, wani sanyayyan abu ya ratsa jikina, da azarɓaɓina kuwa na ɗaga. "Myyyy". Ya kira sunan da wani irin salo da ya saukar min da kasala. Na lumshe ido kana na amsa,"Na'am Salim". Sautin murmushinsa ya fito, yayi yayi na canja masa suna nace ni haka zan ke faɗi, da haka kuma sai ya koma cewa nafi kowa iya faɗin sunan, kamar ni na raɗa yafi daɗi a bakina. "My mun dawo fa, gani a ƙofar gida". Basarwa nayi irin ban damun nan ba na ce,"Ah dama yau zaku dawo, amma kun yi sauri, ai ce na ke sai kun yi good one month". Na tabbata sai da ya tsotsi leɓensa kafin yace da ni,"My abu ɗaya yasa na ke ɗaga miki ƙafa, ni za ki munafurta ki nuna min ba kiji daɗin dawowana ba, to fito da sauri kafin na kasa jurewa na shigo gidan da kaina". Idona a waje na ce,"Kuma sai ka iya?". "Kina mamaki? Ki ƙara five minutes kika ga ni sai dai ki tsince ni ina tsallake mutane, kuma a gaban kowa zan kamo hannunki na fito da ke". Dariya nayi sosai nace,"Yi haƙuri Sojansu kar ka bani kunya". Aje wayan nayi na leƙa na ƙwalawa Yasmin kira na ce taje ta buɗe masa ɗakin Yaya Al'amin. Na dawo daga ciki na shiga shiryawa, kamar wanda zata je gasar kyau, ba fa wani makeup na tsaya yi ba, powder kawai da kwalli sai lip bam shikenan amma kamar a sace ni a gudu, ni kaina ba ƙaramin kyau na yiwa kaina ba. Na fito ina wani takun ɗaiɗai, na leƙa ɗakin Ummani bata nan na bita ɓangaren Ummansu Hindatu, wanda bai sonka dai har a bada ba zai so ka ba, tunda aka fara hidiman bikin nan ƙala Umma bata ce da mu ba, kamar ma bata san da za'ai biki a gidan ba, ranar da aka buɗe lefe ma Sha'awanatu ƴarta ce kawai ta zo taga kayan, amma har yau Allah sanya alkhairi bata ce da Ummani ba, ni kuwa idan taga gimlawata sai da ta harare ni, nima kuwa na koyi shareta ko gaida ita bana yi, me zaka yi da mutumin da bai gamin mahaifiyarka da mutunci. "Ummani zan tafi". Suna awon masarar da za'a kai niƙa ayi tuwon dare na yau saboda baƙi, ta ɗago tana kallona tace,"Kika ce kin ɗau hutu". Umman su Hindatu tace,"A'a ƴata irin wannan kyau haka, ko dai sirikin nawa ne ya zo". Nayi murmushi ina cewa da Ummani,"Bana faɗa miki zan je karɓo sauran ɗinkuna ba". "Ohh haka ne, to ke da wa zaku tafi? Ko ta gidan Safiyya za ki biya". Na ɗan yi ƙasa da kaina ina sosa gira cike da kunya na ce,"Salim ya zo shi zai kai ni". Ta ɗan shiru kafin tace,"To sai kun dawo Allah ya kiyaye ya tsare hanya, kinga idan ki samu dama ki biya asibitin ki duba ƴar gidan Baaba mai ƙosai". "Ai kuwa gwara da kika tuna mini, wallahi na manta kuma fa ko jiya sai da ta kira ni tace ko da nurse ɗin da zan taimaka na haɗa su". "To inda hali sai ki ƙoƙarta musu, yarinyar naji ance sai an ƙara yi mata wankin ƙunar". Ina jinjina kai da tausayawa nace,"Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Bari na tafi". "To sai kun dawo Allah ya tsare, a kula don Allah Sa'ida". Ni wai sai kace wata ƙaramar yarinya, indai zan je wurin Salim ko zance zai ne Ummani ta dinƙa a kula a kula, balle kuma idan na ce zamu fita tare ai sai an ja kusan rabin awa ana min wa'azi da nasiha, yau ɗin ma don tana cikin hidiman aiki ne da tana nan tana min nasihar yau da kullum, ni duk idan tana haka sai nayi ta tsarguwa ina cewa ko bata yarda da ni ba ne. Umman su Hindatu tace,"Ƴar uwar taki dai sai gobe zata samu shigowa". "Ai ki rabu da ni da ita Umma, duk rashin mutuncin da zan mata kar kusa baki". Suna dariya duk ɗin su na wuce Umma na faɗin mun fi kusa, a tsakar gidanmu su Gwaggo Talatu na ta faman yabon kyan da nayi, wata Kakarmu ta ɓangaren su Ummani na zolayata da cewa ko dai gasar kyau zan tafi, wata ƙawar Ummani kuwa na faɗin gaskiya wadda tayi min gyaran jiki tayi mugun iyawa, fatata sai sheƙi take yi na zama kamar ƙwanduwar ƙwai, ko da madara da kankana ake wanke ni kullum ai sai haka, ga ƙamshi na tashin hankali tun daga nesa, su Juwairiyya gulmammu na tsokanata wai ai nan dai da jibi ne in kwantar da hankalina sunga ina ta rawan ƙafa, dama tunda suka ga mota a waje suka san shine ya zo, Mubaraka na bada labari wai ya zo da kakin soja ya fito duk ya tsorata ƴan unguwa, yara har da masu gudu. Zuwana soro ƙamshin turarensa ya dakeni na lumshe ido, har ga Allah ƙamshin nan shi ne ke rikitani na kasa sarrafa kaina a duk sanda na ke tare da shi. Ina tsaye Maman Khairi ta zo wucewa zasu kai buhun fulawa gidan da za'ai kayan gara, ta mintsine ni da cewa kar dai in kai kaina in yi haƙuri in bari su kaini, kunya ta rufe ni nayi saurin rufe fuska ina saurin shigewa ɗakin Yaya Al'amin. Yana zaune gefen katifar Yaya Al'amin, dama ya saba duk sanda ya zo anan yake zama, na ce me yasa bai son zama kan kujeran, sai ce yay gwara ya ke zama kan abu me taushi da ɗumi kar sanyi ya shige shi in zo ina cika shi da mita a shimfiɗa, haka ya saki baki yana ta zuba maganganun da suka sa har ya tafi ban ƙara kallonsa ba saboda mugun kunya, mamaki ya bani sosai sam ban san haka yake ba, hmmm dama namiji ka gansa kawai sai in bai samu wuri ba, duk da na san komai amma haka yasa naji kalaman suna neman su fi ƙarfin kaina. Ni dai ko da na shiga sai na kasa motsi, na maƙale a wuri ɗaya shauƙin ganinsa duk ya game min ilahirin tsoka da jinin jikina, har wani abu na ke ji yana tsikarina a yatsan ƙafa, ƙafafuwana suka yi bala'in sanyi saboda kallon da ya kafe ni da shi wanda ke neman kassara gaɓɓaina gaba ɗaya, ya lumshe ido yana sauke wani wawiyan ajiyan zuciya da yasa na ɗago babu shiri na ƙura masa ido. Yau ne ranar farko da na gansa cikin shigar uniform complete, ashe haka kayan suke masa bala'in kyau, har ga Allah sai da naji ina ma ya zama halalina in ƙarasa gare shi da sauri in rungume shi cikin shauƙin soyayyarsa da ƙaunarsa, ai ko kamar ya san me ke raina sai gani nayi ya buɗen hannaye wai in zo in hugging nasa, ina murmushi na maƙe kafaɗa ina a'a. Abin dariya kuma sai ya kama buga ƙafa a ƙasa sai kace yaro, na ware ido ina cewa,"Kayii". Sai kuwa ce yay,"Ai yaronki ne ni, nan gaba kaɗan ma breast feeding ɗina za ki ke yi". Ya faɗin hakan yana kashe min ido guda, nace,"Ban hanaka ba irin wannan maganan ba". Tasowa yay ya zo gaba daf da ni ya tsaya, nayi saurin sunkwi da kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna, idan na gansa gabana irin haka daf daf duk sai na nemi na ruɗe in kasa fassara irin yanda na ke ji a tare da ni. Ban ankara ba naji hannunsa cikin nawa, da sauri na nemi na zare ya hana hakan, nima kuma sai na tsinci kaina da hana ƙwacewar, sai dai murya can ƙasan maƙoshi nace da shi,"Kasan fa babu kyau, idan kayi haƙuri kwanaki kaɗan suka rage". Bagarar da maganar tawa yayi da cewa,"Baby ina kika je aka sauya min ke haka? Kinga kyan da kika yi kuwa, ga rigar tayi fitting ɗinki, Baby faɗa min sirrin me kika samu da a kwana tara kika ƙara fidda shape". Sai yay shiru yana cewa,"In faɗi wani abu?". Sai na masa wani kallo don idan yayi irin wannan muryan na tabbata zai min katoɓara ne, ile kuwa sai ce yay,"Naga twins ɗina ma sun ƙara cika, ko wani abu kika sa suka ɗago don ni dai ba a haka na tafi na bar su ba". Dukan wasa na kai masa yay saurin ja da baya yana dariya, ya tsare ni da tambayan lallai alalla sai na faɗa masa me na sha na daɗa cika gaba da baya, ƙwayar idona ma har haske ta ƙara yi. Ban iya cewa da shi komai ba kamar yanda na kasa wani ƙwaƙwkwaran motsi dalilin yanda na ke jin yana kewaya babban yatsansa akan tafin hannuna, sai naji ina neman fita a hayyacina na haɗiye yawu ina rumtse ido. Na ƙware wajen buɗe baki nace masa,"Salim ka bari". Ai ban ida rufe baki ba ya sauke min mintsine a weast ɗina. "Ya sunana?". Dariya na ƙyalƙyale da ita dalilin cakulkulin da ya sakar min, na manne jikin bango ina cewa,"Salim sunanka". Ganin yana neman yi min rumfa na rumtse ido da kyau ina marairaice murya da cewa,"Kayi haƙuri ba sunanka haka ba, sunanka Lieutenant Onochie, kuma fa kaga kar wani ya zo wucewa". "Ina ruwana ke za ki ji kunya ai, ni dama a ƙage na ke a bani abata na tafi, dama hotel ɗin da muka sauka idan za ki kwana kina ihu babu me kawo miki agaji". [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR08FT5* Na aje wayar saman fuskata ina faman fitar da murmushi kamar sauna, sai daga bisani kuma naji raina ya ɓaci na kama jin haushin kaina, sai kace wata shashasha ma a soyayyar, ina neman zaƙewa daga ance ana sona sau ɗaya, to shi dama haka ma yake no text no call? Soyayyar ce bai iya ba ko kuma salon tasa kulawar kenan? Ko kuma ya gamata akan matarsa ta farko? Rashin nemana da bai yi ba fa tun zuwan farkonsa ya bani haushi sosai, don har ce nayi yana da girman kai, yana nufin kenan ma ba zan ja ajina ba tunda ni ba budurwa ba ce, sai yanzu da wani karkataccen bakinsa zai kira ni yana Baby, a'a Bebo. To ni ina son miji me raha da zamu zama abokai bana son me ɗagawa, in ma zai sauke abinda ke kansa ya sauke, idan ba zai sauke ba yaje can ya nemi ƴar uwarsa ƙabila ko wadda zata iya da halinsa, Numbernsa na ƙara kalla da kyau don ko ya kira ba zan ƙara ɗagawa ba ehe, kar yaga ya kira ina ta wani zumuɗi ya zaci sonsa na ke yi. Ummani tace,"To ke ya kike ganin za'ai da waɗannan kuɗin? Dukka lefen miliyan ɗaya da rabi za'a haɗa miki? Ni fa kawai nayi shiru ne gudun faɗan Abbaanku, shi yana batun gwara ayi miki kaya na gani na faɗa kar su ce sun bada kuɗi masu yawa an riƙe. amma ai kuɗin ne sun yi yawa, a dai haɗa ko na miliyan guda ne, ke ni miliyan ɗin ma a wajena tayi yawa wanne sutturu za'a siya har na miliyan, ba gwara a raba biyu sauran a haɗa da wancan a bawa Sale kafinta yay miki kaya masu kyau". "Kawai ma da zai dawo ya karɓi kuɗinsa da yafi". Na faɗa cikin muryar da ke shaida faɗa faɗa, ina ta gungunin masifa na ƙorafin yanda ma ya raina ni. Ta ce,"Uhmmm daga baya kenan, ni bana son gulma". Sai na sami kaina da ɗagowa in kalleta, na buɗi ba ki nace,"To Ummani sai ka kama auren wanda bai san kulawa ba balle haƙƙinta, kuma ba zai ke nuna maka da gaske yana sonka ba saboda yana ji da kansa". Harar da ta galla min yasa na sauke kai ƙasa ina ci gaba da masifata ƙasa ƙasa. Lokacin Maman Yasmin ta shigo tana tsokana na da,"Amarsu". Gaisheta kawai nayi ban ko ɗaga kai ba, Ummani tace,"Ƙyaleta". Suka shiga gaisawa Maman Yasmin ɗin na cewa,"Abban Yasmin yace min kina nema mana". Ummani tace,"Ehh dama ce nayi ke da Nafisa ku zo ku shiga kasuwa ku haɗo kayan lefen nan, kunga wata guda kamar yau ne gwara ayi abu a tsanaki, gata nan ita ɗin kuma idan zata biku to". Maman Yasmin tace da Ummani,"Tom shikenan, amma kinga ko za'a yiwa Mrs Arab magana a faɗa mata ga na iya adadin kuɗin da ake so ta haɗa, mu bar mata zaɓi nan da kwana uku za kiga ta haɗo su har akwatuna, kuma wallahi tayi masifar sanin makamar iya haɗa lefe, mayan bikin nan da ake duk ita ake bawa kwangila". Ummani tace,"To idan kin san dai babu wata matsala ai sai ayi mata maganar ko". "To shikenan bari a kirata ma yanzu, ke Sa'ida rubuta lambar wayata babu kuɗi, ai shegun kaya zata haɗa miki, da muka je bikin Surayya duk shegun less ɗin da kika ga tana sakawa ai ita ta haɗa lefen". A ƙasan raina na ce ehh fa shigar Amaryar tayi kyau babu ƙarya. Na ɗau wayata ina,"Karanto lambar". "Oak, 07037599677". Ina gama dialling nayi saving da Mrs Arab Kano. Kiran lambar ya tafi na miƙa mata ina tashi na fita, ruwan wanka na ɗora kana na koma ɗaki na ɗakko wani ɗinki da zan ƙarasa haɗawa, masu shi na ta kirana na gagara ƙarasa musu. Ƙarfe uku na fito a shirye don tafiya wurin aiki, tun uku saura na ke ta ganin kiran Salim na shigowa nayi biris naƙi ɗagawa, har aikowa yayi nayi saurin kora ɗan aiken kar ma Ummani taji. Na shiga ɗaki na yiwa Ummani sallama bayan ta min adu'a na fito, da zuwana soro kiran Maman Khairi ya shigo tana tambayana su siya min jugs ɗin tangaran yafi yawa ko kuwa? Nace ni na bar musu zaɓi kawai, tun ɗazu ta zo suka fita ita da Maman Yasmin yo siyayyan kayan kitchen lefen kuma kamar yadda ta faɗa ne sun gama magana da Mrs Arab zata haɗo komai ta kawo, ina jin Maman Yasmin na faɗin don Allah ta haɗa akwatu set uku, ni dai kam mun yi dacen sirikai don Matan Yayyuna kamar ciki guda muka fito, yanda Ummani ke yabon su haka suma suke yabonta ko ina suka shiga sai sun ce su kuwa babu abinda zasu ce da Allah sai godiya domin ya basu suruka ta ƙwarai wadda ta ɗauke su babu banbanci da abinda ta haifa, kuma babu takurawa sam a al'amuranta, to nima dai bana kukan rashin Yayyu mata don sun maye min gurbinsu, sai dai nayi kukan rashin ƙanne mata kawai. Ina fita ƙofar gida nayi kiciɓis da mutum tsaye bakin mota shi da Yaya Al'amin, yadi ne jikinsa baƙi yay masifar masa kyau, duk yanda na so nayi masa kallo ɗaya hakan ya faskara sai da na ƙara kallonsa, Allah masanin ta inda farinciki ya samu damar lulluɓe ni, a ƙasan raina nace yay kyau kamar ba ƙabila ba, har wani kishinsa naji ya lulluɓe ni ganin ƴan matan layinmu na ta wucewa islamiya. Na kalla screen ɗin wayata da kiransa ke ƙara shigowa a karo na babu adadi, sai na ɗaga ido na kalle shi naga ni yake kallo yana jijjiga kai, hakan yaso ba ni dariya amma na fusge, hankalinsa ma ya dawo kaina gaba ɗaya ya bar Yaya Al'amin can yana ta faman zuba shi ɗaya. Na sha murr na ɗauke kai kamar ban gansa ba, na ɗaga ƙafa zan tsallake na wuce a sumame kar Ya Al'amin ya ganni, aikuwa daidai nan naji yana cewa da ni,"Ke Sa'ida ba ki gan mu ba ne". "Yaya kaina na ƙasa ban kula da ku ba". Na faɗi sa'ilin da na ke ɗaga ido na kalle shi zan harare shi, sai kuwa na kasa aiwatar da hakan dalilin ƙayattacen murmushin da ya sakar min wanda ya samu shiga har cikin ɓargon jikina, ga wani munafukan dariya da ya danne a saman leɓe. Ina ta ciccin magani haka na shiga motar, wai wai tunda uwata ta haifeni ban taɓa shiga mota me haɗuwa da tsada irin wannan ba, sai na zama kamar ƴar ƙauye har wani taɓa kujerun na ke yi da ko cire su a leda ba'ai ba, duk yanda aka yi sabuwa ce fil ma. _"idan kika yi fushi da ni masoyiya hankali zaya tashi idanuwa su yi kuka, ki taimakawa soja kar ya zamo ragon namiji ai masa dariya"._ Haka ya shigo motan yana rera waƙar, da zummar in caccake shi da tsiwa amma ba shiri dariya ta ƙwace min har da sarƙewa, sai tari kwaf kwaf yay saurin miƙo min ruwa, na karɓa na sha idona har ya cika da ruwa tsabar dariya. Na miƙa masa goran ya galla min harara da cewan,"Kina wa me dariya?". Sauran dariyar na danne ina ɗauke idona a kansa idan ba haka ba tsaf zan ci gaba da dariya na zama kamar zararra. Ganin bai da niyyan tashin motan na karkata ina dubansa na ce,"Please kar na makara". Fuskansa a ɗaure yace,"Ba kina wa waƙana dariya ba". Nace,"Ayya sorry ba waƙanka na ke ma dariya ba". Sai ya jijjiga kai yace,"Akwai ranar ƙin dillanci, tara ki kawai na ke za ki shigo hannuna, har ni za kike ganin kirana ki ƙi picking, kuma ma tsawon sati guda ba za ki iya kirana ki ce kin yi missing ɗina ba kina sona". A hankali na ce,"Ai ba ni na fara zuwa nace ina sonka ba da zan ke bibiyanka". "Kika ce me?". "Ba komai". "Har na tausaya miki yarinya". Sai na kalle shi leɓena na daɗa talewa da murmushi nace,"Wacece yarinyar?". Da yatsansa guda ya lakuce min hanci yana faɗin,"Ke me dimple ɗaya da rabi". "Sa ido dai babu kyau, har ina kasan ɗaya dimple yafi ɗaya". Kawai sai ya saki wani murmushi irin nasa na shi kaɗai me tsada da ya kusa sumar da ni, murmushin da ya tsaya min a rai wanda tuni ƙwayar idona tayi capturing nasa, Rufewar ido da buɗewarsa shi kawai na ke gani. Cikin sati uku muka yi wani shaƙuwa na ban mamaki da Salim, shaƙuwan da zaka rantse mun fi shekara guda, ga wani fahimtan juna da muka samu a tsakani, sosai ya fahimce ni haka nima sosai na fahimce shi, zuwa lokacin na gane ashe nayi masa bahaguwan fahimta ne a farko, amma mutum ne shi mai sauƙin kai, ya iya mu'amala bai da damuwa sam sam, sai na ce kusan halin su guda da gidan su Safiyya a ɓangaren kirki da mutunta ɗan Adam, ba ɗagawa ba nuna shi wani ne ko ɗan wani ne, ga kyauta da son yin taimako abin hannunsa sam bai rufe masa ido ba, ina ganin hakan ne duk sanda ya kaini aiki ko ya ɗakko ni, ko idan ya zo gidanmu ya gamu da wani nawa, ko a hanya haka idan yaci karo da masu neman taimako, duk da ni bai fiya sakar min kuɗi ko bani abu ba, kyautansa bai wuce idan ya zo naje raka shi ya miƙo min sauran turarensa, sai wataran da ya cire agogonsa yay alwala na ɗauka na gwada sai yace ya bar min. Na saki jiki da shi sosai ya zama best friend ɗina, bamu fiya waya irin bini bini an yi kira ba, hakan bai dame shi ba sai aka yi dace nima kuma dama ba na son namiji me nacin kira, ko da yaushe a waya ko idan yazo cikin raha mu ke da farin ciki gami da annashuwa, har idan ina tare da shi na kan manta komai, bana jin asaran ɓata lokaci tare da shi domin kuma a duk wata hira tamu sai na ƙaru da shi ɓangaren ilimi ne ko ita kanta rayuwa. Yanzu ko da abu zan aiwatar shi na ke kira na nemi shawaransa, har Safiyya ke min ciwon bakin soyayya tasa na kware mata baya, nace ba za ki gane ba ne Beb, tace ni kuwa na gane tunda na san waye Yayana. Ya haɗa ni da Mahaifiyarsa mun yi waya da ita, ranar ji nayi kamar na nutse a ƙasa don kunya, matan free take na fahimci tana da kirki sosai, tayi ta jana da hira tun ban amsawa har na saki jiki naji ma kamar tare da Ummani na ke, tana tambayan yaushe zan zo in ganta, ban iya cewa komai ba sai ita ke cewa to zata zo da kanta taga ƴarta, Kakarsa ma wadda ta haifi Babansa har da aike ta yo min na wani atamfa ankara me shegen kyau. Har matarsa da yaransa duk mun gaisa da su, matar ma ita ne ta takura masa kan sai ya haɗa mu a waya, ni kishi yasa na ke ta zillewa ranar kuwa muna tare sai gata ta kira, muka gaisa da ita cikin mutunci da girmama juna, da farko ina magana a daddaƙile daga baya da na fahimci ita with all her heart take waya da ni sai na sake kawai, tace min ga yarana ma kafin su zo su ganni, ina ji yaran na tambayanta Maama waye take ce musu New Mommy ɗin su ce wadda Papa zai kawo ta haifo musu Baby Boy, ni dai nayi ta mamaki na ce to Allah yasa dai yanda ake faɗan bata da matsala hakan take, don ni har ga Allah idan na tuna da ita na kan ɗan ji fargaba haka, to amma shi kansa yana yawan faɗa min kamar yanda Ummansu Safiyya ke faɗa min Kudrat bata da problem zan ji daɗin zama da ita sosai, idan kishina ya motsa min zan ta cewa ya tafi wurin matarsa ya ƙyale ni, sai ya nuna min shi ba ya son hakan, yana son matarsa kuma nima yana sona kowacce da matsayinta a zuciyarsa, zai kuma yi ƙoƙarin ganin ya fita hakkin kowaccenmu. Haka Salim yay amfani da salon soyayyarsa yay raga raga da zuciyata a lokaci ƙanƙane, ashe ma ni ban san komai ba a soyayya, soyayya tana inda aka iya a wurin mutumin arziƙi, har tsokanata ake a gida da wurin aiki saboda nema na ke na zauce kamar farin shiga, alerm ɗin wayata duk sai da na cire, in ƙarfe biyu da rabi tayi shi zai tashe ni in yi sallar dare, haka idan asuba tayi, da safe kafin na farka yay min text da daɗaɗan kalamai da suke sawa naji ni a gajimare, har idan ban ji daga gare shi ba na ke takura, in koma kamar mara lafiya, Salim ya mantar da ni duk sauran guntun damuwan da na ke yi na famin ciwo, banda wata matsala ni kam na yarda Allah ya kashe ya ba ni, domin samun namiji kamarsa a wannan marrar sai dacen ubangiji kawai, wai kafin ma na shiga cikin gidan nasa kenan, shi kansa yana faɗa min Baby ba ki ga komai ba a soyayyan da na ke miki da kulawa sai kin shigo gidana tukunna, duk da wani sa'ilin ina cewa Allah yasa kar ya sauya daga baya, aurena na baya yasa na gasgata zancen Namiji bai da tabbas. Ya rage saura kwana uku biki, ana ta shirye shirye, ƴan ƙauyenmu duk sun zazzo wasu daga cikinsu, ni sai mamaki ma na ke ko a aurena na farko irin hidima da zumuɗin da ake a yanzu ba'ai a wancan lokacin ba, na farko kamar wani taron mutuwa haka aka yisa, ni ba'a farin ciki ɗari bisa ɗari ba haka suma iyayen nawa, amma a wannan kam farin ciki da zaƙuwar da na ke ciki sun kai kaso fiye da dubu, farin cikin Ummani har ba ya barinta rufe baki, ta kira wancan ta aikawa wancan, haka Abbaa na ma shi kansa kamar yanzu ne karon farko da zai aurar da ni. Kuma wannan auren sai ya zo da albarka, domin kuwa wani buɗi ubangiji ya kawowa Abbaa, yanzu haka babban teburi ya kama a kasuwa, cikin gida kuwa sai da ya aje botikan fenti huɗu aka shafe mana shi kamar za'a aurar da budurwa, na lura dai kowa yafi farin ciki da wannan auren hatta yayuna, idan nayi magana sai Ummani tace bazawarar ai me daraja ce, ni dai sai in murmushi kawai, idan na ɗauko kuɗi na bayar ayi amfani da su sai Abbaa yace a'a hakkinsa ne yay min komai, nauyinsa ne ba nauyina ne ba, in adana kuɗina za su min amfani nan gaba, amma yanzu na bari su zasu yi min komai, hatta kuɗin ɗunkuna duk shi ya bani yay min kashedin kar na sake na karɓi ko sisin Salim, Abbaa yace shi ba zai ƙarya ba amma zai iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da ƴarsa kunya, haka ya yankewa Yayyuna kuɗi suka haɗa dubu ɗari biyu su huɗu, aka haɗa da kuɗin aurena dubu ɗari biyar, sai kuɗin kayan lefena da aka rage Ummani ta kaiwa Sale dubu ɗari uku tace don Allah yay min furnitures masu na miliyan ɗaya irin wanda ake yayi. To da yake ma aiki ya mayar da shi Delta state satin baya aka yi masa ƙarin girma, Kudrat ma da ta kira ni a waya tana zolayana wai ni ƴar sa'a ce, dama sun gaji da zaman Edo ɗin, ba yanda ba su yi ba a tashi a gidan yaƙi sai ga shi dole tasa an tashi babu shiri, ita da yarana suna min godiya. Salim ɗin na cewa ba sai anyi min kayan ɗaki ba, nayi karaf kuwa nace sam bai isa ba, na wani hasala kamar wanda ya zage ni, na dinka fifiƙa ina masa masifar ai ba'a gidan babu ya tarar da ni ba, Abbaa ma ba zai yarda da zance ba, mahaifina zai yi min kayan ɗakina idan ma ya san ya siya ya aje ya kwashe abinsa ya fitar da su idan kuwa ba haka sai dai idan ba zan zauna a gidan nasa ba, ni kuwa ai ban manta gorin da Nazifi yay min ba sanda zai ƙara aure na cewan iyayen matarsa har kayan ɗaki sun mata ba irin iyayena ba da suka bar miji da ɗawainiyan komai. Saboda yanayin nisa zuwa can garin sai Sale yace zai ɗiba mutanensa suje Delta ɗin a haɗa kayan acan maimakon ace daga nan za'a a tafi, kuɗin mota ma kansa wani babban lamarin ne, hakan kuwa aka yi aka tafi da Yaya Al'amin da Abbayo, Salim ɗin yace akwai wurin zama a gidan nasa ba sai sun nemi hayan wajen kwana ba, Abbaa yace to gwara ayi tafiya ɗaya kawai tunda bikin ƴan kwanaki ya rage a tafi ayi jere gaba ɗaya, sanda ake fito da bahhunan kwanuka sai da nayi matuƙar mamaki, Ummani ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba har sai da na tambayeta ina ta samu kuɗi haka tace rufin asirin Allah ɗan abinda take tarawa ne, sai kuma gudumawar da ƙannenta da yayyunta suka aiko mata, kayan kitchen masu kyau da tsada ni har ce nayi ma ina zan kai su. Kwanansu biyar a can, ranar da suka dawo kuwa suna bawa Ummani labarin gidan, sai santinsa suke yi su maza ma kenan, Anty Shafa da su Anty Lubna da Maman Khairi duk sai lokacin suka ji rashin jin daɗin da Abbaa bai bari sun je tare ba, shi kuma yace ne da akwai ƴan uwa acan ne sai a tafi da su, to ba za'ai rashin hankali ba kawai aje a tarewa mutum a gida, matarsa ma ba zata ji daɗi ba. Abbayo na faɗin wallahi Matar Salim ɗin tana da matuƙar kirki, haka ta karrama su kamar ƴan uwanta, motsi kaɗan sai ta aiko yaranta su tambaye su ko suna da buƙatar wani abun, abinci kuwa har ci suka yi suka ture, yace kuma idan suka yi aiki suka gaji da kanta take zuwa tace musu ga babban falo can ta buɗe musu ko za su yi kallo, iya kwanakin da su kai sun mata shaida me kyau. Da daddare na samu Abbayo ina tambayansa ya fasalin gidan yake, yace min babban gida ne flat ba bene, ɓangarena bedroom uku ne kowanne da banɗaki a ciki, sai falo biyu da kitchen, amma fa kowanne ɗaki tafkeke ne, Yace babu laifi Sale yayi ƙoƙarin yin kaya masu kyau don duk zubin kayan turkey yayi sai kallon ƙurulla ne ma zai sai za a gane b kayan ƙasar waje ba ne, kuma bedroom biyu dukka an zuba kaya a ciki, dama yanda muka yi da su nace idan sunje sunga bedroom yafi ɗaya su kirani su faɗa min sai na tura kuɗi ayi min na ɗaya ɗakin ko ba mai tsada ba, hakan kuwa aka yi da ike ina dashi kuma ina adani na tura dubu ɗari biyar nace sai ɗakin ya zama shi ne nawa wancan kuma masu tsadar sai ya zama nasa. Abbayo har da tsokanata wai Kudrat ta fini kyau ita fara ce ƙal kamar ba ƴar ƙasar nan ba, mene mene ɗinsa dai, sai naji bala'in kishi da haushi ya kama ni har da guntuwar ƙwallana, ranar kuwa har fushi nayi da Salim yana ta kirana naƙi ɗagawa, yayo text nayi kamar ban gani ba. _________________________ _Kuyi haƙuri don Allah wallahi banji daɗin rashin post na jiya ba, tafiya nayi garin sakkowa a mota na faɗi na yi buguwan ƙashi a hannu, duk yanda na so na ƙoƙarta wallahi abin ya faskara, naga adu'oin ku na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi._ *B3ƘR10FT5* Fuska na tamke ina ce masa bana son irin wannan maganan kuma ya daina taɓa ni, ban aune ba kuwa kawai sai naji ya manna min kiss a saman goshi, nan fa na diririce nayi saurin ƙwace hannuna a nasa don a yanda na ke jinsa in ban wasa ba sai ya rungume ni. Fuskarsa ya shafa tare da cewan,"Baby mu tafi, mu tafi kafin a samu matsala, wannan ƙamshin na ki zai iya sawa na aikata ba daidai ba". Na kalla ƙwayar idonsa duk nema ya ke ya rikiɗe, ya ɗan ban tsoro ganin har rumtse ido yake yana cije fuska da kyau, kuma kawai sai jin iskar bakinsa nayi a gefen bakina yana faɗin,"Baby ƙamshin nan fa ya tayar min da sha'awanki, ina neman gaza controlling kaina wajen turmushe ki akan katifan can". Furucin nasa yasa duk jikina ɗaukan ɓari, na watsa masa harara ina ƙara cin magani, da sauri nayi ƙofa shima yay saurin fuzgoni har sai da na gogi da jikinsa, numfashi kawai yake saukewa kan ya kuma manna min kiss a kumatu, kana yace,"Ni Onochie ya zan yi da raina, yanzu haka ina ganin soft lips ɗin nan zan bar su, Baby please ko kaɗan ne". Ƙwacewa nayi na fice da hanzari, sai daga baya ya fito yana dariya wai ni matsoraciya ce mene don an fara lissafi daga ɗakin Yaya Al'amin, na harare shi kawai ban ce masa komai ba. A hanya muna tafe muna hira abinmu ta masoya, yawanci duk yana magana akan kai ni, yana tunanin ko a fara kai ni can gidana daga can sai ya kai ni wurin iyayensa ko kuma a fara kai ni ta wajensu in ya so idan ya dawo sai mu wuce daga can, ni duk ma yasa na kasa sakewa da shi yau ɗin, fagge muka je wurin da zan amso ɗinkunana, ba yanda ban ba akan ya bar ni naje na karɓo da kaina yaƙi, wai ba ya so na fita wani me ɗaukarwa kan zunubi ya kalle masa halal ɗinsa, na ce ai ban riga na zama ba sai ya sha murr kawai ya fice ya bar ni a ciki, ya jima sosai a shagon ɗinkin kafin ya dawo yana ce min,"Kin sa duk an ɗauka yaronki ne". Ina murmushi na ce,"To ai zan tura masa kuɗin ɗinkin". "Na ara za ki biya ni kayana, kuma cash na ke so in doller ba Naira ba". Murmushi nayi ina masa godiya, Calido ya biya da mu yace min yana jin yunwa, nima dama yunwar na ke ji, ai kuwa tunda muka shiga ido ya dawo kanmu, ɗaiku ne ba su tofa albarkacin bakinsu akanmu ba, har da masu satan ido su ɗauke mu vedio ƴan bani na iya a social media. Kuɗi ya kashe sosai a abincin da muka ci, ni da aka yi bill ma sai da na kallesa na ce kuɗin fa sun yi yawa Salim, sai ce yay zai zare a sadakina da za'a harhaɗa masa gudunmawa, wannan kuɗin ogansa ne yake ta bushasha da su. A hanya ya tsaya yay siyayyan kayan dubiya masu yawa, ya bani yace sai na kaiwa mara lafiyan, naji daɗi ƙwarai yau yanda yake ta min sai naji na ƙara son abuna tare da fatan Allah ya barmu tare, Zuwanmu asibitin Murtala na kira jikar Baaba Mai Ƙosai, ita ta zo ta rakani can inda suke kwance, ban wani jima sosai ba a wajensu na fito saboda na bar Salim a mota yana jirana. lokacin da muka yi sallama da Baaba Mai Ƙosai wacca ta rakoni tana ta min godiya, ina tafe kawai naji an faɗo jikina an rungume ni, na kalla matashiyar budurwar da ke maƙale da ni ina sa hannu in jayeta a jikina, har ga Allah ban gane wacece ba sai da ta ga nayi mata kallon ƙurulla sannan tace,"Anty Sa'ida Rumana ce". Ni da ta faɗi hakan ma sai ta saka ni a duhu, sai daga baya kuma na gane baki buɗe na ke kallonta kafin nace,"Rumana!". Sai ta ɗaga kai da sake cewan,"Ehh Anty Sa'ida, Rumanki fa". Mamaki ya ƙara kamani, lallai girman ɗan mutum ba wuya. "Rumana ke ce kika zama ƴan mata haka, Ya akai kika gane ni?". Kawai sai naji tausayin yarinyar ya tsarga min, na sake rungumeta kafin ta zame a jikina tana cewa,"Anty Sa'ida ko a mafarki naji muryanki sai na gane, balle kuma na ganki duk da kin sauya, farko ban ganeki ba sai da na tsaya dai naji muryan da kyau kuma matar da ta rako ki tana faɗin sunanki, Anty Sa'ida naga kin ƙara yin kyau sosai kamar ba ke ba". Wato har ga Allah ban tsammaci zan ƙara ganin iri iri Nazifi ba a duniyata har kuwa na koma ga Allah, ko fatan haɗuwa da wani na nasa bana yi, Murmushi nayi ina shafa kumatunta nace,"Me kike yi anan?". Da yanayin tausayi tace,"Ai mun daɗe anan asibitin, an kwantar da Iyam bata da lafiya". Nace, "Subhanallahi, Allah ya sawwaƙe". "Anty Sa'ida ban san gidanku ba ina ta cewa zan zo, watarana ma na biyo hanya sai ban gane ba". Na ɗan murmusa na ce,"Ayyah, ya school to". "Alhamdulillahi, yanzu ina jss 2 amma ba wancan makarantan da kika san muna zuwa ba, Jakara special primary school na ke zuwa yanzu, mun bar gidan Baba Ƙarami tunda jimawa". Haba ni dai nayi mamakin yanda na ganta yarkace yarkace, a raina sai da nace kamar ba yaran Alhaji Nazifi ba, ashe sun koma gaban iyayensu, Allah masanin dalili. Muna hakan sai ga Atika ma ta iso, itama ta girma yaran duk sun zama ƴan mata ƙirji ya fara fitowa, itama muka gaisa da ita, sai dai ita ɗin ta kasa sakewa da ni sai satar kallona da take yi, Rumana kuwa ta maƙale min a jiki tana ta min surutu. Maganan Rumanan ta katse min gajeran tunanina,"Anty yaushe za ki dawo gidan Baba Ƙarami, naji ance za ki iya dawowa". Lallai yaro yaro ne, Rumana kuma na daga cikin mahaukatan yara, ni kuwa idan ba gawata ba me zai mayar da ni gidan Nazifi, ko da ike ƙarshen hauka na wurin me mafarkin zan koma gidan Nazifi. Mun gama magana da su ina cewa su yiwa Iyam ɗin sannu, zan wuce sai naji suna ga Mama nan, na ɗaga kai na hango Yaya na tahowa, yanda take tafiya bugujin bugujin kamar wadda aka tarewa duk matsaltsalun duniya akanta ita ɗaya, kuma har ga Allah ban shaidata ba saboda yanda ta zaftare ta rame, duk ta fita a hayyacinta, tun kafin ta ƙaraso na ɗauke kai nayi kaman ban ganta ba, ita kuwa baki buɗe ta iso gabanmu tana dubana sama da ƙasa, mamaki bayyane ƙarara a saman fuskarta tana tafa hannu tace,"Wa idanuna ke gane min, Sa'ida!". Ta faɗa da muryan da ya fito da sautin murna. Wani yatsinen kallo nayi mata, fuskarta a sake ta gaida ni,"Sa'ida Ina yini". Na amsa mata babu yabo babu fallasa, sai naga jikinta duk yay sanyi, kamin ƙifta ido sai ga saukar hawaye saman kuncinta tana ce min,"Sa'ida na jima ina cewa zan zo gidanku sai dai abubuwan da ke ta faruwa yau da gobe na kasa samun dama, ashe da rabon anan zamu gana, kin ji labarin muna nan ɗin ne?". Furucin nata sai ya bani dariya, wai naji labarin suna nan, to ko naji na zo nayi musu me? Kaman ta gane zancen zucin da na ke yi ta sake cewa,"Wallahi ni dai sai naji nauyin ganinki, amma ina nan tafe gidan na ku". Nace,"To Maijidda me ma zai kawo ki gidanmu kuma". Tayi murmushi me ciwo da kuma jin amsawar sunan da na kirata da shi kai tsaye, tace,"To ai Sa'ida ya zama dole a zo gareki, to yanayin yanda rayuwar ke ta ƙwallo da mu ne kowa babu sukuni, wallahi muna cikin tsaka me wuya sai dai adu'a kawai, Ni dai Sa'ida ba sai nayi dogon jawabi ba ina me bada haƙuri akan abubuwan da suka faru a baya tare da neman yafiyarki, ni da mahaifiyata da ma dukka ƴan uwana". Nayi murmushin da ni ɗaya na san ma'anarsa nace,"Ah haba ni ai babu komai, yanzu ma banda Allah ya ƙadarta haɗuwarmu ai tuni na mance da ku balle batun mun taɓa rayuwa tare har wasu abubuwa marasa daɗi sun faru, ki manta kawai Allah ya kawo sauƙi cikin lamuran na ku, ni yanzu ai sai godiyar lillahi bana cikin wata matsala da damuwa". A sanyaye tace,"Haka ne wallahi duk wanda ya ganki zai shaida, banda nayi miki farin sani ma ai ba zan saurin shaidaki ba, wallahi kin ƙara kyau kamar sake halittarki aka yi". "Uhum". Ina faɗa ina ƙoƙarin barin wajen, ta dakatar da ni da faɗin,"To Sa'ida ni ina nema mana yafiya, haƙiƙa mun zalunce ki a rayuwa". Na ce,"Na yafe Allah ya yafe mu gaba ɗaya". Sai naga taji daɗi sosai. Nan take bani labarin yanzu ma ta dawo ne daga police station Fati ce suka samu matsala da kishiyarta abin dai babu daɗi tana can tsare wurin ƴan sanda, to kuma ma tana kan hanya aka kirata Barira ƴarta auren ya mutu, Uwar mijin ta sakota gaba akan rashin haihuwa to yanzu can zata tafi taje ta taho da ita wai duk sun watso mata kayanta waje, bayan cin mutuncinta da zarafinta da suke yi ko da yaushe yanzu har suna cewa ma za su yi ƙararta saboda ƴar ƙanin mijinta da aka bata ruƙo ta ƙala mata sharri. Nace,"Allah sarki". A kunyace ta sake cewa,"Don Allah Sa'ida kifa yi haƙuri ko yawun bakinmu zai ƙare wajen baki haƙuri bamu yi komai ba". "Hmmm ni fa Maijidda kin ganni a rayuwar nan tawa da na ke cikin jin daɗi da walwala na mance da ku da abinda ku ka min, yanzu ma ban da kun shaida ni zancen gaskiya daga ke har yaranki babu wanda na gane". Sai ta shiga roƙona akan in daure in ƙarasa na duba Iyam, na ce mata ai bani ɗaya ba ce tare da mijina na ke, furucin da yasata zabura amma haka ta dake ta shiga taya ni murna har da cewa amma har nayi aure ba su da labari, a raina nace uhmm ana nan dai har yanzu da ƙarancin tunani, taron girma ai mutanen arziƙi ake gayyata ba na tsiya ba. Tare da ita muka je wurin Salim, yana daga cikin motar ya buɗe ya zuro ƙafa ɗaya waje yana ce min,"Baby yanzu na ke shirin biyo ki ai, kin barni ni ɗaya babu daɗi?". Na ce,"Sorry Sojana, ga wasu bayin Allah ku gaisa". Yayan ta duƙa ita da yaran su ka gaida shi, yanda take faman gaisuwar ka rantse irin almajiran nan masu baran kan hanya. Ina ta kallonta ni dai a raina sai mamaki na ke yi, mace ƴar gayu da ƙwalisa amma kalleta fuskar hijabi ma a karkace, na kasa yiwa Salim bayanin wacece, ban san me zai iya faruwa ba idan nayi hakan don har ga Allah yana nuna min tsananin kishinsa akan tsohon mijina, sai Allah yasa ma bai tsaya tambayana ba ya zaro kuɗi masu yawa wanda a ƙalla na san zasu wuce dubu goma yace na basu. Ai kuwa kamar anyi mata bushara da aljanna sai gata ta koma ƙasa ta duƙe a gabanmu tana zuba godiya da adu'a, to ina ruwan zuciyan da bata da tsatsan komai a cikinta, sai duk naji mugun tausayinta ya kama ni, idona ya cika da ruwan ƙwalla ganin tana hawaye, kana dai ganinta ka san ba'a jin daɗin rayuwar ana tsaka me wuya. Sai da ta tafi ina kame kame nace da shi zan je na duba Mamarta ce aka kwantar, yace muje tare sai naji ƴaƴan cikina sun kaɗa, ina tunanin abin ce masa aka kira shi a waya yace daga wurin aiki ne naje kawai amma kar na jima, ya koma cikin motar ni kuma na kama hannun Rumana muka wuce. Muna tafe tana bani labarin makarantar islamiyarsu, littafan da ake musu bata jin wuyarsu ta riƙe karatun da nayi mata, jarabawarta ma duk ta biyu take zuwa, ni dai jinta kawai nake yi, dukkan tunanina ya tafi akan ina Nazifi da ya bar Iyam take kwance a asibitin Murtala bai kai ta babban asibiti na kuɗi ba, shi kuwa yana me? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, da naga yanda Iyam ta koma wallahi sai da na nemi ƙarfen gado na dafe har na zube ma ban sani ba. Jikina ya kama rawa tsoron duniya ya shige ni, Lubabatu ta taso da sauri ta riƙo ni, abinka da me ruwan ido tuni hawaye suka wanke min fuska, murya na rawa nace,"Lubabatu me yake damun Iyam?". Sai itama hawaye suka sakko mata tace,"Wallahi ciwon kansa ne na hanta, kinga duk yanda ta ƙare ko". Na rufe ido ina girgiza kai, sosai ta bani tausayi, ko gane wanda yake kanta ba tayi, lamarin ya matuƙar taɓa ni Allah dai yasa mu gama da duniya lafiya. Kusan mintina goma wajensu kafin nayi musu sallama, ban taho ba sai da na kira Sister Khadija ta haɗa ni da Yayarta da ke aiki anan asibitin, nace mata don Allah ga wa'annan bayin Allah'n take taimaka musu, Lubabatun taji daɗi sosai har ta kira Malam ta shaida masa, yay ta mini godiya yana cewa ya so ace yana nan ya ganni yaji daɗi, na karɓi account number ɗin Lubabtu na tura mata 20k na ce don Allah ta bawa Malam 10k, sauran kuma sayi wani butaƙan da shi, godiya ta dinƙa min kaman yawun bakinta zai ƙare. Ta rakoni a hanya take faɗa min ibtila'in da Nazifi ya gamu da shi, wai Zahra'u ta yashe shi ta gudu ta barsa, ƴaƴansa biyu dukka ta hana shi, yanzu ma dai yana nan shima bai da cikakken lafiya, jininsa ne yay mugun hawa, hannunsa guda ya samu matsala dalilin faɗuwan da sanda aka ce ƙaramar ƴarsa ta ƙone, ana dai ta so ayi masa hoto a gano me ya samu wajen to ba'ayi ba har yanzu saboda matsalar rashin kuɗi, dama ga banki na binsa maƙudan kuɗaɗe, ga shi shagon da yake gadi an haura anyi sata an ce da sa hannunsa lamarin dai babban lamari ne, yanzu haka anata cuku cukun gano gaskiya saboda sun ce ba zasu yarda ba sai ya biya su duk ɓarnar da aka yi, take cewa wallahi ta tabbata har da hakkina, tana ta roƙona akan na yafe musu, na ce,"ai ni Lubabatu ba ki min komai ba wallahi, zaman da muka yi ba zan taɓa manta alkhairinki gare ni ba". Tace,"To don Allah na yafewa Iyam da Yaya Ƙarami".nayi murmushi me ciwo da takaici na ce,"Iyam ma ai na yafe mata". Tace,"To Yaya Ƙarami fa? Wallahi Sa'ida ba kiga ba duk yana cikin damuwa, ko ranar nan ina jinsa yana faɗin yayi nadamar abubuwan da ya aikata miki". Wani murmushin kawai nayi nace,"uhumm". Har bakin mota ta rakoni, suka gaisa da Salim itama sai da ya bata kuɗi, haka tayi ta masa godiya itama cikin jin daɗi tana gaya min haɗuwarmu tayi musu rana saboda yanzu haka tun shekaranjiya ake neman kuɗin da za'a siya alluran Iyam da scanning ɗin da za'a mata, bayan nan tana faɗin ta taya ni murna sosai da ci gaban da na samu. Ni dai tunda na shiga mota hawaye na ke ta yi, matuƙa na tausayawa Iyam, haka na tausaya musu dukkansu, Nazifi ne kawai banji komai ba a kansa. Salim kuwa na ta complain akan da ya san da haka bama zamu je asibitin ba, ban iya masa magana ba har muka ƙaraso gida, yay lallashin duniyar nan amma ina ni dai na rasa ta yanda zan dakatar da hawayena zuba, haka ya haƙura muka yi sallama zuƙatanmu duk babu daɗi ni da shi. Ko da na shiga gida ma duk sai suka yo kaina da tambayar me ya faru, na dai ce musu rasuwa aka yi a asibitinmu na shige ɗaki kawai na rufo ƙofa. Wayata na ɗauka na kira Lubabatun don sai da muka yi exchanging number wanda Malam ne yace ta karɓa masa lambata, tana ɗagawa nace ta lissafa min kuɗin bill ɗin na su sai ta tura min account number, haka na tura mata dubu asharin a madadin dubu arba'in da ake nema, to nima babu kuɗin ne da dukka zan tura mata. Ba jimawa sai ga kiran Yayan Shago wanda yake ta min godiya, shima yana bani haƙurin abubuwan da suka faru, ya haɗa ni da Malam wanda yace yana matuƙar godiya da abun arziƙin da na yi musu haka yay ta shi min albarka, yace ai a kasuwarsu ma an faɗa masa Abbaa yaje nemansa bai nan amma yaga ya bar masa invitation, nan yay ta min adu'a tare da fatan alkhairi, nayi godiya kafin nan muka yi sallama. Da magriba na fito zan yi alwala, sanyin magriba duk yasa an shishshige ɗaki, na aje buta zan tsuguna sai ga yaro ya shigo, yace wai an aiko shi wurin Sa'ida, na ce masa menene ya miƙo min baƙar leda an nannaɗeta kamar laya yace wani ne a waje yace a bani. Karɓa kawai nayi, wa zai min aike idan ba Salim ba, ni kuma a yanayin da na ke ciki ban jin zan iya fita na sameshi. Na idar da alwalar na shiga ɗakin Ummani na sauya kayan jikina, take nuna min buhun kayan miyan da ƴan ƙauye suka ƙara kawowa, nace an gode, bata lura da yanayina ba nayi saurin fita gudun kar ta tsare ni da tambaya. Sai da na idar da sallah tukunna na kunce ledar, takarda ce a ciki ƙarama, na warwareta ina duban gajeran rubutun da ke jikinta. _"Amincin Allah da yardarsa su tabbata a gare ki, ina mai wannan rubutu ne gareki yayin da idaniya ke zubar hawaye haka kuma zuciya ke cike da nadama da tarin danasani, haƙiƙa tunda kika bar rayuwata na ke ta ganin ibtila'i daban daban, cikin shekaru shidda har yanzu na kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali, babu jin daɗi babu farin ciki, sai daga baya na ankare da dukkan laifukan da na aikata miki sune ke dawowa gare ni, tabbas hakkinki kaɗai ba zai bar ni sukunin rayuwa ba, ni na sani na zalunce ki, zaluncin da sai dai Allah yay miki sakayyya kawai, na so ace na samu wata dama da zan maido da ke cikin rayuwata domin na gyara kuskurena sai dai lokaci ya ƙure min, bakin alƙalami ya riga ya bushe...na samu labarin kin je kin duba mahaifiyata, na gode Allah ya saka miki da aljannah, kuma naji an ce kin yi aure da irin mijin da kika aura, tabbas har zuciyata naji miki daɗi na kuma tayaki murna, Allah yasa albarka ya tabbatar da alkhairi a rayuwan aurenki, ina me yi miki adu'a tare da fatan samun rayuwa ingantacciya a gidan aurenki, ya dawwamar da ke a farin ciki da kwanciyar hankali, kazalika ba zan ƙi sanar da ke cewa rashinki a rayuwata wani babban giɓi ne da ba zai taɓa cikuwa ba sai da ke, na soki, ban kuma san ranar da zan daina sonki ba, don Allah ki yafe min, ki yafe min ko na samu sassaucin bala'in da na ke fuskanta a rayuwar da babu ke a cikinta, ki yafe min ko na samu salama a lahirata, na rasa da idon da zan iya fuskantarki, ina jin kunyar ganinki, ina kunyar haɗa idanuwa da ke...tsohon mijinki Nazifi Bala Mai Kalwa"._ Tun farkon fara karatun naji zuciyata tayi rauni, kafin na gama karantawar tuni hawaye ya jiƙa rabin takardar, na shiga rera kuka a hankali hanci na ta zubda majina, hawayen da ban san dalilinsa ba, kaina jingine da bango idona a rufe hoton Nazifi kawai ke haska min, hoton da na ke ganin laɓɓansa suna karanto min wannan rubutun. A gefe ɗaya kuwa zuciyata ta matse da tausayinsa da wani abu da ke harbawa a cikinta wanda ban san menene shi ba, kuma kamar an tsikare ni haka na miƙe na ɗauka mayafi, ina fitowa nayi kiciɓis da Ummani wadda ke ce min,"Ke lafiyarki kuwa? Naji ma kaman kukan ki shi ne na taso". "Ina zuwa Ummani". Na faɗa da karyewan harshe, nayi saurin fita, haka na gama leƙena a ƙofar gida, har ɗaya ɓangaren na tsallaka amma banga ko da inuwar Nazifi ba, me yasa zai yi min haka? Me yasa zai zo ɗauke da wannan kalaman a cikin takardar da ke ɗauke da rubutunsa kuma ya kasa jirana? Ban san me zan ce ina ji a tare da ni ba, kamar yanda ban san yanda zan kwatanta yanayin da na tsinci kaina a ciki ba, Ummani na tsaye inda na barta, ta ruƙoni ganin irin yacca na ke zubar da hawaye. "Ke menene wai, wani abu ya faru ne?". Kaina na kifa saman kafaɗarta ina cewa,"Ummani Nazifi ne, Ummani yana cikin wani hali, kuma ya zo ƙofar gidan nan ya tafi bai bari mun yi magana ba". Ƙumm naji kaina ya ƙwalu da bangon tagar ɗakina, haka murfin tagar ta doko min fuska. Sautin tsakin Ummani ya shiga dodon kunnena ta wuce ta barni tana faɗin,"Allah ya shigo da ubanki ki yi masa wannan zancen, saboda wulaƙanci saura kwana biyu ɗaurin aurenki ki tayar da maganar tsohon mijinki, shi algungumin da can bai san da zuwa neman yafiyar taki ba sai yanzu? Ke kuma da babu cikakken tunani da hankali shi ne har da iya barin kalaman ƙaryansa suyi tasirin da za su ɗarsa tausayinsa a zuciyarki, mtsswww". Bayanta na bi da kallo kawai har ta wuce ɓangaren Baba Sabi'u, yanzu kenan laifi ne don halin da Nazifi ke ciki ya taɓa ni? Ɗaki na shige na silale na zauna daɓas kan katifa, na kalla wayata da ke ƙaran shigowan text, ina dubawa naga sunan Salim kawai sai nayi cilli da wayan, na zuƙa wani irin numfashi, na rufe fuskana da dukka tafukana biyu, daki daki rayuwar baya na dawo min hotonta na haska min, haka daki daki kalaman rubutunsa ke maimaituwa cikin kaina, haka kuma labarin da Lubabatu ta bani na halin da yake ciki na haska min a ƙoƙon ka, duk garin ƙaƙa ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali haka? Halin da na magani ma ya gagare shi? halin da har ta kai shi ga cin bashin banki, halin da har ta kai shi ga gadin shago, duk ina tarin dukiyarsa? Ina tarin dukiyar da har muka rabu ban san adadinta ba? sai naji zuciyata ta ƙara tsinkewa. "Na manta da komai, na goge komai da ga raina, na yafe maka, na yafe maka, baka da sauran hakkina". Haka na zama sukuku kamar wacca aka yiwa mutuwa ko take rashin lafiyan da yaci ƙarfinta, Abbaa ma da ya dawo sai da ƙyar na iya miƙewa na fita yi masa sannu da zuwa saboda jikina da na ke jinsa ya mutu, ga ƙirjina bugawa kawai yake yi, ban san meke damuna ba, ban san dalilin sauyar yanayin farin cikin da na ke a ciki ba, Salim ya kira ni ya kuma kira amma ban ɗaga ba, bana jin kuma ina da buƙatar jin muryarsa... *B3ƘR11FT5* Washe gari kiran Safiyya ne ya farkar da ni, na manta ma da batun zamu je ƙunshi da gyaran kai, jin ina bacci ta kama masifan dama ta san halina, sai mun je kuma mun daɗe acan ita na cikata da mita, na bata haƙuri na ce sai ta ƙaraso kafin ta zo ma na gama shiryawa. Zaune na miƙe ina murza idanuna da ke cike da bacci, on period na ke ko da asuba ban farka ba, nayi azkar ɗina na tofe jikina, sai a lokacin abinda ya faru jiya ya shiga dawo min, na kalla gefen filona ina kallon takardar da Nazifi ya yo min aike, wani mugun haushi da takaicin kaina ya kamani, lallai akaina na yarda mutum na haukan gaske na ɗan wani lokacin, ban da hauka da na fita neman Nazifi uban me zan masa? Kukan da nayi kuma na uwar menene? gwara da Allah yasa ma bamu haɗu da shi ba don ina ga da sai na kusa kashe kaina saboda baƙin ciki, takardar na ɗauka na yayyaga nayi gutsi gutsi da ita, akanta dai na huce takaicin rashin tunanin da nayi jiya. Wayata na duba na ga uban misscalls ɗin Salim, tunda na ke da shi bai taɓa bari min miscalls irin haka da yawa ba, kuma na san duk ya damu ne da yanayin da ya tafi ya barni a ciki, lokacin ma da yana da dama ba zai tafi ɗin ba, sai naji ya bani tausayi, haushin kaina ya ƙara kama ni, ban kyauta masa da abinda na masa ba, kawai dai na san duk wanda yaga halin da Yaya suke in har kana da zuciyar imani sai zuciyarka ta karye, lokacin da zaka taimaka musu ɗin ma ba sani zaka yi ba, amma abin takaicin da akan tausayin Nazifi na ƙi picking call ɗinsa, hannu nasa na mari fuskata. Ina shiga message ma naga messages ɗinsa har biyu, ɗaya na lallashina ne da kwantar da hankali, yana faɗin in bar yawan saka damuwa a raina, marasa lafiya ne kamata yay nayi musu adu'a, ɗayan kuma yana faɗa min ya koma tun a daren jiyan sai ranar ɗaurin aure zai biyu jirgi da safe ya taho kafin lokacin ɗaurin aure, kuma za su shiga daji ne ba lallai in sameshi a waya ba ko da na kira shi, raina ya ƙara ɓaci da rashin kyautawar da nayi, na tura masa text ɗin adu'a ina aje wayar na tashi, ban basa haƙuri ba tun da dai ba laifi nayi ba. Yau ɗin sai na ke jina na tashi da wani ƙwarin jiki, lokacin da na fito tsakargida rana ta ƙwalle nayi mamakin irin baccin da nayi, na yiwa su Anty Lami sannu da aiki, gaba ɗaya tsakar gidan ya zama babu masaka tsinke sai ka tabi kana zaka wuce ana baka hanya, gaskiya mu ɗin ƴan dangi ne, Ummani na da tarin ƴan uwa masu karamci da haɗin kai. Ummani bata ɗaki muka gaggaisa da mutanen cikin waɗanda ke ta tsokanata Amarya ƴar hutu. Na wuce ɓangaren Baba Sabi'u can na samu Ummani suna aiki ita da Umman su Hindatu, muna cikin gaisawa da su sai ga Hindatu ta fito a guje ta faɗo jikina tana murna, nima murnar na kama yi ina tambayarta zuwan yaushe tace min ai ƙarfe takwas ma anan tayi mata, ta zo tana ta buga ɗakina ina can ina baccin mutuwa. Jin ta ambaci ƙarfe takwas na waro ido ina faɗin,"Wai har takwas ta wuce kenan". Don ni ko da na ɗau wayata hankalina bai kai kan lokaci ba. "Ummani bara naje na shirya zamu wuce wurin Lalle, Safiyya zata biyo ta ɗauke ni tana kan hanya, tsammanina duk bai wuci takwas ɗin ba yanzu wallahi". "To Allah ya tsare, kin dai gama haɗa kayanki kin kwashe ko?". Goshi na dafe don gaba ɗaya na mance ma da sauran aiki a gabana, shashancin da na buga daren jiya yasa ni baccin da ban shirya ba, don wani zazzafan ciwon kai na kamu da shi, Abbaa ma da ya dawo ban samu damar fita nayi masa sannu da zuwa ba, kuma a lokacin ma na ɗan ji tsoro ne kar Ummani ko ta yi masa wancan batun, in je yaci mutuncina Abbaa ne bai ƙi ya buge ni ba ma. "Zan ƙarasa haɗa su Yanzu kafin Safiyya ta ƙaraso". "To ni dai ki tabbata kin gama duk abinda za ki yi da wuri Sa'ida, kinga jiya Abbanki sai da ya jaddada min ya zamana kin gama komai, goben ana ɗaurawa za su wuce da ke, ƙunshin nan ba lallai ne ku dawo da wuri ba kuma shi ma sai da ya bar min sallahun in sanar miki kar kije ƙunshi ki dawo masa da daddare". Kalaman nata suka sanya jikina yin sanyi. "To an aje min abin karyawa?". "Sai dai ki leƙa gidan Yusra idan kin samu to, in ba ki samu ba kuma ki siyo indomie ki dafa, kunun ma da aka yi babu inda yaje, kinga sai Umman Hindatu ce ta kawo awara aka ƙara da ita". "Bari kawai idan mun je can na siya wani abun". Umman su Hindatun na cewa ko zan shiga kicin na dafa wani abun nace mata a'a bara naje gidan Maman Yasmin ɗin ba za'a rasa a can ba, muka wuce ni da Hindatu, naji daɗi sosai itama ta kawo min gudunmawar zannuwan gado guda biyu da jug ɗin roba. Ita na bari tana kimtsa min wasu kayana da zan ƙarasa haɗawa, lokacin da na fito a wanka ma har ta kammala, sai ga ɗakin yay fayau, jikina ya ƙara yin sanyi ganin da gaske dai barin gidan zan yi, ina son ɗan ƙaramin ɗakin nan nawa fa, na gama shiryawa na fito na tafi gidan Maman Yasmin ni da Hindatu. Ai tun a ƙofan gida yara suka tsare ni Anty Sa'ida kuɗin party, sai arar kuɗin nayi hannun Hindatu na ba su don ko sisi bana magani, sauran kuɗin da na ke tattalawa na rabarwa dangin Nazifi jiya, na nemi suna hankalina ya kwanta, ko da yake ba faɗuwa ba ne taimako nayi har zuciyata saboda Allah, kuma Allah zai ninka min ya kuma bani lada. Ban samu abincin ba sai wata guntuwar taliya na dafa naci da mai da yaji, ina gama ci kuwa sai ga Safiyya, faka faka na wanke hannu na fita muka tafi. Kasa ɓoye mata abinda ya faru jiya nayi ina bata labari, da ta lailayo wata ashariya me zafi ta yarfa min sai da na kusa buɗe motar na faɗa waje, har Ilham sai da ta tsorata nayi saurin cafo yarinyar da ta saki. "Safiyya za ki yarda da yarinya taji ciwo". A fusace ta bige hannuna a jikinta,"Dilla Malama banza shashasha yi min shiru, Sa'ida ba ki da hankali ba ki da shi sam, ji na ke kamar na shaƙe miki wuya ki daina moruwa a duniyar nan, ke yanzu har wani kiga irin Nazifi ne kima tsaya ki saurare shi, wai har kina faɗa min kin je kin duba Uwarsa yen yen yen, Allah da ina wurin sai na ƙwaci bindigar Brother na harbeki gwara na rasa ki in huta da takaici da baƙin ciki, idan ma ba ki mutu ba ƙilan ƙarar bindigan yasa ki razana ki dawo hankalinki don naga alamar ƙwaƙwalar ki babu komai a ciki sai dusarar asara, shegiya ƴar bura'uba da ma da kika fito neman Nazifi kin zame a ƙasa kin yi targaɗe kinga sa dawo su taimaka miki ai". Tagumi na zabga kawai ina dubanta, wannan masifar yanda take ɗaga murya tana faman huci da tada jijiyoyi idan a adaidaita muke ai sai me motar ya sauke mu, a hakan ma bata huce ba sai da ta figo wuyan rigana ta dudduke ni nayi saurin ƙwacewa kar tasa mu buga accident. "Haba Beb sorry mana, ba dai ya wuce ba, kuma nima sai letter na ke ta jin haushin kaina wallahi, don ina ga da na samu ganinsa ma kukan baƙin cikin da zan yi sai na iya haɗiyar zuciya". "Dilla can rufe min bakinki me warin tsiya kafin in ragargazo miki haƙoran gaba, kuma sorry for your self don ni da kika ganni ban sallama kaina wa wasu asararru ajina da darajata sun zube ba, shegiya gwarama a kwasheki a kai can garin inyamuran ai don idan kika zauna nan satan hanya za ki ke yi kina zuwa wajensu tunda karen su ya cinye miki zuciya". Na musamman tayi parking tana faɗin,"Ai yanda kika ga wannan shegiyar Yayar tasa kamata yay ki fakaici idon jama'a kisa ƙafa ki kwarfe asararriya a ƙasa, ki bi ta kan ƙafarta ki wuce, akwai uban da ya isa ya biyoki ne a yanda kike? Sai dai ma ta ɗaure kanta idan ta nemi ta ɗora miki, kai Allah nah ka bawa banzar nan ta kusa da ni hankali, doluwar banza da wofi kawai, a haka kamar ba shashasha ba, ina ji kamar na buɗe motar nan na tankaɗa ki waje ne". "To aikata mana Yayanki kika yiwa asara ai". Sai kuma taci gaba da jarabata, yi take yi bata ko numfasawa. "Idan da ina nan na rantse miki da Allah sai na fita na yiwa Nazifi ihun kwarto, kashh, yanda za'a rugurguza shege a ƙofar gidan nan ai ko ni sai na shiga na ɗakko murhu". A hankali na ce,"A ke dai manta baya". Harara ta watsa min, kuma har muka isa beejay bata ƙara yi min magana ba, ni ɗaya na dinƙa maganata ina wa Ilham wasa. An mana ƙunshi me kyan gaske, ni bana son wani na salatep na zane aka min, duk wanda ya shigo shagon kuwa sai ya tofa wow amma dai ke amarya ce, ƙawar arziƙin nawa ce dai bata ce ƙala ba, da ana kwancewa ma na nuna mata kauda kai tayi, kuma ita ce me nanatawa mai lallen ta ƙure basirarta akaina ko nawa ne zata biya. Gaskiya wajen sun iya aiki babu ƙarya, hatta gashina da aka wanke aka gyara sai da nace anya kuwa nawa ne, sai lokacin Safiyya ta samu damar magana tace ayi min ƙanan kitso nace a'a ba zan iya zaman ba, yanzu kafin a gama ma sai mu wuce bayan isha'i, ina gudun faɗan Abbaa, nan kuwa ba kitson ne ban so ba, Salim ne yace kar nayi kitso yafi son gashina a haka. Bamu koma gida ba sai daf da isha'i, har ƙwalla nayi wajen yiwa Safiyya godiya, ita ta biya kuɗin kitso da ƙunshi har spa da ta dage sai anyi min, kuɗi ba kaɗan ba kuɗi masu yawa. A daren bayan dawowata Hindatu ta raka ni na shiga wasu gidaje da suke mutunci da Ummani sosai aka zama kamar ƴan uwa, kowanne gida na shiga kaji adu'a me daɗi ana yi min, muka dawo nan ma aka saka ni gaba da ƙarasa shanye wasu magunguna da wanda har wanka nayi da shi, ni da kayan sawata duk sai da aka yi mana turaren ƙaiƙayi koma kan masheƙiya. Ban samu zama ba sai ƙarfe goma tukunna, lokacin kuma kewar Salim duk ta cika ni, yau na kira wayarsa yafi ƙarfin a ƙirga bata ko tafiya, na masa text har sau uku sai dai na san da ace ya gani zai min reply wajib ne, amma ban san ba ko jiya yayi fushi ne shi ne zai rama shima, na kasa daurewa sai da na tura masa text na ban haƙuri ina faɗa masa yau nayi kewansa musamman golden voice ɗinsa. Duk sai nayi wani sukuku bana jin daɗin raina, yana ta ɗokin nayi lalle na tura masa ya gani, to a online ɗin ma ba ya kai, rabonsa da hawa tun safiyan jiya, na rasa meke min daɗi, na rasa natsuwata ina ta saƙe saƙe cikin raina, har Safiyya sai da na kira tace min in kwantar da hankalina inda suke ne babu network ɗazu ma da ta biya gida taji Baba na faɗin yana ta neman wayarsa bai samu, amma Sir yace masa sun yi magana da shi ta oba oba irin wannan abar da sojoji ke magana da ita. Yau kam ba batun kwanan ɗakina don anan aka jibge miyar abinci gobe, da kayan abinci da kayan gara. Na fito da zummar tafiya gidan Maman Yasmin na ji inaa yau a kusa da uwata zan kwana, dolen dai haka na wuce na tafi don tun da baƙin nan suka zo ta bar musu ɗakinta ta koma ɗakin Abbaa, to ina ni ina batun shiga cikin su na kwana. Washe gari tunda wuri kafin ɗaurin auren ma sai ga mutanena ƴan amana sun zazzo, Hassana Tijjani ce farkon zuwa don ita ƙarfe tara ma anan tayi mata ita da yaranta, can sai ga Maimuna itama, ƙawayena dai tun na secondry school waɗanda ake tare har yanzu, Safiyya sarkin kishi tuni ta haɗe rai tana aikin ciccin magani, faɗa take wai akan mene Hassana Tijjani zata rigata zuwa, haka ta dinƙi mitarta har sai da suka taɓa da Hassanar don dama sun saba indai akaina ne, suyi ta rigima da juna kamar yara, ni da Maimuna muka zama ƴan kallo don idan suna yi ni bana saka musu baki. Lokacin da na ke fitowa daga wanka lokacin ƴan asibitinmu suka zo su Maman Nana da su Sister Khady, su dai shidda haka suka yo zuga suka taho, suma sun yi min kara da na su gudunmawar na frame da aka sa hotona da na Salim, ni da uniform na asibiti shima da uniform na sojoji, wanda na rasa ma ai na suka samu nasa hoton, merging aka yi wanda yay editing ɗin ya iya sosai ba zaka taɓa cewa haɗa hotunan aka yi ba, da 25k ɗin su da aka haɗa aka ce a bani, nayi ta musu godiya kuwa, sosai naji daɗin kyautar tasu, ban ma shirya ba na fara kai su gidanmu suka gaisa da Ummani, dama Abbaa na ƙofar gida da shi suka fara gaisawa, sai ce min suke sun ji daɗin adu'an da aka musu. Muka baro gidanmu muka shiga nan maƙotanmu gidan wata Umman Habu, nan muka yi zaman mu da mutanena, don ko gidan Maman Yasmin ma ba wajen zama, gidanmu cike itama gidanta a cike, Hassana Tijjani ta kwaso duk abubuwan buƙatana daga gidan Maman Yasmin ɗin ta kawon nan, Safiyya kuma ta tafi ɗakko me min kwalliya duk da nace mata ni bana so, abun da ba dinner ko party ba tace wallahi sai anyi. Ƙarfe sha ɗaya na ranar lahadi, cikin watan ƙarshe na shekarar dubu biyu da ashirin da uku, dubban mutane suka Shaida ɗaurin auran Lieutenant Salim Sadiq Oluwa da Amaryarsa RN Sa'ida Salman Madobi akan sadaki dubu ɗari biyu lakadan. Masha Allahu ɗaurin auren ya tara dubban mutane, don gaba ɗaya kan titin layin kashe shi aka yi sai zagaye aka koma yi, duk wanda ya zo kuwa sai ya tambayi ɗaurin auren wa ake yi haka. Abbaa har sai da yayi mamakin irin jama'ar da wasu ma zai ce bai san daga ina ba, taro kamar da aljanu, kowa kuma ya zo sai ya miƙo masa hannu an gaisa, tawagar mahaifin Salim kuwa ba zai iya cewa ga adadin su ba, motar sojoji kamar tayi magana jiniya kawai kake ji na tashi a faɗin unguwar. Ni dai tunda aka shigo ana ce min an ɗaura aure naji jikina ya mutu, ban san sanda hawaye ya sakko min ba. An gama min kwalliya a sa'ilin sai ga kiran Salim wanda rabona da shi tun shekaran jiya, sai sannan hankalina ya kwanta da naji muryarsa, duk da fushi na ke tayi da shi, fushin nawa ya gushe dalilin jinsa da nayi cikin farin ciki mara misaltuwa, tunda na ke da shi ban taɓa jinsa a irin yanayin murna da annushuwa ba irin haka, yana ta ce min nima in godewa Allah da ya nuna mana wannan rana. Yace ga shi ya yakice da ƙyar ya shiga mota in kunna data muyi vedio call ya ganni, nima ɗin kuma son ganinsa na ke nace ya kira a ta Safiyya nawa babu data. Wani kallo da ya kafe ni da shi ta cikin vedio call ɗin kamar zai fizgo ni, yana ta faɗin nayi kyau ina ma yanzu zai tafi da ni, shi duk ya ƙosa akai masa ni, na ce bayan kana bakin aiki, yace ai sai mu kwana a otel ɗin da suke, na ce a'a ni na fi so mu raya darenmu a cikin gidanmu kan gadonmu na sunnah ba na otel ba. Shima ina ta faɗa masa yayi kyau sosai a babban rigan da yasa, ya cire hulan yana nuna min askin su na sojaji da bana sonsa, ba ranar da bana ƙorafi akai, yace ya so yayi irin wanda na ke so to ba yanda zai yi da Emeka ne. mutane anata kiransa, Sir ma yana nemansa za'ai hotuna, da abokansa haka dole ya yanke kiran, bayan ya sanar min cewa ya bawa Khalid Yayan Safiyya Ticket ɗinmu, can garinsu za'a fara kai ni Anambra wajen iyayensa, zan kwana acan washe gari akwai igbo day da Kakarsa ta haɗa za'a yi, da daddare kuma sai a wuce da ni can Delta gidana, abokansa kuma sun haɗa masa dinner na sojoji da za'ayi ranar da aka kai ni. Cikin gidanmu kuwa sai guɗa ake yi anata taya ni murna, na so ace Salim ya samu shigowa an mana hoto tare da mahaifana to sai bai samu dama ba suna ta sauri za su koma can Abuja fadar shugaban ƙasa. Taron da aka yi a gidanmu sai wanda ya gani, Alhamdulillahi taro yayi masha Allah, ni kaina na fi farin ciki a wannan ranar sama da wancan lokacin, kowa ya shigo adu'a da fatan alkhairi yake min, abinci kuwa shiga da fita da shi kawai ake yi, ba wanda zai ce bai ci ya ƙoshi ba. Bayan dawowar ƴan ɗaurin aure Abbaa yace na shirya nan da awa guda za'a zo a tafi da ni, yace da Ummani kuma a samu mutum biyar da zamu tafi tare da su. Yaya Al'amin ya shigo yake cewa Salim ɗin ya kira shi idan da kayan da za'a tafi da su akwai mota da zata tafi can garin na su yanzu. Aka shiga aka fito da akwatunan lefe na da kayayyakina dukka wadanda zan tafi da su, sai kayan gudunmawa da aka bar bani da na wajen Ummani dukka aka haɗa aka tafi da su, kayan gara kuma Ummani tace a bari sai zamu tafi sai a tafi da su. Ƙarfe Ɗaya na gama shiryawa cikin wani swizz less maroon colour me tsadar gaske, ga shi Habibu yay min ɗinki na garari, Anty Saim ta ɗaura min lafaya milk colour akai, aka fito da ni daga gidan Maman Yasmin zuwa gidanmu, ƙamshi ne kawai ke tashi duk ta inda na gimla, muna shiga muka wuce ɗakin Abbaa ni da Safiyya, yana zaune bisa dardumar sallah a sa'ilin, da rediyonsa a kunne sabuwa wadda na siya masa babu jimawa, na zauna gabansa Safiyya ma na zaune a kusa da ni, muka gaida shi lokacin itama Ummani ke shigowa. Yanda na ke jina tamkar yau ne karon farko da nayi aure a rayuwata, musamman jin irin nasihar da Abbaa ya shiga yi min kamar a auren farko. Duk yanda naso riƙe kukana kasa riƙe shi nayi, hawaye kamar an kunna fanfo sai sauka yake a kuncina, gaba ɗaya yanayina ya canja jikina yayi sanyi kamar sabuwar amaryar da bata taɓa zuwa gidan miji ba. Ummani ta amshe maganar Abbaa tana kallona tace,"Nasan duk kinji abinda mahaifinki ya faɗa, mun amince da hankalinki da nutsuwarki, auren farko ma da kike da ƙarancin shekaru da wayo da kuma ƙarancin ilimi kinyi ƙoƙari wajan riƙe sirrin ki da na mijinki duk da wahalar da kika sha, balle kuma yanzu da kika daɗa hankali, kika ƙara gogewa da ilimi da sanin rayuwa, To ba ma yi miki fatan sake maimaita kwatankwacin abinda ya gabata Sa'ida, amma kamar yanda kika sa ni dole sai an saɓa yau da gobe ta gaji haka, ita zamantakewa haka take, ba sai a aure kawai ba duk da wanda zaka zauna yau da gobe wataran sai an saɓa. Abokiyar zamanki kuma dan girman Allah Sa'ida ki zauna da ita da zuciya ɗaya, kar ki zama cikin matan da burinsu in sun shiga gidan mai mata su kori wacce suka je suka tarar ko su muzguna mata, mijinta kika aura in ma kishin ne ita zata fiki jinsa domin tana zaman zamanta ita da ƴaƴanta kika shiga rayuwarsu. Dan Allah Sa'ida ki riƙe ta kamar ƴar uwarki, kinga mun samu labarin halayenta na gari dan Allah karki lalata tarbiyar da muka yi miki wajan ganin kin ɓata zamanku". Ni dai hawaye nake a hankali wani iri nake ji a jikina, wai yau ni ce nayi aure a karo na biyu wanda ban taɓa hasaso hakan a rayuwata ba, kullum tunanina Nazifi shi ne mijina na farko kuma na ƙarshe har na bar duniya ina tare da shi, ko da na rabu da shi kuwa ban taɓa tsammanin zan sauka akan bakana na cewa ba zan ƙara yin aure ba, ashe ba haka Allah ya tsarawa rayuwar tawa ba. Abbaa ya numfasa kafin ya daɗa cewa,"Ko bayan raina Sa'ida kar ki watsi ki sauka daga kan nasiharmu gare ki, ruƙo da ita shi zai sa kiji daɗin rayuwarki a duk inda kika tsinci kan ki, a wannan karan ba zan ta maimaita miki kalmar haƙuri don kije kiyi ta cutar kanki ba, ba fata na ke ba kuma bana so ranar da zata zo ki kawo ƙorafin mijinki, amma kar kiyi zurfin cikin da za ki zauna ana cutar da ke, kina da mu kina da ƴan uwanki, ki kira mu duk lokacin da kike da wata matsala, wataran zamu zo ni da mahaifiyarki insha Allahu. Ku tashi kuje mota tana jiran ku, Allah ya bada zaman lafiya, yasa kin shiga kenan sai mutuwa ce zata raba ku, idan akwai rabo ina roƙon Allah ya ba ki zuriyya ɗayyiba, Allah yay muku albarka gaba ɗayanku". Safiyya ta miƙe, ta kamo ni na tashi da ƙyar saboda yacca ƙafafuna suka yi bala'in sanyi, Ummani ta miƙe na faɗa jikinta, tana shafa bayana take lallashina, ita ta kama hannuna muka fita, ina jin Abbaa na tambayar Safiyya tare zamu tafi tace masa ehh sai ta kai ni har gidana ma, Abbaa yay aduan Allah ya bar mana zumuncinmu ya ƙara haɗa kawunanmu. Ummani ta kai ni ɗakin Kaka, shima yay min nasa nasihan, Baba Tijjani da Baba Sabi'u dama su tun dawowa daga ɗaurin aure suka kira ni suka min nasu nasiha da faɗan. Yayyuna ma haka duk mun yi sallama da su tun dawowan ɗaurin aure. Ba'a yi wasu motoci da yawa ba, duk da Salim ɗin yace babu matsala ko mutum nawa suke son zuwa za'a tafi da su, tunda ba motan haya ba ne motoci ne na gida kuma duk za'a dawo da su, ni ba da shi ma muka yi maganan ba da Yashaik suka yi, Abbaa dai ya hana yace da mutum biyar za'a tafi, Hajjo, Umman su Batula, Mama A'i, Mama ta kurna, sai Anty Ziyada, sai da ƙyar Ummani ta lallame shi ya yarda za'a tafi da Maman Khairi, Maman Yasmin, Hindatu, Bibalo da Juwairiyya wa'anda duk suke sa'anni na ne. Da kuka sosai aka fito da ni daga cikin gida, kowa adu'a yake min Allah sa na shiga kenan sai mutuwa zata raba, Allah yasa sa'a ce ta kiraye ni, Allah ya kaɗe tsautsayin dare da rana da yini, tarin adu'oin da suke ta fitowa daga bakin ƴan uwa da abokan arziƙi kenan, sai lokacin na buɗe fuskata na yiwa Maimuna da Hassana sallama, da ma su ƴan asibitinmu tun ɗazu suka wuce. Muna tsaye ƙofar gidan kamar ba zan tafi ba Abbaa ya fito Ummani na biye a bayansa, shi ya karɓi hannuna daga hannun Gwaggo Abula ya kamani ya kai ni bakin tsadaddiyar motar da za'a ɗauke ni, ina ta faman sharan ƙwalla ya shigar da ni ciki, ya kama hannuna muka yi musabaha yana daɗa saka min albarka da tarin adu'a, Ummani ma ta miƙo nata muka yi musabaha, zuciyata naji ta tsinke ganin mahaifiyata na goge hawaye, shima Abbaan kansa dauriya kawai yake amma naji a muryarsa, ya rufe ƙofa yana cewa da Abbayo su kori yara daga bakin motar ana daɗa ɓata lokaci, haka muka bar ƙofar gidanmu, Allah sarki Rayuwa kenan, aure babu inda ba ya kai mutum, ni yanzu ina na taɓa hangowa kaina ma garin da za'a kai ni. Ina ta kuka Maman Khairi da Maman Yasmin na ta lallashina, Safiyya na gaba tana ce musu su ƙyale ni kukan munafurci ne. Zuwanmu airpot Salim ya kira wayan Safiyya ta bani, yana ta ban haƙuri na rashin samun space muyi waya, nace masa babu komai, yace na kula masa da kaina kuma idan akwai wani abu na kira shi, da haka muka yi sallama ina ce masa zamu shiga jirgi, yay mana adu'an a sauka lafiya. A cikin jirgin na sake muna ta hira, muna ta shan dariyar Maman Khairi da ke buga mana ƙauyanci, awanmu uku da minti talatin da uku muka sauka a filin jirgi na Anambra International Cargo Airport, lokacin da muka sauka muka tarar da har anzo ɗaukarmu da wasu tsala tsalan motoci na gani na faɗa, dama ina sakkowa a jirgin na yiwa Salim text na shaida masa mun sauka, muka shiga mota ɗaya, ɗaya kuma ƙannensa ne mata da maza a ciki waɗanda suka zo tararmu, gabanmu da bayanmu duk motar sojoji ce, yau ni Sa'ida da ban iya turanci ba ya zan yi, to duk daga yare sai english a bakinsu, Maman Khairi da Maman Yasmin aka yi tsilli tsilli da idanu sai aikin yaƙe baki da suke ta faman yi, har dariya na so yi amma haka na cije, Sisters ɗinsa kamar za su cinye ni saboda murna, da ƴar ƙaramar ƴarsa Rofi'at yarinyar kamar ƴar turawa, bama ta kama da shi gaba ɗaya sai dogon hancinsa da ta ɗakko, naji kishi ya kama ni kar da da gaske Abbayo yake Kudrat ta fini kyau, to idan kuwa haka ne me Salim ya gani a tare da ni?. wata cikin Sisters ɗinsa me suna Apunanwu har sai da ta lotsa yatsanta cikin dimple ɗina tana faɗin zan sammata. *B3ƘR12FT5* Mun yi tafiya me nisa kafin mu kai ga ƙauyen Aguata, kaf ɗinmu ba wanda bai gaji ba duk da a mota muke, Safiyya kuwa da ke ta saba ce mana take babu nisa ga shi ma har an zo. Masha Allah a arean gidajen da suke duk gidan su Salim yafi girma, kyau da kuma tsari. Kusan gari guda sai da muka fito a mota Safiyya ke ce mana ai family house ne, shima Salim ɗin banda yanayin aikinsa da anan zai tare, don ƴaƴa da jikoki kaf anan suke zama idan aka yi aure sai in mata, to da ke ma a matan Ummansu ce kawai tayi aure a wajen ƙabilar su amma sauran duk auren ƙabila ne. Ba wai don zuwanmu ba haka gidan yake baibaye da sojojin da ke tsaron gidan a ko da yaushe, kun san an ce masu abu da abunsu, ga uba ga ɗa dukka masu babban rank ai dole. Tun fakawar motarmu a haraban gidan wasu suka zazzo taranmu, Safiyya tuni ta falle ina gani ta kwasa a guje tayi jikin wata mata, ni kuwa ina tsaye kaina a ƙasa, ƴan uwa duk sun yo kaina ana ga bride ɗin Onochie, abinda na ke iya fahimta kenan daga abinda suke cewa don duk da yare suke magana. Wata dattijuwa ce ta kama hannuna, muna gaba su Maman Khairi na bayanmu, sai kuma wasu daban da ke ƴan waƙoƙinsu daga gefenmu suna rawa irin tasu. A wani tafkeken falo muka yada zango, ban da kar nayi ƙarya sai na ce falon yay girman gidan gaba ɗaya, ashe nan ne main falo na kowa da kowa, falon ya ƙawatu da kujeru na alfarma ga adon mafitai irin na su da aka ƙara ƙawata haɗuwan falon da shi, arziƙi dai yana inda yake, amma kai da ka shigo gidan ka san an aje doller. A ƙasa na so na zauna sai dattijuwan da ta ruƙo ni tace a'a bisa kujera zan zauna, ai fa lokaci guda sai na zama wata abar kallo ko kuma in ce na zama ƴar gata, shigowa kawai ake ana ganina ana yaba irin kyan da nayi, sai ce suke shi dai Onochie ya iya zaɓo mata masu kyau. Ni fa in har za'a dinƙa faɗin kyan Kudrat to lallai sai zuciyata ta motsa da wani bala'in kishi da haushi, har ji na ke kaman dan cin mutunci ne ma Salim ya aure ni, in ba haka ba yana da matarsa me kyan da kowa ke faɗa mene na zuwa ya auro ni, wannan ma ai wulaƙanci ne, ji nayi ma na daina missing ɗinsa na sa sai haushinsa. Salima ƙanwarsa wadda suke cewa Chiagozie, dama ita mun taɓa magana ta waya da ita ranar ta kira shi tana roƙonsa ya sauya mata new phone kuma pocket money ɗinta na makaranta sun ƙare, ta ƙaraso riƙe da dukka yaransa ukun, Ƴar ƙaramar ta ɗazu da suka je ɗakko mu ita ta fallo da gudunta ta haye saman cinyata tana cewa Yayyunta,"Here is our new Mommy". Ni dai murmushi kawai na ke yi mai cike da burgewa, lokaci ɗaya naji yaran sun shiga raina, masha Allah kyawawa da su dukka kai baka ce haihuwar ƙasata najeriya ba, dama ya taɓa faɗa min Foridat miskila ce ko a yanzu ma ita ta noƙe daga baya, su kuwa biyun duk sun maƙale a jikina, Isioma ma kuwa dama yace akwai surutu faɗa suke da shi ma akan yawan maganarta, na ke ce masa ai nafi son yara irin haka muma muna da Walida, yace ba zan gane surutunta ba sai na shigo gidan, ile kuwa tun yanzu ga shi na gani, ta sake da ni tana ta bani labari Paapa yay musu sabbin kaya na biki, shima yayi sabo iri ɗaya shi da Maama, kuma Maama tace musu idan sun ganni suyi hugging ena suyi min peck a kumatu, ina son su da yawa, kuma sai ta faɗawa Maama Big Sis ta ganni bata gaishe ni ba. Dukka haka muka sa dariya, ta maƙale wuyana tana ce min,"New Mommy i love you so much, you are so beautifull". Na kama kumatunta ina ce mata nima ina sonta kuma ai ta fini kyau ma, zata sammin nata kyan, tace ai Paapa ne itama ya sammata. Haka ne kuma duk cikin yaran ita tayo kamansa, biyun dai sai kama ta jini ina ga su kamannin mahaifiyarsu suka yi, Salima ce ta kwashe su tana su bar ni na huta, Rofi'at har da kukanta sai an barta a wurina, ita kuma Isioma na cewa sai ta faɗawa Paapa an ɗauketa a wurin New Mommy, zai sa bindigansa yay shooting ɗin mutum, ina kallo Salima ta talle mata ƙeya ni dai nayi dariya, ina ƙara jin sha'awan yaran. Nan aka barmu kowa ya watse, ina ta baza ido ma na ga shigowan Safiyya ba ita ba dalilinta, Maman Yasmin ta zunguro ni na dubeta, yanda take da fuska abin ya bani dariya, a hankali tace,"Ke mun kawo kan mu, yanzu mu ta ina zamu fara musu bayani baki babu turanci balle yaren da suka fi ji, wannan shi ake kira da kasassaɓa ina zaman zamana na ɗebo ki na kawo ki zanji kunya". Maman Khairi tace,"Kin san ni da tsarguwa ni ta ɗazu ma da taje ta rungumeta sai naji kamar zaginmu tayi, ko yaren ne me yanayin zagi oho". Dariya nayi da ce musu,"To ai Safiyya tana nan, kuma Umma ma na nan". Suka ce,"Ohh tou da sauƙi". Maman Khairi na faman kalle kalle take cewa,"Ohh wuri kamar ba'a ƙasar nan ba, mu dai yi shiru kar wannan abar CCTV ta naɗe ƙauyenci mu ta nuna". Nima sai na ɗaga ido ina ƙarewa falon kallo, ta bakin nata ba za'a rasa CCTV ba kam, musamman a gida irin wannan, Maman Khairi da mugunta ta bushe da dariya tana cewa ita wallahi zuwan su Gwaggo ta hango za'a buga diramar ƙauyanci. Natsuwa muka yi jiyo takun tafiya. Kaina na ƙasa na ke jiyo muryan Safiyya na ta kwara bayani da harshen da ba na ɗaukar komai a cikinsa, ni duk tsayin lokacin da muka ɗauka da ita ma ban taɓa tsammanin ta iya wani harshen ba bayan Hausa, kawai dai na yi mamaki sosai lokacin da muke makaranta yanda kaf makaranta babu wanda ya kaita iya turanci, balle ga shi ta gwamnati muke yi, lokacin har ga Allah ba ƙaramin kishi na ke ba, ashe da dalilin dalilai ba bahaushiya ba ce zuryan, da take ce min suna zuwa hutu Anambra ce na ke ko dai irin ƴan uwa na kalen dangin nne da su, gene ɗin Baba yafi yawa a jikinta shiyasa ba zaka taɓa cewa ita ɗin ruwa biyu ba ce. Cikin aji da takun nustuwa mahaifiyarsa da Kakarsa suka shigo falon, fara'ar da ke saman fuskar Maa kaɗai zai tabbatar maka da ita ɗin macece mai ilimi da iya zamantakewa, haƙoranta duk a waje, ashe itama me kyau ce, na ganta a hoto don ita ce akan wayarsa amma sai naga a fili ma tafi kyau nesa ba kusa ba, tun daga nesa Safiyya ke ce min gulmamman ga surukar ki nan, har da Umma don na jiyo muryarta itama, dama ita tun jiya ta taho. Nayi saurin zamowa na duƙe a ƙasa, Maa ta kama ni zata maida ni kan kujerar sai na kasa zama don gaskiya ba zan iya zama gani gata ba, da nauyi kam. Ta dubi Umma tana ce mata ta faɗa min ita uwata ce, Umman su Safiyya ke cewa ai halinmu ɗaya da Kudrat. Maa tana ta saka min albarka da nuna jin daɗinta, itama har da adu'anta na Allah yasa na shigo family ɗin na su da ƙafan dama. Kakarsa wadda suke kira da Mommi itama muka gaisa da ita tana ta saka min albarka, wata cikin ƙannensa wadda suke cousin ta zago ta bayana tana haɗa gefen fuskarta da tawa tana cewa,"Aunt Dimple you are highly welcome to Chibuzo family". A hankali cike da kunya na ce mata,"thank you". fuskata na fitar da murmushi. Gaskiya family ɗin su Salim mutane ne masu karama, sun karɓemu hannu bibbiyu cikin girmamawa da mutuntawa, babu nuna wani ƙabilanci, kowa haba haba yake da mu, Mommi sai faɗa take yi me yasa sauran matafiyan suma ba su biyo mu a jirgin ba. Aka ce za'a kai ni can ɓangaren Maa na zauna sai Mommi tace a'a a kaini wajenta, can muka tafi muna zuwa duk muka yi alwala muka yi sallah, su Maman Yasmin suka rarrashe domin hutawa sai ga shi ana shigo da flask flask na abinci da lemuka iri daban daban, wani wawaken tray kuwa me zurfi cikinsa aka zubo wasu daƙwala danƙwalan kaji kamar sayi magana, kana kallo yawunka zai tsinke, Mommi ce take muci mu ƙoshi namu ne dukka kar mu rage ko saura. Muna nan zaune tasa aka kira direbobin da suka taho da su Umman Batula, ta ke tambayarsu suna dai tafe lafiya ko. Mun yi waya da su Ummani na faɗa musu mun sauka lafiya, Abbaa yana ta ce min na yi haƙuri a inda na tsinci kaina, za su zo wataran insha Allahu, sai duk jikina ya ƙara yin sanyi kewarsu ta ƙara kama ni. Bayan mun yi sallar magriba ne Mommi tayi min rakiya falon Kakan su Salim, Allah sarki shima ya tsufa tukuf kamar Kaka, yana daga kishingiɗe akan wata kujera, Ƴaƴansa na kewaye da shi ciki har da baban su Salim wanda sai yau shima na taɓa ganinsa, shi ko a hoto ban gansa ba kuma da shi ne dama bamu gaisa ba, ina ganinsa na gane shi saboda zubin ingarman jikinsu ɗaya da Salim hatta sautin muryarsu. Ai ko da fara'arsa shi ma kamar Maa ya karɓe ni, na lura dai family ɗin na su dukka haka suke, babu wani me damuwa a cikinsu Allah ya ba su kyakykyawan zuciya, yana kan kujera a zaune Mommi ta kai ni har gabansa ƙasa gaban ƙafafunsa, sai gani nayi ya miƙo min hannu mun gaisa, naji na kasa sai Mommi ɗin ce ta kama hannuna ta sanya cikin nasa, "Allah yay miki albarka kin ji daughter nah, kuma ina miki barka da shigowa cikin mu, ki ɗauke ni tamkar mahaifinki kin ji, idan kina son wani abu ko kina da damuwa am here for you dont feel shy, babu kunya tsakanin uba da ɗiyansa, kina son ko menene ki neme ni, idan Salim ya miki ba daidai ba ki sanar da ni, amma kema kar ki yi masa ba daidai becouse he is ahead of you, shi mijinki ne aljannarki na ƙasan kafafunsa". Haka Mommi ta dinƙa zagawa da ni ina shiga ina gaida iyayen gidan, muna tafe tana bani labarinta itama freely babu ruwanta, har tana bani labarin asalinta ba musulma ba ce kaman yanda dai Salim ya bani labari. Ashe haka tafiyar garin take da nisa, mu da su Maman Yasmin muna ta zuba idon ganin su Umman Batula sun sauka zuwa bayan isha'i sai ji muka yi Safiyya na faɗin ai tafiya da saura, su da isowa sai cikin dare wajen ƙarfe biyu da rabi zuwa uku, tafiyar tafiyayya ce awa sha uku da mintina, na jinjina kai dole Salim yace ba zai bari a taho masa da ni a mota ba, ashe haka aka kwaso ni gari me uban nisa, ni ƴasu idan zuwa mutum zai yi nawa zai kashe kuɗin mota? Ai kuwa duk tsada insha Allahu ma kuɗin jirgi zan biyawa mahaifana su zo su ga gidana, da inda na faɗa sabuwar rayuwa, Allah dai ya bamu aron rai da lafiya. [2/2, 07:48] Hlm: *B2ƘR13FT5* Zahra'u ce ta taso cikin gigitar yanayi, duk da halin da na ke ciki na tashin hankali sai da nayi matuƙar tsorata da yanda tayo kaina, nayi gefe don bata hanya a tunanina ko zata bi bayansa ne sai ji nayi ta shaƙi wuyana da dukkan ƙarfinta, ta maƙure ni jikin bango tana faɗin,"Wallahi sai na kashe ki kema, tun da kika kashe min yarinya ba zan barki ba, saboda kina baƙin cikin ke ba ki haihuwa shine kika kashe min yarinya". Kiciniyar ƙwatar kaina na shiga yi, Innarta ta taso don ƙwace ni saboda yanda take yi ɗin kamar ba ita ba, amma ina Innar ta kasa taimakona haka nima saboda jikina da ke a mace bani da wani ƙarfi. Ganin zata illata ni muka koma dambe, ni dai ƙwace kaina kawai na ke so nayi, amma ita burinta tayi min rauni, wani ƙarfe da ke jikin bangon ɗakin nata ta ciro zata soka min, har na saddaƙar sai Allah yasa Inna da su Marawiyya suka rufar mata, nima na tattaro kuzarina na fizge su kuma suka riƙeta zuwa ciki. A sannan Iyam ta iso wajen da salati tana cewa,"Wai me yake faruwa ne, menene na ke ta jin hayaniya, ba dai fitina kika tayar ba". Ta faɗa tana kallona kafin ta buɗe ƙofa ta shiga ɗakin, na waiga ina kallonta idona na sauka kan ƴar da ke kwance kan gado tamkar mai bacci. Kasa yarda nayi da cewar ta mutu don haka na faɗa ɗakin na isa gadon na kai hannu zan ɗauketa, aikuwa sai ji nayi an kwashe ni da zazzafan mari, marin da yasani ganin ƙyallin wuta a idona wanda tunda uwata ta haife ni ba'a taɓa min irinsa ba, cikin gigita da ɗimauta na dubi Iyam da bama na iya ganinta da kyau. Nuna ni take yi da yatsa tana so tayi magana, ban san me ya hanata ba sai ta fashe da kuka tana zama wuri ɗaya. "Wannan yarinya Allah ya isa tsakaninmu da ke, Allah ya isa ba zamu taɓa yafe miki ba wallahi, ke annoba ce aurenki musiba ne, aurenki jaraba ne, ban san mummunar ƙaddarar da ta haskawa Nazifi ke a rayuwa ba, tun da kika shigo rayuwarsa yake ta ganin jarrabawa iri daban daban, kin hana shi sakat kina so ki toshe masa duk arziƙin da zai kusance shi, na tabbata dukiyar da Allah ya ba shi ma da kina da iko sai kin ga bayanta, yanzu shine saboda mutuwar zuciya da tsantsar zalunci irin naki na mahassadiya ki ka kashe masa ƴa, ke kin san irin wuyar naƙudar da baiwar Allahn nan ta sha kafin haihuwarta kuwa, amma kika rabata da abin da ta haifa saboda ba ki san zafin haihuwa da daɗinta ba. To da yardar Allah abin da kika yiwa Shalele kema sai ya faru da ke". Inna tana dubanta ta ce,"Don Allah wannan maganar bata kamata ba Hajiya, idan kun duba dama yarinyar nan ai bata da lafiya...". Iyam ta ce,"Kinga Zulai kiyi shiru babu ruwanki a wannan lamarin, ki bari ni da ya shafe ni nayi magana, ba ki san wacece Sa'ida ba ne, ta hana kanta haihuwa da shi, kuma ya auro an haifa masa amma ta raba shi da ƴarsa, dama ni ta tsane ni shiyasa ta kashe me sunan nawa. To wallahi lamari nan sai mun danganta shi ga hukuma, sai Alƙali ya karɓa mana hakkinmu don ba zan yafe kashe min jika da tayi ba, yanda ta kashe itama sai an kasheta". Ƙafafu na rawa nayi gaggawar fita a ɗakin, ɗakinsa na shiga sai na tarar da shi zaune a kan kujera, yana riƙe da Iman a hannu ya kafe yarinyar da idanu, kai kana ganinsa ka san a fusace yake Allah ne da ikonsa kawai yake riƙe da shi a zaunen. na rasa me zanyi, hawaye kawai na san da yana sakko min masu zafin gaske, sai kuma hoton tsautsayin ɗaukar Noor da ke ta haska min a idanu, abin kamar almara! Na ɗauki yarinya lafiya ƙalau kuma ace ta mutu a hannuna, tabbas tsautsayi ba ya wuce ranarsa, sai mai tsantsar imani me zai karɓi wannan mummunar ƙaddarar. Sama na kalla a fili na furta,"Ya ubangijina ka yafe min zunubin da na aikata a gareka da na ke fuskantar hukunci". Duk ashe bai san da shigowata ba sai yanzu, ya ɗago rinannun idanuwansa yana kallona, na zube a gabansa zan buɗi baki nayi magana ya ɗaga min hannu alamun ba ya son jin komai. "Ba na son ganinki, bana son ganin ko da inuwarki, na tsane ki Sa'ida, ki tashi ki fice min a ɗaki, ki bar gabana Sa'ida". "Don girman Allah ka tsaya ka fahimce ni Hub...". Uwar tsawar da ya doka min yana tasowa kaina ita tasa nayi shiru na kare kaina da hannayena. Cikin ɗaga murya yace,"Fita a in da na ke, kar ki ƙara zuwar min ɗaki, kije ki kira ubanki da ya saba yiwa gawa sallah ya zo ya sallaci ƴar da kika kashe...Har yanzu cikin kaina na rasa mummunan matakin da zan ɗauka akanki Sa'ida, kar kiyi tunanin saki a wurina domin ba za ki kashe min ƴa na barki ki tafi kiji daɗin rayuwa ba". "Ban kasheta ba, wallahi ba ni na kasheta ba". Abin da na faɗa kenan na fita a ɗakin kamar zararriya, kamar mahaukaciya haka na koma, ina shiga ɗakina na zube a ƙasa na cire ɗan kwalina nayi wurgi da shi don wani zafi na ke ji ta ko'ina a jikina, kai na ke girgizawa ina ta maganganu ni ɗaya. Duk da sanyin gari amma haka zufa ke tsatstsafo min kamar an watsa min ruwa, da Allah na dogara kuma shi kaɗai zai fidda ni daga taskon da na faɗa. Rumana ta zo ta rungumo ni jikinta tana kuka itama, sai tasa ɗan ƙaramin hannunta tana share min hawaye tace,"Antyna ki daina kuka, ba na so inga kina kuka". Kalamanta sai naji tamkar ɗan cikina ne ke faɗa min, bani da wata kafaɗa da zan kwantar da kaina nayi kuka a cikin gidan nan, ita ɗin kawai na ke da, sai na kama hannunta itama ina faɗa mata ta tayani gaya musu bani na kashe musu ƴa ba. Allah sarki uwa kamar ta san halin da ƴarta ke ciki sai ga kiranta ya shigo wayata, ban iya ɗaukar wayar ba sai Rumana ce ta ɗaga tasa min a kunne. "Sa'ida ya naji kamar kina kuka". "Ummani, Ummani ki zo don Allah, ku zo ku cire ni daga wannan bala'in". "Hasbunallahu wani'imal wakil, me ya faru haka, me ke faruwa Sa'ida? Ke da wa?". Wani irin numfashi na ke yi me wahalarwa na kasa maganar gaba ɗaya, tana ta tambayata sai Rumana ce tace,"Ummani Anty Amarya ce". Sai naji Ummanin na faɗin,"Sa'ida kishiya kike yiwa kuka?". Kaina ya lanƙwashe ina jin numfashina na neman ɗaukewa, muryar Abbaana da naji ita ta saka na buɗe ido. "Sa'ida! Sa'ida! Ba ki da lafiya ne? Menene?". A hankali muryata kamar ba tawa ba nace,"Abbaa ba ni ba ce wallahi, ban yiwa ƴarsu komai ba Abbaa, Allah ne shaidata bani na kasheta ba amma sun ɗora alhakin mutuwarta akaina, Abbaa ku zo ku taimaka min ban san me za su yi min ba". Muryan Abbaan a zabure naji ya furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Sai ƙit naji an kashe wayar. Kaina dai na lanƙwashe a kafaɗar Rumana wacce ke riƙe da hannuna tana ta aikin goge min hawaye, ƙwayar idona ƙafe take a wuri ɗaya. Hawayen ma sun daina zubo min sun ƙafe, na zama dai gani nan kamar me rai kamar mara rai, ai na san zamana da Nazifi kuma ya ƙare, to amma ta ya zai barni haka nan? Sakina kawai ai ba zai sa ya huce baƙin cikin da yake ganin na haifar masa ba, to me zai yi min wanda yake ganin ta nan zai ɗauka fansa? Bani da wani abu da na ke matuƙar so sama da mutuwa a wannan lokacin, ina raye bana raye Allah zai wanke ni na sani. To amma rayuwar na gaji da ita, bana so na ƙara kwana a duniyar nan, da ace nayi haƙuri ban zaɓi Nazifi sama da burin Abbaana ba da ban tsinci kaina a bala'in rayuwa haka ba, danasani ban fifita farin cikin Nazifi akan na iyayena ba, ina nadamar fifita soyayyar Nazifi sama da samarwa kaina rayuwa me inganci. Kusan kamar bayan minti goma haka aka turo ƙofar ɗakin, sama sama na ke jin komai, idan ka ganni zaka tsammaci nayi dogon suma ne. "Bata nan ne?". Naji maganar a tsakiyar kaina amma ban iya motsawa ba, ban kuma shaida muryar ba, sai dai ko wace ma bata gane ni ba ce tunda na bata baya. "Gata nan". Rumana tace da ita, duk wani taku nata da nake ji ina jinsa tamkar ana gutsirar naman jikina. Rumana ta gaida ita tana amsawa lokacin da take zagowa gabana, ta duƙa tana tambayar,"Lafiya dai ko?". Ni dai kallonta kawai na ke yi da ƙwalalan idanuwana irin wacca aka sassaƙa aka dasa, Anty Naim ce maƙociyata, gaba ɗaya layinmu da ita muka fi mu'amala, Farfesa ce a ABU take lakcarin, tana da kirki sosai don ta kan shigo musha hirarmu da ita, ni ce ma ban fiya shiga gidanta ba, farko farkon zuwana ma har yaranta take turo min. Da aka yi haihuwar nan ne na shiga gidanta na faɗa mata sai yaranta suka ce min ai ta jima bata gari. Hannu ta kai ta taɓani, naga tayi saurin janye hannunta, ko bata faɗa ba na san ji tayi tamkar ta saka hannun nata ne a garwashi, don ni kaina zafin jikin nawa ƙona ni yake yi. " Subhanallahi Sa'ida ba ki da lafiya ne haka?". A hankali na ce,"Anty Naim ina wuni". Tace,"Aa ina batun gaisuwa ina ganinki a haka, me yake damunki. Kuma babu kowa a gidan ne naga sai ƙaramar yarinya tare da ke, me zata iya yi miki wannan, tashi muje asibiti". Tayi maganar cike da kulawa da nuna damuwarta, Wahaltaccen yawu na haɗiye na ce,"Ai lafiyata ƙalau, nima ban san me yake faruwa ba Anty Naim, ban san me yasa ƙaddara ke ta ƙwallo da ni ba". Kallona ta tsaya yi kafin tace,"Wata matsala ce Sa'ida?". Kamar wata susutacciya na kaɗa mata kai nace,"A'a babu komai, kawai dai Anty Naim, Ki zauna mana akan gadon". Yunƙurawa tayi ta zauna bakin gadon tana ta dubana da nazari. Na daɗa cewa,"Kin zo ba zan iya kawo miki komai ba, idan na tashi ƙirjina ne zai faɗo zuciyata ta fito kiyi haƙuri". Sai ce tayi,"Kai akwai matsala, kira me gidan naki a waya a shaida masa zan kai ki asibiti, zafin zazzaɓi har ya kai ki ga yin surutai". Ta fada tana cicciɓata ta matsar da ni bakin gado na jingina a jikin gadon, don ce mata nayi ban san ta yanda zan tashi ba, ban san yanda ma ake tashin ba. Rumana ta kawo mata ruwa ta ajiye. Bata bi ta kan ruwan ba tace,"Na dawo tun wancan satin Yara ke faɗa min Amaryar gidan nan ta haihu, har ma kin shiga ki faɗa min kika samu bana nan, to fa ina ta cewa zan shigo kinga sai yau Allah yayi". Idona a gefe ɗaya na ce,"Ehh Anty Naim, wata ɗaya ma kenan. Amma na kashe ɗayar yanzu, na kashe musu Ƴa Anty Naim". Ai kana jin yanda nayi maganar ma kasan ba'a hayyacina na ke ba. Ita kuwa da sauri ta furta,"Auzubillahi kisa! kin san me kike faɗa kuwa, Sa'ida ba ki cikin hankalinki duk yanda akai, akwai matsala ni ba wacca za ki ɓoyewa ba ce, mene yake faruwa?". Sai na kama cewa da ita,"Ai bani da hankali Anty Naim, bani da shi, ya ƙare. Na kasheta na kasheta, amma ban san ta yanda ta mutu ba". Jin ina maganar zararru sai ta toshe min baki tana cewa da Rumana ta dubo lambar mijina ta faɗa masa. Ni kuma sai ce mata na ke yi,"Anty Naim ki taimaka min zuciyata na ke so ki cire min, idan aka gama soyata a waje sai ki mayar min kinji, wayyo jikina ma ki watsa min ruwa me sanyi kinga duk na babbake, kuma don Allah ki taimaka ki kaini inda za'a ciro hotunan da ke cikin idona a nunawa Nazifi ya gani, so na ke ya gani idona ai ya ɗauki hoton komai". Ido na rumtse ina dafe saitin zuciyata, kafin lokaci ɗaya kuma saƙuwa ta sarƙe ni. "Ruwa! Ruwa Anty Naim, zan sha ruwa Anty Naim, ki ban magani ƙirjina zafi yake min". "Anty ga ruwan". Rumana ta faɗa tana kafa min kofin a baki, tun da na kafa baki sai da na shanye, tana saukewa nace ta ƙara min, nan ma na kuma shanyewa na ce su ƙara min, Anty Naim tace ya isa haka. Roƙonta na kama yi akan ta taimaka ta kira min Ummani da Abbaa su zo, su zo yanzun nan, su zo da likitan da zata tashi Noor da ga baccin da tayi, Noor suma tayi amma taƙi tashi, kuma a zo da wanda zai ciro idona a nunawa Nazifi hoton komai. Ruwa ta watso min a fuska na firgita ina ƙanƙameta jikina sai rawa yake yi. [2/2, 07:48] Hlm: *B2ƘR14FT5* Cikin tsananin tausayina Anty Naim ta kewaye ni jikinta. Idona akan Rumana na ce,"Rumana kirawo min Abbaa". Anty Naim tace,"Sa'ida za ki ɗaga musu hankali, barsu tukunna. Duk da ban gama gane kan Al'amarin ba amma kamar kina magana ne akan yarinya ta mutu an ce kece ko?". Kai na ɗaga mata ban iya cewa komai ba. Sai naji ta sauke gwauron numfashi. Nace mata,"Anty Naim da an kirawo min Abbaan nawa don Allah, shi zai faɗa min maganar da zan ɗan samu sauƙin ciwon da na ke ji a ƙirjina". Wayar ta karɓa a hannun Rumana tana faɗin,"Yanzu shi ina me gidan na ki?". "Yana ɗakinsa ban san wanne mataki zuciyarsa zata yanke akaina ba". "To wai ƴar mutuwa tayi ne ko me? ki nutsu ki min bayani". Ido na rufe na ce,"Eyy Anty Naim mutuwa tayi kuma ni na kasheta haka Babanta yace, Babarta ma tace na kashe mata ƴa, Kakarta ma tace na kashe mata jika". Ni dai tun da na faɗi hakan kuma sai naji numfashina na karkatsewa. Waya naji an ɗora min a kunne wadda ko ƙararta banji ba, muryar Safiyya naji tana cewa,"Beb wayar Ummani na kira zanwa Abbaa ya jiki sai naji muryar kamar babu lafiya, na ƙara kiranta kuma bata ɗaga ba na dai ji tana mota". Shirun da taji ta ƙara cewa,"hello Beb, Beb, Sa'ida bacci kike yi ne naji numfashinki na fita da ƙyar, ko ba ki da lafiya ne?". Cikin wata murya da tayi daban da tawa na ce,"Safiyya ba ni ɗaya ce babu lafiya ba komai ma babu lafiya". Sai na fashe da kuka wanda ya katse maganar da take son ƙara yi, na ce,"Safiyya ɗayan yarinyar Nazifi ce ta mutu kuma sun ce ni na kasheta". "Kutumar bura'uba kika kasheta kamar ya? Nazifi da matarsa suna shaye shaye ne? Me ma ya kawo zancen kin kashe musu ƴa, sun bugu ne, taɓa ƴar kika yi ko me?". "Safiyya kuka take na goyata ya ɗaukota, bacci tayi a bayana Safiyya kafin ta farka kuma daga nan...". Kukan da yaci ƙarfina ya hana ni ƙarasa me na ke son cewa. Ita kuma tana cewa,"Daga goyo sai mutuwa, ya za'ai haka abu kamar shiri. Kinga gani nan zuwa gidan". Ƙit ta kashe wayar ina jinta kafin kashwewar tana faɗin,"Anty ba ni aron maƙullin motarki". Anty Naim tace,"Amma abun da matuƙar ɗaure kai, to dama yarinyar bata da lafiya ne ko me?". "Wallahi ban sani ba, ni dai na goyata kuma na sakkota babu rai". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, lallai kin shiga tsaka mai wuya, tabbas kina cikin garari me fitar da ke sai Allah. Amma kwantar da hankali bi'izinillahi Allah zai yayyafawa bala'in sanyi. A hankali nace,"Amin". Rufe bakina kenan sai jin muryar Yaya nayi ta shigo ɗakin tana zage zage, na buɗe ido a wahalce da duk suka ƙanƙance, gayyarsu da na gani ita ta tsorata ni yawu me azaba ya wuce a maƙoshina. "Ai yanda kika kashe mana ƴa muma sai mun ga bayanki". Maganar da suke yi kenan suna ɗure ɗuren ashar suna neman rufe ni da duka, Anty Naim tayi saurin tashi ta kareni. Yayan ta fallawa Rumana mari tace da ita,"Don ubanki fice kafin kema ta kashe ki". Yarinyar na kuka ta fita tana waigowa ta kalle ni. Kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, duk yanda Anty Naim ta so ɓoye ni sai da suka tureta suka fizgo ni. Ba zata iya da su ba haka ta fita da sauri wai tana ƙwalla kiran neman taimako, To waye zai taimake ni a cikin gidan nan? Ban da muryar da zan ɗaga na ce ta dawo ta ƙyalesu suyi yanda zasu yi da ni. Anty Fati ta fizgoni na miƙe Fati ta kawo hannunta zata mare ni nayi saurin kawar da fuskata. Kan na farga kuma Zahra'un ta shiga dukan cikina tana wallahi sai dai idan ta kasheni itama a kasheta. Ana haka sai muryar Nazifi naji yana cewa,"Yaya ku zo, Ke Fati kamo Zahra'un ku fita". "Ai Nazifi ka bari mu raunata shegiya". "Malam ne ya zo". Jin hakan sai ɗakin ya zama kamar anyi ruwa an ɗauke yay tsit, shi ya zo ya fizge Zahra'un wacca ke ta abubuwa kamar me iska, ficewa duk suka yi. Anty Naim ta dube shi tana gaida shi, ni kuma tuni na rikice da ganin nasa tsaye kaina yana jifana da wani irin kallo na me zan miki na huce. har yanzu Iman na hannunsa, hawayen da suka ƙafe tun ɗazu suka gangaro, ban iya ɗago kaina a jikin bangon ba nake ce masa,"Kar ka yanke hukunci cikin fushi, don Allah kar yarda da zancen zuciyarka". A ƙalla ya kai cikakken minti ɗaya kafin ya buɗe baki yace da ni,"Ki sakko ƙasa, jiranki ake kar ki ɓata min lokaci". Yay maganar da wata irin murya yana juyawa. Ni kuma na dubi Anty Naim nace,"Kiyi haƙuri kin zo gidan namu babu yanda yake". Ta kamani tana zaunar da ni tace,"Sa'ida ai ni lamarin duk na rasa ta cewa". Miƙewa nayi a dabarbarce zan fita, sai ta dakatar da ni wajen ruƙo hannuna, ɗankwalina da ke ƙasa ta durƙusa ta ɗauko ta ɗaura min wanda ni ban ma san babu ɗankwalin akaina ba. Rumana na kuka sosai ta riƙe Anty Naim tana ce mata,"Don Allah kar ki kai musu Antyna, kar ki kaita don Allah, Ƴan sanda ne suka zo, kuma Iyam tace tafiya za'ayi da ita". Nima ta kamoni tana cewa,"Anty kar kije, kar ki je Anty". Fita kawai nayi fuuu tamkar iska ce ke hankaɗa ni, wanda bai sani ba kuwa zai iya cewa ga mahaukaciya nan, Anty Naim ta biyo ni da sauri tana riƙe ni saboda nema na ke na faɗi a matattakalar na gangara wajen sauka. A falon na tarar da mamaki da akasin sa, nayi matuƙar kaɗuwa da police ɗin da na ke gani, sai dai fa yanda na gansa da sauran mutanen da ke a falon ba ƙaramin amsawa zuciyata tayi ba wanda ta kai ga har sai da na kai hannu na dafe ƙirjina. Shine tsaye a tsakiya rungume da yarinyar da ta mutu, sai ita Zahraun na kan kujera Inna da Marawiyya a kusa da ita sun riƙeta alamu ife ife take faman yi, su kuma tawagar Iyam duk suna tsaye ƙofar ɗakinta. Daga gefe Malam ne a tsaye hannayensa harɗe ta baya kansa sunkuye a ƙasa, sai Abbaana shima a kusa da Malam ɗin ƙwayar idonsa cak a kaina. Na girgiza sosai da ganinsa don ban san da zuwan nasu ba, can kujerar bayansa Ummani ce zaune ta rufe fuska da mayafi da gani ka san kuka take yi, har da su Yashaik da Yaya Imam. Daga bakin ƙofa kuma ƴan sanda ne guda biyu tsaye masu baƙin kaya, sai ta ɓarin da su Abbaa suke wani ɗan sandan ne amma shi wandonsa ne baƙi rigarsa kuma sky blue. Iyam tayo kaina ta cakumo ni daga hannun Anty Naim ta hankaɗa ni gaban ɗan sandan wanda naji ta kira da Usman. Kafin ta fara kora bayanin,"Don Allah kuyi mata hukunci daidai da abin da ta aikata, wanda ya kashe a kashe shi ne. Ta kashe jaririyar da bata ji ba bata gani ba". Malam ne ya doka mata tsawa da cewa,"Jummai ya isa! Kar na ƙara jin bakinki a wurin nan idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci". Kana ya kalli ƙofar ɗakinta yace da yaran,"Ku kuma kafin na ƙifta ido ku fita ku bar gidan nan, kar wacca tayi gangancin da minti ɗaya zata cika mata a gaban idona, kun sanni sarai zan saɓa muku". Sum sum dukkansu suka yi hanyar fita cikin sauri. Idona ya kai kan Zahra'u da ke kuka tana faɗin,"Yaya itace ta kasheta, Yaya ka ƙwatarwa ƴata hakkinta". Tayi maganar da ɗan sandan kusa da su Abbaa. "Saka mata ankwa". Furucin da Yayan nata yayi kenan, nima kuma yana kallona cikin ɗaga murya wanda har sai da naji tsoro ya ce,"Ke bada hannunki". sai ɗaya daga cikin ƴan sandan da ke tsaye bakin ƙofa ya tako ya zo gareni, ya buɗe ankwar yana cewa na ɗago hannayena. Muryar kukan Ummani ta cika falon da faɗin,"Don Allah a fara bincike tukunna, ku fara bincike amma tabbas Sa'ida ba zata kashe rai ba, ba zata kashe jaririya ba, ajalin yarinyar ne yazo ta hannunta amma ba ita ta kasheta ba". Yanda take maganar a ruɗe take. Ta taso da hanzari zata zo wajena Abbaana ya riƙeta. Sai ta sake fashewa da kuka tana faɗin,"Abbaa kar ka bari su tafi da ita, yarinyar nan sharri aka yi mata wallahi". Muryan Abbaa da Allah ɗaya ya san me yake cikinta yace,"Na sani Sa'adatu, Na sani Sa'ida ba ta aikata abin da suke tuhumatarta da shi ba, sai dai lamarin a zargeka da kisan kai babba ne wanda a halin yanzu ba zamu iya yi mata komai ba. tun da har shi mijinta ya yarda ta aikata to babu me yarda da ba ta aikata ɗin ba, mu bar hukuma tayi nata aikin, mu kuma zamu kwana muna gayawa Allah da shi ne shaidarta, Allahnta shi kawai zai kawo mata mafita". Idona a kansu dukka, a raunane suke maganar, sai naji na bar tausayin kaina na koma tausayinsu. Kallon ɗan sanda nayi babu musu na ɗaga hannayena biyu a haɗe na miƙa masa. Sai Anty Naim tace,"Ku tsaya! Ankwa! Asaka mata ankwa kamar ya? Ina shaidar cewa tayi kisan kan da kuke tuhumarta?". Yayan Zahra'un ya ɗaga mata murya da faɗin,"Wacece ke da za ki hana hukuma yin aikinta, ba ki da hurumi a wannan lamarin saboda haka ki koma gefe". Ta dube shi tace,"Idan da hadasi akanka zaka san cewar ina da hurumi akan lamarin da ya shafi maƙociyata. Ba zan yarda da wannan cin zarafin da ake neman yi ba. Zargi ne kuke yi, baku da tabbacin ta aikata". Ya nunata da bindigar hannunsa yace,"Malama ki iya bakinki, hukuma ba sa'arki ba ce". Safiyya ce ta faɗo falon tamkar an jefota, turus tayi daga nesa tana bin hannayena da ke cikin ankwa da kallo, haka har ta ƙaraso gabana cikin girgizar al'amarin. "Ankwa suka saka miki Sa'ida? Tafiya za su yi da ke? Mene hujjarsu na kin kashe mu yarinya?". Sai kuma ta damƙi kafaɗata da iya ƙarfinta tana jijjigata cikin ɓacin rai take faɗin,"Tun yaushe na gaya miki ki nisanci taɓa mata yara tun da bata so, sau nawa na faɗa miki kar ki ƙara kallon ko da inuwar ƴaƴanta ne, ke me yasa ba kya jin maganata ne, me yasa idan na ba ki shawara ba kya ɗauka? Yanzu ai ga irinta nan, garin nunawa ƴartata ƙauna suna miki ƙazafin yin kisa". Sai ta juya tana kallon ɗan sandan tana cewa,"Cire mata wannan abar da ku ka saka mata". Tayi maganar cikin ƙarajin murya tana neman ta warci maƙullin. Ganin ta ruɗe tana neman itama sanya kanta cikin matsala sai Abbaa yace da Maman Yasmin ta kamota, Maman Yasmin da Anty Naim suka ruƙota tana fiffizgewa tana faɗin,"Abbaa wallahi sharri suke mata, ɗan sanda ƙarya ne kar ku ci mutuncinta, na rantse da Allah ƙarya suke mata sharri ne ba zata aikata ba, Abbaa dama akwai abin da baka sani ba gama da zaman Sa'ida a gidan nan, zan maka bayanin komai Abbaa a wannan karan ka tsaya ka saurareta". Maganar take yi tana kuka sosai tamkar ita aka ce tayi kisan, ta faɗa jikin Ummani ta ƙanƙameta tana cewa,"Nazifi sai Allah ya kamaka, haƙƙinta ba zai barka ba sai Allah ya saka mata da gaggawa, wallahi sai rayuwa ta wulaƙantaka akan baiwar cutarwa da ka yiwa Sa'ida, ka jira yi lokaci talala ne yanzu duniya take ma". Muryar Malam na fidda ɓacin rai tsantsa yace,"To wai ni matsalar cikin gidanka ma me ya kawo hukuma cikinta? Su waye shaidun gani da idon cewar tayi kisan har akai gaggawar gayyato hukuma? Yarinya dai gata nan a hannunka babu ƙwarzanen komai, to da me tayi amfani ta kashe maka ƴa? Ko haka ɗaya ku ke neman ɗora mata laifin da bata ji ba bata gani ba". Muryan Nazifin ta fito tarr a cikin shirun da ya ratsa saboda ɗagawar muryar Malam. "Ban da masaniyar zuwan hukumar. Amma Malam yacca Sa'ida ta tsani yaran nan yanda ka san Annabi da kafiri, wallahi ban da ina da haƙuri babu namijin da zai zauna da macen da bata ƙaunar jininsa irinta, ba na son ace ina kai kararta shiyasa na ke barin takaicinta iya ni, kuma Malam ba ta ɗaukar yaran nan kwata kwata, ko nace ta ɗauke su sai taƙi, amma yau ta ɗauki yarinyar har ma da goyata ta fita da ita yin aiki"... Sai Malam ya katse shi da cewa,"Da ta fita da ita aikin sai ta dafata ko ta soka mata wuƙa ko?". Yay maganar yana jifan Nazifin da mugun kallo. Abbaana ya sauke nauyayyan numfashi yace,"Matsalar ka fito ka nuna ƙiyayyarka ƙarara kenan, ko kayi mummunan furuci, ita ƙiyayya ɓoyeta ake, magana kuma zarar bunu ce, ba komai duk ake gudu ba sai irin wannan ranar". Malam ya dubi Yayan Zahra'un yace,"Kaga kuje zamu san yanda zamu yi da lamarin nan da kanmu, kuje kawai bama da buƙatar hukuma a ciki". Ya kaɗa masa kai yace,"Ai ba zai yiwu ba ranka ya daɗe, lamarin kisa fa ya wuce duk inda tunaninka yake, idan ace ba'a gayyacemu tun farko mun sani ba shikenan, amma yanzu ba zai yiwu mu ƙyaleta ba duk da cewa suspect ce a wurinmu, idan muka barta ko da bata aikata ba zafin zuciya zai iya sawa ta zo ta aikata abun da ba daidai ba, ko kuma ta aikata ɗin an tafi an barta to gaba ma zata ƙara yi, so dole ne sai mun tafi da can wajenmu an shigar da bayanai duba da yanda ita uwar yarinyar ta shigar da ƙorafinta, sannan kaga su da suke ƙarar suna shaidu ita kuma babu wata shaidar nuni da cewa bata aikata ɗin ba, if ace ma da akwai zamu iya duba case ɗin iya nan mu gani idan na ƙyalewa ne mu ƙyale, to amma yanzu zamu tafi da ita ta bayar da nata bayanan suma su ƙara ba da nasu duk mu shigar a rubuce, anan zamu duba muga me ya dace ayi, a'a lamarin zai tsaya iyaka station ne ko kuwa da yiwuwar mu tura shi gaban alƙali". Durƙushewa nayi na fashe da kuka sosai mai tsuma zuciyar duk wani mai imani. "Wallahi ba ni na kasheta ba, wallahi wallahil azim ban taɓa yunƙurin cutar da su ba, ban taɓa ba...". "Kinga ki adana duk wasu kalamanki idan muka je can kya mana bayani, anan babu wani amfaninsu gareki...Amm ku sata a gaba muje". Abbaana yace,"Yallaɓai a yanzu ne zamu iya shigar da tamu ƙarar na cewa bamu yarda da abin da ake tuhumarta ba ko kuwa sai kun gama shigar da rahoto?". "Ehh da zarar mun gama jin bayanansu idan munga da yiwuwar zuwa gaban alƙalin to kuna iya neman lauyan da zai tsaya muku, koma dai me kenan zaku ji daga garemu acan station ɗin". Yashaik yace,"Yallaɓai mu ta ɓangarenmu zamu iya shigo da likita cikin case ɗin don bincike kafin ayi jana'izar yarinyar?". Ɗan jimmm yay kafin ya ɗaga kai yace,"Ehh zaku iya hakan ma dabara ce ta nemarwa kai mafita, da kuma sauƙaƙawa shi lauyan na ku idan har maganar ta kai gaban alƙali kenan". "Bari a saka mata hijabinta". Maman Yasmin ta faɗa yayin da take dakatar da tafiyarmu, hijab ɗin ta saka min sannan muka wuce, ɗan sanda ɗaya gabana ɗaya bayana. Zan shiga motar ƴan sandan Abbaa ya ce,"Babu bawan da ubangiji ba ya jarabrtarsa, taki kalar jarabawar kenan, me cikakken imani shi ke karɓar ƙaddara a duk yanda ta zo masa. Ki yi ta kiran Allah cikin zuciyarki da bakinki, sannan ki nutsu wajen yi musu bayani wanda ba za'a samu matsala ba ki ƙara dulmiya kanki a ciki, ba na so tsoro yasa kiyi musu ƙarya kin ji Sa'ida, ki faɗi dukkan gaskiyar da kike da ita, kar barazana ko tsawa ko duka su sa ki canja daga abin da kika faɗa da farko, babu abin da zai ƙwace ki face gaskiya. Zamu biyo bayanku yanzu, Allah yayi miki albarka ya kuma shiga lamarin". Tun da Abbaa ya fara maganar kallonsa kawai nake yi ta cikin ruwan hawayen da ya cika a idona. To ban san ya zan fassara yanayinsa ba amma daga amon muryarsa zuwa yanayin da ban taɓa ganinsa a ciki ba, zan iya cewa wani al'amarin daban da ban tsammata ba zai iya faruwa. Na fashe da kuka sosai, ƴan uwana ne kawai suka fito ganin tafiyata banda Yaya Imam da ya tsaya daga ciki, ina jin mahaifiyata na gunjin kuka, Safiyya ma na yin nata tana neman zabura ta shigo motar. Sai ga inspector ɗin sun fito shi da Yaya Imam da kuma Nazifi wanda har wa lokacin yake riƙe da gawar a hannu. Lokacin da motar zata ta shi Yaya Imam yace,"Ki bar kuka, daga nan zuwa bangon duniya su shigar da ƙara, kina da Allah kuma kina da mu Sa'ida, zamu tsaya miki ko da silar hakan zamu ƙare, nayi miki alkawarin bayan kukan mutuwar rashi da za ki iya yi anan gaba, to kin bar yin kowanne kalar kuka na ƙunci muddin ina raye". Wani sabon kukan ya zo min, garin na kalli Yaya Imam ƙwayar idona ta shiga cikin ta Nazifi, nayi saurin rufe idona tare da kifa kaina a saman cinyoyina. Haka aka tafi da ni mutane sai kallona suke yi, nayi ƙoƙarin rufe fuskata kamar yanda Anty Naim tace min. Muna zuwa can station ɗin na roƙe su akan su da su taimaka min nayi sallah, aka haɗa ni da ɗan sanda ya rakani zuwa banɗaki nayi alwala sannan ya dawo da ni ofishin insifecta, nayi sallolina na azahar da la'asar, na nemi taimakon a bani ƙur'ani duk ba a hanani ba, na ɗan yi karatu na mintuna uku sannan na ɗaga hannu sama ina faɗawa Allah, kuma lokaci ɗaya sai naji natsuwa tana wanzar min, dukkan wani tsoro na korewa daga zuciyata. Sai da aka yi sallar magriba nan ma aka barni nayi sallah, sannan suka zo shigar da rahotona, aka yi min tambayoyi na faɗin dukkan abin da yake nan, suka kammala rubuce rubucensu bayan ɗan wani lokaci ina nan dai wurin zaune aka shigo da ita Zahra'un da Nazifi. Ita da ta shigar da ƙara ta bayar da nata bayanan sannan aka yi mata tambayoyi, bayan sun gama da ita shima ya bada nasa kana ɗan sandan yace suna iya tafiya zasu neme su daga baya. Ni kuma aka shaidawa su Abbaa za'a tsare ni nan da zuwa gobe su gama bincika bayanai. Iyayena da ƴan uwana suka kasa tafiya, Ummani har lokacin kuka take yi, Safiyya ma haka wacca ke ta kirayen waya, haka Malam ma shi da Yayan Shago, har aka shigar da ni cikin sel duk suna tsaitsaye, bayan an rufe kuma suka juya suka tafi kowa jiki a mace. Ina zaune cikin bayan shafe tsayin wasu lokuta, nayi nisa cikin tunani sai naji an ƙwanƙwasa ƙarfen sel ɗin. Na buɗe ido sai naga Abbaa tare da ɗan sanda, na taso da sauri na zo na tsaya bakin wajen. Ɗan sandan yace da Abbaa,"Minti goma muka baku". Abbaana ya zauna ƙofar sel ɗin ya buɗe kwanon abinci yace na zauna nima, daga bakin ƙofar na zauna shi kuma yana saka hannu cikin kwanon abincin. "Daure ko babu yawa ki ci abinci kin ji. Ba na so ki kwana da yunwa". Ba na jin bakina zai ji ɗanɗanon wani abinci, haka babu buƙatar abincin a cikina. Amma saboda Abbaana haka na buɗe baki yana zuro hannunsa ta ƙarfen yana saka min ina ci, ban daina amsa ba har sai da ya barni da kansa. "Bari a siyo miki lemu ki sha ko". Ya faɗa yana lalubar aljihunsa wanda na san babu ko naira biyar a ciki, na riƙe hannunsa ina girgiza masa kai na ce,"Abbaa na ƙoshi ai". Ya miƙe yana faɗin,"Bara to na ɗauko ruwan kinga na manta shi can kan kanta". Yana tafiya ya dawo jikinsa sai rawa yake yi, kamar yanda sai da ya fara cin abincin a ɗazu haka yanzu ma sai da ɗan sandan yace ya fara shan ruwan duk kuwa da pure water ne. Lokaci na cika ɗan sandan ya cewa Abbaa lokacinsa ya ƙare, Abbaa yace min,"Kar ki hana kanki bacci, kuma ki yi min alƙawarin ba za ki kwana kina kuka ba, sauran pure water ɗin guda biyu kiyi alwala cikin dare kiyi sallah. Sai mun dawo zuwa goben idan Allah ya kaimu". ka ina ji ina gani Abbaa ya tafi ya barni, duk da tun ɗazu yana ta ɓoye min hawayensa amma a yanzu ina ganin yacca yake sa hannu ya share su, gefe ɗaya kuma bayan ruɗani da tashin hankalin wannan case ɗin, na kassa tantance wani yanayi na daban da ke tare da shi wanda tun a gida naga hakan, sai dai zance ɗan iya cewa kamar me shirya wani abun. *B3ƘR14FT5* Na sauke numfashi bayan fitar Safiyya, ɗakin na bi da kallo, masha Allah ya haɗu sosai ga shi ƙatoto, kuma funitures ɗin sai suka yi tamkar daga waje aka kawo su ba haɗi na gida ba, wadrobe ɗin ma irin me zugewa ce gaskiya Sale yay min matuƙar ƙoƙari, ana siyan wadrobe da gado ma kawai na miliyan guda amma shi kaf set ya haɗa min na alfarma, duk da banga kujerun ba amma na san suma sun haɗu. Ina zaune shiru shiru Salim bai shigo ba, zuciyata ta cika fal da kishi da ɓacin rai, ban da tabbacin yana wurin matarsa, to amma in ba can ɗin ba ina ya zauna bayan ya san an kawo masa ni ɗaki, rumtse ido nayi ina jin ciwo a ƙasan raina, nayi ƙwafa na tashi a raina ina ƙudurtar in har na idda sallah bai shigo ba to zai zo ya tarar da ƙofa a rufe ne, sai yay zaman nasa can wajan makiran matansa ɗin da ni ban wani yarda da ita ba. Alwala nayi na fito ina tunanin ina ne gabas ɗin, na ɗauki waya na kira Safiyya ta faɗa min, itama har tana tambayana har yanzu Salim ɗin bai shigo ba, na kashe wayana ba tare da na bata amsa ba don itama haushinta na ke ji, ina cikin gidan zata je ta wani tare wurin kishiyata. Ina raka'an ƙarshe naji sallamarsa da kuma takun shigowarsa, ya ƙaraso ta ɓarin da na ke ya zauna a gefen gadon yana kallona. Duk da sallah na ke yi haka na haɗe rai daidai da lokacin da nayi zaman tahya, har na sallame ina jin kallonsa a kaina. Bai min magana ba har sai da na gama tazbihi, da murmushinsa yana shafa tasa fuskar cikin zallar farin ciki da kuma annushuwa. Ni dai ban dube shi ba irin ban damu da zuwan nasa ba, sai dai fa ina kallonsa ta ƙasan ido, ya sauya daga kayan ɗazu ina ga ko da zamu taho ne ya canja, manyan kaya ne yanzu a jikinsa shadda dakakka irin kalar swizz less ɗin jikina blue, ya saka hula kalar aikin yayi kyau sosai dan kayan sun amshi jikinsa, shi kam kowanne shiga yayi yana yin kyau a ciki. A tsammaninsa duk kunya ce ta hanani ɗagowa, nan kuwa bai san fushi na ke da shi ba da kishinsa, don me zai barni ni ɗaya, ita matan nasa ba jiddan walahairan suna tare ba. ya duƙo kai yana ce min,"Idan amarya ta idar ko zata iya bani aron kanta zuwa falo wajen ƴar uwarta?". Yanda yayi maganar sai da gabana ya faɗi, haka na taushi kaina na daure ban nuna ba, sai naga ya tashi ya riƙe kafaɗuna ya miƙar da ni tsaye, kaina yana ƙasa still ban kalle shi ba, shi ya tallafo haɓata ya ɗago da fuskata, na sake kulle idanu don ji na ke kamar bana son ganinsa, bai kawo komai a ransa ba game da yanayin nawa yayi siririyar dariya yace,"Ko yaushe aka ɗauko wannan sabon salon ban sani ba, amma za'a yi min bayani ne muje mu dawo". Ya faɗa yana riƙe da hannuna muka fita daga ɗakin yana gaba ina bayansa, zuciyata na ta ce min in koma in canjo mayafi maimakon hijab ɗin sallar da ban cire ba, don gani na ke na je a haka Kudrat zata raina ni, ko fa da nayi sallah yanzu sai da na roƙi ubangiji ya sassauta min zafin kishin da na ke ji, ya kuma hane ni biyewa ingiza uwar me kantu da zuciyata ke karanta min a cikin kai. A falon muka tsaya ya saki hannuna ya wuce ya nemi waje ya zauna, Kudrat ma na zaune a kujeran da ke fuskantar shi da ƙaton hijab ɗinta ta duƙunƙune alamar sanyin daren na ratsata, kuma da gani ma daga bacci ya taso ta. Salim ya shafo fuskarsa yana cewa da ita,"Sorry fa na barki da jira, na tadda tana sallah ne, hope babu laifi ko?". Tana murmushinta na bata da matsala da yanayinta da ke nuna gajiya tace,"Ni na isa nace kayi laifi? To koma ba sallah take ba dan ka jima ai ba zaka yi laifi ba balle sallah guda". Sai ta dube ni daga inda na ke tsaye, da zolaya tace min,"Sisi Nah idan nayi bacci anan to ki tabbata ke za ki ɗauke ni ki kai ni ɗaki". Tun kallon farko da na mata na ɗauke sai yanzu da ta ƙara magana tukunna na kalleta a yatsine, kamar wata sauna wawiya sai murmushi take yi hankalinta kwance, lamarin dai ba daraja sam, an miki kishiya kina ta faman sakin baki da tusa kai. Sai da ya dube ni yace,"Wai sarauta kike ji da ita ne? Please have a seat my dear". A fakaice na harare shi tukunna na taka sannu a hankali, zan zauna kusa da shi sai ya girgiza min kai da cewan,"Koma kusa da ƴar uwarki". Haka na koma na zauna kamar yanda yace ba don rai ya so ba, sai don kar na yarfa kaina gaban kishiya. Na sunkuyar da kai zuciyata na zillo cikin yanayin da ban taɓa tsintar kanta a cikinsa ba, ko lokacin da Nazifi ya taramu kamar haka ni da Zahra'u ban tsinci kaina a yanayi na jin ciwon zuciya irin haka ba, ko kuma duk amarya tafi uwar gida kishi ne ban sani ba dai, don kishin da na ke ji a yanzu yafi wanda naji a sanda Nazifi ya ƙara aure. To su wai su Ƙabilar haka suke babu zuciya a ƙirjinsu ne? In ba haka ba miji ne ya haɗamu ta kuma san maƙasudin zaman wai amma sai ta dafa ni tana cewa,"So'ida ki saki jikin ki, indai ta ɓangarena ne insha Allah baza ki samu wata matsala ba, ni matsayin ƴar uwa na ɗauke ki, kuma ƙanwata kuma ƙawata, Sofiyya ta shaida min duk irin kyawun halinki, ta faɗa min ba ki da wata matsala. Na miki alƙawarin zan zauna da ke da zuciya ɗaya kaman wacce muka fito ciki ɗaya, ina fatan kema haka daga gareki, sai dai kuma ɗan sabani na yau da kullum wanda yau da gobe ta gaji haka, kin san ɗan adam ajizi ne ni dai na san ko da zan ɓata miki sai dai bisa kuskure, amma bayan wannan insha Allah za ki ji daɗin zama da ni, ba yabon kai ba ne amma ni na san wacece kuma duk wanda ya zauna tare da ni zai san ni ba mutunce me matsala ko sonta ba". Murmushin yaƙe na mata ina knodding mata kaina, ba ma zan iya ce mata komai ba, ita da taga zata iya dogon bayanin kanta, ƙarƙari dai ba zan yarda da kalaman yaudarar kai ba, kishiyar zan yarda da ita? Ni zata rainawa wayo, wato na saki jiki da ita sai na gama sakankancewa ta shiga ta fita ta raba ni da miji ta raba ni da gida, to ai ba yau ne farau ba, na zauna da ita a baya na gani, kuma na saki jiki da ita ban ji daɗi ba daga ƙarshe, saboda haka ba zan ƙara maimaita kuskuren da ya gabata ba, ta ciki na ciki na sani, idan tana ganin ta iya taku ne to nima yanzu na yi gogewar da sai dai na ɗorata a layi. Idon Salim akanta yace,"Zabiya tun ban yi nawa magana ba har kin ida na ki jawabin ko". Nima dai a raina na ce ƙila ko tana da matsala a kanta ne, idan ba me almatsutsan ka ba kawai ki fara sakin baki da magana wa kishiya, ai kya bari miji yay nasa tukunna. Kudrat ta rumtse ido tace,"Allah ya baka haƙuri". Gyaran murya yayi wacce ta dawo da ni daga duniyar ɓacin ran da na tafi, na ɗago na kalle shi muka haɗa ido ma sake ɗauke idanuna, lokaci ɗaya na ke jin zuciya ta tana harbawa sosai. "Muyi salati ga Annabin mu". Ya faɗa a kamilan ce, dukka muka yi salatin kafin ya sake cewa,"Alhamdulillah, Cikin hukuncin Allah gashi ya nuna mana wannan rana wacce dukkanmu ba muyi zaton zata zo ba, komai muaƙaddari ne na jalla wa azza. Ku sani ban yi auren nan domin na cutar da wani ɓangare a tsakaninku ba, dukkanku matana ne, kuma soyayya ce tasa na aure ku, kyawun hali da ɗabi'a yasa na zaɓi na shimfiɗa rayuwa ta dindin tare da ku, kowacce da irin matsayin da take da shi a zuciyata, kuma kowacce ina ganinta da girma a idanuna, ina fatan kuma yanda Allah ya haɗamu rayuwa anan duniya, haka ma ya haɗamu a aljanna. Kudrat ke ce babba a cikin gidan nan, akwai karin maganar da ke cewa idan babba yaja girmansa yaro komai ƙanƙantarsa bai isa ya tsinka shi ba, Amma idan babba ya zubar da girmansa yaron duk ƙanƙantarsa zai bi ta kansa ne ya wuce. Kin san shi girma ko na ce mutunci tamkar madara ne, indai ta zube babu yadda za'a yi mata dole sai dai a haƙura da ita. Abinda na ke nuna miki a nan shine da kija girmanki matsayinki na babba a wannan gida, don Allah ki riƙe So'ida tamkar ƴar uwarki, in kinga tayi wani abu ba daidai ba ki sanar da ita ko da zata ji haushinki. Abinda taga kinyi shi zata yi, in taga kin gyara kin ɗauke ta kamar ƴar uwa itama haka zata ɗauke ki. In kuma taga kin ɗauketa akasin haka itama haka zata ɗauke ki. Don Allah ba na son tashin hankali da ƙananun maganganu a cikin gidana, yau ko da ni ne nayi ba daidai ba azo a same ni a faɗa min kar a riƙe ni a zuciya, ko ace dan nayi wata yanzu na canja babu wanda ya wuce kuskure a rayuwarsa. Babban abinda na ke so a gareku shine haɗin kanku, hakan shine kawai zai saka kuji daɗin zaman gidan, nima kuma naji daɗi nayi farin ciki, ba fata nake ba a wayi gari iyalina sun zama shashashai, dukkan ku masu ilimi ne, kuma daga gidan tarbiyya ko wacce take a cikinku, gidan mutane masu dattako. A kori shaiɗan a kuma kori zugar mutane da ta zuciya don Allah, ku toshe kunnenku kar ku bari wata zuga tayi tasiri a zuciyarku musamman ta ɓangarenki Kudrat, ke ake ganin anwa kishiya ke abokai za su yi tururuwan ganin sun zugaki sun wargaza miki rayuwan aurenki, don haka ki kula ki kuma kiyaye, na san banda matsala da ke in har ba ke kika canja ba". Ina kallonta ta gefen ido, kai take girgizawa cikin gamsuwa da maganarsa, kafin ya maido da batunsa kaina. "So'ida ke ce ƙarama, ke ce baƙuwa a wannan gidan, gidana gidan zaman lafiya ne da kwanciyar hankali da farinciki, ki kula ki kuma kiyaye, kar naji kar na gani, ba zan lamunta da zuwar min abinda zai tarwatsa farin cikin gidana ba. iyalina ba me fitina ba ce, don Allah ki bata girman da take da shi, kar ki kalle ta matsayin kishiya ki kalle ta matsayin ƴar uwar ki kuma yayarki. Bana son jin ko wanne tashin hankali ta ɓangarenki ba zan ɗauka ba ina daɗa maimaita muku gaba ɗaya". Nima na jijjiga kai cike da gamsuwa da shi, duk da irin abinda nake ji a zuciyata sai dai ban nuna ba domin haka kawai kalaman nasa na ji suna sanyaya jikina, duk da a ɗaya ɓangaren ina jin kamar a nasihar tasa yayi son kai. Ya sake cewa,"Allah ya bamu zaman lafiya, yasa mu sake maimaita wannan zaman a aljanna, Ya kawar da dukkan abun ƙi a cikin zamantakewar mu, ya kau da sharri ya shigo mana da dukkan alkhairi, zan iyakar yina wajen zama adalin miji a gare ku, please duk wacca ta ga na kauce hanya tayi ƙoƙarin ankarar da ni da wuri". Ni da ita muka haɗa ba ki wajen ba shi tabbacin da yardan Allah ba zamu ba shi matsala ba. Ya amsa da good yana sake faɗin,"Kowaccenku tana aikinta, Sa'ida Kudrat ma'aikaciyar banki ce, tana fita aiki 7-4, Kudrat Sa'ida ma'aikaciyar lafiya ce, aikinta zai kasance morning and evening, so a ɓangaren girki ina shawartan kowacce da ta dinga girkinta, in yaso in kayi niyya kuna iya bawa junanku, alkhairi yana da daɗi komai ƙarancinsa. Dalilina na yin hakan shi ne; kar yanayin fita aiki yasa a zo a fara samun saɓani, ga yara a gida azo ana complain". Kudrat ta ce,"Hakan yayi sosai". Ya sake cewa,"Sai maganar raba kwana zance ko?". ya cigaba da faɗin,"Al'ada ta tanadar da kwana uku ga Sa'ida bayan wannan kuma ya ku ke ganin za'ayi? Bana son ayi abinda wani zai cutu a cikinku, kar a yanke hukunci wata tazo tana ce min ai ita bata so ba wancece tace haka ba ita ba. Dalilina na maimaita muku bana son ƙananun magana ne Allah ya sani shiyasa gwara ayi komai a gaban kowa. Ku yanke da kanku in ma waje ne zan baku kuyi shawara kwana nawa kuke ganin za'a raba a tsakaninku wanda babu wacce zata cutu a cikin ku?". Kudrat na murmushi tace,"Wai sai ka bamu waje, to in ka bamun ma ai zaka dawo". Yayi murmushi shima yace,"Ai wai kar kuji nauyina ko kunyata". "Ba wata kunya, ni dai ta ɓangarena sai na ke ganin kamar kwana biyu yayi. Amma Sisi ke ya kika gani?". Shiru nayi ban iya cewa komai ba, sai guntun murmushi me ciwo da ya sauka akan leɓena tunawa da ranar da aka zo min da batun in siyar da kwanana. Ta sake ce min,"Sisi abu ne da ya shafe mu gaba ɗaya, ki faɗi abinda yake ranki, lamari ne na fahimta ke kin fi kowa sanin kanki ko ba haka ba". To ni in ba yanzu zan canja ba ai ina iya riƙe kaina ko za'a shekara, wanne horuwa ne ban yi ba a sanda na ke da mijin, na sauke numfashi na kalle shi kafin na kalleta na ce,"Ni bani da matsala ai, abinda kika yanke yayi min". "A'a dai ki faɗi na ki ra'ayin zai fi". "Na amince da naki tsarin". "Kin tabbatar?". Kai na ɗaga alamun eh. Kudrat ta kalle shi tace,"To kaji, kwana biyu yayi mana". "To Masha Allah. Allah ya bani ikon yin adalci a tsakaninku. Kamar yanda na faɗa ɗazu kar aga nayi ba daidai ba a zagaya ana gulmana, dan Allah a faɗa min ko da zanyi faɗa na tabbatar in na nutsu zan gano gaskiya aka faɗa min. Sannan ba zan dinga yawon bin ɗakunan ku ba gaskiya, duk wacce ta san girki a hannunta yake zata zo inda na ke ne bani zanje inda take ba". Kudrat ta amsa da insha Allah. Ya gyaɗa kansa da cewan,"Madallah, shikenan iyaka abinda zan ce kenan". Miƙewa tayi ta ɗauki Rofi'at da take kujerar kusa da shi wacca ma ni ban lura da ita ba. "Tom Amarya da ango sai da safen ku Allah ya tashe mu lafiya". Tashi yayi shima ya karɓi yarinyar yace,"Muje na kai miki ita, Myy ina zuwa". Ya faɗi sunan Myy kansa tsaye, sai na ɗago ina kallonsa, hakan ba zai taɓa zuciyar Kudrat ɗin ba? tunanin da na ke ya yanke sa'ilin da yake ce mata. "Derling gobe a samar da break fast da wuri saboda baƙi". Ya faɗi hakan suna jerawa, ohh shi bai da wani shayi kenan? A gabana yake kiranta da sunan soyayya, duk sai naji na raina nawa sunan da yake faɗa min, mene wani My? Ita fa Derling yake ce mata. Nan take raina ya sake ɓaci kishi ya mamaye min zuciyata, a fusace na miƙe na koma ɗaki zuciyata na bugawa da sauri, idanuna sun ciko da ƙwalla. A fili na furta,"Mene ma amfanin auren mijin wata?". Jin shiru bai dawo ba ya sake ɓata min rai zuciyata nayi min hasashe mara kyau akan jimawarsa, ji nake kamar na fashe da kuka sai kuma naji ya shigo da sallama, nayi saurin kawar da kaina ina faman cin magani. Bai kula da yanayina ba ya ƙaraso ya sunkuya gab da fuskata, ƙamshin turarensa ya daki hancina wanda ya motsa ni, haka sautin murmushinsa har cikin zuciyata wanda kuma take naji fushin da na ke da shi ya gushe, cikin murya mai sanyi yace,"Myy muyi sallah ko?". Sai a sannan na juyo na kalle shi muka haɗa ido, ya ɗaga min gira ya ja da baya, dole na miƙe ganin ya tsaya a kan ƙaramin carpet yana ƙoƙarin tada kabbarar harama, hijabina na ɗakko, na tsaya daga bayansa muka tada sallar. Bayan mun idar ya gabatar da duk abinda addini da al'ada ta tanadar sannan ya tashi yace,"Ina zuwa". Yana fita na miƙe na isa closet na zuge, kayana ma duk ba'a shirya min ba, haka na janyo ƙaramar trolly na zuge na zaro doguwar rigar bacci mai haɗe da hula na saka, a sannan ya dawo shima jikinsa sanye da kayan bacci marasa nauyi riga da wando. Waigowa yay yana kallona, ya wuce ya aje abu kan dressing mirrow, sannan ya ajiye ledan da ya shigo da shi ya zauna saman carpet yana faɗin,"Baby ina jin yunwa". Ban saurare shi ba na haye kan gado na zauna ina ɗakko ɗan ƙaramin ƙur'ani, ya kalle ni yace, "ki zo kici abinci, bana son wannan cin maganin da kike yi, miskilancin na menene? ban san daga inda ya samo asali ba haka kwatsam". "Haka na ke dama, abincin kuma na ƙoshi". Na bashi amsa da muryan ɓacin rai ba tare da na kalle shi ba. Tasowa yayi ya dawo inda nake yace,"tunda nake jin yunwa kema kina ji dole kici". Ya faɗa yana karɓar qur'anin hannuna ya mayar da shi ya aje. Na kalle shi cikin jin haushinsa na ce,"Na ce maka bana jin yunwa ko". Nayi maganar da tsiwa. Sai kawai ya sakeni daga ɗaukata da yake niyyar yi, ya ɓata rai yanayinsa na canjawa ya fito sak a sojansa yace,"Kina ji, tashi muje bana son musu, ke ba yarinya ba ce ai kin sa me ya kamata". Shagwaɓe fuska nayi kamar zanyi kuka nace,"Nima bana son takura". Ai sai ya koma min zam Salim ɗin da bai taɓa wage haƙoransa ba. "Kar ki bari na ƙara mamaita kaina tashi na ce". Ba yanda zanyi dole na tashi muka ƙarasa kan carpet, ledar da ya shigo da shi ya buɗe, packs na abinci guda uku ya buɗe yana kallona. Abincin na kalla duk da pack ɗaya ne na shinkafa sauran kaza ce gaba ɗaya, sai wani da ya buɗe shi kuma soyayyen dankalin turawa ne an zuba masa sauce a kai sai ƙamshi yake yi. "Bismillah". Na sauke numfashi ba tare da nayi yunƙurin ci ba. Rai a haɗe ya kalle ni yace,"Allah zan miki ɗura, kuma ina ƙara maimaita miki bana son musu". Kallonsa nayi sai naga yana neman ya shareni, dama neman wuri ne irin nawa, ba niyya na kai hannu na soma ci, ina mita a ƙasan raina na dalilin da yasa ba zai ciyar da ni da kansa ba. Dankalin kawai na ci shima ban wani ci da yawa ba na zare hannu, sai ce yay,"ita kazar hararar ki tayi da za ki ƙi taɓa ta?". Ina kumbura murya na ce,"Ni fa bana son cin abu mai nauyi in dare yayi, bana son ajjiye tumbi kamar kai". Na faɗa ba tare da na kalle shi ba. Dariya yayi, ya shafa shafaffen cikinsa, in banda sharri irin na Sa'ida ina shi ina tumbi, ko dan training ɗin da yake sha wajan aiki ai dole ma tumbi yaƙi zama a jikinsa. "Ba fa yarinya ba ce ke da zan ta fama da ke, Allah sai kin ci kazar nan". Jin yace Allah ya saka na ɗauka na saka a baki, raina na daɗa sosuwa, da can bai san ni ba yarinya ba ce sai yanzu da ya kawo ni gidansa zai ta maimaita min ni ba yarinya ba ce, to ya rabu da ni mana ya ci gaba da zama da yarinyar, mtssww. Ina jinsa yana cewa,"Kuma za ki nuna min a inda kika ga tumbi a jikina". Shareni yayi har ya gama nasa cimar, a cup ɗin da ya sha yogot ya zuba ya miƙo min gabana, ya miƙe ya fita ya barni na bi bayansa da kallo. Har ga Allah da kukan da na ke ji zai samu sakkowa da na rage raɗaɗin da ke raina, bayan kusan minti biyar lokacin agogo ya buga ƙarfe ɗaya saura sai ga shi ya dawo, ya ce na taso mu wuce ɗakinsa, ina ciccin magani na ce,"Me ya samu nan ɗin? Ko kayan ciki ne ba su maka ba". Harara ya galla min, na ɗauka hijabina na saka na wuce, yana riƙe da hannuna muka fita a ɗakin bayan yasa key ya rufo ɗakin. Ta falo muka shiga wata ƙofa sai gamu a ɓangarensa mai ƙaramin falo mara kayan hayaniya, sai award da hotunansa duk yayi kyau sosai cikin kakin soja. hannuna ya saki yace,"Ki shiga zan kulle ƙofar". A hankali na taka na shiga daga ɗakin da yake da girma sosai a gyare tsaf da shi, sai ƙamshi yake yi ga tiles ɗin ɗakin fari amma ko jurwaye babu a kansa har ɗaukar ido yake, ko anan a tabbatar da tsaftar matar gidan, idan wata ce yanda ba ya zama ai sai tiles ɗin sun rine, ba zata tashi gyara ba sai zai dawo, wannan kuwa da gani goge shi ake akan kari. Ina tsaye ina raba idanu ya shigo, ya tako inda nake ya ɗaga hijabina ta baya ya cire shi ya faɗi ƙasa, ya saka hannayensa ya zagaye ƙuguna ya ɗora kansa a kafaɗata yana cewa,"Wannan fushin duk akan kishin Salim ne?". Yanda yayi maganar a kunnena ya saka naji wani yarrr a jikina, na runtse idanuna sai naji yayi murmushi ya sake ni ya dawo gaba yana kallona yace,"Ashe haka kike sona da yawa ban sani ba?". Kai na sunkuyar, ya ɗago fuskata yana cewa,"Bana son wannan sunkuyar da kan da kike fa, ki kalle ni ki faɗi abinda yake ranki, ko ɗazun na yi maganar da bata yi miki daɗi ba?". "Ni babu abinda yake raina". Na faɗa a hankali ba tare da na bari mun haɗa ido ba. "Akwai, ni nasan akwai wani abu a nan". ya faɗa yana ɗora hannunsa a ƙirjina yana kallon fuskata. "Ina jin bacci". Ya waro ido da faɗin,"Bacci? Baby bacci a wannan daren! Ko kin manta wanne dare muke ciki ne?". Nayi shiru ina faman lumshe idanu kamar me jin baccin gaske, sam ganinsa da maganarsa ne bana so, muka isa bakin gado ya zaunar da ni saman cinyarsa, hular kaina ya zame ya shiga shafa wuyana, nan take na fara jin wani sabon yanayi, lokaci guda kuma na ruɗe jin yanda ya ƙanƙame ni yana aikin shinshinar jikina yana faɗin idan ina sa irin wannan humran kullum to zan janyo a sallame shi daga aiki ne, don zai koma aikin kan gado till down. Maimakon naji daɗi ya ratsa ni da furucin nasa sai ɓacin rai ya ƙara wanzar min, ya zo ya gama min surutai yaje can itama wata me ƙatuwan murya ya karanta mata irinsu. Sai ga hawaye riii a saman kuncina, mamakin kaina kawai na ke yi, ban taɓa tsammanin ina da kishi haka ba, ba zancen son kai ba ne kana matuƙar kishin abinda ka ke so ne, na kasa dannewa kuma, ban san ta ya zan iya danne kishina ba tsakani da Allah, fatana ɗaya kar ta sanadina na haifar da zaman da ba zai yiwa kowa daɗi ba. Sannu a hankali lamarin ya fara sauyawa, na san komai amma sai na ji kaman ban san komai ɗin ba, ba wai don ba a yi min irin salon a baya ba, a'a abubuwan da yake min ɗin ne cikin irin nasa salon na shi kaɗai daban da irin wanda na sani ne, jikina duk ya ɗauka rawa tun ba'a je ko'ina ba har ina neman shiɗewa. Shi kuwa tuni ya gama susucewa da ƙyar ma ya iya zuwa ya kashe fitilan ɗakin, haka ya koma min tamkar wani mayunwacin zaki, na miƙa ragaman jikina gaba ɗaya wa Salim da ya bi ya susutar da junanmu, tuni ya canja labarin da ya sha banban da wanda na ke tunanin zai afku, kuma babban al'amarin ya faru ne bayan shimfiɗuwar lamarin da ya tafiyu cikin natsuwa da gwanancewa, haƙiƙa jin kaina na ke tamkar a yau ne karon farko da na fara shiga duniyar da sanin irin daɗin da ke cikinta. Ni ɗin ba sabuwa ba ce amma a yanda lamarin ya afku jina nayi tamkar yanzu ne aka ɓare ni, an tsumu, zuciyoyi da ruhi sun samu natsuwa, gangar jiki duk ta mace a cikin shauƙin daɗin da ta tsinci kanta, fitar numfashi da saukarsa kawai kake ji. Yana daga gefe nima ina daga gefe, ya tattaro ni ya janyo ni jikinsa ya ƙanƙame abarsa, ni kuwa sai faman sauke ajiyar zuciya na ke ina faman goga hanci da goshi a gashin ƙirjinsa. "Myyy". Ya kirayi sunana cikin wata irin shaƙaƙƙan muryan da zan iya rantsewa ba nasa ba ne, yana ta aikin yawo da hannunsa a dukka ilahirin jikina. "Thank you Baby, thank you so much, God bless you". Haka yake ta faman jera min kamar wanda ya samu sabuwa fil a leda, kamar wanda ya shekara aru aru bai samu ba tsaban gulma, sai bayan wani lokaci kafin mu tashi mu shiga toilet mu tsarkake jikinmu. [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR15FT5* Tun bayan sallar asuba da na kwanta na ke bacci a jikinsa, ƙarar alerm ne ya tashemu inda muka buɗe ido a tare, hasken ranar da ya shigo ta siririn buɗawan labule ya haske min ido, ya kai hannunsa yana kare min, sannan ya miƙe ya isa gaban window ɗin ya gyara labulen. Dawowa yay ya kwanta yana mayar da kaina saman ƙirjinsa, muka haɗa ido da shi sai nayi saurin kulle idanu tare da kamo hannunsa na rufe fuskar tawa. dariya yayi da hakan yana cewa,"Baby gulma, mene ba ki sani ba to da zai saki jin kunyana". Murmushi kawai nayi ba tare da na ce komai ba, sai ya miƙe zaune yana ɗaukar wayarsa, ganin tafiyar lokaci ya buɗe ido da cewan,"Subahanallah! Ashe haka lokaci ya tafi". Ina kallonsa na ce,"Har ƙarfe nawa dama?". "Sha ɗaya fa Myy, wanne irin bacci muka yi". Sai kuma yay murmushi yana shafo fuskana da cewan,"Ko da yake ai laifin ki ne". Na ɗan juya idanu farr da cewa,"Laifina kuma?". Sai da yaja hancina tukunna yace,"Ehh mana, daɗin da aka jiyar da ni da kuma natsuwar da aka bani". Idanuna buɗe ina kallon fuskarsa ba tare da na bari mun haɗa ido ba na ke shafa gashin gefen fuskarsa da cewa,"To kai ma ai ka bayar". "Ummm na sani ai, shiyasa aka saki baki da hanci ana ta zuba munshari duk aka hana ni bacci". "Kaiiii Salim ban da sharri dai". Leɓena ya ɗalle da cewa,"Ai ba sani za ki yi ba, lokacin ma da kika ƙanƙame ni kina kar na sakeki please continue its very sweet ai duk ba ki sani ba". A jikinsa na tusa fuskata ina ta murmushi cike da jin daɗi. Shi kuma yaci gaba da duba wayansa, waya ya kira ina jin yana magana akan tafiyan da za su yi in the next 5days, za su tafi can America ne da shugaban ƙasa akan tattaunawan da aka yi na ƙasar zata taimakawa Najeriya kan harkan tsaro. Bayan gama wayar tasa attention nasa ya bani gaba ɗaya muna ta hiran mu cike da so da ƙaunar juna, a hiran namu kowanne ke bayyanawa ɗan uwansa irin abinda yake so da wanda ba ya so, yana ce min zai bani babban makamin mallakarsa gaba ɗaya, na buɗa dukka kunnuwa ina saurarensa cike da zaƙuwa kuwa. Sai da ya fara manna min kiss a baki kana yace,"Idan kina so ki mallake ni totally na zamar miki raƙumi da akala to ki so Ƴaƴana, ki riƙe su tamkar ke kika haife su, ba na son ki nuna musu banbancin mahaifa, ko a bayan idona ban yarda ki hantare su ko muzguna musu ba...then". Sai yay shiru, zuciyata dai na ta motsi cikin wani irin rauni da tayi, ina kallon ƙwayar idonsa na ce,"Then what?". Sai da ya sauke numfashi, ya kamo kafaɗuna ya tayar da ni zaune muka fuskanci juna yace,"Ni mutum ne mara ɓoye ɓoye da barin abu a raina ina kallon mutum da shi. Ki sani ina darajta matata, ban ƙaro aure don bana sonta ba, ban ƙaro aure saboda tana da wata makusa a gare ni ba, ban mata kishiya domin ta gaza ba, ban mata kishiya don na wulaƙantata ba... Kuma ba ina faɗa miki hakan ba ne saboda ɓata miki rai ba ko kuma ke bana sonki ba, no! Bana so kiyi amfani da wata damar ne na ganin kamar kin fita a wurin miji ki samu hanyar cuzguna mata, duk ku biyun ina son ku, so da ƙauna ne yasa na aureku na ke fatan kuma har a aljanna mu kasance tare, dole son wata zai fi na wata amma wannan abu ne kawai da ke iyacin cikin zuciyata gudun haifar da fitina a gidana, ina sonki itama kuma ina sonta, Baby please ki controlling zuciyanki, ki iya sarrafa kishinki kamar yanda ƴar uwarki ta sarrafa nata. So'ida a ƙabilarmu idan ka ce zaka ƙara aure tashin hankali hakan ke zame maka tsakaninka da iyalinka, amma tunda na tunkari Kudrat da zancen aurenki zuwa kawoki da nayi ban fuskanci wata aba damuwa ba, hakan yasa ta ƙara samun girma a idanuna, ba wai bata kishina ba ne ta danne ne kawai, kema don Allah ki danne abinda na gani jiya a reaction ɗinki da ƙwayar idonki, if kika ce zamu tafi a haka to zamu samu matsala da ke sincerely speeking, fatana matana su haɗe kansu, ku zama abu ɗaya, ba faɗa ba gaba, sai kun fini jin daɗin zaman ma, duk kuwa wadda ta tayar min da fitina tabbas she will see the other side of me". Zuciyana na zafi kamar zan saki kuka na ce,"To yanzu duk mi ɗaya ka faɗawa haka?". "Yanda na karanta miki haka na karanta mata, shiyasa jiya na jima a wurinta har hakan yay sanadin da kika ƙullace ni a ranki, Baby kar ki bari zuciyarki ta rinjaye ki please, kike kaudar da duk wani abu da ba ki da tabbas akansa, kishi dole ne amma kiyi kishin wayayyu masu ilimi irinki". Hawaye ne ya sakko min, ina wasa da yatsuna na ce,"Insha Allahu zan so yaranka, zan riƙe su kamar ni nayi tsugunon haihuwarsu, and zan zauna lafiya da matarka, ba zaka taɓa samun matsala ta ɓangarena ba nayi maka alƙawarin hakan mijina". Sai ya kwanto ni jikinsa yana shafa kaina yace,"Na gode matata, na gode da kika fahimce ni, nayi miki alƙawarin zan samar miki da farin ciki da dukkan iyawata, zan kuma iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ban haifar da ɓacin rai ko damuwa ba a tare da ke, alƙawarina ne kuma ba zan taɓa bari ki zubar da hawaye ta dalilina ba ko ta dalilin wani nawa". Ya faɗi hakan yana manna min kiss a saman gashina, cikin soyayyarsa da yaƙinin samun kwanciyar hankali da dawwamemen farin ciki na kewaye shi da hannayena ina rugume shi na ce,"Ina sonka Mahbub". Da wani sauri ya ɗago fuskana. "Mahbub?". Na jijjiga kai,"Beloved". Sai ya ƙara rungume ni yana faɗin,"Thank you for the name". Muna haka ya duba wayansa. "Kinga kiran Kudrat har four times, Allah yasa lafiya". ya faɗa yana kiran wayar kafin ya tashi tsaye ya saka doguwar riga ya fita bayan yace min yana dawowa yanzu. Fitarsa duk sai naji babu daɗi, zuciyata na harbawa, daga daren jiya zuwa safiyar yau adadin harbawan da zuciyata tayi yafi ƙarfin adadi, na ƙara nutsewa cikin kogon sonsa da kishinsa. Na bi ƙofa da kallo idona na ƙara haska min yanda ya fita da hanzarinsa saboda kiran Kudrat ɗin, duk yanda na so na danne na kawar amma na kasa, nan take naji raina ya ɓaci, gudun faɗawa cikin wani yanayi nayi saurin sakkowa akan gadon ina ambaton sunan Allah a cikin raina, wadrobe ɗinsa na buɗe na ɗakko jallabiyarsa na saka, sannan na shiga gyaran gadon, ban bar ɗakin ba sai da na gyara ko'ina tass, na je ɗakina na ɗakko turaren wuta na zo na saka, ai fa turaren Ummin Sauma ba na banza ba nan da nan ƙamshi ya gauraye gidan. Bayan na kammala na koma ɓangarena, na shiga wanka haka ina wankan ina aikin ƙunci, turarukan wankan da nayi amfani da su kuwa idan ka shigo ɗakin zaka tsammacin kamfanin turare ka shiga. Ina zuge closet na yi katari da an gyara min ita, kayana an jera su jere me kyau, abayas ɗin duka a hanger suke, ansa wadrob balls sai ƙamshi cikinta yake. Amma ya aka yi haka? Naga ai sai da ya rufe ɗakin da key tukunna muka fita jiya da daddare, ko kuma da ina bacci aka zo aka karɓa, na san gyaran ba zai wuce na su Maman Khairi ba, murmushi nayi ina gode musu da ƙoƙarinsu, ɓangaren da aka jera atamfofi na kai hannu na ɗakko wata super me kyan gaske, ɗinkin riga da skirt ne simple ba me hayaniya ba, dama gani da hips masha Allah, na yi simple make up ena nayi kyau abun burgewa wanda na san dole mijina zai yaba. Bakin gado na zauna tare da ɗakko wayata kafin na fita naje na gaida su Gwaggo, ina dubawa kuwa sai ga misscalls ɗin Safiyya har uku, Allah sarki ƙawar amana tuni fushin da na ke da ita akan kwana wurin kishiyata yabi iska, na bi bayan kiran tana ɗagawa kuwa da karaɗinta tace,"Su Beb an dirji soyayya wato sai ma yanzu naki garin ya waye, to ya amarcin da brother nah? I hope komai dai normal na san harka da sojojin nan ba wasa ba". Samun kaina na yi da jan tsaki nace,"Daman abinda kika kira ki tambaya kenan gulmamma?". Sai tayi shewa da faɗin,"Ahh lallai ne matar soja, kin sha madarar daɗi kin ƙoshi, bakinki a buɗe kike min tsaki ko". "Nayi ɗin". Sai ta sassauta murya da cewa,"Na ji ki a fusace, lafiya dai?". Amon muryarta ya fito da kulawa. Na rumtse ido sosai ina cewa,"Mayi magana idan kin shigo". Na faɗa ina yanke kiran". Abbana na kira, mun jima muna magana da shi a wayar, yana gida yana faɗa min bai ma fita kasuwa ba saboda ana masa gyaran sabon teburin da ya siya, muka yi waya da Ummani ma har da Kaka, duk sunata tambayana ya baƙon waje, albarkar nan tasu da nasiharsu ta kullum ba su fasa sa min ita ba, Jin muryar iyayena sai naji komai da ke zuciyata na rashin daɗi yabi iskar ɗakin ya tafi. Mun gama waya da Yashaik a lokacin Salim ya shigo, yana aikin bina da kallo kamar sabon gani a idonsa, nima kuma kaina na san dole ya kalle ni saboda kyan da nayi. Hannaye harɗe a ƙirji yake ce min,"Yaushe muka yi da ke ki taho nan?". Nayi masa wani irin kallo me tafiyar da imanin masoya nace,"Naga ka ɗan jima ne, ni kuma ina so nayi wanka naje mu gaisa da su Hajjo". Ƙarasowa yay ya zauna kusa da ni yana kama hannayena yace,"To na wa wankan kuma fa? Ni ban iya wanka da kaina ba, ga shi kinyi kwalliyan da ba zan so ya ɓaci ba". Sai ya marairaice min kaman yaro,"Shiyasa da kin ɗan yi haƙuri kin jirani na zo mun yi tare, ba ki san wankan miji da mata tare na ƙara danƙon soyayya ba, ko tsoro kike kar nayi maimaici?". Murmushi nayi ina jan hancinsa da cewa,"Kai bakinka ko, yanzu to ai sai ka tashi muje na taimaka maka ɗin, amma saɓi ɗaya zan maka ka ƙarasa sauran da kanka". Sai da ya ɗan matsa cikina kafin yace,"Ahaf ki yi min saɓi ɗaya saboda kina gudun kar labari yasha banban kenan, dama kema na san ai ba ki ƙoshi da ni ba". Ƙaramin filo ɗin kusa da ni na ɗauka na ƙwala masa, sai ya miƙe yana dariya da cewa,"Tunda kin min wayo ba za ki min wankan ba yanzu bari naje na shirya, idan ban wanku ba ke ce kika ja kar ki zo shimfiɗa kina min ƙorafi. Sai kije wurin su Hajjo ɗin nima naje mun gaisa da su, kafin nan na gama sai muyi break fast ko ma nace lunch tun da dai har azahar ya kusa". Na miƙe ina cewa,"Break fast ɗin ƴan boko ba, ka muje na maka wanka to ko da na ɓaci sai na sauya, kwalliyan ai dama na ka ne, kuma ka gani har ka yaba, so sai a ƙara yin wani ai ba za'a gajiya ba wajen yin abinda zai burgeka". Janyo ni yay jikinsa yana shafa gefen fuskana, sai faman yabon kyan da nayi yake yi, a hankali hannayensa na shafa marata zuwa cikina yace. "Soon wannan shafaffen wajen zai ɗauki ajiya insha Allahu". Maganar ta taɓa zuciyata, na ɗago ido na kalle shi da zummar yin magana, kamar yasan me nake shirin faɗa yayi saurin haɗe bakinmu waje guda, sai da yay me isarsa kana ya rabu da ni yana cewa,"Just sai Allahumma amin". A sanyaye na ce,"To Allahumma amin". "Awwa ko ke fa Myy, adu'a na sauya ƙaddara so muyi adu'a kawai Allah ya bamu me albarka". "Ko ban samu daga gare ni ba ma su Isioma sun ishe ni". Na faɗi hakan ina tunawa da baya, yanda duk sona da yaran Nazifi haka mahaifiyarsu tayi min katanga da su a ƙarshe har aka min ƙazafin kisa. Haɓarsa bisa kafaɗana yace,"My muna da buƙatar ƙarin yara, Baby ina son yara, so na ke ku cika min gidan nan da ƴaƴa inta kallon ku ina jin daɗi". Kunnena ya ɗan ciza tare da raɗa min magana, wai zan basa na rana yaji an fara tsikarinsa, sanyayyan murmushi nayi me faɗi wanda muka yi a tare da shi. Sai ce yay,"Na shiga na samu kuna magana da Safiyya a waya, saboda asaran kati irin na ku kuna cikin gida ɗaya, ko da yake na san gulmana aka yi". Na waro ido waje ina cewa,"Gulmanka kuwa?". "Ehh mana in ba haka ba Me kika ce mata to? Nasan dai ba za ki iya faɗa mata kin wahalar mata da ɗan uwa a daren jiya ba, sai dai zan so ki sanar mata ɗan uwanta ya rasa hankalinsa ta dalilin wannan halittar me kyawun sura, har yana tantamar akan da gaske ne kuwa matarsa ta taɓa wani auren a baya ba rufe shi kawai aka yi ba, Ki ce mata gaskiya ina da ja akan hakan, don ni hanyar da na shiga ba a taɓa taɓata ba". Murmushi nayi kawai ina sunkuyar da kaina, ina jin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ni, ni kaina a jiya nayi matuƙar mamaki, ko da yake ba ƙaramin gyara su Maman Yasmin suka min ba, ni kaina na rikice balle shi. Tare muka fita da shi a ɗakin, sai da na je na haɗa masa ruwan wanka da turarukan wankan da nayi amfani da su, na so nayi masa wankan sai dai yace no na bari nayi masa na anjima yanzu na je wajen su Hajjo kar na barsu da tunanin lafiya, su tsammaci ko yay musu kaca kaca da ƴarsu ne. Ina dariya na fito a toilet ɗin na ɗakko masa kayan sawa na ajiye masa, kana na fito na wuce wajen su Umman Batula, ina zuwa kuwa na faɗa jikin su Maman Yasmin cike da kunya har ina kasa ɗago ido na kalle su. Hajjo tace,"Allah ya dawwamar da ke a wannan farin cikin da na ke gani a fuskarki". Dukka aka amsa da amin. Wai sai naji suna min batun ai yanzu za su wuce, Abbaa ya kira ɗazu yana ta faɗa ba ko kunya sun zo sun yi zamansu a gidan siriki. Na ce,"Kwana biyun kawai? Ni fa nayi zaton ko sai zuwa jibi ma za su ku tafi". Maman Yasmin tace,"To ni har zagina ma sai da yay, yace bai ga amfanin ace sai mun kwana a gidanki b, mene ma na zuwan to tunda mun bada amanar taki ai sai mu kamo hanya, gidan na ki ma zo daga baya". "Kayiii Abbaa to shi da sai na zo gidana babu wani nawa, kenan ma ni na kawo kaina". Mama A'i tace,"Ai kin dai san halin Babanki, shi da ya so ma ku taho da mijin kawai ba sai an miki rakiya ba". "To kuma da gaske yau ɗin za ku tafi?". "Ƙwarai ma kuwa, ai yanda kika ganmu nan ke kawai muke jira dama muyi sallama, shima kansa Salim ɗin da ya zo yana ta mamaki yace ba zamu ƙara kwana ba, muka ce aa bar muku gida zamu yi ba a yi iyayen kawai ba". Ni dai duk sai naji babu daɗi da zancen tafiyar tasu, jikina yay sanyi, Maman Khairi na tsokanata wai ni da naje na ƙule ma na barsu, idan suka ƙara kwana ai abinda yafi haka za su fara gani. Maman Khairi ke ce min,"Ai da safen na fito da ke ƙarfe shida fa Abbaa ya doka mana kira Allah yaso wayar Maman Yasmin ce". Ta faɗa tana dariya. "Da Safiyya ai naci karo a falon, dama ina cewa zamu je ɗakin naki a shirya miki sauran abubuwa sai tace ai ta gyara miki komai". Sai naji raina yay min babu daɗi, na san fa tabbas Safiyya zata iya gyara min ɗakina amma saboda banzan kishi ban wani kawota cikin raina ba. Mama A'i na ta faɗa min kirkin Kudrat, suka ce ita ta zo ta tada su da asuba, da kanta ta shiga toilet ta saita musu ruwan zafi suka yi alwala da shi, kuma kafin bakwai ta kawo musu abin kari tana ta ce musu idan da akwai wani abu da suke buƙata suyi mata magana, sai faɗar kirkinta suke yi, Gwaggo na cewa ance dai baka saurin shaidar mutum amma ita wallahi har zuciyarta taji Kudrat ta kwanta mata, haka kuma ta shaidata shaidar da tana da tabbacin ba za su ji labari mara daɗi ba. Nan suka sakani gaba suna ta min faɗa da nasiha gami da shawarwari, sai ma da Hajjo tasa aka kira Kudrat suka haɗe mu gaba ɗayanmu, hannuna cikin nata haka Mama A'i tasa muka yi musabaha tana cewa adu'anta da dukkan fatanta yasa hannayenmu ba zasu rabe ba. Kudrat ɗin har da hawayenta tana ce musu suyi tayi mana adu'a don Allah kar a samu shaiɗanin da zai raba kawunanmu. Ina zaune nan wajensu anata hira, Umman Batula tace ba don aure me kai mutum inda bai tsammani ba ita ina ta taɓa tunanin zata zo wannan garin me uban nisa, sai ga shi ta kawo ƴa har ta kwana ma. Ana ta shaftan hira ni dai duk a ƙage na ke na tashi na tafi wurin mijina, hankalina na kansa ban son barinsa ahi kaɗai. Can sai ga Kudrat ta dawo da ƙaton tray na abinci ta aje, suka shiga yi mata sannu da aiki da ɗawainiya da su. Hajjo na cewa,"Ya kamata ki huta haka tun safe kike kai komo da mu, kinga mu abincin safe da muka ci har yanzu a ƙoshe muke wallahi, ya kamata ki huta haka kuma, an gode Allah ya shi albarka, munji daɗin yanda kika karrama mu wallahi kin mana kamar na ki". Tana murmushi tace,"To ai dukka ɗaya ne Mama, ku ɗin nawa ne nima ku ɗauke ni taku tunda har zama ya haɗani da ƴarku". Dariya ta suɓuce min saboda hausartata, ban da ɗazu da aka haɗamu ana mana nasihar nan ni ban taɓa jin tayi hausa ba, to ɗazun don ina cikin zafin kishi ne shiyasa ban ji gwarancin da kyau ba, ashe haka ta iya kwaɓa hausa, kuma ba wai kwaɓar ba ne, hausar akwaita a bakinta yanayin fitar maganar ne abin dariya. Ita ta dube ni tace,"Me kina wa dariya?". Ta faɗa da turanci sai na ce,"Ai da hausa za ki faɗa Madam". Ta kawo min duka tana cewa,"Ƴar wulaƙanci, zan zo in fiki iya hausan ne ai". Gwaggo tace,"Rabu da wannan ƙanwar taki, mu dai don Allah ki huta haka kin ji ƴata, hidiman yay yawa". Tace,"Mama waye zai gajiya da yiwa manyansa hidima, idan kana son ganin daidai ai sai ka kyautatawa iyaye, na ɗauke ku iyayena ina kwaɗayin adu'anku da albarkanku, ba zan gajiya da biya muku buƙatunku ba har ku tafi, ko wannan yarinyar ba zan bari ta ƙwacen lada na one second ba, komai ni zan ke yi muku". Naji daɗi sosai da yanda ta mutunta min ƴan uwa. Sai da zata fita ne take ce min,"Sisi na haɗe mana namu gaba ɗaya a dining ko ɗaki za ki tafi muku da shi?". Na ce,"ki yi mana yanda kika ga ya dace". "Ah ah ni dai ki faɗa don Allah". A hankali cikin wani yanayi nace,"To ki haɗa mana, gani nan fitowa". Tana fita baki ya ɗauka da nayi dacen kishiya. Na so naci abincin a wurinsu sai ga Foridat ta shigo tace,"Momi Maama tace ki fito mu ci abinci". Na tashi muka fita tare da ita ina riƙe da hannunta, ina tambayanta ba su je school ba tace min ai suna holiday. Dukkanmu kuwa muka zauna a dining har da Safiyya da yaran, Kudrat na mitan ni da Salim sai mun haɗa har na safe da bamu ci ba, ba zamu bar mata abinci ba, ita tayi girki ba Kuku ba, idan ba haka ba kuwa ɗumamensa zata mana da daddare. Ina dariya na ce,"Ni dai miƙo min plate ɗina, ke dai tunda kin dafa Allah yay miki albarka". A wanda ta zuba min Safiyya ta jaye gabanta, sai wani ta zubo ta miƙo min, haka muka ci abincinmu cikin raha, muna ta hirarrakinmu shi yana faman danna wayarsa, Kudrat na tsokanar Safiyya akan ta zauna mana sai wani lokaci ta tafi Safiyya ta hau bala'in mun rainata, saboda mun mayar da ita bata da miji shine amu mata wannan zancen, haka tayi ta bambami ni da Kudrat dai na ta mata dariya. Na ke cewa Kudrat,"Kema ashe wannan ƴar bata barki ba". Tace,"Idan Sofiyya na masifa to ina yi mata shiru ne, idan ta ise ni sai in kunna wayana in ware kiɗa n abarta da halinta". Cikin nishaɗin da kowannemu yake Sofiyya tace da Salim,"Brother ni ba zan ƙara yini a gidanka ba ka sallameni kafin matanka su saka min ciwon kai". Yana murmushi ya tashi ya barmu anan. Komawata ɗaki ne yake faɗa min su Umman Batula a jirgi za su tafi, na ce masa kuɗi ai zai yi yawa, sai yace Sir ne yace ba zai yiwu su zo a mota su koma a mota ba, zaman motar babu daɗi, tunda akwai hali zasu tafi a jirgin kawai, nayi ta masa godiya kuwa da nuna masa jin daɗina. Gabanin la'asar muka raka su airpot suka tafi, kamar kar a rabu ni dai har da ƙwallata, Safiyya nata min tsiyarta, shi ɗin ma bata barshi ba sai da ya ranƙwasheta a ka, haƙiƙa nayi kewan su tun ba'ai nisa ba, Gwaggo ce take haihuwa me rana yau ga shi silar arziƙin ƴa za su hau jirgi. Bayan mun dawo daga rakiyar tasu ne a mota yake min zancen dinner ɗin da abokan aikinsa suka shirya mana, yace anan cikin barrack ɗin namu za'ai ba a wani waje da nisa ba. Ko da muka koma gidan aje ni yay yace zai je wani waje. Ni da Kudrat muka zauna ita tayi ta min hira tun ban saki jiki ba har na ware, yaran na gefenmu suna na su wasan, da kanta ta kira min Mamanta ta haɗamu a wayan muka gaisa, itama Mamanta mace me halin mutunci, tana ta ce min daughter ne, muka sa wayan a handsfree ita kuwa dai faɗa ta dinƙa mana har da cewanta idan bamu haɗe kanmu ba sai ta zo har gida tayi mana duka, cikinmu duk babu wanda yafi ƙarfin duka a wurinta. Sai bayan isha'i ne Salim ya kira Kudrat, yake ce mata mu shirya da ya zo tafiya zamu yi can wajen dinner ɗin, shirinsa ba mai wuya ba ne. Kudrat ce tayi min kwalliya ashe makeup artist ce, nayi shigan white material na gown, nayi kyau sosai a ciki, su kansu yaran cewa suke Momi kin yi kyau. Ita kuwa haka ta dage tana tayi min hoto a iphone15 ɗinta. Sai da muka gama shirinmu muna ta zaman jiransa a falo tukunna ya dawo, ba ƙaramin daɗi yaji ba da yanda ya same mu, don sai da ya kasa ɓoye farin cikinsa, har da ce mana,"Yawwa kunga yanda na sameku ɗin nan tare kuna hira kuna dariya, haka na ke so na sameku ko da yaushe har sanda zan daina numfashi a doron ƙasa". Ni ce me saurin cewa,"Please ka bar mana zancen mutuwa". Ya murmusa kunci yace,"Mutuwa dole ne". Kudrat tace,"Mun sani ai, yanzu dai jeka shirya". Shima shigar white suite yayi yay kyau sosai, sai dai muna zuwa can wajen taron suka sa shi sai dai ya cire ya saka uniform ɗin su. Ni dai ƴar kallo na zama a wajen don duk wadanda suka zo mana murna magana suke da yare. Ba wani taron mutane aka yi ba na azo aji a gani, iya ƴan barrack ɗin ne suma kuma manyan cikinsu duk da iyalinsu, ai kuwa naga yanda ake shan barasa kamar lemu haka aka dinga fasa kwalabenta. Na kasa daurewa sai da na taɓo Kudrat na yi mata gulman. tana dariya sosai tace ai kusan duk cikin barrack ɗin mu ne kawai Allah ya zaɓa da gidan wani soja Moses nan ne kawai ba'a shan barasa. Amma ko gidan mutum kaje aka tashi kawo ma ruwa sai an haɗo maka da ita. Kiɗin da aka saki shi yaja mana lokaci, ban san Salim haka yake ba ai, ya shiga sai rawa suke tiƙa ba ya ko jin kunyar yaransa. bamu baro wajen dinner ɗin ba sai after eleven, kyautukan da suka ba ni har da na kuɗi, har da ƙaton frame da aka mana na hoton mu gaba ɗayan family ɗin, nawa ne aka yi merging akai nasu kuma already dama akwai shi, lokacin Rofi'at na jaririya. Kafin mu ƙaraso gida yaran duk sun yi bacci a mota, Foridat ce kawai idonta biyu itama don suna buga ludo game ne da Kudrat, Allah sarki babu ruwanta tana kujeran baya ina gaba, ko irin nunawan nan fa sam, dalilin hakan har sai da na tuna ranar da zamu fita da Zahra'u nayi ƙorafin ta shiga gaba Nazifi ya nemi yaci mutuncina, gaskiya samun irin mata kamar Kudrat a wannan zamanin sai an tona. Haka muka dawo a gajiye, duk kuwa gajiyan da muka yi hakan bai hana Salim ƙara ɗora min wata gajiyan ba, don haka yace shi kam bai iya missing zaƙin madaran da ya sha jiyan, hakan kuwa na biye masa muka sha bidirinmu. To Alhamdulillahi a sati uku da nayi cikin sabuwar rayuwar auren da na samu babu abinda zan ce da mahallicina sai godiya, ko a iya haka aka barni. Haka kuma ina yiwa duk wani wanda ya fuskanci ƙalubale irin nawa fatan samun kyakykyawan farin cikin da ta fi tawa, ina ganin soyayya da kulawar da ban sami irinta a baya ba, ban wani san tarairaya daga wurin miji ba irin yanda na ke samu a yanzu, ban san tattalin mace kamar ƙwai ba a wajen namiji, na dai san bautar miji da bautar ƴan uwansa. Kuma a rayuwan baya na san na shaƙu da Nazifi fiye da dukkan tunanin me tunani, haka na so shi wani irin so da na ke jin ba zan iya rayuwa a duniyar da babu shi a tare da ni ba, sai dai mamakin kaina na ke yi a yanzu, to shin anya son da na yiwa Nazifi so ne da ake kira asalin so muraran? Saboda ji na ke yi kamar akan Salim na fara son wani ɗa namiji, son da har na ke jijjiga idan na sami gimlawar tabbatacciyar da zata iya raba tsakaninmu, a yanda na ke ji yanzu ji na ke kamar zuciyata dama can an halicceta ne da jinin soyayyar Salim. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR16FT5* Tsakanina da Salim zaman rayuwa mu ke yi me cike da jin daɗi, tsumammiyar soyayya, kwanciyar hankali, farin ciki da fahimtar juna. shi kam irin mazan da kowacce mace ke kwaɗayin samu ne, wai ance soja bai sakewa iyalinsa to shi dai ba haka yake ba, a waje yake soja amma a cikin gida abokin iyalinsa ne. Namiji ne me kyautatawa iyalinsa, me bawa iyali lokacinsa, me wasa da dariya da su, idan har yana gida to yana cikin matansa da yaransa ayi ta raha, yay ta mana barkwancin da cikinmu sai ya ƙulle don dariya, kuma ko da yaushe cikin tambaya ya ke ba ku da wata matsala? Me kuke so? Zan yi kaza ya kamata nayi mene shawaranku akai?. Duk abinda yaci a waje kuwa in Allah ya yarda muma sai munci sai in ba a garin yake ba amma sai ya rago ya taho mana da shi, babu nuna wani banbanci tsakanin mu, nuna mana yake dukka matsayinmu guda a wajensa babu wadda tafi wata, kyauta idan zai mana iri guda haka zai siyo mana, kuma shi ba irin mazan da sai sallah sallah suke wa mace suttura ba ne, in dai yay tafiya musamman in lagos yaje to zai kwaso mana ƙanan kaya kuma haka zai kwaso su kamar kayan tagwaye kala ɗaya sak, to suna ma ya koma ce mana Hassana da Hussaina. Ni dai yaransa kuwa ba ƙaramin daɗi naji musu ba, samun uba irinsa rahma ne wallahi, bai da kyaran yaransa ko hantaransu, ko kaji yaro yaji muryan ubansa ko gyaran murya ya natsu har yana neman maɓoya, inaa ai shi da sun ji yo shi za su falla a guje tafiya taro shi, haka zai shigo da su a ɗaɗɗafe a jikinsa. zai zauna cikinsu yay ta wasa da su, shi ne yi musu makawuya, doki, ƴar guje guje, ball a compound haka zai tayi da su a cikin gidan, idan kuma karatu ne ya kama nan ma zai zauna ya koyar da su, ga ibada ko tafiya zai yi ya dinƙa roƙonmu akan mu sa ido akan ibadarsu, yaran har sun saba ma ana kira sallah kowacce zata wuce tayi alwala hatta da Rofi'at me shekaru huɗu, in bacci kuwa za su yi wallahi kaf ɗinsu da karatun ƙur'ani a baki haka bacci zai ɗauke su, na lura kuma koyarwar hakan ba daga gare shi ba ne kawai har da mahaifiyarsu don itama ba baya ba. Na ƙara fahimtarsa sosai, shi me son a kiyaye ka'idojinsa ne, shiyasa ko da yaushe na ke iyakar ƙoƙarina wajen yin abinda yake so, na kuma guji duk abinda na san ba ya so, kullum godiya na ke ga Allah da ya sauya min abokin rayuwa, wanda sai a tarayyata da shi ne na san haƙiƙanin jin daɗin da ake kira a zaman aure, za ki yi bautar aure zaku ma ki huta a gidanki, ba irin gidan da na baro ba da ba ki da lokacin kanki. Salim har girki yake tayamu, ko gyara kike haka zai miƙe yace me zan tayaki da shi, idan kika hanasa sai dai ki jisa a toilet yana wankewa, babu girman kai sam a al'amarinsa, wani jin kai na shi me gida ne sam sam bai da shi. Kuma bai hana mu business don yana da kuɗi ba, ko kuma saboda matsayinsa, sam ina business ɗina na kunun aya da na ke yi tun a gida, cikin barrack ɗinmu siyansa suke kamar ruwa, har wani restaurant na ke yiwa suna zuwa su karɓa, to fa duk sanda zan yi indai yana gari muna zubawa a jarka shi kuma yana saka mana murfi da inji. Itama Kudrat ɗin tana yiwa wani restaurant baked meat pie, nan ma shi ke sakawa a oven ya barmu da zuba nama da dannewa, in ya so ma kwaɓin sometyms shi yake yi, kuma sam bai san ya sawa kuɗinmu ido ba, ya san muna samu amma in har mun tambaya kai tsaye zai ɗauka ya bamu, babu zancen tuhumar ina kuɗin da kike samu ko complain ɗin kin fiya a baki a baki, yace kuɗin mu namu ne mu yiwa kanmu hidima, sai in mun yi niyyan taimaka masa ne, shiyasa ga shi nan Allah na ta ƙara buɗa masa. Lokaci lokaci haka zai kwashemu mu tafi yawon shaƙatawa, yanda yara za su hau lilo haka muma zamu hau kai, ni dai wannan rayuwar na min daɗi, to ta ina ma zaka yi baƙin ciki balle ɓacin rai? Ina kake da lokacin tuna baya? Rayuwar gidan Salim rayuwa ce ta jin daɗi da farin ciki, abinci wataran ma ce yake mu huta da girki sai ya ɗebe mu a tafi restauran aci, idan za'a dawo ayo takeaway ɗin wanda za'a ci da daddare, haka ya ɗebemu muje shopping kowa ya jido abinda yake so, wataran ya saki kuɗi kamar bai san ciwonsu ba, wani sa'in kuma sai yace ai siyayya saffa saffa bai da kuɗi sosai, wani sa'in ma sai ana zaune sai yace da da kuɗi da anje shopping, amma tunda babu ya zamu yi sai muyi haƙuri, kuma ba wai babun ba ne, a'a kawai yana koya mana rayuwa ne ta yanda in mun samu lafiya idan babu ma lafiya, musamman ma yaransa. Tuni na koma bakin aikina, ashe already ya sama min aikin tun kafin auren anan wani asibiti Westend Hospital, sai da na cika sati biyu ya ke cewa na shirya muje ayi min interview, asibitin babba ne kuma private, cikin sati sau huɗu kawai zan dinƙa zuwa, monday and wednesday aikin safe, sai friday and saturday aikin yamma, kuma albashina ma har yafi wancan ɗari biyu zan ke ɗauka. Ina ta zuwa wajen aikina, idan morning duty ne da ni tare muke tafiya da Kudrat da ike ita tana da mota, yace nima kafin ya siya min tawa, idan na yi evening kuma zan hau cab a tagiya, Kudrat ɗin ita zata je ta ɗakko ni babu yanda ban yi da ita ba akan ta barni na ke dawowa da kaina taƙi, Salim yace shi bai yarda ya bar matansa da driver ba, gwara ya siya miki mota ki yi ta sakarftunki, Yaran dama kuwa school bus ke kai su ya dawo da su, bokonsu me haɗe da islamiya ce tun bakwai idan suka tafi sai shida da rabi suke dawowa. Duk ranar da na ke evening da ke ina kaiwa tara na dare, kafin nayi closing sai dai naga yara sun zo sun kewaye ni suna Mommy mun zo ɗaukan ki, asibitin har an sanmu an san yaran, da yawansu ma ce suke ni da Kudrat sisters ne, kuma a haka na barsu ba wanda na nunawa abokiyar zamana ce, to in ma na faɗa sai a iya ƙaryata ni dan ba'a san kishiya da kishiya da irin rayuwan da muke yi ba, kanmu haɗe yake, abinda mijin mu ya ɗora mu akai shine mu riƙi juna, shi ma kuma bai fifita wata cikinmu, to ta ina wata zata tsiri buga iskanci? Ni da kishiyata zama muke na mutunta juna da girmamawa, don tuni na tsayar da hankalina waje ɗaya na kama hanyar da ta dace, ki sakawa kanki banzan kishi ne fa ki sakawa kanki damuwa da zubar da aji, gwarama idan ace kisjiyar ce bata da kirki sai kema ki nuna mata kin fita. yanda muke zaune kamar ba kishiyoyi ba, akwai baƙuwar da aka yi sai zuwanta na uku ne ma take cewa wai dama kishiyoyi ne mu, ita wallahi idan ta zo yanda take samunmu ta zaci ya da ƙanwa ne. Kudrat macece wadda ta iya mu'amalantar wanda ke tare da ita, zama na gaskiya da amana babu munafurci ko ƙullaci, macece me sauƙin hali da bata da damuwar komai, zuciyarta a buɗe take, bata da ruƙo sam sam idan abu ya haɗaku kai tsaye zata fito ta faɗa maka ko da zaka ji haushinta, haka ko laifi ka mata wallahi a ƙarshe ita zata baka haƙuri tace maka mece rayuwar? Nawa take? Wataran duk wayan gari zamu yi babu mu? So muke muje mu gamu da Allah lafiya, to don me zamu aikata abinda ba ya so? Gaba bata da wani amfani, idan an sami saɓani a fahimci juna kawai a wuce wajen a ci gaba da rayuwa. Kuma ƙarya ne kayi rayuwa da ita ba ka ɗauki ilimi ba, ina nufin ilimin iya zaman rayuwa da koma waye, nurƙufanci, ɓacin rai, jin kai Kudrat duk bata da wannan. Yaranta ta sakar min su kamar nawa, ko daga baya sai da ta tambaye ni wanne suna na fi so suke kirana da shi na ce mata Mommy ɗin ma yayi ina so, ga yaranta a nutse ba rashin ji, wai irin ma idan ɗa yay ba daidai ba kishiya ta tsawatar masa kiga uwarsa na cin magani ko a hau rigima, inaa ai ita kawai kece uwarsa idan ma zama za ki akan yaro indai laifi yayi ba zata ji haushi ba. Abinci kuwa bata yarda wai muci abinci daban daban ba, a plate ɗaya zata zuba mana musa hannu muci mu ƙoshi, a wurin ta ma na koyi hakan, don farko idan nayi girkina kawai ina zubawa ne na ci, to ita kuma da ta sauke ko da safe ne zata zo tace min na taho muci abinci, tun banci yau da gobe dai da bata gajiyawa da min bismillah ba har na zo ma nima bana iya girki ba da ita ba, idan bata gida na dafa zan aje mata tunda ita aikinta kullum ne, week end ne kawai bata fita. idan damuwarta ta ɗakko ni zata zo ta zayyanawa tana cewa Momin Rofi'a bani shawara, ko Momin Rofi'a abu kaza nace yayi in yi?. Saboda yanda Rofi'a ɗin ke maƙale min kawai ta koma ce min Momin Rofi'a amma da Sisi Nah take cewa, Rofi'a ɗin ma yanzu a wurina take don tuni ta tattaro min kayanta tace mu ƙarata can. Idan baƙon sani ne ma kai zaka ce ko ni ce uwar yarinyar. Haɗin kan kuwa da muka samu ba ƙaramin daɗi yaywa Mijinmu ba, dalilin hakan har kyauta yake yi mana, yace kyautan kun haɗe min kanku ne kuna zaune lafiya, yay tayi mana godiya. To mu kanmu mun fi jin daɗin yacca muke zaunen, ba fa mu san mu ƙule a ɗaki ba, a'a uzuri ne kawai ke kai ki ɗaki sai in bacci, amma falo muke yada zango, in kallo ne ayi in hira ce ayi, ayi wasa ayi dariya ba cin muutuncin juna ko ɓatawa juna. To ni da banda ƴan uwa ma a garin, ita da take da su sun koma kamar ƴan uwana idan suka zo gidan, sai su zo kai tsaye su taho wurina su ce wurinki muka zo Momin Rofi'a. Gaskiya da farko na so na bawa zaman namu matsala, ina iyakar yina wajen ganin na danne kishina amma sai na kasa, har ta kai ga wata rana lokacin watana guda, Salim yay tafiya ya dawo ni kuma naje kai Isioma asibiti taji ciwo a makaranta garin lilo, to dawowan da zai yi a wurina zai sauka, ai kuwa ina zuwa na tarar da shi can ɓangarenta ya baje yana cin abinci suna hirarsu, wannan abin ya ƙona min rai, zuciyata ta sosu, don me a ranata? Duk da dawowan bagatatan yay ai sai ya jira na dawo tukunna na samar masa da abincin da zai ci, mayunwaci ne shi da ba zai iya riƙe yunwar har na dawo ba, ko kuma idan ya zauna a ɓangaren nawa kashe shi za'ai? Haka na cilla musu ledan maganin Kudrat na min magana naja tsaki na fita. Ai kuwa ranar na dinƙa masa banbami na tayar masa da hankali akan kar ya ƙara cin abincin kishiya a ranar shigata, ko kuma ya tafi zuwa wajenta, fuskarsa ta nuna ɓacin rai sai dai sam bai biye min ba, hasalima haƙuri ya shiga bani yana lallashina, amma na fututtuke masa na ɗaura gaba da shi, har ina cewa ni sai ya raba mana gida, haka muka zauna da shi har ya koma ba na masa magana, girki ma sai in yi inci kayana ni ɗaya. Kuma tun wannan lokacin na ɗaukewa Kudrat kai itama na daina sauraronta har yaje ya kuma dawowa, acewata ai ita ta haɗa ni da mijina. Sai bayan dawowar tasa ne yaga bama mu'amala da juna, ya saka ido yaga idan tayi min magana sai dai na gaggaya mata magana ina faɗin makira munafuka macuciya, ranar kuwa ashe ya jini muka gauraya da shi a ɗaki, ranar naga ainihin Salim na san kuma wanene soja, na kuma san asalin kalmar tsayayyan namiji a gidansa, don nuna min yay akan matarsa bai ƙi ya sallame ni ba, kai ni ban ma taɓa tsammanin zan sake kwana a gidansa ba wallahi, har ya fita a ɗakin jira kawai na ke ya dawo yace na kwashe kayana na bar masa gida, ashe fitan kiranta yay itama ya haɗamu a falo yaci mutuncinmu gaba ɗaya tun balle ni, ita kuwa duk ta ruɗe hankalinta ya tashi akan yanda ya hayayyaƙo min, tayi ta basa haƙuri tana ba laifina ba ne nata ne, haka ta dinga kare ni a wajensa har sai dai da gaske faɗan ya koma kanta, kuma ta amshe sai haƙuri kawai take basa. Yay fushi da ni fushin gaske, zan yi abinci yaƙi ci, in magana ya shareni, a zo bacci kamar ba mata da miji ba. Na shiga damuwa matuƙa, sai a lokacin na ke jin rashin kyautawar abinda nayi, to Allah na tuba mutumin da ke hidimta min, yake nuna tsananin so da kulawa, ya wanzar da ni a daddaɗar duniyar da na rasa a baya, ko bai ce kar na tada fitina a gidansa ba ai bai kamata ba ni a karan kaina. Ai kuwa naji jiki da ɗauke min kan da yay, wancan karan ai ni kaɗai na ke gabata shi bai tsaya biye min ba. Naga ba zan iya da shariyarsa ba sam, ranar yana bacci na rungumo abina ta baya ina saukar da hawayena masu zafi a gadon bayansa, muryana ya fito da sautin tausayi da nadama ina faɗin,"Mahbub kayi haƙuri don Allah ba zan ƙara ba, ka yafe min laifin da na aikata, zan zama me kiyayewa insha Allah". Yi yayi kamar bai san ina yi ba, yay kamar bai farka a baccin ba, sai da yaji ina kuka haiƙan sannan a hankali yace min,"Ba sau ɗaya na faɗa miki ba, ba biyu ba, amma kika take maganata. Ba na so So'ida, ba na son haifar da rigima wannan shine last da zan maimaita miki". Rungumesa na ƙarayi ina cewa,"Kayi haƙuri anyi farko an kuma yi ƙarshe". Juyowa yay yana ce min,"Kinga ko a musulunce zargi bai da kyau, idan kika biyewa zugar shaiɗan kuma yana raya miki abubuwa kina ɗauka shikenan ya buɗa miki hanyar rashin samun natsuwa da kwanciyar hankali, ga shi ki kwasarwa kan ki zunubin zargi". "Kayi haƙuri Mahbub ba zan ƙara ba i promise you". Na faɗa ina daɗa lafewa a jikinsa. Washegari da kaina naje na sami Kudrat ɗin da niyyan bata haƙuri, amma matar nan ta inda na ƙara yarda da pure heart ɗin da take da shi rufe min baki tayi, alamu na bama ta so taji maganar, ta janyo ni na zauna kan kujera, ƙoƙarinta kawai sai ta kawar da batun sai take ta ɗakko min zancen bikin sister ɗinta, zamu je can zamu kwan biyu tunda Paapa(Salim) bai gari lokacin. Wallahi ba ƙaramin kunya naji ba, sai abun ya ƙara min ciwo, duk da haka sai da na bata haƙuri, amma hakan take ce min ita bata san ma anyi ba, idan ma anyi ta manta, nima in yi haƙuri don Allah. Tun daga lokacin ne kuma na sauka daga kan keken ƙayar da shaiɗan ya nemi ya ɗora ni akai, muka koma zaman mu lafiya. Ɓangaren Family ɗin Salim tsakanina da su sai adu'ar samun aljannah, sun ɗauke ni tamkar ƙabilarsu haka kuma sun mayar da ni kamar ɗiyar su, dama Kudrat ta taɓa faɗa min haka Familyn Salim su ke wajen mayar da inlaw kamar su suka haifeta. Ku san ko da yaushe sai an kira anji ya muke, idan yau ni aka kira bayan mun gama gaisawa za'a ce na kaiwa Kudrat ɗin, haka itama idan ita aka kira za'a ce ta kawo min duk dai dan aji ya zaman namu yake. Idan ba ya gari kuwa an dinƙa mana aiken abubuwa ba wai don babu a gidan ba, tsaban kulawa ne kawai, da zarar yau ya ɗauke ƙafa Sir zai kira mu da kansa kowacce yace mata ga kuɗi nan ya tura mata. Ɓangaren ƙannensa kuwa ni ban san wani rashin kunyan ƙannen miji ko rashin ladabi ba irin na hausawa, yanda suke girmama Yayansu haka muma suke girmama mu, ba su kaɗai ba hatta Yayyunsa cikin girmama juna muke da su, Babban Yayansa Chibuzo kuwa mutumin nan ya mayar da mu tamkar iyalinsa, da yake bamu da nisa da su shima duk wani aike da zai wa iyalinsa zai sa a kawo mana, musamman Yaran duk abinda ya siyawa Ƴaƴansa to sai ya siyawa ƴaƴan Salim. Ni dai sai kewa ta gida kawai da ta zama dole, banda ina da iyaye a raye ai zai mance ne ma da garin Kano. Iyayena duk sanda muka yi waya da su tambayan farko ya kuke da abokiyar zamanki kafin ya kuke da mijinki zai biyo baya, kuma wannan na san dan sun san yana sona ne banda matsala da shi, ba kuma mayin sallama sai na kaiwa Kudrat sun gaisa musamman Abbaa, kafin yanke kira zai ce min kaiwa Kudrat, ba ƙaramin daɗi suke ji ba da sakamakon canjin da na samu. Ƙarshe ma Abbaa sai karɓan lambar Kudrat yayi, sai dai naji tace,"Momin Rofi'a ɗazu muka yi waya da Abbaa yace yana gaida ke". Har na ke mamaki ganin fa ni bai kirani ba amma ita ya kirata. Wata rana kuwa muna cikin kallo sai ce min tayi,"Da safe mun yi waya da Ummani, tana cewa aiken me zata saka a mota a kawo mana nace mata daddawa da kuka". Ba shiri na juyo ina kallonta nace,"Amma kuwa kin cuce mu, aike tun daga kano mu ƙare a daddawa da kuka". Tana dariya sosai tace,"Idan ba zamu yi amfani da shi ba sai mu koma sana'arsa, za ki kyau da me siyar da daddawa, a bakin gate Paapa zai mana banch". Na kira Ummanin ina cewa ni ban yarda da wannan batun ba, sai ce min tayi ai bani tace zata kawowa ba ƴarta zata kawowa. Ina cikin wata na takwas Salim ya biya mana saudiya, lokacin za'ai aikin hajji, duk bamu san da tafiyar ba sai da ya rage saura satika, ni dai kamar an tsunduma ni a aljanna haka naji, ita kuwa Kudrat da ke ta jajje normal taji ta. Wallahi tsabagen farin ciki ban iya bacci ba a ranar, kwana nayi ina godewa Allah na, kwana nayi ina zabgawa Salim adu'a, godiyan farin ciki har da su kuka. Yace min,"Mene na kukan kuma, in dai saudiya ne yanzu kika fara zuwanta ke dai Allah yaci gaba da buɗawa". Kudrat ita da yaran suka fara tafiya amma banda Rofi'at tunda ita a wurina take, ni da shi sai da muka biya ta kano, sai fa lokacin na zo gida tun auren, duk sanda nayi maganar zanje sai yace na bari sai ya samu hutu me yawa sai ya kai ni da kansa naje in yi kamar two weeks, tun ina maganar ina nacin har ma nayi fushi na daina, Ummani ma da na ke mata ƙorafi take ƙara nanata min auren daa sai afi shekara ma ba'a je gida ba. Zuwan nawa kuwa ba ƙaramin farin ciki iyayena suka yi da ganina ba, musamman ganin na ƙara canjawa kamar ba Sa'idan da suka kai ba, ƴan uwana ma farin cikinsu ba zai misaltu ba. kwana na huɗu ina zazzagawa dangi da ƴan uwa da abokan arziƙi, gidan Safiyya na fara zuwa na yini sai dare ya zo ya ɗauke ni, da yake shi a gidan su Safiyyan yake kwana, naje gidan Hassana Tijjani da Maimuna, duk wanda ya ganni sai yay sha'awata sai yay min murna. Satinmu ɗaya a kano jirginmu ya ɗaga zuwa ƙasa me tsarki, la'ila ha'illah Allah ya kira duk wani musulmi zuwa wannan ƙasa, ni ban ma san ta yanda zan musalta muku irin daɗin da na ke ji ba, wani irin sanyi me daɗi da shauƙi zaka ji yana ratsa jikinka tun a jirgi, a sanda ƙafafunka kuwa su ka taka ƙasar ji zaka yi gaba ɗaya yanayinka ya sauya, Allah Alhamdulillah, godiya gareka a bisa tarin ni'imomin da ka yi min, a can muka samu su Kudrat su har sun buɗe ido ma don satin su guda. Na ziyarci ɗakin Allah, na ɗaga hannu nayi kuka nayi kuka, ba kukan rashin wani ahu ba face zallar farin ciki, kuka na ke na tsantsanin farin cikin ganina a gaban ka'aba ɗakin Allah, ga ni gata ina taɓata, Ya Allah! Hawaye kuwa da yana ƙarewa tabbas zai ƙare a sanda na ke gaban ka'aba. A duk sanda na je ƙabarin manzona da kuka na ke barin wajen, ni kawai ji na ke kaman in ƙare rayuwana a gaban wajen, ko da mutane zasu dinga tattake ni suna bi ta kaina, in sallamar in ƙara yi bana gajiyawa. Mun yi aikin hajji lafiya lafiya sai fatan Allah ya karɓi ibadunmu, ai kuwa na yi adu'an Allah ya bani halin da zan kawo Abbaa da Ummani wannan waje, haƙorin makka ai har biyu na saka, wai muna bidiyo da Safiyya ce take to farin shiga kar dai ki dawo mana kina faman yaƙe haƙwara, Ummani ma tace Hajiya Sa'ida haƙorin ya ƙara miki kyau sosai. Watanmu guda curr da ɗoriya muka fara haramar tafiya, har ga Allah da ni na kawo kaina wallahi ba zan tafi ba, ai nan kuma naga wurin zama, kuka har da su majina zan bar saudiyya. Da saudiya kuwa Dubai muka wuce direct, kaman a zuwa ne Kudrat suka wuce gida najeriya, ni da shi da Rofi'at kuma muka wuce dubai ɗin yace kamar yanda ya kai Kudrat nima hakan ne. Ai ko dai mun yawata a dubai, tun da muka je ba zama kamar wadda taci ƙafar kare, har ce masa nayi dama a can Saudiyan ka bar ni wallahi. Dubai ma fa ba dai kyau ba, arziqi me daɗi, inda kuɗinka ka sha shagalinka, haka na dinƙa bugawa Salim ƙauyanci yay ta dungure min kai yana ƴar madobi kawai. Ni kuwa da na samu sake a wurinsa bai hana ni fita ai sai na nemi wuce gona da iri, ko yana gida saɓar Rofi'a na ke mu fice inje in ta sakar laɓɓa ina ganin dogwayen gine gine, in ta jido siyayyan kaya yanda na ke kwasan abaya kun ce sana'arta zan fara, haka na yita yawon buɗe ido sai dai muyi waya da shi in ce ina wuri kaza. Aikuwa a sati ukun da muka yi a dubai nayi wani fari kamar me shafa mai, fatana tayi sulɓi sai kace hutu na ke samu, ni dai to ban huta ba sai in ƙasar ce ta amshe ni, yo ban zama ina naga ta zama, yawo kullum ina kan hanya, yay ta mitan in barsa ya dirji soyayya a yanda ya samu hutun aikin nan, nace enaa ai soyayya ka jira mu koma delta, haka yake haƙura sai daren nan amma da safe da rana ina can na tafi galantoyina ni da ƴata, nayi wata ƙiba yanda ku ka san ina shan sha ka fashe, shi kansa Salim sai da yace ko sai yanzu Kunun Tamba ɗin da kusan kullum muke break fast da shi ya fara bin jikina, tunda yana saka ƙiba mutum yay mulmul da shi, Kudrat ƴar sharri har da cewa ko dai surgery naje aka min a kumatu suka yi luhu luhu haka kamar fanke. Sai da muka yi sati huɗu ciff kafin mu ɗakko hanya, ina ta ce masa yaywa Allah ya tattaromu mu dawo Dubai da zama, me ake da wata lanjeriya, ya biye min kawai da cewa,"To! mu dawo nan ku ga bayan ATM ɗina ko, ko da yake dama ai ga ƴan naija ɗin nan suna ta tahowa aikatau, idan kun ƙarar da ni sai in koma shara da wanke wanke tunda salery ɗin da yawa". Nace,"Allah ya rabaka ya kiyaye". daga nan nace a bar zancen, sai yay ta dariya. Bamu wuce delta direct ba sai da muka sauka a kano na kaiwa iyayena da ƴan uwana tsaraban Makka da Dubai, aike har da Hassana Tijjani, Salim ya kyauta min muka je har wudil wajenta, ranar tayi farin ciki nima kuma nayi, don gaskiya Hassana tana da matuƙar kirki. kwananmu biyu a kano sannan muka wuce gida. A tsaraban da na yo zan iya cewa gidan su Salim in har a cikin gidan kake ko da tsinke ne kai to ka samu tsaraba daga wurina, kowa yaji daɗin karan da na musu sai cewa suke Allah ya maida ni don na iya tafiya. Shekarana ɗaya da wata biyu da aure na fara shirin tafiya ƙaro karatu, kamar yanda muka yi da Salim dama yace min ba zai hana ni ba idan ina so, sun yi maganar ma da Abbaa, ko ina na ke so zai ƙyale ni naje kamar yanda ya bar Kudrat itama lokacinta. Da muka yi waya da Ummani take cewa,"Sa'ida me yasa ba za ki bari sai gaba kya ɗora ba?". Nace,"Ummani ai gwari in yi in wuce wurin kawai, shekaru ƙara tafiya suke, kayi da ƙwarinka zai fi, kuma wata ƙila yanzu ne damar tawa". Tace,"Haka ne, to Allah ya taimaka ya bada sa'a". Harvard University ita ce makarantar da na zaɓa, da naji kuɗin makarantar sai da na razana, na cewa Salim,"To ko dai kawai na haƙura nayi anan?". Yace,"Babu komai Allah zai yassare, zan yiwa Sir maganar yana da hanya, zai samar mana insha Allah". Nayi farin ciki sosai, Salim ya ƙara ƙima a idona. Sai a lokacin ma na ke basa labarin wancan lokacin ma da na tafi wani bawan Allah ne ya ɗauki nauyinmu, yace,"Allah sarki ai kuwa ya kyauta haka ake so masu shi su dinƙa aikin alkhairi, sai Allah ya daɗa buɗa musu, Allah ya saka masa da alkhairi". Na ce,"Amin Mahbub, wallahi ka ga ni dai har yanzu duk adu'ana sai na saka shi a ciki, ko da muka yi aikin hajji ma Mahbub sai da na ta faɗawa Allah na ce ya yalwata dukiyar bawansa kuma ya dawwamar da shi a farin ciki da kwanciyar hankali, yay masa sakayya da gidan aljannah". Yay murmushi da cewa,"Allah ya amsa Myy kin masa adu'a me kyau, haka ake so ai mutum kar ya zama me manta alkhairi". Na ce,"Wallahi dai wanda yay maka gata haka ina zaka manta da shi, mutumin da ya kawo maka canjin rayuwa, banda silar ina ni ina taka matakin da na kai. Ni dai Mahbub ka ga har sadaƙa ina yi masa fa, wainar da kaga ina sadaƙa duk friday gare shi na ke cewa Allah ya isar da ladan ai ban iya kuskure ba ko?". A lokacin kawai sai naga ya dire laptop ɗin da yake dannawa ya rungume ni, ni dai na jima bai min runguma irinta ba, yay shiru kamar me bacci ina ta shafa kansa ni kuma, don naga kamar natsuwa yake so ya samu da hakan, sai can tsawon wani lokaci tukunna na kira sunansa sai ya sake ni yana cewa,"Allah yay miki albarka Baby, na gode sosai da sosai Allah ya jiƙan mahaifanki ba don sun mutu ba, ki ci gaba da masa adu'a da sadaƙan Allah ya amsa ya raba muku ladan". Na tambayi shi adu'an fa na mene, sai ya manna min kiss yana cewa,"Na soyayyanki ne, Allah ya raya min ke in ga auren Rofi'a". Nan fa na gyara zama na shiga karanta masa wata wasiƙa kamar yarinya, wai zancen tanadin auren Rofi'a na ke tun yanzu yarinyar da gaba ɗaya shekaranta biyar ne. Shi kuwa sai ya kama dariya yana,"To ko Babar Forida ita me shekara goma sha huɗu ma bata fara zancen aurenta ba sai ke, sannu kin ji". Ina jina a cikin nishaɗi nace,"Ita Babarta ba sonta take ba, ni kuwa ina son ƴata, saboda haka ka buɗe asusun tari tun yanzu kafin nan da lokacin da zan aurar da ita ka tara min da yawa, Mahbub tsinke ba zan siyawa Rofi'a anan ƙasar ba kaji ma da kyau". Yay dariya kawai yana cewa,"To Myy Allah ya bamu aron rai da lafiyar kaiwa lokacin, insha Allahu za'a yiwa ƴarki komai kike so, ai Allah ya hore sai dai mu roƙe shi ya ƙaro mana". Nace,"Amin zamu kai ma in Allah ya yarda, mu da har jikoki sai mun gani, magana ake ta shakara ɗari...Wa yaga surukai sun fara min suntiri a gidan nan, ina ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ina kallonsu ta cikin gilashi, Mahbub ba fa zan bawa yarana munana ba kar ma mummuna ya zo ka tsaya ce masa zaka yi shawara da ni matar gidan, ni dai ƴata me kyau zan aura mata, sai in Babar su Forida ce ban san ba ko ita zata aura musu mummuna, ita ka santa ƴar i dont care ce, ni Rofi'a ta me kyau ce kuma me kuɗi ɗan ƙasar waje, me irin halin Babanta. Yauwa kuma ka shiga tsakanina da Babar su Foridat da ke cewa yarinyata mummuna, zan iya shari'a da ita akan hakan, ba mummuna ba ce ni kuma ban haifi mummuna ba, ban kuma auri mummuna ba duk dai shima ba wani kyan garesa ba". Aje laptop ɗin yay ya turmushe ni akan gadon yana rufe bakina da nasa, wai na cikasa da magana, kuma zan ƙara maimaita bai da kyau, muka shiga kokawa akan gadon kaman wasu yara, irin wasan da ban san da irinsa ba a baya, haƙiƙa ina son mijina sosai da sosai. An sama min Harvard University ɗin, da zan tafi ni ɗaya na tafi don lokacin Salim na bakin aiki, naje kano na yiwa su Ummani sallama, Safiyya ma naje gidanta Allah sarki tana ta fama da laulayi, a gidan Hajjo na kwana, washe gari na je gidan Mama A'i kafin na dawo. Da zan tafi Maa da Sisters ɗinsa ne suka min rakiya airpot, Kudrat har da hawaye zan tafi na barta da kaɗaici, Rofi'a kuwa da ƙyar muka rabu yarinyar nan Mommy nah kawai take kira, to ni rabuwarmu da ita ne ma ya saka ni hawaye, ga shi Salim yace ba zai yiwu in tafi da ita ba. Watana takwas a america muna gab da fara exams na kwanta rashin lafiya me tsanani, lokacin Salim yaje min satinsa uku kuwa da zuwa. Yaje ne musamman saboda taya ni murnar birthday, ƙarin shekaran ma da na mance sai ranar ga shi da gift ɗinsa, har ya kira min Yara vedio call na gansu da cake a gaba, Kudrat na cewa suma za su ci na u cake ɗin anan. Ciwo fa ba na wasa ba na kwanta, abu tun ana zuwa asibiti ayi allurai a bani magunguna, ta kai da sai da muka koma haɗawa da tasa tasai iri iri duk sai da na gaji da ɓula ni da ake yi. Ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa abu kamar ba zan rayu ba, Salim da ke ta son tafiya ya gagara tafiyar sai rubuta takarda yay a wajen aiki, abu dai yaga ba zai kai mana ba daman zaman exams ne ya riƙe ni haka dole na aje semester ɗin muka rankayo muka yo gida. Wuya dai iyaka wuya ina shanta, na koma marabata da matacce numfashi kawai, don komai yi min ake bana iya yin komai da kaina. Hankalin iyayena ya tashi a wannan lokacin ne kuwa dole suka ɗakko hanya suka aje kunya a gefe suka zo gidana, Mahaifiyata har da hawayen tausaya min, Abbaa nah kuwa don bai da yanda zai yi ne amma da sai ya zauna zaman jinyata, ga alkunyan iyayen Salim ɗin da ke ta faɗi tashi akaina ba zai barsa cewa za su tafi da ni gida in jinyar a can ba, duk wanda ya ganni sai yace anyi gwaje gwaje kuwa? Salim har ya rasa amsar bayarwa ya dinƙa yi, to babu kalar gwajin da ba'a min babu wani ciwo da aka gani ba, general checkup har sau uku aka yi min, a america sai da ya kashe sama da ɗari biyu akan general check up kawai, dama a can aka min sau biyu, ɗayan kuma sai da muka dawo nan. Ciwo ya daɗa ta'azzara ina ta ƙarewa, lamarin ya bawa kowa tsoro matuƙa, sai da ta kai ga an koma yi min maganin islamic don na hausan ma aje shi aka yi, shima bai yi to, duk irin magungunan da yare ke da shi su kansu sai sallamawa suka yi. Sai aka fara tunanin wai ko sammu aka min, haka aka dinƙa banka min hayaƙi wani sai nayi kamar zan shiɗe, gidanmu ya koma gidan Malamai masu ruƙiyya, sauraron ƙur'ani kuwa 24/7. Watana uku a kwance ina shan baƙar wahala, Mama A'i ita ta zo ta zauna da ni saboda hidimar ta yiwa Kudrat yawa, baiwar Allah nan ita ke min komai, bata samun hutu ga office ga ɗawainiyan yara, kai ai Kudrat ta wuci a kirata kishiya sai dai ƴar uwa, don ni a yanzu ma na fi jinta a jikina fiye da yanda na ke jin Safiyya, tun balle zuwan Ummani da ta mayar da ita kamar mahaifiyarta. Nayi amai ta kwashe, na ƙara yi ta kwashe, ta bani abinci na kasa ci, shi Salim ɗin ma ta fisa ƙarfin halin jinyar tawa, saboda shi hankalinsa ne duk ya tashi gani yake kamar tafiya zan yi na bar su. Wata rana ciwon ya tsananta min cikin dare haka muka ɗunguma sai asibiti, muna tafe kan titi mota na jiniya matar laftanar ba kanta. Da zuwanmu kuwa aka bamu kwanciya. Karon farko tun kwanciyar tawa da aka min allurai aka sa min drip naji daɗi, lokaci ɗaya wani salamman bacci ya zo min. An ce na jima ina bacci don tun cikin daren nan sai washe gari da rana na farka, farko suna zaton ma ko na mutu ne aka ɓoye musu, likita ya ce musu da raina yau ɗin ne dai aka yi nasara alluran baccin ya kama ni, kuma ƙari ma da daɗin jikin da na ɗan samu. Naji daɗin jikin nawa kuwa, don da na farka babu ciwon cikin, babu inda ke min ciwo kwata kwata, sai dai rashin ƙwari da ɗanɗanon baki irin na wanda ya sha doguwan jinya. Har ma na samu damar miƙewa zaune da kaina, muna hira da Mama A'i da wata Aunt ɗinsa da Kudrat sai ga shi ya shigo ɗakin, Allah sarki shima duk ya faɗa sosai sai dai yanayin fuskansa bai nuni da damuwa a washe take. Mama A'i da Aunty Adamma suka tashi suka bamu wuri, Kudrat zata fita ya ruƙo hannunta, kawai sai ya faɗo jikina ya rungume ni sosai yana faɗin,"Myyy Congratulations, Congratulation to us Myy". Kuma faɗin nasa yay daidai da tsala ihun murnar da Kudrat tayi tana buga tsalle ta dire bayan gama duba takardan da ya bata, sai gata itama ta faɗo jikina sun rungume ni gaba ɗaya sai murna suke. Ni dai mamaki ya kamani kaina ya ɗaure, murna a halin da na ke ciki? a hankali na ke tambayarsu menene. Kudrat ta ɗago a jikina tana faman juyi da takarda a hannu, na bita da ido kafin ta miƙo min hannu tana cewa,"Kinga ban tukwici tukunna". Sai na ɗauke ido akanta na maido kan fuskar Salim da ke ta kallona kamar zai cinye ni. Kudrat ta zagayo ta bayansa ta kama kafaɗuna tana girgiza ni cikin wani irin farin ciki. "Ki yi murna mana, kin fa warke Mommy, ki sakko ki yi tsalle muyi rawa, ciki ne da ke har na 5months, za'a ma mummuna ƙani ko ƙanwa". Sai tayi shiru kafin ta ƙara cewa,"Amma dai sai na ranƙwashi kan Babyn nan, ya san shi ne yaƙi bayyana kansa yake ta wahalar da mu, sannu Mommyn Rofi'a, tumbin da na ke ta yiwa tsiyan yana cin maiƙon America yana girma ashe Babyn mu ne a ciki". Hannun Salim cikin nawa yana shafawa ina ga tsabagen farin cikin da yake ciki ne ya hanasa yin magana. Ni kuwa tuni na daskare ina ta kallon Kudrat na kasa wani motsi, sai a hankali idanuna ke ƙiftawa. So na ke na harhaɗo kalamanta in cure su wuri guda su bani ma'anar nufinta, don na kasa fahimtar komai daga abinda tace. babu abinda na gane kuma babu wata kalma da nayi capturing idan ba pregranant ba, Abinda na ke so na gane tana batun cikin wata biyar ko? To cikin haihuwa take nufi ko na cin abinci ko na me? Idan na haihuwa ne a jikin wa yake? Na san dai ba a jikina yake ba, idan kuma a jikin nawa ne to sai in wani cikin na daban ba na haihuwan ba, ina alamar samunsa ma? Ciki har 5month ba alamun fitowansa? To ba dai ni ba domin kuwa na shekara goma sha ɗaya a gidan aure na farko ban taɓa ɓatan wata ba balle ɓarin ciki, haka yanzu cikin aure na biyu ina a shekara ta uku ne kuma tun da na zo ni dai ban san lokacin da na yi ɓatan wata ba. Fahimtata da suka yi ne yasa shi karɓan takardar ya miƙo min, na karɓa ina sauke ƙwayar idona akansa, sai ya ɗaga min gira yana cewa,"Ba ta yanda Allah ba ya lamarinsa, babu me haƙuri da tawakkalin da baya cin nasara, babu wanda ke miƙa lamarinsa ga Allah ubangiji bai dube shi ba, kuma mafi yawan jinkiri alkhairi ne, ga sakamakon jinkirin Myy, ga sakamakon haƙurin Myy, ga sakamakon tawakkalin Myy, dama na faɗa miki kar mu fidda tsammani, Allah ke bayarwa kuma zai bamu to ga shi ya ƙara bamu, ki gode masa Myy". Duk da a daskare na ke amma na gane duk me ya ce, sai dai kuma kalamin nasa ne ba na tsammanin zuciya da ganganar jiki za su ɗauka har su yarda. Na dubi takarda a hankali na shiga karanto bayanin da ke nuni da sunan Sa'ida Salman Madobi da ke rubuce a sama, tana ɗauke da ciki har na tsawon wata biyar. Naji na girgiza akan gadon da na ke, na rufe ido na buɗe, na ƙara rufewa na buɗe har sau uku, na ka kai hannu na mari fuskata kafin na mintsini kaina, ba zan iya gasgata abinda na karanta ba har sai na tabbatar da ba mafarki na ke yi ba tukunna. "Myy ba mafarki kike yi ba, zahiri ne, kuma a zahirin ma kina riƙe da takardan gwajin da ya bayyana kina ɗauke da ciki, kina ɗauke da halittar yarona a cikinki Myy, kin zama BabynBaby". To kukan da ya zo min na menene? Kawai dai naji saukar hawaye kafin fitar sautin kuka ina damƙar gaban rigarsa na shiga girgiza kai ina cewa,"Mahbub ciki fa! Cikin haihuwa da ake samu a haifi yaro?, Mahbub ta ina zan same shi? Ni fa bana haihuwa, Mahbub akan rashinta na wulaƙanta, aka tsangwame ni, aka goranta min, aka daina sona, na rasa farin ciki da jin daɗi, 11years ban taɓa ɓatan wata ba ban taɓa ɓari ba, ko a mafarki ban taɓa ganin na haihu ba, sai da aka sauya min suna na koma Juya, Mahbub Dr ba result ɗina ya baka ba, ba nawa ba ne ka mayar mishi ya bani nawa, ka manta a America ma sun duba ba su ga ciki ba, kar mu yarda da wannan ba namu ba ne". Na ruƙo fuskarsa ina ƙara girgiza masa kai. "Kar ka yarda, ka daina murna Mahbub, ba na so ka saka rai kuma a zo a datse maka farin cikin da aka saka ciki wanda ba zai tabbata ba, ban da ciki, banda ciki Mahbub, ni ɗin Juya ce haka suka faɗa". Na faɗa da murya me raunin da ke taɓa zuciya, ina fashewa da kuka sosai me ban tausayi. [2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR17FT5* Salim ya rumgume ni, hawayena na ta sauka a bayansa, a hankali yake shafa kaina zuwa bayana, kuma cikin natsuwa ya shiga faɗa min tausasan kalamai da suka samar min da natsuwa. Haka na zame daga jikinsa, ina kallonsa da murmushin farin cikin da ba zai misaltu ba nace,"Nima zan zama uwa Mahbub, zan haifa da kaina, zan amsa cikakken sunan mahaifiya, ka tayani godiya ga Allah Mahbub". Sai sabon hawaye ya sake min shatata, na miƙa hannu na janyo mayafina na yafa, na nemi taimakonsa ya sakko da ni akan gadon. Sallayar da ke kan durowar gefe na ɗauka ya shimfiɗa min, na fuskanci alƙibla na yi sujudu shukur, na jima ban ɗago ba hawaye kawai na ke ina miƙa godiyata ga Allah mai girma da buwaya, mai yin yanda yaso abisa dukkan komai. Sai na samu kaina da kasa ɗagowa har sai da Salim ya ɗago ni, dole na shiga ruɗa ni, domin abinda ban taɓa tsammanin zan samu ba ne, kuma rabon da na cire rai da shi tuntuni. Ko bayan aurenmu da Salim na nuna masa damuwar rashin haihuwata sai dai shi ata ɓangarensa ko da yaushe yana faɗa min tausasan lafuza ne na kwantar da hankali da ƙara miƙa lamura ga Allah gami da yin tawakkali da duk yanda mutum ya riski kansa a ciki, balle ma ni Rofi'a kawai da suka mallaka min halak malak ta ishe ni wallahi, sai ga shi kuma ashe ina da rabon samun nawa na kaina. Ina ta ɗokin na karɓi waya na sanar da Ummani ashe tuni Kudrat ta riga ni isar da albishir, Ummani tsaban farin ciki sai da ta ɗauke wuta a sanda ake faɗa mata, domin su kansu iyayena sun fidda rai akan haihuwata, ganin a wannan auren ma cikin shekara ta uku babu wani labari, na su zaton ina daga cikin waɗanda Allah ya rubuta basu da rabon samun haihuwar ne har su koma gare shi. Ina daga zaune kan sallayar na kai hannu saman cikina, farin ciki na ke yi haka kuma mamaki na ke yi, wai ɗan mutum ne a cikina, sai yanzu ma batun rashin yin period ya zo cikin kaina, ni duk wannan kumburin cikin da na yi wallahi ce na ke tumbi ne kawai, don har tsokanata Kudrat ke yi da shi kansa Salim ɗin, to abunda bamu sa ran samu ba ne shiyasa cikinmu babu wanda ya kawo batun ciki a ransa, don har ina ta cewa zan nemi maganin rage tumbi, a lokacin ma har Maman Yasmin na faɗawa take cewa to ai na zama Hajajju ina cikin hutu da jin daɗi ai dole na yi tumbi. Aunty Adamma da Mama A'i suka shigo fuskoki washe cike da murna, barka suke ta min, Kudrat kuwa faɗi take ai sai na bata tukwici zamu bar asibiti, na ce,"To Madam ai in bayarwar zan yi Paapa zan bawa". "Noo ban yarda ba woo Mommy, ki bani kawai in ba haka ba kin san dai na san ai na ATM na ki yake". Dariya nayi sosai, bata barni ba a dole sai da nasa Salim ya tura mata 10k idan mun koma gida zan ba shi, tunda wayata na can. Ni fa banji kunya ba sai da aka sanarwa da su Maa, duk sai naji kamar na nutse, yo ina ta murna kaman zan shiɗe ina na tuna wata jin kunya ma lokacin da muke magana da Ummani da Abbaa. Sai da na ƙara kwanaki biyu a asibitin kafin aka sallame mu, wallahi har a sa'ilin gani na ke kamar daga baya za'a zo ace result ɗin ba nawa ba ne, ko kuma na tashi a bacci naga mafarki na ke yi, sai dai babu ko ɗaya daga ciki rabon nawa ne da gaske Allah ya ba ni, bayan tarin wulaƙanci da gorin da na sha a baya, idan na tuna sai na yi murmushi kawai a fili na furta,"Yau ga Juya zata juye nata rabon". Naji ƙwarin jikina sosai kuwa don asibitin babban asibiti ne sun iya kula da mutum. Maganar farin ciki ba a batunta ta ɓangaren ƴan uwa da abokan arziƙi, Family ɗin su Salim kuwa ka rantse karon farko kenan da Salim zai samu haihuwa, ashe su haka suke farin ciki da tarairayan mace idan tana da ciki ko da kuwa haihuwa ta ɗari zata yi, sai da na zama kamar wata ƙwai ɗanya saboda yanda ake ririta ni tun balle me abu da abunsa mijina abin ƙaunata. Ƴan uwansa haka suka dinƙa zuwa yi min sannu, sai kowa ya zo an ce masa ciki ne sai yace au da ciwon ƴan gayu na ke aka sa su tasowa suyi tafiyayya. Yara kuwa ko da yaushe suna tare da ni suyi ta kallon cikin suna faɗin,"Mommy yaushe za ki bamu Baby?". Rofi'a kam ai ko bacci zamu yi yarinyar nan kanta na kwance kan cikin wai kar a ƙwace mata Baby, idan ranata ne yana wajena sai fa in tayi bacci ne zan mayar da ita ɗakin su Foridat ta kwan a can, dama haka muke da ita ko da yaushe ita tafi son bacci a wurina, Kudrat tace,"Ke kike shagwaɓata shiyasa take miki abinda taga dama ai, ke ƴa mummuna amma ki ta wani faman ji da ita". Na ce,"Ehh komai za'a faɗa a faɗa, baƙin ciki kashe maƙiya". Tasa dariya da cewa,"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, da Baby ya zo zamu ƙara juyawa mutum baya aradu". Nima ina dariyar na ce,"Kar ki manta hajajju kullum ciki azkar muke, kuma bakinmu li'ilafi da yasin ko da yaushe, kinga kuwa haka zaku buga ku barmu, kuma indai muni yasin a fuskar ƴaƴanki ya tare". Cikin wasa da raha muke zancenmu, ni dai Kudrat ba kishiya ba ce a wurina ƴar uwa ce, kuma har zuciyata haka na ke jinta, don ƙwarai da mata za su daure a danne kishin zuciya to za'a zauna lafiya tsakanin kishiyoyi, ba faɗa ba tashin hankali, to ba kowacce mace ba ce kamar Kudrat musamman a wannan zamanin tunda ko a iyayenmu na da ai zamu gani, lafiya suke da kishiyoyinsu sai kaga har a rasa banbance ƴaƴan wance da wance tsabar haɗin kai. Kuma zuciyar kowa fess ake zama ba wadda ma ke tsayawa sauraron zugar mutane, Sai dai fa duk da hakan muma don mun samu jarumin miji ne tsayayye a cikin gidansa, mijin ƙwarai da bai nuna banbanci tsakanin iyalinsa, mijin da bai fito ya nuna fifikon wata ba, shiyasa na ke jinjinawa Mijina domin ya cika namijin ƙwarai. Sai da naji daɗin jikina sosai babu wani ciwo da ke takura ni sannan Mama A'i ta koma gida. Ita da taji daɗin zaman ma so tayi har sai na haihu, Abbaa yay ta faɗan to zaman me zata yi, bacin ma makaranta zan koma. Ni kuma gani nayi zaman me zan yi dama tunda lafiya ta samu, ba wani wahalallan laulayi, saboda haka na yanke shawaran komawa makarantana, ranar da Mama A'i zata koma sai da naji kamar na bita, rabona da gida tun dawowarmu daga saudiyya. Tsaye na ke gaban madubi ina duban kaina, Salim da ya fito daga toilet ya tsaya ta bayana ya rungumeni yana tusa hannayensa cikin rigata ya shiga shafa cikina. Ina kallonsa ta cikin madubin na ce,"Ranka ya daɗe Sir". Yay min cizon wasa a wuya kafin ya amsa,"Na'am ranki ya daɗe Momin Unborn". Nayi murmushin da ya zarce har zuciyata saboda daɗi. Na kai hannu saman kansa ina cewa,"Godiya ga Allah da ya bani ɗaya tamkar ya dubu, mijina abin sona abin alfahari da tunƙahona, jarumin da ya fi dukkan maza, gaishe da kai jigona, matakalar kwanciyar hankali da farin cikin iyalinsa, Allah ya bar mana kai ya faranta maka, ya bani ikon sanyaka farin cikin da nima kake sanya ni a ciki". "Thank you for the praise Momin Huɗu". Ya faɗa yana manna min kiss a kumatu. Na juya idanu da faɗin,"Mahbub ko goma aka bani wallahi ina so, zan yi murna in farin ciki, ba zan ji wahalan kulawa da su ba, ba zan kasa tarbiyantar da su ba, Mahbub ƴaƴa Rahma ne kai ka faɗa min da bakinka, kawai dai idan suka zama huɗun to haihuwa tare da kai". Siririyar dariya yay da cewa,"Ni in haife su ta ina Myy?". Hannu na kai na zungure shi ina faɗin,"Ta nan, haihuwan na zuwa zai buɗe". "Ohhh kiji daɗin cewa na buɗe da yawa ko, ko da yake na fanjama neman maganin maza, in tsuke irin yanda kike tsukewa kina sawa na fita a hayyacina". "Abu me sauƙi kenan, ƙarƙari ka fito da kuɗi, zan haɗa maka maganin da sai ka shekara kana min surutan da yafi wanda ka ke yi, maimakon Myy zan mutu sai dai ka koma cewa Myy na mutu daɗinki ya kashe ni". Na faɗi hakan muna dariyan jin daɗi da shi. Zaunar da shi na yi kan stool na shiga shirya abina, ba na taɓa ƙosawa da yi masa wanka da shirya shi. Ina gyara masa gashi yake min zancen komawata makaranta, duk da ba'a son ransa zan koma ba ɗin, babu yanda bai yi da ni ba akan na bari sai na haihu na koma har fushi yay, ni kuwa ban ga amfanin zaman ba tunda dai lafiya na ke, me zan jira kuma haka kawai sai na fara tara yara kuma karatun ya zo yana min wahala, duk da shekara uku ne na gama. "Myy; Mommi(Kakarsu) ta ce to ba zai yiwu a barki ki tafi ke ɗaya ba, Anty Adamma zata zo sai ku wuce tare, ita zata zauna da ke saboda taimakawa da kulawa". Nayi knooding kaina da gamsuwar hukuncin da Mommi ta yanke na ce,"Ba damuwa ai Mahbub, ina yiwa Mommi godiya da kulawanta". "To yanzu kin gama haɗa komai? Flight ɗin 9 za ku bi". Na ce,"Ni kam na gama duk shirina". Sai na marairaice na zauna saman cinyarsa na shiga roƙonsa. "To Mahbub don Allah kaga tunda ba ni ɗaya zan koma ba har da Aunty Adamma ka bari na tafi da Rofi'a, kaga dai ba kyau raba uwa da ƴa, Allah baka san irin ciwon da na ke ji ba a zuciyata idan na tafi na barta nima har kuka na ke yi, kana kallo idan na tafi duk ramewa take yi". Ido ya zuba min yana kallona kawai, sai na ƙara marairaice masa kaman zan yi kuka ina faman roƙo. Gira ya sosa kana yace,"Shikenan ku tafi ɗin, amma ai kin san dai this session za'a sakata school, yanzu idan kika tafi...". Bakinsa na toshe da kisss, sai da na tsotsi abina son raina kafin na barsa ina murza kunnensa na ce,"Kai dai ba ka yarda mu tafi taren ba?". Yana kallona da idanunsa da suka canja kala saboda tsokano shi da nayi ya ɗaga min kai kawai. Na miƙe akan cinyar tasa ina cewa,"To idan munje can zan saka ƴata a school nima dama na ƙagara ta fara zuwa makaranta, bakinta ya ƙarasa buɗewa a can". Fizgo ni yay sai kan gado,"Ki tsokano ni sannan ki nemi hanyar ficewa". "Mahbub to zan haɗa kayan Rofi'a ne fa". "Tab idan kunje can kya siya mata wasu, amma yanzu madara za ki bani, anjima fa za ki tafi ki barni". "Za ka takurawa BabynBaby fa". "In ji wa? Abinda zan yi lafiya zai ƙara masa ai kin fini sani". Soyayyarmu muka dirza ni da shi, haka muka yini cirr a ɗaki ni har kunya ma naji, don Aunty Adamma ta zo tana ta kiran waya amma mutumin nan ya hana ni fita wai bai ƙoshi ba na ƙyale shi, Baby yasa na ƙara yin daɗi ji yake kamar zai zauce. Ƙarfe takwas na dare Mahbub ya kaimu airpot, da Rofi'a na tafi ƴan uwanta na ta jin ba daɗi, musamman Isioma da ita ma ke ta roƙonsa Paapa nima a tafi da ni please. Komawata America can ni ɗin ma haka aka samu ƙwararran likitan da ke bani kulawa wanda har gida yake zuwa, na faɗa musu ni yanzu bana jin ciwon komai, sun ƙi yarda a haka Dr ke ta cin kuɗinsu, tunda na tafin kuma Salim bai da natsuwa akai akai yake zuwa, ya zo yay ta ririta ni cike da so da ƙaunata a gare shi, haka kuma ya daki bidirinsa, ni kam ban hana shi abinda yake so. Cikina na da wata bakwai ya bayyana sosai, don har ya kai wata shida ba zaka taɓa cewa ina da ciki ba, anata cewa ƙaramin ciki garen, wanda ba su sani ba ma cewa suke tumbi ne, amma ikon Allah shigarsa wata bakwai sai ka rantse ina cikin watan haihuwar ne. Kuma babu wani ciwo da na ɗinka fama da shi tun farkon ciwon da nayi, kawai dai na kumbura ne kamar an zuba min yeast, har bana son kallon kaina a madubi wallahi saboda munin da nayi, Safiyya sai tayi ta kunna ni wai ai ance idan mace tayi muni idan tana da ciki to mummuna take haifa, ai kuwa nabi na damu da maganar, yo wake son haifar mummuna, sai da Salim ya kirata yaci ƙaniyarta tukunna ta shafa min lafiya. Sai dai shi kansa tsokanata yake da girman cikin, idan ya zo America yaje school ɗakko ni haka zai ta min vedio yana daga cikin mota, ni kuwa ina tafe ciki a gaba wurjanjan har kunya na ke ji, don dai ba yanda zan yi ne karatun ya zama dole amma da babu inda zan ke fita har sai na haihu. Yau ya zo ɗaukana, ban san ya sauka a ƙasar ba, don bai faɗa min ba, mun dai yi waya yake cewa tunda mun kusa dawowa ba lallai ya ƙara zuwa ba shima suna bakin wani babban aiki ne, na fito daga gate ɗin makarantan ina tsaye ina jiran taxi, sai gani nayi mutum ya leƙo yana,"Madam turtsitsi shigo na rage miki hanya". Ban mamakin ganin nasa ba don dama na san ba zai iya haƙurin ɗaukan lokacin da ya faɗa ba bai zo ya ganni ba. Na shiga motan ina cewa,"Mijin turtsitsi ya da zuwa ba sanarwa". "To a kora ni mana ace ba'a son ganina ba'ai murna ba". Cikin shauƙi na sarƙafo hannuna a nasa ina kwantar da kaina a kafaɗansa na ce,"Ni a wa na ce ban murna da ganin miji na gari ba, ina sonka mijina idan na ganka sai in rasa kalar farin cikin da na ke riskan kaina a ciki, banda ƴar uwata ma kaima ai ka san ba zan ke barinka ba". "Umm matata nima kasa sukuni na ke idan bana tare da ke, shiyasa za ki ga bini bini na taho gareki, ba takura miki na ke ba wallahi ƙaunarki ce tayi min yawa, ina sonki mace ta gari me ladabi da biyayya, Allah ya ba ki aljannah ko don biyayyan da kike ma mijinki". Na ƙanƙame shi ina amsawa da,"Amin ya Rahman". Sai yace,"Rofi'a fa?". Na ce,"Ai akwai school bus, yanzun ma na san an maida ita". "Weldone Hajiyar Doller, ki zuba uban kuɗi kisata a wannan makarantan me tsada, ni da Kudrat ta faɗi mani fa ban yarda ba". "Amfanin kuɗin uwa tayiwa ƴaƴanta hidima musamman ta ɓangaren ilimi". "Haka ne, Allah ƙaro miki masu albarka, yanzu ban aron dubu ɗari biyu". Ina dariya sosai na ce,"Ɗari biyu jal". "Madam ai ba a naira ba, ina nufin dala dubu ɗari biyu". "To ka sha kuruminka Sadauki, tunda ka ba da wannan ajiyar mene ba za'a maka ba, ka san mu hausawa mun ce yaba kyauta tukwici, so ba bashi za'a baka ba, kyauta ma za'a baka". "Lallai na kusa in zamar miki ɗan maraya kiyi ta jiƙani da doller, Madallah da ke Hajiyan doller Allah ƙara lafiya da buɗi, aci gaba da taimakon marayu". Da jin daɗi mara misaltuwa na amsa da,"AMIN Hubbi nah, ba ni ɗaya ba har da kai". Kiss yay min a gishi sannan yace,"So'ida wallahi nayi matuƙar jin daɗin yanda kika so ƴaƴana, wallahi ban san ta yanda zan misalta miki daɗin da na ke ji ba akan ɗaukan yarana matsayin na ki da kika yi, haƙiƙa kin ƙara samun fada a zuciyata, kin ƙara samun gurbi me girma a raina, Allah yay miki albarka". Satinsa uku da tafiya muka yi hutu, washe garin ranar da na dawo gida na fara naƙuda a tsaitsaye a tsaitsaye, ni ban ma ɗauka itan ba ce nayi zaton dai ciwon mara ne haka tunda ina ɗan taɓawa. Sai da na faɗawa Kudrat yanda na ke ji tukunna tace ai naƙuda ce. A ranar kuwa aka turo mana wata dattijuwa a cikin matan uncles ɗin Salim, da yake da muka sauka direct Aunty Adamma Anambra ta wuce. Suka yi suka yi mu tafi asibiti na ce su bari ba haihuwar ba ce, Kudrat har taji haushina wai zan nuna musu ni likita ce kenan na san aikina. Kwanana uku ina naƙuda a asibiti kafin Allah yasa na sulluɓo ƙaton Jaririna, yo ba dole ciki yay girma ba, kunga yaron kuwa masha Allah, godiya sai ga lillahi domin kuwa lafiya lau da ga ni har yarona, wayyo dama haka ake ji? Ni dai da aka bani yaron ji nayi kamar na tsaga ƙirjina na ɓoye shi a ciki, shi da mahaifinsa kamar an tsaga kara saboda tsananin kama, naji daɗi kuwa domin burina ne haihuwan kyakykyawa, bakin yaron ɗan ƙarami gashin ido har saman fuskarsa, take kuwa na shiga tofe abinda da ayoyin ubangiji, na tauna dabino a baki na zuba masa ruwan a bakinsa. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR18FT5* Zo kuga murna wurin Salim, Yana Abuja lokacin aka kirasa ƙarfe uku na dare, amma bayan asuba sai ga shi ya sauka. Runguma babu kalar wadda ban sha ba a wajensa, kiss kamar zai cinye ko'ina na jikina, farin cikin da yake nunawa zaka ce ko don saboda haihuwar daga gare ni ne, a'a shi haka yake yau ko da Kudrat ce zata ƙara haihuwa iyaka farin cikin da zai nuna kenan da kuma kulawar da zai bada. Ina kwance kan gadon shi yana gefe zaune da Babyn a hannunsa, da na motsa zai ce,"BabynBaby menene? Me kike so? Wani wurin ke miki ciwo? Faɗa min menene me kike so kin ji matata ta gari abar ƙaunata". Sai dai kawai nayi murmushi na kaɗa masa kai in ce,"Babu komai Paapa, lafiya lau na ke, kai kawai na ke so kuma gaka a tare da ni". Hannuna ya daɗa haɗewa da nasa da Babyn, ba zan iya ce masa ina jin ciwon mara sosai ba don sai ya bi ya tashi hankalinsa, ni kuwa ba na son ganin mijina a wannan yanayin, na fi son ganinsa a irin wannan yanayin da na ke ganinsa a yanzu riƙe da ɗansa na tsantsar farin ciki da annashuwa. Sai yamma aka sallame mu muka koma gida. Jego na ke me cike da daɗi, gata ta ko'ina an mayar da ni tamkar ƴar gwal, miji yanai ƴan uwansa na yi, nawa dangin na min, kwanana biyu da haihuwan Mama A'i ta ƙara dawowa ita zata min zaman wanka, ni da ta zo ce na ke da kayan fara sana'a ta taho, wai ashe kayan barka da jego ne kawai aka tulumota da su ta kawo min, dama tun kan haihuwar naji Ummani na faɗin an haɗa sabulu wanka, to ashe har dakan yajinta tayi botikin fenti guda biyu. Ga kayan sanyin jariri na injin saƙa me kyau, set har huɗu don ana zuwa ma da su na cire sky blue colour ɗin na cewa Mama A'i a saka masa kayan Kakarsa. Zannuwan turame kuwa masu sauƙin kuɗi kala shida, abinka da ƴar gidan me siyar da su, banda manyan atamfa da kowacce zata yi dubu bakwai guda huɗu, da sabbin hijabai na ɗinkin zama ni, ga falle falle na wankan jariri guda uku shima, ga zanin goyo na saƙa shima me kauri guda biyu, ko ba'a saka masa kayan sanyi ba aka goya shi da iya shawul ɗin ai ya isa yaji ɗumi, zoben azurfa kuwa ina gani shima na san daga Abbaa ne, takalman jarirai guda uku suma masu kyau haka ya siyawa jikansa. Turarukan wuta kuwa masu bala'in ƙamshi na jego manyan kwalabe huɗu suma, da humran jariri, kai wato ina nan ashe Hajiya Ummanita na can tana shirin saukar jika. Yashaik da Yaya Imam kuwa kuɗi suka tura min, da zolayarsu suka ce,"Duk da ke Hajiya Sa'ida ce amma dai ga wannan a siyawa ɗan mu turare, Allah yay masa albarka". Naji daɗin kyautan na su sosai, muka yi waya da Ummanin ina zuba na ce,"Ummani ina zan kai wannan yajin da aka kawo?". Ta ce,"Yo ai dama na rabo ne ba kawo miki aka yi ki tasa a gaba ki ta ci ba, ki bayar a aika gidan su nasu ne, idan wani zai zo ga na ku ke da Kudrat sai a taho muku da shi. Abbaanku ya ba da rubutu za ki gani ke da jaririn za ku dinƙa sha, wannan baƙin zaren kuma a ɗaura masa a hannu saboda bakin mutane, azurfar ma yace ki saka masa ita ma ta baki ce naji ance jikan nawa kamar balarabe, kinga ba ma zauna ba". Na kada baki na ce,"Ai Ummani na iya haihuwan ɗa, ki gode Allah na haifa miki jika me kama da larabawa, sai ma dai kin gansa tukunna za ki ji kamar ki riƙe". Tana murmushi ta ce,"Ina zan riƙe shi uwarsa tayi ƙarata". kai ni dai ban san haka na ke ƴar gata ba sai da na haihu. Maa bini bini ta kira ni ta ce,"Daughter ya kike da Jikana?". In ce mata muna cikin ƙoshin lafiya. Ana gobe suna ƴan uwana suka zo, Maman Khairi, Maman Yasmin, Hindatu, Saudatu, Umman Batula, Hajjo, har da ƴaƴan wajen Hajjo Juwan da Safna, ƴaƴan wurin Baba Tijjani kuwa babu ko mutum guda, na rasa ranar da zasu gane duniya ba wurin zama ba ce su daina jin haushinmu suna gaba da mu, amma abin na su gaba gaba ma yake yi, musamman ma da suka ga yanda na koma da irin mijin kece rainin da n ake aure, duk sai suka ƙara ƙullatarmu ni da mahaifiyata, mu kuwa duk basa gabanmu. Ni dai naji daɗin ganin iya wa'annan ma da sua zo matuƙa, ranar har rasa inda zan tsoma raina nayi saboda daɗi. Har ranar suna ban san da wanne suna Mahbub yaywa jaririn huɗuba ba, tunda na haifesa na ke ta tambayansa wanne suna ya saka masa sai yay murmushi yace,"Myy ki bari ai sai ranar suna ake faɗa ko". Na ce,"To ai dai ka san wanda zaka saka tunda ka masa huɗuba, ni ba Mamansa ba ce, tsakani da Allah sai ace nima sai ranar da kowa zai ji nima zan ji". Ya ce,"To me ɗa, ai kaɗai kika yi aikin haihuwan, sunana ne to nasa amma sai ranar naɗin suna kema za ki ji, da ake min gori da ban bayar ba a haifa ne, kima gode min ki ban kyauta na iya jefa ƙwallo a raga". Dukan wasa kawai na kai masa a ƙirji, duk nacin da na saka masa sai da na haƙura. Ina ɓata fuska na ce,"Kuma ma idan suna mara daɗi ne ka saka masa idan ba sai ka ƙara yanka rago ka sauya masa ba". Ranar sunan bayan ya dawo daga masallacin asuba, ina ɗaki na fito a wanka kenan, sai ga Rofi'a da gudunta ta faɗo jikina, na ɗauketa ina cewa,"Rofi'a na haneki wannan gudun, tiles ɗin nan bai da amana akwai santsi, wa ma ya tasar min ke da wannan farar asubar?". Cikin gwarancinta tace min,"Paapa yace kije yanzu, Mommy yau a goya min Baby". Na ɗaga mata kai,"Ehh za'a goya miki". Na ajiyeta, na karɓi jaririn a hannun Mama A'i da ta gama shirya shi, ɗan albarka ba dai kuka ba da tsotso, daga karɓarsa har ya farka a barcin da ya fara zai yi halin kukan. Na yafa babban towel akaina ban tsaya shiryawa ba, ni kam ban ɓata lokaci wajen amsa kiran mijina, na fita a ɗakin ina ta yiwa yarona wasa duk da uban kukan da yake tsalawa, ni dai hakan ma daɗi yake min, ina kallonsa da murmushi ina shaƙe ƙamshin turaren da aka fesa ma kayansa masu kyau. Yana zaune kan carpet ya baje alawan suna da biscuite na same shi, hannu ya miƙa ya ɗakko filo yasa min na zauna akai, ina gaida shi bai amsa ba ya hauni da faɗan bar masa yaro da nayi yana kuka. Ni kam ban jin daɗin wannan faɗan nasa wallahi, yana gani fa duk yaron ya ruɗa ni amma ce yake ina ɗaukar hakkin yaro. Ina gyara zan ba shi nace,"Mahbub ka fa san halinsa da kuka, yanzu na fito a wanka na karɓe shi hannun Mama A'i, kuma wallahi bacci ma yake yi fa, na taho zan zame zani ne a hanya ina ba shi". Wani kallo yay min da cewa,"A waje kike, ba cikin gidanki ba ne, zanen ai ba duka za ki kunce ba ko". Ni dai ganin ya hasala na shiga ba shi haƙuri, kuma a hakan saboda yaron yaƙi kama nono nan ma ban tsira ba laifina ne. "Myy ba na son irin haka, bana jin daɗin kukan yaron nan wallahi, ke idan ni ina da nonon basa ma kya ga ina miki faɗan ne balle har kike cin magani kina turo ba ki gaba". Kamar zan kuka na ce,"To kaga fa yaƙi kamawa". "Ta ina zai kama dama, har yanzu kin kasa koyar yanda za ki dinƙa ba shi, wannan rashin imani ne kawai, na rantse miki idan ɗana ya samu matsala akan rashin samun ruwan nono idan ranki yay dubu sai ya ɓaci". Idona ya ciko da ruwa kawai na saki nonon ina ce masa,"Ai sai ka basa da kanka tunda kai ka fini iyawan". Ya galla min harara yana kama nonon ya saka masa a baki, kuma da gasken ne ya fini iyawa, ni ko da yaushe haka muke fama wajen saka masa a bakin, kuma idan na tashi in rufe masa hanci, ko bai niyyan kukan ba sai ya tsanyare dalilin hakan, Mama A'i tayi ta faɗa kamar zata buge ni. Ina aikin ɓata fuska kan faɗan da yay min ina kallon yanda ya riƙe nonon da kyau ya saita yaron na ta sha abinsa, na jisa yana cewa,"Suna yaci, me zamu dinga ce masa?". Lokaci guda na bar fushin, na bar kallona daga kan jaririna na dube shi ina murmushi na ce,"Sunan wa yaci?". "Ke dai ina ruwanki, laƙabi kawai na tambaye ki". Na san ba zai wuce sunan mahaifinsa ya saka ba, na dubi yaron ina kallonsa cike da wannan soyayyar da take daban da kowacce soyayya wato soyayyar uwa, na shafo sumar kansa ina cewa,"Ayman yayi?". Sai shima ya ɗora nasa hannun saman nawa muna shafa kan yaron a hankali yace,"Da yare kuma muce masa Emeka". Nace,"Wow, to Mahbub baka faɗa min ainihin sunansa ba ai". Ya manna gefen fuskarsa da tawa cikin kunnena ya raɗa min,"Sunan Abbaa". Ban san sanda na juyo gaba ɗaya ina sakin Ayman ba in fuskanci mahaifinsa. "Mahbub sunan Abbaa nah ka saka?". Ya jijjiga min kai yana shafa fuskana, na rungume mijina cikin hawayen farin ciki da jin daɗin da suka shiga sakko min. Godiya na ke masa ina kwarara masa adu'a iri iri. Wallahi sai na ƙara jin sabuwar ƙaunarsa ta kama ni, darajarsa da kimarsa da mutuncinsa sun daɗa hauhawa a idona, ina ƙara alfaharin samunsa a rayuwata, ta kai ga har na fashe da kuka wanda ba na komai ba ne sai tsantsan farin ciki. Ban ma iya tashi naje ɗakina ɗakko wayata ba, da wayarsa na kira Abbaa na shaida masa Salim yay masa takwara, Abbaa shima yaji daɗi sosai. Cewa yake,"Da gaske Salman yay takwara Salman, ai kuwa mun gode da wannan kara da aka yi mana, Allah ya albarkaci rayuwan Salman yasa ya zama mahaddacin alqur'ani". Na haɗa su a waya Abbaa na ta saka masa albarka da adu'a, irin adu'an da har sai da jikin Salim yay sanyi. Nima ɗin adu'a na ke daɗa masa ina cewa,"Allah yasa ƴaƴanka su zama masu jin ƙanka". Ƙarfe goma muka shirya muka tafi can gidansu Anambra, da ke a can ne za'a yi taron sunan, gida ya cika maƙil da jama'a, kuma iyaka familyn su ne ba wasu ba, sai abokan wajen aikina, to sai jama'ar Kudrat ma da ta yo gayya guda ita uwar ɗa, sai ƴan uwana da ba su wuce ƙirgen yatsun hannu ba. Ranar dai anyi shagalin suna iya shagali, taro na gani a fada na a buga a jarida, kuma an buga ɗin kuwa, yau an wayi gari Sa'ida Salman da yarona Salman sun kafa tarihin shiga jaridar duniya. Na yi shigan suna na haɗuwa, in saka in cire kace sabuwar amarya, ni da yarinyata Rofi'a shiga iri ɗaya muka dinƙa yi, haka itama Kudrat da yaranta, ashe har anko tayi mana ban sani ba sai a ƙarshe da taro ya kusa watsewa ne take cewa to ga ankonmu har da Mijinmu, haka muka yi shigan irin kayan yarensu na saƙi, mun yi kyau sosai aka mana hotuna, Paapa daɗi ya cika shi baki sam yaƙi rufuwa. Ni dai kyautuka sai in ce har gajiya da karɓa nayi, na samu kyauta Ayman ma ya samu, yo kayan da Ayman ya samu ai har ya girma ba zai saka wasu ba, gaskiya dangin Salim sun yi a rayuwa, dangin mutunci dangin karama, dangin bugar ƙirji, yau ko ba na jikina ba zan wa mace kwaɗayin shigowa cikin wannan ahali na ban girma. Bamu tafi ba sai washe garin ranar suna, lokacin zamu tafi mun jewa Sir sallama ya bani takardun fili ɗauke da sunan Salman Salim Sadiq(Emeka Oluwa), sai naji sunan ya ƙara burgeni, mallakin ƙaton fili kyauta daga kakansa, ashe haka suke, idan suka samu ƙaruwan jika sai kakansa ya mallaka masa kadara me girman gaske, to shi Baban su Salim jikokinsa duk filaye yake ba su kuma manyan filaye, da yake gaskiya ba wani talaka a familyn kowa da rufin asirinsa iya gwargwado, sai dai mahaifin su Salim ɗin duk yafi su kuɗi. *B3ƘR19FT5* Muka koma gida na ci gaba da rainon Ayman cikin kyakykyawan kulawa, Mama A'i na tare da ni har muka yi arba'in, na ƙara samun cima me kyau. Sai bayan mun yi arba'in naje kano, ranar muka tafi gaba ɗaya har Mama A'i, Kudrat kawai muka bari a gida don gaba ɗaya da yaran muka wuce, ba jirgi muka hau ba a mota muka tafi, daga can gidan su Salim aka turo mana da direbobi biyu, Babban motan ƙiran Land Cruiser Prado a cikinta ne ma ake fita da Maa, muka shiga ciki gaba ɗayanmu, tawa kuma Lexus RX 350 wadda Salim ya bani ranar suna sai muka zuba kayanmu a ciki ɗayan direban ya biyo bayanmu, kuma saboda yawon arba'in da zanyi idan munje can ɗin shiyasa muka yi tafiyan motan, Salim yace sai direban yake kai mu duk inda zamu je tunda ban riga na iya motar ba, shi bai son ake masa yawon hawan mota da jaririnsa duk ya kwaso ƙura da iskan hanya. Zuwana gida kamar a cinye ni, Ayman kuwa tunda yaje hannun Yaya Al'amin sai da ya kusa awa guda tukunna ya dawo da shi, har da zolayansa na bari yay yawo da ɗan gidan ƴan gayu masu kuɗi, matarsa na zaune ya nuna mata yana cewa,"Irin wannan me kyan za ki haifa idan kin tashi, ki yi ta saka shi gaba kina kallo har su tafi". Ummani ce ta kora shi a wajen tana faɗin,"Mara kunya". Naji daɗin yanda na samu labarin matar Yaya Al'amin, da yake lokacin da aka yi bikin ina America, ɗakina Yaya Al'amin ya gyara ya haɗe da nasa wanda aka shigo da shi ta ciki, don Ummani ce tayi bata so ya matsa a kusa da ita, Matar ita ma me kirki da ita Ummani tace wallah ji take kamar tana tare da ni, iya ladabi da biyayya da taimakawa dai Buzuwa na yi mata, ita dai Ummani kam tayi dacen surukai saura kuma matar Abbayo, shima Allah ya haɗa shi da ta gari. Ranar dai Ayman ya sha jagwalgwalon hannu, wannan ya ɗauka wancan ya ɗauka, manyan nan maƙota ƙawayen Ummani ai ba su jira gari ya waye na shigar mu ba, shigowa suka dinƙa yi suna sun zo ganin Hajiya Sa'ida da Balaraben Ɗanta. Tun zuwana baki yaƙi rufuwa, haka murmushin fuskata yaƙi ɗaukewa, duk wanda ya ganni sai ya ƙara kallona ya ce,"Masha Allah". Gida kuwa mamakin yaren da bakina ya kama suke. Ummani ta ce,"Gaskiya Sa'ida kin yi ƙoƙari, yo wannan idan ni ce ta ina zan fara iya wannan yaren, ni fa ɗazu da kuna yi da yaren gani na ke kamar ba ku san me kuke cewa ba". Na ƙyalƙyale da dariya na ce,"Ummani kuma fa ba wahala, nima fa da na je ban taɓa tsammanin zan iya ba wallahi, wahalarsa na dinga gani, shima da yaga naƙi mayar da hankali na iya sai ya daina min turancin ya ke min yaren, kuma fa Ummani kin san maƙasudin iyawar?". Ina dariya na ce,"Haushi yaji yace to ya daina magana da turanci a gabana shi da Kudrat, da yare za su dinƙa yi ko na dinga tsarguwa naji haushi". Ummani ta kama dariya,"Ai kin ga yay maganinki". "Wallahi fa Ummani tuni na zuciya, don haushi na ke sosai naji sun sauya yare a gabana, ba shiri kuwa na dage na koya nima, to yau da gobe ga shi ma idan ina yi sai ace nima su ce ba bahaushiya ba". "Haka ne, ai ni dai wannan aure na ki Sa'ida abin jin daɗi abin alfahari, ke dai ki ci gaba da biyayya da ladabi, ki kuma tsaya akan gaskiya, ki kama danginsa kamar na ki, matarsa yanda ya ke so ku zauna ki fishi ƙoƙarin ganin ma kun zauna a hakan kin ji". Na ce,"Insha Allahu Ummani". Muka bar tsakar gida muka koma cikin ɗakinta. Muna cikin hira Buzuwa ta shigo ta duƙa tana cewa,"Anty Sa'ida ko yaran za su mu kwana a can". Na kalli Ummani bata saka mana baki ba. Na ce da ita,"Ba takurawa Buzuwa?". "Ah babu Anty Sa'ida, ai akwai waje". "To shikenan". Sai da muka gama cin abinci da yaran kana na shirya su, Rofi'a ba zata ba dama, maƙale mata ce, Isioma da Forida na turawa Buzuwa can, da ma mun taho da manyan barguna guda biyu tunda na san yanda gidan namu yake. Ai har sha ɗaya muna ta hira da Ummani, zazzaɓi ya rufe Ayman, ina faɗawa Ummani tace,"Yo ba yasha ɗauka ba ai dole yay zazzaɓi, kin san jikin jarirai, don ma ya fara zama mutum". Ai kuwa ba shiri na ɗau takarda na rubuta sunan magani na bawa Mustafa Ƙanin Hindatu yaje chemist ya siyo min. Duk rigimansa yau dai shiru kaman ya san mun zo baƙunta, na ba shi maganin yana sha kuma sai bacci, da yana ta wuntsil wuntsil ɗinsa. Ban kuwa faɗawa ubansa bai da lafiya ba, don faɗa ne zan sha ƙarshe ma ya rage mana kwanakin da muka zo yi. Washe gari can gidan Hajjo muka fara zuwa, muna ta waya da Safiyya na ce min ba zan zo ba sai na gama tsufa a garin. Mun zazzaga ƴan uwa da abokan ariziƙi ni da yarana, wani wurin in muka je har tambaya ake wai ƴaƴan kishiyar tawa barin gidan tayi ko mutuwa tayi. Kwana goma muka yi a Madobi har da matar Yaya Al'amin muka tafi, ita ce me jigilar goyon Ayman, idan ya zo hannuna to nono zan ba shi, ƴan uwan Ummani da na Abbaa ƙalilan ne ban je musu ba, ai kuwa jikina ya faɗa min, haka na yi ta faman shan maganin ciwon jiki, Yaran kuwa sometyms har ƙorafi suke ba ya Rofi'a mage uwar son jiki, shi kansa direban da ke jigilar yawo da mu sai da yaji a jikinsa, da muka je madobin can ya zauna masaukinsa a gidan Baba Audu suna kwana tare da ɗansa Muzammil. Watanmu guda currr a kano, ranar da zamu koma sai da naji kamar kar mu tafi, Salim ne ya zo zamu wuce tare da shi, ya dawo daga Ekiti sai ya biyo ta nan ɗin, yara da suka gansa murna kaman me, ranar har cikin gidanmu ya shigo, sun kanainaye shi sun hana sa ma zama, Abbaa na tsokanar su ai anan za'a tafi a barsu, Salim ɗin ma yana murmushi ya ce dama ai an barwa Ummani su. Da goma sha tara ta arziƙi haka muka bar gida, iyayena sun cika ƴaƴan Salim da abubuwa, Yashaik ma babban kwalin choculate haka ya siya musu, ga yaran da shiga rai da saurin sabo, ba wanda bai kewansu ba da zamu tafi. Da muka biya ta gidan su Safiyya Umman su hanamu tafiya tayi a ranar sai da muka kwana, na yi tawa Salim dariya kuwa, ya azalzalo ni daga gidanmu mu tafi shi kewata yake yi, kuma mun je yaywa Umma sallama ta riƙe mu, ni dai har ya fita a falo dariya na ke masa, ga babu damar mu kwan tare da shi a gidan, haka dole ya haƙura ya riƙe yunwarsa. To haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar min, idan na kalli kaina sai nayi mamakin yanda na koma, Allah ya kai ni matakin rayuwar da ban taɓa haskowa kaina ba, dama an ce nasarar mahaƙurci da wanda aka wulaƙanta ba ta zuwa a ƙarance, har godiya na ke ga Allah da ya rabo ni da waccan rayuwar ta gidan Nazifi ya musanya min da mafi alkhairinsa. Watan Ayman goma sha huɗu na fara sabon laulayi, na faɗa sabuwar duniyar murna da jin daɗi, wallahi ban ƙi ba ayi ta bani, ina so mijina ma kuma na so, don mun tara da yawa ba zamu gaji da su ba, mu abun alfaharinmu tun da ko Annabi ce ya ku hayayyafa domin na yi alfahari da ku. Wannan karan kuwa na wahala nayi ciwo fiye da wanda nayi lokacin cikin Ayman, sai dai shi wannan gwajin farko aka gane ciki ne, bai ɓuya ba kamar na Ayman. Ba shiri na yaye Ayman, ranar har da Kukana sai kace rabamu za'ai, na sha tsiya kuwa wurin Mahbub da matarsa. Wajen Kudrat Ayman ya koma dan ita ce uwar Yayen, kan kace me kuwa yaro yaje hannun kulawa sai ga shi yay ɓul ɓul da shi, har wata ƙiwa ma yake min, na ce lallai ne Ayman ka riƙa ka riƙe. Sai in ya so ne ma wataran idan ƴan rigimar na kansa to fa sai ya zo wajena za'a samu salamar kuka, dama shi indai kuka ne ya iya, har ce na ke da Mahbub kai kuwa wanne irin kuka kayi da kana yaro, yay dariya ya ce ke dai wanne irin kuka kika yi, ni ai da an ganni anga salihin bawa. Na sha wahala fiye da yanda baki zai faɗa da wannan cikin, don sai da ta kai ga mun tattara mun bar ƙasar mun koma America da zama, saboda in samu kulawa me kyau a wajen ƙwararrun likitocinsu na can, wannan lokacin kam da Umman Batula muka tafi Allah sarki da ke mijinta ya rasu satin sunan Ayman da komawarsu. Ni kam har ina rubutawa Ayman wasiyya a diary, gani na ke kamar ba zan kai ba, bai zama lallai na haife abinda na ke ciki ba, ko da na haife ɗin to wataƙila ƴar uwata Fillo zan bi, in mutu in bar yaran da mahaifinsu, haka duk na karaya shiyasa sai na bi na rame saboda fargaban da ke tare da ni, ai kuwa hawan jini da ya kamani ni kaina da aka faɗan sai da na jijjiga, a matsayina na likita na san irin wannan hawan jinin babbar matsala ce ga rayuwar bawa, haɗari ne babba. To amma a hankali da ke ina ta samun kalaman kwantar da hankali daga Mahbub, ga kuma iyayena suma da ko da yaushe cikin waya da su muke suna min kalaman ma su wanzar da natsuwa sai na fara daina damuwa da sanya tunani. Har cikina ya shiga wata bakwai ban daina fama da ciwo ba, wannan cikin kam ɗan ƙarami da shi ana ta cewa mace zan haifa, kuma yana cikin wata na bakwan ne ƙoƙarin shiga na takwas na haife tagwaye na bakwai ni dukka maza, wannan lokacin ma kamar wancan da kaina na haihu kuma lafiya lau, sai dai ban yi dogon naƙuda ba kamar na haihuwan Ayman, wannan yini guda nayi na gama. Yaran sai a machine aka saka su, saboda yanda aka haife su ɗin ƴan ƙananu da su, ni har tsoro ma suka ba ni, ce na ke ko ba su da kyan halitta ne, sai da aka tabbatar min da lafiyarsu lau tukunna hankalina ya kwanta, in ta kuka tunma da naga an raba ni da su an kai su can wani ɗaki daban acan ake rainon su. Bamu komo najeriya ba nan muka zauna, Maa suka zo ita da su Kudrat da yaranmu, suka sauka a wani babban apertment, Ayman yana ganina yaron ko inda na ke bai zo ba yana maƙale jikin Kudrat, haka na figo shi bai san ina nan cikin ciwo cike da kewarsa ba, duk motsina tunaninsa na ke, ramar da na yi har da ƙulafucinsa da na saka a raina. Wannan lokacin ma na ga gata da tarairaya wurin mijina da mahaifiyarsa duk da kasancewar ina kwance a asibiti, basa tafiya sai dare ƙarfe sha biyu, kuma duk inda takwas na safe yake sun tattaro sun taho asibitin, tare da su zamu yi break fast, Tagwayena in aka ciro su a machine aka kawo min haka na ke kwantar da su a ƙirjina cike da tausayin su da ƙaunarsu da ke bin kowacce jijiya ta jikina. Cikar sati da haifan twins ɗina aka musu raɗin suna, Babban shi ne Abubakar Sadiq wanda ya ci sunan mahaifin Salim za mu ke ce masa Ajmal, ƙaramin kuma Umarul Faruq shi kuma yaci sunan sahabin Annabi ne, sunan yaren su Chidera da Kanayochukwu. Wannan karan kam babu taron suna sai dai mun yi shagali iyamu yamu. Yo mene maraban ba mutanene kawai babu, amma batun kashe kuɗi ina kan gadon an kashe su, asibitin nan babu wanda bai samu rabon ordan snack ɗin da aka yi ba, shanu uku Mahbub yasa aka yanka aka soya akai ta rabon nama a asibitin. Sai da yaran suka cika kwana arba'in kafin aka yi discharging ɗina daga asibiti lokacin sun ƙara ƙwari, kuma wani ikon Allah a lokacin ka gansu ba zaka ce bakwaini ba ne, kamar mu guda da Umarul Faruq komai nawa ya ɗakko, Ayman da Ajmal kuwa zaka tsammaci tagwaye ne saboda tsananin kamansu, kuma sune kana ganinsu kaga kamannin mahaifinsu. Bamu dawo najeriya ba saboda ganin likita da na ke kai yaran, Kudrat da ma bayan suna suka koma da yaran saboda makaranta itama da wurin aikinta, Maa itama sai bayan sun tafi ta tafi, amma Ayman anan aka barsa wajena, sai da muka yi wata takwas a America sannan muka dawo najeriya, ba ƴaƴana kawai ba hatta Umman Batula ta sauya kamar ba ita ba, fata taji canjin yanayi. Kan gado na ke zaune ina sawa Ajmal kaya, sa kayan da muke ta fama tun ɗazu, ya ƙi tsayawa sai yawo yake da ni, da yake haka yake gagaraf garaf, kwai ƙarfin tsiya, da kuzarinsa shi kam ba irin sauran ba, har cewa ake ko shi ne zai gaji Babansa ya zama soja. Ban isa fa na ajesa ba, tun bai cika wata biyu ba yake mirginawa, yanzu kuwa bana karambanin ma barinsa kan gado in tafi, tsab zai murgina ya wuntsilo daga kan gadon ya barni da ɗora hannu aka, in shiga uku da jaraban Babansa. Shi ɗin ranar yana hannunsa ya kwantar da shi akan kujeran falonsa, wai miƙewar da zai yi ya ɗakko abu kan dispenser sai jin yaronyay ya timo ƙasa, Allah ya so da katifansa a gefe ya faɗo kanta, kuma ko a jikinsa ba kuka, to ranar da a wajena ya faɗo sai nayi kuka saboda ihun faɗan da zan sha. Umarul Faruq kam ba ruwansa, yanda na kwantar da shi hakan zan zo na samu kayana, idan ba wai bacci yay ba ya juya gefe, yanzu haka yana gefena a kwance salihin bawa in kunji ana cewa, da ace shi na ke sawa kaya muka ɗau lokacin nan da yanzu Ajmal na nan ya ɗagan dubaidar rayuwa da kuka, inaa ai shi bai yarda na barsa, ko bacci zai yo to sai dai fa yayi shi a bayana ko a jikina, shan nonosa kuwa har yay yawa don yafi Ayman, duk ya bi ya zuƙeni yaƙi bari nayi ƙiba, ko saboda shi ba zan bari su shekara biyu ba zan yaye su. *B3ƘR20FT5* Mahbub na zaune ƙasa kan carpet ya na gyarawa yara computer ɗin su da ta lallace, Ayman na tare da shi sai ƙiriniya yake masa yaƙi barsa yay aikinsa da kyau. Sai buga masa gwaranci yake yi. Ai ni kam na gode Allah da ya ban Ayman, yay ta haɗa min shirgi ko gajiya bai yi, idan mace ne ai na huta ina ga shekara biyar zan fara sata ɗora tukunya, wuyarta in gama gyara insha Allah kafin in waigo yayo min ɓari, idan kuwa kitchen na shiga duka durowoyin nan sai ya buɗe murafansu. In ta faman mita ina ni ya ishe ni sai in sa ai masa rubutu ya nutsu, Mahbub yace in ƙyale masa yaro lafiya ce ba zan takura masa ɗa ba, har da shi bai ma ga fitinan da yake yi ba, na ce yo ina zaka gani ka tafi ka barmu da shi. Ile kuwa ranar sai ga shi yay masa ɓarin takardu kuma ya zauna akai ya saki fitsarinsa. Ranar kuwa na yita ƙunshe dariyata, sai basarwa yay bai faɗa ba dai ya ɗauke shi ya kaiwa Babarsa, itama can ai gata da shi jiki duk manja tana faɗin,"Can kuje ku ƙarata, daga shiga kicin na ɗorasa saman island ya kifo min da manja da kayan miya gaba ɗaya, Babansa na gari ya dawo yanzu in banu yace ina sane na barsa ya kifar, daɗin ma kayan miyan ba su shigar masa ido ba da ina ga jaraban Babansa sai tasa na bar gidan yau". Ni dai na ta musu dariya, Ayam ɗina idan yay fitinar sai dai kawai in girgiza kai na ce,"Allah ya gyara min kai". To yanzun ma da Baban nasa ke aikin sai bi ya ke yana kwaso min kayan durowan su Ajmal yana kawo masa, shi kuma ya biye shi suna ta hiran, in ya kawo ya karɓa yace,"Yauwa Ayman ɗina to na gode sannu da aiki". Tun yana biye masa sai da ya dawo ya koma ce masa,"Je kai wa Mommy". Can da ya ƙara kwaso kayan wankinsu sai ya zauna ya leƙa fuskan shi yana cewa,"Toda". Ban san lokacin da na tuntsire da dariya ba, shima Mahbub ɗin dariya ya saki yana ce masa,"Na'am ɗan gidan Soja, Allah yay maka albarka ka ji yaron kirki, sannu da aiki, kwanta ka huta haka ai ka gaji". Still ina dariyan na ce,"Ka ga idan baka hana shi faɗin sunanka haka ba wataran haka zai gatsa maka shi a gaban mutane". "Ah to mene dan ya faɗa ba sunan Babansa ba ne". Nayi ajiyan zuciya a raina inawa mijina adu'a gami da kyakykyawan fatan alkhairi. Haƙiƙa ina alfahari da tsintata cikin rayuwar wannan bawan nasa, idona naji ya cika da ƙwalla wadda ba ta komai ba ce face farin ciki, a kullum adu'a na ke wa uban ƴaƴana Allah yasa ya gama da duniya lafiya, ya raba shi da iyayensa lafiya, kuma ya sadamu da juna har a aljannah, ya kuma dawwamar da shi cikin farin ciki, ya ba ni ikon saka masa da irin alkhairan da yay min a rayuwa, na san ba zan taɓa iya biyansa ba sai dai na kimanta wajen kyautata masa da dukkan buƙatun da ya zo min da su. Ba faɗa ko saɓani ya haɗamu fushin na ɗan ƙalilan ɗin lokaci ne, to idan ma faɗan ne dama akan ƴaƴansa ne zaka ji yana yi, ko sun yi ta'adi an musu faɗa sun kama kuka, ko ya zo ya tarar da Oga Soja yay ɓari to fa in ya fara sai ko ina ya amsa a gidan, yace ai muna kallonsa muka barsa yay ɓarnan, sai kuma azo a dame shi da ya siyo ya siyo. "Myy wannan gyaran yafi ƙarfina, sai dai a barsa zan turo mai gyara ya zo ya duba musu, ko a siyo musu sabuwa dama wannan ɗin ai ta jima, sabuwan ma dai zan siyowa Farida Isioma da Rofi'a sai a gyara musu wannan ɗin, Ni wai garin ya akai ma suka lalata, abar da take saman table ya akai ta kifo". Kallonsa nayi duk don yaji bakina ne fa, ai ya san wanda ya lalata musu ɗin, so yake nayi magana yace ba wani nan rashin adanin yaran ne, alhalin Foridat na iyaka ƙoƙarinta akan adana abinsu, amma Ayman da fitina bai barin masu komai, sun kunna abar suna kallo ya ɗauki lemu ya sheƙa musu akai, kuma ko a jikinsa bai san ma me ya aikata ba, ai kuwa ya ɗalu a wurin Forida. Kudrat ta ce da ni bakinmu alaikum ya tasu. To yanzu da zai ji an daki Ayman ɗin mun shiga uku da faɗa, Forida kuwa sai ya iya bugunta ƙila ma yace ba zai gyara musu ba ita ɗin ma ba zai siyo mata sabuwan ba, ba ya so sam a taɓa masa Ayman, shi ke ƙara tunzura shi ma yayta cewa,"Yayi Oga soja". Ɗaukan Ayman yayi suka fita, ba jimawa ya dawo shi ɗaya, ya kuma ɗaukan Umarul Faruq ya fita da shi, ai ganin hakan na fahimci inda ya dosa, haka zai kwashe su duk ya kai ɗakin Yara. Ya dawo yana faɗin,"Wai ba ki gama ba shi ba ne". Don in tsokane shi na ce,"So na ke ma ya gama sha na bar maka shi in tafi aikina, yau eba na ke so na mana, kar ɓomo ɗin can da na jiƙa ya lalace". Killer smile yayi yana hayowa kan gadon, kuma kamar Ajmal ɗin ya sani ya saki nono. "Kin gani shi ma yaro ya san lokacin Babansa yayi, ita ma Eba sai ta jira a sallami me gidan". Yana dawowa ya faɗa kan gado tare da jawo ni jikinsa, nan da nan kuma labari ya sauya salo. Naga alama so yake in kuma ɗauka tun ban yaye su Umarul Faruq ba. *Bayan Shekara Bakwai.* Ƙaramar ball ɗin da tayi shawagi a sama ta faɗo ƙwal a saman fuskar mutumin da ke zaune bakin Sahad Store na Mandawari kano. Ya dafe fuska cikin jin zafin buguwan, kuma kafin ya kai hannu ya kama ball ɗin ta gangara ta kifar da kwandon kayan gyaransa, kayan duk suka watse a ƙasa. Ba zafin ƙwaluwar ba ma, bin hanya ya bibya tsinto kayan alhalin mutane na ta faman wucewa, wani ma sai ya take shi bai lura ba. Ya ɗago ransa a ɓace yana kai dubansa ga ɗan ƙaramin yaron da ya doka ball ɗin, Rofi'a da ke tsaye kusa da ƙanin nata tayi ƙwafa tana gyaɗa kai ta shiga ƙwala kiran,"Mommy! Mommy! Mommy!". Hankalin Sa'ida yay can bata jita ba ma, sai da Isi'oma ta taɓota tana cewa,"Mommy kinga yaran can ko, kalle su fa acan baya, Mommy wai haka kullum za muke tafiya sai mun yi nisa muke ganinsu a baya, a ke barin su a gida kawai". Na ɗaga kaina don kai dubana gare su sai na jiyo Rofi'a ɗin na cewa,"Mommy Ayman ya ƙwalawa me gyaran takalma ball". Raina ya ɓaci sosai, na rasa irin Ayman sam ba ya ji indai akan ball ne, nayi faɗan nayi har na gaji, kawai duk wurin da ya samu doka ball yake da dogayen ƙafafunsa irin na Babansa, kuma ba'a isa azo fita ba sai ya saka rigiman lallai sai da ball ɗinsa zai fita, a hana shi a rasa kwanciyar hankali da faɗan ubansa, na ce hakan ba kyautuwa ba ne yace babu ruwana kar na ƙara hana masa yaro yin abinda yake so. Kuma har yana cewa Ayman ɗin ka doka ball ɗinka duk inda ka ga dama, wanda ya fasa taɓa min ɗa bai cika isashshe ba, kayi ball a inda kake so Babanka soja ne Kakanka Soja ne Yayan Babanka soja ne kaima kuma soja ne. To wa ya san yanzun ma ko yana wajen, tunda ajiye mu kenan da yayi mun dawo daga rakiyan Ummani da Abbaa airpot za su tafi Umaran da na biya musu. Shi ne ya aje mu nan in yiwa yaran su Yashaik siyayya zai je gidan sarki ya dawo sai mu wuce, yau ɗin muka shigo garin kuma kai tsaye filin jirgin muka wuce, da yake shekaranmu biyu kenan da komawan mu can Abuja, tun ma da muka koma ɗin bamu wani zazzo kano ba tun bayan rasuwan Kaka, Allah sarki Kaka har yau mutuwarsa na taɓa ni, duk da an sha zaman duniyar. Cike da takaici na girgiza kai na kalli Isioma nace,"Kula da yaran nan ina zuwa". Na faɗa ina tafiya na barta da Umarul Faruq da Ajmal. Ai fa tunda ya hango tahowata ya falla a guje yay jikin wani mutumi ya ƙanƙame shi, ga fitina ga shegen tsoron bala'i, idonsa duk yay wurƙi wurƙi ai ya san dole ma sai na murɗe masa kunne, yanzuma yasa hannu ya rufe kunnuwan dama haka muke da shi. Ni ban da yaci sunan Abbaana ma ai zane masa jiki zan ke yi. Mutumin ya ɗauke shi yana dariya da jin sha'awan yaron a ransa, Rofi'a kuma sai dariya take yi na mugunta dama sun saba a tsakaninsu, shi yay mata dariya idan irin hakan ta taso itama tayi masa, gata dai da ƴan uwanta mata amma sun fi shiri da shi, duk wata kitumurmura tare su ke yi, in ce an dai ji kunya Yayar kawai. "Mommy wallahi ki zane shi, sai da ina ta ce masa kar ya buga kar ya buga yaƙi jina, da zan ƙwace ma yace min sai ya faɗa ni da Paapa, ni kuwa na ƙyale shi don na san faɗan Paapa, haka kawai ya zo yana cewa kar in ƙara bugun masa ɗa, dama duk an fi sonsa ai". "Ina wanda ya bugawa ɗin?". Na tambaya idona akanta ita ɗinma kamar na kwaɗeta, ba damar mu fita sai suke tsayawa a baya, kuma har a gaba zan tasa ƙeyarsu amma kafin na farga sun zilla sun koma bayan, sai mun ci uwar tafiya kan in ankare Isioma tace min,"Mommy ga Tom and Jerry ɗin can a baya". Rofi'a ta kai hannu tana yi min nuni da mutumin da ke tattara kayan gyaran takalman nasa yana maida su cikin kwandon, sai naji tausayinsa ya kama ni don da gani yana cikin wani hali na neman taimako, amma ɗan albarkana ya daddage ya buga masa ball, abar da take da shegen zafi ni kaina ranar da ya ƙwalo min ita sai da na kusa ƙwalla. Na gyaɗa kai ina niyyan in tafi inje in basa haƙuri sai kuma dai na fara tunkaran wajen wanda ya ɗauka Ayman, haka kawai ban sansa ba bazan bar masa yarona ba, wani abu ya faru na zo na shiga uku, ubansa ma sai yay min bulalai ya ɗaure ni, ya haka Family sakat sai an nemo masa ɗansa. Muka gaisa da mutumin yana cewa,"To ya za'ai ai haka yara suke sai haƙuri, kar ayi masa faɗa please kuma kar a duke shi, zai daina wataran, bari naje na bawa shi mutumin haƙuri". Kaina na ƙasa na ce,"Shikenan na gode". Ya tafi tare da Ayman ɗin wai ma don kar ya bar min shi in duke shi, yana riƙe da shi a hannunsa, na bi bayan mutumin da ido har ya kai ga wajen me gyaran takalman. "Mommy ɗauke ni". Ajmal ya faɗa cikin nasa rigiman, ba zai barni na huta ba ai, ya girman ma shi bai yarda da kowa ba, shi ko Umarul Faruq dama indai da Isioma bai da damuwa. Na duƙa zan ɗauke shi daidai lokacin kuma da Nazifi ke ɗago kai ya kai dubansa ga Babar yaron da mutumin yaje basa haƙuri yay masa bayani, me idanunsa za su gane masa? Kamannin da ba zai taɓa mancewa ba ne ba fa, fuskar da ya ke ta son gani ce fa, a wani razane yake kallonta har ya kuma yar da kwandon gyaran takalman suka watse a ƙasa, baki a buɗe ya kasa rufewa. Zuciyarsa ta shiga harbawa fat fat kaman zata fito waje, kafin a hankali laɓɓansa su haɗe da furta sunan Sa'ida. Tambayan farko da ya fara shiga ƙwaƙwalwansa ita ce,"Yaran waye a hannunta?". Kuma kamin wata tambayar ta sake gifta masa idanunsa sun haska masa kamannin yaran maza dukka uku a cikin idanuwansa. Ba sai ya nemi ƙarin bayani ba, kuma ba sai an faɗa masa ba, ko makaho ya shafa yaji ya san wa'annan kyawawan yaran maza tubarkalla masha Allah na ta ne. Kawai sai ya tsinci saukar hawaye a saman kuncinsa, haka yaji ƙafafunsa na neman gaza riƙe shi, yay saurin ja da baya yana jingina da bango. Rayuwa kenan, wacca ya wulaƙanta ya tozarta ya gorantawa ita ce ke tsaye haka a gabansa, gata nan ta zama mace cikakkiya mai aji da ilimi da wayewa, wadda ta taka matsayin da shi bai taka ba, kallonta yake daga nesa kallon da ya san tafi ƙarfin ya isa wurin da take, da dukkan nuni ta samu kowanne kalar cigaban rayuwa da ake nema, shi kuma ga shi cikin wata rayuwa na halin ƙaƙa na ka yi, halin rayuwar da cin yau ke masa wahala balle na gobe, godiyarsa ɗaya ma ya samu Allah ya jiƙansa ya sawwaƙe masa manyan basukan da ke kansa, banda haka yana jin da zuwa yanzu kam yana can bursun zaman da babu lallai ya fito. Ya kai hannu ya share hawayensa, ba kowa ya tuna ba sai mahaifiyarsa wadda Allah yaywa rasuwa shekarar da ta wuce, kuma a yanzun haka ya tuna da lokacin da suke tare da Sa'ida ne, irin kulawar da ta bawa mahaifiyarsa abar ƙaunarsa, irin hidimar da ta yi mata, saɓanin matar da ya sake aure wacce zai iya cewa ita ta zama silar ajalin mahaifiyarsa, don ita ta zubar da karkashi bata gyara wajen ba Iyam ta zo ƙofar ɗaki tana ƙwala masa kira, sai Marawiyyan ta fito tana mata rashin kunyar da ta saba, dama bata girmama mahaifiyarsa sam yo auren ma da ƙaƙa aka yi, ita ta aure shi ma don bai da kuɗin auren, to haka kullum take cikin jawa uwarsa kunne na kar ƙara zuwar mata gida tana kiran ɗanta, idan son ganinsa take ta dinƙa kiransa a waya ya zo gida ya sameta. Kuma a ranar da takewa Iyam wannan hargowan lokacin ya fito daga ɗaki da niyyan cin mutuncin Marawiyyan kawai sai ya tadda ta tunkuɗa Iyam baya ta zame akan wannan ruwan karkashin, shikenan daga ƙwaluwar da tayi a ƙasa kuma sai ciwo, ba magana ba motsi. Akai neman kuɗin maganin aka rasa a sa'ilin har sai da ya tuna da alkhairin Sa'ida gare shi, sanda suna tare da ta ɗauka kuɗin makarantarta ta siyar da kayan ɗaki ta ba da kuɗin maganin Iyam har aka mata aiki, haka da sanda yaje asibiti aka ce masa yanzu ta tafi ga kuma kuɗin da ta bayar, ranar yay kuka iya kuka, yayi nadama da danasanin wulaƙanta Sa'ida da yayi a rayuwarsa, ya kuma ji takaici da baƙin cikin sauya kyakykyawan halinsa da yay, ga shi Allah ya nuna masa ƙarshensa, ya tozartata ya mata cin kashi ita da ƴan uwansa akan rashin haihuwa ga ta can cikin gata ita da yaranta. Idanuwansa suka rufe yana jin zuciyarsa na masa ciwo, sai yay murmushi yau ga shi ɗanta ya ramawa uwarsa abinda yay mata, sai ya kai hannu ya shafo wurin da ball ɗin ta ƙwalu, daga jin zafin ball ɗin ma ka san me shegen tsada ce. Ya buɗe idanu a hankali yana kai dubansa gare su, ganin yanzu saɓanin na ɗazu, yanzu tana tare ne da mijinta wanda ya fito daga cikin arniyar mota, tana karanta masa ƙiriniyar da Ayman yayi har tana yi masa nuni da inda Nazifin yake tsaye. _"Nazifi Allah kar ya ƙara nuna min kai a rayuwata, Allah kar yasa na ƙara tozali da fuskarka har na koma gare shi, macuci azzalumi"_ Kalaman nata na wancan lokacin suka haska masa cikin kai, a ƙasan ransa yace haƙiƙa Allah ya amsa miki adu'anki, ga ki ga ni, har kina iya nuna ni daga nesa amma idanuwanki ba su samu damar ganina ba. Hawaye suka daɗa sakko masa masu zafi, a hankali ya duƙe a ƙasa zai kwandon gyaran. Ɗagowan da zai yi kuma Salim ya ƙaraso wajensa, ganinsa ɗin sai da gabansa yay mugun duka, har yana saurin ja da baya. Salim ɗin na dubansa da murmushi yace,"Ba wani abu ba ne". Nazifi ya haɗiye yawun wahala, jiki na rawa ya ce,"To ai ranka ya daɗe ganinku ne akwai furgici, Allah yasa lafiyar". Ya faɗa da tsammanin ko Sa'idar ce ta faɗa masa abubuwan da yay mata ya zo ya kama shi. "Ranka ya daɗe ni dai wallahi ba mai laifi ba ne". Yay maganar cikin rawar murya da ruɗewar ciki. Still da murmushi fuskan Salim ya ce,"Ni ne Mahaifin wannan yaron, Mahaifiyarsa na faɗa min rashin jin da yay ne". Da saurin murya da na jiki Nazifi kamar zai duƙa masa yake cewa,"Laa ai babu komai, yaro ma shi da yake wasa, ball ɗin kuma ai kayana ta buga ba ni ba, batun haƙuri ma ka bari kawai ranka ya daɗe, don Allah a bari ba sai an bayar ba". Foridat ta ƙaraso wajen tana cewa,"Paapa Mommy tace ga takalmin Ajmal a gyara masa, zai shiga mota ya gurɗe ƙasan ya ɗago kaɗan". Da Salim na shirin ya ce a ƙyale kawai a siya masa wani tunda store za su shiga, sai kawai ya bari Nazifin ya gyara ɗin shima ya samu wani abun, tunda ba lallai yay ciniki ba fitowarsa. Shi kuwa Nazifi mamaki ne ya kama shi jin suna yare, ƙarya yake yace bai ji burgewan su ba musamman ma Sa'idan da Ƴaƴanta, yanda ta buga shigan alfarma ga haƙoran makkanta sai ƙyalli suke daga nesa. Hannu na rawa ya jawo kwandon kayan gyaran ya karɓi takalmin hannun Forida ya shiga gyara, ya gama Salim yay yay da shi ya karɓi kuɗin gyaran yace a'a su barshi, takurawan da Salim yay masa dole tasa shi miƙa hannu biyu ya karɓa. Ya shiga zura hannu cikin aljihun koɗaɗɗun kayansa lalubo canji. "Ranka ya daɗe bari na ɗan samo canji a can, da yake ba a samu an yi cinki ba ne tun fitowan nawa". Ya faɗa sai faman buɗa haƙwara yake duk a ruɗe, ya bi ya dabarbarce, Salim da fara'ar nan tasa ya ce,"No barsa kawai ka riƙe gaba ɗaya, idan na koma da shi ma Madam faɗa zata yi ban barwa mabuƙaci kamarka ba, Allah ya bada sa'a". Dubu ɗaya ce sabuwa fil, amma haka Nazifi ya zube ƙasa yana ta jera godiya. "Na gode, Na gode ranka ya daɗe, Allah ya raya iyali, Allah ya ƙara matsayi da ɗaukaka, Allah ya jiɓanci al'amura". Salim yaja yaransa suka tafi, ya so da cash a jikinsa da yawa ya ɗan yi masa ihsani don ba ƙaramin basa tausayi yayi ba, abin a taimaka masa ne tabbas, sai dai bari su fito daga siyayya sai ya cire kuɗi a ciki ya basa, tunda yaga kamar nan ɗin ne wajen zaman sana'ar tasa, duk da masu sana'an gyaran takalman ba su fiya zama wuri ɗaya ba sun fi bin hanya suna kaca cau kaca cau. Nazifi na kallon Sa'ida daga nesa gwanin ban sha'awa ita da iyalinta, Sa'idansa ta zama matar manya, ji yay kamar ya bisu, kamar ya isa gabanta ya duƙa ya ƙara neman gafararta, yana kallo suka shiga cikin Sahad Store ɗin, fuskarta da ta mijinta cikin nishaɗi da farin ciki, ga wani bayyananiyar soyayyar junansu da ka kalle su. Jiki a matuƙar mace ya juya ya shiga ta wani ɗan loko, bai yi tafiya me nisa ba ya isa wani gajiyayyan gida, ƙofar langa langar gidan duk a farfashe ta lanƙwashe. Iman da Ƙanwarta Mubina na can ƙofar wani gida suna wasan ƴanta, suka kwaso a guje ganinsa ya dawo don ya hana su yawo, su kuma rashin jin daɗin zaman gidan ke sawa su fice. To matar gidan jarababba ce, ta daka ta kuma daka, su yi kukan ta kima musu uban aiki, abinci sai taga damar ba su ma, tayi ta musu gorin ai uban na ku me gyaran takalma da kwasan kwata bai kawo ya aje ba, don haka ba zan ba ku ba, sai in su ci sa'a ne wataran ta ke ɗan tausaya musu ta ba su. Duk sun yi furkai furkai da su, da ganinsu ma ka san ba su yi wanka ba, riga daban ɗan kwali daban, rashin uwa ma dai gaban ƴaƴanta babu daɗi. A tsakar gida suka sameshi ya zauna bakin rijiya ya zabga tagumi, suka shigo a tsorace kar ya dake su ko faɗa. Iman me wayon ita ta lura da kaman kuka mahaifin na su yake. Ta ƙarasa da sauri ta zauna kusa da shi tana faɗin,"Baba sannu da zuwa". Kallon su kawai ya tsaya yi, tausayinsu ya kama shi. Iman ɗin ta zare masa hannun da yay tagumin tana cewa,"Baba ka daina tagumi, kuma naga kaman hawaye ka ke yi, Baba wani abu ne ya faru?". Numfashi ya sauke, cikin dabara ya goge hawayensa don ka kaɗan ba ya so yaransa ke ganin cikin irin yanayin nan. "Ina ku ka je?". Tayi ƙasa da kanta a hankali tace da shi,"Baba muna ƙofar gidan Malam Musa muna wasa". Murza fuskarsa yay. "To kun samu abinci kun ci?". Suka girgiza kansu a tare alaman a'a. Ƙwalla ta daɗa cika idonsa yana zura hannu cikin aljihunsa ya zaro dubu ɗayan da Salim ya ba shi. Ya bawa Iman ɗin yana cewa,"Ku je kantin Gambo ku siyo taliya ƴar hausa ta ɗari uku, sai manja na ɗari, sai ki haɗa abinda za ku daka yaji". "Tom Baba". Suka faɗa suna miƙewa cike da murna, sai dai suka je soro Mubina ta dawo tana cewa,"Baba na siyo biskit don Allah?". Kai ya ɗaga mata,"Ehh ki siyo idan akwai canji". Cikin wani irin yanayi da shi kaɗai ya san a halin da zuciyarsa take ya goge hawayensa. Idanunsa hoton iyalin Sa'ida kawai ke haska masa, yaranta tsab tsab da su cikin shiga ta alfarma, yara kamar larabawa kaji ina ma naka ne ko ka sace ka gudu. amma ga nasa yaran kamar waɗanda aka ƙwato daga bakin jaka. Ba su daɗe ma da dawowa hannunsa ba don ba su cika shekara ba, Zahra'u ta kawo masa su zata yi aure, tun rabuwar da suka yi bata ƙara aure ba sai yanzu, to mijin da ta aura yace ba zai riƙe ƴaƴan da ba nasa ba, ta dage ta tafi da su gidan Kishiya ta sakota gaba da sharri da makirci, a dole ta tattaro yaran ta kawo masa abinsa, ga su nan cikin rashin galihu makaranta ma ya kasa saka su. Marawiyya ta fito daga ɗaki, ganinsa ta wurga masa wani matsiyacin kallo tana jan tsaki tare da ɗaukan buta ta shige banɗaki. Haka suke zaune da shi sam bata ganinsa da daraja, ina ma yake da gashi idon da zai samu arziƙin gaisuwa daga wurinta. Dama ita taji ta gani tace da shi su rufawa juna asiri, tunda shima bai haihuwa ita kuma taƙi auruwa sai gantalin zawarci take, ba namijin da ke iya zama da ita, shi kuma saboda yaransa ma ya yarda saboda ya samu me riƙe masa su, to ashe ma gwara bai auren ba ya zauna ya riƙe yaransa a gidan su. Tashi yay jiki a matuƙar sanyaye ya shiga ɗan akurkin ɗakinsa, ya aje kwandon sana'arsa, ya saki yagalallan labulen ɗakin sannan ya kaɗe saman tabarmar ya kwanta idanuwansa na kallon rufin kwanon ɗakin da hasken rana ya shigo ta ɓulolin jiki. Samun kansa yay da rufe fuska da tafukan hannu yana fashewa da kuka, komai na rayuwan baya ne ke dawo masa daki daki, haɗuwansa da Sa'ida, Shaƙuwansu, matsayin da aka ɗaukesa a gidansu kamar ɗan gida, soyayyarsu, aurensu, rayuwar auren da suka shimfiɗa a farko, halin tsananin da ta zauna da shi, irin sadaukarwar da tayi akansa, halaccinta gare shi, samun arziƙinsa ta dalilinta, ɗaukakar da ya samu, wulaƙantata ɗin da yay kamar kare, ƙofar da ya bawa ƴan uwansa na cin zarafinta, mayarsheta baiwar da mahaifiyarsa tayi, gorin rashin haihuwar da ya dinƙa mata, ƙazafin da yay mata, rabuwar aurensu, halin da ya fara faɗawa, abinda Zahra'u tayi masa, zaman kurkukun da yayi, mutuwar mahaifiyarsa zuwa yau da Allah ya nuna masa ita tun bayan shekaru goma sha biyar, ya ganta a mataki na matsayin da bai taɓa tsammanin zata je ba, ya ganta cikin kwanciyar hankali da farin cikin da shi bai sameshi ba sam. Kawai sai ya daki kansa a cikin kayan wankin da yay matashi da su, ya shiga kukan da babu sauti, a hankali muryansa ke fita da,"Allah ka yafe min wulaƙanta rayuwar baiwarka da nayi, Allah na roƙe ka kaji tausayina kasa Sa'ida ta yafe min, Allah ko dan yaran nan guda biyu da ka bani mata ka bani halin da zan inganta rayuwarsu, na ba su ilimi da irin gatan da jin daɗin da ƴaƴa ke samu wurin mahaifinsu". Yana tsaka da hakan su Iman suka yi sallama a ƙofar ɗakin nasa, yay saurin tashi zaune yana goge fuskarsa, sai da ya saita kansa tukunna ya ba su izinin shigowa. Suka shigo Mubina na tafiya wajensa ta faɗa jikinsa, Iman kuma ta duƙa ta miƙa masa kuɗin da cewa,"Baba ga shi ɗari biyu da hamsin ne ya ragu, na taho da gawayi ma, Anty ta hanamu taɓa mata nata". Sai dai yay namijin ƙoƙari wajen hana raunin da ke tare da shi fallasa a gabansu. "To kun siyo komai?". "Ehh Baba, gawayin zaka haɗa min, kuma naga kaman baka da lafiya". Tayi maganar cikin jin tausayin mahaifin nata kamar zata yi kuka. "Ɗagani Mubina in je in haɗa muku wutar can, ko ba kya jin yunwa ne?". Tana wasanta a jikinsa tace,"Ina ji mana Baba, yau fa bamu ci abincin safe ba ka manta, sai da muka je can gidanku fa Amarya ta bamu ƙosai guda biyar, suma ya ƙare lokacin Yaya Iman ce ma tace mun ƙoshi bayan sai da Baba Adamu yace zai bamu kuɗi mu siyo wainar fulawa". "To yanzu dai ai ga shi za'a dafa, irin taliyar ma da kike so, sai kin ci kin ture ƴar lelen Baba". Tare da shi suka fita, Iman ta ɗakko masa kujera ya zauna gaban burkoti, dama basa iya haɗa gawayin sai dai shi ya haɗa musu. Sai hira suke masa wanda hiran na su ne ya ɗebe masa kewa, Mubina na tambayarsa yaushe za su wurin Mominsu, yace to sai yasa kati a waya sai ya basu su kirata su ji. Duk da ya san abu ne me wuya don ko da wasa mijin Zahra'u bai yarda yaran suje gidansa ba, yace hakan a bakin aurenta, ita ganin ta ɗebi shekaru da yawa ba auren yasa ta ke lallaɓa igiyan aurenta. *****Sai dare Mahbub ya zo ya ɗauke mu a gidan Safiyya, can muka yini yau kam, ita ma yaranta huɗu dukka mata, ga dai wani cikin nan da muke ta sa ran zuwan namiji. A mota muke waya da su Abbaa ina alhazawan baɗi insha Allah, don so na ke idan suka dawo a Umra to aikin Hajji ma ayi da su, yanzu haka ma na haɗa kuɗin mutum ɗaya saura na mutum ɗaya, kuma kafin zuwan lokacin Allah zai hore in haɗa, na fi so suje dukka su biyun "Mommy ina bindigan da Mami ta ba ni". Ayman ya faɗa yana zuro kansa ta tsakanin kujeran motan, ni ban so Safiyya ta ba shi bindigar ba duk da ta wasa ce ni bana so, ko da yake Babansa ma ba shi ta gaske yake yi. Nayi masa shiru kamar ban jisa ba. Umarul Faruq ma ya kama cewa,"Mommy nima ai Mami ta bani jirgi irin wanda Paapa ke hawa". Shima na masa shiru, Ajmal kuwa sai taɓo Mahbub yay ya ce,"Paapa har da ƙatuwan mota Mami ta bani nima". Na girgiza kai muka haɗa ido da Mahbub, ya ƙaramar ariya yana cewa,"Hmm duk ma za ki fitowa da yara kayansu ne, sai aiwa yara kyauta ki riƙe". "Naji, ni ɗazu ma ban baka labari ba, sirikata ta kira ni wai don Allah asa musu rana suna so zasu zo ayi maganar aure". Murmushi yay da cewan,"Wacce surukar taki, don naga duk kun tara surukai, ƴaƴan gaba ɗaya kun bayar da su". Nayi dariya da maganar tasa, daga cewa za'a haɗa Ayman da ƴar gidan Safiyya Iftihal shi ne tsaban sharri wai duk mun bayar da su. Na ce,"To dai Allah zancen gaskiya na ke maka, ina saurayin Forida likitan nan na Abuja, to Mamarsa ce ta kira ni". Dariya yay yace,"Sai ku yi magana da Hassanarki ai, lokacin da ku ka fara barin yarinyar zance sani nayi, wallahi ni dai gaskiya na ke faɗa muku ku daina munafurtata". Haka muke ta hiranmu da shi cikin nishaɗi, hankalin yaran ma duk ba ya garemu suna baya suna vedio call da Ummani, shi kuma nan shafo cikina yake yana faɗin,"Daren yau zan samar da uku kyawawa". Na doke hannun nasa ban biye masa ba na maida kallona kan titi. Don na fara tsoron yaran nan, kwanaki Ayman rutsa ni yay na gama shirya shi zasu tafi school wai sai na masa irin kiss da hug ɗin da na ke ma Paapa, to ga Umarul Faruq nan ma daga na sumbace shi a goshi sai yasa min darun irin wanda na ke ma Paapa shima a lips. Na waiga na dubi yaran, kallonsu na ke duk cike da so da ƙauna, kafin na maido da dubana ga mijina wanda na tsare da kallo har sai da ya kawo yatsu sai tsole min ido, ina dariya na sauke ido ina ƴar dariya, wayata na buɗe maimakon shiga whasapp ɗin da nayi niyya sai kawai na ɓige da kallon kaina a kan screen ɗin wayar, ni da Ajmal da Umarul Faruq da Ayman da Mahbub. Rayuwa kenan, Allah mai yanda ya so, ga shi dai yau ya haskaka rayuwar Hajiya Sa'ida, ya haska ni da hasken da ban taɓa zaton samunsa ba. Haƙiƙa ba ka fidda rai da duk abunda yake na Allah ba na wani bawa balle yace zai hanaka. Na sauke numfashi, annurin fuskata na ƙara washewa, na faki idon yarana na kaiwa Mahbub kiss a kumatu, ya waro ido da cewan,"So kike muyi accident akan titi". Ina siririyan dariya na ce,"Ina sonka Mahbub, Ina sonka Miji na gari, Ina sonka ɗan aljannah, ina sonka Abu Ayman da Ajmal da Umarul Faruq, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan kwana, ya dawwamar da mu a cikin farin ciki da jin daɗi har abada". "Amin ya hayyu ya qayyum Ummu Ayman Wa Ajmal Wa Umarul Faruq Wa Sauma Wa Nasrin". Ya faɗj hakan yana min ƙayataccen murmushin da ke nuna shimfiɗaɗɗiyar soyayyata a fuskarsa, tare da kamo hannuna ya riƙe yaci gaba da tuƙin a haka. _______________________________ *_ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! Dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangijin talikai majiɓincin al'amuran bayinsa...A yau 15-Dec-2023 na kawo ƙarshen labarin ƘAYAR RUWA Book 1-3, wanda na fara rubuta shi a ranar 1-Oct-2023, labarin da ya samu rubutu, wallafawa, ƙirƙira, tacewa daga gare ni Halimatus-Sa'adiyya H Zakariyya(Halima.hz), ina roƙon Allah nah da ya bani ladan faɗakarwar da nayi a ciki ni da waɗanda suka karanta ba ki ɗaya, sannan ya yafe mana kuskuren da na rubuta kuma ku ka karanta._* *_Sannan ina miƙa godiya da gaisuwar ban girma na musamman gare ku Masoyana, waɗanda suka yi dafifi wajen sanya kuɗinsu su mallaki wannan labarin nawa, na sani tabbas ƙauna da cancanta ne yasa hakan, na kuma miƙa jinjinata a gare ku, tare da roƙon jalla wa'azza ya ninka muku abinda ku ka kashe, Allah ya faranta muku yasa wa halal ɗin ku albarka...Ina mana fatan samun dacewa a rayuwarmu, iyayenmu waɗanda suka rasu Allah ya jiƙansu da rahmarsa, wa'anda ke raye kuma Allah ya ƙara musu lafiya da nisan kwana, ya kuma sa suyi kyakykyawan ƙarshe mu da su baki ɗaya._* *_Ba ya ga haka zan yi amfani da wannan dama wajen neman yafiyar duk wanda na ɓatawa bisa kuskure ko kuma cikin sani, tafiya ce da muka yita miƙaƙƙa, ɗan Adam ajizi ne, zai iya zamana na ɓatawa wani cikin tafiyar, ba fito na fito muka yi ba, ba cecekuce ba, koma dai ta ya ta kasance ina roƙon ku da a yafi juna don Allah, nima idan akwai wanda muka taɓa samun saɓani haƙiƙa ban riƙe shi ba, batu na yafiya ne kuma na yafe sai fatan Allah ya yafe mu gaba ɗaya._* *_To ban sani ba ko zan ƙara fasowa nan gaba da wani sabon labarin, amma dai zai zama da kamar wuya gaskiya, dalili kuwa sau ɗaya na ke rubutu a shekara, to ban ce ba amma dai ku fi dakona a tafiyar team fitattu biyar na gaba wato next October 2024 idan Allah ya kaimu. Na bar ku lafiya, Halimahz taku ce domin ku ɗin nawa ne, ku ɗin mutane ne na musamman a gare ni, idan ba ku sani ba ku sani ina yi muku son so fisabilillah._* *_Ƙofar aika saƙo gare ni ta lambar wayata a buɗe take gareku a ko da yaushe, sai dai don Allah kar aji ba daɗi idan aka samu jinkiri na bayar da amsa, kun dai san yanda al'amuran suke, dole sai mun dinƙi yiwa juna uzuri, uzuri yana da matuƙar daɗi a rayuwa, ko shawara na ta shi bayarwa na kance da mutum ka zama mai yin uzuri a rayuwa. Murmushi ɗauke a fuskata na ke cewa da ku Bissalam, Saduwar alkhairi._* *Tauraro nawa za ku bawa labarin?* Halimahz 07018098175