💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫 (Love and Destiny) Na UMMUH EYSHAL Mrs. Alkali بسم الله الرحمن الرحيم *Da sunan Allah me rahma me jin kae,Godiya ta tabbata ga ubangijin talikae wanda yabani damar fara rubutamuku wannan littafin,Amincin da taslimi sukara tabbata ga annabin mu annabin rahma annabi muhamammad salallahu alaehi wasallam* *Sadaukarwa* Na sadaukar da wannan littafi ga maigidana, masoyi na, ginshikin farin cikina kuma uban Ya'ya na. Nagode da ƙauna, fahimta, da goyon bayan da ka ke bani a kowane mataki na rayuwa. Haka kuma ga yayana kuma ɗan uwana na jini, *Bashir Ahmad Musa*, wanda kalmominsa suka zame mini garkuwa a lokacin da zuciyata ke da rauni. Ku biyun kun taka rawa ta musamman a rayuwata — wannan rubutu sadaukarwa ce gare ku, alkhairin Allah ya kaimuku a duk in da kuke. *Gabatarwa* Rayuwa wani tafarki ne mai cike da sirrika da sauye-sauye da ba kowa ke iya hango su ba. Akwai lokutan da burin zuciya ke bijirewa kaddara, sai dai a ƙarshe, abinda Allah ya rubuta shi ne zai tabbata. Littafin *Ƙauna da Kaddarah* ya ƙunshi labarin wata mace da ta fuskanci ƙalubale daga kuruciya zuwa girma, cikin soyayya da ciwon zuciya, tsanani da juriyar rayuwa. Kaddara ta raba ta da farin ciki, amma soyayya ta nemi hanyarta ta dawo da shi. Wannan littafi ba wai labarin soyayya bane kawai, har ila yau yana ɗauke da darussa na rayuwa, hakuri, yanke shawara, da ƙarfin zuciyar mace da namiji a lokacin da jarrabawa ta same su. Ina fatan wannan littafi zai tabo zuciyar ki/ ka, ya baka nishadi, da kuma zurfin tunani game da yadda kaddara ke tafiyar da rayuwar mutum. GARGADI *Labarin littafin ƘAUNA DA KADDARAH ƙirƙirarran labari ne, idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, arashi ne.* Wannan littafin mallaki na ne Ban lamunci a juya mini littafi, ta kowace irin siga ba, sai da izinina❗ Page 1️⃣ *"National Hospital Abuja, Garki – Area 11, Central Area, Abuja."* Misalin qarfe 12:30am na rana, sautin karar motoci masu sirri ne ya karade harabar asibitin National Hospital Abuja. Wata mota kirar SUV ce mai gilashi mai duhu ta shigo cikin nutsuwa, tana jagorantar tawagar, motocin ,Bayanta kuma motar limousine baƙa, ce ta biyo, tana tafe cikin natsuwa kamar ba tafiya take ba. A karshe, wasu motoci biyu na tsaro (escort vehicles)suka rufo musu baya, kowacce dauke da ma’aikatan tsaro masu rigar fata da tabarau masu duhu sanye akan fiskar su. Ma’aikatan asibitin da marasa lafiya da ke kai kawo a harabar asibitin ne, su ka tsaya suna kallon tawagar motocin ,ba tare da sanin wanene ya iso ba. A lokacin ne wani daga cikin masu tsaron ya fita daga motar gaba, ya duba gefen kofar motar limousine, d'in sannan ya bude cikin ladabi da nitsuwa. Da sauri wani matashi da akallah zai kai shekaru 37yrs ya fito ya tsaya a bakin mota limousine d'in da alama yana jiran fitowan uban gidan nasa ne. Shiru wajen yayi na wasu mintuna a kallah ya kusa 5 minutes . Kafafunsa ya zuro a hankali sanye suke cikin takalma masu sheƙi baƙaƙen designer cover shoes na Louis Vuitton. a hankali ya fito daga cikin motar, kai kace shugaban ƙasa ne. Dogon mutum ne mai surar jarumta, fuskarsa cike da nutsuwa da kamala, yana da dan kauri kad'an amma ba sosai ba, fari ne irin sosai din nan, don har yellow -yellow fatar sa tayi, kana ganin sa kaga farin bafulatanin usuli, kamar zaka taba fatar sa jini ya fita sabi da hasken sa . Sanye yake da bak'in suit na alfarma – custom-tailored Italian design wanda ya zauna a jikinsa luf-luf tamkar an zana shi ne sabi da shi. Shirt dinsa fara ce mai sheƙi, da silin tie mai launin royal blue. Hannunsa ɗaya na daure da wristwatch mai tsada (Rolex), ɗayan kuma yana riƙe da jakar laptop ta fata da sauri PA ya karbi jakan laptop din nasa tare da dan rusuna masa, alamar girmamawa. Fuskar sa a had'e take ba ta da alamar murmushi amma akwai nutsuwa mai cike da kamala da daraja, akanta. idanuwansa kuwa sun nuna gajiya alamar yafito daga doguwar tafiya , Duk da hakan, in ka kalle shi baza ka iya gane hakan kai tseye ba sa bida korjinin sa da girma da izza. Cikin nitsuwa da kasai ta ya fara takunsa na ingarman namiji maiji da lafiya. P.A din sa ne ya take masa baya ,sauran bodyguard din kuma anan aka barsu a kame kamar wasu marassa rai. Kamshin turarensa ya cika iskar da ke zagaya harabar asibitin. İn ka kalli yadda ya ke tafiya cikin nitsuwa da kasaita, zaka dauka ba shi da wata damuwa a tattare da shi. Haka jama'ar dake wajen sai matsawa sukeyi wasu na kus kus din sa, Wannan shi ake kira banza a banza dan kuwa bai san ma da zaman su ba bare yasan sunayi, haka yaci gaba da sa kai cikin asibitin Sani P.A na biye da shi abaya, duk in da ya wuce sai ya barmusu tsarabar kamshin turaren sa mai sanyaya rai. Obstetrics & Gynaecology Department naga an rubutu a saman department din da ya shiga, da alama asibitin ba bakon sa bane Duk da takunsa mai nauyi da izza, akwai gajiya da damuwa a fuskarsa, amma ba kowa ne zai fahimci hakan ba, Likitoci da nurses ne suka shiga matsawa gefe, suna ba da hanya cikin girmamawa suna miko gaisuwar su ,hannun sa kawai yake daga musu alamar yana amsa gaisuwar da suke masa. Da sauri wata Nurse ta shiga gaban su , da alama sun san da zuwan sa, da Sani PA su ka gaisa , haka tayi gaba domin yimusu jagora , shi ko uban gayyan ko a jikin sa bai nuna ma alamar ya san da wanzuwar wata halitta atare da su ba, dama chan tafiyan kurame ake yi a tsakanin sa da Sani PA. Wani dan corridor ta bi da su a saman shi an rubuta VIP Ward , basuyi wani tafiya mai nisa ba , a kofar wani d'aki ta tsaya , asaman d'akin an rubuta Ward B3 Room 2, cike da yauki ta juyo ta kalli Sani PA tace "This is the room Sir". Sani PA ne yace "thank you nurse" Cike da salo na jan hankali tace "ur wlcm sir" Ganin bai sake ce mata komai bane yasa Nurse d'in juyawa a sukwane. D'an matsawa baya kad'an PA yayi ya Dan kame alamar girmamawa. A hankali cike da nitsuwa, kamar wanda akayiwa dole ya saka farin hannun sa ya Murda handle d'in kofar d'akin a hankali ya saka kan sa cikin d'akin bakin sa d'auke da sallama kasa kasa kamar wanda baya son yin maganar. Dakin ya kasance mai kyau da tsafta sosai, an kafe shi da lafiyayyun gadon asibiti na zamani, masu ikon daidaita kwanciya da tashi bisa jin daɗin mara lafiya. Bangon dakin an shafe su da light cream colour, yana ba da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga me kallon sa, A gefe guda kuma, akwai window mai feshin gilashi, wacce ke barin hasken rana ya dinga shigowa a hankali. An tanadar da split AC, refrigerator, plasma TV, da kuma kujera mai laushi domin mai jinya da wanda ke kula da ita. A gefen gadonta kuma, akwai small digital monitor wanda ke duba motsin jini da numfashi lokaci-lokaci. Wata mata ce Jikinta na kwance a gadon asibitin, sanye take da riga mai launin fari da alama rigar marassa lafiya ce ta asibitin, fuskar ta kumbure kaɗan, ta rame tayi fayau da ita. Idonta a rufe suke ruf, amma numfashinta na tafiya daidai — alamar cewa jikinta na ƙoƙarin murmurewa, zata iya farkawa ako da yaushe. Anty hauwa ce zaune a gefen gadon, tana riƙe da hannunta, tana shafa fuskarta lokaci-lokaci, tana karanta addu’o’i tana tofa mata, Tunanin irin azabar da yâr uwar ta ta sha yana bayyana a saman fuskarta, amma a lokaci guda, zuciyarta cike da godiya ga Allah cewa ta tsira da rainta. A hankali a ka bud'e kofa , cikin nitsuwa ya shigo, bakin sa d'auke da sallama kasa kasa, Sanye yake da black designer suit, fuskarsa cike da damuwa da gajiya, golding eyes din sa ya zuba mata , Kallon farko da ya yi mata ya ya fahimci cewa bakaramar wahala ta sha ba , ramlart ce yanzu kwance ba hayaniya, ba tsiwa, kamar mai bacci, amma kuma ba barci ba ne mai nutsuwa dagani kasan barcin wahala ne. A hankali Ya matso kusa, ya tsaya, yana kallon ta daga sama har ƙasa. Kamshin turarensa mai tsada ne ya cika ɗakin gaba d'aya. Anty hauwa ta miƙe a hankali, ta d'an basar gaishe sa ta shiga yi, ba yabo ba fallasa haka ya amsa mata, babu wata sakewa a tsakanin su, ganin hakane yasa aunty hauwa ta nufi hanyar fita daga d'akin domin bashi waje ya gana da matar sa, cikin nitsuwa Ya zauna a gefen gadon, ya kama tafin hannunta a hankali, yana shafa shi cikin tausayin ta dana kan sa. Ya lumshe idonsa, ya dafe kansa kaɗan, cikin zuciyar sa yake furta, " “Ya Allah, kai ne Mai kowa da komai... na yarda da ƙaddararKa. Na amince da rabonKa. Amma Ya Allah, sai yaushe? Sai yaushe zan riƙe ɗana a hannuna, in ji kamshin jikinsa, in kalle shi ya kirani ‘abba’? Kullum ina karanta ‘Laqad khalaqnal insana fi ahsani taqwim’... amma me yasa ni kake jarabta na da wannan jinkirin?, ya Allah idan hakan yana da nasaba da kaddarah n da ta fad'amini a shekarun baya , Allah na tuba ya Allah ka yafe mini kurakurai na" Ya runtse idonsa da karfi, yana jin wani irin turirin zafi na fita daga kasan Zuciyar sa, a hankali ya shaki iska mai sanyi, yana jin nauyin hawaye a cikin zuciyarsa amma bai bari suka sauko ba. Zuciyarsa ta ci gaba da kuka cikin tawakkali da nadama, batare da ya bar hakan ya baiyana a saman fiskar sa ba. A hankali idanuwanta suka fara motsi Kamar wacce ta farka daga duhun mafarki, a hankali ta ke bude su ganin bata gani sosai ne ya sa ta d'an lumshe idanun a hankali, ta sake buɗe su a hankali, fitilar dakin ta dinga haskawa a cikin idanun ta, tana dauke mata idanu, don har yanzu dishi dishi take gani. A hankali ta d'ago kanta Tana kallon sama, ba tare da fahimtar inda take ba a farko, zuciyarta na dukan uku uku, sannu a hankali. Ta motsa hannunta kaɗan wan da aka sanya masa drip, sanyi ya ziyarci ilahirin jikinta, gaba d'aya. Sake lumshe idanuwan ta tayi, hancinta na kara shako mata sassanyan kamshin sa da yaza me mata jiki , ako da yaushe takan ji hakan ko da ace kuwa baya kusa da ita ,sake bide idonta tayi, cikin sa'a ya sauka akan fuskar sa dake zaune a gefen gadon, yana dubanta da ido cike da tausayi tare da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa, duddah ba sabon abu bane a wajen ta ta saba ganin sa a cikin irin wannan yanayin musamman a duk lokacin da tasamu misscarage, sai dai kuwa a wannan karon yanayin da tagani a tattare da shi ya sha ban ban da sauran lokutan baya. Idanunsu ne suka haɗu, na shi ya cika da Wani irin yanayi mai wuyar fassarawa tare da damuwa, na ta kuma sun cika da tsoro da ruɗani da kuma fargaba a lokaci d'aya ,Bata iya ce masa komai ba, sai ta ɗan yunkura ta ce "Honey... ina ne nake...? Yaushe ka dawo daga london d'in?" Haka ta jerasa masa tagwayen tambayoyi ajere . A hankali ya riƙe hannunta da ya damke shi da sauri, yana girgiza kai, ya ce cikin muryar da ta ke cike da jarumta da murɗewa yace "Lafiya kike ramlart.. kina lafiya yanzu... ki huta, komai zai dawo daidai in sha Allah." Ya kara sa maganar cikin Wani irin classy husky voice dinsa, yan da kasan ba shi yake maganar ba. Sanin da tayi baya son hayaniya ne yasa Zaman kurame suka shiga yi a tsakanin su, kowa da abun da yake sakawa a cikin zuciyar sa. A hankali aka kwankwasa ƙofar d'akin. "Excuse me, sir," wata nurse mai sanye da uniform mai tsafta da badge ta shigo da takarda a hannunta. Ko dago kai da baiyi ba bare asaka ran zai amsa mata, sanin waye ne shidin ya saka ramlart dake konce cewa "Yes, nurse?" ƙarasowa tayi cikin girmamawa, ta fara duba ramlart d'in, tana ya'n rubuce-rubucen ta a takardar chart ɗin jikinta, sai da tagama duka sannan ta juyo da murya mai yauƙi tace: "Sir, I just came to check on madam. Her vitals are stable for now, and she’s responding well to the IV." gyada mata kai yayi, yana fitar da numfashi a hankali. Ganin ya kulata ne yasa Sai ta ƙara langwabe murya tace: "Also, Dr. Farida — the OB-GYN (obstetrics & gynaecology) in charge — asked me to inform you that she would like to see you in her office as soon as you're able. She said it’s important, but no need to panic." Idon sa ya ƙanƙance kaɗan, ya gyada kai a hankali, harta cire ran zai mata magana kamar daga sama taji husky voice dinsa yace "Thank you, nurse. I’ll be there shortly." Da sauri nurse din ta kalle sa sai dai ganin kamar ba shine yayi maganar ba yasa ta kama kanta, duddah yan da take jin muryan yana kara yimata gezo a cikin kwanyar kanta. D'an murmusawa tayi cike da girmamawa, ta juya ta fita cikin yanga da yauki. Kallon ramlart da ke kwance, yayi, a hankali ya miƙe , cikin zuciyar sa yake magana : "In sha Allah, komai zai daidaita..." Ganin kamar bacci ne ya d'auke ta ya sa Ya fice daga ɗakin cikin natsuwa da izzah, a bakin kofar ɗakin ya samu Sani PA a tsaye, sabanin aunty hauwa dake zaune akan d'aya daga cikin kujerun da aka kawata wajen dasu, baice musu uffan ba yanufi hanyar zuwa ofishin Dr. Farida in da yaga nurse din tayi , Sani PA ne ya take masa baya, hannun sa rike da jakar laptop din sa. Aunty hauwa kam tabe baki tayi, tare dacewa "İkon Allah ayi mutum da shigen miskilanci da fad'in rai Allah dai ya yaye maka" Takara sa maganar tare da tura kofar dakin ta shiga ciki. Jin muryan Aunty hauwa ne yasa ramlart ta bud'e idanun ta ,da ma chan bawani bacci da ya kwashe ta , kawai dai tarasa me yake mata dad'i ne jin cewa doctorn tana neman sa, fatan ta dai Allah ya sa kar asirin ta ya tonu. Cikin takun sa na gwarazan maza ya ke bin bayan Nurse din , dake ta yauƙi a gaban sa . Wan da a wajen sa ma bai san tanayi ba dan ko daga kansa ya kalleta baiyi ba ko sau daya, inda kafar sa ta ke taka wa kawai yake kallo. D'an tsayawa tayi tare da pointing wani bakin Office da aka rubutu "Dr. Aishatu Abubakar Modibbo, MBBS, FWACS" *Consultant Obstetrician & Gynecologist* *Specialist in Women’s Health, Pregnancy & Fertility Care* Juyawa nurse din tayi, tanufi reception. Ofishin Dr. Farida, yana cikin sashen OB-GYN, babban ofishi ne mai tsafta da sauƙin kallo. A gefe akwai ɗan teburin karatu, da takardun kiwon lafiya an ɗora su a jere. Zaune take akan kujeran ta na office din Fuskarta a lumshe, tana kallon wani chart na sakamakon gwaji. Tana sanye da jamfa na wani material fari mai ratsin purple d'in flowers a jiki, farar lab coat mai dauke da tambarin sunan ta daga sama wanda aka rubuta Dr.AA modibbo da manyan Baki a jiki, hijabinta neatly tucked, babu rini — alamar mace mai natsuwa da tsoron Allah,duk sun baiyana a gareta akallah zata kai shekara 35yrs , i danun ta sanye suke a cikin farin glashi da alama Medicated ne, kallo daya zakayiwa fuskar ta kasan cewa Allah ya zuba halitta a wajen da alama tana da halittan gashi dan ga alamar shi nan ya nuna a saman goshin ta duddah ta sanya hula da hijab hakan bai hana shi baiyana kan sa ba, tana da cikar gira ,bakake ne irin sosai dinnan, sannan bakin ta yana dauke da pinkish red in color, labbanta suna da d'an kauri kadan, tana da manyan idanuwa masu d'auke da ayes lashis masu dan tsayi, san idanun sun kasan ce lulu ayes ne, duddah a zaune take hakan bai hana baiya nar yanayin halittar jikin ta ba, tana da d'an kiba kad'an amma ba sosai har chan ba, da alama tana da d'an tsayin ta dai dai misali don ba za'a kira ta da gajera ba, fatan jikin ta tsaka takiya ne dan baza'a ce mata fara sol ba sannan kuma baza a kirata da chocolate colour ba, da ganin fatan kasan yana samun kulawa ta musamman hakan ne ma ya sa kalan skin d'in ta ya fita so special dan da wuya kaga mutum mai irin skin d'in ta. Jin an kwankwasa ƙofar ba tare da ta d'ago kanta ba cikin nitsuwa tace "Come in," . Cikin izzah da kasaita wanda suka bi jinin jikin shi batare da shi kan shi yasan da hakan ba ya shigo, sanye da black suit d'in sa mai kyau da ɗan ƙyalli, fuskarsa tamke tamau kamar wanda bai taba dariya ba, dan lumshe idanun sa yayi jin yan da ya shaki daddadan kamshin dake cikin office din, wannan karon ma shi kad'ai ne ya shigo , da alama PA yana jiran sa a waje, Hannunsa yana riƙe da agogon hannu, na Rolex alamar yana cikin sauri ya kosa ya cire kayan. Jin shiru ne ya sa ,Dr. Farida ta tashi daga kujerarta cikin ladabi da nitsuwa ba tare da ta dago ta kalle sa ba tace "Good afternoon, Mr. Turaki," ta ce da muryan ta mai laushi, da sanyi, d'an miƙa hannun ta tayi ta na nuna masa kujerar dake gaban nata, in da ta ke ajiye mutane idan sun zo ganin ta. Tariga da tasan shine mijin matar da akayiwa wankin ciki d'azu bayan tasamu misscarage, d'an Nurse ta kirata daga reception ta sanar da ita iso war sa dan haka bata bukatar bayani. "Good afternoon, Doctor,"ya amsa, cikin Wani kamilalliyar mirya, a lokaci guda kuma yana zama a kan kujeran da ta nuna masa ,cikin kwanciyar hankali. A nitse ta zauna, ta ɗan duba takardan dake gaban ta kafin ta ce: “Mr. Turaki, I’ll go straight to the point. Your wife’s miscarriage… wasn’t spontaneous.” AA Turaki ya ɗaga gira, cike da mamaki da ɗan razana. “I’m listening,” ya ce, yana ƙara maida hankalin sa gare ta . Dr. Farida ta nisa a hankali tace: A“Lab results and examination show clear signs of chemical induction. A drug — most likely misoprostol — was used recently. But that’s not all. The damage done to her uterine lining suggests that… this isn’t the first time.” Kamar ba zai iya magana ba, wani irin zafi da zogi yaji zuciyar sa tana masa,karon farko da ya d'ago kan sa gaba daya ya zuba mata ido, wani irin faduwar gaba ce ta riske shi a lokacin da ya Kalli fiskarta, Wani irin yanayi da ya shiga a da Chan baya ya na sake dawo masa, jin kansa ya sara masa da mugun karfi ne yasa shi rintse idanun sa da mugun karfi, tunowa da yayi a inda yake ya sa shi a ro jarumta ya dake, tare da bud'e idanun sa da suka gama rinewa, daga fari zuwa launin ja, sabi da bakin cikin abun da kunnuwan sa sukeji masa, jikinsa a sanyaye, idanuwansa suna cike da rashin fahimta, cikin kamilar muryan shi yace “Are you saying she intentionally…?” Dr. Farida ta ɗaga hannu cikin kwantar da hankali tace “I’m not accusing her. But medically, what I’m saying is… her womb is no longer as strong as it used to be. If care isn’t taken, she may never conceive again naturally.” Wani irin sanyi da nauyin damuwa ya sauka a zuciyar sa, sunkuyar da kan sa kasa yayi, zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, tamkar ana tsaga masa kirji ji yake yi kamar ciwon sa na barazanar tashi . “Why… why would she do that?” Ya furta ƙasa-ƙasa batare da sanin cewa maganar ta fito waje ba. Dr. Farida ne ta ce : “There could be a thousand reasons. Fear. Pressure. Regret. But for now, she needs healing — physically, emotionally, and spiritually. And she needs you more than ever.” Turaki ya dafe kansa, numfashinsa ya yi nauyi. a hankali yace: “So… there’s no hope?” Dr. Farida ta kalli sa kai tsaye: “I didn’t say that. There are assisted options. But it will take time, patience, and strong commitment. From both of you.” Ya lumshe idanu, sannan ya ce: “Thank you, Doctor… for your honesty.” Dr. Farida ta gyada kai tace: “It’s painful, but you deserved to know the truth. I’ll be here to guide you both… medically and emotionally.” Ya miƙe, jiki ba ƙwari, amma yana jin wata irin kauna da rauni da su ka haɗu a zuciyarsa, Allah ya gani yana son ya'ya duddah ba auren soyayyah sukayi da ramlart ba ya so ace ta haifa masa yara, saidai kash wani gurbaceccen tunanin ta ya ja ta aikata aikin da zatayi nadama a karshe, cikin karfin hali Ya fice a hankali, zuciyarsa na neman amsoshi fiye da wan da likita ta bashi. Ganin irin halin da Ogan nashi ya fito ne yasa ka PA take masa baya cikin hanzari, ganin yanda yake tafiya a gaggau ce ganin ya nufi hanyar fita daga Ward din ne yasa, tun kafin isowar su PA ya sanar da bodyguard din da su kasance cikin shiri, hakan ce kuwa tafaru suna fita aka bude masa mota ya shiga, jin ya zauna a kan sit din motar ne ya sa ya lumshe kyawawan idanun shi , a hankali yake sauke ajiyan zuciya, sunan Allah kawai ya ke iya ambata a kasan zuciyar sa, jin motocin sun fara tafiya ne ya sa ya d'an gyara zaman sa, Wani irin matsanan cin ciwon kai yake ji, ga gajiyar tafiya da ya kwaso, abun duk ya hade masa . A bangaren ramlart kuwa tun tana saka ran dawowan mijin nata har ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Zuwa yanzu Zuciyar ta tashiga tashin hankali da firgici wanda ita kanta ba ta san adadin shi ba, ganin bini bini tana kallon bakin kofa ne yasa aunty hauwa tace "lafiyan ki kuwa ramlart" ganin kar anty hauwa ta rafko jirgin ta ne yasa tace "lafiya qlu anty" daga haka bata sake ce mata komai ba , sai ma zame wa da tayi ta kwanta a bisa gadon jinyar tata tare da lumshe idanun ta kamar mai bacci. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 2️⃣ Yayin da motoci suka shigo babban katafaren gidan AA Turaki a Maitama Abuja, wata ƙofar ƙarfe mai ƙyalli ta buɗe da kanta ta hanyar automatic. Wani irin babban mansion ne, na zamani amma an kawata shi da hadin kayan gargajiya da na zamani, hakan sai yasa ya zama na musamman zaka jima baka ga mansion irin sa ba . Gininsa gwanin ban sha’awa ne, wanda ya sha gyare-gyare daga lokacin da ya gina shi , kasan cewar bai manta asalin sa bane yasa ya zaɓi kawata gidan nasa da Kayan gargajiya game da na zamani. Akwai fitulun wuta masu ba da sanyi da wani haske na Musamman ,a gefen titin cikin gidan, ga wasu flowers da tsire-tsire masu fidda ƙamshi na Musamman ,. Motar sa limosine da ya ke ciki ne ta tsaya a gaban babban foyer, bodyguards dinsa, guda biyu suka buɗe masa ƙofa, yayin da ya bar sauran bodyguard din sa a chan parking space dake haraban gidan. A hankali ya fito, fuskarsa cike da natsuwa amma idanuwansa na bayyanar da damuwa, Tattare da gajiya da ɗan ɓacin rai, yana sanye da suits mai tsada, amma haryanzu babu walwala akan fiskar sa, fuska tana ɗaure tamau kamar wan da bai taba dariya ba, a hankali ya ja wani irin numfashi mai sanyi, cikin nitsuwa ya fara takawa cikin main parlourn gidan ya nufa, da sallama d'auke a bakin sa ya shiga cikin parlourn sai dai kamar ko yaushe idan yayi sallamar bai zama lallai mutum ya ji sa ba. Wata mace ce mai kusan shekaru 60, kyakkyawar, gaske doguwa, mai launin fata fara sol, irin mai sanyi da kyan ido irin na Fulani usuli. Sanye take da atamfa mai Holland da gyale wan da ta lulluɓe saman kanta da shi, kana ganin ta kaga jin dadi a tare da ita. Tana zaune a kan farfajiyar da ke kusa da living room, kallo d'aya zaka mata kasan cewa akoi wani abu mai muhimmanci da take jira. Ganin wanda ya shigo ne ya sa ta fad'a'da murmushin ta. "Yeroh !"Ta ce da murmushi mai sanyi akan fuskar ta, a lokaci guda kuma ta tashi tsaye tana mai cewa, "Lale marhaban da dawowa daga London." Cike da d'an sassarfa Ya ƙaraso ya durƙusa a gabanta ya na mai riƙe hannunta, a lokaci guda , ya sunkuyar da kansa kasa. Ganin irin halin da tagan sa a ciki ne ya sa ta kara zuba masa ido, kallon sa tayi na Yan mintuna, Tuni ta fahimci baya cikin walwala, duddah hakan ba wani sabon abuba ne a gare ta amma sai take ganin kamar na yau din ya sha banban dana sauran lokutan. Cike da na tsuwa tace "Alhaji ya ce mini ka biya ta a sibiti , to Yaya jikin ramlatun, ? Yanzu ace muna gida d'aya ramlatu ta kasa fad'a mana cewa bata da lafiya, sai dai kawai Muji cewa tana asibiti." Dago kansa yayi daya ke jin ya bala'in yimasa nauyi, kallon mahaifiyarsa,ya yi a hankali ya ɗan sauke numfashi. "Mun same ku lpy? Shine abun da yafara fad'a , kafin ya sake cewa jikin ta da sauƙi, amma..." Sai kuma d'an tsaya, yana juyar da kan sa gefe guda, yana ƙoƙarin ɓoye hawayen da suka cika idanunsa, baya son Hajja ta gansa a irin wannan yanayin . A hankali Hajja tace: "Yeroh ..!Na san murmushinka haka zalika nasan kukan ka, sabi da haka" ko fe'ihh" Me ya faru?" Ta karasa maganar cikin harshen fulatanci. muryarsa a rauna ne, yana jin zuciyarsa kamar an tsinke ta, kamar zata faso ƙirjin sa ta fito waje. "Abu ne mai nauyi, Hajja Wani abu ya faru da bazan iya furta shi cikin sauƙi ba..." A dai dai lokacin ne Alhaji Abdullahi Turaki, mahaifin sa, ya shigo daga sashen karatu, na cikin gidan. Alhaji Turaki dattijo ne mai kusan 70yrs, dogo, ne fari, fuskar sa a cike da nutsuwa da dottaku, cikin nitsuwa Ya zauna yana kallon ɗansa d'aya tilo cike da kulawa. " A duk in da namiji yake an san shi da gwagwarmaya da kuma jure ƙaddarah, don haka baka da wan da zaka fad'a wa matsalar ka bayan nida mahaifiyar ka, sabi da duk wani abu da ya same ka ba kai kaɗai, ya shafa ba har da mu" Alhaji Abdullahi ya kara sa maganar tasa cike da hikima da son karantar yanayin d'an nasu. Wani irin yawu ya haɗiye masu dacin gaske, kamar wanda akayi wa dole ya ce: "Doctor tace... Ramlart na iya rasa damar sake haihuwa gaba ɗaya, Kuma... wannan ba shine karo na farko da ta yi amfani da abortion pills ba." Wani irin shiru ce ta ratsa tsakiyar family lounge, din, Hajja ce ta saki ajiyar zuciya, a hankali ta koma dabaya ta zauna deb'es a kan lallausan sofa, hawaye na kokarin cika idonta, wani irin tausayin ɗanta da halin da suka tsinci kansu a ciki shekarun baya ya dawo mata sabo fill a zuciyar ta ji takeyi kamar ma yanzu ne abun yake faruwa da su. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un..." Shine kawai abun da bakin ta ya iya furtawa. Alhaji Abdullahi Turaki ne ya girgiza kai, fiskar sa dauke da tausayi yace "Zamuyi magana da ita, in ta samu lafiya Amma ina son kai ka kwantar da hankalinka, Aliyu Allah yana jarabtar bayinsa masu imani." A hankali ya miƙe yana kallon su, yana jin yadda zuciyarsa ke cike da ƙunci amma yana samun sauƙi da d'an sassauci da ganin irin kulawarsu, a gare shi. “ cikin sarkewar murya yace Zan shiga ɗaki inyi sallah, ina so in huta .” daga haka bai sake cewa komai ba ya juya cike da sassarfa yana jin kamar gangan jikin nasa zata gaza daukar sa. A haka Ya nufi ɗakin sa mai kama da suite dake bisa babban bene na gidan wanda a cikin sa ya ke tattare da komai na more rayuwar duniya, office, library, da bedroom mai kyau kamar na hotel, kitchen da toilet. Zuciyarsa cike ta ke da damuwa… amma a ƙarƙashin zuciyar sa, akwai wani sabon damuwa da yake ji tunani yake akan maganar da Dr. Farida ta fad'a masa. Bayan ya shige ciki, parlourn ya rage saura Hajja da Alhaji , shiru mai nauyi ne ya wanzu a cikin babban falon gidan. Kowa na cikin tunani, kowa da abun da zuciyar sa take saka masa. fuskar Hajja ta fara baiyana fargaba da shakku, a hankali Ta ɗago idonta, ta kalli mijinta da yanayin da ya jima rabon da yagan ta a cikin sa a tare da ita , cike da fargaba da jin tsoro tace "Alhaji… Ina jin tsoro. Tsoron gaskiya. Kar dai ace… kar dai ace wannan kaddarar da muke gujewa shekaru fiye da ashirin ne ke neman biyo mu." Cike da mamaki Alhaji yake kallonta cikin tashin hankali yace: "Kaddara kuma? Habiba me kike nufi?" Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, mai nauyi: "Shekaru ashirin da ɗaya kenan da muke kok'arin ɓoye sirrin nan, Ka manta da abinda muka tafka? Wane hukunci muka tsallake mu ka gudu sabi da kunyar duniya? Yau ga ɗanmu , shekara biyar kenan da auren sa da Ramlartu… amma babu ɗa, babu diya, Yanzu kuma ga wata magana wai maganin zubar da ciki take sha ? Astaghfirullah! Wannan ai ba al’ada bace mai kyau." A hankali ta girgiza kai , idanun ta cike da hawaye tace "Na san yaron nan bai ya son wannan auren , Bai taɓa soyayya da ita ba, Ka duba yadda damuwa ke bayyanuwa a fuskar sa, a mai makon ya samu nitsuwa da farin ciki. Biyayya ce kawai ta sa ya auri Ramlart, Bai dade da dawowa daga asibiti ba, yanzu, amma kallon sa da nayi ya bayyana yanda zuciyarsa ke cikin rauni, da tashin hankali ko da kuwa bai furta hakan da bakin sa ba ni mahaifiyar sa ce ina iya fahimtar sa koda kuwa baice komai ba". A hankali Ta share kwalla da gefen mayafinta. "Duk da cewa ya a zabtu a baya kuma ya jure, amma na tabbata yana cikin azabar rashin haihuwa, a halin yanzu." Cikin hanzari Alhaji ya miƙe damuwa na sake baiyana a saman fiskan shi, yace: "Kull kull kull, Habiba! Nace maki kar na kara jin wannan zancen. Kaddara? Me yasa kike kokarin tona abin da muka rufe da addu'a a tsawon shekaru? Wannan irin maganar taki ne kike so ya jawo mana matsala, gaskiya?" Saba babban rigan sa yayi da sauri Yana tafiya a cikin falon, ya Dan tsaya yana kallonta da fushi amma cike da d'an rudani yace "Mu da muka rasa mafita sai muka yanke hukunci mai nauyi, yanzu kina kokarin dawo da tunanin da muka binne da hawaye? Wallahi bana son jin wannan zancen a cikin gidan nan!". Ya Dan numfasa da ƙyar, yana ƙoƙarin kwantar da zuciyarsa, yace "Wannan fa yaro ne da nake alfahari da shi, mai hankali da mutunci, karki manta yana da kima da da raja a idon duniya, Sai mu ɓata masa goben sa saboda abinda muke ɓoyewa a baya? Wallahi Habiba, ki dakata da wannan shirmen na kin." cikin murya mai rauni Hajja tace: "Toh me kake so na yi? Zuciyata cike take da tsoro… kai ka kalle shi, yaushe rabon da na ga ɗana yana dariya da walwala na gaske? Me zai hana na firgita, Abdullahi?" Ta karasa maganar tare da kiran sa da asalin sunan sa . Shiru ya sake cika dakin, na yan mintuna. Alhaji ne ya share gumin da ke kansa da hannunsa, a lokaci guda ya kalli matarsa cikin kallo mai zurfi,da nazari, amma bai ce mata komai ba, Sai ya juya a hankali, yana tafiya zuwa dakinsa, zuciyar sa cike fall da damuwa. Ba zato ba tsammani taji saukar Muryar sa. "Ki ci gaba da addu’a, Habiba, Wannan kadai ce mafita da muke da ita a halin yanzu." Yana gama fada'r haka Ya fice ya bar ta a falon, tana kallon bayansa, a hankali ta runtse idonta , hawaye na rige rigen gangaro wa a saman fiskan ta. A cikin katafaren dakinsa mai fadi da tsari, a hankali ya shigo , fuskarsa cike da damuwa, da nauyin abinda Dr. Farida ta sanar masa. Dakin nasa na alfarma ne, wanda yasamu gidauniyar ginin zamani, mai tsarin luxury design, tiles d'in dakin masu haske ne ,gadon nasa King-size ne, mai dauke da gadon fata da lallausan katifa , TV screen mai fadi,manne a bango, fitilun da ke fitar da haske mai launin fari da light blue ga kuma zane-zanen classic art manne a bangon dakin. Aword da abubuwan kyauta daga kasashen waje suna shimfide akan wasu shelf na ado . A gefe kuma akwai wardrobe din zamani wan da ake bude ta da fasahar "fingerprint". Cikin nitsuwa ya tsaya a gaban madubi, yana kallon fuskar sa dake nuna alamun gajiya, damuwa, da tsantsar karfin zuciya, a hankali Ya dafe kansa kadan, sannan ya fara tafiya toilet ya shiga domin yayi wanka. Wankan sa ya yi da ruwa mai dumi, da sabulun sa mai kamshi wanda yake odern sa daga Qatar, sannan ya fito yana sanye da farar doguwar rigar sleeping gown mai laushi, da santsi. Bayan ya fito, ya shimfida dadduma a wani sashe na dakin da aka ware don sallah, Ya rama sallolin da suka wuce shi, ya karanta addu'oin sa cikin kwanciyar hankali, Bayan kammalawa, ne ya zauna na dan lokaci cikin shiru mai karfi, yana tunanin abinda ya faru d'azu a asibiti. Zuciyarsa ce ta buga sau daya da karfi, Ya jingina da bango, sannan na dan Wani lokaci a hankali ya mike da d'an sassarfa ya nufi wata madai dai ciyar drawer da aka kulle da key, ya bude ya dauko Wani d'an kwandon da ke d'auke da kwalabe, na magunguna, a ciki ya zabi daya sannan ya sha, yana kallon maganin kamar wan da yake son tambaya: "Shin yaushe zan daina shan wannan magungunan ne?". Ya tambayi kansa. Bayan ya sha maganin, hayewa yayi kan gadonsa mai laushi, gadon da aka lullube da farin duvet mai dumi sosai, da kamshi na musamman. Cikin nitsuwa Yayi kwanciyar shi yana kallon silin d'in dakin, idanunsa na cike da hasken da ke kunshe da zafi da tarihi na shekarun baya. Kafin ya ankara, wani bacci mai nauyi ya dauke shi, sabi da maganin da yasha ma yana saka bacci, ga gajiya da ya taru masa. Nan take ya lula duniyar mafarki in da ya dauke shi, zuwa shekaru 21 da suka wuce lokacin kuruciyarsa, abubuwan da ya tsananta yarda cewa ya riga ya manta da su, ya gama shafe su a babin rayuwar sa sai ga shi a kullum in ya kwanta bacci sai sun dawo masa a mafarki. 💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 3️⃣ Aliyu Abdullahi Turaki shi ne cikakken sunansa wan da akeyi wa lakabi da AA Turaki, in da mahaifiyar sa kuma take kiran sa da suna "Yero" kasancewar sa d'an fari a gunta kuma da d'aya tiloh a gurin su, Alhaji Abdullahi Turaki bafulatani ne daga rugagen Gembu, cikin tsaunukan Mambila Plateau, wanda ya tashi cikin arziki na noma da kiwo asalin Mahaifinsa makiyayi ne mai daraja, amma daidai gwargwado ,mutumin kirki, ne amma babu isasshen ilimi, sai tarbiyya da gaskiya a wanchan lokacin. Aliyu tun yana yaro, yana da hangen nesa da kwadayin canza rayuwarsa da ta iyayen sa, Duk da halin rashin wada ceccen ilimi da suke ciki a yankin su, haka ya dage da karatu yana tafiya makarantarsu mai nisan gaske daga gida, a koda yaushe, kafin wata ƙaddarah ta gifta musu, su ka baro ainihin yankin su sukayi hijira zuwa garin kano, anan garin kano ne Aliyu yaci gaba da karatun sa na secondary bayan doguwar jinya da sha fama da ita wanda iyayen sa suka cire rai da tashin sa cikin ikon Allah da karfin addu'ar su Allah ya sake daga kafad'un sa sai dai ya kamu da ciwon zuciya da ake kira da mild heart condition, saka makon damuwa da ba'cin rai da ya shiga a baya. Bayan ya kammala karatun secondary school, da sakamako mai kyau, ya fito sabi da kwazon sa, a haka ya samu ya jona jami'ar Ahmadu Bello University , in da ya karanci business administration, bayan ya kammala ne ya fito da result in da ya zama first class ya samu scholarship daga wata NGO, Bayan ya gama digirin sa na farko, ya samu damar zuwa UK inda ya yi Master’s a fannin International Business Management a London School of Economics, bayan nan ne ya jona degree din sa na uku a UK wato Phd , bayan haka ya karbi horo na musamman daga Executive Education domin kara kwarewa a harkar jagorahn ci da nazarin kasuwan ci, Daga nan ne rayuwa ta fara sauyawa, inda yafara halartar tarurruka na musamman kamar su , project management profession, Business networking, digital marketing da sauran su. Yana da kwarewa, hikima, da iya sadarwa da kowa, hakan yasa bayan ya dawo Najeriya, ya kafa kamfanin farko mai suna Turaki Global Ventures, wanda ya fara da kasuwancin shigo da kayayyaki daga kasar China da Turkey. Zuwa cikin shekaru 10, AA Turaki ya zamo jigo a harkar kasuwanci a Afrika. Yana da manyan kamfanoni a fannoni da dama kamar su: - Turaki Holdings Ltd – kamfani na kudi da hannayen jari - Turaki Oil & Gas – yana da rijiyoyin man fetur a Najeriya da Angola *Turaki Real Estate – gini da mallakar manyan gine-gine a Dubai, Abuja, Accra, da Istanbul - Turaki Agro & Food Ltd – kamfani mai sarrafa kayan gona da fitarwa zuwa waje - Turaki Airlines (JV project)– wani kamfani da ke tattaunawa da gwamnatin kasar Qatar akan kafa jirgin sama Duniya ta sanshi a matsayin "Africa's Silent Billionaire", saboda hankali da natsuwarsa, baya shiga barkwanci da fallasa sirrin rayuwar shi. Hukumar Najeriya (Federal Government),ta ba shi lambar girmamawa, saboda gudunmawarsa ga ci gaban tattalin arziki, har ta zuba hannun jari a daya daga cikin kamfanoninsa na makamashi da man fetur. Kasashe kamar UAE, Turkey, UK, China, Qatar, da Saudi Arabia suna da hannun jari a kamfanoninsa – sannan ya kasance memba ne a International Business Council. Tattaunawarsa da kasashen duniya kan batutuwan kasuwanci da cigaban Afirka sun sa ana kiransa "Voice of Emerging African Capitalists". 5 YEARS BACK... A lokacin da harkokin sa su ka kan kama ,zuwa wannan lokacin AA Turaki ya zama babban business tycoon a Africa baki daya, zuwa lokacin ya tattara iyayen sa sun koma Abuja da zama, duddah shi kan sa bai cika zama a Nigeria ba. Hajiya Habiba wacce yake kira da Hajja tana zaune a kan kujera mai lallausan fata, a hankali ta gyara mayafinta . Aliyu Turaki ne zaune a gaban ta ya na zaune cikin natsuwa, yana sauraron mahaifiyarsa. da murmushi Hajja tace "Yeroh yau kimanin shekara talatin da biyar fa kayi... Ba aure lokaci yayi da zaka samu mace mai tarbiyya da zaka kira taka. Ga Ramlartu nan ’yar kawata ce, naga halinta tun tana da hankali naya ba da halinta. Yarinya ce mai ladabi da hankali. Kuma ta na girmama ka sosai, uwa uba kuma tana mutuwar son ka." Cikin nitsuwa Aliyu ya dago kai kadan, ya kalli mahaifiyarsa, sai ya sauke ajiyar wata nannauyan ajiyar zuciya. "Ina jin ki Hajja, Idan kina ganin hakan shine mafi alheri, a gareni na yarda da zabin ki." "Ya amince da auren ba tare da soyayya ba... saboda biyayya da girmama mahaifiyarsa. Auren da aka daura cikin girma da kima amma zuciyar sa ba ta tare da auren, sabo gan gan jikin sa ne kawai a auren." Haka ya ke zaman aure da ramlart duddah baya son ta amma bai taba yi mata wulakancin akan hakan ba , sai dai ita kanta ta san zuciyar Aliyu Turaki ba mallakin ta bace. *********** CİGABAN LABARİ GWARİNPA ESTATE. Anguwar tana cikin wurare ne da gwamnati ke ware wa manyan ma’aikata. Unguwa ce mai tsari, tsafta da tsaro. Gidan da Dr. Farida ke zaune da mahaifiyarta da ɗanta yana cikin layi mai natsuwa Da babu hayaniya, a kusa da babban titin Estate din. Kamar kullum, Dr. Farida ta iso gidan da motar ta Toyota Corolla 2021 – metallic grey, motar da asibitin National Hospital Abuja ya tanada mata a matsayin wani daga cikin fa’idar matsayinta a asibitin. Motar ta tsaya a gaban gate din gidan, Gate man ne ya ruga da gudu ya bude, ganin motar ta ne yasa shi washe baki tare da gaishe ta yace "Welcome madam!" tana amsawa da murmushi d'auke akan fiskar ta, kutsa motar tata tayi cike da nitsuwa take tukin, d'an madai daicin parking space din dake cikin gidan ta nufa , parkin tayi tare da tattaro jakan Office din ta ta fito, had'e da rufo kofar motar, main parlourn ta nufa. Cikin gidan, akwai kyakkyawan bungalow mai bene guda Daya, an tsara shi cikin salo irin na zamani, Gidan yana da veranda wan da aka kawata da furanni masu dad'n kamshi, a gefe guda akoi kujerun hutawa. A cikin parlorn kuwa komai yana nan tsaf tsaff da shi ga kyawawan labulaye, kayan dakin masu simple ne babu hayaniya amma masu tsada,ne ga wani kamshi na turaren wuta da yake tashi, mai sanyaya zuciya. A cikin gidan, tana tare da mahaifiyarta Hajiya Zainab wacce take kira da Dada dattijuwar mace mai launin fata, mai dan haske amma ba sosai chan ba, tana da kamun kai da halin kirki, da ɗanta Ameer kyakkyawan saurayi mai shekaru 14, fari ne sol, yana dauke da idanu masu kama da na uwarsa Dr farida. Dr. Farida ne ta shigo cikin gidan cikin nutsuwa, tana sanye da kayan aikin ta, a hankali ta jingina da ƙofar parlor, tana kallon ɗanta, Ameer mai shekaru 14, kyakkyawan yaro ne da ya jima yana bin sahun mahaifiyar sa. Yana da fata mai haske da laushi, fuskar sa na d'auke da annuri da manyan idanu irin na mahaifiyarsa, A lokacin yana zaune kan kujera yana karanta wani littafin sa na school wanda aka basu homework. "Ummi welcome!" Ameer ya miƙe da sauri ya na mai rungume mahaifiyartasa. Ba shiri Dr Farida ta saki murmushi, tare da cewa “Nagode masoyina, ka kammala karatun ka kenan?” Mahaifiyarta, Dada ce , ta fito daga ɗakin girki rike da flask, a hannun ta. fuskan dattijuwar na d'auke da nutsuwa da hikima. “Farida, sannu da dawowa, lale maraba , da gani Kin gaji da aiki?” ta karasa maganar tare da zuba mata idanun ta. “ cike da nitsuwa tace Eh Dada, wallahi yau rana ce mai nauyi a gare ni yau na duba petient da yawa,” Farida ta ce yayin da take kokarin cire hijabin ta a lokaci guda tana kaiwa kan kujeran dake cikin parlorn. Dada ce ta ajiye flask din a kan table, ta zauna kusa da ita, tana kallon ta cike da tausayin rayuwar yâr tata dake cike da jarrabawa da kaddarah. “Farida,” dada ta fad'a cikin tausasawa, “Na san rayuwar ki ba abu bane mai sauki , Kin jure abubuwa da dama, amma Allah zai saka miki, ki Duba Ameer, ya girma cikin tarbiyyar da kika bashi , hakika ke din kin cika mai juriya.” A hankali Dr Farida ta juyo, idonta ya gama cika da ƙwalla amma bata bari ta zubar da su ba. “Dada, kin yi ƙoƙari, a rayuwar mu, Ban taba jin nauyin rayuwa irin yau ba, Amma na godewa Allah da ya bani ke a matsayin ki na mahaifiya ta.” Ameer ne ya matso kusa, da ita ya dafa kafaɗar ta, yace. “Ummi, I’m proud of you.” Mee too shine abunda ta iya fad'a masa tare da sake rungume shi tana mai sauke ajiyar zuciya. Duk da cunkoson aiki da raɗaɗin abubuwan da suka gabata, arayuwar ta Dr Farida tana jin kwanciyar hankali a cikin wannan ƙaramin gidan nata tare da yaron ta da kuma mahaifiyar ta da ke ci gaba da ba ta ƙarfin guiwa akan rayuwa. Dr. Farida ta daga kafarta a hankali ta mike inda take zaune a falon su, tana na mai kallon Ameer ,fuskar ta cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, Tana murmushi kadan yayin da take duba lokaci a agogon bango. Cikin natsuwa da tsafta irin ta likita mai kamala, ta mike tsaye tare da cewa. "Dada Zan shiga na kimtsa jikina," ta karasa fada cikin d'an fara'a, tana kallon mahaifiyarta da dan nata. Cikin nitsuwa Ta nufi dakin ta, tana taka tiles din fale-falen, kamar wacce bata son taka kasa kan bene masu sheki da kyan gani, ta nufa . Dakin nata dan madai dai ci ne da ya cika da tsari da tsafta an kawata shi da kyawawan labulaye masu launin shudi da beige. Gado ne mai dan faɗi, ya na lullube da farin bedsheet mai laushi da tawul dinta nade a gefen pillow. A jikin bango kuwa akwai mirror mai fadi, wardrobe mai launin itace, da shelf ɗin da aka jerawa kayayyakin kula da fata da perfumes masu ƙamshin, gaske . Cike da nitsuwa Ta shige bathroom nata, wanda ke hade da dakin. Tana shiga ta kunna ruwan zafi ta dan surka dana sanyi yanda zai yimata dad'in amfani, ta shiga wanka tana jin sanyi da d'an nutsuwa a zuciyarta. Bayan ta fito, ta shirya cikin kayan shan iska marassa nauyi masu shegen kyau, ta sanya turare wanda ya lullube dakin gaba d'aya da ƙamshi mai shegen dadi. A mai makon ta zauna ta huta sai ma Ta sake fitowa zuwa falon su, inda mahaifiyarta dada ke dora abinci a kan dining table. Yayin da Ameer na gefe yana ta buga game a waya yana dariya shi kad'ai. A hankali Dr. Farida ta zauna a gefen su cikin jin daɗin kasancewa da iyalanta. Ta dora hannunta a kafaɗar ɗanta tana kallon Dada dake kok'arin saving d'in su abinci tace. "Allah ya bar min ku, Dada na, na gode da zama ginshikin farin cikin Rayuwa ta." Cike da kulawa Dada ta d'an girgiza kanta tare da cewa. "Allah ya barmu da kaunar juna ungo maza karb'a kifara cin abincin kar ya huce" Haka ta gama saving din su gaba d'aya wajen ne ya d'auki shiru kowa ya maida hankali akan cin abincin sa dama haka al adar su take in amfara cin abinci to fa ba a magana sai an kammala. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 4️⃣ Ranar Wednesday da safiya, hasken rana ya ratsa tagar dakin da Ramlart ke ciki a Obstetrics and Gynaecology Department. Tana kwance kan gado cikin wani irin shiru mai nauyi, Idonta a rufe, suke ruff kamar mai bacci ,amma tunaninta yana yawo kamar iska mara iyaka, Kusan kwana biyu kenan da AA Turaki ya zo duba ta tun wanchan ranar bai sake leƙo asibitin ba, bashi ba alamar sa, Ba saƙo, ba waya, ko da kuwa takira wayar sa baya shiga, Cikin zuciyarta tana yunkurin kwantar da hankalinta, amma rudani da tsoro sun cika ta. Anty Hauwa ce ta zauna a gefenta tana karanta addu’oin azkar cikin nutsuwa, Ramlart ta juyar da kanta gefe kamar mai jin barci, tana ƙoƙarin boye damuwarta, sabi da bata son Aunty hauwa ta fahim ta, Amma chan cikin zuciyarta ji take kamar za ta fashe da kuka, tsabar tashin han kalin da ta shiga. “Ko dai Dr Farida ta sanar masa ne? Ko dai gaskiyar da na ke boye wa ne... Shike nan ya gaji da ni?” ta furta cikin ranta, tana runtse idon ta da ƙarfi. Sai da Anty Hauwa ta tashi don yin sallah n walaha a masallacin cikin asibitin, nan ne Ramlart ta bude idonta da sauri, Ta kama pillow da hannunta biyu, ta matse shi sosai tana kokarin danne hawayen da suka taru a idonta. A wannan lokacin, ne ƙarar bude ƙofar ya katse shirun nata, Nurse ce ta shigo da takarda a hannunta. "Madam Ramlart, Dr Farida ta aiko da takardar sallamar ku daga asibitin." Ramlart ta kura wa nurse ɗin ido, da d'an mamaki da firgici, ta sa hannu Ta karɓi takardar da hannunta dake rawa, Idonta ne ya sauka kan saƙon Dr Farida cikin rubutun masu kyau da tsafta: “Based on medical recovery and psychological observation, the patient is hereby discharged for home-based care. Further appointments will be communicated if necessary.” Hannunta na rawa ta ajiye dakardan akan cinyar ta a lokaci guda Ta lumshe idon ta, zuciyarta cike da fargaba. Ba kawai sallamar ba ce ba taso ba, a'a sai dai wani ɓangare na zuciyarta ya tabbatar da cewa yanzu abubuwa za su fara canzawa. “Shikenan... ko da gaske Aliyu ya san gaskiya , san nan zai iya fita gaba ɗaya daga rayuwata?” ta tambayi kanta cikin kame-kamen zuciya da kuka. Aunty hauwa ce ta shigo,cikin dauriya da Karfafa wa kanta guiwa ta mikawa Aunty hauwa takardan, ganin anyi discharge din su ne yasa aunty hauwa takira musu motar family drivern da ya kawo su. Bayan sallamar su daga asibiti, aka dawo da Ramlart gida cikin motar family driver, Tana zaune a baya tare da Aunty Hauwa, zuciyarta cike da shakku da fargaban , abun da zata tarar. Motar na tsayawa a gaban katafaren gidan AA Turaki dake Maitama, Ramlart ta sauka cikin nutsuwa amma zuciyarta na bugawa da ƙarfi, Aunty Hauwa ta kalleta tana murmushi mai taushi tace . “Ki kula da kanki kinji? Ki huta da kyau, zan wuce gida yanzu in duba su Momy da yara, na san warhaka duk sun gama damunta” A hankali Ramlart ta rungume ta jikin ta duk yayi sanyi tace “Nagode sosai Aunty. Allah ya saka da alheri.” Bayan ta rakata har bakin ƙofa, ta koma cikin gida kai tsaye ta nufi part ɗin Hajja, mahaifiyar AA Turaki. Tun kafin ta shiga ciki sosai, kamshin turaren dakin da shaukinsa ya ratsa hancinta, amma duddah haka bai rage mata tsoro da fargaba ba. Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka Ta shiga dakin cikin ladabi, ta zauna a gaban Hajja wacce ke zaune kan kujera tana jan tasbihin ta. Hajja ce : ta dago kai da wani ƙyalli cikin idon ta tace “ Ramlart, kin dawo Lafiya?, ya jikin naki.” Cike da kunyar kanta Ramlart tace: “Eh Hajja...jiki da sauki nagode da addu’arku.” Hajja ta aje tasbihinta, ta gyara zama kamar mai son fad'ar wani abu. “Na yi shiru ne ban ce komai ba tun da kike asibiti, Amma yanzu dole ne na fada, Wannan halin da kika jefa kanki da ɗanmu a ciki, ba abu ne da zan iya rufe ido a kai ba.” Ramlart ta saki ajiyar zuciya, ta sauke kai ƙasa. Hajja taci gaba da cewa: “Shan maganin zubar da ciki? Auren shekaru biyar babu haihuwa, yanzu kuma sai ki jefa kanki cikin barna? Kin san irin raunin da kika jefa ɗanmu ciki kuwa?” Ramlart ta dafe ƙirjinta da hannayenta biyu, hawaye na zubo mata, akan kuncinta tace. “Hajja… wallahi nayi nadama ,Na tuba… bazan sake ba, ki yafe mini , sharrin shaidan ne.” Sai da Hajja ta kalle ta na tsayin lokaci kafin ta ɗan sauke muryar ta kasa tace. “Toh idan da gaske kike, ki nuna hakan da kyakkyawan hali, ba da baki kawai ba, Saboda abin da kika aikata na iya hanaki samun haihuwa har abada.” Ramlart ta share hawayenta, ta juya da ƙyar, ta fice daga part ɗin cike da kunya da danne danne. Bayan ta fito daga bangaren Hajja, Ramlart ta shige part ɗinta cike da rudani da tashin hankali, Jikinta ya yi sanyi zuciyarta na bugawa da karfi. Kalaman Hajja sun daki kunnenta fiye da yadda take tsammani. Cike da tsoro da matsin lamba, ta janyo wayarta daga cikin jakarta, ta danna lambar kawarta Zuly,tana dağa wa. cikin rawar murya ramlart tace: Hello... Zuly… please ki same ni a chat yanzu yanzu… wani abu ya na shirin faruwa… we are in trouble! ZULY ce tace: Lafiya? Me ya faru kuma? Wani irin tsaki, ramlart ta sake ,hawaye na kokarin zubo mata tace: An gane Zuly! Wallahi Hajja ta yi min zancen pills… kuma daga ni cewa tana da hujjojin da ke nuna ina sha. Bata bayyana komai ba sosai, amma na gane cewa suna zargin na! cikin firgici Zuly tace: What?! Ta yaya? Waye ya tona mana asiri? Cikin tashin hankali RAMLART tace : Ban sani ba! Amma naga alamar Dr. Farida ce ta sanar da AA Turaki, shi kuma tabbas ya gaya wa mahaifiyarsa, kin san shi Mama's boy ne, Kuma yanzu wallahi na shiga uku… bansan yadda zan fita ba. zama tayi a bakin gado, ta rungume pillow, zuciyarta na tafasa. ZULY ne tace: Calm down babe... ki nutsu. Sai mu nemi wata hanya, kema kinyi ganganci da kika yarda aka kaiki family hospital,ke da zakije private hospital inda muka saba zuwa ,haba ramlart saikace ba Wise ba . Yanzu dai Ki ci gaba da nuna nadamar ki a gaban idon su. Ki dinga nuna kamar kin chanja. Sannan... sai mu shirya sabon matakin da ya dace ,Wannan ba karshen komai bane, sai dai mafarin lamarin. Ajiyar Zuciya ramlart ta sauke tace.. "Zuly wlh bansan ya akayi ba kawai dai na tashi na tsinci kaina national hospital tare da Aunty hauwa, yanzu dai ba wannan ba, kin san kuwa Hajja tana kok'arin shiga sabgata kuma na lura itace matsalata a cikin gidannan, tsohuwar tana bani ciwon kai wlh." Cike da zafin rai ZULY tace: Sai mu fitar da ita gaba ɗaya. Wannan game ne yanzu... kuma dole mu ci. RAMLART ce ta shaki iska sannan tace: Na yarda dake Zuly… amma wallahi bana jin dadin wannan zaman da nakeyi a gidan nan, ke dai kin riga da kinsan komai, kyansa da dukiyar sa nake so,Idan mahaifiyar sa ta cigaba da shiga rayuwar mu… zan iya rasa komai. Kin san da cewa bayan kin kawo mini pills din ,bayan tafiyarki nayi amfani da su ,kamar dai yadda aka saba, kwatsam sai ciwon ciki ya turnuke ni ,tsabar wahala ban san lokacin da nakira aunty hauwa ba a waya ,shine fa tazo ta kai ni a sibitin,kin san in ba haka ba da asirin mu bazai tab'a tonuwa ba. Ke dai karki samu damuwa kawata da zaran mun had'u komai zai dawo dai dai, cewar zuly. Ramlart ta kashe wayar a hankali, ta jingina da jikin kujera tana kallon bango, zuciyarta na shirya mata sabon makirci mai cike da hadari... 💫ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 5️⃣ Bayan sallar isha’i, da misalin karfe 9:30pm Dare ya lullube garin, iska mai sanyi na kadawa ta window. A hankali Ramlart ta turo kofar dakin ,Tana sanye da doguwar riga ta satin mai launin shudi, da santsi, Fuskarta cike da nadama da tsoro a lokaci guda. AA Turaki yana tsaye a gaban mirror yana cire agogon hannunsa, d'an bai jima da shigowa gidan ba,ido ya zuba mata yana kallonta ta cikin madubi. A hankali RAMLART tace. "Na shigo ciki, Honey?" ba tare da waiwaya ya kalle ta ba yace: "Kin shiga ai tuni... tun da kika yanke hukunci da kanki kina shan magungunan da zasu zubar miki da ciki ba tare da shawara ba." A hankali kamar wata munafuka, Ramlart ta karaso kusa da shi, ta tsaya daidai bayan sa, ta sa hannayen biyu ta rungume shi tabaya, ta kontar da kanta a bayan sa tare da lumshe idon ta tana kokarin dakatar da sauk'an hawayenta. Cikin Muryar kuka tace. "Dan Allah kayi hakuri. Ba haka nake so ba... kawai tsoro ne... kuma shawarar kawata ce." Cikin nitsuwa ya juyo cike da izzah, kyawawan Idonsa ya zuba mata, wan da ya sa tafara diriri cewa . Kamar wanda bazai ce komai ba a bazata taji saukar Muryar sa. "Shawarar kawarki ce? Kina da miji, amma har kawarki ce ke tsara miki rayuwar auranki? Wannan ba ƙaramin gazawa bane Ramlart." Shiru ne ya biyo baya, Ramlart ta sunkuyar da kai Ƙasa alamar ta yi nadama. cikin kakkausan murya yace: "Wani irin tsoro ne ya hana ki son haihuwa? A ina kika ajiye tsoron Allah? Kina sane da irin sharrin da zubar da ciki ke da shi? Kina sane da cewa Allah ya haramta hakan?" Ramlart ta fashe da kuka tare da cewa. "Wallahi ban san zai kai haka ba. Nayi kuskure... dan Allah kayi hakuri..." Kai tsaye yake kallonta: "Ba fushi nake da ke don na rasa ciki ba, Ramlart. Fushi nake da zuciyarki mara tsoro da biyayya ga Ubangiji. Abin da na ke nema ba kawai haihuwa ba ce , ina neman mace mai daraja, mai tsoron Allah da sanin hakkin aurenta." Cikin nitsuwa Ya juya, ya zauna a gefen gado, Ramlart ta biyo shi tare da durƙusawa a gaban sa cikin kuka tace. "Na tuba... wallahi bazan sake ba..." ya dauki lokaci kafin ya kalleta, kamar mai karantar yanayin ta, gently yace. "Allah ya sa ki tuba daga zuciyar ki, Amma ina so ki sani... ki kiyaye sake faruwar hakan a karo na biyu." Yana gama fada'r hakan ya mike, ya shiga bandaki. Ramlart ta tashi daga durƙushewar da tayi a ƙasa, tana kok'arin share hawayen ta, gefen gadon ta samu ta zauna tana ta kok'arin danne zuciyar ta. Baiyi tsammanin har yanzu tana cikin ɗakin ba, ya fito daga bathroom yana shafe lallausan gashin kansa da towel, yana sanye da dogon robe mai launin fari, ruwa na diga daga gashinsa. Fuskarsa na nuna alamun gajiya da rashin walwala. Ramlart, wacce ke tsaye kusa da gado , ta nufo shi da murmushi da iyeyi a d'auke a fuskarta. Cikin muryar raɗa-raɗa tace: "Honey... dan Allah kayi hakuri. Na gane kuskurena, Ka gafarce ni…" Tsayawa yayi cak, Ya kura mata idon sa masu kara birkita mata lissafi, Wata irin ƙunya da bacin rai na bayyana a saman fuskarsa, Bai ce mata komai ba, ya wuce ta gefenta yana dan girgiza kai. Cike da iyeyi ta sake matsowa kusa, dashi ta ɗora hannunta a kafadarsa. cikin sanyin murya tace: "Wallahi, ina kaunarka, Duk abinda nayi saboda tsoro ne…" Cike da takaici, ya fizge kafadarsa, cikin kakkausan Murya yace . "Don Allah ki fita daga daki na kafin na rasa haƙuri na! Ki fita Ramlart!" tsayawa tayi, idonta na cikowa da hawaye, amma kafin ta iya ƙara wata magana, ya tura ta da hannunsa har ta ja da baya kad'an. Bai bata lokaci ba, ya karasa bakin ƙofa, ya bud'e kofar, ya nuna hanyar da yatsar sa da karfi yace. "Get out!!" Wani irin kuka mai rauni, Ramlart ta sake tare da ficewa da sauri, tana share hawayen ta. rufe kofar ɗakin yayi da ƙarfi sannan ya juyo, ya tsaya na dan lokaci kamar yana tunanin wani abu. Cikin nitsuwa Ya karasa gaban wardrobe ya ɗauko pajamas dinsa masu taushi, ya shirya jikinsa cikin natsuwa kamar babu abinda ya faru. Daga nan ya nufi gado, ya shimfiɗa kansa kan babban pillow mai santsi, ya rufe idonsa cikin natsuwa. Kamar wanda ya rasa nutsuwar sa, ya juyo gefe guda yana kallon bangon dakin. A zuciyarsa yana tunani, rayuwar sa maiciki da kaddarah. Ramlart da guduTa fado saman gadonta da karfi, ta juyo ta kwanta tare da kifa cikin ta a kan gadon, daya hannunta na rike da wayarta. Tana fitar da numfashi da sauri, idanunta sun kada da sunyi jawur da hawaye . cikin takaicin abunda AA Turaki ya mata tace "Haba na shiga uku... Kamar ni Ramlart ya ke korata daga dakin sa? Ni matar auren sa!" Cike da bacin rai Ta kamo wayarta, ta shiga contact ta danna sunan Zulya a cikin lambobin ta. Bayan kiran ya shiga, tana Jin Zuly ta dağa tafara magana kawai cikin kunar zuciya. "Zuly! Wallahi na gaji! Ni Turaki ya kora daga dakin sa kamar wata ‘yar aiki!" ZULY ce tace . "What?! Haba mana! Me kikayi masa har ya kai ga hakan?" cike da fushi ramlart tace. "Babu abinda nayi masa! Na je ne kawai domin na bashi hakuri akan maganar abortion... Amma wallahi ya na fitowa daga bathroom, ya kalleni kamar wata house maid, ya gwasale ni sannan ya turoni waje ya kullo kofa!" cikin dariyar rainin wayo Zuly tace . "To yanzu ya kamata ki gane cewa wannan mutumin bai taba sonki ba a cikin zuciyar shi. Kawai biyayya ce ta sa ya aure ki. Hajja ce ta tilasta shi. Kuma ki tuna kin riga kin fada cikin auren da ba soyayyah sabi da haka zaɓi yana gare ki." Wani irin hawayen bakin ciki ne suka shiga sauko mata kafin tace. "To ya kike ganin zan yi yanzu Zuly?" Cike da makirci Zuly tace "Ki daure zuciyar ki, ki daina zama mai rauni, a duk san da ya wulakanta ki. Ki saka a ranki cewa ba zaki bari wannan auren ya zama nasara a hannunsa ba. Idan ba zai girmama ra'ayin ki ba, to zai ji da consequences. Shiya sa nace Ki riga ki fara da samun wata hanya da zai daina tunanin wata mace face ke ko da uwar sa ce dan a yanzu na lura ita ce babban matsalar ki." share hawayenta tayi kafin tace. "To Zuly... ki fada min abin da zan fara da shi." Wani irin shewa Zuly tayi tare da cewa "Kar ki damu... zan turo miki wasu abubuwa na musamman da zasu fara aiki cikin kwana biyu. Sai ki kula da komai yadda nace, nan ba da jimawa ba, za ki fara juya shi kamar yadda kike so. " A hankali ramlart tace. "Zan bashi darasi da ba zai taba mantawa ba..." Daga haka ta kashe wayar tare da kwanciya abunta, ranta cike da sake sake. Wani fili ne mai cike da kore-koren ganye da bishiyu, ga wani irin iska mai sanyi yana kadawa. Rana ta d'an hasko kadan daga sama, wata ƙaramar yarinya ce ‘yar kimanin shekara 15, kyakkyawar fulaniya ce, tana sanye da rigar atamfa da gyale a kanta. Idon ta cike da hawaye, tana kuka sosai, Hannunta na rike da wa wani yaro, karami, kyakkyawan gaske . Cikin kuka YARINYAR tace. "Ka tafi ka barni... Ka manta da alkawarin ka... Ka manta da ni..." AA Turaki, wanda ya tsaya can nesa, da yarinyar, yana kallonta cike da rudewa, yana kokarin karasowa kusa da ita. "A’a... ban manta ba. Ki tsaya... don Allah kar ki tafi..." Sai kawai gani yayi tana juya baya, tana tafiya a hankali har cikin wani duhu mai sarkakiya. Yana kokarin bin ta amma yaka sa yin hakan . Cikin firgici ya buɗe idonsa, numfashinsa ya fara hawa sama da ƙasa. Murya cikin wahala yace. "Subhanallah... Pullo a'm (Fulani nah)? Ita ce fa…" A hankali ya shafa saitin Zuciyar sa cikin raunarniyar Murya yace . "Kiyafe mini" har yanzu kina raina ƙaddarah ce taraba mu. Yana rik’e kirjinsa, yana jin wani irin ciwon zuciya da alama ciwon zuciyar na son tashi. Jikin sane yafara girgiza kamar mai shirin faɗuwa, Ƙasa . Cikin sauri da wahala, ya mika hannu ya buɗe drawer na gefen gadon sa. Ya ɗauki kwalin magani na ciwon zuciya (nitroglycerin capsules), ya bud'e, ya dauki daya, ya saka a bakinsa, ruwan da ke ajiye a gefen bed site drower ya dauka ya sha . Cikin mintuna kaɗan, numfashinsa ya dan daidaita, yana ƙoƙarin komawa normal . A hankali Ya jingina da gado yana rike da kirjinsa har sai da ya sauke ajiyar zuciya, da alam yaji relief. cikin raunin murya yace . "Allah ka kare min su... kada ka bari wani abu ya cutar da su, su di'n rayuwata ce..." A hankali Ya lumshe idonsa, yana jin jikin sa na sanyi. Bacci mai nauyi ya sake ɗaukarsa, a wannan karon baccin da ya fi na farko nisa, cike da gajiya da kumburin zuciya. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 6️⃣ GWARİNPA ESTATE. Dr. Farida ta fito daga dakin ta cikin shigar aiki ,medical scrubs masu launin sky blue, farin lab coat a saman, su tana ƙamshin turare mai shegen dad'i da sanyaya rai, Gashinta yana sanye da medical cap. A hankali Ta sauko zuwa falon, murmushi d'auke a saman fiskan ta. cike da annashuwa tace. "Assalamu Alaikum Dada… Good morning Ameer." Ta karasa maganar tare da kallon su. cikin farin ciki dada ta ce. "Wa alaikumus salam, ya'r albarka. Allah ya sa alheri ya cigaba da bibiyar rayuwar ki, har kin kammala shiri kenan?" AMEER dake shirye tsaf cikin uniform din makaranta yace. "Yes Ummi! Na shirya… kawai ke nake jiran kizo muyi breakfast ." Dada ce tace. "Ku zo ku ci kafin lokaci ya kure… ba zan yarda ku fita cikin yunwa ba." Dariya Dr Farida tayi tare da zama akan d'aya daga cikin kujerun dake jere a dinning table din. tea, bread, kwai, da fruits, sai flask da dada ta d'aura a tsakiyar table din. AMEER dake shan kankana ne yace. "Ummi, dada… zan iya kunna TV in duba morning news?" Dr FARIDA ta kalli Umma, ta gyada kai a hankali tace. "To na baka mintuna uku kawai." Cikin jin dadi Ameer ya dauki remote, ya bude channel na Africa Sunrise News. Ya samu Ana maimaita wani exclusive interview da babban Business Tycoon AA Turaki. Sanye yake cikin manyan kaya, yana magana cike da nutsuwa da izza, yana bayyana irin taimakon da yake baiwa matasa da sabbin entrepreneurs, dakuma nasarorin da ya samu a rayuwa da irin gwagwarmayar da yasha kafin taka matakin. Cike da nitsuwa yake jawabi a cikin TV "...muna kokarin ganin an samu cigaba, musamman a fannin ilimi da lafiya. Kowa yana da damar cigaba matukar yana da niyyar aiki tukuru." Ameer ne ya ke kallon shi cike da sha’awa. Sai ya kalli Dr Farida yace. "Ummi..! kin ga wannan mutumin ina matukar kaunar sa, nima irin sa nake so na zama idan na girma, amma ummi kin taba ganin AA Turaki? Cike da basarwa, Dr Farida ta daure fuska tana kai bread cikin bakin ta tace. "AA Turaki? A'a… ban sanshi ba sosai kuma ban taba ganin sa ba." Dada ce ta dauki remote cikin sauri ta kashe TV din, tace "Toh baki abun magana ba kaga lokaci na tafiya ba ne, Za ku makara fa. Dr Farida ne tace. "Tashi mu wuce kafin traffic ya fara." Takara sa maganar tare da miƙewa a lokaci guda kuma tana goge bakinta da tissue. Ameer ya tashi yana murmushi, Dr Farida ta mike ta dauki jakar aikinta, tana kokarin boye sauyin yanayin fuskarta. "Okay ummi, cewar Ameer da ya bi bayan ta hannun sa rike da jakar makarantar sa. A haka Suka karasa mota wata silver Toyota Corolla 2021, mai dauke da plate number na National Hospital. Ta bude masa kofar baya, ya zauna. Ita kuma ta shiga driver's seat, ta kunna mota, suka kama hanya. Ameer yana zaune yana kallon ta ya saki wani cute smile yace . "Ummi, kin fi kowa kyau a cikin wannan uniform din ba kiga yadda kike da kyau ba." murmushi ta sake tare da cewa. "Kai Ameer, baka gajiya da shirme wlh." Haka Dr Farida ta sauke shi a makaranta, ya yi mata bankwana. İta kuma ta ci gaba da tafiya zuwa asibitin, dan da alama yau ta kusa makara. Dr Farida tana parking a filin ajiye motoci na ma’aikata, tana jin sautin iska da shigowar wasu motocin cikin harabar parking lot din. Wani black Toyota Camry ya shigo a dai-dai lokaci daya da ita. Dr. Imam, ne cardiologist Dr ne a cikin asibitin wato likitan da ya shafi bangaren zuciya, ya fito cikin sauri da murmushi, yana nufeta tare dacewa. "Dr. Farida! Good morning. Ya Subhanallah, yau kin kara kyau fiye da kullum my Love." Cike da nitsuwa Dr Farida ta dauki files dinta, ta juya tana fuskantar sa, tare da rufe murfin motar sa tana dan murmushi mai had'e da natsuwa da class tace. "Good morning, Dr. Imam. Ka ga lokacin aiki na Kara matsowa, ga shi yau mun makara ?" Tana fad'an haka ta wuce ta gaban sa. Da sauri Dr İmam yana bita a baya, yana takawa a hankali yace. "Wallahi har yanzu bana jin dadin yadda kike kaucewa maganar da ta shafi tsakanin mu dake. Dr Farida, wannan zuciyar tawa tana bukatar kulawarki… ina da rauni akan soyayyar ki." A haka Suka karasa harabar Office din OB GYN, suka shiga cikin block din a tare. Bud'e office din ta dake jare tsaf tayi, ga wani irin ƙamshin Air freshner dake tashi wanda ya gauraya da asalin ƙamshin turaren jikin ta, DR. IMAM ne ya zauna a wata kujera da ke kusa da teburin ta ya sake cewa . "Ni fa bana jin dadin yan da kika ki bani dama, Kin san zan iya turo iyayena a gobe in kin yarda. Amma sam kin ki ki bani daman hakan..." Bayan Dr FARIDA ta zauna tana gyara files, cike da hikima da kame kai irin na matan da suka san kansu tace. "Dr. Imam, kasan ina girmama ka. Kaima ka san yadda rayuwa take… akwai abubuwan da nake kokarin warwarewa kafin in baka damar turo da magabatan ka. Dan Allah, ka je ka duba patients dinka, kaga Time ya küre,Idan ka gama, sai ka dawo mu karasa maganar." Cike da so DR. IMAM yake kallonta . "To, amma sai kin yi alkawarin cewa zaki shigo Office dina kafin na tashi." murmushi, Dr Farida tay tana gyada kai alamar ta amince da hakan. "Na amince. In Allah ya yarda." DR. IMAM ne yace "Okay, zanyi hakuri Zan jira amincewar ki." Yana gama fadar haka Ya mike, ya fita ya nufi cardiology Ward in da a chan office din sa yake, Dr Farida ta sauke ajiyar zuciya a hankali, tana kallon kofar da ya fita, tabbas Dr İmam ya chanchanci a so shi, sai dai kuma zuciyar ta ta jima da rufe wannan babin a cikin rayuwar ta. Cikin zuciyar ta tace. "Allah Ka bani ikon zaben abun da zai amfaneni a rayuwa..." Daga nan taba wa patients din ta damar shigowa ta hanyar kada yar kararrawar dake gaban teburin ta . ****** Zaune suke , a Wurin da suka saba haduwa ne, wata Private lounge a cikin wani luxury café da ke Maitama. Anguwar na da nutsuwa, kuma wurin ya kasance mai tsit, babu hayaniyar komai. Ramlart ta ke zaune cikin shigar mata masu class, sanye da riga da skirt na zamani, ga wasu manya gilashi a idonta, hannunta sanye da agogo mai tsada. Zuly kuwa ta na zaune fuskarta cike da kwalliya , irin na ya'yan masu kudin nan marassa jin magana . Zuly ce ta zuba ido cikin na Ramlart tace . “Yanzu fa, da gaske Hajja ce ta fara shiga tsakanin ku da AA Turaki? ai kuwa ya kamata muta ka mata birki dan bazai yiwu taci zamanin ta ba sannan a yanzu tace zata had'a da naki ba, never wlh . Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarci fiskar Ramlart tace. “Zuly... ke kanki kin san ba ta taɓa sona ba, Tun farko, ita ta shigo da ni saboda biyayya, ba domin ta yarda dani ba, sai don cikan burin ta akan danta, Yanzu kuma tana kokarin rabani da mijina.” ZULY ce ta harare ta tace . “To, me muke jira? Kin dai ce min tana issue n zuciya da hawan jini. Me zai hana mu taimaka mata ta huta da wuri kawai?” ta karasa maganar tare da shekewa da Wani irin dariya. Ramlart ta lumshe ido, tana sauke numfashi. A zuciyarta, akwai rudani tsakanin gaskiya da makirci, amma kiyayya ta fi karfi a zuciyar ta. cike da zafin rai Ramlart tace . “In har hakan ne hanyar da zai sa ya dawo gareni... zan iya yin komai.” ZULY ta d'an yi murmushi tace . “To sai mu fara da abincin ta, Zan samo wani sinadari da ke kara tashin zuciya a jikin masu ciwon zuciya. Karki damu sai ki ringa sa mata a tea ko soup ɗinta, da zaran taci ko da sau d'aya ne uhumm... sunan ta sorry.” takarasa maganar cike da makirin murmushi. “Hakan zai yi, Amma sai dai mu yi hankali. Ba zan so a gane cewa ni na janyo hakan ba.” cewar Ramlart da ta gama yarda da maganar ZULY. Zuly ce tace. “Ki bar min wannan. Ai ni ce master planner. Kuma fa... idan ta mutu, babu mai hana ki warwasawa da mijinki kin ga gaba d'aya hankalin sa zai karkata kan ki ne, tun da bamu da matsala da wanchan Tsohon na shi kin ga sai kici karen ki babu babbaka.” Ramlart ta lumshe ido tana murza zoben dake hannun ta, A cikin zuciyarta, soyayya ta rikide zuwa kishi, kishi ya rikide zuwa makirci. don kuwa ji takeyi zata iya kawar da kowa akan hanyar ta muddin zai shiga tsakanin ta da AA Turaki. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 7️⃣ Monday morning misalin karfe 8:30 na safe. Ramlart ce tsaye hannun ta rike da wani farin leda. Ga Kayan tea da kayan girki suna nan a jere, a gaban ta da alama an kammala break fast ne. Cike da annashuwa ta bud'e ledan wani irin farin sinadari ne a ciki, Dan kad'an ta ibo ta zuba a cikin flaks din tea, da sauri ta d'an girgiza shi ta yadda ba za'a gane an saka komai ba, nan da nan ya narke a cikin tea d'in, karkad'e hannayen tayi ,ta juya gefe da gefe ganin ba wanda yake Kallon tane ya sa ta sauke ajiyar Zuciya tiren ta dauka ta nufi falon Hajja. Hajja na zaune, tana karanta Qur’ani a hankali, Ramlart ta shigo da tray mai dauke da tea da snacks. Cike da fara'a RAMLART ta ajiye tiren tare da cewa. "Hajja, ga tea dinki… ." HAJJA ce ta kalle ta fiskar ta d'auke da murmushi tace. "Allah ya miki albarka Ramlartu, yau kin kawo mani abun kari da wuri, kamar kinsan cikin nawa bakomai." Takara sa maganar tare da, karba, ta fara shan tea d'in da ramlart ta zuba mata a cup. Bayan mintuna kadan, Hajja ta fara motsa jikinta da wani irin ɗan sanyi, ji take kamar bugun zuciyar ta ta karu. Cike da karfin hali HAJJA tace. "Ah… Ramlart… zuciyata… kamar tana bugawa daban…" Bata karasa maganar ba ,Ta kama kirjin ta, Cikin minti daya, ciwon ya tsananta, jikin ta ya birkice Jikinta ya fara rawa kamar na maijin sanyi. shigowar shi parlourn kenan yana waya da PA ɗinsa, yana magana a waya "Cancel all appointments for this week, I need to… maganar ce ta makale hango mahaifiyar sa tana riƙe da saitin zuciyar ta, a lokaci guda tana faduwa a jikin kujera. Hajja!!" Ya kira sunan ta da mugun karfi. Da sauri Ya ajiye wayar, ya ruga zuwa da d'an sassarfa zuwa gareta. Ganin sa da tayi ba tare da tsammanin sa bane yasa ,Ramlart ta tsaya cak cike da kame-kame na rashin mafita. "Ramlart! Meye hakan? Kira driver! Kira masu taimako!" Cike da tsoro ramlart takira driver A take aka tara mutane, aka kwashe Hajja cikin mota. Wata mota Black Lexus SUV, a ka sanya Hajja tare da AA Turaki yana riketa da ita a kafadar sa. Bodyguards da Sani PA sun biyo su da wata motar gefe, tare da ramlart, kowa hankalin sa a tashe . Suna isa aka wuce da Hajja ,cikin Emergency Ward. Likitoci suna ta kai-komo, suna bata agajin gaggawa. Dr. Imam da wasu nurses ne suka karɓe ta , haka suka rufu akan ta domin ceto rayuwar ta. NATIONAL HOSPITAL ABUJA, ICU Waiting Area. AA Turaki na zaune a bench kusa da ICU, yana kallon kofar dakin da mahaifiyarsa, ke ciki. PA dinsa da bodyguard din sa sun tsaya d'an nesa kadan da shi kowa ka kalli fiskar shi yana cikin tashin hankali. Ramlart na zaune a gefensa, tana kuka mai sauti, sai yarce majina takeyi a jikin mayafin ta , idanun ta duk sun kumbura saboda kuka. cikin kuka mai sauti Ramlart ta ce. "Honey… na shiga uku! Hajja fa! Allah ka dubemu… Hajja zata mutu shi kenan mun shiga uku…" ta karasa maganar tare da jan dogon majina. *Dan juyowa yayi kadan yana kallonta da wani irin kallo mai cike da ma'anoni masu yawa, sai dai yabarwa rai. A hankali Ya ɗan ja numfashi amma har yanzu bai ce mata komai ba, kauda kan sa gefe yayi, d'an ji yake yi kukan nata na damun sa. A cikin ICU, Likitoci biyu ne suke magana Dr. Imam na hannun dama, yana duba takardu, d'an dago kansa yayi yana fadin... "Symptoms ɗinta sun nuna hypertensive crisis ne tare da cardiac complications. But there’s something strange…" DR. RACHEAL ne yace: "Yeah… Her vitals suddenly dropped after ingesting something. Did you run tox-screen?" Yakarasa maganar tare da kallon fiskar Dr İmam. DR. IMAM ne yace: "Just ordered it. Meanwhile, let’s call in Dr. Farida, she’s one of the most trusted consultants here. She might help manage the case, especially now that there’s suspicion of induced triggers." DR. FARIDA tana cikin Office dinta tana duba case file, Nurse Mary ce ta shigo tare dacewa . "Doctor Farida, you’ve been requested to assist in managing a critical case in ICU — Hajiya Habiba Turaki. Dr. Imam asked specifically." Cike da nitsuwa Dr Farida ta ɗaga kai tana kallon nurse mary , kafin tace. "Alright. Give me the patient’s file and vitals. Let’s go immediately." Ta miƙe, ta ɗauki coat da stethoscope dinta, suka nufi İCU AA Turaki na nan har yanzu, yana kai da kawowa. Ganin Dr Farida ta shiga ciki ne yasa , Ramlart ta ƙara fashewa da kuka sosai, kamar za ta zube a kasa, "Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, shikenan munrasa Hajja, ganin bai kulata bane yasa, A hankali ta leƙa ta kalli AA Turaki da gefen ido, tana jiran ya kalle ta, ko ya mata magana, Amma ya ƙi kallonta, asalima kamar baisan da wanzuwar ta a wajen ba . A cikin ICU, DR. FARIDA na duba Hajja tana kokarin yin bayanin abun da tagani ga Dr Imam. DR. FARIDA ne tace: "Heart rate’s unstable. We need to stabilize her BP first. Tox-screen result is vital — I suspect some external compound triggered this. Alert me as soon as the lab result is ready." DR. IMAM ne ya kalleta yace: "Understood. I’ve already instructed the team." DR. FARIDA ne ta matsa kusa da gadon Hajja tana murza hannunta a hankali, tana karanta mata ayatul kursiyu, a zuciyarta, ta na tofa mata ,haka kawai takejin tausayin tsohuwar duddah zata girmi Dadar ta . A hankali Dr Farida tace. "Allah ya yaye miki wannan cuta…" Ganin AA Turaki yatafi masjid ne yasa ramlart ta ciro wayar ta a jakan ta numbern zuly takira direct tana dagawa tace. " Ke zuly muna cikin bala'i kin san kuwa na sakawa Hajja maganin nan da safe a cikin tea d'in ta na safe, tana sha ba wani Bata lokaci maganin yayi reacting a jikin ta, kuma AA Turaki yaga lokacin da nake tare da ita, yanzu haka gamu nan a national hospital wlh duk na tsorata gani nake kamar asirin mu zai tonu".takara sa maganar tare da goge wani zufa da ya yanko mata tun daga saman kanta. Cike da karfin hali ZULYtace. "Ki nutsu mana! Kin manta da sabon matakin da zamu dauka ne? Ki nuna damuwa sosai, ki ci gaba da rike zuciyar shi da tausayi , karki bada kafar da zai zargi wani abu dağa gare ki, ko da yaso zargin ki ki tanadi wasu dalilai da zai hana ya zargeki kai tsaye haba be Wise mana sai kace wata local." Bata kashe wayar ba sai da ta tabbatar da cewa ta gama daukan shawarwarin da zuly ta bata , sabi da haka tana kammala wayar, ta sab'i jakan ta ranta fess ta nufi komawa gida batare da tajira shigowar AA Turaki ba. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 8️⃣ Lab Department, National Hospital – An kira Dr. Farida domin karɓar sakamakon gwajin Hajja wanda aka mata da misalin karfe 9 30am na safe . Dr. Farida na tsaye a gaban Lab technician, tana karɓar takarda da sakamakon tox-screen da blood analysis. Bayan ta gama karantawa ne , fuskar ta cike da damuwa , had'e da mamaki. A hankali a cikin zuciyarta ta furta: “Ya Salam… ta sha sinadarin da ke haddasa hawan jini da matsin zuciya… This isn’t accidental.” Cike da son tabbatar wa Ta kalli Lab technician din tace. "Shin kun tabbatar da wannan sakamakon? Wannan compound ɗin wani nau’i ne na slow poison da ke aiki a jiki cikin sa’a da awa." TECHNICIAN D'in ne yace: “Yes Doctor. An tabbatar, kuma an gano traces of a rare chemical—*Digoxin derivatives*—da ke da strong cardiac effect, especially for hypertensive patients.” A hankali Dr. Farida ta ja numfashi, ta rufe takardar , sannan ta fice tana nufar Office din Dr. Imam. Dr. Imam na zaune yana rubuce-rubuce, Dr Farida ta turo kofar ta shigo da takarda a hannunta. Bayan ta mika masa result din ne tace masa. "Dr Imam, there's more to this. Hajiya Habiba Turaki,was poisoned." Cike da mamaki DR. IMAM ya d'ago kansa tare da cewa: "What?! Are you sure?" DR. FARIDA tace: "Positive. The test confirmed it. Yakamata mu yi report zuwa board. Wannan ba cuta ce ta yau da kullum ba — wani ya sanya mata wannan sinadarin da gangan." Cike da damuwa DR. IMAM Yace:* "Then we have to inform the family and call security for investigation." AA Turaki na tsaye a waiting area na ICU don har yanzu bawani bayani bai samu ganin ta ba, yana kiran PA dinsa a waya, Dr. Farida ce ta iso cikin sauri tace. "Mr. AA Turaki, I need to speak with you in private please." Ta wuce Office din ta, cike da karfin zuciya ya bita a baya, bayan shigar su cikin Office din ne. DR. FARIDA tace. "Mun gano wani abu a jikin Hajiya Habiba Turaki. An samu evidence na wani sinadari mai hadari a jikin ta… It’s poison. Ba ciwon zuciya kawai bane ya haddasa mata hakan." Ji yayi komai nasa ya tsaya cak, Idanunsa sun cika da tashin hankali, da bacin rai. Cikin wata irin Murya mai kauri yace. "Poison? Waye zai aikata hakan a gare ta? Waye zai cutar da Hajja?!" A hankali kwakwalwar sa ta tuno masa da ramlart,A take idanun sa suka yi ja. Ba tare da ya ce mata komai ba, ya juya ya fita daga cikin Office din. NATIONAL HOSPITAL ABUJA – BOARD MEETING ROOM AA Turaki na zaune a gaban babban teburin Board din asibitin tare da Chief Medical Director (CMD), Dr. Imam, Dr Farida, da wasu manyan likitoci. CMD ne yayi jaran murya tare da cewa: "Mr. AA Turaki, considering the results from Dr. Farida’s toxicology report, we’re prepared to report this to the authorities for full investigation. This is a serious criminal matter." cikin nutsuwa da kamala AA Turaki yace : "Ba sai kun dauki matakin doka ba. I appreciate your concern, amma I will handle this internally. It's a family issue and I believe it’s best managed within our home. Please respect my request." Dukan su sai Suka kalli juna, suka gyada kai, saboda girman sunan sa da matsayin sa a kasar. . CMD yace: "As you wish, Sir. But we’ll keep the report confidential for now. We’ll proceed only if you authorize us." AA TURAKI cike da jin dad'in yan da suka amince da request nashi yace: "Na gode, da kuka fahimce ni". ICU – DAKIN HAJJA Dr. Farida na zaune a gefen gadon Hajja. Tana daidaita IV drip sannan tana tausa mata hannaye da lallami, yayin da Hajja ke bacci mai nauyi. A hankali kamar mai tsoron tashin ta DR. FARIDA ta ce : "Ya Allah ka bata lafiya… kamar mahaifiyata ta nake jin ta a zuciya ta ." Wata Nurse ce ta shigo, ta mika mata wasu results, sai ta duba tare da gyada kai cike da kulawa, Ta tsaya bakin gado, ta sumbaci hannun Hajja cike da tausayin ,ta tafita daga d'akin. TYCOON MANSION Ramlart ne ta shigo cikin fargaba, sai dube-dube take da sauri, ta rufe kofar dakin ta. Ta fada kan gadon ta tana shakar wani dogon iska. A zuciyar ta ta ce. "Alhamdulillah… Na fita daga wannan abun na dan lokaci. Yanzu dai ba wani zargi kai tsaye… Insha Allahu, zan sami hanyar kare kaina zuwa gaba." Da sauri Ta dauki wayar ta, ta kira Zuly, ringing d'aya ta dağa. RAMLART ce ta ce: "Zuly, na koma gida,AA Turaki bai zarge ni ba, kuma da alama doctor's din basu gano komai ba, amma kuma wlh na tsani wannan likitar Dr Farida take ko wa." Zuly ce tayi shewa tace . "Kai mutumiyar baki da dama me kuma ya had'a ki da wata Dr Farida, ke dai tunda asirin ki bai tonu ba sai ki godewa Allah". Haka suka gama wayar cike da Nishad'i na samun nasara. Dr. Imam na tsaye a bakin kofar ICU, yana jiran fitowar Dr. Farida. Da ta fito daga dakin Hajja, sai ya mika mata wani mini flask mai shegen kyau da coffee a ciki, Wani irin cute smile ya ke mata, na zallan Love. Cikin shaukin so DR. IMAM yace: "I know you barely slept. Na kawo miki coffee. You’re really amazing Farida… I wish kina fahimtar yadda zuciyata ke bugawa a kanki." Cikin shauki Dr İmam Yana kokarin kama hannunta. da murmushi d'auke a fiskar ta ta ja hannunta baya kadan: "Thank you, Dr. Imam. I appreciate your concern… Amma my patience is my priority for now." Murmushi su kayi dukan su, atare su ka juyo A lokacin ne AA Turaki ya karaso cikin Ward din sai dai kamin ya iso kusa da su, ya dan tsaya kadan, yana jin kowane kalma da Dr İmam yake fad'a mata a cikin zuciyarsa, haka kawai yaji abun ya basa haushi, Wani irin bugun zuciya ya keji kamar za ta fito, waje, wato su ba condition d'in Hajja bane a gaban su ba, ta Love d'in su suke yi, tsofai tsofai da su, Idanunsa suka kada sukayi ja, a hankali idanun sa suka tsaya a jikin Dr. Imam da Dr. Farida, wani irin kallo mai dauke da ma'anoni yake musu. Zuciyarsa cike da fushi, dan ya tsani abun da zai saka Hajja a wani condition, sai gashi Likitocin da suke dubata ne suka buge da soyayyah, kawar da kwayar idon sa yayi ,sai ya kama hannun agogon hannunsa ya duba time da dan karfin murya, yace . "PA… Let’s go. I’ve wasted enough time watching unnecessary conversations." Cikin sauri PA dinsa ya matso , tare da bud'e masa kofar, yad'an ja da baya, bayan ya wuce, san nan ya bi bayansa. Bodyguard d’insa biyu masu siffar karfi, suka tsaya a dan nesa suna jiran sa. Dr. Farida ce ta koma cikin Office din ta zuciyarta na ci gaba da harbawa da sauri. Duk da bata fahimci dalilin sa na fad'in hakan ba , Amma zuciyar ta cike take da tsoro. A bangaren AA Turaki, bayan ya shiga ya duba jikin Hajja ,har yanzu tana kwance kamar mai bacci, haka ya fito su PA da bodyguard din sa suka take masa baya, da sauri yake tafiya, zuwa parking lot. PA dinsa na kokarin bin sa da sauri yana kok'arin yi masa magana, amma ganin kamar yanayin sa ya chanza sai bai ce komai ba. cikin kulawa Sani PA yace. "Sir… are you okay? Shall I cancel the rest of the day’s schedule?" Cikin kokarin danne fushinsa yace: "Cancel everything. I don’t want to see anyone today." Yana gama fada'r haka Ya bude motar da kansa ya shiga, batare da ya jira sun bud'e masa ba, Motar tana dauke da kamshi na musamman, interior nata executive ne da hasken LED masu taushi. Ya zauna, ya lumshe idanu yana jin zuciyarsa na bugawa da mugun karfi. Bayan fitar sa daga d'akin Hajja, Dr. Farida ce ta shigo tana duba drip na Hajja, ta gyara mata bargo. Hannunta na rike da yatsunta a hankali, Hajja ta bude idonta kadan ta kalleta, idonta na dauke da rauni, amma cike da godiyar Allah da kwanciyar hankali, ta karasa bud'e su . Cikin raunin Murya Hajja tace. "Likita… na gode. Allah ya saka da alkhairi." Fiska cike da murmurmushi Dr Farida tace . "Ameen Mama. Allah ya baki lafiya." D'an murmusawa Hajja tayi, jin takira ta da suna mama, cike da kulawa ta kalleta tace. "Ki kirani da Hajja" ,haka Da'na yake kira na. Wani irin faduwar gaba ce ta riski Dr Farida, aranta tace. "Uhumm wannan d'an naki mai shegen fad'in rai duk yabi ya cikawa mutane asibiti da guma ka , wai su bodyguard din sa, sai kace akan sa aka fara tsaron lafiya". Muryan Hajja ce ta katseta. " İna wanda suka kawo ni nan", cewar Hajja. Cikin girmamawa Dr Farida tace. "Basu jima da fita ba amma I'm sure zai dawo anjima." Tana gama fada'r hakan, Ta kamo hannunta tana bubbugawa a hankali, Ta dago ta kalli Nurse d'in dake cikin dakin tace. "Please, call me immediately if anything changes. I’ll be in my office." Tana gama fad'an haka , Ta juya ta fita, tana kokarin mayar da zuciyarta da hankali akan aikin ta – duk da kalaman Dr. Imam da fushin AA Turaki na ci gaba da juya mata lissafi, a cikin zuciyar ta. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 9️⃣ AA TURAKI’S MANSION, PRIVATE MASTER SUITE. Da dare misalin qarfe 10 30pm duhun dare ya mamaye ko'ina,a cikin wannan, katafaren gidan mai alfarma, Fitilun chandelier ne su ka haskaka farfajiyar babban falon sama, kai kace dare batayi ba. Ramlart, ce ta fito cikin kayan bacci masu siririyar hannun lace, suna d'auke da launin ja, sun gama bayyana surar jikinta, Wani irin ƙamshi na musamman ne yake tashi daga jikinta , turaren da zuly ta kawo mata ne na maganin tada sha’awa , wanda zai jawo hankalin AA Turaki zuwa gare ta. A hannunta, tray ne dauke da tea da snacks, zuciyarta cike da niyyar jan hankalin AA Turaki da mallake zuciyarsa, gaba d'aya. Cike da yanga Ta karasa bakin kofar dakina sa, a hankali ta tura k'ofar cike da yanga, kamar wata jarumar Indian film. AA Turaki na zaune a kan sofa da ke cikin d'akin nasa yana duba wani file na Business d'in sa, jin an bud'e k'ofar d'akin ne yasa ya dago idon sa ya kalleta, cike da nitsuwa ya sauke files din, ya dan kame, yana kallonta, shiru ne ya biyo baya na Dan wani lokaci. Cikin murya mai sanyi RAMLART tace. "Naga kana aiki ne shiya sa na kawo maka tea, d'in nan, na ce bari na tayaka hira, ta karasa maganar cikin kwantar da kai." Ganin baice mata komai bane ya saTa karaso, ta ajiye tray din a gefe, sai ta tsaya gabansa. Cikin salo, ta fara shafa kafadarsa, a hankali take shafa shi har zuwa kirjinsa, tana narkewa cikin jikin shi . AA Turaki ya bita da ido, bai ce uffan ba Sai ma ya mika hannun shi ya kamo ta shima, a hankali suka fara romancing din juna, har cikin ransa ya ke kin hakan, amma ya kasa controlling din kan shi, haka ya ci gaba da ya'mutsata, wani irin yarrrrrrr ramlart take ji yana yawo a jikin ta, wannan ne karo na farko a rayuwar auren su, da AA Turaki ya saki jiki yana romancing din ta yanda ya kamata, ba karamin dadin hakan takeji ba, sai wani bank'arewa take yi tare da shishahid'ewa ,sai da ya bari har ta sake jikin ta sosai, ta dinga shafe shi, Wani irin murmushint gefen baki ta sake, cike da jin dad'in nasaran da tayi akan sa. Tana cikin jin dad'in abun da yake yi mata ne, Sai kawai taji ya dakata. Ya dan ture hannunta a hankali. Cikin natsuwa ya mike, ba tare da ya ce komai ba, ya nufi toilet, yana jin wani irin jiri yana kok'arin iban shi. tsayawa cak, ramlart tayi, zuciyarta na bugawa, da sauri sauri, jikin ta har rawa yakeyi, kunnuwan ta suna sauraron karan, ruwan shower na dukan tiles, daga cikin toilet d'in,Kamar wadda aka saka a cikin ruwan sanyi, jikin ta duk ya mutu muruss, dakyar ta ta shi ta zauna a gefe tana hawayen bakin ciki. Bayan wani lokaci, AA Turaki ya fito cikin riga da wando na pyjamas masu matuƙar tsada, jikin sa yana fitar da ƙamshin turaren The King mai daddadan kamshi. Cikin Wani irin yanayi Ya shimfida prayer mat dinsa, ya tsaya, ya tada sallar nafila, Cikin nutsuwa, ya dinga rokon Allah lafiya ga mahaifiyarsa. Ganin yan da yayi banza da ita ne yasa Ramlart ta kara fashewa da kuka, tana jin haushin abinda ya faru. Bayan ya idar da sallah, bai kalle ta ba, ya nufi gado, ya haye gado cikin shiru batare da ya kulata ba, ya kwanta yana Mai karanto addu'ar bacci. Ramlart ce ta tsaya, tana kallon sa, zuciyarta cike da fushi da kunci, wani irin bakin ciki ne ya turnuke ta, Ta kama hijab dinta ta dai dai ta shi a jikin ta, sannan ta fita cikin sauri, kamar wacce zata tashi sama. Bayan ta koma dakin ta, ta fad'a saman gadon ta cikin takaici, Ta dauki wayar ta kira Zuly. Cikin sheshsheqan kuka RAMLART tace . "Zuly… kin san me ya yi mini kuwa? Ya barni tsirara bayan ya gama jagwalgwalani, Yaje yayi alwala! Yayi salla! Wani irin wulakanci ne wannan?" Cike da kara kunna ta ZULY tace . "Yanzu nan, zan biyo ta gidan ki ,maza tashi ki shirya, Ni da Al’ameen za mu zo mu dauke ki, Zamu wuce club! Enough is enough, Ramlart. Wannan wulakanci ya isa haka! Sai kace ba babban yârnya ba zaki tsaya yana wulakanta ki, haba mana sai kace kin manta kece fa Ramcy baby The babbar yarinya mai babbar harka, haba karki ba dani mana ke da maza suke rububin ki sai ka ce kin manta dan fa kin nace masa ne wlh , shine har ya samu damar wulakanta ki." Ramlart ce ta share hawayenta, zuciyarta ta cika da bakin ciki, tace zuly kina ganin....! Bata bar ta ta karasa maganar ba tace . "To shikenan! Ki shirya yanzu, Za mu fito ni da Al’ameen mu d'auke ki, Tonight, you must forget him. Let’s go to club wannan damuwar sai mun danne ta!" Ramlart ta share hawayenta, ta miƙe da sauri, cike da fushi ta nufi cikin close set d'in ta, tafara shirya kanta. Ramlart ce tsaye a gaban madubi, cikin shigar ta mai jan hankali – fitted black gown da takalman golding masu tsini sanye a kafarta, Ta feshe jikinta da turaren ta mai ƙamshi da ƙarfin gaske, Gashin kanta gyare yake tayi parking d'in shi, light makeup mai haskaka fuska tayi, Wayan tane a kunnen ta. A hankali tace . "Zuly, na shirya… ku tsaya a bakin gate yanzu nake fitowa , Ku tsaya a gefe kada mai gadi ya lura da ku." Tana gama fada'r haka Ta kashe wayar, ta ɗauki small purse da wayar ta Ta jefa light jacket a kafadarta, sannan ta fice da sauri cikin natsuwa, kamar babu wani abu dake damun ta. Zuly da saurayinta Al’ameen suna cikin wani sleek black car ,clean tinted Camry, parked a gefe kadan da gate. Zuly na kallon agogon hannun ta tace. "Wannan yarinyar idan bata fito yanzu ba, mai gadi zai iya zargin wani abu." Ramlart ce ta fito tana tafiya a hankali kamar wadda take tsoron wani ya ganta, a hankali Ta kalli gefen dama da hagunta, sai kuma ta sauke numfashi, ta tura gate ɗin a hankali ta buɗe ta fita. Da sauri Zuly ta buɗe mata kofar kafin ta ƙaraso su. Cike da tsokana ZULY tace . " The babbar yarinya Na ce miki yau sai mun bude sabuwar shafi, Ramlart ki saki zuciyar ki ki morewa rayuwar ki!" RAMLART ce ta zauna a baya, tana tafa hannun ta tare da cewa. "Yau raina cike yake da damuwa Let's go burn the night." Al'ameen ne ya ja motar a hankali suka bar harabar gidan. A cikin duhun dare, fitilun club din na haskakawa ta ko'ina da launuka masu rikitarwa, Muryar DJ ne kawai yake tashi yana busa waka mai cike da karfin sauti. ZULY da RAMLART ne su ka shigo cikin mota mai launin baki, Al’ameen saurayin zuly yana driving d'in su . Ramlart ta fito daga mota cikin black doguwar rigar ta mai sheƙi da cut-out, sanye da takalmi mai tsini da jan lalle a hannunta. Idonta na ɗauke da jan eyeshadow, da hancin ta da kunnuwa ta ke dauke da set d'in jewelry na gold ga gashin ta taya sha gyara na “slay queen” salon. Cikin dariya zuly ta ce. "Yau sai kin sha iska, yanzu ne duniya zata ga Ramlart!" Suna dariya suka shiga ciki, club din cike yake da mutane – wasu na rawa, wasu na sha, wasu na zaman romancing din juna. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣0️⃣ VIP SECTION – CLUB Ramlart zaune kusa da Al’ameen da Zuly, suna dariya suna shan drink (non-alcoholic mocktail) fiskar su cikin nishaɗi. Ramlart tana tura hotunanta a Snapchat da Instagram story –nata, ta rubuta, “living my best life” caption, d'in ta. ZULY ce ta leƙa wayar Ramlart tace. "Yauwa ta waje na sai dake haka nake so, kiyi komai ba komai , wlh, a duniya muke ,aljannah ta mai rabo ce." Cike da Nishad'i RAMLART tace . "Zan koya masa rayuwa! Naga yanzu shi da soyayyarsa suna son su dawo mini jidali, ya kamata ace kowa ya ji da kansa, wannan lokaci nane." Takara sa maganar tare da juya wayarta, tana kallon hoton AA Turaki a profile picture dinsa, ta ɗan langwabar da kai tace. "In har ni Ramlart ce, sai na mallake zuciyar ka, babu wata ya' mace da zan bawa damar mallakar zuciyar ka, i promise u that, ta ƙarasa maganar tare da juya manyan idanun ta." Muryar DJ ya ne ya ɗaga wajen da sauti, nan take suka sake shiga cikin nishaɗi. Sannan Ramlart ta miƙe da ƙarfi ta fara rawa a dance floor, tana janyo hankulan mutane, zuwa kanta. Zuly ce tayi dariya tare da kallon al'ameen dake manne a jikin ta, cikin narke wa tace masa baby. "Yau dole club ɗin nan ya ƙonu da sunan mu!" Sabida babbar yarinya ta baiyana, murmurmushi al'ameen yamata tare da ci gaba da shafa jikin ta. Hasken disco lights na ta yawo, music mai ratsa jiki yana tashi. Dancers sun cika dance floor, ana rawa da annashuwa. Ramlart na tsakiya cikin masu rawa, tana juya jiki da salon rawa mai jawo hankalin mai kallon ta, Hannunta a sama, idonta a rufe, tana jin music din har cikin zuciyar ta. Wani gaye, kyakyawa, cikin kaya masu tsada yana zaune a VIP table yana shan drink. Daga can yana hango Ramlart, a hankali ya tsaya kallon ta yana murmushi, a lokaci guda yana kai drink bakin sa yace. “Wannan cikar ba zata kubuta ba a daren nan dole ne na kasan ce yare da ita.” Cike da boomcing Ya mike ya nufo dance floor kai tsaye, yana tafiya yana bubbudawa, kamar wani sarki, sai Da ya ƙarasa kusa da Ramlart sai ya ɗan tabo hannunta a hankali Ramlart ta buɗe ido ta kalle shi, sai ya ɗan yi mata murmurmushi tare da rage sautin Muryar shi kamar mai rada yace. “Ni da ke sai mun karya wannan dance floor tare in ba damuwa ina son muyi dancing tare.” Ramlart ta yi murmushi, sai ta bashi hannun ta, Suka fara rawa tare, jikin ta a jikin sa. Music yana ta Kara karfin sauti, A hankali sai ya sanya bakin sa a kunnenta yana cewa. “Na shirya baki daren da bazaki taba mantawa da shi ba in kin shirya let's go…” A haka ya rika janta zuwa VIP section, inda aka kawata shi da curtains masu haske da d'aukar hankali ,nan fa ya shiga romancing din ta cike da kwarewa, a haka ramlart ta fita daga cikin haiyacin ta, har ya samu nasara ya biya bukatar sa, da ita, Bayan mintuna kadan, ramlart ta fito daga wajen gashinta sun dan bazu, murmushi take cike da gamsuwa. Ramlart tana shirye-shiryen tafiya, tana gyara dan kwalin ta da d'an lullubin veil din ta, Gayen yana tsaye yana kallon ta da murmushi, yana da confidence irin na wanda yasan ta kan bariki, Wurin shiru ne, fitilar lounge din na launin ruwan hoda da blue suna ba da haske na musamman , wanda yake kara musu shauqi. A hankali yake matsowa kusa da ita, yana kallon ta cike da shauki , yace. "Kin cancanci fiye da haka, Ramlart… amma na bar miki wani abu a matsayin tunawa da wannan daren." Ya ciro wata bundle na kudin kasashen waje – euro da dollars – ya saka a hannunta, sannan yace . "Ga wannan… just for your time and your shine." Ramlart ta karba, tana murmushi tana kallon sa da murmushin da ta saba amfani da shi wajen nuna farin ciki da yaudara. Cikin d'an basarwa ramlart tace. "Wannan fa ?." Ya dauko wata karamar card mai sheki, ya mika mata. Akan card din: sunansa, lambar waya, da adireshin email ne. Kallon ramlart yayi yace. "Sunana Majeed Ibrahim Jatau, kuma mahaifina shine Honourable Senator Ibrahim Jatau – sanannen dan siyasa a kasar nan." Ramlart ta zaro ido waje, sai kuma ta saki murmushi cike da farin ciki da burin sabuwar hanyar daukaka da ta zo mata a cikin sauki. Tace. "Oh wow… nice to meet you, Majeed." MAJEED ne ya Dan matso kusa da ita. "Kuma wannan – card ɗin nan – ya bude miki kowanne kofa idan kina bukatar wani abu let me know." Yana gama fada'r haka Ya lumshe ido yana sumbatar goshin kafin yace. "Let’s say this is not goodbye… it’s just the beginning." Ya juya cikin class, na yara marassa jin magana, ya bud'e mota ya shiga. Ramlart ta tsaya tana kallon bayan motar na barin wajen, tana lumshe ido cike da tunani da wani sabon tunani a cikin ranta. Zuly na jiran ta a gefe tana mata dariya. “Na faɗa miki... wannan shine maganin ciwon tunani, amma kinbi zaki kashe kanki a banza akan wani da namiji.” RAMLART ce ta busa iska a bakin ta tare da cewa . “Hmmm, ai yanzu naji sauƙi. Let’s go... kafin wancan mutumin ya tashi ya san bana cikin gidan.” Haka al'ameen ya yi driving d'in su, Suna isa bakin gate na gidan, Ramlart Ta gyara shigar ta, ta feshe jikin ta da turare sannan ta ɗan dafa hannun ta a jikin k'ofar motan. ZULY ce ta sheke da Wani irin dariya tace. “Ki tabbatar baki bar wani alamar da zata nuna cewa kin fita, club.” RAMLART ce ta juyo tana kallon Zuly tace. “Don’t worry. Nasan gidan nan fiye da yadda su ke tunani. Allah ya saka da alheri Zuly.” ZULY ce ta daga gira tana dariya tace. “Alherin club ko? Hahaha... Mun kusa cin nasara, bestie.” Ramlart ta yi sallama da su, ta rufe kofar mota sannan ta ratsa ta bayan wani bangon ginin gidan inda take da wata sirrin hanya ta musamman da take shiga daga baya ba tare da an lura da ita ba, ta yi wuff ta shige ciki, A hankali, ta shiga gidan cikin nutsuwa tana duba gefe da gefen ta domin tabbatar da cewa kowa yana bacci, babu wanda ya ganta. A dai-dai lokacin, ake kiran sallan asuba ya fara tashi daga masallacin anguwa dana cikin gidan AA Turaki, Gidan na cikin shiru, haka Ramlart ta kutsa kanta zuwa part ɗinta tana mai sauke ajiyar zuciya, dayiwa Allah godiya, naganin babu wani mahluqi da ya ganta. Bayan shigan ramlart Cikin dakin ta, ta cire veil da takalman ta high heels dinta sannan ta zauna akan gado tana kallon kyautar kudaden da Majeed ya bata da card ɗinsa. Wani murmushin jin dadi ne ya subuce a saman fiskarta a hankali ta furta. “Senator’s son… hmm. Ramlart, kin soma samun hanyar da zata sa ki mallaki duniya, yadda kike so.” Batare da ta gabatar da sallan asuba ba ta kwanta. Ba da jimawa ba, barci mai nauyi ya dauke ta. 💫 ƘAUNA DA KADDARAH 💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣1️⃣ Da gari yawaye, Ramlart na kwance akan gado tana kallon katin da Majeed ya bata. Ta duba sunansa a jikin katin: “Majeed Ibrahim Jatau– Son of Senator Ibrahim jatau, CEO MJ Holdings”. A gefe, an nannade wasu daloli da euros cikin wata leda mai kyau, ta sanya hannu ta d'auke su. Wani irin shewa RAMLART tayi tace. “CEO... kuma ɗan Senator... Hmmm! Wannan kam dama ce da ba zan bari ta wuce ni ba. In na rasa soyayyar ka, tabbas zanso nayi gogayyah da kai a wajen tara dukiya.” Tana gama fada'r haka ta miƙe, ta nufi mirror tana kallon kanta. Tana murmushi da gamsuwa da kyan jikinta, wayar ta ta dauka Ta latsa layin Zuly, cikin magagin bacci zuly ta d'auki wayar. RAMLART ne ta ce da Zuly ... “Zuly... This guy is different. Yana da kudi, yana da matsayi, kuma yasan yadda ake treating mace. Ya bani cash da card... Can you imagine? Card!” Dariya ZULY tayi tace.. “Toh fa! Kin ga kuwa muna kama hanyan, zama billionaires Yanzu sai ki dinga kula sosai, ki ƙara burgeshi – you never know, maybe kin samu sabon rayuwa daga can, kinga kema zaki shiga cikin jerin manyan, matan da za'a dinga gogayyah da su a kasar nan, kinga gara ki tsaya da kafafun ki kema.” RAMLART ce tace “Wallahi! Pha Ni dai yanzu zan dinga zama on standby. Daga Turaki sai Majeed. Duniya daɗi, kinga na jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya.” Tana fad'ar haka Ta kashe wayar tana dariya, sannan ta nannaɗe katin da kudaden, ta saka a cikin drawer dinta na sirri. Ta haye gado tana murmushi cike da farin cikin irin kamun da tayi. GWARİNPA ESTATE Yamma ce sakaliya mai cike da Wani irin iska mai d'auke da sanyi, Dr. Farida ce ta dawo gida cikin gajiya amma fuskarta na dauke da murmushi mai kwantar da zuciyar ,mai kallon ta, Tana daure da hijabi fari mai laushi, ta shiga falon gidan hannun ta na d'auke da jakar ta. DADA ce ta fito daga daki " Lale maraba da likita bokan turai, sannu da zuwa ya masu jinyan." DR. FARIDA ce ta zauna a kusa da ita tace.. "Alhamdulillah Dada, wallahi naji dadin ganin Hajja ta samu sauki. Tayi responding da kyau sosai, kuma cikakken hanzari ne yasa ba ta shiga koma baya ba." Murmurmushi DADA tayi tace.. "Allah yayi miki albarka, Allah ya kara kare ki daga sharrin masu sharri." Ameen dada'amm cewar Dr Farida. Ameer ne ya shigo cikin falon, yana dariya fiskar sa dauke da walwala yace. "Ummi na, please… kice zamu fita yau! Kinga jiya Na gama exams, kuma yau Saturday ne!" DR. FARIDA ce ta kalleshi da gajiya d'auke a saman fiskan ta amma hakan baisa murmushin saman fiskarta bacewa ba. "Ameer ka bari gobe mana… Dada na gaji sosai." AMEER ne ya hada hannuwansa alamar yana roƙon ta yace . "Wallahi na yi alkawari da friend dina Ahmed! Dan Allah Ummi, koda minti talatin ne." DADA ce ta kalli Dr Farida tace. "To ki yi hakuri, ki kaishi mana, Bawan Allah yana jin dadin fita dake sai dai baki da lokacin sa." Dr. Farida ta mike, ta nufi dakin ta domin canza kaya. Bayan lokaci kadan ta fito cikin simple gown mai launin blue sky, hijabi ta d'aura a akai wanda hakan ba karamin fito da ainihin kyanta yayi ba. Murmurmushi DR. FARIDA tayi tace.. "To mu tafi… Amma wallahi minti talatin d'in kawai." Haka sukayi bankwana da Dada sannan suka fita. Ameer ya bude mata motar, suka shiga ,Suka nufi wajen shan ice cream da fiskar su d'auke da dariya Nishad'i suna Dan taba hira tsakanin uwa da ɗa. MAITAMA PARK Ameer na shan ice cream cike da annashuwa yayin da Dr. Farida ke dan shakatawa a gefenta tana kallon sa tana murmushi. wayarta ce ta fara ringing – emergency call daga hospital. DR. FARIDA ta kalli sunan da ke kan screen din, ta d'an daure fuskar ta dan batayi tsammani ba. "Ohh… My God." AMEER ne yace "Who’s calling Ummi?" A hankali DR. FARIDA tace: "Hospital ne, emergency ne. Amma…" Cike da farin cikin jin hakan AMEER yace . "Zamu je?! Zamu je asibitin da kike aiki?! Yessss!" *Ta d'an kalle sa da mamakin yan da taga yana murna, sannan ta girgiza kai da dariya a saman fiskarta tace. "To shikenan. Amma ka yimini alƙawari, bazaka sani headache ba, zaka nitsu bana son fitinah." AMEER ne yace. "Yes ummi nayi Alkawari!" Haka ta shiga Motar ta ta juya da sauri, ta d'auki hanyar da zata kaisu hospital, duk da cewa ba haka Dr. Farida ta tsara ranar ta ba. Amma ya zatayi, haka taci gaba da driving d'in su, shi dai Ameer sai murna yakeyi for the first time da zai je asibitin da ummin sa take aiki , sabi da haka ya kasance cikin farin ciki. Bayan wani lokaci, Dr. Farida ta kammala duba marar lafiyan da da aka kawo a bangaren gaggawa wato emergency Ward. Hannunta dauke da medical file, fuskarta cike da gajiya amma annurin fiskar ta yana nan bai bace ba. Tana tafe a hankali tare da Ameer a gefen ta, wanda ke kallon kowane sashe na asibitin cike da sha'awa. dakin da Hajja ke kwance Suka nufa, bayan an mayar da ita VIP room saboda saukin ciwon da tafara samu. AA Turaki na zaune a gefen gadon, cikin manyan kaya masu tsari, fuskar sa cike da nutsuwa, amma akwai alamun damuwa, a tattare da ita. PA dinsa, tsaye a gefe yana duba wayar sa lokaci-lokaci. A gefen gadon, Hajja na zaune cikin rigar asibiti, tana dan dariya da alama wata maganar ce ta sata dariya d'an hira suke d'an tab'awa ita da d'an nata. gently,sukaji ana buga kofar dakin, a hankali kuma aka turo kofar. DR. FARIDA ce ta shigo cikin murya mai sanyi tace: "Assalamu Alaikum." HAJJA ce ta washe baki , fiskar ta d'auke da farin ciki ganin ta, tace: "Wa alaikumus salam. Masha Allahu! Gata nan! Doctor Farida… laleh maraba da yâr albarka!" Cike da sakin fiska Dr. Farida ta karaso , sannan ta matsa kusa da Hajja tana kallon fuskar ta , cikin sakin fiska tace "Alhamdulillah, naji dadin ganin ki cikin walwala, Hajja. Hakan Yana nuna alamar sauki yafara samuwa, alhmdullah!." HAJJA ce ta kamo hannunta, tace: "Ke kika cancanci godiya. Allah ya saka miki da alkhairi. Nagode kwarai da gaske , Allah yayi albarka." Cike da girmamawa Dr Farida tace. "Ameen Hajja nima nagode da addu'a". AA Turaki ne ya dago kai yana d'an kallon su. Jin yanda Hajja ta sake da wannan likitar saikace sunjima da sanin juna. A dai dai wanna lokacin ne Ameer ya shigo d'akin bakin sa dauke da yar karamar sallama, daman ya dan shiga restroom ne , shiyasa Dr Farida ta fad'a masa numbern dakin da zai same ta in ya fito. Hajja ce ta d'an juyo ta kalleshi, tare da cewa. "Shi kuma wanene wannan yaron wa yake nema a nan?" Dr. Farida ce ta kalli Ameer, ta dan sosa gefen kanta tace. "Danane… Sunansa Ameer." Hajja ce ta washe baki tare da sake kallon Ameer tana murmushi tace. "Ay mashaa Allah. Yaron ki ne, Abu yayi kyau, Kai yaro, zo nan."ta karasa maganar tare da yafito Ameer da hannun ta da baya d'auke da drip. Cike da ladabi Ameer ya karaso , ya gaishe da ita. Hajja ta amsa cike da fara'a a saman fiskar ta tace . "Allah ya raya shi ya sa ya zama abin alfahari kamar mahaifiyarsa." Murmurmushi Dr. Farida tayi tare da zama a kusa da Hajja, tana kallon result din na'urar dake recording din lafiyarta. A hankali Dr Farida ta Kalli Hajja tace. "Masha Allah, an samu cigaba sosai jiki na ta samun lafiya, may be nan da dan wani lokaci za a iya discharge d'in ki , sai kici gaba da karb'an drugs daga gida". Hajja ce tace "alhmdullah nagode wa Allah, kin ga yanzu ya ke cemin ya kama ta a sallame ni haka , kin san shi yafi son a kula dani a gida, Hajja ta karasa magabar cike da barkwan ci". Jin abun da Hajja ta fada ne yasa Dr Farida ta d'an juya ta kalla direction da Hajja ta nuna mata da yatsa. Wani irin dumm dumm gaban ta ya yanke yafad'i , ganin mutum , a zaune a gefe d'aya, fiskarnan a murtuke ba alamar fara'a kan sa a sunkuye sai danna wayar sa yake hankali konce kamar ma baisan da wanzuwar su a cikin d'akin ba. Sani PA dinsa na tsaye a dan gefe da shi. Ameer ya kalli wajen shima, sake rufe idanun sa yayi ya kara bud'e su, ganin kamar a mafarki ,yau gashi ga role model din sa a go aban sa zahiri muraran ba a cikin TV ba ,kamar yanda ya saba ganin hirarrakin sa a gidajen tv, da sauri ya matso kusa da AA Turaki cikin ladabi, jin dadi yace. "Good morning, sir." Cikin mamaki AA Turaki ya dago kai , yana kallon yaron. Wani kyakkyawan yaro ya gani a tsaye a gaban sa , bai san san da wani murmushi mai nauyi da kwarjini da annuri ya bayyana a saman fuskarsa,ba, cikin nitsuwa da kamewa yace. "Good morning, young man, how are you doing. Cikin murna Ameer yace. "I'm fine sir." "Kullum ina kallonka a TV Sir , yau kuma gashi na gan ka da ido. Kai ne Mr. AA Turaki, ?" Ya karasa maganar cikin sigar shirme irin na yara masu kananun shekaru. Wani irni cute smile ya sake masa.Wannan karon murmushin nasa ya kara bayyana, sosai har Dr. Farida da ke gefe ta kura masa ido ba tare da tasan da hakan ba,tana mamakin yadda fuskar sa ta canza da annuri, a lokaci guda.Ganin haka, sai ta dan janye idonta cikin kunya, ta kawar da kanta gefe. AA TURAKI yana kallon Ameer, yace Mr young man: "To ya sunanka?" Cike da farin ciki AMEER yace sunana. "Ameer." AA TURAKI ne ya dan shafa kan shi kafin yace: "Ameer... Nice name, kana da guts. Me kake so ka zama nan gaba?" Ya jiho masa tambayar a bazata . Wani irin dad'i ne ya ziyarci AMEER jin tambayar da AA Turaki ya ke masa, cike da yaranta yace: "Ni ma ina so in zama business tycoon kamar kai. In yi kasuwanci a duniya, in taimaka wa mutane da yawa." AA Turaki ne ya dago hannun sa ya dafa kafadar Ameer, cikin murmushi wanda ya ke fitowa daga kasar, zuciyar shi. Hajja ce ta kalle su, idonta cike da mamaki d'an nata ganin ya sake da yaron a lokaci guda, ji tayi Ameer ya sake kwanta mata a rai, sai taji ina ma ace Ameer jikanta ne. Tun shekaru 21 da suka wuce baya bata sake ganin murmushin a saman fuskarsa ba sai yau da ya had'u da Ameer.Wannan yarinya... da yaron nan, suna da wani abu mai karfi a tattare da su.” nan taji Dr Farida ta dad'a burgeta. Cikin nitsuwa, AA Turaki ya zaro wallet dinsa ya dauko bandir din kudi da wani card mai design dake d'auke da sunansa na Musamman. Ya mika wa Ameer, tare da ce masa. "Ka rike wannan. Za ka iya tuntubata duk lokacin da kake bukatar shawara. Na yarda kai yaro ne mai cike da buri." Cikin farin ciki Ameer ya karba ,a lokaci guda ya ruga da gudu ya rungume Dr. Farida yana fadin “Thank you, Ummi!” yau kinsa na had'u da roll model d'ina. Hajja ce ta kalli Dr Farida da murmushi, d'auke a saman fiskan ta,cikin tausayi ta ce: "Doctor, dan Allah... wa ya haifi wannan yaro? Ina son in san mahaifinsa." Haka kawai naji kun kwantamin a rai, ina jin Ameer kamar jikana wlh. Dr. Farida ta dan saki numfashi, ta sosa gefen gashinta cikin nutsuwa tace. "Mahaifin sa Ya rasu tun yana karami... A yanzu ni da mahaifiyata muke kula da shi." Hajja ta dafe zuciyarta cike da tausayawa, tace . "Subhanallahi...!Allah ya jikansa. Yaro irin wannan... dole ka yi alfahari da shi." Nasan da mahaifin shi yana raye shima zai yi alfahari da shi. Jin yanda Hajja ta dage tana ta zuba surutu ne yasa ,AA Turaki ya mike tsaye tare da PA dinsa. yana kallon Hajja yace . "Hajja Zan dawo daga baya , ki huta, lafiya." Ya da. matsa kad'an,ya kalli Ameer da murmushi, kad'an sannan ya daga masa hannu, irin bye bye d'in nan sannan yace . "Be good, Ameer. Ka kula da kanka sosai." Dariya AMEER yayi yace "Yes sir!" Bai sake cewa komai ba, daga haka Suka fita tare da PA dinsa, yana tafiya cike da wani nau’in annuri da su kan su bodyguard din sa ba su saba gani a tare da shi ba. 💫 ƘAUNA DA KADDARA💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣2️⃣ Zaune yake a cikin babban falon sa, ya lumshe idanun sa yana nazari. Wayarsa na riƙe a hannunsa , tunani yake yi a game da ciwon Hajja , jin wayar sa ta fara ringing ne ya sa shi bud'e kyawawan idanun nashi a hankali ya duba wayar , ganin sani PA ne ke kiran nashi yasa shi yin picking call din cikin girmamawa PA ya gaishe shi,bayan gaisuwar ne ya d'aura da cewa. "Mun samu access din CCTV footage na kitchen din Hajja! Kamar yadda ka bukaci a duba ranar da Hajja ta kwanta ciwo..." A hankali ya sauk'e ajiyar Zuciya, cikin wata irin Murya yace. "Ina bukatar flash drive d'in yanzu". Yana gama fada'r haka ya kashe wayar, ba a fi minti biyu ba sai ga sallaman PA, bayan ya samu izinin shigowa ne , ya mika masa wani flash drive yana fadin: "Yes sir, an aiko mini da shi kai tsaye daga Head of Security. Ba wanda ya san da wannan footage din." Ganin ya karb'a flash d'in ne yasa sani PA yimasa sallama ya wuce. Karb'ar flash d'in yayi tare da saka flash din a laptop din sa, dake ajiye a table din dake gaban sa. A hankali ya latsa play. Kamera ta dauki cikakken lokacin da aka dafa tea na Hajja. Sai gashi a cikin video, ya bayyana mace sanye da veil ,tana had'a tea. Ta zuba wani abu a cikin flask din tea, ta juya ba tare da an hango fuskarta sosai ba. A hankali , ya kame zuciyarsa, ya saki Wani irin huci, baya son hasashen shi ya zama gaskiya, matsa play forward yayi tare da sake zubawa laptop din idanun sa... A lokacin da ta juyo kafin ta fita dağa cikin kitchen din, fuskar ta bayyana kadan , Wani irin bugawa zuciyar sa tayi, tabbas wannan fiskar Ramlart ce, hasashen sa ya zama gaskiya baya bukatan karin bayani. A hankali,ya dağa kansa yana jin jikin sa ya dau sanyi. Zuciyarsa ta na wani irin bugawa da karfi. Idanunsa sun kada, a lokaci guda,hannunsa ya dunk'ule da karfin gaske, yana jin kamar ya fashe da ihu, ko zai ji saukin abunda ya taru masa a cikin Zuciya. Magana yake da zuciyar sa "Ramlart...? Me Hajja ta mata take son hanlakata...? " Ya dafe kansa, dake barazanar fashewa.Duniya ta fara juyawa a idanunsa. Hankalinsa ya tashi. A lokaci guda, ya gane cewa rayuwar, Hajja ya shiga cikin hadari , tabbass in dai har ramlart zata iya aika tawa Hajja haka tabbas mata ba abun yarda bane duba da yanda Hajja take son ta, hasalima ita ce tayi sanadiyar auren su, don shi baiga abunda zaiyi da ramlart ba, ya aure tane bisa umarnin Hajja amma kuma abun da yagani ya basa mamaki, meya sa Ramlart ta ke son cutar da Hajja tabbas akoi wani abu daya kamata ya sani . Jin ana kiran sallan azahar ne yasa ya tashi, ya nufi toilet din dake cikin falon, alwala yayi yafito, ba bata lokaci ya nufi masallacin dake cikin gidan ,inda anan ne yake sallah tare da sauran jama'ar unguwar in dai yana gari, to jam'i baya wuce shi. Yau takama Ranar Monday ne, a gidan Alhaji Abdullahi Turaki sun tashi da shirye shiryen, taryan mai gidan , Wato Alhaji Abdullahi Turaki a yaune jirgin sa zai sauka a Nigeria daga Saudiyya , dan ya kwashe kimanin wata daya kenan baya kasar yane yin Umrah, kuma a yau ne jirgin su zata sauka a Nnamdi Azikiwe international airport, hakan yasa kowani ma aikaci na cikin gidan ya ke kokarin ganin cewa ya kammala aiyukan sa a kan lokaci, duddah cewa har yanzu Hajja tana asibiti ba a sallamo ta ba. Hajja zaune a bakin gadon dake cikin VIP ward. Tana cikin shiga ta alfarma, ta cire kayan asibitin,fuskarta na cike da annuri , a gefe guda tana gudiya ga Allah da ya azurta ta da samun lafiya, bayan ta cire tsammani. Dr Farida ce ke rik'e da wasu, takardu cikin kulawa, take duba takardun. Hajja ta kalleta tace . "Likita, Allah ya saka da alheri, nagode kwarai da gaske. Gaskiya na ji daɗin irin kulawar da kika bani. Har cikin zuciyata na keji kamar ƴa ta ce ke." Wani irin cute smile Dr Farida ta sake tare da d'an lumshe idon ta, chan kasan zuciyarta tana jin wani irin sanyi yana ratsata a hankali tace: "Alhamdulillah Hajja. Ni ma na ji daɗin zamana tare da ke." Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana, nima kamar dadata nake Jin ki a raina. Hajja tace. "Zan so sanin inda kike zaune...ko zamu ci gaba da zumunci, kinga watarana zanga dadar taki nima, sai muyi zumunci, takarasa maganar fiskar ta d'auke da murmushi." da ɗan murmushi, Dr Farida tace: "Zan baki address ɗinmu Hajja, ai zumunci alheri ne, kuma dada ta zataji dad'i,kullum sai ta tambayeni jikin ki." Jin hakan ne yasa Hajja kara jin dad'i ,haka Dr Farida ta rubuta ma Hajja address dinta , karb'ar takardar Hajja tayi tare da bawa Lami mai aikinta ta saka mata shi a cikin jakarta. A dai dai lokacin, ne AA Turaki ya shigo cikin dakin, kamar kullum yauma yana sanye da wasu hadaddun fararen suit wanda aka kashe makudan kud'ad'e wajen sayan su, ba karamin kyau yayi ba, Sani PA ne a bayan sa, batare da ya Kalli kowa ba ya wuce wajen da Hajja take zaune direct, har kasa ya tsuguna ya gaishe ta, cike da farin cikin ganin shi Hajja ta shafa kanshi tare da jero masa addu'oi . Haka yasa su Lami suka kwashe duk wani abu da Hajja take bukata , sauran kayan kuma haka Hajja tace wa Dr Farida, arabawa mabukata. Dakan shi ya kama hannun Hajja haka ya riketa har jikin wata bakar mota Rolls Royce a hankali ya taimaka mata ta shiga, bayan ta shiga ne shima ,ya shiga ya zauna a gefen ta, haka motocin suka shiga tafiya a cikin nitsuwa, Hajja ce take dağawa Dr Farida hannu, dake tseye tana kallon tafiyan su Hajja. Haka kawai takejin son matar a cikin zuciyar ta duddah d'an nata sam bashi da hali sai na girman kai amma Allah ya gani itakam tana son tsohuwar, ganin motocin sun fita daga cikin harabar asibitin ne yasa Dr Farida ta juya domin komawa cikin Office din ta. 💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣3️⃣ Da misalin karfe 8 30pm na dare Babban falo na cikin gidan AA Turaki. Kowa yana zaune – Hajja, Alhaji Abdullahi Turaki, AA Turaki da Ramlart. cike da natsuwa, suke zaune da alama akoi wata muhimmiyar taron da zasu gabatar, ganin yanda kowa ya natsu ya bawa zaman muhimmanci. AA Turaki ya yi gyaran Murya,a lokaci guda yana kallon kowa da ke cikin falon, da idanun sa masu kaifin basira: "Alhmdulillah, nagode da ku ka halarci wannan zaman .Yana da muhimmanci a san gaskiya, musamman idan lafiyar mahaifiya ta shiga hadari, yana da muhimmanci, a san waye yake da alhakin faruwar hakan." Ramlart ce ta daure fuskar ta, hannunta na Wani irin rawa. Ta kama hijab dinta da karfi ta rike ,don boye damuwar ta. Hajja na kallonta,cike da mamakin ganin yanda yanayin ta ya sauya a lokaci guda, Alhaji Abdullahi ya zuba idanun sa cikin natsuwa, yana karewa kowa kalloh ,dan bakaramin mamaki ya shiga ba da aka sanar dashi cewa Hajja taci wani sinadari a cikin abinci, wanda hakan harya kaita ga kwanciya a asibiti, Dan haka ne ma ya sa shi ya dawo cikin gaggawa. AA Turaki ya juyo da remote, dauke a hannunsa ya danna yana cewa: "Ga wani abu da zan so kowa ya kalla..." Ya kunna TV, ya buɗe CCTV footage na kitchen na sashin Hajja. Kamar wutar lantarki ne ya d'auke a dakin – shiru ne ya ratsa ko ina. Ramlart ta saki wani ihu cikin firgici, ta kifa kanta a gwiwa tana rusa kuka. cikin kuka tace: "Wallahi... Sharrin shaidan ne... Na yi kuskure kuyafe mini!" Cike da mamaki da radadin zuciya Hajja da take cikin shock din abunda idanwan ta suke gane mata tace: "Ke ce? Ramlart... Me na miki har kika son kashe ni?" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Alhaji Abdullahi ne ya tashi tsaye, ya dube ta da idanu masu cike da rashin yarda, na yanda ramlart tayi disappointing nasa, yace. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Me nake gani haka ". AA Turaki ne ya natsu yana kallon mahaifinsa, cikin Wani irin murya yace. "Ina son ka min izini in sake ta. Wannan ba matar aure bace... Ba zan iya ci gaba da zama da ita ba." Ya karasa maganar cikin zafin rai. Hajja ce ta yunkuro tana share hawayen ta tace "Ni dai dama, na zaci ta kirki ce shiya sa na zaɓa maka ita , sabi da na yaba da hankalin ta!amma a yau ba zan hana Ka sake ta, ba Yero i!" Alhaji Turaki ne ya daga hannu, yace "A'a... a dakata da yanke hukunci. Wannan lamarin sai mun tattauna da iyayenta. Ba a yanke hukunci cikin fushi. Zamu tuntubi magabatan ta, in rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba." Alhaji Abdullahi cike da gargaɗi yace. "Ramlart, abin da kika aikata babbar fitina ce. Amma tun da kin karbi laifinki zamu ci gaba da bincike. Ba zamu yanke miki hukunci a cikin fushi ba." Hajja ce ta share hawayen ta, tare da cewa. "Ramlartu kinbani mamaki , amma kisani ba zan sake yarda da ke cikin sauƙi ba." *Ramlart ce ta rushe da kuka, ta rarrafa kusa da AA Turaki tana kokarin riƙe kafafun sa tace. "Don Allah... kayi hakuri. Ka bani dama na gyara..." Wani irin kallo AA Turaki ya jefa mata a lokaci guda ya miƙe, yana duban ta da tsananin bacin rai a fuskar sa Yace: "Ba ni da damar yanke hukunci yanzu... Kamar yan da Baffah ya ce ba za'a yanke miki hukunci a cikin fishi ba, amma nasan daya – bana jin zan iya sake aminta da ke a karo na biyu." Wani irin kuka mai karfi Ramlart ta saki . A bazata suka ji saukan muryan AA Turaki "Hajja kuyi hakuri amma ina son ramlart ta bar gidan nan har zuwa lokacin da Baffah ya gama binciken sa". Hajja da Alhaji Abdullahi Turaki suna gefe suna sauraron sa cikin mamaki da kulawa. Ramlart ta saki hawayen nadama tana kokarin yin magana, amma bakinta ya kasa furta komai. Cike da dottaku Alhaji Abdullahi Turaki yace. "Ramlartu, ki karɓi maganar mijinki da zuciya mai kyau. Ki koma gida, ki nutsu. Ki bani Lokaci na gana da iyayen ki kamar yanda suka bamu amanar ki Insha Allahu za a miki hukunci bisa adalci". Cikin kunar Zuciya Hajja tace. "Alhaji da kayi hakuri ka bar yaronnan ya sauwake mata, karfa kamanta rayuwata taso ta salwantar". Alhaji Abdullahi ne ya dagawa Hajja hannun alamar yagama yanke hukuncin sa. Ramlart ce ta miƙe a hankali, kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. juyawa tayi da kwalla a idonta, zuciyarta cike da rauni da mamakin irin wannan hukunci daga gidan da take tunanin tana da iko da shi, ta gama mallakar shi, shin tayaya ma tayi sakacin mantawa da cewa za'a iya samun CC camera a kitchen, haka ta ja kafafun ta ta wuce zuwa part din ta domin iban kayan ta da zata tafi da su, a gefe guda kowa zuciyar ta na cike da tsoro da fargaban abunda zata fad'awa iyayen ta. 💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣4️⃣ UNGUWAR WUSE II ABUJA Gida ne mai dauke da ginshiƙai masu salo na zamani . Alhaji Musa Ibrahim tsohon ma’aikacin gwamnati ne wanda yayi aiki har tsawon shekaru fiye da 30 a Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida kafin yayi ritaya. Mutum ne mai gaskiya, rikon amana da tsananin tsoron Allah. Bayan ritayarsa ya koma harkar koyarwa a masallacin unguwa da hidimar al’umma. Yana tare da matar sa Hajiya Rakiya, uwargidan Alhaji Musa, mace ce mai nutsuwa da kamun kai, ta taso da 'ya'yanta cikin tsantsar tarbiyyar addini da mutunci. Yaya biyu mata Allah ya azurta su da samu , Aunty hauwa da kuma autar ta ramlart,Ta kasance uwa ta gari, mai tausayi da hakuri, kullum cikin rokon Allah da yi wa 'ya'yanta fatan alheri. Tana da nutsuwa da girmama kowa da kowa, komai matsayinsa. A yanzu aunty hauwa tana gida a gaban iyayen ta tare da ya'yan ta guda biyu, sakamakon mijin ta da Allah yayiwa rasuwa kimanin watanni biyar dasu ka wuce, aunty hauwa macece mai sanyin hali da tsaron Allah, Şaban'ın ramlart da tun tashin ta ta kasance mai tsiwa da son abun duniya, amma a tashi d'aya baza ka taba gane hakan ba sai ka zauna da ita na tsawon lokaci, babu irin nasiha da fad'a da ba a mata a gidan shiya sa ma take badda sawo tana zuba iya shegen ta batare da sanin iyayen ta ba ita da aminiyar ta zuly. Misalin karfe 8 00am na safe a daidai lokacin da Ramlart ta iso gidan su da jaka a hannun ta. Fuskar ta cike da damuwa da tashin hankali, amma duddah hakan tana ƙoƙarin danne komai, bata son a fahimci hakan. Hajiya Rakiya zaune take A babban falon gidan, mata ce mai kamala tana sanye da hijabi, hannun ta na rike da littafi tana karatun Qur’ani. Alhaji musa, dattijo mai kamala yana zaune a gefen ta yana karanta jaridan daily trust. Agefe guda wasu yara biyu ne da ke wasa a gefe, suna ta ya'n tsalle tsallen su. Aunty Hauwa ce ta shigo daga kitchen tana ɗauke da tray, a hannun ta. A daidai lokacin ne ramlart ta turo k'ofar falon bakin ta d'auke da sallama. Aunty hauwa ce ta amsa mata tare da juyawa, ganin kanwar ta ne yasa ta saki wani murmurmushi tare dacewa. "Laa! Ramlart! Masha Allah, sannu da zuwa." Kece a gidan yau . Yaran ne suka tashi da murna suka rungume Ramlart suna ihun ganin ta tare da cewa. "Aunty Ramlart! Aunty Ramlart!" Oyoyohh. Mami dake karatun Qurani ne ta juyo jin irin ihun da yaran keyi na murnan ganin ramlart din, ganin ramlart da tayi da jakane yasa ta rufe littafin hannun ta tare da ajiye shi a gefen table d'in dake kusa da ita tace. "Ramlart? Lafiya kike tafe da sassafe haka ba tare da sanarwa ba?" Wani irin murmushin dole RAMLART ta ƙoƙarta ta kwakulo shi a fatar baki tace. "Wallahi Mami, kawai na gaji ne da komai. Ina bukatar hutu. Zuciyata na bukatar natsuwa, shine nace barin zo na ganku." Sai a lokacin ne Baba ya kalle ta sosai kafin yace "Ramlart, akwai abinda ke damunki. Ki gaya mana gaskiya. Mun san halinki."mu muka haifeki. RAMLART ce ta zauna a ƙasa, ta dora kai a gwiwar Mami tace . "Baba, Mami… babu wani abu. Komai dai dai yake. Ku yarda da magana ta hutawa nazoyi." Mami ce ta shafa bayanta, cikin hikima tace. "Ko da wani abu ne, ki sani iyayenki muna tare dake. Amma kina buƙatar fadin gaskiya don samun mafita, sabi da haka in akoi damuwa kisanar da mu." Wasu hawaye ne suka gan garo mata, RAMLART ta sa hannu ta ɗan share hawayen, tana kallon gefe, sabi da bata son su fahimta: "Na sani Mami... Amma yanzu ba zan iya ba. Kawai ku yarda dani." Ta karasa maganar cikin karfin hali yayin da zuciyarta ke cike da tsoro da nadama – amma har yanzu ba ta da ƙarfin fadin abinda ya faru, wa su baba , dan kuwa tasan kwanan zancen . Da misalin karfe 9 30pm na dare , falon ya lafa da hayaniya. Baba da Mami sun wuce ɗaki, yaran Aunty hauwa suna bacci, a d'akin su.Aunty Hauwa tana zaune da Ramlart a cikin falo, suna kallon wani series. Aunty Hauwa ne ta zuba mata ido, tana kallon fuskarta da ke nuna alamar damuwa da ƙin gaskata cewa komai lafiya yake kamar yadda tafad'awa iyayen nasu. Cikin murya mai rauni, cike da tausayi, Aunty hauwa tace: "Ramlart... Kince komai lafiya, amma ni ‘yar uwa ce gareki. Kina cikin wani irin hali... kuma duk duniya bayan iyayen mu ba wanda yake fahimtar ki sama dani, idan ba ki fad'a mini damuwar ki ba wazaki fad'a wa." Ramlart ta ɗan ɗaga ido, ta ƙara sadda kai Ƙasa, tana wasa da yatsun hannunta. "Wallahi Aunty... Ina jin Wani irin Abu a raina, amma bani da ƙarfin gaya muku komai." Cikin nazarin ta Aunty hauwa tace . "Toh ki saurari zuciyarki. Idan akwai wani abu da ke cutar da ke a ciki, wallahi bayan iyayen mu dani ‘yar uwar ki ba wanda zaki iya fad'awa damuwar ki. Duk abinda zai faru, kisani muna tare da ke . Amma kisani ita gaskiya zata iya fitar da ke daga cikin duhu." Jin abun da Aunty hauwa ta fad'a ne yasa Ramlart ta fashe da kuka, Aunty Hauwa ta rungume ta. Sai da ta dan yi kuka sosai kafin ta lafa, ta na ta sauke ajiyar Zuciya. Cikin sanyi murya RAMLART tace . "Aunty... Na shiga uku. Na aikata abu da har yanzu ban yarda da kaina ba... Amma ina jin tsoro, bana son su baba susani, in sunji zasuyi fishi dani." *(Aunty Hauwa ta dafa kanta, tana girgiza kai da tausayi.)* Aunty hauwa ce ta dafa kafadar ta tace . "Ina tare da ke, ko me kika aikata. Amma dole ne ki tunkari su baba da abin da kika aikata. Idan ba yanzu ba, gobe zai iya bayyana. Karki bari shaitan ya ci gaba da rinjayar ki a al amuran rayuwar ki." Ramlart ta share hawayenta, tana jinjina kai, alamar ta gamsu da maganar Aunty hauwa Baba ne zaune a gefen gadon sa Mami ne ke shafa masa man zafi a kafafun sa, sanye yake da farar jallabiya .Haske kadan ne a cikin ɗakin. Cikin nitsuwa Mami tace "Baban ramlart ,kasan fa har yanzu Ramlart bata ce mana komai ba akan dalilin zuwanta gida,kuma bata taba kwatanta hakan ba." Ajiyar Zuciya Baba ya sauke yace"Na lura da ita tun lokacin da ta zo. Da alama akwai abinda ke damunta amma tana boyewa." Cikin nitsuwa Mami tace: "Na tambaye ta cikin lallama, sai tace hutu kawai take bukata. Amma ni uwa ce, ina ji a zuciyata akwai wani abu fiye da hakan." Baba da ke kallon Mami yace: "In har akwai wata matsala tsakaninta da mijinta, zai fi kyau mu bar ta ta bayyana da kanta. Amma in hakan ya gagara, zan tuntub'i Alhaji Abdullahi Turki sai muji me ke tafiya." Mami ce ta dan girgiza kai tace: "Allah ya shiryeta. Ina fatan kar hakan da muke tsoro ne ya faru... kar dai zaman aurenta ya fara tangal-tangal." "Bana son kisaka damuwar komai a ranki Duka rayuwar jarabawa ce. Amma , dole mu yi addu’a sosai akan yaran mu." Cewar baba dake Shirin kwanciya dan tagama shafa masa man zafin. Mami ce tace "insha Allahu, Zan yi azumi gobe, in roki Allah ya warware mata komai. Koda akwai kuskuren ta, Allah ya gyara tsakaninsu, dan inaji ajiki na zuwan nata bana banza bane." Hakan yana da kyau Allah ya kaimu goben cewar baba. 💫 ƘAUNA DA KADDARA 💫 ✍️Mrs Alkali Page 1️⃣5️⃣ Misalin qarfe 5:30pm na yanma motar Alhaji Turaki ne ke shigowa harabar gidan, tare da ta AA Turaki, a yau bai dauko bodyguard din sa ba daga Motar su Hajja sai motar shi da driver ke jan shi a baya. Alhaji Musa da Mami suna zaune a falo, yayin da Ramlart take gefen Mami da hijab a jikinta, amma fuskarta cike da shakku da jin nauyin su don sun titsiyeta a gaba sai ta fad'a musu dalilin zuwan ta gidan. Jin an bud'e gate d'in gidan ne, ga kuma karan motoci alamar sun shigo harabar gidan ne ya sa baba ya daka ta da tambayar ramlart. Ba a jima ba suka ji an yi nocking din kafar falon, ramlart ce ta tashi da sauri ta nufi k'ofar falon dama tana Allah Allah tasa mu dama ta zullewa su baba sai gashi dama ta samu, bud'e k'ofar tayi batare da tayi tsammanin ganin sa ba ta ganshi tsaye a bakin k'ofar. Yayi shigar alfarma; yau babban riga fara wacce ta sha ɗinki na zamani, a jikin shi ,ga agogon Rolex mai uban tsada a hannun shi, wasu takalma half cover shoes black in colour masu tsada ne sanye a kafafun sa, ga wani sassanyan kamshin turare mai daɗin ƙamshi, da yaci ka wajen, a hankali ya tako , cikin nutsuwa da izza, fuskarsa cike da kwanciyar hankali da tsantsar kamewa. Kamar wani saraki, haka ya shigo cikin falon bakin sa dauke da sallama kasa kasa. Ramlart ce ta zuba masa ido, kamar yau ta fara ganin sa. Idanunta suna ƙara gaskata mata cewa babu wani da'namijin da ya kaisa kyau. zuciyarta ce ta buga da karfi, kamar ana buga gangar yaki. Har ya wuce ta bata sani ba Ta zuba masa idanu tanabin sa da kallo ba tare da ta iya ɗauke idanunta ba. tayi matuƙar rikicewa. A zuciyarta tana jin Wani irin ciwon son sa yana kara tasowa a cikin zuciyar ta. Jin sallama ne ya katse mata tunanin ta ganin Baffah da Hajja ne yasa ta sunkuyar da kanta kasa , zuciyar ta na dukan uku uku, shikenan tata ta kare, dan batayi zaton cewa yana tare da su Hajja ba. Cikin wani juyin zuciya, Ramlart ta daure ta sunkuyar da kai amma zuciyarta na mata kuna . Shi kam AA Turaki yana shiga cikin falon , ya gaishe da su Mami cikin mutunci da ladabi, suka gaisa da su baba. Sai dai ko ɗaya bai kalla inda Ramlart ta ke tsaye ba, da alama bai san ma da wanzuwar ta a wajen ba. hakan da yayi ya kara sosa ran Ramlart – a hankali ta dafe ƙirjin ta dake mata barazanar tarwatsewa, tana kokarin boye hawayen ta. A cikin zuciyarta, ta tabbatar da abu guda: soyayyar ta ga AA Turaki har yanzu ba ta mutu ba… kuma bazata iya rayuwa ba tare da shi ba. A lokacin da Hajja da Baffah suka ƙaraso cikin falon, Alhaji Musa, ne ya mike tsaye cikin murnar ganin su ,ya tarbe su da fara’a, ya rungume abokinsa Alhaji Abdullahi cike da farincikin ganin aminin nasa,Mami cikin murna da farin ciki ta gaida Hajja da fara’a. Aunty Hauwa ma tana falon tare da ‘ya’yanta haka suka gaisa da su Hajja cikin sakin fiska . Alhaji Musa yana murmushi yace: "Wallahi wannan ziyara da kuka kawo mana, ta faranta mana rai sosai. Mun ji daɗin ganinku." Cikin nitsuwa Hajja tace: "Mu ma muna godiya da irin karamcin ku. Mun zo ne saboda zumunci, da kuma wata muhimmiyar magana." AA Turaki yana zaune cikin nutsuwa, kai kace baya cikin falon yanda ya kame yana danna wayar sa kamar ma baya wajen, ga Hajiya ramlart dake rakube a gefe tana aikin kallon sa. Alhaji Abdullahi Turaki ne ya gyara zaman sa tare da cewa: "Alhaji Musa, Hajiya Rakiya… akwai wani al’amari mai nauyi da ya shafi ‘yar mu wato Ramlartu . Wani irin bugawa ƙirjin ramlart yayi ,har wani jiri jiri take ji yana kok'arin ibanta, da kyar ta iya seta kanta, duk wani addu'a da yazo bakin ta karantashi kawai takeyi, jin Baffah yaci gaba da cewa"Mun tabbatar da cewa ita ce ta sakawa Hajja wani sinadari a abinci, wanda hakan yayi sanadiyar kwanciyan Hajja a asibiti…" Kuma Likitocin sun gano hakan ne ta hanyar gwaji inda board na asibitin suka had'a meeting naganin cewa sun tsanan ta bincike angano mai laifin, ganin hakan ne yasa Aliyu ya nemi alfarma yadakatar da su inda ya tabbatar musu dacewa zai dauki mataki da kan sa, bayan bincike da aka gudanar ansamu ganin hoton Ramlartu ta cikin CC camera in da aka tabbatar da cewa ita ce ta aikata hakan ,hakan ne ma yasa mijin ta ya umarce ta da ta dawo gida, toh kaji wannan ne dalilin zuwan mu . Ai a lokacin baba ji yake kamar lokacin ya tsaya masa baya tafiya, kowa dake dakin yayi shiru har Aunty hauwa da ta cika musu gaban su da abubuwan motsa baki cike da mamaki suke kallon ramlart dake rakube a gefe kamar muna fuka. Ramlart na rakube a gefe, ta sunkuyar da kai kasa. Cikin fishi Alhaji Musa ya kalle ta fiskar nan babu alamar rahama a tattare da ita cikin tsawa yace. "Ramlart! Wannan ai ba laifi bane kawai, wannan keta mutunci ne da rashin hankali! Abinda kika aikata ya wuce a yafe miki da cikin sauki, kisan kai fa kike kok'arin yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un baba ya kara maganar cike da rauni." Cikin kuka Mami tace"Na yarda da tarbiyyar da muka baki ba haka take ba. Me ya rinjaye ki har kika aikata hakan?" Cikin bacin rai Aunty Hauwa ta matso tare da zabga mata wani lafiyayyan mari, wan da yasa jinta ya d'auke na wucen gadi, ta sake dağa hannun ta zata sake zabga mata taji Baffah yace kull kull hauwa'u barta haka, ai shi duka baya gyara sai dai ma ya sake lalatawa dan haka addu'a zaki mata, Wani irin kallon zamu had'u Aunty hauwa ta mata tare da cewa. "Na rasa dalilin da zai sa ki hallaka kanki da hannunki. Wannan kuskure ne babba!, kuma ina mai tabbatar miki da sai kin girbi abunda kika shuka." Cikin miryan kuka Ramlart tace "Na tuba… na yarda da kuskurena. Don Allah ku yafe mini…wlh sharrin shaidan ne bazan karaba wlh na tuba." Cike da ta kaicin ta Alhaji Musa ya juya zuwa ga Alhaji Abdullahi Turaki yace ."Wallahi in har wannan abun ramlart ta aikata , to sai dai ta zauna a nan gidan. Ina son Ka umarci Aliyu da ya sauwake mata ta dawo nan ta zauna … tunda ta zubar da mutuncin ta." Cike da jin nauyin shi Alhaji Abdullahi Turaki yace "Alhaji, ba karamin nauyi na ji ba, dana kawo maganar gaban ku sai dai kuwa ba yadda zanyi ne ya zama dole kusan da maganar a matsayin ku na iyayeh a gare ta. Amma ina rokon ku daku dubi girman zumunci, da girman mutuncin mu, ku yafe mata. Mu ma muna bakin cikin faruwar hakan. Amma in ba damuwa, a bata dama ta biyu ta gyara. Allah yana yafe wa bawansa, mu ma mu yafe mata, hakan zai sata ta gyara kura kuran ta na baya." Hajja ce ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli AA Turaki wanda bai ce komai ba, kamar ma wanda baiya wajen. Cikin nitsuwa Hajja tace "To… kamar dai yadda Alhaji ya fad'a Allah ma muna masa laifi ya yafe mana bare kuma ace mu bayin sa , dan haka nima na yafewa ramlartu ,Amma fa wannan kuskuren ba ƙarami bane, sabi da haka saita kiyaye gaba duddah har yanzu bamu san dalilin ta na aikata hakan ba." Shi dai AA Turaki bai ce komai ba, sai ma wayar sa da ya ci gaba da dannawa, amma a chan cikin kasan zuciyar sa bakaramin haushi yake ji ba, a zaton sa Hajja zata sa ya rabu da ramlart amma sai gashi sun buge da yafe mata, duddah iyayen ramlart sun chanchan ci fiye da haka a wajen su dan ba karamin girmama su yake ba sabi da karamci irin nasu, sai dai duddah haka albasa batai halin ruwa ba. Cike da borin kunya Ramlart ta taso ta durƙushe a gaban iyayenta da iyayen mijinta, fuskarta cike da hawaye. cikin rawar murya tace"Na gode… Na gode da wannan dama da kuka bani. Nasan Ban cancanta ba, amma duddah haka kun yafe mini. Allah ya saka da alheri, zan gyara halayena, wallahi zan gyara..." Hajja ta tab'e baki tace"ai kuwa kam gara Ki gyara Ramlart, kada ki sake kuskuren da zai sa mu zubar da hawaye saboda ke anan gaba." Cike da tsantsar girmama wa Alhaji Musa kalle su yace "To amma ina da wani sharadi. Ramlart ba zata koma gidan mijinta yanzu ba. Zata zauna a nan gidan tare da mu na wani lokaci... har sai Aliyu ya sami wata matar da zai aura. Na yi alkawari , zan nema masa auren mace ta gari. Sai ya auri wata, sannan sai Ramlart ta koma d'akin ta Wannan shine hukuncina a gare ta." A hankali AA Turaki ya d'ago ido ya kalli iyayen nashi a karo na farko tunda ya zauna a falon cikin shiru, zuciyarsa cike da rudani da nauyi, jin hukuncin da Baba ya sake yankewa, Hajja ta kalleshi da damuwa dauke a saman fiskan ta sabi da tasan an sake jefa rayuwar d'an ta a cikin tsaka mai wuya, tana tuna auren Ramlartu ma da yaya ya amince bare kuma wani auren a karo na biyu. Cikin hikima Hajja tace"Alhaji Musa, wannan hukunci mai nauyi ne, amma ka nuna mana karamci da adalci. Allah ya saka da alheri." Alhaji Abdullahi Turaki ya gyara zama kafin yace"Mun amince da hukuncin ka, kuma muna godiya da fahimta da muma karɓan uzurin mu da kayi." Baffah ne ya Kalli Aliyu ya ce"ina ce kaji hukuncin da mahaifin ku ya yanke, ina fatan ka fito da matar auren ba da jimawa ba". AA Turaki ne ya ɗago ido ya na kallon kowa, dake cikin falon ba tare da furta kalma ba, ya sauke kan sa kasa, A zuciyarsa kuwa, ya kudirta cewa kasar ma zai bari gaba daya… ba auren da yake so, kuma zuciyarsa har yanzu cike take rauni da kuma dacin abun da yafaru da shi a shekarun baya, sabi da haka bazai yadda ya sake wani auren ba. Ita kam ramlart duddah hukuncin da Baba ya yanke bai mata dad'i ba amma a hakan ta daure zuciyar ta dan tasan taci darajar su Baffah ne da yanzu ba wannan maganar ake ba , duddah tana tunanin cewa su baba basu hakura ba, ga Mami dake gefe guda tana ta kuka tun d'azu da taji abunda ramlart d'in ta aikata, Aunty hauwa ma tana zaune a gefe tana hararan ramlart d'in, da ba don idon su Hajja ba da sai jikin ta ya gaya mata a hannun ta yanzu ma bata tsira ba jira take su Hajja su tafi . Bayan Wani lokaci su Baffah suka musu sallama, haka su rabu cikin mutunci da girmama juna. Bayan tafiyan su Hajja ne Mami tasa Aunty hauwa ta jarawa ramlart zama dan acewar dama jira take su Hajja su tafi, babu bata lokaci Aunty hauwa dake jin haushin ta tafara sauk'e mata gajiya ,duk abunda ake yi baba bai hana ba hasali ma yaji dad'in hakan, bayan Aunty hauwa ta gama kumburawa ramlart jiki ne , Baba ya sake kafa mata sharrudan shi, yace duk wani aiyukan gidan daga yau itace maiyin su, hatta da sharan tsakar gidan nasu, haka ramlart ta ja jikin ta ta wuce d'akin ta jikin ta duk ya mata tsami. 🔚 ƘARSHEN FREE PAGES! _Ahamdulillah, a nan nakawo ƙarshen Free pages... Amma tambayar ita ce:_ Shin ƙauna zata iya shawo kan kaddara? Ko kuwa kaddara ce zata wargaza ƙauna? 😢💔 Wane mataki AA Turaki zai ɗauka bayan sake ganinta? Shin wace yarinya ne AA turaki yake yawan mafarkin ta ? Shin zai sake had'uwa da ita shin wace kaddarah ce ya ke gudu? Ramlart zata iya samun yafiya daga zuciyar AA Turaki? Shine da gaske ramlart tayi nadama? Shin Ya alak'ar ramlar da majeed İbrahim jatau? Shin sabuwar soyayya zata iya dinke tsohuwar rauni? Ko kuwa sabon masoyi zai bayyana daga inda bamu zata ba? Shin AA turaki zai sake aure a karo na biyu? Shin wacece Dr Farida? Mene yake kunshe a cikin rayuwar shin da gaske Ameer dan ta ne? Shin zata auri Dr İmam? Shin wani sirri ne su Hajja su ka boye shekaru 21 baya? Mene musabbabin ciwon zuciyar AA turaki? Shin wannan ƙaddarar soyayya ce ko hukunci? Shin da zuciya Daya zuly take son ramlart? 🔥 *Zuciyoyin ku na da ƙarfi?* _Toh ku shirya domin zuwan sassan da za su girgiza zuciya, su tada hankali, su raunana jiki…_ *📌PAID PAGES sun kusa farawa immediately zamu fara!* 📍Farashin littafi: *₦500 kachal!* 📍PROMO: *₦300* kacal nan da sabuwar shekara! *🟢Zaki iya Biyan kuɗin ki ta: 7025348616 (Opay – Sakina Ahmad Musa)* *📲 A turo shaidar biyan kudin ta WhatsApp: 07025348616* Kokuma kije arewapen ki biya ki karanta complete. 👇👇👇👇👇👇👇 https://arewapen.com/u/mrsalkali01 1. Idan kai ne AA Turaki, zaka iya yafe wa macen da ta kusan halaka mahaifiyarka? 2. Wane hukunci kaddara zata yanke tsakanin ƙauna da laifi? 3. Shin yafe wa alamar rauni ne ko ƙarfin zuciya? 4. Idan soyayya ta mutu, shin zata iya farfadowa? 5. Shin wata mace zata iya jure irin jarabtar da Ramlart ke ciki? *Nasan akwai tarin tambayoyi dake ranku daban daban ku dai ku biyo NI sannu-sannu in sha Allahu ba zaku yi nadamar biyan kudin ku ba, akwai chakwakiyoyi da yawa a gaba* *"Labarin bai fara ba tukunnah… yanzu ne tafiyar zata fara da gaske!* Me kike jira, Hajiya ta? Hanzarta kibiya naki domin kasancewa cikin masu kwasar: **Zallan ilimi, Darasin rayuwa, Nishadi da fadakarwa, Gwagwarmaya a soyayyah, Sadaukarwa, Zallan kaunah, Kaddara, Da kuma tsaftatacciyar soyayya mai tsayawa a zuciya!** Wannan ba kawai labari ba ne — *ƘAUNA DA KADDARAH* ce! Labarin da ba za ki karanta ki manta ba!" *_SAI NA JIKU YA'N AMANA_* *🖋️ RUBUTAWA: UMMUH EYSHAL (Mrs. Alkali)* *📖 ƘAUNA DA KADDARAH – _Labarin da zuciya zata karanta kafin ido ya Fara gani!_*