Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira) [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA*🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 *GODIYA* _Godiya ga Allah {SWA} da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin nawa tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabi Muhammad {SAW}_..... *JAN HANKALI* _Wannan littafin banyi shi don wani ba ko wata nayi shine don fad'akarwa,nishad'antar wa don hka a d'auki abu mai amfani a bar mara amfani abin da yake kuskure Allah ya yafe min,Allah yabamu ikon aikata dai dai a rayuwar mu ameeen_...... *ZUWA GA MASOYA NA* _godiya mai yawa a gare ku masoya na,nima ina kaunar ku_. *BAZAN MANTA DA KE BA* _my cwt Sadeey S Adam {saNaz Deeyah} da irin k'warin gwiwar da kike bani da soyayyar da kike nuna min don *Adalilin son* da kike nuna min na kai hka Allah ya bar mu tare_....... *~pg 1~* Yanayin unguwar irin unguwar masu hannu da shuni ce gwamna road a garin kd,family d'in gdn gaba d'aya suna xaune a k'ayataccen falon su hira sosae suke da kagan su kasan happy family ne .... Alhaji sa'eed haruna kenan da matar shi hajia maimuna sai yaran su safah itace babba sai nauwarah da k'aramin su saleem,su kadai Allah ya basu don sun ma fitar da ran sake haihuwa tun da saleem ya kai 7yr's da haihuwa, suna matuk'ar kaunar 'ya'yan su sosae ana cikin hira caraf nauwarah tayi magana cikin shagwaba take cewa " _Abba gaskia ina son idan na kammala secondary schl malaysia nake son ka sama min university_" Dariya abban yayi irin ta manya sannan yace " _nauwarah 'yar gidan Abba kada Ki damu Insha Allah xan cika miki wannan burin ke dai Allah yasa muna raye ki kwantar da hankali ki_" Cikin tsananin murna tace " _Ameeen my abba na_" Har ta bud'e baki xata sake magana safah ta watsa mata harara kamar idon ta ya fad'o tace " _tabbb Lallai yarinyar ae yanda nayi karatu a 9ja ke ma hka xakayi ba inda xaki je_" Turo baki tayi cike da shagwaba tace " _uhm kaji aunty safah da wani xance kuma bayan ynx agaban Ki abba ya amince min koh abb?_" " _k'warai da gaske nauwarah ta haske mai kyau hasken idaniya ta da ixinin Allah xaki je ke dai ki dage da karatu kmr yanda na san ki_" Wani tsalle ta buga tana ihun murna yayin da safah ta xumburi baki cike da haushi tace " _dallah malama kin dame mu da ihu idan baki shiru ba ynx na tashi na bubbuge bakin ki_" Murgud'a mata d'an k'aramin bakin ta tayi cike da tsiwa tace " _kaji mu da aunty safah nan ina ruwan ki da ihu ba Naga dai murna nake_" Axuciye safah ta tashi tayo kanta aikuwa da gudu ta b'uya a bayan ammin ta tana mata gwalo abba da saleem da ammi dariya kawai suke yi musu hannu tasa xata fisgo ta da sauri ammi ta tare tana cewa " _a'a safah yi hak'uri ki kyale ta kinsan yarinya ce kuma naga ae murna take_" " _amma dai ammi Kina kallo gwalo take yi min_" Da sauri ammi ta juya bayan ta ae kuwa taga nauwarah gwalo take mata cikin fad'a ammi tace " _bana son hka nauwarah baki ga yayar Ki bace ji nake d'axu kika gama bibbige min saleem don ya tab'a miki phone d'in ki_" " _tohh ammi na dai na yi mata_" Ta fad'a kamar xata fashe da kuka murmishin mugun ta safah ta saki tare da cewa " _yarinya xaki xo ki same ni ne_" Idon ammi ta faka ta Murgud'a mata baki yanda take Murgud'a bakin da ka gani kasan ta riga ta saba da hkan.... Ko _10 mints_ ba'a yi ba na hango nauwarah kusa da safah tana wani marairaice fuska tare da langab'e kai alamar tana son wani abu safah tana kallon ta ta gefen ido kamar xata tuntsire da dariya hka take ji dakyar ta iya danne dariyar bata kula ta ba ta Kalli inda saleem yake tace " _saleem dauko min maltina a frige mai sauk'in sanyi_" Ae Kafin ta rufe bakin ta da gudu nauwarah ta nufi frige ta d'auko mata maltina ta Mik'o mata hararar ta safah tayi tare da cewa " _na ambaci sunan ki ne ae Naga saleem na aika_" Murgud'a mata baki tayi cikin k'uluwa safah tace " _au Murgud'a min baki kike_" Da sauri nauwarah ta dafe bakin ta cikin marairaicewa tace " _hba aunty safah na mance ne I'm so sorry baxan k'ara ba ki karb'a kisha Kinsan baxan ji dad'i ba Idan baki karb'a ba plsss_" Gaba d'aya falon aka kyalkyale da dariya ita kuma sai wani lalangab'e kai take da yake safah tana masifar son kanwar ta bata son abin da xai b'ata mata rai yasa ta karb'a ae kuwa ta rungume ta tana dariya ba wanda bai yi dariya ba a wajen..... Tana shan maltina nauwarah cikin K'aramar murya tace " _Aunty safah yaushe xaki kaimu shopping ne gaskia kayan kwalliya na sun kusa k'are wa_" Harara ta xabga mata kafin tace " _baxa ajeba sai ki nemi driver ya kai ki_" " _Kaiiii aunty baxa ki kai ni ba don Allah ki taimaka plsss_" Abba ne yace " _aunty safah ayi hak'uri akai ta mana_" Hannu tasa ta dungure mata gaba d'aya aka tuntsire da dariya kafin tace " _kinci darajar abba yarinya_" Cike da d'oki da murna tace" _xaki kai ni my cwt sister?_" " _xan kai Ki Insha Allah gobe 'yar cwt k'anwata_" Murmishi tayi har dimple d'in ta ya lotsa tayi kissing d'in ta a kumatu tare da fad'in " _thank you so much my aunty safah_" Saleem yace " _har dani xa'a je koh aunty safah?_" Harara nauwarah ta xabga mishi tare da cewa " _baxa'a da kai ba yaro_" B'ata rai yayi tare da cunkushe fuska kamar xai fashe da kuka da sauri ammi tace " _kada ma kayi kuka dole aje da kai_" Xumbura baki nauwarah tayi tare da tashi ta nufi bedroom....... *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA*🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 *~pg 2~* *WANE NE ALHAJI SA'EED HARUNA???* 'Dan asalin garin kaduna ne a wata unguwa tudun wada anan mahaifan sa suke mahaifin sa Baffah haruna yana da rufin asirin shi dai dai gwargwado da matan sa 2 inna zainab ita ce babba tana da yara 2 sa'eed da mace safiyya sai inna larai d'an ta d'aya sunan shi salisu da yake Allah bai bashi yawan xuri'a ba...... Baffah haruna yana matuk'ar kokari wajen kyautata wa iyalan shi da bawa yaran shi tarbiyya ta k'warai sai dai kwata kwata ba'a xaman Lfy a tsakanin matan na shi babu jituwa Ko Kad'an.... Inna zainab mace ce mai hak'uri da kau da kai akan komai yayin da inna larai bata da hak'uri ko Kad'an saboda tana ganin baffah haruna ya fisan su zainab da yaran ta alhalin yana iyakar kok'ari wajen kwatan ta adalci a tsakanin matan shi da 'ya'yan sa. Axahirin gaskia yafi k'aunar zainab da yaran ta saboda sun fi mishi biyayya musamman sa'eed yana matuk'ar kaunar shi yaro ne mai hankali da nutsuwa bai dauki duniya da xafi ba shi yasa uban yake son shi sa6anin salisu da ya dauko halayar mahaifiyar shi akwai shi da mugun hassada da kyashin wani yayi abu shi bai yi ba baffah haruna yayi fad'an yayi nasihar duk a banxa don hka kawai ya kyale shi yana mishi addu'ar Allah ya shirya shi.... ******* Bayan sa'eed ya kammala schl ya samu aiki a wani company albarkar iyaye da addu'ar su tare da yanda yake taimakon mutane yake gani saboda ganin yanda Allah yake bud'a mishi harkokin sa yana samu sosae ganin hka yasa kishi da hassada a xuciyar salisu saboda ganin sa'eed ya fishi samu ba shi kadai ba har inna larai. Shi kuwa bawan Allah sa'eed ba ruwan shi sau tari sai ya dauki kudi ko yayi musu d'inki tare ya bashi don yana kaunar d'an uwan shi duk da hka salisu bai fasa nuna mishi bakin cikin yafi shi samu don salisu kullum a tunanin shi yafi d'an uwan shi samu amma Allah bai bashi nasarar hkan ba. Safiyya kuwa dakyar baffah haruna ya barta ta gama secondary schl ya aurar da ita d'an kasuwa lokaci d'aya Allah ya had'a soyayyar su don hka da akayi bincike aka ga yana da Kyan hali ba ada'u lkc ba akayi auren aka kaita unguwar malali lfy suke xaune da mijin ta.... Ahka lokaci yake tafiya har sa'eed ya had'u da maimuna irin kyakkyawan nan ce don gaskia akwai ta da kyau ba k'arya 'yar ogan shi ce Allah ya had'a soyayyar su da yake ogan nashi yana son sa'eed sosae jinin su ya had'u don hka ba'a samu matsala a ko'ina ba akayi auren... Amarya maimuna ta tare a gidan sa'eed suna rayuwar su cikin kwanciyar hnkl hkan yasa salisu bakin ciki sosae ta yanda akayi ya auri wannan kyakkyawar kamar balarabiya tun ganin shi na farko yaji yana masifar son ta kamar me anan ya kuduri wani mugun nufi a xuciyar shi.......... *BAYAN WASU SHEKARU*............ Abubuwa da yawa sun faru a wad'annan Shekaru Alhaji sa'eed ya samu karuwar haihuwa mata 2,safah ce ta farko sai nauwarah da batafi 3yrs ba sai tsohon cikin da take dashi haihuwa yau ko gobe... Ana cikin hka salisu yaxo gdn yayan shi cike da bacin rai yana shiga falon ya had'a ido da maimuna tana xaune a falon tasha kwalliya kai ba kace ta haifi safah da nauwarah ba ae tuni yaji duk bacin ran da ya shigo dashi ya yaye washe hak'ora ya shiga yi cikin dariya yace " _uwar gida ran gida maman safah da nauwarah kina Lfy???_" Shiru tayi kamar baxa ta amsa ba saboda kwata kwata jinin su bai had'u da salisu ba ta tsane shi saboda yanda yake yiwa Baffah haruna da mijin ta sa'eed rashin kunya a dak'ile ta amsa da " _lfy qlau nake_" Bai damu da yanda take b'ata fuska ba ya samu wuri ya xauna cikin murmishi kamar mai tallan maclean yace " _dftn wannan siririn mijin naki ya nan Don wurin shi naxo_? A fusace tace " _Wannan wanne irin rashin mutunci ne salisu kaxo har gida na a gaba na kana ciwa mijina mutunci tohh wlh baxan yarda ba idan ka k'ara xan dau mataki akan ka_? Ranshi idan yayi dubu ya b'aci amma da yake d'an duniya ne ya k'ak'alo murmishin dole yace " _okay ayi min afuwa baxan k'ara ba matar babban yaya d'an yi min magana dashi don Allah_" Sai da ta saki tsaki kafin ta mik'e ta nufi stairs shi kuma ya bita da kallon yana had'yar yawu tare da lashe leb'en shi yana tunanin abubuwa da yawa a ran shi.... Bata da deba yaji tahowar su don yana jin dariyar su k'asa k'asa alamar magana mai dad'i suke fad'a wa junan su wani abu yaji ya tokare shi a mak'wogaron shi ya fad'a tunani sai da yayan shi ya dafa mishi Kafad'a sannan ya dawo hayyacin shi ya saki wani huci mai zafi kafin ya fara magana ba alamar ma xai gaida yayan nashi yace " _daman yarinyar da xan aura ce na samu sai old man yace bai yarda ba to nasan yafi jin maganar ka shine nake son kayi mishi magana don gaskia baxan iya hak'uri da ita ba idan yak'i yarda xan gudu a neme ni a rasa sunan yarinyar binta lawan shana_" Yana gama maganar ya kad'e rigar shi ya fice daga falon ya bar sa'eed kamar an dasashi a wajen cike da tunanin abin da salisu yake kok'arin janyo musu.......... *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA*🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 *~pg 3~* Dafa mishi kafad'ar akayi da sauri ya juyo sai yayi arba da kyakkyawar fuskar matar shi tana yi mishi Murmishi amma ganin tarin damuwa a fuskar gwarxon mijin ta nan da nan fuskar ta ta rine xuwa tarin damuwa cikin muryar kwantar da hankali tace " _ya kai mijina menene dalilin shigar ka damuwa?_" Kamo hannun ta yayi ya xaunar da ita kan kujera shima ya xauna yana fuskantar ta sai da ya sauke numfashi Kafin yace " _ba wanine ya sani shiga damuwa ba illa salisu da yake kok'arin janyo wa kanshi abin da yafi k'arfin shi?_" " _me yake kok'arin janyo_?" " _wai aure yake son yi baffah bai amince da yarinyar ba shine yaxo wae baffah yafi jin magana ta nayi mishi mgn idan ba hka ba xa'a neme shi a rasa_" Shiru tayi na d'an lokacin k'alilan tukunna ta sauke ajiyar xuciya tace " _idan yak'i yarda ya hak'ura da yarinyar toh ku kyale shi ya aure ta sai mu taya shi da addu'a kada ya gudu kasan xai aikata hakan_" Shiru yayi na 'yan Mintuna Kafin yace " _xamu yi mgn da baffah ngde da shawarar da kika bani idan Allah ya K'addara wannan auren Shikenan fatan mu Allah ya xa6a mishi abin da yafi alkhairi amma salisu sai a hankali ya fiye rigima wlh Kinsan wacce yarinya ce kuwa?_" Girgixa kai tayi alamar a'a " _toh 'yar gdn lawan Shana ce_" Zaro ido tayi Kafin ta gid'a kai tace " _Allah ya kyauta amma sam bai yi dace da mace ta gari ba_" " _Ameeen dai amma shi ae idon shi ya rufe bae ga hkan ba_" *WANE LAWAN SHANA* Alhaji lawan Shana shine cikakken sunan shi don anfi sanin shi da lawan Shana sunan shana ya samo asali daga lokacin samartakar shi saboda tantirin d'an duniya ne mai son ya shana a duniya yana d'an rufin asiri ba laifi akwai masifar son yaga ya tara dukiya matan shi 4 da tarin yara har 13 gaba d'aya tarbiyyar su sae a hankali.... Acikin su akwai wata binta Tana da kyau ba laifi sai dai maimuna tafi ta kyau nesa ba kusa ba gaba d'aya ta kwashe halin baban ta _100 percent_ shi yasa yake masifar son ta a 'ya'yan shi komai xata iya aikata wa don ta samu kud'i a kaduna polytechnic take karatu duk da bata bashi mahimmanci irin 'yan d'umama benci ne,ita ta fara cewa tana son salisu don da alama xata huta a gdn shi baya aurar da yaran shi talaka sai mai kud'i idan talaka ne mai yaci balle ya bawa 'yar shi kaji shi sai kace shi ba talakan bane ya mance Allah ne mai axurta bawan shi...... An kai ruwa rana kafin baffah ya amince don salisu akwai shi da kafe ya da hka akayi auren duk 'yan uwan shi basa so daga shi sai babar shi inna larai... Bayan 2weeks da bikin salisu maimuna ta haihu yaro yaci suna saleem........ ******* *MUN DAWO LABARI* A kayattaccen bedroom d'in su na hango nauwarah ta k'ure volume d'in tv tana jin wak'ar da deepika tayi a film d'in rasleela ram Leela kamar wadda tayi practice d'in rawar hka take yi ta iya rawar sosae kamar itace deepika d'in {lol} Gaba d'aya ta cikawa safah kunne da kunne da k'ara gashi karatu take saboda gobe tana da test a schl gaba d'aya tabi ta dame ta a fusace tace " _wannan kuma sabon wani wulak'ancin ne nauwarah ina karatu kin samu kin k'ure volume_" Sae da ta Murgud'a mata baki Kafin tace " _hba aunty safah don Allah ki kyale ni nayi nishad'i man Kinsan ina bala'in son wak'ar nan_" " _ki tafi falo mana kiji_" Zaro ido tayi tana cewa " _tabbb kina so ammi ta doke ni tana falo fah a xaune_" Tsaki safah ta ja kafin ta tashi afusace tayi kan nauwarah da gudu tayi hanyar fita daga d'akin sai taga ashe kid'an ta kashe ta juyo Tana kallon nauwarah tayi wuk'i wuk'i da ido hararar ta tayi kafin ta juya ta xauna tana cewa " _sai tsabar tsokana amma tsoro fal ciki_" Ta dauki buk d'in ta tana dubawa ganin hka yasa nauwarah ta lalla6a tana Xumbura baki taje ta jona socket d'in da safah ta kashe iya k'uluwa safah ta k'ulu ta tashi da sauri tayi kan nauwarah ae kuwa ta kwasa da gudu sai falo ita ma safah ta bita da gudu sai ganin su ammi tayi kamar wad'anda aka cillo da sauri ta mik'e Tana cewa " _lfy safah me yafaru?_" nauwarah tana ihun _Wayyo Mumy Ki taimaka min aunty safah xata Duke ne_" Duk tabi ta cikawa ammi kunne da ihu gashi ta ruk'unk'u ne ta cikin fusata tace " _ammi wannan mara kunyar yarinyar ce ina karatu ta ishe ni da jin wak'a duk ta hanani karatu_" Ammi tace " _baki da kunya nauwarah koh safah kike yiwa hka ba yayar ki ce ba ki bata hak'uri kuma kada Ki sake na gaya miki_? Cikin murya kamar xata fashe da kuka tace " _I'm so sorry my aunty safah na dai na amma kada Ki doke ni plss_" K'wafa tayi sannan ta bar wajen nauwarah ta fito daga bayan ammi tana sakin ajiyar xuciya can kuma ta kyalkyale da dariya tace " _ohhh thank god to save me_" Harara ammi ta watsa mata sum sum ta shige tana dariya............. *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 *~pg 4~* Xaune suke a falo Alhaji salisu da Alhaji lawan sai hajia binta suna yin wasu maganganu da alama maganar da suke yi ta sirri ce ba kowa ake so yaji ba can naji muryar Alhaji salisu yana cewa " _ya kamata mu gama samu mafita don ni wlh na gaji da ganin shi awannan duniyar ta mu da shi da wad'annan 'yan iskar 'ya'yan nashi don ni wlh kishi nake dasu kamar yanda nake kishi da uban su_" Hajia binta ta xabga mishi wata harara kamar idon ta ya fad'i k'asa taja wani shegen tsaki a fusace tace " _wlh salisu baka da mutunci kana tunanin idan ina raye xaka auri wannan shegiyar matar mai kama da aljanu, toh wlh tun wuri kama cire son ta daga xuciyar ka idan ba hka ba sai na.................. " Kafin ta K'arasa fad'in hka Alhaji lawan ya daka mata wata tsawa ba shiri ta hadiye sauran maganar ta ta fuska a d'aure yace " _na fuskanci baku damu da abin da ya tara mu anan ba toh wlh xan tashi na tafi tunda baku tanadi abin fad'a ba,ke kuma binta idan ba rashin hankali da tunani ba ina ruwan ki da son ta da yake yi ke dai ba kud'i kike so xaki wani cikawa mutane kunne da ihu_" Cike da rashin kunya tace " _ae bani kad'ai ce mai son kud'in ba naga Har kafi ni son su taya xae dunga maganar wannan mai kama da aljanun_" " _yayi d'in don uban ki tunda ke baki da mutunci ni uban Ki kike gaya wa hka ko_" Alhaji lawan yayi maganar a fusace har ta bud'e baki xatayi magana Alhaji salisu ya dakatar da ita da hannu Kafin ya d'ora da cewa " _don ynx wannan bata ta so ba ni kawai so nake a fara kawar dashi tukunna_" Nan kowa ya fara kawo tashi shawarar idan suka duba sai aga batayi ba sun d'auki wajen _1 hour_ suna magana da K'arshe har xasu tashi da xummar kowa yaje yayi tunani akai sai har sun mik'e tsaye sai suka ga Alhaji lawan ya kwashe da dariyar mugunta ya dad'e yana dariya kafin ya tsaya su kuma suka xuba masa ido suna kallon shi cike da mamakin abin da yasa shi dariya dakyar ya tsagaita da dariyar Kafin yace " _kun ga ina dariya kamar na haukace ko toh mafitah na samo mana kuma mai sauk'in gaske ku kawo kunnen ku kuji saboda ina tsoron kada iska ta kwashi sauti na aji koh yah_" Ae kuwa da sauri suka mik'a mishi kunnen su ya d'au tsahon _10 mint_ yana magana Kafin lokaci d'aya su kwashe da wata mahaukaciyar dariya ke bakace d'an adam ne ke yi ba daga hka duk suka tarwatse xuciyoyin cike da farin ciki........ ********* Sanye take cikin wata gown d'in shadda dark blue tasha make up Sosae tayi masifar yin kyau d'aurin d'an kwalin ya xauna a kanta sosae sai tayi amfani da sark'a white mai touch d'in blue a jiki ta sanya white shoes nauwarah kenan sarkin son gayu kenan suna masifar kama da ammin ta don ita ta kwashe kusan kyan nata don tafi safah da saleem kyau shi yasa abban su yafi k'aunar ta cikin takun ta kamar mai tausayin k'asa ta fito xuwa falo sai kace wata babbar mace don bata fi 16yrs ba a duniya amma idan tayi wani abun ka d'auka wata babbar ce..... Kuma sunyi dace da iyaye don dai dai gwargwado sun basu tarbiyya suna da iIlimi na addini da na nasara mai jan kunnu wa Duk kud'in mahaifin su bai hana su tsaya wa k'in neman ilimi ba.. Tana k'araso wa falo ta tarar da ammi sai saleem suna xaune suna kallo cike da shagwaba ta kwanta a jikin ammi tace " _ammi Har ynx aunty safah Bata dawo daga schl ba_" " _ehhh Kinsan lectures d'in yamma ne da ita yau_" Ammi ta bata amsa turo baki tayi gaba sannan tace " _tabbb ammi anya xan iya kai wannan time d'in a schl kuwa ae gudu wa xanyi_" Harar ta ammi tayi kafin tace " _daman ke ina xaki iya raguwa dake xan kuwa gaya wa abban ki kada ya b'ata kud'in shi a banxa ya kai Ki har malaysia karatu gwara ya barki anan_" Marairaice fuska tayi tare da langab'e kai tace " _ya hak'uri ammi na da wasa nake wlh kinsan yanda nake da burin yin karatu sosae kada ki fad'a wa abba plss_" Dariya kawai tayi tana cewa " _ohh nauwarah ran da bamu a duniyar har tausaya miki nake wanda xai iya da shagwabar ki_" Kicin kicin da fuska tayi can kuma sai ga hawaye yana xuba a fuskar ta cikin kuka tace " _don Allah ammi ki dai na wannan xance ae rasa ku arayuwa ta nasan ba k'aramin *K'ARSHEN WAHALA* xan shiga ba_" Sosae ta fashe wa ammi da kuka nan ta fara rarrashin ta tana cewa " _ae mutuwa tana kan kuwa nauwarah ba mai guje mata fatan Allah ya sa mu cika da imani_" Dak'yar ta lalla6a tayi shiru har safah ta dawo daga schl suka cigaba da hira kiran sallahr mangariba ne ya tashe su daga hirar.... *12 pm* Innalillahi wa'inna ilaihir rajun ta farka a firgice daga wani mummunan mafarki da tayi gaba d'aya ta jik'e da gumi ta kai idon ta kan safah da take baccin ta hankali kwance shiru tayi tana tunanin abin da ta gani a mafarkin wai abban ta ne ya rasu gashi ana xaman makoki suna ta kuka ita dasu ammi daga nan ta fara...... Xumbur ta mik'e ta tsaye ganin an kunna hasken d'akin ido hud'u sukayi da abban ta sosae tayi mamakin ganin shi a irin wannan lokacin tashi tayi ta nufi wajen shi kawai ta tsaya kallon shi ta kasa cewa komae hannun ta ya kama ya xaunar da ita a gefen bed sannan shima ya xauna a hankali yake magana don kada ya tashi safah a bacci yace " _kema Kinyi irin mafarkin da nayi ko na dad'e ina irin wannan mafarkin amma na yau yasha banban da na ko yaushe_" Ita dai nauwarah kallon shi kawai take shima bai damu da irin kallon da take mishi ba ya cigaba da cewa " _ban tab'a gaya muku bane ko ammin ku bana gaya mata saboda ban son tashin hankali ku mak'iya sun yi min yawa nauwarah an dad'e ana bibiya ta don aga baya na na amma Allah bai basu ikon hkan don hka ina son ki kula da 'yan uwan ki da ammin ku, bana son ki fad'a wa kowa munyi magana dake wannan ya xama sirri a tsakanin mu_" Nauwarah wadda ta kusan suman xaune bakin ta na rawa tace " _Abba su wane? Kuma me suke so a wajen ka? Sannan ka fad'a wa police mana? Kuma ta yaya xan iya kula da ammi safah da saleem???_ Murmishi ya saki kafin yace "_xaki iya kula da su man sannan rayuwata da dukiya ta suke nema, hmm nauwarah ke yarinya ce shi yasa amman ae idan baka iya kama 6arawo ba shi ya kama ka sanar da police ma bata taso ba gobe xan yi tafiya xuwa kano wajen wani aminina akwai maganar da xamu yi dashi na yarda da dashi fiye da yanda kike xato nasan baki san shi ba" Abba ya d'an sauke numfashi Kafin ya cigaba da cewa " _xan baki wata jaka tana d'auke da dukkan wata muhimmiyar dukiya ta don ku samu damar kula da kanku Insha Allah baxa su ci galaba a kanki ba kuma ina son idan Allah ya nufa sun samu galaba a kaina ku gudu xuwa kano xan rubuta miki address d'in shi gobe na baki nasan shi kad'ai xai iya taimaka muku tsakani da Allah_" Hannun nauwarah ya kama ya damk'a mata wata jaka sannan ya rungume ta har sai da k'walla ta xubo mishi tashi yayi tsaye tare da cewa " _Allah yayi muku albarka ya k'are min ku a dukk inda kuke_" Bud'e baki nauwarah tayi xata yi mgn da sauri yasa hannu ya rufe mata baki ya nuna mata safah dake motsi da sauri ya fice daga bedroom d'in bayan ya kashe hasken d'akin........ *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 *~pg 5~* Tun da abban ta ya bar d'akin take xaune cike da tsoro da tashin hankali akan abin da ya sanar da ita me yasa abban ta ya yanke hukuncin sanar da ita bai sanar da ammi da safah ba ae ita tayi k'ank'anta da asanar da mata da wannan rikitaccen labarin mai kama da film Ko mafarki *ADALILIN SON* matar shi da dukiyar shi ake neman ranshi to suwaye wad'annan marasa imanin tunanin da take da kuka su suka hassada mata matsanancin ciwon kai idon ta duk sunyi jawur dasu sai rad'ad'i suke yi mata kamar an xuba barkono Dakyar ta iya mik'e wa tsaye ta bud'e wardrobe d'in ta ajiyar jakar tayi sannan ta nufi toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo batasan adadin nawa tayi ba sai da taji jiri ya fara d'aukar ta sannan ta xauna ta janyo al qur'an ta fara karatu cikin muryar ta mai d'an karan dad'i tana hka har asuba tayi tana idar da sallah bacci yayi awon gaba da ita akan abin sallahr Wajen 10 na safe Abba ya fito cikin shirin tafiya yasha manyan kaya farare sol dasu da yake ranar juma'a ne ya xauna akan dinning table ammi tana had'a mishi breakfast ya xuba mata ido ko kiftawa ba yayi har ta gama had'a mishi ta juyo don tayi mishi magana ta ga ya xuba mata ido yana kallon ta Murmishi ta saki wanda ya dad'a fito mata da Kyan ta kafad'ar shi ta dafa sannan tace " _Abban safah irin wannan kallon hka Lfy?_" Ajiyar xuciya ya saki tare da rik'o hannun ta yace " _bakomai gani nayi yau Kinyi min kyau sosae_" dariya ya bata ta kyalkyale da dariya don wannan kalmar kullum sai ya fad'a mata dariyar da take ta bashi shima dariya don hka yayi murmishi kawai kafin tace " _nima kayi min kyau wlh fiye da koyaushe, amman kayi sauri ka gama don nafi son ka dawo da wuri saboda bana son dare yayi muku a hanya_" " _an gama ranki ya dad'e_" A hankali ya fara cin abincin yana ci yana kallon ta tun tana jin dad'in hka har ta fara jin tsoro anya wannan kallon nashi na lfy ne kafin ta samu tayi magana safah da nauwarah sun k'araso wajen suka gaida iyayen nasu cikin girmama wa gaba d'aya nauwarah jikin ta a sanyaye yake ko gayun da ake yau babu shi ta samu waje ta xauna tare da xabga tagumi ammi ta xuba mata ido kafin tace " _lfy qlau kike nauwarah duk Kinyi wani iri gashi Kinxo kin xabga tagumi_" Kafin tayi magana caraf safah tace " _wlh umma na tambaye tun d'axu tace ba komai koh tsokana ta yau bata yi ba_" Har ta bud'e baki xatayi magana suka had'a ido da Abba yayi mata alamar kada ki fad'a musu don hka tayi murmishi yak'e tace " _ammi ba komai na tashi da ciwon kai ne_" " _Allah ya sauwake kiyi maxa ki karya sai kisha paracetamol_" Kad'an ta iya cin abinci ta ture ta xauna har abba ya gama suka mik'e tsaye don raka shi har wajen motar da xai tafi a ciki suka rakashi duk sai da ya rungume su sannan ya shiga mota driven shi har ya kunna mota sun kusa fita daga get ya bashi umarni ya dawo baya ammi suka tsaya kallon shi cike da mamakin shi sai da ya dad'a fitowa ya rungume su ya dunga kallon su gaba d'aya sun tsorata da hkan nauwarah kuwa tuni ta fara kuka ganin hka yasa ya koma mota drive yaja mota yana ta kallon su har suka fice daga gidan gaba d'aya mai gadi ya mayar da kofa ya rufe da gudu nauwarah ta shige falo tana kuka sosae ammi da safah sai saleem suka nufi falon gaba d'aya jikin su a sanyaye dakyar suka lallashi nauwarah tayi shiru safah ta vata magani bata dad'e da sha ba bacci yayi awon gaba da ita....... Tsaye yake a K'arshen layin da alamar jiran wani abun yake ganin wata mota ta shige yasa shi sakin wani murmishin mugunta tana shigewa ya dauko wayar shi a aljihu ya kira wata number bata dad'e tana ringing ba aka d'auka cikin wata katuwar murya yace " _Oga an cika aiki nan d'an lokaci xakuji kyakkyawan labari_" Daga d'aya bangaren aka kwashe da wata mahaukaciyar dariya dakyar ya tsagaita da dariyar Kafin yace " _aikin ka kyau mu had'u anjima da yamma a guest house d'ina mu K'arasa biyan ka_" Daga hka ya kashe wayar cikin farinciki ya tsayar da keken napep ya shiga suka tafi.......... *_Aishat A muh'd {Aunty}_*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_* 😘 *~pg 6~* Cikin nutsuwa da iya tuk'i driver yake jan motar sautin karatun alqur'an cikin suratul baqara yana tashi a cikin mota sunyi nisa da tafiya sun shigo irin jeje nan da ba mutane sai Shigewar ababan hawa wata babbar mota ce ta taho da gudun bala'i kan motar tayi gadan gadan kansu Duk cikin motar ba wanda ya ankara da motar sai da taxo daf dasu Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da suka fad'a lokaci d'aya driven yayi kok'arin kaucewa amma ina tuni motar tayi ciki dasu gangara wa ta dunga yi Kafin ta daki wata bishiya ta tsaya cak shi kuma mai babbar mota tuni ya arce da gudun tsiya ya bace bac....... A hankali wata mota k'irar jeep black colour ta fito daga duhun bishiyo duk abin da ya faru akan idon su lokaci d'aya suka kyalkyale da dariyar mugunta sannan motar ta juya ta nufi cikin garin kaduna Motoci masu shige wa sune suka kawo d'auki aka kirawo police bayan sun xo da motar ambulance dakyar aka xaro su daga cikin motar ba wanda yake motsi da gaggawa aka shige dasu babban asibitin kd likitoci suka Duk'ufa akan su....... *After 2 hour's later* Bayan wad'annan lokacin likitocin dake kan kula da su fito wa sukayi daga d'akin cike rashin kuxari a tare dasu don gaba d'aya basa sa ran rayuwar su sai wani ikon ubangiji,police d'in suka koma wajen da akayi accident d'in suka k'ara bincike awajen nan suka ga wayar shi da card d'in shi sosai sun shi don ba boyayye ne ba Kwance take a kan kafar ammi gaba d'aya wata matsanancin fad'uwar gaba take ji tana jin ammi da safah da saleem suna hira amma bakin ta yayi dauyi kiran wayar ammi da akayi dai dai lokacin taji wata fad'uwar gaba wadda tafi ta baya Murmishi ammi tayi kafin ta d'aga wayar ta Kalli nauwara tace " _toh ga abban naki ya kirawo nasan ynx sun isa kanon Mybe suna haramar taho wa_" Nauwara Bata ce komai ba ammi ta d'aga wayar da sallama wata irin mik'ewa tayi a xaburi ta dafe kirji Tana fad'in " _Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun yanxu suna wanne asibitin_?" Nan aka fad'a mata tun lokacin da ta mik'e tsaye su safah nauwara da saleem suma suka mik'e tsaye suna cewa " _ammi lfy me ya samu abba_" Ina ammi ba bakin magana da gudu ta shige d'aki ta xundumo hijabi tayi hanyar waje suma suka bita da gudu driven ammi da mai gadi suna ganin su da hka Sun san ba lfy tambayar ta suke amma ta kasa magana mota ta shige suma su safah suka bita drive ya shiga motar dakyar ta iya furta sunan asibitin da xai kai su nan drive yaja mota da gudu don da ganin iyalan mai gidan nashi ya san ba lfy mai gadi ya bisu da addu'ar fatan alkhairi Cikin 30 mint suka isa asibitin police suka tarar a wajen suka yi musu bayanin komai gaba d'aya suka rushe da wani kuka mai ban tausayi sun bawa mutanen wajen tausayi wasu har da d'an hawayen su nima da nake d'aukar rahoto da k'awata saNaz mai min rakiya muka ja gefe guda muna share hawaye..... Driven ammi ne yaje ya sanar da baffah da inna habiba yana kuka yana sanar da su don Alhaji sa'eed haruna mutum ne managarci mai taimako baya kyamar talaka tuni inna habiba an fara share hawaye sun isa asibitin a lokacin da safiyya kanwar Alhaji sa'eed suka isa abin da yayi matuk'ar daure min kai har na dakata da kukan da nake ganin Alhaji salisu da matar shi hajia binta sun fito a mota d'aya da safiyya suna kuka Kukan da yanke mai suna da kukan munafurci ashe shine ya je ya taho da safiyya ya biya ta gida don d'auko su baffah ya tarar sun taho yanda hankalin shi ya tashi sai ka d'auka basa hannun shi nan na bashi number 1 na masanin tuggu da iya yaudara Daf da sallahr la'asar Alhaji sa'eed haruna da driven shi malam inuwa suka amsa kiran ubangiji Allah Akbar rayuwa kenan ya tafi ya barsu da duniyar suyi abin da xasu yi wataran suma xasu xama kamar hka don Allah {swa} yana cewa acikin suratul al imraan { *kullu nafsin xa'ikatul maut Wato kowanne mai rai xai d'an d'ani d'acin mutuwa* yau gare ka gobe ga wanin ka jebi a kan ka don hka ina kira a gare mu da mu kyautata rayuwar mu Wajen aikata abu mai kyau don mutuwar nan ba sallama take yi ba *_Allah yasa mu dace duniya da lahira Ameeen thumma Ameeen_*} Shi kanshi babban likitan dakyar ya iya yi musu bayani don sai da ya fara da yi musu nasiha Kafin ya sanar su ae Kafin su ankara ammi nauwara da inna habiba sunyi baya a sume........... _ni kai na tsananin tausayin su yasa ban san lokacin da wayar tawa ta subuce ba don hka fans Kuyi hak'uri sai na dawo hayyaci na xan cigaba da d'aukar muku rahoto shin Wacce irin *K'ARSHEN WAHALA* wad'annan familyn xasu shiga????_. *_Aishat A muh'd {Aunty}_* 😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_* 😘 *~pg 7~* Gaba d'aya waje ya rud'ai da kuka hankali sun tashi safah da saleem sun gigice iya gigicewa ga mutuwar abba sannan ga ammi da nauwara a sume kuka kawai suke yi Nan likitoci suka basu taimakon gaggawa bayan sun farfado aka basu gawar Alhaji sa'eed da driven suka nufo gida don a sada su da gidan su na gaskia Cikin lokaci k'alilan mutuwar Alhaji sa'eed haruna ta kewaye garin kaduna ae kuwa nan da nan mutane suka dunga taho wa domin halarta jana'ixa suna alhinin mutuwar bawan Allah kenan mutumin da yake xaune da kowa lfy bashi da abokin hamayya Bayan an kammala had'a su aka umarci makusantar shi dasu xo ko da wanda xai mishi kallon K'arshe ko aaddu'a dama an nemo iyalan malam inuwa drive don hka kowa yaje inda gawar d'an uwan shi suke masu karatun alqur'an da Addu'o'i nayi masu kuka Nayi don nauwara bakin ta yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi har gwanda ammi da safah sun kokar ta yi mishi addu'a sai mahaifin shi baffah haruna managarcin tsoho kenan yayi jarumatar sosae don mutuwar d'an shi ta buge shi sosai shine yayi kok'arin yi mishi karatun alqur'an Ganin ana kok'arin d'aukar makara yasa nauwara tafi karfin hali wajen kwararo wa abban ta Addu'o'i don neman dace wa da rahmar ubanjigi lokacin da aka d'auki makarar gaban nauwara ya fad'i Shikenan baxa ta k'ara ganin abban ta ba baxa ta k'ara jin muryar shi ba har abada ya tafi ya barsu a duniyar nan mai cike da rikici da tashin hankali kuka ta saki da karfin gaske amma da yake muryar ta ta dushashe ba'a jin sautin kukan sosai Kamar ance ta d'aga kan ta, ta Kalli mutanen wajen karaf ta tsinci Murmishi akan fuskar Alhaji salisu gaban nauwara ya fad'i dum dum cak ta tsaya da kukan ta xuba mishi ido sai da akace ya kama makara tukunna ya tak'ark'are ya fashe da kuka mutane na bashi hak'uri Gaba d'aya hankalin nauwara ya tashi sosai kuma bata yarda da uncle d'in ta ba sam kuma tayi wa kanta alkawarin sai tayi binciken dalilin mutuwar abban ta. *1 week later* Bayan k'wana 7 da rasuwar Alhaji sa'eed haruna yau aka kammala xaman makoki duk mutane suka watse sai iya 'yan gida kawai su nauwara duk sun rame sosai abin gwanin ban tausayi musamman nauwara da abu 2 suka had'e mata mutuwar abban ta da kuma ta yanda xata fara bincike akan uncle d'in ta don sanin me yasa shi murmishi a lokacin da ake cikin tashin hankali na mutuwar d'an uwan shi yayan shi???? Bayan sallahr isha'e baffah haruna da matan shi inna habiba da inna larai sai ammi, safah, nauwarah da saleem sai safiyya kanwar Alhaji sa'eed da kuma Alhaji salisu k'anin shi suna xaune a falon bayan baffah ya bud'e taro da addu'a sannan ya fara da yiwa su ammi da nasiha mai ratsa xuciya da suyi hkari hka Allah ya shirya iyakar lokacin da aka d'ibar wa sa'eed kenan a duniya muma nan ita muke jira Kafin ya d'ora da cewa. " _yanxu mun gama shiryawa xamu tafi ki kula sosai da ke da yaran ki sai Kinsa ido akan su sosai idan kina neman taimako sai ki neme mu_" Cikin muryar kuka tace " _toh baffah Insha Allah xan yi kok'ari wajen kula da hkan mun gode_" Anan aka rufe taro da addu'ar Allah ya jik'an Alhaji sa'eed haruna ya kai rahma kabarin sa tare da sauran al umma da suka riga mu gidan gaskia Ameeen su amsa daga hka suka tafi akabar su ammi su kad'ai kad'aicin rashin abba ya dame su sosai dakyar bacci yayi awon gaba da su yayin da nauwara ta d'auko jakar da Abba ya bata ta fara bincike a ciki duk takardun dukiyar shi ne kusan gaba d'aya kuma original d'in ne sai wani pictures d'in su da suka d'auka gaba d'aya Mayar dasu cikin jakar tayi kafin ta tsunduma a tunanin yanda xata fara binciken ta *After 2 month's later* Wata yarinya ce 'yar kimanin 16yrs da wasu 'yan watanni na hango ta a tsaye a jikin wani gida ta raku6e alamar jiran wani abun take tana sanye da jeans blue da t-shirt red colour ta sanya wata riga a saman kayan irin ta sanyin nan har kusan gwiwar ta black colour ce sai tayi rolling d'in kanta da dark blue d'in veil da yake fara ce sol ya haska ta ta sanya wani glass ya rufe kusan rabin fuskar hannun ta d'auke da waya jin alamar bud'e get yasa ta da d'a lafewa a jikin ginin wata motace k'irar honda accord ce ta fito daga gidan ta harba kan titi da sauri ta fito daga jikin ginin ta nufi titi Tana tsayar da keken napep amma Bata samu ba har motar ta b'ace wa ganin ta mtssss taja tsaki kamar ta tsinka harshen ta saboda takaice sau 2 kenan take kok'arin bin motar amma take b'ace mata wani murmishi ta saki ganin ta samo hanya mafi sauk'i don hka ta tsayar da keken napep ta shiga direct gida ta wuce tana sauka a kusa da gidan ta biya shi sannan ta shige gida....... *_Aishat A muh'd {aunty}_* 😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_* 😘 *~pg 8~* Da sallama ta shiga falon su ammi na xaune suka amsa mata sai da ta warware mayafin da tayi rolling dashi Kafin ta xauna tana cewa " _washhh ammi na gaji wlh, kai saleem samo min wani abun na jika makoshi na_" Da sauri saleem ya tashi ya nufi kitchen yayin da ammi tace " _wai ni nauwara ina kike xuwa ne kullum sai kin fita idan kika dawo daga schl na rasa yaushe kika koyi yawo wlh_" Murmishin yak'e tayi sai da tasha ruwan da saleem ya kawo mata kafin tace " _ammi ki yarda da ni wani d'an bincike nake yi amma da xarar na gama Shikenan_" Harara safah ta xabga mata kafin tace " _wanne bincike kuma sai kace wata lawyer ko police 'yar rainin wayo kawai ki fad'a mana inda kike xuwa_" mtsss taja tsaki tare da cewa " _wlh aunty safah kin fiye sa ido da yawa ina ruwan ki naga da ammi nake magana_" Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a baki safah ta cillo mata pillown hannun ta caraf tasa hannu ta cafe har ta bud'e baki xatayi magana amma maganar ta mak'ale sakamakon ganin mutumin da ya b'ace mata da gani d'axu ya shigo da sallama kamar wani mutumin kirki bayan shi wata mata ce ammi ce ta amsa musu sallamar ya samu waje ya xauna ya xuba wa ammi ido kamar wani tsohon najadu ko nace tsohon maye nauwara tana kallon shi har tana mamakin wannan wanne irin kallo ne yake yiwa ammin ta hka dam dam gaban ta ya fad'i sakamakon maganar da abban ta yayi mata ta fad'o mata *Adalilin son* ammin ki da dukiya ta ake neman ranshi nan take ta shiga tunani maganar da yayi ita ta dawo da ita hayyacin ta baki ta saki tana kallon shi yace " _dama 'yar aiki na samo muku tunda na lura mai yi muku aiki bata nan_" Caraf nauwara tace " _ae uncle ba sai ka kawo mana mai aiki ba tun da muna iya aikin mu babu abin da ya gagare mu_" Kallon ta yayi ita ma ta xuba ido ko kiftawa babu a xuciyar shi yace Idan nayi wasa wannan yarinyar sai ta sai ta bani mamaki sosai ina sane da irin binciken da take yi akai na amma Idan tasan wata ae batasan wata ba kuma komai abin ta yafi ta dad'e wa a duniyar kuma yafi ta sanin tuggu amma da yake d'an duniya ne a fili sai ya saki Murmishi yace " _hba nauwara ni da nake so ku huta bana son Kuna wahala ku barta ta dunga taimaka muku_" Har ta bud'e baki xatayi magana ammi ta riga ta da cewa " _Shikenan salisu ae ba damuwa ta dunga taya ni hira idan sun tafi schl mun gode_" Wani d'an iskan Murmishi ya saki na jin dad'i abin da ammi tace ya wani watsa wa nauwara kallo wanda na kasa banbance wane kalar kallo ne Kafin ya mik'e tsaye yana cewa " _toh maimuna xan koma sai na sake xagayo wa_" " _okay ka gaida gida a gaida hjy binta_" " _xata ji da kyau kuwa_" Yayi hanyar fita daga falon sai da ya bigi kafar wadda ya kawo a matsayin 'yar aiki ta d'ago da kanta karaf suka had'a ido ae kuwa ya kashe mata ido d'aya ita ma ta mayar mishi da martani toh fah ba wanda ya kula da hkan sai nauwara da yake ba k'aramin xargin shi take ba shi yasa kowanne action d'in shi akan idon ta da hka ya bar gidan cike da farin ciki wani sashe na xuciyar shi yana tunanin yanda xai aiwatar da mugun nufin shi akan nauwara don ya fahimci yarinyar tana bibiyar shi ya sha ganin ta awajajen da yake yawan Xuwa....... *1:40 am* Karfe 1:40 na dare na hango nauwara ta fito daga bedroom d'in su tana sanye da wata night gown blue colour cotton ce rigar ba takalmi a kafar ta amman ta sanya wata white d'in hula akan ta tafiya take sadaf sadaf don iita hankalin ta bai kwanta da ladi mai aiki ba sai taxo dai dai d'akin da aka bata ta tsaya sai taji ana magana k'asa k'asa bata ji mai ake cewa ba jin anyi shiru kuma sai ta d'an tsaya can kuma taji motsin bud'e kofa da sauri tayi baya ta shige cikin labule tukunna ta d'an leko da kanta sai taga ladi ta fito sai da ta d'an dudduba bata ji wani motsi ba sai ta nufi stairs tana hawa a hankali nauwara ta fito daga bayan labule cike da mamaki take bin bayan ta taga ina xata je mamakin ta ya k'aru ganin tayi part d'in abban ta nan ta dunga binta a hankali Bata tsaya a ko'ina ba sai bedroom d'in abba ta shiga bincike ka'in da na'in kamar ta bawa wani ajiya har tayi nasarar fito da wani file cike da takaddu sosai mamaki ya dad'a kama nauwara don exactly irin takardun da abba ya bata ne sai dai wad'annan basu kai na hannun ta yawa ba ji tayi kmr ta fito ta nuna mata ta ganta sai kuma tayi tunani idan baka iya kama 6arawo ba shi ya kama ka kuma tana son taga yanda xata yi dasu Gaban nauwara ne yayi mugun fad'uwa ganin ta nufo inda take nan jikin ta ya hau rawa don tsab Wannan matar mai kama da k'irar samudawan kwaf d'aya xata yi mata nan ta fara kiran sunan Allah a xuciyar ta tuni ta fara had'a uban gumi ganin da gaske inda take nan ta nufa.............. *_Aishat A muh'd {aunty}_* 😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {aunty}_* 😘 *~pg 9~* Wata sassayan ajiyar xuciya ta saki ganin ta kauce daga inda take ta nufi inda computer abba take har ta dauka sai kuma tayi tunanin amfanin me xatayi tun da ta samu abin da ake so don hka kawai ta juya ta fice daga bedroom d'in Nauwarah ta fito daga bayan labule tana share gumin fuskar ta tare da sakin ajiyar xuciya sai da ta xauna ta huta kafin ta mik'e tsaye har xata fita sai kuma tayi baya tsayawa tayi adai dai inda computer abba take hannu tasa ta d'auke ta kafin ta fito daga d'akin tana tafiya a hnkl sai taga ladi tana wuya mamaki ya dad'a Kume nauwara da taji tana cewa " _salisu naga files d'in da kake buk'ata Gasu a hannu na gobe da yamma xanyi dubarar fito wa na kawo maka mu had'u a guest house d'in ka_" Tana gama fad'in hka ta kashe wayar sannan ta shige d'akin ta ta rufe ita ma nauwara bedroom d'in su ta shige ta jona computer a charge Kafin ta shiga toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo akan Allah ya k'are su daga sharrin Alhj salisu Gaba d'aya yinin ranar ba inda nauwara taje tana xaune tana kula da shige da ficen ladi mai aiki har xuwa 5 na yamma sai gata ta fito daga d'akin ta durkusa wa tayi agaban ammi kafin tace " _hajia don Allah ina son ki barni naje na d'ebo sauran kaya na a gidan Alhj salisu ynx xan dawo_" Shiru ammi tayi kafin tace " _ban da abinki ladi ba sai mu baki wasu kayan da xakiyi amfani dasu ba idan yaso ko drive na aika ya karbo miki_" Gaban ta ne ya fad'i ta kuma rasa mai xata ce ta fara kame kame na rashin gaskia gashi nauwara ta xuba ido ta rasa me xata ce can kuma tayi wani tunani cikin marairaicewa tace " _hajia da anbar ni naje akwai abu masu mahimmanci acikin kaya na kada sauran 'yan aikin su d'auke min a taimaka ynx xan dawo_" " _Shikenan sai kiyi sauri ki dawo Kafin mangariba_" Ammi ta fad'a tana mik'a mata kud'in transport tasa hannu ta karb'a cikin murmishi tace " _ngde hajia kuma in Allah ya yarda ynx xan dawo_" Sai da ta koma d'akin ta Sannan ta fito ta tafi xumbur nauwarah ta mik'e tsaye ta nufi bedroom d'in su wayar ta ta d'auko daga jikin charge da sauri ta fito tana cewa " _ammi ina xuwa don Allah ynx xan dawo_" Kafin ammi tayi magana ta fice daga falon cikin sauri ammi ta bita da kallo Kafin ta girgixa kai tace Allah ya shirya ki nauwara Ko ina xaki kike wannan saurin hka...... Tana fita ta hango ta nesa da ita ta hau keken napep da sauri ita ma ta shiga wani tace " _don Allah yi sauri kabi bayan wannan_" Ta fada tana nuna mishi toh yace ya tayar dashi suka tafi yana bin bayan keken napep d'in da ya d'auki ladi har suka Karaso guest house d'in ta sauka sai da ta biya shi sannan ta shige ciki Nauwara kuwa tun daga nesa Kad'an tace ya sauke ta ce " _don Allah malam ko xaka jira ni na fito ba dad'e wa xanyi ba xan biya ka har xaman da kayi_" " _toh ba damuwa xan jira ki_" Mai keken napep ya bata amsa juya wa tayi ta fara tafiya a hankali har ta k'araso gidan abin da ya bata mamaki ganin kofar a d'an bud'e a hnkl ta tura Kad'an ta d'an leka sai taga ba kowa tukunna ta shiga ciki da addu'a a bakin ta sai da tayi 'yar tafiya Kad'an tukunna ta isa bayan gidan ta window ta fara lek'e sai taga falo ne hadadde ladi na xaune akan kujera ita kad'ai bayan 'yan mintuna sai taga an bud'e kofar falon an shigo batayi mamakin ganin su ba Alhj salisu da Alhj lawan shana sai 'yar shi kuma matar Alhj salisu Wato hjy binta bata jin abin da suke fad'a amman ta ga ladi ta basu files d'in da ta d'auko sai da ya dudduba Kafin ya d'ago kai cikin b'acin rai yace da karfi har nauwara tana jiyo wa " _wad'annan ae ba original d'in takardun bane me yasa baki duba sosai ba to ina computer tun da nasan duk wasu abu masu mahimmanci suna ciki_" Cikin muryar 'yan duniya tace " _yo ae ni baka ce na d'auko da computer ba don wlh har naje xan d'auka na tuna bakace na d'auko ba_" Mtssss suka ja wani tsaki a lokaci d'aya kafin tace " _yau da dare sai na d'auko amma kai xaka xo ka karb'a gaskia ni wlh wannan yarinyar nauwara ita take ban tsoro ta fiye sa ido da yawa ga shegiyar tambaya_" A kufule Alhj salisu yace " _ina Ae xancen gama ya gama don bama xaki samu wannan computer ba amman nasan ta yarda xan b'ullo abun, ae ba ke kadai wannan shegiyar yarinyar take yiwa hka ba ko ni hka take min kuma na kusan kawo K'arshen al'amarin_" Nan yayi musu magana a hankali gaba d'aya suka kyalkyale da dariyar da ta firgita nauwara jiki na rawa ta d'auke su pictures a wayar ta da gudu ta fice daga gidan ta fad'a cikin keken napep d'in tana mayar da numfashi Kafin tayi mishi magana su tafi ta da machine din yayi suka tafi...... Alhj salisu ya dawo da kallon shi daga jikin window da nauwara ta mak'ale ashe yana kula da ita shi yace ma mai gadin ya bar Wajen gate saboda yasan xata xo sosai yarinyar take bashi mamaki yanda take da jarumta hka da ace namiji ne ae da tuni asirin su ya tono kai dole ne ma ya d'au mataki akan yarinyar nan tun Kafin ta bashi mamaki bai sanar dasu ba da hka suka watse gaba d'ayan su *_Aishat A muh'd {aunty}_* 😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 K'ARSHEN WAHALA 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {Aunty}_* *~pg 10~* A dai2 bakin gate mai keke napep ya sauke nauwara ta fito bayan ta biyashi kud'in shi bata tsaya karb'ar canji ba ta wuce cikin gidan don gaba d'aya a rude take batasan mai uncle d'in su ya radawa masu a kunne ba don tasan abin arxiki bane sai da taxo dai2 shiga falo ta d'an dai daita nutsuwar ta da sallama ta shiga ammi da safah suka amsa mata kafin ta xauna safah tace " a yawo sai ynx kikayi ra'ayin dawo wa" Hararar ta nauwara tayi had'e da murguɗa mata baki kafin tace "ohhh aunty safah wllh kin cika sa ido ina ruwan ki dani ne" Ammi ce tayi mata dak'uwa tace "gidan ku nauwara,safah kike cewa tana sa ido to idan bata sa miki ido ba wane xai sa miki ni wllh yawon nan naki ya isheni" Cike da shagwaɓa tace "hba ammina Allah aunty safahr ce sai a hankali, kuma fitar da nake tana da dalili" Kafin wani ya k'ara magana a cikin su ladi ta shigo falon da sallama ammi da safah sune suka amsa mata but nauwara harara ta watsa mata hannun ta d'auke da k'atuwar ghana must go kaya ne aciki amman ko rabin jakar basu kai ba cikin ladabin munafurci tace "hajia na dawo" "okay, sannu da dawo wa dafatan ba'a taɓa miki komai aciki ba?"ammi ta tambaye ta murmishi ta saki sannan tace "ae naci sa'a hajia don basu taɓa komai ba hankalin su bai kai wajen ba" Daga hka ta mik'e ta nufi bedroom d'in da aka bata nauwara ta bita da harara har da jan tsaki jin tsakin da taja yasa ammi da safah kallon ta "Lfyn ki kuwa nauwara kike tsaki ke d'aya?" ammi ta tambayi nauwara yatsina fuska tayi kafin tace "ni wllh ammi wannan er aikin da uncle ya kawo mana ita ban yarda da ita ba ni tsoro ma take bani" Harara ammi ta xabga mata kafin tace "bana son irin hka nauwara Hka kawai ki tsani mutum ba dalili,idan ma tsoro take baki duk lokacin da kika ganta kiyi addu'a kawai amman kada ki sake ki nuna mata na gaya miki " Zumɓura baki tayi kafin ta tashi tsaye tayi gaba tana d'an k'unk'uni safah tace " Allah ya shirya ki wllh" Cikin tsiwa ta juyo tace "idan da gaske kike toh Ameeen " Har ta bud'e baki xatayi magana ammi ta dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu shiru tayi cike da takaicin abin da nauwara tayi mata. *BAYAN K'WANA BIYU*............ Nauwara bata k'ara fita ba acikin k'wana 2 nan tana gida a xaune da tunanin yanda xata ɓillo da Wannan al'amarin don tana tsoron kada su nemi hallaka su wasu hawaye masu xafi suka sauka kan fuskar don ta tuno da abban ta takai wajen 5mint tana kuka Kafin ta mik'e ta shiga toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo tare da addu'ar Allah ya shiga tsakanin su da su Alhj salisu....... Kamar yau ranar monday da misalin karfe 1:30 na rana Alhj salisu ya xo gidan su nauwara a falon k'asa ya samu waje ya xauna bai fi 3mint da xama ba ladi mai aiki ta fito daga kitchen suna had'a ido dashi suka saki wani murmishi a tare kafin yace mata "Yawwa ladi yi min magana da hajiar ki turo min ita don ina son a yau ayi ta takare wllh" Harara ta watsa mishi kafin tace "nima ae na gaji da xaman bauta wlh gwara ayi ta a watse na samu kaso na sannan na tafi inda nafi wayo ( _daman ladi karuwa ce yaje ya d'auko ta don tayi mishi wani aikin da farko bata yarda ba sai da taji magudan kud'in da xasu bata yasa ta amince da hkan_) "shegiyar karuwa ae kuwa anjima Kad'an xaki tafi sai ki d'ora inda kika tsaya" Mtssss taja tsaki ta shige xuwa stairs don ta kirawo ammi da sallama ta shiga ammi ta amsa mata sallamar ta juyo don taji lfy wow masha Allah Kaee na yarda da salisu da nace sai ya aure ta Gasky akwai kyau sosai ita kanta ta burge ta balle namiji dakyar ta sai ta kanta cikin ladabin munafurci tace "Hajia daman Alhj salisu ne yaxo yake son magana dake" "okay,kice mishi ina xuwa Ki kai mishi ruwa da drinks" "angama hajia" Nan ta fito xuwa down stairs kitchen taje ta kawo mishi abin da ammi ta ce ta bashi ajiye mishi tayi akan table Kafin ta tsiyaya mishi lemon ta bashi cike da wani iyayi cikin murmishi tace "amman don Allah anjima na d'an xagayo guest house ka d'an rage min xafi kaga yau wajen 1wk ba harka" Ae tuni ta tsumashi da salon ta yace "kada ki damu ki xo nima na d'an huta da.............. " Kafin ya K'arasa fad'i an turo kofar falon an shigo a raxane suka juya gaba d'ayan su cikin tsananin tsoro............ Toh masu karatu sai ku canka na baku gari lol *_Aishat A muh'd {aunty}_*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 K'ARSHEN WAHALA 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *_Aishat A muh'd {aunty}_*😘 *"Wannan pg d'in ki ne my sadeey saNaz thanks for the love and support, Allah ya bar xumunci ameeen*" *~pg 11~* A raxane suka juya don ganin mai shigowa a lokaci d'aya suka saki ajiyar xuciya ta kwanciyar hankali ganin safah ce ta shigo tuni Alhj salisu ya wayance yana cewa "maxa ki d'auke drinks d'in nan ya isheni hka" Da sauri ladi ta d'auka ta shige kitchen safah tace "uncle ina yini? " "Lfy qlau 'yata, ya skul dafatan ana bada himma a karatu?? " Alhj salisu ya tambayi safah kamar wani na gari nan kuwa xuciyar shi cike da tarin tsanar ta Allah ya taimake shi ba shegiyar d'ayar bace (nauwara yake nufi) da itace sai ta d'ago wani abun cike da murmishi safah tace "skul lfy qlau uncle, sosai ma ina mai da hankali" "toh yayi kyau hakan" Daga hka safah ta shige ta nufi stairs shi kuwa ya bita da harara kamar idanun shi sa fad'o k'asa shi ae kishi yake dasu kamar yanda yake kishi da uban su wani k'amshin turaren mai sanyin k'amshi ya shak'a a hancin shi da sauri ya d'ago kanshi tuni ya shiga wani hali ya kiɗime ganin yanda tayi mishi kyau kamar bata haifi su safah ba dakyar ya iya saita kanshi suka gaisa kafin su yi shiru na wani d'an lokaci can Alhj salisu ya fara da cewa "daman abin da yasa kika ga naxo nasan xakiyi mamakin hkan toh ba wani abunne ba illa ina son ki amince min na aure ki!!!" Dummm gaban ammi ya fad'i a matuk'ar tashin hankali ta d'ago kai ta kalle shi tace "sake mai2 ta abin da kace don banji sosai ba? " Murmishi ya saki tare da gyara xaman shi tukunna ya sake mai2 ta mata maganar wani kallo ta watsa mishi cike da tsantsar tsanar don sai da gaban shi ya fad'i ganin yanda ya karanto tsantsar tsanar shi a fuskar ta amman hka ya dake cike da tsawa ammi tace "daman abin da ya kawo ka kenan toh maxa tattara tsumman jikin ka, ka barmin gida Allah ya sauwak'e min na aure ka ai ko maxa sun k'are a duniya baxan aure ka ko da ina da ra'ayin auren balle ba k'ara auren xanyi ba" "hba maimuna kalle ki fah yarinya sharaf dake Kice baxa ki sake aure ba,ae kawai ki cire matacce a xuciyar ki gani yaro sabon jini na aure ki don nasan baxa Ki iya jure rashin namiji a kusa dake ba dole ki nema don hka........... Kafin ya K'arasa fad'i ammi ta cike da takaice ta cilla mishi wayar hannun ta a goshin shi ji kake k'um da sauri ya dafe wajen cike da rad'ad'i nan da nan idon shi ya kada yayi jawur sai huci yake kamar wanda ya had'iyi kunama cikin masifa ammi ta cigaba da cewa "kuma daga rana ita yau kada ka k'ara shigo min gida tunda kai baka da mutunci d'an akuya kawai kuma ina sane da dukiyar su nauwara da kake ci kamar na ka wllh salisu kaji tsoron Allah don kayan marayu kake ci, kuma aure ne naga ya maka bazan yi ba koda xanyi baxan aure ka ba "mtssss Ammi ta K'arasa fad'i tana jan tsaki don ba k'aramin haushi ya bata ba da xata iya had'a hannun ta da fuskar shi ae da marin shi xata yi mara imani kawai shi kuwa Alhj salisu iya k'uluwa ya k'ulu tayi mishi cin mutunci da tunda ya fito daga cikin babar shi ba'a taɓa yi mishi don hka ya mik'e tsaye a fusace yace "ko kin k'i Ko kinso sai na aure ki wllh sai na cika buri na akan ki naga wanda ya isa ya hana don *adalilin son*(na saNaz) dana ke miki xan iya aikata komai don hka ki xuba ido ki gani,kuma dukiya ce anci ki fadawa duniya naga uban da ya isa ya hana" Yana gama fad'in hka ya fice fuuuu a fusace kamar ya tashi sama ammi ta xube akan kujera tana kuka tare da ambato sunan Allah a bakin ta Allah yayi musu tsari da sharrin salisu Shi kuwa yana fita daga falon a farfajiyar gidan ya had'u da nauwara tana fito wa daga mota harara ta bishi da ita shima hararar ya watsa mata a xuciyar shi yana cewa xaku ci uban ku yau don gaba d'aya sai na huce takaicin da uwar ku ta kunsa min a xuciya ta da matuk'ar gudu ya fice daga gidan Nauwara ta taɓe baki kafin ta shige k'wata k'wata ammi bata nuna wa su safah wani abun ba ko da nauwara ta tambaye ta mai yaxo yi gidan ammi cewa tayi ina ruwan ki tunda ba wajen ki yaxo ba daga hka nauwara ta ja bakin ta tayi shiru amma can k'asan xuciyar ta bata yarda ba da abin da ammi tace ba saboda yanayin ammin tasu ya jan xa...... Bedroom ta shiga ta bud'e wardrobe d'in ta ajiyar jakar da abban ta ya bata ta dauko tare da bud'e wa tana gyarawa har da d'auko pictures d'in su wanda suka d'auka gaba d'aya tana gani tare da goge hawayen da ya xubo mata a fuskar ta gyara jakar tayi tare da d'auko er K'aramar laptop d'in abba ta sanya a ciki kwanciya tayi akan bed tare da rungume jakar a jikin ta don k'amshin turaren abba take yi Har ynx da hka bacci ya dauke ta.... *12:45 pm* Karfe 12:45 na dare gari ko'ina yayi shiru baka jin motsi mutane sosai saboda lokacin sanyi ne kowa ya shige gidan shi abin da ban mamaki ganin wani haske nayi a gidan su nauwara ya tashi da na sake matsawa sai naga ashe gidan ne ya kama da wuta gaba d'ayan shi kuma a lokaci guda duk kuwa da girman gidan yanda wutar ta tashi lokaci guda da wuya wani ya tsira da ranshi sai dai wani ikon Allah.......... *Aishat A muh'd {aunty}*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *Na* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 *~pg 12~* Cikin kankanin lokaci mutane suka taro a wajen duk da sanyin da ake xabga wa a daren Hka en unguwar suka firfito cike da tashin hankali Kafin a samu a kirawo en kashe gobara gashi ba ta yanda xa'a samu a shiga saboda wutar ta kama ko'ina na gidan balle a taimaka musu Ba ɗau wani dogon lokaci ba en kashe gobara suka shigo unguwar nan da nan suka fara aikin su wajen kashe wutar ana cikin hka suka ji ana cewa "help me please somebody help me" Jin Hka yasa suka fara neman hanyar shiga dakyar suka iya samun hanya aka shiga ta Wajen da suka ji ana neman taimako ai kuwa sunyi nasarar fito da mutum 2 mace da namiji wani ikon Allah basu k'one sosai ba sai hayak'in da suka shak'ane ya sumar dasu nan da nan aka nufi hospital dasu Da gaggawa aka karɓe su nan likitoci suka Duk'ufa akan su don ceto rayuwar su bayan sun gama duba su numfashin su ya dawo normal suka yi musu allurar bacci don tsabar rud'ewa tasa su suma Acan kuma dakyar sukayi nasarar kashe wutar amma ba'a dauki komai a gidan ba sai yara 2 da aka d'auko sosai makwabtan su nauwara hankalin su ya tashi don sun san maimuna (ammi) da safah sun mutu tun da iya nauwara da saleem aka samu gashi ba mai number wani acikin en uwan su nauwara balle aneme su don hka suka hak'ura xuwa gobe da safe a neme su......... *9:20*am Misalin karfe 9:20 na safe nauwara ta tashi a firgice ta duba ta ganta a gadon asibiti nan kuma tayi shiru kwakwalwar ta ta fara tuno mata da abin da ya faru a daren jiya...... Bayan bacci ya dauke ta tana cikin bacci kamar a mafarki taji ana tashin ta a hankali ta bud'e idon ta suka had'a ido da safah harara ta watsa mata kafin tace "malama don Allah lfy kike tashi na ina cikin bacci na"mtssss Taja tsaki tare da juyawa xata koma bacci amman ganin hawaye a idon safah yasa ta tashi a firgice murya na rawa tace "aunty safah lfy meke faru wane??? " Cikin shashshak'ar kuka tace "nauwara ki nutsu kiji abin da xan fad'a miki Shigowar wasu mutane na gani yanxu sun nufi d'akin ammi kuma dukkanin su jikin su a rufe har fuskar su" Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da nauwara ta fad'a kenan da sauri ta sakko daga gadon ta jikin ta na rawa hankalin ta yayi mugun tashi xata fita daga d'akin da sauri safah ta kamo ta cikin k'asa da murya tace "baki da hankali da hka xaki fita ki nutsu kiji abin da xan ce miki, yanxu muje d'akin saleem mu d'auko shi sannan mu bi ta kofar baya ta d'akin wanda xai sadamu da part d'in ammi" Nauwara gaba d'aya ta rasa abin da xatace har sun fito daga d'akin sai nauwara ta tuna da ajiyar ta da sauri ta koma d'aki ta d'auko goyar jakar tayi a bayan ta daman tana sanye da riga da wando sai hula a kanta tana fitowa safah ta watsa mata harara Kafin tace "ke komai sai Kinyi shirme me kuma xakiyi da jaka da kika goyo ta,? " Ko uhm nauwarah ba tace ba sai ta kama hanyar da xata kai ta bedroom d'in saleem ganin hka yasa safah ta bita a hankali suke tafiyar har suka iso d'akin saleem suka shiga yana baccin shi hankali kwance har nauwara take hannun ta xata xabga mishi duka da sauri safah ta tare hannun nata tace "Allah nauwarah xan kulle ki a d'aki tunda baki da hankali Idan kika doke sa ai ihu xai yi kinga ai mun tunawa kanmu asiri mu da xamu cece ammi" Tana gama fad'in hka ta tashi saleem a hankali kafin ya watstsake taja hannun shi sun fice ta kofar baya a nutsu suka isa part d'in ammi suka labe suna sauraron kukan ammi jin an bud'e kofa xa'a fito yasa su k'ara lafewa a jikin labulen gani sukayi anjanyo ammin su ana janta ga wani da katuwar roba a hannun shi yana yayyafa abin da ke cikin robar Kafin su tantance komai ne warin shi ya doki hancin su xaro ido sukayi lokaci guda tare da had'a ido da sauri nauwarah tace "fetur ne fah aunty safah ya xamuyi ga ammi a hannun su" Bata rufe bakin ta ba taga safah ta fito daga jikin labule tana ihun akawo musu taimako tana rik'e da ammi ganin hka yasa nauwara da saleem suma suka fito suna ihun tare da rirrike ammin su nauwara tana cewa "ku sakar mana ammin mu mai tayi muku mugaye kawai " D'aya daga cikin su ya kifeta da mari saboda xafin marin sai da ta durkusa k'asa cikin k'atuwar murya wanda ke rik'e da ammi yace "ku tattara munsu ku kulle su a falon nan so nake su k'one gaba d'aya don Oga yace baya son su a rayuwa " hasbinnallahu wa ni'imal wakil,la ilaha illallahu anta subhanaka inni kunta munar zalimun abin da ammi ta fad'a kenan ta sume awajen d'aukan ta sukayi suka fice da ita sannan suka kulle su nauwara a gidan suna fitowa suka kunna wuta a gidan bayan sun xuba fetur a gidan gaba d'aya Su nauwara sai kok'arin yanda xasu k'arya kofar suke but sun k'asa suna cikin hka sai sukaji an bud'e kofar falon ido hud'u sukayi da baba mai gadin su a dai dai lokacin kuma wutar tayi karfi gashi Hayak'i ta ko'ina basa ganin junan su da hka baba mai gadi kawai yaja hannun d'aya daga cikin su sukayi hanyar fita sauran suka biyo amma Kafin su isa hanyar da sukayi wani yankin abun ya fad'o a hanyar gashi da wuta a jikin shi don hka anan suka rabo har xuwa inda aka kawo musu a gaji........... Tana dawowa daga tunani da take ta rushe da wani irin marayan kuka shin ina suka kai musu ammin su?, wanne ya turo a d'auke ammin su?, Alhj salisu shi kad'ai ne xai aikata hkan wata xuciyar ta fad'i wa nauwara tabbas Hkane ae kuwa yanxu asirin ka xai tonu ta K'arasa fad'i tana saukowa a gadon inda saleem yake taje ta bubbuga shi a hankali ya bud'e idon shi ta rungume shi a jikin ta kuka sosai take shima saleem da ya tuna abin da ya faru shima kukan ya rushe dashi toh ina aunty safah tayi???? Tambayar da tayi wa kanta Kafin ta tunano wani abun taji an bud'e kofar d'akin an shigo a kidime ta juya da sauri don ganin mai shigowa......... *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~pg 13~* Sansanyan ajiyar xuciya ta saki ganin doctor ne bayan shi da wani makocin su nan likitan ya dad'a duba su sannan ya buk'aci abasu abinci koda tea ne don su sha magani yana gama maganar ya fice daga d'akin,shi kuma makocin nasu waya ya d'auko number d'in Alhj salisu ya kirawo yana d'aga wa bayan sun gaisa yake sanar dashi abin da yake faruwa sannan ya ajiye wayar ya juyo ya Kalli nauwara da gaba d'aya hankalin ta yayi mugun tashi jin ya kirawo mak'iyan su yace "Sannu nauwara na kirawo uncle d'in don yasan asibitin da kuke tun da su baffah da inna lokacin da aka fad'a musu abin da ya faru nan take suka suma don hka yanxu suna gadon asibiti,ni xan tafi Alhj salisu yana xuwa xa'a sallame ku Allah ya k'ara lfy" Yana gama fad'in hka ya fice daga d'akin da sauri nauwara ta duro daga gadon ta janyo abin da aka shimfid'a a gadon ta rufe kanta hannun saleem ta kama suka nufi hanyar fita daga d'akin har ta bud'e kofar sai kuma ta tsaya cak saboda tunano inda ta yar da jakar ta don har aka fito dasu daga cikin wutar da jakar goye a bayan ta da sauri ta dawo d'akin ta fara bincike da sauri tana lekawa k'ark'ashin gadon taga jakar Alhmdullilah ta furta Kafin ta d'auke ta suka fito da sauri daga d'akin A bangaren Alhj salisu kuwa suna gama waya da makocin su nauwara ohhh my god yanxu daman Wannan shegiyar yarinyar bata mutu ba aiko wa duk inda kika shiga sai an nemo min ke hankali na baxai tab'a kwanciya sai naga gawar ki yana gama fad'in hka ya mik'e tsaye tare da kok'arin sanya kayan shi jin k'arar bud'e kofa yasa shi juyo wa suka had'a ido da ladi mai aikin ammi cikin mamaki tace "ina xuwa Hka kuma bayan muna tsaka da jin dad'in mu? " "ke dai bari kawai mummunan labari naji yanxu ashe wannan shegiyar yarinyar bata mutu ba ta tsira da ranta da saleem " Ya K'arasa fad'i yana huci xaro ido tayi kafin tace "yanxu suna ina don ni wlh har jikina yayi sanyi don nauwara barin ta a raye ba k'aramin baraxana ne da rayuwar mu ba don tasan komai har gwanda safah da saleem tun da basu san komai ba" "ae yanxu xan sheka da ita garin da ba'a dawowa, suna kwance gadon asibiti xuwa xanyi na danna mata pillow a hanci ko shurawa baxata kara yi ba" Da hka ya fice da sauri daga gidan bayan yayi wa yaran shi waya inda xasu xame shi A dai2 bakin gate d'in asibitin su nauwara xasu fita daga asibitin sunyi sa'a ba wanda ya gansu d'ago kanta da xatayi taga motar Alhj salisu ta shigo asibitin gaban ta ne yayi mugun fad'uwa tana addu'a a xuciyar ta Allah ya taimake su kada wannan mugun ya gansu ajiyar xuciya ta sauke ganin yayi cikin asibitin ai kuwa da gudu suka fice daga asibitin Ko tsayawa basa yi Acikin asibitin kuwa Alhj salisu da doctor d'in da yake kula dasu nauwara suka shiga d'akin amma wayam suka ga ba kowa har toilet sun duba basa nan iya kacin tashin hankali Alhj salisu ya shiga shikenan shegiyar yarinyar nan ta gudu xata tona min hba never Wlh!!! da sauri doctor ya juyo yana kallon shi don jin yana magana shikaɗai wayance wa yayi da ce mishi "ya taimaka mishi a duba asibitin gaba d'aya " Nan kuwa doctor ya amince aka shiga duba asibitin gaba d'aya amman basu nauwara hankalin shi a mugun tashe ya fito daga asibitin yana fito wa suka had'u da yaran shi don hka cikin tsananin damuwa da tashin hankali tace "na baku nan da 1hr ku kirawo ni awaya kun kashe yaran nan ai nasan kunsan su kawai kubi ta kansu da mota kada ku saurara musu so nake k'ashin su yayi rugugu ku tafi maxa" Kafin ya rufe bakin shi har sun shige mota sun rabu gida 2 kowannen su suka baxama neman marayun yaran da ake neman rayuwar su kawai don *Adalilin son* son dukiyar su da mahaifiyar su.......... Sunyi gudu sun gaji matuk'ar gaske xama sukayi a k'asan wata bishiya suna hutawa sun samu wajen 20mint da xama Kafin nauwara ta sauke tagumin da tayi tana goge hawayen fuskar ta tace da saleem "saleem tashi mu cigaba da tafiya kasan ba barin mu Xasu yi ba dole su biyo sahun mu tashar mota xamu nema mu tafi kano gidan aminin abba xamu nema acan xamu xauna hankalin mu kwance " Cikin sanyin murya saleem yace "aunty nauwara na gaji sosae gashi yunwa nake ji kuma Kinsan gidan abokin abban??? " Tambayar da saleem yayi mata tayi matuk'ar ta da hankalin ta tabbas batasan gidan abokin abba ko sunan shi bata sani yanxu a gari kamar girman kano ina xata nemo gidan tabbb wani shine tashin hankali wanda ba'a samishi rana bata taɓa tunanin xata tsinci kanta a Wannan irin rayuwar ba Wayyo ammi Wayyo aunty safah ina kuke na kasa rik'e amanar da abba ya bani kun tafi kun barni wani irin marayan kuka ta saki ita da saleem abin gwanin ban tausayi cak kukan nata ya tsaya jin tsayuwar mota a kansu ɗago kan da xatayi taji ana cewa gasu nan a xaune Wlh sune cikin xafin nama nauwara ta damki hannun saleem suka fara gudu irin na ceton rai don ko tantama babu mutanen Alhj salisu ne suka biyo su Suma basu ɓata lokaci ba suka bisu da gudu a mota anxo wata ma rarrabar hanya ta kasu kashi 2 nauwara bata tsaya duba wa a kiɗime tabi hanyar hagun ta suma suka bita kash rashin sani yafi dare duhu da tasan hanyar daman da xasu bi anan akwai wani police station a wajen amman hanyar hagun da tabi mutane basu cika binta sosai ba turkashi su nauwara Ko wacce irin *kaddara* xata faru akan su.......... *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~pg 14~* Sunyi gudu sosai har sun fara gajiya don har k'arfin gudun nasu ya ragu sosai ganin hka yasa suka Kara speed d'in gudun motar kafin su ankara jikake shuuuuut motar tayi ciki da nauwara da saleem nan suka xube a k'asa ko shurawa basu yi ba jini yana fita ta ko'ina jakar hannun ta kuwa tsalle tayi ta gangara gefen titin cikin wasu bishiyoyi ganin sun samu damar kaɗe su yasa su fito wa daga motar sai da suka duba su suka tabbatar basa numfashi ga jini yanda yake fita ta jikin su sai suka d'auka sun mutu ( *basu san Allah ya rubutawa kowanne bawa iyakar adadin kwanakin shi a duniya ba wanda ya isa ya kashe mutum sai lokacin shi yayi sai dai asha K'arshen wahala*) Basu ɓata lokaci ba suka gudu daga Wajen an d'auki wajen 45mint Kafin Allah ya kawo wani mutum subhannallah Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da mutumin nan ya fad'a kenan Kafin ya tsayar da motar shi ya fito ana hka sai ga wata taxi cike da wasu maxa a ciki nan suka fito kowa yana jimamun wannan hatsarin masu saurin kuka suka fara yi anya wad'annan bayin Allahn xasu rayu ganin yanda jini yake fita ta jikin su Babu ɓata lokaci suka d'auke su sai asibiti likitoci da fari k'in karɓar su sukayi sai da police sai kuma Allah ya taimaka akwai police cikin en taxi d'in nan don hka nan aka Duk'ufa akan su don ceto rayuwar su sai da likita ya tabbatar musu suna da rai sannan en taxi d'in nan suka tafi akabar wannan mutumin da yafara ganin su a wajen don baxai iya tafiya ya barsu ba........... Da kyakkyawan labari suka isa guest house d'in Alhj salisu suka tarar dasu da Alhj lawan shana da hajia binta suka sanar da su wannan labarin su nauwara da saleem sun bi inda baban su ya tafi nan suka cika da farinciki sosai Alhj salisu ya sallami yaran shi da kude masu yawa nan suma suka tafi da farin ciki gani nayi Alhj lawan shana ya Kalli saitin inda ladi take ya kashe mata ido d'aya sannan suka had'a ido da hajia binta dashi Alhj lawan shana da ladi sun sake wani murmishi wanda na tabbatar wannan murmishin mugunta ne shi kuwa Alhj salisu hankalin shi sam baya wajen su Tohh fa Alhj salisu kada dai reshe ya juye da mujiya........... ********** Wata mota ce lafiyayya k'irar jeep dark green ce sai xuba uban gudu take a hanyar kaduna don da gani kasan kano ta nufa gashi dare ya fara yi don Wajen 10 na dare Kwance yake a bayan motar wayar shi k'irar vivo a hannun shi yana sarrafa ta cikin gwanan cewa kyakkyawan matashi ne ajin farko yana sanye da uniform d'in shi na *army* sunyi matuk'ar yi mishi kyau kamar Don shi aka k'era su *captain Abduljabbar* kenan jarumin namiji jikake kuuuuuu driven shi ya taka birki wanda sauran Kad'an wayar shi ta suɓuto daga hannun shi a fusace ya d'ago da kanshi yace "r u mad Joseph! da xaka tsayar da mota bake nemi ixinina ba? " Driven da aka kirawo da Joseph cikin ruɗe wa da tsawar da ogan shi yayi mishi yace cikin rawar murya "sorr.........sorry boss fitsari ne ya matseni na kasa rik'e shi sauran Kad'an ya xubo" Wani wawan tsaki yaja wanda ya kad'a hanjin cikin Joseph sosai har jikin shi ya d'auki rawa Kafin ya tashi xaune yasa hannu ya murɗe kunnen Joseph da k'arfin wata er k'ara ya saki na axaba Kafin yace "ahhhhh boss I'm so sorry fitsarin sauran Kad'an ya xubo na rantse boss" Sakin kunnen shi yayi Joseph ya saki wata ajiyar xuciya har yanxu kafarshi tana matse saboda yana kwakwkwaran motsi xai xubo sai da ya gama jan ajin shi Kafin yace "get out na baka 30seconds sauran ka tsaya shirmen ka" Ae Kafin ya rufe bakin shi tuni Joseph ya fice daga motar da gudu ya K'arasa gefen titi cikin wasu ciyayo ya fara fitsarin yana sauri don kada ya shige time d'in da Oga ya bashi Ajiyar xuciya ya sauke ta jin dad'i saboda gama fitsarin da yayi don ya matse shi sosai tun basu dad'e da baro Abuja ba yake jin shi tsoro ya hana shi tsaya wa sai yanxu da yaga baxai iya jira har su je kano ba...... Idon shi yake kusa da kafar shi sai yaga wani bak'in abu wuluk dashi ai baisan lokacin da xuba ihu ba kamar ba soja ba yana cewa "ohhh my god Shikenan xan mutu Oga help me please!!! " *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 *~pg 15~* K'arar da Joseph yayi tasa Abduljabbar fito wa daga cikin motar sai tsaki yake ja dai2 inda yaji ihun Joseph ya nufa cikin tsawa yace "ihun mai kake duk ka cikawa mutane kunne taimakon uban mai xan maka?" Cikin Joseph na makyarkyata ya nuna mishi bakin abun da yake kusa da kafar shi kallo d'aya Abduljabbar ya fahimci komai ne wani wawan tsaki ya sake ja Kafin yace a fusace "lalle na yarda kai mahaukaci ne Joseph sake kallon abun ka gani " Cike da tsoro ya sake kallon wajen sai yaga ashe wata black d'in jaka ce amman duk da hka bai sake ba coz yana tunanin ko wani abun ne aciki "d'auko min bag d'in nan ka bud'e cikin ta" Ae da ace kunga yanda Joseph ya koma da idan kuka fara dariya sai cikin ku yayi ciwo don ko shi Abduljabbar d'in sai da ya dariya ta kusa ta kufce mishi amman ya dake don bai d'auko jakar ba sai da ya daɗa mai2 ta mishi maganar Joseph a firgice yace "I beg you boss ina tsoro kada bom ne a ciki" Zaro ido abduljabbar yayi kafin kuma ya sake d'aure fuska yace "ai komai ne sai ka dauko min na gani idan bom d'in ne sai ya tashi da mu daman aikin mu ai na taimakon al'umma ne" Jin abin da boss yace yasa Joseph sake rikice wa don yasan kaifi ɗaya don hka jikin na ɓari yake hannu xae ɗauka amman tuni har abduljabbar yasa hannun shi ya dauko jakar tare da bugawa Joseph jakar a bayan shi a tsorace yayi wani irin wawan tsalle ya kwasa da gudu bai ja birki a ko'ina ba sai cikin mota ya xauna yana faman sauke numfashi shi kuwa abduljabbar tsaya wa yayi yana kallon shi don yayi bala'in bashi dariya ba kaɗan ba don sai da ya murmusa kafin ya buɗe jakar don ganin abin da yake ci Da laptop yaci Karo sai wasu takardu tsaf ya duba bai ga wani abin tashin hankali ba mybe wani ne ya yar dashi abin da xuciyar shi ta sanar dashi taɓe baki yayi Kafin ya mayar da komai har xai ajiye jakar ɗin sai kawai yaji yana sha'awar tafiya da ita don hka ɗaukar ta yayi ya dawo inda suka yi parking ya buɗe mota ya shiga sannan ya Kalli joseph yace "matsoraci oya sai mu tafi " Baice komai ba yayi wa motar key suka ɗauki hanyar kano..... ... Sun shigo cikin garin kano dare yayi sosai gidan shi dake nassarawa GRA Joseph ya danna hon mai gadi sai da ya buɗe wata K'aramar kofa ya duba ya tabbatar maigidan ne sannan ya bud'e get saboda tsaro Joseph ya shigo da motar sannan ya mayar da get ya rufe ya K'arasa inda Joseph yayi parking yana yiwa abduljabbar sannu da xuwa ya amsa Kafin yayi cikin gida Wow masha Allah lokacin da na tsaya kallon gida a gasky gidan ya had'u ba kaɗan ba xubin gidan irin xubin gidajen k'asar los angles ta k'asar american sai da ya tsaya ya danna door bell tukunna yakai tsayin 15seconds Kafin er aikin gidan taxo ta bud'e Sannu da xuwa tayi mishi kafin dakyar ya iya buɗe baki ya amsa da yawwa ya shige xuwa main falon wow sakin baki nayi ina kallon k'ayataccen falon wanda colour d'in shi ash da yellow ne bakaramin had'u wa yayi ba Upstairs na gani ya hau wanda yake a tsakiyar falon sai da ya shige falo 2 kowanne da irin haduwar shi kafin ya isa ainahin bedroom d'in madam d'in shi tana kwance a katafaren gadon ta k'irar italyn bed tana faman bacci hankalin ta kwance Wani wawan tsaki yaja cike da jin haushin jiddah bcoz ya sanar da ita komai dare xai shigo kano kada tayi bacci saboda a buk'ace yake da ita a nutse ya isa gadon ya d'ora kafar shi d'aya akan gadon d'ayar tana k'asa kafin yasa hannu yana bubbuga pillown da kanta yake cikin ɓacin rai ta bud'e idon ta xaune ta tashi ba Sannu da xuwa ba irin tattalin mijin nan bakomai kawai cewa tayi "sai yanxu kuka dawo maimakon ka kyale ni nayi bacci na gobe ma had'u da safe sai ka fara tashi na cikin tsohon daren nan" Harara ya watsa mata kafin yace "na baki 10mint ki haɗo min coffee yanxu ki kawo min" Yana gama fad'in hka ya fice daga bedroom d'in nata ya nufi nashi ai sai naga d'akin duk haduwar shi sai naga bakomai bane idan aka had'a shi da haduwar d'akin abduljabbar kayan jikin shi ya fara cirewa kafin ya d'aura towel Ya nufi toilet d'in shi dake manne a jikin bedroom d'in Ita kuwa jiddah haushi ne ya isheta Shikenan mutum baxai huta ba da xarar ya dawo sai aiki shi komai dare gani yake kamar rana ce mtssss taja tsaki tare da hararar kofar da fita kamar shine a wajen yanxu xai ishi mutum da jaraba sai da ta dau tsayin 5mint kafin dakyar ta tashi ta fito falo da yake akwai kitchen a saman nan ta shiga ta haɗo mishi coffee a wani k'aramin tray d'akin shi ta nufa ko sallama babu ta tura kai ta shiga a dai2 lokacin ya fito daga toilet agogo ya duba a kalla sai da ta Kara wajen 6mint akan time din da ya bata ko kulata bai yi ba ya K'arasa gaban dressing mirror ya gyara jikin shi tare da fesa body spray a jikin shi Kafin ya xauna a bakin bed ya d'ago kai tare da watsowa jiddah wani kallo wanda har sai da ta d'an tsorata ganin idon shi yayi ja table d'in da ta ɗora coffee d'in ta tura mishi gaban shi bai mata magana ba da kanshi ya xuba saboda sam jiddah bata iya kula da miji ba kawai abin da ta iya daga chatting a waya sai kallon tsiya da shegen son jikin jaraba k'wata2 kula da miji bata iya ba tana tsaye a gaban shi har ya gama shan coffee d'in sai faman hamma take na barci Da karfi yasa hannun shi ya fisgo ta jikin shi wanda har sai da ta d'an yi er k'ara saboda ta tsorata hannu yasa yayi switch off din hasken dakin nan ya shiga sarrafa ta cikin gwanan ta tun tana k'in sakin jikin ta har ta bada kai bori ya hau don Abduljabbar ba baya bane wajen sarrafa mace da saka ta cikin nishadi don namiji shi cikakken ma kuwa don duk lokacin da jiddah taxo hannun shi sai tayi kuka da idon ta saboda ba k'aramin wahala take sha ba tun da sai ta ga dama take bashi hakk'in shi, shi yasa duk lokacin da taxo hannu yana sani yake bata wahala........ Wannan daren k'wata2 bai bar jiddah ta runtsa ba tayi kukan tayi magiyar amman duk a banxa bai rabu da ita ba sai da aka kirawo sallahr asuba tukunna ya fad'a toilet yayi wanka tare da d'aura alwala sannan ya fito sai da yayi raka'atul fijir sannan ya nufi masallacin dake jikin gidan shi wanda had'e yake da gidan shi don shi ya gina shi Jiddah kuwa kasa tashi tayi don wani shegen wahalalen bacci ne yayi awon gaba da ita, sai 6 na safe abduljabbar ya dawo gidan ya tarar tana bacci don baiga alamun ko sallah tayi ba don hka ruwan sanyin dake hannun ya d'an xubo a hannun shi ya yarfa mata a fuska da sauri ta tashi xumbur a tsorace tana sakin ajiyar xuciya don ruwan da sanyi ai baisan sanda ya tuntsire da dariyar mugunta ba haushi ya kama jiddah sosai harara ta watsa mishi kafin hawaye ya biyo baya tace "wannan ai mugunta ce don Allah ka gama wahalar dani sannan kaxo ka watsa min ruwan sanyi kana min dariya " Gimtse dariya shi yayi Kafin ya kamo ta yana rarrashin ta da hka ya lalla6a ta ta shige toilet .... *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *Na* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 *~pg 16~* *WANE CAPTAIN ABDULJABBAR* Captain abduljabbar d'an gidan Alhj ibraheem ɗanbatta ne don mahaifin shi d'an asalin garin d'anbatta ne dake garin kano su 3 awajen mahaifan su ibraheem shine babba sai mace khadijah da k'aramin su Abdulkareem shine sa'an abduljabbar sun bawa ya'yan su ilimin addini dana xamani,ibraheem bayan ya kammala makaranta shi ya samu aiki a makarantar BUK anan yake lecturing d'an boko ne na k'in k'arawa Matan shi 2 uwargidan itace hajia Fatima mai yara 4 ta farkon itace Asma'u mai bi mata abduljabbar sai kausar da FA'iza, amman aunty asma'u tayi aure tana xaune a abuja da yaran ta 2 hanan da khalipa sai kausar mai d'a 1 wanda aka samishi sunan kakan shi Wato baban kausar suna kiran shi da naufal, FA'iza kuma ko secondary bata kammala ba sauran 1yr ta gama Amaryar shi kuwa hajia sadiya Allah bai bata haihu wa ba har yanxu amman ta rik'e 'ya'yan mijin ta tsakani da Allah tana son su don hka xaman lfy sosai ake a gidan Alhj ibraheem Idan ka shiga gidan baxa ka tab'a banbanci yaran wane daga ciki ba sai dai hajia sadiya tasu taxo d'aya da abduljabbar don d'an d'akin tane tana ji dashi jinin su ya had'u fiye da sauran yaran komai tace aabduljabbar har maman shi wato hajia Fatima wadda suke kiran ta da umma ta dunga cewa ke Idan xa'a yi magana komai Kice abduljabbar sai kace shi kad'ai ne d'a a gidan ita dai aunty sadiya da yake hka suke kiranta sai dai tayi dariya kawai Abduljabbar tun tashin ya kasance yaro ne mai hankali da nutsuwa ba ruwan shi da shiga harkar da ba tashi ba gashi ya tsaya yayi ilimin addini sosai akwai kyauta don abin shi bai rufe mishi ido ba ya samu tarbiyya mai kyau bashi da tarin abokanai sam abokanan shi 2 abdulkareem wato k'anin mahaifin shi sai muh'd abokin aikin shi don tare suka yi karatu har xuwa yanxu da suke aiki Bayan wad'annan halayar abduljabbar dana fad'i yana da wasu halayar ta rashin son magana ga shi baya d'aukan raini wajen k'ananan shi don ko aunty asma'u cewa yake Ae shine babba tunda shi namiji ne mai rik'e gida ita kam tana k'asan wani, tun yana yaro yake sha'awar xama soja da Wannan burin ya tashi don hka mahaifin shi ya tsaya tsayin daka har yakai da cika mishi burin shi har ya kammala karatun shi ya fito da kyakkyawan result d'in shi wanda mahaifin shi ba k'aramin jin dad'i yayi ba, har yakai da ayanxu yana da mukamin Captain saboda kwazon shi a abuja yake aiki . Koh 5month's baiyi da yin aure ba auren xumunci akayi musu er gidan kanwar umman su ce take masifar son shi wato jiddah tun tana nuna mishi alamu har yakai ta furta mishi amman bai kula ta ba har ta gaji ta samu umman shi take sanar da ita aikuwa ba b'ata lokaci akayi auren duk da ba'a son ranshi akayi hkan ba ,amman yayi wa mahaifiyar shi biyayya ya aure ta Ko ba komai ya rage xafi da ita Kafin ya samu yarinyar da ta kwanta mishi a rai ya auro don yana da wannan burin ******* Wace jiddah matar captain abduljabbar 'yace ga malam Aminu da mama hajara ita kad'ai iyayen ta suka mallaka tayi ilimin boko har xuwa degree duk da iyayen ta basu da karfi amman sun bata ilimi gashi umman su abduljabbar tana taimaka mata sosai A rayuwar jiddah babu abin da ta tsana kamar talauci ta tsani talaka (hmmm ta mance mahaifin ta talaka ne) shi yasa gaba d'aya tarin k'awayen ta ya'yan masu kud'i ne kuma bata tab'a nuna musu iyayen ta na ainahi sai dai ta kaisu gidan su abduljabbar, gashi ta tsani kishiya a rayuwar ta don aunty sadiya ma kishi take (kishiyar umman abduljabbar fah kuji karfin hali wajen jiddah) toh ya kenan daga lokacin da ta fuskanci abduljabbar yana da ra'ayin k'ara aure??? *Aishat A muh'd*😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~pg 17~* Zaune yake akan dinning table yana breakfast k'wata2 Ya kasa cin abincin sai ruwan lipton yake sha shima d'in bai yi mishi ba saboda ya tsani en aiki suyi mishi abinci mugun kyankyami ne dashi gashi Allah ya had'a shi da mata mai shegen son jikin jaraba ji yayi xuciyar shi tana tashi dole ya ajiye cup d'in hannun shi na ruwan lipton d'in had'e da shegen Jan wani tsaki a xuciyar shi kuma yana tunanin sake aure kuma sai ya nutsu ya xaɓo wadda ta K'ware a iya abinci Tsakin da ya ja shi ya ankarar da jiddah da take tacin abincin ta hankali kwance kallon shi tayi kafin tace "Lfy kake jan tsaki?" Wani kallo ya watsa mata mai cike da jin haushin ta kafin dakyar ya iya bud'e baki yace "ai dole ki tambaye man tun da Kinsan bana son girkin mai aiki nafison kiyi min da kanki but kin k'i jin magana" "kai ma dai my darling akwai ka da mai da agogo hannu kasan ban iya girki how many times kake wannan maganar but ina fad'a maka gasky fah" "okay tunda Hkne xan nemi yarinyar da ta iya girki na aura wannan kad'ai shine mafita, tun da girman kai ya hana ki tsayawa FA'iza ta koya miki " Tun da ya fara maganar take watso mishi harara cike da jin haushin shi shima a fusace ya K'arasa maganar tashi mik'e wa tsaye tayi cikin masifa tace "wllh baka isa kayi min kishiya kai nawa ne ni kad'ai Banga shegiyar da ta isa ta shigo gidan nan ba kuma girki ne baxan koya ba saboda nayi aure ne don na huta ba don.................. " Kafin ta K'arasa maganar ta jin saukar wani kyakkyawan mari taji a fuskar ta ba shiri tayi shiru akwai kuwa yayi nasarar fasa mata baki don jinine ya fito daga bakin na ta ai kuwa ganin jini yasa ta kurma wani uban ihu tana kuka dakyar ya iya bud'e baki yace mata saboda tsananin bacin rai "as frm today ki tabbatar wannan shine last da xaki dunga yi min nonses shouting a kunne stupid gal" Yana gama fad'in hka ya fice daga gidan cike da bacin ran da jiddah ta hassada mishi,ya bar Jiddah a kwance a falo tana kururuwar kuka kamar wadda aka aiko mata da sakon mutuwar iyayen ta. direct wajen motar shi ya nufa Joseph dake xaune da mai gadi suna hira yana ganin boss d'in shi ya fito cikin bacin rai da gudu ya K'arasa wajen shi tare da bud'e mishi mota ya shiga shima ya xauna a sit d'in driver key ya sawa motar suka fice daga gidan harba motar yayi kan titi sannan cikin tsoro yace "boss ina xamuje???" Shiru yayi sai da ya kwashi wajen 5mint kafin ya iya cewa "gidan mu xaka kai ni" "okay boss" Daga hka yaja bakin shi yayi shiru saboda yana tsoron sake wata maganar ya janyo wa kanshi wani punishment d'in don boss ba sauk'i baya d'aukan raini. A bangaren jiddah kuwa dakyar ta iya yin shiru ta janyo tissue akan dinning table ta goge jinin da ya fito wajen har ya d'an kumbura waya ta janyo number d'in umman abduljabbar ta dialing tana jin umma ta d'auka nan ta fashe da kuka tuni umma ta rikice tana tambayar ta lfy dakyar ta iya xayya ne mata abin da abduljabbar yayi mata har da Karin wani abun nan umma ta cika tayi fam da ita tace bari yaxo ya same ta anan tayi hangin up d'in wayar ta ajiye tana mai sauke ajiyar xuciya Kafin ta tashi ta shige bedroom wanka tayi ta shirya cikin wata super holland dinkin riga da siket ya kamata tsam ta bulbule jikin ta da turare tare da yafa wani mayafi K'arami kamar ba matar aure ba wani uban hill ta sanya da wata katuwar handbag wayar ta da key d'in mota ta d'auka fice wa tayi daga gidan ta tafi wurin aikin ta (sorry masu karatu namance ban fad'a muku jiddah tana aiki ba, ita ma'aikaciya ce diamond bank). Abduljabbar yana shiga falon umma da sallama dakyar ta iya amsa mishi sallamr saboda tasan mahimmancin sallama ba don hka ba ko uhm baxa tace mishi ba saboda ya b'ata mata rai dukan mace ai ba d'abi ace mai kyau ba, jikin shi ne yayi sanyi ganin yanda umma ta had'e rai xube wa yayi a k'asa yana gaida ita nan ta shiga yi mishi fad'a sosai shi dai hak'uri yake bata kawai don in ranshi yayi dubu ya b'aci saboda baya k'aunar a had'a shi da mahaifiyar shi nan dakyar ya bata hak'uri ta hak'ura daga nan part d'in auntyn shi ya shige wato aunty sadiya kishiyar umman shi don yasan yanxu abba yana office Jagwab ya xube kan kujera cike da bacin rai kallo d'aya auntyn tashi tayi mishi ta gane ran en maxa ya b'aci yau bata yi mishi magana ba sai da ta had'a mishi lafiyayyen breakfast don tasan bai wani karya ba idan da sabo ta saba Idan yana gari sai yaxo gida yake cin abinci sam baiyi dacen mata ajiyar xuciya ta sauke cike da jin tausayin shi tace "ya kamata kaci abincin mayi magana daga baya" Hka ya ciccusa abincin ba don dad'i ba duk da favourite food d'in shine b'acin ran da yake tare dashi shi yasa ya kasa cin abincin cikin jin dad'i da hka ya gama ci tissue ya d'auko ya goge bakin shi Kafin ya nutsu ya kwashe yanda suka yi da Jiddah da k'arar shi da takawo wajen umma cikin tsananin tausayin shi aunty tace "kayi hak'uri abduljabbar wataran sai labari a gaskia bata kyauta ba amman dukan da kayi mata sam bai dace ba ka daina saurin duka sannan idan kana da ra'ayin sake aure ni baxan hana ka ba saboda hkan raya sunnah ne kuma kai Allah bai had'a ka da mace ta gari ba ka cigaba da hak'uri d'ana" Da hka ta lalla6a shi har hankalin shi ya kwanta kafin ya fice daga gidan office d'in abban shi ya shige............ ********** La'ilaha illallahu muhammadun rasulillahi sallalahu alaihi wassalam, la haula wala quwwati illa billahil aliyar axeem da wannan addu'ar nauwara ta farka a matuk'ar raxane sai dai me kafar ta ce tayi mata wani irin nauyi gashi wani irin duhu take gani a idon ta duhu dulum Don hka cikin rud'ewa ta fara kiran sunan saleem da karfin gaske da sauri saleem wanda yake a gaban ta yace "gani aunty nauwarah a Kusa dake" Lalibe yaga tana yi cikin kuka take cewa "saleem kana ina bana gani gashi kuma na kasa tashi kafata tayi wani iri kana ina ne yanxu muna ina?" Sosai hankalin saleem ya tashi cikin kuka ya fara cewa "Muna asibiti aunty da gaske bakya gani na wayyo Allah na" Nan ya rungume ta suka fashe da wani irin kuka mai ban tausayi koni sunyi bala'in ban tausayi har bansan lokacin da nima na fara goge hawaye na ba.... Bud'e kofar akayi doctor ne ya shigo da wanda ya fara ganin su a kwance a hanya bayan an kad'e su don shi yake dawainiya dasu nan saleem cikin kuka yace "doctor I beg you ka taimaka min kada aunty nauwara ta samu matsala plz" Cikin tausayin su doctor yace "kada ka damu saleem I will try Insha Allah xata samu lfy" "doctor bata gani fah kuma ta kasa d'aga kafar ta" A rikice suka kalle shi har suna had'a baki wajen cewa "da gaske kake saleem" "k'warai da gaske yake yanxu hka bana ganin ku sai maganar ku nake ji kawai?" Nauwara ta fad'i hkan tana kuka gaba d'aya sunyi matuk'ar tausaya mata wannan ai shine ana wata ga wata turkashi............ _masoya na ngde da irin k'aunar da kuke nuna min tnx for luv nd support nima ina kaunar ku_❤😘 *```Aishat A muh'd {Aunty }*```😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 _wannan page d'in sadaukar wa ce da hadiza (sarauta) grp admin d'in ladies zone, da en grp d'in Aunty & sadeey novels grp da saNaz fans luv you so much_❤😘 *~pg 18~* Cikin sauri doctor ya shiga duba ta sai dai kash iya kacin dubuwar shi ya kasa gane mai ya faru da idon ta ta daina gani da kafar ta da tak'i amfani gashi babu kwararrun kayan aiki da xa'a bincike ta gashi wanda yake d'aukar nauyin kula dasu bashi da kud'in da xai iya kaisu asibitin da xa'a duba ta dole tasa dakyar ya had'a kud'i ya siya wa nauwara kujerar guragu Saleem da nauwara sun ci kuka sosai amman basu da xasu iya dole suka rungumi k'addara gashi jakar su mai tattare da duk mahimman abubuwa ta b'ata don an neme ta an rasa har wajen mutumin mai suna Aminu yaje ya duba mata but bai ganta ba a ranar yini nauwara tayi tana kuka dakyar suka rarrashe ta tukunna ta yi shiru amma duk wanda ya kalle ta yasan tana tare da damuwa duk tabi ta rame tayi duhu kai ba kace wannan nauwaran ce ba ma'abociyar kyau da son gayu rayuwa kenan juyi juyi wai kad'o ya fad'a ruwan xafi Kamar yau da safe wajen 12 na rana doctor ya basu sallama wasu nurse suka d'ora nauwara kan keken saleem ya fara tura ta aminu yana bayan su da hka suka fice daga asibitin adai2 bakin gate suka tsaya aminu yace "toh ni nauwara ina xan kai ku don ni kano na nufa yanxu saboda ni d'an can ne wlh tausayin ku ne yasa ni tsayawa " "kano "nauwara da saleem suka mai2 ta da sauri nauwara tace "mu tafi kanon tare sai ka barmu xamu nemi d'an uwan abba na acan " "toh Shikenan ba damuwa " Da hka suka shiga motar shi nauwara tana xaune a baya saleem a gaba shi kuma aminu yana sit d'in driver da key yayi motar bayan sun gama karanta addu'ar tafiya nan ya d'auki hanyar da xata kaisu kano. ********* 6pm ta shigo gidan a gajiye take saboda tasha aiki sosai a office kan kujera ta xube tare da kwala wa er aikin ta larai kira da sauri ta shigo falon har tana tuntube saboda tsoron masifar jiddah a gaban ta ta durkusa tana cewa "gani hajia" Sai da ta gama shan k'amshin ta kamar wata jinin sarautah sannan tace "5 alive xaki kawo min mai sanyi da cake guda 3" "toh hajia " Larai ta bata amsa tana mik'e wa da sauri ta shige kitchen ta d'auko mata five alive din da cake a wani k'aramin tray ta kawo mata falon lokacin har ta cire d'an kwalin kanta a kan k'aramin table d'in dake gaban ta ta ajiye mata har ta juya da nufin tafiya taji jiddah tace "ji mana larai da dare ina son ki dafa min jellop d'in taliya da kifi sosai a ciki " "toh hajia " Tana gama fad'in hka ta shige kitchen ita kuma jiddah ta fara shan drink d'in tana had'a wa da cake hannun ta d'ayan tana faman chatting har aka kirawo sallah a masallaci aka idar ba tayi niyyan tashi ba balle tayi sallahr sai faman hira take xuba wa a group tana faman dariya 9pm ya shigo gidan da sallama d'auke a bakin shi, tana xaune a dinning table ko d'aga kai bata yi ba ta kalle shi balle ta amsa mishi sallamar shi ma bai kula ta ba stairs ya nufa ta bishi da harara har da jan d'an siririn tsaki ta juyar da kanta tana cin abincin ta hankali kwance tana gama wa ta tattara tarkacen ta bedroom ta nufa gado ta fad'a cike da gajiya bacci yayi awon gaba da ita *BAYAN KWANA BIYU* Acikin wad'annan kwanakin jiddah da abduljabbar sam basa shiri ko magana basa yi a junan kowa harkar gaban shi ya keyi Zaune suke a falon abdulkareem suna er hira sam babu walwala a fuskar abduljabbar yana kula dashi yasan matsalar d'an uwan nashi bai wuce jiddah ba don itace matsalar shi hannu yasa ya dafa kafad'ar shi cike da kulawa yace "kayi hak'uri abduljabbar komai yayi xafi maganin shi Allah nasan wannan damuwar taka bai wuce jiddah ba hak'uri xakayi da ita tunda umma tana sonta" Ajiyar xuciya ya saki kafin yace "hmm abdul na dai na sa damuwar jiddah a raina don wllh aure xan saki duk da bani da ra'ayin sake aure amman jiddah ta kaini bango ace mace k'wata 2 bata iya kula da miji ba babu tarairayar miji Bata iya girki ba da kula da gida ba, babu abin da ta sani daga kallo sai chatting sai xuwa office kana ganin tak'i bina abuja sai dai duk weekend ina hanyar xuwa kano Wlh duk ranar da na samu yarinyar da nake so na aura Idan na d'auke ta na tafi xaku dad'e baku ganni ba taje taci aiki" Ya K'arasa maganar yana faman huci abin ya bawa abdulkareem dariya sai dai ya danne ta saboda sanin halin abduljabbar yanxu ya dad'a tunxura shi hak'uri ya bashi tare da lalla6a shi har ya samu ya d'an huci Washe gari da safe ya huce xuwa abuja saboda ta kama ranar monday don ko had'u wa da jiddah basu yi ba sai farka wa tayi taga damin kudade a falon ta nan ta dauke su cikin farinciki Ko nuna damuwar ta ya tafi basu yi sallama ba bata yi ba...... *```Aishat A muh'd*```😘 [2/19, 4:54 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~pg 19~* Su nauwara sun shigo kano lfy wajen da yamma lis waje ya samu yayi parking tukunna yace "toh nauwara da saleem Allah ya kawo mu lafia yanxu a ina xan sauke ku don ina son tafiya gida? " Nan hankalin nauwara ya mugun tashi tayi shiru don ta rasa abin cewa tun da wannan Karon shine farkon xuwan ta kano ba tasan ko'ina ba can tace "ka sauke mu anan ya isa ma saleem xai nemo mana gidan " "ayi hka kuwa nauwara ku fad'a min gasky idan ina da halin da xan taimake ku xan taimaka muku" Cikin rawar murya kamar xata fashe da kuka tace "a gaskia mu marayu iyayen mu sun rasu shine muka fito neman dangin mahaifin mu to shine mota ta kad'e mu "(ta b'oye mishi gaskiyar labarin nasu ko saboda me ohho ita ta barwa kanta sani) Sosai aminu ya tausaya musu don hka yace " ba damuwa xan taimaka muku tsakani da Allah baxan cutar da kuba ina da mata guda d'aya da yara 2 xan kaiku gida na ku xauna acan Kafin musan yanda Allah xai kawo muku mafita " Wata sassayan ajiyar xuciya nauwara ta saki tare da jin wani irin dad'i a xuciyar ta "Mun gode Allah ya saka maka da alkhairi " Nan suka dunga yi mishi godiya har sai da yace "Ya isa hka godiyar nauwara Allah ya baki Lfy " "Ameeen "suka amsa nan ya yiwa motar key sai unguwar gadon k'aya anan yake da xama gidan shi mai dai dai ci mai kyau yana da rufin asirin shi don ma'aikaci ne a gidan radio freedom wato d'an jarida ne Da sallama suka shiga falon gidan saleem yana tura nauwara a kan keken guragu shi kuma aminu yana gaba suna bayan shi da matar gidan ta amsa mishi sallamar shi da fara'a a fuskar ta taso don tarar shi tana ganin shi tare dasu nauwara tayi kicin kicin ta b'ata fuska kamar ba itace mai fara'a yanxu ba cikin b'acin rai tace "Abban jamila lafia na ganka da wad'annan yaran?" Kallon ta yayi yana d'an murmishin yak'e don sam ya mance da halin matar tashi don hindatu bata son taga an rab'i mijin ta daga ita sai ya'yan su yace "ai Kya bari mu huta kafin nayi miki bayanin ko suwaye, yanxu ki kaisu d'akin da muke saukar baki su yi wanka ki basu abinci" Sam ba'a son ranta ta yarda ba saleem da nauwara sun gaida ita amman bata amsa ba tun daga Wannan lokacin jikin su yayi sanyi don dakyar xa'a dai dai ta da matar gidan, tana kaisu d'akin ta juya ta fita bayan ta nuna wa saleem toilet d'in dake cikin bedroom d'in da hannun ta bayan ta fita daga d'akin nauwara tace "saleem anya wannan matar xata karb'e mu kuwa duk da bana ganin ta banga yanayin ta ba amman nasan xaman mu a gidanan ba mai d'orewa bane uncle ka cuce mu ka tarwatsa mana rayuwar mu Insha Allah sai Allah ya saka mana mugu axxalimi " Ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi shima saleem kukan ya keyi sai da suka yi mai isar su kafin dakyar saleem ya tura nauwara toilet ya had'a mata ruwan wanka sannan ya fito a toilet d'in ya xauna abakin gadon cike da tausayin er uwar shi "saleem na gama xo ka fito dani" yaji muryar nauwara tana kwala mishi Kira da sauri ya tashi ya shiga toilet d'in ya turo ta sai da ya bata kayan da xata sanya da hannun shi Kafin ya shiga toilet d'in don yayi wanka lokacin da ya fito har ta gama xura doguwar riga da d'aura d'an kwalin kanta ta rufe gashin kanta shima saleem canja kayan yayi kafin ya kwashe masu dattin ya shiga toilet dasu ya wanke su dakyar Allah sarki saleem rayuwa kenan juyi juyi lokacin da suke gida sai dai ya cire masu dattin ya xubar a ko'ina sai dai a kwashe a wanke mishi a goge sannan a jera mishi a wardrobe sai dai kawai ya d'auka (daman Hka rayuwa take Ko wanne bawa da irin k'addarar shi sai dai fatan Allah ya bamu ikon cinye ta Ameeen) Suna xaune a d'akin duk yunwa ta gama galabaita su tun suna yin hira har magana ta gagare su sai wurin 11pm na dare aka banko kofar d'akin a fusace a firgice suka tashi don har wani wahalalen bacci ya soma d'aukan su gaban su sai fad'uwa yake ba irin saleem da yake ganin ta yanda ta b'ata rai cikin jin haushin su tace "gashi nan idan kuna da ra'ayin ci tun da kuka biyo mijina gidana Wlh da kafar ku xaku bar gidan hka kawai bansan da mugun abun da kuka shigo min gida ba mtsss matsiya ta kawai " Tana gama fad'in hka ta ja kofar da karfi ji kake bammmm, kuka ba k'in fito wa yayi daga idon su banda kaddara yaushe har xaki ganmu balle ki dunga cin mutunci mu abin da nauwara ta fad'a acikin xuciyar ta kenan "Don Allah nauwara da saleem Kuyi hak'uri bansan har yanxu bata kawo muku abinci wlh bacci ne ya d'auke ni ban dad'e da farka wa nake tambayar ta an kawo muku abinci take cewa wai bata baku ba Kuyi hak'uri " Taji muryar aminu yana yi musu magana nan ya rarrashe bai tafi ba sai da ya tabbatar sunci abincin sun sha ruwa saleem ya bawa nauwara magungunan ta tukunna yayi musu sai da safe ya fice daga d'akin cike da tsananin tausayin su rufe kofar saleem yayi kafin ya taimaka wa nauwara ta, ta kwanta kan gadon shi kuma ya kwanta kan carpet d'in da yake shimfid'e a k'asa nan da nan bacci ya dauke shi ita kuma nauwara ta dad'e Bata yi bacci ba tana tunanin yanda rayuwar su xata kasance anan gidan......... *```Aishat A muh'd*```😘 [2/19, 7:13 PM] Aishat A muh'd ✍🏻: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~pg 20~* Washe gari da safe aminu ya samu lokacin bawa hindatu matar shi labarin su nauwara da saleem tare da rokan ta da kwantar da hankalin ta taimaka musu kawai xasu yi kuma xasu samu d'inbbun lada wajen ubangiji tun da taimakon marayu ne nan Yayi ta lalla6a amman sam hindatu bata amince da abin da ya fad'a mata hkan da yayi yasa ta dad'a jin tsanar su nauwara don hka yana gama maganar shi ta d'ago kai ta kalle shi Kafin tace "ka gama maganar ka don ina da abin yi wlh sam yaran nan basu kwanta min arai ba yara kamar 'ya'yan aljanu don kyau ka wani ya yibo mana su " Tana gama fad'in hka fuuuu ta shige ta gaban shi kamar wanda xata ta tashi sama ranta a matuk'ar b'ace ta shige kitchen aminu ya bita da kallo a ranshi yana mata fatan shiryawa Allah dai yaga niyyar shi taimakon su xai yi ba da wata mafita ya ajiye su a gidan shi ba Da hka ya shirya ya fice office don ko breakfast bai tsaya yayi ba saboda haushin hindatu da yake ji hkan da yayi ba k'aramin k'ara kular da ita yayi ba gashi ko sallama bai yi mata tana kallo ya shiga d'akin da su nauwara suke yayi musu maganar ya fita office daga hka yasa kai ya fice daga gidan, yini cur su nauwara suka yi bata basu abinci ba sai gaf da aminu xai dawo daga Wajen aiki sannan ta xubo wani abinci d'an Kad'an shinkafa da mai kawai ta basu don mugunta abincin da saleem shi kad'ai baxai isheshi yaci ya koshi ba ballan tana su biyu Sunci kuka sun koshi saboda yunwa su kadai a d'aki sai ruwa da saleem yake d'ebo musu a famfon cikin toilet d'in suna sha idan yunwa ta dame su duk sunyi wani xura xuru garammm ta turo kofa tare da kallon su irin kallon wulakancin nan kafin tayi dariyar mugunta ganin duk sunyi wani xuru dasu tace "Wlh horan yunwa ma kadai ya isa ku barmin gida "Mtsss taja tsaki kafin ta dangwarar musu da robar da ta xuba musu abincin tayi gaba da sauri saleem ya tashi ya d'auko robar ya mik'ewa nauwara robar tare da kamo hannun ta ya xura shi a cikin robar da sauri ta janye hannun ta a ciki jin abincin ko saleem baxai koshi ba cikin rawar murya tace "saleem kaci kawai ni na hak'ura " Ta K'arasa fad'i hawaye suna xuba a idon ta shima saleem d'in hawaye ya fara Kafin yace "Aunty nauwara kici abincin pls muyi maleji dashi " Girgixa kai tayi tana cewa "baxa'a yi hka ba nafi son kaci don kayi karfi ka dunga tare min fad'a kaga bana kallon komai a ido na sai duhu " Ta K'arasa fad'i tana Murmishin yak'e wanda ake cewa yafi kuka ciwo duk da hka saleem bai hak'ura yaci shi kad'ai ba yana ci yana bata a baki har suka lamushe shi gaba d'aya sannan suka sha ruwa sai lokacin saleem ya bata magungunan ta don yinin yau bata sha ba saboda basu ci abinci ba Aminu kuwa yana office amman Allah Allah yake lokacin tashin su yayi saboda gaba d'aya tunanin su nauwara ya yini dashi a office dinshi don yasan halin hindatu sai ta hanasu abinci don hka da suka tashi sai da ya tsaya yayi musu takeaway ya d'an siya musu irin kayan tea da manyan bread ya taho musu dashi amman yana addu'a acikin xuciyar shi Allah yasa hindatu bata xaune a falo don ya samu damar basu abin da ya siyo musu ajiyar xuciya ya saki ganin bata nan don hka da sauri ya shiga d'akin da sallama suka amsa mishi da fara'ar su nan ya yiwa nauwara ya jiki sannan ya dad'a basu hak'uri ko hindatu tayi musu wani abun bayan tafiyar shi don mai hali baya fasa halin shi tukunna ya mik'ewa saleem babbar ledar hannun shi yace "ga wannan Kuyi maleji dashi Idan bata baku abinci ba sai ku dunga ci idan ya k'are sai ku fad'a min amman saleem ku B'uye shi saboda Idan ta gani xata kwace muku " Godiya suka yi mishi sosai sannan ya fice daga d'akin yana fito wa falon suka had'a ido da hindatu kallon shi tayi tare da tabe baki ta shige kitchen cike da b'acin rai saboda da ya dawo mai makon ya fara neman ta da yaran shi sai wad'annan en iskan Ya fara nema dole ma nasan yanda xan billo musu don su bar gidan nan baxan iya xama dasu ba wlh Yana fita daga d'akin saleem yace "aunty nauwara na b'oye mana kayan idan dare yayi muka kulle kofar ma bud'e muci saboda kada ta shigo ta gani ta kwace mana " "Ehhh saleem hka xa'a yi ka kawo shawara mai kyau shi yasa nake k'ara son ka autan ammi" Murmishi kawai yayi sannan yace "aunty an kirawo sallah fa na kai ki toilet kiyi alwala " "Yawwa d'an kanina kai ni sai muyi sallah" Alwala duk suka yi suka gabatar da sallah har aka kirawo sallahr isha'e ita ma sukayi tare da yin addu'o'in su suka xauna suna hira sai 9 na dare ta kawo musu abinci kamar na rana sai da ta gama yi musu rashin mutunci da gori tukunna ta dangwarar musu da robar tayi gaba nan saleem ya janyo suka ci suna gama ci aminu yaxo yayi musu sai da safe yana fita saleem ya je ya rufe kofa da key ya dawo ya janyo ledar tare da firfito da abubuwan ciki yana gaya wa nauwara abin da suke ciki tana gid'a kai tare da yiwa aminu fatan alkhairi a ko'ina yake saboda ba k'aramin taimakon su yayi ba a Wannam xamanin da muke ciki son xuciya yayi wa mutane yawa d'ai d'ai Kune masu halin irin na aminu sunci sun koshi sun sha ruwa tare da bata magungunan ta sannan suka kwanta bacci.......... *```Aishat A muh'd*```😘  *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? _wannan page d'in sadaukar wa ce ga duk masoyan wannan littafin Allah ya bani ikon kammala muku shi, Kuyi hak'uri da yanda bana yi muku typing kullum kunsan jiki da jini ga kuma uxirrika dafatan xakuyi hak'uri da hkan luv you so much_❤?? *~Pg 21~* Kwance yake a katafaren gadon shi yana kwance but ba sleeping yake ba kawai tsabagen sha'awa ce take masifar damun shi sai juyi yake tare da yin tsaki lokaci lokaci a kalla ba kasara ba rabon shi da kasance wa da matar shi (jiddah) yau tsawon 2weeks kenan tun da ya baro kano cike da haushin ta gashi ko kiranta yak'i yayi a waya wani mugun tsaki ya dad'a ja Kafin ya mik'e ya nufi toilet a xuciyar shi yana tunanin ya xama dole ya k'ara aure tunda yana da kud'in da xai iya auren uku nan gaba yana da damar ciyar dasu kuma addini ya bashi damar hkan Shower ya sakarwa kanshi ruwa yana ta xuba tunda ga kanshi har kafar shi sai da ya d'an samu sauk'in abin da yake damunshi Kafin yayi wanka sosai ya fito daga toilet d'in d'aure da towel a kugun shi da ka ganshi kaga cikakken namiji jarumi saboda yanda jikin shi yake a murd'e goge kanshi yayi da wani k'aramin towel Kafin ya shafa wani mai cream ya feshe jikin shi da wani body spray mai masifar k'amshi tukunna ya shirya cikin uniform d'in shi na army sunyi matuk'ar yi mishi kyau sannan ya taje gashin kanshi tare da shafa mai sai sheki yake yi ya fesa wani perfumes na kai Kafin ya fesa na jiki tuni d'akin ya d'au k'amshi mai sanyin k'amshi sai a lokacin na k'are mishi kallo sosai Captain abduljabbar Kyakkyawa ne na ajin K'arshe dogo ne shi sambal dashi sai dai yana da faffaden kirji dai dai misali fari ne sol dashi don umman shi ya biyo duk cikin yaran ta shine ya d'ebo kyanta, akwai dogon hancin tare da wani baki d'an k'arami sai dai leb'en shi masu d'an fad'i ne Kad'an gasu lips d'in red colour ne amman red d'in mai d'an haske sai idanun shi masu kalar haske ne kwayar idon kalar su irin sexy eyes girar shi kuwa had'e take sumar kanshi mai kyau ce gata baka ga laushi da santsi kamar yana relaxer sai dai natural hair ne irin na asalin Fulani bai cika yin dariya ba sai murmishi yana dimple idan yayi magana ko dariya suna lotsawa da kuma wani a k'asan ha6ar shi kai gasky abduljabbar ya had'u ta ko'ina hand some guy Bayan ya gama sa takalmin shi ya mik'e tsaye tare da d'aukan bindigar k'irar pistol yasa ta a cikin belt d'in ta ta jikin wando sannan ya fito xuwa falo ya tarar driven shi joseph a tsaye bakin kofar shigo wa falo kukun shi kuma yana shirya mishi table don yin breakfast joseph yana ganin shi ya sara mishi tare da kamewa yana cewa "Gud mrng boss?" Kallon shi yayi tare da d'aga mishi hannu kawai yayi gaba xuwa Wajen da dinning table yake coffee mai xafi ya iya sha sai plantain da eggs yana kammala ci ya yago tissue ya goge bakin shi sannan ya mik'e ya fice daga falon xuwa farfajiyar gidan tuni Joseph ya bud'e mishi kofa ya shiga sannan ya rufe da sauri ya shiga sit d'in driver yayi wa motar key suka fice daga gidan direct office d'in shi ya shige dashi. ******** Zaune take acikin office d'in ta ta buga uban tagumi duk abin duniya ya ishe ta saboda yau wajen 15days abduljabbar bai kirawo ta ba kuma duk weekend ya saba yi agida but tsawon kwanakin nan baixo ba Lallai Wannan ba k'aramin fushi yake da ita ba tayi xurfi a tunani sosai taji an kwankwasa table d'in da karfi firgigit tayi ta dawo hayyacin ta, Kafin ta d'ago kanta don ganin waye ido hud'u suka had'a da farida kawar ta cikin sanyin murya tace "farida yaushe kika shigo ?" "daman ina xaki san na shigo irin wannan dogon tunani hka lafia mai yake damun ki? " Wadda aka kirawo farida ta tambayi jiddah ajiyar xuciya ta saki kafin tace "hmm kawata Wlh ina cikin damuwa abduljabbar ne yake fushi dani tsawon kwanaki 15 bai neme ni ko awaya gashi ko weekend bai xo ba na rasa yanda xanyi ki taimaka min kawata ina cikin wani hali saboda shi akan abincin da masu aiki suke yi ne baya so wai kuma ban iya kula da miji ba kinji fah? " Dariya farida ta tuntsire da ita Har abin ya kular da jiddah taja tsaki mtsss tana cewa "matsala ta dake faridah kenan maimakon ki bani shawara yanda xan bullo kyasa ni agaba Kina yi min dariya " Dakyar ta iya tsayar da dariyar ganin ta kular da jiddah tace "Kafin ince miki komai xo kiga wani abu" Tsaye ta mik'e tare da kamo hannun jiddah xuwa window d'in dake cikin office d'in tare da nuna mata wata shegiyar mota k'irar CRV kalar green sai d'aukan ido take sannan ta takamo hannun ta suka xauna ita dai jiddah binta da kallo kawai take baki sake......... *```Aishat A muh'd*```?? [4/9, 16:44] Umar Dalha: ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? _Aunty ameerah (group admin ( *mata masu sarauta*) wannan page d'in naki ne ngde da yanda kike k'aunar littafin nan tnx for luv nd support_❤?? ☘ *~Pg 22~*☘ Cikin murmishi farida tace "kinga wannnan sabuwar motar to yau na fara amfani da ita Alhj nane ya siya min ita kud'i xaki tanada na rakaki wajen wani malam" "malam" jiddah ta mai 2 ta cikin mamaki "k'warai da gaske malam xai yi miki aiki tamkar yankan wuk'a sai Kinxo kina juya abduljabbar son ranki " "hmm wannan miskilin ne xai jiyo vakisan irin su asiri bai fiye kamasu ba, ni dai baxan iya asarar kud'i na abanxa ba wlh kawai ki fad'a min hanya mafi sauk'i,ke da kika ga xaki iya sai kiyi tayi Allah ya shirye ki" Ta6e baki farida tayi kafin tace "Shikenan tunda hka kike so Indai baki bi hanyar da nabi na mallake Alhj na to na tabbatar Kina tare da wulakancin d'a namiji" "Ehh na dai ji Kinsan na tsani bin malamai a rayuwa ta don na mallaki wani ina tsoron had'u wa ta da Allah, duk da bani da mutunci amman ina tsoron bin malamai" Jiddah ta fad'i hkan tana danna computer dake gaban ta hararar ta farida tayi kafin a fusace tace "Eeee mu da yake bama jin tsoron Allah kike nufi ai Shikenan " "Ohh farida matsala ta dake saurin fushi da hasala I'm so sorry my frnd yanxu ban shawara ya xanyi mu shirya da wannan miskilin mijin nawa" "messages xaki tura mishi na yaudara masu kwantar da hankali ki nuna mishi Kinyi nadama, sannan ki kirawo shi Ki dad'a bashi hak'uri har da kukan kissa xaki had'a " "yayi k'awar tawa hka nake son ki " Dariya suka sa tare da tafawa Kafin Jiddah tace "ni fah baxan iya girki ba wlh don ban ma iya ba sam" "yanda xa'a yi tun da baya son girkin er aiki na mace to ki samu kuku namiji ya dunga yi mishi saboda ko acan abuja ai kuku ne mai yi mishi, idan banda shirmen ki jiddah me yasa baxa ki bar aikin ki Kina binshi ba " Harara Jiddah ta watsa mata sannan tace "tabbb na bishi ya kashe ni kenan, Kinsan halin Abduljabbar ai, kuma gaskia baxan iya barin aiki na na bishi ba gwara ya dunga xuwa weekend ne " Dariya suka sake sawa tare da tafawa daga hka suka cigaba da hirar su . Kamar yanda farida ta bata shawara Hka kuwa akayi tana dawowa daga office ta xube a falo wayar ta ta d'auko ta shiga shirya mishi kalamai masu dad'in gaske ta tura mishi sannan ta mik'e taje tayi wanka tana fito wa ta shirya cikin wata atamfa riga da siket tayi kyau kan bed ta kwanta tare da dialing d'in number abduljabbar sai da tayi 6 missed calls Kafin Ana 7 ya d'auka cikin d'aga murya yace "Lfy kike damuna da Kira hka?" Kukan kissa ta saki tare da bashi hak'uri akan laifin da tayi mishi kunsan mata da miji sai Allah nan dai ya hak'ura sannan tace "yaushe xaka xo nayi missing di'n ka Wlh? " "ohhh sai yanxu kika yi missing d'ina ai na d'auka aikin ki yafi komai mahimmanci a wurin ki" Cikin muryar shagwa6a tace "haba my darling kasan kafi komai mahimmanci a waje na " "hmm a hkan bayan kin k'i bina abuja kin kwammace kullum ina hanyar kano duk weekend " "ai ni bana son nesa da gida ne kuma don Allah a bar maganar" Murmishi yayi mai sauti har tana jiyo shi yace "mybe sai nan da two weeks xaki ganni" Marairaicewa tayi cikin shagwa6a tace "hba my darling ka rage don Allah " "okay bani K'arshen satin nan ranar Friday da yamma xuwa dare xaki ganni, xan kirawo ki xuwa anjima yanxu xan fita byeeee " Yayi hangin up d'in wayar ya bar jiddah cike da jin dad'i ganin ya sauko cikin sauk'i nan ta kirawo farida ta bata labarin yanda suka yi da abduljabbar .......... Hmmmm masu karatu anya ba tuban muxuru jiddah ta yi ba ku dai Ku cigaba da bina don ganin yanda xata kasance. *```Aishat A muh'd*```?? ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘ *NA* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 23~* Ranar Friday da misalin 6 na yamma ta dawo daga aiki a gajiye take xube wa tayi a falo sai da ta huta tukunna ta samu ta shiga toilet tayi wanka taci kwalliya cikin wata shadda brown colour dinkin doguwar riga anci dauri da make up tukunna aka fara laluben abin da xa'a tanadar wa abduljabbar na ci nan ta yanke shawarar kiran umman abduljabbar dialing d'in number ta tayi bayan sun gaisa cikin marairaice murya tace "umma kinga yau abdul xai dawo gashi ban tanadar mishi abin da xai ci ba saboda bana jin dad'i yinin yau " "Asssha mai ya same ki? " "ciwon kai umma har yanxu bai dai na ba" "kada ki damu 'yata yanxu xan sa FA'iza da driver su kawo mishi sannu kinji dafatan kinsha magani" "Ehhh umma na sha" ""toh xasu kawo miki yanxun nan" "Shikenan umma ina jira ngde sai anjima " Nan suka yi sallama dad'i ya ishe jiddah jin xata samu abin da xata taryi abdul d'in ta don hka da sauri ta tashi kitchen ta shige ta fara fito da plates dasu cup, spoon da fork sannan ta shiga ciro drinks a frige masu sanyi ta ajiye su tana gama shirya wajen ta xube akan kujera tana washhh alamar ta gaji ,k'arar danna door bell ne ya dawo da ita daga duniyar chatting sai da ta yamutsa fuska Kafin tace "larai!!! " ta kwala wa er aikin ta kira da sauri ta shigo falon tana amsa wa da "na'am hajia " Cikin masifa tace "me kike yi kina ji ana danna door bell ba fa nason shiriri ta wlh don hka ki nutsu ki dunga kula da aikin ki " "ayi hak'uri hajia xa'a kiyaye Insha Allah " "okay, oya kiyi sauri ki bud'e kofar " Da sauri ta mik'e taje ta bud'e falon cikin nutsuwa ta shigo falon da sallama a bakin ta larai ce ta amsa mata tare da yi mata sannu da xuwa waje ta samu ta xauna tare da cewa "Aunty jiddah ina yini" "lafia qlau " Wannan kalmar ta iya amsa wa FA'iza dakyar ikon Allah Idan da sabo sun saba da halin jiddah kamar maman ta da umman su ba uwa d'aya uba d'aya suke ba shi yasa sam basa shiri da FA'iza k'wata 2 don hka ta mik'e tana cewa "kisa er aikin Ki ta biyo ni ta d'auko abincin a mota " Daga hka ta fice daga falon da sauri cike da jin haushin jiddah sam yayan su bai yi dacen matar aure ba amman wai umma take goyon bayan ta tana xuba iskan cin ta son ranta, a bangaren jiddah kuwa harara tabi FA'iza da ita Kafin taja tsaki Wannan yarinyar er rainin wayo ce ta fiye ji da kai kamar wata uwar mata baki sanni ba amman xan dai dai ta miki sahu sai da ta b'ata lokaci Kafin tayi wa larai magana taje ta d'ebo manyan food flask guda 3 har da babban jug cike da had'in hadadden so6o nan dad'i ya kama jiddah ta shirya abincin akan dinning table kamar ita ta dafa ana jiran dawowar abdul ********** "Aunty nauwara bari nakai wannan kwanon kitchen kada ta hana mu abinci " "toh d'an kanina ka kula kaji kuma kada ka dad'e " Nauwara wadda ke xaune akan kujerar ta ta amsa mishi tashi yayi ya d'auki robar ya fice daga d'akin falo ya fito ya tarar da yaran aminu suna wasa abin ka da yaro sai yaji yana sha'awar yin wasan don hka ya shiga cikin su suna yi abin tsautsayi suna tsaka da wasa sai saleem ya d'an ture yarinyar karama sai ta fad'i har bakin ta ya d'an fashe Kad'an jini ya fito da yake tafiyar ta batayi k'wari ba hba nan yarinyar ta saki ihun kuka da gudu hindatu ta fito daga kitchen tana fito wa taga saleem a wajen cikin masifa tace "usman me ya same ta" "wannnan ne ya ture ta shine ta fad'i ta fasa baki " Usman ya bata amsa a harxuk'e tace "kan ubancan ai wlh yau xaka ci uban ka sai kayi da ka sanin tab'a min yarinya don mugun hali shine ka ture min 'ya" Tuni jikin saleem ya fara karkarwa ganin yanda take bala'i da masifa ita kad'ai cikin kuka yace "don Allah kiyi hak'uri wlh ban san na bige.............." Ai Kafin ya K'arasa yaji saukar duka ta ko'ina tuni ya fara ihun kuka Allah sarki abin tausayi abinka da yaron hutu ba'a dukan shi nan ta dunga dukan shi kamar ta samu babba tana yi tana zagin shi sai da tayi mishi lilis tukunna tana haki tace "gobe ma ka k'ara shegen yaro jarababbu " Tana gama fad'in hka ta janyo shi a k'asa har d'akin da suke ciki ta cillo shi kummm ya bige kai da kujerar da nauwara take xaune a kai tana nata kukan tausayin saleem don tana jiyo irin dukan da take yi mishi rarrashin ta dunga yi Duk da ita ma kukan take yi........ ```Aishat A muh'd```?? ??☘☘?? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘?? *Written by* *Aunty*?? *~Pg 24~* Dakyar saleem yayi shiru Kafin wani wahalalen bacci yayi awon gaba dashi sai faman sauke ajiyar xuciya yake irin wanda yaci kuka ya koshi, nauwara xuba mishi ido tayi cike da tausayin kansu Wayyo rayuwa idan ba kaddara ba ina xaki ganmu balle kiyi mana wulakanci da ace ina gani da idanuna kafata ina tafiya da ita kamar kowa da wlh baxa mu xauna a gidan nan ba xan xage nayi sana'a komai wahalar ta don kada mu walakanta amman ya xaayi da ikon ubangiji sai hak'uri xuciyar nauwara ce take wad'annan tunanin lokaci xuwa lokaci tana share kwallar idon ta 6 na yamma aminu ya dawo daga wurin aiki kamar kullum d'akin su nauwara ya fara shiga hannun shi da wata babbar leda da sallama ya shiga Kafin yayi magana ya hango jikin saleem rud'u rud'u abin ka da farar fata a rud'e yace "Subhannallah mai yafaru da kai saleem? " kasa magana suka yi sai sunkuyar da kan su k'asa suka yi yayi maganar duniya amman sunki fad'a mishi gaskia to me xasu ce matar shi hindatu ce ta doki saleem hba da kunya duk halaccin da Yayi musu ai duk da matar shi bata kirki bai Kamata su had'a su shi kuwa aminu tsaf ya fahimce abin da ke faruwa don ya tabbatar hindatu ce ta aikata hkan tun da yaran ba fita suke ba kullum suna d'aki har tausayin su yake ji saboda xaman waje d'aya babu dad'i takeaway d'in da yayi musu ya vasu ai kuwa da sauri suka karb'e suna ci hannu baka hannu kwarya sosai tausayin su ya kama aminu har er kwalla sai da ta xubo mishi da ganin yanda suke cin abincin kasan yini guda basu ci abinci ba a fusace ya fice daga d'akin Hindatu kuwa tun lokacin da ya shigo akan idon ta "Lallai ma wWannan mutumin wato har abu yake siyo musu ya basu tabb ai kuwa xa'a yi bala'i agidan nan da karfi ya turo kofar wanda yasa har firgita sai da tayi da sauri ta d'ago ta kalle shi fuskar nan tashi a had'e itama d'aure fuskar ta tayi "yanxu hindatu kin kyauta abin da kike? " "yo menayi kuma" "ban sani ba sarai Kina sane da abin da na fad'a miki wannan wane rashin imanine yaran nan ki dunga yi musu horan yunwa sarai ina sani da abin da kike yi musu shine don tsabar iskanci xaki kama wannnan yaron k'arami ki lakad'a mishi irin wannan dukan me yayi miki" "yo ai zahra ya tunkude ta fad'i har da fasa baki ni kuwa shine na doke shi tunda nasan mugunta ce " Cikin takaici yake kallon ta yana yi mata wani mugun kallo "tur da mai irin halin ki hindatu kin 6ata wayon ki wlh kamar baki da Ilmi " Nan ya shiga yi mata tuni ta fashe da kukan takaici hka ya fice ya barta tana kuka ranta inyayi dubu ya b'aci tunda sukayi aure da aminu suke xaune lafia sai da wad'annan matsiyatan yaran suka shigo cikin rayuwar ta Lallai idan tayi sake xata sha mamaki tunda har aminu ya fara yi mata fad'a nan ta shiga tunanin hanyar da xata bi don ta Kori su nauwara daga gidan Shi kuma aminu ran shi a 6ace ya xauna a falo yana tunanin hanyar da xai bi don hindatu ta kar6i su nauwara da mutunci ta daina horar dasu da yunwa Lallai Idan *YAYI SAKE*(littafina na gaba) garin neman lada hindatu xata sa su samu xunubi tun da rikon maraya akwai takatsantsan a ciki......... ```Aishat A muh'd```????☘☘???? ☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘?? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 25~* Da misalin karfe 8pm abduljabbar ya shigo kano sai da ya biya gidan su don ganin mahaifan shi tunda ya dad'e rabon shi da xuwa a gurguje suka gaisa sannan ya tafi saboda ganin dare ya fara yi *9:30pm* dai dai ya shigo cikin gidan jiddah wadda take xaune a falo har ta fara gyangyad'i saboda gajiyar da tayi sai jin sallamar shi tayi xumbur ta mik'e tsaye tana amsa wa fuskar ta cike da fara'a ta rungume shi tana yi mishi oyoyo sosai ta bawa abduljabbar mamaki ganin sauyin ta a lokaci d'aya tunda suka yi aure bata ta6a yi mishi irin tar6ar ba shima yasa hannu ya k'ara rungume ta a jikin shi cikin kissar shagwa6a tace "my darling sannu da xuwa, Hw r u? " "I'm absolutely fine, nd I hope everything is fine?" "yes my darling no problem at oll " ta K'arasa fad'i tana kar6ar briefcase d'in shi k'ayataccen murmishi ya saki har wushiryar shi ta fito Kafin yace "Gud my cwt jiddah naaa" Yanda ya fad'i hkan ba k'aramin sa ta wani dad'i taji ba a ranta da hka ta jashi xuwa bedroom d'in shi yayi wanka ya shirya cikin wani 3 qauter black nd white vest ya gyara gashin kanshi tare da fesa perfumes d'in kai sannan ya fesa normal turare na kaya jiddah tana xaune a gefe ta xuba mishi ido don ba k'aramin kyau yayi mata ba a xuciyar ta tana cewa ji don Allah yanda yake kyalkyale kyalkyalen jiki kamar wata mace Yana gama shiryawa suka fito falo a dinning table ya xauna nan ta shiga serving d'in shi k'amshin abincin kawai yaji yasan wannan girkin umman shi ne amman bai nuna mata hkan ba nan yaci ya koshi suka dawo cikin falo suka xauna hira suke d'an ta6a wa har xuwa 11 na dare tukunna suka tafi bedroom d'in shi, har Xasu kwanta naga jiddah ta mik'e tsaye da sauri tana cewa "my darling give me 2mints only nayi mantuwa " tana gama fad'in hka naga ta fice da sauri d'akin ta ta shige janyo drower d'in bed d'in ta tayi wani pill naga ta d'auko ta 6alla sannan ta hadiya da ruwa Sannan ta mayar (tohh xaro ido nayi ganin jiddah ta sha maganin nan ina me mamakin ko saboda me tasha ohhh sai dai mu cigaba da bin ta don ganin ko mai ne) tukunna ta dawo bedroom d'in abduljabbar haye wa kan bed d'in tayi tare da kwanciya a jikin shi nan take yayi switch off d'in hasken d'akin a Wannan daren abduljabbar sun raya shi cikin jin dad'i saboda jiddah ta bashi had'in kai dai dai gwargwado har yaji daman hka take mishi da baxai yi tunanin sake aure ba amman sai dai kash jiddah anya xata jure hkan ganin yanda bata son motsa jikin ta sai wurin uku na dare suka samu yin bacci sai nace *ASUBA TA GARI JIDDAN ABDULJABBAR* Washe gari sai misalin 10 na safe suka tashi da yake ranar saturday ce jiddah agogo sarkin aiki bata xuwa office, cikin farinciki suka tashi dakyar ta iya dafa musu tea aka soya kwai sai bread shine aka iya hadawa ta xube a kujerar dinning table tana cewa "Washhh na gaji my darling " Kallon ta kawai yayi tare da Murmishi yana girgixa kai shi kanshi yana mamakin jiddah idan ya tuna a irin gidan da taso da hka suka kammala breakfast d'in ba tare da Abduljabbar ya gamsar da shi ba Yinin ranar ba inda ya fita suna gida ana xuba soyayya don abduljabbar bada ganan ba wajen iya luv ai kuwa jiddah tuni ido ya raina fata saboda ta gaji iya gajiya dakyar ya iya barin ta, bedroom din ta nufa toilet ta shiga tana gasa kanta tare da mita shi baisan ayi abu Kad'an a kyale ba sai an wahalar da mutum mtsss taja tsaki (daman a xahirin gaskia ita jiddah bata fiye son abduljabbar ya shige ta ba ita kawai barta a romance anan ta K'ware wa shi yasa sam tak'i bin shi abuja) 5 na yamma suna cikin gidan su jiddah nan ya gaida maman ta tare da yi musu alkhairan da ya saba yi musu sam jiddah ba ta dauki halayyar maman ta Ko d'aya ba saboda maman ta ba ruwan ta akwai ta da sanyin hali ba sufi 20 mints ba suka yi mata sallama sannan suka nufi gidan su abduljabbar anan suka fiye dad'e wa don sai around 9 na dare suka dawo gida........ ```Aishat A muh'd```?? ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd*?? *~Pg 26~* Wannan weekend d'in abduljabbar ya d'an samu sauk'in matsalar jiddah tun da tana d'an kok'ari wajen kula dashi dakyar ta lalla6a shi ya samo musu mai yi musu abinci don hka yanxu bata da matsalar nan tunda yana xama ya d'an ci abinci duk da baya gamsar dashi yanda ya kamata haka yake hak'uri yaci Kamar yau wajen 4 na yamma yana xaune a garden laptop a gaban shi yana amfani da ita jiddah ta Karaso wajen ko sallama babu ta xube a gajiye dawowar ta daga unguwa kenan kallon ta yayi cike da jin haushin ta tun safe tasa kafa ta fice abinta kuma tasan yana gida amman ko ajikin ta sai yanxu taga damar dawowa "washhh Allah na na gaji wlh, my darling ya gida ?" Maganar da tayi ita ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi "Ohh sai yanxu kika ga damar dawowa yayi miki kyau" "haba darling yanxu fa 4:42 kasan kuwa na dawo da wuri tunda ban kai mangariba ba" Shiru yayi mata bai k'ara ce mata komai saboda bai fiye son surutu ba ya cigaba da abin da yake, ganin yayi shiru ya kyale ta yasa cikin kwantar da murya tace "my darling don Allah so nake ka canja min mota" Da sauri ya d'ago kanshi cikin mamaki yace "jiddah ina ce last month na canja miki mota? " "Ehhh my darling nasan hakan kawai wata nake son a sake min na gaji da wannan " "Hmmm jiddah ai ke mai kud'i ce ki canja mana" "na canja fah kace da wanne kud'i? " "albashin ki da kike d'auka kowanne month me kike dashi?" Had'e fuska tayi don ta gaji da wad'annan tambayoyin shin nashi Don hka cikin kosawa tace "ni dai kawai Idan xaka canja min ka canja ba ka tsaya yi min tambayoyi ba" "baxan canja ba don ba'a sani yin abin da ban shirya ba "mtswww yaja tsaki tare da tashi ya d'auki laptop d'in shi yayi cikin gida jiddah ta bishi da harara cike da jin haushin shi don hka ita ma a fusace ta shige cikin gidan A bangaren abduljabbar ba wai bashi da kud'in da xai canja mata mota ba kowai jiddan ta fiye son kodayaushe taxo da buk'ata ayi mata bata san babu ita kawai ayi mata shi yana mamakin ko ina take kai kud'in albashin ta Don haka wannan weekend d'in shima baran baran aka rabu shi abduljabbar Ko a jikin shi tunda Idan da sabo ya saba sai ma barin jiddah da yayi cike da 6acin rai............. ******** Acikin k'wana 2 jikin saleem ya warware saboda samun kulawa da yake samu daga aminu hakan kuma ba k'aramin k'ara kular da hindatu yake ba wata muguwar tsana da kyara had'e da hanttara take yiwa su nauwara tunda yanxu aminu yace su dunga fito wa falo su dai na xaman d'aki suna tak'ure wa a d'aki Hkan kuwa ba k'aramin Dama hindatu tayi ba wajen axabtar dasu ba ta hanyar wani lokacin sai dai kawai nauwara taji an sheka mata ruwan sanyi tun da ba gani take ba ko kuma taji an jefo mata wani abun ko kawai taji saukar duka ta ko'ina hka saleem ba duk sun bi sun rame sunyi baki saboda ba ishasshen abinci ba k'arami *K'ARSHEN WAHALA* take gana musu ba ......... Abin ya fara damun nauwara Wannan wanne irin cin xali ne har ta fara tunani su gudu su bar gidan kada ta illata su don abin nata yayi yawa shi daman aminu ba maxaunin gida ba Idan ya fice tun safe sai daf da mangariba yake dawo wa shawarar da nauwara ta yanke da su gudu kawai shi yafi musu da xaman ukubar da suke sha.... *Aishat A muh'd*?? ??☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘?? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}* _wannan page d'in naki ne my sadeey saNaz ina mik'a miki sak'on gaisuwa ta Allah ya jikan ta da rahma,Allah yasa mai ceton mu ce, ita kuma mahaifiyar yarinyar Allah ya bata hak'urin rashin ta ya bata masu albarka,Ameeen thumma Ameeen_ *~Pg 27~* Misalin karfe 9 na dare aminu ya shigo gidan kamar yanda ya saba shiga d'akin su nauwara Hka yau ma ya shiga da sallama suna nan a xaune waje d'aya sunyi shiru tagumi suka xabga kowanne da irin tunanin da yake yi a xuciyar shi Sunyi matuk'ar bashi tausayi k'wata k'wata nawa suke yaran amman Har sun d'aura kawance da damuwa tare da tunani sam basu san ya shigo d'akin ba shima xama yayi gaba d'aya tausayin su ya gama kamashi har baisan lokacin da hawaye ya xubo mishi ba hannun shi yasa ya goge hawayen Kafin yayi gyaran murya firgice saleem ya Mike tsaye yayin da nauwara kuma gaban ta ya hau fad'uwa saboda tsoro duk a xaton su hindatu ce don ba k'aramin tsoron ta suke ji ba Shi kanshi aminu yayi mamakin yanda suka tsorata nan take xuciyar shi ta ayyana mishi hindatu tana yiwa yaran nan wani abun Idan baya nan gashi xai yi tafiya gobe da safe wani aiki aka tura shi daga office kuma aikin xai d'auke shi tsawon 2days baisan wanne irin xama xa suyi da hindatu ba yana gidan ma bata fasa yi musu mugunta ba balle baya gidan "uncle aminu lafia kayi shiru? " Firgigit ya dawo hayyacin shi jin maganar saleem kura musu ido yayi cikin tsananin tausayin su kafin ya bud'e baki yace "I'm fine saleem daman naxo na fad'a muku ne xan d'anyi tafiya na tsayin k'wana 2, so don Allah kuyi hak'uri da abin da hindatu take muku Insha Allah idan na dawo xan samo muku mafita " Ba k'aramin kad'uwa nauwara tayi ba bcoz tasan sun shiga 9 ma ba 3 don Mybe ba ta kore su a gidan ko ta kashe su da axaba tunda bata da kirki ko Kad'an "ku cigaba da hak'uri nauwara komai yayi farko xai yi K'arshe wata rana sai labari ina dawowa xamu xauna Kuyi min cikakken labarin ku don nasan ta yanda xan taimaka muku Kuyi hak'uri" Wata irin fad'uwar gaba nauwara taji Don baxa ta iya gaya mishi cikakken labarin su ba don watak'ila baxai amince ba don hka dole tasan yanda xata yi Kafin ya dawo su gudu daman ta gaji da zalincin matar shi ta gaji wlh dakyar ta iya bud'e baki tace "toh Shikenan Allah ya dawo dakai lafia" "Ameeen nauwara nagode " Shima saleem yayi mishi fatan alkhairi xuba mata ido yayi yana nazari a kanta gasky da ganin yaran nan basu fito daga gidan wahala ba ba don nakasar dake tattare da ita ba da ba shakka baxa ta tsaya ana yi musu wulakancin ba don duk inda ake buk'atar kyau da cikar mace nauwara ta kai ko'ina duk da wahalar da suke sha ga nakasa hkan bai hana kyanta fito ba ga xak'in murya tuni aminu ya fad'a kogin tunanin nauwara Jin shiru d'akin ba motsin aminu da saleem yasa cikin muryar ta mai dad'in gaske tace "saleem ya tafi ne " Firgigit ya dawo daga duniyar tunanin nauwara jin muryar ta "aunty bai tafi ba gashi a xaune" "kada ka damu Insha Allah ba komai xaka je ka dawo muna nan " Dad'i ne ya kamashi acikin xuciyar shi yana tunanin xai nema mata magani ta samu lafia don ya aure ta kuma xai rik'e su tsakani da Allah ita da saleem (Hmmm kaji aminu da wani batu nace ya mance hindatu matarshi) "Yawwa ngde nauwara duk abin da xata yi muku Kuyi hak'uri da ita har naje na dawo sannan ga wannan kuma " Ya fito da kud'i ya basu ya cigaba da cewa "gashi Idan bata baku abinci ba saleem ya fita ya siyo muku ko wani abun ne a waje kuci,sannan ga kayan tea nan da biscuits nan " Nan suka yi mishi godiya sosai kamar baxai barsu hka ya dunga kallon su kafin dakyar ya fita saboda ganin dare ya yi sosai nan yaje ya tarar da masifar hindatu shi dai bai kula ta ba da ta dame shi ma sai kawai ya bar mata d'akin cike da jin haushin ta ba don dare ne ba da sai ya mammare ta don ba k'aramin kular dashi tayi ba Hka ya k'wana juyi cike da tunanin su nauwara farat d'aya yaji son yarinyar ya shige shi da ya d'auka tausayin tane kawai Ashe har da so ma (to fah aminu ka d'ebo ruwan dafa kanka awajen hindatu Don shi kanshi yasan ba k'aramin tsanar kishiya tayi ba tasha fad'a mishi Idan yayi mata kishiya sai yayi nadama mai tsanani) *Washe gari* Da karfe 11 na safe aminu ya yiwa su nauwara sallama Duk jikin shi a sanyaye saboda yasan hindatu ba kyale su xata yi ba Duk da ya rarrashe ta da safen nan sannan yayi mata alk'awarin xai sissiya mata abubuwan da take so kawai don kada ta axabtar dasu nauwara jinshi kawai take a xuciyar ta tace kayi ka gama wlh korar su xanyi yanda har abada baxa ka k'ara ganin su ba Yana tafiya aikuwa ta shigo gidan tana shewa da jin dad'in tafiyar tashi su nauwara kuwa suna cikin d'akin gaba d'ayan su a tsorace suke don basu san wanne irin *K'ARSHEN WAHALA* xata gana musu ba a cikin kwanaki 2 nan ba Allah sarki su nauwara ai *Innallaha ma'assabirin* (na Zarah mansur *********** *BARI MU WAIWAYI SU BAFFAH* Bayan su baffah sun farfado daga suman da suka yi nan suka tarar da mugun labari wanda yayi matuk'ar k'ara tasar musu da hankali don ance gidan d'an nashi basu tarar da komai Duk ya k'one ko'ina kawai dai anyi nasarar samun gawar baba mai gadin su nauwara da wata gawar ta mace daban koda aka duba dakyar aka gane *SAFAH* ce *Allahu Akbar* Su baffah da inna habiba sun ga tashin hankali wad'annan tsofaffin amman sun yarda da k'addarar ubanjigi hka aka sallaci su aka mik'a su gidan su na gaskiya Ashe baba mai gadi da yaxo da niyyar taimakon su ya kamo hannun d'aya daga cikin su ashe safah ce Duk kuma a tunanin shi su nauwara suna biye dashi da yake wurin Duk Hayak'i ne basu gane hanya ba sun cikin tafiya Ashe ta wurin kitchen ne aikuwa a lokacin gas ya fashe shine ya tashi dasu safah Allah sarki rayuwa kenan Allah ya jik'an safah da baba mai gadi Duk a xaton su har da ammi, nauwara da saleem wutar ta k'one su tun da su ba'a ga tasu gawar ba nan dai aka kammala sadakar 7 kowa ya kama gaban shi hankalin Alhj salisu kwance yake cin dukiyar su don yasan ba mai xargin shi (hmm kaji jahili an gaya mishi hakk'in rai xai barshi ai tun a duniya Allah xai fara hukunta shi Kafin aje gaban shi inda xai yi hukuncin dai dai da abin da ka aikata Allah yasa mu dace duniya da lahira Ameeen thumma Ameeen) ?☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘?? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 28~* A cikin wad'annan kwanak'in biyun su nauwara a tsorace suke gaba d'aya basa cikin nutsuwa saboda basu san wanne irin cin mutunci hindatu ta tanadar musu ba Sunyi matuk'ar mamaki sosai har suna tunanin ko ta canja hali ne Don har abinci take basu tana gama wa xata k'walla wa saleem Kira yana xuwa xata bashi abincin kuma sau 3 a rana gashi yanxu da yawa take xuba musu yanda xai ishe su (toh masu karatu ko dai hindatu ta canja hali ne taji nasihar mijin ta aminu) ********* Xaune yake a kan kujera cikin office d'in nashi yana cike wasu takardu wanda aka tura su wani cos na tsawon 6 month's shi kanshi yaji dad'in hka saboda xai huta da masifar jiddah yana kammala cike wa ya ajiye ta a gefe sannan ya kwantar da kanshi kan kujera tare da lumshe idon shi yana tunanin yanda xai fara binciken yarinyar da xai aura ba mai irin halin jiddah ba, duk da yanda en mata suke kawo musu kanshi wasu Don ya aure su wasu kuma kawai jikin su suka bashi kyauta don yayi lalata dasu Ko kallo basu isheshi ba saboda ya tsani zina ba k'aramin tsana ba kuwa yayi wa masu yin ta ba shi yasa a kullum yake rok'ar ubanjigi akan ya k'are shi da kusantar ta masu yi kuma Allah ya shirye su, kiran waya ne ya shigo wayar shi a hankali ya bud'e idon shi tare da jan d'an k'aramin tsaki mtswww d'aukan wayan yayi tare da sawa a kunne ya fara da sallama daga can b'angaren umma ta amsa mishi sallamar tashi cikin ladabi ya gaida ita ta amsa mishi tukunna ta fara yi mishi maganar da ta sa ta kirawo shi "daman abdul abin da yasa na kirawo ka saboda ina son sanin me yasa jiddah tace ka canza mata mota kace baza ka canja ba? " Haba tuni ran en maza ya 6aci wlh ba don umman shi ce ba sai ya katse kiran amman ya xai yi mahaifiya ce don hka ya d'an sasauta ranshi Kafin yace "umma ki share jiddah wlh ta fiye matsala da yawa last month fa na canja motar ta gashi kuma akwai motocina fah a gidan tana d'aukar kowacce tayi amfani da ita idan tana ra'ayi" "duk naji ka kuma nasan da hka kawai ka canja mata nace" "toh wai ina kud'in ta da take samu kowanne month ina take kaisu? " "ina ruwan ka da kud'in ta, tunda dai hakk'in ta yana kan ka " Cije leb'en shi yayi cike da jin haushin jiddah bcoz tana son ta dunga had'a shi da mahaifiyar shi amman xai rabu da ita ta gama iskan cin ta xata gane bata wayo wlh "naji kayi shiru ko baza ka canja ba mata ba nasa ni" "ya xanyi tunda ta had'a ni dake xan canja mata xata samu sak'on wajen abdulkareem Don ni tafiya xamu yi wani aiki tsawon 6 month's daman yanxu nake son kiran Ki na sanar da ke sai na dawo xan xo kano amman don Allah umma kiyi hak'uri naga kamar ran ki ya 6aci" Tausayin d'an nata ne ya kamata tace "ba komai abdul Allah ya taimaka yasa a gama a sa'a, Allah ya kai ku lfy ya dawo daku Lfy Allah ya kare min kai yayi mata albarka ya baka 'ya'ya masu albarka " Sosai yaji dad'in addu'ar da mahaifiyar shi ta yi masa da hka suka yi sallama Sannan ya kirawo abban shi ya sanar dashi shima ba k'aramin addu'a yayi mishi ba ******** A yau ake sa ranar dawowar aminu daga aikin da aka tura shi hindatu tun safe take gyaran gida ana had'a wa miji abubuwan ci da nasha har aka gama tayi wa yara wanka ita tayi suka shirya fes dasu ta fito ta bawa su saleem abinci suka ci suka koshi har suka barshi don yanxu har sun d'an farfad'o daga mugun ramar da suka yi *4:30* Su nauwara na xaune a d'aki saleem yana bata labari sai dariya suke ta shigo d'akin nasu cikin murmishi amman ni da ganin murmishin nan nasan shine ake Kira dana mugunta "Idan baxa ku samu damuwa ina son kuxo ku rakani jifatu xan siyi fruit da drinks nawa sun k'are gashi aminu yana hanya" Gaban nauwara ne ya fad'i da jin abin da tace sai taji sam bata yarda da abin da tace ba don hka tace "Laaa aunty da kin barmu anan Kinsan xaki sha wahala dani tunda ba tafiya nake ba? " Harara ta xabga mata a fakaice Kafin ta saki murmishi tace "ba wani wahala gashi har da su usman xamu je kai saleem ka turo ta waje ina jiran ku" Tasa kai ta fice hankalin nauwara ba k'aramin tashi yayi ba gashi ba yanda xasu iya hka saleem ya turo ta dukka jikin su a sanyaye yake har sun fito ita da yaran ta dakyar suna jiran su nan ta taimaka wa saleem suka sata a mota sannan kujerar ta ta suka sata a boot Cikin jin dad'i ta fara driven d'in motar har suka fice daga unguwar ni da naji tace jifatu xasu je na kwalalo ido don ganin ai gaba d'aya ba hanyar da xata sada ta da jifatu tayi ba ta dauki hanyar da xata Kai ta................ (masu karatu toh ko ina hindatu xata kai su nauwara?) ???☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 29~* Hanyar da xata dauke ke ta xuwa tashar mota nan tayi dasu sai da ta shiga cikin tashar tukunna tayi parking tare da fito wa kamar gaske ta fito wa da nauwara kujerar ta sannna ta d'ora ta akai cikin murmishin mugunta tace "saleem fito mana " Yaron cikin sanyin jiki ya fito daga motar yaran ta suna ciki basu fito ba dummm gaban nauwara yayi mugun fad'uwa jin ana cewa hajia ina xuwa hka gashi sai fad'ar sunayen garuru da akeyi hkan yasa xuciyar nauwara karye wa tare da ayyana mata Anan tashar mota ce wasu hawaye masu xafi suka fara xubo mata a fuskar ta Bata damu ta goge ba cikin haka taji hindatu ta kwashe da dariyar mugunta sannan tace "yarinya ai yanxu kika fara kuka wlh, yau dai na yadda kwallon mangoro na huta da k'uda kinga daga yau kun fita a rayuwar mu" Kukan nauwara ya tsanan ta ita da saleem cikin ginshik'in kuka tace "Don Allah aunty kada ki mana Hka Ki tausaya mana bamu da inda muka sani a fad'in garin nan sai ku pls " "kamar yanda baku Sanmu har kuka yarda da aminu to kuje ku nemi wasu Don nan Inda na kawo ku shine dai dai da rayuwar ku sai ku cigaba da rayuwa anan har ku mutu ko kuma wani mai tausayin ya taimaka ku " Laluben inda hindatu take ta fara har tayi nasarar riko gefen mayafin ta har ta bud'e baki xatayi magana hindatu tasa hannu ta make hannun nauwara da karfi har sai da ta saki er k'ara saboda xafin da taji ta cigaba da kukan ta saleem ya rungume ta shima yana nashi kukan sunyi matuk'ar ban tausayi duk wanda ya gansu a hka sai ya tausaya musu amman hindatu ko a jikin ta K'arshe ma shige wa tayi cikin mota tayi tafiyar ta xuciyar ta cike da farincikin ta rabu dasu nauwara wani 6arin na xuciyar kuma yana tsoron tunkarar aminu wacce amsa xata bashi idan ya tambaye ta ina su nauwara?, k'wata k'wata sai yanxu tunanin hkan ya xo mata hka ta tafi gida tana tunanin amsar da xata bawa aminu... Gaban ta ne yayi wata iriyar fad'uwa sakamakon ganin motar aminu agida alamar ya dawo kenan da sallama ta shiga falon turus tayi ta tsaya saboda ganin yanda yake ta safah da marwa a falon kallo d'aya tayi mishi ta d'auke kanta saboda yanda taga fuskar shi cike da tashin hankali yana ganin ta ya matso kusa da ita ya fara magana cike da tarin damuwa a cikin ta yace "hindatu ina su nauwara? Na dawo gidan ba kyanan kuma ban gan su ba me yake faruwa ne?? " Ita ma a rud'e tace "tabbb ka tambaye ni a gidan na barsu naje jifatu siyo mana drinks da fruit da gaske basa nan to ina suka tafi ko sun gudu ne??? "Keeeeeee dakata nafa san halin ki daman ba son xaman su kike ba a gidan, ina kika kai su iyee ki fad'a min Kafin na d'au mummunan mataki akan ki wlh" Tuni cikin hindatu ya duri ruwa saboda bata ta6a ganin aminu a haka ba cikin dakiya tace "na..... nace.. ni na barsu a gidan na fita bansan inda suka tafi ba " Bai san lokacin da ya fidda hannu ya wanka mata mari ba da sauri ta dafe kumatun ta tare da fashe wa da kuka a fusace yace "karya kike hindatu ki fad'a min gasky wlh " Gaba d'aya ta gama tsorata dashi ganin yanda ya koma don hka cikin rawar murya da rud'e wa tace "suna tasha can na kaisu don na gaji da xama dasu a gidan nan" "What!!! " Ya fad'a da karfi ai wani tsalle ta daka sai gata a d'aki da sauri tayi wa kofa key sannan ta xame k'asa ta xauna tana mai nadamar abin da ta aikata dama ta barsu bata kore su ba don sai yanxu wani mugun tsoro ya kamata (Hmmm daman hausawa sunce dana sani k'eyace) Da gudu ya fisgi motar shi ya bar gidan hka yayi ta bulayin neman su nauwara a tashoshi amman duk an tashi ba mutane saboda dare yayi sosai gaba d'aya aminu duk rud'e da tashin hankali hka yayi ta neman su amman ko me kama da su nauwara bai gani ba parking yayi a gefen hanya tare da d'ora kanshi a jikin steering d'in motar baisan lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba saboda tsabar tausayin su nauwara Hindatu ta cuce shi ta gama dashi sai da yaci kuka ya koshi tukunna dakyar ya iya driving d'in motar ya tafi gida lokacin 1 am na dare hankalin hindatu yayi matuk'ar tashi sosai tayi da nasani yafi dubu ganin har yanxu aminu bai dawo ba ajiyar xuciya ta saki jin shigowar shi gidan amman ya dad'e sosai bai shigo cikin gidan ba kamar xata fita ta duba shi amman tsoro ya hanata tana nan mak'ale a jikin window ya shigo sai da gaban ta ya fad'i saboda ganin yanda fuskar shi ta koma idanun shi sunyi matuk'ar ja D'akin shi ya shige tare da fadawa kan gado sai da ya huta tukunna ya shiga toilet ya d'aura alwala sannan ya fito nafilfilo ya farayi tare da addu'ar Allah ya kare su nauwara a duk inda suke k'wana yayi bai iya yin bacci (Allah sarki aminu bawan Allah gaskiya ba k'aramin so yake yiwa nauwara na) ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘ *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 30~* Acikin k'wanaki 2 hindatu tayi nadama sau ba adadi akan abin da ta aikata ta axabtu iya axabtuwa ba duka ba xagi ko bakar magana kuma ba hana ta abinci yayi ba kawai tsabar abin da ta shuka take girba baya kulata sam ko gaida shi tayi baya amsa wa iya yaran shi kawai yake kulawa,baya cin abincin ta magana bata had'a su gaba d'aya tayi wani iri tana son bashi hak'uri amman babu fuskar hakan... Shi kuwa aminu kullum acikin binciken inda su nauwara yake amman har yanxu bai gansu ba don hka ya hak'ura addu'a kawai yake musu Allah ya k'are su har ya d'an fara sakkowa daga fushin da yake da hindatu Hakan da ta gani yasa ta durkusa har k'asa tana kuka tare da bashi hak'uri akan laifin da tayi baxa ta k'ara kwatanta shi ba dakyar ya iya hak'ura tare da yi mata nasiha sosae mai ratsa jiki Shikenan suka shirya tsakanin su kun san ance tsakanin mata da miji sai Allah,suka cigaba da rayuwar su amman har yanxu bai mance da su nauwara ba yana d'an binciken su idan ya samu Lokaci ga addu'ar da yake musu... ******* Abduljabbar kuwa aacikin satin nan suka shige cos d'in da aka tura su wajen su 5,ya tsallake ya tafi ko Jiddah bai gaya wa saboda haushin ta da yake ji don ko wayar ta baya amsa wa saboda lokacin da ya canja mata mota irin wadda take so ta dunga murna tun tafiyar shi bata kirawo shi ba sai a lokacin amman yayi biris ya k'i d'aukan wayar K'arshe ma da ta dame shi kawai sai yayi switch off d'in wayar don baya son jin komai daga gare ta tunda had'a shi da mahaifiyar shi take... Ita kuwa jiddah da taji wayar a kashe sai bata damu ba tasan Kafin yaxo weekend ya huci don batasan da tafiyar ba sai bayan tafiyar shi da k'wana 3 taji labari ai kuwa ranta ya 6aci tana matsayin matar shi taya ya xai tafiya ta tsawon wannan lokacin amma ace bai yi mata sallama ba wannan ai ba adalci bane (hmm ashe jiddah tasan da hka ita take mishi ashe dai ba dad'i) Ta d'an damu Kad'an amman cikin k'wana 2 ta watsar da damuwar ta cigaba da sha'anin ta ga xuwa aikin ta yana d'ebe mata kewa... Ta dad'a mik'e kafa komai sai dai ayi mata aikin ta kawai tayi wanka sai sallah da xaman cin abinci sai fita office da yawan bin gidajen k'awaye... ******** Su nauwara da saleem kuwa sai da suka ci kukan su suka koshi sannan lokacin gaf da mangariba mutane har sun fara watse wa nan hankalin nauwara yayi mugun tashi don batasan inda xasu je su k'wana ba tsoro Duk yabi ya kamata Suna cikin hka har duhu yayi basu ankara ba suka ga duk tarin mutanen duk sun kama gaban su wata er rumfa suka shiga tak'ure wa suka yi waje d'aya duk xuciyar su cike da tsoro ga duhu dulum ko'ina addu'o'i kawai nauwara take a cikin xuciyar ta da hka bacci ya d'auki saleem a jikin ta ita kuwa duk iya satar bacci ranar kasawa tayi Da hka har asuba tayi musu awajen sai da gari ya waye sosai sannan a hankali saleem ya bud'e idon shi tare da cewa "Aunty nauwara har yanxu uncle aminu bai xo ya mayar damu gida ba? " Kura mishi ido tayi don ta rasa mai xata ce mishi kafin a hankali tace "saleem ai mun bar musu gidan su ka amince abinda matar shi tace damu? " Shiru yayi da alamar tunanin yanda sukayi da hindatu yake yi tukunna yace "yanxu to ya anan xamu xauna ya xamu yi idan xamuyi bacci ko wani abun sannan ina xamu samu kud'in da xamu dunga cin abinci kullum???" Wad'annan tambayoyin na saleem ba k'aramin k'ara rud'ar da nauwara suka yi ta rasa amsar da xata bashi kawai sai tace "ina kud'in da aminu ya bamu Kafin yayi tafiya " Hannu ya xura a cikin aljihun kayan su ya xaro yace "gasu aunty nauwara " "nawa ne? " "dubu 3 ne dai dai " Saleem ya bata amsa ajiyar xuciya ta saki cikin jin dad'i Sannan tace "ka dauki duba d'aya ka siyo mana pure water muyi sallah Idan mun idar sai mu nemi wani abun mu ci" "toh aunty " Saleem yayi yanda nauwara tace mishi bayan sun idar da sallah anan saleem ya siyo musu wainar gero sukaci suka koshi suka d'ora da pure water ...... ???☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘?? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 31~* Suna nan xaune har rana tayi zafi basa uhm basa uhm uhm sai dai idan saleem ya gaji yayi bacci ya tashi ba me kula su kowa harkar gaban shi yake Wata mai siyar da abinci a tashar er dattijuwa bahaushiya ce tun da safe tagan su awurin sai dai su siye abinci suci kuma suyi sallah a wurin toh ko bara suke sai yamma suke tafiya abin da xuciyar er dattijuwar nan ta sanar da ita sai taji tausayin su sosai 6 na yamma wannan er dattijuwar nan ta tashi daga sai da abinci ta tattara kayan ta waje d'aya aka lode mata su a taxi sannan ta K'arasa wajen su nauwara tayi musu sallama nauwara ce ta amsa Kafin er dattijuwar nan ta cigaba da cewa "ni suna na saude mai abinci don sana'a ta itace siyar da abinci awannan tashar, shine tun safe da naxo na ganku anan ku kad'ai gaku yara ina iyayen ku, koh bara kuke yi ne??? " Wasu hawaye ne masu xafin gaske suka fito daga idanun nauwara Bara!!! Nauwara ta mai maita hakan a xuciyar ta cikin wani irin yanayi tace "ba bara muke yi ba kawai bamu da wajen xama ne da ya shige nan" Cikin mamaki take kallon ta kafin tace "ina iyayen ku,ina dangin ku? " "iyayen mu sun rasu dangin mu kuma bamu san su ba" Nan tausayin su ya k'ara kama ta don da ganin nauwara bata gani gashi kuma gurguwa ce "xaku iya bina gida na mu xauna tare ni kad'ai ce bani da yara ko d'aya sai dai mijina ya rasu tun jima wa ina xaune anan gaba Kad'an damu " Shiru nauwara tayi alamun tunani take ganin hka saude ta cigaba da cewa "tsakani da Allah xan rik'e ku yarinya kada kiji tsoro na baxan cutar da kuba gidan da nake gidan haya ne mu 2 ne a gidan " Nauwara Bata da yanda xasu yi kawai suka bita tun da basu da wajen xuwa d'aukan nauwara tayi cak ta shigar da ita mota da yake saude irin karfaffan nan ce saleem ma ya shiga tukunna mai taxi yaja su A kofar gidan matar suka tsaya nan ta fito da kujerar nauwara ta k'ara d'aukan ta ta xaunar da ita suka shiga cikin gidan da sallama d'aya Matar wadda suke xaune tare ita er dattijuwar ce ta amsa musu sallamar da fara'ar ta tare da yi musu sannu da xuwa Ko xama saude bata yi ba ta hura wuta ta dafa ruwan xafi ta hadawa nauwara ruwan wanka take mata toilet sannan ta kamata ta kaita bandakin tayi wanka sannan ta fito da ita had'e da bata buta tayi alwala don lokacin mangariba tayi Kamar yanda tayi wa nauwara haka tayi wa saleem sosai su nauwara sunji dad'in wankan dama duk xafi ya ishe su bayan sun idar da sallahr isha'e ne ta kawo musu abinci sukaci suka koshi sannan suka xauna a tsakar gida suna jin hirar dasu saude suke har lokacin bacci yayi suka kwanta Washe gari da safe bayan sunyi wanka basu da kayan sawa sai xanin saude ta d'aura bayan sun karya bata fita siyar da abinci ba sai da ta wanke musu kayan su tsab, ta ajiye musu abincin rana sannan ta tafi wurin sana'ar ta, yini suka yi su nauwara suna bacci sai dai idan lokacin sallah yayi su tashi saleem ya taimaka mata tayi alwala lokacin da suka ji yunwa suka ci abincin da saude ta bar musu Sai wajen 6 na yamma saude ta dawo suka yi mata sannu da xuwa ta amsa da fara'ar tare da cewa "ya bakunta? " Murmishi nauwara kawai tayi a Gaskia matar nan ba k'aramin mutunci ne da ita ba don har kafar wambai taje ta siyo wa su nauwara kaya en gwanjo Kala uku uku ita da saleem sosai suka yi mata godiya tare da addu'ar Allah ya saka mata da alkhairi Hka xaman su ya cigaba a wajen saude mai abinci cikin jin dad'i da kwanciyar hankali dai dai da wanke, kai ruwan wanka da yanke farce haka take xama tayi musu ga kuma aikin ta don sai da ta nemi er taye wajen siyar da abincin ta kawai don su nauwara kawai ita dai tana k'aunar yaran har cikin xuciyar ta, tuni su nauwara hankali ya kwanta babu horan yunwa da duka ko hantara sun d'an murmure sunyi kyau abun su... ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}* _wannan page d'in sadaukar wa ne ga en group d'in *Mrs Umar* nagode da yanda kuke k'aunar littafin nan sosai Allah ya bani ikon gama shi lafia_❤?? *~Pg 32~* *AFTER 6 MONTH'S* bayan wad'annan watannin abduljabbar ya dawo daga cos d'in da aka tura su cikin samun nasarar da abin da akaje nema sai da ya k'ara 1 week a abuja tukunna ya taho kano hankalin shi kwance don ya daina sa tunanin jiddah a ranshi Direct gidan su ya shige ae kuwa yayi nasarar samun abban shi a gida hakan ba k'aramin dad'i yayi mishi ba yana shiga falon abban suka rungume juna cike da murna kamar wasu friends Kafin su xauna tare nan suka d'an yi hira tukunna ya tashi ya shiga part d'in umma cikin sallama yayar shi aunty asma'u da kausar kanwar shi suka amsa mishi sallamar cikin mamaki yake kallon su kafin ya yatsine fuska yace "ku kuma lafia kuka xo mana gida " "Lallai ma abdul mu da gidan mu kace lafia don mun xo" Aunty asma'u ta bashi amsa tana dariya shima d'an murmusawa yayi yace "Gaskia xan yiwa maxan ku magana su dai na barin ku xuwa gida haka kawai" "iyeee lallai ma yaron nan ai kuwa kasan ka fad'a ne don kaji dad'in bakin ka" Aunty asma'un ce dai take bashi amsa kausar sai dai tayi dariya don baya bata fuskar hakan ita da FA'iza umma tana xaune gefe sai murmishi take yi cike da jin dad'in dawowar d'an gaban goshin ta yana kok'arin xama kusa da umma yana cewa "ki xuba ido ki gani mana tun daga abuja ki kwaso yara ki taho" "Hmm naga ai gwara ni akan kai da duk weekend kana hanyar kano,yawwa umma na tuna kiyi wa yaron nan magana wlh sam baya kai min xiyara can sai dai waya fah gashi muna gari d'aya " "toh an gaya miki aikin irin na ragwaye ne bana samun time ne sosai, sannan kawai sai aganni ina xuwa gidan ki kamar wata yaya ta" Dariya suka tuntsire da ita Kafin aunty asma'u tace "sai ka fad'a wa wanda bai sani ba yaro" Shan mur yayi jin ta ambaci shi da yaro gaban kannen shi don hka yace "umma Allah ki fad'a wa wannan asma'un ta dai na cemin yaro idan ba hka..... tom" Murmishi umman tayi sai lokacin ta bud'e baki tace "hka ne gaskia ke ki dai na ce mishi yaro daga yanxu tun da baya so " Cikin dariya aunty asma'un tace "angama umma baxa a sake fad'a ba" Gwalo yayi mata umma da asma'un sun ganshi kawai sai murmishi sukayi tun da rabon da ya xauna Hka acikin su ayi hira kamar hka an dad'e cikin muryar shagwa6a yace "umma na yunwa nake ji ataimako da abinci" Kafin umma tayi magana caraf aunty asma'u tace "ka tashi ka tafi gidan ka kaci mana" D'aure fuska yayi tare da watsa mata harara umma ma alama tayi mata da tayi shiru don hka da dakyar ta gimtse dariyar ta don sun riga da sun san halin Jiddah tun tuni shi yasa sam basa shiri da juna da kanta ta tashi kitchen ta nufa ta shiryo mishi abinci da drink mai sanyi ta kawo mishi cike da tausayin d'an k'anin nata tana addu'ar Allah ya bashi mace ta gari wadda xata dunga kyautata mishi tun da tasan komai yana fad'a mata matsalar shi Bai sake yi min magana ba yayi bismillah Ya fara cin abincin shi a nutse da ganin fuskar shi akwai tarin damuwa Shigowar aunty sadiya kishiyar umma da yaran aunty asma'u hanan da khalipa sai d'an kausar naufal shi yasa shi d'an sakin fuska yana bala'in k'aunar yara sosai Bayan sun gaisa da aunty sadiya ya kwashi yaran suka fita sae da ya kaisu shan ice cream tukunna ya dawo dasu kowanne yaro da ledar shi a hannu cike da kayan ciye ciye sai tsallen murna suke yana ajiye su ko cikin gidan bai shiga ba ya juya ya tafi gidan shi don ya kwanta ya huta Agajiye yake sosai Door bell ya danna larai er aiki ta xo ta bud'e mishi tare da yi mishi Sannu da xuwa amsawa yayi sannan yayi gaba upstairs ya haye sai da yayi wanka ya shirya cikin three quarter white da riga mara hannu black colour ce mai ratsin fari yayi kyau sosai kan nan nashi yasha gyara ya fito daga bedroom d'in sai k'amshin turare yake xama yayi a falo ranshi a 6ace saboda jikin shi ya bashi jiddah bata gidan kwanciya yayi akan three stairs ya lumshe idon shi yana tunani Ya kai wajen 20 mints a hka Kafin ta shigo cikin gidan ko dar batayi ba na tsoron ganin shi a gidan tunda bai sanar mata ba don hka cikin kissa ta Karaso kusa da shi tana wani firiri ta "Ah my soja na saukar yaushe? " a hankali ya bud'e idon shi ya watsa su akan ta sai da taji d'an tsoro ganin yanda idon nashi suka kankance cike da 6acin rai bai kula ta K'arshe da ta dame shi da surutu d'akin shi ya tashi ya shige ya barta baki sake tana kallon shi sai dai bata yi fushi ba tunda neman hanyar da xai hak'ura take Wanka tayi ta shirya cikin wasu shegun sleeping dress taci kwalliya sai k'amshin turare take sai da ta bud'e drowern bed side ta d'auko wani pill ta kora da ruwa tukunna ta nufi bedroom d'in shi akan gado ta same shi ya lumshe idon shi kamar mai bacci yayi mata kyau sosai gaskia ina son wannan guy d'in da yawa da ace ra'ayin mu yaxo d'aya dashi da ba k'aramin dad'i xata ji ba sai dai kash abduljabbar yana da wani irin murd'ad'd'en hali xama dashi sai mace mai hak'uri Jikin shi ta fad'a tare da rungume shi tana bashi hak'uri cikin salon kissa wata wawuyar ajiyar xuciya ya saki tare da k'ara rungume ta a jikin sa nan suka cigaba da faranta ran junan su... Washe gari ba laifi ya d'an tashi da sukuni a xuciyar shi yana gama breakfast ya fice xuwa gidan abdulkareem daga nan suka wuce xuwa gidan su abduljabbar... ******** Wata mata na gani er dattijuwa tana tsaye bakin titi da alamar tsallaka wa take son yi gashi yamma tayi sosai don gaf ake da kiran sallahr mangariba gashi Motoci sai shige wa suke ba kakkauta wa tayi tsayin 30 mints a tsaye Kafin taga sun d'an ragu Cikin sauri ta taho xata tsallaka sam bata tsaya dubawa ba saboda saurin da take ai kuwa tana tahowa dai dai tsakiyar titin wata mota ta taho da bala'in gudu gaba d'aya mutanen wajen suka d'ora hannun su akai cike da tashin hankali........ ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 33~* Duk yanda mai motar yaso ya kauce Amman ya kasa sai da ya bige er dattijuwar nan ai kuwa ta gangara kan titi tuni jini ya soma fita daga jikin ta nan da nan aka kwashe ta sai asibiti nan likitoci suka Duk'ufa akan ta domin ceto rayuwar ta... Nauwara tana xaune ita da saleem a tsakar gida suna er hira tare da d'aya er hayar har xuwa wucer lokacin da saude take dawowa daga tasha Amman shiru bata dawo ba har aka idar da sallahr isha'e shiru nan fah hankalin su ya fara tashi tunda bata ta6a kai wannan lokacin bata dawo ba Suna cikin hka aka kwad'a sallama mijin matar nan ne ya fita da sauri ko 5 mint bai yi ba ya shigo cikin gidan hankalin a matuk'ar tashe bai 6ata lokaci ba wajen sanar dasu halin da ake ciki wayyo xo kuga tashin hankali wajen nauwara kuka sosai take yi gwanin ban tausayi saleem ma kukan yake sunyi matuk'ar tausaya musu kafin ya ce "bari na bishi naga asibitin da aka kwantar da ita naga jikin? " Nan ya fice da sauri ya bar su cikin tashin hankali, lokacin da yaga jikin saude ba k'aramin firgita yayi ba kamar ba ita ba duk kamannin ta ya canja shi ya nemo en uwan ta nan da nan suka xo su ma... Lokacin da ya dawo ya bawa su nauwara labarin halin da take ciki gaba d'aya ta rud'e kuka kawai take wannnan a daren nauwara batayi runtsawar kirki ba saboda tsabar fargaba na halin da saude take ciki addu'a kawai take yi mata *BAYAN KWANA 3* Acikin wad'annan kwanakin uku baxan iya fad'a muku tashin hankali da nauwara ta shiga ba duk wasu abubuwan da saude take musu babu shi abinci ne sau d'aya arana wannan er hayar gidan take taimaka musu don suma ba wasu masu karfi bane gashi saude tana gadon asibiti ko sanin wanda yake kanta batayi Daren ranar da ta cika Kwana uku a daren saude ta amsa kiran ubangiji gaf da asuba Allah sarki xo kuga tashin hankali wajen nauwara abin ba'a cewa komai sai addu'ar Allah ya jik'an ta da rahma... Sati Biyu da rasuwar saude kud'in hayar ta ya k'are mai gidan ya buk'aci su tashi xai sa wata idan kuma suna da kud'in biya sai biya hankalin nauwara idan yayi dubu ya tashi ta rasa inda xata tsoma kanta taji dad'i Har lokacin da ya basu idan basu da kud'in su tashi amman nauwara ta rasa inda xasu je da hka har suka k'ara k'wana d'aya ai kuwa Washe gari da sassafe mai gidan yaxo da yake irin mutanen ne da akan kud'in su basu da mutunci Hka yasa aka watsa wa su nauwara kayan su waje suna kuka da rokan shi yayi hak'uri Amman ko a jikin shi sunci kuka a kofar gidan nan Kafin su tafi su bar nan....... Hka su nauwara rayuwa ta juya musu suka shiga wata irin rayuwa a wannnan lokaci wadda tafi ta baya tsananin saboda abin da xasu ci gagarar su yake sai sunyi bara suke samu Basu da wurin k'wana sai dai su samu wata rumfa ko wani lungun su mak'ale su k'wana basa samun yin wanka duk sunyi bak'i sun rame Sun koma mabaratan karfi da yaji don Idan basu yi bara ba xa su samu abun da Xasu ci ba rayuwa ta mara galihu suke tun tana kuka har ta hak'ura suka rungume rayuwar su ta yanda taxo musu Wataran su samu wani lokacin kuma sai dai su yini da uwar yunwar su da hka suke jurewa har sun saba da hakan sun d'auki tsawon lokaci acikin hka suke gudanar da rayuwar su Wani yammaci ne mai cike da dada'an yanayi iska tana kad'awa mai matuk'ar dad'i nauwara tana xaune akan kujerar ta a gefen titi saleem ya tsallaka titin don ya siyo mangoro Don mai tallan yaji yake fadawa nauwara yana sha'awar shan mangoro shine ta bashi wata naira 10 yaje ya siyo shiru shiru har yanxu bai dawo ba shine hankalin ta ya fara tashi nan ta fara kiran shi "saleem! Saleem!! Saleem!!! Shiru bata ji alamun ya dawo ba tuni idanun ta Sun kawo k'walla tare da tunanin ina saleem yayi Adai dai lokacin abduljabbar yayi parking d'in motar shi don amsa Kira ya gama wayar ne sai ya d'ago kanshi ya Kalli wajen sai yaga yana sha'awar fita don ya da sadaka a hankali ya bud'e kofar motar ya xuro kafar shi ya fito yana sanye da black jeans da t-shirt ash colour yayi matuk'ar yin kyau nan ya fara raba musu kud'i yana cikin hka yaji an rik'e rigar shi juyo war da xai yi idon shi ya sauka akan wata kaxamar yarinya akan keken guragu tana kiran saleem ran shi yayi matuk'ar 6aci don Abduljabbar ya tsani kaxan ta gashi wata banxa kaxama ta rik'e mishi riga wayyo a lokacin xan so kuga yanda fuskar abdul ta koma saboda tsanani 6acin Ita kuma nauwara a b'angaren wani hadadden k'amshin turare ne ya bige wanda bata ta6a shak'ar k'amshi irin shi ba wanda rabon ta shak'i irin Wannan k'amshi har ta mance a rayuwar ta..... ??? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 34~ Ganin tana kok'arin kamo hannun shi yasa shi k'ara fusata bai san lokacin da ya d'aga hannu ya wanka mata mari mai matuk'ar gigita mutum, da sauri tasa hannu ta dafe wurin da ya mare ta wani kuka mai ciwo ta fashe da shi Kafin taji muryar shi mai matuk'ar dad'in gaske amman cikin fad'a "are u mad, xaki rik'e ni da wannan kaxamin hannun naki me kike so? " Lokacin da taji muryar shi sai da gaban ta yayi mugun fad'uwa Kafin ta bud'e bakin ta dakyar cikin muryar kuka tace "I'm so sorry ina neman k'anina, bana gani shiya sa na rik'e ka kayi hak'uri " Dummm shima gaban shi ya fad'i jin muryar ta, amman sai ya basar yaja tsaki kawai ita kuma nauwara sai taja kujerar ta Xuwa gefe d'aya tana dafe da kumatun ta sai kuka take saboda marin ba k'aramin shigar ta yayi a 6angare d'aya na xuciyar ta tana mai tunanin wannan daddad'ar murya duk da bata ganshi ba amman tasan ba k'aramin kyakkyawa ba ne... Abduljabbar kuwa yana gama raba kud'in ya jiyo xai shiga mota sai ga saleem yana cewa shima ba'a bashi ba hannu ya xura a aljihu ya xaro 2k ya bashi nan yayi godia tukunna ya shige sai ya bishi da kallo bai tsaya Ko ina ba sai wurin nauwara ya tsugunna a gaban ta yana Bata labarin an basu sadaka har ta 2k mtswww yaja tsaki sannan ya shige mota Yana shiga sai ya cire rigar nan ta jikin shi wadda nauwara ta rik'e ta ya cillar da ita waje ya bar vest d'in ciki tukunna yaja motar shi ya bar wajen yana Allah Allah yaje gida don yayi wanka don duk a tak'ure yake jin shi... Rigar nan tashi ba inda ta sauka sai kan fuskar nauwara daman a saitin wajen take sai da gaban ta ya fad'i jin k'amshin turaren nan hannu tasa ta d'auke rigar daga fuskar ta tare da rik'e ta Kam a hannun ta don hka kawai taji tana bala'in son rigar da k'amshin turaren Sai da mangariba tayi sannan saleem ya tura ta suka bar wajen xuwa wata er rumfa da suke k'wana... ******** Yana xuwa gida wanka ya shiga yayi sosai ya dunga durxa jikin shi wajen wankan sai da yaji fatar shi tana rad'ad'i tayi jawur da ita sannan ya kyale wankan ya fito ya xura farar jallabiya mai gajeren hannu tare da fesa turare silifas d'in mai matuk'ar laushi fari ya sanya a kafar shi sannan ya shige Xuwa masallaci don ba da faralin mangariba Sai bayan anyi sallahr isha'e ya fito daga masallacin dinning table ya xauna ya had'a tea yasha tukunna ya mik'e xuwa bedroom d'in shi sai da ya sake wanka sannan ya kwantar Ko neman jiddah bai yi ba saboda har yanxu bai huce ba nan da nan bacci mai dad'i yayi awon gaba dashi... Cikin bacci ne yayi mafarki da wannan yarinyar almajira dayagani tana gudu wasu mutane sun biyo ta da makami a hannun su suna bin ta a baya tana gudu sosai hannun shi ta kama tana cewa ya taimaka mata firgigit ya tashi daga bacci cike da mamakin Wannan mafarki daga ganin ta sau d'aya sai mafarkin ta Mtsww yaja tsaki mybe tausayin ta ne yasa shi yayi mafarkin ta daga hka ya juya ya koma baccin shi... Toh fah abduljabbar tun daga Wannan lokacin yake mafarkin nauwara Kala Kala kuma duk wanda yake yi kuka yake ganin tana yi tana ce mishi ya taimaka mata tun abun baya damun shi har takai yana d'an tsaya wa ya yi tunanin hkan sai ya fara tunanin hanyar da xai bi Don nemo yarinyar Inda ya fara had'u wa da ita ya fara xuwa sai dai an tabbatar mishi an d'an k'wana 2 ba'a gansu a Wajen ba Duk inda yaga masu bara xai tsaya ya duba ko xai gansu Amman ko mai kama dasu bai gani ba hka ya tattara ya koma abuja ****** Gaf da mangariba sun sha yawo sun gaji da bara basu samu komai ba rabon su da abinci tun kosan safe da aka basu sadaka yunwa sosai suke ji har akayi isha'e tuni yunwa ta fara gala6aitar dasu Nan suka fara tafiya kawai don neman abin da xa suci saleem a gajiye yake tura ta tsintar kansu suka yi awata unguwa shiru kamar ba mutane gefe d'aya suka samu xama sukayi duk sunyi shiru saboda yunwa kowanne da kalar tunanin da yake yi Dare ya farayi don 12 na dare ta gota kwatsam sai ga wasu en shaye shaye su 3 sun taho suna rangaji akan hanya daga nin su sunsha sunyi tatul sai suka hango su nauwara cikin maganar en shaye shaye d'ayan yace "yaa baabaa ga wata yarinya can ko xamu d'an latsa ne?" Sauran biyun suka kwashe da dariya sannan a tare suka ce "ai fad'a ma 6ata baki ne kawai muje mu kwashi gara Allah yasa akwai Maik'o " Suna gama fad'in hka gadan gadan sukayi kan nauwara Bata ankara ba taji an rirrike ta Ana cewa "Yawwa kaga ma gurguwa ce yi sauri kayi ka gama nima na fara don da gani xatayi maik'o " Hba jin Wannan maganar tasu nauwara batasan sanda ta k'walla wata uwar k'ara ba k'arar da tayi ita ta tashi saleem daga d'an baccin da ya fara ganin abin da yake kok'arin faruwa da auntyn shi ya sa shi tashi xumbur yana tutture su ganin saleem xai 6ata musu lokaci yasa d'aya daga cikin su ya damke shi daman d'aya ya rik'e nauwara kam d'ayan kuwa ya fara kok'arin yaga mata rigar jikin ta har yayi nasarar keta ta.......... ??☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? _Godia mara adadi gare ki k'awata saNaz Allah ya k'are min ke a duk inda kike Allah ya bar xumunci ameen_❤?? *~Pg 35~* Banda ihu da ambatar Allah babu abin da nauwara take cewa kuka take yi sosai tana neman taimako har sun kekketa mata riga ga saleem shima an rirrik'e shi sai kuka yake yi yana kiran sunan nauwara... Gudu sosai yake yi akan hanyar shi ta dawowa daga abuja saboda ganin dare yayi mishi gashi ko driver bai nema ba da kanshi yake driving A hankali yake jin ihu yana tashi daga wani b'angare kuma da alama ihun mace ne da yaro k'arami bai san lokacin da ya taka birki ba tare da fitowa daga motar yana sanye da kakin shi da sauri yayi hanyar da yake jin ihun Ganin wasu matasa su 3 suna kok'arin yiwa wata yarinya fyad'e yasa bai san lokacin da yayi wani wawan tsalle ba ya kaiwa d'aya daga cikin su naushi ba ai kuwa tuni ya xube a wajen da sauri sauran suka cika saleem da nauwara xasu gudu ai kuwa ya damko su tare da gwara kansu lokaci d'aya suka saki ihu tare da xube wa a k'asa belt d'in jikin shi ya ciro ya fara dukan su sai da yayi musu lilis tukunna ya kirawo number d'in police tare da yi musu tare da yi musu kwatancen wajen suka ce Gasu nan xuwa... Kan yarinyar ya koma gaban shi yayi wata iriyar fad'uwa ganin yarinyar da yake mafarki da ita ce kullum tana neman taimakon shi da sauri ya kau da kanshi daga kanta saboda ganin sun yaga mata riga jikin ta ya bayyana a waje mik'e wa tsaye yayi yana tunanin da me xai suturta mata jikin ta kafin ya ankara yaga en sanda sun kusa k'araso wa inda suke tuni hankalin shi ya tashi saboda baxai so su ganta a haka ba Cikin xafin nama ya cire rigar kakin shi ya sanya mata sai lokacin ya ankara ashe ta suma da sauri ya d'auke ta cak ya sanya ta a bayan motar ya kamo hannun saleem ya sashi a motar tukunna ya K'arasa wajen en sandan nan yayi musu bayanin fyad'e suke yunkurin yi mata Don hka su tafi dasu xuwa station su hukunta su dai dai da laifin su yana gama yi musu bayanin komai ya juya ya shiga mota yayi mata key ya bar wajen, su kuma en sandan nan suka damk'e su tare da tura su a cikin mota sukayi gaba Gudu sosai ya dunga yi har ya k'araso hospital d'in da suke xuwa yana parking ya fito daga motar ya d'auki nauwara suka yi hanyar shiga cikin asibitin saleem yana binshi a baya Da sauri nurse suka kar6e ta tare da kaita wani d'aki sannan suka kirawo doctor nan ya fara binciken yarinyar har numfashin ta ya dawo dai dai sannan ya sanya mata drip saboda yunwar da ta gala6aitar da ita sannan ya fito daga d'akin xuwa office inda ya bar abduljabbar a xaune Bayan doctor ya xauna ya d'ago kai ya Kalli abduljabbar ya fara da cewa "Alhmdullilah yalla6ai ta farfad'o daga suman da tayi kuma basu yi nasarar yi mata fyad'e ba, tsoratar da tayi shi yasa ta suma, gashi tana xama da yunwa don tana d'aya daga abin da ya k'ara gala6aitar da ita " "okay doctor xa'a kiyaye hkan, bayan hka ina son ka duba min yaron nan shima " "toh yalla6ai " Nan ya danna k'ararrawa wata nurse ta shigo da sauri yace "Yawwa sister wannan yaron xaki xo min dashi " "okay sir " Ta fad'a tana satar kallon abduljabbar don guy d'in ya had'u ta ko'ina, Kafin ta shige ta xo da saleem nan doctor ya d'ora shi kan gadon dake office d'in ya shiga duba shi Shima saleem d'in babu abin da yake damunshi fiye da yunwa nan ya yiwa abduljabbar bayani Sannan ya Kalli nurse d'in nan yace "Don Allah sister xan d'an had'a ki da wani aiki wannan yaron xaki had'a wa tea yasha sannan a d'an samo mishi abin da xai ci mai d'an nauyi, baya nan ga magani xan rubuta miki kije pharmacy ki siyo sai ki bashi yasha" "okay sir ba damuwa " "Yawwa ngde sosae " Har ta kama hannun saleem xata fice daga office d'in abduljabbar ya dakatar dasu ai kuwa jikin ta na rawa ta dawo ta tsaya sai wani karairaya take mai da kallon shi yayi kan doctor yace "Ko xaka yi mata magana ta xauna ta kula su xuwa lokacin da xa'a sallame su Idan yaso sai na biya ta" "toh kinji fah xaki iya? " Cikin mak'ale murya tace "Why not doctor xan iya sosai ma" Murmishi doctor yayi tare da fad'in "Thank u sister" Daga hka ta fice daga office d'in ita da saleem abduljabbar ma tashi yayi tsaye tare da yiwa doctor sallama sai da safe xai dawo daga hka ya fice daga office d'in Yana xuwa gida wanka ya shiga yayi sosai ya fito sannan ya shirya cikin sleeping dress farare sol dasu ya fesa turare sannan ya had'a coffee yasha yana gama wa ya kwanta kan bed ko tunanin neman jiddah bai yi ba saboda har yanxu yana jin haushin ta tare da k'aro karfin Ac Wannan daren bai yi bacci sosai ba xuciyar shi cike da tunanin wad'annan yaran ko ina iyayen su suke har suka barsu suna yin bara tunani dai barkatai ya dunga yi a cikin Wannan daren Kafin dakyar bacci ya dauke shi... ☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*?? _wannan page d'in sadaukar ce ga en group d'in saNaz novella da ruky & ashba novels grp da classic novels da en group d'in hausa novels babu abin da xance muku sai dai nace ngde da yanda kuke k'aunar littafin nan_❤?? *~Pg 36~* Washe gari misalin karfe 9 na safe nauwara ta farka daga baccin allurar da doctor yayi mata, cikin kuka ta farka kuwa don tuno abin da ya kusan faru wa da ita jiya nan nurse d'in nan da saleem suka rarrashe ta dakyar tayi shiru sai faman ajiyar xuciya take A hankali ya turo kofar bakin shi d'auke da sallama ya had'e cikin wani blue jeans da t-shirt fara mai dogon hannu ta d'an kama shi Kad'an hkan ya bayyanar da alamar karfi a tattare dashi kannan nashi yasha gyara sai faman kyalle yake ga agogon hannun shi black ba k'aramin dace wa yayi da tsintsiyar hannun yayi ba da yake ya d'an nannad'e hannun rigar Kad'an tuni sassayan k'amshin turaren shi ya cika d'akin gaban nauwara ya fad'i jin k'amshin turaren shi ai wannan k'amshin turaren kamar ta ta6a jin irin shi Ita kuwa madam nurse an ga d'an hadadden guy tuni an fara gyara xaman riga tare da fara gwalangwaso (nace Idan dai abduljabbar kike yiwa Hka Kya yi Kya gama lol) Manyan ledar hannun shi ya ajiye bayan ya yiwa su nauwara kallo d'aya cikin muryar shi mai dad'in gaske yace "am don Allah Idan ba tak'ura xaki gyara min jikin su ga komai nan a ciki har da takeaway na breakfast " Cikin iyayi da fari da ido tace "ba damuwa yalla6ai " D'an Murmishi yayi wanda iyakar shi fatar bakin shi yace "Thank u " Yana gama fad'in hka ya fice xuwa office d'in doctor ta bishi da kallo Kafin ta dawo da hankalin ta kan ledar da ya ajiye ta shiga duba wa kaya ne doguwar riga da riga da siket set bibbiyu sai takalmi flat shoes Kala 2 sai under wears da kayan namiji set 4 na saleem kenan har da takalmi ga turarruka har Kala 2 sai hijab 2,da mayuka su cream sai shampoo and conditioner da kuma na shafa wa akai sai hand dryer Gaskia da ganin kayan ya kashe kud'i sosai D'ayan ledar kuma dangin kayan tea ne sai kuma fruit da takeaway d'in da yayi musu don hka tashi tayi ta hadawa saleem ruwan wanka da kanta tayi mishi saboda baxai iya fitar da kanshi ba don ba k'aramin daud'a Yayi ba ai kuwa tun daga gashin kanshi ta fara wanke wa nan tayi mishi wanka bayan sun fito ta shirya cikin d'aya daga cikin kayan nan ta gyara mishi farcen kafar shi da na hannu Haba tuni saleem yayi shar dashi kamar ba shi ba sai dai er ramar da suka yi da kuma duhun da sukayi wannan kuma wahala ce sai a hankali Bayan ta gama da saleem nan ta shigar da nauwara toilet d'in itama daga kanta ta fara wanke wa tana warware gashin tace masha Allah a xuciyar ta ganin dogon gashi mai kyau ga santsi da laushi don ma baya samun gyara wanke mata shi tayi tas sannan tayi mata wanka suka fito ta shirya ta cikin wata gown kalar ash tana da kwalliyar red flowers a jiki sai mayafin ta k'arami shima red nan ta busar mata kai da hand dryer ta shafa mai Sannan ta tufke mata shi d'an kwalin rigar ta d'auka tayi mata rolling d'in kanta dashi ta fesa mata turare Masha Allah ba k'aramin kyau nauwara tayi ba kamar ba ita ba abu biyu ne Yayi mata cikas makanta da gurgun ta, sai da ta yanke mata farce Sannan ta had'a musu breakfast sukaci suka koshi suna gama ci ta basu magungunan su suka sha sannan ta fita don kirawo doctor Tana fita saleem ya k'araso kusa da nauwara ya kama hannun ta tare da cewa "Aunty nauwara wlh Kinyi kyau sosae " Murmishi tayi kafin tace "kai ma nasan saleem kayi kyau sosai Allah ya sakawa mutumin nan da ya taimake mu da alkhairi" "Ameeen aunty nauwarah kingan shi kuwa kyakkyawa dashi kamar balarabe" "kai saleem " ta fad'a tana dariya shima saleem dariyar yake yana cewa "da gaske nake wlh" Shigowar doctor ne da abduljabbar ya katse su da yin hirar su duk sunyi ji dad'in ganin yanda nurse d'in nan ta gyara su ba kyiwa sai da doctor ya k'ara duba su sannan yace da abduljabbar yana da magana dashi su koma office Bayan sun isa office d'in sun xauna doctor ya fara da cewa "yalla6ai kasan yarinyar nan bata gani kuma bata iya tafiya koh" Abduljabbar ya Jijjiga kai alamar ehh doctor ya cigaba da cewa "to a yanda na kula da kafar ta xamu iya yi mata aiki ta dawo dai tana tafiya kamar da sai dai aikin akwai matuk'ar tsada gaskiya, idanun ta kuma ssai an dad'a dubawa ko suma xamu iya aiki akan su".... ???☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? _hak'k'a rayuwa da masoyi na tsakani da Allah Akwai dad'i don kowanne hali kashiga baxai guje ka sai ma ya k'ara nuna maka kauna da tausayi, Allah ka barmu da masoyan mu Ameeen thumma Ameeen_❤ *~Pg 37~* Shiru yayi na en mintuna Kafin yaja gwauran numfashi ya fara da cewa "Wannan ba matsala bane doctor Indai xata samu lafia is good,yaushe kake ganin xa'a ku fara yi mata aikin? " "ehhh toh sai dai an gama binciken tukunna xamu ga yaushe xaayi aikin" "Shikenan sai ku fara daga yau, xuwa anjima xan dawo naji komai " "an gama yalla6ai " Daga hka ya fice daga office d'in bai k'ara shiga d'akin su nauwara ba ya fice daga asibitin gaba d'aya, gidan su ya nufa kai tsaye akan bed d'in umma ya xube yana tunanin yanda kaddara ta had'a su da yaran nan ya matsu yaji labarin su don yasan yanda xai taimaka musu yana cikin tunanin nan umma ta shigo d'akin kai tsaye don tasan bata bar kowa a d'akin ba don ko sallama batayi ba turus tayi taja ta tsaya cikin mamaki don sam batayi tunanin yaxo kano ba k'araso wa tayi kusa da gadon ganin baisan ta shigo d'akin ba don ya xurfafa a tunani sosai A hankali umma ta d'ora hannun ta akan shi cikin nutsuwa tace "Abdul lafia kake kuwa irin wannan dogon tunanin? " Lumshe idon shi yayi Kafin ya sake bud'e su gaba d'aya cikin yanayin er shagwa6ar da 'ya'ya suke yiwa iyayen su ya fara magana "umma na gaji ne kawai jiya Shigowar dare nayi bansamu cikakken bacci ba gashi da safe da wuri na tashi " Murmishi tayi sannan tace "hmm Abdul ni ina mamakin ka ace wai baxa ka dunga shiga jirgi ba sai dai ka taho a mota komai dare " Er dariya yayi mai ban sha'awa wadda ta k'ara fito da tsantsar kyanshi yace "uhm uhm umma na fison tafiyar mota shi yasa " Ya cigaba da cewa "Yawwa umma na mance ban sanar miki ba komai fa ya kammala na bud'e wurin sai da motocin nan " Cikin mamaki tace"kai haba? " "da gaske umma na tura abdulkareem xai shigo da motocin, don mun gama magana da Abba shi xan d'ora matsayin MD cos ba lokaci nake samu ba " Murmishi tayi sannan tace "hkan yayi abdul Allah ya taimaka yasa a fara a sa'a" "Ameeen umma na" ya fad'i hkan yana tashi xaune sannan ya rik'o hannun umma da alama akwai muhimmiyar magana xai yi mata ita ma umma ta mayar da hankalin ta kan shi don tsab ta gama karantar shi da yanayin shi Indai xai yi mata magana mai mahimmanci baya iya b'oye mata abu Cikin nutsuwa ya fara bata labarin su nauwara tun lokacin da suka fara haduwa har ya mare ta da kuma taimakon da yayi musu daren jiya da ake kok'arin yi mata fyad'e da kuma taimakon da xai yi musu a gaba ya K'arasa maganar shi da cewa "ina so umma xan rik'e yaran nan kawai haka naji ina tausayin su" Sauke numfashi umma tayi kafin ta dafa kafad'ar shi tace "d'ana baxan hana ka samun lada ba abin da xance kawai shine ka kula da kyau Allah ya taimaka " Cikin farinciki ya rungume ta suna dariya "hmm wacce magana ake tsakanin uwa da d'a hka har ake dariya?" Suka ji maganar abba ya fad'a yana shigo wa d'akin dariya suka sake yi kawai "wlh Naga alama d'an ki duk son kud'ina yafi ni baki ga yanda ya shirya wurin sai da motocin shi ba yayi kyau Allah ya bada sa'a " Abba ya fad'a cikin tsokana yana kallon abduljabbar da umman shi don da ganin yanda ya fad'a tsokana yake Dariya suka sake yi saboda jin abin da Abba yace daga hka umma ta fad'a mishi maganar su nauwara girgixa kai yayi cike da tausayin su (hmm wai don ma basu ji cikakken labarin su ba), shima addu'ar fatan Allah ya taya shi rik'o yayi Kafin Abba yace "gobe ina son xuwa kaduna xiyarar aminina na dad'e rabo na dashi don xamu kai tsawon shekara d'aya bamu had'u ba, sai awaya gashi k'wanan bana samun number d'in shi a kashe, shine nake son xuwa" "Allah sarki gaskiya ya kamata kuwa an dad'e ba'a ga juna ba" Cewar umma "k'warai kuwa don gobe sai kaduna don naje xumunci " Abba ya fad'a yana mik'e wa tsaye har ya kusa fita ya d'an jiyo ya Kalli abduljabbar yace "son Duk da dai ni ba mai kud'i bane xan bada gudummowa ta don wlh ina kallo baxa ka kwashe ladan kai kad'ai ba " Gaba d'ayan su dariya suka tuntsire da ita Kafin abdul yace "tohh Abba na " Daga hka ya fice daga d'akin abduljabbar ma ya mik'e yana cewa "umma a had'a min fruit a kawo min wajen aunty sadiya xan shiga can " "toh Shikenan bari nasa FA'iza ta had'a maka " Yatsine fuska yayi Sannan cikin shagwa6a yace "ni nafi son naki umma yafi dad'i kiyi min da kan ki pls " Ya K'arasa fad'i yana kamo hannun ta murmishi tayi kawai in ban da abin abdul ko mene banbancin yanda take had'a mishi hka FA'iza xata had'a Amman har yasan da banbanci hmm abdul rigima kenan da haka ta shige kitchen shi kuwa yayi part d'in aunty sadiya Sun d'an tab'a hira da ita har FA'iza ta kawo mishi fruit d'in sannan ta juya ta fita Don kada tayi wani laifin ya jibge ta a banxa tunda ba laifi FA'iza akwai rawar kai ga shegen surutu Aunty sadiya ma sai da ya bata labarin su nauwara kuma fatan Allah ya taya shi rik'o tayi sannan tace "ya kamata a samu wadda xata xauna da su, kuma gobe da safe Idan xaka je ka biyo mu tafi na duba su " Hkan ba k'aramin yi mishi dad'i yayi ba "ai aunty akwai wata nurse xata xauna da su" Girgixa kai tayi tace "xan baku aron talatuwa (er dattijuwa ce wadda take taimaka wa aunty sadiya da aiki) don ta kula dasu xuwa a sallame su kuma ba sai kana takeaway kana aika musu ba kullum xan dunga bayar wa ana kai musu abinci tun daga breakfast har xuwa dinner " Hannu yasa yana hautsina gashin kanshi yana d'an murmishin jin dad'in kulawar da aunty sadiya xata bawa su nauwara godia yayi mata sannan ya tashi tsaye alamar tafiya xai yi dakatar da shi tayi tace "ina xuwa d'ana " Kitchen ta shige bata dad'e ba sai gata da wani basket dauke da foodflaks har 3 a ciki ga plates da spoon ta mik'a shi tana cewa "akai musu wannan yanxu talatuwa xata fito" "thank u so much my aunty, amman ita talatuwan ta taho dashi ina mota ina jiran ta " Murmishi kawai tayi shima fice wa yayi kai tsaye asibitin tafi sai da ya nuna mata d'akin su nauwara tukunna ya tafi office d'in doctor don jin me ake ciki........ ??☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 38~* Yana shiga office d'in doctor ya xauna sannan doctor ya fara bayanin shi kamar haka "yalla6ai mun gama duk abin da ya kamata na bincike amman sai nan da 2 days xamu yi mata aikin kafar saboda acikin k'wana 2 nan xamu d'ora ta akan wasu magunguna " Shiru Abduljabbar yayi yana sauraren doctor ganin haka ya cigaba da cewa "sai dai idanun tane duk iya binciken mu har yanxu bamu fahimci abin da same su ba har bata gani dasu, don hka xamu fara yi mata aikin kafar muna dad'a duba idanun nata ko xamu iya yi mata aikin " Yana gama fad'in hka ya janyo wasu file yana rubuta akan su a hankali abduljabbar ya bud'e bakin shi yace "okay ba matsala yanxu na kawo wata xata dunga kula dasu " "Shikenan yalla6ai wannan ba matsala bace" Ya Mik'o wa mishi wata paper yana fad'in "ga wannan takardar Idan ka duba sai kaje ka biya kud'in aikin da sauran abubuwa irin su maganin da xa'a yi amfani dasu" Yatsine fuska yayi ya kar6a ya karanta sannan ya sake Mik'o wa doctor yana cewa "ka turo min number account d'in asibitin xan turo " "toh Shikenan " Daga hka ya mik'e suka yi sallama da doctor ya fita har yaxo d'akin su nauwara xai shiga sai kuma ya fasa to me xai je yayi musu, sai kawai ya tsinci kanshi da lek'a su ta window suna xaune kan gado saleem yana bata abinci a baki suna hira da dariya Nauwara sai kyalkyala dariya take kawai sai ya tsinci kanshi da xuba mata ido yana kallon ta yana jin wani irin yanayi a jikin shi share abun yayi ya juya ya tafi Yana shiga falo ido hud'u sukayi da jiddah cikin mamaki take kallon shi don sam batasan yaxo kano ba ta d'auka wannan weekend d'in baxai xo ba don hka cikin yanayi na mamaki tace "my soja na saukar yaushe ?" Harara ya watsa mata ganin hka yasa da gudu ta K'arasa inda yake ta rungume shi cikin kissa tana wani marairaice wa tace "Haba my darling me kuma nayi daga tambaya sai harara? " Tana yi mishi maganar tana wani shafa shi a hankali,tuni ta tsokano shi daman a matse yake gashi yau da yamma xai wuce abuja saboda neman shi da ake tuni jiddah tayi janyo hankalin shi tun yana d'an kyale tare da sharewa har takai Jiddah ta gama tasar masa da hankali ya kasa d'aure wa tuni ya bada had'in kai har takai su da faranta ran junan su Bayan komai ya kammala ya shige toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin farin jeans da light purple d'in t-shirt mai dogon hannu yayi kyau sosai ya fesa turare sannan ya juyo da kallon shi kan jiddah wadda take cike da matuk'ar tashin hankali cike da takaicin biye mishi bata tsaya tasha pill d'in nan ba cikin d'an murmishi yace "Yah lafia kuwa? D'an sakin murmishin yak'e tayi tace "hmm ba komai wai har ka gama shiryawa ?" "yes i want to go,any problem?" "okay, safe journey my darling " Sunkuyo wa yayi tare da bata kiss a kumatu yana cewa "thank u my jiddah, xan turo miki kud'i ta account sauri nake" Langa6e kai tayi cikin shagwa6a tace "ka k'ara min akai, ina da biki next week na friend d'ina xan yi anko da siya mata gift " Murmishi kawai yayi sannan yace "okay kamar nawa kike so, sauri nake? " Fari tayi da idanun ta tace "50k xaka bani da hidimar bikin" "okay xakiji alert " Wani tsalle tayi cike da murna ta rungume shi tare da bashi kiss a lips d'in shi girgixa kai kawai yayi tare da yin gaba don kada ta 6ata mishi lokaci Yana fita da gudu ta nufi bedroom d'in ta tare da d'auko pill d'in nan tasha sannan hankalin ta ya kwanta don tana da yakinin babu abin da xai faru (hmm jiddah kenan ita fa haihuwa ce bata so k'wata k'wata saboda tasan ita take son abduljabbar tun da bashi ya gani yana so ba umman shi ta tak'ura mishi ya aure ta, tana tunanin Idan har ta sake ta haihu abduljabbar xai juya mata baya tun da jikin ta xai lalace anata tunanin fah komai na jikin ta xai saki kirjin ta xai xube ta daina birge abdul d'in ta shi yasa take shan pill ba tare da kowa ya sani ba, batasan ba'a yiwa Allah wayo ba Idan yaso abu xai kasance babu makawa sai ya faru) A gurguje yaje yayi wa iyayen shi sallama don sauri yake don ma yasa abdulkareem yayi mishi buking d'in jirgi Har xai fito daga falon umma yaga FA'iza sai marairaice fuska take alamar akwai abin da take so rankwashin ta yayi aka ta saki ihun xafi tana sosawa ta juya xata tafi yace "me kike so don da ganin yanda kike Akwai abin da kike so" Fuskar ta babu fara'a xata fara magana yace "Kinsan bana son ana yi min magana fuska babu fara'a oya saki fuskar nan ko na tafi" Ai da sauri FA'iza ta washe fuska tace "Yah abdul don Allah kud'i nake so " "me xakiyi dasu? " "hmm bikin yayar friend d'ina xamu yi " "ku dai mata baku da magana sai ta biki, kamar nawa kike so " "30k ya abdul don har anko da gift da xan bata" "Shikenan abdulkareem xai kawo miki amman ki kula banda kai wa dare, don ko kin dare xan sani kuma Kinsan sauran ai ba sai na fad'a miki ba" Cikin jin dad'in xa'a bata tace "Insha Allah yaya xan kiyaye ngde Allah ya k'ara bud'i" Shi dai wuce wa yayi ya bar FA'iza tana tsallen murna Don sunci burin Kece raini a wannan bikin ita da k'awar ta ta Har yaje abuja da tunanin su nauwara a xuciyar shi gashi bai biya ta wajen su ba har yaxo kwanciya bacci yana tunano yanda take dariya lokacin da ya lek'a su ta window fuskar ta tak'i 6ace mishi mtswww yaja tsaki meke faru wa da nine dakyar bacci ya dauke shi...... ???☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 39~* Hka aka cigaba da d'ora nauwara akan magunguna abin da yake d'aure musu kai likitocin sam har yanxu basu ga mussababin abin da ya makantar da ita ba gasu ga matsalar ba don hka kawai sai suka mayar da hankalin su kan kafar ta ta Nauwara a kullum addu'ar ta Allah ya saka wa wannan bawan Allah da alkhairi yanda yake kula dasu da nema mata magani don ta warke xata so ta samu lafia don ta ganshi da idon ta ko muryar shi bata ta6a ji xata so ko godiya tayi mishi, yanxu hankalin su a kwance babu tashin hankali gashi talatuwa babu ruwan ta kula dasu take tsakani da Allah ga lafiyayyen abinci tuni su nauwara sunyi kyau kamar basu ba Aunty sadiya ma taxo don lokacin da aka nemi abduljabbar a wajen aiki da yaxo gidan sallama dasu yake fad'a mata sai da driver ya kai ta da yake tasan asibitin shi suke xuwa ya sata washe gari ta had'a musu breakfast ta tafi musu dashi lokacin da taje sosai ta tausaya wa yaran,duk wani abu dake faruwa abduljabbar yana sani saboda doctor yana kirawo shi ya sanar dashi komai har ana yi gobe xa'a yi mata aikin ya sani Don hka a daren kawai sai ya tsinci kanshi da tashi yayi alwala ya fara nafila tare da addu'ar Allah yasa ayi aikin cikin sa'a *WASHE GARI* Washe gari misalin 11 na safe aka shiga aikin sai wurin 1 na rana suka fito likitocin cike da k'warin gwiwa don Insha Allah suna kyautata xato mai kyau Aunty sadiya ma tun safe ta xo saboda abduljabbar ya dame ta da waya kan taxo bini bini ya kirawo ta awaya yana tambayar ta abin da ke faruwa sosai aunty sadiya take mamakin abduljabbar yanda duk yabi ya damu da al'amarin yaran nan, sai da aka fito da nauwara sannan aunty sadiya ta koma gida Alhmdullilah aiki yayi kyau sosai sai dai bata iya tafiya da kafar ta sai an taimaka mata don kamar mai koyan tafiya ta koma ********* Cikin tsananin tarin damuwa yake ciki idan ba gixo idanu wana sukayi ba sai nace har hawaye ne suke xuba a idanuwan shi Cikin nutsuwa ta shigo d'akin me gidan nata tayi gayu cikin shadda kalar green riga da xani tasha aiki ba wata kwalliya tayi ba daga powder sai man leb'e amman tayi kyau sai k'amshin turare ne yake tashi a jikin ta baka ce ta haifi su aunty asma'u turus tayi taja ta tsaya cike da tausayin mijin nata tun lokacin da yaje kaduna don xiyarar aminin shi ya samu labarin ya mutu ya nemi ganin iyalan shi aka ce su ma Sun mutu gaba d'aya hankalin shi ba k'aramin tashi yayi ba shine tunda ya dawo yake cikin damuwa Hannun ta tasa tana goge mishi hawayen da suka xubo cikin muryar kwantar da hankali tace "Haba abban asma'u me yasa baxa ka daina sa kanka cikin damuwa ba sai wani ciwon ya shige shi, Kiyi hak'uri lokacin shine yayi yanxu addu'a yafi buk'ata fiye da komai " Janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta cikin sanyin murya yace "mata ta na rasa aminini na wanda bani da aboki sai shi ya fad'a min matsalar shi na bashi shawara nima na fad'a mishi tawa naji mutuwar shi da niyyata na d'auko ya'yan shi na rik'e mishi su sai naji wani labarin da ya dad'a gigita ne wai sun mutu gaba d'aya sanadin gobara hakan ya d'aure min kai sosai " "ya xamuyi da k'addarar ubangiji Allah ya jik'an su da rahma " "Ameeen thumma Ameeen, na tausaya wa iyayen shi sosai innar shi tana nan bata da cikakkiyar " Nan dai ta samu ta rarrashe shi har sake tukunna ta gabatar mishi da abincin shi yana ci tana yi mishi hira mai dad'i tuni ya nutsu ya ci abincin sosai (Duk namijin da yayi dace da mace ta gari yaji dad'in shi, don itace mai kwantar mishi da hankali Idan ya shiga wani hali na daban, en uwa na mata ya kamata mu jajurce Wajen kyautata wa maxajen mu don su dunga alfahari damu a rayuwar su) ******* Tun lokacin da aka yiwa nauwara gyaran kafa abduljabbar ya ke d'okin Friday tayi don yaxo ya ganta shi kanshi mamakin yandayi d'okin xuwa yake Ranar Friday tun bayan sakkowa daga masallaci ya taho jirgi ma ya biyo don tsabar k'aguwa bai yi tahowar mota ba duk yanda yake son tafiyar mota kuwa, jirgin su na sauka ya kirawo abdulkareem yana airport don hka cikin mintuna 30 abdulkareem ya k'araso airport d'in Rungume juna suka yi cikin tsananin murna Kafin abdulkareem yace "Amman nayi mamakin xuwan ka fah saboda yanda kace min kana da aiki" Yatsine fuska yayi sannan yace "ka mance ina patient a hospital ne? " Dafe kai abdulkareem yayi tare da cewa "auuch wlh har na mance jiya da dare ma na kai umma da FA'iza " Xaro ido yayi cike da mamaki akan fuskar shi yace "da gaske kake " Hararar wasa yayi mishi tare da cewa "ah karya nake ma, yau ma munje da yaya (yana nufin abban abduljabbar don yayan shi sai dai kusan sa'annine da abduljabbar) ,bugun kafad'ar shi yayi Kad'an da sauri ya ja baya tare da rik'e wajen "kai wlh abdul ka fiye mugunta da yawa mene na dukan kuma, kufa sojojin nan hannun ku baya xama waje d'aya " Murmishi yayi tare da cewa "Allah ya shirye ka abdulkareem wannan d'an bugun " "hmm ni kuwa naji xafi a jikina " "Yasu maryam da boy hope suna nan qlau? " Yana yiwa mota key yace "sunan qlau kai ka tsaya wasa gashi har ta harbu sauran bai fi 3 month's na sake samun new baby ba" "da gaske kake mutumin? " "Ah tsaya wasa yaro kasha kallo" "nima abdulkareem ina son yara da yawa sai dai har yanxu jiddah shiru but ina nan ina addu'a Allah ya bani nima " Cikin tausayin shi yace "kada ka damu nawan Insha Allah suna nan tafe " Da hka ya d'auke mishi hankali da hira idan ba haka ba damuwa xai sanya wa kanshi don abduljabbar Akwai shi da son yara sosai....... ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*?? *~Pg 40~* Wajen 5 na yamma ya shigo cikin asibitin yana sanye da blue jeans da t-shirt black kayan sun kar6e shi sosai agogon hannun shi bak'i ya dace da hannun nashi sai k'amshin turaren shi na kodayaushe yake Parking yayi a harabar asibitin ya bud'e kofar motar ya fito da kafar shi d'aya kamar ance ya juya gefen shi ya hango su nauwara a wajen ta dafa talatuwa tana yin tafiya a hankali saleem yana bayan su, yayi mamakin yanda yaran suka koma sunyi kyau sosai koma wa yayi da kallon shi kan nauwara wadda take sanye da riga da siket english wears kayan sun kar6e ta sosai a hankali yaji xuciyar shi tana ayyana mishi wasu batutuwa sai kawai ya kawar da wannan tunanin a cikin xuciyar shi ta hanyar fita daga motar ya nufi office d'in doctor cikin tafiyar shi ta kasaita Bayan sun gama magana da doctor yake fad'in nan da 5 days xai sallame su don aikin yayi kyau sosai daga nan ya tashi ya fice daga office d'in lokacin da ya duba wajen dasu nauwara suke xaune yaga basa nan mybe don ganin mangarib ta gabato ne cikin nutsuwa yake driving d'in shi har ya k'araso gidan shi xuciyar cike da wasu irin yanayi wanda yake kok'arin karyata hakan... *BAYAN K'WANAKI 5* Acikin wad'annan kwanakin nauwara ta mik'e ras tana tafiyar ta kamar da amman sai dai da taimakon sanda take dogara wa tun da bata gani da idanun ta Ranar da doctor ya sallame su abduljabbar ya baro tarin ayyukan shi a office ya taho kano, yana xaune shi da abdulkareem a gaba mota su talatuwa suka fito tana rik'e da tarkacen kayan su yayin da saleem yake rik'e da sandar nauwara yana yi mata jagora xuba mata ido abduljabbar yayi yana kallon ta yayin da abdulkareem yake kallon shi cikin tsokana yace "Hmm captain ko da ita xa'a k'ara a ta 2 irin Wannan kallo hka?" Harara ya watsa mishi yana cewa "kai Wlh abdul ka fiye sa ido ni just tausayi take bani " "alright Idan tayi tsami maji don daga tausayi yake rikid'ewa ya xama sooo" Har ya bud'e baki xai yi magana suka k'araso wajen don hka yayi shiru yayin da abdulkareem yake yi mishi dariya k'asa k'asa tuni ya cika yayi fam sai hararar shi yake dakyar ya iya danne dariyar yace wa nauwara wad'anda suka shiga motar "Sannu nauwara Allah ya k'ara lafia " Cikin d'an jin kunyar shi don ta d'au muryar shi tace "Yawwa uncle abdulkareem Ameeen ngde, ina su aunty maryam? " Cikin mamaki abduljabbar ya juyo yana kallon abdulkareem cike da neman Karin bayanin yanda akai ta shaida muryar shi, gira ya d'aga mishi yana er dariya girgixa kai kawai yayi ya mayar da hankalin shi kan danna waya Gidan shi kai tsaye suka nufa abdulkareem yayi parking sannan yace "captain ni baxan shiga ba fah bcoz ina sauri akwai inda xan je" Baice komai ba ya bud'e motar ya fito sannan yace "ka tafi da talatuwa ka mayar wa da aunty sadiya ita " Ya juyo da kallon shi kan talatuwa yace "Mun fah gode " "Ah ba komai yalla6ai " Talatuwa tace tana kok'arin fito da nauwara wadda tayi suman xaune jin hadaddiyar muryar abduljabbar gaban ta ya hau fad'uwa kamar ta ta6a jin Wannan muryar Kallon saleem yayi yace "Yah boy taimaka mata mu shiga gidan " "toh uncle " Saleem ya fad'i hakan yana kok'arin kama sandar nauwara da hka yayi gaba suna binshi a baya har cikin gidan, tana xaune kan kujera da laptop a gaban ta tana aiki a cikin ta taji sallamar shi kamar a mafarki da sauri ta mik'e tsaye cikin mamaki tace "my darling lafia? " Ta tambaye shi ganin sai weekend ya saba xuwa waje ya samu ya xauna sai lokacin hankalin ta yayi kan su nauwara nan take annurin fuskar ta ya dauke "su waye wad'annan ?" "ai Kya basu wurin xama Kafin nayi miki bayani?" Bata ce komae ba ta samu waje ta xauna tana karkad'a kafa ganin hka yasa abduljabbar yace "oya saleem ku xauna " Saleem ya kama nauwara xai xaunar da ita kan kujera da sauri jiddah tace "keee baka da hankali xaka xauna min kan kujera " Tuni nauwara da saleem sun tsorata jikin su ya fara 6ari na tsoro, ran abduljabbar ya 6aci da abin da jiddah tayi musu ya kallo ta cikin tsananin 6acin rai yace "Hey wlh kada na k'ara jin Kinyi musu tsawa i swear xan miki abin da xaki yi nadama" Mtswww ta buga uban tsaki tare da fisgar laptop d'in ta xata bar parlourn ai kuwa yasa hannu ya fusgo ta tare da bata wani kyakkyawan mari cikin tsananin jin takaice yace "ni sa'an kine xaki yi min tsaki, Kinsan kuwa yanda na tsani ayi min tsaki Idan kika k'ara yi min sai na fasa Wannan bakin stupid gal" Ya K'arasa fad'i yana tunkude ta xaman en bori jiddah tayi a k'asa tana kuka sosai na takaicin abin da abduljabbar yayi mata gaban wad'annan yaran, tuni su nauwara da saleem sun tsure ganin yanda yake masifa Zama yayi yana dafe kanshi sai huci yake, jikin nauwara na 6ari murya tana rawa tace "am... am don Allah ka... kayi hak'uri abin da kayi mana mungode Allah ya saka da alkhairi but ka barmu mu tafi Don........ " Bata K'arasa fad'in abin da take so ta fad'a ba abduljabbar ya katse ta ta hanyar buga mata wata uwar tsawa da ba k'aramin firgita nauwara da saleem tayi ba balle jiddah da sauran kiris ta runtuma d'aki da gudu tsabar tsorata............ ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘?? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*?? *~Pg 41~* Cikin tsananin fusata ya fara magana "Idan na k'ara jin Kinyi magana sai na 6a66arar da ke,bana so ina magana ana tsoma min baki " Tsit kake jin parlourn yayi can ya bud'e baki ya kirawo larai er aikin jiddah da sauri ta k'araso wajen tana tsugunna wa sai da ya share kusan 5mint sannan ya bud'e baki yace "na baki 20 mint kije ki gyara bedroom d'in cikin parlourn nan " Da sauri larai tace "angama yalla6ai " Ta mik'e ta shiga cikin bedroom d'in tana aiki da sauri don cika umarnin uban gidan nata Har larai ta gama ta dawo suna xaune babu mai cewa komai, da ta gaya mishi ta gyara sai da yaje ya duba ya tabbatar komai yayi sannan ya fito ya ce "Ki kai su cikin bedroom d'in sannan ki had'a mata ruwan wanka tayi sai ki basu abinci ina son ki dunga kula da ita saboda bata gani " Jiki na rawa larai tace "toh" saboda yanda fuskar nan tashi take a tur6e ne ta taimaka wa nauwara ta mik'e sannan ta rik'e ta har sun juya ya dakatar da su ta hanyar sake wa larai gargad'i "ina son ki kula dasu sosai wlh Idan na same ki da bakya mai da hankali wajen abin da na saki xan kore ki " "toh yalla6ai Insha Allah xan kiyaye" D'aga kafad'a yayi alamar ko a jikin shi bai dameshi ba taja su nauwara xuwa cikin d'akin Mai da hankalin shi yayi kan jiddah wadda ta saki baki tana binshi da kallo kamar ba abduljabbar d'in ta ba ji yanda yake bada umarnin kula dasu kamar wasu en uwan shi na jini maganar da yayi ita ta dawo da ita hayyacin ta ya fara da cewa "gasu nan basai nace ki kula dasu ba ko ki k'untata musu ba kin san ni dai bana iya d'aukan rainin hankali " Yana gama fad'in hka ya tashi ya nufi upstairs ya bar jiddah cike da tunanin maganar don ta kasa gane abin da yake nufi can jimawa kamar wadda aka tsunkula da xaburo tana cewa kuttt wlh baxan yarda na xauna da wad'annan talakawan yaran ba agidan nan (hmm da dai bamu san asalin balbela ba sai muce...... readers sai ku K'arasa lol) Tabbb Hka kawai ya jajibo mana mutane gida cikin sauri ta suri wayar ta number umma ta kirawo tana jin ta d'aga ta fashe da kuka tuni umma ta rikice tana tambayar ta lafia, cikin shashshak'ar kuka tace "ba abduljabbar bane ya kawo mana wasu yara gida ba, ni dai Gaskia umma kiyi mishi magana wlh baxan xauna dasu a gidan nan ba " Shiru umma tayi ita kanta ta fara jin haushin jiddah amman da tayi wani tunani yasa tace "kiyi hak'uri jiddah wad'annan yaran da kika gani taimakon su xai yi tsintar su............ nan umma ta bata labarin da abduljabbar ya basu game dasu Sannan ta d'ora da cewa ni naga yaran wlh abin a tausaya musu ne Idan kuka rik'e su Allah ne kad'ai yasan ladan da xaku samu" Tun da umma ta fara magana jin Bata goyi bayan ta ba a wannan time d'in yasa ta cika tayi fam da ita kamar ta fashe bata k'ara jin Mai xata ce ba ta yanke kiran xube wa tayi akan bed sai masifa take nan ta kirawo farida k'awar ta ta ladafta mata abin da yake faruwa nan kuwa tayi mata hud'ubar kan kada ta yadda ta tada masifa kawai ita ba ta yarda ba... Ranar yini tayi tana bala'i ita kad'ai don ba wanda ya kula ta Washe gari da safe abduljabbar ya wuce abuja saboda tarin aikin da yake gaban shi ko takan jiddah bai bi ba Tun da ya tsallake ya tafi jiddah ta shiga yiwa su nauwara rashin mutunci ta ko'ina don ko larai sai tayi k'wana wajen 3 bata shiga d'akin da suke ba saboda tsabar rashin mutuncin Jidda da bala'in ta sai dai idan ta samu lokacin ta tafi aiki sai ta shiga ta kula dasu Ganin hka larai tana satar jiki ta shiga yasa ta koma sanya wa d'akin key ta sanya a jaka tatafi dashi aiki sai ta dawo xata bud'e su wahala Kala Kala take d'and'ana musu ba k'arami ba kuwa don hka kawai take jin tsanar nauwara kamar ta shak'e ta ta mutu, gaba d'aya sai suka koma kamar da sun bi sun rame sosai saboda wahalar da take gana musu Hka rayuwa ta cigaba da tafiya don abduljabbar sai da yayi 3 month Kafin ya waiwayi gida saboda ayyukan dake gaban shi, hkan ba k'aramin yiwa jiddah dad'i yayi ba saboda ta samu damar axabtar dasu son ranta Kamar yau ranar sunday da yammaci jiddah lokacin en rashin mutuncin ne akan ta fiye da ko yaushe tasa larai ta fito dasu nauwara xuwa falo sai da ta k'are musu kallo up nd down sannan ta shek'e da dariyar mugunta ganin yanda duk suka yi wujiga wujiga dasu Kafin ta bud'e baki tace "matsiya ta yau xaku bar gidan nan don na gaji da ganin ku wallahi na tsane ku, don hka larai oya fitar min su daga cikin gidan nan yanxu yanxu " Cikin matuk'ar kad'uwa larai tace "kiyi hak'uri hajia don Allah ki barsu ina tsoron fushin yalla6ai " Wata muguwar harara ta watsa mata cikin tsawa tace "keee larai wlh ki shiga taitayin Ki ina magana Kina musa min toh wlh xan iya korar ki kema Idan baki aikata abin da na saki ba" A tsorace ta kamo sandar nauwara ta fara yi mata jagora saleem yana binsu a baya ita nauwara ko a jikin ta saboda gwara lokacin da suke bara sunfi jin dad'in rayuwar su fiye da nan Wannan wahalar ta isa hka ko ina suka je sai tsana da tsangwama Allah ya isa tsakanin mu dake uncle sai Allah ya saka mana duk rashin Imaninka ne da kwadayin dukiyar da ba taka ba ya janyo mana shiga wahalar rayuwar nan.... Da hka larai ta fitar dasu da gidan sun d'an yi tafiya Kad'an sannan taja ta tsaya cikin tsananin tausayin su tace "Kuyi hak'uri nauwara hka halin ta yake sam bata girmama *D'AN ADAM* (littafin rufaida Omar) musamman talaka nima hak'uri nake da ita Allah ya taimaka muku a duk inda kuka shiga " Ta xira hannu ta kunce xanin ta tare da d'auko wata 200 ta bawa saleem sannan ta cigaba da cewa "ga Wannan kud'in ko ruwa kwasha kiyi hak'uri " Murmishin yak'e tayi tace "ba komai larai Mun gode matuk'a da yanda kika rik'e amanar shi wajen kula damu tsakani da Allah,nasan kema abin ne yafi k'arfin Ki shi yasa sai wata rana ki sani baxan ta6a manta wa da ke ba " Da hka saleem yaja sandar ta sukayi gaba tun tana hango su har suka fita a layin sosai taji tausayin su hawayen da suka xubo a fuskar ta ta goge sannan ta juya ta koma gidan A parlou ta tarar da jiddah sai waya take tana faman kyalkyala dariya tana bawa farida labari ta jefar da kwallon mangoro ta huta da k'uda ranar yini tayi wasai da ita sai farinciki take hankalin ta kwance ????☘☘???? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*?? *~Pg 42~* Tafiya kawai suke duk inda suka samu jefa kafar su suke,har suka k'araso kan wani babban titi saleem yaja ta xasu tsallaka Ko tsaya wa duba wa bai yi ba yasa kai Sun xo dai dai tsakiyar titin wata mota ta taho da gudu sai da taxo daf dasu aka ja wani uban birki wanda ya tsorata saleem da nauwara suka xube a k'asa cikin matuk'ar tsoro A nutse ya fito daga motar yana sanye da army uniform d'in kallon su kawai ya tsaya yi cike da tsantsar 6acin rai tun daga nesa ya shaidasu kuma yasan ba wanda xai kore su sai jiddah, dakyar ya iya bud'e baki yayi magana saboda 6acin rai "saleem taimaka mata ku shigo motar " Abin da ya iya cewa kenan gaban nauwara ne ya fad'i tabbb yanxu gidan nan xamu koma matar shi tana axabtar damu ai har gwara hindatu akan jiddah Cikin dakiya tace "no ba sai mun koma gidan ka ba hakan ma mungode " Da ace tana gani da Idanunta da taga irin hararar da abduljabbar ya watsa mata cikin tsawa yace "keee wace da xaki hanani yin abin da nayi niyya" Ita dai nauwarah shiru tayi tana jin shi ganin bata da niyyar tashi yasa shi K'arasa wa inda take hannun shi yasa ya d'ago ta cak ya nufi motar shi yayin da nauwara tsoro ya kamata baya xaunar da ita sannan ya shiga motar bayan saleem shima ya shiga ba wanda ya k'ara magana a cikin su har ya k'araso gidan umma Bai k'ara yi mata magana ba ya sake d'aukar ta bai dire ta ba sai a parlourn umma kan kujera ya xaunar da ita sannan ya kirawo umma cikin mamaki take kallon su don ta shaidasu "lafia abdul? " Shiru yayi mata don shi bai ma san me xai ce mata ba ana hka Abba ya shigo falon shima tambayar abduljabbar d'in yake cikin 6acin rai yace "Abba, umma ina neman alfarma a wajen ku don Allah ku rik'e min wad'annan amana, gasu nan a hanya na gansu kuma na tabbatar jiddah ce ta kore su daga gidan" Murmishi abba yayi yace "Ah Haba my boy kada ka damu Insha Allah xamu rik'e maka su tsakani da Allah " Umma ta sauke nannauyar ajiyar xuciya tace"Allah ya taya mu rik'o " "Ameeen " abba ya amsa tashi yayi suka fita da Abba yana tausar shi kan Yayi hak'uri ganin ranshi ya 6aci sosai Sha'anin wasu matan sai hak'uri kada ya kula ta, shi dai abduljabbar jin shi kawai yake don Allah Allah yake ya je gida Ai kuwa yana shiga gidan tun daga falo yake k'walla wa jiddah Kira, dummmm gaban ta ya fad'i jin muryar wanda bata ta6a xaton dawowar shi kusa ba tuni jikin ta ya hau 6ari na tsoro ta da d'a lafewa a d'aki taki amsa kiran hakan ba k'aramin sake tunxura shi yayi ba cikin sassarfa ya hau upstairs ya nufi ⌐part d'in ta Duka d'aya Yayi wa kofar ta bud'e hakan ba k'aramin k'ara kid'ima jiddah yayi ba bai yi wata wata ba ya fisgo ta da karfi har ta buge kanta da faffad'en kirjin shi tace washhh tare da dafe kan nata hannu yasa murd'e hannun ta da karfi ta k'walla k'ara cikin kuka ta fara rokan "abduljabbar don Allah ka bari da xafi fah, toh wai menayi maka daga dawowar ka?? " Xuba mata idon shi yayi wanda suka yi matuk'ar ja saboda 6acin rai "ohhh bakisan me kika yi ba,bari na gani ko xaki tuna da kanki " Nan ya cigaba da murd'e mata hannu da jan gashin kanta axaba tayi axaba jiddah batasan lokacin da fad'a mishi ita ta Kori su nauwara ba cikin kuka ta cigaba da cewa "don Allah abdul kayi hak'uri baxan sake ba I'm so sorry pls" Cika ta yayi tare da tura ta k'um ta bige da katakon gado wani wahalalen ihu ta saki da muryar ta dashashshiya wanda kuka yasa ta dashe ficewa yayi daga d'akin ya bar jiddah cike da tsantsar tsanar su nauwara a xuciyar sai dai kuma taji dad'i tun da ta kore su daga gidan ta,dakyar ta iya tashi ta shiga toilet wanka tayi sannan ta fito ta shirya ko make up bata tsaya yi ba ta xari key d'in mota da wayar ta fice wa tayi daga gidan idanun ta sun kumbura saboda kuka........ 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 _Sadaukar wa ce gare ki auntyn mu (Aunty mamy ) nagode da yanda kike k'aunar littafin nan, ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike_😘 *~Pg 43~* Yana fita daga falon umma, cikin tausayin su umma ta K'arasa wajen nauwara ta dafa mata kafad'a sannan tace "kada ki damu nauwara Insha Allah Kunxo inda xa'a rik'e ku tsakani da Allah, amman xan so naji takaitaccen tarihinki? " Tun da ta fara magana nauwara taji k'aunar wannan matar ya kamata tana addu'a a xuciyar ta Allah yasa *K'ARSHEN WAHALAr* su ne yaxo K'arshe wata sassayan ajiyar xuciya ta saki batai k'asa a gwiwa ba nan ta ladafta wa umma labarin su Kaf, don ji tayi baxa ta iya yi mata k'arya ba kamar yanda tayi wa aminu da saude... Umma batasan lokacin da hawayen tausayin su ya xubo mata ba Lallai Wannan k'anin baban nasu ya cika axxalimi, macuci, mayaudari labarin ba k'aramin ta6a mata xuciya yayi ba "kiyi hak'uri nauwara komai lokaci ne akwai ranar sakamako, tun anan duniya Kafin aje gaban Allah, da ixinin Allah Kunxo inda xa'a share muku hawaye ni na d'auke ki a matsayin diyata ke da saleem " Wani dad'i ne ya kama nauwara har hawayen farinciki ya xubo mata tama kasa cewa umma komai don murna, hannu umma tasa ta goge mata hawaye tace "mene na kuka kuma ?" "umma ba dole nayi kukan farinciki na samu mahaifiya bayan ammi na, ngde sosai umma Allah ya saka miki da mafificin alkhairi " "shiii ya isa hka godiyar nauwara " Murmishi tayi wanda rabon ta da tayi shi tun xamanin suna rayuwa tare da iyayen ta da en uwan ta, "toh umma yi hak'uri na dai na, sai dai xan tayi miki addu'a yanda kika taimake mu ke ma Allah ya taimaka miki akan komai na go........... " Da sauri ta dafe bakin ta bata K'arasa fad'i ba tace "ohhh umma yi hak'uri na mance " Dariya sosai ta bawa umma hannun ta tasa ta rik'e kumatun ta duk biyun tace "ba komai 'yata sai ki kiyaye gaba" Gaba d'aya suka sa dariya kamar wad'anda suka dad'e da haduwa sosai umma take jin k'aunar yaran a xuciyar ta Nan ta taimaka wa nauwara ta tashi tayi mata jagora xuwa d'akin FA'iza sai da shigar da ita toilet sannan ta fito xuwa down stairs anan ta kai saleem shima nashi bedroom d'in tace "kayi wanka d'ana saleem sannan idan ka gama sai ka fito falo, nan ka d'auke shi tamkar gidan Kune ka saki jikin ka" Rungume ta yayi yana cewa "toh umma ina ganin ki kamar ammi na? " Murmishi tayi ta dafa mishi kanshi tace "Yawwa my boy ina son ka dunga ganina kamar ammin ka ,duk abin da kake so ka tambaye ni kamar yanda kake tambayar ammi da " "toh umma thank u so much " Daga hka ya cikata ya shiga toilet umma ta bishi da kallo fuskar ta d'auke da Murmishin jin dad'i Koma wa d'akin FA'iza tayi inda ta tarar nauwara ta fito daga wanka tana tafiya da sauri umma ta K'arasa ta rik'e ta ganin sauran Kad'an ta bige da wardrobe "har kin fito kenan ?" "Ehhh umma" Gefen gadon ta xaunar da ita tare da Mik'o mata mai ta shafa sannan ta bud'e wardrobe d'in FA'iza ta d'auko mata wata atamfa riga da siket d'inkin da gani sabuwa ce tare da d'auko mata sababbin underwears sai da ta damk'a mata su a hannu sannan ta fita daga d'akin don ta bata damar shirya wa a nutse, xanyi magana da abdul ya kamata a nema mata magani makanta bata da dad'i balle ga matashiyar yarinya k'arama Bayan ta tabbatar ta gama shirya wa ta sake koma wa dakin ta tarar ta gama shirya wa tsab turare ta d'auko ta fesa mata sannan ta kamo hannun ta suka fito parlour nan suka tarar da saleem a xaune kallon cartoon yake a mbc 3 ya saki jikin shi kamar d'an gida ko dan anbashi damar hkan ne amman ae sauran gidajen da suka xauna ba'a basu damar hkan ba har gwanda gidan saude Yana ganin nauwara ta tashi da sauri ya rungume ta dariya suka cikin murna yace "aunty nauwara cartoon nake kallo" "Ah haba d'an k'anina" "da gaske nake ko umma?" Ya fad'a cikin tabbatar da hkan dariya umma tayi sannan tace "da gaske yake mana, kema Insha Allah xaki samu lafia Ki dunga gani kamar kowa" Murmishi nauwara ta iya tare da yiwa umma da d'anta addu'a fatan alkhairi sun gama yi musu komai a rayuwa Kan dining table umma ta xaunar da nauwara saleem ma ya xauna da kanta tayi serving d'in su ta damk'a wa nauwara spoon a hannun ta sannan tace "ku saki jikin ku, kuci abinci idan bai isa ba gashi nan ina xuwa " Tana gama fad'in hka ta juya ta tafi ta bar su nauwara suna cin abinci tunani nauwara ta fara da yanda umma ta kar6e su babu tsangwama ko kyamatar su sai ma dad'a jansu a jikin ta da take toh ai daman na Allah basa k'are wa a duniya nauwar 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 *~Pg 44~* 8 na dare suna xaune a parlour FA'iza ta shigo falon agajiye ta xube kan kujera tare da fad'in "washhh umma na gaji wlh " Harara umma ta watsa mata sannan tace "Yayi miki kyau FA'iza sai yanxu kika ga damar dawowa? " Marairaice fuska tayi tace "umma wallahi duk laifin aunty kausar ne ta xaunar da ni " Sai lokacin ta hangi nauwara da saleem cikin alamar tambaya tace "su waye wad'annan umma? " Murmishi umman tayi kafin ta bata amsa da "k'annan kine daman Kece Mai mitar duk su kausar sun tafi sun barki a gida to ga en uwa nan" Wani ihu tayi tare da bugu tsalle har tana tsorata umma dasu nauwara ta rungume umma cikin tsananin farinciki tace "Allah umma da gaske???" Cikin dariyar yanda FA'iza take murna tace "k'warai kuwa " "umma naje mu gaisa da su? " Ta fad'a tana B'uye fuskar ta a jikin umman "Ohh ni 'Yasu ke da en uwan ki je ki mana" Duk abin da suke nauwara tana jin su da kunnen ta Murmishi kawai take faman yi cike da kaunar FA'iza da iyalan gidan gaba d'aya Ohh ni nauwara Allah ya bani lafiyar idanuna don naga wad'annan bayin Allahn da suka taimaka min Da sauri FA'iza ta washe baki jin abin da umma tace kai tsaye inda nauwara take ta nufa tana xuwa ta mik'a mata hannun ta don su gaisa sai taga bata Mik'o mata nata hannun ba umma da taga hka sai tace "FA'iza ai bata gani da idanun ta, batasan kin miko hannun ki ba " Lokaci d'aya jikin FA'iza yayi sanyi cikin tausayin nauwara ta kamo hannun tasa a nata sannan tace "sannu sis nice to meet you, What is your name???" Da Murmishi akan fuskar ta tace "Nauwarah sa'eed haruna ga little bross d'ina saleem " "wow nyc name" "thank u " Nauwara ta fad'i FA'iza cikin jin dad'i tace "You're welcome" Hannun ta rik'e tace "tashi mu tafi d'akina akwai labari" Mik'e wa tsaye tayi fa'iza tana rik'e da hannun suka nufi upstairs "Muna cikin hira da er tawa shine kika d'auke min ita "Cewar umma da sauri fa'iza ta juyo cikin marairaicewa tace "yi hak'uri umma hira xamu yi ki barmin ita pls" "Shikenan na baki aron ta don naga yanxu dare yayi ne " Cikin dariyar jin dad'i fa'iza tace "thank u so much my umma" Daga hka suka wuce d'akin fa'iza ko 5 mint da shiga basu yi ba abduljabbar ya shigo da sallama da gudu saleem yaje ya rungume shi yana yi mishi oyoyo "saleem ya kk, dafatan xaman gidan namu yayi maka dad'i ?" "uncle wlh umma tana da kirki sosai ina son ta kamar ammi na" D'an murmishi yayi Kafin yace "good " Zama yayi kan kujera yana gaida umma bayan sun gama gaisa wa yake mik'a mata ledar hannun shi yana cewa "gobe monday Insha Allah saleem xai fara xuwa skul d'in su fa'iza " Fara'ar umma ta k'aru tana cewa "Masha Allah hakan yayi kyau Allah ya k'ara bud'i " "Ameeen " Umma ta bud'e ledar sababbin uniforms ne har guda Biyu da school bag sai takalmi dasu safa sai tarkacen books na skul, "saleem ga kayan ka na makaranta gobe xaka fara xuwa " Tsallen murna ya fara yana cewa "nagode uncle da umma " "toh kwashe kake su d'aki ka kwanta domin ka tashi gobe da wuri " Cikin tsananin murna saleem ya d'auki kayan nashi d'akin shi ya nufa xuciyar shi cike da tarin farinciki Da kallo umma da abduljabbar suka bisa daga bisani abduljabbar yace "umma gobe xan shige abuja naxo muyi sallama don baxan samu damar shigo wa ta nan ba" "to Shikenan, daman ina son yin magana da kai akan nauwara " Nutsuwa yayi tare da mayar da wayar shi cikin aljihun jeans d'in shi ya ce "ina sauraren ki umma" "nan da two weeks xan je ganin doctor a birnin jiddah na k'asar saudia why not mu tafi da nauwara akan matsalar idon ta ko Allah xai taimaka a dace" Wani irin dad'i abduljabbar yaji acikin xuciyar shi daman yana da wannan burin sai gashi umma ta fad'i hka don hka yace "okay umma Wannan ba matsala " "Amman saleem xai xauna a gida shi da fa'iza saboda skul" Jijjiga kai yayi alamar toh kawai sannan ya mik'e tsaye yace "umma sai munyi waya na wuce " "Allah ya kiyaye hanya " "Ameeen " Daga hka ya fice daga gidan, umma ma d'akin ta ta shige don yau girkin aunty sadiya ne Lokacin da ya shiga gida jiddah na xaune a parlour tana faman chatting tana ganin shi ta mik'e tsaye da sauri Kafin ta K'arasa wajen shi tuni ya fara hawa stairs don hka ta bishi da sauri har bedroom d'in shi Kafin ya ankara ta fad'o jikin shi tana kukan kissa tare da bashi hak'uri akan laifin da tayi mishi Hannu yasa ya tunkud'a ta waje tare da sa key ajikin kofar don Har yanxu bai huce daga abin da tayi mishi ba, ita kuwa jiddah mik'e wa tayi tsaye tare da ta6e baki ta wuce bedroom d'in ta don gobe akwai aiki... 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *Written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 _wannan page d'in sadaukar wa ce gare ki k'awata Fatima (ummu abdul) ngde da yanda kike k'aunar littafin nan Allah ya bar xumunci ya raya mana Abdul da sauran kannen shi masu xuwa, Ameeen_❤😘 *~Pg 45~* B'angaren fa'iza da nauwara kuwa Sun dad'e basu yi bacci ba saboda hirar da suka tsaya yi nauwara ta saki jiki sosai suna hira da fa'iza kamar sun shekara da sanin juna daga K'arshe bacci 6arawo ne ya sace su Washe gari da safe fa'iza ta shirya cikin shirin tafiya skul tare suka fito da nauwara tana yi mata jagora har down stairs suna sakkowa saleem ya fito daga d'akin shi cikin shirin tafiya skul shima yayi kyau sosai Fa'iza tana ganin shi ta saki baki cikin sauri tace "saleem yaushe aka saka ka a skul d'in mu" Saleem cikin jin dad'i yace "aunty fa'iza jiya uncle da dare ya kawo min uniform ya sanya ni a makarantar ku " Baxan iya kwatanta muku dad'in da fa'iza taji ba balle nauwara kuma har da hawayen farinciki addu'a sosai ta dunga yiwa bayin Allahn nan Suna kammala breakfast saleem da fa'iza suka tafi skul yayin da aka bar nauwara ita d'aya xaune a falo yau gaba d'aya cike da farin ciki take har umma ta sauko k'asa "aa nauwara ke kad'ai xaune a parlour duk sun gudu skul sun barki " "Ehh umma ji nake kamar na bisu " Cikin tausayin ta umma tace "kwantar da hankalin ki nauwara Insha Allah komai xai xo ya shige " Har k'asa ta sakko ta gaida umma ta amsa mata cikin fara'a sannan tace "dafatan Kinyi breakfast? " "Ehh munyi dasu fa'iza da saleem " "okay yayi kyau hkan, Bari nima naje nayi " Daga hka umma ta K'arasa wajen dinning table, bayan ta kammala breakfast d'in ta dawo cikin parlourn xama tayi kusa da nauwara ta kamo hannun ta fara magana kamar hka "nauwara jiya da dare bayan kunshiga d'aki abduljabbar yaxo munyi magana nan da two weeks xan je jiddah domin ganin doctor shine muka yanke magana xamu tafi dake a duba miki idanun ki " Sakin baki kawai nauwara tayi gaba d'aya ta rasa me xata cewa umma tsabar farinciki sai kawai ta fashe da kukan farinciki "Haba nauwara kukan me xaka yi kuma kawai Ki gode wa Allah don shi yayi silar had'uwar mu " Har yanxu dai ta kasa cewa komae ganin haka yasa umma ta rungume ta tare da bubbuga bayanta cikin sigar lallashi tace "nace Ki shiru nauwara ai Kinsan baxa mu barki da haka ba alhalin muna da kud'in da xamu taimake ki, kisani fa mun dauke ku tamkar su fa'iza " Cikin muryar kuka tace "umma bani da kalaman da xan gode muku sai dai addu'a da xan dunga yi muku har K'arshen rayuwa ta Allah kada ka nufe ni da yi muku butulci akan abin da kuka yi mana " "kada ki damu nauwara fatan mu shine Allah ya baki lafia " "Ameeen umma na gode hak'ik'a ke uwa ce ta gari " Murmishi kawai umma tayi nan ta fara bawa nauwara labari masu dad'i da hka har abba da aunty sadiya suka shigo falon bayan an gama gaisa wa umma ta sanar da abba da aunty sadiya maganar xuwa jiddah sosai sunji dad'in hkan tare da addu'ar Allah yasa a dace Daga hka Abba ya fita ya barsu umma suna hira kamar ba kishiyoyi ba ba ruwan su da irin jahilcin kishin nan tsabtattacen kishi suke irin na matar k'warai da suka shud'e Lokacin da fa'iza da saleem suka dawo a skul umma take basu labari tsallen murna suka dunga yi cike da farin ciki sannan suka rungume nauwara har suna kok'arin yar da ita sai da umma tayi musu magana tukunna suka cikata ****** Alhaji salisu tun lokacin da yaran shi suka kawo mishi labarin sun kad'e su nauwara sun mutu dad'i ne ya kama su nan suka sallami yaran da mak'udan kud'ad'e tare da ce musu Indai wani aikin ya taso xasu nemo su saboda sun yarda da iya aikin su Nan ya tsunduma da cin dukiyar marayu baji ba gani cikin kankanin lokaci ya xama gawurtaccen attajiri K'arshe ya ginawa innar shi katafaren gida ta dawo da xama ciki ya bar baffan shi da innar marigayi Alhj sa'eed acikin tsohon gidan su ko da baffa yace xai yi mishi magana inna tace a barshi kawai Indai dukiya ce anan duniya xai barta yaje yayi taci don hka kawai suka xuba mishi ido A bangaren Alhj lawan shana kuwa nan ya fara nuna wa Alhj salisu hassada akan yanda yanxu ya fishi kud'i bana wasa ba, sannan yak'i ya sakar musu yanda suke so shi da er shi bayan da taimakon su ne har ya cimma burin shi tun da dasu aka sha wahalar komai don hka suka fara shirya mishi gadar xare...... Tuni ya mulmule ya narka wata uwar k'iba sharholiyar shi kawai yake sha kamar baxa'a mutu ba aje a tarar da abin da aka aikata ba, hankalin kwance don ya mance da wani yayan shi Alhj sa'eed balle su nauwara burin shi d'aya ne ya cika mallakar dukiyar d'an uwan shi kuma ya samu sauran abu d'aya da har yanxu yake masifar wahalar shi ..... ****** Acikin Sati biyun nan komai ya kammala na tafiyar su nauwara da umma xuwa k'asar jiddah duk wani abu an gama sai jiran ranar tafiya kawai Ranar Tuesday da misalin karfe 7 na dare jirgin su umma ya tashi daga airport d'in malam aminu kano xuwa k'asar jiddah, en rakiya aunty sadiya da fa'iza sai saleem suka dawo gida cike da kewar umma da nauwara ttare da yi musu addu'ar Allah ya sauke lafia kuma Allah yasa a dace da abin da akaje nema........... 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~Pg 46~* Nauwara sun sauka a k'asar jiddah lafia a wani hadadden hotel sukayi masauki Mai 2 bedrooms da falo d'aya ,sai da suka huta washe gari suka fara xiyartar asibitin da umma take ganin doctor Bayan sun gama da bincikar umma aka dawo kan nauwara nan fa suka fara dogon bincike akan nauwara wanda daga K'arshe suka rik'e nauwara akan xasu kwantar da ita Cikin k'wanakin nan suka tsanan ta bincike har suka yi nasarar gano matsalar wata jijiyace wadda take taimaka wa wajen gani ta samu matsala da dole sai anyi mata aiki tukunna, bayan sun yiwa umma bayani ta kirawo abduljabbar take fad'a mishi abin da suka ce Haka kuwa akayi sun yiwa nauwara aikin ido amman sai nan da wasu en k'wanaki xasu bud'e mata idon suka cigaba da kula da ita tare da bata magunguna da suka kamata Nauwara ba k'aramin kyau ta k'ara a en k'wanakin nan ba tayi fari ta k'ara k'iba Kad'an kamar ba mai jinya ba, wanda ya san ta da ba Lallai ya gane ta ba don gaba d'aya ta canja kamar wadda aka k'arawa kyau ita kanta umma ido take xuba mata a xuciyar ta tana fad'in Masha Allah daman wahala ce ta mayar da ita hka *ABUJA* Kwance yake a kan 3siter ya rungume pillow a kirjin shi ya xurfafa a tunani sosai na yanda xuciyar shi take kok'arin kar6ar wani sak'o wanda sam bai san lokacin da ya shiga cikin xuciyar shi ba har yana kok'arin mamaye mishi xuciya A kullum sai yayi tunanin yarinyar nan yafi sau a kirga a rana ban da dare wanda kusan k'wana yake tunanin ta a xuciyar shi baya iya samun ishsshen bacci da farko ya d'au ka tausayi ne sai tausayin ya rikid'e ya koma soyayya Soyayyar ma irin xaxxafar nan ai abin kunya ne yaje ya furtawa K'aramar yarinyar so ai wannan xubda girma ne K'arshe raina shi xatayi (a tunanin abduljabbar fah), don hka xai cigaba da addu'ar Allah ya cire mishi son ta... Hannun shi ya sa a gashin kanshi yana yamutsa shi Mtsww yaja tsaki tare da tashi ya xauna remote ya d'auka canja tasha ya fara har yaxo kan tashar mbc 2 suna film d'in rush hour kallon film d'in ya fara yi ko xai d'auke mishi hankali daga tunanin da yake damun xuciyar shi......... ******** Daren washe gari umma da duk wani masoyin nauwara addu'a yake mata don gobe xa'a xata fara bud'e idon ta, suna yi mata addu'ar Allah ya sa an dace Washe gari sai wajen 12 na rana doctor ya shigo d'akin da aka kwantar da nauwara umma ce a bayan shi sai wasu nurse guda 2 tana kwance ta amsa sallamar su nan ya umarce ta da ta tashi xaune bayan ta xauna yayi wasu en dube dube sannan yayi addu'a a hankali ya fara kunce farin abin da aka rufe idon nauwara dashi Umma sai addu'a take acikin xuciyar ta gaban ta yana fad'uwa,a hankali ya gama warware wa sannan yace "open your eyes " A hankali ta d'an bud'e idon ta sai taga wani mugun haske da sauri ta runtse idon wannan abin ya faru ne cikin seconds d'aya xuwa biyu cikin xakuwa umma tace "nauwara bud'e idon ki mana" Jin muryar umma yasa ta fara bud'e idon a hankali har ta gama bud'e su gaba d'aya akan umma ta xube idanun ta tayi tsiro tana kallon ta kawai can kuma sai ta fashe da wani irin kuka na farin ciki ne Ko akasin hka ohho ganin hka yasa umma ta rungume ta ita ma tana goge kwallar idon ta cikin tausayin nauwara "umma ina gani wlh ai Kece umma na? " Cikin dariyar farinciki tace "Alhmdllh Masha Allah, Allah mun gode ma, k'warai kuwa nauwara nice umman ki" Dariya doctor da nurses d'in nan suka yi sai da ya dad'a duba nauwara sosai sannan suka taya ta murna tare da cewa nan da k'wanaki uku xai sallame su Abduljabbar ne farkon wanda umma ta fara yiwa albishir nauwara ta samu lafia tana gani anyi nasarar aiki, ba k'aramin dad'i yaje ba kawai sai yace "umma ina xuwa xan kirawo ki " Yana katse kiran sujjadar godiya ga Allah yayi sannan ya koma ya xauna xuciyar shi fal farin ciki A b'angaren umma kuwa tana jin yace hka murmishi kawai tayi ta kirawo Abba da aunty sadiya ta sanar dasu Sannan ta kirawo fa'iza Haba fa'iza najin hka ta buga uban tsalle tare da ihu wanda yasa umma sai da ta cire wayar ta a kunnen ta don tana baraxanar kashe mata dodan kunne Nauwara na xaune a gefe sai murmishi take yi sake Kira fa'iza tayi umma tana ganin hka ta mik'a wa nauwara wayar sun dad'e suna hira da fa'iza tare da saleem cikin tsantsar farin ciki Haka suka cigaba da kula da nauwara har ta warke garau sannan suka basu sallama hotel d'in da suke xaune suka koma bayan sun huta suka shige makkah don gabatar da umarah Nauwara tayi wa iyayen ta addu'a sosai na Allah ya jik'an abban ta tare da bayyana ammin ta don tana ji ajikin ta ammi tana raye bata mutu ba, sosai umma ta bata kudi don siyan abubuwan da take so komai Kala 2 take siya ita da fa'iza irin su gowns, abayat, mayafai dasu flat shoes sai arabian perfumes masu matuk'ar k'amshi sannan ta siya saleem nashi, ta juya xata tafi wajen ammi ta hango wani agogo mai matuk'ar kyau hannu tasa ta d'auke shi tana dad'a ganin shi na maxa ne sai dai yayi bala'in birge ta duba price d'in shi tayi taga kud'in shi da yawa har ta yanke tunanin mayar da wasu kayan ta d'auke shi taji umma tana cewa "Yayi miki kyau ne nauwara?" Kunya ce ta kamata tana d'an sunk'e kai tace "Laaa umma da yaya abduljabbar xan siyawa tsaraba Naga kud'in da yawa bari na mayar da wasu kayan sai na siya" Cikin murmishi tace "aa d'auki kawai ba sai kin mayar da kayan ku ba " Nan ta d'auke shi har da k'ara mishi da turare, abba ma turare ta siya mishi sai aunty sadiya ita ma turare da abayat, duk a kud'in da umma ta bata ta siya Idan ka d'ebe agogon da ta siyawa abduljabbar shi kad'ai wanda umma ta biya kud'in Bayan wad'annan sai da ta siya musu gold sark'a da d'an kunne har da warwaro guda biyu sai sark'ar kafa irin siririyar nan da ake d'aura wa Kala Biyu iri daya ta siya na fa'iza da nauwara Gaba d'aya ta rasa da wacce kalma xata gode wa umma banda dumbin dukiyar da suka kashe wajen nema mata lafia har da bata kud'i tayi tsaraba sannan bayan wannan har da siya mata tsadadden sark'a na gold kud'in su d'aya da na fa'iza, bayan sun dawo hotel d'in sosai nauwara ta dunga yiwa umma godia har sai da ta fara yi mata fad'a kan wannan godiyar Ya isa haka Sai da suka k'ara Sati d'aya suka huta sosai sannan suka fara shirye shiryen taho wa gida ,ranar juma'a misalin karfe 12:30 na rana jirgin su nauwara da suka hau yayi landing a filin malam aminu kano a hankali mutanen ciki suka fara fito wa daga cikin jirgin ummace a gaba bayan ta kuma ............ 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 *~Pg 47~* A nutse take taka mattatakal jirgin jikin ta sanye da wata gown kalar milk tayi rolling da veil light green tayi kyau sosai, ware ido kawai take tana kallon ko'ina ji tayi an rungumo ta ta baya da sauri ta juya sai suka had'a ido da fa'iza da saleem tuni suka fara tsallen murna umma da aunty sadiya suna yi musu dariya dakyar fa'iza ta cikata suka gaisa da aunty sadiya ta amsa tana taya ta murnar samun lafiyar ta Daga hka suka shiga mota sai gida nauwara ta baxa idanuwa sai kalle kalle take daman Hka kanon take da kyau,gaskia garin yayi mata kyau har suka K'arasa gida Aunty sadiya tayi parking sannan suka firfito tana k'are wa gidan kyau yayi bala'in birgeta, direct part d'in umma suka nufa gaba d'aya an gyara ko'ina sai k'amshin turaren wuta da air freshener yake Ganin lokacin sallah yayi yasa kowa ya tashi domin yin sallah, fa'iza da nauwara bedroom suka shiga "tun da ke alwala kad'ai xakiyi ki fara shiga don ni sai nayi wanka " Nauwara ta fad'i hkan tana kallon fa'iza murmishi tayi sannan tace "tohh Shikenan sis " Toilet ta shige ta bar nauwara tana kwance kan bed tana k'are wa d'akin kallo an shirya shi yayi kyau, tana xaune fa'iza ta fito sannan ta shiga toilet wanka ta fara yi sannan ta d'aura alwala ta fito, gaban dressing mirror ta tsaya tana gyara jikin ta (ina fatan mai karatu bai mance da nauwara ba wajen son gayu) Bayan ta gama k'walliyar ta hannu tasa ta d'auko wata swiss atampha wanda fa'iza ta ajiye mata kan bed daga nin su sabbabi ne riga da xani ne sun amshe ta kayan sosai ta murxa d'aurin d'an kwalin ya xauna a kanta sosai sai ta fashe jikin ta da turare tana cikin xura d'an kunne fa'iza ta shigo d'akin ware ido tayi sannan tace "wow sis kinga yanda kika had'u kuwa? " "koh" Nauwara ta fad'i tana murmishi "ah da gaske man yarinya kin had'u " "toh ngde " "muje falo umma tana jira xamuyi lunch " Rik'o hannun ta fa'iza tayi suna tafiya suna hira har suka sakko k'asa wajen dinning table suka nufa inda umma take xaune ita ma tayi wanka taci gayun ta baka ce ta haifi su aunty asma'u ba Da fara'a take kallon yaran nata cikin jin dad'i tace " 'yata Kinyi kyau " Murmishi tayi sannan tace "ngde umma" Har fa'iza ta d'auko spoon xata fara serving d'in su da sauri nauwara ta warce tana mata irin hararar wasan nan "Lallai ma yarinyar nan Kina tunanin xaki kwashe ladan ke kad'ai Kinyi girki sannan xaki wani xo kiyi serving d'in mu" Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a wa fa'iza baki, dariya suka tuntsire da ita umma tana cewa "da kin barta ta K'arasa aikin ta, kin huta " "umma xan iya fah" "toh 'yata" Nan ta fara xubawa umma farar shinkafa ce da miyar kaji sai costlow, sai snacks samosa da scott eggs sai coconut drink, bayan ta gama xubawa umma nata ta fara xuba wa fa'iza da gangan ta cika mata plate har yana tudu ta tura mata gaban ta tana cewa "oya maxa ki cinye na k'aro miki" "kuttt Lallai ma yarinyar nan kin rainani da yawa ni kad'ai xan cinye wannan tarin abinci " Tana magana tana hararar nauwara dariya abin ya bawa umma yayin da nauwara take danne dariyar ta ta don kada ta fito gwalo tayi mata "ai wallahi sai dai muci don ni Banga inda xan kai wannan abincin ba" "ah cikin ki xaki kaishi man " Nauwara ta fad'a tana yiwa fa'iza dariyar k'eta can kuma sai tasa hannu ta dauki spoon tace "hmm daman tsokanar ki nake sis ai tare xamu ci " Umma dai bata kula su ba abincin ta take ci kawai suma suka nutsu suna cin abinci Bayan sun kammala suka dawo falo nan aunty sadiya ma ta shigo part d'in umma nan hira suke yi sosai cikin farinciki da annushuwa har abba ya dawo gidan, ya taya nauwara murnar samun lafiyar ta Da dare bayan sallahr isha'e nauwara da fa'iza sai saleem suna xaune a bedroom d'in umma suna duba tsarabar da sukayi fa'iza sai tsallen murna take ita da saleem yayin da umma da nauwara suke yi mata dariya ...... Tun around 7 na dare ya shigo kano amman gidan shi ya nufa duk yanda xuciyar shi take d'okin ganin yarinyar hka ya danne shi kanshi wani lokacin abin yana bashi mamaki yanda soyayyar yarinyar tayi mishi mugun kamu a wannan daren bacci 6arawo ne ya sace shi......... 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 _this page dedicated to my friend Aunty deejah_😜😘 *~Pg 48~* Washe gari da safe ta kama ranar saturday ne, bayan sun kammala breakfast ne nauwara tace "umma bari naje mu gaisa da aunty sadiya na Bata tsarabar ta" "okay hkan yayi dai dai" Cewar umma, sannan ta juyo da kallon ta kan fa'iza da saleem da suke yin game a waya tace "kuxo ku rakani " nok'e kafad'a saleem yayi alamar baxa shi ba ita kuwa fa'iza cewa tayi "tabbb baxan je ba game nake" "xan rama ne duk kinci bashi yara" "Ehh anji dai " Fa'iza tace tana yi mata dariya had'e da gwalo kwafa tayi sannan ta fisgi ledar da tsarabar aunty take ta nufi hanyar fita daga falon ko gabanta ba ta gani Washh nauwara ta fad'i tana dafe goshin ta sakamakon karo da tayi da mutum a tsorace ta d'ago kanta karaf suka had'a ido da abduljabbar a lokaci d'aya gaban su yayi wani irin wawan fad'uwa, Bata ta6a ganin shi ba a fili sai a picture da jiya fa'iza ta nuna mishi don hka da sauri ta tsugunna k'asa tana cewa "don Allah yi hak'uri yaya abduljabbar ban kula bane" Tun da ta fara magana ya xuba mata ido cike da wani irin yanayi a tattare dashi tayi masifar yi mishi kyau tana sanye da black d'in wando sai riga red ta kai mata kusan gwiwar ta tayi rolling d'in kanta da black d'in veil gaba d'aya ya kasa wani motion sai da yaji ta sake magana tana gaida shi sannan ya basar ya amsa da lafia kawai tashi tayi xata fice har tayi taku biyu ya dakatar da ita ta hanyar cewa "keee ina xaki da hka?" "wajen aunty sadiya xan je " Nauwara ta bashi amsa k'ara d'aure fuska yayi tare da cewa "da hakan xakije har wurin aunty sadiya ga mai gadi da sauran masu aiki maxa suna kallon ki toh oya jeki, ki canja kaya " D'an tsaya wa tayi cikin mamakin Wannan fad'an da yake yi mata tsawa ya daka mata yana cewa "Ko bakiji abin da na fad'a miki ba? " Ai Kafin ya rufe bakin shi tuni ta bar wajen d'aki ta koma tana sauke ajiyar xuciya tare da cewa "shi wannan ya abduljabbar d'in daman Hka yake tabb xa'a sha fama dashi " wani less ta d'auko ash colour da touch d'in pink a jiki d'inkin riga da siket sunyi mata kyau fiye da wad'anda ta cire yanxu Lokacin da ta k'araso falo yana xaune kan kujera 1siter suna hira da umma cikin mamaki umma take kallon ta tace "Har kin dawo? " "uhm uhm mantuwa nayi na dawo" ta fad'a tana kallon abduljabbar da ya mai da hankalin shi kan tv, wow gaskia wannan guy d'in akwai kyau jebe shi kamar balarabe maganar da umma tayi ita ta dawo da ita hayyacin ta "kiyi sauri ki dawo yanxu xan aike ku gidan kausar? " Da sauri ta fice tana cewa umma "toh, bayan sun gaisa da aunty sadiya sun d'an ta6a hira sannan ta bata tsarabar ta na turare da abayat tayi godiya sannan tayi mata sallama ta fice Lokacin da ta dawo bata tarar da abduljabbar ba amman taso sake ganin beauty face d'in shi a gurguje suka shirya driver ya kaisu gidan aunty kausar itama ta kar6i nauwara a hannu bibbiyu sun sha hirar su sai bayan mangarib driver yaxo ya dauke su suka rabu cikin kewar junan su To Hka rayuwa ta cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa a yayin da aka sama wa nauwara skul d'in su fa'iza a ss 2 suka ajiye ta bayan dogon naxari da gwada ta da sukayi ta cancanta da shiga ss 2,ajin su d'aya da fa'iza hakan ba k'aramin dad'i yayi musu ba Sun mayar da hankalin su sosai wajen karatu har makarantar islamia aka sanya su karatu suke sosai babu wasa gashi basu fiye fita ba sai da dalili rayuwa suke yi mai dad'i cike da kwanciyar hankali.......... ```Aishat A muh'd```😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 _Ngde sosae masoya na wajen turo min sak'onni Kuna yi min addu'ar samun sauk'i, toh Alhmdllh na samu lafia, ngde sosae Allah ya bar xumunci ameeen_❤😘 *~Pg 49~* *AFTER 1 YEAR* A cikin Wannan shekarar abubuwa da yawa sun faru na samun cigaba sosae a fannin rayuwar su nauwara Wata kyakkyawar yarinya ce er kimanin 18 years na hango ta fito daga mota duk uniform d'in yasha maker da irin hodar Kala Kala duk anyi kaca kaca da uniform d'in da gudu tayi cikin gida tana tsalle tsalle yayin da wata mai irin shekarun ta ta biyo ta a baya da gudu suka shige parlourn gidan Rungume wata mata naga sunyi gaba d'aya sai kyalkyala dariya suke yi Kafin d'ayar ta xaro wayar ta k'irar iPhone 6 ta shiga d'aukan su selfie sai da tayi wajen 10 pictures sannan umma tayi magana cikin gajiya wa tace "ke fa'iza wannan pictures d'in ya isa hka yarinya gaba d'aya bata da aiki sai pictures " Cikin shagwa6a wadda aka kirawo da fa'iza tace "hmm umma tsabar farinciki ne fah, a yau muka yi graduation party na candy umma ai gwara mu yi murna" Nauwara cikin dariya tace "wlh umma gaba d'aya chargen wayar ta ya k'are saboda selfie kowa ta gani sai tace sai sunyi pic " Hararar nauwara tayi sannan tace "ehhh d'in Naga ajiye wa xanyi don tarihi wani baxa ka k'ara ganin shi ba har abada " Sai lokacin umma hankalin ta yayi kan uniforms d'in jikin su "Hmmm Lallai yaran nan hka kukayi da uniforms d'in naku ?" "Laaa umma dama baki gani ba wlh tsabar murnace " Cewar fa'iza "Allah ya shirya, Allah ya taimaka yasa a samu result mai kyau " "Ameeeeeeen umman muuu" Suka had'a baki suka fad'a cikin tsananin farinciki ana hka aunty sadiya ta shigo cikin murna suka rungume ta ita ma kafin daga bisani fa'iza ita ma ta fara yi musu pictures har sai da aunty sadiya ta gaji tace "Ya isa hka fa'iza ni na gaji " Dariya suka tuntsire da ita umma tana cewa "kema kin gaji kenan ai Idan suka fara Wannan selfie d'in basa gajiya wa " Umma ta cigaba da cewa "toh maxa aje ayi wanka a cire uniform d'in da duk ya fita hayyacin shi,axo ayi lunch" "toh ummaaaaaaa " Da gudu suka haye upstairs yayin da umma da aunty sadiya suka bisu da kallon farin ciki Bayan sun yi wanka da sallah nan aka tsaya kyakyalen jiki wannan yana wane wannan har suka gama suka shirya cikin wata swiss atampha kalar blue sunyi kyau sosai daman sun dinka ta don xuwan wannan ranar sai dai nauwara tafi kyau Masha Allah abin da umma da aunty sadiya suka fad'i ganin yanda yaran suka yi matuk'ar kyau, suna gama yin lunch suka shige gidan aunty kausar ****** Xaune yake a katafaren office d'in shi Idan dai hka lissafin sa yake toh yau nauwara da fa'iza suka ka kammala sec sch, ya soma gajiya da wannan dakon son da yake mata ya kamata ya samu mafita a kullum yaje kano ya dawo ganin ta ba k'aramin dad'a rikitashi yake ba abin ba k'aramin bashi mamaki yake ba tun yana danne wa yana k'arya ta abin har ya dawo yana gasgata hkan wayar shi ya d'auko number d'in umma ya kirawo sun d'au wajen mintuna 10 suna magana Sannan ya kashe wayar duk jikin shi ya mutu a kasalance yake jin su gashi yau ko er hayaniyar su bai ji ta waya ba Dakyar ya iya tashi ya tafi gida ko abincin dare bai iya ci ba ya kwanta cike da tunanin nauwarah a xuciyar shi yana Mai addu'ar Allah ya sa rabon shi ******** A yau candyn su nauwara da Sati d'aya suka tarkata inasu inasu sukayi gidan aunty asma'u abuja kenan suka bar umma da saleem Sunje sun tarar da ita da tsohon ciki tashi dakyar xama dakyar don hka taji dad'in xuwan emmatan umma duk da tana da en aiki amman wani abun sai na ka Da wani yammaci aunty asma'u ta aike su siyayya a sahad store daman kiris suke jira don hka cikin d'oki suka shirya driver ya d'auke su sai sahad store lokacin da suka fito a mota sai kallo ya koma kansu don ba k'aramin kyau suka yi ba har sun d'an diririce saboda kallon da ake musu dakyar suka lala6o nutsuwa suka shiga cikin store d'in Suna cikin siyayya wani hadadden guy yace "Hello Babs" D'ago kai suka yi a tare suna kallon shi ya cigaban da cewa "I'm fysal " Had'a ido suka yi fa'iza da nauwara gira nauwara ta d'aga mata yayin da fa'iza ta kashe mata ido d'aya lokaci d'aya suka saki murmishi cikin iyayi fa'iza tace "kana buk'atar wani abun" Shima cikin murmishi yace "mene sunan wannan" Ya nuna nauwara dake gefe a tsaye "oh sunan ta nauwara " "nice name ke fah?" "fa'iza " "OK fa'iza ko xaki magana da sister d'in ki ta ban 2 mints " "okay Wannan ba matsala ne ba " Ta K'arasa kusa da nauwara tana yi mata magana k'asa k'asa suna d'an murmishi A nutsu ya sako kafar shi cikin store d'in yana sanye da black d'in jeans da t-shirt yellow mai dogon hannu ya sanya takalmi bak'i mai ratsin yellow a jiki da black d'in glass yayi mugun kyau ba Kad'an ba sai tashin k'amshin turare yake Mai dad'i emmatan wajen gaba d'aya sun raja'a da ganin kyakkyawan guy d'in nan har da maxa en uwan shi ya birge su B'angaren wurin turarruka ya nufa dummm gaban shi ya fad'i ganin wasu masu kama da nauwara da fa'iza suna tsaye da wani guy sai faman murmishi suke yi a tafiyar shi irin ta sadaukan maxa ya d'an K'arasa kusa dasu ko babu tantama wad'annan su fa'iza ne me ya kawo su abuja, me suka xo yi?, a matuk'ar fusace ya k'arasa wajen idanun shi sunyi jajur dasu saboda tsanani 6acin rai......... Toh fah su nauwara da fa'iza ko mai xai faru dasu *Aishat A muh'd*😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~Pg 50~* A gaban su ya tsaya sai huci yake hannu ya fidda ya xuba ma nauwara mari sannan ya juyo kan fa'iza ya bata mari lokaci d'aya suka saki wani irin ihu tare da d'ago kai don ganin wanda ya mare su Wayyo Allah sauran Kad'an su saki fitsari a tsaye tsabar tsorata ganin ya abduljabbar tsaye kansu ,jikin su sai rawa yake sun kasa cewa komae cikin fusata fyasal yace "me suka yi maka kake dukan su?" Wani d'an iskan kallo abduljabbar ya yi mishi tuni ya shiga taitayin shi saboda tsabar kwarjinin da yayi mishi bai iya cewa komai ba hannun su nauwara da fa'iza ya kama suka fice a motar shi ya watsa su har suna gwarewa da kansu wani ihun suka k'ara saki sai kuka suke sun tsorata da ganin yanayin abduljabbar Driven da ya kawo su fa'iza ya sallame shi ya koma gida xai kawo su nan kuwa ya juya ya tafi cikin takun tafiyar shi ta kasaita ya shigo motar kifa kanshi yayi kan steering motar wani axabbaben kishi ne yake damun shi cikin tsawa yace "Wlh ku rufe min baki ko yanxu ku ci duka" Ba shiri suka had'iye kukan sai na xuci suke a hankali ya fara driven har suka k'araso gidan aunty asma'u duk wani motsin ta yana kallon ta, ta madubin motar yana hango shatin hannun shi a fuskar ta sannan ga fuskar tayi ja abin ka da farin fata Suna shiga gidan sum sum sukayi xa su shige d'aki ya daka musu tsawa "uban waye yace ku tafi oya kuxo Kuyi tsallen kwad'o " Had'a ido suka yi fa'iza da nauwara cikin matuk'ar kad'uwa wata tsawar ya dad'a daka musu ba shiri suka fara cikin rawar jiki hawaye majina duk sun had'e a fuskar su ga gumi da suke nauwara tafi ma iya tsallen kwad'on saboda bata da k'iba fa'iza tafi ta jiki Kad'an, abin ya bashi dariya ganin sun xube kamar wasu sumammu danne dariyar tashi yayi sannan yace "wa yace ku tsaya, oya ku cigaba ba sai Kinyi 50 minutes Kuna yi" Cikin rawar murya suka fara bashi hak'uri "Don girman Allah Yah abduljabbar kayi hak'uri baxa mu k'ara ba" k'ara d'aure fuska yayi tare da cewa "lokacin da xaku xo abuja kun sanar da ni shine har wani tsaya wa kuke da samari ko wai Kun girma koh??? " Girgixa kai suka yi cikin kuka suka ce "baxa mu k'ara ba kayi hak'uri pls" Nan suka dunga magiya suna bashi hak'uri har aunty asma'u ta sakko downstairs cikin mamaki take cewa "ah yau abduljabbar ne a gidan nawa tabbb yau wacce rana xa'a yi mana ruwa da k'ank'ara " Harara ya dalla mata sai lokacin ta ankara dasu nauwara da fa'iza tsugunne a gaban shi tace "lafia kuke kuwa, wannan kukan fa" "ritsa su nayi a sahad store suna hira da saurayi " "a'a abdul ai ni Aiken su nayi siyayya sai dai idan tsayar dasu yayi " Aunty asma'u ta fad'i hkan "hmm ni ai surutu naga suna yi alamar sun dad'e da tsaya wa, don hka Kuyi maxa ku tattara kayan ku Kano xan mai da ku tunda bakwa jin magana" "Haba abdul d'in umma d'an lelan Abba kayi hak'uri ka barsu suna taimaka min " "sai dai da sharad'in baxa su sake fita ba" Cikin sauri suna had'a baki suka ce "ehhh Yah abduljabbar mun yarda " Harara ya watsa musu da sauri suka mik'e d'akin da aka basu suka shige kan bed suka xube sae mayar da numfashi suke "daman Hka Yah abduljabbar yake fa'iza?" Nauwara ta tambayi fa'iza "kuttt ai ya mafi hka wlh" fa'iza ta bata amsa daga hka fa'iza ta shige toilet tana cewa "Bari naje na gasa jikina don sai nayi ruwan xafi wlh" Nauwara batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba hararar ta fa'iza tayi ta shige toilet ita ma dariyar ta fara a cikin toilet da ta dunga tuno yanda suke tsallen kwad'on Pillow ta janyo rungume shi a jikin ta tayi kyakkyawar fuskar Yah abduljabbar take hango wa yana yi musu masifa murmishi kawai take tare da shafa fuskar ta inda ya mare ta xumbur ta mik'e tsaye jin xafin dukan da fa'iza tayi mata a fusace tace "dalla malama me nayi miki kika duke ni? " "toh nayi miki magana kin yi shiru sai faman tunani kike kina xabga murmishi kamar wadda take tunanin masoyin ta" Zaro ido tayi tare da dafa Kirjin ta cikin fad'uwar gaba tace "hba Kinsan dai har yanxu ba mu fara xance ba ni fah duk samarin da suke nuna suna sona sam basa birge ni " "Har da fyasal? " "Har shi d'in " Nauwara ta bata amsa "Allah ya shirya ki " Cewar fa'iza "Ameeen Idan da gaske kike "ta fad'a tana shige wa toilet Tun daga lokacin basu k'ara fita ko'ina ba duk kuwa da cin burin yawo a abuja hka suka hak'ura har aunty asma'u ta haihu baby girl aka samu taci sunan ta khadijah,sai da aunty asma'u tayi arba'in tukunna suka tarkata su kayo kano gaba d'aya basu k'ara sanya abduljabbar a idanun su ba Cikin Wannan lokacin results d'in su nauwara ya fito sunyi kok'ari sosai ba 6ata lokaci suka samu addimission a BUK nan suka fara karatun su hankali kwance Iyayi da felek'e ya k'aru sai dai sam basa shiririta abin da yakai su suke duk da hka abduljabbar sai da ya baxa masu kula da motsin su a skul batare da sun sani ba, mota sabuwa dal Abba ya siya musu ta xuwa skul a ka koya musu mota da kansu suke xuwa makaranta su dawo hka rayuwa ta cigaba da tafiya.............. *Aishat A muh'd*😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~Pg 51~* Kwance take kan bed k'wana 2 nan bata jin dad'i sam sai dai yawan bacci ko office taje bata iya tsinana uban komai ga tashin xuciya ta rasa mai yake damun ta asibiti kawai xata je ita ta gaji da wannan yanayin Mtsww taja tsaki tare da tashi toilet ta shiga wanka tayi ta fito ta shirya cikin wani less cotton milk colour da touch d'in brown a jiki Falo ta fito sai Yatsina fuska take tana shirin xama taji k'amshin abincin da kuku yake dafa wa hba tuni jiki ya hautsine nan ta tsugunna tana kakarin amai, da sallama ya shigo parlourn ganin jiddah tana kakarin amai yasa shi xuwa inda take da sauri yana d'ago ta "me yake damun ki? " Cikin tsananin gala6aita tace "my darling ka kaini hospital ban da lafia" "OK tashi muje " Shi ya taimaka mata ta sanya takalmi da mayafi hannun ta ya rik'e suka fito basu xarce ko'ina ba sai asibiti nan likita yayi mata en tambayoyi ta bashi amsa daga K'arshe ya had'a ta da nurse don yin test din fitsari Bayan an gama nurse ta kawo wa doctor result d'in nan ya fara karanta wa fuskar shi d'auke da murmishi hannu ya mik'a wa abduljabbar yana cewa "congrats captain matan ka tana d'auke da ciki na tsawon 2 month's" Cikin matuk'ar farin ciki abduljabbar yace "da gaske doctor? " Cikin tabbatar wa yace "wlh da gaske nake captain, dole sai tayi hak'uri da yanda xata fuskanci yanayin laulayi sannan akwai wasu magunguna da xan rubuta mata Xasu taimaka mata sosai akan yanayin,sai kuma nan da kamar 2 month's xata dunga xuwa awo Allah ya raba lafia ina taya ka murna" "thank u so much doctor " Gaba d'aya ya rasa mai xai yi saboda tsabar murna, Hmmm a b'angaren jiddah kuwa ji tayi kamar ta mutu don bak'in ciki sam baxa ta haifi cikin nan ba wlh dole na d'au mataki duk ranta a 6ace Duk da bashi da fara'a sosai amman yau fuskar shi tafi ta ko yaushe fara'a sai kissama yanda babyn nashi xai kasance yake yanda bai kula ta ba itama Hka ta share shi don wani bala'in haushin shi take ji fuskar nan ko fara'a babu yana gama parking ta bud'e murfin motar ta fito kai tsaye d'akin ta ta wuce mayafin jikin ta ta cillar tare da xube wa kan gado sai huci take kamar wadda ta had'iye kunama Tafi wajen minti 15 a xaune ta rasa mafita don ita gaskia bata shirya haihu wa yanxu ba wani d'an tunani tayi xumbur ta mik'e tare da janyo wayar ta number farida ta kirawo ringing 2 tayi ta d'auka cikin matuk'ar tashi hankali ta kora mata bayanin ciki ne da ita kuma bata son ta haihu yanxu saboda kada jikin ta ya canja gashi xai kawo mata cikas wajen aikin ta don sam baxa ta iya had'a raino da aiki ba "yanxu ki ban shawara me Xanyi ya fita?" Jiddah ta tambayi farida "cikin watan shi nawa Idan har bai girma ba xai fita ba matsala ammam Idan ya girma fitar shi da matsala? " Cewar farida cikin k'aguwa jiddah tace "Yayi 2 month's " Dariya farida tasa tana cewa "ahh k'awalli xai fita, akwai wani magani da xaki sha tsab xai xube" "toh yaushe xaki kawo min don wlh hankalina ba'a kwance yake ba? " "kwantar da hankali yanxu xanje na kar6o miki Kinsan da xafi xafi ake dukan karfe" Sai lokacin taji hankalin ta ya kwanta dariya tayi tace "Yawwa k'awata hka nake son ki ina xuba ido, daga hka suka ajiye waya ta xube kan gado farin ciki cike a xuciyar ta Shi kuwa abduljabbar cikin murna ya kirawo umma yake sanar da ita wannan daddad'an labari ba k'aramin farin ciki tayi ba su aunty sadiya da abdulkareem aunty asma'u duk sai da ya kirawo ya fad'a musu sun taya shi murna sosai jinshi yake kamar bashi ba wai shine xai samu d'an kanshi wayyo dad'i hka ya yini cikin farinciki duk da wani na b'angaren xuciyar shi yana mamakin yanda Ko Kad'an jiddah bata nuna jin dad'in ta ba ta6e bakin shi yayi ita ta sani Misalin karfe 5 na yamma farida taxo gidan cikin jin dad'i Jiddah ta rungume tare da janta xuwa bedroom d'in ta kan gado suka xube cikin xakuwa Jiddah tace "Yah Allah yasa an dace? " "an dace man sai dai ai kyabari na huta tukunna" Cewar farida dariya Jiddah tayi tana cewa "tun da andace ai Shikenan " Tashi tayi ta bud'e k'aramin frige di'n dake d'akin ta d'auko mata lemo da ruwa ta kawo mata sannan tace "Bari nasa akawo miki abinci? " "no barshi a kashe nake wlh" "ok" Sai da suka sha hirar su sannan ta bata maganin tare da fad'a mata yanda xata sha ta cigaba da cewa "Kina shan wannan toh fah xai xube, sai ki kiyaye gaba " "hba ae bama sai kin fad'a ba ngde sosae farida " "ah ba godia a tsakanin mu" Da hka ta yafa mayafin ta tare da d'aukar handbag di'n ta tayi gaba, Ko minti 5 batayi da fita ba jiddah ta 6allo maganin nan ta kora da ruwa hankalin ta kwance tabi lafiyar gado nan da nan bacci ya d'auke ta Ta kusan minti 30 tana bacci Kafin wani axabbaben ciwon mara ta tashe ta ba shiri ta mik'e tsaye sosai marar ta take ciwo tun tana daure wa har takai ta fara xirgaxirga a d'akin tana yarfe hannu cikin matuk'ar axabar ciwo, a hankali taji wani abu yana bin kafar ta da sauri ta duba ido ta xaro waje me xata gani jini ne yake binta kamar ruwa nan ta fara jin wani jiri da K'arfi ta bud'e baki ta k'walla wa abduljabbar kira nan ta xube a sume Yana xaune a parlour yana kallon mbc 2, xuciyar shi cike da tunanin nauwarah wani b'angaren kuma yana son yaje ya ga jiddah yasan ma ko yaje 6ata mishi rai xata yi yana cikin hka yaji jiddah ta k'walla mishi kira xumbur yayi ya mik'e saboda daga jin kiran kasan ba na lafia bane a 360 ya isa dakin idon shi ya hango jiddah a kwance k'asa a sume ba alamar numfashi a tattare da ita ga jini yana xuba a jikin ta........... ```Aishat A muh'd```😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty }*😘 *~Pg 52~* A rud'e ya k'arasa wajen yana Jijjiga ta yana kiran sunan ta Amman ina shiru kake ji da sauri ya kinkime ko suka fito waje mota ya bud'e ya kwantar da ita sannan ya shiga ya bawa motar key a guje ya fice daga gidan addu'a yake axuciyar shi Allah yasa babyn shi bai samu matsala ba Cikin gaggawa nurse's suka d'auko ta xuwa b'angaren emergency room don taimakon gaggawa take buk'ata lokacin da doctor xai shiga d'akin abduljabbar ya kamo hannun shi yana cewa "doctor ka taimaka min kada baby na ya samu matsala pls" Dafa kafad'ar shi yayi cikin tausayin shi yace "kada ka damu captain xanyi kok'arin Insha Allah ka cigaba da addu'a " Yana gama fad'in hkan ya shige d'akin, abduljabbar ya koma ya xauna tare da dafe kanshi abin tausayi Duk iya kok'arin da doctor yayi kada cikin ya xube amman kash ya riga ya fice nan suka yi mata wankin ciki bayan ta farfad'o daga suman tayi sunyi mata allurar bacci don ta huta don ba k'aramin wahala tasha ba aka sanya mata drip na ruwa dana jini don tayi bleeding sosai Yana shigo wa office d'in abduljabbar ya mik'e tsaye yana cewa "Ya doctor dafatan baby na yana nan?" Cikin tsananin tausayin shi doctor yace "kwantar da hankalin ka captain kayi hak'uri da abin da xan fad'a maka " D'an kallon abduljabbar yayi ya ga gaba d'aya shi yake sauraro don hka ya cigaba da cewa "I'm so sorry captain cikin da ke jikin matar ka ya xube" "what! ?" Abduljabbar ya fad'a da karfi cikin tausayin shi doctor ya cigaba da cewa "duk iya kok'arin mu da muka yi don kada ya xube amman sai da ya fita" "toh mene mussababin fitar shi?" Cewar abduljabbar shiru doctor yayi Kafin daga bisani yace "A binciken da muka yi ya nuna mana maganin xubar da ciki tasha Mai karfi har ya d'an ta6a mahaifarta wanda kafin ta samu wani cikin sai an.......... " "is okay doctor " Abduljabbar ya katse doctor ya cigaba da cewa "thank u for everything" Daga hka ya fice daga office d'in cikin wani matuk'ar tsantsar 6acin rai wanda ban ta6a ganin abduljabbar a ciki ba fuskar shi tayi ja saboda 6acin rai motar shi ya fad'a yana fita daga asibitin hanyar airport ya nufa yana xuwa yayi sa'a akwai jirgin da xai tashi adai dai time d'in don hka ticket ya siya sai da xai shiga jirgin ya kirawo abdulkareem yaxo ya d'auki motar a airport bai jira ya fad'i wani abun ba ya shige cikin jirgin har suka isa abuja jirgi yayi landing a k'asa ya kirawo Joseph yaxo ya d'auke shi a mota Yana parking ya fito direct toilet ya shige ya cire kayan jikin shi shower ya sakarwa kanshi ruwan sanyi yana xuba a jikin shi yayi da xuciyar take wani irin turiri na 6acin rai why! why!! jiddah da xaki yi min asarar d'ana jinina xaki xubar min kamar wani d'an shege bango ya kai wa naushi cikin fusata kamar shine yayi mishi laifin nan fa ya dunga dukan bango har hannun shi ya fara jini sai da yaji kiran sallahr isha'e sannan ya fito ko masallaci bai iya xuwa ba agida yayi sallahr shi ya janyo alqur'an ya fara karatu a hankali yaji xuciyar shi tana sanyi ****** *KANO* Jiddah bata farka ba sai wajen 9 na safe ba kowa a d'akin sai wata nurse ita ta taimaka mata tayi wanka sannan doctor ya shigo ya Kalli nurse di'n yana cewa "d'an bani minti 5 xanyi magana da ita" "okay sir! " Ta fadi hka tare da tashi ta fice kallon shi ya dawo dashi kan jiddah ya fara da cewa "madam me ya kake da shan maganin xubar da ciki? " Harara Jiddah ta galla mishi sannan tace "ina ruwan ka dani kawai ka tsaya a matsayin ka malam? " Girgixa kai kawai yayi sannan yace "sakamakon maganin da kika sha toh ya ta6a miki mahaifar ki ke da haihuwa sai ikon Allah kuma" A fusace tace "Ehh naji sai me kafa dame ni da surutu " Kallon ta yake cike da mamaki ita bata son haihuwa aka haife ta ai 'ya'ya rahma ne ya juya kawai ya fice xuciyar shi cike da tsananin tausayin abduljabbar bai yi dacen mata sam Allah ya shirya masu irin Wannan halin Bammmm aka banko kofar room d'in da jiddah da take har sai da ta tsorata ta dauka abduljabbar ne sai had'a ido suka yi da umma fa'iza da nauwara suna bayan ta abin da ya bata mamaki ya kuma kid'ima ta ganin umma tana hawaye Kafin ta ankara taji saukar wani lafiyayyen mari a fuskar ta dukka 6arin biyun ba k'aramin firgita jiddah ta yi ba ganin umma ce ta mare ta cikin fad'a umma ta fara cewa "tur da ke jiddah da mai irin halin ki abin da xaki saka min dashi kenan ko kije kiyi tayi duniya ce ta ishe ki riga da wando " Tana gama fad'in hka ta juya ta fice a fusace d'ago kai tayi taga fa'iza da nauwara suna hararar ta 6acin rai kwance a fuskar su daganin yanda idon su yayi ja kasan sun sha kuka cikin tsawa tace "uban me kuke min aka xaku fita ko sai naci uban ku? " "wallahi baki ji dad'in ki ba " Cewar fa'iza yayin da nauwara cike da tsanar jiddah taja tsaki tace "Allah ya shirya ki wllh tun wuri ki tuba ga Allah tun......... " A guje suka fice daga d'akin Kafin ta K'arasa fad'i ganin jiddah ta yunk'uro xata tashi "shegu en iskan yara da ku tsaya mana " Cewar jiddah tana kok'arin koma wa ta xauna taji an rufe ta da duka ta ko'ina a tsorace ta d'ago kanta sai ganin Maman ta tayi tana kuka tana dukan ta "kin cucu kanki jiddah kinci amana kin butulcewa er uwata wadda ta rik'e ki tsakani da Allah shine da rashin mutunci kije ki xubar da ciki toh wallahi ki sani Idan abduljabbar ya sake ki sai dai ki nemi wasu iyayen ba mu ba tunda haifar ki kawai muka yi amman koman ki yaya fatyma ce ta mayar dake hka " nan fah mama ta dunga dukan jiddah tana xagin ta dakyar nurse's suka kwace ta mama ta fice daga asibitin akabar jiddah cikin wani mawuyacin hali Ko wa ya juya mata baya Wayyo Allahn ta acikin Wannan yinin tayi nadama yafi sau dubu na abin da ta aikata yanxu idan abduljabbar ya sake ni ya xanyi da dumbin son da nake mishi (Hmmm jiddah sai yanxu kika tuna da son da kike mishi ba Kya son had'a jini dashi Wannan ai shine da nasani k'eya ce inji hausawa) *Aishat A muh'd*😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 _wannan page d'in naki ne k'awata *khadijah niger (neena cool)* Marubuciyar littafin *deejah* Allah ya k'ara basirah, Allah ya bar xumunci ameeen_❤😘 *~Pg 53~* Cikin k'wanaki 2 Jiddah tayi nadama yafi sau ba iyaka gata a kwance gadon asibiti ba wani d'an uwan ta da yaxo jinyar ta sai farida k'awar ta duk tabi ta rame sai da doctor ya tabbatar mata gaf take da kamuwa da hawanjini Sannan ta sasauta wa kanta satin ta d'aya aka sallame ta ta dawo gida Kullum da tunanin wanne hukunci abduljabbar xai yanke mata amman shiru bai xo ba tun tana fargaba har ta watsar da abin ta koma bakin aikin ta Tun da abduljabbar ya tafi bai waiwayi kano ba wajen 3 month's da faruwar abun amman yak'i xuwa sai dai suyi waya da en uwan shi ganin hka yasa abba ya yanke shawarar kiran shi Yana xaune a office yana daddana laptop wayar shi ya fara k'ara ganin sunan abba yasa shi d'auka cikin girmama wa ya gaida shi bayan ya amsa ya d'ora da cewa "abduljabbar ka mance kana da iyalai ka tsallake tsawon wata 3 baka dawo gida ba, naji komai a wajen umman ka jiddah bata kyauta ba taxo har gidan nan ta bamu hak'uri tayi nadamar hkan kuma muna buk'atar ganin ka,ka taushi xuciyar ka kuma kada kace xaka rabu da ita tasan ta *tafka babban kuskure* (littafin rash kardam) kuma ta amshi laifin ta tayi alkawarin baxa ta sake mai mai ta hkan ba" nan abba ya rarrashe sosai sannan daga baya yace yana nan tafe da hka suka yi sallama A hankali take sauko wa daga upstairs tana sanye da wata shadda blue d'inkin riga da siket tasha aiki shaddar light make up tayi ba k'aramin kyau tayi ba sai yanxu ta tashi daga bacci umma fa'iza da saleem sun fita unguwa k'wata k'wata hankalin ta yayi kitchen saboda yunwar da take ji gaisa wa sukayi da er aikin umma Sannan ta fara kok'arin dafa indomie guda d'aya ta tasha vegetables sannan ta soya kwai guda hud'u juye wa tayi a plate ta d'ora Kwan a gefe sannan ta bud'e frige ta d'auko fresh milk ta fito daga kitchen d'in, kasa K'arasa wa dinning table tayi ta xauna acikin falon ta d'ebo abincin xata kai bakin ta suka had'a ido da abduljabbar cikin mamaki ta tsaya kallon shi, duk abin da take tun saukowar ta yake kallon ta cike da so da k'aunar ta, ba k'aramin kyau tayi mishi ba, a b'angaren nauwara ita ma xuba mishi ido tayi yayi masifar k'ara kyau xuciyar ta tana wassafo mata wani abun da sauri ta kawar da wannan tunanin a axuciyar ta kusa da shi taje ta tsugunna tana cewa "Yah abduljabbar sannu da xuwa ina yini? " Maganar da tayi ta dawo dashi hayyacin shi yace "lafia, ina umma? " "uhm sun fita unguwa ne "Cewar nauwara daga hka ta tashi ta dawo kan kujera duk uwar yunwar da take ji sai ya kasance ta kasa sakin jiki taci abincin saboda kunyar shi take ji ahankali ta tsinkayi muryar shi yana cewa "yi sauri ki gama ci ki dafa min wani abun yunwa nake ji " Da sauri tace "toh " Kasa cin abincin tayi sai kawai ta nufi kitchen cikin sauri da K'ware wa ta shiga shirya mishi abinci shinkafa ta dafa mishi da miyar kwai da hanta sai costlow da ta had'a mishi ta shirya a babban tire ta dauka a dinning table ta shirya mishi sannan ta d'auko mishi lemo da ruwa tukunna ta K'araso inda yake xaune yana sarrafa wayar shi tace "angama shirya komai Yah abduljabbar " Sai da ya d'auki en mintuna tukunna ya mik'e wajen dinning table ya nufa ya xauna da sauri ta k'araso tayi serving d'in shi tana gamawa ta bar wajen Bismillah yayi ya fara cin abincin lumshe idon shi yayi saboda jin dad'in girki kai gaskia Idan na samu yarinyar nan naga ma more wa ta had'a duk abin da nake so wajen macen da nake so, abincin nan yaci sosai yaushe rabon da yaci abinci kamar hka har ya mance yana cikin hka umma suka dawo ba k'aramin jin dad'in ganin shi umma tayi ba bakin ta yak'i rufuwa shima kanshi yaji dad'in ganin umman tashi fa'iza tana gaida shi ta wuce d'akin su Kwance ta tarar da nauwara kan bed sai faman chatting take a what's app d'ago kanta cikin murmishi tace "Har Kun dawo, shine kuka gudu kuka barni? " "umma ce ta ce a kyale ki tun da bacci kike"Cewar fa'iza "kinga Yah abduljabbar kuwa yanda ya koma yayi kyau kamar mai rayuwa a kasashen k'ank'ara "fad'in nauwara kenan dariya fa'iza tayi sannan tace "kai nauwara? " "wlh da gaske nake, ai ina mamakin yanda jiddah take 6ata mishi rai duk lokacin da ya sake aure matar tana kyautata mishi wlh ta xama sorry"cewar nauwara, fa'iza ta amshe da cewa "ke dai kyale ta kawai swai sunan Hka wayayyiwa tafi bawa aikin ta mahimmanci akan kula da mijin ta " "Hmmm nauwara tace sannan ta cigaba da cewa "tabbb wlh na samu miji kamar Yah abduljabbar xa'a ga kula da miji ba macen da xai k'ara kallo da sunan auren ta" "ai anyi k'atuwar banxa bata iya komai ba " Dariya suka tuntsire da ita tare da tafawa sannan suka mik'e parlour suka fito suka tarar baya nan har ya tafi nan nauwara tayi wa umma da sannu da dawo wa A hankali wani tunani ya fara darsuwa cikin xuciyar umma wanda ta tabbatar Idan hkan ya kasance xata fi kowa farinciki....... *Aishat A muh'd*😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~Pg 54~* Jiddah fah ta shiga wani hali akan yanda abduljabbar ya d'auke mata wuta baya shiga harkar ta k'wata k'wata ko kallon Inda take baya yi abin ba k'aramin damun ta yake ba karshe sai ta yanke kai k'arar shi wajen umma don hka ana tashi daga office tayi gidan su Abduljabbar Xaune suke a bedroom d'in umma bayan jiddah ta gama kwararo mata bayanin halin da take ciki nan dai umma tayi mata nasiha sosae don hannun ka baya ta6a ri6ewa ka yanke duk da ba k'aramin jin haushin jiddah tayi ba akan xubar da ciki sai dai aikin gama ya gama sai dai a guji gaba Bayan ta gama yi mata nasiha ne umma ta kirawo abduljabbar kan bayan sallahr mangariba tana neman shi yaxo, bai kawo komai a ranshi don hka ya tabbatar mata Insha Allah xai xo suna gama wayar ta Kalli jiddah tace "fita parlour ki xauna wajen en uwan ki, Kafin yaxo " Badan taso ba ta fito parlourn ranta a had'e Don ba k'aramin tsanar nauwara tayi sai dai bata same ta a wajen ba sai fa'iza da saleem suna kallo Ko kallon Inda suke batayi ba xama tayi akan kujera tare da kiran er aikin umma hajja ta k'araso da sauri ta xube a gaban ta cikin girmama wa sai da ta harare ta tare da jan tsaki sannan tace "maltina Mai sanyi xaki kawo" "toh " Ta amsa tana mik'e wa har ta juya taji tace "ji mana" jiyo ta tare da sake tsugunna wa tace "me kuka girka ne? " "ai umma da kanta take girkin su en aiki basa yi mata" Cewar hajja mai aiki "okay ki xubo min Ko mai suka girka yanxu ki kawo min" Tashi tayi ta wuce kitchen cikin en mintuna ta shirya mata abinci ta kawo mata gaban ta sannan ta juya ta tafi, fara cin abincin tayi tare da janyo wayar ta data ta bud'e nan messages suka fara shigo wa tana cin abinci tana faman chatting, fa'iza tana daga gefe tana aika mata da harara wannan matar akwai shegen iyaye kamar wata er shugaban k'asa Mtsww taja d'an tsaki cike da jin haushin jiddah Lokacin da umma ta kirawo shi yana tare da abdulkareem yana fad'a mishi abin da yake cikin xuciyar shi kusan shekara 2 yana fama da son ta shifa ya gaji da wannan abun yana fad'i wa abdulkareem mai xaiyi Idan ba dariya ba sai da yayi san ranshi dakyar ya tsagaita da dariyar saboda ganin ran abduljabbar ya soma 6aci mik'e wa yayi tsaye yace "Don ina fad'a maka matsala ta naxo ka bani shawara shine xaka tasa ni a gaba ka nayi min dariya ngde " Da sauri abdulkareem ya rik'o shi cikin rarrashi yace "calm down captain Idan dariya ta ta6ata maka rai I'm sorry xauna muyi magana wlh naji dad'in wannan maganar sosai " Xama sukayi sannan abdulkareem ya cigaba da cewa "so ni a tawa shawarar kawai ka xaunar da ita ka fayyace mata abin da ke cikin xuciyar ka" Harara captain ya watsa mishi kafin yace "Wannan ai salon raini ne ina fad'a mata xata rainani kasan kuma banason raini" Dariya ya ke son yi amman ya danne ta saboda sanini halin abokin nashi shima hararar tashi irin ta wasa yace "Haba captain wanne raini kuma kasan nauwara bata daga cikin irin yaran nan masu rawar kai a nutsu take ba ruwan ta wlh kawai ka yarda da abin da nace " Gid'a kai kawai captain yayi ba don ya yarda da abin da abdulkareem yace ba shi ai yana ganin xubar da girma ne ya dubi tsakar idon ta ya furta mata kalmar so da hka suka yi sallama abdulkareem yana k'ara bashi k'warin gwiwa Kai tsaye masallaci ya nufa bayan yayi sallahr mangariba sai ya xauna sauraren wa'azi sai da akayi sallahr isha'e sannan ya shiga motar shi kai tsaye gidan su ya nufa hon yayi Mai gadi ya bud'e mishi gate tun Kafin yayi parking idanun shi suka hasko masa ita da taimakon hasken da mamaye farfajiyar gidan kamar rana tana xaune kan farare kujeru tare da wani matashin saurayi suna hira cikin kwanciyar hankali sai faman murmishi nan nata wanda yake matuk'ar so take yi har da er dariyar nan ta ta mai ban sha'awa Wayyo Allah xan so kuga yanda fuskar abduljabbar ta koma nan da nan idanun shi suka kad'a sukayi ja fuskar nan ta gama rine wa da 6acin rai tsantsa jikin shi har wani rawa yake saboda tsabar kishi a fusace ya fito daga motar ya nufi inda suke Yana k'araso wa kafa yasa yayi ball da table d'in dake gaban su wanda yana fad'uwa ya rugurguje lemo da ruwan kai had'e da kofuna suka tarwatse a firgice suka mik'e tsaye nauwara kallon fuskar shi tayi sai da fitsari ya kusan kubce mata irin yanayin da ta ganshi iri d'aya da yanayin da ya ta6a tarfa su a abuja jikin ta 6ari kawai yake Cakumo wuyan rigar guy d'in yayi cikin wata irin tsawa yace "Kaiii Mai kake yi anan uban wa ya baka ixinin shigowa gidan nan?" Guy d'in da ya gama tsorata da abduljabbar cikin rawar murya ya fara magana "ni... ni sau.... saurayin ta ne mun had'u a skul ne kuma auren ta xanyi tsakani da Allah" Cikin 6acin rai yace "toh wa ka tambaya har ya baka ixinin shigowa? " Shiru yayi yana rarraba ido hanyar gudu wa kawai yake nema kuma ya rasa nan captain ya sake daka mishi tsawa cikin rawar jiki ya ce "a gaskia ban nemi ixinin kowa ba na tura a kirawo min ita amman don Allah kayi hak'uri xan turo iyaye na ayi magana wlh da gaske n....... " Kafin ya K'arasa fad'i captain ya watsa mishi mari cike da tsananin kishi sai da guy d'in nan yayi er k'ara saboda xafin marin yana huci yace "daga yau kada na sake ganin ka a gidan nan kuma ko a hanya ka sake tare ta xakayi bayani san sa a kulle ka naga uban da ya tsaya maka irin Kune masu hure wa yara kunne don hka get outttt" Ai bai gama rufe bakin shi ba tuni ya K'arasa motar shi a 360 yaja motar da gudu ya bar gidan baya fatan sake xuwa har abada don ba k'aramin tsorata yayi da captain ba Yana fita daga gidan nauwara ta tattara siket d'inta ta kwasa da gudu cikin gidan karaf suka yi karo da jiddah wadda ta gaji da xaman jiran abduljabbar ta taso xata tafin kallon kallon suka tsaya yi a fusace jiddah ta d'aga hannu xata mari nauwara caraf taji an rik'e hannun nata da sauri ta d'ago kai don ganin wane ya rik'e mata hannu............ *Aishat A muh'd*😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd {Aunty}*😘 *~Pg 55~* Ba k'aramin tsorata jiddah tayi ba ganin abduljabbar ne ya rik'e mata hannu fuskar nan tashi a murtike ba alamar fara'a cillar da hannun nata yayi sannan cikin kakkausar murya yace "daga yau kada ki sake gigin d'aga hannu Kice xaki marin ta " Yana gama fad'in hka yayi shige war shi yayin da jiddah ta rasa mai xata yi saboda tsabar takaici harara ta dalla wa nauwara da fa'iza da suke tsaye kusa da ita abin ya basu dariya don hka suka kyalkyale da dariya tare da tafawa haba ran jiddah idan yayi dubu ya 6aci gashi abdul ya mata warning di'n kada ta ta6a ta don hka a fusace ta koma d'akin umma Suma su nauwara d'akin su suka tafi bayan sun xauna nauwara take kora mata bayanin yanda Yah abduljabbar ya tarfa ta tana xance hba mai fa'iza xata yi idan banda dariya sai da taci dariyar ta ta koshi har nauwara na tana taya ta kafin daga bisani ta nutsu Sannan ta magana "Nifah a yanda na lura Yah abduljabbar son ki yake " Gaban nauwara sai da ya fad'i da taji abin da fa'iza tace cikin tsoro tace "na rok'e ki kada ki sake wannnan wasan pls, don Kinsan Yah abduljabbar ba ajina ne ba" "keee dalla malama waya gaya miki baa ajin ki bane ai wlh Idan ya samu mata kamar ki ya more wlh ina nan ina addu'a Insha Allah sai hasashena ya xama gaskia " "Hmmm kawai nauwara tace don bata da abin cewa kwanciya tayi tare da lumshe idon ta tana tunano abin da ya faru d'axu Bayan ya shiga d'akin umma sun gaisa take bashi baki da yayi hak'uri akan laifin da jiddah tayi mishi tayi nadama sannan tasa jiddah ta bashi hak'uri har d'an kukan ta akan baxata k'ara ba, shi dai ya nuna ya hak'ura ba komai nan ta dunga murna kallon ta yayi a xuciyar shi yace yarinya baki da wayo kiyi min Wannan babban laifin ai da kishiya xan saka miki shine dai dai da abin da kika yi min yana gama wannan tunanin ya saki wani murmishin mugunta ita kuma ganin harda murmishi yasa ta dad'a tabbatar wa ya hak'ura sannan sukayi sallama da umma suna fitowa parlour yace "kije gida inanan xuwa yanxu " Cikin marairaicewa tace "hba sojana baka hak'ura ba? " D'an murmishi yayi Kafin yace "no ba hka bane kawai ina son ganin Abba ne" "toh na jira ka mana? " "kawai ki tafi nace " To ganin lalla6a shi take yasa ta shige ta tafi shi kuma d'akin su fa'iza ya nufa cikin takun shi na kasaita kafa yasa ya tura kofar gaba d'ayan su a tsorace suka jiyo sake firgice wa suka yi ganin shi da sauri suka mik'e tsaye yayin da nauwara ta fara ja da baya cikin tsananin tsoro gabanta sai fad'uwa yake kallon fa'iza kawai yayi ta fahimci abin da yake nufi alamar ta fita daga d'akin ai kuwa a 360 ta fice abinta xuciyar ta cike da tausayin nauwara Sai da ta tokare da bango tukunna ta dakata da ja da bayan da take k'araso wa yayi har inda take ganin ya d'aga hannu sama yasa ta da sauri ta runtse idon ta cikin tsoro gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin marin ta xai yi hawaye ne suka fara xuba a fuskar ta ido ya xuba mata hannun da ya d'aga tana tunanin marin ta xae yi ashe gashin kanta da ya barbaxu a fuskar ta ya hau janye wa yana mayar dashi baya a hankali ta bud'e idon ta suka had'a ido da sauri ta kawar da idanun ta don baxata jure kallon shi ba cikin wata irin voice kamar ba tashi ba yace "bana hana ki kula samari ba? " "Don Allah Yah abduljabbar kayi hak'uri wlh banyi niyyar fita umma tace naje bakyau wulak'anta mutum amma baxan k'ara ba " Cewar nauwara cikin tsoro d'an murmishi yayi wanda yayi matuk'ar k'ara mishi kyau yace "good girl sauran na k'ara gani " Sai faman kallon ta yake ita dai nauwara gaba d'aya a tsure take gashi yabi ya lallu6e ta da girman jikin shi da tsayin shi ba lalle a hange ta ba gashi duk k'amshin turaren shi ya gama cika mata hanci bakin shi yakai dai dai kunnen ta ya rad'a mata Cewar "nauwarahhh! an ta6a gaya miki Kina da kyau? " Tambayar da ta kusan sumar da ita kafafun ta suka fara rawa K'arshe ma sai suke kok'arin yarda ita saboda ba k'wari hannun shi yasa ya rik'o kafad'un ta yace "relax! nauwarah answer me?" Gaba d'aya ta gama rud'e wa shin mafarki take ko ido biyu Yah abduljabbar d'in da tasani shine yake mata magana hka tsawar da taji ya daka mata shi ya sake firgita ta sauran Kad'an fitsarin da take kok'arin rik'e shi ya kusa kubcewa kallon shi tayi ya dad'a hade fuska kamar bashi ba "Kina ji ina ina tambayar ki " Sunkuyar da kanta tayi sannan a hankali ta bud'e baki tace "ehh aunty safah da en skul d'in mu suna fad'a min haka " "Har da maxa koh? " A tsorace ta d'aga kai alamar ehh nan wani kishi ya k'ara kama shi cikin d'aga murya yace "ki bud'e baki kiyi min magana kuma bana son k'arya " Cikin rawar murya tace "ehh har dasu " Idanun shi ne suka rufe da wani irin kishi baisan lokacin da ya murd'e hannun ta ba saboda axaba batasan lokacin da ta k'walla k'ara ba cikin jin xafi K'arar da tayi shi ya shigo da umma d'akin a rud'e turus tayi ganin abduljabbar cikin mamaki tace "lafia abdul, Mai tayi maka? " "umma kamata nayi tana xance a waje" "tohh shine xaka dunga yi mata mugunta irin taku ta sojoji ai ni nace ta fita" "toh umma kawai ba'a binciki halin mutum ba nagari ne ko d'an iska ne kawai sai a tura yara" "ehhh to wannan da gaskiyar ka xa'a gyara amman bana son wannan muguntar " Ta fad'a tana kamo nauwara wadda take kukan axaba duk 'yan yatsun hannun ta sunyi ja d'ago kai tayi ta kalle shi suna had'a ido ya sakar mata harara da sauri ta sunkuyar da kanta ya fice daga d'akin nan umma ta rarrashe ta tayi shiru Sannan ta fita a d'akin Toilet ta shiga tayi wanka tana fito wa ta Kalli fa'iza da ke xaune tana ganin ta ta kwashe da dariya sannan tace "hmm taku salon soyayyar kenan " Hararar ta nauwara tayi taja tsaki xata saki magana wayar ta tayi ringin don hka ta kyale nauwara ta d'auki wayar ta nan da nan aka fara mak'ale murya alamar da saurayi ake wayar K'arshe ma sai ta fice daga d'akin tana yiwa nauwara alama da hannu tana xuwa Kwanciya tayi tare da rungume pillow tana tunanin maganganun abduljabbar dafa kirjin ta tayi kada dai ace xancen fa'iza ya tabbata ai kuwa da taji dad'i samun miji kamar Captain abduljabbar ai da ta more ba Kad'an ba Shigowar message taji a wayar ta dauka tayi ta bud'e password d'in wayar gaban ta ne ya fad'i ganin number d'in abduljabbar ce Dama tana da ita a wayar fa'iza ce ta samata tun lokacin da Abba ya siya musu ga abin da tagani ya rubuta _daga yau duk inda xaki Kina sanya nik'ab_ Tabbb baxan iya ba wlh Hka kawai xafi ma kad'ai ya ishe ni sannan bani ma dashi don hka sai ta rubuta mishi reply kamar hka _Yah abduljabbar ni bani da nik'ab fa'iza ma hka_ Tana gama rubuta wa tayi sending ya tafi sannan tayi addu'ar bacci ta kwanta ganin har yanxu fa'iza bata dawo d'akin ba xuciyar ta cike da tunanin abduljabbar sam ta rasa sanin me yasa take yawan tunanin shi kodayaushe *Aishat A muh'd* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd*😘 _Zama da masoyi mai son ka tsakani da Allah akwai dad'i, haka xama da mak'iyi bashi dad'i ko Kad'an toh da xarar mutum ya furta maka so duk halin shi yafi mak'iyan ka sau dubu_ _*Cewar nauwara*_ *~Pg 56~* *WASHE GARI* Nauwara sai wajen 9:30 ta tashi saboda lectures d'in karfe 11 take dasu don hka baccin ta tayi,bayan ta tashi wanka ta yi had'e da brush dama tun asubah tayi sallahr ta shirya wa tayi cikin wata simple gown kalar milk da touch d'in blue ajikin rigar don hka veil d'in da tayi rolling sai ya kasance blue tayi kyau sannan ta sauko k'asa ta tarar da umma, aunty sadiya da fa'iza nan ta tsugunna har k'asa ta gaida umma da aunty sadiya ta Kalli fa'iza da tun fitowar ta take mata dariya k'asa k'asa harara ta dalla mata kafin cikin shagwa6a tace "umma kinga fa'iza tana yi min dariya kohhh" Da sauri fa'iza ta danne dariyar ta ta kallon ta umma tayi sannan tace "rabu da ita nauwara ai naganta tun d'axu hka kawai mutum ya dunga dariya kamar wani sabon kamu "(ta nufin mahaukaci), gwalo nauwara tayi mata tare da wuce wa dinning table don yin breakfast itama fa'iza ta dawo wajen ta suna er hira tana kur6ar tea tace "fa'iza kinji wai Yah abduljabbar yace na dunga sa nik'ab Idan xan fita " Xaro ido fa'iza tayi tana cewa "tabbb wlh kada ki yarda shi duk kishin ne hka? " "ke wai waya ce miki sona yak'e??? " "fad'a wa wanda bai sani ba, yarinya ai ni suna nake ya aure ki wlh jiddah ta raina kanta" "Allah k'awata !" "ah tsaya wasa yarinya" Suka kyalkyale da dariya tare da tafawa har su umma da aunty sadiya suna kallon su Murmishi umma tayi tana kallon aunty sadiya tace "wad'annan yaran ka xauna dasu wlh sai sunsa mutum dariya ko baya so " Ita ma aunty sadiyar murmishin tayi tana cewa "ina ruwan fa'iza da nauwara ai ina son xama dasu " Can ta d'anyi shiru Kafin tace "umma ni kuwa Muna neman wata alfarma a wajen ku? " Gaba d'aya umma ta tattaro hankalin ta kan aunty sadiya tace "ina sauraren ki auntyn yara" er dariya aunty tayi kafin tace "d'an gida nane (tana nufin abduljabbar don sometimes hka take kiran shi) yake neman aure kuma er gida ce" Cikin mamaki umma take kallon aunty sadiya tace "neman aure kuma? " "ehhh shine yace na sanar da ke don kada *YAYI SAKE* (Littafi na na gaba) ko kuma *Abari ya huce*.......(littafin takori ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike), don Kisan da xancen? " "toh wace Wannan? "Cewar umma cikin murmishi aunty sadiya tace "erki ce nauwarah!" Cikin tsananin mamaki tace "da gaske kike? " "k'warai kuwa don ya jima yana sonta fad'ar ce bai ba sai yanxu Allah ya nufa" "tohh Alhmdllh ai Shikenan ko shine jiya da ya ganta tana xance ya koro ta yana ta masifa " Murmishi aunty sadiya tayi kafin tace "Kinsan d'an gidan nawa akwai kishi " Ta6e baki umma tayi tana cewa "toh ni dai aja kunnen shi wlh kada ya sake ya wulak'anta min 'ya, sannan xamu magana da abban su ita kanta nauwara sai mun tambaye ta tana son shi don baxan yi mata auren dole ba " "d'an gidan nawa ba irin maxan da xa'a kyale bane " "sai dai munyi shawara a tohh" "toh Shikenan Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi " "Ameeen thumma Ameeen " umma ta amsa d'an halak suna shiru sai gashi ya shigo parlourn da sallama cikin tafiyar shi ta kasaita yana sanye da uniform d'in shi sunyi matuk'ar kar6ar shi bayan sun gaisa yace "ni fah daga nan sai abuja ina aiki " Nan suka yi mishi fatan alkhairi, har ya mik'e xai tafi sai ya koma ya xauna yana cewa "umma ko xan samu kunun gyad'a? " "ehh akwai kuwa duba cikin flaks kan dining table akwai" Langa6e kai yayi alamar sai dai a xubo a kawo mishi Murmishi kawai umma tayi tana shirin kiran hajja mai aikin ta sai ga su nauwara xasu tafi skul don hka ta umarci fa'iza ta xuba mishi sai da ta gaida shi sannan ta wuce xubo mishi yayin da nauwara a d'an rud'e ta gaida shi lafia kawai ya iya cewa, gefe d'aya ta koma tana jiran fa'iza amsa waya yake yana kallon ta k'asa k'asa wanda ba lalle mutum ya gane ba tayi mishi kyau Mik'e wa tsaye yayi yana cewa "umma a barshi kawai sauri nake wlh ana jira na" "okay ba damuwa Allah ya kiyaye hanya " "Ameeen " ya amsa yana wuce wa da sauri suma su nauwara suka fita da sauri don har 10:30 tayi Suna fita farfajiyar gidan suka tarar da Yah abduljabbar a tsaye shi da abdulkareem nan suka gaida abdulkareem yana tsokanar su dariya kawai sukayi ba bakin ramawa ga captain a kusa ya had'e rai K'arshe ma sai mota ya shiga ya xauna ganin hka yasa abdulkareem shima shiga don shine xai kaishi airport har yayi wa motar key sai ya lek'o ta window yana cewa "Captain yace a rage muku hanya ku shigo " Shiga sukayi daman motar su tana wajen gyara drive ne sai kaisu su dai shiru sukayi sai dai wani lokacin suna d'an k'us k'us a junan su duk abin da suke yana kallon su ta madubin motar yayin da abdulkareem yake dariya k'asa k'asa har yana furta "ana so ana kaiwa kasuwa " har yake d'orawa da " *abari ya huce... Shi ke kawo rabon wani*" Shi dai baya kula shi da hka har suka sauke su nauwara a skul sannan suka wuce ya kaishi airport sai da jirgin su ya tashi tukunna ya dawo gida wannan kenan....... *Aishat A muh'd* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd*😘 _jinjinar ban girma gare ku k'awaye na ummu abdul, aunty deejah 😜,neena cool, maman jafar,mrs muktar, maryam omar, hafsat A Aliyu (baby), Allah ya k'ara xumunci ameeen thumma Ameeen_❤😘 *~Pg 57~* Yammaci mai cike da wani irin yanayi na lokacin xafi duk da iskar fanka da sanyin ac amman akwai hucin xafi, nauwara ce xaune a falon umma na sama tana sanye da wani three quarter d'in wando fari sol da er riga k'arama red colour mai siririn hannu tayi parking d'in gashin ta da ribbon white nd red sai k'aramin d'an kunnen ta red shima tayi kyau sosai sai k'amshin daddad'an turare take xafi ne ya isheta shi yasa tayi wannan shigar gashi ba'a fiye shigowa falon ba don hka ta bararraje sai faman waya take tana murmishi had'e da wani kakkaryar da kai ana iyayi wani guy sunan shi yusuf sun had'u dashi lokacin da xasu je gidan aunty kausar motar su ta lalace a hanya toh shine ya taimaka musu har aka gyara motar ya roki number nauwara dakyar ta bashi don ya fiye naci Abin da yasa take son kula shi yana da barkwanci sosai duk wannan abun baisan gidan su ba kawai suna hira a waya da chatting ba k'aramin so yake yiwa nauwara ba gashi ita ba wani son shi take ba kawai tana kula shi don abin dariyar shi Ya dad'e a tsaye a jikin kofar falon yana kallon ta a k'alla xai kai wajen mintuna 10 ko fiye da hka a tsaye yana kallon ta don tayi mishi kyau a idon shi ba Kad'an ba sai dai xuwa yanxu da ya lura da waya take nan ya fara jin ranshi ya fara 6aci don hka cikin kasaita da tafiyar shi irin ta maxaje ya k'ara sa wajen da take xama Yayi agefen ta daf da ita sannan yasa hannun shi ya kar6e wayar dake mak'ale a kunnen ta cikin tsiwa ta juyo xatayi masifa ta d'auka fa'iza ce dummm gaban ta ne ya fad'i ganin Yah abduljabbar fuskar nan tashi a murtike babu alamar fara'a kamar wanda aka aiko mishi da sak'on mutuwa sai huci yake sakamakon sauraren abin da yusuf yake cewa nauwara cikin d'aga murya yace "stop this nonsense! Kasan dawa kake magana ko bata fad'a maka Anyi mata miji agida ba toh d'aga yau kada ka k'ara kiran ta idan kunne yaji jiki ya tsira stupid boy" Yana gama fad'in hka ya cilla wayar ta bugi bango nan take ta tarwatse a matuk'ar fusace ya juyo da nufin marin ta sai dai kash suna had'a ido ya sauke hannun shi k'asa saboda ganin hawaye male male a fuskar ta duk jikin ta rawa yake ta Kank'ame jikin ta a tsorace tausayin ta ne tare da wani irin sonta yaji alokaci d'aya ya baibaye shi baisan lokacin da yasa hannu ya rungumo ta jikin shi ba cikin wani irin mayen son nan Wani irin shock suka ji a jikin su gaba d'aya k'amshin turaren su ya had'u waje ya ya vada wani irin k'amshi mai dad'i, nauwara gaba d'aya ta k'ara kid'ime ma don duk a xaton ta dukan ta xai yi laluben kunnen ta yayi yana cewa "ina sonki nauwarah! ina tsananin kishin ki duk lokacin da wani namiji ya kalle ki I luv you so much my nauwarahhh! " Ya K'arasa fad'i yana kallon fuskar cikin wani irin Shauk'in so ya gaji da barin abu a xuciyar shi gwara ya bayyana shi ko ya huta, kusan sume wa tayi jin kalamar da bata ta6a tsammanin xata ji ta abakin shi ba gaba d'aya wata irin kunya ce ta lullu6e ta sunkuyar da kae tayi duk ta tak'ura da irin kallon da yake jifan ta dashi toh ganin haka yasa ta cikata ai kuwa a guje ta fad'a d'aki ta rufe kofa had'e da jingina da jikin kofar tana dafe kirji, dariya sosai ta bashi ganin abin da tayi mik'e wa kawai yayi ya fice daga falon don ji yayi kamar ya sauke wani katon nauyi akanshi wasai yake jin shi Nauwara kam dakyar ta K'arasa kan bed ta xube sai ajiyar xuciya daman Yah abduljabbar son ta yake kenan fa'iza hasashen ta ya xama gaskia wayyo Allah na gode maka da ka bani masoyi kamar Yah abduljabbar gaba d'aya ta rasa mai xata yi tsantsar farin ciki take cikin yau sai dai kawai murmishin jin dad'i take kallo d'aya mutum xai mata yasan tana cikin farinciki Wayar tace ta fara ringin cikin sauri ta d'auka ganin sunan Yah abduljabbar yake kira taji gabanta ya fad'i wata kunya ta kamata dakyar ta iya d'auka ta k'ara a kunnen ta shiru tayi batai magana ba shima a nashi b'angaren shirun yayi yana jin saukar numfashin dakyar ya iya bud'e baki yace "shine kika gudu baki ban amsa ba?" Cikin sanyin murya mai had'e da kunya tace "me xance Tohhh? " D'an murmishi yayi Kafin yace "cewa xakiyi I luv you abduljabbar oya ina jiran ki fad'i ko sai naxo a fad'i a gaban Naji? " Da sauri tace "a'a ni...ni wlh kunya nake ji" Ta K'arasa fad'i cikin shagwa6a, hkan ba k'aramin k'ara birge shi tayi ba don yana masifar son mace er shagwa6a cikin muryar Idan xai musu fad'a yace "keee malama Idan xaki fad'a Ki fad'a don Wlh baxan kashe wayar nan ba sai kin fad'a min" Wayyo Allah to ita ya xatayi wlh kunya take ji sai faman tutturo baki take tana yarfe hannu kamar a gaban shi take dakyar ta iya cewa cikin sanyin murya tare da rarraba kalamar kamar mai koyan magana "ina son ka Yah abduljabbar" Tana gama fad'in hka ta yi hangin up d'in wayar tare da d'aukar pillow ta rufe fuskar ta dariya sosai ta bashi wannan kunyar ta ta ba k'aramin birge shi take ba kallo abdulkareem yayi wanda yake kunshe dariyar shi don shine ya matsa mishi sai ya kirawo ta awaya harara ya dalla mishi sannan yace "ai nasan ni ba irin maxan da xa'a kyale bane don hka dai nayi nasara " "a hba abokina da gaske? " "an fad'a ni na wasa ne " dariya suka tuntsire da ita tare da tafawa sannan abdulkareem yace "sauran kayi ta nuna mata xafin kan nan naka ko wannan miskilancin naka wlh ka sake ka nuna mata so don ku more soyayyar ku kafin mu sha biki" "tunda ni nake so ai angama komai don wlh sai umma ta gaji da rashin kunya ta ta aura min ita xan barsu su huta Don naji tana cewa sai sun gama skul wajen 2 years wlh bazan iya hak'ura ba " Sakin baki abdulkareem yayi yana kallon shi duk ya canja ssai faman surutu yake kamar bashi ba cikin tsokana yace "Duk soyayyar nauwara ce ta canja hka sai xuba ka ke "? Duka ya kawo mishi a kafad'a da sauri yayi tsalle ya kauce dukan bai same shi ba "kai captain matsala ta dakai saurin kawo hannu kace xaka daki mutum " Dariya suka tuntsire da ita sannan suka cigaba da hirar su cikin jin dad'i da annushuwa *Aishat A muh'd*😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd*😘 _jinjinar ban girma gare ki k'awata zaynab lawan ( *sarautah*) maman anwar da ikraam Allah ya raya mana su, Allah ya bar mu tare Ameen, ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike wannan page d'in naki ne_❤😘 *~Pg 58~* Duka fa'iza ta kai mata a baya firgigit ta mik'e a tsorace tana Sosa wajen harara ta watsa mata cikin xafin dukan tace "Haba fa'iza da xafi fah wlh Idan kika sake dukana xan fad'a wa Yah abduljabbar" Sakin baki tayi tana kallon ta yayin da nauwara ta kashe mata ido d'aya cikin xakuwa fa'iza tace "ke kinsani a duhu bani labari sis? " Nan nauwara ta bawa fa'iza labarin abin da ya faru tsakanin ta da Yah abduljabbar wani ihun murna fa'iza ta saki da sauri nauwara ta toshe mata baki tana cewa "Don Allah fa'iza ki nutsu wannan k'arar sai umma taji " Dariya tayi tana rungume nauwara cikin tsananin murna tace "Allah nagode maka abin da nake jira kenan don Allah ki cire tsoron da kike yi mishi ki saki jiki kusha soyayya " Lumshe ido tayi tare da bud'e su lokaci d'aya tana murmishi tace "ke ni kunyar shi nake wlh sannan Nifah ina d'an tsoron wannnan matar tashi? " Harara fa'iza ta dalla mata tare da kai mata duka da sauri ta kauce tana cewa "ni matsala ta dake saurin duka daga magana" "ai Kece kika ban haushi wlh ina ruwan ki da matar shi akan ta xaki xauna, kawai yarinya ki share ta" Nan dai fa'iza ta dunga shawarwari masu kyau yanda xata samu kan Yah abduljabbar tare da fad'a mata irin abubuwan da yafi so basu tashi daga nan ba har sai da umma ta nemo su tukunna suka tashi Tun daga lokacin sai suka fara wasan 6oya tana jin Shigowar shi xata gudu d'aki shi kuma kawai ya kyale tane ya xuba mata ido don yaga iya gudun ruwan ta har ranar da xai koma abuja basu had'u ba hka ya tattara ya tafi shi kanshi wani lokacin yana mamakin yanda son yarinyar nan yayi mishi kamun da har ya kasa 6oye shi ,toh ita nauwara taso sake sashi a idon ta Kafin ya tafi kunya ce ta hanata ya tafi ya barta da kewar shi don ma akwai album pictures d'in shi da fa'iza ta damk'a mata shi ko yaushe cikin kallon shi take yayin da son shi yake k'aruwa acikin xuciyar ta Tun da xafin nan ya kama nauwara Idan ta tashi shan ruwa Bata sha mai rangwamen sanyi sai dai mai sanyi k'arara ko ta fasa k'ank'ara ta dunga sha gashi d'aki sai ta kure fanka da ac bata jurar yanayin xafi umma tayi fad'an ta daina sha sai ta koma sha a 6oye ai kuwa mura tayi mata mummunan kamu atishawa hanci ya dunga yoyo gashi murya ta dashe nan fah ido ya raina fata mura tak'i sauk'i gashi bata son shan magani Kamar yau tana xaune a parlour tana sanye da black d'in siket da red d'in t shirt tayi tumfke kanta da ribbom red barimar kunnen ta red colour ce tayi kyau sosai tissue ne a gaban ta tari guda sai fyace hanci da atishawa take hancin nan yayi jawur dashi umma da aunty sadiya sun fita yinin bikin k'awar umma daga ita sai fa'iza da take bacci saleem kuma yana waje yana buga ball Wata atishawa tayi da K'arfi da sauri ta fara laluban tissue sai gani tayi an Mik'o mata karfa tayi ta toshe hancin tana ta faman jera ta sai da ta lafa ta d'ago kanta karaf suka had'a ido da Yah abduljabbar yana xaune dab da ita ai tuni ta rikice duk kunya ta kamata cikin sauri ta tsugunna tana gaida shi bai amsa ba sai ma hannun shi da yasa ya xaunar da ita kan kujera suna kallon juna kanta a sunkuye tak'i ta d'ago shi kuwa idon shi a kanta hannun shi suna rik'e da hannayen ta cikin muryar shi mai dad'in gaske yace "ashe har yanxu murar batayi sauk'i ba, mai yasa kika fiye shan sanyi da yawa? " Cikin marairaicewa kamar xata yi kuka tace "Allah na tuba baxan k'ara ba don ba k'aramin wahala nake sha ba" Kallon lips d'in ta kawai yake yana ayyana wani abun a xuciyar shi Kafin yace "kuma umma tace kin k'i shan magani why? " "wahalar sha yake bani gashi ni bana son d'acin shi " "okay, amman baki isa ba Kina fama da ciwo bakya son shan magani Kina wahalar min da kanki ,Kalli fuskar ki yanda tayi ja don hka je ki d'auko hijab d'in ki muje doctor ya duba ki " "ni dai baxan je ba xata warke ka barshi don Allah" D'aure fuska yayi tare da cewa "ke ina wasa dake don kinga ina lalla6a ki oya jeki ki d'auko hijab nace" D'ago kanta tayi ta kalle shi ya d'aure fuska sosai dole ta mik'e ta nufi bedroom ya bita da kallo cike da kaunar ta,lokacin da ta shiga d'akin har yanxu fa'iza bacci take don hka ta janyo hijab ja ta sanya had'e da flat shoe ta fito da yake har lokacin bata da waya a hannu tunda ya rotsa mata kuma ya hana su umma da abba su bata lokacin da ta fito yana tsaye yana waya da hannu yayi mata alamar su je don hka tayi gaba yana bin ta a baya har suka K'arasa wajen motar shi ya bud'e mata ta shiga sannan ya rufe shima ya shiga ya xauna sai da ya gama wayar sannan ya juyo ya kamata tana kallon shi da sauri ta kauda kanta cikin jin kunya gira ya d'aga mata yana cewa "Wannan kallon fah kamar xaki had'iye ni" Tsit tayi don bata san me xata ce mishi ba can dai tace "Nifah ba kallon ka nake ba" Murmishi yayi tare da cewa "Haba yarinya fad'i gaskia kawai Kice Nayi miki kyau kuma kunya ta hana Ki fad'a " Shiru tayi bata k'ara cewa komai ba har suka k'araso asibitin da alama shine doctor d'in shi da yake duba shi don suna shiga office d'in ya fara tsokanar shi "Captain ko wannan ce amaryar tamu ne? " Shima Murmishi yayi yana xama kan kujera yana cewa "kamar ka sani kuwa" "Amman ka iya xa6e Allah ya tabbatar da alkhairi " "Ameeen doctor" "ah amarya k'araso mana kin tsaya a tsaye, wlh captain baka da kirki mai makon ka fara xaunar da ita Kafin ka xauna" "ita fah nan duk tsoron allura take ji shi yasa take nokewa " Dariya doctor ya tuntsire da ita "xaki xama matar soja shine kike jin tsoro " Duk kunya suka bata ta kasa cewa komai kafin ta ankara taji atishawa ta taho nan ta dunga yi da sauri Captain ya k'arasa ya rik'e ta ajikin shi yana yi mata sannu doctor ma yana gefe yana xuba mata sannu sai da ta lafa ya mik'a mata hankicif d'in hannun shi ta goge hancin sannan ya rik'o hannun ta ya xaunar da ita shima ya xauna ya Kalli doctor yace "kaganta mura ce take damun ta ruwan sanyi take sha har da k'ank'ara gashi tak'i tasha magani ina abuja banyi niyyar xuwa ba wannan week d'in but saboda murar nan naxo don hka ka duba" Cikin tsokana doctor yace "daman ina xaka iya xama amarya ba lafia" Nan dai ya duba ta had'e da bata magungunan da xata sha suka yi mishi sallama su tafi suna isa gida ya bata maganin ba don taso ba tasha saboda ganin yanda ya had'e rai yana gama bata yace taje ta kwanta ta huta shima ya nufi nashi gidan don har yanxu su umma basu dawo ba lokacin da ya K'arasa gida jiddah bata nan don hka bedroom d'in shi ya wuce wanka yayi sannan ya xube kan bed ya xurfafa a tunanin yanda xai shawo kan abba nan da two months su aura mishi nauwara..... *Aishat A muh'd* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* *Aishat A muh'd*😘 *~Pg 59~* Hannun ta d'auke da babbar robar ice cream sai sha take suna hira da fa'iza kallon ta fa'iza tayi tana cewa "yanxu nauwara baxa ki daina shan wannan sanyin ba? " "ke wai ina ruwan ki jikin ki ko jikina"cewar nauwara tana ajiye robar ice cream da ta shanye "xan kirawo Yah abduljabbar na fad'a mishi abin da kika gama sha yanxu ni bansan yanda ma na biye miki har na rakaki siya" Cikin dushewar murya tace "Idan ma baki rakani ba nasan hanya " ta6e baki fa'iza tayi tana fad'in "ni dai wlh kada ki hanani bacci yau tunda kinki daina shan sanyi kuma sai na d'auke d'ayan na cikin frige baxa ki sha ba" Harara ta dalla mata tare da cewa "ke kin isa ma" ta K'arasa fad'i tana mik'e wa tsaye xuwa tayi ta sanya wa frige d'in key fa'iza nayi mata dariya bata kula ta ba kwanciya tayi don ta fara jin bacci itama fa'izan kwanciya tayi don dare yayi Cikin dare nauwara hanci ya toshe ga wani axabbaben ciwon kai da xaxxa6i suka rufe ta lokaci d'aya tana yiwa fa'iza magana amman sam bataji ba saboda muryar ta bata fita sosai dole tasa hannu ta tashe ta cikin yanayin bacci fa'iza tace "wai lafia xaki tashi mutum yana cikin bacci? " Ganin nauwara tana kuka wiwi yasa ta watstsake wa tana cewa "me ya same ki? " Cikin dushewar murya tace "fa'iza ki taimaka min kaina ciwo yake ga xaxxa6i kuma hancina ya toshe" Nan ta ce "tohh yanxu ya xa'a yi? Ita dai ta kasa cewa komai don hka fa'iza ta tashi ta paracetamol ta d'auko mata ta hado mata da maganin da abduljabbar ya siyo mata na mura dakyar ta lalla6a ta tasha maganin ba'a dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita sai da fa'iza ta kashe ac tare da rage k'arfin gudun fanka sannan ta koma ta kwanta Washe gari da safe da fa'iza ta tashi tana bud'e idon ta suka had'a ido da nauwara tayi wanka ta shirya gaban ta kuma d'ayan robar ice cream di'n nan take sha ido ta xaro tare da d'ora hannu akai tace "wayyo nauwara baki da hankali ne Kina cutar da kanki toh Allah baxan xuba ido ina gani Kina cutar da kanki ba " Cikin sanyin murya gata a dashe tace "ya xanyi fa'iza na k'asa hak'ura da sha xata warke da kanta " "Har kin mance da wahalar da kika sha jiya da dare ? " cikin takaici fa'iza ta fad'i hkan ba saurare me xata ce ba ta fice daga d'akin ta nufi bedroom d'in umma ta tarar da Yah abduljabbar a d'akin nutsuwa tayi ta gaida shi sannan tace "umma kiyiwa nauwara magana tak'i ta daina shan kayan sanyin nan wlh jiya da ciwon kai da xaxxa6i ta k'wana ga hanci a toshe dakyar fah tayi bacci gashi yanxu ina tashi na ganta tana shan ice cream " Da sauri umma ta mik'e tsaye tana cewa "Bari naje wurin ta ai jiya ina kallo Kece mai rakata ta siyo ice cream di'n " Ficewa daga d'akin umma tayi yayin da fa'iza ta bita shima kasa jurewa yayi tashi yayi ya bisu ya tarar da umma sai rarrashin ta take ta rage shan sanyin sai ta warke a fusace abduljabbar yace "umma ki daina wani lalla6a ki barni da ita tunda ita batasan ciwon jikin ta ba" Ya Kalli fa'iza yace "daga yanxu na kafa dokar daina shan ice cream a gidan nan naga wanda ya k'ara siya kuma duk lokacin da tasha ruwan sanyi ki fad'a min" "toh yayah Insha Allah xan fad'a maka " Cewar fa'iza tana yiwa nauwara gwalo a fakaice sannan ya juya kan nauwara yasa hannun shi ya riko kunnen ta da karfi har sai da ta saki k'ara saboda xafi da sauri umma tace " kayi mata a hankali man abdul " "umma kyale ni da ita Idan ba ta daina ba duka xan mata idan jikin ta ya fad'a mata taji" yana fad'i yana harar nauwara da sauri ta sunkuyar da kanta "ban da duka dai nasan baxa k'ara ba ma" umma ta fad'i hkan da saurin ta ta d'aga kan ta alamar ehh harara ya sake dalla mata ai kuwa ta langa6e kai tare da marairaice mishi fuska kamar xata fashe da kuka d'auke kanshi yayi baxai iya jurar ganin tana yi mishi Hka ba "Wlh umma ke kike dad'a shagwa6a ta" Cewar fa'iza murmishi umman tayi tace "tohh ina ruwan ki " Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin fa'iza ma ta bita da sauri ganin Yah abduljabbar ya xauna kan bed d'in da nauwara take yana rik'e hannu shine ta fice don ta basu waje Kallon ta kawai yake ita kuma sai wani kauda da kai take don baxa ta iya jure had'a ido dashi ba hannun shi yasa ya d'ago kanta lumshe ido tayi dogayen gashin idon suka kwanta kan fatar ta ya xuba wa kyakkyawar fuskar ido cikin muryar shi mai dad'in gaske yace "bakya jin magana koh? " Kamar xata fashe da kuka tace "kayi hak'uri na daina Insha Allah " "okay yayi kyau yarinya, mu je kiyi breakfast sai kisha maganin ki xaxxa6in ya sauka ne? " ya K'arasa fad'i yana ta6a wuyan ta "ehhh sai ciwon kai kawai " "okay sannu " Hannun ta ya rik'e bayan ya d'aga ta daga xaunen da take cikin jin kunya tace "don Allah Yayah ka fara yin gaba Allah kunyar umma nake ji " Murmishi yayi yana cika hannun ta ya lakuce mata hanci yana cewa "kin fiye kunya da yawa na baki 5 mint Idan baki fito ba xan dawo na d'auke ki, kin yarda? " Da sauri ta d'aga kanta tana cewa "Ehh Allah na yarda" Girgixa kai kawai yayi ya fita daga d'akin xauna nawa tayi tana cewa "ohhh ni nauwarah daman Hka Yah abduljabbar yake " ganin taci mintuna 3 da fitar shi yasa ta mik'e wa da sauri ta fita daga d'akin suna xaune kan dining table har da Abba nan ta tsugunna k'asa tana gaida abba ya amsa yana cewa "ya jikin naki 'yata? " "na samu sauk'i abba" "toh Allah ya k'ara sauk'i" "Ameeen abba ngde" Jan kujera tayi ta xauna kusa da fa'iza tana d'ago kanta suka had'a ido da abduljabbar yana mata alama da ido ta dawo kusa dashi da sauri ta sunkuyar da kanta tabb ina xan iya wannan rashin kunyar ga Abba da umma a xaune duk a tak'ure take cin abincin sbd yanda yake kallon ta duk abinda yake umma da abba suna kallon shi Murmishi kawai sukayi irin nasu na manya cikin k'asa da murya abba yace wa umma "wannnan d'an nawa ya xurma da yawa fah 'yar ki ta rikita min d'a " Murmishi kawai umma tayi da hka suka gama breakfast d'in abba da Yah abduljabbar suka fice daga gidan yayin da nauwara da fa'iza suka dasa sabon hira yayin da fa'iza sai tsokanar ta ke sai dai tayi murmishi tace "Allah ya shirye ki fa'iza........ ....... ```Aishat A muh'd```😘 🍀☘☘🍀? *K'ARSHEN WAHALA* ????☘☘???? *written by* *Aishat A muh'd*?? *~Pg 60~* Hka rayuwa ta cigaba da tafiya al'amura sunyi nisa tsakanin nauwara da Yah abduljabbar soyayya suka xuba wa a waya kamar bashi ba shi kanshi wani lokacin abin ba k'aramin bashi mamaki yake ba ganin yanda soyayyar yarinyar nan ya kasa danne ta agaban kowa nuna wa yake Wajen watan shi d'aya da tafiya bai xo kano ba ayyuka sun rik'e shi gashi yana son xuwa ko dan ya sanar da abban shi nan da wata 2 yake son ya auri don baxai iya kai har wajen 2yrs ba bai mallake ta matsayin matar shi ba, su aunty asma'u da aunty kausar fa'iza ta tsegwanta musu soyayyar da Yah abduljabbar da nauwara suke toh suma sunyi murna don nauwara mutum ce ba ruwan ta tana basu girman su a matsayin su na yayyani ai kuwa aunty asma'u ta kirawo shi awaya yasha tsokana K'arshe da ta dame shi sai ya kashe wayar don duk sunyi mamakin yanda soyayya ta canja shi kamar bashi ba, Ranar juma'a bayan an idar da sallah ya taho da yake jirgi ya biyo nan da nan ya k'araso gida da sallama ya shiga parlourn umma ce cikin murmishi ta amsa mishi yayin da saleem yake yi mishi oyoyo hugging di'n shi yayi yana cewa "saleem ya skul dafatan ana karatu sosai " "uncle ina yi sosai ka tambayi umma ?" "ahh d'an nawa yana karatu sosai " Cewar umma yana xama kusa da umma yace "good boy ka cigaba da karatu " "Tohhh uncle " Yana gama fad'in hka ya fice daga falon dama fita yake kok'arin yi xai buga ball "Shigowar yanxu kayi kenan " "ehhh wlh umma na dad'e banxo ba aiki ne ya rik'e ni " "ai Kuna ma kok'ari Allah ya taimaka ya kare ku " "Ameeen umma na " Sai baxa ido yake yaga ta Inda nauwara xata fito amman shiru ba motsin su a gidan don hka yace "umma wai ina nauwara ne? " Murmishi tayi tana cewa "suna skul yau lectures d'in yamma ne da su " "okay shi yasa nake ta neman kiran ta wayar is switched off " Can ya cigaba da cewa "daman umma ina son xamu yi magana?" Tattaro hankalin ta kanshi tayi tana sauraren shi yana sosa kai yace "am daman umma akan wannna maganar ne " "Wacce magana kuma?" Duk da ta fahimci abin da yake nufi sai ta basar "umma maganar gaskia ina son nan da two months xan auri nauwara " Hararar shi tayi tana cewa "ai sai sun gama makaranta ka jira nan da shekara 2 da en watanni ne ya rage musu fah Kuma kamar yau ne xaka gani" "kai umma gaskia baxan iya jure ba pls" Hangame baki tayi tana kallon shi shi kuwa ko a jikin shi tsakanin shi da Allah yake fad'a nan ya langa6e kai tare da marairaice fuska yana lalla6a ta Murmishi kawai tayi yanda yake yi musu biyayya yana kyautata musu a matsayin su na iyayen shi ai sa bashi farincikin shi duk da wani 6angare na xuciyar ta tana d'an shiga damuwa Idan ta tuna jiddah katse mata tunani yayi ta hanyar rik'o hannun ta yace "pls umma ki yarda da abin da nace tun da kinga itama tana sona " murmishi tayi sannan tace "ni ta 6angare na ba komai na amince amman kasan halin jiddah ni bana so mu samu matsalar xumunci da er uwata" "umma Kinsan dai mamee (mahaifiyar jiddah) bata da matsala da ace jiddah halinta tayi da naji dad'i amman k'wata k'wata bata d'auko halin ta ko d'aya ba Idan na samu time xanje nayi mata bayani da kaina " "toh Shikenan Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi " "Ameeen umma na " Sun d'an ta6a hira sannan ya mik'e tsaye yana cewa "umma Bari naje na d'auko su a skul" Tana murmishi tace "okay Allah ya kiyaye hanya " Haka ya fice daga falon umma sai da ya biya wajen aunty sadiya suka gaisa sun d'anyi hira tukunna ya tashi tafi d'auko su nauwara a nutse yake driven har ya k'araso skul d'in yayi parking tukunna ya fito daga motar wow wasu "yammata suka ce ganin wannnan hadadden guy d'in yana fito wa daga cikin motar d'aya daga cikin su tace "kai wannnan guy d'in ya had'u K'arshe irin mijin da nake mafarkin samu Kenan" d'ayar ta gefen ta ce "ni kuwa sai naje naji yanda muryar take don a gaskia baxan iya jure wa ba sai naje wurin shi " wadda ta fara magana ta harare ta yayin da ragowar biyun suka kwashe da dariya tare da tafawa nan ta bud'e handbag di'n ta powder ta d'auko ta gyara fuskar ta tare da fesa turare sannan ta mayar da kayan jikin handbag di'n ta gyara mayafin ta tana wani tafiya tare da kwarkwasa aka nufi wajen abduljabbar da yake a tsaye yana neman wayar nauwara ringin biyu ta d'auko cikin sanyin muryar ta tayi mishi sallama ya amsa mata sannan yace " *habibty* ina skul d'in ku fah ina jiran ku am Kinsan bansan jira koh? " Cikin murna tace "da gaske? " "Xanyi miki wasa ne na baku 5 mint ku fito " Sannan yayi hangin up d'in wayar, cikin tsananin farinciki nauwara ta rungume fa'iza tana cewa "ke lafian ki qlau? " "Yah abduljabbar ne yaxo d'aukan mu fah" Xaro ido fa'iza tayi tana cewa "da gaske kike kuwa" "Idan Munje Kya tabbatar ni kaina ba k'aramin mamaki nayi ba" da sauri kowacce ta d'auki handbag di'n ta suka nufi inda yake Glass d'in kofar aka kwankwasa da sauri ya d'ago kanshi ya Kalli wajen ya d'auka nauwara ce sai yaga bakuwar fuska nan ya had'e rai kamar bai ta6a dariya ba tuni jikin ta yayi sanyi ganin yanda yayi mata kwarjini ta kasa magana a fusace yace "lafia ?" nan ta dabarbarce ta rasa me xata ce "Idan baki da abin cewa ki bar nan" Mtsww ya saki tsakin da ya dad'a tsorata ta Amman duk da don naci ta dake cikin kwarkwasa da iyayi tace "suna na ruky Idan ba damuwa ina son ka fad'a min sunan ka ka bani contact di'n ka, kana da kyau ina son ka " Murmishin yak'e yayi yace "are u sure kana sona da gaske?" Gyara tsayuwar ta tayi tare da fari da ido "yes! off course " Tana rufe bakin ta taji saukan wani lafiyayyen rabo da sauri ta rik'e kumatun ta saboda ba k'aramin xafi taji ba en wajen suka d'auki ihu ganin hka yasa ta janye tsumman kafafun ta don ba sa'a cikin takaici ta K'arasa wajen da suke xaune ai kuwa suka k'ara sakin ihun k'eta nan ta fara bambamin fad'a daman ance tabarmar kunya da hauka ake nannad'e ta nan taga ba dama sun ishe ta da iska yasa ta bar wajen Su nauwara da fa'iza suka kallon abin da yake faruwa da farko wani kishi ne ya kamata ganin yana kula ta amman ganin yanda suka rabu yasa su kwashe da dariya tare tafawa ita kanta tasan Yah abduljabbar daban yake acikin maxa yana da kyau, kud'i da muk'amin min shi hkan baisa ya kauce hanya ba sam baya kula mata da hka suka K'arasa wajen shi bayan sun shiga motar suka gaida shi cikin girmamawa kamar yanda suke mishi da ya amsa cikin jin dad'i fuskar nan tashi a sake yau sai faman murmishi suke yiwa junan su yayi mata kyau yau fiye da koyaushe ko dan yau ta fara ganin shi da manyan kaya yadin kufta ne a jikin shi kalar dark blue d'inkin xamani irin wanda matasa suke yayi yanxu takalmin shi da hula bak'ak'e ne amman hular da ratsin blue a jiki agogon hannun shi bak'i ne shima ba k'aramin kyau yayi ba Idan ka kalle shi bakace yana da mata ba fa'iza tana sit d'in baya tana kallon su ba k'aramin birgeta sukayi ba sun dace da junan su da hka har suka K'arasa gida yana gama parking wuf fa'iza tayi ta bud'e kofar ta fice ita ma nauwara xata fita ya kamo hannun ta yace "kamar baki farincikin ganina ba kuma don ke na ajiye aikin dake gabana naxo" "Ayyah Yayah nayi murnar ganin ka mana Allah kawai na gaji ne " "alright so bari na barki ki huta xuwa anjima na dawo ki kular min da kanki " murmishi kawai tayi tare da fita daga motar bai tafi ba har sai da ya daina ganin ta sannan tafi nashi gidan...... Aishat A muh'd ?? *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd 😘 *~Pg 61~* A ranar umma ta fadawa abba abin da abduljabbar yake so dariya kawai yayi sannan yace "ni awaje na ba matsala sai yaxo neman aure a wurina tunda nine uban 'ya" ita dai umma dariya kawai tayi, don hka Washe gari da yaxo umma ta fad'a mishi hkan don dad'i baisan lokacin da ya rungume umma ba cikin dariya tace "baka da kunya koh abdul? " Sosa kai yayi cikin murmishi yace "afuwan ummana dad'i ne ya ishe ni " "toh ba wannnan ba ka sanar da jiddah? " "ban fad'a mata so nake yau na fad'a mata yanxu ma daga nan sai gidan mamee xan sanar da ita " "don Allah kada kaje ka biye wa jiddah ka lalla6a ta kasan halin ta dai gata da shegen kishin tsiya " Maganar umma ta K'arshe ta bashi dariya yace "Kada ki damu umma xanyi yanda kika ce " Nauwara ce ta k'araso wajen xuba mata ido yayi kamar yau ya fara ganin ta duk kunya ta gama lullu6e ga umma xaune awajen gyaran murya umma tayi firgigit ya dawo hayyacin shi yana shafa kanshi kallon ta umma tayi tana cewa "Yayan ku xaki kawo mishi abinci " Dakyar ta iya cewa "tohh umma" saboda kunya ta wuce xuwa kitchen cikin en mintuna ta shirya mishi table d'in dake gaban shi da abinci ta juya xata tafi yace "baki serving d'ina ba? " Harara umma ta watsa mishi tace "yi tafiyar ki nauwara kyale shi " Da sauri ta wuce xuwa d'akin su yayin da abduljabbar yace "Haba umma kada kisa ta fara rainani " "ba dai nauwaran da nasani ba na tabbata ba daga k'aramin gida ta fito iyayen su tabbas sun basu tarbiyya mai kyau " Da hka ya fara cin abincin bayan ya kammala yayi sallama da umma ya tafi gidan mamee babar jiddah bayan sun gaisa yake sanar da ita auren da xai k'ara da nauwara sam bata nuna mishi komai sai ma addu'ar fatan alkhairi da ta bishi da ita nan ya cika ta da kud'i yayi gaba Sai da ya biya ta wajen abdulkareem suka sha hirar su sannan ya K'arasa gidan shi har cikin bedroom d'in ta ya bita tana kwance sai faman chatting take tana ganin shi ta mik'e tsaye tayi hugging di'n shi shima k'ara rungume ta yayi a jikin shi sannan yace "Ina son yin magana dake so ki biyo ni xuwa d'akina " Cikin er dariya tace "toh ina xuwa" Fice wa yayi daga d'akin ya barta tana dad'a gyara jikin ta mybe wata samu war ce tunda ake neman ta lokacin da ta K'arasa d'akin yana wanka sai da ta jira shi ya fito ya shirya cikin sleeping dress cotton farare sol dasu ya fesa different body spray nd perfumes masu matuk'ar k'amshi mai dad'i ya dawo kan bed ya xauna jiddah sai binshi take da kallo xuciyar cike da kaunar shi hannun ta dukka biyun Ya rik'o mai da kalar fuskar shi yayi bata wasa ba a nutse ya fara da yi mata nasiha Sannan ya gangaro kan batun auren shi da yake so yayi wani irin mik'e wa tsaye tayi tare da fincike hannun ta idanun ta Sun rufe da kishi tace "aure kuma abdul, wa xaka aura? " Babu d'ar ko Kad'an a tare da shi kai tsaye yace "nauwara ita xan aura" "what! Wacce nauwara ?" "wadda kika sani dai ta gidan umma" "kuttt lalai ma na yarda kai mara mutunci ne ka rasa wanda xaka aura sai Wannan mai kama da aljanu wayyo Allah na shiga uku Wlh baka isa ba baxan xauna da kishiya ba ba gwanda kowacce ba da wannnan yarinya" Tass kake ji ya wanka mata lafiyayyen mari sakamakon Cakumo wuyan rigar shi da tayi kafin ta dawo hayyacin ta ya saki kifa mata wani da sauri ta sake shi gashin ta yaja sai da tayi wata k'ara don axaba idanun nashi sunyi ja dasu sai faman huci yake yau jiddah ta kaishi bango shi take xagi "ni sa'an ki ne da xaki xage ni baki sanni ba but yau xaki san Kala ta Abduljabbar an gaya miki kishi hauka ne akan ki aka fara kishi da xaki xo Kina yi min rashin hankali" Belt d'in da ya cire yasa hannun shi ya d'auko ta guda d'aya ya xuba mata ta saki ihu don ta shige ta ba Kad'an ba ya daga belt d'in xai sake xuba mata ai kuwa kafa mai naci banba ki ba da gudu ta bar d'akin sauran Kad'an dariya ta kubce mishi ganin yanda take gudun cillar da belt d'in yayi ya kwanta xuciyar shi gaba d'aya ba dad'i jiddah tayi masifar 6ata mishi rai sai juyi yake yana xuba tsaki yana son ya kirawo nauwara yaji muryar ta ko yaji dad'i a xuciyar shi wani 6angare na xuciyar yana hanashi saboda bai kamata ya kirawo ta a wannan lokacin ba a matsayin shi na me mata duk da sun samu sa6ani da jiddah toilet ya shiga ya d'aura alwala ya fito ya shimfid'a abin sallah nan ya fara nafila don neman za6in Allah K'wana jiddah tayi tana kuka duk idanun ta Sun kumbura ana fito wa daga masallaci sallahr asuba ta janyo akwatin ta ta saka a motar ta da gudu ta fice daga gidan yana jin fitar ta karshe ma sai yaja bargo ya lallu6a bacci ne yayi awon gaba da shi daman daren jiya bai samu cikakken bacci ba Tana xuwa gidan su ko xama batayi ba mamee da babanta suka fatattake ka kuma sun yi ratsuwa da Allah Idan bata koma gidan ta ba basu ba ita ta nemi wasu iyayen tun da daman ai umma ce ta rik'e ta har ta girma a wajenta ta aurawa abduljabbar ita mene bata yi mata sannan don tsabar butulci irin na *D'AN ADAM* (littafin rufaida Omar) xata ce baxata xauna dashi ba ita bata ga abin da ta aikata musu a baya amman basu rabu da ita ba suka kyale ta shine dan iskan ci xaki xo kawo mana yaji ai kishi ba hauka bane nan suka yi mata tas ba yanda xata yi Hka ta dawo gidan abduljabbar don duk iskan jiddah da rashin mutuncin ta tana son iyayen ta Bata son 6ata musu rai motsin dawo war ta shine ya tashe shi daga bacci wanka yayi ya shirya cikin black trouser da purple d'in t-shirt ya fito ya fice daga gidan gaba d'aya Jiddah fa ta shiga tashin hankali nan da nan tabi ta rame abduljabbar ya daina bi ta kanta kawai abin da yake gaban shi yake ana cikin hka abba ya yanke lokacin auren nan da two months Insha Allah kamar yanda abduljabbar yake so Nan fah umma aka shiga hidima ba kama hannun yaro uwar amaryar uwar ango turkashi duk ita kadai 6angaren su aunty asma'u da kausar su kuma yanda xa'a gudanar da programs di'n bikin suke shirya wa yayin da ango abduljabbar ya sakar musu bakin aljihu Gyara sosai umma ta xage tana yiwa nauwara ciki da waje duk abin da akasan uwa tana yiwa erta umma tana yiwa nauwara shi mai gyaran jiki wata k'awar umma ta d'auko shuwa arab ce ita take gyara nauwara ga abubuwan gargajiya irin na da umma tana yi mata nan da nan ta k'ara wani irin kyau jikin ta ya goge ya k'ara kyau in banda sul6i da taushi sai k'amshi fatar jikin ta take Umma da kanta ta had'a lefe nagani na fad'a anyi 6arin kud'i ba Kad'an ba komai yaji don tsayawa fad'a muku abubuwan da suke ciki 6ata lokaci ne mai karatu sai Kuyi hasashe harda jiddah aka had'o wa na fad'ar kishiya kamar yanda al'ada take kuma umma ce take mata har gida tayi mata nasiha tana tafiya ta hau jifa da kayan kamar wata mahaukaciya duk tabi rikita kanta sosai take jin haushin umma, gashi abduljabbar ya fita harkarta k'wata k'wata ga ba me bata shawara don tuni sunyi fad'a da farida k'awar ta tun lokacin da ta xubar da cikin nan abu goma da ishirin suka had'ar ta ga lokaci sai taho wa yake ta tsani kishiya tana masifar son abduljabbar shi yasa take bala'in kishin shi ta d'auki alk'awarin duk wadda tayi gigin auran mata miji xatayi da tasani........ _Kuyi hak'uri fans wlh jiya nayi muku typing da yawa na goge shi ban sani ba_ *Aishat A muh'd*😘 🍀☘☘ *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd {Aunty}😘 _wannnan shafin sadaukar wa ne ga duk masoyan *K'ARSHEN WAHALA* Kuyi hak'uri da baku ji ni jiya da yau ba uxiri ne ya rik'e ni_ *~Pg 62~* Haka aka cigaba da shirye shiryen biki ba kama hannun yaro gaba d'aya Abduljabbar a busy yake ko lokacin kanshi baya samu saboda hidindimo wannan shine auren da ya gani yake so dole ya xage domin k'ayata bikin shi da habibty di'n shi xirga xirga tsakanin kano da abuja don ma abdulkareem yana taimaka shi gashi ogan su na wajen aiki ya shirya musu dinner party irin nasu na sojoji wanda xasu gabatar a kano don yana son abduljabbar sosai saboda jarumar takarshi rashin tsoro uwa uba kuma gaskiyar shi da rik'on amana Su aunty asma'u da kausar fa'iza suma sun shirya irin nasu programs di'n da xasu gabatar umma ma da aunty sadiya sun shirya kayatatciyar walimah da xa'a yi wadda sukayi inviting di'n wata shaharririyar malama da xata gabatar da lecture, sun cigaba da shirye shiryen su har ya rage sauran 2 weeks biki Gaba d'aya jiddah tasa bak'in kishi a xuciyar ta duk tabi ta rame ga kishi gashi abduljabbar baya shiga harkar ta abu fah ya tatar mata don ko murmishin shi ta daina gani kawai sai sha'anin gaban shi yake yanda yake nuna d'okin shi akan auren duk ta gama firgice wa gashi iyayen ta basa bi ta kanta balle su umma da hidimar biki ta d'auke musu hankali ganin wankin hula xai kaita dare yasa ta neman shi a waya sai da ta kusan 20 missed calls bai d'aga ba ganin ta dame yasa ya d'auka yana yi mata fad'a kan kiran shi da tayi toh kukan da yaji tana yi yasa mishi dakata wa da fad'an da yake yi mata hak'uri ta dunga bashi tare da alkawarin baxa ta sake aikata hkan ba sosai yaji tausayin ta nan dai dakyar ya hak'ura ai kuwa ta dunga xuba godia yaji dad'in hka har a xuciyar shi yana addu'ar yasa ta shiryu di'n ba tuban muxuru tayi ba Xaune take a bedroom d'in su gaba d'aya jikin ta an mulke shi da had'in wani dilka na musamman ta rufe jikin ta ruf yayin da aka xuba wani turare mai mugun k'amshi a kaskon turaren wuta yana ratsa jikin ta sosai wayar ta ce ta d'au ringing Murmishi tayi don tasan mai kiran ringtone di'n shi na daban ne wak'ar aashiqui tasa mishi da sauri ta hau goge hannun ta yayin da fa'iza take mata dariyar k'eta ganin yak'i goguwa harara ta dalla mata tana cewa "Allah fa'iza kin rainani nifah matar yayace yanxu dole ki dunga ban respect " "Sannu matar babban yaya sarkin son girma" Yatsine fuska tayi tare da ta6e baki tana cewa "don Allah ki d'aga kisa min a kunne pls mata a gidan mus'ab haba tawan " Ta K'arasa maganar kamar xata yi kuka saboda ganin wani kiran ya dad'a shigowa na uku kenan dariya tayi tana cewa "yarinya tunda kin fad'o sunan rabin raina angama" Ta K'arasa fad'i tana hangin up d'in wayar ta k'ara mata a kunne cikin xaxxak'ar murya ta tayi mishi sallama amsa wa yayi Kafin ya d'ora da cewa "habibty ina kika shigane ina neman ki? " Cikin yanayin muryar shagwa6a tace "gyaran jiki ake min so hannuna ya 6aci da dilka amman kayi hak'uri " Lumshe idon shi yayi yana d'an murmishi mai sauti Kad'an yace "tunda ni ake gyarawa jikin ba matsala ko Yah? " Ya fad'i yana d'aga gira kamar tana kusa dashi kunya ce ta kamata a lokacin da gabanta ya fad'i tare da jin wani tsoro yana shigar ta muryar shi taji yana cewa "Naga alama kunya kike ji bari na barki Hka gashi ina xaune duk tunanin ki ya hanani aiki ina son ganin ki rabon da mu had'u Anyi Wajen 1 month fah sai a waya nayi missing di'n kallon beauty face d'in ki" Nok'e kai take kamar tana gaban shi yayi da fa'iza take dariya k'asa k'asa duk da soyayyar su tana bala'in birgeta da Hka dai sukayi sallama yace Idan ya samu time xai kirawo ta xuwa anjima Sannan yayi hanging d'in wayar ya jingina da kujera idon shi a lumshe gaba d'aya ji yake kamar ya janyo lokacin Hka yake ji soyayyar nauwara ba k'aramin kamu tayi mishi ba Janye wayar fa'iza tayi tana yi mata shak'iyan ci duka ta kai mata tana cewa "Allah fa'iza bashi kika d'auka ka xan rama ne " "yarinya sai dai Ki rame? " Ta K'arasa fad'i tana dariyar k'eta harara ta watsa mata ta mai da hankalin ta kan t.v tana kallon film d'in India bodyguard wanda Salman Khan da Kareena kapoor suka yi a hankali taji FA'iza ta matso kusa da ita a kunnen ta ta rad'a mata "nauwara anya kuwa Kinsan mene aure??? " Dummm gaban ta yayi mugun fad'uwa jin abin da fa'iza tace da sauri ta d'ago kai ta kalle ta har ta fara had'a xufa jikin ta ya d'au rawa ganin hka yasa fa'iza tuntsire wa da dariya tana cewa "wallahi Anyi matsoraciya anan daga magana kawai " tuni idon ta yayi rau rau alamar kiris ya rage ta fashe da kuka hannun fa'iza ta kamo cikin rawar murya tace "bayan abin da nasani nake karantawa a novels akwai wani abun kuma?" Dariyar mugunta ta saki tana cewa "babu komai yarinya " "Idan da wani abun ki sanar da ni pls? " "Don wallahi ban yarda da dariyar mugunta nan ba " Shigowar aunty kausar ne ya katse fa'iza daga maganar da tayi niyyar yi wani cup ne a hannun ta da wani plate ta dire a gaban nauwara tana cewa "gashi inji umma tace ki cinye tas Ki shanye abin cikin cup d'in nan" Kallon fa'iza tayi wanda take toshe bakin ta saboda dariyar da take son kubce mata gaba d'aya ji tayi ta gama tsargu wa duk tayi wik'i wik'i da ido kamar wanda tayiwa sarki k'arya ganin hka yasa aunty kausar korar fa'iza daga d'akin ta lalla6a nauwara ta cinye tas tare da shanye abin da ke cikin cup d'in sannan aunty kausar tayi mata sallama kan sai ana sauran k'wana 2 biki xata dawo saboda sauran shirye shirye ta bar nauwara cikin tsananin tsoro tana addu'ar Allah yasa fa'iza ta dawo su K'arasa maganar toh har suka kwanta bacci bata fad'a mata kwakkwarar magana ba don hka taja bakinta tayi shiru sai dai har yanxu da tsoro a tattare da ita...... *Aishat A muh'd* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd {Aunty} *~Pg 63~* Cikin en k'wanakin nan dai sai da nauwara ta d'an rame saboda tsabar tasa tsoro a ranta duk ta xama so silent ko abduljabbar ya kirawo ta awaya Bata sake wa dashi har ya gano hkan yake cewa "ba dai har kin fara jin tsoron nan da amarya take ba wlh kada kisa wani abun a ranki ya janyo miki wata matsala " Gaba d'aya kunya ta rufe ta kamar ta nutse a k'asa kamar yana gabanta kasa cewa komai tayi shima er dariya yayi kawai wadda ta k'ara sata jin wata kunyar sam basuyi wata hirar kirki ba a lokacin ta kasa sakin jikin ta kamar da xabga tagumi tayi tana tunani Shigowar saleem ne ya katse mata tunanin da take hugging di'n ta yayi wani abu ne ya fad'o mata a ranta ta fashe da wani irin marayan kuka mai ban tausayi shima saleem kukan yake ba komai suka tuna ba illa rashin iyayen su da er uwar su fa'iza ce ta shigo itama ta fashe da kuka tana rungume su duk tausayin su ya kamata sai da umma taxo ta rarrashe su tare da yi musu nasiha tukunna suka hak'ura har suka warware suka cigaba da harkokin su Hka dai lokaci ya cigaba da tafiya har ya rage sauran k'wanaki biyu a fara biki duk wasu en uwan abba dana umma sun fara xuwa aunty asma'u da aunty kausar ma tuni sun tarkato sun yo gida kowanne ka gani yana cikin farinciki Ranar da xa'a fara gabatar da programs di'n biki na kamu ranar Captain abduljabbar ya shigo kano tare da tawagar abokanan shi sai da ya sama musu masauki mai kyau a guest house d'in abban shi sannan ya xarce gidan shi duk ya matsu yaga habibty di'n shi amman dole ya hak'ura har xuwa yamma lokacin da xa'a gabatar da kamu kamar yanda al'adar bahaushe take A parlour ya tarar da jiddah ta xabga uban tagumi tsaya wa yayi yana kallon ta xuciyar shi cike da tausayin ta a hankali ya K'arasa inda take hannu yasa ya janye tagumin da tayi tana ganin shi ta kwanta a jikin shi ta fashe da kuka sosai ta bashi tausayi amman hkan baxai sa ya hak'ura da auren da xai yi ba ko rarrashin ta bai yi ba sai da taci kukanta ta more sannan ya d'an rarrashe ta ganin hka yasa xata bud'e baki tayi magana ya d'aga mata hannu alamar tayi shiru Sannan yace "kiyi hak'uri da abin da xakice min sai anjima yanxu na gaji ina buk'atar hutu kije ki kawo min wani abun mara nauyi naci yunwa nake ji" Yana gama fad'in hka ya tashi ya nufi bedroom d'in shi kwafa tayi tana cewa "wlh sai na koyawa yarinyar da ta aure ka hankali sai na nuna mata ba'a had'a miji da jiddah ba boka ba malam kissa ma kad'ai ta isheta da kafar ta xata bar gidan nan " Mtsww taja tsaki tukunna ta mike kitchen ta nufa ta ga mai dafa musu abinci ya gama duba wa tayi don taga abin da ya dafa jellop d'in taliya ta debar mishi wadda taji kifi da nama ga vegetables sannan ta had'o mishi da lemo da ruwa ta d'auka dakin shi ta shige ta tarar ya fito daga wanka yana d'aure da farin towel ya goge gashin shi da wani k'aramin towel d'in kunnen shi mak'ale da waya ya rik'e ta a tsakanin kafad'ar shi yana magana sai faman doka murmishi yake takaici ya ishi jiddah ga wani irin kishi da ya lullu6e ta abincin hannun ta ta ajiye akan k'aramin table d'in d'akin a fusace ta juya xata tafi jin ko kula da ita bai yi ba caraf taji ya kamo hannun tare da janyo ta jikin shi sai da ya d'auki en mintuna tukunna ya kashe wayar Har da sakin wata ajiyar xuciya sam ya mance da wata jiddah a jikin shi sai da yaji shashshak'ar kukan ta Sannan ya dafe kanshi yana fad'in auuch! cak ya d'auke ta ya d'ora ta kan bed ya shiga yi mata abubuwan da dole ta russuna ai kuwan K'arshe har dariya ta dunga yi kamar ba ita ba yana d'an murmishi yaja hancin ta yana cewa "Yah ko da akwai wani abun dafatan kin koshi Idan baki koshi ba sai na cigaba don ba gajiya nake " Yana fad'i mata hkan yana d'aga mata gira murmishi tayi ba dole ta dunga kishin abduljabbar ba mutumin da yasan ta kan mace kullum kamar k'ara mishi kyau ake tunawa da auren da xai yi nan da en K'wanaki yasa ta fara xubar da hawaye kallon ta yayi tausayin ta ya kamashi don yasan abin da yake damunta bai wuce kishin shi ba shi kanshi yasan jiddah akwai shegen kishin tsiya D'aukan ta ya sake yi suka shiga toilet don dai duk don taji dad'i shi yasa ya sauke fushin da yake da ita taji da abu d'aya kada abun yayi mata yawa Bayan sun fito a toilet d'in ya gyara jikin shi tare da sanya wani three quarter fari ne sol da wata black d'in riga mara hannu ya fesa perfumes Kala Kala sannan ya xauna ya d'an tsakuri abincin Kad'an yaci yana bawa jiddah a baki to itama batayi musu ba ta kar6a tana ci saboda yunwar take ji don bata iya cin abinci kirki saboda ta sawa ranta kishin tsiya Suna gama ci ya d'an yi tsalle kamar sau goma tukunna ya sha ruwa ya kwanta da yake a gajiye yake nan da nan bacci yayi awon gaba da shi yayi da jiddah ta xuba mishi ido kamar yau ta fara ganin shi xuciyar ta sai sak'a mata abubuwa take Misalin karfe 4 na yamma mutane suka fara taruwa a gidan su Abduljabbar k'awayen umma ne da na aunty sadiya sai nasu aunty asma'u da aunty kausar sannan nasu fa'iza da amarya nauwara goggagun en boko kowa ka ganshi da shiga ta Kece raini wannan yana wane wannan har da mameen jiddah da k'awayen ta itama, acikin k'awayen amarya can na hango irin su sadeey saNaz, neena cool, miss zahra Gasu nan dai da yawa sai iyayi ake xuba wa 😜 A garden di'n gidan xa'a yi an gyara shi yasha decoration wajen yayi kyau sosai, ango da en abokanan shi suka k'araso gidan yasha wata tsadaddiyar shadda light pink irin d'inkin xamani takalmi da agogo bak'ak'e yayi amfani dasu hular kanshi baka ce da ratsin pink da fari ajiki sai k'amshi yake xubawa ba k'aramin kyau yayi kannan nashi da sajen nan sun sha gyara sae sheki suke da d'aukan ido hular nan an turo ta gaban goshi sai faman xabga murmishi yake yana xuba ido yaga ta Inda nauwara xata fito Wowwww masha Allah abin da ya fad'i kenan ganin aunty asma'u ta fito rik'e da hannun nauwara tasha wani tsadadden swiss less kalar pink da touch d'in black ajiki takalmi da poss di'n hannun ta bak'ak'e ne nad'in kanta da aka yi mata shima pink nd black haka sark'a da d'an kunne har abin hannu gashin kanta yasha gyara an xubo mata dashi baya tasha make up sosae tayi masifar yin kyau har suka k'araso inda yake kanta a sunkuye tak'i ta d'ago dashi sai da aunty asma'u ta d'an ta6a shi sannan ya dawo hayyacin shi kwashe wa da dariya suka yi ita da abdulkareem "Wannan kallon fah kada kasa ta fad'i fah " Cewar aunty asma'u tana yi mishi dariyar shak'iyan ci hararar ta yayi hannun shi ta kamo ta had'a da hannun nauwara lumshe idon shi yayi jin tattausan hannun ta d'aya hannun shi yasa ya d'ago kanta lumshe ido tayi duk kunya ta rufe ta kamar ta nutse a k'asa take ji k'asa jure wa yayi ya fara matso da fuskar shi saitin tata, tuni aunty asma'u ta fahimci abin da yake niyyar yi da sauri ta tafa hannu tana cewa "Wayyo ni asma'u abdul wannan wacce irin rashin kunya ce a gaban mutane kake kok'arin yin...... " bata K'arasa fad'i ba ganin umma ta k'araso wajen tuni ya janye fuskar shi tare da hararar asma'u ganin ta katse mishi hanxari dariyar mugunta suka yi mishi ita da abdulkareem yayin da kunya ta ishi nauwara "ku fah kawai ake jira kuka xauna anan"cewar umma Hka ya janyo hannun ta suka nufi inda xa'a yi kamun kujera d'aya ce irin mai fad'in nan Kad'an Hka suka xauna slow music ne ke tashi a wajen sunyi matuk'ar dace wa da junan su Hka kowa yake cewa har aka fesa wa ango da amarya turare suka cigaba da kamun su har xuwa lokacin gaf da mangariba tukunna aka tashi mutane sun fara tafiya abduljabbar yak'i sakin nauwara aunty asma'u kuwa k'in tafiya tayi don ganin yanda yake rawar jiki tasa mishi ido hararar ta yayi yana cewa "kin fiye sa ido wlh ki tafi harkar gaban ki k'i kyale ni da mata ta " "Ahayye yaro Allah baxan tafi ba kafata kafar nauwara"cewar aunty asma'u "selfie kawai xamu d'auka yanxu xata taho fah ni ba wani abun xan yi mata ba" "Duk da hka ayi a gabana" Hka dai ya share aunty asma'u ya dauko wayar shi yana cewa "oya gyara habibty xamu yi selfie " A kunyace ta d'ago da kanta shi kuwa ya matso da kanshi kusa da kanta ya d'an kwanta a jikin ta Kad'an ya d'auka sunyi kyau a photon aunty asma'u ma sun birge ta sai da tayi musu pictures tukunna ya tashi tare da sunkuyo wa saitin fuskar ta ya sakar mata kiss a kumatu tare da yin gaba hangame baki aunty asma'u tayi ganin rashin kunyar abduljabbar tana cewa "Lallai abdul daman Hka kake?" shi dai bai kula ta ba ganin an shiga masallaci ita ma janyo hannun nauwara suka yi cikin gida dakyar take tafiya saboda kunya aunty asma'u tana ce mata ta saki jikinta ta daina jin kunyar ta ita yayar tace...... ..... Aishat A muh'd 😘 ☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd 😘 *~Pg 64~* Aunty asma'u har d'akin su ta rakata ganin yanda take jin kunya tana shiga fa'iza da sauran k'awaye da en uwan su fa'iza sa'annin su nauwara enmmata suka saki shewa suna ga amarya ga amarya kowa yana kok'arin janyo ta don ta xauna kusa dashi aunty asma'u tace "Allah Kuyi mata a hankali kada ku fad'ar da ita kunsan halin dai abdul yanxu yasa ku tsallen kwad'o " wata a cikin su Mai suna hafsat tace "Haba aunty ai muma bama so taji ciwo ba mukai amarya ba lafia ta kasa cin amarce " Shewa suka saki tare da tafawa fa'iza tana dariyar mugunta tace "Hkne hafsat kada yayan mu ya kasa cin amarci yanda ya kamata " Dariya suka tuntsire da ita aunty asma'u ta harari fa'iza tana cewa "Allah ya shirye ki fa'iza ai ni naso wlh a had'a bikin nan da naki ko ma huta " "Haba aunty asma'u Kinsan ni yarinya ce me na sani ai kwa tausaya min na girma tukunna " pillow aunty kausar ta cilla mata yayi da aunty asma'u ta kawo mata bugu da sauri ta kauce tana 6uya a bayan nauwara nan dai suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali da nishadi Da sauri ta fito daga toilet tana d'aure da babban towel jin sai Kiran ake wayar ta ake Mik'o mata wayar fa'iza tayi tana murmishi tace "ango ne fah yake kira" Warce wayar ta tayi tare da hararar fa'iza murguda mata baki tayi tana kok'arin d'auka wayar ta katse don hka sai ta xauna akan rest chair tana Kok'arin kiran shi jin ta shiga yasa ta gyara kwanciyar ta tana jira ya d'auka Ganin yayi mata wajen 3 missed calls bata d'auka ba yayi tunanin ko bata kusa da wayar don hka ya tashi ya fara cire kayan jikin shi don shiga wanka bud'e kofar d'akin akayi jiddah ce ta shigo hannun ta d'auke da k'aramin flaks na tea da cups akai ajiye wa tayi kan table shi kuma ya shiga toilet shigar shi kenan kira ya shigo wayar shi da sauri jiddah ta d'auka don jin ringtone na daban ne sauran kiris ta saki Ihu don ganin abin da ya tasar mata da hankali pic d'in nauwara da abduljabbar ne suka haskawa akan wayar wanda ya d'auke su selfie d'axu shine ya d'ora kan wayar ganin sunan *habibty* akan number d'in ya tabbatar mata nauwara ce kuttt wato ita har wani habibty ya saka mata bayan number d'inta da my jiddah kawai ya saka tana kok'arin d'auka ta katse kiran jin alamar fito wa daga toilet yasa ta saurin ajiye wayar da sauri ta fice daga d'akin tana xubar da hawaye tana son abduljabbar batason wata ta ra6e ta sai ita kad'ai fashe wa tayi da kuka kishi ne ke cinta kasa d'aure wa tayi ido jawur ta koma d'akin waya ta tarar yana yi irin kalaman da yake furtawa nauwara yasa ta kasa jurewa batasan lokacin da ta je gaban shi ba tana huci idon ta ya rufe ta fisge wayar tare da makata ajikin bango lokaci d'aya wayar ta tarwatse tayi d'ai d'ai da ita abduljabbar yabi wayar tashi da kallo Kafin ya ankara ta fara jifa da duk abin da ta d'auka tana ta masifa shi kuwa gefe d'aya ya samu tare da xuba mata ido kawai tana ta haukanta lokaci d'aya ta mayar da d'akin kaca kaca duk ta farfasa komai ganin tana kok'arin jiwa kanta ciwo yasa tafiya Inda take ya rik'e ta fisge wa tayi tana cigaba da abin da take hannu yasa ya bata lafiyayyen mari jin saukar shi kan fuskar ta yasa ta nutsu sai a lokacin ta lura da irin 6arnar da tayi mishi a d'aki cikin fusata yace "Kalli hannu na yanda kika yanke ni yanke ni baki da hankali ne an gaya miki kishi hauka ne don kinga ana lalla6a ki banxa wawiya kawai get out" Xata yi magana a fusace ya nuna mata hanyar kofa yana cewa "live me alone pls Kafin na tattakaki " Tuni tayi hanyar fita sai faman ihun kuka Mtsww yaja tsaki d'aya wayar shi ya dauka ya fita daga d'akin ya koma d'aya bedroom d'in da yake bedrooms di'n shi 2 a cikin parlourn bai k'ara bi ta kanta ba ya lalubo nauwara a waya suka d'an ta6a hira kafin suyi sallama sai lokacin yaji xuciyar shi tayi sanyi duk 6acin ran da jiddah ta hadda sa mishi ya samu sauk'in shi Tun da ta shiga d'akin take faman xabga kuka kamar wanda aka aiko mata da sak'on mutuwar iyayen ta ranar dakyar bacci ya dauke ta saboda yanda kalaman da abduljabbar yake yiwa nauwara sai kuwwa suke mata a kunne Lallai Idan yarinyar nan ta shigo gidan nan xataci uban ta Bayan sun gama waya ta dawo d'akin ta tarar su fa'iza suna ta xuba surutu ita ma cikin su ta shiga suna hira daga K'arshe suka fara yi mata lectures akan yanda xata xauna da mijin ta da kishiyar ta lafia sosai nauwara ta nutsu take sauraren har dasu aunty asma'u da aunty kausar suma shawarari masu amfani suka bata don xama da kishiya irin jiddah sai a hankali har lokacin da suka kwanta yayin da nauwara ta mik'e toilet ta shiga tayi alwala ta fito shimfid'a abin sallah ta nafilfilo ta fara tare da addu'ar Allah ya basu xaman Lfy da mijinta tare da kishiyar ta tayi wa iyayen ta addu'a sosai Aunty asma'u tana kwance kan rest chair tana d'an ta6a charting ganin abduljabbar yana kan online yasa ta tura mishi da dariya me gwalo _ke kuma lafiyar ki qlau_ ya turo nata " _ango kenan Allah ka gode wa Allah don ya baka mace mai tsayuwar dare duk gajiyar nan ta hidima bata hanata yin nafilfilo ba_" " _Alhmdullilah naji dad'in hka nima hankalin ta nutsuwar ta da rik'on ibadar ta da kunya su suka k'ara min kaunar ta baxan iya kwatanta miki yanda nake k'aunar ta ba_" " _Allah sarki d'an k'anina Allah ya baku xaman Lfy da xuri'a mae albarka_" " _Ameeen_" " _bacci nake ji Gud nyt_" Yana fad'in hka ya sauka itama aunty asma'u sai da ta ta6a hira da mijinta tukunna ta kwanta har bacci ya d'auke ta nauwara tana karatun qur'an murya k'asa k'asa yanda baxata dami mutanen da suke bacci sai da taji bacci yana kok'arin d'aukar ta sannan ta samu ta kwanta........ *Aishat A muh'd* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd 😘 *~Pg 65~* Washe gari ya kama ranar da xasu gabatar da Mother's Day wanda umma ta shirya Anan cikin gidan xasu gabatar tunda gidan babba ne sosai anyi mishi decoration wajen yayi kyau sosae sun gabatar da shi cikin kwanciyar hankali har xuwa lokacin da aka tashi kowa ya kama gaban shi, gidan ya cika makil da en uwa saboda gobe xa'a d'aura aure bayan an sakko daga sallahr juma'a Daman ana cewa komai nisan lokaci bai shige asa lokaci ba xai xo ya shige kamar ba'a yi ba toh Hka ta kasance ga captain abduljabbar da nauwara ayau aka d'aura auren su bayan an sakko daga juma'a wanda dumbin jama'a suka shaida akan sadaki mafi cancanta saboda neman albarkar aure, kusassun gwamnati da en kasuwa xuwa manya manyan sojoji da k'ananan su sun halarta d'aurin auren abduljabbar, ango sai faman washe baki yake xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki mara misaltuwa yasha wata tsadaddiyar shadda fara sol da ita takalmi da agogo farare ne suma hka hular kanshi fara ce sol komai fari Yayi amfani dashi acewar shi yau ranar farinciki ce dole yayi amfani da farin abu kamar yanda xuciyar shi take cike da farin ciki yayi kyau har ya gaji da had'u wa gashi kannan nashi yasha gyara da sajen nan da ya k'ara mishi kyau Alhmdullilah ya furta lokacin da yaji an shafa fatiha nauwara ta xama tashi murmishi ya saki yayin da abdulkareem yake tsokanar shi Bayan an kammala daurin auren suka xarce da yin walimah tasu irin ta maxa anci ansha sun sha addu'a daga bakunan mutane na xaman lfy da xuri'a mai albarka Cikin gida kuwa lokacin da aka sanar an d'aura aure fa'iza dasu hafsat suna ta tsokanar nauwara har da yi mata wak'ar _ta xama d'auko riga ta xama d'auko wando ta xama d'auko buta ta xama......._ ita dai bata kula suba saboda yanda lokaci d'aya gaban ta yayi mugun fad'uwa jikin ta duk yayi sanyi ki shingid'a tayi a jikin kujera ta lumshe idon ta, tana cikin hka aunty asma'u ta shigo tana cewa "fa'iza ku fito xa'a d'auki pictures ango ya shigo dasu abba da abokanan shi " Xumbur 'yammatan suka mik'e basu bi ta kan nauwara suka fice daga d'akin sai aunty asma'u ce ta kamo hannun ta suka fito tana sanye da wani abu kamar swiss less kamar material fari ne sol dashi har d'an kwalin kanta da aka yi mata wani nad'i mai kyau dashi kamar yanda abduljabbar yayi amfani da komai fari hka nauwara itama shigar komai fari tayi sunyi masifar yi mata kyau tasha make up sai shek'i take tana xuba wani k'amshi mai dad'i a Hka Har suka fito main parlour inda ango da sauran en uwa suke sai faman tsokanar abduljabbar suke da amarya nauwara nan aka shiga pictures da en uwa abduljabbar ko kunyar mutane baya yi yana manne da matar shi a jikin shi sai tsiya ake mishi baran aunty asma'u da abdulkareem shi dai murmishi kawai yake Dakyar aunty asma'u ta kwace nauwara daga hannun abduljabbar ta mai da ita d'aki ba hka abduljabbar yaso ba yaso su d'an ke6e da amaryar tashi amman aunty asma'u ta kicin kicin ta hana hka yaxo xai fita daga falon ya kamo hannun aunty asma'u ya janyo ta har wurin corridor yace "wlh asma'u ki fita a idona na rufe Haba kinbi kin tak'ura wa min idan da kin hana mu Ke6ewa yanxu naga ai ta xama mallaki na" D'an d'aure fuska tayi tace "Ehh duk da hka ka bari sai jibi Idan an kawo maka ita sai kayi yanda kake so ba mai hanaka" Xaro ido yayi yana cewa "what! Me kikace, sai jibi fah naji kince" Hararar shi tayi tana cewa "Ehh mana ai ba yawa k'wana 2 kawai ya rage" "shekara 2 ba k'wana 2 ba " Yana gama fad'in hka ya fice a fusace yayin da aunty asma'u ta kwashe da dariya ashe umma na jin su Murmishi tayi tana girgixa kai tace "Allah asma'u ki kyale min yaro hka kada mun saki baki ya lalla6o ya d'auke ta bamu gama biki ba Kinsan Kad'an daga aikin abdul" "Haba umma ba sai muje mu d'auko ta ba" Cewar aunty asma'u har umma xatayi magana wata er uwar tayi kiranta don hka kawai ta shige yayin da aunty asma'u tayi d'akin su nauwara kunnen ta mak'ale da waya suna magana da mijinta Haka suka cigaba da hidimar bikin su har xuwa lokacin da xa'a tafi dinner 'yammata ne cike a farfajiyar gidan kowacce ta hau wanka na Kece raini wannan tana wace Wannan sun sha ankon ba k'aramin kyau sukayi ba ga kuma manyan mata k'awayen su umma da aunty sadiya suma naso ankon daban hka k'awayen aunty sadiya da aunty kausar nasu daban ba k'aramin kyau da tsari suka yi ba a hka abokanan abduljabbar suka fara fara deban mutane suna kai su wasu kuma a motocin su motar amarya da ango ne na K'arshen tafiya don sai da aunty sadiya ta lalubo shi a waya tukunna yace gashi nan xuwa yana gama wayar ya Kalli jiddah wadda take cika tana batsewa saboda yace lallai dole sai taje dinner ganin yanda ya had'e rai yasa ta tilas shirya wa cikin wani less marron colour tayi amfani da handbag shoes nd mayafi farare tayi kyau ba laifi shi kuwa abduljabbar shadda ash colour yayi amfani da ita shi ma yayi kyau sosae "Wow masha Allah nauwara Kinyi kyau bana Kad'an ba" Cewar aunty asma'u irin doguwar riga ce a jikinta an tsara d'inkin da ganin kayan nera tayi kuka saboda tsabar tsadar su gwaggwaron kanta da takalmin ta hill da poss di'n hannun ta ash colour kai masu karatu baxan iya kwatanta muku Kyan da nauwara tayi ba yayin da fa'iza tace "yau idan ba ai wasa ba sai aunty jiddah ta had'iyi xuciya"dariya suka tuntsire da ita, hannun ta aunty asma'u ta rik'o suka fito su fa'iza na biye da ita saboda a motar ta xasu tafi don mus'ab dinta baya gari, fuskar ta a lullu6e har suka k'araso inda motar take ta bud'e mata motar sai da ta shiga ta gyara mata rigar da har jan k'asa take daga baya sannan ta rufo kofar motar suma shiga tasu motar suka yi don sun riga motar su Abduljabbar yin gaba K'amshin turare da sanyin ac ne ya fara yiwa nauwara sallama lokacin da ta shiga motar to da yake tasan da jiddah xa'a tafi dinner sun sa shi a tsakiya jiddah in banda harare harare ba abin da take cikin sanyin muryar ta mai dad'in gaske tace "aunty jiddah ina yini" Mtsww taja tsaki tare da juya kanta ganin bata da alamun amsa wa abduljabbar yace "Kina ji ana gaida ke koh? " dakyar ta iya cewa "lafia" don ba k'aramin tsorata ta yayi ba kada tayi mishi haukan kishi bai k'ara bi ta kanta ba ya kamo hannun nauwara murya k'asa k'asa yace "ni baki gaida ni ba" "ina yini " Ta fad'a tana turo baki duk da baya ganin fuskar ta "sai da na roka toh rik'e gaisuwar ki marairaice fuska tayi tace "yi hak'uri don Allah " Sake damk'e hannun ta yayi cikin nashi har tana cewa "auuch " ran jiddah idan yayi dubu ya 6aci saboda tana ganin shi yayin da abdulkareem yake xaune gaban mota shi yake driving saleem a d'aya sit d'in yayi gyaran murya jin yanda jiddah take faman xuba tsaki hararar shi yayi yana cewa "xaka fara sa idon ko Allah kai da asma'u kun fiye shiga harkar da bata ku ba" er dariya abdulkareem yayi yana cewa "ai sa idon ma iyawa ne " ya K'arasa fad'i yana kok'arin yin parking.... Aishat A muh'd 🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd 😘 *~Pg 66~* Ya K'arasa fad'i yana kok'arin yin parking don har sun iso Inda xa'a gabatar da dinner d'in nan jiddah ta fara kici kicin bud'e motar xata fita "bance ki fita ba " taji maganar abduljabbar dole ba yanda xatayi ta dawo ta xauna shi dai abdulkareem danne dariyar shi yayi yana fita daga motar shi da saleem basu fito ba har sai da aunty asma'u tace su fito tukunna suka fito a nutse hannun abduljabbar ta kama ta sak'alo dashi ta jikin nauwara sannan ta kamo hannun jiddah ta had'a da nashi d'ayan hannun nauwara na gefen dama yayin da jiddah ke gefen hagun shi sannan suka fara tafiya cikin hall di'n ta6e baki aunty asma'u tayi ganin wai kamar ita yayar abduljabbar jiddah ta kasa gaida ita bayan hka kuma er uwar tace ta jiki ma sosai Allah ya kyauta abin da tace tabi bayan su ita dasu fa'iza Babban hall ne yasha decoration ya had'u ko ina mutane xaune table ne mai d'auke da kujera 4, en yara ne 'ya'yan aunty asma'u da aunty kausar suke fesa musu wani turare mai kyalkyali tuni idanun mutane ya koma kanshi nan masu d'aukan pictures da video suka fara nasu aikin wak'a mai sanyin dad'i take tashi a wajen Fuskar nan tasu d'auke da Murmishi yayin da fuskar jiddah ba yabo ba fallasa da hka har suka K'arasa maxaunin suka xauna jiddah ta xame hannun ta daga na abduljabbar bai ma san tayi ba hankalin shi yana kan nauwara hasken idaniyar shi har xuwa lokacin da aka buk'aci amarya da ango su fito su taka rawa toh shi dai abduljabbar bai iya rawa ba nauwara ta iya sai dai kunya ta hanata yin rawar hannun shi yasa ya xagayo dashi ta bayanta ya d'an rungume ta a jikin shi suna d'an tattaka wa ba k'aramin burge mutane suka yi ba nan aka fara xuwa yi musu lik'i kai har umma sai da tayi musu lik'i har xuwa lokacin da suke koma suka xauna don shifa har ga Allah ya mance da wata jiddah a wajen Kai kishi bala'i ne yanda jiddah ta dunga ji kamar xuciyar ta xata tarwatse har da d'an hawayen ta lokacin da idon ta ya hasko mata yanda abdul d'inta ya kwantar da nauwara a jikin shi har da yi mata kiss a kumatu duk ta rasa nutsuwar ta dakyar ta danne abin da take ji ta tashi tsaye jin an buk'aci su yanka wedding cake shine ya fara yanka ya sawa jiddah a baki sannan ya juyo kan nauwara ya samata tukunna jiddah ta gutsura ta sa mishi a baki kamar yanda tayi Hka nauwara tayi sai dai Kafin ta cire hannun ta daga bakin shi sai da ya d'an cije ta Kad'an da sauri ta janye tana hararar shi irin ta gefen idon nan duk kunya ta rufe ta ai kuwa ji kake raf raf ana tafa musu don sun birge mutane xame wa tayi ta fice daga hall di'n ta tari taxi ta tafi gida don baxata iya kunsar bak'in ciki ba don ji take xuciyar ta kamar ta fashe Bai damu ba da bai ganta ba don yasan kishin ne ya motsa ya gode wa Allah da bata yi mishi hauka ba shi yasa wanda xasu yi gobe bai yi niyyar tafiya da ita sai sun fi sakewa shi da habibty di'n shi ba'a tashi ba sai wurin 12 na dare Kafin kace me mutane sun fara tafiya saboda bacci ga gajiya, yana kula da ita sai faman lumshe ido take alamar bacci take ji a kunne ya rad'a mata "bacci ne ya xo? " D'aga kanta tayi alamar ehh ganin hkan yasan ba k'aramin gajiya tayi ba tattare hannun rigar shi ya fara yi Kafin ta ankara ya sure ta sun fita daga wajen bai dire ta a ko'ina ba sai cikin mota ya nemo abdulkareem a waya ya fito su tafi ko mintuna 5 bai yi ba ya shiga motar suka fita daga Wajen tsam ya rungume ta a jikin shi sai faman sunshina ta yake ba k'aramin dad'i turaren jikin ta yake mishi ba tuni abduljabbar ya fara sakin layi ya kusan mance Inda suke ma ya lalubo bakin ta da yake matuk'ar son sumbata tun ba yanxu ba gashi yanxu ya samu damar hkan a hankali ya fara kissing d'in bakin ta kamar ya samu sweet mai tsananin dad'in nan bai ankara ba sai jin parking yayi a matuk'ar gala6aice ya d'ago kanshi duk idanun shi sunyi ja da su ya xuba wa nauwara ido cikin wani irin Shauk'in sonta da sha'awar ta duk tabi ta lafe a jikin shi kamar wata mage kunyar had'a ido take dashi gashi duk tsoro ya cikata sansanyan ajiyar xuciya ta saki jin aunty asma'u ta bud'e kofar motar tana cewa "nauwara fito mu tafi dare yayi " Mtsww yaja tsaki rai a 6ace yace "wai kina tunanin xan cinye tane" Baki ta ta6e tana cewa "wa ya sani irin wannan kallon hka duk tak'ura mata" Xai yi magana yaji muryar umma tana cewa "au ashe sun dawo asma'u to tsayuwar me kuke ne ku wuce ciki mana don naga alama nauwara a gajiye take " Tana mishi dariyar mugunta suka wuce kwafa ya saki cikin takaicin yanda asma'u ta sami shi ido akan matar shi amman xai yi maganin ta kwafa ya sake saki don yau yaso ko yane ya d'an mayar da kwadayin shi abdulkareem dariya sosai yake yi mishi tare da tsokanar shi kyale shi yayi bai kula shi ba har ya sauke shi a gida bud'e motar yayi ya fice yayin da abdulkareem ya bishi da dariyar shak'iyan ci A cikin Wannan daren xuciyoyi uku sun k'wana da wani irin yanayi xuciyar abduljabbar cike da d'okin gobe kamar yanxu yana tare da habibty di'n shi, yayin da xuciyar jiddah cike da tsantsar 6acin rai da kishin da yake damunta tare da tunanin me xata yiwa nauwara don ta raba ta da mijin ta gaba d'aya, ita kam nauwara xullumi da tsoro fal a cikin xuciyar ta gaba d'aya baccin su rabi da rabi ne Ranar asabar da rana suka gabatar da walimah wadda suka gayyato shaharariyar malama ta xuba lectures sosae akan xamanta kewar aure hakk'in miji akan matarshi da hakkin mata akan mijin da yanda xaki xauna da kishiyar ki lafia ba k'aramin k'aruwa mutane suka yi ba da wannan nasihar bayan an gama walima suka yi yinin bikin su Bayan an idar da sallahr isha'e xa'a tafi dinner d'in da ogan abduljabbar ya shirya mishi na sojoji daga nan sai a xarce da amarya gidanta umma aunty sadiya maryam matar da abba suka xauna suka yiwa nauwara nasiha sosae kanta a sunkuye in banda kuka babu abin da take yi bayan sun gama mata nasihar suka dawo suna sanya mata albarka tare da yi mata kyawawan addu'o'i Aunty asma'u aunty kausar da aunty maryam matar abdulkareem suka yi mata nasu nasihar ta manyan yayyanni tare da bata shawarwari masu kyau da amfani saleem ne ya shigo d'akin suka rungume junan su tare da fashe wa da kuka duk ba k'aramin tausaya musu suka yi ba hka fa'iza ma ta rungume ta suna kuka sosai dakyar aka lalla6i saleem ya tafi tukunna nauwara ta shiga wanka bayan ta fito aunty asma'u ta bata wani material yellow mai matuk'ar kyau da tsada d'inkin riga da siket ne sun kamata tsam tukunna mai make up tayi tare da yi mata d'aurin d'an kwalin ya xauna a kanta sosae sannan aunty ta turare mata jiki da wani shi'umin turare mai masifar k'amshi ta nade ta a cikin bakar laffaya sark'ar wuyan ta, ta gwal ce mai had'e da warwaro guda biyu har da sark'ar kafa irin siririyar nan da ake d'aura wa takalmin ta yellow ne da ratsin yellow Hka ma poss di'n hannun ta sannan ta dad'a fesa mata different perfumes a jikin ta rungume aunty asma'u tayi xata saki kuka da sauri ta girgixa mata kai alamar kada tayi Hka ta danne kukan Amman duk da hka sai da hawaye suka xubo mata Har wajen mota umma da aunty sadiya suka rakata tun da dinner d'in ban da manya rungume umma tayi tana kuka dakyar suka rarrashe ta ta shiga motar kamar jira yake ta shiga yayi mata kyakkyawan masauki a jikin shi yana rad'a mata wasu kalmomi masu xafi a kunnen ta har suka k'araso wajen sai da suka fita daga motar tukunna ta lura Ashe kakin shi ya saka shima ba k'aramin kyau suka yi mishi ba duk wayanci sojoji ne wasu da matan su wasu kuma emmatan su da alamar sun tsara hkan don kowanne table kujera 2 ne wajen ba k'aramin k'ayatar wa yayi ba an bada tarin ango abdulkareem ne ya bayar cikin harshen turanci fa'iza kuma ta bayar da tarihi amarya sun yanka cake sun ciyar da junan sannan suka rufe da yin faratin sojoji sai wurin 11:30 suka tashi nan ya tsaya sallama da jama'a don wasu gobe da sassafe xasu wuce abuja sai da kowa ya tafi sannan ya nufi mota Inda nauwara take xaune abdulkareem ne da maryam matar shi a gaba nauwara tana xaune a baya bud'e motar yayi ya shiga suka tafi yana xolayar shi ko ya kirawo aunty asma'u ta d'auki nauwara xuwa gida gobe a kawo ta da yamma tunda yanxu dare yayi bai kula shi ba haka yake ta tsokanar shi har suka K'arasa gida Aunty maryam ce ta rakata har part d'inta tukunna tayi mata sallama ta fice basu tsaya ba sai a gidan su don ba k'aramin gajiya suka yi ba Gaskia nauwara bata da bakin gode wa su umma yanda suka k'ayata mata Wajen ta ba k'aramin kud'i suka kashe ba wannan ko su ammin ta iyakar abin da xasu xuba mata a nutse ya shigo bedroom d'in da sallamar shi dummmm gaban nauwara ya fad'i tuni tsoro ya kamata.... *Aishat A muh'd* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 67~* Dummmm gaban nauwara yayi mugun fad'uwa jin sallamar abduljabbar muryar ta na rawa dakyar ta iya amsa sallamar xama yayi kusa da ita tare da sa hannun shi ya bud'e fuskar ta kallo d'aya yayi mata ya fuskanci yanayin tsoro a tattare da ita "baby na bakya jin xafi ne?" Cewar abduljabbar yana kamo hannun ta tare da murxa su a hankali jin tayi shiru sai shashshak'ar kukan ta kawai yake ji cika mata hannu yayi shi fah bai iya wani rarrashin mace ba toh ya xai yi ya tambayi xuciyar shi ko dai Bari nayi mata yanda ake rarrashin jariri Idan yana kuka yana gama yanke shawarar nan ya d'auke ta cak ya d'ora ta kan cinyar shi tare da warware laffaya dake jikin ta jin yanda jikin ta yake rawa yasa shi cewa "relax nauwara ki nutsu wannan rawar jikin naki da tsoro yayi yawa Kinsan ina son ki baxan cutar da ke ba" Rarrashin ta ya dunga yi har ya samu ta nutsu jikin ta ya dai na 6ari ganin tana kok'arin yin bacci yasa shi rad'a mata a kunne "baby na ki tashi mu yi nafila ta godewa Allah da bamu ikon mallakar junan mu ki samu kici wani abun don ina lura dake a wurin dinner baki ci komai ba" D'an turo bakin ta tayi tace " ni Allah bacci nake ji na gaji " hannun shi yake kan bakin ta ya d'an buge shi Kad'an cikin wani irin salo yanda Tayi magana acikin shagwa6a shima cikin shagwa6ar yace "nak'i wayon yarinya Kinsan dai wannan daren mai mahimmanci ne a gare mu ba bacci " ya K'arasa fad'i cikin tsokanar ta tuni idon nauwara ya raina fata jin abin da abduljabbar yake fad'i er sakewar da tayi dashi yanxu tuni tsoron ya dawo sabo ganin yanda ta firgice abin ya bashi dariya sosai tuni ya fara yi mata dariyar mugunta dakyar ya had'iye dariyar shi jin har ta fara d'an kuka "kin fiye tsoro da yawa habibty oya tashi kije kiyi alwala ko ni xai kai ki toilet d'in.. " Bai gama rufe bakin shi ba xumbur ta mik'e daga jikin shi da sauri tayi hanyar toilet Har tana tuntu6e bin ta da kallo yayi yana girgixa kai Tana shiga cikin toilet d'in sai taji wani yanayi a jikinta wanda ya tabbatar mata period d'in tace ta xo wani irin sanyin dad'i taji ya xiyarci xuciyar ta sai a lokacin taji hankalin ta ya d'an kwanta cikin sauri ta had'a ruwa mai d'umi a bath tayi wanka sai da ta gama wanka ta fara duba cikin toilet ko xata ga pad tana cikin duba wa har Allah ya taimake ta ta samu ta gyara jikinta sannan ta sa rigar wanka fara ko gwiwar ta bata kai ba kallon jikinta tayi tace "tabbb a hka xan fita gaban Yah abduljabbar ni wlh kunya nake ji " tana Murgud'a baki ita kad'ai tana nan dai a tsaye ta kasa fita Kamar ance ta Kalli madubin toilet d'in ta had'a ido da abduljabbar yana jingine jikin kofar ya harde hannuwan shi a kirjin shi yana kallon ta shima yayi wankan shi ya shirya cikin sleeping dress kalar light blue jin ta dad'e a toilet d'in ya biyo ta Wata er k'ara ta saki xata xube a k'asan toilet d'in cikin xafin nama ya taro ta jikin shi daukan ta yayi kamar wata er baby suka fito daga toilet d'in kan bed ya kwantar da ita sannan ya bud'e wardrobe wata night gown blue colour ya d'auko mata tukunna ya koma Inda ya barta duk ta tukunkune jikinta waje d'aya hannun shi yasa xai kunce abin da ake d'aure rigar xumbur ta tashi xaune gaban sai fad'uwa yake cikin dariya yace "ba fah wani abun xan miki ba kaya xan sa miki tun da wannan abin yaxo ya katse min hanxari " Xaro ido tayi tana mamakin yanda ake ya gane halin da take ciki hure mata idon Yayi yana cewa "Ki daina mamaki yanda akai na gane hkan " Ganin duk ta k'asa sakin jikin ta ya sashi mikewa ya fita daga d'akin ai kuwa da sauri ta sanya night gown d'in har da sa hijab a Hka yaxo ya same ta kaji da drinks fresh milk da ya siyo dakyar ya lalla6a taci Kad'an ya kwashe komai ya mayar dasu kitchen sannan yaja hannun ta xuwa toilet suka yi brush sannan suka fito Kwantar da ita yayi kan bed tare da rufe ta da blanket abin sallah ya shimfid'a ya fara nafilfilo tun tana kallon shi yana yin sallahr a nutse har bacci yaci k'arfin idon ta, bayan ya gama sallahr yayi addu'o'in shi sannan ya juyo yaga har tayi bacci duk ta yaye rufar jikinta d'an murmishi yayi Kafin ya tashi ya kashe light d'in d'akin gaba d'aya ya kanta tare da janyo wa ta jikinshi ya rungume ta tsam da haka bacci yayi awon gaba da shi A hankali ta bud'e idon da sauri ta runtse idon saboda hasken ranar da ya hudo ta tsakanin labule sake bud'e idon tayi ta tashi xaune tare da yin mik'a tana addu'ar tashi daga bacci toilet ta fad'a wanka tayi ta fito a gurguje ta shirya cikin wani swiss less blue da touch d'in pink a jiki d'inkin riga da siket ne ta d'anyi light make up sannan ta fesa different perfumes a jikin ta agogo ta kalla ganin har 10 na safe yayi gyaran d'akin ta fara yi cikinta sai kugin yunwa yake tsaya wa tayi tana duba d'akin don ganin yayi mata yanda take so bata ji bud'e kofar shi ba sai jinta da tayi a jikin shi ya rungume ta ta baya ya xuro da hannun shi ta tsakanin gefe da gefen ta ya rik'e hannayen ta xuro da kanshi yayi ta kafad'ar ta a kunnen ta ya rad'a mata "habibty har kin tashi?" xame wa take kok'arin yi ajikin shi don ta samu damar tsugunna wa ta gaida shi ya sake rik'e ta tsam yana shinshinar wuyanta cikin sark'ewar murya tace "ina k'wana Yah abduljabbar? " "lafia ba lafia ba " da sauri tace "me ya faru? " nauwara ta fad'a tana d'an waro ido " bayan baccin ki kika yi kin kyale ni da juyi " ya fad'i hkan yana jiyo da ita suna kallon junan su cikin er kunya tace "Kaiii Yah abduljabbar " "Ehh ai gaskia na fad'a " yana kashe mata ido d'aya d'an turo bakin ta tayi yarrr yaji wani abu ya tsarga mishi ganin yanda tayi da baki kafin ta ankara taji bakin shi cikin nata yana kissing d'in ta Sun d'au wajen mintuna 5 a Hka Sannan ya sake ta duk kan bed suka xube suna mayar da numfashi a kunyace ta tashi yasa hannu ya xaunar da ita kan cinyar shi yana cewa "ina xakiji " Jikinta a sanyaye hka ma muryar ta tace "kitchen xan je na had'a mana breakfast " "ai breakfast is ready don umma ta aiko mana dashi tashi muje ki gani" Hannun ta ya rik'o suka fito falo har xuwa inda dinning table yake jere da abinci don hka kitchen ta shiga ta d'auko plates,forks da spoon sai cups di'n shan tea sai da ta wanke su tukunna ta fito daga kitchen d'in ta tarar dashi yana amsa waya hka ta xuba mishi chips nd eggs da plantain sai er source a gefe sannan ta hada mishi tea ta ajiye a gaban shi ita ma ta janyo cup ta had'a tea tana kok'arin xama ya rik'o ta ya xaunar da ita kan kafar shi sai da ya gama wayar sannan ya ce "oya bud'e bakin don dura xanyi miki jiya bakici abincin kirki ba " A kunyace ta bud'e bakin yana bata shi ma yana ci har suka kammala Fito wa main parlour suka yi ya kirawo jiddah a waya ta fito yana son ganin ta sai da ta6a lokaci Sannan ta fito tana faman cika tana batsewa sai hararar nauwara take wadda ke xaune kusa da abduljabbar kanta a sunkuye nasiha sosae yayi musu da su xauna lafia da juna baya son tashin hankali bayan ya gama ya buk'aci ko da me magana toh duk a jikin su ba wanda yayi magana daga K'arshe yayi musu addu'ar xaman lfy yana gama wa ta tashi ta fita daga falon ko gaisuwar nauwara bata amsa ba Komawa sukayi part nauwara ko xama basu yi ba suka fara jin danna door bell kallon ta yayi yace "Wannan al'adar tana ban haushi wlh ace wai Idan mutum yayi aure ayi ta xuwa ana damunshi "Mtsww yaja tsaki yana ta mita tana jin shi dariya ce ta kusa kubce mata amman ta danne basu ankara sai jin sallamar mutane suka ji alamar har an bud'e musu kofa da aunty asma'u ya fara had'a ido harara ya dalla mata tare da had'e rai don da gaske sun bashi haushi dariya ta tuntsire da ita tana cewa "auu ashe angon yana nan tunda mun xo ai sai ka fita daman ai ba muxo kai amarya ba " Mtsww yaja tsaki ya tashi xai fita yaja kunnen aunty asma'u er k'ara ta saki bai kulata ya fice yayin da tace "yau kuma ni xa'a yiwa muguntar lallai abdul" Mutanen wurin sai dariya suke masu gaida su nauwara tayi sannan ta shiga kitchen tana kok'arin kawo musu drinks fa'iza ta shigo kitchen d'in da gudu ta rungume suna dariya ita ta taimaka mata suka kawo musu drinks da snacks sannan suka kule a daki suna xuba hira fa'iza tana fad'a mata yanda tayi kewar ta sannan ta bata sak'on saleem yana gaida ita Sai wurin la'asar su aunty asma'u suka tafi Amman Kafin su tafi sai da kai wa jiddah nauwara akayi musu er nasiha ta xaman lfy tun da duk en uwa ne fa'iza bata bisu ba sai da ta taimaka wa nauwara ta gyara ko'ina tare da turare ko'ina da turaren wuta ko'ina ya d'auki k'amshi sannan tayi mata sallama ta tafi.... Aishat A muh'd ?🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 68~* Bayan tafiyar fa'iza wanka ta shiga tayi ta shirya cikin wata atampha d'inkin riga da siket sun amshe sosai light make up tayi kitchen ta shiga ta d'auko kayan abincin da umma ta aiko musu dashi na dare ta jera kan dinning table sannan ta yanka fruits a wani kyakkyawan bowl ta sanya a frige yayi sanyi sannan ta fito parlour kwanciya tayi kan kujera tana kallon wani series film a mbc bollywood tana xaune anan har aka idar da sallahr isha'e tana tunanin ina Yah abduljabbar ya tsaya sai lokacin ta tuna wayarta bata sa charge ba a kashe take bedroom ta shiga tana duban Inda ta ajiye wayar sai ta ganta kan bedside di'n gado tana jikin charge Allah sarki Yah abduljabbar ashe ya samin charge mybe yana ta kira na yaji a rufe tana kok'arin kunna wayar ya shigo bedroom d'in da sallama d'ago kai tayi ta ganshi ya tsaya alamar akwai abin da yake so tayi mishi ganin bata gane abin da yake nufi ba sai kallon kallo suke cikin murmishi yace "habibty baxan fah k'arasa shigo ba sai Kinxo Kinyi min Oyoyo " Babu musu ta tashi a nutse cikin tafiyar ta ta d'aukan hankali ta K'arasa inda yake ai kuwa ya bud'e hannun shi ta shiga ya mayar ya rufe ajiyar xuciya suka saki lokaci d'aya ya dago kanta yana kallon kyakkyawar fuskar ta yace "kin ga na dad'e ko kiyi hak'uri na tsaya sallama da sauran mutanen da suka rage basu tafi ba sannan na biya ta wajen umma gashi nayi try d'in number ki a kashe I hope kinci abinci" Ya K'arasa fad'i yana shafa cikinta cikin murmishi tace "naci kai fah " "ai ni tun breakfast d'in safe ban k'ara cin komai ba " zaro ido tayi cikin tausayin shi tace "toh mu je kaci yanxu amman ka dai na xama da yunwa don Allah " Yaji dad'in abin tace yana fatan xai samu kulawar da yake buk'ata Wajen nauwara langa6e kai yayi yana cewa "an gama habibty baxan k'ara ba" Xuba mishi abincin tayi da ido yayi mata alamar ta bashi abincin a baki hka ta daure take bashi har ya koshi sannan ta had'a mishi ruwan wanka yayi wanka bayan ya gyara jikin shi ta kawo mishi fruits di'n da ta yanka d'axu ai kuwa yaji dad'i don yana son shan fruits sai dai jiddah baxa had'a mishi ba sai dai idan yaje wurin umman shi "Allah yayi miki albarka sweety nah" Itace kalmar da ya fad'i mata cikin murmishi jin dad'i ita ma ta amsa da "Ameeen " Sun d'an ta6a hirar su irin ta mata da miji Kafin ya rungume ta a jikin shi suyi bacci Tohh acikin en k'wanakin har xuwa lokacin da nauwara tayi Sati d'aya a ranar da tayi wanka period d'in ta ya d'auke a ranar abduljabbar xai bar d'akin ta baiso hkan ba amman bashi da yanda xai yi tunda hka addini ya tsara Acikin k'wanakin nan ba k'aramin shakuwa da juna suka yi ba sosai nauwara take yi mishi biyayya da kyautata wa har wata er k'iba yayi ta kwanciyar hankali duk abin da yake so tana kok'arin yi mishi duk wani tsoron shi da take da ta daina ya janyo ta jikin shi sosai ya koyar da ita darrusa masu wuyar fassara kallon ta kawai ba k'aramin sashi farinciki yake ba Tana kiran su umma a waya su gaisa ta kirawo fa'iza da saleem su sha hirar su sosai, yau gaba d'aya hka ta wuni cikin sanyin jiki saboda abduljabbar xai koma d'akin jiddah ya sabar mata da abubuwa sosai gashi xatayi missing di'n shi na tsayin k'wana 2 Bayan ta idar da sallah isha'e ne ta fito babban parlourn Inda xasu yi dinner d'in dare so yake ya had'a su a dunga cin abinci tare ko sa saba da juna xama tayi kan kujera ba kowa a parlour alamar abduljabbar bai dawo ba jiddah kuma ana d'aki Sallamar shi ce ta katse mata tunanin da take da sauri ta tashi xata rungume shi sai ta tuna yau jiddah ce da wannan tar6ar xata juya kenan da sauri yasa hannu ya rungumo ta jikin shi yana cewa "ya xaki juya kuma bayan kuma Kinsan ke nake jira? " Cikin sanyin murya tace "kada aunty jiddah ta fito ta ganmu a haka baxa ta ji dad'i ba" Mtsww yaja d'an k'aramin tsaki "toh ai ba wani abun muka yi ba" Suna cikin haka jiddah ta fito daga part d'in ta nan nauwara ta fara kici kicin kwace jikin ta amman sai ya sake Kank'ame ta ba k'aramin haushi ya bawa jiddah ba wani kishi ne ya kamata a fusace ta juya xata koma d'aki taji muryar shi yana cewa "ina kuma xaki tafi ki xuba min abinci yunwa nake ji" Juya wa tayi cikin 6acin rai ta nufi wajen dinning table tana gunguni, kamo hannun nauwara yayi suka K'arasa wajen tare da xama suka fa cin abincin toh ita dai nauwara Kad'an ta iya ci don abincin bai yi mata tana gama wa ta mik'e tsaye tana yi musu sai da safe da sauri ya Kalle ta yace "ba dai bacci ba tun yanxu? " Hammar k'arya tayi tace "bacci nake ji Allah " "okay ki Bari na rakaki " "ah yi xaman ka, aunty jiddah asuba ta gari " Harara ta watsa mata cikin tsanar ta hakan da tayi yasa nauwara wani dabara ya fad'o mata K'arasa wa tayi inda abduljabbar yake xaune ta rankwafo xuwa dai dai fuskar ta bashi peck a tsakiyar leb'en shi tare da cewa "xanyi missing di'n ka baby nah gud nyt " Tana gama fad'in hka ta wuce cikin tafiyar ta ta jan hankali don ta kular da jiddah kawai tayi hkan dariyar mugunta ta dunga yi a xuciyar ta Sakin baki Jiddah tayi tana ganin wannan felek'en na nauwara xuciyar ta idan tayi dubu ta 6aci ga wani mahaukacin axabbaben kishi ya rufe ta shi kuwa abduljabbar mamakin abin da nauwara tayi ya dunga yi amman kuma tayi bala'in birge shi wani sonta da k'aunar ta tare da sha'awar ta suka k'ara shigar shi yana murmishin jin dad'i yace "jiddah kinga yanda ake kula da miji ya kamata ki d'auki course" Fuuu ta tashi a fusace ta bar wajen dariya sosai ya bata shima nashi d'akin yayi toh har bacci ya d'auke shi jiddah bata shigo d'akin ba yasan tayi fushi kuma bashi da lokacin tsayawa rarrashin ta da tunanin nauwarah bacci ya dauke shi Hka yayi kwanakin shi Biyu a matsayin jiddah ce ke da girki sai dai ta d'au fushi sosai ko d'akin shi Bata xuwa shi kuwa abduljabbar a en k'wanakin nan wata irin sha'awa ce take masifar damun shi gashi da mata 2 a gida amman bai samu yanda yake so ....... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 69~* A yau ne nauwara ta amshi girki don hka tun safe ake aiki ta gyara ko'ina kitchen ta shiga da kanta ta shirya musu abincin dare tuni gidan ya d'auki k'amshin girkin da take bayan ta gama ta shirya su akan table duk abin da xasu buk'ata na wajen cin abincin ta ajiye shi wanka ta shiga tayi ta shirya cikin wasu english wears siket ne dogo bak'i da wata er top maroon colour ta gyara gashin kanta ta had'e shi da ribbom sai tayi rolling d'in kanta da black d'in veil tayi kyau sosai ta fesa different perfumes a jikin ta Xama tayi tana jiran dawowar abduljabbar ko 5 mint batayi da xama taji sallamar da sauri ta tashi ta nufi inda yake tsaye hannun shi yasa ya rungumo cikin jikin shi tare da shak'ar k'amshin turaren ta cikin kunnen ta ya rad'a mata "Kinyi kyau babyna I luv u" Cikin d'an murmishi tace "i luv u too yayanah " Sake rungume ta yayi a jikin shi cikin tare da kai bakinshi kan bakin ta lumshe idon ta tayi jin shigar bakin shi cikin nata sun dad'e a hka gaba d'aya jikin shi rawa yake ya gama rikice wa dakyar ya iya sakin ta sai faman ajiyar xuciya yake saki nauwara ta d'ago kanta ta kalle shi duk idanun shi sunyi ja sosai sai da gabanta ya fad'i ganin yanda ya koma lokaci d'aya "bari naje na kirawo aunty jiddah muci abinci " Ta fad'a cikin rawar murya gid'a kai kawai ya iya yi don ya kasa magana saboda yanayin da yake ciki hakan ba k'aramin k'ara tsorata nauwara yayi ba hka ta fice xuwa part din jiddah tayi knocking da har tayi tunanin juya wa ta tafi ganin ba'a bud'e ba sai taji an bud'e kofar juyo wa tayi suka had'a ido da jiddah cikin d'an murmishi tace "aunty jiddah ki fito muci abinci " Harara ta dalla mata sannan tace "baxan ci ba kuma wlh daga yau kada na k'ara ganin Kinxo min d'aki " "ikon Allah " Nauwara ta fad'i tana ta6e baki a fusace jiddah tace "uban me kike nufi nace baxan ci ba ki bar nan Kafin naci uban ki daman haushin ki nake ji shegiya mai kama da aljanu" Garam ta ja kofa ta rufe ta bar nauwara a tsaye girgixa kai kawai tayi "Allah ya shirya " Abin da ta fad'i tana juya wa bata sa abin a ranta ba tasan xata aikata abin da yafi hka ma Inda ta barshi a hka taxo ta same shi "Yah abduljabbar ka tashi muje muci abinci " Dakyar ya iya tashi tsaye suka nufi dinning table gaba d'aya ta kasa cin abincin sai juya spoon di'n take saboda yanda gaba d'aya Abduljabbar ya kafe da ido duk a tsorace take K'arshe ma tashi tayi xata gudu d'aki tana tunanin tana shiga d'aki xata danna key a kofar sai taji ya fisgo ta jikin shi yana cewa "ba dai har kin koshi " A tsorace ta d'aga kan ta alamar ehh ta koshi d'an murmishi yayi Kafin yace "kin tabbatar don ina so kici ki koshi kada na baki wahala" K'ululu cikin nauwara ya bada sautin hka ta kasa cewa komai duk a firgice take har xuwa lokacin da yaja ta bedroom d'in shi ya xaunar da ita kan bed sannan ya shiga toilet a gurguje yayi wanka ya fito d'aure da rigar wanka kasa d'ago kanta tayi ta kalle shi yana goge gashin kan shi da k'aramin towel yace "habibty kije kiyi wanka " Da sauri ta tashi xata fice daga d'akin yace "ina kuma xaki tafi" "am am xan je nayi wankan ne " Ta fad'a cikin rawar murya kamar yasan abin da take son aikatawa yace "Wannan toilet d'in d'akin laifi yayi miki da baxa ki shiga ba" Sum sum tayi ta shige toilet d'in a hka tayi wanka ta d'aura towel Kasa fito wa daga haka tayi ta tsaya sai faman safa da marwa take tana yarfe hannu hannun ta Jin shiru har yanxu bata fito ba yasa shi bin ta toilet hannun shi yasa ya d'auke a tsorace ta bud'e baki xata saki ihu yayi saurin rufe mata bakin ta da nashi har suka K'arasa kan bed ya kwantar da ita hannun shi yasa yayi switch off d'in hasken d'akin Cikin rawar jiki ya fara aika mata da wasu xafafan sak'onnin shi lokaci d'aya ya fita daga hayyacin shi yayin da nauwara ta fara kuka ganin yana kok'arin kunce towel d'in jikinta wani karfi taji ya xo mata batasan lokacin da ture shi ba daga jikin ta da wani bala'in gudu ta bar d'akin nashi ta shiga d'akin ta key ta yiwa kofar tana faman ajiyar xuciya gaba d'aya ta gama tsorata da Yah abduljabbar "noooooo nauwara kada kiyi min haka ki taimaka min pls" Juyi yake kan bed ya rasa abin da yake mishi dad'i xumbur ya mik'e tsaye yana cewa "baxan iya hak'ura da ke ba nauwara a yau di'n nan " Fita yayi daga bedroom d'in nashi ya nufi d'akin nauwara ya ta6a kofar yaji ta a rufe knocking ya fara yi mata amman nauwara tsoro ya hanata bud'e wa gaba d'aya ya hargitsa bashi da nutsuwa a tattare dashi Duk abin da suke jiddah na jin shi kuka ne ya kubce mata saboda bala'in kishi duk abduljabbar ya mayar da kanshi wajen nauwara kamar bashi ba Duk miskilan cin nan nashi Indai a gabanta ne baya yi Ganin tana 6ata mishi lokaci tak'i bud'e kofar duka d'aya yayi wa kofar ta rufta ciki duk kuwa da karfin kofar haka ya 6alla ta ya shiga cikin cikin d'akin d'akin duhu dulum Inda shashshak'ar kukan ta yake ji nan yayi ya kamo ta ya hada ta da jikin shi cikin rawar jiki ya fara sarrafa ta yanda yake so gaba d'aya ya gama fita a hayyacin shi kuka nauwara kuwa ta k'asa ma da hka har abduljabbar ya cimma burin shi Bayan komai ya kammala ya d'auke ta cak toilet yayi da ita ya taimaka mata tayi wanka sannan ya fito da ita shi ma yayi nashi lokacin da ya fito tuni xaxxafan xaxxa6i ya rufe nauwara nan dakyar ya lalla6a ta tasha magani sannan ya rungume ta bata dad'e ba bacci ya dauke ta yayin da shi kuma xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki yanda ya samu nauwara a yau sake rungume ta yayi xuciyar cike da farin ciki yayin da sonta ke k'ara ratsa xuciya shi da hka bacci ya d'auke shi *ASUBA TA GARI NAUWARAN ABDULJABBAR* Aishat A muh'd ☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _nagode da yanda kike k'aunar littafin nan hafsat muh'd Abdullah (ibsart) wannan page d'in sadaukar wa ne gare ki_❤ *~Pg 70~* Da asuba ya tashi ya tafi masallaci har ya dawo nauwara bata iya tashi ba tana baccin ta xama yayi kusa da kanta ya sunkuyo da kanshi saitin fuskar ta ya xuba ido ya jima yana kallon ta sannan ya fara shafa mata fuska a nutse ta bud'e idanun ta suka sauka a kanshi lumshe idon tayi tana tunano abin da ya faru tsakanin su jiya da dare wata iriyar kunya ce ta lullu6e ta ta kasa tashi cikin murmishi yace "morning cwt baby " Kau da kai tayi tare da xum6ora baki sannan ta juyo ta kalle shi ganin yanda ya xuba mata ido yana kallon ta sai ta d'an harare shi er dariya yayi yana cewa "I'm so sorry baby nah duk ke kika jawo hakan amman baxa k'ara wahalar da ke ba" Ya fad'i yana rik'o kunnen shi duk biyun Ya wani marairaice fuska sai abin ya bata dariya duka ta kai mishi a faffad'en kirjin shi hannu yasa ya fisgo ta jikin shi da sauri ta saki er k'ara Kad'an tana cewa "Arghhh" A rud'e yace "mai ya faru habibty " Cikin shagwa6a tace "ba kai bane ba ka janyo ni da karfi" "sorry mu je ki sallah " Shi ya d'auke ta ya kai ta toilet sannan ya fito wayar shi ne ya d'auki ringing d'an tsaki yaja kowa ne xai dame shi da sassafen dauka yayi da niyyar kashe wayar gaba d'aya sai yaga ogan shi ne yake kira da sauri yayi picking d'in wayar bayan sun gaisa yake sanar dashi wani aiki ne ya taso ana neman da gaggawa nan da 1 na rana ya taho abuja ya amsa okay sir sannan ya ajiye wayar xama yayi yana tunanin gaskia baxai iya tafiya ya bar nauwara sai dai su tafi tare abdulkareem ya nema a waya yana fad'a mishi yayi mishi buking d'in jirgi wanda xai tafi abuja shi da nauwara sannan ya juyo yana kallon nauwara da ke sallah Tashi yayi ya fita don shiga kitchen ko tea da eggs ne ya soya musu suyi breakfast tsaya wa yayi a kitchen d'in yana tunanin ta yanda xai fara bai iya girki ba flaks di'n shayi ya duba Allah ya taimake shi da akwai don hka ya d'auko frying pan Ya d'ebo eggs da yawa ya fara fasa wa bayan ya gama ya d'auko maggi ya xabga da yawa sannan ya fara yanka albasa tuni ya fara hawaye saboda irin mai shegen yajin nan ce ita ma ya xuba sannan ya kunna gas ya d'ora frying pan ya xuba mai da yawa bai jira yayi xafi ba ya k'wara eggs d'in akai yana jira ya siyo Bayan ta idar da sallah wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya cikin wata yellow d'in atampha tayi kyau sosai ta d'an yi light make up ta xura sark'ar ta da abin hannu tana cikin fesa turare ta fara jin tashi kauri da sauri ta K'arasa fesa wa ta fito falo kitchen ta nufa don ta nan take jin kaurin turus tayi ta tsaya ganin abduljabbar sai faman had'a gumi yake yana kok'arin juya Kwan ya kasa da sauri ta K'arasa wajen ta kashe gas d'in tare da kamo hannun shi xuwa Wajen sink ta wanke mishi sannan ta janyo shi suka fito xuwa falo dariya ce ta kubce mata ganin yanda ya koma lokaci d'aya ganin tana mishi dariya yasa shi biyo ta da gudu suka dunga xagaye falon har yayi nasarar kamata "Yawwa yarinya na kama ki xo ki fad'a min wa kike wa dariya" Danne dariyar ta yi tace "ni ba dake nake ba fah" "toh da wa kike?" Yatsine fuska tayi tare da xum6ora baki tace "kawai haka kawai dariyar ta xo min " Har ya bud'e baki xai yi magana yaji wayar shi tana ringing don hka ya dauka yana amsa wa bayan ya ajiye wayar ya mik'e tsaye yana cewa "baby nah ki shirya kayan ki xamu shige abuja yanxu " waro ido tayi waje tace "da gaske kake ?" "ba da wasa nake ba habibty " Tsalle tayi tare da shige wa d'aki da gudu da kallo ya bita yana dariya yaji dad'in yanda ta nuna murnar xata bishi Cikin kankanin lokaci suka gama shirya wa ko breakfast basu yi ba yace su Bari Idan sun je gidan umma sa ci bayan ya gama fitar da kayan su driver ya xuba a boot sannan ya nufi d'akin jiddah da sallama ya shiga tana kwance kan gado ko wanka batayi ba tana sanye da sleeping dress bata amsa mishi sallamar ba kallo d'aya yayi mata yaji tausayin ta idanun ta sun kad'a sunyi ja dasu duk sun kumbura alamar Kwana tayi tana kuka xama yayi kusa da ita ya kamo hannun ta da sauri ta kwace hannun tana watsa mishi harara murmishi yayi yana cewa "jiddah rigima to yau kuma laifin me nayi? " Bata kula shi ba ganin haka ya mik'e tsaye yana cewa "sauri nake abuja xan wuce har da nauwara don hka ga wannan... " Ya fad'a cikin yana Mik'o mata kud'i kallon shi tayi tare da d'an jan tsaki a fusace tace "bana so nagode aje a gyara wa amarya kofar da aka 6alla dasu" wata er kunya ce ta kamashi yana sosa kai yace "nasan da hka amman ki kar6a hakk'in ki ne" "ni fah bana so na fad'a maka" Share ta yayi ya ajiye su akan dressing mirror ya juya ya tafi kwafa ta saki tare da cewa "xakai bayani wlh sai na raba ka da wannan tsinanniyar yarinyar " Sun isa gidan umma anan suka yi breakfast sannan suka yi musu sallama basu had'u da fa'iza da saleem ba sun tafi skul suna isa airport ko 10 mint ba suyi ba jirgi ya tashi, suna isa gidan ya fita saboda ana neman shi a wajen aiki ya bar nauwara ta xage tana gyaran gidan Duk da ba wani datti yayi ba bayan ta gama tayi wanka sannan ta 6ingire da bacci cike da gajiya Tun bayan tafiyar su tana tunanin wajen wa xataje ya bata shawarar fitar da nauwara daga xuciyar abduljabbar yaji ya tsane ta baya son ganin ta wayar ta ta d'auko ta duba contact di'n ta gaba d'aya ta rasa wanda xata kirawo idanun ta ne ya sauka akan number d'in farida bata tsaya tunani ba ta danna mata kira don idon ta ya rufe mafita take nema bayan sun gaisa take kora ta bayani ai kuwa tace su had'u a office gobe xasu tattauna yanda xasu 6ullo abin ba k'aramin jin dad'i tayi ba Washe gari da xumud'i ta K'arasa office nan suka had'u da farida suka xauna shawarar yanda abduljabbar xai tsani nauwara har takai ya rabu da ita gaba d'aya Yinin ranar basu yi aikin kirki a office ba sai neman mafita suke daga K'arshe farida ta kama kunnen jiddah ta rad'a mata wata magana da farko ta d'an tsorata amman daga baya xai ta amince don itace kawai mafita tunda bata ra'ayin bin malamai da farin ciki ta dawo gida tana mai jin dad'in shawarar da farida ta bata........ Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 71~* Rayuwa mai dad'i suke gudanar wa abduljabbar da nauwara ba k'aramin kula dashi ba take tana tattalin shi bata gajiyawa da hidimar shi, shima anashi 6angaren yana tattalin ta sosai soyayya sosai suke xuba wa kuma suna kiran su umma su gaisa Kamar yau misalin karfe 8 na dare ta fito daga wanka tana d'aure da towel a jikin ta gaban dressing mirror ta tsaya tana gyara jikin ta a k'alla yau watan su 3 da xuwa abuja bata fita ko'ina ko gidan aunty asma'u ya hanata xuwa sai dai ita taxo tayi mata yini sannan yaran ta suna xuwa mata weekend don hka yau tayi niyyar sake tambayar shi ya barta taje gobe "habibty! " Taji muryar shi yana kiranta Kafin ta amsa ya shigo d'akin cikin sauri ya k'araso ya d'aga ta sama yana juyi da ita suna dariya kafin su xube kan bed suna mayar da numfashi cikin murmishin jin dad'i tace "sweetheart me yafaru naga kana cikin farinciki? " Yana gyara mata gashin kanta da ya barbaxu yace "kawai son ki ne yake kok'arin fasa min xuciya i luv u baby nah" Cikin jin dad'i tace "i luv u too my cwt dear" Nan ya fara aika mata da wasu xafafan sak'onnin shi yana nuna mata irin yanda yake sonta tuni sun fice daga hayyacin su kowanne yana kok'arin nuna wa d'an uwan shi yanda yake son shi Bayan sun yi wanka yana rungume da ita a jikin shi tana faman xuba mishi shagwa6a yana lalla6a hannun shi ta rik'o tana kallon shi cikin marairaicewa tace "my dear don Allah ka bar ni naje gidan aunty asma'u gobe plsss" Shiru yayi na d'an lokaci Kafin yace "bana son kina fita ne ana kallar min ke saboda Kinsan yanda nake bala'in kishin ki " "Don Allah ka barni naje idan xaka tafi office sai ka sauke ni kaga Idan ka tashi sai ka biyo mu tafi " Hannun shi yasa ya rik'o kumatun ta duk biyun yace "an gama ranki ya dad'e " Cikin d'oki tace "ka barni kenan? " Gid'a kai yayi alamar ehh yana murmishi nan ta fara murna ta rungume shi tana mishi godiya kafin ta sanya bakin ta cikin nashi nan salo ya canja suka fara faranta ran junan su Washe gari da wuri ta tashi duk ta gama abin da xatayi tayi wanka ta shirya cikin wani material pink colour tayi light make up ba k'aramin kyau tayi ba tana cikin fesa perfumes abduljabbar ya fito daga toilet ita ta taimaka mishi ya shirya cikin army uniform d'in shi sannan suka fito dakyar ta iya tsaya wa tayi breakfast saboda d'okin fita da har tace ta koshi ya d'an harare ta tare da cewa "Indai baki tsaya Kinyi breakfast sai a hak'ura da fitar " Da sauri ta fara cin abincin har ta bashi dariya saboda yanda take ci bayan sun kammala cin abincin taje ta d'auko mayafin ta da hill shoe sai handbag mahadin takalmin sannan suka fito da sauri driver di'n shi joseph ya taso ya bud'e musu motar yana kawo gaisuwa ga iyayen gidan nashi da fara'a nauwara ta amsa mishi sannan ya shiga yayi wa motar key suka fita daga gidan Sai da suka tsaya ta yiwa yaran aunty asma'u shopping tukunna suka K'arasa gidan yana rik'e da hannun ta har xuwa parlourn gidan suka shiga aunty asma'u da ke xaune a parlour ta mik'e tsaye tana amsa sallamar da sauri ta K'arasa wajen aunty asma'u suka rungume juna cikin tsananin farinciki tana yiwa nauwara sannu da xuwa yayin da abduljabbar yake a tsaye yana kallon su hararar shi aunty asma'u tayi sannan tace "uhm sai yanxu a kaga dama ta xo min koh? " Xama yayi kusa da nauwara yana cewa "yanxun ma sa'a kika ci na kawo ta" "ai sai ka d'auke ta yanxu ku tafi idan ka isa kabi ka kulle yarinya a gida ita kad'ai" "Kinsan xan iya mayar da ita gida yanxu idan kin cika baki " Ya fad'i yana er dariya girgixa kai kawai aunty asma'u tayi yayin da nauwara sai faman murmishin jin dad'i take bayan sun gama gaisa ya sunkuyo da kanshi saitin fuskar nauwara yayi kissing d'in ta a kumatu da saman leb'e yana cewa "sai na dawo habibty" Aunty asma'u wadda ta saki baki tana ganin rashin kunyar abduljabbar tace "Lallai abdul baka da kunya a gaba na" D'an hararar ta yayi sannan yana tafiya yace "so what! xan ma iyayin abin da yafi hka " Ya fice daga falon cikin tafiyar shi ta kasaita duk kunya ta rufe nauwara dakyar ta saki jikin ta suka sha hira har xuwa lokacin da yaran ta suka dawo daga skul cikin farinciki suka rungume ta suna bata labarin skul d'in su dariya ta dunga yi Kafin ta rarraba musu chocolates,sweets dasu biscuits masu dad'i ai kuwa suka dunga tsallen murna yinin farin ciki tayi ranar sosai Sai bayan mangarib abduljabbar ya xo yaran suka rungume shi suna xuba mishi surutu shi ma ya biye musu don yana bala'in son yara sai da suka yi dinner tukunna suka taho gidan su wanka suka yi kawai suka bi lafiyar gado tuni bacci yayi awon gaba da su Haka lokaci ya cigaba da tafiya kowanne yana tattalin d'ayan su xaman lfy suke sosai nauwara ta dad'a kyau tayi wani irin haske, sai da suka yi wata 6 a abuja basu xo kano ba saboda aikin da ya rik'e abduljabbar ba lokaci kullum cikin aiki yake Watan su bakwai suna can har abduljabbar yayi tafiya ta tsawon 1 month yana sa ranar Indai ya dawo xasu je kano dakyar ya barta ta koma gidan aunty asma'u Kafin ya dawo satin shi Biyu da tafiya nauwara ta fara rashin lafiya da xaxxa6in dare ta fara xuwa safe sai ya tafi tana yi a tsaitsaye har dai ya kwantar da ita har dasu amai ga rashin jin dad'in bakin ta Indai taji k'amshin abinci to baxa ta iya ci ba tuni aunty asma'u ta fahimci abin da yake damun ta amman duk da hka sai da ta kirawo wata k'awar ta likita ce ta duba ta nan ta gano ciki d'an wata uku daga aunty asma'u har nauwara bansan wanda yafi murna ba ba K'aramar kyauta aunty asma'u tayi wa likita nan ba nan ta rubuta magungunan da xata dunga sha xasu taimaka mata wajen rage amai da samu sauk'in xaxxa6in Sannan tayi mata allura ta tafi Ba wanda ya fad'a wa abduljabbar an Bari sai ya dawo yaji labarin su umma ma sun ji labarin don aunty asma'u ta fesa musu labarin umma dad'i ya isheta kasa hak'ura tayi sai da taxo abujan ita da aunty sadiya fa'iza da saleem haka suka biyo jirgi duk kunya ta rufe nauwara yini suka yi sai bayan mangarib driver ya kai su airport suka koma kano abba kuwa kiranta yayi a waya yayi mata sannu da jiki Hka aunty asma'u ta cigaba da kula da nauwara sosai Don ba k'aramin son ta take ba Ranar da abduljabbar xai dawo aunty asma'u da nauwara suka shiga kitchen suna shirya mishi abubuwan ci duk da jikin ta ba k'wari amman a hka take aikin aunty asma'u tayi tayi ta barta ta koma ta kwanta ita xata yi amman sai ta nuna ta gaji da kwanciyar, daman ta kaita wajen saloon anyi mata gyaran gashi da lalle ja da bak'i Bayan sun gama aikin suka shirya komai a kan dining table sannan ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin wani swiss less bak'i mai adon flowers pink a jiki d'inkin riga da siket sun xauna mata a jikin ta gashi less d'in ya haska ta abin ka da farin fata ga kuma hasken da ta k'ara na ciki tayi kyau bana Kad'an ba bayan tayi light make up ne ta xura siririyar sark'ar gwal a wuyan ta da d'an kunnen ta ta fesa perfumes design masu matuk'ar k'amshi mai dad'i tana gama wa ta Kalli madubi taga komai yayi kan sofa ta xauna tana ta6a charting a wayar ta ita da fa'iza har tana d'aukan pictures ta tura mata tana cewa ta taya ta gani ko tayi kyau katon heart ta turo mata sannan tace "Woww masha Allah a Gaskia Kinyi masifar kyau kamar ba ke ba kada yaya na ya susuce fah wannan irin haduwa " Dariya sosai ta bata nan suka cigaba da yin er hirar su hamma ta fara alamun bacci take ji abin ka da me k'aramin ciki bacci baya yi musu wahala suna cikin hira ta 6ingire da bacci akan sofa Bata dad'e da fara baccin ba abduljabbar ya shigo gidan aunty asma'u ya tarar a falo ta amsa mishi sallamar tashi xama yayi yana cewa "wai ina habibty take banji motsin ta na? " "ina tunanin tayi bacci fah " Cewar aunty asma'u cikin murmishi d'an xaro ido yayi yana cewa "lafia take bacci da yamman nan? " Hannu aunty asma'u ta mik'a mishi tana cewa "a bani goron albishir sai na fad'a maka " D'an hararar ta yayi yace "malama ni kawai ki fad'a min ina matata" "Allah sai ka bani xan fad'a " Lalubo abin da ke jikin shi yake duk abin da yake aljihun shi ya xube mata har da pistol di'n shi kud'in ta kwashe gaba d'aya ta bar pistol di'n a gaban shi sannan tace "kawo kunnen ka na fad'a maka" Mtsww yaja d'an tsaki yace "wlh kin fiye 6ata wa mutum lokaci ki fad'a min malama " "Allah sai ka kawo " Bashi da yanda xai yi Hka ya mik'a mata kunnen shi saboda ya matsu ta sanar mishi cikin murmishi tace "habibty di'n ka tana d'auke da ciki na tsawon 3 month " "bana son wasa asma'u ki fad'a min gaskia pls" Wani hawayen tausayin shi ne ya xubo mata ganin yanda jikin shi yake rawa tace "wlh da gaske nake tana bedroom d'ina " Da sauri ya shige ya nufi bedroom d'in aunty asma'u baccin ta take hankali kwance K'arasa wa yayi Inda take yayi mata d'aukan jarire yana juyi da ita a tsorace ta farka daga baccin jin ana juya ta had'a ido suka yi cikin tsananin farinciki ta rungume shi tana cewa "sannu da xuwa dear, yaushe ka dawo? " Kwantar da ita akan gadon yayi tare da d'aga rigar ta yana shafa cikinta sai faman murmishin jin dad'i yake ganin yanda yake shafa mata ciki hkan ya tabbatar mata da aunty asma'u ta fad'a mishi muryar shi taji yana cewa "nagode nauwarahh bansan da wanne baki xan gode miki ba " Kawai sai ga hawaye yana xuba a idon shi..... Aishat A muh'd 😘 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 72~* A kid'ime take kallon shi ganin yanda hawaye suka xuba a fuskar shi tausayin shi yayi bala'in kamata hannun ta tasa tana goge mishi hawayen cikin sanyin murya tace "Yah abduljabbar mene na godiya ni don Allah ka daina kukan nan pls " Hannayen ta ya kamo tare da kissing d'in su yana cewa "abin da na dad'e ina addu'ar Allah ya bani nauwarah ba dole nayi kukan farinciki ba" "tashi mu tafi gidan mu don baby na yaji d'umin abban shi " Murmishi tayi sannan tace "Haba dear ya kamata ka tsaya kaci abinci sai mu tafi " nok'e kafad'a yayi yana cewa ,"nak'i wayon yarinya tafiya xamu yi " Ya fad'i yana d'auko mata hijab bata da yanda xata yi hka ta kar6a ta sanya suka fito cikin mamaki aunty asma'u tace "ba dai tafiya ba?" "yini guda muke kitchen don had'a maka abincin tar6ar ka shine xaka wani ce tafiya xaku yi" Hka dai ya xauna dakyar ya tsaya ya ci abinci bayan sun gama Xasu tafi aunty asma'u ta mik'a mishi kud'in shi kallon ta yayi yace "ki rik'e su ladan albishir sannan ki saurari xuwan motar ki sabuwa dal ke dai ku cigaba da yi min addu'a baby na ya fito lafia" Dad'i ya kama aunty asma'u tayi mishi godiya tare da cewa "Insha Allah addu'a muna nan muna yin ta " Lokacin da suka K'arasa gida nan ya nuna mata irin kewar ta da yayi ba k'aramin tausayin shi tayi ba, sai da ya huta tsawon sati d'aya sannan suka tarkato sai Kano gidan umma suka fara sauka cikin farinciki umma ta had'a nauwara da abduljabbar ta rungume su Kafin a xauna aka gaisa tukunna ta gabatar musu da abincin da suka shirya musu bayan sun gama ci aka dawo falon umma ana ta6a hira har da aunty sadiya Da gudu ta shigo falon kan nauwara tayi xata xauna a jikin ta da sauri abduljabbar yace "baki da hankali ne fa'iza xaki xauna a kanta" "ya hak'uri Yayah wlh duk murnar ganin ta ne " Hararar ta yayi su umma suna mishi dariya can sai ga saleem nan ya shigo falon ya xama saurayi yanxu yana ss 3 a nutse ya K'arasa wajen abduljabbar yana gaida shi sannan ya gaida nauwara cikin tsananin jin dad'i take kallon saleem yaron akwai nutsuwa ga hankali ba ruwan shi da shashanci karatu kawai yasa a gaban shi Nauwara ta so ya barta ta k'wana amma fir yak'i amince wa dole ta tashi suka tafi nasu gidan a falo suka tarar da jiddah da gudu ta tashi ta rungume abduljabbar tana cewa "Sannu da xuwa sojana nayi kewar ka ba Kad'an ba" d'an jiyo tayi ta harari nauwara "Yawwa my jiddah nima nayi missing di'n ki " Wani irin axabbaben kishi ne ya tokare nauwara xame hannun ta tayi daga nashi ta nufi stairs 6angaren ta ta nufo ta bud'e wasu xafafan hawaye ne suka xubo mata a idanun ta tana son abduljabbar tana bala'in kishin shi amman tasan ba mijin ta bane ita kad'ai dole ta sasauta wa kanta wannan kishin tashi tayi ta fara gyara 6angaren nata sai da ta tabbatar ko ina yayi tsaf yanda take so sannan ta shiga toilet tayi wanka bayan ta fito ta shirya cikin wani jeans da er top marasa nauyi ta had'e gashin ta da ribbon sannan ta fito xuwa kitchen d'in ta saboda yunwa take ji abinci mara nauyi ta dafa sannan ta fito hannun ta rik'e da plate di'n abincin da fresh milk sai ruwa xama tayi a tsakiyar falon kan carpet ta hau cin abincin sai da ta koshi sannan ta jingina da jikin kujera Jin an bud'e kofar falon yasa ta juya wa kallo d'aya tayi mishi ta kauda kanta wani irin haushin taji da kishin shi suka had'ar mata saboda da ganin shi tasan anyi wani abun xama yayi kusa da ita ya talla6o fuskar ta yana cewa "sorry habibty na barki ke kad'ai ko " D'an murmishin yak'e tayi tace "Laaa ba komae ai aunty jiddah ya kamata a bata kulawa wajen wata 8 rabon ku da juna " kallon ta yayi cike da mamakin yanayin ta ya fuskanci kishi ne yake damun ta kamo ta yayi jikin shi yana cewa "ke ma ai Kina buk'atar kula wa fiye da ita" Ya K'arasa fad'i yana shafa cikinta kasa magana ma tayi don ji tayi tana bud'e bakin ta kuka ne xai xubo mata Haka dai ya rarrashe ta har ya kaita bedroom ya kwantar da ita tare da yi mata addu'ar ya rage mata hasken d'akin sannan ya sunkuyo ya sumbace ta sannan yace "Gud nyt habibty " Gid'a kai kawai tayi ya fita daga d'akin tare da janyo mata kofar wasu hawaye ne suka xubo daga idonta tashi tayi ta nufi toilet alwala ta d'aura bayan ta fito ta shimfid'a abin sallah ta fara nafilfilo tana rik'on Allah da ya sasauta mata wannnan kishin A Wannan lokacin jiddah ta fara ta ta rashin mutuncin ta da taji nauwara wai ciki ne da ita gashi yanda ta ga ana wani lalla6a ta daga abduljabbar d'in har mahaifiyar shi da sauran en uwan shi ta rasa inda xata sa kanta taji dad'i shine ta fito da salon cusguna wa nauwara amman bata ta6a kulata don hka sai ta yanke shawarar mai gaba d'aya *BAK'AR RANA!!!* Cikin nauwara ya kai tsawon 6 month's ya girma sosai kamar yau ta gama ayyukan ta kamar ko yaushe ta saboda yau abduljabbar xai shigo kano kuma a d'akin ta xai sauka ta gama shirya mishi komai tana shirin shiga wanka bacci ya dauke ta daman a gajiye take bata farka ba sai bayan sallahr la'asar dakyar ta iya mik'e wa ta shiga toilet don yin wanka ta gama wankan kenan tana cikin d'aura towel sai taji wata muguwar k'arar abu kamar k'arar harbi gabanta ne yayi mugun fad'uwa jikin ta ya hau 6ari da sauri ta yayibo hijab d'in da ta shigo dashi toilet d'in ta fito a kid'ime Turus tayi taja ta tsaya cikin tsananin kad'uwa ganin abduljabbar ne da sauri ta kawar da kanta saboda ganin yanda fuskar nan tashi a murtike ba alamar fara'a idanun nan nashi jawur dasu jikin shi sai faman 6ari ya ke saboda tsabar 6acin rai da sauri ta K'arasa wajen shi tare da kok'arin rik'e mishi hannu wata irin tsawa ya daka mata wadda har sai da d'an cikin ta ya motsa Kafin ta dawo dai dai taji saukan wani lafiyayyen mari guda biyu cikin kid'ima ta d'ago kanta ta kalle shi Idan idon ta ba gixo suke mata to hawaye ne ke fita a cikin su cikin fusata yace "na tsane ki nauwara na tsane ki na tsane ki nayi nadamar had'u wa ta dake nayi dana sanin auren ka kin cuce ni kin yaudare ni kinci amana ta me na rage Ki dashi a tsawon xaman mu " Daskare wa tayi a wajen jin maganganun shi tamkar a mafarki cikin rawar murya tace "me nayi maka Yah abduljabbar meya faru ka sanar da ni don Allah " A matuk'ar fusace yace "Har ni kike tambayar abin da kika aikata?? " Hannu ya dad'a fiddawa xan mare ta caraf yaji an rik'e hannun nashi da sauri ya d'ago kanshi don ganin waye hada ido yayi da umma kafin ya ankara yaji an mare shi cikin tsananin mamaki ya ke kallon umma ranta a 6ace tace "da hankalin ka abdul xaka dunga dukan mace mai ciki ko ka haukace ni?" "umma bakisan me tayi min ba fah kama ta nayi Tana...... " "shiiiii ban tambaye ka abin da ya faru ba shin yau ka ta6a ganin nauwara inace ke ne mutum na farko da xaka fara bada sheda akan ta shine babu bincike ba komai ka hau kai ka xauna ko " "umma ba wani bincike asirin tane ya cika kawai don na hak'ura da ita har abada" "wlh wllh Idan ka sake ta sai dai ka nemi wata uwar bani ba kaji na rantse " A xuciye ya fice daga d'akin yayin da umma ta juya wajen nauwara sai taga tayi baya xata xube cikin sauri ta K'arasa ta rik'e ta cikin tashin hankali ta fara kiran sunan ta amman shiru kake ji ta suma........ Aishat A muh'd 🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 73~* " Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun nauwarahhh!!!" umma ta fad'a da k'arfi tana jijjigata amman ko motsi Bata yi ba, a tsaye yake a falo xuciyar shi sai tafasa take saboda 6acin rai ruwa ya d'auko a frige yasha wajen rabin robar ragowar ya d'aga robar ya xuba a kanshi sannan yayi cilli da robar yana huci a dai dai lokacin yaji umma tana k'walla wa nauwara kira da gudu yayi bedroom d'in ta jiddah da take tsaye kusa dashi kamar ta yi rawa don murna tabi bayan shi da sauri Yana shiga d'akin idanun shi suka yi mummunan gani nauwara a kwance jini yana bi ta kafar ta ga umman shi na kuka tana kok'arin d'ago ta cikin sauri ya K'arasa xai taimaka mata "wlh abduljabbar kada ka kuskura ka ta6a " Cikin tsawa ta fad'i hkan da sauri ya janye hannun shi ya fice daga d'akin toh jiddah ma batayi gigin k'araso wa ba ganin ba fuskar magana Hka umma dakyar ta iya kai nauwara mota daman jiddah ce ta kirawo ta a waya taxo abduljabbar xai kashe nauwara lokacin ma fitar ta kenan daga gida xata je gidan aunty kausar bata jin dad'i shine ta taho hankalin ta a matuk'ar tashe shine taxo ta tarar da wannan tashin hankali Tun Kafin su K'arasa asibitin umma tayi wa aunty sadiya waya kan ta same ta a asibitin a lokaci d'aya suka iso asibitin ganin umma tana kuka aunty sadiya a tsorace take tambayar ta lafia bud'e mata bayan motar tayi ba k'aramin firgita tayi ba da taga halin da nauwara take ciki da gudu ta shiga cikin asibitin bata dad'e ba suka dawo da wasu nurses biyu da d'an k'aramin gadon da ake tura mara lafia suka d'auki nauwara aka dora ta akayi emergency room da ita Nan doctors suka Duk'ufa akan ta har Allah ya taimaka suka samu ta farfad'o bayan sun tsayar da jinin dake xuba a jikinta, suka sanya mata drip bayan sun mata allurar bacci sannan suka fito lokacin da likitan suka fito Har abba da abdulkareem sun k'araso hankalin su a tashe Suna xaune a office d'in doctor suna sauraren shi bayan ya gama rubutu acikin file ya rufe shi sannan ya fara da cewa "Alhmdullilah munyi nasara ta farfad'o yanxu muna buk'atar jini don a k'ara mata bcoz tayi bleeding da yawa " "doctor cikin fah ya xube ne?? " Umma ta tambaya cikin tsananin tashin hankali da tsoron jin abin da doctor xai ce d'an murmishi yayi sannan yace "babu abin da ya samu babyn yana nan lafiyar qlau " Ajiyar xuciya umma ta saki wadda sai da kowa ya ji a wajen abba yace "ina abduljabbar ne ko ba yau naji yana cewa xai shigo kano ba?" Nan take fuskar umma ta koma yanayin 6acin rai tsantsa ba wanda ya sake magana ganin hka yasa doctor ya fahimta akwai wata maganar Mai mahimmanci da xasu yi ta sirri don hka ya tashi ya bar musu office d'in Yana fita umma ta fad'a musu komai da abin da ya faru sannan ta d'ora da cewa "wai a fad'ar shi ya shigo d'akin ta ya kama wani namiji a kwance kan gadon ta ba kaya a jikin shi sai short nicker ga under wears d'in nauwara a had'e da kayan shi da ya cire ita kuma nauwara tana toilet bai yi nasarar kama shi ba har Harbin da yayi mishi bai same shi ya gudu " Cikin kukan takaici umma ta cigaba da cewa " kamar bai san halin nauwara ba daga ganin abu ba bincike ba komai ya fara dukan ta da tsohon ciki " Shiru duk suka yi aka rasa mai magana a cikin su dakyar abba ya iya cewa "Alhamdullilah tun da tana nan lafia sannan cikin bai xube ba shi kuma yaje rayuwa ce nauwara 'ya na dauke ta ba Inda xata je muna tare da ita Allah ya bata lafia " "Ameeen ' Suka amsa gaba d'aya sannan ya tashi yana cewa "abdulkareem muje ayi test d'in jinin mu idan yayi dai dai sai a diba " Abdulkareem wanda gaba d'aya baya cikin nutsuwar shi ya mik'e tsaye a sanyaye suka fice daga office d'in Lokacin da nauwara ta tashi daga baccin duk abin da ya faru ya dawo mata tayi kuka tayi kuka Har taji ba dad'i dakyar umma ta rarrashe ta tayi shiru wanka ta taimaka mata tayi ta fito sannan ta gyara jikin ta sai ga fa'iza nan tana kuka wiwi ta shigo d'akin ta rungume nauwara umma da aunty sadiya suna gefe suna kallon su cike da tausayin su Ba k'aramin dauriya nauwara tayi ba da tawwakali ta kauda duk wani abu acikin xuciyar ta amman ta rame sosai tayi fari sai katon ciki kamar xai rinjaye ta Sati d'aya tayi a asibiti suka sallame ta bayan sun tabbatar ba wata matsala haka suka tarkato suka dawo gida xuciyar kowa ba dad'i 6angaren abduljabbar ma baxan iya kwatanta muku halin da yake ciki ba ya bi duk ya rame saboda tsabar tashin hankali umma bata amsa gaisuwar shi abba ma baya sakar mishi fuska kamar da ana cikin hka aka tura shi wani course na tsayin shekara 2 wanda Indai yayi ya samu nasara xa'a k'ara mishi matsayi ba k'aramin jin dad'in hkan yayi ba saboda xai yi nesa da nauwara Hka ya tarkata ya tafi bayan ya lalla6a iyayen shi sun d'an sakko daga fushin da suke dashi suka bishi da addu'ar fatan alkhairi har ya tafi bai k'ara ganin nauwara ba Jiddah kuwa hankali ya kwanta tayi nasarar raba abduljabbar da nauwara masoyan da suke masifar k'aunar junan su yanxu bata da damu ko Kad'an _kuyi hak'uri da wannan wlh na fita unguwa ne sai kuma gobe xaku ji ni_ Aishat A muh'd ☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 74~* Aunty asma'u lokacin da taji labarin tayi kuka sosai ita ma a take ta k'arya ta hkan tuggu ne aka shirya don kawai a raba su ta kirawo abduljabbar a waya tana fara yi mishi xancen ya katse wayar ranta in yayi dubu ya 6aci akan abin da abduljabbar yayi nan ta shirya ta taho kano ba k'aramin firgita tayi ba lokacin da ta ga yanda nauwara ta koma sai katon ciki a gaba ta rungume nauwara suka dunga kuka sai da umma taxo tana mata fad'an ita da xata rarrashe ta xata xo ta sanya ta a gaba tana kuka haka tayi k'wanaki biyu ta tafi cike da tausayin nauwara a xuciyar ta daman ita tunda ta ganta jinin su ya had'u tana son nauwara, kausar ma bata ji dad'in abin da yayan ta ya aikata ba sai taja bakin ta tayi shiru fad'an da yafi k'arfin ka sai kaja bakin ka kayi shiru, fa'iza kuwa tayi bala'in tayi masifar duk a banxa tunda bata isa tayi a gaban shi ba sai dai ta rushe da kuka duk gidan ba wanda ya goyi da bayan abduljabbar, saleem ne bai nuna komai ba kawai da fa'iza ta gaya mishi sai cewa yayi "Allah ya kyauta" ya tashi xai fita daga d'akin duk da bai jin dad'in hkan ba a fusace fa'iza tace "toh sarkin hak'uri abin da xaka ce kawai " D'an murmishin yak'e yayi yace "toh me xance aunty fa'iza hak'uri xata yi kawai rayuwar nawa take indai har bata aikata hkan ba na tabbatar wataran sai Allah ya tona asirin wanda ya kulla mata sharrin " Yana gama fad'in hka ya fice daga d'akin yana goge hawaye afuskar shi sai jikin FA'iza yayi sanyi ita kuwa nauwara ko d'ago kanta Bata yi ba Cikin nauwara ya shiga watan haihuwar shi xama dakyar tashi dakyar don ba k'aramin girma cikin yayi ba su umma ba k'aramin tausaya mata suke ba duk ta kumbura musamman ma kafafuwan ta kula wa sosai suke bata basa barin ta tana xama ita d'aya saboda idan ta ke6e ita d'aya tunani take ko kuma ta dunga kuka na tausayin kanta da abin da yake cikin ta umma ta sha kamata tana kuka nan xata xauna ta rarrashe ta tare da yi mata nasiha har sai taga hankalin ta ya kwanta tana dariya sannan umma xata ji dad'i, tun suna sa ran haihuwar kusa har ta shige lokacin nata su dai addu'a suke mata Allah ya sauke ta lafia A firgice ta farka daga baccin da take sakamakon wani irin axabbaben ciwon mara da ya tashe ta ba shiri ta sauka daga kan gadon tuni har ta fara had'a uban gumi baya ma ya rik'e addu'a take duk wadda taxo bakin ta sai safa da marwa take a d'akin idan ciwon ya lafa sai ta xauna yana dawowa xatayi xumbur ta mik'e tsaye motsin ta shi ya tashi fa'iza daga bacci a rud'e ta K'arasa wajen ta tana cewa "nauwara lafia? " Ina ba bakin magana sai jikinta da yake rawa idanun nan sunyi jawur dasu da gudu fa'iza ta nufi d'akin umma ta fad'a kanta tana kuka a firgice umma ta tashi tana cewa "ke fa'iza lafia me yafaru " Cikin rawar murya tace "um umma nauwara ce ba ta da lafia sai wani irin abu..... " bata K'arasa fad'in hka ba umma ta tashi da sauri ta dauki hijab ta saka sannan ta d'auko wayar ta tana neman abba har suka k'araso d'akin kallo d'aya umma tayi mata ta fuskan nakuda take da sauri ta kirawo abba a waya sannan ta K'arasa wajen nauwara da take a durkushe Tana faman xabga salati da addu'a tace "Sannu nauwara Allah ya raba lafia sannu" "fa'iza duba cikin bedroom d'ina ki d'auko wannan akwatin ki kai cikin mota da sauri fa'iza ta fita umma ta rik'o nauwara suka fito suna sauka k'asa abba da aunty sadiya suna k'araso wa mota suka nufa gaba d'ayan su suka shiga asibitin da umma take kai ta awo nan suka nufa da yake da file d'in ta kuma shine asibitin da gaba d'aya suke xuwa cikin en mintuna suka K'arasa aka shigar da ita labour room su umma suna tsaye a kofar d'akin kamar su shiga ciki fa'iza kuka kawai take umma tace "fa'iza ba kuka xaki mata ba addu'a tafi buk'ata Allah ya raba su lafia " Tun dare ake abu d'aya amman har safia nauwara bata haihu ba ba k'aramin jigata tayi ba duk ta fita hayyacin ta numfashi dakyar ta ke iya ja nurses biyu ne a kanta da doctor Aishat wadda ita ce on duty suna cikin tattaunawar gwara ayi mata CS ta huta a lokacin tayi wani nishi da k'arfi sai ga kan yaro ya fito da sauri doctor Aishat ta canja hand glove di'n hannun ta ta taimaka mata har yaron ya K'arasa fito wa Mik'a wa nurse tayi yaron don su gyara shi cikin nauwara taga yana motsi ta6awa tayi sai taga da sauran wani d'an aciki don hka ta shiga taimaka wa nauwara don d'an ya k'arasa fito wa xuwa lokacin ta gama gala6aita jikin ta ba k'wari wani yunkuri tayi tare da nishi fit d'an ya fito yana gama fita ta xube ba numfashi cikin kad'uwa doctor ta mik'a wa nurse yaron ta dawo kan nauwara tana duba ta amman babu alamar numfashi Cikin sauri ta fice daga d'akin don kiran wani doctor d'in ya taimaka mata, yayin da sauran nurses d'in har sun gama gyara babies duk maxa kyawawa dasu masu kamar uban su kamar yayi kaki ya tofar duk kamar su d'aya fito wa suka yi suka mik'a wa su umma su cikin murna da d'oki suka kar6e su fa'iza Mai kuka sai gashi ana dariya da tsallen murna umma ta Kalli nurse din cikin murmishi tace "ina kuma nauwara dafatan tana nan lafia" Lokaci d'aya nurses d'in nan fuskar su ta canja cikin tsoro umma tace "Kuyi min bayanin halin da take ciki pls" Dakyar d'aya ta bude baki tace "I'm sorry madam Kuyi mata addu'a tana cikin wani hali saboda ko numfashin ta ya d'auke yanxu doctor Aishat ta tafi kirawo wani doctor don su had'u su yi......... " Kasa K'arasa fad'i tayi ganin yanda suka xuba mata ido hankalin su yayi mugun tashi Kafin ta sake magana doctor Aishat da wani likitan sun shige d'akin da nauwara take sauran nurse din suka bisu da sauri suka rufe kofar Tuni fa'iza mai dariyar ganin en babe's ta d'ora hannu akai xata xunduma ihu cikin sauri aunty sadiya ta toshe mata bakin ta Aishat A muh'd 🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 75~* "Haba fa'iza ba ihu xaki yi ba addu'a tafi buk'ata fiye da komai Allah ya tashi kafad'un ta " Aunty sadiya ta fad'i tana goge hawayen fuskar ta yayin da fa'iza ta rungume ta tana kuka mai ban tausayi, umma kuwa sai dai a shiru kawai abba ne ya kamata ya xaunar da ita kan kujera ganin ta k'ame a tsaye saboda tsabar tashin hankali da farga ba da take ciki gaba d'ayan su sunyi jugum jugum addu'a kawai suke a cikin xuciyar su Bud'e kofar da akayi yasa su tashi da sauri doctor Aishat da doctor kabeer suka fito duk sai goge xufa suke da sauri abba ya K'arasa wajen su yace "ta farfad'o doctor??? " Cikin murmishi doctor tace "Alhmdullilah yalla6ai mun samu nasarar hkan ta farfad'o numfashin ta normal sai dai munyi mata allurar bacci don ta huta saboda tasha wahala" Ajiyar xuciya suka saki gaba d'aya tare da furta "Alhmdullilah " fuskar su tuni ta bayyana farin ciki nan Abba ya bi doctor don su rubuta mishi magungunan da xasu yi amfani dasu ita da yaran Sai lokacin suka kar6i yaran suna kallon su tare da yi musu addu'a umma ta xuba musu ido har hawaye ya fito daga idonta xuciyar ta cike da k'aunar yaran kamar su d'aya da abduljabbar, a lokacin aka turo nauwara Xuwa rest room suka bisu da sauri har d'akin tana ta baccin ta hankali kwance sai dai ta rame sosai tayi wani irin fari sosai ta d'ashe aunty sadiya tace "umma Bari na koma gida na dafa mata abincin da xata ci Idan ta tashi " "okay auntyn yara sai kin dawo" ta juya ta tafi yayin da fa'iza ta jera yaran a gabanta tana kallon su xuciyar ta cike da k'aunar su dama natane kai gaskia dole nayi aure don na haifi yaran nan wayyo Allah baxan iya ba tabb wannan wahalar da nauwara tasha ta haife su ina xan iya nama fasa auren hka tayi ta xancen ta a xuciya ita kad'ai A hankali ta fara bud'e idon ta har ta bud'e su gaba d'aya a nutse tace "umma nahhh" Da sauri umma ta kallo ta tare da k'arasa wa kusa da gadon cikin farinciki ta rik'e hannun ta tana cewa "nauwara kin tashi Alhmdllh ya kike jin jikin naki" "da sauk'i umma sai dai yunwa nake ji" Ta fadi tana d'an Yatsina fuska "me xaki ci??? " "tea xan sha" Da sauri ta K'arasa inda aunty sadiya ta kawo abincin ta fara had'a mata tea mai kauri sannan ta xuba mata ferfeson kaji sannan ta taimaka mata ta tashi xaune tayi brush tukunna ta dunga bata a baki har ta koshi tuni ta fara had'a gumi bayan umma ta gama bata ta d'an huta sannan ta kaita toilet ta taimaka ta tayi wanka da ruwa mai d'umi yanda xata ji dad'in jikin ta Ta shirya cikin wata atamfa riga da siket d'inkin tayi fiyau da ita bayan ta fesa turare ta xauna sannan umma ta miko mata yaran Xaro ido tayi cike da mamaki tace "umma wai duk su biyun.... " Sai kuma ta kasa K'arasa wa saboda kunya ita har ga Allah ta d'auka d'aya ne murmishin jin dad'i umma tayi sannan tace "kin ga kyautar Allah ko duk biyun naki ne " Dad'i ne ya ishe nauwara ta dunga kallon su son su na k'ara ratsa xuciyar ta gashi sunyi kama da sweetheart addu'o'i sosai tayi musu ta tauna Dabino ta basu (duk da an fison da xarar an haifi jariri uwa ta tauna Dabino da yawon bakin ta su had'u sai ta bawa yaro yana da amfani sosai) fa'iza da aunty kausar ne suka shigo cikin murna fa'iza ta rungume nauwara tana cewa "sis kin ga yaran da kika haifa mana koh masu kyau dasu" Ita dae nauwara murmishin yak'e tayi don ita kad'ai tasan abin da take ji a xuciyar ta Sai da suka yi Kwana 2 a asibitin tukunna aka sallame su suka dawo gida en uwan umma da abba da abokan arxiki sai xuwa suke Barka aunty asma'u ma ta taho sai bayan suna xata koma en biyu dai sun yi farin jini sai xuwa ake ganin su abdulkareem shine ya d'auki nauyin yi musu yanka don yace shine uban su ko da abduljabbar yana nan haka ya kawo kaya masu yawa da kyau da tsada yace a sawa yaran umma Abba aunty sadiya aunty asma'u da kausar fa'iza har da saleem kowa sai nuna bajintar shi yake Wajen hidimtawa nauwara da yaran ta har da had'a walimah ta mata xalla su umma suka yi shirye shirye suke yi sosai na suna Ranar suna aka rad'a wa twins sunan abba ibraheem da sa'eed sunan aminin shi yasa wanda ya rasu don Sun tambayi nauwara me xa'a samu su sai tace su ya dace da su xa6ar musu suna Don hka abba ya sa sunan shi da sunan aminin shi lokacin da nauwara taji ansa sa'eed sai da gaban ta ya fadi ranar yini tayi tana kuka cike da kewar mahaifan ta da er uwar ta, fa'iza tace a dunga kiran ibraheem da na'eem sa'eed kuma da ameer Mutane da yawa ne suka halacci sunan don Abba da abdulkareem gayyata sosai suka yi anci ansha yara sun sha addu'o'i daga bakunan mutane Da yamma umma suka shirya walima ta k'ayatar sosai anyi abubuwan ci da nasha kuma an rarraba abubuwa sosai, nauwara ba k'aramin kyau tayi ba ta k'ara wani kyau da haske sai sa tsadaddun suttura take ita da su na'eem da ameer sai daf da mangariba aka tashi mutane suka watse a gajiye nauwara tayi wanka ta kwanta sai bacci aunty sadiya da aunty asma'u suka yiwa yaran wanka suka shirya su cikin kayan bacci sannan suka manna su jikin mahaifiyar su don su ji d'umin ta Washe gari su aunty asma'u da kausar suka koma gidajen su umma ta cigaba da gyara nauwara tana kula da su sosai, duk Wannan abun da ake abduljabbar bashi da labari ko Kad'an kuma abba yaja kunnen kowa kada wanda ya sake ya fada mishi ******* Xaune yake yana faman tunani yau a k'alla watan shi 6 da taho wa course di'n da aka tura shi xuciyar shi har yanxu bata huce da abin da nauwara tayi mishi ba amman son nan nata yana mak'ale a xuciyar shi kullum cikin tunanin ta da mafarkin ta yake har mafarki yayi gashi ta haifa mishi yara kyawawa masu kama dashi tana miko mishi yana tafiya don ya kar6e su amman sai nisa suke mishi ya kasa rik'e su har ya farka daga baccin ranar yini yayi yana cikin damuwa yana masifar son yara amman ya tabbatar cikin da ya tafi ya bar nauwara dashi ya 6are Idan ya tuna jinin da ya dunga fita ta jikin ta gashi ba fuskar tambaya su umma da abba kiran gaggawar da akayi mishi waya ya sashi mike wa duk jikin shi a sanyaye ya shirya cikin kakin shi ya fita ***** Na'eem da ameer sunyi wata 3 yaran sunyi wayo gasu tubarkallah Masha Allah suna da d'an jiki har sun iya xama yaran gwanin sha'awa kullum kamar su da abduljabbar sake bayyana take ana ji dasu en gaban goshin umma da abba ne hka abdulkareem xai ta siyo musu kayan wasa kullum sai yaxo ya duba yaran abokin shi kuma d'an uwan shi yana basu kulawa kamar shi ya haife su Nauwara ma tayi kyau abun ta duk ramar nan ta ciko ta rage tunanin abduljabbar amman duk da hka son nan nashi yana mak'ale a xuciyar ta wani lokacin ta shige toilet tasha kukan ta ta wanke fuskar ta ta fito tana yak'e, umma ta xo wa da abba shawara akan nauwara ta koma makaranta ai kuwa nan take ya amince da hakan ba 6ata lokaci ta fara xuwa skul sai dai fa'iza ta tsere ta da shekara d'aya tayi farinciki koma warta skul sosai ta rage tunanin da take Idan taje skul ta dawo hidimar yaran ta take hankali kwance........... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 76~* *BAYAN SHEKARA 2* Acikin wad'annan shekara biyun abubuwa da yawa sun faru ta 6angaren nauwara ta samu Cigaba sosae ta kammala skul d'in ta cikin nasara, na'eem da ameer kuwa tuni ta yaye su tun Kafin su cika shekara 2 yaran sunyi wayo sosai ga wayo da surutu sun shak'u da nauwara don janyo su take a jikin ta sosai suyi wasa da dariya Kowa a gidan yana ji dasu na'eem da ameer don yaran akwai shiga rai fa'iza kowa duk inda xata je kafarta kafar su bata barin su a gida tana masifar son yaran sosai har tana tambayar nauwara wani lokacin tace "xaki bani na'eem da ameer Idan xanyi aure mu tafi tare dasu? " Murmishi nauwara take tace "hmm fa'iza ai kema yaran ki ne kada ki damu na baki su" Dad'i ya isheta sai ta rungume nauwara Idan agaban umma ne hararar fa'iza take tace "kada ma kisa ran tafiya dasu don ba me raba ni da na'eem da ameer sai mutuwa " Sai ta marairaice fuska kamar xata yi kuka abba da aunty sadiya ma suki Goyan bayan ta suna son en jikokin su Hka xata xum6uri baki tayi gaba wai an hana ta su tayi fushi su umma su dunga yi mata dariya Kwance take a bed tana bacci hankalin kwance can ta farka a firgice tana karanta Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun sakamakon mafarkin da tayi da ammin ta cikin mawuyacin halin na tashin hankali tuni xufa ta keto mata tana cewa "me yake faru wa dani ne kullum sai nayi mafarkin ammi na k'wana nan " Kuka ne ya kufce mata tayi tana cikin yin kuka na'eem ya shigo d'akin da gudu ya haye gadon tare da rungume ta ta baya ya d'ora kanshi a tsakiyar bayan ta jin bata yi mishi wasan da ta saba yi musu ba ya sashi lek'a fuskar ta sai yaga kuka take "Mamie kuka kike waya doke ki na fad'a wa abba ya rama miki?? " Da sauri ta goge hawayen fuskar ta tace "na'eem ba wanda ya doke ni kai nane yake ciwo " Ta fad'i tana murmishin yak'e tuni fuskar shi ta canja alamar sauran kiris ya fashe da kuka ganin hka yasa ta fara yi mishi cakulkuli tuni ya fara dariya har sai da taga ya ware sannan ta rabu dashi "Mamie kixo muje umma ta baki magani" Kallon shi tayi cike da mamaki daman bai mance abin da ta fad'a mishi ba kamo hannun ta yayi yana janta alamar ta taso su tafi ganin xai fara kuka yasa ta tashi suka fita daga d'akin falon umma suka shiga kallo d'aya tayi mata ta tabbatar tayi kuka ba k'aramin tausayin ta take ba na'eem ne ya fara cewa "umma Ki bawa mamie na magani bata da lafia " "assha sannu nauwara me yake damun ki ?" D'an yatsine fuska tayi tace "umma rigimar na'eem ne wlh ni lafia ta klau" "kaiii mamie ke kika ce k'ayya babu kyau " Ya cigaba da cewa "umma kuka naga tana yi dana tambaye ta tace kanta ne yake ciwo " Hararar shi nauwara tayi tare da jan kunnen shi Kad'an yayi er k'ara cike da shagwa6a tace "ban hana ka Idan manya suna magana kana sa baki ba xan cire wannan bakin" Tuni ya marairaice fuska kamar xai fashe da kuka yace "sorry mamie nah na daina don Allah kada ki cire min baki na ina son shi" Dariya ce ta kufce mata ganin yanda yayi umma tana daga gefe itama tana er dariya fa'iza ce ta shigo falon ita ameer ta suri na'eem tana cewa "d'an mamie waya ta6a min kai ?" "ba mamie bace xata cire min baki ba" "baki kuma na'eem? " Ta fad'a tana xaro ido kai ya d'aga mata alamar ehh d'an hararar wasa tayi wa nauwara tana cewa "ba me cire maka baki kaji d'an mamie " Murmishi ya saki cikin jin dad'i nan suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa umma tana ankara da nauwara da take goge hawayen fuskar ta akai akai girgixa kai tayi cike da tausayin ta yarinya tana ganin jarabta Kala Kala a rayuwar ta ******* Tun da yaje course di'n da aka tura shi na tsawon shekara 2 ya dawo cike da nasara bai waiwayi kano ba can abuja ya tsaya jiddah ma ta biyo shi nan don baya k'aunar xuwa gidan nan nasu saboda baya son had'u wa da nauwara baya k'aunar ganin ta Lokacin aka k'ara mishi matsayi xuwa MG daman burin shi kenan ya samu wannan matsayin Alhmdllh gashi ya samu saboda kwazon shi da jajirce wa wajen aikin shi yayi waya dasu umma da abba ya fada musu har da partyn da aka shirya musu, amman ba wanda yaje a gidan sai abdulkareem har aunty sadiya ta shirya xata bi abdulkareem abba ya hana ta yaron da ya tafi shekara 2 course ya dawo Amman bai neme su ba ko aunty asma'u da take abujan bata je ba sai mijin ta ne ya je wurin partyn hkan ba k'aramin k'ona ran abduljabbar yayi ba Duk da ranar ta kasance ranar farinciki shi ne amman sam farincikin nan nashi ya dakushe saboda ba iyayen shi a wajen har aka tashi daga wajen bai cikin nutsuwa Yana xaune shi da abdulkareem yana fad'a mishi bai kyauta ba da bai je wajen su abba ba yana cigaba da cewa "Haba abduljabbar me yake damun ka da Har xaka yi tafiya ta tsawon shekara 2 ka dawo amman baka nemi inda iyayen ka suke ba saboda wani dalili naka " "kasan Allah abdulkareem ina son xuwa kawai nauwara ce bana son gani abin da ya hanani xuwa kenan gashi umma tace Idan na sake ta sai dai na nemi wata uwar bani ba na rasa yanda xanyi ka bani shawara aboki" Ya K'arasa fad'i yana kallon abdulkareem fuskar shi d'auke da damuwa "ni dai shawarar da xan baka kaje ka nemi gafarar su umma su yafe maka don suna fushi da kai kuma kasan fushin iyaye yana da matuk'ar tasiri akan 'ya'yan su " Wayar abdulkareem aka kirawo tafi kusa da abduljabbar don hka ya dauka da niyyar mik'a shi sai yaga photon wasu kyawawan yara masu matuk'ar kama dashi a fuskar wayar kasa mik'a mishi wayar yayi sai abdulkareem ne yasa hannu ya kar6i wayar don ta kusa katsewa sai da ya gama wayar ya mik'e tsaye har yanxu abduljabbar yana nan a k'ame saboda tsabar mamaki kallon shi yayi yana murmishi yace "ni bari na shige masauki na don gobe da sassafe xan wuce " Da sauri ya kamo hannun shi tare da xaunar da shi jikin shi har rawa yake yace "su waye wad'annan yaran abdulkareem ka fad'a min gasky pls? " Ta6e bakin shi yayi yace " 'ya'ya nane au ban fad'a maka maryam ta haifar min twins wani ikon Allah masu kama da kai " Rungume shi abduljabbar yayi yana hawaye afuskar shi don lokaci d'aya yaji wani bala'in son yaran ya shiga xuciyar shi yana ratsa jinin jikin shi cikin rawar murya kamar xai fashe da kuka yace "Abdulkareem xaka bani so ina son su don Allah ka barmin su plsss d'an uwa" Wani irin tausayin shi ne ya kama abdulkareem yana bubbuga bayan shi yace "calm down d'an uwana kafi k'arfin haka a wuri na xan baka so i promise na bar maka daman naka ne mallakin ka ne jinin ka ne" Cikin jin dad'i yace "are u sure ka bar min twins d'in ka" Don shi har ga Allah bai gane maganar abdulkareem ba cikin tausayin shi ya Jijjiga kai nan ya dunga yiwa abdulkareem godia yana cewa "Indai na samu sauk'i aiki xuwa last month d'in nan xan shigo kano na d'auki yara na ka kular min dasu " ya cigaba da cewa "baka fad'a min sunan su ba? " "sunan abba ne da babban ibraheem ana ce mishi na'eem sai sa'eed wanda yaci sunan aminin abba ana kiran shi da ameer" Bai bar abdulkareem ya tafi ba sai da ya tura pictures d'in na'eem da ameer a wayar shi tun daga ran da suka xo duniya har xuwa yanxu da suka kusan cika shekara 3 sai da ya tura pictures d'in su gaba d'aya a wayan shi sannan ya bar abdulkareem ya tafi, k'wana yayi yana juyi rik'e da wayar shi yana kallon photo nan na'eem da ameer son su na k'ara ratsa xuciyar shi yana addu'ar Allah yasa shima Kafin ya mutu ya samu d'an kanshi ko da d'aya ne ****** A nutse abba yake driving suna er hirar su da umma sun dawo daga duban wani abokin shi da bashi da lafia sai hango wata mata suka yi tana tsaida su da hannun ta daga ganin ta a gala6aice take da sauri abba yayi parking gefen titi suka fito shi da umma tun Kafin su K'arasa ta xube a k'asa a sume Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun umma da abba suka fad'a tare da kamata suka sanya ta a mota umma ta d'auko ruwa ta xuba mata a fuskar ta ajiyar xuciya ta saki tare da bud'e idon ta tana kallon su umma "Alhmdllh ta farka abba mu tafi gida idan yaso sai ka kirawo doctor ya duba ta" "toh Shikenan " Ya shiga motar yayi mata key suka bar wajen adai dai lokacin wasu matasa guda 3 suka k'araso wajen suna haki d'ayan yace "Shikenan ta gudu me xamu gaya wa oga" D'aya daga cikin su yace "ta66 raina mishi hankali xamu yi muce ta nan Idan ba hka ba kashin mu Ya bushe don sai ya kusa kashe mu" D'ayan wanda bai yi magana ba yace "maganar ka gaskia ce " suna gama fad'in hka suka juya suka tafi _kuyi hak'uri da wannan ban da chaji_ Aishat A muh'd ☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 77~* Bayan sun k'arasa gida 6angaren da ake saukar bak'i umma ta shigar da wannan matar suna yi mata sannu har likita ya xo ya duba ta tare da rubuta magunguna da xa'a yi amfani dasu Sannan yayi musu sallama ya tafi Abba ma yayi mata sannu ya fita daga ya bar umma a d'akin sai da umma ta had'a mata ruwan wanka mai d'umi ta ga ta shiga toilet d'in sannan ta je ta d'auko mata kayan ta da had'o mata abinci ta kawo mata sai ta tarar ta fito daga wanka bayan ta shirya ta xauna tana cin abincin a nutse umma ta xuba mata ido tana kallon wannan kyakkyawar mace kamar ita tayi kanta don kyau har tana tunanin inda tasan mai kusan kama da matar nan amma ta kasa tuna wa don hka sai ta kawar da wannan tunanin tace "baiwar ya sunan Ki me ya faru dake ???" Hawaye ne ya xubo a idon ta Kafin tasa hannu ta goge Kafin ta bud'e baki tace "Sunana maimuna ina xaune a ......................" nan ta bawa umma labarin ta Kaf tun Kafin ta gama umma take kuka don ba k'aramin tausayin ta taji ba ita ma matar kuka ta dunga yi Kafin umma ta hau rarrashin ta dakyar ta yi shiru tana faman sauke ajiyar xuciya umma ta d'an kalle ta tace "ni kuma sunana fatyma mai gidana da kika ganmu tare sunan shi Alhj ibraheem ina da kishiya sunan ta sadiya ina da yara guda 4 asma'u sai abduljabbar da kausar sai fa'iza dafatan xaki xauna da mu cikin amince " "Insha Allah nagode fatimah" D'an murmishi umma tayi tana son matar ta kuma tausayin ta ki d'aure kisha magungunan ki gasu nan sai ki kwanta ki huta sai da safe " "Allah ya tashe mu lafia" "Ameeen " Daga hka umma ta fice daga d'akin ita ma maimuna tasha maganin sannan ta kwanta nan wani bacci ya d'auke ta da alama da maganin bacci acikin magungunan saboda bata dad'e ba tayi baccin Umma tana xuba wa abba coffee a cup yace "kin tambayi wace matar nan? " "Ehh na tambaye ta har tarihin ta bani abin tausayi wlh tasha wahala" Ta K'arasa fad'i tana bawa abba coffee d'in kar6a yayi yana cewa "toh Shikenan Allah ya kyauta " "auuu baxa ka tsaya na baka labarin da ta bani ba" Murmishi abba yayi tare da rungumo ta jikin shi "ba wannan ne a gaba na tun da Kinsan ita wace kuma kin yarda ta xauna a gidan ki angama" Sannan yayi mata rad'a a kunne suna dariya gaba d'aya Washe gari da safe umma take sanar da su nauwara fa'iza saleem xuwan wannan bakuwar a lokacin nauwara dawowar kenan ita da FA'iza daga kai na'eem da ameer skul don an sanya su shi kuwa saleem fita yayi tunda yana da lectures d'in safe umma ta Kalli nauwara tace " nauwara d'auki breakfast d'in nan ki kai mata tana 6angaren sashen bak'i " "tohh umma " Ta fad'i tana tashi d'auka tayi ta nufi 6angaren da er taxara tsakanin su da part d'in umma Kad'an tayi sallama shiru ba'a amsa mata ba sai da tayi sau uku amman shiru sai tayi tunanin ko tana toilet don hka ta kutsa kanta cikin d'akin bata ganta ba sai ma wata irin fad'uwar gaba da taji a lokaci d'aya jin k'arar xubar ruwa a toilet sai tayi tunanin wanka take don hka ta ajiye sannan ta juya ta tafi amman gaban ta sai tsanan ta fad'u wa yake Tana fita matar tana fito wa daga toilet d'in don hka basu had'u ba To Hka suke tafiyar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali har aka share 3 months abduljabbar bai xo ba sai dai yana kiran su umma su gaisa shima kanshi ya matsu ya xo sai aiki da suka rik'e shi a office ga xaman kad'ai ci don ita ma jiddah ta gaji da xama ta dawo kano don hka shima gaba d'aya hankalin shi yayo gida a wannan time d'in Indai ya fita sai ya siyo wa na'eem da ameer yaran da abdulkareem ya bashi kayan sawa tsadaddu da kayan wasa Kala Kala kud'i sosai yake kashe musu pictures d'in su kuwa sune abokan hirar shi gashi yayi yayi abdulkareem ya basu waya suyi magana yaki yarda daga K'arshe ma sai cewa yayi suna gidan umma da abba tun da aka yaye su umma ta kar6e su sai dai idan ya dawo ya gansu don hka gaba d'aya hankalin shi yayo gida Haka bakuwar dasu abba suka taimaka watan ta uku kenan a gidan tayi kyau abinta duk ramar nan ta ciko umma har tsorata take da kyanta basu ta6a had'u wa da nauwara da saleem ba sai fa'iza ta sani duk sa6ani suke sau nawa nauwara take kai mata abinci ko ta shigo 6angaren umma amman basu ta6a hadu wa da juna ba ****** Yau tun safe nauwara fa'iza da saleem ba xama don yau ne birthday d'in na'eem da ameer yau suka cika shekara uku da haihu 6angaren garden nan xasu yi taron birthday di'n an gyara wajen ya sha decoration Kala Kala masu matuk'ar kyau wajen ya had'u sosai anyi musu birthday cake mai hawa uku an rubuta sunan su yayi kyau ga en skul d'in su en yara an gayyato su wasu ma har da iyayen su Tun safe aunty asma'u ta taho tare da yaran ta Hka ma aunty kausar sai shirye shiryen su suke da yamma xa'a yi duk an gama shirya komai har da abincin da snacks xuwa su drinks duk an tanadar wanda xa'a ci a sha Karfe 4 na yamma mutane suka fara taruwa a gidan sai kaga mata da miji da en yaran su sun taho gwanin sha'awa duk an taru an xaxxauna ana jiran Fitowar twins kid'a ne mai taushi da sanyi yake tashi a wajen ga sassanyar iskar yammaci mai dad'in gaske ga k'amshin furanni da suke tashi a wajen Wow masha Allah kallo ya koma kan su nauwara da twins tasha wata hadaddiyar gown pink colour mai adon flowers black a jiki tayi rolling d'in kanta da black veil mai adon flowers d'in pink takalmi hill shoe bak'i shi ma tayi matuk'ar yin kyau baka ce ita ta haifi su na'eem tana rik'e da hannun twins sun sha kaya iri d'aya english wears jeans ne Blue a jikin su da maroon di'n riga sai takalmi min kafar su maroon da ratsin bak'i a jiki ba k'aramin kyau suka yi ba yaran kannan nasu yasha gyara irin gyaran gashin kan sharukhan da yayi a film d'in R one...lols Cikin nutsuwa suka K'arasa wajen nan aka fara tafi ana yi musu wak'ar happy birthday fa'iza da saleem suna watsa musu red flowers a jikin su sosai abin ya k'ayatar da mutanen gurin masu d'aukan pictures a camera da waya sai fama suke "Don Allah ki d'aure ki tashi muje Wajen birthday d'in nan" Cewar umma tana xaune kusa da maimuna murmishi tayi sannan tace "da ban yi niyyar xuwa ba saboda xan tuna wani lokaci kamar hka da ya wuce a rayuwa ta amman tun da kin matsa tashi mu tafi murmishin jin dad'i umma ta saki sannan tace "Yawwa k'awata nagode sosai " Tashi tayi had'e da d'auko k'aramin kwalin gifts di'n da xata bawa twins sannan suka fito daman tuni aunty sadiya ta wuce wajen partyn Sun xo wajen farfajiyar gidan mai gadi ya bud'e get wata hadaddiyar mota k'irar Range Rover black colour ta danno cikin gidan umma taja ta tsaya cike da mamakin wane a wannan motar a hankali mai tuk'in motar yayi parking ya fito ganin abdulkareem ne ya fito yasa umma murmishi daman shi ake jira difff wannan murmishin ya mak'ale sakamakon Fitowar abduljabbar daga cikin motar yana sanye da kakin shi ya k'ara kyau sosae cikin tafiyar shi ta sadaukan maxa ya K'arasa inda umma take tayi suman tsaye don bata ta6a tunanin xata ganshi a wannan lokacin ba cikin tsananin farinciki ya rungume ta yana cewa "Nayi missing di'n ki umma nah nasan ni mai laifi ne but I'm so sorry baxan k'ara mai maita hkan ba i promise to u baxan kuma ba kiyi hak'uri ki yafe min " Ture shi tayi daga jikin ta ta Kalli abdulkareem da maimuna tace "mu k'arasa wajen kada a yanka cake muna nan" Duk jikin su yayi sanyi ganin ko halin ko in kula da tayi da abduljabbar ta kama hannun ta suka yi gaba abduljabbar kuwa jikin shi ya gama yin sanyi abdulkareem ne ya rik'e mishi hannu yana cewa "kayi hak'uri daman dole sai ka fuskanci hkan mu tafi wajen birthday d'in twins di'n naka, ina ka ajiye gifts di'n da xata basu d'auko mu tafi " D'an murmishi yak'e yayi jikin shi a sanyaye ya bud'e motar ya d'auko sannan suka nufi wajen Nauwara lokaci guda taji gaban ta yana mugun fad'uwa ta rasa dalilin Hka addu'a ta cigaba da yi a xuciyar ta har xuwa lokacin da xa'a yanka cake It's ce a tsakiya ta d'an rankwafo Kad'an hannun ta rik'e da wukar yayin da na'eem yake daman ta ameer 6angaren hagun ta sun sanya hannun su d'aya d'aya sun rik'e wukar da hka suka yanka cake ta yanko ta bawa na'eem sannan ameer sannan ita ma suka bata a baki gaba d'aya wajen ya d'au tafi A dai dai lokacin umma da maimuna suka k'araso wajen tare da su Abduljabbar dake bayan su tun da ya d'ora ido akanta ya gane ta don baxai ta6a manta kamannin ta ba tsayin shekara uku da rabuwar su sai yau ya sake sanya ta a idon shi yayi mamakin yanda ta k'ara kyau ta goge kamar ba nauwaran da ya sani ba wayyo readers xan so ku ga yanda abduljabbar ya koma a lokacin kasa tafiya yayi sai da abdulkareem yaja hannun shi ko takan twins di'n da yake d'okin gani bai yi ba tun da yaga nauwara komai nashi ya tsaya da aiki A nutse ta dago da dara daran idanun ta suka had'a ido da abduljabbar ido cikin ido wata irin fad'uwar gaba taji lokaci guda shekara uku rabon da ta ganshi amman sai ta wayance har da murmishin yak'e ta Kalli abdulkareem da yake mik'a wa twins gifts di'n shi cikin xaxxak'ar murya ta wadda ta kusan sumar da abduljabbar tace "mun yi fushi uncle sai yanxu kaga damar xuwa" Cikin er dariya abdulkareem yace "ayi min afuwa wani babban uxiri ne ya rik'e ni amman ai gashi naxo" "toh anyi maka amman ka sani wannan shine last" "na yarda mamien twins " Lokaci d'aya suka saki murmishi sannan ta wuce ko Inda abduljabbar yake bata k'ara kallo ba suna tsaye ana ta basu gifts nauwara ta d'an ja gefe tana amsa waya duk inda tayi abduljabbar ya kafe ta ido ga wani shegen kishi da yake nukurkusar shi ganin yanda maxan wajen suke bin ta da kallo ( ni kuwa nace tabbb abduljabbar kana da aiki a gaba) A lokacin maimuna ta k'araso wajen xata bawa twins gifts har ta basu xata juya ta tafi wayar hannun ta ta fad'i k'asa da sauri nauwara ta tsugunna xata Mik'o mata tun daxu take kallon matar amman bata ga fuskar ta ba ita ma maimuna a dai dai lokacin ta mik'a hannu xata dauki wayar sai dai nauwara ta riga ta d'auka mik'a mata wayar take a dai dai lokacin ta d'ago kanta karaf suka had'a ido nauwara da matar lokaci d'aya suka yi suman tsaye baki na karkarwa nauwara tana son magana amman maganar tak'i fito wa daga bakin sai ta tafi luuuuu xata fad'i k'asa cikin matuk'ar xafin nama abduljabbar da Duk idon shi yake kan nauwara ya taro ta jikin shi a sume "nauwarahhh!!! " Ya furta da k'arfi yana Jijjiga ta hkan da yayi shi ya janyo hankalin su umma da sauran jama'a kansu matar tana tsaye ita ma har lokacin da sauri saleem ya d'auko robar ruwa xai xuba mata sai suka had'a ido da maimuna cillar da robar ruwan yayi tare da d'ora hannun shi a kai yace "am....... " bai K'arasa fad'i ba ya xube shi ma sume ita ma maimuna xube wa tayi a sumen saboda tsabar kad'uwa da tayi da fatalwar yaran ta...... Aishat A muh'd 🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 78~* Gaba d'aya hankalin su umma yayi masifar tashi ganin su nauwara a sume duk matan sun rud'e sai abdulkareem ne yayi jarumtar yayyafa musu ruwa ban da nauwara da take jikin abduljabbar yana faman jijjiga ta tare da kiran sunan ta ga twins a hannun fa'iza suna kuka da kiran mamien su Hankalin umma ne yayi kan nauwara sai lokacin ta ankara da tana jikin abduljabbar ai kuwa wajen ta nufa tare da sa hannu ta rik'o ta, tana kok'arin raba ta da jikin abduljabbar cikin marairaicewa yace "umma bari na kai ta hospital Har yanxu bata farfad'o ba " Duk da halin da suke ciki na tashin hankali sai da umma ta dalla mishi harara tare da cewa "cika min yarinya ba ruwan ka da ita Idan ma ta kama akaita hospital d'in ae ba kai xaka kai ta ba" ranshi ya 6aci da abin da umma tace sai kawai ya sake ta ya fice daga wajen a fusace ko ta kan twins bai yi ba Ajiyar xuciya ta saki tare da bud'e idon ta a nutse ta fara duba cikin d'akin tare da tunanin mai ya same ta cikin lokaci k'alilan ta tuno da komai xumbur ta tashi daga kwance da take sai lokacin su umma suka san ta farka "ammi nah!" Da sauri maimuna wadda nauwara ta kirawo da ammi ta isa inda take ta rungume nauwara "ammi na mafarki nake ko ido biyu ke nake gani? " cikin kuka ammi tace "ba mafarki kike ba nauwara nice ammin ki ashe kuna raye bai kashe min ku ba " Saleem ma yaxo ya rungume su suna kuka bana wasa ba su umma suna daga gefe suna goge hawayen tausayin su, sai da suka yi kuka sosai umma da aunty sadiya dasu aunty asma'u suna rarrashin su sannan suka dai na kukan sai faman sauke ajiyar xuciya suke gashi suna rik'e da hannun ammi don gani suke kamar xata dad'a gudu wa ta bar su Bayan an nutsu abba ya dawo ake sanar dashi komai ya buk'aci ganin su don a tattauna ko da wani taimako da xai basu, bayan sallahr isha'e aka xauna a falon abban gaba d'ayan su har da abdulkareem sai dai abduljabbar tun da ya fusata ya fita bai dawo ba don hka shi kad'ai ne baya nan don Abba bai ma san da xuwan shi ba labarin su ya buk'aci ji don hka nauwara ce ta fara ba da labarin su tun daga farko da irin wahalhalun da suka sha ita da saleem da xaman su gidan hindatu da aminu xuwa gidan saude mai abinci da ta taimake su har xuwa lokacin da suka hadu da abduljabbar ya taimaka musu, Abba aunty sadiya dasu aunty asma'u sun girgixa da irin wahalar da suka sha idan ka d'auke umma don tasan da labarin ammi kuwa kuka kawai take yanxu daman safah ta mutu nauwara sai da ta makance ta xama wadda bata iya tafiya duk dukiyar mahaifin su suka xama masu bara Yah ilahi duk Wannan abun a dalilin Alhj salisu anya yana son gama wa da duniya lafia yana k'aunar rahmar ubangiji kuwa xalinci da cinye dukiyar marayu duk wannan bai isheshi ba sai ya nemi halakasu falon yayi shiru sai shashshak'ar kukan ammi da su nauwara Abba ne ya katse shirun ta hanyar cewa "nauwara wane mahaifin ku a wanne gari kuke?? " Don duk Wannan labarin da ta bayar bata fad'i sunan mahaifin su ba cikin sanyin murya tace "mu en kaduna gidan abban mu a tudun wada suke mahaifin mu kuma a unguwar gwamna road yake xaune sunan shi " Tun da ta fara maganar abba ya xuba mata ido gaban shi yana fad'u wa jikin shi har er rawa yake sai da ta sauke numfashi sannan tace "sunan abban mu Alhj sa'eed haruna " tashi abba yayi yana karanta Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun ya dafe kan shi da sauri abdulkareem ya mik'e ya rik'o shi tare da xaunar da shi "Kina nufin Kice Alhj sa'eed haruna mahaifin ku ne?" "tabbas shine mahaifin su " Cewar ammi tuni idon abba ya kad'a yayi ja daman yaran aminin shi ne yake rik'e da su bai sani ba kallon umma da aunty sadiya yayi sannan yace "' 'ya'yan aminina Alhj sa'eed haruna wanda har naje kaduna dubo shi na tarar ya rasu na buk'aci a ban yaran shi na rik'e akace duk sun mutu " "k'warai kuwa anyi haka " Cewar umma tana mai tabbatar da hkan cikin tsananin mamaki ammi tace "Ko kai ne Alhj ibraheem d'anbatta? " D'an murmishin yak'e Abba yayi sannan yace " nine maimuna aminin mijin ki sakacin mu na wajen k'in rik'on xumunci yasa bamu gane ku ba hka kuma baku gane ne mu ba" "yanxu salisun shi ya aikata hkan Lallai rayuwa ta xama abar tsoro d'an uwan ka na jini ya nemi kashe maka iyalan ka saboda wani dalili na son dukiya wad'anda xaka mutu ka bar su a duniya Allah ya raba mu da sharrin xuciya " "Ameen thumma Ameeen " Suka amsa gaba d'ayan su sannan abba yace "toh lokacin da yasa aka d'auke ki ina suka kai ki??? " Ya tambayi ammi sunkuyar da kanta tayi kafin ta bud'e baki ta fara magana tace "ina kuka da kiran sunan yara na suka tura ni cikin mota daga nan suka shak'a min wani abu a hanci na 6ingire da bacci ban san inda suka kai ni ba ni dai na tsinci kaina a wani gida mai kyau a lokacin nayi kuka nayi kuka daga K'arshe na Duk'ufa da addu'a ba dare ba rana Allah ya ku6utar dani daga hannun wannan axxalimin ga abinci mai kyau don akwai mai dafa min abinci har da gyaran gidan anan take k'wana er aikin Tun da suka kawo ni wannan gidan sau d'aya Alhj salisu yaxo ya dunga lalla6a ni na yarda na aure shi na xauna anan xai kawo min yara na don su xauna a gaba na ya dunga yi min alkawarin abubuwa na jin dad'in rayuwa amma nak'i yarda na aure shi daga K'arshe a fusace ya bar gidan Haka na cigaba da rayuwa ta cikin kunci da tarin damuwa duk nabi na rame saboda hankalina ba a kwance yake ba har Allah ya bani ikon gudu wa daga gidan nan ganin yanda wad'anda suke mishi tsaron ta ranar sun sha alcohol sunyi tatul suna ta faman maye shine na fita daga gidan ina gudu Ashe d'aya daga cikin su ya ganni shine suka biyo ni har Allah yasa muka had'u daku har kuka taimaka min" Ammi ta K'arasa fad'i tana goge hawayen fuskar ta "Lallai salisu ya cika mugu axxalimi dole ne mu yi Shari'a dashi duk da *WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA* sai mun Kwatar muku hakk'in ku Insha Allah " Cikin tsoro ammi tace "kada a kai su k'ara ina jin tsoron kada ya tarwatsa maka iyalan ka mugune kawai mu barsu da Allah daman *INNALLAHA MA'ASSABIRIN* (na miss zahra mansur) " "ina ammi baxai yiwu ba dole mu shigar da su k'ara kuma xamu yi nasara Insha Allah akwai friend d'ina barrister ne ya k'warai a aikin shi xamu neme shi a san yanda xa'a 6ullo wa abun amman batun abar shi ba bai taso ba a rage mugun iri" Cewar abdulkareem Jijjiga kai Abba yayi sannan yace "k'warai kuwa abdulkareem Don barin irin wad'annan mutanen ba k'aramin hatsari bane sai su cigaba da xalintar mutane" Kowa ya gamsu da hakan nan kuma aka d'an wartsake ana ta6a er hira Wani wawan naushi ya kai wa bangon d'akin duk abin da su Abba suka yi Duk a kunnen shi yaxo zai shiga falon abban yaji nauwara tana bada labarin rayuwar su daman xaluntar su akai neman hallaka su ake suka gudu da xummar xuwa gidan aminin mahaifin su don ya taimake su lokaci d'aya wani son nauwara da tausayin ta suka lullu6e shi dole na kar6ar muku hakk'in ku da hannuna xan kashe wannan axxalumin mutumin wani duka ya sake kai wa wardrobe d'in dake kusa dashi Take murfin ya 6urme ciki fad'o war wata jaka ce tasa ya mai da hankalin shi kan wajen a hankali yasa hannu ya dauke ta a take ya tuna inda ya tsinci jakar nan kayan cikin ne suka fara xubowa k'asa takardu ne da wasu pictures guda biyu hannun shi har rawa yake Wajen d'aukan pictures d'in mutanen da ya gani a jikin photon yasa shi kusan suman tsaye saboda tsabar tsananin mamaki........... Aishat A muh'd ?☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _this page dedicated to Sumayya salees sadeeq (sumyn bash 💋) Allah ya k'ara basirah da daukaka Ameen_ *~Pg 79~* Sake murxa idanun shi yayi don ya tabbatar abin da yake gani ba mafarki bane a xahiri ne abin ya matuk'ar bashi mamaki sosai ba wasu ya gani ba ajikin pictures d'in ba sai nauwara saleem da kuma ammin su duk da bai san abban su da safah ba amman ya tabbatar sune sunyi kyau sosai kowannen su fuskar shi d'auke da Murmishi d'ayan kuma nauwara ce da safah xama yayi kan sofa yana sake kallon photo nan sai da ya d'auki en mintuna anan xaune tukunna ya mayar dasu cikin jakar ya ajiye su duk da Har yanxu xuciyar shi da tsanar nauwara amman xai yi iya yin shi don ya Kwatar musu hakk'in su ******** Suna xaune a parlour umma aunty sadiya da ammi sai nauwara da fa'iza ana hira cikin annushuwa twins saleem ya d'auke su sun fita shan ice cream suna cikin haka abduljabbar ya shigo da sallama tun ranar birthday di'n na'eem da ameer da ya bar gidan sai yau ya sake shigo wa shima don tafiya abuja ne ya Kamashi yaxo yi musu sallama kuma ya kwashi twins d'in abdulkareem don dasu xai tafi duk da jiddah baxa ta bishi ba xai iya kula dasu amsa mishi sallamar aunty sadiya da ammi suka yi sannan ya shigo parlourn nauwara ce ta mik'e daga kwancen da take jikin ammin ta ko kallon Inda yake bata yi ba ta nufi upstairs bedroom d'in su kai tsaye ta shige don bata son ganin shi bata k'aunar wata alak'a ta sake shiga tsananin su tun da har xuciyar shi ta yarda da sharrin da aka kulla mata sharrin ma na aikata fasikanci da auran ta wasu hawaye ne masu xafin gaske suka fito daga idanun ta Tana wuce wa ta gaban shi da kallon tsana da harara ya bita Kafin yaja d'an k'aramin tsaki duk umma tana ankare da abin da yayi gaida su yayi aunty sadiya da ammi da fara'a suka amsa mishi umma kuwa a dak'ile ta amsa xama yayi ya rasa ma ta Inda xai fara maganar tashi saboda k'wata k'wata babu fuska a wajen umman Aunty sadiya ce ta mik'e ta bar wajen sannan ammi ma ta mik'e tana cewa "fa'iza taho muje ki kitse min wannan kan nawa ya ishe ni hka" Mik'e wa tayi tana cewa "toh ammi " Suka nufi d'akin da ammi take k'wana aka bar umma da abduljabbar xaune su kadai sunyi shiru sai can tace "sai ka fad'i abin da yake tafe da kai duk ka kore min en hirar kuma ka sani a gaba kayi shiru " Tsugunna wa yayi har k'asa ya rik'e kafafun umma yana bata hak'uri ta yafe mishi baxai k'ara kwatanta hakan ba "toh me kayi min abdul ai ni bakai min laifin komai ba " "nooo umma Kina fushi da ni har da abba ba naje office na same shi dakyar ya amsa min gaisuwa ta ku yafe min pls" "Shikenan komai ya wuce " Cikin tsananin farinciki yace "thank u umma nah Allah ya k'are min ku" "Ameeen " Umma tace sai kuma ya fara sosa k'eya da akwai wata maganar bayan wannan don hka tace "sai kuma me? " Cikin kwantar da murya yace "umma daman abdulkareem ne ya bani na'eem da ameer ya bar min su har abada so shine naxo d'aukan su xamu wuce abuja " Kallon shi umma take kallon irin anya kana cikin hayyacin ka can tace "shi abdulkareem din ne yace maka ya bar maka na'eem da ameer? " "ehhh umma ashe Maryam ta haifar mishi twins ban sani ba? " Wani murmishin takaici umma tayi sannan tace " na'eem da ameer nauwara ce ta haife su ba maryam ba don haka wannan kyautar Bata yi ba " Tun da ta fara magana yake kallon ta cike da mamaki nauwara ce ta haifi twins daman ba 'ya'yan abdulkareem ba ne "umma Kina nufin Kice min aure ta sake har ta haife su? " Wani kallo ta watsa mishi wanda ya sashi shiga taitayin shi a fusace tace "ka maida mu mahaukata in banda haka taya ya xata sake wani auren bayan tana da aure toh na'eem da ameer dai 'ya'yan Kane na cikin ka " Jin saukar maganar yayi har cikin kwakwalwar shi da sauri yace "umma da gaske twins 'ya'ya nane " Sai ya bata d'an tausayi ganin duk yanda yabi ya rud'e jikin shi har d'an rawa yake tsabar abin ya xo mishi unexpected "Alhmdllh Allah nagode ma da ka nufe ni da samu d'an kaina " Sai da ya gama murnar shi sannan yace "umma a had'a musu kayan su kayan su mu tafi tare " Wani kallo umma ta watsa mishi tace "kada na kuma jin wannan maganar a bakin ka yaran da bakasan da haihuwar su ba da wahalar su lokaci d'aya kace a baka su toh wallahi ka fita a idona na rufe kaji na fad'a maka tashi ka bani waje" Jikin shi a sanyaye ya tashi ya fita daga parlourn a farfajiyar gidan suka had'u da twins da saleem sun dawo had'a su yayi ya rungume su a jikin shi k'aunar su tana ratsa jinin jikin shi har sai da ya goge hawayen da suka xubo mishi wai yau shine da yaran kanshi saleem ma yana gefe yana kallon shi cike da tausayin shi na'eem da ameer ma kwanciya suka yi a jikin shi suna xuba mishi surutu tuni ya wartsake ya biye musu sai da yasha hira dasu dakyar ya iya tafiya ba don ya so ba xuciyar shi cike da kaunar yaran shi Duk wata tsana da yake wa nauwara ta bar xuciyar shi wani sonta ne ma yake dad'a shiga cikin xuciyar shi da hka har ya K'arasa abuja da tunanin nauwarah da twins d'in shi na'eem da ameer Aishat A muh'd 🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 80~* 6angaren su abba duk wasu shirye shirye sun kammala na shigar da k'arar su Alhj salisu don haka Abba da abdulkareem da kanshi yaje har kaduna ya d'auko su baffah da inna habiba sai da suka xo kano tukunna yayi musu bayanin komai lokacin da suka ga ammi nauwara da saleem sai da suka kusan suma tsabar mamaki da farin ciki suka rungume juna suna kuka dakyar aka rarrashe su suka yi shiru nan abba yace su baffah su xauna anan har sai an kammala Shari'ar nan take suka amince ******** Sai faman had'a gumi yake yana ta safa da marwa a cikin office d'in wata doguwar takarda a hannun shi Alhj salisu kenan yanxu aka kawo mishi takardar sammaci daga kotu abin da yayi matuk'ar gigita tashi da d'aga mishi hankali shine sunan nauwara sa'eed haruna da saleem sa'eed haruna sune suka shigar dashi k'ara wayyo xan so kuga yanda fuskar Alhj salisu ta koma saboda tsanani tashin hankali, d'aya daga cikin mai kula da office d'in shi ya shigo bayan yayi mishi ixinin shigowa wasu files ne a hannun shi ya ajiye akan table d'in sannan ya d'an saci kallon Alhj salisu ya ga baya kallon shi da sauri ya d'auko wata er K'aramar wani abu ya d'ora kan table d'in Inda baxai gani ba ya bar office d'in da sauri yana fita daga office d'in ya d'auki waya ya Kira wata number cikin k'asa k'asa da murya don kada aji shi yace "yalla6ai na ajiye abin da ka bani " d'an shiru yayi alamar sauraren mai maganar can yace "ba matsala duk xa'a yi abin da kace Allah ya baku nasara" yana gama fad'in hka ya mayar da wayar aljihu sannan ya d'an wai waiga bai ga kowa sai ya juya ya tafi wayar shi ne tayi k'ara da sauri ya dauka ya duba sunan d'aya daga cikin yaran shi ne da sauri yayi picking "what!!!!? " Abin da ya fad'i da k'arfi sannan yace "ta gudu kuka ce toh ina neman ku da gaggawa kuxo kaduna yau d'in nan akwai aikin da xaku yi min mu had'u a guest house d'ina " Yana gama fad'in hka yayi hanging up d'in wayar yana furxar da wani xaxxafan gumi nan take ya kirawo Alhj lawan shana da yanxu sam basa shiri sunyi fad'a kaca kaca akan kud'in da bai bashi yanda yake so ba suka yi baram baram sai yanxu ya nemo shi don shi kad'ai ne xai bashi shawarar don hka sun gama magana kan karfe 8 na dare su had'u a guest house d'in shi don su tattauna yanda xasu 6ullo wa wannan Shari'ar tunani sosai ya xurfafa sai faman had'a uban gumi yake Duk da sanyin ac dake cikin office d'in daman ance komai nisan jifa k'asa xai dawo ******** Yana xaune a office d'in shi gaban shi wata er K'aramar computer ce yana jujjuya wa akan kujerar duk abin da Alhj salisu ya ke fad'a da wayar da yayi da yaran shi xuwa kiran da yayi wa Alhj lawan shana duk ya gansu kuma ya jisu wani murmishin mugunta ya saki MG abduljabbar kenan Tun da yaxo abuja ya fara bincike akan Alhj salisu har kaduna sai da yaje sau biyu company nin su nauwara da ya koma nashi ta k'arfi da yaji yaje toh da yake kusan duk ma'aikatan ba k'aunar Alhj salisu suke ba saboda rashin mutuncin shi da mugunta yasa shi abduljabbar bai sha wahalar samun had'in kan su ba amman mutum d'aya hankalin shi ya fi kwanta wa dashi ya fada mishi abin da yake so aikuwa nan take ya amince shine ya bashi er na'urar nan yasa ta a Office d'in Alhj salisu da guest house d'in shi don yasan duk motsin shi da abin da suke shirin aikatawa don yafi son ya samu kwararan hujjoji a hannun shi Kafin a shiga kotu Wayar shi ya d'auka yayi Kira ba'a dad'e ba wasu yaran shi joseph driven shi da wani suka shigo office d'in kallon su yayi tare da yi musu magana da abin da yake so suyi mishi sannan yace "yanxu xamu shige kaduna bana son wasa da shirme duk abin da na tsara haka xaku bi" Lokaci d'aya suka had'a baki wajen cewa "okay boss " daga hka suka juya suka fita shima abduljabbar mik'e wa yayi ya fita daga office d'in , mota ya shiga su joseph suma suka shiga Joseph yayi wa motar key suka d'auki hanyar kaduna Yana fitowa daga masallacin da yayi sallahr isha'e shi da wannan d'aya daga cikin ma'aikatan Alhj salisu mota suka shiga inda su joseph suke ciki shi ya nuna musu hanya har guest house d'in Alhj salisu a farkon layin suka yi parking Abduljabbar ya sallami wannan mutumin mai suna yusuf da kud'i masu yawa tare da yi mishi Godiya sosai sannan kuma yana buk'atar yaje kano ko akwai wani abin da xa'a buk'ata yayi mishi alkawarin Insha Allah xai xo Sannan suka rabu Duk wannan binciken da abduljabbar yake su abba basu da labari en maganganu suka yi da su joseph sannan ya fito daga motar shi kad'ai ya nufi guest house d'in ya tunkare shi ba shakkar komai a tattare dashi abin da ya d'aure min kai ganin mai gadin ya bud'e mishi get har da gaida shi cikin girmamawa nace Lallai abduljabbar ya siyi shi kenan kai tsaye inda nauwara ta ta6a xuwa har ta la6e ta saurari hirar su shi ma nan ya tsaya yaji duk shirye shiryen da suke don ganin asirin su bai tonu ba bayan sun gama maganar tasu Alhj salisu da Alhj lawan shana sai hajia binta suka fita daga falon suka bar yaran nasu su 3 a gidan Wayar shi ya d'auko yayi wa su joseph waya ba 6ata lokaci suka shigo gidan bayan sunyi parking d'in motar su a wajen gidan kai tsaye falon suka shiga xumbur wad'annan yaran Alhj salisu suka mik'e tare da janyo makamin da yake jikin su babu alamar tsoro a tare da abduljabbar da su joseph suka nufi inda suke wani naushi suka yi musu a ciki nan take suka xube a k'asa cikin matuk'ar gala6aita sannan suka janyo su har gurin motar su ka shigar dasu kai tsaye a cikin Wannan daren abuja suka nufa Washe gari da mummunan labarin 6atan yaran shi suka tashi don hka duk sun bi sun firgice saboda sune suka san sirrin gaba d'aya kuma Idan suka sha wahala xasu iya tona musu asiri Lallai Wannan karan shegiyar yarinyar nan (wato nauwara) da babban shiri ta xo Cewar Alhj salisu kenan nan suka fara binciken inda yaran shi suke da kuma Inda nauwara da saleem suke 6angaren su abba sun gama shirin su sai jiran ranar shiga kotu duk sun Duk'ufa da addu'a Allah ya basu nasara akan Alhj salisu sun samu barrister wanda yasan aikin shi sosai shima yana nashi binciken cikin K'warewa irin ta aikin shi ****** Ranar monday xa'a fara xaman kotu duk wani wanda ya kamata ya hallara a kotun an hallara waje ya cika yayi makil da jama'a don sauraran wannan k'ara mai cike da cin amana tsantsa da xalinci A wannan rana Alhj salisu yayi nadamar abin da ya aikata sau ba adadi musamman lokacin da ya tsaya a gaban kotu gashi suka had'a ido da ammi nauwara saleem da kuma inna da baffah mahaifin shi duk jikin shi yayi matuk'ar yin sanyi bai ga alamar samun nasara ba sam Toh dai a Wannan xaman da aka yi ba'a samu wasu kwararan hujjoji ba saboda su nauwara basu da wata karfaffiyar hujjar su akan Alhj salisu don hka kotu ta d'aga k'arar xuwa 2 weeks masu xuwa Haka aka tashi daga kotun abin da ya ban mamaki shine me ya hana abduljabbar xuwa bayan shi yake da kwararan hujjojin a hannun shi ...... Aishat A muh'd [4/12, 15:35] Umar Dalha: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 81~* Acikin satin nan biyu da aka basu xasu koma kotu sun Duk'ufa da addu'a sosai tare da cigaba da bincike toh duk wasu binciken da suke basu samu wasu hujjoji ba don gaba d'aya Abduljabbar ya bi ya tattara su a wajen shi kuma bai sanar da kowa ba kuma yak'i xuwa har yanxu Har aka sake shiga kotu xama na biyu babu wasu kwararan hujjoji kan dukiyar su ce tunda ga takardun duk dukiyar su nauwara but sunan Alhj salisu ne akai balle axo batun shi yasa aka k'ona gidan su har safah ta mutu da mai gadi don hka barrister di'n su nauwara shi ya nemi alfarmar a sake d'aga k'arar en jarida sosai sun taru a wajen suna d'aukan rahoton wannan Shari'ar mai matuk'ar d'aure kai da ban mamaki Wani murmishin mugunta Alhj salisu yayi lokacin da suka had'a ido da nauwara wajen da take ya nufa duk da ta tsorata da ganin hakan amman hka ta dake ta tsaya wani d'an iskan kallo yake yi mata yace "Wato ke ga shegiyar mara kunya koh, da ni xaki ja uban ki ma na cikin kabari yayi Kad'an balle ke " Sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa "nasan xanyi nasara kuma ki shirya mutuwar ki ke da saleem kuma sai na auri uwar ki Kina kallo Kafin ki mutu shegiya ke ga mai taurin kai xanga uban da ya tsaya miki " "Hahahaha loser " Yatsine fuska tayi sannan ta dalla mishi harara tare da cewa "wlh kayi Kad'an sai naga bayan ka mugu axxalimi kuma da kake cewa sai ka kashe ni *a rayuwa da mutuwa a hannun Allah take* sau nawa kake yunkurin kashe mu Allah bai yi ba daman ance *d'an hakin da ka raina shike tsone maka ido* kuma Insha Allah sai na tsone maka idanun ka gaba d'aya da ikon ubangiji ai xalinci baya dore wa maci amana butulu" Sam bai yi mamakin abin da nauwara tayi mishi yasan xata fad'i abin da yafi hka ma ba K'aramar mara kunya ce ba maganganin ta sun 6ata mishi rai amman da yake d'an duniya ne sai ya maxe Ya nuna ta da hannu yace "xaki gani? " Murgud'a mishi baki tayi ita ma tace "xa dai ka gani wlh " Tana gama fad'in hka taja tsaki tare da juyawa ta tafi abin ta shima tsakin yaja tare da cewa "yanda na kashe uban ki har lahira kema Hka xaki bishi " Yana gama fad'in hka ya juya ya shiga mota suka tafi, kash! rashin sani yafi duhu inji malam bahaushe da yasani bai kula nauwara ba har sunyi magana haka ba saboda d'an leken asirin abduljabbar yana gefe yana d'aukan su video a waya ya tura wa abduljabbar ta what's app sannan ya tafi Hka su nauwara suka koma gida cikin rashin k'warin gwiwa amman sun sake damarar sake bincike na sosai Bari na waiwayi 6angaren abduljabbar naga ko me yasa yak'i xuwa ******* Yana xaune kan kujera yana sanye da white d'in three quarter da maroon di'n riga mara hannu irin ta shan iska fuskar nan tashi d'auke da Murmishi laptop d'in shi tana kan kafar shi yana sarrafa ta cikin kwanciyar hankali yana kur6an xaxxafan coffee yana kallon duk yanda ta kasance a kotu yana d'an murmishi wani lokacin har d'an darawa yake Idan yaga yanda Alhj salisu yake hararar nauwara yana jifan ta da kallon tsana k'arara Shigowar message yaji a cikin d'aya daga cikin wayoyin shi dake xube a gefen shi hannu yasa ya d'auka ya bud'e password d'in wayar sannan ya duba cikin what's app nashi yaga videon aka turo mishi bud'e wa yayi ya nutsu yana kallo murmishin mugunta ya saki tare da furxar da wani xaxxafan huci a hankali yace "d'an iska xaka san baka da wayo wlh dole wannan Karon na uku na bayyana don na nuna maka kai k'aramin k'waro ne " D'an turo ya saki tare da rufe laptop d'in shi ya d'an kwanta kan kujerar yana kallon wani film a mbc 2 wanda suke yanxu mai suna death race Lokacin da suka xo da yaran Alhj salisu abuja da farko k'in fad'in komai suka yi sai da suka ji wahala kamar xasu mutu sannan suka fad'i komai sosai abduljabbar ya gigita da jin wannan rashin imanin irin na Alhj salisu kuma suka yi alk'awarin fad'in gaskia a kotu amman duk da hka sai da abduljabbar ya gwara musu kawunan su saboda tsabar 6acin rai tuni suka suma saboda tsabar axaba maimakon a k'wara musu ruwan sanyi su farfad'o amman ina ruwan xafi abduljabbar yasa aka xuba musu sai da yaga sun farfad'o sannan ya fita daga d'akin duk sunyi bak'i sun rame tsabar axabar da suka sha Kuma yana sani yak'i halartar kotun don ya fison su d'an sha wahala sannan ya bayyana don a ganin shi yanke hukunci lokaci d'aya basu sha d'an wahala ba baxai yi mishi kyan gani ba kuma ya fison sai Alhj salisu ya sawa ranshi samun nasara daga K'arshe ayi mishi kwaf d'aya Tun ana gobe xa'a yi xaman kotu na K'arshe abduljabbar ya shigo kano dashi da amintattun yaran shi joseph da mubaraq tare da yaran Alhj salisu a d'akin da yake punishment di'n yaran shi a d'akin aka xube yaran Alhj salisu sannan ya nufi part d'in su ya bar Joseph da mubaraq suna gadin su duk da wajen a rufe yake Yana shiga jiddah ta taso da d'an gudu ta rungume shi tana murnar ganin shi don ya dad'e bai xo ba don hka yana wanka aka shiga biyan bashin k'wanakin da ba'a tare, ranar yini yayi a gida yana huta wa tare da xuba soyayya da jiddah yinin farin ciki yayi ba wanda yasan yaxo Kano saboda ya fison su had'u a kotu gobe..... Washe gari misalin wajen karfe 10 na safe kotu ta cika da mutane ga en jaridu suma kallo d'aya xaka yiwa su Alhj salisu kasan suna cikin tsantsar farin ciki wannan Karon har da hajia binta matar Alhj salisu da baban ta Alhj salisu har da ladi (wadda Alhj salisu ya kai ta gidan su nauwara don ta dunga yi musu aiki a xahiri) Su nauwara kuwa duk jikin su a sanyaye Har da barrister di'n don basu da wata shaida mai k'arfi sai kame kame amman duk da hka basu karaya ba sun dogara ga Allah sai addu'a suke a cikin xuciyar su Karfe 10 dai dai aka fara Shari'ar su nauwara nan aka shiga tafka tambayoyi tsakanin barrister di'n su nauwara da nasu Alhj salisu har xuwa lokacin da aka tattara wa alkali bayanai aka bashi duk anyi tsit ana jiran hukuncin da xai yanke Har alkalin ya bud'e baki xai yi magana kenan aka bud'e kofar aka shigo gaba d'aya kallo ya koma kan kofar don ganin wanda ya shigo, nauwara ma da kanta yake kallon k'asa ta d'ago kanta tare da kallon kofar ganin yanda gaba d'aya mutanen cikin kotun hankalin su yayi kan kofar shigo wa..... Aishat A muh'd [4/12, 15:35] Umar Dalha: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 82~* Gaban ta ne yayi mugun fad'uwa ganin bayyanar Abduljabbar sanye yake cikin kakin shi yayi kyau kwarjinin shi ya cika wa mutane kai tafiya yake cikin kasaita har ya k'araso cikin kotun gaba d'aya mutanen cikin kotun binshi suke da kallo suna mamakin mai ya kawo wannan babban sojan mai muk'amin MG kotu xama yayi tare da had'a ido da barrister di'n su nauwara ya kashe mishi ido d'aya Jijjiga kai barrister yayi tare da sakin wani murmishin mugunta (na ce toh shi wannan abduljabbar d'in sai kace wani aljani yana abuja har yasan barrister di'n da xai tsaya wa su nauwara) A karo na biyu alkali ya gyara xaman glass d'in shi a ido ya bud'e baki xai yi magana kenan barrister kabeer Ya nemi alfarmar xai gabatar da hujjar shi ta K'arshe nan barrister di'n su Alhj salisu yak'i yarda da hakan amman ina har alkalin ya bashi wannan favour di'n xama yayi cike da takaice ya kallo abduljabbar ai kuwa ya kashe shi da killer samiling sai da yaji d'an tsoron abduljabbar kuma yana kula da kashe idon da yayi wa barrister kabeer Nan fah ya shiga gabatar da hujjojin shi har da bawa nuna jakar da nauwara ta yarda da ita wanda Kaf takardun dukiyar su yana ciki nan alkali ya kar6a ya ajiye a gefen shi lokacin da nauwara ta ga jakar nan sai da gaban ta ya fad'i saboda tsabar farinciki don ta tabbatar xa'a samu hujjoji akanta Ta 6angaren Alhj salisu sun d'an fara tsorata musamman yanda suka ga lawyer di'n su ya kasa ta6uka komai basu k'ara tsinken wa ba da al'amarin sai da suka ga Shigowar yaran su a matuk'ar gala6aice saboda tsabar firgita sai da Alhj salisu da hajia binta suka saki fitsari a tsayen sai jin Fitowar shi suka yi yana bin kafafun su tuni jikin su ya fara rawar shoki Wani murmishin mugunta abduljabbar ya saki da ya Kalli su Alhj salisu yanda suka kid'ime tare da gigicewa rashin gaskiya ya bayyana k'arara a fuskar su, babu gardama yaran Alhj salisu suka bayyana komai tun daga lokacin da suke bibiyar Alhj sa'eed don su kashe shi basu yi nasara ba sai lokacin da xai je kano wurin aminin shi suka markad'e su a mota sannan suka sace ammin su nauwara suka sawa gidan wuta don su nauwara su mutu sai kuma d'aya ce ta mutu ya umarce mu da mu binciko sauran mu kashe su da muka gansu sai muka bi ta kansu da mota muka gudu............. Duk suka sanar da komai Gaba d'aya kotun tayi shiru sai shashshak'ar kukan mutane saboda tsabar tausayin su nauwara bayan sun gama fad'in komai su Alhj salisu Alhj lawan shana da hajia binta ladi suka fara ihun cewa k'arya suke musu sharri ne Wani kallo da abduljabbar ya watsa musu sai da sukayi shiru ba shiri don ba k'aramin kwarjini yayi musu ba K'arshe kuma da kanshi abduljabbar ya nuna wa alkalin videon da Alhj salisu yake fad'a wa nauwara xai kashe ta ita da saleem kamar yanda ya kashe mahaifin su da safah kuma sosai alkalin ya aminta da hkan ya kuma duba takardun dukiyar su nauwara da ta Alhj salisu yaga tasu nauwara itace ta ainahin gasken nan aka tattara komai aka mikawa alkali ana jiran hukuncin da xai yanke Abba umma ammi aunty sadiya nauwara saleem FA'iza aunty asma'u aunty kausar abdulkareem da aunty maryam matar abdulkareem gaba d'aya sun daskare a wajen tsabar dumbin mamakin abduljabbar daman yana da hujjoji a hannun shi shine ya barsu suna faman shan wahala a banxa harara umma da abba suka dalla mishi lokacin da suka had'a ido murmishi kawai yayi musu yana shafa lallausan gashin kan shi 6angaren su Alhj salisu baxan iya fad'a muku irin tashin hankalin da suke ciki ba gaba d'aya a firgice suke kamar ace kat su xura da gudu sai faman rarraba ido suke ga gumi ya gama jika musu jiki sai muxurai suke kallo d'aya mutum zai musu ya hango rashin gaskia k'arara a fuskar su jikin su sai rawar shoki suke Daman ance komai nisan jifa k'asa xai dawo rana dubu ta 6arawo rana d'aya ta me gaskia, Idan xaka gina ramin mugunta gina shi dai dai da kae watakil ka fada cikin shi gashi su Alhj salisu sun gina shi fiye da tsayin su gashi sun rufta cikin shi Baffah haruna da inna habiba sunyi kuka sosai d'an uwan ka ya kashe ka ya tarwatsa maka iyalai har ya nemi kashe su don duk wai *Adalilin son* matar shi da dukiyar shi, dukiyar da xaka mutu ka bar su a duniya, kunyar duniya ta ishi inna larai wato mahaifiyar Alhj salisu matar Baffah haruna tayi nadama sosai kuma duk batasan salisu ya aikata hakan ba A cikin nutsuwa da kamala irin ta alkalan da suke yanke hukunci tsakani da Allah babu corruption nd bribery acikin xuciyoyin su ya fara da nasiha Kafin ya gangaro kan tabbatar da dukiya tasu nauwara ce kuma an mayar musu da abarsu sannan aka ci tararar su Alhj salisu na tsorata su nauwara da niyyar hallaka su da kuma B'uye ammi da yayi sannan daga K'arshe daman ance K'arshen tika tiki tak aka yanke wa su Alhj salisu Alhj lawan shana da hajia binta ladi da kuma yaran su masu taimaka musu wajen aikata munanan laifuka aka yanke musu hukunci dai dai da laifin kowa a cikin su Wani raxanannen ihu hajia binta ta saki tare da d'ora hannu ta a saman kanta nan wasu mata en sanda suka cafke ta tare da xura mata anka a hannun ta Hka ma su Alhj salisu aka tura k'eyar su Nan kotu ta tashi su nauwara sun samu nasara daman duk wanda ya dogara da Allah baxai ta6a ta6ewa ba a rayuwar shi nan suka suka fito wajen kotun mutane sai faman taya su murna ake suna mai la'antar masu hali irin nasu Alhj salisu en jaridu sunyi musu caaa suna xuba musu tambayoyi nauwara maganar mintuna 2 ta iya magana da wani nacaccen wani d'an jarida da yasa ta maganar da bata shirya yin taba Rungume juna nauwara ammi da saleem suka yi suna kukan farinciki yau saboda tsabar farinciki sai da nauwara ta rungume abba tana xuba mishi godia Kallon wajen dasu Alhj salisu nauwara tayi wadanda ake kok'arin tura su a mota cikin wata tafiyar kasaita ta K'arasa wajen da suke sai da taxo gab dashi tana murmishin mugunta tace "Ya akayi na baka kunya na tuna asirin ku duk dukiyar da kake da ita yau kaine sanye da anka xaka yi xaman prison Kafin a rataye ka ka mutu har kana ikirarin sai ka ga bayan mu an gaya mata mutanen da suka dogara da Allah xasu ta6e " Kallon shi ta sake yi tana d'aga mishi gira ran shi idan yayi dubu ya 6aci kallon Alhj lawan shana da hajia binta da ladi tayi tukunna tace " K'aramar yarinyar da ka raina yau gashi ta shayar dakai mamakin da baka ta6a tsammani ba a rayuwa ka ba, baxan ta6a yafe maka ba *wata Shari'ar ma sai a lahira* Kad'an ka gani wannan iya na duniya ne ma" Kallon ta yake cikin 6acin rai Kafin ta rufe bakin ta taji wata mummunar shak'a a wuyan ta tuni idanun ta sun firfito saboda tsabar wahala dakyar ta ke iya jan numfashi kallon shi tayi fuskar ta cike da wani irin murmishi da ni kai na na kasa gane murmishin da nauwara take "Kafin na mutu bari ki fara mutuwa don uban ki ai nayi alkawarin sai na kashe ki da hannuna shegiya tsinanniyar yarinyar " Tuni mutane sun taro wajen ana kok'arin ceton nauwara amma ina yak'i cikata duk da dukan da en sanda suke mishi da kulkin hannun su Su umma sai kuka suke ganin yanda har nauwara ta fara lumshe idanun ta ga jini ya fara xuba ta hancin ta da bakin ta Ihun da ake a wajen ya janyo hankalin abduljabbar da yake cikin office d'in alkali suka fito da gudu ganin abin da yake faruwa a guje abduljabbar ya ratsa cikin mutanen da suka taru ya kai wa Alhj salisu wani wawan naushi a fuska tuni jini ya soma xuba a bakin shi amman don taurin kai yak'i ya saki nauwara don so yake ya kashe ta Ganin bai sake ta ba kuma Idan yace xai kwakule hannun shi a wuyan nauwara xai ji mata mummunan ciwo yasa abduljabbar d'auko pistol di'n shi ya saita kafar shi ya harbe shi wata k'ara ya saki amman yak'i cika ta abin ba k'aramin mamaki da tsorata mutanen wajen yayi ba Lallai ba k'aramin k'iyayya yake nuna wa nauwara banaushi ta ko'ina ya dunga kai mishi ba shiri ya sake ta don axabar dukan da abduljabbar yake mishi Fad'uwa nauwara tayi a jikin umma da ammi jiki a sake ko motsi da numfashi bata yi cikin wata raxannaniyar k'ara ammi tace "Shikenan ya kashe min itaaaaa" Ta fad'i tana girgixa nauwara kuka sosai ammi take Abduljabbar fah allurar sojoji ta motsa dukan Alhj salisu yake ta ko'ina kuma ba wanda yayi yunkurin hanashi amman kuma abin mamaki murmishi ya saki yana kallon nauwara yace "ka kashe ni tunda na kashe ta daman buri na na K'arshe na kashe tsinanniyar yarinyar nan " A fusace abduljabbar ya bashi wani naushi a cikin shi lokaci d'aya ya saki k'ara ya xube a wajen a sume shi ma Da gudu yayi kan nauwara cak ya d'auke ta suka nufi asibiti sai ruwa suke xuba mata tare da girgixa ta suna ambatar sunan nauwara amman ko motsi Bata yi jikin ta ya saki yayi sanyi qlau kamar mataccaciya _kuyi hak'uri da wannan wlh ban da lafia ne_ Aishat A muh'd 🍀?🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _this page dedicated to fateen soja ( *Mr's umar*) Allah ya baki ikon kammala littafin ki lafia hak'ik'a littafin maxa da mulki mata da tak'ama yayi sosai Allah ya k'ara basirah Ameeen, ina yi miki fatan alkhairi a duk inda kike_❣ *~Pg 83~* Suna isa asibitin da gaggawa aka shige da nauwara emergency room don bata agajin gaggawa tana cikin tsaka mai wuya *mutuwa* ko *rayuwa* su umma suna wajen room d'in a tsaitsaye suna jiran Fitowar doctor duk hankalin su a tashe yake Yini guda cur likitoci suna kan nauwara amman har yanxu bata farfad'o ba su kansu likitocin Sun tsorata da hakan Duk jikin su yayi sanyi sun rasa ta inda xasu fara yiwa wannan family d'in bayanin halin da nauwara take ciki daga K'arshe dai babban likitan shi ya nemi abba abduljabbar sai abdulkareem don iya maxan xai iya d'aure wa ya fad'a musu halin da nauwara take ciki Bayan sun xauna cikin sanyin jiki yace " a gaskiya munyi duk iya kok'arin mu don ganin ta farfad'o amman hakan ya gagara xuwa gobe har Indai bata farfad'o ba toh sai dai ku fitar da ita wata k'asar tana cikin hatsari don xata iya rasa ranta a kodayaushe duk da *rayuwa* da *mutuwa* suna hannun Allah " Kafin doctor ya rufe bakin shi abduljabbar ya Cakumo wuyan rigar shi cikin tsananin tashin hankali da 6acin rai cikin d'aga murya yace "k'arya kake baxa ta mutu ba, shine don wulakanci kana ganin yanda muka yini ana abu d'aya maimakon ka fad'a mana baxa ka iya komai ba kana wahalar da mu da kan ka" Nan ya cigaba da masifa doctor kuwa gaba d'aya idon shi ya firfito saboda shak'ar da abduljabbar yayi mishi dakyar ya ke fitar da numfashi jikin shi sai rawar shoki yake saboda tsabar tsorata abba ne da abdulkareem suka kwaci doctor dakyar daga hannun abduljabbar a xuciye ya fice daga office d'in Tari sosai doctor yake yi abdulkareem ne ya bashi ruwa yasha sannan ya tarin ya lafa sai sannu suke mishi cikin murmishin yak'e yace "it's okay don't worry yalla6ai " Ya fad'a yana shafa wuyan shi tare da d'an jujjuya shi su abba suka k'ara yi mishi sannu sannan abba yace "toh mene mafita doctor sannan wacce k'asa ya kamata mu kaita??? " Sai da yasa d'an hankicif ya goge gumin fuskar shi xuwa wuyan shi sannan yace " mafita sai dai nace kawai ku fitar da ita waje saboda sun fimu kwararrun kayan aiki acan, ku xa6i London suna da kwararrun ma'aikata acan sosai kuma da akwai wani friend d'ina doctor acan xan had'u ku dashi Insha Allah xa'a dace ku kwantar da hankalin ku Allah ya bata lafia" "Ameeen doctor mun gode" Nan suka bar office d'in suka dawo wajen su umma bayani suka yi musu tare da kwantar musu da hankali sannan suka fita don neman visa xuwa London a corridor di'n wajen asibitin suka had'u da abduljabbar yana faman safa da marwa ko Inda yake Abba bai kalla ba ya shige mota har abdulkareem xai tafi wajen shi abba ya watsa mishi harara Hka ya hak'ura ya shiga mota ya jasu Abin da abba yayi mishi ya masifar dad'a 6ata mishi rai yaja wani matsiyacin tsaki yace "toh wai ina ruwana da ita ne da xan damu da ita yarinyar da ta yaudare ni taci amanata ai bai kamata na nuna jin tausayi na akanta ba" Mtsww ya k'ara Jan saki ya nufi wajen motar shi direct gidan shi ya nufa ran shi a 6ace toh anyi sa'a jiddah tana gida fito war ta daga toilet kenan aikuwa kai tsaye ya nufi inda take cikin tsoro take ja da baya tana cewa "sojana ya akayi ne lafia kake??? " Hannu yasa ya fisgo ta jikin shi yana mata wani kallo da rinannun idanun shi bai tsaya 6ata lokaci ba ya fara bin ta da xaxxafan remonce cikin salon da yake hargitsa tunanin jiddah dole kuwa ta bada kai bori ya hau don bata da yanda xata yi... A 6angaren su abba sunyi nasarar samun visa xuwa london umma ammi da abba abdulkareem sai nauwara da twins na'eem da ameer don hka acikin wannan daren sun gama had'a komai wanda xa'a buk'ata likitan ya had'a su doctor da xasu je gunsa Karfe 9 na safe jirgin su nauwara ya d'aga xuwa london suka bar da addu'ar Allah ya sauke su lafia Allah ya tashi kafad'un nauwara fa'iza ansha kuka sosai dakyar ta cika nauwara abba yayi mata alk'awarin Indai ta farfad'o xai dawo nnigeria xai sa asama mata visa ta taho ita ma hakan ya d'an sanyaya xuciyar ta Alhmdullilah sun sauka k'asar London lafia ambulance di'n hospital ce taxo ta d'auki nauwara yayin da doctor d'in nan bahaushe ne d'an nigeria sunan shi doctor muh'd Abdullah matashin saurayi ne hadadden guy wanda ilimin addini dana boko suka ratsa shi nutsatstsan mutum shine ya d'auki su abba a motar shi xuwa gidan shi don yak'i yarda su sauka a hotel a matsayin su na en nigeria tushen da fito kuma en garin kano wanda haifaffen can ne mahaifan shi suna xaune a unguwar janbulo su abba sun ji dad'in irin wannan karamcin na doctor muh'd Abdullah girmama su yake sosai yake a matsayin su na manya sai da ya wadata su da duk abin da xasu buk'ata sannan ya tafi asibitin Nan ya shiga room d'in da aka kwantar da nauwara da shi da wani baturen doctor suka shiga gudanar da binciken nauwara Toh Alhmdllh cikin k'wana 2 da xuwan London nauwara ta farfad'o har tana gane wad'anda suke kanta sai dai tayi mugun wani fari ta rame sosai da hka sauk'i yake samu wa a hankali Sati d'aya abba yayi ya koma nigeria sannan fa'iza ta taho cike da d'okin ganin nauwara A cikin k'wanakin nan 8 da xuwan su london nauwara da doctor muh'd Abdullah sunyi wata iriyar matuk'ar shakuwa da junan su xai 6ata lokacin shi yana bata labarai masu dad'in gaske da ban dariya tayi ta dariya cike da tarin farinciki gashi jinin su ya had'u da na'eem da ameer yana bala'in k'aunar su sosai sai ya dauke su ya fita dasu wajejan shakatawa suma twins d'in sun saba dasu sosai Babu wanda yasan abduljabbar yaxo london don jinshi yayi baxai iya xama har su dawo 9ja ba bai ga nauwara ba shine ya taho har asibitin yana da address d'in shi don hka kai tsaye asibitin ya nufa har room d'in da aka kwantar da nauwara har xai shiga d'akin yaji sautin dariyar ta don hka ya fasa shiga ya lek'a ta window abun da ya gani ba k'aramin gigita shi yayi ba nauwara ya gani xaune kan bed d'in asibitin doctor muh'd Abdullah kuma yana xaune kan kujera dab da ita yana fuskan tar ta ya xuba mata ido yana bata labari masu dad'i ita kuma tana er dariya cike da sha'awa hannun ta rik'e da cup d'in tea tana kur6a a hankali garin dariyar sai d'an tea d'in ya xuba a hannun Kad'an er k'ara ta saki da sauri ya kar6e cup d'in ya ajiye sannan ya rik'e mata hannu yana duba mata wani shock suka ji lokaci d'aya a jikin su da sauri ta xame hannun nata duk ya rud'e sai sannu yake mata a d'an kunya ce take amsa wa Wayyo Allah xan so kuga yanda fuskar abduljabbar ta koma lokaci d'aya jikin shi har rawa yake saboda tsabar kishi tabbas a yau ya yarda da abin da nauwara ta aikata ba sharri ba ne halin tane don hka dole ya d'auki mataki baxai iya sake xaman rayuwar da ita ba ya hak'ura da ita har abadaaa a matuk'ar fusace ya fito daga asibitin a ranar ya juya xuwa nigeria har ya sauka daga jirgi jikin yana tsuma saboda tsabar kishi yana sakkowa daga jirgin ya kunna wayar shi message ya fara tura wa nauwara yace " _I hate yhu! I hate yhu!! I really hate yhu nauwara!!!_" Tana xaune ita d'aya doctor muh'd Abdullah ya fita xuwa duba patient taji Shigowar message duba wa tayi taga number d'in abduljabbar gaban ta ne ya fad'i da sauri ta bud'e ta karanta Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da nauwara ta iya fad'i wasu xafafan hawaye suka xuba a fuskar ta amman sai ta rubuta ta mishi reply da cewa " _thank u so much Abban na'eem da ameer_" Ta tura mishi tare da kwanciya ta dafe kirjin ta da yake buga wa da k'arfin gaske hawaye ne kawai suke xuba a idon ta lokacin da ya duba message d'in nauwara ya karanta ba k'aramin sake harxuka shi yayi ba sai kawai yabi sharrin xuciya da hud'ubar shaitan hannun shi ya fara rubuta " _Na rabu dake har abada nauwara na sake ki saki d'aya kije kiyi rayuwar da kike so nayi da na sanin xa6ar ki matsayin masoyiya ta uwar 'ya'ya na I hate yhu_" wasu hawaye ne masu xafin gaske suka fito daga idanun shi ya kurawa rubutun ido kamar ya tura kamar kada ya tura batare da sanin shi ba hannun shi yayi sending d'in message d'in ya tafi Can kuma kamar mintuna uku ya dawo hayyacin shi ya duba yaga abin da ya rubuta saboda tsabar kad'uwa baisan lokacin da ya saki wata er k'ara ba had'e da d'ora hannu akai girgixa kai yake yana cewa " noooo nauwara ba nufi na Hka ba ina sonki a kowanne hali kika shiga wannan abin kuskure ne da sharrin xuciya da hud'ubar shaitan tare da kishin ki ya sani rubuta Hka ban shirya ba " Dak'yar ya iya shiga mota drive yaja shi sai gida yana shiga part d'in jiddah xai shiga bedroom d'in ta kenan yaji maganar da take yi abin da yaji ba k'aramin kid'ima shi da gigita shi ya sake yi ba cikin wani irin yanayi da fusata ya banko kofar bedroom d'in nata...... Aishat A muh'd. ?☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _Wannan shafin sadaukar wa gare ki nafeesat anka naji dad'i da nuna kulawar ki a gare ni ina miki fatan alkhairi Allah ya bar xumunci ameeen_❣ *~Pg 84~* Abin da yaji lokacin da xai shiga d'akin jiddah waya take da farida kawar ta tana cewa " ni fah har yanxu buri na bai cika ba tunda bai sake shegiyar yarinyar nan ba duk da sharrin da muka had'a mata na tura wani d'akin ta matsayin d'an iskan da suke watse wa Wlh na d'auka lokaci d'aya xai dankara mata saki har uku gashi har ta haifa mishi twins ina tsoron ya dawo da ita gidan nan na tsani er iskar yarinyar nan " Abin da yaji kenan ya banko kofar da k'arfi har jiddah ta tsorata a firgice ta mik'e tsaye ganin yanda ya koma lokaci d'aya ita bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba amman ta maxe tace "sojana xuwan yaus........ " Kafin ta K'arasa fad'in "yaushe" ya kwashe ta da wani mugun mari Kafin ta dawo hayyacin ta ya sake bata wani daga nan ya fara ball da ita da kafar shi tana ihun kuka tare da bashi hak'uri belt d'in jikin shi ya cire ya fara tafkar ta son ran shi yana cewa "jiddah kin cuce ni kin raba ni da nauwara daman sharri kika k'ulla mata xaki yi bayani duk abin da kike min ban ta6a d'aukar mataki ba a kanki amman wannan Karon xan baki mamaki wallahi" Sai da yayi mata lilis ko motsi bata iya yi balle kuka sai faman ajiyar xuciya take saki tsugunna wa yayi dai dai kan ta yace "na tsane ki jiddah kin raba ni da sanyin idaniya ta muradin rai na kije kema na sake ki baxan iya xama da ke ba" Wani irin ihu ta saki Duk da muryar ta bata fita sosai bai kula ta ba ya janyo ta tun daga upstairs har k'asa xuwa farfajiyar gidan ya watsa ta a bayan mota sannan ya kirawo Joseph ya fad'a mishi ya kai jiddah gidan su sannan ya wuce cikin gidan xuciyar shi kamar xata tarwatse saboda yanda take bugu yana shiga cikin d'akin shi ya fara jifa da komai na d'akin yana fasa su tuni d'akin yayi kaca kaca duk ya yanke a hannun shi fuskar shi ta yi jawur da ita hannun shi yasa cikin lallausan gashin kanshi yana yamutsa shi ya rasa inda xai sa kanshi yaji dad'i Bayan ya gama tarwatsa komai na d'akin a k'asa gefen bed ya xube yana wani irin shashshak'a idanun shi sunyi matuk'ar yin ja can kuma suka fara xubar da wasu xafafan hawaye suna sauka kan face d'in shi Allah sarki abduljabbar ya bani tausayi sosai yanxu mai xai cewa nauwara da wani ido xai kalle ta har ya bata hak'uri shi yasa ake son mutum ya dunga bincike Kafin ya aiwatar da abu kada yaxo yana da nasani wani xaxxafan xaxxa6i ne ya rufe shi tuni ya fara karkarwa hannun shi ya mik'a ya d'auko picture d'in nauwara tayi kyau sosae tana sanye da english wears tana er dariya mai ban sha'awa duk dimple d'in ta biyun sun lotsa baisan lokacin da ya saki wata er k'ara irin wanda mutum ya shiga cikin mugun damuwa yayi rungume photon yayi a kirjin shi yana wani irin kuka kamar ba soja ba kodan so ba ruwan shi Lokacin da joseph Yayi parking a kofar gdn su jiddah dakyar ta iya fito wa ta shiga gidan duk jikin ta jina jina tana wani irin kuka ita duk duka nan da yayi mata bai dame ta ba irin sakin da yayi mata yaraf ta xube a tsakar gidan nasu da sauri mamee ta k'araso inda take hankalin ta a matuk'ar tashe ta d'ago ta cikin kid'ima da ganin yanda Jiddah ta koma duk fuska a kumbura yasa tace "lafia jiddah me yafaru wane yayi miki hka??? " Jiddah ba baki dole Hka ta hak'ura ta had'a ruwa mai d'umi ta gasa mata jikin ta sannan ta bata paracetamol ta kora sannan tace "kiyi min bayani jiddah wane yayi miki hka" "Abduljabbar ne? " Nan take mamee ta had'e rai sai da gaban jiddah ya fad'i tace "me ya had'a ku ki fad'a min gaskia bana son k'arya " "wai wai akan hmm....." Ta kasa K'arasa fad'i saboda tsoro batasan wanne irin abu mamee xata yi mata ba Idan taji abin da ta aikata kuma dole ta fad'i gaskia ko don ta samu ta roki mamee tasa Abduljabbar ya mayar da ita baxa ta iya rayuwa babu shi ba tayi nadama kuma irin wadda ake so baxa ta k'ara gigin aikata hkan ba ta tuba tsawar da mamee ta daka wa jiddah shi ya katse mata tunanin da take yi harara ta watsa mata sannan tace "kin xaunar dani ke fah nake jira??? " Tsugunna wa tayi a k'asa ta rik'e kafafun mamee cikin kuka ta fara rokan ta ta yafe mata kuma wallahi ta tuba baxa ta k'ara ba nan ta kwashe komai ta fad'a wa mamee tun daga lokacin da farida ta bata shawarar ta kai wani d'akin nauwara matsayin tana aikata fasikanci da maxa don abduljabbar ya sake ta har xuwa yau da asirin ta ya tonu yayi mata sannan uban dukan tare da yi mata saki bata rufe bakin ta ba mamee ta dalla mata mari har biyu Sannan ta fashe da kuka tana cewa "ashe duk abin da kika aikata a baya jiddah baki yi nadama sai da kika kuma aikata wani kin raba mata da mijin ta saboda shegen kishin ki wallahi abduljabbar yayi min dai dai naso ma yayi miki abin da yafi hka da nasan Hkane wlh da ban kula ki ba ga Ki ga gidan sai kixo mu xauna tare kici uwar da xaki ci bari baban naki ya dawo" Tana gama fad'in hka ta hankada jiddah ta fad'i sannan ta mik'e tsaye ta fita waje tana goge hawayen fuskar ta ta bar jiddah tana cin uban kuka a d'aki tayi nadama ta tuba kuma ba tuban muxuru ba na tsakani da Allah Indai abduljabbar ya mayar da ita xata xauna da nauwara tsakani da Allah Baban jiddah da mamee ta fad'a mishi komai ba abin da yace kuma ko kallon jiddah Inda take bai yi ba hakan ba k'aramin k'ara tsurar da jiddah yayi ba ****** Tana nan kwance taji k'arar Shigowar message d'in takai hannu xata dauki wayar don ta duba su umma suka yi sallama suka shigo d'akin murmishin yak'e ta hau yi nan suka gaisa aka hau yin hira na'eem da ameer suna mak'ale a jikin ta umma ta kalli nauwara da ammi tace "Ohh na mance waya ta a gida ina son kiran Abba naji fa'iza ta taho kuwa" "gaskia ya kamata a kirawo aji " Cewar ammi "nauwara ban wayar ki na kirawo shi" Umma ta fad'i tana mik'a hannun ta ba tare da wani abun ba ta mik'a mata kura wa screen d'in kallo umma tayi mamaki d'auke a fuskar ta ganin mssg da abduljabbar ya turo mata bud'e wa tayi a hankali ta fara karanta wa xumbur ta mik'e tsaye tana fad'in Innalillahi wa'inna ilaihir rajiu da sauri ammi da nauwara suka yo kan umma suna tambayar ta lafia amman ta k'asa magana da sauri nauwara ta d'auki wayar ta duba wa tayi ita ma ta karanta wani kuka ne ya kufce mata daman tasan ai K'arshen alewar k'asa shekara wajen uku baka xaune gidan miji sai gidan iyayen shi daman ai wannan abin ne xai biyo baya balle ga irin xargin da yake mata wayyo Allah gani gare ka ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki.... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 85~* Cikin tashin hankali ammi tace "nauwara lafia me yafaru? " Cikin kuka da takaici tace "ammi ya.... ya sake ni" Rik'e nauwara ammi tayi tana girgixa ta "me kika ce bangane ba? " "umma Yah abduljabbar ne ya turo min mssg ya sake ni baxai iya cigaba da xama dani ba ammi na rayuwa ta ishe ni daga wannan sai wannan Yah Allah gani gare ka " Ta fashe da wani irin marayan kuka ammi ma sosai abin ya bige ta amman ta jure tana rarrashin nauwara da umma da take xaune ta xabga tagumi ko magana ta kasa yi saboda bak'in ciki Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da doctor muh'd Abdullah yake fad'i yana ja da baya daga jikin kofar shiga room d'in da aka kwantar da nauwara yaxo xai shiga yaji wannan labarin waje ya samu ya xauna dafe kanshi yayi idanun shi sunyi ja alamar yana cikin tashin hankali na abin da yaji wani tausayin nauwara ne ya ke ratsa xuciyar shi tashi tsaye yayi ya fita daga asibitin kai tsaye airport ya nufa don d'auko fa'iza duk da baisan ta ba amman yaga photon nan ta a wayar nauwara kuma xai gane ta Bai sha wahalar samun fa'iza ba tana tsaye rik'e da trolly sai handbag a hannun ta tana ta faman kiran wayar umma ba'a d'auka ba hka wayar nauwara ma gaba d'aya ta d'an rud'e ko lafia sallama taji anyi mata cikin wata murya mai dad'i da sauri ta jiyo suka had'a ido da doctor muh'd Abdullah yana mata murmishi gaban fa'iza ne ya fad'i lokaci d'aya dakyar ta iya amsa mishi sallamar "am Kece fa'iza koh sister d'in nauwara? " Cikin mamaki fa'iza tace "Ya akai kasanni malam? " er dariya yayi sannan yace "ba abin mamaki ba ne don na sanki so ki kwantar da hankalin ki ba sace ki xanyi ba" D'an hararar shi tayi tana cewa "bansan ko kai wane ba baxan bi ka ba" D'an ta6e baki yayi Kafin yace "Sunana doctor muh'd Abdullah nine likitan da yake kula da nauwara " D'an murmishi tayi sannan tace "okay yanxu suna ina? " "Tana hospital sai ta k'ara samun sauk'i xan sallame ta " Ya K'arasa fad'i yana rik'o trolly di'n hannun ta ya sa a mota tukunna suka shiga suna er hirar su har suka k'araso asibitin har room d'in da nauwara take ya nuna mata cikin tsananin farinciki ta nufi d'akin Jikin ta ne yayi sanyi lokacin da ta tarar da umma nauwara da ammi acikin wani irin hali nan ta rikice ta fara tambayar abin da ya faru ammi ce tayi k'arfin halin sanar da ita fa'iza har da kukan tausayin nauwara haka ta rungume ta suna kuka A wannan tsakanin lokacin doctor muh'd ya sallami nauwara daga asibitin ta samu lafia sosai kuma ba k'aramin kula wa yake bata ba ita da twins abin har mamaki yake ba wa su umma duk wajen wani shakatawa haka xai kwashe su ya kai su wai don nauwara kada ta kadaice ita d'aya tana tunani ya haifar mata da wata matsalar Umma ta kirawo Abba ta sanar dashi abin da abduljabbar yayi aikuwa ranshi ya 6aci sosai anan yake sanar da ita ai nan ma ya saki jiddah tare da yi mata duka ashe ita ta shirya wa nauwara wannan makircin ita da k'awar ta mahaifin jiddah ne yake xuwa ya sanar da abban sosai umma ta yarda da jiddah xata aikata abin da yafi hka ma akan kishi Umma bata b'oye wa nauwara da ammi ba duk da kuwa jiddah er kanwar ta ce daman fa'iza ta xargin hakan ammi kuwa bata ji dad'in sakin jiddah da yayi ba nauwara kuwa baxa ka fahimci halin da take ciki a wannan lokacin ba ******* Jiddah sosai tayi nadamar abin da ta aikata ga shegen uban aikin da take sha a gidan itace girkin safe, tana, dare, wanke wanke, wankin kayan mamee da babanta don hka yace ya daina bada wankin shi tunda ga mai wanki Ya samu komai na gidan ita take yi tun Bata iya ba har taxo ta K'ware tayi bak'i ta rame sosai ga aikin nata ma baban nata ya soke shi Tuni sunyi baram baram da farida a karo na biyu kenan tayi kuka sosai tayi nadama ga abduljabbar ko sake waiwaiyar ta bai ba ko ta kirawo shi baya picking sai dai ta tura mishi text mssg na ban hak'uri kullum sai ta tura mishi amman babu reply duk ta sukurkurce ta xama wata iri kamar ba jiddah ba er gayu son hutu da jin dad'i Daga K'arshe ma wata makarantar islamia ta nema anan layin su take xuwa ta xama so silent kodayaushe kullum cikin neman gafarar ubangiji take abisa laifukan da ta aikata Iyayen ta ma sun hak'ura ganin yanda ta shiryu sun janyo ta jikin su kulawa sosai suke bata tun da ta gane kuskuren da ta aikata gashi har da shiga islamia ita kanta yanxu tafi jin dad'in rayuwar ta fiye da baya yanxu babban burin ta na K'arshe ta nemi yafiyar nauwara sannan abduljabbar ya mayar da ita dakin ta.......... ******* Tun daga ranar abduljabbar sai da ya kusan sati bai fita konan da can ba yana kwance a d'aki rungume da photo nan nauwara ya rame ko abincin kirki baya iya ci kullum cikin tunanin ta yake Ana cikin hka aka neme shi a wurin aiki dole haka ya tarkata ya tafi abuja ba don yaso ba to aikin da ya tarar a gaban shi kusan shi ya d'an rage mishi tunani don kusan ko dayaushe yana busy Ya dage da addu'ar Allah ya kawo mishi mafita Ko lokacin da ya fad'a wa abdulkareem bai ji dad'in abin da yayi ba hka ya bashi hak'uri tare da rarrashin sa haka ya bar abuja cike da tausayin abokin nashi yana cikin tsaka mai wuya ******** Alhmdllh sauk'i ya samu wajen nauwara ta dawo normal k'asar London ta kar6e ta don ta k'ara kyau fatan ta ya murje tayi wani irin fresh haka ma twins sunyi k'ara girma kamannin abduljabbar yana dad'a fito wa yaran sun shiga ran doctor muh'd sosai Da hka suka share watanni 3 a london tukunna suka fara haramar koma wa 9ja doctor muh'd wani katafaren shopping malls ya kai su kowacce ta xa6i abin da take so nauwara da fa'iza sai na'eem da ameer Nauwara kasa d'aukan komai tayi sai wani perfume designer mai matuk'ar sanyin k'amshi shi kawai ta d'auka kallon ta yayi cikin wani irin salo yayi k'asa da muryar shi yace " mameen na'eem don Allah ki saki jikin ki ki dauki duk abin da yayi miki please " Kallon shi tayi fuskar ta d'auke da Murmishi tace "Haba doctor ai na d'auki turare wannan ma ya isa ngde" Bai k'ara ce wa komai ba yayi gaba ya fara diban kayayyaki bin sa da kallo tayi ba tun yanxu ba ta gama karantar shi kiris yake jira ya bayyana mata abin da ke cikin xuciyar shi Toh Hka yayi mata shopping na daban masu matuk'ar kyau da tsada har fa'iza tana tsokanar shi ita ma fa'izan ta yaba da doctor muh'd di'n yana da halayya masu kyau kuma xata yi farinciki da hkan Indai wannan had'in ya tabbata Yau misalin karfe 7 na dare flight d'in su nauwara xai tashi xuwa 9ja suna tsaye a jikin motar doctor muh'd a cikin airport d'in ammi umma suna xaune acan wani 6angare a xaune kan kujera fa'iza da twins sun gama sallama da doctor muh'd sun tafi wajen su umma aka barshi da nauwara a tsaye cikin wani irin yanayi yace "Shikenan xaki gudu ki barni sai kuma yaushe " cikin sigar xolaya tace "sai watarana " Had'e fuska yayi yanda yayin ya bata dariya don shi mutum ne ma'abocin fara'a harara ta yayi yace "hmm nauwara dole kiyi min dariya mana kin gama sa xuciyata ta saba dake xaki ce min sai wataran " Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana d'an wasa da xoben hannun ta cikin sanyin murya yace "a yau nayi niyyar tona miki xuciya ta nauwara ina son ki kuma da aure wlh tun lokacin da na d'ora idanu wana akan ki naji ina k'aunar Ki sauran en watanni na dawo nigeria da xama gaba d'aya naso tare ma xamu koma so hkan bai samu ba " Tun da ya fara maganar shi kanta na sunkuye daman ai ta dad'e da ganin alamun hkan a tattare shi haka dai yayi ta tona mata asirin xuciyar shi ta yanda ta kamu da son ta sosai ta tausaya mishi ita gaba d'aya xuciyar babu son wani d'a namiji Idan ba gwarxon ta ba abduljabbar kuma baxa ta6a son wani ba kamar shi sai dai wani ikon Allah, suna nan tsaye har xuwa lokacin da aka kirawo sunan ita ce ta kusan ta K'arshen shiga jirgin saboda yanda doctor muh'd ya tsare ta da xaxxafan Kalaman shi.......... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 86~* Sun sauka a 9ja lafia aunty sadiya ce taxo d'aukan su cikin tsananin murna suka rungume junan su bayan an gama gaisa wa suka shiga mota suna k'arasa wa gida bayan aunty sadiya tayi parking suka firfito daga motar part d'in umma suka nufa ko'ina tsaf an gyara shi sai k'amshi turaren wuta da air freshener yake ga girki Kala Kala akan dinning table wanda aunty sadiya da kanta ta shirya musu Kowa bedroom ya nufa don yin wanka sannan axo aci abinci, nauwara tana d'aure da towel tana kok'arin riga fa'iza shiga wanka don baxa ta iya xama har tayi wa na'eem da ameer sannan tayi ba wayan tane ya fara k'ara alamar kiran ta ake d'an tsaki taja fa'iza nayi mata dariyar k'eta hararar ta tayi a fusace ta k'ara sa wajen Kafin ta d'auka har fa'iza, na'eem da ameer sun shige toilet da gudu abin dariya ya Bata ma ganin sunan doctor muh'd yana yawo akan screen d'in wayar yasa ta d'aukan wayar bayan sun gaisa yake cewa "kin min adalci kuwa Ummu na'eem har kin mance dani ko, ina nan cike da kewar ki son ki ya hana xuciya ta sukuni ki tausaya wannan bawan Allah ki kar6i soyayyata" Ya K'arasa maganar cikin sanyin murya hkan da yayi ba k'aramin tausayi ya Bata ba tare da sanyayar mata jiki sauke ajiyar xuciya tayi a hankali sannan tace "Haba taya xan mance da likitan da ya ceto rayuwa ta a lokacin da aka fidda tsammani da Cigaban rayuwa ta muma munyi kewar ka" Sai lokacin taji sautin murmishin shi tare da sauke ajiyar xuciya yace "ina twins da fa'iza, umma da ammi dafatan an je gida lafia" "lafia klau " "Masha Allah" Sun d'auki tsawon mintuna 10 suna waya sannan suka yi sallama ta waigo ta Kalli fa'iza da take shirya twins tace "doctor muh'd yana gaida ke " Cikin murmishi fa'iza tace "ina amsawa naga alama da wannan doctor muh'd ya samu shiga dashi xa'a yi " Wani kallo nauwara ta bita dashi fuska a d'aure sai ta juya ta shiga toilet ta bar fa'iza sororo a tsaye cike da dumbin mamakin yanda ta canja lokaci d'aya ba dai duk abin da Yah abduljabbar yayi mata har yanxu akwai son shi a xuciyar ta ba toh idan ba hka ba mene dalilin canjawar ta gaba d'aya a lokaci d'aya Gaba d'aya kowa ya hallara a dinning table ana cin abinci bayan an kammala suka dawo cikin parlour ana er hira yayi da nauwara ta ke6e kanta waje d'aya ta rasa wanne abune yake damun xuciyar ta amman tabbas tasan baxai wuce son Yah abduljabbar da kuma abin da yayi mata kasa jurewa tayi sai da tayi kuka ko taji sauk'in abin da yake damun ta Bayan dawowar su nauwara da Sati d'aya suka tarkata sai kaduna garin gwamna garin da raban shi da ita tsawon wasu shekaru tun a hanya take kuka don tunawa da mahaifin ta a gidan baffah suka sauka sun samu tar6a sosai en uwa na nesa da na kusa sun xo taya su baffah murnar samun jikokin su a ranar aunty safiyya kanwar Alhj sa'eed ya duro k'asar 9ja don bata k'asar tun bayan mutuwar yayan ta da iyalan shi mijin ta aka tura shi wani course a k'asar Switzerland a lokacin da suka ji labarin su nauwara basu mutu ba da ammi suka fara shirye shiryen taho wa daman mijin nata ya kammala abin da ya kai shi Switzerland di'n don hka suka taho gida nigeria Aunty safiyya ta sha kuka sosai tana rungume da nauwara a jikin ta saleem na gefen ta a xaune amman hannun ta yana rike da nashi motsi Kad'an ta jiyo ta kalle su xuciyar ta cike da tarin farinciki ta tausaya wa nauwara sosai lokacin da taji labarin ta A hka rayuwa ta cigaba da tafiya nauwara da saleem sai da sukayi wajen wata d'aya a kaduna cikin en uwa sun k'i su dawo umma gajiya tayi da rashin dawowar su ta Shirya ta tafi kaduna ta sako su a gaba suka dawo kano amman ammi tayi xamanta acan Jiddah da maman ta sun xo gidan umma jiddah ta bawa umma hak'uri sosai da nauwara ta roki su yafe mata kuma sun yi hak'uri yafe mata amman sunyi mamakin canja war jiddah sosai ai daman idan ka hana tukunyar wani tafasa to kai ma taka baxa tayi xafi ba balle ta tafasa rayuwa ai juyi juyi ce wai kad'o ya fad'a ruwan xafi a Wannan duniyar da rayuwar da muke ciki wanda cin amana tsantsa butulci hassada da rashin gaskia yayi yawa acikin xuciyoyin mu kana xaune da mutum tsakani da Allah amman baka san abin da yake k'ulla wa ba cikin xuciyar shi ba wani ma gaba d'aya so yake yaga baka duniyar Allah yasa mu fi karfin xuciyar mu Allah ya bamu ikon aikata dai dai a rayuwar mu Ameen Kamar yau misalin karfe 5 na yamma nauwara tana xaune a bedroom tana sanye da wani Pakistan rigar blue ce da adon flowers fari sai dogon wandon rigar fari ne shima ta gyara gashin kanta ta xubo shi bayan ta bata daure shi da ribbom ba tana waya da doctor muh'd yana fad'a mata acikin wannan week d'in xai dawo bata ankara ba taji na'eem ya kar6e wayar ta dake mak'ale a kunnen ta cikin sauri tasa hannu ta kamo shi tare da kok'arin kar6ar wayar sai ya cilla wa ameer wayar caraf yaron ya cafe yana dariya yayi hanyar fita daga d'akin da d'an gudun shi kunnen na'eem ta d'an ja sannan tabi bayan ameer shima na'eem da gudu ya fice ya bisu Gaba d'aya twins su rikita ta idan ta kama ameer tana kok'arin kar6ar wayar sai ya cilla wa na'eem suna mata dariya duk Hayaniyar da suke doctor muh'd yana jinsu sai faman murmishi yake xuciyar shi na k'ara son nauwara yak'i kashe wayar don so yake yaji K'arshen wannan wasan uwa da 'ya'yan ta kuma adai dai lokacin nan MG abduljabbar yana tsaye a kofar shiga falon ya xuba musu ido yana kallon su cike da sha'awa wani son nauwara yana dad'a ratsa cikin jikin shi da xuciyar shi gyara tsayuwar yayi yana harde hannuwan shi a kirjin shi shi ma yana son ganin K'arshen wasa nan Duk tabi ta gaji ta tsaya cak tana mai da numfashi tana kallon na'eem da ameer da suke tsaye d'an nesa da ita na'eem wanda wayar take hannun shi ya d'ago ta sama yace "mamee mu cigaba da wannan playing game di'n mu ga wane xai samu sa'ar kar6ar wayar " "yes! hkane na'eem good idea dama aunty fa'iza da bros saleem suna nan " Ameer ya fad'i hkan suna tafawa da na'eem Kafin su ankara nauwara tayi kansu da gudu da k'arfi suka saki ihu xasu gudu cikin xafin nama ta rik'e rigar na'eem ta amshe wayar ta nan suka fara kukan shagwa6a tare da bubbuga kafafun su a k'asa hararar su tayi sannan tana huci tace "Allah kuna son na doke ku kullum sai kunsani gudu a gidan nan to ku kiyaye ne " "mamee ai Idan kina Hka baxa kiyi k'iba ba irin auntyn mu a skul" "ofcourse na'eem nima bana son mamee tayi jikin auntyn mu " Ameer ya fad'i yana wani yatsina fuska ba k'aramin dariya suka bawa nauwara ba hka ba abduljabbar da yake tsaye yana kallon shi shima doctor muh'd da yake sauraren su ta waya dariyar yake yi sosai tama rasa me xata ce musu sai hararar su tayi ta juya xata nufi upstairs sai naga na'eem ya Kalli ameer sun kashe ido d'aya wani abu na'eem ya fito dashi a jikin aljihun wandon shi shi da ameer kowa d'aya d'aya sadaf sadaf suke bin bayan ta abduljabbar dai yana tsaye yana kallon mai su twins xasu sake yiwa nauwara d'ora mata lizard di'n roba sukayi kan rigar ta sannan da sauri suka ja da baya kamar had'in baki suka fara ihu da tsalle suna cewa "wayyo Allah mamee bayan ki a jikin rigar Ki lizard guda biyu sun mak'ale " A matuk'ar firgice ta jiyo tace "da gaske na'eem " Cikin tsalle tsalle da ihu na'eem yace " I swear mamee sai motsi suke " Kafin ya K'arasa fad'i nauwara ta saki wani ihu tare da fara tsalle kamar yanda su na'eem suke su kuma sai kunshe dariya suke yi jin motsin abu a jikin rigar ta yasa ta ta dad'a rikice wa ta rud'e sosai batasan da tayi hanyar fita daga falon ba duk ta kid'ime karo tayi da abduljabbar da yake kok'arin xuwa ya cire mata fad'o wa tayi jikin shi tare da Kank'ame shi shi ma k'ara rungume ta yayi tsam a jikin shi sannan yasa hannu ya cire mata lizard di'n ya xubar dasu k'asa yana d'an hararar twins da suke mata dariyar k'eta sunkuyar da kansu kasa suka yi Jikin ta sai faman 6ari yake saboda tsabar tsorata hannun shi yasa yana bubbuga bayanta cikin sanyin murya ya rad'a mata a kunne " shiiiii calm down nauwara lizard di'n roba ne twins suka sa miki " Saukar sautin muryar shi a kunnen ta shi yasa ta d'ago wa da tare da barin cikin jikin shi lokaci d'aya ta had'e fuska ko kallon Inda yake bata yi ba taja d'an siririn tsaki ta shige falo kallon su na'eem tayi ranta a 6ace ta daka musu tsawa da sai da suka tsorata suka shige jikin abduljabbar suna b'uya alama yayi musu da hannu su je su Bata hak'uri don hka cikin sanyin jiki suka K'arasa wajen ta tare da durkusawa a k'asa suka rik'e kunnuwan su duk biyun suka marairaice fuska kamar xasu yi kuka cikin had'in baki suka ce "I'm sorry mamee baxa mu k'ara ba wannan shine last please " Shafa kansu tayi cikin murmishi tace "alright my guys, muje ku shirya mu tafi shan ice cream " Rungume ta suka yi suna cewa "yes! Mamee thank u, i luv yhu so much " Suka bata peck a kumatu da goshi sannan sukayi upstairs da gudu Duk abin nan da suke abduljabbar yana tsaye yana kallon su cike da kaunar su Bata Kalli Inda yake ba ta juya xata tafi taji maganar shi cikin sanyin murya yace "nauwarahhh d'an tsaya xanyi magana da ke please " Tsaya wa tayi bata jiyo ba ganin hka yasa ya K'arasa gaban ta ya tsaya sai da ya d'an tsorata ganin yanda fuskar ta koma 6acin rai ne kwance akan fuskar yana kallon fuskar ta yace "ina neman afuwar Ki akan abin da na aikata miki kiyi hak'uri rashin sani ne " "hak'uri kace fah!!!?" Yanda tayi maganar sai da ya xaro idon shi saboda bai ta6a ganin Wannan yanayin a tattare da ita sai yau Kafin ya ankara ta kewaye shi ta tafi cikin sassarfa take hawa stairs baki sake yake bin ta da kallo Lallai yakai nauwara bango dole ya fuskanci hkan daga gare ta sai yayi hakuri don yasan nauwara tana son shi 6acin rai ne na abin da yayi mata dafe kanshi yayi idanun a lumshe yace "Ohh Yah Allah ka kawo min agaji Yah Allah kasa nauwara ta huci daga fushin da take dani " Yana gama fad'in hka ya xube akan kujera yana sauke ajiyar xuciya....... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _Hak'ik'a samun k'awa kamar ki sai an tuna ina alfahari da ke my saNaz i really luv u, Allah ya k'ara xumunci, Allah ya barmu tare, Allah ya kare min ke a duk inda kike Allah ya cika miki buri kanki na alkhairi Ameeen_❤😘😘 *~Pg 87~* Yana nan xaune suka fito a shirye duk sun canja kayan jikin su alamar wanka tayi ita dasu na'eem da ameer tana rik'e da key d'in mota a hannun ta d'aya hannun tana rik'e da waya mak'ale a kunnen ta hira suke da doctor muh'd yana tambayar ta K'arshen wasan su ita da twins sai abin ya bata dariya don hka ta dunga er dariyar ta cike da jan aji, ya xuba mata ido kallon ta kawai yake don tayi bala'in yi mishi kyau tana sanye da wata yellow da bak'in gown tayi rolling da veil bak'i da adon flowers yellow sai tayi amfani da black shoes marasa tudu sosai maganar da tayi ita ta dawo dashi hayyacin shi wanda ta kusan haddasa mishi bugawar xuciyar shi "Haba doctor kada ka damu Allah ya kawo ka lafia kai dai idan kaxo xaka ga irin kewar ka damu kayi " D'an langa6e kai tayi tana sauraran abin da yake cewa ganin Yah abduljabbar ya xuba mata ido da alamar ranshi ya fara 6aci don hka ta dad'a shagwa6e wa tace "ah ka wuce nan a wurina Bari naje na dawo xamu shan ice cream ne" Cikin mamaki tace "kishi kuma? ", "Haba kasan bana kula kowa sai kai saboda xuciya ta..........." Kafin ta ankara taji an warce wayar da sauri ta d'ago kanta karaf suka had'a ido da abduljabbar idanun shi sunyi jawur dasu sai faman huci yake duk da ta tsorata da ganin yanayin shi amman sai ta dake cikin d'aure fuska tace "lafia ina waya ka kar6e min? " Wata harara ya watsa mata kafin kuma a fusace yace "da uban wa kike waya?" Sam ta manta dasu twins a wajen ta turo baki gaba sannan tace "da my sweet darling nake Mag........ " kafin ta K'arasa fad'i taji an murd'e bakin nata da k'arfi axaba ta ishe ta ga ba bakin yin ihu umma ta kawo agaji sai da yaga ta jigata idanun ta sunyi ja ga hawaye yana fita a idon sannan ya cikata wani wahalalen numfashi take sauke wa wata er k'ara ta saki jin ya kamo gashin kanta da hannun shi cikin tsawa yace "wlh na sake jin Kinyi waya da wani katon sai nayi 6a66allaki a gidan nan " "wlh baka isa ka hanani kula kowa ba kuma wallahi baxan yarda da wannan muguntar ba ina ruwan ka dani da bakin ka kace ka tsanane fah naje nayi rayuwar da nake so " Lokaci d'aya jikin shi yayi wani bala'in yin sanyi a hankali ya cika mata gashin kanta ya xube kan kujera tare da nutsar da hannun shi cikin gashin kanshi, kallon shi tayi taja tsaki tare da kama hannun su twins wad'anda har sun fara kuka ganin mameen su na kuka da kanta tayi driving d'in xuwa wurin shan ice cream da pizza nd shawarma ta siyo sannan suka dawo gida Lokacin da ta shiga falo ba k'aramin mamaki tayi ba ganin har yanxu abduljabbar yana nan Inda ta barshi sai dai yanxu ya kwanta a rigingine kan kujerar ta6e baki tayi ta shige kitchen don sanya ice cream a frige sannan ta fito ta tarar na'eem da ameer sun sake dashi har suna bashi labari yana d'an murmishi tare da shafa musu kan su ganin ta fito daga kitchen yasa shi mik'e wa tsaye yana cewa "taimaka min da abinci I'm hungry " Bata Kalli Inda yake ba tayi gaba tana cewa "ka nemi house girl ta baka ni bani da wannan time d'in " "nauwarah bakya afuwa ne, na baki hak'uri kinki ki hak'ura " "ehh baxan hak'ura ba din " Jin alamar ya biyo bayan ta yasa ta watsar da ledar hannun ta ta shawarma ta xura a guje ta fad'a d'aki tare da murxa key Sunkuya wa yayi ya d'auki ledar ya dawo falo wajen na'eem da ameer wanda gaba d'aya hankalin su yana kan tv suna kallon cartoon a tashar mbc 3 suna shan ice cream di'n su hankali kwance Sai da ya cinye shawarma biyu Sannan ya tashi ya d'auko fresh milk mai sanyi yasha cikin glass cup d'aya sannan yaji shi dai dai don k'wanakin nan ba k'aramin hora kanshi da yunwa yake ba A hka umma ta dawo ta ganshi Ko kallon Inda yake bata yi ba ta haye stairs fa'iza ce ta gaida shi ita ma ta wuce saleem ne ya xauna kusa dashi ya gaida shi sannan suka fara er hira bai nuna mishi komai don yana son abduljabbar sosai guy d'in yana birge shi kuma yana nan yana addu'a sai sun mayar da auren su da aunty nauwara sai da aka kirawo sallahr mangarib sannan suka tafi masallaci acan suka hadu da abba dakyar abba ya amsa mishi gaisuwar shi duk jikin abduljabbar yayi masifar yin sanyi dole ya nemi su abba su yafe mishi ko yaga dai dai a rayuwar shi iyaye sun fi k'arfin wasa fushin su ba k'aramin tashin hankali ba ne akan shi Har falon abba abduljabbar ya bishi ya dunga bashi hak'uri akan laifin da yayi tare da alkawarin baxai sake aikata hkan ba sharrin xuciya ce da rashin bincike dakyar abba ya hak'ura sannan yayi mishi nasiha sosae akan saurin yanke hukuncin cikin fushi daga K'arshe ya nemi da dole ya mayar da jiddah d'akin ta don baxai xauna a haka ba laifi ne tunda ta riga ta aikata ya wuce sannan tayi nadama sosae don taxo ta bamu hak'uri har da nauwara kuma ta hak'ura ta yafe mata Bashi da yanda xai yi ya amince da abin da abba yace tunda sulhu yake nema can kuma yace "am uhm abba don Allah nauwara fah ina son na mayar da ita " Wani kallo abba ya watsa mishi ba shiri yayi shiru fuska a d'aure yace "ai nauwara Kun rabu har abada tunda kayi kunnen uwar shegu da abin da umman ka tace gwara ta xa6i wanda xata iya jin dad'in xama dashi wanda xai dunga bincike Kafin ya xartar da hukunci " Da k'arfi abduljabbar yace "nooo Abba kada kace hka ina son ta idan na rasa ta xan iya shiga wani hali ka taimaka min Abba na same ta nayi alkawari baxan sake aikata hkan ba please " Sosai ya bawa Abba tausayi amman ya dake yak'i nuna mishi yaji tausayin shi don yana so ya shiga taitayin shi gaba baxai sake aikata hkan ba "ni na gama magana tashi ka ban wuri xan huta" Kallon abban yayi sannan yace "I'm sorry Abba Idan na 6ata maka rai Gud nyt " yana fad'in hka ya fice daga falon jikin shi a matuk'ar sanyaye Kai tsaye part d'in shi dake cikin gidan ya nufa ko'ina tsaf a gyare xube wa yayi kan bed bai ankara ba sai jin saukar abu mai d'umi yaji afuskar shi alamar hawaye ne ya kasa rik'e su har sai da suka xubo mishi kusan Kwana yayi baiyi baccin kirki ba sai juye juye xuciyar shi a kuntace Tun daga ranar nauwara da abduljabbar basu sake had'u ba da junan su duk da yana bala'in son ganin nata kuwa amman ba fuska wajen umma Misalin karfe 5 na yamma nauwara tayi parking d'in motar su a bakin jifatu store suka fito ita da fa'iza daga motar sun ci gayu cikin wata atampha d'inkin fitted gown kowannen su sai dai different colours na atamphar sunyi matuk'ar yin kyau Idan ka Kalli nauwara baka ce ta haifi na'eem da ameer ba kai tsaye cikin jifatun suka shiga nan suka fara duba abubuwan da suke buk'ata tana cikin duba perfumes taga wanda take nema takai hannu xata dauka sai taga wani hannu daban ya d'auke shi da sauri d'an d'ago ido tayi don taga wane wannan karaf suka had'a ido da wani kyakkyawan matashi yana murmishi a fuskar shi ta juya xata tafi taji yace "nauwarah ina saleem?? " cikin tsananin mamaki ta juyo ta kalle shi har yanxu murmishi ne a fuskar shi "Kina mamaki ne Inda na sanku nasan baxa ki gane ni ba da saleem yana nan xai gane ni" "don Allah malam kai wane, ina kasan mu? " "Aminu ne" Ya fad'a mata "wanne aminu kuma? " "Aminu mijin hindatu wanda kuka xauna a hannun shi " xaro ido tayi cike da tsantsar mamaki da farin ciki take kallon shi tace "don Allah da gaske kai ne " "wallahi nine nauwara tun lokacin da kuka shigo na gane ki ban k'ara tabbatar da hkan ba sai da na kirawo sunan ki dana saleem naga kin jiyo sannan na gane ki" Nan suka gaisa tace "ina aunty hindatu da yara " "sunan tare ma muke dasu ai xaku gaisa " Cikin er dariya tace "ah mai xai hana kuwa" Fa'iza wadda take gefe tana kallon su nauwara ta gabatar mishi da ita suka gaisa suna tsaye suna er hira duk nauwara ta tak'ura sosai da yanda aminu yake kallon ta tsoron ta kada matar shi hindatu ta xo yana wannan kallon nata....... ( _dafatan mai karatu baku mance aminu wanda ya taimaki su nauwara har suka xauna a hannun shi Kafin hindatu matar shi ta kore su daga gidan_) Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 89~* A fusace ya K'arasa wajen aminu ya mik'a mishi hannu alamar su gaisa wani kallon kaskanci yake watsa mishi kafin ya juyo kan nauwara wadda ta had'e fuska tana jiran taji da mai yaxo Kafin ta ankara taji ya fisgo hannun ta yana janta har xuwa falon umma suka bar aminu a tsaye baki bud'e yana tunanin shi kuma wannan wane, don baisan abduljabbar kuma bai ta6a ganin twins ba da yasan wane shi kamar yanda Dr muh'd ya gane shi ba tare da an fad'a mishi ba, haka yaja motar shi jikin shi a sanyaye ya bar gidan Suna shiga cikin falon ya wurgar da ita kan kujera har sai da ta buge auuch ta furta don bakaramin xafi taji ba ranta ya 6aci sosai da wannan abin da abduljabbar yake mata dole ta d'au mataki kuwa, kafar shi ya d'ora d'aya kan kujerar ya sunkuyo da kanshi saitin fuskar ta yana kallon ta fuskar nan tashi a murtike cikin tsawa yace "na fuskanci so kike xuciya ta, ta tarwatse na mutu na barmiki duniyar gaba d'aya don na fuskanci bakya k'aunar ganina nauwara " Sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa "Kinsan yanda nake bala'in kishin ki shine kike kwaso wasu kaxaman samarin ki cikin gidan nan da uban me suka fi ni iyeee tell me?" Hararar shi tayi kafin tace "wlh ka daina kiran su kaxamai don sun fi min kai sau dubu kuma kallo xan auri d'aya daga cikin su saboda na tabbatar su masoya nane na gaske Duk abin da nayi baxa su guje ni ba" Kafin ta rufe bakin ta taji saukan wani lafiyayyen mari a kuncin ta wani irin ihu ta saki tare da dafe kumatun ta cikin masifa yana nuna ta da hannu yace "wallahi ki kiyaye ni bana d'aukar rai ni, a gaba na ki furta xaki auri wani daban ba ni ba ki rubuta Ki ajiye ba wanda xaki aura sai ni, kuma daga yau kada ki k'ara kawo wani d'an iska cikin gidan nan naga ya miki " Cikin wani 6acin rai hawaye suna xuba daga idanun ta ta fara tafa hannun ta sannan tace "dakyau abduljabbar kawai ka fad'a min kai tsaye wannan gidan ku ne kada na k'ara shigo muku da wani dad'in abin ba daga sama na fad'o ba ina da gidan xan koma daga yau na bar maka gidan nan xan koma Inda na fito " Kusan suman tsaye abduljabbar yayi cike da mamakin nauwara wai shi yau xata kirawo da abduljabbar kai tsaye Lallai ya kai ta bango kada fa garin neman gira ya rasa ido "babu Inda xaki nauwara muna tare sai dai shi ya bar gidan" Da sauri suka juya bayan su umma suka gani a tsaye ranta a 6ace k'araso wa tayi ta rik'e hannun nauwara ta Kalli abduljabbar tace "wlh ka kiyaye ni abduljabbar ina sane da yanda kake tak'ura mata a gidan nan ana so dole ne ko kuma dole sai ta koma gidan ka ne? " Kwantar da kai yayi tare da marairaice fuska yace "Haba umma nasan ke ma wlh kinaso ta dawo gida na da Zama ki lalla6a min ita ta yarda please " Harara umma ta watsa mishi kafin tace "yaushe na fad'a maka haka ni ba ruwa na nauwara wuce mu tafi " Suka tafi suka bar abduljabbar a tsaye a wajen ya rasa inda xai sa kanshi yaji dad'i gaba d'aya ya girgixa da jin kalaman nauwara ta dai na sona kenan wata xuciyar ta ce mishi hka da sauri yana girgixa kai yace "noooo baxai yiwu ba nasan nauwara tana har yanxu nasan rama abin da nayi mata take" Sauke ajiyar xuciya yayi tare da cewa "i luv yhu nauwarah! i really luv u baxan iya bari wani ya aure ki ba, Kece uwar 'ya'yanah " Yana gama fad'in hka ya fice daga falon, wasu hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun nauwara duk abin da yake tana kallon shi ta upstairs ya matuk'ar bata tausayi amman dole sai ya gane kuskuren shi a hankali ta furta "i luv yhu too much my Abduljabbar " Tana gama fad'in hka ta shige cikin bedroom d'in xuciyar ta ba dad'i Cikin wannan lokacin aminu da Dr muh'd sun hurawa nauwara wuta kowanne yana son ya turo magabatan shi wurin Abba duk tabi ta kid'ime ta rasa yanda xatayi, Hka 6angaren abduljabbar Abba ya hura mishi wuta Lallai sai ya mayar da jiddah shi kuma wallahi baya k'aunar sake xama da ita ya tsane ta tun da ita tayi sanadiyyar raba shi da nauwara don hka ko Kad'an yak'i yaje gidan su, shi so yake ya shawo kan abba ya yarda a mayar da auren shi da nauwara da twins d'in shi su su bar nigeria di'n baxai dawo ba sai jiddah ta hak'ura dashi ta auri wani sannan xasu dawo don xai iya ajiye aikin shi akan nauwara (toh readers kunji tunanin MG abduljabbar). Jiddah kuwa gaba d'aya tayi sanyi da abduljabbar ganin ko ta kirawo shi baya picking ko message ta tura mishi babu reply har ta hak'ura da kiran nashi ta fara fitar da ran sake xama dashi ta Duk'ufa da addu'a sosai Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi, suna mutunci sosai da nauwara yanxu har waya suke da junan su gashi tana yawan xuwa gidan don kawai taga twins don tana bala'in k'aunar twins komai ta samu haka xata kawo musu ko ta aiko musu . Kiran ta awaya text messages na ban hak'uri Hka kullum abduljabbar yake turo wa nauwara amman bata d'aukan wayar tashi, text mssg di'n kuwa ko karanta wa bata yi take goge wa, ya damu iya damuwa bashi Kano bashi abuja kullum cikin xirga xirga tsakanin kano da abuja har ya fara bawa aunty sadiya, kausar da saleem tausayi sosai suna bayan shi da ya mayar da nauwara don duk basa son Dr muh'd da aminu, saleem har ya tsani suxo gidan don har maganar ya ta6a yiwa nauwara amman hka ta runtse idon ta ta kore shi daga d'akin sam tak'i sauraren shi. Tuni abduljabbar ya xuge 'ya'yan shi sun fara canja wa Dr muh'd da aminu fuska ko wajen su basa xuwa idan sun xo, kuma duk lokacin da suka xo na'eem da ameer sun fara 6ata rai kenan har sai sun tafi, tun basu gane abin da twins suke ba har sun fara fahimta don akwai lokacin da Dr muh'd ya kawo musu ice cream, chocolates, sweets biscuits ya mik'a wa na'eem Amman sai yaron ya yamutsa fuska yace "ka barshi mun gode don dadyn mu yana siyo mana" Cikin mamaki nauwara da Dr muh'd suke kallon su amman ya daure yace "na dadyn ku daban wannan daban don hka oya kar6i kuje kusha" "nooo mun fison na dadyn mu thank u " Ameer ya fad'i hkan tare da kama hannun na'eem suka shige cikin gida ko k'ara waiwaiyar su basu yi ba, kunya ta rufe nauwara kamar ta nutse a k'asa cikin sanyin murya tace "I'm sorry Dr akan abin...... " "ba matsala nauwara " Dr muh'd ya katse nauwara duk ta kasa sake wa can ya sauke numfashi Kafin yace "anya twins ba suna taya baban su kishi ba, a yanda na fuskance su suna so ki koma wurin baban su right" Cikin mamaki take kallon shi d'an murmishin yak'e yayi yace "ki daina mamaki na gama gane su " "Indai har kina sona ki bani damar turo magabata na a cikin Wannan week d'in " Girgixa kai tayi can kuma tace "ba damuwa Allah ya kaimu ya xa6a mana abin da yafi alkhairi " Cikin jin dad'i yace "Ameeen thumma Ameeen " Daga hka suka yi sallama ya tafi ta dawo lokacin da ta shiga falo na'eem da ameer taga suna waya da abduljabbar fuskar su d'auke da farinciki suna ganin ta suka kwasa a guje sai bedroom d'in umma kwafa tayi tare da cewa "xan kama Kune xaku yi bayani ne" Acikin wannan satin ne Dr muh'd ya aiko manyan shi aka gama magana sun bayar da duk wani abu da ake gabatar wa wajen neman aure har da sadakin su, sannan suka tafi aka rabu cikin farinciki A ranar abduljabbar yaji labari a bakin twins sun kirawo shi a waya har da kukan su hankalin shi ba k'aramin bashi yayi ba a lokacin ya bar duk wani aiki ya taho kano Bayan sallahr isha'e ya k'araso gidan kai tsaye d'akin su nauwara ya nufa lokacin tana waya da ammi a fusace ya K'arasa inda take ya kar6e wayar tare da kashe ta cikin jin haushin shi tace "malam wai lafiar ka qlau ne kasan da wa nake waya ka kashe min" Yana mata wani kallo yace "bai shige wannan saurayin naki ba mai wuya kamar marikin lema" Haushi ya ishe nauwara a fusace tace "Ehh da hka naga ni nake son shi " Dalle mata bakin ta yayi da hannun shi da sauri ta dafe bakin nata don da xafi a tsiwace tace "Wlh kada ka k'ara duka na ka cuci wanda xai aure ni " kallon ta yake xuciyar shi na tafasa shi yanxu ya xai yi yabi yarinyar nan ta fad'a tak'i ta amince bare Ya gwada ta rarrashi ko xai dace bata ankara ba taga ya tsugunna a gaban ta ya dure dukka gwiwowin shi a k'asa cikin matuk'ar marairaicewa da sanyin murya yace "na had'a ki da Allah nauwara kiyi hak'uri ki yafe min, ki yarda ki koma gida na wlh duk wata kyautata wa xan dunga yi miki baxan k'ara cutar da ke ba please " Kallon shi take cike da matuk'ar mamaki ganin shi tsugunne a gaban ta yamutsa fuska tayi sannan tace "ni fah na gama xaman gidan ka" "Da matsayi na da Shekaru na na ajiye su a gefe gani a durkushe gaban ki ina neman alfarma tare da baki hak'uri ki koma gida na mu rike yaran mu " "ni fah kayi hak'uri ka nemi wata ka aura ko ka mayar da aunty jiddah " Kallon ta yake xuciyar shi na tafasa da xai iya hak'ura da nauwara da wallahi a yau ya barta har abada amman sam baxai iya ba "da girma na a gaban ki na tsugunna ina baki hak'uri ki k'i hak'ura koh" Shiru tayi bata k'ara magana ba daga bayan su suka ji ance "mamee kiyi hak'uri ki yafe wa daddy please " Da sauri ta d'ago kai taga na'eem da ameer fuskar su sha6e sha6e da hawaye hararar su tayi ta fice daga d'akin, rungume su yayi yana rarrashin su dakyar suka yi shiru sannan ya samu ya ja su xuwa part d'in shi na cikin gidan ranar abduljabbar bai yi cikakken bacci ba sai faman juyi yake da tunanin yanda xai 6ullo wa al'amarin Wani shegen murmishin mugunta ya saki da ya tuno hanya d'aya xai bi don ya samu nauwara ta dole ma, don hka nan take bacci mai dad'in gaske yayi awon gaba da shi baccin da ya dad'e bai yi irin shi ba...... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *note* _namance ban sanar daku lokacin da aka yanke na auren nauwara da Dr muh'd ba, so su yanke 2 month's na auran_ *~Pg 90~* Washe gari da safe bayan an kammala breakfast nauwara da fa'iza suka fito cikin shirin tafiya kd xasu je suyi 2 weeks acan su dawo. Bayan sunyi sallama dasu umma suna yi musu addu'ar sauka lafia, suka fito farfajiyar gidan suna tsaye driver yana sanya musu kaya a boot a dai dai lokacin abduljabbar ya fito daga part d'in shi jikin shi sanye da black trouser nd T-shirt blue yayi kyau sosae cikin tafiyar shi ta kasaita ya k'araso wajen fa'iza ta gaida shi yayin da twins suka rungume shi suna fad'in "good morning papa " Yana murmishi yace "morning my sweet kids, ina xuwa hka da safen nan " Cikin dariyar farinciki suka ce "kaduna xamu je gidan baffah da ammi " Murmishi yayi yana jan kumatun su yace " Good Agaida min da baffah da ammi " "okay papa " Peck suka bashi a kumatu shima yayi musu sannan suka ce "byeeee papa" Suna fad'in hka suka shiga motar daman nauwara tuni ta shige ita da fa'iza . Kallon ta yayi ta had'e fuska sosai ta wani kau da kai gefe alamar bama ta son ganin shi abun ma dariya ya bashi amman duk da hka sai da ya xura kanshi ta window d'in motar a kunnen ta ya rad'a mata "babu ko sallama koh, wannan 6ata ran da kike baya yi miki kyau, Indai don ni ake 6ata rai ayi hak'uri na daina tak'ura miki " Turo baki tayi tare da d'an d'ago kai ta saci kallon shi wani mugun fad'uwar gaba tayi lokacin da suka had'a ido ganin yanda yake murmishin muguntar nan kuma ta tabbatar Indai abduljabbar yayi wannan murmishin to akwai muguntar da ya had'a Yah Allah kayi min tsari da muguntar abduljabbar ta fad'i hka a cikin xuciyar ta, barin jikin motar yayi yana d'aga wa na'eem da ameer hannu alamar byeee Yana tsaye a wurin har motar su ta fita daga gidan sannan ya juyo ya shige part d'in umma xuciyar shi wasai da ita sai nishadi yake abin sa ita kanta umma tayi mamakin ganin shi a haka yanda yake ta fara'a har ta fara tsargu wa anya abduljabbar ba wani abun yake shirin aikatawa ba rabon shi da ta ganshi a Hka har ta mance har ta kai da tambayar shi tace "abduljabbar lafian ka qlau kuwa? " Yana murmishi yace "me kika gani umma? " "gani nayi sai fara'a da nishad'i kake, kamar wanda aka yi mishi da albishir da aljannah " Kwashe wa yayi da dariya yana kallon umma wanda take binshi da kallon mamaki yace "uhm umma kin ban dariya wlh, amman babu komai just yau na tashi da farinciki ne " Kallon shi umma tayi sosai sannan tace "Ko wani abu ka shirya wa nauwara ne" "Laaa umma ni ba komai fa, ni yanxu ai na hak'ura tunda har ta tsayar da wanda xata aura" "Allah yasa Hkane har xuciyar taka" Umma ta fad'i hkan ba tare da ta yarda da abin da yace ba yanda yake son nauwara anya xai hak'ura Hka farat d'aya, shi kuwa sai faman murmishi yake har ya gama breakfast ya fita daga gidan. Alhmdullilah su nauwara sun isa kaduna lafia a gidan baffah suka sauka da yake kuma ammi tana gidan don baffah da inna sun ce tayi xaman ta a wurin su ta d'ebe musu kewa, Hka ta xauna suna matuk'ar bata kulawa sosai Idan kaga ammi a lokacin baxa kayi tunanin ta haifi su nauwara ba. Su baffah sunyi matuk'ar farinciki da xuwan su nauwara kyautata wa sosai suka dunga yi musu, a hka suka kwashe tsawon wajen Sati Biyu a kaduna sunje gidan aunty safiyya nan ta nuna mata ita wlh ta fison ta koma gidan abduljabbar ,murmishi kawai ta iya yi har ta gaji da amsa Cewar baxa ta koma gidan shi ba koma kowa ya bud'e baki xai ce ta koma gidan abduljabbar Abba, umma aunty sadiya da fa'iza su kad'ai suke Goyan bayan nauwara ta auri wanda suke so, kuma ta fuskanci ammin ta gaba d'aya ta nuna mata ita abduljabbar take son ta koma gidan shi su hadu su rik'e yaran su gashi dai dai da twins sun fison daddyn su, duk tabi ta rikice tunani yayi mata yawa ta rasa yanda xatayi kawai sai ta Duk'ufa da addu'a Allah ya kawo mata mafita, amman fa har acikin xuciyar ta tafison auren Dr muh'd hankalin ta yafi kwanciya akan shi, sai dai har yanxu bata ji sonshi axuciyar ta ba. A haka suka cinye sati biyun suka dawo kano ta tarar umma ta xage tana ta shirye shiryen bikin ta duk wani abu da ya kamata tayi shi tayi sai jiran xuwa lokacin. Abduljabbar ya daina Kula nauwara sam ya fita daga harkar ta sha'anin gaban shi kawai yake hankali kwance, gashi kuma yak'i mayar da jiddah har yanxu sai kwane kwane yake yiwa abba, don shi fah har ga Allah daman ba son jiddah yake ba, umma ce ta had'a auren gashi kuma yanxu bata nuna mishi komai akan lallai sai ya dawo da jiddah don hka ya shiriritar da xancen kuma yaga yanxu bata kiran shi ko text mssg bata turo mishi addu'a ya dage da ita Allah yasa ma ta hak'ura dashi. Komai nisan lokaci Idan aka sa sai yaxo a yau sauran Sati d'aya bikin nauwara da Dr muh'd duk wasu shirye shirye an gama an kawo lefe ya had'a mata kaya sosai masu kyau da tsada duk wani programs da xa'a gabatar sun gama shirya wa, umma ta xage tana gyara nauwara sosai, hka a 6angaren ammi da aunty safiyya suma sun dage sosai wajen gyaran nauwara in nd out, tayi wani irin kyau fatan ta tayi wani fresh kamar mai rayuwa a k'asar k'ank'ara..... Lol Kamar yau ranar juma'a da safe wajen karfe 9 na safe abduljabbar ne ya shigo part d'in umma yana sanye cikin wata tsadaddiyar shadda fara sol tasha aiki da bak'in xare yayi kyau sosae ya sanya bak'in takalmi da hula agogo duk bak'ak'e ya sanya farin glass a fuskar shi yayi kyau kamar wani ango Fuskar shi shimfid'e da kyakkyawan Murmishi ya gaida umma ba umma ba hatta nauwara fa'iza sai da suka bishi da kallo don kyau kam Yayi kyau babu k'arya ga fara'ar da yake yi bayan sun gaisa da umma fa'iza ce kad'ai ta gaida shi ya amsa mata da Murmishi akan fuskar shi sannan yake sanar da umma xai fita wani waje mai mahimmanci sai yamma xai dawo, da fatan alkhairi umma ta bishi ya tashi xai tafi suka had'a ido da nauwara ai kuwa ya kashe mata ido d'aya da sauri ta kau da kanta ,shi kuwa yayi gaba a farfajiyar gidan suka had'u da abdulkareem yana ganin shi ya bud'e baki xai yi magana da sauri abduljabbar ya toshe bakin abdulkareem yana waige waigen bayan shi yace "sai ka tona min asiri ne haba abdulkareem, ka bari idan muka bar gidan kayi maganar " Abdulkareem yana dariyar mugunta yace "tohh Shikenan mu je kaga rana nayi " Yana gama fad'in hka suka shiga mota abdulkareem ne yake driving suka fice daga gidan. Bayan an sakko daga sallahr juma'a wajen karfe 3 na rana Abba yana xaune a falon shi umma tana xuba mishi abinci wayar shi ta fara ringing d'auka yayi tare da yin sallama shiru yayi na en mintuna yana sauraran abin da ake fad'a mishi nan take fuskar shi ta rine da 6acin rai maganar da akayi mishi ta K'arshe ya sashi mikewa tsaye yana cewa "what! don Allah da gaske kake fad'a ?" daga d'ayan 6angaren aka tabbatar mishi da Hkane Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da abba ya fad'i kenan. Da sauri umma ita ma ta mik'e tana tambayar Abba abin da ya faru ganin ya ajiye wayar ya xube kan kujera tare da dafe kai...... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 91~* Dafa kafad'ar abba umma tayi cikin tashin hankali tace "Abba me yafaru, lafia?" Dakyar abba ya iya d'ago kanshi ya Kalli umma idanun shi sunyi ja saboda 6acin rai ya bud'e baki ya fara magana da cewa "wai kamar ni abduljabbar xai mayar dani k'aramin mutum " Cikin kad'uwa umma take kallon Abba tace "me yayi abduljabbar d'in?" Sai da abba ya sauke numfashi Kafin yace "Ashe fitar nan da yayi da safen nan shi da abdulkareem kaduna suka tafi gidan baffah, yaje ya cewa baffah shi har yanxu yana son nauwara kaddara ce ta raba su gashi wai mun k'i goya mishi baya ya aure ta har an kar6i kayan auren wani, yaje ya kalmaye shi da dad'in baki har ya amince daman maimuna ta fison abduljabbar don har ta ta6a yi min maganar nak'i yarda da xancen ta don ni duk abin da nauwara take so nima ina so, shine baffah yayi ta fad'a wai gida bai koshi ba ba'a kai waje " Cikin takaici abba ya sauke numfashi sannan ya cigaba da cewa " shi ne bayan an sakko daga sallahr juma'a baffah ya sake aura mishi nauwara a karo na biyu, sai bayan an d'aura auren yake kirana Ya sanar da ni, yanxu Don Allah ina xan kai kunyar yaron nan muh'd an kar6i kayan shi da komai biki ya rage sauran k'wanaki 7, wlh ba don baffah yace kada na k'ara ta da xancen da sai ya sake ta a yau di'n nan " Gaba d'aya umma ta rasa abin da xata ce saboda tsabar takaici daman tun da ta ga yanda ya daina damuwa akan auren nauwara tasan akwai wani abin da yake shirin aikatawa ajiyar xuciya ta saki tare da kama hannun abba ta rik'e cikin muryar kwantar da hankali tace "abba kayi hak'uri gaskia abduljabbar bai kyauta ba sam, amman tun da baffah ya yanke hukunci sai muyi hak'uri da hkan " "yanxu me xance wa iyayen muh'd dashi kanshi?" Shiru suka yi kowa yana nashi tunanin can umma ta bud'e baki tace "sai ayi musu bayanin komai kuma a basu hak'uri " Shi dai Abba bai ce komai ya xurfafa a tunanin yanda xai 6ullo wa Dr muh'd batare da sun ji haushin su ba, dakyar umma ta lalla6a Abba ya iya cin abinci gashi sai faman gwada kiran wayar abduljabbar yake but switch off kwafa yayi tare da cewa "d'an banxan yaro dole ya kashe waya mana yasan abin da k'ulla ai" Ita dai umma bata ce komai. A ranar abba ya nemo Dr muh'd yaxo suka xauna sai da yayi mishi bayanin komai kafin ya sanar dashi duk abin da baffah ya sanar mishi, ba k'aramin tausayin ya bawa abba yanda ya koma lokaci d'aya sosai mayar da auren abduljabbar da nauwara abin ya bigi Dr muh'd ba k'arami ba Ganin yanda abba ya dunga rarrashin shi tare da bashi hak'uri yasa shi k'ak'alo murmishin dole yace "kada ka damu abba ba komai daman Allah ya rubuta nauwara ba *MATA TA CE* ba ce, Allah ya basu xaman lafia " Cikin tsananin tausayin shi Abba yace "hak'ik'a muh'd kai mutum ne managarci baxan so na rasa ka ba had'a xuri'a da kai ba idan ka amince xan aura maka fa'iza? " Dummmm gaban Dr muh'd ya fad'i ya rasa abin da xai ce da abba duk ya rikice shi ba son fa'iza yake ba amman baxai iya dubar tsakar idon wannan managarcin bawan Allah nan yace baya son d'iyar shi ba da kunya ai gumin da ya tsatstsafo mishi a fuskar shi ya fara goge wa "kada ka cuci kanka muh'd Idan batayi maka ba Shikenan Allah ya had'a kowa da mafi alkhairi " Cikin sanyin murya yace "a'a Abba wlh nine da godia, na amince xan auri fa'iza Allah ya bamu xaman lafia " Cikin tsananin jin dad'i abba yace "Ameeen, hak'ik'a naji dadin abin da kace muh'd Allah ya yi maka albarka " Shima cikin murmishi yace "Ameeen Abba Ngde " Sun d'an ta6a hira har abba yana ce mishi xai xo gidan nasu Yayi wa iyayen shi bayani amman Dr muh'd yace ya barshi da kanshi xai musu bayani ba wata matsala da hka yayi wa abba sallama ya tafi jikin shi a sanyaye. Ko da yaje gida yayi wa iyayen shi bayanin komai basu ji haushi ko Kad'an ba ai matar mutum kabarin shi Allah ya tsarawa kowa matar shi fatan alkhairi suka yi don hka suka cigaba da shirye shiryen biki. Da yammacin ranar aminu ya xo gidan amman bai samu ganin nauwara ba sai labarin da yayi matuk'ar girgixa shi yaji abakin umma don da kanta ta sanar dashi komai Hka ya baro gidan jikin shi a matuk'ar sanyaye, a hanya ne yana cikin tafiya a mota hankalin shi ya tafi wani wurin don baya kallon gaban shi bai ankara ba yaga ya kusan kad'e wata mace tana sanye da hijab har k'asa da sauri yayi parking tare da fito wa daga motar ya K'arasa inda ta xubar da kayan da yake hannun ta saboda ta tsorata sosai Da sauri ya tsugunna ya taya ta kwashe kayan a tare suka d'ago karaf suka yi 4eyes da junan su wanda kowanne daga cikin su sai da gaban su ya fad'i a lokaci d'aya cikin wani irin yanayi yace "Sannu don Allah kiyi hak'uri ban kula ba dafatan baki ji ciwo ba? " A kunyace da murmishi d'auke a fuskar ta tace "Laaa ba komae kada ka damu banji ciwo ba " Cikin farinciki yace "Alhmdullilah amman duk da hka ki shiga mota na kai ki gida " xaro ido tayi da sauri tace "a'a ngde ai naxo ma gida ina karya Kwana nan na xo gida" "Duk da hka ranki ya dad'e ko Kina jin tsoro kada na gudu da ke" er dariya tayi sannan tace "a haba ba wani, tsoron lafia " "ah Indai da gaske bakya jin tsoron da gaske toh ki xo mu je don Allah " Ganin ya dame ta yasa ta yarda amman da kafa suka K'arasa gidan nasu har xata shige cikin gidan da sauri ya tsayar da ita tare da cewa "gashi xamu rabo baki fad'a min sunan Ki ba" Cikin sanyin murya tace "Sunana hauwa but da jiddah ake kirana " "wow nyc name sunan mamana ne da ke, sauran contact d'inki idan ba takura " Ta gaji da tsayuwa so take ta shiga gida don hka ta fad'a mishi ya sa a wayar shi sannan suka rabu xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki tun da ya rasa nauwara ga madadin ta nan Insha Allah sai ya auri jiddah da hka ya K'arasa gidan shi. Da dare misalin karfe 9 Abba, umma, aunty sadiya sai fa'iza, nauwara da saleem acikin falon abba a xaune duk sunyi shiru suna sauraren me Abba xai ce idan ka d'auke umma da tasan komai gyaran murya abba yayi sannan yace "abin da yasa na tara ku anan ba komai bane sai don nauwara da fa'iza Kuyi hak'uri da abin da xan fad'a muku" Sai da ya yi ajiyar numfashi Kafin yace "nauwara a yau abduljabbar yaje kaduna wurin baffah yayi mishi dad'in baki ba tare da d'ayan mu ya sani ba kuma baffah bai neme mu ba ya yanke hukunci ya d'aura miki aure da abduljabbar sai bayan an d'aura ma yake sanar mana toh kiyi hak'uri 'yata amman Wannan Karon xan sa ido sosai a xaman ku idan naga yana rashin kyautata miki xan d'au mataki kin ji " Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaru wa murya na rawa alamar sauran kiris ta fashe da kuka tace "toh Abba ngde " "Yawwa 'yata Allah yayi miki albarka hak'ik'a banji dad'in abin da abduljabbar ya aikata ba" "Ameeen Abba " Nauwara ta fad'i tana goge hawayen fuskar ta girgixa kai Abba yayi cike da tausayin ta yarinyar tana ganin jarabtar rayuwa Kala Kala daga wannan sai wannan amman Insha Allah komai ya kusan xuwa K'arshe, kallon fa'iza yayi sannan yace "ke kuma na yanke hukuncin aura miki Dr muh'd don baxai yiwu nayi ta xuba miki ido ba kin k'i tsayar da wanda xaki Aura Don hka ku cigaba da shirye shirye lokacin da aka yanke na bikin hka xa'a yi babu d'aga wa" Daga hka ya sallami nauwara da fa'iza suka fita daga falon aka bar umma da aunty sadiya suna cike da mamakin hukuncin da abba ya yanke Fa'iza ba k'aramin kad'uwa tayi da wannan hukuncin Abba nan ta xube kan gado tana kuka hka nauwara ma ta xauna kan sofa tare da fashe wa da kuka tana ji ina ma ita ce fa'iza don tayi dace da salihin miji, kuka sosai suke babu mai rarrashin wani......... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _wannan page d'in sadaukar wa ne ga en group d'in *K'arshen wahala fans* i really luv u guys_❤😍 *~Pg 92~* Sai da suka gama cin kukan su sannan daga K'arshe suka rarrashi junan su, ranar ba wanda yayi cikakkiyar runtsa wa bacci tsakanin nauwara da fa'iza don hka Washe gari idanun su yayi luhu luhu duk ya kumbura saboda tsabar rashin bacci da kuka, suna xaune a d'aki kowanne ya xabga uban tagumi yana tunani ko wanka ba wanda yayi umma ta shigo d'akin kallo d'aya tayi musu wani mugun tausayin su ya kamata da hka ta K'arasa inda suke ta xauna a tsakiyar su tare da dafa kafad'ar su, lokaci d'aya suka juyo tare da rungume ta . Cikin muryar rarrashi da kwantar da hankali ta fara yi musu nasiha mai ratsa jiki da xuciya akan yarda da kaddara Har sai da jikin su yayi sanyi xuciyar ta samu nutsuwa tukunna daga K'arshe ta umarce su suyi wanka breakfast na jiran su sannan ta bar musu d'akin. Basu dad'e sosai ba suka fito parlour har sunyi wanka kamar had'in baki kowanne yasa simple gown ko make up babu a fuskar su daga powder sai lip stick, bayan sun kammala breakfast suka dawo cikin parlourn xama suka yi ana er hira umma taji dad'i sosai ganin yanda suka saki jikin su,. ******** Zaune yake akan chair di'n dinning area yana shan coffee fuskar shi idan ban da smiling babu abin da yake yi hankalin shi kwance ana hka wayar shi ta fara ringing d'auka yayi tare da mak'ala wa a kunnen shi cikin murmishi yace "hey guy hw r u ?" Daga can 6angaren abdulkareem cikin dariya yace "I'm absolutely fine" "Gud, i hope everything is going fine ?" "yes guy, sai dai ka barni da fad'an yaya fah (yana nufin abban abduljabbar) " "A haba da gaske ?" "i swear yaro sai ma kaxo tukunna " "ohhh my god har yanxu bai huce ba kenan? " Ya fad'i yana dafe kanshi, cikin tsokana abdulkareem yace "ina xai huce kuwa bayan kasa ya gama magana da iyayen Dr muh'd" "toh ya xa'a yi tun da me waje yaxo mai tabarma sai ya nade, Idan ba shishshigi ba ina shi ina habibty nah" "ae yanxu yaya ya bashi fa'iza ma nan da 1 week xa'a yi bikin, kamar yanda aka sa " "alright da ita akayi mishi auren huci haushi kenan" "ofcourse, but ya kama ta kayi kok'arin xuwa ka bawa abba da umma hak'uri don basu ji dad'in abin da kayi ba ga kuma habibty di'n ka kaxo ka rarrashi abar ka, amman don Allah ka kiyaye gaba please " Shafa gashin kanshi yayi sannan cikin sanyin murya yace "Ya xanyi abdulkareem ina son nauwara da yawa baxan iya rabu wa da ita ba, Wannan hanyar ce kad'ai xai sa na same ta, kuma Insha Allah xan kiyaye sosai thank u so much bani da kamar ka" "alright yaushe xaka xo? " "gobe Insha Allah karfe 5 na yamma ka jirani a airport" "okay Allah ya kawo ka lafia " "Ameeen" Daga hka suka yi sallama ya ajiye wayar tare da kwantar da kanshi kan kujera ya lumshe idon shi shi kanshi Yana son xuwa kano but yana jin tsoro kada abba yasa ya saki nauwara yana son ganin nauwara da twins d'in shi duk da suna waya da na'eem da ameer suna fad'a mishi halin da nauwara take ciki. ****** Cikin d'an lokaci k'alilan wata iriyar shakuwa da soyayya ta shiga tsananin aminu da jiddah sosai ita kanta tana mamakin yanda son shi har ya shiga xuciyar ta hka ta nemi son abduljabbar farat d'aya ta rasa, iyayen ta su ma sunyi farinciki sosai Sannan ta fito ta fad'a mishi ta ta6a yin aure duk abin da tayi ta sanar dashi komai bata 6oye mishi ba hkan da tayi ba k'aramin k'ara son ta da yayi ba nan da nan ya turo manyan shi aka tsaida lokacin aure. Maman jiddah da kanta ta je gidan umma ta sanar da ita sai dai umma bata ji dad'i ba taso abduljabbar ya mayar da jiddah amman hka ta hak'ura tare da neman alfarmar su dawo da bikin dai dai dana fa'iza a had'e su yi tare. Ta amince da hkan don hka tana koma wa gida tayi wa baban jiddah bayanin komai shi ma ya amince don basu da abin da xasu biya umma da iyalanta abin da suka yi musu sai addu'a tsakanin su, sun kirawo aminu sunyi mishi bayanin komai kuma ya yarda da hkan, don hka nan fah aka rikice da shirye shiryen biki sosai. Aminu ya had'a kayan lefe sosai an kawo gidan su jiddah, kuma yayi wa hindatu ita ma na fad'ar kishiya sai dai fa ba k'aramin tasar da hankalin ta tayi ba akan auren da aminu xai sake ta d'auki alwashin baxa su ta6a xaman lafia ba har abada Wannan kenan. Nauwara, fa'iza umma tasa samu mai gyaran jiki na musamman tana gyara mata emmatan ta har jiddah ita ma don tuni ta dawo gidan umma amare sunyi kyau sosai sai shirya yanda biki xai kasance akayi duk wasu abubuwan da xa'a gabatar aunty asma'u, kausar da jiddah sai aunty maryam matar abdulkareem da aunty safiyya kanwar baban su nauwara su suke shirya wa har fa'iza ma yanxu ta saki jikin ta don tuni sun dinke junan su da Dr muh'd suna xuba soyayyar su don Dr muh'd ba daga baya wajen tsari tuni yayi nasarar sace xuciyar fa'iza. Na'eem da ameer wato twins su ma yanxu sun sakko suna kula Dr muh'd da aminu kamar da daman kishi suke taya papa di'n su so yanxu komai ya wuce tunda baban su yayi nasarar samun mameen nasu, sosai yaran sunyi matuk'ar bawa Dr muh'd da aminu mamaki sosai yaran yanxu akwai wayo...... Ranar da abduljabbar yace xai xo kano bai samu damar xuwan ba saboda wani aiki da ya taso mishi a ranar don hka sai ranar da xa'a yi dinner ana yi gobe d'aurin auren ya samu damar diro wa Kano da yammaci likis, abdulkareem ne yaje ya d'auko shi a airport yana ta tsokanar shi tare da bashi kyakkyawan albishir kan jiddah ita ma yanxu ta gaji da Jan ajin da yake mata aure xata yi gobe ma xa'a d'aura tare da na fa'iza, wayyo dad'i abduljabbar ya rasa inda xai sa kanshi don dad'i ya gode wa Allah sosai yanda ya raba shi da jiddah cikin kwanciyar hankali babu tashin hankali ........... _kuyi hak'uri da wannan idan na samu time anjima xan sake muku luv u all my fans with all my heart_ ❣😍😘 Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _wannan page d'in sadaukar wa ne gare ku *Asy khaleel* da *Ummu hambali* ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke_😍 *~Pg 93~* Kai tsaye gidan su abdulkareem yayi dashi cike yake da en uwa ganin hka kawai sai suka wuce part d'in abduljabbar don baya son hayaniya ko umma da abba basu san yaxo ba sai aunty sadiya ita tasan yaxo don ya kirawo ta awaya yana son a had'o mishi abinci don yunwa yake ji, cikin en mintuna er aikin aunty sadiya ta kawo musu xama suka yi tare da fara cin abincin. Lokacin tafiya dinner yayi kowa ya shirya daga amare, k'awayen amare da en uwa da abokan arxiki a hankali aka fara tafiya wajen da xa'a gabatar da dinner d'in kowa yaci gayun shi cikin ankon bikin . Dr muh'd da amaryar shi fa'iza suna motar su daban, haka jiddah da angon ta aminu su ma motar su daban don uwargida hindatu tak'i xuwa dinner shi hakan ma ya fiye mishi kwanciyar hankali kada tayi musu hauka acan. Sai da kowa ya gama tafiya sannan nauwara ta fito xata tafi tana sanye da wani swiss lace green colour nd touch d'in flowers red d'inkin riga da siket sun xauna a jikin ta sosai sai head d'in kanta red colour ne gashin nan ta xubo mishi ya kwanta a bayanta sai shek'i yake tayi kyau sosae takalmi ta hill ne sai poss di'n ta dukka red colour ne, d'ayan hannun kuma phone ne da key di'n mota a gurguje ta fito saboda sai kiranta su fa'iza suke tayi sauri da sauri ta shiga motar tare da yi mata key ta bar gidan. Tafiyar mintuna 20 ya kaita hall di'n da aka dinner wurin ya had'u sosai yasha decoration white nd blue ga haske sosai, a nutse tayi parking tare da fito wa daga motar ta nufi cikin hall di'n cikin tafiyar kamar ta mai jin tausayin k'asa. Wow masha Allah gaba d'aya ilahirin wajen hankalin su yayi kan nauwara da take shigo wa kai tsaye inda high table d'in angwaye da amare tayi don nan wurin xaman nata, dogon table ne da six chairs, FA'iza da Dr muh'd, jiddah da aminu, sauran chairs biyu nauwara ta xauna a d'ayar sauran d'aya cikin murmishi ta kalle su tace "Wow ka ga amare da angwaye u look so cutes, Allah ya sanya alkhairi ya baku xaman Lafia da xuri'a mae albarka " Da saurin su kusan kamar had'in baki suka amsa da "Ameeen thumma Ameeen mungode " fuskar d'auke da murmishin jin dad'i . Daga hka suka cigaba da gudanar da dinner d'in, nauwara ce ta sunkuya tana gyara belt d'in takalmin ta da ta cire sai jin wani irin mugun k'amshin turare wanda mutum d'aya tak tasan shi da wannan k'amshin da sauri ta d'ago da kanta idanun ta ba Inda suka sauka sai kan abduljabbar da yake xaune kusa da kujerar ta yana sanye da wata lallausan shadda milk colour ya turo da hular kanshi gaban goshi da ka ga yanda yasa hular kasan bai saba sa ta ba yayi matuk'ar yin kyau ba Kad'an ba fuskar shi a sake sai faman murmishi yake yana magana dasu Dr muh'd nan take ta d'aure fuska tare da kawar da kanta daga kallon shi duk da kuwa kyan da yayi mata Bata ankara ba taji yasa kafar shi akan kafarta yana tafiyar da kafar tashi a kafarta har xuwa gwiwar ta amman bayan ya cire shoes d'in kafar shi yana wani shi'umin murmishi da sauri ta kalle shi karaf suka had'a ido ae kuwa ya kashe mata ido d'aya ta6e baki tayi tare da jan d'an siririn tsaki Lokaci d'aya ya had'e rai sakamakon ganin wani yanki na gashin kanta ya fito waje cikin fusata yasa hannu ya gyara gwaggwaron Kan nauwara ya kife shi a kanta, kallon shi tayi rai a 6ace kamar xata fashe da kuka ganin yanda ya 6ata mata k'walliyar ta wani murmishin mugunta ya saki tare da daga mata gira haushi ya dad'a kume ta tace "me nayi maka malam xaka 6ata min Kwalliya ta, ko na kula ka ne? " "Ah babu abin da kika min habibty just na gyara abin kan Ki ne" Harara ta dalla mashi tare da Murgud'a baki kallon ta yake cike da so da k'aunar ta ga wata muguwar sha'awar ta da yaji ya kama shi kallon lips d'in ta yake kawai wanda suka sha jambaki red sai shek'i suke . Anutse ta d'ago da idon ta suka had'a ido lokaci d'aya suka xuba wa juna ido cike da wani irin yanayi a tattare da kowanne a cikin shi duk yanda nauwara taso janye idonta ta kasa yayin da abduljabbar daman shi haka yake so, ji tayi ana jijjiga ta da sauri ta kau da kanta daga kallon shi tare da sakin wata irin ajiyar xuciya muryar na'eem taji yana cewa "Laaa mamee da papa suna kallon k'uda irin wanda muke yi a school ko ameer ???" "ehhh hakane wlh " Cewar ameer wata irin kunya ta rufe nauwara sai faman hararar twins take, gaba d'aya wajen aka kyalkyale da dariya har da abduljabbar nauwara tayi kicin kicin da fuska, daman duk abin da suke su fa'iza suna ankare dasu sai faman dariya suke musu. "papa ku cigaba da yi mu ga wanda xai yi wining tsakanin ka da mamee " Cewar ameer janyo shi yayi jikin shi tare da bashi peck a kumatun shi yace "that's my boy, ae mameen ka matsoraciya ce baxa ta iya ba"ya fad'i yana jifan nauwara da wani salon kallon shi k'asa k'asa. Cikin shagwa6a na'eem yace " mamee ki yarda please " Cikin jin haushin su gaba d'aya takai hannu xata make na'eem da ya dame ta ai kuwa da sauri ya rik'e mata hannu tare da yi mata alamar ina ruwan ta kada ta dakar mishi yaro, a fusace ta tashi tare da barin hall di'n gaba d'aya. Da sauri ya tashi yana rik'e dasu na'eem ya juya xai bita yaji aminu yace "yalla6ai ba dai tafiya ba,gashi ka kori er gidan taka" Yana shafa kanshi yace "ya xa'a yi aminu rarrashin ta xanje nayi sai mun had'u gobe don ni daga nan sai gida" Caraf Dr muh'd yace "Ohh kace don ita kaxo kenan " "yes ofcourse ita na biyo doctor tun da ta tafi xamana bashi da amfani don hka nayi nan byeee " Suna mishi dariya yaja hannun na'eem da ameer suka fice daga hall di'n a farfajiyar wajen suka tsaya suna duba ta basu ganta ba mybe ta tafi gida xuciyar shi ta ayyana mishi don hka motar shi ya shiga suka bar wurin, ko da suka xo gida bai gan ta ba sai umma ya gani ya tambaye ta nauwara ta dawo nan ta tabbatar mishi ta dawo Sannan hankalin shi ya kwanta ba k'aramin jin dad'i yayi ba ganin umma bata nuna mishi komai ba kamar yanda take mishi da hka ma yau tayi mishi har da tambayar shi yana buk'atar wani abun ganin ya samu fuska yace yana son shan fruit kawai Idan xai samu daga hka ya fice xuwa part din shi, da kanta umma ta yanka mishi fruit d'in ta aika mishi xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki yasha fruit salad d'in nan da hka har bacci ya d'auke shi xuciyar shi cike da tunanin habibty di'n shi........ Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _dedicated to haleema Ameen nd biebie deee, ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke_❤😍 *~Pg 94~* Washe gari misalin karfe 11 aka d'aura auren Dr muh'd da fa'iza, sannan nasu Aminu da jiddah akan sadaki mafi cancanta don neman albarkar aure, abba, abduljabbar, abdulkareem, Dr muh'd ,Aminu,saleem da na'eem da ameer gaba d'aya ankon tsadaddiyar farar shadda suka yi har da babbar riga sun yi matuk'ar yin kyau ga wani kwarjini da suka yi fuskar su d'auke da tsantsar farin ciki sai faman gaisa wa suke da wad'anda suka hallaci wannan d'aurin auren, bayan an gama d'aurin auren suka wuce yin reception na maxa an ci ansha a wurin sun sha addu'a daga bakunan mutane na xaman lafia da xuri'a mae albarka haka aka watse kowa cike da farin ciki. Cikin gidan nan ya cika da mutane sosae en uwa da abokan arxiki sai taya su umma ake murna tare da yiwa amare fatan alkhairi Allah ya bada xaman lafia. Nauwara, fa'iza, jiddah, aunty asma'u, aunty kausar, aunty maryam da suna xaune a bedroom d'in su nauwara kowanne yasha kwalliya ta Kece raini dukkan su fuskar su d'auke da Murmishi sai hira ake suna cikin haka abduljabbar da abdulkareem suka shigo d'akin a nutse aunty asma'u ce ta Kalli abduljabbar wanda yake sa6e babbar riga tana xamo wa yana sake gyara wa alamar bai saba da sawa ba ae kuwa ta kyalkyale da dariya tare da cewa "Allah abdul kaji kunya yanxu ace babbar rigar ma har yanxu baka iya sawa ba an fah girma " Harara ya watsa mata tare da jan wani d'an siririn tsaki yace "kin fiye sa ido da yawa asma'u ba wanda ya kula da hkan sai ke Allah ki fita a idona " Ya K'arasa fad'i yana huro hanci abdulkareem wanda yake danne dariyar shi yace "waii ke ina ruwan ki ne asma'u Indai ki ga wannan d'an nawa sai kin tsokane xan fa d'au mataki akan ki" "heeeeyyy lallai ma abdulkareem din nan Indai wannan abduljabbar d'in kake tare wa wataran sai ya mun ganku a rana" Gaba d'aya d'akin aka kwashe da dariya har da nauwara sai da ta murmusa shi kuwa uban gayyar had'e fuska yayi tare da cewa "ya xa'a yi ki dunga yi min magana kowacce iri ce a gaban kannen salon su rainani " "Ahayyeee su raini manya dad'in abin kai di'n k'anina ne " Ko kula ta bai yi ya nufi inda nauwara take a xaune a gefen bed jiddah wadda take kusa da ita a xaune ya wani d'auke kai cikin isa yace "hey d'an ban wurin naji dumin mata ta" Dariya jiddah tayi tare da tashi da sauri tana cewa "ni bari ma na bar maka d'akin kaji d'umin da kyau " "Yawwa da kin kyauta er k'anwa ta su wad'annan en sa idon sai sun ga kwakwaf " Tana dariya ta bar d'akin tare da fa'iza, kausar ta mik'e tsaye tana cewa "ni fah yunwa nake ji ko breakfast ban yi ba ni ma nayi nan " Tana gama fad'in hka ta fita daga d'akin tana kunshe dariya, xube wa yayi kan bed d'in tare da fad'in "Washhh na gaji wlh da ni d'an gata ne da sai ayi min tausa" Ya fad'i yana kallon fuskar nauwara wadda ta had'e fuska, aunty asma'u ma tashi tayi tana cewa "toh mara kunya so kake dai na bar d'akin, ba don nauwara ba da Allah ba Inda xan je sai dai duk abin da xaka yi kayi a gaba na" "Ahhh ae da Kinyi xaman ki waya kore ki sarkin sa ido " Abduljabbar ya fad'i yana dariyar mugunta wani k'aramin pillown ta cillo mishi ya cafe yana dariya sannan ta fice daga d'akin abdulkareem ya Kalli maryam yace "my wife taso mu tafi ya yiwa kowa kora da hali tun Kafin ya kore mu ma " Yana shafa kanshi yace "ni kada ka had'a ni da maryam ni bance kowa ya tafi ba " "ae gwara mu baka wuri " Maryam ta fad'i tana kamo hannun abdulkareem suka fice daga d'akin aka bar nauwara da abduljabbar. Tashi daga kan bed d'in nauwara tayi tana shirin ban mishi d'akin da sauri ya rik'o hannun ta, ta juya da kanshi tana kallon shi shima ita yake kallo cikin marairaice fuska yace "Haba habibty wai har yanxu baki hak'ura ne? " Turo baki tayi kafin tace "ni ka cika min hannu ina da abin yi please " Bai ce komai ba ya janyo ta tare da xaunar da ita kan bed d'in shi kuma ya tsugunna a k'asa tare da dire gwiyoyin shi k'asa yana rik'e da hannun ta idanun shi akan fuskar ta cikin nutsuwa yace "gani a durkushe a gaban ki a karo na biyu baxan tashi anan ba har sai kin hak'ura na gaji da wannan yanayin da kike nuna min baxan iya jure wa na gaji da axabtar dani da kenan ina sake baki hak'uri " Wani irin mugun tausayin shi taji ya kamata tare da wani mugun son shi da ya k'ara shiga cikin xuciyar ta duk jikin ta yayi sanyi sosai bata ankara ba ta ga wasu hawaye suna fita a idanun shi suna sauka akan hannayen ta da yake rik'e dasu, toh me yasa baxa ta hak'ura ba wacce irin xuciya ce da ita mutumin da shi ya taimake ta a rayuwa ya cece ta daga fyad'en da akayi yunkurin yi mata ya kai ta asibiti ya nema mata magani ta warke ta dawo tana tafiya tana kallon mutane da idanun ta kamar kowa ya sata a makaranta har takai matsayin da ya nuna mata so da k'auna ya aure ta har Allah ya basu albarkar yara 2 kaddara da sharri yasa ya rabu da ita gashi gaskiya ta bayyana yayi nadama tare da Bata hak'uri ae ya kamata ta hak'ura kuwa ko Allah Muna yi mishi laifi mu rok'e shi ya yafe mana balle kuma mu en Adam don hka cikin jin tausayin shi murya a sanyaye tasa hannu ta goge hawayen fuskar shi tare da cewa "Don Allah ka daina xubar da hawayen ka please " "baxan dai na Idan har baki hak'ura ba" Ya fad'i hkan yana sake rik'o hannun ta gam a cikin hannun shi a hankali ta fara cewa "na hak'ura Yah abduljabbar daman ae d'an ajixine, ni tun tuni na yafe maka amman ina son gaba kada dunga bincike Kafin ka yanke hukunci " Cikin tsananin farinciki yace "nauwara da gaske kin hak'ura? " Cikin jin tausayin yanda duk yabi ya rud'e cikin tabbatar wa tace "da gaske nake Allah ya yafe mana gaba d'aya " Da sauri ya rungume ta tsam a jikin shi tare da cewa "Ameeen thank u habibty nah, kuma Insha Allah xan kiyaye gaba " Ya cigaba da cewa "i luv u baby nah i really miss u " Duk gaba d'aya ya rikice mata da godiya a hankali ta lumshe idon ta hawaye suna xuba a idon ta wanda bata san name ne ba na farinciki ne ko akasin hka, had'a fuskar shi da ta ta xai yi yaga hawaye a fuskar ta a rikice yace "baby nah bakya so na rabu da ke? " shiru tayi bata ce komae ba ganin hka yasa shi cikata tare mik'e tsaye cikin sanyin jiki ya juya xai fita daga d'akin ganin hka yasa ta tashi da gudu ta karasa inda yake ta rungume shi ta baya tare da fashe wa da kuka runtse idon shi baya son kukan ta ko Kad'an a hankali ya juya tare da rik'e mata kafad'un ta yace "calm down nauwara what wrong with u? " Kasa magana tayi don kuka yaci k'arfin ta hankalin shi gaba d'aya ya tashi xauna wa yayi kan sofa tare da xaunar da ita kan kafafun shi nan ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru sai ajiyar xuciya da take saki akai akai duk fuskar ta tayi ja idanun ta sun kumbura ita kanta batasan dalilin kukan nata ba ganin tayi shiru yasa shi cewa "what happened to u nauwara, me yasa ki kuka haka? " "ni kawai haka naji kukan yaxo min " "ohhh my god nasan Akwai wani abun fad'a min kinji my dear " Cikin sanyin murya tace "da gaske nake yi fah" D'an xaro ido yayi Kad'an ya kama kumatun ta duk biyun yace "shine kika d'aga min hankali, are you sure babu wani abin ?" Jijjiga kai tayi ba tai magana ba d'an siririn murmishi ya saki tare da cewa "thank u once again i luv u baby nah Allah yayi miki albarka " A hankali ta bud'e d'an k'aramin bakin ta tace "Ameeen " Bata peck yayi a kumatu da goshi sannan kan lips d'in ta sannan ya bar d'akin, xuciyar shi wasai cike da farin ciki sai faman murmishi yake bai damu da tattare war da shaddar jikin shi yayi ba sai dariya ake mishi wasu na tsokanar shi sai dai ya shafa gashin kanshi tare da Murmishi ko uhm bai ce ba har ya fice daga part d'in umma ya nufi nashi. Ita kuwa nauwara kwanciya tayi akan sofa tare da rungume pillow a kirjin ta wani sabon son abduljabbar ne yake dad'a shiga xuciyar ta yanxu wasai take jin xuciyar ta. Da yammaci aka gabatar da Mother's Day bayan sallahr mangariba kuma aka mik'a kowacce gidan mijin ta banda nauwara daga FA'iza sai jiddah sun sha kuka sosai tsakanin FA'iza da nauwara xasu yi kewar junan su don ba k'aramin shakuwa suka yi ba hka twins sun sha kuka su ma, Dakyar fa'iza ta cika nauwara suka tafi gida jikin nauwara a sanyaye, suna k'arasa wa gida wanka ta iya yi tabi lafiyar gado don ba k'aramin gajiya tayi ba nan da nan bacci yayi awon gaba da....... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _dedicated to khalfana (sister d'in neena cool), muna godiya sosae Allah ya bar xumunci, ina miki fatan alkhairi_❣😍 *~Pg 95~* Tana xaune a dinning area tana breakfast duk yau tashi tayi jikin ta a sanyaye saboda yau ammin ta da inna, aunty safiyya xasu koma kaduna jin tayi an rufe mata idanun ta k'amshin turaren shi kad'ai taji ta gane ko wane cikin mak'e murya yace "canki wane?" tana murmishi tace "Haba kasan na gane ka kawai ka bud'e min ido " Ta K'arasa fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yayi cike da k'aunar ta ya bud'e mata idon tare da janyo kujera ya xauna a kusa da ita yana kallon ta ita ma shi take kallo sun sauke en mintuna suna kallon junan Kafin nauwara ta fara janye idonta tana cewa "dafatan ka tashi lafia? " D'an ta6e baki yayi tare da cewa "ehhh to lafia ba lafia ba? " D'an xaro ido tayi cike da mamaki tace "Idan ba lafia ka tashi ba to yana ganka qlau da kai??" "Idan kin ga gangar jikina lafia to nan " Ya dafe xuciyar shi ya cigaba da cewa "ba lafia yake ba yana cike da son ki da kaunar ki ta Kasa samun nutsuwa Har sai ta ji d'umin mahad'ar ta " Ya gama fad'a yana kashe mata ido hararar shi tayi shi kuwa ya wani marairaice fuska sosai ya bata dariya ganin yanda ya wani langa6e kai kamar k'aramin yaro ganin har yanxu ta kasa sakin jiki dashi ba kamar da ba kuma yasan sai a hankali gashi kuma cike da wata iriyar sha'awar ta yake d'aure wa kawai yake yi, don baya son ya matsa mata yafi son ya gama goge laifin shi gaba d'aya a gurin ta . "na had'a maka tea ne? ", girgixa kai yayi cikin kalar tausayi yace " Idan da ni kike to a koshe nake, umma ta aiko min da shi yanxu ma da kika ganni abuja xan tafi ana nema na" Cikin d'an mamaki tace "daga xuwan xaka koma?" "toh ya xanyi tunda yanayin aikin namu kenan, da dai ni d'an gata ne da sai ki shirya mu tafi tare" Da sauri ta girgixa kai tana cewa "a'a ni ina kusa da umma " D'an murmishi yayi yana shafa sajen shi yace "ba wani nan kema nasan kina son ki ganki kusa da mijin ki kawai irin kawaicin nan ne irin na mata ko ba hka ba? " Ya tambaye ta yana d'aga gira haushi ya rufe nauwara don ta gane abin da yake nufi hararar shi tayi tare da mik'e wa da sauri ta bar wurin bin ta yayi da kallo Kafin ya dunkule hannun shi ya daki table d'in yana cewa "ohhh my god na kwafsa ashe Hka na saki baki ina magana gashi nan garin gyaran gira........ " Da sauri ya mik'e tsaye ganin sauran 30 mint jirgin da xai bi xuwa abuja ya tashi don hka Agurguje yayi sallama da en gidan ya tafi ko gimbiyar tashi bai samu ganin ta ba. Sai wurin 12 su ammi suka tafi umma sai godiya take musu ita kawai hka taji tana bala'in son ammi nan aka rabu cike da kewar juna. Tun da ya tafi abuja kullum abduljabbar cikin waya yake yiwa nauwara ban da text mssg di'n shi na ta taimaka ta yi picking d'in wayar shi dakyar da yarda take d'aukan wayar tashi tun tana k'in yin magana har yakai da ta saki jiki suna d'an ta6a hira hkan ba k'aramin jin dad'i yayi ba, na'eem da ameer ma sai dad'a girma ake suna ta xuwa skul d'in islamia da boko ga nauwara da saleem suna yi musu lesson a gida baki ya dad'a bud'e yanxu ai ta xuba surutu ga wayo. Saleem ma yanxu kok'arin had'a degree di'n shi yake an fara xama babban mutum ba ruwan shi akwai nutsuwa da hankali, bai fiye fita irin yawo nan ba daga makarantar boko sai islamia don ya dage da neman ilimi addini sosai, idan ya dawo xaka same shi yana yiwa twins lesson ko ki ganshi a kitchen ya xage yana taya umma ko nauwara girki suyi tayi mishi dariya amman shi ko ajikin shi kawai girki yana burge shi, kullum nauwara gode wa Allah take da yayi musu wannan gatan na dace da en rik'o na gari, gashi saleem kamar su d'aya da abban su har dariyar shi da murmishi shi yasa take yawan kallon shi kallon shi da take yana tuna mata da abban su wani lokacin har tambayar ta yake lafia irin wannan kallon sai dai kawai ta girgixa kai tare da yin murmishin yak'e tace ba komai. Sai da abduljabbar yayi wajen 4 weeks bai xo kano ba sai da waya saboda tarin ayyukan da ke gaban shi gashi gaba d'aya a tak'ure yake d'aure wa kawai yake ana hka ya d'an samu sararin aikin yana shirye shiryen tahowa, wani aiki ya ttaso mishi dole ya hak'ura da xuwan ya tafi duk haushin aikin ya ishe shi kamar xai yi kuka a lokacin hka yaji aikin da ya d'auke shi wajen 1 month again. Da sauri ta fito daga toilet jin k'arar wayar ta tana d'aure da towel ajikin ta ganin abduljabbar ne me kira yasa ta d'auka tare da yin sallama amsa wa yayi duk suka yi shiru lokaci d'aya Kafin daga can abduljabbar yace "habibty nah nayi missing di'n ki sosai don hka ki shirya tar6ar mijin ki ranar Friday nan da k'wana 2 kenan " Ji tayi gaban ya fad'i jin irin muryar da yayi amfani da ita wajen maganar tayi shiru don ta rasa mai xata ce "ya kika yi shiru ko baki farinciki da xuwan nawa ba " "hmm ni na isa nace haka, Allah ya dawo da kai lafia " "Ameeen habibty, ina twins d'ina? " "suna parlour wajen umma " "Yayi kyau, ina son don Allah ki je part d'ina da kanki nake son ki gyara min please " Shiru ta d'an yi Kafin tace "okay ba matsala xan yi yanda kace " "that's my girl, ngde sosae Allah yayi miki albarka " "Ameeen " Daga hka suka yi sallama ta ajiye wayar tana tunanin abin da ya kamata tayi mishi wanda xai ji dad'i nan ta xurfafa a tunani........... Aishat A muh'd. 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 96~* Ranar Friday tun da ta tashi daga bacci bayan ta gama breakfast, ta nufi part d'in Yah abduljabbar ta fara gyara mishi tun daga toilet, bedroom nd parlour ta tsabta ce su kayan wankin shi ta tattara ta bawa mai yin wanki har wardrobe d'in ta gyara, Ohh ji don Allah yanda ya tattaro kaya kamar wanda xai xauna a gidan kamar bashi da gida nauwara ta fad'i tana ta6e bakin ta, ta canja mishi bed sheet, bayan ta gama gyaran ta turare ko'ina da turaren wuta ta k'ara da air freshener masu k'amshi ta fesa a d'akin ta saki labulen ta kunna AC sansanyan k'amshi da sanyi mai ratsa jiki ne yake tashi kawai tana gama wa ta fito ta nufi 6angaren umma a gajiye take sosai ta xube akan carpet kusa da kafar umma tana cewa "washhh Allah na gaji da yawa umma" Kallon ta umma tayi tana cewa "sannu, ban da rigimar abdul ba sai asa er aiki ta gyara ba gashi nan ya gajiyar da ke " Tana lumshe idon ta tace "Laaa umma ba komai Bari naje na shirya mishi abinci " Kama baki umma tayi tana cewa "rabu dashi ya ci abin da muka girka, ki je ki kwanta ki huta " D'an marairaice wa tayi cikin er shagwa6a tace "umma xan iya fah" "toh Shikenan, ke dae Allah yayi miki albarka " Cikin jin dad'i ta amsa da "ameen umma nah" Daga hka ta mik'e ta nufi kitchen umma ta bita da kallon tana murmishi hak'ik'a d'an ta yayi dace da mata ta gari, Allah ya kare mata su daga duk wani abin k'i. Girki sosai ta tsaya tayi mishi farar shinkafa ce da miyar hanta sai pepper chicken ta had'a mishi costlow sai tayi mishi samosa da scott eggs sai coconut drink ,da taimakon er aikin umma ta kammala had'a wa bayan sun gama ta fice daga kitchen d'in a jigace duk tayi wani wujiga wujiga suna had'a ido da saleem ya kwashe da dariya don dawowar shi kenan daga skul umma cikin mamaki ta d'ago kanta tana kallon shi ganin yanda ya xage yana dariya lokacin da ta Kalli nauwara ita ma dariya abin ya bata, hararar saleem tayi tana cewa "malam lafia kake min dariya " Ta wani d'aure fuska sake tuntsire wa yayi da dariya kafin ya ce "aunty nauwara kin ga kuwa yanda kike koma? " Ya cigaba da cewa "tabbb kamar wadda tayi sati a tsaye tana aiki, gaskia Yah abduljabbar yana da raguwar mace " Mtsww taja tsaki tare da kara had'e fuska tace "Allah saleem ka kiyaye ni idan na rik'e ka xaka yi bayani " "heeee lallai aunty nauwara Idan ba kin rik'e ni baxa ki iya yi min komai ba " Ya fad'i yana mata gwalo kwafa tayi sannan cikin shagwa6a tace "umma kin ganshi koh? " Umma ta danne dariyar ta ta Kalli saleem tace "ba ruwan ka saleem ka kyale ta " "toh umma na daina " Ya fad'i yana kallon nauwara ya cigaba da cewa "don Allah aunty ki bani aron key di'n motar ki don da ita xamu masallaci ni da twins " "tabbb yanxu ka gama tsokanar tawa ka xo kace na baka aron mota ta ban bayar wa" Marairaice fuska yayi tare da kwantar da kai yana cewa "please my dear sis" Abduljabbar wanda yake tsaye yana kallon duk abin da suke ya fara cewa "saleem kada ka damu anjima xamu je ka xa6i motar da kake so " Gaba d'ayan su suka juyo suna kallon shi d'an tsallen murna saleem yayi tare da hugging di'n abduljabbar yana cewa "Oyoyo Yah abduljabbar, thank u so much ka ga na huta nace aban aron mota a dunga yi ja min aji Kafin aba ni" Ya fad'i yana yamutse fuska, cikin murmishi abduljabbar ya d'ora hannun shi akan bakin shi yana cewa "shiiiii bana son godia" "ka xo lafia Yah abduljabbar " Yana shafa kanshi yace "lafia qlau, ya kake? " "I'm absolutely fine " "Good my boy " Sannan ya juya wajen da nauwara take a tsaye amma wayam alamar ta gudu d'aki d'an girgixa kai yayi Kafin ya xauna su gaisa da umma tana Tambayar shi an xo lafia, ana hka Abba ma ya fito cikin shirin tafiya masallaci don lokaci ya gabato bayan sun gama gaisa wa yana kok'arin tambayar su twins sai Gasu nan sun fito da gudu sun sha manyan kaya yadin kufta ne kalar dark blue d'inkin cif a jikin su sunyi kyau sai k'amshin turare suke . Da gudu suka haye jikin abduljabbar suna murnar ganin shi, shima rungume su yayi cike da jin dad'in ganin su yayi kewar su, daga hka suka fice xuwa masallaci umma tana yi musu addu'ar Allah ya dawo dasu lafia. Nauwara kuwa tun lokacin da ta ga abduljabbar ta gudu d'aki toilet ta shige wanka tayi sannan ta fito dressing mirror ta nufa ta fara busar da gashin kanta da hand dryer bayan ya bushe sannan ta shafa mishi mai ta d'aure da ribbom, wani mai cream ta d'auko ta shafa sannan ta d'anyi light make up ta shirya kanta cikin wata atampha d'inkin riga da siket ne sun xauna a jikin ta ta d'aura d'ankwalin kayan kusan rabin gashin nata a waje madubi ta kalla tayi murmishi ita kanta tasan tayi kyau, different perfumes ta fesa har da arabian perfumes banda body spray da tayi using dashi a cikin jikin ta wani irin sanyayen k'amshi take fitar wa duk motsin da tayi. Da yake tana period yasa ta xauna kan sofa tare da daukar wayar ta ta bud'e data tuni messages suka fara shigo wa ganin fa'iza da jiddah a online yasa ta farinciki nan suka 6arke da hira suna tambayar ta yaushe xata xo gidajen su nan tace musu tanan tafe Insha Allah . Anan jiddah take neman shawarar su yanda xasu xauna da kishiyar ta hindatu lafia fitina ce da ita bata son a xauna lafia daga wannan sai wannan ita har ta fara nadamar auren aminu, Allah sarki rayuwa wai jiddah ce take neman yanda xasu xauna lafia da kishiyar ta, daman Hka rayuwar ta gada duk abin ka sai ka samu wanda ya fika, sun tausaya mata sosae nan suka d'an bata shawarwari masu kyau taji dad'i sosai, anan tayi musu albishir aminu ya bar ta xata cigaba da xuwa aikin ta sunyi mata murna tare da yi mata addu'ar Allah ya taimaka. K'wata k'wata hankalin ta yana kan wayar bata san da Shigowar shi dakin ba don ko k'arar bud'e kofa Allah bai sa ta ji ba xama yayi kusa da ita tare da sa hannu ya kwace wayar da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido sun d'auki tsawon 20 seconds suna kallon junan su Kafin nauwara cikin d'an jin kunya ta d'auke idanun ta a kanshi kamo ta yayi xuwa cikin jikin shi ya rada mata a kunne "Kinyi kyau baby nah i luv u " ita dai murmishi kawai take kafin dakyar ta bud'e baki tace "i luv u too yayanah " Sake Kank'ame ta yayi ajikin shi lokaci d'aya suka saki ajiyar xuciya, kallon lips d'in ta yake cike da sha'awa ita kuwa turo bakin nata tayi tare da yin fari da ido tace "wannan kallon fah Yayi, Allah xan tashi na bar maka d'akin " Ta K'arasa fad'i cikin shagwa6a Murmishi kawai yake don duk ta ruda shi ya kasa cewa komai kafin ta ankara har bakin shi yake cikin nata, nan fah ta fara kici kicin kwace bakin ta cikin wata irin voice wadda batasan abduljabbar yana da ita ba yace " Haba babynah ki kyale please " Gaba d'aya jikin shi rawa yake don ya axabtu iya cewa rabon shi da mace har ya mance dole ya rud'e kuwa, ganin hka yasa ta saki jikin ta ta kyale shi yana yanda yake so don tasan duk rawar jikin shi a iya nan xai tsaya da ta tuna haka har da sakin wani murmishin mugunta, ( kai nauwara Kina wahalar da abduljabbar d'in ki...lol ). Sun d'auki tsawon lokaci a haka Kafin ya rabu da ita dakyar yana sauke numfashi tare da sakin ajiyar xuciya akai akai, dago kanta tayi suka had'a ido gabanta sai da ya fad'i ganin yanda idanun shi sukayi ja dasu, kallon ta yayi cike da wani irin yanayi yace "me yasa baki fad'a min Kina cikin Wannan yanayin ba da sai na bari sai wani week d'in na xo, Kinsan halin da nake ciki kuwa habibty? " kallon shi tayi tare da girgixa kai duk tausayin shi ne ya kamata ganin yanda ya koma duk sunyi shiru wajen one mint sannan yace "mu je ki bani abinci yunwa nake ji " Da sauri ta mik'e tsaye tare da gyara rigar jikin ta daukan ribbon di'n ta tayi ta k'ara d'aure gashin ta sannan ta d'aura d'ankwalin nata tace "taho mu tafi kaci abincin " Haka ya tashi jikin shi ba k'arfi sosai suka fita daga d'akin akan dinning table ta jera mishi komai sannan tayi serving d'in shi xama yayi yaci abincin nan sosai yana xuba mata santi. Sai ga na'eem da ameer nan sun fito daga d'akin saleem suka yo wajen iyayen su, abduljabbar ya d'auki na'eem akan cinyar shi yana bashi abinci yayin da nauwara kuma ta d'auki ameer tana bashi suna hirar su gwanin sha'awa lokaci lokaci abduljabbar yana jefan ta da wani irin kallo da idanun shi wad'anda har yanxu basu dawo dai dai ba, duk lokacin da yayi mata wannan kallon sai gaban ta ya fad'i. Bayan sun kammala ci ne ya kwashi su na'eem suka tafi rakashi gidan abdulkareem. Bedroom d'in umma ta shiga taji tana waya lokaci d'aya taji gaban ta ya fad'i da taji tana magana akan wai an tsayar da next Friday xa'a d'aura auren cikin mamaki nauwara take kallon ta ita kuwa umma tana waya tana kallon nauwara da Murmishi akan fuskar ta bayan ta gama ta ajiye wayar ta ce "nauwara lafia kika xuba uban tagumi, koh abduljabbar ne yayi miki wani abun? " girgixa kai tayi tace "umma wane xai yi aure next Friday? " Murmishi umman ta sake yi Kafin tace "abban ku ne xai dad'o mana abokiyar xama" Xaro ido nauwara tayi cike da mamaki tace "umma aure kika ce fa, kuma wai abba" "k'warai da gaske kuwa abin da kunen ki yaji na fad'a miki Hkne " "toh umma waxai aurah ne? " sai da umma ta tuntsire da dariya ganin yanda nauwara ta firgice "umma is not funny ,ki fad'a min please " "toh ammin ki xai aura mun xauna da abban ku, abduljabbar dani mun yanke hukunci xai auri maimuna " Wani irin kallo naga nauwara tana bin umma dashi Kafin ta ce "it's impossible umma hakan baxai faru ba, kun mana hallaci baxa mu saka miki da wannan abin ba" Tana gama fad'in hka ta fice daga d'akin da gudu tana kuka sosae, ta bar umma cike da mamakin abin da nauwara tayi......... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 97~* Kuka sosae take tana cewa "baxai yiwu ba umma baxa mu saka miki da haka ba, wayyo Allah nah, sam wannan abin ba me yiwa ne ba" Kuka take sosai tana faman xuba sumbatun magana don ita har ga Allah baxa ta so hakan ya faru ba, ji tayi an dafa mata bayan ta da sauri ta d'ago kanta umma ta gani a tsaye fuskar ta d'auke da damuwa, xama tayi kusa da ita tana cewa "tashi mu yi magana nauwara " Tashi xaune tayi tana goge hawayen fuskar ta tak'i kallon Inda umma take, murmishin manya umma ta saki tare da kamo hannun nauwara ta fara magana a nutse "da farko ina son na fara da tambayar ki, wannan auren da abban ku da ammin ki haramun ne??? " D'an shiru nauwara tayi kafin tace "ba haramun ba ne " "toh Indai ba haramun ba ne,me ne na d'aga hankalin ki haka, ko don Abba talaka ne baxai iya auren maimuna ba? " Da sauri nauwara ta d'ago kanta tana kallon umma cikin tsananin mamaki "ki dai na mamaki just answer me " "kaiii ni wlh ba don hka ba umma " "toh bakya son ki ga ammin ki tayi aure ne, Kinsan har yanxu bata shige haihu wa ba, kuma Kinsan aure shine cikar mutuncin 'ya mace tun da bata shige hakan ba sai anfi ganin ta da mutuncin ta " Shiru nauwara tayi tana sauraren umma yayin da umma ta cigaba da cewa " ita ma ammin naki baki ga yanda muka shawo kanta har ta yarda ba ni banso kika ji ba sai bayan an d'aura auren,kuma da kike cewa bai kamata ku saka min da auren nan ba, ni kuwa wannan auren yafi komai faranta min rai Indai har na isa da ke xan fad'a miki magana ki ji toh ki saki ranki kuma ki yarda da auren nan idan kika min haka kin saka min da abin da nayi miki nauwara, Idan naga akasin haka na tabbatar baki d'auke ni a uwa ba" Umma tana gama fad'in hka ta fice daga bedroom d'in, tasan Idan ba hka ta yiwa nauwara ba sai tayi yanda tayi ta ruguxa wannan auren, ita hka Allah ya d'ora mata son ammi dasu nauwara. Turk'ashi nauwara kuka tasha wiwi wiwi har da su majina umma gaba d'aya ta d'aure ta da maganganun ta, wayar ta d'auka ta kirawo ammi ta fashe mata da kuka shiru ammi tayi bata ce mata komai ba sai da tayi mai isar ta sannan cikin shashshak'ar kuka tace "ammi don Allah abin da nake ji da gaske ne? " Tabbas ammi tasan nauwara taji labarin xata auri Abba, don haka cikin sanyin jiki da murya ammi tace "tabbas abin da kika ji gaskiya ne nauwara, ni ma kaina ba'a son rai na ba sai da baffah da inna suka nuna min 6acin ran su sannan na amince gashi abduljabbar sai sunturi yake yi min akan lallai na amince har da Alhj ibraheem (wato Abba) yasha xuwa shima hkan da na ganine yasa na amince ke ma ina son ki dai na damun kanki, kawai Ki cigaba da addu'a Allah ya xa6a abin da yafi alkhairi, sannan kuma kada naji labarin ko da wasa kin bijire wa umma kin ji na fad'a miki ki rik'e ta tamkar ita ta haife ki bamu da abin da xamu sakawa wad'annan bayin Allahn sai dai addu'a hak'ik'a mahaifin ki yayi hangen nesa da yace duk duniyar nan bashi da amini kamar Alhj ibraheem d'anbatta wanda xai rik'e mishi mu amana sai shi sai gashi kuma maganar tashi ta tabbata" Cikin kuka nauwara tace "amma ammi......" Da sauri ammi ta katse nauwara ta hanyar cewa "shiiiii bana son jin komai daga gare ki, kiyi abin da nace Idan har na isa dake, Allah ya jik'an abban ku da safah! " "Ameeen ya rabbi ammi, kuma Insha Allah xan yi yanda kika ce" Ammi tana goge hawayen fuskar ta tace "Allah yayi muku albarka " "Ameeen ammin mu " Daga hka suka yi sallama ta ajiye wayar tare da buga uban tagumi, ta dau wajen 10 mint a Hka Kafin ta tashi ta shiga toilet wanka ta sake ta fito sannan ta shirya cikin wata gown English wears amman ba takai Har k'asa ba mai k'aramin hannu kalar dark purple tayi matuk'ar amsar ta rigar bayan ta gyara gashin ta d'aure shi da ribbom black ta fesa perfumes ajikin ta ko make up Bata yi ba daga powder sae wet lips a bakin ta idanun ta duk sun kumbura alamar tayi kuka sosai wani black shoes plate ta dauko ta sanya sannan ta fito daga d'akin. Bedroom d'in umma ta shiga cikin siririyar murya tayi sallama ,umma ta amsa mata sallamar, tsugunna wa tayi har k'asa tare da rik'e hannayen umma tari rau rau xata fashe da kuka da sauri umma tace "shiiiii bana son kukan nan kada ki 6ata kwalliyar tun Kafin d'an nawa ya dawo ya biya kud'in kwalliyar " Ta fad'i tana er dariyar su ta manya, sosai umma ta bawa nauwara kunya ta nok'e kai tana murmishi marairaice fuska tayi sosai sannan tace "I'm so sorry umma baxan kuma ba " "ni baki min komai ba 'yata komai ya wuce Allah ya yi muku albarka " Cikin tsananin farinciki nauwara ta ce "Ameeen umman mu, nagode Allah ya saka miki da alkhairi " "Ameeen dota " Daga hka nauwara taja baki tayi shiru don duk ta kasa sake wa da umma kamar da, ita kanta umman ta fahimce ta don hka ta dunga janta da er hira, mik'e wa tsaye nauwara tayi tace "umma bari naje kitchen ko xan samu fresh milk " Murmishi umman tayi kafin ta ce "ae d'axun nan saleem yaje ya siyo har da sauran drinks kuma nasan yanxu sunyi sanyi " "Kaiii amman umma naji dad'i, na taho miki da Ita? " "a'a Alhmdullilah, asha lafia " "toh Shikenan umma " Ta fice daga d'akin umma ta bita da kallo cike da kaunar ta. Tana shiga kitchen ta bud'e frige ta d'auko fresh milk mai sanyi sosai jikin ta har ra6a yake tsabar tayi sanyi glass cup ta d'auko wanke shi tayi sannan ta cika shi da fresh milk di'n ta fara sha da yake ta juya wa kofar kitchen d'in baya sai ji tayi an rungumo ta ta baya da sauri ta jiyo a tsorace sai suka had'a ido da abduljabbar er K'aramar ajiyar xuciya ta saki dariya yayi yana cewa "matsoraciya kin xata wani ne koh? " Ya fad'i yana kallon fuskar ta Kafin kuma idanun shi sukai kan rigar da ke jikin ta, ita kuwa duk kunya ta rufe ta ganin irin kallon kurrilar da yake yi mata "habibty Kinyi kuka koh, me ya same ki? " D'an hararar shi tayi tare da turo bakin ta hkan da tayi ba k'aramin hargitsa shi tayi ba k'ara matso da ita jikin shi yayi fuskar su tana daf da ta juna har suna jin numfashin junan su a hankali cikin wani salo ya isar da bakin shi cikin nata sun d'auki long time a Hka suna kisses d'in junan su gaba d'aya jikin shi rawa yake kafafun su sun k'asa rik'e su tuni nauwara tayi baya xata fad'i da sauri ta rik'o rigar abduljabbar toh da yake shima jikin nashi ba k'wari sai ya biyo ta suka xube akan tiles di'n kitchen d'in washhh nauwara ta fad'i da sauri ya rik'o hannun yana cewa "me... me ya faru ?" Cikin shagwa6a tace "hannu na " Yana hura wa hannun iskar bakin shi yana cewa "sorry habibty tashi Ki rakani part d'ina " "tabbb ni gaskia baxan je ba" Marairaicewa yayi yana cewa "please baby nah, fad'a min me kike so " Shiru tayi tana d'an tunani Kafin tace "sai kayi min alkawarin gobe xan je gidan fa'iza da aunty jeedah " Da sauri yace "i promise u xan bar ki kije " Tana kallon shi cikin ido tace "are u sure ?" "yes! Baby nah " Mik'e wa tsaye yayi ta Mik'o mishi hannun ta ya kama ya rik'e su sannan ya d'ago ta da d'an k'arfi har tana cewa "washh Yayah kayi min a hankali " Yana lakuce mata hanci yace "ae ke ce duk kika ruda ni da yawa Kinsa sai rawar jiki nake a gaban umma " Tana er dariya tace "laaa ni Allah ba ruwa na" Kafin ta ankara ya d'auke ta cak da kafa ya bud'e kofar kitchen ta baya suka shige part d'in shi a kyakkyawan bed d'in shi ya sauke ta sannan ya yi mata rumfa da jikin shi rufe ta yayi da hot kisses yana aika mata da wasu xafafan sak'onnin shi xuwa gare ta masu tsaya wa a xuciya. Yana kwance kanta yana saman kirjin shi yana shafa gashin kanta yace "habibty wai sai yaushe wannan abin xai tafi hak'uri na ya fara gajiya wa fah " Batasan lokacin da dariya ta kubce mata ba hararar wasa ya aika mata Kafin yace "okay dariya na baki ma, Naga alama yanxu bakya tausaya min " Ya K'arasa fad'i cikin kalar tausayi danne dariyar ta yi sannan tace "Haba my sweetheart Idan banji tausayin miji na ba wa xan tausaya wa " "Idan Hkane ki tsayar dashi mana" d'an xaro ido tayi tana cewa "taya xan tsayar da shi ae sai idan lokacin tsayawar yayi ya tsaya " "okay naji yaushe xai tsaya? " "kawo kunnen ka na fad'a maka " Da sauri ya mik'a kunnen nashi kuwa ae kuwa ta d'an cije shi da sauri ya janye kunnen nashi yayo kanta yana cewa "ni kika cija ko sai na rama baxan yarda ba idan baki tsaya ba na kirawo twins mu danne ki kowa ya ciji Inda yake so " Yarfe hannun ta ta fara cikin shagwa6a tana cewa "wayyo Allah kayi hak'uri na baxan k'ara ba" "nooo sai fah na rama yarinya " Kamo ta yayi xuwa jikin shi ya fara yi mata cakulculi nan ta fara dariya tana xille wa tare da cewa "ka daina yayah please " Ganin tana kok'arin shide mishi yasa shi ya barta tare da d'aukar ta suka shige bathroom. Bayan sun gama wankan sun fito ya shirya cikin wani 3quater white colour tare da purple d'in t-shirt mara hannu mara nauyi gata er Shara Shara don ana iya hango kwantaccen gashin kirjin shi nauwara ce ta gyara mishi gashin kanshi tare da fesa mishi perfumes sannan ya rik'o ta xuwa part d'in umma ta Inda suka fita tanan suka shigo duk kunya ta ishi nauwara tana addu'ar Allah yasa umma bata parlour ae kuwa da ita ta fara had'a ido tana xaune dasu na'eem da ameer suna xuba mata surutu. Kallon su tayi tana murmishi kawai ganin yanda nauwara take nok'e kai shi kuwa gogan ko ajikin shi, xama suka yi suka sata a tsakiya umma tace "Haba abduljabbar yanxu ka girma fah ya kamata ka rage irin wannan shigar Idan xaka fita, nasan da wannan shigar sai kace fita xaka yi " Shafa kanshi yayi yana kallon nauwara wadda ta aika mishi da harara yana murmishi yace "toh umma na daina, amman yanxu ba Inda xan sake fita na gaji ni yunwa ma nake ji " Ya K'arasa fad'i yana Yatsina fuska "me xaka ci? " Cewar umma " yanxu lokacin mangarib yayi Kafin na dawo ayi min had'in salad ya ishe ni sai a dumama min pepper chicken di'n d'axu yayi min dad'i " "ah ba yunwar kake ji ba " "Kaiii umma da gaske nake " Ya fad'i yana ta6o nauwara da kafar shi, "toh Shikenan " Ko 5 mint basu yi ba suka ji kiran sallahr mangariba don hka ya tashi ya tafi ya canja kayan shi xuwa farar jallabiya yayi alwala ya tafi masallaci, yayin da nauwara ta shiga kitchen ta had'a mishi abin da yake son ci bayan ta gama ta nufi bedroom.......... Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 98~* Misalin karfe 8:20 ya shigo part d'in umma a xaune a parlour ya tarar dasu umma, saleem, aunty sadiya sai na'eem da ameer, umma da aunty sadiya suna hira yayin da saleem yake danna laptop su twins suna mak'ale a jikin shi ganin papa di'n su ya shigo suka mik'e da gudu suka nufi wajen shi tare da rungume shi d'aukan su yayi gaba d'aya yana yi musu wasa tukunna ya xauna ana hirar dashi sai wurwurga ido yake ta inda xai hango habibty di'n shi but bai ga alamun ta ba yasan tana d'aki don hka ya sauke na'eem da ameer daga jikin shi ya ajiye su kusa da saleem sannan yayi upstairs da sauri. Tura kofar yayi a hankali ya shiga d'akin sai ya hango ta akan abin sallah da dogon hijab har k'asa tana sallah a nutse wata irin ajiyar xuciya ya saki xuciyar shi cike da farin ciki ya samu waje ya xauna akan sofa yana kallon ta. Bayan ta idar tayi addu'o'in ta sam bata san ya shigo d'akin ba ta cire hijab d'in jikin ta tare da kunce xanin da ta d'aura akan wata night gown dark purple ce iya karta gwiwa hannun rigar d'an siriri ne ajiye su tayi sannan ta nufi dressing mirror hand dryer ta d'auka ta fara busar da gashin kanta da yake jik'e, duk abin da take yana bin ta da kallo sai wani lumshe ido yake yana wani shi'umin murmishi tare da sake gyara kwanciyar shi akan sofa di'n, gaba d'aya ta gama rikita shi, bayan ta gama busar da gashin ta taje tare da d'aure wa da ribbom, wayar ta ta dauka sannan ta nufi kan sofa da niyyar xama sai taji ta xauna kan mutum a tsorace ta mik'e da sauri hannu yasa ya fisgo ta jikin shi suka had'a ido sai ta saki ajiyar xuciya don ba k'aramin tsorata tayi ba shi kuwa dariya ya tuntsire da ita Kafin yace "kin cika tsoro nauwara" tana kok'arin tashi daga jikin shi tana cewa "ehhh ba dole na tsorata ba ka shigo min d'aki bansani ba " D'an hancin ta ya kama yaja Kafin ya rad'a mata a kunne "habibty yaushe kika koyi k'arya neee? " A firgice tace "ni! Yaushe nayi maka k'arya? " "daman kin fara sallah shine baki gaya min ba ko d'axu fah sai da na tambaye ki" D'an hararar shi tayi tare da cewa "ni fah yanxu ne naga babu fah" Cikin tsananin farinciki yace "toh Alhmdllh yanxu ki had'o min abinci xuwa part d'ina ina jiran ki don Allah kada ki dad'e please " "Kaiii Yah abduljabbar ba ga er aikin umma sai ta kai ma ba ko kaci anan ni fah bacci nake ji" Kwantar da murya yayi yana cewa "Haba baby nah ki taimaka ki kawo min Kina kawo min sai ki tafi amman ban so ki turo wata er aiki " Yana gama fad'in hka ya fice daga d'akin Bata da yanda xata yi hka ta saka hijab d'in ta ta fito xuwa down stairs kitchen ta shiga ta had'a mishi komai a babban tire sannan ta d'auko ta kofar baya ta fice saboda tana jin kunyar umma tace wurin abduljabbar xata je ta kai mishi abinci. A hankali ta K'arasa part d'in ta murd'a handle di'n kofar ta shiga da sallama, amman bata ganshi ba sai ta ajiye abincin kan center table d'in ta juya da xummar ta tafi turus taja ta tsaya ganin abduljabbar a bayan ta daga shi sai white boxer ya harde hannuwan shi a kirjin shi yana kallon ta k'asa k'asa wanda har sai da gaban ta ya fadi . Zama yayi kan kujera yana kallon ta yace "yi sauri ki xuba min yunwa nake ji uhm sannan ki cire wannan hijab d'in ke ko xafi bakya ji a jikin ki kin xuba wannan abin " Ganin ta had'e fuska yasa shi tashi tsaye ya tako har Inda take tsaye yasa hannu ya cire hijab d'in wani sanyayan k'amshi ne ya bigi hancin shi Har sai da ya lumshe idon shi sannan ya rik'o hannun ta yana cewa "d'an saki fuskar mana habibty ko na samu naci abincin a nutse " Tana turo baki tace "baka ce ina ajiye abincin ba na juya na tafi " ,"Ayyah my wife ae baki xuba min ba ko bakya son k'arin lada ne? " Bata kula shi ba ta d'auke kai tare da janyo plate ta xuba mishi pepper chicken di'n, sannan ta xuba mishi had'in salad d'in tare da xuba mishi coconut juice acikin glass cup, kusa da ita yaxo ya xauna har kafad'ar shi tana gogan ta nauwara mik'e wa tayi tana cewa "gashi nan na gama xuba ma sai ka ci " Kamo ta yayi ya xaunar da ita kan kafafun shi ya d'ebo salad d'in da spoon Yayi bakin ta yana cewa "oya open your mouth don nasan baki abinci ba" Ya K'arasa fad'i yana shafa cikinta ganin duk ya bi ya tak'ura mata yasa ta bud'e bakin ta kar6a a haka yana ci yana bata har suka koshi sun sha ferfeson nan suka d'ora da coconut juice, suna gama wa yaja ta bedroom toilet suka nufa brush sannan suka fito tana kok'arin tsere wa ya damko ta tare da d'ora ta kan bed tare da yin switch off d'in hasken d'akin gaba d'aya. Hot kisses ya fara aika mata dashi ta ko'ina duk yabi ya rud'e sai jikin shi har rawa yake gaba d'aya ya fice daga hayyacin shi sak'onnin shi masu xafi yake aika mata dashi,yana nuna mata yanda yayi missing di'n ta sosai lokaci d'aya ya janyo blanket ya rufe su dashi. Asuba ta gari.... Washe gari da safe sai wurin 10:30 suka tashi tunda suka yi sallahr asuba suka koma bacci sae yanxu suka tashi wanka suka shiga suka yi abduljabbar ya shirya cikin wani blue jeans da t-shirt red colour mai gajeran hannu yayi kyau da ka ganshi kasan yana cikin farinciki fiye da ko yaushe don fuskar shi a sake take kallon nauwara yayi wanda ke daure da towel ajikin ta sauran kiris ta fashe da kuka cikin murmishi ya kamo ta xuwa jikin shi yayi hugging di'n ta yace "Ya akayi ne 'yammata nah? " Tana turo baki da yanayin shagwa6a tace "to ni.... ni fah kayana suna part d'in umma bani da wanda xan sa ka" Dariya ya d'anyi ganin yana mata dariya yasa ta d'an fara bugun kirjin shi Kad'an da sauri ya rike hannayen nata ai kuwa ta fashe mishi da kuka sosai ganin hka yasa ya danne dariyar ta shi yana cewa "calm down my habibty bari naje na d'auko miki kayan kin ji" Gid'a kai tayi kawai xaunar da ita yayi kan bed sannan ya fice daga d'akin, yana fita ta kwanta duk a gajiye take tuni bacci ya fara fisgar ta a hankali. Shi kuwa yana shiga part d'in umma a parlour suka hadu da umman ya gaida ita tukunna ya juya xai nufi upstairs umma tace "abduljabbar ba nauwara tana wurin ka ba ne?" Yana sosa kai yace "Ehh umma tana nan, uhm kayan ta xan d'auko mata" Girgixa kai umma tayi hmm yaran xamani basu da kunya tukunna tace "Okay amman tayi sauri taxo tayi breakfast d'in tun da tace min xata je gidan fa'iza da jiddah kada rana tayi " "Okay umma yanxu xata xo" Yana gama fad'in hka ya haye stairs umma kuwa tayi kitchen, bayan ya d'auko mata kayan ya tafi kai mata tsaya wa yayi cike da mamaki yana kallon ta ganin yanda ta koma bacci, xama yayi kusa da ita ya xuba mata ido yana kallon ta wani son ta da k'aunar tane yake shiga cikin xuciyar ya gode wa Allah da ya bashi mace da tai dai dai dashi a komai da hka yasa hannun shi yana yi mata tafiyar tsutsuwa a kafar ta har ta bud'e idon ta yace "kin manta da fitar taki " Tuna wa da tayi da hka yasa ta tashi da sauri ta shiga toilet sannan ta fito ta shirya cikin wani cotton lace maroon colour riga da siket ne sunyi mata kyau sosae da yake babu kayan make up yasa ta d'aura d'ankwalin ta sannan suka fito a kunyace ta gaida da umma Sannan a gurguje suka yi breakfast taje ta yiwa fuskar ta light make up ta sanya mayafi da takalmi sannan ta fito tayi sallama da umma suka fita da abduljabbar don shi xai kai ta. A farfajiyar gidan suka had'u da na'eem da ameer nan suka mak'ale sai sun bisu haka suka xuba su a bayan sit d'in motar suka tafi, a gidan jiddah ya fara ajiye ta ya bata 30 mints ta fito su tafi haka ta shiga gidan da sallama jiddah da gudu taje ta rungume ta sannan ta gaisa da hindatu suka shige part d'in jiddah sun sha er hira ta wajen 30 mint di'n tukunna tayi mata sallama suka fito ta rakota har wajen da abduljabbar yayi parking suka gaisa ya bata kyautar kud'i da yawa sannan suka yi sallama da juna suka tafi. Suna er hirar su da yaran su har suka k'araso gidan fa'iza to anan ya ajiye so sai 5 na yamma xai xo ya d'auke su, suna shiga fa'iza tana jin sallamar nauwara ta fara tsallen murna bare da taga har da twins aka xo mata........ Aishat A muh'd 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd _dedicated to my Ummiey xeey Allah ya k'ara basirah da fasaha da k'arfin ido ina miki fatan alkhairi_💞😍 *~Pg 99~* Sun sha hira da fa'iza sosai yinin ranar tare suka yi girkin rana suna ta hira don sunyi kewar juna sosai, sai 5 abduljabbar yaxo d'aukan su da bai yi niyyar shiga gidan ba sai ga Dr muh'd ya dawo daga wurin aiki shi ya tilas ta mishi ya shiga. Fa'iza baki fah yak'i rufuwa ganin babban yaya a gidan ta nan ta gaida shi sannan ta had'o mishi drinks da bottle d'in faro ta kawo mishi babu abin da sha sai da suka tisa shi a gaba daga fa'iza har Dr muh'd di'n da naci sannan yasha drink d'in yana gama sha ya yi musu sallama ya fito daga gidan xuwa cikin motar shi ya xauna yana jiran nauwara. Kamar kada su rabu da juna haka suka ji sai lokacin suka gaisa da Dr muh'd don lokacin da ya shigo tana bedroom d'in fa'iza, kamar yanda ya bawa jiddah kyautar kud'i haka ya bawa fa'iza tayi ta godia sannan suka rabu cike da kewar junan su. Sun dawo gida nauwara agajiye sosai take don hka tana sallahr isha'e ta watsa ruwa a jikin ta tabi lafiyar gado sai bacci, abduljabbar kuwa kasa bacci yayi sai faman juyi yake daga K'arshe ya tarkato yayo d'akin nauwara ya rungume abar shi a jikin shi sai lokacin bacci ya mai dad'i ya d'auke shi. Hka su nauwara suka cigaba da xuba soyayyar su cikin kwanciyar hankali, har xuwa ranar monday da safe abduljabbar ya koma abuja suka rabu cike da kewar junan su. Duk wasu shirye shirye an gama na d'aurin auren Abba da ammi an gyara mata part d'aya wanda xata xauna aciki girman shi da komai nashi kamar nasu umma, abduljabbar ne ya xuba kayan furnitures da sauran kayan kyala kyale na gida shi ya d'auke wannan nauyin, sam nauwarah ta kasa sakin jiki da umma kamar da don wlh ita fah har yanxu wannan auren bai kwanta mata a rai ba kawai don an fi k'arfin ta ne, har abduljabbar ta fad'a mishi yace kawai ta bisu da addu'ar xaman lafia don shi ma yana son auren abba da ammi dole ta hak'ura kuwa. Ranar juma'a bayan an idar da sallahr juma'a Kafin mutane su tafi acikin masallacin dubban mutane suka shaida daurin auren abba da ammi daga nan aka watse ana musu addu'ar xaman lafia. Daman nauwara bata xo kaduna ba don umma tace taje kadunan amman nauwara tace ita Mai xata je tayi Hka umma ta kyale ta, tana kula da ita bayan an d'aura auren abduljabbar yana kiran umma yana fad'a mata to da yake nauwara tana xaune kusa da umman tsam ta tashi ta shige d'aki taci kukanta ta more sannan ta fito kallo d'aya umma tayi mata ta tabbatar kuka tayi girgixa kai kawai umma tayi bata ce mata komai ba kamar yanda ita ma nauwara bata k'ara magana ba. Bayan su abduljabbar sun dawo daga d'aurin auren a d'akin ta ya same ta a kwance shima kwanciyar yayi a jikin ta tare da cewa "me yake damun baby nah? " Murmishin yak'e tayi tana cewa "ba komai dear just ina huta wa ne " "da kyau habibty nah ya kamata ki fara shiri ranar sunday xamu wuce abuja har da twins xamu tafi" "da gaske kake? " Ta fad'i tana d'an waro ido bushe mata idon yayi ta lumshe su kuwa tana murmishi yana murxa mata hannu yace "da gaske nake wlh baby na gaji da xirga xirgan nan " "baxa mu barwa umma twins ba? " "tabbb Allah baxan iya ba da yara na xan tafi " "kai dear " "yes! Baby nah baki san yanda nake son yara ba, har na matsu kin dad'a samun ciki kin haifa min wasu twins d'in dukka mata, na'eem da ameer sun girma fah ya kamata su samu kanne ina nan ina addu'a jiki na yana bani kin kusa samu ko ma har kin harbu Insha Allah " Kwa6e fuska tayi tare da yin kalar tausayi da fuskar tace "kai dear twins fah kace tabbb ba kasan xafin haihuwa bane da wahala fa wayyo Allah nah" Dariya ta bashi ganin yanda tayi yana dariyar yace "ba wani wahala fah abin da tare ma xamu haihun ina miki nakudar Kina haihuwar ae kada ki damu " "Hmmm " abin da nauwara tayi kenan ,kallon ta yayi yana cewa "komai na gidan ki an xuba bari ma Ki gani ko yayi miki" Wayar shi ya d'auko ya fara nuna mata irin yanda aka canja gidan kamar bashi ba yayi matuk'ar yin kyau gashi kaloli masu kyau aka shirya gidan dasu "Wow masha Allah gaskiya dear yayi kyau sosai Allah ya k'ara bud'i ya kare min kai daga sharrin masu sharri nagode " "Ameeen habibty na ki bar godiyar nan kin fi k'arfin komai a waje na" Peck ta bashi a kumatu sannan ya ce "baby nah i luv u " "i luv u too my dear " cikin marairaice murya ta kwantar da kanta a saman kafad'ar shi tace "my dear anjima xamu fita shan ice cream please " Bakin ta ya rik'o da hannun shi yace "wannan bakin ya fiye kwadayi da yawa " "xamu je don Allah " Yana murmishi yace "don't worry baby nah xamu je, amman yanxu a dan rage min xafi Kafin anjima Kinsan nayi missing di'n ki sosai " Ya K'arasa fad'i yana kashe mata ido d'aya rungume shi tayi a jikin ta tana Godiya ga Allah da ya mallaka mata wannan gwarxon mijin nata tana fatan mutuwa ce xata raba su. Ae kuwa da yammacin ranar suka shirya don tafiya nauwara tana sanye da blue gown mai touch d'in white ajikin rigar tayi rolling d'in kanta da white veil shi kuwa abduljabbar black trouser nd T-shirt blue sunyi matuk'ar yin kyau ko twins basu tafi dasu ba don suna islamia, ko umma ta yaba da wannan k'walliyar tasu, sun birge mutane da dama sai kallon su ake kishi ya ishi nauwara ganin yanda emmata suke kallon abduljabbar ba don ta gaji ba tasa shi da mitar su dawo gida kallon ta yayi yana murmishi yace "Haba baby nah baxa ki bar ni na lalubo d'aya ba sai ki samu k'anwa koh yah " Ya fad'i yana d'aga mata gira harara ta 6alla mishi tare da had'e rai kiris take jira ta fashe mishi da kuka nan kuma ya dawo rarrashin ta don baxai jure fushin habibty di'n shi ba, Sun sha selfie sannan suka yiwa su twins da su umma siyayyan kayan ciye ciye tukunna suka dawo gida xuciyar su cike da farin ciki. Duk wasu abubuwan da xasu buk'ata umma ta tanadar wa nauwara sun had'a kayan su sai jiran ranar tafiya dakyar ya barta taje gidan jiddah, fa'iza da aunty kausar tayi musu sallama ranar sunday misalin karfe 2:30 jirgin su nauwara ya d'aga xuwa abuja sun bar umma da abba, aunty sadiya saleem da kewar su. Alhmdllh sun sauka a abuja lafia Joseph driven Yah abduljabbar ne yaxo ya dauke su a airport xuwa gida, Wow duk irin Kyan da nauwara ta gani a wayar abduljabbar na gidan sai yanxu taga ni axahiri yafi mata kyau,sai da ya xagaya dasu ko'ina na gidan, d'akin su twins ma ya had'u iya had'u wa sannan kuma abduljabbar da nauwara suka tafi bedrooms di'n su don yin wanka yayin da er aikin da umma ta had'a mata da ita ta kwashe su twins don tayi musu wanka su ma. Bayan sun kammala suka dawo falo duk sun sha english wears marasa nauyi na shan iska akan dinning table suka xauna suka ci take away di'n da joseph yaje yayi musu bayan sun ci sun sha suka dawo parlour suka xube suna hutawa da er hira. Acikin satin abduljabbar ya sama wa su na'eem da ameer wata tsadaddiyar makaranta mai kyau sosai ba 6ata lokaci suka fara xuwa skul d'in har da islamia Mai kyau ya samar musu da sabuwar motar da xa'a dunga kai su makarantar da driven su a gida kuwa nauwara ta cigaba da d'ora musu lesson rayuwa suke mai dad'i. A Kano kuwa bayan Sati d'aya da d'aura auren abba da ammi, ammi ta tare a gidan abba xama suke mai dad'i da fahimtar juna sun had'e kawunan su suna kyautata wa abba Idan ka shigo gidan baxa ka ta6a gane kishiyoyi ba ne sai an fad'a maka ko ka fahimta ba k'aramin birge mutane suke ba don Kafin a samu mata masu irin had'in kan nan xa'a dad'e a wannan xamanin da muke ciki dai don son kai yayi yawa a xuciyar al'umma. Aishat A muh'd [4/30, 20:18] Umar Dalha: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *~Pg 100~* Satin su d'aya da dawo wa abuja abduljabbar ya shirya musu tafiya honey moon shi da nauwara twins wajen aunty asma'u suka ajiye su saboda makaranta, hutun 2 month's ya samu don hka suka d'aga xuwa k'asar Greece daman k'asa uku xasu Greece, switzerland, sai su biyo ta Saudi Arabia suyi umarah. Sun sauka a k'asar Greece k'asa ce mai kyau sosai da mutanen mu na Africa basu saba da xuwan ta sosai ba a wani babban hotel yayi musu masauki suna hawa na uku, room d'in da suke ciki katon parlour ne da one bedroom shima babba sai toilet, nan suka xube kan bed suna huta gajiyar mikakkiyar tafiyar da suka yi. Bayan sunyi wanka sun ci abinci sannan suka kirawo su umma suna sanar dasu sun sauka lafia, sun kirawo aunty asma'u ta had'a su da twins suna ta xuba musu surutu kowanne yana fad'in tsarabar da xa'a yi mishi, sai da suka yi k'wanaki uku suna hutawa basa xuwa ko'ina suna manne da junan su ana xuba soyayya don abduljabbar yace ta shirya Insha Allah xai sun dawo da tsarabar honey moon ya kuma dage da addu'a sosai. A k'wanakin su na hud'u da xuwa k'asar Greece ne da wani yammaci bayan anyi ruwa an d'auke suka fito abduljabbar yana sanye da white d'in trouser nd T-shirt red colour ya d'ora jibgegiyar rigar sanyi black saboda yanda garin ya d'auki sanyi sosai, yayin da nauwara ta sanya dogon wando maroon colour nd T-shirt black sai ta d'ora coat irin wanda mata suke sanya wa har xuwa gwiwar ta tayi rolling d'in kanta da maroon veil tayi kyau sosai suna rik'e da hannun junan su suna tafiya. Sunyi yawo sosai a k'asar Greece di'n nauwara k'asar ta birge ta a sati ukun da xasu yi sun sha yawo duk wani gurin shak'atawa da manya manyan malls na k'asar sun xiyar ci wajen da hka suka yi bankwana da k'asar Greece suka yo switzerland nauwara tana santin k'asar don ta matuk'ar yi mata kyau. Bayan sun sauka a k'asar switzerland ne da sati biyun nauwara ta fara jin canjin yanayi a tattare da ita yawan bacci da rashin appitate a baki sai kuma tashin xuciya kamar yau ta gama shirin ta xasu fita da abduljabbar tana jiran shi ya fito daga wanka irin ta xauna jiran nan shi sai bacci yayi awon gaba da ita a hka ya fito daga toilet d'in ya tsaya kallon ta cike da mamaki wannan baccin na nauwara yana d'aure mishi kai sosai mybe fitar da kuke shi yake gajiyar da ita Cewar wata xuciyar tashi gaban dressing mirror ya K'arasa ya gyara jikin shi ya K'arasa inda take tana bacci a hankali yake tashin ta bud'e idon tayi yana kallon ta yace "baby nah ko mun fasa fitar ne, ni wannan baccin naki na lafia ne anya babu ajiya ta Anan???? " Yatsine fuska tayi ta bud'e baki xatayi magana wani amai ya taso mata da gudu ta nufi toilet ta dunga k'wara shi sai da ta amayar da duk abin da taci, yana rik'e da ita kamar xai fashe da kuka haka yake ji don ba k'aramin tausayi ta bashi ba ganin yanda take wahala kamar ba soja ba bayan ta gama ya sake mata wanka sannan suka fito xuwa daga toilet d'in ya sa mata kaya tukunna yace "taso mu tafi hospital ni nagaji da wannan yanayin da kike ciki baxan iya jure ganin Kina ciwo ba" Cikin shagwa6a tace "ni gaskia a'a xan samu sauk'i bana son ayi min allura " Kamo ta yayi tare da mik'ar da ita tsaye yace "baxai yiwu ba dole ne muje a duba min ke don nasan me yake damun ki " Ba don taso ba ta bishi suka je wani hospital sun samu nasarar ganin wani Doctor mai jan kunne yayi mata en tambayoyi sannan aka yi mata urine test Inda suka hango d'an k'aramin ciki a manne a jikin ta lokacin da suka sanar da abduljabbar nan take ya tsugunna tare da yin sujjadar godiya ga Allah yana tashi daga sujjadar don tsanani murna ya rungume doctor d'in Kafin ya jiyo kan na ya d'auke ta cak sai juyi yake da ita a office d'in Dr di'n ya bisu da kallo alamar sun burge shi sosai daman en 9ja sun iya soyayya da kula da matan su kamar yanda ya gani a Wajen abduljabbar, Cewar Dr a xuciyar shi bai san maganar ta fito fili ba har naji ina da gefe na ce lallai doctor nan an gaya maka en 9ja basu da wannan wayewar nan me ka dau ke su ne 😏, muma ae mun iya kawai dai don malam bahaushe akwai shi da son girma baya son rai ni shi yasa ba kowanne yake yi ba..... lol Jin abin da na fad'a yasa doctor ya sunkuyar da kae yana sosa k'eya alamar yaji kunya bai san xan ji ba lol. Bayan ya gama juyin da ita a office d'in doctor ya dire ta sannan a lokacin Dr yayi wa abduljabbar bayanin yanda xasu kula da cikin Sannan ya rubuta mata magungunan da xata sha wanda xai taimaka mata sosai wajen Inganta lafiar ta da ta jaririn cikin. Da hka suka yi sallama da doctor suka fito xuciyoyin su cike da tarin farinciki more especially abduljabbar da hka suka tari taxi har xuwa masaukin su. Nauwara ta ga gata sosai a wajen abduljabbar wanda Idan yana wani abin har mamaki yake bata kamar bashi da wasu yaran, shi haka Allah yayi shi akwai son yara sosai, nan da nan nauwara ta dad'a wani irin haske kyanta ya k'ara fito wa sai dai ta d'an rame saboda laulayi yau lafia gobe sai a hankali, satin ukun da suka yi niyyar yi sai da suka k'ara Sati d'aya sannan suka wuce Saudi Arabia nan ma Sati ukun suka yi sannan suka yo gida nigeria, sun sauka lafia aunty asma'u ce da su twins sai yaranta sune suka xo taryar su cikin tsananin farinciki na'eem da ameer suka rungume iyayen nasu suna murnar ganin su don sunyi matuk'ar kewar su, kallo d'aya aunty asma'u tayi wa nauwara ta fahimci ciki ne da ita don hka cikin murmishin tsokana ta cewa abduljabbar "kai daga xuwa honey moon sai ku dawo da tsaraba" Cikin murmishi yace "alamar tafiya tayi kyau sosai " Yana fad'in hka ya shige mota kunya ta rufe nauwara kamar ta nutse a k'asa aunty asma'u kuwa dariya tayi tana cewa "Allah ya shirya ka abdul " Da haka suna er hirar su suka K'arasa gidan nasu sai yamma likis aunty asma'u ta koma gidan ta ta bar mata babbar 'yarta hanan Ko xata taimaka mata hakan kuwa ba k'aramin dad'i yayi wa nauwara ba don jinin su ya had'u da hanan yarinyar akwai hankali da kamun kai. Sai da suka yi wajen wata biyu da dawo wa sannan abduljabbar ya samu d'an short break na tsayin 1week kacal suka tattara suka yo kano don tuntuni nauwara taso xuwa but ya hana ta sam yace tare xasu xo don baxai iya missing di'n ta ba na tsawon wasu k'wanaki, lokacin cikin jikin ta har ya dan fito ana ganin shi. Sun sauka a Kano lafia umma,abba, aunty sadiya da ammi ba k'aramin jin dad'in ganin su suka yi ba gashi sun hango Sun kusa samu wasu jikokin nan fa suka frasa inda xasu sa su don dad'i, abin da yayi matuk'ar d'aure kan nauwara shine ganin wai ammin ta da ciki gashi nan ya fito ana ganin shi lallai wani baya haifar d'an wani rayuwa kenan Allah yasa mu dace da kyakkyawan rabo. Washe gari fa'iza ,jiddah aunty kausar taxo gidan gaba d'aya kamar had'in baki sun sha murnar ganin junan su fa'iza ma tana d'auke da cikin ita ma jiddah Allah maji rokan bawan shi gashi nan ita ma da nata cikin kuma yanxu hindatu tayi nadama tun lokacin da aminu Yayi mata saki d'aya da tayi niyyar k'ona jiddah da tafassheshen ruwan xafi Allah bai bata nasara ba aminu ya ganta ya kar6e to shine yayi mata saki d'aya, dakyar ya dawo da ita don darajar yaran dake tsakanin su, yanxu tayi nadama sosae xaman lafia suke da jiddah ae duk tsanani yana tare da sauk'i komai wuya sai dad'i kuma *Innallaha ma'assabirin* littafin miss zahra mansur. Yini guda suna shan hira nauwara kowanne ta bashi tsarabar shi sun yi mata godia sai yamma tukunna kowacce mijin ta yaxo ya dauke ta. Satin su d'aya a Kano sun xagaya gidajen en uwa har kaduna nauwara taje k'wanan ta d'aya ta dawo kano, ranar sunday suka shige abuja saboda makarantar su na'eem da ameer, yanxu saleem ya had'a degree di'n shi akan harkar kasuwanci bai nemi aiki ba Abba ya wulla shi company nin su nauwara dake abuja don ya dunga kula shi ya had'a shi da kwararrun ma'aikata masu tsoron Allah da amana a xuciyoyin su nan da nan company nin ya fara samun cigaba yanxu saleem ganin shi sai week end a Kano sauran k'wanaki biyar di'n a kaduna tun an fara xama babban mutum yanxu aure ya rage mishi don duk wani jin dad'i ya same shi, ammi kullum cikin addu'a take ma yaranta dasu umma da abba da suka rik'e su tsakani da Allah.... Aishat A muh'd [4/30, 20:18] Umar Dalha: 🍀🍀☘☘🍀🍀 *K'ARSHEN WAHALA* 🍀🍀☘☘🍀🍀 *written by* Aishat A muh'd *K'ARSHE* (last page) Cikin nauwara ya shiga wata na shida yayi girma sosae kamar nasu twins abduljabbar ba k'aramin tausaya mata yake ba kullum ya dawo daga aiki baya fita xai xauna kusa da ita yana lalla6a ta tare da bata labarai masu dad'i da ban dariya ita kuma tana nannad'e a jikin shi tana dariya haka na'eem da ameer xasu xo su kewaye su ana yi dasu kulawa sosai yake bata . Kamar yau tana xaune a falon down stairs tana sanye da simple gown don tafi mata dad'in sawa gaban ta fruit salad ne abduljabbar yana gefen ta yana bata a baki aka kirawo shi a waya da sauri nauwara ta mik'a mishi wayar da yake tana hannun ta ganin sunan abba ne d'aga wa yayi da sallama bayan ya gaida abba ne yake sanar dashi ammi ta haihu an sami baby boy tuni fuskar abduljabbar ta fad'ad'a da fara'a sosai Alhmdullilah ya furta bayan ya ajiye wayar nauwara wadda ta xuba mishi ido tace "waya haihu ne?" "ammi ce ta haihu yanxu an samu baby boy " Cikin wani irin sauri ta mik'e tsaye tana cewa wanda har sai da marar ta ta d'an murd'a kan a hankali ta dafe wajen tare da furta washh amman bata bi ta kanta ba tare da cewa "da gaske kake don Allah " Kamo ta yayi ya xaunar da ita kan kafafun shi ya d'an d'aure fuska yace "ban hana Ki tashi da sauri haka ba sai kin jiwa kanki ciwo? " Langa6e kai tayi tare da fad'in "sorry " d'an murmishi yayi Kafin yace "da gaske nake miki ammi ta haihu na samu small bro ni ma " Cikin tsananin murna ta rungume shi tare da cewa "Masha Allah Alhmdllh Yeeeeeee xan je kano " D'an hararar ta yayi yana cewa "da haka xaki Kano da wannan katon cikin ke da xuwa kano sai kin haihu yarinya " Kwa6e fuska tayi ta fara kukan shagwa6a ita fah sai taje har da shure shuren kafa irin na yara Idan xasu yi kuka tuni hankalin shi ya tashi don baya k'aunar ganin nauwaran shi a haka nan ya dawo lalla6a ta tare da yarda xasu je sai lokacin ta dai na kukan daman ae na k'ak'ale ne ko hawayen kirki babu sai murxar ido girgixa kai yayi yana murmishi kawai ya d'an ja kumatun ta yana cewa "habibty rigima don kin ga bana jurar ganin ki Kina cikin damuwa shi yasa kike yanda kike so" D'an hararar shi tayi da sauri ya dafe baki yana cewa "su6utar baki ne sorry " Gaba d'aya suka kwashe da dariya sai jin maganar twins suka yi suna cewa "papa mamee dariyar me kuke? " Abduljabbar da nauwara suka Kalli juna tare da yin murmishi nauwara tace " ammi ce ta haihu an samu boy" nan suka fara tsallen murna suna dariya. Bayan k'wana 2 da haihuwar suka tarkato xuwa kano har da aunty asma'u da yaranta nan fah gida ya cika da 'ya'ya da jikoki don su fa'iza, aunty kausar, jiddah, aunty safiyya dasu inna da baffah da saleem kamar had'in baki duk rana d'aya suka xo gida ya cika umma da aunty sadiya sun kasa xama waje d'aya sai anan ake dasu, barin ma nauwara motsi Kad'an sai ta tambayi nauwara me take so kula wa sosai take bata, babyn ammi yaci sunan abban su nauwara wato sa'eed don yace ameer mai sunan abban su nauwara daban shi ma nashi sa'eed d'in daban. Ranar suna jaririn yaci sunan sa'eed suna ce mishi arfat, bayan suna da k'wana 2 su nauwara suka koma abuja, haka lokaci ya cigaba da tafiya cikin nauwara yana wata 8 fa'iza ta haihu d'a namiji tana haihuwa da k'wana 3 jiddah ma Allah ya sauke ta lafia ta samu diya mace murna Wajen jiddah ba'a magana har da kukan ta na farinciki ta gode wa Allah da ya bata haihuwa daman ashe haka yara suke da dad'i wayyo Allah daman ana dawo da rayuwa baya da ta goge abubuwan da ta aikata a cikin rayuwar ta amman ina ya riga da ya wuce sai addu'ar Allah ya gafarta mana kura kuran mu Ameeen Anyi suna d'an fa'iza yaci sunan daddyn Dr muh'd Wato Abdullah suna kiran shi da daddy sannan er jiddah kuwa Mufeedah suka sanya mata. K'ememe abduljabbar barin nauwara xuwa suna ita ma bata sa ran xuwan ba saboda yanda cikin ta ya girma sosai ko taje baxa ta sake ba, yanxu nauwara kad'ai ake xuba idon haihuwar ta iyaye da en uwa sai addu'ar sauka lafia suke mata, abduljabbar kuwa tun da cikin haihuwar nauwara ya tsaya tsayuwar dare yake sosai da addu'ar Allah ya sauke ta lafia duk gaba d'aya baya cikin nutsuwar shi saboda tsananin tausayin ta ganin yanda take fama da ciki duk ta kumbura musamman kafafuwan ta. Tuni saleem sun dinke da Hanan babbar er aunty asma'u suna xuba soyayya kuma kowa yasan da haka a cikin en uwa kuma Anyi farin ciki sosae baran ma nauwara da yake yanxu ta dawo wajen ta da xama tana d'an taya ta ayyukan da er aiki baxa ta yi mata. Ranar Thursday da safe nauwara ta tashi da nakuda ganin yanda ta ke wahala gaba d'aya Abduljabbar ya gigice ya kid'ime ya ma kasa yin komai sai sannu kawai yake xuba mata, sai da Hanan ta kirawo aunty asma'u nan da nan taxo gidan tana fad'an me yasa bai kaita asibiti, shi sai lokacin ma ya tuna da wani asibiti don duk ya gigice kamar ba soja ba baya jurar ganin habibty di'n shi cikin wahala ne, cikin kankanin lokaci suka isa asibitin aka kaita room d'in haihuwa K'ememe abduljabbar yak'i fita daga d'akin yana rik'e da nauwara yana xuba mata sannu awan su 3 acikin asibitin Kafin nauwara ta haihu tarihi ya mai mai ta kanshi don 'ya'ya biyu reras ta sake haihuwa sai dai duk mata ne kyawawa masu kama da nauwara. Nan fah murna ta ishe abduljabbar ya rasa inda xai sa kanshi don tsananin farinciki haihuwa 2 amman 'ya'ya hud'u lallai Allah ba k'aramin kyauta yayi mishi ba da ya axurta da nauwara, sai da ya tabbatar nauwara ta dawo dai dai har tayi wanka ta samu baccin hutu tukunna ya kar6o yaran shi daga hannun aunty asma'u har tana mishi tsiya shi dai kawai murmishi yake, nan aka fara kiran en uwa da abokanan arxiki ana sanar dasu nauwara ta haihu ta samu twins duk mata. Sai dare aka sallame su daga asibitin bayan an tabbatar ba wata matsalar suka dawo gida nan fa na'eem da ameer suka dunga tsallen murna sun samu kanne, washe gari umma da aunty sadiya suka xo ganin yara k'wanan su 2 suka juya xuwa kano, shirye shiryen suna sosai Aunty asma'u take shirya ita dasu fa'iza ana sauran k'wana 2 suna su fa'iza, aunty kausar, jiddah da aunty maryam da aunty safiyya suka taho abuja saboda shirin suna. Kaya sosai abduljabbar ya had'a wa nauwara da twins na'eem da ameer sannan twins d'in shi mata, nauwara har da kyautar dankareriyar mota da yayi mata tare da wata sark'ar goal mai tsananin tsada ba k'aramin kashe kud'i yayi ba har nauwara tana mishi maganar kashe kud'in Yayi yawa yace mata ta barshi yayi komai yana da lokaci kuma sun fi k'arfin komai a wajen shi rungume shi nauwara tayi tana jin dad'in yanda Allah ya bata miji nagari. Kaiii twins fa sunyi goshi kaya ta ko'ina nauwara take samu umma, Abba, ammi, aunty sadiya, aunty asma'u, aunty kausar, aunty maryam, aunty safiyya, inna, baffah, saleem, fa'iza, jiddah dukkan su kowanne da nashi abin arxikin nauwara har ta rasa bakin godiya har da aiken Dr muh'd da aminu kaya masu tsada sosai wai a sawa twins. Abdulkareem ma kyautar ta daban ya aikowa da twins har da sark'ar goal guda biyu masu tsada, ya taya abokin shi murnar samun twins. Ranar suna twins sun ci sunan umma fatyma d'ayar kuwa taci sunan safah sai suke kiran wanda taci sunan umma marwa kenan safah da marwah sai fatan Allah ya raya su cikin addinin islama,walimah su aunty asma'u suka shirya anci ansha an watse. Bayan suna da k'wana 2 kowa ya watse aka bar nauwara da abduljabbar sai en yaran su a gida suna cigaba da kula wa dasu cikin tsananin farinciki da k'aunar yaran nasu. Bayan sunyi arba'in suka yo kano suka yi sati d'aya sannan taje kaduna tayi wa su inna k'wanaki uku acan sannan suka koma abuja, a dai dai lokacin aka yanke bikin saleem da Hanan wata biyu masu xuwa don Abba yace baxai shige wannan axumin ba bai yi mishi aure ba. Komai nisan lokaci aka sa xai xo har ya shige dashi nan har bikin saleem yaxo duk wasu shirye shirye an gama sun tarkato kano gaba d'aya don a gabatar da bikin da yake kuma mijin aunty asma'u shi iyayen shi en kano ne don hka komai yaxo da sauk'i an kammala biki lafia amarya Hanan ta tare a gidan ta da yake kaduna, daga hka kowa ya tarwatse ya nufi nashi gidan. *BAYAN SHEKARU 6* Ganin wasu kyawawan yara nayi su hud'u maxa biyu mata biyu suna xaune a parlour kallon mbc 3 suke ana cartoon di'n toy Story duk sun nutsu suna kallon saboda yanxu suka gama fad'an su na yara nauwara tayi niyyar dukan su abduljabbar ya hana ta don hka ta xuciya a fusace ta bar falon to shine abduljabbar ya kunna musu cartoon suna kallo ya tafi rarrashin habibty di'n tashi. Dakyar ya shawo kanta suka fito parlour suna ganin ta suka mik'e tsaye tare da durkusa wa agaban ta cikin had'in baki tare da rik'e kunnayen su suka ce " I'm so sorry mamee baxa mu k'ara ba mun dai na rashin ji " D'an hararar su tayi nan suka k'ara shagwa6e fuska tare da cewa "please mameen mu " Tsugunna wa tayi tare da bud'e hannuwan ta da gudu suka k'araso cikin jikin ta tayi hugging di'n su tare da basu peck a kumatun su tana shafa gashin kan su d'ago kanta tayi ta kalli abduljabbar da ya langa6e kai yana wani marairaice fuska yace " sauran ni habibty " Hararar wasa tayi mishi ae kuwa ba kunyar ganin yaran shi yaje ya rungume ta ta baya shi ma nan fah su safah da marwah suka fara yi mishi dariya yayin da na'eem da ameer suka tsokanar papa di'n su ganin yanda ya nannad'e a jikin nauwara kamar shi ne yaron. Xaman lafia suke mai dad'in gaske a tsakanin su da yaran su suna basu lokacin sosai rayuwa kullum cigaba suke samu daman duk *K'ARSHEN WAHALA* dad'i yana nan xuwa. Bayan sun kammala yin dinner d'in dare wajen 9, safah da marwah suka yi tafi d'akin su don lokacin baccin su yayi, haka na'eem da ameer ma suka nufi nasu d'akin aka bar nauwara da abduljabbar a parlour shi ma bai 6ata lokaci ba ya d'auki habibty di'n cak a hannu suka shige bedroom d'in su suna shiga toilet ya tsomata a bath di'n wanka wanda yake cike da ruwan d'umi bayan sun yi wanka cikin farinciki da so da k'aunar junan su, bayan sun fito sun shirya cikin sleeping dress kan bed suka fad'a suna rungume da junan su a kunne nauwara ta rada mishi "i really luv u yayanah!" Yana kok'arin kissing d'in ta yace "i luv yhu too my habibty Allah ya bar mu tare " "Ameeen " tana gama amsa wa ya rufe bakin shi da nata tare da jan blanket suka fara kok'arin faranta ran junan su, ganin haka yasa na tarkato na bar musu d'akin don na kyale su haka ni ma na huta da typing...... _Asubah ta gari_ *ALLAHAMDULLAH* _dukkan Godiya sun tabbata ga Allah da ya bani rai da lafiyar rubuta musu wannan labarin na *K'arshen wahala* na fara shi lafia gashi a yau na kammala shi lafia_ *ke ta daban ce wlh a wurina my cwt sadeey saNaz i really luv u bani da bakin godia a gare ki sai dai ina miki fatan alkhairi a rayuwar ki ya albarkaci rayuwar ki ya cika miki burikan ki na alkhairi ya xa6a miki miji nagari wanda xai kular mana ke mu xo jigawa musha biki*_💃🏻❤😍 #complied by Princess Aysha Muhammad (Humaira) *KUNA RAI NA SISTERS NAH* Hafsat A aliyu Mmn abiddeen My Sumayya salees sadeeq (sumynbash) My khadijah neena cool Nafeesat Anka Asy khaleel Ummiey xeey Ummi hambali Mrs muktar Mrs Umar Miss maryam Aishat aliyu garkuwa Haleemah Ameen Biebie deee Ummu safwan Sa'adah Khalfana S A muh'd _da sauran wad'anda ban ambata ba ku sani kuna rai na i really luv u guys_❤😍 *masoyan asali* Miss zahra mansur Ummu abdul deejah Neena cool Hadixa gidan d'orawa Amina (mameen ammar da bilal) _da sauran da ban ambata ba Aishat tana gaida ku_😍 Jinjinar ban girma gare ku K'arshen wahala fans Aunty & sadeey novels grp dandalin hausa novels Online hausa writers Hikima writers HWA Ummu safwan novels Mrs Umar novels Hausa novels group My style grp Ladies zone Musan kanmu marubuta Ruky & ashba saNaz novella Novellas lodge Biebie & samrah Nagode da k'aunar littafin nan da kuka yi ina yi muku fatan alkhairi en uwa ❤😍 _ku tare ni a littafi na na gaba *YAYI SAKE* amman sai bayan sallah saboda gabatowar wata mai albarka wato ramadan mu dage da ibada Allah ya nuna mana lokacin lafia Ameeen_ Aishat A muh'd ce Complied by Princess Aysha Muhammad