ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA ƊAYA* *SHIMFIƊA* Farar mota ce mai matsaikacin kuɗi ƙirar lexus ke tafiya cikin natsuwa babu gudu bare rough driving, daga gani matuƙin ba yaro bane ko kuma ya iya kasancewa yaron amma mai tarin sani akan harkar tuki da kuma dokokinta, idan ka tsananta nazari kuwa zaka fahimci ana bin motar a hankali ne saboda wanda ake tuƙawan ba abin wasa ba ne ko na ganganci. Daga cikin motan mutum huɗu ne, ɓangaren mai zaman banza akwai wani matashin saurayi da ya fi yanayi da ɗalibin neman ilimi, sanye da jumpa mai sauƙin kuɗi har da hula rungume da wasu tarukuce na briefcase, Laptop da sauran gadget. A baya ɓangaren hagu nan ma wani matashin ne amma da alama zai iya girmewa wanda ke zaune daga gaban a shekaru, fari ne sanye da baƙar Thobe (jallabiya), ya ɗora hular taɓani-ka-ji-hadisi fara a kanshi mai matsaikacin gashi, fuskarshi cike da saje haka kuma hankalinshi gabaɗaya na ga gefenshi da magana mai sanyin amo ke tashi cike da wani irin natsuwa da waenda ke cikin motan ba don sun natsu kuma sun kasa kunne ba babu abin da zai sa su ji me yake cewa. Mai maganan dake zaune daga ɓangaren dama ya ɗan muskuta, tare da ambaton Allah ya yi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya cigaba da magana a hankali. Duk inda kake neman natsuwa da kamala a kallo ɗaya da zaka yi wa wannan bawan Allah ka same su ka gama, daga yadda yake zaune za ka fahimci dogo ne, yana da matsakaicin jiki amma da alama ƙarfaffe ne, yana da haske fari ne fat, fuskarsa da cikakken gemu wanda da alama ba'a taɓa shi iyakaci gyara, idanunshi sakaye da wasu fararen madubi amma hakan bai hana bayyana natsuwa da zurfinsu ba. Sanye yake da Grey Thobe ya ɗora baƙar shara sharan alkyabba irin ta Larabawa wanda ake kira (jubba) a kai, kanshi akwai Ghutra(wannan gyalen da aka san Larabawa da ɗora wa a kai mai kalar ja da fari da ya zauna mishi sossai a saman ta kuma akwai Agal (wannan baƙin abu mai yanayi da gammo wanda ke hana Ghutra faɗuwa idan ana iska) agogo mai sauƙi amma tsadar a bayyane take ɗaure a tsintsiyar hannunshi, hannunshi ɗaya jikin motar ɗayan na daga kan kafafunshi yana cigaba da yi wa na gefen magana. "Ammar ina fatan ka fahimta?" "Eh Shehi, In shaa Allahu za'a yi komai yadda ka ce" Kai ya gyaɗa kan ya mayar da idanunsa kan titi ya cigaba da azkar cikin natsuwa don shi ma'abocin yawan zikiri da salatin annabi ne hakan ne kan katangeshi da duk wasu surutai marasa dalili. Wani kalar wawan birki matuƙin motar ya ci. Ammar da yake danna waya ya ɗago da ɗan hanzari. "Ya dai Malam Bala?" "Malam Ammar ina ga fa 'yan fashi ne a gabanmun nan, gashi sun rufe hanyar" Malam Bala ya faɗa sai dai ko ɗarr dukkansu babu wanda ya ji don ba yau suka saba encountaring irin waennan ɗin ba tunda aikinsu ne na kai wa dare wurin wa'azi da karatuttukan Shehi na dare. Ko kan wani daga cikinsu yayi yunƙuri an fara bubbuga musu glass kuma tuni Matasa har huɗu sun zagaye motar da Malam Bala ya dannawa General lock. "Ka ga irinta ko Irshad? Sai da na faɗa maka securities are very important to you amma ka ƙi aminta, yanzu idan wani abu ya sameka fa?" Ammar ya faɗa duk tashin hankalinshi na bayyana Dukda adduna ne da sanduna yake hange hannayensu, alamunsu duk sun bayyana tsananin maye da ficewar hayyaci. Sai a lokacin Shehi da Ammar ke yi wa magana ya buɗe idanu ya kalli situation ɗin cikin natsuwa. Ya kalli Ammar "Rayuwa da mutuwa duk na Allah ne Ammar" Jarumtakarshi da tsantsar tawali'unshi na sake bayyana tsantsa a kalaman bakinsa. "Duk da hakan wani sa'in ba mutuwar ce abin tsoro ba wahala ake ji wa" Ko kan Ammar ya gama rufe baki an bugi glass na gefen Malam balan sai da ya daddatase, innalillahi wainna ilaihi rajiun duk suke maimaitawa, kan su ajiye ma an sake kaiwa glass ɗin duka da sandar gora tuni ta tarwatse. "Kai Tsoho me ya biyo da kai hanyarmu a lokacin farauta?" Wata kakkauran murya marar daaɗin ji ta faɗa tana haske su da tourch light, maganan su ya sa hankalin Ammar ya ɗan kwanta da alama zaune gari banza ne, 'yan daba masu kwacen waya da sauransu, wayanshi yake kokarin kunnawa ya kira 'yan sanda cikin dabara aka bugi glass ɗin ɓangaren shi ma ya rushe har yana ji mishi ciwo. "Hasbunallahu wani'imal wakeeel.." Kalmar da ta fito a bakin Shehi kenan don idan akwai abin da ke zama weakness ɗinshi to cutar da makusancinshi ko masoyinshi, yana ƙoƙarin buɗe kofar ya fita don basu duk abin da suke nema ya ji wata murya ta shiga ratsa kunnuwanshi. Mace? Ya raya a ransa yana juya fuskarshi inda sautin Muryar ke fita bayan ya kai idanunsa kadan ya ga time wurin karfe ɗaya da wani abu na dare. "Kaiiiii....wasu ƙananun ƙwarin ne nan?" Yadda Muryar ta fita babu abin da zai hanaka fahimtar mammallakiyar Muryar a Buge take, kuma cikin wani irin salo na dabanci sai dai zaƙin Muryar bai ɓuya ba sam. Waenda suke jikin motan ne suka juya gareta suna hasketa idanunsa suka samu nasarar sauƙa a kanta. Ya subhallah! Ya ambata a ransa, wani cargo baggy trouser, sai sweeter hoodie mai hula jikinta baƙake, kanta sanye da facing cap da ya rufe rabin fuskarta sai ta ɗora hulan rigan a kan facing cap ɗin, hannunta wani coke ne da ba tantama a surke yake da wani abin. Abin da ya ɗaga mishi hankali tabarbarewar tarbiyar wannan zamani, mace ta tsinci kanta cikin wannan kazanta ba ƙaramin abu bane ga malamin addini irinshi. "Ke!" Ɗaya daga cikin waenda suka tare su ya faɗa yana sa hannu a baki alamun mamaki kan ya cigaba. "Babawo... ka ga wata gara chan wai da mu take?" Tsaki ta ja tsiriri ta matso sossai kan ta sa hannunta ta ja hoodie ɗin kanta idanunta dake a lumshe cikin maye amma tsaff kanta ya gama ɗauke wa don tana cikin hankalinta suka bayyana ta kallesu. Zare ido ɗayan yayi "Kaiiiii.... Gayuuuu wallahi DIVA ce..." Bata ce komai ba wasu gayu huɗu da mata uku a bayanta duk cikin shigar da zai tabbatar maka thugs ne, kowa kuma ka bincike shi ba ka rasa mugun makami a tare da shi suka bayyana. "Ku bar nan...!" Ɗaya daga cikin mazan ya faɗa cikin kakkausan murya. "Tuba muke uwar ɗaki, ai ja da ke sai ɗan wahala ko mai kararren kwana! Allah ya taimaki shugaba..." Hannu ta ɗaga kaɗan ta nuna musu hanya fuskarta babu digon fara'a ai tuni suka yi gaba don babu ɗan daban da bai san sunan DIVA ba da click ɗinta waenda suke tamkar yayyunta amma kaman bodyguard suke a gareta umurninta suke bi a komai, kuma su ne ƙawayenta abokan hiranta, yana wuya ka ga Diva na magana idan ba da su bakwan nan ba to Babanta... shiga komarta dai dai yake da yanke kauna da rayuwa, ko bata ɗauki mataki ba Jagaban Uban daban gabaɗaya garin Kano shi ne Babanta dole ya farauceka ko ina ne ya yanke maka mummunan hukunci, bare ita kaɗai ta ishi gayya, wargaza taro ce da idan tayi juyi sai an bata wuri Dukda matsayinta na mace wasu kan ƙirata kwaruwa don fitinanta ya fi ƙarfin giwa. Idanu ta zubawa Malam Bala. "kai dattijo! ka kiyaye fita a irin wannan lokaci na dare da duk karnuka suke waje, idan yau ka taki sa'ata gobe zan iya wucewa tamkar ban ga me ke faruwa ba...gayun nan kuma...ehh ya nee...ina fata kana fahimta?" Tana maganan ne cikin wani salo idanunta suna lumshe wa da buɗewa da kansu. Tsantsar mamaki ya kama su, amma Malam Bala ya daure ya ce "Ɗiyata mun gode, amma don Allah da za ki yiwa kanki faɗa wannan rayuwar bata kama...." Muƙuttt haka maganan ya koma tamkar an tura shi jin sauƙar wata kyakyawar WUƘA mai sheki saman maƙogoronshi. Muryarta ya ƙara kaushi, tana mishi wani jan kallo da har Ammar da Imam sun razana ta ce "Ko da kuskure ka sake buɗe baki da niyyar min wa'azi sai na tsinke maƙogoronka na rantse da Assamadu!! Naaa daɓa ma wannan wukar na ga gatanka" Bai yi magana ba hannunshi dake kan stiring ne ke wani irin rawa, tayi tsaki tare da janye wukar ta nuna hanya "Ware..." Idanunsu ne suka sarƙe saboda shi mamaki da tsoron Allah duk ya rufeshi, wani ɓangaren tausayi ne, idan yana jin labarin akwai 'yan ta'adda bai san abin ya kai har mace ma ta zama shugaban 'yan dabar ba don daga reaction na waenda suka soma tare su zaka san sunanta ya jijjigasu. Kallon seconds biyu yayi mata saboda wani irin mamaki na iya dorawa mutum kaman Malam Bala dattijo wuka a makogoro ya rufe shi. Ita kuwa ba zata ce ta ga na bayan motan ba, bayan wucewansu ta cigaba da tafiyanta da gayunta yadda ta saba na maza kuma 'yan daba kaman yadda take'yar daba itama, cikin unguwar su ne don basu yi tafiya mai nisa ba suka isa wani gida matsakaici, gini ne na block amma babu plaster haka babu penti sai dai akwai gate mai girma da ƙarfi kalar Ja, karamin kyauren ta tura babu wuta solar ne kunne hakan ya haska mata tsakar gidan da kaman rana ne maza ne kala kala a ciki ana shaye shaye da cha-cha. "Barka DIVA! Barka KWARUWA!" Kalaman da ke ta tashi kenan bakunansu cikin yanayin tsantsar dabanci. Hannu ta ɗaga tayi crossing suka amsa "Chauchauuu... Eeeyyy mana" Tayi murmushi ta juya ga gayunta "Sai Allah ya kai mu" "Mu kwana lafiya Diva" Suka haɗa baki wurin faɗa don sun san ba sake fitowa zata yi ba kenan, ta nufi karamin barandar ta haye ta tura kofar parlorn ta kutsa kai babu ruwanta da sallama. "Baaba" "Ƴar Baba!" Wani rikakken murya ya amsata ta riga ta ga abinda yake ɓoye wa don haka dariya kawai tayi. "Babana na kaina... A cigaba da sana'a" Tana kai nan ta wuce su don zaune yake da wasu mutane biyu diloli ne da suke zuwa karbar kwaya wurinshi, ɗakinta ta tura ta shige bata damu da rufewa ba don ko kuda ne Jagaban ba ya bari ya sauka kanta bare ita kanta hatsari ce. Ba rayuwar da ya so zaɓa mata ba kenan amma bahaushe ya ce barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. Gado ta faɗa ko boots na kafafunta bata cire ba ta shiga bacci irin na maye. **** Allah ne ya kawo su gida lafiya don Malam Bala ko uffan bai sake cewa ba yana ji Imam da Ammar suna tattauna batun wacce aka kira da Divaa amma ya kasa furta ko A shi da ya gama ganin mutuwa ganin idanunshi. Irshad Al-Noor kuma dama sun san ba tankawa zai yi ba shiyasa Ammar ya kama Imam suke ta maganan, Horn nasu shi ya tado mai gadi ya zo ya buɗe tamfatsatsen kyauren gidan na Alhj Omar Al-farouq mai kamfanin Twins Enterprises, gida ne mai Girman gaske, gida ne da kallo daya zaka mishi ka fahimci daɗɗaɗden kuɗi ne ciki ba sababbin arziki ba, an zuba kayan alatu iya ganin ido. Yana da gine gine manya manya kuma hakan bai tare faɗi da girman gidan ba, gaban wani building suka yi parking Imam ya fito da sauri ya buɗewa Shehi kofa, sai da ya ɗan ɓata lokaci kadan yana kamalla Adu'a kan ya zura kafafunshi dake cikin simple shoe na maza na kamfanin Gucci da ya bayyana kyaun kafafunshi da kaman baya taka ƙasa ya sauƙa, sai da ya tsaya da kyau ya gyara jubba ɗin jikinshi kan ya taka cikin natsuwa ya isa wurin Malam Bala da ya fito yake shan Iska Ammar kuma na kallon barnar da suka yi musu. "Malam Bala kana lafiya dai?" Muryarshi mai cike da natsuwa ya fita cikin kulawa. "Ba dai ƙalau ba Shehi yau na ga abin da ya fi ƙarfin kakata" Cikin jimami da tsoro yayi magana don Allah ya gani ya ji tsoro, cikinshi wani irin ƙugi yake ba zai manta da mutuwar da ya ga gilmawarta kan idansa ba, 'yan daban nan zare musu imani ake don ta kashe sa da wannan kaifaffen wuƙar ba komai ba ne. "Tsoro halal ne! Amma karka manta da ambaton Allah a yayin da wannan tsoro na abokin hilitta ya ɗarsu a ranka" Ya faɗa yana kokarin wucewa don shiga ɓangaren shi. "In shaa Allahu Allah gafarta malam, Mu kwana lafiya" Ammar ma ya iso yana ce mishi "Sai Allah ya kaimu Shehi" Kai kawai ya gyaɗa, Imam ya bi shi da abubuwanshi. Malam Bala fita yayi ya nufi gidanshi dake nan cikin Layin, Ammar kuwa ciki ya wuce don anan sashenshi yake kasancewar shi Cousin kuma amini na kut da kut da Irshad Al-Noor. Imam kuwa bayan ya zube mishi abubuwan daga parlor ya juyo ya fito, shima waje yayi yana yin sallama da mai gadin don gidansu na dalibai na nan gefen gidan wanda akwai su dayawa daliban ilimin Shehi da kan zo daga garuruwa daban daban saboda ɗaukan karatu, nauyin su da komai a wuyan Shehi yake zama bai taɓa bari sun shiga yanayi ba, kuma suna kwasan ilimi daidai gwargwado ya kan ce musu yana hidimta musu ne saboda kanshi ba don su ba saboda duk wani ilimi da suka koya daga gareshi muddin sun isar to ladan shi a wurin ubangiji ya fi abin da ya basu suka ci a cikinsu har bayan ranshi. Bai zauna a parlorn ba ya wuce sama, wani parlorn da ya fi yanayi da study room saboda tarin littatafan addini da kuma qur'anai Dukda yana da study room amma ya fi gane parlorn saman tunda shi kaɗai yake rayuwa sai hidimtawa addini da ubangijinsa. Kai tsaye ɗaki ya wuce da sallama kan lips ɗinshi, a hankali yake zame komai na jikinshi sai da ya saura doguwar farar cotton wando da farar singlet kan ya nufi toilet. Ya jima ciki kan ya fito a kimtse cikin fararen kayan bacci masu fadi kan dresser ya je ya fesa turarukanshi na Oud masu sanyi da nauyi wurin shaka. Parlorn ƙasa ya koma ya ɗauko laptop ɗinshi ya dawo saman a kan gado ya zauna tare da saka glasses ɗinshi ya buɗe ya fara nazarin wani littafin addini, komai nashi cikin natsuwa da kamala yake yinsu, ya san idan da zai duba parlor akwai abinci da Maamah zata aiko amma babu abin da zai iya ci a yanzu don haka dabino da ruwa ya sha bayan tsawon lokaci yana duba littafin da harshen larabci kan ya rufe. Suratul Mulk da Rahman ya karanto da kai cikin wani irin Muryar qira'arsa mai sanya natsuwa da tada tsikar jiki kan yayi sauran adu'o'in bacci ya kwanta ta hannunshi na dama, dama ba wutan ɗakin ya kunna ba dim light ce ya barta kunne kasancewar ba daidai ba ne kwana cikin duhu mai tsanani da ba'a iya kallon tafin hannu. Babu bata lokaci yayi bacci don kwakwalarsa babu space na wani tunani a lokacin tsantsar gajiya ce da jiki kan yi bayan doguwar hidima na yau da kullum barin ma irin nashi. ******** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA BIYU* Ƙarfe uku da rabi ya buɗe idanunsa, a hankali lips ɗinsa ke furta "Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihin nushur" Cikin natsuwa ya miƙe zaune ya ɗan jima a zaunen kaman yadda sunna ya nusar akan samun cikakken natsuwa bayan farkawa daga bacci kan miƙewa. Ya zura kafafunsa ƙasa ya sauƙa ya nufi toilet, wanka yayi tare da alwala, ko da ya fito sai da ya shirya tsaf cikin farar thob da baƙar jubba mai gold a aikin hannu da kuma gaban daga wuya zuwa ƙasa, ya saka oil perfumes nashi na Oud da har sun kama jikinshi ba kayanshi kaɗai ba, duk kuma inda zai zauna ya tashi sai ya bar kamshin na lokaci mai tsawo, don shi ɗin ma'abocin son kamshi ne kwarai da gaske musamman turaruka irin na Larabawa, ya ɗora farar Ghutra a kanshi ba tare da ya nemi Agal ba don ba buƙata, a natse yake ajiye kafafunsa cikin tattausan rug ɗin ɗakin har zuwa wurin sallarshi, burner ya kunna sai da yayi zafi sossai ya kashe sai ya ɗora turaren wutanshi a kai, a kan sallaya ya daidaita natsuwarshi kan ya fara ganawa da ubangiji cikin kankantar da kai da sallamawa. Sai da ya jima yana nafilfili kan ya zauna ya ɗan yi wasu zikirori anan ya ji an fara ƙiran Sallar farko bai motsa ba, ya karanta shafuka biyu daga cikin qur'ani kan ya miƙe yana gyara Ghutra ɗin shi har wurin fuska ya nufi ƙasa, wata farar mage da bata yi yanayi da na ƙasar Nigeria ba ta taho da gudu ya duƙa ya ɗaga ta zuwa jikinshi fuskarshi na sakewa a hankali daga a kame zuwa murmushi mai sanyi har fararen hakwaranshi na bayyana yana shafata a hankali ya furta. "Sabahulkhairrr yaa humayrah!" Tayi miyauuu ya saki murmushi, ya duƙa ya ajiyeta ya nufi wani locker ya fitarda canfood ta bi shi da gudu zuwa gefen dining inda anan yake saka mata abinci ya juye mata a kwanon ta shiga ci shi kuma ya fice, sai da yayi rakatanil fajir kan ya isa matsayar limami babban masallacin nashi mai suna Al-Noor Mosque ya shiga gabatar da Sallar asuba duka unguwar ya ɗauki tattausan muryarsa mai tsuma zuciya da sanya salama ya kuma tada tsikar jikin duk mai saurare. Bayan sun idar bai motsa ba yana nan zaune yana adu'o'i da azkar har bayan mintuna talatin kan ya juyo gabaɗaya, duk wasu mamun da suka bi Sallar tashi sun fice ya saura dalibanshi ne na kusa su wurin Ashirin da biyar, matso wa suka yi suka yi musabaha kaman yadda yayi musu nuni da hakan suna kuma gaishe shi da Fatan ya tashi lafiya. Bayan gama gaisuwa suka shiga ba da karatu yana nan zaune yana saurare idan ka yi kuskure zai gyara har su ka gama kowa iya abin da ya iya ɗauka ya bayar, idan sun bayar kuma za su shigar a gabanshi su karanta na gobe da Kur'ani a buɗe idan da kuskure ya gyara kan su tafi don koyan haddar. Har sai da suka gama tass kan ya samu ya karanta shafuka uku again, rana na fitowa ya miƙe yayi nafila yadda sunnah ta tanadar kan ya fice daga masallacin ya nufi gate ɗin gidansu dake daga jikin masallacin hannayensa goye a baya bakinsa na ambaton Allah a hankali. "Barka da safiya Baba lawan" Ya faɗa a natse, mai gadin da bai ma ji tahowarshi ba yayi saurin Miƙewa cikin ladabi Dukda Shehi yaro ne da zai iya haifa martabarshi na addini da tarin baiwa da ubangiji ya mishi ya sa har manya kan bashi girma wannan na daga cikin kamalar kowani malamin addini. "Barka da safiya Shehi, mun tashi lafiya?" Cikin girmamawa ya mayar mishi da gaisuwan. "Alhamdulillah Baba, ba wani matsala?" Girgiza kai yayi kan dai ya ce "Babu matsalar komai sai dai na kula iyayenka sun jima jikin motarka da Shi Malam Ammar da Malam Bala don tun bayan fitowansu Sallar asuba suka ga aika aikar da 'yan daba suka yi muku" Girgiza kai yayi, ya san aikin Ammar ne, shi a wurinshi wannan duk ba abin mayar da magana bane ko don shi yana da tsatsauran tsari da ra'ayin shanye koma menene a cikinshi ne oho, yana shirin nufar sashenshi ya ji wayanshi na ƙira sautin larabci marar kida na shiga kunnenshi, zaro ta yayi ya ɗaga tare da makalawa a kunne hannunshi ɗaya na goye bayanshi kanshi na kallon ƙasa "Assalamu Alaikum warahmatullah Abiey" "Wa'alaikassalam warahmatullah ka fito masallacin kenan, same mu sashen Daddah" Ya amsa cikin girmamawa. Yana sauƙe wayan ya nufi ɓangaren kakarsu mace dake cikin gidan, duk suna zaune ana ta tattauna magana jin sallamarshi ya natsar da dayawa har wasu na muskutawa kwarjininshi bai bar har manya ba, Uncles ɗinshi biyu ne a parlorn Twin brother na mahaifinshi wanda shine baban Ammar sai cousin ɗinsu da ya girma ne ma wurin Daddah ɗin tare da su Ishaq sai sisters ɗin Abbiey ɗinshi mata guda biyu da wasu 'yan mata uku waenda yaran aunties ɗinshi ne da duk su biyu suka rasa mazajensu kuma tun sannan a gidan suke wurin Daddah ɗin, su ne zaune parlorn. Yaran matan ganin shi ya sa duk suka tashi suka fita suka bar iyaye, Daddah na zaune daga ƙasa. "Shehi!" Abba ya kira shi. Ya ɗan ɗago sai ya nuna mishi gefenshi ya taka yaje ya zauna kan ya shiga gaishe su suna amsawa. "Ashe kuma Abinda ya faru kenan? Yara ne duk sun lalace in ba lalacewa ba abin wani ne zai tsone maka ido har ka nemi kwacewa? Kai duniya! Allah ya takaita ya tsare mana kai Shehi" Daddah ta faɗa cikin jimami sanye da hijabinta dattijuwa ce da kallo ɗaya zaka mata ka ga cikakkiyar bafulatana, don hausarta ma ba wata nuna tayi ba. Murmushi Irshad Al-Noor yayi kaɗan cikin natsuwarshi ya ce "Daddah Adu'a suke buƙata, Allah ya shirya mana su" Abbiey ya ce "Amma ya kamata ku yi reporting irin wannan lamarin ba abin kawar da kai ba ne, ko ɓarnar da suka yi wa motar ka ya kamata a ce an binciko su an yi musu hukunci daidai da laifukansu idan yau kun tsira gobe Allah kaɗai ya san wanda za su cutar ko su illatar tunda idan suna cikin mayen nan ba sanin me suke aikatawa suke ba" Har lokacin da ɗan murmushi kan fuskarsa idanunsa na a ƙasa ya ce "A'a Abba babu buƙatar hakan tunda Allah bai ba su nasarar yi mana wani ɓarna ba" Uncle Ishaq ya ce "Har da laifinka Irshad, kana da daman daukar masu tsaron lafiyarka amma hakan ya gagara gashi yanzu maganan ya gama bazuwa a media makiya sai su yi amfani da irin wannan daman don ganin bayanka" Ya ɗaga idanunsa masu cike da wani haske da kwarjini ya kalli Uncle Ishaq a yanzu ba murmushi yake ba. ya ce sharply "Babu mai yi mini abin da Allah bai rubuta ba, bana buƙata Uncle" Ya ƙarasa yana dauke kai don zuwa yanzu ma ya fara gajiya da maganar. "Toh Allah ya tsare mana kai ya cigaba da kiyayewa, Amma dai kaima ka sake kiyayewa idan akwai yadda zaka rage commitment ɗinka na dare sai ka yi samun ka dinga shigowa gida kan lokaci" Abba ne yayi wannan bayanin Kai ya gyaɗa bai amsa da baki ba. Suka cigaba da tattaunawa baya cewa uffan sai da ya gaji ne ya miƙe yayiwa Abba da suka fi kusa sallama ya fice. Sashen Maamah ya nufa yana tafiya ne ba tare da waige waige ko kallon baya ba kanshi ƙasa har ya isa ya shiga parlorn da sallama, kan carpet ya hangi Ammar na karyawa ya girgiza kai ya nufi wurinshi ya zauna daga kan carpet ɗin yana tankwashe ƙafafu. "Sai yanzu Ya Sheikh?" Shirun seconds biyu har Ammar ya zaci ba zai ce mishi komai ba kan ya ji yana cewa "Meyasa kake da baki ne?" Ammar ya kalleshi ya kai loma "Saboda in ci abinci" Murmushi kaɗan Irshad yayi. Bai sake magana ba sai ma motsa lips da yake kaɗan kaɗan Ammar ɗin ke faɗa mishi yayi mamaki da daga Safiyar Allahn nan media ta ɗauki dumi har wasu na cewa an ji wa Sheikh Irshad Omar Al-Noor rauni, wasu na cewa yana cikin mawuyacin hali har wasu na ikararin an kashe shi, ba yau ne farau ba duk wani motsinshi kaman jira media take za ta ɗauka, ba da sonshi hakan ke kasancewa ba amma bashi da yadda ya iya. "Ka san me? Wlh har yanzu ina mamakin wannan yarinya da aka kira da DIVA wani irin nisa tayi haka? Ta wani ɓangaren kuma rashin tsoronta ya burgeni" Idanu Irshad ya zubawa Ammar ɗin shi kuma daga ganin hakan ya san bai fahimci ma a kan waye yake magana ba. "Ina magana kan wannan yarinyar da ta kori waenda suka tare mana hanya, ƙaddararta yayi gi..." "Yar daba!" Ammar yayi shiru yana kallon Shehi don da ya kira hakan bai kalleshi ba, seconds kadan tsakani ya ce "Sai na fi gane wa, har me abin burgewa a wanchan kazantantaccen rayuwar? Wuƙa fah ta ɗorawa Malam Bala da niyyar illatasa, Allah kaɗai ya san alhakin da ta tarar wa kanta na bayin Allah, wannan ba kaddara ba ce kar ka ɗora mata ba komai ne yake kaddara ba, a shekarunta da wayonta a yanzu na tabbatar ta san daidai da akasin hakan" Ammar ya ce "Amma Irshad ka fa fi ni sanin babu kyau judging abu daga gani ɗaya, ba mu san background ɗinta ko environment da ta taso ba, definately akwai abinda ya jefa ta cikin wannan halin ruwa bai taɓa tsami banza ba amma dai hali ne kam mai matuƙar muni da hatsari" Shehi bai ce komai ba, da Ammar ya gaji da magana shima yayi shiru ya san ba wai Shehin ya yarda ba ne, yana da wannan idan ya kafe kan ra'ayin shi bai cika uziri ba. Maamah ce ta shigo parlorn a lokacin fuskar Shehi ta sake sossai itama da murmushi ta ƙaraso ta zauna kan kujerar da Shehin ke zaune gabanshi ta ce "Barka da shigowa Babban malami" Kanshi ƙasa ya ce "Maamah mun tashi lafiya?" "Alhamdulillah mun gode Allah" Kan ya sake magana ta kalli Ammar. "Kai kam ban san wani irin dan uwa ba ne kuma aboki, yanzu ka bar min yaro da yunwa kana ta cin abinci yana kallonka?" Ammar ya ce "Toh Maamah ai bai ce zai ci ba kin san shi ba'a mishi gwaninta" "Au dama ban faɗa maka abincin tun asali don shi na yi bane ka zo zaka cinye masa?" Shi dai Irshad murmushi yake don ya saba ganin wannan rigimar ta Ammar da Maamah, Maamah ita ce mahaifiyar Ammar amma kuma shi a wurinta ya tashi don ita da mahaifiyarshi da suke kira Ammiey twins ne kaman yadda Abba da Abbiey suke twins, Ammiey da Abiey suna da wani irin kawaici a kanshi hakan ya sa ragamar rayuwarshi duk a wurin Maamah ne, haka sauran sisters ɗinsu they are mixed up wasu yaran Maamah gabaɗaya a wurin Ammiey suke har mutane daga waje basa gane ma su waye ne yaran wane su waye yaran wance, wasu sun ce kamannin zuri'ar na asalin Fulani baya ɓuya. Musamman Shehi da yayi rayuwa cikin Larabawa har ma ya saje da su don ko hausa yake za ka zaci larabci ne saboda yadda harshenshi ya karye zaman sama da shekaru Ashirin cikin Larabawa ba wasa ba Maamah taje ta shiryo mishi abincin ta kawo da kanta, yayi mata godiya ya miƙa hannu ya wanke cikin bowl na wanke hannun da ta hada mishi da shi don da wuya ka ga yana cin abinci da cokali ya shiga ci da bismillah. Bayan ya gama daga nan sashen Ammiey yayi anan ya gaisheta, ta amsa cikin kamalarta tana kallonshi, a koyaushe ta ɗaga idanu ta ga kyautar da Allah yayi mata sai ta ji natsuwa da sanyi na ratsa zuciyarta, ta kan tsinci kanta cikin yi wa Allah godiya da kuma yi mishi adu'ar samun mace ta gari ta ƙwarai mai halayya da dabi'u irin nashi su cigaba da haifar tsatson ƙwarai, jaje ta mishi akan abin da ya faru ya nuna mata adu'arta kaɗai zata cigaba da yi Allah ya katangeshi da duk wata fitina, sisters ɗinsu sun ta shigowa suna mishi gaisuwa da jaje amma a gajarce ya ke amsawa. Daga nan sashenshi ya koma, ya zame jubba ɗin ya bar thob kawai da Ghutra ya nufi study table ɗinshi ya cigaba da research akan littafin da ya fara nazari don Asabar ne yana da sauƙin commitment. **** Daga gidan Jagaban bata zauna ba ta yi wa sauran click ɗin sallama ta fice, cikin rashin tsoro da sabo da dare ta cigaba da tafiya sai da ta wuce akallah gidaje biyar ta tsaya jikin kofar wani gida da bashi da kyaure, zaure ne kawai a buɗe ciki ta shiga ta cigaba da tafiya hannayenta a aljihu tana isa tsakar gidan aka hasketa da toci hannu ta sa ta kare idanunta kan ta lailayo zagi ta buga. "Wani ɗan abu kazan ne wannan?" "Ubanki ne! Na ce Ubanki ne marar kunya fitsararra, wallahi na gaji na gaji da ganinki cikin gidana kina abin da kika ga dama, rumfar kasuwa ce gidan da za ki fita sadda kika ga dama ki dawo sadda kika ga dama? Ko da shi ke ba laifinki ba ne, laifin Zaliya ce uwaki ba? laifinta ne da ta kasa baki tarbiyar da ta dace" Ta zuba mishi idanu na seconds. "Malam Iro na fa sha gargadinka akan idan kana abin ka ka daina saka mahaifiyata a ciki yawwa, yawo kuwa yanzu na fara shi rashin tarbiya ai kura ba zata ce da kare maye ba..." "Ke Zubaidah!" Wata murya daga cikin ɗaki ta fito tana daka mata tsawa. "Ashe baki da kunya? Ba mahaifinki ba ne?" Taɓe baki tayi tana layi kaɗan kadan "Mahaifina? Allah ya kyauta mijin Asawa ai ba uba ba ne da kanshi ya faɗa ya fi a kirga" "Eh laifina ne a kullum ina ganin laifina tunda na auroki Zaliya kuma na ce na ji na gani zan riƙe miki yaranki, ni Iro ni ne mai laifi..." Ya tashi ya shige wani ɗaki yana cigaba da mita. "Kin kyauta" Ɗakin da ta fito ta juya ta koma. Wacce aka ƙira da Zubaida ta bi bayan mahaifiyartata ta dage labule ta shige, Maman za ta sake magana kenan ta ji an jefeta da kuɗi da sauri ta ɗauka. "Ashe da abin arziki kike shine kika tsaya kina ta fitsara tsakar gida. Sai ki samu wuri ki kwanta" Maman ta faɗa fuskarta fesss tana kirga kudaden babu ruwanta da tambayar inda ta samo. ****** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... Ƙarfe ɗaya ba ya amo by Gureenjoh Daaɗin zama by Seemahwrites Joda by Sadi-sakhna *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION THE TRIO OF TALES THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY. TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA UKU* Ƙarfe Tara da rabi ta farka kaman koyaushe yau ma dai Sallar asuba ya wuce ta dama ɗaiɗaikun ranaku ne take samun sallah kan lokaci amma sai dai tayi daga baya wani sa'in ma ya wuce da haka kenan. Wanka ta yi ta zo tayi Sallar, wani material da aka yi wa ɗinkin garari don a yanke yake ko ta ina ta saka da wando Jean, scarf ne ta ɗaura kanta don bata cika barin kanta ba ɗankwali ba muddin zata fita daga cikin ɗakinta. Parlor ta fito ta samu Baba a inda ya saba zama. "Barka da safiya" "Sarauniyata kin tashi?" Kai ta gyaɗa. Yayi murmushi. "Barka da tashi dama su Pabloo suna chan suna dakonki" Ta miƙe tsaye "Bara na karasa, hajjo ta dafomin indomie yadda na saba ci Baaba" "an gama ɗiyar Baba" Ta fice daga parlorn. Murmushi ta saki ganinsu duka zaune kan plastic chairs suna jiran fitowarta, Shaly da Obafiya ne suka fara ganin Fitowarta don hankalin Pabloo ya ɗauku ne wurin neman jijiyar da zai tsira wa kanshi allurar pentazocine. "Barka da fitowa Diva" Ta ƙarasa tsakiyar su suka bata kujera ta zauna tana karbar allurar don taya Pabloo duba jijiya, su ne 'yan uwan da ta buɗi ido ta gani, su ne ƙawayenta kuma su ɗin ne shaƙiƙanta. Pabloo ta kalla bayan ta gama mishi allurar Penta ɗin idanunsa lumshe ta koma ta jinginu da kujerar tunaninta na komawa wani lokaci chan baya. **** "Pabloo menene wannan?" Ta yi tambayar ne da zuciya ɗaya saboda kwata kwata a lokacin bata haura shekaru bakwai ba, Pabloo ɗin kuma zai iya kai wa sha uku zuwa sha huɗu kuma a lokacin ma da kanshi yake yi wa kanshi allurar. "Sunanshi Penta" "Shi ma Baba na sayar da shi?" Kai ya gyaɗa mata. "Meyasa kake jin daaɗin yi wa kanka allurar bayan na san da zafi? Kuma dama don kawai a bugu aka yin shi?" Yayi murmushi "Za ki fahimta ne daga baya sohana amma bana miki Fatan zama ɗaya daga cikinmu, ina so ki yi rayuwa mai kyau" Ta ɗan tura baki "Ka ba ni amsa Meyasa ka ke yiwa kanka wannan allurar?" "Na fara shi ne saboda Baba ya ce shi ne zai sauƙaƙa min damuwata, shi zai mantar da ni matsalolina kuma da gaskiyar shi tunda na fara bana tunani ko fargabar komai" "Menene damuwar?" Ta Yi saurin tambaya. "Sohana Mahaifiyata ta haifeni ne da wani irin baudadden talakan mutum, talauci irin mai tsananin nan da abin da za'a ci ma wahala yake bare a shayar da ni, suna zama ne a ci yau gobe a kwana da yunwa, a haka kuma ya ƙaro aure ko watanni uku ban rufa ba duk malnutrition ya gama bayyana a siffata, sun yi rigima sossai don ɗan kudin da ya samu ne a gado maimakon ya yi amfani da su wurin gina mu sai ya zaɓi ƙaro aure, ita kuma mahaifiyata ta zuciya sanin irin kangin talaucin da ta juri zama ciki, ganin ba zata iya ba ya sa ta ajiye mishi ni tayi tafiyarta, ba zan ce miki ga yadda na tashi har na shekara bakwai wurin Stepmother na ba, Baaba Salame ta fahimci irin talaucin Baba da rashin makamarshi ne bayan 'yan kudin gadon sun ƙare, ɗawainiyar gidan ya dawo kanta a dole tunda tana sana'a amma fah ko baban kwaryarshi a wulakance, talaucinshi ya ja mishi wani irin raini kuma bashi da bakin magana saboda idan ta bar gidan ma bai san ya zai yi ya ci da mu ba. Salame macece mai baƙar zuciya da mugunta ban samu wani katabus ba saboda irin abusing ɗina da ta dinga yi, physically, emotionally and mentally na azabtu irin azabar da bana yi wa ko makiyina fata, almajiri ya fi ni gata da kima a gidan uban da haifeni, wata rana ta saka ni wanki sai ta aikeni ban dawo da wuri ba na tsaya wasa a hanya har kudin suka ɓace, tsoron hukuncinta ya hanani komawa tunda ita ke ci da mu da ni da mahaifin nawa shima bashi da say a gidanshi, ko da na tattara courage na koma tayi min dukan da ban yi tunanin zan rayu ba saboda mutuwa ya ratsa idanuna a lokacin, ko da ta kyaleni washegari ta ba ni tallarta yadda ta saba na ƙwai dafaffe a kasuwa wani mai babur ya kaɗe ni. Hankalina ya tashi ba ciwon kafafu na nake duba ba sai asarar kwan Baaba Salame, ganin irin kukan da nake da halin da na shiga ya sa wasu dattijai suka raka ni gida don yi wa Baaba Salame bayani tunda mai babur ɗin ya gudu bai tsaya ba, bayan ta gama jinsu tayi godiya suka tafi suna fita ta fusgo ni ta shiga kirba tana tsine min kaman wacce Allah ya aiko daga ni har mahaifina da na tabbatar yana jinmu tunda ya gama kashe zuciyarsa ba neman yake ba bare ya sa tunanin samu, ta ja ni ta rufe a ɗaki kwanana biyu sai ruwa kawai take ba ni wai na ci kwan da na mata asara ba dai abincinta ba, a kwana biyun mutuwa ne kawai ban yi ba Sohana. Kwana na ukun ta buɗe ni na yi furu furu na firgice, ciwon kafafuna basu samu kula ba kudaje ke bi haka ta sake ɗora min tallah a akan idan ban sayar ba yau ma haka zan kwana da yunwa in na ga dama in mata asara. Nayi kuka na ji na tsani kowa da komai zuciyata ta kitsa min irin muguntar da zan mata, har tunanin buga mata tabarya na yi, nayi tunanin kwarara mata rufan zafi haka dai na gama sake sake na har na sayar na dawo ta ban abincin da bai taka kara ya karya ba, tana shiga ɗaki na zuba mata manja a tiles tana fitowa ta shiga wurin wanke-wanke ta zame ta yi mummunan fasa kanta da har aka yi tunanin ta samu brain injury tsoron hukuncin da za'a dauka a kaina ya sa na gudu. Allah ya haɗa ni da Jagaban ya ɗauke ni tamkar danshi, a wurinshi na samu dukkan kulawa, ya ja ni a jiki inda yake ba ni abinci har sau uku a rana kuma bai saka ni aikin komai kan ya ba ni, shine mutum na farko da ya fara yi min kirki hakan ya sa na ji kome zai faru zan mishi biyayya kuma zan zauna da shi har in gina kaina. Na shiga matsanancin damuwa da tsoro haka kawai sai in firgita shi ne Jagaban ya fara yi mini wannan allurar da nufin zai sa in manta duk wani damuwana da tsanar da na yiwa iyayena daga haka na saba da shi har ya zama ina iya yi wa kaina da kaina, allurar na rage raɗaɗin ciwo ne (narcotic) musamman ga masu ciwon sikila ko wani ciwon ƙashi mai tsanani... Tun jagaban na yi min a kyauta har ya sakani a sana'ar gyaran machine ina kawo mishi kuɗin shi a lissafe na yawan allurar da nake karɓa. ***** "Diva!" Shaly ta ƙira sunanta tana taɓa ta ta ɗan yi firgigit tana dawowa daga tunanin da ta tafi, ta sake kallon Pabloo zuciyarta na karta a hankali, a yanzu sana'ar machine yake mai kafa biyu amma duk inda kuɗin ya zo na Jagaban ne ko biyan gidan hayan da ya gina a gefensu da dakuna masu yawa yake accomodating thugs da suke under drug addicts ko kuma ya biya kudin pentazocine da ya zame mishi addiction ƙarfi da yaji. "Me kike tunani ne haka?" Ta girgiza kai "Ga shi Diva maganin damuwan kenan ko ma wace iri ce" Zee baby ta faɗa tana miƙa mata coke mai sanyi da ta juye codein ciki, karɓa tayi ta kalla kaɗan kan ta kai Bakinta ta shiga sha. "Zubash fah?" "Bata shigo ba bai wuce tana chan suna rigima da Mijin Asawanyarta ba" Kai ta gyaɗa Suna ta hiran su tsakaninsu bata tanka ba bata ce uffan ba har sai da ta bugu sossai aka kawo mata breakfast ta ci sossai saboda yanayin shaye shaye da ke saka jin yunwa, daga nan ɗaki ta koma ta zube kan gado sai bacci. Da misalin ƙarfe uku da 'yan kai wani irin hayaniya ya farkar da ita, tsaki ta ja tana mutsitsike idanunta da suke a lumshe farare da su, bata da aukin kirki sai hatsari, doguwa ce mai matsakaicin jiki, tana da albarkatun sama da ƙasa don shape ɗinta mai kyau ne, bata da ra'ayin maza shiyasa duk wanda ya tinkareta da sunan soyayya ma sai ta zubar masa da jini wannan alkawari ne hakan ya sa kowa ke gudunta, ita ba fara ba ce ba...irin wannan warm golden brown complexion ce, bakinta ya ɗan yi duhu daga ƙasa tsakiya kuma da haske saboda shaye shaye da take yi. Miƙa ta yi tana ɗan sosa idanunta, ɗakin har lokacin duhu ne dulum kaman ba rana tsaka ba, ta janyo wayanta ta kunna ta ga time kan ta dira daga kan gadon taje ta kunna hasken ɗakin da kaman na wata princess ya bayyana sai dai komai baki da fari ne don kalar da ta fi so baƙi ne... Toilet ɗinta ta nufa tana zubar da kayakin jikinta a hanya kan ta gama shiga ba komai jikinta tayi wanka Sharp Sharp ta fito da Alwala gefe chan ta nufa akwai sallaya da doguwar riga da ƙimar ta saka ta haɗa sallar azahar da la'asar hakan ya bi jikinta Dukda ba ya mata dadi yawanci in ta bugu sai ta gwamutsa salloli wasu ta rama wasu kuma sun shige daga haka kenan. Wardrobe ta nufa babu abinda ta ɗaga a kayakin da ta zubar ta saka wani wando dogo da trench coat a kai ya kai mata har gwiwa duk baƙake sai a lokacin ta zame ɗankwalin ɗazu tulin gashinta ya bayyana ta aske har ta gaji ta daina don kwana kaɗan zai dawo har ya fi wanda ta asken, tufkeshi tayi kan ta ɗauki vintage scarf fara ta ɗaura sau ɗaya ta baya ta saki jelar gefe da gefe, wukakenta da duk akwai sunanta jikin kowanne ta ɗauko, daya bakinshi ma ziz-zag ne irin wannan tana so idan ta soki mutum da shi ta zaro da tsokokinshi ya fi bata kwanciyar hankali sai ɗayan plain ne ta saka su jikinta. Har lokacin gidan na cike da hayaniya da sauri ta nufi kofa ta fito, ba kowa a parlor ta nufi waje, yaran gidanta ne tsaitsaye suna ta hayaniya. "Wai ya aka yi ne? Me ke going?" Muryarta da suka ji ya sa suka daddare. "Barka da fitowa Shugaba!" Suka hada baki suna miƙa mata gaisuwa. "Pascal ne aka sokaaa ya kusa warewa chan kiyama amma dai bai ware ba..!" Obafiya ya faɗa cikin yanayin maganansu. Lokaci ɗaya fuskarta ya chanza, idan kana kaunar ɓata mata rai ka taɓa daya a cikin mutane bakwan nan da suka zama rabin jikinta. Pablo, Pascal, Skipo, Obafiya, Shaly, Zee da Zubash. Jar uban chann! kayyasaa...Wasu ƙananun fitsararru ne da wannan gangancin na tarar aradu da ka?" "Eh shugaba yaran chan sabon titi ne" Skipo ya faɗa a daddare. "Chan dallah! kun zo kun tsaya kuna menene yaran basu riga sun shiga kogin jini ba? Ku wuce mu je daga Dorayi zuwa Sabon titi kowa bacci dole....." Fitooo mai ƙarfi ɗaya ya yi daga ciki wani ya ja addaa kan dakali ya ba da ƙiiiiiiiii "kowa ya zaburo a bar shi ya kawo... Kafin a yi dare akai kwan, Kuma komin lalacewar masa ta fi karfin kashin shanuuu...kowakkwana lafiya shi ya so... Wallahiiii" Skipo ya zaro mata key ɗin motarta don bata yarda a tukata, da hanzari kusan su goma sha wani abu da suke gidan a lokacin suka chusu cikin SUV baka wuluk ta zagaya ta shiga ɓangaren driver, tun fitowanta mai gadin ya wangale gate don ya san yau ba zaman lafiya yayi mata garaje ma shima kwana zai yi jinya. Da wani irin reckless driving ta fita, matasan suna ta ihu da kirari rike da adduna da sanduna... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA HUƊU* Kaman yadda ta yi alƙawarin hana kowa zaman lafiya a yankunan haka suka yi, sun zubar da jini har da waenda basu ji ba basu gani ba, sun ja wa mutane dayawa asarar kayan sana'o'insu kuma basu samu yaron da suke nema ba. Sanda ne maƙale a wuyanta ita ce gaba suna take mata baya har gaban mota ta shiga su ma duk suka ɗuru sai asibiti inda Pascal ɗin ke kwance, nan ma sai da suka yi rigima amma ta hana a taɓa kowa, daga nan bayan sun duba shi suka yi gida. Magrib ne ta shigo gidan bayan ta yi parking ko oho ta sauƙa, a cikin motar ta bar key ɗin kofar ma bata rufe ba ta nufi cikin parlor, jagaban ta gani zaune yana shan tabar wiwi. "Baaba" "Zo nan 'yar baba" Don niyyar wuce shi ta yi, dawowa da baya tayi ta zauna kan kujera tana harɗe kafafu. "Daga ina kuka fito haka? Ya na ga yanka a hannunki?" Ta ɗaga hannun ta kalla. "Nima ban san ya aka yi na yanke ba... Chan Dorayi muka yi muka ɗaga musu hankali, Pascal nawa fa suka taɓa!!" Pascal kusan idan basu yi sa'anni ba to bai wuce ya girme ta da shekara ɗaya ba hakan ya sa tana da shakuwa sossai da shi a click ɗin nata, bata manta sanadiyar haduwarta da Pascal a nan gidan ne ya zo sayan Tramadol wanda oganninshi suka aike shi a sadda ta tambaye shi shima yana sha? Ce mata yayi **** "Ban taɓa sha ba amma Oga Sanusi ya ce watarana da kanshi zai ɗandanamin wai yana hana gajiyar aiki. Kin san aikinmu ba na rago ba ne" Ta yi dariya tare da kallonshi "To Meyasa kake zuwa gidan bredin aiki ba ka zuwa makaranta?" "Diva idan ban zo gidan burodin ba ina zan samu kudin da za mu ci abinci da kanwata da mahaifiyata? Babanmu babu ruwanshi da ciyar da mu a gidan ya auri mata sama da biyar kuma kowacce ta ajiye 'ya'ya amma kowani ɗaki su suke ciyar da kansu, tufatar da kawunansu da kuma kula da lafiyarsu har ma da makaranta idan suna so su saka kansu shi ya ce ba'a yi mishi ba yana ƙarami shima ba zai yi wa kowa ba" A lokacin tausayinshi ne ya kamata a yadda yake magana, ya taɓa ce mata babanshi na da gidajen haya kaman Babanta haka kuma yana da gonaki a kauyuka da gaske baƙar mugunta ce kawai zai sa ya watsar da nashi da uzurin cewa shima nashi uban bai mishi ba alhali shi ba jalihi bane da iliminshi boko da arabi sai dai ɗan aƙida ne.. Bayan kwana biyu da ya dawo sayan Tramadol ɗin yake sanar mata ai ya sha kuma yayi aiki sossai ya samu kuɗi har kifi soyayye ya sayawa mahaifiyarshi, daga nan rayuwar shi ta lalace daga wannan sanadiyar ya zama addicted to drugs, ya zamana idan bai sha ba baya aikin bredin, idan ta ga mahaifiyarshi da natsuwar ta ta kan tausaya wa rayuwar Pascal amma bata bari ya bayyana ba, tun samuwar click ɗinta yake na gaba gaba a dukkan lamuranta sai dai idan faɗa bai tashi da Diva ba yana ciki hakan ya sa take kaunarshi tamkar ciki ɗaya suka fito. **** "Shi ne kika bari aka ɗauki hotunanki ana yamadidi da su duniya? Bana son kalar bakin da ake yi miki Sohana bana jin daaɗi, ba rayuwar nan na so ki yi ba" Yayi maganar da iyaka gaskiyarsa don yayi iya kokarinsa amma abin da rayuwa ta zaɓa mata kenan karatun ta yi shi iya secondary ta shiga FCE ta fara karatu ya ƙi dadi don ko ɓata mata rai aka yi ta dawo to su Pascal sai sun shiga sun ɗaga hankalin kowa a makarantar bata je ko ina ba aka koreta ita kuma ta ce ta gama karatun tunda ba dole ba ne babu yadda ya iya ya zuba mata idanu. Jin ya kira asalin sunanta ya sa ta tabbatar da gaske ya shiga yanayin damuwa. "Kuttt to na rantse da Allah duk gidan jaridar da suka poster ni har suka yi sanadiyar bacin ranka sai na tarwatsa su..!" "Ba maganan kenan ba, idan wanchan ne ni da kaina zan yi maganinsu ɗaya bayan ɗaya, ina dai so ki rage wasu abubuwan ne ki bar wa su Obafiya ba sai kin fita da kanki ba" "Baaba ba zan iya tura yarana bakin daga in kwanta in yi bacci ba, yadda nake jagabarsu kuma shugaba a garesu dole ni ce kan gaba a duk wani tarzoma da ta shafe mu... Bacci ai sai rago ni kuma babu ragwantaka a tsarinaa" Kallonta kawai yake ta miƙe "Ka huta Baaba" Tana kai nan ta yi ciki. Tana jin shi yana kiran hajjo, wanka ta shiga tana fitowa ta samu abinci ne aka ajiye mata a shirye, ta san aikin hajjo ne kuma da umurnin Baba don haka sallah ta yi ta zauna ta ci codein ta sha ta ƙara da ice, anan ta bar komai don ta san hajjo za ta zo ta tattare, tun ta buɗi ido ta ga dattijuwar hajjo ne ke kula da komai da ya shafe ta, bata taɓa cire ƙaya ta ɗauke da kanta ba sai hajjo ta zo ta ɗauke, bata taɓa sa hannunta kan tsintsiya da sunan shara ko wanke bayi ko gyaran ɗaki ba, kayan jikinta ma idan ta cire bata san ta tsuguna ta ɗaga ba anan zata barshi karshe zata zo ta same shi a goge a shirye cikin wardrobe ɗinta. **** "Ina za ki je ba ki bada kuɗin cefane ba?" Malam Iron yayi magana yana kallon Zubash da ta fito a shirye. Tsaki ta ja ta fiddo dubu biyu ta jefa mishi. "Yaya Zubaida" Ƙanwarta ta ƙirata. "Ya?" "Wai fa waec ne za mu fara kuma kin ga ke ce kike biyan kuɗin makarantar an ce zuwa karshen watan nan idan ban biya ba za'a rufe karɓa sai kuma wata shekarar" Ta lumshe manyan idanunta ta buɗe. "Na ji" Tana kai nan ta nufi kofa, saura kaɗan Salmanu ya hankadeta yayi saurin matsawa gefe. Shi karan kanshi ya san yanzu ba da bane, a da ne ya daka ya zalunta kuma ya zaga amma a yanzu idan ya gwada hakan sai ta bazar da shi kuma a banza. Harara ta zabga mishi tana tsaki ta fice. Mota ce dake Parke a kofar gidan ta buɗe ta shiga. "Ya aka yi?" Matashin dake zaune ciki ya ce "Wani deal ne ya samu, akwai wani babban dan siyasa da ya sa na samo mishi mace da irin siffarki shiyasa na neme ki kai tsaye Dukda a raina kam Uwar ɗakinki ne Diva" "kulll ka sake ambatan sunan DIVA, zan iya yin komai a kanta Jibril.. Sai in shemeka kuma babu abin da aka isa ayi na rantseee...Na sha gayamaka Diva ba haka take ba ni karan kaina da nake wannan harkar babu yadda ta iya da ni ne amma babu abin da ta tsana irin Biye biyen maza...har ka mutu ba za ka iya kawalcin Diva ba" Yadda take magana ya sa yayi shiru Dukda ba a Buge take ba sai ta illata shi akan wannan Diva ɗin. "Za mu je ne ko na sauƙa?" "Ki yi haƙuri, ai ba zan bari mu yi asarar makudan kudade ba daga ni har ke" Motar ya ja suka nufi wani rantsatsen guest house tabbas akwai kudi wurin don karan kanshi kamashonshi ya fi dubu ɗari da hamsin don Alhjn ya ruɗe akan kyaun Zubaidah na cikakkiyar bafulatana, harkar da ta saba ne da shi kowa ya dogara a gidansu don haka babu shakka ko fargaba suka shiga holewa. Sama da awanta biyu wurin wannan Alhjn kan ya sallame ta. "Zubash!" Ta ɗaga ido ta kalleshi yana kallonta yace "Kina da kyau mai ɗaukar hankali" Tayi murmushi "Shi ya zama jari na! Wannan kyaun shi ya ceceni daga rayuwar wahala" "Da za ki yarda da na aureki, ba za ki gane irin features ɗinki ba, baki san baiwar da Allah yayi miki ba ne...amma rayuwar nan bata kamaceki ba" Tayi dariya. "Aure?? Har Aure wani abin alfahari ne? Ka ga malam Sallameni in tafi" Har zuciyarshi ya ji soyayyarta, ta haɗu ne ko ta wani ɓangare amma ya kula rayuwar bariki ce kawai gabanta. Kudadenta ya mata transfer chass kan ta miƙe ta fice. Riga da wando ne jikinta kanta manyan kalaba da bata ko damu da rufe su ba, tafiyarta take hankali kwance ta ji wayanta na ƙara. "Shaly!" "Kina ina? Diva na nemanki tun safe...har tarzoma muka tayar baki nan" "Diva ta fita da kanta faɗa? Me ya faru?" "Pascal ne aka soka a injin biredi" "kuna ina? Gani nan zuwa" Tana jin suna gidan Jagaban ta tari machine ta haura. "A gafarceni Diva ban san abin da ya faru ba" Zubash ta faɗa tana ɗan rankwafawa kaɗan. Diva da ke shan ice ta ɗago idanunta da suka ji kwalli suka kara haske ta kalleta. "Daga ina kike?" Sosa kai kadan tayi bata ce komai ba. Tsaki Diva ta ja ta tura mata kujera. "Zauna" Zama ta yi. "Me yake burgeki ne da maza Zubash?" Diva tayi tambayar ba tare da ta kalleta ba sai lumshe ido take ice ɗin na hawa har kwakwalwarta. Kai tsaye tace "Sulallah... Idan ban je garesu na samu kudade ba wa zai cigaba da kula da gidanmu?" **** Haka ne lallai Zubaidah ɗiyar kwarai ce a farko tana iya tuna ranar da ta fara karɓawarwa Zubaidar faɗa Ɗan mijin mamanta Ya biyo ta da wani ƙarfe har kofar gida yana dukanta har hannunta ya karye, wucewa kawai suke amma zaluncin da aka yi mata ya sa Diva taimaka mata, sai da ta rama mata kariyarta. Bayan kwana biyu Zubaida ta zo mata godiya har gidan Jagaban da dayawa a unguwar suka tsani ko wucewa ne yaransu su yi ta wurin tabbas da akwai dama da sun jima da korar Jagaban a unguwar amma ya riga ya zame musu ciwon ido. Diva ce ta biya komai aka mata gyarar kariyar don haka ta ji dole ta shiga tayi mata godiya saboda Salmanun har tsoronta ya fara ji shima kuma yana fama da Azabar nashi kariyar, da ta zo ta samu Diva ɗin da su Pabloo a harabar gidan suna ta shaye shaye. "Na zo ne na miki godiya" Ta faɗa a ɗarare saboda yanayin gidan da 'yan dabar da ke cike da shi. "Meyasa za ki zauna ana zaluntar ki ba za ki kwatarwa kanki 'yanci ba?" "Ya zan yi? Ba ni da wani 'yancin kwatar saboda alfarma ne muke kai, Ba gidan mahaifina ba ne, mahaifiyarmu ta haifemu mu biyu a chan Taraba kauyen Gassol da aure ya kai ta, bayan mun fara girma da wayo suka rabu da mahaifinmu, ta ƙi barinmu wurinshi ta tattaro mu ta dawo da mu Kano, shi kuma ya rantse cewar idan bata mayar masa da mu ba ko sisin kobo ba zai tura mata don kula da mu ba, ta zo ta sake aure muka zama mu ne bayin manyan yaran mijin da mijin shi karan kanshi. A ƙarshe kin san me mahaifiyata take cewa?" Diva da ta zuba mata ido a lokacin ta girgiza kai. "Ta gaji da ganinmu a gabanta haka mu fita mu nemi kuɗi, babu ruwanta da inda za mu samu, babu ruwanta da ta yadda za mu samu, ina da haddar izu ashirin anan na ce mata zan samar mata kudin amma ta bar khadija kanwata tayi karatu ni kaɗai na isa samar mata da kuɗin haka na ajiye karatun alqur'ani na, na bazama aiki neman kuɗi karantarwa ne na samu na kananun yara tunda ina da ilimin na fara koyar da su daga safe har yamma ana ba ni salaries karshen wata, a haka idan na kawo mata ɗari biyar dubu ɗaya ta kan zara daga ciki ta ba ni matsayin wahalar da nake sha na rana da koyarwa. A haka babu mai godiya Salmanu abu kadan na mishi zai kamani gabanta ya daka to ya zan yi? Agolancin kenan" "Samari na yi na gari har wurin huɗu amma Mahaifiyata ita ke nuna min hanyoyin da zan bi na ci kudinsu a karshe na ƙi aurensu da sunan basu kai su sameni ba, har ga Allah rayuwata tana cikin garari ban san ya zan yi ba ban kuma san ta ina zan fara ba..." Diva ta dafa kafadarta "Zubaidah Bashir, haka sunan yake?" Kai ta gyaɗa mata. "Zubash" Diva ta ƙira da hakan tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sun fahimta. Obafiya ya ɗauki coke me surke da codein ya miƙa mata "Ki sha wannan za ki samu sassauci" Da farko tayi kokonto amma daga baya ta karɓa ta sha ɗin, wannan shan da ta fara shi ya zama kofar shaye shayenta, matsi sai ya ƙaru mata don an koreta a makarantun da take karantarwa saboda fahimtar ta fara shaye shaye, Maama ta uzzura mata saboda sun daina samun kudi daga wurinta har tana barazanar tura ƙanwarta waje neman kuɗi saboda tseratar da khadija da sharrin shaye shaye ya sa ta faɗa harkar bin maza wanda har yau Diva bata farin ciki da hakan. **** Miƙewa kawai Diva tayi bata sake ce mata komai ba ta shige ciki idanunta na lumsuwa saboda bacci. "Shaly ya jikin Pascal ɗin?" "Da sauƙi" Daga nan suka cigaba da hirarrakinsu. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA BIYAR* *Ɓangaren Irshad Al-Noor* Bayan gama duk wani nazari ya ɗauki wayarsa ta pixel ya kunna data, Page ɗinshi ya fara dubawa ko yana da tarin tambayoyi wanda idan akwai dole zai yi live da dare saboda amsawa duk tambayoyin da aka yi mishi, ya kuwa same su birjik dole imamu zai zauna yayi sorting masu muhimmanci sossai. Kiran azahar ya sa ya miƙe ya shirya ya fice, bayan ya gabatar da sallah da imamu suka shigo ya karɓi sauran aikin Shehi ɗin shi kuma ya shiga don bacci saboda a irin waennan ranakun ya kan huta da rana, ƙarfe uku ya tashi ya sake wanka ya shirya cikin Midnight blue thob da White Jubba sai White Ghutra da Agal ɗinshi baƙi sama. Cikin tsantsar kamala ya fito a dining ya zauna ya zuba abincin da ya tabbatar daga wurin Maamah ne ya zuba kaɗan ya ci kan ya miƙe ana kiraye kirayen sallah ya fita, bayan gabatar da Asr aka shirya mishi wurin zama da zai gabatar da karatun littafi da suke yi da yamma, masallacin ya cika da gidajen television na Musulunci kaman su Sunnah Tv, Africa Tv3 da su Manara su Wisal duka sun saita camerori, shi ya zauna akan kujerar gabanshi coffee ne a wani kyakyawar mug da Imam ya kawo ya ajiye, duk ya buɗe mishi system ɗinshi ga littafin ma a buɗe nan ya fara gabatar da wa'azin Magana ya gangaro da shi kan tuba da neman gafara. "Darasin anan shi ne idan an ce a yawaita Istigfari ba sai mai budadden laifi kaman zina, da saura su ba ne a'a asalin bayin Allah na ƙwarai ba sa rabo da Istigfari, da tuba saboda yanayin halittar da Allah ya yi mana. Dama a halittar ɗan Adam akwai wani nau'in kasawa da ubangiji ya yi mana duk ƙoƙarinka bahaushe ya ce tara kake baka cika goma ba, idan ka amince da wannan za ka samu sauƙi a ranka... Mafhumm?" Suka amsa da "Na'am" Ya ce "Dayyib" Kan ya cigaba cikin kamalarsa "Wasu su kan sakankance su ce ai laifukansu ya fi karfin tuba ko sun yi ma a banza don suna da yakinin Allah ba zai karɓa ba Lalala ku sani shi shaidan ba wai yana son ka cigaba da laifi ba ne kawai yana so ne ka yanke kauna daga rahamar ubangiji" An natsu sossai ana sauraronsa wasu na ta tuna ayyukansu. "Idan da fa Allah yana so ya halaka ka saboda zunubinka...da ba zai taɓa buɗe maka kofar tuba ba, kada ku kuskura ku bari wani zunubi ya sa ku ji ba ku chanchanci komawa ga Allah S.W.T ba" Yana kai nan ya ce anan za'a dakata za su cigaba gobe da yardar Allah. Tambayoyi ya amsa Imam na karantawa yana amsawa kan suka tashi daga karatun, sai da ya fita kan kowa ya shiga ficewa daya bayan daya a lokacin karfe biyar, gida ya shiga sai sannan ma yake tuna yana da taron Matasa na awa guda a masallaci don haka Ammar ya kira a waya ya tabbatar mishi yana zuwa, mintuna kadan sai ga shi sanye da dakakkiyar jumpa, musabaha suka yi kan suka koma masallacin ya gabatar da taron cikin ilimi da Allah yayi mishi. Wani abu da Irshad Al-Noor muddin yayi wa'azi to sai ya je viral, mata dayawa ya zama crush ɗinsu kowacce tana son kallonshi don yana da tsafta, natsuwa, kamala da izza irin mai tasiri ɗin nan, yana da taushi amma idan ya murde yana da karfin da babu mai iya tankwara shi, hakan ya sa dayawa daga cikin wasu malaman ya zama kaman makiyi ko abokin gabansu. Wasu yana sane yayinda wasu bai ma san suna yi ba duk ya tarkatasu ya watsar abin da ke gabanshi kawai yake da kuma wanda ya san zai amfani al'umma. Sun idar da Magrib yayi karatu har aka kira isha yana zaune a inda yake saboda kwaɗayin samun wannan ladar na zama tsakanin Magrib zuwa isha, ko da aka kira isha'i suka gabatar, Ammar da Imam da kuma malam Bala suka take mishi baya har zuwa baƙar motarsa da Malam balan ya janyo suka nufi inda yake lecturen dare. A hanya ne Ammar ke ce masa "Shehi wai ka ga abin da wannan yarinya Diva da mukarrabanta suka aikata a garin nan yau?" Hotunanta da irin barna da suka yi ya miƙa mishi wayanshi ya shiga dubawa, bai jima yana kallo ba yayi tsaki kadan tare da miƙa wayar ga Ammar ɗin. Kaman zai basar kuma sai ya ɗauki wayanshi ya shiga contact list ɗinshi ya duba commissioner of police ya kira shi. Ringing na kusan karshe ya yi picking "Allah ya gafarta Shehi barka da warhaka" "Barka dai yallaɓai ya aiki?" "Alhamdulillah ya hidima da jama'a" Ya ɗan lumshe ido ya buɗe kan ya amsa da "Alhamdulillah" "Na ƙira ka ne in yi maka tuni don na san ka sani sai dai tuni ɗin yana da kyau wasu lokutan, a kan Haƙƙin al'ummar da ya rataya wuyanku, abin da waennan 'yan daban suka aikata ina fata ba za ku bari ya tafi haka nan ba! Alhakin gyaran al'umma ba akan iyaye kaɗai ya rataya ba, ya rataya a hannayenmu maluma, har da ku hukumomi da shugabanni da kuma duk wani mai faɗa a ji, idan ana barinsu Scott free shi yake ƙara basu daman maimaita same laifi..." Ya ƙarasa fuskarta na sake dawo mishi, shi mamaki da kyankyaminta ne ke rufe shi a duk sadda ya tuna irin magananta zuwa abin da suka riska tana sha a jiyan da kalar irin dressing ɗinta wa'iyazubillah! Ya ambata a saman lips ɗinshi. "Kwarai da gaske haka yake Ya Sheikh, Na gode kwarai da tunatarwa yanzu haka muna kan bincike ne kan su idan suka shiga hannu kuma za mu tabbatar sun dandani kudarsu daidai da abin da suka aikata" Kai ya gyaɗa kan suka sake tattauna tabarbarewar tarbiya kan suka yi sallama. Ammar bai yi mamaki ba don ya san idan da zai iya ba da gudumawa wurin ganin duk sun shiryu kuma basu lalata matasanmu masu tasowa ba tsaff zai bayar. Ya ɗan kalli Shehi yana sake mayar da kanshi kan wayan yana scrolling yayi murmushi "wa'azin da ka yi ɗazu ɗin nan? Ga Ustaz khalid na sukar ka a media yanzu haka" Karamin murmushi kawai yayi bai tanka ba. Imam ya ce "Ni na rasa irin Ustaz Khalid wallahi, ga tarin ilimi ga shi haziki sai dai ya fi girmama Spotlight akan da'awa da yake yi kuma hakan ba daidai ba ne" Ammar ya ce "Kuma sukar shi ba ya tashi sai Irshad ya yi wa'azi abin shin akwai daure kai.. Addinin ya zama gasa ne?" Malam Bala ya ce "Irin wannan yana jin haushin yadda mutane suke girmama Shehi ba tare da yana nuna hakan ma ya damesa ba don bai taɓa ɗaga murya don a ji sa ba..." "Ammar! Imam Ku sani shi mutum mai tsoron Allah ba ya buƙatar ɗaga murya domin a ji nauyin kalamansa, maganan Ustaz khalid kuma a bar ta haka kila yana da hujjar sukar kalaman nawa matuƙar na kuskurewa fahimta" Daga nan bai sake magana ba su ma basu sake ba don sun sanshi tunda ya ce a barta barinta ya zama dole ba ya son maganan wani a tare da shi sai ya zama dole. Sun isa ya ba da lectures yadda ya saba, Imam ya koma yana nunawa Ammar yadda lectures na daren da mata ne ma ya yiwa ya dusashe sukar da ɗazu Ustaz khalid ke mishi tun kafin ma a farga da shi wanda sun san sai ya kusa kwana da bakin ciki tunda abinda ya ɗora wa kanshi kenan wanda yake da shi bai ma nuna ya sani. Daga nan gida suka dawo kowa ya nufi wurin kwanciyarshi, shi kam Irshad Al-Noor live video yayi ya amsa tambayoyi ya ba da ilimi sossai har karfe sha biyu kan ya sauka yayi wanka ya zo ya kwanta kaman kullum. **** Ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare ta farka, wanka ta sake ta jiƙa har gashinta saboda kanta da ke ciwo tsabar ta sha abubuwa sun yi yawa, da towel blue ta fito daure a kirjinta ta busar da gashinta ta yi sallar isha, ta shirya akwai birthday party da aka gayyaceta wani CLUB, ta shirya kuwa cikin wasu ja da farin riga da wando ta saka hill shoe ta rufe gashinta da scarf red ta fito tana baza kamshi hannunta riƙe da car key. Jagaban yana ganawa da mutane kaman koyaushe don koyaushe yana busy ne ko solving manyan rigima da ya gagari yara ko sayar da kwayoyi yana kirga kuɗi. Ficewa ta yi da Pablo, Obafiya da Zee baby. Chasu ne da ko da suka je an yi nisa da farawa wuri ta samu ta zauna tana kallon masu raye-raye, ana shaye shaye ana rawa. Idanu ta zubawa samari biyu da ta ga sun fara rigima kan wata figaggiyar budurwa, tsaki ta ja tana gyara zama ta san ƙarshen night club ɗin ne ya zo Dukda babban night club ne na manya kuma akwai bouncers dayawa hakan ba ya hana faɗa a lokuta dayawa. Suna cikin jayayyar ta ga kaman an zo ana ƙoƙarin sasanta faɗar ji ta yi ana yi mata magana a ka... "Fine gurl ya dai kike zaune ke ɗaya?" Ta mayar da idanunta kansa ta zuba masa su kawai bata ce komai ba. Karkada ƙafa take har ya zauna gangarta ya kai hannu zai ɗora kan cinyarta cikin rashin zato ko tsammani ya ji wani lafiyayyiyar azaba ya ratsa shi har kwanya, ihu ya tsala yana riƙe hannunshi da ta yiwa wani yanka da wukar da bai ma kula da lokacin da ta zare shi ba, ta miƙe tana kallonshi cikin ido... "Ashe kai ƙaramin ɗan iska ne tunda ɗan wannan yankan ne ba zaka iya ɗauka ba Har kake da tsaurin idon zuwa gabana ka yi min magana?" Wuƙar ta ɗago daidai lokacin da karar fashewar kwalba ya ratsa su kan su ma kula waenchan samarin da suke faɗa ne kan buduruwa ɗaya ya cakawa ɗayan kwalba. Da gudu matashin da ta yankewa hannu ya fita hannunshi na tsiyayar jini, tuni hall ɗin ya rikice mummunan faɗa ya kaure , ita dai bata shiga ba amma garin faɗa wani ya yanketa a baya Dukda bai sani ba ne amma wani yanka da tayiwa hannunshi daga damtse sai da ya kurma ihu. Karshe ita ta wargaza taron da yaranta da suke wurin dab asuba kowa yayi ta kanshi, babu ruwansu da dare ne haka ta saki speed har asibiti don duba Pascal. Mamanshi ta samu kanshi da shabidon da ke zama da su saboda tsaro, dama kuma hajjo ta tura musu abinci don ta riga ta sanar mata za'a na aika musu abinci, Dukda ba lokacin visiting ba ne amma securities ɗin sun kasa tankasu karshe ma sai da suka tashi kowa a ɗakin da hira don pascal ɗin ya ji sauƙi sossai sai karfe shidda na asuba suka yi gida. Innar Aminu ta dube shi. "Yanzu kalar rayuwar da ka zaɓa kenan Aminu? Sunanka ƙarfi da yaji ya tashi daga na yanka ya koma chan wani Pascal da idan ka mutu yau mala'iku basu san da zaman sunan ba bare a yi maka Adu'a ya amsu? Wani irin masifa ne wannan?" Ya tura baki yana gyara kwanciya "Innarmu ke fa baki waye ba ne, amma ai sunan Aminu na 'yan kauye ne a bar ni da Pascal ɗina... Yawwaa" Cikin baƙin ciki da kananun maganganun da mutanen ɗakin suke yi cike da tsoro ta ce "Wallahi Aminu haɗuwarka da wannan yarinyar Diva bai zama min alkhairi ba" "Aaa'aaa Innarmu babu ruwan Diva, wlh bakin rai bakin fama ba'a taɓa mana Divaa mu zura ido darrr ne... Bakin rai bakin fama" "Sai ka rufe ni da duka in san da gaske kake, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba" Yana tura baki ya rufe ido idan shi zata saukewa ko a gyalen shi amma banda Diva don bata mata komai ba. Shabidon ya tafi raka Diva ɗin dawowar shi ne ya sa Innar yin shiru a dole. **** "Nanah" Khadija ta amsa tana tahowa da sauri, tana son 'yar uwartata kaman yadda ita ma take sonta da son mata rayuwa mai kyau ba kaman nata ba da mahaifiyarsu ta lalata ƙarfi da yaji. "Ga shi ki je ki biya kudin waec ɗin" Ta miƙa mata kudaden da sun yi dubu arba'in, Malam Iro ya taso da sauri "yanzu ke Zubaidah wannan makudan kudin za ki kwashe ki ba wannan yarinyar akan bokon banza da wofi? Bokon da babu abin da zai amfane mu da shi? Ko ba ce miki nayi ina da bukatar kudin nan ba kin manna min hauka?" Khadija ta kasa karɓa kanta ƙasa sai da Zubaidar ta daka mata tsawa "Za ki karɓa ne ko sai na tashi? Dallah karɓa ki wuce... Ai dayake mutum ne ya nemar min kudin da har zai faɗa min abin da zan yi da shi" Mamansu da ke hura wuta ta miƙe tana kallonta "Ai gaskiya ne malam ɗin ke faɗa shi ya fi khadijar bukatar wannan kuɗin kina gani dai kullum gidan nan hannu baka hannu ƙwarya" "Mama bana bashin ne? Akwai ranar da zan tashi in yini ban baku wani abu a gidan nan ba? Ko akwai wanda ya san ta yadda nake samo abuna? Wallahi na iya tafiyata in bar gidan nan har abada in ga karshen tsiya" "A'a duk ba'a kai ga haka ba, idan don kuɗi ne rike abinki" Ta ja tsaki tare da ficewa daga gidan tana fito... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjoh6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA SHIDA* Jagaban na parlor ta shigo ganin jini a White ɗinta ya ƙirata ta zo ta zauna da kanshi ya ɗinke wurin don ta yanku sossai amma tsabar taurin rai ko ɗarr bata yi ba don duk bayanta akwai yanka da wasu sassa na hannayenta duk akwai scar na yanka ta riga ta saba in da sabo. Bayan ya gama ta yi ciki bacci tayi don ta sha Ice kan tayi faɗa wurin takwas a lokacin, ƙarfe Ɗaya da wani abu kuma ta farka ta shirya ta fito kai tsaye kitchen ta yi wurin hajjo. "'Yar albarka kin fito? Akwai abin da kike buƙata ne?" Ta ce "No na zo na dubaki ne kwana biyu ba mu haɗu ba" Murmushi kawai hajjo ta saki tana kallon Diva ɗin Allah ya gani saboda Diva ne kaɗai take zaune a wannan gida, kuma ta ɗauketa tamkar ɗiyar da ta haifa Dukda akwai tarin gyararraki da take son yi wa rayuwarta sai dai Diva ɗin bata ba da damar hakan ba, tana kula da hajjon kaman mahaifiyarta don kyautar kuɗi, tufafi, turaruka ba a rufa wata bata samu daga Diva ba. "An kai abincin Pascal?" "Eh Hajiya Shamsu 'Pabloo' ya zo ya ɗauka ya ce da machine hannunshi zai miƙa musu kawai" Sai da ta ɗan shiga nazari kan ta tuna ashe fa sunan Pabloo na asali Shamsuddeen. "Ki dafa min indomie guda biyu da kwai zan shiga wurin Shaly a kai min chan" Tana kai nan ta fice tana tafiya ana miƙa mata gaisuwa wani ta amsa wani tayi kaman bata ji ba har ta shiga babban gidan hayan Baba da ke jikin gidan nasu, mutane ne ratata Dukda rana ne kowa ya tafi neman kuɗi amma akwai wasu da suke gida, gidan haya ne mai dakuna dayawa don za su iya yin talatin, amma kusan duka masu zaman kansu ne ciki. Kai tsaye ɗakin Shaly ta shiga ta same su da zee-zee suna lido a tray. "Barka da zuwa Diva" "Sannunku" Tana kai nan ta kwanta kan katifarta bata sake cewa komai ba sai ido da ta zuba musu har dai aka kawo mata indomie ta shiga ci, idan da sabo sun saba da halinta za ta iya yini a tare da su bata ce kanzil ba kawai dai ya kasance akwai motsin su kusa da ita, sai dai in ta gaji ta ɗan yi chat a wayanta wanda ba kasafai ba don ita ba ma'abociyar mayar da hankali kan waya ba ce. Har dare suna tare kan mazan suka dawo suka fita zuwa gidan suka dasa hirarrakinsu. Anan ne ma ta sake tana 'yar dariyar hirar Skipo dabin da suka yi tsakanin shi da wasu kwalawa(police) yau, Skipo Adaidaita yake ja amma yana amfani da shi ne backup asalin abin da yake yi distributing kayakin Jagaban ne, idan ya gama sai yayi ta daukar passenger. Washegari da safe bayan Diva ta shirya ta fito as usual kayakin dai ba na kirki ba don ma wani bodycon ne jikinta duk wani siffanta a waje ta saka facing cap kawai dai tana da wani irin idon fashion ne, duk yadda tayi styling jikinta sai ya karɓeta kaman wata fashion star, da key ta fito a hannunta tana cewa Baaba dake parlor "Mun tafi asibiti" Ya amsa da Allah ya tsareta ta fice, duk suna nan don haka shiga kawai suka yi suka nufi asibitin don duba Aminu, a lokacin Zubash bata a tare da su sun samu Innar Aminu na zaune sai ganinsu ta yi kaman an jefo su. "Diva..." Aminu ya ƙirata da murmushi. Ta amsa "Ya dai? Ya jikin?" "Ai na ji sauƙi Diva, me kuka kawo min don na gaji da cin abincin nan" Bata ce komai ba Shaly ce ta fiddo tramadol ta jefe shi "Shiyasa na riƙe maka wannan don ya rage maka zafi, Jagaban na miƙa saƙon gaisuwa" "Godiya nake mutuniyata Allah ya bar mini ke, shiyasa nake na fi yinki na kowa anan bayan Uwar ɗakina" Obafiya ya ce "Mu da baka yin mu cinna mana wuta mana kawai mu tabbatar" Suka yi dariya Mamanshi ta miƙe ta fice tana share hawaye Diva ta bita da ido tana sauƙe wa ta ga wani mutumin ya zura mata ido. "Na tsiyayar da idon nan na sake ganin kana kallonaa ba ruwana da ciwon ka... Ka wani zura min ido Uwa mujiya me kake kallo a jikin nawa!" Yadda ta harzuko ya sa dole ya shiga taitayinsa jikinsa na rawa ya natsu. Su Pabloo suka shiga dariya. Duk ɗakin a hankali suke zamewa suna ficewa saboda tsoro ita kam ta baje suna ta hira. Ashe wai ƙararsu aka kai akan suna shaye shaye suna kuma damun patients, securities na asibitin duk sun san wacece kowa tsoron zuwa yake sai Police suka kira su kuma suka kira DPO ya ƙira Jagaban. "Idan bakwa son ganinta asibitin sai dai a sallami yaron amma nima ban isa in hanata zuwa ba" Shi ne amsar Jagaban. Kuma haka aka isar basu bar asibitin ba aka kawo takardar sallama, ita ta biya komai suka tsare napep aka saka shi ciki saboda mamanshi sai da suka tafi kan suka shiga mota suka yi gida. A waje yau ta yi parking suka bubbude kofofin motar suka zazzauna baki baki suna ta hira tsakaninsu ita dai kujera plastic aka dauko mata ta zauna. Wannan zama da su kan yi ba karamin rikita 'yan unguwar suke ba don duk wanda ya doso idan ya gansu sai ya koma da baya saboda abu kadan za ka yi su zalunceka. Cikin rawar jiki ya taho don wallahi bai so zuwa ba amma Malam Iro ya rantse mishi idan suka bari wani abu ya samu khadija to wlh duk sai sun yabawa aya zaƙinta gwara ya zo ya nemi Zubash ɗin. A rikice yake gabaɗaya haka ya zo ya tsaya kyammm kan su ya rasa me zai fara cewa saboda tsoro. Idanu ta ɗaga ta kalleshi ta watsar.. "Obo.." Obafiya ya diro ta kalleshi "Wannan bai iya gaisuwa ba ne?" Sarai ta gane shi shima kuma a rikice yake ya sa bai gaishe su ba, kan yayi wani yunkurin Obafiya ya faska mishi mari sai da ya kusa faɗuwa ya gyara tsayuwa yana dafe kunci idanunshi falll hawaye a zuciyarshi kuwa ya tsinewa kafafun da suka biye wa Malam Iro suka kawo shi gaban Diva. "Babu manya ne a gidanku? Ko gaisuwar ce ba'a koya maka ba" Hannayenshi biyu kan kumatun ya zube jiki na rawa ya shiga cewa "Wallahi an koya min...Na rikice ne ya sa na manta..ina yini... Ammm ahh ina kwana? Ina gajiya?" Babu wanda ya saki fuska a cikinsu Dukda dariyar da ya ba wasu. "Mu aljanu ne dole mu rikitaka ko?" Divaa ta faɗa tana zukar tabar hannunta. "A'aa ki yi haƙuri Diva...kiyi haƙuri" "Me ya kawo ka?" Diva ta tambaya. "Khadija ce tana dawowa makaranta mota ta kaɗeta kuma ta bugu sossai shine...shi ne baba ya ce in zo in duba Zubaidah a kaita asibiti kar wani abu ya sameta" Idanu Diva ta zuba mishi wato duk gidan babu mai iya kaita asibiti sai Zubaida ta zo? Sun mayar da ita saniyar tatsa shiyasa jikinta baya taɓa hutawa da maza, tsaki mai ƙarfin gaske ta ja cikin wani irin takaici don alamu sun nuna tun jiya Zubash ɗin bata tare da su kuma bata gida. "Obo...mu tafi mu kai yarinyar nan asibiti" Ta miƙe da sauri suka shiga mota ta ja zuwa kofar gidan su Zubash ɗin suna parking sai gata tana sauƙa a machine, cikin mamaki take tambayar su me ya faru. Diva bata ce komai ba sai tsayuwar da ta gyara tana wasa da dankwalinta Bakinta na taunar chewing gum a hankali. "Shiga ki duba ƙanwarki" Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta da gudu ta shiga cikin gidan, yadda ta samu Nana sai da ya sa ta kusa faɗuwa, haka suka daukota sai asibiti. Da taimakon Allah dai babu abin da ya faru, an kula da ita sossai kan suka baro asibitin yamma ne don haka Diva wanka tayi har ta ma kwanta ta tuna akwai abubuwan da take son saya a kasuwa don turarukanta sun yi ƙasa. Key ta zara tana gyara trench coat na jikinta, wasu irin takalma hills ta saka ta fito. "Hajjo!" Da sauri hajjo ta zo "Na'am uwar ɗakina" "Idan su Obo sun shigo ki ce musu su jirani ina zuwa yanzu" "Toh Sohana amma yau ke kaɗai za ki fita?" Ta ɗan kalleta sai ta duƙar da kai bata ce komai ba don ba'a yi mata tambayar iskanci ita kanta hajjon ta sani subutar baki ne. Fitowa tayi ta shiga mota ta kunna tare da juyawa ta isa gate ɗin sai dai bata ga alamun Bilya ba. Horn ta yi sau ɗaya bai fito ba ta sauƙa a harzuke, daidai yana fitowa daga bayi da gudu, kafa ta sa ta kwashe shi ya zube timmmm a ƙasa. "Ki yi haƙuri Diva...!" "A karo na karshe da zaka kira sunana, aikin me aka daukeka da za ka barni ina ta Horn shiru??" "Cikina ne ya ruɗe shine na je ba..." "Ka buɗe gate ɗin nan ko sai na ɓurma cikinka in ya so abubuwan su zube nan ƙasa ka huta da zuwa bayin?" Da gudu ya je ya shiga buɗe gate ɗin ta doka tsaki ta koma motar watarana sai ta cirewa Bilya hannaye in bai kiyayeta da sokanci ba. Da gudu ta fice daga gidan jiki na rawa ya zube yana sauƙe numfashi. Allah ya gani ba yadda ya iya ne yake gadin wannan gida, idan ya bar nan ɗin bai san ta inda zai fara neman wata sana'ar da zai ci da kanshi da matarshi ba kuma ya kula da lafiyar yaron su in ba don haka ba da ya bari da jimawa, a haka ɗin sun yi masu gadi sama da goma sha wani abu duk basa iya jure halin Diva don yau za ta iya yi maka kirki gobe ta karta maka rashin mutunci ba damuwarta ba ne, Musamman idan tana Buge kaman yanzu. Kasuwa ta nufa music na tashi a motar kaman zai ɗaga sama, chewing gum take ci tana gyaɗa kai cikin reckless driving da sai dai a bata hanya ba dai ta bayar ba. ******** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjoh6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA BAKWAI* Kasuwar cike yake da hayaniya, masu sayar da kaya na yi hada hada ko ta ina haka ta ratso da motarta inda yayi mata tayi parking, sai da ta ɓata lokaci ta sauƙo wearing all Black hannayenta cikin aljihu, fito ma take yi da Bakinta. Cikin seconds ta ɗauki hankalin mutane dayawa ta inda take duk an yi shiru kawai an zuba mata ido. Wani matashi ya taɓa na gefenshi da suke sayar da kayan dan kunne da sarka "Wallahi ita ce! DIVA ce! Wannan da kake gani Ko manyan maza suna tsoron shiga komarta" "Ita ce wa? Ni ta burgeni" "kambala'i na rantse idan kana son kanka da lafiya ka kama bakinka tun kan ta ji ka, ka santa kuwa? To wannan da kake gani idan ta yanke hukunci kanka babu wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa kaff zuri'ar ku" "Meyasa ake kiranta DIVA kaman wata shugaban 'yan dabar indiyawa" Ya faɗa yana dariya har da sake karkacewa don kallonta da kyau. Ɗayan ya ce "Ai duk ɗaya, babu macen da tayi kaurin suna a dabanci irinta, kuma fa har da ma ɗaurin gindi daga wasu 'yan siyasar garin nan saboda ubanta shi ke tafiyar musu da siyasa yadda suke so idan lokaci ya yi. Sunan DIVA kuma na taɓa ji daga wani dan daba wai tun tana shekaru takwas a duniya ta samu sunan, a lokacin farkon riƙe wukarta ta cire yatsar wani da ya nuna babanta da yatsa...DIVA na nufin mai kwarjini, kyau, da kuma confidence na tarar duk wani aradu da ka, irin waennan boss ladies ɗin ake kira DIVA to daga yanayinta ne aka sa mata sunan ga ta da son gayu kuma Ubanta na kashe mata, ta haɗa kyau, iko ga izza irin na duk wani ɗan daba mai ban tsor..." Wuce su ta zo yi hakan ya sa duk suka yi shiru har ta wuce ta ɗan kallesu kaɗan don ta tsinci maganan da su ke ɗin amma bata yi niyyar kula su ba ne ta shiga shagon turare tana shiga ta zare glasses na idanunta ta tsaya kikam kan ta ce cikin muryarta "Duk ku fita waje...!" Ta yiwa costumers da suke wurin umurni, dayawa tsoron ta da suka ji ya sa suka fita amma wasu Matasa na nan tsaye. "Akan me za ki ce mu fita? Na ga abin da kika zo saya shi mu...." Wukar da ta zaro shi ya datse maganar ta nufe shi tana juya tsinin wukar a fuskarshi. "Ban ji da kyau ba maimaita..." Jikinshi rawa ya kama, yana mamaki. "Naa fyeɗe fatar fuskarka idan na rufe ido na buɗe na ganka tsaye a gabana....." Kaman walkiya haka suka yi waje da gudu. Ta cigaba da riƙe wukar. **** "Nana" Zubash ta kira ƙanwartata da ta buɗe ido ta kalleta ta sake lumshewa. "Yaya Zubaidah ke ce? Kin dawo?" "Eh Nana ya jikin? Fatan kin ji sauƙi?" "Da sauƙi yaya Zubaida" Kallonta ta cigaba da yi har Zubaidar ta tsargu "Menene kike kallona haka Nana? Na chanza ne?" Nana ta girgiza kai tamkar za tayi kuka ta ce "Yaya Zubaidah don Allah ki daina irin wannan rayuwar, bana jin daaɗin ganinki haka... Yaya Zubaida mu gudu mu koma wurin Abbanmu na tabbatar zai riƙe mu...ba na so ki mutu akan wannan tafarkin, yaya Zubaida a makarantarmu har kwatance ake da ke da Diva, idan na shiga mutane a tsarge nake ni karan kaina dayawa kyamata suke, wasu ma cewa suke tare muke yawon iskanc..." Kuka ne ya sarƙe ta. "Dalilin da kika hau hanya kenan ki kashe kanki ki huta?" Zubash ta faɗa cikin sanyin murya. "Ko ɗaya, na san duk wanda ya kashe kanshi wuta za shi Yaya Zubaida ba zan fara ba, wasu seniors ne suka yi bullying ɗina akan ki na fito ina tunanin wani irin rayuwa muke ciki ban kula da na zo hanya ba mota ta kaɗe ni. Don Allah ki amince Yaya Zubaida mu gudu Taraba" Ta ƙarasa da wasu irin hawaye. Zubash ta ɗaga idanunta sama cikin kokarin hana nata hawayen kwaranya, kan ta yi magana Mamansu da ke daga kofa kusan tun fara maganganun nasu ta banko ta shigo. "Wato ciwon ƙara tsirarshi kike kina labgwabewa don karya zuciyar yayarki ku gudu ku bar ni ko? Toh Allah ya kamaki...kina tunanin a banza ne Zubaidar ke kula da ni? Bautar da na yi muku kun yi min ne? Wahalar da na sha daga daukar ciki har zuwa haihuwa da raino wallahi idan kuka gudu duk sai na yi muku Allah ya isa a kanshi don ko nawa kuka ba ni baku biyani ba. Kuna komawa wurin ubanku kuma babu ni babu ku har Abada ko mutuwa na yi Allah ya isa wanda ya zo kan gawata. Munafuka Algunguma" "Mama ta ya zan fara tsirar ciwo? Mama haka Allah ya ce? Ki daina amfani da kalmar tsinuwa kina dulmiyar da mu Mama, babu inda Allah ya ce a miki biyayya a sabonsa ko ita Yaya Zubaida ta sani kin riga dai kin yi brain washing ɗinta ne take biye miki amma wallahi kaso mai girma cikin zunubinta naki ne Mama" Hannu ta kai za ta kai mata duka Zubaida ta riƙe. "Kar ki daketa mama" Yadda tayi magana ya sa maman fusge hannunta. "Ki cigaba da zama Nana ke faɗa miki abin da za ki yi da wanda ba zaki yi ba, idan kika naɗe hannu kika dawo kika zauna zan ga uban da za mu ci har mu rayu kuma wallahi ina kan bakana Yasin zan ja muku akan nonona da kuka sha muddin kuka waiwayi marar zuciyar ubanku" Tana kai nan ta fice fuuuu khadijan ta fashe da marayan kuka yayinda da Zubaida ta saki murmushi, ba yau ne ta fara jin hakan daga Mamansu ba tun kan ta gama mallakar hankalinta take ji, a da idan ta faɗi hakan hankalinta kan tashi damuwa ya shigeta har ta ji zata iya koma menene don cikawa Mamansu burinta na dai a kawo mata kuɗi, amma a yanzu ko ɗarr bata ji ba kuma da ta yi niyyar komawa uban nasu tsaff za ta koma amma ta tsane shi, ta mishi mugun tsanar da bata ji ta taɓa yi wa kowa ciki har Iro da basa haɗa Inuwa. Ko babu komai shi Malam Iro ya bar su sun zauna karkashin inuwarsa, sau dayawa shi ya zama makari kuma jingina a garesu Dukda bai ɗauki ragamar uban gaske a rayuwarsu ba amma ya tare musu wani gibin. "Khadija ki yi shiru haka kin ga ba lafiya ce da ke ba! Komai zai wuce ne" "Har yaushe Yaya Zubaida? Har wani lokaci za mu cigaba da irin wannan rayuwar? Me yasa Allah ya ba mu irin waennan iyayen?" Sai a lokacin zuciyar Zubaida ya karye ta miƙe kawai ta fice don hawa sama ne kawai zai hanata kuka a lokacin kuma tabbas ta shawu ɗin don codein uku ta kwankwaɗe wani nurse ne ya hange ta ya taho "Me kike yi haka a asibiti?" Ta kalleshi ta watsar tare da juyawa ta koma ɗakin Khadija sai ganinta tayi ta dawo ɗakin ta zauna sai bacci. Idanu khadija ta zuba mata tana ta kallonta cikin wani irin tausayi da karayar zuciya. ***** "Kai!" Mai sayar da kayan ya matso da sauri yana zubewa "Ranki ya dade" "Haɗomin abin da na saba saye" Tun ranar da ta zo ta zaɓi turarukan da take so ta tafi bayan kwana biyu ta dawo ya tambayeta waennene ta kikkifa mishi maruka bai sake tambaya ba idan ta zo tana faɗa zai tattaro su ya zube mata a leda ya kai mata har mota. Wannan karo ma haka aka yi ya gama ta bashi Atm ya zara ta juya ya bi ta har mota ya kai mata. Ta jima zaune ciki tana shan ice wanda ita fa shi ne kabb ya zama addiction ɗinta idan bata sha ba har ciwon kai take, ba ma ta fara tunanin yadda za ta yi rayuwa babu shi, idanunta ne ya kai kan wani ya shakure wuyan karamin yaro mai sayar da pure water yana kokarin dukan shi ta buɗe motar ta fita. Ya ɗaga hannu kenan ya ji an riƙe ta murɗe tare da ture shi yayi tangal tangal yana kallonta. "Ƙaton banza Ƙaton wofi idan kwanji kake son nunawa ka samu kato mana daidai kai sai ka samu yaro ƙarami ka zalunce shi?" Miƙewa yayi zai tunkareta wasu kananun ɓarayin kasuwa suka riƙe shi "Kai malam Wuta gabanka wallahi.... Kiyaye kar ta soye ka gwara ka shafawa kanka lafiya ka bata haƙuri idan ba haka ba...." "Idan ba haka ba m...." Ƙulii suka kaiwa bakinshi bai zaci za su dakeshi ba ya riƙe da wuri yana jin gishiri gishiri na jini da ya tarar mishi "Ka ware ko kuwa?" Da sauri ya wuce suka fara mata kirari, Ta juya wurin yaron ta bashi dubu biyu tace ya kara jari yayi sana'a. Yayi mata godiya bata kula shi ba tayi mota waennan Matasa na bayanta su ma sallanarsu tayi suna ta mata kirari har kan ta ja ta fice da wani irin gudu, music na tashi cikin motar, daidai ta zo shan wata kwana motar Malam Bala ma ta sanyo kai Dukda ya yi Horn sossai bai ji alamar wata mota ba ita kuma ba Horn tayi ba kuma gudu take, ta yi wani irin buga musu gefen mota, ƙiiiiiiiii ta jaa wani uban birki a fili ta furta "Kan uba!!" Cikin fushi, motar take kallo da ido ta mirror amma don rainin wayo na cikin bai sauƙo ya bata hakuri ba, ranta ne ya ƙarasa ɓaci da wani irin zafin nama ta ɓalle murfin ta fitoo... Tana kallon yadda gaban motarta ya gurje har danger light ɗinta na gaban ya fashe tayi saurin isa farar motar ta ɓalle murfin, malam Bala da tun da ya ga ita ce yake salati jikinshi na wani irin rawa, Ammar na ƙoƙarin mishi magana sai gani suka yi an janye shi waje, shima malam bala bai gama firgita ba sai da ya ji ta mishi riƙon ɓarayu hannun mata, ta chakumo kwalarsa ta janyosa waje tamkar wani ƙaya ta haɗashi da jikin motar idanunta gabaɗaya a waje suka kara firgita dattijon... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjoh6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *BAABI NA TAKWAS* "Innalillahi wainna ilaihi rajiun..." Ammar da Imam suka faɗa suna balle murfin motar suka fito da hanzari, hill ɗinta ta sa ta take masa kafa sai da ta fasa ya saki karar azaba ta tsinka mishi mari tana furta. "Kai wani irin dakiki ne kana tafiya baka kallon hanya? Ka san Allah yau sai ka gwamnaci kida da karatu tunda ka taɓo DIVA..." Cikin wani kalar murya take magana da ya ƙarasa kaɗa 'yar hanjin shi, ko kan yayi wani motsi ko ɗaya daga cikinsu ya farga suka ji ƙarar ƙarfe.... WUƘA ta zaro tana ƙoƙarin kai mishi yanka ta ji an riƙe hannun, wani irin riƙo da za ta iya cewa ta ji Ƙashin wurin ya motsa. Tana Juyowa don ganin mai wannan zarrar ta ji sauƙar wani mahaukacin mari da ya sa tayi taga taga gyalen kanta na suncewa gashinta ya zuba a fuskarta, hannun da ya sake murdewa ya Buge wuƙar ƙasa ya ɗora kafarsa kai, ita kuma hannun ta kai kan fuskarta ta riƙe tana kokarin dawo da kanta duniyar mutane. Ita wani zai yi wa wannan mari? Ita aka mara a yau? Lallai duk garin Kano babu zaman lafiya, wani irin ɗagowa ta yi Bakinta gefe ya fitar da jini haka idanunta gefen marin ya yi ja. Idanunsu suka sarƙe yana kallonta cikin wani irin fushi da bai taɓa sani yana da shi ba, sossai ya ji ciwon marin da ta yi wa Malam Bala da zai iya cewa idan bai yi shekaru daidai da su Abba ba kaɗan ne za su fi shi, dattijo mai kirki da kawaici wai wata 'yar kwalta har ta samu zarrar marinshi a karkashinsa? A haka ma Allah yake ta ambato don da sai ya ɓallata, wani irin tafasa ranshi ke yi har tsokar jikinshi na rawa don ranshi ya kai makura wurin ɓaci kuma shaidan na ƙoƙarin taking over, bai taɓa duka ba don duk kannenshi presence ɗinshi kawai kan saka su natsuwa bare ya ɗaga idanu ya kalli mutum. Muryarsa da bai iya ɗagawa har chan ba a yanzu sai yayi ƙasa saboda bacin rai, duk su Ammar sun daskare ya kara matsawa, sai ta zama wata 'yar baby a gabansa, bata taɓa jin abin da ya girgiza zuciyarta ba irin idanunsa masu dauke da fushi da bacin rai. "Ashe bayan dabancin ke ɗin mahaukaciya ce? Kai ko mahaukaci ba zai kalli furfurar bawan Allahn nan ya tsinka masa mari ba, ko bai yi jika da ke ba ya haifi ire-irenki dayawa..." Yadda take kallonshi da idanunta waje kaman har lokacin bata fita daga kaɗuwa ba ga shi mutane sun fara taruwa ya ɗauke idanu daga kanta ya ce har lokacin wani kyama, haushi da tsanarta ke sake building a ransa. "Nasiha ne zan miki ba tare da kin roƙa ba idan kin ɗauka ruwanki, kina yawo da jahilci da rashin wayo a dole ke kin waye. Bari ki ji Allah babu ruwanshi da wannan dole ne kowani matashi ya san addininsa, me addininsa ya koya masa? Menene dalilin halittarsa? Wallahi da addini ne ake gamuwa da Allah ba wannan haukar banzar ta dabancin da kika ɗora wa kanki ba, da a ce za ki fita wannan haukar a kasheki sai kin gayawa Allah dalilin fitarki da kuma dalilin kisanki, kuma sai kin faɗi akan me kika mutu a sannan ne Allah zai kalli abin da zai miki hisabi a kai, idan mutuwarki ta Allah ce ko ta Manzon Allah ko wurin kare hakkin addininki to Allah zai tambayeki kuma zai miki shari'a amma idan kika mutu kan wannan fa? Kina tunanin za ki tsira daga azabarsa?" Da yatsa ya nuna ta, Muryarsa na sake zama deep don haka yake idan yana ɓacin rai da wuya ka ji ma Muryar na fita. "Duk sai Allah ya tambayi me kike yi ki ci abinci da nemawa kai tufafi, zalunci ne? Sata ne? Fashi ne? Duk sai kin yi wa Allah bayani, baki isa ki ce za ki zo duniya ki daka tsalle ki zagi uban kowa ki zalunci wanda kika ga dama ki kwana lafiya kuma ki ce za ki shiga lahira lafiya ba wane ke." "Wallahil azeem ba ki da wani abu mafi munin tarnaki a rayuwa kaman laifukan da kike aikatawa, Allah ya ce in da kun yi imani kun kiyaye dokokin Allah da mun kankare musu laifukansu kuma da mun shigar da su gidajen Al'janna na ni'ima. Imani na tsoron Allah imani na bin dokokin Allah...ko duk don saboda samun duniya ne kike wannan haukar? Kina ganin in kin bi Allah ba za ki samu duniyar ba ne? ubangiji ya ba wa waenda ma basu bi shi ba bare ke da kika amsa sunan musulma? Kalmar Mutuwa kaɗai Aya ce mai girma!" Tsaki ya ja, ya juya ya kama Malam Bala da har lokacin jikinshi na rawa ya buɗe bayan mota ya sanyashi, ya kalli Ammar cikin kaushin murya ya ce "Drive" Da sauri Ammar ya shiga mazaunin driver imamu ya zaga da sauri ya buɗe mishi mota ya shiga ya rufe kan shima ya shiga Ammar ya ja suka barta kafe a wurin har lokacin kamar wacce aka dasa. Hannayenta ta dunkule da ƙarfin gaske, wani zafi ya ziyarce ta a wanda ya murɗe ɗin ta runtse ido da karfin gaske wani irin tafasa da bata taɓa ji ba zuciyarta ke yi, idanunta sun rine kwarai da gaske ga shi bata iya kuka ba, wani irin rawa jikinta ya ɗauka numfashinta na fita da ƙarfi da ƙarfi, cikin wani irin sauri ta je ta shiga motar ta ja da karfin gaske ko kallon gabanta bata yi tayi gida. Wani irin Horn da take dannawa da karfin gaske shi ya fito da mai gadin su da gudu kan ya buɗe ta sauƙa ta turo karamin kyauren da sauri, daka tsalle yayi amma ganin bata kula shi ba sai wani huci da take kanta babu dankwali iska na kaɗa gashin kanta tamkar sabon shigar kamun hauka tayi hanyar parlor, akwai Matasa masu ɗan dama a tsakar gidan yadda suka kalleta ya sa duk suka mimmike tsaye suna bin bayanta da kallo, babu wanda zai ce ya taɓa ganinta haka kowa ya rasa abin cewa. Jagaban na zaune kawai ya ga shigarta a haka tamkar wacce aka jefo daga sama, da sauri ya tashi ya tare ta don ta nufi ɗakinta ne. "Ke! Sohana!! Menene?? Me haka? Wa ya taɓa ki?" Wani irin jan numfashi tayi tana ƙoƙarin zagaye shi ta wuce ya sake tare ta yana ɗago fuskarta. "Sohana me ya sameki? Ke da wa?" Idanun da ya sauƙe kan fuskarta ya sa ya zabura yana sake riƙota, Jagaban namijin gaske ne Dukda shekaru sun ja amma tsaye yake kyamm ga tsawo ga ƙira, bashi da imani bai san haƙuri a dukkan lamarinsa ba bare abin da ya shafi ɗiyarshi da duk duniya babu abu da yake ji da shi kamarta... Muryarshi ta sake kaurara "Mari? Uban wa ya mareki haka? Wa ya mareki???" Da wani irin tsawa ya ƙarasa maganar daidai shigowan yaranta, tambayar kuma ya motsa mata irin kalaman bakinsa da suka fi marin zafi a zuciyarta. Bata san ta yi wani irin ihu ba tana kokawa da numfashi, rungumeta jagaban yayi ta sake sakin ihu tana kuka irin mai jijjiga haɗe da ihu. Daga shi har yaran hankalinsu ya ɗaga, basu taɓa ganinta haka ba, janta yayi ɗaki amma suna jin Muryar ihu da kukanta daga inda suke jikinsu na tsuma. Da Jagaban ya ga ba zai iya jurewa ba ya haɗa wata allurar bugarwa ya yi mata da kanshi daga haka ta faɗi sai bacci. Waje ya fito suka yi cirko cirko. "Mari??" Ya faɗa yana kai kawo cikin parlorn hannayensa dunkule idanunsa jajazir. Skipo ya ce "Na rantse da Assamadu yau Kano babu zaman lafiya an taɓa DIVA?? Wallahi babu mai bacci cikin daaɗin rai daga yanzu har gobe" "Faɗa ma ɓata baki ne ai Skipo...aiki da cikawa ya kamata a gani mu jeeee" Pablo yayi maganan yana zaro addarshi Tuni su Bravo sun fice sun yi kira, Jagaban bai hana su ba, don shi nashi ba a kan jama'ar gari ba ne ya tabbatar duk wanda ya iya ɗaga hannu ya mari Sohana har ta yi irin wannan kukan to ba ƙarami ba ne, faɗar su su biyu ne kuma ko waye yayi alkawari sai ya cire hannun, shi da marin wani halitta kuma har Abada.. Kaman yadda su Pablo suka yi alkawari, ƙira kawai suka dinga yi suna sanar da an taɓa DIVA a take gungun 'yan daba suka haɗu tun daga unguwar suka fara kan mai uwa da wabi suna shara... Har arear kasuwa da abin ya faru sai rufe kasuwa aka yi lokacin tashi bai yi ba. Tashin hankalin da ya janyo dole polisawa suka kama fiye da rabinsu ciki har da su Pabloo don su ne gaba gaba, gari gabaɗaya ya rikice. Shaly ce kawai da Skipo ne ba'a kama ba amma an kama Obo, Pabloo da kuma Zee, Zubash tana chan asibiti bata san me ke going ba. *** A lokacin Shehi na zaune a reception na kyakyawar private hospital da ya sa Ammar kawo Malam Bala don duba kafarsa da ke ta jini, tapping kafarsa ɗaya yake a ƙasa yana ambaton Allah amma har lokacin zuciyarsa ta kasa sanyi. Bai yi wa kowa magana ba su Ammar ma duk cikin sanyin jiki suke tsaitsaye, kowa ya san Shehi kallo daya za ka mishi ka san an kai shi makura a yau. Abiey Ammar ya ƙira ya sanar mishi abin da ke faruwa anan Abiey ɗin ke sanar da shi shima yanzu ya fito daga office kenan za shi gida yanzu haka 'yan daba sun tsatsare hanyoyi suna ta barna. Da sauri Ammar ya kalli Shehi, sai ya ce "Abiey yanzu kuna ina? Babu abin da ya same ku?" "Mun samu dai mun fita babu abin da ya same mu, akwai hukumomi a wurin Dukda su ma abin ya fi karfinsu ashe ku kam har da illata Malam Bala suka yi?" "Toh Alhamdulillah, da sauƙi shima dressing ne yanzu za mu taho gidan gabaɗaya ba sai kun zo ba" "Toh Allah ya kiyaye gaba a cigaba da kula Ammar, Allah ya kawo ku lafiya ya tsare mana imaninmu ya shirya mana yaranmu" Ya amsa da Ameen kan ya katse ƙiran ya kalli Shehi. "Irshad!" Idanunsa da suke lumshe ya buɗe har lokacin a rine. "Ka kuwa san abin da action ɗin ka ya haifar?" Bakinsa ya ɗan taune bai ce komai ba. Ammar ya buɗe wayarsa ya shiga Facebook ya miƙa masa videos ne na abin da 'yan daba suka yi yau babu wani shugaba da zai ce yayi maganinsu. Ransa ya sake ɓaci, wato ma ɓata miyaun bakinsa ya yi ba za ta taɓa chanzawa ba? Meyasa shi da yayi mata bata yi masa ba sai waenda basu ji ba basu gani ba? Commissioner of police ya ƙira "Last time na tura maka hoton yarinyar nan da abin da suke aikawa ban ga ka yi wani hobbasa ba, hasali ma cigaba da yawo ta yi freely yau ta jagoranci mummunar hari irin wannan na zalunci haka za ka bari ta tafi Scott free again?" Commissioner da ba zai so shiga bad list na Shehi ba don ya san ja da shi ba daaɗi ya ce "Wannan karo ba ita ba ce! Amma ina maka albishir da cewa mun samu nasarar kama yaran kuma za mu gurfanar da su gaban court cikin gaggawa don a yanke musu hukunci daidai da abin da suka aikata" Ɗan shiru Shehi yayi kan ya ce "Zan cigaba da bibiyar wannan case har sai na ga ka yi abin da ka ce ɗin, ka kula da gaskiya a kan aikinka ka sani duk abin da ka yi Allah na nan yana kallo mala'iku suna rubutawa sai an tambayeka ranar gobe" Yana kai nan ya katse wayan tare da damketa a hannunsa da ƙarfi kaman ita ce ta masa laifi. Daidai nan Malam Bala ya fito yana ɗingisa ƙafa, Imam ya riƙe shi suka yi mota yana yi wa Shehi godiya. Sai da suka zauna Ammar na driving Irshad ya ce "Malam Bala ina roƙon ka da ka yi haƙuri da abin da ya faru, ka yafemin" "Baka yi min komai ba Shehi, ita ma da tayi ina mata Fatan shiriya da samun rabauta don tabbas ina mata tsoron mutuwa a haka" Shehi bai sake cewa komai ba suna isa gida kuma suka samu duk ahalin gidan a waje ana jiran isowarsu shi kam sannu da gida kawai ya musu ya wuce sashenshi don ko a ƙalau ma bashi da wani abin mayar da magana bare har lokacin yana jin zuciyarshi na zafi, idanunshi na hasko mishi marin da ta sauƙe wa malam bala haƙiƙa ya ji zafin marin nan wane Abbiey ɗinshi aka mara, ya san darajar mutum ya san darajar duk wani dake zagaye da shi. Ammar ne da Imam suka basu labarin abin da ke faruwa lamarin ya girgiza su har wasu na cewa a nuna musu wannan mai tsaurin idon su ganta, saboda riƙe waya a gidan sai ka yi aure ya sa duk ba media suke ba basu wani san Diva ba, tuni Ammar ya nemo ta a media ya shiga nuna musu don su Abba sun wuce sashukansu bayan gama tattaunawa don shirin alwala tunda Magrib ya gabato. "Wannan za ta aikata abin da ya fi haka ma na sha jin labarinta, ashe ita ce DIVA?" Sumayya ɗiyar Goggo hindatu ta faɗa. Kanwar Ammar da suke uwa daya uba daya hawwa ta ce "Allah kar ya kawo abin da zai hada mu da wannan don kam abin neman tsari ce kaman yadda za mu nemi tsari da shaidan haka za mu nemi tsari da ita" Ƙanwar Shehi da suke uwa daya Mufeeda ta ce "Ki ga fa irin wukar da ke hannunta, ga gardawan da suke take mata baya?" "Amma tana da kyau" Cewar mai bi ma Sumayya Aisha. "Kyaun banza babu kyaun hali?" Cewar sumayya. "Kai ya isa haka ku ba ni wayata" Ammar ya faɗa yana kwace wayarsa duk suka watse shima yayi sashen da yake. **** Ta ɓangaren Diva sai ɗaya na dare ta farka, ko da ta farka bata ji zafin zuciyarta ya ragu ba, kalamanshi ke dawo mata. Haka kuma ta kasa motsa hannun da ya murɗen don babu tantama ta samu gocewar kashi ko ma kariya kuma yayi tsami daga jin alamu tunda ba yau ne karon farko ba ta kan goce a ƙashi garin faɗa. Ita ce ɓarauniya? Ita ce 'yar fashi? Ita ce Mahaukaciya? Ita ce azzaluma? Ita ce dabba marar hankali... Ita ce...! Janyo bedside lamb tayi ta buga da gini da ƙarfin gaske tana ihu, Jagaban da yake gadin farkawarta ya shiga da sauri ya riƙeta. "Baaba an ci mutuncina irin wanda ba'a taɓa ba a garin nan" Ta faɗa tana taune hakorinta, idanunta jajazir amma babu digon hawaye don ta gama mishi kuka kuma. "Waye ne? Faɗa min sunansa kawai...!" "Ban sanshi ba! Ban taɓa ganinsa ba amma na rantse da Allah sai na ɗauki fansa mai muni a kansa, sai na bincikosa duk inda ya shiga a birnin Kano na nuna masa haukar da yake ambata a kaina, zan nuna masa jahilcin da ya dangantani da shi, zan nuna masa zaluncin da yake ambata da bakinsa...." Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA TARA* Da kyar jabagan ya saka ta bacci bayan hajjo ta kawo mata tea ta sha, da sassafe Shaly ce ta fara shiga wurinta a lokacin ta farka tana ƙoƙarin sauƙa daga gadon ta riƙota. "Diva! Hannunkin nan akwai matsala" Hannun ta kalla raɗaɗin na kaiwa har ga zuciyarta ta ce "Na sani!" "Shi ne kika bar shi yana tsami Diva? In an zo gyara zai miki ciwo sossai" Idanunta da suke sakk na mashaya ta ƙara zura wa Shaly, duk cikin click ɗinta Shaly ta fi zama tamkar babbar ya a gareta fiye da 'yar gida, saboda shekarun da ta bata suna da ɗan yawa, tana ƙaunarta kamar yadda itama take ƙaunarta, kuma duk Shaly ta fi su hankali da hange, shawarar da za ta baka za ka yi mamaki in aka ce maka drug addict ce kuma babbar 'yar daba ce, ta san komai daga kan doka har addini. "Shaly ina son raɗaɗin ya cigaba da fusata zuciyata ne ga ɗaukar fansa don na rantse da Allah ban taɓa kisa ba amma a yanzu da zan ga mutumin nan sai na tabbatar da cewa na kashe shi har lahira" Shaly ta girgiza kai "Ba Za ki yi kisa ba Diva, hakkokin da muke ɗauka ma kaɗai sun ishemu...bari na haɗa miki ruwa ki yi wanka in kira Tala ta duba miki hannun nan" Tala wacce asalin sunan Talatu ne itama tana daga cikin 'yan hayan gidan Jagaban ita dai ba ta kwaya, ta iya ɗauri duk 'yan dabar arear idan sun samu wani matsala na gargajiya wanda ba bukatar zuwa asibiti ita ke yi ana biyan ta taro sisi. Ruwan ta haɗa mata kaman yadda ta ce Diva ɗin ta shige don yin wanka, ita kuma ta fita anan ta je kitchen ta cewa hajjo ta haɗawa Diva abinci tayi mata doya da eggsauce da tea yanzu, daga nan ta faɗawa Jagaban hannun Diva akwai matsala za ta kira Tala, a sama yake ƙwarai kuma yana jira ne ya ji an sakar masa yaran da aka kama amma har yanzu bai ji kira ba. Hankalinshi ya sake rabuwa biyu yana so Diva ta gama samun natsuwa ko za ta iya bashi wani hint kan wannan mutumi don ba zai taɓa kyalesa ba alkawari ne, ba'a yi minti ashirin ba sai ga Shaly da Tala suka shige ɗakin Diva sun samu ta fito tana zaune ɗaure da towel don ta kasa komai da hannun wasa wasa, idanunta na zube a hannun amma zuciyarta hasko mata yake sadda hannunshi ya sauƙa a kai ya kuma murɗe. Ta Yi dauriya don wasu irin gumi ne kawai take tsatsafarwa sai idanunta da suka rine amma bata yi ihu ko kuka ba, tana da wannan kafiyar da taurin ran, Talatu ta mata sannu bayan ta gama ta shafa mata man zafi ta fice, Shaly ce ta duba mata kayan sawa ta saka da kanta ta zaunar da ita ta dinga janta da lalama har ta ɗan ci wani abu kaɗan kan ta sake kwanciya. Yamma likis ta farka again sai lokacin ta gwamutsa sallolin ta, Dukda ranta a hautsine yake har lokacin, Shaly na tare da ita tana kwance idanunta lumshe Shaly tace "Ɗazu Pascal ya shigo kina bacci" "har ya samu lafiyar da zai dinga yawo?" "Hankalinshi ne ya tashi kaman yadda na Zubash ya tashi amma na ce komai na under control babu abin da ya faru ta cigaba da kula da ƙanwarta" "Daidai" Diva ta faɗa har lokacin idanunta a lumshe amma amsa kuwwar Muryar wannan mutumi take ji, kamshinshi na larabawa na zaune raɗam cikin kanta, alkawari tayi wa kanta da sai ta ɗauki fansa a kanshi ko ba jima ko ba daɗe bare ma ba za'a daden ba, sai ta kawo karshen shi kaman yadda ta yi alkawari. Bata cika social media ba sai ya kama, ita rayuwarta idan ba'a Buge ba tana zaune cikin su Pabloo tana sauraron hirarrakinsu sai kuma idan rigima ta taso ayi ta, kowa ya san bata da magana wasu ma har son jin muryarta suke wasu na mamakin irin sarautarta da fadancinta kaman wata Gimbiya idan sun faɗi hakan akan ce musu ai Gimbiya ce tunda Gimbiyar titi ce kuma kowa ya amince da basu da Thug Queen kamarta. "Diva na san zuciyarki bata yi sanyi da abin da ya faru don mun yi kan mai uwa da wabi ba, shi ɗin ne kike so a karan kanshi ban hanaki ɗaukar fansa ta kowacce irin hanya ba amma don Allah kar ki fara tunanin bazarwa, daga sadda kika fara daga nan mun ɗauki hanyar da babu tuba kuma...ba zan iya bari ki faɗa har chan ba" Diva ta buɗe idanunta da suka sauya ta zurawa Shaly cikin ɓacin rai tace "Ai sai ki fita daga tafiyar kin ga jini bai shafe ki ba kenan, amma kin san Allah? Na rantse mutuwa ce kawai za ta hanani zubar da jinin mutumin nan, mutuwa ne kawai za ta hanani fara tura sa lahira kan in je! Sai na mishi mafi munin zaluncin da ya ambaceni da shi na janyowa iyayensa zubar hawaye na har abada. Ki daina abu kaman baki sanni ba Shaly" Jagaban ne ya shigo a kan cushion me kyau dake ɗakin ya zauna "Shaly ki daina ɓata mata rai bana son hakan, idan ba za ki goyi bayan ra'ayinta ba kawai ki yi shiru" Shaly ta kalli Jagaban idanunta cike da kwalla, ba zata taɓa bari ba muddin tana tare da Diva ba zata bari tayi kisan kai ba, sun san kan jijiyoyo sossai duk click ɗinsu idan ka ga sun kai sara ko suka basa kaiwa inda mutum zai mutu sai dai su jiggata shi, ko su mishi sanadin wani ɓari na jikinshi ba zata bari Diva tayi kisa ba idan shi Jagaban ya saba ba zata bari ita Diva ta gaji komai har da kisan rai ba. Miƙewa tayi ta fice, Jagaban ya cigaba da rarrashi Diva da ta narke mishi har dai ta natsu kan ya fice, da kanta ta haɗa ice tun tana sha tana lumshe ido har tayi bacci da haka. Sai Washegari da ta tashi da safe ta ga shaly ta dawo sun kwana tare saboda yanayinta, bayan sun yi wanka an kawo mata abinci ta ci tace wa Shaly "Kira su Obo na san suna son ganina" Shiru Shaly tayi da kyar tace "Skipo ne kawai waje" Diva ta zuba mata idanu alamar ban fahimta ba ganin ba zata yi magana ba alamun rashin gaskiya ya sa Diva ta miƙe tsaye "Kin fara magana ko kuwa?" Babu yadda ta iya ta sanar mata gaskiya. Labarin daren su pablo biyu a cell ya ɗaga hankalinta. "Me Jagaban yake yi basu fita ba?" Key ta ɗauka zata fita Shaly zata bita tace "Don't!! Don't you dare Follow me don a yanzu ban yarda da ke ba!" Tana fita harabar ta ɗauki mota bata kula da gaisuwar da kowa ke miƙa mata ba ma ta fice daidai nan kiran Jagaban ya shigo alamun Shaly ce ta kirashi don ba ya gida, amma tana jin kalaman da ya fara ta katse call din bata ce komai ba. Police station ɗin da suke tayi parking harabar ta fito ta taka ta shiga cikin police station ɗin sanye da wasu baƙaken hoodie riga da wando bata gama jan zip ɗin ba don ta gaba ana hangar farin vest ɗinta, facing cap ne kanta haka idanunta da baƙar space saboda yanayinsu na kwanakin rashin daaɗin rai da ta yi. "Ina son ganin IPO na case ɗin su Pabloo" Ta Yi maganar ba tare da ta kalli kowa ba ma. "Waye hakan? Ya za ki shigo mana wuri da gadara?" "Kai!! ba ni da lokacin batawa a kanku ka faɗa min ina zan ga IPO?" Ta ƙarasa tana matso wa tare da cire glasses ɗin idanunta suka bayyana. Police ɗin kasa sake magana yayi sai hanya ya nuna mata, ko da ta je da zafin ranta IPO ɗin ya nuna dole za'a yi musu hukunci kai tsaye ta kira Jagaban "Baaba! Waennan kwalawar suna neman rigima da ni, duk wanda zaka kira ka kira a sakar mini su Pabloo dukkansu tun kan in kunce musu zaren hauka na rantse" "Ki yi haƙuri! Ban ma so kika je da kanki ba Sohana bari na yi ƙira" Wayan ya saukar ya shiga kiran Commissioner da kanshi don connections da yake da shi alfarmar dabanci da sayar da kwayoyi baya tunanin wani Chairman ko member ma na da irinshi. "Jagaban hakan ba zai yiwu ba a yanzu, don Allah ka ba 'yarka shawara ta ɗan dakata tukuna su kwana biyu case ɗin yayi sanyi sai a sake su" Cewar Commissioner ɗin "Me kake cewa ne? Jiya haka ka sanar da ni amma ka ƙi faɗa min dalili, Toh saboda mene?" "Ko na faɗa ba zaka gane ba amma ka ƙira Excellency zai maka bayani. Kittt ya katse ƙiran. Excellency ɗin ya ƙira "Alhaji Bashir Dantani!" "Jagaban! Ya aka yi kake kirana a irin wannan lokacin? Akwai wani matsala ne?" Babban ɗan siyasan Alhj Bashir da kowa ke yi wa ganin mutumin kirki saboda tarin kyautatawarsa da taimako na ganin idanu ya faɗa cikin Muryar sanayya mai ƙarfi tsakaninsa da Jagaban ɗin. "Akwai wasu Yarana da aka kama na kira Commissioner da kaina yake sanar da ni dole sai na tuntubeka don shi ma faɗan ya fi karfinsa" Jagaban ya faɗa Muryarsa babu wasa don ba zai so a sake baƙantawa diyarsa rai bayan wanda ta sha ba. "Oh tun shekaranjiyan da aka kama yaran ya sanar da ni yaranka ne amma wannan karon bana tunanin zan iya maka ko wani irin ƙoƙari cikin gaggawa don akwai wanda yayi kane kane ciki da taɓashi daidai yake da lalata siyasata" "Wanene shi? Meyasa ya fi karfinka?" "Shi ɗin idon Al'umma ne, ya fi ƙarfina ne saboda ya fi ni kusanci da al'umma magana marar daaɗi ɗaya a kaina zai iya rusa duk wata gwagwarmayana, bari ka ji Irshad ba mutumin da zan yi over looking bane Dukda na tsane sa with passion saboda na sha nuna son sayarsa ta hanyar kudi da sauransu yayi min campaing ta wurin al'umma yana turning ɗina down, ka ga kuwa ya kira Commissioner sau biyu a kan Yarinyarka Diva muddin ya ga ba'a ɗauki mataki ba zai iya bin diddigi kuma zai samu hannuna dumu dumu so ka ga za mun ɓata goma ne biyar bata gyaru ba" "Irshad!" Jagaban ya faɗa cikin nazari kan ya sake cewa "Wannan malamin addinin? Irshad Al-Noor ɗan masu Twins Enterprises?" "Kwarai da gaske!" Jagaban ya ce "To me zai hana a ɓarar maka da shi idan zai hana mu rawan gaban hantsi kowa ma ya huta?" "Jagaban! Ka bar wanda ya riƙe Allah ka ji, amma dai yanzu ka yi haƙuri a bar yaran nan a rufe zuwa kwana biyu i promise you za su fito kuma za'a kula da su ba za su rasa komai ba, ai na san kalar amfaninsu a wurina bare ma nan da lokaci kankani zan bukace su" Sallama suka yi, sai sunan Irshad Jagaban ke nanatawa. Miƙewa yayi ya ɗauki motarsa ya fita, tafiyar mintuna ya kai shi police station ɗin, shiga ciki yayi ya samu Sohana tana zaune ya kama hannunta suka fito waje har jikin motarsa. "Baaba ya kake fitar da ni ba tare na ga su Pabloo sun zama free ba?" Ta Yi tambayar hannayenta duka cikin aljihu. "Akwai babban dalilin hakan, amma ina so ki kwantar da hankalinki mu je gida zan miki bayani" Ta haɗe gira "Ban gane ba? Kana nufin an fi karfinka a wannan ɗan karamin case ɗin?" A ranshi ya ce ba za ki gane ba Sohana a fili ya furta "A'a ai babu abin da zai fi ƙarfina muddin abin ya shafe yaran nan, mu je gida zan miki bayani" Ba don ta so ba ta nufi motarta ta ja tayi gaba ya bi ta a baya har gida, a parlor ya sameta tana kai kawo har ya shigo ciki. "Me kake nufi Baaba?" Wayanshi ya zaro ya shiga media yayi searching sunan Irshad Al-Noor sai ga hotunanshi iri iri sun fito duk cikin shigar kamala irin ta Larabawa wasu yana kan mimbari wasu yana zaune yana wa'azi wasu yana zaune kawai wuraren taruka da dai sauransu. Idanunta ta sauƙar kan fuskar wayar daidai wani bugawa da zuciyarta ta yi, hannu ta ɗaga ta nuna shi da yatsa muryarta na rawa ta ce "Baaba a ina ka...san shi? Wanene shi a garin nan? Kuma a ina ka san zan sameshi?" "Kin sanshi ne Sohana?" "Shi ne!" "Shi ne wa?" "Wanda ya..." Sai ta shafa kuncinta tana runtse ido "shi ya mareki?" Gira ta ɗaga don kalmar yayi mata mugun nauyi a harshe ba zata iya fitarwa ba idan ta fitar tana jin kaman zuciyarta zai babbake don bacin rai da tafasa. Hannunta ya kama suka zauna. "Then wannan malamin shi zai zama makiyinmu na farko a wannan gaɓar, ba zai fito daga No where yayi ta dasa miki baƙin ciki ba Sohana ba zan zuba ido in kalleshi ba! Shi ya sa aka kama su Pabloo a yanzu daga sama kowa na tsoron tsoma baki don kar ya lalata musu siyasa saboda karfin ikonshi cikin al'umma amma idan sun san wata ai basu san wata ba". Ta riƙe hannunshi. "Ka bar ni da shi Baba" Ya girgiza kai "No! Ki bar ma batun sanya kanki a lamarinshi ni zan ji da komai" Ta Yi shiru kawai ba don ta ji maganan baban ba, a ranta tana nanata sunan Irshad. **** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA GOMA* Daren ranar da abin ya faru ko sau ɗaya bai runtsa ba gabaɗaya bacci ya kauracewa idanunsa, duk tsarinsa na dare ya gama har Adu'a yayi ya kwanta amma da ya rufe idanu sautin sauƙar hannunsa kan fuskarta ke dawo mishi. Bai taɓa yin abin da yake jin damuwa a kanshi ba sai wannan bayan ya natsu sossai da alqur'ani sai ya fahimci bai kyauta ba dukda laifinta ne amma yana ganin bai kamata ta haka ya ɗauki mataki ba, despite his anger he was raised to respect women don ko ɗaga murya wa iyayensu mata basu taɓa ji mazan na yi ba wannan tarbiyar gidan ne, sannan beside that addini ma bai yarda da duka a fuska ba saboda irin darajar da Allah yayi wa fuskar dan adam. That guilt eats him alive. Tsam ya bar gadon ya fita balcony ya tsaya hannunayensa duk biyu zube a aljihun kayan baccin jikinsa idanunsa a lumshe yana shakar iskar da ke kadawa kaɗan kaɗan, lips ɗinshi kuma na ambaton Astagfirullah! Har sai da ya ji sassauci kan ya dawo ko da ya duba time biyu har yayi kawai ya je yayi alwala ya zo ya fara nafila sai da yayi ra'aka shidda ya zauna ya buɗe alqur'ani ya shiga karatu, yana yi ɗin amma har lokacin chan ƙasan ranshi guiltness ɗin na nan, hoton jinin lips ɗinta da kuma idanunta na dawo mishi ya san dole ne suka sake crossing path ya bata haƙuri ba wai don ya ramawa Malam Bala mari ba sai don ya san ya ketare iyakar ubangiji a kanta. Sai da ya ja Sallar asuba kan ya cewa dalibanshi yau babu karatun safe, gida ya dawo ya ɗan kwanta bacci saboda headache da ya matsa masa. Ƙarfe tara ma ya farka saboda rashin sabo da baccin safe ya sake wanka ya sauƙo ya karya da abincin Maamah, yana so ya shiga cikin gidan ya gaishe su amma sai wayanshi ya shiga ringing, ko da ya duba Malaminsa ne daga chan saudia. Murmushi ya saki mai sanyi da ya ƙarawa fuskarsa kyau yayi sliding tare da makalata kunne nan larabci ya tashi, sun kusa awa guda suna larabcewa kan suka yi sallama, sai ya ɗan leƙa media don ganin abin da ke faruwa, karo ya ci da trending topic da aka kwana tattaunawa a platforms, shi ne tsaye dab Wanchan 'yar dabar kaman yadda sunanta yake a wurinshi, daga fuskarta har fuskarshi side view ake gani, ba dankwali kanta kuma sun yi dab kowa ya gani ya san magana yake yi mata. Kan Caption ɗin ya kai idanunsa "Your Sheikh is not what you think he is!" Ya jima yana kallon Caption ɗin kan ya sa yatsarsa ɗaya ya danna comment section anan storm ɗin ya ke, wasu na cewa kila wa'azi yake mata daga gani kaman ba musulma ba ce, a haka ɗin wasu na dragging ɗinshi inda wasu ke kare shi. Idanunsa ya lumshe ya sake buɗewa yayi ƙasa ba zai yi scrolling biyu uku bai ga picture ɗin ba different Captions, babu abin da ya tsana irin fake scandals ɗin nan a kanshi, kowani motsi yayi sai an yada duniya kaman da gayya abin amma bai wani damu ba, ya miƙe sanye yake da farar Thob sai jar Ghutra, kafafunshi wasu takalma ne masu taushi baƙake ya fita daga sashen don ya tabbatar samun albarkar iyayensa da ganin murmushinsu ne kaɗai zai sanyaya ransa a lokacin. Sashen Ammiey ya fara nufa, da sallama ya tura kofar ya shiga. Mufida ce da rukayya sai wasu friends ɗinsu zaune a parlorn suna hira, ganinshi ya sa duk suka natsu kan suka amsa sallamar suka shiga gaishe shi. Amsawa yayi cikin kulawa don yana da wannan dabi'ar na mayar da hankali akan 'yan uwansa, ba wai ya saki fuska ba ne kuma ba dogon surutu ya tsaya yi ba ya wuce ɗakin Ammiey. "Wayyyoooo Mufy yau na taki sa'a...! Ruwa zan zuba ƙasa na shaaaa wayyoo Allahnaa yau na ga Sheikh har na ji magananshi a zahiri" Wata kawarsu Farida ta daka tsalle cikin wani irin murna take faɗa. Ta sha zuwa gidan ba ita ba dayawa cikin kawayensu har da na su Sumayya su kan zo gidan musamman don ganin Shehi wasu su dace wasu kuma har su gama wahalar ko ganinshi ba sa samu su yi. Hafsy ta lumshe ido ta buɗe "Yaaaa Allahu! Wai kun ji wani sassanyar kamshinsa da ya cika parlorn nan!" Farida ta ce "ke ta kamshi kike wai kin ga skin ɗinshi? Kafafunsa tsabar fari da taushi a ido kawai za ki kalla ki rantse da Allah ba ya taka kasa ga wani irin tafiya da yake cikin natsuwa kar ki kai ga idanunsa da ba ya wani kallon kurilla wa kowa....Wayyyoooo Allah" Haka suka ta santi suna wasssafa sa, shi kam tuni ya tsufa gaban Mahaifiyarsa, bayan sun gaisa take ce mishi. "Na ga kuma abin da ake ta yaɗawa, na san halinka farin sani shiyasa ma daga ni har mahaifinka muka zubar da zancen don samun natsuwar zuciyarka, ina so in ce maka ka ƙara haƙuri komai zai wuce watarana wannan jayayyar da ake yi wa duk wani motsinka zai zama tarihi" Ba kowa ne zai gane abin da ke ransa ba amma dayake ita uwa ce ta san ya fi kowa tsanar abin da ke faruwa da shi, wannan media ɗin na zama sanadiyar traumatizing mutane dayawa, fake rumors da scandals ɗin idan suka yi yawa suna farautar natsuwar mutum, amma da yake shi ɗin ya riƙe Allah sai ya kan samu sassauci ta wani ɓangaren, so ake a ga ya tozarta ba ya kuma Fatan Allah ya kawo wannan rana. "Allah ya sa Ammiey jazakillahu khairan" Ta Yi murmushi. "Sai batu na gaba!" Ya ɗaga kai ya ɗan kalleta daga fuskarta ya san abin da zata yi magana a kai, kanshi ya mayar ƙasa aiko dai sai ji yayi tana cewa. "Akwai Na'ima ɗiyar Hajiya Hadiza kawata mahaifinta Ustaz Abdallah na san ka san shi" Kai ya gyaɗa "To ita Na'imar na yaba da hankalinta, yarinya ce marar hayaniya, kyakyawa kuma mahaddaciyar alqur'ani ce da littatafai idan ka samu lokaci ina so ka je ku gaisa, zamanka haka ɗin nan yana damun gabaɗaya zuri'ar nan" Bashi da halin musu! Ammiey ce ke ba da umurni don haka cikin kwantar da kai ya ce mata "In shaa Allahu zan samu lokaci in je" "yauwa Allah ya yi muku albarka, Allah ya haɗe kanku ya cigaba da kare mana kai" Murmushi mai kyau ya saki don adu'ar nan ta fi masa duk wani kyauta na duniya. "Ameen ya rabbi" Ya amsata kan ya miƙe. "Na bar ki lafiya Ammiey" Daga haka ya fice, wurin Maamah ya je itama sun yi hira kaɗan ta mishi nasiha da ƙara ban haƙuri akan rayuwa don wani faɗar Allah da annabi ma da zaka yi haushi kake ba sa. Daga nan ya isa wurin Daddah suka gaisa tayi ta mishi Adu'o'i yana amsawa ya ce mata akwai tukwicin adu'arta zai turo mata, tayi murmushi tare da Binshi da ido har ya fita. Ta rasa dalili amma a ranta duk cikin jikokinta babu wanda take yi wa ƙaunar da take yi wa Irshad, tana kuma jin tsantsar tausayinsa shi ne mai gudun duniya amma shi duniya take bi dama haka rayuwa ta gada. "Daddah kina ƙaunar yaron nan, shiyasa kika ƙi matsa masa batun aure ga mata nan iri iri daga nan har Gembu kowa na miki tayi a yi haɗi yadda aka saba kin ƙi" Ta kalli ɗiyarta kuma goggon su Irshad ta ce "Hindatu shi Shehi ba irin mazan da za'a musu dole a abu ba ne darajarshi ta wuce nan, baki ganin kyautar da Allah yayi mana a kanshi? Muna nan zaune Shehi zai kawo macen da za ta bamu mamaki don na tabbatar ba lallai a matan Fulani ko hausa a samu mai irin ilimi da kuma hange da yake so ba sai dai kila Labarawa" "yanzu sai ki barshi ya auro balarabiyar ya kawo?" "Meyasa zan hana? Ba musulmai ba ne?" Ita dai Hindatu bata ce komai ba amma a kufule take ta rasa Meyasa Daddah da mijinta tun kan su rasu ma suka zama cikin Fulani masu ilimin addini da kuma hange su sam ba sa kyamar wani yare kaman yadda cikakkun Fulani suke yi, har ga Allah ko iyayen su Irshad da Ammar an auro sun ne kawai amma dangi na Gembu da ma su Goggo Hindatu duk ba so suke ba amma Alhj Hardo ya fi su iko dole suka haƙura gashi yanzu Daddah tana so ta musu bukulun wanda suke harin ma ya dawo cikinsu ya ɗauki mata. Tashi ta yi ta bar parlorn ta koma daki wurin 'yar uwarta suka dasa mita akan lamarin Irshad ɗin, gani suke kowa tsoronshi yake shiyasa ake kaffa kaffa da shi, ko ɗaga mishi murya ba'a yi sai dai lallami da maganar hankali to yaushe ma yayi abin da za'a daga Muryar banda abin su? Ko da ya isa ɓangarensa shiri yayi don daga an yi azahar akwai wani lecture mai muhimmanci da zai bayar, tsaff ya fita a babban Malaminsa, mai hasken kamala, yana saukowa sai ga Imamu ya tattare gadgets ɗinsa suka yi masallaci, bayan gabatar da Sallar azahar ya zauna kujerar wa'azi, bayan godiya ga Allah da kuma cikakken sallama wa al'ummar musulmi ya kalli camera ɗin ya fara magana... "Karatun mu na yau sunanshi Riga-ka-fi, kaman yadda duk muka san yanzu zaɓe na gab da ƙaratuwa zan yi magana ne a kanmu mu 'yan arewa... Yan arewa ya kamata a ce zuwa yanzu duk mun farka, lokaci ne ya yi da za mu haɗa kai wurin gina kawunanmu da kanmu, al'umma su ke da alhakin zaɓar duk wani shugaba da zai wakilcesu, amma mene? Tarin bayin Allah za su fita dubbani, kwansu da kwarkwatarsu su sha rana, su yini a layi wurin ganin sun ka da kuri'unsu suna gama wannan wahalar daga zarar buƙata ta biya wannan amana da aka bashi na zaɓarshi zai yasar, wannan wakili ko shugaba zai tafi yana amfani da iyaka tunaninsa da kwakwalwarsa babu abin da ya shafe shi da me waennan bayin Allah da suka zaɓeni suke buƙata? Me suke so ko nema wurin gina tasu rayuwar? Saboda haka 'yan arewacin Nigeria akwai babban aiki a kanku na tirjiya da cewa baku yarda ba sai dai ku zaɓi wanda kuke so ya wakilceku kar ku bari a zaɓa muku ko a yi wasa da tunaninku, abin takaici tsabar an mayar da al'umma marasa tunani ɗan siyasa ne zai wakilta wani ya bi Layin zaɓe yana miƙa ɗari biyar ko ɗari biyu yana saye kuri'unku kuna dangwala masa alhali kun san future ɗinku da na 'ya'yanku kuke rushewa na iya shekarun da zai yi da karbar wannan dari biyar din, wani yunwa da wahala zai sayawa kansa tun daga barin gaban wannan Akwatin zaɓe har wasu shekaru huɗun masu zuwa idan ba sa'a ba yunwar ce zata yi ajalinsa. Idan har baku gyara ba har abada za ku zama cikin tankade da rairayar ra'ayoyi da ake yi ba ku da mutanen da za su je su fitar da naku ra'ayin. Ku tsayawa kawunanku da kanku ya ku al'umma kuma ku dage wurin roƙon zaɓin Allah a komai na rayuwa, ku kasance masu duba zuciya ba kalaman baki ba." Ya ɗan dakata tare da ɗaukar ruwa da ke gefensa ya ɗan kurɓa ya ajiye.... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA* "Babban Abin baƙin ciki ne idan kuka yi duba da tarin kudaden da ake fitarwa da sunan sayan wannan form na takara alhali dayawa sun san ba ci za su yi ba, waɗansu 'yan uwansu suna cikin wani hali, waɗansu iyayensu, waɗansu makotansu, waɗansu hakkokin wasu ne ma rataye a wuyoyinsu ba'a sauƙe musu ba. Mutumin da za'a je neman taimakon gina wani masallaci ko islamiyya wani ma ɗan uwansa na kusa kusa ne ke cikin matsanancin ciwo da bukatar wadannan kudi amma ya gwammace ya cire kalilan ya bayar ya ajiye saura don sayan duniya cikin zuciyarsa kuma ba alkhairi ba ne a kan hakan. Wallahi Allah ya ce 'Lallai wadanda suka kafurta suna kashe dukokiyoyinsu ne domin su toshe da barin hanyar Allah, za su kashe dukiya mai yawa sa'annan daga baya su kasance masu nadama, sa'annan a kashe su kuma ba za su samu riba a duniya ba kuma su je lahira su samu tambayoyi iri daban daban' Duk mai neman takara zai rufe ido don neman kuɗi ko ta wani irin hali ko hanya, suna yi kaman domin Al'umma ne alhali karya ne domin kawunansu suke yi da ribarsu wanda ba zai amfane su da komai ba a ranar gobe. Da mun san hatsarin da ke cikin mulkar al'umma da duk mun guje wa ko wani irin mulki ina ƙara jan hankalin shuwagabanni da su yi mulki kan gaskiya da amana su ji tsoron Allah su sani babu wani motsi nasu da ba za'a rubuta shi kuma a yi musu tambaya a kai ba ranar gobe." Sossai ya ja hankali ya kuma yi nasiha kan zaɓen da yake ta karatowa ana ta rigimgimun jam'iyyu da 'yan takara, musamman ya sake jan hankalin mutane akan shugawabannin da suke ci a yanzu kuma suke da niyyar komawa ya nuna musu tunda da hankalulansu jikinsu wanda yayi musu sun sani wanda bai yi musu ba ma sun sani, a shekaru huɗun farkon nan ya kamata al'umma su san zafin kansu kuma su yi wayon tawaye ga duk wanda ya shafe su bai yi musu aikin komai ba, daga karshe yayi Adu'a aka tashi daga wurin wa'azin ranshi duk babu daaɗi saboda irin matsaltsalun da ake fuskanta a kan shuwagabanni a arewacin ƙasarmu. Washegari da safe misalin ƙarfe goma ya samu ƙira daga secretary ɗin Excellency Bashir Dantani. Ɗagawa yayi suka gaisa cikin mutunci kan ya sanar da shi akan Excellency na neman shi, Bashir Dantani gomna ne da ke ci a lokacin kuma yana kan tenure ɗinshi ne na ƙarshe ya dandani gardin mulki da rudin duniya yayi iya zaluncin da zai yi a bayan fage a yanzu kuma ya sayi kujerar Senator mai wakiltar arewa da fatan al'umma su sake zaɓarshi ya ƙara gaba, ya gama kwankwadar giyar mulki kuma babu abin da baya yi wurin ganin ya samu duk wata kujera da ya sa a gaba. "Excellency na gayyatarka zama na musamman da shi a ofishinsa" Ya gyara zama tare da rufe takardar da yake dubawa. "Ba ni da wannan lokacin" Yana kai nan ya katse ƙiran don babu wani ɗan siyasa da ya isa ya kai kanshi gabanshi ko ya duƙa mishi, idan yana buƙatar shi zai iya zuwa ya same shi a inda yake amma ba wai ya saka shi dole zuwa wurinshi ba. Miƙewa gabaɗaya yayi ya shige ɗakinshi don shirin tafiya BUK akwai lectures da zai ba da. Ta ɓangaren Diva ta yi kaman ta manta ta cigaba da harkokin gabanta, ta kan je ta duba su Pabloo, tabbatar mata da suka yi basu da wani matsala ya sa hankalinta kwanciya don kaman a gida suke babu abin da suka rasa, haka ɓangaren Zubash khadija na ta samun sauƙi amma ba hakan ba ne ya sa zubash ɗin chanzawa hasali ma kara kaimi tayi a kan harkokinta na samun kudi. A bayan fage kuwa gabaɗaya Rayuwar Diva ta ta'alaka shi ga Shehi, duk wani motsinshi, tsarinsa da yadda yake tafiyar da jadawalin rayuwarsa kusan ta san komai da komai, ta san a ranar Litinin BUK yake shiga lectures a Arabic and Islamic department, tuesday da thursdays yana shiga Katsina inda nan ma yake visiting lecturer a arabic and Islamic department Alqalam university iyakaci ya tafi da safe ya dawo da rana Kasancewarsa azumin Alhamis da Litinin basa wuce sa baya taɓa kaiwa Magrib inda ba gida ba a irin ranakun, ranakun Laraba yana shiga dutse Jigawa a nan ma lecturing yake yi ɓangaren arabic and Islamic, juma'a, Asabar da Lahadi su ne ranakun kansa Dukda a cikin waɗan chan ranakun ma idan baya makarantun yana wurin wani wa'azi, taro ko karantarwa, yinin juma'a gabaɗaya a gida ya fi yawan yinsu don tun sha ɗaya yake fita masallacinshi har dare yana nan, Asabar da Lahadi kuma mafi yawan lokutansa na dalibansa ne. Duk sai da ta san komai hatta da 'yan gidansu a bincikenta, tana so ta mishi abin da zai matuƙar yi masa zafi amma bata son wani ya ɗaukar masa raunin. Satin su Pabloo biyu aka sake su aka rufe case ɗin aka ma jefar da file ɗin kaman ba'a taɓa buɗe shi ba, (ƙasarmun kenan, daga lokacin da abu ya faru da zafinshi xa'a yi kaman za'a ɗauki mataki mai girma amma daga ya kwana biyu ya lafa sai komai ya wuce kowa ya koma rayuwarsa a manta da akwai waenda aka zalunta, hukumomi sun manta da ayyukansu sun dawo suna bautawa mulki da arziki. Allah ya yi mana mafita) Tun dawowar su Pabloo basu gane kanta ba don bata fita da kowa, haka babu wanda ya san me take planning Dukda Shaly ta saka mata ido amma ta kasa gane kan Diva ɗin don ko magana bata cika yi musu ba sai ta zauna kawai lost ɗin thought zuciyarta bai daina karta ba Dukda raɗaɗin marin ya wuce tun ranar amma ya bar tabon da ya kasa mayar da Diva daidai, tunaninta kawai yadda za ta dauki fansa mai muni bata san cewa wannan fushi zai haifar da ɗa marar ido ba. Satinta uku tana bibiyarsa, a yau tun karfe 10 ta shiga ɗakin taron da ta tabbatar zai zo, taro ne na hafizai waenda suka haddace alqur'ani su goma sha biyar, musamman a yanzu take yawo da Abaya a mota saboda irin hakan don yanzu wani Black Dubai Abaya ne jikinta ta zagaye fuskarta da gyale ta saka baƙin glasses rabin fuskarta, duk wanda ya santa da zai ganta ba zai gane ma Diva ba ce, ba ma zaka ce wannan ɗin 'yar daba ba ce, kaman ta sani bata jima da zama ba sai gasu sun shigo yana cikin manyan baƙin taron, aka rakashi har wurin zamansa ya zauna, an bude taron da Adu'a aka fara gabatar da jadawalin taron kunnenta ma airpods ne duk abin da suke cewa ba ji take ba. Abu ɗaya ta san ta saurara yadda ake khatma ɗin, karatu ne yaran da ba su haura ashirin ashirin ba suke yi da ya tada tsikar jikinta lokaci guda, idanunta da suka juye ta runtse da ƙarfi tana sauraron yadda karatun ke ratsa zuciyarta, idan ta yi karatu to na sallah ne su ma ba sa wuce qulhuwa, falaki da nasi. Ba Za ta ce ma akwai Alqur'ani gidansu ba. Zuciyarta ya cigaba da wani irin hautsinewa, a hankali ta buɗe idanunta ta kai kansa jin ana ambaton sunanshi zai ba da nasiha. Karɓa yayi cikin natsatsiyar Muryarsa yayi sallama ya fara gabatar da wa'azin da ya tsuma kowa, yayi magana kan falalar Alqur'ani, yayi albishir wa iyayen mahaddatan cewa ubangiji yayi alkawarin ɗora su kan kujerun zinari a yi zagaye da su a ranar gobe sakamakon tsayawa da suka yi kan yaransu wurin zama mahaddatan, ya ja hankalin su mahadattan da yawan tilawa saboda shi qur'ani idan ka barshi na kwana daya zai barka ne na kwana goma, hakika ya girgiza hazo don wasu yaran sun kudiri niyyar dagewa, wasu iyayen da yaransu ba sa makaratun haddar sai boko zallah sun ji kwaɗayi da sha'awar wannan hidima da ubangiji yake yi wa mahaddata da iyayensu, ita kam ba za ta ce ga halin da ta tsinci kanta ba. Ta dai ji ba zata iya cigaba da sauraro ba, fita ta yi da sauri ta nufi motarta ta shiga ta zauna tana sauƙe numfashi, wani irin zafi zuciyarta ke mata, runtse idanu tayi sai nasihar da yayi mata akan rayuwarta ya shiga dawo mata, rigar jikinta ta cire ta wullar tare da gyalen ta chusa hannu a gashinta tana hautsinawa, damke sitiyarin ta yi ta ɗora goshinta kai zuciyarta na wani irin ƙuna sai dai bata jin za ta zubar da hawaye don neman sassauci, gefenta kawai ta duba ta ɗauko wani kwaya ta haɗiye kan ta kunna motar ta fice daga harabar hall ɗin cikin matsiyacin gudu. Ranar Lahadi biye da su take kaman kullum bayan isha'i ne, wurin wani taro ne ta ga sun shiga ta yi parking ta ɗauki glass tube da ta zuba kwayar (Ice) ciki saboda idan ta sha ta kan zama very aggitative, shi kaɗai ne ke sakata zama restless har sai ta aikata duk abin da ta kudurta a ranta, lighter ta kunna a ƙasan glass tube ɗin tana zukar ice ɗin da baki, ta jima zaune bayan ta gama bugar da kanta ta zaro Double chiffon Abaya Brown ta ɗora kan riga da wandon da ke jikinta, kunna motar tayi ta ƙarasa ciki ta zame hular kanta tayi rolling gyalen kan ta fito ta shiga wurin taron, a yau ta yi niyyar kawo karshen komai don ta gaji da bibiyar rayuwarsa haka. Tana nan zaune tana gadinsa kafarta ɗaya take ta karkadawa idanunta sun ƙara girma kuma sun sauya, ta ci sa'a ya ɗaga wata waya mai muhimmanci ya tashi ya fita daga dakin taron, zuruf tayi ta fice itama ta zaga ta kofar da ya fita, ya koma ɗan baya inda babu ƙarar speaker don jin abin da na ɗaya ɓangaren ke cewa, cikin kamalarsa yake fitar da maganan yana nan tsaye hannunsa ɗaya a goye a baya, kaman an ce ya ɗaga idanu sai suka faɗa kanta tana tsaye babu wani tazara tsakaninsu sossai, Dukda ba tarr yake kallonta ba idanunsa sun kusa seconds goma a kanta kan ya fahimci ita ce dama ya raya a ranshi sai ta nemeshi. Ta cire duka boturan Abayar yana iya kallon wandon jeans da farar rigar da suke ciki, a hankali ya bi hannunta da kallo wuka ne take riƙe da tsirararsa yana walkiya kanta babu ko gyale ko hula gashinta na ɗaure daga tsakiya, idanunsa ya ɗan sauƙar sai kuma ya kawar daga kanta gabaɗaya yana ta'awizi. Sai ya nufi inda take tun kan ta nufo shi yana sauƙe wayan, dab ita ya tsaya, kamshinshi na gauraye numfashinta, abin da take so da burin gani a cikin idanunsa na tsoro ko shakkarta bata ga ko ɗaya ba sai ma ita da yake shirin karyawa alkadari, wuƙar ta damke tana datse hakorinta hannunta na rawa ba na tsoro ko shakka ba sai na zafin da ya tara na kusan wata guda don samun wannan opportunity na ɗaukar fansa a kansa, sai yayi murmushi mai sauti kaɗan. "Yau ko ni ko kai!" Ta faɗa a fili cikin wata kalar murya tana kallon cikin idanunsa da nata marasa tsoro. Idanunsa babu firgici kwata kwata sai ma cewa da yayi cikin natsuwa da sanyi "Da ma na san za ki zo." Ya ƙarasa yana sake karantarta, idan bai ce ya ji bakin cikin ganinta a Buge ba yayi ƙarya, matasanmu suna lalata rayuwarsu a banza suna ɓata future ɗinsu yanzu ina amfanin wannan? Sai kalamanshi suka ƙara tunzura zuciyarta, hannunta ta ɗaga rike da wukar tana nuna shi ko ɗar bai yi ba Dukda ya san tana iya cutar da shi ɗin kawai ita ɗin bata kai ya ji tsoro ko shakkarta ba ne, a lokaci ɗaya wani ɓari na zuciyarsa na mamakin irin karfin halinta, duk rayuwarshi tsawon shekarunshi ba zai ce akwai macen da ke iya sanya idanunta cikin nasa ba tare da zuciyarta ta girgiza ba, a idanun wannan ba ya ganin komai sai zarrah da rashin tsoro, tabbas ta gama kangarewa ko ma babu zuciyar gabaɗaya a ƙirjinta bare idanunsa su firgitata ko su sanya mata kwarjininsa kaman yadda suke sanyawa mata da mazan da za su yi arangama da shi kila kuma saboda bata cikin cikakkiyar hankalinta ne. Cutarwa na gaske take shirin yi masa. "Ka san me ka yi min? Ka yi abin da ba zan iya yafe maka ba, ka yi sanadin da nake jin muddin na kyaleka ban amsa sunan DIVA ba, a yadda na zuƙi Para ɗin nan yau ko ni ko kai na sake faɗa..!" Fakonshi tayi ta kai wuƙar da iyaka zuciyarta na son cutar da shi cuta mafi muni da wani irin niyya da bata taɓa ɗora hakan a kan kowa ba na son dakatar da fitar numfashinsa saboda yanayinshi ƙara tunzura zuciyarta yake zuwa turiri. ******** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA GOMA SHA BIYU* Cikin hanzari ya riƙe wuƙar wanda take ya yanke hannunsa jini ya shiga zuba, da ƙarfi ya riƙe hakan ya sa ta kasa fusga sai idanunta ta zubawa nashi da suka rine zuciyarta na wani irin bugu da ta rasa na jin daaɗi ne ko na menene? "Yanzu aka barki sai ki kashe ni?" Tambayar ya zo mata wani iri ga idanunsan nan masu cike da masifar kwarjinin da bata taɓa ganin irinsu ba tsaye cikin nata kaman da gayya ya zuba mata saboda sanin tasirinsu da kaifin su ga duk mai kallon cikinsu. "Kana raina abin da Diva za ta iya aikatawa kenan, sake wuƙar ka ga idan ban tsayar da numfashinka ba." "Baki tsoron haɗuwarki da ubangiji a ranar gobe? Baki tsoron abin da zai iya biyowa baya? Wace irin kangarewa zuciyarki tayi da baki tunanin komai sai na zalunci? Kin san makomar ki kuwa da zarar kin kashe rai?" Jikinta tsuma yake yi Dukda tana jinshi amma ba har chan ciki ba saboda already kwayar da ta sha ya ɗauki effect. Shi kuwa har ga Allah tausayi da wani irin karaya akan tarbiya ne ya rufe shi, menene amfanin wannan rayuwar, motsa wuƙar da ya riƙe ta yi wani irin azabar zafi ya ratsa har kwanyarshi da ya sa ya saki wuƙar ta faɗi ƙasa saboda itama ta saki, saurin duƙawa tayi za ta ɗauka ya sa kafarshi ya taka ta ɗago tana kallonshi. A karo na biyu ya nufi yi mata nasiha bayan haƙuri da ya kudurta zai bata "A cikin littafin tirmizi an ibn Abbas (RA) Manzon Allah yace mutumin da aka kashe zai zo da wanda ya kashe shi a ranar alkiyama, wanda aka kashe zai riƙo gashin kai da goshinshi yana janyo shi jiyoyinshi a waje suna zubar da jini har wurin Allah madaukakin sarki zai ce ya Allah ka tambayi wannan me na mishi ya kasheni? Sai dalibai suka ce idan ya tuba fa? Man qatala mu'iminan muta'ammidan.....sai ya ce wannan aya tana Nan ba'a share ta ba ba'a sauya ta ba duk wanda yayi kisan kai da gangan sai ya dauki zunubinsa na har abada.." Ashe baki tsoron gamuwarki da Allah cikin wannan yanayin?" Zuciyarta rawa yake da ta rasa dalilin durkushewarsa, kafafunta sanyi ne ke shigar su tamkar wacce aka jefa cikin tsakiyar ƙanƙara sai kuma a hankali kwakwalwarta ke juyawa a saninta bata da imani, Meyasa mere kalaman bakin wannan ke neman rushe duk wani ƙwarinta? Ya taka da kafarsa ɗaya gabanta yana kallon cikin idanunta da tsantsar gaskiya a kan harshensa da ya tafi ya ratsa zuciyarta ya furta "Idan har don na mareki ne kike neman ɗaukan haƙƙin raina ki rataya a wuyanki ki yi haƙuri! Ina baki haƙuri daga zuciyata bisa kuskuren da na yi..." Waennan kalmomi guda uku na ki yi haƙuri su suka rusa ta gabaɗaya zuwa ƙasa, hawayen da bata san daga ina ba suka cika kurmin idanunta. Tabbas raɗaɗin abin da yayi mata bai kauce nan take ba domin rauni ma yana da nasa lokacin warkewar amma tabbas ta ji saukin nauyin zuciyarta. Dayawa ɗora waennan kalamai kan harsunanmu sun yi mana nauyi. "Shehi!! Shehi!!!" Muryar Ammar ne ke kiranshi don shirun yayi yawa hakan yasa ya biyo bayansa, sauƙe idanunta tayi bata yi magana ba ta zubawa hannunsa da ke ɗigar jini. Hannun ya ɗan kalla ya ɗago sai suka haɗa idanu. "Leave!" Ya faɗa a hankali don ba ya so Ammar ya zo ya sameta wurin, duk wani bibiyar rayuwarsa da take yana so ya ƙare anan, ba kaskantar da kai ba ne a wurinshi kalaman da yayi mata yayi hakan ne saboda duk wanda ya san rayuwa ya kuma san duniya ta fuskar ilimi ba ya barin mutane su zama abokan gabansa, ko da ko akwai wanda ke gaba da shi ma zai yi kokarin chanza sa domin ya dawo masoyinsa makiyinka zai iya zama mai matukar amfani har ma ya ceceka daga cikin wani bala'in shiyasa ake son kyautata zato da alaqa da kuma zamantakewa a dabi'ance da kuma addinance. Ko kan Ammar ya iso ta bar wurin, duƙawa Irshad yayi ya ɗauki wukarta da ta bari nan ya naɗe a hanky ya saka cikin aljihu. "Innalillahi wainna ilaihi rajiun Irshad! Me zan gani haka? Me ya faru?" Ammar Yayi maganan yana kamo hannunshi. "It's an accident ba wani Big deal ba ne in shaa Allah" Zai yi magana Irshad ya wuce daidai suna zagayowa ta enterance na hall ɗin motarta na ficewa daga wurin. Ammar malam bala ya kira a waya akan su zo su kai Irshad asibiti. Duk yadda suka so su samu wani bayani ma ko magana daga bakinshi bai ce komai ba kuma sun san ba zai ce ɗin ba ne tunda bai faɗa ba tun farko. A haka suka yi asibiti aka shiga yi masa dressing na ciwon da kokarin tsayar da jinin. *** Dukda yadda ta fito cikin rashin sanin yanayin da ta ke ciki hakan bai hanata sake sauƙe idanunta kan jar motar da ta kula yadda take tailing Irshad haka shima yake tailing ɗinta ba, bata damu ba don ta san kila Jagaban ne da wannan aiki don haka da wani irin speed ta isa gida. Ko da ta shiga parlor baya nan, ɗakinshi ta je ta yi knocking... "Sohana! Lafiya kuwa na ga yanayinki wani iri?" "Baba ba na ce ka kyale min Irshad na san yadda zan yi da shi ba? Then Meyasa ka tura mutanenka suke bibiyata?" Da ɗan mamaki ya ce "Ban tura wasu mutane su bibiyeki ba Sohana, tun da kika nuna kin fi son handling situation ɗin da kanki na bar zancen" "Then Meyasa sai ta hanyana suke gane inda Irshad ya nufa?" Ta faɗa da mamaki don ta san babanta ba zai mata karya ba. "Ko kuma su ma wani abin daban suke bibiya dangane da shi ba, idan dai har kin fahimci shi suke bibiya ina zaton su ma da nasu 'yar tsamar da shi" Kai ta gyaɗa kawai ta juya ta nufi ɗakinta, a yadda ta ke ta tsaya ƙasan shower babu abin da ta cire saboda yadda take jin wani kunci a ranta, kaɗaici ya ziyarci jikinta Dukda tana zagaye da mutane amma ganin shadows take yi musu basu da wani impact a rayuwarta... Ko da ta fito bata ji daidai ba sai da ta bugu iya buguwa kan ta zube sai bacci kuma. *** Zubash ce zaune ɗaure da towel bayan ta fito wanka tana gyara jikinta, matashin saurayin mai ji da kuɗi ya zuba mata idanu. "Kina da kyau" Ta kalleshi ta madubi ta san tatsuniyar gizo dai ba ta wuce ta ƙoki don haka ta ce. "Na sani" Yayi murmushi "kowani irin magana kina da amsar ta" "hakan ce daidai da ma" "Zuby wlh tallahi da za ki amince da na aureki" "ko?" Ta faɗa tana sanya kayanta. "Da gaske nake yi komai kike so zan yi miki shi muddin za ki killacemin kanki ki zama matata wallahi ba zan kama ki da laifukanki na baya ba" Hannun da ta miƙo masa ya riƙe ya ja ta ta zauna gabansa suka zubawa juna idanu "Sallameni Khalil in wuce, aure ne kake so ka je ka nemi wata ban shirya aure yanzu ba" Ta faɗa tana Miƙewa, a kalaman ta ya jiyo zafin ƙasan zuciyarta daga furucin. Zai kara magana ta juya kawai ta fice. Yana da account number ɗinta don haka yayi mata transfer ɗin kudi masu kauri. Da kafa take ta tafiya hawaye na zuba mata duk dakiyar zuciyarta bata jin za ta iya danne hawayen. "Rayuwar da Mama ta zaɓa min kenan kuma shi zan yi har sai ta fahimci kuskurenta, ba zan taɓa tafiya in bar Nana ta faɗa irin halin da na faɗa ba..." Hawayen ta share ta tari machine zuwa gidan Jagaban, jin Diva bata available suka baje a wurin suna lido da shaye shayensu ana ta shiga da fice na sayan kwayoyi da sauransu. Wani irin jiniya ne ya karade unguwar kan ma kowa ya motsa a gidan wasu jami'ai suka fara shigowa da gudu gudu. Babu wanda ya tsorata ko ya firgita har sai da suka shiga cikin parlor suna bincike, abunsun bai taɓa kai wa nan ba kuma sun tsatsare su da bindigu manya a hannayensu. "Ina shugabanku?" Biggy ya ce "Baya nan" "Ƙarya ne! An tabbatar mana yana cikin gidan nan ko ku fito da shi ko mu shiga mu fiddo shi da kanmu" Ɗayan ya faɗa, babu wanda ya sake magana suka nufi dakunan gidan suna tura murfin farko, na Diva suka buɗe mutum uku suka shiga suka kunna haske ta bayyana a gabansu... ******** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA GOMA SHA UKU* KAUYEN CHEDIYA KARAMAR HUKUMAR TSAFE ZAMFARA STATE NIGERIA Duƙunkune suke a ƙasan gadon su rai huɗu ƙarar harbe-harbe da ya karade garin shi ya saka suka dunkule tamkar kifin gwangwani wuri guda ko motsin kirki babu mai kataɓus na yi. "Inna fitsa..." Da hanzari mahaifinta ya sa hannu ya danne mata baki, da hannu wacce ta kira da Innar tayi mata alama da ta yi a wurin jikinta na rawa ta saki fitsarin haka har gari yayi haske tarrr suna cikin wannan yanayi sai da suka ji motsin mutane kan suka fito jiki duk gajiya. Hawaye Inna da Baba suke share wa har yaushe wannan fargaba zai bar su? Har yaushe za su kwanta a kan gadajensu su yi bacci cikin salama? Babu mai iya cewa uhmm ko uhmm inna ta kama yanmmatan da duk suke ɗigar fitsari ta musu wanka, a lokacin Baba yayi alwala ya gabatar da sallah cikin kuka da roƙon ubangiji na ganin karshen musibun da suke fama da shi a kauyen na 'yan bindiga. Bayan sun yi wanka suka yi sallah inna ta fara kokarin haɗa wutar da za ta dama musu kunu. Baba kuma wani kullin leda ya saka a gabanshi yana aikin kallo zuciyarshi babu abin da bata raya wa. "Atika! Yau ne fa muka yi da mutanen nan" Inna da ta gama ɗora ruwan zafin ta dawo ta zauna kan wani dutse gabanshi idanunta na kan yanmatan guda biyu da babbar bata haura 16 ba karamar ce za ta yi goma sha uku zuwa sha hudu ta ce "Malam ko za mu mayar musu da tallafinsu, ni dama tun chan hankalina bai kama ba wallahi sai in ga kaman duk wuya duk tsanani gwara a ce suna a gabanmu" Ya girgiza kai "kin san lamarin mu ƙara ta'azzara yake Atika, gomnati babu ruwansu azzaluman nan a kan idon iyaye suke haikewa yara kananu wallahi ba zan iya jurar ganin abin ya zo kan 'ya'yana ba, ko babu komai sun yi alƙawarin saka su makaranta kuma su ma za su samu rayuwa mai kyau ba kaman mu anan ba" Numfashi ta sauƙe hawaye na zuraro mata, rayuwar da suke ciki ya tsananta, babu sakewar zuwa gona ko kasuwa, makarantu a rufe ana fargabar tura yara, idan kana so ka yi ko noma ne sai ka je ka yi yarjejeniya da su rabi da kwatar abin da za ka shuka nasu ne kwata ne naka shi ma a wulakance za su bar maka. Rayuwa duk inda suka juya babu daaɗi a kauyen, wani abu da mutanen mu kuwa gani suke nan ne gidansu nan ne marayarsu, nan ɗin ne dolensu duk wuya duk tsanani ba za su iya barin garin ba. Sallama da aka doka a kyauren gidan ne ya dawo da dukkansu tunanin da suka shiga. Baba ya amsa wasu mata biyu sanye da hijabai har ƙasa suka shigo cikin fara'a suka shiga gaisawa da jajen abin da suka samu na Shigowar 'yan bindiga jiya kauyen. "Idan ba matsala za mu wuce yanzu saboda kar su san da zuwanmu" Hakane ko baƙo ne ya shigo gari akwai awannin da idan ya haura zai iya shiga cikin hatsarin kidnapping don waennan mutane suna da idanu da kunnuwa cikin gari. "Ma'u, Jidda yehe hose kare mun un dillah, Allah Lamido renu mun wanne mun barka" (Ku je ku ɗauko kayanku ku zo ku tafi, Allah ya tsare ya kiyayeku duk inda za ku shiga yayi muku albarka) Miƙewa suka yi jiki a sanyaye zuwa ɗakin su kowacce ta ɗauko 'yan tsommokaranta cikin ɗankwali. "Inna... Tafiya za mu yi mu bar ku?" Jidda ta faɗa sai kuka, Innar ma kuka take amma da gaskiyar malam barin kauyen nan shi ya fi musu alkhairi. Rako su suka yi har jikin wata coaster ashe ba su kadai ba ne 'yan mata sun yi sha biyar kowacce da kayanta a ɗankwali suma suka bi ayari suka hau suka zauna a tare suna rungume juna. Haka sai da suka haɗu tass kan bayin Allahn nan suka yi musu sallama suka fice da yaran daga garin. Tafiya iya tafiya suka yi, da suka yi nisa dai an tsaya an ba su pure water da bredi amma daga Ma'u har jiddah kowacce na rike ne da nata. Ita Jidda ji take a ranta cewa wannan tafiya ba daidai ba ne, duk nan iyayensu sun ba da su ne don su yi rayuwa mai kyau ba kaman na kauyensu ba amma tana jin uneasness akan tafiyar, mutanen sun ce daga wata ƙungiya ne na malamai da suka kafa don taimakon irin yaran garuruwan da zaman lafiya yayi musu karanci, za su yi karatu kuma za'a koya musu sana'ar hannu da har za su iya dogaro da kansu, za su na zuwa gida duk bayan wata uku, har form sun cike. Jidda ta ɗaga idanunta ta kalli garin da suka shiga da bata sanshi ba, ta dai san akwai tarin mutane kwarai, akwai kasuwanci na ta tafiya, akwai hayaniya sossai anan ma sun tafi sossai kan suka isa wani gidan sama a cikin wani unguwa dake lungu sossai. "Ku sauƙo" Matar da ta zago ɓangaren su ta faɗa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya har suka kare su goma sha takwas. "Mu je" Wasu maza na daga bayansu matan sun shige gaba har kofar gate ɗin suka buga aka buɗe ganinsu ya sa mutanen suka matsa suka shige ciki, Jidda na bin halittar da bata taɓa ganin irin sa ba da ido, sun fi yanayi da yadda ake fasalta samudawa ga tsawo ga kwanji, bouncers ne da ke gadin gidan, gate uku suka wuce da irin waennan mutane kan suka shiga cikin matsatsen gidan, mata ne kusan duka suna ta hada hada, abin da ya fara buga zuciyar su Jiddah ganin yadda yan mata ke ta shaye shaye. Ma'u ta damke hannun jiddah jikinsu na rawa. Wani mutum ne ya zo ya lissafa su kan ya raba su gida biyar Allah ya taimaki su Ma'u ba'a raba su ba aka nuna musu inda za su shiga, suna shiga dakunan duk aka bi aka rurrufe da kwado hakan ya sake tsinka su. Ma'u da ta fi Jidda jin tsoro ta fara kuka, Jidda taje ta na buga kofar amma har suka gaji suka fadi a wurin basu ji motsin komai ko kowa ba, kaman 'yan prison haka suke yashe a ɗakin jiddah maƙale jikin 'yar uwarta. Sai dare aka kawo musu abinci babu wanda ya motsa har aka ajiye aka fita, Ma'u tace cikin dasashiyar murya. "Jiddah tashi ki ci abinci, zama da yunwa ba shi ne mafita ba, dole za mu ci ko don mu samu ƙarfin fuskantar abin da zai je ya zo" "kin san me suka sa a ciki? Ma'u su waye su? Meyasa suka rabo mu da iyayenmu da sunan taimako suka kawo mu nan suka zubar? Me za mu musu? Me ribansu?" Ta ƙarasa cikin kuka sossai. Ma'u ta share hawayenta "Koma menene za mu rayu jiddah, za mu tsere mu koma wurin su inna, ki ci abinci ba za mu mutu basu san halin da muke ciki ba" Haka suka tura abincin ba don daaɗi ba, wani irin bala'i ne wannan an fita daga mai an faɗa wuta? Bacci ɓarawo ne kawai ya kwashe su, Washegari da safe aka kawo musu abin kari nan ma sun ci har lokacin kaman kace kule su ce chass tsabar firgita duk sun yi zuru zuru. Sai da rana tayi kan aka zo aka tattare su suka fito wani parlor mai girma da kujera ɗaya jal, duk a ƙasa aka zubar da su suka tattakure musamman su da suka san junansu waenda suka fito daga chediya, manyan maza majiya ƙarfi ne zagaye da parlorn. Chan wani mutumi ya fito bayanshi mata ne wurin huɗu kowacce da wani irin shiga. Jiddah ta gane ɗaya daga cikinsu itace ta sa hijabi har ƙasa suka yaudari iyayensu suka kawo su nan ba tare da sun san me za su yi ko me rayuwarsu ke ciki ba. "Waennan su ne daga ƙauyen chediya J" Ya kallesu da kyau kan ya zauna, a hankali yake pointing da hannu ana ware mishi har ya gama sorting. "Waennan su za su mayar mana da kuɗin mu" ya nuna su Ma'u da aka kaisu gefe. "Waennan a yanzu su zama 'yan aike kan idanunsu su sake buɗewa, a zaɓi wasu cikin na farko a rabar kaya sun yi karanci irin wannan wurin manya" "An gama J" Ya miƙe ya fita, matan nan ne suka sake tarkata su Ma'u zuwa wani daki mai gadaje kaman na boarding, Jidda ta tashi da gudu za ta bi Ma'u wani ya riƙota ya wullar ta bugu da ƙasa ta sake rushe wa da kuka. "Me muka muku? Gida muke so gida za mu je ku bar mu mu tafi..!" Ihu take da kuka ganin ba zata yi shiru ba ya gwabeta sai da tayi karamar suma ta farfado, a wuya suka ɗaga ta zuwa wani daki na daban da gadaje irin na boarding, a ciki akwai wata babbar mata ɗaya rike da bulala, ita ta zare mata idanu tayi shiru. "Ba'a mana taurin kai anan don a take za ki karɓi hukunci, ana cewa ku yi za ku yi ku bari za ku bari, ba'a kananun maganganu ko hira mai yawa idan na kama daya daga cikinku da karya min doka za ku ga abin da zan muku." Kowacce ta maƙale a bonk da aka ajiye ta, har lokacin Jidda kuka take na rashin mafita. Da dare aka fitar da su don haduwa ake a ci abinci, a lokacin ne Jidda ta ga Ma'u da sauri taje ta riƙe hannunta. Ma'u ke duba jikin Jiddan cikin diriricewa take cewa "Babu abin da suka miki? Basu miki komai ba?" Girgiza kai Jidda tayi ta riƙe ma'un "basu yi mini komai ba ke fa?" Ma'u ta girgiza kai amma hawaye na zubo mata, a kwakwalwarta take ganin ɗaya daga cikinsu da bayan an shigar da su ɗaki aka zo aka fita da ita kusan awa uku aka dawo da ita aka jefar kan gado jikinta duk jini. A lokacin sauran 'yan matan suka tsorata don abin da iyayensu suka guda ne yake shirin faruwa a kansu ɗaya bayan ɗaya... "Ku wuce ku ci abinci" Ihun da aka yi musu ya sa suka nufi gaban tray ɗin da sauri suka zauna suka shiga ci, kowacce da abinda take tunani. Suna gamawa aka sake raba su sai da Jidda tayi kuka. Rayuwa ya zama babu daaɗi, duniya ta ishe su sun gaza sakewa yayinda wasu daga cikinsu har sun fara sakewa, akwai mata a gidan dayawa amma kaman sashe sashe ne, na kusa da su suna da wani buɗewar ido, su suka shiga jikinsu Jidda suka zama ƙawaye. Suna nuna musu gwara su karɓi rayuwar nan kawai don ba za su taɓa fita ba kila har abada. "Babu wanda ya taɓa tafiya?" Tambayar Jidda ya zo musu kaman daga sama Ɗayar tace "Babu sai dai gawa, sai kuma idan sayar da ke aka yi" Jidda ta sake cewa "Sayarwa? Kaman shanu ko rago?" Dariya suka yi basu ce komai ba suka fice. Ma'u ta fashe da kuka. "Jidda rabon mutuwarmu ne kawai ya rabo mu da chediya, ya zamu yi? Ina za mu sa rayuwarmu?" Sai da suka ci kuka aka zo aka watsar da su, a daren Ma'u ta ga tashin hankalin da bata taɓa gani ba. Tana shirin kwanciya aka zo aka ɗauketa wata mata ta mata wanka aka shiryata da kyau kan suka ja ta zuwa wani ɗaki a cikin gidan. Matar ta zare mata ido fuskarta babu digon fara'a tace "Kwanta!" Kwanciya Ma'u tayi ta buɗata ta yi examining ta tabbatar budurwa ce Dukda fusge fusge da Ma'u ke yi bata kula ta ba sai da ta gama ta bata wani drinks. "Karɓi ki sha" A razane tace "Me..me? Menene?" "Kin sha ko sai na tsinka miki mari?" Ƙin sha tayi kan ta gama girgiza kai ta ji sauƙar marin da ya kusa sumar da ita. "SHA..." Hannunta na rawa hawaye na zuba mata ta karɓa ta shiga sha tana gamawa bata yi ko minti ɗaya ba ta fara ganin duniyar na juya mata. A take ta bugu jikinta ya sake matar ta kama dantsen hannunta ta fito da ita tana layi ta jefawa wani bouncer ya ɗauketa sai mota ya ja ya fice daga gidan. Ba'a dawo da ita gidan ba sai Washegari, Jidda ta fito karyawa tana ta neman Ma'u bata ganta ba, idanunta ya sauka kan 'yan ɗakinsu da sauri ta nufe su tana tambayar su. "Ina Ma'u?" "An fita da ita tun jiya da daddare bata dawo ba" A firgice Jidda ke cewa "Ina aka kaita? Ina aka ce taje?" Kan su yi magana sai ga Ma'u na shigowa kayan jikinta duk jini ne, tana tafiya tamkar za ta kifa saboda layi sam kallo daya za ka mata ka san bata cikin hayyacinta da gudu Jidda ta isa gareta ta riƙeta... "Me ya sameki Asma'u? Me aka miki? Ina kika fito? Ji...ni?" Duk ta firgice sai jero tambayoyin da ma wacce take yi wan ba jinta take ba. "Innalillahi wainna ilaihi rajiun... Asma'u!!" Ta fashe da wani irin kukan tashin hankali, wani bouncer ne ya zo ya ja ta... "Ke kina da hankali? Yi mana shiru anan..." Kan ya ƙarasa ta dankara masa cizo sai da hannunshi ya fashe ta koma wurin Ma'u da ta faɗi ƙasa ta ɗagota tana kuka da jijjiga ta a haukace tana tambayar me ya faru da ita? Tsinka mata mari taji an yi ta rarumi flower vase ta jefa mishi a fuska sai ga jini a take wurin ya kacame, bulala ya zaro cikin bacin rai ya rufeta da duka ita kuma tana kare Ma'u tana ihun kuka don abin da take ji a ranta ya fi ƙarfin bulalar da ake yi mata... Hayaniyarsu shi yayi alerming shuwagabannin gidan. "Kai Shadow! Menene wannan?" Wanda aka dakawa tsawar ya tsaya da dukanta. "J, yarinyar nan ce bata da kunya ko kaɗan nake so in yi maganinta" "Asma'u kina ji na? Me aka miki? Me ya sameki Asma'u?" A zafafe ta juyo suka haɗa ido da wanda aka kira J kuma shi ne yayi kason da yake so da su. Kallonta yake kaman yadda take kallonshi Dukda rashin imanin fuskarshi bata damu ba... "Ku mayar da mu inda kuka ɗauko mu, ku mayar da mu kauyukanmu azzalumai macuta....Allah ya isa Allah ya isa! Wallahi duk ba zan taɓa yafe muku ba mugaye... Allah yayi ma 'ya'yanku abin da kuka yi wa Asma'u" Mutumin ya gyaɗa kai lallai yarinyar nan na da tsaurin ido. "Ita ta maka wannan?" Ya nuna goshin Shadow. Kai ya gyaɗa cikin fushi. "Ka yi mata hukunci, sannan ka sauƙe haushin kan ita wannan da take yiwa faɗar" Girgiza kai Jidda ke yi, Shadow yayi murmushi ya ja Ma'u ba tausayi ko imani yayi wani ɗaki da ita Jiddah na ihu tana neman taimako da kai mishi duka amma bai daina ba... Yana shiga ya rufo ƙofar sai jin ihun Ma'u tayi a gigice ta faɗi a wurin zuciyarta na Gaza ɗaukar abin da ke faruwa da 'yar uwarta... Ina ne nan? Wanene wannan mutumi? Ta ya za mu tseratar da kanmu? Ta ya za mu ɗauki mummunan fansa kan waennan azzaluman? Jiddah ke tambayar kanta tana kuka sossai babu me bata amsa, ya fito yana gyara wando kan ya ja Jiddar yana zaginta babu imani..... ******** Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA GOMA SHA HUƊU* ball yayi da ita sai da ta faɗi ta sake tashi ya shiga duka, sai da ta fita hayyacinta ya barta a wurin ya yi ficewarsa. Duk sauran yaran an kora su sun koma an kukkule su ita ce kawai yashe a wurin tana kukan fitan hayyaci. Sanyin wurin ne ke ratsa ta don daɓe ne na siminti, a hankali ta shiga Miƙewa har lokacin hawayen idanunta basu tsaya ba ganin ba zata iya tashi ba ta shiga rarrafe har ɗakin da Ma'u take, yadda ta ganta babu sutura ya ƙarasa karyata tana kuka sossai ta nufeta ta ɗauketa ta ɗora kan kafafunta. "Allah ya isa! Allah ya saka mana!" Ta faɗa tana kuka, kalle kalle take a ɗakin da babu komai ciki ta hangi wani kofa, da kyar ta miƙe taje ta buɗe ta ga bayi ne, ruwa ta tare babu na zafi sai dai bai da sanyi sossai ta zo ta kama 'yar uwarta zuwa ciki ta dinga zuba mata ruwan Ma'u ta sauƙe ajiyar zuciya tana jin ruwan na ƙara mata raɗaɗin da take ciki. Wanka kawai ta mata suka fito bata san wani taimako zata bata ba, a nan ɗakin suka zauna bayan ta mayar mata da kayan da wanchan azzalumin ya cire ta ɗora kanta kan kafafunta tana cigaba da hawaye me ciwo. Buɗe kofar aka yi, Uwa ce wacce ke kula da ɗakinsu Jidda ɗin haka ta ji ana ce mata. "Sannu me 'yar uwa fitsararra ni Shadow bai burgeni ba ma da bai ɓallaki biyu ba, ki wuce ki koma ɗaki" "Babu inda zan je in bar Ma'u, bakya ganin halin da take ciki? Me muka muku ne kam?" J da yake kallonsu ta cctv ya gyaɗa kai ya kalli na gefenshi "Wannan yarinya akwai abin da ya kamata a mata amma ba yanzu ba, ka ce Uwa ta barta da yayartata a basu abinci kar ayi mana asara..." "An gama J" "sannan yaran da za mu tura kasashen waje...Visa's ɗinsu sun fita ina so a fara shirye shiryen tafiyar su" "Hakan za'a yi" Yana kai nan ya tashi ya fice daga gidan gabaɗaya shi kuma mataimakinsa Ya fice don faɗawa uwa sakon shugaban nasu. **** Miƙewa zaune Diva tayi tana kallon Mazan da suke tsaye a kanta saboda haske da suka kunna mata, ta ɗan cije lip tana mutsutsuke ido kan ta sake kallonsu ta tabbatar NDLEA ne. "Me hakan? Ya za ku shigo mata har ɗaki tana bacci? Idan kuka sameta cikin wani yanayi fa?" Biggy da shi ne me kula da komai na Jagaban ya faɗa yana shigowa saboda kiranshi da aka yi. "No! Barsu su yi aikinsu, Big" Ta gyara zama tana kallonsu, a fuskarta za ka karanci ranta a ɓace yake, su kuma sun zuba mata ido daga ita sai wani long silk gown me hannun vest amma ya sauka har ƙasa kawai ya bi jikinta ne gashinta a ɗaure da Ribbon sakwa-sakwa. Ta sake cewa "Idan kun gama sai ku shirya shari'a da ni don sai na yi sueing ɗinku kun gayamin a wani doka ne aka baku izinin shigowa inda nake cikin kowani yanayi... Me kuka kamani da shi? Ko me aka ce na yi...!" Ogansu ne ya yayi musu hannu akan su fita. "Ba ke muka zo nema ba kuma muna da warrant na kama Jagaban don haka ko bincikenmu ya bi ta ɗakin da kike a cikin gidan Jagaban ba matsala ba ce" Ta sauƙo ta nufeshi tana kallonshi cikin rashin tsoro ta zubawa tag ɗin gaban rigar shi ido. "Ado Alkali! Wow" Tana kai nan ta zagaye shi ta fita a ɗakin zuwa parlor sun wargaza komai amma basu sani ba shi Jagaban da taku yake komai, babu abin da suka samu a gidan har ma jikin matasan, karshe suka gaji suka tafi. "Diva" Ta waigo tana kallon Biggy "Baba ya san da zuwansu?" "Tun kan su zo aka sanar da shi" Ta gyaɗa kai. "Waye ne kuma wannan karon?" "Wani ne Alhj Buba a cikin Layin nan danshi dan sanda ne, su suka shigar da ƙara akan an ishesu da shaye shaye a Layin nan" Tayi murmushi tana nufar ɗakinta take cewa "Gidanshi ne ko haya?" "Nashi ne!" "Ka ba ni kudin da zai sayi gidan" Tana kai nan ta shige ɗakinta. Ba'a jima ba ta fito sanye da wasu riga da wando kanta facing cap ne, da alama kuma ta sha wani abin wukarta na riƙe a hannunta tana kokarin sakawa cikin wandon jikinta. Wani karamin jaka Biggy ya bata don bata da shamaki da duk kudin Jagaban, haka kuma Jagaban bai yarda wani ko wata yayi defying ɗin abinda zata aikata ba shiyasa Biggy be ce komai ba, ta saba magance kananun abubuwan nan. Su Shaly ne suka tare ta a waje suka karɓi jakar, Ta kalli Zubash "Muje gidan Alhj Buba mai yaro ɗan sanda" Zubash ta fi su sanin kowani gida a Layin kuma ta fahimci jagora Diva ke so zuwa gidan don bata sani ba. Tuni suka yi gidan su takwas, babu sallama ko knock suka faɗa ciki kawai. Iyalan sun shiga cikin tashin hankalin ganin su haka a kansu "Ina me gidan?" Fitowa yayi "Bayin Allah lafiya?" "Tambaya kake? Ku ne munafukan da kuke shisshigi a abinda ba'a saka ku ba ko?" Skipo ya shaƙo shi tare da haɗa shi da gini. "Innalillahi wainna ilaihi rajiun...don Allah ku yi haƙuri ku yi haƙuri" Matanshi da wasu daga cikin yaran suna kuka suna basu haƙuri, Obafiya ya zaro Adda ya buga kyauren gidan da ƙarfi suka sake firgita a ruɗe suke ta ba da haƙuri. "Me za'a yi Diva?" Tana zaune kan wani dakali haka daga tsakar gidan ta harɗe kafa tana kaɗawa bata ce komai ba. Ta ɗan kallesu sun yi zuru zuru matan da yaran suna kuka. "Ya kawo takardun gidan duka" "Ki yi haƙuri wallahi sai da na gargadi yaron nan ashe bai ji ba ya zagaye ya janyo min jafa'i..." "Mu ne ma jafa'in?" Shaly ta faɗa tana kai mishi duka Zubash ta tare. "Shaye shaye ne baka so kuma baka isa ka hana ba, kaje ka tattare komatsanka a yanzu ba sai anjima ba ku bar unguwar nan masu shiryayyun yara" Zubash ɗin ne ta faɗa. Pabloo da bai ce komai ba tun fara abin ya daka mishi tsawa "Kana zaune har yanzu?" Ba arziki suka cigaba da basu haƙuri amma sun ƙi dole dolen suka shiga ya fito musu da takardun ganin suna kokarin illata shi, haka Diva ta jefa mishi jakan bayan ta karɓi takardun, sai sannan ta sake magana. "Ka je ka sayi gida a unguwar shiryayyu ka cigaba da zama Na rantse da Allah ko agwagwar gidanka aka ce min an gani a Layin nan sai na sassara duka mutanen gidan nan....idan kana zaton magana nake ku gwada bi ko ta cikin Layin nan ne" "Ku fice!" Obafiya ya faɗa da ƙarfi, ba shiri suka fita mutane sun ɗan tattaru a gefe amma babu wanda ya iya yi musu magana saboda tsoro, a haka Alhj Buba suka bar unguwar bayan kayan sawansu sai kudin da ta bayar, su kuma suka garkame gidan da manyan sarkoki suka fice. Tana zuwa gida ta samu Jagaban ya dawo. Kirari yayi ta mata tana murmushi saboda tayi ƙoƙari a wurinshi a haka ɗin ta tayashi magance kananun ƙwarin unguwa. A waje suka zauna ana ta hira sai ga Pascal ya shigo nan aka shiga mishi ya jiki ita dai tana kallonsu kawai da wani yanayi, har lokacin maganganun Shehi basu bar kanta ba tun daga na farko zuwa na ɗazu amma ta ƙi bari ya shiga zuciyarta har yayi tasiri, kawai ta yanke cewa za ta fitar da duk abin da ya shafe shi daga kanta ta haƙura kuma ba zata bari wani abu ya sake haɗa su ba don baya gabanta. **** "Barka da yammaci mama" Ta kalli matashin da ke ta fitar da kamshi tayi murmushi "Barka dai ɗan saurayi" "Sunana Khalil, za ki ga na zo ba shawara ko sanarwa, Zubaida ce na gani kuma na ji hankalina ya kwanta ƙwarai da ita idan babu damuwa ina so zan nemi aurenta" Ta ɗan kama fuska kaɗan kan tace "Masha Allah, Khalil shine sunan?" Ya amsa da eh yana murmushi "Baka faɗa min sunan babanka ba kuma kai ma'aikaci ne?" Ya ɗan kalleta "Ni ma'aikaci federal government ne Babana retired Navy ne duk 'yan asalin Kano ne mu amma Abuja nake aiki" Ta gyaɗa kai tana sake kallonshi da kyau "Ba damuwa zan yi magana da babanta in ya so duk yadda ake ciki za ka ji daga gareni, saka min layinka anan" Mamaki ya ɗan kamashi amma bai uzzura ba ya saka ɗin ya miƙe ya fice bayan ya ajiye mata dubu ashirin. Baba ya zo gani amma da ya tura a masa iso aka ce baya nan jin da mota ya zo ya sa tace a ce ya shigo, ta dauka tana juyawa a hannunta cikin wani tunani. "Mama don Allah wannan karon ki bar Yaya Zubaida tayi aure matukar har kun bincika kun ga kyaun halinsa" "Sannu 'yar iya! Ni zaki gayawa abin da zan yi? Ko aka ce miki 'yar tawa na kananun mutane ne da zan dauka in ba ma'aikaci ga manyan 'yan kasuwa da sunansu yayi shura suna murza kuɗi? Har yanzu ban ga namijin da zan iya bari ya auri Zubaida ba ke har ke! Bana son shashanci..." Nana hawaye ya cika idanunta tana kallon Maman wani lokacin ta kan tambayi kanta anya matar nan ita ta haife mu? Anya ba sato mu tayi ba? "Mama me kike nema ne?" "Ubanki nake nema...baki san duniya ba yarinya irin waennan masu kyautar dubu ashirin dubu hamsin ana aure ko biyar ba za ki gani ba, gwara ki kama kanki ki san rayuwa" Takaici ne ya sake zuwa ma Nana har wuya ta tattari takardun karatun ta ta shige daki tana hawaye. Sai tsakar dare Zubash ta dawo Nana bata yi bacci ba don damuwar 'yar uwarta na hanata sukuni. "Yaya Zubaida" "Nana! Baki yi bacci ba?" "Ban yi ba ke nake jira" "Lafiya kam? Akwai wanda ya taɓa ki ne? Ke ba zan je makarantarkun nan in ja wa duka ma'aikata da daliban kunne ba kuwa akan taɓaki?" "A'a yaya Zubaida kar ki sa a koreni don Allah ina tsaka da paper, ba ma makaranta ba ne ina so mu yi magana ne Yaya" Zubaida ta zauna tana kallonta. "Ina jinki" "Ɗazu wani ya zo neman izinin iso gidan nan" Murmushi me kyau da ba kasafai ake gani ba a fuskar Zubaidar ta saki. "Alhamdulillah zan aurar da ke hankalina sai ya fi kwanciya Nana" Nana ta girgiza kai tana jin zuciyarta babu daaɗi. "Ba a kaina ba ne akan ki ne. Sunanshi Khalil yana da kyaun hali da natsuwa gashi kyakyawa mai rufin asiri, Don Allah yaya Zubaida ki aureshi" Miƙewa tayi tsaye ranta na ɓaci "Khalil ya zo gidan nan?" Ta gyaɗa kai tana fitar da wayanta don kiran Ghali ta san babu mai kawoshi gidansu sai Ghali za ta mishi rashin mutunci kan ta isa ga shi Khalil ɗin a gobe ba sai jibi ba. "Yaya Zubaidah Don Allah" Nana ta riƙe hannunta. "Ya suka yi da Mama?" Bayani ta mata Zubaida ta sauƙe wayan tare da wani numfashin baƙin ciki. "Ko na yi niyya ba zata bari ba shiyasa ma ba zan yi ba Nana, da dai ke ce zan tsaya kai da fata wurin ganin kin samu ingantaccen rayuwa ta hanyar aure da hayayyafa amma waennan kalaman ba sa cikin rayuwar Zubaida! Mama ba zata taɓa bari ba Dukda a yanzu ba don tsoronta ba ne zai hanani kawai ba zan yin ba ne. Ki yi bacci kina da paper gobe" Tana kai nan ta kwanta tare da juyawa Nanar baya don ɗaki ɗaya suke. Shi dai Khalil Allah yana jin son Zubaida har jininshi, kuma abin da ya gani na Red flags daga mahaifiyarta ba shi zai sa ya ji ya fasa aurenta ba. ***** Yana zaune gaban Maamah yana shan Kunun gyaɗa da farar Safiyar don Dutse za shi, a natse yake sha har ya gama yayi hamdala Maamah ta saki murmushi. "Da ma ina son Magana da kai Shehi" Ya gyara zama yana bata dukkanin natsuwarsa. "Ammie ta kawo min ƙararka" Ya san kwanan zancen, idanunsa na zube kan bandage na hannunshi da yake nan fresh ta ce "Maamah na so zuwa amma ban samu lokaci ba ne" "Ya kamata ka samu ka je ɗin Shehi, kai ne babba duk ƙannenka mazan har Ammar ka tare musu hanya, Ammie kullum tana cikin damuwar rashin auren nan naka don mata dayawa an kawo ka ce ba haka ba kai ka ƙi fitar da naka har yaushe za mu cigaba da zuba ido uhmm?" Ya sauƙe numfashi kaɗan yana ɗan cizan labbanshi. "Ku yi haƙuri zan je" Maamah da ta sanshi sarai ta ce "Ba ni rana, muddin ka bani ranar zuwa na yarda zaka je ɗin amma kalaman zan je basu da tabbas a wurinka" Ya ɗan murmusa kadan "Ko sunday ne sai mu je da Ammar" Kai ta gyaɗa "Allah ya taimaka, yanzu za ku wuce dutsen ne?" Ya miƙe a natse yana gyara Ghutra ɗin kanshi ya sake dan rufe fuskarsa.. "In shaa Allah" "Toh Allah ya tsare ya kiyaye ya dawo da ku lafiya" Ya amsa da Ameen yana ficewa. Malam Bala da Imam suna jiranshi don Ammar yana company yau dama ba koyaushe ba ne suke tare shima yana aiki ne. Don haka mota kawai ya shiga suka bar gidan suka ɗauki hanyar Dutse. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA SHA BIYAR* Kwananta biyu da ƴar uwarta amma ba za ta ce ga halin da Ma'u take ciki ba, wanka sai ta kama hannunta ta kaita har bayi tayi mata, hatta ruwa wannan sai ta bata ta sha idan bata bata ba to ko kwana za su yi Ma'u ba zata tambayi ruwa ba. Hankalin Jidda ba'a karamin tashe yake ba tayi kuka har kaman ba gobe tayi ta rokon su akan su kai mata ma'u ko asibiti ne amma babu wanda ma ya kulata bare su nuna sun san da su take. Yau ta fitar da ma'u harabar gidan inda iyakacinsu nan ne, akwai masu wanki akwai masu shaye shaye akwai masu hira, kusa da su wata ta zo ta zauna Jiddah da tayi wani irin zuru zuru ta kalleta hawaye na cika mata idanu tace "Don Allah har sai yaushe ne za su bar mu mu tafi? Babu wani da zai iya kiran hukuma a cecemu? Iyayenmu na chan a tunaninsu sun sama mana rayuwa mai kyau ashe rami suka haka suka binne mu ba tare da sun sani ba..." Yarinyar ta sauƙe numfashi tana dafa kafadan jidda tace "Da haka za ki saba amma bana tunanin hukuma za su iya aiki akan waennan azzaluman, ta wani bangare ma zan iya cewa bakinsu daya da manyan, kin ga gidan nan ban san shekara nawa yayi yana existing ba amma ni a karan kaina shekaruna shidda, idan kin ga kin fita an sayar da ke ne ko an yi safararki zuwa wani ƙasa da babu yadda za ki yi zama dole, za'a turaki aikatau ko ma zinace zinace, babu yadda kika iya jidda gwara ki saki jiki Ma'u kuma Allah ya bata lafiya don wasu dayawa sun shiga irin wannan trauma amma da kansu suke overcoming har ma su yi adopting wannan rayuwa da muka tsinci kanmu" Jidda da zuciyarta yake bugawa da karfin gaske tace "idan iyayenmu sun neme mu fah?" "Na gayamiki ba ta yadda za ki sadu da iyayenki jiddah, su karan kansu basu san ta inda za su fara nemanku ba komai da aka yi fake ne" Hawaye ne ya shiga zubowa jiddah tana kallon Ma'u dake zaune kawai kaman wacce aka dasa idanunta wuri guda ba uhm ba uhm uhm. "Akwai Allah in shaa Allahu za mu fita, in Allah ya so ya yarda rayuwarmu ba zai tagayyara ba" Ta karasa da kuka, tana jin labari ana safarar mutane, tana jin labarin irin waennan duniya na karkashin kasa amma bata taba sanin da gaske suna nan cikin al'ummarmu ba, suna amfani da 'ya'yan wasu don biyawa kawunansu bukatu, suna zaluntar iyaye su yi musu shigo shigo ba zurfi su yi musu illah mafi muni a rayuwa. "Ke!" Ta ɗaga kai ta kalli Shadow "tashi mu je!" "Ina?" Ba tsoro tayi tambayar don ta ci alwashin ba zata taba jin tsoro ko shakkarsu ba, duk kuma wanda yayi mata a cikinsu za ta rama sai dai su kasheta. "Kin tashi ko sai na saɓeki a kafaɗa?" "Allah ya tsari jikina ya hadu da kazantaccen jikinka..." Ya kai hannu da niyyar marinta tayi saurin mikewa tsaye ba zato ta ji.... **** Iska ne mai karfi ake na alamun ruwa zai iya saukowa any moment, kasancewar farkon shigar daminar ce ba kowa ke da tabbacin zuwan ruwan ba hakan ya sa wasu dayawa basu yanke al'amuransu ba, kaman da wasa ruwan kuwa ya zo da karfinshi wanda tun yamma ya fara zuba har tsakar dare bai daina marka-marka ba. A daidai lokacin Diva tana zaune cikin motarta hankalinta na ga jikin mirror din motar kofan motar a bude yake duk jikinta kuma na ta waje wani hayaki take busawa tana sake nazarin motar. Tun arangamarta da sheikh ta lura da motar amma bata taba zaton ita motar ke bibiya ba sai a kwanakin nan biyu bayan ta manta ma da wani sheikh da wa'azinshi. Tana so ta fahimci me suke so da ita hakan ya sa ta biyo hanyar da ta tabbatar babu wani motsi na jama'a ga kasancewar ruwa ko ina tsitt ko wani mahaluki na gidansa yana bacci. Ta kusa mintuna goma a haka kan ta sauka ta nufi motar, sai suka yi saurin kunnawa suka yi baya in ta matsa gaba sai su yi baya, wani irin bacin rai take ciki idan zaka yi abu da ita kayi kawai bata son rufa rufa ko wani kumbiya kumbiya, rai a bace ta dawo motar ta zauna tana kokarin yi wa motar key sai ta tsaya chakkk, hannu ta kai za ta dora kan wukarta ta ji an saka igiya ba zato an shake mata wuya daga seat din baya, wani azababben zafi na shigewar makami na ratsa har kwakwalta daga kasan hakarkarinta da alama wuka ne suka soka mata kuma ba karamin shiga yayi ba. Kokawa suka fara duk yadda ta so ta ma rike igiyar abin ya ci tura har sai da ta kusa suma suka saki sama sama ta ji an janyeta waje kusan mutum hudu ne suka shiga dukanta da kafa da hannu, gabadaya ta jiggata ta fice a hayyacinta, da kyar suka barta ganin tana aman jini, cikin azaba ta runtse ido jin sun juyata sun sa wuka suna wani zane daga kafadarta daga nan suka juya suka tafi suka barta anan yashe ruwa na zuba mata chab chab chab. Ta tattare duka kuzarin da ya saura mata cikin wani irin karfin hali ta mike tana ganin jiri lalube take saboda idanunta sun rufe da jini dake zuba mata daga kanta da goshinta ga ruwa kuma hannunta ya sauka a kan Tire ta ji shi flat alamun sun fashe shi, jikinta babu inda baya rawa haka ta kama motar ta mike hannunta daya na hakarkarinta da azabar ya fi na ko ina tana tafiya cikin layi idan bata nemi taimako ba mutuwa za ta yi. A lokacin duka rayuwarta ne ke flashing a saman idanunta, wani irin tsoro ne ya mamaye ranta idan ta mutu bata san ta ya za ta fuskanci ubangiji ba, babu abin da ya taba girgizata a rayuwa irin tsoron mutuwa a yanzu kuma dama haka abin yake. Daga nesa take hangen wutar mota, bata tsaya ba ta cigaba da tafiya cikin wani irin layi da juriya, ƙiiiiiiiii haka motar ta taka wani irin birki bayan ta dan bugeta kadan don matukin ba wai ya kula da ita ba ne, bata fadi ba sai dai jikinta rabi na ga motar, da sauri ta ji karar bude kofa, sai ta ji ana magana amma ba zata ce ga abin da ake cewa ba. Ta tafi luuuu za ta fadi ta ji an tare ta, ta ji sadda hannun wanda bata sanin ba ya sauka kan wukar hakarkarinta ta ji sautin salati daga nan bata san me kuma ya faru ba ta karasa ficewa hayyacinta. **** Jingine yake da kujera kafarsa a harde kaman ko da yaushe shigar larabawa ce jikinshi fari sol din jallabiya da yalkinta ya bayyana tsadarsa, golden color din jubba sai gutra fara tass da ya dora a kanshi idanunshi sanye da farar madubi da ya kara masa kyaun zati. Hannunshi wani takarda ne yana dan dubawa daga gefe yake jin maganan Ammar. "Ammar ka fahimta mana ba ni da wani interest kan Twins enterprises duk yadda su Abba suke so nayi aiki chan ba zan iya ba abubuwan gabana kadai sun ishe ni" Ya faɗa yana rufe takardar tare da dora idanunsa farare tass kan Ammar. "Muna bukatar kwakwalwarka a kamfanin nan, kuma field dinka ne harkar kasuwanci amma ban san meyasa kwata kwata baka son alakanta kanka da abin da ya zame mana dole ba, abubuwa dayawa suna faruwa a cikin kamfanin nan yanzu su Abba shekaru sun ja ba komai ne suke iya yi ba abubuwa sun mini yawa a kullum kuma samun ɓace ɓacen kudade ake ba na wasa ba" Ɗan hararsa shehi yayi cikin muryarsa mai natsuwa yace "Duk babu mai iya gano bakin zaren kuma aka ce sai Irshad? Ka daina saka ni magana Ammar ku yi ko ma menene amma ni kam ba zan sa kaina ciki ba" Yana kai nan ya mike ya nufi shige wa dakinshi, Ammar ya girgiza kai bai san meyasa a duniya idan akwai abin da shehi ba ya mayar da hankali kai su ne dukiya da kuma kadarorin iyayensu. Dab zai shige Ammar yace "Ammm Maamah tace gobe ne za mu je gidan su buduruwarka ko?" Da gayya ya fadi hakan don ya ci nasarar dakatar da shehin ya juyo ya zuba mishi ido bai ce komai ba Ammar ya tuntsire da dariya. "Kana kallona ba zance zaka je ba?" Tsaki tsiriri ya ja ya juya kawai ya shige amma fuskarsa a dan sake yana girgiza kai. Kai tsaye rigar saman ya cire ya fito balcony dinshi ya tsaya idanunsa zube wuri guda wasu abubuwa na zuwar masa kai, ya jima tsaye nan kan ya kai idanunsa kan agogon hannunshi sai ya juya ya koma dakin kai tsaye ya shiga bayi yayi alwala tare da fitowa ya mayar da rigarsa ya nufi kasa don tafiya sallar magrib da dab ake da kira. **** "Ni kam Shaly kun ji daga uwar dakinku kuwa?" Jagaban da shigowanshi gidan kenan ya fada don yayi ta kiran layinta baya shiga, bata cika kwana waje ba ko ta kwana to asubar fari zata shigo gidan, haka bata zama inda babu dayansu na awanni dayawa kuma tun jiya da rana bai sanyata ido ba yanzu ana neman magariba bata shigo gidan ba. Dukkansu suka mike tsaye obafiya yace "Tun jiya da ta fita bamu ji daga gareta ba jagaban.... Tattaunawar da muke kenan don babu wanda ya samu layinta, mun ta shigowa Hajjo na cewa bata dawo ba....Anya kuwa lafiya?" A kan fuskarshi suka karanci tashin hankalin da ya fara shiga don idan akwai abin da jagaban ba ya wasa da to Diva ce. "Me yasa kuka barta ta fita ita kadai? Kun sani tana da makiya dayawa kaman yadda nake da su me amfaninku a tunaninku na haɗa ku ne kawai ku zauna zaman banza a gangarta? Maza ku bace duk inda take ku nemomin ita" Skipo yace "Diva fa ko ita kadai ce ba abin wargi ba ce, na tabbatar babu abin da aka isa a yi mata don nan gani nan bari ce wallahii" Tsaki jagaban yayi Zai yi magana zubash tace "Kila dai wani business din take yi mai muhimmanci amma nima ban yarda wai don tana ita kadai wani abin zai iya samunta ba" Jagaban da yayi shiru yana jin zuciyarsa na rawa ya san ko ma menene ba daidai bane don hankalinshi ya ki kwanciya a ranshi yake jin ba kalau ba, zai yi magana cikin fusata ya ji wayanshi na kara. Zarowa yayi ya daga cikin wani salo ya furta "Ya nee?" A take ya zare idanu duka cikin wani kalar murya marar daadin saurare ya furta "Whatttt?" Duk sai suka razana wayan hannunshi ne ya nemi faduwa jikinshi har tsuma yake amma ya kasa magana sai sauraron dayan bangaren yake cikin tashin hankali wayar ta zame a hannunsa. "Jagaban menene! Me ya faru?" Suke jero mishi, ba su kadai ba hatta da sauran 'yan daban da suke cike da gidan sai da suka matso ya furta "Sohana!" Sai ya girgiza kai..... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA SHA SHIDDA* Cikin tashin hankali suka isa asibitin da aka ce musu Diva tana chan tun cikin daren jiya. Kai tsaye Reception suka tsaya suna tambayar wacce aka kawo emergency. Nurse din ta kallesu tace "'yan uwan Suhan?" Shaly ce ta amsa "Eh, tana ina?" Gaba ta shige suka bita har ɗakin da take kwance, sai da Obafiya ya rike jagaban ya zaunar don jiri ne ya kwashe shi ganinta, likitan dake kanta ne ya kallesu yace "Kai ne Babanta?" "Likita me ya sameta? Su wa suka kawota? Garin yaya hakan ya faru?" Pascal ya shiga jerowa likitan tambayoyi. "Ni ma ba zan ce ba amma wani ne ya kawota emergency, hasali ma da asuba ya bar nan don sai da aka yi mata aiki aka iya cire wukar da yake hakarkarinta" Likitan ya amsa yana sanya hannayensa a aljihu. Ya kara da cewa "Ku kwantar da hankalinku she's out of danger dukda dai sai mun yi hoto mun tabbatar da wukar bai ta'ba kodarta ba tukun za mu tabbatar amma duk wani physical ciwo mun magance shi har ta farka ma ta ba ni layinku na kira kan ta sake komawa saboda alluran da nayi mata" Idanunsu duka zube kanta tana sanye da wasu fararen kayan asibiti riga da wando, goshinta bandage ne da ya rufe rabin gashin kanta, a wuyanta akawai ciwuka haka hannayenta, a hankali Shaly ta karasa ta dan d'aga rigarta sai ta runtse idanu bruises ne sossai a shafaffen cikin nata bayan katon bandage da aka rufe inda aka yi mata dinki. Zubash da zee idanunsu suka cika da kwallah, bacin rai da tashin hankali duk sun bayyana a fuskokin mazan, duk wanda zai iya yiwa Diva haka sun san ba karamin dan daba ba ne kuma babu ta yadda mutum daya zai iya hakan, duk sun tafi tunanin waye ne? Sai dai sun san suna da makiya ko ta wani bangare sun taba yara dayawa, sun gagari duk 'yan dabar zagayen kano. Har likitan zai fita jagaban yace "Likita babu wani hint daga wanda ya kawota? Wanene shi? Ta ya kuka karbeta babu hukuma?" "Shi karan kanshi hukuma ne, kuma gaskiya ya yi kokari don da bai yi gaggawar kawota ba komai ma zai iya faruwa da ita, shi ya tsaya ya biya kudin komai hatta jini da aka kara mata shi ya bayar saboda babu jinin da zai hau da nata a blood bank...." Ya ɗan dakata yace "Yauwa abu d'aya akwai rubutu da aka yi a bayanta da kaman wuka JJ" Wani irin mikewa tsaye Jagaban yayi, ya tafi gabas ya dawo yamma da sauri ya nufeta, likitan ya ba shaly umurnin yadda zata dan karkatata, ya bude kafadarta daga sama ga JJ din a zane guda biyu su ma sai da aka dinka don ya shiga sossai. Gasping Air jagaban yayi ya koma da baya baya ya zauna hannunshi kan bakinshi. Likitan ya juya ya fita. Pabloo ne yace "Jagaban ka dauki wani haske ne kan waenda suka aikata mata hakan" Shiru yayi na seconds kan ya girgiza kai sai kuma ya mike zuruf ya nufi fita daga dakin sai kuma ya dakata ya waigo ya kalle su. "Ku tabbatar duk runtsi baku bar dakin nan ba, ku tabbatar baku dauke idanunku akanta ba, ku kuma tabbatar da duk wani likita ko ma'iakacin asibiti da zai shigo dakin nan kan ya ta'ba ta... ku kula" Yana kai nan ya fice daga dakin, duk da kallo suka bi shi. Skipo yace "Anya jagaban bai da masaniyar abin da ya faru fa diva?" Pabloo yace "Ba wannan ba Skipo, ban taɓa ganin tsoro ko shakka akan idanun Jagaban ba sai yau dole akwai abin da ke faruwa da mu bamu sani ba" Shaly tace "Idan harkarshi ne to me ya sako Diva? Idan fa da karar kwana da sai dai mu ji labarin mutuwarta" Duk jikinsu ya yi sanyi kowa ya nemi wuri ya zauna suka zuba mata idanu. **** "Tun yana ƙarami na fahimci cewa zai iya zama barazana a gareni, na tsani ganin yana numfashi..." Ya faɗa cikin ɓacin rai jin mummunan labarin cewa Irshad zai shiga company ranar monday bisa tilastawar mahaifinshi ko da awanni kadan ne ya dinga leƙawa yana yi. Daga ɗaya ɓangaren aka ce "Toh yanzu ya za'a yi da shi?" "Zan yi tunani a kai amma na rantse ko da zan tafi tsirara sai na tabbatar Irshad bai yi min shamaki da cikon burina ba. Za ka ji ni!" Yana kai nan ya katse wayar tare da jefarwa kan kujera cikin nazari da zurfafa tunani. ***** Fusgota yayi ya dora kan wuyanshi tana ihu tana wurge wurgen kafafu da kai mishi duka bai direta ko ina ba sai wani karamin daki. "Natsu!" Ya daka mata tsawa "Duk rashin kunyarki idan na ga dama zan turmusheki ne kamar cinnaka wallahi, kina cin sa'a J ya hana a aikata miki komai ne da yanzu sai wata ba ke ba!" Dukunkunewa tayi wuri guda tana hawaye, wani tv ya kunna sai ga Ma'u nan an saka mata bindiga marar kara a goshinta. Ihu tayi tana kuma rufe baki lokaci guda idanunta duk a waje "Me...me za ku mata? Don Allah kar ku kasheta kar ku kashe min 'yar uwa!" Kuka take yi tana rokonsu. Shadow yayi murmushi "Ba za mu kasheta ba ne kawai idan kin yi abin da muke so" "Ko menene kuke so wallahi zan yi, zan yi ko menene amma don Allah kar ku kasheta...." "Ashe kina da wayo" Wasu uniform ya watso mata kaman na islamiyya "Tashi ki saka!" Ta tattara, ya juya ya fita cikin lokaci kankani ta shirya kamar 'yar makaranta. Ya dawo ya bata school bag "Ki goya wannan jaka a bayanki kamar 'yar makaranta, ki tabbatar kin natsu ko me zai faru sako ne kawai za ki kai ki dawo karki yiwa kowa magana kuma kar ki bari a yi miki, kika kuskura aka samu akasi haka za ki dawo ki kwashi kwakwalwar yayarki a kasa wallahi" Kai take gyadawa har ya gama ta goya jakar ta sauke hijabin da ya kai mata gwiwa a kai, ya mata jagora zuwa harabar akwai mota guda daya da wani da yayi shigar bahaushe amma talaka alamun dai acting yake as driver ta shiga baya shadow ya sake ja mata kunne kan suka fice daga gidan. Duk karfin halinta zuciyarta rawa yake, idanunta cike suke da wani irin tsoro haka matukin ke tafiya cikin garin da ba zata ce ga sunanshi ba kalle kalle take ko zata ga wani signboard tayi kokarin karantawa ko zata fahimci ina suke, ta ya za su kubuta? Ta ina za ta fara neman taimako a yadda suke ta tabbatar tsaff za su iya kashe Ma'u hakan ya sa bata ko motsin kirki cikin motar a hankali suka tsaya inda ake ba da hannu, kasancewar farar glass ce da motar idanunta na ta kalle kalle kaman an ce ta waiga hannun damanta idanunta suka faɗa cikin nashi da a lokacin ya ɗago. Yanayinta bai mishi kama da wacce take cikin natsuwa ba hakan ya sa ya dan tsawaita kallon sai ya ga ta yi sauri ta dukar da kai kuma ya ga sadda bakin driver din ya motsa, idanun ya kawar yana mayarwa kasa a daidai lokacin da wutar ta ba da kalar green suka wuce ta hanyoyi daban daban. "Tsaya...." Ya tsinci kanshi da furtawa haka kawai yan jin zuciyarsa bata natsu ba. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA SHA BAKWAI* Ammar da yake driving cikin mamaki ya ce "Me ya faru?" "Just turn...mu bi wanchan hanyan yi sauri." Kaman yadda Irshad ya buƙata haka ya juya da sauri suka bi hanyar, Allah ya taimaka ya hange su ya nunawa Ammar akan ya bi bayan motar haka ya cigaba da binshi har gaban wata makaranta da aka Rubuta Asasul Islam, daga dan nesa Irshad ya dakatar da Ammar idanunsa na kan motar har jidda ta sauka ta shige cikin makarantar. Sun ɗan jima tsaye har driver din ya ja ya bar wurin. "lafiya kam Shehi?" Girgiza kai yayi "Lafiya, mu je" Juyawa Ammar ya yi ya kallesa "Haka kawai ka sa muka zo nan?" "Akwai abin da na yi tunani ne amma kaman ba haka ba ne, mu je kawai" Ya amsa yana jingina da kujerar idanunsa a lumshe yana tunano fuskar Jiddah especially idanunta da suke cike da wani irin yanayi hade da kwallah. Haka Ammar ya juya suka nufi gidan Ustaz Abdallah, Irshad ji yake kaman kar su isa, sai lokacin yake jin da ma bai saka wa Maamah ranar akan zai zo nan ɗin ba don shi bashi da abin cewa mace. "Manya-manya babban shehi ko in barka daga nan ne ka ƙarasa ciki kar in kalle maka mata?" Tsiririn tsaki ya ja ya buɗe idanu yana kallon Ammar din. "Me kake kallona haka? Ka ga ka sauƙa mu isa ciki a yi a kawo maka ita nan da kwana kusa mu ma mu samu mu shige daga cikin nan" Ya fada cikin zolaya da dariya. "Ammar ka kiyayeni! da ma na hanaka aure ne?" "Eh mana baka ji su Abba na cewa shekaru ya kamata a bi ba, daga zaran ka yi nima zan samu na yi na gaji da cin tuwon Maamah idan kai baka gaji ba" Murmushi kaɗan Irshad ya yi bai ce komai ba sai kallon gidan da yake, har ga Allah bai san me zai shiga ya yi ba ko ya ce. "Ammar ka nema mana iso" "Ni ne ma na ke son matar kenan" Kallon please irshad ke mishi, ya sani dama ko kwana zai yi wurin ba lallai ya iya shiga ba muddin shi kaɗai ya zo. Sauƙa Ammar yayi ya samu mai gadi akan yayi musu iso wurin mai gidan ya ce Shehi ne. Mai gadi ya wuce ciki chan sai ga shi ya fito yace ya sanar za'a fada mishi yanzu, ba'a jima ba sai ga shi ya fito, kamilallen dattijo ne kuma malami fuska a sake yake yi wa su Irshad da suka fito daga cikin motar maraba, wani irin daadi yake ji na kasancewar Irshad a cikin gidansa da sunan nema da 'yar cikinsa babu abin da ya kai mishi wannan farin ciki ya san Na'imatu ta gama dacen mijin kwarai kuma ta kerewa sa'a. Iso ya yi musu har babban parlornshi suka gaisa sossai har yake tambayar shehi Uban gidansa don ya kwana biyu ma ba ya Nigeria. "Sheikh na nan yana maganan shigowa ma kwana kusa in shaa Allah" "Masha Allah, Allah ya tabbatar" Daga nan ya miƙe ya wuce ciki, chan aka kawo musu ruwa da snacks da drinks. Shi dai Irshad gabadaya a takure yake Ammar na ta murmushi don dariya yake bashi wlh kaman me tsoron mata, chan sai gata ta shigo da sallama suka amsa sai dai muryar Ammar ce ta fita shi gogan chan ciki ya amsa sanye take da hijab yadin Mercedes Golden yellow har ƙasa, fara ce kuma kyakkyawa kanta ƙasa ta shigo cikin palorn dan dosanuwa tayi kan kujerar tamkar mai tsoron wani abu. "Barkanku da zuwa ina yini?" Ta fada cikin kamillalliyar muryarta, daga jin muryar ka san ma'abociyar karatun alqur'ani ce don su suka iya ba har kalmomin hausa hakkokinsu. "Barka dai malama Na'imatu kina lafiya?" "Alhamdulillah" Ta faɗa jin murya ɗaya ne ya amsa ya sa ta ɗan dago sai suka haɗa idanu da Irshad da shi ma a lokacin ne ya kalle ta. "Ina yini" Ta gaishe shi, ya amsa chan ƙasa "Alhamdulillah" Ammar ya katse shirun da ya biyo baya tana ta wasa da fingers dinta ta ji yana cewa "Ya fama da school na ji kina Part 3 ko?" "Alhamdulillah! eh ina Part 3 a nan BUK" "Wani program kike yi" Ta amsa "Arabic and Islamic Studies" "Masha Allah, ubangiji ya taimaka" Ta amsa da Ameen ya rabbi. Irshad ya dan yi shiru kenan dalibarsa ce ma bai san da ita ba, kuma babu yadda za'a ce bata san shi a makarantar ba hakan ya sa introducing kanshi da yayi niyya ma ya fasa. Miƙewa ya yi. "Ki gaishe da mutanen gida" Ya kalli Ammar dake kallonshi baki sake ya juya ya fice daga parlorn a dole Ammar ya yi mata sallama shi ma ya bi bayan shi. A jikin mota ya same shi "Shehi wani irin hira ne wannan?" "Me hirar ya yi?" Baki sake Ammar ke kallon sa. "Haka ake hira tsakanin saurayi da budurwa? Ba kyau wulakanci ka sani kuma" "wulakanci? Kai ma ka san ba halina ba ne, Ammar Ammiey cewa tayi in zo in ganta ba gashi kuma na gantan ba? Sai me kuma?" Ya faɗa yana tsatsare Ammar din da idanunsa. Ammar rasa ma abin cewa yayi don takaici. "Allah ya sa a sake saka ka dawowa zan ga wanda zai biyo ka don ni ba da ni ba" Ya juya yana kallon Ustaz Abdallah da ya fito yana cewa har sun fito ko ruwa basu sha ba inji Na'ima. Shehi ya ce "Yamma yana yi ne ina da karatu a masallaci kan magrib" "Masha Allah, Allah ubangiji ya taimaka na gode sosai da sosai a gaishe da su Alhajin" Ammar ya amsa suka yi musabaha kan suka shiga mota suka bar gidan. Driving Ammar ke yi yana tuna wai hirar da Irshad yayi ya yi tsaki ya fi dubu, tattausan Murmushi mai kyau Irshad yake saukewa don shi dariya Ammar ke bashi kaman bai san halinsa ba? Shi dai harkar mata kam ba ya tunani yana da wannan baiwar. Ko ya ce lokacin dogon magana da su ne bashi da shi amma bai kushe ta ba tana da natsuwa kuma tana da ilmi ga kyau daidai gwargwado kuma ta fito daga gidan tarbiya wannan qualities za su sa ya zubawa Ammiey idanu su yi duk abin da suka ga shi ne daidai. Gida kai tsaye suka yi parking... Baƙin jallabiya ce jikin shi yau bai dora alkyabbar ba amma baki da farin gutra da kuma Agal suna kanshi, iska ke dan kada ɗankwalin yana komawa bayanshi yana kuma bayyana fari sol din fatar wuyanshi zuwa kunnuwasa, yana gama sa kafafunsa ƙasa suka jiyo salati da kuka. Da ɗan hanzari ya daga kai ga bangaren sai ya ga Sumayya ce tafe da sauri tana kuka. Ammar yayi hanzarin tare ta Shehi na zagayowa bangarensu. "Menene? Me ya faru?" "Ya Ammar Daddah...! Daddah ce ta zame ta faɗi a toilet ta kasa tashi" "Subhanallahi!" Shehi ya furta yana nufan sashen, Ammar ya rufa mishi baya tun kan su fita su Maamah suka fice Wani Yayansu na aurar da 'ya akwai walima kuma duk Daddah ta saka su Goggo hindatu binsu sumayya ce kawai aka bari ta zauna da ita. Sun same ta kam kafarta da kugunta ba karamin bugu wa suka yi ba. Ammar da Irshad suka ɗaga ta suna mata sannu har mota, sumayya ta shiga baya Ammar ya shiga mazaunin driver Shehi ya shiga seat na gaba suka fice daga gidan Baba Lawan na ta Allah ya kiyaye ya bata lafiya. Asibiti suka yi wa tsinke, a kan wheelchair aka ɗora Daddah wasu nurses suka tura ta zuwa ciki. Likitan da ke duty lokacin ya karɓi file din su, Ammar ne ke ba da umurnin a kai ta Amenity duk da sun sani nan din ne mutanen gidan suke kwanciya. "Ranka ya dade Amenity din nan ya zama out of bond, mun samu wani patient da ake tunani lassa fever ce da shi hakan ya sa mun dakatar da shiga gabadaya ward din sai tests results din shi su fita, akwai dai side ward" Shehi ya ce "Ba komai a kai ta chan din" Likitan ya gyada kai yayi wa nurses din hannu suka wuce da ita, ya bi bayan su su Ammar ma suka rufa musu baya. Shehi na sanya kafafunsa ɗakin idanunsa basu sauƙa akan kowa ba sai Diva Without intending to ya cigaba da Kallonta har lokacin tana kwance ido rufe hannayenta bisa cikinta drip makale a ɗaya, gashinta kuma baje a kan pillow. Something about her face made him pause ko cikin bacci fuskar rashin mutuncin nan bai chanza ba, kallon seconds ya yi mata ya ɗauke kai ya mayar ɗayan gadon da ake kokarin kwantar da Daddah don gado biyu ne ɗakin. Ko a fuska bai nuna alamar sanayya ga Diva ba ya ƙarasa kusa da jaddah ya tsaya daga kanta yana mata sannu, kamshinshi na Asad Elixer da ya haɗa da Art of Arabia I ya cike ɗakin. Sai a lokacin Ammar ya kai idanunsa kan su Diva da tsantsar mamaki yake kallonta Shaly ce kawai a ɗakin zaune gefenta. Ya kalli Shehi sai dai Shehi ya basu baya ne, bai da tabbacin ya kula da ita. Me ya same ta haka? Ya tambayi kanshi duk da babu mai bashi amsa. Likitan da ya shiga duba Daddah ne ya sa ya mayar da hankalinshi kansu, ta gurɗe ne a kafa dole aka yi mata duk abin da ya kamata ta sha wahala kam amma tayi dauriya da addu'a, shaly sai kallonsu take yadda duk hankalinsu a tashe kan matar da ta tabbatar kakarsu ce duba da girmanta. "Sannu Mama" Likitan ya faɗa yana kallonta kan ya kalli su Irshad. "Za ta huta, ga drugs a je a karɓo ta sha ko zuwa safiya sai a yi hoton bayan a tabbatar babu inda yake da wani matsala kan a sallameta" Ammar ya karɓi takardar. "Toh Dr. Mun gode sossai" A tare da Likitan suka fita ya wuce pharmacy. Sumayya ma ta fita ta yi don ba za ta iya zama Irshad na wurin ba sai ta fito gaban dakin don ta kira su Maamah. Shaly ta miƙe ta nufi toilet da ke cikin dakin. Tana shiga wata nurse na shigowa, kan Diva ta tsaya da tray na magani, a hankali ya ɗaga idanunsa ya saukar kansu ta cire drip ɗin tayi mata wasu allurai a canular ɗin kan ta mayar, garin juyawa ta buge sandar drip din sai da yayi taga taga ita ma ta kusa faɗuwa amma ta samu tayi balancing ta juya ta kalli sandar ganin babu abin da yayi ta fice. Sandar drip din ya zubawa idanu ganin yana rawa da alama ya bar jikin ramin kuma nurse din bata kula da hakan ba, ya bi ruwan da ido har kan hannunta dake kwance akan shafaffen cikinta, zai ɗauke ido ya ga ta motsa hannun ta sauƙar gefenta hakan ya ƙarasa jan IV stand ɗin zai faɗo kanta without thinking twice ya miƙe ko kan karfen ya faɗo mata ya tare, a hankali ya mayar da shi cikin ramin dake jikin gadon ya riƙe igiyar ya gyara da kyau don ta ɗan harɗe shi jikin hannunta. Just then, diva's fingers twitched. Idanunta suka ɗan buɗu a daidai ya kalli fuskarta sai ya kawar da idanu ya bar wurin as if ma bai tsaya kanta ba. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA SHA TAKWAS* Ta jima tsaye cikin makarantar sai da wani ya fito yake tambayar "wacece ke?" Kan ta ɗan zabura. "Na ɓace ne yi hak'uri" Ta faɗa cikin rawar murya kan ta fito a lokacin wanchan driver din ya dawo ta shiga motar. "Kin kyauta da baki ja wa 'yar uwarki kwana a lahira ba" Bata ce komai ba don duk yadda take tunaninsu sun wuce nan, tun kallon da wanda bata sani ba yayi mata ta ji yana magana ashe akwai earpod kunnenshi, suna fara tafiya ko da motar su ta bayyana ta ji yana magana cikin Hausar da ko fahimta bata yi, sai da ya ce mata zai sauke ta ta shiga wani islamiyya zai tafi amma zai dawo ya dauke ta, ya kara nuna mata Ma'u da bindiga a kai ya gargaɗeta kan ta sauka. Sai a sannan ta fahimci binsu ake duk da tsoron da ya cika ta bata yi gigin yin wani abu ba, ko da ta tsaya cikin makarantar babu abin da bata tuna ba, a yanzu a ranta ba Ma'u kawai take jin tana son taimakawa ba har ma da sauran yaran da suke gidan da kuma waenda za su iya faɗawa a gaba, don haka za ta jure za ta tsaya ta ga abin da ubangiji ya tsara don zalunci ba ya tabbata. Wani wuri da bata sani ba suka tsaya ya mata umurni ta sauka ta shiga ciki gefen dama za ta ga wani gini kawai ta ajiye jakan bayan nan ta fito, duk da yadda zuciyar ta ke bugawa haka ta aikata ta dawo ta shiga ya ja suka bar wurin, duk da bata san garin ba amma hanyar da ya bi da ita daban da wanda ya biyo a zuwa yayi wasu irin zagaye sosai kan suka iso tana shiga da gudu tayi inda ta san za ta samu Ma'u ta kuwa same ta zaune da gudu ta faɗa jikinta ta sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai. **** Kwance kawai Na'imatu take Idanunta na kallon sama tana jin ta a sama, wai ita ce yau Sheikh Irshad Al-Noor ya tako ya zo zance wurinta? Ita ce mai wannan sa'ar? Yanzu watarana da sunan Mijin ta za'a ƙirashi? Ƙanƙame pillow tayi tana juyi a kan gadon a fili ta furta "Ya Allah!" Har ƙoƙon ranta wani irin farin ciki marar misaltuwa take ciki. Shigowar mahaifiyarta ne ya sa ta natsu kaɗan, ta miƙe zaune. "Sannu da shigowa Umma" "yauwa Na'imatu, ya kuka yi?" "Umma da ma an ce bashi da magana sossai idan kin ji ya jima yana magana wa'azi ne toh hakan ce dai gaisa wa muka yi ɗayan dan uwanshi ne yayi ta min tambayoyi, umma kina ga zan iya kwanta masa a rai? Kai Umma ta gyada cikin murmushi "kwarai da gaske, ai shi duk abinda mahaifiyarsa take so to ba ya ƙi kuma kin ga kin riga da kin gama shiga zuciyarta, mu cigaba a addu'a in Shaa Allah sai ki ga an yi aurenku kuma kun zauna lafiya har Abada" Murmushi kawai Na'imatu ke yi tana gyada kai har Umman ta tashi ta fita ta barta a duniyar farin ciki da ta tsinci kanta. **** Irshad na nan zaune bakin gadon Daddah kanshi ma na ga waya ya ji fitowar Shaly, a lokacin ya ji tana magana. "Diva! Kin farka? Alhamdulillah!" A ran shi ya raya ashe sun san Allah. Da sauri ta fita kiran nurses bata jima da fita ba ma Ammar ya shigo rike da ledar magani Irshad ya karbi ruwan gora da ya taho da katon din ya zari daya ya bude murfin shi kuma Ammar ya fitar da magungunan ya ɓalla suka bata ta sha. "Ba na so in yi bacci ban yi sallah ba" Ta faɗa cikin harshen fulatanci. "Bai kamata ba kam idan za ki iya daurewa Daddah ki zauna har ki yi magrib ɗin" Ta gyada kai. "In Shaa Allah, Ku tafi ku bar sumayya Shehi na san kana da karatu bai kamata ka bari ba tunda ai Alhamdulillah Allah ya taƙaita" Hakane kam, kuma basu musa ba yayi mata sallama akan za su dawo Ammar ya kira sumayya daga waje su kuma suka nufi fita, ko idanunsa bai kai ta inda su Diva suke ba a lokacin Nurses sun shigo da likita suna duba ta, Shaly na tsaye daga wurin kafafunta, bata cikin cikakken lafiya ko natsuwa har kuma lokacin kanta na juyawa don haka bata ma sanin su waye da waye ne a dakin don bata wani bude idanu ba. "Shehi baka yi mamakin ganin Diva kwance magashiyan a dakin nan ba?" Ammar ya faɗa a sadda suke nufan waje don ficewa. Ya ɗan lashi lip din shi na ƙasa idanunsa na ƙasa yace "Wacece hakan?" Shi Ammar ya zaci Shehi ya mantata ne "Wannan 'yar daban da ta kora mana thugs da suka tare mana hanya kwanaki muna dawowa daga wa'azi? Wannan da ta mari Malam Bala ka rama masan?" Cikin ko in kula ya ce "Ooh! Madallah da ta gamu da daidai ita dama ai gaba da gabanta" "Gaskiya kam a yadda taken nan ban yi tunani za'a iya kai ta ƙasa ba" Suna shiga mota Shehi ya ce "Ka daina mamaki, har kasheta sai a yi kuma ta mutu a banza ta je lahira ta yi wa ubangiji bayani muddin wannan abu da ya same ta bai zama mata izina ba" Shiru Ammar yai yana tunanin dama 'yan daba suna sauyawa ne? A sanin shi ko sun gama tsoron mutuwar kwana kadan ne daga sun samu lafiya za su komawa abin da suka bari su ɗora daga inda suka tsaya. Gudu Ammar yayi ta yi saboda sun kusa makara, ko da suka zo basu samu shiga cikin gida ba a nan bakin masallaci suka yi alwala suka shige saboda lokaci ya kure, akwai wani limamin don haka Irshad a Layin gaba kawai suka jera ya barwa wanchan din ya ja don yawanci idan baya nan ko sallah bai riskeshi a gida ba Ustaz Khamis ke yi. Bayan sun idar dole suka shiga gida kan isha saboda Abba da ya kira Ammar, sun samu har lokacin duka mutanen gidan basu dawo ba, daga gidan bikin duk asibiti suka wuce saboda abin da ya faru ya ɗaga musu hankali. Ammar tare da Irshad suka shiga parlorn Abba ɗin suna shiga ya jefawa Ammar takardun hannunsa. "Me wannan Ammar?" Abbiey da ke tsaye ya ce "Usman..." Hannu Abba ya ɗaga masa alamun yayi shiru "Abba..." Ammar da ya ɗauki papers din yana dubawa ya faɗa cikin mamaki da kaduwa "Abba ni? Ni wallahi ban sa hannu a takardar nan ba...me zan yi da makudan kudade haka zuwa personal account da ko suna bai da shi? ba ni ba ne...." Abba ya daka masa tsawa "Yi min shiru Ammar ka daina min rantsuwa a kan ƙarya, dama mutum ba ya taba tsallake jarabawar dukiya! Ammar muna ta jimami kullum yadda kudade suke ɓacewa ba dalili ashe kai ne kake abin da kake so? Ka fa san menene cin Amana... Ka san bala'in dake cikin zamba cikin aminci ka rasa waenda zaka ha'inta sai iyayenka? Wannan ba sa hannunka ba ne?" Hular kansa ya cire yana shafa gashin kanshi ko zai ji iska na shigansa, gabadaya hankalishi a tashe ta yaya? Shi ya san bai taɓa cin amanar company ba ya za'a yi a ce shine yake yin abinda burinshi a gano inda matsalar take? Meyasa zai ha'inci iyayensa? Irshad ne ya kama hannun Abba ya zaunar da shi ya taka ya dauko ruwa ya zo ya miƙa masa, ba musu ya sha don haki yake tsabar yadda yake kidime Sam ba ya so zarginsu ya tabbata ta ya zai cigaba da kallon Ɗan uwansa? Irshad yace "Abba don Allah ka natsu, ka yi hak'uri...Ka daina maganganu cikin fushi hakan ba daidai ba ne, babu ta yadda Ammar zai yi zalunci ko ha'inci, babu ta yadda Ammar zai fara cin amanar Twins enterprises" "Irshad shi yasa nake so yayi min bayanin saka hannun nan da kuma me yake yi da kudade haka?" Abbiey ya ce "Usman ka ƙi saurarata ne kawai amma na tabbatar kaima zuciyarka bata amince da cewa Ammar zai aikata abu haka ba, ka bashi dama yayi magana cikin natsuwa ba faɗa ba" Abbiey yace "Ammar zo ka zauna" Kaman wanda aka jefar haka ya zauna kan kujerar, babu abin da ya kai sharri ko ƙazafi zafi, bai san taya komai ya faru ba, bai san me signing dinshi ke yi wurin ba, bai san ina kudin da aka fitar ya shiga ba Meyasa shi ne zai amsa tuhumar? "Abbiey, Abba wallahil Azeem ban san daga ina wannan ya fito ba kuma ko kusa ba ni da alaka da waennan papers din... Ban san ta yadda signature na ya hau kai ba." Irshad yace "Na yarda Ammar, na san ba za ka taɓa aikata abu makamancin hakan ba! Abbiey mu bi abin nan cikin natsuwa in Shaa Allah za mu gano bakin zaren" Abbiey yace "Haka ne, Nima na tabbatar ba za ka yi hakan ba Abbanku ne ya dauka da zafi amma hakan ba ya cikin tarbiyarku ya sani kaman yadda Nima na sani" Ammar zai yi magana Uncle Ishaq ya shigo. "Na zaci kuna Asibiti me kuke yi a gida? Ba dai maganan da muka gama ba ne Yaya Usman ka sake tasarwa?" Abbiey ya ce "Shi ne Ishaq, amma ya kare in Shaa Allah idan mun yi isha za mu wuce asibitin kuma don Allah maganan nan ya tsaya a tsakaninmu babu amfanin kowa ya sani" Irshad ya miƙe ya kama hannun Ammar yana tattare takardun suka fice ba tare da sun ce komai ba. Sashenshi suka yi a parlor suka zauna Shehi na bin takardun da kallo, duk yadda ba ya son shigar da kanshi kamfanin ya zama dole a gareshi ya shiga. "Ko ma menene da gayya aka yi, Ammar ka kwantar da hankalinka tunda ka sani mun sani baka da masaniya a kan wannan, komai zai daidaita in Shaa Allah with time" Numfashi ya sauke yana shafa fuskarsa a hankali yace "Me yasa sai ni Shehi? Me yasa sai ni za su shafawa kashin kaza?" "Ko ma menene dalilinsu ubangiji ya fi su kar ka tsawwalawa kanka" Sun jima sosai suna tattauna wa akan issuen don har signature Ammar yayi tayi a paper suna comparing da wanchan babu maraba, basu gano bakin zaren ba har isha yayi suka fita suka yi sallah, suna fitowa jama'ar gidan na dawowa Goggo hindatu ce aka bari wurin Daddah din don ta ce duk su dawo su huta da safe za su koma. Abba da Abbiey kuma a lokacin suka wuce, Irshad na da wa'azi don haka shi da malam Bala da kuma Imam suka wuce don Ammar ba ya cikin mood da zai iya zuwa, Ammiey ce ta kira shi yana kokarin nufan Sashenshi. "Ammar idan ka gama abin da kake yi ina son ganinka mana" Ya amsa da Toh kan ya wuce. Bayan yayi wanka ya sauya zuwa kananun kaya ya fito ya nufi sashen Ammie din, ya same ta a parlor tana zaune, dab kafafunta ya zauna "Ammie barka da dare" "Barka dai Ammar, Na ji labarin kun samu zuwa gidansu Na'imatu ko?" Kai ya gyada "eh mun je Ammie" "Ya na ganka wani iri? Akwai matsala ne?" "Akwai Ammie ki taya ni da addu'a kawai" "Me ya faru? Wace iriyar matsala ce da za ta fitar da kai natsuwarka haka?" "Ammie kar ki damu kawai adu'arku muke bukata" "Sai dai mu ƙara Ammar amma kullum kuna cikinta, Allah ya yaye koma menene" Yadda tayi maganan da sanyi sai ya kirkiro murmushi "Ammie Na'imatu tana da natsuwa, hankali da tarbiya bata da wani abin kushewa sosai kuma suka dace da Shehi don bata da rawar kai, shi ma bai kushe ta ba" Murmushi mai kyau Ammie ta yi na jin daadi lallai lokacin auren Shehi ya yi, zuciyarta fess tayi sallama da Ammar bayan sun sake maganar kadan ya fita. Washegari da safe Irshad bai tafi BUK ba, hasali ma class din ya mayar 2-4 saboda daga asibiti company zai je a yau ɗin. Cikin fara sol ɗin thobe ya shirya, farin har tana daukar idanu, yana tsaye gaban mirror ya dauki turarukansa masu kamshin natsuwa ya feshe jikinsa da su kan ya dauki golden colour ɗin jubba ya ɗora a kai, ya dauki Ghutra dinshi gogagge fari sol ya ɗora a kanshi kan ya saka bakin Agal, agogo baƙi na fata ya ɗaura tsintsiyar hannunsa, ya saka wani zoben azurfa mai bakin dutse sosai yayi kyau kaman ko yaushe. Turare ya ƙara fesawa kan ya fito ya saka wa huraira abinci ya karya sama sama saboda Mamaah ta tura masa da abin kari kan ya fito Ammar ya riga ya wuce tun da sassafe saboda bai wani samu baccin kirki ba dole zai tsaya ya wanke sunansa. Don haka yau Shehi da kanshi ya danna remote na hannunsa wata farar Lexus dinshi tayi kara ya taka ya shiga yayi addu'a kan ya ja ya fice daga gidan, ba koyaushe dama yake neman malam Bala ba, wani sa'in yana bashi lokacinshi Imam kuma ya fi fita da su ne idan akwai karatu hasali ma yana da sana'arsa a gefe shima. Kai tsaye Asibiti ya isa, a natse yake takawa har zuwa dakin da Daddah take, ya sa hannu yayi sliding kofar ya shiga. Kamshin da ta ji ya sa ta ɗan yi saurin dago ido daga fruit salad da take sha sai Idanunta suka faɗa cikin nashi da shima gadon ya fara kallo. Dauke kai yayi ya nufi wurin Daddah cikin natsuwa sallama a kan bakinsa. Tamkar doluwa haka ta bi shi da idanu tana mamakin me ya kawo shi ɗakin? Sai ta ga ya ba su baya yana magana da Matar da ta shigo da safe ta karbi wacce ta kwana da tsohuwar gefensu. Jin ya ce "Ammie" Ya sa ta tabbatar mahaifiyarsa ce sai yanzu take ganin kamanninsu har ma da tsohuwar yana kama, dauke kai ta yi ta mayar kan fruit ɗinta. Skipo da Pablo ne tsaye gefenta tana sanye da hoodie navy blue don tun cikin dare tace ita bata son kayan asibitin nan Hajjo da ta kwana da ita ta taimaka mata zuwa bayi tayi wanka ta sauya daga kayan da suka kawo mata. Kasancewar ta kwana babu daadi su Obafiyan duk a sanyaye suke hakan ya sa ɗakin ma yake nan shiru kaman ba su Diva ba ne ciki. Wayanshi yake ɗan taɓawa saboda Daddah riƙe take da Alqur'ani tana karatu. Wani irin buɗe kofar dakin da aka yi da ƙarfi wasu matasa Uku suka shigo ciki har da Pascal da hayaniyarsu suka shigo, shigarsu ya bayyana irin halayensu don daga masu Chain a wuya sai masu abin hannu, gajeren wando da sauransu. "Kaiiii Diva! Abin da ya faru kenan? Shugaba fadi suna kawai ki ga aiki da cikawa ai wallahi sun gama Kwana lafiya ko su waye su..." Daya yayi maganan da ƙarfi. Dayan ya amsa "Iya wuya babu mai taɓa mana ke ya kwan lafiya na rantse da Allah... Duk sai sun ci kutumar babarsuuu" Alqur'anin Daddah ta rufe tana ambaton Subhanallah. Ammie da ta tsorata ma kallonsu kawai take cikin tsantsar mamaki da takaici. A hankali ya juya garesu idanunsa suka sauka a kanta tana ɗan murmushi da bai kai ciki ba, ya mayar da idanunsa kan su "Hala Baku san asibiti kuka shigo ba ko?" Maganan ya zo musu wani iri duk suka juya suna kallonsa, tabdijamm su da idan dayansu na asibiti rasa ma ya za'a yi da su ake bare Diva! Diva ce fa kwance.... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA SHA TARA* "Kaiiii...ya nee? Ka saurara faaa Diva ce nan sai ka jira wallahi" Ta kalli Pablo tuni ya fahimci me take nufi. "Ku yi shiru Kaka ce nan kwance" Ya faɗa yana dan murmushinsu na dabanci sai suka fara shafa kai. "Tuba muke Oga Malam! Kaka barka dai ya jikin dai?" Da kyar ta amsa "Alhamdulillah" Suka shiga mata kirari da addu'a irin dai ladabin 'yan daba, shi dai Shehi tuni ya dauke kai daga gare su. "Allah ya bar mana ke Kaka, Allah ya baki lafiya ai lahira ba yanzu ba sai ya jira wallahi" Ta girgiza kai tana adu'ar Allah ya shirya, Diva ta miƙa musu fruits din tace su sha tuni suka shiga sha suna mata hira hankalinsu ya bar kan su Sheikh. Su ma da yake da ma ba hankali suka wani mayar kansu ba Ammie ta zubawa Daddah abin kari ya karɓa yana zama gefenta sai da suka gaisa kan ya dibo ya shiga bata cikin kulawa. Goggo Dija ta ce "Yau kuma soyayyar ce ta motsa?" Shehi bai ce komai ba sai Daddah ce da ta hadiye abincin bakinta tace "Sa ido dai babu kyau Dija ina ruwanki da shiga shirgin Amarya da angonta" Ammie da Goggo Dijan suka shiga dariya shi dai bai ce komai ba sai ɗan murmushi da yayi har ya gama bata breakfast din ya goge mata baki da tissue ya miƙe. "Daddah zan tafi, akwai abin da kike so in dawo miki da shi?" Cikin natsuwa da kulawa yayi tambayar da harshen fulatanci. "Babu abin da nake so Shehi na gode, Allah ya tsare ya ba da sa'a ubangiji ya kareka" Ya amsa da Ameen kan yayi wa Ammie sallama ya juya. Dole ta gabansu zai wuce kan ya fita hakan ya sa dole idanunsa suka sauka kan gadon tana kwance a yanzu Idanunta lumshe yayinda sauran mutanentan suke ta hira tsakanin su suna cinye duk abin da aka kawo mata, girgiza kai yayi kawai ya fice, zaman Daddah a dakin ya zama dole ne kawai amma da babu abin da zai sa ya bari ta zauna da waennan yaran. Ita kuma Diva ta tafi cikin tunanin abin da ya faru da ita ne da kuma wanda ya taimaka mata, waenchan mutanen basu yi kama da kananun mutane ba kuma a jiya Shaly ke sanar da ita Jagaban ya kasa natsuwa, tashin hankalinshi kaman yana da alaƙa da mutanen da suka yi mata wannan rauni, don tun da ya bar asibitin sau daya ya dawo shi ma a tsaitsaye. Duk yadda za ta yi nazari sai ta rasa makama, tsoronsu yake ji kenan ko kuma dai ya koma gefe ne ya yi aiki a kansu? Meyasa idan da Jagaban suke da dabi za su taɓa ta? Meyasa suka rubuta mata JJ a baya? Waye JJ? Dole ta binciko saboda ba za ta bar su ba, ba su isa su sha ba wallahi. Idanunta da suka rine ta buɗe tana tuna kaɗan daga cikin plate number din su ta kalli Pablo "Akwai Ice?" "Akwai Diva amma bai kamata ki sh..." Kallon da ta mishi ya sa ya zaro tube din kawai ya bata, Skipo ya kunna lighter tana ɗorawa a bakinta suka haɗa idanu da Ammie bata ji ko ɗarrr ba ta cigaba da kallonta dole Ammien ce ta kawar da idanu a ranta tana yi mata fatan shiriya da kuma adu'ar Allah ya tsare mata zuri'a ya shirya su don ba zata iya daukar wannan a ahalinta ba. Abin da Daddah ma ke tunani kenan har ta kasa shiru tace "Yarinya ke da ake maganan ana zargin Wuka ya taɓa miki Ƙoda ke ce da shaye shaye?" Idan akwai abin da Diva ta tsana to shisshigi ne, shiru tayi kaman bata ji ba don kar ta zabga mata rashin mutunci. "Ki kiyayi duniya, wannan abu babu amfanin da yake miki sai ma iyaka ya cutar da lafiyarki, ke macece gidan wani za ki je kuma za ki so ki haihu bakya tunani wannan rayuwa ya taɓa ki a gaba?" Har lokacin Diva bata nuna ta san da ita take yi ba sai Ice ɗin da ta cigaba da sha, su Pablo suna tsaitsaye su ma duk babu wanda ya kalli Daddahn. Goggo Dija ce tace "Ke ma dai ki yi shiru mana Mama, ba rayuwarsu ba? Idan ba ma don babu yadda aka iya ba sun isa ma ko Numfashi ki haɗa da gurbataccen nasu da kwaya ya lalata?" Pascal ya miƙe yana juyowa Diva ta ɗan yi fito sai ya tsaya. "Ku je kawai!" Kwafa yayi sun ci sa'a Diva tana hana su da sai sun yaga bakin mace wallahi. Tuni suka fice daga ɗakin don ta ce su tafin. Pabloo ya tsaya tace shi ma ya je Hajjo ta zo. Shima ficewa yayi suka barta ita kadai sai da tayi high kan ta kwanta tana sake lumshe idanu daidai nan duka 'yan matan gidan suka shigo. Mufida ce ta ɗora Idanunta kan Diva sai ta zaro su gabadaya waje, sauran ta taɓa chan ƙasa tace "ku wannan ba Diva ba? Wannan da ta mari Malam Bala? Wacce Ya Ammar ya nuna mana hotonta?" Tabbas sumayya ta ganta amma ta rasa inda ta santa ashe ita ce! Kuskus suka cigaba da yi duk tana jin su amma bata son shiga harkarsu don bata kaunar wani abu ya sake haɗata da malamin ɗansu ya riƙe wa'azinshi ta riƙe rayuwarta. Su Mufida dai sun kasa zaman kirki suka gudu saboda tsoron kar su mata laifi duk da bata tanka kowa ba kuma bata buɗe idanu ba. **** Shi kam Irshad Company ya fara zuwa, yana da office duk da ba zama yake ba Audit team ya nemi gani waenda su ne a ka'ida duk abin da ya shafi wani ɓarna a company bincike ne ko sauransu su suke yi a sirrance kuma shi ne Head of Internal Audit & Compliance dayawa basu sanshi ba saboda Assistant dinshi ne ke kula da komai don haka karamin meeting suka haɗa farko ya fara da Introduction kowa ma yayi introducing kanshi kan ya shiga abin da ya kawo shi. Ya tattauna da su akan abubuwan dake faruwa ya nemi jin aikin da suke yi a ƙasa, bayan ya duba kananun ayyukan yace duk za su ajiye su dukufa kan ɓace bacen kudi daga ina ake samu kuma su wa suke amfana, ya musu babban gargadi akan rike sirri hakanan idan ya kama cin amana ba zai bari ba su team ɗin Audit ba'a san su da fitar da magana ko cin amana ba saboda su ne masu tsage gaskiya duk yadda take a cikin company. Daga nan suka buɗe file na bincikensu, ya sallami sauran Assistant dinshi zai fice ya dakatar da shi "Hashim!" Ya dawo daga baya "Yes Sir" "Zan wuce yanzu, ka tabbatar ka kiyaye abin da na ce and make sure na ga komai a email dina before asr" "In Shaa Allah" Daga nan ya wuce, shima Sheikh fitowa yayi ya tafi office na Abbiey sun ɗan yi magana kan ya fito ya tafi office na Ammar shima sun yi magana akan binciken ya nuna mishi inda nashi binciken ya kwana da yadda Digits na kudi ke karuwa yana saka hannu bai sani ba, tattare duk bayanan ya sa Ammar yayi ya tura mishi a email akan da dare zai nazarci takardun. Daga nan suka fito tare da Ammar din suka yi sallah a masallacin company kan Shehi ya wuce BUK don gabatar da lectures. *** Har ya gama lectures ɗin bata cikin natsuwarta Allah ya gani tana jin shi har tsakiyar ranta a da crushing kawai take amma tunda ya bayyana matsayin wanda za'a haɗa su ta ji tana mutuwar son shi, sai dai kash ta ɓangarenshi ko kallon inda take bata ga ya yi ba. Bata wani damu ba sanin da ma yana da wannan kamewar za ta mishi uzuri kila sai an ɗaura kan ya fara nuna mata soyayya, ta ki faɗawa kawayenta komai tana jin su kaman yadda suka saba kullum suna ta yabonshi, ko da aka tashi lectures din ma office dinshi yaje yayi alwala ya fito zuwa masallaci bayan ya yi la'asar ya fito ya nufi gida a hanya ya wuce su da mota ta bi motar da kallo tana ji kaman zuciyarta ne ya tafi da shi. **** Gida ya je, da wanka ya fara don jin shi yake a gajiye kwarai, Wata farar jallabiyar ya sake sakawa amma a yanzu Ghutra kawai ya sa ya rufe kanshi ya feshe jikinshi da turarukansa lattafa's masu kamshin natsuwa kan ya fito sashen Mamaah ya nufa. "Wa'alaikassalam warahmatullah Shehi ka dawo?" Ya amsa yana zama daga ƙasa "Eh maamah sannu da gida, Ammar bai shigo ba?" "Ya shigo amma ya ce min kanshi na ɗan ciwo zai kwanta ya huta sai dare za shi asibitin" "Ya kamata ma su sallameta ai ta karasa jinyar a gida zaman asibitin ba daadi yake mata ba" Mamaah tace "Aikam, ni ba zaman ba ne ba ma yadda aka haɗata daki da 'Yan daba masu shaye shayen nan ne bai yi ba samm babu wanda ya san me za su aikata suka sha suka bugu don abin ba gaskiya yake faɗa musu ba" Ji yayi wani abu ya motsa mishi a rai, ya ɗan lumshe idanu ya buɗe "Allah ya shirye su" Ta amsa da Ameen kan ta miƙe ta kawo mishi abinci kaɗan ya ci ya ce mata zai shiga asibitin don da dare yana da karatu ba zai samu zuwa ba. Allah ya tsare tayi mishi ya fito, daga harabar yake tsinkayo hirar su Mufida na irin tsoron da suka ji yau na ganin Diva, hawwa take cewa "Abin mamaki kuma a asibitin ma fa shaye shayen ta take, wani irin bala'i ne wannan ka mutu a buge?" Mufida tace "Baki ji Goggo Dija na faɗawa Goggo hindatu har rashin kunya suka so yi wa Daddah ba don ta nemi yi musu nasiha?" "Ta ce ita Diva din ce ma ta hana su amma na yi mamaki an ce bata daukar wargi komin girma ko tsufanka ya aka yi bata dauki mataki kan Daddahn ba?" Cewar Aisha Sumayya tace "Ni dai fatana a sallami Daddah bata ɓarkawa daya daga cikinmu ciki ba don fa zubar da jini a wurinta ba komai ba ne" Motsinshi da suka ji ya sa suka juyo sai suka natsu, suka gaishe shi ya amsa kawai ya wuce. Malam Bala na nan don haka key ya bashi ya fitar da motar shi kuma ya shiga suka fice zuwa asibitin, a ranshi saƙe-saƙe ne mai yawa haka kawai yake jin wani iri ambaton Allah ya cigaba da yi har suka isa ya sauka suka nufi ciki da malam Bala hannunshi rike da fruits dayawa da Shehi din ya sa suka tsaya suka saya. Shehi ne a gaba hannayenshi goye a baya yana tafiya cikin natsuwa, Malam Bala na daga bayanshi har suka isa ɗakin ya buɗe kofar ya shiga Malam Bala na sanyo kai wa zai gani? Salati ya saki har ledojin hannunshi na shirin kubucewa su watse Allah ya taimaka ya riƙe kammm, salatinshi shi ya ja hankalin dukkansu har su Daddah. "Malam Bala lafiya?" Shehi ya dawo da baya yana tambayarshi ganin yadda ya firgice. Da ido yake kifkifta mishi Diva, a hankali Shehi ya juya ya kalleta itama su take kallo amma fuskarta a kame kaman ko da yaushe. "Shi kuma wannan lafiya?" Skipo ya yi maganan yana sake kallonshi da kyau don tabbatar da ba mahaukaci ba ne. Irshad ya hade rai "Haba Malam Bala, me haka kaman mala'ikan mutuwa ka gani?" "Ranka ya dade ai bata da maraba da mala'ikan mutuwa, duk inda take mala'ikan na tare da ita" Goshi Irshad ya ɗan shafa yana ɗan girgiza kai idanunsa suna fallasa yanayinsa na surkin haushi, bacin rai da takaici hade da kuncin da yake ji a ran shi yace "Ka natsu, babu abin da za ta maka not under my watch" Yana kai nan ya karɓi ledojin ya wuce ciki, da sauri malam Bala ya bi bayanshi yana sake Satan kallon Diva din da ta dauke kai ma daga garesu sabon wayan da Jagaban ya kawo mata take dubawa ya sanar mata nata ya farfashe tayun motanta duka sai an sake saya don sun lalata. Shi kuwa malam Bala na zuwa ya gaishe da Daddah sama sama ya ce wa Sheikh zai jira a waje da sauri ya fice. "Amma lafiya malam Bala ke nan a firgice?" Goggo Hindatu da ita ce ta karɓi Goggo Dija da Ammie da basu wani jima da fita ba Sheikh din ya shigo da alama ma sun yi saɓani ne a hanya tace chan ƙasa kasa da fulatanci. "Wannan ita ce ta kusa kashe shi fah Mama" Zaro ido Daddah tayi ta juya tana kallon Diva ashe hatsarinta ya kai haka? Hanjin cikinta ya kada kenan shiru ta mata tana ta mata nasiha da ta yi niyya tuni za ta kashe ta a banza tunda kashe mutane take? "Shehi ni dai a sallameni ba zan kara awa guda a asibitin nan ba" Ta faɗa da iyaka gaskiyarta. Zama ya yi a kujeran gefen gadon "Za'a sallameki Daddah ba Likitan ya ce da yamman nan zai dawo ya duba hoton ba?" Kai ta gyaɗa mishi "Idan ya zo zai sallameki ki kwantar da hankalinki" Diva ta ɗaga ido tana kallon pascal da ke ba wa Obafiyan da Skipo labarin Dagar da suka yi da Kawunshi akan wai zai kama shi ya kai shi Rehabilitation center saboda kawai Mamanshi ta kai mishi ƙararshi. "Kun ga 'yar tseren da muka yi wai? Yo hauka nake na tsaya ya kama ni ya kai a ɗaure kaman kare ko rago?" "Ya aka yi ya kyaleka to?" Skipo ya tambaya yana dariya don a cikinsu Pascal ya fi iya basu nisahadi barkwanci ne da shi kaman me. "Katanga muka ta haurawa sai da muka yi nisa ya fahimci fa gidan matan aure muke ta afkawa yana bi na a guje, wasu fa har sun zaci ma sabon kamu ne in gaya muku na ɓulla wani layi kawai na yi ihun mahaukaci a taimakeni ya fi ƙarfina, Jama'a suka rufu don taimakona aka yi ramm da shi yana ihun ba mahaukaci ba ne raina musu hankali nake tuni na zame nayi tafiyata na bar shi da su yanzu za su kai shi Psychiatric madadina da zai kai Rehabilitation center" Dariya sosai suke yi har Diva da yana wahala tayi dariya mai sauti, sautin dariyarta ne ya ja hankalin Sheikh Irshad Al-Noor don bai ɗauka tana yin ba duk haɗuwar da suka yi fuskarta tamkar an yi mutuwa, duk yadda ya so ya ƙi kallon wurin idanunsa suka ja sa ya juya a hankali ya kalli wurin. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA ASHIRIN* A hankali kuma sai ya janye idanun ya miƙe ya fice daga ɗakin, ba'a jima ba ya shigo da likita har kuma lokacin hiransu suke tsakaninsu ita sai ya kama take saka baki, yana mamaki a ce mace ce bata da lafiya amma maza ne zagaye da ita, yadda bata nuna ta sanshi ba shi hakan faranta masa yayi don bai san ta ya ma zai nuna wata alaƙa ko min nisanta tsakaninsu ba iyayenshi na wurin don abin Sam ba tsari, bai taɓa cin karo da marar lafiya bai yi masa gaisuwa ba ko fatan waraka daga rabbi ba sai a kanta haka kawai sannu ba ya so ya ji ya haɗa su. Likitan ya duba hoton da aka karbo ya tabbatar ba wani matsala yace za su iya tafiya da ita kawai a kula da kafan Sossai bayan sati biyu a zo a cire POP da aka saka mata. Goggo hindatu ta tattare komai wasu nurses suka zo suka taimaka musu wurin ɗora ta kan wheelchair Goggo hindatu ta tura ta a tsorace suke da su Diva din don a yanzu sun ƙaru hakan yasa ko Daddah da ke son yi mata Allah ya kara sauki bata yi ba suka fice da ma shi ya jima waje yana jiransu. Kofar da suka rufe ta zurawa idanu ba yau aka saba gudunsu ko kiyaye wa inda suke ba hasali hakan na yi mata daaɗi kwarai ta zo wuri a shiga taitayi kuma a natsu har ana kiyaye hasalarta amma a wannan karo ta ji abin babu daaɗi, suna nuna kaman aljana ce ko wata halitta mai muni ba mutum ba hakan ya tsaya mata a rai amma ta basar. Tana sauraron hiran su Shaly kaman ko yaushe, itama a ranar aka yi hoton hakarkarin aka ci sa'a wukar bai taɓa mata koda ba, daga nan hankalinsu duk ya sake kwanciya amma ban da Jagaban da suka rasa kanshi a kwanakin duk ya zama very busy baya zama sun kuma kasa pinpointing matsalar. Ta ɓangaren su Shehi yana driving da hannu ɗaya dayar hannun yana riƙe da waya da Abbiey yake magana akan idan sun tashi aiki kar su je asibitin an riga an sallami Daddah ɗin, bayan sun gama ya ajiye wayan yana sauraron hirar Daddah da Goggonshi Dija duk a kan su Diva ne da irin abin da ta sha a ɗakin da kuma rashin tarbiyarsu har suka isa gida bai cewa kowa komai ba. A kofan sashen Daddah din ya yi parking duk ahalin gidan suna tsaye har ta sauka suna yi mata sannu har cikin parlor, Daddah kaka ce wacce bata da tamka, daga jikokin surukanta har yaranta bata yarda ta takurawa kowa ba hakan ya sa ta zama dattijuwar arziki da kowa ke ji da ita a gidan, ta kan kafe akan lamari amma muddin ka ga ta kafe ɗin to abin babba ne, sun jima zaune ana ta hira a parlorn kan suka watse saboda magrib da ya karato kowa ya tafi shirin sallah. Shi dai Shehi tunda ya sauke su ya wuce bangarenshi wasu ayyuka ya rage Sossai bai tashi ba sai lokacin sallah ya yi alwala ya fito ya saka wa magenshi abinci daga nan ya fice zuwa masallaci. ***** "Abbiey baka ce komai ba" Ammie ta faɗa tana ƙarasa tattare kwanukan abincin da Abbiey din ya gama ci, ya ɗan yi murmushi "Da alama kin matsu ki ga 'yan jikokinki" Itama tayi murmushi "Toh ai na ga ne ku babu ruwanku da musu magana akan auren, har yaushe zai mayar da hankali idan ba'a tuna masa? Shekarun suna ta tafiya gwara a yi din muna raye" Yace "In Shaa Allah zamu yi magana da ɗan uwana sai mu ga yadda abun zai kasance, amma ya je ya ga yarinyar kika ce?" Cikin farin ciki marar misaltuwa da ya zo wa Ammie tace "eh ya je, kuma daga shi har ɗan uwansa Ammar sun yaba kwarai da hankali da natsuwarta Nima kuma na yaba da ita gaskiya" "Amma kina ganin ba mu tauye shi ba kawai mu ce ya yi aure ba tare da shi ya ganta ya ji yana so ba?" "Toh sai yaushe za mu jira Abbiey? Tunda bashi da wannan niyyan gwara mu shige mishi gaba kawai matukar nagartar yarinyar ya yi daidai da nashi" Abbiey ya sauke Numfashi Sam baya son tauye iyalansa amma tunda sun gama yanke hukunci za'a yadda suka ce ɗin. "Shikenan za mu yi magana da Abbansu mu tsara yadda abin zai kasance" Ya faɗa yana Miƙewa itama ta miƙe ta bi bayanshi zuwa dakinshi fuskarta cike da annashuwa. Da daren Ammie ta kasa hakura ta kaiwa 'yar uwarta ziyara suka fara tattauna wa akan abubuwan da za su tsara suna cikin maganan ne ma Shehi da Ammar suka shigo wuraren tara da wani abu. Sun yi mamakin ganinsu tare Ammar sai da ya tanka "Yau kuma hirar 'yan uwantaka ne ya tashi har cikin dare Ammiey?" Maamah tace "Kin ga wanda ya kamata a yi wa aure don yana bukatar abin da zai ɗauke hankalinsa har ya kashe wannan bakin da ba ya shiru" Dariya yayi Shehi na murmurshi ya zo ya zauna kan ya gaishe da iyayen nashi suka amsa cikin kulawa kan Ammiey tace "Rabu da shi Maamah shi waye ya raba shi da nashi ɗan uwan ba gashi kullum suna tare ba?" "Daga gani dai hirar ta nishadi ce mu zauna ko mu yi gaba?" Ammar ya sake faɗa yana zama cikin murmushi shima ya gaishe su haka yake don ma ba ya mood ne amma iyayenshi tamkar kakanninshi haka ya mayar da su akwai wannan sakewar da kuma hira Sossai tsakaninsu ba kaman Shehi ba ko don zaman kasan bai yi shi yana ƙarami bane sai da ya girma oho. "Zancen auren ɗan uwanka ne muke tattaunawa" Haka kawai Shehi ya ji gabanshi ya ɗan fadi amma bai dago ba Ammar ya amsawa Ammiey "Masha Allah! Mu fara shirye shirye kawai mu ma da alama ba za'a ɗau lokaci ba" Maamah tace "In Shaa Allahu soon za'a yi dama matar ne ake jira ba komai ba" Sai ta kalli Shehi "A kawo maka abinci ne Sheikh?" Ya ɗan dago kaɗan "A'a Maamah ba buƙata zan sha Laban kawai ya wadatar" "uhmmm! ka ji Larabawa" Ammar ya faɗa da zolaya, Irshad ya kalle shi ya harareshi ina ruwanshi dariya kawai yayi sai Irshad ya zuba masa idanu. Yana mamakin yadda Ammar ya danne yanayinshi yake wasa da dariya, ƙazafi irin na sata ko ya yake babu daaɗi cin rai ne dashi da hana bacci gashi har yanzu Abba ba kulashi yayi ba bare ya fahimci babu hannun Ammar a lamarin ɓacewar kudin companyn. Maganan Ammiey ne ya dawo da shi ɗan tunanin da ya tafi sai ya kalle su sun miƙe Ammiey za ta tafi Mamaah kuma za ta mata rakiya sai ka ce ba gida daya suke ba, sai da safe suka mata ta wuce sun jira Maamah ta dawo itama suka mata sallama kan suka fice kowa yayi sashenshi. ***** Tsaye take gaban reception ɗin za ta saka Hannu a wani takarda da aka rubuta record book, Rubutun ta zubawa idanu inda aka shigar da sunanta ranar da aka kawota sai ta ɗan lumshe ido tana tuna yadda ya riƙe ta da yadda muryarsa dake fita daga nesa Sossai a cikin kanta ke Salati da ambaton wani suna da ba zata ce ta ji ba. "Suhan Muhammad" Ta maimaita, shi ne rubuce a katin da ya buɗe ya aka yi ya san sunanta? A saninta dai bata tare da kowani identification card da ya bayyana sunanta, babu waya a hannunta ya aka yi ya san sunanta? Canular da ba'a kai ga cire wa ba ta zubawa idanu kuma har jininshi ya bada a lokacin da nata ke shirin ƙarewa aka sanya mata, yanzu jininshi ne ke yawo surke da nata. "Waye wannan?" Ta faɗa chan ƙasa, Jagaban dake tsaye da ita yace "kika ce?" Sai ta girgiza kai kawai ta saka hannun, suka karasa nurses station aka cire canular ɗin kan suka fice daga asibitin, da kanta ta buɗe seat na gaba ta zauna ta kwantar da kanta jikin kujerar. Saboda ita Jagaban ke Driving cikin hankali idan ba haka ba shi ma ya ƙware a rough driving yadda take yi idan na rashin mutuncinta na kusa. "Waye JJ baba? Meyasa ya nemi kasheni?" Sai da motar ta kusa kwacewa daga hannun Jagaban, ya samu ya dakatar yana kallon ta don kaman saukar aradu haka ya ji maganan nata, idanu ya ɗan rufe ya buɗe "Sohana yanzu ba lokacin wannan magana ba ne, ni kaina ban san waye JJ ba da kuma dalilin taɓaki amma na yi alkawari zan nemo shi ko a ina yake sai ya san ya taɓa ki, daga yanzu kuma bana so ko da wasa ki fita ke kaɗai musamman idan cikin dare ne" Ta koma ta jingina da motar tana zubawa waje idanu a karo na farko ta ji bata yarda da maganan Baban ba, amma itama ba za ta zauna ba za ta yi iya bincikenta wurin sanin menene dalilinsu JJ na zaɓarta ya nemi kashe ta, waye ne wannan da ya taimaka mata? Abu biyu ne gabanta a yanzu. Har suka isa bata sake magana ba, sun samu gidan cike sai maraba ake mata cikin salonsu na dabanci tayi murmushi tana hade hannaye alamar godiya da haka ta shige ciki Shaly da Zubash suka bi bayanta. **** "Zainab! Tun muna shaida juna ki fitar da sarkar nan" Dattijon yayi magana da karfin gaske muryarshi na fitar da gajiya da wani irin yanayi marar misaltuwa. "Ni dai sharri ne kawai amma ban ɗauki wani sarka ba Daddy a shafa min lafiya..." Hannu ya kai zai zuba mata mari matar dake zaune daga gefenta tayi zuruf ta tare. "A'a Alhaji ba za ka dukar min yarinya ba, tace bata dauka ba bata dauka ba to me za ta fitar? Don kawai ta zama kaddarar gidan nan sai aka ce duk wani mugun abu ita ce?" "Wallahi wallahi Subai'a idan na miki Allah ya isa sai Allah ya saka min akan yaranki, Allah ya gani kuma shine shaida iya kokari na yi wurin tarbiyatar da yarinyar nan amma ke bata taɓa laifi a idanun ki ba, babu wanda ya isa ya hukuntata a duniyar nan baki ɗaga ido kin kalleshi kin rama mata ba, yanzu yadda take yawo lungu lungu da gungun 'yan daba ashe bai zama miki izina ba? Wallahi ko rantsuwa zan yi babu kaffara Zainab ce ta ɗauki sarkar nan don haka ku fitar na gaji da biyan abinda ban ci ba" Wacce aka kira Subai'a ta kalli Alhajin tace "Ai dama abin da kake nema kenan kiris ka daura min alhakin lalacewar Zainab, kun kyauta ke kuma suwaiba in karya kika mata ma ke da Allah. Zainab ke tashi mu tafi" Ta miƙe tare da jan hannun Zainab din suka fita, Alhj ya tafi da baya kaman zai fadi suwaiba ta tare shi suka zauna. "Ba damuwa Alhj na hakura da sarkar duk da yana cikin zinari na mai tsada amma ba komai, Allah ya shirya mana ita ya sa ta gane don Allah kar ka ɗaga hankalinka" "Suwaiba na gaji da ganin Subai'a da Zainab a gidan nan na gaji" "Na sani amma babu ta yadda hannunka zai rube ka yanke ka yar, kana addu'a baka taɓa gajiya ba ka cigaba in Shaa Allah za su chanza" Ya kalleta "Kin san dai Ƙarfe ɗaya bai taɓa amo ba dole sai ya haɗu da wani karfen, kina ga Zainab ta cigaba da zama da Subai'a da ta watsar da alhakin tarbiya da Allah ya ɗora mata ta ɗauki soyayya mai muni ta ɗora wa kanta akan yaranta zai bari su shiryu? Ba Za su taɓa shiryu wa ba ina tsoron tambayar Allah akan yaran nan" Shiru suka yi cikin jimami, tsawon shekarun talatin da wani abu suke rayuwa tare da 'ya'yansu amma duk wanda ya shigo gidan ya san Yaran Suwaiba daban da yaran subai'a, samm bata yarda da abin da zai taɓa su ba, bata yarda ko da wasa sun yi laifi wani lokacin ko a kan Idanunta kuwa za ta mutsuke ta nuna basu yin ba kuma ya sha kenan. Wannan sakacin ya jefa Zee-zee cikin halin da take ciki har ma take bibiyar Diva dukda kudin mahaifinta, yayi iya kokarinsa har Rehabilitation center ya kai ta Maman taje ta ciro ta, kuma ba ita kaɗai ba har yayyunta biyu duk a watse suke a kan titi babu wanda ya tsaya ya tsinana wa kanshi komai ga yaran Suwaiba har suna iya ɗaga abu da alfaharin nasu ne na ƙashin kansu. Suna fita Zee za ta fice daga gidan Maman ta riko ta "Ina kuma za ki je? Meyasa bakya gajiya da janyomin magana ne?" Kallon yaushe aka fara wannan ta mata kan ta zare hannunta "Wurin Diva za ni" Tana kai nan ta yi gaba, a cikinsu duk babu mai daukar abin wani idan ka ga sun yi abu da abin wani to sun lalata ne don Diva bata shiri da ɓarawo bata son sata kwata kwata, basu damu da inda Zee ke samun kudi take saye sayen abubuwan mayenta ba har wani lokacin ma ta sayawa kowa free sanin cewa babanta mai kudin ne ita kuma ta ishe 'yan gidan da dauke dauke duk abin da suka ajiye mai muhimmanci in dai ta gani sai ta dauke shi. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA* "Ma'u don Allah ki buɗe baki ki ci kin ji?" Jiddah ta faɗa cikin muryar rarrashi don Ma'u yini guda kenan babu abin da ta yarda ta ci kullum lamarin kara ta'azzara yake, bata san me ya same ta ba amma ko a hirar da ta tsinkayi masu tsaron nasu suna yi ta ji suna magana akan rashin ƙarfin kwakwalwa shi yasa trauma din yayi hitting ɗinta Sossai kuma muddin ba kudi aka kashe a kanta kuma aka haɗa da kwararrun ma'aikatan jinya ba kwakwalwarta na shutting kanshi down a je a je za ta iya faɗuwa ta mutu. Dukda hankalin jidda a tsanani tashe yake bata daina addu'a da rokon Allah ya hana kalmansu tabbata ba, tun da suka gano lagonta sai suka kashe mata baki, ya zamana bata iya yi musu musu sam, iyakaci saƙo take kaiwa wanda a wani sashe na zuciyarta tana jin har hakan ma bai dace ba kila amfani ake da miyagun kwayoyi ana lalata al'umma, ta tabbatar babu wani abu da za'a fitar daga gidan da kyakyawar nufi don dukkansu mugaye ne, dukkansu babu mai imani ciki. Kuka kawai jiddah ta shiga yi a wurin cikin rashin makama, ganin irin kukan da take yi yas a Ma'un miƙa hannu ta riƙe nata sai ta dago da sauri, ruwan ta bata ta karɓa ta sha ta shiga bata abinci sai ta ga tana ci, hawaye ke zubarwa jiddah har Asm'aun ta gama cin abincin bata yi ko loma guda ba kuma nasu ne su biyun. J da yake hakimce cikin kujera yana ɗan juyawa a hankali sanye da wasu bakaƙen kaya ya dauke kai ya kalli shadow "Wannan kayan idan ta kara sati bata da amfani a yi da ita kudu a tabbatar ta yi nesa da nan a zubar ta bi ruwa" "An gama J na fahimta" Ya miƙe ya fice yana duba lokaci, Wayanshi ya zaro ya zubawa sakon kai ido na seconds kan yayi wani murmushi. "Yaro yaro ne! Yaro bai san wuta ba sai ya taka!" Mota aka buɗe mishi ya shiga suka fice daga arear gabadaya. **** Shehi ya zama busy kwarai a kwanakin da suka biyo baya, zai iya cewa ma bai taɓa cin karo da kwanaki irin wannan ba ya haɗa stress mai yawa hakan ya sa Sam bashi da wani lokaci, tuni ya manta da wata Na'imatu da ya je ya gani yayin da a gafe su Ammiey ke ta hidimarsu har kuma lokacin Abbiey basu yanke hukunci ba. Shi kam gabadaya damuwarshi sunan Ammar ya wanku, Abba ya rage fushin da yake yi ba wai suna ganin laifin Abba bane don yana fushi a'a abu da dole kowani uba zai ji babu daaɗi abin da idan ya tambaya za'a bashi to me na zamba? Shi kuma Ammar ganin ɗan uwanshi ya shiga lamarin Sossai sai ya ja baya ya bar mishi. A ɓangaren wa'azi sai ya ƙara zafi ya zamana kullum maganan shi kan azzaluman 'yan siyasa da yadda za mu farka mu tsayawa kawunanmu, barazanarshi ga azzaluman sai ya ƙaru shi zai yi ya kwana lafiya amma da zaran ya fita duniya su kuma babu bacci. Yau yana zaune a office dinshi cikin BUK yana duba wasu takardu ya ji an yi knocking. Ya amsa sai aka tura kofar aka shigo, bai ɗago ba sai da ya ji shiru kan ya ɗago sai idanunshi suka faɗa kanta yadda ya tsare ta da su sai ta rasa natsuwa, bakinta ya shiga rawa ta rasa me za ta ce. Cikin rashin sanayya yace "How may I help you?" Wani dummmmmm kanta yayi, yana nufin bai gane ta ba ne ko yaya? Rawa muryarta ya fara dukda maganan da take so ta yi da kyar tace "Na'ima ce" "Na'ima?" Ya maimaita sunan trying really hard to be polite. Sai ta juya da sauri ta fice wani irin kunya mai yawa na rufeta, a lokaci ɗaya hawaye ya shiga zubo mata ashe haukanta take, ashe tana nan tana baza hauka bata sani ba ya mance da ita ma, zuciyarta ya shiga ƙuna tun daga ranar da aka ɗarsa mata shi bayan dogon crushing bata samu isashen bacci ba ta zaci ko a waya zai ƙirata amma shiru, ta yi tunanin to kila ya sake zuwa nan ma shiru ta kasa hak'uri da kyar ta yi gaining courage na zuwa ashe rabon tayi kwanan baƙin ciki ne ya kaita. Shi kam aikin shi ya cigaba da yi yana taɓe baki mata sun sha zuwa mishi haka don sai da ya shata layi mai girman gaske ya buga misali na ban mamaki da wata kan ya shawo matsalar zirga-zirgan su na ba gaira ba dalili da sunan gaisuwa ko wata kyauta(Gift). Sai da ya gama ya miƙe ya bar makarantar yau ma shi kaɗai ne don haka da kanshi yake driving har Company, office ya wuce yana duba inda suka kwana ganin jiya-e-yau ya sa ranshi matukar ɓaci. "Meyasa Hisham? Meyasa?" "Ranka ya dade...." Hannu ya ɗaga mishi sai ya miƙe tsaye "A da ina zaton cewa matsala ake samu na ƙirge har kudin su ke ɓacewa amma a yanzu yadda ake tempering aikina ya tabbatar min da cewa da gaske sama da faɗi ake yi da kudaden nan. Ban san amfanin kiran kanku Audit ba muddin za'a samu wani yana lalata duk ayyukanku daga ciki" Hisham yace "Ka yi hak'uri Ranka ya dade" "Ba zan yi hak'uri ba Hisham!" Ba da tsawa ko ihu yayi maganan ba sai dai abin da ke zuciyarshi ne ya faɗa, ba zai yi hak'uri ba idan ya kawar da ido akan abin aikinshi ya cuta tunda yana da albashi already, ko ba don albashi ba companyn Abbiey kam ai na zuri'arsu ne gabadaya tunda don su aka yi kuma ake kan yi. "Na dakatar da kowa a cikinku zan yi bincike mai tsauri duk wanda na kama da cin amana dole zai bar ma'aikatan ba ɗaga kafa, abun kunya ne a gare mu a ce daga wannan team ɗin ne zance ke fita har muke ba wa azzalumai daman ɓuya.... Ka isar musu da sakon nan you can leave" Kwarjini da kuma yadda ya Kamen ne bai taɓa gani ba hakan ya sa dole bai iya sake furta komai ba ya fice, shima Miƙewa yayi ya fice gabadaya daga companyn saboda ɓacin rai. Gida ya koma bayan yayi parking ya fito yana amsa call a dab kofan sashenshi ya gamu da Imam suka karasa tare don haka a parlorn ƙasan ya zauna Imam na tsaye har ya kamallah kan Imam yayi mishi barka da dawowa. "Ga wannan an ce in baka ne har makaranta aka kawo" Karɓar envelope din yayi ya buɗe ya fitar da farar papern ya karanta, sai ya ɗan yi tsaki... Ya miƙa wa Imam "Ka ƙirasu ka tabbatar musu matukar ɗauke dauken hotuna da kuma videos zai kawo su ba ma buƙata" Imam ya ɗan yi tsaii daga fah gomnati ne suke offering taimakawa Islamiyyarsa ta Al-Noor da kuma makarantar maza ta Auladul-Noor sai kuma masallacin shi Al-Noor Mosque, suna so duk abin da babu su zuba saboda jin Daaɗin ibada amma yana ba da umurnin ban da hotuna? Kallonshi Shehi yayi sai ya ce "Ka daina mamaki Imam, a sanina da 'Yan siyasa suna so ne kawai su yi campaign da hakan, ko ma su yi amfani da wannan daman wurin bata sunana tunda sun san da su azzaluman gomnatin nake faɗa, idan aka ga sun yaɗa ɗan wani abu kalilan da za su zuba ne wa gobensu ba don ni ba cewa za'a yi ina ƙin su amma ina karbar abin su da jin daaɗi su al'umma me zai hana su karɓa su kuma zaɓe su?" Ya miƙe tsaye "Gobe zan tafi Abuja kuma zan yi akallah sati biyu so za su zo bana nan make sure kun yi abin da ya dace dukda ma zan kira Sheikh Mukhtar" "Toh in Shaa Allahu" Imam ya amsa a lokacin Shehi ya gama haurawa Saman. Wanka yayi saboda wani irin gajiya da yake ji, a tsaitsaye ya haɗa loggage dinsa don tafiya ce ta abin da ya shafi musulunci dole kuma ya kasance yana nan ɗin don har cikin gidan aka kawo mishi kati akan gagarumin taron. Kaman yadda yake son jallabiya ya kuma saba da su fiye da kowani kaya farar jallabiya ce jikinsa ya saka Ghutra a kansa don idan bai saka ba ji yake kaman ba komai yake tafiya abu ne da ya riga ya saba for many years, Kasa ya sauka ya nufi wurin Maamah yana shiga ya samu tana duba wasu turarukan wuta. Bayan sun gaisa tace "Yauwa da ma yanzu nake zancenka a raina ga Turarukan wuta masu kamshi da na yi placing order an kawo daga Bauchi na sanka da turarukan wuta na tabbatar za ka ji daaɗinsu kwarai don ba dai daaɗi ba" Tayi maganar tana miƙa mishi Sandal chips na bakhoor by seemah, dukda bai saba sayan turarukan wutan ma anan ba daga Saudia yake zuwa da abin shi jin wannan sai da ya sake kallon sticker ɗin yana tabbatarwa a Nigeria aka haɗa wannan ɗin, Sossai ya san turarukan wuta kuma ya yaba da kamshin wannan Sossai da Sossai. Miƙewa Maamah tayi ta je don ta kawo masa abinci ya ɗauki dayan dake cikin kyakyawar paper bag ɗin ya buɗe yana ɗan kai wa hancinshi ya shaki kamshin kadan ya duba sunan Hawii. Lallai ya samu plug da zai yi holding on to a Nigeria. (Domin samun wannan turarukan wutan masu Daaɗin kamshi ku tuntuɓi bakhoor by seemah a wannan layi (08021689184) babu kalar khumrah, misk ko Turaren da ba za ku samu ba tasted and trusted) Bayan ya gama cin abincin yake sanar da ita tafiyanshi Abuja gobe da yammaci, addu'a tayi masa ya ɗauki paper bag ɗin yayi mata godiya kan ya fice, kyauta mai matukar muhimmanci da aka bashi a kwanakin kenan. Sashen Daddah yaje ya gaishe ta da jiki ta ma samu sauki don tana taka ƙafar lafiya lau suka gaisa da Goggoninsa kan ya nufi wurin Ammiey ƙarshe ya sanar mata batun tafiyar bayan sun gama tattaunawa har zai miƙe tace "Batun yarinyar nan Na'imatu kana kuwa ƙiranta a waya?" Sai da gabansa ya ɗan faɗi da kyar ma ya tuna sai kuma fuskarta ta fara mishi gizo kaman ita ce ta zo dazu ya maimaita sunan a ransa da wanda ta faɗa tabbas ita ce, baki ya ɗan taɓe kaɗan bai ce komai ba. Shirun shi ya tabbatarwa Ammiey da baya kira ɗin. "Ka yi kokari ko baka je ba ka ƙirata a waya" Ya amsa da "In Shaa Allah" Kan ya miƙe ya fice daga sashen, sashenshi ya koma dukda masallaci zai fita sai da ya ƙona turarukan nan duka yana jin natsuwa da kamshinsu har ransa, daga nan ya ɗan saka wasu oils a hannu da bayan kunnensa kan ya ɗora Jubba baka da gold ya fice daga sashen zuwa Islamiyyarsa don supervising kan lokacin sallah ya shiga. ***** "Sohana na tura miki ticket dinki ta waya sai ki shirya gobe ki wuce Abuja" Tana kishingide ne a parlorn Idanunta na kan TV da ake haska wani American film na faɗa, a hankali ta miƙe da kyau tana kallonsa "Abuja? Me zan yi a Abuja kuma?" "Akwai sakon da nake so ki kai min ne" Yayi maganar ba tare da ya bata fuskar wata tambaya ba amma Diva ce bata yi shirun ba sai da ta tambaya "Haka kawai rana tsaka? Anya Baba baka tunanin akwai abin da ya kamata in sani? I'm not a Lil child anymore Idan Abu da ya danganci natsuwa da kwanciyar hankalinmu ne you have to say it out Don mu shirya masa...." Ya katseta "Har yanzu ke yarinya ce Sohana, har yanzu da saura. Bana son musu ki yi abin da na ce!" Fuskarta ta hade tamau ba don shi din ba ne wallahi ba za ta je ba, Sam bata yarda da shi ba dukda dama a irin lokutan nan na siyasa ba natsuwa ya cika samu ba saboda lokaci ne na tashin tashina, zub da jini, rigimgimu iri iri bai cika so ma tana nan ba amma ai zaɓen da saura. Haka ta miƙe ta shige dakinta ranta a hade ya bi bayanta da kallo sai ya ɗan dafe Goshi. Tana kwance Shaly ta shigo ita da Zubash su suka haɗa mata kaya don ta faɗa musu, sun jima a dakin kan suka tarkata suka bar gidan gabadaya. **** A daren ranar Shehi ya zauna da su Abbiey ya sanar musu batun tafiyar sai Abba yake cewa "Yauwa batun wannan yarinya kana ga hankalinka ya kwanta da ita za mu iya zuwa nemar maka aurenta? Ina tambayarka saboda mu fita hakkinka kar mu yi abu daga baya ka ga ba mu kyauta ba, muddin baka sonta za mu san yadda za mu yi da iyayenka mata su bar maganan" Shi sai lokacin ya tuna Ammiey ta ce ya samu layinta. "Abba ba ni da zaɓi duk abin da kuka yanke daidai ne" Numfashi suka sauke amma basu ce komai ba, sai Uncle Ishaq ne yace "Irshad ba'a aure babu soyayya fah, auren wannan zamani da soyayyar ma bai ɗore ba bare haɗi idan baka so kar ya zo ya zamana dayanku na cutuwa" Ya girgiza kai "Uncle duk shawarar da kuka yanke ya yi, Ammar ya binciketa bata da wani matsala dama kuma akan ilimi, kyau da nasaba addini ya yarda a nemi aure" Daga nan ya sanar da su tafiyarsa gobe don ba lallai ma suna nan ba zai wuce, bayan sun gama mishi fatan alkhairi ya fice daga parlorn ya bar su suna cigaba da tattaunawa. A parlorn ƙasa ya samu Ammar, ya zauna yana janyo system dinshi dake wurin ya kunna sai ya ɗan kalli fuskar Ammar yana yatsina fuska kaman ba zai yi magana ba sai ya ce "Ammar! Layin yarinyar nan za ka samar min" "wace yarinya kenan?" Ammar ya tambaya yana ajiye Wayanshi sai da ya kusa Seconds goma kan ya ce "Na'imah" Murmushi Ammar ya saki "Ka ce Amaryarka, amma don rashin kirki ni ne ma zan samar maka? Ni nake neman aurenta ne?" Tsaki kaɗan Shehi yayi "Ka san ba don Ammiey ta matsa ba duk wannan abu ba za'a kai shi da ni ba don bana son bata lokaci da raba hankali akan abin da ya kamata, ka samo min layin ta kan Ammiey ta ƙara ritsa ni in rasa amsar bata pls" "Toh an gama Al sheikh" Anan suka cigaba da hira sama sama Shehi na aiki har Mufida ta kawo musu abinci, anan suka ci sai chan dare Ammar ya fice daga shashen shi kuma sheikh ya haura sama, al'adarsa na bacci duk ya gama kan ya kwanta yana lumshe idanu. Washegari bai yi wani nisa da gidan ba sai da ya tabbatar ya gama komai da ya kamata, la'asar lisss Ammar ya kai shi Airport. Luggage dinshi babu wani yawa don haka shi yake turawa don zai shiga da shi cikin jirgin. Farin thobe ne jikinsa da wani golden Jubba, Ghutra dinshi fari ne sol sai baƙin Agal daga sama takalmarsa bakake ne hannunshi ɗaya na tura Luggage din ɗaya na riƙe da alkyabba ɗin yana tafiya cikin natsuwa har ya gama duk abin da zai yi ya zauna wurin jiran flight, VIP section ne don haka kujeru ne masu kyau da tsari maroon colour zagaye da wurin, Ac na aiki haka kamshin Airfreshner a cike da wurin. Tasbihi yake yi da yatsun hannunsa dayan hannun na riƙe da waya yana dannawa ya shiga jin sautin takalmi na shiga kunnenshi don sauti ne na takalmi mai tsini da ya haɗu da tiles sai yake ba da ƙarar marar Daaɗin saurare a wurinshi bai ɗaga kai ba Sam. Ita kuwa kujerar da yayi mata ta samu ta zauna bayan ta tura milk color traveling bag ɗinta da ta ɗora mishi kit din Saman hannun gefenta kaɗan kafa ɗaya ta ɗora kan ɗaya tana cigaba da cin chewing gum yana ba da sauti fuskarta na kan waya. Tsakin da bai san ya fita ba ya ɗan yi rashin manners din yayi yawa, ga kamshi da take bazawa tamkar namiji da alama bata da masaniyar ubangiji ya haramta irin wannan kamshi ga mace, saka Turare har ya cike wuri ga mace ba ado ba ne illa kwasarwa kai zunubi saboda duk namijin da ya Shaka har ya burge shi tamkar yayi zina ne da macen alhakin kuma baya kan kowa sai kanta. Waya aka ƙirashi ya amsa yana ɗago fuskarsa Kasancewar suna saitin juna sai idanunsa suka sauka kan fuskarta, sallamar da yayi ita kuma muryar ya sa ta ɗago ta kalli wurin sai karab suka haɗa idanu... Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba. NOTE: Wannan littafi na Ƙarfe ɗaya...ba kyauta ba ne, zai zo muku ne akan farashi mai sauƙi kaman koyaushe Naira dubu ɗaya kachal 1k. *SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU* Kowannensu idanu ya janye a take, Wayanshi ya cigaba da amsawa yayinda ta fitar da nata wayan ta shiga taɓawa dukda ita ba gwanar media ba ce amma zaman shirun ya ishe ta. For over 30minutes babu wanda ya motsa cikinsu, ganin lokacin magrib yayi ya sa ya miƙe ya tafi ɓangaren masallaci yayi sallah ya sake dawowa same spot ya zauna, har aka yi isha saboda yanayin delayance na jiragenmu suna zaune kan aka fara announcement za su yi boarding, shi ya fara Miƙewa ya ja trolley ɗin shi yayi gaba, sai da ta bari ana final announcement ma kan ta miƙe kamar ba za ta tafi ba ta nufi wurin shigewa ɗin, duba ticket ɗinta aka yi ta wuce zuwa ciki a hankali take duba seat number ɗinta tana zuwa inda yake zaune ta ɗaga kai ta kalli number ɗin abin mamaki ita ce daga ciki jikin Window shi yana daga gefe kuma ya riga ya zauna. Luggage ɗinta ta ɗora a sama tana jin bai ma isa ta ƙi zama saboda shi ba, dukda yadda take jin wani abu mai kama da nauyi da bata taɓa ji kan kowa ba. "Excuse me pls!" Faɗin haka da ta yi ya sa ya ɗaga kai ya kalleta suka haɗa ido sai ta nuna seat na gefenshi wurin zamanta, dole ta yi baya ya miƙe ya fita kan ta shiga shima ya zauna. Har suka ɗaga babu mai magana, ta kwanta jikin kujerar tana kallon waje shi kuwa karatun alqur'ani yake yi chan ƙasa ƙasa amma muryar na shiga har cikin zuciyarta, tsikar jikinta ke tashi, ta rasa Meyasa take jin amsa kuwwar karatun har cikin kanta dukda ba lallai ma wani ya san yana yin ba amma fessss take ji, karatun ya saukar mata da wata natsuwa da bata san akwai shi a jininta ba, ko da aka kawo musu snacks ma ruwa ta karɓa kawai ta sha tana sake yin lufff shi kam babu abin da ya karɓa. Sun sauƙa Abuja dare ya ɗan fara ga ruwa da ake ta tsulawa kamar da bakin ƙwarya, kusan kowa ya fita yana zaune bata motsa ba sai da ya miƙe ya ɗauki akwatinshi ya fice itama ta miƙe ta ɗauki nata ta fita. A terminal ta tsaya tana kallon yadda ruwan ke zuba gashi babu wani taxi, kalle kalle take ɗan yi wannan ne karonta na biyu zuwa Abuja din kuma ba wai ta san yanayin garin ba ne dukda ko ɗarrrr babu uban da take tsoro ko shakka kawai bata san yadda za ta fara ba ne. Wayanta ta kalla ta sake duba sunan hotel da Jagaban yayi mata booking akan anan za ta zauna har sai ya ce ta dawo. Numfashi ta ɗan sauke Idanunta na yawo kan mutanen da ake ta ɗauka ta ɗan lashi lips kaɗan kan ta harɗe hannu tana tsaye kawai bata gama yanke hukunci ba. A hankali ta ga wata black Mercedes ta yi parking gabanta sai matukin ya sauko yana rike da lema ya zo inda take cikin girmamawa ya ce "Madame ko za ki shiga mu rage miki hanya? Kin san nisan dake tsakanin nan da cikin gari kuma taxi sun ɗauke saboda ruwa" Wani irin kallo ta mishi don bata yarda da shi ba, sai glass na motar ɓangaren da yake na baya yayi ƙasa Idanunta suka sauka kan Shehi dake zaune a baya yatsina fuska ta yi. "Dukda ban nemi taimakonku ba amma mu je!" Da sauri ya ɗauki Luggage ɗinta ya sa a baya ta buɗe gaba ta shiga don bata jin za ta iya sake zama kusa da wanchan mutumin, haka ya ja ya fara tsula gudu a titin na Abuja a lokacin sheikh ya amsa waya yayi biyar zuwa shidda sai tsaki take ja don an cika mata kunne. "Ina za mu ajiye ki ma?" "Grand Cubana hotel, Jabi" Ta faɗa kai tsaye. "Wow! What a coincidence ai mu ma chan muka nufa" Baki ta taɓe kaɗan shi kam sheikh bai ma san suna yi ba. Har zuciyarsa kuma taimakon musulunci ne yayi mata don za ta zama stranded a inda take, hakan ya sa yayi wa drivern umurnin su rage mata hanya zuwa open place da za ta iya samun abin hawa, ganin ta fara fuskar rashin mutunci ya sa ya sauke glass din don ta tabbatar ba cutarta za su yi ba bare ma su cuceta su ce sun cuci wa? Ya ayyana a sadda drivern ke saka mata kayan da shigowarta kamshin ta da yayi ta hawa mishi kai gabadaya zaman flight din ya sake yi mishi sallama, Sam ba ya son kamshi mai ƙarfi irin nata shiyasa lattafas suka zama best perfumes dinshi kamshi ne masu sanyi da natsuwa dukda shima ya kan cika waje musamman na maza ɗin amma nata ya yi over a hancinshi. Ko da take Faɗin hotel da za ta je bai yi mamaki ba, haka suka cigaba da tafiya shiru yana amsa call sa'i da lokaci har suka isa hotel ɗin, drivern ya sauƙa ya buɗe mishi ko kan ya gama sauƙa ta zagaya ta buɗe booth din ta fitar da akwatinta da kit ɗinta. Har ta taka baya kaɗan kan ta ce "Thanks" Ya kalleta kaɗan sai ya gyaɗa kai ta juya ta yi ciki, sunanta kawai ta basu suka bata key a daidai shi ma ya shigo ya faɗi sunanshi suka karbeshi zuwa cikin elevator, tuni an kaita corridor din da room ɗinta yake ta ƙagu kwarai ta ga ta kwanta ga shi yunwa take ji na bala'i don rabonta da abinci tun safe, tana shiga ɗakin ta tura Luggage ɗinta ta faɗi kan gadon rigingine Idanunta rufe. Bata san adadin lokutan da ta ɗauka ba kan ta miƙe ta fara zame kayan jikinta sai da ta cire tas kan ta nufi toilet tayi wanka, hotel room din ya mata kyau kwarai hotel ne mai matsakaicin tsada amma komai intact har da kayan bacci sabbi fill a Leda bayan towel da su tissue da ake tanadarwa duk wani sabon customer. Ɗaure da towel din ta nufi akwatin ta janyo ta buɗe me za ta gani? Neat and clean jallabiyoyi ne Kala daban daban a jere ga su Ghutra da jubba har nan a shirye a kuma goge. Baya ta koma ta zauna dabas fuskarta a kwaɓe! "Garin ya muka yi exchanging akwati da wanchan mutumin?" Ta faɗa a bayyane kan ta ja tsaki ta miƙe tsaye ta tafi ta dauki kayan baccinsun farare tass ta sa bai mata yawa ba riga da kuma wando ne free sai ta ɗaura dankwalinta a kanta. "Allah ya sa bai buɗe min akwati ba don wallahi zan iya yi masa rashin mutunci akan akwatin nan abubuwan da ke ciki sun fi karfin karamin kanshi na wa'azi" A bayyane take maganan cikin sauri. Dankwalin kawai ta mayar ta ɗaura a kayan da ta cire ta zura lofas na hotel din farare ta ja akwatin ta fice daga ɗakin kai tsaye reception ta koma don bata san inda yayi ba ma a cikin hotel din. "Sannu! Akwai wani da muka shigo tare mun yi exchanging Luggage can you please check his room number for me?" Matar ta fahimci frustration dake muryar Diva ga gajiya don haka ta amsa mata da "OK ma lemme check" Ta duba numbern ɗakin sai dai ba ta so ta yi gaggawar exposing customer sai ta shiga kiran landline na dakin amma bai ɗauka ba sai da Diva ta buga kan desk na gabanta. "Malama jiranki nake kin bar ni tsaye wata tsiyar zan je in ɗauka dakin da sai kin sanar masa? Faɗamin numbern in je da kaina kafin ya buɗe min akwati!" Ta ɗan firgita kan ta ce "Sorry ma! It's room 409 block B" Tana A ne, ginin kuma A na kallon B ne, wanda ke tsaye a corridor din A tsaf zai kalli wanda yake corridor din B, layin kowani block kuma da farkon number ya fara wato dakuna goma ne kowani floor har hawa biyar. Lift da zai kaita ɓangaren ta hau ta danna 4 ta tsaya tana ɗan bubbuga ƙafa saboda sauri da take kar ya buɗe mata akwati. Shi kuwa ta bangarenshi shima zama yayi ya ɗan huta saukinta ba wani sallah a kanshi, ya cire jubba da rawanin ya bar iya gashin kanshi mai spring asalin na Fulani amma da yake yana ɗan tarawa sai ya ba da wani style mai kyau, system dinshi ya ɗauko daga jakarta dake daban ya shiga dubawa ya fi awa zaune dukda yunwar da yake ji amma ba zai iya cin komai a lokacin ba sai ya ja waya yayi placing order na tea daga restaurant na hotel din. Daga nan ya miƙe ya shiga toilet don aikin ba ya mishi yadda yake so sai ya fara da wanka kan ya fito ɗaure da towel a ƙugunshi ginannen jikinshi da bai murde dayawa ba tsaka tsaki na yalƙi, shi ma kayan baccin da suka ajiye sabbi ya saka sai ya nufi akwatin ya buɗe don duba files da yake so yayi amfani da su kan ya kwanta sannan kuma ya fesa turare. Kasancewar girgida da akwatin yayi Sossai yana buɗewa da yake a kan gado ya ɗora sai ya ji abu ya faɗar masa a ƙafa, tsuguna wa yayi ya ɗauka yana mamakin menene wannan ɗin don bai tuna sa abu haka a jakanshi ba, Yana buɗe karamin envelope ɗin da bai san dashi cikin kayanshi ba wani strong abu ya shige hancinshi da sauri ya yar yana ambaton "Subhanallah!" Tari ya ɗan fara fuskarsa har ta sauya, idanu ya kai kan akwatin sai ya ga kwata kwata ma babu abin da ya haɗa shi da nashi daga ciki ta waje ne dai suke kama da nashi ɗin. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... La haula wala quwwata illah billah" Abinda yake ta maimatawa kenan. "Akwatin 'yar daba!" Ya sake faɗa a zahiri don tabbas nata ne, hannu ya sa ya riƙe waist dinshi bai taɓa tunanin zai rike irin wannan abu ba a rayuwarsa. What sort of nonsense? Ya sake ayyanawa yanzu idan mistakenly wani abu ya faru jakarnan ya buɗe cikin mutane matsayin nashi ai ta gama zubar masa da ƙima nan duniya. Bai ma gama sanin abin yi ba ya ji ana knocking da ƙarfi, ya kalli kofan kan ya nufi kofar ya buɗe tana tsaye dab har sun kusa cin karo yayi baya. "Me ya sa za ka chanza min akwati? Me zan yi da akwatinka?" Kallon ba ki da hankali yayi mata don ta gama raina masa wayo, da ma duk natsuwar da tayi dazu kaman ba ita ba na munafurci ne ya zaci ta fara sauyawa don ya zauna da ita for over 4hours a ranar bai ga tayi faɗa da kowa ba, amma ji abin da take ce mishi a kan kayan maye? "Wannan tambayar daga bakina ya kamata a ji shi, me zan yi da kayan maye? Me zan yi da abin da Allah ya tsinewa? A'uzubillah! Wa'iyazubillah" Wani abu ne ya daki zuciyarta ranta ya shiga tafasa, ɗan kirkin da take mishi tuni ya kau don ya zo inda ba za ta bari ba. "Wa ya sani kila kana da abin yi da shi? Ai maye shi ya san makwancin maye idan baka sha ta ya ka san menene ciki...." Ido cikin ido suke kallon juna don ji yayi kaman ya rufeta da duka, shi take kallo take gayawa wannan magana? Shi dai Irshad Omar Al-Noor? Wonderful! Ya ayyana a ranshi kan yayi magana ta ce "Malam ka dauƙo min akwatina ko ka ba ni hanya in ɗauki abata!" Matsawa yayi don ba zai ma iya sake cewa komai ba tunda tace shima shaye shayen yake baya so ma wani ya ji su ko cikin baƙin taron su fito su ga yana magana da irin wannan, ciki ta shige ta ga akwatinta a buɗe tana mita tana rufewa har ta gama ta ja abin ta ta fice, nashi ya ja ya shigar ciki yana rufe kofar cikin adu'ar Allah kar ya sake kawo abin da zai haɗa su. Yana shiga bai zauna ba Wayanshi ya shiga kira ya ɗaga ya duba Ammar ne sai yayi picking yana komawa ya zauna har da kishingiɗa. "Ammar!" "Ya na ji muryarka haka ko ka fara bacci ne na tasheka?" Tsaki ya ja yana sake Miƙewa zaune wai shi za ta cewa yana shan wani abu! Duk yadda ya so yayi shiru ba ya jin zai iya abokin taya kuka yake nema, sai yace wa Ammar ɗin "Yau ni aka kalla tsakiyar ido aka ce ina shaye shaye." Ammar yayi kasake...kan ya ce "Ban gane ba! Wa zai ganka ya furta hakan? Waye bai san fuskarka ba da zai iya jefanka da wannan maganan? Ko kwarjininka da kamalanka sun fi ƙarfin a yi musu irin wannan suɓutar bakin lallai ko ma waye ne da tsaurin ido yake" Irshad ya sauke Numfashi "Mace ce!" Sai da ya ɗan muskuta ya furta "Wannan 'yar daban!" "Mace?" Ammar ya maimaita da tsantsar mamaki, shi karan kanshi wani lokacin Irshad kan mishi kwarjini kai hatta iyayensu suna matukar jin nauyin shi a abubuwa dayawa saboda tarin baiwa da Allah yayi masa har mace ta faɗa mishi hakan a cikin ido? Lallai ko wacece bata da kunya kuma fitsararriya ce. "Wace 'yar daba? Me ya haɗa ku haka?" "Wannan da ta yi sharing hospital room da Daddah" "Diva!!!" Ammar Ya faɗa yana Miƙewa daga zaunen da yake mamakinshi na ƙara ninkuwa. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA UKU* Tana tafiya tana mita chan ƙasa har ta shiga ɗakinta, ta ajiye akwatin kan gado tana kokarin buɗewa a fili take furta. "Allah ya sa in samu an taɓamin abina mai raba mu yana China kan ya karaso sai mun ɗaga Nigeria..." Don haka kawai take jin wani hasala na buɗe mata akwati da yayi har da sanin me a ciki. Wani zuciyar yace kai Diva kema fah kin buɗe nashi, a fili ta sake furta "Ai dai ban taɓa komai ba Meyasa da ya buɗe ya ga ba nashi ba ne bai yi gaggawar rufe wa yadda na yi ba?" Tsaki ta ja bayan kuma ta tabbatar da komai na nan sai ta zauna gefen akwatin, wani abu kaman guiltness take ji irin dai wannan feelings na rashin jin daaɗi a kama ka kana yin abu marar kyau. Amma Diva ce tuni ta watsar tana furta "Oho! Ai shi ya so gani don haka shi ta shafa...we move on" Tana kai nan ta kai akwatin ɓangaren wardrobe ta ajiye shi a haka kan ta dawo tayi ordering chips and chicken saboda tana jin yunwa, Wayanta ta cigaba da dannawa har ma tayi call da su Jagaban da su Obafiya kan aka kawo mata abinci. Ta ci Sossai ta sha ruwa, kan ta jinginu da jikin gadon bayan ta haɗa ice da ta saba sha don zaman da tayi for over 6hrs yau ba tare da ta sha ba ji take har tsikar jikin ta na tashi kanta na wani yammmm, ji take kaman za ta yi hauka don haka enough ta sha abinta kan ta kwanta tuni ta yi bacci. Shi kam ta ɓangaren sa rufe ido yayi yana tuna abin da ta ce mishi, yana jin Ammar na maimaita Diva dai? Sai ya jefa mishi tambayar "Me taje yi a Abuja har hotel da kake?" Baki ya ɗan taɓe kaɗan "Ina zan sani Ammar? Ni na fara tunanin ko dai yarinyar nan bibiyata take?" "Saboda ka mareta?" Sai kuma ya tuna ashe har yau babu wanda ya san sun haɗu bayan nan har ta yanke shi a hannu. "Kila! Kila kuma abu ne ya kawota kaman yadda ya kawo ni but koma menene I'm very sure ba alkhairi ba ne duba da tarin kayan maye da na gani a akwatin chan, ƙasar mu ya zama abin da ya zama to walk freely da irin wanchan abin a Airport from one state to another" Ammar ya ce "Allah ya kyauta to ya kiyaye, sai ka saka ido kar ta cutar da kai Shehi irinsu baka sanin me za su aikata don su kashe mutum har lahira ba komai ba ne a wurin su" Murmushi mai sauti ya ɗan yi kan ya ce "Ammar za mu yi magana da safe I'm sleepy" Sallama suka yi yana juya maganan Ammar, ai ya san ba shi ba koma waye ba zata kashe ba matukar da zuciya a kirjinta yayi mata nasiha kan kisa, matukar ta san za ta mutu itama ta komawa Allah. Knocking ake mishi ya miƙe ya je ya buɗe ya karɓi tea dinshi ya dawo ya sha daga nan ya rufe aikin da yake ya je yayi alwala ya zo yayi karatuttukan da ya saba kan bacci tare da adu'o'i da addini ya tanadar kan ya rage hasken ɗakin ya kwanta. Washegari Kasancewar da wuri yake da program din ya shirya tsaff turaren wutan da ya taho da shi na bakhoor by seemah ya turara a jikinshi bayan ya gama shiri cikin shigarsa na ko da yaushe, yau ma white thobe ne ya saka da brown jubba sai ya saka farin Ghutra a kansa tare da baƙin Agal ya saka half cover da ya karbi kafarsa Sossai, bai karya ba sai a chan saboda akwai abubuwa da za su yi organizing kan lokacin lectures din wurin da nisa ga yanayin Abuja don haka da wuri zai fita ya isa akan kari, jakar system kawai ya ɗauka da wayarsa ya fice daga ɗakin yana fitar da ni'imtaccen ƙamshi. Yana isa parking lot ɗin sai ga drivern jiya da aka haɗa shi da shi ya zo da sauri ya karɓi briefcase din suka tafi wurin mota ya buɗe masa ya shiga ya zaga ya shiga suka fara ficewa daga hotel ɗin. A natse yake driving irshad din na ɗan kallon tsiririn titin hotel ɗin kaman an ce ya kalli ta gefen ya hangeta sanye da baƙaƙen spotwear na kamfanin Addidas tana jugging a gefen hanyar ido ya zuba mata yana mamaki, ita dai duk wani abu na addini bata ciki, Sossai yake mamakin rayuwarta. Ya tsinci kanshi da yi mata adu'ar shiryuwa kan ya ɗauke kai suka fice daga layin. ****** "Ya Khalil!" Nana ta kwala kiran sunanshi ganin zai ta da motar, dakata wa yayi ta zo da sauri ta tsaya daga jikin windown tana gaishe shi. Ya amsa a hankali dukda ya ga kamanninta da Zubaidah Sossai da Sossai amma bai santa ba. "Sunana Nana Khadija kanwar Zubaidah" Yayi murmushi "Oh Allah sarki khadija ya school?" Ta amsa da "Alhamdulillah!" "Wurin Yaya zubaida ka zo?" Ta tambaya bayan shirun dogon lokaci da ya ɓace cikin tunani. "Eh Nana amma ta fito ta min gargadi akan in fita harkar ta babu aure gabanta" Ya karasa cikin wani yanayi, a kan Zubaidah ya bi shawarar aboki ya fara ketere iyakokin ubangiji ya aikata abin da bai taɓa tunanin aikatawa ba dukda tarin laifukan Fatsuma matarsa na banzatar da buƙatunsa kuma ta shiga ta fita mahaifiyarshi ta hana batun karin aure a zamansu, amma daga lokacin da ya san Zubaidah yaji zai iya auren ta a hankali kuma ya fahimci rayuwarta tausayinta ya ninku a ranshi ya ji yana kwadayin cire ta daga wananan baƙin rayuwar, yana sane da irin gwagwarmayar da zai yi da Mamanshi da kuma Fatsuma amma bai damu ba muddin zai sami Zubaidah. "Abu ɗaya nake tunani za ka yi ka mallaki Zubaidah" Nana ta faɗa a hankali tana kallonshi "Menene wannan ɗin?" "Ke je wurin mahaifinmu ka nemi aurenta" Dukda tsoro da take ji na tura Khalil har Taraba amma muddin da gaske yana son Zubaidah zai iya zuwa ko China ne soyayya da ma tana cike da sadaukarwa. "Ki ba ni full Address na yadda zan same shi in Shaa Allah zan je, muddin zan yi nasara kan Zubaidah" Takarda ta fitar ta rubuta mishi yadda ta haddace bata haddace komai haka ba, rayuwarsu ya wargaje tun daga yaranta a kan idanunsu komai da ba za su taɓa manta wa ba ya faru, a kan idanunsu mahaifinsu ya yafe su ya sallamawa mahaifiyarsu ya zame hannayenshi, a kan idanunsu ya sa almakashi ya yanke alakar da ta haɗasu dukda jininshi da ke yawo a nasu jinin. Hawayenta ta mayar tana miƙa mishi papern ya karɓa yayi mata godiya kan ta fita ta shiga gidan, abin mamaki ta samu Zubaidah na kuka irin wanda bata taɓa gani ta yi ba! Kuka ne da ke fita daga cikin zuciyarta, a hankali ta ƙarasa wurinta hawayenta na zuba ta dafa ta. Zubaidah ta ɗago ta kalleta. "Me ya sa kike kuka Aunty Zubaidah? Mama ce?" Girgiza kai Zubaidah ta yi sai ta koma ta jinginu da gini tana rufe Idanunta. "Baba?" Ta faɗa dukda ta san Malam Iro a yanzu ba dai ya sa Zubaidah kuka ba sai dai ma ita ta saka shi aiko Zubaidah ta buɗe ido ta zabga mata harara. Nana ta ɗan yi murmushi "Toh menene kike kuka haka Yaya Zubaidah?" "Babu Nana! Babu abin da ya faru" Tana kai nan ta miƙe ta fice daga ɗakin, tana tafiya a hankali jikin ta a matukar sanyaye kanta ƙasa tana ji Wayanta na kira tana kallon sunan Ghali amma ta ƙi picking, saboda ta san hookup ne ya samar mata kuma ba ta cikin mood. A dakin Shaly ta samu click ɗin nasu Pablo ya tafi kabu kabu, Pascal yana injin bredi, Obafiya gym coach ne saboda gyming ya samu ƙirar da ya zama na hannun daman Diva don kowa ya ganshi sai ya ji shakkarsa bare yana wuri ko kallo Diva ta yi ya san ma'anar, a lokacin Kasancewar yammaci ne shima baya nan. Daga Zee, Shaly sai Skipo. Ta zauna kawai bata ce komai ba. Skipo ne yace "Ya ne Zubash? Na ga jikinki duk yayi wani la'asarrr" Ta ɗan sauke Numfashi "Kawai kewar Diva nake ji wlh ko ya take a chan da bata san kowa ba?" Zee tace "Nima wlh ina jin kewarta sossai dukda kin ga ba wani hira take na a zo a gani ba amma Diva mutum ce da in tana wuri spirit dinka sai ya haɗu da ita ko baku yi magana ba" Shaly tace "Za ta dawo ne soon ku daina damuwa, ba tafiyan ne ni ya tsaya min a rai ba...dalilin Jagaban na tura ta ne ya tsaya min. Anya bakwa ganin akwai wani da abu ta haɗosu da Jagaban kuma ya fi ƙarfinsa yake so ya yi amfani da Diva don lankwasar da shi ba? Suna fa aka rubuta mata a jiki da wuƙa daga kuma ganin saƙon sunan Jagaban ya rasa natsuwarsa" Zubash ta amsa tana gyara zamanta "Tabbas na kula da yadda baya da natsuwa a kwanakin nan gabadaya, waye ne kenan? Me kuke tunani zai haɗasu haka?" Shaly tace "Ban sani ba gaskiya har ita kanta Diva din bata sani ba dukda kokarin bincike da take ita da Pablo da obafiya amma sun kasa gane komai akan mutanen da suka illatata a karshe zagayensu kuma ya kawo su wurin Jagaban" Skipo ya ɗan yi shiru cikin nazari "Kina nufin Jagaban dinne kenan suke zargi?" Zee tace "Me ya sa zai cutar da ɗiyarshi?" Shaly fuskarta na nuna damuwa tace "Zai iya yin hakan akan business amma ba zai yi da nufin cutarwa ba, kun san yanayin yadda underground war yake ina kyautata zaton ko saboda ya yi framing wani saboda ya karbe kasuwarsa daga sama zai aikata. Don gaskiya idan ba shi ba ban san mai tsauri idon da zai iya taɓa Diva har haka ba" Magananta ya fi kama hankalinsu don a yanayin zuciyoyinsu Jagaban ya dame su ya shanye, yana da hatsari kwarai fiye da zato kuma yana riƙe ne da baƙar duniyar laifuka masu yawa da ba komai ne suke da masaniya a kai ba, hakan ya sa irin su babu abin da ba za su yi ba don ganin ba'a jijjigasu ba. Shaye-shayensu suka cigaba da yi suna hira zubash dai tun da aka gama maganar Diva ma bata sake sa baki ba ta ma bugu ne lisss ta kwanta Idanunta a rufe amma har lokacin bata daina jin abin da take ji ba, bata daina jin tasirin kalaman Khalil a zuciyarta ba, bata daina jin tsoron makoma ba, kwakwalwarta kuma bai karɓi ta sauya ko ta chanza ba don ta tabbatar mama ba yarda za tayi ta aurar da ita ba ko ana ha maza ha mata kai ko ita ce ta samu damar auren muddin Nana bata yi ba ba zata tafi ta barta mama ta lalata mata rayuwa ba. **** "Mama Ya Sheikh ba ya ƙaunata, bana tunanin zai taɓa ƙaunata mama bai fa gane ni ba! Nunawa yayi bai taɓa sanina ba" Cikin hawaye tayi maganan. Maman tace "Laifinki ne Na'ima kina mace me zai kai ki inda yake? Ai shi ya kamata a ce ya zo ya same ki har inda kike, da kin yi shawara da ni wlh ba zan goyin bayan zuwanki office dinshi ba don zub da aji ne." Karfin kukanta ta ƙara "Ki daina wannan kukan, kuma zai kiraki ya baki hakuri in Shaa Allah bari zan kira mamartashi, amma gaba ko da wasa kada ki nuna zaƙewa a kansa in ba haka ba za ki sha wahala" Sam hankalinta bai kwanta ba, idan komai sai Mamanshi ta saka shi in sun yi auren ya zai yi da ita kenan? Dole ta nemawa kanta mafita ba za ta bari ta rasa abin da ta kwallafa rai ba don tana son shi Sossai tana tunanin duk duniya babu wanda ya kaita sonshi. Mamanta na fita ta janyo Wayanta ta kira wata secondary school friend ɗinta da ta san ta haddace kalolin maza iri iri tun daga kananun shekaru, ita ce kawai za ta bata shawarar yadda zata kama zuciyarsa tun kan ta shiga gidan. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU* Kusan awanni uku da zama cikin conference hall ɗin an fara program ɗin ne da basu abin kari wanda serve ur self ne ya dibi abin da zai iya ci ya ci ya sha coffee, kan aka soma abin da ya tara su gabadaya vibration na Wayanshi ne ke daukar hankalinsa ganin ba za'a daina kira ba ne ya sa ya fitar ya fara dubawa sai ya yi mamaki. Abbiey bai taɓa yi masa ƙira sama da ɗaya ba ga jerin calls nashi uku, ga na Ammiey ma har uku Maamah biyar Abba biyar Ammar duk ya fi su yawa goma sha wani abu sai hankalinshi ya tashi tunaninshi kawai wani abu ya faru a gida ne, Excuse ya nema kawai ya bar ɗakin taron sai da ya samu wuri marar hayaniya kan ya shiga ƙiran Abbiey. Yana ɗaga wa bai ko samu daman sallama ba Abbiey yace "Irshad! Menene hadinka da yarinyarnan 'yar daba wacce dabancinta yayi shura a garin Kano? Da gaske kazamtaccen soyayya kuke? Ana cewa ba'a shaidar ɗan yau Irshad tarin saninka za ka take?" Ya shiga wani yanayi ba yanayin komai ba sai jin ɓacin rai tsantsa akan harshen mahaifinsa wannan fushi sanadiyarsa ya zama tamkar an ɗiga masa dalma ne ko wuta a cikin ransa. "Abbiey ka yi haƙuri ka zauna idan a tsaye kake" "Image ɗinka da ya fi na gidan nan shura a duniya Irshad kana shirin tarnishing ɗin shi" "Abbiey har yanzu ban fahimci menene laifin ba? Babu abin da ya haɗa ni da wata 'yar Daba Abbiey...schedules dina ma babu lokacin kaina bare wanchan lokacin, Abbiey kar wani zargi ko kokonton zan saɓawa Ubangijina ya ɗarsu a ranku. Har abada mu'amala da wata macen bana fatan ya zama kaddarata bare wannan 'yar daba, mashayiya da kuke magana" Hankalin Abbiey ya ɗan fara kwanciya don a yanzu muryarsa ya ɗan yi sanyi "Ka hau online ka ga abin da ke faruwa" Yana sauke wayan kan ya hau ɗin Ammiey ta kira shi dole yayi Picking itama dai ranta a bace take mishi faɗa irin wanda gabadaya rayuwarsa bai taɓa ji ta mishi ba, sai ya sake shiga wata damuwar. Idanu ya runtse yana sauraronta har ta ƙarashe da "Irshad Idan ma akwai wani abu tsakaninku ko tsaftataccen soyayya ce na haramta shi har abada, har gaba da Abada wannan yarinyar da take kallon tsabar idanuna take kwalfar kayan maye ba zan taɓa iya haɗa jini da ita ba gwara ma ka sani" Ko da ta katse ƙiran bai cire daga kunnensa ba na seconds masu yawa kan ya saukar ya ja a hankali ya kunna data, Karon farko gabanshi ke faduwa na abin da zai tarar da ya bata ran iyayensa, Facebook ya shiga don magana ya fi yaduwa cikinta kamar wutar kara scrolling uku ya yi sai ya runtse idanu ya sake bude wa akan caption da aka yi. Hoton Diva ce a sadda take shiga dakinshi ɗauko akwatinta shi kuma ya ɗan karkata yana kallon bayan ta tsaye a jikin kofar. "Wai ka bi maganan Malam amma kar ka bi halinsa" Shine caption ɗin, wani abu mai daci ya haɗiye ya sake scrolling ƙasa nan ya ci karo da hotuna huɗu, suna zaune a Airport, suna zaune cikin jirgi, tana shiga motar da yake ciki sannan tana shiga dakinshi. "Wato Malam ba zai iya tafiya shi kaɗai ba dole da mai debe masa kewa" Comment section ya shiga ya Subhanallah! Da sauri ya fita yana mamakin mutanen arewa, wani irin yanayi yake ji da ba zai iya fasaltawa ba, idanunsa har yaji yaji suke masa amma ya dake ya shiga ambaton Allah, idanunsa na haska masa wani comment da ke rantsuwar dama Ai da walakin rashin aurensa babu namijin da zai haura talatin bai nemi mace ba muddin bashi da aure. Ya jima kwarai yana kokawa da zuciyarsa cikin ambaton Allah da kuma neman agajinsa a hankali sai natsuwa ya fara saukar masa, scandal me muni ne wannan a kansa zina! Sai yayi saurin a'uziyya bai motsa ba har lokacin daga inda yake tsaye. Call na Ammar ya yi picking amma bai ce komai ba kawai yayi shiru. "Shehi!" Bai amsa ba don ko ya amsa muryarsa ba lallai ya fita da kyau ba. "Are you okay?" "Uhmm zan koma program we talk later!" Yana kai nan ya katse wayan dama da kyar maganar ya fita, juyawa yayi ya koma cikin hall din bayan ya saka wayar flight mood don ya san kira kam zai sha shi idan ya bari buɗe. Har karfe wurin biyar suka tashi na ranan iyakaci sallah ke fitar da su daga ɗakin taron sai lunch da aka tsaya aka yi, bayan sun tashi bai jira komai ba ya wuce hotel yana shiga reception idanunsa basu faɗa kan kowa ba sai ita, idanu ya ɗan zuba mata yana jin zafin abin da aka fitar a kanshi game da ita, idan zai neme mata ma sai ya nemi ta titi? Dressing ɗinta duka takaici yake ba shi tamkar ba musulma ba, yadda kullum idan zai ganta da gashi waje hakan ya fi komai baƙanta masa a matsayinsa na wanda ya san addini amma karshe ita aka haɗa da shi. Ɗauke idanunsa yayi ganin ta waigo waya a kunnen ta tana kallon mashigar a daidai ya wuce ya shiga elevatorn ɓangaren da yake, kai tsaya kaya ya kwaɓe ya faɗa toilet ya sakarwa kansa ruwa masu sanyi. **** Bayan ta gama exercise ɗinta na safe wanka tayi ta kwanta bacci, ko da ta tashi sha biyu ta gota Wayanta dake bedside ta ɗaga ta duba ganin almost 50 missed calls sai ta shiga mamaki kiran Shaly tayi da duk calls ɗinta ya fi yawa. "Diva ki duba online ki ga abin da ke faruwa! Me ya haɗa ki da Sheikh Irshad Al-Noor?" "Me haɗina da shi kuwa? Babu!" "Diva na sanki da riko da rashin yafiya har yanzu kina bibiyarsa ne? Don shi kika tafi Abuja?" Tsaki ta ja ta katse ƙiran da a fili ne da Idanun Divan kaɗai ba za su bar Shaly ƙarasa zancen ba. Media ta shiga ita kanta tayi mamaki dukda ita din ko a jikinta sai ma a fili ta furta "Na ja maka shiga bakin duniya" Dira ta yi bata bi kiran kowa ba ta shiga wanka bayan ta fito ta shiga cikin wani oxblood long sleeve t-shirt da ya amsheta ta saka blue cotton palazzo trouser da abin wuya tsiriri ta feshe jikinta da turaruka tare da gyara gashinta ta ɗora facing cap ta fice. A wani fancy restaurant ta ci abinci bayan ta gama ta miƙe tana biyan kudi ta fito ta dawo hotel dinsu da ƙafa ta taho saboda rage lokaci don har ta gaji ma da zaman Abujan dukda a chan Kanon ma ba wai hira ko surutu take ba anyhow amma ko yaya akwai motsin su Skipo. Fahimta tayi kaman ana bin bayanta abin ya bata mamaki, me hakan ke nufi? Har ta shiga hotel ɗinta ta tsaya reception tana kallon kofar bata ga an shigo ba, Wayanta ta fitar ta kira Jagaban zuwa yanzu sam bata yarda da shi ba. Yana ɗaga wa ta fara tuhumarsa akan abubuwan da ke faruwa ya nuna mata ta kula Sossai shima kuma daga Kano zai yi abin da ya dace babu abin da zai faru, she's not convinced sam tana cikin wayan ne ta ɗaga ta kalli kofar Shigowar sai ta ga gilmawansa fuskarsa na nuna wani yanayi marar daaɗi karo na farko ta ji bata ji daaɗi ba akan abin da ya faru amma ta danne ta ɗauke kanta ta cigaba da waya. Ita don an ƙirata 'yar iska ko ƴar daba duk ba komai ba ne amma shi da ya riƙe kamalarsa bai kamata a ja shi a taɓo haka ba, mutane suna da daukar dala ba gammo, suna kwashe zunuban mutum ba tare da sun sani ba, irin wannan har depression zai iya jefa mutum ba tare da sun yi la'akari da hakan ba kowa na tofa abin da ya mishi masu rantsuwa na yi masu jin daaɗi na yi. Barin wurin tayi itama ta nufi ɗakinta fuskarshi na dawo mata da yadda ya shigo. ***** Tana zaune tana juya shawarar da kawarta ta bata na muddin tana so ta mallaki Shehi da gaske sai ta nemi taimako, ko da ta tambayi wani irin taimako? Abin da ta faɗa mata ya barta speechless, wani zuciyar na nuna mata ba komai ba ne muddin za ta mallaki sheikh wani zuciyar kuma na kwaɓarta da tuna mata irin gidan da ta fito. Numfashi mai nauyi ta sauƙe kan ta janyo Wayanta ta shiga media, wani irin bugawa zuciyarta yayi ta zubawa Irshad da Diva idanu hankalinta na tashi, da gudu ta dira tayi wurin Mamanta tana kwala kiran suna ta "Mama! Mama!!" "Menene wai Na'ima?" "Kalli ki ga... Wannan shahararriyar 'yar dabar Sheikh zai lalacewa? Anya ba asiri a lamarinta?" Maman ta karɓi wayan tana dubawa ita kanta zuciyarta ya buga, maganganu babu irin wanda ba'a yi ba kowa neman followers yake da post ɗin, har post na baya inda suke tsaye a titi bayan ya mareta sai da aka dawo da shi dama tun lokacin ake zargin alaƙarsu gashi yanzu ya tabbata (a cewar 'yan media). "Babu batun Asiri Na'ima kuma ni ban yarda zai nemeta ba dukda namiji ko ya yake namiji ne amma da ayar tambaya kan alaƙarsu" Baya ta koma ta zube a kan kujera tana dafe kai tuni hawaye ya shiga wanke mata fuska don yadda take ji kuka ne kawai za tayi ta ji sanyi. **** Ma'u na kwance kan cinyar jiddah Idanunta a rufe jiddah na shafa kanta cikin damuwa da kulawa, a haka ma basu bar Ma'un ba jiya sai da wani ya taɓa ta sun kwana kuka daga ita har Ma'un da bata hayyacinta, addu'a kawai jiddah ke yi tana rokon Allah ya kawo musu mafita ko daga ina ne ta san yana ji kuma zai amsa mata. Shadow ne ya shigo "ke tashi!" Babu musu ta ɗaga jiddah ta kwantar kan pillow "Kina da aiki yanzu" Wucewa tayi ta karɓi kayan uniform din ta saka kan ta nufi waje ta shiga mota duk a wani kalar yanayi na sanyin jiki haka kawai take ji a ranta kaman wani abu ne zai faru dukda bata san menene ba. Awanninta biyu da fita ta dawo, inda ta bar Ma'u ta je sai dai bata nan kuma ta san idan ba ɗaga ta aka yi ba ba za ta tashi ba, dakuna ta fara dubawa tana tambayar duk wanda ta ci karo da shi "Ina Ma'u? Kun ga Ma'u?" Tun tana yi da rawar murya har ta fara kuka mai sauti kaman za ta zauce duk inda ta shiga bata ganta ba wurin su shadow ta dawo tana rokonsu su fito mata da Ma'u amma ko ci kanki babu wanda yace mata kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciya tana yi tana ihun su fito mata da Ma'u amma kaman duwatsu haka suka zuba mata idanu suna kallo ta faɗi a wurin tana kuka. ***** Duk yadda ya so yayi bacci a daren kasa wa yayi, yayi nafilfili mai yawa yayi karatun alqur'ani, Miƙewa yayi yaje jikin windown hotel din ya buɗe sai dai iskar bai mishi ba, a hankali ya fita sanye da baƙaƙen Pjamas dogon wando da V neck silk shirt dinshi, elevetor ya shiga ya danna sama gabadaya har ya haye da shi don hotel ɗin mai open rooftop ne. Yana ƙarasa hawa wani iska mai ni'ima ya shiga kaɗashi, duhu ne Sossai dukda a kan titunan Abuja har lokacin akwai zirga zirgan motoci, a hankali ya ƙarasa jikin ginin wurin yana sanya hannaye a aljihu. Warin kayan maye ya shiga ji yana sarƙe mishi iskar da yake shaƙa mai ni'ima a hankali ya waiga sai idanunsa suka faɗa kanta tsaye sanye da wasu coffee brown Pjamas abu take sha don yana iya ganin hayaƙin a iska.... Yanzu wannan ce ake alaƙantashi da ita? A hankali haushinta da tsantsar takaici ke mamaye mishi zuciya har zuwa harshe, itama juyowa tayi don ta ganshi tun yana shigowa ganin sun haɗa idanu ya sa ta kawar da nata tana tsintar kanta da kashe abin da take sha ɗin ta cigaba da tsayuwa a wurin, nufarta yayi yana takun kaman ba zai je ba idanunsa har lokacin basu bar kanta ba. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR* "Why do you keep tailing me? Me yasa kike cigaba da bibiyata? Saka ki aka yi? Ko biyanki aka yi don ki ɓata min suna saboda already ke ba ki da wani mutuncin karewa?" Bata taɓa tunanin zai iya gayamata hakan ba, ba kuma don ta san shi farin sani ba sai don sanin bashi da tsauri a kalamai matukar zai isar da wani saƙo mai muhimmanci ciki. Kaman yadda ya faɗa ne bashi da buri ko nufin a ce wannan maƙiyinshi ne yana iya kokarinshi wurin ganin bai zama abokin gaban kowa ba amma this particular girl ta shigo rayuwarshi rana tsaka and abin is really getting out of minds. Yadda yake kallonta haka take kallonshi, idanunta na nuna ɓacin ranta da kalamansa. "Me yasa zan bibiyeka? Me zan ɗauka a tattare da kai?" Ya ɗan yi baya da kanshi yana kawar da fuska sai kuma ya kalleta "Ashe kema kin san babu gami, then me zan ƙira haɗuwar mu a asibiti? Haɗuwar mu a Airport, haɗuwarmu a hotel guda? Ina kyautata zaton da gangan kika sauya akwatunanmu tunda ke ce kika fara ɗauka saboda kawai ku yi framing dina right? This is not a coincidence and no one will convince me in yarda cewa coincidence ne" Kasa magana ma tayi don mamaki, sai ta ɗan yi murmushi tana sauƙar da Idanunta ƙasa sai kuma ta kalleshi ta ce cikin gargaɗi da kaushi bata ko duba yadda duk ya fita girma ko daren da yayi Sossai ba a idanunta Sam babu tsoro... "Ka san mene? Ka fita a sabgata tun ban nuna maka kalolin rashin darajata ba don yanzu ka gama faɗa ba ni da mutunci, kuma a rashin sanin mutuncin kamewar ban ga abin marmari da zan bibiya a rayuwarka ba, kudi kuma sun yi kadan su sa na ɓata lokacina a kanka idan ma zargi kake to tun maza ka daina! A baya ma na bibiyeka ne saboda in ɗau fansar abin da ka min kuma mun gyarota idan ba kana son na janye ma hakurar da nayi ba ne ka daina nuna min fuskarka a tawa don babu abin burgewa a rayuwarka wurina" Bakin da take tsiwar yake kallo zuwa idanun da take tsayarwa cikin nashi tana rashin kunyar da ta ga dama. Taku ya ƙara gangar ta sai ta ɗan kawar da idanun tayi baya yace "Ƙarya ɗabi'a ce ta duk wani ɗan maye, kalaman bakinki ba su za su sa na amince da batunki ba, kuma muddin nayi bincike na gane wallahi billahi sai na yi shari'a da ke!" Ranshi a matukar ɓace ya ƙarasa. Ta kalleshi suka sake haɗa idanu tayi baya baya kan ta furta... "Then do your worst Mr. Sheikh" Tana kai nan kawai ta juya ta bar wurin bata ƙara ba saboda idan za tayi ɗin kila wuta ne zai na fita daga bakinta, wanene shi da zai yi tunanin har akwai wanda zai biyata ta bibiyi rayuwarsa? To ta ɗauki me ciki? Wannan shirun da tayi sai kuma ya ji babu daaɗi, goshinshi ya ɗan shafa ya furta "Ya Allahu ya rahman am I too harsh on her?" Wani zuciyar yace yeah baka da hurumin zarginta akan abin da baka da tabbaci but she's in all the pictures duk wani angle da zai juya tana nan ciki Meyasa hakan?" Ya jima tsaye nan yana saƙa da warwara, kiran da ya amsa daban daban a yau suna dawo mishi kowa kuma kokari yake ya ga ya ja hankalinshi akan faɗawa wata mu'amala ko ta kusa ko ta nesa da yarinyar nan, sai da ya samu masalaha a ranshi kan ya koma ɗakinshi ya kwanta, da sassafe ya shirya ya tattare duk abubuwanshi ya ƙira drivern dake zirga-zirga da shi, sai da ya ce mishi ya zo kan ya janyo akwatin ya fito reception ya yi check out ya bar hotel ɗin gabaɗaya. Sai da suka hau titi drivern ya tambayi ina zai kai shi? Idanunsa a lumshe yana kwance cikin seat ɗin yace "Area 11 Garki" Ya faɗa a hankali kila idan yayi nesa da inda take babu wani kaddara da zai sake haɗasu, akallah yana da sauran aiki a garin yadda kuma hazo ya yamutse dole zai cigaba da zama a Abujan da sanayyarsa tayi ƙasa ba kaman a Kano ba. A irin lokutan nan da zai zama topic of discussion kowa haushi yake bashi, hakan ya sa a lokutan ya fi mayar da hankali ma kan ibada saboda shi ne kadai abin da ke sanyaya zuciyarsa tunda ba fitowa zai yi ya ce ba haka ba, hakan da zai yi ma shi zai karawa abin fetur ya cigaba da ci ya ƙi mutuwa. Wani hotel ya kai shi a nan cikin Area 11 ɗin ya fi ma wanchan tsaruwa nesa ba kusa ba, yayi booking ya ajiye kayakinshi kan ya fito suka wuce wurin program tea kawai ya sha ya cigaba da program din yana cire duk wata 'yar Daba daga kwakwalwarsa a cewarsa. Ta ɓangaren Diva abin da yayi mata na cinta a rai amma ta zaɓi shiru fiye da mayar da martani hakan ya sa ta ci alwashin kiyaye ma haɗuwarsu, wai ɗabi'ar dan maye ƙarya ita duk duniya bata ga wanda ya rainata ba ma kaman wannan Shehin akwai wanda ya isa ta masa ƙarya? Ai ko click ɗinta sun sani ba'a yi mata ƙarya kaman yadda bata yi don ta tsaneshi fiye da komai, ta yi mita ita kaɗai har ta gaji, har tambayar kanta take me ma abin bibiya a rayuwarsa mutum ina ka fito wa'azi ina za ka wa'azi? Kullum ana fama da litattafai ita Sam ba abin burgewa ba ne a gareta. kadaici ke damun zuciyarta haka shirun yayi mata yawa don babu abin da take yi iyakaci ta ci ta sha ta sha abin maye tayi bacci in ta tashi kuma tayi exercise har ji take kaman ta kira su Shaly su zo tunda Jagaban ya ƙi amincewa ta koma, sannan anan bata rigimarta don babu wanda ya taɓota hakan ya sa tayi kewar Kano. A chan Kano kuwa ɓangaren su Abbiey abin da suka gani din ya sa sun yanke hukuncin bin shawarar Ammiey kawai a yi masa auren hakan zai rage maganganu dayawa, don haka tuni suka fara shirin kai gaisuwa cikin farkon wata mai kamawa. Ɓangaren Jiddah tana cikin tashin hankalin rashin sanin inda suka kai mata 'yar uwa ta yi kuka har ta gaji ta dawo shiru kawai, sai addu'a bata san wani hali iyayensu ke ciki ba suna chan cikin kwanciyar hankali ko kuwa ga hankalinsu tashe bisa rashin ji daga garesu? Tana fata su ji a jikin su su kuma dage musu da Adu'a dukda ta wani fannin ta gama karaya wannan azzalumi da ake kira J duk inda za ka zaci zalunci da rashin imaninsa ya wuce nan. A chan cheɗiya Inna da ta zabga tagumi ta kalli malam tace "Malam ni dai har yau hankalina ya kasa kwanciya, a jikina nake jin yaran nan basa cikin kwanciyar hankali." "Ba ke kaɗai ba Atika, tun daga ranar da suka bar kauyen nan hankalina yake a tashe, sai in ga kaman mun yi kuskure mai girma, layin da suka bamu na kira na kira baya shiga" Ta muskuta "Toh ko za mu dauki fom din a wakilta wani ya je chan Kanon ya duba mana su?" "Zan je yanzu in samu dagaci da maganan tunda kin ga ba su Hauwa'un kawai ba ne akwai yaran jama'ar garin nan dayawa." Haka suka tsayar ya miƙe ya fice. Kaman yadda ya faɗa kai tsaye wurin mai gari yayi ya same shi bayan yayi gaisuwa aka tambayi me ke tafe da shi. "Da ma akan wannan tallafi da aka mana na fitar da yaranmu koyon sana'o'i ne, wallahi daga ni har mai ɗakina hankalinmu ba'a kwance ba ya kamata zuwa yanzu mu ji ɗuriyarsu tunda wata ukun har ya wuce" Kaman jira waenda akwai yaransu ciki suka fara gyada kai suna cewa tabbas wannan gaskiya ne shirun ya fara yawa. Dagaci yace "Ban da abun ku ai tunda gomnati ce ta turo mana su na tabbatar babu cuta ko ha'inci a lamarin su kuma shiru ai wata alamar lafiya ce idan babu lafiya ba za'a ji shiru ba amma ban ƙi ta taku ba mu ƙara musu ko sati biyu ne idan bamu ji daga garesu ba da kaina zan ɗaga mutum na aika chan birnin Kanon mu ji lafiyarsu" Ba don hankalin malam buba ya kwanta ba ya amsawa dagacin da godiya don kusan sun yi na'am da zantukanshi don baƙin ma da suka zo ai sai da suka fara mishi bayani har ma suka bashi yayi waya da commissioner ta mata. Daga nan dai ya tashi ya bar wurin ya koma gida bai boyewa inna Atika duk yadda suka yi ba tace Allah ya kai rai. *** "Da gaske Mama? Da gaske wani watan za'a zo tambayar aurena daga gidan su Shehi?" "Kwarai ai na faɗa miki ki dinga hak'uri da uzuri gashi nan komai na shirin kankama? Gaggawa babu inda zai kai ki" Tsalle ta yi ta dire ta yi ɗakinta da gudu tana murna, mahaifiyarta ta bita da kallo tana murmushi sai ta ɗaga kai sama tayi godiya ga Allah da Babanta Ustaz Abdallah bai ƙi batun Shehi ba, shi mutum ne mai tsauri da tsanani a kan yaranshi, baya yardar musu wata mu'amala ko soyayya har sai kin kamallah jami'a da kanshi zai zaɓi wanda yake so ya aurar da ke. Tun Jss 2 Na'ima tayi wani saurayi da ta so aurenshi mahaifinta ya ƙi babu abin da ba'a yi akan yaron nan ba ta kai har auren mahaifiyarta sai da ya tsinke kan aka sake mayar da shi a sannan ne tana Ss3 ta hakura da zancenshi saboda ganin tana shirin shiga tsakanin iyayen ta a hakan tayi ciwo tayi kunci kaman ba zata rayu ba don bata iya saka abu a rai ba, kwatsam kuma ta gamu da sheikh ta fara sonshi, tun babu wanda ya sani har mahaifiyarta ta sani kuma dama kawar Ammiey ce ita ta nemi haɗa ya'yansu kuma Ammiey ta gamsu da tarbiyar gidan don haka hankalinta kwance take shirin auren ɗan nata na fari. **** Yau Diva ta tashi da farin ciki bayan kusan kwana goma a Abuja Jagaban ya saya mata ticket akan za ta koma jibi, ba ita kaɗai ba har su pabloo shirye-shiryen tarbarta suke, yau da wuri ta tashi don akwai sakon da za ta karbar wa Jagaban a Apo amma bata fita ba sai da ta gama duk wani abin da za tayi a hotel ɗinta kusan uku da wani abu ta bar hotel ɗin. Bolt ta yi zuwa unguwar sai da ta sauƙa inda aka ce mata kan ta shiga takawa da kafa kaman yadda ya ce mata har ta isa daidai wurin ta danna earpod na kunnen ta ta sanar da isowarta mintuna goma bayan nan aka sake kiranta daga cikin wayan ake bayanin kayan jikinta baƙin wando, farin top, blue and white over-size shirt, black vail and facing cap. Kai take gyadawa a hankali ba'a katse wayan ba wani ya zo ya ajiye mata jaka a kan kafarta ya wuce, babu wani shakka ta saka a kafadarta ko kallon inda ya bi bata yi ba ta miƙe ta naushi dayan barin, bata hau abin hawa ba kawai ta cigaba da tafiya a ƙafa har ta iso wani crowded road. Akwai holdup tsallakewa take son yi kaman an ce ta kalli motar gabanta, sak Suv ce irin nata tana iya kallon maza uku dake ciki da wata mace dake galabaice tana dukan jikin windown, har ta dauke kai sai ta sake kallon wurin a daidai nan ta ga dayan ya ja ta baya ya kai mata duka ido ta runtse kaɗan ta buɗe, ba tinted mai duhu ba ne amma idan baka mayar da hankali ba ba zaka iya ganin abin da ke wakana ciki ba hakan ya sa mutane ke ta hada-hadansu. Jikin motar ta isa a bazata ta duƙa ta zare wukar dake jikin takalminta, cikin seconds tayi picking lock na jikin kofar kan su kula sai ji suka yi an buɗe na gefen kofar tayi ma wani yanka da ya sa ya kwalla ƙara kan su ankara ta fusgo wannan baiwar Allahn dake galabaice ƙasa ta ja ta baya, wukar da ta riƙe da ihun da na ciki yayi shi ya ja hankalin mutane suka fara ihu, Road safeties da police da ke kusa suka taho a guje ganin haka ya sa suka ja motar a dari sai kakkaucewa aka shiga yi. Duk waenda suke kusa da ita da wannan mata sun gudu, waiwaye take ko akwai wanda zai zo ya taimaka a kai ta asibiti saboda bakinta da hancin ta jini yake fitarwa gata kamar matacciya, idanunta suka sauƙa kanshi yana tahowa. Ya fito daga taron su da jibi za'a rufe, a gajiye yake tilis Kasancewar anan cikin Apo din suke program din nasu zai koma hotel nashi, tsayuwarsu holdup din ya sa ya buɗe idanu yana kallon mutane na ta hada hada Kasancewar yamma ya fara wasu makarantun sun rufe kuma wuri ne mai jama'a. Ihun da ya ji ya sa ya kai idanunsa wurin sai ga mutane sun fara gudu idanunsa suka sauka a kanta riƙe da wuka, mamaki tsantsa ne ya rufe shi, wannan kanta ɗaya kuwa? A tsakiyar mutane a tsakiyar gari irin wannan mai tsaro? Buɗe murfin motar ya tsinci kanshi da yi ya fita, sai da ya matsa dab da ita ya fahimci abin da ke faruwa ga ma'aikata sun bi wanchan motar da ganinsu ya sa suka buga wa motar wuta don tsira. Idanun da suka haɗa ta tsayar tace "Stay away! Ban nemi wani taimako daga gareka ba" Ya girgiza kai yana kallon yarinyar dake kwance a ƙasan with genuine concern da Bai ɓuya ba a muryarsa yace calmly "Saving a life comes first before everything else" Ya fahimci tana son nuna bata son taimakon da zai yi ne saboda kar ya ce ita ta sake bibiyarsa amma ba zai tafi kaman yadda sauran mutane ke gudu wasu ma na daga nesa suna video da wayoyinsu don posting ba, ya tabbatar da iyayensu ne ko 'yan uwansu babu mai fidda waya da sunan posting amma a yadda taimako yayi karanci yanzu har tsoro abin yake bashi. Ita ta kama yarinyar suka nufi mota da wani police ɗaya yana ta kokarin kira a kawo mota ne ma tace mishi su je kawai basu sani ba kar jinkirinsu ya ja mutuwar yarinyar a kallo biyu ta mata ma ta fahimci an ɗora ta kan mummunar drug. A gaba Shehi ya zauna police da ita da yarinyar suka shiga baya tuni drivern ya ja yana alhinin wannan abu da ya faru yana kuma jinjinawa kokarin Diva da bata ce komai ba sai hijabin jikin yarinyar da ta cire don bata iska saboda yadda take jika da wani irin zufa. Babu ɓata lokaci suka isa wani kyakyawar asibitin kudi aka shiga da ita police din ya tsaya cike cike inda Sheikh duk abin da aka kira kudi zai cire Atm card ɗin shi ya bayar. Ita dai Diva wuri ta samu ta zauna sai lokacin ta ji jakan sakon Jagaban a jikinta a fakaice ta kalli police din, dole ta bar wurin yanzu amma bata son tafiya bata san halin da yarinyar ke ciki ba, dukda a yanzu ta san she's safe police za su yi duk wani abin da ya kamata, a hankali suka fara ƙaruwa damuwarta sai ya kasu biyu waennan ba police na Kano ba ne bare tayi ikirarin Jagaban zai shiga ya fita, komai zai iya faruwa don haka tana bukatar tafiya. Tana Miƙewa tsaye police da ya kawo su ya nuna ta yana yi wa oganshi bayanin ai ita ce ta cece yarinyar. "Za ku tafi da ita ta ba da statement su kuma za'a cigaba da neman su don sun tsere" Ta kawar da kanta tana komawa zaune, Shehi na tsaye a gefe bai ce komai ba amma idanunsa na kanta yana mamakin damuwar na halin da yarinyar da bata sani ba ne take ciki ko kuwa wani abu daban? Yarinyar lamarinta na ɗaure mishi kaiii. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA* Police din ne ya nufeta "Baiwar Allah za mu je da ke division mu karɓi statement da kuma phone number dinki incase in kin tafi muna bukatar karin wasu bayanan sai mu ji daga gareki" Ta kalleshi sai ta ɗan sauƙe Numfashi kan ta miƙe tsaye taku biyu ta yi ta ga ya shiga gabanta a hankali yana cewa officer ɗin "We will be going together, ba za ta shiga motarku ba" Cikin mamaki take kallonshi, me nashi don ta shiga motar 'yan sanda? Ina ruwanshi ma da rayuwarta? Juyawa police din yayi ya tafi sai ya juyo ya kalleta suka haɗa idanu kallo me kama da harara ta mishi a fili take furta "Ina ruwanka idan ma kan motar zan hau su tafi da ni?" Bai ce komai ba ya juya kai ya fara tafiya sai ta bi shi "Ina fata ba za ka gama acting innocent gobe ka kalleni da zargin biyana aka yi in yi framing dinka ba don Allah ya gani ban saka ka ba ni dai" Idan dutse ya tanka to ya tankata haka ta karaci mitarta kuma ta shiga motar tashi da tuni ya jima zaune a gaba. Motar police din na gaba suna binsu har cikin police station duk wani bayani ta yi musu yana zaune gaban desk din kaman yadda take zaune, biro aka miƙa mata ta rubuta phone number kan ta saka hannu ya sa nashi da ta bi da kallo ya amshe. Fararen zara zaran fingers din nashi ta zurawa idanu a sadda yake rubuta numbers ɗin har ya gama kan ta kalleshi sai suka haɗa idanu nata ta zaro tana tambayarshi da ido me haɗinsu? Ta ina layin Wayanta ya zama nashi? Bai ce komai ba sai ido da ya kawar yana ɗan girgiza kai. Ko da suka fito daga police station din asibitin suka koma, ana kiraye kirayen magrib dole ya je yayi sallah kan ya dawo, tana nan zaune sai ga likitocin da suka shiga kan yarinyar sun fito. Asp din ne ya ke tambayar su. "Ya take? Babu wani abu da ya same ta?" Babban Likitan cikin jimami yace "Ta fuskanci mummunan cin zarafi ta jiki da kuma fyade, kuma hakan ya yi matuƙar tasiri ga lafiyar kwakwalwarta da ta tunaninta. A halin yanzu tana cikin yanayin firgici (psychological shock), kuma ba ta cikin yanayin da za ta iya ba da cikakken bayani. Mun fara ba ta kulawar gaggawa tare da daidaita yanayinta. Za mu ci gaba da kula da ita aƙalla na tsawon kwanaki biyu domin sa ido da kuma ƙarin bincike" Ya ɗan ja numfashi "Dangane da zargin fyade, za mu tattara dukkan shaidun likitanci da sakamakon gwaje-gwaje, sannan mu rubuta cikakken rahoto da za a miƙa muku don cigaba da gudanar da bincike. A halin yanzu an ba ta magungunan da suka dace domin rage raɗaɗi, tashin hankali, da kuma taimaka mata ta samu hutu. Da zarar ta farfaɗo kuma ta samu ƙarfi, za mu ci gaba da sauran bincike da kuma ɗaukar bayaninta." Diva ta riƙe bakinta tana ambaton Allah hakan ya sa Shehi da shima ya shiga damuwa da halin da yarinyar take ciki don duk mai imani idan ya ganta sai ya tausaya mata, yayi mamakin ganin cikar hawaye a idanun Diva ita kuwa idan akwai wani kalma da ke ɗaga mata hankali ya biyo bayan kalmar rape, ina ma za ta ga waennan mutane da kafin su je ga hukuma sai ta tabbatar ta gana musu azabar da ko mace suka gani tsirara ba za su taɓa jin sha'awarta ba. Duk tattaunawar da ya kamata Likitan ya yi da police din waenda zai bayar a rubuce ma zai bayar, Adu'ar samun lafiya Shehi yayi mata kan ya kalli Diva da har lokacin take cikin damuwa da bai buya akan fuskarta ba yace "let's go" Ta kalleshi shima ita yake kallo kwarjinin da ta ji ya mata da kuma yanayinta ya sa ta kasa mishi musu sai da ta miƙe kan ya ɗauke idanu daga kanta yayi gaba ta bi bayanshi har mota, ta shiga ne kawai ba tare da ta san inda za su ba shi ya faɗawa drivern ya kai shi hotel ɗin shi har suka isa babu mai magana a motar, sai da ya sauƙa ya cewa drivern ya kaita hotel ɗinta daga nan ya juya ya shige ta bishi da kallo a ranta tana raya ji ƙarfin hali ɓarawo da sallama ko ina ruwanshi da sadda za ta bar asibitin? Shi ya kaita ne ko me? Haka dai ta gama mitarta har ta gaji kan ta yi shiru drivern na sauke ta ta wuce ciki ta adana sakon Jagaban. Wanka ta fara kan ta rama sallolin kanta, kayan bacci kawai ta saka karamar riga da iyaka cinya ta yi waya da Jagaban kan ta kwanta Kasancewar flight ɗinta da wuri ne bata sha komai ba gudun matsala, da kyar bacci ya dauketa kuwa tsabar tunanin yarinyar nan da bata san ko sunanta ba. Ina za su kaita? Ta ya suka sace ta? Ya iyayenta suke ji a yanzu? Duk babu abin da bata raya ba ta yi tsaki ya fi cikin kwando kan bacci ya dauketa, da sassafe kuma ta farka ta yi wanka ta shirya ta kira Bolt ta kuwa ci sa'a ta samu ya zo ya ɗauke ta zuwa Airport da yarinyar ta farka amma ta tabbatar tunda tana hannun police za su yi duk abin da ya kamata. Babu ɓata lokaci ta gama duk abin da za tayi karfe takwas na safiyar ranar jirginsu ya ɗaga daga Abuja zuwa Kano, tana sauƙa a Airport na Aminu Kano ta lumshe idanu ta buɗe tana shakar iskar Kano da tayi kewa kwarai, murmushi ne kwance a kan fuskarta don ji take kaman ta shekara da barin jihar da ta fi wayo, tana fitowa Arrivals kuwa ta ci karo da su Shaly ɗaya bayan ɗaya sai da tayi hugging nasu dukkansu shidda suna ta murmushin ganinta itama haka. "Barka da sauƙa Shugaba mun yi matukar kewarki" Pascal ya faɗa Skipo da ke saka jakan ta a SUV ɗinta yace "Ai faɗa ma ɓata baki ne Kano ya zama lami da baki a cikinsa Diva, amma tunda kin dawo komai zai koma norrrmal neee" Suka yi dariya tace "Na gode, ku muje" Baya ta shiga Pablo ke driving Obafiya na gefenshi su kuma duka suna daga ciki. Hira kawai suke suna bata labarin wasu abubuwan da suka faffaru bata nan wani tayi takaici wani ta yi dariya cikin yanayinta na yanga. Jagaban shi kanshi yayi murna da ganinta don hugging ɗinta yayi itama ta mayar suna murnar ganin juna daga nan ta shige ɗakinta don ta huta kan a ɗora daga inda aka tsaya. **** Waya yake da Ammiey cikin natsuwa suke tattaunawa yake sanar mata cikin wani sati ma zai dawo Kanon in Shaa Allah za su gama program din jibi akwai dai abin da zai ƙarasa wanda ba za'a rasa ba. Ta yi masa Adu'a kan tace "Ni ko kana ƙiran yarinyar nan da na ce kuwa? Idan ma fa baka kira ya kamata ka ƙirata ku na gaisa wa Shehi don wani satin ne za'a kai kudin aurenku" Ya ji daaɗi da bata tsaya jiran jin amsar tambayar farkon ba don bai san me zai ce mata ba, ya amsa kawai da in Shaa Allah daga nan suka yi sallama. Yana ajiye wayan Ammar ya ƙira. "Ya Sheikh!" "Ammar kana lafiya?" "Alhamdulillah ya Abuja?" "Alhamdulillah" Sun fara tattaunawa kan harkokin Shehi da ya bari nan Kano sai da ya ji komai na kan tafiya lafiya kan suka shiga wata firar, shi ne ma ya ke cewa Ammar ɗin "Ammar layin yarinyar nan nake so ka samo min" "Wace yarinyar?" "Amm Na'imah yeah ita" "Ka ce min dai your wife to be" Yana buɗe system na gabanshi yace "Koma dai menene ni dai layi kawai nake so Malam" Yayi murmushi yana ji Ammar na mishi barazanar idan yayi tsiya sai ya fasa samowar shi dai bai ce komai ba suka yi sallama. Aikin da yake yi duk dare ya cigaba da yi yana mamakin yadda har yanzu ya kasa gano daga ina matsalar take, duk yadda zai yi bincike akalar akan Ammar ne amma zuciyarshi kwata kwata ta kasa yarda cewa zai aikata abu irin hakan kuma tare suke idan yana spending irin wanchan kudin dole zai sani ne, ba zai sare ba zai cigaba da binciken har sai ya gano gaskiya. Tunanin yarinyar chan ta asibiti ya tsarga mishi hakan ya sa dole ya tuno da Diva, sai ya ɗan girgiza kai yana ƙaramin murmushi bai san me zai kira yarinyar ba samm, tana bashi mamaki komai nata ya bambanta da na mata 'yan uwanta, yadda take tsayar da Idanunta kansa kadai mamaki yake bashi har harara da mitarta sai da ya tuna ya tsinci kanshi da tunanin ko ta koma asibitin ne ko bata koma ba! Don shi bai koma din ba kaman kuwa jira yana cikin tunanin ya ji ƙira ko da ya duba number ne. Ɗaga wa yayi da sallama bayan sun gaisa yake sanar da shi daga police station ne idan babu damuwa suna son ganinsu a gobe, shi dai bai san ta yadda zai samu Diva ba amma bai ce komai ba bayan Allah ya kai mu gobe ɗin bayan katse wayan ma bai tsaya tunanin neman ta ba ya cigaba da abin da yake. **** Dagacin cheɗiya ne ya kalli mutanenshi da suke zazzaune ya muskuta yace "Toh ni dai don kun ɗaga hankulanku ne amma har yanzu ban ji kaman akwai matsala kan yaranmu ba, amma saboda kawar da zargi za mu wakilta Malam Musa zai bi wannan adireshin na jikin fom ɗin ya tafi har chan Kanon ya dubo mana lafiyarsu da yardar Allah" Kowa a wurin ya gamsu kuma ya yi na'am, Malam Musa na da ɗan ilimin boko don har NCE ce da shi yana kuma harkar tafiye tafiye shi ne kadai zai iya yi musu wannan, guzurin kudin mota da na abinci da suka hada mishi aka damka mishi ya karɓi fom ɗin yayi musu sallama ya nausa inda zai samu machine ya haye don kai shi ga inda zai samu motar shiga cikin gari zuwa Kano. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI* Tsaye yake a cikin asibitin, kaman koyaushe irin shigarsa ta labarawa ce jikinsa Grey thobe da black and gold Jubba, Ghutra kawai ya ɗora a kanshi ya zauna mishi da kyau, fuskar nan kaman ko yaushe cike da kamala da tarin natsuwa, hannunsa ɗaya a aljihu ɗaya kuma na dafe da stand da wasu polisawa guda hudu ke tsaye daga gabansa suna mishi bayani. Na farkon yake kallo yana sauraronsa a sadda yake cewa "Toh Sheikh mun ƙira ku ne ba don komai ba sai don sanar da ku halin da ake ciki da wannan baiwar Allah dukda mun san taimakonta kuka yi, sannan daga lokacin da muka karɓeta ya kamata a ce hakkin kula da ita ya koma kan gomnati amma wani abin dole ne muna bukatar saka hannu da kuma tallafi Kasancewar mu ma ba access muke da shi da gomnatin kai tsaye ba. Wato halin da ake ciki bayan duka binciken da muka yi mun gano cewa wannan yarinyar an yi kokarin safararta ne wato trafficking victim ce so yanzu case din ya tashi daga hannunmu mu regular police ya koma wurin National Agency for the prohibition of trafficking in persons Wato (NAPTIP) ko da muka dawo nan ɗin mun tarar da ta farka sai dai ba cikin yanayi mai daaɗi ba. Bari Likitan ya sake yi mana gamsashen bayani duka" Sheikh ya ɗan gyara tsayuwa yana saurarensu ba tare da ya ce komai ba, Likitan da ya ke buɗe file ɗinta ya ɗora da "Toh Alal hakika binciken da muka yi dai mun sameta da abin da ake kira a likitance Dissociative amnesia a hausa za mu iya kiranta da 'mantuwar kwakwalwa sakamakon tsananin firgici ko raɗaɗin zuciya' ba za'a kira shi da gama garin cutar mantuwa ta (dementia) ba ko bugun jini domin shi illa ne da ke faruwa a lokacin da kwakwalwa ta kasa daukar nauyin wani mummunan abu da ya faru" Ɗaya daga ciki police din ya kasa shiru sai da ya ce "Ashshaa! likita daman hakan na iya faruwa?" Yayi murmushi ya kalli ɗaya daga cikin police na NAPTIP ya ce "Su da suke hulda da mata ko kananun yara da suke faɗawa victims na trafficking sun san fiye da hakan ma na faruwa idan mutum ya fuskanci abin da ya girgiza rayuwarsa kaman su fyade, azabtarwa ko yawan duka mai tsanani, ganin kashe-kashen rayuka ko ma hatsari mai munin gaske, wani lokaci kwakwalwa da kanta ta kan kulle wasu bayanai domin kare mutum daga faɗawa tsananin ciwon tunani" Dukkansu suna cikin jimami babu mai kwatantata hakan a kanshi ko wani na jininshi itama kaddara ce ya jefa ta wannan kangi amma duk suna jin cewa za su yi iya yinsu sai dai kuma idan abin ne ya ci tura. Likitan ne ya cigaba "Mun fara fahimtar hakan ne bayan farkawarta daga irin ƙwayoyi da aka bata ta fice hayyacinta, bata iya tuna komai da ya shafeta ko sunanta, tana kallon mu duka cikin ruɗani kaman bata taɓa ganin halittu irin namu ba, sai kuma da muka matsa da tambayoyi sai ta tsorata har ta nemi firgice mana dole muka dakata don ta huta ta kuma samu natsuwa" A lokacin ne Irshad ya magantu. "Amma Dr. Shin cutar tana daɗewa kan a maganceta?" Likitan ya ce "Tambaya mai kyau, a gaskiya ba za mu iya dibar ma wannan cuta wa'adi ba, it depends wasu suna iya ma samun sauki cikin sati guda wasu satuttuka wasu har ma watanni sannan ba lallai ya dawo gabaɗaya ba sai dai da kaɗan kaɗan, ko kuma yawan ji ko sauraren abin da aka saba da jinsa a baya kan wannan cutar kaman muryoyin makusanta, wani waƙa ko karatu da aka saba da saurarensa wata murya ko fuska da za ta iya harba saƙo kwakwalwa cikin sakanni. Yanayinta na iya tafiya da PTSD (post-traumatic stress disorder) Don za ta iya fama da mafarkai, tsoro ko firgita da wuri da yawan son kare kai ko da ba abin cutarwa ba ne ya nufeta." Babban cikinsu wanda ma'aikaci ne na NAPTIP ɗin yace "Toh likita muna godiya da wannan bayanai amma akallah zuwa yaushe ku za ku iya rike mana ita anan?" "Ba Za Ta fi kwana goma zuwa sha biyar ba, sauran sai a hankali so ko a gida za'a cigaba da kula da ita" Irshad ne ya ce "Wani irin kula take so?" Likitan yace "wuri suke bukata mai kyau da aminci, kada a matsa mata ko a gaggautawa kwakwalwarta tunanin komai, sai an haɗa da hakuri da kwantar mata da hankali in Shaa Allah za ta warke" Godiya suka mishi Likitan ya wuce, Irshad ya kalli babba cikin NAPTIP ɗin da ya shiga yi mishi wannan bayanin "Za mu yi amfani da kwanakin zamanta a asibiti zamu ƙara kaimi wurin investigation, za mu gwada su fingerprint ɗinta ko tana da wani registered abu da shi, za mu duba duk wani missing person reports da aka samu a ƙasa na kusa ko ma na nesa sannan za mu ɗan taɓa media appeal da mun kama su ne tabbas za mu san yadda za mu matse su su faɗi inda suka ɗaukota amma a yanzu da muka rasa su dole waennan hanyoyi ne kawai za mu iya bi don identifying ɗinta musamman idan bata samu lafiya ba" Irshad da yake jin tsananin tausayinta da na iyayenta a wannan lokaci yake ji musu raɗaɗin wannan al'amari ya ce "Idan duk hakan bai yi working ba ba fata ba menene mataki na gaba?" "A tsarinmu idan an samu irin wannan mataki da mu ke ɗauka bayan sallama daga asibiti mu kan kaisu shelter dinmu na NAPTIP Inda aka ware musamman don irinsu amma ka san yanayin ƙasar a yanzu kula ba lallai ta same shi 100% a chan ba, akwai shelter na Women affairs ma wanda Minister of women affairs ke kula da shi muna iya kaiwa chan ajiya, ko kuma dai wasu trusted NGO da za mu iya biya su kular mana da ita" Hakan Sam bai zaunawa Irshad ba amma bai ce komai ba, bills na asibiti yayi clearing har na kwana sha biyar da zata yi, bayan ya gama kuma yayi sayayya mai yawa ya kai har dakin shi da driver tana bacci suka same ta bai wani zauna ba ya fice bayan yayi magana da police din akan shi ba dan nan bane zuwa yayi program kuma zai koma a washegari don haka ko ya tafi zai cigaba da bibiyar al'amarin in Allah ya yarda, sun yaba mishi Sossai sun kuma yi mishi godiya don samun irinsu a yanzu yana wahala masu yi don Allah. Daga nan wurin program ya isa aka yi closing da shi program ya watse lafiya ƙalau cike da nasarar ƙaruwa da suka samu ta hanyoyi daban daban, hotel ya wuce bayan yayi wanka yayi ordern tea saboda shi fa a duniya idan akwai abinda baya gajiya da shan shi to tea ne, ko wani iri ma in dai tea ne zai sha. Yana cikin sipping a hankali idanunshi na kan TV da ake haska mataimakinshi na wa'azi a masallacinshi da Imam na ja mishi baƙi, wani farin ciki da natsuwa ne ke ziyartarshi dukkansu training dinshi ne abin da ke mishi daaɗi ba karatun ba ne sai irin ladar da zai samu da yardar Allah a kansu, sai irin nasarar da ya samu na ko ba ya duniya yana da tabbacin babu wani abu nashi naa addini da zai tsaya hatta wannan lada zai kasance mai gudana zuwa cikin makwancinshi. Yana cikin wannan tunani ya ji Wayanshi na ringing ko da ya duba sai da ya gyara zama saboda wanda ya kira ɗin tamkar Abbiey yake a gareshi, Godfather ɗin shi kuma mentor ɗin shi Sheik Nasser Al-Rasheed, Aminin mahaifinshi ne don an yi zama na amana Kasancewar Sheik Nasser babban malami kuma balarabe da ya yi zaman Kano dalilin kasuwanci na shekaru da dama tun Irshad na ƙarami, he's a very respected person by both Nigeria and Saudi community saboda duka sun amfana da shi ta ɓangarori da dama har yanzu kuma suna kan amfana tunda da taimakonshi Irshad ya zama abin da ya zama a yau har ake alfahari da shi. Sheikh Nasser Al-Rasheed fitaccen dan kasuwa ne a duka kasashen Nigeria da Saudi Arabia saboda yana fitar da su riɗi, ƙaro, zobo, ginger, gyaɗa da su spices dai daga Najeriya zuwa Saudi kuma yana shigowa Nijeriya da su Dabino iri daban daban, man zaitun, litattafai haka na addini, kayan gine gine da dai sauransu a gefe guda yana sana'ar real estate yana da manyan shopping plazas, warehouses, apartments da hotels a kewayen Nigeria da Saudi, wanda Irshad ya samu asalin dukiyarsa na ƙashin kansa a karkashin waennan sana'o'i na ubangidansa yana da tarin arziki da bai fito fili ba sai wa kalilan na makusantanshi. Cikin natsuwa da ladabi ya ɗaga tuni ya sauya harshe zuwa larabci suka shiga zubawa tamkar a Saudi Arabia, labari mai daaɗi da Irshad ya samu a gabaɗaya kwanakin shi ne na Shigowar Sheikh Nasser wani satin kwarai yayi murna dole kuma a gobe ya koma Kano zama bai ganshi ba, sun fi awa uku suna magana kan suka yi sallama bayan sun gama tattauna harkar kasuwanci da kuma na hidiman addini da zai kawo shi Kanon. Miƙewa Irshad yayi ya shige toilet yayi alwala ya zo ya yi karatun da ya saba na suratul mulk kan yayi adu'ar bacci ya kwanta don flight nashi da safe ne. Ko da ya tashi tsakar dare bai koma ba har yayi sallar asuba da ya idar din ma bai tashi ba yana karatu sai bakwai yayi nafila raka'a biyu kan ya shige bayi yayi wanka ya zo ya shirya dama driver na jiranshi a ƙasa bai damu da ya karya ba ma ya bar hotel ɗin zuwa Airport, Allah ya taimaka bai samu wani delay ba jirginsu ya ɗaga zuwa Kano. A Airport ya samu Ammar suka yi hugging juna cikin kewar da suka yi na juna kan suka nufi mota, kafin su isa har Ammar ya fara tsokanar Shehi wai ina ya baro Diva, takaici ya hana ma sheikh magana har ya shiga ya zauna. "Ka yi wa Allah Ammar ka daina haɗani da 'yar daban chan, wanda aka yiyyi a baya ma ya isa" Ammar yayi dariya "Gaskiya mutane basu da adalci, ai ko da gami kurna ta fi magarya zaƙi hanyar jirgi kuma daban da ta mota me zai hadaka da wanchan yarinyar da shaye shaye ya zama jininta, zubar da jinin mutane ya zama ado a wurinta kuma rayuwar titi ya zama duniyarta?" Irshad ya ɗan sauke Numfashi ya ce "Ni karan kaina ina mamaki Ammar, ko kusa ko alama ba na jin wani ɗabi'a ko halayyarta yayi kamanceceniya da rayuwata bare har a alaƙantata da ni, bayan musulmi da nake ita ma kuma take amsa wannan sunan." Ammar ya ce "kawai so aka yi a ɓata maka suna da ita, har ma na yi zargin ko an biyata ne musamman don ta lalata maka mutuncin da miliyoyin al'umma suke kallonka da shi" *"Ka san mene? Ka fita a sabgata tun ban nuna maka kalolin rashin darajata ba don yanzu ka gama faɗa ba ni da mutunci, kuma a rashin sanin mutuncin kamewar ban ga abin marmari da zan bibiya a rayuwarka ba, kudi kuma sun yi kadan su sa na ɓata lokacina a kanka idan ma zargi kake to tun maza ka daina! A baya ma na bibiyeka ne saboda in ɗau fansar abin da ka min kuma mun gyarota idan ba kana son na janye ma hakurar da nayi ba ne ka daina nuna min fuskarka a tawa don babu abin burgewa a rayuwarka wurin DIVA"* Kalamanta da suka dawo mishi kai kenan kaman yanzu take jero su gareshi cikin gargadi da kaushin murya, ido ya ɗan runtse yana hango yadda Idanunta da suke lumshewa da maye suke ƙara girma da raguwa cikin nashi da sauri kuma ya buɗe idanun yana ambaton Allah tare da riƙe goshinsa. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS* "Ya dai?" Ammar ya tambaya yana ɗan kallonshi while driving. Ya saki goshin yana zubawa titi idanu ya furta "Babu, gajiya ce kawai" Babu wanda ya sake magana cikinsu har suka isa gida, kusan mutanen gidan sun fito yi mishi maraba don suna da wannan ɗabi'ar a gidan idan wani yayi tafiya ranar da zai iso za su fito duka su jira saukarshi daga mota a yi maraba kan a barshi ya je ya shirya ya kuma bibiyi iyaye yayi gaisuwa da fatan samunsu lafiya. Yanzu ma sun yi murnar ganinsa Sossai, cike da kaunar ahalinshi yake amsa sannu da dawowa da suke mishi tuni Mufida da sumayya sun ja trolley dinshi da jakar system sun nufi sashenshi kan ya gama ya nufi sashen ma sun fito, cikin natsuwa ya shiga sashen dake ta fidda kamshi ya san aikin kannenshi ne bisa umurnin Maamah don har abinci gashi an jere mishi. A natse ya haura samanshi, ya wuce parlorn zuwa bedroom ɗin shi da sallama kan lips ɗin sa sai yake jin kaman ya shekara ba ya gidan yayi kewar Kano Sossai ashe bai farga ba. Rage kayan jikinshi yayi don ba ya jin zai fita wajen ma sai azahar, farin dogon wando na yadi da farar shirt ya saka, shirt din irin mai roba da ke kama jiki ne don haka ya fitar da kirarsa gabadaya wuyan kuma V line ne mai guntun hannu, bayan ya feshe jikinshi da turarukansa masu sanyin kamshi ya nufi parlorn ƙasa a chan ya zauna ya karya don tun jiya sai a lokacin yake sa wani abu bakinshi. Yana cikin cin abincin ne Imam ya shigo bai takura masa ba sai ya zauna a parlor har ya gama ya zo ya samesa yana zama hurairah na shigowa da gudu ya dauketa ya sakata kan cinyarsa yana shafa gashinta. "Ya hurayr kaif haluki? Istaqtu ilayki..." Ya furta da murmushi don da ma ba hausa yake yi wa kuliyar ba kuma jin yaren take tsaf na larabci "Hurayr kina lafiya? Na yi kewarki" Imam yayi murmushi yana miƙa gaisuwa Shehi na cigaba da shafa kuliyar suka gaisa, nan Shehi ya fara tambayar sa abubuwan da suka faru ba ya nan wani Imam din ne zai tuna ya faɗa masa wani kuma zai tambaya sun jima suna magana kan ya tafi, shi kuma Shehi ya haura sama yana ɗan sa hannu cikin gashin kansa da ya ji yana bukatar ragewa don ya fara damunsa, system ya janyo ya shiga inda ya tsaya da batun companyn Abbiey shawarar Sheikh Nasser ya bi sai gashi ya fara ɗaukar haske cikin kankanin lokaci. **** Khalil ne tsaye kofar gidan da aka yi mishi kwatance sallama yake yi cikin ɗaga murya har aka amsa, bai jima yana tsaye ba wani yaro ya fito "Yaro ina neman Malam Sule ne" "Yana ciki" "Ka ce mishi yana da baƙo" Komawa yaron yayi chan sai gashi ya dawo "Wai ka shigo" Bin bayan yaron yayi zuwa ciki yana kallon gidan ganin yadda yake nan a rushe rabi da kwata daki daya ne na taɓo wanda aka rufe bakin da buhu daga gefen bishiyar tsada ya ga wani dattijo da wahala da talauci suka bayyana jikinshi zaune kan wani kujera. Tsugunawa yayi "Baba ina yini?" "Lafiya yaro, ka zo lafiya?" "Alhamdulillah baba" Sai yayi shiru ya rasa me zai ce ya zubawa almajirin dake dibo ruwa daga rijiyar gidan yana zubawa a randar dake gefen ɗakin. "Sai dai ban sheda ka ba yaro" Numfashi ya sauƙe kaɗan yace "Sunana Khalil na zo daga Kano ne" "Wai wai wai ashe daga nesa kake yaro sannu da zuwa! Kai Usmanu kawo masa ruwa" "A'a Baba ai ba ma yau na zo ba tun jiya ne, da ma na zo ne kan maganan 'yarka Zubaidah" Tuni jikin wannan dattijo ya fara rawa cikin rawar murya yace "'yata? Ƴata Zubaidah?" "Kwarai kuwa Baba..." Sai dattijon ya fashe da kuka mai tsuma, kukan da ya ɗaga hankalin Khalil. **** "Ranka ya dade akwai matsala fah!" "Matsala? Meyasa za ka kiramin matsala?" "Ranka ya dade wannan yaro ya fa fara shirin bankaɗoka idan ma bai bankado din ba kenan don bincike ne ke shigar da shi cikin wani binciken" Da hanzari ya miƙe tsaye ya fara jeka ka dawo zufa na karyo mishi. "Dole a yi wani abu! Dole a yi wani abu..." Ya maimaita ya kai sau hudu kan ya katse wayan" ***** Fadar gomnati, zaune yake yana nazari idanunshi na kan fai-fain videon da aka mishi playing na wa'azin Irshad na bayan magrib da ya dawo a ranar wa'azi ne da ya ɗaga masa hankali. Musamman a lokacin da Irshad ya kalli camera ya ce "Wannan saƙo ne zuwa ga kai shugaba marar adalci mai mantawa da Allah... Ya kai shugaba! Ka tuna cewa kujerar da kake kai ba za ta bi ka kabari ba. Duk ikon da kake da shi a yau amana ce daga Allah, ba mallakarka ba ce. Idan kana neman ci gaba da mulki saboda hidimar al'umma da adalci, Allah Ya taimake ka. Amma idan kana neman zarcewa ne saboda son mulki, girman kai, ko tsoron rasa iko, to ka tuna cewa ranar da za ka tsaya gaban Allah ba za ka zo da jami'an tsaro, kuɗi, ko mukamai ba. Manzon Allah ﷺ ya ce: "Kowannenku makiyayi ne, kuma za a tambaye shi game da abin da aka ba shi amana." Shugaba ba sarki ne a kan bayin Allah ba, bawa ne da Allah Ya ɗora wa nauyin jama'a. Hawaye na maraya, kukan al'umma, yunwar talaka, da zaluncin da aka yi wa mabukata ba sa ɓacewa a wajen Allah. Ka ji tsoron ranar da mulki zai ƙare, amma hisabi bai ƙare ba. Ka ji tsoron ranar da waɗanda ka zalunta za su karɓi hakkinsu a gabanka. A ranar ba kuɗi za su amfana ba, ba iko ba, sai ayyukan ƙwarai. Ka tuna: mutane na iya tsoronka a duniya, amma kai ma kana ƙarƙashin ikon Allah. Wanda Ya ba ka mulki zai iya ƙwace shi a lokacin da bai zo maka a zato ba. Saboda haka, ka yi adalci. Ka guji zalunci. Ka tuna cewa shugabanci ibada ce idan an yi shi da gaskiya, amma babban nauyi ne idan aka mayar da shi hanyar son kai da tauye haƙƙin mutane" Masallacin yayi tsit babu tsoro ko shakku ya cigaba da jan hankalin mutane akan tashi tsaye su kwatarwa kansu 'yanci daga azzaluman shuwagabanni daga ƙarshe ya rufe da adu'a "Allah Ya shiryar da shugabanninmu zuwa ga adalci, ya kare al'ummar annabi Muhammad (SAW) daga zalunci, Ya sa mu kasance cikin masu tsoronSa da kiyaye dokokinsa Ameen" Kalaman sun zo wa Bashir dantani ta fuskoki biyu, dukda wani zuciyar na cewa ba da shi yake ba amma saboda ya san kanshi sai yake jin kaman da shi yake kai tsaye, ji yake kaman zai iya faduwa a yadda Irshad ke nusar da mutane da jan hankalinsu kai har sunanshi yaji yana amsa kuwwa da muryar Irshad na cewa mutane da shi yake kar su zaɓe shi. Scrolling yake yana duba comment section na wa'azin, wasu na tamabaya kan batun Diva ya dawo bai ce komai ba, wasu na kiran wasu daga cikin azzaluman shuwagabanni suna cewa ya kamata a saka musu don idan wa'azin nan bai shige su ba tabbas sun rasa imani. Scrolling yayi biyu uku sai ya sake ganin wa'azin a duet wani matashi na kawo ayyukan da yayi ya rubuta daga sama BASHIR DANTANI DA KA SAURARI MALAM Wa'azin na playing kwaltan da yayi commisioning a satin chan ruwa ɗaya aka yi mai karfi ya kwashe shi har ya fara rami rami, daga nan videon makarantun da ya ce ya kawo tsarin free education har da ikirarin ya kashe makudan kudade kan uniform da zai rabar kyauta sai aka hasko makarantun babu board, babu benchuna babu dai duk abin bukata na karatu yara na zazzaune a ƙasa suna karatu, aka sake hasko asibitoci babu gyara babu kayan aiki da wasu kauyuka da suke fama da rashin tsaro gomnati ta nuna ko-in-kula yana shiga comment dai da ya fi dubu biyu zagi ne da tsintuwa ake mishi wasu na cewa ya gama kenan babu shi ba zuwa senate har wasu na kawo shawarar a tilasta Irshad shiga siyasa ya zama gomna dukda ya nuna baya ra'ayin siyasa kila shi zai tallafawa ƙasar. Ranshi idan yayi dubu ya ɓaci, Wayanshi ya fidda yana jin dole komai ya zo karshe wannan gaskiya da Irshad ke ikirarin yana faɗa sai dai ya cigaba da faɗarta a lahira. Kira yayi na seconds goma sha biyar kan ya ce "Za ka ga saƙo" Daga haka ya katse wayar yana jefar da na hannunshi ya koma ya kwanta kan kujerar dake juyawa da shi idanunshi a rufe. **** "Pablo fa? Ni sai nake ga kaman bashi da lafiya don tun na dawo na kula yanayinshi ya chanza Sossai" Diva tayi tambayar tana juya Idanunta a kansu ganin bata ganshi ba kaman yadda jiya ma bai yini da su ba. "Bai shigo ba fa" "Ya kamata ku duba shi ai!" Bata gama rufe baki ba Skipo ya miƙe ya fice ita kuma ta zauna. "Shugaba ya kamata fah ki ce wani abu kan wanchan banza gajan, me za'a yi masa?" Tace "Ya ma sunan shi?" "Bullet" Zubash ta faɗa tana kashe Sigarin da take sha Ta Yi dariya "Paskal ka duba inda za ka same shi daga yanzu zuwa gobe zai san ya shigo territory ɗin Diva har yana ikirarin shine shugaban wannan kwaltan" Shaly tace "Laifin Obafiya ne da bai tarwatsa shege tun kan ki dawo ba" "Kin san Jagaban ya hana mu duk wani motsi ya ce babu ruwanshi idan wani abu ya faru a yanzu" "kar ku damu da kaina zan ganshi in yi maganinshi duk inda ya shiga cikin wannan birni" Dawowar Skipo ya hana kowa magana yace "Pablo fah ba lafiya Diva!" Duk Miƙewa suka yi tana tambayar "Me ya same shi?" Basu jira amsar shi ba ma suka wuce zuwa gidan sun yi mamakin yadda suka sameshi tuni Diva ta koma ta ɗauko mota Obafiya ya dauke shi zuwa motan suka bar unguwar zuwa asibiti. An karɓeshi amma bayan tsawon lokaci Likitan yana fito yana kallonsu "Lafiya Dr?" Diva tayi tambayar har ranta tana jin tashin hankali don bata son komai ya sami dayansu tana kaunarsu tamkar jininta. "Patient da kuka kawo ba za mu iya yi mishi komai ba" "Why? Meyasa alhali ba ya cikin hayyacinshi?" "Na sani yana sume, kai tsaye zan iya ce muku ya kamu da cutar da ake kira Nerve damage jiyoyinsa sun yi damage duk wani hanyar da za mu bi don basa taimako ba zai yiwu ba don mun nema mun rasa sun ɓace" "innalillahi wainna ilaihi raji'un" Yadda suka hada baki suka faɗa sai da Likitan ya sake kallonsu yana jin dariya na shirin taso masa ba na mugunta ba sai don tsantsar mamaki ji yadda suke ambaton Allah. "A matsayinka na likita na san akwai hanyoyin da za ka iya bi don taimakonsa don Allah ka taimaka ka sake duba shi kar mu rasa shi" Diva ta faɗa hawaye na cika Idanunta a Karon farko. Da gangan ya zo ya ce musu ba yadda za su yi dukda hakan ne babu wani jijiya da za'a samu lafiyayye a jikinshi duk sun lalace amma ba shi ya hana suka taimaka masa numfashinsa ya dawo daidai ba, yayi hakan ne don ya tsorata su akan bayanin da zai musu in anjima akan illar Penta da suka gama gane abinda ya kashe duka jijiyoyin Pablo kenan har ya fara haddasa ruɓewar tsokokinsa. "Ina zuwa" Ya faɗa yana komawa don ba zai yarda su san da gayya ya tsorata su ba tsaff sai su illatasa a yadda hankalinsu ya tashi. ***** Shi kam Shehi na haurawa shirin azahar yayi bayan sun gabatar ya dawo yayi bacci bai tashi ba sai la'asar yayi sallah kan ya dawo cikin gida ya fara da shiga sashen Daddah ya gaishe ta ya jima nan har ya ba Mufida Atm akan Malam Bala ya kaisu shopping su sayi abin da suke bukata as tsaraba, manyan kuma a wurin yayi musu transferm kudi masu tsoka su Goggo hindatu na ta godiya don yana da wannan kyauta a kai a kai. Daga nan wurin Maamah yayi suka gaisa ta mishi godiya kudin da ta gani yayi murmushi kawai, sai ya nufi wurin Ammiey karshe sun taɓa hira ya kuma ci sa'a bata kawo mishi zancen Wanchan yarinyar da ya mance layin ta a inbox don Ammar ya tura mishi tun jiya. Daga nan ya dawo ya shirya ya fita sallar magrib bayan nan ne ya yamutsa hazo da wa'azin da yayi don ya sosawa mutane ne inda yake musu ƙaiƙayi, bayan isha kuma ya nufi parlorn Abbiey da ya san a chan zai same su da Abba ya ci sa'a kuwa suna nan zaune har da uncle Ishaq da ya fara mishi tsiyar yana mantawa da su saboda shi gidanshi a jikin gidan ne ta waje kuma Shehi gaskiya bai cika shiga ba ribibinshi na dayawa sai in sun haɗu cikin gida a gaisa. Haƙuri ya bashi kan ya zauna suka shiga gaisuwa cikin tsanaki. Ya sanar da Abbiey batun zuwan Sheikh Nasser duk sun yi murna Abba yace "Ai to dole a ɗaga batun zuwa neman auren nan sai Ubangidanka ya iso a yi da shi Irshad" Abbiey ma yayi na'am don wannan aikinshi shine uba ga Shehi. Sun taɓa hira kan ya bar su ya wuce sashenshi yana tunanin da gaske fa suke auren nan dai shi suke shirin dole sai yayi. Layin yarinyar ya zubawa idanu na seconds kan kuma ya sa hannu yayi copying ya mayar calls ya ƙira. Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA ASHIRIN DA TARA* "Na san duk kun san da cewa allurar pentazocine ba'a yi ta don bugarwa ba, allura ce mai ƙarfi ta rage raɗaɗin ciwo sannan dole ana amfani da ita ne bisa umurnin likita kuma a asibiti, don rage raɗaɗi da zafin ciwo mai tsanani misali bayan tiyata ko wasu manyan raunuka, saboda tana iya haifar da jaraba da sauran matsaloli ya sa bai kamata a yi amfani da ita gaba-gaɗi ba tare da umurnin likita ba. Wannan patient da kuka kawo yana cikin abin da yake fuskanta na daga cikin manyan hatsarinta." Duk sun sani duk sun san Pablo is addicted to penta, irin addiction da zai iya yin hauka idan ya ɗauki awwani masu tsawo bai yi ba haka kuma duk inda zai samu jijiya yi yake idan zai yi a wuri ɗaya sau goma muddin jijiyar bai ɓace ba a wurin zai cigaba amma basu taɓa sanin illarta ta kai haka ba. "Likita zai iya warkewa ko? Jijiyon da ka ce sun ɓace har suna haifar da ruɓewar tsokokinsa duk za su dawo daidai?" Diva ta tambaya muryarta na bayyana damuwarta don tabbas hankalinta ya tashi. Likitan ya dubeta yace "Abu na farko da za'a fara shine dakatar da shi daga wannan allurar saboda lalacewar bata yi tsanani har chan ba za mu ɗora shi kan wasu magunguna da zai murmure a hankali bayan watanni amma muddin bai daina ba zai zama ya ƙarasa lalata jijiyoyin nashi na har abada" Hankalinsu ya ɗan kwanta har ma Diva ta sa a ranta dole ya daina ko da zai koma wani abin buguwar ba damuwa ba ne tunda duk suna yi din sai dai kowa da abin da ya fi so ne amma dole ya bar penta. Sun bar Pascal ne asibitin suka koma gida ko da ta yi wa Jagaban bayanin yadda abubuwan suka faru tayi mamakin rashin ganin kololuwar damuwa a tattare da shi har kaman ta yi shiru sai ta ce "Baba" Ya kalleta "Ina so bayan an sallami Pablo daga asibiti ko da ya zo neman penta kar ka sayar masa" "Meyasa?" Yadda yayi tambayar sai da ya sakata ɗan tsayar da Idanunta kansa "yanzu fa na gama maka bayani Baba idan bai daina ba komai zai iya faruwa da shi gaba, tsokokinsa ruɓewa za su yi Baba" "Sohana ba zan miki ƙarya ba muddin ya kawo kudinsa yana so sayar masa zan yi, ni sana'ata ce hanyar samun kudina kenan" Mamaki tsantsa ya bayyana a fuskar Diva. "Na zaci da ni da su Pablo duk ka daukemu ɗaya ne, idan ni ce na zama addicted to penta har yana neman rayuwata za ka cigaba da ba ni?" "Sohana sana'ata ce ba damuwa ko rashin damuwa ba, muddin shi ya kawo kudi yana so zan sayar masa abin da ya fi muhimmanci kudina ne" Wani irin abu da bata taɓa ji kan Baban ba ke taso mata, a hankali hawaye suka cika Idanunta amma bata bari sun yi tasiri ba ta haɗiye ta miƙe kawai ta fice daga gidan gabadaya ya bita da kallo a fili yayi dariya "Hmmm Sohana har yanzu ke yarinyar ce, har yanzu da sauranki a sanin Underground world" Ɗakin Shaly ta ya da zango kawai ta kwanta tana runtse Idanunta, a hankali ta shiga tunanin ya matsayin tarin waenda babanta ya jefa cikin duniyar kwaya? Meyasa bayan ta san yadda rayuwarsu ke tafiya ba kan daidai ba ne amma ba za ta iya daina wa ba? Ta ya za ta fara hana Pablo allurar penta alhali itama ta riga ta zama addicted to Ice? Har ranta ta fara jin ƙiyayyar yadda mahaifinta ke tafiyar da rayuwar matasa amma ba za ta iya wani abu ba sai ma ta bashi gudummawa ta wani ɓangaren. Maganan Shaly da Zee ne ya ɗan dawo da ita daga tunanin da ya fara addabarta sun riga sun san halin ta za ta iya gama zamanta ma a dakin idan bata yi ra'ayi ba ba zata musu magana ba, hakanan dama yanayinta ba mai wasa da dariya ba ce bare su fahimci abu na damun ranta. "Zee ni kam baki fahimci Zubash kwanan nan tana cikin damuwa ba?" Zee ta ce "Ai tun tafiyar Diva na fahimci ta rage walwala kuma fa yanzu ko yawan zuwa hotels hotels din nan bata yi, na kula har kudin abin da za ta sha bata da shi shiyasa jiya ta sha codein da bata cika so ba" Diva ta buɗe Idanunta tana kallonsu "Shaly menene matsalarta?" "Wallahi bamu sani ba amma zan bincika Diva" Numfashi ta ɗan sauƙe ta koma ta kwanta shiru, sai tayi tsaki kawai ta miƙe tana kiran Skipo. "Raina a wuya yake ina so a yau ba gobe ba ka binciko min bullet din nan in sauƙe masa zafin kan nan" Yace "An gama Diva" Ficewa tayi daga gidan gabadaya ta koma gida zuwa ɗakinta haka ta haɗa ice ta shiga sha ko zai rage mata abubuwan da suka fara tarar mata a kai. Kaman yadda ta umurta a yammacin Skipo ya sanar mata ai yana wani restaurant gashi nan shi da Obafiya sun tsare shi, ficewa tayi daga gidan bata nemi su Shaly ba ma ta ɗauki mota ta nufi restaurant da ya ce mata suna nan ɗin. ***** Shehi ne ke driving Ammar na daga gefenshi yau ya shiga BUK yayi lectures Kasancewar ya kwana biyu ba ya gari abubuwan sun ɗan taru a son shi ne ma gobe ya wuce Katsina ya dawo a goben saboda yana so ya fara batun gyaran Gidan sheikh Nasser da tsara yadda zai sauƙa har ya tafi, daga BUK company ya je kai tsaye inda ake shigo musu da kuma fitar da kaya ya nufa ya ɗan yi magana da wani a sirrance kan ya bar wurin ya nufi office na Ammar a chan ya zauna har Ammar ya gama abin da yake suka fito a tare. "Bari na bika kawai mu wuce gida motan nan zan kira mechanic ya ɗauka a nan birkinta ta sake ina zuwa da safe kadan ya saura ban yi hatsari ba" Dalilin da ya sa ya bishi kenan, a natse yake tukin har ya nufi hanyar gida ma duka sai wani da zai bashi saƙo ya ƙirashi akan komai ya kamallah ga takardun hannunsa. "Kana ina?" "Ina dab Majlis restaurant" "mu haɗu a chan kawai" Ya faɗa yana juya kan motar, dukda gajiyar da yake ji yana son kawo karshen abubuwan da yake bincikowan nan, wanda tabbas idan bai gano ba cikin kankanin lokaci komai zai iya faruwa da companyn bayan ɓacewar makudan kudade. Kai tsaye chan suka nufa sanye yake da Ox blood jallabiya da jubba da ya zama mahadar jallabiyar don kalar su ɗaya sai dai akwai adon ruwan gold daga jikin riga mai kama da alkyabbar, Ghutra da ya sa a kansa ma mai surkin Ox blood din ne da baƙi sai baƙin Agal da baƙin takalmi. A natse yayi parking motar suka sauka suka shiga ciki, bayan sun zauna waiter din ya zo sai Ammar ya umurceshi da ya kawo musu coffee, matashin mai sanye da kananun kaya ya zo ya zauna suka gaisa kan ya ɗauki brown envelope din ya ba Shehi, ya karɓa tare da furta "Jazakallahu khairann" Matashin yayi murmushi cikin girmamawa ya tashi zai fice Shehi na mishi tayin ma ya tsaya ko coffee da suka yi order ne ya sha ya ce a'a kan ya wuce. An kawo musu coffee din suna sha Ammar na tambayar shi ko ya kira Na'ima ɗin yace ya ƙira bata yi picking ba kuma ba ya tunanin zai ma sake kiran, Ammar yayi murmushi kawai daidai lokacin suka shiga jin hayaniya... Duk hankulansu suka mayar kai idanunsa basu sauƙa ko ina ba sai kanta tana sanye da wando dogo baƙi da wani blouse kalar maroon haka jersey vail din kanta ma kalar maroon ne, dab da su suke don za su iya cewa table nasu ne yake kusa da inda suke ɗin, ƙafanta ɗaya na kan kujerar gefen kato kuma jibgegen mutumin da suka zagaye su uku wanda daga kallo ɗaya ma za ka masa ka san cewa ba bahaushe ba ne ga mamakinsu hannu ta ɗaga ta tsinka masa mari. Sai ga muryarta cikin kaushi da ƙarfi tama cewa "Kai ne akuyar da ya tsallakemin danga? Kai ne dattin da ka rasa inda zaka yi da ruwa ya kwaso ka sai hanyana? Me ka ƙira kanka ma?..." Jikinshi na rawa yace "Babu! Babu komai..." Kallon Obafiya tayi sai ya kai mishi naushi yana chakumo kwalarsa "Me kake kiran kanka?" "Boss...boss da ya kori Diva" Skip ya sake kai masa naushi a baki "Kana kara ambatar sunanta sai na zubar maka da hakwara, Shugaba har wasu daga cikin yaran da ba'a taɓa mana su a layi ya taɓa da ikirarin ya riga ya ɓatar da ke yanzu mu ma duk karkashin sa muke" Wuƙa ta zaro tare da ɗora mishi kan wuyan da Obafiya ya danne Skipo kuma ya riƙe shi gamm suka hana shi motsi "Bari na sheƙe ka in ga uban me zai faru... Za ka san ka shiga hurumina" Waiters da kuma securities din wurin ne suka zube suna roƙonta kar ta zubar musu da jinin kowa a wurin ta yi hak'uri don duk sun san labarinta sun kuma sun san bata ɗauruwa. Lip ta cije ta saukar da kafarta daga kan kujerar tana juya Idanunta a wurin don bata son yawan magiya, idanunta basu sauƙa ko ina ba sai kanshi da shima yake kallonta mamakin fuskarshi ya koma takaici don har ranshi ganinta hakan yana jin ɗaci da takaicin ta amsa sunan diyar musulmi a irin wannan ɓata. Miƙewa yayi kawai ya sa hannu aljihu ya zaro kudin da bai san nawa ba ya ajiye kan table ɗin ya kalli Ammar "Mu je" Miƙewa Ammar yayi suka nufi fita, baya baya ta ɗan yi ta zauna kan table da suka tashi ta kalli Obafiya "Ku kyaleshi for now! Ku tabbatar duk inda kuka sake ganinshi a birnin Kano ya baƙunci lahira umurni ne" Baya suka matsa ya fice da gudu, tana Miƙewa ta taka abu, ido ta kai wurin sai ta duka ta ɗauka wallet ce ta maza, buɗe wa tayi Idanunta suka sauka kan ID cards da kuma Atms, sunanshi ta fara gani kan hoton shi na passports, ta kalli kofar da basu jima da fita ba sai ta miƙe ta nufi kofar don har ranta tana son jin ko police sun kira shi batun yarinyar chan? Ko iyayenta sun same ta? Don bata taɓa jin tausayin wani mahaluki a duniya yadda ta ji na yarinyar ba. Dab motar su ta hange su da sauri ta ƙarasa tana furta "Excuse me!" Babu wanda ya juyo a cikinsu Karon farko da bakinta ya furta sunansa "Sheikhhh!" Babu zato ba tsammani ta ga ya juyo cikin kaushin murya da tsawa girman idanunsa duka a waje yace "Whatt??" Har Ammar sai da ya waigo yana kallonshi don Shehi ba gwanin ɗaga murya haka ba ne, sai ya fahimci ranshi a ɓace irin ɓacin da yana wuya a gani a tattare da shi. Yadda ya juyo a zabure kuma idanunsa na kallon nata ya sa ta ji ta tsaya chakk ta kasa motsi Karon farko da wani murya ya girgiza zuciyarta don tsawar ya sauƙa har cikin zuciyarta ga idanun da ya tsare ta da su lokaci ɗaya abin ya zo mata bazata. Tattaro jarumtarta tayi ta hade fuska ta watsa masa harara tamkar Idanunta za su faɗi ta shiga furta "Da ma abin kirki ai bai karɓi kare ba... Idan da ban nemi na taimake ka ba ba za ka min ihu a kai ba.." Wallet ɗin ta miƙa masa dukda wata zuciyar na cewa ta jefar in ya so ya je ya ɗauka amma bata yi hakan ba sai da ta miƙa mishi. "Idan ba za ka karɓa ba wallahi cilli zan yi da shi ko ma me a ciki sai dai ya salwanta" a ranta tana ƙirge don tana kirga uku bai sa hannu ya karɓa ba sai ta yi cilli da shi wallahi dab ta gama uku tana kokarin wullar da shi ya sa hannu sai ta kalleshi suka haɗa idanu ta sakar masa kan ta juya ta bar wurin a fusace laifinta ne da har ta taimake shi ma zai tsaya yana mata tsawa a kai ta yi tsaki ya fi cikin kwando kan su isa gida. Kanshi ya ɗan dafe yana jan tsiririn tsaki kan ya wullawa Ammar key ɗin yana nufar seat na mai zaman banza don ba zai iya tukin ba kuma. "Shehi me ke faruwa ne?" Tambayar ya zo mishi ne a daidai sadda yake tambayar kansa me nashi ma na jin haushi don ya ganta cikin yanayin da halinta ne kuma dabi'arta? Menene bai san tana yin ba shaye shaye ne ko dabanci? Ko ko ganinta cikin shiga da ta saɓawa shari'a da ma tsarin musulunci? Me ya sa zai ji haushin da ya kamata a ce uban da ya haifeta shi ya kamata ya ji mata? Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤 ƘARFE ƊAYA BA YA AMO ✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN (GUREENJOH) @Gureenjo on Arewapen @Gureenjih6763 on Wattpad ADABI WRITERS ASSOCIATION #THE TRIO OF TALES (THREE MINDS, THREE STORIES, ONE JOURNEY) *SHAFI NA TALATIN* Ammar ya yi ta mishi magana amma ya ƙi amsawa don Sam ba ya son maganar ta ma, wani fanni na zuciyarshi na tambayar Meyasa take shiga rayuwarsa haka? Meyasa duk inda zai juya sai ya ganta? Zai iya rantsuwa duka rayuwarsa bayan danginsa babu wata mace da ta taɓa crossing rayuwarsa kaman yadda yarinyar take yi daga haɗuwa sau ɗaya wani kaddara ne yake cigaba da haɗa su haka? Ya tsinci kanshi da adu'ar ko alkhairi ne ko sharri ne duk baya so kawai baya son sake haɗuwa da ita ne a rayuwarsa. Suna isa gida ya sauƙa ya nufi sashensa ba tare da ya cewa Ammar komai ba haka ya gyara parking ya sauƙa shima yayi nasa ɓangaren cikin tunani shima da mamaki. ****** Tun da motar ta tsaya al'ummar rumfar Dagaci duk suka zuba mata ido har motar ta buɗe malam Musa ya sauƙo, ai da sauri suka mimmike kowa na Allah Allah ya ƙaraso su ji lafiyar yaransu barin ma Baffan su Ma'u da kullum sai ya zo yayi zaman wurin ko Allah zai sa Malam Musa ya dawo a idonsa. Ganinshi a yanzu ya ƙara musu ɗokin son ganin 'ya'yan na su da jin labarin su, Malam Musa ya nufo su a gajiye ya zube ya miƙa gaisuwa ga dagacin kan yace "Ranka ya dade Al'amarin nan babu haske, adireshin jikin Takardar nan babu shi don unguwar da ke rubuce babu inda ban shiga ba kusurwa kusurwa amma babu haka kowa na tambaya bai taɓa sanin abu haka ba" Wani irin tension ne ya hau kawunansu aka rasa ma me fara magana sai Salati kuma ya kaure wurin. Dagaci ya ce "Ka tabbatar da batun ka Malam Musa?" "Kwarai da gaske na tabbatar Ranka ya daɗe" "Toh ina za su je? Ta ya yara za su ɓace haka kaman kudi?" Wani ya faɗa inda Allah ya taimakesa babu nasa don sai da ya riƙe mahaifin su Ma'u da ya nemi faɗuwa ya zaunar kan ya shiga maganar cikin mamaki. "Yaranmu babu abin da zai same su in Shaa Allahu, zan shirya yanzu na tafi cikin gari na kai report na abin da ya faru na san za su tsaurara bincike kuma zan yi takarda in aikawa mai martaba ku kwantar da hankalinku" Ya faɗi hakan ne amma ya san babu mai iya kwantar da hankali cikinsu kuma shima ya rasa natsuwa don tsoro ne ya fara shigarsa akan yaran da aka fita da sunan taimakon. Mota aka kawo Dagaci ya shiga suka tafi yayinda mahaifin Ma'u ya nufi gida yana ganin hazo hazo, babu mai gane halin da ya shiga sai uban dake tsananin kaunar yaransa da musu mafarkin rayuwa mai kyau da inganci bai san me zai faɗawa innarsu ba idan ya shiga gidan haka ya ƙarasa jiki a sabule tana amsa sallama kuwa ta jefo mishi tambayar da yake tsoron "Ya dai Malam shi wanda aka turan ya dawo? An samu labarin Yaran nan???"..... ***** "ke Zubaidah wai menene matsalar ki ne? Tun yaushe yanzu rabon da na hura wuta a gidan nan ina ta binki kudin chefene kin min banza ga Malam chan yana fama da ciwon kai yana neman magani ki ba da kudin a amso kin yi shiru" Idanu Zubaidah ta ɗaga ta zubawa Mamartata dake wannan zance sai ta ji wani irin ɗaci da raɗaɗi na mamaye mata harshe da jiki, zuciyarta na wani irin karyewa dukda taurin ran da take jarumtar arowa kwana da kwanaki ta yafawa kanta. "Mama ni ce alhakin ciyar da gidan nan ke wuyana? Ko kuma ni ce nake da alhakin samawa Mijinki magani idan bai da lafiya? Ba ni da kudi bani da hanyar samu" Ta faɗa tana kallon Mamar da ta sake baki "Me? Me kike cewa? Ke kin ma isa? Toh na rantse da Allah idan ba za ki nemo mana kudi a gidan nan ba sai dai ki bar sa ba za ki zauna ba, uban wa ke hure miki kunne? Nace uban wa ke neman sauƙar da ke turbar da na ɗora ki? Idan baki nemi kudi ba uban wa zai nemo mana?" "Da turbar kwarai kika ɗora ni sai ki samu zarafin ihu da masifa idan na sauƙa amma me? Don na ce na bar yawon banza saboda ciyar da ku shine kike tada jijiyoyi? Ba zan je ko ina ba idan za mu mutu duka da yunwa sai dai mu mutu" Mama ta riƙe haɓa "Eh lallai ne! Lallai ne toh Daaɗin abin ba ke kaɗai na haifa ba Zubaidah. Ke Khadija! Khadija??" Khadija da ke daga ɗakin tana kukan bakin ciki ta fito "Ki wuce ki je ki fara naki neman kudin tunda yayarki ta yi ritaya" "Mama a ina zan nemo?" Ta zaro mata ido "Ke ba mace ba ce? Ko ma a ina ne ki fita ki nemo babu ruwana ko me zaki yi ki samu ki yi kawai kudi nake so" Kuka Khadija ta fashe da shi Mamar ta rarumi icce za ta daketa in bata fita ba sai karab Zubaidah ta riƙe ta. "Ki koma ciki..." Tana kai nan ta kalli Maman tana jin tsana, baƙin ciki da wani irin kiyayya na uwar na mamayeta. Ta ya za ta fara amincewa Khalil cewa tana son shi? Ta ya za ta fara Shiga zuri'ar wasu da irin wannan uwar? "Zan kawo!" Tana Faɗin haka ta juya ta fice tana jin Mamar na cewa "Gwara miki don wallahi muddin baki kawo ba wannan da baki so a taɓa sai ta fita ta nemo uban da ya haifeku bai tsaya ya yi wahalar ku ba ni da nayi dole in fanshe!" ***** Ko da Shehi ya shirya fita taron da yammacin da Imamu da kuma malam Bala ya fita, taro ne na seminar don haka ya dauki lokaci Sossai don anan suka yi magrib ko da suka idar aka cigaba har tara na dare aka tashi. Tun ana adu'ar tashi Aka kawo mishi shayi kaman yadda aka kawowa kusan duka manyan wurin, saboda yadda yake jin gajiya ya sa ya ɗauka ya shiga kurba a hankali Amma cikin yan mintuna, idanunsa suka fara nauyi, kunnuwansa suka fara daukar amo kamar daga nesa kila gajiyar ce ta haddasa masa hakan ya raya a ransa yana Miƙewa Imamu ya taso ya tattare komai nasa suka fice malam Bala ne ya bude masa kofa ya shiga ya zauna yana miƙe bayansa jikin kujerar, glasses na idonsa ya cire ya ajiye yana shafa fuskarsa a hankali har suka fice daga wurin. Akwai nisa Sossai kuma hanya ce mai shiru musamman da dare ya fara sun sha kwanar wata titi da gidajen wurin suka zama sabbi kuma uncompleted suka ga wasu sun tare hanyar kaman faɗa suke yi don hayaniya ya ɗan cike wurin ga motoci har biyu Parke a kan titin. "Ko me ke faruwa?" Imam ya tambaya yana kallonsu "Kaman rikici ne suke yi gashi na riga na shigo da sai mu sauya hanya kawai" Malam Bala ya faɗa yana danna horn. Shehi ya buɗe idanu yana kallon wurin ya sake lumshewa yana jin suna mishi nauyi, dukda Ac da ke cikin motar zafi ne yake ji Sossai ya cire alkyabbar jikinshi ya ajiye kan ya buɗe kofar "Shehi da baka fita ba, bari na je!" Imam ya yi kokarin hanasa amma sai ya ce "No ka zauna! Zan musu magana ne..." Yana kai nan ya fice daga motar ya nufesu. Yana isa wurin kaman jira suka mishi kawanya dama an faɗa musu motar shi duka bullet proof ce, bibbiyu ya fara ganinsu yana jin kafafunsa suna masa nauyi, daga nesa yake jin Imam na kwalla kiran sunansa sai ya ga wasu daga cikin mutanen sun nufi wurin su da gudu, Malam Bala kokarin fitowa yake suka rufu musu da duka daga shi har Imamu. "Maganin ya riga ya gama taking effect mu gama da shi kawai mu yi gaba" Ɗaya daga ciki ya faɗa cikin kakkaurar murya. "Akwai police station kusa dole ce ta sa muka zo nan don sun yi nan ɗin amma muna harbi za su jiyo mu" Wuƙa babban ya zaro Shehi da ba ya ma ganinsu da kyau yana jiyo maganasu daga sama sama yana jinshi yana shawagi Ya yi yunkurin magana, amma kalmomin suka rikice a bakinsa, babu zato wani irin zafi da bai tantance ba ya ziyarci gefen cikinsa da sauri ya dafe wurin yana fusgo sunan Allah duk da ya zo bakinshi yana ambata. Hannunshi ɗaya na kan gefen cikinshi da yake jin zafin na ƙara tsananta sai jin wani hannu yayi ya shiga cikin hannunshi na hagu da ke lilo, ko kan ya motsa ya ji an fusgo shi taka kafafunsa ya shiga yi ba tare da ya san inda yake saka su ba sun jima kwarai don ya jiyo ƙarar harbi ya ji haki da magana da muryar da yake jin kaman ya san muryar kokarin faɗuwa yake yana ji muryar na cewa "Ka daure kar ka tsaya anan mu ƙara gaba" Amma innaaa ba ya cikin hankalinsa tunaninsa ya riga ya gushe yana ji ta rikesa suka ƙarasa inda ba zai ce ba ta ajiye shi zaune ta tsuguna daidai fuskarshi yana jin sunan Sheikhhh na fita daga muryarta a hankali kuma sai ya shiga buɗe idanu dukda rufuwa da suke da kansu fuskarta ya gani wannan fuskar da ya gama adu'ar kar Allah ya sake haɗa shi da ita ko a mafarki ko a zahiri, wannan fuskar da yake jin duk duniya ya washi gani fiye da komai. "SUHAN!" Lips ɗin shi suka furta ba tare da kwakwalwarsa ta sarrafa kalaman ba, a hankali kuma duhu ya mamaye ganinshi gaba daya. BAYAN AWANNI! A hankali ya ɗan motsa wani azaba da raɗaɗi da bai taɓa jin irinsa ba na ziyartarsa amma yanayin da ya ke ciki ya sa dole ya buɗe idanunsa, hasken rana ne irin na safiyar nan dake fita tarrr ya shige mishi idanu da ya sa yayi saurin rufe wa saboda zafi da ya ziyarcesa kan ya sake tattare ɗan ƙarfin da ya rage masa ya buɗe idanunsan da suka sauya kwarai. A kan gefen cikinsa da yake jin azabar ta fi yawa ya sauƙe idanunsa yana tunano abin da ya faru a jiyan, tabbas wani abu aka bashi a cikin shayin da ya sha amma ba zai ce ko abin bugarwa ba ce ko guba amma ya san ya fice a hayyacinshi, kan Wuƙa ne kuma a jikinshi jini ya lalata duka ɓangaren farar jallabiyarsa ta sauya zuwa ja. Ya runtse idanun a hankali ya sake bude wa kan ya juya kanshi zuwa gefen kafadarsa da yake jin nauyi idanunsa suka sauka kan gashinta da ya wargaje ya rufe mata fuska gabadaya, hannunta na cikin nasa ɗaya kuma kanta na kwance a kan kafaɗarsa dayan hannunta na riƙe da cikinta. Sai a lokacin ya tuna a jiyan ya ganta kamar almara, ya tuna yadda take rikesa take kuma jansa don tseratar da rayuwarsa, ya tuna yadda take kara masa karfin gwiwar yayi gudu idan suka riskesu ita kaɗai ba za ta iya ba! Hannu ya sa a kanshi ya cire Ghutra dinshi da har lokacin yana kanshi ya saka mata yana rufe mata gashin, motsin da yayi ya farkar da ita sai idanunsa suka sauka kan jinin da duk ya bata jikinta, idanunsa ya tsayar a kai kan ya kawar ya mayar kan wuƙar jikinshi ya na kokarin taɓawa tayi carab ta kama hannunsa. "Kana motsa wannan wuƙar ko ka cireta babu abin da zai hanaka mutuwa! A jiyan ma da sun zare da yanzu wani maganar ake ba wannan ba!" Ta faɗa chan ƙasa yanayinta babu ƙarfi sammm Idanunta suna ta lumshewa, hayaniya suka soma ji kaman mutane sai kuma suka ji ana ta kwalla kiran sunanshi don wuri ne uncompleted buildings na dayawa cikin ɗaya daga ciki suke, ta miƙe da kyar ya sake kallon jikinta amma bakinshi ya kasa furta komai ta riƙe shi ya miƙe suka fito daga nesa suke hangen motoci da hukumomi ana ta cigiyarsa! Sai da suka fito sarari har wasu sun gansu kan ta sake shi ko kan yayi magana ta juya ta bar wurin yayi ƙasa a daidai nan aka janyo hankalin su Ammar "Ga shi chan! Ga Sheikh chann!!" Kan ka ce kwabo an rufu mishi aka ɗauke shi Ammar na ta kiran sunanshi amma bai buɗe idanu ba aka sanyashi a ambulance sai asibiti. Tashin hankali karamin suna ne da za'a ƙira halin da ahalin Familyn suka shiga don a daren da abin ya faru yayi munin da ko ina maganan ya baza Malam Bala yana coma, Imam na kwance asibiti sai kuma ga labarin an kama Abbiey an kuma rufe companynsa don ana zarginsa da safarar miyagun kwayoyi da sunan Company! Ammar ya rasa inda zai sa kanshi shi da Abba dole Abba ya tsaya wurin hukuma shi kuma Ammar ya bi ayarin masu neman Shehi don Imam ya tabbatar musu mutanen basu kashe shi ba ya gudu sun neme shi sun rasa a kan idanunsa komai ya faru kuma Shehi ba zai iya nisa ba saboda raunin da suka ji masa! Surgery kai tsaye aka shiga da shi don wukar a ƙasan cikinsa ne, Ammiey kam ta fice hayyacinta Maamah da su Daddah sun yi kuka har sun rasa hawaye a iya jiya rayuwarsu na neman juyewa daga sama zuwa ƙasa! Neman faɗuwa Ammar ke yi a sadda yake jin wasu kalamai da suka girmi tunaninsa cikin TikTok da mutumin gefensa ke kallo zaune cikin reception na asibitin da Shehi yake, da sauri ya kalli su Maamah tabbas su ma sun ji don Tuni sun miƙe tsaye! Girgiza kai tayi ta isa ga mutumin ta fusge wayan tana kallo tana girgiza kai Idanunta na tsiyayar da kwalla! "Tabbas 'yata ta dawo gida amma cikin wani mummunan yanayi, daga taimakon wannan babban Malamin Sheikh Irshad Al-Noor Kasancewar ba ya hayyacinsa ya yi Mata FYADE! Hotunan dake zagayawa ba ƙarya ba ne!" Bugawa ne ya saura zuciyoyinsu basu yi ba, scrolling hannun Maamah yayi sai ga hoton Irshad ɗin riƙe a jikin Diva jikinta akwai jini kaman yadda nashi yake da jini, basu san daga ina ya fita ko wa ya ɗauka ba amma tabbas a safiyar ne kuma media ta ɗauki dumi dama kiris ake jira nan Scandal ya fara Shehi ya yi wa wata 'yar Daba fyade daga taimako! Abu ne da hankali ba zai taɓa ɗauka ba amma sanin Imam ya ce musu kaman tun farko Shehi ba ya cikin hankalinsa don tabbas akwai abin da ya shiga kansa a lokacin don har hana shi sauƙa yayi amma yadda yake abu kaman cikin maye ya tsinka musu gaba! Tabbas idan wani abun maye ne aka shayar da shi zai iya aikata hakan ba tare da ko ya sani ba Innalillahi wainna ilaihi raji'un...!!!!! *Toh jama'a anan muka kawo ƙarshen free pages za mu tafi hutun kwanaki, da yardar Allah bayan kwana goma za mu dawo muku da cigaban wannan labari! Idan har Shehi ya aikata fyade wa Diva me kuke tunanin zai faru? Zai ma rayu kuwa? Me ya haɗa Abba da Safarar kwayoyi? Zubaidah kuna ganin mahaifiyarta za ta cigaba da cin galabar tarwatsa rayuwarta? Ma'u na hannun NAPTIP Jiddah na hannun J shin waye ne ma J ɗin? Iyayensu za su samesu kuwa ko sun tafi kenan? Kuna tunanin Dagaci da ya kama gomnati ya kama dahir kuwa a taimakon al'umma? Menene Jagaban ke ɓoyewa? Waye ke sace kudin company kuma yake ɗora wa Ammar? Diva za ta shiryu kuwa? Waye yake neman ran Shehi?? Ko anan muka tsaya na san kun fahimci wannan kalma ta ƙarfe ɗaya ba ya amo dole sai ya haɗu da wani ƙarfen ɗan uwansa! Hmmm akwai fah sauran tafiya a gaba ku dai ku gyara zama kawai ku mu cigaba da tafiya* Trio of tales za su zo muku cikin farashi mai sauƙi.... DAƊIN ZAMA BY SEEMAHWRITES JODA BY SADI-SAKHNA ƘARFE ƊAYA BA YA AMO BY GUREENJOH *A whatsapp One 1k Two 1800 Three 2400* *Telegram One 700 Two 1200 Three 1500* Account details 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Sai a tura shaidar biya ta 09039206763 🖤Gureenjoh🖤