[11/13/2017, 6:26 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing.......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* _Sadaukarwa_ *_miss Xoxo na_* *_Zarah bukar_* *_Ayusha muh'd_* *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._* _Bismillahirrahmanirrahim_ _ya ALLAH kabani ikon fad'ar abinda zai amfani al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'an abinda zai cutar da al'ummarka, ameen_ _ina farin cikin sake had'uwa daku a sabon littafina mai suna *KARAYAR ARZEEK'I*, ina fata zaku bani had'in kai, ngd da k'aunarku gareni, nima ina k'aunarku lodi Lodi._😘😄 *_duk Wanda ya canja wani Abu a buk d'innan ALLAH ya isa ban yafeba.🙄_* *_page→1_* ..........6urum aka turo k'ofar tamkar za'a cireta. Zaune yake a bakin gado yana harhad'a wasu takardu, hankad'o k'ofar basashi ko gezauba barema ya d'ago Dan yasan bai wuce matarsace lubna ba, da wanan d'anyen aikin. Ta huro hanci had'eda rik'e k'ugunta da hannu biyu, wata uwar harara ta watsa masa, wadda baimasan tanayiba. *_Umar fharuq!!._* takira sunansa cikeda masifa. Bai amsataba baikuma d'agoba, harkar gabansa kawai yakeyi. Lubna dake tsaye tana karkad'a jiki takuma k'ufla, Dan haka tacigaba da magana cikeda tsiwa....... Gsky nikam nagaji, kasan yadda zakayi dani wlhy, shekaranjiya kacire yara daga makaranta bance maka komaiba, yaukuma shine zakazo da mutane suna zazzagaye gida?, shin mikake nufu?, ko shima gidan saidashi zakayine?, to wlhy idanma tunanin haka kakeyi ka canja, Dan bazan rayu banida tsuntsu baniga tarkoba. Aidama nasan tunda aka aura maka waccan 'Yar k'auyen, saimun shiga bala'i, gashinan tun ba'aje ko inaba komai yak'are, mayya mai farar k'afa tashigo rayuwarmu, saura kuma kurwarmu ake bibiya alashe yanzun... d'an tsaki yaja idonsa akan takardun dayake zubawa acikin wata 'Yar jaka, saida yagama tsaf sannan yad'ago fararen idanunsa yana kallonta, yanunata da d'an yatsa lubna kishiga hankalinki, kinsan banason shirme ko?, gidakam zan saidashi idankuma nakine saiki hana, inama yimiki albishir daki fara shiri Dan nanda kwana biyu zamu barmusu gidansu............. Jar ubannan kai, wlhy Umar baka isaba, ainima inada hak'k'i da gidan, tunda 'ya'yana sunada gado. Kansa ya girgiza yana rataya jakar akafad'a, ya ce, "mahaukaciya kawai, saiki bari saina mutu kafin yazama gadon nasu mtsoww. Umar nikake kira mahaukaciya?!. Bai tanka mataba yatako cikin nutsuwa yanufi hanyar fita...... Da Sauri tasha gabansa tana huci, wlhy babu Inda zakaje saika sanar dani wacece mahaukaciyar?. Kallon sama da k'asa yay mata, batareda yayi maganaba yaja tsaki tareda ra6awa ta gefenta zai wuce. Da Sauri takuma shan gabansa. Afusace ya ce, " wlhy koki tashimin a hanya, kokuma na kashe fuskaeki da mari...... Toka marenin mana, nagadai Nima ALLAH yabani hannun dazan rama. Ya ce, "ko?. "eh, kozaka gwadane?." Wani k'asaitaccen murmushi yasaki, yara6a tad'ayan gefenta yafice yana cije le6ensa. Binsa tayi da kallo tana girgiza jikinta alamar tsumuwar bala'i, saikuma ta rushe da kuka. Na ce, "tofa, anayinta." Shikam koda yafito d'ayan 6angaren ya Shiga, babu kowa a falon, sai sassanyan k'amshi dana AC dake tashi, TV ma a kashe take, hanyar wani d'aki yanufa. Tana zaune abakin gadonta dayasha gyara, ananma k'amshine mai dad'i dasaka zuciya nutsuwa ke tashi, ta rabga tagumi, daga ganinta Kasan tana duniyar tunani. Gyaran murya yayi had'eda sallama. Firgigit tad'ago tana kallonsa, sai kuma tazamo daga gadon Baki narawa ta ce, "yaya ina yini. Atak'aice ya amsa da lfy, yacigaba da fad'in kifara shirya kayanki nanda kwana biyu zamubar gidannan...... Baijira cewartaba yafito abinsa. Wasu siraran hawaye suka zubo daga kumatunta, Afili ta ce, "na Shiga uku ni Asma'u, shima gidan ka saida ya Fharuq?!, nikam naga ta kaina, karfa maganar aunty Lubna yazama gsky, ta rushe da kuka maiban tausayi........ _nakalli zarah, Zarah takalli Xoxo, mukayi tsuru tsuru tamkar munafukai, Xoxo ta ce, " tawan ta'ina zamu fara?, na ce, "umm tawan tambayi Zarah kotanada idea nikam banida fus._ _Zarah ta gyara tsayuwarta, hannunta rik'eda Biro da 'Yar takardar d'aukar rahoto, ta ce, " bily nimafa na toshe Dan naga gidan kowa a rikice yake bansan wazamu tunkara yabamu labariba?, Xoxo kozakije wajen lubna?._ _Kam bala'i babu inda zani daga rakkiya?, agabankufa mijinta yakirata mahaukaciya, sannan kucemin naje tasaukemin na jaki._ _Dariya muka gumtse nida Zarah danjin zancen Xoxo, Zarah ta ce, "bily fa?._ _Na ce, " um um kodai ke ki gwada, nisainayima wannan magana?._ _Shiru Zarah tayi, Dan itama batason komawa wajen lubna........_ _Zuwacan Xoxo taja numfashi idonta akan Zarah, ta ce, "Zarah nibamfa gane mi tawan take nufiba?, catayifa murakota d'aukar rahoto, amma sai wani shirin lik'a mana aiki takeyi?._ _Harar Xoxo nayi, amma tawan idan kuntayani na buga labarinnan naga ba fad'uwa kukayiba ko?._ _Hakane, amma gsky nikam bazan iya da wannan iya bala'in matar tasaba, kumafa ni sonsama nakeyi, Dan guy d'in yahad'ufa._ _Dariya muka shek'e da ita nida Zarah, Zarah ta ce, " haba 'Yar uwa kice kishi bazai barkiba kawai, ammafa Nima bily bawai zan tayaki bane, namiki rakkiyane kawai, saidai mukoma gidan zan tayaki da shawarar yanda zaki d'auki wannan rahoto._ _To shikenen ngd Zarah muje, kekuma tawan dazanmiki hanya ki aureshi ammafa yanzu nafasa._ _Kai tawan nidakefa ba'a jin kammu?._ _Aikodai yau za'aji...........🤥😏._ *_tab masu karatu akwai aiki Dan bansan yanda zaku sami cikakken labarinba, tunda masu d'aukar Rahoton duk matsoratane._* *_Daga miss xoxon Zarah Bukar, harni bilyn Abdul duk fararen kurayene򓰽򗀮_* _amma ni bilyn Abdul zan kawo muku cikakken labarin, tunda su o e anji tsoro😏._ Kikasance dani danjin yadda zata kaya😻😘. Bilyn AbDul ce👌🏼 *_luv you all_* *_(((S))).....2017_* [11/14/2017, 5:05 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing.......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* _Sadaukarwa_ *_miss Xoxo na_* *_Zarah bukar_* *_Ayusha muh'd_* *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._* *_page→2_* ...........Tundaga k'ofar gida nafaracin karo da wasu manyan motoci akorikura har uku, duk an loda musu kaya, ra6awa nayi tagefensu nashiga cikin gidan, lallai tashi ya tabbata nafad'a azuciyata ina bin ko'ina nagidan da kallo. Asma'u naga tafito da akwatuna biyu ahannu tanaja, Umar dake jingine da motarsa yana latsa waya yad'ago yana kallonta, d'an ta6e bakinsa yayi yana kauda kai daga kallonta, aransa ya ce, "yarinya tamkar mara laka ajiki?, komai nata salaf-salaf...... Maganartace ta katse masa tunaninsa ta ce, " yaya gasu. Baiyi maganaba ya ajiye wayarsa saman motar, but yabud'e mata tasaka akwatunan, yarufe sannan yad'auki wayarsa yabud'e motar yashiga. Asma'u tana tsaye sai faman bin gidan da kallo takeyi, kwata-kwata zuciyarta babu dad'i takeji, tasan yaya umar ma yana dakewane kawai kasancewarsa mutum jarumi mai dakiya da kawaici, duk 6acinran da Umar zai shiga mawuyacine kagansa shinfid'e afuskarsa, mutumne daya iya 6oye sirrin zuciya........ Ganin bata shigoba yay mata horn. Da sauri tabud'e motar amma bata shigaba, tad'an sunkuyo ta ce, "ya Fharuk Anty Lubna fa?. K'aramin tsaki yaja, yace batana canba tund'azu, kinafa 6atamin lokaci. Jiki a sanyaye tashiga motar yaja yafice daga gidan zuciyarsa namasa zafi, amma sai ambatar innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un yakeyi. Tuk'i yakeyi ahankali tamkar bayaso, dagashi har ita babu mai iya magana, lokaci-lokaci ita takan share hawaye, yana kallonta ta gefen ido. Ak'ofar wani matsakaicin gida yay farking, koba'a fad'aba nanne gidan dazasu dawo, domin annan muka tadda motocin akoru kurarnan sunata aikin sauke kaya dashigar dasu cikin gidan. Kad'an ya kalleta, kishiga ciki su Hasiya da Rafi'a da fatee duk sunanan sune zasu tayaki gyara kayanki, ni bara naje wani waje. To ALLAH yatsare, saika dawo. Ameen, yafad'a akan la66ansa. Bud'e motar tayi tafita, harta d'an fara tafiya saikuma tajuyo, ya Fharuk kayanfa?. Baitanka ba saida yatada motar, kije idan nadawo zan shigo dasu yanzu Sauri nakeyi, magana yakeyi amma ko Inda take baya kallo. Itama kanta ta jinjina tajuya tashiga cikin gidan, abakin matsakaicin bak'in gate d'in sukai karo da matasan samarin dasuka gama Shiga da kayan nata. Sannu tayi musu sannan tashige ciki. Bin ko'ina takeyi da kallo, gidan k'aramine irin ginin talaka mai k'aramin k'arfi, ko'ina shage yake da siminti lumus, haka tak'arasa cikin gidan tana raba hanya. Abakin fanfo taga Afrah da Amrah yaran Anty Lubna sunata wasa da ruwa, bata musu maganaba gudun kar cibi yazama k'ari Dan Anty lubna batason abinda zai ta6a 'ya'yanta ko kad'an. K'ofar falon tatura tashiga, Rafi'a da fatee Hasiya sukazo da gudu suka rungumeta, itama rungumesu tayi sunamai murnar ganin juna. Hasiya ta ce, "kai Anty Asma'u kinganki kuwa, wlhy kinyi bala'in k'yau, gidan ya Fharuk ya kar6eki. Hararar hasiya tayi cikin sigar wasa, Hasiya kina nandai baki canja haliba wlhy. Dariya sukayi suduka, Asma'u tabi falon da kallo, babbane sosai, sai kowace kusurwa da akwai k'ofa. Ganin kallon da takema falon yasa Rafi'a fad'in wlhy Anty tsarin gidan yayi sosai, kinga nan family falone, wancan k'ofar shine naki, akwai falonki da bedroom sai bathroom, wancan kuma na Anty lubna ne, itama iri d'ayane da naki, wancan na tsakkiyar kuma na ya Umar ne. Murmushi Asma'u tayi, tace ALLAH ya tabbatar da alkairi to. Ameen suka fad'a suduka. Kama hannunta fatee tayi, tana fad'in zomuje kigani harmun fara had'a miki bedroom d'inki. d'akin daya kasance NATA suka nufa, tuk'uru suka Dage suna aiki, kafin k'arfe biyu sungama komai har babban falon sun saka kujerun dasuka kasance ada na 6angaren bak'i agidan dasu dasuka taso, d'akin Ya Umar suka shiga, shima tsaf suka gyara masashi ko'ina yad'auki haske. Duk bidirinnan dasukeyi basuji motsin Lubna ba sai yanzu, duk sunzube a family falo suna maida numfashin Hajiya lubna tashigo itada Suhaima k'anwarta. Suhaima tabi falon da kallo tana wani yatsine fuska, Anty lubna wai kina nufin anan ya Umar zai ajiyeki?, aiko 'yan aikin gidanmu sunfi k'arfin zama acikin wannan kangon?. Baki lubna ta ta6e kibarsa kawai Suhaima Nima INA rakashine naga iya gudun ruwansa, amma wlhy bazan zauna awanan k'onannan gidanba saikace wata fak'ira, shima yasan bamu gaji tsiyaba wlhy. A to yakamadai kid'auki mataki, wannan gidan saidai su o e wad'anda dama atsiya aka taso, shigarta wannan gidan ai ita k'arin cigabane. Rafi'a tamik'e danufin maida murtani dantasan sarai da Asma'u suke. Da Sauri Asma'u tarik'e hannunta tana girgiza mata kai alamar a'a kartacr komai. Lubna ta gallama Rafi'a harara, to tabbatacciya da dakika tashi dukanmu zakiyi?. Shiru Rafi'a Tamata Dan Asma'u tahanata magana. Suhaima ta tuntsure da dariya Anty lubna kinga muje nifa kinganni bakowace bola bace abin kallo agareni. Fatee ma tabud'e baki Zata maida murtani Asma'u ta harareta. Daga k'arshema tashi tayi takad'a Kansu suka shige cikin falonta. Daga Lubna har suhaima Bahaka sukasoba, sunso su Hasiya su kulasu ayi badad'i, dama Neman dalili sukeyi da dangin Umar d'in. Suna Shiga Asma'u tarufesu da fad'a akan itafa batason tashin hankali, danhaka komi sukaimata karsuce zasu sake kulasu. Shiru sukai mata kowa tana turo Baki, dansu hak'urin Asma'u haushi yake basu. Sai magriba ya Umar yadawo gidan, suna zaune bayan sun idar da sallah yashigo. Suduka rissinawa sukai suna gaisheshi, ya amsa babu yabo babu fallasa. Ya ce, ''kutashi namaidaku gida. To, suna fad'a kowa tana mik'ewa daneman mayafinta, kowa yashirya sukaima Asma'u sallama, hawaye tafara da rok'onsu Dan ALLAH su ringa zuwa mata akai-akai. Hak'uri sukabata sukace zasuringa zuwa, dama makarantace take hanasu. Ya Umar duk yana jinsu, ganin sunk'i tahowa yadoka musu tsawa, kai banason rainifa........ Bama su bari yak'arasaba suka fita dad'an gudunsu. Asma'u tacusa kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka saboda kewar 'yan uwan nata, koba komai yau taji dad'in ganinsu, sunyi hira taji farinciki aranta. Bata kuma saka ya Umar a idontaba har wayewar gari, dama bazuwa kwana d'akinta yakeyiba, itakuma bata zuwa d'akinsa Dan duk hak'urinta tanada matuk'ar zuciya, dukda tasan basonta yakeyiba hasalima taimakonta yayi, amma ai baidace yarik'a mata hakaba kodan darajar zumincin dake tsakaninsu...... Share hawayenta tayi tamik'e zuwa kichin domin had'a breakfast. Ruwan shayi kawai tadafa da Lipton da kayan k'amshi Dan bataga wani abuba a stor d'in gidan. A tsakkiyar falon tazo ta ajiye kofuna da filas d'in shayin Dan ya Umar bayacin abinci akan dinning. Tana cikin d'an gyara kayan yafito daga d'akinsa sanye cikin farar jallabiya. Rissinawa tayi ta gaisheshi, saud'aya ya amsa yafice. Mintuna kad'an yadawo d'aukeda bak'ar Leda ahannnusa, Asma'u na zaune a babban falon tana jiran dawowarsa danta tambayesa yanda za'ayi. Ledar yamik'a mata, hannu biyu tasa takar6a tana masa sannu. Kujera yasamu daga d'an nesa da ita yazauna, itakuma tabud'e ledar, biredine aciki sai madara irin 'Yar sacet d'innan guda uku, sai sukari da bota ta Leda............. *_luv you oll_* *_(((S))).......2017_* [11/20/2017, 6:20 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing.......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* _Sadaukarwa_ *_miss Xoxo na_* *_Zarah bukar_* *_Ayusha muh'd_* *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._* *_page→3_* ....... Ganin yanda kayan shayin yake yasata rarrabama kowa akofi ta ajiye, gamawarta babu dad'ewa saiga su Amrah sun fito da gudu. Jikin babasu suka fad'a suna fad'in daddy?. Ya ce, "na'am twin's d'ina kuntashi lfy?. Lfy lau, daddy yaushe zamu koma gidanmu?, nan gidan babu dad'i sai zafi babu AC. Murmushi kawai yamusu, yakama hannunsu suka sakko k'asa inda Asma'u tahad'ama kowa shayi. Dai-dai nan Lubna tafito, taci kwalliyarta cikin pink d'in shadda sai zabga k'amshi takeyi. Afrah data kur6i shayi tayi saurin zuboshi ak'asa tareda cillama Asma'u bread d'in data bata bayan tashafeshi da bota, nidai bazan sha tea d'innanba momy babu dad'ifa, ni dankali da kwai nakeso. Galala Asma'u tayi tana kallonta, ganin haka itama Amrah tayi cilli da nata gefe. Ya Umar duk yana jinsu amma yay kunnen uwar shegu dasu sai danna shayinsa da bread yakeyi hankali kwance. Lubna ta harareshi, tokaji sufa bazasu iya shan wannan tea d'inba maikamada ruwan wankin kai, koni wlhy bangoyi bayan sushaba tundasu ba dabbobi bane. d'ago idanunsa dasukayi d'anja yayi yana kallonta, baice komaiba yamaida kamsa yacigaba dayin break d'insa. Asma'u ma tea d'inta taja tahausha batareda tasake kallon inda Lubna da yaranta sukeba. Aiko ganin haka yasa Lubna fara zubar da ruwan masifa da tijara, sai zabgama Ya Umar gori takeyi. Wai aii babantane dama silar arzik'in nasa, wlhy tayi nadamar aurensa Dan aurensa bai amfaneta da komaiba sai fad'awa tarkon wahala, dan haka dolene yasaketa ita bazata zauna dashiba taringa shan ruwan wankin kai amatsayin shayi......... Haka taita zabga ruwan masifa babu Wanda ya kulata barema ya tanka mata, Asma'u tana gamawa ta tattara komai takoma d'akinta. Shima mik'ewa yayi yashige nasa d'akin. Itama ganin babu sarki sai ALLAH taja hannun Afrah da Amrah suka bar gidan. Bayan wasu 'yan mintina Umar Fharuk yafito tsaf sanye cikin k'ananun kaya sai zabga k'amshi yakeyi. Araina nace bawan ALLAHnnan ya iya d'aukar wanka wlhy. d'akin Lubna yashiga, amma saiyaga wayam, baice komaiba yafito yashiga na Asma'u. Tana falo kwance a doguwar kujera, chart takeyi abinta sai faman murmushi take zubawa. Sallama yay mata sannan yazauna kujerar dake fuskantarta. Itama tashi tayi zaune ta ce, "sannu. Bai amsaba amma idonsa na kanta, Ita saima duk kunya takamata, ganin haka yasashi d'auke kai daga gareta, ya ce, " zanje shagunana Dan inaso afara gyaransa muga kuma abinda ALLAH zaiyi, idan kud'in sunkai angama gyaran to ko haya saina bada, idan kuma basu kaiba saimuga kuma abinda yadace ayi. Jin yayi shiru tagane cewa yagama maganarsa, cikin sanyinta ta ce, "ALLAH ya tabbatar da alkairi aciki, Yakuma mayar da alkairi fiye da abinda aka rasa. Yaji dad'in addu'arta danhaka ya amsa da ameen yana mik'ewa. Saina dawo, yay maganar yana fita. Itama tace ALLAH yatsare takoma ta kwanta. %%%%%%%%%%%% Umar nafita daga nan gidansu yanufa, gidan babu laifi mai k'yaune Dan tuni Umar yagyarashi tsaf, komai na more rayuwa saida yazubama iyayensa shi, horn yayi maigadi yabud'e masa gate, saida suka gaisa sannan ya ida shiga ciki, yasamu guri yay fakin. Da sallama yashigo falon, Rafi'a ce kawai ta amsa cikeda farinciki, amma mama da Mufida da Harris sun amsane babu yabo babu fallasa. Waje yasamu yazauna ak'asa yana gaida mama. Dak'yar ta amsa masa, bai damuba yajuya yana amsa gaisuwar Rafi'a, harara ya gallama Harris da mufida Ku baku iya gaisuwa bane?, wai yaushe kuka rainanine?....... Kafin suyi magana mama ta cafe, a'a yabazasu rainakaba? Tunda kagaza yimusu maganin abinda yadamesu. Ajiyar zuciya yasauke, idanunsa harsun canja kala, ya ce, ''kiyi hak'uri mama abubuwane sai ahankali, kinsan dai halin Dana tsinci kaina aciki, inda Dane kobasu tambayaba zan basu, amma wlhy yanzu banida sh...... Kai dakatamin!!!, mama takatsesa cikeda tsawa, harni zaka bud'e baki kacema bakadashi, koma kunyar yin k'arya bakaji?, shekaranjiyafa kasiyar da gidanka miliyoyin kud'i amma har bakinka yafurta bakadashi, duk dai Wanda yagaza godema ALLAH to zai godema azabarsa. Wani yawun 6acinrai ya had'iye, muryarsa cikeda girmamawa agareta ya ce, "kiyi hak'uri mama, wlhy kud'in gidannan acikinsu aka cire aka sayi gidan damuka koma, sauranne kuma zanje nayi gyaran shaguna nana, bammayi zaton kud'in zasu kaini ko inaba. Hummm tonaji baban tsari tashi kabani guri, kama gyara duniya dasu ba shagunaba, itadai rayuwa duk Wanda yakedashi yagaza taimakon d'an uwansa aiyayi asara.... Da sauri Umar yad'ago yana kallon mahaifiyar tasu, idonsa yayi jajur, Rafi'a ma kuka takeyi, tana mamakin hali irinnan mahaifiyar tasu, kwatakwata mutumce dabata godiyar ALLAH, atunaninta ya Umar yafi k'arfin cin fuskarta kodan k'ok'arinsa nason k'yautata mata, duk cikinsu babu mai hak'urinsa dakuma kula da iyayensu, amma tunda iftila'in nan yasamesa 'yan gidan suka fara canja masa........ Maganar ya Umar ce takatse mata tunaninta, rissainawa yayi ya ce, " sai anjima, ALLAH ya huci zuciyarki, yakalli su Harris ya ce, "zantura muku insha ALLAH. baki suka washe suduka harda mama, ko kaifa d'an nan to ALLAH yayi albarka kaji, ameen yafad'a ala6ansa. Suma su mufida sai zabga godiya sukeyi, shidai ficewarsa yayi. Koda yashiga mota saiya fice daga gidna, tafiya yakeyi amma zuciyarsa namasa zafi, gefen titi yasamu yay fakin, yakifa kansa jikin sitiyari yana duk addu'ar datazo bakinsa, wlhy yana mamakin hali irinna mahaifiyarsu, alokacin da yakedashi tafi kowa sonsa da tattalinsa, kullum addu'a take masa dafatan alkairi dagamawa da duniya lfy, amma abin mamaki tunda komai yak'are masa saita fara canjawa, yanzu babu Wanda tatsana samadashi, batada magana saita ya Abubakar da Anty Sa'a da Harris da mufida, suma Kansu 'yan uwansa sun canja masa gaba d'aya, anty sa'a ce kawai da Rafi'a suke sonsa, yasa handky yana share hawayen dake kwarara a kumatunsa. Yakai tsawon lokaci awajen sannan yabirka motar yanufi kasuwa. Alhmdllh aiki yayi nisa Dan anata kwashe tokar gobarar data k'ona shagunan, ganin komai natafiya dai-dai saiya shiga mota yanufi majalissar abokansu. %%%%%%%%%%%% Zazzaune suke sunata kwasar hira da dariya, motar Umar tatsaya. Motsowwww ga k'aban nan cewar Hafiz. Waye k'aba?, Salman yatambaya idonsa akan hafiz?. Umar mana, kokai bakada ganewane, cewar Tasi'u. Al'kasim yata6e baki kaini wlhy fa banason yana ra6armu karya goga mana talauci. Ashe kagane d'an uwa, yanzufa d'angidan dayake mana tak'ama dashifa ya saidashi. Kai Dan ALLAH kabeer dagaske kakeyi?. Wlhy kuwa Hafiz da gsk, nima jafar take bani labari jiya, kunsan shi kunya bazata bari yafad'a manaba. Tofa, yanzu to ina Yakoma?. Wani kangon gida yasiya... Dariya suka shek'e da ita, Al'kasim ya ce, "su k'aba anji yaji........ Umar dake tsaye duk yana jinsu yagirgiza kansa tareda musu sallama............ Afurgice suke kallonsa, duksun tsargu kardai yaji firar tasu?, dansu basusan yama iso inda sukeba. Kowa yakama 'yan kame-kame. Hannu yamik'a musu suka gaggaisa fuskarsa d'aukeda murmushi, suna gama gaisawa ko zama baiyiba ya ce, " bara nawuce, Dama nabiyo gaishekune....... *_(((S)))....2017_* *_luv you all my fan's_*😻 [11/20/2017, 6:20 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing.......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* _Sadaukarwa_ *_miss Xoxo na_* *_Zarah bukar_* *_Ayusha muh'd_* *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._* *_page→4_* ..........ah mungode angon Asma'u da uwargida Lubna. Baice komaiba sai murmushin takaici dayayi yajuya yashiga motarsa, suduka binsa sukayi da kallo, kai jama'a Kodai yaji mimuke fad'a?. Kai baiwani jimuba, idanma yaji saime kune kukejin tsoronsa. Mtsowwww miye abin tsoro a can?, mutumin da duk talauci ya gwaguyeshi, ni gwarama dabai zaunaba...... Umar da takaici yacika yana shiga motarsa yabar wajen zuciyarsa namasa k'una, waishi kowa ke gudu tamkar wani mai mugun hali, babu komai yagodema ALLAH, komai na duniya fararrrene kuma k'ararrene, zaiyi hak'uri insha ALLAHU, hak'uri irinna bayin ALLAH, hakadai yayta tunani harya isa gidansa, tun ak'ofar gida yaga motar mahaifin Lubna, cikeda mamaki yake kallon motar, tokodai Lubnace tazo da ita?, yatambayi zuciyarsa. Ajiyar zuciya yasauke tareda fitowa daga motarsa yashiga cikin gida, ganin takalma reras ak'ofar falon yatabbatar masa da babu lafiya. K'uru yayi yashiga da sallama, abin mamaki mahaifin Lubna ne da Mahaifiyarta, sai yayunta biyu da suhaima k'anwarta, Asma'u na tsigunne agefe da'alama kuka takeyima. Dukda babu Wanda ya amsa gaisuwarsa haka yak'arasa cikin falon, yarisina yana gaida iyayen nata, fuska babu yabo babu fallasa suka amsa, yad'ora dafad'in Abba lfy kuwa?. Lfy lau sai alkairi, Ameer yayan Lubna yafad'a amasife. Yawu Umar ya had'iye na 6acin rai, amma baice komaiba. gyaran murya mahaifin Lubna yayi, ya ce, "Umar nasan zakayi mamakin ganina agidanka?, toba abin mamaki baneba, baby ce takai k'ara akan bazata iya zama awannan kangon gidan nakaba, shiyyasa nazo ni dakaina na shaida maka nima banyarda d'iyata ta zauna anan ba, alfarma d'aya zan maka shine nabaka d'aya daga cikin gidajena kakoma kaida baby amma banda waccan sai farar k'afar, yanuna Asma'u. Sai yanzu Umar yad'ago yana kallonsa, yayi wani d'an murmushi sannan yamaida kansa k'asa. Duk azatonsu yaji dad'in k'yautarne shiyyasa ya murmusa, amma sai furucinsa ya tabbatar musu da sa6anin haka. Ya ce, " ngd sosai Abba da wannan k'yauta, saidai inamai baka hak'uri dabazan kar6aba, wannan shine gidan daya kasance dai-adai k'arfina, idan Lubna tana sona tayi hak'uri muzauna anan, danni gsky babu inda zan koma..... To aiko wlhy Umar saidai kasakeni........ Maganar Lubna takatseshi. Shiru yayi baice komaiba, Safwan ya ce, "tokaji fa, saika za6a sakinta kokuwa bin abinda takeso?. Kuyi hak'uri ya Safwan bazan iya sakintaba, kuma bazan koma ko inaba. To aikuwa zakaga sammaci, Dan yarinyata bazata zauna awannan kangonba tanacin gabza. Mom Dan ALLAH kuyi hak'uri, kufa iyayenmune baikamata irin wad'an nan zantukan suna fitowa bakinkuba. Mtsoww to ubana gayamin yanda zanyi?. Shiru Umar yayi Dan yasan wacece Mahaifiyar Lubna, masifaffiyace dama tafad'a aji. Mik'ewa sukayi suduka har Lubna d'in, kawai saiyajin anci kwalarsa. Cikeda mamaki yake kallon Lubna daketa girgiza jiki, ta ce, " wlhy saika sakeni. Tsawa yadaka mata ke banason iskanci sakemin Riga. Bazan sakiba wlhy saika bani takardata, kuma saki uku nakeso. Zuciyar 'yan mazan tazo kusa, aiko ya sharara mata mari..... Baisauke hannunsaba Mahaifinta shima yamareshi. Umar kana haukane?, agabana zama mari yarinyata, wlhy saikayi nadamar hakan, baby sakesa idan bai bayar da arzik'iba, aizaibada datsiya akotu. Sakinsa Lubna tayi suka fice suduka. Binsu kawai da kallo Umar yayi. Asma'u kuwa dama tun d'azu kuka takeyi, suna fita tashige d'akinta da gudu tana kuka. Itama binta kawai yayi dakallo. Zubewa yayi ak'asa yana sauke numfashi da hawaye, shikenan Dan *_KARAYAR ARZEEK'I_* tasamesa sai kowa yatsanesa?, shin shiya d'orama kansa?, miyasa mutane basa ganewa?, ya ALLAH kabani ikon cinye jarabawarka, ALLAH ka k'aramin hak'uri da Wuyan d'auka, yadad'e awajen zaune abin tausayi, dak'yar ya rarrafa yabar falon Yakoma d'akinsa. %%%%%%%%%%%% Bayan kwana biyu da faruwar hakan, ya Umar dukya k'ara ramewa yafita hayyacinsa, abincima sai Asma'u tasaka masa kuka yakeci, baya fita ko ina, yama tsaida aikin shagunan nasa, kud'in da k'annansa suka buk'ata yabasu. Yauma haka yatashi yanajin jikinsa duk babu dad'i, yasan tabbas da likita zai gwadasa saiyaga jininsa yayi hauhawar farashi zuwa dubu k'arewa 180+, yanzuma zaune yake afalo Asma'u ta ajiye masa abinci amma yakasa ci. Sallamar dasukajice tasakasu kallon k'ofar suduka, har Asma'u tamik'e ya ce, "tazauna yaje. Hannu yabama bak'on nasa suka gaisa, Umar ya ce, " kayi hak'uri ban wayekaba. Eh bazaka sannuba, sunana Ahmad ilyasu daga kotu aka aikoni nabaka wannan, yamik'a masa zungureriyar farar takarda. Jiki asanyaye Umar yakar6a, sallama yamasa yatafi, shikuma yajuya cikin gidan. Asma'u tabishi da kallo, tasan ko tambayarsa tayi dawuya ya amsa mata Dan haka taja bakinta tayi shiru. Zama yayi ya warware takardar ya karanta, girgiza Kansa yayi yana cije le6ensa, waishi Lubna takai kotu akan ya saketa?, tamanta da alk'awarin dasukaima juna?, tamanta da soyayyar dasuka Gina atsakaninsu?, tamanta hidima da k'aunar daya Nuna mata?, tamanta?, tamanta?, dayawa. Ninke takardar yayi yasaka aljihun jallabiyarsa. Yasakko yazauna ak'asa yaci abincin sannan yatashi yakoma d'akinsa yakwanta. Asma'u kam shiru tayi tana mamakin komi takardar ta k'unsa oho. %%%%%%%%%%%% Bayan kwana hud'u ya amsa kiran kotu. Bayan kammala wata shari'a aka fara tasu. Tashin farko lauyan Lubna yanemi takardar saki dabin kadin hak'in Marin da Umar yayma Lubna ranar. Umar ya ce, "shifa bazai saketaba, mari kuma it's tajama kanta. Alk'ali yaci kud'i, Dan haka yace tilas Umar yayi saki Dan Lubna tace yana barinta da yunwa, babu sittirar kirki, sharridai sosai suka shirya masa wad'anda dole suka tirsasashi yamata saki d'aya. Tayi tsalle tadire ta ce, ''uku takeso, Alk'ali ya ce, " yacika biyun. Ran Umar yakai k'ololuwar 6aci musamman da Lubna taci kwalarsa acikin kotu gaban d'unbin mutane, cikin 6acin rai yacikashe uku amma yace tabasa 'ya'yansa, nanma ta ce, "bai isaba tabada 'ya'yanta mayya tarainesu. Indai tak'aice muku tilas Umar yahak'ura, alk'ali yasashi biyan Tatar Marin dayayma Lubna, dakuma kud'i milyoyi akan rainon yaransa. Kukane kawai Umar baiba amma tuni duniyar tafara juya masa, a take anan yamata transpar d'in kaf kud'insa na Account zuwa Account d'inta, bai barma kansa ko nera d'yaba. Suna fitowa daga kotu yashiga mota yay gida ransa a6ace. Sukuwa su Lubna da 'yan uwanta sai farin cikin samun nasara sukeyi. Umar natsaida motarsa yafito, dak'yar ya iya shiga cikin gidan yana dafeda k'irjinsa, dak'yar ya iya sallama yashiga falon, aiko yana shiga ya yanke jiki yafad'i............... 😕wayyo ya Umar Fharuk😥. *_(((S)))....2017_* *_luv you all my fan's_* [11/21/2017, 4:33 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻typing.......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!._*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* _Sadaukarwa_ *_miss Xoxo na_* *_Zarah bukar_* *_Ayusha muh'd_* *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO....😜._* *_page→5_* ........da sauri Asma'u da Rafi'a sukayo Kansa, jikinsu sai rawa yakeyi, summa rasa taimakon dazasu bashi, Rafi'a ce tai k'ok'arin fita waje da gudu, cikin sa'a tayi gamo da mak'ocin ya Umar d'in zai fita. Kuka tasaka masa tana nuna masa cikin gidan, amma takasa magana. Ya ce, "yammata lfy kuwa?, fad'amin mike faruwa ne?. Dan ALLAH ka tai makemu ya Fharuk karya mutu....katai makem..... Ai baima bari tak'arasaba ya afka cikin gidan. ALLAH yasa ya iya mota, Dan danan suka taimaka masa suka d'akko ya Umar dayayi jagaf tamkar gawa. Rafi'a tafad'a musu asibitin datasan ya Umar d'in yana zuwa shida iyalansa harma dasu yakansa akaisu idan basuda lfy. Suna zuwa asibitin Rafi'a ta ce, " sukaishi office d'in Dr jafar. Babu marasa lfy ak'ofar office d'in Dan haka suka sami damar Shiga kai tsaye, Dr Jafar nazaune yana rubuce-rubuce jin anshigo ko sallama babu yasakashi d'agowa yaga wanene. Kafin yayi magana,... Rafi'a ta ce, "Ya Umar muka kawo Doctor pls ka taimakemu karya mut...... Kafin takai k'arshe anshigo da ya Umar, doctor yatashi ya taimaka musu aka d'orashi ad'an gadon da'ake d'ora marasa lfy. 'Dan duddubashi yayi sannan yadawo ya zauna yana kallonsu Rafi'a. Ya ce, " miya sameshi?. Fad'uwa yayi. Numfashi doctor yasauke tareda fad'in ALLAH ya sawak'e. Ameen, Asma'u da Rafi'a suka fad'a. Doctor yacigaba da fad'in, gsky bazan 6oye mukuba Umar yana cikin matsala, yanzu haka sai mun kwantar dashi sannan musan taimakon dazamu basa, zakuje kubiya kud'in gado dasauran Mayan aiki. Da sauri Asma'u ta ce, "doctor nawa ake buk'ata?. Uhmm kamar 100k insha ALLAH zasu isheku komai harma da canji. Idanu suka zaro waje harda had'a baki wajen fad'in 100k fa doctor?. Eh, haka nafad'a, aikunsan asibitin kud'ine wannan. Rafi'a ta ce, " to doctor tunda ya Umar abokinka ne kumasa duk abinda yadace idan yadawo hayyacinsa saiya Baku. Kai yagirgiza mata, bazai yuwuba aii, shima yasan dokar asibitinmu aii, kuma ma idan nace zanyi k'uri namasa komai idan yatashi yanada abin biyanane?, kuma kunsan Umar bashida ko sisi yanzu saidai yazamemin kaya, so kuke kawai kunemo kud'i kunga yana cikin danja. Wash hawayene masu zafi sukrbin kumatunsu Asma'u, sudai sunsan doctor Jafar aboki ya Umar ne nakusa, Wanda sunada tabbacin yana cikin jerin wad'anda sukaci gajiyarsa da dukiyarsa fiye da kowa, amma yau danyaga bayidashi shine yake furta wad'an nan kalamin akansa. Asma'u tadurkushr masa yana kuka da rok'on doctor jafar, amma yay kunnen uwar shegu da ita, saga k'arshema masifa yahauyimusu, kai nifa kuna cikamin kunne da 6atamin lokaci, idan kunada kud'in daza'a lura da Mara lafiyarku kubada, idan bakudashi kud'aukeshi kukaisa asibitin gwamnati. Ran Asma'u ya6aci sosai, dama ita akwai zuciyar tsiya, mik'ewa tayi fusace taja hannun Rafi'a suka fita. Saida sukaje harabar asibitin Rafi'a ta tirje tana ad'in Anty Asma'u wai ina zamujene?. Hawaye Asma'u tashare, ta ce, "Rafi'a kirakani inda ake sqida wayoyi, zansaida wayata, nasan insha ALLAH ko 25k zatayi. Ajiyar zuciya Rafi'a tayi ta ce, "to kije shagon su labaran na anguwarku, nikuma sainaje nafad'ama su mama king a yakamata su sank ko?. Eh hakanma yayi, saimun had'u to. Saga nan kowa yanufi inda zashi, sukabar makwafcin nan nasu tareda ya Umar. Shagonsu labaran Asma'u take, babban shagone da'ake saida wayoyi daduk abinda yashafi hakan, had gyara sunayi, matasane sunkai Bihar masu tsaron shagon, kowa da abinda take kula dashi. Asma'u tashiga da sallama, wani matashin saurayi ya ce, ''yammata kina buk'atar wani abune?. Fuskarta takuma tamkewa damage Asma'u babu damace wajen rashin walwala. Ta ce, " inaso na said a wayane. OK to naga wayar. Wayarta taciro tamik'a masa. Yakar6i wayar yana jujjuyawa tareda d'agowa yana kallonta. Ganin kallon mamakin dayake binta dashi yasata fad'in malam lfy kuwa?. Eh to Hajiya dadai sauk'i, amma tsakaninki da ALLAH wayarnan takice?. Cikeda mamaki take kallonsa, tagyara tsayuwarta sannan ak'ufule ta ce, "namaka kama da a6rauniyane?. A'a wlhy Hajiya ko d'aya, kinsandai rayuwarce sai'a hankali kawai, amma idan ranking ya6aci kiyi hak'uri. Idanma ban hak'uraba dukanka zanyi, kashiga cikin wayar sosai insha ALLAHU zakagane idanma tawace ko akasin haka. Shawararta yabi yashiga bincike awayar, tabbas tatace Dan hotunantama dake kai sun Isa shaida, yad'ago yana kallonta to Hajiya nawa zaki sayar?. Kasiya yanda yadace, nidai ina rok'onka kamin adalci kawai, nima dolece tasakani saida wayar badan nasoba. Jinjina kai yayi, ya ce, "nasiya 150k. Idanunta tazaro waje, kai malam kallifa da k'yau kaga wayar dake hannunka. Murmushi yayi Hajiya nagani sosai, wlhy nama saya da daraja aii....... Kafin tayi magana wani dake kusadasu yana sayen waya ya ce, " gsky kacuceta Dan wayarnan bata sha wahalaba. Asma'u da mamaki yakashe ta ce, nifa duk bamma fahimci inda kukadosaba, wayar dabata wuce 25k ba kuke kira mata 150k?, ahankama har ana fad'in an cuceni?. Wanda yasaka musu bakin ya ce, "Hajiya amma dai bake kika sayi wayarnanba?. Eh bani nasayaba, yayanane yasiyamin. Haba shiyyasa bakisan kud'intaba, wannan wayar dakike gani, ana saidata 400k wlhy. Idanu sosai Asma'u ta kwalalo waje, sai maimaita yawan kud'in take azuciyarta, dubu d'ari hud'ufa?, tabd'ijan, lallai ya Umar yayi k'ok'ari...... Tunaninta yakatse yayinda taji maganar labaran abayanta. A'a Asma'u lfy kuwa?. Lfy lau wlhy Labaran, nazo nasaida wayane. Tofa ina wayar?. Kaganta nan, tayi maganar tana nunama masa wayarta dake hannun saurayin. Hannu yamik'ama saurayin yabashi wayar, saida ya rissina sannan yabashi alamar girmamawa. Labaran yakar6i wayar ya jujjuya sannan ya ce, " nawa kasiya?. In ina saurayin yafarayi alamar rashin gsky, labaran ya girgiza kai kawai danyasan halin yaran shagon dason zuciya. Baice komaiba yak'irgo kud'i masu yawa yabata, Asma'u ga 330k kiyi hak'uri datayin farko dayayi mini. Babu komai tafad'a tana murmushi, ngd sosai labaran, amma Dan ALLAH kozan samu memory nakwashe abin kan wayar?. Babu damuwa, idan nakwashe zanbama Rafi'a takawo miki. To ngd sosai labaran. A babu damuwa Asma'u. Agurguje tafice tasamu adaidaita cikeda kwarin guywa suka nufi asibitin.......... *_(((S))).......2017_* *_luv you all my fan's_* [11/21/2017, 4:33 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR AZEEK'I!!_*💎 *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO......😜_* *_page→6_* .......Anshigar da ya Umar babu dad'ewa su mama suka iso, suduka sukai kan Asma'u suna tambayar jikin ya Umar d'in?. Jikin Anty sa'a tafad'a tana kuka, wannan yasa suka k'ara rud'ewa. Makwafcinsune yamatso, cikin hikima yamusu bayani. Godiya sukai masa sosai, daganan aka koma zaman jigum-jigum. *_3h...ago_* Dr yafito shida Nurse's dasuka taimaka masa. Shimadai rufuwa akansa sukayi suna tambayarsa jikin ya Umar. Yabuk'aci ganin wasunsu a office d'insa, amma babu Wanda zaya iya hak'uri abarsa abaya, Dan haka suka tafi suduka. Dr bai hanasuba saima gurin zama daya nuna musu. Kowa yasamu waje yazauna yanajiran bayani, bayan Dr yagama 'yan rubuce- rucensa yad'ago yana kallonsu, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Alhmdllh, gsky Ku k'ara godema ALLAH akan taimakon daya bama Alhaji Umar danba kowane yake irin fad'uwarnan yatashi dai-daiba, amma shi Alhmdllh babu wata Marsala, saidai yana cikin matsannanciyar damuwa wadda saida taimakonku aikinmu zaikai ga nasara, yanzudai yasamu barci kuma bazai farkaba harsai nanda 24h Dan munaso zuciyarsa tasami Hutu sosai. Yanzu ga wannan zakuje kubiya kud'ad'en sannan kuma asayi wad'annan magungunan kafin ya farka. Atare sukace to Dr mungode sosaifa. Karku damu aikinane. Godiya suka masa sannan suka fita. Suna fita Mama ta kalli ya Abubakar, ta ce, " Abubakar saika amshi takardun kaje kabiya kakuma sayo magungunan ko?. Fuska ya murtike tamkar zai fasa kuka ya ce, "to kuzama shaida idan yatashi zai bani kud'ina Dan na kasuwane. Asma'u da Anty sa'a, mufida, Rafi'a duk kallon mamaki suke masa, shikansa ya fahimci haka amma saiya basar yamik'ama Asma'u hannu alamar tabashi takardun. Kanta ta girgiza ta ce, ''ya Abubakar kabarsa akwaima kud'i awajena kuma insha ALLAH zasu ishemu komai. Babu kunya ya washe bani yana fad'i a to kinyi k'yankai Asma'u. Babu Wanda yatanka masa acikinsu, Asma'u da Anty sa'a suka tafi wajen da Dr yafad'a musu. Sunbiya kud'in komai sannan sun sayo duk magungunan da ake buk'ata, dawowarsu babu dad'ewa ya Abubakar yawuce kasuwa akabarsu mama anan. Sumadai zuwa dare duk suka tafi akabar Asma'u kawai awajensa, da mamace zata tsaya Asma'u tace taje tahuta ita zata zauna dashi, dak'yar tayarda saida su Anty sa'a suka saka bakima. Bayan tafiyarsu Asma'u tayo alwala tashimfid'a sallaya, sallar isha'i tagabatar tayi addu'a sosai darok'on ubangijin al'arshi akan yakawoma mijinta d'auki da sassaucin halin daya tsinci kansa aciki, tashafa addu'ar tanamai zubar da hawaye, bayan kammalawarta saman kujerar dake d'akin tadawo ta zauna ta talsurama k'yak'yk'yawar fuskar ya Umar idanu, duniyar tunani tafad'a wa rayuwarsu tabaya maicikeda abubuwa na ban mamaki, ban haushi, al'ajabi, tausayi, farinciki, da jarabawoyi kala-kala........... *_SHEKARUN BAYA DASUKA SHU'DE_*🤔 Malam Tsalha baduku tsohon kirki mai mata d'aya da 'ya'ya uku aduniya. Hajara tsohuwa mairan k'arfe uwargida kuma amarya agidan malam Tsalha baduku, ta haifamasa yara uku 2maza 1mace. Usman, Kabiru, Binta. Sun rasu suduka tun shekarun baya dasuka shud'e. Usman yanada mata d'aya da yara Uku shima, Mero itace matarsa suna kiranta da mama, malam Usman mutumne mai hak'uri da kawaici, yanada son 'yan uwansa sosai dakuma iyayensa, bawani mai k'arfi banebashi amma mutumne mai Neman nakansa cikin tsaftatacciyar hanya, akwaishi da wadatar zuci dakuma Nuna godiyar ALLAH kan abinda yabashi walau kad'an kokuma mai yawa. Saidai Bahaka bane ga matarsa Dan itakam akwai hange-hange da son kud'i damai kud'i, Indai Kanada naira tokuwa kai abokin tafiyane, idankuwa babu to kana gefene awajenta. Yaransu uku Sa'adatu, Abubakar, Umar Fharuk. Sai kuma Kabiru matarsa d'aya wasila amma basu ta6a haihuwaba. Halin Kabiru shima yasha banban Dana malam Usman dankuwa shimadai akwai son 'yan canji, toshikam babu laifi yanada d'an hali danyafi malam Usman arzik'i. Sai Binta itamadai tayi aure harda yaranta, halintakam irinna malam Usman ne dantanada hak'uri sosai da kuma zafi idan ka k'ureta. Yaranta hud'u duk mata, Saratu, Asma'u, Fateema, Hasiya. ALLAH yayima malam Usman rasuwa tunsu Umar suna k'anana danshi bama sosai yasanshiba, bashida wayo sanda yarasu. Bayan Rasuwar malam Usman rik'on yaran yacigaba gudana hannun mahaifiyarsu mama, ta taka rawar gani sosai wajen kula dasu har bayan shekara uku da rasuwar malam Usman sai kawu Kabiru yazo da buk'atar auren mama abisa shawarar da inna binta k'anwarsu tabashi. Dagudu kuwa mama ta yarda Dan tasan Kawu Kabiru yanada d'an abin hannunsa gashi kuma baita6a haihuwaba, ba'a wani 6ata lokaciba aka d'aura auren, anan gidan tacigaba da zama, cikin ikon ALLAH kuwa saiga ciki, wayyo zokaga murna wajen kawu kabiru da family gaba d'aya, tattali sosai yakema mama, ciki yanakai wata Tara da wasu kwanaki ta sunkuto d'anta Namiji Wanda yaci suna Usman suna cemasa Harris, shekarar Harris biyu mama takuma haihuwar mace Mufida, daganan sai Auta Rafi'a. Rafi'a nada shekara biyar aduniya Anty sa'a tayi aure bayan ta kammala karatunta na Secondary, taso cigaba da karatu amma hakan bai samuba, shima Ya Abubakar a daddafe da buga-buga yakammala Diploma d'insa, daganan yay aure yanad'an sana'ar saida kayan provision awani shago dake k'ofar gidansu. Bata sake zaniba akan Umar Fharuk dan shimadai duk ajirgi d'aya suka sauka, bayan kammala secondary yafara karatun nasa a B,U,K saboda k'yawun result d'insa kai tsaye degree suka basa, dahad'a gabas had'a yamma aka kammala, ALLAH yabashi nasarar fita da result mai k'yau, yayi farinciki sosai hakama 'yan uwansa musamman ma mama Dan aganinta itamafa karan 'ya'yanta yakai tsaiko yanzu. Umar yadawo zaman gida babu aikinyi, tun zaman yana masa dad'i harya fara gundurarsa, tuna maganarnan ta hausawa dasukance babu maraya sai rago tamasa allurar tashi domin Neman abinyi, duk abinda yasan zai rufa asirinsa yinsa yakeyi babu sanya ko girmankai irinna 'yan bokon nan, ana haka wani abokinsa yay masa hanyar Babur na adaidaita sahu, sosai Umar yaji dad'in wannan taimako, cikin farin ciki yazoma mama da kawu Hamidan wannan labari. Hummm, amma saisuka gwaleshi da nuna masa wannan k'ask'ancine, yaza'ayi kamarsa dayakeda kwalin degree yak'are da tuk'a babu, gsky yacanja shawara amma ba wannanba. Wannan lamari ya6ata ran Umar sosai, Dan haka ransa a6ace yanifi gidan inna binta. Tarba sosai yasamu agurinta Dan d'an gatantane. Inna tasaka Fatee takawo masa abinci da ruwa, saida yaci yak'oshi sannan yakwashe komai yafad'a mata. Itama ranta ya6aci sosai Dan haka taita fad'a kamarsu mama na gabanta, takuma kwantar masa da hankali akan zata samesu, shikuma yaje yakar6i adaidaita sahud'in yafara aikinsa. Yaji dad'i sosai Dan haka yayta mata godiya, daganan hira maidad'i suka cigaba dayi Dan akwai shak'uwa tsakaninsu sosai. Sallamar Asma'u da Hasiya ne yasakasu katse hirar suka amsa. Asma'u tazube littatafanta na islamiyya tana fad'in wash inna wlhy nagaji yau. Binna ta ce, "to sannu ragguwa, amma bakiga yayankiba. Idanunta tad'ago ta kallesa, saikuma ta kauda kai tace ina yini. Bai amsataba saima hararta dayakeyi, takuma fad'in inayini, Dan ita azatonta baijibane, d'an yatsine fuskarsa yayi sannan ya amsa, yamaida kallonsu ga Hasiya da itama take gaidashi, ya ce, " Autar inna ya islamiyyar?, kinadai yin k'ok'ari ko?. Hasiya ta jinjina kai ta ce, "eh yaya munayi, yanzu hakama ina ajin sauka nida yaya fatee, yaya Asma'u kuwa sune manya Dan sune 'yan ajin hadda. d'an satar kallon Asma'u yayi, suna had'a ido ya kauda kai. Asma'u tad'an ta6e baki tareda mik'ewa tashige d'akinsu tana k'unk'unai Dan haushin ya Umar takeji saboda abinda yay mata shekaran jiya, tana hira da saurayinta ya koreshi, abin bak'aramin haushi yabataba. Bata k'ara fitowa falonba saida taji yatafi sannan tafito. Inna tabita da kallo, kekuwa Asma'u mikikeyi ad'aki tun d'azun?. Kanta tad'an sosai ta ce, "inna ina wayane da Anty saratu fa. Inna batace komaiba ta mik'e, saida takusa zuwa k'ofa sannan tajuyo tana kallon Asma'u, ta ce, "idanma laifi kikaima Umar to wlhy kiyi gaggawar bashi hak'uri Dan kinsan Sam banason raina nagaba. Asma'u ta kwa6e fuska kamar zatayi kuka, nifa inma ban masa komaiba. Ohodai nidai nafad'a miki, inna tafad'a tana ficewa daga falon........ *_(((S)))......2017_* *_Luv you all_* [11/22/2017, 1:23 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→7-8_* ......Umar kam tun aranar yaje yakar6i Babur d'in Adaidaita sahu, kuma aranar yafara aiki, ganin alkairin daya samu yasakashi farinciki sosai tareda samun kwarin guywa. Bai sanarma kowa yafara aikiba agidansu saida inna tazo washe gari sukai magana dasu mama, badan mama tasoba ta amince, amma babu yanda zatayi Dan tanason inna binta sosai kodan k'aunar datake nunama 'yayanta, ta taka rawar gani sosai akan karatun Umar Dan d'an gidantane. Tundaga ranar Umar yacigaba da hayar adaidaita sahunsa, dukda mama bata nuna farincikinta aikai hakan bai hanashi yimusu hidaimaba da d'an abinda yasamu, babu yabo babu fallasa suke kar6a, shikam Umar ko kad'an hakan baya damunsa harkokinsa kawai yakeyi. Ana haka sai wani al'amari yafaru a wani daren Juma'a ranar alhamis kenan da daddare. Bayan Umar yagama aikinsa misalin k'arfe 11 saiyayi harama tafiya gida. Yana cikin tafiya saiyaga ana d'aga masa hannu tundaga nesa, lamarin yabashi tsoro Dan azatonsa 'yan fashine ko 6arayin Babur, haka yak'arasa wajen guywarsa asage yanata ambatar duk addu'ar datazo bakinsa. Yataka birki agaban dattijo da wani matashi daketa k'ok'arin tsaidashi, matashin saurayinne yayma Umar magana. Abokina Dan ALLAH kozaka kai alhaji gyad'i-gyad'i?. Shiru Umar yayi na 'yan sakwanni zuwacan yasauke ajiyar zuciya tareda kallon agogon hannunsa, ya ce, "abokina darefa yayi duba kagani, gashi kasan akwai tazara daganan zuwa gyad'i-gyad'i. Nasani abokina amma Dan ALLAH ka taimaka, wlhy daga airport na d'akko mai gidana saikuma mota tamana tsiya, tun d'azun muke tsumayen abin hawa amma bamu samuba. Kafin Umar ya ce, " wani Abu dattijon Alhaji yalek'o yanafad'in yaro kadauro Dan ALLAH, wlhy nagaji sosai burina kawai nahuta. Ajiyar zuciya Umar yasauke tareda gyad'a kai ya ce, "shikenan shigo mutafi baba. Alhaji yaji dad'i sosai, Dan haka yashiga sakama Umar albarka, kayansa direban yakwaso zuwa adai-daitar sukaiyi sallama Umar yaja suka tafi. Tunda suka tafi babu maima wani magana, Umar yana tuk'i yana tunanin rayuwa da yanda take tafiya, Alhaji kam yayi shiru abaya saboda gajiyar zaman jirgi dake nuk'urk'usarsa, saida suka isa gyad'i-gyad'i sannan Alhaji yanuma Umar layin dazasu shiga. Ak'ofar wani katafaren gida suka tsaya, Umar yajinjina kai azuciyarsa yana fad'in wani kaya sai amale..... Alhaji yakatse masa tunani da mik'a masa kud'i masu yawa Wanda shima baisan adadinsuba. Umar ya yakalli kud'in ya kalli alhaji sannan ya ce, " baba 350 ne kud'inka aii. Murmushi alhaji yayi ya ce, "d'ana karka damu kaidai kar6i. A'a baba ngd kabani iya hak'k'ina kawai, girgiza kai Alhaji yayi dakuma ajiyema Umar kud'in akan cinyarsa, babu yanda Umar ya iya dole yakar6a yay godiya sannan yatafi gida da addu'ar ALLAH yakaisa lfy. Inda yake kai adai-daitarsa yanufa, yasamu guri yay fakin, abinda yake lilli6eta yajawo zai rufe sai idanunsa suka sauka akan wani d'an k'aramin akwati, shiru yayi yana nazarin kowaye ya manta?. Wata zuciya ta ce, " masa Alhajin Daka sauke yanzu. Afili ya ce, "hakane kuma, ya kalli agogonsa saiyaga har 12:36, gsky yanzu yana tsoron sake hawa titin nan, kuma idanma ya iya komawa yanada tabbacin za'a barsa yashiga wannan gidan a irin wannan lokaci?, d'an tsaki yaja tareda d'aukar akwatin yana fad'in insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu da sassafe saina kai masa. Da wannan shawarar yanufi gida, dama kullum shine k'arshen dawowa gida shiyyasa yake rik'eda key d'in gidan guda d'aya, bud'ewa yayi yashiga sannan yamaida yarufe tareda addu'ar rufe gida, d'akinsa yashiga yay wanka da shirin barci sannan yay nafilfilinsa kamar yanda yasaba ya kwanta. _washe gari_ Tunda yatashi yay sallar asuba bai koma barciba dama shi haka yake bai iya barcin safeba kullum yana dawowa daga masallaci zai d'auki alkur'ani yahau karatu, saida gari yay sha sannan yay addu'oi yatashi, wanka yashiga. Shigarsa babu dad'ewa mama ta shigo d'akin, idontane yasauka akan bak'uwar jakar mai k'yau, jikinta har rawa yakeyi tabud'e jakar, idanu tazaro amatuk'ar razane Dan ganin mak'udan kud'in dake cikeda d'an akwatin duk daloline sababbi k'ar. Razanuwa da ganin kud'in yasa takasa aikata komai har Umar yafito daga wanka, shimadai bak'aramar razana yayi dagani kud'inba, Dan yauce rana ta farko daya fara ganin zunzurutun kud'i tsirara agabansa masu yawan haka. Jikin mama amace ta ce, " Umaru INA kasamo wad'annan kud'in haka?. Zama yayi abakin katifarsa, yajanyo jakar yana rufewa mama ba nawabeneba, wanine nad'auka jiya da daddare shine yamanta da jakar. Mama ta washe baki tana fad'in Umaru aii yamzun sunzama naka tunda tsuntuwa kayi, lallai kagodema ALLAH da wannan arzik'i daya yimaka, dama masu iya magana necewa dare d'aya ALLAH kanyi bature. Kallonta kawai yakeyi damamakin ganin rikicewar datayi Dan kawai taga kud'i, shi rabonma dayaga fara'ar mama agareshi harya manta wlhy, amma duba daga ganin kud'i dukta rikice, ya kauda Kansa saboda 6acin rai, amma kasancewarsa jarumin 6oye sirrin zuciya sai fuskarsa bata nunaba ko kad'an, cikeda ladabi ya ce, "mama zan maida MASA kud'insa ne, Dan zan gane gidan Dana saukesa insha ALLAHU. 6ata rai mama tayi, ta gallama Umar harara to Uban masana basaikaita maidawarba, idan banda ga6anci ALLAH yabaka irin wannan dukiyar har kayi tunanin maidama mai ita?, shi Kasan ta hanyar daya samu?, k'ilama 6arawon gwamnatine. Kiyi hak'uri mama ALLAH ya huci zuciyarki, abinda zaki duba wannan kud'i ba hakkina bane, koma tayaya maisu yasamesu wannan shiyya d'aukarma Kansa kaya, inada damar maida masa kud'insa, to aii gara na maida domin ubangijinafa da barci ko gyangyad'i baya d'aukarsa yana kallona, kuma baya yafe hak'k'in wani akan wani face kanemi gafarar Wanda ka zalunta, tonikuwa mizaisani butulcema ni'imar da mahalliccina yay mini? na tsarkakakkiyar zuciya. Mik'ewa mama tayi a fusace tafice tanata masifa. Umar ya girgiza Kansa tareda sauke zazzafan huci, afili ya ce, " mama ALLAH ya shiryeki. Niko bilyn Abdul sai na ce, "ameen ya Umar🤷🏽‍♀. Koda Umar yagama shirinsa yanufi d'akin mama Dan mata sallama kamar yanda ya saba. Da sallama yashiga falon, babu kowa sai Mufida da Rafi'a dake break fast kowanne sanye cikin kayan makaranta na gwamnati. Gaisheshi sukayi, ya amsa yana tambayar ina mama?. Mufida ta ce, "tafita makwafta yaya. Makwafta kuma?, yanzu da sanyin safiyarnan?. Shiru sukayi basuce komaiba, ya ce, " to kutashi mutafi idan kun gama?. Rafi'a ta ce, "yaya bazakayi kari ba yau?. A'a Rafi'a yau ina saurine, kudai kutashi muwuce, to suka fad'a suna mik'ewa, kowa yad'auki jakarsa ta makaranta suka fice. Atsakar gida suka gamuda kawu, Umar yadurk'usa har k'asa yana gaida shi, Abba ina kwana. Lfy lau Umaru anfito?, eh Abba mun fito, to wannan akwatinfa haka?, Abba wlhy wanine ya mantashi jiya dana d'akkoshi shine zanje na mayar masa, tofa yo kai Umaru banda abinka aii wannan tsintuwace, karik'e abinka kawai mana, nasandai bai wuce kaya bane aciki?, murmushi Umar yayi yanamai jinjina halin iyayen nasu aransa, ya ce, " karka damu abba nasan gidansa zankai masa dan takardune aciku, aikin 6ur inji tusa, a'a jeka kakaimasa abinsa, mizakayi dawasu tarkacen takardu dadai kud'ine ko kaya saika rik'e, nanma murmushi kawai Umar yayi harsu Mufida na tayashi. Rafi'a da Mufida ma suka gaidashi, suma amsawa yayi cikeda fara'a. Sallama sukai masa sannan suka fice, wajen adaidaitarsa sukaje, saida ya goge sannan suka shiga, makaranta yafara saukesu daganan yanufi gyad'i-gyad'i. Da gyar ya iya gane layin, yatsaya adaidai inda yasauke dattijon Alhaji, gidan dayaga alhajin yashiga yake kallo, shi saima yanzu yaga gidan sosai, katafaren gidane na mai jida 'yan canji, komakaho yashafa katangar gidan yasan mai gidan ya shahara kuma yagama jik'ewa da data. Yad'an dad'e atsaye yana tunanin yanda zai shiga gidan, baigama tunaniba yaga an wangale k'aton gate d'in gidan, wata dalleliyar motace tafito bak'a wulik sai d'aukar ido takeyi, k'arfin hali Umar yayi yamatsa kusada motar yana d'aga masa hannu. Ahankali aka sauke bak'in Gila's d'in motar, wani matashin saurayi dabaifi sa'an Umarba ya bayyana. Umar ya ce, "sorry Dan ALLAH inada tambayane?. Inajinka saurayin yafad'a cikeda isa. Umar ya ce, " jiya nakawo wani dattijo gidannan, to bayan mun rabu sainaga yayi mantuwa Dan haka nakawo masa abinda ya manta d'in. Saurayi ya kashe motarsa sannan yacema Umar ya kamannin dattijon yake?, danshi ko kad'an baikawo dad d'insu bane. Lissafa masa Umar yashigayi, cikeda mamaki Saurayin ya ce, "my dad, tomiya kaishi hawa adaidaita sahu?, bud'e motarsa yayi yafito, ya ce, " to muje cikidai. Umar yad'auki d'an akwatin suka shiga cikin gidan, saurayi na baya Umar nabinsa abaya............ *_(((S)).....2017_* *_Luv you all_*😻🤝. [11/22/2017, 1:24 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→9-10_* .........Wata had'ad'diyar k'ofar Gila's suka nufa, saurayin ya danna wani abu k'ofar tabud'e da kanta, Umar dai yanadaga baya yana kallon ikon ALLAH. Bayan k'ofar tabud'e suka shiga k'aton falon dayagama k'awatuwa da kayan alatu, gurin zama saurayin ya nunama Umar sannan yashiga cikin gidan domin Neman iso. Umar na zaune yanata Rarraba idanu tsakanin falon da kayan dasuke ciki saurayin yadawo. Bismillah yafad'a yana nunama Umar hanya, mik'ewa yayi yad'auki jakar suka tafi, gaba da gabanta Umar yafad'a aransa yayinda suka shiga falo na biyu, saiyagama falon farko Ashe bai had'uba, yayinda suka shiga na Uku sai kan Umar yakusa kwancewa Dan maganama ta gagaresa, benen dake tsakkiyar falon suka hau anankam Umar yakasa daurewa saida ya ce, "masha ALLAH, falone nafad'a aji Wanda koda saga binnin sin kazo dolene ka yaba, nanma gurin zama ya nunama Umar. Umar yazauna kad'an akujerar tamkar bayaso, sai 'yan kalle-kalle yakeyi. Woow!!...... Yaji wata zazzak'ar murya yafad'a. d'ago fararen idanunsa yayi ya sauke akan k'yak'yk'yawar fuskar mamallakiyar muryar, ya sauke numfashi ahankali tareda kauda idonsa akanta Dan itama nata icon nakansa kam ko k'yaftawa batayi. Batasamu damar yin maganaba dad da Safwan suka fito. Umar yamike domin nuna girmamawa ga dattijon, dattijo yay dariya tareda fad'in a'a saurayi kaine?. Nine Alhaji, Umar yafad'a cikeda girmamawa. Bismillah zauna mana, zama Umar yayi ak'asa, Alhaji ya ce, " a'a tashi ka koma saman kijera mana, nanma yayi wlhy Alhaji ngd. Daganan Umar ya gaida Alhaji, cikin fara'a ya amsa masa, Umar yad'ora da fad'in Alhaji dama mantuwar sannan kayi, to jiyan naso dawowa na maida maka saikuma naga dare yayi shiyyasa nabari sai yau. Tunda Alhaji yay tozali da akwatin kud'insa sai mamaki da al'ajabi ya lullu6esa, damage akwai sauran mutane nagari aduniya irin Umar?, Alhaji yajawo akwatinsa gabansa yabud'e, kud'insa na nan yanda ya shiryasu, yad'ago yana kallon Umar cikeda mamaki, Safwan ma dai kallon Umar yakeyi, hakama budurwarnan tad'azun. Ajiyar zuciya Alhaji yasauke tareda fad'in yaron kirki kenan, nunama rasa abin fad'a saboda lunbin mamaki daya cikani, yaro yaya sunankane?. Umar Fharuk!. Masha ALLAH Umar Fharuk mai gaskiya da rik'on amana, lallai kadace da k'yak'yk'yawar zuciya maicikeda alkairi, ALLAH yasa kad'ore haka har karshen rayuwarka, wlhy bammasan namanta jakarnan awajenka ba, amma saboda adalcinka ka kawomini, kila dasai natashi amfani dakud'in naita bulayin Neman, kaidai ALLAH yayi maka albarka. Gaba d'aya suka amsa da ameen har mom da Suhaima dake fitowa yanzun, Safwan yamik'ama Umar hannu sukayi musabaha sannan ya ce, "d'an uwa munfa gode sosai, nizan wuce abujane lokaci NATA tafiya, To ALLAH yatsare Nina ngd sosai. Safwan yayma iyayrnsa da k'annensa sallama harya kama k'arfen bene zai sauka budurwar d'azu ta ce, " ya Safwan Dan ALLAH karma manta da sak'ona wajen Fidoo. Karki damu baby zan fad'a mata insha ALLAH. hannu tad'aga masa tana murmushi harya sauna. Umar ya ce, "zaitafi wajen aiki, harya mik'e Alhaji ya ce, " Hana Umar Fharuk koma ka zauna aii alkairi dank'one baya fad'uwa k'asa banza, baby kusa kuku yashirya mana break fast. To dad, Budurwar d'azu wadda suke kira baby ta amsa. Babu yanda zaiyi dole yahak'ura ya zauna har aka gama shirya had'ad'd'en break fast a dinning. d'unguma sukayi gaba d'aya zuwa dinning, Umar dukaya takura, musamman akan kallon k'urullah da baby ketamasa tun d'azun, dasun had'a ido saita sakar masa k'ayataccen murmushi, adaddafedai yakammala break d'in yamik'e, Alhaji yakama hannunsa har falonsa dashima ya amsa sunansa dankuwa komai yaji tamkar baza'a mutuba, zaunar dashi Alhaji yayi akan luntsumemiyar kujerar ta alfarma sannan shima ya zauna, idonsa akan Umar ya ce, "Umar Faharuk kayi karatu?. Eh Alhaji nayi. Wane mataki ka taka?. Nahad'a degree d'ina Alhaji harda bautar k'asa. Masha ALLAHU, ammafa kabirgeni wlhy, awannan zamanin bokowane matashine kamarka zai kammala karatun Degree ba yadawo tuk'a adaidaita sahu, Dan aganinsu hakan zubar da girmane, kuma bahaka baneba. Umar dai kansa na k'asa yana murmushin jin dad'i. Alhaji ya ce, " to yanzu insha ALLAHU zan taimakeka domin nima ka taimakeni taimakon dabazan ta6a mantawa dakaiba atarihin rayuwata, idan kanason aiki kakawo takardunka zan nema maka, idan kuma kasuwanci kakeso wannan mai sauk'ine daga gobe ma zaka fara insha ALLAHU?. Wani dad'ine yatsarga zuciyar Umar, yad'ago yana kallon Alhaji, zamowa yayi k'asa ya tsigunna yana masa godiya, Alhaji yakamashi yamaida saman kujera yana fad'in karma damu Umar kaima kazama d'ana aii, yanzu wanne kaza6a?. Alhaji naza6i kasuwanci Dan dama shine burina, nayi karatune Dan kare mutuncin kaina amma badan aikiba. To Alhamdllh naji fad'in za6inka nima sosai, Alhaji yamik'e yana fad'in jirani ina zuwa. Babu dad'ewa yafito, yazauna kusada Umar tareda mik'a masa makullin mota, Umar ga wannan tukuycin alkairinka gareni. Idanu Umar yazaro bakinsa na rawa ya ce, "baba motacrfa?. Dariya Alhaji yayi ya ce, " nasani Umar motace tana nan aharabar gidannan, zansa direba yakaimaka har gida, idankuma zaka d'auka da kankane babu laifi. Hawayen farinciki Umar yakeyi, ya ce, "baba dakabarsa, wlhy ban kawo maka jakarnan danka sakamin dawani abuba, namaido maka da itane saboda tsoron ALLAH da cin hak'in saba nawaba. Alhaji yakamo hannun Umar yasaka masa key d'in Hana fad'in nasani Umar, nima namakane badan na biyakaba aii. Godiya sosai Umar yayma alhaji sannan yafito. Afalo yatarar da baby da Suhaima, suna ganinsa baby tamik'e tsaye cikin fara'a ta ce, "ya Umar kafito?. d'an murmushi yamata tareda jinjina Kansas. Takashe masa ido d'aya tana wani far da idanu, tobara namaka rakkiya ko. Baice komaiba Dan tafara gundurarsa, kusan at are suka sauka, ganin haka yasaka Suhaima bin bayansu da sauri danson ganin abinda zai faru. Har wajen gate suka rakoshi, yashiga a adaidaitarsa yatada, baki Suhaima ta ta6e afili tace kambu tak'ashinnan, yanzunan duk had'uwar bawan ALLAHn Nan a adaidaita sahu yazo?. Hararta Baby tayi sannan tak'arasa kusada Umar dake k'ok'arin tafiya, ta ce, " ya Umar mungodefa sosai, inafata zaka cigaba da ziyartarmu Dan sada zuminci?. Kallonta kawai yayi baice komaiba ya kauda kai. Murmushi tayi azuciyarta ta ce, "ka cancanta my guy, afili kuma ta ce, " I Love you so much.💋 Da sauri Umar yad'ago yakalleta amma tuni harta bar wajen ta isa inda Suhaima ke tsaye tana kallonsu. Kasa tafiya yayi yatsaya binsu da kallo, harsaida suka isa gate sannan Baby tajuyo ta kanne masa ido d'aya tashige cikin. Wata sassanyar ajiyar zuciya yasauke sannan yakuma tada baburd'in yafice daga anguwar cikeda farin ciki. Tunanima yake wayakamata yafara fad'ama albishir d'innan, su mama ko inna ko Anty Sa'a?, baisan dawa zai faraba. Daga k'arshedai ya yanke shawarar fara zuwa gidan inna, dankoba komai itace ta k'arfafa masa hayar adaidaita sahun, togashi tasilar hakan yayi gamon katar da tarin alkairi, kunga kuwa aii ita yafi cancanta tafara sani ko?.🤷🏽‍♀ Kai tsaye gidan inna yanufa kuwa........ *_(((S)))........2017_* *_Luv you all_* [11/23/2017, 4:57 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO......😜_* *_page→11-12_* ........Tun'a k'ofar gida yaci karo da abinda yasaka farincikinsa rauni, wato ganin Asma'u da wani saurayin ranar, Asma'u na ganinsa ta 6ata fuska Dan gudun karya k'ara bata kunya kamar ranar, abisa tsautsayi suka had'a ido, yamaka mata wata uwar harara. Kauda kanta tayi daga kallonsa, saurayin na gaisheshi amma ko kallon bai isheshiba yashige cikin gidan. Asma'u tarakashi da harara. Saurayin ya ce, "Asmy wanene wancan kuma?, nagafa sai hararmu yakeyi?. Baki Asma'u ta ta6e ta ce, " yayanmune. Kai Asmy shine baki fad'aminba na gaisheshi da k'yau?. Uhmm kaga Zayyan share batunsa kawai, yanzu yaushene zaka dawo a tafiyar?. Uhmm insha ALLAHU bazan wuce 2year's ba zan dawo. Kai kana nufin bayan mun kammala s,s,c,e fa kenan?. Eh hakane my Asmy, amma kiyi hak'uri nima Bahaka nasoba wlhy, kinsan karatunane yakawo haka, kuma umarnin Abba ne babu yanda na iya. Shikenan ALLAH yatsaremin kai, yasa kaje a sa'a kadawo a sa'a. To ameen my Asmy, shiyyasa nake k'ara sonki da k'yaunarki akowacce dak'ik'a ta rayuwata. Murmushi Asma'u tayi, tareda fad'in nima ina sonka sosai zayyan, tayi maganar tana rufe fuskarta da hijjabi. Dariya zayyan yayi yace Asmy sarkin kunya kenan...... A6angaren ya Umar kuwa ransa a6ace yashiga gidan, inna data fito daga d'akin baba mahaifinsu Asma'u ta ce, "a'a Umaru kaine agidan?. Murya acinkushe ya ce, " nine Inna, sannu. Yauwa Umaru, amma yanaga kamar Ranka a6ace yake?. Da sauri ya saisaita nutsuwarsa, shikansa yana mamakin yanda baya iya 6oye Bacin ransa idan yaga Asma'u da saurayi, kuma aii hakan bata faruwa akan Mufida kosu fatee, wata zuciya ta ce, "aigara Mufida tayi girma tunda tana 100L a jami'a, amma Asma'u fa SS 1 take a secondary........ Innace ta ta6ashi, firgigit yadawo daga duniyar tunani, ta ce, " tunaninmi kuma kakeyi Umaru?. Cikin inda-inda ya ce, "babu komai Inna wani albishir Nazo miki dashi, amma mi Asma'u yakeyi awaje da safennan?, mima yahanata zuwa makaranta. Dariyace taso kufcema Inna saboda hango kishi k'uru-k'uru a idanun Umar, amma saita dake tace kasan suna Exam, toyau basuda ita shiyyasa, wancan kuma Zayyanne wai zaiyi tafiyane shine yazo suyi sallama. Kansa kawai yagyad'a amma bai iya cewa komaiba yamik'e yana fad'in bara nagaida baba. To kashiga yana ciki. Ak'ofar d'aki yayi sallama, saida aka bashi izinin Shiga sannan yashiga. Baba na zaune yana karin kumallo Umar yashiga, cikeda fara'a yataresa, Fharuku kaine agidan namu?. Nine baba ina kwana?. Lfy lau Umar ya hidimomin duniya?. Alhmdllh baba. To masha ALLAHU, kaga matso muci abinci ko?. A'a wlhy baba nakarya nikam. Kai Umaru karfa filako kakeyi?, a'a baba yazanyi filako agidanmu, nak'oshine kawai, to shikenan, yawajensu Maman taku?, lfy lau suke baba sunama gaisheku, a muna amsawa wlhy. Umar yamik'e to baba bara naje mugaisa da Inna natafi wajen nema. To Umaru ALLAH yabada sa'a kaji, ayitadai hak'uri da yanayin rayuwa, duk Wanda kaga yayi hak'uri baici ribaba to d'an kad'an yayi, duk abinda ALLAH ya albarkaci mutum dashi karya raina yace Alhmdllh, to insha ALLAHU ALLAH zaibasa mafiyinsa agaba kajiko?. To baba ngd sosai, ALLAH yak'ara yawancin kwana. Ameen Umaru ALLAH yayi albarka kuma. Amen summa ameen baba, naira 500 ya ajiyema baba, baba ga wannan asha fura. Kai a'a Umaru zoka d'auki kud'inka kaji, nikam bazan kar6aba, airik'e kankuma dakukeyi abin alfahirinmune basai kumbamu ko sisiba. Hhh baba Dan ALLAH ka kar6a kasamusu albarka, nima banisu akayi. To shikenan Umaru ALLAH yak'ara bud'i na alkairi ngd sosai. Babu komai baba Umar yafad'a yana ficewa daga d'akin. d'akin Inna yashiga, azaune yatadda ita tana jiransa, yasamu waje yazauna suka k'ara gaisawa da tambayar lfyar juna. Alhmdllh Inna sai godiyar ALLAH. To aii haka akesonji Umaru, wanekuma albishir aka kawo mini?. Murmushi yayi tareda gyara zama yazayyane mata komai tundaga jiya har safiyar yau. Farinciki sosai Inna ta Nuna harda kukan dad'i, tashi tayi tagad'oma baba shima yayi farinciki sosai, har d'akin inna yashigo yataya Umar murna da wanan k'yauta. Suna cikin farincikinsu saiga Asma'u tadawo hannunta d'auke da Leda. Itadai kallonsu kawai takeyi, data kasa jurewa saita ce inna wai miya farune kuketa murna haka?. Inna ta zayyane mata komai, itama sosai tanuna farincikinta akai, ya Umar kam sai antaya mata haarar yakeyi, ko a jikinta wai antsikari kakkausa. Bayan sun gama murnar yatashi yatafi akan zaidawo gobe yanuna musu motar. To d'an Albarka, ALLAH yayi albarka kaji. Ameen inna saina dawo......... Daganan sai gidan Anty sa'a, ita kad'ai yatarrar agidan Dan yara suntafi makaranta, tamik'e da k'yar saboda tsohon cikin dake jikinta, oh ni Umar dama kana duniya?. Dariya yayi ya ce, "Anty Sa'a ina zanje?, hidimomine kawai sukaimin yawa. Haka kuka iya kullum kaida Abubakar da Harris bakwa rasa uzuri aii. Tab Anty aii garani da wad'annan, kema kinsan ina k'ok'arin zuwa wajenki fiye dakowa agidanmu. Eh to hakane kuma, amma aii kaima wani lokacin saika 6ace 6at. 'Yar dariya yayi ya ce, " hakadai kikace Anty sa'a. Oh hakama zakace?, Anty sa'a tafad'a tana fita daga falon. Babu dad'ewa tadawo d'aukeda tire shak'e da kayan ciye-ciye. Da sauri Ya Umar yamik'e yatarota, kai Anty yakamata ki saukema kanji irin wad'annan aiyukan, ai kinyi nauyi dayawa. Zama tayi da dabara, shima ya ajiye tiren sannan ya zauna. Ta ce, "k'anina yazanyi, aii dole natashi nayima kaina, 'Yar mai aikin dake taimakamin kakarta tarasu taje gida tun shekaranjiya, jabeer da Laila kuma mizasu iyamin inbanda su 6ata. To da wannan Dan wannan kuma, amma gsky mata kuna bani tausayi matuk'a, koda rainon cikinnan kad'ai akabarku aiba k'aramin k'ok'ari kukayiba, balle ga haihuwa, raino, tarbiyya dukfa suna kanku, kai ALLAH yasaka muku da aljannadai. Amin d'an k'anina, Anty sa'a tafad'a tana dariya. Shima dariyar yayi yana kai kofin zo6o bakinsa, saida yasha sosai saboda k'aunarsa da zo6o sanan ya ce, "big aunty dawani daddad'an albishirfa nazo miki. Tofa k'anina ko ansami matar aurene?. d'an tsaki yayi ya ce, " Anty wane matar aurefa, aii aurena banan kusaba kuma dainamin zancensa. Umar kanka d'aya kuwa?, wai sokake saika tsofe agidane?, shekararka fa 28 yanzu, amma ace babu aure agabanka?. Hummm Anty sa'a kenan, Ku kawai auren kuke ambata, amma bakwa tunanin inda mutum zai ajiye matar, abinda zataci, Wanda zai mata sittira dakuma matsalolin yauda kullum musamman na rashin lafiya dakanzo tamkar ha6o. Hakane Umar amma aii duk ALLAH ne mai komai da kowa ko?. Hakane Anty ALLAH yasa mudace to, dama albishird'in nawa shine..................tas ya zayyane mata komai. Saboda farinciki jitake kamar tatashi taita tsalle, ta ce, "ALLAH sarki Umar kaga ribar hak'uri ko?, lallai yau nayi farinciki sosai, ALLAH yasa iyakar wahalar kenan. Amen Anty sa'a ngd. Sund'an dad'e suna hira sanan yatashi yaymata sallama yatafi. Daga nan aikinsa yatafi, yau cikin d'unbin farinciki yakeyin komansa har zuwa dare daya koma gida. Yaukam dawuri yakoma gidan Dan ana isha'i yakoma. Afalo ya iske mutanen gidan suduka, har yaya Abubakar yazo, suka gaisa Harris da su mufidama suka gaisheshi, mamadai ta had'e masa gabas da gamma, amma wanan bai hanashi gaishetaba. Kamar yafad'a musu saikuma yayi shiru da bakinsa, and'anyi hira ya Abubakar yatashi yatafi, shima Umar mik'ewa yayi yamusu sallama yatafi d'akinsa, ganin haka Harris ma yamik'e akabar mama da 'yan matanta.......... *_(((S)))........2017_* *_luv you all_*🤝😻. [11/23/2017, 4:57 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_Gaisuwa da fatan alkairi agareku, Action baby & Maman Khaleed, alkairin ALLAH yakai muku aduk Inda kuke, ALLAH yabar zuminci, INA alfahari daku😻😍❤👌🏼._* *_page→13-14_* ........washe gari Umar yay shirinsa, kamar yanda yasaba yalek'a ya gaida mama, dukda bata wani amsa masa yanda yakamataba amma hakan bai damesaba yamik'e yashiga d'akin Abba shima ya gaisheshi, baisake bin takan kowaba yafice abinsa sai gidan Alhaji. Yau har ciki mai gadi yabarsa yashiga da Babur d'insa, yananan tsaye saiga baby tafito yaudai tayi kwalliyarta sa6anin jiya dayasameta cikin kayan barci. Cikeda rangwad'a tak'araso garesa, Umar yajanye idonsa daga kallonta, Hii my guy, tafad'a tana dafa adaidaita sahun. d'aure fuska Umar yayi, ko kallonta baiyiba barema tasamu amsa. Abin ya6ata mata rai, amma saita dake, ta ce, "sorry Assalamu alaika. Sai yanzu Umar yajuyo fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce, " wa'alaikissalam. Murmuahi tamasa tareda fad'in dama haka kake babu sauk'i?. No bahaka bane, yadace duk inda d'iyan musulmi yashiga farko yafara sallama kafin yasamu damar aiwatar da Abu nagaba, ina fata daga yau zaki gane kuskurenki ki gyara. Tayi far da idanunta, cikin sanyin murya ta ce, "kayi hak'uri zan gyara insha ALLAH. Wani murmushin daya kasheta yamata, talumshe idanunta domin jin wani dad'i ya ratsa zuciyarta, bata dawo daga magagin shauk'in so ba muryarsa tadaki kunnenta......... Wai miye cikakken sunankine?, nasandai baby ba suna baneba...... Da sauri taware idanunta akansa, cikeda salo ta ce, "sunan Lubna." Shima maimaita sunan yayi a la66ansa, ya ce, "lubna!, nice name. Cikeda jin dad'i ta ce, "da gsk?. Kansa ya jinjina mata yana murmushi. Wani uban tsalle tayi Wanda yasakashi tsayawa kallonta, ngd ya Umar I love you wlhy. Umar kam yadaskare atsaye, mamakinta yakeyifa, tun jiya take ambatar kalmarnan akansa, amma yagaza gane inata dosa......... Muryar alhajice takatse masa tunaninsa, Umar kayi hak'urifa baby tacikaka da magana. Murmushi Umar yayi ya ce, "babu komai Alhaji aii muna gaisawane. Duk'awa yayi yana gaida Alhajin, Alhaji ya amsa yanamai kamasa ya tadashi tsaye, Lubna tazo saitin kunnen Dad d'inta tagaya masa wani Abu danima banjiba. Dariya dad ya ce, " baby da gsk koda wasa?. Dad serious wlhy, tarufe idonta. Masha ALLAH babyna ALLAH yatabbatar mana da alkairi, kisa aranki kinsameshi kinji, kanta tagyad'a tanamai farinciki, shidai Umar dabaisan miye zancen nasuba kallonsu kawai yakeyi. Tundaga Ranar Alhaji yad'ora Umar akan dukiyarsa, Umar ya ajiye daidaita sahu, yafara hawa motar da Alhaji yabasa, lokacin dayakaima su mama wannan zance mama tamkar zata goyashi Dan farinciki, tundaga ranar yazama d'an lelenta, komai Umar, duk wani motsinta Umar, abinci saiya za6a, idan yadawo daga kasuwa tayita nannan dashi tamkar wani jariri. Shi Umar ma wani Abu dariya take bashi damamaki. A6angaren kasuwa kuwa komai yaaa tafiya masa daidai saboda kasancewarsa mai ilimi, kullum cikin dabarar kasuwanci yakeyi Dan haka dukiyar Alhaji tak'ara bink'asa, ga Umar mutumne mai gsky da rik'on amana Dan haka Alhaji yake matuk'ar son Umar Fharuk. Umar yazama d'an gida sosai, bashida wani shamaki agidan Alhaji, ko ina shiga yakeyi, ahaka kuma soyayaya mai k'arfi tak'ullu tsakaninsa da Lubna, soyayya mai tsafta suke nunama juna. Umar kam komai yacanja masa yanzu, yafara zama babban mutum, ga d'inkuna na alfarma Alhaji namasa, duk motar dayaso hawa yake agidan Alhaji, gashi kowa sonsa yakeyi agidan. Ganin yanda abubuwa suke tafiya daidai Alhaji yabama Umar jarin kansa ya ce, "shima yajuya, amma duk da haka yana kula masa datasa dukiyar. Ubangiji mai hikima cikin k'ank'anin lokaci Umar yabunk'asa yazama babban d'ankasuwa abin kwatance, ga abokai masu kud'i daji da Kansu, kowa sonshi yakeyi, agidansu kam yazama shine babba, sai abinda yace, yamaida k'annensa makarantar kud'i, yagyara gidan tsaf tamkar bashiba, hakama inna binta bai mantataba, dakansa yacanjama Asma'u wata makaranta tafara zuwa, suma su Hasiya ya canja musu makaranta, dangi kowa yanacin amfanin Umar, mamako sai d'agawa da Nuna isa itama d'anta yazama wani Abu, zannuwa take sakawa masu tsadar gsk, harta canja k'awaye, komaidai zamzam. Ana cikin haka Alhaji yabashi damar turo iyayensa domin Neman auren Lubna. Sosai Umar yay murna da wanan batu Dan yana tsananin k'yaunar Lubna sosai, babu Wanda bai Santaba a family nasa, taje gidansu sau babu adadi domin gaida mama, har inna da Anty sa'a saida aka kaita ta gaida. Manya sun shiga ansaka ranar auren Ya Umar da Lubna watanni kusa. \\\\\\\\\\\\\\\\\\\\\\ Asma'u takalli 'yan uwannanta dasuka baje kayan alawa da biskit sunata rabo, baki ta ta6e tareda kauda kanta daga Kansu tacigaba dacin abincinta. Antu Saratu ta harareta, kekuma miye kike wani ta6ema mutane bakine?. Nifa yaya Saratu bance komaiba. Fatee dake 6are cingam ta ce, "yaya Asma'u kodai kina kishine?, Dan sainaga kamar kinason ya Umar. Kutttt, Asma'u tafad'a tareda jifan fatee da murfin kwano. Kaucewa fatee tayi tana dariya, suma 'yan d'akin dariya sukeyi duka, Asma'u tayo kan Fatee tana masifa, da gudu Fatee tafito Asma'u ta biyota. Gaf tayi karo da Abu, baya taja da sauri tareda dafe goshinta tana fad'in wash ALLAHna, abisa tsautsayi ta taka 6awon ayaba, aiko tazame suuuuu zata fad'i. Da sauri yaruk'o hannunta ta fad'o jikinsa, daddad'an kamshin turarensa ta shak'a ta lumshe idonta, saikuma tabud'e da sauri danjin antureta gefe. Ya harareta kewai bakida Kaine?. Idanunta ta kwalalo waje, saikuma tahau kakka6e jikinta tana wani had'e fuska, yakatseta da fad'in ina hankalinki yatafi?. Saida tad'an murgud'a bakinta amma bai ganiba sannan ta ce, " yana jikin...... Bata k'arasa fad'aba ta hango fatee, dagudu tawucesa tabi Fateen suka afka d'akin inna. Girgiza kai Ya Umar yayi shima yanufi d'akin. Afalon yatarar dasu suna zagaye kujeru, hasiya da Anty Saratu sunata tuntsura dariya, cikin dariya Anty Saratu ta ce, "wlhy Ma'u kifad'i gsky, Dan nima nadad'e ina zargin soyayya kukeyi da ya Umar, kumafa wlhy kun dace, kardai ki cuci kanki, kifad'a sai'a had'a masa biyu kawai. Dan ALLAH Anty Saratu kibari, ALLAH zakusa nakuma TSA....... Bata k'arasaba ta hangi ya Umar tsaye abakin k'ofa, mak'alewa maganarta tayi amak'oshi. Suma duk kallonsu Yakoma kansa, yak'araso d'akin shima, guri yasamu ya zauna suka gaisa, ya ce, " innafa?. Inna tana gidanku aii tunda safe. Ayya aiban saniba, dayake badaga gidan nakeba. Ruwa Hasiya takawo masa da zo6o, zo6on yasha Dan yanaso sosai, domin shima Inna takeyin zo6o ta ajiye . Asma'u kam d'aki tashige, tana shiga hawaye suka fara bin kumatunta, tabbas son Yaya Umar na neman illata mata zuciya, tadad'e da d'umbin sonsa azuciyarta tun tana karama, haka taketa dakonsa, saboda alkunya irinta 'ya'ya mata Hausa Fulani dakuma tsoronsa Dan tuni ta lura ya Umar kam haushintama yakeji, wannan yasa take dannewa da k'ok'arin ciresa aranta, amma hakan na Neman gagara. Ashe duk k'ok'arin danne zuciyarta da takeyi akan ya Umar 'yan uwanta harsun fara fahimtarta?, ya ALLAH ka kawomin agaji akan wannan lamari, idan ya Umar mijinane ALLAH ya karkato da hankalinsa kaina, idan kuma ba mijina bane ya ALLAH kaciremin sonsa azuciyata na hak'ura da zayyan d'ina, daya dawo muyi aurenmu..... Share hawayen fuskarta tayi da sauri danjin muryar ya Umar na kwala mata kira. "Husna!." "Husna!!." Lumshe idanunta tayi sannan ta amsa, shikad'aine yake kiranta da Husna, shiyyasa takanji sunan daban kamar ba nataba. Asanyaye tafito, yana tsaye a bakin k'ofa da alama fitama zaiyi, kallo d'aya tamasa ta kauda kanta, tad'anje nesa dashi tashaya kamshin turarensa na bugun hancinta, shima idonsa akanta yamik'a mata kud'i yana fad'in da safe kije gidan matar Yousif kikaimata ta ajiye masa, saura kuma idan kinje ki kai dare. Saida ta tura baki gaba sannan ta kar6a, yamik'a mata d'ari biyar na mashin, nanma kar6a tayi, baijira cewartaba yafice. Da harara tarakashi, tajuyo cikin falon tana k'unk'uni. Anty Saratu dasu Fatee suka shek'e da dariya harda tafawa suna fad'in soyayya ruwan Zuma. Asma'u bata kulasuba tashige d'akin inna domin ajiye kud'in............ *_(((S))).......2017_* *_Luv you all😻🤝 ._* [11/25/2017, 5:37 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_masha ALLAH, ALLAH yasauki k'awata Ayusher Muh'd lfy, ya azurtata da samun haihuwar baby gal, Ubangiji ALLAH yaraya mana ita akan turbar musulinci, ALLAH yasa Bad'i mudawo sunan twin's kuma_*😻😜 *_page→15-16_* ............Shirye shiryen biki ya kankama sosai, ya Umar yagama gyaran gidansa tsaf, gidane na garari Wanda za'a iya kira namai kud'i, kowa yagani dolene ya yaba Dan gidan yaginu babu k'arya. Agidansu amaryama shirin biki akeyi na 'Yar gata Dan wannan shine karo na farko dazasu aurar, komai na 'yan gata aka shirya, damma mahaifiyarta batason auren, Dan taso ace lubna ta auri d'an shahararren mai kud'i irinsu amma ba Umar ba, to amma babu yanda zatayi tunda takafe shitake so. Mama kam wannan aure yamata dad'i d'anta zai auri d'iyar masu kud'i, sai d'agawa da fariyya takema 'yan anguwa. Asma'u tunda aka fara shagalin bikinnan tashiga matsanan ciyar damuwa, amma haka tadage da addu'oi harda azumi tana addu'ar ALLAH ya danne zuciyarta tazama mai hak'uri, inna tana kula da duk halin da Asma'u tashiga amma babu yanda zatayi saidai ta taya d'iyar tata da addu'a tunda haka ALLAH yatsara lamarinsa. *_biki buduri_* Ansha biki na nunawa a duniya Dan taron d'aurin aurene daya halarci manya-manyan masu fad'a aji ak'asarnan, sarakuna, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, harda shugaban k'asa, lamarin bak'aramin girgiza Ya Umar yayiba, Dan baita6a zaton ko kansilan anguwarsu zaizo d'aurin aurensaba bare shugaban k'asa gaba d'aya. Biki kam saidai Sam barka Dan nera tayi kuka sosai. Bayan biki amarya da ango ansha amarci babu k'arya, sosai suke zuba soyayya kamar babu gobe, saida ya Umar yay sati biyu baya fita kasuwa, koda yaushe yana gida manne da lubna, abinci saidai suje su sayo. Tsawon wata d'aya ana kashe kan amarci, amarya babu abinda takeyi dagaci sai barci, komai saidai 'yan aiki, wani lokacinma ya Umar keyimata wankan, abinda yafara 6ata masa rai da ita shine son jiki, komai saidai ayi mata tana a kwance, daidai da ruwan dazaisha saidai tasaka 'yan aiki sukai masa, gyaran d'akinsama haka, wani abin k'arin haushinma shine duk sanda zaidawo gidan saidai ya Tatar da ita shame-shame kwance 'yan aiki namata tausa, wannan lamari na 6ata masa rai matuk'a. Daya kasa daurewa yafad'ama mama saitace yacika k'orafi shikam, ya yarinya tatashi cikin Hutu yanzu zai k'ok'arin tsinke mata, itafa bata yarda ko fad'a yaringa yima Lubna ba, abin ya6ata masa rai, yarasa wane irin haline da mahaifiyarsu?, haka yabar gidan ransa a6ace. ////////////////+//////////// A6angaren Asma'u kuwa abubuwa sun mata sauk'i, tanata k'ok'arin cire ya Umar azuciyarta, tamaida hankalinta sosai akan karatu babu wasa, burinta bai wuce Zayyan d'inta yadawo suyi aureba. Ana haka Lubna ta fara laulayin ciki, zazza6i da yawan amai sun addabeta Dan haka ya Umar yakaita asibiti, gwaji farko akace cikine. Cikin tashin hankali lubna ta ce, "doctor jafar cikifa kace?". Dariya Doctor jafar yayi, ya ce, " hakane lubna kina d'aukeda babynmu. Afusace takalli ya Umar da farinciki yacika zuciyarsa shima zai zama baba, ta ce, "Umar kanajindai abinda doctor yafad'a aii?. Murmushi ya Umar yayi yarungumota zuwa jikinsa yana fad'in naji sweet d'ina, kuma inacikin farinciki...... Bai k'arasaba ta fisge jikinta daga nasa, ta6d'i jan Umar wlhy bazata sa6uba, yaza'ayo kamarni 24year's ace inad'aukeda ciki, lallai akwai lale awannan batun. Cikin mamaki ya Umar ya ce, " Lubna akwai lale kamar yaya?, wannan ba abin farinciki bane?. Abin farincikine agareka Umar, ammani abin kunyane da bak'inciki agareni, ace kamarni beby wata hud'u da aurena aganni da ciki, haba saikace dai wata akuya, asaima k'awayena sumin dariya wlhy. Daga ya Umar har doctor jafar kallonta sukeyi cikeda mamaki, ya Umar ya kwantar da murya cikin Nuna damuwa ya ce, "haba Lubna miye abin kunya ga samun k'yautar ALLAH?, kitunafa akwai dubunmu dasuke nema amma ALLAHA bai basuba muyabamu, bakuma dan munfisu agurinsa bane, a'a ikonsane yasa yabamu sukuma baibasuba, amm....... Hannu tad'aga MASA cikin masifa ta ce, " kaga Umar Dan ALLAH sauraramin da wannan wa'azin naka mana, nifa nace banason ciki yanzu, danhaka saikasan yanda zakayi dani, ban shirya rainon cikiba ayanzu kuma babu mai tursasani nayi. Ran ya Umar yafara 6aci, Dan haka afusace shima ya ce, "to wlhy Lubna babu mai zubarmin da ciki, dukma abinda zakiyi saidai kiyi, yamik'ama doctor jafar hannu sukayi musabaha, abokina ngd, yadaka mata tsawa dallah malama tashi muwuce. Mik'ewa Lubna tayi Dan tsawar Umar d'in ta razanata sosai Tundaga wannan ranar zamansu yafara rawa, kullum cikin fad'a da tashin hankali, abin kamar wasa har yakaisu ga zuwa wajen iyaye, mahaifiyar Lubna ta goyi bayan lubna ta zubda ciki, amma mahaifinta ya hana, sosai lamarin ya6ata ran Lubna, tundaga wannan lokacin komai ya canja musu, shidai yana nuna mata kulawa sosai da tattali, duk abinda ta ce, "tanaso zai saya matashi, ga cikin NATA da saka shagwa6a, tattalin dayake nuna mata yasakata sakin jiki itama ta manta da komai suka koma zuba soyayyarsu, mama bata had'a sati d'aya batazo gidanba ganin Lubna. Ahaka cikin lubna yashiga watan haihuwa, kuma Yakama lokacin hutunsu Asma'u suna gida. Ya Umar yaje ga inna tabashi Asma'u danta taya Lubna zama tunda tace bataso akawo mata kowa, dayace to yad'akko Asma'u?, saitace ta amince zata zauna da Asma'u Dan mutuniyarta ce. %-%-%-%-%-% Tunda Asma'u tazo saita raina tsaftar matar gidan Dan bawani zuwa sukeyi sosaiba, batayi k'asa agwiwa ba tace duk 'yan aikin su huta tazage sosai tagyara gidan har d'akin ya Umar ko INA yad'au k'amshi, takuma shiga kichin tamusu abinci mairai da lafiya. Lubna dakebin Asma'u da kallo ta ce, "lallai sunnunki da k'ok'ari, wai bak'yajin ciwon jikine?. Dariya Asma'u tayi tareda fad'in wlhy aunty Lubna banajin komai, aiini ban d'auki aikin gidannan aikiba, idan dawani bayan wannan tom zanyi kuma natashi garau. Baki luban ta ta6e tace lallai wahala da rai. Asma'u batace komaiba saidai dariya. Da ya Umar yadawo tun a harabar gidan yaga canji, yashigo falon shima cikeda mamaki yakebin ko ina da kallo, Asma'u dake zaune tana kallo tamik'e tana fad'in sannu da zuwa ya Fharuk. Kallonta yayi ya ce, " yauwa Husna sannunki, Lubna kam ko kallo bai ishetaba tana zaune turus ak'asa, ya Umar yak'arasa gareta yana murmushi, rungumota yayi had'eda manna mata kiss akumatunta, Uwar biyu ykk?. Fuska ta yatsine masa tana wani kumbura Baki, kacefa yanake tunda kahad'ani da aiki, murmushi yayi acikin kunnenta ya ce, "aitare mukayi bani kad'aiba ko?, bare amin d'agwaiy, dukan wasa tamasa ak'irji, yatashi yana dariya, daidainan Asma'u tafito daga kichin d'aukeda k'aramin tire tad'ora ruwa da lemo da cup, ganin yamik'e ta ce, ''ya Fharuk ga ruwa. Kallonta yayi acikin wani yanayi, tunda yay aure ba'a ta6a akawo masa ruwaba ayayin daya dawo gida, wani lokacinma saizaici abinci za'a bashi kokuma ya rok'a, kansa ya jinjina mata yakoma ya zauna, Asma'u ta tsiyaya ruwa ta mik'a masa, kar6a yayi tareda bismillah yasha, Lubna ta ce, " Asma'u kedai bakya gajiya, yanzunan k'ato dashi saikin kawo masa ruwansha?. Kallonta kawai Asma'u tayi amma bata iya furta komaiba, shimadai ya Umar zuciyarsa ta sosu da maganar ta Lubna amma saiya share yamik'e bayan yagama sha, d'akinsa yashiga danya rage gajiya, Kallon ko ina yakeyi cikeda sha'awa, yasan wannan aikin Asma'u ne Dan matarsadai bata iya komaiba sai addabama 'yan aiki, dawad'annan tunane-tunanen yay wanka yashirya sannan yadawo falon, inda yabar Luban nan yasameta da wahalallun 'yan aikinta suna faman mata tausa, harya zauna Asma'u ta ce, "ya Fharuk ga abincifa. Kallonta yayi saikuma ya kauda idonsa, ya ce, " yaushe kika iya abinci?, idanu Asma'u ta kwalalo danjin rainin hankalin mutuminnan, saikace yau yafara cin abincinta, tad'an murgud'a baki sannan ta ce, "aibani nayiba Anty Lubna CE. Da sauri ya kalleta, saita kauda idonta, ya jinjina kansa Dan yagane bak'ar magana tamasa, itako Lubna saita washe baki tana fad'in a'a kedai kikayi abinki, ni inani ina aikin wahalarnan, my Honey kaje kaci wlhy akwai dad'i sosai dantafi kuku iyawa, nidama zata dawo nan gidan danaso haka.. Kallonta kawai yakeyi cikeda al'ajabi amma yagaza furta mata komai, saida ya mula Dan kansa harma Asma'u tayi fushi sannan yasakko k'asa Dan bayacin abinci a dinning, Asma'u tajere masa komai tazuba masa, aii mutuminku dayayi cokali d'aya saida ya lumshe idanu, sosai yakejin dad'in abincin, wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa ya d'akko Asma'u ta zauna dasu. Tundaga ranar komai Asma'u takeyi agidan, tazama tamkar itace matar gidan, kwananta takwas dazuwa Lubna ta haihu 'yan biyu duk mata, wayyo zokaga murna wajen ya Umar da sauran dangi harma da family d'in Lubna, ranar suna yara sunci sunan mama da momyn Lubna, wato Maryam da Haleematu, za'a ring a kiransu Amrah da Afrah. Bayan suna dakamar sati biyu su Asma'u suka koma makaranta, Dan haka ta tattara ta koma gidan d'aukeda shatara ta arzik'i daga Lubna da Ya Umar............... *_(((S))).....2017_* *_Luv you all_* [11/26/2017, 4:48 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* _masu karatu karfa Ku rikice, har yanzu muna cikin tunanin Asma'u ne_. *_page→17-18_* .........Shekaru sun shud'a sosai Dan su Asma'u harsun kammala s,s,c,e d'insu, amma haryau Zayyan bai dawoba, abin yana damunta, hakama iyayenta, gashi bata kula kowa Dama saishi, iyayenta sunso Sumata aure tunda ta kammala secondary amma hakan ya gagara, suna zaman jiran dawowar Zayyan, a haka Asma'u takusan cinye shekara agida. Ranar ya Umar saiyazoma Inna da shawarar mizai hana Asma'u takoma makaranta da wannan zaman?, idan saurayin nata yadawo koda tana karatunne sai ayi auren tacigaba agidan mijinta. Da farko inna da baba sunk'i, amma ya Umar yadage da nuna musu fa'idar karatun sai suka amince. Babu 6ata lokaci yafara nema mata makaranta, dandanan kuwa aka samu Dan yanzu su Yaya Umar sunzama manya, komai shine yayi mata, tafara zuwa makaranta nan FCE kano. ___________________ Agidan ya Umar kam abubuwa na tafiya daidai, yaranshi sunyi girma ko ina zuwa sukeyi, ga surutun tsiya abakinsu, soyayakam shida matarsa sai abinda yay gaba, hakama danginsa kowa sonsa yakeyi tamkar ya goyasa musamman mama da kawu kabiru, ga abokaimadai hakane, abokai gareshi tamkar tsiya, shikansa yana mamakin wasuma a ina ya sansu?, 6angaren kasuwarsa saidai godiyar ALLAH, kullum k'ara cigaba yakeyi, yabud'e babban super market akasuwa, komai kashiga zaka samu awajen, tundaga suturu akwai 6angarensu, kayan kwalliya, kayan mak'ulashe, kayan abinci, kayan d'inki, kayan wuta, kai harsu wayoyi dukzaka samu, ya bunk'asa sosai, gashi yabuga musu wani k'aton gida na garari mai 6angare buyu, tuni Lubna tarud'e da tambayar d'ayan 6angaren nawaye?. Ya ce, "mata na yarane, idan sunyi girma can zasu koma, hankalinta yad'an kwanta amma ba sosaiba Dan bata yarda dashiba ko kad'an. Rayuwadai ta shud'a sosai, hargasu Asma'u sun kammala karatu na tsawon shekara uku, tafito da result mai k'yau, masha ALLAHU Asma'u tazama cikakkiyar budurwa mai kimanin shekaru 22 Aduniya, har yanzu bata kula kowa wai tana jiran Zayyan, amma k'ark'ashin ranta tana mak'ale da son ya Umar har yanzu dan dai babu yanda zatayine, ayanzuma ganin take yamata nisa fintin kau danya zama babban mai kud'i matashin maiji da kansa, tako ina ya Umar yagama had'ewa gashi da d'abi'u irin na manya wad'anda suke matuk'ar k'ara masa kwarjini a idon jama'a. Ayanzukam bak'aramin bud'ema Asma'u wuta su inna sukayiba akan ta fidda miji, hankalinta yakai k'ololuwar tashi, idan tana kuka saidai su Fatee suyita lallashinta da bata baki. Ana cikin haka saiga Zayyan tamkar an jehoshi, Asma'u tayi farinciki mai yawa, amma daga baya tayi kuka harya kaita ga kwanciya asibiti saka makon maganar da Zayyan yazo mata dashi mai ratsa zuciya. Lokacin da Zayyan yazo Asma'u tafito bayan ya aika kiranta, batayi zaton shibane Dan haka tafito cikin fushi, yayinda tayi tozali da Zayyan yaci wani uban wanka yana jingine da motarsa saita rikice Dan farinciki, cikeda zumud'i tak'araso garesa tana fad'in zayyan da gsk Kaine?, kokuwa mafarkin Dana saba yine?. Zayyan yad'ago yana kallonta babu yabo babu fallasa, tun anan jikin Asma'u yayi sanyi Dan ganin halin ko in kula da Zayyan ya nuna agareta, jiki a sanyaye tace sannu da zuwa, bai amsaba amma yamik'a mata IV. Cikeda mamaki ta amsa tanamai Kallonsa, tayi k'arfin halin fad'in zayyan wannanfa?. Yatsine fuska yayi ya ce, "IV d'in aurenane nanda kwana 30 kacal, kiyi hak'uri tunda natafi ban sake nemankiba, wlhy nayi gamon katarne da tsaleliyar budurwa a can yayin karatuna, gata 'Yar masu kud'i, ke idai tak'aice miki ta kereki a komai na rayuwa, tun shekara uku dasuka wuce nadawo k'asarnan ALLAH bai bani ikon zuwaba saiyau, naga kuma bai daceba ace ansha bikina baki saniba shiyasa nakawo miki katin gayyata, nabarki lfy... Yana gama fad'a yashige motarsa yabar anguwar tareda bud'a mata k'asa. Ai Asma'u saikawai tayanke jiki tafad'i, ya Umar ne dayazo gaida inna yaganta kwance ak'ofar gida, da farko masifa yafara mata amma dayaga bata koda motsi sai tsoro yakamasa, yagirgizata amma shiru kakeji, anahaka saiga baba dasu hasiya, arikice suma suke tambayar lfy kuwa?. Nima wlhy baba ban saniba, a haka na Tatar da ita, dasukaga magana bazata musuba suka kwasheta sai asibitinsu Dr jafar. Natak'aita muku zance saida Asma'u tayi kwanta biyu assume sannan ta farfad'o, tashin hankali kuwa ba'a maganarsa wajen family d'inta. Bayan kamar sati d'aya Asma'u tadawo daidai aka tambayeta sanadi?, tafad'i yanda sukayi da Zayyan. Ransu inna ya6aci matuk'a harya kai ga inna tasamu ciwon hawan jini itama, ga Asma'u jikinta yak'i dad'i yauda lfy gobe babu. Wannan 6acin ran yasa ya Umar cewa ad'aura masa aure da Asma'u kafin ranar d'aurin Auren Zayyan. Kowa yayi na'am da wannan batu a family, Dan haka bayan kwanta uku da faruwar haka aka d'aura auren Asma'u da ya Umar batareda tasaniba, saidaga bayan shima ba'a fad'a mata mijinba. ____________________ Hummm randa wannan lamari yafaru ya Umar yaga tsantsar tashin hankali agidansa, Dan Lubna tamkar zata kunna musu wuta su k'one, zage-zage da tsine-tsine dangin ya Umar sunshashi, tundaga ranar zaman lfy ya k'aura agidan, bayan kwana Uku Asma'u ta tatare agidan Dan ba'ayi wani shagalin bikiba, amma dukda haka saida abokansa suka shirya musu denner, bayan kawo Asma'u aka halarci wannan denner wadda ta tata hankalin Asma'u dataga waye aka aura mata amatsayin miji na har abada, shin murna zatayi kokuwa bak'inciki?, batada za6in ko d'aya sai aikin kuka a 6oye har aka tashi denner, daganan kowa yakama gabansa, ya Umar Yad'auki Asma'u suka tafi gida, har 6angarenta yarakata, suna shiga yajuyo batareda yace da ita uffanba. 6angaren Lubna yadawo Inda yatarar da shika-shikan bala'i Dan ranar kwana sukayi babu barci harya shashshek'a mata mari biyu, taci kuka sosai tamkar ranta zai fita. A6angaren Asma'u ma bawai barcin tasamuba, kwana tayi kuka ita kad'ai. ____________________ Tsawon kwana uku Sam babu zaman lafiya agidan Yaya Umar, Lubna ta tada hankalin kowa agidan, adaren kwana na hud'u kuma wani tashin hankalin yazoga ya Umar customs suka rik'e masa kaya babu gaira babu dalili, ya Umar yarasa inda zai saka kansa, yabi duk wata hanyar daya dace kayansa su k'u6ta abin ya gagara, haka ya hak'ura, ba'a k'ulla wataba ranar aka wayi gari kuma wai shagonsa yayi gobara komai ya k'one ba a mori komaiba, wannan tashin hankalin ne yahad'u yayma ya Umar yawa, komai yazo yak'are, har aka koro masa yara daga makaranta, yazo ya saida gidansa, ga kowa ya gujesa ciki harda matarsa Lubna, ammasa k'arfa-k'arfa akan 'ya'yansa, hargashi da tsintar kansa agadon asibiti batareda ya shiryama kansa hakanba. _______ _______ _____ *_Mun dawo labari_* Firgigit Asma'u tadawo daga tafiya dogon tunaninta na tsawon shekaru dasuka shud'e abaya, takai dubanta ga agogon dake d'akin karfe 2:47am, idanunta tazaro tana mai mamakin doguwar tafiya datayi atunani batareda tasan dare yayi nisa hakaba, ahankali tasauke idonta akan ya Umar dake barci, fuskarsa tayi fayau, ya k'ara haske dukda kasancewarsa bak'i sosai, yarame sosai sai dogon hanci, tashare hawayen dasuka cika mata fuska sannan tamik'e, bayin dake d'akin tashiga kasancewar ya Umar kad'ai aka kwantar aciki Dan baya buk'atar hayaniya, alwala tayo tazo ta shimfid'a sallaya tayi nafilfilinta tareda karatun alkur'ani mai girma, tayi addu'oin samun lafiya ga mijinta sosai sanan tashafa ta kwanta awajen saman sallayar barci yay awon gaba da ita........... *_(((S)))......2017_* *_Luv you all my sweet Fan's_* [11/27/2017, 5:23 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→19-20_* _Washe gari_ Amakare Asma'u ta tashi kasancewar bata kwanta da wuriba,, ta tashi da addu'a abakinta, ganin yanda haske ya gauraye d'akin yasata zaro idanu waje, ta kalli agogo k'arfe 7:06am, zummbur tatshi Dan gabatar da sallah, agaggauce tayi sallar, tana idarwa saiga doctor Al-Ameen ya shigo, suka gaisa ya tambayeta mai jiki?. Da sauk'i doctor, Asma'u tafad'a tana d'an murmushi. Shima murmushin yayi ya ce, "Alhmdllh, yad'an duddubashi sannan Yakuma kallon Asma'u, Hajiya insha ALLAHU nanda awa d'aya zuwa biyu zai iya farkawa. Alhmdllh doctor, mungode sosai. Karki damu hajiya, mugodema ALLAH kawai, fita yayi. Ita kuma ta tsurama ya Umar daketa barcinsa idanu cikeda shauk'in so. _ya Umar bak'ine kuma k'yak'yk'yawa masha ALLAH, bazamu kirasa dogoba haka kuma ba gajere bane yana dai tsaka tsaki, yanada cikar hallita mai k'yawun haiba dan bai kasance siririba, yanada d'an jikinsa dai-dai misali, mutumne mai yawan hak'uri da kawaici, bakomaine abin magana awajensaba, bashida yawan hayaniya amma akwai yawan fara'a ga wanda yasani, bayason raini arayuwarsa, yanadason 'yan uwansa da mahaifiyarsa, so ya Umar dai yakai akirasa cikakke kuma nutsatstsen namiji abinson kowace mace._ Asma'u tasaki wani k'asaitaccen murmushi Wanda batasan tanayiba, gsky tana bala'in son ya Umar, harma tana ganin tafi kowa sonsa aduniya..... Da sauri tad'ago danjin an dafa kafad'arta, Rafi'a tagani, sukaima juna dariya, Rafi'a ta ce, " haba Anty Asma'u irin wannan tafiya haka?, ya Umarfa nakine. Murmushi Asma'u tayi, ta ce, "wai yaushe kikazone?. Nakai Minti biyar akanki wlhy, amma ko kad'an bakisan da shigowataba, kina cikin shauk'in so. Kai wai Rafi'a yaushe kika koyi rashin kunya ne?. Hhhhh daga fad'ar gsky auntynmu, wai ni inama Anty Lubna ne, kobatasan bashida lfya bane?. Wlhy Rafi'a ban saniba nima, rabonta da gidan tun washegarin randa kukaje datazo itada iyayenta. Tofa ALLAH ya k'yauta, kardai ace itama butulcin zata masa?. Asma'u ta ce, "Hmmm Rafi'a kenan, aii mutanen duniya sun wuce yanda kike tsammaninsu wlhy, yanzu jiya kinsan kuwa mina Tatar a asibitinnan bayan dawowata daga saida waya?, bakiga mun canja likitaba?. Nagani, kuma tunjiya naso tambaya amma tashin hankalin halinda ya Umar yake ciki ya hanani tambaya, miya farune?. Asma'u tashare hawayen fuskarta sannan ta ce, " lokacin Dana dawo a waje na tadda su ya Umar, makwafcinmu ya tallafesa yana kwance ak'asa, da hanzari nak'arasa garesu Dan azatonama ya Umar ya rasune, cikin kid'ima na tambayi koya mutu?." Makwafcinmu ya CE, "a'a da ransa, wai Doctor jafarne yafito dasu waje saboda mun dad'e bamu dawoba. Kaina kawai na jinjina Dan bak'incikinsa bashine agabanaba, lfyar ya Fharuk nake dubawa, na ce, " babu damuwa mu maidashi nasamo kud'in. Dak'yar ya Fharuk yad'agamana hannu alamar a'a karmu maidashi, na marairaice murya INA fad'i haba ya Umar daka dai daure mun maidaka tunda lfyarka Muke nema..... Makwafcinmu ne yakatseni da fad'in gaskiya Hajiya koni ban goyi bayan hakaba, Dan bakiga wulak'anci da cin zarafin da likitancan yamanaba, mutane sukaita kallonmu, dazaki amince akwai wani d'an uwana shima likitane anan dasai na kirashi. Da Saudi nace kirashi kawai. Bayan yakirashi babu dad'ewa saiga Doctor Al-ameen, cikin mamaki ya ce, "wannan ba Alhaji Umar bane?. Mukace shine, agaggauce makwafcinmu yabashi labari, ran doctor Al-ameen ya 6aci matuk'a, babu 6ata lokaci yasa aka kawo gadon d'aukar Mara lafiya aka d'auki ya Umar, namatsa kusadashi INA MASA godiya, na ce, " ammafa bamu biya kud'in komaiba. Harya fara tafiya yajuyo gareni ya ce, "haba Hajiya aiba kud'i yakamata mufara damuwa dasuba lfyarsa, kije ki ajiye mufara fuskantar matsalarsa, wlhy Rafi'a har kukan dad'i nayi danjin furicin likatannan. Rafi'a ta share hawayen fuskarta itama ta ce, " ALLAH sarki ya Umar kana ganin rayuwa, bakomai ALLAH yana tareda masu hak'uri aii, ALLAH yabaka ikon jurewa. Asma'u ta ce, "Ameen dai Rafi'a. Rafi'a ta ce, "ga abinci nan inji mama. Wayyo mama munsata aiki. Baki Rafi'a ta ta6e ta ce, " kebar Maman nan itama haushi take bani, inaji inama ace ba ita ta haifemub...... Da sauri Asma'u ta rufe bakin Rafi'a, a'a karki fad'i haka Rafi'a, duk lalacewar mahaifi mahaifine, mubita da k'yak'yk'yawar addu'a kawai kinji. Rafi'a batace komaiba saima hawaye dasuka cika mata idanu. _Bayan 3h..._ Zuwa sannan asibitin yacika da dangi,harsu inna sunzo, amma duk doctor ya tsaidasu awaje Dan yana saran farkawar Ya Umar. Cikin ikon ALLAH kuwa agogo na nuna k'arfe 10:00am sai ya Umar yafarka, dagashi sai Harri's a d'akin Dan Asma'u taje gida tayi wanka, cikin gaggawa Harris yafita zuwaga likita, yana sanar masa suka iso tare, bak'aramin farinciki Dr Al-ameen yayiba Dan ganin Ya Umar ya farka cikin hankalinsa, Dr al-ameen yad'an k'ara duddubashi sannan yafito yasanarma su mama. Gaba d'ayansu suka shiga d'akin ya Umar na zaune jingine jikin gado, mama tazauna akusadashi tareda kamo hannunsa ta ce, "Umarina sannu kaji?. Murmushi yamata, Dan bayason yin magana, suma su Rafi'a, Anty sa'a, Anty Saratu, inna, mufida, hasiya, Fatee dadai sauran 'yan uwa suka shiga yimasa sannu, kansa kawai yake iya d'aga musu, aransa ya ce, "ko ina wannan yarinyar?.'" Bayan kamar minti talatin doctor yashigo ya ce, "suyi hak'uri sukuma bashi waje ya huta, duk fita suka kumayi akabar Harris kad'ai, doctor ya ce, " kataimaka masa yaje bayi danyayi wanka sannan yaci abinci yasha magani. To doctor mungode sosai. Doctor nafita Harris yataimakama Ya Umar yarakashi har cikin bayi, saida yaji yafara wankan sannan yafito waje indasu inna suke. Babu dad'ewa Asma'u tadawo, abinda tafara tambaya shine ya Fharuk yatashi?. Mufida tayi dariya, ta ce, "Asma'u amaryar ya Umar, yatashi yana nan zaune kekad'ai yakeson gani. Fuska Asma'u tarufe tana dariya, ALLAH yasoma mama da inna sunacan zaune agefe su kad'ai, Anty sa'a ta ce, " jeki kigansa kinji ma'u, k'yale Mufida. Ba musu Asma'u tashiga d'akin, babu kowa Dan haka ta kakka6e gadon tagyara sannan tazauna jiransa. Tana nan zaune aka bud'e k'ofar bathroom d'in, d'ago idanunta tayi sai suka had'a ido da ya Umar, tai saurin kauda kanta Dan ganinsa dagashi sai tawul, cikin tafiyar mara lfy dabayajin k'arfi yak'araso kan gadon, saida ya zauna sannan ya kalleta, kanta ak'asa ta ce, "ya jikin?. Kallonta yakumayi tareda fad'in da sauk'i, yayd'an tsaki wai ina Harris d'in?. Asma'u ta ce, " yaje gida yadawo." Shiru yayi, zuwacan kuma ya CE, "sakama k'ofarnan key zan shirya kar wani yashigo, jikin Asma'u a sanyaye tamik'e amma saita fara k'ok'arin fita, ya ce, " ina zakije kuma?. Uhmm dama zanjiraka awaje, idan ka kammala saina dawo, yad'an d'aure fuska sannan ya ce, "dawo. Babu musu Asma'u tadawo tazauna inda take ada. Man shafawa yamik'a mata, kar6a tayi tana mai satar kallonsa, duk yayi wani cid'in-cid'in da fuska, ya ce, " d'an shafamin mannan hannuna duksunyi sanyi saboda k'arin ruwa.. Yanda yake magana a cikunshe babu alamar wasa yasa Asma'u mik'ewa da mai ahannnunta, ta lakata amma saitata murzashi Dan takasa ta6a jikinsa, ganin yanda taketa mulmula man takasa ta6ashi saiya mik'a mata hannunsa, cikeda kunya tafara shafa masa, jitake tamkar k'asa tatsage tashiga ciki Dan kunya, shikam gogan naku ko a jikinsa shi dad'inma shafa man yakeji, jiyake tamkar tana masa tafiyar tsutsa, idonsa a lumshe harta gama. Tashi yayi yana shiryawa, Asma'u kam tazauna kanta ak'asa. Saida yagama shiryawa sannan tajawo kulolin abinci tazuba masa, yana zaume yana kallonta harta gama, tad'ora masa filet d'in abincin a bak'in gado, shiru yayi bai d'aukaba baikuma yi maganaba, ganin haka yasa ta ce, "ga abinci. Fuska ya yatsine dawane hannun zanci?, nacemiki hannuna yanamin ciwo. Cikeda mamaki take kallonsa, wannan wane irin sabon salone daga ya Umar kuma?, yana nufin itace zata bashi abincinma?....... Yakatsemata tunani da fad'in jeki kiramin mama ko inna subani tunda ke bazaki iyab..... Bata bari yak'arasaba ta d'auki abincin tamatso tana bashi, yanda take basa abincin takasa kallonsa saita bashi dariya, amma baiyiba yadaure ya gimtse, tana cikin bashi abincin aka kwankwasa k'ofa, tashi tayi taje ta bud'e, su mamane da matan anguwarsu sunzo dubashi. Babu kunya yamik'ama Asma'u filet d'in abinci wai tacigaba da bashi, wayyo ALLAH Asma'u tamkar zata fasa ihu, babu yanda zatayi tacigaba da bashi harya k'oshi, tazuba ruwa a cup tamik'a masa, yanzudai kar6a yayi yasha da Kansa........... *_Luv you all_* *_(((S)))......2017_* [11/28/2017, 3:27 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *Amma saga yau na sakad'a Xoxo da hajja ce & zeety, 🤔kona had'a da Rano?, umm baradai nabarta kawai.*🤥 _muhud'u writer's Asso..... Kenan._😜😂 *_page→20-22_* ..........Alhmdllh jikin ya Umar yana yin k'yau, yaji sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba. Dangi kam balaifi suna d'an zuwa ganinsa, musamman wad'anda zuciyarsu bata manta da d'umbin alkairinsaba sanda yakeda kud'i. 'Yan uwansa dai suna mamakin rashin zuwan Lubna asibitin, kuma duk Wanda ya tambayesa saiyayi kicin-kicin da fuska alamar baya buk'atar maganar, ganin haka kowa ya daina tambayarsa Lubna. Yauma duk suna asibitin har kawu kabiru da babansu Asma'u, 'Yar hira akeyi da raha irinta family idan an had'u, ya Umar kam shiru baya cewa da kowa k'ala, Harris ya kalli ya Abubakar ya nuna masa ya Umar da baki (zind'e kenan, kuma babu k'yau😏.) Baki ya Abubakar yata6e shima suka had'a ido da matarsa Haleesat. Asma'u duk tana kula da abinda sukeyi, hakama Anty Sa'a, hawaye yacika idon Asma'u tamik'e ahankali tafice. Ya Umar dake kallon duk wani motsin kowa, har abindasu ya Abubakar sukeyi masa, yabi Asma'u data fita tana kuka da kallo, ahankali yalumshe idanunsa yanamai jin tausayinta, shima sakkowa yayi daga gadon yanufi hanyar fita....... Inna ta ce, "Umar ina zuwa kuma?. d'an shafa kansa yayi, idonsa ak'asa ya ce, " inna zand'an tattaka ne, na gaji da kwanciyarne". To aii dakayi magana sai ko Harris ya taimaka maka, kaida bakajin k'warin jikinka". A'a inna yayi zamansa zan iyama, nafison nayi dakaina. To shikenan, jeka, idan kagajidai kadawo kaji. Kansa ya jinjina mata tana murmushi, sannan yafice. Asma'u na zaune akujerun dake jere a tsakkiyar reception d'in asibitin, kanta a duk'e yake shiyyasa ya Umar baiga halin datake a cikiba, takawa yayi zuwa gareta. Da sauri tad'ago danjin mutum ya zauna a Kusada ita. Had'a ido sukayi da ya Umar, sai kawai tad'auke kanta, tamaida k'asa tana k'ara share hawayen dasuka silalo mata yanzun, girgiza kansa yayi tareda kamo hannunta ya rumtse anasa, yaarrrrr tsigar jikinta ta tatashi, yauce rana ta farko da ya Umar yata6a rik'e hannunta amatsayinta na matarsa, ta rumtse idanunta harda cije le6e....... Bata gama dawowa dai-daiba taji muryarsa na kuwwar fad'in Husna!. K'ara rintse idanunta tayi sosai takuma kasa amsashi. Shima baya buk'atar amsar tata Dan haka yacigaba da fad'in, Husna shin bazaki zama jaruma baneba?, kina ganin rayuwa zata cigaba da tafiya komai da kuka?, Husna bamusan randa rayuwa zata canja bafa, kenan hawayenki basuda ranar k'afewa?, kinga d'ago ki kalleni. Shiru Asma'u takasa d'agowa, amma tana sauraren dukkan maganganunsa. Ya kuma fad'in husna kalleni mana. d'agowa tayi cikeda kasala, suna had'a ido tayi azamar janye nata, yad'aga baki zaiyi magana Anty Sa'a tak'araso wajen..... A'a d'an k'anina mikuma kukeyi anan wajen?. Baice komaiba saidai nuna mata Asma'u da kanta ke k'asa yayi. Anty Sa'a tad'anyi murmushin takaice tareda zama Kusada Asma'un suka sakata tsakkiya itada ya Umar. Itama dafa kafad'arta tayi, cikin sigar lallashi ta ce, "Asma'u kik'ara zama mai hak'uri da jarumta dukda nasan kinadasu, kicigaba da yima mijinki kuma yayanki addu'oin fatan alkairi, kizama mai k'arfafa MASA gwiwa kinji?. Karki sake damuwa da abinda wasu suke masa barema harya sakaki kuka, ALLAH daya basa shiyya kar6i abinsa badan baya son Umar ba, sanda ya azurtasa baiyi shawara da kowaba, hakama yayin amshewa, suma basufi karfin ya kar6e daga garesuba. _antambayi Mazon ALLAH (s,a,w) waye talaka?._ _sai ya ce, "Wanda zaitashi ranar k'iyama babu komai na aikin alkairi a gidauniyar ayyukansa._ To Ashe talaucin duniya bashine talauciba, dukiyar duniya ba itace arzik'iba, Dan *_KARAYAR ARZEEK'I_* ta riski Umar ba hakan na nufin ALLAH baya sonsa baneba, ya jarbceshine Dan kawai yaga nauyin imaninsa, wannan itace *Kaddararsa* Dan haka bashida ikon tsallakewa, inhar d'an Adam bazai iya gujema kaddarar ranar mutuwarsaba, to tabbas bai Isa gujema duk wata k'addara a yayin rayuwarsaba, kibar kuka kinji. Jin jina kai Asma'u tayi, cikin raunin murya ta ce, " Anty sa'a ngd da tunatarwarki agareni, ALLAH yak'ara bamu jarumtar cinye jarabawarsa, Ameen ya rabbi Asma'u, ALLAH ya albarkaci rayuwar aurenku. Murmushi Asma'u tayi, azuciyarta ta ce, "Ameen Anty Sa'a". Ta juya tad'an kalli ya Umar, muryarta kasa-kasa ta ce, " ya Fharuk kayi hak'uri da d'aga hankalinka danayi harka taso kafito, insha ALLAH wannan shine na farko kuma na k'arshe. Mik'ewa yayi yana fad'in ni bakimin laifin komaiba dama. Daga Asma'u har Anty Sa'a da kallo suka bishi harya shige d'akin dayake jinya. Asma'u tajuyo tana kallon Anty Sa'a, kanta a langwa6e ta ce, "ya Umar yanada wuyar sha'ani anty". Murmushi Anty Sa'a tayi tareda fad'in duk taurinsa kece zakisakashi yayi sanyi k'anwata, nakumasan zaki iya saboda jarumtarki... Itama tana kaiwa k'arshe ta tatashi tabar wajen. Da kallo Asma'u tabita harta shige, ta sauke ajiyar zuciya tana wani murmushi da juya maganar Anty sa'a a zuciyarta, indai hakane to tabbas zata zama zaruma wajen maida ya Omar sanyi kamar yanda Anty Sa'a tafad'a, tabbas tanason ya Umar sosai kuma zata zauna dashi aduk halin dayake ciki, itama mik'ewa tayi tashiga d'akin Da sallama tashiga, wad'anda sukaji suka amsa, tanemi waje kusada Fatee ta zauna, data d'ago ido saita kama ya Umar na kallonta, Anty sa'a na kallonsu tana dariya ciki-ciki..... _____________________ Kwana biyu tsakani aka sallamai ya Umar suka tattara sai gida, duk dangi sun musu rakiyya zuwa gidan nasu. Wani abun mamaki tundaga babban falo suka fara gani, kaf abinda ke falon an kwasheshi babu komai sai agogon dake manne abango, kallon-kallo aka koma kowa yayi cirko-cirko kamar zakaru na shirin fad'a, Asma'u ce tayi k'arfin halin d'aga k'afafunta tashiga cikin falon sosai tana kalle-kalle. Babu Wanda ya iya cewa Uffan aduk taron, Dan Ya Umar baibama kowa damar hakanba, hasalima d'akinsa yashige yabarsu anan, a falon nasama abin mamakin ya tarar Dan nanma komai babu sai agogo dawata kujera guda d'aya dayakan zauna domin hutawa, sai tebiri agefenta Wanda yakan d'ora abubuwa, dak'yar yaja k'afarsa zuwa cikin bedroom d'in zuciyarsa cikeda tunani kala-kala, nanma dai bata canja zani ba Dan babu komi sai katifa da jibgin sutturunsa akai, saikuma tarkacen daba'a rasaba, jin hajijiya na neman d'ibarsa ya dafe bangon d'akin, cikin zuciyarsa yake tunanin wayayi masa wannan aikin?, badai za'a danganta ta'asarnan da 6arayiba Dan babu abinda 6arawo zaiyi da katakai, zuciyarsa tafara rawa akan ina Asma'u tasamu kud'in biya masa asibiti?, can wata zuciyar ta ce, "ita ta saida kayan gidan kenan?. Damm gabansa ya fad'i yay shiru batareda iya koda kwakwkwaran motsiba, yama rasa wane tunani zaiyi akan Lamarin........ A 6an garen Asma'u madai tunani take yaushe ya Umar yay cinikin kayan gidansu?, kanta bai ida kwancewaba saida tashiga nata d'akin, babu komai an kwashe sai katifa, hattada akwatinanta na lefe ankwashesu kaf, sai kayan datazo dasu daga gida aka zube a katifa, innalillahi wa'inna ialaihirraji'un kawai take iya amabata, yaraf tazube bisa katifar tana sauke numfashi, wai miya shiga kan ya Umar ne haka?, Dan kawai *KARAYAR ARZEEK'I* ta riskeka sai komai daka mallaka yazama hajar rabawa a kasuwa?, haba wannan wace iriyar rayuwace?....... 6angaren dangima dai kowa lamarin yagirmi tunaninsa, amma babu halin magana, dansu duk tunaninsu su ya Umar sun saida kayan gidanne dan nema masa lfy, wannan yasa tausayinsu ya d'arsu a zukatan wasunsu, Anty sa'a ma kasa zama tayi ta tattara 'ya'yanta suka tafi tana kuka da tausayin k'anin nata, ganin haka sauran sukaima Asma'u sallama suma suka tattafi. Daga Asma'u har ya Umar sun riski kansune a halin shiru da zargin juna, kuma har zuwa yammaci babu Wanda ya iya neman d'an uwansa balle tambaya agareshi, ganin agogo ya nuna 3:45pm yasaka Asma'u tashi tafito da k'yar saboda jin cikinta yafara kiran Ciroma tasan kuma ga ya Umar ma hakane. Kicin tanufa da nufin dafa musu komi yasamu su zirarama hanjinsu, mamaki al'ajabi da tsinkewar zuciya duk suka risketa alokaci guda, wayam babu komai akicind'in koda kuwa cokaline, hakama sitod'in babu alamar kwayar gero acikinsa, ta nisa tareda sauke numfashi, tama rasa abin fad'a Dan haka tafito zuwa d'akin ya Umar. Tofa. ta ambata yayinda tayi tozali danasa d'akin shima wayam, ta hard'e hannayenta ak'irji tana k'ara raba idanu akan komai, shin kuka zata fasa kokuwa kururuwa?, da sauri tafito zuwa d'akin Lubna, nanmadai an kwashe komai ko tsinke ba'a bariba, nasu d'akunan yafi dama-dama tunda anbar musu katifu da agogunan kallon lokaci. Ayanzun kam ba tsinkewar zuciyace kad'ai ta risketaba harda tsinkewar 'Yar hanji da daskarewar jini, da k'yar taja k'afafunta takoma d'akin ya Umar, masu iya magana kance ta inda aka hau aii tanan ake sauka. Bedroom d'insa takutsa kai batareda neman iziniba bare tsoron shiga, babu kowa ad'akin saidai k'arar ruwan wanka daga bathroom d'insa, wannan yasa tazauna abakin katifar tanabin tulun kayansa dake jibge bisa katifar da kallo............... *_luv you so much my sweet fan's, ALLAH yabar zuminci, inata godiya da k'aunarku gareni, wlhy nima ina matuk'ar k'aunarku aduk inda kuke alkairin ALLAH yakai muku😻😻😻😻❤❤❤❤❤❤🤝💋._* *_(((S))).......2017_* *_Luv you all_* [11/29/2017, 2:40 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* _Na gaisheku my Deexerh da Billy S Fari & Deejerh, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, ina alfahari daku._😻😻🤝💋 *_page→23-24_* .......Yana fitowa tamik'e zumbur tamkar wadda aka tsikara, da sauri tafice a d'akin, shikuma ya rakata da kallo, baice komaiba ya zauna yana shafa mai, duk jikinsa babu k'arfi yake jinsa, jallabiya kawai ya zura yafito domin tafiya masallaci sallar la'asar. Afalonsa ya tadda Asma'u, harzai wuce saikuma yajuyo ya kalleta, itama shi take kallo, amma suna had'a ido tajanye nata, ya ce, "lfy kuwa?". Tashi tayi tsaye tana tura baki gaba, muryarta na rawa ta ce, "ya Fharuk miyasa zakayi haka?". Kallonta yakeyi sama da k'asa Dan baisan inda maganar tata ta dosaba, hasalima shiyya dace yamata wannan maganar saboda saida kayan gidan datayi. Ganin kallon dayake mata yasaka jikinta yin sanyi. shima juyawa yayi yafice abinsa batareda yasake cewa komaiba. Dak'yar ta iya jan k'afarta takoma d'akinta, itama sallar ta gabatar, tana nan zaune akan sallayar cikinta na k'ugin yunwa taji alamar shigowar mutum, kafin tayi wani yunk'uri k'amshin turarensa ya sanar da ita shine, sosai yake bin d'akin da kallo, jiyayi wani haushi yakuma turnik'e zuciyarsa, to aii 6annar tayi yawa, kujerun babban falo kad'ai zata iya saidasu sama da dubu d'ari biyu, amma shine hardana d'akinsa Dana d'akinta?, afusace ya ce, "k! Waimike damunkine?. Asma'u tad'ago tana kallonsa, tuni tsoronsa ya tasirantu azuciyarta Dan ganin yanda idanunsa suka kad'a sukayi jajur. Muryarta na rawa ta ce, "yaya babu abinda ke damuna fa"...... Wata Uwar harara ya galla mata wadda tasakata saurin tsuke bakinta, Yakuma Daka mata tsawa ubanwaye yasakaki saida kayan gidannan!?. Cak jikin Asma'u yatsaya daga rawar dayakeyi, sosai take kallonsa dakuma mamaki, shi Kansa ya lura da hakan. Ta d'auke idonta daga kansa tana fad'in niban saida ko cokaliba agidannan, nima kuma d'azu maganar danaje yimaka kenan, dai-dai da kicin ba'a bar komaiba hakama d'akin Anty Lubna babu komai........ Shiru yayi yana kallonta, zuwa can kuma ya ce, " to idan bake bace wanene?, kinsandai 6arawo bazai saci katakai yabar kayan sakawaba?, shin inama kika samu kud'in biyamin asibiti?. Zuwa yanzun kam zuciyar Asma'u tafara tunzura, Dan haka tafara maganar dad'an karsashi, wayata nasayar nayi hidimar asibitinka, Dan alokacin banida abinda yawuce wayar saikuma kayan lefena Dan sukad'ai na mallaka agidannan, sukad'ai kuma zan bigi k'irji nace nawa, ko a shekaranjiya danazo gidannan komai yana nan, na tabbata duk Wanda yay wanan aikin ajiya yayishi.... Fuuuuu tashige bathroom batareda tajira cewarsaba. Cikeda mamaki yabita da kallo, dama yasan tuni Asma'u tanada tsiwa daga bayane tabari saboda tana shakkarsa, fita yayi zuwa d'akin lubna danya gaskata maganar Asma'u. Ilai kuwa babu komai acikinsa, kamarma ba'a ta6a ajiye wani Abu daya danganci mutumba, can jikin k'ofar window ya hango wata farar takarda, ahankali yataka ya zareta tareda bud'ewa, anutse yafara karanta takardar, baikai da zuwa k'araheba yasaketa awajen yana ambatar addu'ar da akeso musulmi yayi yayinda al'amura suka tsananta a gareshi. ↓ *_“Allahumma laa sahla illaa maa ja'aaltahu sahlan wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan”._* _(ya ALLAH! babu wani Abu mai sauk'i, sai abinda kasanyashi yazama mai sauk'i, kuma kai kana Sanya tsanani idan kaso yazama sauk'i)._ Haka yayta maimaita wanan addu'a ahankali nutsuwa tafara zuwa agareshi, d'aukar takardar yayi yafice daga d'akin Yakoma nasa. Asma'u dake la6e tana kallon duk abinda ke faruwa takoma baya da sauri Dan ganin zai fito, koda yashiga d'akinsa saiyayi wurgi da takardar a katifar, shima yafad'a saman kayan ya kwanta domin samun sauk'in zafin da yakeji. Asma'u nanan zaune afalo shiru saiga Rafi'a da abinci, sosai tayi murna da hakan, bata 6oyema Rafi'a damuwarta tasanar da'ita komai. sosai lamarin ya girgiza Rafi'a. Asma'u tamik'e takaima ya Umar abincin, tadad'e akansa tana masa magana amma ko motsi baiyiba bare tayi tunanin zai amsata, hakan yasa tadire abincin tafitowarta. ++++++++++++++++ Haka rayuwar gidan tacigaba datafiya cikeda k'unci da damuwa, babu mai shiga harkar wani acikinsu, gaisuwa kawai take had'asu saikuma kaimasa abinci Wanda Rafi'a tajuri kawowa kullum bada sanin mamaba. Ranar yashirya fita, tsaf yafito yanata zabga k'amshi, idan baka saniba bazaka ta6a cewa yana cikin wata damuwaba, fuskarnan fayau sai Annurin hak'uri ketashi, saidai duk Wanda yasan ya Umar ya kalleshi a yanzu yasan ya rame sosai, sai dogon hancinnan dayay ziri-ziri, jin k'amshin turarensa ya yawaita awajen yasaka Asma'u dake kwance d'agowa tana kallonsa, tashi tayi zaune. Shima sai binta yakeyi da kallo, gani yake dukta canja masa, kamarma tayi bak'i, tausayinta ya d'arsu azuciyarsa, zama yayi abakin katifar kusada ita, cikin taushin murya ya ce, "Husna bakida lafiyane?. Kwalla suka cika mata idanu, kanta ak'asa ta ce, " a'a lfyta k'alau". Shiru yayi yana nazarinta, zuwa can yasauke numfashi, d'aya daga cikin wayoyinsa yazaro saga aljihu, yacire sim Cart d'insa sannan ya kalleta, ina cim cart d'inki?. Yana nan, tafad'a kanta ak'asa. "d'akkomin". Tashi tayi tamkar kazar da k'wai yafashema aciki, yabita dakkalo sanye take cikin sket da Riga na shadda ruwan ak'asa mai turuwa, ada kayan sunmata kad'an amma yanzu data rame sunmata yawa....... Katse masa tunani tayi da mik'a masa sim Cart d'in, baice komaiba ya kar6a ita kuma takoma inda takeda ta zauna. Saka sim Cart d'inta yayi a wayar ya sassaita mata abubuwa sannan yamik'a mata yana mik'ewa. Galala take kallonsa da waya a hannu, ganin haka ya d'ora mata bisa cinyarta, ya ce, " zanje wani waje yanzu Dan inaso nafara Neman aiki. Muryar Asma'u a sanyaye ta ce, "ALLAH yatsare yabada sa'a". Amin yafad'a yanamai jin dad'in addu'arta har cikin zuciyarsa. Tunda yafice taketa juya wayar a hannunta tana murmushi, aranta ta ce, " ko wayarnan takai nawa?, Dan tabbas daga ganinta an sayeta da kud'i masu nauyi. Ta sumbaci wayar tana murmushi tareda shak'ar daddad'an kamshinsa dake tashi a jikin wayar, ahankali tafurta ALLAH yabarmu har Abadan my Umar Fharuk!, abinsona, farincikina, Nusfulhayat d'ina, hawaye suka gangaro abisa fuskarta....... Kamar wadda akaima magana akunne tamik'e zummbur tanufi d'akinsa, takardar ranar tafara bulayin nema, amma duk inda take zatonta babu ita, tacije le6e tana yarfe hannun jin bak'in ciki, harta kama hanyar fita saikuma tadawo, bai k'yautu ace tacigaba da Barin d'akin da kayansa akan katifarnanba, komawa tayi tazauna ahankali tafara ware gogaggu da wankakku wad'anda babu guga, harma damasu daud'a aka had'a awajen, zagewa tayi sosai tagyara d'akin tsaf, tad'akko zanin gado ta shimd'a, kamar ance tad'an d'aga katifar saiga takardar ranar, wani murmushi jin dad'i tasaki, ta d'auki takardar ta ajiye gefe saida tagama gyara komai tsaf sannan tafice zuwa d'akinta cikeda son ganin abinda takardar ta k'unsa....... Ya Umar kam koda yafita ak'ofar gida sukaci karo da makwafcinsa, hannu yabasa suka gaisa, ya Umar yamasa godiya sosai akan taimakon daya masa ranar, babu komai d'an uwa aii anzama d'aya, amfanin makwaftakar kenan. Hakane gskyarka ngd sosai ALLAH yabar zuminci, saidai bansan sunankaba. Murmushi makwafcin nasa yayi ya ce, "hakane. Ni sunana Muktar". Masha ALLAH malam Muktar, nikuma sunana Umar Fharuk. Masha ALLAH Umar, daga yau ina fata zamu zama abokan juna, matanmmuma zasu zama k'awaye. Babu damuwa Muktar ALLAH yabarmu tare, suma saimuyi k'ok'arin had'asu. Sund'an dad'e suna hira, sannan Muktar yamasa sallama yakoma wajen aikinsa, dama yayi mantuwane yadawo d'auka. Ya Umar ma mashin ya tsaida yahau suka nufi inda zaije........ *_(((S))))......2017_* *_Luv you all_* [11/30/2017, 3:19 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→25-26_* ........Jikin Asma'u har rawa yakeyi wajen bud'e takardar, ta jingina da k'ofa bayan ta rufe tafara karantawa. *↓* *_hii Umar Fharuk_* _Hummm abin mamaki da al'ajabi._ _hhhhh Umar nasan abinda zaku fara ambata kenan kaida matsiyatan danginka da Mayyar matarka a yayin da kuka shigo kangon gidanka kuka tarar babu komai a cikinsa, hhhhhh to kasan wacece ta shirya wad'annan abubuwan mamakin da al'ajabi kuwa?. nice nan Lubna, nayi hakane saboda bazan ta6a barin kacigaba da morar wani Abu daga dukiyarmuba, bazan ta6a barin wannan shegiyar matar taka jin dad'in rayuwa da kaiba wlhy Umar, nice nan na kwashe komai nagidannan kuma nayi k'yauta dasu, Ku k'arata acikin talaucinku dama ahaka kuka taso kuma ahaka zaku k'are, Dan matiyaci ko'a tulun manshanu kasakashi haka zaifito bai dangwali komaiba, nasoka tamkar babu wani namiji aduniya, mahaifina yamaka gata tamkar shine ya haifeka, amma saboda butulci irin na talaka karasa dami zaka sakamin saida wata abar banza wai kishiya, tom ga fili gamai dokinan, saura kuma sukuwa ko?, ALLAH yabada sa'ar cin gabbaza mukan nagaba yayi gaba nabaya sai labari, abinda yasa zan barka katsira da gidan dakake cikima saboda yazama tukuyci wa tsaron dukiyar mahaifina dakayi abayane kawai, afrah da amrah kam kasaka aranka baka ta6a haihuwar wasu 'ya'yaba aduniya, nikam kamanta dani hakan zaifi yimaka sauk'i._ _wassalam matarka ada😜._ Ajiyar zuciya Asma'u tasauke, k'irjinta har wani d'agawa yakeyi sama saboda bugawar da zuciyarta takeyi da k'arfi, tadafe k'irjin tareda lumshe idanunta hawaye na zurara akumatunta, wani tausayin ya Umar ne yaketa walanked'uwa azuciyarta, ashe dama duk abubuwanan saboda ita yake faruwa dashi?, haba Anty Lubna miyasa zakiyi hakane?, gara'ace kin rabani da ya Fharuk da'ace kin cutar dashi da k'untata rayuwarsa sabodani, inason ya Fharuk banason wani Abu dazai ruguza duk wani cigabansa, ya ALLAH ka kawoma wanan bawa naka d'auki, tazame ta zauna k'asa da6ar tamkar wata mai shirin hawa bori. Tadad'e a wajen tana kuka kamar wadda akace inna ko baba sun mutu, ganin babu sarki sai ALLAH tamik'e tawanke fuskarta, hijjabinta ta d'auka tasaka tafito. Hartaje k'ofar fita saikuma ta fasa, komi ta tuna?, dawowa tayi tazauna a tsakar gidan tanabin k'adangaru daketa guje-guje da kallo......... Ya Umar kam yanacan yanata bulayin Neman aiki, duk inda yasan yanada wata alfarma ada saida yaje, amma k'alilannema acikinsu suke Nuna sun ganeshi, wasuma nunawa sukeyi basuta6a ganinsaba, murmushin takaici kawai yakeyi yatafi, har yamma lik'is babu wani cigaba saima wahalar kishirwa da yunwa data addabesa, ganin magriba takawo kai yahau mashin yanufo gidansu. Atsakar gida ya iske Mufida da Rafi'a suna hada-hadar girkin dare, Rafi'a dake wanke naman kaji tad'ago tana kallonsa da murmushi, yaya Sannu da zuwa. Yauwa Rafi'a, aiki kukeyi?. Eh yaya INA yini. Lfy lau ya makaranta?. Alhmdllh yaya. Mufida itama ta gaisheshi. Amsa mata yayi itama cikeda kulawa, Dan itama yanzu tausayinsa takeji tunda ya kwanta a asibiti. Ya ce, "mamafa?". Tanan ciki itada ya Abubakar. Okey shima yazo gidanne?. Eh yaya. Cikin falon yashiga da sallama, ya Abubakar da mama suka d'ago suna amsa MASA babu yabo babu fallasa, durk'usawa yayi yana gaida mama, ta amsa MASA kadaran kadahan, hannu yamik'ama ya Abubakar shima suka gaisa, suna gama gaisawa ya Abubakar yamik'e, to Mamana bara nawuce gida saikuma gobe, babudai abinda kike buk'ata ko?. A'a Sadiq d'ina bana buk'atar komai wlhy kawadatamu dakomai saidai nace ALLAH yayi maka albarka yak'ara arzik'i. Ameen Mamana saida safe. ALLAH yakaimu ka gaidamin 'yan jikokina da d'iyata. Zasuji insha ALLAH. saida yaje bakin k'ofa sanan ya ce, " o Umar sorry fa namanta kananan bamuyi sallamaba Ashe, saida safe konace saiwani jik'on danku kunyi wuyar gani yanzu. Ya Umar dakansa ke a duk'e tun d'uzun yana sauraren tad'in Nasu mama, ya d'ago idanunsa dasuka fara canja launi zuwaja saboda 6acin rai, yasan sarai habaici ya abubakar yamasa amma ko kad'an fuskar jarumin naku bata nunaba, fuskarsa shimfid'e da murmushi ya ce, "babu damuwa ya Abubakar saida safe agaida iyalin, ficewarsa yayi batareda ya amsaba. Ya Umar yadawo da kallonsa ga mama datake k'irga kud'in da ya Abubakar yakawo mata yanzu sai murmushi takeyi ana dangwalar yawu da k'ara Tisa k'irgar, baice komaiba yamaida Kansa k'asa yana jiran takammala. Saida tagama tsaf sanan yad'ago ta kalleta, gabad'aya fuskarta ta canja yanzu babu walwala, amma kuma idonta na kan ya Umar d'in. Muryarsa a raunane ya ce, " mama dama Nazi nasanar dake yanda mukayi da Lubna ne. Baki mama ta ta6e amasife ta ce, "Umaru kaini rabani dawata lubna tunda kud'in ubanta basu ammfaneka da komaiba, idanda su wasu mutanene arzik'ine Aida sun taimakeka kodan ganin halin masifar dakake ciki, amma mutanannan sunyi funfurun fus saboda bak'in ciki irinna mai arzik'i dabayaso talaka yasamu, wace irin wahalace bakaima ubantaba fisabilillahi amma yamzu suka watsar Sakai, kofa dubaka basuzoyi asibitiba harkayi kwanakinka kagama jinya.... Shidai Umar tunda mama tafara sababinta baice komaiba kansama na k'asa, saidai zuciyarsa tana mamakin halin *_MANTA ALKAIRI_* irinna mahaifiyarsa, koba komi iyayen Lubna sun taka rawar gani akansa, kuma har gobe yana ganinsu da mutunci bakuma zai manta da karamcin dasukai masaba a baya...... Jin mama tayi shiru yagane tagama NATA, muryarsa a tausashe ya ce, "tom mama kiyi hak'uri amma bawannan maganarce dama kawoniba. Tsaki mama tayi ta ce, " kaji zancen banza to miya kawoka!?". Saida ya had'iye wani yawu k'irjinsa yana dukan uku-uku ya ce, ''mama na saki Lubna tunkafin na kwanta a asibiti". Ba mamaba har Mufida da Rafi'a dake k'ok'arin shigowa saida suka daskare awajen, maganarsa ta razanasu. Cikin tsawa mama ta ce, "Umaru bakada hankaline!!?, kokuwa kafara shaye-shaye bansaniba!!?". d'ago jajayen idanunsa yayi yana kallonta, cikin girmamawa ya ce, " wlhy mama bana shan komai, amma idan kin bani dama zan fad'a miki dukkan abinda yafaru harna saketa. Wani huci mama tasauke harda hura hanci ta ce, "ina jinka. Ya Umar ya sauke ajiyar zuciya sanan cikin nutsuwa yafara zayyanama mama komai, Rafi'a da Mufida sai hawaye sukeyi, mama kanta jikinta yayi sanyi, wani k'auna da tausayin d'an nata suka ratsata, tabbas tana matuk'ar son 'yayanta mafisifar son kud'i da hange-hangene kawai suke dakusheta, ya Umar yayi shiru ayayinda yakai karshe, zuciyarsa sai zafi takeyi da rad'ad'i, jiyay k'irjinsa yafara nauyi, addu'arnan ta yaye bak'inciki da tafiyar da k'uncin zuciya yafara ambata..... *↓* *_“Allahumma inni abduka ibnu abdika ibnu amatika, naasiyatin bi yadika, maadhin fiyya hukmika adlun fiyya k'adha'uka as'aluka bi kullis min huwa laka sammaita bihi nafsaka au anzaltahu fiikitaabika au allamtahu Ahdan min khalk'ika awista' asarta bihi fii ilmil gaibi indaka an taja'ala k'ur'ana rabii'a k'albii, wa nuura sadrii, wa jalaa'a huznii wa zahaaba hammi”._* _(ya ALLAH ni bawankane kuma d'an bawanka, kuma d'an baiwarka, makwarkwad'ata a hannunka take, hukuncinka zartaccene akaina, kuma k'addararka gareni mai adalcice ina rok'onka dakowanne suna Naka, Wanda ka ambaci kanka dashi, koka saukar dashi acikin littafinka, koka sanar dashi ga wani daga halittarka, koka ke6ance kanka da saninsa acikin ilimin fake da ke wurinka daka Sanya alkur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske ga k'irjina, da kwaranyewa ga bak'in cikina, dakuma mai tafiyar da damuwata)”._ *↓* *_“Allahumma inni a'uzu bika minal hammi wal huzni, wal ajzi wal kasali wal bukhli wal jubni, wadhal'id daini wa galabatir rijaali”._* _(ya ALLAH! ina neman tsarinka daga damuwa da bak'in ciki, da gajiyawa da lalaci, da rowa da ragwantaka da nauyin bashi, da rinjayen mazaje)._ Ahankali k'irjinnansa yafara rage nauyi, zuciyarsa yafara sanyi, wata nutsuwace tafara riskarsa babu abinda yakeyi sai sauke ajiyar zuciya, da sauri Rafi'a tabud'e firij ruwa tad'akko batareda ta nemi kofiba ta mik'a masa, shima bai tsaya tambayar kofinba ya 6alle murfin yana kwankwad'awa cikinsa, saida yashanye ruwannan tas sannan yadire gorar, dama k'aramar gorace, kansa yad'ora jikin kujera yana sauke numfashi ahankali, bayan wasu 'yan mintuna nutsuwarsa tadawo gaba d'aya, har bak'in cikin da mutane suka cusa masa d'azu wajen neman aiki dukya kwaranye, saima wani nishad'i da farinciki daya mamayesa....... Maganar mamace ta sauka a kunnensa, cikin tausayawa ta ce, "ALLAH ya k'yauta, saikadage yanzu kafara neman aiki da takaddunka, dama kaine kak'i aii tuni, yanzu da aikin kayarda ya samama maka alokacin daya baka za6i aikaga da haka bata faruba ko?........ Kallon mama yakeyi k'ur da mamaki wai ita har yanzu batayi laushi bane?, wai sai yaushene mahaifiyarsu zata daina wanan masifaffen son kud'in nata da hange-hange, (wata zuciyarsa ta ce, " addu'a kawai zakucigaba da mata"). Yananan zaune harta gama surutanta, jin ankira sallar isha'i yamik'e yamata sallama. Awaje yatadda k'annen nasa mata duksunyi tagumu, yata6a Mufida dake kusadashi, "k! Lfyarku kuwa?". Figigit suka dawo hayyacinsu, babu komai yaya. Okey tomni nawuce saida safe. Lah yaya munfa kusa gama abinci katsaya kaci mana. No ngd saida safe... Yafad'a yana fita. Rafi'a da Mufida suka bishi da kallo cikin tausayawa. Kai tsaye gidansa yanufa, baishigaba saida yayi sallar isha'i a masallacin anguwarsu sannan yashiga gida. Tun a tsakar gida yaga canji Dan yau gidan yasha gyara, yana shiga abban fallo wani k'amshi mai dad'i yabigi hancinsa, dukda babu komai afalon sai agogo amma yasharu tas sai k'amshi ke tashi, jin tafiyar abayansa yasakashi d'agowa da Sauri.............. *_(((S))).......2017_* *_I Love you all my sweet fan's_*💋 [12/2/2017, 4:11 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→27-28_* ........Asma'u ce sanye cikin doguwar riga ta atanfa, kayan sunyi bala'in zama ajikinta d'as, taci kwalliya ta alfarma sai bulala k'amshi takeyi, cikeda yanga tak'araso gareshi, shikam tsaye yake gingiringin tamkar wani gunki, harta k'araso gareshi amma bai motsaba. Cikeda mamaki Asma'u take kallonsa, miya samesa haka?, kokuwa kwalliyar tatace batayibane?, shiga tayi bin jikinta da kallo tamkar mai Neman wani wani Abu, can tad'ago tana kallonsa itama, ya Fharuk lfy kuwa?. Firgigit yadawo hayyacinsa tareda sauke wata nannauyar ajiyar zuciya!, 'yan kame-kame yafara na basarwa, no. babu komai yafad'a yana nufar d'akinsa. Binsa da kallo tayi saikuma ta tab'e baki, kadaiji dashi tayi maganar tana masa gwalo😜. Ya Umar nashiga d'akinsa yazube bisa katifar datasha d'an karan gyara, lumshe idanu yayi yana murmushi, yadad'e baiji farinciki irinna yanzuba, a 'yan watannin nan yama manta shi macene kokuwa namiji?, kwata-kwata bayajin wata sha'awa ko son kasancewa da mace, damuwa ta mantar dashi farinciki da nishad'i, yaukam Asma'u ta tunatar dashi koshi waye, Dan kwalliyarta tasakasa begen wani Abu, babu k'arya yarinyar tanada jiki irinna mata masha ALLAH, hannu yakai yashafa sumar Kansa wadda ba gayubane yasakashi tarata, a'a damuwace kawai da rashin lokacin kai, tashi yayi zaune yanamai bin ko'ina na d'akinsa da kallo, komai tsaf kamar ba d'akin daya zama bolaba acikin kwana hud'u dasuka wuce. Ajiyar zuciya ya sauke tareda furta *_“Alhamdllh alaa kulli hallin”._* A gaggauce yatashi yacire kayansa, wanka yashiga sauri-sauri ya kammala Dan yana burin sake ganin Asma'u da k'yau, baiwani d'auki dogon lokaciba yagama shiryawa cikin wando iya gwiwa da k'aramar Riga mara hannu, turare yafesa sanan yasaka silifas yafito babban falon dayake tamkar zaure, babu kowa afalon Asma'u takoma d'akinta, shima d'akin nata yanufa, tana a falonta zaune kan tabarmar data shimfid'a waya taketa latsawa tana kallon hotunan ya Umar sannan yana Umar Fharuk d'insa, tana murmushi, Dan sanda akayi hitunan yana wasa da nairane, shikansa yana son hotunan sosai, yad'an dad'e tsaye yana k'are mata kallo, ganin batasanma yanayiba yay mata gyaran murya. Jikinta har rawa yakeyi wajen 6oye wayar. Baice da ita komaiba yazauna kan tabarmar, saida yazauna sanan yamik'a mata hannu alamar tabashi wayar yagani. Idanu ta kwalalo masa waje, ya Fharuk bafa wani Abu baneba. Uhm nasani, kibani dai. Marairaice fuska tayi tamkar zata FASA kuka Dan batason yaga mitake kallo, ALLAH ya bawani abun ashsha bane hotuna nake kallo. Hotunan waye?, yay maganar cikeda cin magani. Uhm uhm namunefa nidasu Hasiya da Fatee....... Batama bari ya tanka ba tamik'e tafita Dan kawo masa abinci. Binta yayi da kallo, dukda bai yarda da itaba. Yana nan zaune tashigo da tiren abinci, kallon tiren yayi dake d'aukeda komai sabo, kuloli Kofi cokula filet duk sababbi, kallonta yayi da k'yau yanzukam fuskarsa amatuk'ar d'aure take, ayatsine ya ce, "wad'annan abubuwanfa INA kika samu kud'in siyensu?. Ad'arare ta kallesa muryarta na rawa ta ce, " uhm ya Fharuk sauran kud'in wayarnanne dama nabama Fatee tasiyo mana saboda naga ko kofin shan ruwa babu agidannan, dama sonake ka kammala cin abincin namaka bayani amma kayi hak'uri nayi Abu batareda Neman shawararkaba. Ahankali ya furzo huci daga bakinsa yana kauda kai daga gareta. Jiki a sanyaye tahad'a MASA abincin agabansa, tuwon masarane daya tuk'u da k'yau saikuma miyar k'u6ewa d'anya dataji d'anyen kifi da daddawa sai k'amshi ke tashi, a jok d'in kam zo6one shima sai k'amshin kayan yaji yakeyi. Tunkafin yafara cin abincin k'amshin yawunsa keta tsinkewa, sosai ya k'agara yafara saka lauma, amma jinkai da k'asaita irinta mazaje yasakashi mazewa harda kauda kai gefe. Cikin sanyin Murya Asma'u ta ce, "ya please kaci abincin, Dan ALLAH kada kamin horo akan hakan." Tausayi tabashi Dan muryarta har rawa takeyi, amma baice komaiba, hannunsa takama tasaka acikin ruwan data aje arobar wanke hannu, Fes ta wanke hannun yana jinta, bai ankaraba yaji hannunsa acikin miyar, kallonta yayi da sauri, ta langa6e kai gefe tamkar zata FASA ihu, kona baka da kaina?, tayi maganar hawaye na zurara akumatunta. Kad'an yarage ya fashe da dariya amma saiya gimtse ya antaya mata hararama. Tashitayi tamkar Mara laka tashige bedroom, shikuma yaraka bayanta da murmushi, tana shigewa yafara saka lauma yana lumshe ido saboda dad'in da tuwon kemasa. Saida yaci yak'oshi sanan ya wanke hannunsa, tuwon yad'iba a filet yatafi d'akinta danyasan itama bataciba, kwance take akan katifa rubda ciki da alama ma kuka takeyi, aransa ya ce, "idon kuka kenan". Zama yayi abakin katifar yana ambatar sunanata, Husna tashi kici abincin. shiru tamasa batayi koda motsiba. Ganin haka yakamo hanninta yana murzawa ahankali, zumbur Asma'u ta tashi zaune tana muzurai, wani yarrrr! Taji yayinda yake Mirza tafin hannunta, batareda yace mata komaiba yad'ora filet d'in abincin saman cinyarta, maza kicinyeshi tas. Fuska ta shagwa6e tana turo baki nima na k'oshi tunda kaima bakaciba, ido d'ya yad'age yana kallon shagwa6a, saikuma yayi murmushin gefen baki yana fad'in waya gaya miki banciba?, saida nakusa cinyewama nakawo miki sauran. Ya Fharuk da gsk?. Kansa ya jinjina mata. Bismillah tayi tafara cin tuwonsa, shikuma cikin dabara ya d'auki wayarta yafara bincike, ganin hotunansa take kallo d'azu yasakashi sauke ajiyar zuciya, tayi sagare tana kallonsa Dan mamakin wannan ajiyar zuciya, saida tagama tsaf taje ta wanke hannu sannan tadawo ta zauna abakin katifar hannunta d'aukeda kud'i masu d'an yawa har kashi biyu. Naminene?, yafad'a batareda ya kar6aba. Zan maka bayani aii. Yau bayan fitarka Inna tazo gidannan, takawo mana kayan abinci, sannan tace nabaka wad'annan kud'in tanuna masa kashi d'aya acikin kud'in, wad'an nan kuma na sauran wayatane, saidai kayi hak'uri nata6a wasu aciki. Amma ya Fharuk nayi wani tunani. Mizai hana shagonnan na k'ofar gida kazuba kayan provisions acikinsa har muga abinda ALLAH zaiyi akan Neman aikin naka. K'yawawan idanunsa ya tsura mata yanamai kallonta cikeda so da tsananin k'auna, tun Asma'u tana yarinya yake sonta amma wasu abubuwa suka hanashi nunawa dakuma soyayyar Lubna data rud'eshi kasancewarsa mutum maison wayayyar mace. jiyake tamkar ya rungumeta. amma bazaiyi hakaba Dan gudun karta rainashi. Jin yayi shiru gashikuma ya tsura mata idanu ta ce, "ya Fharuk! Mike faruwane?. Ko shawarata batayi daidai baneba?. Ajiyar zuciya ya sauke, a'a Husna shawararki tayi, amma kibari zanyi tunani. Kud'in inna kuwa gsky bazan amsaba, za'a maida mata abinta, idanni har ban bataba, amatsayinta na uwa agareni, tom baik'yautu na kar6a daga garetaba. Humm yaya kasandai halin Inna sarai, wlhy na tabbata bazata amshi kud'innanba, tunda har tayi niyya. Amma kagwada kagani, Dan kunfi kusa. Hararta yayi, kokina kishine?. Asma'u tazaro idanu waje, ya Fharuk nikam kishinmi zanyi dakai? bayan inna tabamu labari tunkan tasamemu kaine d'anta, yanzukuwa danta samemu bazata ta6a had'a soyayyarka da tamuba. Tokaga idanma nayi kishin, ainayi abanza. Ammafa inad'anyi kad'an. ‘tayi maganar tana dariya damasa gwalo.’ Shima murmushin yayi, yamik'a hannu zai cafkota ta zulle. Filo yad'auka yajefeta dashi, wlhy nakula yarinyarnan kinrainanifa. Hannu tasa takare kanta daga filon, cikin dariya ta ce, "ALLAH niban rainakaba." ‘ashagwa6e take masa magana.’ Shikam yayi sagade yana kallon yanda takeyin dariya k'yawawan fararen hak'oranta suna burgeshi. Saida tamik'e tsaye sannan tad’auki filon itama ta jefa masa, ta antaya da gudu waje. Lalala nikika jefama fillo? Lallai yau jiki magayine. Yay maganar yana mik'ewa yabita abaya da filon. Tana ganinsa tafita babban falo da gudu tana dariya, zagaye falon sukaitayi yana tilla mata filo, itakuma tana gudu. Sunkai wasu mintina ahaka har Asma'u tagaji sosai tafara bin bango tana haki. Taku biyu ya damk'ota, zille zille tafara tana fad’in ya Fharuk natuba, ALLAH bazan sakeba. Zaki gayamin hakane idan kika horu, gaba d’aya yad'auketa yakoma d’akinta. Sai fad'in yayi hak'uri takeyi ALLAH bazata sakeba. Ahaf yarinya zancen kikeso kuma, aii daga yau idan ance kimin rashin kunya bazaki sakeba kuma. Wayyo na Inna plss, narantse bazan sakeba. Ko saurarrta baiyiba yajefata bisa katifarta. Zuwa yanzukam da gsk tsoronsa tafara shigar Asma'u, kardai mutumin nan yace mata wani Abu zai mata, nashiga uku ni Asma'u, wlhy tsoro nakeji, atsorace ta yunk'ura zata tashi ya damk'ota da sauri suka fad'a saman katifar atare.......... _“kuyi hak'uri da wanan wlhy murace taketa nuk'urkusata, ga ciwonkai🤧, da k’yar na iya wannanma.”_ *_(((S))).......2017_* *_Love you all_* [12/5/2017, 5:34 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* _Wayyo mura🤧🤧🤧🤧🤧🤧🤧🤧._ *_page→29-30_* ........Humm miye labarin Lubna ne? Su Lubna anagida hankali kwance, tak'ara k'yau da k'iba tamkar ba itaba, hakamasu Afrah sunyi 6ul-6ul dasu, an maidasu wata had'ad'd'iyar makaranta ta 'ya'yan manya. Lubna duk inda taso zuwa takeyi, gakud'i ga Hutu, babu ruwanta dawani maganar iddah sai kula samari takeyi yara k'anana. (Dan mamanta ta ce, "bazata auri mai mataba, saidai saurayi d'anyen jini). Tako hau kan wannan magana tayi d'ane-d'ane. dukda ta ce, ''ita yanzu aure baya gabanta. Karatuma zata koma." Gantalin zuwa biki kuwa itada Suhaila sunmaidashi tamkar cin gwaza, Lubna tabiye mata sosai tamkar wata budurwa, ko bak'i akayi a gidan ba'a cewa Afrah da Amrah 'ya'yan Lubna ne, Dan basaso ace tata6a aure barema harta haihu. Dad bazama yakeba sosai Dan haka baisan wainar da'ake toyawaba agida, Ameer da Safwan yayyensu suma dai samma kal, Dan duk taron kwara da ama ne, babu mai tada wani suma shaid'anun kansune, Neman mai gyarasu sukeyi barema su gyara wani. Ayanzu hakadai cikin hidimar shirye-shiryen bikin Ameer d'in sukeyi, zai auri d'iyar wani babban k'usa a gwamnati, shirin biki takeyi na garari na d'angata. Duk suna zaune afalo dad ne kawai babu Dan yaje k'asar Chaina, akwatinane guda 30, set biyar kenan, kowanne da kalarsa, dank'are suke da kayan alfarma na garari, kayan lefen Ameer ne dasukaje gabad'aya gidan har k'asar Dubai suka had'osu, jiya da daddare suka dawo, shine yau ake duba abunda babu, kayane na garari babu na k'asa da dubu d'ari biyu, kayan sakawa kawai na less, shadda, atanfa, material, dadai sauran yayi, kala d'ari hud'une, banda su jallabiya, k'ananun kaya..etc, kayan shafa kam da takalma jakunkuna aiba'a magana, barema azo kan yari, sark'ok'in zinari goma sha biyu, 'yar dubu d'ari biyar itace k'arama. Humm masu karatu! Mahaifinsu Lubna fa bak'aramar dukiya ya taraba, suma 'ya'yansa babu Wanda bashida hannayen jari a ciki da wajen k'asarnan, saidai kuma acikinsu babu mai aikinyi Dan bama su nutsu sunyi karatunba, kasuwancin kuma bazuwa sukeba bare su koya, to anrigada antara musu. _wlhy 'ya'yan many an k'asarnan basa karatu ko kad'an, 'ya'yan talakawa muke maida hankali muyi karatu komai wuya komai dad'i, amma da zaka karad'e madafun ikon k'asarnan zakaga duk 'ya'yan masu fad'a ajine awajen, akuma many an kujeru, mu 'ya'yan talakawa mune ak'asa k'alilanma kenan acikinmu da'aka d'auka aikin, shiyyasa kullum k'asarmu tana cikin masifu iri-iri, tomasu rik'eda k'asar duk basusan ciwon kansuba ballantana su taimaki na k'asa dasu, basusan ana talauciba bare su taimakawa talaka, basusan komaiba saibin k'asashen duniya suna shek'e ayarsu yanda suka gadama da karuwan kafirai._ ALLAH yasa mudace. Lubna tad'aga wata sark'ar zinari tana fad'i kai 'yan uwa sark'arnanfa tawuce dani wlhy, dolene nakoma Dubai kafin biki nima nasaka ayimin. Harararta Ameer yayi, ya ce, "kefa dad'ina dake kenan, babu yanda za'ayi mutum yayi Abu mai k'yau saikinyi copy copy, ai abin kunyane ma ace aga amarya da sark'ar k'anwar ango ma da ita." Safwan ya ce, "bar yarinyarnan kaji, aidama agidan wancan k'aban take har a yanzu dabata samu yanda takesoba." Cikin shek'ewa da dariya Suhaima ta ce, "bro's kubarta, wlhy badan ceton da momy taima baby ba dayanzun k'ila mun fara bata kwancen kaya." Duka Lubna takaima Suhaima, tana fad'in bakinki ya sari d'anyen kashi muguwa kawai. Kuma wlhy duk Wanda Yakuma had'ani da Umar zamu kwashi 'yan kallo agidannan, natsaneshi! Na tsaneshi wlhy!." ‘tayi maganar tana hawaye.’ Safwan dake Kusada ita yaruk'o hannunta, sorry babyn dad! Karki damu bazamu sake fad'aba kinji, sark'a kuwa dakud'inama zan saya miki. Murmushi tamasa tana mai share hawayen fuskarta. Daga nan Suhaima da Ameer ma suka bata hak'uri, murmushi mom tayi tana cigaba da birkita kayan Dan bincikawa......... ____________________ Koda ya Umar yajefa Asma'u kan katifa shima saiya fad'a Kusada ita. Idonta cikeda kwalla tadubeshi, pls ya Fharuk natuba, ALLAH bazan sakeba. Ido d'aya yad'age yana kallonta da d'ayan, yamatso daf da ita tamkar zai shige jikinta, k'amshin turarensa na matuk'ar dukan hancinta, gadad'in k'amshin da turarensa kemata ga fargabar abinda zai mata, tad'an runtse idanunta danjin bai tankaba. Jin hannumsa akan k'irjinta Yakuma firgitata, tawaro idanunta yayinda shikuma ya ida kai hannunsa kan kunnenta na dama, Wanda dama shiyakeso ya damk'o. Jin anmurd'a mata kunni da k'arfi yasakata sakin wata kasalalliyar k'ara tareda ruk'o hannunsa tana shiii da baki. Wayyo ya Fharuk wlhy akwai zafi, sheeeeeee! Plss natuba wlhy. Shikam murmushinsa kawai yake saki tana k'ara Murza kunnen saboda salon mugunta, saida ya tabbatar taji gargad'insa sanan yasaki kunnen yatashi yana wata dariyarsa wadda Asma'u batasanma ya iyaba. Ficewarsa yayi, itakuma tana rik'e da kunnenta dakemata rad'ad'i da zugi, jitake tamkar tarushe da kuka, afili ta ce, "mugu d'an masa, ALLAH yasakamin. Yana shiga d'akinsa yafad'a kan katifarsa fuskarsa shimfid’e da murmushi. Lumshe idanunsa yayi tamkar mai barci, tabbas abaya yayi soyyaya da Lubna, kuma har yana ganin bazai ta6a son wata 'ya maceba bayan ita, saboda yasameta wayayya yanda yake buk'ata. Ya burkita kwanciyarsa zuwa rubada ciki tareda k'ara k'an k'ame filo ak'irjinsa, shikad'ai yasan miyakeji. dannidai bilyn Abdul bazan saniba🤷🏽‍♀........ Washe gari dawuri Ya Umar yashirya cikin shadda milk color, d'inkin zamani, tamasa k'yau aynun, idan bakasan yana cikin wani haliba saika d'auka irin masu kud'innanne ko 'ya'yan masu kud'i da Hutu ya huda, duk wannan bitada k'ullin da ya Umar yashiga hakan bai canja kalar fatarsaba, tana nan lumi da ita, sai shek'i da Annuri ketashi, gakuma gashi daya kwanta luf luf afatar tasa. Fitowar Asma'u kenan daga wanka yashigo d'akin, dasauri taja hijjab tasaka. Shima kauda kansa yayi gefe, zanje nagaida Inna, kokinada sak'o?. Kallonsa tayi sosai da mamaki, yaukuma wani sabon salonne akazo dashi?. Ganin kallon datake masa yasashi juyawa yana fad'in tunda bakida sak'on saina dawo. ‘batareda yajira amsartaba yafice abinsa. Ta6e baki Asma'u tayi, afili ta CE, "hummm ya Fharuk kai zumane nalura saida wuta, indai banda Neman magana yau kafara zuwa gaida inna? Kata6a fad'amin zakaje? Bare sallamar saika dawo?.... Cigaba tayi da mitarta tana shafa mai, saida tagama tsaf tasaka kaya sannan tafara shirin gyaran gidan....... Agidan inna kam bayan ya Umar yashiga ya gaida baba sukad'an ta6a hira sannan yashiga d'akin inna, tana zaune tana karyawa, Fatee nagefenta tana yankan d'inki Dan bayan ta kammala secondary d'inta sai baba ya ce, " tashiga wani makaranta nan kusadasu na koyon d'inki tunda basuda k'arfin dazata cigaba da karatu kafin kuma ALLAH yakawo mata miji, sosai tadage a makarantar takoyi d'inki acikin wata shida, zuwa yanzukam takware harma kawomata mutane sukeyi. Inna ta washe hak'ora tana fad'in lale dakai yarona. Shima fuskarsa shimfid'e take da murmushin yaje Kusada inna yazauna yana fad'in yauwa innata, nasameki lfy?. Lfy lau Umaru ya iyalin naka?. Lfy lau suke inna, tamace agaidaku. To ina amsawa. Fatee ta ce, "ya Umar ina kwana?. Lfy lau Fateema tela, ya d'inkin? Kinadai k'ok'ari ko?. Eh wlhy Yaya inayi sosai, yanzuma kayan gidansu zaliha naketa d'inkawa na ankon bikin kareema nanda next week, kusan kala 20 kenan na d'inka na manya da yara. Masha ALLAHU, amma kinyi k'ok'ari, kuma naji dad'i, inason mitum mai k'ok'ari akan Sana'a komin k'an k'antarta, ALLAH yak'ara bada sa'a. Ameen Yaya ngd sosai, ina Anty Asma'u?. Tana gida nabarota tace agaisheku. Muna amsawa da k'yau. Inna Hasiya fa? Tana inane?. Hasiya tana islamiyya kasan malama za'ayi wanan waje Umaru. Da k'yau Inna, aii anason Haka, itama ALLAH yacika mata burinta. Ameen Umaru yacikamana gaba d'aya. Ya Umar yagyara zama yana fad'in inna dama akan kud'in jiyane dakika kaima Husn........ Hannu inna tad'aga masa batareda ya k'arasaba, kaga Umaru nidai banbaka kud'innan Dan wani abuba, nabaka amatsayina na uwa agareka, tsakanin uwa da d'akuwa aii babu jayayya ko?. Ya Umar yad'aga mata kai. Tacigaba dafad'in to Indai kasan hakane bana buk'atar jin komai daga bakinka, kaje kasamu sana'a koda k'aramace kafara ALLAH yasaka albarka acikinta. Kokad'an banaso kacigaba da wahalarmin da kanka awajen Neman aiki, ALLAH yabada nasara akan duk abinda aka saka hannu. Ameen inna, ngd sosai dakasancewarki uwa agareni, lallai nayi dace dasamu uwa tagari mai share hawayena, ngd sosai inna, ALLAH yak'ara tsawon kwana da lafiya, ng...... Kaga godiyar ta isa haka, ALLAH yayi muku albarka gabad'aya. Ameen suka amsa shida Fatee daketa zuba murmushin jin dad'i. Inna mikuka dafa yunwa nakeji?. Umaru kokone da Alala da Fatee tayi, Fatee maza tashi ki kawo masa. Amma ita lalatacciyarnan tana ina kafito baka karyaba tabarka?. A'a inna balaifinta baneba, nine, nayi sakkon fitowane da wuri saboda nabiya wajen wani abokinane kafin nazonan dayace zaimin hanyar aiki, amma koda najema saisukace yawuce Abuja tun ajiya, dama yamin k'aryane kawai irinna 'yan boko. Karka damu Umaru inna tafad'a tana kwafa, komai zaizama labari wataran, kama ture batun samun aiki karungumi 'Yar sana'ar da ALLAH yaza6a maka, inada yak'inin wataran sai sundawo suna nemanka da kud'i kagagara ganuwa agaresu. Shikenan inna nahak'ura, yanzudai munyanke shawara nida Husna............nan yazayyanema inna komai akan maganarsu tajiya da Asma'u tamasa. 100/100 inna tabada goyon baya tareda addu'ar alkairi. Yadad'e agidan, Dan har shabiyu sanan yatafi......... _____________________ Tundaga ranar suka shiga gyaran shagon dake k'ofar gidansu kamar na 'yan tireda, cikin kwana hud’u aka zuba komai, dukda kayan bawani yawane dasuba amma Alhmdllh sund'an k'ayatar. Tun aranar suka fara ciniki kasancewar dama babu wani shagon tireda a anguwar, sai idan anje can k'asan layinsu ko baya. Tunda safe ya Umar kezuwa yabud'e saboda masu sayyar safe, idan Asma'u ta kammala break taje takai masa shagon tunda da k'ofa tacikin gidan. Hakama da rana, da daddarema haka, zuwa 11:30 saiya rufe yashigo gida. Tsakaninsa da Asma'u kam babu komai sai gaisuwa da girmamawa, ita tsoronsama takeyi, aganinta tunda yafara mata gargad'in ranar to aii zuwa nangaba duk abinda yazo zuciyarsa zai iya mata. Yaukam antashi da muku-mukun sanyi, wanan yasaka Asma'u tashi da zazza6i mai zafi da mura......... *_(((S)))).....2017._* *_luv you all_* [12/6/2017, 4:15 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→31-32_* ........Tunda tayi sallar asuba takoma ta k'udundune a bargo. Shikam ya Umar tundaga masallaci baima dawo gidanba yana shago, agogo ya kalla dake cikin shagon har 9:37am amma Asma'u bata lek'oba, sallamar wani saurayi tak'atse masa tunani, ya amsa yana mik'a masa hannu suka gaisa, saurayin yace abashi Sabulun wanki, d'akkowa Ya Umar yayi yabashi, saikuma ga wasu yara, doledai ya hak'ura yacigaba dabama mutane abinda sukeso, haka shagon yake wuni cikin shige da fici namasu siyayya. Har 11 tayi baisamu damar shiga gidanba, gashi Asma'u ma bata lek'oba, yanaji azuciyarsa badai lafiyaba. Can zuwa 11:30 mutane sukad'an lafa saiya rufe shagon yashiga gida. Har yanzu Asma'u nak'udundune abargo, sai rawar sanyi take faman yi da sambatun zazza6i, dama ita haka take indai tana zazza6i tatayin sambatu kenan. Da sallama ya Umar yashigo, ganin Asma'u a kwance cikin bargo sai gabansa yafad'i, k'arasawa yayi cikin d'akin sosai yana fad'in lafiya kuwa?. Asma'u dabatasan yanayiba sai rawar sanyi takeyi tana sambatu dakiran baba, inna, Fatee, Rafi'a, hasiya, kuzo kutaimakeni, wayyo ya Fharuk zan mutu kazo plzz..... Ganin yanda take abirkice yak'arasa da sauri yazauna bakin katifar, husna lafiya kuwa? Yay maganar yana yaye k'aton bargon data lilli6a ajikinta, wani hucin zafin zazza6i yabigeshi, da sauri tarik'o hannunsa tana fad'in wayyo Yaya rufeni sanyi nakeji sheeeeee!!!!. Lilli6eta yayi tareda fad'in sannu, amma miyasa baki fad'aminba tun d'azun? Haba mutum yata zama da ciwone?. Mik'ewa yayi zai fita tarik'o hannunsa tana kuka, wayyo ya Fharuk kaina kamar zai fashe, k'irjinama haka, kataimakeni wayyo. Tausayi tabashi sosai, dawowa yayi yazauna akusada ita, tad'ago da dak'yar tad'ora kanta saman cinyarsa, kokad'an bataso yatashi data Kusada ita, (dama itakam wanan salon zazza6inta kenan, saitaji wani akusada ita). Ya Umar yad'an rintse ido danjin yanda zafin zazza6inta ya ratsamasa jiki, tausayinta yakuma kamashi, kanta yashafa ahankali, husna kikwanta zanje nama muktar maganane kozai samo mana doctor d'in dazai dubaki. Uhm uhm Yaya banason allura wlhy, kabarni kawai. Yaya zan barki husna! Kinta6a ganin anbar mutum cikin ciwone? Kiniji yanda jikinki yayzafi kuwa?........ Kafin tace wani abu sai sukaji sallaman Rafi'a. Ya Umar ne ya amsa, tatsaya ak'ofar d'aki danjin muryarsa, jin shiru nawani lokaci ya ce, "shigo mana." K'arasowa tayi cikin d'akin, ta gaida ya Umar sanan ta tambayi miya sami Asma'u?. Batada lfyne, yauwa shiga nan makwaftanmu kima muktar magana kozai samo mana doctor dazaizo gida?. To Yaya, ammafa masu sayen Abu suna jiranka a k'ofar shago. O!. kinga kar6a key d'in, idan kinmasa magana saiki bud'e ki zauna, kafin nagama. OK, tana kar6ar key d'in tafice da sauri. Mintina k'alilan saiga Muktar yazo, dak'yar ya Umar yasamu Asma'u tabarsa yatashi, fitowa yayi wajen Mukhtar, hannu yabasa suka gaisa sanan yamasa bayanin ga doctor Al-ameen nan zuwa. OK Abokina ngd sosaifa, ALLAH yabar zuminci. Abokina aii babu godiya tsakaninmu, munrigada munzama d'aya, ciwon madam kodai munsami baby ne?. Dariya ya Umar yayi yana fad'in abokina baby kuma? A INA?. Hhhh babu wani baby abokina, zazza6ine kawai wlhy. To shikenan ALLAH ya k'ara sauk'i, cikinma muna addu'ar zuwansa nan kusa. Murmushi kawai ya Umar yayi batareda yace komaiba. Babu dad'ewa saiga doctor Al-ameen ya iso, suna gaisawa ya Umar yamasa iso zuwa cikin d'akin Asma'u. Har yanzun kuka takeyi da surutanta, ya Umar yazauna Kusada ita, yayida doctor Al'ameen ke a zaune bisa wani tum-tum da lubna bata d'aukaba, Mukhtar kam na tsaye daga k'ofa. Tambayoyi yamata tana basa amsa, amma fad'i take pls doctor kada kamin allurafa. d'an dariya doctor Al-ameen yayi, ya ce, "madam kina tsoron allurane?." Kanta ta jinjina alamar a'a, cikin muryar Mara lafiya ta ce, "doctor banasone kawai." Gashi kuma dolene amiki ita, Dan teiport nadamunki sosai. K'an k'ame hannun ya Umar tayi sosai tana fad'in pls Yaya kace karyamin banaso. Harararta yayi danshi surutun yafara bashi haushi, yanada kishi sosai. Magun guna yabata sanan ya ce, "zai mata alluran dabata so d'in. Hawaye tafara zubarwa Rana k'ara k'ank'ame ya Umar tamkar zata koma cikin jikinshi. Kamo hannunta yayi yamik'ama doctor Al-ameen Wanda yake rik'e da igiya dansan d'aura mata yanemo jijiya. Igiyar ya d'aura mata, cikin sa'a aka samo jijiyar. Hawaye takeyi sosai Rana k'ara k'ank'ame ya Umar. Tana ganin yanufota da allurar yak'ara sautin kukanta, taso tabama Umar dariya amma saiya gimtse, doctor da Muktar kam saida suka murmusa. Wata uwar harara da ya Umar ya galla matace tasakata nutsuwa waje d'aya, amma hawayen basu daina zubaba. Tanaji tana gani akamata allurarnan, har aka gama tana k'ank'ame da ya Umar. Doctor ya kalli ya Umar ya ce, " Alhaji insha ALLAH zazza6in zai sauk'a, taci abinci tasha maganidai, ammafa idan har zuwa yamma akwai Matsala saika kirani. Okey doctor ngd sosai ya Umar yafad'a yana bashi hannu, saida suka rakashi har motarsa sanan ya Umar yadawo Muktar kuma yashiga gidansa. Babu dad'ewa saiga matan Muktar Sadiqqa tashigo gidan, lokacin ya Umar na k'ok'arin had'ama Asma'u shayi. Gaisuwa sukayi da ya Umar, ta tambayeshi mai jiki, sanan ta ajiye kular abinci data kawo. A'a Maman Faisal abokina yatadoki ko?. Lah babu komai wlhy, aii kawai kama koma shagon saina lura da ita, abincima nanan na ajiye a shop d'in. A'a aii hidimar tayi yawa Maman Faisal. Wlhy babu wani yawa Indai ba rainawa kayiba. Mik'ewa ya Umar yayi yana dariya, ni na' Isa?, aii sadai nace ALLAH yasaka da alkairi yabar zuminci kawai. To Ameen. Yana fita saddiqa tashiga hidimar bama Asma'u abinci, saiga Rafi'a da ya Umar ya kar6eta ya ce, "tashigo gida. Atare suka gyara gidan tsaf, bayan Asma'u taci abinci Saddiqa tasakata tayi wanka tasha magani, sanda tafito angyara d'akin tsaf, saikawai tasaka wasu kayan takuma kwanciya sai barci. Saida suka gama komai sannan Maman Faisal tawuce gida, Rafi'a kam saida tamusu abincin dare takuma gyara gidan tsaf sannan tawuce gida Dan tanaso taje islamiyya. Ya Umar yanata zagayata danyaga yajikin, amma har yamma bata farkaba. Sai bayan isha'i daya shigo yataradda ta tashi. Kintashi?. Kanta tad'aga masa, har yanzun tana cikin bargo. To yajikinnaki?, da sauk'i amma har yanzu inajin sanyi wlhy. Zai daina shima, tashi kiyi sallah ko?. Nanma kanta ta jinjina sannan ta yatsina fuska, yaya dama akwai ruwan zafi sainayi dashi, bazan iya da ruwan sanyiba. OK bara naduba ko Rafi'a tazuba a filas. Rafi'a tawucene?. Eh tun d'azun tawuce, tanason zuwa islamiyya tace. Batace komaiba, shima yafita yakawo mata ruwan zafin, dakansa ya taimaka mata zuwa bayi, tsayawa yayi kanta yak'i fita. Tajuyo tana kallonsa kamar zatayi kuka, kafita to. Gira yad'age sama tareda d'an langa6e kansa gefe, bazaki iyayi agabana baneba?. Gyad'a kanta tayi cikeda shagwa6a. Murmushi yayi, ya jingina da bango harda hard'e hannu ak'irjinsa yana kallonta. Ta marairaice murya tana k'ank'ame jikinta, yaya sanyi nakeji wlhy, kuma zanyi fitsarin atsaye... d'an zaro idonsa yayi waje, ya CE, "da gsk?." ALLAH kuwa. Murmushi yayi mata sannan yafice batareda yace komaiba. Tana idar da sallan takuma zuwa zata kwanta, rik'o hannunta yayi yana fad'in no zauna ki huta. Wayyo ya sanyi fa. Toni wannan sanyi namiyene? Dayak'i tafiya. Bara nakira doctor namasa bayani...... Kafin Asma'u ta ce, wani Abu saiga Faisal (babban yaron Muktar), rissinawa yayi ya gaidasu, yayma Asma'u sannu, sanan ya ce, "uncle Abba ya ce, "kakawo key d'in shop yazauna, kaikuma kazauna wajen aunty. To yarona ALLAH yayimaku albarka kaji, gashi kacemasa ngd. Rissinawa yayi yakar6a yafita. Shikuma yashiga kiran doctor. Bayan sun gaisa yaymasa bayanin harfa yanzu Asma'u tanajin sanyi. 'Yar dariya doctor yayi, ya ce, "wanan aikinkane Alhaji, indai babu zazza6in to Alhmdllh, maganar sanyi kam tana buk'atar d'umin jikinkane kawai. Da sauri Asma'u da ya Umar suka kalli juna Dan yasaka wayarne a Hans Free. taja bargo ta kwanta, shikuma yad'auke idonsa daga kanta yamaida hankalinsa akan maganar doctor. Okey doctor babu damuwa ngd sosai, saida safe. ALLAH yakaimu Alhaji, agaidamin da madam. Okey zataji, agaida iyali. Koda ya Umar ya kammala wayan baikalli Asma'u ba yatashi yafice, itako tak'ara k'udundune kanta a bargo, tamkar wadda ake shirin sacewa. Waje yaje wajen Muktar, saida sukad'anyi magana ta mintuna sannan yadawo gidan. Kaitsaye d'akinsa yanufa, yay wanka tareda shirin barci tsaf sannan yakoma d'akin Asma'u. Harma tafara barci ita. Yad'an dad'e akanta yana k'are mata kallo cikeda tunani kala-kala tamkar bayason abinda yay niyyar yi agareta na bata taimakon da doctor yabashi shawarar. Tsawon mintuna sannan yazauna abakin katifar tareda d'aga bargon yashiga ahankali. Jawota yayi ya manna da jikinsa, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke tareda rinmtse idanunsa. Itakam sai kawai tagyara kwanciyarta danjinta cikin wani lallausan jiki, gawani d'umin mai dad'i da k'amshi. Barcin yaci k'arfinta shiyyasa ko farkawama batayiba. Amma ga mutumin naku ba haka baneba, jinsa yakeyi tamkar bashiba, tuni yasan shi mutumne mai yawan buk'ata shiyyasa yake tausayin fara kusantar Asma'u, amma yazaiyi? Zuciyarsa takasa daurewa, akwana biyunnan hak'uri kawai yakeyi. Yanason kasancewa da matarsa amma yana gudun karkuma ta rainashi. Yakuma k'ank'ame ta sosai tamkar za'a kwaceta daga gareshi, jin anrik'eta tamau yasakata motsawa, shima saiya sassauta mata. Addu'a yamusu ta barci, tanata barcinta amma shi yagagara yin nasa saboda kwad'ayin kasancewa da ita................ *_"ngd duknaga sak'on gaisuwarku, harma damasu kirana, harma wad'anda basu sami damaba, dukna gode ALLAH yabar zuminci, nama warke, ammafa ina jiran kazar😋😋🤷🏽‍♀😄"_*. Luv you all💋💯 *_Luv you all_* *_(((S))).......2017_* [12/9/2017, 8:40 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→33-34_* .......Haka yakasance yana gadinta har asubahi baisamu wani barcin kirkiba, itakam bamatasan yanayiba, barcinta tasha sosai, musamman datajita cikin wani ni'imtaccen jiki mai yalwataccen k'amshi, ga d'umi na musamman dayafi bargon data wuni aciki. Kiran sallar asubahine yasakata farkawa, akuma lokacin wani barci mai dad'i ya d'auki ya Umar kasancewar baisamu yiba farkon dare, ahankali ta bud'e idanunta tanamai ambatar addu'ar farkawa daga barci, saukar numfashin datakeji ahankali visa gadon bayanta yasakata juyawa ta sauke idanunta akan fuskar ya Umar daketa barcinsa. Sosai tawaro idanu waje, azuciyarta ta ce, "la'ila. miya kawo ya Fharuk nan? Kardai tare muka kwana? Nabani wannan abin kunya har ina. Tana k'ok'arin zame jikinta ya Umar yafarka. K'ara rik'eta yayi danjin zata bar jikinsa, kokad'an baiyima zaton asuba tayiba. Jin haka Asma'u ta ce, " ya Fharuk asuba yayifa." 'Muryarta narawa tayi maganar.' Bud'e idanunsa yayi shima, ahankali cikin muryar barci ya ce, "Asmah da gsk asubahi tayi?." Kanta ta iya d'aga masa kawai, amma takasa magana. Yunk'urawa yay yatashi zaune shima yana binta da kallo, kauda idonta tayi daga kansa tashige bayi. Shima saiya tashi yafita zuwa d'akinsa. Yana dawowa daga masallaci yalok'o d'akinta, tana zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani, saida takai k'arshen surar sanan tatsaya, dama takusa kammalawa. Kanta ak'asa ta ce, "ina kwana." Ya ce, "Lfy lau, yajikin naki?. Alhmdllh. Nama warke. Masha ALLAH, har sanyin kindainaji kenan?. K'asa takumayi da kanta Dan kunya, haka kawai yau taji tana matsanancin jin kunyarsa, kokad'an bataso su had'a ido, musamman idan ta tuna cewa aguri d'aya suka kwana, manne da juna kuma.......... Katse mata tunani yayi dafad'in, kinyi shiru, ko har yanzundai kinajin sanyinne? Idan kinaji kuma to sainak'ara baki d'umin jikina. Tusa kanta tayi cikin cinyoyi, kai ya Fharuk kabari plss. Hummyim toni minayi kuma?. Shiru tayi tana k'ara k'ank'ame kanta acikin cinyoyin nata. Ganin haka ya Umar yamik'e abinsa, shikenan bara naje shago kinsan 'yan makaranta da saurin fita. Kanta ta jinjina amma bata d'agoba ta ce, ''ALLAH yabada sa'a. Ameen yafad'a yana fita........... ____________________ Akwana ukunnan sosai ya Umar ke kulada Asma'u, wanan karonkam sunci gari, Dan har mama saida tazo dubata, hakan yayima ya Umar dad'i sosai, dazata tafi yahad'a mata abubuwa sosai. Dukda batawani d'auki shagon da muhimmanciba tamasa godiya tawuce. Bayan tafiyar mama saiya shigo gidan, Asma'u nazaune akan katifarta tana canja zanin gado, canjama filo riga takeyi. Yay sallama. d'ago k'yawawan idanunta tayi tasauke akansa, gira yad'aga mata tareda sakin wani sassanyan murmushi. Itama murshin tamasa sannan tajanye idanunta tacigaba da abinda takeyi. Harta wuce?. Uhm tawuce, yafad'a yana zama bakin katifa. Ya ce, " lallai kekam 'yar gatan mamace, yau har tana zuwa dubaki?. Ya Fharuk kenan, dama can ni 'yargatan mamace koka mantane?. Ban mantaba my Asmah Husna!. Murmushi Asma'u tayi danjin wani salon suna daga yayan nata. Kwanto da kansa yayi saman filon data d'ora akan cinyarta bayan tagama saka rigar, ya hard'e hannayensa a k'irji tareda lumshe idanu. Itadai Asma'u tana kallon ikon ALLAH, Tunda tayi zazza6in nan take ganin sabon salo wa yayan nata, ta tsurama k'yak'yk'yawar fuskarsa ido, sosai ya Umar ya had'u, gashi bak'i sosai, kuma bak'insa mai k'yaune, kwanakin baya yarame amma yanzu saitaga yamata k'iba, kodan hankalinsa yafara kwanciyane?. Hannu takai ahankali zata ta6a girarsa dake matuk'ar burgeta sosai, girarsa tanada yawa, tayi kamar zata had'e dajuna, kasancewarsa bak'i kuma bai hana bayyanartaba. Bud'e idanu yayai ahankali danjin motsin hannu akan idonsa. Da sauri Asma'u tasa hannu tarufe fuskar tata. Yayi murmushi mai sauti. My Asmah miyafaru?. Babu komai fa. Hummm k'arya babu k'yau. 'Yar dariya tayi, batareda ta ce, "komaiba". ‘zuwa can kuma ta ce, " Yaya bazakaje shagobane?.’ Bud'e idonsa yayi sosai tareda d'age gira d'aya yana wani murmushin gefen bak'i, ya ce, "kingaji daganinane?." Lah a'a bafa haka nake nufiba. To mikike nufi?. Uhm damafa dankar mutane suyita jirankane, jibafa har 9:48. Juyawa yayi yana kallon agogon shima, saikuma yadawo da dubansa kanta, karki damu akwai mutum a shagon. Akwai mutum?. ‘Asma'u ta tambaya cikin mamaki. Tashi yayi zaune sosai, yad'auke filon daga cinyarta yagyara asaman katifar sosai ya kwanta. Itadai binsa kawai takeyi da kallon mamaki. Bata ankaraba taji yajawota, ta fad'o jikinsa. Kafin tayi wani yunk'uri ya rungumeta tsam tamkar za'a kwaceta. Tuni jikin Asma'u yafara rawa, tamarasa mizatayi ta kwaci kanta. Gogan naku kuwa abubuwa yake mata masu nuna tsananin k'yauna da bege agareta. Tun tana iya yunk'urin hanashi harta Gaza komai sai kuka ahankali damasa magiyar yayi hak'uri bafatada lfy. Kokad'an bai saurari furicin nataba, sosai cukirkud'ata ya cigaba dayi yanda yakeso. Saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana maida numfashi. Itakam kuka takeyi sosai, ganin yasaketa tatashi da hanzari tabar masa d'akin. Binta kawai yakeyi da kallo yana zuba murmushi tamkar wanda yasamu abinda yakeso.. _____________________ Tsawon kwanaki hud'u kenan tsakanin Asma'u da ya Umar ana 'yar wasan 6uya, ko kad'an bata yarda su had'u dan harga ALLAH tsoronsa takeji, shago kam ko lek'e bata lek'ashi. Yauma suna zaune atsakar gida itada maman faisal tana mata kitso (dan Asma'u ta iya kitso sosai), hirarsu suketa zubawa irinta mata, maman faisal tana tambayarta kozatasha wani magani takawo mata?. Anty magani kuma? Maganin miyene?. Dariya maman Faisal tayi sannan ta ce, "magani dai na mata. Asma'u bata fahimci zancen na Maman Faisal ba ko kad'an, dan haka tayi dariya, kai anty saddiqa mu mata har wani magani ke garemu daban?. Maman Faisal tajuyo tana kallon Asma'u da k'yau danson gaskata maganarta. Banganeba Asma'u! Kina nufin bakisan miye maganin mataba? Kina matar aure. Asma'u dake kallon maman Faisal tad'an yatsine fuska, wlhy Anty saddiqa kiyarda dani bansaniba. Jinjina kai kawai Anty saddiqa takeyi cikeda mamakin furucin na Asma'u. Dama har yanzu akwai matan dabasusan ire-iren wad'annan abubuwanba arayuwa kenan?. Idan akayi la'akari da yanda mata suka lalata kansu dashan magunguna yanzu, wasuma cutar dasu sukeyi amma sun gaza ganewa, dolene duk wadda tanuna bata saniba ayi mamaki. Asma'u dai tacigaba dayima maman faisal kitsonta, sauraren k'arin bayani kawai takeyi daga gareta. Jin tayi shiru ta ce, " anty Saddiaqa kigayamin dan ALLAH, miye maganin mata?. Bak'aramar dariya tambayar tabama Maman Faisal ba, dan haka tadara, saidatayi dariya sosai sannan ta ce, "Asma'u nabaki dama kitambayi Umar nasan zai fad'a miki miye maganin mata. Shiru Asma'u tayi tana tunani azuciyarta, mizaisa anty saddiqa ta ce, " ta tambayi ya Fharuk? Shimiye had'insa da wanan maganar? tunda maganin mata akace. Badai takuma cema Anty Saddiqa komaiba, amma ta k'udiri aniyar tambayar ya Fharuk d'in kamar yanda anty Saddiqa tafad'a mata. Maman Faisal kam tayima Asma'u gatsene dantaga shin rainamata hankali tayi (tasan maganin Matan) kokuwa batama San miye ma'anar shan maganin matanba. Amma amamakinta saitaji Asma'un tayi shiru batace komaiba. Itama daganan wata hirar takawo mata, ta watsar dawaccan maganar gefe kawai. Bayan sun kammala k'itson sukad'anyi hira har yara suka dawo daga islamiyya, sunsan babu Inda mamansu take zuwa sai gidan Anty Asma'u, Dan haka suka shigo Nanal. Oyayo 'yan islamiyya antaso?. Eh Anty INA yini. Lafiya lau yarana, ya makaranta?. Lafiya lau. Daga nan suka gaida mamansu ma. Maman Faisal ta ce, "kunga kuje gida acanja kaya, Faisal kacanjama kowa kajiko, karfa Ku hargitsa kayan. To mama, Faisal yaja k'annansa suka fita. Asma'u da Maman Faisal kuma sunata hirarasu. Suna nan zaune saiga ya Umar yashigo, da alama dai akwai abinda yazoyi cikin gida. Da Sauri Maman Faisal taja hijjabi tasaka. Shi koma Inda take bai wani kallaba, yadai amsa gaisuwarta sannan yakalli Asma'u da ak'alla yad'au tsawon kwana Biyar bai gantaba, tun randa abinnan yafaru basu sake had'uwaba. Itama kallo d'aya tamasa ta d'auke kanta daga gareshi. Yana shigewa Maman Faisal ta zunguri Asma'u. Asma'u kitashi gafa mijinki yashigo. Yatsine fuska Asma'u tayi, yo Anty nimizan masa? K'ilama wani abun yazo d'auka. Idanu Maman Faisal tazaro waje, Asma'u bangane mizaki masaba? Mijinkine fa? Yashigo gida amma bazakije kiji matsalarsaba?. Anya kinada wayau kuwa? Kamar yanda nake tsammani?. Hummm Anty kenan inada wayau mana. Inafa kikaga wayau tunda bakisan yazaki kula da mijinkiba. Bara kigani natashi idan Dan ganina zai hanaki bama mijinki kulawa. Da Sauri taruk'o hannunta, lah wlhy Anty Bahaka bane, yihak'uri kizauna Dan ALLAH, kinad'an d'ebemin kewa kuma kice zaki gudu? Nidai yanzu fad'amin mikikeso nayi to?. Maman Faisal ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin wai dama haka Asma'u take? batada wayo, ta girgiza kai tareda fad'in yanzu kije kikaimasa ruwansha, sannan kiji miye matsalarsa. Shike nan Anty zanje, amma kimin alk'awari bazaki tafiba?. ALLAH babu Inda zanje, jeki kidawo. Da azama Asma'u tamik'e, kicin tashiga tad'iba ruwa a jok sannan tanufi cikin falonsu. Ganin babu kowa anan tashiga d'akinsa da sallama k'irjinta na dukan tara-tara. Gabantane yafad'i yayinda tayi tozali da Ya Umar tsaye yana goge jiki da Alama wanka yayi. Taisaurin kauda kanta daga gareshi, zuciyarta na faman tambayarta wankan mi ya Umar yayi yanzu da yamma haka? d'azunfa babu dad'ewa yayi wanka?. Ganin mutum agabanta yasaka rawar jikinta k'aruwa, jok d'in ruwan haryana girgiza. Ya Umar ya jinjina Kansa kawai yana kallonta, ruwan hannunta ya kar6a kafin ta zube masashi akan katifa, Dan yakula arikice take sosai. Tana bashi takama hanyar fita. Dasauri ya ce, "wai saurin mikikeyine haka?. In INA tafara namarasa gsky, u...u....um....dama zanjene Anty Saddiqa tana jirana awaje. Hum Kodai kinason guduwa saboda kina tareda dodo? Miyasa kike tsorona yanzun Husna? Konamiki kama da abin tsorone?. Azuciyarta ta ce, " sosaima wlhy". ‘amma afili sai ta girgiza MASA kai.’ Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai, kokad'an babu walwala afuskarsa, ya ce, "jeki kawai..... Aibama tabari ya k'arasaba tafice da Sauri har tanayin tuntu6e zata fad'i. Tayi saurin tare Bango sannan tafice. Ya Uamar yacije le6ensa da k'arfi yana naushin iska, yamatse hannayensa da k'arfi yana magana afili kamar wani sabon kamu. Gashinan Umar dama abinda naketa gudan maka kenan, gashinan tanajin tsoronka, guduna takeyi, dama abinda Yasa ban nemi komai daga garetaba Kennan. Jiba wai d'an abinda naimatannan yasa har tafara guduna. Wayyo nikam miye fafita!!.............? *_Luv you all_*. *_((((S)))).........2017_* [12/11/2017, 8:57 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→35-36_* .......Haka yayta zagaye d'akin yana surutai, saida yagaji Dan kansa sanan yashirya cikin wankan k'ananun kaya yafito sai baza k'amshi yakeyi. Idan kaga ya Umar saika d'auka irin matashin saurayinnan ne dabai wuce 26 ba, yanada tsafta Da son k'amshi sosai. Atsakar gidan Yakuma tarar da su Asma'u, wadda tun d'azun tadawo wajen Maman Faisal. Saina dawo yafad'a yana k'ok'arin ficewa. Adawo lafiya sukafad'a suduka, shikuma yafice. Yana fita Maman Faisal tashiga yima Asma'u fad'a (Dan ta girmeta gsky, zata iya zama sa'ar Anty saratu ma). Haba Asma'u yanzunan mijinki zai fita bazaki masa rakkiyaba? Idanfa kika saka wasa wata zatazo ta kwace miki miji. Nakula kinada sakaci sosai. Hakamafa d'azun abirkice kika fito, kamar wadda taje wajen dodo. Kodai akwai matsalane?. Girgiza kai Asma'u tayi, Dan aganinta baikamata tabama Anty Saddiqa labarin abinda yafaru itada ya Umar ba. Maman Faisal tacigaba da fad'in to gsky ki gyara kinjiko. maza sunason ana kula dasu tamkar kwai a cokali. Indai kinama namiji haka to tabbas zai koma miki tamkar jinjiri wlhy. Hakane anty amma wlhy ya Umar daban yake, yacika tauri dayawa. Wani lokacinma dolene kiji matuk'ar tsoronsa. Hummm Asma'u kenan, duk taurin namiji mace saita sakashi laushi. Shawarar dazan baki ki fara karatun Hausa Novels, insha ALLAH zaki k'aru matuk'a da ilimin zama da miji. (Musamman idan kin had'u da buk d'in marubutan dasuka san Kansu) akwai wasu buks dana karanta na bilyn Abdul, na tabbata zaki k'aru acikinsu. To a ina zan samu?. Bak'yayin charting?. Inayi da, amma yanzu banayi. Tom Indai ba mijinki ya hanakiba kikoma yi zan baki no. d'inta. To Anty ngd sosai. Maman Faisal tamik'e dak'yar saboda tsohon ciki datakedashi, haihuwa yau ko gobe, bara naje gida, nasan sunacan sunamin 6arna tunda sukak'i dawowa. To Anty ngd..... .................................. Su Lubna anata hidimar biki, shiri sukeyi na garari Dan bikin namasu akwaine babu k'arya. Komai awadace yake tafiya, party kam aii anshirya yafi kala 10, su Lubna sune amarori k'irjin biki. Yau kamu Dan haka sukaci uwar kwalliya nawani sky blue d'in less itada Suhaima, sai walk'iya sukeyi, idan kagansu kai kace sune amaren, bakowa zaiga Lubna ya ce, "ta ta6a aureba bareba harda yara biyu. Harabar gidan suka fito inda abokan Ameer suke birjik, duk sunci wankan bak'in wando da yellow d'in Riga, wanan shine kwalliyar kamu na maza. Matankuwa yellow d'in wando da bak'ar riga. Sudai su Lubna basu sakaba. Wani abokin Ameer ya ce, " kai yarinyar canfa tawuce dani wlhy, wai k'anwar Amee CE?. Inaganin k'anwarsace, ammafa in k'aramar tafimin k'yau, kasanni ko aure zanyi banason yar 20+ gsky. Nafison daga 16 zuwa k'asa. Dariya abokin yayi, ya ce, "humm aikai mugunta kakeji....... Wucewarsu Luban tagabansu tahanasu cigaba da hirar. Sukam basusan sunayiba, sun wuce sun barsu da k'amshinsu. Mota suka shiga, Lubna tajasu suka bar gidan. Kaitsaye hall d'in daza'ayi kamu suka nufa. Dangin amarya Suma sunyi shirinsu sosai, amarya tad'auki k'yau, naira tayi kuka agidannan. Su Lubna sai nan nan akeyi dasu, sukuma suna fankama da Nuna isa, su adole dangin miji. Babu dad'ewa su Ameer suka iso. Ba awani tsaya 6ata lokaciba aka fara gudanar da kamu Wanda yak'ayatar. Sai wajen 9pm aka tashi, ansha casu kam babu k'arya. Idan kuga yanda Lubna tadage tana rawa saikusha mamaki...... ____________________ Tunda Anty Saddiqa tafad'a mata idan tana sakaci wata zata kwace mata miji tashiga damuwa, tana matuk'ar son mijinta, tanajin ya Umar yafi sauran maza awajenta, idan akace wata zata iya kwaceshi agareta takanji tamkar an soki zuciyarta da mashi. Wasu zafafan hawaye suka gangaro bisa kumarunta. Bata sharesuba, saima cigaba da matso wasu datayi. Duvanta takai ga agogon d'akin, karfe 9:23pm amma har yanzu ya Umar bai dawo gidanba, tun fitar d'azu da yamma. Tana mamakin ina yajene har zuwa wannan time d'in?. (Zuciyarta ta ce, ''yaje tad'i.") Rushewa tayi dawani kuka mara dalili.... Ni dariyama tabani aradu😂. Tana nan tana kukanta saitaji motsin bud'e k'ofa, da sauri tad'ago tana kallonsa. Ya Umar ne sanye cikin kayan barci, da'alama ma yadad'e da dawowa gidan. Shima kallonta kawai yakeyi amma fuskarsa ko kad'an babu walwala. Cikin d'akin yak'araso, yaja tum-tum yazauna har yanzu idanunsa akanta. Itadai nata na k'asa, ga hawaye sha6e- sha6e a fuskarta. Ahankali ya firzo huci daga bakinsa yana mai kauda kansa daga gareta. Ko kad'an bayaso yaga mace na kuka. Shi mutumne mai tausayi sosai musamman akan mata. Yakuma dawo da kallonsa gareta, kukan mikikeyine? Ko har yanzu bakida lafiyar?. Shiru tamasa, bata d'agoba, bakumata tanka masaba. Dan zuciyarta wani irin zafi takeji, gani takeyi kamar da gsk daga tad'in yake. Cikin d'an fad'a-fad'a ya ce, "wai bakijinane!!?. Da sauri tad'ago takalleshi, ganin yanda yakuma tur6une fuska sai tsoronsa yakuma kamata. Bakinta na rawa ta ce, "bakaine kaje tad'iba." Tad'i!?. ‘ya Umar yafad'a cikin sigar tambaya da mamaki.’ Itama kanta tad'a tana wani kumbura baki. Siririn tsaki yayi, amma batajiba. Ya ce, "kewaye yagaya miki naje tad'i?. Gabantane yafad'i, dan kuwa dai zuciyartace ta sak'a mata, bawanine yafad'a mataba. Shima ganin haka sai kawai ya girgiza kai. Yakuma yin k'aramin tsaki tareda fad'in kinga ni bar wannan banzan shirmen naki gefe, magana nazo muyi. Tashi kije ki wanke fuskarki kidawo. Ahankali tamik'e kamar wadda kwai yafashema aciki tashiga bayi. Fes tawanke fuskarta sanan tadawo gareshi. Saida sukaja wasu 'yan mintuna sannan yay gyaran murya:- inaso kibani hankalinki nan muyi magana. Kanta ta jinjina masa alamar to. _d'azu fitar danayi naje office d'in su muktar ne, dama tun kwana hud'u daya wuce munyi magana, ya ce, " nabada takarduna zai kaima ogansu yanemamin aiki. Dafarko ban aminceba Dan narigada na fidda raina ga aikin. Amma saiya nace sosai da magiya da kawomin hujjoji akan fa'idar Neman aikin harna amince. Jiya yakai takardun, yaukuma ogan nasu saiya buk'aci ganina. Shine Muktar yakirani ina shago yasanarmin. Wanna dalilin yasa nashirya naje. Tom saidai kuma abinda yagirgizani shine ogan su muktar abokine ga dad (mahaifin Lubna) akwai dangantaka mai k'arfi a tsakaninsu ta kasuwanci gsky, Dan sanda ina k'arkashinsa yasha aikena awajensa. Abu na biyu kuma shine Alhaji Ahmad mai kano yad'aukeni aiki ak'ark'ashin kamfanin nasa, ya ce, "kuma yana buk'atar bayani daga gareni akan abinda yasa muka rabu da mahaifin Lubna. Yabani dama daga nan zuwa gobe, idan nafad'a masa yace zuwa Monday zan fara aiki. Yakika gani nafad'a masa gsky?, kokuwa na hak'ura da aikin kawai?. Ban fad'ama kowa maganarnanba saike, koshi Muktar baisan yanda mukayiba. Asma'u tasauke ajiyar zuciya sanan ta gyara zama. Yaya nidai abinda nake gani kafad'a masa kawai, Dan ALLAH yagani bacin amana ko cutarwace taravaku da mahaifin anty Lubnar ba, yanzu kuma aiki za'a d'aukeka idan kayi kuma za'a biyaka, kaga kuwa guminka zakaci bawai a k'ark'ashin wani zaka zaunaba. Kuma ina ganin koda kafara aiki tom nikuma saina cigaba da lura da shagon harmuga abinda ALLAH zaiyi. Sosai ya Umar yagamsu da bayaninta Dan haka ya jinjina mata kai alamar gamsuwa, gawata k'aunarta na ratsashi, wani lokacin idan tayi Abu tamkar wata babba. Idan shirmen yamotsa kuma sai an sauke masa cikin tirela😂. Asma'u tayi murmushi mai kwantar da zuciya, ya Fharuk natayaka Murna, ALLAH yabada nasara da sa'a. Ameen Husna ngd. Filo yajawo ya kwanta. Gaban Asma'u ne yafad'i, karfa asake irin ta ranar. Kamar yasan tunanun datakeyi saiya mik'e zaune yana fad'in yau baza'a bani abinci bane?. Da sauri Asma'u tamik'e, Dan danan tacika gabansa da kulolin abinci, tashi yayi zaune tazuba masa komai. Yanzukam babu laifi yad'an saki fuskarsa, Dan yanacin abinci yana satar kallonta. Sukan had'a ido lokaci-likaci, ganin haka ya Umar yad'auke idonsa gaba d'aya daga kanta yamaida ahankali kan cin abincinsa. Kamar daga sama yaji Asma'u ta ce, "ya Fharuk inada tambaya?." Idanunsa masu haske yad'ago yana kallonta, saida ya had'iye abincin bakinsa sannan ya ce, ''ina saurarenki?." Shiru nawani lokaci tanata juya maganar a zuciyarta, kamar tayi kamar kartayi, can wata zuciyarta na angizata akan ta tambayesa da ace tazauna cikin duhu. Jin tayi shiru yace yadai? Kokin fasane?. A'a. Dama inason tambayarka minene maganin mata?. Sosai ya ware idanunsa akanta. Aransa yace mike damun kan yarinyarnan?. (Inhar bai mantaba Lubna ta ta6a fad'a masa kayan k'arin ni'ima sune ake kira Maganin mata. Dan yata6a rutsata tana sha saiya tambayeta maganin minene wannan?. Dayake Lubna macece da batada kunyar Abu kai tsaye, musamman ga mijinta, sai takecemasa maganin k'arin ni'imane).......... Ganin yayi shiru yadaina cin abincin, kuma gashi ya tsura mata idan ko k'yaftawa bayayi saitasha jinin jikinta. ad'arare ta ce, "ya Fharuk akwai matsalane?. Girgiza mata kai kawai yayi yacigaba dacin abincinsa, Dan aganinsa dawata manufa daban tamasa tambayar, ashema k'aryar gudunsa takeyi, tasan komai, tana raina masa hankaline kawai. Wani d'an murmushin gefen baki yayi, shikad'ai yasan miya kitsa wa zuciyarsa. Asma'u kam tayi gum, Dan sosai tasha jinin jikinta akan tambayar. Harya kammala cin abincin babu maicewa da d'an uwansa k'ala. Bayan ta gyara wajen ta kwashe kwanikan tadawo d'akin. Inda tabarsa anan ta iskesa. Ya ce, " kinason amsar tambayarki?. Kanta ta jinjina da sauri. Yalumshe idanunsa yana wani murmushi na musamman Wanda Asma'u bata ta6a gani daga gareshiba. Zan baki amsar tambayarki amma nima zan tambayeki Abu biyune, idan kinsani bazan amsa mikiba. Idan baki saniba zan had'a duka nabaki amsa, amma bayauba, zan baki amsar Abu d'aya a daren yau, biyun kuma saida safe. Bata kawo komai arantaba ta ce, "to ina saurarenka. Mizakiyi da maganin mata?. Na biyu:- miyasa kika tambayeni. Gefen wuyanta ta Sosa Dan batasan amsar dazata bashiba. Ganin haka ya ce, "shikenan, tashi kiyo alwala zan baki amsar farko dakika tambayeni............... _kuyi hak'uri danifa, yanzu bakwajina yanda ya kamata, wlhy nayi matuk'ar busy ne kawai, kutayani da addu'ar samun nasara kawai._ *l Love you all*😍 *_((S)).....2017_* *_luv you all_* [12/12/2017, 10:20 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→37-38_* ..........Bata kawo komai arantaba tatashi zuwa Bathroom, babu dad'ewa tafito d'aureda alwala. Ya Umar baya d'akin, da alama shima yaje d'auro Alwalane. K'ok'arin canja zanin sallah tafara, saigashi yashigo. Babu Wanda yace da d'an uwansa k'ala. Ya Umar yad'auki sallaya ya shimfid'a musu guda biyu. Sallah suka gabatar raka'a biyu. Ya Umar yadafa kanta yay addu'a kamar yanda addinin islama ya koyar mana. Sai ayanzu wani tunani yazo zuciyar Asma'u. Gabanta yashiga fad'uwa da dukan tara-tara. Duk addu'oin dayaketa kwararawa bata fahimtar komai, kawaidai tad'aga hannunta samane. amma ko ameen tagagara furtawa. Nashiga uku ni Asma'u! Shin mi ya Fharuk yake nufine? Nidai nasan wannan sallace da MAZON ALLAH (SAW) yakoyar damu muyi aranar da aka kawo mace amatsayin amarya. To amma shi ya Fharuk miye tasa manufar?. ‘wani ras gabanta yafad'i yayinda zuciyarta tabata wata bahaguwar amsa.’ Bata dawo hayyacintaba taji ya Fharuk na girgizata. "K!. Tunanin mi kikeyine haka?. Firgigit tadawo hayyacinta, sai mazurai takeyi da idanu. Murya na rawa ta ce, " ya Fharuk mizai farune?." Kallonta yayi kamar zaiyi magana, saikuma yafasa ya mik'e, saida yazauna abakin katifar sannan ya ce, "mizai faru, kamarya?. Shiru tayi Dan gane kato6arar datasoyi. Baikamata ta nuna masa tama fahimci wani abuba, tunda yamaidata k'aramar yarinya. Itama bara zata nuna masa tanada wayo fa. Bai kuma cewa da ita komaiba taga yad'auki keys d'in shago yafita. Ta k'ofar cikin gida yabud'e, mintuna kad'an yadawo hannunsa d'aukeda yogot mai sanyi. Sau d'aya takalleshi ta kauda kanta. Shima zama yayi da yogot d'insa ahannu. Husna bani kofi biyu. Tashi tayi tamkar mara laka ajiki tafita batareda tayi koda tariba. Ya Umar yabita da kallo yana murmushin mugunta, 'Yar rainin wayo zaki fad'a musu yau da bakinki. Kigama wani langa6e-langa6en jikinki yau babu fashi saina mire sadakina. Haka Asma'u tadawo da kofuna jiki duk a sanyaye. Tanata tunanin abinda zatayi Dan ku6ta daga tarkon ya Fharuk. Kofunan yakar6a a hannunta, yazuba musu yogot mai dad'i, sai k'amshi yakeyi tamkar na kwakwa da abarba. Yacika Kofi d'aya sannan yamuk'o mata. Bismillah. Fuska ta yatsine sosai, kaikace batada lafiya. ya Fharuk nak'oshi, ni koma abincin dare banciba saboda cikina yanamin ciwo sosai. Dariyace taso kwacema ya Umar Dan ganin yanda Asma'u tawani narke fuska da narke jiki, amma dayake jarumin kamewane saiya dake, aransa ya ce, "zaki fad'a musu yarinya, ak'alla nabaki shekara 15 a duniya, duk wani shirinki a tafin hannuna yake. Amma afili saiyayi murmushi, ayya Husna sannu kinji, kar6a kisha kida kad'anne saina kawo miki magani. Ciwo bayason zama da yunwa aii. Shiru tayi tana satar kallonsa, kardai yagano shirinta shima?. Jin sanyi a hannunta ya katse mata tunani, kofin yogot d'inne yasaka mata ahannnu. Suka had'a ido, yad'age gira d'aya yana kallonta da ido d'aya, kona baki da kainane? Naga kamar kinajin jiki sosai. Ahankali ta kad'a kanta alamar a'a. Shima murmushi yayi yaja Kofi yazuba nasa. Hankali kwance yakeshan abinsa. Itakam Duk a d'arare take. Dukma zamansa a d'akin ya gundureta, tak'agara yagama yatafi. Amma amamakinta koda ya kammala saitaga yayi mik'a tareda zamewa ya kwanta akatifarta yana fad'in Alhmdllh. Tana nan tana cancana yogot d'in tamkar maiba yaron goye abinci har nawani adadin mintuna. Ganin shan yogot d'innata bana k'are bane yasa ya Umar mik'ewa yafita. Kamar yasan mitake shiryawa a zuciyarta yacire key d'in k'ofar yatafi dashi. Yana fita ta tashi da sauri danufin kulle k'ofa amma saitaga wayam babu key. Wani haushi da tsoro suka kamata lokaci d'aya, afili ta ce, "wayyo ya Fharuk dama mugunta ka shiryamin? Sai hawaye sharrrrr akumatu. Ganin kuka bazai mataba ta tuna dawani d'an kwalbar turare da Anty Saratu tabata ta ce, " tayi amfani dashi Daren farkonta bazata sha wahalaba. Cikin saurinta kuwa tafara lalubarsa, ALLAH kuwa yabata sa'ar ganinsa harma dawasu daban, bata ta6a amfani dako d'ayaba. Shid'in kawai ta d'auka sai wasu turare guda biyu masu fitinannen kamshi. Da hanzari tad'auka tashige bathroom. Duk yanda Anty Saratu ta koya mata haka tayi bayan tayi brush ta matsa ma bakinta wani Abu maid'an karan k'amshi. Sosai tagyara jikinta dukda tanata addu'ar ALLAH ma yasa karya dawo d'akin. Rigar barcin data d'akko maid'an kauri tasaka saboda yanayin sanyi da'ake ciki. Agurguje tagama tadawo d'akin, katifarta ta haye, yau babu zancen doguwar addu'ar barci. Dandanan ta kammala taja bargo ta k'udundune har kanta, ita adole barci takeyi. Shiru har minti kusan 20 suka shud'e kamar ya Fharuk bazai dawoba. Harta fara murnar rashin dawowarsa taji anturo k'ofa dawani fitinannen turare. Tasan ya Fharuk a 6angaren k'amshi babu sanya. Dukda k'irjinta na dukan uku-uku saida tayi murmushin jin dad'in k'amshin mai saka nutsuwa da farinciki........... Jin shigowarsa bargon gabanta yasake sabon salon lugude. Da Sauri tamatsa danjin ya mannata da jikinsa. Murya a raunane ta ce, ''ya Fharuk! Lafiya kuwa?." Lafiya k'alau, miya farune?. Um....um...dama naga kazo nanne, yau bakajin barcine?. Inaji mana Husna!, bagashi Nazo zanyiba. Idanu ta kwalalo waje, kasancewar akwai wuta, kuma baikai ga kashewaba yaganta sosai yanda take zare ido kaikace taga wani ojujune. Ya Fharuk kana nufun anan zaka kwana?. Umm. Kenifa kincikani da surutu. ranar dabakinki kikacemin kinajin sanyi, damma Nazo na taimakeki shine zakimin salo?. Baki Asma'u ta turo gaba, afili ta ce, "yo aii ranar kace, nikuma yau sumul nake, babu abinda ke damuna. Humyim dama d'azu k'arya kika zabgamin wai bak'yajin dad'i ko abinci bakiciba cikinki na miki ciwo?. Asmah arink'adaijin tsoron ALLAH. k'arya batada k'yau. K'ara turo baki tayi gaba. Shikuma yasaka d'anyatsa ya d'alli bakin. Da sauri tadafe bakinta hannu tana kukan ta6ara wai zafi. Baikuma bi takantaba harya mik'a hannu yakashe fitilar d'akin. Asma'u batason duhu, shima kuma sarai yasani amma yakashe Dan Neman magana. Tana ganin duhu tak'ank'amesa da sauri. Wayyo ya Fharuk kataimaka ka kunna, ALLAH bazan iya barci cikin duhuba. Kunnenta yalaluba, ahankali yake mata magana. Karki damu da duhu My Noor, kid'auka nine fitilarki, zakiga haske ya mamaye d'akin.. Yarrrrr tsigar jikin Asma'u yatashi saboda salon da ya Fharuk yake mata magana akunne. K'ok'arin barin jikinsa tafarayi. yakuma ruk'ita da k'yau yanda bazata guje masaba. Fitinannan k'amshin jikinta yake sunsuna. Wannan wane irin turarene kika saka Husna;?. ‘yay maganar murya asark'e, tamkar mai shirinsa yin kuka.’ Itama cikin Rawar murya data jiki ta ce, " turarene kawai yay.........." Batakai ga k'arasawaba ya manne bakinsu waje d'aya. Itakuma rawar jikintane yak'aru, dukda jikinta yana kar6ar sak'onninsa 100%, amma zuciyarta na razanar da ita wahalar dazata sha. Wannan yasa tafara kuka wuywuy da mutsu-mutsun kwace kanta. Gogan naku kam aii abin nema yasamu, aikin gabansa kawai yakeyi, yanda yake cikurkud'a Asma'un kaikace baita6a kusantar wata maceba a duniya. Nidai bilyn Ku sim sim nafito gudun aikata laifin kallon k'urulla🚶🏻‍♀.............. _kuyi hak'uri da wannan_.😻 *_Nagaisheku da k'yau 'yan group d'ina, ALLAH yabarmu tare.🙏🏻 irin tamau-tamau d'innan😉😻._* *_(((S)))........2017_* *_Luv you all_* [12/13/2017, 8:38 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→39-40_* ..........Idanun Asma'u biyu aka kira sallar Asuba. Amma koda motsin kirki takasayi daga inda take. Ciwon jiki da zafi a k'asanta duk sun addaba mata, sun taru sun zubar matama da zazza6i. Ga kukan datasha adaren jiya. Ya Umar kuwa barcinsa yakeyi sosai, shima barcin baiwani dad'e da d'aukarsaba saboda kukan da Asma'u takwana tanayi. Shikuma yana aikin lallashi. Sai wajen k'arfe 3 da 'yan mintuna barci ya saceta, shima yasamu yayi nasa. Ita dayake barcin wahala tayi, saita rigashi farkawa da wuri. Har aka fara kiran sallar farko ya Umar bai motsaba, itama Asma'u barcine yasake saceta.(kunsan dai aikin shaid'an). Wannan barcine yakaisu har 6:48 na Safiya. Ya Umar ne yafara farkawa ayanzunkam. Ganin haske ya yawaita, yasakashi mik'ewa zumbur, bakinsa d'aukeda addu'ar tashi barci. Innalillahi yashiga ambata Dan ganin agogo. Baima bi takan Asma'u ba yashige bayinta, wanka yayi agaggauce yad'auro alwala yafito. Jikinsa sai rawa yakeyi, arayuwa yana matuk'ar shiga damuwa idan lokacin sallah yawucesa. Hakan na 6ata masa rai. Anutse yagabatar da sallar Asubahi, yanamai cigaba daneman gafarrar ALLAH na jinkirta yinta akan kuskuren barci. Saida ya kammala hankalinsa ya kwanta yadawo kan Asma'u. Dubansa yakai gareta, anyi sa'a kuwa fuskarta tana fuskantarsa. Wani k'asaitaccen murmushi yasaki yana wani lumshe idanu, ahankali ya furta Husna daru kenan!, ALLAH yay miki albarka, ya dawwamar da ruhinki cikin farinciki, kamar yanda kika sakani adaren jiya. Nidake la6e agefe na ce, "ameen ya Umarin mu."🤸🏻‍♀😻 Tashi yayi daga kan sallayar yakoma kan katifar ya zauna saitin fuskar Asma'u. Sosai ya tsira mata idanu tamkar yau yafara ganinta, jiyake wata k'aunarta naratsa 6argonsa da jinin jikinsa. "ada yaso Lubna harma yake ganin bazai ta6a son wata mace bayan itaba, amma zuwa wannan ranar labarin yasha banban, dankuwa jiyake abayama baiyi wata soyayyaba, yanzune zaisan miye soyayyar, yanzune zai amayar da ita inda yadace, yanzune zaisan miye farinciki acikin soyayya. Ahankali yakai hannunsa saman d'an bakin Asma'u daketa barcinta. Zagaya d'an yatsansa yakeyi akai cikeda shauk'i. Sannu ahankali Asma'u tafara motsawa harta bud'e kumburarrun idanunta akansa. Suna had'a ido tamaida nata idanun tarumtse gam. Murmushi yayi tareda fad'in haba my Husna! bud'e idanun mana. bud'e ki kalleni da k'yau ni nakine ke kad'ai, zan kasance dake har Abadan Hayatee na. Wani sanyin dad'ine ya kwarara azuciyar Asma'u, itakam yau wace irin godiya zatama Ubangijin talikai mai sassauya al'amura. Yanzunan ya Umar ne dabakinsa yake furta mata kalmomin nan? Ya Umar d'innan mai tsada da aji mijin Anty Lubna? Ya Umar d'innan da sonsa yazama garkuwar farincikinta tun tana k'arama? Ya Umar d'innan da takema kallon Wanda yafi k'arfinta abaya? Ya Umar d'innan daya mallake zuciyarta da dukkanin komai nata batareda yasan tanayiba? Ya ALLAH kaine Sarki mafi Girman iko da Rahma, ALLAH Kaine kake bayarwa ka k'ara batareda ka k'osaba.........hawaye sosai keta kwarara a kumatunta. Ya Umar yakuma matsawa gareta zuciyarsa dukba dad'i, azatonsa har yanzu kukan abinda yay mata takeyi. Rungumeta yayi tsam ajikinsa, murya a raunane ya ce, "kiyi hak'uri my Husna! nasan ban k'yautaba amma ki gafarceni." ALLAH yay miki albarka, kisaka azuciyarki Umar Fharuk nataredake har Abadan. Yanda kika saka ruhina da zuciyata acikin farinci kema ALLAH ya dauwamar danaki Ruhin a farinciki. I love you so much my Husna. Aii Asma'u batasan sanda tak'ara k'ank'amesaba tana zubda hawayen farinciki. Shikuma yana aikin shafa kanta da lallashi. Saida tayi mai isarta sanna yad'auketa cak zuwa bathroom. Ananfa akeyinta Dan Asma'u bazata iya tsayawa ya Fharuk yamata wankaba. Tun yana had'a ruwan zafin daya d'akko daga kichin tagwada fita daga bathroom d'in, amma kamar yasan mitake nufi ya dinkare ko'ina na k'ofar. Da d'an zafi sosai yahad'a ruwan zafin sannan yadawo da kallonsa ga Asma'u. Suna had'a ido tayi k'asa da kanta tana hawaye. Murmushi yayi ahankali yamatso gareta, murya k'asa-k'asa ya ce, " my Husna kincika shagwa6a. Kodai nakira Inna ko mama?. Sosai tawaro idanu akansa. Saikuma wasu hawayen suka kuma gangarowa. Tunawa batayi sallar Asubaba yasakashi sungumarta yasaka arobar daya had'a ruwan zafin, dama daga Ita sai riga iya guywa. Wani zallo tayi tareda k'ank'amesa tana kuka. Wayyo ya Fharuk wlhy akwai zafi. Innata kice yabarni wayyo ALLAHNA. Sake dannata yayi da k'yau yana murmushin wannan kuka. Afili ya ce, "Husna karfa kisaka gaban inna yayta fad'uwa, tun jiya kiketa kiranta. Ya Isa haka kada ki k'aremin sunan Innata!. Zuwa yanzu tad'an daina mutsu-mutsun tashi, saidai hawayen dasuka kasa k'arewa. Saida ruwan yahuce yakuma zuba ruwan zafi, baibartaba saida ya tabbatar tagasu dak'yau sannan ya ce, "kin iya wankan tsarki?. Kanta tad'aga masa kawai, har yanzu hawaye takeyi. Baifitaba har saida yaga yanda tayi, ya tabbatar tayi dai-dai sannan yanad'ota a tawul ya d'akkota kamar wata jinjira. Akatifar yadireta, yagoge mata jikinta yasaka mata kayan data ware domin yin sallah. K'ara d'aukarta yayi yakai inda abin sallar yake. Baibar wajenba saida ta kabbara sallar. Dawowa yayi inda katifar take, yacire bargon. Ido yazaro waje Dan ganin yanda zanin gadon yad'an 6aci kad'an. Mamakine yakamashi, dama bakowace macece ake ganin jini a Daren farkontaba? Yasan Lubna tagirmi Asma'u amma ita jinin data zubarma har tsoro yabashi a lokacin. Saikuma gashi Asma'u ita babu sosai. Ubangiji mai iko, matanma akwai banbanci atsakaninsu kenan?. *_hattara samari, kudaina d'aukar cewa dolene sai kunga jini adaren farkon matanku zaku yarda takawo budurci cikakke gareku. Mata kala-kalane, bakowacce bace ake ganin jini adaren farkonta. Mutanen da, suna aurar dayara suna k'ananane, shekara 12-13-14 kaga kuwa wad'annan yarane d'anyu dolene a iya ganin jinin. Kuma alokacin matan basa yawan yin abubuwan dazai saka burcinsu yin rauni._* *_ayanzunkam bahaka bane, mafi yawanci ana aurar da mata 18-19-20-21-22+ ne, gakuma abubuwan 'yan matan kanyi dake saka buducinsu yin rauni batareda sun saniba. Yawan d'aukar Abu mai nauyi, horo da ake bama yara a makaranta, hawa mashin, tsallaka kwata, yawan tsalle-tsalle, musamman dayanzu 'yammata suka lalata kansu wajen rawa. Irin wad'annan abubuwan da dama dawad'andama ban lissafoba duk suna saka budurci yin rauni koda mace takasance ma'bociyar kamewa. Mata saimu kula. Kukuma maza Ku fahimcemu, bawai ganin jini face-face agado bane alamar mace takawo cikakken budurci gidan miji. ALLAH yasa mugane, ameen._* Yaye zanin gadon ya Umar yayi zuciyarsa fes babu wani wasiwasi akan Asma'u, domin kuwa shine sheda akan tsam yasameta, bama k'aramar wahala yashaba wajen fasata. Lallai yakamata sauran maza irinsa su fahimci haka suma. Asma'u kam tuni ta idar harta kwanta awajen. wani zanin gadon yasake, dukda wannand'in bai 6aci dayawaba, amma baidace abarsaba. Yana canjawa ya d'akkota yamaida saman katifar dan barci takeyi sosai. Zanin gadon yakai bayi yasaka a bokiti ya wanke tas yaje waje ya shanya. Yana gamawa yadawo d'akin yakwanta tareda rungume abarsa suka koma barci mai dad'i. *_1:4pm_* Sai k'arfe d'aya da minti hud'u ALLAH yabasu ikon farkawa kusan atare, amma Asma'u tariga ya Umar tashi, motsin tashintane ma yatadashi. Tanajin motsin tashinsa ta lafe ita adole barci takeyi. Murmushi ya Umar yayi tareda yimata cakulkuli. Dariya sosai tazo mata, dukda zafin datake d'anji idan tayi motsi babba hakan baisaka ta dainaba. Ganin yanda take dariya yasaka ya Umar dariyar shima. K'ank'amesa tayi sosai tana cigaba da dariyarta dafad'in ya Umar yi hak'uri Dan ALLAH, ALLAH kuwa abinnan babu dad'i. Daina yimata yayi, yajawota jikinsa ya rungumeta tsam zuciyarsa fal farinciki. Sunkai 30minutes ahaka yana gaya mata dad'ad'an kalamai wad'anda suka sakata k'ara ganin kimarsa a idonta. Dama can ita bataji haushinsaba, aganintama hakan zai iya zama sanadin dazaisa ya sota. Sa6anin da da ita keta fama da dakon sonsa a zuciyarta. Bayan wani lokaci yad'auketa cak sai bathroom. Zille-zille tafarayi ita adole bazatayi wanka dashiba. Shikuma yace bata isaba, aii daga yau tarema zasu ringa wanka, danshi hakan yana cikin tsarinsa. Ganin zata fita yad'ebo ruwa yazuba mata ajiki. Dole tatsaya awajen cak, shikuma yashiga yimata dariyar tsokana. Ta6ara tafara zuba masa shikuma yana lallashi har aka kammala wankan yad'akko kayarsa kamar d'azun. Da k'yar tasamu ya yarda yatafi d'akinsa yabarta ta shirya itama. Kowa shirinsa yayi mai k'yau. Asma'u tad'an daure tagyara d'akinta da babban falo sannan tashiga kicin Dan nema musu abinda zasu saka abakin salati. Ganin rana tayi sosai sai kawai tad'ora jalof d'in taliya da dankali. Tasaka busashshen kifin da ya Umar yasaya musu shekaran jiya. Cikin 'yan mintuna k'alilan gidan yacika da k'amshi ainun. Dama Asma'u gwanace a wajen abinci. Ya Umar daya tsaya had'a wasu takardu yay shirinsa tsaf cikin shadda fara tas, dakakkiyar shaddace 'Yar ubansu, yad'inkata tun yana shanawa da naira. Shaddar d'inkin zamanine fetet, tayi masa k'yau aynun, yad'akko bak'ar hula yasaka, yasaka safa da takalmi bak'i sau ciki. Wayyo masu karatu tamkar ba ya Umar dake cikin k'angin rayuwaba. Idan kagansa zaka d'auka har yanzu ajik'e yake da laimar kud'i. Fitowa yayi yanata bulbula k'amshi, tamkar Wanda yay wankan turare. Yalek'a d'akin Asma'u bata nan. Jin motsi akicin yasakashi nufar can. Asma'u dake jera abinci akan tire Dan ta kammala komai tajiyo k'amshin turaren ya Umar ya yawaita awajen. Lumshe idanu tayi ahankali tabud'e akansa, bak'aramin tafiya da ita wankansa yayiba. Shima tayi masa k'yau sosai. K'arasowa yayi cikin kichin d'in ya rungumeta, cikin kunnenta yarad'a mata, haba My Husna! Waya gaya miki amarya na aikin a irin wannan ranar?. Fuskarta tashiga sinnewa a k'irjinsa ita adole kunya. Yad'ago fuskar tata a acikin tafukan hannunsa, idanunsa suna yawo bisa k'yak'yk'yawar fuskarta. Kiss ya manna mata agishi da hanci, ahankali ya furta ALLAH yay miki albarka my Husna. Ina k'yaunarki sosai. Saida ta k'ara sinne kanta a k'irjinsa sannan ta ce, "nima haka yaya ina k'yaunarka." Rungumeta yayi tsam yana juyi da ita Dan murna. Sundad'e ahaka sannan yad'auki tiren abincin sukaje falo. Tare sukaci abincin dukda Asma'u akunyace take, ko ido batason suhad'a dashi. Bayan sun kammala yatayata suka gyara wajen sannan ya ce, " bara yaje wajen Alhaji mai kano, dama k'arfe biyu yace yadawo. Addu'ar fatan nasara da dawowa lafiya tamasa. Shikuma ya ce, "taje ta kwanta tasake hutawa Dan anjima za'a k'ara irin amsar jiya......... Aibata bari ya rufe bakinsaba takwasa dagudu zuwa ciki. Dariya yafita yanayi da jinjina shirme irinnna Asma'u............ *_(((S)))........2017_* *_Luv you all_* [12/14/2017, 8:28 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* *_page→41-42_* ..........Itama daida tashiga ciki gudun nata yabata dariya, Dan haka tayi dariya sosai harda rik'e ciki. ALLAH nagode maka daka nuna min wannan rana mai cikeda tarin farinciki. Wai yau nice da ya Fharuk manne da juna, yana gayamin kalamansa masu dad'i da tsada. Ya ALLAH ka d'orar mana da wanan farinciki har k'arshen rayuwarmu.... Ameen Asma'u. ____________________ Su Lubna ansha shagalin biki, kud'ikam sunyi kuka abikinnan, komai anyishi asarauce. Su Lubna kam ashiga wanan afita wanan. Dama d'inkuna sukayi na garari itada Suhaima. Zuwa yanzu kam amarya tazo gida. Taroma yatashi kowa yakama gabansa. Su Lubna suna d'aki anata zabga barcin gajiya, gidan tsit kamar babu bil'adam acikinsa. Sai can nad'an jiyo hayaniyar su twins ad'akinsu. Can na nufa danna ganema idanuna. Aiko sune suketa tsalle-tsalle agado, duksun hargitsa d'akin. Babu laifi yaran sunyi girma sosai, ga kamanninsu da ya Umar sunfito sasai. Saidai Hassana farace. Usainace dai komai na ya Umar bata bariba, har dariya idan tayi kamar tasa... Barisu nayi nafito Dan inada abunyi..... ____________________ Alhamdulillahi ya Umar yayima Alhaji Ahmad mai kano bayani gamsashshe akan rabuwarsa da mahaifin Lubna. Dayake mutumne mai fahimta, saiya gamsu da komai, yakuma bama ya Umar hak'uri. Kayi hak'uri Umar, da abinda suka aikata maka. Amma inada tabbacin babu laifin Alhaji awannan lamarin, saidai idan matarsace tazugashi. Nasan halinta batada kirki kokad'an, bataso kowa yara6i Alhajin Dan aganinta za'a k'are musu dukiya. Murmushi Ya Umar yayi ya ce, ''to ALLAH ya kiyaye." Ameen dai Umar. Yanzu zaka iya fara zuwa aiki daganan zuwa Monday. Alhamdulillah ngd sosai Alhaji, ALLAH yak'ara bud'i na alkairi. Ameen Umar.. Daga nan Ya Umar yatafi sai kuma gidan inna. Babu kowa a tsakar gidan, sai kaji da su Inna ke kiwo sunata kaida kawo. Yakuma yin sallama ak'ofar d'akin da takalma suke birjik har wajen k'afa shidda. Kusan atare suka amsa. Sannan yashiga. Sannu da zuwa suka shiga yimasa da gaisheshi, yayinda shikuma idonsa kebin Harris da kallon mamaki. Dama yana zuwa gidannan?. Shima kansa Harris d'in yalura da kallon da yayan nasa kemasa, Dan haka yay k'asa da Kansa alamun jin kunya. Inna duk tana kallonsu. Ya Umar yaje kusada inna ya durk'usa cikeda ladabi ya gaidata. Cikin fara'a ta amsa masa da tambayar lafiyar iyali?. Ya ce, komai Alhamdulillah. Asma'u ma na gaishesu. Muna amsawa. Kallonsa yamaida ga Anty Saratu, ya ce, "sarkin yawo kenan, kekam kina iya sati d'aya bakizo gidannanba?.. Kanta ak'asa ta ce, " ya Umar wlhy har sati uku inayifa." Harara ya balla mata, a'a har shekara kinayi, inna ba kwana hud'u dasuka wuce Nazo gidannan natarar da yarinyarnan ba agidannan?. Dariya inna tayi, wlhy hakane Umar, nima yanzu babu jimawa nagama mata fad'an yawo, dan ba abune mai k'yauba. Ya Umar yakuma harararta, mijin nakine sakarai dayake barinki, ke ko saboda yara yawon baya damunki?. To daga yau karna sake ganinki agidannan sainan da wata uku. Idan bahakaba kuma ranki zai 6aci matuk'a. Gyad'a kai tayi dukda hukuncin NASA bawai yamata dad'i baneba, Dan Anty Saratu akwai d'ambazan yawo kamar taci k'afar kare. (Shima mijin NATA bayaso, amma saboda yana matuk'ar sonta saiyake barinta).. Daga nan hira akad'an ta6a, wadda ya Umar bawani saka musu baki yakeyiba sosai, garama idan inna tayi magana. Zuwa can ya ce, "inna Nazo wajenkine." To yaron arzik'i, nima kuwa dama ina nemanka. Saratu da Hasiya, fatee kufita. Amma Harris yatsaya. d'agowa ya Umar yayi ya kalli Harris d'in da yay k'asa da Kansa, Dan bak'aramar kunyar ya Umar yakejiba. Bayan fitarsu Inna ta kalli ya Umar. Umaru! Inaso kabani Aron hankalinka nan, mufara maganar da Harris yazo da ita, dukda nasan bakazomin da sakaren maganaba kaima, amma na Harris ma yanada matuk'ar muhimmanci. To inna ina saurarenku. Inna ta kalli Harris daya marairaice fuska tamkar zaiyi kuka. Harisu taso kazo nan. Jiki a sanyaye Harris yataso, yazo kusada ya Umar yazauna. Inna ta nuna masa ya Umar da ido. Zamansa ya gyara muryarsa na rawa ya ce, "yaya Dan Girman ALLAH kayi hak'uri, ka yafemin duk abinda namaka. Wlhy na tabbata duk gidammu babu mai mana Abu tsakani da ALLAH kamarkai. Abunda yafaru abayama sharrin shaid'anne. Ka gafarceni, insha ALLAH bazan sakeba. Wlhy yanzu ina tareda kai 100%....... Ya Umar yakatseshi da fad'in wai Harris miya farune? Nifa bakamin komaiba wlhy. A'a yaya namaka wlhy, Dan ALLAH karkace ban maka komaiba, idan kace haka zan d'auka bazaka yafeminba. Hummm shikenan Harris nayafe maka, harma sauran, damani banrik'e kowa acikinkuba, saidai inason kuringa fahimtar miye rayuwa akowane yanayi tazo gareku. Wlhy ya Umar nagane kam yanzu. Jiya naje wajen ya Abubakar akan yabani naira dubu goma na kar6o result d'ina. Amma shine ya hauni da masifa wai bashidashi, shima somuke mu karyashi kamar yanda muka karyaka *_KARAYAR ARZEEK'I_* tasameka. Yanzufa nauyin kayan d'akin Mufida yana kansa. Shi wlhy bazai iya da fitinarmuba mudasu mama........ Ya Umar Yakuma katseshi da Sauri, Harris ban ganeba, ansakama mufida ranar aurene? Da har aka fara maganar kayan d'akinta?. Inna da Harris suka kalli juna cikin mamaki.... Har had'a baki sukeyi wajen fad'in kana nufin baka saniba?. Ahankali ya Umar yakad'a kansa tamkar k'aramin yaro. Sallallami inna tafara tana tafa hannu, oni binta wannan wace irin rayuwace haka?. su yaya Kabiru suka d'auki duniyane?. Ammafa ranar da'aka kawo kud'in danaje ban gankaba saida na tambayi Maman taku, shine ta ce, "anfad'a maka amma kace aiki yamaka yawa Abubakar ya wakilceku tunda shine babba. Shekaran jiya kuma daza'a saka ranama saida nayi magana, naga babukai babu iyalinka, nanma tace anfad'a maka harma kazo, anasaka rana wai katafi saboda Asma'u batajin fad'in jikinta. Wani huci mai zafi ya Umar yashiga furzowa daga bakinsa, idanunsa sun kad'a sunyi jajur, yay ka d'a kansa yana ambatar *_" innalillahi wa'inna ilaihirraji'u."_* Ganin haka mama takwalama Hasiya kira. Ta ce, "takawo ruwa mai sanyi. Saida ya Umar yasha sosai sannan hawaye suka fara gangarowa akumatunsa masu zafi kuwa. Babu Wanda yahanashi, Dan hawayen zasu saka zuciyarsa yin sanyi tarage nauyin datayi. Harris ma hawayen yakeyi, danshima yafara fuskantar matsala irinta ya Umar awajen mama da Abba. Kullum saita masa gori baita6a yimusu komaiba itada abba. Inna ta ce, " ya isa haka, kuyi hak'uri, kucigaba dama iyayenku addu'a kunji. Komai zaizama labari. Ya Umar yasauke ajiyar zuciya yana fad'in babu komai mama, yawuce, amma yanzu wane wata aka saka bikin Hamidan?. Nanda wata biyarne Umaru kaji. Murmushi yayi ya ce, "ALLAH yakaimu inna. Kuma insha ALLAH bazan nuna musu nasan komaiba, kaima Harris karka nunama kowa ka sanarmin. Harris ya jinjina masa kai kawai. Daga nan mama tamusu nasiha da nuna musu muhimmancin zuminci da kula dajuna, had'inkai suzama tsintsiya mad'aurinki d'aya. Suduka nasihar tashigesu dak'yau. Sukaitama mama godiya. Ya Umar kuma yafad'a musu shima alkairin daya samu ayaud'in daduk abinda yafaru. Farin ciki sosai suka shigayi, Harris harda rungume ya Umar, shima yarungume d'an uwansa suna farinciki. Bayan sun nutsu ya Umar yace to Dan ALLAH su binne maganar anan kar kowa yaji. Inna ta ce, " hakan yayi Umaru!, koni ban goyi bayan wani yaji zancennanba. Harrisu kakula kaji. Insha ALLAH inna babu maiji wlhy. Amma yaya tunda zaka fara aiki zandawo tsare shagon, basai Asma'u tazaunaba. Murmushi ya Umar yayi, dama bayason zaman Asma'u ashagon Dan yanada tsananin kishi sosai. Godiya sosai da farinciki ya Umar yanuna akan abinda Harris yamasa. Daga nan hira mai dad'i suka cigaba dayi har zuwa wani lokaci sukaima inna sallama suka tafi. Daga nan gidansu suka nufa. Duk afalo suka iskesu har ya Abubakar da matarsa, anbaje alawa da biskit anata rabo. Ya Umar yagaida mama cikeda fara'a, ko kad'an bai nuna musu komaiba, ya Abubakar ma suka gaisa, suma hamida da Rafi'a suka gaisheshi. Matar ya Abubakar sai wani cika da batsewa takeyi ita adole matar mai kud'i. Kota kanta baibiba yamuk'e yamusu sallama. Kowa yayi mamakin da yau bai zauna hiraba, tunda yaga duk suna nan, (kuma kowa yasan ya Umar dason ahad'u gaba d'aya ayi hira) amma yau sai sukaga sa6anin haka. Gashi ko alawa da biskit d'in gabansu bai tambayi kona miyeba, kuma fuskarsa asake babu wani alamar 6acin rai agareshi. Sallama yamusu yafice. Mamadai tasha jinin jikinta, hakama ya Abubakar, dama shine yazuga mama wai kar agayama ya Umar, idanma angaya masa mizai musu? Mutumin da bashida ko sisi. Kayan dake shagon nasa basu wuce na dubu 60 ba gabad'ayansu. Da ire-iren wannan musalan yabige hankalin mama da Abba, ya ce, ''kuma shine zaima Hamida kayan d'aki. Su su Rafi'a basusan ya Umar baisaniba, amma sunsha mamaki dabasuga Asma'u ba awajen saka rana. Daga nan gidansa yanufa hankali kwance. Yana tsaye abakin titi zai tare adaidaita sahu, harma ya tsayar dawata suna ciniki saiga wata ash d'in mota ta giftasu. Har mai motar yad'an wuce saikuma yadawo baya. Horn yayma ya Umar, ya Umar bai d'agoba, dan kokad'an baid'auka dashima akeba. Mai motar nan yasake yin Horn harsau uku. Ganin haka mai adaidaita yayma ya Umar dake k'ok'arin Shiga magana. Malam dakaifa mai motarcan yake. Dani kuma? Ya Umar yay maganar yana lek'o kansa Dan tabbatarwa. Hannu kuwa yaga and'ago masa. Tofa bara naga wanene ina zuwa. Babu damuwa mai adaidaita yafad'a. Ya Umar yafito zuwa motar. Maimota yabud'e yafito yana fad'in *_Umar bin Usman!_* dama rai kanga rai?. Soasai ya Umar yazaro ido waje, Yazeed! Dama Kaine?. Cikin farinciki suka rungume juna. Yazeed ya ce, "Umar ina kashige haka? Nayi nema harna gaji. Natambaya amajillisa su alkasim sunce min suma basusan inda kakeba yanzu, wai tunda mall naka yak'one ka gujesu gaba d'aya. Murmushi ya Umar yayi kawai, ya ce, " Yazeed wannan bamaganar titi bace, kabari next time Idan mun had'u zamuyita. Amma yaushe kadawo k'asarnan?. Wlhy tun sati biyu daya wucefa. Tunda nadawo kaina fara nema awashe gari, naje gidanka akace aii katashi, natambayi abokai sukace basu saniba. Naje gidansu Lubna natarar suna biki. Cikin ikon ALLAH yanzu har zan wuce saina hangoka. ALLAH Sarki Yazeed, yanzu dai ina zamu had'u mai Babur yana jirana. Wai inama motarka naganka zaka hau adaidaita?. Murmushi kawai ya Umar yayi ya ce, "Yazeed kaidai babu abin fad'a abakina sai Alhamdulillah. Yazeed ya jinjina kai, shikenan sallami mai adaidaitar kazo muwuce. A'a kaje uzurinka, baikamata na katse makaba. No. Babu Inda zanje wlhy, nakai Zuhrah gidane suna wani taro a family d'insu. Yazeed yaje dakansa yabama mai adaidaita d'ari biyar sannan ya sallamesa. Mai adaidaita sai zabga godiya yakeyi yatafi. Ya Umar kam yashiga motar Yazeed suka tafi suma.............. *_(((S)))........2017_* *_Luv you all_* [12/15/2017, 7:37 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_*💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO........😜_* _sak'onki ya iso gareni *Ummu sadeeq* alkairin ALLAH yakai gareki aduk inda kike._ Luv you zam zam😻 . *_page→43-44_* *........Wanene yazeed?.* Yazeed Mudansir kura. shine cikakken sunansa. d'ane ga Alhaji mudansir kura shahararren d'an siyasa kuma d'an kasuwa. Mutumne shi mai gaskya da tsayawa agidansa, wannan shine yabama 'ya'yansa damar tsayawa sukayi karatu, dakuma samun ingattacciyar tarbiyya. Yazeed sun had'une da ya Umar awajen bautar k'asa. Sosai suka shak'u awannan lokacin, dan abotace maicikeda k'auna da gskya acikinta. Bayan kammalawarsu kowa yakoma gida. Akuma wannan lokacinne rashin lafiya takama Alhaji mudansir, aka kaishi k'asar London domin yin jiyya. Yazeed ne yake zaune awajensa. Tundaga lokacinnan ya Umar yadaina samunsa awaya. Har ALLAH ya azurtashi alokacin. Kusan shekara biyu basu sake had'uwaba har akayi bikinsa da Lubna sannan su Yazeed suka dawo. Dawowarsu babu dad'ewa mahaifinnasu yarasu Alhaji Mudansir kura. Tunda ya Umar yaji Rasuwa hankalinsa yatashi, dayake lokacin Yakama k'asa yanada kud'i babu laifi shine yaja abokansa su Dr jafar, Alkasim etc....... Dadai sauransu sukaje gaisuwa. Murna sosai yazeed yayi daganinsu, yabama Ya Umar hak'urin rashin nemansa, sannan suna arikice ko wayar da Number sa ke aciki bai d'aukaba. Ya Umar ya ce, "babu komai yamasa uzuri. Tundaga nan yazeed yazama d'an cikinsu shima, idan yanada lokaci haka zai shiryo yazo majalissar matasan masu kud'in asha hira. Daga nan aka saba sosai. Gafda za'ayi aurensa da Asma'u yazeed yatafi k'asar Indonesia wani course, wanan yasa basu sake had'uwa da ya Umar sai yau.. Wannan kenan *mundawo labari.* Suna tafiya ya Umar yana bama Yazeed labarin abubuwan dasuka faru abaya. Idon Yazeed yayi jajur saboda azabar 6acin rai, yanason ya Umar sosai. Muryarsa cikeda damuwa ya ce, " amma miyasa bana samun no d'inka kusan shekara d'aya kenan?. Hum kabari kawai yazeed, wlhy cire sim cart d'in nayi gabad'ayama na ajiye, nabar na family na kawai, amma na kasuwa bana buk'atar kowa taredani, saboda abubuwan da mutane suka aikatamin. Hakane Umar, d'an Adam sai abarsa da halinsa, kaga yanzu yakamata kagane bakowane ke k'aunarka Dan ALLAH ba saidan kud'inka. Wlhy Umar haka rayuwar take tafiya ga kowa, idan kanadashi saikaga anata sonka, amma dasun k'are sai kowa yafara gudunka. Dan Adam kenan mai manta alkairi. Amma gsky Lubna da family d'inta da Dr Jafar sunfi kowa bani mamaki. Babu komai kayi hak'uri Umar, ALLAH yanason mutane masu hak'uri. Wlhy komai ya wuce yazeed. Yanzu kam bana tareda kowacce irin damuwa. Dariya sosai yazeed yayi, ainasan bazaka damuba tunda kana tareda amarya kanashan amarci. Harararsa ya Umar yayi, yana fad'in aikai dama matsalarka kenan bakada kirki kokad'an. Duk hanyar tsokanar magana kasani. Hhhhhhhh abokina aikaine kanada abubuwan mamaki Dana dariya. Ankawo maka yarinya kanata wani mata mazurai. Kuma babu kunya saika lalla6a daga baya hhhhhhhh. Kai waya gaya maka na lalla6a? Masheranci. Hhh nasanka Umar wlhy sosai. Inaga daga Family d'inka babu Wanda yaymaka irin sanin dana maka. Kaji dashidai masheranci. Saika tsaya munzo gidan. Yazeed yataka burki amatsakaicin k'ofar gidan na ya Umar, jiyayi tausayin ya Umar yakuma shigarsa. Dabadan karyayi kuka akirashi maceba da wlhy saiyayima ya Umar. Lokacin anak'ok'arin shiga sallar La'asar. Ya Umar ya ce, "sufara yin sallah sannan. Suna idar da sallah cikin gidan suka nufa. tun atsakar gida wani farinciki yaratsa zuciyar ya Umar. Dama Yasan Asma'u tuni mai tsaftace. Shiyyasa baita6a fargabar zuwa dawani gidansaba akowane yanayi. Tunda suka shigo yazeed ketabin ko'ina nagidan da kallo. Tabbas rayuwa nada abin tsoro. Idan yatuna yanda Umar yasamu kud'i abaya, ko'a mafarki wani baxaiyi tunanin ganinsa a irin wannan gidanba. Amma abin birgewa kokad'an babu wata k'asurgumar damuwa tartare da Umar d'in. Tab aii da wanine dayanzu yabi daji ciwon hauka yakamashi. Kai gsky Umar jarumin namijine abin kwatance awannan zamanin. Ya Umar yakamo hannun Yazeed Dan ganin yana tafiya ahankali. Ajiyar zuciya yazeed yayi tareda dawowa cikin hankalinsa. Ya Umar baice dashi komaiba sukai sallama ak'ofar falon. Asma'u ta amsa cikin nutsuwa. Jin kamar muryar ya Umar yasakata fitowa daga bedroom. Adaidai nan kuma su ya Umar suka shigo falon. Komawa tayi ciki da saurinta Dan d'aukar hijjab. Carpet d'in dake falon ya Umar ya nunama yazeed. Saida yaga ya zauna sannan yabi Asma'u. Abakin k'ofa sukayi karo tasako hijjab. rungumeta yayi, daddad'an k'amshinta na kuma sakashi a shauk'in k'aunarta. Kanta ak'asa ta ce, ''sannu dazuwa." Yauwa Sarauniyata, ykk? Ya jikin?. Lfy lau, kuma ni lfyta k'alaufa. Murmushi yayi yana kallon yanda take cuno baki. Ya sunkuyo kad'an yabata kisses guda uku, abakinta da goshinta. Kunyace takuma kama Asma'u, Dan haka tayi k'ok'arin kwace kanta ta gudu amma saiya ruk'ota da k'yau. Humm guduwa kikeson yine? To aiia tare Muke da babban bak'o. Da sauri tad'ago ta kallesa, yaya bak'ofa?. Kansa yad'aga mata, har yanzu idonsa akanta. To amma miyasa Baka kirani kafad'aminba? Da saina masa binci na Musamman, tunda kace abban bak'one. Hakane my Asmy yazeed babban bak'one agaremu. Amma kiyi hak'uri Nima a ahanya na tsintoshi. Ayya to babu damuwa. Amma yanacin garau-garau?. Gira yad'aga mata, tareda k'ara rungumeta ajikinsa ya ce, "aibakinkine garau-garau d'in. mizai hana yaci sarauniyata." Dad'ine yake ratsa zuciyar Asma'u aduk lokacin dataji ya Umar yasauya mata wani suna daban, musamman sarauniyata dayake cemata. Jin tayi luf ajikinsa yasakashi d'agota. Yadai Husanata? Ko kina buk'atar d'umin mijinkine?. Da Sauri ta d'an tureshi tafice daga d'akin. Shima bayanta yabi yana dariya k'asa-k'asa. Afalo ya isketa suna gaisawa da yazeed. Sosai yazeed yaba da tarbiyyar Asma'u. Ya Umar na fitowa Asma'u tana mik'ewa tafita. Akusadashi ya Umar ya zauna. Yazeed ya kalleshi daikuma ya bushe da dariya. Harararsa ya Umar yayi. Mikuma yabaka dariya kaikuma?. Yazeed bai iya maganaba sai dariya, daya kalli ya Umar saiya sake tuntsurewa da dariya. Ganin haka ya Umar Yakuma harararsa. Kai malam yafa isheka, wai miye matsalarkane?. Cikin dariya yazeed yakunna waya yayma ya Umar hoto. Da Sauri ya Umar ya warce wayar danson ganin miya faru?. Idanu yazaro waje, shima saiya fara dariyar. Bakinsa yagani duk jambaki. Da Alama kiss d'in dayayma Asma'u ne yakwaso jambakin. Sunacikin dariya Asma'u tashigo. Itama suna had'a ido da ya Umar tayi murmushi ta ajiye tiren hannunta. Tun d'azun tana ganin jambakin amma tak'i Sanar masa. Saving d'insu tayi. Had'd'd'iyar jallop d'in shinkaface wadda taji kayan lambu, dukda babu nama aciki bare kifi sai zabga k'amshi takeyi. Tunkan sufaraci yawunsu ya tsinke suduka. Ta tsiyaya zo6onta dayaji kayan k'amshi a kofuna guda biyu sannan tamik'e. Bismillanku, tafad'a tana mik'ewa. Tunda suka faracin abinci babu mai iya yima d'an uwansa magana. Ta kurma kawai akeyi, babu Baka sai kunne. Sosai sukaci abincinnan, Dan abincin yayima yazeed dad'i. Shi matsalar dayake fuskanta kenan agidansa, matarsa bata iya girkiba. Ko indome tadafa masa saidai yaci kawai da hak'uri. Amma badan dad'iba kam. Bayan sunci sunyi dam, suka kora da sassanyan zo6on. Ayanzu kam yazeed yakasa daurewa saida yayi magana. Kai abokina kana kwasar gara wlhy. Yoni Ina samun haka mizai dameni. Kallonsa ya Umar yayi yana murmushi jin dad'in an yabama Asma'unsa. Haba abokina Kanada matafa? Yakake fad'ar irin wannan maganar. Hummm abokina kenan aii kasan ko'a Matan wata tafi wata. Hakane. ALLAH yasa mudace. Ameen yazeed yafad'a yana k'ara tsiyaya zo6on akofi. Bayan sun kammala Asma'u tafito ta kwashe komai. Jok d'in zo6on kawai tabar musu. Daga nan suka cigaba da hira har zuwa magriba. Sun tattauna abubuwa da dama, ciki harda kud'i da yazeed yabama ya Umar har na 10millions yayi gyaran shagonsa. A take anan kuma yay masa transfer a Account d'insa. Yanda kasan gumaka haka ya Umar da Asma'u suka koma awajen. Ya Umar yarungume yazeed yana masa godiya. A'a Umar babu godiya a tsakaninmu, kayana nakane. Hakama kayanka nawane. ALLAH ne yahad'amu, to dan haka saimu gode masa. Hakane abokina amma kaid'in nadabanne acikin al'umma. ALLAH ya saukar da farinciki da alkairi arayuwarka da zuriyarka. Yanda ka k'yautata mana kaima ALLAH ya k'autata maka damafiyin haka. Ameen Umar ngd sosai da addu'arka. Yanzu abinda yakamata gobe idan ALLAH yakaimu kashirya zamuje wani waje akan kayanka da custom suka rik'e. Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke. Yazeed wlhy dama mun hak'ura kawai. Duk hanyar danake tunanin kayannan zasu fita nabi, amma kowa saiyace babu yanda zaiyi. Murmushi yazeed yayi, yadafa kafad'ar ya Umar, karka damu Umar, awannan karon insha ALLAH zasu fito. Aii komai na k'asarmu hanyace. Kaidai karka fidda rai da rahamar ALLAH. Shikenan yazeed ALLAH yakaimu goben. Ngd ngd ngd......... Katseshi yazeed yayi da sauri..... Nifa banason godiyarnan. Idan kanayi sainaga tamkar baka d'aukeni d'an uwaba. Tom kayi hak'uri na daina. Daganan yazeed yamik'e, rafar 'yan d'ari biyar yabama Asma'u wai tukuycin ciyar dashi daddad'an girki datayi. Girgiza kanta tayi, idanunta ak'asa, a'a ya yazeed ngd basai kabani tukuyciba. Banmmasan zakuzo tareba da anmaka na musamman aii. Kai aii wlhy wanna danacima na musamman ne. Ke dai kawai ALLAH yak'ara dank'on k'auna keda abokina. Ngd sosai.. Asaman kafet d'in ya ajiye suka fita.. Godiya sosai tamasa, da sak'on gaisuwa ga iyalinsa sannan takoma ciki, tana mamakin yazeed. Dama akwai irin wad'annan mutanen har yanzu adoron k'asa?. A can kuwa ya Umar yarakashi har mota yana k'ara masa godiya da k'yak'yk'yawar addu'a shida zuriyar sa. Saida yaga yabar Layin sannan yashigo cikin gida. *_(((S))........2017_* *_Luv you all_* [12/18/2017, 4:29 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* _gaisuwar da shafin duk nakine dear Zarah Bukar. barkakanki da dawo online, Alkairin ALLAH ya iso gareki aduk inda kike._ Luv you sosai-sosai😻 *_page→45-46_* ............A falo ya iske Asma'u tsaye tanata k'ara mamakin halin kirki irinna Yazeed. Sallamar dayayi ta amsa. Yad'ora dafad'in Husna uana ganki atsaye, lafiya kuwa?. Lafiya lau yaya, kawai ina mamakin halin kirki da dattako irin na ya yazeed ne. dama har yanzu duniya tanada mutane irinsu acikinta?. Yaya 10millions fa 1 time, batareda tunanin komaiba. Murmushi ya Umar yayi, my Husna hakane, yazeed ya cancanci yabo ainun, tunda k'addarar nan ta sameni babu Wanda yata6a taimakamin dako sisi dagake sai innata, saiko Anty sa'a. Abokaina, wasu daga cikin 'yan uwana duksun gujeni saboda banidashi yanzu. Atunaninsu zan zame musu nauyi, naringa binsu inacewa subani. Humm lallai naga rayuwa, ALLAH ya shirya zukatanmu. Shikam yazeed aibammasan mizance akansaba, saidai kawai naita masa k'yak'yk'awar addu'a shida zuri'arsa daganan har k'arshen numfashina. Gsky ne yayana, Nima zan tayaka insha ALLAHU. ammafa gsky su ya Yazeed sunada kud'i. Sunada kud'i sosai Husna, mahaifinsu yatara musu, kuma yakoyama kowa yanda zai nemi nasa, kina ganin yazeed nan bak'aramin d'an kasuwa baneba. To ALLAH yasakanya masa da mafiyin abinda yabamu. ga wad'annan suma. Ameen ya rabbi husna, amma wad'annan nakine, kije ki ajiye abinki. Nida akabama 10millions niyakamata nak'ara mini aii ko?. A'a yaya, Dan ALLAH karik'e, ni babu abinda zanyi dasu, aii komai nawa nakane. Murmushi yayi yana d'aga mata gira, hakane kuma sarauniyata. To yanzu ki ajiyemin su zan kar6a kinji. Kanta ta jinjina a sanyaye. Ya Umar yakamo hannunta yana fad'in yauwa wana kama?. d'azu wakikema dariya?. Dariyarce takuma zuwama Asma'u alokacin da tatuno jambaki a la66an ya Umar. Takuma shek'ewa da dariya harda rik'e ciki. Ya Umar tsayawa yayi kawai yana kallonta. Saida tayi mai isarta sannan tadaina tana sauke numfashi. Humm kingama? Ya Umar yatambaya yana matsowa gareta, itakuma tana matsawa baya, har suka dangane da bango. Sosai idanun Asma'u sunfito waje. A yanzukam sai tsoro ya kamata Dan ganin yanda fuskar ya Umar tasauya. Hannunsa yadafa ajikin bangon yamda babu ta inda Asma'u zata tsere masa. Yatsirama fuskarta idanu. Na ce, "kingama min dariyar?. d'ago idanunta tayi suka had'a idanu. da Sauri ta janye nata. Muryarta har rawa takeyi, ta ce, " kayi hak'uri bazan sakeba." Yanda tayi magana a sanyaye saita bashi dariya. Amma saiya dake, yasa hannu yad'ago ha6arta. Maimakon ta kallesa saita lumshe idanun ta. Ya ce, "bud'e idonki ki kalleni. Girgiza kai tayi alamar a'a. Shikenan za6i hukunci dazan miki da kanki, ga za6i biyu. Kodai kimin abinda namiki harna d'ebo janbaki a bakinki, kokuma ak'ara abinda yafaru jiya............ Aii baima k'arasaba tawaro manyan idanun ta a kansa. Yanzukam yakasa daurewa saida ya murmusa. Saikuma ya gimtse fuska ya ce, " wanne kika za6a?." Asma'u ta marairaice fuska tamkar zatayi kuka. Murya na rawa ta Ce, "aii gwamma na d'azu d'in......... Jin ankwala kiran sallar magriba yasakashi k'yaleta yanufi d'akinsa, yana fad'in kishirya kafin nadawo. Da gudunta tashige d'akinta harda saka key. Aii yaya nariga nasha. Saidai kanemo mai maka kiss. Wayyo, ALLAH ya Fharuk ma ya iya rashin kunya. Da INA ganinsa shiru-shiru kamar bazai iya wani abunba amma shimafa A ne. Ya Umar nayin Alwala masallaci yawuce. Koda aka idar da sallah baishigo gidaba, saiya tsaya shago wajen Sadam k'anin Muktar. Dama shine yakad'an zauna idan babu makaranta. Sadam yagaida ya Umar da tambayarsa ya aikin?. Murmushi ya Umar yayi, Sadam aii bama afara aikinba ko? Ya kasuwar taka?. Alhmdllh yaya, saidaifa yogot ya k'are. "o namanta nace kaje wajen Sabi'u ka kar6o, jiya da yamma nakai masa kud'in, amma aii yakamata yau yama aiko dashi koba'a jeba. To k'ila baidawo daga kamfani dawuriba. Ito dakuma wannan Dan wanan. Kashiga gidato kahuta, saina k'arasa. Lah a'a yaya, wlhy kayi tafiyarka wajen Anty Asma'u, kasanfa tace in bana barinka Shiga gida da wuri zata hanani Rafi'a. Dariya ya Umar yayi, ya ce, "lallai kaikam aiki yasameka ashe. Shima Sadam dariyar yayi. Ya ce, " aii shiyyasa zan Dage da k'yau Dan kar a hanani fita sukayi suna dariya Dan gabatar da sallar isha'i. Bayan an idar ya Umar yadawo shagon, d'an abin motsa baki ya d'aukama Asma'u, sannan yatambayi sadam ko Muktar yadawo?. Eh yadawo tun d'azun, amma naga sun fita shida kawu labaran. Okey, tobara nashige ni saida safe. ALLAH yakaimu yaya, agaidamin da auntyna. Zataji insha ALLAH. ____________________ Tunda Asma'u ta idar da Sallah taketa hanzarin yin kaye-kayen kaya, tasan yau ya Umar bazaici abincin dareba tunda sunci abinci da yamma lik'is, shiyyasama batayi yink'urin dafa komaiba. Sokawai take tagama k'imtsa gidan tashige d'aki ta kulle kanta Dan tasan ya Umar akwai fad'a da cikawa. Tana Shiga d'aki yana shigowa, gabantane yafad'i tafara k'ok'arin son kulle d'akin. Saidai ta makaro Dan harya Shiga. Kallonta yayi, miya baki tsoro haka?. Cikin in INA ta ce, babufa komai. d'an murmushin gefen baki yayi, tareda d'age gira d'aya yana kallonta da ido d'aya, kin tabbata?. Kanta ta jinjina masa, amma k'irjinta sai dukan hamsin-hamsin yakeyi. Shimadai yafahimceta, Dan haka ya ajiye ledar hannunsa yazauna bakin katifar. Zonan. Wayyo ALLAH kamar tafasa ihu hakataji, amma yazatayi? dole ta k'arasa garshi, tana niyyar durk'usawa k'asa yajawota saman cinyarsa. Humm Husna yaushe kuma aka fara zama shiru-shiru? Ko yanzu Sabon hankali yazo mikine?. Itadai shiru tayimasa, sai tsoro fall ranta. Wlhy duk son datakema ya Umar bazata iya k'ara bashi kantaba a yau. Yanzu haka dauriya kawai takeyi... Jin tayi shiru ya girgizata, inafata kina tunanin abinda kika za6ane. Kai yaya baka mantaba. Kema dazakiyi baki mantaba bare nida za'ayimawa. Shiru tayi tana tunanin dabarar dazata masa....... Muryarsace takatseta.... Ya ce, "kin shirya?." Yatsine fuska tayi kamar wadda batada lafiya. Ya kuma fad'in yadai?. Kaina yake ciwo. Dariya yayi aransa, afili kuma saiya rungumota da k'yau yana fad'in o ni Umar Fharuk ALLAH yabani mata raguwa. Kafin tace wani Abu, saijin bakinsa tayi acikin nata. tuni zaman ya gagaresu ya mirginata suka fad'a saman katifar sosai. Hummm bara na cika rigata da iska. 🏃‍♀ ____________________ Amma Alhaji kana ganin bakayi wautaba wajen d'aukar yaronan aiki kuwa?. Alhaji mansur wautar mi kenan?. Hummm wauta saboda Alhaji Ubangidansa nada. Eh to Alhaji Mansur, mutane zasu iya kallon hakan akan abinda bai daceba, to amma idan akaduba halin da yaron yashiga sai a tausaya masa. Musamman danaji cikakken bayani akan abinda yarabasu da Alhaji. Yaron yanada hankali da nutsuwa wlhy, kokad'an bashida damuwa gakuma rik'on amana. Alhaji Ahmad duknaji bayaninka, kuma na gamsu, amma tabbas akwai damuwa. Inaga gara kawai kabashi wani taimako yaje yayi wata 'Yar sana'a, ALLAH shine maiyi, saiya sake d'agashi idan yaso. Amma kabi komai asannu, karka aikata abinda zaidawo yadami kowa Company d'innan. Ajiyar zuciya Alhaji Ahmad ya sauke, harga ALLAH yana tausayin Umar, kuma har a zuciyarsa yaso ya taimaka masa. Amma shima haka ya kwana jiya zuciyarsa na tunane-tunane akan abinda zaije yadawo gameda d'aukarsa aikin. Dukda yasan halin Alhaji mutumne mai sauk'inkai. To amma bazaiji dad'iba aii. Haka yakwana yana tunani, hardai matarsa ta fahimta da safe ta tambayesa damuwarsa. Bai 6oyemataba ya sanar mata komai. Ita kanta ta jinjina lamarin, kuma ta tausayawa Umar. Amma irin shawarrar databasa, irintace yanzu Alhaji Mansur yake basa......... Alhaji Mansur yakatse masa tunani dafad'in yakagani?. Ajiyar zuciya Alhaji Ahmad yasauke. Shikenan nayarda da shawarrar ku, zuwa anjima zankirashi har gida namasa alkairi tunda nayi niyyar taimakonsa. To haka yafi sauk'i kam. ALLAH shima yabasa nasa. To ameen. Ya Umar kam yau tunda suka tashi sallar asuba baidawo gidanba yana shago Sadam yawuce makaranta. Asma'u tagama had'a break fast tagyara gidan tsaf. Wajen k'arfe 10 tad'an lek'a shago, saita hango ya Umar tareda Mukhtar. Sallama tayi tanadaga cikin gida, suka amsa, ta gaida Mukhatar da tambayar yara suntashi lafiya?. Cikin fara'a ya amsa mata kamar yanda yasaba. Ta kalli ya Umar dake jera yogot a firij. Ya Fharuk break fa?. d'agowa yayi yana kallonta cikeda so da k'auna, keda nace kiyi barci ki huta shine kika kama yin aiki?. Fuska ta shagwa6e amma batace komaiba. Shima saiyayi murmushin nasa na k'asaita. to jeki kawo. Cikin gida takoma, Dan danan saigata da tire. Baibari tashigoba yatareta ya kar6a, ahankali ya ce, "I Love you my Husna." Itama cikin nata salon ta ce, "Love you more my boss." Murmushi yakumayi, yajuya cikin shagon yana maimaita sunan aransa, my boss!. Yasaki murmushi akaro na babu adadi. Muktar dake kallonsa ya ce, "lafiyarka kuwa?." Murmushin yakumayi, babukomai mikagani?. A abubuwa dayawa mana. Muktar yafad'a cikin tsokana. Hummm kadaiji dashi, zomuci abinci........... ________________________ Bayan sati d'aya. Abubuwa dayawa sun faru acikin sati d'ayannan, ciki harda kiranda Alhaji Ahmad mai kano yayma Umar. Bai nuna masa k'iri-k'iri baizai d'aukeshi aikiba. Amma cikin hikima irinta manya yayma Umar bayani yanda zai fahimceshi. Ya Umar yace wlhy babu komai Alhaji na fahimceka. Kuma ngd sosai da irin kulawar daka nuna akaina, ALLAH yak'ara bud'i na alkairi. Ngd ngd. Babu komai Umar, amma ina k'ara baka hak'uri, ga wanan kaje kaja jari. A'a alhaji wlhy basai kabani komaiba. Karmuyi haka dakai Umar, ninayi niyya aii, kuma babu mai maida alkairi sai shaid'an nasan kasan haka kuma. Hannu biyu ya Umar yakar6a yayma Alhaji godiya sosai sannan yatafi gida. Naira Million 1 Alhaji Ahmad yabama Umar. ranar harkuka ya Umar yayi. Ashe dama mutane na sonsa har yanzu?. Alhaji Ahmad yasha addu'oin alkairi kam. Abu na biyu kuwa shine shige da fici da yazeed ketayi akan kayan Umar su fito daga hannun custom. Na uku kuma ya Umar yasa Muktar agaba wajen gyaran mall d'insa daya k'one, aiki akeyi tuk'uru, ankwashe sauran tokar, harma Anfara d'ora ginin inda ya rushe. Aiki sosai yayi nisa, fatansu ak'arshen sati amaida rufi kawai. Na ce, "ALLAH ya taimaka ya Umar d'inmu😄🤸🏻‍♀. Tunda aka fara aikin abokansa suke mamaki, dan majalissarsu kusada Mall d'in take. Nan suka fara Gulma wai kodai ya Umar ya saida wajen ne. Harda dariyar mugunta sukeyi, wai lallai maza anji yaji. Duk abinda sukeyi Muktar yana kallonsu idan yaje duba aikin, kuma yana kawoma Ya Umar labarin komai. Ya Umar bayacewa komai, saidai yayi murmushi da fad'in ALLAH ya shryesu. Na hud'u kam ko kusa ko kad'an bainunama kowa acikin family d'insaba yasamu wata waraka, dagashi sai Asma'u sai inna. Ko Harris baifad'amawaba duk da ayanzu Harris d'in yana bayansa d'ari bisa d'ari, Dan yanzuma shine yake zama ashago. Ya Umar kam koda yaushe ya manneda Asma'unsa suna shan sharafin soyayyarsu. Sosai yake nuna mata k'auna itama a 6angarenta hakane. Duk abinda mijinta yakeso shitake masa, soyayya kam nuna masa takeyi k'uru-k'uri afili. Idan kagansu tamkar zasu cinye juna sabida so da k'auna. Abu d'ayane takasa sabawa dashi ga ya Umar, shine fitinarsa, ko kad'an takasa zama jaruma awannan fannin. to shima dai yana tausaya mata, Dan haka yakan d'an d'aga mata k'afa awasu lokutan koda yakasance amatse. Yazeed kam yanzu kullum anan gidan yakecin abinci. Dan girkin Asma'u yana masa dad'i. Tun lamarin baya damun matarsa harya fara tada hankalinta matuk'a. Ayanzukam tak'udiri aniyar shiga makarantar koyon girki, duk da batasan inda yake zuwa cin abincibama. Yauma kamar kullum Asma'u da ya Umar suna kwance ad'aki kasancewar safiyace, ga garin antashi dawani d'an karen sanyi. Sunacikin bargo manne da juna kamar masu tsoron kar a rabasu. Ya Umar yaja hancin Asma'u daketa faman lumshe idanu tana k'ara nanewa ajikinsa. Kalli yanda kiketa nanemin duk kinbi kin d'agamin hankali. Yanzu kuma danace inaso kihau raki. Asma'u tad'an janye jikinta tana fad'in yi hak'uri nidai Dan ALLAH. maidota yayi jikinsa yakuma rungumeta, murya k'asa-k'asa tamkar mairad'a ya ce, "zanyi hak'uri idan anbani." Wata zabura tayi kamar wadda aka fad'ama mutuwa, murya na rawa ta ce, ''kai ya Fharuk kofa awa 1 bakayi dayiba. Dan ALLAH ka tausaya min. Tausayi tabashi, to amma shimafa bawai laifinsa baneba, inhar zaiga Asma'u akusadashi tofa sai hankalinsa yatashi (yatuno Lubna, itakam tanada juriya tanan 6angaren, inhar zai nemeta bazata ta6a masa gardamaba balle nuna gajiyawa. Duk lalacinta da rashin son aiki bata masa awajen sunnah). Jin yayi shiru yasaka jikin Asma'u yin sanyi. Bada sonta take bijire masaba, fitinar ya Umar d'ince tayi yawa. Saboda fa wanan abun saiya baro shago sau wajen uku arana. Dukta rame saboda yawan yi dayakeyi, itakuma ga tsoro, data gansa agida sai tsoro ya mamayeta. Amma harga ALLAH tanaso tazama jaruma wajen kula da mijinta. Bataso sanadin ragwantakarta yafara tunanin kaucema UBANGIJIM AL'ARSHI. Dan rashin samun had'in kanta zai iya jefashi cikin tarkon ZINA. (wa'iyazubillah. ALLAH ka karemu muda zuriyarmu da al'ummar MANZON ALLAH (S,A,W) gaba d'aya). Jikinta a sanyaye tafara masa abinda tasan yanaso. Amma amamakinta saitaji ya ture hannunta, ya juya mata baya. Hankalinta yakai k'ololiwar tashi. Jikinta na rawa takoma inda yajuya. Saiya k'ara juyawa d'ayan gefe. Ganin haka sai kawai ta rungumesa ta baya ta rushe da KUKA.......... 🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀kunjini shiru?, munasha bikine o. Ina fata kuna cikin k'oshin lafiya kuda family's naku??.❤❤💋 *_(((S)))).......2017_* *_I Love You all my Fan's._* [12/19/2017, 4:59 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→47-48_* ..........Sosai kukanta kecin zuciyarsa, amma saiyayi burus da ita. Saida tayi mai isarta sannan barci 6arawo ya saceta. (Wanan halin Asma'u ne, Indai har zatayi kuka, to k'arshe sai barci kuma). Jin shiru dakuma alamar jikinta yad'an saki, yasaka ya Umar juyowa yana fuskantarta. Girgiza kai kawai yayi tareda rungumeta. Wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, aransa kam tausayintane ya mamaye zuciyarsa. Saida ya tabbatar barcin nata yayi nisa sannan yazare jikinsa ahankali yamaye gurbinsa da filo. Kwanciyarta ta gyara tacigaba da barcinta. Shikuma saiya nufi d'akinsa yay wanka ya shirya tsaf cikin ka'nanun kaya, bak'in wando da farar riga mai layi-layin bak'i, sosai yayi k'yau sai zabga k'amshi yakeyi kuwa kamar shagon my Abdul d'ina na turarurruka😉 lol. d'an lek'ata yayi yaga haryanzu barci takeyi. Aransa ya ce, "kasa kenan." Shago yafito, Harris nata kaikawo saboda masu sayen abubuwa musamman 'yan makaranta. Dan akwai wata Secondary acan samansu, kuma tanan 'yan makaranta sukebi su wuce. Kujera yaja ya zauna yana binsu da kallo d'aya bayan d'aya. Saida Harris yagama sallamarsu duka sannan ya zauna suka gaisa da ya Umar. Lallai Harris nagafa alama babban d'an kasuwa za'ayi anan. kadage sosai. Dariya Harris yayi yana Sosa kai, Yaya damacan shashancine yasa ban maida hankaliba. Amma yanzukam nagane saikanadashi akeyi dakai a wanan duniyar. Murmushi kawai ya Umar yayi, amma baice komaiba. Suna nan saiga Muktar yafito zaikai su Faisal makaranta. Duk yaran suka gaida ya Umar da Harris. Shima Muktar suka gaisa. Ya Umar yahad'a musu kayan kwad'ayi na yara aka sakama kowa a cikin lunch box d'insa. godiya sukayi. Muktar ya ce, ''gsky abinnan yayi yawa Umar, wanan aiisu Faisal aka bud'ema shagon. Gira ya Umar yad'age ya ce, ''ko." Eh mana, kullumfa saisun cinye ribar. A to kai ina ruwanka, shagonsune aii, idan bazaka iya ganiba kabar shigowa. Dariya kawai Muktar yayi, ya ce, "to ALLAH yasaka da alkairi, ya k'ara bud'i. Bara nakaisu School nazo nawuce aiki kada na makara. OK saika dawo to. *_9:00am_* Sai k'arfe tara Asma'u ta farka, waige-waige tafara na Neman ya Umar, amma saitaga wayam. tashi tayi a sanyaye tashiga bayi domin yin wanka. Batawani jimaba tafito, 'yar kwalliya tayi daidai misali tashirya cikin siket da Riga na atanfa. Haka tagyara gidan duk jikinta asanyaye, agurguje tahad'a break mai sauk'i. Na Harris ta had'a tanufi shago kaimasa Dan batayi zaton mai gayya mai aikin ya Umar yana canba. Sallamarta tasakasu d'agowa suduka biyun. Harris yay saurin tararta yana fad'in kai k'anwata yau kad'an garage nafara kukan yunwa. Murmushin yak'e tamasa, kayi hak'uri ya Harris namakarane yau. ‘tayi maganar tana satar kallon ya Umar daya canja fuska tunda yaji sallamar Asma'u.’ d'auke idonta tayi daga kallonsa ta cema Harris ina kwana. Lafiya lau Asma'un Yaya. Kin tashi lafiya?. Alhmdllh. Kanta ak'asa ta ce, ''ya Fharuk ga Break. Saboda Harris yadake ya ce, " ina zuwa." Batace komaiba takoma cikingidan tana mamakin ya Fharuk d'in nata. Ganin har wasu mintina bai shigoba tazauna tayi tagumi. Talula sosai duniyar tunani taji sallama. Afirgice tad'ago danjin an jijjigata. Anty Sa'a ta ce, "Asma'u lafiyarki kuwa?." Ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi, fuskarta d'aukeda murmushin yak'e, ta tatshi ta k'ank'ame Anty Sa'a tana mai farincikin ganinta. Itama Anty sa'a saita rungumeta. Bayan ta shimfid'ama Anty Sa'a tabarma ta zauna ta ce, "Anty inazuwa." Kai kawai Anty Sa'a ta iya d'aga mata, amma sai binta takeyi da kallo. Sosai Asma'u ta rame mata. Aranta ta ce, ''tomike damun yarinyarnan ne haka?...... Tana cikin zancen zuci Asma'u tadawo d'aukeda ruwa da kayan break d'inta dabataciba. Anty Sa'a bismillah. A'a nikam ak'oshe nake ma'u, baradai nasha ruwan kad'an tunda rana tad'aga, sanyin yad'an rage kafin yamma. Fuska Asma'u ta shagwa6e kai Anty Sa'a Dan ALLAH kici ko kad'anne. Ganin zatayi kuka Anty Sa'a ta ce, "to naji maida hawayen zanci. Murmushi Asma'u tayi, yauwa Anty babba. Itamadai Anty Sa'a murmushin tayi. Sai sannan Asma'u ta gaisheta. Ta amsa cikeda fara'a. Ta d'ora da fad'in Ma'u! Shin bakida lafiyane? Kika rame haka?. Sunkuyar dakai Asma'u tayi k'asa, cikeda jin kunya ta ce, " a'a lafiyata k'alau Anty. Kai Asma'u ban yardaba, kinga kuwa yanda kika rame?, damacan gaki babu auki kamar a hure. Kodai Umar ne yake takura miki? Dan nasansa wata sa'in akwai fad'a. A'a Anty babu komai wlhy, kawaidai idonkine yake nuna miki na rame. Humm Asma'u kenan, saikace wadda tafara saninki yau. Sati Ukufa dasuka wuce na ganki, kuma da k'ibarki kodai cikine dake?. Da sauri Asma'u tad'ago tana kallon Anty Sa'a, suna had'a ido tamaida kanta k'asa cikeda kunya. Murya can k'asa ta ce, a'a Anty banida komai. Ajiyar zuciya Anty Sa'a ta sauke, tasan akwai abinda ke damun Asma'u zahiri. To amma tak'i fad'a. Shiru nawani d'an lokaci babu Wanda yasake magana. Can Asma'u ta ce, "Anty ya yara?. Suna lafiya, duksun tafi school. Lah Anty harda Abba?. Eh shima aii ansakashi wata kusan 1 kenan. Eye yakaga abbati a school. Dariya Anty Sa'a tayi kawai. Shigowar ya Umar yasakasu kallon k'ofa suduka. Suna had'a ido da Asma'u ya harareta. Anty Sa'a ta ce, " d'an k'anina kadawo?. Eh wlhy Anty, saukar yaushe?. Yanzu babu dad'ewa nazo aii. Nalek'a shago naga sai Harris kawai, ya ce, "min kaje nan k'asan layi wajen wani. Wlhy kuwa, sannu dazuwa, ‘yafad'a yana zama.’ Yauwa kaima sannunka. Gaisuwa sukayi irinta wad'anda suka shak'u d'innan. Daga nan akahau hirar yaushe gamo. Asma'u dai batacewa uffan, daga bayama saita tashi tsaye tana fad'in yaya abincinfa?. Kansa ya girgiza mata alamar a'a. Mikewa tayi a sanyaye tabar wajen tashige bedroom d'inta. Daga ya Umar har Anty Sa'a da kallo suka bita, saida ta 6acema ganinsu sannan ya Umar yata6e baki. Anty Sa'a kuma ta ce, " Umar da matsala ko?." Kallonsa ya maido gareta ya ce, "Anty matsalar mi?." Kaida Asma'u mana. Kansa ya girgiza alamar a'a, amma baiyi maganaba. Hummm kaima haka zaka cemin kenan?. Ita mita gaya miki?. Yanda kafad'amin mana, ta ce, "babu komai, nayi tambayar duniya tace babu komai. Ni nazatama batada lafiya ko cikine?. To ammafa naga kana harararta, kuma yanzu tace ga break. Kace ka k'oshi. Kodai bakaso nasan matsalar gidankane?. Bahaka baneba Anty, gsky muduka muka fad'a miki babu komai. To kudai kuka sani, dukda nasan ayanda akayi aurenku kaida Asma'u babu wani shiri ko shak'uwar soyayya, amma yakamata zuwa yanzu komai yazama tarihi. Musamman yanda Asma'u tayi halacci agareka. Bata zama mai rama alkairi da muguntaba. Kaikaga yanda tashiga Rud'ani alokacin dabakada lafiya? duk Wanda yaganta yasan tana tsananin sonka. Kadaure kaima Umar kanuna mata soyayya, karungumi matarka kusami zuria mai albarka, tunda an rabaka da *_Afrah & Amrah_* kanaji kana gani. Ajiyar zuciya ya sauke, tuni zuciyarsa tafara bugawa da sauri-sauri. Harga ALLAH yanason 'ya'yansa, kullum dasu yake kwana yake tashi. Rana d'ai-d'aine baya mafarki dasu........ Anty Sa'a takatseshi dafad'in kayi hak'uri bawai natunomaka dasubane dan katashi hankalinka, ALLAH yana sane da kowa. Amma ka gyara mu'amullarka da matarka kuma 'yar uwarka. Karki damu Anty Sa'a komai yawuce wlhy. To shikenan, yamzu bara nakirata tabaka break d'in ko?. Kansa kawai ya jinjina mata. Babu dad'ewa saiga Asma'u da Anty Sa'a sun fito. Abinci ta shirya masa kamar yanda Anty Sa'a ta fad'a mata. Duk tsoronsa ya mamyeta. Zata koma d'aki Anty Sa'a ta ce, "tadawo tazauna suyi hira. Babu yanda zatayi tadawo ta zauna. Sund'an ta6a hira sannan ya Umar yafita saboda kiran da Yazeed yay masa na gaggawa. Bayan tafiyarsa Anty Sa'a tatsare Asma'u da tambayoyi cikin lallashi da lalama. Haba Ma'un inna, kobaki d'aukeni amatsayin yayarki bane? Indai har zaki iya fad'ama Saratu damuwarki aii nima d'aya nake nida saratun. Kokuwa bahaka baneba?. Hakane Anty, ‘Asma'u tafad'a murya na rawa kamar zatayi kuka.’ To kinga fad'amin na taimaka miki koda da shawarane inma bazan iya maganin matsalar takiba. Asma'u tayi shiru tana tunanin ta fad'a kotayi shiru? To amma aii koda shawara Anty Sa'ar ta taimaketa aii kamar yanda tafad'a. To aii kuma wanan sirrintane, kuma ALLAH ya tsinema mai bayyanashi. Kai itakam yazatayine?. Gsky tana cikin matsala, Dan inhar bata fad'ama waniba ya taimaketa da shawarar yanda zata kula da mijinta tofa tabbas tana cikin matsala, koda yaushe aurenta zai kasance cikin yin rawane......... Anty Sa'a ta katseta da fad'in kinyi shiru Asma'u. Kokin gammace kita zama cikin matsala keda mijinki?. Kowacce mace batada fadar farinciki irin gidan mijinta. to amma ke kin gwammace yazamemiki gidan wak'afi!!??. Girgiza kai Asma'u tayi tana zuraro da hawaye. Tabama Anty Sa'a tausayi, Dan haka tarungumota jikinta tana share mata hawayen. Fad'amin kinji Asma'u zakiji sassauci azuciyarki.... Cikin shashshekar kuka ta ce, "ya... Fha...ruk... ne." To miyayi miki?. Shiru nawani d'an lokaci, sannan Asma'u tafad'i abinda zata iya. Shiru Anty Sa'a tayi tana tausayin Asma'u. Baiwar ALLAH shiyyasa dukta rame, kai aii fitinannen miji saimai hak'uri da juriya, amma insha ALLAH zata taimakawa k'anwar tata kodan taku6uta wajen damk'e mijinta ahannunta gam-gam. Karki damu Asma'u, indai akan wannanne Umar bazai sake fushi dakeba saidai ya sanya miki albarka. Ki kwantar da hankalinki, sannan kidaina nuna masa kinajin tsoronsa aduk lokacin daya bukaceki kinji, idan har kika cire tsoro da fargaba tom zaki zama jaruma insha ALLAH. Yanzu idan yadawo kuma kibasa hak'uri, insha ALLAH zai hak'ura. To Anty duk zanyi, ngd sosai. Karki damu Anty Sa'a ta fad'a tana shafa kan Asma'un. Anty Sa'a batabar gidanba saida takoyama Asma'u dabaru kala-kala, sannan ta ce, ''tajira sak'o nanan zuwa gareta, zatabama Rafi'a takawo mata, zata rubuta mata bayanin komai. Godiya sosai Asma'u tama Anty Sa'a, sanan suka shiga shago wajen Harris, bayan and'anyi wasa da dariya Anty Sa'a tatafi da tarin alkairi da Harris ya had'a mata bisa Umarnin ya Umar. Ya Umar kam koda yafita sai office wajen Yazeed. Kamar yanda suka saba suka tari juna cikeda farinciki, bayan d'an barkwanci irinna abokai suka shiga abinda ya kawosu. Yazeed ya ce, "abokina albishirinka............. *_tofa masu karatu, wane albishir yazeed zaima ya Umar Fharuk ne?._* *_kubiyo ni mata agidan Abdus'salam danjin yanda zata ritata👌🏼😉_* *_(((S)))........2017_* *_I Love you all._* [12/20/2017, 6:27 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_ina kuke masoyan Karayar Arzrek'i? ku marmatso-ku marmatso, yaufa shafin da gaisuwar fatan alkairin duk nakune, ina godiya da nuna soyayyarku gareni, inamai kuma baku hak'uri darashin posting d'ina akoda yaushe, alkairin ALLAH ya tabbata agaresu aduk inda kuke, banida damar ware sunan wani bansa nawaniba, amma duk kuna raina, masu kira a waya, damasu toromin sak'o, kai harma wad'anda ban saniba, ina alfahari da masoyina akowane lokaci, nagaisheku da k'yau abokan tafiya._* *_Hakama ya Umar & Asma'u suna mik'o gaisuwa._* _I love you so much💋_ *_page→49-50_* ..........Goro fari k'al abokina. Yazeed yayi murmushi tareda mik'ama Umar wani file. Ya Umar yakar6i file d'in zuciyarsa cikeda tunani. Bud'ewa yayi yahau dubawa. Cikin maruk'ar farin ciki ya rungume Yazeed yana fad'in Alhamdulillahi ya Ubangijin talikai. Yay hanzarin sakin yazeed yashige bathroom d'in dake office d'in, mintuna kad'an yafito d'aure da alwala. Yazeed dai sai kallonsa yakeyi yana dariya. Ya Umar bai kulashiba ya d'auki abin sallah ya shimfid'a a office d'in. Sallah yayi raka'a biyu, yadad'e awajen sujuda bai d'agoba, yanata mik'a godiyarsa ga ALLAH, harda kukan farin ciki. Yabama yazeed tausayi sosai. Saida yadad'e yana addu'oi sannan yatashi yadawo Inda yazeed yake. Tsirama yazeed ido yayi tamkar mai Neman wani abu, a jikinsa........zuwacan kuma yaja wata sassanyar ajiyar zuciya!....Abokina......... Yazeed yay saurin d'agama ya Umar hannu Alamar baya buk'atar godiya. Shiru kuwa ya Umar d'in yayi, yakulle bakinsa yana cigaba da kallon yazeed. Shima yazeed d'in shiyake kallo, saikuma sukaima juna murmushi, yazeed ya ce, "abokina natayaka murna matuk'a wlhy, amma tabbas akwai lauje cikin nad'i dangane da rik'e kayanka, saidai koma waye shida ALLAH kawai. Ajiyar zuciya ya Umar yasauke, tuni idanunsa sunyi jajur, cikin muryar 6acin rai ya ce, " nadad'e ina zargin hakan, tun lokacin da akaita min yawo da hankali Dan Neman ku6tar kayan. Amma babu komai, koma wanene nayafe masa, ALLAH kuma ya shiryesa. Ameen namijin duniya. ‘yazeed yafad'a yana sarama Umar.’ Ya Umar yayi murmushi mai k'ayatarwa, murya a sanyaye ya ce, "yazeed kahana namaka godiya, bansan miya saba?." Bana buk'atar godiya Umar, inhar kad'auka nida kai 'yan uwan junane, to karka godemin. Humm yazeed kenan, wlhy tunbama yauba dama kallon d'an uwana najini nake maka, akullum darajarka k'aruwa takeyi bisa mizanin zuciyata, ALLAH yajik'ansu Abba da rahma, ALLAH yaraya zuri'a, ALLAH yayi maka sakayya da mafificin alkairi, yanda kayi sanadin dawowar farinciki agaremu kaima ALLAH yasaukar da farinci wa rayuwarka mai albarka har Abadan. Ameen Abokina ngd sosai, ALLAH yabarmu tare. Sundad'e suna hira abinsu cikeda farinciki da k'aunar juna. Sun yanke hukuncin raba kayan na ya Umar gamasu buk'atar sari, shikuma kafin ya kammala gyaran mall d'insa sai ayi k'ok'arin shigo dawasu kayan. Wannan shawara tayima ya Umar dad'i, Dan haka ya rungume yazeed yana kwararo addu'ar alkairi agareshi. Daganan sallama sukayi ya Umar yatafi gida........ •∆• Tunda Anty sa'a ta tatafi Asma'u tatashi takuma gyara gidan tsaf, abincin rana tayi na musamman Dan sotake su shirya da ya Umar d'in. Taje ta tsala wanka, yaukam hardayin kwalliya, abinda baicika damun Asma'u ba. Ita da'ayi kwalliya Dakar ayi duk d'ayane agareta. Yaudai haka tayi mai sauk'i amma Tamata k'yau. Zani da Riga tasaka na lemon green d'in shadda, tayi d'auri mai k'yau tareda feshe jikinta da turare mai dad'in k'amshi. Faisal tabama abinci yakaima Harris da Sadam a shago. Tana zaune ad'aki tanata latse-latsen waya ya Umar yashigo gidan da sallama. Babu kowa a babban falo Dan haka yawuce d'akinsa abinsa. Wani ni'imtaccen k'amshine yaratsashi kamar na falon, shak'a yayi ya lumshe idanunsa yana sakin murmushin jin dad'i. Ahankali ya furta ALLAH yay miki albarka my Asma'u husna!. Nikam danake a la6e nida su Manshat mukace amin. Yana Shiga bathroom yatarar dawani abin mamakin, ruwan wankane na musamman aka had'a masa. Baimayi niyyar wankanba, yashigane domin sauke nauyi🤐, to amma ganin ruwan wankan yasakashi sha'awar yi. Aiko yatu6e ya zabga wanka abinsa. Duk shagalinnan da ya Umar keyi Asma'u batasan yadawoba. Tanacan tana zabga charting da 'yan *_TASKAR LITTATAFAN HAUSA_*😻, su o e sai zabga mata surutu akeyi🙄bandai fad'i sunaba ehe😏, amma nasan kun gane aii😜 *_Ina sonku da Alfahari daku 'yan group d'ina, taskar littatafan Hausa, I love you so much my Darlings._*💋❤❤ Saida yashirya tsaf cikin doguwar riga mara nauyi ash color sannan yanufo d'akin Asma'u. Azatonsama barci takeyi. Yadad'e tsaye abakin k'ofa yana kallonta amma batasaniba. Gyaran murya yayi wadda tasaka Asma'u razana tajefar dawayar gefe tareda kwalla k'ara. Yanda tatsorata sosai saiya bama ya Umar dariya, aiko yashiga tuntsura dariya tamkar bashiba. Jin dariyarsa yasaka Asma'u dake shirin shigewa bayi Dan Neman gurin 6uya ta tsaya cak. Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki tana fad'in kai ya Fharuk! Wlhy kabani tsoro ainun, kaji kuwa yanda zuciyata ke bugawa da k'arfi?. K'arasowa yayi inda take, har yanzu dariyar yakeyi, itama zuwa yanzu tafara darawa, yakama hannunta suka koma gefen katifar suka zauna. Kai Husna dama haka kike matsoraciya? Kinga kuwa yanda kika birkice? Hhhhhhhhh!!!!! Yakuma saka wata dariyar harda kwanciya akan katifar. Baki Asma'u ta tunzuro gaba, kai yaya kabani tsoro kuma kadawo kanamin dariya. Nidai kabari plss. Tashi yayi zaune, to aiked'ince kamar farar kura. Kai ammafa kin iya gudu zazuuuu! kenan. ‘yay maganar yana rungumota jikinsa. Itama k'ank'amesa tayi tana 'Yar dariya k'asa-k'asa. Ya Umar ya ce, "to azatonki wanene zai shigo d'akinki idan baniba?. Kasanine wlhy banji koda motsin dawowarkabane, kuma yanzu hira mukeyi a group wai ana shiga gidan mutane da ranar ALLAH sata, wani lokacinma har fyad'e akema matar gidan ko idan sunada 'yammata. Tofa shine nikuma kawai naji gyaran murya batareda sanin shigowar mutumba. Aikaga dolene na firgita!. Murmushi yayi yana kuma jawota jikinsa, hum kudai mata kuncika tsorone kawai, yanzu hakama agida d'aya aka ta6ayi amma kunzo kunata cancana magana a chatting. ALLAH yaya dgsk anayifa. Bakamar gidan amare, da ankai amarya sai 6arayi suje satar kayan lefefa. Lallaikam to ALLAH yatsaremu da tsarewarsa. To amen ya rabbi. Sannu da zuwa. Yauwa ya gidan? Ina Anty Sa'a d'in. Tab wannan aitadad'e da tsufa agida, saboda kar yara sutaso daga school su tarar bata nan tatafi. gashi zata biya gidansu mama. Okey. Asma'u tayunk'ura zata tashi daga jikinsa yakuma rik'eta da k'yau. Ina zuwa kuma?. Yaya kofa ruwa ban bakaba bare abinci. Murmushi yayi ya ce, " to aii banajin yunwa. Nidama wani k'aton albishir nazo miki. Da Sauri ta ce, "goro fari k'al yayana." A'a saifa kin bani. Shiru tayi alamar tunanin mizata bashi to? Zuwa can tad'ago tana kallonsa, yaya komai nabaka yayi?. Kansa ya jinjina mata batareda yayi maganaba. Hummm babbar magana. Ya Umar bai tsammaci haka daga Asma'u ba, Dan baita6a tunanin zata iyaba, musamman idan yay la'akari da kunyarta dakuma tsoro. Amma abin mamaki saiga bakinta cikin nasa. Wani salon kissing take masa wanda shikansa daya d'orata ahanya baisanshiba. Dandanan jikinsa yasaki, (kundai San su ya Umar sai a slowly😉). Shima ruk'ota yayi sosai suka zube akatifar yana bada gudummawarsa, dukda jikinsa babu wani kwarin kirki. Suntafifa basajin kira, Dan haka sad'af-sad'af nafito nida gayyata. ♥ Saida suka kwashi wani d'an lokaci sannan nalek'asu. Hangosu nayi sunfito daga wanka. Nazaro idanu waje dan mamaki😳, yanzunan daga albishi har an zarce?. Ta6d'i itamafa Asma'u nakula tafara zama 'Yar hannu. Asaman katifar suka zube, Asma'u na lafe jikinsa ya Umar yabata labarin kiran da yazeed yay masa.. K'ank'amesa tayi tana kukan farinciki da kwararo addu'oin alkairi ga ya yazeed da dukkan ahalinsa. Shikansa ya Umar saida 'Yar kwalla ta tarumasa agen ido. Sund'an dad'e suna tattauna lamarin kafin daga bisani Asma'u tabashi hak'uri akan fishin dayakeyi da ita. Murmushi yayi mata, cikin rad'a ya ce, "aikin wanke laifinki tas my Asmy, ALLAH yayi miki albarka, yabamu zuriya tagari." ‘Ameen yayana.' Daga nan suka cigaba da hirarsu har barci yay awon gabadasu....... *_____________________* Yanzu baby bazakuyima kanku fad'aba akan wannan yawon gantalin dakukeyi keda Suhaima? Kince karatu zaki koma bazakiyi aure yanzuba, amma kosau d'aya baki k'arama dadynku maganar karatunba. Shekaran jiyafa a club Safwan yacemin ya ganku. Anya wannan hanyar kuna ganin zata 6ille daku kuwa?. Baki Lubna taturo gaba itada Suhaima, Lubna ta ce, "yo momy shida yakawo miki gulmar ganinmu a club shi miya kaisa club d'in? Kodan gwano bayajin warin jikinsane? Zai take laifinsa yahango nawasu. shimafa Safwan d'innan magulmacine, shiyyasa nakeson Ameer, arayuwa bashida saka ido akan abinda babu ruwansa wlhy. Suhaima ta ce, " aii indai ya Safwan ne haka ya iya gulma tamkar mace wlhy, ke yamafi wata macen narantse. Shi sau nawa muna ganinsa a inda bai daceba amma bama fad'a, Dan kawai ya gammu a club zaizo yana gulmarmu. Naga miye aibun club Dan ALLAH? gurinefa kawai na hutawa bawani abuba.......... Ke dallah yimini shiru anan shashar banza, kemi kika sani dangane da duniya?. Kucigaba karku fasa, aii duniyace, Wanda baizobama jiransa takeyi. Tana gama fad'a tabar musu wajen. Suduka baki suka murgud'a. Lubna ta ce, "kaini wlhy watarana momy saitaita Abu kamar bata wayeba. Dan ALLAH miye aibun club?. Humm kemadai k'ya fad'a, amma balaifinta baneba, wancan algunguminne yahad'a, shibaiga abinda yake aikatawaba saimu?, ALLAH ranar har kwalbar *_Guilder_* Nagani a d'akinsa. K da gsk?. Wlhy kuwa baby da gsk nakeyi, amma kinsan dana tambayesa miya cemin?. Girgiza kai Lubna tayi alamar a'a. Suhaima tacigaba dafad'in, saboda ya rainamin hankali cewa yayi abokinsane yasha bashiba. Dariya suka shek'e da ita. Lubna ta ce, " k'arya yakeyi, bayaso kifad'ama dadyne. Shiyyasa Ameer yake birgeni shida lamarinsa babu wani 6oye-6oye, komai afili yakeyinsa kowama yagani. Amma kinga Safwan... Hummm mai fuska biyu kenan. Dariya suka shek'e da ita, harda tafawa kamar wasu k'awaye. Suhaima ta ce, "yaya zamuje casun Mufy ne?. Tafd'i yo mizai hana, ba'a gayyacemubama munje balle Abu namu maganin a kwa6emu. Aii zuwa kobabu tayar gaban mota, bikin birthday d'in aminiya aidole saidamu awajen zai k'ayatar. Gskyne babyna, shiyyasa nakesonki fiye da kowa agidanan. ammafa Umar yaso ruguzamu wlhy, kai ALLAH yataimakeki ya ku6uto mana dake. Inaji ajikina dankibar gidanan ALLAH ya talautar da Umar. Dariya suka koma sakawa. Lubna ta ce, " k'aba, yanzudai kam nasan aii yagama Fita hayyacinsa, dagashi har shegiyar yarinyarnan maikamada ojuju.🙃. Hhhhhhhhh kai baby bakida damafa kema. Kinsan dabaku rabuba k'ila dayanzu kinmasu Amrah k'ani ko k'anwa. Tab, keni barima jinginani dashi, har abada nashafeshi daga rayuwata. Kisaka aranki bamma ta6a Sanin wanishi Umar ba arayuwata. Suhaima ta ce, "k'aba kenan?." Ke aii Umar yawuce k'aba wlhy, saidai yanyan!. Mtsooww. Nikoma hirarsa banaso matsiyaci kawai, haka zai k'are rayuwarsa a talauci........... Na ce, "Hummm.... Yeeeeeeeeeeee💃🏻💃🏻💃🏻, ankwana ana mana ruwa. ALLAH mungode da tarin ni'imominka garemu, kana bamu badan halinmuba, ALLAH ka k'arama ANNABI fadila da wasila🙏🏻. *_((((S)))........2017_* *_I Love you all_* [12/21/2017, 6:47 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_writer's kuna ina!!?._* _masu zaginmu dacin zarafinmu mungode sosai, kuna aiko mana da addu'oin alkaba'i da kiranmu jahilai. Hum jahilci! Jahilci!!....wannan kalmace data dace ga Wanda baisan kansaba, mai ilimi shine keyin gyara ba zagiba. Amma yau harmu wata take kirada mazinata marasa tarbiyya, Fasik'ai, wai har kinacewa ALLAH ya wargaza rayuwarmu😭, kekuma takin rayuwarfa? Mi ALLAH zai mata?. maganar gsky shine bamu yafeba, duk Wanda yaymana wanan sharrin, sharrin zina bala'ine masifane._ _wlhy tallahi bazan yafeba nidai, ya ALLAH kayi gaggawar sakamana akan Duk wanda yayi wani mummunan lafazi akanmu, mubazamiyi masa mummunan furiciba, amma indai munada hakk'i agareshi ALLAH kayi gaggawar fidda mana._ _ALLAH kaine shedarmu bamu ta6a rubutaba books dan lalata d'an waniba, amma akace aikinmu kenan, ya ALLAH ka saka mana da sakamako mafi cancanta._ _Kowacece munbarki da ALLAH, shine zai zaka mana, kuma insha ALLAH duk addu'ar dakikayi agaremu koke wacece ALLAH ya maidata agareki, yanda kikaci zarafinmu kema ALLAH yamiki daidai da abinda kika aikata mana._ _Duk Wanda yakaranta Novels idan ALLAH yabashi fahimtar abinda writers suke nufi Dan fad'akarwa falillahi hamdu, idan ka kasa fahimtarmu kuma harka zagemu ALLAH yasaka mana._ _ALLAH ya Isa wlhy, ALLAH ya isa, ALLAH ya Isa!!😭._ *_Banta6a kuka akan rubutuba sai yau, ya ALLAH ka sakamana, kaikafi sanin dukmasu zaginmu da abinda suke aikatawa agaremu, wlhy koda uwarmu d'aya ubanmu d'aya bazan yafe mataba, da aurenmu ake kiranmu mazinata😭, da tarbiyyarmu ake kiranmu marasa tarbiyya!, da imaninmu ake kiranmu fasik'ai, baki sanmuba bamu sankiba, bamu taka mikiba bamu karya mikiba kike addu'ar ALLAH ya wargaza mana rayuwa, Narantse bamu yafeba._* _Da duk yawun marubutan online nake wanan maganar, bamu yafeba, bakuma ZAMU ta6a yafewaba, ALLAH yasakamana._ *_Kince daga k'ungiyar shiriya ta mata daga jihar kano?._* _Wannan k'aryane, idanma daga k'ungiyar kike kekika sani, amma kije ALLAH yaymiki abinda kikaimana._ _ALLAH yayi mana maganinki jahila kawai, munbarki da ranar k'arshe ALLAH yamana hisabi😭._ *_Duk wata writer datasan kanta koda bata karanta posting d'inan da akayi zagi akanmuba tota mik'a kukanta ga Ubangijin Al'arshi akan yasaka mana, kullum sai anfito da Sabon salon cin zarafinmu, idan aka zagi wannan writer yau gobe sai a koma kan waccan, haba jama'a kuji tsoron ALLAH wlhy. Writers kufad'a a sujudarku, mufad'a a cikin kowacce sallar farillah data nafila, insha ALLAHU, ALLAH zaimana sakayya._* Kije keda ALLAH, shine zaimana maganinki, ALLAH ya shiryeki, kuma kikoma islamiyya danneman ilimi akan hak'ik'in Dan Adam a musulince, damunin fad'ar mummunan kalma ga musulmi. Kema kifara gyara kanji kafin kigayara wani, kuma kema kinada damar rubuta tarihin Nana Aysha (RA) harmu karanta mu amfana kamar yanda kika fad'a. Tunda mu bamuda ilimin addini rubutawa. Kai kai kai ALLAH ya Isa tunda kika dangantamu da zina. 😭😭😭😭😭😭 *_page→51-52_* ..........Alhamdullahi abubuwa sunata gyaruwa, riba sosai su ya Umar suka samu akan kayansa, wayyo zokaga farinciki wajensu. A 6angaren gyaran mall NASA kam aiki yayi nisa, yanzu hakam fenti akeyi. Mutanedai sai zind'e da dariya sukeyi wai ya Umar ya saida mall d'insa, musammanma abokansa. masu k'aunarsa Dan ALLAH kuwa bak'inciki sukeyi dak'ara tausayinsa, Dan azatonsu yasayard'in da gsk. Muktar yana zaune amota yana kallon masu aikin Fentin, fitowarsa kenan daga wajen bayan yagama duddubawa. Sallamar da akai masace tasakashi d'agowa, matasan samarine su biyu, d'aya aciki ya ce, "sunana Tasi'u, wannan kuma Salman, idan bazaka damuba kazomuje can mana, suka nuna majalissarsu, munga kullum kazo saidai kaita zama a mota, wanan ba girmanka baneba. Murmushi Muktar yayi, Dan dukansu yaganosu abokan Umar ne. OK babu damuwa ngd sosaifa. 'Yafad'a yana fitowa'. Yana kallon sanda Salman da Tasi'u suka kalli juna suna murmushi. aransa ya ce, " Niba Umar baneba, wuju-wuju zan muku wallhy. Har majalissar suka k'arasa, dukyabama sauran hannu suka gaisa, yasami guri a zauna, hira akacigabadayi cikin raha, zuwacan Hafiz ya ce, "kai ammafa wajennan yayi k'yau wlhy, kunyi k'ok'ari wajen gyarashi, daga gani ya lashe miliyoyin nairori gsky. Murmushi Muktar yayi, wlhy d'an uwa yaci kud'i kam, bak'aramar 6arna wutar taima wajenba, shiyyasa nake tausayama wannda yakeda wajen. Aidolene a tausaya MASA Cesar Kabeer yana turo baki gaba alamar zund'e, to amma shine yasayar maka da wajen?. Saida muktar ya kallesa sannan yasaki wani murmushin mugunta, eh shine ya sayarmana, amma da sainaji kamar ance bokinkine. Kamar antsikari Dr jafar ya ce, " eh adakam abokinmune amma yanzu ko Inda yake bama musaniba, ranar wani abokinmu harda zuwa nemansa, inagadai baisan yanzu yazama karfaba..... Gabad'aya suka bushe da dariya amma banda muktar daya tsaya kallonsu, k'asan zuciyarsa kam yanajin wani d'aci. Shimamakima yakeyi yanda Dr Jafar d'in bai ganeshiba. Haka sukaita tattaunawa da zagin ya Umar, shidai Muktar suna bashi mamaki, sai gab da magriba yamusu sallama yatafi gida cikeda mamakin halin d'an Adam. Koda wasa Muktar baita6a bama ya Umar labarin yanda sukayi dasu Hafiz ba, amma kullum yana nusashsheshi akan yadage da addu'ar Neman tsari, Dan tabbas yana zagaye da mak'iya, kuma komai zasu iya aikatawa akansa idan sunga ALLAH Yakuma d'aukakashi. Sosai YA UMAR yakar6i shawarar Muktar, haka suka duk'ufa addu'a shida matarsa, yanzu sundage tashi duk dare suyita nafilfili da mik'a kukansu ga ubangijin talikai, ga azumin litinin da alhamis sunatayi, sadakama ba'a barsu abayaba. Duk hidimarnan da akeyi babu Wanda yasan abinda ke faruwa a family d'in ya Umar. Inna Ce kawai tasan komai. Itama kuma tayi gum abinta. Ranar ya Umar yaje gaigaida iyayensa, yana zaune ak'asan kafet yayinda mama take saman kujera, sai cika take tana batsewa. Kan ya Umar na ak'asa. Mufida da Rafi'a sunama islamiyya. Cikin masifa mama ta ce, "Umar ni wacece awajenka?. Saida yad'ago yad'an kalleta sannan ya ce, " mahaifiyatace!." Inafa mahaifiyarka Umaru!, aidaka d'aukeni matsayin mahaifiyarka dabaka saida shagunankaba harka kasa fad'amin. Wato kamaidani lasha money ko?. Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, murya a sark'e ya ce, "kiyi hak'uri mama, koda nasayar aii bama abani kud'inba, sunce saisun gama gyarashi sun tabbatar babu matsala sannan subani kud'in, shiyyasa Nima na 6oye miki, nafison da anbani kud'in sainazo na nuna miki saikinfi yin farinciki. Mama tagyara zama tana k'ara washe hakwara, eh kumafa da gskyarka Umaru, dama kaga gashi ansaka bikin mufida wata biyu kenan, yanzu saura wata uku, ninasan mak'on Abubakar bazai barsa yaymata kaya masu tsadaba alkur'an kuwa. Inadai fata kafin bikin kud'in namu sun fito ko?. Kai kawai ya Umar ya iya jinjina mata saboda 6acin rai, uwa uwace babu mai canjata, shibaisan wane irin haline da mamaba........?. Maganartace takuma katse masa tunani. Yauwa Umaru ALLAH yayi maka albarka, ammafa kayi hak'uri ankgaya maka maganar bikin Mufida amakare, wlhy Abubakar ne yahana afad'a maka, kasandai halinsa na nunkufurci...... Da Sauri ya Umar ya ce, " babu komai mama, nibara nawuce, inaso nad'anyi wani aikine. To...to....to Umarina, amma bazaka tsaya ko d'an wani Abu kaciba?, inada wani dambun nama kuwa zauna kaci. Mama kibarsa kawai, ina saurine aii. A'a aiba'ayi hakaba, bara na k'ulla ka kaima d'iyata Asma'u. Tana maganar tana shiga d'aki. Ya Umar yagoge wasu 'yan kwalla da suka tarumasa agefen idonsa:- dawanine yafad'a masa akwai iyaye masu irin halin mahaifiyarsu walhy dasai ya k'aryata, da'a film yagani saiyace wasan kwaikwayone, da a Novel yakaranta dasaiyace k'aryace kawai da wasa da hankalin mutane irinna marubuta. To amma gashi ra'ai-ra'aini yana gani. Ya ALLAH ka shiryi irin wad'annan iyaye!....... Yauwa Umarina gashi, mama tamik'o masa bak'ar leda wadda aka k'unshe k'aramar roba a ciki. Kar6a yayi yaymata godiya sannan yatafi. Yana fita mama tafara rawar murna, kai ALLAH mungode maka kud'in zasu shigo, wlhy dama inata tunani akan yanda zanyi shagalin bikinnan Dan nasan Abubakar da shagen mak'o, k'ark'ari yabani dubu hamsin, amma kinga Umar konawa nace inaso wlhy yaronnan zai bani. Kai talaucima baiyiba wlhy, aigarama daya saida shagunan koba komai aii zamud'an shana kwana biyu. _Humm kai jama'a wanan wace irin uwace? kamata yayi tayi bak'inciki dayima ya Umar fad'a akan miyasa ya sayar, amma kuduba murna takeyi akan zasu sami kud'i, bata kallon halin dayake ciki da Wanda zaishiga nan gaba, a'a ita burinta kud'i, gashi tanata bin matakan dazata raba zumincin 'ya'yanta, yau ta nuna tafison wanan, gobe kuma tafison wancan, kaiconmu da masu hali irinna mama, wlhy iyaye kugyara, shikenan da 'ya'yanka sunfara girma saika d'auki duk nauyinka ka maida akansu, wlhy hakan yana kawo raini tsakanin 'ya'ya da iyaye. Indai d'a yakasance nakwarai kuma d'an halak bazai manta da halaccin iyayeba, bazai manta da gwagwarmaya irinna iyayeba musamnamma uwa, kahanata barci tun kana acikinta, kahanata cin abinda take so tun kana acikinta, kahanata sukuni tun kana acikinta, ta haifeka cikin magagin wahala, ta raineka, idan bakada lafiya kana kuka tanayi, idan kaji yunwa tabaka kaci koda ita bataciba, tagoyaka, ta wanke kashinka, idan anta6aka ranta ya6aci, konawa tasamu zata kashesu akanka dankayi farinciki, katuna gwagwarmayar da mahaifinka yakeyi wajen nema muku abinda zakuci da kud'in makarantarku Dana asibiti._ _Amma dan rashin tunani harka iya kasa k'yautata musu sai sun rok'eka, kai wlhy kaicon wad'annan 'ya'ya. Iyaye mugyara, 'ya'ya mugyara Dan ALLAH._ Koda ya Umar yafita saiya samu adaidaita yashiga zuwa gida. Zuciyarsa namasa ciwo da tunanin hali irin na mahaifiyarsu, amma kokad'an abinda take masa bai gutsiri ko kwayar zarrah daga k'aunar dayake mataba irinta d'a da uwa, yanason mahaifiyarsu, akullum kuma yana mata addu'ar neman shiriya wajen ubangiji. Har suka iso baimasan sunzoba, saida mai Babur yata6ashi sannan yakawo nimfashi, kud'insa yabasa yay masa gidiya. Shago yafara Shiga suka gaisa dasu Harris sannan yak'arasa cikin gida. Idonsa nakan Asma'u dake a kwance a tsakar gida bisa tabarma, agogon hannunsa ya kalla 5:13pm. Ya girgiza kansa, afili ya ce, "yarinyarnan bazaki daina wanan barcin la'asar d'inba dakika koya ko?. Narasa mike damunkine haka?. Yana maganar yana tafiyane gareta, harya k'araso yazauna Kusada ita. takalmin k'afarsa yafara k'ok'arin cirewa yana fad'in Husna! Ke Husna! Tashi mana. Asma'u batada nauyin barci sosai tabud'e ido ahankali, ganin ya Umar zaune Kusada ita yasata yunk'urawa ta tashi da k'yar. yad'an juyo ya kalleta ya kakka6e safar daya cire. Waini barcinnan dad'i yakemikine dakika kasa dainawa? Magana tanawa nayi miki akan barcin la'asar?. Hamma Asma'u tayi tanad'anyin mik'a, kayi hak'uri Yaya wlhy nima bansan sanda barcin ya sacenibamafa, zaune nake ina kallo awaya. Takalmansa yagyarama zama, yad'ora safar akansu sannan yamatsa baya sosai ya zauna tareda jingina da bango. Jawo Asma'u yayi kusadashi. Husna kodai akwai abinda ke damunki? Wanana barcin naki yafara yawa, yanzufa mawuyacine nashigo gida ban tarar dake kina barciba. Kalli yanda tsakar gidanan yay datti amma kinkasa sharewa, kuma aii da bahaka kikeyiba, kalli wancan wanke-wanken tunda zan fita naganshi acan gurin, haba Husna sokike kikoyi k'azantane?. Kanta ak'asa ta ce, "a'a!." Tomike damunkine?. Wlhy Yaya nima ban saniba, haka kawai barci baya isata yanzu, koda zanyini inayinsa. Shiru yayi yana kallonta, itama shitake kallo, ajiyar zuciya yasauke yana fad'in to ALLAH ya k'yauta. nibara narage kayan jikina. To tafad'a tana binsa da kallo. Silifas d'inta yasaka, yad'auki takalmansa yanufi cikin falon. Yana shigewa Asma'u takoma ta kwanta abinta. Bayan kamar minti 16 ya Umar yafito, kallon Asma'u kawai yayi ya girgiza kai. Shibaima San yazai mataba wlhy, amma zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dolene yakaita wajen Dr Al-ameen, k'ilama shawarace ke damunta, dama gata makwad'aiciya. Tsintsiya ya d'auka yafara k'ok'arin share tsakar gidan. Tas kuwa yashareshi, dama bashida wani girma, yajawo ruwa a rijiyar dake gidan ya ciccika bambun waje dana toilet d'insu duka sannan yafara wanke-wanken. Duk abinda yadace saida yagyarashi sanan. Aikodai yaji jiki, jiyakema bayansa ya rik'e. Mik'a yayi yana mammotsa ga6o6insa. Kai mata mafa suna aiki, kana ganin aikin cikin gida kamar k'aramin Abu ammafa ba k'arami baneba, wlhy bayana harya k'age, aidole nayi wanka da ruwa mai zafi. Shikad'ai yaketa surutanta yayinda yake kwashe kayan wanke-wanken yana kaiwa kichin. Yana gamawa ana kiran sallar magriba, alwala yayi kawai. matsowa yayi Kusada Asma'u yana tada'ita, k kasa sarkin barci tashi lokacin sallah yayi. Da k'yar ta iya tashi, Dan jin jikinta take dukyayi nauyi, saidama ya taimaka mata sanan tamik'e tsaye. Zaki iya kona rakaki kiyi alwalar?. Asma'u daketa faman lumshe ido ta ce, "a'a zan iya." To ni saina dawo. Bai wani tsaya jirantaba yafice masallaci. Itakam sororo tatsaya tanabin ko'ina nagidan da kallo, abin mamaki wai yau ya Umar dakansa yay aikin gidan? K'arasawa tayi wajen banbunan ruwa, ko ina cike yake da ruwa, talek'a kichin nanma tsaf, dukda dai yasaka kayan wanke-wanken duk ba daidaiba. Murmushi tayi ta ce, "ina sonka dayawa yayana, ALLAH yabarmu tare. Itama sallar taje tayi. Tana idarwa tafito da zummar nema musu abinda zasuci, leda ta hanga saman tabarmar data kwanta, tak'arasa tad'auki ledar tabud'e, tofa wayabama Yaya dambun nama haka?. Mamace tace nakawo miki. Da sauri tad'ago danbataji shigowarsaba. Tayi murmushi kai amma nagode, tana nan lafiya itada Abba dasu Rafi'a?. Lafiyarsu k'alau, bamma tadda kowaba agidan, Abba yana wajen aiki, su mufida kuma suna islamiyya. Ayya. Robar tamaida ta k'ulle tana fad'in bara nashiga kichin yaya.. Kichin kuma? Mizakiyi akichin?. Yaya abinci mana, da ranafa banyi komaiba Dan naga bakanan. La'ila misu Harris sukaci to?. Anty Saddiqa takawo musu abinci. To kekumafa?. Ni kawai nasha garin kwaki. Garin kwaki kuma?. Eh wlhy Yaya shinake sha'awar sha. K'arasowa yayi daf da ita, Yakama hannunta suka zauna atabarmar, sai binjikinta yakeyi da kallo kamar mai Neman wani abun. Husna anya kuwa kinada lfy?. Yaya lafiyata k'alau wlhy. Kin tabbata babu abinda yake damunkine?. Kanta tad'aga masa alamar eh. Shiru yayi yana nazarinta, zuwa can ya ce, "kinga shirya muje wajen Dr Al-ameen. Asma'u tazaro ido waje, Yaya wlhy lafiyata k'alau, kuma awanan daren zamuje wajen Dr Al-ameen? Aii yanzuma yatashi aiki. Shiru yayi yana nazarin maganarta, zuwa can kuma ya sauke ajiyar zuciya to ALLAH yakaimu safiya. To Ameen, saidaifa nidai lafiyata k'alau. Inafa kikaga lafiya my Husna? Wai kinga yanda kike ramewa kuwa?. Hannu tasaka tana shafa wuyanta, azuciyarta ta ce, "rama kam aii fitinarkace takawota, amma afili saitace yanayine kawai Yaya. Baice komaiba, yadai jawota jikinsa ya matse. *_washe gari_* Tunda wuri ya Umar yasaka Asma'u tashirya badan tasoba, shima shirinsa yayi cikin d'anyar shadda green mai duhu, yayi k'yau ainun. Yafito sai zabga k'amshi yakeyi, itama haka Asma'u tana k'amshi mai sanyi bawai irin nasaba. Kai my Husna ALLAH kuwa jikina ciwo yakemin har yanzun. Dariya Asma'u tayi, kai Yaya dagayin d'an aiki duk ka cikamu da raki tun jiya. Sharafa da wanke-wankene sai d'ibar ruwa, amma jiya saida namaka tausa, kayi wanka da ruwa mai zafi kuma. Kibari kawai har yanzu ban dawo garauba gsky, inagama sai Dr Al-ameen yabani maganin ciwon jiki. Dariya sosai Asma'u take masa. Shikuma yatsuke fuska wai yaji haushi.................😄 *_(((S)))........2017_*. *_I love you all_* [12/22/2017, 9:00 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* _ina kike my k'anwa Marak'isiyya?, wanan shafin nakine, gaisuwa agareki da fatan alkairi, ALLAH ya tabbatar da farinciki agareki my sweet lil d'ina💋_* *_page→53-54_* ..........Lokaci k'an k'ani suka isa Asibitin, ko kad'an ya Umar baya buk'atar had'uwa da Dr Jafar, Dan haka yasa sukabi tabaya shida Asma'u. Saidai kumar abin fad'a suna karya kwana saiga Dr jafar shida wasu Norses. Ya Umar Harya d'auke kansa saikuma yaga rashin dacewar hakan, gyara tafiyarsa yayi yadawo kan hanya sosai, sa6anin da daya koma gefe. Shima kansa Dr jafar baiyi niyyar gaisawa da ya Umar ba, amma ganin ya Umar yanufoshi ga wani kwarjini daya masa saiya dake shima. Sallama ya Umar yamasa, da k'yar Dr jafar ya amsa, ya Umar yayi murmushi yana mik'a masa hannu, haj Jafar talaka baya ganinku?. Wata dariyar k'eta Dr jafar yayi tareda fad'in mu mun Isa? Aikune manya-manya maganin k'ana-k'ana. Dariya sosai ya Umar yayi wadda har zuciyarsa yayita, yazame hannunsa daga na Dr jafar yana fad'in to mungode, ya aikin?. Alhmdllh Dr jafar yafad'a cikin 'yar kunya. Asma'u kam tana gefe ko kallo baima ishetaba, Dan yana jerin manyan wad'anda tatsana wlhy. Koda yad'ago suka had'a ido, yawashe baki zai gaisheta saita daka masa wata uwar harara. Ruf yarufe bakinsa yakasa magana. Abin nasu yaso bama ya Umar dariya, amma saiya gimtse yayima Dr jafar sallama yabi bayan Asma'u dahar takusa shan kwana. Harara Dr jafar yaraka bayan ya Umar da ita. Nikam bilynku na ce, "ohodai ihu bayan hari kenan."🤷🏽‍♀😜 Da k'yar ya Umar yacimma Asma'u suka k'arasa office d'in Dr Al'ameen batareda suma juna maganaba. Cikeda fara'a Dr Al-ameen yakar6esu Dan dama yasan da zuwansu, cikin barkwanci aka gaisa sannan yafara tambayar waye bashida lafiyane?. Ya Umar yanuna Asma'u, wlhy doctor my wify ce babu lafiya, kullum sai yawan barci datakeyi, so gashi sai ramewa takeyi babu gaira babu sabar. Dr Al-ameen ya maida kallonsa kan Asma'u yana fad'in madam abinda oga yafad'a gskyane?. Fuska tad'an marairaice, Dr nifa nagaya masa k'alau nake amma yak'i yarda, babu inda yakemin ciwo saidai yawan barcin kawai. Murmushi Dr Al-ameen yayi batareda ya ce, ''komaiba. Rubutu yayi atakarda kafin yad'ago yana mata 'yan tambayoyi. Duk tana basa amsa yanda yakamata. Bayan yagama tambayarta ya ce, "ga bayinan tashiga tayo masa fitsari a wata 'yar kwalba daya mik'a mata. Kar6a yayi jiki a sanyaye Dan itama tafara zargin Kodai batada lafyarne da gsk?. Mintuna kad'an tadawo, Dr Al-ameen ya kar6a sanan yay kiran Norse Hafsat. Saida ta gaisheahi sanan yamik'a mata kwalbar, sister plz ina buk'atar result dangane da fitsarinan yanzu. Rissinawa tayi takar6a tana fad'in okey sir. Sunanan zaune a office d'in, marasa lafiya suka cigaba da shigowa Dr Al'Ameen yana dubasu. Bayan kamar minti talatin saiga sister Hafsat da takarda ahannunta. Rissinawa tayi tabama Dr Al-ameen sanan tafice. Kallon farko da Dr Al-ameen yayma takardar fuskarsa ta Nuna alamar farinci. Yad'ago yana kallon ya Umar da Asma'u. Alhaji Umar congratulations, madam tana d'aukeda babbar k'yautane. Doctor kana nufin matata tanada ciki kenan?. Hakane Alhaji Umar, ALLAH ya inganta. Ya Umar yad'aga hannu sama yana muk'a godiyarsa ga ubangijin talikai. Asma'u kam mamakine yakamata, dama haka akeyin cikin salin alin? Itafa wlhy ko ciwonkai bataji, babu wani wuri dake mata ciwo, saidai kawai kasala da barcin datakeyi yanzu babuji babu gaini........ Ya Umarne ya rungumeta yana fad'in Alhamdllh, wanan yasaka Asma'u dawowa hayyacinta. Har k'yautar agogo mai masifar k'yau na azurfa ya Umar yayma Doctor, agogo ahannunsa yake amma yacire yabashi. Ya Umar ya ce, "amma Doctor kofa laulayinnan namasu ciki batayi, saidai barcin kawai, da rama?." 'Yar dariya Dr Al-ameen yayi, karka damu wanan bawata matsala bane, kowacce mace akwai salon cikinta. Wasu zakaga sun farane da amai, wasu kwad'ayi, wasu ciwon ciki, wasu zazza6i, wasu basason abinci, yanayin kala-kala yake zomisu, wasukuwa kamar na madam d'inkane babu ciwo komai, watama saitaje watan haihuwa ko irin ciki yakai wata biyar d'inan sanan take fara laulayi. Jin jina kai ya Umar yayi Alamar gamsuwa, magunguna yarubuta musu da Asma'un yakamata tad'an fara amfani dasu Dan inganta lafiyarta da jaririn cikinta. sukai masa godiya sanan suka tafi. Daka kalli fuskar ya Umar Kasan yanacikin farinciki, yanason yara amma aka rabashi da nasa, ALLAH gafurun rahimun gashinan ya azurtashi da samun wani. Itadai Asma'u tayi shiru, dukda tana cikin matuk'ar farinciki itama zata zama uwa, amma tana fargabar ranar haihuwa Dan ance akwai wahala.... Ganin sun tsaya k'ofar gidansu tad'ago da sauri tana kallon ya Umar. gira yad'aga mata yana biyan mai adaidaita kud'insa. Hannunta yakama suka nufi cikin gidan, itama fuskarta d'aukeda farincikin ganin innarta da abbanta. Kwace hannunta tayi zata shek'a da gudu, da Sauri ya Umar yarik'eta, k" tsaya karkimin ganganci mana, tsayawa tayi saboda rik'e hannunta dayayi, ya harareta kinmanta da abinda ke jikinkine?. Bakinta tad'an turo gaba amma batace komaiba. Jan hannunta yayi suka k'ara cikin gidan. Afalo suka tadda fatee da Hasiya suna yankan d'inki, sunajin sallamar Su Asma'u suka tashi suna ihun murna, rungume juna sukayi, ya Umar yazauna yana murmushi. Ihunsune yafito da inna daga d'akinta, tana fad'i kai lafiyarku kuwa kuke mana ihu haka?. Asma'u tana ganin inna tasaki su fatee tanufi inna ta rungume. Wai! Asma'u zaki karyani aii. A'a innata, INA murnar ganinkine. Itama saita rungumeta tana fad'in sannunku da zuwa to. Ya Umar ya ce, "inna barka da fitowa." Barka kadai Umaru, wannan rigimammar tahanani zama. Dariya yayi shima, inna ai tana murnar ganinkune, kwana nawa bata gankuba?. Da sauri Asma'u ta ce, "wata bakwai kenan rabona da gidannan, tundafa nayi aure saud'aya nata6a zuwa saikuma yau." ‘tak'are maganar tamkar zatayi kuka.’ Hasiya da fatee kam dariya suke mata, inna ma saida ta dara, ta ce, "umaru kana fama wlhy." Murmushi yayi, yana sunkiyar dakai k'asa. Asma'u da fatee da Asiya kam tuni sun shige d'aki, kira inna ta kwalama fatee tafito, inna gani. O yau Dan kunga Asma'u shine ko ruwama bazaku kawoma yayankuba. La'ila wlhy inna na mantane, da sauri tafita saigata da ruwa harma da zo6o da abinci. Ya Umar yafad'ama inna abin farincikin daya samesu. Yana maganarne kansa ak'asa. Dariya inna tayi Dan ganin yanda ya Umar yamaida ita surukarsa yau. To Umaru ALLAH ya inganta. Ameen yafad'a a la66ansa. Hirarsu suka cigaba dayi shida inna, dukda dai yaud'in akwai 'Yar kunya tsakani. Itama Asma'u tanacan itada k'annenta. Sunkai wajen awa hud'u agidan sanan suka tafi, Asma'u nata zum6ura baki ita bayanzu zata tafiba. Ya Umar bai kulataba suka tafi, daga nan sai gidan mama. Tarba sosai mama tamusu wadda tayi matuk'ar bama ya Umar mamaki, amma saiya danne mamakinsa yasaki jiki da ita sosai kodan Asma'u. Itama yafad'a mata Asma'u nada ciki. Rungumeta mama tayi tana saka mata albarka, duk mugun halin mama nason kud'i tana k'yaunar jikokinta, sosai ta nuna farincikinta, suma Rafi'a da Mufida sunyi matuk'ar farincikin ganinta, nanko sukaita shan hirarsu. Anan Umar yabarta sai bayan isha'i yadawo suka koma gida. ____________________ Bayan wasu satittika. Abubuwa nata tafiya yanda yakamata, Asma'u tanata rainon cikin dabatajin kamar akwaishi, har yanzu tana nan da barcin tsiyarta. Ya Umar ma yana bata kulawa ta musamman, jiyake da ita aynun, komai takeso shine daidai. Ana haka matar Muktar ta haihu, sosai akasha hidima, ya Umar yataka rawar gani, hakama su Asma'u sune amarori. Taro yatashi lafiya, Asma'u tacigaba da rainon cikinta. Wata ranar laraba da safe Anty Sa'a tazo dakanta takawoma Asma'u alk'awarinta. Bayani tamata sosai yanda zata fahimta, amma ta ce, "kada tasha sai nan gaba cikinta yayi kwari. Godiya sosai Asma'u tamata. Anan takusan yini, sai gabda azuhur tatafi gida. Angama komai danganeda mall d'in ya Umar, kuma kayan dasukayi oda sun iso, komai anzuba awajen, yakoma tamkar yanda yake ada, dukda dai kayan basu cikaba tamkar da d'in. Amma kokad'an ya Umar baya zuwa wajen da rana ballema wani yagansa, muktar da Harris da Sadam ne ke kula da wajen, shikuma Yakoma zaman shago kamar da. Harris ma bai fad'ama kowa ya Umar ya bud'e mall nasaba, yadai Sanar da iyayen nasa yasamu aiki a tsohon gurin ya Umar, wad'anda suka sayi wajenne suka d'aukeshi aiki. Bikin Mufida nata matsowa, kullum mama tana zuba idanu taga ya Umar yakawo mata kud'i, amma saitaji shiru wai malam yaci shirwa. Tunda tana kawaicin jira har ranar ta tambayesa maganar kud'in. Murmushi yayi kamar yanda yasaba, muryarsa a tausashe ya ce, "mama har yanzu basu baniba, amma kitayani da addu'a ALLAH ya kwato min......" Da sauri tad'aga masa hannu, cikin masifa ta ce, " kai sauraramin! Nizaka madai sakarai Umaru!? Shin wane shegene zai sayi Abu ya hanaka kud'inka?. Nafa lura yanzu kaima ka canja, harma gara Abubakar d'in dakai. Kud'i karik'e karka bada, ALLAH bazai hanamu yanda zamuyiba, nitashi kabani guri shashasha kawai. Anutse ya Umar yatashi yafita batareda yace da ita komaiba. Yana fita wayarsa tafara wringing............ _kuyi hak'uri da wanan._ *_(((S))).......2017_* *_Love you all_* [12/27/2017, 3:16 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_Mutuwa! mutuwa!! Mutuwa!!!. Mutuwa maiban tsoro, batabarin kod'an yaro, ko jinjiri saita d'auka, takaishi koda bayaso mak'abarta. Sarki ALLAH jallah, Jallah nidai natuba ALLAH, rabban kayafemu albarkacin manzo nawa d'an gata._* _wannan wak'a gsky Ce, kuma tana ta6amin zuciya aduk lokacin Dana tunata wlhy._ 😭😭😭 *_page→55-56_* ..........A kasalance yad'aga, dan wringing d'in wayar bak'aramin fad'uwar gaba yasashiba. Komiye dalili oho. Asslamu alaikum, yayi maganar cikin sanyi. Daga can yazeed ya amsa masa shima muryarsa a raunane, yad'ora da fad'in abokina kakalli labarai kuwa?. Yanzuma a sanyaye ya Umar ya amsa masa da a'a abokina, amma miya faru?. Jimmm yazeed yayi, zuwa can kuma ya sauke ajiyar zuciya, Umar sirikinkane sukayi had'arin jirgi yanzunan babu dad'ewa. Da Sauri ya Umar ya dafe k'irji, cikin matuk'ar razana ya ce, "kana nufin dady mahaifin lubna!!!?. Eh Umar, idan kana kusada TV ka kalla gashinan suna nunawa........ Bai bari yazeed yagama fad'aba yajuya cikin gidansu arazane. Mama tana zaune har yanzu tana mita da zagin ya Umar saitaga yashigo aburkice, baibi takantaba yanufi TV ya kunna, NTA yakamo, ilai kuwa abinda suke nunawa kenan, had'arin yafarune a hanyarsu ta zuwa legos daga nan kano. Mama ma sai jikinta yayi sanyi tatsaya sagare tana kallo. Bak'aramar tarwatsewa jirgin yayiba, ga mutanenan kwance, wasuma Kansu yacire, wasu k'afa, wasu hannu, wasuma babu ta yanda za'a shaidasu dan duk sun canja kamanni. d'aya bayan d'aya akebi ana nunasu dan ana kwashe gawawwakinne da duba masu rai, dukda babu alamun akwai wani mahaluki dake numfashi acikinsu. gawar mahaifinsu lubna aka nuno, cikin amincin ALLAH shikam kamanninsa na nan, saidai jini dukya 6atashi, sannan hannunsa d'aya yafita. Ya Umar yaruntse idonsa hawaye na kwarara, mama kanta kuka takeyi, (bak'aramin abune yake raunana jarumtar gwarzo namiji irin ya Umar ba) zuciyarsa da kwakwalwarsa suka Shiga tuno masa waye dady?, mutumin kirki maison talaka da son k'yautata masa, ya tuno ranar daya fara ganinsa shida direbansa, alkairin daya masa ya d'aga darajarsa fiyema da 'ya'yan cikinsa, wasu zafafan hawaye suka k'arayo ambaliya akumatunsa. Mamace tayi k'arfin halin kama hannunsa ta zaunar akujera, a hankali take shafa kansa tana lallashinsa, ita kanta tasan miye matsayin dady azuciyar ya Umar, kosu sukace sun manta da halaccinsa akan d'ansu sunyi butulci ba k'aramiba. Lallashin ya Umar takeyi sosai Wanda yake kuka harda shashshrka, kansa yana saman cinyar mama.....Umaru yanzu ba kuka yake buk'ataba, yana buk'atar addu'a ne daga garemu, babu abinda zamu sakanka masa dashi aduniyarnan inba addu'aba, Wanda ya haliccesa shine ya kar6i abinsa, muma nan duk irin wannan ranar muke jira Umaru...... Da ire-iren wad'annan maganganun ta kwantar masa da hankali. Ahankali yafara sassauta kuka nasa saidai ajiyar zuciya, haka su Rafi'a suka dawo daga gidan inna suka samesu. Suma sungani agidan inna dan haka basa buk'atar k'arin bayani, saidai ya Umar yabasu tausayi ainun. Baibar gidanba saida aka kira sallar magriba. Atsakar gida yatarar da Asma'u zaune saman kujera 'Yar tsugunno. Ta rabga tagumi. Ko motsin shigowarsa batajiba barema sallamarsa, shima bashida k'arfin mata magana, saikawai yajingina da bango yazuba mata idanu tamkar mai nazarin wani abu. Sunkai minti20 ahaka sanan ALLAH yabama Asma'u ikon d'agowa danjin kamar alamar mutum tsaye akanta. Tarazana sosai, dan haka tayi shirin takewa da gudu, muryarsa a sanyaye ya ce, "Asma'u ninefa." Gabantane yay azabar fad'uwa danjin muryar ya Umar dakuma sunan daya kirata dashi, Wanda zata iya rantsewa bata ta6ajin sunan abakinsaba sai yau. Ya Fharuk lfy kuwa?. Ajiyar zuciya ya sauke wadda yayita sau babu adadi, muryarsa hard'an rawa takeyi ya ce, "dadai sauk'i Husna." Shiru tayi tana nazarinsa, saikuma yabata tausayi, gashi sunyi azumi, takama hannunsa suka shiga ciki. A babban falo ta zaunar dashi bisa tabarmar data shirya kayan shanruwan. Baice mata komaiba, tazuba zo6o mai sanyi tamik'a masa, kai ya girgiza mata alamar a'a ya k'oshi. Tuni idanunta suncika tab da kwalla, ganin haka sai kawai ya kar6a ya shaya kusan rabi, daganan yajingina da bango yay shiru. Itama Asma'u shiru tayi, tasan bak'aramin abune yata6a zuciyar mijin nataba. Haka sukaita zaman shiru har aka kira sallar isha'i. Bai iya fitama masallaciba yayi sallar agida. itamadai Asma'u tayi tata sallar. Har k'arfe kusan goma babu Wanda yazubama cikinsa komai. Cikin Asma'u ne yafara kiran Ciroman yunwa, dama 'yan kwanakinnan bata iya jure zama da yunwa saboda cikinta yafara girma, azuminma dak'yar take kaishi aduk ranar litinin da alhamis dasukeyi yanzu. Zamewa tayi ta kwanta akan abin sallar, ya Umar yabita da kallo saita bashi tausayi daya tuna bafa ita kad'ai baceba, gakuma azumi dasukayi. Tasowa yayi daga inda yake zaune yadawo kusada ita, ya had'a shayi mai kauri akofi, yazuba soyayyen dankali afilet da kwai (dan yanzu alhamdulillahi, basuda Matsala a a6angaren abinci. Ko abayama dasuka Shiga halin ha ula'i suna samu suci koda baikai yanda suke soba). batareda yamata maganaba yakamata yatayar zaune, jinginata yayi da jikinsa sannan yad'akko kofin shayin daketa turiri kad'an-kad'an yakai bakinta. Kauda kanta tayi gefe alamar bazata shaba. Bayason yawan magana yanzun amma yakula saita sakashi yayi akan dole. muryarsa asanyaye ya ce, "kidaure koda shayinne kisha mana, kinga bake kad'ai baceba. Itama idanunta tad'ago tana kallonsa, yaya Indai kanaso naci to saidai muci tare. Ahankali ya girgiza mata kansa alamar shi ya k'oshi. Itama saita kauda NATA kan ta ce, " Nima nak'oshi, tayunk'ura zata tashi daga jikinsa. K'ara rik'eta yayi dak'yau dukda jikinsa babu kwari, kinga to zauna zanci. Babu musu tazauna da k'yau, yana bata tana bashi harsuka d'anci babu laifi. Asma'u tagyara wajen tsaf, lokacin data dawo yashiga d'akinsa, itama saita wuce NATA d'akin cikeda tunanin mike damun ya Umar ne?. Saida tayi wanka tai shirin barci, zaman jiransa ta zaunayi, ganin lokaci yanata tafiya kuma ko alamarsa babu yasakata mik'ewa takashe komai tafice, tasaba kwanciya ajikin ya Umar dan haka bazata iya barciba ayanzu idan baya a kusada ita. d'akin tatura tashiga da sallama, turus tayi dan ganin ya Umar kwance bisa katifa a yanda yashigo, ko Riga bai cireba barema asaran yayi wanka. Jikinta asanyaye tak'arasa gareshi, jin motsinta da k'amshin turarenta yasakashi tashi zaune. Idanu yakafa mata kamar mai hango wani Abu, tazo ta zauna ajikinsa tana tambayarsa abinda ke damunsa. Awanan karon bai 6oye mataba yafad'a mata komai. Itama har kuka tayi dukda bawani saninsa tayiba sosai, ranar ma dasukazo da family d'insane har ya Umar yamari Lubna, aranar tafara ganinsa. tundaga ranar kuma bata kuma ganinsaba. Daga k'arshe sai ya Umar ne Yakoma lallashinta. Ta ce, "ALLAH yajik'ansu yagafarta musu ya yafe musu. Ameen ya Umar yafad'a yana kuma rungumeta da k'yau........ _____________________ Washe gari yazeed yazo sukaje gaisuwa shida abbansu dakuma baban Asma'u, da muktar, Harris, Sadam. Sun sami gidan cike da al'uma kala-kala, dan yaune ake jana'izarsa, sarakuna, 'yan siyasa, 'yan kasuwa, masu madafun iko a gwamnati, harda mutane daga k'asashe daban-daban. Dan shi d'an kasuwa babu inda babushi, musammanma irinsu dady dasuka zama manya dolene adama dasu ako ina. Suma su ya Umar anyi jana'izarsa dasu, sai yamma lik'is suka sami damar ganinsu safwan, sannan mutane sunragu sosai. Har cikin gidan akai musu iso sukayi gaisuwa, saidai su ya Umar basuga Lubna ba. Amma ya hango 'yan biyu ajikin momynsu Lubna d'in. Ko magana basuyi masaba dan ayanzukam summa manta dashi. Shima baice dasu komaiba tunda ana cikin rud'anine. Kwana uku suka jera suna zuwa kullum. Sai'a rana ta k'arshene ya Umar yaga Lubna tsaye aharabar gidan tayo rakkiyar wasu 'yan uwansu dazasu tafi. Sanye take da dogon hijjabi mai hannu haryana Jan k'asa, balaifi tarame sosai dan mutuwar tarazanasu ainun, tanata jan carbi. Suna had'a ido da ya Umar gabanta yafad'i, shima kansa saida yaji wani Abu. d'auke kanta tayi daga garesu, tamaida hankali wajen yin sallama da 'yan uwan nasu dasuka shiga mota. Saida motocinsu suka fice sannan tajuya zasu koma itada Suhaima, da Jiddah matar Ameer. Yazeed ne yay k'arfin halin kiran lubna d'in. Tatsaya cak itasu Suhaiman, amma babu Wanda yajuyo acikinsu saidai Jiddah. Su yazeed basu damuba, dan yauma subiyune kawai, dagashi sai ya Umar. K'arasawa sukayi inda suke. su ya Umar suka gaishesu tundasu sungaza gaisheau. Jiddah ce kawai ta amsa da arzik'i, amma Suhaima da Lubna sai wani yatsine-yatsine sukeyi. Sudai su ya Umar basuwani biye musuba sukai musu gaisuwa. Fuuu suka shige ciki, jiddah kuma tatsaya ta amsa musu harda musu godiya da fad'in ALLAH yabada ladah. Haka sukabar gidan, tsakanin ya Umar da yazeed babu maicewa uffan. Har k'ofar gidan yazeed ya sauke ya Umar, sukayi sallama. Yazeed ya ce, "yakamata kashirya gobe idan ALLAH ya kaimu muje wajen saida motoci Umar. Baikamataba ace kacigaba dayawo hakaba. d'an murmushi ya Umar yayi, karka damu yazeed kasan abinda yasa kaga inata zamewa gameda sayen motarnan, kayi hak'uri na kwantar dawata k'ura sannan, kasan babu Wanda yasan halin da ake ciki har yanzu. Hakane kuma, namaka uzuri, ALLAH yakaimu lokacin, ubangiji yagyara mana komai cikin hikimarsa da ikonsa. To ameen ngd sosai abokina, ka gaidamin madam da yara. Zasuji insha ALLAHU, Nima ka gaidamin madam. Sallama sukayi yazeed yaja mota yatafi, shikuma yashiga cikin gidan. Asma'u na kichin tana k'ok'arin had'a kayan bud'a baki. Jin motsinta akichin shima saiya nufi can. yad'an zaro idanu waje dan ganin tana cin k'osan datake soyawa, madam ina azumin?. Hannu tasa tarufe fuskarta tana murmushi, ALLAH yaya na karya, jinayi bazan iyaba, ga cikina yanata juyamin. d'an murmushi yayi, dan yau babu laifi yad'an saki jikinsa, sa6anin kwana biyu dasuka wuce bashida walwala ko kad'an. Yakuma matsowa kusada ita yana fad'in lallai kinzama ragguwa to. Yaushe kika karya?. ALLAH yaya ba ragwantaka baceba, tun sandasu Rafi'a sukazo. Sune suka sakaki kika karya kenan?. Idanu tazaro lah bafa subane wlhy, kayarda dani ALLAH. na yarda dake, cigaba da aikinki to, k'osan zai k'one. Da sauri takoma kan aikinta tafara kwashewa danya soyu. Yaukam babu laifi bayan shanruwa ya Umar yazauna sunyi hira, acikin hirar tasunema yakecewa tadakata da azumin tahuta hakanan. Ta ce, "aii zata iya, yau d'inma dan and'anyi ranane. A'a kibarshi haka, dama inada niyyar tsaidaki saboda babyna baya samun isashshen abinci awajenki. Hannu tasa tarufe fuska tana fad'in kai yaya. Dariya yayi yana kwanto da kansa bisa cinyarta tareda tura hannunsa arigarta yana shafa d'an matashin cikin NATA dayayi d'as ajikinta, ya ce, " my baby ALLAH yakawoka, ko yakawoki duniya lafiya. Kullun mafarkin isowarka nakeyi. Asma'u dai shiru tayi tana kallonsa yanda yake magana da ciki tamkar maiyi da mutum............ _kunjini shiru. Babana ne babu lafiya wlhy, amma Alhmdllh jikin da sauk'i, muna buk'atar addu'oinku plss._🙏🏻 *_(((S))).......2017_* *_I Love you all_* [12/27/2017, 4:01 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→57-58_* ..........Bikin Mufida ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro. Ya Umar dai baice dasu komaiba, ko kwayar shinkafa baikai gidanba, dukda mama tamasa magana. Cemata yayi baida kud'i, kuma ba yaya Abubakar duk yace zaiyibane?. Shiru tayi dantasan inda maganar tasa tadosa. Har ana gobe d'aurin aure babu wani abin arzik'i daya sauka gidan. Babu kayan miya bare nama kokuma wanidai Abu daya danganci abinci har hud'u na yamma kuwa. Ana nan zaune jigum-jigum. Kowadai yasan al'adar makwafta da danginka nakusa sukan shigo domin rage aiki ana gobe d'aurin aure. Gakuma gida cike damk'an da dangi na nesa wad'anda tun ajiya suka fara sauka gidan. Ana nan zaune jigum-jigum kowa yana raba idanu yaga ta inda abinda ake jiran zai 6ullo. Cikin amincin ALLAH saiga yi anfara shigowa da kayan gado na Mufida. Nan take kallo yakoma sama, mamaki al'ajabi yacika mutane, kayan gadone irinna da-da d'innan, kuma kallo d'aya zaka musu kagane tsofaffine akaima kwaskwarima kawai. abin mamakin baigama k'arewaba saida aka dire rabin kwandon tumatur, da attarugu da tattasai acikin yellow d'in leda mai layi-layi, sai alayyahu buhu guda maicin arba'in🙊. Saikuma ga garin tuwon dabai wuce kwano ashirinba, gefe kuma da shinkafa 'Yar Hausa mai tsakkuwar tsiyarnan dabata wuce kwano ashirinba itama. Kowa yayi cirko-cirko yana kallon ikon ALLAH, Saiga ya Abubakar yashigo saiwani bud'awa yakeyi yana washe hakwara, shi a adole yayi abin arzik'i yau. Sai gaida mutane yakeyi washeda baki, amma ganin kallon dasuke masa saikuma jikinsa yayi d'an sanyi. Yakai dubansa kan mama da inna, sumadai kallonsa sukeyi cikeda mamaki, amma a can k'an zuciyar inna tana fad'in ALLAH ya k'ara. Inda suke yak'araso, har yanzu bakinsa awashe yake, dukda jikinsa yayi la'asar. Mama inna! gafa kayannan sun iso, kunata kirana mutane suna jira sufara aiki ko?, wlhy inacikin kasuwa nayi matuk'ar busy, gashi dak'yar nasami motar data d'akko yakayan gadonnan, kiranma dakukemin yasakani azamar tahowa, kaji na nan za'a kawo guda Biyar manya-manyanema wlhy. Inadai fata komai zai wadatar da kowa?, kuzo kuduba kayan gadonma, kafintan ya iya aiki wlh........... Hannu mama tayi saurin d'aga masa dan surutunsa yafara addabar kunnenta. Hawaye suka zubo bisa kumatunta, cikin shashshekar kuka ta ce, "Amma Abubakar kaji haushin rayuwarka, kaje, nidai kawulak'anta ko? babu komai ngd. ALLAH sarki Umaru ALLAH yayi maka albarka. Basai mutum yamutuba ake tuna alkairinsa. Dama duk Wanda yagaza godema ALLAH na tabbata zai godema azabarsa. Banga laifinkaba abubakar saidai nawa, yau ga abinda halina ya jazamin, ALLAH kamin ni'ima maimakon nagodemaka saina butulce, ya ALLAH ka gafarceni, natuba ALLAH, wlhy natuba. BakI ya Abubakar yata6e waike mama miya kawo wad'annan surutan ne haka?. Ubankane yakawosu matsiyaci kawai....... Bata k'arasaba inna ta to she mata Baki tareda janyeta suka koma baya saboda idon mutane, ya Abubakar baifasa bin bayansuba. Shima ya Umar saiya biyo bayan ya Abubakar dan shigowarsa gidan kenan shima, amma yaga dukkanin kayan dake zube a tsakar gidan, harma yayi gamo damai kawo kaji ak'ofar gidan. Lafiya kuwa inna? Maganar ya Umar tadaki kunnuwansu. Atare suka d'ago suna kallonsa, mama tasake fashewa da kuka tana koroma ya Umar bayani dalla-dallah. Shiru yayi yana saurarenta, tausayinta yacikama masa ciki, kafin ya ce, " wani abu saiga Abba yashigo shima afusace. Ganindai komai zai kwa6e agaban mutane inna ta ce, ''sushiga d'akin Abba. Zaune suke suduka a falon Abba, wannnan karon harda Harris da mufida da Rafi'a. Inna ce tayi magana duk tana bin kowannensu da kallo..... Ita gsky d'ayace, kuma daga k'inta said 6ata, lallai inamai jaddada muku Abubakar bashida wani laifi, laifinkune wanan, tunda tun farko kune kuka d'ora yarannan akan wannan mummunar tarbiyyar. Kuna Nuna banbanci akan 'ya'yanku saboda wane yanadashi, wane bashidashi. Kund'auki dukiya tamkar itace jigon rayuwa. Kudubafa halin da Umaru yashiga a watannin baya, amma acikinku babu Wanda yata6a waiwayarsa yasan yaya yaci, balle ya yaciyar da iyalinsa. Bak'aramin tashin hankali yaronnan yashigaba, badan mai tawakkali bane Aida yanzu an mance kamanninsa ko?. Amma maimakon kujawoshi jikinku, kuringa kwantar masa da hankali, saikukayi watsi da labarinsa kuka kama Abubakar mai kud'i kuka rik'e ko?. Wannan wace iriyar rayuwace haka?, aurenfa mufida aka saka agidanna amma Umaru baison komaiba akai saboda son zuciya irin naku. Kuji tsoron had'uwarku da ALLAH mana, kufa iyayene masu tarbiyyantarwa bamasu ruguzarwaba, ALLAH fa baya d'orama bawansa abinda bazai iyaba. Shin ku'a tunaninku kunada wata dabara ta gujema talauci kenan?. Hummm shidai Ubangiji aiba abokina wasan wani shege bane. Ai yanzu ba tsinar Abubakar zaku hauyiba, hak'uri zakuyi da abinda yakawo ayi bikin haka, arurruma akaita kowa yahuta...... A'a inna idan ya Abubakar zaibani rancen koda dubu d'ari biyarne sai ayi komai yanda suke buk'atar d'in...... Carab ya Abubakar ya kar6e zancen, a INA naga wata dubu d'ari Biyar in? Kokuwa kud'in kasuwata zan gird'e nabaka rance saboda kanaso ayi biki waje-waje?. Wlhy Umar kafita idona narufe, yanzu wannan siyayyar dakuke rainawa tawajen dubu d'aricefa. Ko kayan gadonnan hallidu kafinta a dubu arba'in da Biyar yayimini su babu Ragin ko sisi wlhy. Ince yanzudai inna tagama wa'azi akan rashin godiyar ALLAH ko?.... Ba godemakane ba a yiba ya Abubakar, kawaidai INA buk'atar rancenne. To banidashi d'an jonin masifa, kaid'in baca akayi ka saida mall d'inkaba? Ina kakai kud'in? In ba neman alagidigo da hankalin mutaneba kakeyi?. Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, ya marairaice murya, (amma a can k'asan zuciyarsa dariyace ke bal'in cinsa, daurewa kawai yayi ya gimtseta) ya Abubakar bawai inayin Alagidigo da hankalinku baneba, har yanzu wad'anda suka sayi wajennan basu bani kud'in baneba. Amma munyi alk'awarin nanda wata shida zasu bani adunk'ule, dan banason kud'i gutsin-gutsin......... Kai dallah sauraramin, wlhy Umar kafita sabgata nasha iska, inbanda raini taya zanyi nad'auki dukiyata nabaka har tsawon wata shida, nikuma nazauna fanko, saboda inajin tsoronka, angaya maka nid'in sallamammene ko shashasha?........ Mamace tak'atse musu zance cikin raunin murya, kabarsa Umaru Shiba sallamamme baneba, nasan babu yanda za'ayi nunkufurci irinna Abubakar yabarsa baka bashi.....kuka yahanata k'arasawa. Abbah dai yayi shiru, dan tsorone fal ransa, idanfa Umar baisamu kud'innanba dolene shizai nemosu, tundadai mufida diyar cikinsace, atsarima shiya halatta yayimata kayan d'akin. Wani haushin Abubakarne ya kuma tunik'e zuciyarsa. Agefe kuma dariya na cin zuciyar inna da Harris, dan sunsan ya Umar yanayin pretending ne kawai. Rafi'a da mufida kam sai ballama ya Abubakar harara sukeyi, karma mufida taji labari, dan zuciyarta akuntace take, wai itace za'akai gidan miji da kayan gado nawajen halladu kafinta?. Ita bamatasan yanda ya Abubakar ya tsanetaba. Tafashe dakuka Wanda yadawo da hankalin kowa akanta, cikin kuka ta ce, "Abba aidai kai kanada kud'in yimini, kowadai yasan halin da ya Umar yake aciki? Inhar ba'a tausaya masaba to ai ba'a tsine masaba. Niko wlhy Indai kayan wajen halladu kafinta za'a kaini dashi to na hak'ura da auren, ta tashi fuuuuu tafita tana kuka. Babu wanda ya iya cewa komai, daga nan ma suma taron ya watse. Ya Umar ma gidansa yakoma yay kwanciyarsa, dama kansa namasa ciwo. Asma'u kam tana gidan bikin, bama tasan wainar da'ake toyawaba. Sudai makwafta suka hau gyara abinda yasamu, masu gulma nayi masu tu'ajjibi nayi, harda masu dariyar mugunta dan kowa yasan mugun halin mama a anguwar. Zuwa bayan isha'i aka kammala miyar dataji uban alayyahu ko kayan miyar ba'a gani saboda yawan alayyahun. Tun adaren aka kusa shanye rabin miyar ma, mama tamkar tayi hauka dan bak'in ciki, tarasa inda zata tsoma kanta taji sanyi, gashi batada ko sisi, dan bata ta6a tunani ajiye wasu kud'iba saboda aurennan, tasaki jiki komai Abubakar zaiyi. Abba madai hankalinsa atashe yake, dukda shida yanada 'yan kud'insa amma mak'o da ganin k'yashi yahanashi fiddosu afita kunya. Adaren mama da inna sunkira ya Umar yafi sau hamshin-hamsin amma yak'i yad'aga, hakama Abba yakirashi yafi ak'irga amma bai d'agaba. Hankalinsu dukya tashi, musamman ma inna. Ita duk zatonta ya Umar yayi pretending ne, fitar dayayi zaije yayo sayayyane, amma har shad'ayan dare babushi babu alamarsa. Ya Umar kam yana kwance agidansa, kuma duk kiran dasuka masa yana kallo ya sharesu. Duk kiran daya shigo saiyayi murmushi sannan ya ce, "inna mama Abba kufayi hak'u wannan ba Umar d'in dakuka Sani bane, na yanzu ya canja, yasan dad'in dukiya shima, ni babu abinda zan muku, koma wajen d'aurin auren babu mai ganina. Wannan zai zamemuku izina aii. Inna ki gafarceni wannan karon kema bazan saurarekiba. Dayagaji dajin wringing d'in wayar saikawai yamaida wayar salient........ *_washe gari_* Har kusan 11 babu wani canji agidan, mutane sun sami abun tsogumi sai gulma sukeyi, harda cikin 'yan uwan mama danasu inna. Zuwa yanzu mama tayi lak'e-lak'e, tayi kuka da nadama har babu iyaka, tasandai yau kunya zasu shatane bata wasaba kam. Amaryama kuka takeyi rurus, ko wanka tak'i yarda tayima, ta tubure akan tafasa aurenma gaba d'aya, anyi lallashin duniya tak'i sauraren kowa. Har shabiyu babu wani bayani, gidakam haryama fara d'inkewa da mutane, wasuma badan ALLAH sukazoba, sunzo ganin kwakwafne tunda tun ajiya labari yafara zaga anguwar. Mutane na tsaye tsirko-cirko akan mama data suma. Dan tashin hankali, ko abincin daza'aci agidan babu to, d'an Wanda Ya Abubakar yakawo ana gama dafawa tun'a gindin murhu mutane suka kwasheshi. Wannan 6acin ran yasaka mama zubewa. Ana cikin haka sai akaji k'ugin motoci ak'ofar gida. Kafin mutane suyi wani yunk'uri anfara shigowa da manya-manyan kuloli na abinci. gefe kuma ana shigiwa da kayan gado na gani na fad'a. Ai sai mama ta tashi tashiga jerin 'yan kallo. Saida aka shigo da kula kusan d'ari ta abinci, gakuma kayan gado na nunawa a sa'a, saikuma ga kayan kichin suma akwalayensu. Inna dai data kasa hak'uri saida tamatsa tana tambayarsu waya aikosu?............ Kuyi manage da wannan. *_(((S)))........2017_* *_I Love you all_* [12/28/2017, 6:35 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→59-60_* ..........Kai daga ina? Waya aikoku kuma?. Wani a cikin masu sauke kwalayen ya ce, "Alhaji Umar ne. Kowa baki ya hangame sama dan mamaki, tuni fuskar mama da inna ta washe, mama kukan farinciki takeyi sa6anin da datakeyin na bak'inciki. Sunan tsaitsaye tamkar an dasasu saiga ya Umar yashigo, sanye yake cikin kananun kaya, yayi k'yau sosai, kwarjininsa da k'yawun haibarsa sunk'ara bayyana saboda gyaran fuska dayayi. Mama tak'araso da sauri ta rungume ya Umar. Shima dai yau ya kar6i Maman tasa 100%, kukan dad'i takeyi, haka shimad'in hawayene kebin kumatunsa. Innace tamusu magana sannan suka koma ciki. Acan k'uryar d'akin Abba ya Umar ya ce, " mama inna dan ALLAH kugafarceni saboda rashin d'aukar wayarku danayi jiya. Wlhy mun yafe maka, mun yafe maka umaru, mamace take maganar a cikin kuka. Inna ma ta ce, "tayafe masa." Ana haka Abba ya iskesu a d'akin, cike da farinciki ya rungume ya Umar. albarkadai yashata har babu adadi. Daga nan hidimar biki tacigaba da gudana cikin farin ciki, bakin mak'iya, masu gulma da dariya kuma anrufeshi ruf🤐. Mufida kam jitayi aduk duniya batada kamar ya Umar. And'aura aure da k'arfe 2:30pm. Ango yayi shar dashi, sai washe baki yakeyi yana gaisawa da jama'a. Hakama amarya mufida a cikin gida, tayi k'yau harta gaji, dangi da k'awaye suna zagaye da ita. Mama da inna ma dai suna cikin farin ciki mara musali. Hakama Abba ba'a barsa abayaba, shima yau ya aurar da d'iyar farko a cikin 'ya'yansa. Ya Abubakar kam bak'aramar k'ullatar ya Umar yayi ba, ko'a awajen d'aurin aure da sun had'a ido saiya d'auke kansa. Shidai ya Umar saidai yayi murmushi kawai. Zuwa yamma taro yarage na mata a cikin gida. Can na hango muku Asma'u itama taci kwalliyarta cikin wani ubansun less pink da ratsin milk, bak'aramin k'yau tayiba gsky, tana tareda matar yazeed da Anty Saddiqa matar muktar. Zuwa dare aka mik'a amarya d'akinta dayasha Jere da su Anty sa'a da Anty Saratu, saikuma wasu a cikin danginsu na uwa dana uba dasuka biyosu, tun wajen k'arfe d'aya akayi, dukda dai sai yamma lik'is suka gama, ko d'aurin auren basu halartaba. 6angaren abinci kuwa babu Matsala, anci har an barsa, komai ya wadatar da jama'a, dan abincine kala-kala aka kawo, tundaga jalof d'in shinkafa, fankasu, waina, tuwo, gurasa, alala, kai komaidai yawadata, ga ruwa shima, hakama lemuka kowa yasha iya gwargwadon iko. Bayan ankai amarya akace sushirya za'a dinner da abokan Ango suka shirya. Su Asma'u anata shiri saitaji wayarta na wringing, d'agawa tayi da hanzari dan ganin ya Umar. Ko amsa sallamarta baiyiba ya ce, "kin shirya?." Eh, tafad'a cikin rawar kai. Cikin dariyar mugunta ya Umar ya ce, "kisameni awaje to." Aida hanzarinta ta kammala shirinta tafito. Waige-waige taketayi dason hangoshi. d'it-dit taji motar kusada ita ana mata horn. Kallon motar tayi saita hango ya Umar aciki. Idanu tad'an fiddo waje dan mamaki, ko'a ina yasamo mota?. Da wannan tunanin tak'arasa inda yake. Zagayo mana yafad'a tana bud'e mata k'ofar gefensa. Babu musu tazagaya ta Shiga ta zauna, wani k'amshin dad'i da sanyi suka ratsata, ta shak'a talumshe idanunta. Duk ya Umar yana kallonta, dariya kuma nacinsa azuciya, ga wani k'yau da kwalliyar tata tamasa. d'agowa tayi tana kallonsa, ya Fharuk wannan motarfa?. Gira yad'age sama yana kallonta da ido d'aya, ta aroce yafad'a cikin wani salon magana. Amma fa motar tahad'u wlhy cewar Asma'u tana shashshafa kujerun motar na baya. Saida yatada motar sannan ya ce, "kokinasone?." Asma'u tarik'e ha6arta, ya Fharuk rufamin asiri, inani ina Mota? Nida ko keke ban iyabama. 'Yar dariya yayi yana k'ara dafe sitiyari dan harsun fara tafiya. Kedai inhar kinaso kifad'a kawai?.. Tab indai maganar soce kam aii inaso, amma a ina zan samu? anan gizon ke sak'a aii. Murmushi yayi kawai batareda ya ce, "da ita k'alaba. Daga nan motar tayi shiru nawasu mintuna. Wani gurin hutawa yakaita, yasa aka kawo musu abubuwan motsa baki, itadai Asma'u cikawai takeyi, amma hankalinta nacan wajen dinner, kad'an-kad'an saita kalli agogon hannunta. Duk abinda takeyi idon ya Umar na kanta, amma saiya basar yanata danne-danne awayarsa. Candai Asma'u takasa daurewa, tad'ago tana kallon ya Umar daketa murmushi yana latsa waya, dan hotuna yaketa mata batareda tasaniba, wajen yak'awatune da hasken lantarki tamkar rana. Itafa dabadan kar ace ta zura k'aryaba dasai tace ba'a 9ja sukeba. Wajen babu hayaniyar, mutane ma d'ai-d'aine keta shawagi awajen, daka gansu kuma kasan masoyane, saidai asamu banbanci namasu aure da masu zuwa sa6on ALLAH. ya Fharuk tara saurafa?. batareda yad'agoba ya ce, "kingaji mutafi kenan?." Bawai nagaji baneba, amma nasan yanzu anfara dinner d'in. Fuskarsa yad'an yatsine, ad'age ya ce, "dinner kuma? A ina kenan?. Sosai tawaro idanunta waje, saikuma ta kwa6e fuska, kai ya Umar kafasan za'aje dinner, kuma nazatama ka d'akkonine dan mutafi. Kai! Shima yafad'a yanad'an zaro ido. Husna yaushe nacemiki wajen dinner zan kaikai? Nibammasan za'ayi dinner ba gsky. Shiru tayi masa dan tak'ulu sosai, jitake tamkar tamakeshi dan haushi. Dukda yakula dayanda tacika tayi fam dan haushi, saiya share, dariya yayi cikin zolaya ya ce, " dinner aii ta 'yammatace bawai cus irinkuba. Baiyi zatoba saiyaga hawaye sun gangaro akumatunta, wai ita ya Umar kekira da cus!. Tashi tayi zata bar wajen ya damk'o hannunta. Ta tirje tana fad'in nika sakeni, badai nice cus ba?. Ina bafa dake nakeba, haba ma'una sorry yeee. Yafad'a yana jawota tafad'o saman cinyarsa, dukda mutsu-mutsun kwacewa datakeyi amma takasa, yaymata k'yak'yk'yawan rik'o, ganin zata tara masa mutane saikawai yafara💋 d'inta. Muk'us kakeji Asma'u tayi shiru. Dasalon soyayarsa da wayo irin nasa ya lalla6ata tahak'ura da zuwa dinner d'in. Dama bayaso taje shiyyasa yaje ya d'akkota. Sai wajen goma suka bar wajen. Gida suka nufa, amma tun amota Asma'u tayi barci. Koda suka isa gida saiya d'auketa cak yashiga da ita ciki. Tayi matuk'ar gajiyane, dan duk yau batayi barciba, rabonta dashi tunna dare, tundaga sallar asuba batasake komawaba. Da kansa yacanja mata kayanta zuwa nabarci, yayi mamakin dabata farkaba, dan yasan Asma'u batada nauyin barci. dukda yanatareda uzurinsa haka yahak'ura shima yay shirin barcin ya rungume matarsa suka lula duniyar barci.......... _______________________ A6angaren su Lubna kam an raba musu gadonsu, saboda matsawar dasu Safwan sukayi, ran momy ya6aci matuk'a, amma babu yanda zatayi tunda hak'k'insune. Tunda akayi addu'ar arba'in suka addabi kowa, dole aka raba kowa yad'auki kasonsa. Ba k'ananan kud'i da kaddarori suka samuba kuwa, dan mahaifinsu babu laifi yatara musu. Hummm tunda kowa yakwashi kasonsa saiya kama alk'ibilar data dace dashi kuwa. Babu Wanda yanemi Sana'a acikinsu kuwa. Dan basu iyaba, ba'a koya musuba, abinda suka Sani kawai shine sukashe kud'i komin yawansu, dasunzo dady zai basu wani. To yau babu dady, yatafi yabarsu cikin babban fili na gwagwarmaya, wato duniya. Basu Lubna ba kawaiba, hattada mama karenta takeci babu babbaka, sunkoma rayuwarsu tamkar da, kamarma babu abinda yata6a zuciyarsu abaya. Su Lubna kam aii likafa taci gaba itada Suhaima, murzar kud'insu sukeyi tamkar babu gobe. Sun sayi motoci na garari, hakama sitturu yanzu sai shigar dasuka gadama. To mom dake musu fad'a ada itama ayarta take shek'ewa ayanzu, tataka Wanda taso babu mai abin fad'a tunda tanada 'ya'yan banki masu magana da kowa. Maganar aurema babu ita a ajandar rayuwarsu, daga bin club sai bin k'awayen banza da boy friends masu tatsesu cikin dabara. Mom bata bincikar kowa akan dukiyarsa dan acewarta hankali yazoma kowa, idan ka6ata kaikasani, idan ka adanama nakane. Safwan dayafi kowa rawar kai kam aii inasa-inasa ya had'a yabar k'asarma gaba d'aya. acewarsa yawuce da ajin zaman 9ja yanzu. Ameer ne kawai zamu iya cewa ALLAH ya taimakesa, ya had'a shi da mace tagari, nuna masa tayi yaraba hannun jari kawai tundashi bai iya kasuwaba. Dayake yana sonta saiyabi shawararta kuma taimasa amfani. Dama ko a bayan aurensu dataga tarbiyyarsa bata cikaba saita duk'ufa wajen gyarawa, dukda tasha hantara da wulak'anci awajensa hakan baisa tabariba saida taga yadawo hanya d'od'ar. To yanzu haka tanada tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Lubna da Suhaima ne ke sakkowa daga saman benen gidansu suna taku d'ai-d'ai. Jikake kwas! Kwas!! Kwas!!! Takalmansu nabada sauti. Ba mamaba hattada Amrah da Afrah dake zaune a falon saida suka d'ago suna kallonsu. Sanye suke cikin matsatstsun kaya, wandone mai mannewa ajikin nan, sai wata 'Yar mitsilar riga wadda dukansu dazasuyi kwakwkwaran motsi duk sai anga cibiyoyinsu. Lubna tad'an yane k'aramin gyale, amma Suhaima ko'a jikinta dan ko hula babu a kanta. Suduka cingom ne abakinsu, kowa nata tauna k'as-k'as. Idan ka gansu basuda maraba da karuwai😥. Mom ta d'auke kanta cikin matuk'ar 6acinrai, amma batada damar musu magana. Afrah da Amrah ne suka taso suna fad'in momy muma zamuje. Lubna ta yatsine fuska tana harararsu, zakuje gidan ubanwa?!! Kujimin yara da d'aukar dala babu gammo. Dallah kutashimin agaba kafin jikinku yay tsami. Jiki a sanyaye Amrah da Afrah suka matsa baya. Lubna da Suhaima suka d'agama mom dake zaune tamkar gunki tana kallonsu, hannu, mom bye... Basu jira cewartaba suka fice, kowa motarsa yashiga yanufi inda zaije. Amrah da Afrah kam dasuka fara wayo sosai, dan ayanzu haka shekarunsu takwas, gefe suka koma suka zauna, zuciyarsu cikeda sha'awar abinda sukaga momynsu da k'anwar tata sunayi. Mom kam hawaye takeyi sosai, jitake mutuwar mijinta tadawo mata sabuwa fil yau. Afrah da Amrah kam saisuka cigaba da wasansu hankali kwance........ *_duk naga sak'onninku na addu'a ga baba, ngd sosai ALLAH yabada ladan zuminci, masu kiranama ngd sosai wlhy. Kuyi hak'uri, wad'anda sukamin maganaba ta groups zasuga ban amsasuba, messages ne sukamin yawa ta PC wlhy, kunsan nakwana biyu bana online. Kumin afuwa duk naga messages naku INA godiya harbabu adadi 'yan uwana._* Luv you so much all💋 Bilyn Abdul d'inkuce👌🏼 *_(((S)))........2017_* *_I love you aall_* [12/30/2017, 4:54 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→61-62_* ..........A daddafe Asma'u tayi sallar asuba takuma zamewa akan abin sallah ta kwanta. Kafin ya Umar yadawo daga masallaci tuni barcinta yayi nisa awajen. Kansa kawai ya jinjina yad'auketa cak yamaida kan katifa tareda zame mata hijjabin, shima barcin Yakoma. Sai kusan goma suka tashi, Asma'u cema tafara tashi. a gaggauce ta afka kicin tana k'ok'arin had'a musu abin kari mai sauk'i. Cikin 'yan mintuna kad'an kuwa ta kammala, sosai talura da yanda gidan yay datti amma takasa d'aukar tsintsiya tayi koda sharace. Wannan k'azantar data aureta a kwanakinnan tana damunta, tasan ya Fharuk ko kad'an bayason k'azanta. Dantasha ganin 6acinransa sanda yana tareda Lubna kafin ita kuma ya aureta. Tana zaune afalo sai k'ulla wasik'ar jaki takeyi na yanda zata tashi tarage aikin. Motsin datajine abayanta yasakata juyawa, ya Umar sanye cikin wando dogo da vest yacire jallabiyar dayaje masallaci kenan. Asma'u ta ce, "Yaya katashi?." Bai bata amsaba, saidai bin ko'ina na falon yakeyi da kallo a yatsine. Duk sai Asma'u tasha jinin jikinta. fuskarsa da alamun 6acin rai, saidai kwarjininsa ya6oye kaso mafi tsoka a 6acin ran nasa. Husna wai wane sabon hali kikeson koya akan tsaftar gidannanne?. Kallafa kigani, gida Yakima tamkar turken dabbobi, nifa banason k'azanta kuma kinsani sarai. Sosai idanunta suka cikada kwalla, amma tayi jarumtar rik'esu......cikin rawar murya ta ce, "kayi hak'uri Yaya zan gyara, insha ALLAH bazan sakeba daga yau. d'an k'aramin tsaki yaja yashige d'akinsa, shima kansa d'akin a harmutse yake, yakai kwana biyar rabonsa da shara. Ananma tsakin yaja mai k'arfima kuwa, Dan har Asma'u tana jiyo sautinsa saboda gidan yakasance babu kayan dazasu hana girmamar sauti komai k'ank'antarsa. Runtse idanunta tayi Dan harcikin ranta tsakin yashigeta sosai. Tashi tayi akasalance tad'an fara aikin, da k'yar tagama gyaran d'akinta, shima ko morphing bata gamaba taji k'irjinta yafara zafi. Ajiye morpher d'in tayi tazauna dafeda k'irji. Abaya batama tuna tanada ciki inba fad'a akayiba. Amma acikin watannan ko kad'an batada cikakkiyar lafiya, dauriya kawai takeyi, ciwon k'irji da kasala suke addaba mata, gashi yanzu tadainama yawan barcin bakamar daba dasaita wuni tanayi bata gajiba. Shigowar ya Umar yasakata d'ago kanta da sauri, kallo d'aya taima fuskarsa ta maida kanta k'asa. Tunkafin ya tuhumeta tafara magana cikin rawar murya, Yaya kayi hak'u wlhy k'irjina ciwo yakemin.......tak'arasammaganar tana dafe cikinta da k'irjinta dake zafi. Tausayi tabashi, Dan yagane balaifinta baneba, shi abinda yabashi haushi dabata nuna k'azantar na damunta. Durk'usowa yayi gabanta yadafa bayanta yana shafawa ahankali, sund'an ja lokaci ahaka kafin yad'ago fuskarta datayi sha6e-sha6e da hawaye. Gogemata yashigayi amma baiyi maganaba, itakuma tamkar yana zugata sai kuma matso wasu takeyi. Ganin haka ya Umar ya ce, "kukan ya isa haka kuma malama." Sassauta kukan tayi saida ajiyar zuciya lokaci-lokaci. d'agota yayi suka koma bakin katifar, saida yaga tanutsu sannan yay gyaran murya, idonsa akanta ya ce, "zansa asamo miki mai aiki kawai, Dan bazai yuwu mucigaba datafiya ahakaba gsky, inada k'yank'yami Husna kema kinsan haka, kokad'an banason k'azanta. Amarairaice take kallonsa, muryarta adashe ta ce, " a'a Yaya nidai banason mai aiki. Saidai idan Rafi'a ko Fatee da Hasiya cikinsu wata tadawo nan. Hannunta yakamo ya rumtse anasa, idonsa nakan fuskarta, husna bazai yuwu mud'aukema mama Rafi'a ba a irin wannan lokacin, kinsan yanzu babu mufida, Fatee kuma tana sana'a itama zamu takurata gsky, saidai idan Hasiya, itama sai idan baba ya amince yabamu tunda dolene tazauna harki haihu, kinga kuwa wata wajen hud'u kenan zuwa biyar. Kanta ta jinjina tana godiya. Yad'an murza yatsunta yana murmushi, to amin dariya mana, wannan d'aurewa haka. Dariyace ta su6ucema Asma'u, tarufe fuskarta tanayi. Jawota yayi jikinsa ya rungume shima yana murmushi, hannunsa nakan cikinta yana shafawa, murya k'asa-k'asa ya ce, "ALLAH dai yasa kada yarona ko yarinyata suyo gadon wanan saurin kukan naki. Kanta na bisa cinyarsa tayi 'yar dariya tareda turo baki gaba, tokaima dai karsuyo halinka d'innan na mazurai. Dariya yayi sosai, cikin dariyar ya ce, " nihar wani mazuraine dani?. Tab ya Fharuk aii wlhy idan kad'aure d'inan yanda kasan wani soja haka kake. Yatsansa yasa ya d'alli bakinta yana fad'in mashe ranciya kawai. Da sauri tasaka hannu tadafe tana fad'in wayyo zafi. Fuskarsa d'aukeda murmushi ya janye hannunta daga kan bakin, o sorry, namanta zan fasa d'an bakin rage zafin. Hararar wasa tasakar masa, ta yunk'ura zata tashi, ya maidota, sorry my Queen. Baki tabud'e zatayi magana ya manna nashi. 🚶🏻‍♀ _______________________ Tare suka wuni agida suna shan sharafin soyayyarsu, da k'yar Asma'u ta lalla6a ya Umar yakaita gidan bikin, yanzuma amotar jiya suka tafi. Asma'u tayi masa tambayar duniya akan motar wage? Amma yak'i yabata amsa, saidai ya ce, "takice." Daga baya saita tsuke bakinta. Ak'ofar gidan Mufida ya sauketa, tareda gargad'in da anyi magriba zaizo sukoma gida. Ta ce, "to." Sanda tashiga gidan cike yake da danginsu, Dan harsunzo walima. Gaisuwa taitayi da dangi, wasu har tsokanarta sukeyi wai sai yanzu take zuwa?. 'Yar dariya kawai takeyi cikeda jin kunyarsu. Ahaka harta k'arasa d'akin Mufida, a can ta iske Anty Saratu da Anty Sa'adatu. Bayan sun gaisa, Anty sa'a ta ce, ''o ke ma'u sai yanzu kike zuwa? Halan Umar ne?.... Hannu tasa ta 6oye fuskarta tana fad'in a'a fa Anty, banajin dad'ine. Dariya duk 'yan d'akin sukayi, mufida dake zaune taci kwalliya da'akasan amarya dashi ta ce, "a'a Asma'u fad'i gsky dai, jiyafa agabana yakiraki, runda ya d'aukeki bamu sake ganinkiba dagake harshi bakuje dinner ba. La'ilah, Anty Mufida munfaje. Fatee ta ce, "ki rantse kunje Anty Asma'u!." 'Inafa kallonku kuka tafi amota.' Hararta Asma'u tayi, to 'Yar saka ido anji. Yanzummadai dariyar akayi. Haka akacigaba da gudanar da biki, manyan iyaye irinsu inna sunacan suna rabo, su Asma'u kam ana d'aki anashan shargalle. Shaf tamanta da sharad'in oga, saida taji anata kiraye-kirayen sallar isha'i sannan ta tuna. Jikinta har rawa yakeyi tajawo Handbag d'inta tafara laluben wayarta. Wayyo ALLAH ni Asma'u naga banu, tafad'a yayinda idanunta suka sauka akan screen d'in wayar. Missed call d'in ya Umar har 7. Anty Saratu dake gefenta ta ce, "k lafiyarki kuwa?." Yaya Saratu inafa lafiya, ya Fharuk yacemin da anyi magriba zaizo mu wuce gashi har isha'i tayi. 'Ashe kuma yamin kira har 7 ban d'agaba.' Yanda tarud'e saitabama Anty Saratu tausayi, duk mace tasan tashin hankalin da ake shiga idan kashiga irin wannan k'angin. Wayar Anty Saratu ta kar6a, itadai Asma'u tayi sagale tana kallonta. Anty Saratu ta kira ya Umar sau uku amma bai d'agaba, tunawa tayi ko yana masallaci, saita d'an dakata da kiran. Ana idar da sallah takuma kira, shima saida rakira sau biyu sannan yad'aga. Bata bari yayi maganaba ta ce, "Assalamu alikum, yaya ina yini." Kamar bazai amsaba, saikuma ya ce, "lafiya." Tundaga yadda ya amsata tasan akwai Marsala. Amma saita dake zuciyarta ta ce, "dama sonake naji kokun tafine? Asma'u ce ta manta da wayarta awajena, kuma tunda aka kira magriba tafito dankarkaita jiranta. Ta fito!? Zuwa ina?. 'Ya Umar yay tambayar.' Jin muryarsa tad'an sassauta Anty Saratu ta gyara zama, k'ofar gida tafito, saidai ban saniba kotana tsakar gidan, danni ina d'aki. Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, Dan d'azun ransa amatuk'ar 6ace yake, azatonsa Asma'u tak'i d'aga wayarne saboda batason tataho...... Ya ce, " kifito tsakar gidan ki dubamin ita, ganinan zuwa gidan. To. Anty Saratu ta fad'a tana murmushin nasara. Asma'u ta rungume Anty Saratu dantaji komai, ngd yaya Saratu, wlhy kin taimakeni, ya Umar d'an barazanane sosai. Dariya kawai Anty Saratu tayi, ta ce, "kinga tashi muje k'ofar gidan yasamemu a can kawai. Asma'u taima kowa sallama, sannan suka fito k'ofar gida. Suna zuwa ya Umar na isowa kuwa. Asma'u ta shagwa6e fuska, kai yaya ina kashige inata zaryar lek'oka tun d'azun kamar nayi k'arya. d'an hararta yayi ya ce, ''ai ita kika zura, dakina lek'owa dabaki ganniba, tunkafin magriba nazo wajennan inata kiranki amma baki d'agaba. Lah namanta wayarne awajen yaya Saratu, kumani ALLAH ban gankaba. To naji shiga mutafi nagaji nikam. Motar tashiga sukayi sallama da Anty Saratu akan saitazo. Ya Umar ya harareta, wato haryanzu kina yawon tsiyar nan naki ko Saratu. Anty Saratu tad'an Sosa gefen wuyanta, ALLAH yaya banayi, zanzo zumincine kawai, nakwana biyu banzo mungaisaba shiyyasa. To shikenan, kigaida yaran. Yabata dubu biyar. Godiya tamasa sannan takoma cikin gidan, shikuma yaja motar suka tafi. ________________________ Haka rayuwa tacigaba da shurawa, tun bayan bikin Mufida Hasiya tadawo gidansu Asma'u tanad'an taimaka mata da ayyuka. Asma'u anata jan ciki, saidai ad'an tsakaninnan tana d'an wahala Dan yanzu ita take nata laulayin cikin. Sosai take samun kulawa daga ya Umar da danginta, hakama Anty Saddiqa tana iya k'ok'arinta. Akwana atashi babu wuya, yanzu Asma'u kam tashiga watan haihuwa. Zuwa yanzu tazama alalla6a, sai shagwa6a da rakin tsiya, Abu kad'an sai kuka, wani lokacinma dariya take bama ya Umar, kullum tunaninsa randa Asma'u zata tsinci kanta ad'akin haihuwa. Yasandai zasusha raki ainun.... A6angaren mall nasa abubuwa nata tafiya dai-dai Alhmdllh, har yanzudai baya zuwa sai lokaci-lokaci, shima saiya faki idanun mutane. Komai yazeed yatsaya akai, gakuma muktar dasu Harris. Yanzukam kud'i nashigo masa Alhmdllh. A6angaren haihuwa kam yatanadi komai, har kayan gado yasiyo da kujeru daza'a zuba agidan, amma Asma'u bata saniba, dan bai kawosu gidanba. Aranar wata Alhamis da yamma Asma'u tafara nak'uda. Ya Umar na shago Hasiya taje a hargitse. Hasiya lafiya kuwa?. Yaya Anty Asma'u ce, gatacan tan..... Baibari tak'arasaba ya afako cikin gidan. Sosai Asma'u tafara jigata, hakan yasa baisaurari komaiba ya sungumi kayansa yakai mota. Hasiya ce tai k'arfin halin d'akko akwatin dasuka shirya kayan haihuwar. Suna isa asibitin aka kar6esu da gaggawa. Dr Al-ameen sai kwantar masa da hankali yakeyi. Wasa farin girki, har wayewar garin ranar Asma'u bata haihuba, sai bak'ar wahala datakesha, duktayi laushi ko nishi bata iyawa. Zuwa sannan 'yan uwa duksun cika asibitin, hardasu mama, dayake yanzu ta canja hali sosai. Ya Umar kam aii kamar shima nak'udar yakeyi, dukaya fita hayyacinsa. Ganin yanda Asma'u ta jigata ko motsin kirki takasa Dr Al-ameen yabada shawarar amata CS kawai. Kowa yabada goyon baya, ya Umar yasaka hannu a takardar. Babu 6ata lokaci akayi shirin shiga yima Asma'u theater. Addu'a da fatan nasara 'yan uwa suka bita dashi. Ya Umar kam saiyayi Alwala yashige masallacin dake asibitin, alkur'ani yad'auka yayta karatu da mik'ama ALLAH kukansa............... *_Asma'un ya Umar! ALLAH yasa afito lafiya kihaifama ya Umar d'inmu d'a ko 'ya maikama dashi😥._* Ameen _kowa yay shiru na second 1 Dan nuna jimami😂_ *_(((S)))........2017_* *_Luv u all._* [1/1, 3:05 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→63-64_* ..........Sai wajen 1:30pm su Dr Al-ameen suka fito, kowa yana yarce gumi. 'Yan uwa sukayi Kansu suna tambayar Asma'u harma da abinda ta Haifa. Hannu kad'ai Dr Al-ameen ya iya d'aga musu, cikin hanzari yashige office d'insa. Ya Umar dake binsa abaya ya ce, "Dr matatafa?. Karka damu, muna fatan nasara, amma muna neman jini da gaggawa. Dr kud'ebi nawa kawai. Ya Umar yay maganar cikeda hanzari. Wasu Abubuwa Dr Al-ameen ya d'auka suka fice, kai tsaye wajen d'ibar jini suka nufa. Cikin amincin ALLAH jinin yazo d'aya kuwa, d'iba akayi aka tace sannan cikin hanzari Nurse d'in tad'auka ta kaima Dr Al-ameen...... Yamzuma saida suka kwashe kusan minti 40 sannan suka fito. Yanzukam akwai canji dan fuskokinsu a sake suke. Duk mik'ewa sukayi ayanzunma, tunkafin suce wani Abu Dr Al-ameen ya ce, "Alhmdllh congratulations, ansami baby boy." 'Yay maganar yana matsawa gefe, Nurse d'in dake d'aukeda babyn ta bayyana.' Gaba d'aya sukayi cahhh akan Nurse d'in, kowa nafad'in Alhmdllh. tamik'a musu k'aton jaririn Wanda kallo d'aya zaka masa ka gane dolene yabama mamarsa wahala saboda girmansa. 'Yar rige-rigen d'auka akeyi, ALLAH dai yabama mama nasarar amsarsa. Ya Umar kam wajen Dr Al-ameen yamatsa, Dr matatafa?. Murmushi Dr Al-ameen yayi masa tareda dafa kafad'arsa kwantar da hankalinka baban baby, madam ma tana lafiya, yanzu haka anashirin maidata d'akin hutune danta huta. Ajiyar zuciya ya Umar ya sauke, Ahankali yafurta Alhmdllhi Ala kulli halin. Dr zan iya ganinta kuwa?. Babu damuwa muje narakaka dai ka ganta, inaga hankalinka zaifi kwanciya. Ya Umar baice komaiba sai murmushin dakan k'awata fuskarsa dayayi. Atare suka shiga d'akin da akakai Asma'un, su hud'une ad'akin, ya Umar yama sauran sannu sannan yak'arasa gaban gadon da aka kwantar da Asma'u. d'aure take da bedsheet fari sal, said'an d'igo-d'igon jini dayad'an 6atashi, amma ansaka mata k'aramin hijjabi shima fari, idanunta biyu kuma tana iya magana, Nurse natsaye agefenta tana saka mata jinin da aka d'iba ajikin ya Umar Dan k'ara mata. Ya Umar yak'arasa gaban gadon, yaja farar kujerar dake gefe ya zauna, hannun Asma'u yakamo yarimtse anasa, my Asmah sannu kinji. Bata iya amsashiba, saidai idonta na kansa, sai hura hanci takeyi. Yamatso sosai yashafa kanta yana fad'in ALLAH yayi miki albarka kinji. Kad'an tad'aga masa kanta, muryarta can k'asa-k'asa take magana. Bayajinta, Dan haka yamatso da kunnensa kusada bakinta. Ta ce, ''Yaya k'afata nanan kuwa? dubamini." Murmushi yamata, yakuma shafa kan nata, k'afarki nanan My Husna. bakijintane?. Yanzuma saida yamatsar da kunnensa sannan yaji mitake fad'a. ALLAH jinake kamar babu k'afar. Ya Umar ya kalli Dr Al-ameen dake tsaye yana gyarama Nurse d'in yanda zatayi. Dr kaji wai jitake kamar k'afarta bata a jikinta. Ko akwai matsalane?. No, babu wata matsala, allurar da akamatace takawo hakan, zuwa safiya zatajita daidai insha ALLAH. Ya Umar ya ce, "tokinji." Nanma kanta tajinjina tanad'an lumshe ido. Dr Al-ameen ya ce, "mubarta inaga zatayi barcine". Ok ya Umar yafad'a yana mannama Asma'u kisses agoshi. Sannan suka fice. Zuwa yanzu kowa yad'auki baby daketa barcinsa, suna zuwa mufida amarya ta mik'ama ya Umar babyn tana fad'in Yaya ga bak'on duniya. Murmushinsa ya fad'ad'a, yakar6i yaron maicikeda lafiya, kiss uku ya manna masa afuska sannan yarungume abinsa yanajin wani farinciki na ratsa dukkan ga6o6in jikinsa. Yakai minti kamar 5 ahaka, kowa yanata kallonsa cikeda tausayi, sunsan yanadason yara, amma aka rabashi danasa. Bakinsa ya manna akunnen yaron yaymasa hud'uba, a la66ansa ya furta ALLAH ya raya *_Usman Fhodeeyo_*. 🤗nikad'ai najishi, Dan haka na ce, " Ameen ya Umar🤓. Babu Wanda aka bari yashiga gunta har magriba, bayan magribane kuma ya Umar ya ce, "duksu tafi hakanan." Badan sunsoba suka fara shirin tafiya, Anty Saratu, Anty Sa'a, mufida, Anty Saddiqa, fatee, Rafi'a, hasiya. Mama kad'ai za'a bari anan, Rafi'a da hasiya ance subi fatee gidan inna, Dan ita batazoba, tama mama kara. Kowa yaje yaga Asma'u dahar yanzu take barcinta sannan suka tattafi. 9:30pm Mama ta kalli ya Umar da Harris, muktar, Sadam, yazeed da matarsa dasukazo suma tun bayan magriba, ta ce, "yakamata kutafi hakanan dare yayi, bakamar su yazeed kuda kuka baro yarama. Yazeed yay murmushi mama aisuna tareda mai aiki babu damuwa. Eh dukda hakadai yakamata kutafi, ALLAH yasaka da alkairi, yabada ladan zuminci. Gaba d'aya suka amsa da Ameen. Muktar yamik'ama mama jaririn daketa barcinsa nannad'e a showal. Sallama sukai mata suka fice, amma dana kalli fuskar ya Umar sainaga bahaka yasoba. Amma babu yanda ya iya, dan maza basa jinyar mata awajen, saidai mace 'Yar uwarka. Shima namiji haka. Saidasu yazeed suka tafi sanan suma suka shiga mita suka tafi...... Ya Umar duk saiyaji gidan babu dad'i, amma fuskarsa cike take da fara'a na farincikin k'yautar da ALLAH yamasa yau. Aikam kusan kwana yayi yana sallah da mik'a godiyarsa ga sarkin sarakuna. ★★★ Washe gari tundaga sallar asuba ya Umar ya koma gida yay wanka a gaggauce yay shirin tafiya asibitin, kai tsaye asibitin yanufa. Saida yafara zuwa suka gaisa da Dr Al-ameen sanan yatafi d'akin da aka kwantar da Asma'u. Tana zaune akan gadon, tajingina da filon wata Nurse tana taimaka mata wajen bama babyn nono. Mama kuma na zaune akan kujera tana shan shayi (su mama babu juriyar yunwa😉lol). Kamshin turarensa yacika d'akin, Asma'u dabatasan da shigiwarsaba tad'ago kanta. Murmushi yamata Wanda yasakata jin wani sanyi aranta, saima tadainajin zafin shan nonon da yaron keyi. Rissinawa yayi yagaida mama sannan yakoma yabi sauran gadajen suma yana gaishesu. Abakin gadon yazauna kusada k'afafun Asma'u, yad'auki yaronsa da'aka kwantar agefe bayan yasha nono yak'oshi. My Husna! Ya jiki?. Cikin sanyin murya ta ce, "Alhmdllh, ina kwana?." Lfy lau, kuntashi lfy?. Kanta ta jinjina batareda tayi maganaba. Ya Umar yamaida kallonsa kan mama yana fad'in mama babu dai wata matsala ko?. A'a wlhy, lafiya lau muka kwana, shima yaron yanata barcinsa, yanzuma yatashi babu jimawa yad'an fara kuka, saikuma ga Nurse take kowa? tace yunwa yakeji abashi nono yasha, shinema kasamesu suna bashi. To Alhmdllh, ALLAH yak'ara lafiya. Ameen ya rabbi. Ya Umar yakuma kallon Asma'u data zuba musu ido shida babyn cikeda sha'awa. Maman baby k'afar tadawone?.. Fuskarta tarufe tana fad'in kai ya Fharuk babu wani Maman baby. Dariya yayi k'asa-k'asa dan yagane tanajin kunyar mamane. Suna nan zaune Dr Al-ameen yashigo, saida yafara duba sauran marasa lafiyar d'akin, sumadai duk theater's aka musu, sanan yak'araso gadon Asma'u. Kan yaron dake hannun ya Umar yashafa yana fad'in my son katashi lfy a sabuwar duniyarmu?.. Ya Umar yay dariya, gashinan k'alau yanata k'yalla idanu. Dr Al-ameen yak'arasa kusada Asma'u yana fad'in aii yaran yanzu da wayonsu ake haihuwarsu. Ya gaida mama sanan yayma Asma'u ya jiki?. Ta ce, "da sauk'i, saidai bayanta namata ciwo kad'an-kad'an da kanta. Sannu yamata sanan yasaka Nurse d'in dake binsa amma bata d'azu baceba, takuma d'aurama Asma'u k'arin ruwa. Mama ta ce, "Ameenu bazataci komaiba ita Ma'un?. A'a mama sai zuwa yamma za'a bata ruwan Lipton tasha kawai. To ALLAH yakaimu lafiya. Daga nan Asma'u takoma barci, dan anaso tahuta saboda kanta datace yana mata ciwo. Mama da ya Umar kam suka cigaba da hirarsu. Kafin wani lokaci asibitin yacika da dangi, yaukam harda inna da baba da Abba akazo, matar ya Abubakar ma tazo, shima hardashi.......... *_bayan sati d'aya_* Da safe aka rad'a sunan yaron bayan an idar da sallar asubahi a masallaci. Yaro yaci sunan Usman mahaifinsu ya Umar (ALLAH ya gafarta masa, ameen) amma za'ana kiransa Fhodeeyo. To ALLAH ya albarkaci rayuwar Duk wani jariri ko jinjira ameen. Har yanzu Asma'u na asibiti ba'a sallamesuba, amma suna sakaran sallama ayau d'innan, Dan Alhmdllh jikinnata yayi k'yau. Batada k'an jiki, kuma kowadai yasan CS d'in yanzu ba'a wani dad'ewa a asibiti musamman idan anhad'u damai jarumta. Tana zaune akan gadon abinci takeci (Dan yanzun tanacin abinci), yaron kuma yana hannun Anty Sa'a, mama da Anty Saratu da mufida sunata hirarsu. Ya Umar yashigo shida yazeed da Muktar, saida suka gaida d'ayar matar data rage ad'akin, Dan yanzu su biyune kawai, ansallami sauran biyun. K'arasowa sukayi, kowa ya ajiye ledar hannunsa sannan suka rissina suna gaida mama. Su Anty sa'a ma suka gaishesu, itama Asma'u haka, suka tambayeta ya jiki?. Ta ce, "Alhmdllh. Mufida tatashi tajawo musu kujerun dake d'akin suka zauna. Jaririn aka basu, har anmasa wankansa, yana cikin kayan sanyi masu laushi jajaye. Yazeed daya d'aukeshi ya ce, ''masha ALLAH Fhodeeyo". Mama tawashe baki Dan farincikin sunan dayaci, ta ce, "lallai Ashe wanan mijin na katakone bana robaba?." Dariya aka sanya duka, mama tad'ora dafad'in to ALLAH yaraya Usmanu. Ameen suka amsa. Muktar ya ce, "mama aidama na k'arfenema koda baici sunanba." A'a rabanifa muktar, indafa baici sunanba tona robane, amma yanzu kun k'ara masa girma yazama na katako baikai na k'arfenba. Dan nasan bazaiyo jarumtar nawa Usmanun ba. A'a mama karfa ki fidda rai, nangabafa shine mai kama miki sanda, Cewar mufida. ALLAH ya tsareni mama tafad'a tana kaima mufida duka. Kaucewa mufida tayi suna dariya. Asma'u data d'ago ido saita kama ya Umar na kallonta. Baki ta murgud'a masa daga k'arshe. Ya nuna Kansa wai shi takema murgud'e?. K'ara murgud'a masa bakin tayi sanan tad'aga kai alamar eh. Shima Kansa ya jinjina wai aii zasu had'une. Mufida da Anty Saratu dake kallonsu suka tuntsure da dariya. Mama ta ce, "kai kukuma lafiyarku kuwa?. Cikin dariya sukace k'alau mama, wata drama muke kallone. Kudai kuka Sani mama tafad'a tana maida hankalinta wajen hirarsu yazeed da Anty sa'a. Da yamma aka sallamesu. Kowa yayi farincikin faruwar haka kuwa, bakamar Asma'u, jitake kamar tayita tsallen murna. Da mama ta ce, "awuce da ita gidanta, amma ya Umar yayta rok'onta akan a'a shidai sutafi gidansu, har itama mamar saita zauna kodan tasakama gidan albarka. Da wanan dad'in bakin nasa mama ta ameence aka wuce da Asma'u gidan ya Umar. Sun Tatar da gidan tsaf, dansu Rafi'a sunje sun gyara, nanfa makwafta sukaita shigowa dubata da jariri............. *_(((S))).......2017_* *_I love you all_* [1/1, 3:05 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→65-66_* ..........Shiru momy tayi tamkarma bataji abinda Lubna tafad'aba. Lubna tak'ara maimaitawa, Dan atunaninta mom batajitane. Mom zanyi aure kwanannan nacefa. Mom ta sauke ajiyarzuwa tareda maida dukkan hankalinta akan Lubna da Suhaima. Baby kinsandai banason shashanci, idan kinsan wanan maganar taki ba gsky baceba karki sake maimaitamin ita anan. Suhaima da Lubna suka kalli juna suna murmushi, mom ALLAH kuwa da gsk baby takeyi, aure zatayi. Murmushi mom tasaki awanan karon, Dan tagaji da gantalin da 'ya'yan natakeyi ana gulmarsu a anguwar. Ta ce, "Alhmdllh, aii aure shine mutuncin d'iya mace, naji dad'i sosai, kema Suhaima saiki fiddo da mijin ahad'a gaba d'aya ayi, nikaina mamarku auren zanyi Dan kare mutuncin kaina. Atare Suhaima da Lubna suka had'a baki wajen fad'in mom aurefa kikace!?. Mom tayi 'Yar dariya, kai kajimin yara, shin nawuce da aurenne?. A'a mom, amma yakamata kima dad kara gsky, kik'arasa rayuwarki haka, tunda dai duk abinda kike nema ALLAH yabaki. Shiru tayi batace komaiba, zuwa can kuma tayi ajiyar zuciya, shikenan zan duba naga mai yuwuwa, shima Ameer idan yazo zamuyi maganar dashi. Amma ke baby waye mijin?. Lubna tayi d'an tsaki, abokin wancan fak'irinne nada, Umar!. Abokin Umar kuma baby?. Eh mom, ammafa ada, Dan yanzu ko hanya basa had'awa dashi, Dan babu yanda za'ayi mai Arzeek'i da fak'iri suzauna a inuwa d'aya. To, amma kina gani babu matsala baby?. Wlhy babu wata matsala mom, Dan nikam ina sonsa, kuma kodan nak'ara haddasa bak'in ciki arayuwar Umar saina auri Hafiz. Shike nan, ALLAH ya Sanya alkairi, saiki gaya masa yayi k'ok'ari su Gana da uncle d'inku Abdullahi, Dan banaso aja dogon lokaci, idanma san samune ayi bikin nanda k'arshen wata. Lubna ta turo baki gaba, kai mom bagwara yaje wajen uncle habeb ba, kinsandai mugun halin uncle Abdullahi nan, 'ya'yansama bawani dad'insa sukejiba, sai ak'idar tsiya, shi adole (Ustaz). Humm baby kenan, amma idan baki mantaba aii Abdullahi shine babba, yanagaba da mahaifinkima bare habibu. Nidai mom dukda haka uncle habeeb naza6a, yau kwana tarafa kenan Uncle Abdullahi yazo yagama mana cin mutuncin agidannan, kuma hardake, amma shine harkin manta, zaki d'au ragamar 'ya'yanki kibasa. Baby aiba cin mutunci yamanaba, gsky yafad'a, kumanikam koda bazan d'auka dukaba zan d'auki tayin aure, kema Suhaima kifito danaki ahad'a duka kawai. Daga Suhaima har Lubna baki suka cuno gaba, ciki-ciki Suhaima ta ce, "nima aii Ramadan yace zaituro iyayensa." Alhmdllh, amma naji dad'i sosai, insha ALLAH zan sanarma su habebun dakaina. Daga nan taron ya watse, baima Lubna da Suhaima dad'iba.... Washe garin ranar mom dakanta ta shirya taje har gida suka tattauna da uncle Abdullahi. Yanuna jin dad'insa sosai, shima uncle habeb sun sanar masa. Shima sosai ya nuna farin cikinsa, Dan sungaji da zagin da'ake musu agari akan gararin da yaran sukeyi. (Sukuma harga ALLAH ba laifinsu baneba, suna iya bakin k'ok'arinsu). Amma ko kad'an su Lubna basa saurarensu, Dan tun mahaifinsu nada rai bawani ganin girman Uncles d'in nasu sukeyiba, tunda sunsan babansu dukya fisu kud'i. Hasalima alfarmarsa sukeci. Sun yanke hukunci akan sati mai zuwa zasusa akawo kud'i, amma saisunyi bincike akan yaran tukunna. Mom tamusu godiya sannan tatafi............ ________________________ Suna zaune afalo kasancewar lokacin zafine, ko ina abud'e yake. Mamace takema Asma'u fad'a akan shan kunu dabata sonyi. Itadai Asma'u tayi luk'us Dan tasan batada gsky. sai Hasiya dake dariya k'asa-k'asa, Dan babu lalla6ar dabataima Asma'un ba akan shan kunun d'azu da rana amma tak'i, ai gashinan yanzu yahuce tanasha da tsiya ko. Harara Asma'u tasakarma Hasiya tana tura baki gaba, mama kinganta ko?. Nagantafa, cewa mama, amma babu abinda zance da ita tunda kece kika jama kanki. Ku yaran yanzu babu abinda kuka iya sai shan shayi da wainar kwai, yo ALLAH natuba ni nata6a ganin jego haka?. Shidai jegon farko inbaka ingantashiba aibazaka inganta nagababa ko? Kuma kayi wasa ahaka zaka taso sakaka, harma mijin yaringa gudunka, kullum ayita fama akan shan kunu, inbanda lalata bashine zaikawo ruwan nonoba yaro yasha yak'oshi. Anty Sa'a tafito daga d'akin Asma'u tana dariya, dama tun d'azun suna aciki itada Anty saddiqa da anty Saratu suna saka sababbin punches da ya Umar yasa aka kawo d'azun da safe. Tun d'azun suna jiyo diramar mama da Asma'u sunata musu dariya acikin d'akin. Yanzuma Anty sa'a tafitone tabama Hasiya kayan Fhodeeyo dazata wanke wad'anda sukad'anyi datti. Yauwa Hasiya ga kayannan, tashi yamma nayi kok'yayi kigama. To anty, Hasiya ta amsa tana kar6ar kayan. Mama ta kalli Anty sa'ar, yo harkun gama jeren?. A'a mama sauradai kad'an, inagama munkusa tashinku daga falonnan dan munkusa dawowa kansa. To idan kun kammala ai saimu koma falon Umaru tundashi aii kun gama ko?. A shikam mungama tun d'azun shida kicin. Asma'u ta ce, "anty sa'a sannunku." Yauwa ma'un mama sannu kema, tad'an rissina tana lek'en fuskar Fhodeeyo dake bayan mama. Mama! ALLAH kuwa kamannin fodeyo da Umar sako fitowa sukeyi, yaronnan haske kawai zai nunama Umar. Mama tayi 'yar dariya, yoni sa'a aii kallon Usmanu nakeyi kamar sanda na haifi Umaru, har d'an banzan kukannan nashi na dare dayake hana mutane barci, haka Umaru ya wahalar dani da kukan dare nida mahaifinku, to d'an kwal uban shima gashinan yayo gado. Dariya anty sa'a da Asma'u sukayi, Anty sa'a tashafa kan fodeyo, kanata barcinka sai dare yayi kahana mamummu barc....... Shigowa ya Umar tahanata k'arasa maganar. Ya rissina yana gaida mama, Asma'u tamasa sannu, suka gaisa da Anty sa'a itama. Yad'ora da fad'in anty sa'a sannunku da aikifa. Yauwa Umar, ya shagon?. Alhmdllh wlhy, dama zan tambayekine midami kuke buk'ata na hidimar sunan?. Ai dukma mun rubuta komai, takardarma na d'akinka. Okey babu damuwa. Mama ta ce, "tonifa inaga zuwa gobe zan koma gidan mijina gsky." Suduka suka kalleta cikin alamun tambaya. Ya Umar daya kasa daurewa ya ce, "haba mama miyasa?." A'a babu komai Umaru, bazan zauna ananba har ranar suna aii, kumama alhmdllh jikin Asma'u yayi k'yau, inama laifi, yau kwananafa Tara agidanan, ga zaman asibiti damukayi na sati d'aya, aii abin ba hauka baneba. Ya Umar yay murmushi batareda yace komaiba. Anty Sa'a ta ce, "shikenan mama, amma kibari sai jibid'in da safe, tundadai sunan sai rana." A'a insha ALLAHU gobe da daddare zan tafi. Shiru duk sukayi, Dan sunsan halin kafiyar mama sarai. Zuwa yamma lis suka gama gyara gidan fes, puneches d'in sunyi k'yau sosai, dukdadai basukai tsadar nada da Lubna takwasheba, amma wad'annanma babu laifi kam. Na d'akin ya Umar kujerune na leda bak'ake, da labuloli green, hakama carpet shima green, sai madaidaiciyar TV plasma dasuka ajiye zuwa gobe za'a nemo mai sakawa. Hakama cikin bedroom d'in komai kamar na falonne. d'akin Asma'u kuwa, lemon green & Orange ne, itama komai tsaf. A babban falo kuwa kujeru jaa da milk d'in labulayene dakuma ratsin jaa kamar kujerun, nanma kowa yagani dolene ya yaba saidai mak'iyi. Mamace ta ce, "aidabasu saka na babban falon ba, dasun bari taro yatashi sannan, inba hakaba kuma duk za'a 6atasune. Sunyarda da shawarar mama kuwa, Dan haka sukace zuwa gobe da yamma sai a kwashe Dan yau sungaji ainun. Bayan anyi magriba harris yazo ya maidasu Anty sa'a amotar da har yanzu Asma'u batasan tawayeba, Dan shima ya Umar d'in yakan had'a wata guda bai shigetabama, yafi hawa mashin lifan daya saya bayan bikin Mufida. Yauma kamar kullum Hasiya taje takaima ya Umar abinci d'akinsa, akan sentar table d'in tsakkiyar falon ta shiya masa yau, sa6anin da datake jerawa akan tabarma. Sosai falon ya birgeta Dan haka takebin ko ina da kallo. Shigowar ya Umar tasakata saurin waigowa, sannu tamasa ya amsa shima yanabin falon da kallo, Hasiya falon yayi k'yaune?. Wlhy kuwa yaya ya had'u, yamafi na yaya Asma'u kyau. Dariya ya Umar yayi yana zama, ya ce, " kidai dage tajiki." Itama dariyar tayi tana dafe bakinta, aikodai yaya bara nayi shiru, Dan yanzu Abu kad'an zakama yaya Asma'u tahau mutum da masifa. Murmushi kawai yayi, amma baice komaiba yashige bedroom d'insa. Daga ciki ya ce, "rediyo jeki kiramin Husna, kuma tataho da fodeyo." Fita Hasiya tayi tana zum6ura baki, dama idan tana zabga surutu haka yake cemata redio. Data tuno wani Abu kuma saitayi dariyar mugunta, tasan dawuya mama tabar Asma'u zuwa wajensa musamman yanzu da daddare, ko kad'an bata barinsu su k'e6e sukad'ai. batasan miyasaba itama.🤷🏽‍♀ Afalo ta iske Asma'u zaune a inda ta barsu, amma yanzu tanama fodeyo shirin barcine. Mama kuma tana kwance a doguwar kujera, harma barci ya d'auketa. Zama hasiya tayi kusada Asma'u, cikin magana k'asa-k'asa ta ce, ''yaya Asma'u! ya Umar na kiranki, yace kuma kije da fodiyo. Da sauri Asma'u ta kalli inda mama take, Alama tayima Hasiya data fad'a ahankali. Hasiya tak'unshe baki tana dariya k'asa-k'asa. Asma'u batace da ita komaiba tak'asa sakama fodeyo famfas, tasaka masa riga mara nauyi saboda yanayin zafin garin, hoda ta shafa masa ta k'uraje, a wuyansa da goshinsa sannan ta nad'eshi a showal ta sa6ashi akafad'a tafice cikin sand'a da waugen mama dabatasan sunayiba. Hasiya ta guntse baki tana dariyarta.😂 Yana zaune abakin gado, dagashi sai tawul, da'alama yanzu yafito daga wanka. Mai yad'auka yad'an shafa sama-sama saboda zafi. Yana cikin fesa turare Asma'u tashigo da sallma. Fuskarsa d'aukeda murmushi ya amsa mata. Yamik'e tsaye yana saka gajeren wando. Yayinda Asma'u ta zauna abakin gadon tana kwantar da fodeyo. Ya Umar yagama saka wandon yadawo bakin gadon shima, Rankwafawa yayi yayma Fodeyo kiss akumatu yana fad'in my son rigima, ya shafa kan yaron daketa barcinsa, yanzu gaka kana barcinka? Sai anjima kahanamu barci ko?. Asma'u dake kallonsu tayi d'an tsaki, kabari wlhy ya Fharuk, yaronnan yana d'aukar hankalinmu, shi yasha barcinsa da rana, mukuma yahanamu dadaddare. Ya Umar yazauna akusada ita yana rungumota jikinsa, acikin kunnenta ya ce, "sorry momy zamu daina wata rana aii?." Baki ta tunzuro gaba, o bama zaka masa fad'aba? Saidai ka goyida bayansa kenan?. Dariya tabashi sosai, Dan haka yadara, yakuma matseta sosai yana dariyarsa, kai my Husna kinada abin dariya wlhy. Yanzu miye abin fad'a ga Fodeyo Dan ALLAH. hummm zaka fad'i haka kuwa, tunda bakai yake hanawa barcinba, wani lokacinma saiyayi wajen Rabin kukan kake zuwa. Hannayensa yasa yaruk'o fuskarta suna kallon juna. lumshe idanunta tayi Dan hango buk'ata kwance a idon mijin nata. Aii tama yabama k'ok'arinsa sosai wannan karon, Dan rabonta dashi tun ana jibi zata haihu. Kusan sati uku kenan...... Jin bakinsa akan nata yasaka tunaninta tsayawa cak waje d'aya. Hummm su ya Umar fa andad'e ba'a gamuba🤐. Ganin zai zarce gona da iri yasakata rik'e hannunsa. Shima saiya dakata da zagayen dayakeyi da hannunsa ajikita d'in, Dan yatuna akwai d'inki tareda ita. Wasa yaciga dayi da bakinta harya d'an rage zafi sanan yazube akatifar yana maida numfashi. Ahankali tazame itama ta kwanta gefensa, 'yan dabaru take masa irin namu na mata dakakanyi idan kana al'ada. Luf yayi dan sak'wanninta na isa agareshi. Saida ta tabbatar yasami nutsuwa sannan tabarsa, gefe takoma tana kallonsa, yayinda shikuma ya duk'unk'une waje d'aya yana sauke numfashi. Yad'an bata dariya amma tadake dankarta tsokanosa. Bayan kamar minti 10 yad'ago yana kallonta da rinannun idanunsa, ahankali ya ce, "ngd my Husna, ALLAH yayimiki albarka. Murmushi tamasa mai kwantar da hankali, tareda wani salon kallo, saikuma tarufe idonta, Dan taji kunya. Yasauke ajiyar zuciya yana murmushin shima, mik'ewa yayi ya ce, " ina zuwa." Ganin yanufi hanyar bayi ta ce, ''yaya mukam tafiya zamuyi kafin mama tafarga bama nan." Juyowa yayi ya kalleta, babu wani mama taga bakwa nan, to tayaya kuka fito yanzu. Yaya wlhy barcifa takeyi, kuma nasan zata iya tashi tunda bata kwanta gaba d'ayaba. Dawowa yayi yana dariya, ya d'auki fodiyo ya manna masa kiss, my son kafad'ama kakarka iyayenkafa suna buk'atar jin d'umin juna. Idanu Asma'u tazaro waje tareda mik'ewa zumbur, yaya wa kake gayama hakan?. Dabaki yanuna mata fodeyo. Kanta kawai ta jinjina tana fad'in kaga banishi mutafi, saida safe. Bai bata fodeyon ba, amma yad'an rage fara'a, towai saurin mikeyine? Koma maganar dana kiraki Dan ita bamuyibafa, jiba agogo ko tara batayiba. Asma'u ta langa6e kai gefe, kai yaya ka tausaya mini plss, ALLAH inajin kunyar mama ainun. To naji muje falo muyi maganar saiki tafi. Babu yanda zatayi dole tabishi falon dantaji maganar dazasuyi d'in........... *_(((S))).....2018_* *_I love you so much my fans_* [1/2, 7:48 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→67-68_* ..........Su Uncle Abdullahi sunyi bincike akan mazajen nasu Suhaima, duk dadai binciken yad'an nuna musu matsaloli. Dan haka suka kira mom dasu Lubna suka shaida musu. Lubna da suhaima suka bad'ama idonsu toka babu kunya sukace sudai zasu auresu ahaka. Babu yanda su Uncle habeb suka iya dasu Dan aganinsu auren yafi yawon gararin dasukeyi. Cikin sati d'aya komai ya kammala, antsaida biki sati biyu kacal. Sai alokacin Ameer yaji labari, masifa yaytayi, ya ce, "kuma babu abinda ya shalleshi. Ransa a6ace yatashi yana fad'in mom dama nazo na sanar miki jiddah ta haihu d'azun, amma 'yar batazo bada raiba. Baki mom ta ta6e ta ce, " ALLAH ya k'yauta gaba." K'ala baice da itaba yakad'e rigarsa yafice. Suhaima & Lubna suka raka bayansa da harara suna zagi. Mom bata hanasuba, Dan itama yanzu haushi. ameer d'in takeji ainun, musamman yanda ya janye kansa daga garesu, komai saidai matarsa......... ★★★ Afalon suka yada zango, ya Umar yazauna saman 2sita, ita kuma Asma'u tanufi kujera mai kallonsa zata zauna. Hannunta ya kamo, tajuyo tana kallonsa, da ido yay mata nuni da gefensa. Itafa harga ALLAH fitinarsa take gudu bawani abuba, amma babu yanda zatayi dole tazauna kamar yanda ya umarceta. Juyowa yayi yana kallonta sosai, itama saita nutsun, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi.... Kuma yak'i magana. Ganin haka Asma'u tad'ago ta kalleshi, muryarta a sanyaye ta ce, ''Yaya ina saurarenka. Kauda kansa yayi daga gareta yana dariya k'asa-k'asa, zuwa can ya ce, "to abani abinci mana." Batareda ta tanka masaba tasauka k'asa ta shirya masa abincin, Dan tasan yafison cin abinci ak'asa. Fodeyo ya mik'a mata sannan ya sauka k'asan. Anutse yakecin abincinsa, lokaci-lokaci yakan d'ago yakalleta yana murmushi. Itakuma ta zun6ura baki gaba tana nuna masa agogo, dan bata k'aunar mama tagane tannan. Ga ya Umar yanata wani cin abinci a yangance tamkar mace. Yana kammalawa tafara gyara wajen, kwanukan ta kwashe tafita dasu zata kai kicin sukai karo da mama a babban falo. Kallon tuhuma tabi Asma'u dashi, itakuma tayi k'asa da kanta tashige kicin, duk kunya ta rufeta. K'in fitowa tayi, har saida tajiyo mama tashiga d'akin ya Umar sannan. A hanzarce tashige d'akinta. Hasiya tabita da kallo tana fad'in yaya Asma'u lfy kuwa?. Bata bata amsaba tashige cikin bathroom. Dariya ta kufcema Hasiya, ahankali ta Ce, "ALLAH yak'ara muku aii." Har mama tadawo d'akin d'aukeda fodiyo Asma'u takasa fitowa daga bathroom. Itama mamar batabi ta kantaba ta kwantar da yaron ta kwanta. Saida Asma'u tagaji Dan kanta sannan tafito cikin sand'a tayi shirin barci ta kwanta, dama mama afalo take kwana.......... *_bayan kwana biyu_* Bayan kwana biyu akasha suna. Anrakwashe an kwalle kuwa, munsha bidiri harda bired'e. Mama kuwa tunda daddare tagudu, aka maye gurbinta da inna baito k'anwar maman. Asma'u taji dad'in hakan, Dan Dama tana tsoron ya Umar gsky. Kar ganin babu kowa agida yamata aika-aika, gata da d'inki ajiki🤪. Zuwa dare taron suna yatashi lafiya, su Asma'u sun samu alkairi sosai, fodiyo yayi goshi. ★★★ Su Lubna ma anata shirin biki na garari, tamkar wata budurwa🤭. Hakama mom bikin ake shiri sosai, aranar alhamis aka sakasu a lalle, juma'a sukayi kamu, ranar Asabar d'aurin aure. ____★______★______★_____ Ranar juma'a da daddare ya Umar yana gidansa wajen 8pm. Yabarsu Harris a shago Dan harsun dawo sunbar muktar da yazeed a mall, saikuma ma aikata sababbi da aka zuba masu dutyn dare. Asma'u da Hasiya, inna baito duk suna afalon, ya Umar da inna baito dai hirarsu sukeyi akan rayuwa. Asma'u da Hasiya kam hankalinsu nakan kallon film d'in Kalan dangi, sai dariya suketa zubawa. Fodeyo na goye abayan Hasiya, tunda aka masa wankan yamma yaketa barcinsa. Sallama suka jiyo daga k'ofar falon, ya Umar ya amsa tareda bada Umarnin shigowa, Dan yaji muryar Sadam Ce. Sadam yashigo ya gaida inna baito, ya gaida ya Umar da Asma'u. Hasiya ta gaidashi. Wata farar ✉ ya mik'ama ya Umar, Yaya gashi wanine yakawo yamzu wai abaka. Ya Umar yakar6i yana jujjuyawa cikeda mamaki, shikam wazai kawo masa letter yanzu?. Sadam yaymusu sallama yakoma shago. Ya Umar ya ajiye takarda yacigaba da hirarsa da inna baito. Saidai k'asan zuciyarsa nata zungurarsa akan ya duba. Warwarewa yayi yabud'e saiga IV ya fad'o, yazaroshi yafara dubawa. Murmushin takaici yad'anyi Dan ganin sunan Luban da Hafiz ajiki, wai harma gobe d'aurin aure su. Acan k'asan zuciyarsa kam abin ya k'ona masa ransa. Amma yadake, Dan bayaso su Asma'u su fahimci komai. Tundaga nanma saiyaji hirar ta gunduresa. Sallama yayma inna baito yashige d'akinsa. Asma'u kam tuni ta karanto damuwa afuskar mijin nata, tunda aka kawo masa takardar dama hankalinta na kansa, so take tabishi dantaji matsalarsa, amma kunyar inna baito ta hanata. Inna baito babu ruwanta, bakamar mamaba, bakomai take saka musu idoba. Saidai idan taga rawar kan Asma'u tayi yawa saita taka mata birki, ta hanyar tuna mata takula da kantafa. Wannan yakansa Asma'u kama kanta. Ya Umar kam yana d'akinsa cikin damuwa, da bak'in cikin abinda Lubna da Hafiz sukai masa. gawani k'arin bak'in ciki Asma'u bata shigo d'akinba har yanzun. Yaja wani dogon tsaki, tareda kai dubansa akan agogon dake manne a bangon d'akin. Wayarsa ya d'auka yafara Neman layin yazeed. Saidai harta yanke ba'a d'agaba, tsaki yakumayi Dan yasan shegen saurin barcin yazeed, duk inda 9 tayi saika sameshi a gado nad'e...... Wringing d'in wayar tasane takatseshi daga dogon tunanin, ganin yazeed ne ya d'auka da hanzarinsa. Kai kasa halan kanacan kana barci?. Dariya yazeed yayi, cikin sigar zolaya ya ce, "malam wanefa barci, inadai shan sharafin soyayyane." d'an iska naji, ya Umar yafad'a cikin 'yar dariya. Shima yazeed dariyar yayi, o namantafa Ashe kai yamzu gwaurone, karna tada maka da hankali....... K'atseshi ya Umar yay saurin yi, malam saurareni ba wannan bane agabanani. Cikin dariya yazeed ya ce, "to miye agabanka Alhaji?. Ya Umar yashiga zayyanema yazeed zancen iv da aka aiko masa. Wata dariya yazeed ya k'yalk'yale da ita, saida yayi mai isarsa sannan ya ce, "haba abokina, kaifa jarumine, yanzu wannan d'an abinne yatayar maka da hankali? Miye Hafiz balle Lubna?. Kaida ALLAH ya azurta da samun nitsatstsiyar mata kyakykyawa, gashi har ALLAH ya baku k'yautar fodiyo. Ai kamata yayi wannan sak'on yabaka dariya ba 6acin raiba. Nidai nasan waye Hafiz, kuma tabbas dawata manufa yakeson auren Lubna, humm itama bazan tayata jajeba Dan ta had'u da daidai itane. Ajiyar zuciya ya Umar yasauke, murya a sanyaye ya ce, "ngd yazeed na fahimta." Yauwa abokina, yanzu abinda nakeso dakai, ka shirya cikin wanka iyaka wanka mu halarci d'aurin auren gobe, kasanarma muktar shima. Sannanfa lokaci yayi dazaka fito kanunama kowa kaima kaine. Dan duk wani 6oye-6oye yakamata yak'are hakanan. Gsky ne yazeed, nima nayi wannan tunan. Hira suka cigaba dayi, yazeed ya kwantar masa da hankali, ahaka har suka koma hirar kasuwancinsu kuma.... Sai wajen 11 ya ajiye wayar, bayan yakira Muktar shima ya sanar masa. (Dan yanzu sun k'ulle tamau su ukunnan, komai nasu tare yake). Harya kammala wayar Asma'u bata lek'oba. Itakam alokacinma tuni tayi barcinta. Abin yabashi haushi, yay shirin barci ya kwanta..... ★.....★......★.......★.......★ Washe gari wajen k'arfe sha biyu ya Umar yashigo gidan, daga shago yake. Asma'u da Hasiya ne kawai a tsakar gidan, Hasiya tanadaga kicin tana girki, Asma'u kuma tana zaune akujera 'yar tsigunno tana d'auraye kayan fodiyo. Hirar Fatee sukeyi suna dariya ya Umar yashigo gidan. Asma'u tamasa sannu, amma saiya d'auke kansa yashige. Ta cije le6enta na k'asan, Dan ita batasan laifin dataima ya Umar ba, tunda safe yaketa wani ciccije mata, lafiya lau yake magana da kowa agidan amma banda ita. Cigaba tayi da wankinta batareda tabi takansaba. Wani haushine yakuma turnik'e ya Umar, haryayi wanka yafito Asma'u bata shigoba. Inna baito ce talek'o daga windown falo takira Asma'u. Asma'u ta amsa tana mik'ewa, hannunta ta d'auraye aruwa mai k'yau sannan taje. Inna baito ta mata dak'uwa, kinci gidanku Asma'u, yanzunan mijinki yashigo amma bazakizo kiji matsalarsaba. Baki Asma'u ta d'an turo gaba, amma batace komaiba. Inna baito ta nuna mata hanyar d'akin ya Umar tana mata fad'a, kudai yaran yanzu saiku haihu goma amma babu hankali ajikinku?, badole kusa mazanku 'yan kalle-kalleba awaje. Yo ALLAH natuba aii yanzu ake gidadanci agidan aure ba daba. Itadai Asma'u tanajiyo mitar inna baito amma tashige d'akin ya Umar. Abakin gado ta iskeshi yana shafa mai. Ko motsi baiyiba barema yad'ago ya kalleta. Tana nan tsaye harya gama shafa mansa, shiri yafara cikin wata dakakkiyar milk d'in shadda wadda tasha Brown d'in sirfani, sabuwa dal, yad'akko sabon takalmi sau ciki Brown ya saka, hularsa zanna Bukar itama Brown da ratsin milk ya kwama, bak'aramin k'yau na d'aukar hankali ya Umar yayiba, yana cikin fesa turare Asma'u tamatso kusadashi, ta madubi ya hangota, Dan haka yakuma tsare gida. Matsawa tayi kusadashi ta amshi turaren zata fesa masa, amma saiya kauce, idonta cikeda da kwallah tarik'o hannunsa, yafara k'ok'arin kwacewa tasaki kuka. Tsayawa yayi cak amma bai juyoba, cikin muryar kuka ta ce, "haba ya Fharuk! Laifinmi namaka haka da zafi? Dahar na cancanci irin wannan hukuncin daga gareka?. Ni bakimin laifin komaiba, yafad'a yana k'ok'arin zame hannunta daga nasa. Kuma rik'ewa tayi sosai tana kuma k'ara sautin kukanta. Bayason jin kuka ta ko kad'an, amma dolene ya nuna mata kuskurenta kodan gaba ta gyara. Kuma k'ok'arin zame hannun nasa yayi, tayi saurin k'ank'amesa ta baya. Ya cije le6ensa sannan yajuyo da ita gabansa, cikin tsare gidan nasa ya ce, "keda laifin, amma kinfi kowa raki?." Kinga kibarni natafi, su muktar na jirana ak'ofar gida. Nidai saika fad'amin laifina. Hummm tom kibari idan nadawo saimuyi maganar, yanzu d'aurin aure zamuje kuma bani kad'ai baneba, gashima sai cud'emin kaya kikeyi ni. Kuma narkewa tayi ajikinsa tana raira kukan. Yasan halin kafiyar Asma'u sarai, rungumeta yayi cikin sigar lallashi ya ce, "tom kiyi hak'u idan nadawo zan fad'a miki laifinki, kuma nayimiki hukumci, yanzudai kimin uzuri na tafi kimji my Queen. Yay maganar yana d'ago fuskarta, Sumba mai k'yau yabata akumatu da goshinta. Dak'yar tayarda tabarsa yatafi. Afalo sukayi sallama da inna baito, yafice sai zabga k'amshi yakeyi abinsa. Sun halarci taron d'aurin auren, Wanda mutane da dama suka halarta. Amma wannan karon akwai banbanci, babu manyan mutane kamar lokacin aurenta da ya Umar, dakuma na Ameer. (Kunsan yanzu rayuwar wani abumma na ganin ido akeyi, dak'asa tarufe idonka wani ya shafeka a babin sabgoginsa kenan). To su Lubna dai sunga dahir, Dan duk manyan k'asarnan abokan mahaifinsu awannan karon babusu kwata-kwata. Ahaka aka shaida auren Lubna & Hafiz, Suhaima & Ramadan. To ALLAH yabada zaman lafiya. Lokacin da aka kammala d'aurin auren, ya Umar, Yazeed, muktar, suka doshi gungun na abokansu, wato Hafiz, salman, Dr jafar, alkasim, Kabeer, Tasi'u dadai sauransu, suna tsaitsaye sunsha anko cikin faraen shaddoji, su adole abokai masu had'inkai da k'ud'i............... Nikam bilynku nace hummmm. 🤫shiiiiiiiiii!!!!!!!. *_(((S))))........2018_* *_Luv you all_* [1/3, 4:10 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→69-70_* ..........Assalamu alaikum. sallamarsu ya Umar tadaki kunnuwansu Dr jafar daketa kwasar dariya suna tsokanar Hafiz ango. Kusan atare duk suka juyo, mamaki, al'ajabi, razana duk tasaukar musu alokaci d'aya. Cikin murmushi su ya Umar suke mik'a musu hannu. Haka suka dinga basu hannayen tamkar sokaye. Tabbas ganin ya Umar cikin shiga ta kamala da dattako ta razanasu, hakama ganin muktar da ya Umar tare yakad'a hantar cikinsu, saikuma ga yazeed ma, towai yaushema yazeed yasamu Umar? Amma ko'a wancan satin yazo majallissa haryake tambayarsu babu labarin Umar dai har yanzu ko?. Sukuma suka shiga gulmar Umar d'in alokacin. Amma yaukuma saiga Umar da yazeed, harda Muktar Wanda basu ta6a tunanin yama had'a iri da ya Umar ba. Sudai su ya Umar ALLAH Sanya alkairi suketa zubawa. Ya Umar yasauk'e kwayar idonsa cikinta Hafiz, fuskarsa d'aukeda wani murmushin mugunta, angon Lubna kasha k'amshi! ALLAH yasanya alkairi abokina, inatayaka farinciki gsky.... Yana gama fad'ar haka yad'auke idonsa daga kan Hafiz. Sosai jikin Hafiz yayi sanyi, gawata kunyar Umar d'in ta baibayesa. Can ya tsinkayi muryoyin su Umar suna musu sallama zasu tafi. Bai fargaba saida ya hango ya Umar zaune a mazaunin direba, yazeed na gefensa, muktar na baya, duk cikinsu babu mai irin kwatankwacin motarcan...... Dr jafar ne yafara jan tsaki lokacinda motarsu ya Umar ta shillah sukabar wajen.... Mtsoow wai wancan wawan waya bashi motane?. Salman yaywata dariyar mugunta, yo kaimadai Kasan ta munafikin canne yazeed, kokuma wannan dasuke tare, muktar yake kowama? Mtsoww. Kabeer yay kwafa yana fad'in aikin banza kawai, Dan anbashi aron kaya da mota, shine zaizo yana mana wata burgar banza. Dabamusan asalin balbelaba, dasai tace mana daga masar take. Tasi'u dayay shiru yana jinsu, danshi tabbas jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya ya ce, "kai abokaina, anya kuwa Umar bai warkeba? Idan mumce Aron mota da kaya aka bashi, to kwanciyar hankalin dake tartare dashifa?. Kunga kuwa yanda Umar yayi k'iba da haske? Wlhy fatarsa har wani walk'iya takeyi. Nikamarma yafini k'yan jiki, nidake kwana na tashi a AC. Zasu hayayyak'oma Tasi'u, alkasim ya dakatar dasu, kai kutsayafa, wlhy maganar Tasi'u gsky ce, tabbas akwai wani Abu ak'asa dangane da Umar. Hafiz dai yakasa cewa komai. Suma sauran kowa yayi gum yana dogon nazari........ Na ce, " hummm, kowadai yadaka rawar wani, aiya rasa turmin Daka tasa..... ★ Acan kuwa su ya Umar tunda suka tafi suketa shek'a dariya. Cikin dariya Muktar ya ce, "wai kunga idanun Hafiz kuwa, kuru-kuru... Hhhhhhhhhhh!!!. Suka tuntsure da dariya, yazeed ya ce, ''ai duk mamaki ya kashesu k'ananun 'yan iska kenan. Wani abuma sai sunganka a kasuwa Umar. Hhhh Ya Umar yay dariya harda dukan sitiyari, wai nifa abinda yabani dariyama shine kallon da Tasi'u da Alkasim sukemin, kaikace yau suka fara ganina. Ina kalon salman harda ta6a gefen rigata yaji wace shadda na saka. Haka sukaita hira suna dariya, daga nan gidan yazeed suka wuce. A can sukaci abincin rana mairai da lafiya Wanda matar yazeed tadafa, Dan yanzu Alhmdllh ta iya girki, yanda su ya Umar sukaita Santi sai yazeed yaytajin dad'i aransa, lallai shawarar Umar d'in tamasa amfani, danshi ya ce, ''yasakata makarantar koyon girki. Gashi kuma shawararsa tayi musu dad'i su suka, Dan yanzu ko yawan fad'an nan basayi da ita. Saida sukayi sallar la'asar a masallacin anguwar su yazeed sannan muktar da ya Umar suka taho sukabar yazeed a gidansa. Da sallama yashigo gidan nasa, ganin takalma reras ak'ofar falon yasashi jan birki, Dan muryoyin mata yake jiyowa dayawa sunata hira da dariya. Harya juya zai koma saiga inna baito tafito daga band'akin tsak'ar gidan. A'a Umaru kadawo?. Eh wlhy inna, ya gidan?, wani biki ake haka?. Dariya inna baito tayi, ta ce, "a'a su Sa'adatu nefa. Kallan takalman yakumayi, ya ce, " inna amma naga talkalmane reras, harsu nawane?. Su 6 ne, fatee, Rafi'a, kaltume (d'iyar inna baito Ce), Sa'adatu, saikuma Saddiqa matar muntari. O wlhy nama zata wasu bak'ine daban. Shida inna baito suka shiga. Saddiqa naganinsa tatashi tana musu sallama, dantasan itama nata mijin ya dawo, gaisawa sukayi da ya Umar tatafi. Shima ya zauna suka gaggaisa, Anty Sa'a ta ce, "Umar wannan d'aukar wanka haka? Daga ina?. Shafa kansa yayi yana dariya, idonsa akan Asma'u dake tsiyaya masa ruwan sanyi a cup, ya ce, " Anrty Sa'a d'aurin aure mukaje wlhy." Tofa, waye yayi aure a irin wannan time d'in haka?. Ya Umar yakar6i ruwan da Asma'u take mik'o masa, yad'an ta6e bakinsa sannan ya ce, "wani banzane,.... saida ya shanye ruwan sannan yajuyo yana kallon su Anty sa'a dasuka had'a baki wajen fad'in banza kuma!!?.'" O sorry, wani abokina zance mukufa. To ALLAH ya sanya lkairi suka fad'a atare. Ya Umar yamik'e tsaye batareda yace aminba. Asma'u ta ce, "Abincifa?." Shiru yayi yashige d'akinsa. Anty Sa'a ce ta ce, "mata tashi kibishi d'akinsa, waya gaya miki ana tambayar miji yanason Abu acikin mutane? Asma'u nakula sainayi training d'inki gsky akan kula da miji." Shiru Asma'u tayi tamik'e zuwa d'akin ya Umar, tanata tunane-tunane aranta, ita kanta tana ganin wataran kamar batayin abunda yakamata wa mijinta, to amma tayaya zata gyara? Gsky itama tanason taga suna rayuwa da mijinta kamar yanda akeyi acikin Hausa novels, abin Na birgeta sosai, musamman data kula ya Umar d'an son soyayyane. Itama tanason soyayya, to amma saita rasa yanda zata nunama ya Fharuk d'inta, Dan ita mutumce mai kunyar tsiya, dukda tad'anyi karatunta har zuwa diploma, yakamata kuma ace kanta yawaye, amma matsalar da'aka samu shine harta gama karatunta batada wata k'awa, k'annenta sune k'awayenta, wannan yasa batasan wasu abubuwanba dayakamata mata tanayima mijinta danya zama NATA ita kad'ai. Kamar yanda Anty Sa'a ta ambata to zata nutsu danta samu training d'in kama ya Umar d'inta ahannu ita kad'ai.......... Tunda tashigo yake binta da kallon mamaki, shin mike damun matar tashine haka? tana tafiya tana tunani?. Shigowarta takai minti 15 a tsaye, amma alamu sun Nina masa bamata tareda duniyarsu baki d'aya, hankalinta yatafi zuwa wata duniya tadaban. Ya girgiza Kansa tareda tasowa har zuwa Inda take atsaye tana cigaba da sak'a wasik'ar jakuna. Bata ankaraba saitaji an d'alli bakinta. Cikin Sauri tasaka hannunta tadafe bakin, tareda kai dubanta gamai mata wannan aika aikar haka. Ya Fharuk ne tsaye agabanta, yacire kayansa dagashi sai best da gakeren wando, ya hard'e hannayensa ak'irji idonsa k'ur akanta. Ta sauke ajiyar zuciya ahankali sannan takauda kanta. Ajiyar zuciya ya sauke shima tareda warware hannunsa, Asmah kinada gyara sosai ta hanyar kula dani wlhy, akwai abubuwa masu yawa dakikemin inajin dad'insu dakuma yaba miki. Akwaikuma masu yawan gsky da idan kikaimin suna 6atami6n rai, nidai asanina mace kullum k'ok'arinta yanakan tarairayar mijintane, ammafa ke agareki Bahaka baneba. Tabbas abinda nagaza samunsa abaya sanda inatareda Lubna nasamesu agareki, harma mafiyansu, saikuma abinda nake samu ga lubna kekuma bakiyiminsu. Asma'u ni mutumne maison zama da wayayyiyar mace, bawai wayewa ta rashin kunyaba, wayewa irinta zamantakewar aure, nifa a ganina idanhar mace tanason mijinta yazama NATA 100% tofa saita zama Mara kunyar k'arfi da yaji.KeKekuma kunyarki tanad'an cutar damu gsky.. Duk wannan magamar da ya Umar keyi Asma'u natsaye idanunta Na zubar da hawaye, tabbas tasan akwai gazawa a al'amuranta Na kula da mijinta, amma tana buk'atar shawara. Suduka kowa yayi shiru, ita tana kuka, shikuma yatsura mata idanu yana kallonta, amma yakasa wani yunk'urin lallashinta. Sunkai tsawon minti 7 ahaka sannan ya Umar Yakama hannunta suka koma bakin gado suka zauna. ganin kukan NATA bamai k'arewa bane yasakashi jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa bayanta alamar lallashi, amma uffan baiceba. Nanma saida sukaja wasu lokuta sannan Asma'u tad'ago tana kallonsa, ya Fharuk Dan ALLAH kayi hak'uri zan gyara, Nima kaina inaji a raina akwai abubuwan danakeyi ba daidaiba, amma rashin nunawarka yasa bana fahimta sosai balle na nemo hanyar gyaran. Murmushi ya Umar yayi yana kamo hannunta, to yanzun Na nuna da kaina my Asmah, saiki gyara ko? Namiki hakane saboda kar agarin sakakinkifa Na hango wata awaje ta kwace miki ni. Yay maganar cikeda zolaya yana d'age gira sama. Bakinta ta turo gaba, ni wlhy kabar fad'a, ALLAH banason kishiya. A indaifa kina sakaci da rik'ona aiko zata kwankwaso miki k'ofa, dama ga d'aki nan inadashi. Jibafa tun kayan danatafi nabarki dasune ajikinki, tunfa na wankan safene, nasan kuma bazaki ciresuba sai wankan barci, amma sanda kina amarya bakyayin wannan kazantan? tundagadai cikin fodeyo kika fara wannan abun, gashinan yanason zame miki jiki. Shiru tayi tana kallon hannayensa masu laushi da santsi dake rumtse da nata, tasan gsky ya Umar duk yake fad'a mata. Ganin tayi shiru yad'an girgiza hannunta, kifayi hak'uri badan cin fuska nake fad'a miki hakaba, inaso kigyarane Dan nazama naki kekad'ai da yaranmu my Husna, inasonki dayawa, shiyyasa banason wani Abu yazo yasaka sonnaki yin rauni azuciyata kinji, tunkina 'Yar k'aramarki nake sonki har kika girma..... Da sauri Asma'u tad'ago tana kallonsa, yamata murmushi, baki yardaba ko?. Shiru tayi batace komaiba, ya matsa hannunnata, takuma d'agowa tana kallonsa. Muryarsa can k'asan mak'oshi ya ce, "nasan kema kina sona aii, amma kikaita 6oyewa, amma ni tuni naganoki. Ban gaskata hakanba sai aranar da aka sakamin rana da Lubna. to karki damu, yauga Umar fharuq mallakinki ke kad'ai da fodiyonmu. Ammafa idan kika cigaba da sakaci zai samo miki mai tayaki kula dash.... Ai bata bari yak'asa fad'aba tafad'a jikinsa ta k'ank'amesa tareda sakin wani kukan shagwa6a. Shima saiya rungumeta yana dariya, 'yammata bimin kanki ahankali karki 6allomin ruwa d'inkin yafarke nashi 12. yakamatama nakira Dr Al-Ameen naji yaushe zamuje a kwancene?. Itadai tana lafe ajikinsa tana shashshekar kuka. Cikin 'Yar dariya ya ce, ''nasan inda wannan kukan yadosa da abinda kikeso, bara kigani namiki kar asaka uwata awak'a. d'agota yayi ya manne bakinsu waje d'aya. Tun Asma'u na mutsu-mutsin kwacewa hartayi lif itama tafara bada gunmawarta.... Hummm masu karatu! Wata sa'in muma matafa akwaimu da gulmar tsiya aradu🤔🤪. ♣♣♣. Tundaga ranar Asma'u da ya Umar suka shirya, yanzukam abubuwan datasan yanaso komai kunyar datakeji haka take dannewa tamasa. ga Anty Sa'a daga gefe tana koyar da ita wasu darussan. hakama inna baito, tunda ta fuskanci Asma'u sokuwace saita d'auki d'ammarar kowa mata yanda zata kula da mijinta. Ayanzukam shikansa ya Umar yaga canji sosai, farinciki yacika zuciyarsa, wani son Asma'u nak'ara ratsa jijiya da 6argo zuwa jininsa. Shima tattalinta yakeyi sosai. Yakaita asibiti an kunce d'inkin CS d'inta, Dr Al-ameen kuma yabasu shawarar yanda zata kula da kanta batareda samun matsalaba, yakuma bata wasu magunguna. Har harabar asibitin yarakosu hannunsa d'aukeda fodiyo, yanata yaba k'iba da lafiyar yaron, gashi masha ALLAH k'yak'yk'yawa son kowa k'in Wanda yarasa. Gaban Dr jafar yafad'i Dan hango su Umar tsaye sunata dariya shida Dr Al-ameen cikeda nishad'i. Ga Asma'u agefensu cikin k'yak'k'yawar shiga ta alfarma, shikansa ya Umar d'in sanye yake da wata d'anyar shadda blue sai maik'o takeyi, tad'inku da d'inkin zamani, ga hularsa k'ube ya Murza mai adon farin zare da ratsin blue. Sai annurin farin ciki da kwanciyar hankali suke fitarwa. Ganin ya Umar yakar6i Fodiyo daga hannunta Dr Al-ameen, Dr jafar ya ce, "kai, dama matarsa ta haihu?. Dukda sunad'an nesa dashi yana hango k'yak'yk'yawar fuskar fodeyo, da a ka masa kwalliya da milk d'in kayan sanyi na alfarma, ya sauke wata ajiyar zuciya alokacin da ya Umar yabud'ema Asma'u mota tashiga, ya rankwafa ya saka mata fodiyo akan cinya, wannan yarufesu yadawo sukai sallama da Dr Al-ameen shima yashiga motar suka tafi. Jikinsa har rawa yakeyi yashiga motarsa shima sai majallissa kai rahoto, Dama yatashi daga aiki Dan yamma tayi............ 🤣🤣🤣🤣🤣. *_Amarya Lubna_* Su Lubna amarya, antare akatafaren gidan data samu gado, Dan tace bazata zauna gida d'aya da matar Hafiz ba, a gidanta zata zauna. Babu musu ya yarda kuwa. Komai na alfarma tazuba agidan, kud'inta kam bak'aramar girgiza sukayiba, ga 'yan aiki data Loda agidan, kowa da aikinsa, harda masu yimata tausa daban. Amarci kam itada Hafiz ana dirzarsa, jitake kamar yanzu tayi auren farko. Tamanta da kowa da komai, komai NATA sai Hafiz. Shikam tarairaya iya tarairaya yake Nuna mata, matarsama ko lokacinsa bata samu, barema 'ya'yansa da iyayensa. Danginsa kam babu Wanda ke zuwa gidan, Dan Lubna tasaka dokar batason had'in gambiza. Dayake lalla6ata yakeyi saiya yarda da zancenta, babu kuwa mai zuwa musu gida, shikam aii yazama mijin Hajiya, danko kwayar gero baita6a ajiyewa a gidanba, komai da kud'in Lubna akeyi tunda ta nuna tanadasu. Suci mai k'yau su saka maik'yau, suyi barci amai k'yau, dama su Amrah awajen mom aka barosu dansu d'ebe mata kewa.... *_Suhaima_* Itadai Suhaima akwai banbanci da Lubna, Dan ita amarcin NATA yazo da gargada. Ashe Ramadan d'an talakawane lik'is, irindai matasannanne masu son k'arya da burgar tsiya, shine Aron kaya shine na mota, dawannan abubuwan yabige tunanin suhaima harta amince ta auresa, Dama kuma tun awaje suke shek'e ayarsu. Sai lokacin da'aka kaita taganta awani d'an gida kamar BQ d'in gidansu, aiko ranar kwana sukayi tafka bala'i. Dole washe gari ya yarda suka koma gidanta data samu agadonta itama. Hakan yamasa dad'i kuwa, Dan kobabu komai ansamu cigaba, dama wancanma babansane Yakama masa Hayar, Dan Ramadan baya aikin komai sai tsalle-tsallen 'yanmata. Sune samarin shaho na wannan zamanin. ('Yammata sai ayi hattara da samarin shaho, Dan akwai irinsu Ramadan dayawa suna yawo cikin duniya). *_(((S)))......2018_* *_Luv you all_* [1/4, 4:45 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→71-72_* ..........Kiyyyyyy!! Yaja wani wawan birki agabansu. duk arikice suke kallonsa, Salman da shima isowarsa kenan yasa k'asan rigarsa yana toshe hancinsa saboda wata k'ura da Dr jafar ya tayar awajen. Ganin yanda yafito abirkice yasaka sauran mik'ewa gaba d'aya, har sassarfa yakeyi yana had'a k'afa kamar zai kifa Dan k'ok'arin k'arasawa inda suke zaune. Saidai kuma yana zuwa garesu kallonsu yacanja akala daga gareshi zuwa bayansa, Hafiz da Kabeer hard'an tureshi gefe sukeyi danson kallon abinda suka gani sosai. Shima sai kawai ya waiga domin bawa idonsa abinci. Motar ya Umar ce ta tsaya awajen, gaba kad'an da motar Dr jafar. Fitiwarsace taja hankalinsu wajen kallon mamaki agaresu. Shikam koma Inda suke bai kallaba, ya zagaya inda Asma'u take yabud'e mata k'ofar, fodeyo tafik'o masa, yakar6eshi hannu biyu yana murmushi da fad'in yauwa my dear son! Yau kanashan yawo ko?. Asma'u tafito tana murmushi, yaya shima aii gara yasan gari ko?. Cikin kallon k'auna ya ce, ''Kodai ke kinaso kiga garin? yafad'a tareda lakace hancinta. Dariya sukayi gaba d'aya sannan suka jera atare suka nufi ainahin cikin mall d'in, ya Umar na rungume da fodiyo, ga Asma'u a gefensa cikin farinciki. Su Hafiz kuwa tamkar sokaye haka suka dafama su ya Umar baya da kallo. Tun a k'ofar wajen masu bud'e k'ofa suka fara rissinawa suna kwasar gaisuwa wajen uban gidansu. Shikam cikeda fara'a irinta sanin hak'k'in d'an Adam yake amsawa, da nuna musu iyalinsa. Sunajin haka suka rissinawa suna gaida Asma'u itama. Acikima bata canja zaniba sai rissinawa ma aikatan sukeyi suna kwasar gaisuwa. Masu siyayya kam sunyi tsai tsaye suna kallonsu ya Umar d'in. Wasu 'yammatanma harsun k'yasa😉. (Kunsandai rayuwarnan indai kanada 'Yar daud'ar duniya, to yanzu zakaga 'yan mata Na rawar kai akanka). ALLAH yasa mudace. Da Sauri sadam yataso ya tarbesu, kar6ar fodiyo yayi daga hannun ya Umar tareda gaishesu. Cikin zolaya Asma'u ta ce, ''lallai Na Rafi'a dolene kuyi Fari kaida ya Harris, Ashe kullum cikin Ac kuke wuni?. Dariya sadam yayi, kai antymu kin iya Sheri wlhy, amma nidai bazance komaiba harsai kin bani Rafi'a zakiji bakina. Dayawan mutanen dake gurin saida suka dara, Asma'u ta birge dayawan mutanen wajen, Dan da watace matar mai irin wannan wajen ai da irin shegen mai girman kannan za'ayi, da d'aukar kai, amma jiba yanda take wasa da dariya da ma'aikatan wajen. Dukdadai da alamar sanayya tsakaninta dashi, amma ta birgesu gskiya. Ya Umar dake musu dariya ya kamo hannunta, kinga my Husna bar shiriritarnan idan kunje gida kwayi, muje kisayi abinda zaki saya mu wuce. Kallonsa tayi cikin langa6e kai, yaya sayafa? Muda shagonmu?. Cikin tsokana ya ce, "kema saikin biya aii". Juyawa tayi tana kallonsu Harris da hankalinsu gaba d'aya yake kan Fodiyo suda wasu ma'aikata, Baki tad'aga zata kira Sadam, ya Umar yasa hannunsa ya toshe bakin. K lafiyarki kuwa? Mizakiyi?. Kiransu zanyi naji waye ya kafa dokar?. Cikin dariya ya Umar ya janye hannunta suka shige wani d'an d'aki, Ashe Office d'insane awajen. K'ofar yamaida yarufe yana dariya, kai my Husna ALLAH ya shiryaminke?. Itama dariyar tayi tanabin ko'ina Na falon da kallon. Manya-manyan hotunansu guda biyar tagani a kowace kusurwa ta office d'in, itadashi da fodiyo, akowace kusurwa, saikuma asaman tebur d'in an ajiye wani madaidaici itadashi nanma da fodiyo. Kallonsa tayi, shikuma ya d'aga mata gira yana murmushi. Itama ta sakar masa da murmushin tareda zuwa ta rungumeshi, hannu biyu ya kar6eta shima ya k'ank'ame kayansa, burinsa kullum yaga Husnarsa cikin farinci, yarinyar data masa hallacci alokacin damutane masu yawa da muhimmanci arayuwarsa suka gujesa, yarinyar dake sonsa Dan ALLAH badan dukiyarsaba, yarinyar data sadaukar daduk wani farincikinta domin NASA ya inganta, yo idanma yagaza Nuna mata k'auna aii yayi butulci mai yawa..... Asma'u tad'ago tana kallonsa, amma fuskarta tad'an sauya, cikin langa6ewar kai ta ce, "ya amma banga su twins ba?." Shima fara'arsa ya rage, sannan ya kauda zancen ta hanyar cewa muje yamma nayi karmu kwasarma fodiyo sanyi yazo yana mura. Komawa tayi takuma k'ank'amesa, yaya kabani amsar tawa tambayar mana. Wannan ba maganar nan bace, bari saimunje gida. Baijira amsartaba yafice abainsa. Itama dolene ta take masa baya Dan tasan halin kayanta sarai. Ak'ofar office d'in tasameshi yana jiranta, ahankali suketa zagayawa suna d'aukar abinda suke buk'ata, dawanda fodiyo yake buk'ata, harda Hasiya da inna baito dazata koma gobe idan ALLAH ya kaimu. Sosai suka Lodi abubuwan buk'ata, suna gamawa wani ma'aikaci yazo ya kar6i kayan, wajen kashiya's yaje Harris da sadam suka kar6a akai total. Amamakin Asma'u saitaga ya Umar yaje yabasu ATM d'insa sun cire kud'in, aranta ta Ce, "Ashe da gsk yaya yakeyi. Bayan sungama komai tsaf suna shirin fita saiga Yazeed da Muktar sundawo daga wajen aiki, dama haka sukeyi, idan suka dawo saisu lek'o suga yanda komai yake tafiya kafin sutattafi gida. Juna suka rungume suna murna. Muktar ya ce, " mutumina kace soyayya kafito?. Dariya ya Umar yayi tareda fad'in ALLAH yashiryaka Muktar. Ameen suka fad'a cikin dariya. Asma'u ta gaidasu da tambayar aikinsu, duk suka amsa cikin fara'a sannan yazeed yakar6i fodiyo yana fad'in kud'an rakamu wani waje mana kaida madam. Ya Umar ya ce, ''to aja zuga!, ina kuma zaka kaimi? Mudake shirin tafiya gida?. Kudai kubiyoni kawai. Haka kuwa suka rankaya suka tafi, Asma'u Na a bayansu. Ganin inda suka dosa ya Umar yaja tunga. Cikin had'e fiska yazeed da Muktar sukace babu jayayya a tsakaninmu. Ya Umar baice komaiba yakad'a kai suka cigaba da tafiya har majallissarsu Dr jafar. Suna ganin sun nufosu kuwa sukayi gum daga sambatun surutun dasukeyi tun d'azun akan ya Umar. Hannu sukaita basu ana gaisawa, duk jikinsu yayi sanyi, yazeed yamik'a musu fodiyo, to 'yan uwa gafa Usman fodiyo, ankawoshine shida madam domin Susanya albarka awajen dadynsa Umar daya gyara. Kalan kallon aka fara, salman d'aya kar6i fodiyo yayi murmishin takaici, aransa ya ce, ''gashi k'yak'yk'yawa kuwa. Asma'u ta ce, "ya gajiyarku ya iyali? Idan bazaku damuba muna gayyatarku walima ta mik'a godiyarmu ga ALLAH akan ni'imomin daya azurtamu aciki, ga d'aya daga cikinan shine gyara mall d'inmu daya dawo kamarma wuta bata cishiba, na biyu shine ku6utar kayan ya Fharuk daga hannun custom, na Uku shine albarkar haihuwar fodiyo da ALLAH ya azurtamu dasamu. Yanda take magana adake tayi mugun basu mamaki, shikansa ya Umar kallonta yakeyi cikeda al'ajabi da birgewa, baita6a tunanin matar tasa jaruma baceba sai ayau. Dukda dai yasan dama Asma'u akwai tsiwa, amma azatonsa ta daina. Muktar da yazeed kam bak'aramin birgesu Asma'u tayiba, Dan sai zabga murmushi sukeyi. Tana gama fad'a kuwa ta ce, " inafatan zaku amsa gayyatarmu, nabarku lfy, yaya idan kun gama INA mota, tajuya cikin takun girma tabar wajan. Duk binta sukayi da kallon, saikuma kishi yata6a zuciyar ya Umar, dad'an k'arfi ya ce, "malamai kallon ya Isa haka, ko kun manta matar aurece?. Ajiyar zuciya suka sauke suduka, kowanne yanamai janye idonsa daga kanta. Yazeed yamik'a hannu ya kar6i fodiyo dahar yanzu yake a hannun Salman, sai wani k'ara k'ank'amesa yakeyi tamkar nasa.. 😉 Yana kar6a suka bar wajen, acikinsu Dr jafar babu Wanda ya iya koda kwakwkwaran tari har su muktar suka kai ga mitar Ya Umar. Asma'u naciki yazeed yamik'a mata Fodiyo, sannan ya ce, " madam sannu da k'ok'ari, aibansan haka kema kikeba da jarumta. Dariya sukayi gaba d'aya, ya Umar ya ce, "tab, ai dama Husna matsiwaciyace, Ku kawai takema alkunya, koba hakaba tawan? Yafad'a yana d'aga mata gira. Harar wasa Asma'u tama ya Umar ta ce, ''bandadai Sheri my boss." Nanma dariya sukeyi sosai. Su Tasi'u duk suna kallonsu, kuma azatonsu su sukema dariyar, Dan haka duk jikinsu yakumayin sanyi, wasuma harsum fara nadamar abinda suka aikata ayau. Ya Umar yatada motar sukayi sallama dasu yazeed suka tafi. Dayazo saitinsu Dr jafar ma saida yad'aga musu hannu, amma ko tari babu Wanda yayi acikinsu, Dan duk sunyi gum, tundasu ya Umar suka bar wajen babu Wanda ya iya cewa A acikinsu, saidai kallon kallon kawai da zare idanu. Nikuwa na ce, "hummmm. __________________________ Ahanya ya Umar da Asma'u sai hirar abinda yafaru sukeyi suna dariya. Dahaka har suka isa gida. Ya Umar yakwashi ledojin itakuma tasa6i fodiyo suka Shiga. Afalo suka iske su hasiya da inna baito sunacin tuwo. Bayan sun musu hannu suka zauna, ya Umar ya ce, " inna yau tuwo akamana?." Wlhy tuwo nayi Umaru, nidai nagaji dacin shinkafarnan. Aii wlhy inna kin taimakemu, nikaina bawani damuwa nayi da irin wad'annan abubuwan naiba, nifa aka bani tuwo to anmin dai-dai. Amma su o, e, aii ba'aso, saidai kayan kwad'ayi. Asma'u datasan da ita yakeyi, ta cuno baki gaba amma batace komaiba. Ya Umar yace nidai kar aji haushina bankira sunaba dai ko Hasiya?. Oho dai, aikowa yay zagi akasuwa yasan dawanda yake. Cewar Asma'u tana Barin wajen. Dariya suka rakata da ita suduka. Ya Umar ma yamik'e yana fad'in inna bara na rage kayan jikina naje massalaci, danyau zaman cin tuwo zamuyi. To Umar afito lafiya. To innarmu, gobe iyanzu munyi kewarki wlhy, dama kiyi zamanki taredamu kawai, zamuyi farinciki wlhy. 'Yar dariya kawai inna baito tayi, ta ce, "a'a Umar, mijinafa?. Saidai kuma haka inna, amma jimuke kamar karki tafi. Dariya kawai inna baito tayi. shikuma yashige d'akinsa. *_Lubna_* Zaune take a k'ataccen falonta, ta mik'e k'afafu gabanta kayan fruit ne da aka yanka k'anana, gefe kuma ga farfesun kaza daya gama had'uwa. Nikaina 'yar rahotonku saida yawuna ya tsinke😋. Ahankali takeci tamkar bataso, gefe kuma masu aikintane kemata tausar k'afafunta. Wayarta dake wringing tamik'a hannu ta d'auka, ganin mai kirannata yasa murmushi fad'ad'a afuskarta. Hello Hajja Sadiya ykk?. Daga can aka amsa mata da lfy lau Hajiya lubna, dama kayane suka iso shine nace bara na sanar miki kafin mutane su za6e. Wani murmushin k'asaita Lubna tayi, tareda danna tsokar nama abakinta, cikin tauna naman ta ce, "OK Hajja sadiya ngd fa, zuwa anjima kad'an zan shigo insha ALLAH, Dan munada biki satin sama. To shikenan ALLAH ya kaimu lafiya. Uhum tafad'a tana ajiye wayar batareda ta yankeba. Kad'an takumacin naman ta tureshi gefe tana yatsine fuska. Bilki akaimin fruit d'innan cikin firij saina dawo zansha. Tayi maganar idonta akan 'Yar aikin dake dama da ita. Cikin hanzari kuwa bilki mai aiki ta amsa, d'aukatayi tanufi kicin domin cika umarnin madam. Lubna kuwa d'aki tashiga, aka sake sabon wanka, cikin shiga ta alfarma, saigata tafito rik'eda key n mota, da k'aramar handbag mai azabar kyau. Takun lubna kawai abin kallone, Dan tabbasa 'Yar gayuce ta fad'a da k'ari, komai nata mai ajine🧐. Motarta tashige sai gidan Hajja sadiya dillaliya, amma mai lasisi, dankuwa kayane Na manyan k'asa take kawowa. babu tambayar miji atsarin Lubna, ayayinda zata anguwa, saidai yazo ya iske bata nan. Yanzuma tana fita yana shigowa anguwar, yad'anga gilmawar motarta, amma zuciyarsa bata amince itad'in baceba. Saida yashigo harabar gidan ya faka tashi motar sannan yakula babu d'aya daga cikin motocin Lubnar. (Dan kuwa motar Lubna ak'alla takai hud'u agidan, kuma duk Na gararine da nunawa sa'a). Baice kimaiba yanufi cikin gidan............. *_(((S))).......2018_* *_I Love you all my fan's_* [1/6, 5:08 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→73-74_* ..........Babu kowa afalon sai k'arar AC dana TV. Su bilki sunacan kan sauran farfesun da Lubna ta rage sunaci itada saude. Cikin d'akinta ya k'arasa, ko INA k'al yake, dama a 6angaren tsafta bashida Matsala da Lubna, dukda dai 'yan aiki keyi ba itaba, saman sofa ya kwanta yana k'arema ko INA na d'akin kallo, amma zuciyarsa da tunaninsa nakan ganin da sukaima Umar ayau. Lallai suma sunsan Umar yagama kama k'asa, kuma kaf d'insu yafisu komai. Dama can yafisu d'in, ayanzuma garashi dayake auren Lubna kud'i sun k'ara zauna masa. To amma aii banasa baneba, dan yamzudai kam Lubna babu abinda bata fishiba, koda kaddarorin data samu a gadonta sun Isa ta keremasa sa'a, shiyyasa yakula take kallon kanta samadashi. Wata kwafa yayi yana kad'a kai, yakula idanfa yatsaya jiran ya huce, tofa rabon wani zai ratsa. Da sauri yatashi zaune, haryanzu yana a duniyar tunani. Tabbas a farko ya auri Lubna ne dansu bak'anta zuciyar Umar. Ammafa ayanzu tunaninsa yafara sauya akalar tafiya wani 6angare. Yatuna da maganar Kabeer alokacin dasuke kulla wazai auri Lubna d'in?. *_tab wlhy dabadan matana biyuba, kuma ko sati biyu ban k'ullah da k'ara aureba, ga dokar da dady yasamin akan k'aro ta uku, toda wlhy nizan auri Lubna koda Umar zai mutu. Sannan ita kanta saina tatseta tas, dan fak'iriya ta gsk zan maisheta aradu kuwa. Suma aii Tara musu akayi, kunga kuwa nima saina dangwali arzik'i._* Alokacin Hafiz babu haka kokad'an aransa, da zuciya d'aya ya amsa zai auri Lubna tunda yad'an fisu k'yau da kud'i, kaitsaye zatafi kar6arsa fiye dakiwa a majalissar. Ya wani mik'e tsaye yana tafa hannaye, _"ni shegiya inji d'an daudu!"_ dazanma kaina sabalula, baijira wani dogon tunaniba yafara bincike ad'akin Lubna, duk wasu muhimman takardu Na filaye da gidaje Na Lubna saida ya lalubesu Tas, k'ananun kawai ya bar mata, yana gama had'awa Yakama hanyar fita, harya kai falo saikuma yadawo, wani tunanine yazo masa, baikamata yakwashe komai lokaci d'ayaba, Dan tabbas zata gane shine. Saikawai yajuya yamaida komai, takarda d'aya ya d'auka da wasu kud'i 200k daya gani a dirowar gefen gado yafita zuwa gidan Uwargidansa, dama yau itace dashi, yazo yima Lubna sallamane kawai. Lubna tana zaune dirshen gaban Hajja Safiya, kaya kawai taketa lodama kanta Na garari, Hajja sadiya kam saida dad'i takeji, dama tasan Lubna babu wasa, data saya zata Baka kud'inka, gashi kuma zata yaya dayawa, Dan yanzu batada babbar customer kamar Lubna. Saida ta Lodi kayan 2millions NATA Na kanta, sannan shima Hafiz ta d'iba masa. (Yo ba ita tataraba, batasan zafinsuba, sanda aka nema tana gado tana barci hankali kwance)😎. Aledoji Hajja Safiya ta jibga matasu, tasaka 'yan aikinta sukaita kaiwa mota, todama kayan bawani d'inbin yawane dasuba, tunda Na 'yan k'aryane, daga less d'in 300+, sai tanfar 200+, hakama gyale dukna manyanne, barema takalma da jaka, ga yari da kayan kwalli, Dan komai Hajja sadiya saidawa takeyi. Amma dukda haka saida bayan motarta da but suka cika taf, Dan Lubna nason kayan Hajja sadiya, tana siyo kaya masu k'yau da Qualities, gasu designers. Shiyyasa bata k'yashin kashe konawane ta kwashi kaya, dama ga kud'in abanza ana gani. Sallama sukayi da Hajja Safiya taja mota tatafi, sai gida........ 'Yan aikinta ta tura suka kwaso kayan amota, ta kalli bilki amintacciyar mai aikinta kenan, bilki my Sugar yazo gidannan kuwa?. Eh Anty yazo babu dad'ewama yatafi, inaga yagaji da jiran dawowarkine. Baki Lubna ta ta6e batareda tace komaiba. Bilki da sauran 'yan aikin suka fice, itakuma tafad'a bathroom Dan tayi wanka........ ___________________________ Safwan kaine ka iya tunawa damu agidannan haka? Kodai 6atankai kayine haka?. Wata 'Yar dariya Safwan dake gaban mom zaune yayi, mom dama kuna raina wlhy, yanzuma muhimmin abune yakawoni gareku, amma saina k'ara hutawa zamuyi maganar. To shikenan, ainama godema ALLAH dana ganka yanzuma, jeka huta to, bara nasa ashiryamaka abinci. To mom, amma yanaji gidan shiru? Inasu baby?. To ka gujemu ina zakasan mike faruwa agidanku, baby da suhaima sunyi aure, yanzu dagani sai su twins agidan. Kai yanzunan mom su baby sunyi aure?. Amma banji dad'iba da akayi bananan, ALLAH ya sanya alkairi to. Insha ALLAH dukzanje gidajensu. Matar Ameer fa ta haihu?. Baki mom tad'an ta6e, ta haihu amma 'yar batazo daraiba. Ayya my bros ALLAH ya canja damai alkairi, itakuma ALLAH ya jik'anta. Mom dai batace komaiba, amma mamakin canjawar safwan takeyi sosai, dukya canja mata, ga wata k'iba dayayi ta alamun yanajin dad'i. Shikam d'akinsa yashige yana wata dariyar mugunta, humm mom dakinsan da shirin danazo gidanan, wlhy datuni kin korani baya, ammafa da ikon ALLAH sainaci nasara akanku..... 😨tofa Safwan dami kazo?. __________________________ Yanda takeyin komai a kasalance yau kamar mara laka ajiki saita bashi mamaki, dukdadai yasan miya assasa sanyin jikin nata, hakan bai wuce tafiyar da inna baito zatayi yauba. Itako bama tasan yanayiba, idonta na kan Fodiyo dake shan nono shima yana kallonta. Inna baito dake kallonsu ta ce, "ALLAH yaronnan kukayi wasa k'iywa zaiyi nan gaba, jibifa ko wata 2 bai cikaba amma yafara sanin fuskar uwarsa. Asma'u ta duk'ar dakai k'asa saboda kunya. Ya Umar kam dariya yayi, inna aii yafara k'iywarma, kikula indai yana hannunta bakajin kukansa, amma inhar wani ya d'aukesa mintuna kad'an zai fara. Cikin zaro idanu Asma'u ta ce, ''kai ya Fharuk, Dan ALLAH kadaina fad'a, ALLAH wani yaji saiya d'auka hakane. Yo da k'arya nakeyi?. Shiru tayi amma tana hararsa ta gefen ido. Inna baito dai dariya take musu. Hasiya kam tana school dan suna zana exam na S,s,c,e. Haka sukaita hirarsu, dukwanda tsokana ta juyo Kansa za'ayi. Har zuwa la'asar da inna baito ta fara shirin tafiya. Yanzu kam hak'urin Asma'u yazo k'arshe, sai hawaye takeyi, daga inna baito har ya Umar dariya suke mata. Suduka suka shirya har Hasiya data dawo gidan, inna baito sukaima rakkiya har gida da shatara ta arzik'i. Godiya sosai inna baito tamusu sannan sukai mata sallama suka taho cikeda kewarta. Daganan gidansu ya Umar suka nufa. Cikin farin ciki mama ta tarbesu, Rafi'a kam kamar ta tashi sama dan farin ciki. Suna nan zaune anata hira saiga ya Abubakar, kallo d'aya zaka masa kasan abirkice yake, baya cikin nutsuwarsa. Suduka da kallo suke binsa, bayan an gaggaisa Asma'u ta zame jikinta tabi su Rafi'a dake d'aki suna magana itada Hasiya, inaga sunayine akan Sadam k'anin Muktar. Mama ta kalli ya Abubakar cikin kulawa sosai, Abubakar mike faruwane haka? Naga tamkar bakada wadatar lfy?. Idanunsane suka cika da kwallah, yasharesu yana fad'in mama Sakina tagama dani wlhy. Sakina kuma? Ya Umar da mama suka fad'a atare. Ya Umar ne yay k'arfin halin fad'in wai Maman Jameela?. Kansa ya d'aga ahankali. Mama ta ce, "tomiya kuma had'aku yau?." Hummm mama dama asheni aikin banza nakeyi, Kullum Sakina cin dunduniyata takeyi, sakina taruguzani, kullum na ajiye kud'ina danufin tari saitabi ta kwashe, ga shagon ya durk'ushe saboda ragad'ar sa datakeyi. Jiya na had'a kud'i har 1 .5million zanje kasuwa yau shine Sakina ta kwashesu tas, sannan yau dasafe ta titsiyeni saina saketa, hardacewa idan nahaifi cikin uwata na saketa. Nikuma raina ya6aci na saketa, ni bansan ta kwashe kud'inba saida ta tafi sannan naduba kud'i sukace na d'aukesu Inda na ajiyesu. Ina k'ok'arin kiranta sainaga wannan takardar awajen data d'auki kud'in. Yafad'a yana mik'ama ya Umar dake kusadashi takardar. Rubutune d'an kad'an awajen. ↓ _Abubakar bazan iya cigaba da zama dakaiba, Dan kaima nakula *Karayar arzeek'i* na haskoka, gwamma kafin ka durk'ushe kazamemin kaya na kama gabana, nakuma yagi rabona, nidai nayi gaba, 'ya'yanka kuma idan kanaso kazo gidanmu ka kar6a._ Iya abinda ta rubuta kenan, ya Umar yafad'a yana kallon mama dake saurarensa. Ajiyar zuciya mama ta sauke ta ce, "ALLAH ya k'yauta to." Cikin ma rairaicewar murya ya Abubakar ya ce, "abinda kawai zakice kenan mama?." To, mikakeso nace Abubakar? yarinyarnanfa matarkace, abayama nunamin kayi tafini muhinmanci arayuwarka, watsar da kowa da komanka kayi sai sakina. Sai abinda tace shi zakayi, Toni kuwa yanzu miye NAWA?, wanan ai fad'an masoyane. Kuka Abubakar ya fashe dashi, tamkar wani mace, ya rarrafa gaban mama yana rok'onta gafara da bata hak'uri. Wlhy mama Sharrin shaid'anne dana zuciya, amma tun bayan bikin mufida nayi nadama, Umar Dan Girman ALLAH katayani bawa mamanmu hak'uri, natuba wlhy, kaima ka yafemin abinda namaka, tundaga kan biya maka kud'in asibiti daduk abinda namaka abaya. Wlhy nayi nadama kunji na rantse muku. Ya Umarne yataso ya rungumesa, yana fad'in nidai wlhy na yafe maka ya Abubakar, dama can ban rik'eka arainaba. Ngd Umar, kaidama mai sauk'in kaine, ALLAH yak'arama rayuwarka albarka. Ya nusanta shaid'an daga tsakaninmu. Ameen ya Umar yafad'a sannan yajuya kan mama yana taya ya Abubakar Neman gafara. Suna cikin haka saiga Abba yadawo. Yatanbayi ya akayi? Ya Umar yamasa bayanin komai. Abba ya ce, "kai ALLAH ya k'yauta mana wannan duniya, lallai na tabbata alhakin Umaru ne ke bibiyarmu, Dan ALLAH umaru ka gafarcemu, wlhy yanzu haka Nima cikin iftila'in nake, Dan ALLAH kamana afuw...... Da Sauri ya Umar ya ce, " wlhy Abba na yafe muku, dama can ban rik'eku arainaba. Kuma nayarda dak'addara k'yak'yk'yawa kokuwa mummuna. To mungode Umaru, ALLAH yayimaka albarka kaida iyalinka, Yakuma kareku da sharin duk wani mai sharri. Amen Abba. Dak'yar suka shawo kan mama ta yafema ya Abubakar, itama ta rok'i gafarar ya Umar d'in, duk ya ce, ''ya yafe musu shikam." Bayan lafawar komai Abba ya ce, "ai aturama Sakina 'yan Sanda kawai. Ya Umar ne ya ce, " a'a Abba kubarta, aii duniya makarantace, Wanda baizobama jiransa takeyi. Kubarta taje taci aizasu k'are. A take anan yayma ya Abubakar alk'awarin kud'i domin yatada jarinsa. Kallonsa sukeyi cikeda mamaki, Dan sunsandai shima bashidashi. Kallon dayaga suna masane yasakashi yin murmushi, yagyara zamansa sannan ya zayyane musu komai danganeda alkairin yazeed agareshi, dakuma Wanda Alhaji mai kano yamasa shima, har dawowar kayansa Wanda custom suka kama, har bud'e mall d'insa zuwa yanzun. Rungumeshi ya Abubakar da Abba sukayi, mama kam harda kukan dad'i, murnarsuce tafito dasu Rafi'a. Nandai akaita mik'a godiya ga ALLAH. kowa yak'ara Nuna nadamarsa dabama ya Umar hak'uri, akan abubuwan dasukaita faruwa abaya. Ya ce, "shikam komai ya wuce agareshi. Ya Abubakar ya d'auki fodiyo shida Abba, sai Albarka suke sakama yaron dabaima San a INA yakeba. Ya Umar da Asma'u saidai su kalli juna suyi murmushin jin dad'i. Sai bayan isha'i suka tafi, harda Rafi'a data mak'ale zataje. Daga nan gidan inna sukaje, itama tayi farincikin ganinsu sosai, musammanma d'an jikanta. Sunsha hirarsu har baba yadawo akayi dashi, ananma baba ke sanar dasu saurayin Fatee yace zai turo da iyayensa. Murna sosai sukayi, har Asma'u na tsokanarta. Oh ni fatee abin dama 'Yar kunshe-kunshece? Yanzu kin sami miji amma ko labari?. Ayya sorry yaya Asma'u, wlhy bamu wani dad'e da had'uwaba, auren ne kawai yazo lokaci, amma dama inada shirin zuwa nafad'a miki, harnayi kwana biyu. Oh to shikenan na hak'ura, ALLAH ya Sanya alkairi, yasa ayi damu. Murmushi kawai fatee tayi, azuciyarta tace amin. Har goma suna gidan, saida baba ya ce, "su tafi haka nan." 'Sannan sukai musu sallama suka tafi. Amota ya Umar sunata 'Yar hirarsu shida Asma'u. Abayama Rafi'a da hasiya sunayin tasu. Fodeyo na hannunsu hardai suka isa gida....... *_Gidan mom_* Mom & Safwan.......... 🏃‍♀🏃‍♀muhad'u gobe idan ALLAH ya kaimu. *_(((S))).....2018_* *_I Love you my fan's_* [1/6, 5:08 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→75-76_* ..........Wlhy mom nake gaya miki riba sodai ake samu a harkar, kikalleni yanda na canja, to kud'ine keta shigomin tako ina, shiyyasa naga yadace kuma nazo naji idan kuna buk'ata, dakuyita cinye kud'in abanza aii gara a juya mukusu kuma Ku k'aru. Koya kika gani?. Ajiyar zuciya mom ta sauke, cikin gyad'a kai ta ce, ''nayarda da maganarka 100% Safwan, kuma Na amince zan bada nawa kud'in, saidai bansan sauran 'yan uwankaba kozasu yarda?. Zasu yarda mom, Dan zan musu bayani yanda zasu gamsu insha ALLAH. to shikenan saikayi k'ok'ari, tunda kace sati d'aya kawai zakayi a k'asar. Insha ALLAH haka nake fata, saboda kasuwar tamu bata buk'atar wasa. To shikenan, direba saiya kaika gidanjen 'yan uwan naka............... _________________________ 'Yammatana wai har yanzu kewar inna baiton bata sakekibaneba?. Asma'u dake kwance gefen ya Umar tayi murmushi, yaya kasan ance sabo tirken wawa. Hakane my Queen, to amma aigani akusadake ko?, yaufa kwanan inna baito hud'u da tafiya, amma kinkasa hak'ura. Karka damu ahankali zan manta aii. To ALLAH yasa. Yay maganar yana tashi zaune. Itama tashi zaune tayi, um bara kaga naje k'ilama fodeyo ya tashi. Da sauri ya Umar yarik'o hannunta yadawo da ita jikinsa, k bawani fodiyo kinji, natabbata daya tashi dasu Rafi'a sun kawoshi, bagama fatee tana a gidanba. Kai yaya kallafa agogo, kobabu fodiyo aii akwai had'a breakfast ko?. Shima su Hasiya zasu had'a, wai bada safennan fodiyon yakoma hannunsuba? Naga taredashi muka kwana. Shiru tayi batace komai, Dan dama sotake tagudu, tagaji da fitinarsa, jikinta said ciwo yake mata wlhy. Abu yad'akko a dirowar gefen gadon ya rimtse a hannunsa sannan yamik'a mata hannayen nasa, canki d'aya anan. Kallonsa Asma'u tayi ta ce, " minene?." Kedai babu ruwanki dako miye, canki kawai. Raba idanu Asma'u tafarayi tsakanin hannun haggunsa dana dama, candai ta canki Na dama. Dariya yayi tareda rungumeta zuwa jikinsa, kinci gari my Queen. 'Yaya maganar yana d'aga mata key d'in mota'. Da Saudi ta kar6e tana tashi zaune, yaya wannanfa?. Saida yabata kiss akumatu sannan ya ce, "nakine". Zumbur tamik'e tana jujjuya key d'in mortar, saikuma tafad'a jikinsa ta rungumesa tana farinciki da godiya agareshi. Shidai dariya kawai yaketa mata. Ya Fharuk ni Asma'u nice da mota yau? Wayyo yaya ngd sosai, ALLAH yak'ara bud'i Na alkairi, ya tsareminkai da tsarewarsa, ngd ALLAH ya albarkaci su twins da fodiyo. Shima rungumeta yayi sosai yana farincikin. Sundad'e ahaka sannan daga isani tasauka daga adon, yana kiranta amma INA tasheka kaimasu fatee rahoto. Duk suna zaune agadonta, novel fatee ake karanta musu, saidai kawai sukaji tafad'a tsakkiyarsu tana murna. Wayyo yaya Asma'u lafiya kuwa? Fatee ta tambaya. Key d'in mota tashiga d'aga musu tana dariya dafad'in ya Fharuk ya sayamin mota........ Aibata k'arasa fad'aba suka hau ihin murna sums wadda harta taxa fodiyo fake barci. Ya Umar yana jiyosu, Kansas kawai ya girgiza yana fad'in ALLAH ya shirya.......... ________________________ Tab wlhy da ahanya Na ganka bazan yards kai baneba bros. Dariya Safwan yayi, to aii yanzu agidankine Suhaima. Wlhy kacanja sosai, danasani Nina turai d'innan nai tafiyata, gashinan tsautsayi yasa Na 6ige da Auden matsiyaci, Wanda baida sisin kwabo said kud'ina dayake ragad'a. Ban ganeba suhaima mikike nufine?. Humm Viking bak'in ciki take bashi labarin Wanda ta aura, da k'ayar dayayta shirya mata kafin auren, said a ta aureshi taga babu komai, wlhy dakaga gidamn da'aka fara kaini saika tayani kuma, aiko was he gari dole muka tattaro muka dawo gidannan. Jinjina kai Safwan yayi ya ce, "ALLAH ya k'yauta to. Nina da dawata shawarar kasuwanci Nazi muku, mom ma harta Nada NATA kud'in saboda ta amince 100%. Cikin zumud'i Suhaima ta ce, " yimin k'arin bayani akai naji. Yanda ya tsara mom itama haka ya tsarata, aii babu wani dogon tunani ta ce, "ta amince, Dan da Ramadan yacigaba da cin kud'inta gara tabama Safwan, kuma gashima a in farinciki kasuwanci zasuyi, kud'in zasiyita k'aruwa. Komai NATA said a ta had'a NASA, takardun kaddarorinta daduk wani abinta Na kud'in, 1million kawai tabarma manta, shima saboda matsalolin yauda kullum dazataimabkanta magani, tunda dai tasan Ramadan babu uwar days ajiye aduniyarnan said masifaffiyar k'arya da fafa. Safwan yana gama kar6ar komai yamata sallama yatafi akan said sunyi ways kuma. Yana FIFA ya k'yalk'yace da dariya yana fad'in nasara ta biyu.🤣👌🏼 Daganan said gidan Lubna, it's yatararma bata gidan tafita wajen Niki, yakai away d'ya yana jiranta sannan saigata tadawo. Itamadai tayi matuk'ar mamakin ganinsa, itama kuma haka ya tsarata Lamar yanda yatsara mom da suhaima. Itadai ta farko bata aminceba, Dan race saitayi shawara da Hafiz, amma data kanainayeta da dad'in baki, dakuma nuns mata Mayan kud'in suhaima said itama ta aminve, stake an an ta tattaro NASA komai NATA tabashi, it's koma dabatarra suhaima batayiba nabarin wani Abu a hannunta, Dan it a anata ganin Hafiz Na nan. Nanma komai yahad'a yay gaba, saga nan said gidan Ameer. Sosai yasamu tarbar mutunci awaken jiddah matar Ameer, sunata hirarsu cikin mutunci Ameer yadawo, rungume juna sukayi shida Safwan saboda farinciki, saida sukayi hira mai tsawo kafin Safwan yasanar dashi abinda yakawoshi k'asar. Sosai Ameer ya jinjina maganar aransa, baice zai bayarba baikumace bazai badaba. Saida sukadawo saga massalaci sallar la'asar sannan yasamu cikin hikima ya ke6e da matarsa. Zancen da Safwan yazo dashi yasanar mata, zancen bai wani kwanta acikin zuciyartaba, amma kai tsaye baidace tanuna masa hakaba tunda d'an uwansane. Ta sauke ajiyar zuciya sannan tace abin farincikine wannan my One, to amma kaga kai kana 'yan kasuwancinka aii, kuma bai kamata karuguzashiba, amma kasamu koda 5million's ne kabashi, lokacin dazai dawo kad'an kuma samin wani Abu saika k'ara NASA ko yakagani?. Haka yayi wlhy sosai, shiyyasa kullum nake k'ara sonki dear, ALLAH ya barmu tare, yay maganar yana rungumeta. Ta ce, "nima ina Sonja sosai mijina a in alfaharina. Cikin sati d'aya Safwan yagama kammala mak'udan kud'ad'en, duk wata kaddara tasu Lubna ya saidata, yahad'a inasa-inasa ya d'age yabar k'asar.🧐 _________________________ Zuwa yanzu ya Umar yafara koyama Asma'u mota, sosai kuma take maida hankali awajen, Dan tafara iyawa babu laifi. Agefe kuma sunata zabga soyayyarsu. Ansaka ranar Fatee, yanzuma maganar Rafi'a da Sadam akeyi dansun daidaita Kansu dama. Saikuma Harris ya ce, " shimafa indai Hasiya ta amince ahad'a dasu, Dan yadad'e yana sonta. Yayi shirune saboda bashida abinyi, amma yanzu kam Alhmdllh. Kowa yayi farinciki da wannan batu, Hasiya kuma ta amince. Gabad'aya aka had'a saranar itada Rafi'a, sai aka daidaita bikin dana fatee. Su Asma'u manyan yayye anata shirye-shirye, ya Umar kam tuni ya kammala had'a kayan gadonsu su duka ukun. Alhmdllh yanzu fodiyo yafara zama abinsa, yaron yayi 6ul-6ul gwanin sha'awa, Asma'u da ya Umar kam soyayya sai abinda yay gaba, yanzu ta iya mota, duk inda takeso zuwa takeyi a abunta. Ya Abubakar ma shagonshi ya mik'e, Dan ya Umar yabashi jarin dayace. Yaransa kuwa tuni ya kar6osu ya bama mama, takar6a hannu biyu tarik'e Dan yanzu mama tacanja sosai wlhy. Duk abinda 'ya'yanta suka bata takan kar6a da hannu biyu tayi godiya, babu nuna banbanci a tsakaninsu, da Wanda yabata da Wanda bai bataba duk d'ayane awajenta. Ya Umar yabama Anty Sa'a da Anty Saratu jari suma. Yahad'a 'yan uwansa yarik'e gam, yazama bishshiya maid'aukeda nauyin kiwa gwargwadon iko. Yanzu kam koda yaushe yana mall d'insa, shagon k'ofar gida kuwa an samo wani yaro yana kula dashi, ya mallakama Asma'u shi gaba d'aya, kuma Alhmdllh komai yana bunk'asa a shagon. Abokansa kuwa komai ya sukurkuce musu, suna mamakin dawowar arzeek'in ya Umar, dukda baikoma kamar Daba, amma Alhmdllh, yanzukam sun yard a ya Umar ya keresu tako ina. Shikam duk sanda yaje mall d'insa zaije wajensu su gaisa, daga gaisuwa babu abinda ke had'asu, idan yatashima zai musu sallama, babu abinda yadameshi dashi. Dr Jafar yana dana sani da cizon yatsa akan abinda ya aikatama ya Umar, gashi yarasa hanyar dazaibi yarok'i gafararsa, Dan yanzu ya Umar d'in nunawama yakeyi tamkar bai sonsuba. Ana haka akasha bikinsu Rafi'a da fatee da Hasiya, su ya Umar suntaka rawar gani sosai, sune iyayen amare sune Na angwaye, ansha biki lfy, angina da amare duksun tare agidajemsu. To ALLAH ya sanya alkairi amen😁. _________________________ My Husna wai haryanzu jikin NASA?. Wlhy kuwa ya fharuk, haryanzu akwai zazza6in, gashi fodiyo bayason shan magani, jibifa yanda nake matseahi amma yana zizzilewa, bawani Abu baneba hak'orane kawai. Ya Umar yad'auki fodiyo daketa kuka saboda maganin da Asma'u tamasa d'ura dashi, rungumesa yayi ajikinsa yana lallashinsa. Asma'u dake kallonsu ta ce, "ana murmar fara tafiya ciwo yazo ya hana. Karki damu insha ALLAH zai warke, ALLAH yakawo masa tafiyarmane dawuri, watansafa Tara kenan da haihuwa. Eh hakane wata tara, tunda yaron mufida watansa 1 kenan da sati biyu, aranar sunan kuwa akecewa watan fodiyo takwas. Kai yanzu nan har mufida tayi wata 1 da haihu?. Harma da sati biyu yaya, ALLAH dai yasa mucika da imani, aii duniya na gudu wlhy. To ALLAH yasa mucika da imani. Ameen ya rabbi. Kwanannan zakaga cikin su fatee ma wata tafara laulayi. Dariya ya Umar yayi, to ai abunne babu wuya, wuyartadai a d'aura auren. Hakane kuma wlhy. Sunata hirarsu cikin nishad'i. Can ya Umar ya ce, " af namanta wlhy, amaeyar ya Abubakar mafa babu lafiya, kishirya Dan ALLAH anjima mije mu dubata. Tofa ko itama cikinne?. Ina k'yautata zaton haka kam, d'azu nima yake sanar dani damuka had'u a gida. Ayya ALLAH yak'a lfy, da yamma idan kundawo saimuje. Humm nikinma tunamin wlhy, su yazeed sunyi zamansu, gashi har 1 saura, kumafa k'arfe biyu za'a fara meeting d'in..... Sallamar yazeed takatse ya Umar. Amsawa sukayi. Sannan Yashigo cikin falon suka gaisa da Asma'u tareda d'n barkwanci da'aka saba. Saida takawo masa ruwa da zo6o yasa, (Dan bata rabo da zo6o saboda k'aunar da ya Umar me mass). Babu dad'ewa saiga muktar shima. Sallama sukayi mata suka tafi. Bayan tafiyarsu tad'an k'ara gyara gidan, tagoya fodiya tatafi gidan Anty saddiqa dansu d'anyi hira kafin mazajen nasu sudawo........... 7:23pm Sukayi shirin zuwa asibiti duba matar ya abubakar daya aura kwanakin bata, babu rsuwanta, bakamar sakinaba. A asibitin sun tararma har an sallamesu, suna shirin tafiya gida, dama mamace awajenta. Bayan and'an gaggaisa da ya jiki suka shirya tsaf. Sun fito kenan saiga wasu mutane suma sunfito suna kuka d'aukeda gawar d'an uwansu. Audai su ya Umar suka matsa gefe suna bada hak'uri. Mamar mamacince k'arshen fitowa, tanata rabzar kuka dafad'in ALLAH ya isa tsakaninmu dake Zainab, kin cucemu, kin kashe mana d'a, zayyan ALLAH ya gafarta maka. Gaban Asma'u ne yafad'i danjin an ambaci sunan Zayyan. Kad'an tamatsa kusada gadon da aka turo gawar zayyan za'a saka a mota. Idanu tazaro sosai waje Dan ganin Zayyan d'inta, cikin rawar murya tace ya Fharuk wlhy Zayyan ne, ALLAH sarki Zayyan, ALLAH ya gafarta maka. Cak Maman Zayyan tatsaya da kukan datakeyi, hakama sauran 'yan uwan Zayyan duk hankalinsu nakan Asma'u da ya Umar dake lallashinta. Maman Zayyan tamatso kusadasu, tana fad'in yarinya ina kikasan Zayyan d'ina?. Cikin kuka Asma'u tamusu bayanin dangan takarta da Zayyan abaya. Rungumeta Maman Zayyan tayi tana kuka, dabama Asma'u hak'uri, tad'ora dafad'in ai tsinanniyar yarinyar days aura dalilin kwad'ayinsa ita ta manna masa cutar k'anjamau, bai fargaba saida taga yimasa illah, watanmmu biyu kenan a asibitinnan muna jiyya, sai yau ALLAH ya kar6i kayansa. Zayyan yayi asarar kamilar mace irinki Asma'u, nadad'e ina bak'incikin rashin Aurenki da Zayyan baiyiba dukda ban sankiba. Amma babu yanda zanyi tunda mahaifinsa ya goya masa baya akan auren Zainab, saboda kwad'ayin abin duniya ita 'Yar mai kud'ice. To dama ance k'uda wajen kwad'ayi yake mutuwa, naga zahiri akan Zayyan kuwa. Ta kuma rushewa da kuka. Dak'yar su ya Umar suka lalla6eta tashiga mota, Dan tuni ansaka gawar zayyan d'in. Haka suka tafi sukabar Asma'u na kuka itada mama. Dak'yar ya Umar ya lallasheta acikin mota. To ALLAH ya jik'anka Zayyan😭. *_Lubna_* Lubna kam abubuwa sun rikice mata, itada Hafiz kullum fad'a harda dabbe, yafita k'arfi, haka zai kamata ya jibga, yazageta tas. Yanzu batada komai, d'an kud'in daya rage mata sun k'are. Hafiz kuwa bakomai yake iya mataba, Dan yace bazai iya da yanda take cin uban kud'iba. Wannan dalilin yasa zaman lafiya ya k'aura agidansu, inhar zata nemi Abu yace mata bashidashi to yanzu zasuyi sama kuwa. Yau danben yakaisu da zagin uwaka ubaka, atake anan Hafiz ya yanka mata Jan kati da saki uku 6aro-6aro ajiki. Shewa tabuga da fad'in tafi nono fari, itadama tagaji da zama dashi, Dan haka ya tattara inasa-inasa yabar mata gidanta. Ko'a kwalar rigarsa yakwashe kayansa yabar gidan, dama shimad'in yanzu babu komai, matsalolin lubna sun ida durk'usar dashi. Bashida komai yanzu na azo agani. Awashe gari lubna tad'aga gidan ta sayar dakomai dake cikinsa. Sutturunta kawai ta d'iba, ta sallami 'yan aikinta. Bilki kawai tabari ta tattara suka koma gidan mom............ *_(((S)))).......2018_* *_I love you all my fan's_* [1/6, 5:11 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻‍💻......... 💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎 *_NA_* *_Bilyn Abdul_* *_Sadaukarwa_* _miss Xoxo na_ _Zarah Bukar_ _Ayusher Muh'd_ *_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_* *_page→77-78_* ..........Agidan mom d'imma bawani dad'i baneba, Dan itama komai yak'are, daga ita harsu 'yan biyu duksun fita hayyacinsu, ga ciwon yinwa dake barazanar kamasu. Tashin hankali goma da ashirin, su 'yan biyu Na ganinta suka fad'a jikinta suna kuka, momy yunwa mukeji sosai. Rungumesu tayi itama tana kuka tausayi. Mom tashare hawayenta tana kallon lubna dake rungume da twins, ta ce, "baby kema bak'ya samun number Safwan d'in?." Humm mom kenan, wlhy ak'alla watana biyu kenan bana samun number sa, anya kuwa Safwan ba cin amanarmu yayiba mom? Ak'alla watan Safwan biyar kenan da tafiya da kud'inmu, amma ko nera d'aya baita6a turo manaba da sunan riba, a lokacinma damuke samun nasa kullum zancensa bai wuce mijirasaba dai. Gsky mom nafarajin tsoro. Hummm baby wlhy bake kad'aiba, nikaina a tsoracen nake. Amma lfy naganki da kaya haka?. Mom Hafiz ya sakeni. Saki kuma baby? Miyayi zafi haka?. Mom bar matsiyaci, tunda Safwan yatafi mana da kud'i 'yan kud'in dake hannuna suka k'are Hafiz yafara canjawa, idan Na tambayesa kud'i bazai bani isashsheba, saiyace aibani kad'ai baceba yanada wata matar harda 'ya'ya. nidashi kusan kullum dambe, yoni mom ina ruwana da matarsa ko wasu 'ya'yamsad'in wofi. Jiya dasafe muntashi ko kayan abinci babu agida sainace yabani kud'i naje nasayo. Shinefa yad'auki 50k yabani, nikuwa uwarmi 50k zatamin, ko a sayen naman gidan bata k'areba. Nace masa sunyi kad'an, shikuma yacemin bashida wasu, haushi yakawoni wuya Na zageshi, shine ya mareni, aikuwa naita danna NASA ashar yabani saki uku. Ayau Na saida gidan anjima kad'anma zasu turomin kud'ina. Kuka mom tasaka tana fad'in lalai baby Na k'ara tabbatarwa bakida hankali wlhy, yanzunan saboda kud'in cefane kuka kashe aurenki? To ina motocinki?. Yo mom run yaushe Na saidasu, d'ya kawai taragemin wadda nake shiga, itama bawani lafiya tacikaba. Kuka sosai mom takeyi, lubna kam ko'a jikinta, Dan bataga a in kukaba anan. Saga k'arshema 'yayanta tad'iba suka fita. Urban shopping tayo musu mai yawa sannan suka dawo gida. Turus tayi Dan ganin Suhaima zaune tana rabzar kuka, dukta rame ta lalace, said urban ciki rindimeme. A sanyaye Lubna tazauna tana fad'in Suhaima kekuma lfy? King a kuwa yanda kuka koma Lamar matar k'auye?. Kuka Suhaima takuma fashewa dashi tana fad'in badole kiganni hakaba baby, Ramadan ya niyyar kasheni da raina. Kiduba duk alaccin danaima Ramadan arayuwa bai ganiba, dukda nagane bashida komai nayimasa sutura Na zauna dashi. Yau kusan wata biyu kenan yamin wayau da dad'in baki yakar6i 'yan sauran kud'in hannuna way zai fara kasuwance, nikuma daboda yarda danayi dashi Na d'auka Na bashi, Ashe tikitin iskanci da karuwai a hotels yabud'e da kud'in ban saniba. ahankali yabi duk ya said a motocin gidan, Ashe hard a gidan ban saniba. Yau dasafe saiga wad'anda suka sati gidan sunzo wait sun bamu notes nanda gone my kama gabanmu. Ina cikin tararrabi da jiran Ramadan saiga ta karda ya aikomin wai ya sakeni kuma nafara zuwa ganin likita saboda shi an tabbatar NASA yanada HlV😭, Yakima tabbata Nina INA tareda iya, tak'are maganar da rushewa da matsanancin kuka😫. Data mama har Lubna ma kukan sukeyi, su twin's dai said kallonsu sukeyi da 'yan aikin gidan. Yau sukam duniya tamusu gwatson k'yanwa🙁. ALLAH yasa mudace ameen. *_Bayan wash shekaru._* Abubuwa sun faru dayawan gsk, ciki harda ciwon 6arin jiki data kama mom, sakamakon Nina Safwan da akayi ankamashi da hodar iblis shida wasu abokan kasuwancinsa su takwas. Harma an Yankees musu hucin Lisa ta hangar harbewa, wannan yasa ta yanke jiki ta fad'i awajen, tundaga nan babu wani sashe Na jikinta take mitsi. Wannanne yasa jinya tazamema Lubna biyu, damage ga Suhaima kwance waken shekara d'aya kenan, tuni ta haihu mace, yarinyarma hartayi wayo, abaya tana shan magani dad'n kukad'ad'en dasuka rage musu, dawanda Ameer take taimaka musu, Dan yanzu shikad'aine mad'an a in hannu acikinsu. Shiyyasa yad'ik'e matarsa GAM, Dan itace sila ta zamowarsa Na gari harya iya rik'ekansa, yanzuma yaransu biyu. Suhaima tana ganin tasamu lafiya tafara wasa da shan magani, shinefa ciwo ya dirkusar da ita. 'Yan aikinsu kuwa aituni kowa ta gudu ta barsu. Abinci Kansas badan Ameer ba dabasuciba kuwa, duk wata yana k'ok'arin kawo Mayan abinci gidan. Su 'yan biyu kuwa dasuka zama 'yammata aii saidai add'a kawai, damage dance yaro yana koyine da abinda yagani anayi agidansu, yanzu haka saisu had'a kwana biyu NASA gidan, sunacan yawon gantalinsu. Kuban tayi kuka harta rasa hawaye. Said yanzu tunanin ya Umar me addabarta,Neman ganinsa takeyi ruwa a jallo amma tarasa hangar hakan........ ★★★★★ Su ya Umar kam aii saidai muce Alhmdllh, k'ofofin arzik'i sun kuma bud'ewa tako ina, dagashi har Asma'unsa sun murje sunzama manya ababen Alfahari ga dangi. Yanzu haka yaransu uku, bayan fodiyo ta haifi mai sunan inna Binta kenan, amma suna kiranta Batul, sai kuma mai sunan ya Umar, wato Umar Fharuk, shima suna kiransa Affan. Tuni ya canja musu gida mai k'yau da tsari, rayuwarsu sukeyi cikin soyayya da k'aunar juna, ga 'yan 'ya'yansu ababen sha'awa da birgewa, dolene ka gansu su baka sha'awa. Fatee, Rafi'a, Hasiya duksun haihu, suma anatashan soyayya suda mazajensu. Hakama 6angarensu inna dash mama, komai Alhmdlh, Anty sa'a da anty Saratu, da mufida sumadai komai normal, kiwa yana cikin kwanciyar hankali. Abotar yazeed da ya Umar da Muktar kam said abinda yay gaba, sun k'ulle kansu tsam, basa sakeda wata kwafa dazata rusasu, hakama matansu da 'ya'yansu...... ★★*★★*★★*★★ Amrah da Afrah na zaune afalon k'asa, duksun baje kayan sweet da samarinsu suka siya musu. Lubna dake zaune agefe tana d'urama mama ruwan tea Dan shine kad'an yake wucewa, shima saida cokali ake d'an zirara mata, lubna dukta lalace tayi bak'i Lamar ba Lubnar nan 'Yar gayuba, tafita hayyacinta sosai, ayanzuma saita had'a kwana hud'u batayi wankaba saboda damuwa da tashin hankali dasukai mata yawa. Mama ma dake kwance wadda idontane kawai ke aiki, tanata kallonsu Amrah da hira ta kaure a tsakaninsu kowa Na kid'a saurayinta yafi Na 'Yar uwarta. Da k'yar Suhaima dake kwance gefe ta ce, "Afrah tazo tabata ruwa tasha". Baki Afrah ta turo gaba tana k'unk'uni, dak'yar tabata ruwan tana yatsina fiska Dan k'yank'yaminta sukeyi yanzu. Hawayene ya ziraro a kumatun Suhaima, tatuna kanta ada, dayanda tayi holewar datafi tasu Amrah. Amma gayanda rayuwarta takoma?. Lubna ta harari Amrah, itako babu tsoro tarama tana fad'in kijimin momy, minamiki zaki harareni?. Afrah ta ta6e baki tana danna sweet abaki. Itadai Lubna batace komaiba. Saican kamar an tsikari Afrah ta ce, " momy! Yau munga wani abin mamaki wlhy. Kamar lubna bazata tankaba, saikuma zuwa can ta ce, "nami?." Humm mall d'in da guys d'inmmu suka kaimu dayagama had'uwa, wlhy momy komai akwai awajen, Raine kawai ba sayarwa, yafa had'u sosai. Amma kinsan mi muka gani?. Hoton wani k'yak'yk'yawan mutum shida matarsa da yaransu uku, shine mai wajen, wlhy abin al'ajabi tana masifar kama da Amrah. K'armin d'ansa kuwa kamar ni nahaifeshi saboda kamar damukeyi. Tab ai kamar ta 6aci. Amrah ta kar6e zancen dafad'in aii wlhy Afrah har mukazo gida inata tunaninsu. Nidai haka kawai naji ajikina munada dangan taka dash. Gaban Lubna ne yafad'i. Da sauri ta ajiye kofin tea d'in datake bama mom, ta ce, ''ya sunansa?." Ummmm anfa rubuta ajikin pic d'in. Afrah yama? Nikam Na manta. Da sauri Afrah tace, matardai sunanta Asma'u, shikuma mutumin Umar Fharuk, sai yaranau Usman fodiyo da batul, Affan...... Zumbur Lubna tamik'e tana fad'in kutashi muje Ku nunamin wajen. Wani kallon sama da k'asa sukai mata, sai kuma suka bushe da dariyar shak'iyanci. Cikin dariyar Amrah ta ce, ''gaba momy ahaka zaki bimu wajen kamar an kwatoki daga bakin kura?. Inama laifin kid'anyi wanna ki canja kayannan. ALLAH mom tsamimafa kikeyi, yau kwananki uku bakiyi wankaba, shiyyasa ko kusadake banason zama. Hawaye suka cikama Lubna ido, wai itace yau 'ya'yanta kekiranta da tana tsami? Lallai rayuwa kenan, ta tababata alhakin Umar kad'ai ya Isa tatsinci kanta fiyema da yanda take ayanzu. Haka tatafi tayi wanka, sannan tazo suka tafi, suka bar mama da Suhaima agida, Dan harda Habiba d'iyar Suhaima suka tafi. Hankalin Lubna yatashi sosai daganin hoton ya Umar da Asma'u. Da alama 'ya'yansune taredasu ahoton. Jiki a sanyaye suka k'arasa indasu Harris da sadam ke zaune. Bayan Lubna ta gaishesu Dan Amrah da Afrah babu wannan atsarin tarbiyyarsu, NASA Haida kowa, ko gidan Ameer sukaje haka sukeyi. Lubna tafara tambayarsu ko Alhji Umar nan?. Sudai su Harris kallonsu kawai sukeyi, Dan kokad'n bai gane Lubna ba, shidama Sadam bai santaba, amma idonsa nakan su Amrah daketa taunar cingam k'as-k'as, kamarda Amrsah takeyice da ya Umar tabashi mamaki, hakama Afrah da Affan. Harris ne yay k'arfin halin fad'in baya nan yaje gida yanzunnan kai yara. Da sauri Lubna ta ce, "kozaku bamu kwataccen gidan Dan girman ALLAH?. shiru sukayi suduka, Dan sukam bama su yards dasuba, kowadai yasan yanda rayuwar ta lalace yanzu. Lubna ta rissina kamar zata duk'a tana k'ara rok'on Harris, Dan itama bata ganeshiba. Sadam ya ce, ''baiwar ALLAH kekam miyasa kike son ganin ya Umar. Dak'yar ta iya had'iye yawu ta ce, " ni tsohuwar matarsace, wad'annan kuma 'ya'yansane. Ta nunasu Afrah. Idanu Amrah da Afrah suka zari, suna fad'in 'ya'yqnsa!!?. Can kuma Harris tayi wani uban zallo shima yana k'qrema lubna da twins kallon mamaki. Tabbas alamu dayawa sun nuna gskyar Lubna, musammanma kamainnin Amrah da ya Umar. Cikin masifa yakirasu waje, ana cikin haka saiga yazeed, yatanbayi abinda ke faruwa Harris yafad'a masa. Hannu Yazeed yad'aga masa ya ce, "a'a daina korarsu. Kushiga Mora na kaiku. Badan Harris yasoba yazeed yad'auki su Lubna amotarsa sai gidan ya Umar. Afrah dake gaban mota tuni har zuciyarta ta k'yasa yazeed😨🤣. -*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*- Asma'u dake zaune Afalo taci wwalliyarta, gefenta masu aikintane suna zaune sai hira Duke zuba mata tana dariyar. It's babu ruwanta da German kan nan irinna hajiyoyi. Da gudu fodiyo da Batul suka shigo falon suna kiran Ammi! Ammi!! Mundawo mundawo. Itama cikin azama tamik'e ta taresu Rana farincikin dawowar 'ya'yanta ababen alfaharint. Suna cikin murnar saiga ya Umar yashigo d'aukeda Affan ahannu, shima sanye cikin Mayan makaranta. Shida Affan d'in tahad'a ta rungume tsam ajikinta, shima ya Umar k'yak'yk'yawar tarba yamata tareda manna mata Sumba agoshi. Affan ya ce, ammi yau antynmu tace Nafi kiwa kokali a class d'inmmu. Masha ALLAH autana, haka nakeaonji. Ya Umar ya ce, ''autan lfy hajiyata, idanmma zaki dage ki Dage, autana bai zoba har yanzu, shine zaizama k'anin Affan na tara. Sosai Asma'u tazaro ido, gaba ya Fharuk rufamin asiri mana, ukunnan ma aii ansha fama kafin suzo. 'Yar dariyar ya Umar tayi, ya ce, "ahaka kuma nake jiran tara nan gaba. Habadai wasa kakeyi wlhy. Said a suka zauna sannan yace babu wani wasa da gsk nakeayi. Shiru tamasa taje takawo masa abinsha, sannan tafara cirema Affan Mayan makarantar. Suma su fodiyo duksun cire, kowa yama k'ok'arin nuns mata homework d'in da aka basu, sukaji sallamar yazeed. Yaran kowa ya yard a abinda ke hannunsa suka kwasa da gudu suna fad'in oyoyo dady. rungumesu yazeed tayi, shima yama fad'in oyoyo yarana. Ya Umar da Asma'u dai kallonsu kawai sukeyi suna dariya. Lubna dasu Amrah kam suna baya said kalle-kalle sukeyi agidan. Saima yanzu su Asma'u suka gansu. Ko kad'an Asma'u bata gane lubna ba bare su Amrah. Amma kuma kamar dasukeyi dashi yasakata taura musu idanu. Shikam ya Umar suna shigowa yaganesu suduka, Dan d'azu yaga Afrah da Amrah a mall d'insa tareda wasu samari biyu. Kuma yaji ajikinsa 'ya'yansane. Har hawaye saida tayi alokacin, yana k'ara yima Lubna ALLAH ya Isa, Dan asanadinsa yaransa suka lalace, shidai bai ta6a Yar kowaba tunyana saurayi bare yanzu. Amma gawasu suna lalata 'ya'yansa ta dalilin halin ma haifiyarsu. Yazeed ne yacema su Lubna su zauna. Duk suka zazzauna. Asma'u takawo musu abubuwan motsa Baku. Ran ya Umar a6ace yatashi zaibar falon. Da sauri yazeed yarik'e hannunsa yana fad'in karfa ka manta, a tsakaninmu babu jayayya. Idon ya Umar yayi jajur saboda 6acin rai, yajuyo yana kallon yazeed, kayi hak'uri d'an uwana, wannan jayayyar tasha banban da wadda bakaso. No Umar duk d'ayace, Dan ALLAH kayi hak'uri kazauna plss. Saida ya Umar yay kwafa sannan ya zauna. Amrah da Afrah kam aii tuni sun nutsu, Dan basuga wajen wargiba. Sudai su fodiyo suna tsaye agefe suna kallon iyayensu. Lubna ta Haida ya Umar, bai amsa mataba. Bata damuba itama, ta kalli Afrah da Amrah tace augaidashi. Amamakinta saigashi sun gaidaahi, harma da Asma'u. Sumad'in bai amsa musuba, saima cikin tsawa ya ce, "Lubna! Miyakawoki gareni? Dawane shiri kuma kikazo yau?. Tsawar babu Wanda bata razana a falonba, Affan ya k'ank'ame Asma'u yana kuka, Dan basu ta6a ganin baban nasuba a irin wannan yanayinba. d'aukarsa tayi tana lallashi, fodiyo da Batul ma duksun mak'ale jikin yazeed. K'asa Lubna tadiro tana kuka da neman gafarar ya Umar. Ka gafarceni nida iyayena da 'yan uwana Umar, wlhy duniya takoyar damu hankali, munyi nadamar abinda mukaimaka. Umar yanzu bamuda abin jayayya Sakai, dukiyar damuke tak'amar da ita tak'are. Ciwo da bak'in cikin rayuwa sune suka maye gurbin arzeek'inmu. Umar kayi hak'uri, ga 'ya'yankanan zan maido maka, Dan ALLAH karkace bazaka kar6esuba, Umar wlhy nasan nikaina ina gab da kamuwa da wani ciwonne, rayuwar dasu Amrah da Afrah suka saka kanau kawai ta Isa lafiyata baraza...... Da sauri ya Umar yad'aga mata hannu a hasale, yana fad'in suka saka kamsu, kokuwa kika sakasu ciki. ALLAH shine zaidata van ta6a zina da 'Yar kowaba amma ta sanadinki ga 'ya'yana sunayi. Lubna kin cuceni, kin zalinceni, yama za'ayi Na yafe miki?, kin rabani da 'ya'yana Ashe badan ki kula dasuba? Saidai ki watsa musu rayuwarsu? Wata 'yan kwallah ta taru masa a gefen ido...... Yazeed da Asma'u ne suka saka baki wajen taya Lubna Neman gafara. Dak'yar ya hak'ura, Afrah da Amrah aukazo suka rungumeshi suna kuka suma. Yauce rana tafarko dasuka gane kuskuren dasukaso tafkawa rayuwarsu, ALLAH ya taimakesu ya tsaresu basuta6a bama wani saurayi kansuba, saidai soyayyar shan minti da romances da samarin sukanyi dasu. Shima ya Umar rungumesu yayi, yau ga 'ya'yana sundawo gareshi, bayan kwacesu da akayi daga hannunsa Na tsawon shekaru. Daga nan wajen Asma'u sukazo itama suka rungumeta, basu manta da itaba, suka rungume 'yan kannensu dabasu sansuba. Lubna sai dad'i takeji, ga hawauenta sunk'i tsayawa, ta rungume su fodiyo itama tanajin dayanzu k'ila itace ta haifesu, amma San zuciya da rud'anin duniya yahana tsaida zuciyarta waje d'aya. Aigatanan a makarantar nadama....... Anan tabarsu Twins kamar yanda Asma'u ta buk'at. Aiko hakan yamusu dad'i, saijan 'yan k'annensu sukeyi ajiki, suma dayake sunada saurin sabo harsun saki jiki dasu. Washe gari, ya Umar yaje har gidansu Lubna d'in yad'auki mom da Suhaima yakaisu asibiti. Mom sai kuka takeyi, babu bakin magana, hakama Suhaima tanata kuka da Neman gafarar ya Umar, tasanar dashi sune itada mom sukaita zuga Lubna, akan tarabu dashi, run bata aminceba harta amince. Ya Umar saidai kawai yayi murmushi ya ce, ''ya yafe musu. *+++++++++++++*. Cikin wata biyu jikinsu mom da Suhaima yayi k'yau, Dan yanzu mom nad'an iyayin magana kad'an ², dukda dai bata fita sosai, hakama Suhaima alhmdlh, jikin nata yayi, k'yau. Mom sai sakama Ya Umar albarka takeyi da k'ara Neman gafararsa. Koda yaushe yakance ya yafe musu. Asma'u kam bata ta6a gazawa wajen kawo musu abinciba kullum safe da yamma. Duk sanda Lubna ta gansu dasu da 'yan 'ya'yansu saitayi kuka, da nadama, mai makon Umar yayi baya, kullum saima gaba yake k'arawa. Tagujeshi saboda *,"karayar arzeek'i"_* yau gashi shine yake taimakonsu da dukiyarsa. Tayi kuka harta godema ALLAH, tayi nadama rayuwarta, shiyyasa akace idanu gemun d'an uwana Yakama da wuta to yayyafama naka ruwan. Idanu kuma ALLAH ya jarabci bawansa badan bata sonshi baneba. Itakam taga zahiri akan Umar. Itada 'yan uwanta kam duk ga yanda tasu rayuwarsu tak'are, sun rasa alokacin Dana Umar yadawo. ALLAH ka shirya zukatanmu, ka ganar damu gsky. Ni bilynku nace ameen😭. Alhamdulilahi. Anan nakawo k'arshen wannan d'an littafi NASA mai suna *_KARAYAR ARZEEK'I_* abinda nafad'a saidai, ALLAH kabani lada, Wanda nati kuskure ALLAH ka yafe mini. Ina godiya ga d'umbin masoyana, musamman masu bibiyar buk d'innan Na *_karayar arzeek'i_* ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, Nina INA k'aunarku da alfahari daku aduk India kuke. *_Writer's 'yan uwana kuma inata mik'o godiya agareku, ALLAH yabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci, ALLAH yak'arama kowa baseeer da hak'urin typing._* Bilkisa Ibrahim Bilyn Abdul. Marubuciyar. _rashin Sani_ _auren k'addara ko biyayya?._ _k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_ _nida aminiyata_ _kukan kurciya_ _sabon al'amari_ _nawaff_ _ban saketa ba_ _Abdul-maleek bobo_ _karayar arzeek'i_ *_Sharhin littatafaina 10 nanan zuwa agareku insha ALLAHU_* _NGD SOSAI, ALLAH YABAR ZUMINCI._ *_BILYN ABDUL CE._*👌🏼😁 *_(((S))))........2018_* *_I love you more...._*