[10/25, 5:27 PM] Fatima Fans: 🦋*ƘANWAR SHEHU*🦋 EP 2 By Nanamaryama *TEAM WOW 3 ELEGAN WRITTERS* *ƘANWAR SHEHU* *Nanamaryama* *RIKICIN DUNIYA* *MEENAT A YAN DOMA* *GIDAN AURE NA* *OUM SHARIFAT* Posting Room👇🏼 https://chat.whatsapp.com/FUeULeu12Is1lcTscF5Je6?s=cl&p=i&mlu=4 Comment section👇🏼 https://chat.whatsapp.com/DrrHAf8xE7P56YCUZkhGlG بسم الله الرحمن الرحيم Baba Nura ya tsaya kallon ta saboda yarinyar ta bashi mamaki kamar bazata iya faɗar haka' sai gashi ba kunya ba tsoron Allah tana faɗa ma mahaifin ta wannan maganar ya ce'' Jawahir ke yanzu ni kanin mahaifin ki kike faɗa ma wannan maganar?". A'a baba ni ba magana na faɗa maka ba illa gaskiya! Tunda baba na ya mutu ka ƙara waiwaya mu nida mahaifiya ta ? Tun lokacin da aka raba gado ku ka amshi nawa waye ya ƙara taimako na? Daga kai har "gwaggo ba wanda ya kara zuwa wai ya ga ya muke ci game da rayuwa, sai yanzu za'a zo ace wai aure a'a bazata sabu ba bindigar soja a ruwa wallahi ta idasa maganar tare da barin ɗakin!" Ehh! Lalle "dije kin koya ma yar ki rashin kunya tabbas, ku tabbatar da magana ta sai na aura mata shi ko tana so ko bata so bai daman ba abinda ke gaba na shi zanyi, ya tashi ya fita fuuuuu...." Bayan a wanni Inno ce tare da jawahir zaune a kan tabarmar kaba suna cin abincin rana ta kalli jawahir tare da faɗin mi yasa kika ma babanki haka? Ƙwalla ce ta kawo cikin fararen idanun ta ta ce'' wallahi bana san auren wannan mai shaye-shayen inno taya zai ce zai min aure da shi? Nidai bana so kuma ni karatu zanyi ba aure ba yanzu, ina so na zama likita yanzu idan aka min shi ai za'a lalata min shiri na ta idasa faɗa tare da matso ƙwalla!" Ita kanta inno ɗin tausan yar ta ya kamata ta ce'' to ki daina ma babba rashin kunya don Allah rashin kunya bata da ƙyau fa nan dai ta cigaba da mata nasiha mai ratsa jiki......" *Baba Nura* Yana tafe yana ni wannan yarinyar zatayi ma dibar albarka? Kamar ni babanta ai da uban nata na raye ba zata yi haka ba, amma yanzu tunda ko tai min haka zata gani a ƙwaryar shanta gida ya faɗa ko sallama babu, matar da ke tsakar gida ta ce "malam lafiya nake tajin maganar ka tun kafin ka shigo cikin gidan??" Hmmm!. Bari ke dai naje gidan su wannan yarinyar ne kan batun auren ta da "jibo amma ta watsa min ƙasa a ido wai bata san shi, ita ba zata iya auren mai irin halin sa ba!'' Ohh to kai "malam duk wata mace mai hankali ai ba zata so ta auri jibo ba duba da halin da yake ciki ni kaina na goya mata baya wallahi, taya mace mai hankali da natsuwa ace za'a ɗauka a ba wanda ko sallah bata dame sa ba a'aa ba zai yiyu ba auren budurwa da ciki ba...! Ikon Allah ashe ina da maƙiya dai a cikin gidan dole na tashi tsaye tabbas... * Zaune suke a falon Alhaji suna cin abinci "aunty ta kalli Alhaji tare da faɗin ina san zan yi tafiya gobe?" Kallon mamaki yake bin ta da shi tare da faɗin na faɗa maki bana San sai unguwa tazo gab sannan kice min haka ko? Amma kinki dai nawa yanzu mai kike so na ce maki kenan? Ɗan marairaicewa tai kamar zatayi kuka tace" haba Alhaji ayi hakuri yaron ƙawata ne bai da lafiya suna asibiti shi ne zan je ayi hakuri naje ta idasa maganar da alamar lallashi.." Okay ya faɗa! Wani dogo ne shi ba fari ba ba baƙi jikin sa ɗauke da farar jallabiya da baƙin hula fuskar sa ɗauke take da saje idanun sa farare tasss ya shigo cikin falon tare da sallama a cikin bakin sa.....wata Young girl ta taso da gudu ta tana faɗin "hamma well come fatan ka dawo lafiya?Hamma muna ta jiran ka mu ci abinci baka dawo da wuri ba har mun fara ci fa kana waje!'' Ohh sorry sister wallahi ina can masallaci ne, ai yanzu dai gani muje ciki ɗin.. Mummy dake gefe ta ce'' ina ka tsaya ne?" Mummy masallaci waya mukai da ogah ne shi ne dalili.. Alhaji ya ce'' nidai yau bazan ba hamma abinci ba, yaje matarsa ta bashi idan yana da ita!''. Duka aka sa dariya saboda kusan kullum sai Alhaji ya ce haka Abeed ya ce'' uhmm Ni dai ayi hakuri kada a hora ni aban ko Lipton ne!'' Aunty tunda ta gama cin abincin tai masu sallama zuwa ɗakin ta da minti 30 da tafiyar ta ita ma ta tashi zata tafi, mummy ta ce'' aunty zubaida ke ma tafiya zaki ne?" Ehh! Mummy ina san yin guga ne yanzu.. Okay! Falon ya rage daga mummy sai Abeed da Alhaji da sister (meenal) Lipton aka sa mashi ya fara sha ana yi ana fira Alhaji ya kalli Abeed ya ce" kodai sai mun kai hoton ka masallaci ne mata su zo su duba ko zakai kasuwa" Lipton din da yake sha ya ƙware sa, sai tari taya kamar shi ace za'a kai hoton sa don bai fitar da matar aure ba gaskiya, mummy dake gefe tai murmushi dai tare da faɗin ina ga dai da alama Hamman sister dai yai kwantai aka sa dariya..... Ya ce'' wayyo papi kada akai in Sha Allah very soon zaku ga mata ta da zan aura nidai a cigaba da min addu'a Allah ya ban ta gari shi ne fata na, but gashi yanzu an tura mu aiki ya bata rai abin da ya fi ban haushi ƙauye ma aka tura ni da Haroon fa ko wuta babu wayyo Allah na ya ida sa maganar kamar zai kuka... Alhaji ya ce'' sai ku koyi darasi a cikin rayuwa ai in Sha Allah lafiya lau zaku dawo kada ku damu kaji My son ya faɗa yana ɗan buga mai kafada" Mummy ina so kafin na tafi muje ingaida su "jadda tunda idan muka tafi zamu kai almost 1 year ko to 2 year in Sha Allah!" Okay yaushe zaka tafi kenan? Sister dake gefe ta ce'' mummy please nima zani don Allah!" Aunty da tafi ta kai tsaye ɗakin ta ta shiga ta kira kawarta tare da faɗin Please don Allah gobe zaki raka ni wajen boka saboda naga asirin yana neman karyewa, tana cikin wayar ne zubaida ta shigo ciki ta ce'' Aunty wallahi ina san Abeed kada ki bari na rasa shi!'" Ta ce........ [10/25, 5:27 PM] Fatima Fans: 🦋*ƘANWAR SHEHU*🦋 EP 3 By Nanamaryama *TEAM WOW 3 ELEGAN WRITTERS* *ƘANWAR SHEHU* *Nanamaryama* *RIKICIN DUNIYA* *MEENAT A YAN DOMA* *GIDAN AURE NA* *OUM SHARIFAT* Posting Room👇🏼 https://chat.whatsapp.com/FUeULeu12Is1lcTscF5Je6?s=cl&p=i&mlu=4 Comment section👇🏼 https://chat.whatsapp.com/DrrHAf8xE7P56YCUZkhGlG بسم الله الرحمن الرحيم Wani kallo mai wuyar fassara tai mata tare da faɗin don Allah "zubee ki bari na gama kashe wannan wutar tawa Please, nace maki indai Abeed ne kin Aure sa kin gama ma ki kwantar da hankalin ki kawai ta idasa faɗa tare da dafa mata kafada"........Ohh mummy shikenan nidai ina jira kada nazo ina jira kuma na rasa sa don naji ana maganar auren sa, so ki yi duk ƙoƙarin da zaki ki samar min shi ta faɗa tare da fita ɗakin!!.. Sako ne ya shigo wayar ta ta ɗauka domin ta gani number ƙawar tata ne ta turo mata test kamar haka “Hajiya ki kwantar da hankalin ki na samo mana wani sabon malami a Niger ne so ki shirya muje can ɗin gobe, aikin shi kamar yankar wuƙa yake”... Ohh Allah ya kaimu sai nazo ta tura mata da reply din ta!. Washe ƙarfe tara na safe suka haɗu a darling table domin yin break fast "Aunty ce ta haɗa ma kowa lokacin Abeed yana wajen motsa jiki, daga can ne ya shigo zubaida ta tashi ta gaida sa ta haɗa masa sai wani shige masa take kamar wadda zata haɗiye sa, ta ce hamma Abeed ina so zaka min wani assignment please!'' Okay kawai ya faɗa sai ki tura min ta was app' zan maki na turo maki badamuwa... Ohh "Hamma na ɗauka ai anjima idan kadawo zaka min but kuma naji kana maganar wai was app nidai zan zo ai min a fili Yadda zan gane karatun {munahuka yadda zata kalle sa da ƙyau 😅} don Allah!'' Baya san magana da yawa ya ce'' don Allah zubaida kiyi hakuri na maki a can banda lokacin da zan maki a fili but yau ina san zuwa wani gu ne kinga ko banda lokacin yin sa a haka..." Minti 30 suka ɗauka ana kari Alhaji ya tashi ya tafi aiki kowa ya koma part ɗin sa shi "Alhaji indai yana gari to kowa haduwa yake a karya tare da shi sai dai idan bai gari ne kowa yake yi bangaren sa".. Abeed ya ce''Aunty gobe nake san zuwa fa...'' Ohh ubangiji Allah ya kai mu lafiya dai but yau sai a shiga kasuwa ai masu tsaraba dai ko?.. Ehh! Mummy Wallahi kawata ina ganin asirin da nayi ya fara karyewa, saboda Alhaji gardama yake yake min gashi kuɗin da yake ban ya daina, ke nifa naga jalala cewar mummy!.. Ohh gaskiya na tausaya maki yanzu dai kafin muje can ɗin ko zamu fara zuwa gidan malam Babba? Muga ya abun zai kama.... Toh kawata duk yadda kika ce!.. Gidan Malam Babba suka nufa suna shiga tai sallama ya ce'' keeeee ba a mana sallama anan gidan kuma ta baya ake shigowa". Canzawa tai ta koma ta baya ta shiga ya ce mai ke tafe dake?? Uhmm Alhaji Alhaji ne, duk ta rude yace nssan mai zaki ce' bai baki kuɗi sannan kuma kina san raba shi da matar sa da yaran sa...! Eh haka ne.. Kin samu amma kuma sai kin kawo mana kwan sauro da idon maciji guda huɗu jan macijiya ma muke so...! Ido ta zato tare da faɗin wallahi ban san ina zan samu wannan abin ba, bansan ta ina zan fara ba........ Okay ki bada kuɗin sai a ba aljani ilgusu ya kawo!! Ma ƙudan kuɗi ta bada domin ai mata wannan aikin {ubangiji Allah ya rabamu da irin halin mummy} ya bata wani kullin magani ya ce wannan a Lipton zaki sa mai, wannan kuma turare ne ki rinƙa shafawa yana jin kamshin sa....! To to Nagode sosai tashi ta tafi.......sauran aikin kuma sai mu zamu idasa! * Jawahir don Allah ki daina ma babba rashin kunya ' kinga wannan fa kanin mahaifin ki ne kinji ko?? "Inno baba Nura ba abinda ya mana ke ma kanki kinsan haka ne, to name don na faɗa masa yaji ba daɗi nidai bazan auri wannan yaron ba wallahi, ba mai min auren dole ta faɗa tare da tashi wajen" Kamar kullum suna zaune suna cin abinci ita da inno sai ga "Jabiru ya shigo cikin gidan da sallama, ba gaisuwa ya ce ke matata ya akai ne?'' Kallon banza ta watsa masa tare da faɗin ka futar mana a gida wallahi ko na tara ma mutane sha_sha kawai mara ilimi...! Nuna kan shi yake tare da faɗin Ni kike zagi? Wallahi sai na aure ki ko kina so ko baki so ki rubuta ki aje ya fice gidan.... Inno tace Ohh mu muna ganin rayuwa amma zanyi maganin wannan mutanan!. Ƙarfe goma suka shirya domin tafiya Katsina "Alhaji ne ya karo masu kaya domin tsaraba ɗin'' mummy ta fito ita ma ta murmushi irin na muna fukai tana masu sallama! Aunty ta ce Abeed ga amanar sister nan ....... [10/25, 5:27 PM] Fatima Fans: 🦋*ƘANWAR SHEHU*🦋 EP 4 By Nanamaryama *TEAM WOW 3 ELEGAN WRITTERS* *ƘANWAR SHEHU* *Nanamaryama* *RIKICIN DUNIYA* *MEENAT A YAN DOMA* *GIDAN AURE NA* *OUM SHARIFAT* Posting Room👇🏼 https://chat.whatsapp.com/FUeULeu12Is1lcTscF5Je6?s=cl&p=i&mlu=4 Comment section👇🏼 https://chat.whatsapp.com/DrrHAf8xE7P56YCUZkhGlG بسم الله الرحمن الرحيم Aunty wannan yarinyar sai kin ban amanar ta kenan? Gaskiya bazan ɗauka idan ta mun a hanya ma sai na zane ta balle can da zan mata hukunci mai tsoka ya idasa maganar da murmushi a fuskar har dimple din sa na lotsawa.. Alhaji ya ce'' agaida jadda sai yazo in Sha Allah " motar suka shiga tada motar ya yi suka masu sallama suka fito har sunzo get sister ta ce ba zata ba ita ta fasa, ta fara kewar aunty tun yanzu.! Ya kalle ta tare da faɗin ikon Allah kin manta jiya kika takura sai an tafi dake? Ko kin manta ne na tuna maki ya wullama ta harara.... Kanta ta ɗukar ƙasa tana ƙwalla.... Abeed yace wallahi ko kukan jini zaki bazan komar dake ba har sai mun je, mun dawo sannan ya kunna karatu suratul Yusuf yana saurara, Abeed mutumin ne mai san karatun addini na boko ma ba'a baro baya alhamdulilah ta ko wanne ɓangare bai da matsala, minti 30 da tafiyar su barci ya ɗauke ta... * Mummy yanzu wannan shi zan zuba masa a lemon? Ta nuna mata ledar da ta bata.. Ehh kuma wallahi kada ki mun hauka' wallahi idan kika kuskura ki bari aka gani ko kika min ba dai-dai ba tabbas auren ki da "Abeed" fa bazan bari ya yiyu ba saboda nima ba kimin abinda kika min tabbas!.. Mummy wace ni na maki shirme, ta faɗa tana rufe fuskar ta irin ta ji kunyar nan... Ɗakin ta ta koma ta ci-gaba da chat a waya! *Wacece zubaida* Ita ƙanwa ce ga "mummy" (hadiza) tunda ta kyalla ido taga gidan iyayen ta basu dashi take cikin damuwa, daman zubaida akwai ta akwai san ƙarya a rayuwarta, ko makarantar su bata ƙawance da ke idan har gidan ku basu da kuɗi anan ne ta samu sunan zubee money, Hadiza ta taba aure da ta fito ne Alhaji wata rana yaje kasuwa ya haɗu da ita, kuɗin ta sun zube ta shiga damuwa sosai tun daga wannan taimakon da ya mata shikenan take san shi, tun Alhaji bai amince mata ba har ya amince suka fara soyayya ya aure ta, ga ta da mungun kishi ko lokacin da ta auri Alhaji akwai su "Abeed da Maryam"(sister) idan ta ga Alhaji na masu wasa wani haushi take a ranta, Alhaji mutun ne mai san yaran sa ga kulawa da yake masu tun daga nan mummy taji ta tsani aunty ita da yaran ta, amma ta kudiri niyar raba su wannan shine cikekken tarihin zubee yar wanka... *Back to story* Basu isa garin bakori ba sai la'asar lokacin da suka isa jikin "sister duk yayi evening 😀 ta gaji sosai sai barci take yi kamar wadda tai maye" yace Allah sarki baiwar Allah ta gaji, ɗan buga mata ka faɗa ya yi domin ta tashi, firgit ta tashi da addu'ar tashi daga barci ta ce wai Hamma har mun iso?? ina ga so kike mukai dare da bamu zo ba komi? Ni dai Please sauka muje Cikin gidan don wallahi na gaji over ya idasa faɗa yana kallon tare da mata murmushi, hannun ta ya kamo tunda yaga bata da alamar tashi ya fito da ita cikin motar....! Wallahi nagaji sosai kamar ni nayi driver ɗin..! Wani kallo ya watsa mata tare da faɗin Ehh man ce ke kika kawo mu gashi ma yanzu mun iso, ni matsa kada na buge ki, ki ɗauki wannan ledar dai ki shiga da ita ciki......ledar ta ɗauka ta shiga cikin gidan da sallama a bakin ta, jadda da ke zaune tana sauraron gidan rediyo na FM Funtua taji sallama kamar ta taƙwarar ta, ɗaugo kan da zatayi tai ido biyu da kyakkyawar yarinyar da take cike da so da begen ta, ita kanta da sauri ta idasa inda take ta rungume ta tare da faɗin "jadda yau dai Allah ya kawo mu domin ganin ki, wallahi munyi missing din ki jadda naga kin kuma wani kyau kamar wata budurwa?'' Jadda da murmushi ta ce''to idan banyi kyau ba to mai kike so nayi, kaji mun mata ta faɗa tare da dungure mata goshi hannun ta ta kama suka shiga ciki a palo suka tsaya ta faɗa kan kujera tare da faɗin wash Allah na!'' Duk kayan boot ɗin ya fito dasu, almajiri ya samu ya shigar mai dasu sannan ya shiga ciki "jadda" ce ta zo ta rungume sa tana masa oyoyo oyoyo daɗi ne ya kama shi kamar me ta ce yau ango na ke tafe lalle ina cikin alheri dumu dumu.. Dariya yasa mata tare da gaida ita cikin ladabi, ya ce ina uncle bash da mummy teemah?? Alhamdulilah"uncle bash dai yanzu zai shigo gidan, teemah kuma tana gidan ta kila Friday su shigo".. *Aunty* Zaune take kan kafet tana cin abincin ta sai ga wayar Alhaji ta dafa mai tsomo da duwon shinkafa, shi mutun ne mai bala'in san abincin gargajiya ko da yace ma mummy ta masa bata yi shiyasa idan ra'ayin abincin ya tashi ya ke kiranta tace badamuwa in Sha Allah zata yi tana aje wayar zubee ta shigo ta fuskar da murmushi ta ce aunty barka da hutawa? Alhamdulilah zubaida!. Uhmm daman zuwa nayi na tayaki fira naga mai surutun ba tana' ko idan akwai aiki sai na maki shine nace bari nazo.. Ita dai aunty har ga Allah zubee tana burge ta saboda yadda yarinyar take a natse bata da wata matsala a rayuwar ta ta ce'' zubee tom badamuwa Daman yanzu muka gama waya da Alhaji zai ci tuwo sai a daura masa bari na gama muyi tare ko?'' A'a gaskiya "aunty kina dani ace sai kin shiga cikin nidai zanyi ni ɗaya!'' Okay we can go now yata komi asa enough don Allah.. Daɗi har cikin zuciyar ta zata ai watar da Abinda take so, kitchen ɗin ta shiga miya ta Fara daurawa anan ne ta fito da maganin ta zuba ciki tuwon ma saida ta zuba masa kaɗan sannan ta ci-gaba da aiki sai da ta kusa gamawa ne "aunty" ta shigo cikin kitchen ɗin tare da mata sannu tasa mata albarka ta ce Masha Allah zubee kinga yadda kamshi ke tashi kuwa? Gaskiya kin iya girki sannu da kokari... Murmushi tai cikin zuciyar ta tare da faɗin ƙarshen farin cikin kin kine yazo a gidan wallahi sai kinyi dana sani tabbas, a fili kuma ta ce Nagode sosai aunty! Bakomi bari na dafa sobo tunda kin gama da wannan ko? Sai na rage maki da shi.. No zan dafa shi ma in Sha Allah yanzu kada ki damu kanki..... okay badamuwa ina zuwa sai naje part ɗin Alhaji na gyara idan kin gama ina can kinji ko?! Ehh dadi kamar ya kashe zubee saboda komi ya tafi mata need... Baba Nura ya kira matar shi yace yanzu saboda irin tabewa irin taki a hana ɗan mijin ki aure amma kice kinji daɗi yanzu haka adalci ne? Saboda Allah ba zaki ji tausan yaron nan ba saboda me? Nifa bawai naji daɗi bane a'a tun farko kai ka lalata shi ya koma haka miyasa nace haka duk Abinda zai yi baka kwaɓa masa, duk Abinda yake so shi yake yi yaron nan ga raina manya ga shaye-shayen da yake ta ina ko. Zan so a dauki yarinya mai tarbiyya a bashi Allah na tuba ai ko da an cuceta!... Tunda ta fara magana yake kallon ta saboda maganar tata mai zafi ce tabbas matar nan bata ƙaunar sa, kuma bai so ya sake ta saboda akan "jibril'' ya auri mata da dama kuma sun rabu saboda basu san shi suna suna mai tarbiyya shine dalili ya ce wallahi da ace zan iya rabuwa dake da tuni na wuce da ajin ki ya faɗa rai ɓace ya tashi ya tafi waje!.... Jibo harta mata yana bi taya za aba yar mutane mai mutunci ko don an ga mahaifin ta ya rasu haba "malam in Sha Allah bazata auri wannan yaron ba" tana zaune nan inda ya barta ya shigo a make tare da faɗin keeeee a ku..ya.. ina..wu..ni.. ji..ya.. na..ga..ki..bar..ci..... Ohh innalilahi wa'inna ilahir raji'un ubangiji Allah ya yaye maka wannan damuwar dake damun ka' kai da Musulmai baki ɗaya!! Wai daman ke ...ce... Anan... Na..gai...da...ki! Tashi tai ta bashi waje da shirmen da yake mata... Continue [10/25, 5:27 PM] Fatima Fans: 🦋*ƘANWAR SHEHU*🦋 EP 5 By Nanamaryama *TEAM WOW 3 ELEGAN WRITTERS* *ƘANWAR SHEHU* *Nanamaryama* *RIKICIN DUNIYA* *MEENAT A YAN DOMA* *GIDAN AURE NA* *OUM SHARIFAT* Posting Room👇🏼 https://chat.whatsapp.com/FUeULeu12Is1lcTscF5Je6?s=cl&p=i&mlu=4 Comment section👇🏼 https://chat.whatsapp.com/DrrHAf8xE7P56YCUZkhGlG بسم الله الرحمن الرحيم Kamar kullum tun ƙarfe 6 na asuba basu koma barci ba sai gyaran gidan ake yi "Inno ta ce Jawahir kinga yanzu an kusa komawa makaranta ko? To abincin kawai zamu rinƙa yi a gida ne ana zuwa sai ki daina tallar kawai kinga ba lokaci to!'' Inno kuma kina ga za'a zo a siya kada fa mu kwana ciki? A'a in Sha Allah za'a siya ma ki kwantar da hankalin ki, daga yau zamu fara a cikin gidan in Sha Allah zamu yi nasara haba Dr jawahir ya da sarewa haka a'a Allah na tare damu in Sha Allah... Allah yasa mu dace ta faɗa, karfe 8 dai-dai suka gama aikin su aka shinfida tabarma domin ƙari tana gamawa kuma suka huta inno ta daura abincin ita kuma kwanon da suka bata ta wanke su... Ƙarfe 12 dai-dai inno ta gama abincin inda can kasuwar ana ta jiran "Jawahir" ta kawo abinci amma shiru saboda inno tana gyara kayan ta, ita kuma mai saidawa ga tsafta komi nata tsaf take tafiya dashi, sallama aka fara cikin gidan abada abinci cikin kan kanin lokaci sai gashi har nema ake babu, inno ta ce kinga ni ai yanzu shikenan munyi dabara daga yau a gida zamu rinƙa komi kawai bazan iya wannan tallar ba kullum gaskiya!.. Wallahi kam anyi dubara kinga wanda ya siya yau zai faɗa gobe a gida aka yi ya saya ... Tabbas haka ne mudai Allah ya dafa mana! Suna zaune majociyar su ta shigo da sallama a bakin ta, suka gaisa da Inno ta ce don Allah tana san "Jawahir ta raka ta birni saro kaya ita yar ta bata da lafiya ne!'' Inno ta ce har ina zaki je haka? Ashe rabii ba lafiya ubangiji Allah ya bata lafiya to!! Amen ya Allah zanje Kano ne in Sha Allah.. Ubangiji Allah ya kai mu lokacin badamuwa! Godiya tai mata tare da tafiya.... Sai da ta tafi ne inno ta ce wai lafiya na daina ganin" rabi ne gidan nan?'' Bata rai tai tare da faɗin inno mun bata da ita fa.. Kai innalilahi wa'inna ilahir raji'un shiyasa nadaina gani