[7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA.... _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ NA UMMI A'ISHA DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI 1 ****Room 204 (A'isha specialist Hospital), a saman ƙofar ɗakin akwai nameplate wanda aka rubuta shi da kalar ruwan zaiba rangadaɗaɗau Dr. Mimi B. Muhammad MBBS, FMCOG, a cikin office din teburi ne guda ɗaya dake dauke da stethoscope yashe kamar mataccen miciji,patients file a gefen dama sai medical journals a ɓarin hagu kusa dasu wani framed ne dake dauke da hoto yana kallon ƙasa gefen shi littafi mai tsarki izu sittin ne ƙanana gwanin burgewa cikin gidansu,kujeru guda biyu gaban teburin, kujerar zaman ta lanƙaye da white coat dinta yayinda wani taftekeken window yake bayan kujerar wanda kana iya hango ƙaton lambun cikin asibitin da ko yaushe ke kaɗo iska mai daɗi mai kunshe da ƙamshin tsirrai da ciyayi yana kawowa cikin office din amma hakan baya hana ƙamshin antiseptic da mint gum bayyanuwa kowanne lokaci she told patients "fresh air helps healing" but she never opened it for herself,a jikin bango medical certificates dinta ne kakkafe tare da wani babban frame a jiki an rubuta "sometimes the doctor needs healing too". A hankali ta yunƙura ta tashi daga kan kujerar da take zaune wacce ke dauke da tarin tulin takardu da files na marassa lafiya bisa kan teburinta, wani ɗan ƙaramin katako ajiye akai sannan sunanta maƙale jikin katakon inda aka rubuta Dr Mimi Basheer Anda, ji take kamar ta ɗora hannu a kai saboda tsananin damuwa da baƙin cikin da take ciki, bata san ta fara zagaye cikin office din nata ba saboda tana cikin duniyar tunani, fargaba da kuma alhini ga tarin takaici da ya cika kwanyarta da kuma zuciyar ta baki ɗaya. Jikin teburinta taje ta tsaya ta dafa shi kanta na kallon sama, sanye take cikin bakar doguwar riga abaya wadda ta dace da jikinta, kanta ta saka dan ƙaramin farin hijabi amma duk da haka bai ɓoye tulin gashin da ya lullube goshinta ba baki sidik dashi, fara ce amma amma ɗau ba saboda wani irin kala fatar ta take dashi kamar gyadar da ta soyu (roasted groudnut), her eyes deep brown, tired but sharp like a surgeon's scalpel, she didn't wear makeup to hide she wore it like armor, madaidaiciya ce wurin tsayi da yanayin jikinta matsakaiciya dan bata cikin sahun masu kiba haka kuma bata cikin sahun sirara sai dai ta kirar jikinta tana da kiba ta kirjinta da kuma hips dinta dan tamkar tayi ciko sai dai kallo daya zaka yi mata ka gane natural halitta dinta ce haka a ƙalla zata kai shekaru 32 to 33 but her beauty didn't shout it whispered,she wasn't "pretty" she was presence, the type of woman who walks into a room and the air adjusts, Mimi's beauty was the kind that heals others, even when she was breaking. Tana jin lokacin da aka bude kofar office din nata aka shigo amma hakan bai sa ta iya sauke kanta ba daga kallon saman da take yi bare har ta juya taga wanda ya shigo, "Dr..... What's going on? Ga patients awaje da yawa suna jiran ki......." Cikin damuwa ta sauke kanta ta ja wata doguwar ajiyar zuciya kafin ta juya ta kalli Dr jalila, "Dr am not fine..... These days am not myself...... Am tired of everything....." Kallonta Dr jalila tayi na yan mintunan da basu wuce biyu ba zuwa uku tace da ita, "Dr why are you like this? You are a doctor and you are saying you no fine? Kina duba wasu ma bare kuma ke kanki? Idan kina ganin kina bukatar hutu you have to take a leave and rest.... But karki takura kanki, kina nemawa wasu lafiya ke kuma kina kokarin cutar da taki lafiyar we don't want this.... " " Okey Dr thank you.... Insha Allah i will think about it.... " " ok Dr, don't mention it " Bata ƙara magana ba wayarta dake ajiye kan tebur dinta ta fara ƙara hakan ya bawa Dr jalila damar juyawa dan fita daga cikin office din ita kuma ta kai idonta kan wayar tata ta tsura mata ido tana kallonta tare da kai hannunta ta ɗauka amma ta kasa ɗaga kiran sai kallon kan screen din wayar take _Hayatie_ shine sunan da tayi wa mai kiran nata saving dashi wanda harda heart guda biyu da padlock duk maƙale jikin sunan, tana ji kuma tana gani har wayar tayi ta katse wani kiran ya sake shigowa wanda shima bata ɗauka ba shi kuma mai kiran tamkar baida niyyar haƙura har sai ta ɗaga, Kan kujerarta ta koma ta zauna cikin damuwa ta ɗaga kiran ta kai wayar kunnenta sai dai bata yi magana ba, "Mimi..... My love can you hear me?" "ina jinka..." "My love.... I have been missing you, i have been missing you every day......." Numfashi ta ja da kyar kuma ta fesar dashi da kyar saboda sarkewar da kirjinta ke yi time to time, cikin damuwa tace, "Wannan shine abinda na jima ina nuna maka amma taurin kanka da zafin fushin ka da kuma fusatacciyar zuciyarka ta hanaka gani da kuma fahimta..... Yanzu gashi muna ji muna gani ka haramta mana rayuwa da juna...... And you know what? The most painful part of it is that ban taɓa jin ina mugun sonka ba sai yanzu da hakan ta kasance yaya Aliyu.... Wallahi yanzu son da nake maka ya ƙaru da irin yawan da ni kaina ban san ta yanda zanyi explaining ba..... Ka sakani cikin damuwa, am always thinking about you..... Kullum dama acikin zaman mu ina fada maka mu ba yara bane idan matsala ta faru kamata yayi mu zauna muyi discussing da juna ba wai muyi ta fada ba, munyi girman da ya wuce muyi irin wannan since we are not a child......" Daga can inda yake zaune taji shima ya ja ajiyar zuciya kamar wanda yayi kuka ya ƙoshi, babu abinda yake hangowa sai irin kyakkyawar surarta da dirin da Allah yayi mata, " Mimi i know that I mess up...... Yanzu dai duk wannan maganar bata da muhalli kawai mu nemi mafita kamar yadda na fada miki daren jiya a waya, kema kin san ba zan iya rayuwa batare da ke ba.... Kema kuma na san ba zaki iya rayuwa ba tare da ni ba, dan Allah mimi kar ki haramta mana cigaba da zama da juna, wannan shawarar da na fada miki ita kadai ce mafitar mu, kinyi tunanin?? " " Yaya Aliyu har yanzu ban gama yanke hukunci ko tunani akan wannan maganar ma ba wallahi, asalima tun bayan da muka gama waya da kai na kasa komawa bacci gashi har yanzu da na fita office bana cikin hayyacina kawai ina ta tunani kamar wata tababbiya..... Ka sake bani lokaci" "Mimi bamu da lokaci fa, kin san iyayen mu, komai na iya faruwa..... Dan Allah ki amince da wannan shawarar tawa dan wannan hanyar ce kadai mafita a gare mu, we have no option... Ni ban yarda da kowa ba sai shi" "ka bani time zuwa lokacin da zan koma gida..... Duk abinda na yanke zan fada maka.... Insha Allah I will let you know" "to shikenan mimi na, I love you" "I love you more yaya haidar..." Katse wayar tayi ta ajiye ta zuba mata ido bayan tayi tagumi, ita kanta ta san a yanzu dai bata da nutsuwar da zata iya duba patients yanda ya kamata har ta yi musu abinda ya dace shiyasa ta tattara nata yanata kawai ta nufi gida ba wai dan lokacin tashinta yayi ba. * Kyakkyawan saurayi ne matashi fari dogo siriri mai manyan idanuwa da dogon hanci ɗan kimanin shekaru 27 zuwa 28.Tashinsa daga bacci kenan yaji wayar shi na ƙara, mika hannu yayi ya dauka fuskarshi dauke da murmushi sakamakon ganin sunan wanda ke kiran nashi, "Irfan yane? ya ake ciki?" "gani nan zan zo gidan na dauke ka yanzu...." "ok to sai ka shigo, bari nayi wanka before ka karaso...." Daga haka ya ajiye wayar ya sauka daga kan tafkeken gadonshi ya shiga toilet wanka yayi bayan yayi brush ya fito yana kallon time yaga 1 saura wasu mintuna cikin kasala mai hade da gajiya ya soma shiryawa, yana saka kayanshi ya jiyo shigowar Irfan cikin gidan take kuma ya fara damunsa da wani irin mahaukacin horn, wayar shi kadai ya dauka ya fesa turare a jikinsa sosai ya fita, babu kowa a gidan sai iya masu aiki kadai shiyasa batare da ya saurari kowa ba ya fice yaje ya samu Irfan cikin mota yana yin waya, bude gaban motar yayi ya zauna yana kallon Irfan din dake waya, "Yanzu ina gidansu Daddy ne naje dauko Afeef zamu karasa gidan yanzu insha Allah kafin ki dawo.... Zan fada mata..... Ok to adawo lafiya" Kallon Afeef din Irfan yayi bayan ya gama wayar ya ajiye ta, "Anty Mimi ce.... Saƙo ta fada min wai in fadawa hajiya saboda tana ta kiran wayarta bata shiga" "Oh Allah sarki ni tunda na dawo ma har yau ban hadu da anty Mimi ba fa...." "Hmmmmm ai akwai matsala ne.... Anty Mimi na cikin damuwa sosai" Cike da mamaki Afeef ya kalleshi saboda jin abinda ya fito daga bakin sa, "me ya faru? Ko damuwar rashin haihuwa dinne?" "harda wannan dinma amma yanzun dai ka san sun rabu da yaya Aliyu....." Bude baki Afeef yayi yana kallon Irfan cike da mamaki, "yaya Haidar ya saki anty Mimi?" "wallahi kuma har saki uku Afeef.... Ashe ba muyi maganar da kai ba.... Har fa ta gama idda ko yanzu ta samu miji aure zata yi" "innalillahi wa inna ilaihir rajiun..... Ban taɓa sani ba wallahi sai yanzu.... To shi kuwa yaya Haidar me ya sameshi haka? Me yayi zafi shi da ba shaye shaye yake yi ba, saki har uku...... This is bad.... Soo sad" "very very sad Afeef....." "gaskiya banji dadin jin wannan labarin ba, Allah ya rufa asiri yasa haka shine yafi zama alkhairi" "amin ya Allah..... Anty Mimi na cikin damuwa tun bayan da abin ya faru wallahi" "to ai mutuwar aure babu dadi ne Irfan, gashi kwata kwata auren nasu kamar bazai fi 6 years ba ko?" ina iya tuna time din da akayi bikin nasu" "ehh 6 years yanzu...... Idan ma bai karasa ba to kadanne fa..." "kai amma yaya Aliyu bai kyauta ba" "babu komai ai, suma su Abba duk basu wani damu sosai ba, tunda abune na family, duk gida ne to babu ma amfanin fushin..... Hajiya ce dai kawai ta damu" "wannan dama ai sai tafi kowa bala'i ni shiyasa zaka ga bana son abu ya hadoni da ita..... Ta fiya masifa wallahi" Dariya Irfan yayi ya juya ya kalleshi sannan ya mayar da idanuwanshi kan titi yaci gaba da driving dinsa kafin yace, "wallahi bari su daddy dai su ji ka, hajiyan tasu kake kira da masifaffiya ko?" "to karya nayi, mace kin tsufa ma ba zaki hakura da faɗa da masifa ba" "zaku gauraya ne.... Kai ai ɗan lelenta ne ma na manta, duk cikin jikoki tafi ji da kai" "na sani ai" ya fada yana dariya, har suka je unguwar GRA maganar da suke yi kenan, gidane babban gaske mai dauke da gate guda uku, biyu suna kallon juna yayin da suka saka ɗaya a tsakiya gaba ɗaya gidajen upstairs ne na alfarma wanda ya ƙawatu kuma ya wadatu da shuke shuken flowers da manyan bishiyoyi kala kala a tsakiyar wawaken filin gidan akwai round about wanda ke zagaye da fitilu masu kyau da tsari dan ƙarawa gidan ado da ƙawa, ko ina manyan motoci ne lafiyayyu a faffake suna numfash, wanda yake tsakiyar suka shiga gidane madaidaici dan sauran sun fishi girma, masu aikin gidan suka fara cin karo dasu suna ta aikace aikacensu na abincin rana, ciki suka shiga inda wani babban falo yake sai bedrooms guda uku, biyu a ƙasa guda ɗaya a sama, wata farar dattijuwa na zaune kan kujera da farin glass a fuskar ta, a shekaru zata kusa shekara casa'in koma ta ɗora, Da sallama suka shiga ta amsa tana kallon su ɗaya bayan ɗaya har suka samu wuri suka zauna, "Afeef..... Sai yau ka gadamar zuwa ka gaishe ne lele?" "hajiya ni tunda na dawo babu inda naje ga Irfan nan ki tambaye shi kiji" "to Allah ya sawwake..." ta fada tana mayar da kallonta ga Irfan, "Hajiya anty Mimi tace in fada miki yau da wuri zata dawo kisa ayi mata lunch kafin ta dawo wai faten dankalin turawa take so asa mata wake kadan da ganye aciki..." Kai ta gyaɗa sannan tace "Allah ya dawo da ita lafiya... Bari in fada musu" yunkurawa tayi ta tashi ta fita, bayan ta fita Irfan ya kalli Afeef yace, "zo mu shiga gida muci abinci dan ni yunwa nake ji" "nima yau banyi ko breakfast ba ina ta bacci amma mu bari wannan tsohuwar ta dawo kafin tayi mana sharri tace mun ɗaukar mata wani abu ka san halin ta....." "kuma tsaf zata fada ba..." Shuru dukkan su suka yi saboda shigowar hajiya kaka kamar yadda suke kiran ta, zama tayi tace, "kuma din da ban gayyatoku ba gashi nan nasa a kawo muku abincin ba dan halinku ba...." "ai mu dama kin bar kayanki dan bama son gori..." Afeef ya faɗa yana ciccin magani, muficin dake kusa da ita ta ɗauka ta jefa masa tana cewa, "ai kuma ka dawo lele..... Zaka yimin shuru ko sai na fasa bakinka" "hajiya kaka wallahi gaskiya fa ya faɗa, ke ba abin ki bawa mutum abuba gori ya biyo baya..." Irfan ya fada yana dariya, "ku dai kuka sani... Kwa kai shi in kayane" Ahaka masu aiki suka shigo suka same su suka kawo musu abinci, jallop din shinkafa da salad sai farfesun kaji a wani mazubin na daban sai kuma waina da miyar taushe, ƙasa suka sauka suka zauna kan carpet suka zuba abincin suna ci suna tsokanar hajiya kaka, shigowar Mimi yasa gaba ɗaya suka mayar da kallonsu da kuma hankulansu gareta wanda kallo ɗaya zaka yi mata ka gane dunbin gajiyar da take tattare da ita wadda ta bayyana ta kasa ɓoyeta......... This is where it all starts, where the pain begins, where the love refuses to break............! The question is would you have stayed if love stopped looking like it used to?? Please don't scroll fast..... *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now and it's 1k,pay to 7044644433 Moniepoint micro finance bank ,send your evidence to 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifi ɗaya# #EmotionalRomance# #Haidar# #MimiAndAfeef# Ummi Shatu 👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA...! _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ NA UMMI A'ISHA 2 ***Hankalinta baya tare da ita shiyasa bata ma gansu ba har sai da ta shiga cikin tsakiyar falon inda suke baje suna cin abinci ga hajiya a gefe sun sakata a gaba kowa sai faman yi mata yake yi, "Anty sannu da zuwa...." Irfan ya faɗa daidai lokacin da tazo kusa dasu, "yawwa sannu....ya gida" "sannu da zuwa anty..." Ai cikin sauri ta juya nan ta ganshi zaune shima yana cin abinci yana sanye da shadda milk colour, take taji gabanta ya fadi saboda abinda yazo kwakwalwarta wanda ta tuna yanzu yanzu, "yawwa sannunku yagida" daga haka kawai ta wuce cikin bedroom dinta duk suka bita da kallo ciki harda hajiya, Tana shiga cikin bedroom ta zauna gefen gado gabanta na cigaba da faduwa da karfi fat fat, wannan menene abinda Aliyu ke shirin yi? Ya sunan wannan abin da yake ta kokarin sai ya shawo kanta sun aikata? Afeef fa? Kai gaskiya kamar da sake, wannan abun bazai yuyu ba,watsi tayi da wannan tunanin kawai ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito har lokacin kwanyarta cike take da abubuwa iri iri, tabbas tana son Haidar kuma a yanzu bata da wani buri illa taga sun koma matsayin ma'aurata amma kuma wannan shawarar da yazo da ita kamar ba zata haifar musu da ɗa mai ido ba it will not end well, zama tayi bakin gado ta dauko lotion zata shafa amma kuma tunani ya hanata yin hakan. Babu wanda yayi magana bayan Mimi ta shiga daki, shi dai Afeef acikin ransa yana ta mamakin yadda bata tsaya ko ta zauna sun gaisa sosai ba saboda a sanin da yayi mata da tana da son hira haka kuma tana zama tare dasu sosai cikin su ayi ta tsokanar kaka shima kuma tana yawan yin waya dashi saboda rashin lafiyar da yake dauke da ita, sai dai da yake yanzu tunda ance ga matsalarta akwai abinda yake damunta dole ayi mata uzuri, suna gama cin abincin Irfan yace masa, "zo muje wurin anty Mimi kafin mu fita salla..." Tashi yayi yabi bayan sa suka nufi bedroom dinta har lokacin tana zaune daga ita sai towel daure a jikinta iya cinyar ta, ba tare da sun yi knocking ba suka shiga, da kallo ta bisu kafin suka ji tace, "menene haka ku kuma? Get out...." "anty Mimi Afeef ne fa yazo ya gaida ki....." "baku ganin daga wanka na fito, ku fitar min a daki......" "we are sorry anty..." Afeef ya fada tare da yin baya ya fita shima Irfan yabi bayan sa yana ce masa, "kaji anty da wani irin abu, yanzu dai kawai haka ta koma fa koda yaushe tana cikin fada da bacin rai" "A'a she's right fa bai kamata mu shigar mata ɗaki haka ba, she need her privacy..... Munyi laifi dai kawai" "to ai dan mun ganta ahaka ba wani abu bane tunda she's our blood sis..." "you are not serious" Afeef ya fada yana dukan kafadarshi, masallaci suka je kai tsaye bayan sun fito daga sallar ne suka shiga gidan su Irfan wato gidan Abba Fari kamar yadda yaran ke kiransa saboda shi fari ne yayin da dan uwansa kuma baƙi ne sai dai kamar su daya sak, Ammi suka samu tana zaune kan carpet din sallah inda ta idar tana zaune tana lazimi ita kuma Suhana tana kitchen ita da Janan suna haɗa abinci, ganin shigowarsu yasa Janan zungurar suhana tana yi mata magana a hankali, "Yaya Afeef yazo.... Wow.... Kalleshi" Murmushi suhana tayi ta dan kalli inda su Afeef din suke sannan taci gaba da abinda take yi kafin tace, "Janan kina son yaya Afeef da yawa gashi kuma kin kasa sanar dashi..... The earlier the better...." "ki bari kawai suhana, ina so ne in sanar dashi a lokacin da ya dace..... Ban son yayi rejecting dina...." "babu wani rejecting dinki fa da zai yi..... Do you see yourself? Kin hadu fa yanmata" "ai yafini haduwa.... Kalleshi fa, haba yaya Afeef ai duniyar kyau ne...." "ni dai Kinga kibar wannan santin mu kai abincin dining kafin Ammi ta gaji tayi magana" Tun kafin ta rufe bakinta taji muryar ammin tana kiran su, komai da ya dace suka fara tattarawa suka nufi ciki nan suka iske su Irfan gaban Ammi suna gaisawa tana sake tambayar Afeef, "Afeef ya jikin naka? Da sauki dai ko?" "ehh da sauki Ammi.... Alhamdulillah" Da kallo Janan keta faman bin Afeef kamar zata hadiyeshi, zama suka yi suma suka gaida su sannan cikin alamun jin kunya tace, "yaya Afeef an dawo lafiya? Ya jiki?" "alhamdulillah Janan, da sauki..... Yasu Umma? Ai zan shiga in gaida su...." "duk lafiya lau" ta fada cikin jin kunya sannan ta koma gefe ɗaya ta zauna tana kallon Afeef din wanda ya sake suna ta hira da Ammi domin dama ko a waya ne suna kwashe lokaci mai tsawo suna hira bare kuma da gashi gata yanzu, "kai matsalar ka baka son maganin gargajiya ne Afeef amma irin wannan lalurar taku dole sai ana hadawa da na Hausa...... Zan karbo maka indai zaka sha" "to Ammi.... Insha Allah zan sha" "kamar gaske..." Irfan ya fada cikin tsokana. Sun jima zaune a part din Ammi har zuwa la'asar lokacinne suka fita, bayan sun yi salla suka shiga part din umma, itama kamar Ammi haka take da kirki da haba haba da mutane anan yanmatan gidan suka kewaye su a nata hira bama ya Janan da take ta jan Afeef da hira a takaice dai basu suka samu kansu ba sai magriba lokacinne suka zauna suna hira shida Irfan, cikin damuwa ya kalli Irfan yace, "ni damuwata Allah yasa wannan matsalar ta anty mimi da yaya Aliyu bata taɓa zumuncin iyayenmu ba...." "babu abinda ya taɓa zumunci kawai dai ka san dole kowa zaiji babu dadi, gashi nan dai kawai lamarin sai dai mu rakashi da addu'a..." Irfan ya bashi amsa yana kai kallon sa gate dan ganin wanda zai shigo saboda an bude gate din nan yaga Abbansu ne sai kuma Abban su Yaya Aliyu shima yana biye dashi cikin tasa motar a bayansu kuma Daddy ne wato mahaifin su Afeef, yanayin yanda zumuncin iyayensu yake dole ya burge kowa bama iya kadai su da suke matsayin ƴayansu ba, Tashi suka yi suka nufi wurin iyayen nasu, nan kowanne ya fito fuskarshi dauke da fara'a da kuma farin ciki, kusan kullum dama a al'adarsu nan suke haduwa wurin hajiya suyi hira zuwa bayan sallar ishah kuma kowa sai ya nufi gidansa, idan akwai wata magana da zasu tattauna duk a wannan lokacin suke tattauna ta, "soja marmari daga nesa....." Abba fari ya fada cikin tsokana yana kamo hannun Afeef dake kokarin tsugunnawa domin ya gaida shi, "Mazan fama ba.... Soja mazan fama" shima Abbansu yaya Aliyu ya fada yana dafa kafadar Afeef din wanda daidai lokacin Daddynsu ya karaso tare da Irfan yana rike da hannun Irfan din, tare gaba daya suka rankaya suka shiga part din hajiya wanda dama tuni ta saka masu aiki sun yi shimfidu irin na alfarma kamar yadda aka saba yi musu kullum sannan ga kunun shinkafa nan da aka yi yasha madarar ruwa wadatacciya sai fruits da farfesu, kullum ta Allah wannan hidimar haka ake yinta, Can gefe suka samu suka zauna shida Irfan wanda gaba daya yafi mayar da hankalinsa kan wayar shi dake hannunshi yana ta faman murmushi shi kadai, "wai wannan murmushin da kake ta faman yi me yake faruwa ne? Kai da waye?" Dariya Irfan yayi kafin yace "kayi min alkawari idan na fada maka ba zaka titsiye min budurwa ba kasa ta a gaba da tambayoyi.. “ " I promise... " " ni da Manal ne..... Tana yimin wata hira ne " Tsaki Afeef yayi yace," kuna gulmata dai... " Shigowarsu yaya Aliyu da yaya faruk yasa gaba daya kowa ya maida hankali kansu, cikin girmamawa Irfan da Afeef suka gaida su saboda sune manyan yayu kuma suma age mate ne,fuska a sake yaya faruk da yaya Aliyu duk suka amsa, wurin da suke zaune kafin shigowar su yaya faruk din suka koma suka cigaba da hirar su har zuwa lokacin da su ka fita sallar ishah bayan sun idar Irfan ya maida shi gida, bai shiga ciki ba daga waje suka yi sallama ya wuce shi kuma ya shiga gida, mommy na zaune a falo ita da Manal ya shiga ya zauna kusa da mommy yana kallonta, "mommy bakya nemana ne....." yace da ita yana turo baki, "to ba ka tafi can danginku ba mu ka manta damu...." Dariya yayi ya kwantar da kanshi jikin kujera yace, "kai mommy nida tunda na zo ma ban fita ko ina ba sai yau....." "to ai shikenan....." Kafin ya kara magana wayar shi ta fara kara, duk tunanin shi zai ga Irfan lokacin da ya ciro wayar daga aljihunsa amma sai yaga yaya Aliyu ne, dauka yayi cikin nutsuwa yace, "hello yaya haidar....." "hello.... Afeef ya kake?" "alhamdulillah yaya..." "gobe dan Allah ina nemanka.... Zan kiraka da safe insha Allah sai in fada maka inda zaka same ni" "ok to shikenan yaya, Allah ya kaimu" Katse wayar yayi yana kallon Manal dake kallonsa ta zuba masa ido kamar yau ne ta fara ganin sa, "what?" yace da ita shima yana kallonta, "yaya..... Bani aron wayarka" Mika mata yayi yana kokarin tashi, dan kallonta yayi yace "kina gama abinda zaki yi ki dawo min da wayata bacci zanyi" "abincin fa? Ko kaci wurin kakar ku?" mommy ta tambaya idanuwan ta a kanshi, "ehh wallahi na koshi mommy.... Kunu muka sha nida Irfan" Daga haka ya tashi ya nufi part dinsa yana shiga wanka yayi kawai ya kwanta lokacin da ya kwanta kuma sai ya fara tambayar kansa to me kuma ya faru da yaya Aliyu ke son ganin sa? Bayan dazun nan suka rabu a gidan hajiya ai da idan akwai wani abu tun lokacin zai yi masa magana, da wannan tunanin bacci ya dauke shi baima san lokacin da Manal ta gama amfani da wayar shi ba ta kawo masa. Tunda anty Mimi ta tashi yau haka ta tashi jikinta a sanyaye haka kuma ranta gaba daya a ɓace zuciyarta nata faman harbawa da kuma jin kunci, cikin wannan yanayin tayi wanka ta shirya ta fita aiki batare da tayi ko breakfast ba, tana fitowa hajiya na zaune falo tana shan tea saboda lokacin wurin karfe 11 na safe, "Hajjaju ina kwana?" Kallonta hajiya kaka tayi kafin ta gyara zaman gilashin idonta tace, "takwara ya naga kamar har fita zaki yi baki karya ba?" "ehh wallahi hajiya inada patients da yawa ne nasani suna can suna jirana...." "to ai ko suna jiran ki dole ke kici abinci tunda aiki bazai yuyu ba sai an koshi..... Baza ki rinka nemawa wasu lafiya ke kuma kina janyowa kanki wata rashin lafiyar ba Mimi.... Ulcer fa gaskiya ce kin fini sanin haka.... Tsaya ki tafi da abinci kuma lallai lallai idan kinje asibiti ki ci karki zauna da yunwa " Ba dan zata ci dinba kawai ta amsa da to aka yi mata packaging ta tafi dashi tana driving hankalinta duk a rabe sai tunani take yi, wannan shawarar da Yaya Aliyu yazo da ita wallahi gaba daya bata kwanta mata arai ba kawai dai dan babu yanda zata yi ne, da tunane tunane fal ranta ta shiga asibiti tayi parking motarta kai tsaye ta nufi office dinta kuma tana zama taji knocking, "come in...." kawai ta fada ba tare da ta daga kanta ba dan ta janyo wani file ta fara rubutu a jiki, Aliyu ne ya shiga ciki yana sanye da farar shadda kar mai tsadar gaske kansa babu hula, "good morning my love...." ya fada idanuwansa narai narai kamar zai fashe da kuka, sai lokacin ta dago da kanta tana kallonsa take taji ta kasa cigaba da rubutun da take yi kawai ta zuba masa ido tana kallonsa shima yana kallonta har tsawon mintunan da basu san adadinsu ba dan ahaka Afeef ya shigo ya samesu, Cikin wani irin yanayi da ba zata iya fassara shi ba ta janye idanuwan ta daga kallon da take yiwa Aliyu ta mayar dashi kan file din da yake gabanta, tana tsananin son Aliyu irin son da bata san shi ba sai yanzu da saki har uku ya shiga tsakanin su ya zama katangar da ta raba tsakaninsu, "Afeef ka karaso..... Bismillah" "ehh wallahi yaya, ina kwana... Anty mimi ina kwana?" Afeef ya fada yana sanye da kananan kaya jeans baƙi da t shirt coffee, fari ne sosai siriri dogo mai kyakkyawar sura, a haife bazai wuce 27 years ba saboda sa'an Irfan ne amma Irfan dinma ya girme masa da wurin watanni shida zuwa bakwai, ba tare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba ta amsa ciki ciki, "lafiya lau..." Zama yayi kan kujerar dake gaban teburinta tana fuskantar yaya Aliyu, cikin damuwa da nutsuwa yaji yaya Aliyu yana yi masa magana kamar haka, "Afeef.... Kasan kai matsayin ƙani kake gare mu nida Mimi, duk duniya yanzu banda wani wanda na yarda dashi sai kai haka itama Mimi, wallahi Afeef muna cikin wata masifa da jarrabawa, muna bukatar taimakonka.... Kai kaninmu ne na jini tushenmu ɗaya haka kuma mu ahali ɗaya ne sannan duk daga cikin tsatso ɗaya muke.... Tunda na saki Mimi rayuwata ta hargitse ta shiga garari itama kuma haka, dan Allah muna son kayi mana wani taimako ka auri Mimi na tsawon watanni biyu zuwa uku saboda bama son su Abba su gane ko su hajiya su fahimta.... Ba sai ta tare ba zaka saketa dan ina so ne zan mayar da ita..... Mun san idan wani muka samu na waje ba lallai ya cika alkawari ba sai azo ana samun problem ana kai ruwa rana watakila idan ba ayi sa'a ba har asarinmu ya tonu...... " Cikin razani da tashin hankali Afeef ke kallon yaya Aliyu cikin ransa yana tambayar kansa anya yaya haidar bai haukace ba kuwa? Anya yasan abinda yake fada? Anty Mimi fa? To shi yanzu ta ina zai ma fara auren anty Mimi idan har lissafinsa bai rushe ba yana tafe daidai she's 32 or 33 yanzu dan wurin 4 years ta bashi, "Afeef kana jina? Ka samu su hajiya ka fada musu kana son Mimi su aura maka ita na san ba zasu musa maka ba kuma baza su hanaka auren ta ba tunda duk gida ne...." "yaya wai ka san abinda kake fada kuwa? Anya yaya lafiyarka ƙalau? Are sure you are okey" "Afeef wallahi lafiya ta ƙalau kuma ina cikin hayyacina sannan na san abinda nake fada, ni dai kawai dan Allah ka taimake ni ka yimin wannan alfarmar tun kafin na shiga wani hali dan ina son matata itama kuma tana sona.... Karka wani damu auren kisan wuta za kuyi da ita ba wai wani abu ba..... ". Hmmm what do you think will happen in the next chapter? Drop your guesses, comment what you think......... Next chapter loading...... ✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifi ɗaya # #EmotionalRomance# #MimiAndAfeef# _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA.... _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ NA UMMI A'ISHA 3 ***Mamaki, fargaba da kuma zulumi duk shinfide kan fuskar Afeef yake kallon Aliyu zuciyarshi na lugude kamar zata faso kirjinsa ta fito, wai wannan wanne irin kwaɗo ne? Da wanne suna zai iya kiran wannan kwamacalar wacce Aliyu yazo da ita, "ka fahimceni Afeef? Wani abun fa dole sai naka ne zai iya yi maka..... Nasan zaka yimin wannan alfarmar ko ban baka ko sisi ba..... Ka fadi duk abinda kake son inyi maka a duniyar nan, wallahi zanyi maka idan har zaka amshi wannan bukatar tawa...." "wai dan Allah kai waye ya baka wannan shawarar Aliyu? Me yasa sai wannan ɗan jaririn? Afeef nawa yake da za ayi wannan abin dashi...." Juyawa yayi ya kalli anty Mimi wacce ke magana cikin zafin rai, tunda aka fara maganar dama bata saka baki ba sai yanzu, " Anty Mimi ina ganin girman ki amma kar ki sake kirana da jariri..... " shima ya fada cikin zafin rai, babu kalmar da tafi bakanta masa rai ta hassala shi irin jaririn da ta kira shi da shi a iya saninshi ai shi yanzu yafi karfin a kirashi da jariri tunda jariri na can bayan tsohuwar sa,kamar dama jira take ya tanka ta rufe shi da faɗa ta fara balbala masa masifa kamar zata doke shi, "kai wanene idan ba jariri ba awurina, kana da wani girman ne wanda yafi wannan? Yaushe ma kazo duniyar da har ka girma? Tatsitsi da kai....." Murmushi yayi mai cike da takaici da kuma baƙin ciki, "yaya haidar ba zan iya wannan abun da kake son inyi maka ba..... Sai anjima" daga haka ya tashi ya fice ransa a ɓace zuciyarsa na faman tafarfasa wallahi ba dan yana ganin darajar anty Mimi ba idan wata ce ba ita ba bata isa ta faɗa masa haka ya ƙyaleta ba da sai ya dauki matakin da gaba daya baza su ji dadinsa ba, ransa a mutukar ɓace ya shiga motar sa ya fita daga cikin harabar asibitin ya nufi wurin Irfan. Bayan fitar Afeef Aliyu kallon Mimi yayi cikin damuwa da fuskar lallashi yace, "My love..... Fushi yanzu da zafin rai duk ba naki bane, dole sai kinyi hakuri kin dauke kai sannan zamu samu abinda muke so daga wurin yaron nan, idan muka ce zamu bishi ta zafin kai to bukatar mu ba zata taɓa biya ba...." Dafe kanta tayi cike da damuwa idanuwan ta a lumshe tace, " ni dai haka kawai banji hankalina ya kwanta da Afeef ba cikin wannan batun, me yasa ka dage lallai sai shi? Why? " " Afeef cousin dinmu ne daga ni har ke dan haka na san zai yi wahala yaci amanarmu gaba daya, sannan na san yana ganin girman ki dan haka da wuya yace zai cimin amana ta hanyar raɓarki sabanin idan wani ne a waje na san zai yi wahala bai yi yunƙura aikata hakan ba ni kuma hakanne bana so, bana fatan wani namiji ya shigar min gona ta.... Wannan shine reason dina na son ayi sabgar nan da Afeef... Ki daure kiyi hakuri har mu shawo kansa ya amince, idan bukatar mu ta biya shikenan... " " it's fine.... " shine kawai abinda tace ta kifa kanta kan teburin dake gabanta dan ta rasa me yake yi mata daɗi kuma, sallama Aliyu yayi mata ya fita kuma yana zuwa motar shi ya fara kiran Afeef bayan ya tura masa sako, Afeef na cike da damuwa ya ƙarasa gidan Hajiya inda Irfan ke can yana jiransa, gashi yana dauke da damuwa amma kuma babu halin faɗa ko sanar da wani, duk yadda yake biye hajiya suyi ta haurawa amma yau bai kula ta ba kuma yana zuwa ta fara caccakeshi da masifa, "sarkin zurfin ciki.... Na jima banga mugun mutum irinka ba lele, kowa yana bude baki yayi sallama amma kai sai dai kawai in ganka ka faɗo min cikin ɗaki sai kace kaine ka gina min dakin..... Wannan isar taka da ikon nan da kake yi a gidan nan ya isa haka, ko iyayen ku idan sun zo shigowa sai sun yi sallama da budaddiyar murya amma kai da yake isasshe ne sai ka gadama..... " " wallahi nayi sallama kawai dai baki ji bane tunda yanzu ba wani ji kike yi ba sosai.... " ya fada cikin nuna alamun ƙosawa da maganar, " to yanzu da naka kunnen nake ji da zaka ce bana ji..... Nace naka kunnen ka bani aro nake ji yanzu da kake ikirarin bana ji? " " ohh Allah..... Ni dai yau na shiga uku, dan Allah hajiya Allah ya baki hakuri naji banyi sallama ba shikenan...." ya fada yana dafe kansa wanda yaji yana shirin fara yi masa ciwo, shigowar Irfan ta sa hajiya mayar da kallonta kansa shima ta fara balbale shi da fada, " kai ba tun jiya nace akira min kai ba shine ka ki zuwa sai yanzu da wannan marar kunyar yazo sannan zaku haɗo kai kuzo...." Zama Irfan yayi kusa da Afeef ya kyale hajiya bai tanka ba hakan ya sake tunzura ta tace, "marassa kunya.... Ku tashi ku fice min daga cikin ɗaki ko inci muku mutunci yanzun nan...." Afeef zamewa yayi ya kwanta kan kujera yana harararta batare da yayi magana ba dan ransa dama a ɓace yake kuma yana cikin damuwar wannan matsalar da yaya Aliyu ke kokarin lallai sai ya saka shi aciki shima ta shafe shi, Yana kwance yana jinsu sai fafatawa suke yi ita da Irfan ahaka wayar shi ta fara kara ganin yaya Aliyu ne sai yaki dauka shikuma cigaba yayi da kiransa babu kakkautawa, ɗan kallonsa Irfan ya juya yayi sannan yace, "your phone is ringing fa..... Afeef..... Are you sleeping?" "wallahi bana jin dadi ne Irfan.... Kaina ma ciwo yake yi" "sannu.. Allah ya sawwake" Ita kuwa hajiya karkace kai tayi tana kallonsa zuwa can kuma tace, "yi hakuri lele ai ban san baka da lafiya ba..... Na zata iya shegen naka ne ya tashi" Lumshe idanuwansa kawai yayi bai ce komai ba, kwata kwata ya rasa me yake yi masa daɗi shi dai kawai yana jinsa gashi nan gashi nan dai shi ba mai lafiya ba shi ba marar lafiya ba, bayan hajiya ta fita Irfan ya dafa shi yace, "Afeef wai me yake damunka ne? Naga kamar fa kana cikin damuwa, ko kai da mommy ne?" Girgiza kai yayi dan baya jin zai iya sanar da wani wannan damuwar tashi, "kaina ke ciwo Irfan..." "bari na duba bedroom din anty Mimi na san is hardly a rasa paracetamol.." "ok" Ganin Irfan ya tashi itama hajiyan ta tashi yasa shi daukar wayar yaya Aliyu da har yanzu bai hakura ba wurin miss calls 10 yayi masa, "Afeef.... Haba ƙanina... Nine fa yaya Aliyu yayanka, why are you like this? Yarda ce fa tasa nake son baka amanar Mimi..... Na san kai kadai ne zaka iya cika min alkawari" "yaya Aliyu am very sorry...... Gaskiya bazan iya karbar wannan amanar ba, beside ma ni ban ko fara tunanin yin aure ba a yanzu" "A'a Afeef..... Ka dai yi tunani dan yanzu daga ni har Mimi da kai muka dogara kaine kadai gatanmu a yanzu dan kaine zaka fitar damu daga cikin halin da muke ciki na damuwa da tashin hankali..... Dukanmu muna bukatar taimakonka dan Allah.... Please" "Yaya haidar gaskiya bazan iya yi muku wannan taimakon ba..." "kafi son muje mu samo bare wanda zai tona mana asiri Afeef? Kaifa dan uwanmu ne...." "dan Allah yaya Aliyu kayi hakuri mu bar maganar nan dan wallahi kaina ba zai iya dauka ba tayi masa girma" "ka dai zauna kayi tunani Afeef..." Ganin Irfan na tahowa yasa Afeef katse wayar ya ajiyeta kan kirjinsa tare da lumshe idanuwansa, zama Irfan yayi yana mika masa paracetamol din sannan cikin son jin karin bayani yace, "naji kamar kana waya, kai da waye?" "babu kowa... Ba waya nake yiba" Shuru Irfan yayi amma shi dai ya san kunnen sa ya jiyo masa kamar Afeef din yana yin waya sai dai amma tunda yace ba haka bane dole ya barshi a haka din. Bayan azahar yabar family house kamar yadda suke kiran gidan ya nufi gidansu zuciyarsa cike da tunani iri iri kuma daban daban, part dinshi kawai ya shiga ya kwanta bai ko leka side din mommy ba sai ita mommy dince ta shiga wurinshi, kwance ta iskeshi harda su lulluba kamar wani mai yin bacci, "Afeef baka da lafiya ne?" "mommy am fine kawai ina hutawa ne...." "ok to shikenan dama nace bari inzo in duba ka..." daga haka mommy din ta juya ta fita taja masa ƙofa, kashe wayar sa yayi saboda damunsa da yaya Aliyu keta faman yi da kira, bai kunna wayar tashi ba sai bayan magrib nan ya kula da sakon da Aliyun ya turo masa tun da safe bayan ya baro office din anty Mimi, kudine har 5m, dafe kansa yayi wanda yaji ya sara masa, "shi kuma wannan kudin duk na menene?" ya tambayi kansa hankalinsa na sake dugunzuma, gaskiya Aliyu ya takurawa rayuwarsa haka kuma ya na neman hana shi sukuni, yayin da shi kuma Aliyun ke can yana ji acikin ransa da kuma jikinsa cewa Afeef din shine kadai zai iya yi masa abinda ya dace dan Mimi bata wasa dashi shima kuma baida lokacinta dan haka ya san baza asamu matsala ba komai zai tafi yadda ya dace kuma ya shirya ba tare da wata tangarda ba. Tsawon kwanaki biyu shi dai Afeef ya kasa gane kansa ma dan ya rasa yaya zai yi da matsalar yaya Aliyu da anty Mimi, kullum cikin takura masa da kira Aliyun yake har hakan yasa yaki zuwa family house dan bama ya son su hadu acan, kwana yake yana sake sake cikin ransa dan ya rasa a inda mafita take. Yau ya jima yana bacci kamar yadda ya saba dan kwana biyu baya samun bacci sosai, sai after 1 sannan ya tashi, wayar shi ya dauka ya kunna yana kunnawa massages din Aliyu suka yi ta shigowa duk na roko ne da magiyar ya taimaka musu ya ceto rayuwar su shi da Mimi saboda idan bai taimake su ba komai zai iya faruwa, bai kai ga karanta massages dinba gaba daya kiran Aliyu ya shigo, dauka yayi a hankali yace, "hello yaya haidar.....nima yanzu nake cewa zan kiraka fa sai gashi ka kirani" "A'a Afeef wannan ba gaskiya bane.... Kwana nawa wayarka a kashe" Murmushi yayi tare da cewa "ehh wallahi yaya..... Dama zan kira ne in fada maka na amince sannan dan Allah wannan kudin da ka turo min zan dawo maka dashi ai ba sai ka biyani ba akan wannan..... We are one family...." "No Afeef ka barshi ka dauka kawai wata yar karamar kyauta ce daga yaya zuwa kaninsa...." "A'a yaya wallahi ba zan karɓa ba indai har kana son inyi maka abinda kake bukata.... Bana son inji araina kudi ka biyani dan yi maka wani abu wanda zan iya yi maka koda baka biyani ba saboda karfin zumuncin dake tsakaninmu...." "to shikenan Afeef na gode Allah ya bar zumunci, yanzu ya za ayi?" "babu matsala yaya komai zai tafi daidai insha Allah..... But ka jawa anty Mimi kunne Allah karta yarda ta sake ce min jariri...." dariya Aliyu yayi yace, "insha Allah, gata nan ma tana jinka ai ina office dinta...." Katse wayar yayi sannan ya tashi ya fita zuwa part din mommy. Kallon Mimi Aliyu yayi bayan sun gama waya da Afeef, ajiyar zuciya ya sauke jin Afeef din ya amince da kyar, "ban tsammaci yaron nan zai amince ba.... Kawai na yi tunanin sai dai mu nemi wani..." Shuru yaji tayi bata amsa ba saboda bata san me zata ce ba ko me zata kira wannan abun ba, ance dai auren kisan wuta to amma a rasa da wa zasu yi auren kisan wuta sai da Afeef? " My love baki ce komai ba.... You didn't say anything.... " " to wai me zance Aliyu? Yanzu a rasa da wanda zamuyi auren kisan wuta sai da Afeef?" "calm down my love.... Shifa RUWAN KASHE GOBARA ba sai mai kyau ba.... Bukatar mu in dai zata biya bamu da damuwar koma waye shi.... Kiyi hakuri..... Kar wannan ya dameki...." "Ai duk Kaine ka janyo...... Ka rinka abu kamar wani mai shaye shaye ko tabin hankali yanzu ga abinda ka janyo mana nan.... Zaka sa inyi auren kisan wuta da kanin bayana...." daga haka ta dauki wasu files ta fita ta barshi cikin office din, babu abinda yake bata mata rai irin yanda idan ta tuna cewa Afeef ne zai zame mata mijin auren kisan wuta wannan wacce irin lalacewa ce, sai dai amma idan kuma ta tuna da cewa auren na ɗan wucin gadi ne zasu koma su hade da yaya Aliyu sai ta ɗan ji sanyi cikin ranta dan tana mutukar sonsa da kaunarsa haka kuma tana ta faman missing dinshi kamar yadda kullum shima yake yi mata korafin cikin missing dinta yake, to da su cigaba da wannan zaman lalurar wanda shaidan zai iya cin nasara a kansu gara asamu a ganganɗa da Afeef din har bukata ta biya....... Hmmmmm masu karatu wannan cakwakiya ta ɗaure min kai, please comment what you think..... Next chapter loading✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifi ɗaya# #lovetriangle #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA.... _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ NA UMMI A'ISHA 4 ***Cike da kasala da damuwar da yake ta boyewa cikin ranshi ya shiga part din mommy, babu kowa cikin part din kamar yadda gidan ya saba kasancewa dan ita Manal ta tafi makaranta ita kuma mommy ta fita aikinta kamar yadda ta saba, table a shirye shiyasa kawai zama yayi ya fara zuba breakfast din da yaga mommy ta ajiye masa, yana cin abincin yana tunani cikin ransa yanzu ta ina ya dace ya fara sannan wa ya kamata ya tunkara da wannan maganar ta yana son a daura musu aure da anty Mimi? Har ya gama breakfast din bai tsayar da magana guda daya a cikin ransa ba kawai ya san ayau dole sai ya magantu ko ayi ko a ƙi yi, fata yaji yana yi acikin ransa ma Allah yasa iyayen nasu suki amincewa inyaso shikenan kowa ma ya huta sannan shi yaya haidar din ba zai zarge shi da yaƙi yi masa taimakonba kamar yadda yake ta fadar taimako taimako, Part dinsa ya koma ya samu wuri ya zauna bakin gadonsa yana bin dukkan cikin bedroom din nasa da kallo, katafaren gado ne babba kirar Turkiyya fari tas komai tsaf tsaf kuma fes fes babu wasu tarukuce masu yawa aciki dan daga gadon sai wardrobe da mirror sai bedside drawers sai shoe rack shikenan komai a kammale kuma a tsare, kowanne lungu da saƙo na cikin ɗakin ƙamshi ne mai daɗi ke tashi na turaren oad, Gani yayi zaman shurun ba zai kai shi ba shiyasa kawai ya tashi ya nufi cikin toilet ya sakarwa kanshi shower, bai wani jima cikin bathroom dinba ya fito daure da towel, cikin kankanin lokaci ya shirya sannan yayi salatul duha raka'a biyu kafin ya dauki key din motar shi ya fita, yana driving yana tunanin ta inda ya dace ya bullowa wannan lamari da haka har ya isa family house, bai shiga ko ina ba sai wurin Hajiya tana zaune cikin bedroom dinta tana gurza goro jikin wata yar karamar greater ta roba, zama yayi kusa da ita, "Hajiya kaka wai dama har yanzu baki hakura da cin wannan goron bane....." "to sarkin iyayi da sa ido..... Ban daina ba sai kuma yaya?" Dariya yayi ya girgiza kansa yace 'babu komai..... Allah ya baki hakuri.... " " amin..... Ɗan neman sababi " " to ai maganar ta wuce nace kiyi hakuri...... Ashe hajiya auren anty Mimi ya mutu?" Tamkar ya sosa mata inda yake yi mata ciwo yaji tayi kwafa kafin cikin takaici tace, " Aurenta ya mutu mana Mai sunan malam, ai wannan shashashan yayan naku baida ta ido sam..... Ya kasa riketa kullum cikin saki har sai da igiyar auren ta kare kowa ma ya huta...... Yar uwarka cikin ku ɗaya amma ka gagara riketa..... Wallahi takaicin mutuwar auren nan da nake ji mai sunan malam takaicin ya isa.... Tsakanina da Aliyu sai dai ince Allah ya isa... " " subhanallahi Haba hajiya menene kuma abin yi masa Allah ya isa? Dan Allah kiyi hakuri ki cire bacin ran daga cikin zuciyarki.... Ai shi aure rai gareshi fa, ki dauka kawai dama zaman auren nasu ya kare Kinga dole a rabu idan ma saki bai raba ba sai ki ga wani aciki ya mutu... To Kinga da mutuwar ai gara ace auren ne ya mutu ko..... " " Hakane lele..... Ai sakarai ne wannan yayan naku... " " a dai yi hakuri Hajjaju..... Ni yanzu wata magana na zo muyi dake ta sirri idan har kin amince... " " ina jinka ɗan lele na... " Tankwashe kafafuwansa yayi ya sake gyara zamansa a gabanta kamar mai shirin daukar karatu, " cewa nayi tunda auren anty Mimi ya mutu Hajiya.... Ni ina son zan aure ta " Fasa hambada goron da yake hannunta zuwa bakin ta tayi ta tsaya tana kallonsa bayan ta gyara zaman gilashin ta sosai, "mai sunan malam..... Kai ma ka fara irin wannan shaye shayen na zamani ko?" Girgiza kai yayi yana kokarin danne dariyar sa, "me kuma ya kawo maganar shaye shaye Hajjaju na?" "to idan ba shaye shaye kake yiba Afeef ina kai ina auren Mimi?" "saboda me kika ce haka? Ke ya dace ince ko kin fara gigine?" "Mimi sa'ar ka ce? Shekaru nawa ta baka? Dan raini ko me?" "Hajiya waye yace dole sai wadda kafi a shekaru zaka aura? Sunnah ce fa mai karfi auren wadda ta fika kuma wadda ta taɓa aure, annabi ma ai haka yayi shiyasa nima nake son yin koyi da shi, so nake in yi sunnah kan sunnah.... Sai dai ko idan bakin ciki zaki yimin kawai " Shuru Hajiya kaka tayi kamar me yin tunani yayinda shi kuma ya zuba mata ido yana kallonta, " Allah mai iko..... Ka tabbata abinda ka fada haka ne mai sunan malam? Bafa na so sai daga baya kazo ka mayar dani sakarkara... " " wallahi Allah da gaske nake indai za a aura min anty Mimi ko yau ɗinnan a daura min auren am ready......" "wallahi idan daga baya ka sake dawowa kace zaka canja zance bazan saurareka ba Afeef..." "na yarda wallahi....." "shikenan...... Naji kuma na gamsu sannan ka kawo kukanka inda za a share maka hawaye...... Kana da ni ai sai wadda kake so zaka aura koda ace akwai wani bare ma babu wani din duk taki bazawaran korarsu take ashe rabon sha lele na ce...." Dariya shi dai yayi ya karbi goron nata yaci gaba da gurza mata, sallamar Irfan tasa gaba daya suka mayar da hankalinsu kanshi shigowa yayi yana murmushi kafin yace, " soyayya ake sha ne hajiya kaka da mai gidanta.... " Dariya Afeef yayi ya kalleshi yace, "ka san dai fada yafi yawa cikin wannan soyayyar...." "ai tsohuwar nan tana abinda take so wallahi..... Haka kawai sassafe ina bacci tasa Abba yaje ya taso ni wai sai naje har gidan anty Batool dake karshen gari na kai mata abu....." Dariya Afeef ya fara yi sannan ya kalli hajiya yace "gaskiya ki daina tashin sa idan yana bacci..... Kaima ka dawo gidan daddy kawai bacci a gidan daddy har azahar ake kaiwa" "kuma fa ka kawo shawara mutumina..." Irfan ya fada yana harararta, Ita dai tana jinsu bata kara bi ta kan maganar tasu ba tayi iska dasu kamar bata ji,. Afeef yana so ya fadawa Irfan abinda suka tattauna da kaka amma kuma sai bai san ta ina zai fara fada masa ba dan kamar cin fuska ne ko kuma reni yace yana son zai auri yayarsa tunda ba wai zai fito fili ne ya fada masa yaya Aliyu ne ya matsa masa ba, Tare suka wuni har magriba amma koda wasa bai fada masa ba. Suna farfajiyar gidan da misalin ƙarfe uku da rabi na yamma motar anty Mimi ta shigo gidan, gaba ɗayansu mayar da hankulansu wurin suka yi har zuwa lokacin da ta kammala parking ta fara kokarin fitowa, tashi Irfan yayi ya nufi wurinta yana yi mata sannu da zuwa shi kuma Afeef na zaune yana kallon su kuma daidai lokacin Janan ta fito daga part din hajiya ganin motar anty Mimi sai itama ta nufeta cike da farin ciki dan anty Mimi na da mutukar kirki da kulawa shiyasa kowa na familyn ke kaunarta, "Anty Mimi barka da zuwa..." "yawwa Janan... Ya gida?" "Alhamdulillah" ta fada tana bude mata kofa, fitowa tayi Irfan ya karbi handbag dinta ta dan kalleshi tace, "part din Ammi zanje, ka kai min handbag din part din Hajiya kaka...." Tare da Janan suka nufi part din Ammi kuma sai lokacin ta dan saci kallon Afeef dake gaishe ta daidai lokacin da zasu gifta ta kusa dashi wani musulmin ƙamshi yaji lokacin da suka zo dab dashi, ita kam tun shigowar ta gidan idanuwan ta suka sauka kan ɗan tatsitsin yaron da Aliyu ya zabar musu dan zama tsanin kaiwa ga nasararsu, "Anty mimi sannu da zuwa.... Ina yini" "lafiya.... Afeef ya kake.." ta fada ba tare da ta kalleshi ba dan tana tafiya suna gaisawa nan ya bita da kallo atamfa ce a jikinta dinkin straight gown golden color ta yafa mayafi ƙarami golden color shima ƙafarta ta saka baƙin sneaker mai kyau da tsada, shuru yayi yana tunani gami da mamaki to idan har shi yaya Aliyu yana yi mata irin wannan soyayyar da ta kai kololuwa me yasa ya kasa hakuri ya kasa jure duk wani bacin rai dan su cigaba da zaman su cikin kwanciyar hankali har sai da ya haramta zaman su, dawowar Irfan yasa shi watsi da tunanin da yake yi suka cigaba da hirarsu. Bayan sallar magriba kamar yadda iyayensu suka saba hallara da kuma haɗuwa a falon hajiya yau ma hakance ta faru, suna tsaka da hirarsu suka ji hajiya ta ɗan yi gyaran murya sannan ta dube su gaba ɗaya tace, "Gobe idan Allah ya kaimu bayan an idar da sallar juma'a ina so za a daurawa Mimi aure.... Ga sadaki nan nice nan zan bada gudunmawar shi...." Baki bude cike da mamaki kowannensu dake cikin falon yake kallonta banda Afeef duk da shi dinma hukuncin hajiyan yazo mishi a bazata, daga yin maganar dazu dazun nan shine har za a daura aure a gobe gobe?, " Hajiya aure? Ita mimi dince ta kawo mijin kenan? Yaushe suka hadu har suka daidaita? Waye shi?" duka wadannan tambayoyin Abban Aliyu ke jerowa hajiya wanda kamar ya shiga cikin zuciyoyin Abban Mimi da daddyn Afeef da faruk da kuma Aliyu dan shima Aliyun so yake yaji da wa za a daura auren dan ta yuyu wani ne daban, " Abun ai duk na gida ne.... Mai sunan malam yace yana son Mimi zai aureta, tunda duk daga tsatso guda ɗaya suka fito shiyasa naga babu dalilin ɓata lokaci gara kawai a daura musu aure......." Shuru dukkansu suka yi kowa da abinda yake ayyanawa cikin ransa zuwa can Daddyn Afeef ya nisa yace, " amma Hajiya ita Mimi din an tambayeta anji ta bakinta tana son shi ko kuma akasin haka? Saboda ita yanzu ba karamar yarinya bace da har za ayi mata dole ko kuma a tirsasa ta a aura mata wanda bata so...." "Ai ko tana so ko bata so tunda shi ya gani yana so to magana a wurina ta kare, gobe insha Allah za a daura musu aure wannan umarni na ne ba shawara ba....." "to shikenan hajiya Allah ya nuna mana goben kuma Allah yasa albarka aciki, Allah yasa yin Allah ne, mutuwa zata raba...." Mikewa yaya Aliyu yayi ya fita batare da ya yiwa kowa magana ba bayan ya sauke boyayyiyar ajiyar zuciya, kowa dake falon binsa yayi da kallo cikin zuciyoyinsu suna tunanin ta yuyu wannan hukuncin da hajiya ta yanke ne baiyi masa dadi ba sai dai shi sam ba haka bane a gareshi, wani sanyi da farin ciki yaji yana ratsa zuciyarsa dan ya san shikenan plan dinsa ya tafi yadda yake so kuma burinsa zai cika cikin kankanin lokaci, Yana fita daga cikin part din hajiya cikin motar sa ya shiga ya zauna ya dauki wayar shi ya soma kiran layin Mimi, fitowarta daga wanka kenan daure da towel a jikinta ta dauki wayar tashi ranta a cunkushe babu dadi kuma tamkar zata saka kuka dan bacin rai, "My love..... Albishirinki..... Hajiya ta amince da maganar auren nan, to cut the long story short gobe za a daura muku aure da Afeef...." Wani haushi taji ya sake turnuke ta a maimakon murna ko farin ciki, sai da ta ja tsaki ciki ciki kafin yaji tace, "soo why are you excited??" "Love, you will come back to me soon....... That's it" "it's fine" "Dan Allah koda su Abba zasu tambayeki ko hajiya akan kina son shi zaki aure shi just say yes...... Please" "ok" Daga haka ta katse wayar tana jin ranta yana cigaba da ɓaci haka kawai ba tare da wani dalili ba. Bayan fitar Aliyu babu wanda ya iya magana sai hajiya da ta rakashi da harara sannan cikin mita tace, "kafi ruwa gudu shashasha kawai, da kana son nata amma shine kayi mata saki ɗai ɗai har uku.... Aure babu fashi baza a fasa dan kai ba...." Shi dai Afeef tunda aka fara maganar ya sunkuyar da kai kirjinsa na dukan uku uku haka kawai yaji yana fargaba wacce bai san ko ta mecece ba.......... Tirƙashi, wani shagalin sai a next chapter, what do you think will happen?? Comment your guesses...... Next chapter loading..... ✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #lovetriangle #Kaifi ɗaya #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA..... _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ NA UMMI A'ISHA 5 ***Da mamaki akan fuskar Irfan yake kallon Afeef cike da son jin ƙarin bayani saboda wannan lamari ya bashi mamaki haka kuma ya ɗaure masa kai, to duk tayaya wannan maganar ta faro ko kuma ta samo asali, "Afeef wai me yake faruwa ne? Anty Mimi fa naji ance zaka aura, ko dai Suhana kake so wannan tsohuwar ta rikirkita maka magana?" Ɗan murmushi Afeef yayi ya juya ya kalli Irfan da idanuwansa gaba daya ke kansa yana kallon sa baya ko kiftawa sannan yabada gaba daya attention dinsa kansa alamar yana son yaji amsar da zata fito daga bakin sa, " Wallahi ba rikirkita magana Hajiya kaka tayi ba Irfan.... Ni na fada mata ina son in auri anty Mimi...." Shuru yaga Irfan yayi yana ta faman kallon sa kamar wanda ke son gano wani abu akan fuskarshi, "look Irfan.... Na san baza kaji dadi ba sannan zaka dauka kamar reni ne ya sani auren anty mimi..... Allah ba raini bane ko kuma wani abu mai kama da haka...." "Amma dagaske kana son anty Mimi ko dai kawai tausayinta kake ji saboda aurenta ya mutu?" Wani ɗan kyataccen murmushi Afeef yayi ya shafa kansa yace da Afeef, "to kai ka taba ganin inda mutum ya auri mace idan baya son ta? Ina son ta mana kuma ina tsananin tausayinta wallahi....." "Allah yasa albarka.... But ka shirya karɓar wuju wuju daga wurin anty Mimi dan wallahi na san definitely she will reject you...." "shine abinda nake tsoro Irfan..... Amma dai zamu gwada mu gani" Sallama suka yi Irfan ya shiga gida shi kuma Afeef ya nufi gidansu. Daga Afeef har daddy babu wanda ya sanarwa da mommy abinda yake faruwa kuma kamar abin hadin baki suma su Abba babu wanda ya fadawa iyalin sa shiyasa gaba daya matan basu sani ba sai iya mazan ne suka sani, Afeef baccinshi yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, bayan gari ya waye da ya tashi baima fita da wuri ba har sai da yaya Aliyu ya kira shi sannan ya shirya ya fita, farar shadda ya saka harda babbar riga kamar wani angon gaske, Anty mimi kam tun 9 ta fita saboda tana da theater da zata shiga har guda biyu, kallonta Hajiya tayi lokacin da zata fita tace, "Yau dai insha Allah addu'ata da na jima ina yi miki zata tabbata Mimi, yanzu zaki san kinyi aure insha Allah....." Bata kula ta ba ta fita abinta, sai dai kuma cikin ranta tana ta sake sake da haka har ta isa hospital tunani dai yaki kare mata sannan duk yadda taso ta manta da lamarin ko ta cire shi daga cikin ranta ya gagara. Bayan an idar da sallar juma'a aka daure auren Anty mimi da Afeef kuma hajiya kaka ce ta bada sadaki kamar yadda ta alkawarta naira dubu ɗari sabbi filfil, wata hamdala da ajiyar zuciya yaya Aliyu yayi bayan yaga an kammala ɗaurin auren, kowa dai cikin iyayen nasu da yan uwa sai murna suke yi duk da ba wani shagali za ayi ko kuma ake shirya yi ba dan abune da yazo musu babu shiri kuma babu tsammani, Bayan su Abba sun dawo daga daurin auren Abba fari ya shiga part dinsa inda ya iske Ammi tana zaune cikin kitchen ita da Suhana suna hada dambu, cikin kitchen din Abba ya shiga fuskarshi cike da fara'a, "Yau dambu ake dafa mana Ranki ya dade..." "Abba sannu da zuwa..." Suhana ta fada tana dariya, "sannu auta..... Sannu da aiki" "sannu da zuwa...." ammi ta fada kafin ta fara yunƙurin mikewa, murmushi Abba yayi yace, "yi zamanki ba sai kin tashi ba kici gaba da aikin ki.... Nima wurin hajiya zan shiga..... Ungo karbi wannan kudin...." Hannu ammi tasa ta karba tana jiran karin bayani dan bata san ko kudin menene ba, "sadakin mimi ne..... Yau aka daura mata aure" Cike da mamaki Ammi da Suhana suke kallon Abba kafin ammi tayi ta maza wurin tambayar sa, "aure kuma Abba? Da wa aka daura musu aure?" "ehh aure fa, da Afeef aka daura..." "Afeef kuma? Wanne Afeef din?" "Afeef nawa muke dashi? Wanda dai kika sani" Daga haka Abba ya fita yabar ammi da Suhana daskare awurin dan tsananin mamakin da suke ciki, "Wai ammi yaya Afeef dai da na sani abokin yaya Irfan? Na gidan daddy?" "Suhana shine nima abinda nake ta mamakinsa, taya mimi zata auri Afeef, Anya kuwa Afeef din da muka sani ne?" Shigowar Irfan yasa gaba daya suka mayar da kallonsu gareshi da kuma hankalinsu gaba daya, "Irfan wai me yake faruwa ne? Yanzun nan abbanku ya fita bayan yazo min da wata magana mai rikirkita kwakwalwa....... Wai waye ya auri yayar ku?" "Ammi Abba bai fada miki Afeef ne ya aure ta ba?" Shuru ammi tayi wanda ita kadai ta san abinda take tunani, "yaya Irfan kuma antyn ta sani?" Suhana ta bukata cikin al'ajabi, "ta sani...." "kuma tana son shi?" "wallahi shine ban sani ba amma dai shi yana son ta dan shine ma ya samu hajiya kaka da maganar jiya shine kawai ita kuma hajiya tace yau a daura musu aure...." Babu wanda ya sake magana a cikin su har Irfan ya gama basu labarin abinda ya faru ya fita, ita dai ammi ta rasa wanne irin tunani zata yi dan sai take jin abun wani gwangwaragwan amma kuma ba a san me Allah ya shirya ko kuma ya ɓoye ba. Afeef bayan sun dawo daga daurin auren da yake jinsa kamar wasa dan shi har yanzu ma ya kasa gaskata cewa wai shine yayi auri ya auri anty mimi, wurin hajiya kaka ya shiga tana zaune ita kadai, "Yawwa lele na yanzu nake son insa a kira min kai dama inji...." "to gani ai, ya aka yi?" "cewa nayi yaushe kake son amaryar taka ta tare?" "A'a ba yanzu ba hajiya...." "sai yaushe kenan?" "ba yanzu ba dai, za ta tare a hankali.... Sai na gama wasu shirye shirye" "to ai shikenan Allah ya kaimu, tunda dai an daura muku auren ai anyi mai wuyar" Daga haka ya wuce cikin bedroom dinta ya kwanta, yana jin lokacin dasu abba suka shigo wurin hajiyan harda daddynshi, cike da farin ciki da jin dadi hajiya tace, "nagode, sannunku da kokari, yanda kuke yimin biyayya ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi yayi muku albarka, Allah yasa yayanku suyi muku fiye da haka, Allah yayi muku albarka ya faranta muku...." Yana jinsu sai tattauna maganar suke yi da maganar inda ya dace su zauna shi da anty mimi amma sai ya jiyo hajiya tana cewa ta tambayi mai sunan malam yace ba yanzu ba tarewa sai nan gaba, ita dai duk wani abu da yace shi ake yi, tun dai yana jiyo su har ma ya daina jiyowa gaba daya, yaga daga hajiya har su Abba sun dauki wannan auren nashi serious basu san na dan wani lokaci bane. Anty Mimi tana fitowa daga theater ta iske yaya Aliyu yana cikin office dinta yana jiranta, jikinta babu wani kwari fuskar ta babu fara'a ta shiga cikin office din tana rike da files din patients din da ta yiwa theater, zama tayi ba tare da ta kalleshi ba ta fara rubutu cikin files din yana zaune yana kallonta cike da soyayyarta cikin ransa, "my love..... An daura aurenku da Afeef....." Yi tayi kamar bata ji shi ba taci gaba da rubutun ta har zuwa lokacin da ta kammala, cike da wani yanayi mai wuyar fassarawa ta ɗago ta kalleshi jin ya kira sunan ta, "mimi kamar ba kya farin ciki da wannan plan din nawa?" "Wai dan Allah yaya Aliyu what's your problem? Ba dai abinda kake so ba kenan kuma gashi ya tabbata? What do you want again? Kana dai gani ina aiki ne...... Don't distract me please......" Numfashi taji ya sauke kafin ya kamo hannunta ya riƙe cikin nashi, " am very sorry my love, kiyi hakuri da wannan halin da na saka ki, Insha Allah idan muka sake komawa ma'aurata I will do better i promise you..... " Zuba masa ido tayi tana kallon sa bata ko kiftawa kamar yadda shima yake kallonta ba tare da kiftawa ba, a hankali ta janye nata idon ta fara kokarin janye hannunta daga cikin nasa, sakin hannun nata yayi cikin kalar ban tausayi yace, " insha Allah 3 weeks kadai wannan auren naku zai yi daga nan zan saka shi ya sake ki......" Kai ta ɗaga masa hakan ya bashi damar tashi yayi mata sallama ya fita. La'asar sakaliya ta tashi daga office ta nufi gida, tunda ta doshi gidan taji gabanta yana faman faduwa ras ras amma ahaka ta daure ta karasa tayi parking tana kokarin fitowa ta hango suhana na fitowa daga part din Ammi zata shiga part din umma wato part din su janan, itama suhana ta hangota shiyasa ta nufo wurinta fuskarta dauke da murmushi, "Anty mimi sannu da zuwa.....kamar kuwa kin san yanzu nake tunaninki cikin raina....." "Suhana akan maganar auren da aka daura yau ne ko?" Cike da mamaki suhana ta kalleta tace, "anty mimi kin samu labari ashe? Soo you know? I thought ma ko baki san da maganar ba" "na sani...." "to amma anty mimi da yardar ki?" Bata amsa mata ba ta fito rike da handbag dinta ta rufe motarta ta shiga wurin Ammi suhana na biye da ita, Ammi na zaune cikin sitting room suka shigo, Kallon Anty mimi Ammi tayi da kyau kamar wadda take nazarinta kafin tace da ita, " Mimi wai me yake faruwa ne? Dazu abbanku ya kawo min sadakinki wai an daura muku aure da Afeef...... Taya akayi akai haka?" "Ammi wallahi nima ban sani ba kawai yau da safe before in fita naji hajiya tana yimin maganar....." "ikon Allah..... To ko hukuncin hajiya ne? Dan idan ba ita ba babu wanda ya isa ya zartar da wannan hukuncin...." "amma dai hajiya gaskiya bata kyauta ba dan wallahi janan idan ta samu wannan labarin zata shiga damuwa dan tana tsananin son yaya Afeef sosai.... Sannan shi kansa yaya Aliyu ba zai ji dadin wannan abun ba...." suhana ta fada tana turo baki kamar itace aka daurawa auren, " ni duk ma ba wannan ba, ya za ayi ace ciki ɗaya tushe daya tsatso ɗaya amma ayi irin wannan kwamacalar? Abinda yayi Aliyu shi yayi Afeef amma kuma a rasa da wanda za a daurawa Mimi aure sai da Afeef? Saboda dai kawai babu wanda ya isa yayi turjiya?" Ammi ta fada cikin bacin rai, " wallahi Ammi Allah dai ya kyauta kawai " Ita dai Anty Mimi tashi tayi ta bar sitting room din dan ta san bata da abinda zata ce.............. KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #lovetriangle #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA..... NA UMMI A'ISHA 6 ***Nuƙu nuƙu anty Mimi tayi ta faman yi ta gagara sakewa gaba ɗaya dan ko abinci ta kasa ci daga karshe dab da magriba ta fito daga part din Ammi ta nufi na hajiya bayan ta bar Ammin tana ta faman nanata maganar auren da aka daura musu ita da Afeef, haka kawai ta rasa me yake damunta dan jinta take yi gaba daya zuciyar ta babu dadi, Lokacin da ta shiga part din hajiya babu kowa dan itama hajiyan tana cikin bedroom dinta ita da Irfan da Afeef, kai tsaye cikin bedroom dinta ta wuce bata ko leka hajiyan ba, zama tayi ta rafka uban tagumi ba tare da ta san abinda zata yi tunani ba har sai da taji an shiga salla a masallaci sannan ta iya tashi ta shiga tayi alwala ta fito, koda tayi sallar magriba anan wurin da tayi sallar ta cigaba da zama har lokacin sallar ishah yayi bayan ta idar ta shiga tayi wanka tana fitowa tasa sleeping gown ta kwanta duk ranta a bace, Kiran da ya shigo cikin wayarta ya sake tunzurata amma sai ta kai zuciyar ta nesa ta dauki kiran dan ta san muddin idan bata dauka ba to haka zai cigaba da kiran ta babu ji babu gani indai Aliyu ne. Bayan an idar da sallar ishah Afeef gida ya nufa batare da ya koma wurin hajiya ba daga nan waje suka yi sallama da Irfan ya tafi, yana zuwa gida tunda ya shiga part din mommy yake jiyo fadan da take yi kamar zata ƙone gidan, "Afeef aka ɗaurawa aure da Mimi saboda mugunta da wulakanci? Duk family din naku a rasa da wanda za a daura mata aure sai da Afeef ? Saboda shi kadai ne namijin da ya rage a duniya ko me? Wallahi ba zan yarda da wannan zaluncin ba, wannan ai mugunta ce, yaro bai kai ya kawo ba a aura masa bazawara? Afeef din nawa yake.... " Daidai lokacin Afeef ya shiga falon mommy wanda yake babban gaske komai yaji kuma ya dace da yanayin falon, suna zaune ita da Manal wacce ke bata hakuri, da kallo mommy ta bishi har ya samu wuri ya zauna yana kallon su, " mommy lafiya? Me yake faruwa? " "Dagaske ne an daura muku aure da mimi?" "ehh mommy dagaske ne...." "to uban waye ya bada izini aka yi hakan wanda yafi ni uwar da ta durkusa ta haife ka?" "mommy calm down..... Bafa abin tada hankali bane ko kuma abin damuwa...." "ni kake cewa wannan ba abin tada hankali bane Afeef? Ina matsayin mahaifiyarka har a daura maka aure kai da ubanka ku kasa fada min saboda ban isa ba? Sai yanzu Manal take gani a group dinku na family ana maganar...." "mommy wallahi wannan auren kawai dai kaddara ce...." "to ko abinda yafi kaddara zaka kirashi dashi wallahi bazan lamunta ba kuma bari daddy din yazo ai ina daidai daku daga kai din har shi..." daga haka ta tashi ta wuce cikin bedroom dinta dake sama, suka bita da kallo, Manal dawo da kallonta kanshi tayi cikin sanyin jiki tace, " yaya what's going on? Wai dagaske ne auren nan ko kuma prank ne?? Dan Allah ka fada min this is a prank.... " Girgiza kai yayi yace "unfortunately this is not a Prank Manal, wallahi dagaske ne an daura mana aure da anty Mimi" "amma yaya Afeef meyasa? Me yasa zaka yarda a daura muku aure da ita?" "saboda ina son ta mana, ko an fada miki dole aka yi min?" "amma dai yaya ai ka san Janan kai take so shiyasa ta rinka rejecting din samari tana korarsu...." "ban son shirme fa..." daga haka shima ya tashi ya fita zuwa part dinshi cikin zuciyarshi yana addu'ar Allah dai ya huci ran mommy ta sauko daga wannan dokin fushin da ta hau. Bayan yayi shirin bacci har ya kwanta ya jiyo hayaniyar mommy da daddy tana tashi bayan daddy din ya dawo, tashi yayi ya saka silifas dinsa ya fita zuwa part din mommy din a ranshi yana cewa wannan shine kalubalenshi na farko dangane da aurensu da anty Mimi, tamkar kazar da ƙwai ya fashewa acikin ciki haka ya shiga cikin falon duk jikinsa a sanyaye, "Daddy... Mommy..... Me yake faruwa ne? Cikin dare kuna hayaniya haka bai dace ba kowa dake cikin gidan nan yana jinku...." "idan ka kuskura ka sake magana sai naci maka mutunci..... Bada kai aka hada kai aka munafurceni ba aka aura maka matar da ba sa'ar aurenka ba....." mommy ta faɗa cikin zafin rai, "to ai ba auren dole aka yi masa ba ɗan naki, gashi nan ki tambaye shi kiji shine da kansa yace a aura masa ita yana son ta...." Wani kallo mommy tabi Afeef dashi babu shiri yayi ƙasa da kansa daidai lokacin Manal ta fito daga cikin bedroom dinta sanye da sleeping dress idanuwanta cike da bacci, " mommy dan Allah kuyi hakuri..... " " wallahi ko sama da ƙasa zata hade ba zan taɓa yarda wannan auren ya dore ba ya zama dole kuma tilas a raba auren nan..." mommy ta fada cikin fushi kafin ta haye upstairs ta barsu tsaye nan kowannensu yana binta da kallo lokacin da take taka steps, " Afeef jeka abinka ka kwanta.... Manal kema wuce kije ki cigaba da baccin ki.... " " Daddy amma kamar mommy tayi fushi da yawa" Afeef ya faɗa cikin damuwa, "babu komai zata sauko ka san halin mommynku ai... Tafi ka kwanta abinka" Juyawa yayi ya fita itama Manal ta nufi bedroom dinta yayin da shi kuma daddy yabi mommy zuwa upstairs, tamkar mommy zata fashe dan tsabar bakin cikin da take ciki a haka Daddy ya shiga ya sameta, cikin zafin rai da jin haushi ta juya ta kalli Daddy, "wai meke damunki? Yanzu fa mun wuce wannan lokacin da zamu zauna muna musayar yawu a gaban yaranmu, daga Afeef har Manal duk sun girma babu karamin yaro yanzu a cikin su, dan Allah ki rinka sassautawa ranki...." "haka zaka ce? Iyakar wannan kadai zaka ce? Ohh yanzu gaba daya laifin ma ka dauka ka ɗora a kaina kenan.... Yanzu laifina kake gani kamar nice na kirkiri matsalar ko..... Taya za ace ɗana ƙwaya ɗaya tal a daura masa aure da yarinyar da ba budurwa ba wadda ta girmeshi kuma ba tare da amincewa ta a matsayina na mahaifiyarshi ba..... " " kiyi hakuri duk wannan ba abun tada hankali bane, kiyi musu addu'a kawai ta fatan alkhairi..... " Shuru yaji tayi bata sake tanka masa ba saboda bakin cikin da take ciki ji take kamar ta hada su gaba ɗaya ta rufe da duka. Zuciyar Afeef cike da damuwa ya koma cikin part dinsa ya zauna gefen gado, wannan shine kalubale na farko da ya fara fuskanta ya ayyana hakan cikin ransa, ya jima idonsa biyu kafin ya samu bacci ya dauke shi wanda bashi ya farka ba sai bayan asuba, wani baccin ya sake komawa har sai da rana ta fito, brush kadai ya iya yi ya fita zuwa part din mommy sakamakon yunwar da yake ji kamar me, Mommy ce kadai cikin falon tana marking scripts kasancewar yau weekend ne tana gida bata fita ba amma sai dai fuskar ta kadai idan ka kalla zaka fahimci ranta a mugun ɓace yake, ya san mommy tana da zafi sosai kuma mace ce mafadaciya wadda bata da hakuri ko kadan, "mommy ina kwana....." "lafiya..." daga haka bata sake kula shi ba taci gaba da aikinta ba tare da ta ko kalleshi ba, shi dai dan gatan mommy ne kowa ya san wannan amma kuma yanzu ya san dole mommy ta canja masa saboda wannan abun da ya faru, zama yayi a ƙasa kan rug ɗan nesa da ita kaɗan kafin yace, "mommy dan Allah kiyi hakuri...... Na san na ɓata miki rai kuma tun farko ya dace in sanar dake maganar auren mu da anty Mimi, na san nayi laifi kuma ban kyauta ba amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe min....." shuru yaji tayi masa bata amsa ba ahaka har ya gaji da zama ya tashi ya ƙarasa kan dining ya zauna kunu da ƙosai ya zuba yaci ya tashi ya fita zuwa part dinsa yana tambayar kansa to wai ma wacce kaddara ta aike shi yaje yayi wannan auren? " tsautsayi....." ya fada a cikin zuciyarshi, ajiyar zuciya ya sauke ya shiga cikin toilet yayi wanka ya fito, gaba daya ji yayi zaman gidan yayi masa kunci shiyasa kawai ya dauki motar sa ya fita, sanye yake cikin bakaken kananan kaya jeans da t shirt a gaban rigar tashi an rubuta Trust, can wurin da babu kowa ya tafi yaje yayi zamansa shi kadai cikin mota bayan ya saka wayar shi a flight mood da yaga lokacin salla ya yi ruwa ya dauka daga cikin boat dinshi yayi alwala ya dauki prayer mat ya shinfiida kasan bishiya yayi sallar shi yaci gaba da zama a wurin har la'asar sai lokacin ya tashi ya shiga motar sa yabar wurin ya nufi family house, yana zuwa ya samu yaya Aliyu tsaye kamar dama shi yake zaman jira, parking yayi ya fito yaya Aliyu ya mika masa hannu suka yi musabaha kafin yaji Aliyun yace, "Afeef ina fata ka fara lissafi saboda bana son ku wuce 3 weeks zuwa 1 month....." "babu problem yaya Haidar Allah ya nuna mana lokacin....." "yawwa na gode Afeef.... Ban san irin godiyar da zanyi maka ba" "Babu komai yaya, we are one family...." Fitowar yaya Faruk da Irfan tasa suka bar maganar, kallon Afeef Irfan yayi yace, "yau ina ka shiga ne wai wayarka bata tafiya...." "na yi bacci ne..." "to zo muje ciki..." binsa yayi zuwa ciki bayan sun gaisa da yaya faruk wanda yake kallon Aliyu cike da mamaki saboda a iya sanin sa Aliyu yana da masifar zafin kishi da kuma riƙo musamman akan Mimi shiyasa duk wanda yayi yunkurin zuwa wurinta da sunan yana son ta to fa masifa ce take tashi daga wurin Aliyu amma yau gashi abin mamaki Afeef ya aure ta baiyi musu wannan haukan ba, gaskiya bai taba kawowa zai ganshi haka ba ko cikin mafarki, "Aliyu wai ni abinda yake bani mamaki sai naga kamar baka damu da auren mimi da Afeef ba, anya kuwa Haidar din da na sani ne mai zafin kishi......." Dariya Aliyu yayi ya mikawa Faruk hannu yace, "to ya zanyi faruk, Afeef ai kanina ne dole banida yadda na iya dashi, da dai wani ne bashi ba sai in tada bore....." "gaskiya ka kyauta, kuma naji dadi da ka gane hakan har ka sassautawa zuciyarka ka cirewa kanka damuwa, life goes on..... Just move on....." "yes I moved insha Allah faruk...." runfa suka nufa wacce ke dauke da kujeru a cikinta suka zauna suna cigaba da tattaunawa kamar yadda suka saba. Anty Mimi tun bayan da ta shiga cikin bedroom dinta jiya bata sake fitowa ba Hajiya tayi mitar tayi mitar har ta gaji ta ja bakin ta tayi shuru,ko breakfast da lunch ma sai cikin dakin aka kai mata, lokacin da Afeef suka shiga part din hajiyan samu suka yi tana tambayar Hajjo daya daga cikin yan aikinta, "ita wannan gimbiyar ko sarauniya zan kira ta dashi ne ban sani ba ta ci abincin da ake kai mata??" "wallahi hajiya ban sani ba sai dai ko idan zuwa za ayi a duba...." "rabu da ita tayi ta kare ƙalau...." Bayan Hajjo ta fita Irfan ya kalli hajiya yace "wacece?" "Amarya mana, ban sani ba ko amarcin ta fara tun jiya dai da ta shiga ciki bata sake fitowa ba..." "kuma lafiya lau take?" Afeef ya bukata yana kallon hajiya, "to ni ina zan sani ne, ni da ban ganta ba" "ina zuwa..." ya fada kafin ya mike ya fita zuwa bedroom dinta dan jiki da jini sannan yau da gobe sai Allah, a bakin kofa ya tsaya yayi knocking tana zaune kan gadonta da laptop a gabanta tana wani research......... Wai shin yaya zata kaya?? Drop your comments...... Next chapter loading...... ✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifi ɗaya #lovetriangle #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef *_Ummi Shatu_*👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA..... NA UMMI A'ISHA 7 ***Shuru kamar ba zata amsa ba saboda haushin kowa take ji, shi kuma bai fasa ƙwankwasa kofar ba, a hankali tamkar bata so ta tashi ta sauka daga kan gadon nata ta nufi bakin kofar tana tsaki cikin ranta, "Wai hajjo me kike bukata ne...... Bana fada miki kar ku sake kawo min komai ba....." tana budewa taga Afeef tsaye hannayenshi cikin aljihun wandon shi, kallon juna suka yi tsawon mintunan da baza su wuce ɗaya zuwa biyu ba kafin ta dauke idonta ta kalli gefe, "Anty Mimi fatan komai lafiya?" "Lafiya lau......." "Ok, dama na zo in duba ki ne ko ba ƙalau ba saboda naji Hajiya tace tun jiya bata ga kin fito ba...." "lafiya....." "shikenan tunda lafiya...... Amma kin ci abincin?" "naci" ta fada a takaice kamar bata son cigaba da maganar " " to shikenan, sai anjima" ba tare da ta amsa ba kawai yaga ta mayar da kofar ta rufe tayi komawarta ciki, shima juyawa yayi ya koma inda ya fito inda ya tarar da hajiya da Irfan suna cigaba da maganar anty Mimi dan yanzu kamar haushin kowa take ji, wuri ya samu ya zauna kusa da hajiya cikin ransa shima yana fatan lokaci yayi yayi ya zo ko ya huta da wannan tsaka mai wuyan da ya jefa kansa. Har dare yana family house amma babu ko alamar motsin anty Mimi kai tamkar ma bata cikin gidan bayan kuma tana nan a cikin daki sai tufka take yi da warwara ita kaɗai, shi kam yana son ya koma gida amma yana tunanin halin da zai sake zuwa ya tarar da mommy dan yanzu babu fuska ko kadan daga gareta shiyasa yaji gaba daya baya son komawa gidan sai dai kuma idan har bai koma dinba nanma wata sabuwar matsalar ce dan haka ya lallaba ya nufi gida kuma tunda ya shiga part dinsa ya rufe bai sake fitowa ba har zuwa lokacin da yayi bacci. Washe gari bayan ya tashi a fusace ya hango mommy ta fito daga cikin part dinta ta wuce wurin motar ta sai faɗa take yi, yasan ita da daddy ne kuma ba zai wuce akan wannan maganar kwaya daya ba ta aurenshi da anty Mimi, sakin labulen da yake hannunshi yayi ya shiga cikin toilet, ji yake a ransa ma kawai gara ya shirya yayi tafiyar sa calabar dama a yanda ya tsara zuwa upper week zai koma amma yanzu tunda zaman nashi baida wani amfani ko alfanu ai gara ya koma bakin aikinsa saboda baya jin dadin wannan rashin jituwar da yake ganin yana faruwa kullum tsakanin mommy da daddy kuma duk a ta silarshi da sanadiyyarsa, ko breakfast bai yi ba kawai yayi wanka ya fita family house acan ya yi breakfast dan yana shiga gidan Ammi ya tarar suhana da Irfan suna kokarin karyawa suhana ta soya musu dankali tare da sos din kwai ita kuma Ammi din bata nan ta tafi raka hajiya gaisuwa, Zama yayi yana kallon Suhana da tun bayan shigowarshi take kallon sa tana kunshe dariyarta, "Yaya Afeef sannu da zuwa ina kwana?" "Lafiya lau, ya aka yi ne? Dariyar me kike yi?" "dariyar yanzu ka zama in law dina mana...." Murmushi yayi ya zauna ya dan kalli Irfan kadan kafin ya mayar da kallonsa gareta, "Bana son ki rinka yimin kallon in law, am your blood brother....." "na sani ai yaya..." "good...." Shi dai Irfan yana jin su bai yi magana ba hankalinsa na kan breakfast dinshi da wayar shi dake hannun sa, janye flate din Afeef yayi ya kai gabanshi ya fara ci yana hararshi, girgiza kai Irfan yayi ya saki murmushi ya kalleshi yace, "Good morning in law....." Wata sabuwar hararar Afeef ya sake aika masa yace "bana son neman magana fa" Dariya suhana tayi dake zaune tana jinsu sannan cikin ranta tana jin dadin yanda zumuncin ahalin nasu ke tafiya ta yadda har sun zamo tsintsiya, haka kuma kowa na kaffa kaffa da dan uwansa babu bambanci bare waraki, sallamar janan ta katse mata tunaninta kuma ta dawo cikin hayyacinta, atare duka suka amsa sallamar nan ta shiga cikin falon inda suke yin breakfast din, "yaya Irfan ina kwana, Yaya Afeef ina kwana...." janan ta fada tana ajiyewa suhana dan karamin food flask din da ta kawo mata wainar fulawa, "lafiya lau...." Afeef yace kadai yayin da shi kuma Irfan yaci gaba da tsokanar janan bayan ya amsa gaisuwar ta, cike da kunya kunya take amsawa Irfan kafin taja hannun suhana suka fice gaba daya daga cikin falon. Bayan fitar janan da suhana Afeef ya kalli Irfan wanda idonsa ke kan screen din wayarsa yana kallo yace, "Irfan ina jin zuwa gobe zan koma calabar....." ajiye wayar Irfan yayi ya kalle shi yace, "saboda me? Ba da naji kace sai zuwa upper week ba?" Ɗan murmushin takaici Afeef yayi wanda ke kunshe da damuwa sannan ya kalli Irfan ya bashi amsa da, "ehh but i change my mind..... Inada ayyuka da yawa.... I have alot of works soo kaga is better na koma instead of nayi ta zama a nan gida ina hutun jaki kaya aka...." Ajiyar zuciya Irfan ya sauke yace "hakane but ya maganar ku da anty Mimi? Ko ba yanzu zaku tare ba?" "Anty Mimi zata cigaba da zama a nan har zuwa lokacin da komai zai zama settled kamar hakan zai fi...." "ok to hakanma yayi, in dai har kun riga da kun gama tsara komai kun fahimci juna ai shikenan ni ina ganin babu problem...." "Yeah..." shine kawai abinda Afeef yace ɗan shuru ya ratsa falon kafin Irfan ya katse shurun da cewa, "itama kamar bata nan taje hospital tun da sassafe.... May be an kirata emergency ne..." "Allah ya dawo da ita lafiya" ya fada a hankali kuma daga haka bai sake cewa komai ba har suka kammala breakfast din, nan suka cigaba da zama suna kallon ball ahaka Ammi ta shigo ta same su sun dawo tare da hajiya daga ta'aziyyar da suka je, Sauka daga kan Kujerar da yake zaune yayi ya durkusa ya gaida Ammi ta amsa cikin sakin fuska da kulawa sannan ta wuce ciki, "wai ko har an fara yar surukuntar ne?" Irfan ya fada cike da tsokana saboda yaga har lokacin kan Afeef din na ƙasa bai ɗago ba sannan bai tashi daga tsugunnon da yayi ba, "you are not serious..... Ammi ai uwata ce ba suruka ba" "to ai naga kana ta faman sussunne kai ne...." "to yanzu dai ka tashi mu tafi wurin hajiya...." "muje... Fada ne zamu sha shi marar dalili tunda idan tsufanta ya motsa haka take yi" Dariya Afeef yayi yace "dambun nama nake son a sammin tunda gobe zan tafi" "zata baka ai.... Kuna shiri ai sosai" "amma dai ai ka san hajiya ba tabbas nima wata rana tana birkice mun idan ƴar rikicin na kusa" Da wannan hirar suka ƙarasa part ɗin hajiya wacce ke zaune tana faman lasar farfesun naman kai wanda ya dahu rigif, zama suka yi suka fara tsokanarta wani ta kula su wani ta rabu dasu, zuwa la'asar anty Mimi ta dawo gidan amma babu wanda ya san dawowarta bare har ya ganta dan bedroom dinta ta wuce ba tare da ta nemi kowa ba, Shima Afeef yau bai nemi inda take ba yayi sallama da Hajiya ya tafi, iya hajiya da Irfan ne kadai suka san zai koma aiki gobe, da yake yawanci idan zai koma tafiyar asubanci yake yi shiyasa tun dare ya yi kokarin shirya jakar kayansa kamar yadda ya saba, bayan ya kammala haɗa komai ya fita zuwa part din mommy iya Manal ce kadai cikin falon tana kallo ya shiga ita kuma mommy din tana cikin kitchen, har cikin kitchen din ya bita cikin sanyin murya yace, "mommy sannu da aiki......" "yawwa" "mommy na gama shiryawa gobe zan koma calabar..." ɗan sanyi mommy taji acikin ranta da taji cewa zai koma aiki gobe saboda bata son yaci gaba da zama auren nan da aka lankaya masa ya ɗore, "Gara ka koma ai tunda zaman naka anan baida wani amfani..." "insha Allah gobe zan tafi mommy...." "Amma me yasa baka fada min da wuri ba, ai da anyi maka snacks kamar koda yaushe...." "babu komai mommy, hajiya ta bani...." "to shikenan" Ganin yanda mommy din ta dan sauko har tana tarairayarsa yasa ya dan ji sanyi da dadi cikin ransa, 12 na dare ya kwanta bayan ya saita alarm dan yana son ya tashi kafin asubah tayi saboda gudun makara sai dai amma baccin yaƙi zuwar masa a maimakonshi ma tunani yaji yana ta bijiro masa cikin wannan lokaci wanda gaba ɗaya akan lamarinsu ne da ya shafi yaya Aliyu haidar, Anty Mimi da kuma shi, tun farko mema yasa ya yarda har yaji tausayinsu ya karɓi wannan tayin nasu? Juyi kawai yake ta faman yi har misalin karfe 1 da rabi na dare, da ya tabbatar baccin ba zai dauke shi a wannan lokaci ba sauka yayi daga kan gadon nasa ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito, sallar nafila yayi raka'a biyu sannan ya samu wuri ya zauna kan abin sallar tashi yana mai cigaba da yin addu'o'i har 3 saura kuma sai lokacin ya dan ji bacci a idanuwansa babu ɓata lokaci ya koma saman gadon shi ya kwanta, makara ya so yi saboda bai kwanta da wuri ba amma dai da kyar ya iya tashi ya shirya ya fita bayan yayi salla, sun yi sallama da kowa na gidan sannan ya tafi yana ji a cikin zuciyarsa wannan tafiyar tashi itace zata bawa zuciyar mommy damar hucewa cikin kankanin lokaci. Yaya Aliyu tun ranar da aka ɗaurawa Afeef da anty Mimi aure ya fara jera lissafi wato ranar da ya dace Afeef ya saketa kamar yadda suka yi alƙawari, cikin bedroom dinta yake kwana hotunanta kafe a kowacce kusurwa ta bangon ɗakin, wani lokacin su kwana suna waya wata rana kuma su raba dare suna waya saboda irin dafin soyayyar da kowannensu ke ji cikin ransa, haka da rana da safe da yamma baya samun sukuni komai kankantarsa har sai ya kirata yaji muryar ta, sosai yanzu take jin abun yana bata tsoro dan kamar wanda Aliyun ya zautu abubuwan da yake yi a kanta sun fara wuce lissafin hankali, Tun tana cikin bathroom tana wanka taji yana kiranta amma bata dauka ba saboda ta makara yau sosai kuma ba kowane ya makarar da ita ba face shi saboda shine ya hanata bacci suna ta faman hira har asubah, gashi yau akwai aiki shiyasa take ta sauri bata tsaya wani daukar wayar shi ba, cikin sauri ta fita ta bar gidan ta tafi asibiti kuma tana zuwa ta shiga theater, shi kuma ganin yana ta kiranta bata dauka ba yasa shi fita daga gida ya nufi asibiti dan ya san tana can tunda yau akwai aiki, daga shi sai kayan bacci ya shiga motar sa ya figeta zuwa asibiti, ta shiga theater dan haka ya zauna yana jiranta wanda ba ita ta fito ba sai 12, "Aliyu yau baza ka fita aiki bane?" ta fada tana kallon sa bayan ta zauna kan kujerar ta, "wallahi zan je aiki My love, in fact ma akwai wani important meeting da nake dashi but ba zan iya zuwa ba mutukar ban jiki ko kuma na ganki ba..." girgiza kai tayi cike da tausayinshi tace, "Am fine... Dan Allah ka daina wasa da aikin ka, ina nan lafiya lau...." "ta yaya zan iya tabbatar da hakan alhali ban sameki ba koda a waya ne?" "Kaga ai na shiga theater ne and you know idan na fito dole zan kiraka back...." Ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta cikin sanyin murya yace, "insha Allah saura 1 week daidai Afeef ya sake ki kamar yadda muka shirya......" "Babu problem, Allah ya kaimu...." "yana nan ma kuwa? 2 days bana ganinsa, ko ciwon nashi ne ya tashi ko ya motsa? Bari na kirashi naji...." wayar shi ya dauka dake ajiye kan teburinta ya fara kiran layin Afeef..........✍️ KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifi ɗaya #lovetriangle #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 8:56 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA..... NA UMMI A'ISHA 8 ***Zuba masa ido tayi kawai tana kallonsa cikin ranta tana jin wani irin bala'in tausayinshi saboda yana yin abu kamar wani wanda ya ɗan taɓu ko kuma ya zautu banda haka yanzu kalli fa a yanda ya fito ya taho office dinta dan kawai ya kirata a waya bai jita ba,ɗan tsakin da taji ya ja ne ya dawo da ita cikin hayyacinta, "wannan yaron ko bacci yake yi bai tashi bane..... Na kira tana ta ringing bai yi picking ba" "may be bai tashi daga bacci ba...." "amma anya kuwa yana gari..... Nifa bana ganin shi ko a family house" "shine dai nima ban sani ba dan na jima ban ganshi ba nima...." "to babu matsala dai, zuwa anjima zan sake taɓa shi inji" "ok" "bari naje gida na shirya na fita office" "ok to thank you" Tashi yayi ya fita amma sai faman waiwayenta yake yi kamar yau ne ya fara ganin ta yayin da ita kuma ta janyo wani file ta bude ta fara rubutu aciki. Bayan da Afeef ya koma bakin aikinsa gaba daya tattara maganar aurenshi da anty Mimi yayi ya ajiye a gefe dan a takaice ma shi ya manta da cewar akwai wani aurenta a kansa, baya waya da kowa sai Irfan kadai idan ya samu lokaci sai kuma mommy da daddy suma din kawai yana kiran su ne saboda ya kwantar musu da hankali domin duk ranar da basu ji shi ba hankalinsu tashi yake suyi ta tunanin ko ba ƙalau ba,kusan kullum sai yaga miss calls din yaya Aliyu amma bai taba kiran sa back ba abinda ya fara ƙonawa yaya Aliyun rai kenan shida anty Mimi dan a ganinsu wannan rainin wayo ne dan suna neman abu a wurin shi bashi ne zai bashi lasisi ko kuma damar wulakanta su ba yadda yaso, Misalin ƙarfe 1 harda rabi na dare ya kira Irfan, yana kwance cikin dakinshi kuma dawowarshi kenan daga aiki, jin Irfan ya daga wayar ya sashi yin murmushi kafin a hankali yace, "wai bacci kake yi?" "wallahi idona biyu yanzun nan naje na dauko anty Mimi daga hospital na dawo da ita gida....." ai sai lokacin Afeef ya tuna da maganar auran shi da ita da kuma uban kiran wayar da yaya haidar ke ta faman yi masa babu dare ba rana, "ohh matata ka dauko min daga aiki kenan.... Thank you for taking good care of her for me....." Dariya Irfan yayi yace "you see your life?" "yanzu dai menene labari? How is everyone? Ya anty Mimi hope she's fine?" "baka da number dinta ne kake tambayata? Call her and ask....." "yanzu ma sai da na gama waya da ita before na kiraka" ya fada cike da tsokana, "kamar gaske...." "am serious young man" "yanzu dai wai zuwa yaushe zaka dawo?" Ɗan dogon numfashi ya ja sannan a hankali yace "i don't know gaskiya.... I can't say, but idan na samu time zan zo" Sun jima suna hira kafin suka yi sallama kowannensu ya ajiye waya, Irfan tunani yake yi cikin ransa anya kuwa anty Mimi da Afeef suna communicating? Dan bai ga alamar hakan ba dan baya mantawa tafiyar Afeef dinma shi take tambaya wai abokinsa yana nan kuwa taga bata ganin shi kwana biyu shi kuma yace ai ya koma calabar bai yi mata sallama bane? Daga haka yaga tayi shiru bata sake yin maganar ba, A bangaren Afeef kuwa yana ajiye waya ya ɗan yi shuru na wasu yan mintuna kamar me yin tunani, iya gajeren wando ne a jikinsa tashi zaune yayi yana shawarar to ko ya kira yaya Aliyu yanzu? To kuma idan ya kirashi yanzu anya dare bai yi ba? Fasa kiran nasa yayi ya koma ya kwanta kan yar karamar katifarshi, kullum shi kadai yake kasancewa a ɗan karamin dakin nashi saboda tarbiyar da iyayenshi suka bashi duk wata rayuwar shashanci bata burge shi kuma baya cudanya da ita. Jugum anty Mimi tayi bayan ta danna number yaya Aliyu tana jiran taji ya ɗauka, yana ɗauka taji yace, "my love akwai wani labari ne?" "gaskiya yanzu na fara zargin yaron nan da sanin sa yake kin daukar call dinka..... Kullum fa yana yin waya da Irfan, yanzun nan Irfan ya fita daga cikin bedroom dina kuma ya tabbatar min da ko a daren jiya sun yi waya, anya kuwa babu wani abu da yake shiryawa, ta yaya za ace baya ganin miss calls dinka and bai taba calling dinka back ba.... " " calm down my love, bari zan sake kiran sa, mu bashi benefit of doubt.... Zan kirashi zuwa anjima sai naji me zai ce kuma wanne uzuri zai bamu.... " " ka san me? Kawai idan ka same shi kasa shi ya sake ni a lokacin tunda already time din yayi har yana neman ya wuce.... Ni na gaji da wannan maganar guda daya, na kasa gane me yake nufi dani am tired.... " Shi kansa yaya Aliyu jikinsa yayi sanyi da wadannan maganganun da yaji daga gareta amma sai ya dake yayi ta maza wurin kwantar mata da hankali, abun yana daure masa kai to me yasa Afeef zai yi masa wasa da hankali har haka? Rasa amsar da za ta dace da wannan tambayar tasa yayi dan haka ya tashi ya hau zagaya cikin dakin sa yana tunani, "me Afeef yake nufi? Anya yaron nan yana da gaskiya kuwa?" Kiran Afeef din ya fara yi a waya sai dai har tayi ta tsinke bai dauka ba, sake kira yayi nanma shuru ahaka har sai da yayi masa miss calls guda biyar a na shidan kuma yaji ya kashe wayar hakanne ya harzuka yaya Aliyu cikin takaici da damuwa yace, " Afeef ni zaka kashewa waya? Okay yayi maka kyau...." Wuni yayi cikin bakin ciki da takaici da ɓacin rai kuma har lokacin wayar Afeef a kashe dama yawanci sai dare aka fi samun sa, bai faɗawa Anty Mimi yanda suka yi da Afeef dinba kawai ya bar abin cikin ransa yana ta kokarin samun hanyar da zai shawo matsalar ko kuma ma ya magance ta gaba ɗaya. Afeef yana ganin kiran yaya Aliyun yaƙi dauka saboda ko ya dauka bai san me zai ce masa ba shiyasa kawai ya zabi ya ki dauka din daga karshe da yaga baida niyyar daina kiran sai kawai ya kashe wayar wanda bai sake kunnawa ba sai da ya zo kwanciya da daddare, yana kunnawa kiran yaya Aliyu na shigowa, dauka yayi, "Afeef menene haka? Haka muka yi da kai?" shuru Afeef yayi bai ce komai ba har sai bayan da yaji yaya Aliyun yayi shuru sannan a hankali yace, "yaya haidar you are angry why? Kayi hakuri ni na manta ne ma gaba daya da wannan maganar fa, sannan 2 days banida lafiya kuma aiki yayi min yawa ka san yanayin aikinmu am soo sorry please" ajiyar zuciya yaya Aliyu ya sauke wanda yanzu yaji ya dan samu nutsuwa sannan kuma damuwarshi ta ragu, "to ai Afeef duk kamata yayi kayi min bayani ba wai kayi shuru ba, baka picking calls dina baka kirana back..." "am sorry yaya...." "yanzu ya jikin naka? Dama akan maganarku ne da Mimi, time yayi da zaka sake ta..." "alhamdulillah jiki da sauki,ok to shikenan yaya babu matsala zan sake ta..." "yawwa Afeef nagode sosai, Allah ya bar zumunci, mun gode, tnx alot.... This means alot to us..." "you are welcome yaya" Sallama suka yi Afeef ya dora wayar akan kirjinsa ya lumshe idanuwansa sannan a hankali yace "am sorry yaya... I can't..... Dan Allah ka yafe min" Da murna Aliyu ya kira anty Mimi bayan sun gama waya da Afeef tana dauka yace, "my love ki fara shirin dawowa gareni dan yanzun nan muka gama waya da Afeef..." "ya sake ni dinne?" "no, ai saki ke zai kira ya fada miki my love, munyi magana" Dan gajeren tsaki ta ja kafin tace "kai ma kana da abun haushi haidar, tunda ka same shi meya hanaka kasa ya sake ni?" "zai sake ki baby.... Na fada miki munyi magana dashi" Bata sake ce masa komai ba ta katse wayar dan haushi tana faman kunkuni, "wannan wanne irin rainin hankali ne kuke yimin daga shi har kai din, tunda ka same shi menene amfanin kirana da zai yi" shi dai yaya Aliyu duk tunaninshi zuwa washe gari Afeef zai sakar masa matarsa amma sai yaji shuru sannan koda ya kira wayar Afeef din rai da rai tana kashe, abin da ya sake ƙonawa anty Mimi rai kenan ganin har an sake share sati ɗaya babu wata sabuwar magana, bata son kiran Afeef din a waya amma gani take yanzu ya zamar mata dole ta kirashi da kanta tunda shi Aliyu ya kasa samun sa bayan kuma Irfan ya tabbatar mata da kullum shi suna yin waya da Afeef din. Tana zaune tsakiyar gadonta ranta a cunkushe haka ma fuskarta ta soma kiran wayar tashi kuma bata san dalili ba haka kawai ta samu kanta dumu dumu cikin tsoro tsoron da bata san ko na menene ba ga faduwar gaba dan kirjinta tara tara taji yana duka musamman ma da taji wayar ta shiga har ta fara ringing, "Assalamu alaikum.... Anty Mimi" Lumshe idanuwan ta tayi ta finciko numfashinta da kyar take taji bakin ta kamar an kulle dan ta gagara furta koda kalma ɗaya, "Hallo.... Anty Mimi" taji ya sake fada daga bangaren shi, daurewa tayi ta bude bakinta da kyar tace, "Afeef baku gama magana da Haidar bane?" "wacce magana?" take taji gabanta ya yanke ya faɗi da mugun karfi haka kuma tsoron da take ji shima ya sake karuwa da kaso mafi yawan na baya da take ji, "maganar sakina da zaka yi...." shuru taji yayi kamar bama ya tare da ita, "hello....." "ina jinki anty Mimi.... I can hear you" "maganar sakina da za ka yi ko baka ji ba" "naji anty Mimi, yanzu ya za ayi?" "ka sake ni shine yanda za ayi" "yaushe?" taji ya bukata cikin rainin hankali banda haka ta yaya duk zai rinka yimata wadannan tambayoyin marassa amfani, "yanzu" ta fada cikin bakin ciki da kuma bacin rai, "ok to amma ai akwai abu ɗaya da bamu riga da munyi ba...." "menene?" ta tambaye shi cikin sauri bakinta har yana rawa, "ban dandani zumarki ba kamar yadda ka'idar take... " Ji tayi idan har ta tsaya bashi amsa to tabbas za ayi abinda ba zai haifi ɗa mai ido ba, cike da bacin rai ta katse wayar tare da cilla jifa da ita ta fada can kan sofa bata faɗi a ƙasa ba, kugunta kawai ta rike cike da takaici, tabbas biri yayi kama da mutum, dama ashe ba banza ba yake ta faman yi musu yawo da hankali? Anya Afeef bazai basu matsala ba akan maganar sakin nan? Da sauri ta nufi wayarta ta dauka hannunta yana rawa tayi dialing number Aliyu............ ✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifiɗaya #lovetriangle #Aliyu #DrMimiAndAfeef *_Ummi Shatu_*👌🏻 [7/18, 9:03 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA..... NA UMMI A'ISHA 9 ***Bugu biyu taji yaya Aliyu ya ɗauki wayar tata, can ƙasan maƙoshinsa taji yace, "hello my love...." "Haidar na faɗa maka yaron nan Afeef akwai wata a ƙasa, ni dama na san sai haka ta faru... I knew it.... Wallahi na san dama sai ya bamu problem....... Na san za ayi haka...." "wait..... Calm down Mimi, talk to me..... What's going on?" ya faɗa yana kokarin tashi daga kwancen da yake saboda damuwa da tashin hankalin da bai san wanne iri bane kuma, "Wai me yaron nan yake nufi dani? Yanzu na kira shi akan maganar saki kaji irin banzar maganar da yake faɗa min dan rashin kunya?" "easy Mimi, me ya fada miki? Cewa yayi bazai sake kiba?" "something like this...... Yana maganar wai bai dandani zuma ta ba taya zai sake ni......" "what....... Shi Afeef dinne yake iya fada miki wannan maganar? Yaron nan baya shaye Shaye kuwa? Ni zai nunawa ƙwaya...... Sai naci kutumar ubansa wallahi....." ya fada cikin zafin rai sannan cikin gaggawa ya katse kiran nata ya fara kiran wayar Afeef, da farko ya zaci kamar bazai dauka ba sai kuma yaji ya daga, cikin fushi yaya Aliyun yace, " Afeef.... Ina wasa da kai? Da ni da Mimi cikinmu akwai sa'anka? Wacce irin magana naji kana faɗa mata saboda baka da mutunci ko?" "Haba yaya Haidar me kuma ya faru?...." "yanzu dai ka sakar min matata saboda naga abun naka rashin mutunci ne da iskanci....." "shikenan zan sake ta...." ƙit daga haka Yaya Aliyu yaji Afeef din ya kashe wayar shi nan ya sake kokarin kiran sa amma wayar bata tafiya ya sakata a DND, kwafa yaya Aliyu yayi ya hau zagaye cikin bedroom dinsa tamkar zararre, "ni Afeef zai kashewa waya? Ni? Matata zai ce zai dandani zumarta?" kasa zaune yayi ya kasa tsaye sai aikin kiran wayar Afeef yake yi amma bata tafiya wanda hakan ko kadan bai dameshi ba kawai cigaba yake da kira har dare ya raba kuma ya tsala, Ita dai anty Mimi tana zaune tayi tagumi ta zubawa wayarta dake gaban ta ido tana kallonta zuciyar ta na tafarfasa kamar zata ƙone ko kuma ta tarwatse dan bakin cikin da take ji cikin ranta, wai ita Afeef zai fadawa haka? Wannan shine dalilin da yasa tun farko bata so aka hada wannan deal din dashi ba saboda zai iya samun dama yayi musu kowanne irin cin kashi yaso, "why me? Why always me?" take fada cikin bakin ciki da damuwa, tunaninta ya katse ya tsaya cak daidai lokacin da kiran Aliyu ya shigo, numfashi ta sauke da kyar saboda nauyin da yayi mata, cikin ranta tana addu'ar Allah yasa Afeef yayi sakin kowa ya huta dasu dashi, " ya kuka yi dashi?" ta fada gabanta na faman faduwa da karfi, "ya kashe wayar shi batare da mun gama magana ba...." "Aliyu anya yaron nan babu abinda yake nufi kuwa? Nifa na jima ina zarginsa dama, is like zai bamu problem" "ki kwantar da hankalinki my love.... Wallahi bai isa ba, nawa yake ma, dole sai ya sake ki ko baya so...." "am confused....... Haidar am confused...... Wallahi na rasa wanne irin tunani zanyi.... Aliyu am lost ....." "bake kadai ba.... Yaron nan ya goge min hadda gaba daya amma zanyi maganinsa" Ajiye wayar suka yi a tare Mimi ta cije lips dinta na kasa cike da takaici ta zubawa wuri daya ido tana karkada kafarta ba tare ta san me zata yi tunani a wannan lokacin ba. Kwana yaya Aliyu yayi a zaune bai samu bacci ba saboda damuwa da ɓacin rai da kuma tarin takaicin dake kai komo cikin zuciyarsa, ji yake da ace yana iyawa da yabi Afeef har calabar dan suyita ta ƙare, a fusace kuma a kidime da gari ya waye ya nufi gidan yaya faruk wanda Allah ya takaita basu yi saɓani ba saboda ya shiga wanka kenan idan ya fito zai shirya ya bar gari zuwa Abuja saboda wani taron gaggawa da aka kirasu matsayin su na ƴan jaridu, yanda yake huci sannan kana ganin fuskarshi kasan ba ƙalau ba ya sanya Jiddah matar yaya faruk saurin zuwa cikin bedroom dinsa inda yake wanka bayan sun gaisa da yaya Aliyun, "Abbah kayi sauri dan Allah ka fito kar kayi irin wannan jimawar taka da ka saba yi cikin toilet...... Yaya Haidar ne yazo" Komawa ta sake yi falo wurin yaya Aliyun wanda ke zaune ya dunkule dukkan hannayensa ya sarke su wuri ɗaya ransa a ɓace, "na faɗa masa zai fito yanzu insha Allah...." "ok nagode Jiddah...." Bata zauna ba ta koma kitchen inda take hada breakfast, Aliyun na nan zaune Yaya faruk ya shigo sanye da rigar wanka dan yana fitowa daga bathroom kai tsaye falon ya nufo saboda gaba daya jikinsa yana bashi duk yadda akayi ba lafiya ba, " Haidar lafiya kuwa?" "Faruk ba lafiya ba, yaron nan Afeef nake son ka kira min a waya saboda ni inata faman kiranshi a waya amma bana samun sa...." "yayi maka wani laifin ne? Me ya faru?" "ka kira min shi first zanyi magana dashi" "ok ina zuwa..... Bari na dauko wayata" Yaya faruk bai kawo komai cikin ransa ba haka kuma maganar auren mimi da Afeef bata taba zuwa cikin kwanyarsa ba a daidai wannan lokaci bare har ya gane ko ya fahimci musabbabin neman da Aliyu ke yiwa Afeef, number Afeef ya kira bayan ya dawo cikin falon amma kuma bata tafiya, Tsaki yaya Aliyu yayi kafin yace "shikenan rabu dashi ka daina kira.... Zanyi ta trying da kaina dama na zaci ko ni kadai yayi blocking...... Babu damuwa" "wai me yake faruwa ne? Wani laifin yayi maka ko ƙaƙa?" "no bai yimin laifin komai ba, dama munyi magana dashi ne jiya yake ce min baida lafiya to shine dazu na kira na duba shi naji ban same shi ba shiyasa hankalina ya tashi...." "Allah ya bashi lafiya...." "amin bari na wuce...." "ba zaka tsaya kayi breakfast ba" "No alhamdulillah...." Sallama suka yi ya fita ya shiga motar sa ya nufi gida yana girgiza kai, ƙarar wayar shi ta sa ya kai duban shi kan wayar nan yaga mimi ce da alama itama hankalinta tashe yake saboda rashin samun wannan yaron, "My dear ka same shi kuwa?" "wallahi my love ban same shi ba yanzu ma kin ganni a hanya daga gidan faruk mun neme shi ta wayar faruk amma bata shiga...." "Haba Haidar Meyasa kake haka? Idan asirinmu ya tonu kuma fa? Idan yaya faruk ya fahimci wani abu fa?" "ba zai fahimci komai ba i promise you.." "innalillahi wa inna ilaihir rajiun...." ta faɗa cikin damuwa da tashin hankali, ita dai tun daga wannan lokaci komai nata ya rikice haka kuma ta shiga cikin damuwa, shi kuwa yaya Aliyu kullum baida aiki sai kiran wayar Afeef da tura masa da massages amma shuru baya responding ba kuma ya samunsa, Daga call din har massages din duk Afeef yana gani amma babu wanda yake kulawa aikinsa kawai yake yi kuma shi ya saka a gaba har ya kwashe kimanin watanni uku a calabar kuma sai lokacin ya samu dan hutu dan haka ya nufi gida kamar yadda ya saba. Ya samu tarba sosai daga wurin mommy wacce yaga kamar ta manta da batun aurensa da yayi ko kuma ta sauko ne ta haƙura Allahu a'alamu, tuwon biskin masara ya samu tayi masa da miyar taushe kamar yadda ya bukata, miyar tasha man shanu da naman kaza sai kamshi take yi, Irfan ne ya dauko shi shiyasa tare suka ci abincin, bayan mommy ta haura upstairs Irfan ya kalleshi yace, "ban ji ka tambayi anty Mimi ba alhali kuma naji kana ta tambayar mutanen gida daya bayan ɗaya...." Murmushi Afeef yayi cikin ransa yana ayyana yanda zasu kwashe da yaya haidar da kuma anty Mimi din wanda ya san sun jima suna zaman jiran wannan lokacin na dawowarsa sai dai amma ko ɗar bai jiba bare har hankalinsa ya tashi, rayuwar sa yake yi hankali kwance ya barsu da matsalar su dan ba matsalar shi bace, "na san tana nan lafiya ai....I knew she's fine" "waye ya fada maka? To 2 days bata da lafiya ko aiki bata fita...." "Allah ya bata lafiya" ya fada a hankali yana tunani a ransa, "amin ya Allah..." "kace ina gaida ta kafin inzo...." "Insha Allah zan fada mata" Bayan tafiyar Irfan part dinshi ya shige ya kwanta yayita shirgar baccin shi bayan ya kashe wayar shi. Anty Mimi tana zaune tare da hajiya kaka tana yankewa hajiyan faratanta Irfan ya shigo, bayan ya zauna ya kalli hajiya kaka yace, "mijinki yana gaida ki shalelenki.... Ya dawo naje na dauko shi...." "Au lele ya dawo shine bazai zo in ganshi ba?" "yana nan zuwa ai idan ya huta, anty Mimi kema yace yana gaida ki" ai idan ta amsa masa to kujerar da suke kai ta amsa, tana jin su har suka ƙaraci hirar su akan shi Irfan ya tashi ya fita bata tofa tata ba aciki, bayan ta kammala yankewa hajiya farce ta koma bedroom dinta ta kira yaya Aliyu ta sanar dashi dawowar Afeef wanda tsabar rainin wayo harda sakon gaisuwa ya bada a kawo mata, ƙwafa yaya Aliyu yayi yace, "ba dai ya dawo ba, barni dashi zanje har gidan in sameshi...." Suna gama wayar yaya Aliyu ya nufi gidan daddy, part din Afeef yaje bai ko leka na mommy ba saboda bama ya son ta san yazo kai kusan kowa ma dake gidan baya son su san da zuwan sa, knocking ya jima yana yi wanda yana da tabbacin Afeef din yana jinsa amma yaƙi budewa ya rabu dashi har ya gaji da jira ya tafi, yanzu kam ya fara ji a jikinsa kamar maganar mimi na shirin zama gaskiya, kamar sai sun kai ruwa rana sannan Afeef din zai dawo cikin hankalinsa har ya cika musu alƙawarin da suka yi dashi ya yi musu abinda suke so. Tsawon sati guda da dawowar Afeef din yaya Aliyu nata faman sintiri a gidan amma baya bude kofa haka kuma baya daukar waya bare reply na massages, daga mimi har yaya Aliyu sun gama zuwa wuya dashi sun ƙulu ƙarshe, shi dai sai yau ne yake jin zai iya fita sakamakon baccin da yayi na kwana da kwanaki yana hutawa, daukar wayar shi yayi jin kira ya shigo kamar yadda yanzu wayar bata rabo da kira kaca kaca, ganin yaya Aliyu ne yasa ya dan yi murmushi, "hello.... Yay...." "Afeef ka gama rashin mutuncin naka? Are you done?" "yaya kana ina? We need to talk...." "Ina office din mimi..... Talk about what?" "ina zuwa yanzu...." Katse wayar yayi ya fara shiryawa, jar t shirt ya saka sai blue din jeans da bakin agogon fata ya fesa turaren black oad ya dauki key din mota ya fita ba tare da yayi sallama da kowa ba.......✍️ KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifiɗaya #lovetriangle #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 9:03 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA......! NA UMMI A'ISHA 10 ***Zuciyarshi cike da saƙe saƙe kala kala ya nufi office din anty Mimi yana driving yana lissafin yanda zai bullowa wannan lamarin da haka har ya ƙarasa hospital din, Kai tsaye office dinta ya shiga bayan yayi knocking, suna zaune ita da yaya Aliyu kan kujera 3 sitter wacce ke girke cikin office din daga gefe ɗaya, "Afeef wai me kake nufi damu ne? Munyi magana dakai munyi alkawari munyi yarjejeniya, har kudi na baka dan komai ya tafi bisa tsari amma ka dawo min dashi yanzu kuma tsawon watanni ina shan kanka akan ka sakar min mata ta amma abu yana neman faskara sai faman wasa da hankali kake yimin....... To yanzu kazo ka sake ta ne ko me ya kawo ka? " tunda yaya haidar ya fara wannan bayanin Afeef ya zuba musu ido yana kallon su daga shi har anty Mimin, baiyi magana ba sai da yaji yaya haidar ya ɗiga aya alamar ya gama sannan ya ja ajiyar zuciya a hankali ya sauke yace, " Yaya kuyi hakuri da ɓata muku lokaci da nayi a baya, wallahi ko kadan hakan ba da niyya nayi ba sannan ba wai da son raina bane it wasn't intentional..... Amma yaya ni ina ganin da mu hakura da maganar sakin nan kawai mu dauka haka Allah ya kaddara kuma ya tsara sannan zamanku da ita ya kare ne shiyasa har aka yi haka..... " ai daga Anty Mimi har Yaya Aliyu jin maganarsa suka yi tamkar saukar aradu ko kuma saukar guduma a tsakiyar kansu, zaro ido Aliyu yayi yana kallon Afeef cikin fushi da fusata yace, " kai me kake nufi ne, what do you mean? Ba zaka sake ta ba ko yaya? Mun nemi shawararka ne da zaka zo kana ce mana haka Allah ya tsara? Zamana da mimi bai kare ba dan mutuwa ce kadai zata rabamu...." "yaya Haidar mu daina yaudarar kanmu......let's stop deceiving ourselves Wannan itace gaskiya, kun rabu da anty Mimi ni kuma na aureta and bana jin zan iya sakinta bare har ta dawo gareka in fact dama ban aureta dan in saketa ba..." Tsaye anty mimi ta mike ba tare da ta sani ba jikinta yana faman rawa fuskar ta cike da tashin hankali, ta kasa magana ta kasa koda kwakkwaran motsi, shima yaya Aliyu tashi yayi daga zaunen da yake dan bai ga alamar cewa Afeef da wasa yake ba dan babu alamar wasan a tare dashi dan yana magana ne cike da nutsuwa da kuma gaskiya, "lallai ka cika maci amana..... Ka cika mazambaci kuma mayaudari Afeef....... Amma ina son ka sani Mimi ba kalar matarka bace, wallahi ko kana so ko baka so sai ka sakar min mata tunda baka da mutunci.... Nafi ka hauka" "yaya wannan fa ba maganar cin amana bane maganar gaskiya ce wallahi ba zan saketa ba sai dai idan mutuwa nayi sai ta koma maka amma indai ina raye to kun gama zaman aure....." "Afeef me nayi maka? Me muka yi maka da ka zabi ka tarwatsa rayuwar mu ka wulakanta mu? Ashe dama ba taimakonmu kayi niyyar yi har cikin zuciyarka ba? Wannan wanne irin yaudara ne?" Anty Mimi ta fada idanuwanta sun cika da kwalla dan tsabar bakin ciki da tashin hankali, " ka bude kunnen ka da kyau ka jini Afeef, na rantse da girman Allah ko sama da ƙasa zata hade sai ka sakar min mata ta, na fika iskanci kai karamin dan iska ne, ka bar ganin kana shan kwaya wallahi na fika tijara ƙwayarka da neman matanka da kake yi duk a tafin hannuna kake..... " Jin abubuwan da yaya haidar ke fada masa yasa kawai ya mike da niyyar ya tafi yabar musu office dinma gaba ɗaya, wani kukan kura yaya Aliyu yayi ya nufe shi ya finciko shi ya fara kifa masa mari baji ba gani amma ko gezau baiyi ba, " wallahi ko zaka kashe ni ba zan saketa ba....." wani wawan marin ya sake kifa masa, ƙara anty Mimi ta ƙwalla kamar wacce keda aljanu ko kuma take shirin tayar dasu babu shiri yaya Aliyu ya nufeta, juyawa Afeef yayi ya fita daga cikin office din fuskarshi rado rado da shatin yatsun yaya Aliyu saboda marin da yayi masa ba na wasa bane gashi bahago ga kuma fushi da zuciya duk a lokaci guda, shima a kule yake kuma a fusace ya koma gida, yana shiga yayi parking motar sa ya nufi cikin part dinsa ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskarsa, idanuwansa jajur saboda bacin rai haka itama fuskar shi tayi ja musamman wurin shatun hannun yaya Aliyu, shi ba wai yana son anty Mimi bane kamar yadda ya san itama ba sonshi take yi ba amma zasu zauna ahaka har lokacin da zasu koyi son junansu wannan alkawari ne ya daukarwa kansa, ba zai taɓa sakinta ba duk bala'i, kashe wayar sa yayi yai zamansa cikin bedroom dan baya son kowa ya ganshi. Kamar wata mai aljanu haka anty Mimi ta koma ta zubawa yaya Aliyu ido wanda yake rike da hannunta hawaye na bin kumatunta, "kaga irin abinda na jima ina fada maka ko.... Kaga ni ko? Dama sai da na fada maka mu nemi wani mu biya shi zai yi mana abinda muke so amma kace baka yarda da kowa ba kai sai shi...... Gashi yanzu yace ba zai sake ni ba kuma na san maganar na iya zuwa kunnen su Abba..... Hajiya tana jin wannan maganar cewa zata yi in tare a gidansa shikenan an rabamu..... Wallahi bazan iya zaman aure da kowa ba sai kai.... Mutuwa zanyi yaya Aliyu..... Wallahi mutuwa zan yi na sani.... " wannan shine abinda take ta fada tana hawaye, " Yaron nan yaudara ta yayi ya shammaceni Mimi, he deceived me.... Amma nayi miki alƙawari ba zan taɓa barinsa har yayi nasara a kanmu ba.... Bai isa ya rabamu ba.... " Numfashi take yi sama sama kamar mai ciwon asthma ko wani ciwo mai kama da haka, sam bata ma fahimtar abinda yake fada dan ta jima bata cikin hayyacinta kafin ta dawo daidai amma kuma a mugun hargitse take, tare suka fita daga office din nata anan ta bar motar ta ya dauketa a tashi zuwa gida, ta kasa magana dan ko kalma daya bata iya fita daga cikin bakin ta ba har suka je gida duk sai bata tabbaci yake na cewa zai shawo kan wannan matsalar, bedroom dinta kawai ta shige ta kwanta kan gado tana hawaye, tun tana kukan zuci har ta fara na fili babu wanda ya sani ko kuma ya san halin da take ciki daga ita sai yaya Aliyu sai kuma Afeef. Shi kam yaya Aliyu bayan ya ajiye ta ya wuce gidanshi fashe fashe yaje yayi kamar wani mahaukaci haka ya zama daga karshe ya yanke jiki ya fadi da kyar ya iya kiran yaya faruk yazo ya kai shi asibiti, Washe gari anty Mimi bata fita aiki ba kuka kawai take yi ta kasa cin abinci saboda bakin ciki, bata so su ɗaga maganar har ta fito manya su ji dan idan su Abba suka ji to kashin su ya bushe gaba daya sannan dole Afeef shine da nasara dan ta san su Abba baza su taba goyon bayan su ba bare har su biyewa wannan shirmen nasu, sam bata da labarin abinda ya faru da yaya haidar har sai da aka sallame shi daga asibitin ya koma gida sannan ya kirata yake sanar da ita, tagumi ta rafka cikin ranta tana cewa yanzu ita ya zata yi? Wayarta ta dauka ta fara rubutawa Afeef massage, ai durkusawa wada ba gajiyawa bane, Yana tsakiyar cikin dakin sa yana training kamar yadda ya saba yi duk safiyar duniya sai yayi wannan training din na awa ɗaya ko mintuna talatin yaji shigowar massage, bai buda ba sai da ya gama training din ya zauna yana hutawa lokacin ne ya bude massage din nata, _Bai kamata ka zama silar rushewar farin cikinmu ba matsayin ka na jininmu, bai dace ka kasance dalilin zubar hawayena ba Afeef, nida yaya Aliyu wanne laifi muka yi maka? Karka manta alkawari fa muka yi da kai, Afeef na roke ka da girman Allah ka tausaya mana ka sake ni._ Shuru yayi yana kallon massage din yana sake karantawa bayan ya karanta a Karon farko,sai faman jujjuya sakon yake yi acikin zuciyarsa daga karshe ya ajiye wayar ya tashi ya shiga toilet saboda gaba daya ya hada gumi wanka kawai yake bukata daidai wannan lokaci, bai ko kula da massage din nata ba bare yayi reply al'amuransa ya cigaba da yi hankali kwance, Tun bayan da yazo gari bai je family house dinba sai yau ya kuduri niyyar zuwa, blue din shadda yasaka amma bai saka hula ba, agogon azurfa ya daura a hannunshi ya fita, gidan umma ya fara shiga wato ɓangaren Abba baƙi suka gaisa babu kowa a gidan sai ita kadai, fitowa yayi ya shiga ɓangaren Ammi itama din dai sai ita kadai dan hatta Irfan baya nan haka itama Suhana shiyasa bai wani jima ba yace bari yace wurin hajiya, yana fitowa ya hango yaya Aliyu da anty Mimi da alama tare suke, shima yaya Aliyu ya gano shi lokacin da yake fitowa daga part din Abba fari shiyasa ya nufoshi a fusace, "kai.... Dama neman ka nake yi, yau babu inda zaka je sai ka sakar min mata ta" "ta ina ta zama matarka?" Afeef din ya fada yana yi masa kallon raini, "a gidan uwarka ta zama, ni zaka rainawa hankali? Dan kutumar ubanka ka sakar min mata" "to idan matarka ce menene alakata da maganar sakinta?" "ka sakar min mata dan kutumar ubanka..." "ba kutumar ubana ba sai dai naka ai uba bai fi uba ba......" wani wawan mari Aliyu ya kai masa yasa hannu ya tare, cikin zafin rai yace, "ka bar ganin ina rabuwa dakai wallahi duk abinda ka sake yimin sai na rama, Mimi kuma ba zan saketa ba zan kai ta gidana and i will have her on my bed ko kana so ko baka so....." Shake shi yaya Aliyu yayi ya fara kai masa duka shima yana ramawa daidai lokacin yaya faruk ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya fito daga cikin motarsa ko kashewa bai yi ba ya nufe su cike da mamaki, " Aliyu..... Haba ya haka? Kai Afeef sake shi, ku bari mana.... Haba Haidar ya kake fada da ƙanin ƙanin bayanka..... Afeef har nawa yake da zaka rinka kokarin fada dashi?" yaya faruk ya fada cike da mamaki, ita dai anty Mimi kuka ta saka ta shige cikin sashen hajiya da gudu, " wannan yaron ɗan iska ne bashi da mutunci faruk, da ka barni naci ubansa...." "Ka fadi duk abinda zaka fada amma daga yau ban yarda ka sake kula mata ta ba bare har ka dauko ta acikin motar ka......" "Afeef ya isa haka jeka ka tafi abin ka, kar na sake jin bakinka...." yaya faruk ya fada har lokacin shi dai yana cike da mamaki sai yanzu ya fahimci abinda watakila shine musabbabin fadan nasu ta yuyu kishi Afeef yake yi saboda Aliyu ya dauko mimi a mota shiyasa har ta kai su ga haka, " Ɗan ƙwaya..... Dama idan banda ƙwaya da neman mata ku sojoji me kuka iya..... Ka sha tana karanta maka hauka ko..... Zanyi maganin ka" Shi dai Afeef bai sake kula shi ba saboda maganar da yaya faruk yayi masa ya wuce cikin motarsa yama fasa shiga wurin hajiyan ya fita daga cikin gidan ransa a ɓace, wannan kallon da yawancin mutane ke yi musu su sojoji yana ɓata masa rai, ai a ko ina akwai ɓata gari kuma akwai mutanen kirki ba duk soja ne ke wannan harkar ba, Bayan tafiyar Afeef yaya faruk kama hannun yaya Aliyu yayi har zuwa cikin runfa, "Haba Aliyu me yasa zaka biyewa Afeef bayan ka san shi yaro ne, ai bai kamata ba a ce ka tsaya kana fada dashi sai kace wani sa'anka...... Idan akan matarsa ne ka rabu dashi kar ka sake bata lift shikenan, duk da na san yar uwarka ce amma hanyar lafiya sai abita da shekara " Shuru yaya Aliyu yayi saboda baya jin zai iya fadawa faruk gaskiyar abinda ke faruwa duk da shine abokin shawarar shi kuma babban amininshi........✍️ KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifiɗaya #lovetriangle #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 9:03 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA......! NA UMMI A'ISHA 11 ***Duk bayanin da yaya faruk ke yi masa baya fahimtar su dan gaba ɗaya hankalinsa da tunaninsa da kuma nutsuwarsa basa tare dashi he was out of his sense, baƙin ciki da wani irin radadi sune suka lullube zuciyarsa suka hana shi tuna komai a wannan hali wani abu mai nauyi ya sauka ya dirar masa akan ƙirjinsa even his breath was heavy, wai shi Afeef ya dubi tsabar idonsa yace zai tare da Mimi acikin gidansa, lallai ta tabbata wannan yaron bai shiryawa zaman lafiya ba sannan bai so a rabu lafiya ba he don't want peace, Ganin babu abinda zai fahimta ko kuma zai gane kawai yasa ya yiwa Yaya Faruk sallama ya figi motar sa ya fita, ganin ya fita yasa yaya faruk shiga ɓangaren hajiya wadda duk gidajensu guda uku babu wanda yasan abinda yake faruwa, kitso ya tarar ana yiwa hajiyan bai zauna ba ya nufi bedroom din anty Mimi dake can upstairs, tana kwance tana sharar hawaye kamar koda yaushe cikin yan kwanaki nan, "Mimi..... Tashi..." taji yaya faruk ya fada bayan ya shigo har cikin bedroom din nata, tashi zaune tayi tana sharar hawaye, "Mimi me yasa zaki rinka shiga motar Faruk da sunan lift? Yes na san dan uwa ki ne ko babu aure, amma tunda mijin ki ya nuna baya so to ina baki shawarar ki hakura da hakan, kibi umarnin mijinki....." Wasu hawaye masu ƙuna da raɗaɗi taji sun fara tsere kan kumatunta, wannan kuma wacce irin masifa ce? " Dan Allah ki kiyaye kar na sake jin wani abu ya faru makamancin haka please..... " Zubawa faruk ido kawai tayi tana hawaye bakin ciki ya hana ta magana koda yake bata da abinda zata fada daidai wannan lokaci, shiyasa har ya ƙaraci fadansa cikin nasiha ya gama ya fita bata ce uffan ba, wani tashin hankali take ji irin wanda bata taɓa jinsa ba, Afeef ya cuci rayuwar su sannan ya yaudare su, bayan fitar yaya faruk kwanciya ta koma ta sake yi tana zubar da hawaye. Baƙin cikin maganar da Afeef ya faɗawa yaya Aliyu itace ta tsaye masa a rai ya kasa zaune ya kasa tsaye kuma ya kasa ci ya kasa sha sannan bacci ya kauracewa idanuwansa, wai har shi wannan dan tatsitsin yaron zai saka a gaba yana fadawa magana any how? Ƙudurcewa yayi a ransa duk ranar da Allah ya sake hada shi da Afeef sai anyi ɓacacciya sai yayi masa mugun duka irin duka na mutuwa. Afeef gida ya koma ransa a ɓace kuma a jagwalgwale, yana shiga Irfan ya kirashi a waya kamar ba zai dauka ba amma ya daure ya dauka yana kokarin saisaita kansa, "Naje family house ban same ka ba, gashi har na dawo gida ma...." "ok shine ba zaka jirani ba?" "zan sake dawowa an jima...." Daga haka ya katse wayar yana nazari, dole ya dauki mataki akan anty Mimi da yaya Aliyu, ba zai zuba musu ido suna wulakantashi ba sun mayar dashi kamar wani soko ko kuma dolo, baya jin ƙarfin jikinsa dan kamar ciwon sa na kokarin tashi shiyasa ya wuce part din mommy ya hada coffee mai zafi tafasasshe ya sha amma duk da haka bai ji shi daidai ba, part dinshi ya koma ya hada ruwan zafi sosai sannan ya shiga cikin bahon wankan ya kwanta yana jin zafin ruwan yana ratsa kowacce kafa ta jikinsa yana gasuwa, ya jima ciki yana juyi daga bisani ya fito ya saka kaya ya zauna saboda ya dan ji dama dama, a duk lokacin da yake irin wannan ciwon nashi anty Mimi ke kulawa dashi dan wani lokacin ma can family house din yake tattarawa ya koma har sai yaji sauki sannan ya dawo gida. Bai sake fita ba sai bayan magriba lokacin ne ya tafi family house dan yana son ya samu iyayen su maza gaba ɗaya kamar yadda ya tsara cikin ransa, Yaga motar yaya faruk da ta yaya Aliyu wannan ya bashi tabbacin suna cikin gidan gaba ɗayansu, kamar koda yaushe suna zagaye da hajiya kaka yayanta da jikokinta anata hira ana raha, Da sallama a bakinsa ya shiga cikin falon nan gaba daya hankalin kowa ya dawo kansa aka fara yi masa sannu da zuwa dan da yawa basu ganshi ba tun dawowarsa sai yanzu, ya gaida kowa ya amsa banda yaya Aliyu da ko kallonsa bai yiba in banda harara da yake aika masa, kusa da Afeef yaje ya zauna suka fara gaisawa, zuwa can ya matsa kusa da kaka yace, "Hajiya ina son Magana dasu Abba...." "ya isa.... Sha lele yana son magana da iyayensa.... Lele na me ya faru?" hajiya ta fada cikin kulawa, "Hajiya akan maganar auren mu da anty Mimi ne...... So nake ayi mana tsakani da yaya Aliyu daga yau babu shi babu ita....." ai tun kafin ya rufe bakinsa Aliyu yayi kukan kura ya cakumo shi ya fara kifa masa mari nan wani fadan ya kaure a tsakanin su Irfan da yaya Faruk suka tashi suna kokarin raba su yayin da su kuma iyayen su maza kowa ya fara daka tsawa, " Kai har ka isa...... Dan kutumar ubanka nawa kake....." "innalillahi wa inna ilaihir rajiun....... Wai me yake faruwa haka? Kai Aliyu me ya hadaka dashi?" hajiya ta fada cikin tashin hankali, shi dai Daddy wato mahaifin Afeef bai ce komai ba saboda ganin yayyensa na nan wato Abba fari da Abba baƙi, wata tsawa Abba fari ya dakawa Aliyu, "Aliyu you must be very stupid, Idan na sake jin bakinka Haidar sai naci mutuncinka..... Ashe dama baka da mutunci? Kai Irfan kira min Mimi...." cikin sauri Irfan ya tashi ya haura upstairs bedroom din anty Mimi inda take kwance tun bayan da ta idar da sallar magrib, "Anty Mimi Abba yana kiran ki..... Kiyi sauri ki zo dan a fusace yake he's upset" daga haka ya juya ya fita dan yasan halin Abba idan ransa ya baci bai da sauki, "Abba gata nan zuwa...." Tun daga nesa gabanta ke faduwa tana kallonsu daya bayan daya, idonta ne ya sauka kan Afeef da ke zaune cikin fushi hancinsa duk jini wanda gashi nan har ya zuba a gaban rigar sa ya ɓata, Tsugunnawa tayi ta durkusa daga nesa dasu kadan, " Abba ina yininku?" Bai amsa gaisuwar ta ba ya juya ya kalli Afeef yace, "Afeef me kace akan mimi da Aliyu?" "Abba so nake ayi mana tsakani da yaya Aliyu daga yau babu shi babu ita, ban yarda ya sake daukar ta ko acikin motar sa ba ko ya kirata a waya, gaisuwa kadai na yarda ta hada su...." "saboda Kaine wa? Kai ka isa ka raba ni da ita? Who do you think you are?" ya Aliyu ya fada yana kokarin sake tashi faruk yana rike shi, "Aliyu baka da mutunci ko? Bance kar ka sake magana ba? To duka ku bude kunnen ku gaba daya ku jini da kyau, daga yau daga yanzu ban sake yarda irin wannan ta sake faruwa ba, kuna yan uwa ciki daya kuna fada har da dambe, ke mimi kar na sake ji ko gani ko da wasa kin shiga motar Aliyu tunda mijin ki baya so sannan ban yarda ki sake wata magana dashi ba a waya..... Idan kika sake kuma ban yafe miki ba...... Kai kuma Aliyu daga yau babu kai babu ita ban yarda in sake jin wani abu ba makamancin wannan... Afeef shine mijinta a yanzu kuma duk dokar da ya kafa dole ta bita........ " Kuka kawai anty Mimi ta fashe dashi ta tashi ta koma upstairs yayin da shi kuma yaya haidar ya cika fam ya kawo har wuya, mintuna kadan da zartar da wannan hukuncin da Abba yayi Aliyun ya tashi ya fita yana yiwa Afeef kallon zamu gamu ne, a fusace ya figi motar sa yabar gidan wanda har su Abba na jiyo kugin motar tasa, gudu kawai yake shararawa zuciyarsa na tafarfasa sai zancen zuci yake, yazo kan wani junction suka yi taho mu gama da wata babbar mota tirela, Su Abba na kokarin shiga sallar ishah aka kira wayar yaya faruk, bai fada musu abinda yake faruwa ba kawai ya shiga mota ya fita da sauri, motar haidar din tayi kwatsa kwatsa haka shima yaji raunuka sosai har an wuce dashi asibiti mafi kusa, sai bayan da suka fito daga masallaci sannan yaya faruk ya kira Abba ya sanar dashi, gaba daya gidan suka dunguma suka tafi asibiti domin duba shi inda yake emergency, duk da abinda ya faru hakan bai hana Afeef bin Irfan ba suka tafi tare, yana kwance yana ta bacci lokacin da suka je duk jikinsa raunuka amma anyi sa'a babu karaya, misalin karfe 11 na dare duk aka tattafi sai iya umma mahaifiyarsa da Janan sune zasu zauna a wurinsa. Anty Mimi tamkar zata yi hauka saboda hukuncin da taji Abba ya yanke a kanta ita da Aliyu, yanzu shikenan Afeef ya samu nasarar raba su da haidar? Wannan wacce irin mugunta ce da cuta mai girma? Kuka take kamar ranta zai fita haka ta kwana bayan gari ya waye kuma Suhana ta shigo bedroom din nata dauke da breakfast dan babu kowa agidan duk suna asibiti hatta hajiya ma ta tafi, tana kwance cikin bargo kamar marar lafiya, "Anty Mimi ina kwana? Ga breakfast dinki inji Ammi...." "Abba ya fita?" shine kawai tambayar da ta yiwa Suhana, "ehh duk sun tafi asibiti wurin yaya Aliyu...." "me ya samu yaya Aliyun?" ta fada bakinta na rawa sannan wuf ta tashi zaune tana son jin amsar da suhana zata bata, "baki san yayi accident ba jiya da daddare?" "innalillahi wa inna ilaihir rajiun......" ta fada tare da dafe kanta, cikin zuciyar ta kuma cewa take "Allah ya isa tsakanina dakai Afeef.... Allah ya isa" "nima zanje in shirya.... Ga breakfast din nan" Da kallo tabi suhana har ta wuce ta fita daga cikin bedroom din, yanzu shikenan ko duba shi ta san ba zata samu damar zuwa ba tunda ga sharadin da Abba ya gindaya mata shima kuma ta san wannan bakin cikin hukuncin na Abba ne yasa har yayi accident dinnan,wayarta ta dauka ta fara kiran number Afeef, bacci yake yi abinsa hankalinsa kwance amma yana son idan ya tashi zaije hospital ya dubo yaya Aliyun, ɗaukar wayar yayi yaga Mimi ce ke kiran sa, bai dauki kiran ba ya mayar da wayar ya ajiye yaci gaba da baccinsa har tayi kiran ta gaji, cikin bakin ciki ta ajiye wayar kafin daga bisani ta sake dauka ta kira hajiya tana dauka ta fara tambayar ta ya jikin Aliyu hajiya tace da sauki yana bacci har yanzu bai farka ba, katse wayar tayi ranta na yi mata wani irin suya. Bayan Afeef ya tashi daga bacci ya yi breakfast yayi wanka asibiti ya tafi dan kusan kowa yana can in banda su Abba da suka tafi aiki bayan sun duba shi, shima bai jima sosai ba yacewa Irfan bari yaje gida yaga anty Mimi ta kirashi dazu ta yuyu ko tana neman sa ne, tare suka tafi da suhana ya sauketa itama a gida zata ɗora girki, part din hajiya ya shiga inda anan ne anty mimin take, tana zaune bakin gado daure da jan towel ta fito daga wanka idanuwan ta jajur saboda kukan da ta sha, knocking yayi tace "come in..." saboda duk tunanin ta hajjo ce ko kuma ɗaya daga cikin hadiman gidan, har ya shiga cikin dakin bata san shi ne ba dan gaba daya tunani ya cika kwakwalwarta, tsaye yayi yana kallonta wanda ita sai da taji shurun yayi yawa sannan ta kai dubanta hanyar ƙofa nan taga ya zuba mata ido ko ƙiftawa baya yi......✍️ KAIFI ƊAYA.. ✨ What happens after “happily ever after” gets broken? 💔 After the scandal fades.💔 After the accident steals her steps.💔 After a mother whispers, “Marry another.” 💔 There’s still a man who brings tea at 2 AM. 🩷 There’s still a woman who learns to stand in new ways.😥 There’s still a love called _Kaifi Daya_ - One Blade.❤️ Sharp enough to cut through gossip. Strong enough to hold two people together. 🫂 If you believe love is not about perfection, but about presence… This book was written for you. 🤝🗣️ _KAIFI ƊAYA_ - Read it with tissue in one hand, hope in the other........🤪 Available now 07044644433 #Kaifiɗaya #lovetriangle #EmotionalRomance #AliyuHaidar #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 9:03 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA.....! NA UMMI A'ISHA 12 To my old fans, the ones that reads me years ago❤️, it's been a while since I heard from you and honestly I miss you, i miss us, am back with KAIFI ƊAYA a story of love pain and hope to heal. If u still think of me, come meet Dr Mimi & Afeef their story will touch your hearts. I need ur opinions like before, i miss chatting with you in the comment, please come back let's start again together, thank you for being with me from the beginning, I love you all. 💙 Dear Rahama, thank you for the gift you sent me yesterday, the coffee was delicious..... Tnx alot! ***Tsantsar tsanar da ta bayyana ƙarara akan fuskartace tasa ya dauke idanuwansa daga gareta ya kalli gefe, tamkar ta tashi taje ta rufe shi da duka haka take ji saboda irin bakin cikin da ya ƙunsa mata, wani irin nauyi take jin ƙirjinta da numfashinta sunyi mata, "Naga miss calls dinki any problem?" ya fada idanuwansa na kallon wani wuri, "kai wanne irin macuci ne mayaudari azzalumi maci amana? Mun shirya abu da kai rimi rimi amma daga karshe kana kokarin mayar damu kananan yara....... Soo listen and listen good, ko mazan duniya sun kare babu abinda zanyi da kai da sunan miji, tun wuri kaje ka warware abinda ka sarƙa domin wallahi tallahi bazai yi mana kyau ba gaba dayanmu.... Idan har baka warware wannan abun da ka kulla ba you will see the other side of me that even me never knew its existing...... " " wallahi tallahi Anty Mimi banyi muku haka da niyyar in saka ku cikin matsala ko fushin iyaye ko wani abu mai kama da haka ba, ni kawai nayi hakane dan in tseratar daku daga faɗawa halaka da kuma fushin ubangiji........ Na san yanzu ba zaki fahimta ba amma wata rana ina yi muku fatan ku fahimci tsantsar soyayyata da kaunata gareku, banda mugun nufi akanku Allah shine shaida, maganar yaya Aliyu kiyi hakuri ki manta dashi ki cireshi daga cikin ranki ki dauka Allah gata yayi miki shiyasa ya canja miki dani wanda idan kin karɓa da kyakkyawar niyya zai zame miki mafi alkhairi fiye da auren Aliyu....... Insha Allah zamu rayu tare har gaban abada..... " Gaba ɗaya wannan maganganun nasa jinsu take kamar yana watsa mata wuta shiyasa bata san lokacin da ta tashi daga inda take zaune ba ta nufe shi tana zuwa ta wanke shi da mari zuciyar ta kamar zata buga dan ɓacin rai, " ƙarya kake yi ni bazan taɓa rayuwa dakai ba maci amana makaryaci mayaudari.... Wanne aure ne kake maganar zai yi albarka? Auren da aka gina shi da ƙarya da yaudara da cin amana da kuma zalunci? Idan har ka san ba zaka sake niba meyasa tun farko baka fito ka fada mana ba ka nuna mana zaka yi yanda muke so? Ba zan taɓa rayuwa dakai ba idan ma wannan shine plan dinka wallahi ni nafi karfin ka...... " " Anty Mimi ki fahimceni...." Kunnuwanta ta toshe ta kurma ƙara tamkar mai aljanu babu shiri ya fita daga cikin dakin yana jiyo ihunta kamar wata karamar yarinya, yana fita daga cikin part din hajiya yaci karo da suhana tana kokarin shiga, motar shi kawai ya shiga yabar gidan ya koma asibiti wurin Irfan, Kayan kwalliyar ta dake jere reras gaban mirror taje ta fara watsi da su tana ƙara saboda tsabar bakin cikin da take ciki kenan ma bashi da niyyar rabuwa da ita ko sakinta? Shiga cikin bedroom din suhana tayi a kidime tana shiga ta rike ta, "Anty Mimi me yake faruwa? Me kike yi haka?" "suhana ba zan iya zama da wannan yaron ba..... Akan me? Saboda me?" ta karasa maganar cikin ƙara, "ya isa anty Mimi, calm down...... Yi hakuri, zo ki zauna..... Yi hakuri..... Yi shuru.... Zauna" suhana ta fada cikin lallabawa, kama hannunta tayi suka je bakin gado ta zauna tana haki, "Haba anty Mimi komai yayi zafi fa maganin sa Allah, wannan abun da kike yi kamar karamar yarinya bai dace dake ba..... Kiyi hakuri ki nutsu...." Shuru Anty Mimi tayi tana mayar da numfashi idanuwanta a runtse, ta san duk yanda zata yiwa suhana bayani ba zata fahimceta ba tunda ba wai zata fito ne fili ta sanar da ita yanda abin ya faro ko kuma ya samo asali ba, " Breakfast din da na kawo miki baki ci ba anty Mimi why?" suhana ta tambaya tana duba warmers din da ta ajiye mata tunda safe, "bana jin yunwa..... Am no hungry" "daurewa zaki yi anty please....." "zanci idan ina jin yunwa" Tashi suhana tayi ta gyara mata kan mirror dinta ta tattare wanda suka fashe ta fita. Tun daga wannan ranar bata sake saka shi cikin idanuwanta ba ko taji motsin shi duk da cewa time to time yana zuwa gidan, kwanan yaya haidar biyar a asibiti ta tambayi hajiya tana son taje ta duba shi amma hajiya tace ba zata je ba tayi masa fatan samun sauki daga gida Allah zai amsa ba sai taje ba, duk da tana son zuwa dole tana ji tana gani haka ta hakura domin bayan hanatan da hajiya tayi harda sake fadawa Abba nan shima ya hana yace koda wasa kar yaji ta je duba Aliyu idan kuma ta matsu da dole sai taje to ta kira mijinta suje tare, ta rasa yaya zata yi da bakin cikin da take dawainiya dashi cikin zuciyarta. Yaya Aliyu tunda yake kwance gadon asibiti bai san wanda ke kansa ba sai yau da ya farfaɗo har ya samu bakin magana, Umma mahaifiyar shi dake tare dashi ya kalla sai janan kanwarshi cikin bakin cikin da yake jin har ya koma ga Allah bazai bar cikin zuciyarsa ba yace da umma, "umma Mimi ta zo?" "Mimi bata zo ba Haidar amma kowa yazo ya duba ka, ka koma ka kwanta ka daina magana...." "umma Abban anty Mimi bai kyauta min ba, abinda yayi min ko bare ba zai yimin ba, ya zabi Afeef sama dani, he takes Afeefs side......." Haushi, ɓacin rai da damuwa umma ta shiga bayan Aliyu ya gama rattaba mata duk abubuwan da suka faru wanda sune suka ja har yayi wannan accident din, umma cika tayi tai fam shiyasa da daddare bayan magriba kowa yana zuwa ganin haidar ana ta murnar ya fara magana yana gane kowa da Afeef yazo umma kicin kicin tayi da fuska ta hade rai kamar bata taɓa dariya ba haka kuma da kyar ta amsa gaisuwar shi ita kuwa janan ko gaishe shi bata yi ba dan gaba daya haushinsa suke ji bama shi kadai ba har da iyayen anty Mimi da ita Mimin, ita laifin ta wai bata zo ta duba shi ba, su kuma Abba da Ammi laifinsu sun fifita Afeef akan Haidar, shi dai Afeef bai kawo komai cikin ransa ba ya juya ya fita duk da cewa Aliyun bai amsa gaisuwar shi ba, yana fita Abba ƙarami ya shigo wato Abba baƙi mahifin su Aliyu, har lokacin umma a turɓune take, "Ya mai jikin? Ya dan ci abincin kuwa?" "Au dama ka damu dashi ne? Ai na zaci kai baka damu dashi ba yanda sauran mutane suka damu da ƴayan su...." Kallonta Abba yayi cike da mamaki, "ban fahimce ki ba.... Ban gane abinda kike fada ba.... Duk me ya kawo wannan maganar?" "Ai bazaka fahimta ba dama, kowa ya nuna nasa yake so sai kaine baka son naka, kowa ya koma daga bayan ɗansa ya goyi bayansa amma kai banda kai, to idan kai baka son sa ni ina son sa saboda yanda kowanne ɗa ya tsaga jikin uwarsa ya fito nima haka ya tsaga jikina ya fito, wallahi bazan taɓa ƙin ɗana ba akan na wani.. " gaba ɗaya maganganun nan na umma ɗaurewa Abba kai suka yi saboda a iya saninsa abinda ya faru bai wani kai ya kawo ba, sannan hukuncin da ɗan uwansa ya yanke akan wannan saɓanin da su haidar suka samu yayi daidai dan ko shine irinsa zai yanke, ya san idan ya tsaya yi mata bayani ba lallai ta fahimta ba sannan nan asibiti ne bai kamata su zauna suna hayaniya ba akan marar lafiya da girman su da komai dan haka ya juya ya fita kawai ba tare da ya zauna ba, duk da ya fita din umma bata iya yin shuru ba haka ta cigaba da fadar duk abinda yazo bakinta. Washe gari kamar yadda Ammi ta saba da kanta ta shiga kitchen ta hada abinci wanda za a kai asibiti dan tunda ya kwanta kullum ita ke kai musu abinci safe rana dare sannan ana kaiwa daga bangaren hajiya kaka ma, yau harda kunun tsamiya ta yiwa Aliyu saboda shi masoyin kunun tsamiya ne, tare da suhana suka tafi Irfan ya kai su, tun shigar su cikin dakin da Aliyu yake Ammi taga kamar fuskar umma babu walwala sannan ta canja, zama tayi tana tambayar ya mai jikin umma ta amsa ciki ciki, "Allah ya bashi lafiya, ga kunun tsamiya nan da na iyo masa idan ya tashi sai ya sha..." "Ai da ma kin barshi kawai, wanda akayi a baya ma ya isa amma wannan yanzu ku koma dashi kawai mun gode...." Shuru Ammi tayi tana nazarin maganar da umma ta fada amma sai taga bai dace tayi shuru ba gara koma menene su warware shi a yanzu, "umman janan me yake faruwa? Yanzu dan na kawowa Aliyu abinci ai ba wani abu bane, ba duk ɗaya bane..." "ba ɗaya bane, ada shine ake ɗaya amma yanzu kowa nasa yake so.... Banda haka me zai saka ku amince ku yarda ku aurar da Mimi ga Afeef bayan Aliyu ne ya aureta ai ana barin halal dan kunya, sannan kun fi kowa sanin so muke mu haɗa Afeef da janan aure tun suna ƙanana, tun janan tana jaririya da aka haife ta muka kuduri niyyar aurawa Afeef, amma saboda kowa kansa ya sani kuma nasa ya sani shine kuka murde magana kuka karkatar da ita kuka bawa Afeef Mimi, idan har akwai zumunci da kaunar juna ya dace Aliyu ya saki mata Afeef ya aura? Idan har akwai kara da kunya ya dace ku bawa Afeef yar ku bayan Aliyu ne ya taɓa auren ta? Idan ma zaton ku Aliyu ne baya haihuwa shiyasa kuka dage har sai da kuka raba su kuka kashe auren yanzu kuka aurawa Afeef to ɗana lafiyar sa ƙalau kuma bashi da matsalar haihuwa dama ai maza basu cika zama juya ba sai mata ne ke zama juya..... " " Yanzu duk akan wannan umman janan kika kullace mu har kike irin wadannan maganganun a gaban yara? Ai da Aliyu da Mimi da Afeef ni duk daya ne awurina.... " " wallahi karya kike yi ba ɗaya bane, daga ke har mijinki iya kanku kuke so.... Kuma anyi walkiya " " Ammi tashi mu tafi... " suhana ta faɗa cikin dacin rai, wannan wacce irin masifa ce daga zuwan su shikenan kamar dama ana jira? " A'a suhana bari tukunna ta gama fadar duk abinda take son ta fada, ni bani na hada auren Afeef da Mimi ba nima ina zaune aka kawo min goro haka bani naje na raba auren mimi da haidar ba shine dan radin kansa ya saketa to yayi mata saki ɗai ɗai ɗai har uku ya zamuyi da su? Ai dole a hakura ta auri wani tunda ba a garin mahaukata muke ba.... " " ai shiyasa kuka aura mata kanin bayansa wanda suka fito tsatso daya saboda babu kunya bare kara.... " Tashi suhana tayi ta fice daga cikin dakin bayan ta dauki basket din dake dauke da abincin da suka zo da shi, tana fita ta hango hajiya da Afeef da ya kawota sun nufo dakin Irfan yana gefen su....✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifiɗaya #lovetriangle #EmotionalRomance #DrMimiAndAfeef *_Ummi Shatu_*👌🏻 [7/18, 9:02 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA....! NA UMMI A'ISHA 13 ***Yanda umma ke magana a zafafe cikin zafin rai shine yafi komai bawa Ammi mamaki, to ko umma ta manta irin zazzafar soyayyar dake tsakanin Haidar da Ammi ne? Itace fa ta raineshi tun daga yaye ta hada su da Faruk ta raina har suka girma suka kai minzalin aure, shi Aliyun ma sai bayan da ya girma sannan ya gane ba sune iyayen sa ba su umma ne saboda a hannun Ammi ya taso, "Wadannan maganganun da kike yi ummansu sai nake ji a raina kamar dama can akwai wani miki acikin zuciyarki ko kuma akwai wani kulli da kika ajiye...." "babu abinda na kullata acikin raina, kawai dai gani nayi lokaci yayi wanda zamu fadawa kawunanmu gaskiya tunda kowa yanzu nasa shine nasa sannan iya nasa yake so...." Suhana tana tsaye ranta idan yayi dubu a bace yake su hajiya suka ƙaraso, babu wanda ta iya buda baki ta yiwa magana tana ji suna tambayar ta har sun fito zasu tafi ne? " ku kyale ƴar jakar uba, tana ji ana yi mata magana.... " inji Hajiya ita dai Suhana bata tanka ba tana ganin su suka shiga ɗakin da yaya Aliyu yake kuma suna shiga suka ji Ammi na cewa, "maganar fa kowa Nasa yake so bata taso ba dan kece kika fahimci abin ahaka sannan kika juya shi izuwa hakan shiyasa kike kallon kamar yanzu kowa bayan nasa yake bi, ni har gobe Aliyu matsayin ɗa yake awurina, baida banbanci da yaran da na haifa dan duk ɗaya nake kallon su... " " wallahi ƙarya kike wannan maganar ba har zuciyarki ba..... Da ɗaya kike kallonsu da yayanki kamar yadda kika fada ai da baki goyi bayan a rusa rayuwar sa ba.... Auren cin amana auren ɓata zumunci " " wai me yake faruwa ne nake ta jin maganganu satata kamar saukar ruwan sama? " hajiya kaka ta bukata lokacin da ta kai tsakiyar cikin ɗakin, " hajiya sannu da zuwa, babu komai dama magana ce akan abinci da na kawowa Aliyu umman sa tace baya bukata in koma dashi, duk dai maganar akan auren Mimi ne da Afeef...... " " to me ya faru da auren Mimi da Afeef din? Aure nice nan na bada umarni aka daura shi sai akayi yaya? " " to umman janan ta dauki laifin ta dora a kaina tana ganin kamar da saka hannuna ko hadin bakina..." "ko da hadin bakinki ko babu, ko da saka hannunki ko babu aurene dai na cin amana aka yi da rashin kara...." umma ta fada cikin faɗa da matsanancin fushi, "Au haka akayi? Amanar wa aka ci?" hajiya ta fada cike da mamaki, "Hajiya..... Ammi.... Umma dan Allah abar maganar nan haka, a asibiti fa muke, muna tare da marar lafiya bai kamata a saka shi a gaba da hayaniya ba..." Irfan ya fada cike da damuwa, "hakane Irfan, muje dama tafiya za muyi...." "Dan Allah idan kun tafi ba sai kun sake dawowa ba mun gode iya haka ma" Hajiya bata ce komai ta juya ta fita nan suma su Ammi suka bita daya bayan ɗaya suka fita haba sai yanzu suka gane dalilin shurun da suka ga Suhana tayi musu lokacin da suka zo ashe itama bakin ciki ne ya fito da ita kuma ya hana ta magana. Har suka koma gida babu wanda ya iya cewa uffan akan maganar, hajiya ɓacin rai kamar me, ganinta bai kamata umma ta farfadi irin maganganun da ta fada ba ko dan ganin idonta, Suna isa gida hajiya tace da Ammi su wuce part dinta, anty Mimi tana zaune a falo tana kokarin haɗa coffee ko wai zata samu taji karfin jikinta saboda rabon ta da abinci 2 days kenan shiyasa gaba daya jikinta babu kwari, shigowarsu hajiya ya katse mata tunanin ta da take yi, "wai me ma ya sakata duk ta yiwa mutane irin wannan dibar albarkar? Akan wanne dalili? Saboda me?" hajiya ta tambayi Ammi wadda ta samu wuri ta zauna suma su Afeef duk sun zazzauna, "wallahi hajiya ban sani ba ko dama akwai wani abu acikin ranta sai Allah, nifa abinci kawai muka je mu kai musu nida suhana sannan mu duba Haidar, shikenan fa daga zuwanmu umman janan tace basa bukatar abinci mu koma dashi kuma kar a sake kai musu wai ai mun koma daga bayan ƴarmu mun ware Haidar maganganu dai iri iri ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba..... " " Kina ji? Ranar da Aliyu yayi accident faɗa suka yi da shalele, Ya daddaki Afeef akan dai wai kawai Afeef yace kar ya sake ganin ya daukar masa mata a motar sa, shine fa nan Abbansu ya yiwa tufkar hanci yace bai yarda ba kar kuma a sake, shine Aliyu ya futa cikin fushi yaje yayi wannan hatsarin, to menene abin laifi anan?" " ita tace wai ai bayan yayan mu muka koma su muke so kuma abayansu muke.... " " ki rabu da ita, kar ku sake zuwa asibitin da sunan duba Aliyu, nima ba sake zuwa zanyi ba, tunda haka take so kuma ta zaba " Anty Mimi duk tana jin abinda yake faruwa take ta sake shiga damuwa jin wata sabuwar matsalar tana kokarin kunno kai cikin family din, gaske dai Afeef ya zamar mata masifa inama tun farko Aliyu ya fahimce ta sannan ya gane hakan zata faru da duk ba akai ga haka ba da tuni hakan bata faru ba gashi nan yanzu abubuwa sai sake damalmalewa suke yi suna sake tsananta suna yin tssmari, ba za ta iya shan wannan coffee dinba duk da ta san tana da bukatar sa, barin falon tayi ba tare da ta ji karshen maganar ba, shi kansa Afeef abun ya bashi mamaki saboda bai taba zaton umma zata iya rufe ido tayi wani abu makamancin hakan ba duba da irin hadin kai da kuma kyakkyawar alakar dake tsakanin ahalin shekara da shekaru kai kusan ma tun daga tushe dan baka gane ɗan wannan da ɗan wannan saboda babu bambanci kuma kowanne ɗa yana iya zama a gidan duk wanda yake so babu mai takura masa ko karara bare nuna banbanci, ita dai Ammi tashi tayi ta koma ɓangarenta ranta duk babu dadi dan wannan shine Karon farko da irin hakan ta faru a tarihin zamansu kuma tun daga ranar bata sake komawa asibiti da sunan duba Aliyu ba kamar yadda hajiya ta bada umarni, duka iyayensu maza babu wanda ya san hakan ta faru sai Abba baƙi da yake dan zargi kan lamarin saboda shima umman ba wai kyale shi tayi ba. Bayan faruwar lamarin da kwana biyu suhana ta fito daga side dinsu da safe zata shiga side din hajiya anty Mimi na nemanta ta hango janan itama tana fitowa daga side dinsu dauke da warmers da alama girki tazo daukar musu zata koma asibiti, duk da taga janan din ta dauke kai tayi kamar bata ganta ba amma hakan bai hana ta karasawa ba inda take, "janan.... Ya jikin yaya Haidar?" "yana nan kullum yana ƙara samun lafiya, ɗan bakin ciki sai dai ya mutu....." "me kuma ya kawo maganar yan bakin ciki anan? Wa yake bakin ciki da samun lafiyar tasa?" "oho, yo abu a duhu, ai ta yuyu ba haka aka so ba a ganshi ya cigaba da rayuwa shiyasa aka yi masa turin jeka ka mutu, amma da yake ranshi da lafiya awurin Allah yake ba mutum ba gashi nan a raye...... Aikin banza" Janyo mayafinta suhana tayi saboda ganin ta juya zata tafi, "ai komai aka yi da jaki sai yaci kara, ke yanzu banda jakanta ko wani ne kika ji yana fadin haka a kanmu ai sai inda karfin ki ya kare..... Dan yaya Afeef bai aureki ba sauran maza sun kare a duniya ne?" "naji dadi da kika fahimci haka,kuma sai me dan bai aureni ba, auren da yayi auren cin amana, auren son zuciya, insha Allah wannan auren babu inda zai je....." "ehh anji anyi cin amanar, ke me ya hana ya aureki, insha Allah idan ma wannan shine fatanki da burinki auren anty Mimi da yaya Afeef mutuwa ce zata raba...." Faɗa ne ya kaure tsakanin suhana da janan a haka anty Mimi ta fito saboda ta gaji da jiranta ta same su suna cacar baki kamar zasu dambatu, ko kallonta janan bata yiba ta ja tsaki ta fice ganin ta karaso inda suke, " suhana menene haka kuma? "anty Mimi wallahi bance mata komai ba daga tambayar jikin yaya Aliyu shikenan ta hau farfada min maganganu....." "ya isa koma gida kawai, bari naje office.... Dama abu zan saki kiyi min bari kawai sai na dawo" motarta taje ta shiga ta fita daga cikin gidan ita kuma suhana ta koma wurin Ammiey. Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa acikin ciki haka ta samu kanta lokacin da take driving gaba daya hankalinta baya kan tuƙin da take yana can wata duniya daban ta tunani, ada family dinsu abin sha'awa ne sannan abin kwatance agari kuma awurin duk wani wanda ya san su amma yanzu akan wannan maganar gashi nan kawuna sun fara rarrabuwa gaba tana shirin shiga tsakani, bata san traffic lights ta tsayar da ita ba kawai sai ji tayi garammm ta bugi wata mota dake gabanta, cike da masifa da bala'i mai motar ya fito dan har danger dinshi ta baya ta fashe haka kuma wurin da ta bugeshi ya lotsa ya mokaɗe motarshi sabuwa mai kyau da tsada, "innalillahi wa inna ilaihir....... Ya salam" ta faɗa gabanta yana faduwa kuma babu shiri ta cire sit belt dinta itama ta fita, "ke makauniyar ina ce? Are you blind? Bakya gani ne ko yaya? Saboda kawai baku san zafin nema ba kuna kwance a gida an siyo muku motoci an baku shiyasa zaku fito kuna tuki na gadara da ganin dama ko?....." "Dan Allah bawan Allah kayi hakuri, ina da emergency ne da yawa zanje hospital in duba su...... Kayi hakuri ka fada min amount din da zai yi fixing motar, please am very sorry....." ta fada tana ɗaga masa ID card dinta, gani yayi da gaske din ita medical doctor ce sannan ya gamsu da bayanin da tayi shiyasa kawai ya jijjiga kai yace, " Babu komai kawai kije...." "nagode madalla, kuma ina mai sake baka hakuri akan abun da ya faru...." Komawa cikin motar ta tayi ta nufi asibitin. Days on *** Rayuwa take cikin bakin ciki da ɓacin rai da kuma damuwa, rabon da ta ga Afeef tun ranar da suka dawo daga asibiti dasu hajiya da Ammi, ko aikin ta ma yanzu kam sai a hankali dan tamkar bata san aikin nata ba yanzu dan yadda take gudanar dashi akwai damuwa acikinsa, duk patients din da take dubawa da wadanda take yiwa theater matsaloli na biyo baya kawai sa'ar da ta samu kuma Allah ya taimaketa shine ba asamu asarar rai ta silar ta ba, Yau dai da taje office kira ta samu daga sama wato hukumar dake kula da asibitin har da ƙarin baƙi da suka zo daga hukumar lafiya ta ƙasa wadanda keda alhakin kulawa da duk wani likita, lokacin da ta shiga conference hall din nasu taga dai MD na asibitin sai sauran manyan Doctors da consultants sai kuma baƙin da suka zo, "Dr a gaskiya ba zamu cigaba da zuba ido kina kokarin salwantar da rayuwar al'umma ba, ranar kin bawa wata mai ciki injection wadda bai kamata abawa pregnant women ba, a dai wannan ranar kin bawa wata mata mai diabetes wata injection wadda ba ayiwa masu wannan ciwon, kinyi theater sama da guda goma duk matsala tana biyo baya, gaskiya ba za mu cigaba da taking wannan risk din ba...... Ina ganin lokaci yayi da ya kamata ki koma gida ki kwanta ki huta ki samu isasshen bacci...... Dr we are concerned your performance has declined, patients safety is at risk" wannan shine bayanin da Chairman yayi mata bayan sauran baƙin da manyan likitoci sun gama yi mata tambayoyi masu kama da na ƙurulla, sannan sun yi doguwar tattaunawa da ita, license dinta suka karɓa da identity card dinta da coat sannan ta tashi ta fita dan bata da wata hujja wacce zata kare kanta ko kuma wani abu mai kama da haka, office dinta ta shiga ta tattara nata yanata ta fita daga cikin asibitin idanuwanta jajur duk da bata yi kuka ba, gudu take shararawa har Allah ya kaita gida lafiya, Hajiya da jikokinta suna falo ta shiga ta zauna jikinta ba ƙwari, kallo ɗaya hajiyan tayi mata ta gane bata cikin nutsuwarta, sai da hajiyan ta matsa mata da tambayar me ya faru da ta dawo yanzu bayan lokacin dawowarta bai yi ba sannan ta fada mata anyi suspending dinta a asibiti kuma an karɓe license dinta, lokacin ne ta samu damar barin hawayen da suka jima cikin zuciyarta suna tafarfasa samun damar zubowa...........✍️ KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifiɗaya #emotionalromance #lovetriangle #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 9:02 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA..! NA UMMI A'ISHA 14 ***Ba anty Mimi kadai ba hatta hajiya da Irfan da Manal da kuma suhana gaba ɗaya jikinsu yayi mugun sanyi da jin halin da anty Mimi take ciki a yanzu, Anan ta bar handbag dinta da sauran kayanta kawai ta wuce upstairs, tana shiga ta fada kan gado ta fara kukan da sautinsa ke fita, tayi kuka sosai tamkar idanuwanta zasu fice kafin ta iya hakura tayi shuru tana jan zuciya wacce tayi mata wani irin nauyi, suma su hajiya acan falo din suna cike da jimami suna ta faman jajantawa ahaka Afeef ya shigo ya same su, "Wai me yake faruwa ne naga kamar duk kunyi wani tsuru tsuru......? " Ajiyar zuciya Irfan ya sauke ya kalleshi yace "Anyi suspending din Anty Mimi a hospital sannan an kwace license dinta......" "Innalillahi..... Yaushe? Akan me?" "yau ɗinnan...... Saboda ta zama confused...... Komai bata yin sa yanda ya dace, suna da gaskiya dan za a iya samun rashe rashen rayuka saboda she's not herself a yanzu even the management board noticed she's not herself soo they are right....." "where is she?" Afeef ya tambaye shi yana kallon sa, da hannu ya nuna masa upstairs alamar tana can, babu ɓata lokaci ya tashi da sauri ya nufi bedroom dinta, knocking yayi sau biyu kafin ya murɗa handle din kofar ya shiga, har lokacin tana kwance pillow din da take kai ya jike da hawaye tana jin wani irin nauyi akan kirjinta tamkar zai fasa mata zuciya her heart was heavy and even breathing hurts the pain is too much, "anty Mimi......" jin muryarsa ya sata tashi zaune kamar an mintsineta, a hankali ya karasa gaban gadon yayi kneel down agabanta yana kallonta itama tana kallonsa cike da baƙin ciki da kuma jin haushinsa fuskarta sharkaf da hawaye, "anty Mimi am very sorry......." "what are you doing here? Are you happy now? Now that you have destroyed my life are you happy?? I love my job..... I love to consults..... I love to diagnose and prescribed........ I love to see people cured, I love seeing people live happily because of me but now i can't do it anymore because of you, ta sanadinka komai nawa ya lalace ya tabarbare..... Shikenan burinka ya cika ka raba ni da komai nawa kuma ka rusa duk wani mafarki nawa, Afeef ba zan taɓa yafe maka ba... I will never forgive you, because of you everything of mine got ruined and fell apart....." " anty Mimi dan Allah kiyi hakuri everything will be alright...... Am very sorry..." "Get out....." ta fada cikin tsawa, Hannunta yayi niyyar kamowa yaji ta sake daka masa tsawa "I said get out....." her voice shook with rage and heartbreak, Babu shiri ya tashi ya fita dan ya gane kamar yanzu bata cikin hayyacinta tana cikin tsananin fushi da bacin rai she was in extreme anger and deep sadness, falo ya koma wurin su hajiya amma kuma shima jinsa yayi ya shiga damuwa saboda gaskiyar abinda ta fada haka dinne duk ta dalilin shi ne wadannan abubuwan suke faruwa tabbas shine sila. Tun a ranar da abin ya faru labarin dakatar da itan da aka yi ya karade ko wanne lungu da saƙo na cikin asibitin sai jajanta mata ake yi yayin da masu murna kuma keyi suna cewa she deserves it shiyasa kwana tayi bata yi bacci ba dan damuwa, yanda take cikin damuwa haka shima ya samu kansa cikin damuwar shiyasa jikinsa a sanyaye ya fita daga cikin bedroom dinta lokacin da ta kore shi, falo ya koma wurin su Irfan ya samu wuri ya zauna duk ransa babu daɗi taɓashin da yaji Irfan yayi shine ya sanya ya kalleshi ba tare da yayi magana ba, "tashi muje masallaci lokacin salla ya yi....." Tashi yayi suka fita tare kuma har lokacin ya kasa magana, acikin masallacin ma duk hankalinsa ya rabu biyu rabi na can wurin anty Mimi dan haka kawai yaji yana tausaya mata wannan halin da take ciki, bayan sun idar da salla sun fito anan farfajiyar gidan suka zauna Irfan na ta hirarshi shi kadai dan shi Afeef din tamkar kurma baya uhmmm bare uhmmm uhmmm, daga karshe ma gida kawai ya tashi ya tafi duk da yaga su Abba sun fara dawowa, Bai shiga part din mommy ba kawai ya wuce nasa, tunanin anty Mimi ne fal ransa dan ya san yanzu tana can watakila har lokacin bata daina zubar da hawaye ba wanda yake jinsu suna taɓa har cikin ransa her sobs cut straight through his heart, ya san tana masifar son aikinta kamar yadda ta faɗa mishi haka tana farin ciki da zumudin taga marassa lafiya sun warke sun samu lafiya wannan kam ko shima shaida ne saboda yanda take tattalinsa take kulawa dashi a duk sa'ilin da ciwonsa ya tashi, babu abinda yake gani a wannan lokacin sai fuskarta sharkaf da hawaye wacce take ɓoye da bakin ciki da kuma fushi (deep sadness), gefe ɗaya muryar ta mai sanyi da daɗi tana yi masa yawo cikin kunnuwa sa a lokacin da take zazzaga masa masifa, Wayar shi ya ɗauka ya fara kiran layinta amma har tayi ta katse ba a dauka ba kuma dama yasan baza a ɗaga dinba duk da zai yi wahala idan tana nesa da wayar tata, wani kiran ya sake gwadawa amma bata ɗauka ba, ai ko bata fushi dashi haka bata faru ba yasan da wuya ta dauka bare kuma ga abinda ya faru, yanda bata runtsa ba shima bai wani runtsa sosai ba, washe gari bayan yayi wanka yayi breakfast ya fita asibiti ya fara biyawa zai duba yaya Haidar dan har lokacin ba a sallame shi ba kimanin sati biyu kenan, Daddy ya gani shima yana fitowa daga wurin su yaya Aliyu din, "Afeef ina zaka je?" Jin tambayar da daddy yayi masa yayi banbarakwai tunda yaya Aliyu na asibitin ai ba bukatar a tambaye shi ina zai je, "Daddy zanje duba yaya Aliyu...." "wuce ka koma...." Bai yi musu ba kuma bai ce komai ba bai tambayi dalili ba ya juya ya koma ya shiga motar sa ya fita zuwa family house yana ta tunane tunane cikin ransa na dalilin hanashi shiga duba yaya Aliyu da daddy yayi to ko yau dinma wata rigimar aka sake? Shi dai bai da amsar komai dan haka ya hakura ya shiga cikin part din hajiya, sam bai samu ganin anty Mimi ba saboda tana cikin bedroom dinta ta rufe ƙofa ɓam kamar yadda take yi idan bata gadama ba, wuni guda yayi a gidan dan sai bayan da suka yi sallar isha sannan ya tafi amma duk da haka bai ganta ba idan ya kirata a waya kuma bata ɗauka gashi tunanin ta da wani irin mikin tausayinta sun ƙi barin zuciyarsa ta huta his heart ached for her while his mind raced with worry. A gajiye kuma a kasalance ya koma gida kamar wanda yayi wani aikin ƙarfi, tunaninsa ɗaya abinci da bacci shin anty Mimi tana samun wadannan abubuwan guda biyu? Duk da dai Irfan ɗazu yace masa su Abba sun kirata sun yi mata nasiha kuma sun kwantar mata da hankali akan ta fitar da komai daga cikin ranta kar ta damu komai zai daidaita a yanzu dai ta samu ta bawa kwakwalwarta dama ta huta sosai ta yadda komai nata zai zama daidai. Kullum yake zuwa gidan kuma acan yake wuni saboda gaba daya tunaninta ya hanashi sakat bare sukuni, baya iya tuna komai sai ita haka kuma baya jin daɗin komai, amma har yanzu bai yi tozali da ita ba tsawon kwana hudu kenan, bashi kadai ba kusan kowa ma baya ganinta, yau dai tunda yaje gidan ya haura upstairs ya tsaya a kofar ɗakinta yana knocking tare da magiyar ta bude masa ƙofa, "Anty Mimi please na roƙeki da girman Allah ba dan ni ba kiyi hakuri ki bude min in ganki koda na 1 seconds ne, dan Allah ba dan ni ba, i know i mess up but am sorry..... Kiyi hakuri" Sama sama take jin sa saboda wani irin ciwon kai ne da zazzafan zazzabi suke rinjayarta, jiri yana ɗan ɗaukarta haka ta sauka daga kan gadonta tana dafa bango taje ta buɗe ƙofar, blue din riga ce a jikinta marar nauyi kanta babu ɗan kwali gaba ɗaya gashin kanta ya barbazu ya sauka kan shoulder dinta amma kallo ɗaya zaka yi mata zaka gane a galabaice take dan tayi bala'in fita hayyacinta, "me ya..... Dawo.... Da.... Kai??" yaji ta faɗa sai dai yanda tayi maganar a rarrabe shine ya sake tabbatar masa da ba ƙalau take ba, "na zo ne kawai in ganki..... Na kasa daina tunaninki acikin zuciyata...... You are always on my mind.... I didn't stop thinking about you" Baki yaga ta bude amma sai ta gagara magana kawai yaga ta dafe kanta sannan ta tafi luuuhhhh zata faɗi, cikin sauri kuma cikin zafin nama ya tarota ta faɗa jikinsa sharafff, gani yayi kamar bata numfashi cikin tashin hankali ya soma jijjigata, " Mimi...... Mimi..... Mimi...." ya fara kiran sunanta cikin ƙaraji daidai lokacin Dr jalila ta hawo upstairs din, "what's wrong with her? Me yake faruwa?" "kawai faduwa naga tayi nima ban sani ba..... Bari in dauketa a kai ta hospital..." "no ba sai ka kaita hospital ba..... Muje ciki" Cikin sauri ya dauketa zuwa cikin bedroom dinta ya ajiyeta saman gado duk ya birkice kamar ba soja ba gani yake kamar cewa za ayi ta mutu, handbag dinta yaga Dr jalilan ta bude ta ciro joter da pen ta dan yi rubutu, mika mishi tayi tace, "fita ka samo mana wannan......" cikin sauri ya karɓa ya fita jikinsa yana rawa, ai bai bi ta kan kowa ba yawuce ya fita zuwa pharmacy duk hankalinsa yana can gareta, tsoro yake ji sosai wanda bai san ko na menene ba, gani yake idan ya koma za ace masa ta rasu, Zuciyar shi na bugawa ya koma gidan bayan ya siyo abunda Dr tace masa wanda drip ne wurin guda shida manya da kanana sai allurai, lokacin da ya koma samu yayi dakin nata cike dasu hajiya da Ammi, suhana, Irfan harda yaya faruk, tana numfashi amma bata ko motsi, shi kam lokacin da ta fadi ma ai kamar numfashinta ɗaukewa yayi haka ya gani, karɓar ledar hannun shi Dr jalila tayi tace su jira su awaje babu matsala insha Allah zata samu lafiya, firfita suka yi gaba dayansu aka barta ta fara kokarin saka mata drip. Bayan wani dogon lokaci biyu Dr jalila ta fito daga cikin bedroom din, Afeef ta gani yana ta faman kaiwa da kawowa,yana ganin ta fito ya karasa wurinta, "Dr how is she?" "she feels better...... A samu dai taci abinci ko babu yawa......" "thank you....." daga haka ya shiga cikin bedroom din, da kyar ta iya ɗaga kanta ta kalleshi lokacin da ya shiga kananan kaya ne a jikinsa jeans da t shirt wanda suka yi mutukar karɓarshi, gefen gadon ya ƙarasa ya zauna har jikinsa na haduwa da nata, hannunta ya kamo ta fincike da dan guntun karfin da take dauke dashi, "sannu..... Ya jikin naki?" Banza yaji tayi masa, a hankali ya kai hannunsa saman goshinta wanda yake zafi ɗau, hannun nashi ta ture, yana kokarin yin magana yaji knocking daga bakin ƙofa, bada izni yayi cewar a shigo nan suhana da Irfan suka shigo harda hajiya tana biye dasu, " sannu yajiki?" gaba daya suka tambayeta, "da sauki..... Abinci dai za a kawo mata taci...." ya fada yana kallonta tare da kai hannunsa kan nata ya hada ya riƙe, "ni bana jin yunwa...." ta fada tana kawar da kanta gefe fuskar ta a daure, "anty rabon ki da abinci fa tun kafin abin nan ya faru.... Please ki daure kici wani abu" jin abinda suhana ta fada yasa hajiya fadin "zo muje ki kawo mata abinci.... Ai dole taci abinci, haka zata yi ta zama da nufinta?" Fita suka yi gaba ɗaya suka bar ta da iya Afeef kadai, fuskar ta ya zubawa ido yana ta kallo kamar yau ne ya fara ganin ta wanda tana jin hakan a jikinta...........✍🏻 KAIFI ƊAYA.. ✨ What happens after “happily ever after” gets broken? 💔 After the scandal fades.💔 After the accident steals her steps.💔 After a mother whispers, “Marry another.” 💔 There’s still a man who brings tea at 2 AM. 🩷 There’s still a woman who learns to stand in new ways.😥 There’s still a love called _Kaifi Daya_ - One Blade.❤️ Sharp enough to cut through gossip. Strong enough to hold two people together. 🫂 If you believe love is not about perfection, but about presence… This book was written for you. 🤝🗣️ _KAIFI ƊAYA_ - Read it with tissue in one hand, hope in the other........🤪 It's available now 07044644433 #Kaifiɗaya #lovetriangle #emotionalromance #DrMimiAndAfeef _*Ummi Shatu*_👌🏻 [7/18, 9:02 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 _A story of scandal, sacrifice and a love that refused to break, a love that says am still here._ KAIFI ƊAYA...! NA UMMI A'ISHA 15 ***Wani irin baƙon yanayi yake ji a game da ita wanda bai taɓa jin irinsa akan wani ba sai ita kaɗai, na farko jin ta yake tana yawo cikin jinin jikinsa tamkar rayuwar su na manne da juna wuri guda, na biyu kuma wani irin abu mai girma yake ji game da ita shi ba tausayi ba sannan kuma shi ba tsoro ba to menene wannan abun? Shine tambayar da yake ta faman yiwa zuciyarsa amma ya kasa gane ko menene saboda kowanne seconds da awanni jin abun yake yana sake girma, hannunta yaji ta fincike daga cikin nasa har tana kokarin fama ɗaya hannun dake ɗauke da cannula, "yi a hankali....." ya fada yana sake bude idanuwansa a kanta, babu abinda yake tunawa sai irin yanda ta sandare masa ɗazu ta faɗi a jikinsa shi kansa yasan ba dan yana cikin firgici da tsoro ba ai da an samu matsala, fuskarshi ɗauke da murmushi ya zuba mata ido yana kallonta yayin da ita kuma ta kawar da kanta tare da juya masa baya, wani knocking din ya sake jiyo ana yi nan ya tashi yaje ya bude, suhana ya gani dauke da farfesun kayan ciki da kuma tea acikin dan madaidaicin mug, "yawwa thank you...." ya fada bayan ya karbi farfesun da tea din, juyawa tayi ta fita shi kuma ya karasa bakin gadon anty Mimi ya zauna, "tashi ki sha tea din gashi an kawo...." "ni bana jin yunwa...." "ko bakya jin yunwa ki dan daure ki sha kici wannan farfesun zaki ji dama dama please ..." "na ƙoshi...." "to zan jiraki har zuwa lokacin da zaki ji yunwa sai kici koda kuwa hakan na nufin zan kwana ne anan...." Kallon sa tayi fuskarta a turbune nan ta ga yana kokarin ajiye tea din da farfesun,yunƙurawa tayi ta tashi zaune ta mika masa hannu alamar ya bata nan ya mika mata ta karɓa ta fara shan tea din tana cin farfesun duk da ba wani dadinsa take jiba dan gaba daya bata da apatite ma, ido ya zuba mata yana kallonta ko kiftawa baya yi kamar wanda yau ne ya fara ganin ta, sai da taji tana kokarin yin amai sannan ta barshi ta mika masa ta sake komawa ta kwanta, jin ana kiran sallar la'asar ya sa shi tashi ya fita zuwa masallaci ana idar da salla ya sake komawa bedroom din nata, a hanya suka yi arba da Ammi wacce itama ta fito daga wurin anty Mimin, a iya saninsa babu wata kunya ko surukanta tsakanin shi da Ammi amma sai ya ji yana dan jin nauyinta yau, har ƙasa ya durkusa ya gaisheta ta amsa cikin kulawa sannan ta wuce shi kuma ya tashi ya shiga wurin anty Mimi wacce ya tarar tana bacci suhana kuma tana gyara mata bedroom din wanda harma ta gama ta kunna turaren wuta dakin ya fara gaurayewa da kamshi mai dadi na turaren bakhoor, fita tayi ta barshi yana tsaye yana kallon anty Mimin bayan fitar suhana ya karasa gefenta ya zauna, hannunta da idan ya kama take ta faman fusgewa tana ture shi yanzun ma hannun ya kama ya riƙe cikin nasa yana murzawa a hankali bayan ya dan hada jikinsa da bayanta kaɗan hannun nata laushi tamkar na jaririn da yazo duniya yanzu fatarsa bata jima tana shan iska ba, duk tayi wani buzu buzu da ita kamar wacce ta shekara tana jinya,wayar shi ya ciro daga aljihu ya saka a silent saboda kar akira shi karar wayar ta tada ita daga wannan daddadan baccin da take yi dan Allah kadai yasan yaushe rabonta da samun bacci, yana nan zaune a gefenta bai matsa ba har sai bayan da aka kira sallar magriba sannan ya tashi ya fita ita kam har lokacin baccin ta take yi ba kakkautawa. Sun fito daga masallaci shida Irfan yaga kamar su Abba da daddynsu harda yaya faruk zasu je duba anty Mimi, bai bisu ba wuri ya samu ya zauna wurin hajiya har sai da suka fito suna maganar basu samu dubata ba ma saboda sun tarar da ita tana bacci sannan ya faki idonsu ya sulale ya koma cikin dakin, Inda ya mayar mazauninsa wato gefenta nan yaje ya zauna yanzu dinma ya kama hannunta yana wasa da yan yatsunta, bai san dalili ba haka kuma bai san me yasa ba kawai ya samu kanshi da kissing hannun nata sannan goshinta, ita dai bata san me yake yiba dan wani mugun bacci mai nauyin gaske take yi, sallar isha ce ta sake tayar dashi bayan sun fito ya zauna suka yi dinner da su hajiya da sauran iyayensu maza kamar yadda suka saba, shi dai kam yau baya jin zai bar part din hajiya shiyasa bayan kowa ya baje an watse ya shige bedroom din anty Mimi harda saka key ya rufe ƙofa, kan gadon ya hau ya kwanta kusa da ita yaja duvet ya rufe musu rabin jikinsu ya zaro wayar shi a aljihun wandon jeans din da yake jikinsa, ɗan short video yayi mata ita kadai sannan yayi musu tare tana ta bacci bata san abinda yake yi ba, text massage ya turawa mommy cewar zai kwana a family house wurin Irfan, ya san ba zata ce komai ba dan dama ya saba kwana tun suna yara wani lokacin sai yafi 1 month idan ta raya masa, latse latsen shi yake ta yi a waya har kusan 12 lokacin ne ya ajiye wayar kan bedside drawer dinta ya kwanta bayan ya shige jikinta sosai. Bayan asubah ya farka nan ya ganta har lokacin bata farka ba, shifa baccin nan nata fa kuma ya fara bashi tsoro, bacci tun jiya da safe wuni guda, awa nawa tana bacci, Allah Allah ya rinka yi a idar da salla ya koma ya tashe ta, Irfan na ta son ya zauna a masallacin saboda akwai ƴar takaitacciyar nasiha da ake yi kullum amma yaƙi yace zai rinka jiyowa daga dakin anty Mimi, Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya shiga cikin bedroom din sakamakon ganinta da yayi a zaune kan gadon fuskar ta duk ta kumbura da idanuwanta duk tana jinsu sunyi mata nauyi, da kallo ta bishi har ya karasa shiga cikin dakin ya zuba gwiwowinsa a ƙasa ya dafa gadon yana kallonta, "sannu..... Ya jikin?" "Bani ruwa insha..... Mai sanyi" yaji ta fada ba tare da ta amsa sannun nashi ba, tashi yayi ya fita downstairs ya dauko mata bottle water mai sanyi ya koma, bude mata yayi ya mika mata ta karɓa yana kallonta bata ajiye robar ba sai bayan da ta shanye ruwan tas, komawa tayi ta kwanta ta juya masa baya mintuna kadan wani baccin ya sake kwasheta, zama yayi gefenta ya zuba mata ido a hankali ya kai hannunshi goshinta ya ɗora idanuwansa na kanta ko ƙiftawa baya yi, Tun bayan da ya dawo daga masallaci bai matsa ko nan da can ba har 10 ta ɗan gota a lokacinne yan dubiya suka fara shigowa suna duba ta kuma hayaniyarsu ce ma ta tashe ta daga baccin da take yi, da kanta ta cire cannula din dake hannunta dan ta dameta sannan ta takura mata, breakfast suhana ta kawo musu amma tace a bari sai ta fara yin wanka sannan zata ci, jin hakan da ta faɗa ya sanya kowa dake cikin bedroom din fita, shima Afeef bin Irfan yayi suka fita zuwa part din Irfan, wanka yayi ya saka farar jallabiya sannan ya koma dan yasan yanzu kam ta gama shiryawa, knocking yayi sau ɗaya kuma bai zauna zaman jiran a bashi izni ba ya tura kansa cikin dakin, tana zaune gefen gado daure da towel da cup a hannunta tana shan tea, "ya jikin naki?" ya tambaya yana kallonta kamar yau ne ya fara ganin ta,shuru yaji babu amsa nan ta cigaba da shan tea dinta har ta sha rabin cup din sannan ta ajiye ta tashi a hankali ta wuce gaban closet ta ɗauki doguwar riga ta shan iska ta saka bayan ta feshe jikinta da turare, komawa kan gadon tayi ta zauna fuskar ta duk a cunkushe, tea din da yaga ta rage ya dauka ya fara sha yana ta faman aikin kallonta, kwanciya yaga ta sake yi ta dan lulluba da duvet duk da ba bacci zata yi ba, Zaman kurame suka cigaba da yi har Ammi ta zo, kallon Afeef Ammi tayi bayan sun gaisa tace, "Afeef ai ya kamata kaje gida ka huta kaima, ka samu kayi bacci...." "A'a Ammi babu komai.... Bana jin bacci, I don't want to leave her side...." "duk da haka ko baka jin bacci kana bukatar hutu, tun jiya kake zaune anan kuma daga ganin idanuwan nan naka baka samu isasshen bacci ba da daddare, kaje gida ka huta......" "to Ammi bari naje zuwa azahar sai na dawo...." "A'a azahar ai baka wani huta ba, kaje zuwa dare sai ka dawo, zan turo suhana ta zauna tare da ita kafin ka dawo..... Kana bukatar hutu kaima kaji...." "to Ammi..... Bari naje, Allah ya bata lafiya" "amin, Allah yayi maka albarka" Tashi yayi ya fita, duk abinda yake faruwa anty Mimi tana jin su, bayan ya fita Ammi ta zauna tana kallonta, "wannan yaron yana ta faman kokari a kanki..... Tunda kika kwanta yake dawainiya dake baci ba sha..... Ubangiji Allah ya saka masa da alheri, hakika wani hanin ga Allah baiwa ne" tana jin Ammi har tayi ta gama dai bata tanka ba, so take ta tambayi jikin yaya Aliyu amma ta rasa wa zata tambaya, so take taji har yanzu bai samu lafiya bane ko yaji sauki? Ta san bata isa ta tambayi Ammi ba ko hajiya shiyasa ta ja bakin ta tayi shuru amma kuma tana son sanin halin da yake ciki. Koda Afeef ya koma gida kamar yadda Ammi ta saka shi every 30 minutes yake kiran Irfan yaji ya jikin anty Mimi, bayan sallar la'asar video call ya kirashi yace yaje bedroom dinta yana son ya ganta, tashi Irfan yayi daga kusa da hajiya ya nufi upstairs wurin anty Mimi, kai gaskiya Afeef fa kamar ya shiga da yawa dan abubuwan da yake yi sun zarta hankali, tana kwance tana baccin dai kamar jiya yau ma din ta wuni tana bacci ne, kallonta yake yi ta cikin wayar tashi, "hankalinka ya kwanta yanzu?" Irfan ya fada cikin tsokana, "ba sosai ba, me yasa zaku barta ita daya?" "ba ita daya bace wallahi ita da suhana ne na jiyo motsin ta acikin toilet...." "ok tom sai na zo, anjima nima zan shigo, bana son in saɓa umarnin Ammi ne" Magriba nayi ya tafi shida Manal, yanzun ma jallabiya ce a jikinsa amma baƙa ta ciki yasa wando jeans, niyyar shi yau ma ya kwana wurinta amma tunda ya shiga dakin shida Msnal yaga tana ta faman ɓaɓɓata rai iya Manal kadai ta amsawa shi kuma tayi banza dashi, fita yayi zuwa masallaci saboda lokacin salla ya yi, bai koma wurinta ba sai bayan sallar isha bayan su abba sun gama zaman majalissun su, tare da daddy Manal suka tafi shi kuma ya zauna kuma a lokacinne ma yake jin labarin yaya Aliyu yaji sauki dan yanzu daga wurinsa yaya faruk ya dawo. Daren yau kam bata jin bacci ko kadan, lokacin da Afeef yaje bedroom din jinsa yayi ta garkame kayan ta da key nan yayita knocking amma taki budewa, "sauki ya samu kenan...." ya fada cikin ransa tare da juyawa ya koma wurin Irfan, kallonsa Irfan yayi amma sai bai ce komai ba saboda yanzu wasu abubuwan da suka shafi anty Mimi da shi babu bukatar ya rinka tsoma bakin sa sai dai ya zuba ido kawai dan sun fi kusa............✍🏻 KAIFI ƊAYA... ✨ *When the world called her “useless”… he called her “mine.”*💘 _KAIFI ƊAYA_ is not just a love story. It’s the story of Mimi - a doctor whose name was dragged through scandal, whose body was broken by fate… 💔 And Afeef - the man who chose to stay when everyone told him to leave. 😥 They won the fight against the world. But can they win the fight for each other, when silence is louder than lies, and love is tested by things neither of them chose? 🥺 *One blade. One choice. One love that refuses to break.*❤️ _Kaifi Daya_ - because true love doesn’t walk away when you can’t walk anymore..😥 It's available now 07044644433 Your heart will not be the same after the last page🥰✍🏻✍🏻 #Kaifiɗaya #emotionalromance #lovetriangle #AliyuHaidar #DrMimiAndAfeef *_Ummi Shatu_*👌🏻 [7/18, 9:02 AM] Oum Jasrah: https://www.arewapen.com/book?id=6a50f2f571e75baab6622006 KAIFI ƊAYA....! NA UMMI A'ISHA 16 ***Kamar zai yi kuka saboda bata barshi ya kasance acikin dakin ba, haka kuma baccinshi sama sama yayi domin kowanne bugun zuciyarshi tunaninta ne gaba daya ya kasa gane wanne irin yanayine wannan ya samu kansa and it's not just pity anymore its turning into something deeper, ita kam anty Mimi tana can cike da tunani kala kala hakika wannan sharadin da Abba ya saka mata tsakaninta da Aliyu yayi mata tsauri da yawa tunda ko babu komai ɗan uwanta ne bai kamata a raba su har haka ba, tashi tayi ta lallaba ta fita zuwa wurin hajiya wacce har ta kwanta amma dai ba bacci take yiba, "hajiya wurinki na zo.... Dan Allah wata alfarma nake nema, ki taimaka min ki rokar min Abba akan ya sassauta min wannan sharadin da ya saka, wallahi yayi tsauri da yawa, ai ko babu komai yaya Aliyu dan uwana ne tayaya za ace ko gaisawa baza muyi ba? Naji na yarda bayan gaisuwa babu abinda zai kara hadani dashi amma a bani dama in duba shi ko ta waya ne dan Allah hajiya " "Kinga ki kiyaye ni da maganar duba Aliyu dinnan fa, yadda uwarsa take tashen rashin mutunci yanzu wallahi komai zai iya faruwa tom...." "ni babu ruwana da Umma iya yaya Aliyu nace...." "shikenan na baki dama kiyi masa ya jiki, zuwa gobe da safe shikuma Alhaji ƙarami zanyi masa bayanin komai..." "yawwa hajiya nagode...." Ai sai taji har taji kwarin jikinta, da sauri ta koma bedroom dinta ta zauna ta dauki wayarta ta fara neman layin yaya Aliyu, babu kowa cikin dakin sai shi kadai dan umma ta fita saboda suna sa ran za a basu sallama zuwa gobe, "Mimi..... Mimi ashe dama zan sake ganin kiranki cikin wayata?" "yaya Aliyu kayi hakuri ka san ba laifina bane ai, babu yanda zanyi ne.... Abba ya hanani magana da kai bare ganinka...... Ina cikin tsaka mai wuya....." "Mimi nafi ki shiga masifa..... Iyayen mu basu duba mana ba, Afeef baiyi mana halacci ba bare adalci...... Yaci amanar mu kuma ya ha'incemu, dan Allah mimi kar ki bari yayi nasara a kanmu, kar ki bari yaci galaba akan ki, don't let him win, wallahi yanzu duk duniya bani da makiyin da ya wuce wannan yaron, na tsane shi kuma na tsani koda sunansa ne bare ganinsa i hate him with passion.." "ka kwantar da hankalinka yaya Aliyu, insha Allah sai inda karfina ya kare, ba zan taɓa yin rayuwa dashi ba matsayin miji, yanda kake jin ka tsane shi to ni ina jin tsanar shi fiye da haka, ya zalunce ni ya cuceni ya rabani da kai sannan ya rabani da aiki na, anyi suspending dina an kwace license dina duk saboda shi..... Gaba daya ya gama rusa rayuwa ta...." "kika ce anyi suspending dinki an kwace license dinki? Saboda me? Yaushe?" Labarin abubuwan da suka faru gaba daya ta fara zayyane masa daidai lokacin umma ta shigo, "Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba insha Allah everything will be alright..... I will talk to you tomorrow morning....." katse wayar yayi yana kallon umma wacce tun shigowarta ta tsaya ta kafe shi da ido tana kallonsa, "umma me ya faru ne?" "kai Meyasa baka da zuciya ne Haidar? Me yasa baka kishin kanka? Yarinyar da ubanta ya gama wulakanta ka uwarta ta gama tozarta ka ita kanta ta nuna bata san da kai ba yanzu kuma me zata fada maka? To daga yanzu babu kai babu ita, tunda sun guje ka sun zaba mata wani sun aura mata ka bar su suje alhaki kwikwiyo ne.... " Shuru yayi cikin ransa yana cewa ai inaah bazai taɓa iya rabuwa da mimi ba dan ba ya jin zai iya rayuwa babu ita he can't do without her, itama anty Mimi bayan sun gama wayar wani sabon sonsa take ji acikin ranta, ko bata fada ba ta san bazata taɓa rabuwa da kwayar sonshi dake cikin zuciyarta kullum tana sake kara yaɗo da rassa da girma ba. Ita dai anty Mimi bayan sun kammala wayar shuru tayi tana jin wani sanyi har cikin ranta sakamakon muryar yaya Aliyu da taji, tana yi masa wani irin sone wanda bata san yanda zata misalta ko kwatanta shi ba, wani irin farin ciki take ji cikin ranta tun bayan da taji muryar tasa, tana rungume da wayarta a chest dinta ta kwanta lamo taji karar shigowar massage, a hankali ta cire wayar daga kirjinta ta bude massage din, Afeef ne taga ya turo mata da, "Mimi me yaya jikin naki? How do you feel now? Allah ya baki lafiya.... I miss you...... Sleep well...." Tsaki tayi tana jin wani irin haushinsa cikin ranta, ta ajiye wayar a zuciye, jin karar shigowar wani sakon yasata sake tunzura saboda duk tunaninta shi dinne sai dai tana dubawa taga yaya Aliyu ne, cikin jin dadi fuskarta dauke da murmushi ta karanta massage din tare da yi masa reply. Kasa bacci Afeef yayi yana ta kallon Irfan da sai baccinsa yake yi cikin kwanciyar hankali babu abinda yake damunsa sabanin shi da tunanin anty Mimi ke kokarin zautar dashi ko kuma fitar dashi daga cikin hayyacinsa, ganin da yayi mata daga ita sai towel lokacin da ya shiga bedroom dinta yana kokarin haukatar dashi gaskiya anty Mimi kyakkyawa ce ta bugawa a jarida ko kuma mujalla, fatar jikinta kadai wani irin kyalli take tare da daukar ido ga laushi da santsi, lumshe idanuwansa yayi tare da lasar lebensa na ƙasa dan babu abinda yake bukatar gani ko kuma yake so a daidai wannan lokacin sai ya ganta gashi ga ita koda kuwa ita din ba zata kula shi ba, text massage ya tura mata duk da ya san zai yi wahala ta kula shi amma dai ba zai iya daurewa ba dole sai ya tura mata, bayan ya tura mata video din da yayi mata ranar da ya kwana a bedroom dinta ya fara gani yana ta maimaitawa kamar wanda ke son haddacewa ahaka har bacci ya dauke shi. Kwana yayi cur yana mafarkinta shiyasa washe gari ya tashi cike da farin ciki da wani irin zumudin son ganinta, yayin da ita kuma ta kwana da tunanin Aliyu acikin ranta da hanyar da zasu bi su koma ma'aurata su cigaba da rayuwar su hankali kwance. Bayan yayi wanka ya shirya bai saurari Irfan ba ya fita zuwa part din Hajiya kaka wacce ke karyawa tana yi sai faman mita take na yau ba abata abincin karyawa da wuri ba bayan ita kuma ba zata iya wannan horon yunwar ba, sanye yake da farar t shirt sai bakin jeans yana ta faman zuba kamshi, "Hajiya anty Mimi ta tashi?..." yace da hajiya bayan sun gaisa, Wani kallo hajiya tayi masa kafin tace "bana son munafurci lele.... Da ni kake tambaya idan ta tashi, ko wuri daya muka kwana da ita?" "yi hakuri kawai tambaya ce..." "to ban sani ba tunda ni dai ban ganta ba...." "to bari naje na duba da kaina" "da dai ya fi maka" Tashi yayi ya nufi upstairs inda anty Mimi ke zaune da laptop a gabanta gefe daya kuma glass cup ne ajiye dauke da coffee aciki, knocking yayi sau ɗaya daga haka ya bude kofar ya shiga bai jira ta bashi izni ba, kamshin turarensa da taji ne yasa ta ɗago manyan idanuwanta ta kalleshi, "sannu ya jikin?..... Kin samu sauki ko akwai sauran abinda yake damunki?" Wani mugun kallo ta yi masa kafin ta gyara zamanta ta kalleshi cikin takaici tace, "Afeef wai me kake so dani ne?" Ɗan jim yayi saboda bai fahimci maganar tata ba, idanuwanshi yayi kokarin sakawa cikin nata amma sai ta kawar da kanta gefe tana sake daure fuska, "Anty Mimi wallahi babu abinda nake nufinki dashi sai alkhairi....... Kawai dai abinda na sani yanzu shine ina jin wani abu mai girma a tattare dake wanda ban san menene ba......" "Afeef ka dai san ni ba sa'ar aurenka bace......" "Anty Mimi abinda nake ji a game da ke yafi karfin tunanina sannan bazai bani damar hango age gap din dake tsakanin mu ba...... Ina ji a raina da zuciyata ba zan iya rabuwa dake ba" ya fada cikin wani irin yanayi wanda ta kasa fassara shi, "Afeef aurena da kai bazai ɗore ba, dole zamu rabu koda kuwa hakan zai kawo karshen zumuncin dake tsakaninmu....." "Insha Allah babu abinda zai rabani dake sai mutuwa....." ya fada yana lumshe idanuwansa bayan ya hadiye wani irin yawu, Gani yayi ta matso kusa dashi sosai har numfashinsu na haduwa suna gwaruwa da juna, rigar baccine a jikinta light pink mai santsi mai gajeren hannu da botira gaban rigar, botiran dake gaban rigar tata yaga ta fara budewa zuciyarta na tafarfasa, "Na san abinda ke ranka bai wuce son ka hada shimfida dani ba.... Ai abinda kake so kenan ko ka ɗandani zumata kamar yadda ka taɓa faɗa..... Tunda so kake ka sanni matsayin ƴa mace bismillah...... Let's have sex sai hankalinka ya kwanta ka sakeni....." tana gama faɗa yaga tana kokarin zame rigar daga jikinta dan har ta kammala bude botiran gaba daya.............. Hmmmmm...... I'm stopping here, the free pages are over, soo what will happen next? Will Afeef divorce anty Mimi? Will the secret come out? Will yaya Aliyu give up and let them live in peace? Will the secret they buried remain a secret or will it come out for everyone to hear? All of these are in the continuation of the story, Mimis heart is broken...... And Aliyu he's not done yet..... Someone is about to pay, someone is about to break someone is about to confess.... The secret is about to explore...... What comes next will shake you, divorce? Secrets? War with the parents? The continuation of the story is waiting for you, Don't get left behind 👇👇👇 Pay via 7044644433,Moniepoint micro finance bank, send your evidence of payment to 07044644433. 1000 Naira only *_Ummi Shatu_*👌🏻