Jamila Tanko: KAI KA FI CANCANTA... Na Jamila Umar Tanko (JUT) Bayan tsawon lokaci da b'atansa an samo shi kuma an rubuta shi a zamanance. Domin yara da su ka taso yanzu ba su san shi ba da kuma wadanda suka karanta a baya da dadewa sun manta. Part 1,2 & 3 PAGE: 1️⃣ La'asar sakaliya garin Kano ya yi sanyi, ga yanayi irin na farkon shigowar damuna. Iska mai sanyi ta na kad'awa tana fifita duk wani mai rai da ke cikin wannan garin. Babu abinda za ka dinga hangowa sai korayen ganyen dake kadawa, tufafin jamaa yana kadawa, don haka jama'ar da ke giftawa su na tafe cikin nishadi ba tare da gajiya ko wahalar tafiya ba. Alhaji Bakura matashin mutum ne dan kimanin shekaru arba'in cif-cif. Wanda ke tafe cikin tsaliliyar motarsa qirar INFINITI EX 32 SUV. Mai launin ruwan toka (silver), kasancewar sanyin iskar da ke kadawa tafi sanyin A.C motarsa dadi sai ya kashe ya bude gilasan wanduna, ya na tafe iska na kada shi. Nan da nan ya tsinci kansa cikin nishadi, kallo daya za ka yi' masa annurin fuskarsa ya tabbatar maka da hakan. Dadin dadawa ma kid'a da wakar D'an kwairon da ke tashi a hankali daga cikin rediyon motarsa ya k'ara masa nishadi. Mace duk kawaicinta da kunyarta idan ta kalli Bakura sai ta sake kallonsa saboda mutum ne kyakykyawan gaske mai kyawun fasali, Allah Ya tsara halittarsa a jikin Bakura. Dogo ne sosai mai bakar fata lallausa mai shek'in kyau, gashi da dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, bakinsa madaidaici mai k'unshe da wasu kyawawan hak'ora masu matukar haske har da wasu siraran wushiryoyi a sama da k'asan hakoran, yana da bak'in dadashi wanda ya kara fito da tsananin farin hakoran. Duk da kyawun da Rabbul samawati Yayi masa sai Ya yi shi mutum mai tsananin tsafta da son kwalliya hakan ya sake fitar masa da kyawawan suffarsa a fili. Kwalliya ba ta tafiya daidai Idan babu kudin da za'a sayi kayan kwalliyar, amma Bakura yayi sa'a Allah Ya hada masa dukka. Ya bashi arziki mai yawa don a yanzu haka shahararran dan kasurwa ne a cikin k'asar nan har ma da kasashen k'etare baya ga dinbin ilimin qur'ani da na boko da Allah Ya bashi. Domin mahaddacin kur' ani ne, a bangaren boko kuwa Masters gare shi a bangaren Engineering. Kallo daya za ka yiwa yadin dake jikin Bakura ka tabbatar da tsadarsa saboda kwanciyar da yayi luf a jikinsa don laushi, yadin mai launin ruwan madara(cream) sai ya saka bakar hula da bakin takalmi tsadaddu. Kamshin turaren jikinsa kuwa duk ta inda ya gifta fiye da minti talatin kamshin baya barin wajen. Bakura dan mutanen Maiduguri kana ganinsa ka ga Kanuri kasancewar anyi masa tsage irin na barebari fashin goshi da tsage bibbiyu a kuncinsa, amma sai idan ka k'ura masa ido sosai sannan za ka iya tantancewa akwai tsaga a fuskarsa domin zanen bai fito rangadadai ba. Mutum ne mai yawan fara'a da son zolaya idan ya ga dama, amma fa wasu lokutan akwai tsare gida, idan ya b'ata rai babu mai iya sa shi dariya. Dokoki ya gindayawa iyalansa da duk wasu da suke zaune a qarqashinsa kala-kala a, kuma dole su bi idan su na son su zauna da shi lafiya. Mutum ne wanda baya son raini, baya son rashin tarbiyya da rashin kamun kai. Baya son sakaci da addini. Hatta yadda ake yin magana ya koyawa yaransa da matarsa, yadda za su dinga fitar da sautin maganarsu a nutse ba'a baragada ba. Idan ka shiga gidansa za ka tabbatar akwai tarbiyya domin qarami ya na girmama na gaba da shi duk qanqantar shekarun da ke tsakaninsu. Gashi d'an boko komai a tsare yake an rubuta a time table kamar lokacin tashi daga barci, lokacin sallah, lokacin cin abinci, lokacin makarantar boko da islamiyya, lokacin kallon talabijin ko hira, lokacin da yara za su dinga fita farfajiyar gidan da kekuna su zazzagaya. Haka lokacin fita wuraran shaqatawa ma an ware kamar Zoo, shopping a super markets, cinema da dai sauransu. Idan aka yi dogon hutu kuma an rubuta qasar da za' ayi visa su dunguma su tafi har da wasu daga cikin masu aiki. Tsanani irin na Bakura ba akan iyalinsa kad'ai ya tsaya ba, abun ya shafi 'ya'yan makwabtansa ma. Za ka ga yaran makwabta sun ga mahaifinsu ba su razana sun daina fitinar da suke yi ba, amma su na ganin Bakura za su nutsu dan tsoro da kwarjini hade da girmamawa da suke yi masa. Domin shi halinsa ko wucewa ya zo yi ya ga yara su na rashin da'a zai dawo baya ya kira yaron yayi masa fada, idan ta kama da murde kunne ya murde, idan kuma ya ga ya san mahaifin yaron ko yarinyar lallai kuwa zai yi sallama a gidan ya fad'awa mahaifinsa cewar ga fitinar da d'anka yake yi a waje don haka a kula a saka ido. Duk da wadannan tsauraran matakai da ra'ayi nasa bai sa jama' ar unguwa da iyalansa sun tsane shi ba saboda Allah Ya gani tsakani da Shi ya ke duk abinda ya yake yi ba dan ganin ido ba ne, dan haka Allah Ya zamar masa jagora, Ya bashi farin jini a wajen iyayen yara da kwarjini a idon yaran gari. Haka kuma a zamani irin wannan da wuya ka sami mutum mai arzikin da yake taimakon jama'ar gari da daukar nauyin iyalinsa irin Bakura. Mutum ne mai matukar kyauta da kyautatawa. A kullum kuma a koda yaushe bayarwa yake dare da rana mikawa yake, saboda haka ubangiji Ya ke sake buda masa. *** *** *** Akan Titin Lamido cresent ya ke tafiya da zummar zai tafi masallacin Sheik Aminuddin don daukar karatun yamma da na bayan magruba kamar yadda ya saba zuwa duk ranar jumaa da ranar asabar. Tafiya yake yana bin waqa wacce baitocinta ke burge shi saboda an zuba hikima da habaici da zambo. Kamar daga sama ya ga wata budurwa ta tsallako ba tare da ta duba titi kafin ta tsallako ba. Saura qiris ya buge ta sai da ya yi da gaske sannan ya iya taka burki gami da yin sauri ya dauke kan motar, saura kadan ya afka cikin kwalbatin da ke gefen hanyar. Irin qaran da burkin ya yi, hayaqi da warin taya kai ka ce gagarumin hadari aka yi Allah Ya sa babu mota a bayansa. Ya jima a zaune a cikin mota zuciyarsa na bugawa ba tare da ya san abinda zai yi ba kuma amma ya ji dadi matuqa da ya ga yarinyar a tsaye ba ta fadi ba dan haka ya tabbatar bai taba ta ba. Ya ci gaba da yiwa Allah godiya a bayyane. Abin mamaki yarinyar ba ta firgita ba ko kadan ta juyo ta dube shi a fusace ta harare shi ta yi tsaki ta ce " ka je a koya maka tuqi, banza kawai." Ta tsallaka da sauri ta ci gaba da tafiya har tuntube take yi, kallo daya za ka yi ma ta ka tabbatar a gigice take. Daga nan ya tabbatar abinda ya biyo ta ya fi kadewar mota firgici. Ya ji kalamanta tamkar a mafarki yadda yarinya qarama 'yar cikinsa ta tsaya ta zage shi bayan laifinta ne ma.Ya ji zafin zagin nan sosai, ya tabbatar ba ta da tarbiyya. Amma bai gama yanke hukunci gaba daya ba don ta burge shi kasancewar sanye take da dogon hijabi tun daga kanta har idon sawun kafarta, ya na yi mata kyakykywan zaton ba rashin tarbiyya ba ne firgicine kawai ya sa ta zage shi. Ya bi ta da kallo ya na mamakin irin sauri da ta ke yi. Tana tafe tana ta waiwaye-waiwaye kamar marar gaskiya har. Ya ji a jikinsa in bai bi bayan yarinyar nan ya bincike ta ba bai yiwa kansa adalci ba. Ya juya kan motarsa da sauri ya fara bin ta a hankali. Wani lungu ta shige, tun kafin ta shiga ya hango ta yaye burgujejen hijabin nan da yake burge shi ta cusa a leda, sai ga mace cikin matsatstsun kaya ta bayyana. Babu jimawa ta fito sanye da riga da wando da wata 'yar jaka da takalmi mai tsini, wani dan yalolon gyale ne ta yafa akanta ana hango gashin kanta gara ma ace babu gyalen. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi daga nan ya fara jin sanyin zagin da ta yi masa tunda ya tabbatar ba mutuniyar kirki ba ce, za ta yi abin da ya fi haka ma. Ya yi sauri ya d'aga gilasan motar dan kada ta gane shi. Tagumi ya yi kawai yana kallonta nan da nan ya fita daga cikin hayyacinsa ganin halin da yarinyar nan ta shiga, yayi matukar tayar masa da hankali. Yarinyar ta dubi motar Bakura duba sosai don ta gani ko akwai mutum a ciki ya na kallonta ko kuwa parking kawai a kayi ba kowa. Amma ta kasa gane inuwar mutum kasancewar ba farin gilashi ba ne ya na da dan duhu, na ciki na ganin na waje na waje baya ganin na ciki . Sai hankalinta ya kwanta ta wuce ta na rangwada ta nufi wajen wata farar mota kirar AUDI A4 4dr dake can gefe guda a ajiye. Babu alama mutum a ciki kasancewar gilashin motar bakikirin ne.Ta tsaya a jikin motar a daidai wundon direba ta na kwankwasawa, fiye da mintuna biyar ba'a bude ba, sai daga baya aka bude kofar motar. Sai ga wani dogon saurayi wankan tarwada mai dogon hanci gami da dara-daran idanuwa, ya bayyana, ya fito ya tsaya a gabnta. Hakika saurayin ya hadu yana da kyau wanda duk wata mace za ta so shi a matsayin saurayinta, sai dai kyawun d'an miciji ne idan ka zauna da shi za ka san bashi da tarbiyya gara ma ka zauna da kumurcin miciji akan ka zauna da mai irin halayensa. Sanye yake da bakin wando jeans da farar riga matsatstsiya 'yar qarama mai dan qaramin hannu, fuskarsa cike da wani kwabcecen gilas baqi qirin. Takalmin qafarsa kuwa wani danqareran kambas ne tattaura mai launin fari da baqi irin na samarin zamani, wanda idan aka jefe ka da shi ko aka taka ka da shi ka tabbatar gadon asibiti zai yi bakuncinka. Yatsun hannayensa dukka goma zobbuna ne rangada rangada. Askin kansa kuwa kai kace shataletalan titi ne (round about) da rassan titina guda hudu gabas da yamma kudu da arewa, wanda duk ta inda aka bullo za'a hadu a tsakiya. Bakura ya na zaune a cikin motarsa ta mudubin saman gilashin gaba ya na hango bayansa ya na dubanşu tsaf cike da takaici ya rasa da lilian da ya sa zuciyar ta ke bugawa dan fargaba da b'acin rai. KAI KA FI CANCANTA 1 0️⃣2️⃣ Gabansa sai faduwa yake yi tamkar, 'yarsa ce ta fad'a hannun tantirin niga irin wannan. Sai dai kaşh sun yi masa nisa ba zai iya jiyo abinda suke cewa ba. Ya yi zuruf ya fito daga cikin motar ya rufe, sai ya yi tamkar sabgar gabansa yake yi kamar bai san abinda suke yi ba, ya na tafiya ya na wayencewa kamar bai san da su ba amma wajensu ya tunkara. Bai yi wahalar qarasawa inda suke ba ya fara jiyo abinda suke fada tar a kunnuwansa. Sai kuwa ya ci sa'a akwai wani qaramin masallaci da famfo a wajen. Ya qarasa wajen famfon ya bude ya dinga kurbar ruwa yana wanke fuskarsa, ya kasa kunnuwansa sai ya ji yana jiyo komai ba tare da sun gane su yake saurara ba. Sunan daya ta ambata shi ne Abdul majid shi kuma ya ambaci sunanta Sajida. Abdulmajid ya ce da Sajida 'ni ba bawanki ba ne, kuma ba direbanki ba ne da zan yi miki waya fiye da awa daya sai yanzu ki ka fito. Daga an yi magana sai ki ce Baba da Umma ne suka hana ni fitowa. Ai babbar matsalar iyaye 'yan gargajiya kenan komai sai ace addini kuma addinin na su duk kame-kame ne, sun hana yaransu shakatawa a banza. Wallahi ba dan Allah Ya jarrabe ni da sonki ba da tuni na rabu da ke, tun sanda tsohonki ya hana ni zuwa qofar gidanku, har yanzu ina jin zafi da quna irin wulakancin da tsohon nan ya shuka min a gaban mutane har yanzu bai bar zuciyata ba. Ke ana son a wayar dake a kwatar miki 'yancinki amma kin k'i yarda, kin zauna ki na bin dokar 'yan gidanku gidadawa. Wai ku ustazai, malamai kuma almajirai." Babu abinda Sajida take yi sai karkarwar jiki, babu furucin da yake fita daga bakinta sai " Abdul majid kayi hakuri, dan Allah dan Annabi ka yi hakuri." Abdul majid ya yi mata wani kallo na wulakanci ya zare bakin glashin dake fuskarsa ya tabe baki. Ya ce "ki na nufin da wadannan kayan na jikinki za ki bi ni party? Ki na nufin da dogon wando da gyale zan shiga dake wajen hadadden party da hadaddun abokaina? Ke bakauyiya ce har yanzu kin kasa wayewa." Sajida ta dubi jikinta sama da kasa ta rasa illar dake tattare da ita. Wandon jeans ne hadadde kuma matsatstse shine ma ya siyo mata daga America, haka itama rigar a matse take. Tunanin da take yi ya katse ya ce "dole in kai ki wani kanti in siya miki kaya, mini skirt za'a saka iya cinya da zurmukeken takalmi mai tsini irin mai zif din nan har gwaiwa da riga shimi iya kirji wacce ba ta rufe cibiya ba, kuma babu ke ba zancen dankwali, kin ci sa'a ma ki na da gashi ba sai an qara miki ba." Sajida ta zabura ta dubi Abdul Majid cike da fargaba ta ce "riga iya kirji?" Ya daka mata tsawa ya ce "to meye, ki na nufin ba za ki iya sawa ba ne?" Tsoransa take, sonsa ta ke don haka ba ta iya yi masa musu. Ta ce "zan saka mana." Ta dubi agogon dake daure a hannunta daga dukkan alamu ta qagu ta koma gida don kada a nemeta. Wannan karon ma tsawa ya daka mata mai firgitar da wanda ke kusa da su, ba ma wacce aka yiwa ba. Nan da nan jikinta ya hau karkarwa. Ya ce "duba agogon me kike yi, ko yau ma an baki lokacin da za ki komą gida ne?" Sajida ta na karkarwa ta ce "a'a ba duba agogo nake yi ba, yi hakuri." Ya ce "to zagaya ki shiga mota mu tafi." Sand'a ta ke kamar wacce kwai ya fashe ma ta a ciki, saboda ba ta son shiga motar amma tsoransa ta ke ta kasa ce masa ba za ta je ba. Bakura ya dago da sauri zuciyarsa tamkar ta fashe, tashin hankali ya rufto masa lallai kuwa zai shiga wani mummunan hali idan har ya bari yaron nan ya fita da yarinyar nan ya je ya ba'ta mata rayuwa ba tare da sanin iyayenta ba. Tabbas abin zai dad'e bai fita daga cikin zuciyarsa ba zai ga kamar ya ci amanar musulumci da iyayenta da ita kanta. "Tabbas yaron nan ya na niyyar ruguza tarbiyyar da iyayenta yarinyar nan su ka dade su na gina mata." Ya fada a ransa. Sai ya ji wani hawaye mai zafi ya surnanu masa, yaransa ne kawai su ka fad'o ma sa a rai, gaba d'aya ya ji ya shiga zargi anya kuwa shima ba ci gaban mai haqar rijiya ya ke yi ba kuwa, kullum haqa ya ke amma ya na qara yin qasa. Anya kuwa ba tufka ya ke yi wani ya na warware masa a waje ba kuwa? Ya tuna hadisin da Manzon Annabi (S.A.W) ya koyar damu ce wa "idan ka ga ana aikata 6arna to ka hana da hannunka, idan ba za ka iya ba to ka gyara da bakinka, idan ba halin haka to ka qi abin a zuciyarka wannan shine mafi raunin imani." Nan da nan ya ji a ransa zai iya zuwa ya hana da baki tunda bashi da ikon gyarawa da hannu. Ya zabura zai je wajensu kenan don ya ba ta shawara da baki ya ce kada ta bi shi. Sai ya ji Abdul Majid ya ce da ita "da fatan kin fad'a a gida cewar kwanaki biyu za ki yi ko?" Gabanta ya fadi 'rass' ta dafe kirji ta tambaya cikin firgici "kwana biyu?" Ya yi mata tsawa ya ce "toh meye abin fargabar, ban isa da ke ba ne? A Abuja Nicon Hotel za'a yi casun kuma sai qarfe d'aya na dare za'a fara dan haka daga nan ma Abuja za mu wuce. Sajida ta zagayo da sauri in da yake ta tsugunna a gabansa ta fashe da kuka ta ce "Abdul majid ka taimake ni, ka rufa min asiri kada ka yi fushi da ni. Da ka san ta yadda aka yi na fito yanzu ma da sai ka tausaya min. Sai da na yi dubara da magiya Babana ya bari na fito da zummar zan je gidan su Asiya kawata in karbi qur'ani. Mintina talatin ya ba ni kasancewar gidan babu nisa ya na gida ya na jirana. My dear, idan na bi ka Abuja har kwana biyu kashe ni ne kawai ba za' a yi a gidanmu ba, ka rufa min asiri. Ina sonka Abdul Majid fiye da yadda na ke son rayuwata."KAI KA FI CANCANTA 1 JUT Jamila umar tanko 0️⃣2️⃣ Gabansa sai faduwa yake yi tamkar, 'yarsa ce ta fad'a hannun tantirin niga irin wannan. Sai dai kaşh sun yi masa nisa ba zai iya jiyo abinda suke cewa ba. Ya yi zuruf ya fito daga cikin motar ya rufe, sai ya yi tamkar sabgar gabansa yake yi kamar bai san abinda suke yi ba, ya na tafiya ya na wayencewa kamar bai san da su ba amma wajensu ya tunkara. Bai yi wahalar qarasawa inda suke ba ya fara jiyo abinda suke fada tar a kunnuwansa. Sai kuwa ya ci sa'a akwai wani qaramin masallaci da famfo a wajen. Ya qarasa wajen famfon ya bude ya dinga kurbar ruwa yana wanke fuskarsa, ya kasa kunnuwansa sai ya ji yana jiyo komai ba tare da sun gane su yake saurara ba. Sunan daya ta ambata shi ne Abdul majid shi kuma ya ambaci sunanta Sajida. Abdulmajid ya ce da Sajida 'ni ba bawanki ba ne, kuma ba direbanki ba ne da zan yi miki waya fiye da awa daya sai yanzu ki ka fito. Daga an yi magana sai ki ce Baba da Umma ne suka hana ni fitowa. Ai babbar matsalar iyaye 'yan gargajiya kenan komai sai ace addini kuma addinin na su duk kame-kame ne, sun hana yaransu shakatawa a banza. Wallahi ba dan Allah Ya jarrabe ni da sonki ba da tuni na rabu da ke, tun sanda tsohonki ya hana ni zuwa qofar gidanku, har yanzu ina jin zafi da quna irin wulakancin da tsohon nan ya shuka min a gaban mutane har yanzu bai bar zuciyata ba. Ke ana son a wayar dake a kwatar miki 'yancinki amma kin k'i yarda, kin zauna ki na bin dokar 'yan gidanku gidadawa. Wai ku ustazai, malamai kuma almajirai." Babu abinda Sajida take yi sai karkarwar jiki, babu furucin da yake fita daga bakinta sai " Abdul majid kayi hakuri, dan Allah dan Annabi ka yi hakuri." Abdul majid ya yi mata wani kallo na wulakanci ya zare bakin glashin dake fuskarsa ya tabe baki. Ya ce "ki na nufin da wadannan kayan na jikinki za ki bi ni party? Ki na nufin da dogon wando da gyale zan shiga dake wajen hadadden party da hadaddun abokaina? Ke bakauyiya ce har yanzu kin kasa wayewa." Sajida ta dubi jikinta sama da kasa ta rasa illar dake tattare da ita. Wandon jeans ne hadadde kuma matsatstse shine ma ya siyo mata daga America, haka itama rigar a matse take. Tunanin da take yi ya katse ya ce "dole in kai ki wani kanti in siya miki kaya, mini skirt za'a saka iya cinya da zurmukeken takalmi mai tsini irin mai zif din nan har gwaiwa da riga shimi iya kirji wacce ba ta rufe cibiya ba, kuma babu ke ba zancen dankwali, kin ci sa'a ma ki na da gashi ba sai an qara miki ba." Sajida ta zabura ta dubi Abdul Majid cike da fargaba ta ce "riga iya kirji?" Ya daka mata tsawa ya ce "to meye, ki na nufin ba za ki iya sawa ba ne?" Tsoransa take, sonsa ta ke don haka ba ta iya yi masa musu. Ta ce "zan saka mana." Ta dubi agogon dake daure a hannunta daga dukkan alamu ta qagu ta koma gida don kada a nemeta. Wannan karon ma tsawa ya daka mata mai firgitar da wanda ke kusa da su, ba ma wacce aka yiwa ba. Nan da nan jikinta ya hau karkarwa. Ya ce "duba agogon me kike yi, ko yau ma an baki lokacin da za ki komą gida ne?" Sajida ta na karkarwa ta ce "a'a ba duba agogo nake yi ba, yi hakuri." Ya ce "to zagaya ki shiga mota mu tafi." Sand'a ta ke kamar wacce kwai ya fashe ma ta a ciki, saboda ba ta son shiga motar amma tsoransa ta ke ta kasa ce masa ba za ta je ba. Bakura ya dago da sauri zuciyarsa tamkar ta fashe, tashin hankali ya rufto masa lallai kuwa zai shiga wani mummunan hali idan har ya bari yaron nan ya fita da yarinyar nan ya je ya ba'ta mata rayuwa ba tare da sanin iyayenta ba. Tabbas abin zai dad'e bai fita daga cikin zuciyarsa ba zai ga kamar ya ci amanar musulumci da iyayenta da ita kanta. "Tabbas yaron nan ya na niyyar ruguza tarbiyyar da iyayenta yarinyar nan su ka dade su na gina mata." Ya fada a ransa. Sai ya ji wani hawaye mai zafi ya surnanu masa, yaransa ne kawai su ka fad'o ma sa a rai, gaba d'aya ya ji ya shiga zargi anya kuwa shima ba ci gaban mai haqar rijiya ya ke yi ba kuwa, kullum haqa ya ke amma ya na qara yin qasa. Anya kuwa ba tufka ya ke yi wani ya na warware masa a waje ba kuwa? Ya tuna hadisin da Manzon Annabi (S.A.W) ya koyar damu ce wa "idan ka ga ana aikata 6arna to ka hana da hannunka, idan ba za ka iya ba to ka gyara da bakinka, idan ba halin haka to ka qi abin a zuciyarka wannan shine mafi raunin imani." Nan da nan ya ji a ransa zai iya zuwa ya hana da baki tunda bashi da ikon gyarawa da hannu. Ya zabura zai je wajensu kenan don ya ba ta shawara da baki ya ce kada ta bi shi. Sai ya ji Abdul Majid ya ce da ita "da fatan kin fad'a a gida cewar kwanaki biyu za ki yi ko?" Gabanta ya fadi 'rass' ta dafe kirji ta tambaya cikin firgici "kwana biyu?" Ya yi mata tsawa ya ce "toh meye abin fargabar, ban isa da ke ba ne? A Abuja Nicon Hotel za'a yi casun kuma sai qarfe d'aya na dare za'a fara dan haka daga nan ma Abuja za mu wuce. Sajida ta zagayo da sauri in da yake ta tsugunna a gabansa ta fashe da kuka ta ce "Abdul majid ka taimake ni, ka rufa min asiri kada ka yi fushi da ni. Da ka san ta yadda aka yi na fito yanzu ma da sai ka tausaya min. Sai da na yi dubara da magiya Babana ya bari na fito da zummar zan je gidan su Asiya kawata in karbi qur'ani. Mintina talatin ya ba ni kasancewar gidan babu nisa ya na gida ya na jirana. My dear, idan na bi ka Abuja har kwana biyu kashe ni ne kawai ba za' a yi a gidanmu ba, ka rufa min asiri. Ina sonka Abdul Majid fiye da yadda na ke son rayuwata."Kai ka fi cancanta 1 Na Jamila umar Tanko (JUT) 0️⃣3️⃣ Abdul Majid ya dakatar da ita da hannnun ya katse ta. Ya ce "ba na bukatar bada hakurinki, ai na fad'a miki a baya hakurin da na yi ya isa nan gaba ba zan sake ba. Kin manta alkawarin da kika daukar min har na yarda na sake dawowa muka shirya? Ban taba gayyatarki fita kin yarda kin bi ni ba, sai kin kawo min ba'adi da qa'bali, rawawul Baba rawawul Umma. Kar ki manta na ce miki na gaji na daina zuwa wajenki, ki ka lallaba ni na dawo a bisa sharadin kin yarda ko a ina ake party za ki bi ni shine yanzu ki ke duban kwayar idanuwana kike fada min Babanki ya na jiranki a gida? Ma'ana dai ba za ki bi ni ba ko? To shikenan daga yau ba za ki sake ganina ba, kada ki kira ni a waya. Baby kina da kyau, ke kalar shiga taro ce amma ki na kwabsawa da yawa iyayenki sun tauye rayuwarki dan haka sai anjima." Ya juya ya shiga zai shiga motarsa ta na tsugunne ta na magiya. Idanunta kamar za su fita dan kuka, hawaye su na zuba ratatata. Ta yunkura ta rike kofar motarsa ta na bashi hakuri. A fusace ya daga qafa ya cije baki zai mangare ta da tafkeken takalmin qafarsa. Sai ta yi tsalle gefe bai same ta ba, ya shiga motarsa ya fisga da qarfi gami da qure sautin kid'a kamar zai tashi kunnuwan wanda ke wajen. Bakura ya durkusa' a gaban fanfo ya na ajiyar zuciyar dad'i, domin sanda Sajida ta yi kamar za ta shiga motar sai da numfashinsa ya fara cikewa baya dirawa huhunsa saboda tashin hankali. Da Allah Ya sa ba ta bi shi ba ya ji dadi, kuma ya godewa Allah. Ya kunna famfo ya na wanke fuskarsa ya na satar kallon Sajida wacce ta zo ta wuce ta bayansa ta na sharcar hawaye. Ta yi wuf ta fada lungun nan ta zurmuqa hijabinta ta fito tsaf a kamilarta, ta na tafe tana kwararar da hawaye. A rude take tamkar wacce aka yi mata aitken cewa uwarta ta mutu ko kuma tamkar wacce aka sace d'anta ta yi duban duniya ta rasa shi. Ta dauko wayarta ta na ta gwada kiran Abdul majid sai ta fara ringing sai ya katse daga qarshe ma ya kashe wayar gaba daya. Kukan da Sajida ke sharba sai ya qaru, tashin hankali ya qaru sai taji ta tsaní kowa a duniya babu kuma kyautar da za'ayi mata ta ji dadi idan ba Abdul majid dinta aka kawo ma ta ba. Bakura ya tura hula qeya ya nad'e hannayen rigarsa kamar wani dan garuwa ya biyo ta a baya da sauri, ya na isa gare ta sai ya rafka ma ta sallama. Ta ki daga ido ta dube shi sai da gefen ido ta dan waiwaya sannan ta dauke kai ta ci gaba da tafiyarta ta na sharbar kuka. Bakura ya sake biyo ta ya na yi mata sallama, Sajida ta ki sauraransa balle ta amsa. Ya ce " 'yan mata kukan me kike yi ne?" Wannan karon a fusace ta dago da jajayen idanuwanta a cike da hawaye. Cikin tsawa ta 'ce "dalla malam ka rabu da ni, ni ba sa'arka ba ce, kowacce kwarya da abokin burminta, haka kuma kwarya ta bi kwarya idan ta bi akushi ba za ta moru ba. Ka je ka samu sa' arka, ballagaza marar aji irinka." Sai a yanzu Bakura ya kalli fuskarta tangararai, ya ji gabansa ya yanke ya fadi ras, kan kace kwabo ya gigice ya fita hayyacinsa, mamaki, d'imuwa, rikirkicewa da d'aurewar kai suka rufto masa. Kallo daya za ka yi masa ka gane haka, babu kalmar da Bakura ya ke fada sai "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji' una. Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai. Allah mai iko, Allah mai halittar bayinsa. Yarinya wacece ke? Su waye iyayenki?" Sajida ta yi masa kama da Zuhuriyyarsa. Ikon Allah ta yaya hakan ta faru? Saboda dimuwa sai ya durqushe ya dafe kai yana jujjuyawa. Sajida ta ga alamar tabin hankali a tattara da wannan mutumin sai ta ci gaba da tafiyarta. Ya miqe a guje ya sake biyo ta ya na yi mata dan kira. Ta tsaya cak ta kalle shi ido cikin ido cikin tsiwa da futsara ta ce " kai dabba in baka da tunani zan tuna maka, na fada maka ni ba ajinka ba ce ka rabu da ni." Ta juya za ta tafi, a fusace ya fisgi hijabin ya juyo da ita ta fuskanci shi ya na magana cikin fusata. Ya ce "Na haifi kamar ki 'yata tana a gida amma kike kallon idanuwana kike zagina dan baki da kunya. Ga dan iska can mayaudari ya tafi yanzu, ya na zaginki ki na lallaba shi.Sai ni kika raina saboda ni kamili ne na yi shiga ta kamala da manyan kaya. Ni ne abin wulakanci a wajenki ko? To ni shawara zan baki kiyi hankali da samarin zamani, ki daina ha'intar iyayenki su na yi miki tarbiyya ki na biýewa wani qato ya na rusa musu." Tsananin tsanar Bakura ta cusu a zuciyar Sajida sai hawayen takaici ya kece mata. Ya ci gaba da cewa "har ki na ce min kwarya ta bi kwarya idan ta bi akushi ba za ta moru ba, ke ba ajina ba ce don haka kowacce kwarya da abokiyar burminta. Shin kin san kwayar da ki ke kira kuwa? Kwarya ai kala-kala ce kwaryar dake tunb'ele a tsakar gida ana rigar tsakuwar shinkafa ko gero da ita, ana bakace, ana zuba tuwon dumame, wacce ake d'orawa gardawan maza a kai su kai gero ko masara surfe da niqa kasuwa. Ko kuwa kwarya ta gari wacce aka rataye a ragaya, aka sakale a daki, mata su na kwalliya da ita, ba'a bari a sauko da ita qasa balle a damqeta ta yi datti? Duk wata kwarya ta gari ta na ragaya asirinta a rufe. kwarya marar kyau ce a tsakar gida in anso a kifa, in an so a bude, idan anga dama a fasa ko kuma a kada ayi kida da ita kowa ya jiyo sautinta ayi rawa. Dan haka ke kwaryar tsakar gida ce waçce take tangaririya a gari. Ke kwaryar kida ce wacce kike barin wani d'a namiji ba mijinki ba ya jiyo muryarki. Duk wata 'ya mace ta gari ta na qunshe a gidansu ba ta bin maza su na yi mata wulakanci domin mace daraja ce da ita har tafi lu'ulu'u idan ta kama kanta, to ita ce nake kwatanta ta da Kwarya ta gari tana ragaya. Ado ake yi da ita ba a wanke-wanke a cikinta." A fusace Sajida ta dube shi duba na tsana don ba ta taba tsanar wani bil-adamama a duniya yadda ta tsani Bakura ba. Hawaye ya sake kwararowa daga idanuwanta. Ta ce "yarka da ka ce ka haifa kamar ni ita ce wulakantacceyar kwaryar nan da ka suffanta." Bakura ya tsinci kansa yana murmushi maimakon ya yi fushi kasancewarsa mutum ne mai yawan fushi, baya son raini daga mutumin daya bawa kwana d'aya ma ba shekara daya ba balle kuma 'yar cikinsa daya haifa. Ya ce "idan zan dauki kwaryata in mutunta, in adana ta a ragaya, in saqale ta k'i zama, in sake saqalewa a sama ta k'i zama to lallai ta zama kwaryar tsakar gida mai garari. 'Ya ta da kike magana kuwa a tunanina kwarya ta gari ce wacce na sakale ta a ragaya bata fita tsakar gida tayi garari, kamar yadda a tunanin iyayenki sun dauki Kwaryarsu mai kyau sun saqale a ragaya basu san tana ballewa ba ta fita tayi gararinta ta dawo ta d'ane ragaya tayi luf. Don haka had'uwata dake naga abinda yake faruwa yasa ni dole in koma gida in zauna inyi gadin wannan kwaryar dana sakale don karta sauko ta fice ta yi ta garari a gari." Sajida ta qurawa Bakura ido ta na dubansa dubu irin na tsana da takaici sai wani d'aci ta ke ji a ranta na bacin rai, ji take tamkar ta d'aga hannu ta dora masa mari sai dai tana shakkar aikata haka kasancewar taga shima a tsaye yake ya fita fitsara. Tunda ta ke a rayuwarta bata taba haduwa da mutumin daya cusguna mata irin Bakura. Ta fada cikin kuka da takaici."Na tsane ka." Ta juya ta ci gaba da tafiya. Bakura bai bita ba sai ya dawo jikin motarsa ya jingina yana kallon Sajida. Zuciyarsa cike da tsananin mamaki da son yaga shin su waye mahaifan Sajida, ya aka yi ta yi kama da Zuhuriyyarsa? Maganarsu, kallonsu, harararsu, kukansu, kirar jikinsu,. hannayensasu, kafafuwansu. Babu yadda za'ayi mutum da mutum ba dangantaka ayi irin wannan kamar sak, dole sai anga ta inda suka bambanta. Ganin Sajida da yayi sai ta tuno masa da Zuhuriyyarsa. Ya fashe da kuka shi kadai kuma ya lallashi kansa ya goge hawayen ya yi zunbur ya shiga motarsa don kada Sajida ta b'ace masa domin ta fara yin nisan da ya daina hango ta sosai. Sai yake ta bin ta a baya, Idan yayi tafiya kad'an sai ya tsaya har sai da yaga gidan da ta shiga, ba tare da Sajida ta san ya na biye da ita ba. Ya qarasa qofar gidan ya kashe mota ya fito ya qarewa gidan da unguwar kallo ya tabbatar Sajida 'yar talakawa ce liqis kuma daga dukkan alamu 'yar malamai ce domin daga ka doso zauren gidan allunan almajirai ne cike a zauren kuma kowacce kusurwar bangon zauren kundun kur' ani ne a sassakale. Ga almajirai nan reras su na shige da fice a cikin gidan. Shi dai burinsa yadda zai yi ya ga mahaifan Sajida ba makawa su na da alaqa da Zuhuriyyarsa. To amma ya san Zuhuriyya, ya san duk wani d'an uwanta, kakaf dangin Zuhuriyya babu ko daya a Kano gaba daya suna qauyensu Cinkilawa. Amma yaya aka yi Sajida ta yi kama da Zuhuriyya? Tambayar da ya ke yi a ransa kenan. Ya jingina a jikin motarsa kamar wani gunki zancen zuciyarsa har ya fara fitowa fili. Maganar wani yaro ce ta katse shi ya ce "d'anwake za'a kawo maka ko kunun kanwa?" Bakura ya yi firgigit. ya dubi yaron ya maimaita abunda yaron fada "dan wake, kunun kanwa?" Bakura ya yi minti biyu ya na tunanin menene ma dan wake, yaya ma kunun kanwa yake? Yaron ya sake cewa "yanzu akaKai ka fi cancanta 1 Na JUT 0️⃣4️⃣ Bakura ya yi murmushi ya cewa yaron "yaya sunanka?" Yaron ya ce "sunana Yahuza." Sai Bakura ya ciro Naira dari biyar ya miqawa Yahuza. Ya ce "je ka ka sayi kunu kasha sadaka, sauran ka bawa almajirai 'yan uwanka." Yahuza ya karba cike da murna ya na godiya. Ya ce "ai gidanmu ne ni ba sai na saya ba sai dai in b'oye in yi dinkin sallah." Bakura ya zabura ya ce "gidanku daya Sajida kenan?" Yahuza ya ce "yayata ce uwa daya, uba daya." Sai Bakura ya yi turus, ya dubi Yahuza ya ga shi kamarsa daban, Sajida kamar ta daban. Ya fada a ransa "to lallai kama ce kawai amma ba had'in Sajida da Zuhuriyya." Bakura ya yi shiru can ya sake tunano fuskar Sajida ya taluna ta Zuhuriyya ya tabbatar sak kamarsu daya, sai ya girgiza kai. Ya ce a ransa "ruwa baya tsami banza dole da wani boyayyen al' amari a nan." Yahuza ya katse Bakura daga tunanin da yake yi, ya ce ga Babanmu nan ma ya fito." Bakura ya dago da sauri ya dubi kofar gidansu Sajida sai ga wani tsoho a tsaye dauke da tafkekiyar dorina a hannunsa ta dukan almajirai. Daga ganin fuskarsa ba wasa, tsoho ne wanda baya son wargi. Yahuza ya dubi Bakura ya ce "karka fada masa ka bani kudi dukana zai yi, zai ce ni na roqe ka, ya hana mu karbar kudi a hannun baqi." Bakura ya yi murmushi ya ce "ba zan fada masa ba Yahuza." Baban Yahuza ya kwalla masa kira, ya amsa ya tafi da sauri wajen mahaifinsa. Mahaifin Yahuza yą dube shi cikin bacin rai da rashin sakin fuska, ya gyara dorinarsa tsaf tafka kawai yake so ya fara yi. Ya ce "ka san shi ne da za ka je ka naniqe masa, ko kiranka ya yi? Ba na hana ka zuwa wajen baqi kana yi musu surutun banza ba?" Bakura ya qaraso da sauri ya ce "Baba ka da ka dake shi ba laifinsa ba ne, ni na kira shi na tambaye shi." Baba ya dan saki fuskarsa ya cewa Yahuza "wuce gida." Yahuza ya arta gida da gudu, dan har ya saddakar yau sai ya sha duka. Baba tsoho har yanzu fuskarsa babu walwala ya dubi Bakura ya ce "yaro ina ka ke tambaya ne?" Bakura ya ce "mahaifan Sajida na ke nema" Wannan tambayar ta bawa Baba tsoho mamaki, ya dago da sauri ya dubi Bakura. Ya ce "kamar yaya mahaifan Sajida kake son gani, me ya faru?" Ganin yadda tsohon nan ya razana, ya dimauta shine yasa Bakura ya kasa tambayar kwakwab din nan tasa. Ya sosa qeya ya ce "an ce min kai ne Babanta ko?" Baba ya ce "kwarai kuwa." Bakura ya sake cewa "Babanta wanda ya haife ta ko?" Baba ya tsuke fuska ya ce "kamar yaya?" Bakura ya yi ajiyar zuciya ya ce "Baba abunda ya sa nake wannan tambayar ina da dalilina ka yi hakuri a hankali zaka ji komai. Shin mahaifiyar yarinyar nan Sajida ta na raye?" Baba ya ce "ta na raye in dai ba wannan fitowar ta yanzu-yanzu ba rai yayi halinsa, dan yanzu na bar ta tana juya kunun kanwa. Me kake so ka ji ne yaro? Idan wani bayani ka ke da shi ka fada mana in ji, me ke tafe da kai?" Bakura ya nisa sannan ya ce "Baba ba komai ba ne, sai dan ina son na sanar mu ku cewa ku na tufka ne wani ya na warwarewa. Ku na yiwa 'yarku tarbiyya wani ya na warware muku, magana na ke akan 'yarka Sajida da Abdul majid." Sai tsoho ya dauki dogon salati ya ce "au, har yanzu Abdul majid bai rabu da yarinyar nan ba? Duk irin yaqin da mu ka yi da shi a baya. Lallai yau sai na lahira ya fita jin dadi." Ya juya a fusace zai shiga gida. Bakura ya tsayar da shi ya ce "na fada maka badan hankalinka ya tashi ba, haka kuma ba dan ka daki Sajida ba, sai don ka sake saka ido ku raba su. Duka ko zagi ba shine a'ala ba, ku yi mata nasiha kuma a karbe wayar hannunta don idan an hana ta fita ai ga waya. Ina da zafin rai kamar ka amma ban cika duka ba ko kuma ince ban taba dukan 'ya'yana ba, ina da tsoratarwa, ina yawan yi musu nasiha da wa'azi cewar su ji tsoron Allah su san duk inda suka shiga suka labe Allah na ganinsu, idan ni bana ganinsu." Baba ya dubi Bakura ya ce "yaro na ji abinda ka ce, kuma na gode." Ya juya ya shiga gida da sauri, Bakura ya shiga motarsa ya tafi gida. *** *** *** Ya na isa gida Auwalu mai gadinsa ne ya taso a guje ya wangale tafkeken get din shiga farfajivar gidan. Sanyin ni'ima da qamshin fulawoyi ne za su daki hancinka. Yayin da korayen fulawoyi da jajaye da ruwan dorawa da fararen furanni ne zasu dinga haskake kwayar idonka. A tsakiyar farfajiyar gidan wani round about aká yi shi da tiles amma an dankara fulawoyi a tsakiyarsa don haka akwai wani ruwa da yake bululowa ta ciki ya na tashi sama yana ban ruwa. Ga filin ajiyar motoci nan fiye da mota goma za su iya tsayawa a lokaci guda, gefe kuwa liluka ne a jejjere na wasan yara kai ka ce a 'Wander land Abuja' kake ( wajen wasan yara). Tsuntsaye ne masu kyawun gaske suke kai kawo a farfajiyar gidan, kamar dawisu, talo-talo, jimina, aku, da 'yan qananun tsuntsaye masu launuka daban-daban, gefe kuwa qaton fili ne aka kewaye da birirruka da maguna da burguza-burguzan Karnuka irin na turawa masu gashi buzu- buzu gidan kowananansu akwai bangarensu akwai masu kula da su. Masu kula da filawowi dabam masu wanki da guga daban, direbobi daban-daban. A cikin gida kuwa mata masu aiki kala-kala, akwai makekiyar boy's quarter a bayan gidan akwai dakunan masu aiki burjik. sauke kunun da zafinsa."Kai ka fi cancanta 1 JUT Paid book 0️⃣5️⃣ Ya na shigowa farfajiyar gidan dan girmamawa sai dukka ma'aikatan kowa ya durqusa ya na kwasar gaisuwa. Dakyar Bakura ya ke daga hannu yana amsawa saboda d'imuwar da ya ke ciki. kai tsaye ya zarce da motar runfunan da aka yi su don ajiye motoci ya tsaya ba tare daya kashe motar ba ya dora kai akan sitiyari ya yi shiru ya na tunani mai zurfi. Bayan 6acin ran halin da Abdulmajid yake kokarin saka Sajida, sai tunanin yaya aka yi Sajida ta yi kama da Zuhuriyyarsa? Lallai kuwa kamar ta baci, dömin idan ya rufe ido ya hango fuskar Zuhuriyya ada, sai ya hango fuskar Sajida, da maganar da yanayin jikinsu sai ya ga sak iri daya ce babu abinda ya raba su. " Ina cikin wani hali. Yaya zan yi na gano bakin zaren ne? Qarshe magana dai na je na ga iyayen Sajida kuma babu hadinsu da qauyen Cinkilawa. Kuma na san dangin Zuhuriyya gaba dayansu babu had'insu da unguwár Kawo amma Allah cikin ikonsa ya halicesu kamarşu daya sak." Bakura ne ya fada a bayyane. Fiye da mintuna talatin Bakura na zaune a mota ya kifa kai ya na tunani. Ma'aikata su na ta kai kawo su na tambayar kansu da kansu shin yau maigida lafiya, ya zauna a mota ya kasa fitowa? Tsananin girmamawa da shayinsa ya hana kowannansu qarasowa su tambaye shi. Da kansa ya duba agogo, ya ga magaruba ta yi, sai ya kashe mota ya fito. Idanuwansa sun kada sun yi jawur da alamar tashin hankali a tattare da shi. Kallo daya ya yiwa ma'aikatan da su ka yi layi a bayan motarsa sai su duk suka watse domin sun tattaru a waje daya sun yi jugum, hankalinsu ya tashi saboda ganin sabon al'amarin da ba su taba gani ba. Ya kwallawa Magaji direban yara kira, Magaji ya amsa cikin ladabi ya zo ya duqa ya gaishe shi. Bakura ya ce da shi ya miqe tsaye kuma ya d'ago da kansa ya dubi kwayar idonsa zai yi masa wata tambaya. Kuma ya tabbatar amsar da zai bashi gaskiya ce kada ya sake ya yi masa karya. Jin haka sai hankalin Magaji yayi mummunan tashi, kan ka ce kwabo ya fara gumi, muryarsa ta hau karkarwa ya tambaya "maigida me ya faru?" Bakura ya yi ajiyar zuciya ya qurawa Magaji ido, Magaji ma ya qurawa Bakura ido zuwa wani dan lokaci. Bakura ya ce "daga makarantar boko da ta islamiyya ina da ina Zahra take cewa ka kaita?" Magaji ya sake zazzare ido ya fad'a cikin rawar murya "daga makaranta ba inda na taba kaita wallahi." Bakura ya gyada kai ya yi shiru can ya ce "wallahi, Allah kenan fa. Na yarda amma ka tabbatar abinda ka fad'a min gaskiya ne, zanci gaba da bincike, daga lokacin da na gane ka yi min qarya daga sanda na lahira zai fi ka jin dadi. Domin ka fi kowa sanin halina a duk cikin ma' aikatan nan. Shekararmu goma sha daya kenan tare." Bakura ya wuce cikin gida ya bar Magaji a nan ya na muzurai gami da mamakin wannan tambaya. Kofar wani katafaran falo ya nufa wanda aka yi shi a cikin wata kayatacciyar baranda mai dauke da tukwanen fulawoyi a jejjere kana shiga dosar kofar falon za ka ji sanyin na' urar sanyaya daki (AC) ta daki hancinka gami da qamshi mai dadi. Ka na shafa labulen da ke zagaye da falon za ka tabbatar bada gujari-gujarin auduga gama gari aka halicci yadin labulen ba, saboda laushinsa. Zanen fulawar jikin labulen zai tabbatar mu ku da cewa ba daqiqan mutane ne suka qera labulen ba. Haka yanayin dinkin da yadda aka liqa labulen kansa sai wanda ya yi masters akan dinki, wanda ya karanci design and decoration ne. Labule ma kenan ina ga kayan alatun dake cikin falon nan? kallo daya za ka yiwa kujerun, center table, flower bases din falon ka gasgata cewa an qera su ne da ruwan gwal, anyi musu design da azurfa. Komai na falon anyi masa kalar kore da ruwan goro (green and orange) kama daga fentin jikin bango har centre kafet dake tsakiyar kujcrun har su kan su kujerun da dining table da yake dining area a falon. Hatta fitulun falon abun kallo ne domin su ma hasken da suke bayarwa kore ne da ruwan goro. Qatuwar talabijin woto LCD ce a maqale a jikin bangon falon kai ka ce mutum ne a jikin bangon ba hoto ba. Akwai qofa wacce za ta kai ka cikin gida, ka na fita tsakar gida za ka gani. Wanda aka qawata shi da tiles tsakiyar kuma anyi masa dan zagayyen tudu an dora flower veses da wata qatuwar bishiyar (unbrellar) wacce take hana rana shigowa. Wasu qawatattun kujeru na kaba aka jejjera domin shan iska. Qofofi ne guda shida a zagaye da tsakar gidan, idan ka bude na farko wani qaton kicin ne mai girman gaske wanda babu abunda za ka hango illa kayatattun kitchen cabinet kalar ruwan dorawa (yellow) sai Gas cooker da electronics kala-kala. Hakika kallo daya za ka yiwa kitchen din nan ka tabbatar wadanda su ka hada kicin din karanta su ka yi ba kai tsaye suka tari aradu da ka ba. A takaice dai duk abunda ya ke cikin kicin din nan fari da ruwan dorawa ne. Sauran qofofin kuwa guda biyar kowannensu qaton falo ne, da kuna bibbiyu da kayataccen bandakai guda biyu. D'aya na Zahra ne, d'aya na 'ya'ya maza ne, daya na matar gidan ne, d'aya na mai gidan, d'aya kuma a rufe ya ke ba kowa na saukar baqi ne. Sai dai dakin Bakura (master bed room) ya fi sauran girma sosai da qawatuwa domin girman falonsa ya kai girman wani qaramin gidan kacokan. Falon hade yake da dining area, da kicin sai ka shiga bed room maimakon dakuna bibbiyu irin na sauran d'akunan shi guda d'aya ne aka yi shi makeke, ya yi dukka biyun girma in abun a fashe su ne. Biro na da takarda baza su iya zaiyana haduwar bangaren maigida ba sai dai na kan iya fadar kalar da aka hada a ciki. komai na ciki kalar uwan madara ne aka dan sirka da fari. Kama daga fenti, kujeru, dining table, kayan kicin, set din gadon da kayan toilet shima ko ba'a fada maka ba ka san turawa ne su ka zo Nigeria su ka baje fasahar da Allah ya ba su, suk a shiryawa Bakura gidan nan. Haka ma dakin matarsa aka qawata mata falonta, dakuna biyu da bandakanta, ita kuma kalar jan duhu (maroun) ne komai. Dakin Zahra babbar 'yarsu kuma ita ce 'yar su mace kadai itama na ta bangaren falo da dakuna biyu da bandaki a kowanne daki. Itama an zuba mata funiture da su ka dace da budurwa, duk ko ina tayi like-liken hotunanta dana iyayenta, qannenta da qawayenta. Komai kalar pink ce a dakin. Dakin 'yaya maza kuwa su uku ne, na biyun sunansa Abubakar shekararsa goma sha uku, shi ya dauki daki daya. Mai bin sa Umar shekarunsa bakwai da d'an autansu Usman shekarunsa hudu su biyu a dayan d'akin. Kowannensu da d'an qaramin gadonsa da lokar kayansa da mudubi da kujera da teburin karatu da rabutu. Falo kuwa durowar litattafai ce iri-iri da set din kujeru, sai Talabijin da settelite game da tashoshin cartoons da karatun qur'ani kadai aka jona musu. Duk abinda ke cikin dakin kama daga fenti har furniture da bandaki kalar Blue ne aka sirka da pupple. Dakin dake rufe ma ba'a bar shi a baya ba wajen kyau da tsari duk da ba kowa a ciki amma akan yi baqi mata daga wani gari su ake saukewa, shi ma duk abunda ya ke ciki kalar brown ne. Bakura na shiga katafaren falon nan ya iske matarsa abar qaunarsa Samira, ta caba ado ta na jiran mai gidanta ya dawo. Ya na shigowa ta daga ido ta dube shi, sai ta yi masa fari da fararen idanuwan nan na ta dara-dara. Irin farfarin da ta gane yana kwantar masa da hankali. Ya yi murmushin qarfin hali gami da yi mata sallama. Samira ta amsa cikin jin dadi tare da miqewa da sauri ta na rangwada ta nufo shi sanye da wata atamfa koriya super Holland wacce ta yi mata hadadden dinki na matsatstsiyar riga da siket mai daukar hankalin maigida. Ta na qarasowa inda ya ke sai hancinsa ya daki qamshin turaren jikinta designers, hade da na hadaddiyar humra da turaran wuta. Ta fada cikin sanyayyiyar murya mai kama da rada "sannu da zuwa Sweety." Kafin ya bude baki ya amsa ta sumbaci gefen kumatunsa, ya sa hannu ya dakatar da ita gami da zare jikinsa daga gare ta ya wuce abinsa. Ya shiga cikin gida Samira ta tabbatar yau hankalin Sweety ba'a kwance ya ke ba, sai ta fara jerowa kanta tambayoyi ta na tuhumar kanta da kanta ko ta yi ma sa laifi ne kafin ya fita. Ta tuno ai lafiya kalau su ka rabu har ta raka shi mota su na wasa da dariya da yamman nan ya fita ya na nishadi. Samira ta fada a bayyane "waye ya tsokano min maigidana? Ya b'ata ma sa rai mutumin da idan ransa ya b'aci ya kan yi fushin kwana uku bai huce ba." Fushin Bakura shi ne babban tashin hankalin Samira domin ba zai kula ta ba, ba zai ci abincinta ba, babu wasa balle hira, ga mummunar harara da daka tsawa. Dan haka yadda take lallaba jaririn da ta haifa sabowar haihuwa haka take lallaba maigidanta don kada ya yi fushi. Allah ya jarrabi Samira da tsananin qaunar Bakura, ta na ji a jikinta da a raba ta da Bakura gara a rabata da rayuwarta.Kai ka fi cancanta 1 JUT Paid book 0️⃣6️⃣ A sanqare a tsaye Bakura ya bar Samira ta na tunani hade da fargaba da karanto addu'o'i a zuci. Addu'ar Allah Ya yayyafawa zuciyarsa ruwan sanyi koma me aka yi masa a waje. Shigarsa dakinsa ba dadewa ya fito jikinsa da ruwa da alama dai alwala ya dauro. Ta yi sauri ta saki fuskarta ta dube shi ta yi murmushi ta ce "alwala kayi, za ka je masallaci?" Ya amsa a ciki-ciki "eh:" Har ya kai qofar fita ya juyo ya dubeta ya ce "ina Yagana?" Ta amsa cikin jin dadin maganar da ta samu ya yi mata. Ta ce "ta na daki ta na karatu, saboda sun kusa fara jarabawa." Ya sake cewa "ina Abubakar, Umar da Usman? Ta ce "su na nan a masallacin qofar gida tunda yamma, Malam Hashim ya zo su na daukar karatu." Ya juya ya fice ba tare daya ce komai ba. Mamaki ya sake lullu6e zuciyar Samira ta kasa gane halin da yake ciki yau, kamar ya na farin ciki kamar ya na baqin ciki. Ta shiga dakinta ta yi alwala ta yi sallar magrib. Tayi ta lazumi tana addu'a kamar yadda ta saba kullum akan Allah ya sassauta zuciyar Bakura, ya so ta d'ari bisa d'ari kamar yadda take son sa, ya dinga sakar mata fuska, ya rage wannan muzuran da kwarjinin da ya ke yi mata don haka kawai ta ji ta na tsoransa. Kada Allah ya hada shi da wacce zai ji ya na so a rayuwarsa balle ya yi mata kishiya, duk da ta san tsautsauran ra'ayinsa ba shi da niyyar yin mata biyu a rayuwarsa. Mata basu cika burge shi ba amma ta san lallai idan ya hadu da yarinya mai tarbiyya wacce take da ladabi da biyayya za ta iya burge shi ya aure ta, ita kuma tsantsar sonsa ne ya dasa mata tsananin kishinsa. Addu'ar Samira kenan, dan duk wanda ya santa ya san ta ya san ra'ayinta. Aka kira sallar sha'i a masallacin qofar gida, su Bakura suka bi jam'i aka tayar da sallah. Samira ma daga dakinta ta aiwatar da ta ta sallar, bayan ta idar ta yi shafa'i da wutiri da laziminta sannan ta miqe ta qarasa wajen kayan kwalliya ta sake caba ado. Aka sake saka huda, jagira, jan baki, ta sake yin daurin dankwali ta feshe jiki da turararruka designers sannan ta fito. Ta na fitowa ta nufi dakin Zahra, ta iske Zahra ma ta idar da sallah. Cikin ladabi Zahra ta dubi mahaifiyarta tayi murmushi, Ta ce "Mama sannu da gida. Kin yi kyau." Samira tayi murmushi ta ce "Zahra sannu da karatu, ki fito mu ci abinci, Abbanki ya dawo ki yi masa sannu da zuwa don ya tambayeki kafin ya tafi masallaci." Zahra ta amsa da "to Mama." Su ka d'unguma suka fito, Zahra sanye doguwar riga baqa (abaya) kanta a lullu6e da qaramin hijab baki mai hula iyaka Rirji. A babban falon gidan suka ci karo da Bakura tare da yaransa Abubakar, Umar da Usman sun dawo daga masallaci. Samira ta ce "yauwa sai mu wuce kan dining table mu ci abinci ko Abban Zahra? Yau da kaina na shiga kicin na dafa maka burabusko irin na ku na barebari." Ta ga ya yi turus bai juya ya kalli dining table din ba ma balle ya bude ya ga abinda aka dafa masa balle ya burge shi. Zahra ta ce "Abba sannu da zuwa, shugabar makarantarmu ta ce in gaisheka." Sai su ka ga ya tsuke fuska ya kada kai zai nufi dakinsa, har ya kai qofar fita sai ya juyo ya dubi Zahra. Ya ce " Zahra ki kula da rayuwa, ki tabbatar kin saka tsoran Allah a cikin zuciyarki a duk inda kike. Ba ruwanki da lalatattun qawaye da samari bata gari. Na sakale Kwaryata ta gari a ragaya ba na fatan kwaryar nan ta tsinke ta fado daga ragaya ta dinga garari a tsakar gida." Yajuya ya tafi abinsa ya tafi. Cafdijam!!! Wannan Hausa ta yiwa Uwar Zahra tsauri balle ita Zahrar kanta. Daman idan aka dunkule Hausa, ko karin magana Zahra ba ta ganewa, ta fi gane yaren kanuri sai kuma turanci. Tabbas tana jin Hausa amma ta ina za ta fahimci wannan maganar ta da? Samira bahaushiya ce gaba da baya amma ya aka yi wannan Babarbaren ya yi ma ta Hausa cikin Hausa ba ta fahimce shi ba? Dadin dadawa ba su san kan maganar da ya ke yi ba balle su gano bakin maganar. Hanakalin Zahra ya tashi, ta kalli mahaifiyarta ta dafe kirji. Ta ce "Mama me na yiwa Abba, wacce kwarya ya ke magana?" Samira ta fita da sauri ta bi shi dakinsa, ta iske zai shiga wanka, ta dube shi. Ta ce "Sweety Zahra ta damu ta na tambayar ko wanni laifi ta yi maka." Ya girgiza kai ya ce "ba laifin komai ta yi min ba dama ba lallai ne ku gane abinda na ke nufi ba yanzu sai a nan gaba." Ya juya zai shiga bandaki Samira ta qara dakatar da shi. Ta ce "sai kayi wanka za ka fito mu ci abinci ko na kawo maka na ka kan daning table din nan dakinka?" Ya girgiza kai ya ce "ba zan ci ba na qoshi." Hankalin Samira ya tashi ta fara magana kamar mai shirin fashewa da kukan kissa da nuna damuwa. Ta ce "haba Yayana, maigidana, abin qaunata. Ya zan dage in yi maka abincin daka fi so a rayuwarka wato burabuskon gero, kuma ka ce ba za ka ci ba. Mu yaya za' ayi mu iya ci...?" Kafin ta rufe bakinta ya dakatar da ita ya ce "ki je ke da yaranki ku ci, ni na qoshi. zan yi wanka in kwanta idan kin shigo kada ki kunna min fitila, jada ki tashe ni ba zanyi hira ba yau. Ka da ki kuskure abinda na fada miki wannan doka ce." Samira ta juya sadan-sadan ta fice daga dakin ba tare da ta sake cewa komai ba kuma bata san me hakan yake nufi ba. Sai ta ji ya yi magana ya ce "ka da ku damu ke da yaranki babu wanda ya yi min wani laifi a cikinku." Ta juyo da murna ta dube shi ta ce "kawai yanayi ne ya canja?" Ya ce "yanayi ne kawai, yau na ga mai kama da Zuhuriyya sak kamar an tsaga kara shine hankalina ya tashi." "Mai kama da Zuhuriyya fa ka ce? A ina? Bakura ka san abinda kake fada kuwa?" Samira ta tambaya cike da mamaki. Ya daga mata hannu ya dakatar da ita. Ya ce " tambayoyin sun isa haka. Sai da safe." Samira ta fito zuciyarta cike da mamaki da kokonton anya kuwa Bakura ba shi da wata aljana a jikinsa? Ko dai aljanun ne su ka tashi yau?" Samira mace ce dirarriya mai tsawo da 'yar qiba. Fara ce sosai, sai dai ba ta da dogon hanci , bakinta madaidaici ta na da dara-daran idanuwa farare qal ma su kyau. Ba ta da gashi mai tsawo amma kuma ba gwaguyyaye ba ne. Mace ce mai tsafta gami da taushin murya, mai tsananin haquri domin idan ba ita ba ba mai iya zama da Bakura. Ta iya lallashi ta iya tausar ran mijinta, ta na da tausayi da kyautatawa masu aikinta. Ta na da son wasa da dariya da yaranta har da ma sauran jama'a. Ta na da ilimin addini daidai gwargwado da na boko duk da iyakacinta daga sakandire ta tsaya ba ta ci gaba ba haka kuma bayan ta auri Bakura bai bar ta ta ci gaba ba. Samira ta fito ne daga babban gida ma'ana gidan arziki da mutunci. Mahaifin Samira mutumin Kano a unguwar yakasai yake. Ta na da qanne da yayye ba adadi kasanceyar mahaifinta mata hudu gare shi. Dukkansu su na nan da ransu reras. Amaryar gidan ma har yanzu ta na haihuwa. Ta auri Bakura saboda ta na sonsa Zahra ce babbar 'yarsu ta fari kasancewar sunan mahaifiyarsa ne yake kiranta da Yagana. Zahra tayi matukar yin kama da Babanta ko ba'a fada maka ba idan ka kalli Bakura ka kalli Zahra ka san irin su daya.Banbancin shi namiji ita kuma mace. Da wuya ka kira shi Babanta sai dai ka dauka Yayanta ne kasancewar auren wuri yayi da haihuwar quruciya. Zahra tafi mahaifinta haske kasancewar ta dauko hasken fatar mahaifiyarta amma ba dukka ta dauko farin ba ta hada da baqar fatar mahaifinta sai ta bada kala mai kyau wato hasken duhu (chocolate colour). Wannan kalar ta Zahra ta sake fitar mata da kyawunta, dogon hancinta siriri har baka irin na barebarin asali, bakinta dan qarami har ya fi na mahaifinta kyau, haka fararen haqoransu da wushiryar sama da qasa duk iri daya. Ga wani Iallausan gashi har qasan qeyarta bakikiirin mai tsawo. Jikinta abin sha' awa, doguwa ce siririya. Kirar kamar Bakura ba su da kiba. Mazan kuwa Abubakar, Umar da Usman ga farin har gajeran hancin sak irin na mahaifiyarsu sak, daba dayan su sun yi kama da mahaifiyarsu, amma sun dauko tsayin mahaifinsu dogaye ne sosai. Allahu Akbar!! Allah mai halittar bayinSa duk yadda Ya so. Kwana biyu Bakura ya kasance cikin yawan tunani da damuwa ga uwa uba rikirkicewar tunani. Ya na cikin damuwa, gigita da tsantsar son binciko wai shin menene alaqar Sajida da Zuhuriyyarsa, idan akwai. Bakura ya taso daga wajen aiki, sai ya ji a ransa ba zai qara iya daurawa ba bari kawai ya zarce gidan su Sajida ko Allah zai sa ya samu abinda ya ke nema, ma' ana labarin asalin su Sajida. Bakura ya na tsayawa da motarsa a bakin qofar gidan su Sajida sai ya bude qofar ya fito yayin da gardawan da ke zazzaune a qofar gidan su ka zuba masa idanuwa su na kallonsa su na gasgata ni' imar da Rabbul samawati ya yi masa. Ya yi shigar fararen kaya, farin takalmi da farar hula, motarsa kuma kirar BMW 7 SERIES mai launin ruwan zuma. Ya fito ya tsaya yayin daya zare farin gilashin dake fuskarsa ya dubi jama'ar da ke zazzaune a qofar gidan daga dukkan alamu makarantar allo ce karatu su ke dauka. Malam Yakubu shine mai makarantar wato mahaifin Sajida. Ya na zaune akan kujerar katako rike da zabgigiyar dorina, yara su na gabansa su na daukar karatu, da zarar sun kuskure sai ka ji ya faula musu bulalar. Malam kenan! Bakura ya qarasa gaban Malam Yakubu ya yi sallama sannan ya durqusa ya gaishe shi. Cikin fara'a Malam ya amsa gami da ce wa "yaro ban gane ka ba." Bakura yayi murmushi ya ce "watakila saboda ba waccan motar ba ce shiyasa ba ka gane ni ba. Ni ne wanda na zo kwanakin baya da yamma game da maganar Sajida da Abdul Abdulmajid." Sai Malam ya fahimta ya fada cikin sakin fuska "to, to, to na gane ka yaro, to mu je wajen motarka mu tsaya." Su ka qarasa jikin motar su ka tsaya. Bakura ya sosa gefen kunne yayi dan murmushi ya ce "Malam yaya yara, yaya jama' a? Malam ya ce "Alhamdulillahi, mun godewa Allah. Yaro ka taimaka mana fa matuqa domin ni a iya sanina Sajida ba ta da waya. Ashe waya ya hada mata take labewa su na yin magana ba tare da mun sani ba. Har takai ta kawo Sajida za ta yi min dubara ta fita ta je su hadu a wani a waje ban sani ba. Saboda yaron nan fa na cire Sajida daga makarantar boko ta na aji biyar na sakandire. Saboda a hanyar makarantar bokon ne ya ke tare ta su dinga zance. Ni dai na fada duk lokacin da ta yarda Abdul majid ya lalata ma ta rayuwa, ma ana ta bari ya yaudare ta, ya san ta 'ya mace ya cuce ta kuma daga lokacin da na aurar da ita na yi bincike aka tabbatar min ba cikekkiyar budurwa ba ce sai na yanka ta." Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci kansa a sunkuye a qasa kamar mai tunani. Can ya dago da kansa ya yi ajiyar zuciya. Ya ce "Allah ya kyauta." Malam yakubu ya dubi Bakura ya ce "wai daman ka san Sajida da Abdul majid ne ko ka na da labariKai ka fi cancanta 1 JUT Jamila umar tanko 0️⃣7️⃣ Ko ka na da masaniya akan taqardamar da ke tsakanina da shi?" Bakura ya ce "ko daya ban san su ba, na hadu da su ne akan hanya zan wuce, na kalli Sajida na dubi Abdul majid na tabbatar ba abokin huldarta ba ne. Na ba ta shawara ba ta saurari ni ba, sai na ga ya dace in biyo ta don in hadu da mahaifanta in fada mu su don su san halinda 'yarsu ta ke ciki. ka san mu barebari akwai mu da tsawatarwa Baba." Su dukka suka bushe da dariya. Malam Yakubu ya ce "ai mu Fulani mu aka sani da kara, kunya da kawaici, ai Sajida ba ta biyo Fulatancinmu ba, na rasa yadda zan yi da ita. Amma yanzu na saka ma ta takunkumin da ko ita ce uwar dubara da wayo ba ta isa su hadu da wannan dan iskan yaron ba, marar tarbiyya." Bakura ya ji dindirin kansa ya yi masa nauyi ya fada a ransa "su Sajida Fulani ne kenan ashe babu hadin Sajida da Zuhuriyya." Hikimar Bakura daman ita ce ya ambaci Barebari ne don ya ji ko su Sajida su na da alaqa da Barebari idan da alaka to ta ina, waye da waye ko kuma ta ina alakar ta hada zuhuriyya da ita. Amma babu wata alaka kwata-kwata. Bakura ya nisa ya ce "Malam ku fulanin ina ne?" Malam ya yi murmushi ya ce "fulanin Shanono ne amma mazauna Kano, tun ina yaro na zo Kano yawan almajiranci, daga nan ban koma ba." Bakura ya sakc jin ya kidime yayin da yake jinjina da yabo ga Rabbul samawati wanda Shine ya halicci Sajida tayi kama da Zuhuriyyarsa sak. Bakura ya dubi malam Yakubu yayi murmushin nan nasa mai faranta zuciyar wanda ya yiwa. Ya ce "Malam ina son in zama daýa daga cikin almajiranka domin nima asalina almajiri ne yawon almajiranci ne ya rabo ni da garinmu Maiduguri zuwa Kano." "Almajiranci fa ka ce?" malam ya tambaya cike da mamaki. Bakura ya gyada kai ya ce "kwarai kuwa malam." Malam ya nisa ya gyada kai yå na shafa dogon gemunsa ya ce "Allahu Akbar!!! Yanzu yaro kai almajiri ne ada? Allah ya rufa maka asiri ya maka arziki? Haka Allah' Ya ke ikonsa. Yaya sunanka?" Bakura yayi murmushi ya ce "Sunana Bakura, sunan mahaifiyata Yagana, mahaifina kuwa sunansa Bahna. Ina da mace daya mai suna Samira. Yarana hudu babbar sa'ar Sajida ce shekarunta goma sha shida sunanta Zahra, ina kiranta da Yagana don sunan mahaifiyata ne. Na biyun Abubakar sai Umar da Usman. Ina zaune a unguwar Amadu Bello Way." Malam Yakubu ya dubi Bakura cike da sha'awar dama nine na sami irin wannan ni' imar taka. Ya ce "yanzu yaro ka haifi yarinya budurwa kamar Sajida 'yar shekara goma sha shida? Amma a haka kamar baka yi auren fari ba ma." Bakura ya yi dariya ya ce "haka ne, nayi aure da wuri ina dan shekara ashirin da uku, yanzu shekaruna arba'in kenan." Qaunar Bakura ta sake shiga zuciyar malam. Ya ce "'yaro ka zo duniya a sa'a, Allah ya yi maka baiwa wacce ba kowa ya samu haka ba, ka godewa Allah." Bakura ya ce "Alhamdulillahi Ala kulli halin." Malam Yakubu ya ce "Allah Ya sanya albarka a cikin dukiyarka da iyalinka, Allah ya qara budi. Yaro Allah ne Ya hada mu, Allah ya dad'a mana dankon zumunci." Bakura ya ji dadin addu'ar malam Yakubu ya na amsawa da "amin summa amin malam. Bakura ya sake gyara tsayuwa ya ce "Sajida da Yahuza ne qananan yaranka kenan?" Malam ya gyada kai ya ce "na' am, su ne qanana kuma su ne manya." Bakura ya tsurawa malam ido ya na kallonsa duba irin na rashin fahimta. Sai Malam yayi murmushi ya ce "ni da matata Furera mun yi aure tun quruciya amma Allah bai ba mu haihuwa ba sái da muka manyanta, Su biyun nan da ka gani su ne kadai 'ya'yanmu." Bakura ya yatsune fuska kamar mai ciwon kai wanda har hakan ya ja hankalin Malam Yakubu ya tambaye shi "Bakura lafiya ko kwaro ne ya fada ma ka ido?" Bakura ya ce "a'a Malam na dai ji dadi da Allah ya ba ku haihuwar kafin kų tsufa yadda ba za ku iya haihuwar ba ma kwata-kwata." Nan kuwa tsabar firgita ce, ya ji gabansa ya fadi kasancewar babu sauran wani tunani ko bincike akan alakar Sajida da Zuhuriyyarsa kuma da zai sake yi. Ya fada a ransa "yanzu babu dangin Zuhuriyya guda daya da zan kalla in ji dadi a doron duniya? kan ka ce kwabo jikinsa ya yi sanyi idanuwansa sun kada sun yi jajawur, muryarsa ta yi qasa sanyi kalau. Amma sai ya daure ya na hira da Malam don kada ya gane. Hira su ke ta yi tamkar d'a da uba, ko kaka da jikansa kai ka ce sun yi shekara da shekaru da sabawa. Daga karshe su ka yi sallama su ka tsayar da shawara akan Bakura zai dinga zuwa daukar karatu da daddare tsakanin sallar magaruba da isha'i sau uku a sati wato ranakun Juma'a, asabar da lahadi. Ba tare da Bakura ya bawa malam komai ba ya shiga mota ya tafi. Hikimar hakan kuwa shine Bakura mutum ne mai yawan kyauta amma mai yawan gwada mutane don ya gane masoyansa na zahiri. Ya na sane sai ya qi yin kyauta don ya ga shin mai zuwa gaishe shi zai ci gaba ko zai daina daman ba don Allah ba ne. Bakura kenan!!! Bayan tafiyarsa Bakura ya tsinci kansa cikin farin ciki da tsananin qaunar Sajida da mahaifinta. Kauna ta saboda Allah ma'ana ya na son su so na tsakani da Allah saboda albarkacin kamar da tayi da Zuhuriyya, yą sa a ransa cewa Allah ne Ya hada shi da mai kama da wacce ya fi so don su yi zumunci. Kullum Zuhuriyya ce a ransa Allah ya dubi halin da ya ke ciki Ya kuma amsa addu'ar da yake ta yi shekara da shekaru ya aiko masa da Sajida dan ya dinga ganintaya na jin sanyi. Allah ne kadai Ya san boyayyan sirrin daya shirya. Irin koyar da tarbiyya da jajircewar da mahaifin Sajida ke da ita shine ya sa ya kwantawa Bakura a cikin zuciyarsa, uwa uba yadda ya ke koyarwa da al'ummar Annabi karatun kur'ani mai girma. Allahu Akbar!!! Ranar juma'a kafin sallar magaruba Bakura ya dira a kofar gidan malam Yakubu, tare da shi aka yi Jam'in sallar magriba aka idar sai aka firfito da fitilar kwayaye guda uku daga cikin gida. Manyan maza da dattijai ne suka zagaye malam su na daukar karatu, kowannce da qur'aninsa. Abin ya yi matuqar burge Bakura bai taba zaton haka maza ke cika su na daukar karatu ba, a kalla sun yi su ashirin duk da haka ma mutane da yawa ba su sami damar zuwa ba. A lokacin da malam ya fara dora musu karatu sai ya fuskanci Bakura ya riga ya haddace duk inda aka bude, sai bayan da aka gama daukar karatu aka yi sallar isha' i kowa ya watse sai Bakura da Malam ne kadai su ka rage. Malam ya ke tambayi Bakura shin saukarsa nawa? Bakura ya ce "ba adadi, amma haddata sau bakwai, ną haddace kur'ani, na sake maimaitawa har sau bakwai." Malam ya gyada kai alamar ya jinjina masa ya ce "sai dai ka zama mataimakina ka dinga taya ni koyarwa amma kai ba dalibi ba ne, malami ne." Su dukka suka yi dariya. Bakura ya ce "Malam anya ayi haka kuwa?" Malam ya ce "haka za'ayi Bakura. " Bakura ya ce "to malam ai kai uba ne ba zan yi ma ka musu ba. A can gidana ma akwai masallaci a qofar gidan, mazan unguwar su na zuwa daukar karatu. Ni da limamin masallacin muke koyar da su, Yanzu ma haka su na can su na yi, na fito ne neman ilmi ko akwai abinda zan samu in koya, ka san ance ilimi kogi ne ya na da yawa." Malam ya ce "haka ne, ai gobe sai mu yi hadisi, fikihu da tauhidi." Bakura ya ce "to madalla Allah ya kaimu goben Malam." Bakura ya miqe tsaye ya na shirin tafiya sai ya ji Malam ya ce "Bakura ka jira ni in shiga gida in fito." Bakura ya amsa da "to malam." Ya bi malam da kallo har ya shige cikin gida Bakura ya shiga zulumi, ya na tunani ya na tambayar kansa da kansa meyasa malam ya ce ya jira, kuma ya shiga gida? Wa zai kira, ko me zai dauko masa daga cikin gida? Allah Ya sa mahaifiyar Sajida zai kira su gaisa ko Allah zai sa ya gane ko wacecc. Ya ci gaba da sake-sake a ransa tabbas Sajida da mahaifiyarta za ta yi kama tunda ba ta yi kama da mahaifinta ba ko kadan, amma qaninta Yahuza kallo daya za ka yi masa ka yiwa mahaifinsa ka ga kama. Bakura ya na tsaye qikam kamar itacen bishiyar da bata da reshe balle ganye, idonsa kyam akan qofar shiga zauren gidan, ya na jiran fitowar malam Yakubu. Ba tare da Malam ya dade da shiga ba sai ga shi ya fito dauke da wata baqar leda a hannunsa ya qaraso inda Bakura ya ke tsaye. Ya mika masa gami da cewa "Bakura ga wannan, shadda ce tsadaddiya wani daga cikin jama'ata dan siyasa ne mu ke yi masa addu'oi shine ya kawo min su kala-kala da yadiddika har kala bakwai shine nace bari in dauko maka daya kaima ka dinka irin taku ce ta manyan 'yan gayu. Ni kuwa ina fama da tuwo da miyar kuka ina faman cakuduwa a cikin almajirai ina ni ina saka farin kaya." Bakura yayi mamaki matuka, ya bude baki ya na kallonsa sai ya hau jujjuya shaddar,. tabbas babbar shadda ce ta gaske irin shaddojin da ya ke dinkawa ne. Sai ya dubi malam ya yi dariya ya ce "Malam ayi haka kuwa? Me zai hana kaima ka dinka ka caba adonka ga daurin aure, fatiyar suna, kwalliyar idi ko juma'a sai ka saka kayanka. Shima wanda ya baka idan yana gani a jikinka zai ji dadi gobe ya qaro maka wadanda su ka fi haka tsada da kyau." Malam ya yi dariya ya ce "kai haba, meya yayi Saura da har zamu zauna muna caba ado ai fatanmu yanzu sauran shekarun ko watanni ko kwanakin da suka rage mana ya zamanto zikiri ne, salla, azumi da karatun kur' ani mu cika da imani. Ka sàn Allah Ya ce sittuna au saba'una. Ga shi yanzu ina sittin da biyar. Je ka da ita Bakura ba'a mayar da hannun kyauta baya, kyauta ce na yi maka saboda jin dadin zumuncin daka qulla a tsakaninmu" Sai Bakura yaji jikinsa ya mutu bakinsa ya kasa cewa komai, kalmar da ta fito daga bakinsa itace "Allah ya saka da alkhairi, nagode malam. Sai gobe Idan mai dukka ya kaimu da magaruba zan zo." Ya Juya ya shiga motarsa ya tafi, ya na tafe ya na mamakin malam Yakubu. Lallai Malam Yakubu dattijon arziki ne wanda abun duniya bai dame shi ba. Yadda Malaman zamanin nan da yawa suka lalace saboda kwadayin abun duniya shi kuwa Malam mai bayarwa ne ba mai saka ran zai samu ba. *** **** *** Washegari asabar da yamma Bakura da Samira matarsa ne su ke zaune a kan dogowar kujerar babban, falonsu su na kallon wani dadadden bidiyo casset na da can wato wakokin Dan anace wanda ya yiwa Shago. Yara gaba daya su na makarantar islamaiyya. Domin idan ka ga Bakura ya zauna ya na kallo to ka tabbatar wakokin shata, dan kwairo, Dan anace, Dan maraya, Haruna uji, Garba 'Super, Sani Aliyu Dan dawo, Barmana coge, Uwaliya mai amada ne. Ma' ana wakokin 'yan dambe, 'yan farauta, 'yan tauri da dai sauran finafinan al'adunmu na Hausa wanda gargajiya ce tsagwaro babu kwaikwayon turawa a ciki. Da Samira ta san da haka sai ta bazama ta shiga nemowa maigidanta abinda za ta ja hanklinsa, ta Siyo masa su kala-kala. Na, bidiyo, na CD da na radio, ta zuba masa a mota, wasu a dakinsa, wasu a afalonsa Don haka duk lokacin da Bakura ya ke gida ya na zama tare da iyalinsa su yi ta kallo cikin nishadi annashuwa. Waqoqin su kan tunawa Bakura labarai na can-can shekarun baya sanda ya ke yaro qarami. Bakura ya dubi Samira duba irin na jin dadin Ya ce "Gimbiya, da ace ni shugaban qasar Nageria ne da na rusa duk wani qyale-qyale da kwaikwayon al'adun turawa, ana ganin shine wayewa alhalin ba wayewa ba ce ci baya ne. Duk wani dan Nigeria mata, yara da manya dole atamfa za su dinga sakawa, kar kice atamfar za su yi dinkin da suke so ko matsatstsan siket da matsatstsiyar riga, a 'a wadatacciyar riga da mayafin atamfa ma'ana falle biyu irin na da, da ake yi riga da zani da mayafi a samo dan kwali daban a daura. Maza kuma yara da manya sai sun saka riga da wando da babbar riga da hula, kowa a qasar nan shigar da zai yi kenan. Saina hana saka mini siket, shirt, jeans, short kneekers, 3 duater, suits da dai sauransu." Samira ta kwashe da dariya ta ce "haba Sweety, babbar riga fa ka ce? Yanzu ko ma su aikin a bankuna da likitoci babbar riga zasu dinga sawa, ai sai ta hana su aikin." Ya yi dariya ya ce "to na yarda su cire idan Likitoci za su yi operation, ma su aikin Bakin su cire su ajiye a gefe su na gama kirga kudin sai su mayar da ita." Ta gyara zama ta ce "yanzu tsakani da Allah yaya za'ayi ka hada Inyamurai da Yarbawa da mayafin atamfa?" Ya ce "ai har yanzu Matan Inyamurai su na dinkin zannuwa biyu sai dai ba sa yafawa Sai su daura daya akan daya kin ga idan na saka dokar daukar dayan kawai za su yi su yafa a jikinsu." Su dukka su ka kwashe da dariya. Samira ta ce in laifin ka ce mata suyi shigar abaya doguwar riga bawa mai dankwali ko hijab. Maze kuma doguwar riga fara da hirami, irin na Saudia ina ganin ai sun dan fi rashin nauyi." Bakura ya girgiza kai ya ce "na yarda shigar larabawa shiga ce mai kyau itace shigar musulunci, amma al'adar Hausa na ke so in farfado da ita saboda al'adar Hausa al'ada ce mai kyau wacce ke tafiya da Addinin Musulunci." Samira ta riqe haba ta ce "wai, wa ya ga ka zama shugaban qasar Nigeria 'yan Nigeria sun hadu da doka." Ya ce lallai kuwa zan takura musu da dokoki kuma kowa sai ya bi. Dole ne ayi da' a, dole ne ayi aiki,dole ne ayi tsafta, babu zalunci. Na qasa dole ne ya yiwa na samansa biyayya, shugaba dole ya biya na qasa hakkinsa da dai sauran matsaloli dake buwayarmu 'yan Nigeria." Ya sake kishingida kansa akan hannun kujera ya dube ta ya ce "Gimbiya ina cikin wani hali wanda yake rikirkitacce mai daure kai, mai tsoratarwa matuqa." Ta gyara zama ta ce "me ya faru? Wani abu aka ce maka ya na faruwa a cikin gidan nan, a kaina ko a kan yara ko kuma a cikin masu aiki ne?" Bakura ya girgiza kai ya ce "ko daya, babu komai game da cikin gidan nan. A can wata unguwa ne da ake kira Kawo." Samira ta maimaita "kawo? Na san unguwar Kawo me ke faruwa?" Yayin da ta dafe kirji zuciyarta na bugun uku-uku. Ya dube ta ya yi murmushi. Ya ce "kwantar da hankalinki ba wata matsala ba ce uwar tsoro." Su dukka su ka kwashe da dariya.Tabbas kishiya ce ta fara fado mata a ranta. Ya sosa qeya ya gyara zama. Ya ce "Na ga wata yarinya budurwa matashiya wacce shekarunta ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba." Tuni hawaye ya cika idanuwan Samira domin ta san qarshen maganar. Ta fashe da kuka ta dube shi. Ta ce "Abban Zahra, meye hadinka da yarinyar har ka zo ka ke bani labarinta?" Bakaru ya girgiza saboda har ya ji ransa ya baci, ya dubi agogo ya juya ya dubi teburin da ke gefansa sai ya suri mukullin motarsa ya dora hularsa akai ya miqe tsaye. Ya dubeta duba na takaici Ya ce "babbar matsalata da ke kenan, ba ki da matsala wajen ladabi da biyayyar aure, ba ki da matsala wajen tarairayar miji, ba ki da matsala wajen koyawa yara tarbiyya, ba ki da matsala wajen iya girki da tsaftace gida. Babbar matsalarki itace mummunan tunani da tabarbarewar fahaimta akan kishiya, shi yasa hira ta da ke ba ta dadewa domin daga an fara labari sai ki fara maganganu ki na koke-koke dan haka ni yanzu zan bar miki gidan idan kin gama kukan can bayan sallar isha'i zan dawo." Ya juya zai fita, ta sake zubo da hawaye. Ta ce "ashe daman zance ka fara zuwa shiyasa jiya ba ka yi sallar magaruba da isha'i a masallacin qofar gida ba? ka je ka dawo da wata shadda ashe ita ta ba ka. Ai ba a nan kasar ka ke siyan shaddar da ka ke sawa ba." Tsawa ya daka mata wacce ta razanar da ita ko tari ba ta sake yi ba, ya fara magana cikin fushi. Ya ce "ya ishe ni haka, ba na son ki qara daga wannan maganar, labarin da na ke niyyar baki na fasa kuma kar ki sake tambayata." Ya juya a fusace ya fice, ya zabi dankareriyar mota wacce ba ta jiya ba ya shiga ya tafi. Bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan malam Yakubu. Kamar jiya yauma anan suka yi Sallar magaruba suka yi karatu sannan su ka yi sallar isha'i sannan kowa ya watse. Sai Malam da Bakura su na ta zuba hira. Yahuza ne ya fito dauke da farantin abinci ya ajiye a gabansu, languna ne na tuwo da miya, Yahuza ya durqusa ya gaishe da Bakura cike da fara'a da tsananin saka ran yau ma zai sami wata dari biyar din. Ya sami gefe ya zauna ya ci gabaKai ka fi cancanta 1 Na Jut 0️⃣8️⃣ Malam Yakubu ya gallawa Yahuza harara ya fada cikin tsawa "tashi ka shiga gida. Waye ya ce ka zo ka zauna anan?" Sum-sum Yahuza ya miqe har ya wuce zaure ya fito da sauri Ya ce "ah Baba na manta Sajida ta ce ka ba ni kudin igiyar leko(mosquito coil) in siyo ma ta." "Malam Yakubu ya b'ata rai kai ka ce ruwan zafi aka watsa masa. Ya ce "ba zan siya ba, ai na fada ma ta jiya, igiyar lokon kwana biyu ne, domin guda biyu na ba ta amma ta qi ji ta kunna dukka biyun jiya, daya a wajen kanta wata a wajen qafarta wai ita isasshiya. Igiyar lekon biyu naira goma sau biyu a rana daya sai ka ce buga kudin nake yi. Dama guda shida na siyo jiya na miqawa Sajida biyu, na ce ma ta jiya daya yau daya. Na miqa ma ka guda biyu, na kai biyu dakinmu mu ka kunna daya, yau zamu kunna daya. Ko kaima dukka biyun ka kunna jiya?" Yahuza ya zabura. Ya ce "a'a ni saura daya da rabi da asuba na tashi na kashe dan kar ta qare." Malam yayi murmushin jin dadi. Ya ce "yauwa ka ji yaro mai tattali haka ake so ka ga kai kwana hudu za ka yi kana kunnawa, ita kuwa Sajida yau idan za ta mutu don cizon sauro babu mai ba ta maganin sauro a gidan nan. Ka je ka ce ma ta ba zan siya ba, ai ta kwana biyu na ba ta kuma kar ta sake damuna." Bakura ya ciro kudi naira dubu zai bawa Yahuza malam ya hana. Ya shiga roqar Malam, ya na yi masa magiya ya taimaka ya bari Yahuza ya siyo shaltos, malam ya fisge kudin daga hannun Bakura ya tura masa a aljihun gaban rigarsa. Ya ce "Bakura ba za mu yi musu da kai ba ko jayayya tunda na ce ka bari ka bari, Sajida zuma ce sai da wuta ta na da taurin kai da rashin jin magana. Kuma laifin mahaifiyarta ne, ita ta shagwabata ba'a kwabarta, ada muna ganin kamar yarinta ce sai da ta girma na ga tsiwar ta yi yawa sannan na tabbatar tantiriya ce sannan na fara saka mata takunkumi." Bakura ya yi shiru kawai zuba tagumi." Malam ya dubi Yahuza ya daka masa tsawa. Ya ce "tsayuwar me kake yi ne har yanzu? Na ce ka je ka fada ma ta ba zan siya ba." Yahuza ya shiga gida da sauri. Malam ya ce "shi kuma Yahuza bashi da matsalar rashin jin magana amma fa akwai shi da kwadayi da son kudi kamar wani quda idan ya ga koko haka ya ke wajen kwadayi." Bakura ya kwashe da dariya ya ce "haka yara suke a ko' ina ma, sai dai fatan Allah Ya shirya mana zuriyarmu baki daya." Malam ya ce "amin summa amin." "Bakura bismillah ga abinci fa an fito mana da shi, tun jiya na ce daga yau abincin mutum biyu za'a dinga zubawa ni da kai." Malam ne ya fada. Bakura ba zai iya cin abincin gidan Malam ba, ga kunyar malam da nauyinsa yana ji. Malam ya jawo farantin abinci ya bude tuwon dawa ne da miyar kuka ta sha daddawa da wake amma ba nama. Babu shakka Bakura ma'abucin son miyar kuka ne, to amma tambayar ita ce ta yaya aka sarrafa miyar shine bai yarda ba, ma'ana tsaftar mai girkin, da tukunyar miyar da ruwan da aka dafa miyar, da tsaftar dan aiken da ya siyo kayan hada miyar shine babban tashin hankalinsa. Domin Bakura mutum ne mai tsaftar gaske ga yawan tsantsani. Sannan miyar kukar da ake yi masa a gidansa ta sha bamban da irin wannan kasancewar sai an jefa kaji biyu ko uku a cikin ruwan miyar sun dahu luguf, qashin ya sallube sannan atsame qashin sai a kada kukar a kai. Malam ya sake maimaitawa "Bismillah Bakura ga abinci, kuma kar ka ce min ka qoshi domin anan mu ka yi magriba ka ga kenan ba ka ci abinci a gida ba. Sai dai idan ba za ka iya cin abincin almajirai ba marar kaji da naman talo-talo." Bakura ya yi dariya ya ce "haba malam miyar almajirai, nima ai almajiri ne sai dai kawai na ci abinci da yamman nan na qoshi." Malam yayi turus da alama bai ji dadi ba. Ya ce "bari na kira Yahuza ya karbo ma ka balangun naira dari a zuba maka a miyar ko dan ka ga babu nama shiyasa ba za ka ci ba." Bakura ya zubura ya ce "a'a malam ka bari kawai, ba dan rashin nama ba ne." Gaban Bakura yayi mummunan faduwa saboda har ga Allah ko ba'a bude kwanon abincin ba ya san ba zai iya ci ba. Ya ci gaba da cewa "wallahi ba rashin nama ba ne.Ni waye da zance dole sai da nama a abinci zan ci, nawa rayuwar duniyar take? Na qoshi ne kawai." Malam ya yi zugum kamar mai tunani da alama bai ji dadin qin cin abincin da Bakura ya yi ba. Can ya dubi Bakura. Ya ce "ba zan boye maka ba d'ana, amma ban ji dadin qin cin abincin nan da ka yi ba, ai sai ka saka albarka ko ba za ka ci da yawa ba. Ni da na ke ganin ka zama dan gida, zá ka iya zuwa ka ce min Malam yau abu kaza nake so a dafa min, in saka Sajida ta dafa maka ko menene ma." Bakura ya tambaya cike da zumudi."Sajida ta iya girki ne?" Malam ya ce "ai fiye da shekara biyar Sajida ta hutar da mahaifiyarta, girkin dare da rana, safe da yamma ita take yi sai dai idan ta tafi makaranta a lokacin da take zuwa makaranta kafin a cire ta. Ita mahaifiyarta ta na fama da abincin siyarwa yaushe za ta samu damar dafa mana abincin gida. kwalla-kwallar kunu da daro-daron dan wanke take dafawa ta sayar a rana." Babu abinda Bakura ya tuna da aka ce masa Sajida ce ta dafa sai lokacin da Zuhuriyyarsa take dafa masa tuwo miyar kuka sai yaji kamshin miyar kuka iri daya da na Zuhuriyya. Bai san sanda ya sa hannu suka fara cin tuwon ba, a idonsa ya na tuna yadda Zuhuriyya take kada miyar komai a cikin tsafta don haka bai sake jin kyamar miyar da yake ci ba. Malam ya ji dadin ganin yadda Bakura ya ke loma ba tare da kyama ba. Sai ci suke har sai da su ka kusa cinyewa. Sannan Bakura ya cire hannunsa. Malam ya cinye tas ya sude kwanon sannan su ka wànke hannu, bayan sun taba 'yar hira Bakura ya ce da Malam zai koma gida sai küma gobe idan Allah ya kaimu. Yauma kamar jiya Malam ya tsayar da Bakura ya shiga gida ya fito dauke da turare. Ba laifi ya na da kamahí amma ba irin designer da Bakura yake fesawa ba ne shi da iyalinsa. Bakura zai ki karba, malam ya ce ba zai yiwu ba sai ya karba dole. Bakura yayi godiya ya karba ya tafi zuciyara cike da mamakin halin kyauta irin na Malam Yakubu.Tabbas ko ba'a fada ba malam Yakubu ya na matukar kaunar Bakura a ransa, Bakura ya shiga sake-saken shin shi kuwa wacce irin kyauta zai yiwa wannan bawan Allah don ya fitar da shi da iyalinsa daga cikin qangin talauci da wahala? Amma kuma can a cikin ransa ya na son ya jira zuwa wani lokaci mai tsawo don ya sake tabbatarwa shin Malam saboda Allah ya ke kaunarsa, yake yi masa wadannan kyaututtukan ko don ya linka masa ne a gaba? Samira ta lura yau ma Bakura ya shigo da leda a hannunsa ya wuce dakinsa don haka ta sake tabbatarwa lallai maigidanta ya Shiga sabuwar rayuwa ba irin tasa ta da ba. Idan hankalinta yayi dubu ya tashi, sai zagaye take cikin gida ta rasa wanda zata tara da wannan matsalar ya share mata hawaye sai shi kansa Bakura. Ya shiga dakinsa fiye da awa guda bai fito ba, a tunaninta wanka ya shiga yi zai fito ya ci abincin don haka ta ci gaba da jira, ta ji shiru bai fito ba, sai ta shiga dakin ta iske shi har yayi wanka ya kwanta ya kashe fitilar dakin. Ta tura kofar ta shiga can cikin dakin yayin da duhu ya hana ta hango shi. Ta laluba zata kunna fitilar dakin sai ta ji muryarsa. Ya ce "kada ki kunna min fitila na- riga na kwanta." Ta laluba ta qarasa jikin gadon ta zauna a gefe cikin sanyi jiki ta ke magana. Ta ce "Abban Zahra tun dazu ina daning area ina jiranka ka zo ka ci abinci ashe shigowa kayi ka kwanta." Ya fada cikin gadara "eh na kwanta, a qoshe nake." Ta rusa kuka kai ka ce mutuwa ya fada mata. Ta ce "yau me zan gani, yau me yake shirin faruwa da ni? Me nayi na kuskure da har haka yake faruwa da ni, wacece wannan mai matsayi a wajenka wacce har ta fi ni?" Bakura ya ji hankalinsa ya tashi matuka, yayi figigit ya yaye bargon da yake ciki a lullube. Ya kunna fitiila ya matso gare ta ya na tambaya cike da tashin hankali. Ya ce "Samira lafiya, me yake faruwa? Dan na ce na qoshi shine abin da zai sa ki duki kukan irin na mutuwa haka? Mu je dining in ci abincin, shikenan?" Ta sassauta da kukan ta fara goge hawaye. Ta fice ya na biye da ita a baya su ka fito zuwa danning area da yake a babban falo, ya jawo kujera ya zauna. Ya dubi teburin yaga abinci ne burjik kala-kala kamar kala shida. Ga taliya fara da miyarta, farfesun kaji, farfesun kayan ciki, ga gasasshen kifi, ga hadaddan salad, Gefe kuma yankakkun kayan marmari ne wato (fruit Salad) ga lemuna nan kala-kala woto (Juices) nikekkiyar abarba ce da markadaddiyar kwakwa kamar yadda ta san Bakura bai cika son lemon kwali ba ko na gwangwani sai dai ta siyo kayan marmari ta markada ta sarrafa masa a gida. Yayi murmushi ya dube ta wacce ke tsaye qiqam, ido ya yi mata jawur don kuka da ta sharba, ta cika ta yi fum kamar za ta fashe don fushi. Ya ce "Gimbiya zauna mu ci mana, yaya za ki tsaya min a kai ?" Ta jawo kujera a can gefe ta zauna. Ya yi dariya. Ya ce "haba Gimbiya yau ba za ki zauna a kusa da ni ba ma, balle a bani a baki, ki dawo nan kusa da ni mana." Ta girgiza kai ta ce "nan ya isa ba sai na qaraso ba." Bakura ya miqe ya jawo kujerarsa kusa da ita ya zauna ya ci gaba da lallashinta ya na mata magana mai kwantar da hankali har sai da ta saki fuskarta ta fara cin abincin. Bakura zura abincin nan yake yi a cikinsa kawai ba don ya na jin yunwa ba, sai don gudun bacin ranta. Duk lauma daya da zai kai bakinsa sai ya ji malam Yakubu da iyalinsa sun fado masa a rai, sai ya ji inama zai iya kwashe abincin nan ya kai kofar gidan malam su hadu su ci tare. Sai yake ji kamar rashin adalci ne ya zo gida yana cin dadi shi kadai. Domin Malam ya zame masa tamkar dan uwa na Jini. Ya na ci yana tunani, daga Samira ta harare shi sai ya hau yi mata hira don kada ta ci gaba da zarginsa. Bayan sun gama cin abincin ta kwashe kwanukan ta kai kicin ta goge kan teburin tsaf sai ta kunna masa wani wasan kwaikwayo da tasa aka suyo masa yau, wato fim din Boloko a Kano. Su ka koma kan doguwar kujera su na kallo cike da nishadi su na kyalkyala dariya, idan maganar budurwa ta fado ma ta a rai sai ya ga ta tsuke fuska. Mamakinta ya rufe Bakura ya dubeta. Ya ce "Samira lafiya kina dariya kuma kina fushi?" Kan ka ce kwabo idanuwanta sun cika da hawaye, ta yi narai-narai da ido. Ta ce "budurwarka na tuno, wacce ta fara dauke maka hankali kwana biyu." Ya gyara zama ya yi marmushi ya dubi ta. Ya ce "da ban yi niyyar fada miki ba, har abada ba za ki ji wannan labarin ba saboda abunda kika yi min dazu. Baki da wayo ashe har na ke yi miki kallon mai wayo, ai ya kamata ki tsaya ki daure ki ji karshen darin sannan ki dauki mataki, amma daga farawa kin fara surutu ga shi ke baki fahimci komai ba kin shiga damuwa da sumbatu ki na kuka. To, bana son irin haka daga yau don ki sani." Ta matse hawaye ta ce "na yi kuskure Sweety, zan kiyaye nan gaba." Ya yi murmushi ya ce "Allah ya yi miki albarka. Kamar yadda kika san halina, ba na boye miki komai yau idan na hadu da wata na yaba da hankalinta na ji ina son in aure ta a ranar zan sanar miki. Me za ki iya yi min, ko za ki dake ni ne, ko kuwa za ki zage ni?" Samira ta amsa da "A'a." Ya ce "ke kin san bana boye miki komai, to amma me ya sa kika fara zargin na ci amana ko ina miki nuku-nuku? Samira tayi kulu-kulu tana muzurai, ba tare da ta san amsar da zata bashi ba. Ta na rayawa a ranta tabbas ta yi kuskure, da batan basira wajen zartar da hukunci akansa. Ya yi shiru na wani dan lokaci sannan ya ce "wata yarinya ce mai suna Sajida, mai kimanin shekaru goma sha shida. Iyayenta sun yi mata tarbiyya amma wani saurayi na kokarin ya russ mata rayuwa. Na yi kokarain haduwa da mahaifinta na sanar masa, Alhamduliliahi ya dauki kyaukykyawan mataki ya hana ta fita. Mahaifin Sajida Malam Yakubu babban malamin karatun alkur ani ne, don haka na zama almajirinsa nake daukar karatu a ranakun Jumaa, asabar da lahadi zan dinga zuwa tsakanin sallar magriba da isha' i. Dadin abunda na yi masa ya sa dúk sanda na je sai yayi min kyauta, shine kike ganina da leda. Hankalina ya na tashi matuka akan yadda naga a boye Sajida ta na zaluntar iyayenta shine yasa na kasa samun nutsuwa ina fargabar kada dai ace Zahra ma haka take yi mana." Samira ta dafe kirji ta fada cikin fargaba "Abban Zahra ina Yagana ta sani ko wa ta sani da za ta fita ba'a sani ba? Abban Yagana kai kanka ka fi kowa sanin halin Yagana, ba za ta yi haka ba." Bakura ya ce "tabbas na san Yagana, amma na san zamani ya canja dan haka ki taya ni saka ido sosai ki taya ni da yi mata nasihohi ta sigar tatsuniya ko labaru masu dauke da gargadi da darasi ki tsoratar da ita." Samira ta yi ajiyar zuciya ta sunkuyar da kai kasa. Ta ce "zan yi mata nasiha Allah må zai kiyaye ta insha Allah ba zata bamu kunya ba." Tsawon lokaci mai dan mai nisa babu wanda yayi magana a cikin su,sai Samira ta dubi mai gidanta ta yi murmushi ta maqale murya. Ta ce "Sweety, yarinyar nan nake tunani Sajida, ka ce shekarunta ba su wace goma sha shida ba ta kuwa gama sakandiri?" Ya ce "mahaifinta ya ce sun cire ta daga makaranta saboda saurayin ta na S.S 2, kuma duk da talaucinsu makarantar kudi mai kyau ya saka ta mai Suna EL-LITININ COLLAGE. Wani abun daya sake daure min kai shine kamanin Sajida ya tsaye min a rai, ya zame min wani mummunan fami a cikin zuciyata." Ra-ga-gas! Haka qirjin Samira ya buga cikin karkarwa murya da fargaba. Ta ce "Abban Yagana ban fahimce ka ba. kamar yaya kamaninta sun zaune maka a zuciya? Abun mamaki sai ta ga hawaye ya na zubowa daga Idanuwansa. Hanakalinta ya sake tashi ta fada a gigice "Abban Yagana kuka kuma naga kana yi. wai meke faruwa ne?" Ya fada cikin lallausar murya mai hade da Jimami. Ya ce "yarinyar kamarsu daya da Zuhuriyyata." Samira ta zuba masa ido ta na kallo, kallo irin na anya kuwa ba tunanin zuhuriyya ba ne yayi masa yawa har ya fara yi masa gizau?" Ya juyo ya dubi Samira yayi murmushi ya ce "yaya ki ka zuba min ido kina kallona kamar kina kallon tababbe? Ina cikin hayyacina naga mai kama da Zuhuriyya sak. Shine ma makasudun da ya sa na dage na nemi gidansu don naga mahaifanta. Na ga uwar, naga uban, naga qaninta basu da alaka da Zuhuriyya. Na damu na shiga rudani, fuskar yarinyar nan ta tuno min da Zuhurriya, sai in ji gabana ya yanke ya fadi saboda kamar fuskar Zuhuriyya ce sak, ke har maganarsu iri daya ce sak." Samira tayi ajiyar zuciya sai yanzu hankalinta ya kwanta da ta ji dalilin daya cika maganar yarinyar nan. Hankalinta ya kwanta, ranta yayi fari kwal musamman yadda ta ga bai yabi tarbiyyar yarinyar ba ta san ba za ta taba burge shi ba. Nan da nan ta hau kisisina ta na fitar da kalaman bada hakuri da kwantar da hankali. Ta ce "kama ce kawai, kuma daman a duniya ba'a rasa irin wannan kamar." Bakura ya mike tsaye, kallon ya fita a ransa hakika ya fara shiga yanayin daya saba shiga idan tunanin Zuhuriyya ya juyo masa. Babu wata kalma, babu wani mahalukin da zai iya hana shi zubar da hawaye da dogon tunani. Sai yayi ta addu'a da zikiri sannan abun yake fada masa. Don haka Samira ta dade da sanin haka, amma bata barinsa haka tana kokarin zama da shi ta bashi baki, ta nuna masa ta fi shi damuwa akan haka. Ya mike ya nufi dakinsa cikin sauri ta kashe kallon ta bi shi, su ka raba dare tana fada masa maganganun kwantar da hankali, shi dai yayi shiru yana sauraranta bai ce da ita uffan ba. Da ya gaji da kwanciyar sai ya tashi yayi alwala ya dinga salloli ya na addu'a har asuba. Kwanci tashi Bakura ya shafe watanni hudu yana zuwa daukar karatu wajen malam Yakubu, a sati sau uku bai taba fashi ba. Haka sabon zumunci da shakuwa ya dasu a zuciyoyinsu. Abu kamar wasa har abun ya fara bawa Bakura kunya domin kusan duk haduwar da zasu yi da Malam Yakubu sai ya dauko wani abu ya bashi, kuma ya tilasta masa dole sai ya karba. Ga uwa uba hidimar abinci da yake sawa a dafa masa duk sanda suka gama karatu ya kuma tilasta masa sai ya ci, amma har rana irin ta yau Bakura bai taba ido hudu da Sajida ba balle mahaifiyarta sai dai yakan jiyo muryarsu sama-sama daga cikin gida. Wata rana, ranar Litinin da yamma Bakura ne ke tafe cikin jibgegiyar motarsa Jeep Murano. Gefansa kuma babbar 'yarsa ce Zahra, sanye take da qaton hijabi. Babu abin da za ka iya gani a jikinta daga fuskarta, sai tafukan hannayenta. Daga dukkan alamu daga makarantar Islamiyya take, domin ga jakarta a rataye a kafadarta cike da Kur'anai. Ta juya ta dubi mahaifinta wanda ke kallon gabansa yana tuki da alama ya na cikin matsanancin tunanin da ya saba yi a kwanakin nan. Ta mika hannu ta kunna C.D da ke jikin motar. Kan ka ce kwabo wakar Sani Aliyu Dan Dawo wacce ya yi wa gwamnan Sokoto ta fara tashi, yayin da speakers din da ke kusurwoyin motar suka fara fitar da sautin ganguna. Bakura ya juya ya dubi Zahra, sai ta yi murmushi. Ya sa hannu ya kashe radiyon ya juya kansa ya ci gaba da kallon gabansa ba tare da ya ce mata komai ba. Ta yi shiru na wani dan lokaci mai tsawo. Can ta murda makulli ta bude gaban motar inda gaba daya disc din C.D kala-kala a layi ta zabo wani, shi kuma na karatun Kur'ani ne wanda Sudes limamin masallacin Makkah ya yi. Ta cire wancan na ciki ta saka wani. Cikin 'yan sakonni qira'a mai dadi ta fara tashi. Bakura ya juya ya dubi Zahra sai ta yi murmushi a karo na biyu, ya sa hannu ya kashe. Sai mamaki ya rufe Zahra kamar za ta yi magana sai ta fasa don ba ta ga fuskar yin magana ba. Ta sake bude wajen ajiyar za ta dauko wani C.D na-wakar Shata sai Bakura ya ture hannunta gefe ya mayar da wajen ya rufe. Ya ce, "Wai yaya haka ne Mamana. Kin cika kiriniya kamar wata karamar yarinya, ko ke ce Usman dan auta?" Ta yi dariya ta gyara zama ta zare farin gilashin da ke fuskarta. Ta ce "Abba, kwana biyu kamar kana cikin damuwa, Umma ta ce wai ka ga wata mai kama da Zuhuriyya?" Ya yi shiru yana dubanta yayin da amsa ta qauracewa bakinsa. Can jimawa Zahra ta sake cewa. "Abba, ni kuwa zan so in ga mai kama da Zuhuriyyarka ko ba komai zan dinga tuna kamanninta a rayuwata." Wannan karon ma da sauri ya waiwayo ya dube ta ba tare da ya ce mata komai ba, sai ta ga ya juya kan mota sun canza titi sun baude daga hanyar gida su na ta tafiya ba tare da wani daga cikinsu ya sake magana ba. Zahra ta yi shiru tana tunani a ranta. "Shin me yasa Abba ya juya da kan mota, ina za mu je ne?" Musamman da ta ga an wuce Lamido Cresent an shiga Badawa Layout. Su ka wuce sai ta ga su na ketawa cikin gidajen gargajiya. Zahra ta gyara zama ta dubi unguwar sosai ta juya ta dubi mahaifinta. Ta ce "Abba, ya sunan nan unguwar?" Ya dube ta ya kawar da kai gefe kamar ba zai ba ta amsa ba, dan daga dukkan alamu baya son yin magana. Can ya bude baki da kyar. Ya ce, "Sunan nan unguwar Kawon Alhaji Sani." Zahra ta gyada kai sannan ta maimaita sunan unguwar. Ta ga yana sake danna kan motar cikin lunguna, ga kwata ga gidajen kasa. Sai Zahra ta ji hankalinta ya fara tashi a tunaninta wani kauye ne suka shigo ba cikin Kano ba.Tsoro ya hana ta sake yi masa wata tambayar. Daidai wani kofar gida ta ga ya ja burki ya tsaya. Zahra ta dubi kofar gidan da suka tsaya ta daqa-daqa babu ko fenti ga almajirai nan tsibiri-tsibiri a qofar gidan su na ta karatu. Ta juya ta dubi mahaifinta cike da mamaki take tambayarsa. "Abba, ina ne nan?" Ya yi dan murmushi ya ce, "Na kawo ki gidan mai kama da Zuhuriyya. Ba kin ce ki na so ki ganta ba, ko kin fasa mu juya?" Ta yi dariya ta ce, "A'a mu shiga mu ganta." Ya yi dariya ya ce, "Ki shiga dai ni ina kofar gida, ya ya zan shiga gidan matan aure? Ki shiga tana ciki Sunanta Sajida." Zahra ta tambaya, 'Sajida sunanta? What a nice name? I like the name Sajida." Su ka bude kofar mota suka fito gaba daya. Malam Yakubu cike da mamaki mai hade da farin ciki ya mike ya tari Bakura ya na fadin, "Lale marhaban, yau muna da manyan baki sannunku da zuwa. Kai da 'yar jikar tamu ce?" Bakura ya duqa ya gaishe da Malam. Nan da nan Zahra ta zube har kasa ta kwashi gaisuwa. Bakura ya nuna Zahra ya ce, "Malam ga Zahra 'yata ta fari na dauko ta daga Islamiyya na ce bari in biyo da ita ta gaishe ku saboda wata rana, kar a hadu a hanya ba a san juna ba." Malam Yakubu ya fada cikin jin dadi, "Lallai na ga Zahra ai daga gani babu tambaya naga kamarta da kai sak, Zahra kai ta biyo kama daina wahalar da kanka wajen gabatar da ita duk inda ku ka shiga kallo daya za'asan 'yarka ce,na dade banga irin dan da yayi kama da uba ba haka. kuma ka kyauta daka kawo min Zahra, amma fa na ji dadi. Allah ya yi muku albarka, Allah ya qara zumunci. Zahra shiga cikin gida gani nan zan shigowa zan yi musu bayani. Alh. Bakura bari in dauko maka tabarma in shimfida maka a kofar gidan makwabtanmu saboda kofar gidan namu yau a cike yake da yan makaranta." Bakura ya yi dariya ya ce, "A'a babu komai Malam, zan koma cikin mota in jira har ta fito saboda ba dadewa za ta yi ba, za mu wuce Magriba ta kusa." Malam Yakubu ya ce, "To bari in shiga cikin gidan in gabatar da ita a wajen Sajida da mahaifiyarta, don ba su sanku ba, ita ba ta san su ba." Bakura ya ce, "Haka ne, lallai ba ta san yadda za ta gabatar da kanta ba, don nima ban yi mata bayani ba." Malam na shiga cikin gidansa ya iske Zahra a Zaune kan tabarma, mahaifiyar Sajida kuwa Furera na Zaune akan kujera a gaban murhu tana hidimar siyar da kunun kanwarta da dan wake. Yahuza kuwa ya zo ya saka Zahra a gaba a jima ya faki idonsu ya ce mata. "Bakuwa za ki ba ni naira hamsin idan za ki tafi?" Sajida kuwa ta dauko turmi ta hau tana hira da makwabta. Wayar da aka hana ta yi shi ne take lekawa makwabta ta katanga kawarta Hajiyayye tana ba ta aron waya tana kiran Abdulmajid. Don haka tana jin muryar mahaifinta ta yi sauri ta wurga musu wayarsu ta daka tsalle ta diro. Malam ya daka mata tsawa ya ce, "Sajida ban hana ki hirar nan da kawayenki ta katanga ba? Idan hirar suke so da ke su zagayo mana dan dai ke ba zan bari ki leka kofar gida ba, balle ki shiga makwabta mutaniyar banza. Ga bakuwa nan kin yi ko kula ta ba ki yi ba, baki iya sannu da zuwa ba, balle ga ruwa. Kun qi shimfida mata tabarma kowa ya juya yana harkokinsa, ko ruwa ba ku iya kawowa bakuwa ba. Yanzu Furera da girmanki a matsayinki na uwa sai an fada miki, sannan za ki kula bakuwa dan baki san ta ba." Furera ta zabura ta ce, "Wallahi ni na dauka bakuwar Sajida ce ko 'yar makarantarsu ce ta ga kwana biyu ba ta zuwa ta zo ta gani ko lafiya. Ta shigo ta yi sallama na ba ta tabarma ta zauna muka gaisa, ai ban san daga kofar gida ka ce ta shigo ba." Malam ya fusata ya daka tsawa, "rufe min baki, bakya kula ni, ni kaina idan kina gaban kunun nan baki da lokacin kowa ta sayar da kununki kike yi kawai. To wallahi ząn hana sana'ar nan." Ya juya ya dubi Yahuza ya yi masa tsawa ya ce, "Me ye kai kuma ka zo ka saka ta a gaba? Tashi ka dauko mata ruwa ta sha." BFurera ta tambaya, "Malam yar gidan waye wannan din." Malam ya ce, "Tsagwaron zumunci da girmamawa ce tsakanina da mahaifinta, shi ne mai zuwa daukar karatun nan wanda nake cewa a dinga zubo min abicin mutane biyu ni da shi. To 'yarsa ce ya kawo ta ta gaishe mu." Furera na budar baki sai ta ce, "Wai wa yaga dorin dosano 'yar gidan mai daukar karatu a kofar gida. To mu da ba kofar gida muke lekawa ba yaya za a yi mu sa mahaifinta, balle mu san 'yarsa? ka ga dole sai ka shigo ka yi mana bayani." Zahra ta dago da sauri ta dubi Furera da alama kalaman Furera bai yi mata dadi ba. Malam ma bai ji dadin maganar ba, sai ya ji kunya ta lullube shi. Yahuza ya kawo wani dakalallen ruwa a cikin wani ragargajejjen kwano mai lamba da tsatsa. Sajida na tsaye ta na kallon Zahra kasa-kasa, Allah-Allah take Malam ya fita ta kara hawa turmi ta leka katanga kawarta ta miko mata aron waya ta kira rabin ranta Abdulmajid. Malam ya harari Sajida ya ce, "Ki dauki ruwan ki ja ta dakinki ku gaisa mana ki dawo ki zuba mata kunu." Furera ta zabura ta dube shi ta ce, "Kunun nawa zan zuba?Ai ka san na siyarwa ne." Zahra ta yi saurí ta ce, "Ah! Alhamdulillah, a bar shi na koshi." Malam ya ji wani mummunan bacin rai, ya kudira a ransa idan Zahra ta tafi sai ya tozarta su kamar yadda su ka tozarta shi a gaban baquwarsa. Bai ce komai ba sai ya kada kai ya fice. Ya na fita Sajida ta dubi Zahra ta ce, "Ke dan Allah ki na da waya?" Zahra ta tambaya "Wacce irin waya?" Sajida ta ce, "Ashe fa 'yar gayu ce ba ki san waya ba, ina nufin hanset." Zahra ta ce, "Yes, ina da hand set." Sajida ta yi fari da ido ta ce, "Akwai kudi kuwa a wayar? " Zahra ta ce, "Akwai dubu shida a ciki." Sajida ta yi ihu ta fada cike da mamaki mai yawa ta ce, "Dubu shida? Lallai wannan 'yar gidan masu maiko ce. Saurayinki ne ya hada miki wayar ya ke sako miki kati haka da yawa?" Zahra ta bude baki tana kallon Sajida cike da mamaki, yayin da kalmar saurayi take yi mata reto a kwakwalwa. Furera ta tsaya tsai daga zuba kunun da take yi. Ta ce "Wayar ce dubu shida ko kudin cikin wayar? Sajida ta ce, "Umma! kudin cikin wayar ne dubu shida, wayar kuma ai sai dubu hamsin." Furcra ta gyada kai ta fada a hankali, "Cafdijam dan qarawa mai karfi-karfi za a ce in zuba ma ta kunu kyauta." Sajida ta ce "To kawata dan ba ni áron wayar ta ki in ci ko dubu daya ne." Zahra ta bude jaka ta dauko wayarta tsaleliya kirar N85 ta miqa mata. Sajida ta latsa wasu lambobi kan a jima network ya hada ta da abin kaunarta Abdulmajid. Ta fada cikin lallausar murya. "Hello darling Abdulmajid, Sajimajid ce, kar ka damu ba flashing nake ba wallahi wayar wata girl ce 'yar gidan masu naira. Ka san nawa ne a cikin wayar? Naira dubu shida, ka ga za mu iya kaiwa tsakar dare muna magana." Furera ta dubi Sajida ta ce, "Shegiyar yarinya. marar jin magana, ai sai ki shiga daki ki yi wayar kafin Malam ya shigo ya hada mu dukka ya zage." Sajida ta ce, "Umma ba abin da nake fada muku kenan ba, ga Zahra nan ita iyayenta sun yarda ta kula samari, na tabbata saurayinta ne ya hada mata wayar nan, yake zuba mata kudi." Furera ta ce, "A to 'ya'yan masu hali ma kenan balle mu 'yan Allah Ya baku ku ba mu. Laifin mahaifinki ne da ya hana." Abdulmajid da yake kan layi har yanzu yana jin abin da Sajida da mahaifiyarta su ke fada. Ya yi murmushi ya ce, "Ki ce kina magana a wayar big girl, wanne irin model ce." Sajid ta ce, "N85 ce." Ya ce, "Lallai babbar harka take yi. Ya ya sunanta ko Allah zai sa wani lokaci in kira layin kuna tare ta ba ni ke mu yi magana?" Sajida ta ce, "Ina jin Zahra sunanta, but l'am not Sure, kar ka damu ta zo ne za ta tafi ba lallai ne mu sake haduwa ba, mu yi maganarmu kawai." Sajida ta dubi Zahra, ta juya ta dubi mahaifiyarta sai ta ga gaba daya sun zura mata ido su na kallonta su na sauraronta. Sai ta ji kunya ta tashi ta shiga daki ta cigaba da yaryada masa zakakan kalamai na so da Kauna. Malam ya turo Yahuza fiye da sau biyar kiran Zahra ta fito za su tafi, babanta ya gaji da jira. Ba Zahra, ba dalilinta, domin har yanzu Sajida ba ta gama da wayar ba. Ita kuma nauyi da kunya ya hana ta je cikin daki ta sami Sajida ta karbi wayarta. Sai da Malam ya shigo da kansa ya sami Zahra a zaune a inda ya barta ya dube ya yi dariya. Ya ce, "Zahra hira ta yi dadi ko? Abbanki ya ce ki zo ku tafi, nayi-nayi ma ya barki ki kwana ya ce gobe da safe akwai makarantar boko:" Zahra ta sunkuyar da kai kasa ta ce, "Baba yanzu zan fito Sajida nake jira tana daki tana..." Furera ta katse ta ta yi sauri ta mike tsaye ta ga asiri zai tonu. Ta ce "Sajida take jira ta fito ta raka ta, ka san har sun zama kawaye, wato dai yau rakiyar kura za a yi idan ta raka ta ita ma sai kaga ta rako ta. Bari in kira Sajidar a daki ina ga kuka ma take yi na rabuwa da zahra in ce ta zo ta rakata." Malam ya ce, "Kai rakiyar meye za a yi ta yi mu tafi kawai." Zahra ta mike ta bi Malam a baya suka nufi qofar waje. Har sun kai zaure sai ta ji Umma Furera ta jawo hannunta ta cikin hijabi ta sunna mata wayar a hannunta, gami da yi mata rada a kunne. Ta ce, "Yarinya kar ki fadawa Malam ko mahaifinki sai ya yi fada." Zahra ta gyada kai ta duqa ta ce, "Na gode." Malam ya waiwayo a fusace ya ce da Furera. "Me ye kuma kike yi ma ta rada?" Umma Furcra ta yi sauri ta ce, "Lah! Ba komai kudin mota na ba ta." Sai ta tuna da mota suka zo sai ta ce, "Au! Kudin da za ta sayi 'yar alewa ta kaiwa Kannenta." Malam ya yi murmushin jin dadī ya ce, "Madalla Allah ya saka da alkhairi, to ki koma ciki rakiyarta isa." Mamaki marar musaltuwa ya rufe zuciyar Zahra da ta ga babba tana karya. Furera ta dade a zaure tana leken Zahra da mahaifinta har suka shiga mota suka tafi. Zahra ta na zama a cikin mota ta dubi mahaifinta. Ta ce "Abba ka yi hakuri na dade." Ya girgiza kai ya ci gaba da tuki. Ya ce, "Ba damuwa. Ina fatan kin ji dadin ziyarar da kika kai?" Ta ce "Eh, to gani nan dai, na yi farin ciki ban yi farin ciki ba." Bakura ya waigo da sauri ya dubi Zahra yayin da ya ji zuciyarsa na bugawa, don fargaba. Ya tambaya ya ce, "Me yasa kika fadi haka MamaKai ka fi cancanta Na 👇🏻👇🏻👇🏻 Ta yi dan murmushi ta ce "Abba Sajida da Umma Zuhuriyya ta yi kama ko Mamarta Furera?" Bakura ya yi shiru na dan wani lokaci sannab ya ce "Sajida da mahaifiyarta Furera su na kama ne?" Zahra ta girgiza kai Ta ce "Ba sa kama kwata-kwata. Mamar Sajida fara ce sol, amma duk fuskartka tsage-tsage irin na Fulani kuma ita mai qiba ce sosai. Hancinsu ba iri daya ba, bakinsu, idonsu, kafarsu, qirar jikinsu, duk daban-daban ko kadan ba su yi kama ba. Sajida tana da kyau sosai ta fi mahaifanta da wannan qanin nata Yahuza kyau." Bakura ya yi shiru yayin da tsananin rudanin da yake ciki ya sake linkuwa a zuciyarsa. Ya dade ya na tunani a ransa. Ya na kuma tambayar kansa da kansa, "Shin ya ya aka yi haka? Ta ina Sajida ta samo kamanninta, tunda ba ta yi kama da mahaifinta ko mahaifiyarta ko qanninta Yahuza ba? Ita kadai kamarta daban, kuma sak kamar Zuhuriyata. Qalu innalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Kamar daga sama ya ji Zahra ta ba shi amsar duk wadannan tambayoyin da ya jero a cikin zuciyarsa. Ta ce "Abba, ikon Allah ya wuce haka. Allah Ya na tsara halittarsa yadda ya nufa. Zai iya halittar d'a bai yi kama da uwa ko uba ba, a can cikin dangi sai ya yi kama da wani d'orin d'osano. Ko kuma ma sai su yi kama babu danganta ko daya." Ya gyada kai ya ce " zai iya faruwa kadan daga cikin ikon Allah." Zahra ta gyara zama ta ce " bana son Sajidar nan don bata da tarbiyya bata jin maganar iyayenta kuma mamarta ke taya ta." Wannan karon kallonta ya yi da sauri cike da mamaki har da bude baki. Cikin rawar murya ya tambaya " me ta yi ?" Zahra ta tabe baki ta ce " da alama Babanta ya hana yin waya da samari sai ta taka turmi ta leqe maqwabta ta ari waya ta yi masa." A tsakiyar titi ya taka burki ya tsaya Allah Ya sa babu mota a daf da shi da an buga masa. Zahra ta firgita matuqa ganin yadda ya razana abin har ya bata tsoro. Da kyar ya dawo hayyacinsa sannan ya gangara gefen hanya ya tsaya. Zahra tana jero masa tambayoyin da ya gagara bata amsa mata. " Abba me ya faru? Me ya as ka taka burki? Me ya as muka tsaya?" Ya dade a kishingide a jikin kujera ya rufe ido ya dago ya gyara zama muryarsa na rawa ya ce " bank labarin abinda ya faru dalla dalla." Zahra ta bashi labarin komai amma bata ce an karbi aron wayarta ba, dan kada ya huce akanta yadda ta ga ya hasala yana cije baki. Ya daki sitiyarin motar da qarfi ya na magana cikin jin kakkausar murya da fusata. " daga yau babu ke babu Sajida, kada ki sake cewa in kai ki ki ga me kama da Zuhuriyya. Na yi kuskure, na yi nadama, daman ban kawo ki ba." Haka yake fada yana nanatawa kamar karatu. Ya tashi mota ya fisga kamar zasu tashi sama. Zahra ma ta yi nadamar zuwanta gidan su Sajida da kuma bawa mahaifinta labarin abinda ya faru. A lokacin fadan yin samari a boye ya taso har suka isa gida gargadi ya ke yi mata akan kada ta biyewa qawaye masu yin samari kada itama ta ce za ta yi saurayi ko a makaranta kada ya ji ko ya gani. Duk ranar da ya kamata da maganar saurayi sai na lahira ya fi ta jin dadi. Da alama Bakura ya kwana bai yi baccin kirki ba, walwalarsa ta ragu kowa ya kasa gane kansa. Zahra ce kadai ta sani ita kuwa ba zaa ji mutuwar sarki a bakinta ba. Aiki ya shawa Bakura kai bai samu ya je wajen Malam Yakubu daukar karatu ba sai bayan kwanaki hudu. Ranar da ya je kuwa ko karatun bai tsaya ya dauka ba sai da ya fayyacewa Malam komai akan halinda Sajida take aikatawa a cikin gida. Ya fada ne dan tausayin Malam Yakubu ya na qoqarin yin tarbiyya amma ana ruguza masa. Yadda ya ga hankalin Malam ya tashi sai Bakura ya shi ga lallashi akan ya kwantar da hankalinsa ya bi abin a hankali. Ya qara saka ido kuma yayi mata nasiha da addua . Malam ya amsawa Bakura da "insha Allah ba zai aikata wani abu marar dadi cikin fushi ba, zai bi abin a hankali." Anan suka yi sallama Bakura ya juya ya tafi gida. *** *** **** Malam ya shigo cikin gida ya iske Umma Furera da yaranta su na zaune a tsakar gida. Bayan ya yi sallama bai ce komai ba, sai kawai su ka ga ya tunkari Sajida ya zakulo wata qatuwar bulala dorina mai baki biyu daga cikin aljihunsa ya fara shadada mata a doron bayanta. Ta na ihu saboda azaba, amma ta kasa gudu a sanadiyar cukuikuye kanta da ya yi a cikin burgujejen hijabin da ta zunbula. Umma Furera ta zaburo da gudu za ta kwace ta sai ta ga alamunsa ya na niyyar zanbada ma ta, idan ta kuskure ta qaraso inda yake. Sai ta daka tsalle gefe ta na kwakwazo ta na cewa "Malam me ta yi maka? Kar ka kashe ta fa." Malam ya daki Sajida har ya gaji liqis yayin da ya tabbatar ya farfasa ma ta baya, sannan ya rabu da ita. Tun muryar Sajida na fitowa ta na ihu har sai da ta dishashe kamar mai mura. Ta fadi a q qasa ta yi shame-shame ta na nishi mai hade da kuka. Yahuza kuwa tuni ya arta waje da gudu a tunaninsa dukan kan mai uwa da wabi ake yi duk wanda aka samu zaa daka. Malam ya dubi Umma Furera ya juya ya dubi Sajida ya ce "Wannan somun tabi ne, kadan ku ka gani. Ni da ku mu zuba a cikin gidan nan. Ni da Abdulmajid zan ga wa za ku zaba, idan na jinyata ki ko na tsiyaye miki ido ai kun ga Abdulmajid zai guje ki don daman ba son Allah ya ke yi miki ba. "Umma Furera ta zabura ta ce,"Wanne rin Abdulmajid kuma? Tsohon zance, yaushe rabon Sajida da maganar wani Abdulmajid? Ai tunda ka kwace wayarta zance ya wuce." Malam ya daka mata tsawa ya ce "rufe min baki maci amana, ba a gabanki take hawa katanga ta ke karbar aron waya ta na yi wa dan iskan yaron nan Abdulmajid waya ba. To zamanku ku dukka ya kusa qarewa a gidan nan, don wallahi idan na sake jin wata magana game da Abdulmajid sai na kore ku daga gidana, sai dai ku koma gidan Abdulmajid din." Ya fice qofar gida a fusace ya na huci. Umma Furera ta qaraso wajen Sajida a guje, ta tashe ta zaune gami da yaye hijabin da ke jikinta ta wurgar gefe. Ta kwaye rigar don ta ga irin raunin da ya ji mata a bayanta, sai ga shatin bulala sharba-sharba fatar duk ta farfashe ga jini. Umma Furera ta dau kukan mutuwa ta na cewa "na shiga uku, wannan wacce irin kiyayya Malam ya ke yi wa Abdulmajid haka ne. Akan Abdulmajid ya na qoqarin ya kashe 'yarsa ta cikinsa. Wannan wanne munafukin ne ya ke bibiyarmu, duk abin da mu ka yi akan idonsa ya kwashe ya fadawa Malam?" Cikin sheshsheqar kuka Sajida ta ce, "na san Yahuza ne, gashi nan ya ruga da gudu daga gani an fara dukana." Umma Furera ta ce, wallahi kuwa shi ne zai fada masa. Idan ba shi ba to waye a cikin gidan nan? Lallai yau Yahuza sai ya yabawa aya zaqinta, sai ya gwammace bai barka ni ya fito daga cikin cikina ba, domin ni ba zan haifi dan da zai jawo a tozarta ni a duniya ba. Tozartawa mana idan muka sake Malam ya kore mu daga gidan nan, sai dai mu koma ruga mu yi tallar nono mu da muka saba zama a burni. Mu sha lafiyayyan kunu, ga dan wake har da albasa da salad, tuwan masara da na dawa sai wanda muka zaba. A sati mu ci shinkafa sau biyu. Naira biyar dinka ta isa ka sha pure water mai sanyi. A ruga a ina za mu ga firji?" Wani qululun bakin ciki ne ya tokare wuyan Sajida game da maganganun mahaifiyarta. Ta fada a fusace "Umma ke ta ruwan sanyi da shinkafa kike, ni ta Abdulmajid nake. Yanzu duk motsin da na yi tare da Abdulmajid sai an fadawa Baba ya dake ni. Ba ni da wata hanya da zan ji muryar Abdulmajid kuma a rayuwata bayan haramta min ganinsa da aka yi kwata-kwata. Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai Baba ya kore mu ai gara mu koma rugar kin ga Abdulmajid zai dinga zuwa ya na ganina, idan aka daura mana aure sai in tafi da ku gidana shi kenan mu rabu da Baba." Umma Furera ta daka tsalle ta dafe kirji da hannu biyu ta zazzare ido ta ce, "rufa ni ki saya ni 'yar nan, kar ki min sakiyar da babu ruwa. Yaushe za a yi wannan danyen aikin da ni? Ai kuwa in ba ki rabu da Abdulmajid ba za mu raba hanya. Yaron mayaudari. Aka ce miki aurenki zai yi? Ai ni tunda na rabu da ruga fulani insha Allah ko gawata anan birni za a bunne ni. Wannan wasiya ce na bar miki. Haka idan Malam ya shigo zan bar ma sa wannan wasiyyar. Kuma zan shiga maqwabtan idan Malam baya nan, sai na ja kunnen Iyayye da take miqo miki aron waya in kada ta sake baki. Ahirr dinta kar in ji kar in gani. Ko Abdulmajid din ne ya bugo ya ce a baki ta ce mahaifinki ya hana ku yi magana. Ke in ki na da zuciya ma har za ki tsaya ki na shan duka akan dan iskan nan Abdulmajid, yaron da ya ke shigowa har zaure ya na zagin mu ya na kiranmu mutsiyata. Idan da gaske yake son naki ba lalata yake nema ba, ai ko boye zai ringa ambulo miki kudi, amma ni dai ko sisinsa ban taba ci ba sai alewa cakulet mai zaqi da askirim babu abin da su ke qara min illa su sagar min da hakora. Ni ba atamfa ko leshi yake aiko min ba. Idan ya yi tafiya ne yake ciko leda da riga da skirt da wanduna ya ce ga nawa ga naki. Dan iskanci ya dube ni ya aiko min da jeans da T-shirt. Har da suyo tafka-tafka wanduna wato daidai jikina in tsuke in fita qofar gida cikin almajirai mu yi wakar Micheal Jackson kenan, ko mu yi rawar nanaye." Sajida ta fusata ta miqe da sauri ta na buga qafa, ta shiga cikin daki ta na cewa "To wallahi tunda takura min za'a yi, cikin dare zan hada kayana a neme ni a rasa tunda abin haka ne." Umma Furera ma ta na ta babbamin fadanta a gindin murhu inda ta kunna itace ta dora ruwan zafi cikin qatuwar tukunya don gasawa Sajida jikinta don duk ya farfashe. Bayan Umma Furera ta gamawa Sajida gashin baya da tsumma da ruwan dumi, ta umarci Sajida ta daure ta shiga bandaki ta yi wanka da zazzafan ruwa, saboda ciwon jiki. Bayan Sajida fito daga wanka suka dasa kujerar zama su na jiran shigowar Yahuza, domin su dauki fansa akan masifar da ya jawo mu su a sanadiyyar gulma, munafunci da tsegumi dukka ya iya. Shiru-shiru Yahuza bai shigo gidan ba, dare ya fara nutsawa, goma tayi har Malam ya shigo ya shiga daki ya kwanta babu Yahuza, babu dalilinsa. Daga nan su ka gasgata zargin da suke yi wa Yahuza cewar shi ya aikata, don haka ya qi dawowa. Ba su damu su dauki gyalensu su fita nemansa ba, haka ba su damu su fadawa Malam cewar har yanzu Yahuza bai shigo gida ba. Daman ya saba idan ya ga dama ya kwana a qofar gida cikin almajirai. Idan ya so ya kwana da almajiran zaure, haka idan ya so ya shigo cikin dakinsa ya kwana. Daman ba rufe gida ake yi ba qofar daki ake sakayawa. Don haka Yahuza bai dawo ba su ka gaji da jira sai suka yankewa kansu shawara su tafi su kwanta.Allah ya kai su gobe ai dole zai shigo da safe daukar kayan makaranta a dakinsa, to anan sai su yi caraf su damke shi. Umma Furera ta shiga dakinta, Sajida ma ta shiga na ta akurkin. Kowa ya jawo bushashshen katakon da aka laqabawa da suna qofa ya rufc. Sabanin Umma Furera Wacce tana shiga daki minti biyar ya yi yawa ka fara jin jiniyar munsharinta na tashi, amma Sajida fiye da awa biyar bacci ya yi wa idanuwanta yajin aiki. Juyi take akan 'yar kațifarta yaloluwa irin ta 'yan makaranta, ta kasa bacci saboda tsananin takaici da tashin hankali. Sai a lokacin ne ma ta yi kukan dukan da aka yi mata, don dazu azaba ta hana ta kuka. Sheshsheqa take tana ajiyar zuciya, fadi take bayyane. "Wayyo Majid dina." Kaico! Soyayya gamon jini, ko shi Abdulmaji din da ake yi dominsa a wanne hali yake a daidai wannan lokaci? Ohoooooo!!! Asubah ta gari SajiMajid. *** *** *** Washe gari da sassafe Sajida ta fito tsakar gida tana mika game da doguwar hamma, ta cije baki ta matsa gabobin hannayenta ta danna doron bayanta, saboda ciwon da suke yi mata a sanadiyyar bugun da ta sha.jiya. Umma Furera kuwa tunda Asuba kiran fari ta hau hidimar dora ruwan koko da wainar geron da take yi da safe ta siyarwa, dan haka tana gindi murhu a tsakar gida. Malam kuwa tun kafin kiran fari na asuba ya yi alwala ya fice, sai kuma da hantsi zai shigo gida. Yahuza ne ya shigo cikin gida cike da fara'a da farin ciki. Wata qaramar baqar leda ce a hannunsa. Ya dubi mahaifiyarsa ya juya ya dubi Sajida bai kula da kibiyoyin harare-hararen da suke harbo masa ba. Yayi dariya ya ce, "Kun san meye a cikin ledar nan kuwa? Soyayyan dankalin turawa ne da kwai, na bi almajirai bara cikin Badawa layout gidan da Abashe yake aiki aka ba mu sadaka. Ashe almajiran nan dadi suke ci. Nima daga yau idan zasu je sai na bi su. Wallahi attajirai nan wayo suke yi mana dadi suke ci. Idan Baba baya nan almajiran nan zan dinga bi bara. Haka jiya shinkafa da kaji muka ci a qofar gida. Muzanbilu ne ya samo mana." Umma Furera ta daka masa tsawa, ta ce "rufe min baki munafuki, kai za ka yi laifi a rufa maka asiri, amma kai ka kwashi maganar da ba a saka a ciki ba ka je ka yi gulma. Yau sai na fasa maka baki. Bari Malam ya shigo, sai na fada masa ashe har yanzu ka na zuwa bara." Sajida ta fisgo ledar dankalin da ke hannunsa ta zazzage a cikin bokitin sharar da ke kusa da ita, tasa tsinke ta daddanna ta cakuda da bolar. Yahuza ya ji tamkar 'ya'yan hanjin cikinsa ta yi wa haka. Don a halin yanzu ya fi son dankalin nan akan rayuwarsa. Ya kwalla wani ihu kai ka ce ransa ake kokarin fitar masa. Ihu yake ya na kiran "Wayyo dankalina, na shiga uku na lalace. Wallahi sai na fadawa Baba." Sajida ta ce, "Ka fadawa Baba ka tonawa kanka asiri, daman ai ya hana ka zuwa bara." Sajida ta jawo shi ta durkusar a gabanta, sannan ta kwaye masa riga ta bayansa, sai ga doron bayansa muraran ta dauko takalmin danko ta yi ta lafta masa, ya na ihu ya na tambayar abin da ya yi mata. Kamar yadda lokacin da Malam ya dinga nadarta ba ji ba gani, har sai da ya gaji haka ita ma ta lode shi har Sai da ta gaji da kanta, ta sake shi. Bayan da ta tabbatar bayansa ya dau shaida kamar yadda na ta ya dauka, wannan tabon in ba sa'a ta ci ba har mutuwarta ba zai bace ba kuwa. Umma Furera na can ta na saka gayan koko fadi take, "Bar shi haka, ai ya daku." Yahuza ya laftu a qasa ya na narkar kuka gami da gungunin da ba a fahimtar abin da yake cewa ba. Amma idan kunnuwansu ba su yi kuskure ji ba sun jiyo musu yana cewa, "Haka kawai dan cin zali ki yi ta dukana babu abin da na yi miki." Umma Furera ta fada cikin daga murya ta ce, "Ka san abin da ka yi mana. Idan ba ka san abin da ka yi ba yaya za a yi daga fara dukan Sajida za kä arce waje ba ka sake shigo ba sai yau." Sajida ta zo ta murde masa kunne ta ce, "To bari in karanto maka abin da muke nufi. An yi walkiya mun ganka munafuki asha kai ne ka ke zagayewa ka ke fadawa Baba maganar Abdul majid. Ka dade ka na hada min tuggu, kasa na bata da mutane da yawa, wadanda kake cewa sune suke fadawa Baba in an ganni da Abdul majid. Musamman na rannan da na fita karbo littafi a gidan su Asiya na hadu da Abdulmajid ina dawowa gida Baba ya shigo ya yi min duka har ka ke ce min wani mutum ne ya zo a mota qofar gida shine ya fadawa Baba har da cewa za ka nuna min mutumin.Ashe babu wani mutum kai ne munafukina. Idan rannan ka ce wani mutum ne ya ganni a waje ya zo ya fada, a cikin gidan nan da nake hawa katanga ina karbar aron waya ina kiran Abdulmajid waye ya shigo ya ganni, shi ma munafukin mai motar ne ya zo ya fada?" Umma Furera ta ce, "Ke kike biye masa ma, kike maganar wani mai mota, wanne mai mota ne ya zo ya fada? Wanne babban mutum ne mai mota wanda ba shi da ailkin yi har zai zo ya ce ya ganki da Abdulmajid? Yaushe wani mai mota ya sanki har ya san gidanku, har ya san a gidanku an raba ki da Abdulmajid kin ki ji? 'Yan unguwar nan ne kawai suka sanki, suka san Malam ya raba ki da Abdulmajid su ne suka sha kawo gulma, kuma babu wani mai mota a cikinsu. In har da gaske ne ka fadi sunan mai motar mana, ai kai ne idon gari babu wanda baka san shi a cikin unguwar Kawon nan ba, har unguwar Giginyu shiga ka ke ka nemo labari." Sajida ta ce, "Ga gaskiya ma ta fito abu a cikin gida akan katanga har Malam ya sani na san da Iyayye ba za ta fada ba ta ce ita take ba ni aron waya in yi, idan ta fada ma ta tonawa kanta asiri, don sai Malam ya shiga har gida ya zane ta. Babanta ma idan ya ji sai ya kwace wayar. Waye zai fada in ba kai ba" Yahuza ya zabura ya miqe tsaye cikin kuka yana cewa, "Wallahi ban taba fadawa Baba ki na aron waya ta katanga ki na yi wa Abdulmajid waya ba. Saboda na san irin dukan da yake yi miki. Ni kuma tunda ku ka ce ni na fada masa, Baban ya zo nan gani, ga shi, ga ku a tambaye shi idan na fada masa wata magana. Yaushe ma muke zama da Baba mu yi hira shi da yake da baqi ko da yaushe kora ta yake ko na zauna a cikinsu." Yahuza ya fice da sauri ya na kuka sharkab. Sajida da Umma Furera suka bi shi su na kwalla kiran sunansa, amma abu ya ci tura. Tuni Yahuza ya keta zaure, ya wuce dandamalin qofar gida, ya tsallake kwata, ya bi ta kan bola ya tunkarí masallaci. Bai dire a ko'ina ba sai a lungun liman a gaban mahaifinsa. Yahuza. magana take amma ba'a fahimtar abin da yake fada wani tsatstsaman kuka da yake tasowa daga can cikin zuciyarsa a inda jiyiyoyin idanuwansa suke zuqo wani ruwa mai dumin gaske su na fesarwa saboda tafarfasar da zuciyarsa ke yi da tsananin quna da soyuwa. Malam ya dade ya na tambayarsa haka Yahuza ya dade ya na bada amsa, amma ganewa ta ci tura, saboda hayaqin da bakinsa yake na takaici. Malam ya kamo hannun dansa, abin qaunarsa Yahuza ya nufo gida don jin ba'asi. Sajida tsaye take a tsakar gida ta na kai kawo cikin zulumi da fargabar abin da zai je ya zo. Fada take, "Umma, kar fa yaron nan ya je ya hada min tuggu, Baba ya zo ya sake yi min duka irin na jiya." Ta na rufe bakin sai ta ji sallamar mahaifinta ya danno kai cikin gida riqe da hannun Yahuza. Ta zabura ta daka tsalle sai ga ta a bayan Umma Furera ta buya. Malam ya fada cikin sanyayyiyar murya, "Tsaya daina gudu, ba dukanki zan yi ba. Don me zan dinga dukanki kamar jaka? Ai bambancin dabba da mutum shine hankali shi ne tunani da jin magana. Me yake faruwa ne Yahuza ya je min da kuka?" Da Yahuza ya ga sun fara hanya-hanya su na qoqarin baudewa su gyara magana, sai ya yi qoqarin kashe gobarar da take ci a makogaransa, don ya ceto muryarsa ta fito radau dan ta cece shi. Ya rangada bayani tas yadda aka yi tun daga farko har karshe. Kan ka ce kwabo idanuwan Malam sun ciko da hawaye, ya dubi Yahuza duba irin na tausayi. Ya sa hannu ya share masa hawaye. Ya ce, "Allah sarki, sun dauki alhakinka, sun zarge ka da laifin da ba ka aikata ba. Sun yi kuskure wajen yanke maka hukunci. Idan ba yafe musu ka yi ba, Allah sai ya kama su da hakkin zalumci. Ka je ka saka kayan makarantarka, ka karbi koko ka sha ka zo in raka ka makaranta, saboda sun sa ka makara." Yahuza ya nufi dakinsa ya na goge hawaye yayin da zafin da ke qona zuciyarsa ya fara hucewa a sanadiyyar haqurin da mahaifinsa ya ba shi. Malam ya juya ya dubi Sajida da mahaifiyarta wadanda kowannensu ya yi wuqi-wuqi da ido a lungu su na jiran hukunci a game da ta'addancin da su ka aikata da sanyin safiyar nan. Ya ce, "Kun dauki alhakin yaron nan, ku nemi gatararsa wallahi Yahuza bai taba fada min wata magana game da Abdulmajid ba, sai dai ma ya dinga boye min abin da ke wakana don kada in doke ki. Kin manta irin tashin hanklin da yake shiga tun ya na yaro idan ina dukanki?Kin san dai ba na tsoronki kuma ba na mahaifiyarki, da har zan yi muku rantsuwa Alan dan kar ku qara dukan Yahuza. Ina da ikon da zan saka dokar kada a qara dukan Yahuza har ya girma, kuma dole a bi maganata. Dan haka kar in sake ji ko in gani an bakantawa yaro a bisa laifin da bai ji ba kuma bai gani ba. Ko yau kika kula Abdulmajid a fili ko a waya labari zai ruske ni, zan dauki mataki mafi tsaurin gaske akan ku, ku dukka." Daidai lokacin Yahuza ya gama shan koko ya dauko jakar makarantarsa, Malam ya kama hannunsa suka fice ya raka shi har cikin Giginyu Primary. Sajida ta sulale ta zaune gami da jan wata doguwar ajiyar zuciya mai dauke da jimami hade da rudani. Haka Umma Furera ta shiga irin wannan hali ba shiri ta lalubo 'yar kujerarta ta zauna ta doka tagumi. Lokaci mai tsawo aka dauka aka rasa wanda zai fara magana a junansu. Ba tare da Sajida ta yi niyyar furtawa ba bakinta ya yi caraf ya fitar da tambayoyin da suka addabi zuciyarta. "Wannan wanne munafikin ne yake bibiyata akan Abdulmajid? Wallahi sai na gano munafukin nan da yake so ya raba ni da Abdulmajid, ko waye ko kuma ko wacece, duk tsufanta ko kuma duk tsufansa ko da gemunsa ya na ja da qasa, sai na ci mutucinsa na tozarta su ko da yin haka zai jawo a raba ni da numfashina a duniya." Umma Furera ta ce, "hakika na yarda ba Yahuza ba ne ya fada, don da Malam ba zai boye ba. Kuma duk abin da Malam ya yi rantsuwa gaskiyar ta kai gaskiya. Daman Yahuza ban san shi da gulma ba, shi dai a bar shi da kwadayi da roqo. Kash na dau alhakin d'ana." *** **** **** Da daddare misalin qarfe goma, bayan Zahra ta yi sallama da mahaifanta t shiga kwanciyar barci. Ta cikin falonta ta wuce kai tsaye zuwa dakin da gadonta yake. Shigarta ke da wuya sai ta zarce bandaki don ta watsa ruwa. Ta fito ta wuce kai tsaye durowar da ta jera rigunan bacci kawai kala-kala wanda a kalla sun fi kala hamsin. Riga da wando, riga da siket, doguwar riga ba masu santsi da masu laushi (cotton). Ta zabi wata 'Yar yaloluwar riga iya gwiwa ta saka, ta zo ta shiga bargo. Bayan ta gama addu'o'in kwanciya barci ta shafe jikinta tun daga kanta har kafafunta. Ta lumshe ido yayin da sanyin split A.C da ke kunne a dakin yake bi sanka-sanka yana ratsa hudojin jikinta. Ba ta ankara ba sai ta ji wata muguwar girgiza a qarqashin filonta, a tunaninta garin ne gaba daya yake girgiza. Ta tashi zaune gami da daga filon da sauri ta son ta ga abin da ke ciki ashe wayarta ce ta manta ba ta kashe ba, ashe wayar a ta vibration take. Ta yi wata ajiyar zuciya domin tuni numfashinta ya qauracewa huhunta, saboda tsorata. Ta miqa hannu ta dauki wayar ta duba sunan Hassana Ummi Sulaiman ne ya fito dara-dara. Ta yi mumushi gami da farin cikin jin kira daga kawarta, aminiyarta, makarantarsu ta boko wato PRIME COLLAGE, haka Islamiyyarsu daya Hassan Gwarzo islamiyya dake Sulaimanu Cresent. Ta fada cikin tsokana. Ummi 'yar autar Mama ya kike? Ya gari? Ya aka yi kika kai goma da rabi baki kwanta ba, don na ji hayaniyar Nura, Sulaima da Faruk?" Ummi ta yi dariya ta ce, "albishir na kira in miki. Ashe gobe mid-term break ne babu makaranta har muke damun kanmu da karatun test mun manta, sai yanzu Khadija Rabi'u Gumel ta kira ta tuna min." Zahra ta kama kai ta tsuke fuska ta ce, "Oh God! na manta, amma ban ji dadi ba wallahi na karantu sosai. Don dazu bayan na dawo gida daga makaranta da yake babu Islamiyya, Na kira Abbana a waya ya zo ya kaini Kano State Library mu ka yi ta karatu da shi. Ya sake koya min Physics sosai sai qarfe shida muka dawo gida. Shi ma ya manta gobe ba makaranta yanzu ya gama cewa in zo in kwanta, saboda gobe in tashi da wuri. To bari in bar wayana a kunne idan Mama ta tashe ni da Asuba, in ce mata ta yi kwanciyarta gobe hutu ne. Thank you very much Hassana Ummi kin taimaka da kika tuna min. Ki gaida gaida su Mama dan Allah." Hassana Ummi ta ce "Za su ji insha Allah. Good night partiner." Su ka kashe waya a lokaci guda, Zahra ta mayar da waya qarqashin filo ta kwanta tana tunano hirar da suka yi da kawarta wacce koda yaushe Su na tare a wani 6angaren kuma rashi yin makarantar taimaka mata aka yi da aka fasa yin test din saboda yau ta karantu idanuwanta har ja suka yi saboda barci. Ai ko ba komai ta san za ta bar kwakwalwarta ta huta, kafin ranar jarabawar. Sai ta ji wayarta ta sake daukar qara wannan karon mamaki ne ya rufe Zahra. Sai ta ce a ranta, "Na san Sadiya Idris ce ko Bilkisu Hamisu za su fada min gobe ba makaranta, ba su san Hassana Ummi ta riga su ba." Tana duba wayar, sai ta ga lamba ce ba suna, don haka ba su ba ne, amma zai yiwu su din ne ko wayarsu ba kudi suka yi amfani da ta 'yan gidansu. Kamar yadda a da kafin a hada mata waya take amfani da wayar Mamarta wajen kiransu. Ta danna wayar cikin farin ciki gami da cewa. To Hassana Ummi ta riga ku, na sani gobe mid-term break babu makaranta, don haka babu test." Sai ta ji an yi wani lallausan murmushi an ce, "Hello, dan Allah Zahra ce akan layi?" Gabanta ya yanke ya fadi ragagagasss!!!! Domin muryar namiji ce. Tunanin da ya fado mata shi ne, to tunda ba Babanta ba ne yake kira tabbas Baban daya daga cikin kawayenta ne. Abin da ta dauka wata kawarta ce marar waya ta roqi Babanta ya kira mata qawarta shi ne ta ji muryar namiji. Nan da nan Zahra , ta gyara zama ta duka ta gaishe shi cikin ladabi. Ta cigaba da sauraron abin da zai fada mata. Ya na magana cikin sanyayyar murya, nutsatstsiya. Ko wanene wannan mai maganar hakika ya san darajar bil'adama. Tunanin Zahra sai ya fara banbanta da manufar wannan mai wayar, ma'ana ba ta ji ya ce ma ta ga kawarta ba wance. Bayani kawai yake yi mata akan ya yi matukar farin ciki da jin muryarta. Ta gigice yayin da hankalinta gaba daya ya tashi. Ta tambaya cikin wata hardaddiyar murya mai rawar disko, saboda gigicewa. Ta ce, "Malam ko ka yi kuskure ne ka bugo ba ni Zahrar ka ke nema ba?" Ya yi murmushi mai fitar da sigar muradi ya ce, "Ban yi kuskure ba, ke Zahra nake nema, domin lambarki ko daga barci aka tashe ni zan kawo ta." Saboda tsabar firgicewa sai tasa hannu ta katse wayar jikinta ya dau karkarwa tamkar mai jin sanyi.Matukar mamaki ya rufe ta. Ta ina wannan mutumin ya sami lambarta? Me yasa ya kira ta'? Me yake nema a wajen ta'? Babu amsar wadannan tambayoyi na ta.Tana cikin wannan hali sai kuwa ta ji wayarta na girgiza ta sura da sauri ta duba lambar dazu ce, don haka sai ta ki dauka yayin da kuka ya fara rufto mata, tsoro ya addabi zuciyarta ta rasa abin da yake yi mata dadi. A zaune take akan gado ta yi quri, domin kwanciya ta gagari hakarkarinta. Mutumin nan dai bai hakura ba, kira yake sake yi tsakaninsa da Allah. Ta miqa hannu ta danna kai ka ce kashi ne a jikin wayar yadda take kyamar wayar. Ba tare da ta bari ya yi magana ba ta fada cikin kuka da rawar murya. "Malam waye kai? Me kake nema a wajena?" Ya yi murmushi ya fada cikin lallausar murya ya ce "Zahra cool do down my dear, Za ki ji ko ni waye, kuma da kuma dalilin da yasa na bugo miki." Ya yi ajiyar zuciya mai hade da murmushi ya ce "Na san baki sanni ba, kuma za ki yi mamaki da na kira ki, actullaly my name Is Abdulmajid El-Museh ina kira daga Bampai quaters." Zahra ta maimaita sunan, "Abdulmajid El-Museh ban sanka ba, ban taba jin sunan nan ba." Ya yi dariya, "Allah sarki daman na san ba za ki sanni ba. Sai dai ina fatan ki san ni nan gaba," Zahra ta fada cikin fushi, gami da daga murya, "Me yasa ka kira ni, me kake nema?" Ya sake lanqwasa murya ya ce, "Haba baby me yasa kike tayar da hankalinki, ko ban ganki ba daga ji muryarki na san kina da kyau. Ba'a son mace me kyau ta dinga wahala cool down." Zahra ta ji wani dacin takaici yana qokarin shaqe mata wuya, sai wani hawaye mai dumi ne ya ke zubo mata. Hankalinta gaba daya ya tashi, abin da take ji wai-wai-wai a gari ya iso gare ta. Ya katse mata tunaninta ya ci gaba da cewa, Zahra gaskiya abin da ke tafe da ni alkhairi ne, babu komai a ciki sai tsananin so da qauna. Kin fahimce ni ko? I love u so much Zahra." Yayin da Zahra ta dafe qirji, domin ta ji wani abu daga cikin kirjinta ya na zillo zai fado qasa, don a fargaba. Ba tare da ta iya cewa komai ba, ta katse wayar. Daga nan ta tabbata lallai wannan bawan Allah ya dauko hanyar da zai rugurguza Zaman lafiya a gidan nan. Ba ita kadai ba har mahaifiyarta kashinta ya bushe daga lokacin da mahaifinta ya san abin da yake faruwa. Kuma nan da nan Bakura Zai Iya ganewa saboda duk sanda za ta tafi makaranta ya kan karbi wayar ya riqe har sai ta dawo sannan zai ba ta. Haka kuma duk bayan wata yana karbar wayarta data mahaifiyarta ya fita da ita ya sako musu credit. Ya na yawan bincike wayar har wani lokaci ya yi game. Bakura yana yawan ja mata kunne cewar ta kiyaye kada ta sake ta kira saurayi ko wani ya kirata. Ya hada mata waya don ya dinga tashinta da Asuba ko idan ta fita unguwa a kira aji in ta isa lafiya, sai kuma don ta dinga hira da kawayenta mata. Kuka mai yawa ya karu. Ta fito falonta ta zauna a kan kujera yayin da ta dora kafafunta biyu akan kujera tasa hannayenta biyu ta matse kafafuwanta tana mai karanto, "Inna illlahi wa'inna ilaihir raji'un." Wayarta ce a gefenta ta sake daukar ruri, ma'ana waya na shigowa. Ta juya fuskarta a hankali tana duban wayar, saboda tsabar tashin hankali, lambar Abdul majid ce ke shigowa don haka sai ta qi amsawa. Matukar mamaki ya rufe zuciyarta, ta na tunanowa a duniya a ina ma ta ta6a jin mai su Abdulmajid. Don ita ba ta taba hulda ko a danginta na wajen uwa da ba kacokan babu mai irin wannan suna Abdulmajid, sai kira yake tun karfi. Ya kira ta yi ringing har ta gama Zahra ta qi ta amsa. Sai ta ji massage ya shigo. Cikin rawar hannu ta dauki wayar ta bude sakon, ta ga dai har yanzu Abdul majid ne abin da ya rubuta kuwa shi ne kamar haka: Hi sweety, answer my calls. I will explain pls. Ma'ana ya abar zazzaqar kauna ki amsa wayata žan yi miki bayani." Firgita kan firgicewa yayin da ta kwatanto a zuciyarta ace mahaifinta ne ya bude sakon nan wayar na hannunsa, ya ya za ta yi ai na lahira sai ya fita jin dadi in ji Bahaushe. Abdulmajid ya cigaba da kira, Zahra ta yanke hukunci mafi sauki akanta gara ta dinga amsa wayarsa akan ta qi amsawa idan ya ci gaba da turo mata irin wadannan sakonnin matsala ne. Amma in waya ce a gaban iyayenta ta iya dauka ta ce wrong number ta katse, amma idan a rubuce ne babu mai fitar da ita sai Allah. Zahra tasa hannu ta danna ma'ana wajen amsa waya, ta fada cikin dakakkiyar zuciya, domin tsananin tsoron da take ji ya fita yanzu, fatanta ta kwaci kanta. Ta ce, "What do you want from me?" A wannan karon shi kuma tasa muryar ce take karkarwa. Ya ce, "Zahra ki saurare ni mana ina sonki ne, na yi miki alkawari zan canja miki rayuwarki. I will do anything for you." Ta fada cikin fushi, "Kamar ya ya?" Ya ce, 'Waya mai tsada, in zuba miki kudi a ciki account babu adadi, English wears kala-kala. Ke zan iya siya miki mota saboda ina sonki, ki rabu da sauran samarinki..." Ta daka tsawa ta katse shi ta ce, " enough is enough, ka sanni kuwa? Ka san yaya nake? I'am a small girl, I am just 15yrs ya za ka dinga kirawo min sunan samari? Ya za ka ce za ka siya min mota? Me ye Abbana ba shi da shi da kake so ka nuna min kudi? Abdulmajid please I beg you ka rabu da ni kana so ka jawo min matsala infact ka jawo abin da Abbana zai aikata kisan gilla a kaina ko a kanka. Akwai manyan 'yan mata a gari ka je ka tsara su ka rabu da ni please. Yaushe ka san ni? A ina ka sami number na for God sake, za ka jawo min problem." Sai ta fashe da kuka. Abdul majid ya fada cikin nadama da tausayawa "Oh God baby don't cry. Ni mai sonki ne zan kawo miki farin ciki ba zan jawo miki problem ba. Na sami number a dalilin wata sister ta Sajida." Zahra ta dakata da kukan ta maimaita sunan "Sajida, Sajida, Sajida." Har sau uku a inda kwakwalwarta take kai kawo tana so ta tuna inda ta taba jin mai suna Sajida ta na ta kokarin tuna a duniyar da ta taba haduwa da mai suna Sajida a rayuwarta. Abdul majid ya ci gaba da cewa, "Ba kawarki ba ce Sajida? Ai ta taba kiraną da wannan lambar anan na sami lambarki, ta fada min sunanki Zahra." Zahra ta sake maimaitawa, "Kawata Sajida, a ina nake da qawa Sajida? Ni gidan wacce kawa ake barina in je?" Abdul majid ya ce, "Common baby, ki tuna mana a cikin satin nan Sajida ta kira ni da wannan lambar da yamma. Baki tuno Sajida Yakub Kawo ba?" Sai a lokacin computer kwakwalwarta ta fito mata da Sajida muraran ta gane wacce yake nufi, sai ta ji wani sanyi a ranta, ta fada cike da murna. "Okay na gane Sajida a Kawo ka kira ne a bata waya, ai bama tare. Ko ba SajiAbdulmajid ba budurwarka. Ai Sajida aminiyata ce duk sanda mu ka hadu zan kira ka in ba ta waya saboda haka ba sai ka qara kira ba." Abdulmajid ya yi dariya ya ce, "Kina da wayo da yawa Zahra. Tunda kin fahimci Sajida budurwata ce, no need in boye miki harma kin riqe sunan da ta hada Sajimajid. Abdulmajid so yake yanzu in zama na an hada mana SAJI-ZAH-MAJID ma'ana Zahran Abdulmajid." Zahra ta tsuke fuska yayin da wani mummunan sabon tashin hankali ya far mata. Ta mike tsaye a fusace. Ta ce "Kai ba zai yiwu ba, ba zan iya ba, ba zai yuwuwa ba. Gara ka rabu da ni tunda wuri kafin mahaifina ya sani. Kar ka kara kirana. Ka zama mai bata tarbiyyar da iyaye suka yi wa ya'yansu. Mace kwarya ce me kyau wacce iyayenta suka adana ta suka saqale ta a ragaya, don karta fito tsakar gida a yi amfani da ita ta yi datti. Amma kai ka zuga kwaryar an mai kyau take ballowa daga ragaya take fita titi tana tunbele kana garari da ita, har sai da ta baci, sannan ta zagayo ta haye ragaya kamar ba ta yi datti ba a tunanin Iyayenta, kwaryar nan ta su tana nan da kyawunta," Ta ci gaba da cewa "Abdulmajid, Abbana ya ce ni kwaryarsa ce mai kyau, ya saqale ni a ragaya don kada in yi datti ya ce min yana fatan wannan kwaryar tasa ba ta fakon idonsa tana ballowa tana fita ta yi yawan garari ta yi baki ta zo ta d'ane a ragaya, kamar wata kwarya ta gari kamar yadda Sajida ke yi." Zahra ta na gama fada sai ta murtsike wayar gaba daya ta kashe. Yayin da take murza idanuwanta ta ji ko mafarki take a cikin barci. Ta ga daram ba mafarki ba ne, ido biyu ne. Babu abin da take hangowa a cikin idanuwanta sai lokacin da suke tafe da mahaifinta a mota bayan sun taho daga gidan su Sajida sanda ta yi masa zancen Sajida ta na lekawa katanga ta ari waya su yi magana da saurayi. Hankaiinsa ya yi matukar tashi kamar zai jawo ya dake ta ita mai ba shi labarin. Ina ga idan ya ji ita ce take zance da saurayi a waya? Jikinta na karkarwa ta koma kan doguwar kujera ta takure yayin da wannan dare ya zame mata shine daren farkon da ta taba haduwa da irin wannan gagarumin tashin hankali a rayuwarta ta duniya, tun da Allah ya halicce ta. Dan haka yau ne dare na farko da barci ya kauacewa fatar idonta. Yadda ta ga rana, haka ta ga dare tana zaune tana tunani. Ba tare da tasan Asubah ta yi ba, Abbanta ya gwada kiran wayarta ya ji a kashe, don haka sai ya zo da kansa har kofar dakinta yana bugawa. Saboda tsabar ba'a cikin hayyacinta take ba, haka ta zurawa kofar ido tana kallo ta manta idan ka ji ana buga kofa budewa ake a ga ko wanene. Muryar mahaifinta ta ji ya ce "Yagana, bude kofa mana. Wanne irin bacci kike yi haka ne?" Sai ta yi firgigit ta tashi zaune daga kishingiden da take ta amsa cikin rawar murya. "Na'am." Ta yi duru-duru ta fisgo wani 'dogon hijab ta maqala ta bude kofar falon da sauri. Nan, aka hau kallon-kallo tsakanin Zahra da mahaifinta. Shi ya na kallonta saboda yadda yaga tana kallonsa galala tana zare ido kamar wata sabuwar tababbiya da alama idanuwanta su na tattare da barci mai yawa don sun yi luhu-luhu. Ita kuma tana ganin mahaifinta sai tsoro ya kamata don ta kwatanto irin tashin hankalin da za a yi duk lokacin da ya kama ta Abdulmajid ya bugo mata waya ko ya turo mata sako ta waya. Bakura ya fada cike da mamaki, "Mamana, lafiyarki kalau kuwa? Kin yi bacci yau ko karatun test din kike yi tun dare?" Zahra ta ji dan sanyi a ranta da ta ji ya fadi haka, ta amsa da sauri. "Eh karatu na kwana ina yi." Bakura ya yi shiru na wani dan lokaci, sai ya girgiza kai. Ya ce "Ba kya jin magana, maimakon ki yi bacci yau ki tashi a nutse meye amfanin kin kwanciya ba ki yi barci ba, ki shiga dakin jarabawa kina gyangyadi? Ki shiga ki shirya ki je makaranta da wuri." Tana rawar jiki ta rufe kofar falonta, ta shiga ciki da gudu ta lalubo wayarta a karkashin filon kujera, hannunta na karkarwa ta kunna wayar cikin 'yan dakikai sai ga waya radau ta kunnu, yayin da kunnuwanta suke jiyo mata wani sauti daamm, daamm sakon text message yana shigowa, har guda uku.Wannan karon ma firgita ta sake yi tun kafin ta bude ta ga me aka rubuta babu tantama ta ji a jikinta Abdulmajid ne mai wannan danyen aikin. Ta bude sakon farko, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsantsar kaunar da yake yi mata. Sai ta ji kwallar takaici. Ta bude sako na biyu, sako ne daga Abdulmajid yana bayyana mata tsananin begen da yake yi mata. Sai ta ji hawayen qunar rai. Ta bude sako na uku, sako ne daga Abdulmajid ya na bayyana mata tsagwaron halin da ya shiga a sanadiyar kin ba shi hadin kan data yi, ya baza hajarsa bai siyar ba ma'ana bata karbi soyayyarsa ba. Sai ta ji wuyanta ya hau makakin tashin hankali. Wannan ne karo na farko da Zahra ta ji ta fara tsanar rayuwarta. Bugun da ta ji ana yiwa kofar falonta ne ya zaburar da ita, ta cillar da wayar gefe ta mike tsaye tana muzurai, sai ta ji muryar mahaifinta yana kwalla kiran sunanta. Ta na karkarwa ta je ta bude sai ga mahaifinta da kaninta Abubakar a tsaye carko-carko sai zare ido take, ta kalli wannan ta juya ta kalli wancan. Bakura ya ce "Da gaske ne yau babu makaranta kun fara mid-term break?" Zahra ta fara gwagwarmaya da makoshinta. "Eh, eh, ashe haka ne na manta." Bakura ya tsuke fuska ya ce "Me yasa kika kashe wayarki? Na san kawayenki su Khadija Rabi'u za su kira su fada miki tunda ke kin manta. Ki na 'yar yarinyarki qarama kina matuwa, kamar wata tsohuwa? Ki je ki dauko wayar ki kunna ki kawo min in yi magana da principal. Ya za a yi a ce ana hutun mid-term ba'a ba ku a rubuce ba." Zahra ta na karkarwar jiki ta koma cikin falonta da sauri yayin da fargaba da tashin hankali suka qaru akan na da. Abubakar ya dubi mahaifinsa ya ce "Abba an bamu takarda a rubuce a cikin mota muka bar su, bari in je in duba." Ya nufi wajen mota kafin Bakura ya bude baki Zahra ta fito cikin muzurai da rawar jiki ta mikawa mahaifinta waya. Ya karba ya juya ya nufi dakinsa da wayar. Juyawarsa ke da wuya sai wavar ta yi qara alamar sako aka turo (Test massage). Bakura ya yi sauri ya tsaya Cak ya duba wayar bai yi wata-wata ba sai ya bude sakon ya karanta ya juyo da sauri ya dubi Zahra. Tuni numfashin Zahra ya fara tafiya kamar mai shirin tafiya barzahu. Ya dube ta, ta dube shi, sai taga ya gyada kai ya juya ya tafi. Ta sulale ta tsugunna don tsananin tashin hankali, ta san tabbas Abdulmajid ne, sakonnin kuma soyayya duk da ta goge wadancan na jiya kafin ta mika masa wayar. Ta irin matakin da mahaifinta zai dauka akanta, yanzu ta sake tsanar kanta, takaicin da dana sanin dama bata nace ta ce mahaifinta ya kai ta ta ga Sajida mai kama da Zuhuriyya. Ba dan ta je gidan ba, da tsautsayi bai sa ta bada aron wayarta ba. Da a ina Abdul majid zai sami nummbar wayarta? Hawaye ya dinga surnano mata babu tunanin da bai zo mata ba a rai ba, ta ji kamar ta hada kayanta ta gudu wajen dangin mahaifinta a Maiduguri a neme ta a rasa, saboda ta san yau hukuncin da zai dauka akanta ba kadan ba ne. Muryar mahaifinta da mahaifiyarta ta ji su na fitowa daga dakinsa, Zahra ta zabura ta miqe tsaye gami da goge hawayen da ya yi mata faca-faca a Idanuwanta. Ta yi zuruf tana kokarin shigewa cikin daki da gudu sai ta ji muryar mahaifinta ya kwalla kiran sunanta. Ta waiwayo a firgice cikin rawar murya ta amsa. Ya qaraso kofar falonta a inda take tsaye ya mika mata wayarta. Ba tare da ya sake duban inda take ko ya yi wata magana ba, ya zarce zuwa babban falo. Mahaifiyarta ce ke biye da shi ita ce ta tsaya tana kallon Zahra kallo irin na lafiyarki qalau kuwa? Zahra ta gaishe da mahaifiyarta cikin firgici. Samira ta amsa gami da jero mata tambayoyi har guda uku a jere. "Lafiyarki kalau kuwa? Me ke damunki duk ki a susuce? Me yasa kika kashe wayarki?" Amsar wadannan dogayen tambayoyi su ne, "Ba komai." In ji Zahra. Ba tare da Maman Zahra ta sake cewa komai ba ta jüya ta nufi falo. Zahra ta yi wuf ta afka cikin falonta gami da datse kofar da mukulli, ta dade a jikin kofar a jingine, ta yi ajiyar zuciya mai fitar da tsantsar tashin hankali. Sannan zuciyarta ta tuno mata da addu'ar da ake karantawa idan ka gamu da wata masifa. "Inna lil laahi wa innaa ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fii musiibatii wa aq-likini khairan minhaa." Ta fada ta maimaita ta sake ta maimaita har sau uku, sannan ta ji numfashinta ya fara dira daidai. Ta wuce bandaki domin dauro alwala. Rabon Zahra da ta rasa sallar Asuba har ta manta, amma yau saboda tsananin tashin hankalin da Abdul majid ya jawo mata ya sa ta rasa sallah akan lokaci, sai da gari ya waye tangararai. Sallamar sallarta ke da wuya. sai wayarta ta dau ruri. Ta yi ta maza ta suri wayar gami da dubawa, sai Ta ga lambar Abdulmajid ce, a take ta ji wani takaici da daci a ranta. Ta danna a fusace ba tare da ta ce masa komai ba ta kasa kunne tana sauraronsa. Ya yi ta magana tamkar da itace yake waya. Ya yi gyaran murya ya ce, "Ko ba Zahmajid ba ce, shin kin ga sakonnina na jiya da na yau da safe kuwa ??" da tsurawa aljihun Bakura ido.?JUT Tun daga nan Zahra ta sake susucewa tabbas shi ne ya turo wannan sakon mahaifinta ya karanta. Babbar matsalar Zahra shine ita ba ta iya tsiwa ba, ba ta san yadda za ta cashewa Abdulmajid ba. Muryarta na karkarwa cikin kuka take masa magiya ta ce "Abdulmajid me yasa kake son jawo min masifa da bala'i a rayuwata? Ba ka sanni ba, ban sanka ba, na fada maka ni yarinya ce qarama yar makaranta. Abbana ya hana ni kula samari, wani lokacin wayata a hannunsa take, sai ya kusan kashe ni a duk lokacin da ya kama text massages dinka ko kiran wayarka. Ka rabu da ni ba na soyayya, ba na sonka." Ya yi wata shamilalliyar dariya mai kara takaici ga wanda ake yiwa. Ya ce, "Zahrah wallahi ba zan rabu dake ba, ko da za a kashe ki, nima a kashe ni. Ban taba hanuwa ba idan ina son yarinya ko da iyayen yarinya za su hadiyi zuciya su mutu." Zahra ta razana ta dora hannu aka ta fasa kuka tana cewa, "Wa iyazubillah, Allah ya yi min tsari da kai." Ta murtsike waya ta katse. Hannunta na karkarwa ta bude inbox don ta karanta sakon dazu, don taga me mahaifinta ya karanta. Sakon Hassana Ummi Sulaiman ne ta rubuto mata akan maganar yau ba makaranta anjima zata zo a ta koya mata lissafi. Zahra ta yi ajiyar zuciyar jin dadi. Amma sai ta tuna cewa Abdulmajid da bakinsa ya ce ya turo da sako da sassafen nan. "Anya kuwa ba sakon Abdulmajid Abba ya karanta ba kuwa da gama ya goge? Kai sskon Hassana ne ya shigo dazu da na Abdulmajid ne a take zai yi magana ba zai yi shiru ba ya kyale ta ya gyada kai ya wuce ba. Zahra ta shiga wani matsanancin kokonto da wasi-wasi. Abdulmajid ne yake ta tutturo mata sakonni a jere a jere wannan na bin wannan wancan a bayan wancan. Yana kara jaddada mata shi fa yana sonta, kuma ba zai rabu da ita ba. Kuma ko a ina take sai ya nemo ta. Tun tana karantawa ma har ta daina sai dai tayi ta gogewa, daga ya shigo sai ta goge. Sallamar kaninta Usman ce ta tunasar da ita a duniyar da take, don tuni ta zurfafa a fagen tunanin yadda za ta yi da rayuwarta. Ya shigo ya durkusa a gabanta ya gaishe ta. Zahra na zauno akan sallayar da tayi sallah a tsakar dakinta, ta zubawa Usman ido tana kallo sai can ta bude baki dakyar ta amsa gaisuwar, saboda ba ta kaunar yin magana, ba ta so a kusance ta yau. Ya ce "Sister Zahra, Mama ta ce ki fito mu yi break fast ke ake jira tun dazu." Ta yi kamar ta ce ta koshi, sai ta tuna ashe bata Isa ba lafiyarta kalau ta ce ta koshi mahaifinta na raye a doron kasa tabbas zai hukunta ta. Ta fada cikin siririyar murya. "Ina zuwa." Fitarsa ke da wuya ta mike da sauri ta fada bandaki bayan ta yi brush sai tasa sabulu ta wanke fuskarta tas, ta zo ta rangada kwalli a kodadden idanuwanta. Ta saka doguwar jallabiya mai hade da hula ta fito, Kai tsaye ta wuce babban falo kan dining table. Ta iske su su dukka a zazzaune ba wanda ya fara ci ita ake jira. Ta yi musu sallama, gaba daya suka amsa mata. Ta jawo kujera ta zauna ba tare da ta yarda sun hada ido da daya daga cikin mahaifanta ko qannenta ba. Kowa ya zuba nasa a plate bayan sun yi Bismillah da addu'o'i, kamar yadda Bakura ya koyar da iyalinsa tun su na kanana. Dole idan sun zo cin abinci su yi addu'a su ce, "Ya Allah ka kara bamu lafiya, ka raba mu da yunwa, kishirwa, talauci, da fatara. Allah ka raba mu da rowa da hassada da bakin ciki. Allah Ka bamu ikon taimakon mabuqata. Allah Ka taimaki mai nemowa duk sanda ya fita nema kada ya rasa." Ire-iren wadannan addu'o'i Bakura da iyalansa suke yi, duk sanda suka zo cin abinci sun haddace tsaf kamar karatu. Bayan sun shafa addu'ar a fuskokinsu, sai kowannensu ya farwa plate din dake gabansa ga kofin shayi a gefe. Soyayyen dankali ne da soyayyen kwai, ga farfesun talo-talo a gefe. Sannan ga ferarrun yankakkun kayan marmari kamar gwanda, ayaba, lemo a cikin katon faranti a tsakiyar teburin kowa da cokali mai yatsu (folk) a gabansa wanda zai nutsa ya danko ya kai bakinsa. Duk wannan rashanar ba dadinta Zahra ke ji ba, tamkar dusa take cusawa a cikinta. Kallon kurillar da mahaifinta ke.yawan yi mata shi yake sake tayar mata da hankali, sai ta ji abincin ya tokare makoshinta ta kasa hadiya. Ta yankewa kanta shawata gara ta fita da gudu ta kelaya aman karya ko ta sami sukuni, ta fake da rashin lafiya dan kar a gane ta na cikin matsala. Hankalin Maman Zahra ya yi matuqar tashi haka ma qannenta a lokaci guda su dukka suka zabura za su bita bakin qofa inda ta fita ta durqusa tana kakarin amai, Bakura ya daka tsawa ya ce duk su koma su zauna, su ci gaba da cin abincinsu su qyale ta. Wannan al'amari ya yi matuqar ba su mamaki musamman Zahra. Hankalinta ya tashi matuqa a yanzu bata tantama ta san dalilin da yasa ya yi mata haka, tabbas yaga sakon da Abdulmajid ya turo mata. Ta shigo tana layi yayin da ta nufi hanyar dakinta. Bakura ya fada cikin bata fuska."Zo ki dauki plate din abincinki da kofin shayinki ki shiga da shi dakinki ki ci a can." Hannuwanta na karkarwa ta zo ta kwasa, kallo daya za ka yi wa mahaifiyarta da qannenta kaga alamar tausayinta a fuskokinsu. Sai kalmar "Sannu, sannu, sannu." ce ke fita daga bakunansu. Zahra na amsawa dakyar ta wuce zuwa dakinta. Ta na shiga sai ta bude wani shafin kuka, musamman da ta jawo wayarta taga missed calls din Abdulmajid da text massages guda biyu, sakonnin dai na soyayya ne har yanzu. Samira ta dubi maigidanta Bakura ta ajiye cokalin da yake bannunta ta yi ajiyar zuciya. Ta ce, "Abban Yagana, ko dai tsananin son karatų da naci ne ya jawowa yarinyar nan ciwon ulcer saboda rashin maida kai ta ci abincin kirki?" Shiru yayi bai ba ta amsa ba. Aka jima Samira ta kasa daurewa ta dube shi ta ce "Oga baka ganin rashin baccin da yarinyar nan ke yi shi ya jawo mata kasala da jan ido? Ya kanmata a kaita asibiti tun dazu na lura da ita kamar tana fama da zazzabin cikin kashi. tana zazzabin dare ne?" Wannan karon ma danna abinci yake a cikinsa ko kallonta bai yi ba. Samira ta fusata ta miqe ta yi wuf ta fada dakin 'yarta Zahra, a rigingine ta iske ta ta na kallon silin da fankar da ke jujjuyawa a hankali. Daga dukkan alamu tunani ke damunta. Zahra ta yi firgigit ta miqe zaune da ta hango mahaifiyarta na shigowa. Kafin Samira ta ce wani abu wayar Zahra ce ta dau ruri. Ta na dubawa sai taga lambar Abdulmajid ce. Tashin hankali marar musaltuwa ne ya rufto mata, ta kalli wayar ta daga kai ta kalli mahaifiyarta. Sai Samira ta ce, "Ki amsa wayar mana." Zahra ta ce "Mama ban san lambar ba." Samira ta ce "Sai an san lamba ake amsawa, ko ke ma mulkin ne irin na Abbanki maganarsa ma sai an siya wataran?" Zahra ba ta daga wayar ba har ta katse. Samira ta zauna a gefen gado ta dubi plate din abinci da kofin shayin, dankar yake da abinci ko dandanawa bata yi ba. Ta juya ta dubi Zahra ta ce, "Yagana me yake damunki ne yau?" Zahra ta lumshe ido ta yi murmushin karfin ta ce, "Mama bani da lafiya." "Ciwon mai yake damunki?" Samira ta tambaya. Kafin ta ba ta amsa shigowar Bakura ce ta katse su, Samira ta miqe a fusace ta fice daga dakin dan ta ji haushin share ta da yayi dazu tana yi masa magana. Zahra ta firgita ta daga kai ta dube shi ta zabura ta gyara zama. Ta ce, "Abba sannu da gida," Ya ce "Yauwa, Mamana ya jikinki? Wai me yake damunki ne." Ta sosa weya ta ce "Abba, ciwon kai ne." Ya ce "Ba wani ciwon kai rashin barci dai. Ki ci abinci ki sha maganin ciwon kai ki kwanta ki yi barci, rashin bacci ne yake damunki. ...." Kafin Bakura ya rufe bakinsa wayar Zahra ta dau ruri. Yayin da zuciyarta ta fara dukan uku-uku, musamman data duba ta ga lambar da ake kiranta, Abdulmajid ne. Saboda gudun zargi ta yi sauri ta danna yayin da hannunta ya dauki rawa, cikin karkarwar murya ta yi sallama. Ya amsa mata da cewa "Wa'alaikis salam ya abar qaunata. Zahra, me yasa kike azabtar da ni, kike wulakanta ni a dalilin tsantsar son da nake yi miki?" Ta yi caraf ta ce "Wrong number." Ta katse wayar. Kafin ta ce wani abu tuni Bakura ya juya ya fice ba tare da ya yi mata salama ba. Zahra ta shiga halin la'ila hau ilahi da matsananciyar damuwa. Zuciyarta ta shiga zullumi. Ta ce a ranta" Anya kuwa Abban bai jiyo abin da Abdul majid ke fada ba? Tabbas rayuwata tana cikin garari, hakika za mu raba gari da Abbana." Ya iske Samira a falo tana tsaye, ya zo ya wuce ta da sauri ya nufi kofar fita gami da ce mata "Mun tafi, sai mun dawo." Ta bi shi a baya tana masa fatan alkhairi har sai da ta ga fitarsu daga cikin gidan, Sannan ta dawo ciki, ta dawo zuciyarta cike da mamakin irin wannan hali na maigidanta. Wani murdadden mutum ne, mai rikakken ra'ayi, kamar ba yanzu ta dinga yi masa maganar rashin lafiyar Zahra ba, ya yi shiru kai ka ce da dutse take magana. Amma gashi da kansa ya shiga ya duba ta. Tayi murmushi ta Ta fada a bayyane"Malam Bakura kenan, Kanuri na Samira sarkin mulki." Tafi-tafiya kwanaki uku kenan da Abdul majid ya fara takurawa Zahra ta waya, don haka kwanaki uku kenan da susucewar Zahra. A takure take ta kasa sukuni, ba ta kaunar zama a cikin 'yan gidansu, saboda takura ma ta da Abdulmajid yake a waya. kullum tana qunshe a daki tana cutar karya. Tana ji tana gani aka kai ta asibiti aka tulo mata magunguna iri-iri tana sha, dan dolenta. Don haka take yawan kwanciya, jikinta duk kasala, sai yawan barci kullum a kwance a daki. La'asar sakaliya Samira da Bakura za su fita unguwa, gaisuwar mutuwa zasu je gidan wani abokin Bakura da mahaifiyarsa ta rasu a unguwar Na'ibawa. Samira ta iske Zahra a kishingide akan doguwar kujerar falonta ta kafawa akwatin talabijin ido, amma hankalinta baya kan abin da yake gudana, babu abin da take fahimta tunaninta na kan halin da Abdulmajid ya jefa ta. Wayarta na gefenta ta saka ta a silent saboda damun da Abdulmajid yake yi mata da kira da text massages. Samira ta dubi Zahra ta ce "Ya ya jikin naki, kin sha magani?" Zahra ta langwabe kai ta yi magana cikin marainiyar murya ta ce "Mama da sauki." Samira ta dafa kanta ta ji ba zafi. Ta yi murmushin jin dadi ta ce "Yau babu ciwon kan, na ji kan ki ba zafi. Za mu fita ni da Abbanki, za mu je gaisuwa gidan su Maman Zulai yau kwana uku. Ki fito babban falo ki zauna tare da yara ki kula da masu shigowa. Ki fadawa cook abin da kike so su dafa miki, kada ki zauna da yunwa, ba'a son masu ulcer su dinga zama da yunwa." Zahra ta mike tsaye ta yi murmushin karfin hali. Ta ce "To Mama sai kin dawo." Su ka dunguma suka fito tare. Kafin su fito har Bakura ya shiga mota yana jiran Samira, don haka da sauri ta fice. Zahra ta kishingida akan doguwar kujera tana kallon talabijin yayin da Abubakar qanninta yake Zaune akan kujerar gefenta yana kallon shi ma, a jima kadan ya dube ta ya girgiza kai don tausayin yanayin da yaga take ciki. Ya ce," Sister Zahra sannu." Ta amsa da "Yauwa." Sauran kannenta kuwa Umàr da Usman suna farfajiyar gidan su na kwallo. A hankali a hankalin bacci mai nauyi ya kwashe Zahra. Kamar daga sama take Jiyo muryar Abubakar yana ta magana. Inda hankalinta ya sake karkata da sauraron abin da yake cewa ambaton sunanta da ta ji yana yi a hirar. Dakyar take bude idonta ta hango shi a zaune da alama waya ce a hannunsa. Abin mamakin shine ta san Abubakar ba shi da waya. A ina ya sami wáya yake ta magana tun dazu? Me yake cewa kuma da wa yake magana har yake ta ambaton Zahra, Zahra? Cikin magagin bacci ta laluba gefenta za ta dauki wayarta sai ta ji wayam babu komai. Ta zabura ta miqe zaune ta dubi Abubakar ya dube ta shima. Ta tambaye shi "Wayata ce a hannunka?" Ya gyada kai ya ce "Ita ce kina barci ake ta kira ba ki ji ba kin saka a silent? Ya sake kara wayar a kunnansa ya cewa mutumin da suke magana a waya "hold on ga ta ma ta farka daga barcin bari in bata." Ya taso da sauri ya dungura mata a kunne gami da cewa "Sunansa Abdulmajid." Kafin Abdulmajid ya yi magana Zahra ta yi sauri ta dauke wayar daga kunnenta kai ka ce garwashin wuta aka dana mata. Ta yi sauri ta katse wayar. A fusacc take yi wa Abubakar magana. Ta ce "Ba ka da hankali, ya zaka amsa waya? Ba ka san mutum ba, baka san lamba ba ka hau hira da shi. Watakila ma wrong number ya kira don ni ban san wani Abdulmajid ba." Abubakar ya ce "Shi ya sanki har ya fadi sunanki." Zahra tayi shiru ta kasa magana don ta rasa abinda zata ce masa. Cikin sanyin jiki tayi ajiyar zuciya. Ta ce "meya ce maka?" Abubakar ya ce "ce min yayi ni kaninki ne, a wacce makaranta muke? In ne gidan mu?" Zahra ta zabura ta dafe kirji ta ce "meyasa zaka bashi address dina har ka fada masa makarantarmu?" Abubakar ya rude gaba daya ganin yadda idanuwanta suka firfito suka cika da hawaye saboda damuwa. Ya ce "ban fada masa ba, mun fara wayar kenan kika farka." Ta ji zuciyarta tayi sanyi kadan, hankalinta ya kwanta. Ta mike ta nufi dakinta dauke da wayarta a hannu. Tana shiga daki ta bude wayar ta zare sim card din ta balla shi gida biyu taje ta jefa a toilet ta kwara ruwa ya tafi. Ta dawo ta kwanta a kan gado tana huci don takaici. Can ta tuna a ranta ai kuwa tayi aikin banza da ta karkarya sim card shi kadai. Ya za'ayi ace sim card ya bata waya bata bata ba? Ai hankali ma ba zai dauka ba. Tayi zumbur ta mike zaune tana tunanin hanyar da zata bi ta salwantar da wayarta ta hanya mafi sauki ba tare da an gane ba. Da farko tayi tunanin ta jefa wayar a toilet tayi flushing, sai ta tuna ashe ba zai wuce ba zai toshe toiet din. Tayi tunanin ta je swimming pool ta jefa, Sai ta tuna ai za a tsinta idan aka tashi wanke wajen. Idan ta jeta a shara masu zubar da shara zasu tsinta su kawo. Sai ta yanke shawara ta tafi bayan Katanga ta wurgar. Da ta isa bayan katangar sai ta cire bayan wayar daban, sannan ta wurga ta cire batir din wayar ta koma wata kusurwar ta wurgar ta sake koma wata kusurwar ta wurgar da fuskar wayar. Haka ta aiwatar amma sai da ta faki idanuwan 'yan gidan ta tabbatar babu wanda yake ganinta ta je ta wurgar ta dawo ta kwanta tana mai shakar iskar farin ciki da kwanciyar ta hankali. Ta ci gaba da tunanin karyar da zata zabgawa iyayenta a game da batan wayarta. Ba ta damu ta fada musu ba ta san babu wanda zai yi mata fada a cikinsu. Matsalarta su gane Abdulmajid yana yi mata waya amma ba ta batan wayarta ba, waya ba komai ba ce. Jinta take wasai tamkar ta sauke wani kaya daya dame ta da nauyi a kanta. Salwantar da wayar da tayi ta farfado mata da dumbin farin ciki da walwalar da ta rasa a kwanakin baya a sanadiyyar takura mata da wayar da AbdulAbdulmajid yayi. Kan kace kwabo Zahra ta dawo kamar da,ta sa karatunta a gaba. Kuma tuni ta tsara mahaifanta akan batan wayarta babu wanda ya tuhumeta ko ya tsareta da tambaya akan dalilin batan wayarta. Bayan kwana biyu Bakura ya siyo mata sabon layi na Glo da kan waya kirar Iphone. *** *** **** Sajida ce a zaune a cikin rana taną Juye-juye. Kallo daya zaka yi mata ka tabbatar bata jin dadin jikinta ga tsananin damuwa. Umma furera ce ta fito daga dakinta dauke da katuwar fanteka a cike da geron kunun kanwarta na Siyarwa zaa kai mata Surfe.Dakyar take tafiya saboda nauyi, ta cije baki ta ajiye a kasa yayin da ta dafe kashin bayanta tana sallati. Ta juya ta dubi sajida. Ta ce "yanzu Sajida ba zaki tashi daga rana ba? Tun dazu nake faman yi da bakina amma kinki tashi, hantsin har ya fara zafi. Idan sanyi kike ji ki shiga daki ki lulluba, rana ciwon kai da zazzabi zata sake jawo miki." Sajida ta dago da luhu-luhun idamuwanta wadanda suka kumbura a sanadiyyar koke-koke da zafin zazzabi ta dubi mahaifiyarta.Ta ce "Umma, tabbas kun kusa ku nemeni ku rasa kuma idan na tafi na tafi kenan." Umma Furera tayi kasake a tsaye ta hada hannu ta rike ciki tana duban Sajida. Can ta karaso inda take ta ciccibo hakarkarinta ta daga ta tsaye. Tana fadin tashi daga rana mu koma inuwa sai muyi maganar. Umma Furera ta mayar da Sajida inuwa ta zaunar da ita akan wata tsohuwar tabarma ta jawo kujera ta zauna a kusa da Sajida. Ta ce "yanzu Sajida ba zaki hakura ki fauwala Allah komai ba, akan Abdul majid ki ringa kokarin ki kashe kanki. Babu ci ba sha har kike tunanin guduwa a nemeki a rasa ki jefa iyayenki da yan'uwanki da duk wani mai sonki cikin damuwa da bacin rai dauwamammiya. Idan kika gudu kin tashe mu tsaye musamman ni da mahaifinki, zaki tasar mana da ciwon da zai iya zama ajalinmu. Ga mahaifinki ya tsufa fuk daya zuciyarsa zata iya fashewa, nima gashi girma ya zo kece abokiyar shawarata tamkar qawata nake hira dake ga dan karamin kaninki yahuza duk inda ya fita ya samo labari wajenki yake nufowa kai tsaye ya fesa miki. Idan kika tafi kika bar mu yaya zamu yi?" Ummma furera ta fashe da kuka. Sajida ma kukan ya kece mata. Har tsawon lokaci babu mai iya lallashin wani. Sajida ta dago da jajayen idanuwanta ta dubi mahaifiyarya. Ta ce "Umma, ina tunanin yarinyar nan Zahra da ta zo kwanakin baya, turo ta aka yi ta zo taga halinda nake ciki da Abdulmajid ta kai rahoto domin ita tasan ina lekawa ta katanga ina aron waya in bugawa Abdul majid." Umma furera ta tsagaita da kukan ta dubi Sajida fuskarta cike da rudani. Tayi doguwar ajiyar zuciya. Ta ce "Sajida ban fahimce ki ba. Wacce yarinya kike magana?" Sajida ta ce "Zahrar nan wacce Baba ya shigo da ita kwananakin baya ya ce 'yar gidan mai daukar karatu ce a kofar gida. Har na ari wayarta na bugawa Abdul majid. A dalilin bamu bata kunu ba Baba ya hana ki yin kunun siyarwa har sati guda." Umma Furera ta ce "kwarai kuwa na tuno ta tabbas anyi haka. Ba lallai ba ne ita ta fada amma akwai alamar tambaya. Da farko ma a ina ya santa har zai kawo ta ya tafi ya barta a cikin gida? Na biyu bayan tafiyarta ne ya shigo yayi miki wannan dukan har muka dauki alhakin Yahuza. To ko budurwa Abdul majid ce take bibiyarki don ta san ya fi sonki, ko daman ita take hada miki tuggu don babanki ya raba ku duk motsin da ki kayi da Abdulmajid sai an fadawa mahaifinki?" Sajida ta girgiza kai ta ce "Abdul majid bashi da budurwa, ni kadai ce budurwarsa a duniya haka ni kadai ya taba so kuma yayi min alkawari har karshen rayuwarsa ba zai taba son wata 'ya mace ba. Yayi min rantsuwa tun sanda ya hadu dani bai taba jin yana son wata ba. Umma, wallahi na rantse da ubangijin daya halicce ni tunda Zahra ta zo har gida tayi min gulma tayi min sanadiyyar da na daina samun damar yin magana da Abdulmajid a waya har tsawon wata guda kenan. Asanadiyyar wannan na daina cin abinci, na daina bacci sai kuka, ga zazzabi da ciwon kai. Na yi alkawari duk ranar da na yi ido hudu da Zahra sai nayi mata rashin mutuncin da ' ban taba yiwa kowa ba ldan ma son Abdulmajid take ko a dangin Abdul majid take daman da yawansu basa sona hakika sai na nakasta ta, nakasar da itama nata sauranyin zai daina sonta ta ji yadda nake ji data rabani da nawa masoyin." Umma furera ta rike baki ta ce "a'a Sajida kada ki jawo mana abinda za a maka mu a kotu daga mu har ke. Kada kiyi kisan da zaki jawo a kashe ki a dalilin wani Abdulmajid. klnga yarinyar nan daga gani 'yar gidan masu kudi ce, ko bata da gaskiya ubanta ya na da halin da zai fada aji a hukunta mu balle ma ki nakasta ta ko ina aka je ke ce marar gaskiya. Sajida ina raba ki da wannan banzar zuciyar taki, saurin fushi da yawan dacin rai, tsiwa da futsara." Sajida ta hasala ta mike tsaye tana gatsine, tana murguda baki, tana zare ido irin na tsantsar futsarar da ta saba. Ta ce "Umma, me naji kina cewa? Kina nufin in hadu da Zahra ta wuce in wuce ban tanka mata ba? Haba ashe ba'a haifeni da jini ba, daga sama na fado. Don ubanta yana da kudi sai tayi min laifi in kyaleta? Wallahi na yarda in dauwama a daure a kurkuku har karshen rayuwata da in zubawa makiyiyata ido. Ni kuwa a rayuwata me zanyi da mutumin da baya kaunata da Abdulmajid?" Kafin Sajida ta rufe bakinta mahaifinta ya sako kai cikin gidan, domin har kofar gida yake jiwo tsiwar Sajida duk da cewa baya gane abunda take fada amma ya san zancen bana dadi ba ne. Sajida na ganinsa tayi shiru amma taci gaba da harare-harerenta. Ya dubeta cikin fushi Ya ce "ke kuma hayaniyar me kike yi kamar kina magana da sa'arki? Mahaifiyar taki kike dagawa murya har kofar gida?" Sajida tayi shiru tana ta fusge-fusgen kai alamar ko a mutu ko ayi rai, ayi duk wacce za'ayi wai da bera ya zubar da garin mage. Umma furera tayi caraf Ta ce "ah, ba wani abu ba ne malam. Zafin zazzabi ne yake sakata surutai barkatai." Malam ya ce surutan zazzabi daban haka rashin kunya daban. Nasan dalilin zazzabin nata ai shiru nayi muku kawai, a dalilin raba ta da dan iskan yaron nan Abdulmajid shine yasa take kokarin kashe kanta saboda taurin kai irin nata. To bari kiji in fada miki Sajida ko ki warware ki ci gaba da walwalar ki, ko ki ci gaba da takura kanki cikin kunci ki hadiyi zuciya ki mutu a wajena duk daya ne kuma ina nan akan bakata har abada ba zaki sake haduwa da Abdulmajid ba balle ya lalata ki, daman ba aurenki zai yi ba." Sajida ta fusata ta murguda baki ta fada cikin tsiwa "an takurawa rayuwata a gidan nan, gara in mutu ma in huta. Haka kawai kowacce yarinya ana barinta ta kula wanda take so sai ni za'a takurawa. An kulle ni a gida, an hana ni karatu, an hanani fita makarantar Islamiyya da makarantar dare sai duka da zagi kullum ba kakkautawa.." Ba ta rufe bakinta ba ta ga ya wurgo tabarya ta gefen fuskarta, saura kiris ta same ta a kunci. Malam ne a fusace ya wawuro tabaryar ya wurgo mata bai damu da ko zai fasa mata kai koma ya kasheta ba. Da turmin zai cicciba ya wurga mata, yaji da nauyi ba zai ya dauka ba. Ihun Umma Furera ne ya qara tunzura shi ya ji dama ace ya same ta tayi ihun da hujja. Sajida ta zura da gudu ta shige dakinta da gudu ta sakale da şakata. Malam na huci yana ta "har fitsarar taki ta dawo kaina ina fada kina fada saboda kin raina kowa. To wallahi ba'a gidana ba, inyi wahala dake tun da aka haifeki zuwa girma sannan kice ban isa in fada miki ki ji ba to sai dai idan ba'a karkashina kike ba ki tattara kayanki ki tafi kiyi zaman kanki tunda kina ganin ke kika haifi kanki, kin girma kinfi karfin kowa. Ni kuwa idan ni na haifeki kuma da sauran numfashina a duniya wallahi ba zaki auri Abdulmajid ba ko zaki mutu. Ya juya ya dubi furera ya ce "ke ce uwar banza da ba kya tsawatarwa 'yarki.Banga amfanin zama da ke ba tunda ya'ya biyu kin kasa ba su tarbiyya da sun kai guda goma ma ban san tabarar da za'ayi min a gidan nan ba. To bari in fada miki zamanki a gidan nan ya kusa karewa, ke ki rasa aurenki itama ta rasa Abdul majid din kuyi biyu babu. Dan haka kisa ido, idan na sake jin maganar dan iskan yaron nan Abdulmajid a gidan nan zaku ga yadda zanyi muku.Sajida albishirinki a cikin satin nan zan yi miki miji ko kina so ko bakya so shi zaki aura kuma dole ki zauna, ba zaki sake yin wata guda a gidana ba insha Allah" Ya kade babbar rigarsa ya fice yana huci ya bar umma furera a takure a lungu ta buga tagumi. Zuciyarta sai dukan uku-uku take saboda tashin hankali. Yayin da Sajida ta kwalla ihu ta fada kan katifa tana rusa kuka kamar ranta zai fita. Umma furera tayi ta buga kofa tana magiya Sajida ta qi bude kofa. Sai da tayi kuka ta gaji da kanta sannan ta bude kofar. Umma furera ta shiga lallashinta akan ta daure ta ci abinci amma Sajida ta qi ci.Paid book #300 Bakura ya iso qofar gidan Malam Yakubu daf da magariba kamar yadda ya saba zuwa. Ya iske Malam tare da dalibansa wato manyan mazan da suke daukar karatu tsakanin sallar magarib da isha'i. Kamar yadda su ka saba bayan sun idar da sallar magariba sai suka shiga daukar karatu, har zuwa lokacin da Isha'i ta yi, su na idarwa sai kowa ya watse. Bakura da Malam ne kadai su ka rage. Hira suke kamar abokai, hirar dai ba ta wuce hirar siyasa ba. Da aka fito da abinci sai Bakura ya nemi afuwa akan yau dai sai dai Malam ya yi masa hakuri ba zai ci abinci ba saboda duk randa ya je gida cikinsa a qoshe rigima ake da uwargida. Malam yayi dariya ya ce "kwarai kuwa na fahimce ka, mata su na da wannan dabi'ar." Malam ya bude kwanon tuwo da miya kamar kullum tuwon tsari da miyar busashshi kubewa ce babu nama a cikin miyar sai dai qamshin wake da daddawa ne ya ke tashi. Bakura yana hira ya na satar kallon Malam. Tausayinsu ya rufe shi ya shiga sake-saken yadda zai taimakawa wadannan bayin Allah. Sai ya yanke shawara a ransa in dai ya tashi tafīya yau zai yiwa Malam alkawarin wani kudi mai tsoka da buhunhunan abinci wanda zai agaza masa wajen samu ya ciyar da iyalinsa da abinci mai kyau. Malam cin abincinsa yake kai kace ba garau- garau yake ci ba kamar wanda yake cin naman talo-talo. Malam ya gyara zama ya dubi Bakura ya ce "Alh. Babura na yaba da hankalinka, ka zama tamkar d'a na cikina ko in ce dan uwana na jini. Na yarda da kai sosai ina so ka bani shawarar da zata amfane ni. Bakura ina so ka tsaya cikin nutsuwa ka bani shawara akan wata matsala da ta addabe ni" Bakura yayi quri yana duban Malam zuciyarsa cike da tsananin mamaki ya na tambayar kansa shin wacce irin alfarma haka Malam yake nema a wajensa yake jero irin wandannan kalamai? Malam ya ci gaba da cewa "Bakura, ka bani shawara akan Sajida." "Shawara akan Sajida?" Bakura ya tamabaya cikin murya mai tafe da tsananin mamaki. Ya qara da cewa "me yake faruwa ne game da Sajida?" Malam ya nisa ya ce "so nake in aurar da Sajida domin in sami nutsuwa da kwanciyar hankali. Saboda yaron nan Abdulmajid ba zai barta ba. Kuma duk garin nan kowa ya san ba aurenta zai yi ba lalata ta yake niyyar yi. A dalilinsa na hana ta karatu, a dalilinsa na hana ta fita amma duk da haka basu rabu da juna ba kwanciyar hankalina shine kawai in sami wani babba mai hankali wanda zai riqe min Sajida a matsayin matarsa. Wallahi Bakura ko baccin kirki ba na iya yi saboda kullum gani na ke Sajida zata bude qofa cikin dare ta je wajen Abdulmajid." Bakura yayi shiru kamar wanda ruwa ya cinye ya rasa abunda zai ce. Can ya nisa ya dubi Malam ya ce "bayan Abdulmajid akwai wasu masu neman ta?" Malam ya girgiza kai ya ce bayan Abdulmajid ba ta tsayawa da kowa. Akwai wani mai naci da ya qi tafiya duk wulakancin da za ta yi masa baya fasa zuwa shima yanzu ya hakura ya daina zuwa.Yanzu al'amarin Sajida ya kai ya kawo akan Abdulmajid za ta iya rufe ido tayi tsiwa a gabana ta ce babu mai hanata auren Abdul Abdulmajid." Sai hawaye ya surnano daga idanuwan Malam. Hankalin Bakura yayi mutuqar tashi yayi shiru ya na tunanin irin shawarar da zai bawa Malam a matsayinsa na mai ilimi. Malam ne ya katsewa Bakura tunani, ya ci gaba da cewa "ranar wanka ba'a boyen cibi. Bakura, KAI KA FI CANCANTA ka auri Sajida." Jin wannan kalma ta fito daga bakin Malam sai ya ji tamkar an harba bindiga a kirjinsa, ya ji kamar wani abu ya harba a cikin zuciyarsa saboda firgicewa. Ya dago da' sauri ya dubi Malam, duba irin na rashin fahimtar abunda yake nufi. Malam ya dubi Bakura duba na fuska da fuska.Ya ce "kai nake so ka auri 'yata Sajida idan kayi haka ba karamin jahadi kayi ba, ka taimaki rayuwarta ka taimaki rayuwata ni ubanta. Babu wanda ya fi ka sanin illar haduwar Sajida da Abdul majid. Saboda a hanya ka tsince su kaga halin da zasu shiga ka garzayo ka fada min don in tsawatar ba qaramar qaunarmu kake yi ba. Na yarda da tsananin tsoronka, saka ido akan tarbiyyar iyalinka. Na yi sha'awar hada zuri'ata da taka ba don komai ba, ko don wani abu ba sai don saboda Allah. Idan kana ganin baka da ra'ayin qara aure ko baka da ra'ayí akan Sajida kar ka boye min Bakura ka fada min, wannan magana muke ta fahimta. Na yarda a cikin jama'arka ko daga cikin abokanka zuwa yaran gidanka ko Malaman masallacin qofar gidanka ka zabi mai hankali, mai addini mai tsoron Allah ka bashi Sajida. Na amince maka na san ba za ka cuce mu ba, ko ina raye ko ina a mace. Sajida 'yarka ce, kanwarka ce ka dauke ta tamkar Zahra." Bakura yayi shiru kansa a sunkuye a kasa kamar wanda aka saka igiya aka daure shi tamau ko yatsa baya iya dagawa saboda rikirkitaccen tunanin, kwakwalwarsa ta kasa warwarewa. Malam ya ci gaba da cewa "wanda zai auri Sajida ba na buqatar ya kawo min komai in banda sadaki. Sadakin ma kalilan ya isa kamar yadda shari'a ta yarda, ina da filina anan ringi road zan saka shi a kasuwa in sayar na san zai isa in yi mata gado da 'yan kujeru da zannuwan daurawa. Me kuma ake nema a rayuwar aure dai? Burina a killace min ita ta zauna lafiya ta cire ranta daga kan dan iskan yaron nan. Na fada ma ta nan da sati guda zanyi ma ta miji ko ta na so ko bata so, nan da wata guda ayi biki. Hankalina bai kwanta da masu zuwa wajena ba ne. Da yawa sun sha nuna min su na son auren Sajida na qi amincewa saboda ban yarda da rikon da za su yi mata ba haka ina tantama da tarbiyyarsu. Kudi ba komai ba ne, mutunci shine ya fi komai. Ko dan dakon da yake neman halalinsa mai tsoron Allah, wanda ya san Allah ya san yadda zai bautawa Allah mai ilimin addini, wannan mutum shi ya fi cancanta a zauna da shi ba mai kudin da yake takama yana da kudi ba don haka yake ganin yafi karfin ya bautawa Allah ba." Bakura har yanzu kalma guda daya ta gagari bakinsa ya na kallo, yana sauraron Malam babu abinda yake sai kada kai alamar yana gasgata zancen Malam. Daga karshe malam ya ce "na baka wuka, na baka nama Bakura ka je kayi tunani nan da sati biyu ka zartar da duk hukuncin da ka ga yayi daidai akan 'yata Sajida." Ba tare da Bakura ya furta wata kalma ba ya mike zuwa wajen motarsa. Malam ya raka shi har jikin mota yana mai yi masa addu'ar Allah Ya kai shi gida lafiya. Bakura ya duqa ya cewa Malam "na gode Malam, zan tafi sai kuma gobe idan Allah Ya kaimu." Ya shiga motarsa ya ja ya tafi. Malam ya dawo kofar gida ya ci gaba da tunanin shin wacce shawara Bakura zai yanke akan Sajida? Bakura kuwa tsabar tunani sau biyu yana shiga layin daba layin gidansa ba, bayan fadawa a ramuka da kwatoci ba adadi. Ya rasa abinda zai zaba wanda yafi cancanta a ciki game da Sajida. Na farko a sanadiyyar tsanananin kamar da Sajida take yi da Zuhuriyyarsa ya ji baya gajiya da kallonta tamkar wata talabijin haka Idan ya tuna tsantsar rashin kunyar Sajida sai ya ji gwbansa ya fadi saboda shi yana da kunya kuma baya son ayi masa rashin kunya. Kalmar farko da Sajida ta fara furta masa ido da ido tawa Bakura ita ce "na tsaneka." Dan haka babu tantama wannan tsanar tana nan a dauwame a cikin ranta babu mai goge ta. Zahra yarinya qarama ba ta san Sajida ba amma har ta gane halin Sajida bashi da kyau a take ta ce bana son Sajida bata da tarbiyya. Ga matarsa mai tsananin kishi muddin ta sami labarin Bakura zai kara aure tabbas zata iya hadiyar zuciya ta suma idan ma bata zarce gaba daya ba. Bakura ya sake Juyawa ya dubi amintar da take tsakaninsa da mahaifin Sajida Malam Yakubu ya san zai ji nauyin ya ce masa baya son 'yarsa. Yaya za'ayi kenan? Sajida ta zame masa kadangaren bakin tulu. *** *** *** Washegari da yamma Bakura ya koma daukar karatu gidan Malam, har suka yi hira suka gama babu wanda a cikinsu yayi maganar Sajida. Sai dai sun sha hirarsu har Bakura ya shaidawa Malam cewar sati na sama ba zai sami damar zuwa ba saboda zai je Abuja kuma a qalla zai yi kwanaki goma a can. Malam yayi addu'ar Allah ya kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya ya samo abinda ya je nema. Bakura ya gyara zama ya ce "Malam ka san ina harkar man fetir, ina da gidajen mai kala-kala a garin nan da super market wato ZUHURIYYA STORE da ZUHURIYYA PETROLIEUM STATION. Shekaru biyu da suka wuce na bude branch a Kaduna, yanzu kuma uwargidana Samira na ginawa babbar plaza a Abuja. A unguwar gwarumpa mai suna ZUHURIYYA PLAZA. To shine zan je ayi bikin budewa." Malam ya gyada kai ya ce "au kai ne mai gidan man nan zuhuriyya? Yanzu zaka bude a Abuja kuma? Bakura ya ce "Eh, plaza ce, ma'ana qatan gini ne mai hawa-hawa har hawa hudu kowanne hawa akwai kantina manya-manya guda hamsim ka ga kantina dari biyu da hamsin kenan. Kantina hamsim na kasa duk ni zan zuba kaya amma hawa na daya zuwa na hudu dukka haya zan bayar shine zan je ayi bikin budewa." Malam ya gyada kai ya ce "wane mutum, ikon Allah. Kantina maka-maka har guda dari biyu da hamsim a waje daya wannan ai itace kasuwar duniya." Bakura ya bushe da dariya ya ce "haba kasuwar duniya, sai dai kasuwar uguwar dai." Malam ya ce "wanne irin bikin budewa kuma za'ayi?" Bakura ya ce "ni da matata da ya'yana da abokaina da matansu da 'ya'yansu ne zamu hadu mu je wani hotel mai tsada mu ci abinci a yanka kek." Malam yayi dariya ya ce "ka ga turawa 'yan boko. yanzu meye amfanin a yanka kek ayi tafi ayi dogon turanci, ina albarka take? Shawarar da zan baka Bakura shine kar ka tara jama'a ana wani yanke-yanken kek bai yi tsari ba ace ka hada matarka ta aure da wasu mazan ana cin abinci ga 'yarka baliga a cikin maza, abokanka ba muharramansu ba ne. ka kalli matar wani a kalli matarka wanda yake haramun ne. Me zai hana ka dibi mahaddatan alkur'ani daga masallacinka su bazu cikin shagunan su sassauke kur'anai a ciki da zummar Allah Ya kawo ciniki, da kariya daga sharrin 6arayi da 'yan damfara. Matarka kuwa da 'ya'yanka ba'a hanasu su taya ka murna ba sai suyi tasu liyafar a cikin gida iyakacinsu mata kadai su gaiyaci 'yan'uwa da abokan arziki su zo su ci, su sha, ayi karatun kur'ani. Ka dauko mace tayi musu wa'azi a cikin gida. Haka bai fi ba?" Bakura ya gyada kai ya ce "gaskiya ne Malam, tabbas na yarda cewa abinda da babba ya hango daga zaune yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Sai dai ina neman wata alfarma a wajenka Malam. Babu wanda ya fi cancanta ya je. ayi saukar nan sai kai da almajiranka." Malam ya girgiza kai ya ce "a'a tunda ka na da naka malaman da almajiran ai su suka fi cancanta su je ba ni ba. Ni fa ban taba zuwa Abuja ba, idan aka ce za'a kashe ni akan sai na nuna hanyar Abuja to sai dai a kashe ni ban san inda take ba. Ga tsufa ina zan iya jure zaman mota daga Kano zuwa Abuja?" Bakura ya ce "zaman mota ba matsala ba ne daman da jirgi zamu tafi. Zancen cancanta kuwa KAI KA FI CANCANTA ka yi min saukar kur'ani saboda bajintar da ke tsakanin mu. Zan iya samun daci da quna a cikin zuciyata idan ka bijirewa bukata." Malam yayi shiru ya na dan murmushin jin dadi ya nisa sannan ya ce "Bakura babu wata buqata da zaka nema in qi yi maka ita.Ba damuwa zan baka yardaddun almajiraina dana yarda da qwazonsu su je suyi maka sauka ko ta kwana nawa ce sai dai ina so in ja hakalinka karka biya su kudin aikin da suka yi maka, Baya da ci da sha ba na buqatar ka basu wasu kudi na daban domin tsakanina da kai babu wannan." Bakura yayi murmushi ya ce "Malam har yanzu baka yi min abinda nake so ba, zan so tafiyar nan a tafi da kai don kasa min albarka da bakinka." Malam yayi dariya ya ce "to shikenan Bakura ba zan qi zuwa ba tunda zuwan zai qara maka farin ciki." Bakura ya ji dadi sosai ya tsayar da ranar tafiya, nan da kwanaki uku su shirya zai sa a zo a dauke su zuwa filin jirgin sama zasu acan Abujar zasu same shi don shi washegari zai tafi. Kamar yadda Malam ya bashi shawara haka Bakura ya umarci iyalansa su aiwatar, wato su hada walimarsu a gida mata kadai ba sai sun bi shi Abuja ba. Ya bawa Samira da yaransa izinin su je Zuhuriyya super market dinsa su dibi duk abinda suke buqata komai yawansa, komin tsadarsa daga naira daya zuwa naira million daya ya yarda su kashe. Su gayyaci kowa da kowa daga kan masu kudi zuwa talakawa a dangi da makwabta. Ya umarce su da su ware abinci tukunya daban wacce za'a tara almajirai a qofar gida a rabar sadaka saboda Allah. Sannan Bakura ya tafi Abuja, bayan tafiyarsa da kwana biyu yayi waya Kano ya ce direbansa ya kwaso Malam yakubu da almajiransa guda goma zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano suka hau jirgi zuwa birnin tarayya Abuja. Kamar yadda aka yi a kano a Abuja ma Bakura yana da gida da direbobinsa don haka tun kafin su Malam su sauka daga jirgi direbansa ya zo yana jiransu. Su na sauka daga jirgi ya kwaso su ya kawo su gida. Bayan sun gama hutawa a kwana daya washegari suka kama karatu a cikin plaza, suka yi ta saukewa qur'ani su na maimaitawa. *** *** **** Zahra da mahaifiyarta Samira kuwa su na kano Su na ta faman shirye-shiryen walima. Don qarfin hali har wani dan qaramin katin gayyata Zahra ta buga ta rarrabawa qawayenta na makaranta. Ranar asabar ne ranar da za'ayi walimar. Don haka ranar Juma'a da yamma washegarin ranar da za'ayi. Samira ta iske Zahra a falonta a zaune ta na kallo. Ta ce da ita ta je Zuhuriyya super market ta hado mata kayan qamshin girki (spices) kamar curry, thyme, dakekkiyar citta da dai sauransu. Zahra ta shirya tsaf ta fito caras sanye take da wani dandantsetsen leshinta shudi anyi masa zanen fulawa ruwan goro. kallo daya za ka yiwa leshin ka gasgata tsadarsa duk da daman dallar aka siyi leshin idan aka kiyasta kudinsa zai kai Naira dubu dari da tamanin. Kwararren telan da ya sarrafa dinkin leshin da ace qasar America zata sami labarinsa data dauke shi aiki a kamfanin dinka kaya (English wears). Domin idan ka kalli kayan a jikin zahra sai ka rantse daga kamfani leshin ya fito a dinke. Yankan siket din das a jikinta haka rigar, abinka da marar jiki, doguwa santaleliya kai ka ce taliya ce ke nutso a cikin ruwan zafi, idan Zahra ta na tafiya. Duk da tsayin da Allah yayi mata ta qara da wani cogen takalmi mai tsinin gaske a qafarta shima takalmin kalar ruwan goro ne. Ta nada daurin dankwali a gaban goshi, gashi keyarta kuwa lallausa mai raushi ne ta tufke shi da ribbon ruwan goro. Ta dauki dan siririn mayafi ta yafa a jikinta. Ta na rike da mukullin mota a hannunta. Samira ta dubi Zahra ta yi murmushi ta ce "baby kinyi kyau yau sosai. Ko za ki bar leshin nan gobe ki saka? Kamar zai fi na gobe kyau." Zahra ta ce "a'a mama kin manta kudinsu ne? Ai yellow da zan saka gobe ya fi wannan tsada kudinsa da na kiyasta naira dubu dari biyu ne da hamsim wannan kuwa dmdubu dari da tamanin ne. Kin ga ai ba kudinsu daya ba. Allah Ya kaimu goben shima za ki ga yadda zai yi min kyau." Samira ta ce "Magaji deriba ne zai kai ki ko?" Zahra ta ce " sabuwar motarki Discussion continues zan tuqa da kaina." Samira ta ce "ba wai ban yarda da tukinqinki ba ne amma fa har yau mahaifinki bai san kin koyi tuqi ba, ka da ki je wani abu ya faru Allah ma Ya kiyaye ya ce yaya aka yi ma ki ka fita ke kadai?" Zahra ta ce "Allah ma Zai kiyaye yanzu zan je na dawo." Samira te ce "Allah ya kiyaye mamana." Zahra ta saka bakin gilashinta saboda hasken gari, ta sakala hands free a kunnuwanta saboda amsa waya, ta shiga tsaliliyar motar nan mai launin silver nufi ZUHURIYYA SUPER MARKET. Daf da qofar Zuhuriyya Surper Market ta ja ta tsaya a inda ta dubi gefanta wata baqar mota ce qirar Brama mai bakin gilashi, ko kafi quda na ci ba za ka iya hango abinda yake ciki ba. T Tabbas ita ma motar ta hadu domin irin sautin kidan da yake tashi daga cikin motar da irin daukar idon da motar ke yi saboda da sheqi. Kamar yadda shekin motar Zahra take daukar idanuwan masu kallonta har 'yar qarama rigima ce ta tashi tsakanin saurayi da buduwar da ke cikin motar saboda yadda yake kallon Zahra har da leqe. Ba tare da Zahrar ta san abinda ke gudana ba. Zahra ta yunkura ta fito daga cikin motar in da ta danna remote alamar ta rufe motar. Ta na fitowa ta fuskanci wasu 'yan mata guda biyu sun fito daga cikin wannan baqar motar, daya daga gaba ta fito daya kuma daga gidan baya. 'Yan matan dukkansu sanye suke da wandon jeans da riga iya gwaiwarsu, sai dan gyale yalolo a maqale a kansu da cogen takalma a qafafuwansu. Nan da nan suka dunguma tare da Zahra suka shiga cikin Super market din. Daga yadda 'yan matan nan biyu suka ga ma'aikanta super market su na dukawa Zahra su na kwasar gaisuwa Hajiya sama Hajiya qasa sun san tabbas yarinyar nan 'yar wani ce a qasar nan. Inda su ka sake tabbatar da hakan sai sanda suka ji ta umarci daya daga cikin ma' aikatan cewar ya samu leda ya je ya zabo mata spices kalą-kala masu qamshi daban-daban kamar roba ashirin ya kai mata mota. 'Yan matan biyu sun ci gaba da zazzagayawa su na zazzabar abinda suke so. Kicibus su ka yi da Zahra a daidai kantar greeting cards. Yayin da su dukka ukun suka duqufa wajen karantawa don su zabi wanda yayi dai-dai da kalaman da suke buqata, kamar daga sama kunnuwan Zahra su ka jiyo mata daya daga cikin 'yan matan ta ce da dayar. " Iyayye, kin ga wani kati wanda yayi daidai da wanda zan bawa Abdulmajid." Jin sunan Abdulmajid ne ya sawa Zahra wata mummunar faduwar gaba ta dago da sauri ta dubi mai maganar. Zahra ta zare bakin gilashin dake fuskarta ta dube ta sosai inda ita ma mai maganar ta tsaya cak ta na duban Zahra yayin da su ka dauki 'yan dakikai ba su daina kallon juna ba kowa ya na qoqarin tuno inda ya san wannan fuskar. Lokaci guda kwakwalwarsu ta sanar musu cewa wannan Zahra ce, kwakwalwar Zahra ta sanar mata wannan Sajida ce. Qara-qara- qa-qa, ga Zahra, ga Sajida. Ya za'ayi kenan'? Zahra ta yi murmushi ta ce "kamar na sanki, ba ke ce Sajida ba?" Cikin gadara Sajida ta ce "Sajimajid ce, kwarai ashe kin tuna ni kamar yadda na tuna ki Zahra. Ina neman ki daman tamkar ruwa a jallo. Na dade ina addu' ar Allah ya nuna min irin wannan rana." Sai Zahra ta ji gabanta ya yanke ya fadi kan ka ce kwabo zuciyarta ta fara harbawa ta na dukan uku- uku. Ta tambayi Sajida cikin kidemewa "me ya faru?" Sajida ta yi murmushin mugunta ta dubi kawarta Iyayye ta ce "ki taya ni duban yarinyar nan, Ki taya ni fada mata ko ni wacece ko kuma yaya nake. Dan rainin hankali ma wai tambayata take me ya faru? Ba ta ma san me ta yi min ba ko? To bari ki ji Zahra babu yadda za ki yi da ni da Abdulmajid sai dai kallo da Ido babu mai raba mu, ke ko uban daya tsugunna ye haifeni ma sai dai ya yafe min amma ba zai iya hana ni son Abdulmajid ba." Gaban Zahra ya sake faduwa ta shiga saqe-saqe a ranta "tabbas Sajida ta ji labarin Abdul majid ya na yi min waya ada." Sajida ta rike kugu sai girgiza take tana huci tana hararar Zahra, tamkar mayunwacin zakin da yaga nama. Zahra ta juya ta dubi Ibrahim ma'aikacin da yake biye da ita a baya. Ta ce ya matsa ya bar wajen ta na son ta yi magana da qawarta, ya amsa mata cikin ladabi ya tafi da sauri ya bar wajen. Zahra ta matso kusa da Sajida ta ce "Sajida, wallahi ban san Abdulmajid ba, ban taba sanin yaya kamanninsa su ke ba, ba ni da wata alaqa da shi dan haka ne ma nake mamakin tuhumar da kike yi min a akansa." Sajida ta ji tamkar Zahra ta soka ma ta mashin wuta a qahon zuci. Ta fada a fusace "dubi bakin qofar shigowa." Zahra ta waiga da sauri, sai ta hango wani dan kyakykyawan saurayi a tsaye. Sajida ta ce "to Abdul majid dina kenan, ki koma ki sake fadawa Babana kin ganmu tare." Sajida ta kwallawa Abdul majid kira nan da nan ya qaraso in da suke. Ta ce da shi "ga Zahrar da nake fada maka wacce na taba kiranka da wayarta, daga qarshe ta hada min tuggu wajen Baba." Abdulmajid ya ji gabansa ya yanke ya fadi kamar yadda na Zahra yake faduwa lokaci guda suka zubawa juna ido har wani lokaci mai dan tsawo kowannan su ya na tunani a ransa. Abinda ya fara fadowa Zahra a ranta sai kalmar "inna lillahi wa'inna ilaihi rajiî'un. Yau me ya ke shirin faruwa da ni ne haka? Na rabu da Abdulmajid a waya ga shi na gan shi yau a zahiri?" Abdulmajid kuwa kan ka ce kwabo farin ciki ya lullube zuciyarsa da Allah Ya nuna masa Zahra a zahiri, kwakwalwarsa ba ta taba kwatanto masa haduwar Zahra ta kai haka ba, ba makawa Zahra itace irin kalar macen da yake burin ya mallaka a rayuwarsa.Tun fitowarta daga motarta tun ma bai san wacece ita ba zuciyarsa ta fara muradinta domin ta cika gaba daya abubuwan da namiji yake bukata a wajen mace. Nan da nan ya ji qafarsa ta kasa daukar jikinsa.Ya kidime ya fita daga hayyacinsa, amma gudun kada Sajida ta gane halin daya shiga sai ya juya da sauri ya fice ya nufi wajen motarsa ya shiga ya zauna ba tare da ya ce uffan ba. Iyayye ta ce "au daman itace munafukar da kike fada min ta na hada miki tuggu?" Idan hankalin Zahra yayi dubu ya tashi, nan da nan idonta ya cika da hawaye. Ta girgiza kai ta ce "actually I don't understand what is happening here...." Kafin ta rufe bakinta Sajida ta daka tsalle ta kinkimo qaton gwangwanin madara babba wato (giant size) ta datsa mata wajen kaifin a goshi, ko sakon daya ba'a qara ba jini ya wankewa Zahra fuska. Zahra ta kwalla ihu mai tsanani ta yanke jiki ta fadi qasa. Kafin kiftawar ido Sajida da kawarta Iyayye sun bace daga cikin kantin. Ma'aikatan shagon kacokan dinsu suka taru su ka zageye Zahra su na mamaki, su na al'ajibi yadda gwangwanin madara zai fado mata a goshi. Daya daga cikin ma'aikanta ne ya ke bayani wato Ibrahim cewar akan idonsa wannan budurwar ta jawo gwangwanin madara ta rotsa ma ta a goshi Sauran ma' aikatan gaba daya suka yiwa Ibrahim caaa akai su na tuhumar sa da cewar me yasa bai damqe yarinyar ba har ya bari ta gudu?" Hankalinsu a tashe suka garzaya da Zahra asibiti dan tsayar da jinin da yake zuba, aka kuwa ci sa'a ba a yi mata dinki ba, iodine da plasta aka saka mata aka liqe suka kawo ta gida. Samira suka iske a falo, ta na ganin goshin Zahra sai ta dauki salati mai hade da kuka dadin dadawa ma bushashshen jinin da ta gani a jikin tufafinta. Abinda ya fara fado ma ta a rai shine ko hadari ta yi a hanya, amma ganin ma aikantan shagon sai ta fara tunanin ko a bakin kantin hadarin ya faru. Zahraa rungume mahaifiyarta tana rusa kuka, Samira ta zaunar da Zahra akan kujera itama kukan ta fara yi tana tausayin 'yarta tana tausayin kanta, domin arangamarta da Bakura ba zai yi kyau ba dalilin da ya sa ta bari Zahra ta dauki mukullin motarta ta fita ita kadai. Ga gargadin da yake yi mata cewar ta sa ido sosai akan Zahra, yana fatan, yana kumå addu'a Zahra bata fita ta raqashe a bayan idonsa. Cikin karkarwar jiki Samira take tambayar ma' aikatan da suka rako Zahra har su hudu. Daya daga cikinsu ya ce "ina jin tuntube tayi ta daki jikin kanta gwangwanin madara ya datso mata a goshi." Daya yayi karaf ya ce "ba gaskiya ba ne babu yadda za' ayi dan mutum ya dan daki kanta gwangwani ya fado, wannan ba abin rufa-rufa ba ne don idan muka rufa mu kuma zai iya shafar aikinmu, idan maigida ya zo zai iya korar dukkan mu ya ce bama lura. Akan idon Ibrahim abin nan ya faru dan haka Ibrahim ka yi bayani." Ibrahim ya matso ya ce "îna biye da Zahra a baya sai wasu 'yan mata suka hau zaginta sai ta ce da ni in matsa daga wajen zasu yi magana. Matsawata ke da wuya sai na ga daya daga cikin 'yan matan tayi tsalle ta ciccibo gwangwanin madara qato ta kirba mata a goshi amma ko Sama ko qasa ban ga ta inda 'yan matan suka bi suka gudu ba." Samira ta juya ta dubi Zahra ta ce "wadanne 'yan mata ne waɗannan? Me kika yi mu su haka har da zasu fasa miki kai? Ke da baki da abokin fada tun ki na yarinya. Me kika yi musu har ya tunzura su suka fasa miki kai?" Zahra hawaye take ba tare da ta iya bada amsa ba. Ana cikin wannan hali Bakura ne ya kira wayar Samira tana jin ringing sai ta ce "yauwa ga Abbanki nan ya kira bari na fada masa tunda ni kin qi fada min gaskiya." Samira na dannawa ko gaisawa basu yi ba ta ji Bakura ya na fada har da kumfa baki, hankalinsa a tashe. Ya ce "wai me yake faruwa ne aka yi min waya aka ce wata yarinya ta fasawa Yagana kai a cikin Super Market? Wacce yariya ce, kuma waye Ubanta a Kano?" Samira ta ce "yanzun nan su ka shigo min da ita ban ma gama jin abinda ya faru ba. Yagana kuka take ta qi yin magana, sai dai ga Ibrahim wanda abin ya faru akan idonsa zai yi maka bayani." Samira ta miqawa Ibrahim kan waya, Ibrahim ya karba gami da yin sallama. "Me ya samu 'ya ta?" tambayar da Bakura ya yiwa Ibrahim kenan kafin ya amsa masa sallamar. Ibrahim ya hau bayanin iya abinda ya gani akan idonsa. "ina yarinyar take?" in ji Bakura. Ibrahim ya ce "kafin na ankara na neme su na rasa sun gudu." Nan da nan Bakura ya hau Ibrahim da bambamin fada yi yake yana dukan teburin da yake gabansa. Ya na yiwa Ibrahim barazanar rasa aikinsa akan wannan sakacin da yayi. Malam Yakubu ne a zaune a gefen Bakura yana lallashinsa, yana bashi baki cewar ya kwantar da hankalinsa abi abin a hankali. Bakura ya kashe waya sai huci yake yi, wani gumi mai zafi ne yake ta keto masa. Ya ce da Malam Yakubu "wallahi, wallahi sai na dau fansa akan wannan yarinyar da ta bi Yagana har cikin kantin Mahaifinta ta dau katon gwangwani ta fasa mata kai, sai na ga mahaifin yarinyar nan inji ko shine ya sa take rashin mutunci a Kano. Ban taba rigima akan yarana ba, ban taba rigima da kowa ba tun sanda na zo Kano, amma zan fara akan wannan yarinya." Malam Yakubu ya ce "daman bai kamata a bar maganar nan ba, saboda idan aka bar maganar nan gaba waya san abinda zata yi mata idan taga ba'a dau mataki ba, amma abi abin a hankali saboda yanke hukunci cikin fushi yana jawo dana sani ko nadama." Bakura yayi ajiyar zuciya ya ce "to malam, na ji zan bi a hankali amma Ko me Yagana ta yiwa yarinyar nan bai kamata ta bi ta har cikin shagona ta fasa mata kai ba, har da jini face-face. A iya sanina Yagana ba ta fada, ko an tsokane ta bata tankawa. Ba ta iya fada ba, bata ma san yadda ake yinsa ba. Haka kawai ta bi ta har cikin kanti ta fasa mata kai ni kuwa sai na ji da wa take taqama a qasar nan kuma sai na ga mahaifinta inji dalilin da yasa 'yarsa ta fasawa 'yata kai, shari'a ni da shi babu mai saka ni na janye." Malam Yakubu ya ce "tabbas kar ka bar maganar nan nima ban goyi da bayan ka bar maganar nan ba,zan tambayi Yagana da kaina ta fada min gidan su Yarinyar sai mu je har da ni mu ji dalilin da yasa 'yarsa ta fasawa Yagana kai. Idan ya nuna 'yarsa bata yi laifi ba ko tayi daidai to ya cancanci a kai maganar kotu suyi musu tsakani." Bakura ya gyada kai ya ce "Allah ya kai mu Kano lafiya." Malam ya ce "amin Allah Ya kai mu lafiya." Na JUT Paid book Washegarin ranar ne ranar walima, taro yayi taro sai dai shagalin ya raunana saboda da goshin Yagana ya kunbura suntum duk wanda ya dube ta sai gabansa ya fadi, kowa yana tambaya me ya sami Yagana a goshi? "faduwa ta yi." Amsar da Samira take basu kenan. Itama Yagana amsar da take bawa kawayenta kenan. Tun ranar da abin ya faru, safe da rana da yamma da dare Bakura sai ya bugo waya yana tambayar Zahra me ya hada ta da yarinyar, kuma wacece yarinyar? Sai Zahra ta hau nuku-nuku tana kame-kame da alama bata da niyyar fada masa, Malam Yakubu ma ya sha kar6ar wayar yana lallashinta yana lallaba ta akan ta fadi sunan yarinyar don ayi musu tsakani amma Zahra ta qi fada idan aka takura mata da tambaya sai ta fashe da kuka duk da Zahra bata san da wanda take magana ba ma'ana bata san mahaifin Sajida ba ne. Idan ran Bakura yayi dubu ya gama baci a yanzu ya fi jin haushin Zahra akan yarinyar da ta fasa mata kai. Allah- Allah yake kwanakin su cika ya dawo Kano ayi wacce za ayi. *** *** *** Ranar da su Bakura suka cika kwanaki goma sha biyu, a ranar suka dungumo suka dawo Kano, daga filin jirgi ba'a wuce da su Malam gidansu ba sai suka zarto gidan Bakura kai tsaye sai suka kutsa farfajiyar gidan. Malam da almajiransa sun ga aljannar duniya, sai kallon gidan suke zuciyarsu cike da sha'awa, suka wuce cikin katafaren falon inda suka iske an shinfida katuwar darduma an jera abinci kala-kala da abubuwan sha iri-iri. Bayan sun zazzauna Samira da Zahra sanye da dogayen hijabai tare da kannen Zahra gaba daya suka biyo layi suka zo gaban su Malam suka zube suka kwashi gaisuwa. Zahra na ganin Malam Yakubu ta tuno da fuskar cewa Mahaifin Sajida ne, sai taji gabanta ya fadi. Daman ita Samira bata san shi ba bata san ma daga in da Bakura ya samo su ba, ita dai ya bata umarni a dafa abincin mutane goma sha biyu zai zo da su, kuma ta dafa shikenan abinda ta sani bata damu ta tambaye shi su waye ko daga ina suke ba. Bayan sun gaisa sai Samira ta ce da yaranta "to mu shiga ciki mu barsu su ci abinci. Har sun juya baya za su tafi Bakura ya kwallawa Zahra kira, gabanta ya yanke ya fadi ras, Jikinta ya dau karkarwa kan ka ce kwabo sai hawaye ya dinga kwararowa daga idanuwanta. Ta zo ta durkusa a gabansu. Bakura ya harare ta, ya juya ya dubi Malam ya ce "dubi goshin yarinyar nan ka gani. Yau wajen sati kenan amma har yanzu da sauran kunburin a goshinta. Wa yasan yadda gurin yayi a lokacin da akayi abin? Wallahi Yagana ban taba dukanki ba amma idan ki ka yi min taurin kai sai na bubbugeki." Zahra ta fashe da kuka yayin da jikinta ya dau rawa. Malam yasa hannu ya dakatar da Bakura. Ya ce ka ""kyale ta a hankali zan tambaye ta za ta fada cikin lumana da kwanciyar hankali." Malam ya shiga jawowa Zahra ayoyin Kur'ani da nasihai kała-kala masu ratsa jiki, ita dai kuka shaf-shaf-shaf take. Ta na tunanin yadda zata dubi kwayar idon Malam ta fada masa 'yarsa ce ta fasa mata kai. Ta kudiri niyyar yau ko mahaifinta zai kashe ta ba zata iya fada masa wacce ta fasa mata kai ba. Bakura ya ce "Malam ka ci abincinka ka rabu da ita har ta gama kukan, ko kukan jini zata yi yau sai na saka ta a gaba ta nuna mana gidan su yarinyar. Ta yaya za'ayi ma tace bata san yarinyar ba, kuma ta qi fadar abinda ya hada su?" Ya dakawa Zahra tsawa ya ce "koma can gefe ki zauna ki gama kukan, ko ki fada ko karki fada muna gama cin abincin nan zamu saka ki a gaba ki nuna mana gidan, idan kika qi za ki ga abinda zan yi miki a yau. Me za'ayi da irin shiru-shirun nan naki? zurfin cikinki yayi yawa." Zahra ta koma gefe tana ta rusar kuka ta rasa abunda yake yi mata dadi, tunda take a rayuwarta bata taba shiga irin wannan tashin hankali ba. Tayi nadamar zuwa gidan su Sajida da ta yi. Sautin kukanta ne ya ke tayarwa da Samira hankali ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da Marwa take a tsakanin qofar falo zuwa cikin gida. Ta san Zahra da zurfin ciki, Bakura kuma da zuciya. Idan ya hasala zai iya mangare ta a sake yin rauni na biyu. Ta ji kawai ba zata iya ba gara kawai ta matso daga kusa tana ganin abinda zai faru. Ta yi sallama ta shigo falon bata damu da hararar da Bakura ke yi mata ba .Ta sami kujera ta zauna a kusa da Zahra , magana take yi mata cikin rada, shawara take bata kawai ta fadi sunan yarinyar da adireahinta babu abinda zai faru hakkinta zaa kwato mata. Su Bakura su ka gama cin abinci tas, Zahra ta san kanta zai dawo. Zahra ta dubi malam Yakubu ta juya ta dubi mahaifinta sai ta ji gabanta ya sake faduwa. Tsawa mai firgitarwa Bakura ya dakawa mata daga ita har Mahaifiyarta sosai da suka razana ya ce "wannan shine tambayar da zan yi miki ta karshe ki fada min wacece yarinyar? Kuma waye ubanta a Kano? Kuma da wa take taqama a kasar nan?" Bakin Zahra yana karkarwa, haka hannunta yana rawa sai ta nuna malam Yakubu cikin rikikitacciyar murya ta ce "Malam ne mahaifinta, Sajida ce." Malam ya kalli Bakura, Bakura ya dubi Malam gaba daya suka juyo suka dubi Zahra. Su ka hada baki a tare su ka tambaya "Sajida? " Samira ma ta tambaya "Wacece Sajida?" Wannan amsar ta gagari bakin Zahra, ba ta san amsar da za ta bata ba. TAMBAYA??? *Shin wacece Zuhuriyar nan da Bakura yake mutukar kauna fiye da iyalansa, fiye da kan kansa? *Meye dangartakar Zuhuriya da Bakura da yake tsananin begenta? *Shin ina Zuhuriyar take ne, ko ina ta tafi? *Shin Bakura zai yarda ya auri Sajida? musamman yadda tsantsar rashin tarbiyyarta ya bayyan a fili?. *Shin yaya za'ayi a raba soyayyar Abdulmajid da Sajida? yadda Sajida take tsananin kaunarsa haka? *Shin yaya soyayyar Zahra da Abdulmajid zata kasance? Musamman daya ganta a zahiri kuma tayi masa? *Shin wanne mataki Bakura zai dauka akan mahaifin Sajida da ita Sajidar kanta? Tunda yayi rantsuwa sai ya dau fansa ba zai qyale wacce ta aikatawa 'yarsa Jalli daya kwal wannan ta'asar ba? *Shin wanne mataki malam Yakubu zai dauka akan Sajida da mahaiiyarta musamman idan ya ji ance da Abdulmajid suka fita? Amsoshin wadannan tambayoyin suna nan tafe ku ci gaba da saurarona Kai ka fi cancanta paid book #300 Bakura ya ji gabansa ya yanke ya fadi, kamar yadda irin wannan fargaba ta ruftowa Malam. Bakura ya juya ya dubi Malam, yayin da shi ma Malam ya juyo ya dube shi, duba mai cike da dimaucewa, gami da gigicewa, lokaci guda suka juyo suka dubi Zahra. Bakura ya ji gabbansa sun yi sanyi, har ba shi da kuzarin da zai iya ci gaba da rike qaton faskaren itacen da yake hannunsa. Cikin sanyin jiki ya tsugunna ya ajiye faskaren itacen a qasa, yayin da Malam ya sulale ya durkushe a qasa yana karkarwa. Yana fadin."Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Sajida, Sajida kin cuce ni,ba zan barki ba har sai an fitarwa da Zahra hakkinta kamar yadda muka kudira, saboda kada mu yi kaffara ni da kai gaba daya. Sajida ta cancanci a hukunta ta, saboda yarinya ce marar jin magana, mai tsiwa. Ka haifi mutum ba ka haifi halinsa ba. Ya ya zan yi da rayuwata? Ina zan saka raina? A ce ni a rayuwata ba zan matsa nan da nan ba, sai dai in zauna in yi gadin Sajida da Abdul Majid. Yanzu Sajidar da na hana zuwa makaranta, ita ce aka hadu da ita har a Super market....." Kafin Malam ya rufe bakinsa, kuka ya kece masa saboda takaici. Hankalin Bakura ya tashi, tausayin Malam ya lullube shi, yayin da ya ji kwalla ta cika masa ido. Ya yi sauri ya mayar da ita. Tsananin fushin da tafasar da zuciyar ke ciki sai ya ji zuciyaryarsa ta yi sanyi qalau, hade da sanyin jiki. Ya girgiza kai ya ce da Malam "Na yafe, na bar zancen nan duniya da lahira, tunda Sajida ce. Sai dai na yi mamakin abin da zai hada ta da Zahra har ya kai su ga haka. A iya sanina, sanda Zahra ta ziyarce ta sun rabu lafiya, ba tare da sun yi fada ba. To me yake faruwa?'" Malam ya rike kai yana jujjuyawa, don takaici yana magana cikin zubar da hawaye. Ya ce, "Mugunta ce kawai tsagoranta, amma me Zahra za ta yi mata har ya kai su ga yin fada. Ai ko baka sa an kulle Sajida ba, yanzun nan zan biyo ta police station, in tafi da 'yan sanda su kulle ta." Bakura ya zabura, gami da daga hannu biyu yana yi wa Malam magiya akan ya yi wa Allah ya bar zancen nan. Yasa hannu ya tashi Malam tsaye, gami da ci gaba da lallashinsa, yana mai ba shi baki ya kwantar da hanakalinsa ya bi abin a hankali, kada ya biyewa sharrin zuciya ya lahanta 'yarsa. Ita ma Zahrar ba kyalle ba ce, watakila wani abu ta yi wa Sajidar har ta kai su ga haka. Da kyar Malam ya jefa qafafuwansa ya qarasa wajen mota, Zahra da Samira su ma suka dungumo dan su yi musu rakiya. Bakura na gefensa ya yi sauri ya bude masa kofa ya shiga gidan gaba ya zauna, yayin da sauran almajiran suka shiga baya. Har Bakura zai rufe masa qofa, Malam ya rike qofar, gami da juyowa ya dubi Zahra ya kwalla kiran sunanta. Ta yi firgigit ta karaso gabansa ta durkusa, yayin da bugun zuciyarta ya sake qaruwa. Malam ya dube ta cike da tausayi da nadama. Ya ce, "Zahra ki yi wa Allah ki fada min duk abin da ya faru tsakaninki da Sajida?" Zahra ta dago da sauri ta dubi mahaifinta, yayin da ta ci karo da galleliyar hararar da yake gallo mata, ta durkusar da kai kasa, yayin da muryarta ta hau rawar disco tana sama tana kasa don fargaba. Babban tashin hankalinta kada zancen saurayi ya fito a cikin maganar, saboda yadda mahaifinta yake kyamar abun. Ita kuma ta san saboda Abdul Majid yana yi mata waya, Sajida ta kullace ta. Zahra ta yi narai-narai da ido. Ta ce "Babu abin da na yi mata ta jawo gwangwani ta fasa min kai." Tsawa mai firgitarwa Bakuřa ya daka ma ta, ta ji har tsakar kanta á karkarwa, Ya ce, "Ki fada mana gaskiya, ko mahaukaci ka ga ya bi yara tsokanarsa suka yi." Cikin kuka Zahra ta ce, "Abba, wallahi na rantse da wanda numfashina yake hannunsa, tun ranar da muka je da kai ban sake ganin Sajida ba, kuma babu abin da ya hada ni da ita sai ranar da muka hadu a Super market dinmu. Kalmar da na ji ta ambata itace ta cewa kawarta Iyayye ga munafukar da take hada min tuggu. Kafin in tambaye ta munafuncin da na yi ma ta ta wawuro gwangwani ta kwada min." Kuka ya sake kece mata, Malam ya gyada kai ya ce, "Ita da Iyayye suka fita Super market sayayya kenan?Ina suka sami kudi? Wannan ma abun tuhuma ne, tabbas kwarya ta gari tana ragaya, Sajida ba ta yi sa'ar uwa mai tarbiyya ba. Zahra goge hawayenki zan bi miki hakkinki. Tashi ki tafi ki yi hakuri, ki yafe mana, ki yi mana afuwa ba za a sake ba." Zahra ta ce, "Na yafe mata Malam." Ta yunkura ta tashi ta nufi inda mahaifiyarta da kannenta ke tsaye carko-carko, suna kallo suna sauraron wannan al'amari mai kama da al'mara. Bakura ya ce da Malam, "kamar yadda kake ba ni shawara nake dauka, ka yi min alfarmá guda daya nima a yau. Dan Allah idan ka je gida kada ka daki Sajida, balle ka ce za ka dauki itace ko wani makami ka fasa mata kai, ko ka ce za ka hada ta da 'yan sanda da dai sauransu. Ka lallaba ta ka tambaye ta dalla-dalla abun da ya faru tsakaninta da Zahra, kamar yadda ka tambayi Zahra cikin sanyin rai. Ka mata nasiha, kada takurar ta yi mata yawa har ta falle fiye da yadda take a yanzu." Malam ya gyada kai ya ce, "Na yi maka alkawari ba zan dake ta ba. Sai dai ina gudun kada wannan abu ya jawo silar tabarbarewar zumuncin da ke tsakanina da kai." Bakura ya zabura ya ce, "Haba, haba Malam me zai sa ka yi wannan tunanin, babu abin da zai sa in canja. Jibi ma zan zo daukar karatu insha Allah. Sajida 'yata ce, ko in ce kanwata ce. Ita da Zahra duk daya ne." Malam ya ji dadin kalaman Bakura, ya yi murmushi ya ja kofar motar ya rufe. Ya ce "Allah ya saka da alkhairi, na gode ina sauraron zuwanka jibin." Direba ya ja mota suka tafi, kallo daya Bakura ya yi wa dandazon 'yan aikin da suka taru don bada hakuri, sai kowa ya warwatse sum-sum-sum, ya kama gabansa. Yayin da ya sake wurga idonsa ya dubi iyalinsa suma suka dibi 'yan kafafuwansu zuwa cikin gida. Bakura ya sami kujera a gindin wata bishiya mai sanyi dake farfajiyar gidan ya zauna yana mai tsananin tunani, yana jujjuya kalmar da Sajida ta fadawa Zahra. "Ga munafukar da take hada min tiggu." Wanne munafunci Zahra ta yi mata a karon farko da ta fara saninta? Wannan al'amari ya dimauta zuciyar Bakura matuqa. A cikin gida kuwa, Zahra ce da Mamarta ake fafatawa, domin ran Samira ya baci matuqa. Ta saka Zahra a lungu ta ritsa ta, ta ce sai ta fada mata. Wacece Sajida? A ina take? Yaya aka yi har suka je gidansu, amma ba su taba fada mata ba? Zahra ta zayyaanawa mahaifiyarta duk yadda aka yi da dalilin da yasa suka je ta ganta. Samira ta ji hankalinta ya tashi, duk da ta san labarin yarinya mai kama da Zuhuriyya, amma ba ta ga dalilin da Bakura zai dauki Zahra ya kai ta gidansu ba. Lallai akwai wani boyayyen al'amari, akwai wata hujja mai karfi a cikin wannan magana,.musamman ga wanda ya san tsatstsauran ra'ayin Bakura." Samira ce take tattaunawa a zuciyarta, yayin da take kai-kawo a tsakiyar falo. Zahra ta takure akan kujera ita da kannenta gaba daya sun rasa abin da yake yiwa rayuwarsu dadi a yau, domin su ba su saba haduwa da irin wannan tashin hankalin a gidansu ba. A koda yaushe iyayensu a cikin nishadi suke, amma yau komai ya hautsine. Samira ta juyo a fusace ta dubi Zahra, ta ce "Mahaifinki ne abokin shawararki, mahaifinki ne abokin hirarki, shi ne ki ke fadawa damuwarki, ban da ni." Zahra ta bude baki za ta yi magana, Samira ta dakatar da ita da hannu, gami da daka mata tsawa mai qara. Samira sai bambamin fada take har da kumfar baki, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, domin ranta ya baci matuqa. Zahra ta yi shiru, yayin da kuka ya addabi idanuwanta ta yi nadama tayi dana-sanin zuwa gidan su Sajida a rayuwarta. Ana jiyo Muryar Samira har farfajiyar gidan, inda Bakura ke zaune, hakan yasa ya shigo gidan don ya ji me yake faruwa. Shigowarsa ba ta sa Samira ta daina fadar maganganun da take fada ba akan Sajida. Yau ba ta tsoro, daga dukkan alamu ta zama 'yar ta kife, ko a samu ko a rasa. Yau ba ta tsoron a yi duk wacce za a yi, in ji beran da ya zubar da garin mage. Bakura ya fahimci zancenta bai wuce akan kishi ba, wai kumallon mata in ji masu iya magana. Sai ya wuce zuwa dakinsa abinsa ba tare da ya ce da kowa uffan ba. Ya na shiga ta bishi a baya, kalmar da ta fito daga bakinta ita ce, "Wacece Sajida? Kuma meye dangantakarka da ita, har za ta fasawa 'yarka kai amma ka ce ka yafe ba tare da bincike ba? Shin Baban nata asirce ka ya yi da har kai ka ke ba shi hakuri? Ko ya zo ne ya samarwa 'yarsa dan mutsugunni a gidana, saboda ta yi kwantai, ko kuma in ce talauci ya yi musu kanta?" Saboda takaici bai iya ba ta amsa ba, ko kallon inda take bai yi ba. Ya cire rigar da take jikinsa ya hau gado ya kwanta, gami da matsa remote din A.C, don sanyaya gumin da ya addabi jikinsa. Samira ta sake cewa "Ka yi zumucinka da Sajida da mahaifinta, amma ban da ni da 'ya'yana." Wannan karon nuni ya yi mata da hannu, alamar ta fita ta ba shi waje. Ta fice a fusace ba tare da ta sake cewa komai ba. Fitarta ke da wuya Bakura ya yi zumbur ya tashi zaune, ya rike kai yana Jujjuyawa saboda al'amura sun tsananta a gare shi. Ya rasa abun da yake yi masa dadi. Wayarsa ce ta dau ruri yana dubawa sai ya ga sunan Malam Yakubu, wato mahaifin Sajida. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, ya danna wayar da sauri gami da rada sallama. Sai ya ji muryar Malam na karkarwa, alamar yana cikin tashin hankali. Bakura ya tambaya cikin kidiméwa. "Malam lafiya?" Malam ya nisa ya ce, "Kamar yadda ka ba ni shawara in bi abun a hankali, na bi shawararka, na kira Sajida da Iyayye na tambaye su na ji duk yadda aka yi. Ka ji ashe da Abdul Majid suka fita, shi ne ya kai su Super Market siyayya. Uwarta na gida, ta amince musu suka fita dan haka na yanke hukunci akan Sajida. Ba duka, ba zagi, amma ba za ta wuce sati biyu a gidana ba zan daura mata aure ga duk wanda na ga dama, mahaifiyarta kuma dole ta fice ta bar min gidana." Bakura ya miqe tsaye, gami da dafe kirji ya ce,"Baba kada ka yi min haka. Ina fatan dai yanzu baka furta saki ba?" Malam ya matse hawaye ya ce"Ban sake ta ba, amma gara ta tafi gidansu can rigarsu ta huta, nima in huta, ta ga ko ina da amfani. Bakura ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka yi hakuri ka bar ta, kada ta tafi, kai namiji ne kada ka hada tunanin ka da na mace, ba ka ganin ko da ta hana Sajida fita sai ta fice din tunda bata tsoron kowa, yara ba su cika jin tsoron iyayensu mata ba. Musamman Sajida yadda take son Abdul Majid ba ta jin maganar kowa sai tasa, tana shakkarka shi yasa ba ta fita idan kana nan. Babu yadda Umma Furera za ta yi da ita ne shi yasa ta bar su suka fita, amma ka yi hakuri Malam. Zancen aure kuma nan da sati biyu ba zai yiwu ace Sajida ta yarda ta auri wanda ba ta sanı ba, wanda ba ta so, kuma ka ce a zauna lafiya. Ka bari a tsanake ka na addu'a sai ta dawo kan hanya ko Allah Ya shiryi Abdul majid din su yi aure, ko Allah ya yaye mata sonsa, ta sami wani nagari ta aura." Malam ya ji tamkar Bakura ya watsa masa wuta a zuciya, ya yi farat ya ce, "Wallahi idan kaga Sajida ta auri Abdul majid a duniya, sai dai in ba na numfashi, amma idan ka ga na ci gaba da zama da Sajida a cikin gidana fiye da sati biyun nan to duk mazajen duniya sun guje ta, amma idan da namijin da zan bawa ya karba, to na aurar da Sajida na gama duk talaucinsa, duk naqasarsa, kuturu ko makaho. A yanzu haka na aika almajirina Usman ya je kasuwar Dawanau ya kira min Sama'ila, wani almajirana da yake can yana kasuwanci, na ce ya zo ya aure ta na tabbatar ba zai qi ba. Domin Sama'ila yana da hankali, ya na yi min biyayya, duk da matansa biyu, ita sai ta zama ta uku. Kuma in kafe ta da addu'a sai ta zauna a gidan ba za ta iya fitowa ba, balle ta gudu." Hankalin Bakura ya tashi matuqa, duk da sanyin A.C da ke dakin amma zufa yake. Ya ce, "Baba kada ka yi haka amma kashe wayar zan kira ka, saboda kada in cinye maka kati maganar tamu ta na da tsawo." Malam ya kashe waya, Bakura ya koma ya kwanta yana mai tsunani akan wannan matsala. Hakika ya tausayawa Malam, haka yana tausayawa rayuwar Sajida, Ya tuno irin matsananciyar rayuwar da yara matan da ake yiwa auren dole suke shiga, haka duk akasarin karuwai daga auren dole suke fallewa. Ya tuno irin tsananin son da Sajida take yi wa Abdul majid, ya hasko irin barnar da za ta iya afkuwa idan Sajida ta samu ta fice daga gidan mijinta ta gudu wajen dan iskan nan Abdulmajid. Sai ya tuno 'yarsa Zahra, ya kwatanto a ce bayan ransa komai zai iya faruwa da ita. Ya shiga tunanin hanyar da zai bi ya warwarewa Malam da 'yarsa wannan matsalar, ba tare da kowa hankalinsa ya tashi ba. Da ya rintse ido babu abin da ya hango sai fuskar Sajida da tsananin kamar da suka yi da Zuhuriyyarsa, ya ji a ransa ya kamata ya taimakawa rayuwar Sajida ko don albarkacin kamar da ta yi da Zuhuriyya a matsayinsa na mai ilimi, mai dukiya, kuma cikakken Musulmi. "Ina mafita? Ina mafita?" Haka Bakura ya fada a bayyane yana ta nanatawa, tamkar karatu, ko kuma in ce tamkar wani tababbe, sabon kamu. Abdul majid, zai iya yiwuwa ma gama lalata rayuwar yarinyar nan." Ya jawo waya ya bugawa Malam, bugu daya Malam ya amsa ya ce da Bakura. "Ka kira ni anjima, ina tare da Sama'ila an kirawo min shi, zan isar masa da buqata ta, duk yadda muka yi zan sanarmaka." Bakura ya dakatar da Malam da sauri ya ce, "Kada ka yi haka Malam, ka bari mu yi shawara, yin haka zai iya cutar da rayuwar Sajida, ya wargazawa Sama'ila lissafi, ta rugurguza masa tsarin gidansa, ta wargaza kan iyalansa. Malam ka yi min wata alfarma yanzu ka taso daga gabansu Sama'ila ka fito qofar gida mu yi magana." Malam ya ce, "Yanzu haka na bar su a zaure na fito qofar gida." Bakura ya nisa ya ce, "Da za ka bi shawarata kada ka yanke wannan hukuncin, ka kirkiro wani dalili daban ka fadawa Sama'ila na dalilin kiransa, amma ba wannan ba. Tun da a kasuwar Dawanau yake na san awo yake, ka ce masa ina son buhun gero biyu, buhun masara biyu, ya kawo min zan saya, ka sallame shi ya tafi ba tare da ka fada masa ba." Malam ya ce "toh na ji shwararka, amma idan na sallame shi, ya tafi ya bar ni da Sajida ya ya zan yi da ita?" Bakura ya numfasa ya ce, "Sajida ka barta kamar yadda na fada a baya, har Allah Ya sa ta gane Abdul majid ba mai qaunarta ba ne sai kaga ta canja shawara, Allah zai kawo mata wani." Malam ya dakatar da Bakura ya ce "Na rantse Sajida ba za ta wuce sati biyu a gidana ba insha Allah, Bakura ka kasa gane halin tashin hankalin da hatsari da illar da ke tattare da zaman Sajida ba aure.Takai-ta-kawo Sajida ta fara daukar hure kunnen da Abdul majid yake yi mata akan ta daina jin maganar iyayenta ta bi shi su watse daga nan sai ya koya mata shaye-shaye. Ba ka ganin daga tafiyata ta fice, uwarta ma ta ce ba ta san da Abdul majid suka fita ba. Da ta fita kuma ta je ta debo min magana, har da fasawa yarinya kai, ba dan 'yarka ba ce da yanzu ina kulle. Ta jawo mutuncina ya zube a unguwa, ana ganin mota na zuwa ta na daukar 'yata ana fita da ita."Kai kafi cancanta Bakura ya yi ajiyar zuciya, ya ce "ta fadi gulmar da Zahra ta yi mata, har ta kai su ga batawa?" Malam ya ce, "Abin da na fahimta, zancen nan ne dai da Sajida ke aron waya a makwabta ta buga masa, wanda Zahra ta fada maka, kai kuma ka fada min, ni kuma na dake ta.shine take ganin babu wanda ya san ta ari waya sai Zahra ta zargin ta yi mata gulma." Bakura ya ji tausayin Zahra ya kama shi, ya jawo an fasa mata kai a banza, ba tare da hakkinta ba. Malam ne ya katse dogon tunanin da Bakura ya tsunduma ya ce, "Bakura, zan je in sallami Sama'ila kamar yadda ka shawarce ni, kuma zan yi tunani zuwa kwana biyu idan na rasa mafita, zan sake kirawo Sama'ila in fada masa bukatata. Amma duk shawarwarin da zan je in yi, da wacce za ka yi akan wannan magana ba zai kai wacce nake kwatantowa a raina ba. Bakura KAI KA FI CANCANTA ka samarwa Sajida miji." Wata hanta ce ta yi girgiza daga cikin cikin Bakura, ya fada cikin wata gigitácciyar murya mai kama da rawar nanaye, dan dimauta ya ce, "Na'am, na'am." Malam ya nanata ya ce, "Babu abin da hankalina ya fi kwantawa illa in aurar da ita, kuma KAI KA FI CANCANTA ka taya ni zabar mata miji saboda illiminka, na yarda da tarbiyar gidanka, da tsananin tsaron gidanka. Ka yi tunani ka samo måna mafita, nima zan je in yi tunani." Malam ya kashe waya ya bar Bakura nanike da waya a kunne, tamkar gunki. Ya kasa ajiye hannunsa qasa, don kidimewa da tsananin tashin hankali. Babu abin da yake masa yawo a cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa, sai kalmar Malam KAI KA FI CANCANTA ka aurar da Sajida! KAI KA FI CANCANTA ka samo mata miji!" "Cafdi jam! Abun da kamar wuya." In ji Bakura. Bakura ya ji a ransa shi ya fi CANCANTA ya auri Sajida amma rana quna, inuwa quna, shi da wanne ido zai kalli Samira ya ce zai auro Sajida? Irin wannan falli da ta fara tayarwa tun kafin ta gano gaskiyar magana? Ko kuwa da wanne ido zai dubi 'yarsa Zahra ya ce zai auro yarinyar da ta so ta nakasta ta? Da wanne ido zai dubi Sajida ya ce ya zo neman aurenta, shi da ta furta masa da bakinta ta tsane shi? A wacce hujja yana ji yana gani zai je ya jajobo fitsarartiyar yarinyar da ba ta jin maganar kowa, sai ta saurayinta? Ko da wanne ido zai dube ta ya ce ta rabu da rabin ranta ta zo su zauna? Sannan da wanne ido zai dubi Malam ya qi share masa hawayen da yake zuba saboda ya rasa yadda zai yi da 'yarsa a matsayinsa na Malaminsa tamkar mahaifinsa ya dauke shi? Daga qarshe kuma Bakura yake tambayar zuciyarsa wanne tsautsayin ne zai sa yana ji yana gani ya rabu da mai kama da Zuhuriyyarsa sak bayan duk sanda yake son farin ciki a rayuwarsa to sai ya hasko rayuwarsa da Zuhuriyya. Sai ya hasko kamanninta zuciyarsa, sannan yake jin sanyi a ransa. A yanzu haka fuskar Sajida, muryarta da siffar jikinta ce ta maye kamannin Zuhuriyyarsa. "Ya ya zan yi?" Bakura ya tambayi zuciyarsa. *** **** *** Kwanaki biyu Bakura ya yi a cikin gida, a cikin wannan hali mai tsananin dabarbarcewar tunani. Daga wanka, sai sallah ce take tashinsa daga kan gado. Abinci har kan gado Samira take kawo masa, amma sai ya ji ya kasa ci, idan ya ci kadan sai ya bari sai dai ya na yawan shan ruwa da juices din da ke shaqe a cikin firij din da ke gefen gadonsa.Yanayin Bakura yasa Samira ta bar fushin da take yi, ta shiga ba shi hakuri, ta na lallashinsa tana yi masa nasiha, duk da ba ta san me yake damunsa ba kuma bai fada mata ba. A bangaren Zahra kuwa, ita ma hankalinta a tashe yake koda yaushe cikin fargaba take, tana gudun kada Sajida ta fadawa babanta dangantakar da ke tsakaninta da Abdul majid wayar da yake yi mata , duk da dai ba ta san dalilin da ya sa Sajida ta kira ta da munafuka ba. Zancen dai bai wuce Sajida ta gane Abdul Majid yana yi mata waya ba, abun ka da munafukin namiji zai iya ce mata Zahrar ce take yi masa waya ita kuma ta kullace ta. Don haka ganin yanayin da Abbanta ya shiga, na rashin walwala, sai hankalin Zahra ya tashi matuqa suka shiga wasan 'yar buya da shi. Daga sun idar da sallar Asubah, idan ta gaishe shi to sai tayi wuf ta fada daki ta shirya su tafi makaranta. Zahra ta yi zuguf ta rame, sabo da fargaba, tunani, kuka da uwa-uba tsayuwar dare tana addu'a akan Allah Ya rufa mata asiri, kada a fadawa mahaifinta cewar Abdul-Majid yana sonta. Allah yasa dai shirun da ya yi bai ce mata komai ba, ba wani tsatstsauran mataki yake shirin dauka a kanta ba. Kaico!!! Rashin sani yana damun Zahra, ba ta san abin da yake damun Bakura daban ba ne, shi har ya manta da rigimarta da Sajida. Abun da yake damunsa ba zai fadu ba, sai shi sai Rabbul Alamin, sai Malam wanda ya hada abun. A rana ta uku Bakura ya yanke hukuncin zuwa gidan Malam Yakubu, don su zauna su yi magana qeqe-da-qeqe, babu zancen nuqu-nuqu ko 6oye boye ko kara, kunya, da jin nauyi. Gara a yi fito-na-fito kowa ya fadi rá'ayinsa, ba tare da wani ya cutu ba. Yamma na yi, Bakura ya yi qarfin hali ya miqe ya shiga bandaki ya fesa wanka, gami da caba ado da wata galleliyar shaddarsa fara sol sai walkiya take tana santsi kamar tarwada. Ya dora farar hula, gami da farin takalmi, hade da farin gilashi a fuskarsa. Rangadi! Wa ya ga baqar fata a cikin fararen kaya, ya yi 'karr' da shi, son kowacce 'ya mace. Mai ya yi saura? Sai ya feshe duk illahirin jikinsa da zabga-zabgan turarurruka (designers), wanda babu na qasa da dubu ashirin da biyar. Kan ka ce kwabo qamshi ya karade ciki da wajen gidan. Samira ce dauke da farantin yankakkun kayan marmari ta shigo dakin Bakura. Daga ganin irin duban da take yi masa ka san duba ne irin na mamaki, hade da farin ciki. Ta ajiye farantin akan durowar gefen gado, ta mayar masa da lallausan murmushin da yake yi mata, irin na ma'aurata masu farantawa juna,ta qarasa inda yake tsaye gaban madubi. Ta ce "Ran maigidana ya dade, ina za'a je ne? Ko kai fa? ka ga yadda na ji dadin ganinka kuwa? Ka yi kyau yau fiye da kullum, na dade ban ga ka yi kyawun kwalliya irin ta yau ba." Bakura ya yi dariya, sai ga fararen haquransa tarr a fili masu dauke da wushiryoyinsa sama da qasa sun bayyana, sai kwalliyar ta qara qawata. Ya ce "Ke kin cika zuga, kullum ki yi ta zuga ni ina fasa kai, ina daukar kaina kyakkyawa, alhali ke kadai kike ganin kyawun." Su duka suka bushe da dariya. Samira tasa hannu tana balle masa maballin gaban rigarsa. Ta lankwashe murya ta ce, "My dear, ka qi ka fada min halin da kake ciki, ka saka ni cikin zullumi da kokonto. A ce yanzu tsakanin miji da matarsa akwai boye-boye? My love ka kawo agaji wajen fitar da ni daga wannan damuwa da zuciyata take ciki. Ka daina boye min gaskiyar al'amari, na sanka, na san halinka. Kai jarumi ne, ba ka tsoro, na san za ka ce bai shafe ni ba, amma ya kamata in sani. Wace ce Sajida? Mene ne dangantakarka da ita?" Bakura ya ji zuciyarsa ta harba '6amm'!!! Don fargaba da tsananin firgici. Ga idanuwan Samira tsai a kansa, tana kallonsa tana jiran jin amsar tambayarta. Ya ji yawun bakinsa na qoqarin qafewa, yayin da sautin maganarsa ke qoqarin kifewa cikin cikinsa. Ya yi ta maza, musamman irin wannan kirari da kodawar da ta yi masa. Ya ce, "My heart kenan, tambayar da ki ka yi wacece Sajida. Amsa ita ce Sajida wata yarinya ce qarama, 'yar kimanin shekaru goma sha shida. Sunan mahaifinta Yakubu, mahaifiyarta kuwa Furera. Su na zaune ne a unguwar Kawo, da ke kusa da Giginyu a qaramar hukumar Nassarawa, da ke cikin garin Kano. Kamannin Sajida da Zuhuriya shi ya ja hankalina na sanin wacece Sajida? Su waye iyayenta? A wacce unguwar suke?" Samira ta yi murmushi ta ce "Na ji amsar tambayata ta farko, sai tambayata ta biyu. Bayan ka gano wacece Sajida ka tantance ba su da alaqa da wacce kake tunani, mene ne dangantakar ka da ita?" Bakura ya yi ajiyar zuciya, gami da murmushi ya lumshe ido. Ya ce, "Wannan amsar ta ki ba za ta fadu ba a yanzu, amma ki ba ni awa hudu zan fita in dawo, za ki ji cikakkiyar amsa marar gargada." Samira ta yi masa duba irin na rashin fahimta, ta bude baki za ta yi magana kenan, Bakura yasa hannu ya rufe bakinta. Ya ce, "Kada ki ce komai, ki yi addu'ar Allah ya kai mu, shi ne za ki ci ribar zama da ni da samun labarin da kike nema daga gare ni. Mace ta gari ba ta jayayya da mijinta, na yi alkawari zan fada miki komai." Ya sumbaci kumatunta, ya juya zai fita, yayin da ya barta a tsaye tamkar bishiyar da aka dasa, ta bishi da kallon kawai. Ta ambaci sunansa, nan da nan ya juyo. Ta ce "Na dauki fiye da awa guda ina yanka maka fruits din nan na ga ko kallon inda suke baka yi ba, balle ke sha." Ya dafe kai alamar mantuwa ya dawo da sauri ya ce, "i am sorry my dear, bari in sha yanka biyu, kada in yi laifi in yaso sai a ajiye min sauran sai na dawo da daddare, ina baki labari muna sha zai fi dadi." Samira ta yi dariya ta ce, "Ko kai fa, shi yasa ka ke burge ni akwai ka da gudun bacin raina." Ta sa cokali mai yatsu (folk) ta dauko yankan abarba ta saka masa a baki, ya cinye. Ta cako yankan gwanda ta saka masa a baki, ya cinye. Ya juya zai tafi ta sake cewa, "Saura guda daya ga kankana ba ka sha ba." Ya dawo ya bude baki ta saka masa yanka daya. Ya yi murmushi ya ce, "Kina shagwaba ni kamar wani yaro qarami dan goye." Ya rungume ta tsam a kirjinsa, har zuwa wani lokaci mai dan tsawo, sannan ya sake ta. Ta fada cikin wata 'yar siririyar murya mai kama da rada, "Allah ya bada sa'a." Ya amsa cikin murmushi ya ce "Amin my Wife." Ya juya ya fita da sauri yana yi yana duban agogo. Ta biyo shi a baya tana fadin, "Yau dai sauri ake har ba a jiran rakiya ta." Su ka dunguma zuwa farfajiyar gidan, a inda ake ajiye motoci. Ta dube shi ta ce, "Ina fatan dai mukullin farar motar nan ka dauko ko? Domin ita ce ta dace da fararen kayanka, na sanka mutumina akwai hada to march." Ya yi dariya ya ce, "Ita zan hau, sai dai idan kin ce in hau baqar mota, kada fararen kalar su yi yawa." Ta ce "A'a, ka hau farar, za ka fi yin kyau." Ya shiga ya ja ya tafi, tana daga masa hannu, yana daga mata, har ya fice daga cikin gidan. Samira kuwa sai ta tsinci kanta yau cike da farin ciki, kai ka ce an mata albishir da gidan Aljanna. Ita kanta ba ta san dalilin wannan farin ciki ba, duk da dai kowa ya san farin cikinta yana da nasaba da farantawar da maigidanta ya yi mata a yau. Domin farin cikin 'ya mace bai wuce idan mijinta yana dadada mata ba, haka musgunawa daga namiji ya kan susuta 'ya mace ta shiga damuwa, har ya kaita ga samun tabun hankali, hawan jini, ko bugun zuciya. Don haka farin cikin Bakura shi ne farin cikin Samira, farin cikin Samira shi ne farin cikin yaranta. Da yake Alhamis ce, babu Islamiyya, Samira ta hado kan 'ya'yanta gaba daya zuwa cikin lambu su na hira, su na wasa da dariya, kai har da tatsuniya da waqe-waqen gargajiya suke rerawa ita da su. Hakika Zahra ma ta saki jikinta, hankalinta ya kwanta, ta gasgata cewar mahaifinta bai ji maganar Abdul majid ba, ta dora da addu'a kada Allah Ya sa ya ji wata magana nan gaba. Da Bakura ya fita bai tsaya a ko ina ba sai a qofar gidan Malam Yakubu. Su ka zauna a qofar gidan su na hira, duk da a cikinsu babu wanda ya tabo zancen Sajida. Can Bakura ya dubi zauren gidan Malam ya ce, " Sama'ila ya kawo min gero da masarar ne, na ga buhunhuna a jibge?" Malam ya yi dariya ya ce, "Af ka ga shaf na manta, ai tun jiya ya kawo har ma na ba shi kudin." Bakura ya ce "Me yasa ba ka yi min waya ba tun a jiyan ai da na bar abin da nake yi na zo na biya shi, da ba ka biya ba." Malam ya ce "Gero duk buhu daya naira 5,000, masara kuma duk buhu naira 6,500." Bakura yasa hannu a aljihu ya dauko kudin ya miqawa Malam, sai Malam ya dakatar da shi. Ya ce "Ka bar shi kawai zansa ya kawo maka naka har gida. Wannan ni na saya, saboda sai a ci a bikinSajida." Bakura ya bude baki ya na duban Malam, duba irin na mamaki, ya tambayi Malam cike da tangardar sauti, "Bikin Sajida da wa, yaushe ne bikin?" Malam ya gyara zama, gami da tsuke fuska ya girgiza kai don takaici. Ya ce "Al'amarin Sajida da yaron nan Abdul majid sai Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un. Wato bayan mun yi wayar nan da kai, na je na sallami Sama'ila ban fada masa abin da nake so in fada masa ba, na hakura har sai mun yi tunanı ni da kai, kamar yadda ka shawarce ni. Sai rana tsaka ba aka nemi Sajida aka rasa, ta katanga ta haura da qullin kayanta wai za ta gudu wajen Abdul majid." Wata mummunar faduwar gaba ce ta tabbata a zuciyar Bakura, ya dafe kirji ya fada a bayyane, "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un. Yanzu ina Sajidar?" Malam ya girgiza kai ya tabe baki ya ce "tana cikin gida a daure, a mari na saka ta har yanzu bakinta bai daina ambaton za ta fita ta gudu ba. Ai tana kama hanyar gidan su Abdul majid ba ta kai ga qarasawa ba, wasu almajiraina suka ganta da gudu akan babur suka zo suka sanar da ni, muka runtuma akan babura muka damko ta, ni kuwa na sa mata mari na daure hannuwa da kafafuwan na jefa ta a akurkin dakinta." Bakura ya yi wata doguwar ajiyar zuciya a bayyane ya sunkuyar da kansa qasa yana mai tsananin tunani da daurewar kai. Malam ya katse masa tunani ya ci gaba da cewa "Kai har ta kai ta kawo na kira kawarta Iyayye na ritsa ta na karbi lambar wayar Abdulmajid, na zo gida. Ga ni, ga Sajida, ga mahaifiyarta na bugawa Abdul Majid waya, kuma na bude wayar (hand's free) yadda kowa zai ji." Bakura ya dago da sauri ya dubi Malam ya ce "Ka kira Abdul majid saboda me?" Malam ya ce saboda ina so in ga karshen soyayyarsu, ina so Sajida ta san wannan yaro ba sa'an auranta ba ne, ba tsarin su daya ba, ba martaba da tarbiyyar gidansu daya ba ce. Ina so ta san ba kaunarta yake ba, ba kuma aurenta zai yi ba." Bakura ya ajiye kudin da yake rike da shi tun dazu ya hada gwiwoyinsa biyu ya rike da hannayensa ya ci gaba da sauraron Malam. Malam ya ci gaba da cewa, "Bugu daya waya ta yi ringing, dan iskan ya dauka, abunka da lalatacce maimakon ya yi sallama, sai ya yi fito. Ya ce, "Ya ya aka yi ne babyna?" Ashe ma ya san lambata, har wayata take sata ta buga masa, idan na ajiye a caji na tafi masallaci." Bakura ya tsuke baki, sai kada kai yake kamar wani kadangare. Ya rasa ta cewa, sai tsananin bugun da zuciyarsa take yi, tamkar 'yarsa ce ta fada hannun mayaudari. Hakika ya tausayawa Malam, ya kudiri niyyar taimakawa Malam da 'yarsa Sajida wajen yaqi da Abdul majid, mayaudaran samarin da suke yaudarar 'yan mata. A kan me?" Malam ya ci gaba da cewa, "Sai na yi masa sallama, amma yaron nan bai razana ba ma da ya ji muryar tsoho. Har wani turanci ya juya yake yi min. Na ce masa ba na jin wannan yaren mu yi Hausa. Na tsufa, ga rashin isasshiyar lafiya." Sai hawaye ya surnano daga idon Malam. Bakura sai ajiyar zuciya yake yi, har yanzu gyada kai yake, yana huci kamar wani kumurcin miciji. Ga wata zufa da yake yi kai ka ce a gaban wuta yake. Malam ya ci gaba da cewa, "Dan haka auren Sajida da Sama'ila ya tabbata, don har na fadawa Sajida kuma yau din nan na kira Sama'ila na shaida masa." Bakura ya dago da sauri ya dubi Malam ya ce, "Ka fadawa Sama'ila?" Malam ya ce "Kwarai, kuma ya amince duk da shi ma ya yi tantamar iya zama da Sajida, amma ya amince har ya yi murna, gami da godiya. Ya ce zai je ya hado dan abun da Allah ya hore masa ya zo a daura aure. Don haka ne ma na ce ni na sayi gero da masarar, sai ya kawo maka wasu." Bakura ya buga kansa da hannu, ya ja dogon numfashi mai ribas, ya girgiza kai. Ya ce, "Malam ba ka nemo mafita ba, wannan abu bai yi ba, wannan qofar ba mai 6ullewa ba ce." Malam ya yi tsuru yana duban Bakura. Can ya ce "Me yasa ka ce haka?" Bakura ya ce, "Sajida za ta dauwama a daure a mari ne? Za'a yi zaman aure ne a haka a daure? To idan ba haka ba Sajida ba za ta yadda ta zauna a gidan Sama'ila ba guduwa za ta yi. Auren dole yana iya jawowa mace ta falle ta gudu, ta shiga yawon bariki. Auren dole kan iya sawa mace ta nemi ta kashe kanta, ko ta kashe mijin, koKai kafi cancanta paid book #300 Malam ya yi zugum, can ya ce, "Bakura ina mafita? Ya ya zan yi da rayuwata? Yaya zan yi da Sajida? Muddin Sajida na zaune a gidana duk dabarata sai ta yi yadda zata hadu da Abdul majid, so yake ya cuci yarinyar nan ya bata mata rayuwa, Bakura babu amfanin zama da Sajida a gidana, tunda Sajida ba makaranta take yi ba. Ba na barcin kirki, saboda gadinta." Bakura ya miqawa Malam kudin nan, gami da cewa, "Ka yi min izinin ganin Sajida zan yi mata magana." Malam ya zabura ya miqe da sauri ya ce da Bakura, "Bismillah mu shiga ciki." Malam na gaba Bakura na biye da shi, har tsakar gida. Bakura na tafe yana waiwaye, yana duban kowacce kusurwa ta cikin gidan. Babu abinda idanuwansa suke nuna masa, illa ragargajejjen bango da dakwalkwallallan fenti baqiqirin. Su ka iske Umma Furera a zaune akan kujera a tsakar gida ta buga tagumi tana tunani, kallo daya za ka yi wa jemammun idanuwanta ka tabbatar ta narki kuka son ranta, har ta gaji. Cikin nutsuwa da sanyin jiki Bakura ya yi mata sallama, gami da rusunawa don girmamawa. A tsorace ta dago ta dube shi, duba na ban mamaki. Ta sake wurga idonta gefe ta dubi maigidanta. Sai ta sadda kai qasa ta gyara lullubinta, gami da amsawa Bakura sallamar da ya yi mata. Malam ya ce da ita. "Ki bawa baqo kujera mana ya zauna." Ta yi sauri ta sauka daga kan kujerar da take zaune ta tura a gaban Bakura. Ya ce, "A'a, babu komai yi zamanki ba zama zan yi ba." Bakura ya durkusa a gaban Umma Furera ya gaishe ta, ta amsa cike da fara'a mai hade da mamaki, tana yi masa duba inin na ban gane ka ba. Babu abin da Bakura yake nanatawa a ransa sai "Allahu Akbar, na ga mahaifin Sajida, na ga mahaifiyarta, ammá babu hadin ta da Zuhuriyyarta." Bai ma taba cin karo da mai kama da siffar Umma Furera ba, balle su hada dangantaka da Zuhuriyya. Kalmar da ta fara fitowa daga bakin Bakura ita ce "Ina Sajida?" Wannan tambaya tasa ita tasa Umma Furera dago da jajayen idanuwanta, ta dube shi. Ta tambayi zuciyarta."Wanene wannan? Daga ina yake? Mene ne dalilin zuwansa? A ina ya san Sajida? Menene dalilinsa da yake neman Sajida?" Furta wadannan tambayoyi ba za su yiwu ba dan haka ta hada tambayoyinta ta kunshe a cikin zuciyarta. Malam ya nuna dakin Sajida ya ce "Ta na ciki, tana baqin ranta da ta saba. Mu shiga ka ganta." Malam a gaba, Bakura na biye da shi, har qofar dakin Sajida. Abin ka da dogo, ga 'yar gajeriyar qofa a rashin sani bai durqusa ba ya doke kai a jikin qofa, yayin da burbushin jar qasa suka kado a jikin fararen kayansa, har da idanuwansa. "Subhanallahi, sannu ka buge kai ko? Qofar ce irin tamu ta al'majirai." In ji Malam. Bakura ya murza ido ya ce, "Ba komai, na manta ban durqusa ba, ka san tsawo gare ni kamar dare masha Allah." Shigarsu cikin dakin ke da wuya Bakura ya yi ido hudu da wani gaftareren hoton Sajida (Lamination) a kafe a jikin bango. Ta kuwa tsala kyau, kai ka ce ba ita ba ce. Ta yi dariya a hoton, yayin da siririyar wushiryarta ta hadu da fararen hakoranta, suka hade da hasken kyamara suka bada wani haske. Duk wancan ganin da ya yi wa Sajida bai kare mata kallo ba ma ashe, a dalilin kukan da take yi, sai yanzu a hoto ya qare mata kallo.Tashin farko da ya dubi hoton, sai ya dafe kirji, saboda mummunar faduwar gaban daya riske shi, ya ce a ansa "Ianalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Saboda tsantsar kamar da Sajida ta yi da Zuhuriyyarsa. Kamarsu ma har ta baci kamar an tsaga kara, in ji Bahaushe. A ce har wushiryar cikin baki da jerin haqora iri daya, dariyarsu iri daya, har da lobawar kuncinsu iri daya (beautiful point) idan sun yi dariya. Kai wannan kama tasu ta yi yawa, in dai babu dangantaka. Kallon hoton Sajida kawai Bakura yake bai ma kula da Sajida ba, tana maqale kanta a cikin gwiwoyinta a lungu, ga sarka a daure a hannu da qafa, kamar wata 'yar fashi. Malam ya kula Bakura fa bai ga Sajida ba, saboda dan akurkin dakin ya fara duhu, kasancewar yamma ta yi, sai ya ce da Bakura. "Ga ta can fa a takure a lungu." Bakura ya juyo da sauri ya dubi lungun. Bai ci sa'a ba dan bata dago da kanta ta dube shi ba, kasancewar kukan da take shararawa, amma idonsa ya nuna masa kafafuwanta da hannayenta suma sak irin na Zuhuryya, don haka su ya tsaya yana duba kawai, ba tare da ya iya furta kalma daya ba, don kidimewa. Zuciyarsa ta shiga aikin tantance masa wannan abin al'ajabi, kwakwalwarsa ma wannan aikin ta shiga gaba daya jini da tsokar jikinsa suka canja, saboda rikcewa. Gumi take yi tun karfi, jayayya ake tsakanin huhunsa da numfashin da yake shiga da fitar iske saboda dimaucewa. Idanuwansa suka yi jawur, yayin da yawun bakinsa ya qafe, don haka ba shi da wata kalma da zai iya fadawa Sajida. Ya juya ya sake duban hoton Sajida, kamar ya kira sunan Zuhuriyýa ta amsa, sai ya ji kansa ya fara sarawa saboda tunani ya yi masa yawa. Ya yankewa kansa hukuncin ficewa daga dakin, kafin ya shide ya suma. Wannan al'amari ya fi qarfin ace sai ya nemo kwakwab gara ya barwa Allah ikonsa. Malam ya yi tsaye yana jiran Bakura ya wanke masa Sajida tas, ya so Bakura ya turance masa ita, don ta san ba ita kadai ba ce 'yar boko. Malam ya so Bakura ya fito mata da dara-daran idanuwansa, kamar yadda yake ritsa 'yarsa Zahra, amma sai ya ga Bakura ya fice daga dakin da sauri ba tare da ya ce uffan ba. Malam ma ya biyo shi suką fito tsakar gida Umma Furera ta fashe da kuka, ta durqusa gwiwoyinta guda biyu a qasa ta dubi Bakura. Ta ce "Yaro, ka roqi Malam ya cirewa 'yar nan sarqa a qafa. Na dauka ma kwance ta za ku yi. Sajida ta qi ci, ta qi sha, tunda safe fa take daure." Bakura ya ji hankalinsa ya dada tashi, ya yi sauri ya ce da Umma Furera. "Tashi Iya, ki daina durkusa min, ni danki ne, za a kwance ta ki daina damuwa." Ta koma ta zauna tana sharbe hawaye. Bakura ya dubi Malam ya ce, "Baba, ka taimaka ka kwance ta, ba inda za je." Malam ya bude baki zai yi magana Bakura ya dakatar da shi, ya ci gaba da cewa, "Ka bani wuqa, ka ba ni nama, a kan Sajida da Abdul majid." Malam da matarsa suka yi sororo su na duban Bakura, duba na rashin fahimta. Bakura ya gyara tsayuwarsa, gami da duban qasa. Ya fada cikin wata murya mai dauke da tsananin kulawa, hade da tausayawa. Ya ce, "Na yarda, na amince, zan aure ta, ni na fi cancanta in auri Sajida." Malam ya ji tamkar an zuba masa wani ruwa mai sanyi a cikin zuciyarsa. Ya ji kamar an masa albishir da gidan Aljanna. Ya ji tamkar Allah Ya yi masa Albishir da aljanna, Ya gasgata Allah Ya amshi adduarsa Ya aiko masa da bawanSa dan da ya zo ya fitar da shi daga cikin wata gagarumar matsala da take so ta zama ajalinsa. Ya ji a jikinsa ya yi sallama da matsalar Sajida a duniya. Daga qarshe sai ya ji hawayen farin ciki ya fara kwarara. Ya ce da Bakura, "Allah Ya yi maka albarka, Allah Ya tabbatar da wannan al'amari. Allah Ya sa an hada alhairi" Umma Furera kuwa daga dukkan alamu ta shiga sarqaqiya, ta bude baki tana duban Bakura da Malam. Can ta tambaya ta ce, "Malam wacce Sajidar ku ke magana?" Malam ya tsuke fuska ya ce, "Sajida nawa gare mu? Ki na ganin Sama'ila zai iya da Sajida ko Abdul majid? Bakura sunansa wannan shine wanda ya kai mu Abuja muka yi masa aikin addu'a. Ya yarda ya amince zai auri Sajidą saboda ya taya mu kula da tarbiyarta." Kafin Malam ya rufe baki, Umma Furera ta rusa kukan dadi, gami da jawo albarka iri-iri ga Bakura. Bakura ya fice da sauri ba tare da ya ce komai ba. Malam ne ke biye da shi a baya har bakin motarsa suka yi sallama Bakura ya ja mota ya tafi. Malam ya dawo cikin gida suka ci gaba da tattaunawa da Umma Furera, game da wannan abin farin ciki da ya same su. Malam da matarsa ne suka shiga dakin Sajida har yanzu ta qi dago da kanta, balle ta dubi masu shigowa. Malam ya tsugunna ya kwance sarkar da ya yi mata dabaibayi, ya ce da matarsa. To ki yi mata bayani." Ya fice ya bar su a dakin, kasancewar magruba ta qarato. Umma Furera ta matsa kusa da Sajida ta zauna gami da rungumo ta jikinta, ta dago kanta tana mai murmushi ta ce da Sajida. "Albishirinki, aure ke da Sama'ila babu." Wannan kalamai sun sa Sajida tattara hankalinta gaba daya ga sauraron mahaifiyarta. A wani bangare na zuciyarta kuwa, wani haske ne gami da farin ciki suka rufto mata. Umma Furera ta ci gaba da cewa, "Bakon da ya shigo dazu ya ce shi zai tsaya miki mu ba shi wuqa, mu ba shi nama." Sajida ta ji wani farin ciki ya lullube ta, ta zabura ta rungume mahaifyarta, ta fada cikin farin ciki. "Mutumin ya roqi Baba ya bari in auri Abdul majid ne?" Umma Furera ta yi 'dumm'! Can ta ce, "Ina wani sabon aminin Babanki, wanda kwanaki ya kai Babanku da su Abashe almajiri Abuja, mai arzikin nan da yake da kamfanoni, to shine ya shigo har cikin dakinki, shi ne yasa Malam ya kwance miki sarkar nan ya ce bai kamata a daure ki ba. Kuma na lure Malam ya na daukar shawararsa, duk da yaro ne ba sa'an Malam ba ne. Ga kudi, ga kyau, ga nutsuwa, mai ilimi dan boko." Sajida ta yi ajiyar zuciya ta gyara zama ta ce, "To Umma me ya ce? Ya bawa Baba shawara ya kyale ni in auri Abdul majid ne?" Umma Furera ta ce, "Sajida ki nutsu, kin san Abdul majid ba sonki yake ba, ba kuma aurarki zai yi ba. Amma wannan babba mutum ne ya san darajarki." Sajida ta tsuke fuska ta ce "Ban fahimce ki ba, kamar yaya?" Umma Furera ta yi murmushi ta shafa gefen fuskar Sajida da bayan hannunta ta ce. "Shi ya fi cancánta ya aure ki." Sajida ta zabura ta miqe tsaye, kai ka ce cinnaka ne ya galla mata cizo, ko in ce kunama, don firgici. Ta daki wani tebur inda kayan kwalliyar da ke kan teburin suka watse kasa. Hawaye marar kakkautawa ya fara shatata daga idanuwanta. Ta ce "WallahI ba zan aure shi ba, ko shi wanene. Haka ba zan auri Sama'ila ba, ko da kuwa za a kashe ni a gidan nan. Har a je a kirawo wani wanda ban sani ba, ban taba gani ba, a ce in aura, saboda an tsane ni." Umma Furera ta ce, "Za ki gan shi zai zo, daga kin ganshi za ki so shi, har ya fi Abdul majid kyawun gani," Ho ho hoo! Tamkar Umma Furera ta zubawa zuciyar Sajida wuta, haka ta ji wani zazzafan baqin ciki. Ta kufula ta fice daga dakin ta fito tsakar gida tana huci, don takaici. Ji take tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu, kar ta kai gobe. *** *** *** A bangaren Bakura kuwa, ya na isa gida sai ya tsaya a masallacin qofar gidansa ya yi sallar magruba da Isha'i, ya đaga hannu sama ya yi ta addu'a akan Allah Ubangiji Ya yi masa jagora, ya zaba masa abin da ya fi alkhairi akan wannan al'amari. Da ya isa cikin gida, sai ya iske iyalansa kakaf a falo. Bayan ya rungume kowannansu, an yi sannu da zuwa. Sai suka wuce kai tsaye kan daning table, inda Samira da masu dafa musu abinci suka sarrafa abincicika kala-kala. Suka ci, suka sha, kowa ya qoshi. Sannan suka raba dare suna hira, har wajen sha biyun dare. Bakura ya ce yara duk su je su kwanta. "Good night mama. Good night Abba. Good night my lovely Daddy, good night Mum." Sautin da kake ji yana fitowa daga bakin Zahra da qannenta kenan. "Good night my babies." Amsar da Bakura da matarsa suka ba su kenan. Sannan suka dunguma suka wuce dakunansu. Samira ta matso kusa da maigidanta ta dube shi cikin fara'a da murmushi ta karya murya ta ce, "My dear, ka dawo lafiya?" Ya dube ta da gefen ido ya yi murmushi ya lankwashe murya ya ce, "Lafiya my love. " Ta sake naniqarsa ta riqe yatsun hannunsa ta ce, "Alkawari kaya ne, ina alkawarina?" Bakura ya ji 'rass-rass'!!! Gabansa ya yanke ya fadi. Babu yadda zai yi ya gocewa maganar a matsayinsa na babba, mai halin dattako. Amma duk da haka ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya furta wata kalma. Can ya rufe ido, domin abin ya fi qarfin a fada ido a bude. Ya ce, "Samira, za mu shiga wata sabuwar rayuwa, wacce ta sha bamban da irin wacce mu ke ciki a baya. Kin yi min biyayya, iya biyayya a zamanmu.Kin nuna min qauna, iyakar qauna. Amma sai yanzu da za mu shiga sabuwar rayuwar nan zan tabbatar da biyayyar da qaunar da kike yi min ta gaskiya ce. "Sabuwar rayuwa?" Samira ta tambaya cike da mamaki. Bakura ya bude ido ya dube ta ya yi murmushi ya gyara zama ya ce, "Sajida yarinya ce da take neman taimako, wacce rayuwarta take daf da rugurgujewa, domin ta rasa karatunta na boko da Islamiyya a sanadiyyar wani mayaudarin yaron da yake kade mata hankali. Don haka take buqatar a taimaka mata." Samira ta sake jin wani mamaki mai kama da mafarki ya daure mata kai. Ta ce, "Ban fahimce ka ba, Sajidar da ta fasawa 'yata kai, ka ke so mu dauko mu riqe ta a gidan nan ta ci gaba da karatu, har mu aurar da ita'? Ko kuma yaya kake nufin a yi? Abban Yagana, ka kula da irin mutanen da za ka jajibo. Duniya a yanzu ba gaskiya, ka daina la'akari da yadda zuciyarka take, ka dauka kowa haka yake. Rayuwa ta canja, ka yi wa mutum rana ne shi kuma yayi maka dare. Daga haduwa da Baban yarinya, yana koya maka karatu, shi kenan, kun zama 'yan uwa har za ka jajibo mana 'yarsa fitsararriya ta zo ta batawa namu 'ya'yan tarbiyya." Bakura ya dakatar da ita ya ce, "Ba haka ba ne, mahaifinta ma baya so ta ci gaba da karatu, aure yake so ya yi mata." Samira ta yi ajiyar zuciyar dadi ta ce, "Oho kayan daki yake so ka taimaka mu su da shi, ai ba komai zan dauki nauyin kayan kicin, ai sadaka ce." Bakura ya yi shiru kansa a kasa. Can ya dago ya dubi Samira ya ce, "My wife, kin fi kowa sanin yadda Zuhuriyya take a wajena ko?" Samria ta gyada kai ta ce "Na sani." Ya sake cewa, "Kin fi kowa sanin irin tsananin quncin da nake ciki, tun daga ranar da Zuhuriya ta tafi ta bar ni, har zuwa yanzu ko? Kin fi kowa sanin yadda zan iya salwantar da rayuwata a wajen nemo inda Zuhuriyya take da a ce zan iya nemo ta don kawai in sake ganinta ko? Samira na san irin halaccin da ki ka yi min a rayuwata, wanda ba dan na hadu da so da qaunarki ba da ban kawo ga wannan matsayi ba. Ba ni da wacce ta fi ki, domin duk inda aka bata min rai Allah-Allah nake in dawo wajen ki, kece me kwantar min da hankali. Samira, ina so in taimaki rayuwar Sajida, saboda abu biyu." Samira ta yi murmushin jin dadi, zuciyarta cike da annuri ta ji rabin ranta, abun qaunarta yana yabonta. Ta gyara zama tana mai muradin ta ji abin da zai zano mata. Bakura ya lumshe ido gami da kankame yanyatsun hannunta ya ce, "abu na farkon da yasa nake jin ba zan iya barin rayuwar Sajida ta wulakanta ba, shi ne ina da 'ya'ya, akwai mutuwa, akwai laurara, ba na fatan yau a ce babu ni 'yata Yagana ko qannenta su shiga irin rayuwar da Sajida take shirin fadawa. Ni Musulmi ne, Sajida Musulma ce, ya cancanci in taimaka mata." Samira ta gyada kai ta ce, "Haka ne my dear. Allah zai taimaki duk wani mai taimakon jama'a. Bayanka zai yi kyau, da izinin Ubangiji." Bakura ya ci gaba da cewa, "Sai abu na biyu kamar yadda na fada miki a baya, Sajida ta yi kama da Zuhuriyya, tamkar kafar hagu da dama, tamkar an baskara goro gida biyu. Tun da nake ganin tagwayen da ake haifa tare su yi kama daya, ban taba ganin irin wannan kamar ta Sajida da Zuhuriyya ba. Na rasa Zuhuriyya, na hadu da Sajida, bana jin zuciyata za ta iya barin Sajida ta kauracewa idanuwana, ma'ana in daina ganinta a doron qasa ba, ba na so ta yi nesa da ni." Wannan karon Samira ta ji kirjinta ya buga,bamm'!! Kamar an buga ganga. Ta zare ido ta ce, "Kamar yaya, ban gane ba?" Bakura ya sunkuyar da kai kasa ya ce, "Ni ne kadai na cancanci in auri Sajida. Har na amsawa mahaifanta." Kamar wani garwashin wuta, haka Samira ta warbar da hannun Bakura daga hannunta, ta zabura ta miqe tsaye. Yayin da gaba daya gidan ya fara jujjuya mata, ji take tamkar kanta ya koma kasa, qafafuwanta ne a sama. Ta rasa gabas, ta rasa kudu. Ta ji kwakwalwarta ta rude, ta kasa tuno duk wani abin da ya taba faruwa a rayuwarta, wato ta yi (loosing memory). Bakura ya taso yana qoqarin ya riqe ta, sai ta daka tsalle gefe tana ja da baya. Fadi take. "Kar ka taba ni, kar ka qaraso inda nake, ba na son ganinka." Bakura cike da mamaki ya ce, "Samira, nine fa. Ni kike cewa ba kya son ganina?" Daga yadda ya ga idanuwanta na wurwurgawa daga inda ya tabbatar Samira ba ta cikin hayyacinta. Bin ta yake yana lallashi, ita kuwa sai ja da baya take, daga qarshe ma ta bude qofa ta fice waje da gudu. Bakura ya bi ta a guje suka dinga tsere a farfajiyar gidan, ba tare da masu gadi sun san abin da yake faruwa ba. Bakura ya yi ta maza, ya damkota ta na fisgewa tana fadin ita ya bar ta ta fice ta tafi ko'ina ne ma a rasa ta da ta ci gaba da zama da shi. Ya kankame ta tsam a kirjinsa babu kalmar da take fitowa daga bakinsa sai "I'm really sorry my dear, I love you my love." Kalaman maigidanta sun zame mata tamkar zuma a zuciyarta, sun zame mata tamkar ana hura sarewa a kunnuwanta, don haka ta ji ta kasa fisgewa saga jikinsa. Sai ta fashe da kuka, mai tafe da hawayen kunar zuci. Hankalin Bakura ya tashi matuqa, idan ya duba hawayen Samira sai ya tuno hawayen Sajida, sai ya tuno hawayen Zuhuriyya, sai ya ji zuciyarsa tamkar an diga darmar wuta, ma'ana hawayensu dafi ne a ransa. Ya fada a bayyane "Hawayenku tamkar dafi ne a cikin zuciyata. Ku yi hakuri zan mayar da kukanku dariya, in Allah Ya yarda." Da kyar da sudin goshi Bakura ya lallashi Samira ta yarda suka shiga dakinsa suka kwanta, yadda ta kwana bata runtsa ba, haka ya kwana bai runtsa ba. Kuka take, shi kuwa Kwanakin Bakura uku a cikin gida baya fita ko qofar gida, yana nan yana gadin Samira. Ta tubure, ita sai ta fita an neme ta an rasa. Bakura ya damu, ya rasa yadda zai yi ya shawo kan wannan matsalar, daga qarshe ya buga waya ya sanarwa da babbar yayar Samira, mai suna Hajja Farida, da ke zaune da maigidanta a unguwar Janbulo. Ko awa guda ba ta yi ba ta diro cikin gidan su Bakura. Aka zauna ga Samira, ga Bakura, ga Hajjiya Farida aka mayar da magana. A tunanin Samira yayarta za ta bi bayanta, sai ta ji yayar ta bi bayan Bakura, har take yi mata fada cewar shashanci ne wannan. Ta nuna mata qara aure ga namiji ba wani abu ba ne, domin ita ma kishiyoyinta biyu, ita ce ta uku, kuma ita ce uwargida. Da yake 'yar kasuwa ce qasashe take zuwa tana kawo kaya, sai ta ce da Bakura ya ba ta kwangila ma ta hado masa lefen amarya da uwargida. Cikin farin ciki Bakura ya amsa mata cewa. "ki yi min lissafin duk abinda ya kamata a saya musu, zan zo har gida mu zauna." Wani kullutun bakin ciki ne ya kakare a wuyan Samira a halin yanzu ta fi jin haushin yayarta Hajjiya Farida a kan Bakura ma. Bakura ya yi wa Farida sallama ya dauki mukullin motarsa ya fice don ya ba su waje, ya san Farida za ta taimaka masa wajen bawa matarsa shawara mai kyau, dadin dadawa kuma Samira na matuqar jin tsoron Hajja Farida, kasancewar ita ce babba a dakinsu, ga ta mafadaciya ce, kuma mai kudi ce. Bakura ya bude mota ya shiga ya zauna kenan, kafin ya jawo qofa ya rufe sai ya ji muryar Zahra. Ya yi sauri ya waiga, sai ya ga Zahra a durqushe jikinta a sanyaye kamar marar lafiya. Cikin harshen turanci take magana ta fara da tambaya. Ta ce, "Abba, me yake faruwa ne tsakaninka da Mamanmu kwana biyu take kuka?" Bakura ya rasa amsar da zai ba ta. Kafin ya gama kame-kamensa Zahra ta qara da cewa. "Yanzu kuma da Hajjiya Farida ta zo Abubakar ya ce min yaji ana cewa za ka qara aure. Haka ne?" Bakura ya gyada kai cikin sanyin jiki ya ce, "Haka ne Mamana." Hawaye ya cika mata ido, sai ta yunqura ta miqe ta ce "Allah ya sanya alkhairi," Bakura ya ce da ita, "Zo nan, kin san wacce zan aura ne?" Zahra ta girgiza kai alamar a'a. Ya ce, "Yagana, ki yi hakuri da abinda zan fada miki, na san ba zai yi miki dadi ba. Kada ki girgiza, kada ki ga laifina ina da dalilin yin haka, wanda ba za ki gane ba sai nan gaba." Zahra ta sharbe hawaye ta girgiza kai ta ce, "Ba zan damu ba Abba kowace ce. Ya yi huci, wanda ya fitar da iska mai zafi ya ce, "Sajida zan aura." Zahra da ke durkushe sai ta fadi zaune tubus. Can ta fara jan jiki kamar yaron da yake koyar rarrafe. Kafin mahaifinta ya ce wani abu Zahra ta fashe da kuka, ta miqe ta runtuma cikin gida da gudu. Ba ta tsaya a ko ina ba sai cikin đakinta, ta rufe kanta don takaici. Fiye da minti talatin Bakura na zaune a cikin mota ya kasa kunna motar ya tafi, saboda damuwa. Ya rasa madafa, ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa. Hakika Bakura ya shiga tsaka-mai-wuya. Namijin duniya da ya fita daga gidansa gidan su Sajida ya nufu, ita kuma ya je ya ga wanne gumurzun za a yi. Faduwar gaba asarar namiji, amma ya san za a yi gagarumar rigima da fetsararriyar yarinyar nan musamman idan suka hadu ta ganshi, mutumin da ya raba ta da rabin ranta Abdul majid kuma yanzu ya zo ya ce zai aure ta. A kofar gida ya iske Malam, bayan sun gaisa, sun taba 'yar hira. Malam ya dubi Bakura ya yi murmushi, ya ce, "Ka bar mu da rigima, Sajida tana da taurin kai, har yau ba ta haqura da yaron nan ba. Inda muka sami sauqin abun da muka ce mata kai dan sanda ne, tuni kasa an kama Abdul majid an daure shi har sai ta daina tunanin guduwa wajensa sannan za' a sako shi. Ka san yaran yanzu marassa kunya, kullum roqar uwar take wai a ba ka hakuri ka sake shi ba za ta gudu ba." Bakura ya yi dariya ya ce, "Allah Ya kyauta, ai mata kwakwalwarsu qarama ce, tunaninsu gajere ne. Nima kwanaki ukun nan ina gida muna gumurzu da uwargidana na sanar mata zan yi aure. Amma yanzu Alhamdulillahi rigimar ta lafa, shi yasa ma na samu na fito. Ai mata ba sa son kishiya." Dadi ya rufe Malam ya ce, "Ikon Allah, har ka sanarwa uwargida, amma wannan abu ya yi min dadi. Nima a nan ni da almajiraina kullum sai mun yi saukar Kur'ani daya, an yi sadaka akan Allah Ya tabbatar da wannan abu, ya kawar da duk wasu fitintinu." Bakura ya ce, "Amin Malam, ai kamata ya yi a dinga yin saukar nan sau uku a rana daya, zan dinga biyan masu karatun a qaro Malamai, domin abubuwan da yawa. Ka ga har yanzu Sajida ba ta san ko ni wanene ba, don ba ta daga ido ta ganni ba." Malam ya ce, "Kar ka damu ta fara laushi, jikinta ya yi sanyi kamar ta saduda, saboda Furera tana ba ta baki kullum ba dare ba rana. Sama'ila ma na kira shi na ba shi haklquri, na nuna masa illar da na hango masa idan aka yi wa Sajida tilas ta aure shi. Yaron mai hankali ne bai damu ba, kuma ya fahimce ni. Mu shiga ciki ku gaisa da Sajidar mana." Bakura ya zabura ya ce, "Ah! Haba ai ba komai ba sai mun gaisa ba, idan aka yi auren ta ganni." Malam ya yi dariya ya ce, "Haba, haba kamar a mutanen da, ai gara ku dinga gaisawa, ku san juna kafin lokacin, bari in turo ta ko a zaure ne ku tsaya ku gaisa." Malam ya shiga cikin gida da sauri, yayin da Bakura ya je zaure ya tsaya, sai kai kawo yake daga wannan bango zuwa wancan, zuciyarsa cike da zullumi da fargabar abinda zai je ya zo. Kamar an wurgo ta haka ya ganta 'dif a gabansa sanye da wani zunbulelen hijabi ruwan toka. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, domin ganinta ya sake tono masa zafin rabuwa da mai kama da ita wato Zuhuriyyarsa. Kallon-kallo ake tsakanin Bakura da Sajida. Kallo irin na qeqe-da- qeqe, ido cikin ido ba tare da daya ya rusuna idonsa ba. Kowannensu ya na nasa tunanin a ransa. Shi al'ajabi yake yadda kamannin Sajida da Zuhuriyya suka zama daya. Ita kuwa kallo daya da ta yi masa ta tuno inda ta taba sanin fuskarsa. Tabbas wannan shi ne mutumin da ya taba musgunawa rayuwarta. Wannan shi ne mutumin da ta ji ta tsana a cikin qanqanin lokaci a ranar da ta fara ganinsa a rayuwarta. Nan da nan kwakwalwarta ta tuno mata da kamannin Zahra, ta hada fuskokinsu ta tabbatar kamanninsu daya. Ta sake tuno kalmar da ya fada mata cewar yana da 'yarsa sa'arta Zahra, wacce yake kwatanta ta da ita ce kwaryarsa ta gari da ya saqale ta a ragaya. Lallai akwai wani tuggu da mutumin nan ya hado mata na ya raba ta da abun qaunarta don shi ya aure ta. Sajida ta fada a ranta, "Sai dai a kai gawata ta zauna da wannan amma ba ni ba." Bakura ne ya katse tunaninta ya ce, "Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa barakatuh. Sajida mun hadu a kashi na biyu, sai dai wannan haduwar tamu ta sha bamban da ta farko. Sajida, da kin san irin girma da darajar wacce kike yi min kama da ita da baki shiga damuwa ba. Ba zan iya wulakanta ki ba, ba zan iya cutar da ke ba.." Bai rufe bakinsa ba ta daka masa wata tsawa mai tsoratarwa, ta ce, "dakata Malam, rufe min baki, yi min shiru." Dariya ce ta subuce masa, domin ya tuna wasansu da Zuhuriyya, tabbas muryarsu da yanayin maganar Sajida da Zuhuriyya iri daya ce. Haka sak wannan kalmar Zuhuriyya take furtawa. Dariyarsa ta sake hargitsawa Sajida fushinta, ta dada 6ata rai ta ce, "Ka yi dariya mana tunda ka hada min tuggu, Zahra 'yarka ce ashe ka kawo ta ta shigo gidanmu ta ga abinda nake, don ku raba ni da Abdul dina, kai ka aure ni, to bari ka ji in fada maka da in aure ka gara in halaka kaina, kamar yadda Abdul majid ya rasa ni, kai ma ba za ka same ni ba Kada ka manta tun ranar da na fara haduwa da kai na ji na tsane ka, yanzu na qara tsanarka, kuma na tsani 'yar ka Zahra." Kallonta kawai ya tsaya yana yi, tsiwa take yi tana murguda baki, ta gama cashe masa ta Juya ta shiga gida. Ya bi ta da kallo har da leqe. Ya fito jikin motarsa ya tsaya ya yi shiru, tamkar gunki. Ba baqaqen maganganun da ta fada masa ba ne suke yi masa reto a zuciya ba, a'a tsantsar kamar ta da Zuhuriyyarsa ce mamaki ya sake damqarsa. Sajida na shiga tsakar gidansu ta yaye hijabi ta yi zaman 'yan bori 'dabas' ta rafsa wani uban ihu kamar wacce ake cirewa rai. Ta ce, "Wallahi ba zan auri wannan mutumin ba gara in auri kuturu ko makahon da yake bara a titi." Malam ya fito daga bandaki ya dire buta da sauri, yayin da matarsa ta fito daga daki a guje suka rintimo wajen Sajida suna tambayarta. "Lafiya? Me ya yi miki mutumin? Daman kin san shi?" Cikin kuka ta ce, "Shi ne Baban Zahrar nan da take hada min gulma. Ashe shi ne ya aiko ta, don a raba ni da Abdulmajid. To gara in auri kowa da in aure shi." Umma Furera ta ce, "Ya aka yi ki ka san shi ne, wannan waçce irin magana ki ke yi?" Malam ya ja dogon tsaki ya ce, "Ai kin aure shi kin gama da izinin Ubangiji, zancen banza. Har kin isa ma ki zabi abinda kike so? Ai mutunci da lallashi a tsakanina da ke ya wuce." Ya fice ya bar Umma Furera riqe da Sajida. Da alama Umma Furera ta shiga tabarbarewar tunani ta rasa kan zancen. Tana zanowa kanta tambayoyi. "A ina Sajida ta san wannan mutumin? Ya aka yi ta san mahaifin Zahra ne?" Malam ya qaraso wajen motar Bakura, Bakura ya yi sauri ya saki ransa ya hau murmushin qarfin hali. Ya ce da Malam, "Zan koma gida sai gobe idan Allah Ya kai mu." Malam ya ce "Kun gaisa da Sajida ko? Bakura sai haquri fa, ka qara hakuri da Sajida." Bakura ya katse Malam da cewa, "Kai haba, ai ba komai yarinta ke damun Sajida." Malam ya ce, "Har ina tunanin in ce maka kar ka dauki fasagurbin kwai ka hada shi da kwayayenka masu kyau. Ma'ana kada ka dauki Sajida ka kai gidanka ta 6ata maka tsarin gida. Ni da Allah Ya bawa in ci gaba da hakurin zama da ita." Bakura ya yi sauri ya ce da Malam "Ka daina fadar haka, haba Malam wadannan kalamai su daina fitowa daga bakinka a kan Sajida saboda karfin bakin iyaye a kan 'ya'yansu agar ka dinga furta alkhairi. Halin da Sajida ke ciki ba wani abu ba ne na daban, a kowanne gida yana faruwa. Bai kamata ka dauki Sajida kangararriya, ta gagari jama'a ba, har ana daure ta a sarka. Ka ci gaba da ba ta baki ku lallashe ta,a qarshe ku yi tayi mata addu'a." A haka dai suka rabu da Malam, Bakura ya nufi gida. Gidan Bakura tamkar ana zaman makoki. Samira da 'ya'yan jugum-jugum, haka Bakura ya samu waje ya zauna ya yi jugum. Duk da ya na daurewa yana jan su da hira, amma shi ma hirar bata kai har zuciya ba, saboda tashin hankalin da yake ciki ta bangarori guda biyu, ko ina ba dadi. Sai ya ji a zuciyarsa kamar ya fasa auren kasancewar damuwar da iyalansa suke ciki, sai ya tuno kamannin Sajida da Zuhuriyya, sai ya ji ba zai iya fasa aurenta ba, komai runtsi. *** *** *** A cikin satin Bakura ya je gidan Hajjiya Farida ta dauko masa dogon list din abubuwan da ya kamata ya zuba a lefen amarya da uwargida iri daya, kamar yadda Bakura ya umarce ta da ta yi komai iri daya kada ta bambanta. Hakika kayan suna da yawa, kuma tsadaddu ne, don haka miliyoyi za su sha kashi, akwatuna shida-shida har da kite din gwalagwalai. Ya ce ta lissafa akwatunan bibbiyu na Mahaifin samira da mahaifiyar Samira sannan Akwatuna bibbiyu na Mahaifin Sajida, biyu na Mahaifiyarta. Sai akwati guda ta Zahra, Akwati guda-guda ta Abubakar, Umar da na Usman. Cas ya caske mata kudin ya miqa mata cek, don haka a satin ta shigar da visa tafiya qasashe biyu don hado lefen, wato London da Dubai. Ta ba shi tabbacin a cikin sati biyu komai zai kammala. A cikin satin Bakura ya yi wa kamfanin da suke yi masa gyaran gida da kawatawa waya ya ce su zo ga aiki, turawa ne, ofishinsu ya na Abuja. Ya sanar musu yana so su zo su sake masa fenti, labulaye da gaba daya furniture gidan, na zamani, sabon yayi. Sun san Bakura, sun san halinsa akwai naira, kuma baya tsoron kashewa. Abun ka da Nasara a sarar duniya a ranar suka hawo jirgin yamma daga Abuja zuwa Kano, su uku ne mace daya, maza biyu suka fara aune-aune, gwaje-gwaje, rubuce-rubuce da lissafe-lissafe. Babu irin lallashin da magiyar da Bakura bai yiwa Samira ba a kan ta zo su zauna da ma'aikatan nan ta fada musu yadda take son a tsara gidanta, ta qi fitowa. Ta ce duk yadda yake so ya je ya yi shi da amaryarsa Sajida. Duk da aikinsu ne, amma hankalin Bakura bai kwanta ba sai da ya yi kiran Zahra ta zo ta zauna da su ta fada musu kaloli da irin yadda take ganin zai yi kyau. Bakura ya yi ajiyar zuciya ya dubi Zahra ya ce, "Wancan dakin da ku ke kira dakin baqi shi ne zai zama dakin Sajida, za a zuba mata kaya iri daya dana Mamarki, sai dai kalar ta bambanta. Haka bandakunan ma duk a ciccire tiles da kayan ciki a zuba masu tsada." Zahra ta yi 'dumm' yayin da shi ma Bakura ya kula da hakan. Da alama ba ta ji dadin batunsa ba. Babu yadda ta iya haka ta kaikace ta zabarwa Sajida kalar fenti, labule, kujeru, gadaje, talibijin, C.D, hometharter, kayan toilet da dai sauransu, wadanda darajarsu daya da na Mamarta. Haka ta tsara dakin Bakura, haka na ta da na qannenta da kicin. Kacokan farfajiyar gidan aka canja yanayinta. Duk wannan abinda ake Samira ko uffan ba ta cewa, daki ta shige ta yi kwanciyarta. *** *** *** A cikin satin aka duqufa aka fara gyara, aka fitar da tsofaffin kayan gidan aka rabarwa 'yan uwa da abokan arziki, masu aiki ma suka kwashi rabonsu. Aka fente gida aka zuba komai sabo daga cikinnkwalayensu. Duk da ma'aikatan su na da kayan aiki na zamani sai da gyare-gyaren ya dauke su tsawon sati biyu, amma fa gida ya tsaru. Idan wanda bai sani ba ya shigo gidan sai ya rantse da Allah batan kai ya yi ba gidan ba ne qasar waje ne. Daidai sanda aka gama gyaran gidan daidai lokacin da Hajiya Farida ta gama hado lefe. Me ya yi saura? Hajiya Farida da kawayenta guda biyu, sai matan abokansa uku da kannensa biyu daga Maiduguri ne suka hadu suka kai lefen Sajida. Umma Furera da 'yan uwanta da maqwabta sai suka bude baki kawai su na kallon wannan abin al'ajabi, sun ga lefen da duk tsurkukin unguwarsu ba a taba kawo irinsa ba. Naira ta yi kuka, lallai ko ba a fada ba kowa ya san Sajida ta yi tuntube da kasaitaccen miji mai arziki. Sal dai Hajiya Farida da tawagarta sun shiga wani hali na mamaki da ta yadda aka yi Bakura ya fada hannun wadannan talakawa liqis, sun yi bazata ba su dauka irin wannan gida da irin wadannan mutane za su kawowa wannan uwar dukiya ba. Bayan lefen har da damin kudin dinki da buhunhunan abinci. Kai hatta nama da juices da za a sha a ci ya aiko da su, domin dirkeken SA' aka turkewa Malam a qofar gida. Allah sarki yaku-bayi, zobo, kunun aya da lemon kwalba guda goma su Umma Furera suka tanadarwa baqi, sai dan cincin. Hajja Farida suka shigowa Samira da albishirin cewar ta kwantar da hankalinta tamkar tsumma a randa. Yarinya dai ba kishiyarta ba ce mai aikinta ce, domin babu wayewa a tare da ita. Su ka yi wa Samira hudubar ta saki ranta ta dinka lefenta ta dinga caba ado, yadda ita kanta yarinyar da 'yan uwanta masu kawo amarya za su kidime. Haka shi ma mijin zai san ya yi kuskure wajen jajabo bakauyiya, 'yar talakawa likis. Hakika Samira ta dauki shawararsu ta dan saki ranta, don haka ta shiga gyaran jiki ciki da waje. Abu kamar wasa qaramar magana ta zama babba,in ji wani mawaqi. Auren Bakura da Sajida ya tabbata. Sai dai tun ranar da Bakura da Sajida suka hadu a zaure ba su sake ganin juna ba. Haka daidai da sakon daya Sajida ba ta ta6a saduda ta furta da bakinta ta ce yarda za ta auri Bakura ba. Ko da yaushe zillo take ana riqo ta kamar wata kifi. Duk da dinbin dukiyar da ta ga an kawo an jibge a gidansu kace-kace, bai sa Sajida ta ji digon son auren nan ba. Ta rame, ta Jejjeme, saboda tsananin kiyayyar auren. Sai kuka, sai tabara da tsiwar da take tafka musu a cikin gidan. Dole ce tasa Umma Furera ta shiga cikin qawayen Sajida suka yi ta fita tare don aiwatar da abubuwan biki, kamar su kai dinkunan da amarya za ta saka ranar biki, da buga katin gayyatar biki. Haka Malam da almajiransa suma suka bazama suka shiga kasuwa don siyo fenti, tabarmin da zaa shimfidawa baqi su zauna 'yan daurin aure da katin gayyata. Domin daga dukkan alamu manyan baqi, jiga-jigan masu kudi, masu sarauta, 'yan kasuwa, da 'yan siyasa ne za zu halicci daurin auren nan. hakuri yake bayarwa baya gajiyawa. ta qona gidan, Allah ya kiyaye." RANAR DAURIN AURE Allah mai yadda Ya so, duk abinda ka ga ya faru da bawa to bawan ya kudira a ransa rubutacce ne daga Rabbul samawati. Babu wanda ya isa ya tsallake kaddarar da Allah ya rubuto masa. Matar wani ba ta auren mijin wata, haka Baban wani baya haifar dan wani. Ranar Asabar da misalin qarfe goma na safe ne, daurin auren Alh. Bakura da Haj. Sajida. Haka kuwa aka yi, kafin goma ta cika kofar gidan Malam Yakubu ya cika maqil da bil-adama. Dangin Sajida na wajen uwa da uba sun hallara, yaransu da manyansu . Haka dangin Bakura daga Maiduguri na wajen uwa da na uba suma sun hallara kacokan dinsu. Ga uwa-uba abokan Bakura, abokan kasuwancinsa daga garuruwa daban-daban. Tsofaffin abokanansa tun na sakandire suma ba a bar su a baya ba. Don a cikinsu har da masu girma gwamnoni da mataimakansu na jihohi uku, Kano, Maiduguri, dana Yobe. Haka kusan gaba daya dangin Samira sun zo kama daga mahaifinta, yayansa, surukansa da 'yan uwansa suma ba a bar su a baya ba. Saboda su na son Bakura, suna ganin mutuncinsa, saboda ya san mutuncin kowa. Gashi su na jin dadin yadda ya riqe musu 'yarsu hannu bibiyu ita da 'ya'yanta asirinsu a rufe. Don haka da Bakura ya je ya sanarwa mahaifin Samira zai qara aure bai damu ba, sai ya yi masa addu'a gami da yi masa nasihu masu ratsa jiki. Ya nunawa Bakura hatsarin rashin nuna adalci ga namijin da ya hada mata biyu. Daga karshe ya sa aka turo masa 'yarsa Samira ya yi mata fada sosai, ya ja mata kunne akan kada ta tayar da hankalinta, kuma ta bi mijinta sau da qafa, ta zauna da kishiryarta lafiya. Ba gidan Malam Yakubu kadai ba, gaba daya layin ya cika. Kowacce kofar gida cunkoson jama'a ce makil. Babu abun da ka fi hangowa sai galla-gallan shaddoji a jikin jama'a dinkin Tazarce da manyan riguna malum-malum. Ga kamshin turararruka yana tashi. Maroka kuwa ba a iya kirga su, masu busa kuwa Suma yi suke saboda masu sarautar da suke wajen. Dakyar ake hango ango, saboda taron jama'ar da yake bi yana ta gaggaisawa da su. Hakika daga ka ga ango za ka gasgata shi ne ango ko ba ka taba ganinsa ba.Saboda ya fi kewa caba ado ya zankada kyau da wani tsadadden yadi fari tas, wanda ya sha surfani a rigar ciki da babbar rigar. Ya dora baqar hula da baqin takalmi tsadaddu. Masu daukar hoto da bidiyo suka hau aikinsu, duk inda Bakura yasa kafarsa su na biye da shi. Saboda hayaniya da kyar suka tsagaita, misalin karfe goma sha daya da rabi aka daura auren. Waliyan ango suka miqawa waliyan amarya sadaki naira dubu hamsin lakadan. Aka yi sallati ga Shugabanmu Manzon Allah (S.A.W.) aka shafa, sannan kowa ya kama gabansa. Kowa ya shaida Sajida ta zama matar Alh. Bakura, kowa na yi musu fatan alhairi Allah Ya bada zaman lafiya. Mata ma ba a barsu a baya ba wajen nado 'yan daurin kayansu su ka dungumo gidan biki. Don haka gidansu Sajida da makwabtansu a cike yake da 'yan yinin biki. Sai dahuwar abinci ake kace-kace komai a wadace. Uwar biki Umma Furera kuwa, sai shiga leshina da shaddoji take, kai ka ce ita ce amaryar. Danginta na kauye sai bin ta da kallo suke zuciyarsu cike da sha'awa, dama su ne suka sami irin wannan. Duk wadannan hidindimu da ake yi ina amarya? Amarya na daka, a dakin ma a bayan qofa, ba wanka balle a cancada ado, duk da tulin leshina, atamfofi super, shaddoji masu tsada kala-kala, materials na zamani bayan gwala-gwalai 'yan kunnaye, sarkoki, zubbuna, da awarwaraye. Amma Sajida ta yi qiirmisisi ta toshe kunnuwanta ta qi sauraron kowa.Juyin duniyar nan da lallashi babu wanda Ummarta da danginta ba su yi mata ba, amma Sajimajid ta kekashe kasa ta ce sai dai a kashe ta, amma ba za ta yi wanka ba. Kawayenta ma ba su ji dadin wannan al'amari ba, sun so Sajida ta ware su karbi kudi a wajen ango su hada hadadden party a cashe, amma Sajida ta ki daukar shawararsu. Haka aka dinga kai kawo ana cashewa, amma biki ba amarya, har da masu kidan kwarya a tsakar gida mata suna ta shan rawa, amma Sajida ko tsakar gida ta qi leqowa. Tana bayan qofa a takure zuciyarta cike da tsantsar takaici, idanuwanta sun jejjeme. Duk ciye-ciyen nan da ake yi tun safe ko kwayar shinkafa Sajida ba ta jefa a bakinta ba, duk da tulin abincin da aka jere mata a gabanta. La'asar sakaliya Sajida ta yi niyya da kanta ta fito tsakar gida, sanye da wata kodaddiyar doguwar rigarta ja da zurmikeken hijabinta ruwan toka. Fitowar ma ta dole ce, domin fitsari ne ya cika mata mara, ga salloli a kanta Azahar da La'asar. Nan da nan masu daukar hoto da masu daukar bidiyo suka yi ruddugu suna daukarta, ba tare da ta shirya ba. Da kyar Sajida ta samu ta shiga bandaki, saboda jama'ar da suka baibaye burtintinar amarya su na daukar hoto da ita. Shigarta bandaki ke da wuya, kafin ta rufo kofa Umma Furera ta danna kai dauke da ruwa bokiti guda da kwandon soso da sabulu na wanka. Mata uku ne suka shiga bandaki su na yi wa Sajida magiya ta daure ta yi wanka, idan ba ta yi da kanta ba zasu danne ta su yi mata. Sajida ta cije, ta tubure ta ce ita fa ba za ta yi ba, amma da ta ga da gaske shirin tube ta suke da karfi za su wanke ta, sai ta saduda ta ce su fita za ta yi da kanta. Su ka fito suka bar ta a bisa sharadin idan ba ta yi wankan kirki ba sai sun sake yi mata wani. Sajida ta fashe da kukan takaici, tana wanka tana kuka babu abun da take tunawa sai Abdul Majid' dinta. Ta yi wanka mai kyau, ta yi brush, ta dauro alwala ta fito ta wuce daki fuskarta a murtike haushin kowa take ji. Bayan ta idar da sallolin da ke kanta, nan ma iyaye da qawayenta suka baibaye ta kowa đauke da kayan kwalliya. Masu taje kai na yi ana mulka mai, masu yanke farce na yi, masu shafa mata mai na yi, masu shafa hoda da jagira na yi. Ta yi ta fizge-fizge tana fadar baqaqen maganganunta da fitsara iri-iri babu wanda ya damu da abin da take fada kowa burinsa amarya ta yi kyau, domin yau da daddare za a kai ta gidan angonta Bakura. Wani tsalelen leshi ne baqi, wanda aka yi masa ado da fulawa ruwan goro, wanda ya sha dinkin riga da siket matsattse, shi ne aka sakawa Sajida. Yayin da aka dandan bara mata gwal-gwalai a kunne, wuya, yatsu, da awarwarye a hannunta kan ka ce kwabo Sajida ta fito sak amaryarta. Abarka da Kai ka fi cancanta.. Gashinta kuwa mai laushi ne aka gyara aka zubo mata da shi har bayan qeyarta, aka nade mata daurin dankwalin leshin a samansa, sannan aka yafa ma ta mayafin da ya dace da leshin wato mai ruwan goro, takalmi ma kalarsa ne, yayin da aka feshe duk illahirin jikinta da turarurruka masu qamshi na cikin lefe. Aka ruqo ta zuwa tsakargida aka zaunar da ita akan wata doguwar kujera aka fara daukar hotuna. Babu yadda Sajida za ta yi, domin an ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma zuciyarta cike take da baqin ciki da damuwa. A zaune take tamkar gunki, sai kallon mutane take sasarai kai ka ce ba ta da laka a jikinta. Duk sanda ta tuna ita da Abdul majid shi kenan sun rabu sai ta ji zuciyarta ta harba kamar ana harba bindiga. Idan ta tuno mutumin da aka daura mata aure sai ta ji ta qara tsanarsa. Ta ce a ranta "Lallai kuwa mutumin nan ya yi kuskuren aurena. Iyayena sun yi kuskuren ba shi aurena, sun yi kuskuren karbar dukiyarsa saboda asara ce. Sai na zame masa tamkar kunama mai cizo a shimfidarsa. Zan zame masa duhu alhali da hasken rana. Sai na disashe farin cikin zuciyarsa, ya koma tsananin baqin ciki da damuwa kamar yadda ya sakani ni da Abdul Majid dina. Sai na fardo wannan kyakkyawar kwaryar tasa da yake ji da ita wacce ya saqale a ragaya, idan ta fado qasa ko ba ta fashe ba, zata yi gagari a tsakar gida. Sai na yaqi uwar gidansa na hana ta sukuni a gidanta. Sai na takurawa duk wani mai rai a gidan in ya so idan ya gaji zai sake ni, ko ya kore ni, sai ya ji ya tsani zama da ni." Sajida ta yi murmushin mugunta, wanda har wushiryarta ta fito ta girgiza qafa, 'yan biki suka dau shewa hadi da guda a tunaninsu amarya ta saki ranta ta amince da auren. *** *** *** A daidai wannan lokacin Samira da tawagarta na can su na ta su walimar. Samira ta dage ta cije ta danne tsananin kishinta ta shiga cikin 'yan uwa da qawayenta su na taya Bakura farin cikin aurensa. Don haka an zuba kujeru a farfajiyar gidan, an yi dafe-dafe, an hado kayan maqulashe, mata ne zalla suka taru. Wata Malama ce mai suna Malama Jamila take wa'azi, tana tunasar da mata darajar miji a wajen matarsa. Ta na fadakar da mata su cire zafin kishi a ransu su zauna da kishiyoyinsu lafiya. Daga qarshe ta fadakar da mata da su kula da tarbiyyar 'ya'yansu, musamman 'ya'ya mata. Daga dukkan alamu wa'azin yana ratsa zuciyar Samira, ta yi shiru tana sauraro. Cancandi! Amma fa Samira ta zuba kyau, kai ka ce ita ce amaryar idan ka duba tsadaddiyar material da ke jikinta, sai walkiya take gata da iya kwalliya. Sai dai duba daya za ka yiwa Samira ka tabbatar ta rame, tana cikin damuwa. Haka 'yarta Zahra ta yi tsuru ita da qawayenta a gefe da alamar damuwa a tare da ita. Tun qarfe takwas na dare Alh. Bakura ya tura motocinsa kakaf dana abokansa gidansu Sajida don dauko amarya da masu rakiyarta. Amma ba a samu an fito da amarya ba sai qarfe goma na dare, saboda gwagwarmayar da ake ta yi da amarya, ta bujere ta ce ba za a kai ta ba. Ihu take tana bori, tana faduwa tana burgima a qasa. Hankalin kowa ya tashi, babu wanda bai zo ya tsaya akan Sajimajid ya yi mata nasiha ba. Malam da kansa ya shigo ya tashi Sajida tsaye, ya goge mata hawaye, ya dau lokaci mai tsawo yana ba ta haquri, sannan ya shiga yi mata nasihohi masu ratsa jiki, gami da jawo mata manya-manyan ayoyin Kur'ani mai girma, wadanda suka yi magana akan bin iyaye da bin miji. Daga qarshe ya yi mata magiya da roqo akan ta rufa masa asiri ta shiga mota a kai ta gidan mijinta, kada ta ba shi kunya idan ta je kuma ta zauna lafiya da kowa. Ya yi mata addu'a, gami da fatan alkhairi ya dora da godiya. Domin ya ga jikinta ya yi sanyi, tana hawaye kanta a sunkuye a qasa. Ta dauko gyalenta ta yafa, ta dauko dankwalinta ta karkade ta daura ta sharbe wani zazzafan hawaye ta fara tafiya a hankali kai ka ce kwai ne ya fashe mata a ciki, ta nufi qofar fita ba tare da ta cewa kowa komai ba. Duuuuu'!! Haka mata suke biye da ita har qofar gida inda motoci suke. Galla-gallen motoci ne duma-duma masu sanyin A.C da sautin kida reras a qofar gidansu Sajida. Wacce ta fi kyau da tsada ita ce aka Kawowa amarya gabanta aka yi mata tayi ta zo ta shiga gidan baya, amma ta qi shiga. Daga qarshe aka ba ta zabi ta shiga duk wacce take so, Sajida tsaye take qiqam ta qi motsawa. Ijiyayye awartaq ce ta zo ta rada mata wata magana a kunne ko sakon daya Sajida ba ta qara ba aka ga ita Ijiyayyen sun nufi wata jifgegiyar mota qatuwa a cikin jerin motocin da suke laye. Sajida ta bude gidan gaba ta zauna, yayin da Ijiyayye ta shiga baya. Umma Furare ta yi sauri ta ce da wasu tsofaffi biyu yayyanta su je su shiga motar da Sajida ta shiga, don ba ta yarda da wannan radar da aka yi ba. Haka kuwa aka yi, zuruf su Sajida suka ga tsofaffi biyu sun fado cikin motar sun zauna. Babu wanda ya ce da kowa komai. Sai diddika ake cikin motoci, duk motar da ka leqa mata ne jingim da 'ya'yansu wasu kan wasu. Haka suma 'yan mata sun cika motoci da yawa ana ta falli ko Allah zai sa daga cikin abokan ango daya zai dasa. Duk yawan motocin nan sai da aka bar wasu a qasa, saboda yawan mata, wasu ma 'yan gayyar sodi ne sun zo su ga qwakwab. Umma Furera na küka tana dagawa Sajida hannu, haka shi ma Malam kwalla yake yana tsaye a gcfe, har motocin suka ja suka tafi a laye. Motar da amarya ke ciki tana tsakiya, suka hau titi dodar aka nufi gidan Bakura. Sajida ta juya gefenta ta dubi direban da yake tukawa sanye yake da rawani ya rufe fuskarsa Idanuwansa kadai ne a waje, shi ma ya dube ta ya yi murmushi. Cikin harshen turanci Sajida ta yi magana, saboda tana gudun kada tsofaffin nan su ji abinda a suke cewa. Ta ce "Who are you?" Ya lankwashe murya ya ce, "Sajimajid." Haqiqa wannan muryar tayi kama da muryar abin qaunarta Abdul majid. Kan ka ce kwabo Sajida ta saki ranta farin ciki ya gauraye zuciyarta. Ta waiwayo da sauri ta dubi Iyayye wacce its ce umul aba'isin da ta hada wannan tuggun tayi yadda ta yi ta hado Sajida da Abdul majid har sai da suka hadu suka ga juna. Su na hada ido suka yi wa juna dariayar farin ciki. Ya saka hannu ya zame rawanin da ya nada don yin badda kama ya dubi Sajida duba na so da qauna cikin harshen Turanci. Ya ce, "Kin rame, kin kode, kin lalace, iyayenki su na cutarki baby." Ta yi naira-nairai da ido hawaye ya kwararo ta sunkuyar da kai qasa ta ce, "Yaya zan yi? Yaya ka ke tunanin rayuwata zata kasance idan ka bar ni a cikin wannan halin? Don haka yanzu ba zan bari ka tafi ka barni ba sai dai ka Juya kan motar nan mu gudu a neme mu a rasa." Saboda dimaucewa bai san sanda ya taka burki gaba daya suka kusa buga baki da gaban mota, sannan ya ci gaba dà tafiya. Ya ce Baby, ya ya zan yi da tsofaffin nan da suke kallona tsuru-tsuru?" Sajida ta juya ta dube su cike da takaici ta galla musu wata uwar harara mai firgitarwa.mai kyau, kowa ya kalle ta sKai ka fi cancanta Ta ce, "Sai mu zubar da a daji kawai. Ijiyayye ma kwakwalwar irin ta tsofaftin ce ba turanci, don haka su dukka sun yi turus suna kallon su Sajida, ba su san abinda ake shirin aikata musu ba. Abdulmajid ya girgiza kai. ya ce, "Ba zai yiwu ba baby, ki tafi kawai gidan mijinki, amma ki dinga bin duk wani abu da zan gindaya miki. Daddy na yana gari ya kira ni ya yi min fada cewar ya sami labarinki, don haka kada in sake in hana ki zaman aure. Idan ya ji mun gudu zai hukunta ni, koma ya kore ni daga gidansa. Mutum ne mai zafi, ga shi dan ka'ida , zai iya bi na da bindiga ya ce zai harbe ni." Sajida ta rushe da kuka ta ce, "ni fa ba zan sauka daga motar nan ba, bin ka zan yi, daman mutane suna cewa ba ka sona, ba ka damu da ni ba." Abdul majid ya yi ajiyar zuciya a bayyane ya tsuke fuska, yayin da ya fara magana cikin wata kakkausar murya mai nuni da bayar da umarni. Ya ce "Ki kula da abun da nake fada miki, kuma ki bi duk abun da nake fada miki. Ba zan gudu da ke ba, kuma ba za ki qi zuwa gidan mijinki ba, sai dai kada ki yarda wani abu ya shiga tsakaninku. Nan da wani dan lokaci idan na gama shirya abinda nake shiryawa zan san yadda zan fito da ke mu gudu a rasa mu. Kinaji na ko?" Sajida ta amsa cike da ladabi da tsananin tsoro. Ya ce, "Ki goge hawayenki ki daina kuka, ki dauka tamkar na kai ki ajiya ne nan da wani loakci zan zo in dau ajiyata." Su duka suka yi murmushi, Sajida ta goge hawayenta ta ci gaba da kallon abin kaunarta Sajimajid tana sauraron dadadan kalamansa. Daya daga cikin tsofaffin nan ce ta zuro da kanta tsakiyar Sajida da Abdul majid ta ce "Daman kin san dircban nan ne ku ke hira? Na ga alamar ma Buzu ne, don na ji kuna yaren Buzaye, daman kin iya yaren? Wacce irin hira ku ke yi idan kika yi kuka sai ki yi dariya kuma?" Haushi ya rufe Sajida da Abdul majid, har suka rasa abun da za su ce mata. iyayye ce ta ba ta amsa. Ta ce, "Iya, dan Allah ki gyara zamanki, ina ruwanki da hirarsu." Tsohuwa ta koma ta zauna. Ta ce "A'a, 'yar nan kar ki ga laifina, dole in tambaya, don in sani. Na sani ko wannan dan iskan ne Abdul majid da take so ya aiko Buzu ya sace ta." Daya tsohuwar ta ce, "Ai kuwa da mun cî ubansu, don idona idon Abdul majid sai na sharara masa mari, saboda wahalar damu da yake yi. Gaba daya ya hargitsawa yarinya lissafi, ya hanata zama lafiya, ga gidan arziki da wadata ta samu, amma ta qi kwantar da hankalinta. Ai shi ma Abdul majid din ko hauka yake ba zai fara tako qafarsa qofar gidanmu ba, ko ya turo a saçe ta ba." Sajida ta juyo ta dube su, duba na takaici da bacin rai sai ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe. Abdul majid kuwa mudubi ya seta baya yana kallon tsohuwar da take niyyar kwashe shi da mari, sai ya yi murmushi kawai. iyayye kuwa kunshe baki ta yi da gyalenta tana ta dariya a ciki-ciki. Daidai lokacin ne motocin da suke gaban su Abdul majid suka saka siginal din shiga wani katafaren gida. Nan da nan masu gadi suka wangale get a jere a layi motocin daukar amarya suka dinga kutsa kai su na shiga. Abdul majid ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa, sai idanuwansa ne kawai a fili, ya wangale idanuwan nan nasa kwala-kwala yana duban farfajiyar gidan. Ya gasgata, ya tabbatar Bakura ba sa'an yinsa ba ne ya cara masa wajen naira, sai dai su goga da babansa, koma Bakura ya fi Babansa kudi. Kalmar da yake ta fada kenan. "Wonderfiul, fantastic, beatiful. " Wata tsoka ce daga cikin qirjin Sajida ta yanke ta yi wani qarai, yayin da kuka ya tunkarowa kwayar idanuwanta. Ta dubi Abdulmajid ta fada cikin harshen turanci. "Ka kawo ni gidan wanda ba na kauna a rayuwata ka ajiye ni za ka tafi ka bar ni ko?" Ya cije baki ba tare da ya ba ta amsa ba. Ta sake cewa "in har kana sona ba za ka so in zauna da wani kato a gida daya ba da sunan mijina. Mai zai hana ka tunkari hatsari, wuya da duk wani wulakancin da za a yi mana kamar yadda na yarda zan gudu koda za a kashe ni." Ya sami waje ya tsaya ya zare mata jajayen idanuwansa da suka cika da hawaye ya ce, "Fita ki shiga gidan nan kafin wadanda suka sanni su zo su gane ni. Zan bawa iyayye sabon layi da wayar da na siya miki zata kawo miki, za mu dinga magana. Na fada miki ki daina kuka, kuma ina tare da ke a duk inda ki ke." Kaico! Soyayya gamon jini, sai Abdulmajid ya fashe da kuka . Cikin shashshekar kuka Sajida ta bude kofa da sauri ta fice tamkar ranta zai fice. iyayye da tsofaffi suka fita suma suka bi bayan Sajida. Duk wanda yake qoqarin ya riqe ta sai ta fusge. Babu yadda ba a yi ba akan ta sa mayafi ta rufe fuskarta amma ta qi, haka ta shiga gidan mayafinta a kafada, dauri a gaban goshi wato ture ka ga tsiya, ga wani kodadden idon da ya sha koke-koke. A babban falo suka iske Samira da 'yan uwanta da makwabta jingim suna jiran isowar amarya. Bayan 'yan uwan Sajida sun yi sallama, su Samira suka amsa musu, sai tsofaffi biyu 'yan uwan Sajida suka shiga tsakiyar Sajida suka kaita gaban Samira suka durkusar, sannan kowa ya sami waje ya zauna. Bayan an gaggaisa aka fara bayani, dangin Sajida ne su ka ce. "To uwargida, ga Sajida mun kawo miki ku zauna lafiya qanwarki ce, koma mu ce 'yarki ce ki gyara mata, idan ta yi kuskure. Ke kuma Sajida yi na yi, bari na bari, ke ce qarama." Samira na murmushin qarfin hali, dan ba qaramin yaqi ta yi ba da ta danne kishinta ta zauna tana sauraron wadannan bayanai. Sajida kuwa idonta tsai akan Samira da tawagarta bayan kallon banza ma har da harara take harba musu daya bayan daya. Can idonta ya hasko mata Zahra a zaune a lungu, nan fa ta kafa mata ido tana harara sama da qasa har da girgiza kai wato 'ada kai kawai na fasa miki, yanzu kuma sai na ragargaza kan dukka'. Zahra ta yi sauri ta sunkuyar da kai qasa, yayin da jikinta ya dau rawa, a halin yanzu tafi tsoron Sajida a kan mutuwarta. Haka Hajja Farida ta riqe baki tana kallon Sajida tana gyada kai, tana jinjina fitsarar Sajida. Ta tabbatar yarinyar nan ba ta shigo da niyyar zaman lafiya ba. Haka suka dinga kallon-kallo tsakanin Samira da tawagarta da 'yan uwan Sajida. Tun kafin a gama bayani Sajida ta yi zumbur ta mike tsaye ta yi kiri-kiri da ido tana duban jama'ar, ma'ana idan za ku daina bata yawun bakin ku gara ku daina, don ni babu zaman lafiya a tare da ni. Manufarta kenan duk da ba ta furta ba. Ba shiri 'yan kawo amarya suka miqe suka saka ta a tsakiya aka ja ta zuwa dakinta, tun kafin ta bude baki ta fadi wata magana da za ta kunyata su. Sajida na tafiya ta na girgiza tana tabe baki. "Lallai wannan falalliyar 'yar za a yi da ita." ln ji Hajiya Zuwaira. Daya daga cikin yayyun Samira. Samira ta koma ta jingina da jikin kujera jikinta a sanyaye, sai gyada kai take tana al'ajabin yadda Bakura yana ji yana gani ya dauko wannan halittar ya kawo musu gida. Hajja Farida ta dau dogon salati ta salallame ta ce, "Tun da nake a doron kasa shekaruna arba'in har da doriya, ban taba ganin fitsararriyar amarya irin Sajida ba." Nan dai kowacce mace ta fara tofa albarkacin bakinta, tana zayyano abun al'ajabin da idanuwansu suka hango game da Sajida. Daga karshe suka bawa Samira hakuri da nasihar ta ci gaba da hakuri komai nisan jifa qasa zai fado. Ta ci gaba da yi wa mijinta biyayya ta zuba musu ido ta yi kallon yadda za ta qarqe musu, wato tsakanin ango da amarya. Daga karshe dangin Samira suka kaiwa dangin amarya abinci kala-kala, abun sha da snacks da aka yi musu, sannan kowacce ta kama gabanta. Sajida ta yi mamaki matuqa yadda Bakura ya kashe kudi ya gyara mata daki, ba tare da sisin yayenta ba. Ta yi matukar mamakin inda Bakura ya santa har ya kamu da sonta haka. Wasu abubuwan ma daga ita har yan uwanta ba su san shi ba, na turai ne, Musamman da suka shiga cikin bandakuna sun hadu an zuba kayan Kamshi da na decoration. Aka yi shawara a bar qawayen amarya guda hudu da tsohuwa daya su kwana da ita ko Allah zai sa hankalinta zai dan kwanta. Haka kuwa aka yi kafin sha biyun dare gaba daya 'yan rakiyar amarya da masu karbar amarya sun watse. Kawayen amarya ne guda hudu da tsohuwa daya suka rage a dakin Sajida. Samira da 'ya'yanta ne jugum a zaune a falo har Bakura ya shigo gidan ba su iya tashi sun je sun kwanta ba, abun duniya ya ishe su kasancewar Bakura ya san abinda zai tarar don haka bai bari ko da daya daga abokansa ya rako shi ba. Haka ya shigo hannunsa ziqai bai siyo kazar amarci ba irin ta al'ada. To duk abinda zai suyo na marmari akwai shi jingim a gidansa, masu aiki ma ya ishe su, balle iyalansa. Kaza ce, juices, fruits, duk su na nan a shaqe a firij. Ya yi sallama ya shigo falon, gami da murda mukulli ya kulle kofar. Su duka suka amsa masa a sanyaye. Ya dube su ya yi murmushi ya ce, "Yara ba ku yi barci ba, har yanzu? Gobe fa Monday. Yau ba a cewa Abba oyoyo ne?" Abubakar ya taso ya miqawa mahaifinsa hannu suka tafa, haka Umar da Usman ma a layi suka zo suka tafa. Zahra ta taso ta dubi mahaifinta a sanyaye ta ce, "Congratulations Abba, ina muku fatan alkhairi." Sai qannenta duka suka hada baki, "Congratulations Abba." Mamaki ya kama Bakura ya tabbatar Zahra tana taya mahaifiyarta kishi ba kuma kishin kadai take taya ta ba, wacce ya auro ita ce damuwarta. Da a ce wata ya auro ba Sajida ba, ya san Zahra za ta bi bayansa ba za ta bi bayan mahaifiyarta ba, saboda Zahra tafi son abun da mahaifinta ke so. Yaran ne suka katse masa tunaninsa suka hada baki, "Good night Abba, Good night Mama." "Good night children. " Samira da maigidanta suka fada cike da fara'a. Yara suka nufi dakunansu ba tare da su na jin dadin zuciyoyinsu ba. Bakura ya matso kusa da Samira ya zauna ya dube ta ya yi murmushi ya fada cikin wata 'yar siririyar murya. Ya ce, "Samira, kin yi kyau, kamar ke ce amaryar, har kin fi amaryar." Hohoho! Idan ka tona zuciyar Samira za ka yi mamakin irin baqin da ta yi, don takaici. Ta bata rai, gami da daga hannu ta dakatar da shi. Ta ce, "Ba na so, kar ma ka fara wannan zancen. Ni a suwa? Ka tashi mu je in rakaka dakin wacce yau za ta ji dadin kalamanka, amma ba ni ba." Ta mike tsaye zumbur ta rike kugu tana girgiza kamar mai shirin dambe, sai huci take tamkar kasa. Ba musu Bakura ya mike bakinsa cike da magana, haka dariya take son kufce masa, amma yana tsoron furtawa. Su na isa kofar dakin Sajida sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi. Samira ta daga hannu za ta murda kofar ta bude, sai Bakura ya rike hannunta. Ya ce, "Kar ki bude, mu je dakina ki taya ni kwana, ni ba sai na ganta ba." Haushinsa ya sake rufe zuciyarta, ta fusge hannunta ta murda kofa ta tura kai cikin dakin, gamị da kwada sallama. Sun yi dayday a falo su duka kowacce ta lumtsuma cikin kujera mai laushi, sai lumshe ido suke yi. Ga A.C na ratsa sassan jikinsu, ga talabijin su na kallo. Lokaci guda suka dago da idanuwansu suna kallon Samira, ta waiwaya bayanta ta tsuke fuska ta ce da Bakura. "Shigo mana." Ya shigo cikin falon, yayin da idanuwansa suka dira akan Sajida kiri-kiri yana kallonta, kasancewar haske tar gashi ba ta bunjima hijabin nan na ta ba. Ba mayafi, ba dankwali tana zaune ta harde kafa tana saqe-saqen tuggu a zuciyarta. Kan ka ce kwabo Sajida ta murtuke fuska ta fara harbo masa kibiyoyin harara. "Wai wannan yarinyar wacce irin kama su ka yi da Zuhurriyya haka kamar an tsaga kara ?" Bakura ya fada a zuciyarsa. Ya yi karfin hali ya durkusa ya gaishe da tsohowar nan, yayin da su iyayye ma suka gaishe shi, ya amsa cike da fara'a, gami da cewa. "Me ku ke bukata a kawo muku?" Su duka suka hada baki, "Babu komai." Samira ta yatsune fuska ta ce, "To amarya ga angonki na kawo miki, babu abinda zan ce sai addu'a, Allah ya bada zaman lafiya, ya kawo kazantar daki. Sai ku dunguma ki bishi dakinsa ni dai na tafi sai da safe." Samira ta juya za ta fita Bakura ya yi zuruf ya bi ta a baya, suka fice. Sajida ta ja wani dogon tsaki ta murguda baki ta ce, "Wa ya ga amarya, amma kuwa kin yi batan kai da ki ka shigo min da wannan mutumin dakina." Caraf Iyayye ta yi sauri ta toshewa Sajida baki, don kada su Samira su juyo ta. Nan fa suka hau rokar Sajida akan ta tashi ta shirya ta je dakin ango. Saboda takaici ko kallonsu ba ta yi ba ta tashi ta shige uwar daki ta kwanta kan gado ko kayan jikinta ba ta cire ba. A kofar dakin Samira suka tsaya suka dauki lokaci mai tsawo su na tataburza har da kokaye-kokaye. Bakura zai shiga dakinta, ita kuma ta ce ba zai shigar mata daki ba sai dai ya tafi dakinsa don ta san in anjima amaryarsa za ta je ta same shi. Kalmar da ta fito daga bakin Bakura ita ta bawa Samira mamaki da ya ce "Ko Kur'ani ki ka ba ni zan dafa cewar Sajida ba za ta zo inda nake ba, saboda ba ta sona." Wani kallo na takaici, gami da karka raina min hankali mana, haka Samira ta kalle shi ta tabe baki. Ta ce, "Ai kai kana sonta, tunda ka auro ta sai ku je can ku karata." Ta yi wuf ta shige dakinta ta datse ta bar shi anan a tsaye. Ya yi shiru yana tunani, ya kalli kofar dakin Sajida, ya juya ya dubi dakin Samira sai ya girgiza kai ya yi murmushi, ya juya ya nufi dakinsa. Yana shiga dakinsa ya tura qofa ya rufe yasa hannu a aljihunsa ya zaro wasu hotuna guda biyu ya ajiye a tsakiyar gadonsa. Hotunan Sajida ne, wanda aka dauke ta a tsakar gidansu dazu da yamma a wajen yinin bikinta. Daya kafin ta yi wanka aka dauka, dayan kuma bayan ta yi wanka ta caba ado daidai lokacin da ta yi wannan murmushin nata aka dauka. Wato mai daukar hoton har ya wanko ya kawo masa shi ne ya bar sauran a mota ya zabo guda biyun nan wanda take ita kadai don ya tantance abinda ya ke so ya tantance. Ya shiga bandaki, ya dade yana kwara ruwa a jikinsa, saboda duk jikinsa danko yake yi masa. Yana fitowa daure da tawul, sai ya zura doguwar riga 'yar yaloluwa marar nauyi. Ya taka gado ya kinkimo wata 'yar akwati akan wadurof ya zo ya zauna akan gado, ya baje wasu hotuna a tsakiyar gadonsa. Ma'ana hotunan Zuhuriyyarsa ne ya hada da hotunan Sajidarsa, don ya ga ta inda suka bambanta. Ai kuwa sak kamarsu daya, kirar jikin ma daya, ga dariya da murmushinsu iri daya. Sai mamakinsa ya sake daduwa. Surutai yake shi kadai cikin dare, kamar tababbe. Hakika Bakura yana cikin wani hali domin akan ya san asalin wannan kama ya sa ya auro Sajida, amma har yanzu babu wata shaida da ta nuna masa alaka ko kadan tsakanin Sajida da Zuuriyya. Haka Bakura ya raba dare, sannan ya hakura ya kwanta. Gajiya, gami da dogon daren da ya raba bai yi barci ba basu hana shi tashi da Asuba ya je masallaci ba. Ya na dawowa ya bi dakunan gidan gaba daya yana bugawa har da dakin Sajida. Kowa ya tashi wuri-wuri ya shiga bandaki, don dauro alwala. Bakura kuwa da ya tabbatar kowa ya tashi sai ya shiga nasa dakin ya kwanta, saboda barcin da ya addabi idanuwansa ya sake kwanciya. Samira kuwa tana farkawa bayan ta yi sallah, sai ta shiga kicin ita da kukunta suka shiga shiryawa yara 'yan makaranta abinci. Haka abincin mai gidanta da na Sajida da 'yan uwanta daban. Yau Samira ta sake zagewa wajen qara qawata abinci fiye da kullum, saboda tana so ta nunawa su Sajida bakin rijiya ba wajen wasan yara ba ne. Ta na so Bakura ya san ba irinta ake aurowa kishiya ba, saboda babu abin da amaryar za ta fi ta. Bayan komai ya dahu, ta dauko tsala-tsalan food fasks hade da plates da cokula da saving spoons hadaddu wadanda ta suyo su daga Saudiya na sarakai ne, domin an diga ruwan gwal da azurfa a jiki. Burinta ta burge qauyawan nan da suka zo gidanta da sunan amarya da qawayenta. Ta kira masu aikinta guda biyu Hajara da Grace suka dinga diba su na shigarwa dakin Sajida su na jerawa akan Dining table, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar qawayen Sajida. Sai kalmar "Sannu, mun gode." Suke fadi, daidai lokacin Sajida ta fito falo das da ita, ta yi wanka ta caba ado da wata atamfarta Super Holand kalar kore da ruwan dorawa (Green and ycllow) wacce ta sha dinkin riga da zani daidai jikinta. Ta kuwa nada dauri cas da ita kai ka ce ango ta yi wa wannan ado. Sai kamshi ne ke biye da ita a sanadiyar feshe jikinta da ta yi da turare (Designers). Hakika yunwa ce taf a cike a cikin Sajida, kasancewar jiya ba ta ci abincin kirki ba. Dan yunwar dare ma ta so ta hana ta barci, bakin ciki ne ya hana ta tashi neman abinci cikin dare. Don haka ta yi farin cikin ganin wadannan galla-gallan warmers. Kai tsaye Sajida ta haye kan tebur ta kalli kawayenta. Ta ce, "Mai ci ta zo don ni ci zan yi, wanda ya ga bati ya kyale jahili ne. Wahalallun har sun gama abinci da sassafen nan, sai dai su dafa su ba ni dan ni babu wanda zan dafawa abinci a gidan nan, saboda ajiya aka kawo ni in ci in yi gaba." Suka taso kowacce ta sami tata kujerar ta zauna. Zainab ta dubi Sajida ta yi dariya.Ta ce "Sajida ba ki da mutunci." Tsohuwa ta ce, "Ba zan hau tebur ba kar in fado saboda dadi ku zubo min nawa a kasa zan ci." Tun kafin su Sajida su kai loma daya bakinsu suka fara santin kyawun cokulan da plates din nan. Ai da suka fara ci, sai suka ji cikin kunnuwansu ya dau kaikayi, saboda dadi. Tunda suke ba su taba cin abinci mai dadin irin wannan abincin ba. Wasu abubuwan cusawa suke ba tare da sun san sunansa ba. Kamar bangaren fruits irin su straw berry, inibi, duk sai dai su ganshi a talabijin ko a hoto ko kuwa su ga fukawar su. Misalin karfe goma sha daya, Bakura ya farka daga barcin da yake yi, ya yi wanka ya fito a shirye tsaf sanye da wata shadda shudiya (blue), wacce aka yi masa gajeren dinki iya gwiwa, wato (boda), ya dora shudiyar hula. Kamar wadanda suka hada baki Samira ya iske a falo ta ca6a ado da wani shudin leshi, sai walkiya take. Bayan ta gaishe shi sai ya shiga janta da wasa yana zolayarta, duk da ya san haushi yake bata shi kuwa dadin zolayar yake ji. Suka wuce kan tebur don karya kumallo, domin Samira ba ta iya cin abinci ita kadai, duk dadewar da Bakura zai yi a waje ko yana barci sai ta jira shi ya zo sun ci tare tun sanda suka yi aure. Sun fara cin abincin kenan, sai Samira ta dube shi ta yi gatsine. Ta ce "Af, ya za a yi ka zo ka zauna kana cusawa cikinka abinci, ba ka damu da amaryarka ba, yaya ta kwana, ko me ta ci, ko me za ta ci?" Bakura ya yi dariya ya ce, "Ai bakuwarki ce, na san ba za ki bar ta da yunwa ba." Takaici gami da daci ne ya dasu a zuciyar Samira. Ta tabe baki ta ce, ai gara aje a kira ta ta zo mu hadu mu karya tare ka ga sai ka fi jin dadin cin abinci kana yi kana kallonta, don na ga alamar har wata nutsuwa ka ke idan a gabanta ka ke." Bakura ya kwashe da dariya Ya ce, "Kishi, kishi, Samira kishi sunanki daga yau. Yaushe aka kawo Sajidar da har ki ka lura ina nutsuwa idan a gabanta ne? Jiya-jiya ne fa." Haka dai suka dinga fafatawa har suka gama cin abinci. Bakura ya yi zunbur ya mike, gami da duba agogo. Ya ce, "Kaduna nake so in je akan maganar wadannan motocin da nace an turo min daga America sun zo, sai kin zaba kin darje kafin kowa ya zaba, saboda ke ce gimbiyar gidan." Ta harare shi, ta ce, "Ka ce dai ka yi sauti a siyowa amaryarka mota ba ni ba." Ya kwashe da dariya ya suri mukullin mota yana shirin ficewa. Ta sa hannu ta kamo hannunsa, ta ce, "Ka fita ka je ina? Ai dole ka shiga kaga lafiyar abar qaunarka, kafin ka fice tunda ba ita ta kawo kanta ba, kai ka ajiye ta." Bakura ya yi dariya ya ce, "Kai! Kai! Nima na jawowa kaina, na zama kamar waina sai juya ni ake ta ko'ina. To mu je ki raka ni dakin." Samira na gaba yana biye da ita har falon Sajida. Sajida na ganin su ta daina fara'a ta dauke kai ta juya musu keya. Sai kawayen ne suka gaishe su. Su Kuma su Samira suka gaishe da tsohuwa. Tsohuwa ta amsa, gami da cewa "mu yanzu za mu koma gida, ga Sajida nan amana, kuma ku yi hakuri da halinta, har Allah Ya sa ta gane." Samira ta danne zuciyarta ta kalli Sajida ta ce, "Amarya ina kwana. Ko ba ki gaisa da ni ba kya gaisa da angonki ai ko." Sajida ta yatsune fuska ta tabe baki ta amsa gaisuwa a ciki-ciki. Bakura kuwa ba a raba shi da qurawa Sajida ido. Ya tafi can wata duniyar tunani yana tuno kamannin Zuhuriyya, yana hadawa da abinda idanuwansa suke gane masa. Kamar daga sama yaji muryar Samira ta katse masa tunaninsa da yake. Ta ce "Sai ka sa direba ya kai su gida, kuma ka kawo kudin budar bakin amarya a bawa qawayenta su raba." Nan da nan qawayen amarya suka warware kowacce fadi take, "A ba mu kudin siyan bakin amarya." Bakura ya yi dariya ya ce, "To zan bawa Samira za ta sallame ku." Ya juya ya fice, Samira na biyo da shi su na tafe Su na kallon dakwalkwalallen darning table din Sajida kaca-kaca da abinci da kwanukan da suka ci. Kowanne a watse ba tare da an kinkintsa wajen ba, balle a kwasa a kai kicin. Kowacce da ta gama ci sai ta koma Kan kujera ta nade. Don haka Samira na fita ta kira Grace ta ce ta shiga ta kwaso mata kwanukanta ta gyara musu kan tebur. Bakura da Samida suka dinguma wajen motoci, ya zabi wacce yake so ya shiga, ta zo ta dafa murfin mota. Ta ce, "Kawo kudin 'yan mata da ka yi alkawari." Ya ce, 'Ke za ki sallame su ba ni ba, tunda baqinki ne." Kafin ta ce wani abu ya jawo kofar motarsa ya rufe ya ja dogon ribas yana sheka mata dariya. Ta tsaya tana kallonsa kawai tana takaicin wannan al'amari, domin ita tafi jin haushin kanta da take shiga safgarsa da amaryarsa, ga shi ta zame masa abar tsokana tamkar wata kakarsa. Ta gyada kai ta yi qwafa, gami da cije baki alamar za ka dawo ka same ni. Ta na shiga falo ta yi kicibus da qawayen amarya da tsohuwa sun fito za su tafi. Cikin fara'a take yi musu magana. "Ba dai har kun fito ba, ba za ku yinin mata ba har ta sake warwarewa ba?" Su ka amsa cike da murmushi, "A'a daga gida aka yi waya aka ce mu dawo." Samira ta ce, "To ku jira ni ina zuwa." Ta shiga dakinta zuwa wani dan lokaci ta fito dauke da kudi, gami da wata leda a shaqe da sabulai kala-kala. Ta miqa musu ta ce "Ga shi dubu ashirin ce yace a baku, wannan kuma sabulai ne kwa yi wanka ni na baku." Suka ji wani tsagoron farin ciki ya rufę su, sai suka zube su na godiya. iyayye ta lankwashe murya ta ce, "Hajiya Samira, gaskiya ba zan 6oye miki ba ko a bayan idonki za mu fada kina da kirki, kuma samun mace kamar ki sai an tona a cikin mata." Samira ta yi dariya ta ce, "Ba komai ai mun zama daya. Ku je bakin get ku tambayi Lurwanu direba ku ce na ce ya kai ku gida da mukullin mota a hannunsa." Haka tsohuwar nan ta dinga shi wa Samira albarka, har suka fice. Samira ta dawo ta zauna a falo tana huci, tana fitar da zazzafar iskar da ta mamaye huhunta. Saboda ba karamin karfin hali ta yi ba wajen danne kishinta, duk wannan kissar da kisisinar ba ta kai zuci ba. Zuciyarta tafasa take tamkar ruwa akan wuta. Daman Sajida jira take kowa ya watse, Allah- Allah take duk su tafi su barta ta kunna sabuwar wayar da Abdulmajid ya aiko mata, don su yi magana. Fitar su iyayye ke da wuya ta dauko wayar ta saka a caji, ba tare da ta bari cajin ya cika ba ta kunna, gami da saka sabon layi da recharge card ta matso lambarsa wacce daman tuni ta haddace ta akai. Koda kuwa daga barci aka tashe ta za ta karanto lambar a Kwakwalwarta. Bugu daya ya dauka, duk da bai gane kowace ce ba, domin bai haddace sabon layin ba. Daga yadda yake amsawa ka san baya cikin farin ciki, don da kyar yake magana. Ko tashi daga kan shimfidarsa bai yi ba. ya sake kallonta.Kai ka fi cancanta Balle karya kumallo, bashi da shirin yin wanka ya fita. Daga dukkan alamu zafin rabuwa da Sajida ya shige shi, don a da yana ganin wasa ne ba auren za ta yi ba yanzu kuwa ya tabbata. Har suka gaisa bai fahimci ita ce ba, sai da ya ji kalamanta masu ratsa masa jiki, sannan ya farga. Kan ka ce kwabo ya ware murya. Tambayar da ya fara jero mata ita ce, "Da fatan dai baki yarda wani abu ya hada ku ke da wannan banzan mutumin ba kö? Ina fatan ba kya sakar masa fuska, balle ya yi hira da ke ko?" Ta amsa masa da, "Shi ya isa ma ya matso kusa da ni. Ai ko kallon inda yake ba na yi." Ana badakala, haka Sajida da Abdulmajid suka dau lokaci mai tsawo su na waya, har sai da kudin wayarta ya qare, shi ma ya kira kudin wayarsa ya qare. Sai ya turo mata text massage cewar ta yi hakuri idan ya fita waje zai sa kati zai kira ta. Yau farin ciki a zuciyar Sajida baya faduwa, ta sumbaci wayar ta rungume filo, gami dą lumshe ido tamkar tana tare da Abdul a kusa da ita. Yini guda Sajida na nade a daki, sallah ce ke tashinta daga kan gadonta. Grace ce take kai kawo tsakanin kicin da dakin Sajida. Samira ba ta gaji ba ta aika aka kai mata abincin rana, da a ka kai na dare aka kwaso kwanukan rana. Ba kunya ba tsoro Allah Sajida take nadar abinci ta koma ta kwanta. Bakura bai shigo gida ba sai bayan sallar Isha'i.Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya zauna a babban falo, tare da 'ya'yansa da uwar gidansa Samira. Ya taya yara Home work, suka yi 'yar hira, sannan ya sallami kowanne yaro ya je ya kwanta. Samira ma ta yi zumbur ta mike, gami da yi masa sallama ta nufi dakinta. Bakura ya yi kiran duniyar nan Samira ta qi dawowa, ta shige dakinta ta rufe. Yana qoqarin kiranta a waya ta murtsike wayar ta kashe. Ya dade a zaune, sannan ya miqe don tafiya dakinsa ya kwanta, domin ya gaji.Daidai qofar dakin Sajida ya jiyo muryar Sajida na hira har da kyalkyala dariya. Hakan ta ja hankalinsa ga tsayawa tsai yana sauraro. Da farko ya dauka talabijin ce, amma da ya kara kunnensa ya tabbatar muryar Sajida ce ya yi mamaki, sai ya shiga tunanin da wa Sajida take hira haka, to ko qawayen nata ba su tafi ba ne? Sai ya yanke hukuncin shiga dakin ya gani. Yana murda kofa, sai qofa ta bude ya ci sa'a a bude take ba an datse ba. Tsuru-tsuru ya ga Sajida ita kadai, ta yi daidai a kan doguwar kujera tana waya. Sanye take da atamfar dazu, amma kanta babu dankwali ta zubo gashinta har baya tana shafawa, Saboda dadin hira. Ya kalle ta, ta kalle shi kallon Kallon ake yi. Sai yaji ta ce, "Ka gan shi ma ya shigo dakina ya tsaya yana ta muzu-muzu da ido, ka san kallo ne da shi kamar wani baqauye." Da jin haka sai Bakura ya sami kújera a setinta ya zauna cike da mamaki. Can ya yi qarfin hali ya tambaya. "Da wa kike waya, Sajida?" Ta fada cikin gadara ta ce, "Abdulmajid." Yadda ta ga Bakura ya tunkaro ta a fusace kamar mai shirin mauje ta, sai ta tsorata, ta wurgar da wayar ta qanqame akan kujera. Bakura ya tsugunna ya dauki wayar a qasa, sai ya ga har yanzu wayar a kunne take Abdulmajid ne ke ta magana. Bakura ya kara wayar a kunnensa yana sauraronsa, kalmar da yaji yana cewa. "Baby, are you there?" Bakura ya yi gyaran murya, gami da' cewa, Ba baby ba ce, wannan mai gidanta ne." Abdui majid ya fada cike da gadara, "Alhamdulillahi, daman ina nemanka. Kai wawa ne, banza, jahili, ta yaya za ka auri yarinya bata sonka, saboda kana da kudi? To wallahi ka kuka da kanka. idan ba ka saki Sajida ba sai na sa an farfarda min cikinka." Bakura ya yi murmushin haushi ya gyada kai. Ya ce "Yaro, idan ni da kai zaa hado mutane masu hankali mu zauna akan teburi daya kowa ya bada labarin abin da ya faru, to jama'a za su tantance waye wawa, banza, jahili. Ka san kai ne wawa, tunda ka bari na kwace maka Sajida a cikin dan qanqanin lokaci, alhali kun dade tare har kun shaqu, don da kana da wayo ba za ka bari in kwace ta daga hannunka ba. Idan jama'a suka ji haka zasu tabbatar maka kai banza ne, tunda aka baka dama ka fito ka aure ta ka kasa fitowa ka qi yin amfani da damar da aka ba ka, har sai da ta subuce maka. Sannan daga karshe ko jama'a ba su fada maka ba, kai da kanka ka san kai jahili ne, marar tarbiyyar addini, tunda za ka raba dare kana magana da matar aure, wacce ba matarka ba. Kuma ina jiran ranar da za ka sa a farde min ciki." Bakura ya katse wayar ya kashe ta gaba daya ya juya ya dubi Sajida wacce tuni ta kufula tana harararsa. Ya koma ya zauna a kan kujerarar da take fuskantarta, ya dube ta. Ya ce "Abdul majid din ne har yanzu ba ku rabu ba, shin idan shi bai san darajar aure ba ke ba ki sani ba? Ina tabbatar miki halaka ce da azabar Ubangiji akan matar auren da take magana da da namiji, wanda ba muharraminta ba. Sajida ba kya jin maganar iyayenki, ba kya jin maganar mijinkı, alhali mu ne masu qaunarki da gaske." Ta ji tamkar Bakura yana mata yayyafin ruwan zafi a sassan jikinta, domin kalamansa tamkar zaginta yake haka take ji a kanta. Ta miqe tsaye tana mai sharara kuka, tana zubar da hawaye ta rike kugu tana girgiza ta ce, "Malam ka rufe min baki ka daina shiga rayuwata, na fada maka na sake maimaitawa na tsane ka, kuma ba zan zauna da kai ba. Wannan wayar da ka kwace ita ce ginshiqin zamana a gidanka, amma tunda ka kwace wallahi sai an neme ni an rasa." Bakura ya ce "Babu inda za ki je Sajida, ina da kyakkyawan tsaro a gidana, wanda ko jikin get ba za ki iya tabawa ba balle ki bude ki fita, kin shigo gidan nan kenan. Yanzu kin zama killatacciyar kwaryar da na rataye a ragaya, don yin ado da ita, kin fita daga sahun kwarya mai garari a tsakar gida." Daman kalmar da Bakura ya fara fada mata kenan ita ce ta jawo tsanar da ta yi masa tun farko, yanzu ma an kuma. Ta sharbe hawaye ta ce "Zahra 'yarka ita ce kwarya mai garari a tsakar gida ba ni ba." Ta juya a fusace ta na rusa kuka kamar ranta zai fita. Kukan Sajida tamkar dafi ne a cikin zuciyarsa, saboda ji yake tamkar Zuhuriyya ce take kuka. Ya ji hankalinsa ya tashi, ya miqe da sauri ya bi bayanta har cikin daki tana danna qofa yana turawa, har ya kutsa kai. Ta tafi jikin bango ta maqale ta zazzare masa jajayen idanuwanta masu zubar hawaye. Ta ce "Ka fita ka ba ni waje, ba na sonka, ba na son ganinka, na tsane ka na tsani mai sonka gara in kashe kaina da in zauna da kai." Bakura ya yi tsaye yana dubanta, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi. Ya fada cikin sanyayyiyar murya Ya ce "Me kike so in yi miki a duniya, don ki yi farin ciki?" Ta ce "Ka bar ni in auri Abdul majid." Ya yi shiru, can ya ce, "Abdul Majid ba zai aure ki ba, da na bari ya aure ki." Ta ce "To ka ba ni wayata don sai na ji muryarsa nake jin dadi." Abin mamaki sai Bakura ya kunna waya da sauri ya danno lambar Abdul majid, bugu daya wayar ta shiga, sai ya miqa mata, gami da cewa, "Ga Abdul majid dinki" Cike da mamaki, gami da sanyin jiki ta miqa hannu ta karba ta kara a kunnenta, tabbas shi din ne kuwa. Nan da nan ya ga ta fara murmushi. Ta zo ta wuce Bakura a tsaye kamar gunki ta koma falo ta luntsuma akan kujera ta na hirar soyayyarta ba tsoro, balle fargaba. Bakura ya zo falo ya sami kujera ya zauna, ya tsura mata ido ya na kallo. Hakika dariyar Sajida ita ce farin cikinsa, domin ji yake tamkar dariyar Zuhuriyya ce. Sai ya tsinci kansa ya na murmushi, tamkar Zuhuriyya ce take cikin farin ciki. Ta yi ta waya ita da abin qaunarta har sai da suka gaji, sannan suka yi sallama ta kashe waya. Ta harari Bakura ta tabe baki ta mike tana tafe tana girgiza ta shige daki ta datse ta yi kwanciyarta. Tsawon awa guda Bakura bai motsa ba, yana zaune kansa ya kulle. Ya kan raşa abinda yake faruwa da shi. Abu na farko, ba wai tsananin son Sajida yake ba, kuma baya sha'awarta, amma yana ji a jikinsa ba zai iya rabuwa da ita ba saboda kamar da ta yi da wacce ya fi so a rayuwarsa. Haka ko kadan bai ji kishin wayar da suke yi da Abdul majid ba. Ya rasa dalilin da yasa baya gajiya da duban surar Sajida da sauraron muryarta ba. Ya kasa gane daliin da yasa baya Son ganin bacin ranta, balle ya ga hawayenta. Baya taba jin haushin rashin kunyar da take tafka masa, balle ya ji ya tsane ta. Idan ya zo gabanta baya iya yi mata musu, saboda girmamawa. Amsar ita ce Sajida na cin albarkacin Zuhuriyya a wajen Bakura. Ya miqe a sanyaye ya fito daga dakin Sajida, ya nufi dakinsa. A jikin labule ya hango Samira tana lekensa ta wundon dakinta. Su na hada ido ta yi sauri ta saki labulen ta koma, da alama kishi ya hana ta barci. Ya yi murmushi ya ce a ransa, "Kya yi kya gama, da kin san yadda muka yi da Sajida da kin tausaya min. Na san duk bayanin da zan yi miki ba za ki yarda ba, don haka shiru shi ya fi alkhairi." Yana shiga dakinsa ya kulle ya kwanta, sai dai ya dade yana jujjuya abubuwan da suka faru tsakaninsa da Sajida da Abdulmajid. *** *** *** Haka gidan Bakura ya kasance, tamkar gidan 'yan adawa. Bakura da Samira ba dadi, tsakanin Sajida da Samira da 'ya'yanta ba dadi. Tsakanin Bakura da Sajida ba dadi. Sajida ta sake kudirar sai ta damula gidan gaba daya, don haka rashin mutunci kala-kala, na yau daban na gobe daban, sai futsara da tsiwa take yi wa Bakura, ta yi wa matarsa. Samira ta ce ta gaji, don haka babu ruwanta da abincin Sajida, balle ta taka qafarta a dakinta. Grace ce Bakura ya wakilta kacokan ta kula da ci da shan Sajida da kula da gyaran dakunanta da wankin bandakuna. Kai hatta undies dinta Bakura ya ce Grace ta dinga wanke mata zai biya. Tsawon wata guda kenan da zuwan Sajida bai fi sau biyu ba Zahra ta ga Sajida. Shi ma a qofar dakin Sajida suka hadu, Sajida ta leqo kiran Grace, Zahra kuma ta zo wucewa za ta shiga dakinta suka yi kallon- kallo kowa ya dauke kai. Duk ranar girkin Samira, Bakura zai kame a dakinsa, Samira ta zo, amma ranar kwanan Sajida sai dai ya bi ta daki, shi ma datse qofar falon take sai dai ya shigo ta qofar baya wacce shi kadai yake da mukullin. Kada ku ce idan ya shiga dakin wani abu ne zai faru, a'a a gaba take sa shi sannan ta danno lambar Abdulmajid su yi ta soyayya don ta saka shi takaici dan idan ya gaji ya sake ta, amma sai ta ga Bakura ko damuwa ba ya yi. Kai har in credit din wayarta ya qare sai ta ga ya zaro recharged card na dubu daya da dari biyar ya ba ta ya ce ta ci gaba da wayarta, ya na gefe yana kallonta cike da murmushi. Al'amarin Bakura wani lokaci yana ba ta tsoro, don ba ta san abinda yake hada mata ba, dan wannan kasaqen da ya yi mata akwai magana. Sajida ta ga an doshi watanni biyu da aure, babu alamar gajiyawa a tare da Bakura, ba shi da niyyar jin haushi, balle ya sake ta.Sai ta yi yunqurin hada kaya ta gudu cikin dare, amma abu ya ci tura.Ta kalli tsawon katangar gidan nan ta ga ba irin katangar gidansu ba ce wacce take iya haurawa ba. Ta nufi get ta tabbatar masu gadi su na aikinsu tun karfi ko da yaushe get a datse yake da manya-manyan kwado. Kafin a bude maka get sai sun jero maka tambayoyi, balle a ce su ganta da kayanta a hannu ba a mota ba ta ce za ta je unguwa, ko daya ba za su bar ta ba. Gashi an hana kowa zuwa daga gidansu. *** *** *** Wata rana da daddare, dare har ya fara nutsawa Bakura bai dawo gida ba. Sha daya na dare, har ta wuce ba Bakura babu wayarsa, don haka hankalin Samira da 'ya'yanta ya tashi, ko barci suka kasa yi. Yi suke su na qara yi wajen buga wayarsa, amma wayar a kashe. Babu abokinsa da ba ta kira ba, sai su ce ba sa tare da Bakura a yau. Sha biyu daidai wayar Samira ta yi qara alamar ana kiranta, ita da Zahra suka hau rige- rigen dauka. Samira ta danna wayar, gami da kadawar hanta da fargaba. Ta fada "waye yake Magana?" Cikin harshen turanci mutumin ke magana da alama Inyamuri ne, ya fara da gabatar da kansa. Ya ce, "Sunana Doctor Isreal daga International Hospital. Dan Allah ina magana da Samira ne Mrs. Bakura ne?" Ai tuni Samira ta rusa kuka ta fara kwakwazo. "Doctor ni ce Samira. Me ya faru da maigidana, ya mutu ne?" "Bai mutu ba, amma ya sami rauni." sai ta sake fashewa da kuka ta ce, 'Hatsari ya yi ne?" Ya ce"A'a an kawo mana shi dai ana tunanin yan fashi ne suka dake shi har an farfasa motarsa. Ki kwantar da hankalinki ga shi nan ya miqe yana magana, shine ma ya ba ni lambarki ya ce in kira kı." Doctor ya sakawa Samira muryar Bakura yayin da ita ma ta danna speaker yadda yaranta za su jiyo muryar mahiafinsu, don su dukka kuka suka zo suka kewaye ta su na yi. Cikin kuka suke kiran. "Abba, Abba me ya faru da kai?" Cikin sanyin murya Bakura yake lallashinsu fadi yake, "Na ji sauki, ku daina kuka." Dukka wannan abinda ake Sajida na bayansu a tsaye ta jingina à jikin bango ta kama kirji ta qame kamar soja. Da alamar akwai sanyin jiki a tare da ita. Amma da ta ga sun juyo gaba daya su na kallonta, sai ta tabe baki ta harare su sama da qasa ta wuce zuwa dakinta, don kada ma su đauka ya dame ta. Samira ta aika Zahra da Abubakar, Boy's quater su taso Lurwanu direba ya zo ya kai su asibiti wajen Bakura. Da gudu Zahra da qaninta suka nufi Boy's quater suka taso shi, a gigice ya dauko mukullin mota ya fito. Ba tare da bata lokaci ba Samira da 'ya'yanta suka duru a mota suka nufi asibiti, sai addu'a suke su na koke-koke a hanya. Sajida na shiga falonta ta jawo wayarta ta bugawa Abdul majid, zuciyarta cike da 6acin rai, domin tana zargin da sa hannunsa a cikin wannan al'amari, Ya na amsawa ta harbo masa wannan tambaya. "Abdul majid me kasa a yiwa Bakura?" Ya tabe baki ýa ce "Me ki ka ga an yi masa, wannan wacce irin tambaya ce kike yi min? Kar ki raina min hankali mana." Ta fada cikin tsawa da bacin rai, "An ce 'yan fashi sun tare shi sun dake shi, har sun fasa masa mota. Ina tunanin kai ne kasa a yi masa haka." Ya ce, "Ki daina tunanin nasa an dake shi, nine da hannuna na tare shi ni da su Shehu abokaina muka farfasa masa kai dazu da magruba a Hotoro G.R.A. Kin fara sonsa ne, ina ruwanki ko mutuwa ya yi?" Ta fada a fusace, "Ka ga Abdul majid ba na son haka, ya za ka nemi ka kashe mutum ba da hakkinsa ba. Me ya yi maka? Mutumin nan ya ba mu damar mu yi magana har ma katin waya yake siya ya ba ni in kira ka. Me ye laifinsa?"Kai ka fi cancanta.. Gashinta kuwa mai laushi ne aka gyara aka zubo mata da shi har bayan qeyarta, aka nade mata daurin dankwalin leshin a samansa, sannan aka yafa ma ta mayafin da ya dace da leshin wato mai ruwan goro, takalmi ma kalarsa ne, yayin da aka feshe duk illahirin jikinta da turarurruka masu qamshi na cikin lefe. Aka ruqo ta zuwa tsakargida aka zaunar da ita akan wata doguwar kujera aka fara daukar hotuna. Babu yadda Sajida za ta yi, domin an ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi, amma zuciyarta cike take da baqin ciki da damuwa. A zaune take tamkar gunki, sai kallon mutane take sasarai kai ka ce ba ta da laka a jikinta. Duk sanda ta tuna ita da Abdul majid shi kenan sun rabu sai ta ji zuciyarta ta harba kamar ana harba bindiga. Idan ta tuno mutumin da aka daura mata aure sai ta ji ta qara tsanarsa. Ta ce a ranta "Lallai kuwa mutumin nan ya yi kuskuren aurena. Iyayena sun yi kuskuren ba shi aurena, sun yi kuskuren karbar dukiyarsa saboda asara ce. Sai na zame masa tamkar kunama mai cizo a shimfidarsa. Zan zame masa duhu alhali da hasken rana. Sai na disashe farin cikin zuciyarsa, ya koma tsananin baqin ciki da damuwa kamar yadda ya sakani ni da Abdul Majid dina. Sai na fardo wannan kyakkyawar kwaryar tasa da yake ji da ita wacce ya saqale a ragaya, idan ta fado qasa ko ba ta fashe ba, zata yi gagari a tsakar gida. Sai na yaqi uwar gidansa na hana ta sukuni a gidanta. Sai na takurawa duk wani mai rai a gidan in ya so idan ya gaji zai sake ni, ko ya kore ni, sai ya ji ya tsani zama da ni." Sajida ta yi murmushin mugunta, wanda har wushiryarta ta fito ta girgiza qafa, 'yan biki suka dau shewa hadi da guda a tunaninsu amarya ta saki ranta ta amince da auren. *** *** *** A daidai wannan lokacin Samira da tawagarta na can su na ta su walimar. Samira ta dage ta cije ta danne tsananin kishinta ta shiga cikin 'yan uwa da qawayenta su na taya Bakura farin cikin aurensa. Don haka an zuba kujeru a farfajiyar gidan, an yi dafe-dafe, an hado kayan maqulashe, mata ne zalla suka taru. Wata Malama ce mai suna Malama Jamila take wa'azi, tana tunasar da mata darajar miji a wajen matarsa. Ta na fadakar da mata su cire zafin kishi a ransu su zauna da kishiyoyinsu lafiya. Daga qarshe ta fadakar da mata da su kula da tarbiyyar 'ya'yansu, musamman 'ya'ya mata. Daga dukkan alamu wa'azin yana ratsa zuciyar Samira, ta yi shiru tana sauraro. Cancandi! Amma fa Samira ta zuba kyau, kai ka ce ita ce amaryar idan ka duba tsadaddiyar material da ke jikinta, sai walkiya take gata da iya kwalliya. Sai dai duba daya za ka yiwa Samira ka tabbatar ta rame, tana cikin damuwa. Haka 'yarta Zahra ta yi tsuru ita da qawayenta a gefe da alamar damuwa a tare da ita. Tun qarfe takwas na dare Alh. Bakura ya tura motocinsa kakaf dana abokansa gidansu Sajida don dauko amarya da masu rakiyarta. Amma ba a samu an fito da amarya ba sai qarfe goma na dare, saboda gwagwarmayar da ake ta yi da amarya, ta bujere ta ce ba za a kai ta ba. Ihu take tana bori, tana faduwa tana burgima a qasa. Hankalin kowa ya tashi, babu wanda bai zo ya tsaya akan Sajimajid ya yi mata nasiha ba. Malam da kansa ya shigo ya tashi Sajida tsaye, ya goge mata hawaye, ya dau lokaci mai tsawo yana ba ta haquri, sannan ya shiga yi mata nasihohi masu ratsa jiki, gami da jawo mata manya-manyan ayoyin Kur'ani mai girma, wadanda suka yi magana akan bin iyaye da bin miji. Daga qarshe ya yi mata magiya da roqo akan ta rufa masa asiri ta shiga mota a kai ta gidan mijinta, kada ta ba shi kunya idan ta je kuma ta zauna lafiya da kowa. Ya yi mata addu'a, gami da fatan alkhairi ya dora da godiya. Domin ya ga jikinta ya yi sanyi, tana hawaye kanta a sunkuye a qasa. Ta dauko gyalenta ta yafa, ta dauko dankwalinta ta karkade ta daura ta sharbe wani zazzafan hawaye ta fara tafiya a hankali kai ka ce kwai ne ya fashe mata a ciki, ta nufi qofar fita ba tare da ta cewa kowa komai ba. Duuuuu'!! Haka mata suke biye da ita har qofar gida inda motoci suke. Galla-gallen motoci ne duma-duma masu sanyin A.C da sautin kida reras a qofar gidansu Sajida. Wacce ta fi kyau da tsada ita ce aka Kawowa amarya gabanta aka yi mata tayi ta zo ta shiga gidan baya, amma ta qi shiga. Daga qarshe aka ba ta zabi ta shiga duk wacce take so, Sajida tsaye take qiqam ta qi motsawa. Ijiyayye awartaq ce ta zo ta rada mata wata magana a kunne ko sakon daya Sajida ba ta qara ba aka ga ita Ijiyayyen sun nufi wata jifgegiyar mota qatuwa a cikin jerin motocin da suke laye. Sajida ta bude gidan gaba ta zauna, yayin da Ijiyayye ta shiga baya. Umma Furare ta yi sauri ta ce da wasu tsofaffi biyu yayyanta su je su shiga motar da Sajida ta shiga, don ba ta yarda da wannan radar da aka yi ba. Haka kuwa aka yi, zuruf su Sajida suka ga tsofaffi biyu sun fado cikin motar sun zauna. Babu wanda ya ce da kowa komai. Sai diddika ake cikin motoci, duk motar da ka leqa mata ne jingim da 'ya'yansu wasu kan wasu. Haka suma 'yan mata sun cika motoci da yawa ana ta falli ko Allah zai sa daga cikin abokan ango daya zai dasa. Duk yawan motocin nan sai da aka bar wasu a qasa, saboda yawan mata, wasu ma 'yan gayyar sodi ne sun zo su ga qwakwab. Umma Furera na küka tana dagawa Sajida hannu, haka shi ma Malam kwalla yake yana tsaye a gcfe, har motocin suka ja suka tafi a laye. Motar da amarya ke ciki tana tsakiya, suka hau titi dodar aka nufi gidan Bakura. Sajida ta juya gefenta ta dubi direban da yake tukawa sanye yake da rawani ya rufe fuskarsa Idanuwansa kadai ne a waje, shi ma ya dube ta ya yi murmushi. Cikin harshen turanci Sajida ta yi magana, saboda tana gudun kada tsofaffin nan su ji abinda a suke cewa. Ta ce "Who are you?" Ya lankwashe murya ya ce, "Sajimajid." Haqiqa wannan muryar tayi kama da muryar abin qaunarta Abdul majid. Kan ka ce kwabo Sajida ta saki ranta farin ciki ya gauraye zuciyarta. Ta waiwayo da sauri ta dubi Iyayye wacce its ce umul aba'isin da ta hada wannan tuggun tayi yadda ta yi ta hado Sajida da Abdul majid har sai da suka hadu suka ga juna. Su na hada ido suka yi wa juna dariayar farin ciki. Ya saka hannu ya zame rawanin da ya nada don yin badda kama ya dubi Sajida duba na so da qauna cikin harshen Turanci. Ya ce, "Kin rame, kin kode, kin lalace, iyayenki su na cutarki baby." Ta yi naira-nairai da ido hawaye ya kwararo ta sunkuyar da kai qasa ta ce, "Yaya zan yi? Yaya ka ke tunanin rayuwata zata kasance idan ka bar ni a cikin wannan halin? Don haka yanzu ba zan bari ka tafi ka barni ba sai dai ka Juya kan motar nan mu gudu a neme mu a rasa." Saboda dimaucewa bai san sanda ya taka burki gaba daya suka kusa buga baki da gaban mota, sannan ya ci gaba dà tafiya. Ya ce Baby, ya ya zan yi da tsofaffin nan da suke kallona tsuru-tsuru?" Sajida ta juya ta dube su cike da takaici ta galla musu wata uwar harara Kai ka fi cancanta Ta ce, "Sai mu zubar da a daji kawai. Ijiyayye ma kwakwalwar irin ta tsofaftin ce ba turanci, don haka su dukka sun yi turus suna kallon su Sajida, ba su san abinda ake shirin aikata musu ba. Abdulmajid ya girgiza kai. ya ce, "Ba zai yiwu ba baby, ki tafi kawai gidan mijinki, amma ki dinga bin duk wani abu da zan gindaya miki. Daddy na yana gari ya kira ni ya yi min fada cewar ya sami labarinki, don haka kada in sake in hana ki zaman aure. Idan ya ji mun gudu zai hukunta ni, koma ya kore ni daga gidansa. Mutum ne mai zafi, ga shi dan ka'ida , zai iya bi na da bindiga ya ce zai harbe ni." Sajida ta rushe da kuka ta ce, "ni fa ba zan sauka daga motar nan ba, bin ka zan yi, daman mutane suna cewa ba ka sona, ba ka damu da ni ba." Abdul majid ya yi ajiyar zuciya a bayyane ya tsuke fuska, yayin da ya fara magana cikin wata kakkausar murya mai nuni da bayar da umarni. Ya ce "Ki kula da abun da nake fada miki, kuma ki bi duk abun da nake fada miki. Ba zan gudu da ke ba, kuma ba za ki qi zuwa gidan mijinki ba, sai dai kada ki yarda wani abu ya shiga tsakaninku. Nan da wani dan lokaci idan na gama shirya abinda nake shiryawa zan san yadda zan fito da ke mu gudu a rasa mu. Kinaji na ko?" Sajida ta amsa cike da ladabi da tsananin tsoro. Ya ce, "Ki goge hawayenki ki daina kuka, ki dauka tamkar na kai ki ajiya ne nan da wani loakci zan zo in dau ajiyata." Su duka suka yi murmushi, Sajida ta goge hawayenta ta ci gaba da kallon abin kaunarta Sajimajid tana sauraron dadadan kalamansa. Daya daga cikin tsofaffin nan ce ta zuro da kanta tsakiyar Sajida da Abdul majid ta ce "Daman kin san dircban nan ne ku ke hira? Na ga alamar ma Buzu ne, don na ji kuna yaren Buzaye, daman kin iya yaren? Wacce irin hira ku ke yi idan kika yi kuka sai ki yi dariya kuma?" Haushi ya rufe Sajida da Abdul majid, har suka rasa abun da za su ce mata. iyayye ce ta ba ta amsa. Ta ce, "Iya, dan Allah ki gyara zamanki, ina ruwanki da hirarsu." Tsohuwa ta koma ta zauna. Ta ce "A'a, 'yar nan kar ki ga laifina, dole in tambaya, don in sani. Na sani ko wannan dan iskan ne Abdul majid da take so ya aiko Buzu ya sace ta." Daya tsohuwar ta ce, "Ai kuwa da mun cî ubansu, don idona idon Abdul majid sai na sharara masa mari, saboda wahalar damu da yake yi. Gaba daya ya hargitsawa yarinya lissafi, ya hanata zama lafiya, ga gidan arziki da wadata ta samu, amma ta qi kwantar da hankalinta. Ai shi ma Abdul majid din ko hauka yake ba zai fara tako qafarsa qofar gidanmu ba, ko ya turo a saçe ta ba." Sajida ta juyo ta dube su, duba na takaici da bacin rai sai ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe. Abdul majid kuwa mudubi ya seta baya yana kallon tsohuwar da take niyyar kwashe shi da mari, sai ya yi murmushi kawai. iyayye kuwa kunshe baki ta yi da gyalenta tana ta dariya a ciki-ciki. Daidai lokacin ne motocin da suke gaban su Abdul majid suka saka siginal din shiga wani katafaren gida. Nan da nan masu gadi suka wangale get a jere a layi motocin daukar amarya suka dinga kutsa kai su na shiga. Abdul majid ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa, sai idanuwansa ne kawai a fili, ya wangale idanuwan nan nasa kwala-kwala yana duban farfajiyar gidan. Ya gasgata, ya tabbatar Bakura ba sa'an yinsa ba ne ya cara masa wajen naira, sai dai su goga da babansa, koma Bakura ya fi Babansa kudi. Kalmar da yake ta fada kenan. "Wonderfiul, fantastic, beatiful. " Wata tsoka ce daga cikin qirjin Sajida ta yanke ta yi wani qarai, yayin da kuka ya tunkarowa kwayar idanuwanta. Ta dubi Abdulmajid ta fada cikin harshen turanci. "Ka kawo ni gidan wanda ba na kauna a rayuwata ka ajiye ni za ka tafi ka bar ni ko?" Ya cije baki ba tare da ya ba ta amsa ba. Ta sake cewa "in har kana sona ba za ka so in zauna da wani kato a gida daya ba da sunan mijina. Mai zai hana ka tunkari hatsari, wuya da duk wani wulakancin da za a yi mana kamar yadda na yarda zan gudu koda za a kashe ni." Ya sami waje ya tsaya ya zare mata jajayen idanuwansa da suka cika da hawaye ya ce, "Fita ki shiga gidan nan kafin wadanda suka sanni su zo su gane ni. Zan bawa iyayye sabon layi da wayar da na siya miki zata kawo miki, za mu dinga magana. Na fada miki ki daina kuka, kuma ina tare da ke a duk inda ki ke." Kaico! Soyayya gamon jini, sai Abdulmajid ya fashe da kuka . Cikin shashshekar kuka Sajida ta bude kofa da sauri ta fice tamkar ranta zai fice. iyayye da tsofaffi suka fita suma suka bi bayan Sajida. Duk wanda yake qoqarin ya riqe ta sai ta fusge. Babu yadda ba a yi ba akan ta sa mayafi ta rufe fuskarta amma ta qi, haka ta shiga gidan mayafinta a kafada, dauri a gaban goshi wato ture ka ga tsiya, ga wani kodadden idon da ya sha koke-koke. A babban falo suka iske Samira da 'yan uwanta da makwabta jingim suna jiran isowar amarya. Bayan 'yan uwan Sajida sun yi sallama, su Samira suka amsa musu, sai tsofaffi biyu 'yan uwan Sajida suka shiga tsakiyar Sajida suka kaita gaban Samira suka durkusar, sannan kowa ya sami waje ya zauna. Bayan an gaggaisa aka fara bayani, dangin Sajida ne su ka ce. "To uwargida, ga Sajida mun kawo miki ku zauna lafiya qanwarki ce, koma mu ce 'yarki ce ki gyara mata, idan ta yi kuskure. Ke kuma Sajida yi na yi, bari na bari, ke ce qarama." Samira na murmushin qarfin hali, dan ba qaramin yaqi ta yi ba da ta danne kishinta ta zauna tana sauraron wadannan bayanai. Sajida kuwa idonta tsai akan Samira da tawagarta bayan kallon banza ma har da harara take harba musu daya bayan daya. Can idonta ya hasko mata Zahra a zaune a lungu, nan fa ta kafa mata ido tana harara sama da qasa har da girgiza kai wato 'ada kai kawai na fasa miki, yanzu kuma sai na ragargaza kan dukka'. Zahra ta yi sauri ta sunkuyar da kai qasa, yayin da jikinta ya dau rawa, a halin yanzu tafi tsoron Sajida a kan mutuwarta. Haka Hajja Farida ta riqe baki tana kallon Sajida tana gyada kai, tana jinjina fitsarar Sajida. Ta tabbatar yarinyar nan ba ta shigo da niyyar zaman lafiya ba. Haka suka dinga kallon-kallo tsakanin Samira da tawagarta da 'yan uwan Sajida. Tun kafin a gama bayani Sajida ta yi zumbur ta mike tsaye ta yi kiri-kiri da ido tana duban jama'ar, ma'ana idan za ku daina bata yawun bakin ku gara ku daina, don ni babu zaman lafiya a tare da ni. Manufarta kenan duk da ba ta furta ba. Ba shiri 'yan kawo amarya suka miqe suka saka ta a tsakiya aka ja ta zuwa dakinta, tun kafin ta bude baki ta fadi wata magana da za ta kunyata su. Sajida na tafiya ta na girgiza tana tabe baki. "Lallai wannan falalliyar 'yar za a yi da ita." ln ji Hajiya Zuwaira. Daya daga cikin yayyun Samira. Samira ta koma ta jingina da jikin kujera jikinta a sanyaye, sai gyada kai take tana al'ajabin yadda Bakura yana ji yana gani ya dauko wannan halittar ya kawo musu gida. Hajja Farida ta dau dogon salati ta salallame ta ce, "Tun da nake a doron kasa shekaruna arba'in har da doriya, ban taba ganin fitsararriyar amarya irin Sajida ba." Nan dai kowacce mace ta fara tofa albarkacin bakinta, tana zayyano abun al'ajabin da idanuwansu suka hango game da Sajida. Daga karshe suka bawa Samira hakuri da nasihar ta ci gaba da hakuri komai nisan jifa qasa zai fado. Ta ci gaba da yi wa mijinta biyayya ta zuba musu ido ta yi kallon yadda za ta qarqe musu, wato tsakanin ango da amarya. Daga karshe dangin Samira suka kaiwa dangin amarya abinci kala-kala, abun sha da snacks da aka yi musu, sannan kowacce ta kama gabanta. Sajida ta yi mamaki matuqa yadda Bakura ya kashe kudi ya gyara mata daki, ba tare da sisin yayenta ba. Ta yi matukar mamakin inda Bakura ya santa har ya kamu da sonta haka. Wasu abubuwan ma daga ita har yan uwanta ba su san shi ba, na turai ne, Musamman da suka shiga cikin bandakuna sun hadu an zuba kayan Kamshi da na decoration. Aka yi shawara a bar qawayen amarya guda hudu da tsohuwa daya su kwana da ita ko Allah zai sa hankalinta zai dan kwanta. Haka kuwa aka yi kafin sha biyun dare gaba daya 'yan rakiyar amarya da masu karbar amarya sun watse. Kawayen amarya ne guda hudu da tsohuwa daya suka rage a dakin Sajida. Samira da 'ya'yanta ne jugum a zaune a falo har Bakura ya shigo gidan ba su iya tashi sun je sun kwanta ba, abun duniya ya ishe su kasancewar Bakura ya san abinda zai tarar don haka bai bari ko da daya daga abokansa ya rako shi ba. Haka ya shigo hannunsa ziqai bai siyo kazar amarci ba irin ta al'ada. To duk abinda zai suyo na marmari akwai shi jingim a gidansa, masu aiki ma ya ishe su, balle iyalansa. Kaza ce, juices, fruits, duk su na nan a shaqe a firij. Ya yi sallama ya shigo falon, gami da murda mukulli ya kulle kofar. Su duka suka amsa masa a sanyaye. Ya dube su ya yi murmushi ya ce, "Yara ba ku yi barci ba, har yanzu? Gobe fa Monday. Yau ba a cewa Abba oyoyo ne?" Abubakar ya taso ya miqawa mahaifinsa hannu suka tafa, haka Umar da Usman ma a layi suka zo suka tafa. Zahra ta taso ta dubi mahaifinta a sanyaye ta ce, "Congratulations Abba, ina muku fatan alkhairi." Sai qannenta duka suka hada baki, "Congratulations Abba." Mamaki ya kama Bakura ya tabbatar Zahra tana taya mahaifiyarta kishi ba kuma kishin kadai take taya ta ba, wacce ya auro ita ce damuwarta. Da a ce wata ya auro ba Sajida ba, ya san Zahra za ta bi bayansa ba za ta bi bayan mahaifiyarta ba, saboda Zahra tafi son abun da mahaifinta ke so. Yaran ne suka katse masa tunaninsa suka hada baki, "Good night Abba, Good night Mama." "Good night children. " Samira da maigidanta suka fada cike da fara'a. Yara suka nufi dakunansu ba tare da su na jin dadin zuciyoyinsu ba. Bakura ya matso kusa da Samira ya zauna ya dube ta ya yi murmushi ya fada cikin wata 'yar siririyar murya. Ya ce, "Samira, kin yi kyau, kamar ke ce amaryar, har kin fi amaryar." Hohoho! Idan ka tona zuciyar Samira za ka yi mamakin irin baqin da ta yi, don takaici. Ta bata rai, gami da daga hannu ta dakatar da shi. Ta ce, "Ba na so, kar ma ka fara wannan zancen. Ni a suwa? Ka tashi mu je in rakaka dakin wacce yau za ta ji dadin kalamanka, amma ba ni ba." Ta mike tsaye zumbur ta rike kugu tana girgiza kamar mai shirin dambe, sai huci take tamkar kasa. Ba musu Bakura ya mike bakinsa cike da magana, haka dariya take son kufce masa, amma yana tsoron furtawa. Su na isa kofar dakin Sajida sai ya ji gabansa ya yanke ya fadi. Samira ta daga hannu za ta murda kofar ta bude, sai Bakura ya rike hannunta. Ya ce, "Kar ki bude, mu je dakina ki taya ni kwana, ni ba sai na ganta ba." Haushinsa ya sake rufe zuciyarta, ta fusge hannunta ta murda kofa ta tura kai cikin dakin, gamị da kwada sallama. Sun yi dayday a falo su duka kowacce ta lumtsuma cikin kujera mai laushi, sai lumshe ido suke yi. Ga A.C na ratsa sassan jikinsu, ga talabijin su na kallo. Lokaci guda suka dago da idanuwansu suna kallon Samira, ta waiwaya bayanta ta tsuke fuska ta ce da Bakura. "Shigo mana." Ya shigo cikin falon, yayin da idanuwansa suka dira akan Sajida kiri-kiri yana kallonta, kasancewar haske tar gashi ba ta bunjima hijabin nan na ta ba. Ba mayafi, ba dankwali tana zaune ta harde kafa tana saqe-saqen tuggu a zuciyarta. Kan ka ce kwabo Sajida ta murtuke fuska ta fara harbo masa kibiyoyin harara. "Wai wannan yarinyar wacce irin kama su ka yi da Zuhurriyya haka kamar an tsaga kara ?" Bakura ya fada a zuciyarsa. Ya yi karfin hali ya durkusa ya gaishe da tsohowar nan, yayin da su iyayye ma suka gaishe shi, ya amsa cike da fara'a, gami da cewa. "Me ku ke bukata a kawo muku?" Su duka suka hada baki, "Babu komai." Samira ta yatsune fuska ta ce, "To amarya ga angonki na kawo miki, babu abinda zan ce sai addu'a, Allah ya bada zaman lafiya, ya kawo kazantar daki. Sai ku dunguma ki bishi dakinsa ni dai na tafi sai da safe." Samira ta juya za ta fita Bakura ya yi zuruf ya bi ta a baya, suka fice. Sajida ta ja wani dogon tsaki ta murguda baki ta ce, "Wa ya ga amarya, amma kuwa kin yi batan kai da ki ka shigo min da wannan mutumin dakina." Caraf Iyayye ta yi sauri ta toshewa Sajida baki, don kada su Samira su juyo ta. Nan fa suka hau rokar Sajida akan ta tashi ta shirya ta je dakin ango. Saboda takaici ko kallonsu ba ta yi ba ta tashi ta shige uwar daki ta kwanta kan gado ko kayan jikinta ba ta cire ba. A kofar dakin Samira suka tsaya suka dauki lokaci mai tsawo su na tataburza har da kokaye-kokaye. Bakura zai shiga dakinta, ita kuma ta ce ba zai shigar mata daki ba sai dai ya tafi dakinsa don ta san in anjima amaryarsa za ta je ta same shi. Kalmar da ta fito daga bakin Bakura ita ta bawa Samira mamaki da ya ce "Ko Kur'ani ki ka ba ni zan dafa cewar Sajida ba za ta zo inda nake ba, saboda ba ta sona." Wani kallo na takaici, gami da karka raina min hankali mana, haka Samira ta kalle shi ta tabe baki. Ta ce, "Ai kai kana sonta, tunda ka auro ta sai ku je can ku karata." Ta yi wuf ta shige dakinta ta datse ta bar shi anan a tsaye. Ya yi shiru yana tunani, ya kalli kofar dakin Sajida, ya juya ya dubi dakin Samira sai ya girgiza kai ya yi murmushi, ya juya ya nufi dakinsa. Yana shiga dakinsa ya tura qofa ya rufe yasa hannu a aljihunsa ya zaro wasu hotuna guda biyu ya ajiye a tsakiyar gadonsa. Hotunan Sajida ne, wanda aka dauke ta a tsakar gidansu dazu da yamma a wajen yinin bikinta. Daya kafin ta yi wanka aka dauka, dayan kuma bayan ta yi wanka ta caba ado daidai lokacin da ta yi wannan murmushin nata aka dauka. Wato mai daukar hoton har ya wanko ya kawo masa shi ne ya bar sauran a mota ya zabo guda biyun nan wanda take ita kadai don ya tantance abinda ya ke so ya tantance. Ya shiga bandaki, ya dade yana kwara ruwa a jikinsa, saboda duk jikinsa danko yake yi masa. Yana fitowa daure da tawul, sai ya zura doguwar riga 'yar yaloluwa marar nauyi. Ya taka gado ya kinkimo wata 'yar akwati akan wadurof ya zo ya zauna akan gado, ya baje wasu hotuna a tsakiyar gadonsa. Ma'ana hotunan Zuhuriyyarsa ne ya hada da hotunan Sajidarsa, don ya ga ta inda suka bambanta. Ai kuwa sak kamarsu daya, kirar jikin ma daya, ga dariya da murmushinsu iri daya. Sai mamakinsa ya sake daduwa. Surutai yake shi kadai cikin dare, kamar tababbe. Hakika Bakura yana cikin wani hali domin akan ya san asalin wannan kama ya sa ya auro Sajida, amma har yanzu babu wata shaida da ta nuna masa alaka ko kadan tsakanin Sajida da Zuuriyya. Haka Bakura ya raba dare, sannan ya hakura ya kwanta. Gajiya, gami da dogon daren da ya raba bai yi barci ba basu hana shi tashi da Asuba ya je masallaci ba. Ya na dawowa ya bi dakunan gidan gaba daya yana bugawa har da dakin Sajida. Kowa ya tashi wuri-wuri ya shiga bandaki, don dauro alwala. Bakura kuwa da ya tabbatar kowa ya tashi sai ya shiga nasa dakin ya kwanta, saboda barcin da ya addabi idanuwansa ya sake kwanciya. Samira kuwa tana farkawa bayan ta yi sallah, sai ta shiga kicin ita da kukunta suka shiga shiryawa yara 'yan makaranta abinci. Haka abincin mai gidanta da na Sajida da 'yan uwanta daban. Yau Samira ta sake zagewa wajen qara qawata abinci fiye da kullum, saboda tana so ta nunawa su Sajida bakin rijiya ba wajen wasan yara ba ne. Ta na so Bakura ya san ba irinta ake aurowa kishiya ba, saboda babu abin da amaryar za ta fi ta. Bayan komai ya dahu, ta dauko tsala-tsalan food fasks hade da plates da cokula da saving spoons hadaddu wadanda ta suyo su daga Saudiya na sarakai ne, domin an diga ruwan gwal da azurfa a jiki. Burinta ta burge qauyawan nan da suka zo gidanta da sunan amarya da qawayenta. Ta kira masu aikinta guda biyu Hajara da Grace suka dinga diba su na shigarwa dakin Sajida su na jerawa akan Dining table, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar qawayen Sajida. Sai kalmar "Sannu, mun gode." Suke fadi, daidai lokacin Sajida ta fito falo das da ita, ta yi wanka ta caba ado da wata atamfarta Super Holand kalar kore da ruwan dorawa (Green and ycllow) wacce ta sha dinkin riga da zani daidai jikinta. Ta kuwa nada dauri cas da ita kai ka ce ango ta yi wa wannan ado. Sai kamshi ne ke biye da ita a sanadiyar feshe jikinta da ta yi da turare (Designers). Hakika yunwa ce taf a cike a cikin Sajida, kasancewar jiya ba ta ci abincin kirki ba. Dan yunwar dare ma ta so ta hana ta barci, bakin ciki ne ya hana ta tashi neman abinci cikin dare. Don haka ta yi farin cikin ganin wadannan galla-gallan warmers. Kai tsaye Sajida ta haye kan tebur ta kalli kawayenta. Ta ce, "Mai ci ta zo don ni ci zan yi, wanda ya ga bati ya kyale jahili ne. Wahalallun har sun gama abinci da sassafen nan, sai dai su dafa su ba ni dan ni babu wanda zan dafawa abinci a gidan nan, saboda ajiya aka kawo ni in ci in yi gaba." Suka taso kowacce ta sami tata kujerar ta zauna. Zainab ta dubi Sajida ta yi dariya.Ta ce "Sajida ba ki da mutunci." Tsohuwa ta ce, "Ba zan hau tebur ba kar in fado saboda dadi ku zubo min nawa a kasa zan ci." Tun kafin su Sajida su kai loma daya bakinsu suka fara santin kyawun cokulan da plates din nan. Ai da suka fara ci, sai suka ji cikin kunnuwansu ya dau kaikayi, saboda dadi. Tunda suke ba su taba cin abinci mai dadin irin wannan abincin ba. Wasu abubuwan cusawa suke ba tare da sun san sunansa ba. Kamar bangaren fruits irin su straw berry, inibi, duk sai dai su ganshi a talabijin ko a hoto ko kuwa su ga fukawar su. Misalin karfe goma sha daya, Bakura ya farka daga barcin da yake yi, ya yi wanka ya fito a shirye tsaf sanye da wata shadda shudiya (blue), wacce aka yi masa gajeren dinki iya gwiwa, wato (boda), ya dora shudiyar hula. Kamar wadanda suka hada baki Samira ya iske a falo ta ca6a ado da wani shudin leshi, sai walkiya take. Bayan ta gaishe shi sai ya shiga janta da wasa yana zolayarta, duk da ya san haushi yake bata shi kuwa dadin zolayar yake ji. Suka wuce kan tebur don karya kumallo, domin Samira ba ta iya cin abinci ita kadai, duk dadewar da Bakura zai yi a waje ko yana barci sai ta jira shi ya zo sun ci tare tun sanda suka yi aure. Sun fara cin abincin kenan, sai Samira ta dube shi ta yi gatsine. Ta ce "Af, ya za a yi ka zo ka zauna kana cusawa cikinka abinci, ba ka damu da amaryarka ba, yaya ta kwana, ko me ta ci, ko me za ta ci?" Bakura ya yi dariya ya ce, "Ai bakuwarki ce, na san ba za ki bar ta da yunwa ba." Takaici gami da daci ne ya dasu a zuciyar Samira. Ta tabe baki ta ce, ai gara aje a kira ta ta zo mu hadu mu karya tare ka ga sai ka fi jin dadin cin abinci kana yi kana kallonta, don na ga alamar har wata nutsuwa ka ke idan a gabanta ka ke." Bakura ya kwashe da dariya Ya ce, "Kishi, kishi, Samira kishi sunanki daga yau. Yaushe aka kawo Sajidar da har ki ka lura ina nutsuwa idan a gabanta ne? Jiya-jiya ne fa." Haka dai suka dinga fafatawa har suka gama cin abinci. Bakura ya yi zunbur ya mike, gami da duba agogo. Ya ce, "Kaduna nake so in je akan maganar wadannan motocin da nace an turo min daga America sun zo, sai kin zaba kin darje kafin kowa ya zaba, saboda ke ce gimbiyar gidan." Ta harare shi, ta ce, "Ka ce dai ka yi sauti a siyowa amaryarka mota ba ni ba." Ya kwashe da dariya ya suri mukullin mota yana shirin ficewa. Ta sa hannu ta kamo hannunsa, ta ce, "Ka fita ka je ina? Ai dole ka shiga kaga lafiyar abar qaunarka, kafin ka fice tunda ba ita ta kawo kanta ba, kai ka ajiye ta." Bakura ya yi dariya ya ce, "Kai! Kai! Nima na jawowa kaina, na zama kamar waina sai juya ni ake ta ko'ina. To mu je ki raka ni dakin." Samira na gaba yana biye da ita har falon Sajida. Sajida na ganin su ta daina fara'a ta dauke kai ta juya musu keya. Sai kawayen ne suka gaishe su. Su Kuma su Samira suka gaishe da tsohuwa. Tsohuwa ta amsa, gami da cewa "mu yanzu za mu koma gida, ga Sajida nan amana, kuma ku yi hakuri da halinta, har Allah Ya sa ta gane." Samira ta danne zuciyarta ta kalli Sajida ta ce, "Amarya ina kwana. Ko ba ki gaisa da ni ba kya gaisa da angonki ai ko." Sajida ta yatsune fuska ta tabe baki ta amsa gaisuwa a ciki-ciki. Bakura kuwa ba a raba shi da qurawa Sajida ido. Ya tafi can wata duniyar tunani yana tuno kamannin Zuhuriyya, yana hadawa da abinda idanuwansa suke gane masa. Kamar daga sama yaji muryar Samira ta katse masa tunaninsa da yake. Ta ce "Sai ka sa direba ya kai su gida, kuma ka kawo kudin budar bakin amarya a bawa qawayenta su raba." Nan da nan qawayen amarya suka warware kowacce fadi take, "A ba mu kudin siyan bakin amarya." Bakura ya yi dariya ya ce, "To zan bawa Samira za ta sallame ku." Ya juya ya fice, Samira na biyo da shi su na tafe Su na kallon dakwalkwalallen darning table din Sajida kaca-kaca da abinci da kwanukan da suka ci. Kowanne a watse ba tare da an kinkintsa wajen ba, balle a kwasa a kai kicin. Kowacce da ta gama ci sai ta koma Kan kujera ta nade. Don haka Samira na fita ta kira Grace ta ce ta shiga ta kwaso mata kwanukanta ta gyara musu kan tebur. Bakura da Samida suka dinguma wajen motoci, ya zabi wacce yake so ya shiga, ta zo ta dafa murfin mota. Ta ce, "Kawo kudin 'yan mata da ka yi alkawari." Ya ce, 'Ke za ki sallame su ba ni ba, tunda baqinki ne." Kafin ta ce wani abu ya jawo kofar motarsa ya rufe ya ja dogon ribas yana sheka mata dariya. Ta tsaya tana kallonsa kawai tana takaicin wannan al'amari, domin ita tafi jin haushin kanta da take shiga safgarsa da amaryarsa, ga shi ta zame masa abar tsokana tamkar wata kakarsa. Ta gyada kai ta yi qwafa, gami da cije baki alamar za ka dawo ka same ni. Ta na shiga falo ta yi kicibus da qawayen amarya da tsohuwa sun fito za su tafi. Cikin fara'a take yi musu magana. "Ba dai har kun fito ba, ba za ku yinin mata ba har ta sake warwarewa ba?" Su ka amsa cike da murmushi, "A'a daga gida aka yi waya aka ce mu dawo." Samira ta ce, "To ku jira ni ina zuwa." Ta shiga dakinta zuwa wani dan lokaci ta fito dauke da kudi, gami da wata leda a shaqe da sabulai kala-kala. Ta miqa musu ta ce "Ga shi dubu ashirin ce yace a baku, wannan kuma sabulai ne kwa yi wanka ni na baku." Suka ji wani tsagoron farin ciki ya rufę su, sai suka zube su na godiya. iyayye ta lankwashe murya ta ce, "Hajiya Samira, gaskiya ba zan 6oye miki ba ko a bayan idonki za mu fada kina da kirki, kuma samun mace kamar ki sai an tona a cikin mata." Samira ta yi dariya ta ce, "Ba komai ai mun zama daya. Ku je bakin get ku tambayi Lurwanu direba ku ce na ce ya kai ku gida da mukullin mota a hannunsa." Haka tsohuwar nan ta dinga shi wa Samira albarka, har suka fice. Samira ta dawo ta zauna a falo tana huci, tana fitar da zazzafar iskar da ta mamaye huhunta. Saboda ba karamin karfin hali ta yi ba wajen danne kishinta, duk wannan kissar da kisisinar ba ta kai zuci ba. Zuciyarta tafasa take tamkar ruwa akan wuta. Daman Sajida jira take kowa ya watse, Allah- Allah take duk su tafi su barta ta kunna sabuwar wayar da Abdulmajid ya aiko mata, don su yi magana. Fitar su iyayye ke da wuya ta dauko wayar ta saka a caji, ba tare da ta bari cajin ya cika ba ta kunna, gami da saka sabon layi da recharge card ta matso lambarsa wacce daman tuni ta haddace ta akai. Koda kuwa daga barci aka tashe ta za ta karanto lambar a Kwakwalwarta. Bugu daya ya dauka, duk da bai gane kowace ce ba, Kai ka fi cancanta Balle karya kumallo, bashi da shirin yin wanka ya fita. Daga dukkan alamu zafin rabuwa da Sajida ya shige shi, don a da yana ganin wasa ne ba auren za ta yi ba yanzu kuwa ya tabbata. Har suka gaisa bai fahimci ita ce ba, sai da ya ji kalamanta masu ratsa masa jiki, sannan ya farga. Kan ka ce kwabo ya ware murya. Tambayar da ya fara jero mata ita ce, "Da fatan dai baki yarda wani abu ya hada ku ke da wannan banzan mutumin ba kö? Ina fatan ba kya sakar masa fuska, balle ya yi hira da ke ko?" Ta amsa masa da, "Shi ya isa ma ya matso kusa da ni. Ai ko kallon inda yake ba na yi." Ana badakala, haka Sajida da Abdulmajid suka dau lokaci mai tsawo su na waya, har sai da kudin wayarta ya qare, shi ma ya kira kudin wayarsa ya qare. Sai ya turo mata text massage cewar ta yi hakuri idan ya fita waje zai sa kati zai kira ta. Yau farin ciki a zuciyar Sajida baya faduwa, ta sumbaci wayar ta rungume filo, gami dą lumshe ido tamkar tana tare da Abdul a kusa da ita. Yini guda Sajida na nade a daki, sallah ce ke tashinta daga kan gadonta. Grace ce take kai kawo tsakanin kicin da dakin Sajida. Samira ba ta gaji ba ta aika aka kai mata abincin rana, da a ka kai na dare aka kwaso kwanukan rana. Ba kunya ba tsoro Allah Sajida take nadar abinci ta koma ta kwanta. Bakura bai shigo gida ba sai bayan sallar Isha'i.Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya zauna a babban falo, tare da 'ya'yansa da uwar gidansa Samira. Ya taya yara Home work, suka yi 'yar hira, sannan ya sallami kowanne yaro ya je ya kwanta. Samira ma ta yi zumbur ta mike, gami da yi masa sallama ta nufi dakinta. Bakura ya yi kiran duniyar nan Samira ta qi dawowa, ta shige dakinta ta rufe. Yana qoqarin kiranta a waya ta murtsike wayar ta kashe. Ya dade a zaune, sannan ya miqe don tafiya dakinsa ya kwanta, domin ya gaji.Daidai qofar dakin Sajida ya jiyo muryar Sajida na hira har da kyalkyala dariya. Hakan ta ja hankalinsa ga tsayawa tsai yana sauraro. Da farko ya dauka talabijin ce, amma da ya kara kunnensa ya tabbatar muryar Sajida ce ya yi mamaki, sai ya shiga tunanin da wa Sajida take hira haka, to ko qawayen nata ba su tafi ba ne? Sai ya yanke hukuncin shiga dakin ya gani. Yana murda kofa, sai qofa ta bude ya ci sa'a a bude take ba an datse ba. Tsuru-tsuru ya ga Sajida ita kadai, ta yi daidai a kan doguwar kujera tana waya. Sanye take da atamfar dazu, amma kanta babu dankwali ta zubo gashinta har baya tana shafawa, Saboda dadin hira. Ya kalle ta, ta kalle shi kallon Kallon ake yi. Sai yaji ta ce, "Ka gan shi ma ya shigo dakina ya tsaya yana ta muzu-muzu da ido, ka san kallo ne da shi kamar wani baqauye." Da jin haka sai Bakura ya sami kújera a setinta ya zauna cike da mamaki. Can ya yi qarfin hali ya tambaya. "Da wa kike waya, Sajida?" Ta fada cikin gadara ta ce, "Abdulmajid." Yadda ta ga Bakura ya tunkaro ta a fusace kamar mai shirin mauje ta, sai ta tsorata, ta wurgar da wayar ta qanqame akan kujera. Bakura ya tsugunna ya dauki wayar a qasa, sai ya ga har yanzu wayar a kunne take Abdulmajid ne ke ta magana. Bakura ya kara wayar a kunnensa yana sauraronsa, kalmar da yaji yana cewa. "Baby, are you there?" Bakura ya yi gyaran murya, gami da' cewa, Ba baby ba ce, wannan mai gidanta ne." Abdui majid ya fada cike da gadara, "Alhamdulillahi, daman ina nemanka. Kai wawa ne, banza, jahili, ta yaya za ka auri yarinya bata sonka, saboda kana da kudi? To wallahi ka kuka da kanka. idan ba ka saki Sajida ba sai na sa an farfarda min cikinka." Bakura ya yi murmushin haushi ya gyada kai. Ya ce "Yaro, idan ni da kai zaa hado mutane masu hankali mu zauna akan teburi daya kowa ya bada labarin abin da ya faru, to jama'a za su tantance waye wawa, banza, jahili. Ka san kai ne wawa, tunda ka bari na kwace maka Sajida a cikin dan qanqanin lokaci, alhali kun dade tare har kun shaqu, don da kana da wayo ba za ka bari in kwace ta daga hannunka ba. Idan jama'a suka ji haka zasu tabbatar maka kai banza ne, tunda aka baka dama ka fito ka aure ta ka kasa fitowa ka qi yin amfani da damar da aka ba ka, har sai da ta subuce maka. Sannan daga karshe ko jama'a ba su fada maka ba, kai da kanka ka san kai jahili ne, marar tarbiyyar addini, tunda za ka raba dare kana magana da matar aure, wacce ba matarka ba. Kuma ina jiran ranar da za ka sa a farde min ciki." Bakura ya katse wayar ya kashe ta gaba daya ya juya ya dubi Sajida wacce tuni ta kufula tana harararsa. Ya koma ya zauna a kan kujerarar da take fuskantarta, ya dube ta. Ya ce "Abdul majid din ne har yanzu ba ku rabu ba, shin idan shi bai san darajar aure ba ke ba ki sani ba? Ina tabbatar miki halaka ce da azabar Ubangiji akan matar auren da take magana da da namiji, wanda ba muharraminta ba. Sajida ba kya jin maganar iyayenki, ba kya jin maganar mijinkı, alhali mu ne masu qaunarki da gaske." Ta ji tamkar Bakura yana mata yayyafin ruwan zafi a sassan jikinta, domin kalamansa tamkar zaginta yake haka take ji a kanta. Ta miqe tsaye tana mai sharara kuka, tana zubar da hawaye ta rike kugu tana girgiza ta ce, "Malam ka rufe min baki ka daina shiga rayuwata, na fada maka na sake maimaitawa na tsane ka, kuma ba zan zauna da kai ba. Wannan wayar da ka kwace ita ce ginshiqin zamana a gidanka, amma tunda ka kwace wallahi sai an neme ni an rasa." Bakura ya ce "Babu inda za ki je Sajida, ina da kyakkyawan tsaro a gidana, wanda ko jikin get ba za ki iya tabawa ba balle ki bude ki fita, kin shigo gidan nan kenan. Yanzu kin zama killatacciyar kwaryar da na rataye a ragaya, don yin ado da ita, kin fita daga sahun kwarya mai garari a tsakar gida." Daman kalmar da Bakura ya fara fada mata kenan ita ce ta jawo tsanar da ta yi masa tun farko, yanzu ma an kuma. Ta sharbe hawaye ta ce "Zahra 'yarka ita ce kwarya mai garari a tsakar gida ba ni ba." Ta juya a fusace ta na rusa kuka kamar ranta zai fita. Kukan Sajida tamkar dafi ne a cikin zuciyarsa, saboda ji yake tamkar Zuhuriyya ce take kuka. Ya ji hankalinsa ya tashi, ya miqe da sauri ya bi bayanta har cikin daki tana danna qofa yana turawa, har ya kutsa kai. Ta tafi jikin bango ta maqale ta zazzare masa jajayen idanuwanta masu zubar hawaye. Ta ce "Ka fita ka ba ni waje, ba na sonka, ba na son ganinka, na tsane ka na tsani mai sonka gara in kashe kaina da in zauna da kai." Bakura ya yi tsaye yana dubanta, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi. Ya fada cikin sanyayyiyar murya Ya ce "Me kike so in yi miki a duniya, don ki yi farin ciki?" Ta ce "Ka bar ni in auri Abdul majid." Ya yi shiru, can ya ce, "Abdul Majid ba zai aure ki ba, da na bari ya aure ki." Ta ce "To ka ba ni wayata don sai na ji muryarsa nake jin dadi." Abin mamaki sai Bakura ya kunna waya da sauri ya danno lambar Abdul majid, bugu daya wayar ta shiga, sai ya miqa mata, gami da cewa, "Ga Abdul majid dinki" Cike da mamaki, gami da sanyin jiki ta miqa hannu ta karba ta kara a kunnenta, tabbas shi din ne kuwa. Nan da nan ya ga ta fara murmushi. Ta zo ta wuce Bakura a tsaye kamar gunki ta koma falo ta luntsuma akan kujera ta na hirar soyayyarta ba tsoro, balle fargaba. Bakura ya zo falo ya sami kujera ya zauna, ya tsura mata ido ya na kallo. Hakika dariyar Sajida ita ce farin cikinsa, domin ji yake tamkar dariyar Zuhuriyya ce. Sai ya tsinci kansa ya na murmushi, tamkar Zuhuriyya ce take cikin farin ciki. Ta yi ta waya ita da abin qaunarta har sai da suka gaji, sannan suka yi sallama ta kashe waya. Ta harari Bakura ta tabe baki ta mike tana tafe tana girgiza ta shige daki ta datse ta yi kwanciyarta. Tsawon awa guda Bakura bai motsa ba, yana zaune kansa ya kulle. Ya kan raşa abinda yake faruwa da shi. Abu na farko, ba wai tsananin son Sajida yake ba, kuma baya sha'awarta, amma yana ji a jikinsa ba zai iya rabuwa da ita ba saboda kamar da ta yi da wacce ya fi so a rayuwarsa. Haka ko kadan bai ji kishin wayar da suke yi da Abdul majid ba. Ya rasa dalilin da yasa baya gajiya da duban surar Sajida da sauraron muryarta ba. Ya kasa gane daliin da yasa baya Son ganin bacin ranta, balle ya ga hawayenta. Baya taba jin haushin rashin kunyar da take tafka masa, balle ya ji ya tsane ta. Idan ya zo gabanta baya iya yi mata musu, saboda girmamawa. Amsar ita ce Sajida na cin albarkacin Zuhuriyya a wajen Bakura. Ya miqe a sanyaye ya fito daga dakin Sajida, ya nufi dakinsa. A jikin labule ya hango Samira tana lekensa ta wundon dakinta. Su na hada ido ta yi sauri ta saki labulen ta koma, da alama kishi ya hana ta barci. Ya yi murmushi ya ce a ransa, "Kya yi kya gama, da kin san yadda muka yi da Sajida da kin tausaya min. Na san duk bayanin da zan yi miki ba za ki yarda ba, don haka shiru shi ya fi alkhairi." Yana shiga dakinsa ya kulle ya kwanta, sai dai ya dade yana jujjuya abubuwan da suka faru tsakaninsa da Sajida da Abdulmajid. *** *** *** Haka gidan Bakura ya kasance, tamkar gidan 'yan adawa. Bakura da Samira ba dadi, tsakanin Sajida da Samira da 'ya'yanta ba dadi. Tsakanin Bakura da Sajida ba dadi. Sajida ta sake kudirar sai ta damula gidan gaba daya, don haka rashin mutunci kala-kala, na yau daban na gobe daban, sai futsara da tsiwa take yi wa Bakura, ta yi wa matarsa. Samira ta ce ta gaji, don haka babu ruwanta da abincin Sajida, balle ta taka qafarta a dakinta. Grace ce Bakura ya wakilta kacokan ta kula da ci da shan Sajida da kula da gyaran dakunanta da wankin bandakuna. Kai hatta undies dinta Bakura ya ce Grace ta dinga wanke mata zai biya. Tsawon wata guda kenan da zuwan Sajida bai fi sau biyu ba Zahra ta ga Sajida. Shi ma a qofar dakin Sajida suka hadu, Sajida ta leqo kiran Grace, Zahra kuma ta zo wucewa za ta shiga dakinta suka yi kallon- kallo kowa ya dauke kai. Duk ranar girkin Samira, Bakura zai kame a dakinsa, Samira ta zo, amma ranar kwanan Sajida sai dai ya bi ta daki, shi ma datse qofar falon take sai dai ya shigo ta qofar baya wacce shi kadai yake da mukullin. Kada ku ce idan ya shiga dakin wani abu ne zai faru, a'a a gaba take sa shi sannan ta danno lambar Abdulmajid su yi ta soyayya don ta saka shi takaici dan idan ya gaji ya sake ta, amma sai ta ga Bakura ko damuwa ba ya yi. Kai har in credit din wayarta ya qare sai ta ga ya zaro recharged card na dubu daya da dari biyar ya ba ta ya ce ta ci gaba da wayarta, ya na gefe yana kallonta cike da murmushi. Al'amarin Bakura wani lokaci yana ba ta tsoro, don ba ta san abinda yake hada mata ba, dan wannan kasaqen da ya yi mata akwai magana. Sajida ta ga an doshi watanni biyu da aure, babu alamar gajiyawa a tare da Bakura, ba shi da niyyar jin haushi, balle ya sake ta.Sai ta yi yunqurin hada kaya ta gudu cikin dare, amma abu ya ci tura.Ta kalli tsawon katangar gidan nan ta ga ba irin katangar gidansu ba ce wacce take iya haurawa ba. Ta nufi get ta tabbatar masu gadi su na aikinsu tun karfi ko da yaushe get a datse yake da manya-manyan kwado. Kafin a bude maka get sai sun jero maka tambayoyi, balle a ce su ganta da kayanta a hannu ba a mota ba ta ce za ta je unguwa, ko daya ba za su bar ta ba. Gashi an hana kowa zuwa daga gidansu. *** *** *** Wata rana da daddare, dare har ya fara nutsawa Bakura bai dawo gida ba. Sha daya na dare, har ta wuce ba Bakura babu wayarsa, don haka hankalin Samira da 'ya'yanta ya tashi, ko barci suka kasa yi. Yi suke su na qara yi wajen buga wayarsa, amma wayar a kashe. Babu abokinsa da ba ta kira ba, sai su ce ba sa tare da Bakura a yau. Sha biyu daidai wayar Samira ta yi qara alamar ana kiranta, ita da Zahra suka hau rige- rigen dauka. Samira ta danna wayar, gami da kadawar hanta da fargaba. Ta fada "waye yake Magana?" Cikin harshen turanci mutumin ke magana da alama Inyamuri ne, ya fara da gabatar da kansa. Ya ce, "Sunana Doctor Isreal daga International Hospital. Dan Allah ina magana da Samira ne Mrs. Bakura ne?" Ai tuni Samira ta rusa kuka ta fara kwakwazo. "Doctor ni ce Samira. Me ya faru da maigidana, ya mutu ne?" "Bai mutu ba, amma ya sami rauni." sai ta sake fashewa da kuka ta ce, 'Hatsari ya yi ne?" Ya ce"A'a an kawo mana shi dai ana tunanin yan fashi ne suka dake shi har an farfasa motarsa. Ki kwantar da hankalinki ga shi nan ya miqe yana magana, shine ma ya ba ni lambarki ya ce in kira kı." Doctor ya sakawa Samira muryar Bakura yayin da ita ma ta danna speaker yadda yaranta za su jiyo muryar mahiafinsu, don su dukka kuka suka zo suka kewaye ta su na yi. Cikin kuka suke kiran. "Abba, Abba me ya faru da kai?" Cikin sanyin murya Bakura yake lallashinsu fadi yake, "Na ji sauki, ku daina kuka." Dukka wannan abinda ake Sajida na bayansu a tsaye ta jingina à jikin bango ta kama kirji ta qame kamar soja. Da alamar akwai sanyin jiki a tare da ita. Amma da ta ga sun juyo gaba daya su na kallonta, sai ta tabe baki ta harare su sama da qasa ta wuce zuwa dakinta, don kada ma su đauka ya dame ta. Samira ta aika Zahra da Abubakar, Boy's quater su taso Lurwanu direba ya zo ya kai su asibiti wajen Bakura. Da gudu Zahra da qaninta suka nufi Boy's quater suka taso shi, a gigice ya dauko mukullin mota ya fito. Ba tare da bata lokaci ba Samira da 'ya'yanta suka duru a mota suka nufi asibiti, sai addu'a suke su na koke-koke a hanya. Sajida na shiga falonta ta jawo wayarta ta bugawa Abdul majid, zuciyarta cike da 6acin rai, domin tana zargin da sa hannunsa a cikin wannan al'amari, Ya na amsawa ta harbo masa wannan tambaya. "Abdul majid me kasa a yiwa Bakura?" Ya tabe baki ýa ce "Me ki ka ga an yi masa, wannan wacce irin tambaya ce kike yi min? Kar ki raina min hankali mana." Ta fada cikin tsawa da bacin rai, "An ce 'yan fashi sun tare shi sun dake shi, har sun fasa masa mota. Ina tunanin kai ne kasa a yi masa haka." Ya ce, "Ki daina tunanin nasa an dake shi, nine da hannuna na tare shi ni da su Shehu abokaina muka farfasa masa kai dazu da magruba a Hotoro G.R.A. Kin fara sonsa ne, ina ruwanki ko mutuwa ya yi?" Ta fada a fusace, "Ka ga Abdul majid ba na son haka, ya za ka nemi ka kashe mutum ba da hakkinsa ba. Me ya yi maka? Mutumin nan ya ba mu damar mu yi magana har ma katin waya yake siya ya ba ni in kira ka. Me ye laifinsa?" firgitarwa. Kai ka fi cancanta Paid book 300 0023843938 Unity bank Jamila umar tanko 0803719670i Ya fusata ya ce "To ki je police station ki yi qarana da kan ki kafin ya warke ya sa a nemo mu, don na fada masa ko mu su waye, kuma na haska masa fuskata tangararai ya ganni, kuma zai shaida ni. Tunda kina sonsa kada ki qara kirana a waya." Ya yi tsaki ya kashe wayar, Sajida ta dade zaune tana ta tunani tana zullumin abinda zai je ya dawo. Hakika har cikin ranta ba ta ji dadin abinda Abdulmajid da abokansa suka aikatawa Bakura ba. Don haka babu irin kiran da Abdul majid bai yi mata ba a cikin daren nan Sajida ta qi amşa wayarsa, daga qarshe ma ta kashe wayar gaba dạya ta yi kwanciyarta. Tana jiyo motsin dawowar su Samira har da Bakura, amma ko leqowa qofar dakinta ba ta yi ba, balle ta yi masa sannu. Haka washe gari Bakura ko falo bai fito ba, yana dakinsa a kwance ya hana Samira ta fadawa kowa cewar bashi da lafiya, don haka masu aiki ma ba dukkansu ba ne suka san Bakura na kwance ba lafiya ba. Wannan al'amari na Sajida ya yi matukar batawa Samira da 'ya'yanta rai, sai shige da fice take tsakanin dakinta, falo zuwa kicin tana nuna halin ko in kula bai dame ni ba. Rashin lafiyarsa ku ta dama ba ni ba. A fusace Samira ta zo shiga kicin yayin da a fusace Sajida ta zo fitowa daga kicin suka bangaji juna a bakin qofar kicin, Sajida dauke take da qatan kwalin juice da kofi a hannunta. Samira ta ce, "Mutum ko dabba ne ai ya san mai ba shi abinci, don haka baya samun sukuni idan ya ga kwana biyu bai ga mutumin nan ba. Ma'ana shi mai ciyar da ke, mai tufatar da ke, mai siyo wannan juice din da ki ke yini kina sha, ba shi da lafiya a ce ko Sannu, yaya mai jiki baki iya ba. Duk rashin tarbiyyarki ai kya tausayawa rai, saboda idan mutumin nan ya fadi ya mutu, sai dai fa ki koma gargajiya zancen juice ya kare." Sajida ta yi wurgi da kwalin juice din hannunta, gami da rada kofin tangaran a qasa ya ragargaje. Samira ta ce "Dole ki fasa min kofi, saboda ba ku taba sanin yadda ake siyan kayan gado ba balle kayan kicin." Sajida ta fusata ta cakumi kwalar Samira. Ta ce, "Ke dakata kada ki fada min magapar banza akan wani banzan mijinki. Bakura har mutum ne da zan yi kishi a kansa? Ko an ce miki na zo da niyyar aure har da-zan shigo da kayan daki, shi ya ce ya ji ya gani, shi ya maqale ya nace ya raba ni da wanda nake qauna, ya kawo ni gidansa ba dan ina qaunarsa daidai da kwayar zarra ba." "Sakar min kwalar riga kafin in wanka miki mari." In ji Samira. Zahra ta fito daga dakinta da gudu, don ta jiyo hayaniya, haka qannenta suka fito daga falo a guje, don su ganewa idanuwansu abinda ke faruwa. Cikin fushi Zahra ta zo ta fusge hannun Sajida daga wuyan mahaifiyarta ta daki kirjin Sajida da hannayenta biyu ta shiga tsakanin Samira da Sajida. Ta ce, "Mama koma daki ki zauna ki bar ni da ita, ni ce sa'arta ba ke ba." Mamaki ya hana Sajida magana, har murmushi take na hamdala daman tana neman irin wannan rana da za su gwabzu da Zahra, saboda haushinta da take ji tuntuni. Zahra ta ce, "Sajida yau ne rana ta farko da zan yi fada a rayuwata, yau ce rana ta farko da zan tabbatarwa mahaifiyata ta iya haihuwa ba ta sha wuyar banza ba. Yau ita ce rana ta farko da zan nuna miki ba na tsoronki, shiru-shiru ba tsoro ba ne. Ke ba ajina ba ce, domin halinki irin na 'yan matan da ba su taba zuwa makaranta ba ne sai talla a titi. Ba ki da tarbiyya, ba ki sami tarbiyya ba a matsayinki na 'ya mace. Ba kya jin maganar iyayenki, hakan ne ya jawo miki yin aure da wuri maimakon karatu. Kin amsa sunanki na kwaryar tsakar gida mai gagari, ke ba kwarya ta gari ba ce, wacce aka saqale a ragaya don yin ado da ita ba." Wannan kalamai na Zahra ya yi matukar burge Samira, Zahra ta ba ta mamakin yadda wadannan kalamai suka fito daga bakinta. Yayin da ita kuma Sajida ta qufula, ta fusata, ta sake tabbatarwa wannan kalmar mahaifinta ce, don haka bakinsu daya komai a shirye suka hada mata don su raba ta da Abdul majid . A fusacc Sajida ta kaiwa Zahra mari, Zahra ta riki hannun Sajida, yayin da ita ta kai mata mari har sai Sajida ta ga hasken wuta. Zahra ta ce, "A da kin fasa min kai, kin ji dadi, kar ki sake tunanin za ki iya cin galaba a kaina kuma. Sai dambe ya hautsine tsakanin Zahra da Sajida, Abubakar, da Umar sai suka shiga fadan, qafar Sajida kawai suka kwaso sai ga ta a qasa, yayin da suka hau ciccibarta wai za su fitar da ita daga gidansu. Samira ta ga abin yana kokarin lalacewa sai ta shiga rabiya tana jan 'ya'yanta tana cewa, "Ku sake ta, ku kyale ta haka." Duk wannan abu da ake Bakura na jiyo hayaniya daga dakinsa, tun yana zaune yana kwalla kiran Samira, har ya daure ya sauko daga kan gado yana dingishi ya fito, ga tsananin ciwon da kansa yake yi masa saboda raunin da ke gefen idonsa ya kumbura ya aune. Ya na fitowa ya ji hankalinsa ya tashi, ganin yadda 'ya'yansa ke cali-cali da Sajida a qasa. Ya rafsa ihu, kai ka ce bindiga aka burma masa ya danno da gudu yana kurma salati, har da tuntu6e saura kiris ya fadi qasa. "Me zan gani? Samira me ki ke nufi da za ki sa 'ya'yanki su daki matata? ku sake ta kafin in kakkarya ku." Su ka watse gaba dayansu suka gudu gefe sai huci suke. Ya taho da sauri ya tashi Sajida tsaye yana karkade mata jiki, fadi yake, Yi hakuri Sajida, kwantar da hankalinki zan rama miki." Ta rushe da kuka ta fizge jikinta daga gare shi ta ce, "Wallahi zamana ya qare a gidan nan yau, ko awa daya ba zan qara ba tafiya zan yi. Zahra sai na nuna nıiki ko ni wacece, sai kin gwammace baki dora hannunki a kaina ba." Bakura ya juya ya dubi Samira da 'ya'yanta ya ce "Ki shirya ke da 'ya'yanki ku bar min gidana." Gaba daya suka bude baki don mamaki ko a mafarki ba su zata akwai ranar da Bakura zai iya furta wannan kalma ba komai girman laifin da suka yi masa ba, balle a kan Sajida. Sajida ta yi murmushi ta goge hawaye ta kalle su sama da kasa ta ce "A qara gaba ko, ni dai kun ga shiga ta daki, kada ku yi addu'ar inyi arangamata da ku a kashi na biyu dan haduwata da ku ba zatayi kyau ba." Ta shige dakinta ta datse. Zahra cikin kuka ta ce "Abba, yanzu akan Sajida za ka kore mu? A kan matarka za ka rabu da uwar 'ya'yanka?" Samira ta dakawa Zahra tsawa ta ce, "Ki rufe min baki, don me za ki dinga roqarsa? Ki bar shi ya zauna da Sajida. Kowannenku ya je ya dauko kayansa ku zo mu tafi ba za mu kwana a titi ba, Allah yasa ina da iyaye da gatana." Yara har murna suke suka shiga dakunansu su na hada kaya. Haka Samira ta wuce zuwa dakinta da sauri har karkarwa take tana hado kayanta. Zahra ce ke shar6ar kuka tana tafiya tamkar babu laka a jikinta ta wuce zuwa dakinta, ta fara hada kayanta. Bakura ya dora hannu aka kira yake, "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Ya fice da sauri wajen masu gadi ya ce su daddatse kowacce qofa da mukulli, su ba shi 'yan mukullan, yau ba shiga ba fita duk wanda ya zo kar a bude masa, haka duk wanda zai fita kada a bude masa Ya zuba mukullai a aljihu ya shiga gida. Ya ci karo da su kowannensu yana jan akwatuna riki-riki. Ya dakawa yara tsawa "Ku koma da kayan nan ciki kada in ga qafar wani a waje!" Usman dan auta ya ce "Abba kai fa ka ce mu tafi mu mun fi so mu tafi." Umar ya ce "Tunda Aunty Sajida ta zo gidan ba dadi, gara mu koma Yakasai mu zauna mu bar mata gidan." Abubakar ya ce "Gaskiya Abba mu tafiya za mu yi, tunda ka ce mu tafi." A fusace Bakura ya yo kansu kamar zai dake shi yana fadin, "Ku kwashi kayan nan ku koma da su daki." Jikinsu na rawa suka dinga juyawa da akwatinansu ciki gida. Zahra ba ta ce uffan ba ta ja akwatinta ta nufi dakinta sai sharbar kuka take. Samira ta ci gaba da jan tata akwatin ta nufi kofar fita fadi take, "Idan ka hana 'yaranka tafiya daman ba da su na zo ba. Ni kuwa babu abinda zai sa in qara sakon daya a cikin gidan nan. Na tafi na tafi kenan ba zan dawo ba." Bakura ya rike akwatin gam yana ja tana ja. Samira ta ce "Ka sakar min akwatina tafiya zan yi. Zamana da kai ya qare." Ya durkusa gwiwoyinsa guda biyu a qasa yana mai tsananin nuna nadama da bada hakuri. VYa amsa da bakinsa, "Na yi kuskure da na furta wannan kalma, na yi dana sani dana yanke hukunci cikin fushi. Ki rufa min asiri kada ki fita da kayanki, saboda masu aiki da masu gadi za su ganki. Ko da kin je get ba su da mukullan da za su bude miki get ga mukullan a aljihuna. Samira, ba zan iya rabuwa da ke ba, kin zama ni, na zama ke. Ranar rabuwarmu sai ranar da aka saka min likkafani aka kai ni kabarina aka binne, ko ranar da aka saka miki likkafani aka kai ki kabari aka binne. Babu yadda za a yi daya ya bi daya kabarinsa, saboda Allah bai halatta mana yin hakan ba da ba za mu rabu ba. Ki yafe min, na yi kuskure. " Hawayen Bakura shi ya sa Samira rushewa da kuka ta taho da sauri ta rungume shi, su duka kuka suke yi. "Kanka da zafi da alama ciwo yake. Mu je daki ka sha magani, ka kwanta." Samira ta ce da Balkura. Allahu Akbar! Soyayya saboda Allah ba karya ba ce. Ina masoyan zamani? Washe gari Sajida ta bude ido ta ga su Samira daram a zaune a gida suna ta hidindimunsu kamar kullum. Haushi ya rufe ta ta sake tsanar Bakura. Idan zai kwana yana yi mata magana ko kallonsa ba ta yi. Haka ta dinga takale-takalen masifa a cikin gidan nan babu mai kula ta, kasancewar Bakura ya ja musu kunne kar su kara sauraronta duk abinda za ta yi a zuba mata ido. Ta bangaji wannan, ta harari wancan, ta yi tsaki ta tsartar da yawu, babu wanda ya damu da ita. Har tsawon sati biyu Bakura na jinya ko sannu ba ta hada shi da Sajida ba. Ya warke ras ya ci gaba da harkokinsa bai taba cewa kowa ga abinda ya same shi ,ba, ko Sajida da Samira bai fada musu cewar ya san wadanda suka yi masa wannan ta'addancin ba. Haka Malam Yakubu ya yi ta bugowa Bakura waya yana tambayarsa lafiya kwana biyu bai ganshi ba, Bakura ya fake da cewa baya gari ya yi tafiya.Koda yaushe Malam na tambayar Bakura yanayin zamansa da Sajida, Bakura yana nunawa Malam ai yanzu Sajida ta yi laushi lafiya kalau suke zaune. Bai taba fadawa Malam halin da suke ciki ba, don haka hankalin Malam da matarsa a kwance. Ba su san Sajida na da waya ba, don haka har tsawon watannin nan uku ba su yi magana da Sajida ba, kuma ba su zo sun ganta ba. Malam ya hana kowacce qawa ta tako gidan Sajida ba, ko danginsu ma ya hana su zo. Ya ce abar ta sai ta shekara ta cire duk wani baqin rai, sannan a je a ganta sannan ita ma ta zo a gaisa. Yamma sakaliya Bakura ya dira a kofar gidan Malam. Malam ya yi marhaba da ganin Bakura, domin sun dade ba su hadu ba. Bayan an dau karatu, an yi sallar Magriba jama'a sun watse sai Bakura da Malam ne suke hira. Can Malam ya ce, "Af, na manta ban fada maka ba, Baquwa muka yi daga nesa kuwa take. Wata kakar Sajida ce, wacce ba su taba ganin juna ba tunda suke a duniya.Ta niko gari tun daga Gashuwa ta zo ganin Sajida ta sami labarin auren ta, duk da bata samu ta zo ba amma an kai mata kayan biki da atamfar da aka rarrabawa kakanni da iyaye, daga cikin atamfofin da ka ce a rabawa dangi sai yanzu ta sami damar zuwa." Bakura ya gyara zama, gami da cewa, "Allah sarki, tun daga Gashuwa ta zo ba ta samu ta zo bikin ba kenan?" Malam ya ce, "Ai ta tsufa ga ciwon qafa, shi yasa ba ta zo ba." Bakura ya ce, "Amma na ji ka ce ba su taba ganin Juna ita da Sajida ba. Baku ta6a tunanin kai ta ba duk tsawon shekarun nan? Ko dangantakar da nisa ne?" Malam ya ce "Wallahi dangantakar ta kusa ce, jini daya. Ka san kowa da halinsa, Furera wata irin mata ce ba ta da zumunci sosai, ba ta mayar da kai ta kaita Gashuwa ba." Bakura ya ce "Kakarta ta wajen dangin uwa kenan?" Malam ya ce "Kwarai, ta bangaren Furera suka hadu." Bakura ya ce "Idan na je wa zance mata sunanta, ko yanzu zan tafi da ita can su kwana su na hira?" Malam ya ce "Gobe da safe dai za su taho ita da Furera, don a yi mata bayani tunda ba ta san ta ba. Idan na fada mata sunanta ba za ta gane ba, amma ka ce mata kakarta Iya Azumi ta zo daga Gashuwa za ta zo gobe su gaisa." Bakura ya ce "Insha Allah zan fada mata, Allah ya kai mu goben, ni ma za su same ni a gidan, don ba na fita da wuri har sai wajen sha biyun rana nake fita." A haka Bakura suka yi sallama da Malam ya shiga motarsa ya tafi gida. A masallacin qofar gidansa ya jima yana tattaunawa da liman akan abinda masallaci yake buqata, sannan ya shiga gida. Bayan ya yi wanka ya ci abinci, sai ya tura qofar dakin Sajida ya shiga da yake yau ita ce da kwana, Samira tuni ta shige dakinta ta rufe. Kamar kullum, kamar yadda suka saba sai dai Bakura ya shiga dakinta, iyakacinsa kan kujera ya tsura mata ido yana kallonta, ita kuwa tana ganinsa sai ta danno lambar Abdulmajid dinta don ta ba shi haushi. Da alama ba ya jin haushin don har yau bai taba bata rai idan tana waya ba. Bai kuma daina kara mata recharg card ba, idan kudin wayarsu ya qare. Sajida ce a kwance a kan gado, ba tare da ta ji motsin shigowa ba ta ga Bakura a tsaye a kanta. Ta fada cikin tsiwa, "Malam ya aka yi ne ka shigo min har cikin daki ba izini, lafiya?" Ya yi murmushi ya ce, "Lafiya ranki ya dade, sako na zo in isar miki." Ta maimaita "Saqo, wanne iri?" Ya ce "Baba ya ce in sanar miki gobe da safe Umma Furera da wata kakarki its Azumi daga Gashuwa ta zo za su zo su ganki." Ta tabe baki ta ce "Duk danginmu babu Azumi, haka ba mu da dangi a Gashuwa, ka (tuno dai wajen wacçe aka ba ka sako, amma ba ni ba." Bakura yana niyyar magana sai Sajida ta jawo wayarta ta matso sunan Abdulmajid ta kashe murya ta ce, "Hello darling, ka kwanta ne?" Bakura ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar da zai bata ba. Ya tabbatar korarsa take so ta yi, don ba ta Son ganinsa. Ya wuce dakinsa ya kwanta yana juyi a gado ya rasa yadda aka yi rayuwa ta zame masa haka. Don haka yau bai ga ta zama ba, alwala ya dauro ya dauko jarbi mai dubu ya fara kiyamullaili yana tasbihi yana roqo, ya na hawaye a gaban Ubangiji da Ya yaye masa duk wata damuwa, hargitsi da sarkakiyar da take a tsakanin shi da Sajdia. Domin Sajida ta zame masa tamkar qadangaren bakin tulu, idan ya jefe shi ya fasa tulun, ko ya fada ruwa, ruwan ya lalace. Haka ya kai Asuba bai rintsa ba har sai da ya yi sallar Asuba ya je ya tashi iyalansa sallah, sannan ya dawo ya kwanta. Barci mai dadi ne ya sure shi mai hade da kyawawan mafarkai. Abun mamaki sai ya yi mafarkin Sajida da Zuhuriyya su na tare. Wannan mafarki ya bawa Bakura mamaki matuka, tun daga cikin barci har ya bude ido yana mamaki. Samira ya gani a tsaye akansa,ya sake gwale ido don ya tabbatar ita din ce kuwa? Kai ka fi cancanta Paid book 300 0023843938 Unity bank Jamila umar tanko 08037196708 Ta yi murmushi ta ce "Wanne irin barci ka ke yi yau tunda safe. ka san qarfe nawa ne yanzu? Qarfe daya saura har yara şun kusa tasowa daga makaranta kuma kun yi baqi ina jin mahaifiyar Sajida ce da kakarta. Sau biyu babar Sajida na leqowa kicin tana tambayata ba ka tashi ba ne. To kar su ga ko ni ce ba na so ku gaisa, gara ka je ka gaishe su sannan kai ma ka ci abinci." Bakura ya murje ido ya ce "Ki je zan yi wanka yanzu zan fito." Ta na fita ya miqe ya shiga bandaki ya yi wanka, gami da dauro alwalar Azahar. Tunda rana ta yi zafi ba shi da niyyar fita sai da yamma, amma jin surukansa sun zo sai ya saka manyan kaya. Rigar shadda ce koriya tazarce da wando ya dauko hula ya dora, sannan ya fito. A nutse ya wuce falo, don cin abincin safe. Samira ya iske a zaune a falon tana ganinsa ta tambaya. "Ka je kun gaisa da bakin?" Ya ce "So na ke in ci abinci yunwa nake ji, ko so kike in je gaban surukai yunwa ta buge ni in kwanta? Samria ta kwashe da dariya ta ce, "Allah ya kiyaye ma, ci abincin tukunna sai ka je ku gaisa. Ba na so dai su qara leqowa su tambaya." Bayan sun gama cin abinci, domin ita ma ruwan shayi kawai ta kurba tun safe kasancewar idan ba da Bakura ba, bata iya cin abincin kirki. Bakura ya miqe ya ce da Samira "To zo ki raka ni in gaishe su." Samira ta fada cike da mamaki, "Wai ni ce zan yi maka zaman auren ne Abban Yagana? Ka ji mutum, na san sanda ka je ka yi durqushe-durqushe da gaishe-gaishen dangi har aka baka 'ya? Babu inda zan je, ka je kai kadai kun fi kusa." Bakura ya tafi fuskarsa cike da murmushi, ya qwanqwasa qofar falon Sajida cikin ladabi ya murda ya bude. A falo ya iske su, su dukka ukun su na zaune a qasa akan kafet. Sajida na ganinsa ta tsuke fuska ta kawar da kai gefe kamar ta ga maqiyinta har sai da Umma Furera ta lura da haka, ta shiga tunanin ashe daman har yanzu da matsala a zamansu? Ashe Sajida ba ta saduda an zauna da ita lafiya ba?" Yayi sallama ya zo a nutse ya durkusa a gabansu yana mai sunkuyar da kai kasa, don kunya da girmamawa. Ya gaishe su suka amsa dukkansu a kunyace. Umma Furera ta ce da shi, 'Wannan kakar Sajida ce ta zo jiya daga Gashuwa, don ba ta samu ta zo biki ba, sunanta lya Azumi." Bakura ya ce "Ai jiya Malam ya fada min, Allah sarki ya yaya hanya?" Daidai lokacin ne Bakura ya dago ido ya dubi Iya Azumi. Ta ce, "Angona lafiya kalau." Ita ma ta na dubansa, amma wannan karon duban da suke yiwa juna ya tashi daga surukai ya koma duban qeqe-da-qeqe mai dauke da alamar tambaya. Duba ne irin na ban mamaki da tsantsar gigita mai hade da tashin hankali tamkar su kurma ihu, haka yanayin kowannensu ya canja. Karkarwa Bakura yake yana nuna iya Azumi ita ko hannu ta dora a ka ta na hawaye da salati. "Lafiya, me ya faru?" Haka Umma Furera da Sajida suke tambayarsu a gigice suma . Babu wanda ya iya ba su amsa a ciknsu. Bakura ya yi karfin hali ya ce "Innono" Ta amsa masa "Na'am, Bakura kai ne?" Sai su duka suka fashe da kuka mai tafe da zazzafan hawaye. Babu kalmar da take fitowa daga bakin Innono sai "La'ilaha illallahu Muhammadul Rasulullahi sallallahu alaihi wasalam, Bakura kana raye ashe?" Wannan dogayen salatai ne yasa Samira shigowa cikin dakin, don ta ganewa idanuwanta abinda ke faruwa.Ta iske Bakura tsaye ya kifa kai da bango yana wani kuka mai tsanani, har idanuwansa sun yi jawur. Ta riklqe shi a gigice tana tambayarsa lafiya. Haka Sajida da mahaifiyarta suka shiga wannan rudanin suka riqe Iya Azumi su na tambayarta "lafiya". Ta ce, "Labarin yana da tsawo, yana da ban mamaki." Da jin baka sai Umma Furera ta dauko waya ta danno lambar maigidanta ta na sharbar kuka. Ta ce "Malam, ka taho gidan Sajida yanzun nan akwai magana." A gigice ya ke tambayarta "Lafiya, guduwa ta yi?" Umma Furera ta ce "Ko daya babu abinda ya faru, illa Iya Azumi ce da Bakura suka shaida juna su na ta koke-koke. Na san lallai akwai wani 6oyayyen al'amari sun san juna. Ka san kuwa dole yau a fayyacewa Sajida komai." Malam ya fada cikin sauri "To gani nan zuwa. Hankalin Sajida ya tashi matuqa da jin bayanan Ummarta. Sai ta dora hannu a ka ta rusa kuka, ta ce, "Umma, ba dai tsintata ku ka yi ba, ba ke ce ki ka haife ni ba ne?" Umma Furera ta girgiza kai ta ce, "Ni na haife ki Sajida ba tsintarki na yi ba." Sajida ta koma gaban Iya Azumi ta durusa, ta ce "lya ki fada min gaskiya me ya faru da ni? lya Azumi ta runtse ido hawaye ya surnano sai ta nuna Bakura. Ta ce "Bakura ne ya fi kowa sanin ko ke wacece, amma ni ban sani ba." Sajida ta miqe da gudu ta nufi inda Bakura ke tsaye ta durqusa a gabansa cikin kuka. Ta ce "Bakura ni wace ce? Me yake faruwa ne?" Bakura ya matse hawaye yasa hannu ya tashi Sajida tsaye, Ya ce, "Je ki ki zauna bari Malam ya zo, bari su Zahra su dawo daga makaranta, sannan in zo in bayar da tarihin rayuwata. Zan sanar da ke ko ke wacece, amma kada ki damu kanki ki na da uwa, kina da uba ba 'yar tsuntuwa ba ce." Sajida ta sulale ta zauna zuciyarta na dukan uku-uku, qwaqwalwarta ta kasa shiryo mata abinda zai iya kasancewa. Fatan ta dai kar ace ba Furera da Malam ba ne suka haife ta ba, kada dai ace Bakura ne Babanta.. Haka Samira ta shiga wannan hali na mamaki da tambayoyi iri-iri. Umma Furera ma kukan take da alama ta san komai. Bakura ya fice, Samira ta bi shi da sauri zuwa qofar fita. Ta ce da shi "Ina za ka je ne?" Ya tsaya cak ya ce da ita "Masallaci zan je yanzu zan dawo." Samira ta tambaya "Me yake faruwa ne Malam?" Ya ce "Yau zan ba ku tarihin rayuwata kacokan. Yau zan bayyana muku ko ni wanene, kuma daga ina na fito, mene ne asalina? Yau za ki ji ko wacece Zuhuriyya kuma ya ya take a wajena. Yau za ki tabbatar da maganata da na ce Sajida ta yi kama da Zuhuriyya. Yau za ki tabbatar da dalilina da na dage na auri Sajida dan ada ban yarda na fada muku komai ba." Samira ta tsaya tana kallon Bakura jikinta a sanyaye. Ta fada cikin cikin siririyar murya mai tafe da rashin kuzari, "A dawo lafiya." Ya fice da sauri zuwa masallaci. Fitar Bakura ba Jimawa sai ga 'yan makaranta sun dawo, wato Zahra da qannenta suka yi sallama suka shigo. Da sauri Samira ta jawo su gefe ta ce da su "Ku yi sauri ku je ku cire kayan makarantarku, ku yi sallah, ku ci abinci akwai meeting a dakin Sajida in ji Abbanku." Cike da mamaki suke tambayarta. "Wanne irin mecting?" Ta ce, "Ku je ku yi abinda na fada mu ku kawai, ko mene ne ma za ku ji in an je can." Har Zahra ta shiga daki ta ajiye jakarta sai ta ji zuciyarta ta kasa kwanciya ta yi wuf ta fito tana neman mahaifiyarta ta leka ko'ina ba ta ganta ba, sai ta leqa dakin mahaifinta a can ta ganta. Samira na ganin Zahra ta tambaye ta. "Lafiya?" Zahra ta ce "Mama qararmu ta sake kaiwa wajen Abba?" Samira ta ce "A'a, wani boyayyen al'amari Allah Ya bayyana, wata kakar Sajida ce ta zo daga wani gari. Ashe Abbanku ya santa, don haka dole Sajida tana da dangantaka da Zuhuriyya." Mamaki ya rufe Zahra ta ce, "To bari in je in yi sallah in zo mu ji labarin." Bakura da Malam Yakubu ne suka shigo kai tsaye dakin Sajida suka wuce suka iske Umma Furera, Sajida da Iya Azumi kowanne zugum ya doka tagumi babu mai cewa komai. Su ka sami kujera suka zauna. Haka Samira da 'ya'yanta suka shigo a nutse suka sami waje suka zazzauna. Bayan an gaggaisa sai Bakura ya fara gabatarwa iya Azumi 'ya'yansa da matarsa Samira. Ta jawo Zahra jikinta ta rungume ta shafa kayukan, mazan tana mai shi musu albarka tana hawaye. Fargaba marar musaltuwa, haka dimbun tashin hankali ne ya cika zuciyar Sajida. Ba Sajida kadai ba kowa ya qagu ya ji labari. Bakura ya matse hawaye zazzafa daga cikin idanuwansa ya fara magana cikin wata marainiyar murya, mai nuna tsananin damuwa da alhini.Kai ka fi cancanta LABARIN BAKURA Ya ce "Sunana Muhammad, sunan kakana ne wanda ya haifi Babana aka saka min don haka ake kirana da Bakura wato Babban Baba. Ni haifaffen garin Mangono ne a cikin kasar Maiduguri. Sunan mahaifiyata wacce ta haife ni sunanta Fatukamba, Mahaifina kuwa Usman ana kiransa da Bawa. Na taso cikin matsananciyar rayuwa marar gata, kasancewar iyayena talakawa ne liqis, talaucin da har ma ya kai mu da yin bara, don haka iyayena almajirai ne masu bara da roqo. Dadin dadawa mahaifiyata tana da larurar tabin hankali , mahaifina kuma makaho ne, wanda bai taba ganin hasken rana ba. Dama a haka suka hadu suka yi aure, suka haife ni." Malam ya gyada kai ya ce "Allahu Akbar, Allah mai girma, tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai." Samiia da 'ya'yanta suka bude baki su na mamakin abinda Bakura yake zanowa. Saboda bai taba basu irin wannan tarihin ba. Haka Sajida ta tsura ido ta na kallonsa zuciyarta cike da zulumi. Iya Azumi (Innono) sai gyada kai take ta na cewa "Haka ne, duk an yi haka." Bakura ya matse hawaye ya ce "Saboda tsantsar talaucinmu har ba mu da takamaiman gidan zama, a bakin bola a cikin kasuwa muke yini ni da mahaifiyata, mahaifina kuma a bakin tasha yake zama yana bara. Idan dare ya yi sai mu je bakin shagon kasuwa ko bakin tasha mu shimfida kwalaye mu kwanta, saboda an kore mu daga gidan haya. Hayar gidan kara dakin bukka ma talauci ya hana iyayena su biya kudin haya. A lokacin duka-dukka shekarana uku kacal a duniya. Rigata daya ta wani yadi fari, saboda datti ya zama baqiqirin ko wando ba ni da shi, haka nake rayuwa. Bayan busasshiyar majina da hawaye a idanuwana sanoda ba a yi min wanke. Bakina kuwa dambar yake da busasshen koko, kamar yadda aka ba ni tarihi. Ina cikin wannan hali na wahala da talauci, Allah (S.W.A) ya Jeho min mai agaza min, wacce ta zame min haske a lokacin duhu a cikin rayuwata, wacce ta kula da ni har na girma, wacce ta wanke min dattin da ya addabe ni, wacce ta kwantar da ni a daki na daina barcin bakin titi, wacce ta sadaukar da rayuwarta a kan ta ga na rayu. Ta saka ni a makarantar allo da boko, har na zama yadda nake a yanzu." Sai Iya Azumi tą rushe da kuka kamar yadda Bakura ya fara kuka ya kasa ci gaba da magana. Kan ka ce kwabo idanuwan duk wanda yake wajen ya cika da hawaye, manyansu da yaransu. Zahra ta sharbe hawaye ta ce "Wacece wannan Abba?" Bakura ya ce "Wannan ita ce wacce nake baku labari, wato Zuhuriyya." Malam ya ce "Oho, ita ce Zuhuriyyar da duk kadarorinka sunanta ne ka saka?" Bakura ya gyada kai ya ce "Ita ce Zuhuriyya, yanzu za ku san kowace ce Zuhuriyya? Kuma me yasa nake ji da ita a rayuwata na kasa mantawa da ita." WACECE ZUHURIYA? Bakura ya gyada kai ya sharce hawaye da bayan hannunsa ya sunkuyar da kai qasa kamar mai tunani, ya dago ya dubi jama'ar da ke zaune a falon. Ya ce "Zuhuriya ita ce uwata, ita ce ubana, ita ce yayata, ita ce qawata. Ba ni da kowa a duniya sai Zuhuriya. Allah shi ne gatan bawanSa sannan Zuhuriyya ita ce gatana. Ban san kowa a rayuwata ba sai Zuhuriya, tun daga yarinta har izuwa girmana." Daga dukkan alamu ba su fahimci abin da Bakura yake nufi da wadannan kalamai da ya fassara Zuhuriya da su ba. Akwai alamar daure kai da zuzurfan tunani a zuciyoyinsu. Zahra ta ce "Abba, da farko ka ce kana da iyaye har kuna bara tare sannan ka ce Zuhuriya ce uwa ita ce uba? lyayenka sun rasu ne?" Bakura ya yi murmushin qarfin hali ya girgiza kai ya ce "Alhamdulillah, da kika yi min wannan tambayar, Mahaifana ba su rasu ba. Na kira Zūhuriya da wannan Sunan na uwata kuma Ubana, saboda wasu dalilai masu yawa. Kamar yadda na fada muku a cikin kasuwar garinmu Mangono muke yini a cikin kasuwar ma a bakin bola muke zaune. Tun daga safe har dare, wata rana mu kwana a nan idan kuma an koro mu daga cikin kasuwar mu fito waje mu kwana a waje ko mu je bakin tasha mu kwana in da mahaifina yake bara." Kuka ya kecewa Zahra don tausayi, yayin da idanuwan Samira ya cika taf da hawaye. Abubakar kuwa tuni ya shiga wani hali na daurewar kai, duban mahaifinsa yake ta yi, tamkar hoto, domin bai zaci mahaifinsa ya san wani abu mai su na talauci a rayuwarsa. Malam kuwa ya shiga rudani yana zuci-zuci ya ji qarashen labarin da yadda aka yi Bakura ya san lya Azumi. Sajida kuwa gaba daya qwaqwalwarta ta rikice, domin ta ji labarin Bakura bai shafe ta ba, to me yasa Umma Furera ta ambaci sunanta a waya'? Me yasa Iya Azumi ta ce ta tambayi Bakura shi ya fi kowa sanin ta? Ta ina Bakura ya santa har ya fi kowa saninta? Wannan al'amari ya razana zuciyar Sajida. Babu yadda za ta iya katse shi, dole ta ci gaba da sauraron Bakura, amma ta qagu ta ji qarshen labarin. Bakura ya ci gaba da cewa "Na hadu da Zuhuriyya a cikin kasuwar garinmu Mangono, a daidai inda nake kiransa da gidanmu wato bakin bola, ita kuma sun zo wani shago siyayya, shagon yana daf da bolarmu. A lokacin ina da shekaru uku, Zuhuriya na da shekaru goma sha hudu a duniya. Amma a lokacin an dade da yi mata aure har ta haifi da kafin a yi suna ya rasu. Sun zo Mangono ne ita da mahaifiyarta ganin danginsu. Domin mahaifin Ummata Zuhuriya Alh Umar dan asalin garin Mangono ne, kuma ma dan sarauta ne a lokacin ya rasu sai Yayansa shine hakimin garinmu haka aka ba ni tarihi." Samira ta buga tagumi tana duban Bakura, duba cike da tausayi tana mamakin duk wannan shaquwar da suka yi amma bai taba zama ya faiyace mata irin wannan tarihin rayuwarsa ba sai yau da yake fada take ji. Ta tambaye shi "daga nan ya aka yi?" Bakura ya yi shiru, saboda tsananin zafin da zuciyarsa ke yi. can ya ci gaba da cewa."Ina qarami sosai, amma mahaifñyata tana dukana, dukan da ko wani qato ake yi wa sai ya kwanta jinya, amma ba laifinta ba ne kamar yadda na fada muku a baya tana da tabin hankali. A daidai lokacin da Ummata Zuhuriya da mahaifiyarta da kuma qanwar mahaifin Zuhuriya suke cikin shago su na siyayya ni kuma na tafi yawo cikin kasuwa. Mahaifiyata ta kamo ni ta kawo ni bakin bola ta jibge ni yayin da ta samo bulala ta yi ta duka kamar ta sami casar gero. Bulala ta kakkarye tasa hannu ta daka har ta gaji sannan ta saka haqoranta ta cije ni bakina ya fashe, goshina ya yi loti, yayin da bayana da duk ilahirin jikina ya daddare ya yi shatin duka. Tana dukana tana fada tana cewa, "Indara na'aduwa kozina famdime." Malam ya ce "Me take cewa kenan?" Zahra ce ta fassara musu domin ta fi sauran qannenta jin yaren. Ta ce "Abin da take cewa shine ina kake da shi, inda ya fi nan bakin bola?" Iya Azumi ta ce "Haka aka yi kuwa, hankalinmu ya tashi, musamman Zuhuriya har kuka take saboda tausayin yaron nan, abin ka da mai son yara domin Zuhuriya Allah Ya yi mata son yara." Gaba daya suka juyo su na kallon Iya Azumi, duba na mamaki. Sajida ta tambaya cike da mamaki "lya Azumi, ya aka yi ki ka sani kina wajen ne?" Iya Azumi ta gyada kai ta ce "Ina wajen, ai muna tare da Zuhuriya a cikin kantin." Bakura ya ce "lya Azumi ita ce mahaifiyar Zuhuriya, wacce ta haife ta." Kamar an tsikara musu allura haka kowa ya zabura ya waiga yana duban Iya Azumi. Daidai lokacin kowa ya gyara zaman don jin labari, don labari ma yanzu aka fara. Sajida ta ce a ranta "Kenan idan Iya Azumi kaka ce a wajena, ashe ina da dangantaka da Zuhuriya. Ashe Zuhuriya 'yar uwar Umma Furera ce kenan?" Iya Azumi ta ci gaba da cewa "Zuhuriya ta tambayi mai shagon da muke siyayya a shagonsa. me yasa take dukan dan qaramin yaron nan da bai wuce shan nono ba?" Mai shagon ya yi murmushi ya ce, "Ai tana da tabin hankali. Dukan yau ma kadan ne ai, wata ran tana yi masa wanda ya fi haka." Zuhuriya ta fashe da kuka tana. Ta ce masa "Me yasa bakwa kwatarsa idan tana dukansa?" Ya ce, "Ai babu mai iya zuwa kusa da ita idan tana dukansa, zafin rai ne da ita idan ka je sai ta hada da kai." Zuhuriya ta sake tambayarsa "Ina Baban yaron, ai da an kwace shi daga hannunta, don kar ta kashe shi." Mai kanti ya ba ta amsa, "Baban yaron makaho ne, shi ma almajiri ne, bara yake." Ta ce" ko a dangi ba za'a sami mai daukarsa ba?" Ya ce, "Ina ji babu, amma wasu sun so su dauka ta hana su. Ai ba za ku tausayawa yaron nan ba sai idan uban ya kai shi wajen wanzami ya yi masa aski kwalkwal. Yini take tana dukan kan yaron nan, wai sai ta ci ladan aski. Duk juyin da ta yi sai ka ji raff-raff ta dalla masa duka a kai, sai ka ji ya dau kuka. Yini suke 'ana abu daya har sai gashi ya fito akan sannan yake hutawa." Bakura ya kwashe da dariya, sannan kuma ya fashe da kuka ya girgiza kai alamar tausayawa kansa da kansa. Iya Azumi ta ci gaba da cewa "Tun a lokacin Zuhuriya ta je wajen yaron ta goge masa hawaye ta ba shi alewa, ya yi shiru ya daina kuka. Ta bawa mahaifiyarsa sadaka, sannan ta dawo shagon da muke zaune. Ta dube ni ta ce da ni, "Innono (sunan da suke kirana kenan) ina son yaron nan, ina so in dauke shi in riqe shi kamar dana tun da yaron da na haifa ya mutu." Ni kuma na zazzage ta na ce kada ta sake cewa za ta dauki wani yaro don ta rike. Dalilina kuwa shi ne daga nesa muka zo baqunta tafiya za mu yi, idan muka tafi kuwa a shekara biyar ba za mu dawo ba don jifa-jifa muke zuwa, saboda nisa ga tsadar kudin mota bamu da hali da kyar muka hada wannan kudin motar da muka zo da dan abin tsaraba. Gashi mahaifin Zuhuriya ya dade da rasuwa na yi wani auren a Cinkilawa can qaramar hukumar Warawa dake kusa da lahadin makoli a hanyar Wudil cikin jihar Kano. Da Zuhuriya na je garin a matsayin agola, saboda ita kadai ce 'yata a duniya na wi yarda dangin mahaifinta su karbe ta a Mangono. Ita ma Allah cikin ikonsa ta sami miji a Cinkilawar na aurar da ita tana da shekaru goma sha daya a duniya. Ta samu ciki ta haihu kafin a yi suna yaron ya rasu. Bayan ta yi arba'in ne na ce to ta shirya in kawo ta Mangono ta gaishe da dangin Babanta saboda sun dade ba su hadu ba ko bikinta ma ban samu na fada musu ba, mijina ne ya wakilce su. Dan haka sai naga ta ina? Ta ya ya za mu dauki wata dawainiyar bayan muma muna ta kanmu a can, don haka na hana ta. Ta yi ta kuka tana yi min magiya har muka isa gida. Kowa ya fara tambaya me aka yi wa Yagana take kuka, domin su a can dangin uban Yagana suke kiranta. Ni da ita babu wanda ya fada musu abinda ya faru. Kamar yadda Bakura ya shaida muku a baya yayan Babanta shi ne hakimin Mangono, don haka hakimi da kansa ya kira ta, don yana jiyo hayaniyar mata a tsakar gida su na yi da bakin su su na tambayarta dalilin kukan da take. Ya tambaye ta sannan ta fada masa abun da take so, da yake qaramin gari ne kowa ya san kowa sai ya yi dariya. Ya ce "Wannan ba wata matsala b8 ce, in har za ki iya riqe shi a dalilina za a baki shi. Daman ya kamata a ceto rayuwar yaron nan yana shan wuya a wajen mahaifiyarsa. Sai dai sai kin daure, za ki dinga kawo shi lokaci-lokaci ana ganinsa yana ganin iyayensa." Hakimi ya shaidawa Zuhuriya ai su na da alaqa ta jini da mahaifiyar Bakura, don haka dangimsu sun san komai. Washe gari ba tare da kowa ya sani ba Zuhuriya ta dauki abincinta na safe koko da qosai ta tafi bakin kasuwa ta kaiwa Bakura da mahaifiyarsa suka ci. Kan ka ce kwabo hira ta gauraye tsakanin mahaifiyar Bakura da Zuhuriya. Bakura kuwa tuni ya haye cinyar Zuhuriya kamar ya sami wata uwar. Da rana ma ta dibi abinci ta kai musu, bata tashi dawowa ba sai daf da magariba, sai ga ta goye da Bakura a bayanta, mahaifiyarsa na biye da ita ta ce mata ta zo Hakimi yana kiranta. Cikin dabara da wayo hakimi yake yi wa Fatukamba bayanin cewa Zuhuriya za ta dauki Bakura ta dinga goya shi, tana bashi abinci, za ta dinka masa Sabon kaya ya yi kyau, ita ma za a dinko mata sabuwar atamfa. Abin ka da marar hankali. sai ta hau murna tana tsalle, aka cika mata kwanon ta da abinci ta tafi ta bar shi. Hakimi ya sa aka kira Baban Bakura aka sanar da shi, shima ya yi amanna ya yi murna da wannan taimako da aka yi masa. Daman iyayen Fatukamba sun rasu, yayanta ne guda daya a garin mai suna Bukar Shima hakimi ya kira shi ya shaida masa cewa Zuhuriya 'yarsa ce a Kano ba ta da d'a tana so ta riqe Bakura za su dinga zuwa akai-akai yana ganinsu. Bai yi musa ba, saboda shi ma baya taimakonsu korarta ma yake ita da danta daga gidansa, don haka ya yi farin ciki da jin haka. Kafin mu bar Mangono Bakura ya canja, Zuhuriya tana yi masa wanka tsaf-tsaf, ta samar masa kwancen riguna da wanduna a wajen matan hakimi. Abinci kuwa idan ta dinga tura masa bai san ya qoshi ba sai an hana ta. Goyo kuwa riqi-riqi ko sallah a bayanta yake yi. Farin ciki da shaquwarsu kuwa cikin 'yan kwanaki sai ka rantse sun shekara da sabawa ko ka zata ita ta haife shi. Ni kuwa haushinta nake ji don babu yadda zan yi in hana ta, so nake mu je gida in mata duka. Abinda babba ya hango yaro ba zai hango ba ko da kuwa ya hau bishiyar rimi. Kunyar sirikina nake ji Hakimi da na hana ta daukar yaron nan, idan na hana ta gari gaba daya za'a ce baqin hali gare ni, daman na yi qaurin suna a wajen dangin miji su na cewa ba ni da kirki, don a garin muka yi zaman zauna har mijina ya mutu mahaifin Zuhuriya. Ranar da za mu tafi, jama'a suka raka mu har tasha su na ta shi albarka su na yaba yadda Bakura ya canja cikin dan qanqanin lokaci. Jama'ar gari kacokan sun yi amanna da daukar Bakura. Ni kuwa wacece da zan ce ban yarda ba? Amma tun daga mota na fara dunguri, ina rankwashi, ina zagin Zuhuriya. Bakura ba zan boye maka ba idan ma na qi fada ai ka san komai, tun da tun baka fahimta har ka girma ka fahimci bana son zamanka da mu. Bakura ka yafe min, domin na zalunce ka, na zalunci kaina." Iya Azumi ta rushe da kuka Hawaye ya surnano daga idanuwan Bakura Ya ce "Ka da ki yi küka Innono, kada ki damu na yafewa wasu ma a dalilin Zuhuriya balle ke da kika haife ta da kanki." Babu wanda idonsa bai cika da hawaye a wajen ba, don tausayin Bakura. Hatta Sajidar da take iqirarin ta tsani Bakura kamar yadda ta tsani mutuwarta dan yaron nan Bakura ya bata tausayi har sai da hawaye ya surnano daga idanuwanta. Bakura ya ci gaba da cewa "Mu ka isa Cinkilawa, garin da Zuhuriya da mahaifiyarta suke aure a nan ne na fara bude ido, na fara sanin menene rayuwa. Sunan mijin Innono malam Audu ba shi da wata mata sai Innono. Sunan mijin Ummata Zuhuriya kuma Hashimu, shi ma yaro ne ita ce matarsa ta farko. A da an ce su na zamansu lafiya, amma tunda ya kyalla ido ya ga Zuhuriya da yaro ta yi masa bayani sai ya bata rai ya nuna baya so, ba zai riqe ni ba. Ita kuma ta ce duk wanda baya sona ba ta sonsa, dan haka sai dai ya sake ta. Daga nan dai zama ya rikice kullum ba dadi, domin duk wanda ya taba ni sai inda qarfinta ya qare da yake ita ma in an taba ta ba kyalewa take yi ba, akwai ta da tsiwa, yanzu nan idan ta jiyo kukana zata figo gyale ta fito a yi fada da wanda ya dake ni ko da iyayen yaran. Daga qarshe dai zama ya wi dadi, Hashimu ya saki Zuhuriya a kaina. Muka kinkimo kayanmu a amalanke da Magaruba muka taho gidan Innono. Tana ganinmu ta ce "Bakura ya kashe miki aure ko?" Ta kwana tana dukanmu, ni da Zuhuriya muka takure a jikin katanga kamar wasu qadangaru ta hana mu abincin dare har na yi barci a haka, amma sai da Zuhuriya ta tashi da tsakar dare ta gutsirar min tuwon dumame ta tashe ni ta ba ni a baki har na qoshi." Samira ta yi ajiyar zuciya ta ce "Allah sarki, Allah Ya saka mata da alkhairi." Bakura ya ce" Amin, na gode Samira." Ya ci gaba da cewa "Haka muka yi zaman zawarcin nan da wahala, saboda tsangwama. Abin ka da qauye da zarar an ji bazawara tun bata gama iddah ba zawarawa sai su fara kawo hari balle Zuhuriyar da duk surquqin qauyukan nan tafi kowacce mace kyau. Idan bazawari ya zo sai ta aika ni in leqa in gani da jaki ya zo ko keke, idan jaki ne ko keke sai ta kama hannuna mu fita da gudu ta ce ya yi ta dana ni akan jakinsa ko keke, ina jin dadi. Idan kuwa ba shi da jaki ko keke, daman ba za ta fito ba. Wannan al'amari namu yana batawa Innono rai, wanda take kiransa rashin hankali. Don haka kullum fada take da kumfar baki a kan Zuhuriya ta fitar da miji ta yi aure. Ni kuma ta mayar da ni gidanmu kada in sake kashe mata aure. Ko kadan Zuhuriya ba ta yarda da zancen mahaifiyarta ba, ta nuna akan ta mayar da ni gara ta goye ni mu tafi mu bata a rasa mu. Duk wanda ya fito aurenta sai ta sanar masa cewa tana da d'a da shi za ta je, idan ya ga bai yarda ba kada ya sake dawowa. Da yawa idan sun tafi basa dawowa, amma Mutari wanzami ya yarda ya amince zai aure ta tare da ni, sunan qauyensu B'alle bantai, qauye na kusa da Cinkilawa daga kudu. Ya kawo kayan aurensa atamfa uku, sai sadaki a kowacce atamfa sai da aka dinka min ma'ana anko muka yi ni da amarya. Aka daura aure muka kwashi kayanmu kacokan muka koma qauyen Balle bantai muka bar Cinkilawa. Sabuwar rayuwa a Balle bantai, ga uwar miji ga kishiya, gani kuma agola dan haka ba zaman lafiya a gidan. Zuhuriya ba ta da aiki sai goyona ko'ina rabe- rabe abun ka da marar jiki har rinjayarta nake kamar Za mu fadi, ga shi duk atamfar da za ta saka anki muke nima irinta take sa tela ya dinka min riga da wando. Na Zama dan shagwa6a idan na ga dama sai in qi taka qasa in ce sai dai ta goya ni, abinci in qi ci sai dai ta bani a baki. Wannan al'amari nawa yana bawa mutanen gidan nan haushi. Uwar mijin har wani suna ta saka min wai "tarar ni wuce ni. Wato na zo na sami 'yan gida har na fi su zaqewa. Mutari wanzn ya na sona, saboda yana son Zuhuriya, dan haka Zuhuriya ita ma take sonsa saboda yana sona. Amma kishiyarta Rahi da mahaifiyarsa Ingade ba sa son ganina a gidan. Don haka fadan safe daban, na rana daban. Idan ranar girkin Zuhuriya ne abinci tun yana kan wuta ake fara ba ni tabi, idan ranar girkin Rahi ya zagayo ba ni da kashi sai dai Zuhuriya ta ba ni nata in ci, idan na qoshi ta ci sauran idan na cinye dukka ta kwana da yunwa. A haka a daddafe muka yi wata takwas a Balle bantai, sannan uwar miji ta tubure ta tilasta dole har sai da danta ya sake mu. Dolensa ya sake ta yana son mu a nan ma Zuhuriya ba ta samu ciki ba. Ba na mantawa da hantsi rigimar ta taso don haka da muka hada kwanukanmu na tsakar gida muka datse a daki, sai yan kayanmu seti biyu muka kullo a dankwali muka taho. Da qafa ake tafīya a lokacin, duk nisan tafiya babu mota. Don haka muka kamo hanya zuwa Cinkilawa tana riqe da hannuna idan na cije na qi tafiya ta goya ni, idan ta gaji da goyon ta dauke ni, haka muka yi ta yi. Na dube ta na ce "Juhuliya, lokacin ba na iya cewa Zuhuriya ta ce na'am Bakura. Na ce, "Tsoro nake.ji kada Innono ta dake mu." Sai ta fashe da kuka, don tausayina ba ta damu da dukan da za a yi.mata ba, ni take tausayawa ta san akwai matsala, idan ta je gida ta ce an sake ta, kuma su ji labari a kaina ne. Innono za ta tubure ta ce sai ta mayar da ni garinmu ni nake hana ta zaman aure. Dan haka muka yanke shawarar kada mu koma gida mu yi zaman mu a cikin dawa qarqashin wata bishiya. Muka yini a dawa muna tsalle-tsalle, ta dora ni akan wuyanta in tsinko mana dinya, aduwa, dorawa, tsamiya da dai sauransu. Idan na kasa tsinkowa ita sai ta hau bishiyar ta tsinko mana. Haka muka, yini muna ta walagigi har Magruba. Akwai gidan gonar wani tsoho a kusa da inda muke. Ashe tun da safe yake lura damu ya ga har rana ta fadi ba mu da niyar tafiya, don haka ya zo da bulala ya ritsa mu. A tunaninsa Zuhuriya yayata ce aka aike mu da qulin kaya muka zo muka zauna muna wasa, dan haka yake yi mana fada mu hanzarta tafiya inda aka aike mu. Simi-simi ya saka mu a gaba har kusa da garinmu Cinkilawa ya raqe da bulala. Kan ka ce kwabo an hango mu, yara suka hau tsalle su na fadin "Ga Zuhuriya, ga Bakura." Labari ya iske kunnen Innono, tana jin haka ta san ba zuwan lafiya ba ne da magrubar nan, dan haka ta girka kujerarta a tsakar gida ta tanadi bulalarta ta na jiranmu. Mu ka qi shiga cikin gidan muna jikin katanga a labe. Can Zuhuriya ta dora ni a wuya na leka cikin gidan daidai lokacin muka yi ido hudu da ita. Ta ce "Waye wannan?" Na ce "Bakura ne, Inonono an sake mu." Su Malam suka kwashe da dariya, har da Bakura. Da alama labarin nan ya na ratsa zuciyar duk wani mai sauraro. Akwai hikima a wajen shi kansa mai bayar da Labarin. Babu abin da zuciyar Zahra ke aiyanawa sai sha'awa da marmarin ta je wadannan qauyukan ta dandana yadda suke rayuwa. Ji take dama ita marubuciya ce ta rubuta' labarin nan har take tunanin sakawa littafin su na LABARIN BAKURA. Bakura ya katse mata tunani ya ci gaba da cewa "Takaici ya qara rufe Innono. Ta ce "An sake ku ko? Ni kuma zan daure ku. Ka sake kashe mata auren ko? Za ku shigo ku same ni." Mu na bin katanga muna rabewa, ga yunwa da kishirwa. Can na sulale na zauna na fara gyangyadi. Da sauri Zuhuriya ta tashe ni ta kama hannuna muna sauri muka je gidan wata mai abincin siyarwa. Ta kwance gefen zaninta ta kwanto wasu 'yan kudadenta sulalla fa kwabbuna ta siya min tuwo malmala guda na cinye, ta bani ruwa na sha, ta kai ni bandaki na yi fitsari sai ta saba ni a baya na yi barci. Ban tashi farkawa ba sai da tsakar dare da na ji tururruwa ta baibaye ni tana cizona. Ashe zauren qofar gidan Innono ta shige ta labe bayan Malam Audu ya shigo gida ya rufe ba tare da ya san muna labe ba anan ta yi mana shimfida da zani muka kwanta, ashe da ramin tururuwa. Sunanta na kwallawa kira cikin kuka na ce wani abu yana cizo na ga tsananin duhu. Zuhuriya ta daka tsalle ta tashi ta ciccibe ni ta kade min jikina muka koma tsakar gida muka qarasa kwana. Da duku-duku gari bai waye ba Innono ta tsara mu a lungu. Zuhuriya ba ta bari dukan ya same ni sosai ba, karewa take yi tana fadin "Bakura yaro ne ni ki dake ni bai san komai ba." Sai Bakura ya surnano da hawaye zazzafa ya ce "Zuhuriya na sona a rayuwarta, haka nima nake matuqar qaunarta a rayuwata. Muna cikin wannan hali na tsangwama ga aiki, kamar bayi sai Zuhuriya ta ga gara ta sake aure ko gidan mijin zai fiye mana kwanciyar hankali. Ta auri wani tsohon malami don a lokacin ana ta surutun wai ta auri tsohon mutum tana yarinyarta son kowa qin wanda ya rasa, Malam yana da makarantar allo duk karkarar nan babu makaranta mai yawan almajiransa. Sunansa Malam Idi mahaddacin Kur'ani ne sosai matarsa daya ta rasu a shekarar da zai auri Zuhuriya. 'Ya'yansu kuwa sun yi aure har suma sun hayayyafa, don haka muka ji dadin zaman gidan ba mace, ba 'ya'ya. Alhamdulillahi, a wajen malam idi muka fara samun ilimin addini daga ni har Zuhuriya. Don idan aka fara karatu tun da Asuba har sai rana ta fito. Haka da yamma ma har sai Magaruba. Bayan sallar Isha'i kuma har kusan sha biyun dare ana karatu sannan mu kwanta. Ina cikin almajirai ina wadaqata ga abinci a gidan ba yankewa. Duk da dai dawa ce da masara sai gero kullum. Shckarar mu kusan uku a gidan malam ya rasu. kasancewar ba ta haihu da shi ba, bata da gadon komai dole muka tarkato kayanmu bayan ta gama takaba muka dawo Cinkilawa gidan Innono. Rayuwa ta dawo irin ta da, dole Zuhuriya ta fara sana'a tana danwake da safe mu dauka aka mu kai makarantar boko da ke Jalawa da qafa muke tafiya tunda ga Cinkilawa kullum. Idan an yi break 'yan makaranta su yi ta siya. Ni ba dan makaranta ba ne, amma ina jiyo abin da ake koyarwa caraf sai na riqe ABCD har zuwa Z. Akwai wani Malami mai suna Isa, dan asalin garin Jalawa ne sai ya nuna yana son Zuhuriya kullum sai ya sayi dan wakenta. Ya ba ta shawara mai zai hana ta saka ni a aji daya, nima in yi karatun maimakon zaman gindin bishiya muna jiran yara su fito, ai gara ni in dinga shiga aji. Sai ta jira a tashi mu tafi gida. Zuhuriya ta qi amincewa amma ni na ce ina so har da kukana. Malam Isa ya ce shi zai karbar min uniform lokacin komai kyauta ake bayarwa har littattafai. Sai ta yarda ta saka ni a makarantar tunda ta ga ina so. Har na zo na fi duk 'yan ajin qoqari. ldan mun fito break da gudu zan taho wajenta ta zuba min danwake har yara suke kirana dan gidan mai dan wake.Kai ka fi cancanta Idan an tashi da rana sai mu doro daron d'an wakenmu aka mu koma garinmu Cinkilawa. Innono ta huta ciyar da mu yanzu, muna da sana'armu don haka rigimar ta dan lafa, ba ma yini a gidan ma balle a ce mun yi laifi. Abu kamar wasa Malam Isa ya ce yana so ya auri Zuhuriya su zauna a Jalawa, saboda mu huta zirga- Zirga kullum, gidansa ba nisa da makaranta ya yarda zai riqe ni, zai kuma bar ta ta dinga zuwa tana sayar da danwakenta. Ta amince suka yi aure, muka dawo Jalawa da zama. Lallai mun sami ci gaba, saboda gidan Malam isa na siminti ne, ga shi da babur dinsa na hawa. Yana da mata daya mai suna Sahura da 'ya'ya biyar. Ko ban fada muku ba, kun san za a yi dauki ba dadi a gidan nan. Inda aka sami saukin rigimar Sahura na tsoron Zuhuriya, dan sun goga ta ji karon bai yi mata da dadi ba. Zuhuriya ta iya tsiwa bakinta caicai baya mutuwa, damara take ci a yi ta fada ga ta ba ta da kiba, amma ko a dambe ba a kayar da ita. Ta kwatar min 'yancina, duk da ni ba dan gida ba ne amma ba ta yarda wani ya takura min ba. Dole Sahura da 'ya'yanta suka daga min qafa na miqe qafata na yi dayday a gidan kamar gidan ubana. Karatu nake tukuru ba na fashi har Allah yasa na Kai primary 4. Kokari da cancanta aka saka ni a cikin masu daukar jarawar tafiya sakandire na zana. Allah CIkin ikonsa na ci, na sami tafīya makarantar 'yan maza ta Wudil. Malam Isa ya taimaka min wajen karbo min akwati, katifa da bokiti daga qaramar hukuma, amma sauran siyayyar Zuhuriya ce ta quge 'yan kudadenta ta siya min duk abin da zan buqata. Duk da a lokacin ba a matsalar abinci a makarantu. Na je makarantar kwana na dace da abokai na gari na ci sa'a shugaban makarantarmu (pricipal) mai suna Malam Abbas Shagari yana sona, saboda qokarina. Aka yi jarrabawa na zo na daya, aka ba mu hutu, local government dinmu ta kai mota aka kwaso mu. Ina isowa gidan Malam isa na iske shi a qofar gidansa yana zaune a kan tabarma. Da murnata na qaraso wajensa na duqa na gaishe shi na zaro report card dina na miqa masa cike da murna. Ya yi dususu kamar bai sanni ba, ya duba galala ya miqo min abu na. Sai mamaki ya rufe ni saboda a zatona zai yi farin ciki da ganin sakamakona, shi yake koda ni yana yabon qoqarina har hakan tasa nake qara dagewa ina karatu sosai. Saboda shi ne ma yasa na dage ba dare, ba rana ina ta karatu har sai da na fi kowa cin jarrabawa a ajinmu. Na tashi jikina a sanyaye na dauki buhun kayana na shiga gida farin ciki ya rufe ni ina murna saboda zan ga Zuhuriya na sha wahalar rashin ganinta da kyar na daina kukan rashinta a makaranta, ba mu taba rabuwa daidai da kwana daya tun daga sanda muka hadu. Ina shiga na iske dakinta a bude na fara washe baki na san tana ganina za ta rugo da gudu ta rungume ni. Na yi sallama na bude labule na tura kai zan shiga sai na ji an hankado ni waje, na yi tagal-tagal zan fadi a baya. Sahura na gani ta fito daga dakin ta ce da ni "Kai mahaukacin ina ne da za ka fado min har cikin daki?" Wannan maganr ta ba ni mamaki, saboda dakin Zuhuriya nè. Yaranta suka yi caa suka fito daga dakinsu suka zagaye ni. Wasu na yi min gwalo, wasu na yi min daquwa su na tsokana ta. Abin da suke fada shi ne an saki Babata ta koma Cinkilawa. Gabana ya yanke ya fadi sai na fara kuka. Na ce musu to bari in dauko sauran kayana a dakin yara. Nan ma suka hana ni shiga suka ce ta kwashe kayanmu kacokan babu ko tsinke nawa, dan haka in tafi in ba su waje. Na dora buhuna aka, ga tsananin yunwa da kishirwa ga doguwar tafiyar qafa daga Jalawa zuwa Cinkilawa, na fito jikina a sanyaye. Duba daya Malam Isa ya yi min ya dauke kai, na dube shi duba na takaici da tsantsar tsana tunda ya kori Zuhuriya sai na ji ba na sonsa, na wuce na kama hanyar Cinkilawa. Ban isa garin ba sai daf da Magruba. Ina isa tsakar gida na wurgar da buhun da ke kaina na fadi yararaf a qasa. Innono ce a bakin murhu tana tuqa tuwo ta dau salati ta kwallawa Zuhuriya kira ta taho da gudu daga daki, don ta ga abinda ya gigita Innono har take kwalla mata wannan kira haka. Ta na ganina a kwance ta rafsa ihu ta riqo ni ta tashe ni zaune tana tambayata lafiya. Na ce yunwa da kishirwa, a guje ta shiga daki ta dauko min langa a cike da alala na fara ci, kamar ban taba cin abinci ba haka nake turawa a cikina,ta ba ni ruwa a qwarya na sha. Haushi da takaici ya rufe Innono ta ce Bakura, ka zayyano min da bakinka aure nawa ka kashewa Zuhuriya?" Na zabura na ce "Innono wannan karon bana nan aka yi sakin." Ta ce "Ai a dalilinka aka yi rigimar har aka sake ta." Na shiga rudani hade da fargaba. Zuhuriya na zaune ba ta ce komai ba sai hawaye take sharaf-sharaf. lnnono ta zaiyano min duk abinda ya faru daga qarshe ta ce to an yi na qarshe tunda na girma dole in koma garinmu idan ma zan yi karatun anan in je makaranta ana yin hutu in hau motar garinmu Mangono. Hankalina ya tashi, domin ba na son a ambaci sunan garinmu ballantana a kai ni." Bakura ya zubo da hawayen da ya addabi idonsa. Malam ya girgiza kai ya ce "Lallai ka dandana maraici da wahala a rayuwarka." Cikin kuka Zahra ta ce "Abba, menene dalilin rabuwar lya Zuhuriya da Malam Isah?" Bakura ya ci gaba da magana cikin marainiyar murya "Wai ashe Sahura ta kullace ni, haushi take ji danta-bai ci jarrabawar tafiya sakandire ba, ni kuma na ci na tafi. Ina tafiya ta je ta hada mana munafunci." Abubakar ya tambaya, "Abba, wanne irin munafunci?" Bakura ya yi murmushin qarfin hali ya ce "Zuwa wajen mahaifin Malam Isa ta yi ta dinga kuka tana cewa wai bai kamata a ce ina kwana a cikin gidan nan ba, tare da yaranta dakinmu daya akwai mata, tunda na je sakandire yanzu na girma dole a mayar da ni gidanmu. Daman dakunan gidan uku ne. Daya na Sahura, daya na Zuhuriya, daya namu ni da 'ya'yanta. Shi mai gidan ba shi da daki, dakunan matan yake bi. Iyayyen Malam Isah suka kira shi, suka shaida masa cewar dole ya fadawa Zuhuriya ta fitar da yaron nan daga gidan. Dole ya sami Zuhuriya ya sanar mata halin da ake ciki, Da ya zo ya fada mata buqatar iyayensa sai ta ce muddin tana raye to tana tare da danta ta yarda za ta dauke ni daga ckin ya'yan Sahura, sai in dawo dakinta da kwana, In ya so ta hakura da mijin ya dinga kwana a dakin Sahura kullum. Malam Isah ya hau fada ya ce bai yarda ba sai na bar gidan. Ita kuma ta ce sai dai mu bar gidan tare, sai ya sake ta tun kafin in dawo. To wannan shi ne silar rabuwarsu. Na fara wayo, na fara sanin zafin magana, dan haka na shiga damuwa. Na fara tunanin yadda zan yi da rayuwata, don in daina jawowa Zuhuriya mutuwar aure, don an fara qirga mata yawan mazan da ta aura an mata shaidar ba ta zaman aure kowa ya san ni ne sila. A lokacin alalar gwangwani Zuhuriya take siyarwa da rana har gida ake shigowa ana siya. Ni da ita muke wanke wake in kai markade in kawo ta hada mu zuzzuba a gwangwanaye mu dora akan wuta. Idan ta dahu ni ne mai zubawa ina miqawa kofar gida. Mu ka tara kudi sosai a cikin hutun nan. Zuhuriya ta lalashe ni ta lallaba ni har sai da na yarda zan bi ta Mangono wajen danginmu. Domin ba na son zuwa gani nake idan ta kai ni ba za ta dawo da ni ba, kamar yadda Innono take fada kułum tun ba na fahimta har na gane cewar nan ba gidanmu ba ne, iyayena na can kuma can din ukuba ne tunda sai na yi laifi ake cewa a kai ni.." Umma Furera ta sharce hawaye ta ce "Ka san ba ita ta haife ka ba kenan?" Bakura ya nisa ya ce Eh, na sani dan na ji ana fada, amma ban damu ba, na sa a raina Zuhuriyą, ce uwata ita ce ubana don ita kadai na budi ido na gani babu mai sona mai wahala da ni sai ita. Dan a lokacin da aka fara kai ni makaranta dakyar na yarda Malam Isa ya saka min Bakura Usman Mangono dan ni tuburewa na yi na ce Bakura Zuhuriya sunana. Saboda duk sanda na yi laifi Innono tana cewa a mayar da ni Mangono na tabbatar babu alkhairi a tattare da Mangono tunda sai na yi laifi za a kai ni, don haka na ji na tsani garin duk da ban san shi ba. Zuhuriya kadai na şani a rayuwata, ita ce mai share min hawayena, idan ina cikin damuwa da ita nake so in kasance har karshen rayuwata." Sai yanzu Umar ya yi magana dan tunda ya zauna- yake kallon mahaifinsa yana sauraron wannan abun al'ajabi. Ya ce "Abba, ka yarda kun je Mangono a lokacin'?" Bakura ya ce "Mun je har da Innono ma tare muka je da ita. A wannan lokacin ne na fara ganin mahaitiyata, na ga mahaifina, dan a lokacin da na baro su ina qarami sosai ba zan iya tuno su ba. Har na ga qannena guda biyu da aka sake haifa. Babban namiji ne su na kiransa Babagana, qaramar da aka yaye kuma su na kiranta Yaana." Abubakar ya tambaya cike da mamaki "Uncle Babagana da Aunty Yaana kake nufi?" Bakura ya gyada kai ya ce "Kwarai kuwa qannena ne uwa daya, uba daya. Kamar yadda na tashi cikin wahala suma haka suka tashi cikin wahala da garari." Zahra ta ce "Su ba a sami mai karbar su ba?". Bakura ya yi murmushi ya ce "Babu wanda ya karbe su a wajen mahaifiyarmu suka girma sai dana girma ne na je na tallafa musu na sa su a makaranta nake yi musu aiken kudi a koda yaushe." Usman dan auta ya ce "Abba, mamarka ta gane ka kuwa, ba ta manta ka ba tunda ka girma?" Gaba daya aka kwashe da dariya. Bakura ya co, "Very good Usman, ashe kana fahimtar labarina Mamana ba ta manta ni ba, tana ganina ta shaida ni ta yi ta murna. Ashe bayan tafiyata ta yi ta zuwa gidan hakimi neman danta, kuka da ihu kullum. Aka yi a lallabata da kyar aka samu sauqin abun aka ce za aje dauko ni. Amma da ta sami wani cikin ta haifi kanina Babagana sai ta daina damuwa da ni. Innono ta san ma Zuhuriya ba za ta bar ni acan ba, nima ba zan yarda in zauna ba, dan haka ma ba ta fara cewa a bar ni ba, muka dingumo muka dawo Cinkilawa." Samira ta ce "A iya sanina Mama Fatukamba bata jin yaren Hausa sai Barbarci. Da wanne yare ku ke magana kai da sauran 'yan uwanka saboda na ga a qasar Hausa ka girma?" Bakura ya yi murmushi ya ce "Hausa ai a Cinkilawa na koya, kin manta ba na jin Hausa sai Barbarci sanda Zuhuriya ta dauko ni, kun manta Zuhuriya babarbariya ce ta wajen uwa da uba. Mahaifinta dan Mangono ne, mahaifiyarta kuma 'yar asalin Gashuwa ce aure ya kawo ta qasar Kano. Dan haka Barbarci muke a gidan, a wajen yara na koyi Hausa. Mun dawo Cinkilawa ba dadewa hutuna ya qare, Zuhuriya ta harhada ta ba ni duk abun da nake bukata, motar qaramar hukumarmu ta kwashe mu zuwa makaranta. Duk garin babu mai taimaka min da sisinsa sai Zuhuriya, babu mai agaza mata ita kuma. Ta yi min alkawari idan ribar alalarta ta taru za ta yi min aike makaranta. Ina son a yi hutu, saboda in ga Zuhuriya, amma na fi sakewa a makaranta fiye da a gida. Ni da Zuhuriya a rabe muke, saboda fada ko gore-goren da ake yi min. A haka a daddafe har na kai aji uku na gama qaramar sakandire. A hutun da zan tafi aji hudu wato babbar sakandire (SS1) a hutun Zuhuriya ta yi aure kuma, ta auri wani mutum a garin Yan lanya mai suna Malam Yahuza. Matansa biyu Aya da Umaima, bai taba haihuwa ba. An sha surutu a wannan auren jama'a suka yi ta ce masa kada ya auri Zuhuriya, ita ma ba mai haihuwa ba ce, ita kuma a ce kada ta aure shi matansa kashe kishiya suke. Daya an yi mata shaidar maita, daya an ce 'yar tsibbu ce bokaye take bi. Sun hada kai su biyu duk wacce ya aura sai sun kore ta ko su haukata ta. Hankalina ya tashi kafin a yi auren na kira Zuhuriya gefe ina kuka na ce ko za ta hakura da auren. Ta yi murmushi ta shafa kaina ta ce "Allah yana tare da mu Bakura ba komai. Ni ma bana son auren nan, na gaji da aure-auren nan Innono ce ba za ta kyale ni ba in zauna lafiya ba." Na yi mata addu'a Allah ya sanya alkhairi.Tun sanda aka kai amarya kauyen Yan lanya na ga yanayin gidan dan tsurkuki, zana ce da qasa zalla ga qanqanta, na tabbatar Zuhuriya ta ci baya ba ta taba aure a quntace irin wannan ba. Na haska na hasko ban ga daki ko zauren da zan yasar da filona in kwanta hakarkarina ba. Na shiga zulumin yadda rayuwa za ta kasance min. Na san muddin Zuhuriya ba ta Cinkilawa zamana a Cinkilawa ya qare, dan Innono ba za ta bar ni ba. Haka na dinga safara tsakanin Yan lanya da Cinkilawa. In kwana a Cinkilawa a dakin Zuhuriya gari na wayewa in niqi gari in tafi garin Yan lanya wajen Ummata Zuhuriya ta ba ni abincin safe, rana na dare. Idan Magaruba ta yi in dawo Cinkilawa in kwanta. Har hutu ya qare na koma makaranta na shiga S.S.1. Na fara girma na fara hankali, don a lokacin shekaruna goma sha hudu zuwa goma sha biyar, dan haka na fara tunanin yadda zan canza rayuwata, ba tare da na sake jawowa Zuhuriya matsala a aurenta ba. Don na fahimci kishiyoyinta sun fara harare-harare su na yi mata habaici akan tuwan da take ba ni. Na yankewa kaina hukuncin ko an yi hutu in yi zamana a Wudil ina dako ina cin abinci, har a dawo makaranta. Haka kuwa aka yi da aka yi hutu na ki tafiya har da guduwa na labe dan kada 'yan garinmu su ganni, sai dai na bawa wani abokina dan kusa da garinmu sallahu wajen Mamana Zuhuriya na ce ya ce mata ina makaranta lafiyata qalau ba zan zo huta ba, saboda ina zana jarrabawa. Haka ya je ya shaida mata jikinta ya yi sanyi ya ce min sai hawaye take tana tambayarsa me yasa su ba su zauna sun zana jarrabawar ba sai Bakuranta shi kadai tunda shima ta san ajinmu daya? Duk da ba ta da ilimi, amma tana da kaifin basira." Umar ya ce "Abba, kai kadai kake kwana a dakin dalibai (hostel)?" Bakura ya girgiza kai ya ce "Daf da Magaruba wani Malami ya ritsani a lungun da na maqale ya jawo kunnena har gidan principal. Kamar yadda na shaida muku tun farkon zuwana makaranta principal dinmu ya san ni, kuma yana sona koda yaushe yana yaba qoqarina yana bada misalai da ni a wajen assembly, dan haka yana ganina ya ce da malamin ya sakar min kunne. Bakura yana da hankali akwai dalilin da yasa ya gudu ya buya bai tafi gida ba." Bayan malamin ya tafi ya zaunar da ni a gabansa yasa matarsa mai suna Asiya ta zubo min abinci na ci na qoshi dan ya ga alamar yunwa da wahala a jikina, Na ci abinci na qoshi, ya fara yi min nasiha hade da dabara gami da lallashi a kan in fadi dalilina na ain tafiya gida. Da farko na 6oye masa daga karshe na zayyana masa tarihin rayuwata tun daga farko har karshe. Na kuma fada masa dalilina na qin komawa gida hutu. Abun mamaki sai na ga ya tausaya min matuka kamar zai rusa kuka, ya kira matarsa Asiya ya laburta mata labarin rayuwata ya fada mata dukkan labarin dana ba shi. Mutuniyar kirki ce, sai ita ma ta tausaya min ta ba shi shawarar to ya bar ni in dinga yin hutun a nan wajen su mana. Malam Abbas Shagari ya ce 'A'a sai na je garin ko na aika an tabbatar min haka ne, sannan zan bar shi ya zauna. " Da ya aika aka tabbatar masa haka ne sai ya qyale ni na zauna a gidansa, kamar yadda na ce masa zan dinga dako ina cin abinci sai ya hana ni yin dako, ya dinga ciyar da ni a kyauta. A lokacin yana da yara guda uku babban Abdul Wahab, sai mace Amina da wani dan jariri da ake goyo shi ma Abdul sunansa. Na ji dadin zama a gidan Malam Abbas Shagari saboda shi da matarsa su na da kirki su na kula da ni kamar dansu. Kamar yadda na ji dadin zama da su su ma sun ji dadin zama da ni, saboda ba na gajiyawa wajen aikace-aikacen gida kamar mace, babu abin da ban iya ba. Shara, wanke-wanke, wanki, aike, noma Koyawa yara karatu da rainonsu duk ni nake yi wa Aunty Asiya. Kafin hutu ya qare sai ga Zuhuriyya wurjanjan an rakota gidan da nake. Ina ganinta gabana ya fadi, saboda yadda na ga ta rame ta lalace akwai alamar damuwa da wahala a tattare da ita. Na riqe ta ina tambayarta ko lafiya? Ta rushe da kuka ta ce "yanzu Bakura ni ka ke guda, an yi hutu kowacce uwa ta ga danta ni ban ganka ba, wacce irin jarrabawa ce a cikin hutu? Ba na barci ko da yaushe ina leken hanya, idan na ji maganar wani sai in fito da gudu daga daki in zaci kai ne." Na ba ta hakuri, sannan na shiga da ita cikin gida na shaidawa Malam da matarsa ga mahaifiyata. Bayan ta zauna sun gaisa ta ci abinci, sai ta fara kuka tana shaidawa Malam irin halin da ta shiga na damuwa da fargabar akan rashin ganina. Malam ya yi mata bayanin dalilan da na shaida masa. Sai ta sake shiga damuwa ta ce ba ta taba tunanin har akwai gidan da Zaa ce ita kadai zata zauna baa yarda Bakura ya zauna ba kuma ta ci gaba da zama a gidan ba, dan haka in har tana gidan dole Bakura ya zauna tare da ita. Kasancewar ta tubure ba za ta bar ni ba Malam ya ce in shirya in bi ta mu tafi. Da yake yamma ta yi ya shawarce ta ta kwana gobe sai mu tafi, ta ce maigidanta ya ce lallai-lallai ta koma a ranar, dan haka a lokacin na hada 'yan kayana na bi ta duk da hutun ya kusa qarewa. Kamar yadda na fada muku ba daki a gidan, Zuhuriya sai haya ta kama min daki daya a makwabtansu na zauna duk da surutun akan abincin da ake ba ni kishiyoyin suke yi mata. Na lura cewar su na takura mata tashin hankali da masifa kullum. Wannan ta yi mata yau, gobe wancan ta yi mata. Duk da irin haqurin da nayi ta yi na cije ban je na rama mata ba. Wata rana kasa daurewa na yi, na shigar mata fadan. Domin sun tarar mata su biyu za su yi mata duka har sun kaita qasa, na zo na tade qafar daya ta fadi qasa, dayar kuwa angaje ta na yi ta fadi gefe. Na tashe ta tsaye na karkade mata jikinta. Da maigidan ya zo suka shaida masa karya da gaskiya sai ya kore mu ni da Zuhuriya, amma bai sake ta ba ya ce dai ta bar masa gidansa. Mu ka tafi Cinkilawa da Magaruba, saboda tsoron Innono sai muka qi zuwa gidan muka kwana a gidan wata qawar Zuhuriya mai suna Tabawa. Washe gari muka kama haya a nan Cinkilawa. kan kace kwabo Innono ta ji labari, ta diro mana.Ta yi ta fada ta shaidawa Zuhuriya cewa marmaza-marmaza ta shirya ta koma gidanta, don mijinta ya aiko 'yan uwansa biko, amma kada ta sake komawa gidan da ni. Zuhuriya ta ce ta amince za ta koma, amma sal hutuna ya qare na koma makaranta, sannan zata koma. Innono ta ce ba zai yiwu ba ta yarda in koma gidanta in qarasa hutun ita kuma ta koma. Daga yadda Innono ta ga na yi ta san ban amince ba. Haka ita ma Zuhuriya ta dai amsa mata ne kawai, sannan Innono ta tafi. Ai kuwa bata koma ba har sai da hutuna ya qare ta harhada min komai na koma makaranta, sannan ita ma ta koma gidanta kasancewar mijin kullum sai ya zo bada hakuri. Na koma makaranta ina ta karatu, har shakuwarmu ta sake kulluwa tsakanina da principal da iyalansa. Har sai da sauran daliban makarantar suke tunanin ashe daman mu 'yan uwa ne. A gidan nake yin week end haka komai dare Aunty Asiya take aiko maigadinsu ya kawo min abinci har hostel. Ina jin dadin rayuwar makaranta, amma jikina ya kan yi sanyi, kwalla ta cika min ido idan na tuno halin da na baro Zuhuriyata. Na qagu in gama makaranta in fara aiki a local goverment dinmu in gina mata gidan siminti, in dinga ajiye mata buhun-buhunan abinci, in dinga dinka mata suturu kala-kala, ita ma ta huta wahala. Burina kacokan a kan Zuhuriya duk da ina tuno mahaifana da qannena na Mangono. Aka yi hutu, don haka na koma staff quarters gidan principal, amma da kyar ya bar ni na zauna saboda gudun abinda ya faru wancan hutun. Na sake ba shi labarin abinda ya faru bayan Zuhuriya ta zo ta dauke ni. Ina kuka ina shaida masa cewar ba na so in sake kashe mata aure. Tausayina yasa dole ya kyale ni.Kamar kullum na bawa abokina wasiqa ya kaiwa Zuhuriya, tasa ya karanta mata. Ta ji irin magiyar da na yi mata cewar kada ta damu, kada ta biyo ni makaranta ina nan cikin qoshin lafiya. Kuma idan hutu ya kusa qarewa zan zo in yini sai in dawo makaranta. Abokina ya shaida min cewa yana gama karanta mata sai ta rushe da kuka ta tashi ta shiga dakinta." Bakura ya matse hawaye yayin da tausayinsa ya rufe masu sauraronsu. Da yawa daga cikinsu suma kwalla suke. Ya girgiza kai yayin da ya cije baki ya damqe tsakiyar kirjinsa, saboda zugi da radadin da zuciyar ke yi masa. Ya ci gaba da cewa "Da wayo, da dabara nake ficewa daga gida in shiga cikin garin Wudil ina yi aikin qarfi ina samun kudi mai yawa sai in boye kafin rana ta fadi sai in dawo gida. Idan suka tambaye ni sai in ce ina bakin get wajen masu gadi ina hira, saboda na san Malam Abbas Shagari ba zai bar ni ba, abin kunya ne a wajensa a ce dalibinsa na dako, sara itace, diban ruwa da dai sauransu, musamman ma ni da kowa ya dauka dan uwansa ne. A haka na tara kudi mai yawa ba tare da kowa ya sani ba. Sai da hutu ya rage kwana biyu na shirya na shaidwa Malam Abbas cewa zan je in ga Zuhuriya. Ya dauko kudin motar zuwa da dawowa ya ba ni na tafl na shiga mota na tafi kai tsaye garin 'Yan lanya na nufa wajen Zuhuriya. Hankalina ya tashi da na ga halin da take ciki daga dukkan alamu kishiyoyin nan nata sun hada kai su na wahalar da ita. Ta rame, ta yi baqi da alamar rashin cikakkiyar lafiya a jikinta. Mace ce mai fara'a da hira, ga zaqin murya, amma da kyar kake jiyo abun da take fada idan tana magana. Gashi yanzu ba ta sana'ar komai, jarin ya qare. Sai ta yi matuqar yin farin ciki da mamakin da ganin irin kudin da na tule mata a gabanta. Ta riqe baki don mamaki ta tambaye ni. "Bakura ina ka samo kudi haka?" Na ba ta labarin duk yadda aka yi, sai ta fashe da kuka ta shaida min cewa daman tana rashin kudi ga bashi a kanta dankar. Su suke siyan omo, sabulu, kudin kitso, ga cikon kudin cefane idan ya ba su tsabar gero, dawa ko masara shi kenan ya gama. Su za su surfa su daka har ya zama gari, sannan su nemo abin kada miya. Na sake tausaya mata, sannan kuma na sake kudirar niyyar zagewa in yi aikatau in samo kudi in ba ta idan an yi wani hutun. Ta raba kudin gida biyu ta miqo min rabi ta ce in yi sayayyar makaranta daman ta hada zannuwanta za ta siyar ta aika min kudin. Na ce ta bar shi pricnipal ya gama siya min komai. Ba ta ji dadi ba da na ce yau zan koma ba zan kwana ba. Kuka take, ni ma ina kuka muka rabu. In takaice muku kowanne hutu haka ake yi har na gama aji biyar (Ss2), muka fara rubuta jarrabawar fita don haka na dade banzo ba. Kowa ya yi hutu ban da masu zana jarrabawar fita, sai dai aka yi mana taron iyayen yara. Ranar taron iyayen yara(visiting) ban sa rai ba, ko a mafarki ba na tunanin zan ga iyayena. Don haka ban ma tunkari cikin Hall ba na sami bishiya na zauna ina karatun littafina. Kamar daga sama na ga Jamilu abokina ya nufo ni a guje yana shaida min ga mahaifiyata ta zo min. Na dube shi a shelake na ce "Karya ne." Ya yi min rantsuwa gami da rike hannuna ya ja ni har karkashin bishiyar da Zuhuriya take tsaye.Hakika ita ce a rakabe a jikin bishiya da kwanon abinci akanta. Yayin da manja ya yi kaca-kaca da kayan jikinta, musamman farin mayafinta, da alamar gajiya da wahala a tattare da ita. Na qaraso da sauri cike da gigita na sauke kwanon da ke kanta na zaunar da ita qasa ta miqe qafafuwanta da suka kukkumbura suntum, kasancewar tsohon cikin dana gani a jikinta. Idanuwanta a kumbure, leben bakinta a suntume ga bushewa kayau-kayau saboda yunwa da kishirwa, kamanninta ya canja kamar ba ita ba. Na rasa abun da yake yi min dadi na ruga da gudu gidan Malam Abbas Shagari na karbo ruwan sanyi a firji na kawo mata ta sha, na bude kwanon na ga wata cakudaddīyar shinkafa da miya ce wacce ta sha wuya. Na tura kwanon gabanta na ce ta ci. Ta girgiza kai ta ce "Kai na kawowa Bakura ka ci." Ta shaida min cewar Babar Jamilu ce ta shaida mata za a yi wa yara taron ziyara za su jewa Jamilu idan zan zo wajenka in shirya. Tunda Asuba suka fara soye-soyen kaji, cincin, naman rago da dai sauransu." Zuhuriya ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa "Ba ni da kudi, bare in sayi kaji, ba ni da kudin da zan yi cincin, na aika ko'ina a samo min bashi ba a samo ba. Da kyar na ranto shinkafa gwangwani biyu da kaza daya na dafa maka. Kudin motata bai cika ba na qaraso da qafa." Bakura ya fashe da kuka ya ci gaba da cewa "Na sa hannu a kwanan abincin ina ci ba don ina so na ci ba sai don ta yarda ta ci itama. Sannan tasa hannu muka ci shinkafar nan a karkashin bishiya, cusawa nake yayin da zuciya ke cike da tausayinta kwalla ce ke cikowa daga idanuwana ina damben mayar da ita don kada Zuhuriya ta gane. Na dube ta na ce Zuhuriya ciki gare ki ne na ga cikinki babba kafarki a kunbure? Ta langwabar da kai tasa gefen gyalenta ta share hawaye ta ce shi yasa ka ji ni shiru, tun sanda na sami cikin ba ni da lafiya. Ban taba lafiya ba tunda na sami cikin nan ga mugayen mafarkai Allah dai yasa in haifi cikin nan lafiya." Na goge mata hawaye yayin da na fara farin ciki ina murmushi na ce da ita za ki haihu lafiya da izinin Ubangiji, amma na fi son ki haifi mace in dinga siya mata ribon." Ta yi dariya ta ce "namiji dai ka sami abokin shawara ko bana raye idan na haifi mace kuwa mata na haifa maka." Na tambaya cike da mamaki na ce "mata kin manta ni yayanta ne wa yana auren qanwarsa ne?" Ta yi dariya ta dafa kafadata ta ce "idan ba su sha nono daya ba zai iya aurenta tunda ba uwarsu daya ba." Na girgiza kai na ce na fi son ki haifi mace in dinga yi mata wasa ina goya ta a bayan keke." Zuhuriya ta saki jikinta muka dinga hira cikin farin ciki har rana ta fadi, sannan na tuna ashe ba ta da kudin mota, kuma ba za ta taba fada min cewar bata da kudi ba tafiya zata yi tayi da qafa har ta isa garinmu, don haka na shiga zulumi ina tunanin yadda zan samo mata kudin mota ko rance ne. Don haka na shiga hostel wajen abokaina da kyar na samo rance na kawo mata, ta qi karba da farko sai da ta ga raina ya 6aci sannan ta karba. Na rakata har get tana daga min hannu, ina daga mata hannu, ashe mun yi sallamar qarshe kenan har abada." Bakura ya rushe da kuka mai tsanani, yayin da Innono ta dau kuka mai ruri har da dora hannu aka. Gaba daya suka dafe kirji suka tambaya "mutuwa ta yi a hanya?" Bakura ya girgiza kai ya ce "ta isa gida lafiya. Bayan zuwanta da kwana biyu ta haihu." Samira ta tambaya cikin damuwa hade da qaguwa, "Da ta haihu me ya faru?" Bakura ya ce "Allah shi Ya barwa kan Sa sani har yau ban sami wanda ya fada min gaskiyar al'amarin ba." Sai ya sake rushewa da kuka. "Kamar yaya ba ka san gaskiyar abun da ya faru ba?" Malam ne ya tambaya. Bakura ya dago da luhu-luhun idanuwansa jajaye ya kalli Malam ya qyada kai ya ce "Babu wanda ya fada min gaskiya har yanzu. Mun rabu da Zuhuriya a lokacin da ya rage min saura sati biyu in gama makaranta. Da sati biyu ta cika muka na zana jarrabawar qarshe sai na yiwa Malam Abbas da iyalansa sallama har da koke-koken rabuwa Aunty Asiya da 'yayanta muka yi,saboda mun shaqu. Mu ka yi hotuna da koke-koke ni da abokaina, sannan kowa ya kama hanyar garinsu. Da jakar kayana kacokan na nufo gida. Ina tafe ina zulumi, ina tunanin da Magarubar nan ina zan nufa gidan Innono ko gidan Zuhuriya? Na yanke shawarar gara in je wajen Zuhuriyata, don na damu na ga lafiyarta in ya so ko a zauren gidan sai in kwana kafin mu yi shawarar inda zan zauna. Ina isa kofar gidan na iske Malam Yahuza mai gidanta da sauran mutane. Na gaishe su, amma sai kowa yake yi min duba irin na tausayawa na lura da haka, amma ban kawo komai a raina ba na wuce zuwa cikin gida. Na iske sauran matan biyu su na zaune bisa tabarma daya sun hada kai su na qus-qus su na ganina sai na ga sun zabura sun miqe tsaye yayin da daya take qoqarin zurawa da gudu su na tambayata, Lafiya? Me na zo yi a gidansu? Sai na yi mamakin wannan tambaya ta su, amma ba su da wata amsar da zan iya ba su, domin bai kamata su tambaye ni abun da na zo yi ba a wajen Zuhuriya ba. Na kada kai na nufi dakinta. Abun da na gani shi ya firgita ni na tsaya cak yayin da na juyo da sauri na dube su. Yayin da bakina yake karkarwa na tambaye su "Ina dakin Zuhuriya, ina Zuhuriya?" Sai Bakura ya riqe kai ya barke da wani zazzafan kuka mai zubo da hawaye ba kakkautawa. Hankalin kowa ya tashi, yayin da gaban kowa ke faduwa. Yara da manya hawaye ne fal a idonsu. Sajida ta tambaya cikin damuwa "Me ya faru da dakin Zuhuriya?" Bakura ya dago da kyar ya dube ta ya fada ciki wata nakasasshiyar murya, "Dakin Zuhuriya ya kone kurmus sai toka." Zahra ta ce "Ina Umma Zuhuriyar? Ina bebin da ta haifa?" Bakura ya, girgiza kai saboda tsabar jimami ya ce "Zuhuriya na ciki ita da baby lokacin da wutar ta kama don haka suma sun qone." Su ka hada baki su duka "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un." Kowa ya yi shiru babu wanda ya iya cewa komai, fuskar Bakura na tsugunne a qasa sai hawaye ne ke zuba a kan tiles fat-fat-fat daga nan ya kasa ci gaba da labarin. Innono ce ta ci gaba ita ma cikin rurin kuka, hawaye ke zubowa kamar ruwan famfo ta ce, "Daga sanda Bakura ya ji Zuhuriya ta qone qurmus ko gawarta ba a fitar ba, sai toka, a take ya suma har bayan Isha'i bai farfado ba ana zuba masa ruwa. Washe gari da safe ya nufo Cinkilawa wajena. Bakura ka yafe min abun da na yi maka a rayuwa. Iyalan Bakura kuma ku yafe min shiyasa ake son mutum ya shuka abun alkhairi a rayuwarsa, ina ganinsa zai shiga Cikin gidan sai na zo na tare qofa da hannuna na tambaye shi ina zai je? Ya kalle ni galala kamar Zautacce sai na nuna masa hanyar waje na ce yau babu Zuhuriya a duniya, don haka babu kai babu zama a Cinkilawa ka hada kayanka ka koma Mangono. Ya Juya a sanyaye yana tafiya sai na ga idan ya tafi aka rasa shi ni za a kama a Mangono a ce ina dan da muka dauko sai na kira shi ya dawo na ba shi tabarma a zaure na ce ya zauna nan da kwana biyu zan hada kudin mota in mayar da shi Mangono da kaina. Bakura baya kuka sai dai ajiyar zuciya ko ba a fada maka ba ka san turniqin qunar da yake ji ba zai fasaltu ba. Kuma baya magana sai kallo da ido. Da Magaruba ya tashi ya fice ban sake ganin Bakura ba sai yau, neman duniya nasa a yi ba a ganshi ba. Baya Cinkilawa, baya Balle batai, baya Yan lanya, baya Jarawa, baya Warawa, baya Lahadin makoli baya kadara, baya Rimi,baya Token, haka baya Larabar gadon sarki sannan baya makarantarsu Wudil, don haka na ja bakina na yi shiru, duk wanda ya tambaye ni Bakura sai in ce ai tun bayan mutuwar Zuhuriya iyayensa suka zo suka dauke shi sun tafi da shi Mangono." Har wani lokaci mai tsawo Bakura ya dauka kansa a sunkuye bai dago ba. Can ya dago ya dubi kowa daya bayan daya ya sharbe hawaye. Ya ce "Kun ji yadda mutuwa ta raba ni da Zuhuriyar da nake matukar kauna take matukar sona a duniya. Na yi rashin uwa, na yi rashin uba, na yi rashin yayata, na yi rashin aminiya, na yi rashin mai sona. Daga sanda na ji Zuhuriya ta rasu daga lokacin na ji wani qaton abu mai kama da dutse ya zo ya tokare min a tsakiyar kirjina har yau bai sauka ba. Ban fara kukan mutuwar Zuhuriya ba da hawaye sai da na shekara biyar zuwa shida bayan mutuwarta, saboda abun da nake ji ya fi kuka ciwo. Kukan da na fara shi ne sauqin ciwon mutuwar har yau ban taba kwana biyu ba cur ban zubar da hawayen dacin mutuwar Zuhuriya ba a zuciya ba. Ban taba samun naira daya, ban yi hawayen daman Zuhuriya na nan in ba ta ba. Ban taba miqawa wani kudi ko kaya ban tuna dama Zuhuriya nake bawa ba. Alhamdulillah Alakulli halin, Allah ne mai yadda ya so da bayinsa. Tsakanina da ita sai addu'a marar adadi, sai na dinga sadaukar mata da sadakatul jariya. Ina addu'a, Allah ya kai mata rahama cikin kabarinta." Su duka suka amsa masa da, "Amin." Zahra ta sharbe hawaye ta ce "Abba, a lokacin shekarunka ba su wuce goma sha shida zuwa sha bakwai ba kana yaro, ina ka tafi da ba'a ganka ba, ko Mangono ka koma?" Bakura ya girgiza kai ya ce "Ban yi tunanin Mangono ba, ban yi tunan komawa Wudil ba. Ban yi tunanin a duniyar da na ke ba, ni dai na sa gabana gadi ina ta tafiya a dawa cikin dare. Ban damu da duhu ba, ban damu da maciji ba, ban damu da 6arayi ba ko 'yan fashi, ba ko gajiya, tafiya nake ni kaina ban san matsayina ba a raye nake ko a mace? Ban san ina na nufa ba ko ina na dosa. Ashe cikin Kano na nufa a cikin kasuwar Singa Asuba ta yi min na fadi a bakin hanya sumamme." Ya dubi Zahra ya ce "Daga nan Allah ya hada ni da kakanki, mahaifin Mamanki Samira. Allah ya yi wa Alhaji albarka shi yasa aka dauke ni aka kai ni asibiti aka yi ta qaramin ruwa har kwana uku, sannan aka sallamo ni ya fara tambaya ta garinmu. Ban fada masa komai ba na dai ce masa ban san kowa ba anan kuma ba ni da inda zan je sai dai ya dauke ni aiki. Ya saka ni a cikin yaransa muka fara aiki, sai ya yaba da hankalina gashi kuma ni kadai ne na iya rubutu shi ma bai iya ba. Don haka ya ja ni a jiki. Ya na aikena har cikin gida in kai sakon cefane, ko kuma kafin ya fito kasuwa ya kira ni in shigo har falonsa in yi masa lissafi da cike-ciken takardu. Anan sai Allah Ya jarrabi Samira 'yarsa da tsananin sona, nima ina sonta, amma abun da kamar wuya a ganina ba zai yiwu ba. Babu abin da ya gagari Ubangiji, Alhaji ya amince min na aui Samira, amma sai da ya tisa ni a gaba na kai shi Mangono ya ga mahaifana. Sai da Samira ta qare sakandire aka yi aurenmu lokacin tana da shekaru goma sha shida, ni kuma ina da shekaru ashirin. Ya ba mu aron gida muka zauna ina zuwa kasuwa na ci sa'a na sami mace ta gari mai tsananin sona, mai lallaba ni, mai ba ni hakuri, idan ta ga ina cikin damuwa. Amma duk da haka ba na jin dadin rayuwata. Wata rana na hadu da wani babban ma'aikaci ya yaba da hankalina ya samar min tallafí daga gwamnatin tarayya. wato (Scholarship) zuwa qasar England don yin degree. Gwamnati ta dau nauyina da matata muka tafi England har tsawon shekaru uku a can muka haifi 'yar mu ta fari na saka mata sunan Zuhuriya, muke kiranta da Zahra, ko in kira ta da Yagana. Tun daga lokacin Allah Ya fara buda min hanyoyin samu. Na dawo Nigeria na fara aiki ina kasuwanci ina zuwa England ina saro kaya ina shigowa da su. Har rana irin ta yau kullum ci gaba nake samu a rayuwata. Na shiga cikin matsananciyar fargaba a lokacin da na fara ganin Sajida a rayuwata, saboda tsananin kamar da ta yi da Zuhuriya sak kamar an tsaya kara" Sajida ta dago da sauri ta dubi Bakura ta dafe kirji ta ce "Ni, ta yaya zan yi kama da Zuhuriya?" Bakura ya gyada kai ya ce "Haqiqa duk wanda ya san Zuhuriya, yaga Sajida sai ya fadi haka. Wannan dalili yasa na bi Sajida gidansu, dan ganin su waye iyayenta, kuma ta ina ta samo kamannin Zuhuriyata. Na ga mahaifinta, na ga mahaifiyarta, na ji tarihinsu babu ta inda suka hadu da Zuhuriya. Hankalina ya qi kwanciya, tun ranar da na baro Cinkilawa ban sake komawa ba sai sanda na hadu da Sajida, anan na fara zuwa Yan lanya na tambayi wani tsohon makwabcin gidan malam Yahuza ya shaida min malam Yahuza ya rasu tuntuni matansa ma daya ta sami tabin hankali. Na tambaye shi game da abun da ya faru da Zuhuriya, sai ya ce Zuhuriya da 'yar da ta haifa suka qone a cikin dakin. Na fito daga Yan lanya na shiga Cinkilawa na tarar Innono ba ta garin, mijinta ya dade da mutuwa. Na tambaya ko Zuhuriya ta bar 'yar da ta haifa? Sai aka ce min ai namiji ta haifa, shi ma daga baya yaron ya mutu. Na rasa gaskiyar magana, hankalina ya kasa kwanciya." Umma Furera ta gyara zama ta goge hawaye ta ce "Malam Yahuza yayana ne uwa daya uba daya, amma ni a garin Shanono na girma shi kuma a Yan Lanya ya girma kasancewar yawon almajiranci ya je yi. Ya yi aure-aure da dama, amma Allah bai bashi haihuwa ba, na ji labari ya auri Zuhuriya, amma ban taba zuwa lokacin da suke tare ba, ta samu ciki ta haifi 'ya mace. To kamar yadda aka ba ni labari da muka je zaman makokin Zuhuriyya. An ce ta haihu da kwana biyu sai ba ta da lafiya, saboda haka tana kwance a daki akwai wani Malami da ya zo daga Balle bantai ya ce a kawo yarinyar zai yi mata addu'a, sai Malam Yahuza ya shiga ya dauko 'yar a kwance a gaban Zuhuriya ya ce min har Zuhuriyar ta yi masa magana ta ce masa kada a yi wa jaririyarta zane, dan Allah a bar mata fuskarta haka, kasancewar mu Fulani ne ta ga duk 'yan uwanmu da zane irin nawa nan, ya ce ai ba wanzami ba ne, malami ne ya zo zai yi mata addu'a. Ya ce min ya fito ya bar ta da garwashin wuta a gabanta cikin kasco saboda sanyin da ake yi sai dai idanuwanta lumshe kamar mai magagin barci. Ita kadai ce a dakin kasancewar babu wata wacce ta zo ta zauna da ita daga Cinkilawa, amma mahaifiyarta na zuwa ta yini, sannan ta koma. To bayan ya fito da 'yar jaririyar zaure aka mata addu'a ya karbe ta zai mayar da ita wajan mahaifiyarta sai ya iske wuta ta gauraye dekin har rufin dakin babu ta inda mutum zai fito. Babu kowa a tsakar gidan sauran matan su na dakunansu. Sai da Malam Yahuza ya yi ruri yana kiran "Jama'a ku taimake ni wuta!" Sannan kowacce ta fito daga dakinta da gudu, maza daga qofar gida suka shigo ana ta zuba ruwa da qasa, amma ina abu ya ci tura, sai da daki ya qone kurmus Zuhuriya na ciki ko ihunta ma ba a jiyo ba, sai toka babu alamar bil adama." Bakura ya gyara zama yayin da Sajida ta qurawa mahaifiyarta ido tana dubanta zuciyarta cike da mamaki hade da tunani mai firgitarwa ta qagu ta ji qarshen labarin, kwakwalwarta ta kasa tantance mata abun da yake shirin faruwa. Umma Furera ta ci gaba da cewa, "Labarin rasuwarta ya iske mu muka dungumno daga Shanono muka iso Yan lanya don yin gaisuwa. Ba tare da doguwar magiya ba na roqi yayana Yahuza cewar ya ba ni 'yar in rike tunda ban taba haihuwa ba a lokacin. Nan da nan ya ce in dauka ya ba ni ita tunda ba mu da iyaye ni da shi ne kawai mu ka rage" Sajida ta ji wani jiri ya fara tasowa daga cikin kwakwalwarta, ta dubi Umma Furera yayin da hawaye ya cika idonta ta fada cikin wata murya mai karkarwa "Umma, baki taba fada min kin taba rike wata 'ya ba, rasuwa ta yi ne daga baya?" Umma Furera ta girgiza kai yayin da wata fargaba ta rufto mata. Ta dubi maigidanta Malam Yakubu ta rushe da kuka ta ce "Malam ka fadawa Sajida gaskiya, yau ne ranar farko da ya kamata ta san gaskiya." Sajida ta waiga da sauri ta dubi Malam ta fada cikin tashin hankali ta ce "Baba me yake faruwa ne? Ka fada min gaskiya." Ta tashi da gudu ta tafi wajen lya Azumi (Innono) ta rike ta tana kuka. "Ki fada min abun da ban sani ba, mene ne yake faruwa ko ba ni da iyaye tsinta ta aka yi?" Samira, Zahra da kannenta suka shiga rikitaccen tunani, sun kasa gane abun da zai faru. Innono ta sharbe hawaye ta ce, "Ke ce yarinyar da Zuhuriya ta mutu ta bari. Ma'ana ke 'yar Zuhuriya ce da malam Yahuza ba Furera da Yakubu ne suka haife ki ba." Ba ta rufe bakinta ba Sajida ta cukuikuye ta kame a gefe ta rusa kuka, saboda tashin hankali. Bakura ya yi kabbara hade da hamdala ya dubi Sama ya ce "Allah Kai ne mai hikima, Kai ka san abun da yake boye. Ni ban san gaibu ba, amma na san tabbas akwai wani sirri na boye game da kamar da suka yi." Umma Furera ta je wajen da Sajida ta qame ta dafa kanta gami da murza bayanta ta na kuka itama ta ce, "Sajida ki yi hakuri ki yafe mana, na san ba za ki ji dadi ba, ya kamata ki sani tuntuni musamman lokacin aurenki. Ban san yadda zan fada miki ba, kasancewar mun shaqu ko Malam baya so ki san babu wata alaqa a tsakaninku.' Umma Furere ta zauna a gefen Sajida tana rungume da ita, ta ci gaba da cewa "Na karbi Sajida daga hannun dan uwana a bisa amana zan rike ta har aurenta. Bayan da aka yi sadakar bakwan mahaifiyarta Zuhuriya ko da yake Fatsima na ji mijin yana fada mata, don haka ya ce a mayarwa 'yar sunan mahaifiyarta Fatima, shi ne muke kiranta da Sajida tunda duk Fatima ce. Mun hadu da Iya Azumi a zaman makokin sau daya, amma ta yi fushi ta fice daga gidan mutuwar da ta ji labarin ni a ka bawa jaririya ba ita ba. Ta so a ba ta jikarta ta rike mahaifin Sajida ya qi amincewa, don haka da ta tafi ba ta sake waiwayar yarinyar ba, amma qanwarta ta taba zuwa ta nemo mu kuma ta zo bikin ita ce ta tafiwa da iya Azumi kayan biki , sai jiya da muka ganta kwatsam. Na dawo gidana goye da jaririya, sannan na yi wa Malam bayani sosai ya yi farin ciki, kasancewar ni da shi dukka muna tsananin son haihuwa, Allah bai ba mu ba. Muka dinga qulla-qulla, muna tanade-tanaden kudin madarar da muka shayar da 'yar jaririya har Allah ya raya ta, ta fara cin abinci sosai. Na shaqu da Sajida, haka Malam ma, sajida ta kasance yarinya ce mai wayo da yawan suruu, don haka ne ma ko da wasa ba na fadawa kowa wannan sirrin cewa Sajida ba 'yata ba ce, haka shi ma Malam yake cewa 'yarsa ce ta cikinsa. Da ta isa sawa a makaranta ma Nursey School mai kyau muka saka ta.Akan keke yake kai ta, ya dauko ta, har ta shiga primary tana amfani da sunan Malam wato Sajida Yakub. Allah mai amsa addu'ar bayinsa, kwatsam sai na ganni da ciki Allah ya ba ni ciki a lokacin da ya so in haihu na haifi da namiji muka sa masa suna Yahuza, sunan mahaifin Sajida kenan da Allah ya yi masa rasuwa tun tana da shekaru biyu kacal a duniya. Don haka Sajida da Yahuza suka taso a matsayin uwa daya, uba daya, ba tare da sun ga wani bambanci daga wajen Malam ko daga wajena ba." Umma Furera ta yi shiru tana sharce hawaye da gefen gyalenta, yayin da kowa ya yi tsuru kamar masu zaman makoki. Sautin kukan Sajida ne kawai yake tashi, yayin da ta miqe qafa a qasa ta kifa kai a kan kujera. Tana rusa kuka mai tsanani, gami da cewa, "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, ba ni da uwa, ba ni da uba ashe, ban san uwata ba, ban san ubana ba, babu wanda ya taba fada min gaskiya. Kakata wacce ta haifi uwata ce ta rage min amma ba ta taba neman in da nake ba. Sai yanzu? Ashe ba ni da kowa, ba ni da wa ba ni da qanwa, ko qani, ban san asalin garina ba, balle in san dangin uwata da ubana ba. Wannan baqin ciki ya ishe ni har gara a ce Allah Ya đauki raina in mutu in je in sadu da mahaifaina, zamana a duniya ba shi da amfani. Wayyo Allah Zuhuriyya, ban sanki ba, ban taba sanin kamanninki ba, ko a mafarki ban taba kwatanto ki a raina ba. Allah yayi miki gafara." Kowa ya fashe da kuka, musamman Bakura, ji yake zuciyarsa na tafasa tamkar za ta fice, saboda tashin hankali. Ya sunkuyar da kai qasa sai hawaye ke ta shatata. Ya damqe kai dam da hannayensa guda biyu yana jinjina ikon Allah mai yadda Ya so Yake tsaro rayuwar bayinSa. Malam Yakubu ma hawaye yake yayin da kalaman Sajida ya ji kamar an watsa wuta a zuciyarsa. Ya yi gyaran murya ya ce, "Sajida, hakika za ki ji ba dadi lokaci guda a tare ki a ce iyayenki da kika dauka su suka haife ki ba iyayenki ba ne na gaskiya.To amma sai ki duba ki ga wanne irin riko suka yi miki, wanda ya sha bamban da na dan da suka haifa a cikinsu. Kin ga ai ba bambanci, bambanci daya ne Allah bai kaddaro ta jikinmu za ki tsaga ki fito ba, wannan kuma Allah ne ke tsarowa kowa daga cikin wance, wane zai fito. Domin uwar wani, ko uban wani baya haihuwar dan wani. Allah ya kaddaro Zuhuriya ce za ta haife ki, bayan tsawon shekarun da ta yi ba haihuwa, ta same ki ashe mu ta haifawa ta mutu ta bar ki. Mu ka ga ba anmfanin sanar miki gaskiyar al'amari, saboda ba komai zai qara miki a rayuwarki ba sai damuwa, daman da ace iyayenki na raye ne sai mu kai ki ki gansu, to yanzu ko mun fada miki basa nan, duk da mun san komai dadewa wata rana za ki ji labari, idan na mutu ko Furera ta mutu. Dangin da kike cewa ba a nuna miki ba, ai duk dangin Furera da kika sani sune dangin mahaifinki, kasancewar uwa daya, uba daya suke da mahaifinki Malam Yahuza. Garinku da kike kira ba akai ki ba, ai Shanono ne garinku na ainahi, Yaya Yahuza yawan almajiranci ne ya kai shi can amma ba ku da dangi a garin. Dangin mahaifiyarki kuwa da ba a nuna miki ba, ba da gangan müka qii nuna miki ba, ba mu san su ba ne, kakarki Iya Azumi ita kadai ce a Cinkilawa, ita ma tun ranar da aka taho da ke ba a sake jin labarin inda take ba, domin ita ma mijinta da take zama dominsa a Cinkilawa ya rasu jim kadan bayan mutuwar mahaifiyarki. Ba mu taba sanin Mangono ba, balle mu kai ki wajen dangin baban Zuhuriya. Sajida, ki yi hakuri ki yafe mana kada ki ga laifinmu wajen 6oye miki boyayyen sirrin daya bayyana yanzu. Har yau ban daina jin tamkar ni na haife ki ba." Kowa hawaye yake har yanzu, babu wanda ya iya cewa komai har zuwa lokaci mai tsawo. Kowa yana saqawa yana jujjuya wannan lamari a zuciyarsa. Sajida ta fada ta sake maimatawa a ranta Zuhuriya Super Market, ashe ni sunan mahaifiyata ce ban sani ba na ke shiga ina fita koda yaushe. Allah cikin ikonsa ya jarrabe ni da tsananin son Zuhuriya Super Market, komai zan siyo can nake zuwa, ko an hana ni fita can zan aika Yahuza ko almaijirai su yi min siyayya. Allahu Abkbar! Jini daya ba wasa ba ne. Ta sharbe hawaye ta dago da kanta ta duba Bakura, yayin da ta ji wannan tsananin tsanar da qululun baqin cikin da ya tokare a wuyanta tun ranar da ta fara ganinsa a rayuwarta yayi 'zuguf" ya fada, ma'ana ta ji ta daina tsanarsa, ta ji tamkar ya zama dan'uwanta na jini. Idan ta dube shi sai ta ji tamkar ta ga Zuhuriyarta. Zahra kuwa babu abun da take jujjuyawa a ranta sai tsananin mamaki, ta sake gasgata maganar mahaifinta da ya dage da cewa shi dai fa ya ga mai kama da Zuhuriyarsa. Duk da rashin tarbiyarta ya nace mata ashe shi ya san abun da yake gani, domin shi kadai ya san Zuhuriyya mu ba mu san ta ba. Abba yana son Zuhuriya don haka ban ga laifinsa ba da ya auro mai kama da ita ba." Samira ma a ranta nanatawa take tana sake gasgata gaskiyar Bakura, a da ta yi tunanin ya so ya kara aure ne kawai ya fake da cewa ya ga mai kama da Zuhuriya, ashe gaskiya ne Sajida 'yar Zuhuriya ce ta cikinta, don haka kamarsu daya sak. "To bayan Bakuta ya gane Sajida 'yar Zuhuriya ce menene matsaya Sajida a wajensa'? Menene matsayin aurensu kuma?" Wadannan tambayoyi Samira ta jero a ranta, ta na zaune tana jiran amsoshinsu kafin a tashi daga taro. Bakura ya dago da jajayen idanuwansa ya yi Sajida duba na tausayawa da kulawa ya girgiza kal, Sannan ya fara magana cikin wata marainiyar murya sanyayya. ya ce "Sajida, hankalina ya kwanta yadda ba zan iya kwatanto yadda zuciyata ta washe ba a sakamakon da aka tabbatar min cewa ke 'yar Zuhuriya ce ta cikinta. ldan na kalle ki sai in ga tamkar na ga Zuhuriya, haka Idan na ji muryarki. Hakika Allah Ya amsa addu'ata ya Yaye min kokonto da dimuwar da na shiga wajen tantance meye alaqar ki da Zuhuriya har ku kayi kama haka. Ban yi karya ba, ban yi kuskure ba ashe ke jinin Zuhuriya ce.Na rantse da Allah tun lokacin da aka sanar min Zuhuriya ta rasu wani abu ya taso ya tokare min a kirji bai taba sauka ba, sai yau na ji ya diro tsakiyar kirjina da na ga 'yar Zuhuriya ta cikinta, ba zai sauka qasa ba gaba daya, sai ranar da na mutu na hadu da Zuhuriya a lahira insha Allah a cikin Aljanna. Haka Allah Ya so, kana taka Allah na tasa, ta Allah kuwa ita ce gaskiya. Mahaifana da na ke shaida muku dazu cewar almajirai ne masu bara a titi yanzu idan ku ka gansu za ku rantse ba su taba sanin wani abu shi talauci ba. Na musu gini na gani na fada wanda a garin Maiduguri ana kwatance da gidan da na gina musu, idan za a zano gidaje na alfarma. Na zuba su a ciki na zuba musu ma'aikatan da za su kula da su. Na zuba musu kayan more rayuwa da abincin da ko shugaban qasa iyakar abun da zai ci kenan. Na hada su da manyan likitocin da za su kular min da laifiyarsu. Wannan mai tabin hankalin da ku ka sani a da ta canja ta nutsu tana shan magani za ku zauna ku yi magana ta hankali da ita tas, daman ba haukan ne kadai yake damunta ba har da talauci da rashin samun kulawa. Makahon nan mai bara ya daina yawo a titi, duk da har yanzu makaho ne, amma yana zaune waje daya duk inda zai je direba zai kai shi a mota. Qannena biyu, Babagana da Yaana kuwa babu wanda baya cikin daula, na dauki nauyin Yaana da 'ya'yanta duk abun da suke bukata su kirani a waya in turo musu. Babagana ma na ba shi jari yana rike kansa da iyalansa a Kaduna. Iyalan marigayi Hakimin Mangono ma ban manta da su ba a dalilin Zuhuriya ko da yaushe ina zuwa in gaishe su in yi musu alkhairi, ina yi musu aike akai-akai. Me ya yi saura? Babu Zuhuriya, babu wanin Zuhuriya da zan taimakawa. A ganina duk wannan taimakon da nake yi wa iyayena da yan uwana ba zai kai kashi daya a cikin goma da na kudira a zuciyata zan yi wa Zuhuriya ba, amma Allah bai yarda ba. Tsakanina da ita sai addu'a, daman ba ta yi min wannan halascin dan in saka mata a duniya ba. Allah ne kadai zai ba ta ladan taimakon da ta yi min. Yanzu da ba Zuhuriya sai ke 'yarta ta cikinta, ga kuma mahaifiyarta da ta tsugunna ta haife ta, babu abin da zai sa nan gaba ku ce wayyo babu, saboda kamar yadda iyalina ba su taba sanin babu ba kuma insha AIlahu daga rana irin ta yau kun rabu da babu in har ina raye kuma Allah Ya ci gaba da buda min kamar yadda ya buda min a yanzu. Sajida ban ji dadin maganar da kika yi a cikin kuka ba, kike ambaci ba ki da uwa, ba ki da uba a duniya. Sajida, ina so ki dauka Umma Furera da Malam Yakubu sune iyayenki da suka haife ki, kamar yadda kika dauka ada. Sannan idan kina neman dan uwa to ki dube ni sannan ki juya ki dubi kakarki Innono jininki ce. Hakika da ciwo a ce da ya tashi bai taba ganin kamannin mahaifansa ba ko a hoto ba, to ki kudira Allah bai sa ki gansu ba, sannan ki juya ki duba Innono kakarki idan kina so ki ga kamannin mahaifiyarki saboda kamar su daya sak, amma ke har ki kin fi kama da Zuhuriya, tamkar an tsaga kara babu abin da kika rage ta. Don haka ku uku kamar ku daya. Rokon da zan yi miki shi ne ki cire damuwa kada wannan magana ta dame ki, saboda wanda ya mutu ya mutu kenan baya dawowa. Zuhuriya ta tafi ta bar ni, ta bar ki, ba za ta dawo ba. A da baki san ta ba, dan haka ba kya yi mata addu'a, amma daga rana irin ta yau ki saka su a cikin addu'arki duk sanda kika yi sallah, suna kwance a cikin kabarinsu suna jin ki, soyayyar da za ki nuna musu kenan a duniya. Daga qarshe tsakanina da ke sai fatan alkhairi da fatan samun ci gaba a rayuwarki. Ki yafe min laifukan da na yi miki, domin na san na 6ata miki rai da aka tirsasa ki ka aure ni, wannan kamar da kuka yi da Zuhuriya ta ja hankalina na ji ba zan iya barin ki ki fada muguwar rayuwa ba, wannan ne dalilina kawai. Sajida ina yi miki albishir da komawa sabuwar rayuwa wacce za ta fi miki farin ciki da samun nutsuwa fiye da rayuwar da kike ciki a yanzu." Kowa ya yi wa Bakura duba na rashin fahimta, musamman Sajida, ta yi sauri ta goge hawaye ta ci gaba da tsurawa Bakura ido. Ya yi shiru kansa a sunkuye a qasa. Can ya dago ya goge gumin goshi ya dubi Sajida. Ya ce "Sajida, farin cikinki shi ne farin cikina, don haka zan so ki dauwama cikin farin ciki, domin nima in samu nawa farin cikin. Na fuskanta haka duk wanda ya san ki ya san abun da kika fi so a duniya, wanda idan ki ka same shi to a burinki ya cika. Wannan abu kuwa shi ne Abdul Majid." "Dadadamdam!" Bugun zuciyar Malam, Umma Furera da Zahra kenan. Haka wannan bugun zuciyar ya farwa zuciyar Sajida suka dago da sauri suka dubi Bakura a lokaci guda, yayin da kowa ya zazzare ido, don mamaki. Hakika Zahra ta firgita da ta ji sunan Abdul majid ya fito daga bakin mahaifinta sai ta ji tamkar yana da labarin wayar da yake yi mata. Bakura ya katse tunaninta ya ci gaba da cewa,"Na yarda, na amince, ki je ki auri Abdul Majid ku zauna har karshen rayuwarku, in har yin hakan zai zame miki farin ciki a rayuwarki." Malam da matarsa suka wangale baki, don mamaki mai hade da dimaucewa, yayin da suka zabura a lokaci guda tamkar an muntsine su. Sajida ta sunkuyar da kanta qasa tamkar mai jin kunya, yayin da kallo daya za ka yi mata ka ga alamar murmushi a fuskarta. Irin wannan mamaki shi ya ruftowa Samira da Zahra, yayin da wani sanyin zuciya ya dirar musu mai hade da hamdala. "Bakura, me kake fada ne haka? Me kake shirin aiwatarwa? Ka na nufin saboda Zuhuriyya ce ta haifi Sajida, kana ganin aurenka ya haramta da Sajida?" In ji Malam. Bakura ya daga hannu alamar Malam ya yi shiru, su ka zuba masa ido kawai. Ya yi dan murmushin karfin hali Ya ce, "Sajida, baki da idda a kanki, dan haka ki kirawo min Abdul majid ya zo mu zauna mu yi magana idan ya amince zan aura miki shi, kuma na dau nauyin kayan lefe, kudin sadaki, gidan zamanku da motar hawanku da garar da za ku ci har tsawon shekaru. Zan ba shi jari don ya kula da ke, zan dauki nauyin ci gaba da karatunki, idan kina so ki ci gaba, domin ina so ki dauwama cikin farin ciki" Bakura ya juya da sauri yayin da ya daina duban Sajida. Kwalla ta cika masa ido ya ce, "Ina fatan Malam da Umma Furera za ku gafarce ni, ku gafarci Sajida a kan hukuncin da na yanke, na fi kowa sanin dalilina. Hakan da na yi shi ne ya fi alkhairi a gare ni da ita Sajidar da ku kanku." Umma Furera ta bude baki za ta yi magana, Bakura ya dakatar da ita ya ce kada ta ce komai, sai ta koma ta gyara zama ta zuba musu ido. Iya Azumi ma ta yunkura za ta yi magana Bakura ya dakatar da ita itavma. Zuciyar Malam ta fara tafasa, ya ji kamar zai kurma ihu, don tashin hankali daga dukkan alamu hukuncin da Bakura ya yanke bai yi wa 'yan uwan Sajida dadi ba. Sajida ta mike, yayin da take tafiya a hankali ta shiga daki ta dauko gyalenta, gami da turo jifgegiyar akwati shaqe da lefe ta fito ta juya ta dubi mahaifinta ta sake juyawa ta dubi kakarta, ta juya ta dubi Zahra da mahaifiyarta, yayin da su dukka suka zura mata ido tamkar hoto. Ta juya ta dubi Bakura, sai ya kawar da kai gefe bai dube ta ba. Ta yi ajiyar zuciya gami da sharbe hawaye. Ta qarasa bakin qofar fita, sai kuma ta juyo ta dubi mahaifanta babu wanda ya ce da ita uffan, ta juya ta fice. Bakura ya dubi Usman ya ce ya je ya ce da Lurwan direba ya kai Sajida gida. Da Sajida za ta tafi, maimakon su Samira su ji ba dadī, amma sai kowa jikinsa ya yi sanyi.