[7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     *SHAWWAL/JUNE.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *SADAUKARWA WA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 1📑* *__________📖* BARCELONA Duk yadda naso nayi bacci abin ya gagara, tsabar farin ciki tun lokacin sallan Asuba bai yiba na shiga toilet nayi wanka na ɗauro alwala, ina fitowa a parlon na kalli ɗakin yadda aka ƙawata mun shi, nika ɗai na naji na sake fashewa da dariya, murya a bayyane na furta. "Wayyo Daddy nah, ni a rayuwa mai zan maka na nuna maka irin farin cikin da ka sakani a rayuwata"? Na faɗa ina maida hannu na da kyau ina ƙara kankame towel ɗina. Sallaya na shimfiɗa nayi raka'atul fajir, na cigaba da jan carbi inata istighfari, har naji wayata tana sanar dani lokacin sallan Asubah tayi, don tunda zan kwanta Daddy ya karɓi wayana ya saka mun alerm. Tashi nayi nayi sallan Asubah sannan na zauna ina askhar, fuskana ɗauke da murmushi, ina gamawa na ɗauko qur'ani na na fara bitan karatu na, har saida gari ya fara haske tukun na miƙe na tafi gaban mirrow. Wata Red dogin riga na nasaka, wanda yayi bala'in fito da kyau na da ƙuruciyata, wanda banfi 16yrs ba, don banfi 5month da cikawa ba, dai-dai lokacin naji muryan Daddy yana ƙirana dai-dai da buga ƙofan da yakeyi. Da sauri naje na buɗe ƙofan ina dariya na ɗan sunkuyo dai-dai fuskan Daddy ina faɗin, "Good morning my dad," zaro ido Daddy yayi cikin mamaki yana kallona, a hankali yasa hannu akan haɓan shi yana cewa, "sweet heart har kin shiryah"? Dariya na fara yi ina kallon Daddy nace, "ae nayi 2hrs da shiryawa Daddy", sannnan na fito daga ɗakin na saka hannu na riƙe na Daddy mukayi hanyan parlon, inda cikin rawan kaina kaman zan koma cikin shi nace, "Daddy kasan daɗin dana ji kuwa? Daddy kullum zan ta maka addu'a Allah ya baka abinda kake so duniya da lahira", na faɗa ina duban fuskan Daddy da yake ta murmushi. Muna zama a kan dinning ya dube ni hannun shi riƙe da nawa yace, "sweet heart ni abinda nake so ɗaya zuwa biyu ne a wurinki, na farko ki maida hankali akan abinda ya kawoki kinji?, na biyu kuma ki riƙe mutuncin kanki saboda Allah kinji HUMMAIRAH nah". Jikinta duk yayi sanyi ta ƙurawa Babanta ido, kaman bazata yi magana ba, can kuma sai tace insha Allahi Daddy bazaka same ni da aikata wani mummunan abu ba, kodan ma....." sai kuma ta sunkuyar da kanta tana zubar da hawaye. Daddy runtse ido yayi kaman shima zai zubar da hawaye, yana girgiza kanshi, can ya dube yace, "komai zakiyi sweet heart kiyi shi saboda Allah bawai don kina gudun maganan mutane ba, shi zai ki gyara rayuwar ko ko babu idon kowa, kisaka wa ranki Allah yana kallonki kinji". Muna gama shan tea, Daddy ya sakani na fito muka fita har bakin titi, wanda tunda muka fito kallon unguwan da muke nakeyi, wanda yayi matuƙar ɗaukan hankalina, kaman Daddy ya san tunanin da nakeyi ya ƙara damƙe hannu na yace, "BOCABELLA, PASSATGE. sunan street ɗin da kike kenan sweet heart, ya miki kyau"? Murmushin da yake kan fuskana ne ya ƙara ƙaruwa, na damƙe hannun Daddy da ƙarfi kaman zanyi tsalle nace, "Daddy na gode wallahi wurin ya mun kyau, kuma insha Allah na maka alƙawari da first class zan dawo maka, bazan taɓa sakaka kaji kunya ba", na faɗa ina ƙara saurin tafiya ta yadda naga Daddy ma yanayi. Muna isowa kan titin saiga taxi ya tsaya, Daddy ne yace mishi *UNIVERSITY OF BARCELONA* da sauri na buɗe na shiga na zauna, munkai kusan 30mnt kafin muka isa school ɗin, jikina har wani rawa yake yi tsabar yadda naga school ɗin ya mun kyau. Da sauri na kalli Daddy ina ɗan murmushi nace, "Daddy schooƙ ɗin yayi kyau" shima murmushin kawai yayi ƴa tare mana wani bus da naga yana shiga cikin school ɗon da student, wani gini mai kyau naga mun tsaya, nidai kawai bin Daddy nake har muka shiga wani office mai girman gaske, wani bature ɗan luti mai katon tunbi nagani a zaune cikin wannan makeken office ɗin, fuskan shi ɗauke da murna da farin ciki ya taso ya miƙawa Daddy hannu suka gaisa, sannan ya miƙo mun hannu don mu gaisa, amma cikin murmushin da yaƙi barin fuskana, na haɗa hannu na guri ɗaya na matse su a cinyana ina ɗan jujjuya jikina, na amsa mishi gaisiwan shi batare dana miƙa hannu ba, shima dariyan ya ɗanyi yana buga kafaɗan Daddy cikin turancin shi mai daɗin sauraro ya ke cewa Daddy, "Nice doughter ɗin shin"?. Wuri Daddy ya zauna inda baturen ya nuna mishi, nima gefen Daddy na zauna kaman zan koma cikin shi, haka sukayi ta hira a ƙarshe naga ya ɗaga waya ya ƙira wata yarinya, tana shigowa nagan ta kaman zata ɓalle don rama, har inda yake ta ƙarisa ta gaishe shi, daga nan ya mata bayanin department ɗinmu ɗaya da ita, kuma nima doughter shine, saboda haka ta tafi dani har class ɗin da muke lectures. Hannu ta miƙo mun cikin sakin fuska, ban ɓata lokaci ba na miƙa mata muka gaisa inda tana riƙe da hannu na tace, "my name is *VICKY*, ina binta da murmushi nace mata, " *AISHA HUMMAIRAH*" cikin murmushi ta sake cewa, "nice name". Daddy sai binmu da murmushi yakeyi har muka fita, inda kafin mu fita na zo na rungume Daddy nace, "Daddy zaka jirani ne"? yana ɗan dariya ya ɗaura hannun shi a kafaɗa na yace, "zan koma gida akwai abinda zanyi, kina tashi ki nemi taxi ki bashi wannan card ɗin har gidan zasu kawo ki ko sweet heart", ya faɗa yana bina da kallo har muka fita. Muna kan hanya vicky take ta bani labarin yadda last week suka fara lectures, da kuma yadda tayi mamakin tana ganewa, domin ita tun a secondry babu abin da take so irin *ACCOUNTING* Nima murmushi nake binta da shi saboda yadda nake son course ɗin, kuma buri na kenan naga na karanta Accounting, don burina naga na zama chartart acoountant wata rana, har class muka isa vicky sai labarin daɗin course ɗin take bani, amma muna dai-dai da zamu shiga class ɗin take gaya mun wahalar wani course wai shi *FINANCIAL ACCOUNTING* amma ita tanaga tsoron lecturer suke ji shiyasa suke ganin kaman da wahala. Kallonta nayi cikin mamaki nace, "yana baku matsalah ne lecturer"? ɗan ya mutsa fuskanta tayi tana girgiza kanta tace, "no kawai baya dariya ne, kuma yana ɗaukan attendance, kawai dai baya dariya ko kaɗan". Haka muka shiga class ɗin, abin mamaki sai naga bamu fi mu 15 ba, cikin mamaki na dubi vicky nake tambaye ta "ina sauran ƴan class ɗin"? Tana murmushi tace mun mu 15 ne dama, amma kusan class uku ne ko wanne 15, sai lokacin exam zamu haɗu dasu a hall ɗaya. Muna zama bamu 5mnt ba sai ga wani lecturer ya shigo, kana ganin shi kaga ɗan gayu, gashi bayida wani tsayi amma sai wani bouncing yake yi, ƙasa-ƙasa vicky tace mun, "mr solomon, yana ɗaukan mu *COST ACCOUNTING* Ina jijjiga kai batare da na dube ta ba na maida hankalina kanshi, abin sha'awa duk da yau na fara shiga class ɗin amma na fahimci lectures ɗin mutumin yadda baku tsammani, inda yamana wani topic *BUDGET CONTROL* gaskiya na gane lecturers ɗin sosai, haka mikayi lectures huɗu a ranan, a ƙarshe mace ce ta shigo ta mana *TAXATION* india ce amma taji turanci na fitar hankali. har gate muka zo da vicky, inda na samu taxi har gida ya kawo ni, gaskiya na daɗe ina sha'awar kasar spain, inda yau Allah ya kawo ni ɗaya daga cikin state ɗinta, da farin ciki na shigo gidan, daga ɗaki Daddy ya fito yana ware mun hannu, da gudu naje na faɗa jikinshi. *Masoya novel ɗina wannan karon kumun uzuri ba zan dinga typing kullum ba, haka pages ɗina ba za suna yawa ba, nagode da ƙaunarku* *HAKA ZALIKA MRS ZERKS BAKI BAZAI IYA FURTA KALMAR GODIYA ZUWA GAREKI BA, NA BAKI KYAUTAR WANNAN SHAFI BESTY NAH, ALLAH YA BAR ƘAUNA* *©AUNTY NICE•* ✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 3📑* *__________📖* Girgizamata kai kawai nayi alamun babu wani dangantaka a tsakanin mu, wuri ta nema kusa dani ta zauna ƙasa-ƙasa tana gaya mun wai yanzu taji wani ɗan class ɗin mu yana cewa a tarihin Dr Hussain bai taɓa fita a class ya dawo ba, sunyi mamaki da sukaga ya dawo, shiyasa suke tunanin ko yasan ni ne. A hankali na dubeta sannan nace, "Vicky ban san shi ba, a school ɗin nan na fara ganin shi, kuma shima ina tunanin bai sanni ba, don na lura ko kallon fuskana bai yi ba, kawai may be yaga laifina na farko ne, shiyasa yamun uzuri". na faɗa ina kallon ta, ita ma girgiza kai tayi alamun magana na haka yake. Bayan mun dawo break ne muka yi lecture ɗaya sannan muka ta shi, Amal ta dube ni lokacin muna fita a school ɗin tace, "Hummy yaushe zamuje muyi shooping ne? Don gaskiya akwai abubuwan da nake son na ƙara"......kaman bazan yi magana ba saboda tunanin daya cika zuciya ta, har ta manta dani sai kuma na samu bakina da furta, "Mu bari ranan saturday sai muje wani mall dana gani kusa da inda nake, naga wurin yana da kyau da girma, ina ga zamu samu duk abinda muke buƙata a wurin". dafa kafaɗa na tayi muka tsaya dai-dai lokacin da ta tsayar mana da taxi, BAILEN, CARRER DE ta faɗawa mai taxi ɗin sunan unguwan da take, nima na gaya mishi inda nake, saboda ni nafita kusa da school ɗin, haka muka shiga har inda nake na sauƙa ita kuma ta wuce. Ina ƙarasowa gidan da nake wanda gida huɗu ne a compound ɗin gidan, wanda yake kusa danawa ban taɓa ganin an buɗe gidan ba, sai biyun da suke gaban namu suma wasu students ne a ciki amma dukan su maza ne, ina ƙarasowa wanda muke haɗe da shi naga yau alaman akwai mutane a gidan don ina zuwa kusa da wurin naji ƙamshin kaman ana soya ƙwai, har cikin zuciyata naji daɗi domin ina tunanin ko macece a gidan nima na samu wacce zatana tayani hira wani lokacin. Naso ace naga wanda take gidan amma har na shiga gida na ban ga kowa ba, ina shiga direct toilet na shige na ɗan watsa ruwa, riga dai-dai gwiwa na nasaka domin na samu sakewa na ɗan taɓa karatu, ina shiga kitchen naji nayi missing Daddy da yanzu har ya dafa mana abinci, amma yanzu gashi yunwa na keji kuma ina jin lalacin dafa komai, KunKumi na na riƙe ina hararan kitchen ɗin kaman shi ya haɗa ni da yunwan, zuwa can na juya na koma parlon na zauna akan dinning ina ta tunani. Kaman an zabure ni na miƙe na shige kitchen ɗin da sauri, egg guda uku na ɗauko na fasa na fara soyawa saboda na tuna ita ma neighbor nah ma shi naji tana soyawa, ni kaɗai na fara murmushi a zuciyata ina cewa Allah kasa macece a gidan. Bayan na gama na dawo parlor na sauƙa akan ƙwaina gefe ɗaya kuma na haɗa cornflakes ina sha, ko cin rabi banyi ba naji ana nocking ƙofa na, dariya naji ya ɗan suɓuce mun a fuskana, a zuciyata nace hala neighbor na taji na dawo shine ta zo duba ni, sai kawai nayi tsalle na miƙe, ko duba kayan jikina banyi ba saboda murna da ɗaukin zuwa ganin neighbor. Ina buɗe ƙofan sai naji da ƙaran buɗe ƙofan da bugawan zuciyata sunyi a lokaci ɗaya, da ƙarfi na rike ƙofan don kada na faɗi, idona kuma a zare kaman zasu zazzago ƙasa, kuma alokaci ɗaya naji na kasa rufe bakina dana buɗe zanyi magana. Haka zalika shima a gefen shi ba ƙaramin faɗuwar gaba da gigita yayi ba, domin bai taɓa tsammanin ganina ba, domin yayi tunanin namiji ne a gidan don last week kaman namiji yagani ya fito ya daɗe tsaye a ƙofan gidan, shi kuma tun ranan Allah bai nufa ya dawo gidan ba sai yau. Sake juya idon shi yayi yana Ƙara zuba mata ido kuma zuciyar shi tana harbawa kaman zata faɗo ƙasa, kaddai wannan yarinyar da yaji muryanta sak ina na *AISHA* ce a gaban shi, yarinyar da tunda yaji muryanta ɗaxu faɗuwar gaba yaƙi barin shi da wani irin mummunan tsoro a zuciyar shi, duk da ɗazu bai kalli fuskarta sosai ba, kawai muryanta da tsarin maganan ta babu maraba dana Aishan. saidai zuwa yanzu duk ta kunce mishi notinan kanshi daya ga hattah zaro idonta da ɗan bakinta data buɗe kaman na Aisha, kai shi idan ba karya yake so yayi wa zuciyar shi ba sai yaga hatta fuskan kaman na Aisha aka maka mata, sannnan kuma tsayin ta ma kaman na Aishan ne, ba zuciyar shi ba yau yana ji hatta huhunshi ma kaɗawa suke yi, yau wani irin gamu yayi? Shiyasa tunda tayi mishi magana yaƙi yabar kanshi ya dubi fuskanta ɗazu. "Dr mu kai...ne...a..nan...wurin?" Lokaci ɗaya ta samu kanta dayin in'inan da bata san ko tana yi ba ko yanzu ne ya zo mata. Shi dai bai ce mata komai ba sai kaɗuwan da zuciyar shi ta sake yi don jin yadda tace mi shi wai, "Dr mu". innalillahi ya furta a zuciyar shi, kaddai Aisha ce tazo har inda yake? Wato duniyan ƙaramar wuri ne ko? Duk inda kaje sai an tarar da kai? A hankali ya buɗe baki yana kallonta yace," *AISHA*" Zaro ido Humairah tayi da sauri tana duban shi cikin mamaki, sannan tace, "lahhh kaima Aisha kake son ƙirana da shi? Kasan kakana ne kawai suke ce mun Aisha, Daddy yace mun duk ranan da yace mun Aisha sai ya wuni bashi da lafiya, dama kasanni ne? Shiyasa ɗazu dana baka haƙuri sai kaima kamun uzuri a rayuwa ko? Don kasan laifin da mutum zai yi a farko yaka mata ana mishi uzuri, idan ya sake kuma sai ace gangancine ko kuma da son ran shi yayi, ta ƙarisa maganan tana mishi murmushi, wanda lokaci ɗaya yaji faɗuwar gaban shi ya ƙaru, wanda baisan ya dafa jikin bangon gidan da ƙarfi ya furta. "Aisha ya ya kike bina kuma a rayuwa ta, meye ya saura kuma? Bana ce......". sai kuma ya rufe bakin shi da hannun shi da ƙarfi, ya kifa kan shi a kan hannun shi ɗayan daya dafa bangon yana mai runtse idon shi, a hankali yana bawa kanshi haƙuri yana gayawa kan shi ba zai taɓa yiwuwa Aisha ta zauna yadda take kaman daba, bayan yanzu rabon shi da ita ya kai 18yrs, wannan da take gaban shi kuma bazata wuce 16yrs zuwa 17yrs ba. Ya kamata zuwa yanzu ace Aisha ta kai 35yrs, tunda shi dai yanzu yana 39 zuwa 40yrs. Sake ɗago idon shi yayi yana kallonta wanda ita ma zuwa lokacin ta fara tsorata da yanayin da taga ya shiga, tana bin shi da kallo cikin damuwa tace, "Dr mu baka da lafiya ne? Na baka paracetamol?". Juyawa yayi da sauri yayi hanyan gidan shi, duk illahirin jikin shi kuma yana rawa, wannan wani irin kamane tayi da Aisha hatta yanayin yarintar su da shagwaɓar su iri ɗaya ne, idan bai manta ba babu hali da ya zaina yayi shiru za kaji Aisha tana cewa, "na kawo maka paracetamol? Wato ɗabi'un suma ɗaya ne, to ko dai ita ce? A haka har ya wuce gidan shi ya rufe kanshi, sannan ya runtse idon shi bayan ya faɗa kan gadon shi. Humairah tana tsaye har saida ta daina ganin shi tukun ta koma nata parlon ta zauna, sai da ta daɗe idonta yana kallon abincin tana tunanin meye ya samu mutumin nan? Can taji kan ta ba zai ɗauki tunanin ba kawai sai ta share ta cigaba da cin abincinta. Har ranan friday Humaira bata sake ganin Dr ba a cikin compound ɗin su, ko alaman ana zama a gidan ba taga anayi ba, kawai sai tayi tunanin ko yana tafiya wurin familyn shine, don bata jin motsin mata ko yara a gidan, can kuma ta saka hannun ta da riƙe haɓanta kaman mai tunani zuwa can sai tayi dariya tace yes hakane ma tunanina dai-dai ne, wato matar shi da yaran shi suna wani gida, may be matar shi tana aiki a wani wurin ne shiya sa ya barta da yaran shi, shi kuma nan yafi kusa mishi da school ɗin da yake aiki, wataran ya zauna anan wataran ya koma wurinta, sai tayi tsalle ta jinjinawa kanta tana dariya irin tunaninta dai-dai yake. Ranan friday suna da Dr Hussain a 8:00 to 9:30, tun 7:30 suka shiga class, don duk ƴan class ɗin suna tsoron Dr Hussain, suna zama class reps ya tashi yace, "duk ku kashe wayoyin ku gudun abinda ya faru ran monday". kaman ance na bar wayana a kashe sai duk aka juya ana kallona, murguɗa musu baki nayi na juyar da kaina gefe, dai-dai lokacin da ya shigo class ɗin, sai kaji kaman babu sauran wasu halittu masu numfashi a class ɗin duk an ɗauke wuta. Yafi minti uku a tsaye yana duban books ɗin da suke hannun shi, ba tare da ya dubi kowa ba, can ya rufe ya fara musu lectures yana yi yana ɗan zaga class ɗin, wanda bai taɓa musu haka ba sai ranan, yana zuwa dai-dai inda Humairah take zaune ya tsaya ya cigaba da bayanin shi yana tsaye a wurin, can ya miƙa mata hannu alaman ta bashi abu. Duk sai taji ta ruɗe ta waiwaya ta dubi class ɗin taga kowa ita yake kallo, haka shima Dr idon shi yana kanta ya ƙura mata su, batare daya daina bayanin da yake mata ba, a hankali ta nuna mishi bata fahimci mai yake nufi ba, abinda bai taɓa yiba yayi shine ya saka hannu ya buɗe handbag ɗinta ya ɗauko wayanta ya duba yaga a kashe yake, amma duk da haka bai maida mata ba, sai kawai ya jefa a aljihun shi, ya wuce gaban class ɗin inda yake tsayuwa da. A haka yayi musu lecture har ya gama ya fita, kuma ko tunanin ya miƙa mata wayan bai yi ba kawai fitan shi yayi, ita ma ba tayi wani yunƙurin tashi ba ballantana ta nemi ya bata. yana fita Amal ta dube ta tace, "Hummy yaya baki karɓi phone ɗinki ba"? Juya ido tayi cikin yanga da yabi jikinta tace, "idan yana so zai bani ai, ba lallai sai na bishi ba". Amal ta sake cewa, "yaufa friday ne Hummy, kinga sai monday ne fa ya dawo class ɗinnan, zaki iya zama babu wayan?". "idan bai bani ba yaya zanyi Amal?". Kowa class ɗin da abinda yake faɗi, can uwar rawan kai ta taso jiki na rawa ta zo wurin su ta zauna tana cewa, "Humairah yaya me yake faruwa ne?". Humairah ta juya idon ta kaman mai jin bacci tace, "me yasa kuke damun kan ku ne?". Sai ta juya tana buɗe book ɗin da yake gaban ta ba tare data ce komai ba, ganin ba zata ce komai ba sai kowa ya ƙunshe guntun gulman shi yayi shiru, har wanda yake ɗaukan su Eng ltr ya shigo. Har na kai yamma banga alaman Dr a compound ɗin gidan mu ba, duk damuwata yau friday kada Daddy ya ƙirani yaji wayan a kashe ko kuma a hannun wani, nasan Daddy ba zai ji daɗi ba. Can nayi tunanin bari na leƙa ɗayan neighbor na da yake yawan gaishe ni idan zan fita na tambaye shi ya bani aron wayan shi, idan na ƙira phone ɗina naji a kashe, sai na kira Daddy nace mishi na manta wayan a school ne, ina fitowa na kusan cin karo da mutum a ƙofan shigowa gida na, sai dana razana ban san lokacin dana saka ihu ba na juya da gudu kaman wanda naga ƙadangare. Ido ya sake rutsewa yana tunawa wani yanayi kaman irin haka daya taɓa faruwa tsakanin shi da Aisha, ta fito daga kitchen shi kuma zai shiga kitchen suka haɗu, a take ta zunduma ihu ta juya da gudu har saida ƴan gidan suka fito ana tambayan lafiya? Shi dai kallon su ya keyi yana nuna ta da hannu akan su tambayeta shima bai san me ya saka ta ihun ba, duk kan su dariyan Aisha su keyi suna maganan tsoron ta, sai yaji hawaye ya cika mishi ido a ran shi yana cewa, _to ita wannan yarinyar wacece ita ne?_ Duk kamanin su da yanayin su iri ɗaya ne da Aisha, shi yau ina zaiga Aishan shi ya nuna mata mai irinta, amma ya saka wa ranshi yadda ya bar nonon uwar shi to ya bar Aisha har abada, sai yana jin wani hawaye mai zafin gaske wanda duk ranan da yayi wannan tunanin sai yayi hawayen da bai shirya ba, haka ya shige ya rufe kan shi. Humaira tana komawa cikin parlon sai kuma abinda tayi ya fara bata dariya, a ranta tace kullum fa Daddy sai ya mata faɗan yawan tsoron ta, faɗawa kan kujera tayi tana ta dariya, can ta tuna ko wayanta fa bata karɓa ba, sai tayi saurin tashi don tabi bayan shi ta karɓi wayan. *MAI DAMBUN AUNTY NICE, WANNAN SHAFI NAKI NE KE KAƊANKI, KIYI YADDA KIKE SO DASHI, AUNTY NICE TANA MAI KARA JINJINA MIKI, KUMA AMIƘA MUN GAISUWA GUN MAI SUNAN ƳAN GAYU, (JAN PARIH)* *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:35] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 2📑* *__________📖* Daddy duk yaji daɗi ya lulluɓe shi don ganin Humairah cikin farin ciki, a haka yakama hannun ta har kan dinning suka zauna, yana dubanta cike da farin ciki yace. "sweet heart ci abincin ki bani labarin school", itama tana murmushi ta fara cin abincin wanda a tsarin sune idan kana cin abinci babu magana, saboda haka har tagama ci bata ce uffan ba, saidai ta ɗago ta dubi Daddy suyiwa juna murmushi, har ta gama ci sannan ta dubi Daddy tace. "Daddy bari naje na ɗan watsa ruwa sai nazo na baka labari", shima murmushi yayi yana jijjiga kai yana dubanta, itama da sauri ta shige ɗakinta, batafi 20mnt ba sai gata ta fito cikin wando three quater da rigan shi, sai zuba ƙamshi takeyi, gefen Daddyn ta tazauna tana lanƙwashe ƙafanta akan kujeran tana duban Daddyn, cikin zumuɗi ta ringa bashi labarin school ɗin tare da hiran lecturers ɗin. Haka sukayi ta hiran su har lokacin sallan magrib yayi, dukkan su tashi sukayi kowa ya shiga ɗakin shi, bayan sunyi ishaa Daddy ya saka ta ta fito da books ɗinta yana tayata dubawa, dayake shima Accounting yayi sai yana ƙara mata haske akan abinda ya gani a book ɗinta. Daddy bai tafi ba sai da ya mata 2wks, yaga ta ɗan sake sosai tukun ya fara shirin tafiya, Allah sarki Hummairah ranan da zai tafi kaman zatayi hauka takeji, haka tayita kuka har ya tafi, bayan nasihohi daya mata masu shiga jiki. Tafiyan shi da 1wk ta ɗan samu nutsuwa, ta mai da hankalinta akan karatun da tazoyi, zuwa wannan alaƙanta da Vicky ya koma kawai su yi gaisuwa ne, saboda ita Vicky tafi son rayuwa cikin maza, ita kuma Humairah sai suka ɗinke da wata Balarabiya mai suna Amal, wacce sai da Humairah tayi 2wks da zuwa tukun ita tazo, duk da tazo first week da aka fara lecturers, ta kuma gida saboda tana fama da ciwon sickle cell, toh bata dawo ba sai bayan 3wks, anan Humairah taga tafiyan su zaizo ɗaya, saboda Amal akwai son karatu ga kuma nutsuwa. Ranan wednesday around 10:00 muke da *ECONOMICS* dai-dai lokacin wata kyakkyawar indiyar budurwa wanda bazata wuce 30yrs ba ta shigo, wanda ita ke ɗaukan mu economics ɗin, gaskiya matar taji kyau sai wani yauƙi takeyi kamar wata ƴar 16yrs, fuskanta a ɗaure take mana lectures ɗin, wanda ko kaɗan bai mana wuyan fahimta ba, duk da babu wanda tafi takurawa da tambaya irin mu matan class ɗin, don naga daga dukkan alamu macece mai son ƙure mata ƴan'uwanta. 2hrs lecturers ta mana, dai-dai lokacin kuma Financial accounting ya iso ƙofan class ɗin, fuskan shi ɗauke da glass wanda yayi masifan karɓan shi, Dr Khadijah tsayawa tayi da lecturers ɗin ta ƙura mishi ido, abin mamaki ɗaurarren fuskanta lokaci ɗaya ya wadatu da murmushi, ta mishi wani ƙayataccen kallo, ɗagowa yayi ya dubeta sai kuma ya maida hankalin shi kan wayan da yakeyi yana jiran ta fito, haka ta gama yauƙinta ta juya tayi hanyan waje, dai-dai inda yake ta tsaya suka ɗanyi magana kaɗan, shi ya shigo ita kuma tayi hanyan waje. Tunda ya shigo muka maida hankalin mu kanshi domin kowa yana tsoron a wuce shi da abu ɗaya, don munji yace next shigowan shi zai mana text ne, yana cikin lectures kawai sai ƙaran wayata ta karaɗe class ɗin, wanda hankalin kowa ya dawo kaina saboda dokan shine duk ranan da aka bar waya a kunne yana class ɗin toh zai fita. Barin abinda yake yayi yana duban inda ringing ɗin ya fito, har idon shi yakai kaina lokacin dana kashe wayan na ɗago a tsorace ina kallon shi, don bantaɓa tsammanin nabar wayan a kunne ba, don ni babu wani silent danake sakawa kasheta gaba ɗaya nakeyi, saboda ni idan ba Daddy ba babu wani danake da shi da zai ƙirani. Ina buɗe da bakinshi naga yana tattare books ɗin shi ya nufi hanyan waje, fuskan shi ɗaure tamau, yana fita duka class ɗin suka min chaaa akaina, kowa da abinda yake furtawa wanda duk na kasa gane mai suke faɗi tsabar tsoron da nakeji cikin raina. Banyi aune ba kwai na samu kaina da miƙewa cikin gudu nayi hanyan waje, kai tsaye inda nake kallon shi na nufa da gudu, ina isa wurin shi kuma ya buɗe marfin motan shi zai shiga, banyi wani jinkiri ba na sha gaban shi na riƙe marfin motan da saurina ina sauƙe numfashi da sauri da sauri kaman zan shiɗe. Tsayawa yayi yana kallo na cike da mamaki, don shi a iya sanin shi babu wanda ya taɓa gigin taɓa mishi mota ballantana har a sha gaban shi. Cikin hakki na ɗago da sauri ina duban shi nace, "sorry sir, wallahi bantaɓa barin wayana a kunne ba idan na shiga class yauma akasi aka samu, da kuma Allah ya ƙaddara zan maka laifi, ina haɗaka da Allah ka mun uzuri a karo na farko kada laifina ya shafi mutanen class ɗin", sannan na sake murfin motan na haɗa hannaye na wuri ɗaya na ɗaga su, alaman ina neman yafiyan shi, idona suna zubar hawaye na karkata kaina na sake cewa. " plz Dr kamun uzuri kada ƴan class ɗin su tsane ni, wasu zasu gayawa parent ɗinsu, kaga idan Daddy nah yaji zaiyi fushi dani, ka kuma ni kuma zan fita har sai ka gama lectures ɗin kaji Dr mu"! ........ Da sauri ya ɗago yana kallo na da alama zuciyar shi cike take da mamaki na. Baice komai ba ya juya ya koma class ɗin, ni ma na bishi har wajen class na zauna ina ta share hawayena, na nemi wuri na zauna ban sake komawa class ɗinba, tunda ya shiga baice musu uffan ba a game da abinda ya faru ba, kawai ya cigaba da abinda yakeyi, ni kuma ina waje ina sauraran shi, kuma Alhamdulillah duk da bana class ɗin amma ina picking wasu daga abinda yake musu bayanin. Yana gamawa ya fito amma ko kallon inda nake baiyi ba, har zai wuce ta inda nake, sai na samu kaina dacewa, " Nagode Dr mu Allah ya haskaka rayuwar ka yasa kagama da iyayenka lafiya, yadda kamun Uzuri kaima Allah yasa duk wanda ka ɓata mishi ya maka, Allah ya albarkaci rayuwar ƴa'ƴanka" na faɗa ina share hawayen da ya zubo mun. Ina kallon shi yadda ya ɗaga ƙafan shi amma sai ya kasa maida ƙafan ƙasa, gaba ɗaya sai ya kasa tafiya a wurin, har Amal ta ƙaraso ta miƙa mun hannu, hannun ta na riƙe mukayi hanyan class, har muka shiga ina waiwayo wa ina kallonshi bai bar wajen ba, sai naji babu daɗi don bansan meya saka shi kasa tafiya ba. Muna shiga class naji Vicky da ƴan class ɗinmu suna magana akan sunyi mamakin dawowan *DR HISSAIN* sai ɗaya yace, "yadawo ne saboda yariɓyar ƴar country ɗin sune, bakuga har suna wani ɗan kama bama? Toh hala ƴar'uwar shi ne", yana faɗa Vicky ta juyo da sauri tana duba na, sannan tazo wurina tana tambayana dama Dr Hussain ɗan uwa nane?. *HUSAIN 80K, WANNAN SHAFIN NAKANE, IDAN KASO KA SAMMA HASSAN KAƊAN, AMMA NI AUNTY KA AUNTY NICE WA KAI KAƊAI NABAYAR, INA KUMA SANAR MAKA KAI ƘANINE MAI AMANA, NAGODE*. *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 4📑* *__________📖* Ina zuwa ƙofan shi na tsaya ina murmushin gudun da nayi, a zuciya ta nace _hala shima ya razana ne yasa ya tafi ya barni a wurin_ ko kuma shima tunanin shi iri ɗaya ne da Yaya Ahmad ɗin mu, don shi kullum cewa yake al'janu nake da shi shiya sa nake yawan jin tsoro, tunanin haka ni kaɗai sai ya sakani dariya domin tunawa da nayi wata rana bayan Yayan mu ya gama mun faɗa akan yawan jin tsoro na, na juya zan tafi ɗaki fuskana a ɗaure kawai sai naji ihun shi ya tashi da gudu yayi ɗakin Maman su. Nima bayan shi nabi da gudu har ɗakin Maman, sai naji yana cewa Maman, "Gatanan ma sun sakata ta biyo ni, don Allah Mama ki koreta a ɗakin nan wallahi ina mata faɗa sai naji wani abu yabi ta ƙafana ya wuce mai shegen laushi". yana faɗa duk zufa ta jiƙa fuskan shi. Da tsawa Mama ta mun magana akan na fita na bata wuri da shegen ido na irin na mayu, cikin sauri na fito ,ina zuwa parlor sai ido na ya sauƙa akan ƴar kyanwata da ɗazu na same ta a wurin Baba maigadin mu, dariya ne ya so suɓuce mun don sai yanzu na gane abinda yabi ƙafan Yaya Ahmad wato wannan ƴar magen ne yaji laushin jikin ta a kan ƙafar shi, shi kuma yayi tunanin jinnu ne, ina ƴar munafukar dariya naje na ɗauketa na fita da sauri zuwa wurin Baba maigadi, miƙa mishi magen nayi a hankali nace, "Baba ɓoye mun ita anjima zan kawo maka madaranta da kuɗin ƙosai idan Daddy nah ya sauƙo, yanzu idan Yaya Ahmad ya gani zai mun jifa da ita don yana tsoron mage". na faɗa ina komowa cikin gida da sauri na. Ina tsaye a bakin ƙofan Dr Hussain ina ta dariyan abinda ya faru sai kawai naga ya buɗe ƙofan yana kallo ne. Da sauri na saka hannu na na rufe bakina ina maida dariya na, ido na cikin na shi nace, "Dr mu kaima kaji tsoron ko ina da al'janu ne yasa ka gudu ko? Kasan a gidan mu Yaya na Ahmad bai taɓa yadda cewa bani da al'janu ba tsabar tsoron shi, kaima kana tsoro ne?". Na faɗa ina mishi dariya. _*Hasbunallahu wa ni'imal wakil*_ ya faɗa cikin zuciyar shi, bayan ya ƙura mun ido, ganin abinda na faɗa ya sake tuna mishi cewa wataran fa *AISHA* ta taɓa faɗin irin wannan kalman, nacewa ko yana mata kallon mai jinnu ne?, runtse idon shi yayi har zuwa wani lokaci, kaman ba zai buɗe ba amma sai ya sake jin muryana ina cewa. "Dr mu don Allah kayi haƙuri ka bani phone ɗina zan gaishe da Daddy ne, kuma ina tsoron ya ƙira yaji shi a hannun wani kaga ba zai ji daɗi ba, kasan Daddy ya damu da rayuwa ta, kullum yana cemun na nisanci tarayya da maza saboda basu da amana, kaga idan yaji yana hannun ka zai ce amma yarinyar nan ƴar kawai ce, ita dana turo ta karatu me ya haɗata da maza? Bai san kuma kai ɗin ba maza bane kai Dr mu ne ba zaka cuce ni ba ko?". na faɗa ina turo kaina gaba irin ina jiran ya bani amsa. Zuciyar shi ce ta sake yankewa, domin tunawa da irin wannan kalaman daya taɓa ji a wurin Aisha, kuma tsarin maganan Aisha ne cewa, "Yaya Hussain ɗin mu". komai zata faɗa mishi sai ta dangana shi da shi nasu ne, kuma Aisha ce mace a duniya daya taɓa ganin idan bawai mutum ya cuce ta bane ta bata taɓa ƙin yarda da shi, ita kullum tunaninta zuciyar kowa mai kyau ne, saboda haka ita duk macuci sai ya nuna kaman shi, to yau ga wata Aishan a gaban shi irin Aishan su tana mishi irin maganan ta, da kuma nuna mishi yarda a lokaci ɗaya. Hawayen da yake ɓoye wane suka gangaro mishi, amma gudun kada wannan yarinyar mai surutun tace yana kuka a gaban ta sai yayi sauri ya saka hannun shi a al'jihun wandon shi ya fito da phone ɗin ya miƙa mata. Zuba mishi ido nayi cikin alamun rashin jin daɗin yanayin dana ganshi a ciki, a hankali na ɗan matso kusa da shi a hankali nace, "ka tuna da Maman kane?". Sai kuma na ɗan leƙa cikin parlon da kaina, kaman ina neman wani abu, a hankali na dawo da kaina waje cikin ƙasa-ƙasa da murya nace, "Kunyi faɗa da matar kane? Bata maka abinci bane?". Ina kallon shi idona duk a waje domin jiran me zaice mun. Babu shiri naga yayi murmushi kaɗan, kuma sai ya maida fuskar shi irin tada, baice mun komai ba naga yamayar da ƙofan ya rufe shi kuma yana shirin zuwa jikin motar shi domin ya fita a compound ɗin gaba ki ɗaya. Gudu-gudu na ƙarasa inda yake, kaman zan riga shi shiga cikin motan, ganin haka ya saka shi tsayawa yana kallo na cikin mamaki, ni kuma ɗan murmushi nayi sannan nace. "Dr'n mu hala zaka tafi weeƙend wurin wife ɗinka da yaran kane ko? To meyasa su basu zuwa maka sai dai kullum kai kaje? Ko kuma kaine kafi son zuwa ita bata so?". Shi dai kallo na kawai ya keyi cike da mamaki na, bai iya yace mun komai ba sai ido daya ƙura mun, murmushi na sake mishi sannan na cigaba da magana na, wanda ko kulawa da rashin bani amsan da yayi tun fitowar shi banyi ba, nace "Dr'n mu to ka kawo mun yaran ka mana, kaga Daddy ya hanani yawo da naje na gan su, kuma na gajji da zaman shiru ni ɗayan nan". na faɗa ina ya mutsa fuskana alaman har zuciya ta zaman ya ishe ni. "AISHA ki koma kije ki ƙira Daddyn ki, ni kuma plz ki bar ni na fita akwai abinda zanyi". kaman daga sama naji muryan shi yana faɗa mun haka. Matsawa nayi har ya shiga motan ya zauna, ni kuma hannu na yana riƙe da marfin motan, cikin shagwaɓa nace, "Dr'n mu yaushe to zaka dawo? Don Allah ka dawo yau, ni nafi soma ka dawo da su nan na dinga ganin mutanen da zan dinga hira da su". "Hira aka kawo ki kiyi ko karatu?". Ya faɗa yana rufe ƙofan shi, ina kallon shi bai sake cewa komai ba har ya fita da motan shi, na buɗe baki na zanyi magana kawai naji ƙiran Daddy na yana shigowa, da sauri na koma nawa side ɗin domin na nutsu muyi hira da Daddy na. Duk zuba idon da nayi ganin Dr ya dawo yau amma shiru har dare bai dawo ba, ina zaune ni kaɗai na naja tsaki sannan nace, _hala a wurin su zai kwana, to shi in banda shiririta meye na raba gida da matar ka? Kawai ka dawo ku zauna a wuri ɗaya ai ina ga zai fi bada ma'ana._ a zuciya ta nake faɗin hakan, can kuma na faɗa murya a bayyane nace, "Nikam ni Humaira bazan taɓa yadda na raba gida da miji na ba, duk in da yake to nima a wurin nake". ni ka ɗai sai na bawa kaina dariya ni da bani da ko saurayi mai ya kaini ma tunanin wani miji kuma? To idan ma zanyi auren wani irin miji nake so? Kuma ya ya irin tsarin mijin dana ke so zai zama, rufe idona nayi ina wassafa ya ya tsarin shi da kamanni shi yake. Nifa ina son miji fari, ina son miji dogo kaman Nuhu Arabi marigayi, to amma kuma ina son miji mai son ado da kuma son saka turare, to ya ya zai kasan ce kamanin shi?......... Da sauri na tashi daga jingunuwan da nayi domin gaba ɗaya sai naga yanayin Dr nake so, kuma kamanni shi ne suka bayyana mun a zuciyar tunani na, baki na buɗe nace, "Dr kuma ai ya girma da yawa, don daga ganin shi yana da ɗa ko ƴar da ta kai 10yrs, kai haba ba zai yiwu ba, wannan daga gani mata ɗaya ta ishe shi don tsarin shi duk na turawa ne". na faɗa ina kuma kwanciya ta a kan kujeran parlon. Agogon ƙasa ya nuna 10:00pm, ni kuma dai-dai lokacin na fito a wanka, rigan bacci iya gwaiwa na nasa ka, sannan na shafe jiki na da turaren Humra da na taho da shi, hula na mai kama da net na saka, ina cikin gyara gado na wanda ya bi jiki na dole idan zan kwanta sai na sake gyarawa, a lokacin naji an buɗe gate ɗin gidan, kuma naji ana shigowa da mota, da sauri naje na leƙa ta window kawai sai naji dariya ya suɓuce mun ganin Dr ne ya dawo, kaman wani ɗan'uwa na naji zuciya ta ta yi haske. Da gudu na fito a ɗakin nayi hanyar waje, ina buɗe ƙofa na shi kuma yana rufe motan shi, hannun shi riƙe da wani leda mai ɗan girma, banyi shiri ba kuma banyi shawara da zuciya ta ba, kawai na samu kaina da zuwa da gudu na saka hannu zan karɓi ledan hannun shi, fuska na cike da farin ciki ina faɗin, "oyoyo Dr'n mu, dama jiki na ya bani yau kam zaka dawo, ba zaka kwana a can ba, ka taho da ƴaƴan ka ne?". Na faɗa ina leƙa bayan motan. Ina tunanin ya sake mun ledan, amma sai na ji ya ƙi sakewa, da sauri na dawo da fuska na kan ta shi fuskar nace, "Dr'n mu ka bari na ɗauka maka mana, kasan na kasa bacci ina ta tunanin zaka dawo ko ba zaka dawo ba? Kasan ban ci abinci bama saboda tunanin ba zaka dawo ba, yanzu kuma ka ƙi yarda na ɗauka maka kaya? Haba Dr'n mu". na faɗa cikin sakalci da muryan kuka. Sai ji nayi ya sake mun ledan a hannu na, ni kuma da sauri na ƙarasa na shi ƙofan, wanda muke jere da shi, kuma namu yana kallon na waƴan can, ina tsaye ya ƙaraso har in da nake, baice mun komai ba ya saka key ya buɗe ƙofan ya miƙa mun hannu alaman na bashi ledan. Ido na zuba mishi alaman ya barni na wuce mishi da shi ciki, runtse idon shi yayi ya buɗe ya sauke akan nawa, kaman bazai ce uffan ba, sai kuma ya dube ni sama da ƙasa sannan yace, "Dubi irin shigan da kika yi Aisha? Ba kiji Daddy'n ki yace kada ki shigewa maza ba domin zasu iya cutar dake? To ke baki jin maganan Daddy'n kine ko kuma sakacin daga kece? Baki tunanin ni na cutar dake? Duk da kince ni ba namiji bane ba ko?". Ya faɗa yana ɗan buɗe mun idon shi a kaina. Turo mishi baki na nayi gaba kaman zanyi kuka, ina kallon shi nace ai samari ne suke cutan mata ko ƴan matan su, kai kuma ai Malamin mune idan babu idon iyayen mu ai kune iyayen mu ko? Kaga kenan kai ba zaka cuce ni ba, kuma zaka ga ai kaman ni ƴar kace tun da ban riga dana zama budurwa ba, 16yrs fa nake, kasan Daddy da wuri ya saka ni schhol". na faɗa ina langaɓar mishi da kaina. Baice mun komai ba ya juya ya shige parlon, da sauri ni kuma na bishi a baya hannu na ɗauke da ledan, wanda gaba ɗaya nauyi yamun, muna shiga nayi karo da wani daddaɗan ƙamshi mai masifar tafiya da tunanin mutum, ajiye ledan nayi ina lumshe ido, ina buɗewa muka haɗa ido da shi, ya ƙura mun ido yana kallon yadda nake nuna jin daɗi na akan ƙamshin da naji. "Yaya Hussain kai fa ɗakin ka idan mutum ya shigo sai yaji kamar kanshi zai kunce tsabar daɗin ƙamshin da yake yi, ni wallahi duk duniya ban taɓa ganin ma'abocin son ƙamshi ba irin ka, motan ka ya kama ƙamshi, kai kanka ƙamshine sunan ka, ɗakin ka kuma kaman shine company turare". muryan Aisha ya tuno wani lokaci yace ta dafa mishi indomie ta kawo mishi ɗakin shi yaji a kunnen shi kaman yanzu abun yake faruwa. Buɗe ido nayi ina duban yadda ya runtse idon shi, abin sai ya ɗaure mun kai, matsuwa nayi kusa dashi na kira sunan shi a hankali, "Dr Hussain". A razane ya buɗe idon shi ya kalle ni, sannan a zuciyar shi yace _wannan hatta muryan da yadda Aisha ke kiran sunan shi irin nata ne_. wuri ya nema ya zauna bai kalle ni ba yace, "nagode ki tafi kije ki kwanta dare yayi". yana faɗa ya komar da kanshi ya kwantar a saman kujeran da yake zaune yana runtse idon shi. "Dr gobe nayi breakfast da kai? Kana son cin ƙosai da kunun gyaɗa? Kasan ina da abin markaɗa wake, kuma last week ma nayi kunun gyaɗa na saka mishi milk yayi daɗi irin wanda ba a bawa yaro mai ƙiwuya tahm! tahm!! tohm!!!". na faɗa ina jijjiga kaina alaman idan yayi wargi bazan bashi ba. Ƙura mun ido yayi ya sake faɗi a cikin zuciyar shi _wannan kam ko dai Aisha ce su Abba suka turo ta wuri na? Don daga Ummin shi sai Aisha suka fi kowa sanin abinda yafi so da irin girkin da yafi so, to idan ba Aisha bace ya ya aka yi tasan yana son ƙosai da kunun gyaɗa kuma a saka milk a ciki?_. "AISHA Abba ne da Ummi na suka ce kizo nan ki same ni? Sunce miki idan kinzo ki gaya musu ina nan ne?". Ya faɗa idon shi a kaina. A hankali na tako har inda yake na zauna a hannun kujeran da yake, ina duban shi a nutse nace, "Daddy na bai san ka ba, amma yace mun a kwai wasu a gidan da kake, saboda lokacin da ya kama gidan ance mishi dama saura na mutum ɗaya ne, amma bai san ka ba, kuma da ya san ka daya gaya mun don ba ya ɓoye mini komai". na faɗa ina maida fuska na kaman zanyi kuka, don ganin yadda hankalin shi ya ta shi. "Don Allah kije ki kwanta nima kwanciya zanyi". ya faɗa mun ba tare da ya buɗe idon shi ba. Tashi nayi tsaye ina gyara ɗan riga na sannan nace, "don Allah nayi breakfast ɗin da kai"? Jijjiga kanshi yayi alamar eh. "What time kake ta shi saboda nasan time ɗin da zan yi so that kada ƙosan ya yi sanyi, kasan shi idan yayi sanyi baya daɗi, kuma idan an saka shi a cooler zufa ya keyi, baza kaji daɗi ba, shida indomie halin su ɗaya, kawai kyan su ana yi aci a lokacin". "Ya Rabbi". ya sake faɗa a fili bayan ya sauƙe idon shi a kaina, wanda zuciyar ji yake kaman zata ɓalle ta fito tsabar al'ajabin abinda yake faruwa. Ganin nayi hanyar waje da sauri ya buɗe bakin shi yace, "10:00am is okay". ka ɗa mi shi kai kawai na yi na buɗe ƙofan na fita. Ni Aunty Nice to meye wannan ruɗanin da yake damun Dr Hussain? na tambayi Miss Zerks da muke bin bayan Humaira, ita ma duba na tayi cikin mamaki ta ce ni fa Aunty Nice abin yana ɗaure mun kai, don kawai kada kiyi fushi ki kore ni ne kawai yasa ban tambayi Dr Hussain ɗin me yake faruwa ba. tsayawa nayi da tambayan nawa nayi ina kallon ta nace, "ko tayi kama ne da Aishan?". watsa hannun ta tayi alaman bata sani ba, sannan ta ce, "nidai Aunty Nice zan tambaye shi, amma don Allah kada ran ki ya ɓaci, haba hankalina duk yana kan nasan me yake faruwa". hararanta nayi da sauri tace, "Na fasa to". _Plsss and Plsss comment kunji mutanen kir ki._ *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°* *1441H/2020M.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _Shafin Sadaukarwar ki ce Hauwa Alhassan Yunus._ *SHAFI NA 5📑* *__________📖* Ina shiga parlon nayi tsallen murna, a fili nace, "yehhhh gobe idan Allah ya kaimu Dr'n mu zai ci girki na". har ɗaki na shiga baki na bai iya rufuwa ba, sai wani murmushin daɗi nake yi, a zuciya ta nace gaskiya ban taɓa jin zuciyata ta damu da wani halitta ba bayan Daddy na, sai yanzu da nake jin Dr kaman ɗan'uwa na, wanda muka daɗe muna mu'amala tare, ina shiga na wuce toilet na sake ɗauro alwalah, domin yabi jikina bana iya zama babu alwala, ina fitowa na ɗale gado na sai bacci. Washe gari da wurin misalin 8:00 na shiga kitchen, na gyara wake na jiƙa shi, sannan na markaɗa shinkafa da gyaɗa na a tare, ina gamawa na ɗaura kunu na, 8:30 kunu na ya gamu da sauri na markaɗa wake na, ina gamawa na wuce naje nayi wanka, yau ɗaya sai naji kayan mu na hausa nake son sakawa. Wata dogon rigan atamfa na saka wanda gaba ɗaya gaban ta stones ne a jere reras, sai wani ɗaukan ido suke yi, kitchen na koma na buga ƙullin ƙosai na, bayan ya bugu na saka mangyaɗa, yana zafi na fara zuba ƙosan, baifi kasko biyu nayi ba na sauke na juye su a cikin wani kwano mai kyau, dama ina da yaji mai daɗi wanda da zan taho wata ƙanwar Daddy ta kawo mun shi mai yawa, haka na zuba a ɗan ƙaramin rober, na ɗaura akan basket ɗin dana saka ƙosan, ɗayan hannu na kuma ina riƙe da flask ɗin kunun wanda yaji peak milk. Ban daɗe da yin knocking ba Dr yazo ya buɗe mun, ina kallon shi nayi murmushi wanda na rasa me yasa nake jin daɗi idan na kalle shi, yana sanye da baƙin wandon jeans da red ɗin t-sheet a jikin shi, har ila yau idon shi ɗauke da farin glass ɗin da baya barin idon shi kullum. Hannu ya saka ya karɓi flask ɗin hannu na, sannan ya ɗan matsa mun na shigo cikin parlon da yake fitar da daddaɗan ƙamshi, rufe ƙofan yayi ya shigo, kai tsaye wurin dinning ya wuce ba tare da yace mun komai ba, nima ganin inda ya nufa na bishi a baya, muna ajiyewa ya juyo ya kalle ni tun daga sama har ƙasa, amma bai furta ko kalma ɗaya ba, sai dai ƙura mun ido da yayi. Ina ɗan murmushi mai alamar dariya nace, "Dr'mu nayi kyau ko?". Harara na yayi sannan ya buɗe baki yace, "Ni banga wani kyau anan ba, tunda ke baki iya gaisuwa ba, ni kuma bazan gane kin yi kyau ba". ya faɗa yana jan kujeran dinning ɗin ɗaya ya zauna a kai, nima ganin ya zauna sai nayi sauri naja ɗaya na zauna, ɗago kanshi yayi yana duba na, wanda ni kuma a dole raina ya ɓaci sai na zunɓuro baki na gaba, fuska na kaman zanyi kuka a dole bai ce nayi kyau ba, bayan irin zagewan dana yi ina adon. Taɓe bakin shi yayi bai sake bin ta kaina ba, ina gani ya ɗago cups ɗin guda biyu da nasa a basket ɗin ya zuba kunun gyaɗan da sai turiri yake fitarwa, gashi yayi fari sol sai ƙamshin gyaɗa yake fitarwa, ga wani ƙamshin flavour mai daɗin ji yana tashi, ɗaukan ɗayan cup ɗin da bai cika sosai ba yayi ya turo mun gaba na, sannan ya ɗauki ɗayan cup ɗin ya ɗan kurɓi kunun kaɗan, amma sai naga ya juyo da kanshi kaina yana bina kuma da harara, ganin abinda yayi sai gaba na ya faɗi da sauri na kalle shi da bakina kaman zan fashe da kuka nace. "Dr'n mu kunun ma bai yi daɗi bane?". Ko kallo na bai yi ba ballantana nayi tunanin zai bani amsa, buɗe kwannon ƙosan yayi ya ɗauki ɗaya bayan ya buɗe rober'n yaji, ya saka a bakin shi ya tauna, ina ganin shi ya runtse idon shi, sai kuma ya buɗe da sauri ya sake harara na. Ganin abinda yayi kawai sai na fashe da kuka ina buga ƙafa na a ƙasa ina faɗin, "nikam wallahi nasan yayi daɗi Dr'n mu, kullum Daddy yaci abinci na sai yace duk duniya nafi kowa iya girki, kai kuma tun dana shigo baka yaba kwalliya na ba, baka kuma yaba abinci na ba, bayan Daddy yace ina da kyau kuma na iya gayu sosai, idan ya tashi aurar dani sai an yi layi ya zaɓa mun miji". na faɗa ina ƙara fashewa da kuka. "To ki bari hawaye ya ƙara sa ɓata miki mummunan kwalliyan kin, dama ba kyau ki kayi ba". naji muryan shi yana gaya mun ba tare da ya kalli inda nake ba. "Dr'n mu banyi kyau ba ne?". na tashi tsaye ina juyawa a gaban shi ina ƙara gaya mishi bai ganni bane da kyau. Bai sake kallo na ba yace, "zauna kici abincin ki kada yayi sanyi, duk ranan da kika koyi gaisuwa zan gaya miki kinyi kyau ko ba kiyi ba". ya faɗa yana cigaba da cin ƙosan shi da kunu. "Dr'n mu ina kwana". na faɗa ina zunɓuro baki na gaba. Gyaɗa kanshi yayi ba tare daya amsa mun ba, amma ya mun alaman ya amsa, saboda haka jawo plet nayi na zuba ƙosan na saka yajin a gefe na fara ci nima, ya rigani gamawa, bai ce mun komai ba, ya ƙara jawo flask ɗin ya ƙara kunun kusan rabin cup ɗin sannan ya ɗauka ya miƙe tsaye ya koma cikin parlon, kunna T.V yayi sannan ya nemi wuri ya zauna yana kallon news yana kuma kurɓan kunun shi, maida hankalina nayi kan abinci na har nagama ci, ina gamawa na tashi ina maida cup da plets ɗin da muka ci ƙosan cikin basket ɗina. "Aisha ki bar mun flask ɗin kunun". ya faɗa idon shi yana kan T.V ɗin, nima bance komai ba na mayar da flask ɗin na ajiye, sannan na ɗauko basket ɗin na taho inda yake, ina kallon shi nace. "Dr zan tafi me kake so a lunch?". Idon shi masu tsananin kyau a cikin glass ɗin shi ya ƙura mun, ganin haka ya saka ni saurin ɗauke nawa idon ina ƙara maida fuskana alaman zanyi kuka, don ni bana so nayi abu ba'a yaba mun ba, wanda kullum hakan shi yake haɗa ni faɗa da ƴan gidan mu, amma Daddy komai nayi sai ya yaba mun, shi yasa nake jin daɗin yi mishi komai. "Jeki ɗauko mun books ɗin ki kizo". ya maida idon shi kan kallon da ya keyi bayan ya gama faɗin abinda zai ce. Buga ƙafa na nayi a ƙasa ina ƙananun gunaguni, "nikam har yanzu baka ce mun abincin yayi daɗi ba, tunda baka ce nayi kyau ba ai ya kamata kace abincin yayi daɗi, tunda nasan dai ni ɗin mai kyau ce, tunda Daddy yace duk family'n mu babu mai kyau na". na faɗa ina murguɗa mishi baki na don ganin ya juyo yana gani na. Harara na yayi sannan yace, "zaki wuce da shirmen ki kije ki ɗauko mun books ɗin ki ko sai na kira Daddy'n shi na gaya mishi baki son karatu"?. "Toh ai baka da number'n Daddy, ta ina zaka gaya mishi". Kallo na ya ke yi can sai naji ya karanto mun number Daddy. Baki na buɗe ina kallon shi da mamaki, "dama ka san Daddy ne?". "Wuce ki bani wuri ko na kira shi". Da sauri na ɗauki cup ɗin da ya gama shan kunun nayi hanyar waje, ina fita yayi murmushin shi kaɗan yana girgiza kan shi, a hankali yace, "Rigimammiya, komai nata irin na Aishan'n mu, nasan dai Ummi na bata sake haihuwa ba, da nace wannan ƴar Ummi ce, domin Aisha kowa yaganta sai yace babu abinda ta bari na Ummi, yadda nida Hassan babu abinda muka bari na Abban mu, sai dai banbancin hali da mukayi da Hassan". da sauri ya kawar da tunanin a zuciyar shi, domin baya so ya dinga tunawa da su a rayuwar shi, fatan shi yadda yabar su har abada ya zama har cikin zuciyar shi ya manta da su, wanda duk yadda yayi a wannan tsawon shekarun da yayi babu su ya kasa, sai dai idan sun faɗo mishi a rai yayi sauri ya kawar da su. Dai-dai lokacin da yaji Abban shi ya faɗo mishi a rai na furucin da yake yawan yi kullum a kan shi, ni kuma na dawo, ina kallon yadda ya ƙurawa ƙasan parlon ido kaman yana ƙirge, nima yasa nabi wurin da kallo, banga komai ba sai zanen flower carpet ɗin shi da yake tsakiyan parlon kawai nabi da ido, da sauri na ƙaraso wurin shi dai-dai fuskan shi nace. "Dr'n mu yanayin ka irin na mutane masu haƙuri da nutsuwa wallahi, kuma baka da hayani amma ni kuma gaskiya ina da surutu kaman wanda naci.....". Sai kuma na rufe baki na ina dariya. Da sauri ya ɗago idon shi da suka yi ja ya ƙura mun ido, ina dariya na sake cewa, "Dr'n mu idon ka kaman na zaki, dama *ALIYU* aka saka maka". na faɗa ina binshi da murmushi. Da ƙarfi ya runtse idon shi, kuma da ƙarfi ya furta, "Ya Allah". sannan ya buɗe idon shi ya ɗora a kaina yana mai da numfashi kaman wanda yayi tsere, a zuciyar shi kuma yana maimaita, _innalillahi wa'inna ilahir raji'un_, ya fara tuna wata rana haka Aisha ta taɓa gaya mishi lokacin suna zaune a parlon Abba ana karya wa sai ga Hassan ya shigo da fuska a ɗaure yana duban Hussain yace, "Bros wani irin wulaƙanci ne an kirani a waya ba zaka ɗauka kace ina wanka ba, irin haka sai mai kiran yace ina wulaƙanci ne". ya faɗa ya na ture mun ƙafa na da nashi ƙafan don neman ayi faɗa, ni kuma a rayuwa na tsani ka hau kaina da masifa kaman kai ka haife ni, don duk shiru na da haƙuri na bana iya ɗaukan raini da wulaƙanci, shi yasa kafin kaji baki na a abu sai komai ya ɓaci, cikin ɗaure fuska da nuna bana son raini na ɗago zan mishi masifa, kawai sai naji Abba ya dafa kafaɗa na yana ɗan bubbugawa yana cewa. "Ubana Aliyu tabbas kai mai haƙuri ne da nutsuwa kaman mai sunan ka, kada ka yadda ka dinga biyewa ɗan'uwan ka ana jin kan ku, domin shi haƙuri baiwa ne wanda ba kowa yake da shi ba, tabbasa *ALIYU* da mai suna *ALIYU* basu son raini, amma sun kasa masu haƙuri da kuma nuna soyayya wa ɗan'uwan su mai tsafta, shi baka ga sayyadina Aliyu yadda yake son ɗan'uwan shi (Annabin rahma S.A.W ba?) to kayi koyi da shi kaji *ZAKI NA*". Babu ɓata lokaci Ummi ta amsa da cewa, "gaskiya Abban su baka yi mun kara yadda nake maka, nima fa Hassan yaci sunan nawa mahaifin *ABUBAKAR* Kuma kasan yadda shima Sayyadina *ABUBAKAR* ya kasance babban amini kuma masoyin manzon Allah (S.A.W), kuma koda ya kasance shi Hassan mai neman faɗa ne da ɗan'uwan sa ai zaka na min kara saboda dai Baba na mai haƙuri ne da kuma kawar da kai, don dai shi Hassan ya ɗauko halin ƙanwa tace *HAUWA* domin ita ce mai yawan neman tsokana da son ayi rikici". ta faɗa wanda gaba ɗaya parlon muka kwashe da dariya saboda tunawa da halin Aunty Hauwa, wanda babu inda Hassan ya bar halinta kaman ita ta haife shi wurin neman tsokana da kuma masifa, don kullum ta zo gidan mu sai sun kacaɓe da Ummi duk kuwa da haƙurin Ummi, sai dai duk gidan su Ummi babu mai son ƴan'uwa da zumunci irin nata, ga kuma faɗan gaskiya, wanda idan ka ganta sai ka rantse mutum ɗaya ne ita da Ummi tsabar kaman nin su, sai dai banbancin shekaru, tunda mutane biyu ne a tsakanin su. Ina dariya na kalli Ummi nace, "hmmm Ummi wallahi neman faɗan sune da yawan surutun su kaɗai iri ɗaya da Hassan, amma ita Aunty Hauwa ai nine na ɗauko son faɗin gaskiyar ta da halinta na son zumunci, amma shi wannan ai idan na gaya miki halin shi sai kin wuntsila shi ƙauyen ningi, kince sam wannan ba halinki na dattaku irin na mutanen garin *MISAU* yake da shi ba". na faɗa ina kallon Hassan da yake harara na, dariya na fara mishi ina cewa, "ko na faɗa ne my heart?". "Munafur ci kenan zaka koma, don nasan duk inda mai shiru yake, randa ya falle to munafurci zai haɗa, kuma ni nasan Ummi na da Abba na sun yadda da ni kawai nema kake su fi sonka a kaina shiya sa zaka mun sharri". ya faɗa yana jinginuwa da jikin Ummin mu. Abba dariya yayi yace, "kaga shalelen Ummi'n shi, daɗinta ma ga Aisha nan, dole kayi haƙuri da cinyar Ummi". A lokacin Hassan hararan Aisha yayi, ita kuma ta murguɗa mishi baki, wanda kullum na rasa mai yasa basu zama inuwa ɗaya, amma ni bana da lokacin tanka musu. "Dr'mu ka kula ni mana". na mishi magana cikin shagwaɓa, don tunda yayi mun tsawa ya razanani sai kuma ya koma yayi shiru idon shi a runtse, wanda daga dukkan alamu tunani ya tafi. Ƙura mun ido yayi duk alaman hawaye ya cika idon shi, a hankali ya miƙo mun hannu muryan shi can ƙasa yace, "Aishan mu taho wurina ki bani labarin Hussain da Ummi na da Abba na, yanzu ciwon Ummi na yana tashi? Ko kuma tunda komai ya riga ya faru zuciyar ta bazata sake barinta ta samu lafiya ba, zo kusa da ni Aisha na, ni kaɗai nake son ki sama da irin wanda Ummi ta ke miki". Tsoro naji ya lulluɓe ni domin hawaye ne masu gudun gaske suke biyo fuskan Dr mu, wanda duk sai naji na rasa abinda yake mun daɗi, da sauri ina jijjiga kaina alaman ba haka bane, nima hawaye yana zuba mun amma nawa na ganin abinda nake girmamawa yana hawaye shi ya dame ni nace. "Dr'n mu bani bace fa Aisha'n, ni fa Hummaira ake gaya mun, Dr'n mu wacece Aishan? Matar ka ce? Ƴar'uwar kace? Wacece ita ne Dr na?". na faɗa lokacin da sautin kuka na ya ƙaru. "Aisha ce kaɗai take ce mun Yaya Hussain ɗina, ke kuma kina cemun Dr'n mu keda sauran students ɗina, yanzu kuma kince mun Dr'n ki? To wallahi kece Aisha ta, kina neman yi min wasa da hankali nane, Ki taho wuri na Aisha na!!". Ya faɗa da iya ƙarfin shi wanda sai da na zubar da books ɗin hannu na, na fita da gudu a parlon nayi nawa gidan ina kuka, da ƙarfi na shiga na mayar da ƙofar na rufe ina kuka, ina jingine da ƙofan naji muryan Dr'n mu yana cewa. "ki buɗe ƙofan Aisha ki gaya mun wacece ke? Tabbas kece Aisha na, kuma yau zan tabbatar miki da cewa ke ɗin Aisha tace". Da ƙarfi yake maganan wanda lokaci ɗaya naji tsoro ya rufe ni, a zuciya ta nace, "ko dai Aisha'n ba mutum bace? Ko shima Dr aljani ne?". Can kuma nayi sauri na girgiza kaina nace, "Dr na mutum ne, amma Aisha'n ba mutum ba ce". Buga ƙofan yayi da ƙarfi yana cewa, "ki buɗe Aisha ko na ɓalle ƙofan na shigo". Jin furucin shi ya saka na ruga da gudu na shige ɗakina na sake rufu ƙofan ɗakin, duk jikina rawa yake yi, tsabar tsoron da ya shige mun zuciya ta. "Aunty Nice ko ta kitchen zamu koma mu samu hanyar guduwa ne?, don idan wannan aljanin mutumin ya shigo ina ga har da mu zai haɗa". cewar Miss Xerks da tayi zuru-zuru da idon ta tana kallo na a tsorace, nima haɗiyan yawun tsoro nayi ina maida numfashi da sauri-sauri nace, "Miss Xerks ina cikin zama na kika ce anyi sallah lafiya mu fito ɗaukan rahotanni domin masoyan Gaskiya writers su samu goron sallan da bamu basu ba, haka kika izo ƙeyata muka taho har nan spain, tsabar mita bamu tsaya a ƙasar mu ba, da yanzu a nigeria ne kiran Ummu Nabeel zamuyi su taho da rundunan ƴan Gaskiya writers su fitar da mu ko ta saman kwanon gidan nan ne". na faɗa ina fashewa da kuka don wallahi yanayin Dr Hussain ya bani tsoro. Ƙaran buga ƙofan ya saka naga Miss Xerks ta sandare a wurin, nima daga ganin haka naji komai na hannu na sun zube, babu sauran ɗaukan rahoto sai mun farfaɗo, saboda haka a jiraye mu tukun mu dawo hayyacin mu. _Masoya na masu bibiya ta godiya nake a gare ku, Kar dai ku manta da danna min vote da kuma yin comment domin jin ra'ayoyin ku._ *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 6📑* *__________📖* Nafi awa ɗaya a tsugune a wurin ina kuka, don ina jin hayaniyar sauran ƴan gidan da suka fito suka bawa Dr haƙuri, kuma nayi tunanin ko sun ɗauka laifi nai mishi yasa yazo yake masifan na buɗe ƙofan, a hankali na tashi na hau kan gado na, wata zuciyar ta bani shawarar na gayawa Daddy, amma wata zuciyar tana kwaɓa na da cewa, "ke Humaira Daddy'n ki yana sanin abinda ya faru zai zo ya canja miki gida ko kuma ma ya canja miki school, kuma daga wannan ranar zai zamo kin daina ganin Dr ki". Ɗan juyawa gefe ɗaya nayi har lokacin ido na bai daina zubar da hawaye ba, a fili na furta, "Dr'n mu me ya sa ka ke mun kallon wata ce? Nifa wallahi Humaira ce ba Aisha ba". na faɗa hawayen ya na ƙara bin fuska na. Da ƙyar na ta shi nayi sallar azahar na sake komawa gado na kwanta, haka la'asar ta same ni, shima tashi nayi na sake hawa gado, banfi ƴan mintuna ba Daddy ya ƙirani, jiki na har rawa yake don fargaban ko zai gane murya na nayi kuka, ina ɗauka a sanyaye na ce. "Hello Daddy na". sannan na yi shiru ina jin bayanin da ya ke mun cikin mamaki. "Sweet heart jiya wani lecturer ɗin ku ya ƙira ni, sunan shi Dr Hussain ya gaya mun shine yake gefen gidan ki wanda na ce miki mai shi baya nan ne lokacin da mu ka zo, amma ance mun a kwai mutum a gidan, ya gaya mun kin fito za kije school kika yar da wayan ki a ƙofan gida shine ya ɗauki number na, mun gaisa ya gaya mun kina ƙoƙari a school sannan kina kula da tarbiyan da na baki, sannan idan na amince zai dinga miki extra lesson a gida". Rufe ido na nayi hawaye yana bin fuska na, wanda ni kaina bansan dalilin shi ba, can naji muryan Daddy yana cewa. "Kin amince da yanayin shi da kuma mutuncin shi? Ko kuma na ba shi haƙuri? Don ni naji daɗi da ya iya gaya mun kanshi da kuma niyyan shi, kuma daga dukkan alamu ba yaro bane, don ban ji rawan kai a al'amuran shi ba, amma ke me kika gani? Saboda shi mugu baida kama, kullum ina gaya miki". "Daddy ba yaro bane, kuma ina ga ma kaman yana da family shima, aka sari ma yana yawan mun faɗa ko idan na fito da ƙaramar riga, kuma babu shirme a al'amuran shi ko kaɗan Daddy, ni dai ta wuri na ba bu komai, umurnin ka nake jira". "Ba bu komai sweet heart, sai dai zan ja miki kunne ki kula da tarbiyan ki da kuma mutuncin ki a duk inda ki ka samu kan ki, ki kuma tuna rayuwar mace da na namiji a kwai ban-banci, Allah ya miki albarka". Bayan munyi sallama da Daddy na ta shi na shiga na sake wanka, ɗauko jaka na nayi da niyyan na yi karatu amma abu ya gagare ni, a hankali na fita zuwa parlor na, na daɗe a tsaye ina jayayya da zuciya ta, shin na leƙa Dr ne ko kuma na bari, kada naje bai huce ba ya sake rarako ni. Zuwa wani lokaci dai na haƙura na daure, ina zuwa bakin ƙofan shi zan fara knocking sai ɗaya daga cikin ƴan gidan mu mai suna Peter ya fito daga na shi gidan, yana ɗan murmushi ya ƙaraso inda na ke tsaye, yana kallo na da dariya kaɗan a fuskan shi yace. "Preety me ya faru naga kina gudu Oga kuma ya biyo ki ran shi a ɓace? Any way ba sai nasan me ya faru ba, don nasan almost shekaru uku muna tare da shi anan, ban taɓa ganin yayi faɗa da kowa ba, babu ma mai zuwa gidan shi idan ba ke dana fara gani kin shiga ba, gashi kin saka naga ɓacin ran shi sosai ɗa zu, don na ba shi haƙuri amma naga ya fita a motan shi ran shi a ɓace". Yana gama bayanin shi naji raina ya ɓaci, wato Dr yayi fushi ne shiya sa ya bar mun gidan? Hala ma wurin matar shi ya tafi domin ta kwantar mishi da hankali, ni kuma zuciya ta ta fashe ni ka ɗai ko? Hmmm dawo da kallo na nayi kan Peter ina murmushi, domin bana son ya fahimci wani abu, ina kallon shi nace. "kasan shi cousin ɗina ne, so baya son yaga bana karatu, shi yasa ɗazu dana ce ni zanje na kwanta ne ba lokacin zanyi ba shi ne ran shi ya ɓaci, ni kuma na gudu ne ka da ya saka ni yi dole". na faɗa ina ƙara murmushin fuska na. Shima murmushin ya yi ya na ƙara gyara tsayuwar shi, yana duban cikin ido na yace, "gaskiya preety baki kyauta ba, ai duk wanda ya ke so ka yi karatu shi mai son ka ne, kinga gaskiya ki daure kiyi karatu idan kina so ku shirya da brother'n ki, kinga shi mayen karatu ne fa". Ya ƙara sa faɗa ya na juyawa da dariya a fuskan shi. Ganin ya juya nima na koma nawa side ɗin zuciya ta cike da tunanin me yasa ran shi zai ɓaci irin haka? Nifa na gaya mishi gaskiya bani bace Aishan amma yaƙi yadda, to ko dai yana da wani problem ne a brain ɗin shi? Kai nasan ma ba shi da shi, kawai hala yana son Aisha ne yasa yake ga kaman mu ɗaya saboda nima suna na Humaira duk Aisha ne, to koma meye ne ohoo, ni dai bazan sake yadda ya mun maganan ta ba, kada wata rana naje ya mare ni, na faɗa ina zunɓura baki na gaba. Har na kwanta barci babu alamar dawowar shi, ban ji daɗi a raina ba amma haka na kwanta, banda firgici da faɗuwar gaba babu abinda yau na keji cikin bacci na, wanda ko kaɗan bai mun daɗi ba, har a kayi asuba a haka na ta shi nayi salla, bayan nayi azkhar nayi karatun ƙur'ani na koma na ɗan kishingiɗa a kan sallayar. Da safe ina tashi nayi wanka amma duk yadda na so na daina damuwa da rashin dawowar Dr abin ya ƙi barin zuciya ta, haka naje na dama quaker oats na sha a dole ba don raina ya so ba. Wuraren ƙarfe 10:00 kiran Amal ya shigo mun, a hankali na ɗauka na kai kunne na, da ƙyar baki na ya amsa mata da sallaman da tayi mun, tambaya na tayi akan da yaushe zamu je shooping ɗin? Cikin kasala nace mata ta bari muje next week domin yau da ciwon kai na ta shi da shi, tausaya mun tayi sannan tace mu bari sai next week ɗin. Ranar monday da naje school na ji ana cewa Dr Hussain yayi tafiya ba zai samu daman zuwa mana lectures ba, gaba ɗaya sai naji na nemi nutsuwa na na rasa shi, haka aka yi ta mana lectures amma bana ganewa. Gaba ɗaya school ɗin da ƙasar sun fitar mun a raina, kasan cewar har ranan friday babu Dr Hussain babu labarin shi, duk wanda ya ganni yaga rashin nutsuwa a tattare da ni, domin tsabar zuwa duba ko Dr ya dawo har sai da muka saba da Peter da ɗaya neighbor ɗin mu mai suna David, don kullum na je in duba shi sai mun haɗu da su, har muka fara zama muna hira da su, wataran David zai ce na fito da books ɗina ya ɗan nuna mun wani abu, don yafi zaman hiran, saboda shi David bai cika son surutu ba, don shima alama ya nuna mayen karatu ne, dukkan su suna master ne a school ɗin mu, don bayan sun gama first degree ɗin su basu tafi ba, karatun su suka ci gaba da yi. A haka kullum yamma za ka gan mu mu dukan mu ukun a zaune a ɗan wani wuri da aka saka kujerun ƙarfe, kuma wurin akwai shuke-shuke a wajen, don dama a wurin nake yawan ganin David yana karatu. Har ranan friday ban ji ɗuriyar Dr Hussain ba, kawai sai na samu kaina da kwanciya kaman mai rashin lafiya, don ranan saturday ko fita kasa yi nayi, har a kayi sallar la'asar saiga Amal ta zo a kan muje shooping, babu yadda na iya dole na ta shi na shirya domin muje. Ina shirin rufe gidan sai ga kiran Daddy ya shigo, jiki a saɓule na ɗauki wayan na kara a kunne na, ina jin kaman na saka mishi kuka. "Sweet heart! Yaya na ji muryar ki wani iri, ko ba ki da lafiya ne?". Ya faɗa muryan shi cike da damuwa. "Daddy kawai karatun yana yawa ne shi yasa nake jina kullum a gajjiye, yanzu ma har na kwanta na tuna a kwai shooping ɗin da za muje mu yi ni da Amal, shine na ta shi mu ka fito". "Sweet heart idan ba za ki iya zuwa ba ko zaki bari na gayawa Dr'n ku yazo ya kai ku? Don yanzu muka gama waya da shi yake ce mun shima yanzu haka yana hanyar dawowa gida, ina ga idan bai gaji ba ya kama ta yazo ya kai ku ko?". Ajiyar zuciya na sauƙe tare da runtse ido na, sannan a hankali na furta, "Daddy kuna waya da shi ne dama?". Dariyan Daddy naji sannan naji yana ce mun, "Kullum sai mun yi waya da shi, kuma yana gaya mun irin ƙoƙarin da kike yi, yanzu ma haka yace mun kina kula da kan ki ba ki kula ƙawayen banza ko samarin banza, kuma naji daɗin hakan, don har nace shima yana tsawatar miki idan yaga za kiyi ba dai-dai ba, duk da nasan baki da problem ta nan Humaira na". Kallon inda Amal ta ke tsaye nayi, sannan na maida hankali na kan wayan ina tambayan Daddy, "Daddy nan gidan kaji yace zai zo ko gidan wife ɗin shi?". Na faɗa ina tsoron kada Daddy yace mun can zai je. Dariya Daddy yayi sannan yace mun, "Gaskiya ni ban iya mita ba, don ban taɓa tambayan shi yaya matar shi ba, don shi ma bai taɓa gaya mun ba". Haka mu kayi sallama da Daddy, na ƙara sa wurin Amal mika wuce bakin titi domin zuwa shooping ɗin mu. MAREMAGNUM MALL na gani rubuce a gaban mall ɗin da muka je, gaba ɗaya wurin sai naji ya tafi da hankali na, domin ba ƙaramin kyau ya mun ba, cikin jin daɗi da na ji damuwa na ya ƙaurace mun na wannan lokacin, muka saka ƙafan mu cikin mall ɗin. Muna shiga Amal ta fara ɗiban abin amfanin ta, aka sari kayan maƙula she naga tana ta ɗiba, sai can kuma naga ta maida hankali wurin sayan cosmetics ɗin ta, Amal tana ɗan jan ƙafanta yau tunda muka fito, wanda alaman ciwon ta ne yake sanɗan ta, ganin kaman kayan ya fara mata nauyi, don sai ya mutsa fuskan ta ta keyi, ya saka na miƙa hannu ina mata murmushi na ɗauka mata. ita ma murmushin tayi ta miƙa mun, sannan naga tayi hanyan wurin wasu takalma flats, ganin haka ni kuma nayi wajen turaru ka. Dr Hussain? Dr Khadija economic lecturer ɗin mu ƴar india, su na gani a gaban turaruka suna zaɓan turare, gaba ɗaya Dr Khadija cikin fara'a take, ga wani azababben kyau da tayi da shigan su na sarii, wani Red colour da Golden a jiki, sai miƙo mishi su ta keyi tana nuna mishi, amma shi kuma fuskan shi a matuƙar ɗaure, kaman bai taɓa dariya ba, sai wani kakkaucewa ya keyi, gaba nane yayi mummunan faɗuwa, a zuciya ta nace. _Kaddai ita ce matar shi?_ Lokaci ɗaya na ji ido na ya ciko da hawaye, kuma ni ban ci gaba da abinda na keyi ba kuma ban tafi ba, ƙura musu ido nayi hawaye yana shirin zuba mun a ido na, ga wani zafi da bansan irin shi ba ya ziyar ci zuciya na. Kaman ance ya ɗago kan shi, caraff Sai idon mu suka haɗu dana juna, dai-dai lokacin hawayen ido na suna gangarowa, wanda ko kaɗan ban san da zuwan su ba sai dai ɗumin su kawai naji, ƙura mun ido ya yi, yadda nima ƙura mishi ido na nayi. Juyowa Dr Khadija ta yi don nuna mishi wani turaren da ta ɗauko, amma abin mamaki sai taga Dr ya ƙurawa wata ƴar ƙaramar yarinya ido, gaba ɗaya ji tayi ya ɗaure mata kai al'amuran, domin yaushe babbar mace ma ta ke ɗauke hankalin Dr ballanta na ƴar ƙaramar yarinyar nan, da ɓacin rai Dr Khadija ta juyo ta dubi Dr tace. "Me ka ke nufi ne Dr?". Ko kallon inda Dr Khadija ta ke bai yi ba, kawai ƙura mun ido yayi shima yana kallo na. Hararan shi nayi na juya na bi inda Amal ta ke, ita ma ta gama ta na nema na. Wurin biyan kuɗi muka je na a jiye mata kayan, kallo na ta ke da mamaki amma bata ce mun uffan ba ganin yadda hawaye ke bin kunci na, haka aka buga mana aka bamu total, ɗauka mata kayan nayi har inda zamu hau taxi ba tare dana ce uffan ba, ita ma ba tace mun uffan ba. Muna shiga sai gasu sun fito dukkan su ransu a ɓace, daga ganin su kasan a ɓace ran su ya ke, ƙura mishi ido nayi har muka bar wurin. Muna isa gidan Amal naga ta ɗan jumm kaman baza ta fita ba, can kuma sai ta fita tana ya mutsa fuska, a hankali na dube ta nace, "Me yake faruwa da ke ne? Naga kaman ba kya jin daɗi ko"?. Kallo na ta yi wanda idon ta gaba ɗaya sun ɗanyi kaman green kaman yellow, tana duba na fuska a ɗan ya mutse sannan tace, "sister tun da yau na ta shi ƙafa na ya ke mun ciwo, amma na sha magani, idan Allah ya yarda zai yi sauƙi". ta faɗa ta na fita cikin dauriya. Duban ta nayi nace, "sister ko dai mu tafi gida nane ki kwana? Kada na tafi ciwon ki ya tashi cikin dare, hankali na ba zai taɓa kwanciya ba idan na tafi na bar ki". Amsa mun tayi da "to", sannan muka sallami taxi ɗin, kayan na ɗauka mata har cikin gidan ta, wanda suke su biyu ne a compound ɗin, har parlor na a jiye mata kayan, sannan ta ƙira Abban ta ta faɗa mishi yadda muka yi. Karɓan wayan yayi ya mun godiya sosai, sannan muka ɗibi kayan ta da maganin ta, abin tausayi kafin mu fita a gidan sai da ts shafa wani magani mai ɗan karen zafi a ƙafan ta, wanda zafin sai dana ji shi har ido na, amma ita alaman bata ma jin zafin, haka muka fito muka tari taxi har gidan mu. *_FATIE YAWALE, WANNAN SHAFI NAKI NE KYAUTA NA BAKI SABODA KASAN CEWAR KI ƘAWAS MAI BABBAN DARAJA A WURINA, ALLAH YA BAKI ƳAN UKU SAU UKU NAKE MIKI FATA, MASOYAN ANNABI SUCE AMEEN_* *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 8📑* *__________📖* Muna fita waje ya sa ke hannu na ya na bina da harara, tsayawa na yi baki na a zunɓure ina ta ƙunƙuni ban ko kalli inda yake ba, ba mu daɗe da tsayuwa ba, ya tsayar mana da taxi mu ka wuce gidan mu. Muna fitowa a taxi ɗin ya bini da harara, ni dai bance komai ba sai murguɗa baki na da na ke ta yi, kuma ban kalle shi ba, amma nasan yana kallo na, kuma yana sane da abinda na keyi. Har na saka key ina buɗe gida na ya matso inda nake, cikin nuna iko da gadara yace, "kada na sake ganin kin shiga motan Dr nan, idan ba haka ba kuma zan mugun saɓa miki, idan kin tashi tafiya ki mun magana". yana gama faɗin hakan ya juya yayi na shi hanyar gidan. Tsayawa na yi ina bin shi da kallon mamaki, baki na a buɗe saboda mamakin shi, yana ƙarasawa gidan shi ni kuma na ɗaga murya da ƙarfi nace, "To kai ɗan'uwa na ne da za ka takura mun? Kuma sai na ƙira shi ya kaini asibiti, ai kaima na ga matar ka kake ɗauka a motan ka, ko na hanaka ne?". Tsayawa ya yi kaman ba zai juyo ba, amma ganin ya juyo yana kallo na bakin shi ɗauke da murmushi, na yi sauri na shige gida na na rufe ƙofan, don na san murmushin naugunta ne, don banga alaman na tsakani da Allah ba ne. Ganin na gudu sai ya wuce parlon shi yana ta murmushin shi. Kowan mu yana shiga yayi hanzarin ɗalewa gado, ranan da ƙyar na tashi nayi sallan asuba, sannan na sake komawa baccin, bani na tashi ba sai after 10, a razane na buɗe ido na ina kallon time, ganin da gaske haka lokacin ya yi ya sakani tashi da sauri na shiga toilet na yi brush na yi wanka, ina fitowa na ɗauki waya na na ƙira number'n Amal. Yana fara ringing bai daɗe ba aka ɗauka, naji muryan Amal a hankali ta ke mun magana, haƙuri na fara bata ina gaya mata wani irin bacci ne ya tafi dani, don sai yanzu ma na tashi daga bacci, amma tayi haƙuri me zan kawo mata tayi breakfast? Sautin dariyan ta naji sannan ta ce, "Ki kwantar da hankalinki sister, komai da ka ke buƙata asibitin suna maka, kuma already ma Dr Hussain tun 7:30am ya kawo mun break, amma yasamu ma har suna bani, so kar ki damu kan ki, kawai kizo na ganki kafin su Abbu na su iso". ta faɗa tana mun dariya a hankali. Ina ajiye wayan na wuce kitchen na haɗa tea cikin sauri-sauri, ina gama sha na fito nayi ɗaki na, shima da sauri na shirya na fito domin tafiya duba Amal, ina fitowa na harari gidan Dr Hussain sannan na murguɗa baki na, dai-dai lokacin Peter ya fito daga nashi gidan, sauƙa nayi na ƙarasa inda yake muka gaisa, yana duba na da tausayi yace, "jiya a can ki ka kwana Preety?". Dariya na ɗanyi kaɗan na ce, "gida muka dawo ni da Dr Hussain saboda hospital ɗin basu bari a kwana da patient". sai naga ya yi sauri ya duba gidan Dr Hussain sannan ya juyo in da na ke yana murmushi yace, "Dr yana kishi akan ki Preety, halan yana so ya ɗauke sister shi ba zai bari ma kowa ba". Baki na buɗe cikin mamaki ina duban shi, sannan nima na kalli gidan Dr da wuri nace, "rufa mun asiri, ni kuma mai ya kaini auren tsoho? Kasan Dr nan ya kai 40yrs kuwa, kuma baka ga matar shi mai kyau ba ce, me zai yi da ni ƴar cukala dani, kawai masifan shi ne ya sa ka ya bimu bawai so ba". Peter yana duba na da mamaki yace, "dama yana da mata ne bamu sani ba?". Zaro ido nayi na ce, "tuntuni kuna ta re da shi baku san wife ɗin shi ba sai ni dana zo daga baya? To Dr Khadija ce fa wife ɗin shi". na faɗa kaman zanyi kuka. Dariya mai ƙarfi Peter yayi sannan yace, "your not serious baby, ai Dr Khadija kowa yasan tana son Dr, amma shi bai taɓa kula ta ba ma, kuma kin bani haushi da ki ke cewa wai tafi ki kyau, ke kinsan irin kyaun ki kuwa?". Yana bina da kallo yana duba agogon shi kuma, lokacin David ya ƙaraso in da muke tsaye, idon shi cikin ido na sai bina da kallo yake yi, yana ƙarasowa yace, "Preety kinyi kyau sosai, an taɓa gaya miki babu mai irin kyawun ki kuwa"?... Da sauri Peter ya amsa da cewa, "gaya mata dai tasan irin yadda ta ke da masifar kyau, amma kyawun wata Dr Khadija yana ba ta tsoro". Ni dai yau wani daɗi nake ji a raina, saboda sun yabe ni sunce nafi kowa kyau, sannan kuma Peter yace mun Dr na ba shi bane mijin Dr Khadija, sai wani smilling kawai na ke yi, a haka David yace, "ina za kije? Ko hospital za ki koma?". Ɗaga mishi kaina nayi alaman ehh. "To bari mu kai ki, muma church zamu wuce yau sunday, sai mushiga mu duba jikin friend ɗin kin". muna shiga motan naga Dr ya buɗe gidan shi ya fito, kuma daga ganin shirin nashi na fita ne, lokaci ɗaya naji gaba na ya faɗi, a raina nace, "Allah yasa kada ya mun masifan na bi su David". har muka fita idon shi yana kan mu, nima kuma shi ɗin na ke gani. Har ɗakin da ta ke muka shiga tare da su David, suna gaishe ta suka tafi, har lokacin tana kwance ana mata ƙarin ruwa, gefen ta na matso na zauna, na saka hannu na a kan ta ina ƙara gaishe ta da jiki. Murmushi ta yi tana maida idon ta tana rufewa, alaman wani baccin ta ke shirin komawa, abin tausayi gaba ɗaya kwana ɗaya tayi wani mummunan ramewa, wani irin tausayin ta na keji a cikin raina, na daɗe ina kallon ta cikin jimami, can naji ƙira yana shigowa waya na, da sauri na ɗaga wayan don kada ta tashi. Daddy na na gani yana yawo a saman screen ɗin, da sauri na ɗauki wayan na kara a kunne na, gaishe shi nayi, shi kuma ya tambaye ni ya ya jikin Amal? Bayan mun ɗan gaisa da shi na ajiye wayan, sai naji an buɗe ƙofan ana shigowa, kafin na ɗaga kai na dube shi ƙamshin shi ya fara isowa gare ni, da faɗuwar gaba na ɗaga ido na nadubi in da ya ke, shi ma idon shi duka biyu sauƙe suke a kaina, kaman ba zai shigo ba ya tsaya ya ƙura mun ido daga in da yake tsaye, ganin haka na sauƙa a kan gadon na ƙara sa gaban shi, turo baki na nayi ina kallon shi, cikin shagwaɓa nace, "To ba kai bane kazo asibitin ba ka tashe ni ba, shi ne nima na taho ban gaya maka ba". Na faɗa ina ɗan kawar da kaina saboda irin kallon da ya ke jifa na da shi. Kukan shagwaɓa wanda babu ko ɗigon hawaye na fara yi, ina bubbuga ƙafa na a ƙasa, "to ni me na maka kake kallo na haka? Bayan nasan ban maka komai ba". na faɗa ina kallon shi. Wucewa yayi zuwa kan kujeran da suke ɗakin guda biyu ya zauna a kan ɗaya, bayan ya daina kallo na ya maida idon shi kan Amal. "Aisha baki gaya mun meye gyenotype ɗin ki ba? Tun jiya kuma na ke tambayan ki, ko kin raina ni tunda kina da su Peter ko?". Matsowa na yi in da yake na zauna a ɗayan kujeran ina kallon shi, fuska na ɗauke da murmushi, ƙasa-ƙasa da murya don kada na tashi Amal nace, "Dr mu kasan yau su Peter da David suka ce wai ina da kyau har ma nafi matar ka Dr Khadija kyau". Na faɗa ina riƙe haɓa na alaman abin ya ban mamaki duk irin kyawun ta amma a kace na fita kyau. Harara na yayi sannan yace, "saboda baki da hankali kinje kin tsaya a gaban ƙattin banza suna ce miki wai kina da kyau, ke kuma don shirme har kina biye musu kina yarda ke mai kyau ɗin ce ko? Har kina haɗa kan ki da kyawun Khadija?". Tsaki ya ja mun ya maida kan shi kan Amal da yaga tana ɗan motsawa. Ƙura mishi ido nayi ina jin zuciya ta kaman zata faɗo, don wani irin masifan zafi na ke ji, ina kallon shi kaman na tashi na shaƙe shi, murya a hankali domin rawa ya ke mun nace, "Dr'n mu don ita wife ɗin ka ce shi yasa kafi ganin kyawun ta a kaina ko? To kai me ya sa ba ka ganin ina da kyau ne? To wallahi sai na gayawa Daddy ka ce matar ka ta fini kyau". Ɗauko waya na nayi ina neman number Daddy, sai ji nayi ya ƙwace wayan a hannu na, "saboda hankali ya miki karanci shi yasa za ki ƙira Daddy a wannan shirmen banzan na ki ko? To ke me ya dame ki idan ni bance kina da kyau ba? Ba sauran wanda kike so suga kyawun ki sun gaya miki ba". "To ni kai na ke so kace ina da kyau, ai ita kana ganin kyawun ta, ni me yasa baza kace ina da kyau ba, ni kai nafi so ka faɗa". na faɗa ina zunɓuro mishi baki na. Tsaki ya ja yana duban agogon hannun shi, sannan yace, "ni ai banga kina da wani kyau ba, saboda kyawun Khadija ba ya bari na naga kyawun kowa". "Dr'n mu ba kace ina kama da Aisha ba, to ita Aishan bata da kyau ne? Ai ya kamata saboda ita kace ina da kyau, tunda ina kama da ita ai ya kamata kana ganin kyau na saboda darajan ta, kasan ko a lahira wani yakanci albarkacin wani". na faɗa ina matsuwa kusa da shi. "Yayan mu don Allah ni mai yasa baka ganin kyau na ne? Kullum sai kace Fatin Aunty Hauwa tana da kyau saboda tana kama da Aunty Hauwa, to ai nima ina kama da Ummi da Aunty Hauwa, kuma ni nafi Fatiman kyau saboda ita bata ɗauka asalin kaman Aunty Hauwa ba, ta ɗan ɗauko kaman Baban ta ai, ni ma don Allah Yayan mu kace ina da kyau mana". muryan Aisha ya ji wani lokaci Aunty Hauwa tazo da ƴar ta Fatima wanda bata fi 5yrs ba, yarinyar ta mishi kyau saboda gashin ta da Aunty Hauwa ta gyara, shi dai yana so yaga mace mai gashi sosai a rayuwar shi, shiya sa Fatiman ta mishi kyau, bai iya ya ɓoyewa ba kuma ya faɗa, shine Aisha ta ke mitan ita bai ce tayi kyau ba, wanda ɗabi'an Aisha ne ita kullum ace tana da kyau, gashi kuma yau wannan mai rikicin ita ma haka ta ke. Tunawa da hakan ya saka ya dawo da kallon shi kaina, ƙura mun ido yayi yana kallo na, can sai yace, "mai yasa ki ka damu dani sai nace kina da kyau?". Kallon shi nayi kaman zanyi kuka nace, "ni kawai kai kaɗai na ke so kace ina da kyau, kasan me yasa na ke son hakan Dr'n mu"? Girgiza mun kai ya yi alaman a'a, dariya nayi mai ɗan sauti, sannan na sunkuya ƙasa-ƙasa da murya nace, "nifa kana mun kyau sosai Dr'n mu, kuma ai ni nace kana da kyau kuma kai mai ƙamshi ne, ya kamata kaima kace Humaira kina da kyau kuma kin iya girki mai daɗi". na faɗa da yanayin kwaikwayon muryan shi, ina duban shi ina dariya a hankali don kada na tashi Amal. Ƙura mun ido yayi amma fuskan shi kaman zai yi murmushi, sai kuma ya kanne yace, "to ke in banda abin ki ta ya ya ina da khadija zan ga kyawun wata? Ni fa banga kyawun da ake cewa kina da shi ba, kawai dai suna son ki ne kuma suna son ki kwantar da hankalin ki ne kawai, shi yasa su ke yaudaran ki". "Baki na a buɗe ina kallon shi kaman na zunduma ihu nace, "Dr Khadijan da gaske matar kace? Kuma kana son ta sosai"? Tashi ya yi ya tsaya yana gyara rigan shi, alaman kuma zai tafi ne, yana duba na yace, "idan ta tashi ki gaishe ta, 2:00pm zan zo na ɗauke ki muje kiyi lunch". sannan ya juya zai fita. Da gudu na bishi har wajen, hannu na saka na juyo da shi da ƙarfi na, idona yana zubar da hawaye nace, "bana son Dr Khadijan, kuma bata mun kyau, kuma bazan bika lunch ɗin ba, babu ruwa na da kai daga yau, munyi faɗa Dr'n mu! Munyi faɗa Dr na!! Bana....". Sai kuma nayi shiru ina riƙe da hannun shi ina kuka na. "To sa ke mun hannu na tafi wurin mai sona, wanda baza ta taɓa fushi da ni ba, wanda ta ke mun kyau sosai, kema ki koma wurin su Peter suyi ta ce miki ke mai kyau ce kinji". ya faɗa yana neman zare hannun shi daga cikin nawa. "Nima ai banyi fushi da kai ba, ni bana so kaje wurin Dr Khadija ne". na faɗa lokacin Dr Abdallah yana shirin ƙarasowa in da muke. Bansan dalila ba kawai sai naji Dr Hussain ya mayar da hannun shi ya sake riƙe nawa hannun, ya saka hannu ɗaya yana share mun hawaye na, murya ƙasa-ƙasa yace, "mun shirya to, zaki bini muje lunch tare?". Ɗaga mishi kai nayi alaman na yarda, sai ya yi murmushin da ban taɓa ganin irin shi a fuskar shi ba yace "to bana son ki kula wancan balaraben Dr, kinga shi bai san ki ba, bai san Daddy'n ki ba, zai iya cutar da ke, tun da shi namiji ne ko? Saboda haka idan kina son mu shirya wataran na gaya miki abinda kike so to kada ki kula shi kin ji?". Murmushi nima nayi sannan nace, "bazan kula shi ba ko yayi mun magana zan ɗaure fuska na". na faɗa ina kwatan ta mishi yadda zan yi da fuskar, wanda abin mamaki sai gani nayi ya tuntsure da dariya, nima cikin mamakin abin da ya yi nima na yi dariyan, sannan na ce, "Kaima baza kaje wurin Dr Khadija ba yau? Kamun alƙawari ka daina ganin kyawun ta sama da nawa?". Matse hannu na ya yi da ƙarfi ya na murmushi yace, "bazan je ba yau, sai ranan da naga kin kula Dr nima zan je, kuma ba zan sake shiryawa da ke ba, su Peter ma kawai gaisawa zaku na yi, bana so kina zama da su kuna hira kinji". Ɗaga mishi kaina na yi ina murmushi, shima yimun yayi sannan ya sake hannu na ya juya ya fita, ban bar wurin ba har saida na daina ganin shi tukun na koma ɗakin. Ina shiga ya yi dai-dai da Dr Abdallah zai fito a ɗakin, Amal kuma ta na zaune an saka mata pillow ta ɗan jingina kaɗan, gefen ta kuma nurse ce a tsaye tana taimaka mata. Kallo na ya yi yana murmushi yace, "Hello Preety" Hararan shi nayi na ja baki na na yi shiru ban kula shi ba, sai naga ya yi ɗan dariya ya juya yana duban Amal, "Amal friend ɗin ki bata magana ne? Bayan yanzu na ganta a gaban tsohon saurayin ta ta na ta doka murmushi, sai ni ne zata ƙi amsa gaisuwa na?". Ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushin fuskar shi. "Saurayi na kuma? Dr Hussain ɗin ne saurayi na? Baka san yana da mata mai kyau ba zaka ce mun saurayi na, ni kam".... Sai na rufe baki na tunawa da Dr yace ka da na kula shi. Amal kallo na ta tsaya tana yi, saboda a ɗan zaman da tayi dani taɗan fahimci wasu daga halaye na, don bani da ɓoye a abu so za kayi saurin fahimta na. "To idan ba saurayin ki bane mai yasa Dr Abdallah yana miki magana ki ka yi shiru?". Amal ta gaya mun da muryan ta mai fita a hankali. Kama baki na yi ina kallon ta sannan nace, "kema baki da wayo ko Amal? Bakiga Dr Hussain yana da mata ba, ta ya ya za'ayi ya zama saurayi na? Kawai ya hanani kula maza ne saboda kada su cutar da ni, kuma ni bazan sake kula kowa ba". na faɗa ina zama a kan kujeran. Dariya Dr Abdallah ya yi yana kaɗa kanshi ya fita a ɗakin. Amal ma dariya ta ke yi tana kallo na, sannan ta jijjiga kanta ta koma ta kwantar akan pillow tana ta dariyan ta, hararanta nayi na ja tsaki nace, "kema kina da problem, ta ya ya ma za'ayi na so Dr Hussain? Ni dai kawai burgeni ya keyi, kuma yana mun kyau, gashi yana da class, kinsan ina mai son turare a rayuwa ta". Dariya Amal ta sake yi sannan tace, "Allah ya nuna mana lokacin". Nima Aunty Nice ina kallon Amal da alaman tambayan ban fahimci me ta ke nufi da Dr Hussain saurayin Hummy ba ne, amma sai naga tana mun dariya alaman baza ta faɗa ba, naje na yi nawa tunanin na gane, kallon Miss Xerks na yi da alaman tambaya, amma sai ta kawar da kanta gefe alaman baza ta ce komai ba, saboda haka readers don Allah ku gaya mun mai kuka fahimta ne?. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 7📑* *__________📖* Tun da muka shigo compound ɗin gidan mu ido na ya sauka a side ɗin Dr Hussain, gaba na sai faɗuwa ya ke yi, domin hango motan shi a parking lot ɗin gidan, wanda daga motan shi ne sai na David, daga dukkan alama sune suke gidan, don nasan Peter ba sosai ya cika zaman gida ba. Hannun Amal na riƙe, ɗayan hannu na kuma ina riƙe da jakan kayan ta, duk na rasa samun nutsuwa a zuciya ta sai faɗuwar gaba na ke ji, a haka har muka ƙara sa na buɗe ƙofan gidan mu ka shiga. Muna shiga parlon Amal ta kwanta tana ta ya mutsa fuskan ta, ni kuma na wuce ɗaki na kai mata kayan ta, cikin parlor na dawo na zauna a gefen ta ina duban ta da tausayi. Miƙo ƙafan ta tayi in da na ke ta ce, "don Allah Sister danna mun ƙafa ta, duk ciwo suke mun". ta faɗa kaman zata zubar da hawaye. Tausayi ta bani na ta shi da sauri na fara daddana mata ƙafafun ta, sai nishi ta ke yi, muna cikin haka wayan ta ya fara ringing, (Ammi na) na gani yana yawo a kan screen ɗin wayan, da sauri na bar abinda na ke na miƙa mata wayan, abin tausayi da ƙyar ta ta shi zaune ta ɗauke wayan, bayan sun ɗanyi magana da Ammin ta, sai Abbun ta ya karɓi wayan shi ma suka yi magana, can sai ta miƙo mun wayan, ina karɓa Abbun ta yace mun, "Humaira na gode da ɗawainiya ko, idan kin ga jikin zai tsanan ta ki kira number Dr'n ta don Allah, yanzu zan kira shi na sanar mishi, za ki ga Dr Abdallah a contact ɗin ta, duk yadda ake ciki ki sanar mana, mun gode da ƙoƙarin ki, Allah ya miki albarka". Ina a jiye wayan na dube ta da alaman ta na son yin bacci, a hankali nace, "Sister me zan dafa miki?". Da ƙyar ta buɗe idon ta, girgiza mun kai ta yi alaman a'a bata son komai, bance mata komai ba na ci gaba da daddana mata ƙafan, har sai da naga bacci ya ɗauke ta, sannan na miƙe naje kitchen na ɗaura faten dankali, sannan na gyara ganye alayyahu mai yawa na ajiye a gefe. Ina fitowa parlor na ƙura mata ido, ganin bacci ya ɗauke ta babu yadda zanyi na ta she ta ta yi sallah ina tsoron ciwon na ta, ga shi kuma lokacin sallan magrib ya gaba to, haka na wuce ɗaki na ɗauro alwala nayi sallah, bayan na idar da azkhar na wuce kitchen na zuba wadataccen ganye na, sannan na ɗauko apple guda huɗu na wanke su, na yanka na zuba a blander nayi blanding ɗin su, saboda ina ji ana cewa yana amfani a jikin masu ciwon sickler, a fridge na ajiye sannan na sauke abincin na juye a cikin cooler na kai su kan dinning. Ina fitowa da komai na dawo gefen ta na zauna na ƙura mata ido, har lokacin sallan isha ta yi ba ta ta shi ba, bayan na idar da sallah ne na fito nazo na same ta tana zaune dirshan a ƙasa ta mimmiƙe ƙafan ta a ƙasa tana ta ya mutsa fuskan ta. Da sauri na ƙaraso in da take ina duban ta nace, "ya fara miki ciwo ne? Ko zaki iya ta shi ki yi sallah?". Bata ce mun komai ba ta miƙo mun hannu alaman na taimaka mata ta tashi, da sauri na saka hannu na miƙa mata, ta na tashi muka wuce har toilet ɗin ɗaki na, sannan na barta ta shiga ta ɗauro alwala, tana fitowa na shimfiɗa mata sallaya, abin tausayi a zaune tayi sallan kaman za tayi kuka har ta idar. Jingina kanta ta yi a jikin gado tana ɗan shirin komawa bacci, gefen ta na zauna nayi ta lallaɓa ta a kan taci abinci, da ƙyar ta yarda, haka naje na zuba mata abincin a plet na kawo mata har ɗakin, ɗayan hannun kuma ina ɗauke da ƙaramin jug dana zuba taceccen ruwan apple ɗin a ciki. Duk yadda ta so taƙi cin abincin ban barta ba, sai dana takura ta ta cinye abincin, sannan na miƙo mata magungunan ta tasha, tana gamawa Abbun ta ya kira wayan ta, ni na ɗauki wayan muka gaisa, tambaya na jikin ta ya yi cikin damuwa da nuna kulawan su a kanta da ciwon ta. "Humaira kina ga zaku iya kwana a gida ko kuma Dr'n ta yazo ya tafi da ita hospital"?. "Abbu babu komai, zamu iya kwana, yanzu ma ta samu ta yi bacci, bayan ta tashi ne tayi sallah kuma taci abinci, yanzu ma tasha drugs ɗin ta, ina ga babu komai insha'Allahu, don naga kaman ya fara mata sauƙi". Bayan mun gama wayan ne na wuce parlor domin naci abincin, da ya ke ban yi mai yawa ba, duka na juye a plet ɗin sannan na zauna na fara ci, amma gaba ɗaya zuciya na ya kaso kashi biyu, ɗaya ina tunanin ya ya zamu yi ni da Amal idan ciwon ya tashi cikin dare? Ɗayan zuciyan kuma ina tunanin Dr Hussain da Dr Khadija dana gan su tare, ko yanzun ma tare suke ita da shi ko kuma ya ya abin yake? Haka dai nayi ta hira da zuciya ta har na gama cin abincin. Books ɗina na baje su a parlon ina karatu, bayan na duba Amal na ga tayi bacci. Bani na tashi ba sai around 11:00 pm, ina shiga ɗakin na duba ta naga still baccin ta ta keyi, a hankali kada na tashe ta na wuce toilet domin nayi wanka. Ina fitowa a toilet na ɗauki turare na mai sanyin daɗi na shafe jiki na da shi, sannan na ɗauko wando da riga masu ɗan kauri kaɗan na saka, domin gaba ɗaya yau naji garin kaman da ɗan sanyi, hula na saka na ɗale gadon, bayan nayi addu'a na shafa na kashe mana wutan na kwanta. Kaman a cikin mafarki na ke jin nishin mutum a kusa dani, a firgice na tashi zaune na kunna wutan ɗakin na juya inda Amal ta ke, abin tsoro ita ɗin ce kuwa zaune ta riƙe cikin ta ta na ta nishi, da sauri na matso kusa da ita na rungume ta, ido na cike da hawaye ina tambayan ta, "Sister ina yake miki ciwo? Ko na kira Dr ne"?. Ta riƙe ni da ƙarfi duk idon ta sun yi fari ƙal na alaman babu jini, tana nishi hannunta riƙe da cikin ta ta ɗaga mun kanta alaman na ƙira shi. Da sauri na jawo wayan ta da yake kan bedside na buɗe, inda naga 2 misscall ɗin Abbun ta, amma ban bi takan shi ba na danna ƙiran Dr Abdallah, bai fi ringin biyu ba ya ɗauka bakin shi ɗauke da sallama, jiki na yana rawa na ce. "Hello Dr Amal ce.." na faɗa kaman wanda aka ƙwaci sunan a baki na, a cikin nutsuwa yace mun, "in da ku ke a kwai abin hawa ne? Ko kuma nazo na ɗauke ta za ki bani address"? Ta shi na yi tsaye na ce, "ka zo don Allah". sannan na ba shi address ɗi na, da sauri na shiga toilet ɗin nayi fitsari kuma nayi brush, ina fitowa na buɗe sif ɗina na ɗauko wani after dress na ɗaura akan kayan baccin sannan nayi rolling ɗan gyalen a kaina, jaka na na jawo na jefa carbi na da waya ta, na riƙo Amal muka ta shi tsaye ina kallon ta nace, "sister za ki shiga toilet"? Ɗaga mun kai tayi alaman zata je, da sauri na kai ta, da ƙyar ta na kuka zuwa lokacin ta yi fitsari, tana ta shi ta yi alwala da ƙyar, na saka hannu na riƙo ta muka fito parlor. Na lura kullum Amal a cikin alwala ta ke, yau ɗaya na ji ta burgeni wato duk zafin ciwon da ta ke ji bai hana ta yin alwalan da ta saba ba ko? Ya Allah nima ka bani ikon yin shi a rayuwa ta, muna zama bamu daɗe ba naji an buɗe gate ɗin mu, motan Dr ta shigo, kafin na yunƙura sai jin wayar ta ta fara ringing, ban tsaya ɗaukan wayan ba, na kama hannun ta muka yi hanyar fita waje. Muna fitowa na tsaya rufe ƙofan sai ga Dr Abdallah da sauri ya fito a motan shi ya ƙara so in da mu ke, dai-dai lokacin na ga Dr Hussain ma ya buɗe ƙofan shi yana tsaye yana kallon mu. Amal ta kasa ɗaga ƙafan ta ta yi tafiya sai kuka ta ke yi, ganin haka na yi sauri zan riƙe ta, amma sai Dr yace a'a ki riƙe bag ɗin ki bari na taimaka miki, kallon shi na yi kaɗan na juya kaina gefe a zuciya ta ina cewa _ashe ma Balarabe ne shima Dr._ Ban san lokacin dana juya na kalli Dr Hussain ba, wanda har lokacin yana tsaye yana kallon mu, jikin shi ɗauke da wasu kayan bacci masu masifar kyau green colour, alaman bazai ce mun uffan ba, sai nima na daure na bi bayan su Amal, a lokacin David da Peter suka fito, ganin mune zama fita naga sun ƙara so in da muke da sauri. "Preety bata da lafiya ne?". Peter da ke ƙarasowa kusa da ni ya tambaye ni, cikin damuwa na ke gaya mishi ita sickeler ce kuma ta samu crises tun jiya da yamma, yana bin mu da kallon tausayi, sai David ya jeho mun tambayan. "Preety why baki kira mu mun taimaka muku zuwa hospital ba? Naga kin nemo wani da ga wani wuri bayan muna tare kin kuma san akwai abin hawa?". Ya faɗa yana duban Dr Abdallah daya buɗe bayan motan ya kwantar da Amal. Kafin nace komai, sai Dr Abdallah ya ɗa go kan shi da murmushi yana miƙawa David hannu kuma yana gaya mishi yayi haƙuri bawai mun nemo shi daga wani wuri ba ne, dama shi Dr'n Amal ne. Bayan sun tambaye shi asibitin da zamu je ya gaya musu, ni kuma na buɗe gaban motan na shiga, ko tayar da motan ba'ayi ba kawai naji an buɗe in da na ke zaune, sai jin muryan shi ya na cewa. "koma back seet in da ta ke ki zauna". ban iya mishi musu ba jiki na yana rawa na fita na koma bayan, sannan shi kuma ina ganin shi ya shige ya zauna, idon shi a kan Dr Abdallah sannan ya ce mishi. "Aisha Sister na ne". Dr Abdallah bai ce komai ba sai smilling da ya yi ya ja motan da sauri muka tafi. Tun da mu ka shiga motan babu abinda ka ke ji sai sautin kukan Amal, ga wani miƙewa da ta ke ta yi, muna isa Dr Abdallah ya fito da sauri ya buɗe motan, lokacin kuma wasu nurses sun turo ɗan gadon su na ɗaukan marasa lafiya suka ɗauke ta, cikin gudu-gudu muka bi su ni da Dr Hussain, emargency room Dr ya wuce da ita, bamu daɗe ba wasu Drs guda uku suka bi bayan shi ɗaya namiji biyu kuma mata. A reception ɗin asibitin muka zauna ni da Dr Hussain, babu wanda ya kula wani a cikin mu, har tsawon wasu mintu na, sai ga Dr Abdallah ya fito hannun shi riƙe da waya, da ga dukkan alamu shi da Abbun Amal suke wayan, har in da muke zaune ya zo ya tsaya ya kuma cigaba da wayen shi haka zalika idon shi a sauke a kaina ya ƙura mun ido yana amsa wayan. Suna gama wayan ya dube ni da murmushin dana lura kaman baya barin fuskan shi, murya a nutse da ya nuna yanayin maganan shi ke nan ya dube ni yace, "ƙawar ki mun samu tayi bacci, pain ɗin ya ɗan mata sauƙi, amma kuma tana buƙatan ƙarin jini, shi ne muke magana da Abbun ta". ya faɗa har lokacin fuskan shi ɗauke da murmushi yana duba na. "Da ka ke mata bayanin abinda zaka yi to ita mai ta sani a game da aikin ka? Ina ce kun gama magana da mahaifin yarinya? Ina ga kaman ba lallai bane sai kazo ka mata bayani kawai ka aiwatar da abinda ya ke aikin kane". Dr Hussain ya faɗa fuskan shi a matuƙar ɗaure, wanda sai da naji kunyar abinda ya faɗa, amma abin mamaki Dr Abdallah juyawa yayi yana duban shi fuskan shi har lokacin ɗauke da murmushi. Shi kuma Dr Hussain kawar da kai yayi gefe kaman bai lura da kallon shi Dr Abdallah ya ke yi ba, "Yayan mu kada ka samu damuwa da magana na, kasancewar ta re su ke ciwon ya tashi, kuma naga ita ƴar'uwarka irin damuwan da ta shiga shiya sa na mata baya ni don hankalin ta ya kwanta, don ɗazu da muka yi waya na jita cikin yanayin damuwa". ya faɗa ya na duba na kaman wanda ya ke son fahimtan wani abu a tattare dani. Bai jira mai Dr Hussain zai ce ba ya juya ya koma in da ya fito, muna zaune shiru babu mai cewa uffan sai wucewar mutane kawai ta gaban mu kaman safiya da ce ta yi, daga dukkan alamu asibitin na manya mutane ne, kuma babban asibiti ne. "Wa to ke har wani kiran wayan shi ki ke yi ko? To kiyi deleting number'n tun da dai an kawo ta asibitin". Dr Hissain ya faɗa yana bina da harara. Fuska na a tsuke na dube shi sannan nace, "ni fa babu number'n shi a waya na, dama ta wayan Amal Abbun ta yace na kira shi idan jikin ya ƙi.....". Ban ƙarasa ba faɗar abunda ke baki na ba, na ji yayi tsaki ƙasa-ƙasa, sannan ya ɗan dube ni ya ɗa ga kafaɗa alaman babu abinda ya dame shi, ganin hakan da ya yi sai na ji raina ya ɓaci, tashi nayi zan bar wurin, kawai sai na ji yace, "Meye ya ke damun ta?". Dr Hussain ya tambaye ni. "Sickler ce". na bashi amsa a taƙaice. Zaro ido yayi yana kallo na a razane, can kuma sai yace, "shi ne kuma kika ɗauke ta zuwa yawo bayan kinsan ciwon su baya son wahala?". Zunɓuro baki na yi ina hararan shi ƙasa-ƙasa ina ɗan ƙunƙuni na. Ya na kallo na yace, "zagi na ki ke yi Aisha?". Ina kallon shi kaman zan yi kuka na ce, "ni mene zai sa na zage ka? Kawai cewa na yi kaima ai yawo ka je kaida matar ka, kuma kaƙi kula ni da ka ga tana gun, bayan ka tafi ka daɗe baka dawo ba, ko zuwa duba ya ya na ke ba ka yi ba saboda kana wurin matar ka". na faɗa kaman zan zubar da hawaye. Kallo na ya tsaya yana yi kaman yaga sabon abu, amma abin mamaki ko bin ta magana bai yi ba kawai sai na ji yana tambaya na, "Meye gyenotype ɗin ki?". Turo baki na yi ina duban shi kaman zan zunduma ihun haushi, bansan lokacin dana harare shi ba, na kaɗa kaina nace, "meye problem ɗin ka da sanin gyenotype ɗi na? Ina ce kasan na koɗaɗɗiyar matar ka". Na faɗa ina tashi tsaye zan bar wurin. "Ka da ki yadda ki bar nan wurin, kuma ki shirya yanzu zamu koma gida, don asibitin nan ba a kwana, yana fitowa muka ji ya ya ta ke, zamu ta fi gida". ya faɗa idon shi tsaye a kaina, zuciyar shi kuma yana tuna wani lokaci kusan irin haka, lokacin yana service a central bank branch ɗin su da ke bauchi, sun shigo gida da wasu corpers ƴan'uwan shi, amma har da mata a cikin su, suna tafiya ya ce Aisha ta kawo mishi abinci, amma firr yarinyar nan ta dinga mishi tsiwa kaman ba ita ba, "Yayan mu to me ya sa ba ka ce wa ƴan matan ka su kawo maka ba? Ni sai kawai ka dinga zuwa da ƴan matan ka suna yiwa mutane kallon banza kaman sun ga sa'o'in su, ni wallahi suka sake zuwa sakawa zanyi a ɗaura maka aure da figaggiyar ciki, idan yaso ka samu mai kawo maka abinci". Aisha ya tuna yadda ta mishi ranan, babu ko ɗigon tsoron shi a idon ta, gashi yau ma Humaira ta sa ke maimaitawa. Yana kallo na bai ce uffan ba, ni kuma sai harare-harare na ke yi, can jumawa yayi ɗan murmushi yana duba na ya ce, "Ko ta burge kine matar tawa?". Ya faɗa yana jiran ya ji nata irin amsan ko zai zo ɗaya da na Aisha a wancan lokacin. Juyowa nayi da sauri na kalle shi fuska a ɗaure nace, "kai ka ke ganin kyawun ta tun da ka na son ta, ni dai nasan ko kusa ba za'a haɗa ta da ni ba wurin kyau, bari kuma kaga lokacin da nawa masoyin zai iso, za ka ji ya tabbatar maka da samun irin mai kyawuna sai an tona". na faɗa ina girgiza jiki na ina fari da ido na. Miƙewa yayi tsaye yana duba na da mamaki, domin lokacin da Aisha ta gama mishi wannan mitan duban ta yayi yace, " Sister Aisha ko dai Blessing ta burge kine? Halan kema kyawunta ya burge ki"? Harara Aisha ta mun a wannan lokacin sannan ta dube ni tace, " kai kaga kyawunta don ka na sonta, amma ni ko ku sa dani a ka kawota wallahi zan dushasheta, kuma ka jira ranan da zan fara samari zaka ji an faɗa maka haka". ta faɗa tana wucewa parlon Ummi a lokacin, ni kuma nayi murmushi na wuce side ɗin mu da Hassan. Duban fuska na ya tsaya yana yi, har Dr Abdallah suka fito daga ɗakin, wasu nurses biyu mata suna gangaro Amal a gado tana bacci, hannun ta ɗauke da ledan jini, zuwa in da suke na yi na tsaya ina kallon ta. Suna shiga wani ɗaki mu ka bi bayan su har da Dr Hussain, bayan an kwantar da ita ne nurses ɗin ɗaya ta fita ɗaya kuma ta nemi wuri ta zauna, Dr Abdallah yana duba na da murmushi ɗauke a fuskar shi yace, "Ƴan mata Alhamdulillahi mun samu jinin da ya yi dai-dai da nata, kinga har ta samu ta yi bacci, yanzu za ki iya komawa gida sai wurin 8:00am za ki iya zuwa ki duba ta". ya faɗa ya na ƙura mun idon shi. Kallon shi na yi a marairaice nace, "Plz Dr kabar ni na kwana ina ganin ta mana, kaga asuba ma ya kusa". Na faɗa ido na yana cikowa da ƙwalla. Hannun Dr Hissain na ji ya kamo nawa a hankali na ji yana cewa, "kibar su suyi aikin su mana Aisha, Kizo mu koma da safe zan dawo da ke insha'Allahu". na buɗe ba ki zan yi mishi musu, sai na ga ya lumshe ido ya buɗe yana juya mun kanshi alaman baya son musu. Bance komai ba na bishi yadda yake jana muka fita a ɗakin, ni kuma ina ta waiwayen Amal da ke bacci kaman zanyi kuka, amma haka Dr Hussain ya jani mika fita, shi kuma Dr Abdallah sai bin mu yake da murmushi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 10📑* *__________📖* "Kinsan duk wanda ya gan mu zai yi tunanin mu miji da mata ne, so idan nace mata ba haka bane ba zata yadda ba, zata tsaya ta yi ta damun mu da tambaya, kuma ma na lura so na ta keyi, tun ranan da na fara zuwa cin abinci nan wurin". ya ƙara sa maganan yana kallo na. Tsakin da ban shirya ba na yi, ina duban shi kaman zan fashe a wurin na ce, "tun da ka lura tana son ka ba sai ka daina zuwa cin abinci wurin ba, in banda kai ma, kana da mata ya ya zaka dinga sayen abinci a waje? Kawai ka daina zuwa don Allah Dr'mu". "Saidai idan zaki na dafa mun to sai na daina zuwa wurin, amma mata na ita bata iya girki ba, saya itama ta keyi kullum, ko kuma ni na dafa mana". cewar Dr Hussain. Baki na buɗe ina kallon shi cike da mamaki, "amma dai wallahi ta yi kyawun banza, ace mace ba zata yi girki wa mijin ta ba kam ai da sauran ta kuwa, kyawunta bai amfane ta komai ba, kace ashe dole su kazan mayu su dinga tsintar ka a wurare da yawa a ƙasan nan". "Hmmm wata rana naje wani wurin cin abinci ma haka su kayi ta bina, ɗayar bakiga kyawun ta ba, ina ga duk duniya ban taɓa ganin mai kyawun ta ba, gata ƴar duma-duma da ita, ranan kwana nayi banyi bacci ba, ina rufe ido na sai na ganta a ido na". ya faɗa yana jinjina irin kyawun da ya gani. Kallon shi na ke yi baki da ido na a buɗe, "amma dai kam aljana ce ba mutum ba, don duk wacce ta fini kyau kam ai ta zama aljana, wallahi kadai na yawon sayen abinci, gara ma na dinga da fa maka kada wata rana ƴan gidan ku su samu labarin ka shiga jeji". na faɗa ina jin zuciya ta kaman zai fito waje. Ɗaga kafaɗan shi yayi alaman duk yadda na gani haka za'ayi. "Hmmm". kawai nace domin raina yayi matuƙar ɓaci da jin yadda ake son shi. "Kinyi shiru baki ce komai ba". ya jefo mun tambaya yana tsaya a gate ɗin gidan mu domin jiran a buɗe mishi. "To ni Humaira me zance? Kawai sakarar matar ka ta kasa kula da kai, common girki ba zata zauna ta maka ba, har sai kajin mayu sun haɗu sun lashe ka tukun tazo tana kukan wai ita ma tana son ka ko? Da ƙafanɓta a sandare kaman taɓarya, ni shiyasa ban cika son naga mace mai kyau da yawa ba, don wahalar da miji su keyi irin su, ballanta na kai da baka ganin kyawun kowa sai nata, to ko me zance? Sai dai na yi ta addu'an Allah ya kare ka daga sharrin su, ni daba ka ganin kyawuna ni yazama mun dole na Kula da kai ai". Na faɗa raina a ɓace. Haka muka yi parking na fita a motan ina duban shi nace, "to what time zamu koma asibiti wurin Amal? Kasan yau su Abbun ta zasu iso da dare". "Ki bari sai 6:00pm sai muje, idan yaso 9:00pm sai mu dawo" Kaɗa kaina nayi alaman ya mun, sannan na wuce na yi side ɗina, ina shiga kwanciya nayi a parlor ina ta tunanin labarin da Dr ya bani wai yaga kyawun wata, ikon Allah ko me yasa ni baya ganin kyau na? Hmmm shi ya sani na faɗa a zuciya ta. Muna shiga hospital ɗin muka ci karo da Dr Abdallah ya fito shi da wasu nurses guda biyu daga ɗakin, amma sakarai har ya manta abinda ya faru jiya, yana ganin mu ya fara mana murmushi kaman yaga wasu ƴan'uwan shi. Da sauri Dr Hussain na ji ya saka hannun shi ya riƙo nawa hannun, fuskar shin nan kaman bai taɓa dariya ba, yadda kuka san ya shigo class yana lectures haka ya yi da fuskan, koma nace yama fi hakan. Kallon fuskar shi na yi da nufin zan ƙwace hannu na, amma ganin yanayin fuskan na shi sai na nutsu na cigaba da bin shi a hankali, muna zuwa dab da Dr Abdallah, kawai sai yaja ya tsaya yana miƙawa Dr Hussain bakin shi ɗauke da murmushi, hannu Dr na ya miƙa amma fuskar shi bai ko sa ke ba, sai wani ƙara tantame ta da ya yi, suna gaisawa Dr Hussain ya ja hannu na da sauri muka shige ɗakin da Amal ta ke ciki, ko jiran mai Dr Abdallah ya ke faɗa mun bamu yi ba. Muna shiga Amal ta harare ni ta kawar da kanta gefen da Dr ya ke tsaye tana gaishe shi, ita kuma nurse ɗin da ta ke zaune ta tashi ta fita ta bar mu, dariya na yi ina kallon ta nace, "to laifin me na yi kika ƙi kallo na ballanta na ki amsa gaisuwan da na ke yi miki?". "ki koma da gaisuwan ki, tunda sai yanzu kika ga daman da wowa". ta faɗa ta na ƙara ɗaure fuskan ta. Kallon Dr na yi da yake zaune a wani 2sitter da yake gefen gadon ta yana ta daddana wayan shi, bai ko kalle mu ba, dariya na yi na koma gefen shi na zauna ina cewa, "Dr'n mu don Allah ka bata haƙuri, ka gaya mata kaine kace muje cin abinci shi yasa ma ban dawo ba ko". na faɗa ina neman shi ma ya ƙara na shi bayanin. Kallon ta yayi ba tare da yace mata uffan ba, sai na ji tana cewa, "Allah ya soki kinci Albarka cin Dr, amma da yau nayi fushi da ke, kinsan ɗazu ƙafana su kayi ta ciwo, har saida aka mun allura kusan guda biyu, kuma Abbu zasu iso wurin 7:30pm, shi yasa duk na damu da rashin ki". Haƙuri na bata nace mata ina nan har 9:00 insha'Allahu, sannan na matsa kusa da Dr ina leƙa abinda ya keyi a cikin wayan shi. Juyowa ya yi kaɗan ya dube ni ta gefen idon shi, baice komai ba ya cigaba da abinda ya ke yi cikin wayan na shi, a hankali nace, "Dr nah bani nima nayi game ɗin Angellah ɗin". bai kula ni ba ya cigaba da dannan wayan shi, ba'a ɗauki lokaci ba muka ji buɗe ƙofa da shigowan Dr Abdallah, ina ganin Dr babu shiri ya saka hannun shi ya matso dani kusa da shi sosai, yana miƙo mun wayan yana cewa, "Babyn baby zo ki buga naga irin naki ƙwarewan? Idan kin kaini to zan miki kyautan ban mamaki, idan kuma na fiki to zaki mun kyautan duk abinda na faɗa". nima murmushin na keyi na karɓi wayan ina buga game ɗin, ko in da Dr Abdallah ya ke ban kalla ba. Juyawa ya yi ya bar kallon mu, idon shi ya maida kan Amal yana gaya mata isowan su Abbu, yanzu zai wuce airpot, amma wurin 7:30 zasu shigo hospital ɗin, yana gama faɗa ya juya da sauri ya fita. Da ido Dr Hussain ya bishi, sannan ya maido da hankalin shi kaina, a hankali yace, "bari na fita mosque nayi sallan magarib da isha, idan na idar zan dawo". Amsa mishi da kaina ina miƙa mishi wayan, kallo na yayi kaɗan kafin ya saka hannun shi ya karɓa ya fita a ɗakin. Dawo da kallo na nayi kan Amal ina murmushi nace, "sis ya ya jikin dai?". Harara na tayi ta ce, "ban sani ba, sai da ki ka gama soyayyan ki da Dr Hussain bayan ya tafi tukun zaki dawo nuna mun kulawan ƙarya". Buɗe baki nayi ina dariya nace, " me yasa baki yadda da cewa babu komai tsakanin mu da shi ba? Mutumin da yake da mata da buhu-buhun ƴan mata kyawawa mai zai yi dani ƴar cukulan nan?". "Za kuji da shi ai daga ke har shi ɗin, mutumin da ake cewa ko cikin lectures ƴan uwan shi baya kula su, amma ke gaba ɗaya ya ɗauki time ɗin shi yana baki, kuma har yana fita da ke, yana kuma biye duk wasu shirmen ki, amma kina raina mun hankali wai babu komai tsakanin ku? To kada ki gaya mun, a barshi idan ya yi tsami zanji ai". Kama baki na yi ina hararan ta, " amma Amal baki da hankali, ki rasa da wanda zaki ce ina soyayya sai da wanda yayi kusan haihiwa na? Bakiga yayi mun girma bane? ak wannan wayo zai na mun isan na aure shi, kawai dai muna shiri ne ki gane hakan". "Zan gane ai ranan da duk nagan ki a gidan shi". ta faɗa tana kuma tana kwanciya. Dariya na yi ban ce mata komai ba, sai tashi da nayi na shiga toilet ɗin nayi alwala domin yin sallan magrib. Wallahi yau bazan iya typing mai yawa ba, duk a gajeye na ke, kuyi haƙuri da wannan. _*JIKAR KULU, WANNAN SHAFIN NAKI NE KYAUTA NA BAKI, DUK YADDA KI KE SO KIYI DA SHI, NAGODE DA ƘOƘARIN DA KI KE MUN, ALLAH YA BAR ZUMUNCI.*_ *©AUNTY NICE CE* ✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*HAUWA ALHASSAN YUNUS, WANNAN SHAFIN NAKI NE KYAUTA AUNTY NICE TA BAKI, DOMIN TUKWUICI NE DAGA IRIN COMMENT ƊIN DA KIKAYI, NAJI DAƊI ALLAH YA BAR ZUMUNCI*_ *SHAFI NA 9📑* *__________📖* Hararan ta na yi ina kaɗa kaina alaman ta faɗi ba dai-dai ba, amma dai bazan kula ta ba, ina duban fuskan Amal da ta rufe kaman mai bacci, amma wani munafukin murmushi ne ƙunshe a fuskar ta, ni kuma sai bin ta da harara na ke yi, can naga abun na ta ya yi yawa, ina hararan ta nace. "Amal idan kinsan kin warke munafurci ne a zuciyar ki, to ki faɗa na tashi na ta fi, amma kin sa kani a gaba sai murmushin munafurci ki ke yi?" Dariya ne ya kufce ma Amal, daga gani irin wanda ba ta shirya yi ba ne, buɗe ido na yi na ƙura mata ina kallon ta baki na a buɗe, ganin yadda na yi kawai sai ta sake fashewa da dariya. "Haba Hummy na ƴar rikici, idan ban yi dariyan drammer ko da Dr ba, to dariyan me zanyi? Gaba ɗaya son junan ku ya muku yawa amma kun kasa ganewa, sai wani kishin juna ku ke yi, yau ayi fushi gobe ayi faɗa, amma dai na yi shiru tunda kin ce babu soyayya a tsakanin ki da tsoho, sai ki saurari Dr Abdallah don shi ma na lura yana miki ƙauna zalla". ta faɗa tana ci gaba da dariyan ta. Tashi nayi nai hanyar waje ina cewa, "na ta fi gida sai ranan da cutan gulman ya sake ki sai na dawo, yarinya in banda shirme, me zanyi da Dr wanda ya mun tsufa, kuma don lalacewa mai matan ki ke mun fata, gaskiya ni kin gama da ni". Na fita a ɗakin da sauri saboda muryan dariyan Amal da naji ya ƙaru. Ina shiga compound ɗin mu na hango shi ya buɗe motan shi zai ɗauki abu a ciki, hararan shi nayi a zuciya ta ina cewa, "in banda tunani irin na Amal wannan mutumin kam ai kaɗan ne ya hana shi ya haife ni, amma ta ke ga kaman muna soyayya? Nikam sun kasa fahimta ta ne, burge ni kawai ya ke yi, kuma yana mun kyau amma bana mishi son da suke tunani". ina ganin ya juyo nayi sauri na ɗaga mishi hannu sannan na shiga gida na. 2:00pm naji text ya shigo waya na, da sauri na jawo wayan na duba, "ki fito muje lunch da kika mun alƙawarin zamuje". da ga Dr Hussain text ɗin ya shigo. Tashi na yi na sa ke yin wanka, wani material gown na saka, baƙi ne mai jajayen flower a jiki, ban ɗaura ɗankwalin kayan ba, na ɗauko red ɗin ƙaramin gyale na yafa a kaina, wanda tuntun gashi na ya ƙara ƙawata yafa mayafin, gashi duk in da na juya sai ƙamshi mai masifar daɗi na ke yi. Jikin mirrow na koma na sake kallon kaina, ina juyawa ina kallon kaina da sha'awa, a fili nace, "yau kam nasan Dr Hussain zai ce kaiii Hummy kinyi kyau". ina faɗa ina dariya saboda ni kaina nasan ba ƙaramin kyau na yi ba, ina cikin kallon kaina na ji ƙiran shi ya shigo waya na, ban ɗauka ba nayi sauri na ɗauki pouse ɗina red na riƙe a hannu bayan na jefa handset ɗina a ciki na fita. Ina fita na hango shi tsaye suna gaisawa da su David, wanda daga dukkan alamu daga service suka fito, cike da mamaki na ke duban shi, domin shima baƙin jeans da red polo ya saka, ƙafan shi ɗaure da baƙin sandal mai kyau, ga glass ɗin shi daya yi matuƙar ƙawata fuskan shi ɗane a fuskar shi. Ƙura mun ido suka yi ganin na tsaya da tafiyan, shima yau ina ganin shi sai da ya daɗe yana kallo na tukun ya maida kallon shi kan wayan hannun shi, Peter ne yace, "kai Preety wankan ki ya yi kyau, kaman wata queen? gaskiya duk mijin da ya aure ki ya more da mata mai kyau, don za kiyi ta haifa mishi kyawawan yara". murmushi na yi ina kallon Dr don jiran shi kuma mai zai ce, amma bai ce mana komai ba, sai kallon Peter ya yi kaɗan sannan ya maida kanshi kan handset ɗin shi, ganin haka David yayi ɗan murmushi ya dube ni yace. "Ki rabu da Peter ki zo ki shiga mota ku fita, haka ya ke duk in da yaga abu mai kyau sai yayi magana, kaman wacce zai aura ba kyakkyawa ba". Ƙarasowa jikin motan na yi ina murmushi, ganin su Peter sun wuce gidan su ya saka nima na buɗe gaban motan na zauna, har lokacin murmushi na keyi ina duban Dr don inji mai zaice, amma abin mamaki ko kallo na bai yi ba, jan motan kawai ya yi muka fita a gidan. Muna tafiya shiru bai ce mun komai ba, a hankali na dube shi nace, "Dr mu baka ce komai ba"?. Baice mun uffan ba kuma bai kalli in da na ke ba, ganin fuskan shi a ɗaure ya saka naja baki na na yi shiru, muna haka babu wanda ya kula kowa sai ni da nake kallon gefen hanya, a haka har muka isa wurin cin abincin. Tun da nazo garin ban taɓa ganin wurin da ya mun kyau da ban sha'awa irin wannan wurin ba, kallon wurin nayi baki na ɗauke da murmushi nace, "Dr'n mu wurin nan ya mun kyau sosai, ban taɓa ganin wurin da ya mun kyau irin nan ba tun da na zo garin nan". Kallo na ya yi baice komai ba ya buɗe ƙofan ya fita, ganin haka ya saka na yi sauri na buɗe motan nabi bayan shi. Woow gaskiya wurin cin abincin yayi kyau na gaskiyan gaske, da ya ke ba cikin wurin muka shiga ba kai tsaye, wurin swiming full ɗin muka je shi yasa wurin ya yi matuƙar burge ni, in da muka zauna ya yi ɗan gefe da mutane, kuma ma wurin mutanen basu da yawa, sit biyu ne a kan table ɗin, muna zama ya ƙurawa ruwan idon amma har lokacin fuskan shi a ɗaure tam. Kallon shi nayi jiki na a sanyaye na ce, "Dr mu mai ya same ka naga ranka a ɓace? Ko nayi maka laifi ne?". na faɗa ina kallon shi kaman zan yi kuka. Ɗago idon shi ya yi ya ƙura mun ido, baice mun uffan ba sai kallon da yake mun, wanda har na fara jin wani iri a jiki na, can na hango wata ƴar budurwa da fararen kaya ta nufu in da muke, daga ganin irin ma'aikatan wurin ne, ganin ta ƙaraso in da muke da wani ɗangalallen skirt ɗin ta duk sai na ji haushin ta ya kama ni, na dube ta a ya tsine ganin gaba ɗaya ita hankalin ta akan Dr ya ke ba a kaina ba, sai wani rausaya ta ke yi kaman wata ganyen bishiya, miƙa mishi menu ta yi ya zaɓi abincin da ya ke so, hararan ta nayi bansan lokacin da naja tsaki ba, bayan yayi ticking abinda ya ke so ya miƙo mun, ni dai kawar da kaina gefe nayi ban ƙara kallon shi ba. Shiru ya yi yana kallo na yana jiran yaga me zan ɗauka, ni dai ƙara juyar da kaina na yi na dubi cinyar yarinyar wasu sirara da su farare, na sake ɗaure fuskana na dubi Dr daya ƙura mun dukkan idon shi a kaina, alaman zan mishi kuka nayi. "Ranka ya daɗe to ka zaɓa mata abin da kasan ta fi so mana? Don naga daga dukkan alama wannan amaryar ta ka yau shagwaɓa ta ke ji da shi, kai ta ke jira kamata komai". yarinyar ta faɗa cikin harshen turanci tana duba na da murmushi. Kallon ta ya yi yace, "ita haka ta ke wai duk abunda na ke so shi ta ke son ci itama, saboda haka ki kawo mana komai iri ɗaya kada yau ta hanani sukuni da fitinar ta". ya faɗa yana duban yarinyar, wanda ta juya tana ta murmushi tana cewa, "haka halin amare ya ke ai, sai ta haihu kuma kaga ta koma son abinda ɗan ta ke so". Harara na bita da shi daga baya naja tsaki baki na a zunɓure na juyo da fuska na kan na Dr, gaba na ne naji ya faɗi da ƙarfi domin ganin idon Dr Hussain sauƙe a kaina yana bina kuma da murmushi. "Yarinyar tana da kyau sosai gashi ta iya karrama baƙo". na ji muryan Dr Hussain yana faɗa mun a hankali cikin nutsuwa. Da sauri na ɗago na dube shi, har lokacin idon shi yana zube a kaina, da sauri na sa kai na duba in da yarinyar ta bi amma ban ganta ba har ta wuce, zunɓura baki na yi ina kallon shi kaman zanyi kuka na ce, "Dr bata fini kyau ba fa, kaga ƙafanta fa kaman bulugari". na faɗa ina turo baki na gaba, kallo na ya yi yana ɗaga kafaɗan sama, sannan yace, "ni dai a ido na ta mun kyau sosai". "Dr to ni fa bana maka kyau ne? Kullum sai kai ta faɗin kyawun wasu amma ni ko sau ɗaya baka taɓa cewa ina maka kyau ba". na faɗa ina kifa kaina akan table ɗin zan mishi kuka. "Kina mun kuka idan ta dawo zan faɗa mata a gaban ta duk duniya babu mai irin kyawun ta, saboda haka gara ma ki ɗaga kan ki don gata can dawowa". Ɗago kaina na yi na dubi hanyar da ta ke tahowa na ƙura mata ido, can na juyo da ido na kanshi na ce, "amma baka gani da kyau Dr, don Allah dube ta yadda kasan kazar mayu haka ta ke, amma har ka iya ganin kyawun ta ba ka ga nawa ba, ni da na ke ƴar duma-duma mai kyawun asali". na faɗa ina juya ido na ina kuma hararan in da ta ke tahowan. Dariya Dr Hussain ya yi wanda abin mamaki har sai da sautin ya fito sosai, ƙura mishi ido nayi baki na a buɗe ina kallon shi da mamakin dariyan da ya keyi, dai-dai lokacin kazar mayun ta ƙaraso. Fuskar ta ɗauke da fara'a tana duban shi tace, "oga lallai yau kana cikin jin daɗin amarci, ya kama ta ayiwa amarya kyauta don ta na ra saka ka farin ciki, amma ita kuma naga kaman baka sa ka ta farin cikin, don sai shan magani ta keyi". ta faɗa tana jera mana komai akan table ɗin, gefe ɗaya kuma wani abokin aikin ta ne yake ajiye mana drinks ɗin. Hararan ta na yi nace, "ke wai baki da abin faɗi ne sai akan Dr na! Gaba ɗaya daga kinaraso sai ki maida hankalin ki kanshi jiki yana rawa, to Dr matar shi ta ishe shi, don tafi kyau da siraran ƙafan ki a wurin". na faɗa ina murguɗa baki na gefe, shi dai Dr sai dariya ya ke tayi, duk jikin yarinyar a sanyaye ta bar wurin cikin sauri. Harara na bita da shi nace, "ga ɗuwawun ta kaman an maka mata mara, ni banga wani abin burgewa ba anan wurin in banda abin nimiji". na faɗa ina kallon shi fuska na a murtuke, saboda irin dariyan da ya ke ta yi. Kallon shi na ke yi baki a buɗe, don na fara ƙuluwa da dariyan da yake ta yi, ganin bazai daina ba kawai na miƙe tsaye zan bar wurin, sai ji nayi an cafko ni da sauri har sai danayi kaman zan faɗo kanshi, har lokacin idon shi yana kaina fuskan shi ɗauke da murmushin, sannan ya ƙura mun ido ta cikin glass ɗin shi. Kallon in da yarinyar ta bi nayi, sannan na dawo da ido kanshi, shima har lokacin kallo na ya ke yi, sai can yace, "idan kin tafi wa zai ci abincin da ki ka saka nayi order'n shi"? "Sai na kira maka ƙazar mayun ta taya ka ci ai, tun da na ga hankalin ka baki ɗaya ya tattara gare ta". Ƙunshe bakin shi ya yi kaman yana son maida dariyan shi, yana kallo na yace, "to ai kince ɗuwawun ta kaman an maka mara, to me zan kalla a jikin ta har naji daɗin cin abincin? Kawai ke ƴar duma-duman nake son ki zauna ina kallon fuskar da Peter yace mai kyau ne, ki sakani na yi ta cin abincin, ina tunanin wani irin miji zan nema miki wanda zaku haɗu ku haifi yara masu kyau". Zama nayi ina duban shi da murmushi sannan nace, " yanzu kaima kaga bata da kyau ko?". Ɗaga mun giran shi yayi alaman "ehh" Sai na ji daɗi ya rufe ni, ina kallon shi da jin daɗi ɗauke a fuska na nace, "to ni fah ina maka kyau?". Girgiza kai ya yi alamar "a'a". turo baki na na yi kaman zan yi kuka nace, "to ni yaushe za ka ce ina da kyau ne kam Dr? Bayan kai kullum kyawun ka na ke gani, amma ni sai dai kaga na wasu amma baka ganin nawa?". Murmushi ya yi ya ce, "sai ranan da wasu suka daina ganin kyawun ki, to ranan zan gaya miki abinda ki ka daɗe kina so kiji daga gare ni". yana gama faɗin hakan ya turo mun pilet ɗi na gaba na, ganin haka yasa na harari abincin na juyar da kaina gefe. "me yasa ta ce ni amaryar kace amma baka ce mata ni sister ka bane? Yanzu idan wani yana so yace yana sona ai fasawa zai yi idan tace ni matar aure ne, bayan kuma kasan kai ɗin kana da mata ƴar wada". na faɗa ina kallon zoben hannu na. Murmushi ya yi sannan a hankali yace, "don Allah kici abincin ba na so kuma ki ɓata yammacin da kika ƙawata mun shi yanzu-yanzun nan, kada ki bari ɓacin rai ya ziyar ce ni Aisha, idan mun ci abincin zan gaya miki dalili na na gaya mata hakan kinji ƴar rigamar Dr'n ta". ya faɗa har lokacin ya na murmushin. Muna gama cin abincin ya ƙurawa ruwan ido, ganin ba zai ce komai ba yasa nace, "mun gama ci baka gaya mun dalilin ba". Lumshe idon shi ya yi bai ce komai ba, sai murmushin da yake ƙawata fuskar shi kawai ya ke yi, ina kallon shi a zuciya ta nace, _anya a kwai mai irin kyawun Dr Hussain kuwa? Allah yasa idan na ta shi aure na samu mai irin kamanin shi, don gaskiya Dr Hussain mai kyau ne, kuma mai aji ne na ƙarshe._ "Dr idan na girma zanyi aure zan samu mai irin kyawun ka kuwa". Na faɗa hankali na kwance ina duban shi. Buɗe ido ya yi yana kallo na fuskar shi ɗauke da murmushi, "anya idan na tashi ƙara aure zan samu mai irin yanayin ki kuwa? Ina son macen da zata buɗe mun gaskiyar zuciyar ta a kaina, ina buƙatan macen da ni kaɗai zata na ganin nafi kowa ni namiji a rayuwar ta". ya faɗa idon shi cikin nawa. Matso da kujera na na yi kusa da na shi, murya a hankali nace, "Dr Khadija bata gaya maka ne? Kuma zaka iya ƙara aure bayan kace tafi kowa yi maka kyau?". "Kyawun ta baya ruɗi na, saboda ni soyayyar mace na tsakani da Allah na ke so, kuma irin halayen...". sai kuma ya yi shiru bai ƙarasa faɗin abinda zai faɗa ba. "Me ka ke so kace mun Dr? To ni nace maka kana da kyau mai kyau, nima ka ce ina da shi mana, kasan nafi son na auri mijin da zaice mun Hummy kina da kyau, Hummy gayun ki yana burge ni, kai Hummy yau kin mun kyawun da ba bu macen da taɓa yin irin na ki". na faɗa ina kwaikwayon irin muryan da mijin zai dinga faɗi. Kallo na ya ke yi fuskar shi cike da farin ciki, shima matso da kanshi ya yi kusa da nawa a hankali yace, "kyautan me ki ke so na miki yau?". Duban shi nayi fuska a yamutse na ce, "kyau ta kaman ya ya? Ni da na ce ka ce mun ina da kyau ka ƙi, sai kuma kace mun kyautan me na ke so kamun? Ni bana so kawai kace ina da kyau, kuma ga shi baka ce kaya na sun mun kyau ba". Na faɗa ina hararan shi, wanda fuskar mun ta yi kusa dana juna. Lumshe idon shi ya yi sannan ya sake buɗe su a kaina, a hankali yace, "kazar mayun nan ba kiji ta ce yau yakamata na miki kyauta ba? Saboda kin sakani ina ta farin ciki". "Rabu da ita ai ni ba ka sakani farin cikin ba, saboda haka bana son kyautan komai, sai ranan da kace kai Hummy kin yi kyau, to zan gaya maka irin kyautan da na ke so". "Ko ki gaya mun abin da na kike so ko kuma yau Dr'n ki ya yi ta miki kuka har sai kin faɗa mishi ya baki". Ya faɗa kaman zai yi kuka yadda na ke yi. Dariya na ke yi mai sauti ina kallon shi ya zunɓuro bakin shi irin yadda na ke mishi rigima, "Dr ashe kaima ka iya sakalci? To kada kayi kuka Babyn baby, zan gaya maka abinda na ke so". Tsayawa ya yi da abinda ya ke yi ya ƙura mun ido fuskan shi gaba ɗaya ya canja lokaci guda, a hankali ya furta, "Babyn baby" sai kuma ya runtse ido yana tuna ranan da Aisha tana kallon shi a gefen Ummi ya nata sakalci ta ce, "to sannu Babyn baby, don ka kusa ka ɗauki babyn ka amma kana sakalci kaman baby". sa ke buɗe idon shi ya yi yana duba na a hankali ya ce, "tashi mu tafi gida Aisha Humaira". Muna shiga mota na kalle shi na ce, "Babyn baby baka gaya mun dalilin da yasa baka gaya wa kazar mayu ni sister ka ba ne". Juyowa ya yi ya dube ni, sannan ya maida kanshi kan tuƙin da ya ke yi yace, _*KU KASANCE AKO YAUSHE DA ALƘALAMIN AUNTY NICE DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA, TSAKANIN DR HUSSAIN DA HUMAIRA, SANNAN KUMA KU SAMU SANIN WACECE AISHA?*_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*SADAUKARWAR PAGE ƊIN NA KUNE, HAFSAT ISAH PZ & HAUWA MUSTAPHA JAJERE A (Gaskiya Fans H) KUYI YANDA KU KE SO DA SHI, INA JIN DAƊIN YANDA KU KE SON WANNAN NOVEL ƊIN, SABODA HAKA MA BESTY NAH (Miss Xerks) TA CE NA GAISHE KU BOHOT-BOT... Kuji daɗin karatu lafiya.*_ *SHAFI NA 12📑* *__________📖* Daga Abbu har Ummi sun ji daɗin karrama su da na yi musu, bayan munga ma dinner ta re da su, Abbu ya maida hankalin shi kan kallon News da ake yi na ƙasan, ni da Ummi kuma kaman wanda mu ka shekara muna tare, sai hira muke yi na rayuwar Amal da irin wahalar da ta ke sha. "Ummi to me zai hana Amal ta dawo wuri na mu zauna tare? Saboda yanayin ciwon ta ina ga bai dace ta zauna ita ɗaya ba, saboda wataran ina ga baza ta iya samun sararin yiwa Dr waya ba, ko me ki ke gani Ummi?". Na faɗa ina matsawa jikin ta, tsabar samun wuri irin nawa, dama asali ni mai son naga ana nuna mun kulawa ne, domin duk ranan da kaka ta tazo gidan mu ko naje wurin ta, sai Daddy yayi ta mana shari'a, zata yi ta mitan ina tumurmusan ta, amma ina primary 6 Allah ya yi mata rasuwa, Allah ya jiƙan ta da rahma. Abbu ne ya juyo ya ƙurawa Ummi ido don jin mai za ta ce, amma sai Ummi naga ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai tunani, har tsawon wani lokaci sai ta ɗago tace, "Humaira ba wai naƙi shawaran ki bane, iyayen ki ina ga ba lallai ne su yadda ba, and secondly kuma ciwon Amal ba ita kaɗai ba, duk wanda ya raɓe ta ma sai ya sha wahalar jinya, keda aka kawo ki karatu, ai bai kamata mubar ki da jinyan Amal ba". Ummi ta faɗa tana share guntun hawayen da ya biyo idon ta. "Ummi Daddy na ba shi da matsala bazai hana ba, shima kullum sai yace tausayi na ya keyi na zama na ni kaɗai, kawai babu yadda ya iya ne, ciwon Amal kuma kawai nawa idan ya tashi ne na ƙira Dr ya tafi da ita asibiti, tun da asibitin su ba zama akeyi a wurin ba, ba kai musu abinci akeyi ba, komai acan ake musu, kinga ai babu wani matsala, bana son ta zauna ita ɗaya ne". Abbu ya yi gyaran murya yace, "Humaira bani number shi mahaifin kin, nima nayi tunani irin naki tun da muka shigo gidan nan, idan Allah yasa ya amince ni zan fi samun kwanciyar hankali ma". ya faɗa yana miƙo mun wayar shi. Da sauri na amshi wayar tsabar murna jiki na har rawa ya ke tayi, number Daddy na juye mishi, na miƙo mishi ina ta murmushi. Bai daɗe wayan yana ringing ba naji muryan Daddy yana sallama, alamar ya ɗauki wayan, Abbu ne ya fara gaishe shi, sannan ya mishi bayanin shi ne mahaifin Amal ƙawar Humairah, Allah sarki Daddy daga muryan shi za kaji yaji daɗin ƙiran da Abbu ya mishi, tambayar jikin Amal ɗin yayi, Abbu cikin farin ciki da jin daɗin an nuna kula akan ƴar ta shi ya amsa da sauƙi, sannan Abbu ya gayawa Daddy manufar ƙiran shi da ya yi. Daddy ma ya nuna jin daɗin shi in da ya ke cewa Abbu ai daman kulum zama na ni kaɗai tausayi na ya ke ji, don ma ya bada amana na wurin Dr Hussain ne ya samu ɗan sauƙin tunanin abun, amma ai bakamar yadda zasu zauna su biyu ba, don kuwa zata daina jin kaɗaici, kuma za suyi karatu tare. Daddy yace mishi kuma zai yi bayani wa Dr Hussain ya saka musu ido sosai a rayuwar su da kuma karatun su, duk da kullum alkhairin mu yake gaya mishi, shima Abbun yace insha Allahu kafin ya tafi zai sake samun Dr Hussain ɗin, haka suka yi sallama kaman wanda su ka daɗe da sanin juna. Kallon mu Abbu yayi yana murmushi, ya jawo flask yana zuba shayi mai cike da kayan ƙamshi, irin su citta da su kanamfari, "wato Humaira ina ga a wurin mahaifin ki ki ka gaji karamci, mutumin nan bai san wacece Amal ba da kuma iyayen Amal amma ya amince ku zauna tare, domin shi ɗin ɗan halak ne". sannan ya mana bayanin duk yadda su kayi da Daddyn, kowan mu sai farin ciki ya ke yi. Ina kallon Ummi nace, "Ummi gobe zanje na kwaso kayan Amal ɗita, ina dawowa a school". Ummi tana mun dariya ta ce, "ki bari mana a sallame ta sai kuje tare, Ke kam ai gobe school ya kamata kije ki nutsu ki maida hankali a abinda za'a muku, ɗebo kayan kuma sai kubar shi sai weekend ko". Ɗaga kai nayi ina murmushi, sannan na ɗauki wayana da ake kirana, ganin sunan Dr Hussain sai ya sakani tashi na wuce bedroom ɗina. Kan bed ɗin na hau na kwanta sannan na ɗauki wayan da ya sa ke shigowa a karo na biyu, manna shi kawai nayi a kunne na ba tare da nace uffan ba, sautin murmushin shi naji, sannan naji yace, "Babyn baby muna faɗa ne?". Turo baki na yi kaman yana kallo na, yadda kasan jikar kulu idan sun haura da amininta Hussain 80k, na yi magana ƙasa-ƙasa nace, "to ba kai bane ba". "To kuma ba ke bace ba". ya faɗa yana kwaikwayon murya na. Dariya nayi a ɓoye ina rufe baki na, ya sa ke cewa, "kawai sai kice mata na kaman kwandon wanke-wanke, bayan irin kyawun ta da na ke gani bana tuna ita ɗin gajeruwa ce, amma yau kinsa na fara tunawa ashe fa da kaɗan tafi kwandon wanke-wanke". Ina dariya na ce, "Dr'n mu zaka daina son ta kenan?". "Idan na daina son ta wacece zan so? Ko zaki sama mun wata?". Rufe ido na yi ina jin daɗin da ban san meye dalilin shi ba, "To kace mun bata da kyau, kuma ka dai na son ta". "Tun da ki ka ce mun kaman kwando ta ke, sai na daina son ta, kuma na daina ganin kyawun ta". ya faɗa shima yana jin daɗi da wani nutsuwa a ranshi daga in da ya ke. Dariya na dingayi na daɗi wanda har sai da naji Dr ma ya fara dariyan, don yadda na kasa dainawa, ina wani jin daɗi a raina. "Hummy'n mu kina jin daɗi ne?". Ya tambaye ni murya a hankali cikin nutsuwa. "Allah Dr'n mu yau daɗi na ke ji sosai, to yanzu zaka daina zuwa gidan ta ko? Kuma idan nayi kwalliya za ka ce ina da kyau?". Rufe idon shi ya yi daga in da ya ke yana ta murmushi, shi kanshi ya rasa yau wace irin rana ce a wurin shi mai girman gaske, shi fa ko lokacin da yake tsokanan ƙanwar shi Aisha baya samun jin daɗi da nutsuwa irin yadda ya keji yanzu idan ya zolayi Hummy, ɗari bisa ɗari Hummy ta canja mishi tsarin rayuwar shi, da ko kaɗan baya jin sakewa a zuciyar shi, idan bai yi ƙarya ba ya kan yi good 1yr wani abu bai saka shi dariya ba, amma yanzu kullum ne, kuma ko wani lokaci sai ya yi dariya ko da shi kaɗai ne idan ya tuno ta a ranshi, yanzun ma wani dariyan yayi sannan yace. "To ai ke yarinya ce Hummy, bazan iya ganin kyawun ki ba yanzu, ki bari sai kin girma sai na duba naga kina da kyawun, abu ɗaya kawai nasani yanzu, Hummy ta mai hankali ce, Hummy ta mai baiwar ilimi ce, Hummy ta mai sakalci da shagwaɓa ce, Hummy ta mai rikici na, wanda kullum sai ta birkita ƙwaƙwalwar Dr ta da rikici". "Uhmm ni kan ban yadda ba, wallahi na girma Dr ni kam kace ina da kyau, kace na fi ko wacce mace kyau, Allah Dr'n mu har na kusa iso ka tsayi fa, idan na ƙara 2yrs fa tsayin mu zai zama ɗaya". Yana murmushi mai sauti yace, "to mu bar shi ya kai 2yrs ɗin sai na gaya miki a lokacin". "To bazan sa ke kula ka ba sai lokacin, kuma kaima ba za ka sake kula kowa ba, sai ka jirani har lokacin". ta faɗa kaman zata mishi kuka ta wayan. "Wayyo Baby idan kin daina kula ni a mutuwa zan yi, kullum kuka zan ta miki fa Baby". ya faɗa shima yana kwaikwayo na. Dariya ya sa ka ni sannan nace, "Ba zaka mutu ba insha'Allah sai na girma kace Humaira ta fi sauran mata kyau, Humairah tafi ko wacce macce iya kwalliya da girki, Hummy kin fi Aisha kyau". na faɗa ina rufe baki na. Shima dariyan ya fara yana cewa, "Hummy har Aisha'n mu baki so nace ta fiki kyau? Lallai ina da aiki a gaba na, anya zaki bar ni na kalli wasu matan kuwa? Hala daga ranan da nace kin fi kowa kyau to ƙwalele na da ganin kowacce mace ko?". Ina dariya na ce, "Dr'n mu na fiso kai ta ganin ni kaɗai ce mai kyau a duniya, duk ranan da kaga kyawun wata to mutuwa zanyi". na faɗa mishi jiki na a sanyaye. Ajiyan zuciya ya yi bayan ya daɗe dayin shiru, "Hummy na miki alƙawari duk ranan da nace kinfi sauran mata kyau to bazan sa ke ganin wata nace tana da kyau ba, bazan so ki mutu na zauna a duniya ba bu ke ba, na fi so na riga ki mutuwa, don ke nasan za ki iya riƙe mun yara na ko bayan bana duniya ko Hummy nah". "To ai baka kawo mun su nagan su ba". na faɗa ina mishi shagwaɓa. Dariya ya yi yace, "Hummy kema ai bai wuce na yi rainon ki ba, shiyasa bazan kawo miki nawa yaran yanzu ba, don zasu haukata mun ƴar Baby na da na su irin rikicin, ni kuma yanzu karatu na ke so Baby'n baby ta yi". "Ni dai naƙi wayon, ka kawo munsu a weekend, wallahi ina son yaran ka Dr". "Nasani ai Baby, duk duniya ai babu wacce zata fiki son ƴaƴana sai dai Ummi na ta biyo bayan ki, amma bana son yanzu su wahalar mun da ke ne, don nafi damuwa da kiyi karatu sama da kula mun da yaran". "Kana nufin ko Maman su ma na fita son su"? "Kema ai Maman su ce, ko baki so suce miki Mama?". Ina dariya na ce, "kasan me nake so suce mun"? "sai kin faɗa". Ina dariya nace, "Mamie, saboda idan na girma na yi aure na haihu haka na ke so yarana su ce mun Mamie". na ci gaba da dariyan alaman naji kunya. Shiru ya yi na wani lokaci, sannan yace, "ni kuma Abbie ko? Hummy kin taɓa son wani ne a zuciyar ki?". Shiru nayi, daga baya nace, "Dr ni ban san ya ya ake jin soyayyan ba, ai sai na girma tukun nasan yadda ake soyayya, kasan Daddy baya bari na naje ko ina, don baya son a cutar dani yace mun, kaga ni ko friends da maza ya hanani, ni kai kaɗai na taɓa sabawa da kai bayan Daddy na, sai na girma idan nayi saurayi zan gane, ko zaka gaya mun yadda akeyi tunda kai ka taɓa yi?". "Irin wanda ki ke yi yanzu". Dariya nayi nace, "Dr ance maka ina soyayya ne? Nifa bana kula kowa, kuma zaka na gani, Dr Abdallah ma da kace kada na kula shi, ai ɗaure fuska na na keyi kaman na zama Boss". Dariya ya yi tayi wanda har nima sai da na fara taya shi, a ƙarshe nace, "Dr'n mu yaushe za kaje wurin su Aisha?" Lokaci ɗaya naji ya yi ɗiff bai ƙara cewa komai ba, magana nayi ta mishi amma bai kula ni ba, har sai da na fara mishi kuka tukun yace mun, "kada ki ƙara gaya mun haka, ke baki son na zauna da ke ne"? Ina share hawayen ido na nace, "ina so Dr, ai na tambaye ka saboda bana son ka tafi ka bar ni ne". "Insha'Allahu bazan bar ki ba har iya ƙarshen rayuwa ta, sai dai ke idan kin guje ni". Murya ta tana rawa a hankali nace, "Dr nah! Bazan taɓa barin kaba, ko aure nayi da kai zan tafi, bazan bari mu rabuba har abada muna tare". "Bazan biki gidan mijin ki ba, saboda idan ya ɓata miki rai zan ƙarasa shi, kawai mu zauna tare, ko na miki tsufa?". "Ni bana ganin ka tsufa, ni kyau ka ke mun sosai, kuma kana burge ni, kai kaɗai na ke son na dinga gani kullum, na fasa auren ma, da kai zan zauna, amma kai ma ba zaka auri kowacce mace ba, mu kaɗai zamu zauna tare". Tashi Dr ya yi daga kwancen da yake ya riƙe kanshi, idon shi a lumshe yace, "me ki ke ji a kaina Hummy"? Nima tashi nayi na zauna kaman zanyi kuka, don na rasa ni mai na keji ne yau akan shi, ina jin kaman zuciya ta zata fito, kuma na kasa gane yanayin da na ke ciki, a hankali nace, "Dr nah! Ni kan kazo wuri na yanzu". na faɗa kuka yana kuɓuce mun mai ƙarfin gaske. Dafe kanshi ya cigaba da yi da ƙarfi ya furta, "ya Rabbi". a zuciyar shi yace, "wayyo Baby nah kin yi nisa ya ya zan miki ne ni Aliyu Hussain". Shima hawayen ya samu kanshi yana fito mishi. "Dr kazo". "Baby kwanta kiyi bacci gobe akwai school, zamu ƙarasa maganan gobe". "ni kam naƙi Dr'n mu, to zuciya ta tana mun ciwo, zan gayawa Daddy yazo ya kaini asibiti". na faɗa ina kuka. "Kada ki gaya mishi, ki bari gobe zan kawo miki wani magani zaki daina ji, rufe idon ki na gaya miki wani abu". Da sauri na rufe, amma sai naji yana mun waƙan wani tsohun film ɗin india, wanda yawanci na kanji Daddy yana jin shi amma ni bai taɓa mun daɗi ba, amma yau sai naji daɗin shi kaman zai saka ni kuka, wani tsohun waƙa ne da Amit ya yi na film ɗin *KHABI KHABI*. *©AUNTY NICE CE*✍🏼 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*MAMAN ABDALLAH*, *MAMAN BASH*, *SA'EEDA SADIYA* *NA GASKIYA FANS D, WANNAN SHAFIN NAKU NE, DOMIN TUKWAICIN IRIN ZAFAFAN COMMENT DA NAKE GANIN KUNA MUN AKAN WANNAN NOVEL, NAGODE ALLAH YA BAR MU TARE, IDAN BA KU BABU BOOK.*_ *SHAFI NA 11📑* *__________📖* Tun da na idar da sallan ban tashi a wurin ba, har lokacin ishaa yayi na tashi na fara yin sallan, ina cikin yin shafa'i da wutiri naji ana shigowa cikin ɗakin, ina cikin sujuda naji muryan su Abbu da Ummi, suna gaisawa da Amal, daga baya kuma naji Dr Abdallah ya musu sallama ya bar ɗakin. Ina idar wa na juyo fuska na ɗauke da murmushi ina gaishe su, kaman wanda muka shekara da sanin juna mu kayi ta hira da su, in da Ummi ke bani labarin ciwon Amal da yadda yake ba ta wahala, "yaran mu uku a duniya, daga babba Yayan Amal wanda shi tun yana ƙarami Allah ya mishi rasuwa, kuma shi sai ya kasan ce, AA, sai mai bi mishi shi kuma AS ne, yana karatu yanzu haka a Oxford university, mai suna Faisal yana shekaran shi na ƙarshe kenan, in da ya ke karantar medicine, Amal ita ce mace a cikin su, kuma ita Allah ya ɗaura mata wannan laruran, amma kuma mungode Allah da ya bamu juriya da haƙuri na kula da ita, saboda shi ciwo ne wanda mai ciwon da mai jinyan kullum a wahale suke, mun so tayi karatu a kusa da mu cewar Ummi, amma sai nayi tunanin wata rana fa Amal in tana da nisan kwana, za tayi aure kuma bamu san in da auren zai kaita ba, shiyasa muka yanke shawaran kawota nan tayi karatu, amma kullum a cinkin fargaban ciwon ta muke". Ummi ta faɗa tana ta daddanawa Amal ƙafa, wanda tun shigowan ta abinda ta ke tayi mata kenan. Haka mu kayi ta hira har Dr Hussain ya shigo, gaisuwa ya musu na girmamawa, wanda daga gani Abbu yaji daɗin hakan, haka ina lura da Abbu sai jan Dr da hira ya ke tayi, shi kuma cikin kunya da rashin sabo da yawan magana ya ke amsa mishi. Muna ta hira ni da Ummi akan karatun mu, ita kuma Amal ta rufe idon ta kaman mai bacci, amma idon ta biyu don wani lokacin ta kan buɗe idon ta tana amsa mana wani maganan, wani kuma tayi shiru tana kallon mu, ko kuma ta rufe idon ta, ita kaɗai tasan irin azaban da ta ke ji a cikin ƙasusuwan ta, sai kuma ƴan uwan ta masu irin wannan lalura. Dr Abdallah ne ya shigo fuskan shi ɗauke da murmushi yana duban Abbu cikin yaren su na larabci yace, "Abbu lokacin cin abincin Amal yayi, mai kula da ita zata shigo, sannan a ƙa'ida ba asan visitors a ɗakin, ko zan kai ku masauƙi ne Abbu". Ya faɗa yana bin Abbun da kallo fuskan shi yana ta fitar da murmushin da baya barin fuskar shi. "Ba sai ka nema musu wurin kwana ba, ina ga kaman babu takura idan sun kwana a gidan Humaira ko gidan Amal". Dr Hussain ya faɗa ba tare da ya dubi idon kowa ba. Murmushi Dr Abdallah yayi sannan ya dubi Abbu wannan karon cikin kalmar turanci, don yayi matuƙar mamaki da yaji Dr Hussain yana jin larabci yace, "Abbu zaku iya zama a gidan Humairan ko na Amal ɗin?". "Nikan ina ga idan babu ta kura kuzo gida na kawai Ummi, saboda akwai extra room wanda Daddy ma anan ya zauna, ina ga zaku iya zama da Abbu idan bazan takura ku ba". na faɗa ina matsawa kusa da Amal ina riƙe hannun ta. "Babu komai Humairah wurin ki dana Amal ai duk ɗaya ne, so babu komai zamuje gidan ki, tunda 2days ma kawai zamuyi mu juya, saboda munga jikin Amal ɗin Alhamdulillah, bai yi mata tsanani ba sosai". Abbu ya faɗa yana shafa kan Amal ɗin, wanda tun da taji maganan tafiyan mu ta buɗe ido tana bin mu da kallo ɗaya bayan ɗaya. A hankali ta buɗe baki tace, "Ummi kuje gidan Humairah zata baku kula sama da yadda zan baku, kuma Hummy bata da problem, za kuji daɗin zama da ita sosai". ta faɗa hannun ta riƙe dana Ummin. Haka muka yi sallama muka fita, muna zaune nida Dr Hussain a mota muna jiran fitowan su Abbu, don a ciki muka bar su saboda suyi sallama da ƴar su, bayan shima Dr Abdallah shima ya bar ɗakin. "Me kika shirya musu for break fast"? Dr ya tambayeni ba tare da ya kalle ni ba. Kallon shi nayi na kawar da kaina gefe ina kallon hanyar fitowa daga asibitin nace, "ina ga aiɓchips is okay, sai na sayi bread su sha da tea, saboda larabawa basu wasa da cin bread". na faɗa ina juyowa ina kallon shi. "Kina da enough potatoe ɗin?". Ɗaga mishi kai nayi alaman ehh, saboda ganin tahowan su Abbu. "Idan babu na kira wife ɗina ta musu acan, idan yaso da safe sai na karɓo da sauri". ya faɗa yana wani munafukin murmushi, kallon shi kawai nayi bance mishi komai ba, saboda ganin su Abbu suna shirin buɗe ƙofan motan. Haka muka yi ta tafiya kowannen mu bakin shi shiru, sai Ummi da Abbu da ke zaune a baya ne kawai suke magana, in da daga baya Abbu yake tambayan Dr ya ya za'ayi da maganan school ɗin Amal? Tun da gashi gobe monday ita kuma tana asibita, ya ya za'ayi kenan"? Yana shiga gate ɗin gidan mu ya amsawa Abbu da cewa, "gobe insha'Allahu zan yi report a school, duk abinda akayi tunda bata nan sai ƙawarta ta nuna mata daga baya, tunda ba laifi suna maida hankali akan karatun, so abin bazai musu wuya ba, sai dai addu'an Allah yasa kada abin ya ɗau lokaci". "Ameen ya rabbi". Abbu da Ummi suka amsa mishi. Gidana na buɗe musu suka shiga, muna shiga suka zauna a parlor, ni kuma na shiga ɗaki domin na shimfiɗa musu bedsheet, domin tun da Daddy ya tafi na cire, sai dai bayan 2dys ina sha re wurin na goge komai, don ni ban yadda da zama cikin ƙazan ta ba, ina ta tunanin mai zan fito na ɗaura musu mai sauƙi for dinner. Ina fitowa na dube su ina murmushi nace, "Ummi ko za kuyi wanka kafin na girka mana abinda zamu ci?". Na faɗa ina ƙarasuwa parlon. "My luv kada ki wahalar da kan ki, kawai tea za musha da bread, saboda Abbun ko baya iya zama babu tea". Ummi ta faɗa tana miƙewa tsaye tana dariya. Shima dariyan ya yi yana miƙewa yace, "Faɗi gaskiya dai, kice bamu iya zama babu tea daga ni har ke". Ni dai dariyan su kawai na keyi domin kaman basu suka haifi su Amal ba, babu wani girman kai ko raini suna wasa da junan su kaman ƙawaye, suna shigewa na ɗauki waya na da yake neman a ɗauke shi, domin ringing ɗin da yake yi. "Ki fito waje ina jiran ki". cewar Dr Hussain, ajiye wayan nayi bayan naji ya ajiye ta shi. Ina fita nagan shi tsaye a jikin mitan shi, ina ƙarasa wurin ya miƙo mun wani babban laida, mai ɗauke da tambarin *MCDOULS* take away yai mana, sannan ya miƙo mun ɗayan leda wanda yake cike da bread da wasu snacks ɗin kala-kala, ɗagowa na yi ina duban shi. "Kinsan larabawa da son kayan flour, saboda haka ki shiga musu da shi, ni kuma bari na shigo da Potatoe ɗin da kuma plantain da egg, na ƙaro miki ne saboda kada ku takura". Hararan shi na yi cikin wasa nace, "hala matar ka bata iya soyawa ba ko? Shiyasa ta koro ka da shi kadawo min, dama dai nima nayi tunanin matar da ta ƙware da barin mijin ta da yunwa yana bin gidajen cin abinci? To yaushe tasan tayiwa baƙi idan ba neman magana irin na mazaje ba". na faɗa ina ƙarasawa balcony ɗi na, wanda shima yana biye da ni abaya yana ta murmushi bai ce mun uffan ba. Har kitchen ya raka mun da kayan hannun shi, nima ajiyewa nayi na miƙe ina kallon shi ganin yadda ya ƙura mun ido bayan ya ajiye kayan hannun shi. Murguɗa mishi baki nayi na juya ina ɗaga eggs ɗin ina saka su a wurin dana ke ajiyewa, sannan na zuba potatoe ɗin a cikin wani standing storage na zuba dankali da onioun, "to ai sai ka tafi tun da ka gama aikin ka". na faɗa ina kallon shi nima. Murmushi ya yi yace, "kin fara raina ni ko? Ni ba Malamin ki bane?". "Kuma Baby na ba, sannan kuma friend ɗina, kuma.... ". sai nayi shiru ina kallon yadda ya ƙura mun ido. "Kuma ɗan aiken ki ko?". Ya tambaya yaɓa ɗaga mun giran shi sama, alaman tambaya da son jin ƙarin bayani. Dariya na yi nace, "ni idan ba sharri ba yaushe na taɓa aiken ka?". "Gashi yanzu kin fitar dani naje miki aika, saboda kina ganin kin taddo ni tsayi ko". Matsowa nayi kusa da shi ina dariya nace, "kaiiii wlh duk tsayi na ban fi zuwa ƙirjin ka ba, kaifa dogon gaske ne Dr'n mu, don ina mamakin mai ya haɗa ka da mata wanda bata wuce kwandon wanke-wanke ba a tsayi". Na faɗa ina dariya ƙasa-ƙasa. "Yayan mu ina mamakin mai yasa ka ke son wannan corper? Wallahi kai dogo ne sosai gara kasamu mata doguwa, amma wannan corper kam ai bata wuce tsayin ragon da aka yanka na layyan bana ba, ƴar ƙuƙur kenan". cewar Aisha lokacin da ta rutsa ni a kitchen tana mitan neman corper da na ke yi. Kallon Humaira na yi sannan na bata irin amsan dana bawa Aisha a wancan lokacin, wanda shi ne kawai nasan zai sa ka ta rufe bakin ta, "to ke bakiga irin kyawun da ta ke da shi bane? Ina ruwa na da wani tsayin ta tun da ni ina dashi ai ya ishe mu, kawai kyawunta da yasa bana iya ganin na kowacce mace ne ya ɗibe ni na aure ta, kuma har yau bana ganin wacce ta fita a ido na, kowa ganin ta na ke yi kaman biri a gaba na don muni". ya faɗa yana wani jujjuya kanshi alaman abin ya mishi daɗi. Fita nayi daga kitchen ban ko bi ta kanshi ba, wucewa ɗaki na kawai nayi don ganin su Abbu basu fito ba. Ina wucewa ya yi dariya shi kaɗai yana tuna Aisha wanda lokacin ita tsabar haushi kuka ta fashe da shi taje tana gaya wa Ummi wai nace tana kama da biri, wanda Ummi ta ƙira ni tana cewa, "saboda Allah Hussain ko wani kaji ya cewa ƙanwar ka tana kama da biri ai sai in da ƙarfin ka ya ƙare, ko dan Albarkacin ita tayi kamanni na ai za ka ce tafi kowa kyau a duniya". Hassan ne ya amsa da wuri yana cewa, "Ummi to wai ita meya sa ta damu da sai Hussain yace tana da kyau? Saunawa ina gaya mata kafin a samu mai kyawun ta sai antona, saboda kaf zuri'ar mu babu mai kyawun ta, amma nawa baya burgeta sai na amininta ta ke jira ya faɗa, wanda har ta mutu bazai faɗa ba, kuma ta haɗu da aiki wallahi, garama ta haƙura mijin auren ta wataran zai gaya mata". Hararan shi Aisha ta yi tace, "kafin nayi auren miji na yace ina da kyau, Yaya Hussain ɗin nake so yace ina da kyau, ai kai na gajji da faɗan da ka ke yi na shi kaɗai na keso ya faɗa, tun da shi ai bai taɓa faɗa ba". sannan ta kalli Ummi tace, "Ummi nah don Allah kice mishi ya faɗa mun ko sau ɗaya ne". ta faɗa tana kwanciya a jikin Ummin. Ummi ce ta dube ni da faɗa tace, "bana wasa da kai Hussain kazo kagayawa ƴar uwar ka tafi kowa kyau a cikin matan duniyan nan, idan kana so mu zauna lafiya da kai yau a gidan nan". Dariya na yi har ina buga ƙafa na, muka tafa da Hassan sannan nace, "Allah Ummi bazan faɗawa wata mace tana da kyau ba har sai matar da zan aura, ita ma kuma har sai ta shigo gida na zan gaya mata, domin zai fi mata daɗi, amma haka kawai na ƙarasar da kalma mai girma da daraja tun a waje? Lokacin da ya kamata na faɗa kuma ya zama bai mata daɗi ba? Gaskiya Ummi na ma gudu". da gudu na fita a ɗakin Ummi, wanda ina jin dariyan Hassan kaman zai tada Parlon ita kuma Aisha sai kuka ta ke tayi, Ummi na bata haƙuri. Fita ya yi a kitchen ɗin cikin jimamin rashin familyn shi da ya yi na shekaru da dama a tare da shi? Ko ya ya Ummi ta ke? Ya ya Hassan zai ji idan ya buɗi ido bai ganshi ba a rayuwar shi? Duk da suna yawan faɗa amma suna son junan su wanda babu wanda ya ke shiga tsakanin su, don ko suna faɗa idan wani ya saka baki to sun daina, sai dai su rungume junan su suna dariya, kuma ko ya ya Aisha ta ke? Ko yanzu yaran ta nawa? Wata aura? Allah sarki Abban su ko ya ya zai ji idan babu ni a rayuwar shi? Duk da sun kasance ƴan biyu amma Abba yafi nunawa Hussain soyayya, Allah sarki Aunty Hauwa ita kam yasan hala sai tafi Ummi shiga damuwa. Har ya shiga part ɗin shi hankalin shi a tashe, yarasa me yasa tun haɗuwar shi da Hummy ya zama kullum suka haɗu sai ta tuna mishi da wani abu na familyn shi. Kwanciya ya yi a parlor, sannan ya ƙira ni, ina ɗauka muryan shi a hankali yace, "Babyn baby na tafi don Allah ki bawa baƙin nan abincin, naga kin wuce ɗaki bamuyi sallama ba". "Naji yanzu ma ina kitchen ɗinne, gudnyt". na faɗa mishi ina kashe wayan, don har yanzu raina a ɓace ya ke da shi. *#Comment, Vote & Share.* *©AUNTY NICE CE* ✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*RIGIJI GABJI,RANAR KUKE JIRA YAU GATA TAZO MASOYA_* _*MARUBUCIYAR NAN TAKU WADDA TA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI INGANTATTU MASU TSUMA ZUCIYAR ME KARATU WATO HASSANA D'AN LARABAWA ,MARUBUCIYAR*:_ _SANADIN HOTO_ DA _HASSANA DA HUSSAINA _ _*YAU TA SAKE DAWO MUKU DA SABON LITTAFINTA WANDA YA ZARCE DUK LITATTAFANTA A KOMAI WATO CIN AMANAR RUHI,KAI DAGA JIN SUNAN KUN SAN AKWAI TAFKA TAFKA DA K'ULLE K'ULLE ,AMMA ZATA WARWARE MUKU K'ULLIN DA ZARAR KUN BIYA 200 DOMIN SAMUN LITTAFIN,KAR KU BARI YA WUCEKU ,DOMIN WANI IRIN LABARI NE DA BAKU TAB'A CIN KARO DA IRINSA KO MAI KAMARSA BA,FAD'AKARWA ,NISHAD'ANTARWA,ILIMANTARWA,TAUSAYI,DA SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA ,TARE DA WATA IRIN CIN AMANA DA BAKU TAB'A RISKAR IRINTA BA,KU DAI KU HANZARTA NEMAN MARUBUCIYAR DOMIN KU SIYA KU KARANTA AKAN KUD'I K'ALILAN 200*_ _*ZAKU IYA NEMANATA AKAN LAMBARTA KAMAR HAKA,08080049548 DAGA NAN ZATA GAYA MUKU YADDA ZAKU BIYA KUD'IN ,KU DAI KU HANZARTA KAR AYI BABU KU ,KU TUNA DA SUNAN LITTAFIN*_ CIN AMANAR RUHI _*NA MARUBUCIYAR KU HASSANA D'AN LARABAWA*🥰🥰🥰🥰_ *SHAFI NA 13 📑* *__________📖* Ni dai ban san me ya faru ba, sai farkawa na yi cikin dare naga waya ta a yashe a gefe na, murmushi na yi ni ɗaya wayan na ɗaura a bedside drower, wato bacci nayi Dr yana mun waƙa ko? Kaɗa kai na nayi na shiga toilet. Bayan na idar da sallan asuba, kitchen na wuce na zauna na fere dankalin, sannan na soya na soya ƙwai da plantain, na so na yi peppesoup, amma ganin babu time yasa kawai na kai musu kan dinning na ajiye ketchup a kan dinning ɗin, flasks na cika da ruwan lipton mai kayan ƙamshi, ina gama jerawa nayi sauri na shige toilet na yi wanka, gudu-gudu na fito na shirya, sannan na ɗauki breakfast ɗin kaɗan naci, note na ɗan rubutawa su Ummi sannan na ɗauki handbag ɗina na wuce zuwa school. Ina fitowa na haɗu da Dr shima ya fito zai wuce school ɗin mu, murmushi yamun nima na mayar mishi, ƙarasowa yayi har in da na ke, sannan ya buɗe mun front sit na shiga, shi kuma ya zagaya wurin zaman driver. Yana ta da motan na gaishe shi, yana kallon kan hanyan ya amsa, sannan ya tambaye ni ya ya baƙi na suka kwana? Ina murmushi na ce mishi, "lafiyan su ƙalau, amma basu fito ba na fito yanzu". "Break fast fa, kin musu dai ko"? Ɗaga kai nayi alaman ehh na musu. "Ni ne kawai ba kiyi dani ba ko?". Hannu na saka na rufe baki na ina dariya. "Hmmm dole kiyi dariya mana, tun da kin cika cikin ki ni kuma kin barni da yunwa, amma babu komai zanje wurin khadija nasan zata soya mun egg nasha da tea", ya faɗa yana murmushi. Hararan shi nayi na turo baki na gaba ina ta ƙunƙuni. "Ki faɗi abinda ya ke bakin ki zaifi miki sauƙi, amma harara na ba zai miki sauƙi a ranki ba". "Ni bance komai ba, tun da nasan matar ka bata iya girki ba, hala ma idan taje soya ƙwan ya ƙone bata san yadda akeyi ba". Dariya ya yi ya na shiga gate ɗin school ɗin, juyowa ya yi ya kalle ni bai ce komai ba sai murmushi, yana ta rawa da kanshi yana murmushi yana kallo na. Muna isowa ƙofan department ɗin mu ya yi parking idon shi yana kallon wani wuri yana munafukin murmushi. Hararan shi nayi a hankali na dubi in da ya ke kallon, Dr Khadija ce tsaye tana rufe motan ta, gefen ta kuma wata friend ɗin ta ce a tsaye suna magana, dawo da kallo na nayi kanshi, buɗe motan nayi na fita bata re da na ce mishi komai ba, ganin saura 15mnt a shiga mana class nayi sauri na ƙara sa hall ɗin da muke lectures, ina ganin yadda Dr Khadija da ƙawar ta suka bini da kallon mamaki, haka ma wasu daga cikin students da lecturers suka dinga bina da kallon mamaki. Ina wucewa shima ya fito bayan yayi parking motan shi, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce office ɗin shi, ganin haka yasa Dr Khadija bin bayan shi da sauri ranta a ɓace, duk ƙiran da ƙawarta ke mata bata kula ta ba, ita dai sauri kawai ta iso shi taji dalilin shi na ɗauko ni a motan shi. Ina shiga class ƴan class ɗin mu suka yi ta tambaya na ina Amal, wasu na gaya musu bata da lafiya, wasu kuma na sha re su ina duba note ɗin cost accounting da Ezeh ya miƙo mun, kuma ina maida hankali na kaɗan kanshi da naji shi ƙasa-ƙasa yana ce mun. "Beauty dama Dr Hussain brother ɗin kine ko?". Ina kan buɗe note ɗin ban kalle shi ba nace, "Uncle ɗina ne, shi ɗin ƙanin Daddy na ne". "Heyy no wonder mana naga yana tolerating ɗin ki, kaman wancan ranan da ki ka ba shi haƙuri ai ya dawo ya ci gaba da lectures, so yanzu kawai kice zan kama ƙafan ki don gaskiya bana son na faɗi a course ɗin shi seriously, kinsan 4 credit unit ne, kuma ga shi shine *PROGRAMME CO-ORDINATOR* Namu, don ma naji ance Professors ɗin nan ake bawa Heads of Departments, amma da an bashi na department na mu, saboda ƙoƙarin shi a department ɗin". haka muka yi ta magana akan course ɗin, kafin lecturer su fara shigowa. Dr Khadija tana shigo mana ranan naga bala'in ɓacin rai kwance a fuskar ta, sai wani ɓata rai ta keyi kaman an saka ta dole, kuma tambaya ɗaya zata ɗaga ni tayi mun, abinda na lura nema ta keyi ta ga gazawa na, amma daya ke ni ɗin ba kanwar lasa bace, sai ta kasa samun in da zata ƙure ni, domin idan ba yabon kai ba, idan ku ka cire Ezeh to duk class ɗin ba zaka samu na sama dani ba, amma baza kasan hakan ba, sai an taɓo ni, saboda ni karatu na bana nunawa mutane bane. Tana gamawa ta dubi ƙofa dai-dai lokacin Dr Hussain ya iso, dawo da kan ta tayi ta dube ni, fuska a ɗaure cikin shegen haɗaɗɗen turancin ta kaman na tsohuwar baturiyar england tace na sameta a office after na gama lectures. Bance mata komai ba sai bin ta da ido da nayi ta tayi har ta bar class ɗin, a lokacin Dr Hussain kuma ya shigo, ina ganin shi ya kauce ma ta ta fita, domin da yi tayi kaman zata bangaje shi, amma ba zaka gane ya ya yanayin fuskar shi yake ba, saboda babu yabo babu fallasa akan face ɗin shi. Tun da ya fara lectures bai kalli in da nake ba, sannan idan ya yi question baya duban in da na ke ballanta na ya mun tambayan, haka ya gama lectures ɗin shi, yana gamawa ya tako har in da na ke zaune, yana kallon cikin ido na yace, "kada na yadda naga kinje ƙiran da Khadija ta miki kin ji ko". Ɗaga mishi kai nayi alaman naji. Yana duba na fuska a ya mutse yaɗan sunkuyo da fuskan shi saitin in da nawa ya ke yace, "yunwa na keji Babyn baby". ya ƙarasa faɗi kaman zai mun kuka, juyawa nayi da sauri na dubi ƴan class ɗin amma sai naga duk idon su yana kan mu. ya mutsa fuska na yi ina nu na mishi alaman ana kallon mu fa, amma sai ya wani ɗaga kafaɗa irin ko ajikin shi, ya sa ke sunkuyowa ya kwaikwayi murya na yace, "Baby yunwa, wayyo babyn baby". ya faɗa yana ɗaura hannun shi akan cikin shi. Dariya nayi na miƙe tsaye ina kallon shi, a hankali nace , "to muje gida na soya maka egg ɗin da singulura ta kasa yi maka, muje na samu ladan ka". yana dariya shima ya biyo baya na muka fita a class ɗin. Ko sauƙa a brandan class ɗin ba muyi ba muka ji ihu da buga desk da ƴan class ɗin suka yi, ina jin muryan wani yana cewa wallahi girl friend ɗin shi ce, Ezeh yana ta rantse musu akan uncle ɗina ne. Kallon Dr nayi baki na a buɗe ina nuna mishi yaji mai ƴan class ɗin suke cewa, shima dariyan yayi ya dawo kusa dani yana cewa, "To girl friend ɗin ne ko ni Uncle ɗin ki ne?". Tsayawa na yi da tafiyan ina kallon shi cike da mamaki nace, "kai kuma sai ka biyewa abin da zasu ce maka?". "To ya ya zan yi da rigan da babu wuya? Nikam kawai yau baki isa ba sai kin gaya mun waye ni a wurin ki". "Nikam ba bu ruwa na Dr, kai kawai Dr'n mu ne, kai malamin mu ne". "ni dai baki isa ba sai kingaya mun a tsakanin abin da su ka tambaya". Hararan Aunty Faraa nayi don ganin Hummy zata mishi bayani ita kuma ta wani daka tsalle tana ihu tana cewa, "sai Dr da Hummy Allah ya bar ƙauna ta gaskiya". da sauri Miss Xerks ta jawota da ƙarfi tace, "to kin yiwa kan ki, gobe baza mu ta ho da ke ba, kuma yau zan saka *NEAT LADY* ta turo jet ɗin ƴan gaskiya writers a koma da ke nigeria, saboda ihun nan da kika yi gashi kin sa ka sun yi shiru suna kallon mu". Juyowa ta yi tana duba na irin na hana Miss Xerks sakawa a maida ta gida, hararan ta nayi nace, "wallah komawa za kiyi yanzu yanzu ma, tun da ihu za kiyi a dinga jinmu, da naso ranan da za ace.........". *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _*NANA FIDDAUSI, ƊIYAR JIKAR KULU WANNAN SHAFI NA KINE KYAUTA, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR KI, YA KAWO MIKI ƘANNE MASU ALBARKA*_ *SHAFI NA 15📑* *__________📖* Kan bed ɗina na faɗa ina kuka mai zafi a zuciya, ni na rasa me yasa na damu da sai Dr ya yaba ni, bayan nasan ba zai ta ɓa yabawa ba, gara ma nayi haƙuri kawai, ina cikin kukan naji an buɗe ƙofan ɗakin an shigo. Dafa baya na naji anyi, wanda daga dukkan alamu Ummi ce, ban ɗago na kalle ta ba, amma na rage sautin kukan nawa. "Tashi Aisha Humaira muyi magana kinji". cewar Ummi, tashi nayi zaune ina ta sauke ajiyan zuciya. Hannu na ta riƙe gam a cikin nata tana duba na cikin nutsuwa, a hankali ta jeho mun da tambayan da ya kusa sakani dariya, "Humaira kina son Dr ne?". Kallon ta na yi kaman zanyi dariya nace, "Ummi son Dr kuma? Ni kam ban taɓa jin son shi ba, ni Ummi ba bu wanda na taɓa so a duniya irin Daddy na, sai kuma Amal da na ke son ta, ni bayan su bana son kowa". "Har maman ki baki son ta?". Kallon ta na yi ido na yana cikowa da hawaye, juyar da kaina nayi gefe sannan nace, "Mama na ta rasu". Jawo ni jikin ta tayi ta rungume ni saboda ganin hawayen da ya fara gangaro mun, a hankali tace, "Allah ya jiƙan ta da rahma, Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya na rashin ta". ni dai ban ce komai ba ina dai kwance a jikin ta nayi shiru hawaye yana bin fuska na, tun ranan da na bar ƙasar mu na daina zubar da hawaye na rashin Mama na, amma yau kuma kewar ta ya dawo mun zuciya ta mai rauni. _*ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU DA SU KA RIGA MU GIDAN GASKIYA, TABBAS RASHIN UWA WANI BABBAN MIKI NE WANDA BAYA CIKEWA, DUK WANDA TAYI RAYUWA BABU UWA GASKIYA ABUN TAUSAYI CE 😭😭😭ALLAH KA KAI HASKE A KABARAIN MAMA NAH!* 👏🏻👏🏻 "A hannun wa kika tashi?". ta jeho mun wani tambayan kuma. "Hannun Daddy nah da matar shi wanda muke ce mata Mama, tana da yara guda uku, Yaya Ahmad shine babba a cikin yaran ta, sai kuma Yaya Aliyu shike bin shi, sai Yaya kabir shi ne ƙara min su, shi kuma ya bani 2yrs, yanzu haka yana karatu a ATBU, ni kuma ni kaɗai Mama na ta haifa, kuma ni kaɗai ce ƴa mace a wurin Daddy nah, shi yasa ya ke sona sosai". na faɗa hawaye yana ɗan bin fuska na kaɗan kaɗan ina sharewa. "Hummy tunda kince ba son Dr ki ke yi ba, to zan baki shawara a matsayi na na mahaifiya a gare ki, daga yau ki daure ki daina damuwa idan baice kina da kyau ba, ko baice kin iya abinci ba, yaga kin damu ne shi yasa yake bawa zuciyar ki wahala, saboda duk ranan da ya tunkari zuciyar ki bazai samu matsala ba, saboda ya gama lugwaigwaita ta da soyayyar shi, kowa ya ganki yasan tsakanin larabawa da indiyawa sai anyi da gaske a samu mai irin kyawun ki, saboda ranan da na fara ganin ki na ɗauka aljanu ne zasu buɗe mun ido, Humaira ke ɗin ɗiya ce mai kyau da daraja, kada ki yadda da ga yau Dr ya sa ke saka ki kuka kin ji, daga yau ki nuna mishi baki son yabawan shi tunda ke mai kyau ce, kuma kin iya girki mai daɗi da kwanci a zuciya, domin ina hankalce da shi, lomar farko da yafara yi sai da ya lumshe idon shi don daɗi, saboda haka ko ya faɗa ko kada ya faɗa, girkin ki ya mishi daɗi". ta faɗa tana mun murmushi, saboda ganin nima na ke ta murmushi. "Humaira kin ji daɗi ne da nace miki yaji daɗin girkin?". Dariya nayi ina ɗaga mata kai alaman na ji daɗi. Lumshe ido tayi ta buɗe a hankali, a zuciyar Ummi tana jin tausayi na, domin tasan babu yadda za tayi na riga da nayi nisa a son Dr, sai dai fatan Allah yasa shi kuma ya riƙe amana, tasan komai zai ta gaya mun ba zaiyi tasiri ba, saboda bani da wayon da zan fahimce ta, saboda shi wayo bawai a shekaru bane, kawai baiwa ne, wasu kuma zama da iyaye suna nusantar dasu abinda ya kamata shi ke sakawa su fahimci rayuwa, wasu kuma irin mutanen da suka zauna dasu yake sakawa su fahimci rayuwa, amma abin tausayi tasan ni nayi rayuwa ne da giɓi na rashin uwa. "Ummi to ya ya ake jin so ɗin?". Na jeho mata tambayan da ba ta yi tsammani ba. Shiru tayi na wani lokaci, sannan ta ɗago ni zaune tana duban fuska na, "zaki na yawan tunanin mutumin, Za ki na yawan jin kishin wata akan shi, za ki na yawan jin tausayin shi, Za ki na son kina yawan ganin shi, ba za ki na gajjiya da jin muryan shi ba, Za ki na so kiga komai ki ka yi ya yabe ki, Komai aka faɗa na laifi akan shi baza kina gani ba, zai zama kullum hasken shi ki ke gani Za ki na ......". abubuwa da yawa Ummi ta lissafo mun akan yadda za ka ji kana son mutum. Da sauri na dafa zuciya ta ina lumshe ido na, duk wani tsoro naji ya kamani, a hankali na sa ke buɗe ido na ina kallon Ummi, "Ummi daga shekara nawa ka ke ji ka fara son wani?". Dariya ta yi mai ɗan sauti, sannan ta dube ni tace " soyayya bata da shekaru, ba ta da lokaci, ba ta shawara, bata zaɓe, duk lokacin da Allah ya hukunta za ka fara to babu makawa ko kashirya mata ko baka shirya ba zaka fara". "Na shiga uku Ummi, to wallahi zuciya ta tana son Dr Hussain, amma ni kam bana son shi Ummi". na faɗa ido na yana cikowa da hawaye, saboda gaskiya ni ban shirya yin soyayya ba, kuma bamuyi haka da Daddy na ba. "To ita kuma zuciyar ki ta shirya karɓan soyayya'n Dr, to ya ya za kiyi kenan?". Cewar Ummi. "Ummi ni kam bana son shi". "Me yasa baki son shi? Yana da wani problem ne?". "Ummi ni fa saurayi na ke son aure kuma yaro iri na, amma shi fa yana da mata, kuma ya yi mun tsufa, kuma Daddy yace mun kada nayi soyayya da kowa saboda maza basu da kir ki". Shiru Ummi tayi har zuwa wani lokacin tukun tace, "to ai ke baki da Laifi, tun ke baki san kin fara son shi ba, kawai yanzu abu ɗaya za kiyi ki kare kan ki". Da sauri nace "me zanyi Ummi"? "Kada ki gayawa kowa kina son shi, ko da Amal ce, shima kada ki bari ya gane kina son shi, don zai gayawa Daddy'n ki, itama Amal idan taji zata gayawa Abbu'n ta, shi ma zai iya faɗawa Daddy'n ki". zaro ido nayi ina duban ta da tsoro, sannan a hankali murya can ƙasa nace, "Ummi to ai bazan taɓa gaya mishi ina son shi ba, ban ma san ina son shin ba". na faɗa kaman zan yi kuka. "Yauwa ɗiya ta Hummy, kada ki bari kowa ya sani, shima ki daina damuwa da matar shi, ki dena damuwa da sai yace kina da kyau ko kin iya abinci, amma kiyi ta kwalliya da abinci mai daɗi kina bashi yana ci, kuma kada kina shiga gidan shi ke kaɗai, kina zuwa tare da ƴar'uwar ki Amal kuna kai mishi, ina miki albishir wataran da kan shi zai furta miki kin fi kowa kyau, amma sai kin kama kan ki, ki daina nuna kin damu da komai, kuma idan mun tafi duk abinda ya shige miki duhu ki kira ni ki gaya mun, ni kuma na miki alƙawarin warware miki komai kin ji doughter na". Abun tausayi yau jirgin ƙarfe 12:00pm na dare su Abbu suka tashi, ba Amal ba har ni sai dana yi kukan tafiyan su, saboda tun da nazo duniya ban taɓa jin na shaƙu da wata mace ta nuna mun ita uwa bace a gare ni sai ita, gara-gara kakanni na guda biyu duk sun nuna mun ƙauna, wanda ta haifi Daddy na ina primary 6 Allah ya mata rasuwa, amma ina tuna yadda ta ke masifa idan an mun abu ba dai-dai ba, sai kuma wanda ta haifi Mama na, duk da ba wani yawan ganin ta na keyi ba, saboda bata ƙasan, sai tayi shekaru kafin ta zo, amma duk ranan da tazo gani na takan nuna mun soyayya kaman ita ta haife ni, amma Daddy baya taɓa barin ta ta tafi dani gidan ta, haka kuma bai taɓa sakawa ta nuna ɓacin ran ta ba, saboda a gidan mu gefe na daban ne, in da ya zama na Mama na shi aka gyara mun, ina tare da masu mun aiki, so ko tazo ma takan iya wuni guda bata ga Matar gidan ba, a sake muke zama da ita. Basu bar mu mun rakasu airport ba, saboda yanayin jikin Amal, basu suka dawo ba sai wurin after 1, domin naji shigowan motan Dr Hussain. Da safe bayan mun yi wanka, sauri-sauri na soya mana egg muka sha Tea da bread da shi, haka muka fito domin tafiya school. A waje muka haɗu da Dr Hussain yana tsaye jikin motan shi, daga dukkan alamu mu ya ke jira, rufe ƙofan mu nayi, sannan muka ƙarasa in da ya ke tsaye, gaishe shi muka yi amma ban kalli idon shi ba, sai dai a jiki na naji ni ya ke kallo, tuna maganan Ummi nayi kada na bari ya gane na damu da shi, ina tuna hakan nayi saurin na buɗe sit ɗin baya na zauna, ƙura mun ido suka yi daga shi har Amal, amma naƙi kallon su, sai gyara books ɗi na da suke cikin bag ɗina kawai na keyi. Ganin zamu ɓata mishi lokaci gashi ni ban fito ba, ita kuma Amal bata shiga ko'ina ba, sai yayi sauri ya dube ni yace "ya ya kika zauna a baya?". Ina kallon books ɗina nace, "ai duk ɗaya ne da zaman bayan da gaba, ga Amal ta zauna a gaba kada mu mayar da kai driver bayan kai lecturer mu ne". Shiga ta yi ta zauna, haka yaja motan babu wanda ya sake cewa uffan acikin mu, muna isa Department ɗin mu nayi sauri na riga fita a motan domin na hango su Ezeh zasu shiga class ɗin mu, da sauri na isa in da suke muka tsaya muna gaisawa, sannan na jira Amal ta ƙaraso in da nake muka wuce class. Muna zama akayita zuwa ana gaishe ta, bayan kowa ya koma sit ɗin shi ta dube ni tace, "me yasa ki ka yi haka Hummy?". "Me nayi kuma yau?". Hmm tayi tsaki tana harara na tace, "meye ana cewa ki dawo front sit ɗin ki zauna ki ka ƙi? Bayan kinsan ke ya kamata ki zauna a wurin". "wani irin ni ya kamata na zauna? Yadda Dr ya ke malami na kema fa malamin kine, yadda Daddy ya bashi amana na, kema fa naki Parent ɗin sun bashi, yadda yake neighbour na kema yanzu ya zama naki, duk ɗaya yake a wurin mu, kuma ɗaya muke a wurin shi". Tsaki ta sake ja sannan tace, "amma dai kinsan da ke yafara sabawa ko". "kema zaku saba sosai, yau da gobe ne ai babu wuya, kuma daga yau ke zaki dinga zama a gaban motan saboda ku saba kema da shi". ina faɗa na juya na bar maganan da mu keyi haka. Ranan yana shiga mana lectures duk ya maida hankalin shi kaina, duk abunda ya ke yi idon shi yana kaina, sannan tambaya ɗaya zai jeho mun, amma tashi na keyi na mishi bayani babu wani tsoro ko shakku a ciki. Muna tashi na ɗauko mana handbags ɗin mu har dana Amal muka fita domin tafiya gida, a zaune a cikin motan muka sa me shi, yana ganin mu ya ƙura mun ido, amma sai nayi kaman ban ganshi ba, na kawar da kaina gefe har muka ƙarasa jikin motan, buɗe bayan nayi na shige ,ita kuma Amal ta buɗe gaban motan ta shiga. Ina ɗaga kaina naga ya sauke mun wani mummunan harara ta madubin motan, murguɗa mishi baki nayi na kawar da kaina, jijjiga kanshi yayi irin alaman zai haɗu da ni, kallon Amal ya yi yace, "Amal zaku iya dafa wani abu ko muje mu yi take-away?". Juyowa ta yi ta dube ni, tana jiran taji me zance, ni kuma ganin haka ya saka na harare ta na mayar da kaina window ina kallon waje, ganin haka yasa ka ta juya tace, "yanzu yunwa muke ji, ina ga muna yin take-away da lunch, idan yaso breakfast da dinner sai mu dinga yi da kan mu". ta faɗa tana juyo tana kallo na. "Hakan ma ya yi, amma maganan breakfast kam ai baku san mun, sai dai naji ƙanshi ana soya abu, saboda haka dinner ma ina tsoron na saka a raina zan samu". ya faɗa yana kallo na ta glass ɗin motan. Dariya Amal tayi sannan tace, "kayi haƙuri wallahi yau mun makara ne, egg kawai Hummy ta soya mana, muka sha da tea, amma insha'Allahu zamu dinga yi da kai daga yau, kuma dinner ma da kai zamu dinga yi". Take-away yaje ya mana, muna isowa gida Amal ta ɗauki ledan da ya miƙa mata, ni kuma na ɗauki bags ɗin muka fito, har nayi kusan ƙarasawa ya ƙirani, dawowa nayi wurin shi, kallo na ya yi ganin bance komai ba yace, "wani abu yana damun ki ne?". Turo baki na nayi gaba kaman bazan yi magana ba, can kuma na dube shi ganin irin kallon da ya ke bina da shi nayi saurin sauke ido na ƙasa ina jin faɗuwar gaba, "ni babu abinda ya ke damu na". "To me na miki ki ka ƙi zama a front sit yau?". Ina duban shi nace, "ba Amal ta zauna ba". "Amal ɗin na saba da ita ne?". ya faɗa yana hararana da wasa. Ɗan ya mutsa fuska na nayi sannan nace, "ita ma ai zaku saba, ni yunwa na ke ji sai anjuma". ina faɗa na juya na bar shi a tsaye a wurin. Kasa ɗaga ƙafan shi ya yi ya bar wurin saboda mamakin irin yadda na mishi, ko kulawa na ƙi nuna mishi yau, sai yaji babu daɗi a ranshi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 14📑* *MUM SAYYEED YADDA BAKI GAJJIYA DA JINJINA MUN, HAKA NIMA BA ZAN TAƁA GAJIYAWA DA BAKI ƊAN ƘARAMIN KYAUTANA NA SHAFI BA, DUK DA NASAN BA MAI YAWA BANE AMMA KIYI HAƘURI DA SHI, NA BAKI WANNAN SHAFI KYAUTA MUM SAYYEED, ALLAH YA BARMU TARE* 🤝🏻 *__________📖* Kaman bazan yi magana ba kawai na zuba mishi ido, can nace, "Toh ni ai ka zama Uncle ɗi na, kuma ai kamun girma ace kai boy friend ɗi na ne, ai Daddy idan yaji ina da boy friend ranshi zai ɓaci". na faɗa ina lanƙwasa kai na ina kallon yadda ya ƙura mun ido. "Na ji abinda ki ka ce, nima nasan tunanin ƴan class ɗin ku baya gaya musu gaskiya, ke ai baki wuce ƴar ciki na ba da nayi aure da wuri, dama ina son naji me zaki gaya musu idan kin koma class ɗin ne, saboda haka koma kice musu ni Baban ki ne". ya faɗa yana kama hanyar barin wurin. Da ɗan gudu na bishi a baya ina cewa, "Dr'n mu to egg ɗin fa? Kafasa ci ne?". "Bana da sha'awan shi yanzu, ki koma bana son damuwa yanzu". ya faɗa tare da barin wurin da sauri. Na daɗe a tsaye a wurin ina mamakin yadda ya ɗaure fuska lokaci guda, ya kuma juya ya tafi kaman bai san da ni ba a wurin, haka na ƙara ci tsayuwa na na juya na koma class raina a ɓace. Ina shiga Ezeh ya zo kusa da ni ya zauna, hannu ya saka ya buɗe text book ɗin *TAXATION* ko tambaya na komai akan Dr bai yi ba, kawai bayani ya fara mun akan in da na tambaye shi ban gane ba, muna cikin yi sai ga Vicky, zama tayi kusa da ni tana murmushi, can ta tambaye ni, "ya ya Amal da jiki?". bayan mun yi gaisuwa ta ce da yamma zata je ta duba ta, ni kuma na gaya mata hospital ɗin da Amal ɗin ta ke, daga nan muka maida hankalin mu kan karatun da mu keyi. Ƙaran takun takalmi muka jiwo, da sauri na ɗago na dubi mai shigowan, sanye da takalmi mai tsinin gaske, *Eesha* wannan ƴar india ne wanda ta ke ɗaukan mu *TAXATION* kuma ƙawar Dr Khadijah ce, sun yi kyau sosai, sai dai Dr Khadijah tafi kyau, ita kuma Eashaa tafi gayu, irin kallon da naga tana mun yau sai ya saka ni na kasa samun nutsuwa a class ɗin. gashi ita ma kaman haɗin baki sai jeho mun quetions masu girma ta ke tayi, amma ko kaɗan basu ban tsoro ba, yadda nake bada amsan sai da ta tsaya wuri guda ta ƙura mun ido, can tace. "Dr Hussain meye relation ship ɗin ku da shi?". Ban san ya ya aka yi ba sai samun kaina nayi da ce mata, "Uncle ɗi na ne, don shi ƙanin Dad ɗi na ne". "To me yasa yake yawo da ke? Kuma naga baya sakewa kowa fuska ya mishi murmushi amma ke yana miki? Kin tabbatar the same parent su ke da Dad ɗin ki ko kuma cousins ne?". "The same parents su ke da Dad ɗina, Dr Hussain ne ƙaramin su, sai Aunty Aisha, ita muna kama da ita, shi kuma yana kama da Dr Hassan". lokaci ɗaya naji na mata ƙarya don su rabu da ni, tun da naji yace ina kama da Aisha sai na gaya mata hakan. Murmushi tayi tana kaɗa kanta alaman ta yarda, sannan tace, "me yasa Dr Khadijah Khan tace ki same ta a office ɗin ta baki je ba?". Tsuru-Tsuru nayi da ido, can kuma sai wani dabaran yazo mun da sauri nace, "Dr'n mu yace na daina yawon zuwa office, na ce mishi tace naje yace mun no, bai yadda naje ba, amma ita ta tambaye shi tun da yana son ta zai yadda". Murmushi tayi ta matso in da na ke yadda ba maijin mu tace, "ya ya ki ka san Dr yana son Khadijah?". Juya ido na nayi kaman wata mai shirin yin bacci nace, "shi ya gaya mun tana da kyau, bai taɓa ganin mai kyau irin ta ba". Murmushi ta sa ke yi tana duba na, "har ke duk kyawun ki bai gani ba sai na Khadijah?". Turo baki na nayi gaba nace, "shi ai ko sister'n shi Aisha bai taɓa cewa tana da kyau ba, ballanta na ni, amma ita Dr yana gaya mun tana da kyau kuma ai wife ɗin shi yace mun". Jin haka ko ɓata lokaci Eashaa ba tayi ba ta fita da sauri tayi office ɗin Dr Khadijah, daga gani zata isar da saƙo ne wa Dr ƙawar ta. Ni dai daɗi na mun rabo da su lafiya, sai suje suyi ta damuwar su a tsakanin su da Dr. Lokacin break ya yi ni dai ban so ba haka na fita na sayi coke na sha, sannan naje nayi sallan azahar mosque. Lectures ɗaya muke yi bayan mun dawo a break, saboda 2:30pm muke ta shi, haka aka yi muna tashi kai tsaye na wuce gida. Sallah nayi sannan na yi wanka, ina fitowa da sauri na shirya na fita domin zuwa duba jikin Amal, ina fitowa naga motan Dr Hussain alaman yana gida, hararan gidan shin nayi, sannan na murguɗawa gidan baki na wuce na fita abuna. Ina shiga ɗakin da aka kwantar da Amal na same ta zaune suna ta hira da Abbu da Ummi, sai dariya Amal ta keyi kaman bata yi jinya ba, wuri na samu na gaida su Abbu, sannan na tambaye su me zasu ci naje nayi mana take away? Ummi ce ta miƙo mun wani ledan Mrs Bigs, wanda na buɗe naga fried rice ne a ciki sai queter kaza, tana murmushi tace, "ai tun wurin 2:00pm Dr Hussain ya kawo mana abinci, yace ke sai kusan 3:00 zaki shigo, saboda haka gana ki ma, mun gode mishi da ɗawainiyan shi a gare mu wallahi". Haka na zauna ina cin abinci na hankali kwance, ita kuma Amal sai zolaya na ta ke tayi wai, "ina Dr'n ki ne baby?". tana yi tana dariya, amma ni ko kallon ta ban yi ba, Abbu ne kawai ya ke ta taya ta dariyan Ummi kuma tana ta mata mitan ai zasu tafi su bar ta da ni ak, kuma tana bayan nima na rama abinda ta mun. Wurin 6:00 Dr Abdallah yazo ya bamu sallama, yana cewa Abbu jikin da sauƙi sosai, sai dai duk bayan 2wks ya kamata tana zuwa follow-up, haka muka tattara kayan mu Dr Abdallah ya maida mu gidan, sannan ya dube ni yana murmushi yace, "ki gaida Yayan ki kuma friend ɗin ki". ya faɗa yana mun murmushi, ni dai ko kula shi ban yi ba, haka muka shige gidan muka barshi da Abbu suna tattaunawa. Muna sallan magrib na shiga kitchen, in da Ummi ta biyo ni, amma nayi ta roƙan ta dole ta fita ta barni, cous-cous na dafa wanda ya yi green, domin yaji food colour, sannan nayi vegetable soup wanda hanta yaji kacha-kacha a ciki, juice kala biyu na mana, ɗaya 5alive na mana, ɗaya kuma Apple ne kaɗai nayi blanding wa Amal. Ina gamawa na wuce ɗaki nayi sallah, ina fitowa naga Abbu suna zaune da Dr Hussain suna ta magana a hankali a tsakanin su kaɗai suke jin abinda suke faɗi, gefe kuma Ummi ce da Amal ke zaune suna kallo, Amal ta kwantar da jikin ta a kafaɗan Ummi. Shirya abincin nayi akan dinning, sannan na musu maganan su zo suci abincin, Amal ce ta fara ƙarasowa tana mun magana a hankali dai-dai kunne na tace, "Ke za kiyi saving Dr ko?". Tana faɗa taja kujera ta zauna tana murmushin shaƙiyan ci. Hararan ta nayi cikin wasa nace, "to sannu Mama na". Dariya tayi mai sauti lokacin kowa ya zauna har shi Dr ɗin, "ni na isa na haifi zabgegiyar budurwa mai tashen farin jini irin ki? Wacce ni ai nayi kaɗan". Ta faɗa tana saving kan ta tana ta dariyan ta. "To ku mana shiru muci abinci, idan yaso sai ku tashi daga in da ku ka tsaya". Ummi ta faɗa tana zubawa Abbu abinci, bayan ta zuba nata ta turawa Dr shima ya zuba. Wurin gaba ɗaya ya yi shiru baka jin komai sai sautin ƙaran TV sai kuma ƙara spoons ɗin mu, kowa ya maida hankali kan abinda ya keyi, gashi daga ganin abincin ya yi daɗi, sai bin kowa da ido na ke yi, can nace. "Abbu amma dai abincin nan ya yi daɗi ko?". Girgiza kai kawai yake tayi, "Doughter ban taɓa cin cous-cous da ya mun daɗin wannan ba, har tunani na ke yi ko zaki gwada wa Ummin ko yadda ki ka yi, idan mun koma ta na yimun". Dariya nayi tsabar daɗin jin abinda ya faɗa, ina kallon Ummi nace, "Ummi kema ya miki daɗi?". Tana murmushi tace, "sosai ma, don ni ban damu da cous-cous ba, amma daga yau nima zan dinga yi saboda gaskiya ya mun daɗi, don Abbun ku da sauran ƴan uwan ku duk suna so, ni kaɗai ne bai dame ni ba, amma daga wannan naji ina so, gaskiya ya yi daɗi, Allah ya miki albarka". ta faɗa tana duba na. Bansan lokacin da nayi tafi ba tsabar jin daɗi, kallon Dr nayi amma shi ko alaman yabawa ban ga ya yi ba, turo baki na nayi gaba kaman zanyi mishi tambayan, amma sanin yanzu zai kushe kawai sai na fasa. Dariya Amal tayi sannan ta ajiye spoon ɗin ta ta dubi Dr, "Dr kai ka ɗai fa Hummy ta ke jira taji ka yaba mata, don ni ko na yaba ko kada na yaba ba zai burge ta ba". ta faɗa tana ƙunshe dariyan ta. Ko ɗago kan shi baiyi ba, naji yana cewa, "To ni ai kunyar Abbu ne ya saka ni cin abincin, tun daga ƙamshin girkin har ɗanɗanon shi bai yi mun ba, kawai babu yadda na iya ne, amma girki kaman ba a saka maggi ba". Bansan lokacin da kuka ya zo mun ba da ƙarfin gaske, tashi nayi tsaye ina kallon Abbu nace, "Abbu kaji shi ko? Wallahi bai taɓa cewa nayi abu dai-dai ba, kuma ko wani irin kwalliya nayi baya cewa nayi kyau, kuma gashi a gaban ka yace abinci na ko maggi babu, don Allah Abbu kace yace ya yi daɗi, idan ba haka ba wallahi ihu zan tayi". na faɗa ina ƙara sautin kuka na. Banda dariyan mugunta babu abinda Amal ta keyi, kaman bada ga gadon asibiti ta taso da ƙyar ba, amma ganta yadda ta ke dariyan mugun ta. "Ummi kinga Amal ko". Na sake faɗa ina kukan. "Allah Amal zan saɓa miki idan bakiyi shiru ba, ke koda wasa za kiyi quater wannan girkin ne? Ke banda indomie me ki ka iya dafawa". Cewar Ummi da ta ke hararan Amal. Abbu ne ya dubi Dr Hussain yace, "haba Dr, yanzu tsakani da Allah haka zanta fi na barka da ƴaƴan amanan kana saka mun su kuka? Yanzu fa akan ido na ƴata tayi girki mai daɗin gaske amma ka ƙi yabawa? Ashe kuma dama haka ka ke kushe mata girkin ta, yau ne Allah ya kama ka ka yi a gaba na? Sannan mai kyau kaman tauraruwa amma baka taɓa yaba kyawun ta ba? Ka gaya mun akwai sauran wata mai kyau da ka taɓa gani sama da ita?" Ɗago kai ya yi yana duba na kaman yaga kashi, sannan ya dubi Abbu yace, "Allah Abbu bana ganin kyawun yarinyar nan, kuma ni girkin ta tayar mun zuciya ya keyi, kawai saboda kaine na ci, amma yarinyar nan jagwalgwale kawai ta keyi mutane suna ci basu sani ba". ya faɗa yana ajiye spoon ɗin hannun shi. Ban jira mai za ace mishi ba na juya da gudu nayi ɗaki na, ina kuka kaman ance yau ba'a ga iyaye na ba. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 18📑* *__________📖* Gari na wayewa muka haɗa break, a wani food wormer na zuba na Dr, mu kuma mukaci namu da sauri, muna fitowa muka samu Dr shima yana buɗe motan shi, bayan yagama duk abinda zai yi ya matso kusa da mu, muka shiga kowan mu ya gaishe shi, muna isa school na miƙa mishi breakfast ɗin shi, mu kuma muka wuce class. Mr Solomon ya shigo mana cost accounting, bayan ya gama lectures yace next week muna da test, duk sai mukaji kanmu ya ɗau zafi, kowa ya fara maida hankalin shi kan karatu. Dr Khadijah ce ta shigo mana ta saka wani yellow sarii, sai wani ƙamshi ta keyi mai masifan daɗi ga wani yauƙi da ta keyi kamar tarwaɗa, ina ganinta naji raina ya ɓaci, amma babu yadda na iya haka muka zauna muna binta, muna haɗa ido zata mun wani smilling, a zuciyata nace, "kazar mayu kawai, tanata wani smilling irin na neman gindin zama, irin ga ƴar uwar miji", tsaki nayi a fili wanda bansan nayi ba ma, har saida Amal ta taka mun ƙafa. Tana gamawa Dr Hussain yana shigowa, sai wani smilling ta ke mishi lokacin da zata fita, amma shi kaman bai san da ruwan tsironta a wurin ba, amma ita abin haushi sai rangaɗi ta keyi. Yana gama lectures yace mu shirya test ɗinshi next week monday, yana fita bai daɗe ba naji wayata tayi haske, ina dubawa naga txt ɗin shi ya shigo, da sauri na buɗe ina muushin ganin abinda ya turo, _"babyn baby ya naga kaman maganan test ɗin nan ya firgita ki? Kada ki rasana babyn ki zai koya miki komai"_ muna tashi Dr yazo ɗaukan mu, muna fitowa muka ga Dr Khadija ta fito da sauri ta biyo shi, ganin haka yasa naja na tsaya saboda naga kaman Dr Hussain masifa yake mata, ita kuma ta tsaya a gaban shi kaman zatayi kuka, yana gama maganan ya nuna mu fuskan shi a ɗaure yana cewa, " baby kuzo mu wuce gida". Take-away ya mana muka wuce gida, da yamma ya ƙirani a waya akan na fito na same shi a wurin da muke karatu, wanka na shiga nayi, ina fitowa na yi shiga mai kyau, sai ƙamshi nake zuba mai daɗin gaske. Cake na ɗauka na tafi mishi da shi, bayan na haɗa da juice na coconut da muka haɗa da kanmu, ina kai mishi ya karɓa yana murmushi, ajiyewa yayi a gefe yana kallona da murmushi yace, "Baby mai kika yiwa babyn ki ne"? Buɗe mishi plet ɗin nayi ina murmushi, ɗaukan ɗaya nayi na miƙa mishi, "Dr mu muna dawowa fah mukayi baking wannan, Allah yasa ya maka daɗi", na faɗa ina binshi da murmushi. "Allah yasa ba jagwalgwale kika mana ba" ya faɗa yana tauna cake ɗin yana murmushi, hararan shi nayi na murguɗa baki na. "Dr Khadija inaga tayi kusan 5yrs ko 6 tana sona, tun lokacin da muka je karatu na fahimci tana sona amma bata samu fuskana a lokacin ba, saida muka dawo daga karatu, a lokacin gidan da aka bani a staff queters itace neighbour nah, yau da gobe na bata fuska muka fara gaisawa, har wataran takan nemi alfarman na shiga da ita school, na amince mata, kawai sai ta takura rayuwata, duk inda nayi tana bibiyata, ni kuma ganin zata ta kura ni sai nazo na kama wannan gidan, nagaya mata nayi aure daga country ɗinmu, a wancan shekarun sai na samu sauƙin ta, amma yanzu kusan 2yrs ta na neman ta kurani, shiyasa nake ƙin amsa gaisuwan ta, domin akwai uncle ɗinta, daya same ni akan ta amma na nuna mishi ina da mata kuma bana ra'ayin zama da two wifes, toh abin yayi ɗan sauƙi, saidai daga zuwanki naga alaman tana neman dawo da abin baya, wanda idan kin kwantar da hankalin ki bazan taɓa cewa ina sonta ba". "toh meyasa na ganku a wannan mall ɗin ranan tare? Kuma me yasa kake tafiya chan ka kwana"? Murmushi yayi yana kallona, "wallahi idan kin yadda a wurin muka haɗu da ita, kuma na koma gidan ne saboda naga alaman tana son neman inda nake shiyasa wancan lokacin na koma na daɗe a wurin, shi ne lokacin da Daddyn ki ya kawo ki, tafiyan danayi na baya kuma ke kika mun laifi shiyasa nayi yaji", ya faɗa yana faɗaɗa murmushin shi, sannan ya ɗauki coconut juice ɗin ya sha, ina ganin shi ya runtse idon shi ya sauƙe a kaina, sannan yace, "Juice ɗin nan baimun daɗi ba, kaman sugar yayi yawa". Hararan shi na sakeyi cikin wasa, "Drn mu toh ni bana son Dr Khadijan, ka daina kula ta". "Duk yadda kika ce haka za ayi, nima bana sonta don bani da burin auren mace sama da ɗaya". Zaro ido nayi ina kallon shi da mamaki nace, "toh kana da matar ne dama"? "ina dai shirin yi yanzu"... "a ina zakayi auren? Wacece zaka aura"? Na tambaye shi cikin sauri. "Uhmmm wata yarinya nagani nake so idan ta amince zan aure ta, yarinya ce amma haka nake son aurenta idan ta amince", ya faɗa yana dubana idon shi a kanne. Miƙewa nayi zan tafi na bar shi a wurin, yayi charaf ya riƙo hannu na yana bina da kallon mamaki. "nidai ka sake ni zan tafi gida", na faɗa ina buga ƙafa na a ƙasa kaman zan mishi kuka. "Toh ae bamu gama labarin mu ba zaki tafi ki barni"? ya faɗa yana dawo dani kan kujeran da na tashi. "nidai bana son labarin, kaje ka auri duk matan duniyan ma ni bani da case da kai, kawai ka barni na tafi, bana son ganinka", na faɗa hawaye ya fara bin fuskana. Tashi yayi da sauri ya tsaya yana riƙe da dukkan hannu na, cikin murya mai sanyi yace, "babu ruwanki da ni kuma ina zan saka kaina naji daɗi baby"? "wurin matan da zaka aura wanda kake son so mana" na faɗa ina juyar da kaina gefe ɗaya, bana son ganin face ɗinshi. Shiru yayi na wani ɗan lokaci kaman bazai tanka ba, ni kuma sai kuka na ke tayi, kuma har lokacin yana riƙe da hannu na. "Baby zaki iya ƙarasa rayuwar ki da tsoho kaman ni? Baby zaki iya bani kafaɗan da zan jingino na share hawayena daya ki tsaya a rayuwata na tsawon wasu shekaru? Baby zaki bar zuciyar ki ma wannan tsohon da yayi miki zarra da nisa a shekaru"? Ya faɗa bayan ya kulle idon shi. _Wayyo na gajji gaskiya yau, kumun haƙuri bazaku samu jin amsan Hummy ba a yau sai a wani karon, don zanyi hutu_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 17📑* *____________* 📖 Muna cikin haɗa girkin Amal ta kira brother'n ta Faisal, su ka shiga tsara yadda zasu dinga ɗaga hankalin Dr Hussain, ni dai sai dariya da sha'awan su kawai na keyi, domin a handsfree ta bar wayan, burge ni su keyi kaman wasu friends. Ina sauraren su ina ɗan dariya ƙasa-kasa, can naji muryan Faisal yana cewa, "ina ƴan mata na ɗin? Bani ita naji muryan ta". dukkan mu dariya muka yi tukun ta miƙo mun wayan na kara a kunne na. "Hello sweety". ina dariya nima nace, "hello honey". dukkan mu dariya muka yi, sannan ya dinga tsara mun yadda zan dinga amsan wayan shi a gaban Dr, haka muka yi ta hira har muka gama girkin mu, ƙamshi kam nasan ba gidan Dr ba, yau ina ga hatta gidan su Peter ma sai sun ji. 8:30pm dukkan mu mun yi wanka, dogon riga muka saka kowa ta yafa ɗan gyalen kayan, ɗiban abincin muka yi dukkan mu muka fita zuwa gidan Dr. Bamu daɗe muna knocking ba yazo ya buɗe mana, har zuwa lokacin fuskar shi a ɗaure, haka ya bamu hanya muka kai abincin har kan dinning ɗin shi, wucewa ya yi parlor ya cigaba da kallon shi ba tare da ya kalli in da muke ba, ganin haka Amal ta mun signa, dariya nayi na wuce in da yake na zauna a hannun kujeran ina leƙa fuskan shi ina murmushi. "Babyn baby yau na maka girki mai daɗi, taso muje na zuba maka kaji daɗin shi". harara na ya yi sannan ya juya ya kalli in da Amal ta ke zaune, ganin hankalin ta yana kan wayan ta sai ya dube ni yace, "bazan ci ba ni na ƙoshi". "Haba baby'n baby! Ko ka fiso yau na kwana banci komai ba? Kuma na kwana ina kuka?". Na faɗa kaman zan fara mishi kukan a lokacin. Sa ke duban in da Amal ta ke ya yi sannan yace, "baki damu da ni ba ai, to me yasa zaki damu da cin abinci na?". "Duk duniya ba bu wanda ya damu da kai bayan ni, kuma na damu naga kaci ka ƙoshi, saboda nafi so na dinga ganin ka cikin kwanciyar hankali". na faɗa ina tashi tsaye domin mu wuce dinning ɗin. Tashi ya yi ya tsaya yana kallo na ido cikin ido yace, "waye darling forever?". Juya ido na nayi sannan na lumshe su na buɗe, "nafi damuwa da naga kaci ka ƙoshi sama da maganan darling forever, saboda haka muje na samu nutsuwan ka tukun kafin wani ya biyo baya". Amal ta riga mu gama cin abincin, sai ta koma cikin parlon ta zauna jiran mu, channels ɗin ta ke ta canjawa, muna gama ci na miƙe zan tafi, da sauri yace, "dawo ki bani labarin shi, kuma daga yau idan kungama girkin ki kirani a waya zan zo gidan ku kawai muna ci acan, bazan so ku wahala kullum wurin ɗaukan kaya ba". ya faɗa yana sauƙe mun kyawawan idon shi a kaina. Bansan me yasa na ke yawan jin kunyar shi ba idan ya kalle ni, murmushi na yi na sunkuyar da kaina ina kallon yatsuna ina wasa da su. "Faisal matashin yaro ne fari kyakkyawa mai nutsuwa da ilimi, Faisal farin balarabe ne ɗan gata a wurin Ummi da Abbu, Faisal shine ɗa na farko a wurin iyayen shi, yana karatun medicine a oxford university, yana shekaran shi ta ƙarshe, Dr naj ina matuƙar ƙaunar Faisal, saboda irin so da kulawan da yake nuna mun, faisal ba ya haɗa soyayya ta da ko wacce mace a duniya, ko dan ba bu wanda ya taɓa so nane sama da na shi? Oho ina ga don duk duniya babu mai mun irin soyayyan shi shiya sa nake ganin hakan". "ƙarya ya keyi bashi kaɗai bane yake sonki, ƙarya ne shiɗin ba son ki ya keyi ba yaudara ne, ina ma yasan kanshi ballan ta na ya soki". Cikin tsawa yake maganan bayan ya miƙe ya tsaya a kaina. "Kada ki sake barin zuciyar ki ta yarda wani yana miki so sama"....... sai kuma ya yi shiru yana kallon Amal da ta taso ta miƙo mun waya tana, "ga bros yana kira". tana miƙa mun ta ɗauki kwanukan tayi hanyar fita a parlon, ni kuma ɗauka nayi fuskana cike da murmushi, amma ƙasan zuciya ta kaman na ranta da gudu. "Hello honey nah". Banji amsan da Faisal ya bani ba kawai naga waya ta a hannun Dr, kashe wayan ya yi sannan ya nuna ni da yatsan shi. "Duk abinda ya ke rawa a kan ki Aishatu zan ɗaure miki shi, baki da hankaline a gaba na zaki tsaya kina waya har kina ƙiran wani ƙaton banza wai Honey? Baki da tunani ne? To daga yau ki bashi haƙuri kigaya mishi gaskiya karatu za kiyi ba soyayya ba, nawa ma ki ke da zaki damu kan ki da soyayya. Ko dama abunda Daddy ya turo ki yi kenan?". Juyi na farayi a gabanshi ina magana cikin shagwaɓa, "Dr'n mu dubi fa wallahi na girma, kuma ni son shi ya mun yawa kaman bazan iya karatun ba ma gara a mana aure kawai". na faɗa ina ɗaura hannu na a gefen heart ɗina ina wani lanƙwashewa kaman tarwaɗa. ya daɗe yana kallo na, sannan murya a hankali ya nuna mun hanyar waje yace, "fita don Allah kije ki ƙarashi fitinan ki wa Amal, amma nikan nawa ya isa haka, wuce kifita". ya faɗa kaman idan ya buɗe baki ya yi magana da ƙarfi zuciyar shi zata faɗo. Buga ƙafa na fara a wurin ina nikan bazan tafi ba sai kaba ni waya na, kasan fa zai kira ni anjima, kuma ni sai ka rakani Dr nah". na faɗa ina kan dire ƙafan a ƙasa. Riƙo hannuna ya yi muka nemi wuri muka zauna, yana duba na a nutse yace, "Don Allah ki taimake ni ki rabu da yaron nan, bana so naga kina son kowa Humairah, ban shirya samun damuwa ba a tsakanin mu yanzu, don Allah ki barshi bana so, ko baki so na samu kwanciyar hankali ne?". "ina so mana Dr'n mu". "tunda kina so to bana so naga kina son kowa idan kin tashi aure ni zan zaɓa miki miji, amma yanzu karatu na fi so kiyi kin ji Baby nah". Turo baki na nayi gaba ina kallon shi kaman zan yi kuka nace, "Dr ni fa auren shi zanyi, ina son shi fa sosai, da ƙyar fa nake iya bacci this days, daga na kwanta sai na fara mafarkin munyi aure ya kaini mall, wataran har yara masu na ke ganin mun haifa kaman yaran Larabawa". "Ya rabbi! Don Allah ki daina kwantan ta kan ki da wani namiji Baby, har kina tuna wai za ku haihu tare? Zaki kashe ni ne kawai kwanana bai ƙare ba". ya faɗa yana matse yatsun hannu na da ƙarfi, wanda har sai da nayi ƙara da ƙarfi tukun ya sa ke su. "Baby kaima fa kana da mata, to ni me zai sa ba zanyi aure ba?". "ni bani da wata mata". ya faɗa da ɗan ƙarfi yana ƙura mun ido, nima ƙura mishi idon nayi cike da mamaki, baki na a buɗe nace, "Dr Khadijah fa?" "Ni ba mata ta bace, ita ta ke shirmen ta, ke kuma ki ka dame ni wai mata ta ce, ni tun da nazo ƙasan nan ban taɓa son kowa ba sai mace ɗaya, ni kuma ban taɓa aure ba har yanzu". Gaba na yana faɗuwa ina duban shi nace, "wacece ka taɓa so a ƙasan nan? To me yasa na gan ka da Dr Khadijah ranan a wuri ɗaya? Idan ba son ta ka ke yi ba mai ya haɗa ka da ita?". Na faɗa kaman wata mai tuhuman ɗan ta. Sa ke riƙo hannu na ya yi cikin ƙasa da murya yace, "ni dai bana son Khadijah, kuma ban taɓa son ta ba ballanta na na aure ta, amma na miki alƙawari idan kin rabu da yaron nan zan baki labarin komai game da Khadija". "har wanda ka taɓa so zaka bani labarin ta?". Yana murmushi yana duban ido na yace, "har su Hassan ɗi na, Ummi nah da Abba nah duk zan baki labarin su, amma sai kin mun alƙawari ba zaki sa ke kula kowani namiji ba, kuma ba zaki so ko wani namiji ba sai wanda na zaɓa miki". Shiru na yi na zuba mishi ido, ganin yadda shima ya ƙura mun ido nace, "to nima kamun alƙawarin ba zaka so ko wacce mace ba, idan ka so wata nima zan so faisal, don yana da kyau kuma fari ne". "Baby ya kai ni kyau?". Kallon Dr na yi baki na a buɗe nace, "ni fa ban taɓa ganin mai irin kyawun ka ba, kai fa kyawun ka mai kyau ne". Runtse ido ya yi zuwa can ya buɗe su a kaina, "ta shi muje na raka ki dare ya yi, kuma Amal za ta gajji da jiran ki". ya faɗa bayan duk mun tashi mun tsaya muna kallon juna. "Baby kina da".... Sai kuma ya yi shiru yana murmushin da ya ke cije leɓen shi, turo baki nayi nace, "baka ƙarasa ba". Dariya ya yi ya jawoni muka yi hanyan waje, a waje muka ga David da Peter suna shigowa gidan, zuwa su kayi suka gaida Dr, sannan Peter ya dube ni yace, "preety yau kin yi kyau sosai, kaman wata star". Ya faɗa suna wuce gidan su suna dariya. Nima dariyan nayi na matso kusa da Dr nace, "kai kaɗai ne baka taɓa ce mun ina da kyau ba, kowa sai yace kyawuna ya yi yawa ma, amma kai ko kaɗan baka taɓa cewa ba". na faɗa ina hararan shi. Yana rako ni ya tsaya yana mun wani duban da har sai da naji tsikar jiki na yana tashi yace, "bana son kibar su Peter suna cewa kina musu kyau ba, bana jin daɗi, sufa students ɗina ne, bana jin daɗi gara ki hana su". "zan gaya musu su daina, amma da gaske goben komai zaka gaya mun"? "idan kin daina son Faisal ba". ya faɗa yana komawa gidan shi, bayan ya sa ke mun hannu na. Ina shiga Amal ta taso tana tambaya na yadda a kayi? Labarin abinda ya faru na bata, haka muka yi ta dariyan shi, duk da Amal ta mun masifan me yasa nace yana da kyau, me yasa kuma nace, shi bai ganin kyawu na?. Hararan ta nayi nace, "ce miki a kayi ina sani ne na ke gaya mishi? Kawai idan ina ta re da shi manta kowane shawara ku ka bani nake yi, sai ɗaɗɗaya, ke dai Allah ya kaimu goben muji labarin komai. _NIMA AUNTY NICE NA CE ALLAH YA KAIMU GOBEN DA RAI DA LPY, IDAN KUNA BIYE DA ALƘALAMI NA ZA MUJI ME ZAI KASANCE A TSAKANIN SU._ VOTE COMMENT SHARE *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 16📑* *____________* 📖 Muna cikin haɗa girkin Amal ta ƙira brother ta Faisal, suka shiga tsara yadda zasu dinga ɗaga hankalin Dr Hussain, nidai sai dariya da sha'awan su kawai nakeyi, domin a handsfree ta bar wayan, burgeni sukeyi kaman wasu friends. Ina sauraren su ina ɗan dariya ƙasa kasa, chan naji muryan Faisal yana cewa, "ina ƴan mata na ɗin? Bani ita naji muryanta", dukkan mu dariya mukayi tukun ta miƙo mun wayan na kara a kunne na. "Hello sweety" ina dariya nima nace, "hello honey" dukkan mu dariya mukayi, sannan ya dinga tsara mun yadda zan dinga amsan wayan shi a gaban Dr, haka mukayi ta hira har muka gama girkin mu, ƙamshi kam nasan ba gidan Dr ba, yau inaga hatta gidan su Peter ma sai sunji. 8:30pm dukkan mu munyi wanka, dogon riga muka saka kowa ta yafa ɗan gyalen kayan, ɗiban abincin mukayi dukkan mu muka fita zuwa gidan Dr. Bamu daɗe muna knocking ba yazo ya buɗe mana, har zuwa lokacin fuskar shi a ɗaure, haka ya bamu hanya muka kai abincin har kan dinning ɗinshi, wucewa yayi parlor ya chigaba da kallon shi batare da ya kalli inda muke ba, ganin haka Amal ta mun signa, dariya nayi na wuce inda yake na zauna a hannun kujeran ina leƙa fuskan shi ina murmushi. "Babyn baby yau na maka girki mai daɗi, taso muje na zuba maka kaji daɗin shi," harara na yayi sannan ya juya ya kalli inda Amal ta ke zaune, ganin hankalinta yana kan wayanta sai ya dube ni yace, "bazan ci ba ni naƙoshi". "Haba babyn baby! Ko kafiso yau na kwana banci komai ba? Kuma na kwana ina kuka"? Na faɗa kaman zan fara mishi kukan a lokacin. Sake duban inda Amal ta ke yayi, sannan yace, "baki damu da ni ba ae, toh me yasa zaki damu da cin abinci na"? "Duk duniya babu wanda ya damu da kai bayan ni, kuma na damu naga kaci ka ƙoshi, saboda nafi so na dinga ganin ka cikin kwanciyar hankali", na faɗa ina tashi tsaye domin mu wuce dinning ɗin. Tashi yayi ya tsayah yana kallona ido cikin ido yace, "waye darling forever"? Juya ido na nayi sannan na lumshe su na buɗe, "nafi damuwa da naga kachi ka ƙoshi sama da maganan darling forever, saboda haka muje na samu nutsuwanka tukun kafin wani yabiyo baya". Amal ta riga mu gama cin abinchin, sai ta kamo cikin parlon ta zauna jiran mu, channels ɗin take ta chanjawa, muna gama ci na miƙe zan tafi, da sauri yace, "dawo ki bani labarin shi, kuma daga yau idan kungama girkin ki ƙirani a waya zanzo gidanku kawai muna ci achan, bazan so ku wahala kullum wurin ɗaukan kaya ba" ya faɗa yana sauƙe mun kyawawan idon shi akaina. Bansan meyasa nake yawan jin kunyar shi ba idan ya kalle ni, murmushi nayi na sunkuyar da kaina ina kallon yatsuna ina wasa da su. "Faisal matashin yaro ne fari kyakkyawa mai nutsuwa da ilimi, faisal farin balarabe ne ɗan gata a wurin Ummi da Abbu, Faisal shine ɗa na farko a wurin iyayen shi, yana karatun medicine a oxford university, yana shekaran shi ta ƙarshe, Dr nah ina matuƙar ƙaunar Faisal, saboda irin so da kulawan da yake nuna mun, faisal ba ya haɗa soyayyata da ko wacce mace a duniya, kodan babu wanda ya taɓa sonane sama da nashi? Oho inaga don duk duniya babu mai mun irin soyayyan shi shiyasa nake ganin hakan"...."ƙarya ya keyi bashi kaɗai bane yake sonki, ƙarya ne shiɗin ba sonki ya keyi ba yaudara ne, ina ma yasan kanshi ballanta na ya soki"!? Cikin tsawa yake maganan bayan ya miƙe ya tsaya a kaina. "Kada ki sake barin zuciyar ki ta yarda wani yana miki so sama"....... sai kuma yayi shiru yana kallon Amal da ta taso ta miƙo mun waya tana "ga bros yana ƙira", tana miƙa mun ta ɗauki kwanokan tayi hanyar fita a parlon, ni kuma ɗauka nayi fuskana cike da murmushi, amma ƙasan zuciyata kaman na ranta da gudu, "Hello honey nah"! Banji amsan da Faisal ya bani ba kawai naga wayata a hannun Dr, kashe wayan yayi sannan ya nuna ni da yatsan shi. "Duk abinda ya ke rawa a kanki Aishatu zan ɗaure miki shi, baki da hankaline a gabana zaki tsaya kina waya har kina ƙiran wani ƙaton banza wai Honey? Bakida tunani ne? Toh daga yau ki bashi haƙuri kigaya mishi gaskiya karatu zakiyi ba soyayyah ba, nawa ma kike da zaki damu kanki da soyayyah"? Juyi na farayi a gabanshi ina magana cikin shagwaɓa, " Dr mu dubi fa wallahi na girma, kuma ni sonshi ya mun yawa kaman bazan iya karatun ba ma gara a mana aure kawai", na faɗa ina ɗaura hannu na a gefen heart ɗina ina wani lanƙwashewa kaman tarwaɗa. ya daɗe yana kallona, sannan murya a hankali ya nuna mun hanyar waje yace, "fita don Allah kije ki ƙarashi fitinki wa Amaal, amma nikan nawa ya isa haka, wuce kifita", ya faɗa kaman idan ya buɗe baki yayi magana da ƙarfi zuciyar shi zata faɗo. Buga ƙafa na fara a wurin ina nikan bazan tafi ba sai kabani wayana, kasan fah zai ƙirani anjima, kuma ni sai ka rakani Dr nah", na faɗa ina kan dire ƙafan a ƙasa. Riƙo hannuna yayi muka nemi wuri muka zauna, yana duba na a nutse yace, "Don Allah ki taimake ni ki rabo da yaron nan, bana so naga kina sonka kowa Humairah, ban shiryah samun damuwa ba a tsakanin mu yanzu, don Allah ki barshi bana so, ko baki so na samu kwanciyar hankali ne"? "ina so mana Dr mu"."tunda kina so toh bana so naga kina son kowa idan kin tashi aure ni zan zaɓa miki miji, amma yanzu karatu na fi so kiyi kinji baby nah!" Turo bakina nayi gaba ina kallon shi kaman zanyi kuka nace, "Dr nifah auren shi zanyi, ina son shi fa sosai, da ƙyar fa nake iya bacci this days, daga na kwanta sai na fara mafarkin munyi aure ya kaini mall, wataran har yara masu na ke ganin mun haifa kaman yaran Larabawa". "Ya rabbi! Don Allah kidaina kwantan ta kanki da wani namiji baby, har kina tuna wai zaku haihu tare? Zaki kashe ni ne kawai kwanana bai ƙare ba", ya faɗa yana matse yatsun hannu na da ƙarfi, wanda har saida nayi kara da ƙarfi tukun ya sa ke su. "Baby kaima fah kana da mata, toh ni me zaisa bazanyi aure ba"? "ni banida wata mata" ya faɗa da ɗan karfi yana ƙura mun ido, nima ƙura mishi idon nayi cike da mamaki, bakina a buɗe nace, "Dr Khadijah fah"? "Ni ba mata ta bace, ita take shirmenta, ke kuma kika dame ni wai mata ta ce, ni tunda nazo ƙasan nan ban taɓa son kowa ba sai mace ɗaya, ni kuma ban taɓa aure ba har yanzu". Gaba na yana faɗuwa ina duban shi nace, "wacece ka taɓa so a ƙasan nan? Toh meyasa na ganka da Dr Khadijah ranan a wuri ɗaya? Idan ba sonta kake yi ba mai ya haɗa ka da ita"? Na faɗa kaman wata mai tohuman ɗan ta. Sake riƙo hannuna yayi cikin ƙasa da murya yace, "nidai bana son Khadijah, kuma ban taɓa sonta ba ballantana na aure ta, amma na miki alƙawari idan kin rabo da yaron nan zan baki labarin komai game da Khadijah". "har wanda ka taɓa so zaka bani labarinta"? Yana murmushi yana duban ido na yace, "har su Hassan ɗina, Ummi nah da Abba na duk zan baki labarin su, amma sai kin mun alƙawari bazaki sake kula kowani namiji ba, kuma ba zaki so ko wani namiji ba sai wanda ɓa zaɓa miki". Shiru nayi na zuba mishi ido, ganin yadda shima ya ƙura mun ido, "toh nima kamun alƙawarin bazaka so ko wacce mace ba, idan ka so wata nima zan so faisal, don yana da kyau kuma fari ne". "Baby ya kai ni kyau"? Kallon Dr nayi bakina a buɗe nace, "nifah ban taɓa ganin mai irin kyaunka ba, kaifa kyaunka mai kyau ne". Runtse ido yayi zuwa chan ya buɗe su a kaina, "tashi muje na rakaki dare yayi, kuma Amal zata gajji da jiranki", ya faɗa bayan duk mun tashi mun tsaya muna kallon juna. "Baby kina da".... Sai kuma yayi shiru yana murmushin da yake cije leɓen shi, turo baki nayi nace, "baka ƙarasa ba". Dariya yayi ya jawoni mukayi hanyan waje, a waje mukaga David da Peter suna shigowa gidan, zuwa sukayi suka gaida Dr, sannan Peter ya dubeni yace, "preety yau kinyi kyau sosai, kaman wata star", ya faɗa suna wuce gidan su suna dariya. Nima dariyan nayi na matso kusa da Dr nace, "kai kaɗai ne baka taɓa ce mun ina da kyau ba, kowa sai yace kyauna yayi yawa ma, amma kai ko kaɗan baka taɓa cewa ba", na faɗa ina hararan shi. Yana rako ni ya tsaya yana mun wani duban da har saida naji tsikar jikina yana tashi yace, "bana son kibar su Peter suna cewa kina musu kyau ba, bana jin daɗi, sufa students ɗinane, bana jin daɗi gara ki hana su". "zan gaya musu su daina, amma da gaske goben komai zaka gaya mun"? "idan kin daina son Faisal ba", ya faɗa yana komawa gidanshi, bayan ya sake mun hannu na. Ina shiga Amal ta taso tana tambayana yadda akayi? Labarin abinda ya faro na mata, haka mukayira dariyan shi, duk da Amal ta mun masifan me yasa nace yana da kyau, meyasa kuma nace, shi bai ganin kyau na?. Hararanta nayi nace, "ce miki akayi ina sani ne nake gaya mishi? Kawai idan ina tare da shi manta kowane shawara kuka bani nakeyi, sai ɗaɗɗaya, kedai Allah ya kaimu goben muji labarin komai. _NIMA AUNTY NICE NACE ALLAH YA KAIMU GOBEN DA RAI DA LPY, IDAN KUNA BIYE DA ALƘALAMINA ZAMUJI ME ZAI KASANCE A TAAKANIN SU_ VOTE COMMENT SHARE *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 19📑* *__________📖* Baki na a buɗe na ƙurawa kyakkyawan fuskar shi ido bana ko ƙyaftawa, yana gama maganan ya buɗe idon shi ya ɗaura su a kan fuskata. "Ya Rabbi"na furta a bayyane, domin ban taɓa ganin kyaun Dr irin na yau ba, hannuna na fara shirin ƙwacewa daga nashi hannun, don naji bazan iya tsayawa a inda yake ba yau kam, sannan ban san wacce irin amsa zan bashi ba. "Ki nutsu ki bani amsan tambayana kinji babyn baby" ya faɗa cikin muryan shi da ban taɓa jin shi da ita ba sai yau. "Alhamdulillah" na faɗa a zuciyata ganin Amal da ke tahowa inda muke, fuskanta ɗauke da murmushi ta gaida Dr, wanda har lokacin yaƙi sakin hannu na, waya na ta miƙo mun tana cewa, "gashi Hummy kusan 2 miss call darling forever ya miki, shi ne nace bari na kawo miki ko nasamu ya barni nayi aikina", ta faɗa tana munafukin murmushi. A dole ya sake hannu na domin na karɓi phone ɗina, ina karɓa wani call ɗin yana shigowa, saida na kalli Dr Hussain a fakaice tukun na ɗaga ƙiran. "My luv kayi haƙuri mana ina wurin lecturer mune yana gwada mun karatu", na faɗa wa Faisal bayan irin ƙorafin da ya fara akan na yar da wayan ba kusa da ni ba, shi kuma Dr Hussain ya kasa yiɓ komai sai ƙura mun idon shi da yayi kawai. "don Allah rufa mun asiri kayi zamanka a school, idan ka taho nan kuma ae soyayyanka bazai barni nayi nawa karatun ba, gashi next week test babu iyaka muke da su", na faɗa mishi da muryan lallashi. Ratsa gefe na yayi zai wuce nayi sauri na riƙo hannun shi, ban kuma kalli inda ya ke ba, ban kuma daina wayana ba, ina gamawa na juyo da murmushi na dube shi, "Drn mu bansan wani irin so muke yiwa juna ba nida Faisal? Kasan wai saboda ban ɗauki wayan shi akan lokaci ba da har yayi niyyan tahowa inda nake, gaskiya da yazo da babu abinda zai saka na iya fahimtan karatun da ake mun", na faɗa ina nuna ban ma fahimci wani hali Dr ya shiga ba. Ƙwace hannun shi yayi ya wuce ya barni a wurin, dariya nayi na bishi da gudu-gudu, har zai shige gidan shi na sha gaban shi, na lanƙwasa kaina gefe kaman me neman a yafe mata, ina murmushi nace, "Drn mu yaushe zamuyi karatun? Ko sai after munyi dinner zaka gwada mana"?. "Allah ya kaimu" ya faɗa ya wuce ya barni inata dariya a ɓoye, ina shiga parlon mu da gudu naje na rungume Amaal, dariya ita ma takeyi muka gama zagaya wurin tukun muka zauna, "bani labari babyn Dr", ta faɗa muna dariya. Bayan nagama bata labarin duk abinda ya faru, sai ta ɗaga kanta kaman mai tunani, chan ta sauƙo da kanta tana kallo na tace, "mistake ɗaya Hummy, baki ce mishi komai ba sai kika fara bashi labarin soyayyan ku da Faisal, hujjah"? Dariya nayi na miƙe tsaye ina kallon ta, "16yrs nake fa Amaal, Drn mu 40yrs yake, kinga akwai 24yrs a tsakanin mu, yaushe zan tura mishi tunani na kusa da na shi? ae bazai dinga mun uzuri ba a rayuwa kullum zai mun kallon mai hankali da shekaru, amma yarinta na kullum zai zamo abinda zai banbantani da sauran mata, sannan zaina haƙuri da ni a kowani lokaci, kinga shi fah yanzu zaiyi tunanin ban fahimci abinda yake nufi ba, toh zaije ya zauna yayi ta wasa ƙwaƙwalwar shi da lissafin wani hanya zai sake bina da shi, kuma wani hanya zai ya kuce mun wannan yaron a raina, kuma ko daga baya bazaice shi kaɗai na taɓa so ba, dole shima ya haɗu da rival ta wurina, ki barshi ni bazan bashi amsa ma, yanayina kaɗai zai wadatar da shi, har ya aminta babu wani a zuciyata sama da shi, amma a hankali", na faɗa bayan na koma gefen Amaal na zauna. "hmmm shiyasa akace ko wacce mace da irin nata kissan ake haihuwarta da shi inji kakarmu, babu wacce ka isa ka zaunar da ita ka koya mata kissa, saidai ka tunatar da ita kawai, domin ko ka koyawa mace abinda zatayi, toh bazatayi exactly irin yadda aka gwada mata ba, sai nata baiwan ya shiga ta sarrafa shi ta wani wurin daban, kaman yadda yanzu kikayi, bayan Ummi ta gwada miki nata hikiman, nima na gwada miki, sai kika yi naki hikiman, gaskiya ƴar'uwata kin burgeni, Allah ya barki da Drn ki ɗan tsoho kusha soyayyah", ta faɗa tana dariya na. Nima dariyan nayi nace, "musha soyayyah yayi ta goyani ina jin daɗi". Wayata na ɗauka nayi dialing number Dr ina ɗan murmushin shaƙiyanci, yana ɗauka nace, "hello Dr na baka shigo munyi dinner ba, kuma wallahi yunwa na keji", na faɗa kaman zan mishi kuka. "ku ci kawai bana yare da yunwa", ya faɗa ya kashe wayan, kallon Amaal nayi ina dariya nace, "bari naje nayi biko". Kaman bazai buɗe mun ƙofan shi ba bayan nayi knocking, yana buɗewa na ratsa gefen shi na wuce cikin parlon na tsaya ina duban shi babu dariya a fuskana, shima ƙura mun ido yayi yana mun wani irin kallo. "Dr meyasa bazaka zo muci abincin ba"? "Nace miki bana tare da yunwa, kwanciya ma zanyi zo ki wuce ki tafi, na hanaki shigowa nan ae". Wucewa nayi na nemi wuri na zauna ina kallon TV da ake news, kallona ya tsayayi bai ce komai ba, ganin haka yasa na dube shi nace, "ka rufu ƙofan mana kazo mu zauna, tunda kace baka jin cin abinci nima ae bazan iya ci ba, kuma yau anan gidan zan kwana tunda kai yayah nane, kuma uncle ɗina ne", na faɗa ina shirin miƙewa na kwanta a wurin. Da sauri yazo ya tsuguna a gabana yana kallo na, ƙura mun ido yayi kafin yace, "saboda me zaki kwanta anan? Baki tsoron komai ne kam ke"? Tashi nayi na zauna, na rufe idona naƙi kallon shi, domin bana jin daɗin ƙura mishi ido, "ban taɓa tunanin zaka iya cutar da ni ba, nayi imani da Allah yadda Daddy na zai kareni ya kare mun mutuncina haka kaima zakayi, ina ji ajikina zaka iya sadaukar da rayuwarka domin tsare mun mutuncina, kuma koda a jikin ka zan kwana zaka fi kowa tsare mun mutuncina, saboda haka bani da shakku akanka". Ajiyan zuciya ya sauƙe mai ƙarfi, sunkuyar da kanshi ƙasa yayi bai iya cewa komai ba, hannu na saka na riƙo hannun shi, wanda yayi sauri ya ɗago kanshi yana duba na, gaba ɗaya ganin idon shi sai naji ya bani tausayi, a hankali na furta, " Dr nah! Nafi son na ganka kana murmushi, amma yau kaƙi kayi, narasa me ya sameka, sai naji bana jin daɗin komai a rayuwar, don Allah me kake so"? Nunani yayi da kanshi, duk da na fahimci yana nufin ni yake so saboda tambayan dana mishi me yake so? Amma sai nayi kaman ban fahimta ba, sai na buɗe ido nace, "kana son na fita nabaka wuri"? Runtse idon shi yayi da ƙarfi, alamar ba haka yake nufi ba, jijjiga hannun shi nayi da ƙarfi nace, "wayyo Dr na ko na ƙira Dr Abdallah ya duba mun kai ne? Dr na baka da lafiya ne"? "Abdallah, Faisal, duk kinfi damuwa dasu sama da ni ko"? ya faɗa da wani yanayi kaman na yaro ɗan 20yrs. Tashi nayi na tsaya, shima tashi yayi ya tsaya ya ƙura mun ido, ni kuma turo bakina nayi gaba nace, "Faisal masoyina ne, Dr Abdallah friend ɗin Amaal ne, kai kuma na damu da kai ne, ina jin ka sama da komai da kowa, saboda haka zo mutafi bana son musu muje muci abinci sai kamun karatu", na faɗa ina tafiya hanyar waje, babu musu kowa ya biyo ni. Duk wani text da zamuyi munyi shi, Dr Hussain ɗina babu abinda ya bari ƴa shige mana duhu, duk da rabin karatun zolayan shi nakeyi, na hana shi saƙat, ita kuma Amaal banda dariyan mu babu abinda ta keyi, idan na fara shirmena ajiye komai ya keyi ya ƙura mun ido, har sai Amaal ta gama dariyan ta tayi mun masifa tace nabar mu muyi karatu, amma shi kam baya iya hanani komai sai yadda naso. Wataran ana karatun zan tsaya nace, "Dr mu nikan muje musha ice creem, kaina ya daina ɗaukan karatun", haka zai tattara mu muje, idan munje kuma na dinga mitan mata suna kallon shi, kuma nayi kane kane a kusa dashi ina hararan su, haka zaiyita kallona bazai ce uffan ba. Watarana kuma ana karatun ƙiran Faisal zai shigo don neman tsokana zan ɗauka nayita maganan soyayyah, har na miƙawa Dr nace dole sai sun gaisa, toh irin wannan lokacin baya iya daurewa, tashi yakeyi ya barmu, kuma naƙi nuna wani abu ya faru, haka zanyi ta binshi har sai ya sake dolen shi. Gashi yanzu na tsiro da wani hali sai naga muna school lokacin da muke break zan kira shi na fara damun shi da fitinan ni sai naganshi, na dinga mishi kaman zanyi kuka, babu yadda ya iya dolen shi yake zuwa ƙofan class ɗinmu, ni kuma ina fita zan je nayita gaya mishi magana kaman na soyayyah amma a fakaice, " Dr mu kasan bana jin daɗin komai idan ban ganka ba, wallahi ɗazu ma har saida nayi hawaye fa", "toh me yake saka ki son ganina"? Ya tambayeni bayan ya jingunu da jikin wani mota, ina binshi da murmushi nace, "nima fah ban sani ba, shine nake son kagaya mun, Dr nah nifah so nakeyi kayita goyona fa, zakayi"?. Dariya yayi ya ƙura mun ido yana ta cizon lips ɗin shi, rufe ido na nayi alaman naji kunya nace, "ni idan kana kallona sai na dinga jin wani iri". "Don Allah me kike ji baby nah"? Ya tambayeni da sauri. Dariya nayi nace, "sai ka goyeni tukun na gaya maka". "Baby toh kinƙi ki yarda mu rayu dake ballantana na dinga goyonki kullum, ki amince mana". Ina kallon shi nace, "wai baby a ina zamu rayune ni dakai? Bayan yanzu ma kullum muna tare baka taɓa goyo na ba"? "Idan mun koma gida zan gaya miki, kinga nan school ne idon kowa yana kanmu", sallama yamun ya tafi office, ni kuma na koma class. Muna gama dinner muka fito da books ɗinmu ya ɗan koya mana abinda ya sha mana kai, muna gamawa na matso kusa dashi nace, "Baby nah me zaka gaya mun ɗazu"? Ɗago kai yayi ya kalli Amaal, sai ya maida kallon shi kan TV, ganin haka Amaal ta tashi ta wuce ɗakin mu tana ta dariyan drammer mu. Juyowa yayi ya kalle ni, sai naji kaman bazan iya zama.kusa da shi ba, ina ƙoƙarin matsawa naji ya riƙo hannu na da sauri, kasa kallon shi nayi kawai sai na turo bakina gaba, "Babyn baby ina son mu rayu irin na ma'aurata, ina nufin mu rayu a ƙarƙashin inuwar aure, ina so nazama abokin rayuwar ki ni kaɗai, kuma kizama tawa kema, toh a wannan lokacin kullum kike so zan dinga goyonki har sai kince kin gajji". Kasa ɗago ido na nayi domin na kalle shi, duk sai naji yau yamun wani girma, ina so na gudu shi kuma ganin haka sai ya ƙi sake hannuna, "Baby ki yadda dani don Allah, na rasa abubuwa masu muhimmanci a rayuwata, banida kowa sai ke, banida family, bani da komai, ki taimakeni mu zauna a inuwa ɗaya nima na samu family kafin na bar duniya". "kana da family, bakana da Ummi da Abba ba, kana da Hassan da Aisha, kuma ni ƴar yarinya yayah zanyi na aure ka? Kamun girma, kuma ae bakace Hummy ina sonki ba, shi kuna Faisal kullum sai yace yana sona, ni yaro nake so kamun tsufah, za ayita mun dariya ne, Amaal ma dariya zata mun". Lumshe idon shi yayi kaman bazai buɗe ba, chan kuma sai ya buɗe yana murmushi, wanda har abin yaso ya bani tsoro, na ɗauka masifah zai mun sai naga sai murmushi yakeyi, Hannun na ya ɗaga ya ɗaura a dai-dai saitin heart ɗinshi, gaba naji ya faɗi saboda yadda heart ɗinshi yake bugawa da ƙarfi, ajiye hannu na yayi a ƙasa sannan ya miƙe ya zura hannun shi a aljihun wandon shi ya juya mun baya, har saida yaje zai fita tukun ya tsaya batare da ya juyo ya dube ni ba yace. "Abinda kike so kiji na miki alƙawari zakiji shi a wurina har sai ya hau kanki, na daɗe da sanin ga abinda kike so kiji daga gareni wanda ke baki san kina cikin yanayin hakan ba, amma na miki uzuri saboda ƙananun shekarunki, *HUMMAIRAH* tun ranan da na ganki wannna bugun zuciyata ɗin yaƙi daidaituwa, kuma tunda ga rana na sakawa raina keɗin kece mahaɗin zuciyata, shiyasa ganinki yasata ta fara aikin da yake so ya fi ƙarfinta, kece ƙaddaran da ta gifta rayuwar mutane da dama, kece ƙaddarar da ta raboni da iyayena da ƴan uwana, kece ƙaddarar data raboni da soyayyar ahalina, kece ƙaddarar da zata sake haɗa ni da farin ciki na, kada kiyi duba da shekaruna, ina so kiyi duba na dacewan masu mabanbanta shekarun da sukayi, shi kaɗai zai baki nutsuwa sa samun kwanciyar hankalin ki domin ki rayu a inuwa ɗaya da mai miki".... Sai ya yi shiru, daga baya ya buɗe ƙofar parlon ya fita. _*SALAMATU ABUBAKAR, (SALMA D.O)*_ tare da _*ZAINAB ALƘALI (ZEE GOMBE)*_ wannan shafi na kune ƙannena, domin nuna muku irin godiyata da jin daɗina na yadda kuke nuna jin daɗin ku akan book ɗinnan, Allah ya albarkaci rayuwar ƴaƴanku, nagode Allah ya bar zumunci *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 20📑* *__________📖* Tunda ya fara maganan na ke jin hawaye suna bin fuska ta, har ya fita ban samu ikon tashi daga wurin ba, ina zaune a inda ya bar ni Amaal ta fito, da sauri ta rungume ni tana faɗin, "ALHAMDULILLAH, yau Dr ya bankaɗo sirrin zuciyar shi". Juyowa na yi ina duban ta, hawaye na zuba kan fuska na, girgiza ma ta kaina na keyi alaman a'a, ɗaure fuska tayi tana tambaya na, "me yake sa ka ki kuka? Kefa murna ya kamace ki da yi". Tashi nayi tsaye na riƙo hannun Amaal, "Amaal ko ɗaya banji kalmar yana sona daga bakin shi ba, kawai cewa ya yi yana son muyi rayuwa tare a inuwa ɗaya, kawai aure na ya ke son yi bawai yana so na ba, ina ga akwai wacce ya tana da ma ta wannan matsayin". na faɗa ina sha re hawayen da ke zubowa. Ɗakin mu na wuce Amaal tana bina a baya, wanka na shiga nayi, ina fitowa ta shiga domin itama tayi wankan, mun kwanta bayan kowa ta gama shirinta, amma babu wacce tace da ƴar'uwarta uffan. "Hummy! Kiyi haƙuri ki bi Dr da irin nashi tsarin, na miki imani da Allah Dr yana son ki, kuma ba ƙaramin so ba, insha'Allahu kuma wata ran ke da bakin ki zaki bani labari, kuma ina miki albishir duk ranan da Dr ya furta miki kalmar ina son ki, sai kinfi jin daɗin kalmar da ganin muhimman cin ta sama da yanzu". cewar Amaal. Juyowa nayi ina hararanta da wasa, "to Amaal saboda Allah a hakan zan yadda yana so na? Shi bazai buɗe baki ya furta mun kalman so yadda ko wani saurayi ya ke yiwa budurwa ba?". Na faɗa ina shirin sa ke sabon kuka. "Don Allah bance kimun kuka ba, wai ke Hummy har sai zuwa yaushe za kiyi wayo ne? Ni fa ban ɗauki wai sai saurayi yace yana sona da ba jin shi ba za muyi soyayya, ai ɗabi'un shi da idon shi ma kaɗai ya wadatar da mace, kawai namiji yace miki yana son ki ai tun zamanin su Ummi a kayi shi". Ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya. Kallon ta nayi baki na buɗe, "kina nufin kina soyayya da wani ne Amaal?". na faɗa ina duban ta tana shiga cikin duvet tana ta ƙyalƙyala dariya. Sai da taga na dame ta da magiyan sai ta gayamun, tukun ta buɗe idon ta tana kan dariyan, ta wani kashe ido ɗaya tace, "to ke banda shirme ya yi miki yawa har yau baki fahimce meye ke tsakanina da Dr Abdallah ba ko?". Ido na zaro ina duban ta cike da mamaki, "kina nufin Dr Abdallah yace miki yana son ki?". na faɗa cike da mamaki. Dariya tayi mai ɗan sauti, sannan ta tashi daga kwancen itama ta zauna bayan ta jingina bayan ta da jikin gado, tana duba na tace, "kina tunanin ni irin kice sakaliya wacce ban san ya ya rayuwa ta ke tafiya ba? Mufa ko acikin larabawa muna da family sosai, kuma akwai kyakkyawan zumunci a tsakanin mu, ina ganin yadda ƴan mata da samarin family'n mu suke tafiyar da al'amarin su, kinga basai an mun bayanin yanayin maza ba, zan iya karantar su". Ɗago ido nayi na dube ta, sai naji lokaci ɗaya kewan mahaifiya yazo mun, wato da gaske ne wata friend ɗi ta Ruƙayyah muna secondry school ta ce mun, "Humairah wataran idan kin yi abu sai naga kaman goyon kakace ke, gaba ɗaya baki da wayo, sai buhun wauta, yanzu banda ke Humairah baki lura Umaimah gatse ta miki ba ko? Ke sai yaushe za kiyi wayo ne?". Ta faɗa tana dariyan wautan da nayi a wancan lokacin, sai Umaimah ta dube mu tana dariya tace. "Ruƙayyah ai na gaya miki Humairah rayuwar kan carpet ce, domin ni kullum ƴan aikin gidan su nake ganin suna hidima da ita, tunda na ke zuwa gidan su ban taɓa haɗuwa da Maman ta ba sai dai step mum ɗin ta, kuma sai su wuni basu haɗu ba, to ina za tayi wayo bata zauna a gaban masu saita ta a kan layi ba, shiyasa wataran idan tayi abu sai taban haushi wataran ta ban tausayi". ta faɗa dukkan su suna mun dariya, nima dariyan nayi dana lura da shirme da wautan dana tabka musu a lokacin. Ina dawowa gidan mu daga school kai tsaye parlon Daddy na wuce, in da na tarar da shi da Mama da Yayah Ahmed da Adda Hafsat da Adda Halima a zaune kan dinning suna lunch, gaishe da su nayi na ƙarasa gefen Daddy na rungume shi ina faɗin, "oyoyo Daddy nadawo a school". shima murmushi yayi yace, "oyoyo Humairan Daddy, zo muci abinci". ya faɗa yana manna mun kiss a forehead ɗina. Da sauri na juyo na dubi Mama jin wani tsaki da tayi, muna haɗa ido ta sauƙe mun wani harara wanda sai dana ji zuciyata ta yanke, Adda Halima da Yayah Ahmed ma hararan suka bini da shi, Adda Hafsat ce kawai ta mun murmushi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta cigaba da cin abincin ta, ganin abinda suka mun yasa na dubi Daddy ina murmushi nace, "Daddy ni banyi wanka ba banyi sallah bama fa, kawai nazo na tambaye ka wai da gaske duk ɗan da bai girma agaban Maman shi ba baya wayo?". "Jeki kici abinci sai muyi labarin, amma ki kwantar da hankalin ki, kinsan duk yadda Allah yaso mutum ya yi rayuwa haka zaiyi, wani zai yi rayuwa babu uwa babu uba, to shi kuma ya yi ya ya a rayuwa? Wani kuma bai san kowa na shi bama, a gidan marayu ya tashi, to shima ya ya zai yi? Dole duk haƙuri akeyi a rayuwar, ke da duk duniya babu wata ƴar da tayi dace da soyayyan uba irin ki to mai zai dame ki Humairah na? Kawai kiyi addu'a wa Mama'n ki Allah ya kai rahama da haske kabarinta, ni kuma nine uwa kuma nine uba a gare ki, kada ki damu, nima soyayya ta ya isa ya hanaki zama marar wayo, kina da zuciya mai kyau ne, shiyasa ake ganin kaman baki da wayo, je kiyi wanka my dear". ya faɗa yana buga kafaɗa na. Hawayen idona na sha re da sauri na dubi Adda Hafsat da itama ta ke sha re hawayen ta, murmushi na mayar mata yadda itama ta mun, sannan na wuce sama domin tafiya nawa side ɗin, amma ina ganin Mama da su Adda Halima sai bina da harara suke yi. Ajiyan zuciya nayi na saka hannu na sha re hawayen ido na, sannan na dubi Amaal nace, "Amaal nima ina so naga ina rayuwa da Mama na da Baba na da ƴan'uwa na, ina son naji ya ya kuke ji, amma Allah bai nufa ba, bani labarin ki da Dr Abdallah". Na faɗa ina ƙara sha re hawayen da yaƙi tsaya mun. "Dr Abdallah tun ranan da muka zo registration Abbu ya haɗa ni da shi a matsayin Dr na, kuma tun lokacin na fahimci ya faɗa cikin soyayya ta, amma ban ƙarasa fahimta ba, sai da nayi ciwo na tafi gida, ya kasa zama ya bini har ƙasan mu, duk da shima ɗan can ne kuma cikin gari ɗaya muke, amma nasan ya yi haka ne don ni, soyayya ce kawai zai kawo haka, sannan wannan kwanciya ta ɗin ya nuna mun babu wata mace da ya ke so da tausayi iri na, ranan farko yace mun, ya kamata na auri likita domin na dinga samun kula, sannan ya dawo yace shi zai sama mun wanda zai kula dani, washe gari yace duk duniya shi zai fi bani kula saboda haka ya zaɓa mun kanshi don ya kula dani, ai dai baki ji yace so na yake yi ba, amma kuma yanzu ni da shi mun san soyayya muke yi, ke kuma abunda kika kasa fahimta da Dr Hussain kenan, yana miki son da ko a gaban waye sai ya nuna, amma ke duk bai ishe kiba kinfi son yace yana son ki kije kiyi tunani bayan 2 days ko? Irin yadda su Ummi suka yi da ko?". Ta faɗa tana harara na. Bansan lokacin dana kwashe da dariya ba, duk wannan ɓacin ran lokaci ɗaya naji ya gudu, duk dariya muke yi ni da Amaal, sai naji waya ta ta fara ringing, da sauri na jawota ina dubawa, ganin sunan Dr Hussain ya saka ni zaro ido na duban Amaal. Harara ta mun taja duvet ta shige ta bar ni, haka na ɗauki wayan yana dab da tsinkewa, "hello babyn Baby ba kiyi bacci ne bane?". Naji yana tambaya na da wani irin murya wanda baza ka taɓa cewa muryan shi bane. Lumshe ido nayi a hankali na furta, "na kasa bacci saboda bansan ko Baby ya yi bacci ba". na faɗa ina jin yadda zuciya ta ta ke bugawa da sauri da sauri, saboda ban taɓa tunanin baki na zai iya furta haka ba. Daga in da Dr yake ya tashi ya zauna, murya ƙasa-ƙasa yace, "da gaske?". "iya kacin gaskiyan da yake zuciyata kenan my Dr". na sa ke tabbatar mishi. Ajiyan zuciya ya yi yace, "Baby ina son ganin ki wallahi yanzu a gaba na, Baby bugawan zuciyata yana ƙaruwa, Baby ki leƙo na gan ki don Allah". Runtse ido na nayi saboda yadda na kejin muryan shi yana rawa, a hankali nace, "Baby ni sai dai kazo ka ɗauke ni wallah tsoron fitowa nake yi ni ɗaya, kuma ni sai nagan ka kafin nayi bacci". na faɗa ina mishi sheshsheƙan kukan ƙarya. "Ba,,byy,yy!" Yaja sunan da ɗan sauti sannan yace, "bana gajjiya da ganin ki, bana gajjiya da jin muryan ki, ki fito na ganki kin ji". Tashi nayi wayan na riƙe a kunne na ina ta sauƙe mishi buhun shagwaɓa har nazo jikin ƙofan parlon na tsaya, ina jin shi ya buɗe na shi ƙofan ya ƙaraso, sai na kasa buɗe ƙofan, shi kuma sai magiya yake ta mun, ganin nayi da shi ya koma ya ƙi kawai sai na saka hannu na buɗe ƙofan, kallon shi nayi sanye da wasu kayan bacci cotton masu masifan kyau, three quater da riga mai kyau, ƙafan shi sanye da wani silifas fari, ido ya ƙura mun wayan shi yana kare a kunnen shi, har lokacin bai yanke ba, nima ina kallon idon shi ban yanke wayan ba, naji yace, "Baby'n baby!" ta cikin wayan, ina kallon shi nace, "baby nerh!". runtse ido yayi. _*MUM SAYYEED GA KYAUTAR WANNAN SHAFIN,BAWAI DON YA ISA YA NUNA MIKI IRIN ƘAUNAR KI DA MUKE YI NIDA BESTY BA, KO ƊAYA KINFI KYAUTAN LITTAFI GUDA MA A WURIN MU, KINA NAN CIKIN RAN MU, MUNA MIKI SON SO.*_ *Plsss keep following, commenting, voting and sharing.* *Love you all my fans❤️😘.* *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/9, 22:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _Wannan shafin nakine MUM SAYYEED Allah ya bar zumunci_ *SHAFI NA 21📑* *__________📖* Murmushi nayi ganin ya buɗe idon yana mun alaman da yara sukewa iyayen su idan suna son abu a hana su, ganin ina murmushi shima ya maida mun martanin murmushin, "Baby kaman yau bazan iya bacci ba idan bamu tare, yayah za'ayi ne wai? Babyn ki fa abin tausayine fah", ya faɗa yana ƙara matsuwa kusa da inda nake. Murmushi nayi na ɗan matsa baya kaɗan, don yazo dab da ni har ina jin numfashin shi a kusa da ni, "Baby toh kasan babu yadda zan maka, domin Allah bai halattah kwanan mu wuri ɗaya ba, saboda haka kayi haƙuri ka koma ka kwanta, da safe zamuyi magana, yanzu kam ae ka ganni", na faɗa ina ƙara sauƙe mishi murmushi. "Babyn baby toh ae yakamata nayi wa Daddy magana domin ayi auren akan lokacin, don gaskiya ni nafara nema na rasa nutsuwa na akan ki, kuma ni irin su Faisal ɗin nan ba zasu barni na samu kwanciyar hankali ba", ya faɗa yana harara na da wasa. Dariya nayi mai ɗan sauti, "Baby aure kuma tun ban girma ba? Gaskiya ni sai nayi masters ma tukun nayi aure, nidai gaskiya naƙi ba yanzu ba", na faɗa ina dariyan yadda ya buɗe ido da bakin shi yana kallo na cike da mamaki. "Gaskiya bazai yiwu ba baby, ni bana son kodawo wani semester ma ba muyi aure ba, idan ba haka ba zan taro gidan nan da zama, da kike cewa baki girma ba, bazaki iya ɗaukan Babyn ki bane?" ... Faɗin haka da yayi nayi sauri na rufe ƙofan da ƙarfi, na juya da gudu nayi cikin ɗakin mu ina dariya, da yake duk abun da mukeyi wayan mu yana kunnen mu bamu wanda ya kashe, inajin dariyan shi ta cikin wayan yana cewa, "ƙarya na miki? Kuji mun ƴan matan nan da wayo, kina birkita ni da salon soyayyah ki kuma kina cewa baza muyi aure yanzu ba"? Ina jin shi nayi sauri na katse wayan nima ina dariya, kan bed ɗin na faɗa ina dariya ni kaɗai na. "Don Allah ki koma parlor ki kwanta, sai kiyi ta sakarcin dariyan ki achan, yarinya anje an kunche miki kai da soyayyah zaki dawo ki sauƙe mun buhuhhunan haukan anan ko? Toh baki isa ba, koma kije chan ko kwana kuna gigita junan ku", Amaal ta faɗa tana turo ni daga kan gadon. Dariya nayi ina faɗin, "baza ki gane bane Amaaƙ ɗita, bansan me nakeji ba acikin zuciyata ga me da Dr, ina mishi wani fitinannen so, wanda yana nema ya fi ƙarfin xuciyata", na faɗa ina dafa zuciyar bayan na runtse idona. Kallon mamaki Amaal ta ke mun, "kice bazamu gama school ba za a muku aure"? Hararan ta nayi, "kaji mun Amaal, bamu gama school ba kuma a mun aure? ae ban girma ba tukun, gara dai sai nagama masters sai amana, lokacin na ƙara girma". "Chabb ae ko ba son shi kikeyi ba, tun da har son ya fara fin ƙarfin zuciyar ki ae sai a tattara mishi ke a haɗa ku gida ɗaya, ku cinye kanku da soyayyah, amma ni bazan yadda kije ya birkita ki kizo kina hana ni bacci ba, ehen gara ma ki gane", Amaal ta faɗa tana komawa tana kwanciya. Rayuwar yana ta tafiya, a yau muka fara exams ɗin wannan semester, gaba ɗaya mun koma wasu iri, domin dukkan mu muna so mu fito da sakamako mai kyau, duk da irin zafin da muke bawa kanmu, bamu rage komai ba ga me da soyayyah mu, duk abinda muke yi dole sai mun bada lokaci na musamman wa junan mu,una yiwa junan mu so na fitar hankali, gashi bamu iya ɗaukan lokacin bamu neme junan ba, haka wurin Amaal da Dr Abdallah, kullum suna tare da juna, duk yadda kake tunanin sun wuce wurin, domin wani irin kula Dr yake bawa Amaal, kaman ya maida ta ciki. Daddy hankalin shi ya kwanta sosai, gashi Abbun Amaal yace mishi idan munyi hutu zai haɗa ni da Amaal muje muyi hutu tare a wurin su, domin shi Daddy yace baya son nazo hutu har sai na gama karatu na gaba ɗaya, saboda shi baiga me zai saka na taho hutun ba, gara shi idan anyi hutun ya zo mun, amma jin cewa Abbu yace zamuje wurin shi sai Daddy ya samu nutsuwa, domin dama tunanin shi ko naje gida bawani daɗin zama zamuyi da su Mama ba, gashi anyi auren Adda hafsat Adda Halima ce a gida, shima Yayah Ahmed dama na taho ana shirin auren shi, ganin basu damu dani da rayuwa ta ba, Daddy bai ko gaya mun anyi auren Yayah Ahmed ba. Ranan da mukayi final exam ɗin mu, rana ce da bazan taɓa mantawa ba, domin a wannan ranan zuciyata ta aminta da irin son da Dr nah yake mun, sannan a wannan ranan na barwa zuciyata ko bai taɓa furta mun kalmar I Luv U ba, toh zan iya ƙarasa rayuwata da shi, domin ya nunawa duniya babu wata mace a zuciyar shi sama dani. Bayan mun gama paper muna ta sallama da ƴan class ɗinmu, shi kuma yazo ɗaukan mu domin mu wuce gida, Amaal ta gajji da jirana saboda complain da ta keyi na ƙafan ta da yake ɗan mata ciwo, sai ta wuce cikin motan ta zauna, shi kuma Dr nah ya buɗe mun gaban motan yana jira nah, duk i da nayi idon shi yana kai na, chan na gama abunda na keyi na taho zan shiga gaban motan inda yayi sauri ya buɗe mun daga inda ya ke zaune. Ina dab da zan shiga kawai sai naji anyi wulli da ni gefe, wanda sai da nayi ƙoƙarin gaske na daka tar da kaina daga faɗuwa, juya wan da zanyi kawai sai naga Dr Khadijah ce ta wullar dani, ita kuma tayi sauri ta shige gaban motan. Da sauri Dr Hussain ya fito daga motan ya taho inda na ke da gaggawa, hannun shi ya saka ya riƙo hannu na, hankalin shi tashe ya fara tambaya na, "Baby bakiji ciwo ba? Babu abinda ya same ki"? Ya na tambayan muryan shi da ƙarfi wanda yaja hankalin mutanen da suke wurin, kuma cikin tashin hankali ya keyi, ni kuma ganin hankalin shi ya tashi kuma duk idon mutane ya dawo kanmu, na juya na dubi Dr Khadijah, naga yadda ta buɗe baki da ido tana kallon Dr cike da mamaki, a zuciyata sai naji na raya bari na nuna mata matsayina a wurin Dr, kuka na fara nayi sauri na rungume shi ina faɗin, "Dr nah kaman hannu na data jawo zai tsinke na keji, Dr nah ciwo yake mun har bayana, ni tsoron ta nakeji Baby nah, kace ta tafi bana son ganinta", na faɗa ina ɓoye fuskana a ƙirjinsh, wai duk na nuna mishi tsoron ganin ta nakeyi. Ranshi a matuƙar ɓace ya saka hannu ya fisgota da ƙarfin gaske daga cikin motan wanda har sai da kanta ya bugu da jikin motan, wuntsilar da ita yayi da ƙarfi har saida ta faɗi ƙasa, sannan ya dawo dani gefen shi na hagu ya rungume ni ta gefe, ya ɗaga hannun shi na dama yana nuna ta da yatsa yace, "daga yau na miki tsakani da matar da zan aura, Khadijah daga yau na miki iyaka da rayuta, wallahi na rantse miki da Allah idan wani abu ya faru da ita daga rana mai kaman ta yau hukuma za ta mana iyaka ni dake, domin, Hummy bana iya haɗata da komai a rayuwata saboda ita ɗin rayuwa tace, itaɗin haskene a gare ni, duk wani abu da ya sameta marar kyau bazan taɓa yafewa kaina ba, saboda haka ki maida hankalin ki, kuma a yau zaki fuskanci waye Dr Hussain Mohd Aliyu, kuma a yau hukumar makaranta zata miki iyaka dani da iyalina, idan kuma ba a ɗauka hukuncin da yaka mata ba, toh dole na haɗaki da hukuman ƙasan ra ɗauka ƙwaƙwaran mataki akan ki, domin taɓa baby", ya saka hannu ya nuna mata ni, "kaman kin gayyato tashin masifar da tafi ƙarfin cutar cirona virus na a wurina, saboda haka ki kiyaye". A lokacin shugaban makarantar dana department ɗin suka iso wurin, ga kuma wasu securities mata da aka ƙira suka iso, gaba ɗaya idon Dr Hussain yayi wani irin ja don tsabar masifah, ga wani rawa da jikin shi ya keyi, hannu shugaban makarantar ya saka ya ɗaga Dr Khadijah wanda gaba ɗaya kunya da tsoro ya kamata, sannan ya bubbuga kafaɗan Dr Hussain a hankali yace, "Dr zamu sake jan kunne wa Dr Khadijah a kashi na biyu, wanda idan bata gyara tsarin rayuwarta ba mun maka alƙawarin Makaranta za ta ɗauki hukunci mai ƙarfi gaske akanta, saboda kowa ya maka shaidah baka da abokin faɗa, kai ka bada rayuwar ka da lokacinka ne kawai akan aikin ka, babu wanda ya taɓa jin tsakanin ka da kowa, sai Khadijah da ta ke maka shishshigi, amma kayi haƙuri ka ɗauki sister ka ku tafi hospital a duba mata hannun, don bamu so iyayen yarinya suji wani abu ya samu ƴar su ta dalilin staff ɗinmu, domin zai jawo mana matsalah mai girman gaske". Sannan ya sallami student ɗin da suke tsatstsaye a wurin da sauran staffs ɗinsu, ya kuma umurchi Dr Khadija da ta wuce office ɗin shi, sannan ya ɗubi Dr Hissain yace, "Dr kamaida su ka taho akwai zama da zamuyi da kai da Khadijah a office ɗina". Muna isowa gate ɗin gidan mu ya juya ya dubi Amaal yace, "zaku iya shiga ciki ko na shigar daku"? Da sauri Amaal tace, "zamu iya gara kaje tun da ana nemanka da sauri a school, Dr kuma don Allah kayi haƙuri kaji". Kallona yayi bai iya amsa abinda Amaal ta faɗa ba, a hankali naji yace, "Baby hannun yana ciwo? Zaki iya daurewa na dawo sai na kaiki hospital, ko kuma na ƙira Dr Abdallah yazo ya duba mun hannun ki"? Sheshsheƙa na fara yi alaman zanyi kuka, nayi sauri na kwanta akan ƙirjin shi inda na ɗauki hannu na na ɗaura a daidai saitin heart ɗinshi, inajin yadda heart ɗin ya ke bugawa da sauri- da sauri na fara kuka ina cewa, "baby ni na daina jin ciwo a hannuna, kawai inajin ciwon ta ɓata mun ranka ne, baby kaji heart ɗinka yadda yake bugawa da sauri da sauri, idan wani abu ya saman mu kai wallahi bazan yafe mata ba, ni wallahi sai na faɗawa Daddy na", na faɗa ina ƙaea sautin kuka na. Ɗago ni yayi a hankali yana duba na yace, "baby kada ki gayawa Daddy, zaiyi tunanin na gaza da baki kulawa ne, kiyi haƙuri babu abinda zai same ni insha Allahu, kawai na damu ne don bazan iya barin wani ma haluƙi yaci zarafin ki ina gani ba, kuma ina baki tabbacin baxan taɓa barin Khadijah ta sake maimaita miki ba, sai dai ta bar school ɗin nan, nidai kiyi haƙuri bari naje na dawo sai muje hospital ɗin". "kada ka damu baby na, zan shafa maganin Amaal, dama damuwa na kai ne, kaje sai kadawo my dear, Allah ya tsare mun kai", na faɗa ina buɗe motan, haka yaja ya tafi, ni kuma na dubi Amaal muka shigo cikin gidan. muna shigowa Amaal ta kalle ni tace, "munasira babu maganin da zan baki ki shafa, don nasan babu inda yake miki ciwo, sai tsabar sakalcin soyayyah da yake ɓuɓɓula duk wani gaɓa na jikin ki, toh yau hankalin ki ya kwanta , Dr Hussain ya nuna wa duniya babu kaman ki a zuciyar shi ƙorafi ya ƙare daga yau", ta faɗa tana buɗe mana gidan mu. Dariya nayi na faɗin ƙasan carpet ɗin ina ta juyi a ƙasa ina cewa, "wayyo my one and only, wayyo babyn baby, wayyo my heart, wayyo honey na, yau kasa ina maka ɓulɓulan so, babu abinda ya saura sai kadawo na riƙe ka wunin yau inyi ta shagwaɓa iya son raina, kai kuma kayita jinya", na faɗa ina ƙara kwashewa da dariya. Harara Amaal ta mun tace, "amma ke baki da imani, kibar bawan Allah nan yaji da tafiyan da zamuyi gibe mubar shi, har na tsawon 1month, kibari kuyi sallama basai kin ɗaga mishi hankali ba". Tashi nayi na zauna ina kallonta, "lallai ma Amaal, ae saina lugwaigwaita mishi zuciya, wanda idan na tafi tsanani ya daure yayi 1week bai bi baya na ba, kina ganin zan iya 1month babu shi kusa dani? Bazai taɓa yiwuwa ba, tunda Abbu suka ɗauki nauyin Hummy toh dole su haɗa dana Dr nah", na faɗa ina ƙyalƙyala dariya, ganin yadda Amaal ta bar abinda ta keyi tana kallo na. "Hmm Hummy kice yau na yi laɓe naga yadda zaki birkita mun kan Dr"? Dariya na sakeyi nace, "ki tsaya gulma dai kada kije ki birkita kan naki Dr, nidai babu ruwana idan kinga Dr na ya biyoni ke kuma na barki da zaman hira da Ummu". "Hummm ni Hummy yanzu gaba ɗaya mamaki kike bani, yadda kika iya ɗauke hankalin wannan babban mutumin, babu wani fargaba yau ya yanƙwana ƙatuwar mata kaman Dr Khadijah akanki"? _Nima Aunty Nice mamaki nakeji na yadda mutumin da bazai iya furta kalmar so ba, amma yayi mata abinda yafi ƙarfin furta kalmaɓ so ɗin ma yau a idon student da malaman su, besty ta dubeni tace "humm Aunty nice mamakin namiji kikeyi?ae ya wuce haka ma idan akan abinda yake sone, kawai yanzu ki bari mujira da wuwan shi muji yayah za ayi sallaman nan", kallonta nayi nace , "toh bari na tafi na nemo neat lady, saboda mutane suna ta neman book ɗin ta amma ni ban san ina take laɓewa ba, gara naje har gida na fito da ita taxo tayi typing dole yau_. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/10, 14:46] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 22📑* *__________📖* Babu ɓata lokaci muka shiga bedroom ɗinmu muka fara haɗa kayan mu, muna cikinyi akayi azahar, muna idar da sallah Dr ya ƙirani a waya yace, "Baby kije bakin gate akwai masinjan mu ya kawo muku abinci, don Allah kiyi haƙuri har yanzu bamu gama case ɗinnan ba", haƙuri na bashi sannan na mishi godiya. Wajen gate ɗin na fito na karɓi ledan da aka mana take-away ɗin, na shigo haraban gidan muka haɗu da Peter da David, murmushi suka fara mun, Peter kuma yana harara na da wasa, domin fuskanshi ɗauke yake da murmushi, "preety wato Dr ya ɓoye mana ke ko"? Ya faɗa yana duban ƙofan gidan Dr. Dariya David yayi yace, "ba dole ya ɓoye mata mai kyau ba, kaga laifin shi ne bros"? Nima dariya nayi ganin sun harbo jirgin mu, ina duban su nace, "baku fahimta bane Dr ba soyayyah muke yi da shi ba, yayah nane fah". Dariya sukayi suna kallon junan su, peter yace "mun yadda ba soyayyah kukeyi ba, amma yau meye ake faɗa a depertment ɗin mu? Ko ina ka tsaya guys sai labarin tashin hankalin da Dr yayi akan ki ake tayi, toh duk wannan ma ba soyayyah bane ko"? Zaro ido nayi na juya ina dariya nayi hanyan side ɗinmu, suma dariya sukeyi suna cewa na gudu don naji zasu faɗi gaskiya. Barin duk abinda mukeyi na shirin kayan mu mukayi, muka zauna muka ci abinci, da yake dama yunwa mukeji, muna gama ci muka ɗauko apple juice da mukayi tun daren jiya muka sha, kallo na Amaal tayi tace, "nikan bacci zanyi kafin la'asar" ta miƙe tayi hanyar bedroom, nima tashi nayi na bi bayan ta. Bamu muka tashi ba sai wurin 5:00pm, saboda rashin bacci da bamu samu kwana biyu ko alarm bamu ji ba, da sauri mukayi sallan, sannan Amaal ta kalle ni tace, "Hummy yau kam muhuta ɗaura abinci, kawai musha cornflakes da dare, don wallahi duk wani ciwon jiki nake ji, addu'a na ɗaya musamu mu bar ƙasan nan lafiya ciwo na bai mutsa ba", ta faɗa tana daddana ƙafan ta da kanta. Duban ta nayi nace, "Dr fah me zai ci kike nufi"? Harara na tayi tace, "sai yaje yayi abinda ya saba tun da chan baya", ta fara tana dubana da dariyan tsokana. Turo bakina nayi gaba nace, "ke kika sani bari yazo na gaya mishi, kuma babu inda zaki bimu idan yace muje shan ice cream", na faɗa ina tashi tsaye don zuwa na duba abubuwan da suke kitchen ɗin mu. Dab za'ayi sallan magrib Dr Hussain ya dawo, knocking gidan mu yayi, da sauri kaman jiranshi na keyi naje na buɗe, tsayawa yayi yana dubana da murmushi a fuskar shi, nima mayar mishi nayi, sannan na bashi hanya ya shigo ciki. Yana zama na wuce kitchen na haɗo mishi sauran cake ɗinmu da apple juice mai sanyin daɗi, gefen shi na samu na xauna ina zuba mishi juice ɗin a cup. Sai bina da kallo yake yana murmushi, a hankali nace, "Dr nah me yake saka ka farin ciki bayan gobe zan yi maka nisa"? Dariya yayi mai ɗan sauti sannan ya dube ni yace, "ina farin cikin hukuncin da akayi wa Dr Khadijah ne kawai baby, kinsan an mata doka mai tsanani akaina da ke baki ɗaya, kuma management sun tabbatar mata da cewa idan har ta sake maimaita makamancin irin haka zasu dakatar da ita, kuma tayi mugun razanan, don har aka tashi a taron bata daina sha re hawaye ba", ya faɗa yana ƙara murmushin kan fuskan shi. Ina kallon shi da mamaki, "Dr mu toh meye yake saka ta kukan"? Yama ajiye cup ɗin bayan ya shanye wanda na zuba mishi ya dube ni yace, "Ni wallahi baby har tsoron irin son da Khadijah ta keyi mun nakeji, kinsan bayan ance ta bani haƙuri, saida ta ban tausayi, domin a hankali babu maiji tace, zan bar ƙasan nan tabbas sabida kai Dr, domin zuciyata bazata ɗauki ganinka da wata ba bayan ni", Ya faɗa yana dariya. Wani iri naji cikin zuciyata, domin ko babu komai macece ƴar uwata, kawar da maganan nayi ina duban shi nace, "Baby nah yau kaman mun gajji, ko zakayi take-away ne da dinner kaci? Muma cornflakes kawai zamu iya sha duk muna jin gajjiya yau a tare da mu", na faɗa ina duban shi da alaman damuwa a fuskana. Shima turo baki yayi yana kwaikwayo na yana buga ƙafa a ƙasa yace, "nikan bazan yadda ba, yau abincin Baby zanci, ni wallahi bazan yadda da wayon nan ba", dariya muka farayi ni dashi a tare, ina kallon shi nace, "haba baby ni da yakamata nayi shagwaɓa sai kaine yau zakayi, toh ni yayah zakayi dani idan kai kanayi"? "Kawai sai a raba kowa da turn ɗin yin sakalcin shi, idan nayi na 2dys sai kema kiyi na 2dys, kowa yayi ta fama da ɗan uwan shi ko ba haka ba"? Dariya nayi na miƙe ina cewa, "bari naje kitchen ɗin na duba me zan dafa maka". Da sauri ya kamo hannu na bayan shima ya tashi ya tsaya, dab da bayana yazo ya tsaya kaman wanda zai jinginu da ni a hankali yace, "Baby nah bana son ki wahala, kawai ki gayawa Amaal idan anyi ishaa zamu fita muci abinci ko, bana son ƴar baby nah ta wahala", ya faɗa yana ɗaura haɓan shi a kafaɗa na, da sauri naja jikina na shige bedroom ɗinmu da gudu, dariya ya fara yi yana girgiza kanshi, ya juya ya fita a gidan, sai da na tabbatar ya bar parlon tukun na fito na rufe ƙofan na ƙoma bedroom wurin Amaal. Zama nayi ina ajiyar zuciyar mai ƙarfi, juyowa tayi tana hararah na tace, "zakuji da shi dai magulmata". Murguɗa mata baki nayi ina jujjuya mata ido nace, "ki shiryah anjima zamu fita dinner da Baby nerh"! Hararana tayi tace, "sai ki fita da Babyn ki, nima Hubby nah zai zo mufita yawon sallama kafin ya iso ni a *DAMMAM*". Zaro ido nayi ina dubanta, "laillai yarinyar nan wuyanki yayi kauri, toh babu inda zaki tafi da shi ke kaɗai, Ummi idan ta samu labari ranta zai ɓaci, saidai yaxo mu fita tare dukkan mu, ina gadinki kina gadina", na faɗa ina rawan india a gabanta. Gaba ɗaya daga ni har Amaal ƙamshin daɗi mukeyi, gashi munyi shigan wasu english wears masu masifar kyau, munyi rolling kanmu da wani gyale mai kyaun gaske, nawa colour red and green, na Amaal kuma red and black, haka muka fito muka shiga bayan motan Dr Hussain, inda shi kuma da Dr Abdallah suna gaba. ranan munyi yawo kam bayan mun ci abinci, har wurin 11:00pm tukun muka je muka sauƙe Dr Abdallah, sannan muka dawo namu gidan, Amaal sallama tayiwa Dr nah ta wuce ciki, mukuma muka zauna a parlon, ƙura mun ido Dr yayi, ni kuma ganin kallon bana ƙare bane sai na matsa nesa da shi ina ta kame-kamen abinda zance, don gaskiya ni bana son irin kallon da yake mun. "Baby yanzu gobe kenan zaku gudu ku bar ni ko"? A hankali na dube shi ganin yadda yayi mun maganan kaman bazai buɗe bakin shi ba, juyar da kaina nayi na bar duban shi, nima murya cikin nutsuwa nace, "Baby ko na zauna ne nayi hutun anan tare da kai"? "Ban isa ba baby, ki tafi kawai nima xan fi so naga kin samu masu ɗebe miki kewa", haka mukayi ta hira, da ƙyar muka rabu wurin 12:30pm, bayan ya tafi na shigo ɗaki, baki a buɗe nake kallon Amaal da mamaki, ta wani bararaje akan gado sai wani luv ta ke kwasa a waya ita da Dr Abdallah, ganin haka na wuce toilet nayi wanka nazo na kwanta ina ta ja mata tsakin sun dame ni. Saida mukayi wanka muka saka kayan mu tukun aka ƙira sallan asuba, jirgin mu 9:00am zai tashi gashi airpot ɗin da nisa shiyasa muka tsayar 6:00 zamu fita domin tafiya, tunda muka shiryah nake ji kaman nayi kuka saboda tafiyan da zanyi na bar Dr nah shi kaɗai, a haka jiki a sanyaye muka shiryah. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/13, 18:31] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* ```13/07/2020.``` *ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!!!.* *a yau GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION na cika shekara ɗaya da kafuwa.* *muna roƙon ubangiji Allah ya ƙara ɗaukaka wannan ƙungiya mai tarin albarka tare da mutanen cikin ta, Allah ka ci gaba da basu nasara da sa'a, Ya ƙara wanzar da zaman lafiya, fitina da sharrin masu sharri da idon maƙiya Allah duk ka kauda akan wannan ƙungiya da jama'ar cikin ta. Allah muna roƙon ka kaci gaba da bawa wannan ƙungiya da jama'ar cikin ta ikon faɗakar da Al'ummah ta hanyar GASKIYA hanyar da ta ke dai-dai bata kaucewa ba. Allah kar ka nufi wannan ƙungiya da fitar da abinda zai zama yaɗa fasadi ne zuwa ga Al'ummar Annabi Muhammad {S.W.A}, Allah ka bawa wannan ƙungiya ikon tsarkake alƙaluman ta ba tare da ta rubuta shirme ba, sai dai abinda Al'ummah zasu karanta su amfana da shi.* *AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM.* Jinjina zuwa ga shugabar wannan ƙungiya *UMMU NABIL.* Allah yaci gaba da taimakon ki da ke da members na ki. _Shafin Sadaukarwa ne ga Gaskiya Writer's domin murnar cika shekara guda._ *SHAFI NA 23📑* *__________📖* Duk wanda ya dubi fuskan Dr Hussain sai ya ji tausayin shi sosai a ranshi, kuma sai kayi mamakin wani irin so yake yiwa Hummy, domin Dr Abdallah kaɗai yake ta fice-ficen tafiyan su, amma sam Dr Hussain ya kasa yin komai, yana zaune gefe na ya kama hannu na kaman wani zai ƙwace mishi ni, muna nan haka Dr Abdallah ya dawo ya zauna gefen Amaal, yana duban Dr nah yace, " Dr saura 15mnt jirgin su ya tashi, gashi an fara neman passinger su shiga jirgi, ina ga ya kamata mu barsu haka su wuce ko?". Da sauri na ɗago kaina don jin irin ƙanƙame mun hannu na da Dr Hussain ya yi, shima ƙura mun ido ya yi kaman zai furta abu amma ya kasa, sai lips ɗin shi kaɗai na gani suna ta motsawa, matsowa na yi kusa da shi na kwantar da kaina a kafaɗan shi, lokaci ɗaya na ji hawaye yana bin fuska na, murya ƙasa-ƙasa nace, "Dr nah zamu tafi, don Allah ka kula mun da kan ka". ina gama faɗa mishi na miƙe tsaye, wanda shi ma haka ya saka ya miƙe amma hannun shi yana riƙe da nawa hannun, murya ƙasa-ƙasa shima ya furya. "Baby bana son ki tafi ki bar ni, kin amince na sanar da Daddy'n ki relationship ɗin mu". Damƙe hannun shi na yi da ƙarfi cikin nawa, "Dr bayan zu ba, kabari mugama wannan session ɗin tukun ya sani, kayi haƙuri Baby nah, ni dai ka kula mun da kan ka". "Baby ki kula mun da kan ki, kiyi hankali da larabawan nan, don Allah ko brother Amaal bana son ki bashi fuska kin ji baby nah". haka muna ji muna gani muka tafi muka bar su Dr da sai ɗaga mana hannu suke yi. *DAMMAM.* Abbu da Ummi ne suka zo taryan mu, haka muka shiga motan su in da driver ya ke jan mu har gida, a hanya Amaal kaman zata shige cikin Ummi, sai wani shagwaɓa ta ke ta mata, akan ko ina a jikin ta ciwo yake yi ma ta, ita kuma Ummi sai rarrashin ta ta ke yi, a haka har muka iso gidan, ni dai sai bin su da kallo kawai na ke yi, don gaba ɗaya sun ban sha'awa, sai smilling na ke tayi ina kallon su. Kai gidan su Amaal ya haɗu, domin bansan yadda zan kwatan ta muku irin kyaun shi ba, duk da gidan mu yana da kyau amma tsarin ginin larabawa ba wasa bane, duk da muma daga waje Daddy ya kawo zanen da za'a mishi, amma gidan su Amaal ya ɗauki hankali na over, muna shiga parlon gidan gaba ɗaya ma sai naji ya tafi da hankali na, gaba ɗaya wani tsari ne da bazan iya rubuta shi ba a ɗan ƙaramin book ɗi na ba, sai dai kawai ku kwatantashi. ga wani ƙamshi na musamman da ya ke yi, ɗakin Amaal Ummi ta raka mu in da shima aka mishi gyara na musammam, duk yadda ɗaki na ya kai da girma na Amaal ma ya yi biyun shi, domin wani gyara da akaman sai ya baka mamaki, bed biyu aka saka amma duk da haka da sauran space a ɗakin, bamu daɗe ba Ummi tace muyi wanka mu fito parlor mu ci abinci, haka muka shiga muka yi wanka, wani riga da wando ɗan pakistan Ummi ta kawo mana muka saka, sai ƙamshi muke yi kaman daga paris muka fito. Muna kan dinning babu abinda ka keji sai ƙaran spoons, sai kuma daga parlor kana jin sautin news da a keyi a TV, gaskiya larabawa sun iya girki, idan ba wai santi ba sai nace sun fi ko wani ƴan country iya abinci, domin naji daɗin abincin da Ummi ta mana, domin duk dukiya na gidan su Amaal amma Ummi tana shiga kitchen, duk da yawan masu aiki da ke gidan amma tana saka hannu a aikin kitchen kaman wata ƴar nigeria, hakan yasa naga Amaal ta iya girki kala-kala, ga snacks da drinks iri da kala da ta iya, don bansaka girman kai ba duk sai da na koya a wurin ta, nima na gwada ma ta na ƙasan mu. Parlor muka dawo muka zauna muna ta hiran school, anan Ummi ta ke gaya mana next week Faisal ma zai zo hutun 3weeks, haka muka yita hira kaman zasu ƙashe mu. Kullum garin Allah ya waye sai mun yi waya da Daddy, yana gaya mun irin dauriyan da yake na rashin gani na, hakan zan ta bashi haƙuri, har da yace mun dabadan wani business daya sako shi a gaba ba zai tafi china, da yazo ya mun ko 1week ne, haka kullum za muyi ta hira, kuma yana gaya mun sunyi waya da Dr Hussain. Allah sarki Baby nah, kullum dare idan muna waya ya dinga ƙorafin wai rana baya gudu dare ma baya gudu, haka zan ta mishi dariya, watara na muna hira nace, "Dr mu to kaje wurin su Ummin ka mana ka yi hutu, kada kaɗaici ya dame ka kaji Dr nah". Na faɗa kaman zan mishi kuka. Kashe wayan ba tare da yace mun uffan ba, da sauri na saka hannu na rufe baki na ina tuna ranan fa yace mun kada na sa ke mishi magana su Hassan da su Abban shi, a zuciya na nace, "me yasa bana jin magana ne". Da sauri na ƙira wayan shi amma firr yaƙi ɗauka, haka na yi haƙuri na kwanta ina ta saƙe-saƙe a zuciya ta. _DON ALLAH KUYI HAƘURI BANA JIN DAƊIN JIKI NA NE._ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/20, 12:37] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 24📑* *__________📖* 2dys da zuwan mu DAMMAM Faisal ya iso, kai masha Allah wato Faisal ya ninka Amaal kyau sau babu adadi, ga wani class a tattare da shi, lokacin da na fito parlor inda suke ta murnan ganin shi tsayawa nayi ina kallon inda yake bakina ɗauke da murmushi, Amaal ce ta nuna mishi ni tana dariya tace, "Humairah" da sauri ya juyo inda nake ya ƙura mun ido yana murmushi shima. Ganin haka ya saka ni takowa zuwa inda suke cikin tafiyata kaman na tarwaɗa tsaban yauƙi daya mun yawa, wani ɗan sautin dariya ne marar ƙarfi ya ɗan suɓuce mishi a bakin shi, a hankali ya furta, "woow beautifull" sannan ya juya ya kalli Ummi yana murmushi yace, "Kai Ummi yarinyar tana da kyau da yanga, Ummi ina son yanga a wurin mace" hararan shi Ummi tayi tace, "Hummy sister ka ce fa, don haka bana son fitina". Ina ƙarasowa na mishi sallama har lokacin bakina ɗauke da murmushi, da sauri ya kamo hannu na ya jawo ni jikin shi ya rungume ni irin yadda suke gaisuwan su, sannan ya sumbaci kuncina, ba karamin faɗuwar gaba naji ba don gaskiya ni ba'a taɓa mun haka ba, gara ma Abbu da safe haka yake mana amma bana jin komai saboda shi ae uba ne, amma wannan gantsamemen saurayin fah? Ga wani ƙamshi da yake tashi a jikinshi kaman wani amaryah, cikin ƙarfin hali nake gaisheshi saboda har lokacin bai sake ni ba saidai ya ɗago ni daga jikinshi yana riƙe da kafaɗa na duka biyun, ga wani murmushi mai masifan kyau a fuskan shi. Ya kamata naji haushin abinda yamun amma sai naji na kasa saboda wani irin kyau da kwarjini da ya mun, ga shi mai tsafta ɗan gayu, ina murmushi na saka hannu na ina cire nashi da yake kafaɗa na, a hanakali yace, "kina da masifan kyau Hummy, kyaun ki mai kyau ne" gabana naji ya faɗi, gaskiya Faisal ya haɗu duk da bai kai Dr nah kyau ba, amma yau ɗaya yamun abinda Dr na ya kasa yimun kusan 4month, yau kalman da nake so naji a na yawan furta mun ni mai kyauce Faisal ya furta mun har yana wani kashe mun ido. Wucewa nayi inda Ummi ta ke zaune na zauna a gefenta , har zuwa lokacin fuskana ɗauke da murmushi, domin haka kawau Faisal ya sauƙe mun wani nishaɗi a zuciyata, gaskiya ni Humairah me kyauce, amma haka kawai nake jin son kyawawan mutane, don bana mantawa idan kakata wadda ta haifi Mamana idan tazo duk inda tayi na dinga kallonta kenan, domin ba ƙaramin kyau takeyi mun ba, gata da gashi mai tsawon gaske, bana gajjiya da kallonta, haka ita kanta Amaal bana gajjiya da ganinta domin kyau ta keyi mun, yau ɗaya naga Faisal yafi mun Amaal kyau, gashi shima yana yaba nawa kyaun. Da sauri na ɗaga kaina domin jin abinda Faisal yake gayawa Amaal, "sister dama haka Hummy ta ke da kyau shi ne baki taɓa nuna mun ita ba? bayan na biki ko a photo ne ki nuna mun ita amma kinƙi, ashe mai kyau aka ɓoye mun? gaskiya gara da nazo na ganta da kaina", ya juya wurin Ummi yana murmushi ya dafa cinyan ta yana magana cikin shagwaɓa, "gaskiya ni Ummi ina son Hummy na gaskiya bana wasa ba, gaskiya Ummi nikan dani ta dace, ko ajiye mun ita na kusa gama karatuna", ya faɗa yana kwantar da kanshi kan cinyan Ummi, idon shi kuma duk ya sauƙe mun su, sai wani kashe mun ido kawai ya keyi da zaran mun haɗa ido, nidai kunyan shi kawai nakeji, sai wani smilling mai ɗauke hankali na ke tayi. "Baka isa ba wallahi bros Faisal, ta yayah ma zanyi wa Dr Hussain haka? gaskiya toh wasan ma ya isa haka, bayan Hummy da Dr sun amincewa junan su, gaskiya kabar maganan nan bazai taɓa faruwa ba", ta faɗa tana miƙewa tsaye, idon ta akan Ummi tace "Ummi ki gaya mishi gaskiya ya dai na irin haka, ni bazai saka naji kunyan Dr ba", sannan ta kamo hannu na tace, "mu tafi ɗaki hummy". Miƙewa yayi shi ma yana hararanta yace, "wallahi sis baki isa ba, kinsan haka ta ke shi ne zaki wani sako ni acikin shirmenki, toh ni ma ae namiji ne saidai kowa ya gwada jarumtar shi, wanda yayi nasara Humairah ta zama rabon shi, kuma kibar yarinya ta zauna a inda ya mata bawai ki kai ta bedroom ki kulleta ba", ya ƙarasa faɗin maganan yana kamo hannu na, da sauri na juyo na dubi Ummi da ta zuba mana dukkan idonta akan mu bakinta a buɗe, maida kallo na nayi kan shi amma da sauri na kawar da kaina ina ƙoƙarin ƙwace hannu na, domin ni ban san me nake gani a cikin idon shi ba, gashi bana son ya riƙe ni amma kuma bani da ƙarfin gwiwan hana shi, narai-narai nayi da ido alaman zan mishi kuka domin nakasa ƙwace hannu na. Sun kuyawa yayi dai-dai kunne na yace, "kada ki tafi da bugun zuciyata ya ke ma'abociyar kyau na duniya, nafi son na dinga ganin kyakkyawan idon ki da ɗan ƙaramin bakin ki mai matuƙar tafiya da hankalina a kusa dani ya mai kyau", wayyo Allah jina nayi numfashi na yana shirin tafiya lokaci ɗaya, abin na kwace hannuna daga nashi sai na samu kaina da ƙara damƙe hannun shi cikin nawa, wanda bansan dalilina nayin hakan ba. Ganin haka ya daka Ummi miƙewa da sauri tace, "sakar mata hannu fav, baka san abunda kake yi mata ya saɓawa shari'an musulunci ba, ko ce maka akayi hannun Amaal kake rike da shi? bana son sakarci, sake mata hannunta ta bi ƴar'uwarta". Da sauri ya sa ke mun hannu yana sauƙe numfashi kaman wanda yayi gudu, ya juya yana kallon Ummi cike da shagwaɓa yace, "haba mana Ummi!! nifa wallahi bazan cutar da ita ba, kawai ki gane Ummi sonta fah na keyi over", bayan ya saka hannu yana wani dafa ƙirjin shi kaman wanda yake jin wani ciwo a wurin. Hararan shi cikin so da ƙauna Ummi tayi, sannan ta buɗe mishi hannu alaman ya taho gareta, da sauri yaje ta rungume shi ta wani bubbuga mishi bayan shi kaman wani yaro ƙarami, murya ƙasa-ƙasa ta ke rarrashin shi, "haba fav kasan fa Humairah amana ce a wurin mu, yayah karon farko zaka fara riƙe mata hannu kana jawota jikin ka? Kuma kasan akwai wanda sukayi alƙawarin aure kuma ya maida mu kaman iyayen shi, ae bai kamata mu baka daman ka so ta ba, saboda bazai ji daɗi ba kuma bazai yadda damu ba a gaba, kayi haƙuri farin cikina Allah zai baka wacce tafi Humairah insha Allahu". bamu jira munji mai zai ce ba Amaal ta jawo hannuna da sauri muka wuce ɗakinta, muna shiga ta fara masifa kaman zata mare ni, "haba Hummy ki zama very careful da ɗan'uwa na domin kada ki bari yaje ya ɗauke hankalinki akan Dr, don wallahi Dr bazai taɓa yafe miki ba, kuma nima zaki sakani jin kunyan shi, don wallahi tsab Faisal zai gama da zuciyar ki acikin kwanaki kaɗan", ta faɗa tana hararana. Murmushi nayi ina duban ta, a hankali na zauna a kusa da ita na saka hannu na riƙo nata hannun nace, "nikan Amaal kibar tunanin akwai abinda zai ɗauke hankali na akan Dr, ni ina yiwa Dr son da ban taɓa tunanin wata mace tana yiwa wani ɗa namiji ba, kai ko tunanin wani zai ɗauke hankali na akan Dr bana yi, saboda haka ki kwantar da hankali ki besty nah", na faɗa ina bin ta da murmushi. "Hmmm bazaki fahimta bane, wallahi bros Faisal tsab zai ɗauke hankalin ki domin yasan yadda zai nuna miki kulawan da baxaki iya tunawa da wani ba bayan shi, nifa ɗan'uwa nane kuma nasan halinshi akan abinda yaga yana so, don ko abu yake so a mishi yasan yadda zai ɗauke hankalin su Ummi da Abbu su mishi babu shiri, kedai ki maida hankali kawai, bana son kina bashi haɗin kai ko yazo inda kike kinji", ta faɗa tana duban cikin ido na. "Ashe baki sona da alkhairi ko ƴar'uwata? wato kin fi son farin ciki wani bari akaina ko Amaal? toh bana so ki zugata kibarta tayi amfani danata baiwan ta zaɓi wanda yayi mata bawai sai kin mata shishshigi ba", Faisal ya faɗa ya na tahowa inda muke shima ya zauna a kusa dani, sannan ya dawo da hankalin shi kaina. Yana murmushi ya saka hannun shi ya riƙo nawa, ido na nayi saurin buɗe su a kanshi, amma sai na kasa ce mishi uffan domin yadda naga ya runtse idon shi bayan ya riƙe dukkan hannuna yana ta matsa mun yatsuna a hankali a hanakali, da sauri na dubi Amaal da ta buɗe baki tana kallon ɗan'uwanta. "Mine kice mun wani abu mana da daddaɗan muryanki hankalina ya kwanta", yana wani langwaɓe mun kaman mai yaron da yake shirin shan nono, murmushi nayi na ɗaga idona ina kallon shi, a hankali na buɗe bakina nace. _Toh ina team Dr, ku fito kada Faisal ya ƙwace muku Hummy, don jikina ya fara sanyi da al'amarin Faisal, amma bari mujira muji yyh zata kaya a tsakanin su_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/24, 04:59] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* _jin kanta ta ke ta musamman saboda farincikin dake ratsata gata ga Sadauki idanuwan ta raɗau tana kallon kowa. Sadauki ya kasa tantance yanayin da ya ke ciki don bai taɓa shiga irinsa ba. farin-ciki ne ko kuma tausayi? ko dai zuciyar sa ke yaudarar sa akanta?_ _yanzun ma farfesun kifin ta ke ta tsaƙura tana ci tana tunanin ko a wanne hali yanzu ya ke ciki ? kar dai yana cen tare da ƴan iskan mata ? ko kuma yana cen yana shan giya ba, ajjiye hannunta ta yi ta fasa cin kifin hankalin ta amatuƙar tashe. tana son shi, ko ayaya zata iya rayuwa da shi ko da abinda yake aikata wa ya fi haka muni._ _"Jasra kin amince da hakan? kina so na ?" ɗaga kai ta yi tana zabga murmushi. "a a, magana za ki yi." Sadauki ya ce yana jin wani irin ƙwarin gwiwa. "na amince." kasa tsayuwa Madaki ya yi maganarta ta dakar masa zuciya. hakan ya sa ya jinginar da jikinsa da ya ke jinsa tamkar ƙwarangwal saboda tsananin shafal da ya ke jin kansa._ _"kin ga mutumin ki ya zo ko ? yana cen kullum yana tare da mata a gidajen giya kin san garin nan komai na zunubi suna aikata shi, ban san inda ya sauka ba saboda yana tsoron kar na je naga matan da yake mu'amala da su......"._ *ZAIBA! ZAIBA!! ZAIBA!!!* na ƙara ce maku *ZAIBA* ku neme shi ku karanta kar da ku bari a baku labari, rashin karanta shi kuma zai sanya ka yi takaicin hakan. *SHAFI NA 25📑* *__________📖* "me kake so kaji? Bayan kasan kai ɗin yaya nane, akwai abinda ya fi shi girma ne a wurina"? na faɗa bayan na xare hannu na daga na shi ina binshi da kyakkyawan murmushi a fuskana. Juyar da kanshi yayi alaman yayi fushi, "gaskiya ni bazan taɓa amincewa da wannan hukuncin ba, kawai da ne kike ƙanwata da ban ganki ba, amma yanzu nima zuciyata ta amince da miƙa miki ragamar rayuwata, saidai kawai idan baki sona ki fito fili yau ki gaya mun, don bana barin ɗakin nan sai naji abinda ke zuciyar ki game da ni", ya faɗa yana ƙara ɗaura hannun shi saman kafaɗa na, ya kuma ƙura mun idon shi masu masifan haske da kyau akaina. A hankali na sauƙe a jiyar zuciya, sannan na ɗago ido na na dubi Amaal alamar neman a gajinta,... Tsaki taja ta harare ni, "common my friend ki gaya mishi gaskiyan yadda ya ke a mine ɗinki, kawai kina da wanda kukayi alƙawarin aure da shi, wanda sanadin soyayyan da kike mishi ne muka sako shi a rayuwar ki don ya kawo mana a gaji bawai shima ya dawo yace yana sonki ba", ta faɗa tana wani abu kaman zata zo ta yanka mun mari. "Don Allah kibar shirmen da kike yi a wurin, idan ba zaki iya zama a wurin ba ki fita ki bamu wuri, so kam zata soni, me zatayi da mutumin da ya kusa haifanta, kuma bai damu da miƙa mata soyayyan shi gaba ɗaya zuwa gareta ba", yana gama hantarar Amaal ya juyo kaina cikin sassauta murya, "plzz mine kiji dani mana". Ɗaga mishi kaina nayi ba tare da na furta komai ba, sai dai murmushin da bai bar kan fuskana ba nakeyi, "nikan mine ki buɗe baki kimun magana kada zuciyata ta fashe, wallahi ina miki son da zai iya halakani a yau ɗaya, plz kice wani abu mana dear", ya faɗa yana damƙe kafaɗa na da ɗan ƙarfi sosai. "Na amince muyi soyayyah amma bance maka zan aure ka ba, domin nayi alƙawarin auren Dr", na faɗa ina juyar da idona kan Amaal. Mtssss taja tsaki ta kalleni cikin ƙanƙance ido, "wallahi sis babu ruwa na nikan baza ki sakani jin kunyan Dr ba, kuma ke kaɗanki kiyi shirin amsan tuhuma a wurin shi, kada ma ki yadda ki sako ni a ciki, amma kin ban mamaki Hummy, ashe akwai wani sauran ɗa namiji da zai ɗau hankalin bayan idon Dr"? Ta faɗa tana bin mu da kallon banza daga ni har Faisal ɗin. "Get out my friend, ki fita a ɗakin nan ki bamu wuri, ke wacce iriyar ƴar'uwa ce wanda bata kishin nata ɗan'uwan sai wani daban da a sama kika sanshi, kuma kije ɗin itama bazata nemi taimakonki ba, shi ma ya sani wannan flower mai kyaun ae bazai zama ta shi bace shi kaɗai, dole muma mu so ta, Allah ya bawa mai rabo sa'a kawai, fita kibani wuri kafin na tashi nazo inda kike yau kiyi kwana hospital". Kuka Amaal ta fara yi, wanda daga gani na ɓacin raine, tana duban shi tace, "bros don tsabar son kai irin naka na rashin gaskiya shi ne kake fatan ka tashi ka dake ni har nayi kwanan hospital? Wallahi sai na faɗawa Abbu abinda kake shirin yi na rashin amana", sannan ta ƙarasa bakin ƙofan ta riƙe tana kallona tace, "ke kuma idan baki rabu da shi ba sai na gayawa Dr kuma yanzu ma zanje na haɗaki da Ummi, kuma babu ruwa na da ke, bana son ƙawa da ke tunda baki riƙe amana" ta juya ta fita cikin ɓacin rai. "Bros toh kayi haƙuri mu bar wannan maganan, kaga ran Ameel ɗita ya ɓaci, ina tsoron taje ta gayawa Dr Hussain zaiji haushi na, don Allah kayi haƙuri". Yana wani murmushin da ba kai ciki ba yace, "bafa zan taɓa haƙuri ba, domin sonki shi ne rayuwata, kina son ganin bana a raye ne"? Juya kaina nayi alaman a'a, "toh ki bar ni a yadda nake so, mai rabo ya samu cikin mu" ya faɗa yana tashi tsaye. Hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ƙura mun ido bakin shi ɗauke da murmushi, nima ƙura mishi idon nayi domim wani irin kyau Faisal yake mun, ga shi da wani ƙwalisa kaman shi kaɗaine namiji a saudi, murmushi na sakeyi da naga yadda yake wani bina da kallo kaman zai lashe ni, ina kallon yadda yakeyi yasa naji kunya na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsuna. "Ki shiryah da yammah na kaiki yawo kiga wurare, yanzu zanje naci abinci na kwanta na huta ko ƴanmata na", ya faɗa yana fita a ɗakin. Buga ƙofan da ƙarfi ya saka ni ɗago idona da sauri, Amaal ce kaman a wani jehota ta faɗo ɗakin, sai harara ta ke sauƙe mun, tayi kaman zata yi magana kuma sai ta fasa ta juya ta fita ta bar mun ɗakin, ajiyan zuciya na sauƙe ina taɓe baki na ɗaga kafaɗa ta alaman ko a jikina, kallon wayata nakeyi cike da tsoro, ganin number Dr nah da yake yawo a saman screen ɗin, har ya yanke ban iya na ɗaga ba, a karo na biyu wani ƙiran ya sake shigowa, bansan lokacin da naji zufa a jikina ba, chan cikin zuciyata ina raya kodai Amaal ta gaya mishi wani abu ne? har zai yanke shima da ƙyar na ɗaga. "Hello" na iya faɗi ba tare da wani kuzari a jikina ba, daga ɗaya ɓangaren naji shi yana cewa, "yes hello baby, yayah naji voice ɗinki kaman kina bacci na tashe ki"? Da sauri na gyara zama na da muryah na nace, "bansan na fara baccin ba yanzu fah na ɗan kwanta", na faɗa ina jin bugun ƙirjina yana ƙaruwa. "toh ina Amaal ta tafi ta bar mun ke? Nifa idan bazata baki kulawa ba zan taho na ɗauke abuna kawai muje Daddy ya mana aure, don nafi so ni da kaina na dinga baki kula baby, ki gaya mun bata baki kulawa ko"? lokaci ɗaya naji tausayin Dr nah cikin zuciyata, runtse idona nayi sannan nace "lahh Dr na muna tare da uta fa, sai da taga na rufe ido ne inaga ta bar ɗakin, amma Amaal tana bani dukkkan kulan daya kamata har ma ina jin nauyi da kunyan yadda suke mun, ka kwantar da hankalinka babyn baby", na faɗa ina ɗan fitar da muryana don hankalin shi ya kwanta. Ajiyan zuciya ya sauƙe da ɗan ƙarfi, sannan yayi ƙasa da muryah yace, "baby komai na duniyan nan yayi mun zafi, ashe bansani ba mun shaƙu haka? Gaskiya baby na gajji da kaɗaici, next week insha Allahu zan zo na dubaki, idan yaso ko 1week sai nayi mu juya tare, don na gajji wallahi baby, ko ina baya mun daɗi", ya faɗa kaman zaimun kuka. Dariya nayi a hankali nima cikin kewan shi nace, "baby toh ae da sauran hutun mu, kuma inajin daɗin wurin wallahi, kawai kaima kazo mu zauna har sai mun gama hutun tukun mu tafi gaba ɗaya", na faɗa ina dariya. Shima dariyan yayi, "haba baby bakijin kunya dukkanmu muje mu taru musu a gida? ae suma zasu kuremu, nidai zanzo nayi 1week, kuma a hotel zan sauƙa ba a gidan ba". "Baby meyasa bazamu zauna wuri ɗaya ba? Nikan da kai nake son zama baby", na faɗa ina masa kukan sakalci. "idan kina son mu zauna wuri ɗaya ae babu matsalah baby, kawai zanje na gayawa Daddy mun amince aure muke so, sai kawai a ɗaura mana mu zauna a gida ɗaya tunda kema yanzu kina son hakan", ya faɗa yana dariya. Da sauri nace "nifa bance aure zamuyi yanzu ba baby, kawai nafi so mu zauna wuri ɗaya ne dakai", na faɗa ina zaro idona don ganin Faisal daya buɗe ƙofan ɗakin ya shigo. Kai tsaye inda nake zaune ya taho fuskan shi a ɗaure, ni dai zuba mishi ido kawai nayi ina ganin ikon Allah, daga cikin wayan kuma inajin dariyan da Dr nah yake ɓaɓɓakawa, abin tsoro da mamaki kawai jin Faisal nayi ya hau kan gadon ya ɗaura kanshi akan lap ɗina, sannan ya ɗauki ɗayan hannu na ya ɗaura akan shi yana shafa kan nashi da hannuna, kuma ya wani runtse ido kaman maijin bacci, ga wani ɗan ubansun ƙamshin da yake tashi a jikin shi, wanda lokaci ɗaya naji yana sanyaya zuciyata daga bugawan da tafara daga farko. "Baby tunda kina son mu zauna wuri ɗaya ae kawai aure ne ya kamace mu, domin gudun kada Baby yayiwa babyn shi ɓarna, azo ana cewa ba haka aka soba, kinga zance ya lalace *_ƘADDARA TA RIGA FATA_* kenan, wanda ba hakan za a so ba, so kawai muyi haƙuri na zauna a hotel ɗin ko baby nah". kasa bashi amsa nayi saboda yadda Faisal ya saka hannun shi yana ta matsa mun cinyoyina kuma yana mun wani tafiyan tsutsa, runtse ido na nayi bansan lokacin da na sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfi ba, wanda saida Faisal ya buɗe idon shi ya ɗaura su akaina, shi kuma baby daga ɗayan gefen shima ajiyan zuciyan yayi, murya ƙasa-ƙasa yake cewa, "baby ko dai na zo ne kina da buƙatan ganin babyn ki kusa da ke"? kasa bashi amsa nayi saboda maida hankali da nayi kan Faisal domin na ture hannun shi da yake mun yawo da shi akan cinyana, wanda yanzu yake shirin kaiwa kan gwiwa na, kuma lokaci ɗaya naji numfashina yana shirin ɗaukewa, bansan lokacin dana furta, "wayyo don Allah kabari inajin wani iri". Faisal murmushi ya farayi batare da ya daina ba saima ƙoƙarin kai hannun shi kan gwiwa na yakeyi, daga ɗayan ɓangaren kuma cikin wani irin murya mai cike da shauƙi naji Dr yana cewa, "wayyo baby nima abinda nakeji kenan ki daure na samu Daddy ko auren muyi daga baya sai muyi bikin auren yadda kike so", ya faɗa yana sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙarfi. Runtse ido na nayi da ƙarfin don abinda Faisal ya keyi yafara shiga jikina, amma da Allah ya taimakeni kawai sai naji muryan Amaal da ihu tana cewa, "meye haka bros"? Da sauri ya tashi ya zauna ni kuma nayi saurin kashe wayan na ƙura mata ido bayan na miƙe tsaye. _Kallona besty nah miss xerks tayi, cike da damuwa tace, "besty dama ma'anan sunan book ɗin naki kenan yau nake gani a tare da Faisal da Hummy"? Ba tare dana ce mata komai ba na runtse ido na cikin damuwa na cije lips ɗina_ Don Allah ku yi subscribing channal namu da ke dandalin youtube, ku latsa wannan link ɗin. Kar ku manta ku taya mu yaɗawa ga ƴan'uwa da abokan arziƙi. Mun gode. https://www.youtube.com/channel/UCeThSFXe9yNlA2iJA_IAqqA *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/23, 11:52] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 26📑* *__________📖* "Amaal me kike nufi da wannan irin ihun da kikayi? sai kace wani mummunan abu kika samu munayi"? Faisal ya faɗa kaman mai shirin kai mata duka, hankali a tashe Amaal ta dube shi tace, "abu mara kyau kake aikatawa mana bros, saboda Allah Hummy fah amanace a wurin mu, amma duk kabi kana son chanja mata rayuwa, haba bros ka daina abinda kakeyi mana, ba halinka bane fah", ta faɗa idon ta ya ciko da ƙwallah. Jan ƙafana nayi a hankali na ƙara gabanta, duk hankalina a tashe domin tunda na kashe waya Dr yake ta ƙirana amma tsoro ya hanani ɗauka, hannu na saka na riƙo na Amaal murya a hankali nace. "Amaal ba laifin shi bane, laifi nane dana bashi yake zuwa inda nake, kuma bana son na ɓata mishi raine saboda danganta kar ku da shi, amma ki sani bazan taɓa juyawa Dr baya ba, ae soyayyan Dr bata da abokin haɗi a wurina, don Allah kiyi haƙuri kuma bana son maganan nan yaje wurin su Ummi, ya tsaya a tsakanin mu insha Allahu zamu magance komai haka bazai sake faruwa ba",na faɗa nima hawaye yana zuba mun don ganin yadda hankalin Amaal ya tashi. "Hummy na yadda akwai laifinki, amma gaba ɗaya laifin nawa ne dana taho da ke ƙasan mu, yanzu idan wani abu ya faru ne zamu ce da Daddyn ki saboda Allah? don Allah Hummy ki kiyaye bana son wani abu ya faru da rayuwar ki ko kaɗan". Rungumeta nayi inajin wani irin rashin jin daɗi a zuciyata, domin ko babu komai nasan Amaal ta damu da rayuwata, kuma bata son wani mummunan abu ya faru da ni. Mtsss.... Faisal yaja tsaki yabi ta gefen mu ya fita a ɗakin, ɗagu da kaina nayi na dubi hanyar da fita, sannan na dawo da kaina kan Amaal, fuskana cike da damuwa nace, "Amaal bana so ta dalili na ku samu saɓani da ɗan'uwanki, domin nasan irin son da kuke yiwa junan ku, bana so ta dalili na kuka sa samun fahimta, ni kawai naji ma zan koma school", na faɗa ina juyawa zuwa kan bed ɗin. Takowa Amaal tayi tazo ta zauna a kusa dani tana dubana da damuwa ɗauke a fuskanta, "Hummy don Allah kada ki bari faisal ya ɓata mana jin daɗin hutun mu, don wallahi kikace zaki tafi toh nima binki zanyi mu tafi tare, ni in banda neman fitina ma, sainan da 5dys fa ya dawo, amma narasa wani fitinan ne ya dawo dashi daga kammala exams ɗin shi, yawanci yana ƙara wasu kwanaki kafin ya dawo, amma ji don ya zo ya ɓata mana hutun mu sai ya dawo, ni banji daɗi ba, kema hummy ki daina sake mishi fuska, kuma gashi Dr yana ta ƙiranki bakiyi picking call ɗin ba, har ya fara ƙiran nawa, toh yanzu me zamuce mishi bayan yaji ihuna hala". Cikin damuwa nace, "Amaal toh kisan dabaran da zakiyi kada ya fahimci wani abu don Allah", na faɗa ina zaro ido tsabar fargaba. Ɗaukan wayan Amaal tayi, bayan ta amsa mishi sallaman shi naji tana ce mishi, "wallahi na buɗe ƙofa zan shigo kawai na tafi zan faɗi ban sani ba, shiyasa na yi ihu, ina ga anyi mopping wurin bai gogu da kyau ba, kaman da sauran santsin ruwa a wurin, ita kuma hummy sai ta razana ita da Bros Faisal da yake bina a baya, amma ba komai banji ciwo ba kawai naji tsorone", ta faɗa tana maida abun dariya. A jiyan zuciya na sauƙe, ina dubanta fuskana cike da jin daɗin taimakon da tayi mun a wurin Dr. Miƙo mun wayan tayi tana dariya, da sauri na amshi wayan na kai kunne na, ina karɓa naji dariyan Dr yana cewa, "haba baby gaba ɗaya kin ɗaga mun hankali, na ɗauka wani mummunan abu ya same ki ne? Da wallahi saidai na taho babu shiri, don ko takalmi bana sakawa sai nazo naga halin da kike", ya faɗa yana ajiyan zuciyaa, nima ajiyan zuciyan nayi sannan na ƙara ninka wani ƙaryan da cewa, "na ɗauka fa Amaal zata faɗi taji ciwo ne, shiyasa naji tsoro sosai, toh Allah ma kiyaye Faisal yana binta a baya shi ya riƙeta bata faɗi ba". "Gaskiya baby nikan bana son irin wannan tsarin, ta yayah za'ayi ƙato da shi yana shigowa bedroom ɗinku? Gaskiya banji daɗiba don zai dinga kalle mun mata", ya faɗa ranshi a matuƙar ɓace. "Baby kasan fa ɗakin sister shi ne, ni ban isa ina baƙuwa na hana shi shigaba", na faɗa ina ƙasa da murya na. "Baby shima ba escuse bane, ae ɗakin sister nashi yanzu kina ciki, ke yakamata ya dinga shigo miki anyhow ne? ae ko a musulunci ɗakin ita Amaal ɗinma bai kamata ya dinga shigowa yadda ya mishi ba, shiyasa fitinu suka yi yawa a duniyar mun ta yanzu, rape yayi yawa tsakanin ɗan'uwa da ƴar'uwa, ko kuma tsakanin uba da ɗa, nidai bana son jin yana shigowa, don yau ɗaya kinsa naji hankali na yayi matuƙar tashi, kinsa wasu abu da suka wuce shekaru da yawa sun fara dawo mun cikin zuciyata, baby yanzu muna wani irin rayuwa da rape a gida ɗaya yafi faruwa, don Allah ki kula mun da kanki idan wani abu ya faru da ke, wallahi zuciyata zata fashe, don yanzu bazan sake iya ɗaukan abinda ya faru dani a baya ba, wallahi yanzu kam saidai na rasa rayuwa ta bawai nayi nesa da mutane ba, ina kuma zan sake tafiya"? Ya faɗa daga ji hawaye ne yake zuba mishi. "Wayyo baby wani abu ya taɓa faruwa da kai ne irin haka a baya? Don Allah baby kaban tarihin rayuwar ka, don Allah ka gaya mun wani abu kaɗan akan su Ummin ka da ƴan'uwanka, nima inaji a zuciyata zan iya taimaka ma koda da abu kaɗan ne domin hankalinka ya kwanta". Kashe wayan yayi, daga inda yake kuma ya fashe da kuka kaman ba Dr ba, muryah a raunane ya furta, "Baby na damu da ke, bana son wani abu ya faru da rayuwar ki, ni dama ban amince kin tafi ba, inajin tsoron larabawan nan, domi. Sun kowanne irin mazan duniya fitina akan mace, gashi ya ga irin ki mai wuyan samu, wayyo Allah ka tsare mun rayuwar future wife ɗina, Allah uwar ƴaƴanane ka tsare mun ita", ya ƙarasa yana kuka mai zafi, ya juyar da kanshi gefe ya furta a fili, "wayyo Ummi nah, wayyo Abba nah, ko ina ɗan'uwana Hassan da ƴar'uwata Aisha suke? Ko a wani irin ƙuncin rayuwa suke bayan bana nan? Don nasan abinda ya faru da familyn mu, duk zafin da sukaji zasi sake faɗawa wani yanayi bayan kuma sun tashi rana ɗaya sunga bana cikin su, gashi basu san inda nake ba a raye ko amace, wayyo Allah Aunty Hauwa na ko ina ta ke? Ina kakarmu? Gaskiya ina mssn ahalina, dama na yadda da ƙaddara na zauna da su, nasan da yanzu abun ya bar zuciyata, don nasan yanzu sukan sun samu sauƙi akan ni dana kasa mance komai, saboda nayi nesa da duk wani wanda zai kwantar mun da hankali, gashi zasuji tsoron nema na, saboda irin abunda na bar musu na kada su neme ni bayan sun tarar nayi nesa da su, Allah sarki ɗan'uwa na Hassan ko yayi aure? Ko ya tara iyali"? Sai kuma yayi murmushi shi ɗayan domin tona da Hassan idan yayi wanka yana wani taku, Ummi zatace "sai kuma wurin surkuwata ko twin"? Dariya ya keyi yace "haba Ummi gaye da ni wani batun surikuwa kuma, ae sai na cika 30yrs Ummi nah, kedai kimun fata na samu mai kyau da haɗuwa wanda tafi ƴar ki mummunan nan" zai faɗa yana nuna Aisha tsabar neman tsokana, ita kuma bata jiran komai sai ta fashe da kuka domin ta tsani ka dangantata da muni, domin Aisha ji ta keyi duk duniya babu sauran macen da tafita kyau, sai Ummi ta kwantar mata da hankali tace, "kada ki damu ƴata shima bai isa ya ƙira ki da mummuna ba, don kowa nima zai iya ƙirana da mummuna, kuma duk matar da dukkan su zasu aura ƙarya ne su samu wacce ta kaiki ballantana wacce ta fiki, sai dai ƙasa da ke auta na", a haka Ummi ta ke kashe rikicin. Nidai bana ce musu komai sai dai nayita murmushi, domin babu yadda za'ayi a zauna wuri ɗaya Aisha da Hassan basu yi faɗa ba, kuma kullum sai ya saka ta kuka, saidai a barni ko Ummi da aikin lallashi, idan Aunty Hauwa tana nan kuwa ta dinga goyon bayan Hassan kenan, akan sai ya auri wacce tafi Aisha komai da komai, shi yasa Aisha bata cika zuwa kusa da Aunty Hauwa ba, yanzu zakaji kukanta, domin Aunty Hauwa idan ta ga daman saka Aisha kuka sai dai kaji tace mata _CINCIN BREADI_ wai girman jikin Aishan, shi kuma Hassan ya samu abin dariya kenan har sai Aisha tayi kuka faɗan ya ke lafawa. _NI AUNTY NICE SHA RE HAWAYE NA NAYI DON GANIN YADDA DR YAKE SHA RE HAWAYE KUMA YANA SMILLING, GA DUKKAN ALAMU YANA MSSN ƳAN GIDAN SU SOSAI._ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/28, 15:44] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°* *1441H/2020M.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_ ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* ```RIGIJI GABJI.``` *SHIN KE/KAI KUN TAƁA TSINTAR KAN KU CIKIN ƘANGI NA RAYUWA KAMAR HAKA:* *MUTASIM ya taso bai san su wane iyayen sa ba, be san wane shi ba, be kuma san dangin sa ba, ya tsinci kansa yana rayuwa ne shi ɗaya cikin ƙunci da wahala, Allah shine gatan sa, Mutane na ƙyamar sa, babu wani mai raɓar sa, ba shi da muhalli ba bu makwanci, ba shi da cin yau bare na gobe, talauci, damuwa, gararin rayuwa.* ```KWATSAM!``` *Ta shigo rayuwar sa, ta tausaya masa, taji ƙansa, ta taimaka masa, ta bashi Muhalli da makwanci, ta ba shi ci da sha, suka shaƙu, bata barin sa da damuwa, farinciki da walwala su ka yi masa maraba.* ```KWATSAM.``` *Soyayya mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin su, ƙauna ce zazzafa suke yiwa junan su, idan ba bu ita ba zai rayuwa ba, idan babu shi ba zata rayuwa ba, farin cikin ɗaya baya samuwa sai dana ɗaya, tayi kuka, ya yi kuka, tayi dariya, ya yi dariya, suka yi nisa a so da ƙaunar juna, burin su kasancewa a inuwa guda ɗaya, maganar aure ta shiga tsakani, a ranar ɗaurin aure.* ```KWATSAM!!!.``` *wani murɗaɗɗan AL'AMARI ya faru, aka shiga alhini, tashin hankali, damuwa ta zama sabuwa, farinciki yay ƙaura.* ```SHIN ME KUKE TUNANIN YA FARU? ME ZAI FARU? YA ABIN YA KE?.``` Read Out... *MUƘADDARI! MUƘADDARI!! MUƘADDARI!!!* Mallaki NAKI ko NAKA ta wannan hanya👇🏼 _Tura ₦200 a cikin ɗayan wannan account numbers ɗin 2209854592[ZENITH] & 0005151981[JA'IZ]._ _Ko kuma ɗaukar hoton katin waya na ETISALAT or MTN, transfer ko kuma VTU._ _Aika da shedar biya a yayin da aka yi screeshot ta ɗaya daga cikin wannan numbobin whatsapp ɗin 09066828184 & 08164475119._ *Kada ka bari, kuma kema ka da ki bari a baku labari.* *SHAFI NA 27📑* *__________📖* Amaal ce ta shigo ta sa me ni nayi nisa cikin tunani, maka mun duka tayi a lap ɗina tana hararana da wasa tace, "a haka kaman kina son Dr, amma kuma ƙasan zuciyar ki tsantsan yaudara ne". Tashi na yi zaune ina sosa inda ta maka mun marin nace, "amma kina aikata babban saɓo Amaal, ni kike gayawa bana son Dr? to ki gaggauta zuwa ki kuskure bakin ki a toilet, don kin yi mun babban laifi wanda ya kai na miki hukunci". tashi nayi na miƙa mata hannuna alaman ta riƙe ni na miƙe tsaye. Hararana tayi ta neme wuri ta zauna, "gaskiya Hummy ki daina kula Faisal, ni na haɗa ku ne don Dr ya razana ya ƙara baki muhimmanci, yasan ba shi kaɗai bane, amma ki kuma sai kina son wuce gona da iri, gaskiya ki canja tsari". ta faɗa kaman za tayi kuka. Dariya nayi mai ɗan sauti, "Amaal wallahi bana tunanin akwai wani namiji da zai juyar mun da hankalina akan Dr, babu shi saboda haka kima manta da maganan Faisal, zan kula da wannan". Faisal gaba ɗaya ya saka na daina zaman cikin ɗaki, saboda babu hali nayi wasu mintuna zaka ganshi ya shigo, kuma babu inda yake dusa sai kan bed inda nake zaune ko nake kwance, ganin haka da yake yi naji duk hutun ya fita mun a rai, saboda haka kullum ba zaka rasa ni a kitchen wurin Ummi da masu aikin gidan ba, ko kuma ina parlor ko ɗakin Ummi, abin haushi kuma babu hali yaga ina waya da Dr zai fara ƙoƙarin kai hannun shi jikina, ni kuma idan naga haka na gwammace na kashe wayan na bar wurin, wanda hakan yake saka ran Dr nah yana ɓaci. Ranan da Faisal yayi 3weeks da zuwa Ummi ta fara mishi maganan komawan shi school, amma firr yaron nan ya ƙafe shi bazai tafi ba sai ranan da zamu tafi. "Kasan dai hutunka ya ƙare, su kuma sauran 1week, to ina ruwan ka da zaman su ne kam Faisal?". Ummi ta faɗa tana duban shi. "Ummi gaskiya ni na gaya miki auren Hummy nake sonyi, to ya ya za'ayi nabarta ita kaɗai ni kuma na tafi? gaskiya ni sai ranan da zasu tafi tukun na tafi". ya faɗa da wani yanayin shahwaɓa. "Hmmm ka gamu da wahala wallahi, na gaya maka Humaira akwai wanda ta ke so, me yasa kake da son haɗa fitinane? kawai ka kama hanyar komawa ko na haɗa ka da Abbu". Ummi ta faɗa tana binshi da harara. Dariya ya yi ya tashi ya fita a ɗakin, yabar Ummi da mamakin yaushe Faisal ya canja hali haka ne wai kam?. "Baby mai kake so na shirya maka? Kasan daɗin da nake ji kuwa yau?". na faɗa mishi cike da jin daɗin wai gobe zai zo, idan munyi 5dys sai mu juya tare da shi, shi dai bai faɗa mun abinda yake so ba sai dariya na da yake ta yi. Ranan tun safe Ummi ta saka mu tashi muka fara aikin abinci domin zuwan Dr, ni dai banda farin ciki babu abinda na keji, sai snacks muke ta haɗawa iri da kala, wasu bamu soyawa ake saka su kawai a friedge, ga wani ƙaton cake da Amaal tayi baking ɗinshi, yayi matuƙar kyau sosai an rubuta sunan shi a jiki, ni dai sai farin ciki kawai na keyi. Driver ne ya ɗauke mu nida Amaal domin tafiya taryo Dr, lokacin da mukayi ido biyu da shi sai da naji gaba na ya faɗi, domin ganin irin raman da yayi, amma ya yi kyau sosai, tsabar farin ciki bansan lokacin da na tafi da gudu na rungume shi ba, shima tsabar murnan ganina rungume ni yayi ƙamƙam a jikin shi, ita kuwa Amaal tana tsaye a inda ta ke sai murmushi ta keyi cike da tausayin mu, don daga ganin mu kaman mun shekara dayawa ba muga juna ba. Da ƙyar ya iya ɗago da fuskana yana murmushi domin ganin murnan da nake yi ya koma zuban hawaye, yana goge mun hawayen yana fitar da na shi, murya a hankali yace, "to ba gani nan na zo ba, kiyi shiru ana kallon mu fa, kada wata ta balarabiya ta ƙyasa miki babyn ki". ya faɗa yana sauƙe hancin shi kan nawa. Buga ƙirjin shi nayi da ɗan ƙarfi nace, "ni kan babu mai sonka sai ni ɗaya, kuma kai baby nane ni kadai, baby naji daɗi dana ganka, nayi mssn ɗin ka sosai". shi dai murmushi yake tayi yana matsamun kafaɗa na bayan ya ɗaga idon shi daga kaina ya dubi Amaal wanda tayi saurin share hawayenta, tana murmushi ta ƙara so inda muke tsaye. Bag ɗin hannun shi ta karɓa, tana mishi sannu da zuwa, shima miƙa mata yayi yana tambayanta ya ya su Ummi? Bayan sun ɗan gaisa ne yana riƙe da hannu na muka wuce wurin motan. Gaskiya su Ummi sun yi mishi kyakkyawan tarya, daga Ummi har Abbu sun nuna jin daɗin zuwan Dr, bayan ya huta yaci abinci, sai ya gaya musu zaije ya nemi masauƙi, duk yadda su Ummi suka yi dashi ya zauna anan gidan firr ya ki amincewa, babu yadda suka iya haka suka barshi driver ya kai shi wani hotel da yake kusa da gidan su, banji daɗin ƙin zaman da yayi ba, amma da muka fito domin yi mishi rakiya, yana riƙe da hannuna muna tsaye a jikin motan ya ƙura mun ido, don sai wani shagwaɓa nake ta sauƙe mishi akan banji daɗin ƙin sauƙan da yayi anan ba. shi dai dariya kawai yake yi baice mun komai ba, can sai ga Faisal ya fito daga side ɗin shi, tunda ya ganmu tsaye da Dr ya wani ja birki yana kallon mu cike da mamaki, ganin haka ya saka Dr ya ƙara riƙe hannu na gam. Tafiya kaɗan Faisal yayi ya iso inda muke tsaye, ina tunanin zai wuce amma kawai sai yaja ya tsaya yana bin Dr da kallon banza, "Me ya fito da ke waje wurin wani bayan kin san ina sonki?". ya faɗa yana ƙoƙarin saka hannu ya jawo ni. Murmushi Dr ya yi ya maida ni ta ɗayan side ɗinshi ya rungume ni sosai a jikin shi, nima da sauri na saka hannuna duka biyu na rungume shi, hannu Dr ya miƙa mishi alaman su gaisa, amma Faisal tsaki yaja mishi yana duban idon Dr yace. "Yayah zaka shigo har gidan iyaye na kuma ka rungume matar da zan aura a gaban ido na? Kasan duk wani abinda na maka kai kajawo". *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [7/29, 20:10] Miss Xerks🌺: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     *SHAWWAL/JUNE.* ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_          ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 28📑* *__________📖* "Yayah zaka shigo har gidan iyayena kuma ka rungume matar da zan aura a gaban ido na? Kasan duk wani abinda na maka kai kajawo". Murmushi duk na ya sake yi yana duban Faisal da ya koma kaman wani ɗan ta'adda, sai wani zare ido yakeyi kaman tsohon maye, "saurayi kayi haƙuri nazo har ƙofsn gidan mahaifinka ina ɓata maka rai, very sorry ƙanina ban so hakan ba, matsalan da aka samu na biyo wife ɗinane, amma babu komai zamu kiyaye", Dr ya ƙarasa faɗa yana ta zuba smilling yana kallon idona. Ban shiryah ba nima na samu kaina da maida mishi martanin murmushin, wanda gaba ɗaya muka maida Faisal kaman wani gunki a tsaye a kanmu, ranshi a matuƙar ɓace yaja tsaki ya wuce cikin gidan yana ta wasu ƙananun surutai wanda bamu jin abinda yake faɗi. Dawo dani gaban shi Dr yayi yana duban cikin idona, cikin nuna mun zallan so da ƙauna yace, "Baby nah don Allah ki kula mun da kanki, kinsan dai yaran larabawa ba kirki bane da su akan mace, saboda haka don Allah ki maida hankali da yaron nan, don akwai rawan kai na yarinta a kanshi sosai". Murmushi nayi ina mai ƙara damƙe hannun shi nace, Dr nah baka da matsalah da wannan, insha Allahu zan kiyaye babu abinda zai faru da yardar Allah, nidai kawai bana son wulaƙanta shi ne bayan nazo gidan su". "Toh ce mishi akayi kema baku da gida? Yasan ae kin wuce sa'ar shi a maganan soyayyah amma banda rawan kai irin na yara zai wani tsaya cike da rashin kunya a gaba na ko? Toh ya maida hankalin shi kan karatu yabar masu abu da abinsu", ya faɗa yana kanne mun ido ɗaya, "baby kinga abunda nake gudu da sauƙa a gidan nan ko? Yanzu yaron nan da anan na sauƙa zai dawo yana mun rashin kunya na kwana a gidan su ina mishi hira da mata, while kuma matar tawa ce". Murmushi nayi na sake hannun shi, marairecewa yayi shi ba zai tafi ya bar ni ba, da ƙyar na sha kanshi mukayi sallama na dawo ciki. A parlor na same su suna zaune dukkan su, daga Abbu har Ummi suma suna zaune, gefe ɗaya kuma Amaal ce zaune a kusa da Ummo, chan kan dinning kuma rasa kunya ne yake cin abinci. Zuwa nayi kusa da Amaal na zauna ina duba abinda ta keyi cikin wayanta, murmushi tayi ta ɗago mun screen ɗin wayan don naga abinda ta keyi, "abinda kika fita yi nima shi nakeyi daga nan magulmaciya", ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda ba mai jin mu tana dariya. Nima dariyan nayi na sunkuyo dai-dai kunnen ta nace, "naku salon ba irin namu bane, mu bamu kwaikwayo amma ke gashi kinayi". Hararana tayi tace, "me na kwaikwaiya ƴar rainin wayo"? Dariya nayi ina buge bayan ta nace, "dubi abinda yake kan screen ɗinki kiga yadda kika kwaikwaye mu nida Baby". "Toh mayun soyayyah an kwaikwaya ɗin, tashi ma a kusa dani ki dena ƙare mana tanadi". Ummi ce ta dube mu fuskan ta ɗauke da murmushi tace, "sirrin me kukeyi ne ƴanmata nah"? Dariya nayi na ƙara sa gefen Ummi na zauna a ƙasa kusa da ƙafanta ina dariya nace, "Ummi kwaikwayon mu da Dr suke yi, yanzu naga ta tura mishi txt wai baby nah me kake yi? Bayan salon mu ta kwaikwaya", na faɗa ina ɗaura kaina akan cinyan Ummi ina dariyan Amaal da ta buɗe baki tana kallona. "Ashe Hummy har yanzu kina nan da halin ki na kwafsi? Toh wallahi idan kin wasa kema zan faɗi abinda kike turawa Dr". Abbu ne ya kalle mu yace, "yau kuma fallashe-fallashe akeyi a gidan nan ko?" sannan ya dubi Faisal da yake ta howa yace, "kaima kazo kaji tonan asiri da ƙannen ka suke yi, kaima kazo muji ko sun san naka", Abbu ya ƙarasa da murmushi a fuskar shi. Ya mutsa fuska Faisal yayi yana turo baki yace, "Abbu ae ni Humairah nake so, amma naga wani hali da sis Amaal ta ke nuna mun akan wani chan daban", ya faɗa yana hararan Amaal, gefe na yazo ya zauna kusa da ɗayan ƙafan Ummi. "Amma baka da hankali ne son? Yarinyar da ta ke da wanda ta ke so, yasan mu, muka san shi zaka ɓullo da wani shiririta kuma? Kai kan ae matar ka bata wuce ss1 ba a secondry, saboda haka kada na ƙara jin wannan shirmen a bakin ka daga yau", Abbu ya faɗa cike da ɓacin rai. "Gaya mishi dai Abbu don na lura Faisal yana son ya chan ja halayen shi masu kyau da muka san shi dasu zai kwaso wasu, kuma hakan ba dai-dai bane, da wani ido Dr zai kalle mu? Wands basu san alƙawari da amana ba? Faisal sai wani ƙara tamƙe fuska ya keyi yana hararan Amaal a fakaice, wanda ita kuma sai murmushin iya yi ta keyi, nidai kasa ɗaga ido nayi na dubi kowa, wasa kawai da yatsuna nake tayi, domin koma meye Faisal ya ban tausayi, domin ganin yadda kowa ya nuna mishi bai kyauta ba sai yaban tausayi. "Humairah bana son ki bar yaron nan ya shiga rayuwar ki, domin bazan ji daɗi ba idan Dr ya fahimci da akwai shirmen Faisal na cewa yana sonki, zanji kunya don zai ganni ƙaramin mutum, na ɗauko ki na kawo gidana, ɗana kuma yana nemanki, gaskiya bazan so faruwar haka ba, kaima ka kiyaye kana jina ko Faisal"? Abbu ya faɗa cike da ɓacin rai. Amsawa a hankali Faisal yayi cike da jin haushi, bai kuma ɗau wani lokaci ba ya tashi yayi sallama da jowa ya wuce ya bar parlon. Ummi ce ta bishi da kallo fuskanta ɗauke da murmushi tace, "in banda rikici irin na Faisal ina zai kai Hummy? Kawai neman kada a zauna lafiya ne", Abbu ya harari ƙofan da yabi yace, "shiririta dai irin na yara, amma ae Humairah ba sa'ar shi bace". Dariya Amaal ta kwashe da shi tana kallon Abbu tace, "Abbu sai kaga irin hararan da ya bini da shi, kuma ina ganin sai da ya ta ke hannun Hummy kafin ya bar wurin, amma ta yi wani shiru bata ce komai ba, da nine kan ae sai gadon asibiti", ta ƙarisa faɗi tana dariya. Kowa a parlon dariya ya fara Ummi tana duba na tace, "doug kodai kina son shine kada muyi shishshigi"? Dariya nayi na sunne kaina akan cinyan Ummi . "Ta isa tace tana son wani bayan Dr", inji Abbu. "ae sai na ɗaura auren gobe naga yadda zata saurari wani, shima Faisal rikici ne ae". Hutun mu tare da Dr yamana daɗi sosai, don kullum sai yazo ya fita damu, mune zuwa shan ice-cream, mune zuwa nan mall ɗin miyi shooping, wataran muje park mu zauna ayita shan soyayyah, gaba ɗaya rayuwar sai naji ban taɓa jin daɗi irin na wannan lokacin ba, a haka har hutun mu ya ƙare, a na saura 2dys mutafi, shi kuma Faisal ranan ya koma school, lokacin da zai tafi ya shigo har ɗakin Amaal, dai-dai lokacin na fito daga waka ɗaure da towel a jikina. Faisal yana shigowa ya tsaya ya ƙura mun ido, ganin kallon na shi bana ƙare bane jikina a ɗan firgice nace, "kana neman Amaal ne"?. Ina jiran naji amsan da zai bani amma sai naga ya maida ƙofan ya rufe ya kuma murɗa key ɗin ɗakin. Wani irin mummunan faɗuwar gaba naji ya zo mun, wanda har sai da naji kaman wani guntun fitsari ya ɗigo mun, jikina yana rawa na sake tambayan shi, "Amaal kake nema ne bros"? Munafukin murmushi yayi yana matsowa inda nake tsaye yace, "wurinki nazo muyi sallaman da kowa bazai taɓa mancewa da ɗan'uwan shi ba har ƙarshen rayuwar shi, kuma ina so yau ki yadda dani kika dace ba wannan tsohon ba". Juyawa nayi da sauri zan koma cikin toilet ɗin, amma sai naji charaf ya chafke ni. Ban san lokacin da zunduma wani uban ihu ba iya ƙarfina. _Ni Aunty Nice nima sai da naji zuciyata zata buga domin jin irin ihun da Humairah tayi, wanda sai danaji shi har cikin ƙwaƙwalwata, wanda naji typing ɗin ma yana neman gagara na, don ni kaina na razana da Faisal, amma kada ku gajjiya da alƙalamin Aunty nice, ku jiraye ni zuwa bayan sallah idan Allah ya kaimu da rai da lafiya, kuma kada kumanta da naman sallah, kowa ta ƙullah mun na bawa Babyn Baby._ *©AUNTY NICE•*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/6, 12:11] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *MISS XERKS (BESTY NAH)* *AISHA ALIYU GARKUWA* *UMMI GARKUWA (ZAIBAI)* *SADNAF* *NABILA RABI'U ZANGO* *MAIDAMBU* *KHALISAT HYDAR* wannan shafin nakune domin kuɗin daban ne a cikin duniyan marubuta, kunmun alkhairin da baki bazai iya furta kalman godiya ba, hannu bazai iya rubutawa ba, har abada godiyata da girmama *AL'AMARIN* ku bazan gajiya ba, *NAGODE!* *NAGODE!!* *NAGODE!!!* Allah ya kare mun ko da zuri'an ku duniya da lahira *SHAFI NA 29📑* *__________📖* Da sauri Faisal ya sakeni yana duba na a razane, domin shima ba ƙaramin razana yayi ba da jin irin ihun dana yi, ƙura mun ido yayi shi kanshi jikin shi rawa yakeyi, dai-dai nan mukaji buga ƙofa da ƙarfi. A razane ya juya yana kallon ƙofan, domin jin muryan Ummi da Abbu, ta ɗayan gefen kuma Amaal ce ke ta faɗin, "sis Hummy ki buɗe ƙofan, mai ya sameki ne"? Da ƙarfinta ta ke ƙirana, ni kuma ganin hankalin mugun yayi jikin ƙofan, sai nayi wuff na faɗa toilet da danna key a jikin ƙofan, bansan lokacin da na furta "wayyo Dr nah, wayyo Daddy nah kuzo kada ya cuceni don Allah, kuzo ku fitar dani a cikin gidan", da ƙarfina nake faɗi ina wani irin kuka kaman raina zai fita, don idan kun gani alokacin sai kunyi tunanin ko mutuwa aka mun. Amaal ko da taji kuka na, gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa tana duban iyayenta tace,"Ummi kuyi wani abu mana, bros ne hala a ciki, Ummi kada ya cutar da ita fah", ta faɗa tana zubar da hawaye. Jin haka ya saka Ummi ɗaga murya da ƙarfi tana ƙiran sunan Faisal, "Faisal ka buɗe ƙofan nan kuma kabar yarinyar nan, wallahi ka yadda wani abu ya sameta ban yafe maka nono na da kasha ba, banyafe maka ba Faisal" ta ƙarisa faɗin kalmarta tana kifa kanta jikin Abbu tana kuka, cikin ɓacin rai Abbu ya sake buga ƙofan da ƙarfi yace, "idan baka buɗe ba Faisal yanzu zan ƙira securities su buɗe ƙofan kuma a tafi da kai a matsayin mai raping, kuma kasan irin hukuncin da ƙasan nan zata yanke maka, secondly kuma zan yafe ka cikin ƴaƴa na. Daga jin abin da Abbu ya faɗi Faisal da sauri yazo ya buɗe ƙofan jikin shi yana rawa, da sauri Ummi ta saka hannu ta wanke shi da kyakkyawan marin da sai dayayi namijin gaske kafin ya iya tsayawa da ƙafan shi, bai samu azaban ya sake shiba yaji sauƙan wasu tagwayen mari a fuskar shi, wanda da ƙyar ya samu nutsuwan gane daga inda suka fito, basu ankara ba kuma suka ga jini ya fara biyo hancin shi, saboda tsananin azaban mari, da ƙyar ya ɗaga kanshi ya dubi Abbu da yake wani irin hakki kaman zuciyar shi zai faɗo, da ƙarfi ya furta, "me kayiwa ƴar mutane Faisal? Na rantse da Allah idan ka cutar da ita zanyi shari'a da kai kuma zaka nisanta dani har abadan, shin kasan yarinyar Amana ce kowa a hannun mu? Kasan yadda Mahaifinta yake jaddada mun riƙon amanan ta? Kaico da hali irin naka Faisal", Abbu ya faɗa yana ƙara wanke shi da mari. Muryan Dr sukaji daga bayan su yana tambayan, "Don Allah ina Aisha Humairan? Fatan dai bai mata komai ba"? Ya faɗa duk illahirin jikin shi yana rawa, suma cikin mamako suke kallon shi, don basu san da shigowan shi ba, domin yayi sallama ya shigo suna gaisawa suka jiyo ihun Hummy, kuma sun manta da shi a wurin suka taho sama. Amaal ce jikin ƙofan toilet ɗin tana ta bugawa tana ƙiran sunan hummy akan ta buɗe mata, ganin haka yasa Dr shigowa har inda Amaal ta ke ya jinguno da ƙofan muryan shi kaman zaiyi kuka yace, "Baby nah! Baby na ki buɗe mun ƙofan kada na shiga wani hali, ki buɗe na tabbatar da babu abinda ya sameki kafin numfashina ya ƙaurace mun", ya faɗa duk dauriyar sa sai da hawaye ya zubu mishi. Buɗe ƙofan nayi jikina yana kan rawa har lokacin, ga hawaye na kaman zasu ƙare a wannan ranan, ina kallon su bansan lokacin dana faɗa ƙirjin Dr na ba na sake wani irin kukan da bansan daga inda yaxo ba, muryata na rawa nace, "Dr na tsoron shi nakeji, nikan kamayar dani wurin Daddy na, tsoro nakeji Dr na". Da sauri ya kankame ni a ƙirjin shi, jikinshi yana rawa yake cewa, "Baby bai miki komai ba ko? Baby nah bazai miko komai ba insha Allah, kiyi shiru zan tafi da ke", ina ƙara kankame shi ina kuma ƙara sautin kuka na nace, "Baby ya razana ni, ya bani tsoro, tsoron shi nakeji, ka gudu da ni, baby ina sonka kai ɗaya bana so ya mun wani abu ka tafi dani baby nah, na yadda kai kaɗai kake sona baka da niyyan cutar da ni". Kuka Amaal ta keyi kaman zata shiɗe, da sauri Ummi ta ƙaraso ta riƙeta tana faɗin kiyi shiru Amaal insha Allahu wani abu bazai taɓa faruwa da Hummyn ki ba mara kyau, kiyi shiru kada ciwonki ya tashi, da sauri na ɗago kaina daga ƙirjin baby nah, na ƙurawa Ummi ido, ganin ta juyo tana kallo na nayi sairi na tafi jikinta na rungumeta ina kuka, muryah a hankali tace, "babu komai doughter babi abinda zai faru dake insha Allahu, ki kwantar da hankalin ki kibar kuka, fatan dai bai miki komai ba"? Ta faɗa tana ɗago ni daga jikinta, ɗaga mata kaina nayi alaman ehh, sannan ta dubeni tace Amaal ta jirani mu shiryah sai mu same su a parloon ƙasa. Dr yana bina da kallo da ƙyar yabi bayan su Ummi suka sauƙa ƙasa, ni kuma Amaal tazo ta rungume ni tana kuka, dukkan mu kukan muka saka muna rungume da juna, da ƙyar ta lallaɓa ni muka je na wanke idona, duk yadda tayi dani na shafa mai kasawa nayi, kawai wani dogon rigan atamfah na batik ta ɗauko mun acikin kayana na saka, da ƙyar na yadda ta shafa mun wasu turaruka a jikina, na ɗauki wani ƙaramin gyale green mahaɗin rigan na yafa shi akaina. A parlor muna zuwa naga Faisal zaune a ƙasa wurin ƙafan Abbu, ɗayan gefen kuma Dr nane a zaune ya sunkuyar da kanshi ƙasa, Ummi kuma tana gefe kusa da Abbu suna zaune wuri ɗaya, shigowan mune ya saka dukkansu suka ɗago da kansu suna kallon mu, tsayawa nayi na kasa cigaba da tafiyan domin ganin Faisal zaune a wurin. Ummi ce ta miƙo mun hanni alaman nazo wurinta, amma ganin Faisal kusa da su yasakani kallonta ban ƙarasa ba, idona na juya gefen da Dr yake zaune naga shima ido ya ƙura mun, kawai bansan yyh akayi ba kawai sai na samu kaina da tafiya inda yake, na zauna kusa da shi na takura sosai a jikin shi, kaman wani zaizo ya taɓa ni nake ji, lokaci ɗaya naji Dr yayi ajiyan zuciya, sannan ya saka hannunshi ya riƙe ni gam ajikin shi, shima a lokacin idan ka dube shi sai kaji kaman kayi kuka, domin gaba ɗaya a wani firgice yake. Amaal ce ganin haka ta juya ta harari Faisal, murya a raunane tace, "Ummi Hummy na tsoron shi ta ke ji , kice ya bar wurin bazata iya zuwa wurinki ba", ta faɗa tana share hawayenta. Ummi ta miƙa mata hanni alaman tazo, haka Amaal ta ƙarasa ta kwanta gaba ɗaya a jikin Ummi, shi kuma Abbu yayi murmushi ya dubi Amaal yace, "ki barta a wurin Dr ta, yau inaga idan ba Daddyn ta ba toh babu inda zata samu nutsuwa idan ba wurin Dr ba, a razane ta ke sosai" ya faɗa yana dawo da kallon shi kanmu, nidai ban iya yin komai ba sai na ƙara matsawa jikin Baby sosai, har ina jin yadda jikin shi yake ta rawa, da sauri na ɗago kaina na dube shi, ganin ya ƙurawa Faisal ido kuma jikin shi sai rawa yakeyi, sai naji ya bani tausayi, a hankali na furta, "baby nah kayi haƙuri", muryana ya fita a hankali kuma yana rawa, dawo da duban shi yayi kaina, sai naga hawaye suna zuba a idon shi babu kakkautawa, bakinshi har rawa yakeyi yace, "baby tsoro nakeji a cikin zuciyata, bana so tarihi ya sake maimaita kanshi akaina, ina tsoro sosai baby", sannan ya juya ya dubi Abbu jikin shi yana rawa yace, "Abbu ka ƙira Daddynta kace yazo yau ya ɗaura mana aure, wallahi idan wani abu ya fari da Humairah bazan taɓa yafewa kowa ba, wallahi wannan karon zan ɗauki doka a hannuna, ina sonta sosai bazan iya barinta wa kowa ba, meyasa kullum saini? Me yasa kullum sai abinda nafi so? Wayyo Mama na! Wayyo Babana", ya faɗa yana sauƙowa ƙasa inda nake zaune ya saka dukkan hannayen shi ya rungume ne dasu, kanshi ya ɗaura akan wuyana, muryan shi na rawa yace, "Baby kinsan ina sonki, idan wani ya sameki mutuwa zanyi, kinsan me yafaru dani abaya? Kinsan me ya baroni da family nah? Kinsan zafin danaji na rabuwa dasu da abinda nake so da akayi raping ɗinta? Kinsan gararin da rayuwata ta shiga ta dalilin wancan mummunan ƙaddaran? Toh yanzu kam mutuwa zanyi wani ya yi gangancin cutar mun dake, don ban taɓa jin irin son da nake miki ba akan kowa", a hankali ya sake ni ya matsa a kusa dani ya ɗaga hannayen sama hawaye suna zuba a cikin idon shi yace, "Astagfirullah! Astagfirullah!! Astagfirullah!!! Allah na tuba, Allah don girman zatinka, don tsarkakayen sunayenka guda chasa'in da tara, don darajan wanda ka fifita fiye da kowa da komai, babban masoyinka annabin rahma, kayi mun maganin abinda ke faruwa dani da abinda dake faruwa da rayuwata, kaine masanin sirrin sarari dana ɓoye, nasan kafini sanin halin da nake ciki, da abinda ke faruwa dani,, Allah ka dubani da idon rahma kaji ƙaina ka sassauta mun abinda ke damuna, Allah kaine mabuwayi babu abin bautawa da gaskiya sai kai, a gareka na dogara, kaine mai kawar da baƙin ciki, mai yaye ɓacin rai, mai amsan addu'ar mabuƙata, Allah ka tsare mana gaban mu da bayan mu, Allah ka kare mu da aikata zina da ƙuwaɗi da maɗigo, damu da ƴaƴa yenmu da na ƴan uwanmu, ka nisan tamu da aikata shi, Allah ka kare mun wannan baiwa taka, ka tsare mun ita daga dukkan sharrin masharrata, Allah ka kawo mun nutsuwa a zuciyata, Allah ka kare dukkan musulmai gaba ki ɗaya", yana gamawa ya sunkuyar da kanshi ƙasa hawaye yana bin fuskan shi. Hawaye Ummi ta share, tana duban mu cike da tausayi tace, "Abbu inaga ya kamata ka ƙira Daddyn tan, don bansan yayah Dr yakeji ba a ranshi, amma a matsayina na uwa nasan da ciwo a rayuwar shi, yakamata a hanzarta mallaka mishi Hummy", ta faɗa tana ƙara rungume Amaal da take ta zubda hawaye. Hmmm abin tausayi hattah Faisal kuka yakeyi, yana duban Dr yace, "don Allah Dr ka yafe mun, wallahi sharrin sheɗan ne, ni wallahi ban taɓa zina ba, kuma ban taɓa kusan tan shi ba, kawai sheɗanne yau yaso ya buga mun gangan shi, kuma Allah ya kare ni, wallahi dama a razane nake, na gode Allah kuma da kukazo, domin ni kuka taimaka, kuma nayi alƙawari ba Humairah ba ni ko waccce mace ma a duniya zan kiyaye kaina daga gareta, domin gudun faɗawa mummunan ƙaddara", sannan ya riƙo hannun Abbu yana kuka yace. "Abbu don Allah ku yafe mun wallahi nayi nadama tsakanina da Allah, kuma bazan taɓa maimaita hakan ba, kuyi haƙuri naci amanar tarbiyar dakuka daɗe kuna mun, wallahi wani abokina ne nagaya mishi yadda ake ciki, shi ne yace idan nayi raping ɗinta dole za a haƙura abarni na aureta, amma wallahi nayi nadama bazan sake aikatawa ba". Yana kuka ya ƙara sa gaban Ummi, riƙo hannunta yayi zaiyi magana amma sai ya kasa, domin ganin irin kukan da Ummi da Amaal sukeyi, kawai sai ya rungume su duka yana faɗin, "Ummi nah, Ummi nah ki daina mun kuka kada Allah yayi fushi dani, na tuba Ummi na", ɗagowa Ummi tayi tana shafa kanshi tace, "na yafe maka Faisal kuma nayi imani da Allah ba halinka bane na yadda sharrin shaiɗanun abokaine yake wasa da rayuwar ka, kuma na raba ka da wannan abokin, na kuma raba ka da hidiman mace idan ba ka tashi aure bane, ni ina kuka domin tausayawa Dr ne, amma bana zubar maka hawaye, domin ina addu'an Allah yasa ku gama damu lafiya, ku gama da duniya lafiya". Gyaran murya Abbu yayi, kowan mu sai da ya ɗaga ido ya ƙura mishi, jiki a sanyaye Abbu ya saka tissue ya sha re hawayen dayake ta biyo kan kyakkyawan fuskar shi, a hankali ya dube mu gaba ɗayan mu, sannan ya sauƙe idon shi akan Faisal yace, "Ɗana Allah ya kare mun ku daga sharrin abokai da rayuwa, kuma ni bazan ce na yafe maka ba har sai naga hummy ta bar gidan nan lafiya, kuma ina mai ƙara jan hankalinku daku ji tsoron Allah a duk inda kuke, kuma kada kayi tunanin cewa aboki ya sakaka a abu, toh wallahi ranan lahira Allah zai maka hukunci da abinda ka aikata, bawai za ace a barka ba saboda kai abokine ya saka ka, shiyasa ake so ayi abota dana gari, kuma wallahi duk inda kake kasa ka tsoron Allah a zuciyar ka, babu abinda yake cikin zina sai masifa da azaba, kuma sai anrama kaima akanka watarana", sannan Abbu ya dubi Ummi yace, "Muma muna da laifi domin mun bar Faisal yana shiga ɓangaren Amaal kaman ɓangaren namiji ɗan'uwan shi, kuma hakan babban kuskure ne, shiyasa yanxu alfasha yayi yawa ko acikin ƴan'uwa ma, amma insha Allahi daga yau nayi duba da kuskuren mu, daga yau Faisal ka tsaya iyaka naka ɓangaren sai kuma nan parlor, amma bana so ka ƙara zuwa ɗakin Amaal, kema Amaal ban yadda kije ɓangaren shi ba daga yau, sai kuma mu nemi yafiya a wurin ubangiji". Dawo da kallon shi yayi kaina yace "Humairah kiyi haƙuri, bansan haka zai faru ba amma duk da haka kiyi haƙuri insha Allahu zamu ƙara saka ido akai", sannan ya dubi Dr yace, "kai ma kayi haƙuro Dr da yadda aka ɗaga maka hankali, kuma insha Allahu zan ƙira Daddynta zan mishi bayani kuma inda hali zan ce mishi yazo nan ya same mu sai muyi dukkan magana da zamuyi a nan, ina fatan kowa zai yafewa ɗan uwanshi", gaba ɗaya kowa ya yafe wa ɗan'uwan shi, sannan akace mu tashi mu tafi ɗaki, ɗago ido nayi ina kallon idon Dr, wanda shima kallo na yake, da ƙyar ya sake mun hannu na ya tashi ya yi sallama dasu Abbu ya tafi. Jikina a sanyaye na riƙe hanjun Amaal muka wuce ɗaki, inda muka bar Abbu da Ummi da Kuma Faisal a parlor. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/7, 17:36] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 30📑* *__________📖* A daren Abbu ya ƙira Daddy ya mishi bayani, hankalin Daddy na a tashe ya ƙirani, "Humairah nah kimun bayanin da zan fahimta, kina cikin ƙoshin lafiya dai ko? Kinaga babu wani matsalah na zamanki a gidan kafin na zo"? Duk cikin rawan jiki da tsoro Daddy yayi mun tambayoyin. Share hawaye na nayi, na ƙwaƙulo murmushin ƙarfi da yaji na ɗaura shi a fuskana, tukun na amsa mishi a cikin nutsuwa, son bana son hankalin shi ya ƙara tashi, "Daddy na babu komai da ya faru, Allah ya kiyaye kuma ina cikin tsaro sosai yanzu, ka kwantar da hankalina Daddy nah, yaushe zakazo"? Na ƙarasa tambayan cike da rauni a maganan nawa. Ajiyan zuciyar Daddy naji, chan kuma yace, "Gobe insha Allahu zan taho, domin a yanxu har na neme wani egent a Abuja ya bani tabbacin gobe akwai jirgin da zai tashi kuma zai san yadda zaiyi na samu mu taho, don Allah ki kwantar da hankalinki, idan nazo ma kawai zan taho da ke Berselona ki ƙarasa hutun ki tare da ni kinji sweet heart". Har mun fara bacci nida Amaal sai mukaji ana knocking ƙofan mu, a razane muka tashi dukkan mu, da yake yau Ummi tace mu rufe ƙofan, mudaina barinshi a buɗe, a tsorace Amaaƙ tayi ƙarfin halin ta tambayi waye ne? Muryan Ummi mukaji tana ƙiran Amaal ta zo ta buɗe mata ƙofan, da sauri Amaal ta sauƙa taje ta buɗe ƙofan, wanda nima dole na natashi na zauna ina kallon bakin ƙofan da Ummi zata shigo, riƙo hannun Amaal tayi suka shigo cikin ɗakin a tare, har gefe na Ummi tazo ta zauna, kuma har lokacin idona duka suna zube akan ta, ko ƙiftawa banayi na ƙura mata su don ganin yadda sukayi ja sosai, alaman bayan tafiyan mu taci kuka ba kaɗan ba. Hankalina gaba ɗaya naji ya tashi, lokacin da Ummi ta saka hannunta ta riƙo nawa kawai sai ta fara kuka mai ratsa zuciya, ganin haka ya saka ni ƙarasawa jikinta na rungumeta, ina kuka nace, "Ummi na mai ya sameki kuma"?. "Humairah gobe mahaifinki zaizo, inajin tausayin shi bakaɗan ba, kuma inajin tausayinki, zai ga kaman da gangan muka bar ɗan mu zai keta miki daraja, wallahi Humairah ba halin Faisal bane, narasa dalilin da ya saka shi aro wannan ɗaɓi'an, kiyi haƙuri Hummy kada zumuncin mu ya ɓaci, don Allah kiyi haƙuri"? Ta ƙarasa tana mai matuƙar zubar da hawaye. Jikina a sanyaye na fara share mata hawayen idon ta, "Ummi don Allah kidaina kuka, insha Allahu har abada zumuncin mu yana nan, ni ae ke uwace a gare ni, kuma Faisal yayah nane, kawai yanzu ma sharrin shaiɗan ne ya shige shi, amma insha Allahu zakiga Daddy nah ya fahimci komai, kuma zumuncin mu yana nan Ummi, sai ma abinda ya ƙaro", na ƙara ina kuma jikinta na kwanta ina kukan, wanda Amaal daga inda ta ke a takure itama ta ke nata kukan. Wannan ranan dai kam mutanen gidan gaba ɗaya basuyi bacci mai daɗi ba, duk zuciyar kowa babu daɗi har asuba tayi. Wunin ranan gaba ɗaya Dr kin zuwa gidan yayi,dana gajji da rashin shi na ƙira shi amma sai ya nuna mun kanshi ne yake mishi ciwo, amma zuwa dare zai zo. Haka dai muka wuni sukuku a gidan, kai hattah Faisal ɗin ma sai dana dawo ina tausaya mishi, sbd duk yadda akayi ya shigo gidan ƙi yayi, da aka matsa mishi yazo ayi breakfast sai ce wa yayi ya tashi da azumi, haka kowa ya zauna ranshi da zuciyan shi a dagule. Daddy sai washegari da asuba jirginsu ya sauƙa, da yake ta sowan dare sukayi, jiki a sanyaye Abbu yaje taryenshi tare da driver, mu kuma aka barmu da haɗa breakfast, na lura Ummi gaba ɗaya a rashin walwala ta ke, ganin haka ya saka na matsa kusa da ita, a hankali na saka hannu na a kafaɗanta cikin hankali na ce mata, "Ummi don Allah ki kwantar da hankalinki, wallahi ni babu abinda zai raba mu fah, wannan abin mu ɗauke shi a Ƙaddara ne da yazo mana, don Allah Ummi ki kwantar da hankalinki, nasani kina damuwa ko Daddy na zai ƙullace ku ko? Toh ina mai tabbatar miki babu abinda zai faru, don Daddy na mai fahimta ne", ajiyan zuciya Ummi tayi ta juyo tana duba na cike da damuwa, "Humairah wallahi bana son kuga kaman mun bar Faisal bamu ɗauki wani mataki akai ba, kuma ina tsoron hala Daddyn ki yaƙi tarayyan ku da Amaal, gaskiya Faisal bai kyauta mana ba ko kaɗan", ta ƙaresa faɗi kaman zatayi kuka. Ƙara shigowan motan su Abbu ne ya saka mu saurin sauƙowa downstairs nida Amaal, da sauri nayi hanyan waje domin taryan Daddy, ina ganin shi da gudu na ƙarasa na faɗa jikin shi, lokaci ɗaya naji hawaye yazo mun, amma don bana son hankalin Daddy ya ƙara tashi sai nayi dabaran dana mayar da shi, ina rungume da shi na ɗaga kaina kawai sai naga Dr na a bayan Daddy yana duba na da murmushi. Abbu ne yayi gyaran murya da nufin mu karasa parlor, Daddy yana rungume dani a gefen shi muka ƙarasa parlon, gaba ɗaya idon Dr yana kaina kaman zai jawo ni jikinshi. Haka muka ƙarasa kowa ya nemi wuri ya zauna, Ummi ta fito fuskanta ɗauke da murmushi. _*JAMA'A DON ALLAH KUMUN HAƘURI WALLAHI YAU MUNA TA BIKI NE, PAGE ƊIN BABU YAWA*_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/10, 16:43] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 31📑* *__________📖* Tunda muka zauna nake kwance gefen jikin Daddy nah, amma gaba ɗaya hankali da idon Daddy yana kan Dr Hussain, sai kallon shi yakeyi yana tunanin ina ya taɓa ganin mai irin kamannin shi, haka dai ya haƙura da kallon aka shiga gaisawa. Abbu sunyi tarya wa Daddy na girmamawa, dole Abbu ya saka Faisal ya zo ya gaida Daddy, Abbu yana kallon Daddy yace, "Alhaji Mohd ko zakaje ka ɗan huta ne kafin zuwa dare muyi abinda ya tara mu? don maganan gaskiya ka ɗauko gajjiya yakamata ka ɗan huta". "No babu komai Alhaji, idan babu matsalah ya kamata mu tattauna abinda ya kamata", Daddy ya faɗa hannunshi ɗaya ya na dafe dakai na, amma yawanci idon shi yana kan Dr, wanda gaba ɗaya Dr yakasa sakewa. Cikin mutsuwa Abbu ya lallaɓa Daddy, babu yadda ya iya haka ya haƙura akabar zaman sai anyi sallan ishaa. Ana idar da sallan ishaa Daddy da Dr Hussain suka iso gidan, da yake Dr yaja Daddy sun tafi hotel ɗin da ya sauƙa, anan sukayi dinner sannan aka taho cikin main parlon gidan aka zazzauna. Dubawa Abbu yayi yaga babu Faisal, da hanzari ya ɗauki wayan shi ya ƙira shi, babu ɓata lokacin ya shigo duk jikin shi a sanyaye, gefen ƙafan Abbu yaje ya zauna. Addu'a Abbu yayi ya buɗe taron da addu'a, sannan ya karanto wa Daddy duk abinda ya faru daga farkon neman mu da Dr har zuwa case ɗinmu da Faisal, da kuma niyyan da Dr yayi na bada labarin shi sai dai yagaywa Daddy, daga nan ya fara neman gafaran Daddy na abinda Faisal yaso aikatawa. Murmushi Daddy yayi ya dubi Abbu yace, "haba Abbu yanzu don wannan tsautsayin da ya faru ne zai saka kayi fushi da Faisal? Ni ae banga laifin Faisal ba sai naku iyayen shi, abinda yasa kuma ɗaya ne, a wannan rayuwa da muke ciki dole ne fah ka hana yaranka maza zuwa sashin yaranka mata, haka zalika suma ƴaƴan mu mata su daina zuwa gefen yayun su mazaa, koda kowa kai musu saƙo ne, domin masifun da yanzu suka mana yawa a duniyar mu, hadda sakacin mu iyaye, wallahi Alhaji zaka sha mamaki idan kaga yadda fyaɗe yayi yawa a wannan lokacin, kuma abin munin sai kaga mahaifi ne yayiwa ɗiyar shi, ko kuma yayah yayi da ƙanwar shi, ko ƙaninka yayi da ɗiyarka ko ƙanin matar ka, munyi sake da barin yaranmu suna chuɗanya kaman jinsun su ɗaya, haka kuma irin suturun da ƴaƴanmu mata suke sakawa a cikin gida, duk yana contributing lalacewan yaran namu, saboda haka mu iyaye mu gyara kafin mu koma kan ƴaƴanmu". Daddy ya dawo da kallon shi kan Faisal da yake ta share hawaye yace, "Faisal Amaal da Humairah dukkan su ƙannen kane, tunda Allah ya kiyaye babu abinda ya faru, toh Alhamdulillah, sai dai nace maka don Allah ka ƙara saka tsoron Allah a ranka, kaga nan gaban iyayen kane kayi niyyan aikata haka, toh ina kuma babu idon iyayenka?" Daddy ya daɗe yana mishi nasiha sannan ya neme kowa ma ya yafewa juna kuma muyi ƙoƙarin kula da zumuncin mu, sannan nima da Amaal ya mana namu faɗan akan mudinga kula da shigan da zamu dingayi, daga nan ya dawo da duban shi kan Dr Hussain yana murmushi yace. "Dr Allah bai sa mun taɓa haɗuwa da kai face to face ba sai yau, duk zumuncin mu through phone muke yi, ashe kuma suruki zaka zama mun ban sani ba", ya ƙarasa faɗi yana murmushi mai kaman dariya, wanda ya nuna tsananin farin cikin Daddy a fuskar shi, kowa da yake cikin parlon saida ya ɗan dara, nidai ban iya darawa ba sai ma ɓoye fuskana da nayi a jikin Daddy, shi kuma Dr ya sake sauƙe idon sho ƙasa. "Toh Dr Hussain muna saurarenka" cewar Abbu da yake bin Dr da murmushi. Ƙara tanƙwashe ƙafan shi yayi a ƙasa yana murmushi, kan shi ya ɗago ya kura mun ido yana duba na. "Alhaji Gambo Aliyu, shi ne mahaifin mu, wanda ya kasance haifeffen garin misau ɗaya daga cikin ƙaramar hukumar Bauchi, misau shi ne asalin garin su mahaifina, sun kasance su uku ne a cikin mahaifansu, yana da yayu guda biyu dukkansu mata, twins ne wato hassana da hussaina, mahaifinmu shi ne Gambon su, wanda sun bashi yakai shekara biyar, bayan an haife sune da shekara biyu suka yi ciwon ƙyanda, idan anan Hassanan Allah yayi mata rasuwa, bayan an haifi mahaifinmu ne suka kasance su biyu kenan a hannun iyayen su, mahaifinsu ɗan kasuwa ne a wancan lokacin, yana kasuwancin shi har zuwa garin jos. Mahaifina yayi karatu har zuwa matakin digiri, wanda yayi a garin jos inda mahaifinshi yake zuwa kasuwanci, a hannun aminin shi ya da suke kasuwanci da shi ɗan garin Narabi dake jos ya barshi yayi karatu, inda mahaifin mu suka shaƙu da ɗan Baban Narabi mai suna Umar, wanda dukkansu sun kasance masu ilimi sosai. Goggo Hussaina tayi aurenta a garin misau, amma har zuwa girmanta Allah bai bata haihuwa ba, sai daga baya mijinta ya ƙara aure, inda abokiyar zamantan ta haifi yara kusan huɗu, kuma dukkan su zaka ɗauka Goggo Hussaina ce ta haife su, don tsabar kulawan da ta keyi da su, abin babu wuya Abban mu suna final year a digiri ɗin su Allah yayi rasuwa wa mahaifin su, inda suka shiga cikin tsananin tashin hankali, amma da yake basu da yawa sai Baban Narabi ya ɗauki ɗawainiyar karatun Abba har suka gama. Abba na lagos aka tura shi service, shi kuma Baba Umar kaduna, haka suka tafi suna kewan junan su. Bayan 1yr suka gama suka dawo jos, babu ɓata lokaci Baban Narabi ya tsaya kai da ƙafa har saida ya nema musu aiki, inda Abba ya samu aiki da Central Bank, shi kuma Baba Umar ya samu aiki da Custome. Zuwa wani lokaci komai ya fara musu daidai, sun fara fin ƙarfin komai, sai Abba ya fara neman auren wata yarinya a garin misau, ana shirin auren su Allah yayi mata rasuwa, gaba ɗaya Abba ya shiga cikin wani irin tashin hankali, har sai da yafara kasa aikin shi, ganin haka mahaifiyar shi Umman Misau ta nemi shawaran Goggo Hussaina akan ko zasu bashi auren babbar ƴarsu da yanzu ta gama secondry school a wannan shekaran mai suna *FATIMA* babu ɓata lokaci Goggo Hussaina ta amince kuma ta bar maganan zata je tayi shawara da iyayen yarinyar, basu wani ja ba dukkansu suka amince inda mijin Goggo Hussaina Alhaji Abubakar dama ya kasanceai matuƙar haƙuri magana ma nan baza kaji shi yana yi ba, malamin gidan gona ne, idan baya wurin aiki toh kullum yana ƙofan masallacin unguwar su da yake manne da gidan shi yana zaune, jama'a da dama suna mutunta shi da halinshi na dattaku, itama mahaifiyar Fatima wato Aishatu itama ba mai magana bace, ta kasance bafulatanan garin gabɗori, duk wanda yasan garin misau ya san gabɗori garin wasu farare kyawawan fulani ne a wurin, gashi ta kasance mai haƙuri da kawaici, ana ƙiranta da suna Addagana, tun ranan da malam Abubakar ya aureta babu wanda zai ce ya taɓa jin tsakaninta da mijinta ko abokiyar zamanta Goggo Hussaina, kuma ta ɗauki iyayen Goggo Hussaina kaman nata iyayen, domin ita ta kasance marainiya ce, babu uwa babu uba, kuma ƴan uwanta sun mata riƙon wahala, toh da ta samu Gogho Hussaina irin mutanen nan ne masu amana da maida ɗan wani nasu, sai ta rungumeta suka zama kaman ƴan'uwa ba kishiyoyi ba, suma iyayen Goggo Hussaina sai suka riƙeta kamar ƴa. Lokacin da ta haifi Fatima bata cika shekara ba ta samu cikin ɗanta na biyu, dole Goggo Hussaina ta karɓi riƙon Fati ya dawo hannunta, bayan Addagana ta haihu, an samu Muhd Auwal, ko shekara baiyiba sai ga wani cikin a jikin Addagana, haka Goggo Hussaina ta sake karɓan shi ta haɗa da fatima ta riƙe shi, yana da shekara ɗaya da ƴan watanni Adda gana ta haihi ɗanta namiji inda Malam Abubakar yayi kara ya saka sunan mahaifin su goggo hussaina wato malam musa, amma suna ƙiran shi da Baba, Addagana wanannan karon bata sake haihuba, don tayi ɓari kusan sau biyu kuma ta haihu kusan sau uku suna komawa, ba ita ta sake haihuwa ba har saida Fatima ta kai shekara goma sha uku, Auwal yana da shekara gima sha biyu, Baba kuma yana da shekara goma da rabi, sai lokacin ta haifi *HAUWA* Fatima da hauwa sun kasance suna tsananin kama da mahaifiyar su, domin kana ganin farinsu da gashin su babu abinda suka bari na Addagana, Auwal kuma da Baba duk mahaifinsu suka ɗauka, duk da suma farare ne amma basu yi kyaun su Fatima ba. Fatima da ƙannenta sun kasance yara masu tarbiya da nutsuwa, domin Goggo Husaina babu abinda ta bari daga tarbiyan su, ta riƙe su kaman ita ta haife su, babi wani mugunta a tarbiyanta, sai kuma yaran suke sonta kaman itace mahaifiyar su, Baba ne kawai wani lokacin sai ya koma ɗakin Addagana, idan sun ɓata kuma ya tattaro ya dawo ɗakin goggo hussaina, kowa zaka ga yana mishi dariya, akan yarasa wurin zama guda ɗaya. Lokacin da aka gayawa Abban mu maganan auren shi da Fatima bai wani ja ba ya amince, amma ita Fatima sai da tayi ƙorafin ita fa kawun tane kawu Gambo, amma da taga ran Yayah zai ɓaci sai ta amince, da yake haka suke ƙiran Goggo Hussaina, don duk sunbi bakin Addagana ne. Ba'a ɗauki lokaci ba akayi auren Abba da Ummi nah, aka kaita garin bauchi inda Abba na yake aiki, sun zauna a wani unguwa wai shi dutsin tanshi, gida ne ɗan madaidaici ma ɗakuna biyu, sai kitchen da wani ɗan store, babu laifi gidan ya dace da sabbin ma'aurata. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/11, 11:08] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 32📑* *__________📖* Abba na da Ummi na suna cika shekara uku da aure Allah ya basu mu, inda aka same mu nida ɗan'uwa na Hassan, daga lokacin Allah yayita buɗi wa Abban mu, inda aka maida shi branch ɗinsu na lagos, babu ɓata lokaci muka tattara tare da Aunty Hauwa muka koma chan, ita kuma tana taimaka wa Ummin mu da wasu ƴan aikace aikace, inada a lokacin tana tayata har renon mu don bamu fi six month ba, ita kuma Aunty hauwa tana 14yrs kuma zata shiga ss 2 a lokacin, haka Abba ya sama mata wani private school kusa damu ta shiga. Muna cika 2yrs Aunty hauwa ta gama rubuta waec ɗinta, murna kaman zatayi yayah, haka muka ɗunguma muka taho Misau mukayi hutu. A wannan hutun ne Baba Umar yayi aure da wata yarinya ƴar tilden fulani, ƙanwar matar abokin shi ce mai suna suwaiba, shi kuma a wannan lokacin yana katsina da zama. Result ɗin su Aunty hauwa na fitowa Ummi suka yi shawara da Abba akan a sama mata school of nursing bauchi, haka Abba yayita fafutukan nema har Allah ya yarda da rabonta a ciki, tafiyan ta ummi taji babu daɗi, domin Aunty Hauwa akwai kazar-kazar ɗin aiki, saidai akwai yawan faɗa, wanda kullum akace ta ɗauki Hassan sai ta zungure shi tayita mitan ya cika yawan kuka, amma idan Ummi zatayi aiki tafi so ta bata riƙon shi, don aikin zai fi tafiya mat, domin ni duk inda akayi dani haka nakeyi bana da rikici inji Ummin mu, shi yasa ita bata damu ta ɗaga hankalinta akaina ba, sai dai kullum rikicin Hassan ke rikota su dukkan su gidan. Aunty hauwa tana 2yrs a school of nursing, taxo mana hutu lokacin muna 4yrs, a lokacin kuma Baba Umar an dawo da su Lagos, ranan da tazo Abban mu tare da Baba Umar suka je ɗaukota a airpot, tunda Baba Umar ya ganta hankalin shi yayi mugun tashi, sai tambayan Abba ya keyi "yaushe Hauwa ta girma haka? Kaga fa yadda ta koma kaman Fatima sak, har ma tafi Fatima tsayi da fari wallahi", ya faɗa yana duban Abba da ya ƙura mishi ido. Murmushi Abba yayi mishi yana duban Aunty Hauwa ta mirror yadda duk ta kasa sakewa sai wani kunya ta keji kaman ta nutse a ƙasa, yana ɗan dariya yace, "haba Umar duba dai da kyau ka gani, ta ina Hauwa ta kai Fatima kyau? Tsayi kuma don ita yanzu yarinyace batayi jiki ba, amma Fatima nah tafi komai, wannan da wani hancinta da baikai na matata kyau ba", ya ƙarasa yana dariya domin ganin yadda Aunty Hauwa tayi saurin ɗago idon ta tana kallon shi da mamaki, chan kuma ta saka hannunta ta shafa hancin ta, muryah cike da shagwaɓa tace, "yayah da Bappan mu sunce nafi Adda Fatima kyau, wataran Addagana ma tace nafi kowa kyau a gidan, kuma ka tambaya yayah kaji", ta faɗa kaman zatayi kuka. "kwantar da hankalin ki Princess babu ta inda Fatima ta fiki kyau, kawai haushi ya keji don matar da zan aura tafi tashi matar kyau, kada ki wani ɓata hawayenki zan karɓa miki ba sai kin ɓata yawun bakin ki ba", ya faɗa yana kai duka wa Abban mu, wanda shi kuma sai dariyan su yake tayi yana chigaba da driving ɗinshi. Har suka iso gidan mu faɗan bai ƙareba, mu kuma nida Hassan da gudu muka zo muka rungume Aunty Hauwa, itama da murnan ta ta rungume mu, kaman zatayi yayah don daɗin ganin mu, Hassan yana duban ta yace, "Aunty Hauwa inace kinfi sona akan Hissain? tunda nine babanki ko?" ya faɗa yana shan gaba na kada na matsa kusa da Aunty Hauwa. Tana dariya ta sunkuya ta riƙo hannun mu tace, "dukkan ku ina son ku iri ɗaya, amma kai nafi sonka saboda sunan Baba na kaci, shi kuma nafi son shi saboda shiɗin rayuwata ce, Hassan farinciki nane, Hussain kuma rayuwata ce, kaga dukkanku ina sonku, amma yanzu zan fi son wanda yafi jin magana a cikin ku", ta ƙarasa faɗi tana miƙa mana sweet wasu manya-manya dasu kowa uku-uku a hannun shi. Haka muka fara tsalle da murna, domin gaskiya Aunty Hauwa ba dai nuna mana so ba duk masifanta amma akwai ta da alheri, gashi ko cin abu zatayi taga idon mutum toh babu yadda zatayi sai ta baka, ita dai abunta bai rufe mata ido ba, kaman ƴan garin su mamanta idan sunzo, duk da tasan irin muguntar da sukayi wa mamanta amma haka zata tattaro kayanta ta basu tace suje su raba, gaskiya halinta babu abinda ta bar na Goggo Hussaina, kaman tasha ne a nononta, saidai faɗa kam sai a hankali, wasu sukance ta ɗauko wani yayan Baban sune amma ya daɗe da rasuwa, domin wuni yakeyi akan kujeran katako a ƙofar gidan shi, duk wanda ya wuce sai yayi masifa, shi ne ƙiran mai gyaɗa, shi ne mai gujjiya, mai rogo bata tsira ba, kuma yana saya yana masifa, toh haka Aunty Haiwa ta ke, domin gidan su family house ne, duk yaron da ya shigo sai ta hantare shi, amma kuma kullum jakanta da sweet tana raba musu, Allah sarki Aunty Hauwa nah", Dr Hussain ya ƙarasa faɗa yana sha re hawayen shi, kuma lokaci ɗaya ya sunkuyar da idon shi a ƙasa yana ta share hawaye, gaba ɗaya parlourn kowa sai jikin shi yayi sanyi, babu wanda yace uffan, sai Faisal ne ya tashi ya ɗauko goran ruwan sanyi ya miƙa mishi, karɓa yayi ya sha kusan rabin roban, sannan ya ɗago idon shi ya dube ni, ganin ina share hawaye na sai yayi murmushi ya maida idon shi ƙasa. "Ummin mu da fara'a ɗauke a fuskarta ta miƙa hannu ta rungume ƴar uwarta, itama Aunty Hauwan tana murmushi ta rungume Ummi, bakinta bai rufu ba tace, "Adda Fati kiji mijinki wai kinfini kyau? Nidai da mutanen gida duk mun san muna kama da ke amma maganan gaskiya nafi kyau, ni banma taɓa jin wanda ya taɓa cewa kinfini kyau ba, haba dubi ido na kaman ni na ɗusana abuna, kowa ya ganni sai ya sume da kyaun idona", ta ƙarisa faɗi tana murguɗa baki tana juya idon nata. Dariya gaba ɗaya parlourn sukayi, Abba yana hararanta da wasa yace, "amma Hauwa bakida wayo, waya ce miki kinfi Fatima kyaun ido? Ke baki san ana zolayanki bane ake cewa kuna kama? ae kinfi kama da Auwal da musa, domin Fatima ae ta muku zarrah a kyau, don ke macece shiyasa ake kwatanta kamanin ku, kuma kunfi su Auwal fari". Kuka Aunty Hauwa ta fara tana duban Ummin mu tace, "don Allah Adda Fati ki gaya mishi gaskiya saboda Allah, wallahi yayah Auwal da Yayah Baba ƙananan ido suke da shi, sufa irin idon su Bappanmu suke da shi ƴan ƙanana, kuma hancinsu bai kai namu ta shi ba, Adda kimishi bayani ya lura, wallahi ni ina da kyau mai ɗaukan hankali, ranan fa zan wuce wani DPO yazo wucewa kasa tafiya yayi yace sai yaga gidan su wanann mai kyaun, wallahi yanzu a school Hauwa beauty ake cemun, ko Hauwa golden girl", ta ƙara sa maganan tana share hawayenta, wato Aunty Hauwa komai zakayi kada kace bara da kyau domin ita ta yadda ita mai kyau ce, saboda haka kullum Ummin mu idan zata saka ta aiki ta mata babu ɓacin rai, zakaji tace zizar gidan mu, autar Adda da yayah da bappanmu, maza tashi kimun aiki, toh babu musu zata tashi tayi yadda ya dace, shiyasa Aishan mu ta gaji halin Aunty Hauwa, gashi kuma kullum ɗabi'un da Humairah ta keyi kenan, wanda shi yaja hankalina gareta, don ni tun ina yaro abinda Aunty hauwa ta keyi burgeni yakeyi, ban fahimtan komai amma idan tana rikicin tafi kowa kyau, abin daɗi yake mun. Domin wataran sai ta jamu cikin ɗaki nida Hassan ta tsaya gaban mirrow tayita kallon kanta, ta juya ta gyara tsayunta, ta lanƙwashe nan ra juya na, ta baza gashinta mai azaban kyau tana duban mu zata ce, "yarana amma dai duk ƙasan nan kafin a samu mai kyauna za a sha wahala ko? Kunga irin kyaun ido na kuwa"? Hassan idan ya kalleta zaice amma baki kai Ummin mu ba fah, toh hannu ta ke sawa ta kai mishi ran ƙwashi ta fatattake shi a ɗakin tana cewa, wannan kam kuskure akayi aka saka maka sunan mahaifinmu, ɗan banzan yaro mai goshin tsiya dama isubu aka saka maka, sunan wani ɗan ajinmu a lungun fada, ko kuma a saka maka gedau ko kantara, shashan yaro kawai," sannan ta dawo da kallonta kaina, "kaifa me kace"? Murmushi nakeyi ina da shekara huɗu amman nasan wayon ince mata, "kinfi Abba da Ummi kyau, kinyi irin india", tsalle ta keyi ta ɗaga ni sama tace wani abunma sai naje turai na ɓaro kyau tukun yaro na mai kama da larabawa, nima daɗin abinda ta ke faɗi nakeji. "Dr na toh ina ita Auntyn Hauwan yanxu ta ke? Nima naji ina sonta, don nima ina son ace ina da kyau, duk da nasan ina da kyau amma ina son ace nafi kowa wallahi", na faɗa ina duban dr da yake kallona idon shi na zubar da hawaye bakinshi kuma da guntun murmushi. "Toh ae ke baki mun kama da ƴan india, asali ma ni banga kyaunki ba, kaman Aishan mu da Aunty Hauwa sunfi kyau", Dr ya faɗa yana fito da sautin murmushinshi, kuma hawaye yana kanbin fuskan shi, gaba ɗaya parlourn dariya aka fara mun, yadda na turo bakina gaba kaman zan falla ihu. Amaal mai ta samu banda dariya, tana duban Dr tace, "ga goshin ta kaman na gedau da kantara", gaba ɗaya parlourn dariya akeyi, Dr yana dariya yace, "Amaaƙ sunan kakanunae fah na wurin uwa, ƙannen maman umman mu ne fah, in kinyi wasa sai na haɗa ki da gedau babu ruwa na". Daddy ƙurawa Dr ido yayi duk yana cikin ruɗani, duk dariyan da akeyi shi bayayi, idan ya dubi Dr ɓa wani lokaci sai kuma ya dawo da idon shi kaina, nidai ina satan kallonshi kaman wani mai nazari, chan kuma sai naga yana share hawayen da bansan me yasa suka zubu mishi ba, gaba ɗaya hankalina sai ya tashi, kawai sai na fashe da kuka na riƙe shi ina tambayan shi, "Daddy me yafaru kake kuka"? Murmushi yayi ya riƙo hannuna muryah a hankali yace "babu komai na tuna da mahaifiyar kice", ya faɗa yana sha re hawayen shi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/13, 11:38] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 33📑* *__________📖* Ana haka magana ya fara ƙarfi tsakanin Aunty Hauwa da Baba Umar, domin wani so sukeyiwa junan su kaman me, amma Ummi nah ita bata so hakan ba, domin tanaga kaman Suwaiba zata ce ita ta haɗa ƙanwarta da mijinta, amma koda Abba yace mata babu ruwanta, kada ta damu da maganan mutane sai kawai ta yi shiru ta bisu da addu'a. Ranan da Aunty Hauwa ta gama huta, Baba Umar ya matsawa Abba akan shifa dole su tafi tare da ita, domin aje anema mishi aurenta, don bada wasa yakeyi ba, kada yana chan lagos wani yazo ya ƙwache mishi ita, babu yadda Abba ya iya dole suka biyota. Tadawo da washe gari mutanen jos sukazo har misau neman aure, babu wani wasa da hankali akayi komai cikin mutunci da dattaku, a ranan iyayen Aunty Hauwa suka bawa Baba Umar auren ta, shi kuma Baban Narabi ya sake neman a saka musu auren bada daɗewa ba, da ƙyar dai aka yadda akan idan tagama wannan year ɗin sai ayi, domin da iyayenta sun fi son sai ta gama karatun haba ɗaya, amma haka aka tsayar da magana nan da 5month. Ko wani ƙarshen wata sai Baba Umar yazo mata hira har bauchi, toh ganin irin rawan kan da yakeyi ne ya tunzura matar shi ta fara buri, wanda har gidan mu taje tayiwa Ummi kacha-kacha, Ummi ko kaɗan Ummi bata mayar mata magana marar daɗi ba, sai haƙuri kawai da take bata. December Ummi suka tafi misau domin saura 1week bikin su Aunty Hauwa, daɗi nida Hassan mukeji, domin zamuje misau muci masan gidan sarkin dabji, sai murna mukeyi. Ranan thursday Aunty Hauwa tayi walima a cikin fadan sarkin misau, a cikin wani hall mai suna *GWANI MUKHTAR* waliman yayi matuƙar armashi inda malamai mata kusan kala uku sukayi wa'azi, ranan friday 2:300pm aka ɗaura auren Aunty Hauwa da Baba Umar, kuma a ranan akayi wuni, ranan saturday aka wuce da ita kai tsaye chan Narabi, inda dama Baba Umar yayi gidan shi mai kyau, wanda idan sunzo suke sauƙa a wurin, gida ne mai 4bedroom, saboda haka sai aka bawa Aunty 2bedroom inda kowani ɗaki ɗaya yana kallon ɗaki ɗaya, da toilet a tsakiyan su, ɗaya aka maida mata parlour ɗaya kuma bedroom, ita ma Suwaiba haka aka mata, shi kuma Baba Umar aka bar mishi main parlour da toilet ɗin ciki don baƙi, amma ya yanke shawaran yanzu zaina bin ɗakunan su, amma idan ya samu sarari zai zo yayi ɗaki a cikin parlourn. Baba Umar Allah bai taɓa basu haihuwa ba, domin sau biyu suwaiba tana ɓari, amma daga baya abun sai yayi shiru. Ranan Baba Umar ya nuna murnan shi da yaga Aunty Hauwa a gidan shi, kuma matsayin matar shi, daɗin abinma suwaiba ba tazo bikin ba, saboda haka ya samu ya mori amarchin shi da Aunty har na tsawon 2weeks da aka bashi hutu, daga nan ya mata sallama ya wuce lagos, inda ita kuma sauran 3weeks suka ma ajin da shekaran zasu gama, wato sauran mata 1yr ta gama, kuma ya mata alƙawarin duk bayan 2weeks zai dinga zuwan mata, haka suka rabo suna ta begen junan su. Rayuwar babu wuya, yau Aunty hauwa sun dawo hutun first term, kai tsaye misau ta wuce, domin zata jira sai Baba Umar yazo tukun su wuche lagos, domin yace wannan hutun lagos zata je tayi, domin hutun 3 weeks zatayi, shi kuma yaga ya kamata su fara sabawa da suwaiba. Tana shiga gidansu tayi karo da Baba wato yayanta Musa, yana ganinta ya fara dariya yana cewa, " jama'an gidan nan ku fito kuga wata afiruwa kazar mayu", yana dariya lokacin da Goggo hussaina ta fara fitowa yana dubanta yace, "Mama don Allah kiga ƴar ki duk ta wani fige babu daɗin kallo, sai wasu ido girkima girkima kaman na hajiya umma ƴar madara", ya ƙarisa faɗi yana dariya domin yasan ya tsukano Mama, wato goggo hussaina, harara ta bishi da shi tana kaɗa kanta tace, "kayi damu iyayenka ba namu iyayen ba, ɗan tselanƙwa mai ƙananun ido kaman ƙaramar tocilan", ta faɗa tana kamu hannun Aunty hauwa da ta fara zuban hawayen tsokanan da Baba yake mata, domin babu hali su zauna inuwa ɗaya da shi zakaji ya tiso ta gaba har sai tayi kuka, amma yayah Auwal ɗinta tattalinta yakeyi kaman wata ƙwai, Mama tana hararanshi tace, "zakaje gidan umman neman ɗumamen safe da kunu ae, namaka alƙawarin yau zan tura ɗan saƙo ya gaya mata irin tonon sililin da kake mata", ta jawo hannun Aunty hauwa suka shige ɗaki, ita dai Addagana tana zaune a ɗakinta tana biya karatun ta, bata wani fito ba sai dariyan drammer su kawai ta keyi daga inda ta ke, amma har cikin zuciyarta tana jin wani iri da akace hauwa ta fige, toh komai ke damun ta? Allah kaɗai ya sani. Tunda Mama ta lura laulayin ciki Aunty hauwa ta keyi, domin suna shiga ɗakin ta dawo da bayan kaman zatayi amai tace, "Mama kaman anci miyar stew a ɗakin nan, warin shi na ke ji", mama da sauri ta ɗauki kwanon miyan ta fitar zuwa kitchen, sannan tazo ta ɗaga labulayen ɗakin tana duban Hauwa data faɗa kan gado ta kwanta rub da ciki, cikin kallon tausayawa tace, "buɗɗo nah mai kike so toh a dafa miki?" juyar da kai kawai Aunty haiwa tayi alaman ba tason komai. Mama tana duban ta tace, "haka bazai yiwu ba hauwa, kinga yadda kika fita hayyacin ki kuwa? Kodai bakyacin komai ne a makarantan? Kuma kin takura kanki da karatu ko? Don Allah gaya mun me kike so kafin wannan mai neman maganan yayi gaba na rasa ɗan aika". Juyowa Aunty hauwa tayi tana duban mama fuska a murtuƙe tace, "Mama komai naci amai nakeyi, ni bansan me zanci ba, kawai fanta nake iya sha", ta ƙarasa faɗi hawaye yana bin idonta. Mama na duban ta kaman ta tayata zub da hawayen tace, "toh zakici faten tsaki"? Da sauri Aunty hauwa ta tashi ta zauna tana duban mama tace, "yauwa mama amma na gidan umma nake so, wanda ta ke saka mishi gauta", ta faɗa tana tasowa tayi parlour wurin fridge ta buɗe tana kallon ƙullin zuɓun da mama takeyi na sayarwa, har ƙasa ta zauna tukun ta ɗauki leda ɗaya mai sanyi ta ɓula ta zuƙe shi, mama kuma tayi waje tana ƙwala ƙira wa Baba ƙarami, sannan ta dawo ta neme kujera ta zauna ta ƙurawa Aunty hauwa ido da ta ɗauki leda na biyu ta ɓula tana wani lumshe ido tana sha. Baba ƙarami ya ɗaga labulen ɗakin bayan yayi sallama mama ta amsa, idon shi ya sauƙa akan Aunty hauwa da take shirin ɗaukan leda na uku tasha, da karfi yace, "kutt hauwa inace dai kin bada kuɗin tukun kike sha bawai kinga na bati ba ko"? Ya faɗa yana ƙara sowa cikin ɗakin baki a buɗe yana kallon mama akan tayi magana. Bappah ne ya shigo gidan da sallama, yana dariyan halin Baba ƙarami ya ƙaraso ƙofan mama yana cewa, "kaidai baba ina ruwanka da tambaya, kasan ko duk zuɓun fridge ɗin ma ita aka yi"? "caɓɗi jam, amma ko nima dole nasha ɗaya don ita har uku fa take sha Bappah", Baba ƙarami ya faɗa yana kallon idon mama da take binshi da harara. Yana dariya ya karkata kanshi wurin mama yace, "mama gani ina zanje miki"? "kaje gidan umma kace ina son faten tsaki mai gauta wa Hauwa, yanzu ta dawo daga makaranta ta kasa cin abincin mu, gwaten kawai ta ke son cin kaji". Juyowa hauwa tayi ta gaida Bappah daya nemi wuri gefen mama ya zauna yana dubanta da tausayawa yace, "bakiji daɗin jikin bane baɗɗo nah? Duk kin rame kin wani ɗashe gaba ɗaya kaman bakida jini? Me kike son ci nasaya miki"? Bappah ya ƙarasa faɗi shima yana duban ta da tausayawa. "Bappah ferfesun kayan ciki nake so", ta faɗa tana kwanciya akan ledan tsakar parlourn Maman, "kutt amma hauwa kin tunkuɗu rikici wallahi, ke kaɗanki kin shanye zuɓu leda uku, gashi yanzu kinsa za a haɗa tsuhuwa da aikin yin gwate, a haka ma mai gauta wanda da ƙyar idan umma bata sake cillani kasuwa ba, yanzu kuma kin matsawa bappan mu ya sayo mana kayan ciki a dafa mana, haba hauwa cikin mu ae baxai ɗauki abinci dayawa ba", ya faɗa yana fita da sauri a ɗakin yana dariya, domin irin kallon da mama ta ke mishi kaman zata mare shi, yana tsayawa a tsakar gidan ya kwaɗawa Addagana ƙira yace, "fito kiga halin wariyar da mama da Bappah suke mun, don Allah Addagana nima ki saya mun kazar alka mana na huce", fitowa tayi tana kallon shi tace, "nikan ba aikanka akayi bane Baba"? Addagana ta tambayeshi. Haka ya fita yana cewa daga nan zan leƙa gidan yayah Auwal nace mishi zizar ƴaƴa fa tazo, gida ya kache me da girke girke, shima ya saka ƴar lukutan matar shin nan ta dafa nata ta kawo", yana dariya ya fita a gidan. Da yake anyi auren hauwa december, febuary akayi na yayah auwal, da matar shi da takasance ƴar bappan su ce, Ummi kyakkyawar bafulatana da suke yanayin kama da Yayah Auwal. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/14, 11:45] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 34📑* *__________📖* Murmushi Bappah yayi yana duban mama yace, "kinji abinda ɗanki yake faɗa ko"? Tana dariya ta dubi Aunty Hauwa tace, "kije ki gaida Adda ko", tashi Aunty hauwa tayi ta nufi ƙofar ɗakin Adda, wanda ta shimfiɗa taburma tana ƙulla ayanta mai sugar. Gefen tabarmar Aunty hauwa ta zauna, idon ta na kan ayan, ta gaishe da Adda, bayan sun gaisa ne Aunty hauwa ta saka hannu ta ɗebi ayan ta kai bakin ta, lokaci ɗaya ta rufe idon ta don tsabar daɗin da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, ganin haka Adda ta ɗago wani ledan ta ƙullu mata mai yawan gaske ta miƙa mata, gyara zamanta tayi a gefen Adda ta maida hankalinta kan cin ayan. Adda tana gama ƙullawa ta dubeta tace "ko zakici rogo"? Ido Aunty hauwa ta ɗago tana kallon Addan cikin nutsuwa tace, "dama ki soya mun shi ya koma ƙosan rogo". Tashi Adda tayi ta ɗauko rogon ta saka attaru da ajino da albasa ta kirɓaci yayi laushi, sannan ta haɗa murhunta ta ɗaura mangyaɗa, ta fara soya mata, lokacin kuma Mama ta fito tsakar gidan domin Bappah ya koma ƙofar gida domin fara ƙiran sallan azahar da akeyi. Dukkan su alwala sukayi, bayan sun idar da sallah ne Adda ta zuba mata ƙosan rogon a pilet, tace ta karɓo yaji a wurin Mama, da sauri ta tafi parlourn mama ta karɓo yajin, a tare suka fito ita da maman, kafin kace me ta cinye rogon nan, mama ta miƙo mata zuɓu guda 2, a wurin ta zuƙe su, sannan ta yi hamdala ta wuce ɗakin mama ta kwanta akan three sitter maman, lokaci ɗaya bacci ya ɗauke ta. Ana ƙiran sallan la'asar ta buɗe idonta da ƙaran wayanta ya tasheta, amma bata iya ta tashi ba ta jawo wayan ta kai kunnen ta, muryan Baba Umar taji yana mata sallama, hira sukayi na zuwa wani lokacin yana kuma tambayanta yanayin jikintan, haka dai suka ɗan ɓata lokaci kaɗan, sannan ta tashi ta fito domin yin alwala. Tana idar da sallan mama ta shigo ido ta ƙura mata ganin ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jan charbi, a hankali ta ɗago suka haɗa ido da mama. "Hauwa ga gwaten tsakin an kawo miki, amma ina ga bayanzu zakici bako?" murmushi Aunty hauwa tayi tace, "yanzu kai mama, kinji wani irin yunwa dana ta shi inaji kuwa"? Mama ko da sauri ta jawo kulan ta ɗauko pilet ta miƙa mata, wani murmushin daɗi Aunty hauwa tayi, ta ɗauko ta zuba cikin pilet ɗin, sai wani ƙamshin gyaɗa yakeyi, ga tantaƙwashi rututu a ciki, Aunty hauwa dariya tayi tace, "Allah sarki hajiya umma, irin wannan daɗin yau ina zan kaishi"? Sannan ta dubi mama tace, "mama kada abawa kowa duk zan cinye zuwa anjima, don nasan Baba ƙarami yana zuwa ya gani toh sai wani ikon Allahn, don sai yaci", ta faɗa tana ɓoye coolern a bayanta. Dariya mama tayi tace, "muma umma ta mana coolern mu daban, kuma Baba kam ae shi ya kawo, babu yadda banyi da shi bama ya tsaya yaci, amma yaƙi yace pepesoup ɗin kayan cikin kawai yake jira, amma wannan kam ya bar miki". "Chabb ɗi jam, mama kada ma kibashi, ni nafi son saifa da hanji ma kawai, idan akwai yaɗi a ciki ki bashi mama", ta faɗa tana kai loman gwaten, kallon mama tayi tana murmushi tace gaskiya umma badai iya kwamacalan girki ba kam, zwaii kenan", ta faɗa tana maida dariyanta. Hararanta mama tayi, "da yake ta rufa miki asiri ta farfaɗo da ke ae dole ki faɗi haka, amma akwai gobe zan ce kada ta dafa miki komai ta barki da halinki", dariya dukkan su sukayi. Zuwa dare mama har ta mata pepsoup ɗin, ga wani bread muƙeƙe da Bappah ya sayo mata, tana zaune a gefen Adda tana ci, sai zuba santi ta keyi, Baba ƙarami kuwa sai mita yakeyi wai ancika mata kwano, shi kuma an saka mishi ɗan kaɗan, Bappah yana dariyan su yace, "banda kai Baba, ae dole naka yazama kaɗan, saboda yanzu ae tana gaba da kai, kuma ita ta zama baƙuwa, dole a karramata, kai kamma da tuwo miyar kukan ka aka baka, kabarta ta cinye daɗin", gaba ɗaya su mama dariya sukeyi, wanda Baba ƙarami kuma ya turo bakin shi gaba yana hararan Aunty hauwa. Ranan kam anji daɗin hiran, don ana idar da sallan ishaa yayah Auwal yazo, basu sukayi bacci ba sai wurin ƙarfe sha biyu, shima don ganin hamman da Aunty hauwa keyi ne yasa suka tashi. Kwanan Aunty hauwa uku Baba Umar yazo ɗaukanta, acikin kwanakin kuma ta zaga duk inda yakamata taje gidan ƴan'uwa, ranan da yazo duk wani abu namu na gargajiya, umma da Mama da Adda duk sun haɗa mata ita da Ummi, hattah ƴan gabɗori saida suka aiko musu da bushashshen zogale mai yawan gaske, haka Baba Umar ya tattara ta sai *NARABI* kwana ɗaya sukayi suka wuce lagos. Gidan Baba Umar 2bedroom ne, dole sai ya bar mun room ɗinshi, ya zama yana bin ɗakin mune, ranan da naje ansha drammer tsakanin su da suwaiba, don firr ta rufe idonta tayita zazzaga mishi rashin kunya, a dole babu inda Aunty hauwa zata kwana a gidan, ae tana da gidan ƴar'uwa ta tafi ta kwana mana acan idan ba neman magana ba, a wurinta kenan. Kusan dukanta Baba Umar yayi tukun ta nutsu, Aunty hauwa kuma ko kallun ta batayi ba, ɗakinta da aka nuna mata ta wuce, bata jira komai ba ta wuce toilet don yin wanka, tana fitowa ta ɗaukin wayanta dayake ta ringing, ganin sunan Ummi akai ya saka Aunty hauwa murmushi, da sauri ta kai wayanta kunnen, suna gama gaisawa, ummi ta mata sannu da zuwa, sanin halin Aunty hauwa da rashin haƙuri, suwaiba kuma da baƙin kishi, yasa ta ja kunnen Aunty hauwa sosai, dariya Aunty hauwa ta je tayi, "Ummi kenan, kina ga daga zuwan mu mata ta so ta maida gidan kaman filin sambisa, toh nidai na yau nayi shiru saboda naga yadda mijinta zai ɗau mataki, amma wallahi! Wallahi!! Ummi zuwa gobe kam zan nuna mata hauwa'un kule mage", Aunty hauwa ta ƙarasa faɗi tana kwashewa da dariya. "yanzu hauwa saboda Allah kin mun dai-dai? Ina gaya miki komai haƙuri akeyi amma kina nuna mun ke baki san da haka ba? Toh wallahi naji kinyi wani abu na rashin mutuncin toh zaki haɗu da ɓacin raina", ummi ta karasa faɗa ranta a ɓace. Aunty hauwa dariya tayi tayi kaman bata damu ba, haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayan. Duk yadda suwaiba take tunanin hauwa ta wuce saninta, domin da Aunty hauwa ta buɗe buhun bala'inta har saida suwaiba ta daina zaman parlour, kullum sai da kaji ta a ɗaki ta ƙure volume ɗin wayanta tana jin waƙa, wai don ta ɓata ran Aunty hauwa, dayake Aunty hauwa bata son hayani sai ta zama shine hanyar ɓata mata rai, amma Aunty hauwa ko kula ta batayi, watarana, sai da tabari suwaiba ta cikata da ƙaran waƙeƙe ta gama, ta fito zata shiga kitchen ɗaura abincin rana, da yake girkin suwaiba ne, wanda sukeyi kwana ɗaɗɗaya, Aunty hauwa ta ɗauko wani wayan cavel, ta samu suwaiba a gadon baya ta dinga tsula mata tana, "ni sa'ar kice da zan ce na hana ƙure vulome a gidan nan amma zakiyi kunnen uwar shegu", suwaiba irin ƴan firit ɗin nanne masu ƙaramin ruwa, kuma ga ruwan ciki, amma sai neman faɗa, Aunty hauwa kuma ƴar duma-duma ce, ga faɗa inda ta shiga bata nan ta ke fita ba, sai da tayiwa suwaiba lilis, kuma tace dole ta dafa musu doya da miyan stew don yau ita shi ta ke kwaɗayi, babu yadda suwaiba ta iya haka ta tafi kitchen ta fere doya tana kuka ta ɗaura , a zuciyar tana ƙissama abinda zata gayawa Baba Umar idan ya dawo, don ita bazata iya da dukan Hauwa ba, don yau shi ne rana na biyu kenan, gashi Aunty hauwa sauran ta 10days kafin ta koma, ita kaman bazata iya zaman kwana gima tare da ita a gida ɗaya ba, haka tayita aikinta tana share hawaye. Baba Umar sai dare ya dawo gida, da yake kullum sai 8:00 na dare yake shigowa, idan ya tafi tun 7:00am na safe, ko ruwa bai shaba, suwaiba ta fashe da kuka ta fara zayyana mishi irin dukan da Aunty hauwa ta mata, har da ƙari saida Suwaiba ta faɗa, shidai kallonta ya tsaya yana yi, wani zubin sai yaji kaman ya fashe da dariya, amma ya dake yace ta ƙira mishi hauwan. Aunty hauwa tana fitowa cikin wani jeans da t.shirt mai shegen kyau, ta ɗaure tulin gashinta da wani yellow ribon kalan t.shirt ɗin, har inda Baba umar yake zaune taje ta tsuguna a gaban shi ta gaishe shi cike da ladabi, ga wani juya ido da take mishi, sai wani ƙamshin daɗi ta keyi, fuska a sake ya amsa mata yana ta duban fuskanta da yasha kwalliya, har yaso manta dalilin ƙirantan da ya saka aka mishi, don ba ƙaramin son ƙamshi ya keyi ba, amma ga suwaiba sam taƙi turare, sai tace wai yana sakata mura da ciwon wuya, haka ya haƙura da ita, iya kacinta ta guga roll-on. Bayan Aunty hauwa ta gaishe shi sai ta gyara zamanta a ƙasa dai-dai inda ƙafafunshi suke tana mai binshi da murmushi, sai wani rangwaɗa ta keyi, gaba ɗaya ya maida hankalin shi kanta, sai jin muryan suwaiba yayi cikin kika tana cewa, "bazaka mata maganan abinda ta mun bane, ka tsaya kana kallonta"? Kallonta yayi fuskan shi a ɗaure yace, "me kika gaya mun tayi miki ma"? Hararan Hauwan tayi tana turo baki alaman zata fashe da kuka tace, "babu abinda na mata ta kamani ta min dokan kawu wuƙa, kuma wallahi bazan yadda ba sai ka sakata ta tsaya na rama duka na". Murmushi mai inganci Aunty hauwa tayi, muryah ƙasa-ƙasa irin na cikakkun mata da suka san kansu a gaban miji tace, "Hero kaci abincin tukun ka huta sai ka saurari haushin da ta keyi, Allah ya huci zuciyar ka, haushi mana zance domin miji ya wuni a waje nema mana halal ɗin mu, ya dawo a gajjiye ko ruwa bai sha ba, ki haushi da ƙorafi akan kishiya? Gaskiya Suwaiba ki gyara tsarinki, ta yayah hero zai samu nutsuwa da mu? Ya dawi bamu san a wani hali yake ba mu hau kai ƙara wurin shi? Ki bari yaci abinci yayi wanka, idan yazo parlour ya xauna sai ki kawo mishi ƙaran yau ni Hauwa na dake ki da kika ce mun karuwar gwamnati, ni kuma na kasa haƙuri nayi miki dukan tsiya domin kada bakinki ya saba da faɗin mun gama karuwanci mukayi aure, kinga idan na haihu ɗanmu yaji abinda kike jifan iyayen shi da shi bazai ƙira ki da mummy ba, kuma ni nafi so yarana suce miki mummy, ni kuma mamie, Hero kuma daddy", ta ƙara faɗi tana wani kanne mishi ido tana shafa cikinta tana ta rausayawa. Kuka suwaiba ta fara murya da ƙarfi ta faɗi,"wallahi da gaske ki karuwar ce hauwa, domin duk wacce taje school of nursing sunan ta karuwa, kuma karuwancin kikayi ae kika aure mun miji, yanxuma shi kikeyi agabanshi, jaka karuwa kawai", ta ƙara tana kuka mai sauti. Rausaya kai Aunty hauwa tayi kaman zata yi kuka ta dubi Baba Umar bayan ta miƙe tsaye tace, Hero zan koma ɗaki, don bazan iya cigaba da jin kalmar karuwa da matar ka ta ke yawan jifa na dashi ba, saboda bana son hayani, nafi so kaɗan huta tukun sannan ka sanar mata yadda na kawo maka budurcina lafiya ƙalau gidanka, kuma ka....." sai ta kasa ƙarasawa ta yi ɗakinta tana share hawayen idonta. Juyawa yayi yana hararan suwaiba, zuciyar shi sai tafasa ta ke mishi don jin kalmar karuwa da ta dangana matar shi mai daraja da tayi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/17, 14:32] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 35📑* *__________📖* Cikin muryan ɓacin rai Baba umar yace, "wallahi suwaiba na rantse miki da Allah, kika sake jifan matata da sunan karuwa, toh a bakin auren ki, ke idan kina da hankali koda karuwa na aura tana shirin haifa mun ɗa ko ƴa, ya kamata ki jefe ta da sunan karuwa? Ni na ɗauka idan kinji mai ƙiranta da wannan sunan sai inda ƙarfinki ya ƙare, amma kece da bakinki kike faɗa? Gaskiya banji daɗi ba, kuma bana son sakeji da ga yau", ya karasa maganan yana miƙewa tsaye ya wuce toilet ɗin da yake parlourn, don wataran yafi son shiga wurin, especially idan dare ne, don yasan lokacin babu baƙon da zai shigo ballantana yaga fitowan shi. Suwaiba kuma haɓa ta riƙe tana mai matuƙar jin tsoron furucin Baba umar, gashi ta sha dukan tsiya, ga rashin iya maganan ta da kula da miji ya jawu ko ta kan maganan ta ba abi ba, juyawa tayi ta dubi ƙofan ɗakin Aunty hauwa da ta leƙo ta ƙurawa suwaiba ido tana murmushi, a hankali Aunty hauwa ta ƙaraso cikin parlourn ta zauna gefen suwaiba tana ta jujjuya idon ta tana rausaya jikinta, ta gefen ido ta kalli suwaiba tana murmushin iskanci tace, "suwie darling! Wato ke baki san ta yadda ake bariki ba kuma kice zakiyi bariki? ae ba'a kishin banza yanzu, an waye suwaiba, ana kishi ne na nuna kulawa da miji da tsafta da kyautatawa, bawai banzan kishi irin naki ba, idan kince irin shi zamuyi toh ina mai tabbatar miki kece a ƙasa, gara ma ki saduda mu zauna lafiya, don ni babu mugunta a zuciyata, idan kace zaka shiga gona nane kawai zan taka maka burki iya sanin ka, so ina mai jan kunnen ki da babban murya suwaiba, idan kunne yaji toh jiki ya tsira", bata jira mai suwaiban zata faɗa ba ta wuce ɗakinta ta barta tana share hawayenta. Wani irin kulawa Aunty hauwa ta ke nunawa Baba umar, har sai da yakai ranan da zata karɓi girki dole sai ka gane rawan kan shi, don ko zaman parlour ba ya iya yi, a haka har hutun Aunty hauwa ya ƙare, tazo gidan mu yakai kusan sau biyar, wani lokacin Ummi zata je damu gidan mu ɗauki Aunty hauwa muje shan iska cikin lagos, wataran muje gidan abokan su Abba da Baba umar, a haka har Aunty hauwa ta koma Narabi, ko kwana biyu bata wuce ba ta koma school. Ten october 1980, shine ranan da aka haife mu nida Hassan, yau kuma ya kama 10 october 1985 Aunty hauwa ta haifi ɗiyar ta mai masifar kama da ita, lokacin da Aunty hauwa ta haifi ɗiyarta munyi tsalle da murna nida Hassan badon komai ba, sai don jin daɗin date of birth ɗinmu yazo ɗaya da sabuwar ƙanwar mu, ranan Aunty haiwa saida ta gajji da amsan wayan mu, don ko ta ajiye bata wuce 1hr zamu sake ɗauka muce, "Aunty ki saka mana kukan sistern mu", ita dai dariya kawai ta keyi, a dole sai ta ɗan bugi babyn ta fara kuka. Munajin muryan kukanta zamu fara tsalle nida Hassan muna tambayan Aunty, "Aunty don Allah muryan babyn irin na waye a cikin mu"? Dariya Aunty ta keyi tace, "muryan kukanta na rikici irin na Babana hassan ne, idan kuma tayi muryan wasa na Aminina Hussain ne, saboda haka muryan kune dukan ku", dariya zamuyi tayi muna murna, chan kuma sai Hassan yace, "Auntƴ dani take kama ko"? Nan ma dariya Aunty hauwa ta keyi tace, " toh maganan gaskiya baby kam da Ummi ta ke kama". Mu kuma jin tace da Ummi take kama sai duk muka fara tsalle muna cewa, "yehhhh Ummin mu tayi baby mai kyau", ita dai ummi da ta gajji sai ta karne wayanta tama kashe gaba ɗaya ra ɓoye. Umma ce ta tafi zama wa Aunty hauwa, inda Goggo da Addagana sukaje suka ga baby suka dawo, Kawu Auwal ma da Aunty ummi sunje sunga baby tare da Uncle Baba, ranan da sukaje kuma ranan muka zo tare da Ummi ana sauran kwana uku suna, Uncle baba yana kallon babyn yace, kai wannan yariya tayi kwaɗayi kam, dubi bakinta ɗan mitsul kaman ba ita bace tazo ta cinye mana ayan gidan mu, zuɓun mu, ferfesuop, gwaten tsaki, kai Bappah da su Mama sun kashe kuɗi kam a ɗan wannan mutsilan bakin, na ɗauka yara uku ne zasu fito domin irin cin da tayi ashe ɗaya ce me kama da uwa ma bada mama", ya juya yana kallon ummi yana dariya yace, "Adda Ummi nah! Duk da kuna kama da wannan mai kan zabuwan", ya nuna Aunty hauwa da bakin shi yana dariyan neman tsona, ita kuma sai hararan shi ta keyi tana kallon kawu auwalu akan ya saka baki, shi kuma sai kallon su ya keyi yana murmushi, don shi kafin kaji bakin shi a abu toh sai abu ya ɓaci, don dayawa ana cewa na ɗauko halin shi, amma har gara ni sau babu iyaka ina magana fiye da shi, uncle baba ya cigaba da maganan shi yana dariya, "wato ummi yarinyar nan sak ke, kaman ke kika haifeta, wallahi kyaun nan dai naki ta ɗauko, don uwar ta kanta yayi kojeje haka kaman na ƴan gabɗori", ya ƙarisa yana dariya, kowa da yake parlourn dariya yayi, ita kuma Aunty hauwa hararan shi tayi tace, "kuma wallahi kada kazo mun ranan suna, don ban gayyace kaba, kuma ƴar nan ko ta girma bazata ce maka kawu ba, kana ji kana gani zata ce maka Baba ƙarami mai kan kwakwa", ta faɗa tana hararan shi, hattah umma da tashigo da abinci wa su Ummi sai da tayi dariyan maganan Aunty hauwa, nida Hassan kuma duk wanda ya ɗauke ta sai mu koma kusa da shi muna taɓa yatsun ƙafan ta, Ummi ta karɓi babyn a hannun Uncle Baba tana murmushi tace, "naga ranan da zaku girma wallahi Baba, daga kai har hauwa ban san waya fi shiririta ba", ummi ta ƙurawa babyn ido tana duban ta da murmushi, chan ta dubi Kawu auwal tace. "Auwal dubi ƴar nan babu ƙaryah fa gaba ɗaya da ni take kama, nifa ko su Hassan dana haife su a cikina toh wallahi banji son su ba yadda nake jin son wannan yarinya, don Allah dubeta tun tana ƙarama kamanin ta ya nuna sosai, wannan kam idan ta girma za a daina cewa muna kama da hauwa trouble, sai dai ace ga mai kama dani", Ummi tana dariya tace, "hauwa wannan yarinyar kam ni zan raine ta, don gaskiya ta shiga raina matuƙa, ke kuma na sanki da dauriya zaki haifu wasu kwanan nan", ta faɗa tana duban Aunty hauwa da ta buɗe baki tana kallon ta, kawu auwal yana dariya yace, "maganan ki dutse babbar ya uwa, nima ina bayan ki, kinga su twins sun samu sister". Kallon Aunty hauwa uncle Baba ya tsaya yanayi, yana jiran yaji abinda zata ce ta tofa, Aunty hauwa ta kalli ummi tace, "gaskiya Ummi kinga wannan ƴa macece, ki bari sai na haifi namiji sai na baki ki haɗa ki zama maman ƴan maza, nikan ina son wannan ɗin, amma kiyi fatan Yayah auwal su haifi ƴa mace sai su baki, don kinga Aunty ummi sai wani ɓoye cikinta ta keyi cikin hijabi, bata san sa'idawa har sun gani sun sanar dani ba", ta faɗa tana dariyan uncle baba daya buɗe baki yana matan kallon marar sirri. "zakuji da shi ae da gulmar ku, kullum kuna ɓatar da mutane akan ku baku zaman lafiya, kuma wallahi Adda Ummin mu, duk gidan mu babu masu gulma na haɗin kai kaman wanda sukayi gware suka zo duniya irin Hauwa da Baba ƙarami, babu garin Allah da zai waye basu ƙira junan su ta waya sunyi gulma ba, kuma duk halin da hauwa ta keyi shiyake ƙara ɗaurata akan network", Kawu auwalu ya faɗa yana duban su yadda suke ta dariya har da tafawa. Daidai lokacin Baba umar ya shigo suka gaisa da su ummi, inda ummi take gaya mishi yadda sukayi da Aunty hauwa akan babyn, yana murmushi yace, "wallahi babbar ya nidai na baki uwata duniya da lahira, duk ranan da hauwa ta yaye ta ki karɓeta, ko ina raye ko bana raye, na baki ita don na yaba da karamcin ki, kuma wallahi naso saka miki takwara da yarinyar nan, toh sai mahaifina yace yana so nasaka sunan mahaifiyata, amma insha Allahu idan Allah ya sake bamu ɗiya mace toh tabbasa, *NANA FATIMA* zan saka, amma wannan ma bai ɓaci ba in sha Allahu na baki ita duniya da lahira". Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi, murya a hankali Aunty hauwa tace, "insha Allahu ma hero kana nan sai munyi ƴaƴa goma sha biyu tare da kai, kuma insha Allahu wannan yarinya shayar da ita kawai zanyi, ina yayeta zan bawa Ummi nah, don nima ikon tace ballantana abinda na haifa", hawaye ta share a idon ta ta dubi Ummi da ita ma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi, "Ummi na miki alƙawari ko nuna so bazanyi wa wannan yarinyar ba, kuma zan nuna miki ni ɗin ƴar halak ce, domin zan kawar da kaina akan ɗiyar nan, dama ni Hassan da Hussain ne nawa ƴaƴan", ta faɗa tana share hawayen ta. Ranan sunan ƙanwar mu taci suna mai girma da daraja, wato sunan uwar muminai, *NANA AISHA* ƴar uwar da babu irin ta a duniya ƴar'uwar da muke mata son da bamuyiwa kan mu, wanda muka kasance ƴan biyu kyautar Allah, amma bamu son junan mu yadda muke son ƙanwar mu Nana Aisha, wanda yawan ci munfi ƙiranta da Aisha". anyi suna da kwana biyu mukaje misau muka gaida su Bappah, muka ƙara kwana biyu tukun kawu auwal suka rako mu jos domin mu shiga jirgi mu tafi lagos, mun tsaya a Narabi muka sake ganin sistern mu Aisha, muna cikin farinciki muka shige airpot muka tafi lagos. Aisha tana da shekara ɗaya Ummin mu ta haɗa mana birthday party a lagos, lokacin Aunty hauwa ta gama school ta dawo lagos da zama, Ranan kaman baza mu mutu ba don daɗi, gashi Aishan mu tana tafiya abin sha'awa, ga wani kyau da gashi da yarinyar ta ke dashi, wanda kowa ya ganta sai ya ƙara ganinta, kaya iri ɗaya Ummi ta saya mana, wani wandon jeans ne Blue da wasu rigunan polo Red colour, sannan Baba umar ya saya mana wasu kuma, namu baƙin wandon jeans da blue riga, ita kuma Aisha blue skirt na jeans da pink riga, ranan iyayen mu sun kashe mana kuɗi ba kaɗan ba, Aunty suwaiban Baba Umar babu yadda ta iya da masifan Aunty hauwa, dole ta dawu kaman wata yarinyar ta don tsoro, duk inda Aunty hauwa ta juya ta haka take juyowa, sai dai kuma Aunty hauwa babu matsalan cutar da mutun, saida buhun bala'i kawai, shima idan an taɓo ne, mun samu kyaututuka kam babu iyaka. Mama da Addagana da su kawu auwalu da uncle baba da Aunty ummi da Ɗanta wanda baifi 5month ba mai sunan Bappah, ana ce mishi Affan, duk sun zo mana lagos, daɗi muke ji kaman babu gobe, haka akayi ta pictures ana raha, da dare ranan Aunty hauwa tace ita a gidan mu zata kwana, domin ganin ƴan uwa duk sun haɗu, haka Baba umar ya amince mata, akan tayi kwana biyu idan su Mama da Adda sun tafi zaizo ya ɗauke ta, abin daɗin kuma aranan ya bawa Aunty hauwa da Aunty suwaiba kyautar mota, Aunty hauwa ta ɗauki Ash, Aunty Suwaiba kuma ta ɗauki black, duk muka haɗu muka taya su, murna, baby Aishan mu kuma ya bata kyautan gidan gonan shi da yake garin Narabi, sannan ya buɗe mata account ya saka 5million a ciki. Duk wannan kyaututtukan a gaban Abban mu akayi shi, bayan an ƙira baban narabi an sanar mishi, Baban Narabi yana dariya yace, "Toh godiya muke Baban mu, domin wannan kyauta da kayiwa uwargida na wani da ita kayiwa, domin zan cigaba da riƙe mata har sai ta girma, idan mai sonta ya fito sai muyi shaɗi da shi, wanda yaci gasan ya aureta ya riƙe mata, don nasan ni zan cinye gasan", ya faɗa yana dariya, duk su Abba ma dariyan sukayi domin a handsfree Baba Umar ya saka. Aunty Suwaiba tana dariya bayan ankashe wayan tace lallai muƙi wayon Baban Narabi, wannan golden girl ɗin ƴar mun ae sai mun darje mazan duniyan nan kafin mu yarda mu bata mijin, ina zata kai Baban namu alokacin"? Kowa dariya yayi ana kallon Aisha da ta ɗale kan cinyan Babanya sai ja mishi gashin gemun shi ɗan kaɗan da ya ajiye ta keyi, shi kuma sai bin ta da dariya yakeyi. Chan kuma ta koma tana jan gashin kanshi sai gwalamniyan surutu ta je mishi yana ta dariya, yana duban ta da murmushi a fuskarshi, batare da ya dubi idon kowa ba yace, "Gambo" Abba ya ɗaga kai yana duban shi batare da ya amsa ba, Baba Umar yayi murmushi yana kan wasa da jelan gashin Aisha yace, "Gambo duk duniyan nan idan ka cire Baban narabi da uwata da ta daɗe da rasuwa, toh Allah bai taɓa sakamun son abu ba aduniyan nan irin Aisha Humairah, ina sonta har ban san irin shi ba, wataran idan suna bacci da uwar sai na tashi basu sani ba, na ɗauketa nayita kuka, domin ina jin ajikina kaman bazata samu gatan mahaifi ba, kaman bazan daɗe tare da ita ba, sai inajin tausayinta hala ko ita kaɗaice rabo na? Ko bazata samu ɗan'uwa ba? Hala ita kaɗai zata kasance abinda zan haifa, amma idan na tuna tana da kai tana da Ummi, tana da Hassan da hussain, sai na samu nutsuwa a zuciyata, domin nasan bazata taɓa maraici ba a duniya, bazata taɓa kukan rashin ƴan'uwa ba, domin Hassan da Hussain sun ishe ta rayuwa, ga kuma Affan ta samu ƙanin ta abokin wasan ta, yadda Hauwa da Baba ƙarami sukeyi haka ita ma zata samu nata ƴan'uwan", ya faɗa fuskan shi da murmushi yana share hawayen idon shi kuma. Jikin kowa yayi sanyi gaba ɗaya a parlourn, a hankali Aunty suwaiba ta saka hannu ta ɗauki Aisha tana share hawayen idon ta tace, "narasa mai yasa kake yawan irin wannan zan tukun kwanan nan, nifa har kasa ina jin tausayin kaina da kuma hauwa da wannan yarinyar da Allah ya bamu kyautanta, duk da ka ƙwace mana ita ka kyuatar, amma bamuyi fushi ba, muna fatan baɗi hauwa ta haifa mana ƴan biyu, ta bani ɗaya ta riƙe ɗaya, bayan wani shekara ta kawo mana ƴan uku, lokacin kuma ni zan ɗauke su dukkan su, amma idan kana wannan furucin sai kasa jikina yana sanyi, faɗuwar gaba na yana yawaita, tsoro yana kamani, ina ji ajikina kodai bani da rabon riƙe ɗan ka a hannuna ne har na koma ga ubangiji"? Ta faɗa tana share hawayenta. Juyar da kai Aunty hauwa tayi tana kuka a hankali, murya yana rawa tace, "nidai ka daina faɗar mun da gaba na hero, muna nan tare har tsufan mu insha Allahu, ke kuma suwaiba ki daina mun fatan haihuwa dayawa, kema insha Allahu baɗi zaki haifa mana ƴan biyun, kidai na fitar da rai daga alkhairin Allah, kuma ni nama fasa kwanan ku tashi mutafi gida kawai, idan yaso mubar musu Aishan a gidan su ni nama yaye ta daga yau," ta faɗa tana miƙewa. Baba umar yana dariya yace, "wallahu baki isa cire mun uwata a nono tana shekara ɗaya ba, ke hauwa kifita a idona fah", ya faɗa yana dariya, sannan ya dubi Ummi da ta sunkuyar da kanta tuntuni yana dariya yace, "Babbar ya uwa, wallahi kada kibari koda wasa Haiwa ta cire mun uwa a nono, kuma ko wani irin tashin hankali ne zai sameta toh ta maida hankalinta akan uwata", ya faɗa yana miƙa hannu wa Abba da yakasa cewa uffan sai kallon kowa yake yi kawai. Aunty suwaiba ita ma miƙewa tayi tana dariyan hauwa tace, "ke kululwa yaifa babu inda zaki bimu, kima je ki gyara wurin kwanciyar da kyau yau a gidan nan, kibar ni yau nabi mijina, ke kuma bayanzu ba, ki zauna ciki ƴan'uwanki kusha hira, ki kula mun da sanyin idona kuma da kyau, ki bata non tasha ta ƙoshi bayan kin mata wanka ta huta gajjiyan yau", sannan ta ɗago Aisha ta sake duban Ummi tace, "Ummi naso ace idan ɗiyata ta girma na haɗa ta aure da Hassan ko Hussain, amma kuma Babanta yace su ɗin ƴan'uwanta ne, ke kuma uwace, toh na haƙura ina yiwa hasken zuciyata addu'an Allah ya bata miji nagari jarumin gaske, wanda zai sota da amana, saboda bana son Aisha tasan ba Ummi bace ta haifeta, kuma bana son ta san su Hassan ba ƴan'uwanta ciki ɗaya bane, saboda haka Ummi da Abba mun bar ku da ɗawainiya Allah ya baku ikon riƙewa, ke kuma Hauwa kiyi haƙuri da rayuwa ki rungumi kowani irin ƙaddara da hannu bibbiyu a rayuwar ki, ki yafe mun rashin fahimtar ki danayi a baya, kuma insha Allahu zaki haifo mana wasu yaran masu irin kyaun ki da sakalcin ki da wannan rikici da yangan," ta kara faɗa tana guge hawayen ta tana dariyan Aunty hauwa da ta tashi ta rungumeta tana kuka, daga baya ita ma Aunty suwaiban kukan ta fara. Ganin haka sai Baba umar yazo ya jawo hannun Aunty hauwa yana dariya yace, "bari muyi waje na rarrashi kayata kafin ku fito," ya jata sukayi waje, parlourn kuma duk anyi tsit, sai sautin muryan kukan Aunty suwaiba ,Ummi da uncle Baba da Aunty Ummi da wata ƙanwar Baba Umar da tazo daga jos kawai akeji, wanda ita ma a wurin su Aunty hauwan zata kwana, sai da suka bawa Baba Umar da Aunty hauwa good 30minutes tukun suka bi bayan su, lokacin nida Hassan duk mun yasu a parlourn munyi bacci, ɗayan gefen ma Affan yayi bacci acan ɗaki wurin su Mama wanda basu san me akeyi ba a parlourn, amma Aisha idon ta biyu tana rungume jikin Aunty suwaiba, a haka suka fita waje inda su Aunty hauwa suke zaune a mota ita da Baba Umar yana ta aikin rarrashinta. Kiss Baba Umar yayiwa Aisha bayan ya miƙa ta wa Aunty hauwa, sannan ita kuma ya ɗan lakuce kumatun ta yana murmushi yace, "bye bye my heart"! Aunty suwaiba tana tsokanan ta tace, "hauwa yau kam na miki wayo na tafi da miji na, zamuje muyita shan soyayyah babu ke, yau har rawan da kika taɓa mishi ina kallon ki ban kuƙa ki ba zanje na mishi", ta faɗa tana dariyan Aunty hauwa da ta ke hararan ta da wasa, a haka suka shiga mota suka tafi suna ta ɗaga mana hannu. Dama su Aunty suwaiba basu bar gidan mu ba sai wajen 12:00pm na dare, toh Ummi suna dawuwa aka tattare gift ɗin da muka samu aka kai ɗakin mu, sannan kowa yayi wanka yayi shirin kwanciya, wanda Aunty hauwa ko Aisha batayi wa wanka ba, sai share hawayenta ta keyi, Ummi ce ta ɗauki Aisha tayi mata wanka ta bata cerelac ta sha, ta tafi da ita ɗakinta wurin Abba, suna nan har wajen 2:00 ita da Abba basuyi bacci ba, Abba sai juyi yakeyi, chan sai Ummi ta dube shi tace, "me ya hanaka bacci ne"? Murmushi yayi yace, "ke mai ya hanaki baccin"? Ajiyan zuciya Ummi tayi ta dubi Aisha da ta ke ta kallon sillin ido ta nuna mishi ita tace, "ga wanda ta hanani bacci, domin nafi so tayi bacci tukun", juyawa yayi ya kalli Aisha, a hankali ya jawo ta kusa da shi yace, "auta na me ya hanaki bacci"? Aisha ta kalle shi kaman ta gane mai yace, tana gwalamniyanta tace, "Dada" wato tana nufin Daddy, yadda take ƙiran Baba Umar da shi. Abba zai bata amsa sai yaji ƙaran wayan shi, da sauri ya tashi ya ɗauka ya kai kan kunnen shi, bayan ya amsa Ummi taji yana amsawa da "ehh nine, akwai wani matsalah ne officer"? ya faɗa jikin shi duk rawa yakeyi, da sauri ya miƙe jiki na rawa ya ce, "INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN" , sannan da ƙarfi yace, "Officer kuna wani asibitin ne"? A ɗakin su Aunty hauwa kuma Aunty Ummi da take kwance gefen Aunty hauwa ta fara bacci kawai taji Aunty hauwa ta miƙe zaune da ƙarfi tace, "Wayyo Mama zuciyana yana tsinkewa, nikan mama kawai zan bi mijina, ina tsoron wani abu ya same shi", ta tashi da sauri tajawo hijab ɗin da sukayi sallah ta saka ajikinta, tayi hanyar parlour tana faɗin, "nikan sai naje na tashi Abba ya kaini wuron miji na", Adda zuba mata ido tayi tana kallon ta, Aunty Ummi da ƙanwar Baba Umar ma tashi sukayi suka miƙe tsaye suna kallon ta, suma daga dukkan alamu shirin binta sukeyi, Mama da sauri tace, "ke Hauwa kada kije ki tashi bawan Allahn nan, kiyi haƙuri zuwa safiya sai ya kaiki idan Allah ya kaimu", amma ina Aunty haiwa tunin tayi parlour, wanda da sauri su Aunty Ummi suka bi bayan ta, tana fitowa parlourn kuma yayi dai-dai da fitowar Abba cikin gudu-gudu Ummi na binshi a baya a ruɗe tana tambayan shi lafiya ina zaije a cikin daren nan? Abba yana ganin Aunty hauwa yaja ya tsaya ya ƙura mata ido jiki shi sai rawa yakeyi, itama ƙura mishi idon tayi tana kuka tace, "nikan Abba ka kaini wurin mijina nikan", ta ƙarasa da sunkuyawa ƙasa tana kuka, rufe idom shi gam da ƙarfi ba tare da ya furta komai ba, Ummi kuma sai tambayan shi ta keyi abinda ya faru? *ZAINAB IDRIS* ta group ɗina mai suna *MUYI NISHAƊI* wannan shafi nakine kyauta na baki, kuma na cika miki alƙawarin yi miki typing mai yawa yau, da fatan zai faranta miki, nagode sosai da kulawanki gareni, da kuma book ɗina. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/18, 14:07] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *FAUZIYYA A.A WANNAN SHAFIN NAKI NE, INA ƘARA MIKI TA'AZIYAN RASHIN MIJINKI ALIYU BABAGANA ZAKI (ABBA). TABBAS INA KUKAWA KAINA INA KUKA MIKI RASHIN GWARZON MIJINKI MAI MIKI ƘAUNA FISABILILLAH, INA MIKI ADDU'AN ALLAH YA BAKI MADADIN SHI, ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR HIDAYA, ALLAH YA SA MIKI DANGANA A ZUCIYARKI, TABBAS FAUXY NA TAUSAYA MIKI, HAR YAU ABIN YAƘI BARIN ZUCIYATA*. *SHAFI NA 36📑* *__________📖* Daidai lokacin su kawu auwal suka shigo daga ɗakin ƙofar gidan shi da uncle Baba, kowan su cikin firgici yake kallon Abba, ganin haka Abba ya buɗi baki yace "duk kanku kuyi haƙuri ku zauna a gida, idan naje na dawo sai kuji me yake faruwa, amma yanzu nima bani da tabbacin me ya faru, amma Auwal da Baba su zamuje tare da su, duk yadda ake ciki zan ƙira na sanar da ku", ya faɗa yana shirin fita daga parlourn. Ummi ta riƙo hannun shi tana duban shi da kyau tace, " ba haka naji ka faɗa a waya ba, daga dukkan alamu wani abu ya faru kake ɓoye mana, ko wani abu ya samu Baba Umar ne kam"? ta ƙara sa faɗi hawaye na zubu mata. Da sauri Aunty hauwa ta matso kusa da Ummi tana zare ido, hannun ta duka biyu akan ƙirjinta, "Ummi nah me kikaji yace ya faru da miji na? Ina fatan dai ba hatsari sukayi ba ko?" sannan ta juya wurin Abba da sauri da yake shirin barin parlourn, hannun shi ta kamo murya na rawa tace, "zan bika naje wurin miji na," tana jijjiga kai tana hawaye tace, "nikan babu abinda ya faru da mijina, ka kaini gidan mu nagan shi kawai", ta ƙarasa faɗa jikinta yana rawa sosai. Kawu auwal ne yazo yakama hannun ta ya miƙawa Mama ita, sannan ya dubi Ummi yace, "haba ummi uwa, keda zaki kwantar wa hankali kuma kece mai son dagula komai? Kuyi haƙuri yadda Abba yace muje duk abinda ake ciki ni da kaina zan ƙiraku ko shi bai ƙira ba" yana gama faɗi yabi bayan Abba da suka fita tunda ya matsar da Aunty Hauwa a jikin shi, suna shiga motan Abba yaja su sai asibitin da aka musu kwatance, suna parking saiga wata motar ƴan custome tana parking a gefen su, Abba zaro ido yayi don ganin shugaban su Baba Umar ya fito da sauri saura suna binshi a baya, ga police sama da goma a asibitin. Jiki na rawa Abba ya dube su yace, "Allah yasa bai wahala sosai ba, Umar ne suka samu accident a hanyar su, ya faɗa ganin yadda duk suka fita a nutsuwar su, babu wanda ya iya buɗe baki ya amsa mishi sai binshi kawai sukayi zuwa cikin asibitin. Suna shiga kai tsaye emergency suka wuce inda suka hango yawan ƴan custome ɗin a wurin, da sauri Abba ya ƙarasa, Dr ne da suke tsaye da police ɗin ya ƙarasu gaban Abba, yana duban shi yakaranto mishi number shi na waya, gyaɗa kai Abba yayi alaman shi ne. Dr dafa kafaɗan Abba yayi yana ce mishi "am sorry sir, munga number ka a wayan shi da sunan ɗan'uwa, kuma kaine last mutumin da kukayi waya da shi, toh ganin faruwar accident ɗin shine muka neme ka, sannan a aljihun shi muka samu I.D Card ɗin shi da ya nuna mana shi custome ne", sannan ya maida kallon shi kan ogan ƴan custome ɗin yace "mu ƙarasa ku ganshi," da sauri kowa yabi bayan shi. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shi ne kalmar da yake fita daga bakin kowa da ya ɗaura idanu akan Baba Umar da Aunty suwaiba. Jiki na rawa Abba ya ƙarasa kan gawan Aminin na shi kuma ɗan'uwan shi Baba Umar ya kife kanshi a dai-dai inda jini yake ta kwaranya, ya kife yana kuka yana salati iya ƙarfin shi, da ƙyar aka ɗago shi, jiki na rawa ya dubi Dr yace, "meyasa kace mun accident yayi? Yayah kake so na fuskanci dattijon mahaifin mu da wannan mummunan labarin? Yayah ma zanyi na sanar da matar shi wannan batu yadda tun ɗazu bata da nutsuwa? Waye zai iya gaywa ɗiyar shi ƙwalli ɗaya ta rasa mahaifinta data kasa runtsawa a daren yau"? Riƙe shi Kawau auwal yayi yana faɗin kalman "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un", sannan ya samu wuri ya zaunar da shi, a hankali ya dubi Baba ƙarami da ya kife a ƙasa ya ɗaura hannu akai kaman mace yana ta rusa ihu, gefe ɗaya kuma shugaban su Baba Umar ne da girman shi shima kukan yake tayi baya kallon kuwa. A hankali police ɗin yace," Anyi abu bai daɗe ba mutanen mu suka ƙarasa wajen, domin jin ƙaran harbi, abinda ya faru wato mun fi tunanin kidnafers ne suka aaikata musu hakan, domin alama ya nuna sunƙi tsayawa ne aka harbi mai tuƙa motan, ita kuma matar motar ce data ƙwace suka dinga kifawa, anan kwananta ya ƙare domin babu harbi a tare da ita, saidai wuyanta ya karye, shi kuma ga harbi akan shi kuma ga karaya a kunkuminshi da sauran wurare masu yawan gaske", bayani Dr shima ya cigaba da yi musu, wanda daga uncle Baba har Abba babu mai fahimta, Kawu Auwal ne kawai yake fahimtan abinda suke faɗa, tare da shugaban su. Abba basu aka basu gawan ba sai wurin Asuba, inda Abba ya bawa shugaban su Baba Umar number Baban Narabi akan ya gaya mishi, da ƙyar yayiwa Baban Narabi bayanin rasuwa, wanda shi kuma Baban mai ƙarfin imani yayi ta godiya wa ubangiji, sannan yace su taimaka su taho mishi da gawan zuwa jos, yana son a rufe su anan, haka shugaban ya bashi tabbacin zasu aikata. Shawara Dr ya basu akan a musu wanka a asibitin saboda ɗaga hankalin mutanen gidan, kuma su Abba sukayi na'am da hakan, ma'aikatan asibitin suka wanke gawawwakin, aka shirya su a cikin likkafani, sannan su Abba suka wuce gida domin sanar musu, tunda sukayi parking Abba ya kifa kanshi akan sitiyarin motan ya fashe da kuka, Kawu auwal ne ya saka hannu ya riƙo uncle Baba da ƙarfi ganin zai fita da gudu yaje ya tayar musu da hankali, zaunar da shi yayi yace, "ka zauna a motan bari na fara shiga". Yana shiga ya tarar da dukkan mutanen gidan zaune zuru-zuru a parlourn, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce kwance akan cinyar Mama sai kuka ta keyi, da sauri ta tashi ta nufi kawu auwal, jiki na rawa ta kamo hannun shi tace, "ka kaini wurin miji na yayah auwal, ina sukaje ne shida Aunty suwaiban"?, duk yadda yaso ya daure kawu auwal ɗin sai ya kasa, kawai samun kanshi yayi da fashewa da kuka ya rungume hauwa gam a jikin shi, Addagana ganin haka ya saka ta sunkuyar da kanta tana ta wasa da ƙasan hijabin jikin ta, ga wani haki da ta ke tayi lokaci ɗaya, Ummi ce ta matso jikin su tana tambayan kawu auwal, "ina sauran suke? Me yasamu Baba umar ɗin ne? Ya samu rauni ne sosai"?. Buɗe ƙofan yasa hankalin kowa ya koma kan Uncle baba da ya kafe a wurin yana kuka kaman ƴa mace, da gudu Aunty hauwa ta je ta rungume shi tana, "ɗan'uwa na kai ne kafi kowa damuwa dani, nasan zaka gaya mun komai, don Allah ina mijina da ƴar'uwata? Sun koma gida lafiya ko"? Uncle Baba yana ɗaga mata kai yace, "tabbas mijinki da ƴar'uwar ki a yau sun koma gidan su na gaskiya, tabbas sun amsa ƙiran ubangijin mu a lokaci ɗaya, sun tafi sun bar mu da tsananin kewar su a zuciyar mu," ya saka hannu ya dafa shoulder Aunty hauwa ya cigaba da faɗin, "tabbas ƴar'uwata yau kam zuciyar ki ta ƙuna, yau kinyi rashi mafi girma a rayuwar ki, yau kam mun rasa jarumi, nagarin mutum Baba umar da matar shi, sakamakon harbi da iskan gari suka mishi a hanyar komawa gida, lallai sun jefa zukata dawa cikin maraici ƴar'uwata, Allah yajiƙan su da rahma". Kumawa da baya da baya Aunty hauwa ta farayi tana bin uncle baba da kallo bakinta a buɗe, har saida tayi tuntuɓe da ƙafan mutum tukun ta tsaya, a hankali ta juya tana bin kowa da kallo, bata iya cewa komai ba bata cigaba da kukan ba, sai ido da take ta buɗewa kaman zasu fito su faɗi ƙasa, a hankali ta riƙe hannun Ummi tace, "Ummi Baba umar da Aunty suwaiba wai sun rasu? Wai sun mutu dukkansu yau, kinsan me Hero yace mun ɗazu? No baki sani bama, ni kaɗai na sani", sai ta sake hannun Ummi ta juya wurin Addagana da ta fara share hawaye da ƙasan hijabinta, har ƙasa ta tsuguna ta dafa ƙafan Adda tace, "Adda mijina ya rasu, baban ɗiyata wancar", ta nuna Aisha da ta kwanta a jikin sister Babanta da take ta kuka kaman ranta zai fita, sannan ta dawo da kallon ta kan Adda ta sake cewa, "mijina ya rasu yau, mijin na ya rasu shida suwaiba yau," sannan ta sake mikewa ba tare da ta furta komai ba, ta tafi gefen Mama ta kwantar da kanta a kafaɗan mama. "Mama mijina ya rasu ya barni, idan mun tashi za a binne shi a kabari shi kaɗan shi, ni kuma za a dinga ce mun kiyi haƙuri," ta juyo da fuskar Mama da ta ke ta kuka kaman ranta zai fita tace, "bazan kula kowa ba, zanyi shiru ina kallon kuwa, hala mijina yaji tausayi na ya dawo, zan kwanta nayi bacci yanzu", ta faɗa bayan ta miƙe ta hau kan tree sitter parlourn ta kwanta. Kowa da yake parlourn kallon Aunty hauwa ya keyi yana kuka na fitar hankali, don duk sun lura abun ya mata yawa ne, har ta rasa tunanin da zatayi, ita kuma Aunty hauwa rufe idon ta tayi gam, Ummi da sauri ta juya tana kallon kawu auwal da ya durƙusa a wurin yana kuka kaman ba shi ba, "auwal ina Abban su ne"? Ba tare da yace mata komai ba ya nuna mata hanyar waje, a guje Ummi tayi hanyar waje. Bayan sun idar da sallan asuba Abba ya wuce asibiti shida uncle baba, acan suka haɗu da shugaban ƴan custume da wasu abokan Baba Umar, anan aka yi ta shirye-shiyen tafiya da gawawwakin, bau ɓata lokaci aka gama komai zuwa 9:00am, dukkan su suka shiga jirgi sai jos. A chan Narabi kuma duk mutanen misau sun iso tun wajajen 9:00 na safe, an cika a ƙofar gidan Baban Narabi, ga mutanen tilde ma duk sun hallara, cikin gida kuma sai kuka mata sukeyi, inda Baban Narabi ya fito ta kofar parlourn shi ya zubawa ƙanwar mahaifiyar Baba Umar da take aure a cikin Narabin da ƙannen Baba Umar ɗin mata da suka rungumeta suna ta kuka kamar ransu zai fita, murya a hankali ya ƙira sunanta. "Halima! Soyayyar da zaku nunawa Umar kenan? Irin Godiyar da zaku nunawa Ubangijin mu kenan? Don Allah kuyi haƙuri kuyi mishi addu'a don yanzu shi yafi buƙata a gareku, sannan ki kwantar wa yaran da hankali ga shi sun shigo gari da mamatan, kuma zasu shigo dasu cikin gidan domin muga fuskan Umar ɗan aljannah", ya ƙara faɗi muryan shi yana rawa, a hankali ɗan shi na biyu ya riƙe shi suka fita zuwa ƙofar gidan, domin jin tsayuwar mototi da yawa. Har cikiɓ parlour aka shigo da gawan su Baba Umar, inda Baban Narabi yace maza iyayen Suwaiba da ƴan'uwan Baba Umar su fara zuwa su gansu su musu addu'a kafin mata su zo. Ɗaɗɗaya aka dinga zuwa ana musu addu'a, tunda bawai fuskarsu aka rufe ba, duk wanda ya musu addu'a cikin ƙanne da iyayen Baba Umar sai sun zubar da hawaye, Baban Narabi ya sunkuya kan gawan Baba Umar Ya mishi addu'o'i masu yawan gaske, sannan a ƙarshe ya saka hannu ya share hawayen shi yace, "ya kai wannan ɗa mai yawan biyayya a gare ni, ina maka albishir da ni kam mahaifinka na yafe maka duk abinda kake tunani kamun da ga zuwan ka duniya Umar, halinka na gari ya bika har cikin aljannar fiddausi, Umar na yafe maka duniya da lahira, Umar ka tafi ka barni da tarin yawan kewar ka a zuciyata, amma Allahn da ya bani kai yafini sonka, Allah ya maka rahma kai da iyalinka", ya saka hannu ya shafa fuskan sanna ya miƙe ya koma kan kujera ya zauna yana jan charbi. A haka iyayen suwaiba da ƙannenta da yayunta mata suka shigo suka mata addu'a, daga nan aka shigo da Aunty gauwa da ta ke rungume a jikin Ummi, da sauran ƴan'uwan Baba Umar mata da umma halima da su umman misau da su Mama, kuma har zuwa lokacin babu hawaye a fuskar Aunty hauwa, gefe ɗaya kuma ƙanwar shi na rungume da Aisha a hannunta. Umma Halima ce ta sunkuya akan Baba Umar tana kuka, addu'an ma kasawa tayi, ganin haka Mama ta riƙo hannunta ta matsar da ita, tana ta bata haƙuri, Ummi ta riƙo hannun Aunty hauwa har gaban gawan suka durƙusa kusa da fuskar su, murya na rawa tace, "Hauwa kiyiwa mijinki addu'a, ki yafe mishi shi da ƴar'uwar ki. Murmushi Aunty hauwa tayi tana kallon Ummi tace, "bai mun komai ba, na yafe musu gaba ɗayan su", "toh ki musu addu'a Hauwa" cewar Baban narabi daga inda yake zaune. A hankali Aunty hauwa ta dinga yi musu addu'an samun rahma, sannan a ƙarshe ta miƙa hannu aka bata Aisha, ta dubi fuskar Aunty suwaiba ta dubi fuskar Aisha tace, "wannan maman kice ta tafi ta barki ba tare da ta jira girmanki ba, din naso kada tayi kukan rashin haihuwa irin yadda maman mu batayi, amma sai ta tafi ta barmu tun yanzu, Aisha mun yafewa Aunty suwaiba duniya da lahira, kuma zamuyita mata addu'a har ƙarshen rayuwar mu ko Aisha"? Sannan ta dubi fuskar suwaiba tace, "dama mutuwa zakuyi tare shine kuka mun wayo kuka tafi tare ku kabarni ni kaɗaiko?" ta shafa kan Aunty suwaiba tana share hawaye taja likkafanin ta rufe mata fuska, ƴan'uwan Suwaiba kuma sai kuka sukeyi ganin yadda hauwa ta yi, sannan Aunty hauwa ta juya saitin Baba Umar tace. "Baba Umar ɗina, zan tamaka addu'a yadda kace, ban san da gaske mutuwar zakayi ba da na biyoku mun tafi tare, bansan me kake so nayi ba babu kai ka tafi kabarni, bayan Ummi zata kula da Aisha, Abba zai maye gurbinka a wurin Baban Narabi, me yasa kuka tafi babu ni? Sannan ta juya ta dubi Baban Narabi wanda lokacin muryanta ya fara rawa tace, "Baba nifa ina son mijina, amma yanzu kowa zai ta cewa mijina ya rasu nayi haƙuri, toh ta yayah zanyi haƙurin?" ta ɗago Aisha ta nuna mishi tace, "Baba sunanta marainiya, ni kuma maman marainiya, Baba ina zan rufe kaina na yita ƙiran mijina da ƙarfi har sai ya tashi? Ina so Baba Umar yaji tausayina ya tashi muyita zama, ni kuma nayita haihuwa ina bawa Aunty suwaiba har yara goma sha biyu, vazan gajji ba, yadda ta keso hakan zanyi," sannan ta dubi mutanen da ke parloun da suke ta kuka tace. "kowa ya fita ya barni da su, zanyi ta xama dasu, idan sun tashi sai mu fito tare, amma ina son so, sukuma sun tafi sun barni, bazan iya ba Ummi, bazan iya zama babu su ba , Baba nah", ta kara sa tana kuka mai ƙarfin gaske, dukkan su ƴan parlourn kuka suke yi, hattah Baban Narabi kukan yakeyi bai hanata maganganun da ta keyi ba. Bappah ne ya taso daga inda yake ya saka hannu ya ɗago ta daga kan gawan da ta kefe tana kuka, bai iya ce mata komai ba, ya miƙar da ita tsaye, suna haɗa ido ya dinga jijjiga mata kai alaman tayi shiru, bai iya cewa komai ba sai hawaye yakeyi, "Bappah miji nane fa kwance a ƙasa wai ya rasu, Bappah kuna nufin mun rabu kenan da shi har abada? Wallahi Bappah ina son mijina sosai, nifa yarinya ce, kaga gawan mijina, amma ka chan mijin Ummi shi bai rasu ba sai nawa, Bappah kai ma fa ka tsufah kaida Baban Narabi amma duk kuna nan sai mijina da bai tsufah ba", ta rungume Bappan tana kuka mai ƙarfi. Liman ne ya bada umurnin a fitar da gawawwakin, ana ɗaga su za'a fita Aunty hauwa ta ƙwala ƙara ta faɗi a wurin a sume, lokaci ɗaya kuma Aisha ta saka kuka mai figitarwa, tana kallon Abba tana "Dada, dada". *KULLU NAFSIN ZA'I KATUL MAUTI, TABBAS DUK MAI RAI SAI YA ƊANƊANA ZAFIN MUTUWA, HAKA SHI ZAFIN MUTUWA BAYA FITA A ZUCIYAR MU DUK TSAWON SHEKARU, WAYYO MUTUWAR MIJI AKWAI CIWO SOSAI* *FAUZIYA A.A, WANNAN SHAFI NAKI NE, DOMIN TUNAWA DANAKEYI NA ZAFIN DA KIKAJI NA RASUWAR MIJINKI ALIYU BABAGANA ZAKI(ABBA)* *TUNDA NA FARA PAGE ƊIN NAN KE KIKE FAƊU MUN ARAINA, INA JIN RAƊAƊI A XUCIYATA KAMAR YAU MUKA SAMU LABARIN RASUWAR ABBA, ALLAH YA JIƘANSHI YA MISHI RAHMA, ALLAH YA ƘARA MANA HAƘURI AKAN RASHIN MAZAJEN MU, IYAYEN ƳAƳAN MU, ABIN AƘFAHARIN MU* 😭😭😭😭😭 *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/19, 12:27] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 37📑* *__________📖* Kowa kaga idon shi a gidan zaka san ba ƙaramin taɓa su mutuwan tayi ba, ko wani ɗaki ka shiga bazaka ga ana surutu irin na gidan rasuwa ba, kowa zaka ganshi yayi jigum, wasu hannun su rike da charbi, wasu kuma suna karatun qur'ani, ɗaiɗaiku ne kawai zaka ga suna magana ƙasa-ƙasa, amma duk da haka wanda sukayi shirun sun fi yawa. Ɗakin mahaifiyar su Baba Umar nan aka buɗewa Ummah halima da ƙannen Baba Umar mata, da ƴan'uwan Aunty suwaiba, sannan akwai wani ɗaki a gefen shi, shima ciki ne da parlour, nan aka ajiye Aunty hauwa da ƴan'uwanta. A ƙofar gida kuma tun Baban Narabi da Bappah suna rarrashin Abba har suka gajji suka zuba mishi ido, sai addu'a kawai suke mishi a zuciyar su, uncle Baba ma gaba ɗaya ya shiga wani yanayi, da yake shiɗin dama mai rauni ne, ko gaisuwa aka musu sai ya share hawayen shi, a na ɗan ɗaukan wani lokaci kuma zai tashi ya shiga har ɗakin da Aunty hauwa ta ke zaune, har gabanta yake ƙarasawa ya tambayeta ko tana son wani abu? amma haka cikin kuka ta ke nuna mishi bata buƙatan komai, haka zai fito jiki a sanyaye. Aisha kuma gaba ɗaya sai kukan rikici ta keyi wa mutane, firr ta ƙi karɓan kowa sai nida Hassan, idan taji yunwa mu haɗa mata tea tasha, mu sake fita da ita, nono kam zan ce a ranan bai fi sau uku muka kaita ta sha ba, shima tana sha, ƙafanta yana ɗaure akan cinyan ɗayan mu, saboda kada mu gudu mubarta. Idan muna zaune a waje kuma duk yadda mutane abokanan Babanta suka zo, zasuyi tazo wurin su sai ta ƙi, idan kaga ta karɓi mutum toh daga ni da Hassan sai Abban mu, sai kuma Baban Narabi da wani ƙanin Baba Umar mai masifar kama da shi, duk inda yabi zaka ga tana ta bin shi da kallo, idan ya karɓeta kuma kuka zai fara, ya kifa kanshi akan ta yayita kuka, dole zakaji Baban Narabi yace, "Abdallah! Na haneka da zubar da hawaye wa ɗan'uwanka, shin ba addu'an mu Umar yafi buƙata ba? Don Allah ayi haƙuri da kukan nan, baka ga ita kanta Aishan kuka kuke sakata ba"? Haka Uncle Abdallah zai share hawayen shi, ya kuma kasa riƙe Aishan saidai ya miƙo mana ita, amma yana barin wurin kuma zata fara kuka, a dole Abba yace mu koma cikin gida da ita. Rayuwa babu wuya, a kwana a tashi kwana sai tafiya yake tayi, yau har an wayi gari Baba Umar ya cika sati ɗaya da rasuwa, inda kowa ya fara shirin tafiya. Baba Umar shine babba a wurin mahaifiyar su da mahaifin su, sannan aka haifi mace tukun Uncle Abdallah, sannan aka sake haihuwar wata macen, a lokacin kuma Baban Narabi ya ƙara aure da wata ƴar cikin Narabin, inda suka sake haihuwa tare da mama Aisha, bayan ta haifi yara mata guda biyu, wanda ƙaramar su itace sa'ar Aunty hauwa, wacce taje musu hutu lagos, wato indo, a haihuwarta maman su Allah ya karɓi ranta, inda aka maida sunan maman su. Aunty Amina ita ke bin Baba Umar wanda yanzu ta ke aure a cikin jos, sai uncle Abdallah, sai Aunty Hadiza wanda ita ma ta ke aure cikin garin jos ɗin, sai mai bi mata kuma Aunty Umaimah, wanda ta ke aure a cikin garin bauchi, duk cikin su mijinta yafi wadata sosai, sai ƴar auta kuma Aunty indo, wanda itama ake shirin auren ta kwanan nan, da wani ɗan Azare, amma mazauna garin kano, shiɗin kuma abokin uncle Abdallah ne. Ɗayan ɗakin kuma, wanda take amaryar Baban narabi mai suna Baba kaltum, tana da yara guda huɗu, babban su shine, uncle sabo, wanda shi sa'an Aunty umaima ne, sai mata uku da suka biyo bayan shi,Aunty asma'u, Aunty Nana khadija, Aunty Zahra, duk gidan basu da irin halin ƴan ubancin nan, don ko kaɗan Baban Narabi bai yadda da wannan a gidan shi ba, shi mutum ne mai tsayin daka a gidan shi sosai,. A ranan su Bappah suka koma misau, inda Bappah ya gana da Baban Narabi cewa Aunty hauwa idan tayi 40dys za su maida ita gida, amma Baban Narabi bai amince ba, lokaci guda hawayen da ya daɗe yana ɓoye su cikin mutane suka fara zuba, yana duban Bappah yace, "Ni da nafi son tayi takabanta gaba ɗaya a ɗakinta, yanzu haka shawaran da muka yanke da ƴan'uwan Umar zata koma gefen shi Umar ɗin, zasu tafi da Indo,da kuma mata biyu wanda zasu tayata zama, kaman ɗaya daga gefen ko, sannan ita ma Uman shi tace zata zauna dasu har su gama takaban, amma idan kace zaku ɗauke ta sai maga kaman akwai kasawan mu", ya ƙarasa maganan hawaye yana zuba mishi babu kakkautawa. "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wallahi ba haka nake nufi ba, amma tunda kun shawarta hakan babu komai, dama ita Maman suce zata zauna tare da ita, saboda haka duk yadda kuka tsara ɗaya ne ae, ae ko babu Umar ae munzama ɗaya, ga Aisha a tsakani", Bappah ya faɗa cikin yanayin shi na nutsuwa. Haka sukayiwa Aunty hauwa sallama tana kuka suka tafi dukkan su, gidan yazama babu kowa sai mu, wanda muke shirin tafiya gobe, a ranan muka koma da Aunty hauwa gidanta, da yake tun kwana biyu su Aunty hauwa sukaje suka gyara gidan tsaf, ranan da aka koma Aunty hauwa da su Ummi na sun yi kukan rashin Baba Umar ba kaɗan ma. Washe gari tun safe muka tafi domin zuwa airpot, Aunty hauwa tayi kuka lokacin da zamu tafi, rungume Ummi tayi tana ta kuka, gefe ɗaya kuma Umma Halima da Mama sai haƙuri suke bata, ita kuma Ummi bata iya cewa komai sai kukan da ta keyi, don zan iya cewa Ummi na tayi kukan da ko Aunty hauwa batayi shiba a rasuwan nan, domin cewa ta keyi, ciwon hauwa ae nata ne, kukan haiwa shima na ta ne, Abba fita yayi bai musu sallama ba, domin bazai iya ba, amma ya bada kuɗi mai yawan gaske a hannun Mama akan idan ya tafi ta bawa Aunty hauwa, suma su Maman da Umma halima ya basu masu yawa. Lokacin da muka ajiye Aisha a parlourn zamu tafi, kuka ta fara nida Hassan sai muka kasa fita, muma kukan muke tayi muna tsaye muna kallon ta, a haka uncle Abdallah yayi sallama ya shigo, ganin kukan da mukeyi sai ya ɗauki Aisha da ganin shi ya sata tayi saurin hawa jikin shi ta kwanta tana ta ajiyan zuciya, hannun shi ɗaya ya saka ya riƙo mu muka fita waje inda motan uncle Abdallah ta ke, wanda dashi za' a kaimu airpot, uncle sabo ne zaune a mazaunin driver Abba yana gefen shi. Muna tafiya Uncle Abdallah ya koma parlour ɗauke da Aisha a kafaɗan shi, zaunawa yayi suka gaisa da su Umma halima da suke ta share hawayen su, gefe ɗaya kuma Aunty hauwa ce a tsugune a ƙara ta rungume ƙafan Mama tana ta kuka mai ƙarfin gaske, kaman zuciyata zai fito. Runtse idon shi yayi da ƙarfi na zuwa wani lokaci kuma ya buɗe su akan Aunty hauwa, ya daɗe yana duban ta kaman bazaice uffan ba, chan kuma ya ƙira sunan ta a hankali, " *HAUWA*"! bata amsa ba amma ta rage sautin kukan, bai sake cewa uffan ba har zuwa wani lokaci da yaji sautin kukan nata ya ragu sosai. Juyawa yayi ya dubi Umma halima yace, "Ummah ku ae haƙuri zakuna bata bawai idan kunga ta fara kuka kuma kuyita tayata ba, kukan rashin Yayah Umar idan muka ce yin shi zamuyi tayi, toh ina mai tabbatar muka har mu koma ga rabbana bazamu daina ba, domin shi ya zama mana wani jigo acikin rayuwar mu, kuma wani haske ne a cikin zuciyar kowanmu, toh manta shi a zuciyar mu abune mai matuƙar wahala, kuka bashi bane mafita addu'a ne zai zama muna mishi", yayi shiru yana bin kowa da ido, wanda umma halima tana share hawayen ta tana ta amsa mishi da hakane, daga nan ya juya yana duban Aunty hauwa a hankali yace, "Hauwa kina jina"? ɗaga kai tayi alaman taji, sannan ya ci gaba da kwantar musu da hankali yana ta nuna musu ƙarfin addu'a da haƙuri shi zai rage musu zafin a zuciyar su. Nasiha sosai ya musu sannan ya miƙe ya tako har gaban Aunty hauwa ya sunkuya hannun shi riƙe da Aisha, jin ƙamshi turaren shi ya saka Aunty hauwa ɗago da kanta ta dube sho, zuciyarta ya buga da ƙarfi domin tsananin kaman da sukayi shida Baba umar, bambanci kawai yafi Baba Umar tsawo da farar fata, sannan Baba Umar mutum ne kowa ga fara'a da mutane, amma shi kuma Abdallah sai ya so ya ke kula mutane, kuma kullum fuskar shi a ɗaure ta ke tamau, baya wasa da kowa, a hankali ta mayar da idon ta ƙasa jin wani hawayen mai zafin gaske ya taho mata, don hattah muryar su iri ɗaya ne da yayan shin. Miƙa mata Aisha yayi akan ta karɓeta, amma firr Aisha taƙi yadda kuka ma ta fara mishi alaman bazata je ba, ganin haka yayi murmushi ya lakuce kumatun Aishan, sannan ya dubi Aunty Hauwa yace, "toh bata nono tasha sai mutafi gidan Baban Narabi", girgiza kai tayi alaman bazata bata ba. Hararanta yayi murya ƙasa-ƙasa yace, "dole kuma ki bata tasha abincinta, ko na ɓata miki rai", ya faɗa babu wasa a fuskar shi, ganin haka Aunty hauwa ta turo bakinta gaba ta miƙa hannu ta karɓi Aisha, sannan ta dube shi ta gefen ido tace, "toh ka tashi a kusa da ni mana", ta ƙarasa maganan tana murguɗa baki kaman zatayi kuka. Kallonta yayi na wasu seconds, sannan ya miƙe ya koma gefen Umma halima ya zauna suka shiga magana da shi, wanda da wuya ka dinga jin muryan shi idan yana magana, kawai sai dai kai da kake hiran da shi ne zaka dinga jin muryan shin, ita kuma Mama tashi tayi ta wuce kitchen wurin Indo domin ta yata ɗaura abincin rana, wanda tun jiya Uncle Abdallah ya cika store ɗin da kayan abinci. Hijab ɗinta ta ɗaga ta saka Aisha a ciki ta fara bata nonon ta cika, sannan kuma duk bayan wasu seconds sai ta share hawayenta, duk abinda ta keyi a fakaice Abdallah yana kallon ta, kuma zafin kukan da ta keyi ya keji, suna haka har Aisha ta sake nonon ta ɗago da kanta da ya cika da zufa tana kallon Abdallah, da gwalantayin ta ce ,"Dada"! Da sauri ya dubeta yana tambayan Aunty hauwa wai me ta ke faɗa ne? Kallon Aishan tayi cike da tausayi tace mishi, "wai Daddy ta ke ce maka, halan tana maka kallon Baban ta ne", ta faɗa tana cigaba da share hawayen tan, hararan ta yayi yace, "dama waye idan ba Daddyn ta ba? Ni yarinyar nan ma da wuri zaki yaye ta ki bani ita, don naga baza ki iya kula mun da ita ba", ya faɗa yana miƙawa Aisha hannu ganin ta taho da gudu wurin shi tana buɗe hannu alaman ya ɗauke ta. Hararan shi Aunty haiwa tayi sannan tace, "Daddyn ta ranan da zai rasu yace ya bawa Ummi ita kyauta duniya da lahira, kuma yace a barta tasha nono sosai, saboda haka ni bazan baka ƴata ba, bayan baka da mata, kuma ni bazan yayeta da wuri ba", ta faɗa tana share hawayenta. "Wannan kuma tunaninki na shirme kikeyi, ke zaki hanani auren ne? Zan ɗauki ƴata, don yayah haifa mun yayi ya tafi ya bar ni da ita, kuma bazan barki da ita ba don naga baki san yadda ake renon yara ba, don kema baki wuce rainon ba", ya faɗa yana miƙewa tsaye, dai-dai lokacin indo ta shigo parlourn tace. "Yayah Abdallah da gaske nima ina zaune a wurin yace yabawa Abban kyautar yarinyar shida Ummi, kuma yace kada a yaye mishi ƴar shi da wuri", hararanta yayi yace, "ina wasa dake ne? Nawa Haiwan ta ke da za abarta da yarinya"?. Tsaki yaja, sannan yayiwa Umma halima sallama sannan ya juya ɗauke da Aisha a kafaɗan shi, da ta ke tayi musu bye bye. Suna fita Aunty hauwa ta dubi Umma halima tace, "Umma kinjo abinda ya faɗa ko? Kadafa ya ƙi dawo mun da ƴa ta"? Umma halima tayi murmushi tace, "bai isa ba ae Hauwa, kada ki damu da maganan shi, babu mai ƙwace miki yarinyar yanzu, ae zata zama miki rarrashi ne, yadda Umar yace haka za'ayi, mu koma duk mai son ganinta sai ya bita inda ta ke, shi kuma Abdallah idan yana son riƙonta ae sai ya haɗa gaba ɗaya ya riƙe ku". "Chabɗi jam, ae Umma halima ni ban taɓa maganan minti goma da shi bama, kullum sai naga kaman kallon banza ma yake mun, shiyasa ma bana shiga shirgin shi, tayaya ma zan zauna a gaban shi bayan ba ɗan'uwa na bane", ta ƙara faɗa tana turo bakinta gaba. Dariyan da Umma halima bata shiryah ba yazo mata, tana duban Aunty hauwa tace, "hauwa ae yanzu mun zama ƴan'uwan juna, ae Umar ya haɗa mu tun da yabar mana Aisha a tsakanin mu, kuma akwai yanayin da Abdallah zai iya ajiyeki daga ke har Aishan a gidan shi, mu kan ma zamu fi son hakan, amma yanzu tashi ki koma ɗaki kici gaba da addu'o'in ki, kada mi shagala ko". Murmushi Mama tayi tana duban idon Umma halima lokacin da Aunty hauwa ta wuce ɗaki tace, "Allah ya amsa mana hakan ae zaifi kawo kwanciyar hankali" umma halima ta juya suka cigaba da zantawa a tsakanin su. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/24, 14:40] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1441H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 38📑* *____________* 📖 Tashi Aunty hauwa tayi zata wuce ɗaki tace wa Umma halima, "hmmm nikan ae bazan iya zama inuwa ɗaya da Abdallah ba, don wani irin son girma ne da shi, kuma bazan bashi Aisha ba don duka zai na mata, fuskan shi babu fara'a ko kaɗan", ta faɗa lokacin data ƙarasa shiga ɗakinta. Murmushi Umma halima tayi tana jujjuya kanta, "yaro yarone" ta faɗa ita kaɗai tana murmushi, a haka Mama ta fito suka ci gaba da hiran su. Uncle Abdallah lecturer ne a ABU Zaria, yana koyar da English, sannan kuma masters yake da shi, zuwa yanzu yana PHD ɗin shi, kuma ya kusa ƙarasawa, shi mutum ne ɗan bokon gaske, saidai wani halinshi guda ɗaya na ƙin son shiga mutane, shine abun da duk familyn su basu so, domin kafin kaga murmushi a fuskar shi toh sai wani muhimmin abu na gaske, kuma baya shigewa kowa kuma koda mahaifin shi ne, da sun gaisa zaka ga yaja bakinshi ya tsuke, saidai yayita bin mutane da kallo, sau dayawa ma idan kaji muryanshi toh shida Baba Umar ne, amma ya wuce shi bazaka ji bakin shi ba, kullum zaka ganshi da laptop kawai ya na danne dannen shi a ciki, Abdallah kenan. Rayuwa babu wuya, yau ana saura kwana ɗaya Aunty hauwa tafita a takaba, duk wani a halin gidan Baban Narabi sunzo wuni gidan, duk wanda ka dubi fuskan shi zaka ga yanayi na jimami a tare da shi, zuwa azahar su Ummi da Abba suka ƙaraso Narabi, domin mu an bar mu a chan lagos, gidan abokin Abba aka kaimu, da yamma kuma sai ga Uncle Abdallah ya iso, amma ko kaɗan bai leƙa inda Aunty hauwa ta ke ba, aikowa yayi aka ɗauka mishi Aisha kawai, inda suka san shine yazo, ganin haka Aunty hauwa tafara nuna ɓacin ranta da fargaban kada ya ɗauke Aisha, Ummi ce tayita bata haƙuri tana nuna mata ta kwantar da hankalinta Abdallah bai isa ya ɗauki yarinyar ba bada izinin Baban shi ba, kuma ae bayi da mata ina zaikaita? Haka dai Aunty hauwa ta kwantar da hankalinta. Washegari Baban Narabi yasaka aka taho da ita chan main house ɗinsu, inda lokacin kuma ƙanin Bappanta da kuma Uncle Auwal sunzo daga misau, a lokacin ne taga limamin garin da wani alƙali da wasu ƴan'uwan Baban Narabi guda biyu, abin tausayi a ranan aka raba gadon Baba Umar kaf, bayan anyi mishi addu'o'i, dukkan ilahirin gidan kuka sukeyi, abin tausayi hattah Baban kasa daurewa yayi, shima kukan ya dinga yi kaman yau aka mishi rasuwan. Bayan komai ya lafa, Baban Narabi ya danƙa gadon Aisha gaba ɗaya a hannun Abba, sannan ya ɗauki kason shi daya gada ya raba shi kashi uku, ya ɗauki kashi biyu ya ƙarawa Aisha, sannan ya ɗauki kashi ɗaya ya danƙawa Uncle Abdallah yace, "Abdallah wannan dukiyar dana gada ne a wurin ɗan'uwa, amma ina son duk wani abu da zai kai lada kabarin shi kamun da shi, yazamo sadaƙatul jariya wa Umar ɗina", ya ƙarasa yana share hawayen shi, shima Uncle Abdallah sunkuyar da kai yayi yana share hawayen shi. Baban Narabi hana su Aunty hauwa tafiya yayi a ranan yace su bari sai gobe da safe idan Allah ya kaimu, babu yadda suka iya haka suka kwana a gidan, washe gari da safe motan Uncle Abdallah yazo ya ɗauke su har misau, amma bashi ya kaisu ba wani abokin shine, Ummah halima tayi kuka kaman ranan aka mata rasuwan, haka dukkan su ƴan gidan suka haɗa mata da kaya mai ɗumbin yawa wai na fita takaba, mazan su da matansu, har da iyayen Aunty suwaiba sun aiko mata kusan kala uku da kaya wa Aisha, uban gayyan kuma akwati guda ya haɗawa Aisha, amma ita ko zani ɗaya bai mata ba. Sun koma misau basu fi kwana biyu ba Ummi ta tattara su suka wuce lagos,ta kai kusan wata uku acan aikin ta ya samu a specialist hospital bauchi, lokacin ya zama dole ta yaye Aisha, bayan ta tafi ne kuma Uncle Abdallah yazo ya duba Aisha. Duk yadda mutane suka so auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah abin yaci tura, don Baban Narabi babu yadda baiyi da uncle Abdallah ba amma sai yace wai ae ita bata ƙiran shi ta gaishe shi, haka Baban zaiyi ta faɗa amma Uncle Abdallah yayi shiru. Aisha tanada 3yrs mu kuma muna da 8yrs uncle Abdallah yayi aure, inda ya auri wata yarinyar ƴar zaria, student ɗin shi ce, a lokacin ya fara tayar da maganan shifa so yake riƙon Aisha ya dawo hannun shi, ganin haka Abba ya neme shi yayi mishi kacha-kacha, yace mishi koda Baba Umar yana raye tunda yayi mishi alƙawarin ya bashi Aisha, to ko shi bai isa ya karɓi Aisha ba ballantana shi Abdallan, shima Baban Narabi bai ƙyale shi ba, inda Umma Halima da Aunty Amina suka nuna mishi bai kyauta ba, dama ya yadda ya auri hauwa ne toh ko hutu sai Aisha ta dinga zuwan musu, amma bayi da ikon karɓan Aisha a hannun Baba Gambo, haka suka mishi babu daɗi, rai a ɓace ya miƙe yana duban Aunty hadiza da tunda aka fara maganan bata ce uffan ba, ita dai kuka kawai ta keyi, ya dubeta yace, "kin sa mutane a gaba kina ta kuka, toh ni kuma yayah kuke so nayi? Kullum sai kuce wai na auri Hauwa, meye riban auren tan bayan ba bani riƙon ƴar za'ayi ba? Kuma ita kun taɓa ce mata ta aure ni? Kala kusa yarinya ta rainani nace ina sonta", ya faɗa kaman zaiyi kuka. Hararan shi Aunty Amina tayi sannan tace, "dalilin ka kenan da yasa kaje ka auri wanda ta kusan sa'ar ka? Don wallahi wannan mata taka fadilan tayi kusan sa'ar ka, kuma tunaninka ita hauwan ce yakamata tace tana sonka? Ina ka taɓa ganin anyi haka"? "Toh ae sai kuce mata kun bata ni bawai ni ayita mun masifan naje na zubar da girmana a gabanta ba, ga shi dama yarinyar ba kunya bane da ita, sai tayi tayiwa mutum kallon sa'anta, ni ko na aure ta wallahi bazan ɗauki raini ba a wurinta, gashi ita tana bauchi ni ina zaria yayah za a yi"? Yana gama faɗin abinda yake ranshi yaja tsaki shi kaɗai, murmushi Umma halima tayi, tana duban shi tace, "tun farko mai yasa baka ce kai girman kai bane yake damunka a ranka, har saida komai ya ƙure tukun zaka nuna mana gaskiyan abinda na daɗe ina ganin zahirin shi a fuskar ka"?, Aunty Amina ta dubi Umma halima tace, "kaman yayah lokaci ya ƙure Umma"?. Ajiyan zuciya Umma halima tayi, "Amina wallahi tun rasuwar Umar Allah yaga zuciyata naso Abdallah ya auri matar nan hauwa, saboda gaskiya ƴar mutuncine, amma Abdallah yaƙi ɗaga kai, toh ni muna zumunci da iyayenta sosai, yau baifi sati ba Mamanta ta ke gaya mun wani likita a wurin aikin su ya tura manyan shi domin neman auren ita hauwar, kuma iyayenta sun amince da shi, yanzu maganar danake miki ma zuwa nanda wani watan auren za'ayi". Share hawayen ta Aunty hadiza tayi ta dubi Umman su tace, "toh Umma ayi wa Baba magana mana a tura maganan yayah Abdallan, ina ga ae zasu fi sun na yayah Abdallan akan wani daban", ta faɗa kaman zatayi kuka. Shima Abdallan shiru yayi yana jiran yaji mai Umma halima zata ce, amma abin mamaki sai Umma Halima tace, "gaskiya bamu isa yanzu mu tura maganan Abdallah ba, bayan tun farkon rasuwar Mahaifinta sai da yayi magana da Baban ku akan ko zai tuntuɓi Abdallah akan Hauwan? Amma firr Abdallah yaƙi maganan, toh yanzu kuma ae bamu da bakin cewa muna so". Tashi yayi bai ce musu uffan ba ya bar cikin ɗakin Umma haliman, dukkan ido suka bishi da shi babu wanda ya hana shi fitan da zaiyi. Aunty hauwa tana zaune a gidan wani cousin ɗinta wani likitane, yayah Aunty Ummi matar uncle auwal, yana zaune a cikin drs quaters da take kusa da asibitin, da yake night duty ta keyi ranan tana gida babu inda taje, suna zaune da matar yayan nata mai suna Aunty uwani, matace mai matuƙar kirkin gaske, duk yadda mutane suke nuna mata illar zaman Aunty hauwa a gidan ta bai dame ta ba, kowa yana ce mata mace kyakkyawa kuma yarinya ƙarama bata tsoro ta aure mata miji? amma ko kaɗan bata kula su, a haka har Aunty hauwa ta haɗu da wani Dr ɗan garin Azare wato Dr basheer. Suna zaune akan dinning ita da ƴar Aunty uwani mai suna Nabeeha, tana ta mata assignment ɗin da aka bata, ita kuma Aunty uwani tana cikin parlourn tana zaune tana kallon wani indian film. Ringing wayan Aunty hauwa ya fara, ganin baƙon number ta daɗe tana kallo har sai da ya kusa tsinkewa tukun ta ɗauka, "idan kina gida ki fito ina ƙofar gida", abin mamaki ya bata, ɗago wayan tayi ta duba numbern sannan ta mayar da wayan kunnenta tace, "ban gane da wa nake maganan ba, don banida number"?, "Baban Aisha ne, kina gida ne"? Jiki a sanyaye ta amsa mishi da "ehh" bai jira wani abu ba ya kashe wayan, shiru tayi tana duban Aunty uwani da ta ke kallon ta ita ma, ta gane mai wayan tun ɗaukan ta taji irin muryan Baba Umar, amma tsoronta shine, bai taɓa ƙiranta ba a rayuwar shi, toh ko lafiya yau yazo har inda take"? *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/25, 13:41] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/ Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 39📑* *__________📖* Bata daɗe ba ta fito daga cikin gidan, hannunta ɗauke da tray, har inda yake ta ja table ta ɗaura akai, juq ne cike da zoɓo mai ƙamshin gaske, sannan cooler kuma cike yake da jaloop rice, wanda yaji kayan haɗi har da hanta, bayan ta zuba mishi ne ta koma cikin gidan ta barshi a wurin. Busmillah yayi ya fara cin abuncin yana ɗan sipping zoɓon kaɗan-kaɗan, sai wani lumshe ido yakeyi na jin daɗin zoɓon, haka yayita ci har yaji ya ƙoshi, bayan ya gama ne ya ɗauki jug ɗin ya cika shi da zoɓo, sannan ya ɗauki wayan shi ya danna ƙiran Aunty hauwa, tana ɗauka yace, "ki fito nagama". Zama tayi a kan kujeran sannan ta fara gaishe shi, bayan sun gaisa ta ce, "naganka kwatsam ina fatan ba wani abu mukayi maka ba ko"? ta ƙarasa faɗi tana duban shi, murmushi yayi mai kyaun gaske yana kurɓan zoɓon yana kallon ta har cikin idonta, sannan yace, "nazo tafiya da ke ne". Hararan shi tayi, "ni kayace da zaka zo kace zaka ɗauke ni ne"? Murmushi yayi yace, "zanje na aurar da ke ne, don naji ance baki iya zaɓe ba kin zaɓo mana wani sunduƙi", ya ƙarasa faɗa yana ajiye cup ɗin zoɓon. "Hmmm batun yau ba na ke zaɓo sunduƙan ba kenan, tunda bashi kaɗai na fara zaɓa ba", fuskan ta a murtuƙe ta faɗa masa. Zuba mata ido yayi batare da yace komai ba, hakan yasa ta kasa cigaba da maganan ta ta sunkuyar da idonta ƙasa. "Hauwa bana son wannan auren da kike shirin yi, domin ina kishin wani ya aure matar ɗan'uwa na, saboda haka ni nan zan aure ki domin kada ki haɗa mana zuri'a da wasu irin kuma daban". Tashi tayi tsaye tana bin shi da wani irin kallon mai cike da raini a ciki, "lallai Abdallah idonka baya cike da kunya, ni matar yayankan zaka duba kace wai ni zaka aura? Toh a wani hujjan? Ina ce ana wannan auren idan da akwai yara a tsakani ne? Toh ni babu wani sauran abu a tsakanina da kai, yarinya kuma ko nayi aure ba wurina zata zauna ba ballantana kace zataje gidan wani baka so, saboda haka gara ka farka daga baccin da kakeyi, ni Hauwa nafi ƙarfin na auri yaro mai raina mutane irin ka, kaje chan ka ƙarita da tsohuwar matarka ni bana so", tana faɗa ta juya cikin gidan ta bar shi zaune a parlourn yana murmushi mai cike da ɓacin rai. Kuka ta keyi mai ƙarfin gaske inda taje ta samu Aunty Uwani ta zube tana ta kuka, Aunty uwani duk ta ruɗe sai tambayarta ta keyi mai ya faru amma taƙi faɗa mata komai sai kuka da ta keyi, ganin bazata kula ta ba yasa, ta wuce parlour wurin Abddallah, inda ta samu ya miƙe yana shirin tafiya. Bayan sun gaisane ta tambayeshi abin da ya faru, cikin girmamawa ya gaya mata komai, yana kuma ƙasƙantar da kai alaman yana neman ta tsaya mishi akai, Aunty uwani ta yaba da Abdallah shiyasa ta bashi tabbacin zata samu ɗan'uwanta da maganan, shi kuma godiya yayi mata ya kama hanyar shi sai misau. Tunda ya isa Bappah yake ta nannan da shi, bayan kuma ya gaya mishi abinda ya kawo shi, Bappah ba ƙaramin jin daɗi yayi ba, ƙiran Uncle Auwal yayi a waya yazo ya same shi, bayanin komai Bappah yayi mishi, shima abun yayi mishi daɗi, domin sanin kirki da karancin iyayen Baba Umar. Bappah ya ƙira Abba ya gaya mishi duk abinda ake ciki, Abba ya nuna farin cikin shi amma yace a haƙura har sai ita Hauwan ta amince, sannan Bappah ya ƙira Baban Narabi ya zayyana mishi komai, shidai Baban Narabi murmushi yayi, a zuciyar shi yace dama yasan za'a rina wai an saci zani mahaukaciya. Uncle Abdallah a misau ya kwana, da safe ya kama hanyar bauchi, lokacin da yaje yayi dai-dai da dawowar Aunty hauwa daga duty, tana ganin shi ta wuce bata kula shi ba, ko damuwa baiyi ba, wucewa kai tsaye yayi har parlour yayi salllama, inda Aunty uwani da yayan su Aunty hauwa suke zaune, wurin zama suka bashi cike da kulawa, bayan sun gaisa aka haɗa mishi breakfast, amma yace musu yayi a misau. Zama sukayi shida dr Alƙali, yayan su Aunty hauwa sukayi magana mai muhimmanci, amma firr Aunty hauwa da aka mata maganan taƙi basu haɗin kai, da yake Dr Alƙali ba mai yawan magana bane sai yabawa Abdallah haƙuri akan ya tafi zai shawo kanta daga baya, babu yadda ya iya haka yayi musu sallama ya tafi, Abdallah irin mutanen nanne masu ƙin yadda suga sun faɗi a neman abu, kuma shi idan yaso abu nacin shi yana dayawa, ballanta wannan da yake ganin idan ya rasata toh zai sha kunya, a ransa ya saka duk abinda zatayi zai daure, don shi Allah kaɗai yasan irin son da yake yi mata kawai ƙarfin hali ne da kuma kada a gane ya damu da ita shiyasa bai nuna ba, kuma a tunanin shi ae Hauwa yarinya ce, dole zata koma tayi karatu ne bawai maganan aure ba, hakan da yayi niyyah ya saka shi wucewa Narabi. A parlourn Baban Narabi ya zauna ya dinga sauƙe mishi rikicin shikan aje a nema mishi auren hauwa, inda hali ma a tafi da sadaki, Baban Narabi ƙura mishi ido yayi har na tsawon lokaci, saida ya karanci ehh tabbas Abdallah da gaske ya keyi son Hauwa ya keyi tsakani da Allah, sai yayi gyaran murya yace, "toh in banda abinka Abdullahi tun yaushe aka bika akan ka aureta kaƙi, sai yanzu da yarinya ta haɗu da wanda ta keso zamuje muce ga zance ga magana? Ina ce Aishan ko ka aureta ba baka ita za ayi ba, toh meye dalilinka na auren Hauwa?" Kallon Baban yayi sannan ya sunkuyar da kanshi ƙasa, "nidai Baba ina sonta ne, ae nima zata haifa mun irin Aishan, ko basu bani riƙon Aishan ba hala ta haifa mun mai kama da Aishan". Dariya baba yayi yana duban Abdallah cike da ƙaunan ɗan na shi yace, "Abdallah wato kaima sake zakayi hauwa ta sake haifan me kama da ita ba mai kama damu nan ba ko? Wani irin so kukeyiwa Hauwa ne kam"? Baba ya ƙarasa yana murmushi mai cike da jin daɗin al'amarin. Sunkuyar da kai Abdallah yayi ƙasa, "Baba don Allah kuje ko gobe nema, naga hauwan so ta keyi ta mun yarinta, gara aje da wuri kada ta auri wancan ɗayan, ni bana son zamanta a bauchi ma wallahi don zasuna haɗuwa". Wannan lokacin dariya mai ɗan ƙarfi Baba yayi, yana duban Abdallan cike da mamakin irin nashi kishin, "toh ka gayawa ita maiɗakin kane zaka ƙara aure"? Baba ya jefa mishi tambaya. Abdallah ya dubi Baba yace, "Banida matsalah da Fadilah nidai damuwata a fara zuwa gidan su hauwan". Babu ɓata lokaci Baban Narabi washe gari da ƴan'uwanshi mutum biyu, sai uncle sabo ƙanin uncle Abdallah dayaja zuwa misau. Bappah ba ƙaramin karɓa ya musu ba, bayan sun gaisa sun sha ruwa Baban Narabi yayiwa Bappah bayanin abinda ya kawosu, Bappah tashi yayi ya ƙira ɗan'uwanshi wanda yake mahaifi wa Aunty Ummi da Dr Alƙali, da yake shi bamai son wargi bane yace su tsaya ana sallan azahar a ɗaura aure kawai, babu maganan jeka ka dawo a tsakanin su, Bappah ma yayi na'am da batun ɗan'uwan shin, suma su Babam Narabi sunji daɗi ba kaɗan ba da irin dattakun da aka musu. Ana sallan azahar aka ɗaura auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah a masallacin ƙofan fada da yake garin misau, hattah su Mama dasu Addagana sunji daɗin wannan auren ba kaɗan ba, domin farin cikin yaxama musu biyu, inda Uncle Auwal yazo musu da labarin aikin shi daya samu da NNPC, inda Baban Misau, kuma ɗan Mutanen Misau, Dr maikanti baro Allah yajiƙanshi da rahma ya sama mishi aiki a wancan lokacin. *ALLAH KAJIƘAN DR MAIKANTI BARU, ALLAH KASA YANA CIKIN RAHMAR UBANGIJI, ALLAH KA DUBA BAYAN SHI KASHIGA AL'AMURAN SU YADDA SHINA YA SHIGA NA MUTANE, ALLAH YA HASKAKA RAYUWAR IYALANSHI* Lokacin da aka gama ɗaura aure Baban Narabi da kanshi ya ɗaga waya ya ƙira Abdallah yana murmushi yace, "Albishir Abdallah!" cikin zaƙuwa ya amsawa Baban nashi da "goro". "Toh yau dai Allah ya nufa an ɗaura aurenku da Hauwa, sai ka shiryah mana goron Albishir ɗinmu", Baban ya faɗa mishi cike da murna, ae babu shiri Abdallah yace, "Baba nabaka kujeran zuwa umrah kaida su Bappah, insha Allahu ku uku kushiryah tafiya zuwa nan da sati biyu", murmushi mai cike da dattaku Baban ya amsa mishi da sun gode, tukun yace ya bar maganan tarewar har sai ita hauwan ta shiryah, daga nan sukayi sallama ya kashe wayan. Saida akayi sallan La'asar tukun su Baban Narabi da bappanun Abdallah suka dawo Narabi cike da murnan abinda ya faru, suma mutanen gidan kowa ka ganshi cike da murna a fuskar shi. Bappah ne ya ƙira Dr Alƙali yagaya mishi an ɗaura auren Aunty Hauwa, sannan kuma yace ya sanar mata, sannan ya ƙira su Ummi ya sanar musu, ita dai Ummi taji daɗin wannan haɗin, don ko baɓu komai, baza'a rabawa Aisha hankali yadda zata fahimci wani abuba, duk ranan da taje wurin Aunty hauwa zataje ne a matsayin gidan Ummanta, Abdallah kuwa Mijin Ummanta, kenan komai zai zo mata cikin sauƙi, gaskiya Ummi taji daɗin abun ba kaɗan ba. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/27, 12:09] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 40📑* *__________📖* Dr Alƙali yaji daɗin al'amarin ba kaɗan ba, dama yana zaune a office ne, kawai sai yaji kaman yayi tsuntsuwa ya koma gida, haka ya daure ya gama duba patients ɗin da suke gaban shi, yana gama ganin su ya kamo hanyar gida. A parlour ya samu Aunty hauwa tare da Aunty uwani suna cin abinci suna kallo kuma, yana murmushi yace, "ƴan mata sai yanzu kuke cin abinci? Laillai kuna jin daɗi fah", ya nemi wuri gefen matar shi ya zauna. Bayan sun gaishe shi ne, suka cigaba da cin abincin sun hankali kwance, shidai sai duba abu yake a wayan shi batare da yace uffan ba kuma, suna gama ci Aunty hauwa ta miƙe zata bar wurin domin mata da mijin su samu sakewa, ganin haka yasa ya ɗago da manyan idanunshi yana murmushi yace, "amaryah dawo ki zauna, tafowan da nayi ae duk don ke ne". Wurin data tashi ta koma ta zauna tana kallon shi, "yauwa Hauwa ɗazu Bappah ya ƙirani yake gaya mun cewa na gaya miki yau ya ɗaura miki aure da ƙanin mijinkin nan Abdallah"........ Wani irin miƙewa tayi da murya mai ƙarfin gaske tace, "a wani hujjan za'a ɗaura mun aure da mutumin da bana so" wallahi auren nan bai ɗauro ba, ko sama da ƙasa zasu haɗu toh aure bai haɗu ba", ta faɗa tana zare ido kaman zata kai duka wa Dr. "Saboda ke kin isa da kanki ko? toh ki sani bawai barinki ake yi ba kike abinda kika gan dama hauwa, kuma baki isa kija da iyayen mu ba, aure an riga da an ɗaura ya rage naki kiyi biyayyah wa mijinki ko akasin hakan", yana gama faɗa ya miƙe yayi ɗakinshi, ita dai Aunty uwani sai juya kanta take tayi alaman bata so hakan ba, tafi so abi komai a hankali, hakan yasa ta fara rarrashin Aunty hauwa, ita kuma bata sararara ba kawai ihu da kuka ta fara, daga baya ta fita da gudu zuwa ɗakinta, inda suke tare da yaran Aunty uwani, kwanciya tayi ta fara rera kuka mai azabar taɓa zuciya. Har akayi magrib Aunty hauwa kuka ta keyi bata saurari kowa ba, bayan tayi sallah ne ta shiga wanka domin tayi shirin tafiya night duty da ta keyi, wanda yau idan tayi zata shiga up na 1week, tana wanka ta shirya, lokacin aka ƙira ishaa, babu ɓata lokaci tayi sallan ta miƙe ta ɗauki jakanta ta fito domin tafiya, a parlourn ta samu Dr da Aunty suna cin abinci, yana dubanta yace, "amaryah kinci abinci kuwa"?. Hararan shu tayi bata ce mishi komai ba tayi hanyar waje, tana fita yayi murmushi ya dubi bayanta yace, "zama ki ɗame ae", suka cigaba da cin abincin su shida matar shi, wanda ta ke ta mitan ya dinga bin ta a hankali da lallaɓi, bawai yayita ɓata mata rai ba, shidai dariya kawai ya keyi bai ce mata ƙala ba. Tana shiga office ta samu wanda zasu karɓe su suna shirin tafiya, gefe ta samu ta zauna, bayan sun gaisa taji wayanta yana ringing, da sauri ta fito da shi kawai sai taga Baban Narabi ne, jikinta yana rawa ta ɗauka sannan ta miƙe ta bar office ɗin tayi waje. Bayan ta gaishe shi ne ya fara mata maganan yadda auren ya taso sannan ya bata haƙuri na gaggawan da aka mata, Aunty hauwa ce mishi tayi babu komai ae sun isa da ita ne, amma tana maganan tana kuka, jin haka yasa Baba yayita saka mata albarka daga baya yayi mata nasiha sosai, wanda har saida sautin kukanta ya dinga fitowa, suna gama wayan ta ƙira Ummi har lokacin kuka ta keyi, itama Ummin haƙuri tayita bata tana rarrashinta da kalamai masu daɗin gaske, wanda Aunty hauwa ita kuma tayita mitan yayah zata iya zama da Abdallah bayan ya raina ta, itafa matar yayan shu ne kawai din raini yazo ya aureta? Ita dai Ummi haƙuri ta ke bata chan ƙasa-ƙasa kuma tana dariyan hauwan da ta je ta maganan wai ya rainata, haka suka gama maganan Aunty hauwa ta koma ciki, nan kuma an kawo masu haihuwa har mutum uku, dole ta zage ta fara aiki. Tunda Abdallah yaji an ɗaura mishi aure da hauwa, farin ciki ya taso shi gaba, jiki na rawa ya ƙaraso gida wurin Baban shi, inda shi kuma Baban ya fara mishi nasiha da yayi adalci a tsakanin matan na shi, kuma ya gaggauta gayawa fadilah abinda ya faru, sannan ya mishi nasiha sosai. Abdallah yana fita a parlourn Baba ya ƙira fadila, cikin nutsuwa ya mata bayanin komai, amma abin mamaki bata nuna mishi damuwarta ba, kawai fatan Allah ya basu zaman lafiya tayi, daga baya ta tambaye shi yaushe zai dawo zaria? Jiki a sanyaye yagaya mata zuwa gobe ko jibi, haka sukayi sallama ya shige motar shi yayi cikin garin jos gidan Aunty Amina. Washegari da safe Abdallah ko karyawa bai yiba ya kama hanyar garin bauchi, amarya tayi ƙira, tunda yaje yake ƙiran wayarta amma firr taƙi ɗagawa, yananan ƙofar gidan saiga Dr ya fito wurin 9:00am zai wuce office, mamakin ganin Abdallah yayi a kofar gidan, cikin mamaki yace, "Hauwan bata san kazo bane?" ya tambaye shi da sauri, yana murmushi kanshi a ƙasa yace, "yanzu na iso ina shirin ƙiranta kenan", Abdallah ya faɗa yana ɗaga wayan shi alaman zai ƙirata. Da sauri Dr ya koma ciki, inda ya tarar da Aunty hauwa a tsaye gaban dinning tana tattare kayan da yayi breakfast da su, "mantuwa kayi Dr"? "babu wallahi, kawai na fita sai naga mijin yarinyar nan Abdallah tsaye a ƙofar gidan, daga dukkan alama ya nemeta taƙi fitowane, don daga gani ya daɗe a ƙofar gidan", ya faɗa yana wucewa zuwa ɗakin su Aunty hauwa, daga ƙofar ɗakin ya tsaya yana ƙiran sunan ta, amma firr tayi shiru kamar mai bacci taƙi amsawa, ganin haka Aunty uwani ta shiga. Ganin bazata fitoba yasaka shi shiga ɗakin ranshi a ɓace, kaman zai wanka mata mari yake mata masifah, "ke hauwa wa kika ɗauka yaronki ne a gidan nan? Kinsan Allah idan raina ya gama ɓaci bansan me zan miki ba, banzar yarinya mai masifar tsiya, ke har kin isa iyayen mu su zartar da abu kidawo kina nuna basu isa ba? Ke wacece? Wuce kifita kije wurin mijinki kafin na nuna miki ɗayan halina ɗin". Fuska a ɗaure ta fita wurin Abdallan, shi kuma Dr yazo ya mishi tasss akan kada ya fara sakewan da Hauwa zata raina shi, gara ya rage nuna mata damuwan shi akanta kafin raini ya biyo baya. Tsayawa tayi a gaban motan sai cin magani ta keyi tana harare-harare, tsayawa yayi na wani lokaci yana dubanta, chan ya koma Abdallan shi yana dubanta fuska a murtuƙe yace, "nifa bana son rashin hankali, hakan yayi miki mutunci kizo gabana kina wani jiye-juyen jiki kamar ke kaɗaice mace a duniya? Ko kuma haka aka ce miki ana taryan baƙo? Toh ni bazan ɗauki rainin hankali ba", ya faɗa mata fuskan shi a murtuƙe, da sauri ta juyo da ɓufin ta maida mishi martani, amma ganin fuskar shi ya sakata juya da fuskarta gefe tace, "toh ni nace maka kada ka shigo ne,? Ni ae jira nakeyi ka shigo", ta faɗa tana ta murguɗa bakinta ta gefen shi. "Nidai koda wasan wasa kada ki nemi raina mun hankali, maganar auren nan nayi ne don samun kwanciyar hankalinki gaba, amma k8na ta wani nuna isan ke wata ce, bayan na samu Baba nace mishi bana son maganan abarki ki auri wanda ki ke ganin kun dace amma firr ya tafi akan maganan, ni bana son nunawa iyayena ban haihu ba a wurinsu shiyasa na amshi buƙatun su da hannu bibbiyu, amma hakan bazai saka ki raina mun hankali ba don ina da wacce ta fiki komai a gida", ya faɗa yana tafiya hanyar shiga parlourn. Baki a buɗe ta bishi da kallo cike da mamakin shi, tana tambayar kanta dama ba wai sonta yake ba? Har yana nufin matar shin tafita komai da komai, kodai don ita matar shi yana sonta ne yake ganin ta haɗu? amma ita dai taga photon matar da ta je gidan Umaima, kuma bataga ta fita komai ba, banda ma wani bleaching da ya ɓata mata fuska gata gajeruwa lukuta sosai, tsaki taja ta bi bayan shi zuwa parlourn. Gaisawa ta samu su nayi da Aunty uwani, itama ta nemi gefe ɗaya ta zauna, har Aunty uwani ta fita bata ɗaga kai ta dube shi ba, shi kuma babu abinda yakeyi sai kallonta, domin ba ƙaramin shiga ranshi tayiba, shiru zuwa wani lokaci yace, "ke kam Hauwa baki ɗauki halin kirki irin na ƴan gidanku da iyayenki ba, amma har yaushe baki san yadda ake mutunta baƙo ba, ballantana kuma ina da ƙarin darajar matsayin miji a gare ki, kina son albarka kuwa"? Ɗago kai tayi tana duban shi, murya cike da sonyin kuka tace, "ba kai bane kace dole aka maka ka aureni, kuma wai ban kai matar ka komai ba, kuma wallahi na gani na fita kyau, kawai faɗa ne baza kayi ba don ita kana sonta", ta ƙarasa faɗi kaman zatayi kuka. Dariya yayi yana dubanta cike da nishaɗi a ranshi yace, " kin taɓa ganin inda aka fi son wata mace sama da uwargidan ka? Toh ki daina ruɗin kanki matar farko baka ganin wacce ta fita a komai, ballantana wanda kukayi soyayyah kana sonta tana sonka", ya ƙarasa yana gyara zaman shi. Turo baki tayi gaba, " hmmm nidai nasan Hero duk da a ta biyu ya aure ni yafi sona akan Aunty suwaiba, kuma kullum ce mun ya keyi ina da kyau, saboda haka nasan ni mai kyauce, don muna secondry school *Hauwa golden girl* ake cemun", ta faɗa tana jujjuya idonta. Kallonta ya tsaya yanayi a cikin zuciyar shi yace, "wato duk matar mamaci magana ɗaya sai ta kwatanta da mijinta ko? toh yanzu don Allah idan da ba don ɗan'uwan shi bane da yaya zaiji a ranshi?" a fili kuma yace, "shiɗin ae ya aure ki yana sonki ne duk da ma ance Abba ne ya tura mishi ke, shi kuma yayi biyayyah ya karɓa kaman yadda nima nayi yanzu, shi kuma bansan dalilinshi na ganin kyaunki ba? nikan bana gani gaskiya, ko dan banji ina sonki bane ohoo", ya faɗa yana wani ya mutsa fuska. "Wallahi baka isa kace mijina baya sona ba, don ni nafi kowa sanin irin son da yake mun, kaidai da baka sona kai ka sani, don ni ban maka dole ba, idan baka so akwai mai so kabar mishi ni kawai zai fi mana zaman lafiya", ta faɗa tana share hawayenta. Dariya yayi yace, "nima haƙuri zanyi don kada iyayena suga ban mutunta su ba, amma ke idan kinga zaki nunawa duniya iyayenki basu isa da ke ba, toh kiyi gaggawan taimaka mana ki gaya musu baki sona, ko nima zan samu kwanciyar hankali". Shiru tayi na zuwa wani lokacin, sannan ta dube shi baki ta murguɗa mishi tace, "da yake nice wanda akace jeki kya gani ko? wanda bansan darajan iyaye na ba, toh bazan faɗan ba, kai da baka son kaje ka faɗa". Miƙewa yayi yana zurma hannun shi cikin aljihun shi yace, "nidai babu ruwana ban iya jayayyah da yayuna bama ballantana iyaye na ba, ke kuma na barki lafiya da halinki na rashin mutunta baƙo, zanje gidan umaimah nayi breakfast na wuce, domin gobe da safe xan wuce Zaria wurin my luv ɗita", yana dariya ya ajiye mata kuɗin da yakai 20k a cinyarta yace, "ki dinga transport kafin na dawo ko". *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/28, 14:26] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 41📑* *INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN, MISS XERKS, NEAT LADY, INA MUKU TA'AZIYYAH DA WANNAN RASHI DA AKA MUKU, ALLAH YA JIƘANTA DA RAHMA, ALLAH YASA TA HUTA* *__________📖* Duk yadda Aunty hauwa taso ta dinga ƙuntatawa Uncle Abdallah abin ya gagara, domin ya riga da ya tsare gida baya ɗaukan raini ko kaɗan, duk bayan sati biyu yake zuwa dubata, kuma kullum da irin rikicin da akeyi a tsakanin su, shi zaice sai ta bishi inda ya sauƙa, ita kuma ta dinga surutun ya raina ta kenan, haka za'asha dirama a tsakanin su har ya koma. Wani ranan jumma'a Abdallah yazo Narabi inda ya samu Baban su ya tashi babu lafiya, duk hankalin ƴan gidan a tashe, haka ya ɗauke shi da uncle sabo suka kaishi asibiti a cikin jos, don Baban su bai cika son zuwa asibiti ba shiyasa yaƙi faɗawa kowa bayida lafiya, suna zuwa a ka basu gado, domin an tarar yana ɗauke da hypertension, ga kuma diabetics, duk hankalinsu ya tashi, inda Aunty Amina da Aunty hadiza da suke zaune a jos duk suka hallara a cikin asibitin. Da yammah Uncle Abdallah ya ƙira Aunty hauwa yake gaya mata suna asibiti da Baba shi yasa bai samu daman ƙarasowa ba, jikinta a sanyaye ta gaishe da jikin Baban, kuma tace mishi gobe insha Allahu zata zo ta duba shi da jikin, bayan sun gama wayan ne ta gayawa Dr Alƙali da Aunty uwani da suke zaune a parlourn tare, Dr yace "babu komai suma zasuje idan yaso sai su dawo a goben ita kuma ta kwana", turo baki gaba tayi tana duban Dr tace, "mu dawo dai tare yayah, ni kuma kwanan me zanyi a can, kawai mu tafi tare mu dawo tare". Dariya yayi a hankali yace, "Hauwa problem", Aunty uwani dariya tayi tana, "ni dai bansan me yasa kike gudun wannan haɗaɗɗen mijin naki ba, gaskiya hauwa ki gyara halinki da ɗabi'un ki, idan ba haka ba za'a ƙwace miki miji da gaggawa",.......turo baki tayi a hankali tace, "ba sai a ƙwace ba ni na damu da shi ne, yaje chan su ƙarata da buskuɗan matar shi", ta faɗa bayan ta tashi ta kama hanyar ɗaki tana ta mita. A chan asibiti kuma bayan anyi sallan magarib mama kaltume suka zo tare da uncle sabo a motar uncle Abdallah tare da Nana khadijah da Zahra, don Aunty indo da Aunty Asma'u tare akayi auren su, yanzu kusan shekara 2 kenan, yanzu haka maganan auren Nana khadijah akeyi, suna shiga ɗakin Zahrah ta ƙarasa gefen Baban ta zauna bayan ta riƙe hannun shi, cikin shagwaɓa da nuna ita ɗin auta ce tace, "Baba da wai mama tace baza a zo dani ba, ni kuma nayi ta kuka tukun yayah sabo yace suzo da ni, amma Nana khadijah kam don baƙin hali zuga mama tayi wai kar azo dani, Baba don Allah a airar da ita na ɗan huta". Ganin autar ta shi ya sauƙar mishi da farin ciki, yana duban ta cike da so da ƙauna yace, "Duk yadda kikace haka za'ayi Fatin Baba, nima na gajji da zama dasu, na fi so gidan yazama daga ni sai ke nayita saya miki abinda kike so, kina walwalanki yadda ya kamata", sannan ya juya gefen Mama kaltum da Nana khadijah yace, "ina mai jan kunnen ku akan autata, na sake jin wani ya ɓata mata toh ni dashi a gidan nan, ke kuma Khadijah tunda kina takura mun yayata danafi so a duniya Nana Fatima toh zan dawo da ranan auren kin baya idan yaso ayi ta samu sakewa" ya faɗa yana hararan Khadija da wasa. Murmushi Zahrah ta farayi tana gwalo wa Nana Khadija, Mama kuma ta kai mata ranƙwashi tace, "ke ɗin tabbata zakiyi ae a gaban Baban naki ko? Toh ki shiryah ke kam ma baɗi war haka ana shirin kaiki nako gidan, ki bar ma murna", dukkan su ɗakin dariya sukeyi na rikicin Zahrah da Babanta, Aunty Amina tana kallon Zahra cike da kulawa tace. "Autar Baba Umaimace fah mai sunan maman Baba, amma ke kuma sunan yayarshi kikaci amma yafi ji da ke, kodai don kin zamo auta ne aka fi son ki"? Ta faɗa tana bin ta da murmushi. Baba tashi yayi ya zauna yan bin ƴaƴan shi da kallon so da ƙauna yace, "Adda na Fatima ta nuna mun ƙauna, lokacin da take makaranta duk kuɗin tara idan an bata bazata sayi komai taci ba sai tayi ta asusu, idan kuɗin ya taru zata ɗauke ni ta tafi dani kasuwa duk kayan dana ke so zata saya mun, lokacin aurenta kukan ta na rabuwa dani ne bawai na tafiya tabar iyayenta ba, ranan da za'a kaita gidanta da yake garin toro sukayi hatsari ita da wata goggon mu Allah ya karɓi ransu a wannan lokacin, mutuwar ta taɓa mana zuciya ba kaɗan ba, wanda ni har gobe na tuna sai nace zafin danaji yafi na mutuwan iyayena ma, naso tun haihuwar Amina na saka sunanta, amma sai mahaifin mu ya umarce ni da saka sunan jatumar shi, Hadiza kuma ya umarceni da saka sunan kakarku ta wurin uwa, umaima kuna na saka sunan tawa mahaifiyar, haihuwar indo kuma yazo da rashin mahaifiyar ku wanda dole sunan ta ya chanchanta na saka, da na haifi Asma'u kuma na saka sunan goggona wanda suka rasu tare da Adda fatima, Nana khadija kuma nayi karawa Maman ku kaltume na saka sunan nata mahaifiyar, kinga autata taci soyayyah uku, na farko sunan Adda na, na biyu sai ta ɗauko kamnnin Adda na ɗin, shiyasa suke ɗibi da Umar da Abdallah, sannan na uku kuma autata, kunga dole ta zama aminiyata". Gaba ɗaya dagowa sukayi suka dubi Baba suna dariyan yadda ya ƙarasa maganan shi cike da zolaya, Uncle Abdallah da tunda ya zauna bai tanka musu ba sai lokacin ya dubi Baban su yace, "Baba insha Allahu idan na haifi yara zan saka sunan yayah Umar da sunan Fatima, domin na ƙara faranta maka, don na lura baka haɗa son su da kowa a duniyan nan, ni kuma insha Allahu zan sake faranta maka da maimaita sunan su a ƴaƴana".......murmushi Baba yayi yace, "kaiɗin daban kake acikin ƴaƴana Abdallah, tun kana yaro burinka ka dinga faranta mun, kaima ina maka Addu'a Allah ya faranta maka duniya da lahira, tabbas ina jin Umar da Zahrah a zuciyata daban a cikin ƴaƴana, saboda sunan wanda suka ci a zuciyata, haka Indo ita kuma nafi jin tausayinta sama da kowa a cikin abinda na haifa, shiyasa babu garin Allah da zai waye ban ƙirata naji yayah ta tashi ba acikin ku, duk ranan da ban kira ta ba sai naji kaman nayi rashin wani abu a tare dani, dukkanku ina sonku kuma kowa da irin rawan da yake takawa acikin ku, Allah ya muku albarka da zuriyar ku gaba ɗaya". Aunty Hadiza ne ta dube shi tana murmushi tace mukan bansan me muke takawa ba a cikin ƴaƴan, don Baba baka cika faɗin abu akaina ba," ta faɗa kowa tana mata dariya, don duk tafiso ɗan zafi kaɗan, toh abu kaɗan sai ya tunzurata. Gyara zaman shi Baba yayi fuskar shi ɗauke da murmushi yace, "Umar, Amina, sabo duk cikin yarana ba masu haƙuri da zumunci irin nasu, ke kuma Hadiza duk kinfi kowa son nuna mun ƙauna keda Abdallah a cikin yarah na, kuma kunfi kowa nuna tausayawa a al'amurana ku ɗin kuna da wani shashi na musamman a raina, wanda bana haɗaku da kowa, kuma araina inaji idan daku kowa baziyi maraici ba dije na. Uwata umaima kuwa ita da Nana khadija, babu masu kawo farin ciki da walwala a cikin gida na irin su, wani lokacin idan suna raha da zolaya a cikin gida na sai naji anya akwai wanda nakejin son su irin waƴannan biyun kuwa, domin basu bar kowa ba, bani ba ba manaku ba wurin zolaya da neman magana, su ɗin kurwan gidana ne, idan babu su cikin gidan sai kaji maraici ya isheka, shi yasa da umaimah tayi aure sai danayi zazzaɓi, haka yanzu maganan auren Nana khadijah, idan na tuna sai naji kaman na bita gidan ta mu zauna kawai, don gidana zaiyi maraicin masu raha a gidana", yana faɗa Nana khadija tayi tsalle tace. "yehhhh daga dukkan alamu Baba yafi son mu nida Aunty umaima," ta juya tana duban Zahra hannunta riƙe da ƙugunta ta karkace tace, "auta ki kiyaye ni kinemi sulhu dani, don daga dukkan alamun bayanin Baba bawai sonki yafi ba, kawai kinci darajan wasu ne, ni kuma tsantsar sone yake mun, don yace gidana ma zai bini", ta juya tana kallun Baba tace, "Baba yanzu zan gayawa mahmood ya nemi gida mai ɗaki uku, domin kaima tare zamu taho, kuma kasan wani abu ma Baba? Saboda kai zan daina baccin safe na tashi na maka ƙosai da kunu don ka karya, shima kaga zai samu kulawa saboda kai", ta faɗa tana ta rawan ta kaman ba a asibiti suke ba. Duk yadda Uncle Abdallah yakai da ɗaure musu fuska amma sai da yayi dariya yace, "mama dama hankali bai wadaci Nana khadijah ba? Yanzu anata haukan sai fa tagaya wa mijin nata tare da Babanta zasu taho"?. Dariya Baba yayi yace, "kai baka san umaima dole na lokacin da tayi aure ba nake zuwa bauchi gidanta? Ina zuwa zata gyara mun ɗakin su na parlour tace Baba yau fa agidana zaka kwana, haka zan ta lallaɓata da ƙyar zata haƙura na tafi, lokacin da ta haifi ɗanta na fari, naje ina riƙe da ɗan, kawai sai ce mun tayi Baba da ina labour room da naji azaba nace, nagode Allah da Baba na bai zama mace ba, da bazan so kasha wahalan haihuwa ba Baba na am, gara su mama da mama ƙarama su karata da wahalar akanka," Baba yana cigaba da dariya yace, "wallahi tun ranan nace bansan ranan da Uwata zata yi hankali ba, hala sai tayi suruki", ya ƙarasa dukkan su suna dariya. Aunty Hadiza tace, "nikan Baba baka taɓa zuwa gida na ba wallahi", ta faɗa tana turo baki gaba, Mama ta dubeta tace, "Hadiza kefa baki sati bakizo duba babanki ba, ae inaga shiyasa baya zuwa miki, ae ke kinfi kowa damuwa dashi," Baba dariya yayi ya koma ya kwanta, rufe ido yayi yana ɗan murmushi, a hankali yace, "damo sarkin haƙuri ma ae ban taɓa zuwa mata ba, kuɗin ae kune yanzu iyayena, ku zaku dinga zuwa duba ni, su kuma yaran zan dinga zuwa duba su," damo da Amina yakeyi, wanda yana yawan ƙiranta haka. Washegari da safe su Dr suka kama hanyar Jos, wurin ƙarfe 10:00am, suka iso cikin asibitin, bayan anyi gaishe gaishe, Baba ya tambayi Aunty hauwa ina labarin amaryar shi? Tana murmushi bata ce komai ba, Aunty Amina ce ta dubi Aunty hauwa tace, "sun ma san kuwa Baba na asibiti"?....... "ni bandai gaya musu ba, amma bansan ko uncle Abdallah ya faɗa ba", Aunty hauwa ta faɗa kanta na sunkuye a ƙasa. Uncle Abdallah ne ya shigo idon shi akan Baba yace, "wallahi sai yanzu kafin na iso mukayi waya da Abban ta nake gaya mishi, amma yace mun shi da kansa zaizo zuwa gobe ya duba ka, amma bansan ko tare zasu zo ba". "Abdallah am da baka ɗago shi ba wallahi, yau baifi sati biyu bafa yazo ya gaishe ni, kawai ku ƙiramun amaryar tawa naji muryan ta", ya faɗa yana tashi zaune. Uncle sabo ne ya ɗan taimaka mishi ya gyara zaman shi, shi kuma Uncle Abdallah ya ƙira wayan Ummi, bayan ta ɗauka ne sun gaisa yake gaya mata Baba ne baiji daɗi ba, Ummi hankali a tashe take tambayan yayah jikin shi? Daga nan ya miƙa wa Baba wayan suka gaisa, bayan sun gama Aka bamu muma muka gaisa da shi, don mu ganin kaka muke mishi, duk magana da akeyi a handsfree aka saka mu, Aisha ce ta karɓa daga ƙarshe, muryar ta mai cike da rawan kai tace, "kakan ƙauye bangan kaba"? Baba zuciyar shi cike da ƙaunar yarinyar yace, "amaryar birni nazo nayita ɓata a garinku ban gane gidan ba, sai aka sakani a boot ɗin jirgi aka wurgo ni ƙauyen mu". Dariya tayi mai ƙarfi cike da yarinta tace, "sun maka turanci ne baka iya ba, shine suka saka ka a boot ɗin jirgi suka wirgar da kai ko?" tana ci gaba da dariyanta tace, "ka sake zuwa ina son naja gemun ka, ina son ka saya mun gyaɗa da ummm....mango", ta faɗa tana dariya. Shima dariyan yayi yace, "toh zaki koya mun turancin sai na dawo na kawo miki"?....... Dariya tayi tace zan gayawa Abba na da Ummi na su saka ka a school sai Uncle ɗin school ɗin mu su koya maka turanci, Yayah Hussain ɗina da Yayah Hassan ma sun iya suna koya mun, kaima zasu koya maka sai kayi tayi". Duk kansu ɗakin dariyan hiran Baba da Aisha sukeyi, ita kuma Aunty Hauwa sunkuyar da kanta tayi tana murmushi, uncle Abdallah kuma kallonta kawai yakeyi babu ƙiftawa. Bayan anyi sallan azahar Dr Alƙali da matar shi suka musu sallama suka kama hanyar bauchi, ita dai Aunty hauwa duk sai tajita wani irin tunda su Dr suka tafi, duk yadda Aunty Amina tayi tajata suɗan sake irin na da duk ta kasa, ganin haka Uncle Abdallah yace bari ya maida Mama Narabi ya dawo. Tunda ya tafi bai dawo ba sai bayan Sallan magrib, daya dawo bayan ya gaida Baba bai kula kowa ba sai danne danne kawai yakeyi a cikin wayan shi, ana sallan isha su Aunty Amina suka yi wa Baba sallama suka tafi tare da Aunty Hadiza. Wurin 9:30pm, Abdallah ya yiwa Baba da ya fara bacci sallama, sannan ya miƙawa Uncle sabo hannu sukayi sallama, kallon Aunty hauwa yayi yace ta taso su tafi. Kaman zata tashi kaman bazata tashi ba, haka ta ke kallonshi, Baba ne yace, "kuje mana Hauwa kada dare ya muku", haka ba don ta so ba ta tashi jiki a sanyaye tabi bayan Uncle Abdallah, suna shiga cikin motan ya ɗan dube ta sannan ya kawar da kanshi, baice mata uffan ba har suka iso wani hotel a cikin jos ɗin mai ɗan banzan kyau, zaro ido tayi baki a buɗe tace, "na ɗauka Narabi zamu tafi fa"? "Toh ki ajiye anan zamu kwana" ya faɗa bayan ya fita yana tattara ledodin da suke bayan motan shi, ganin ya ƙura mata ido fuska a ɗaure tayi sauri ta buɗe motar ta fito. Cikin hotel ɗin suka shiga hawa na biyu, inda taga ya ɗauko key ya buɗe ɗakin da yake number 38, haka tabi bayan shi suka shiga ɗakin da yake da matuƙar kyau da tsari, sai ƙamshi yakeyi ga wani sanyin AC da ya cika ɗakin, gefe ɗaya kuma sai ta ga wani jakan Abdallah a ajiye a gefen table ɗin ɗakin, ajiyan zuciya tayi ta nemi gefen gadon ta zauna a nutse idon ta yana kan Abdallah. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [8/29, 14:17] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Facebook page:- https:/www.facebook.com/Dokinkarfe2019/ Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 42📑* *__________📖* Uncle Abdallah jawo ledan da yayi musu take away yayi zuwa kusa da ita, "sauƙo muci abinci ƴan mata nah", kallon shi tayi ta juyar da kanta gefe, "nifa na ƙoshi, kawai ka mayar da ni Narabi na kwana achan wurin su Mama ƙarama". Wani kallo ya bita da shi babu shiri ta sauƙo tana murguɗa mishi baki ta jawo nata take away ɗin ta fara chi, bai sake ɗaga kai ya kalleta ba har sai da ya gama chin na shi, tashi yayi ya ɗauki wayan shi ya fita a ɗakin, ita kuma ganin fitan shi yasa ta ja dogon tsaki tana furta, "ni wallahu baka isa ka takurani ba don kaga ina tsoronka, ni idan ba masifah bama ban taɓa ganin wanda nake jin shakkan shi irin wannnan mai fitinannen idon ba". Miƙewa tayi ta ɗaura sauran abincin a saman fridge, bakin gadon ta koma ta zauna, tana zama yana shigowa ɗakin, ledan da yake ajiye a ƙasa ya miƙa mata ɗaya, "ki tashi ki shiga kiyi wanka, wannan kayan bacci ne", hararan shi tayi ta gefe, "an na taho da nawa kayan baccin". Bai wani bata amsa ba sai juyowa da yayi ya kalle ta, babu shiri ta buɗe ta ɗauki kayan ciki da towel ta wuce toilet ɗin, wanka tayi da brush, sannan ta gyara jikinta a cikin toilet ɗin, duba kanta tayi ta mirrow, ganin kanta ya saka ta kama haɓanta tana faɗin, "mutumin nan nufin shi da wannan kaya mai kama da net ɗin zan kwanta da shi? Kuma a gaban shi"? Ɗaukan hijab ɗin ta da ta shigo dashi ta mayar jikinta, sannan ta buɗe ƙofan ta fito ɗakin. Ko kallonta baiyi ba ya wuce ya shiga toilet ɗin, yana shiga tayi sauri ta ɗauki jakan kayanta, fito da turarukanta tayi ta shafa a dukkan jikinta sannan ta fesa hair spray a gashinta, gaba ɗaya fakin sai ya juye da ƙamshi mai daɗin gaske, tana gamawa ta ɗale kan gadon da sauri taja duvet ɗin ta rufe har kanta. Yana fitowa yayi murmushi daya ganta kwance ta duƙunƙune, wucewa yayi ya saka kayan baccin shi masu matuƙar kyaun gaske, feshe jikin shi da turare nasu ƙamshin gaske yayi, taku kaɗan yayi ya hau kan gadon gefenta ya zauna. Da sauri ta buɗe ido ta kalle shi, shima yayi sauri ya tamke fuskan shi, murya ciki-ciki yace, "tashi muyi sallah", yana faɗa ya miƙe ya ɗauki carpet ɗin ya shimfiɗa, kallon shi tayi taga babu hanyar jayayyah, kawai sai ta tashi ta ɗauki zaninta dayake jakanta ta ɗaura, hijab ɗin data naɗe ta ɗauka ta saka shi, sannan ta fesa turare a jikin kayan, binshi tayi sukayi sallah raka'a biyu, ya zauna ya dinga jera addu'o'i, suna idarwa ya tashi ya buɗe fridge ya ɗauko goran fresh milk ya wuce gefen gadon ya xauna, bayan ya buɗe ya cika mata glass cup ya miƙa mata, ganin yadda ya tamƙe fuskan har zuwa lokacin yasa ta karɓa babu musu, kafa kai tayi ta shanye, karɓan cup ɗin yayi ya ƙara cika mata, amma sai ta yi fuskan zata mishi kuka, "don Allah uncle na ƙoshi wallahi, kabar ni haka mana". Hararanta yayi, "nine kuma yau uncle ɗinki? Bazan fasa miƙa miki ba, ki karɓa kada na nuna miki halina", ........babu yadda ta iya kawai ta karɓa ta fara sha a hankali, da ƙyar ta sha rabin cup ɗin, ta juyo tana duban shi cikin ƙaramar muryah, "uncle Abdallah don Allah kayi haƙuri ka barni haka wallahi na ƙoshi ne, kuma kaga dare yayi kada nayita cika cikina da abu". Hannu ya saka ya karɓa, baice mata uffan ba ya shanye sauran wanda ta bari, sannan ya sake cika cup ɗin ya shanye, ita dai tana zaune har lokacin ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman mai jiran a biya mata karatu. Sun kai kusan 25mnt tukun yace mata ta gyara ta kwanta, babu musu tayi sauri ta ɗale gadon batare da ta cire hijab da zanin ba, "Hauwa meye haka zaki kwanta da hijab da zani kuma"?....... bai gama rufe bakin shi ba tayi sauri ta tashi ta cire su ta naɗe, duk abinda ta keyi idon shi yana kanta babu ƙiftawan ido. Asuban fari Uncle Abdallah ya tashi cike da farin cikin kasancewar shi da Hauwa a daren jiya, kallon fuskarta da take bacci kawai yake cike da farin ciki, a zuciyar shi ji yake kamar tana tashi ya damƙa mata duk abinda ya mallaka, yana murmushi ya furta, "Hauwa ina sonki! Allah ya bani kyawawan yara masu kama da ke golden girl ɗina", ya miƙe yayi toilet fuskar shi cike da murmushi. Murguɗa baki tayi bayan taga shigewan shi toilet ɗin, don tunda ya bar jikinta ya tashi ta farka, a bayyane ta furta, "jarababbe kawai, duk wani ɗaure fuskar kan ka na banza tunda bai hanaka cika wa mutum kunne da ihu ba, hawaye ko kamar ranan zai ƙarar da su, amma idan ka tashi a ɗauka kai zaki ne bayan"...... Sai kuma tayi shiru ita ɗaya tana murmushi don tuna wasu sirrikan zuciyar shi da yayi ta amayar mata a daren jiya. Yana fitowa itama ta miƙe bata kalli inda yake ba ta wuce toilet ɗin, shi kuma har ta wuce binta da kallon yake yana murmushi. Suna idar da sallah bayan sunyi azkhar sun karanta qur'ani, kawai sai ya miƙe a ƙasan wurin ya kwanta ya ɗaura kanshi akan cinyar ta, rigingine ya kwanta yana duban fuskarta, itama zuba mishi ido tayi tana kallon kyakkyawan idonshi daya sauƙe mata a kanta, murmushi yayi ya saka yatsan shi manuniya yana zagaya shape ɗin bakinta da shi a hankali, bata ce mishi uffanba sai hannun ta data saka cikin gashin kanshi tana shafawa. "Hauwa ina sonki!" murmushi tayi tana duban shi, "ka gaya mun daga daren jiya zuwa yau yafi cikin buhu, na haddace su ka ƙara mun wani kuma", ta faɗa da yake hauwa barikinta baya gaya mata gaskiya, domin daga jiya zuwa yau tasan Abdallah dai-dai yake da ita, don duk yadda taso ta ƙi ba shi haɗin kai abin ya gagareta, Abdallah yasan ta kan mace wuce tunaninta. Murmushi yayi mai ɗan sauti, ya dawo da hannunshi dai dai kan haɓanta inda ya ɗan lutsa kaɗan yace, "daɗinki yayi mun yawa hauwa nah, har ya kusa zautar dani", jin haka bata san lokacin da tayi sauri ta ture kanshi akan cinyarta ta miƙe zuwa kan gado tana faɗin, "nikan baka jin kunya na wallahi, ni ba haka nake nufin ka faɗa ba", hayewa gadon tayi tana rufe fuskanta. Dariya yayi ya biyo bayanta yana cewa, "sweety akwai abinda zan faɗa mai daɗi da ya wuce hakan ne? Ba gashi kina neman na ƙara ba kin gudu kan gado don na biyoki ba, ni yau ban san ta yayah zaki barni na tafi zaria ba?" ya faɗa yana hayewa kan gadon, ita kuma buɗe baki tayi tana kallon shi, amma ganin zai jawota ya saka ta fara kokawa da shi tana cewa. "Wayyo uncle Abdallah wallahi bance ina son ka ƙara ba, nifa na gajji ka tashi muyi wanka muje wurin Baba, kai kuma sai ka wuce kada kayi dare", yana ƙara jawota jikin shi yana dariya yace, "ni ae bazan iya tafiya ba gaskiya sai dake, don gaskiya ban gajji da faɗawa maliya ba". Duk yadda taso ƙi amma babu yadda ta iya haka ta barshi ya sake maimaita wa, da kyar ya barta suka tashi sukayi wanka, bayan sun shirya suka wuce zuwa a sibiti wurin Baba, jikin Baba ɗa sauƙi zuwa yau, saboda haka ana sallan azahar uncle Abdallah ya yi sallama wa Baba, yayiwa Aunty hauwa ma da dole saida ta raka shi zuwa jikin motan shi, ita dai sai mamakin shi takeji na yadda duk wannan fuskan shi yau babu, sai wani shagwaɓa ya ke mata shi baya so yayi nisa da ita, ita dai bata ce mishi komai ba sai mamakinshi kawai data keyi, haka ta lallaɓa shi ya tafi, ita kuma ta dawo cikin ɗakin inda suke zaune da Aunty Umaimah da tazo yau, kuma dama tare zasu juya da ita zuwa bauchi, Aunty umaimah sai tsokananta takeyi da matar so, ita dai batace mata uffan ba sai murmushi kawai ta keyi. Uncle Abdallah da ƙyar ya daure yayi sati ɗaya ya taho zuwa Narabi ya duba jikin Baba da aka sallane shi yana gida, ko awa ɗaya baiyi ba ya wuce bauchi, ranan Aunty hauwa sai da ta raina kanta, don tunda Uncle Abdallah yazo ya ɗauke ta bata samu hutu ba, har saida ta fara nuna mishi zatayi kuka tukun ya sarara mata, ga duk inda tayi idonshi yana kanta kaman wani tsohun maye. Da kyar ya barta wurin ƙarfe tara na dare suka zo gida domin ta ɗauki kaya, Aunty uwani tana ganinta ta fara dariya, suna shiga ɗakin Aunty uwani, Aunty hauwa ta turo baki gaba kaman zatayi kuka tace, "Aunty nifa gaskiya bazan bishi ba, kisan dabaran da zakiyi ya tafi, ni na gajji sosai". Aunty uwani dariya tayi tace, "banda ke hauwa ni na'isa na ce mishi bazaki samu daman binshi ba? ae haka zaki haƙuri da irin mijin da Allah ya haɗa ki dashi, yanzi kinga dolenki ki maida hankali da shan kayan mata masu kyau da inganci domin yanayin mijinki, idan ba haka ke zaki wahala". Aunty hauwa ta miƙe kan gado ta kwanta tana ya mutsa fuska, "Aunty uwani gaskiya ki nema mun, yanzu ma idan kina da wani ki bani, don wallahi baya gajjiya, ga daɗewan tsiya ni har tsoro nakeji kaman ba ciki ɗaya suka fito da Baba Umar ba". Aunty tana dariya ta buɗe fridge ta miƙo mata wani kwaƙba da yake cike da wani ruwan abu ruwan ƙasa, kai Aunty hauwa takafa sai da ta sha kusan rabi duk da rashin daɗin shi, Ita dai Aunty uwani dariyanta kawai ta keyi, sannan ta miƙo mata goran tsumi mai matuƙar kyaun gaske, Aunty hauwa shima kafa kai tayi ta sha, sannan ta dubi Aunty uwani tace, "zan tafi da wannan". Haka ta bata wani gumba mai cike da kwakwa taci kusan rabin farin roban, Aunty uwani sai dariyanta ta keyi, don duk alama ya nuna hauwa ta sha wahala, wani markaɗaɗɗen kanakan da Aunty uwani tayi blanding ɗinshi ɗaxu ta miƙa mata, dama ta haɗa da wani garin haɗin kankana mai kyaun gaske, Aunty hauwa ko sauraron Aunty uwani data ke ce mata kada ta shanye duka bata shaba fa, kawai sai da ta shanye ta miƙa mata roben. Miƙewa tayi saboda ƙiranta da Dr yakeyi ta fito zasu tafi, tana kallon Aunty uwani tace, "kiji rashin kunya fa Aunty? Shi ko damuwan ban tare ba bayayi, sai dai son kawai naje na bashi yayita tumurmusana, kai namiji baiyi ba wallahi, yama manta da ni matar yayan shi ne, sai sarbaɗe kawai yakeyi", ta faɗa kaman zatayi kuka. Ita dai Aunty uwani kunshe bakinta tayi tana maida dariyanta, haka su Aunty haiwa suka tafi inda ya sauƙa, wanka kawai tayi ta ɗale gado, shima wankan yayi ya biyo bayanta, ranan sai da Aunty hauwa tayi dana sin abinda tasha, don har saida ta koma tana saka hannu tana rufe mishi baki saboda irin ihun da yake mata, abinda ya bata tsoro da shi wani vibration yake yi akanta, ya ƙira sunanta yafi babu iyaka, ƙarshe kawai ya fara faɗin, "hauwa ni'imanki zai kashe ni, kibar kawai na shige gaba ɗaya", dole saida ta rufe bakinshi ta samu sauƙin magana. Ganin jelen da Uncle Abdallah yake yi duk sati kawai Baban Narabi yayi magana wa Abba akan Aunty hauwa ta tare, dole a lokaci kaɗan aka sakata ta tare, lokacin baifi sati biyuba, a cikin sati biyun kuma ba ƙaramin gyara, Aunty uwani da Mama daga misau suka mata ba, don hatta wannan gadali na sirrin garin dass ɗin nan sai da aka bata taci, (Allah sarki duk matar da bata ci gadalin dass ba an barta a baya, mata ku daure ku same shi a kuɗinku da bai wuce 5k ba, amma sai kun bada labarin yadda mazajenku zasu ɗaukake ku). Matar Abdallah fadilah dama mai haƙuri ce, dolen ta ta aro ƙarin haƙuri ta karawa kanta, don ba kaɗan ba Abdallah yake nuna rashin haƙurin shi akan Aunty hauwa, kuma babu ɓata lokaci transfer ɗinta ya samu zuwa zaria, anyi zama na nuna so da ƙauna tsakanin Aunty hauwa da Uncle Abdallah, wanda kaman bata taɓa zama da wani mijinba ta keji, tana son Uncle Abdallah babu iyaka, shi kuma tana mata ninkin so, a haka tana cika 10month, Aunty hauwa ta haifi ɗanta mai kama da Uncle Abdallah sak. Ranan suna yaro yaci sunan Baba Umar yadda baban shi yayi alƙawari, amma suna ƙiran shi da Amir, Amir yana da 2yrs Aunty hauwa suka haihu tare da Fadila, ita fadila ta haihu friday, Aunty hauwa ta haihu tuesday, Fadila ɗa namiji wanda yaci sunan Baban Narabi, kowa kuma ta mata murna, inda dayawa suke cewa dama ba rabonta bane a farko shiyasa saida Aunty hauwa tazo ta fara haihuwa tukun ita ta haihu, Aunty hauwa ta haifi ƴar ta mai matuƙar kama da ita, wanda babu maraba da Aisha. Ana haihuwar yarinyar uncle Abdallah kaman zai zauce ranan, kaman ba'a taɓa haihuwa ba sai akanta, waya kawai yake tayi da mutane yana gaya musu ya samu Faɗimatul zahra'u. Ita kuma zahra haka ta haɗa kayan mai suna cikin akwati, wanda bata fi 2month da aure ba, wanda sukayi aure da uncle Baba ƙarami, wanda tun auren su Aunty hauwa suka fara soyayyah, yanzu uncle Baba yana aiki a cikin bauchi, inda yake lecturing a federal plytechnic bauchi. Kyaun Fatima har yana so yafi na Aisha, saboda fatima tana fi Aisha fari, amma Aisha tafi gashi, bayan suna Abba yayi retire suka yi Parcking zuwa gidan shi mai girman gaske da yake bauchi a GRA, wanda yake makurɗi road, gidane wanda Abba ya daɗe yana tsara shi, idan ka shiga gidan sai kaji kaman ba a bauchi kake ba, yayi matuƙar yin kyau sosai. Aunty hauwa tana arba'in suka taho mana bauchi hutu, inda ta haɗamu dukkanmu mukaje mukayi 1week a misau, lokacin shekaran Aishan mu takwas, nida Hassan kuma muna 13yrs, muna hutun jsce a lokacin, Ameer kuma yana 2yrs, inda Fatima tayi 40dys, duk inda mukaje sai an sake binmu da kyau, haka duk wanda ya kalli irin haɗuwar da Aunty hauwa tayi da kyau, bazai ce ita ta haifi Ameer ba ballantana a danganta ta da Aisha, saidai kawai kace Fatima ce haihiwar ta na fari, gashi Uncle Abdallah ya saya musu mota ita da Fadila, so duk inda zamuje Aisha na riƙe da Fatima ni kuma ina riƙe da Ameer, Hassan kam na zaune a gaba gefen Aunty hauwa, don taso tana zuwa ɗaya wani lokacin shida Aunty hauwa, duk inda mukaje aka mata maganan da bai mata ba tunin zata watse mutum, hassan kuma ya tayata, haka da mukaje garinsu Ummi wata cousin ɗinsu tana ganin Aunty hauwa tace, "kaga hauwa mutanen birni, ke kam wa zai ganki yace tare aka haife mu, duk kin maida kanki kamar ƙaramar yarinya, baki san kin tsufah ba ko? Ga shegen tauri ko ɗan kuncen kaya baki aiko mana irin na Adda". Hararanta Aunty hauwa tayi, dama matar aurenta ya ƙare tana gidan kawun su Ummi ne, "ke rufe mun baki da shegen hassada da baƙin ciki, kina nan kina bugun gero a turmi kina ƙyashin wanda bai san da zamanki ba ina ko za'ayi baki tsufah ba? ae tsufah kam ya waja ba akanki, kuncen kaya kuma bazan taɓa baki ba don ni ba'a saka ni dole nayi sai nayi niyyah, kuma ni ba shasha bace da zan zo na kawu muku ziyara na tafi ku fara bina da zagi na baki tsummah na, kije Addan ta baki, amma banda na hauwa kam". Tana faɗa Hassan ya amsa da faɗin, "ae abunda yayi Ummi shi yayi Aunty hauwa, saboda haka ita ma ummin daga yau zan gaya mata kada ta sake baki kaya, hatta nawa dana Hassan andai na sambaɗo muku shi ƙauyen nan, haba jama'a mutane kana zaune suna maka *KAKKU* kana kwance ana binka da *KAKKU* bacci ma kakeyi *KAKKU* ake maka, idan ba kakku ba inake da kike ƙaute zaki haɗa kanki da Aunty na da ta ke birni", buge bakin shi nayi ina mishi alaman yayi shiru, amma saida ya ƙarasa Aunty Hauwa na tayashi, tukun matar kawun sun ta bawa Aunty hauwa muka fita sai misau, tunda mukaje Aunty hauwa mita da surutu ta keyi, Hassan Da Uncle Baba da yazo yau sai tayata sukeyi, nidai ina gefe sai murmushi nakeyi. Dr Hussain yana zuwa wurin yayi shiru yana kallon ƙasa yana murmushi hawaye yana zuba a idon shi, Abbu ne yayi ajiyar zuciya ya dube shi yace, "kayi haƙuri Dr, ina fatan dai ba wani mutuwan aka sake ba bayan na Baba Umar? Don naga kana kuka". Murmushi Dr Hussain yayi ya ɗago kai ya dubi Hummy, sannan ya maida kanshi kan Abbu yace, "abun da ya fari ae yafi mutuwar ma zafi, don mutuwa ae kowa yayi imanin sai ya tafi," bai ce komai ba ya tashi yana duban su yace, "yaka mata muje muyi sallah, mu huta ko"? A jiyan zuciya Daddy yayi yana duban shi yace, "so nake naji ƙarshen labarin ka don a matuƙar dame nake, ballantana kwatancen gidan ku dakayi ya saka na ƙara raya wani abu a zuciyata", Daddy yayi sauri ya dubi Hummy ya girgiza kanshi. Kowa tashi yayi domin ayi sallah a huta, ita kuma Hummy sai bin Dr ta keyi da kallo don su haɗa ido, amma firr yaƙi yadda su haɗa ido har ya fita a Parlourn. Shi ma Daddy duk idon shi yana kanta, zuciyar shi cike da tausayinta, don ya lura ba ƙaramin so ɗiyar shi take yiwa Dr ba, sai ya fara tsoro Allah dai yasa akwai aure tsakanin Dr da Hummy, don idan tunanin da ya keyi ya kasance gaskiya ne ina zai saka zuciyar shi tayi sanyi, don bai san yayah zaiyi da tausayin Hummy ba a ranshi. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/1, 15:16] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Facebook page:- https:/ www.facebook.com/Dokinkarfe2019/ Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 43📑* *__________📖* Gaskiya wannan hutun ya mana daɗi ba kaɗan ba, domin uncle Baba ma saida yayi three days tukun ya koma bauchi, ya gayawa Aunty hauwa ranan da zamu dawo zaizo da motan kasuwa sai ya ɗauke mu a motanta ya maida mu. Munsha ziyaran da muka daɗe bamuyi ba, saboda Aunty hauwa badai zumunci ba kam, dama ita da uncle Baba babu inda basu shiga a dangi, Ummi ma tanayi amma bai kai nasu ba, uncle Auwal kam dama shi na ɗakine, don komai akeyi baka ganin shi a waje. Kwanaki yanata tafiya, haka muka gama hutun mu Uncle Baba yazo ya ɗauke mu, tunda muka shiga mota Hassan ya fara mitan Aisha tana mishi rashin kunya, haka sukayi ta faɗa, Aunty hauwa na taya shi, muna isowa Darazo incle Baba yace Hassan ya dawo gaba ni na koma baya, don shi Uncle Baba baya son yaji an taɓa Aisha, don tasu ta zo ɗaya dashi, hakan Hassan ya fita yana hararanta ya koma gaba, ni kuma na dawo baya. A bauchi Ummi ta mana shirye-shiryen dawuwa, ta tarye mu da girki masu daɗi, muna shiga nida Hassan da gudu mukaje mukayi hugging ɗin Ummi muna murna kaman mun shekara bamu tare, itama daɗin ganin mu ta keji sai shafa kanmu ta keyi, chan idonta ya sauƙa kan Aisha da ta zunɓura baki gefe tana hararan mu. Da sauri Ummi ta ture mu a jikinta ta kamo Aisha tana faɗin, "waya ɓatawa autana ranta?" turo baki Aisha ta sakeyi tana hararan Hassan da shima hararanta yakeyi, ummi ta harare shi tace, "biyu ranka zaiyi mugun ɓaci akan autana fa, kai babu hali ku zauna inuwa ɗaya da ita sai ka ɓata mata rai? toh ka kiyaye ni", ta ƙarasa faɗi tana janyo Aisha jikinta, nidai sai binsu da murmushi nakeyi, na ƙarasa gaban Aunty hauwa da take ta hararan Aisha da Ummi, karɓan Fatima nayi muka ƙarasa parlour muka zauna, Ameer kuma yana kwance akan kujera inda Uncle Baba ya kwantar da shi tunda muka shigo, wasa nakeyiwa Fatima amma idona yana kan Ummi da Aisha, don ganin wani irin sakalcin da Aisha ta keyi, dariya suke bani saboda ko kaɗan Hassan baya iya jurewa ganin hakan, amma ni ko ɗaya bai dame ni ba, saboda nasan daga Abba har Ummi da ƴan gidansu, Allah kaɗai yasan irin son da suke mun, don duk abinda ya shafeni kowa daban ya ke ɗauka, yanzu a zahiri Aunty hauwa sunfi jitawa da Hassan, saboda hayaniyar su tazo ɗaya, amma da zan nuna ina son wani abu, toh jiki na rawa Aunty hauwa take tashi tayi, ko chanji suka gani a face ɗina sai ya ɗaga musu hankali, haka su Uncle Baba da uncle Auwal ma, saboda haka ni duk wani kulawa da Ummi ke nunawa Aisha dariya nakeyi. Ranan da Aunty hauwa ta gama hutunta zata tafi har kuka saida nayi, ba don komai ba sai don yadda nake jin baby fati a raina, kullum zan ɗauke ta nayita kallon ta ina kallon ɗan idonta masu masifar kyau irin na Aishan mu, wataran zan tambayi ummi nace, "Ummi kin taɓa ganin baby mai kyaun baby fati kuwa? Ummi nakan rasa ita da Aishan mu waya fi kyau ne"? Murmushi Ummi ta keyi tace, "har akwai wani halittah na mace da zai kai Aisha na kyau kuwa Hussain"? Tunin zakaji Aunty hauwa ta maida martani, "amma Ummi bakida kara, akan idona zaki ce ƴarki tafi tawa ƴar kyau? Gaskiya da sakel, kubani ma ƴata kafin kyaun ta ya kufce ya koma kan taku ƴar". Tana faɗin haka Hasan zai fara tarawa Aisha ɓacin rai ita kuma tayita kuka har sai da ƙyar nake rarrashinta tayi shiru, mun fito raka Aunty hauwa wanda Uncle Abdallah ya turo drivern da zai ɗauke ta da motan ta, har ƙofan gida muka rakota ina rungume da baby fati a hannuna, ita kuma Aisha ta riƙo hannun Ameer, don dama shi na hannun damanta ne, shi kuma Hassan yana rungume da Aunty hauwa kaman yaro ƙarami, muna tsaye a jikin motan na kasa miƙa mata baby Fatima, gaba ɗaya nayi kaman zanyi kuka, sai Ummi ta matso kusa dani don ta lura Aunty hauwa bazata taɓa cemun na miƙo mata fatima ba, muryan rarrashi Ummi take mun magana dashi. "Hussain bata fatima mana kada suyi rana a hanya sosai, idan yaso sai muja mata kunne ta kula maka da Fatima kada ko ƙuda ya taɓa maka ita, don inaga hala ƴar gida za'ayi kaida babyn ka", dariya suka fara mun ni kuma na miƙa fatima ina cewa Ummi, "haba Ummi lokacin da zan tashi aure ae ta mun ƙarama, 13yrs fa na bata, sai dai idan".......sai kuma nayi shiru ina kallon Aisha da take ta wasa da hannun Ameer, sannan na dubi Ummi nace, "da Aisha ba uwa ɗaya aka haife mu ba da sai ita na aureta, don ina son baby fati ne don tana kama da Aishan mu, amma nafi son Aishan mu". Kallon Ummi Aunty hauwa ta tsaya tanayi, wanda itama Ummin duk sai ta ɗan razana da magana nah, "Hussain ae babu aure tsakaninka da Aisha, tunda nono ɗaya kuka sha, kaga ta zama ƙanwarka ko". Murmushi nayi ina kallon Aunty hauwa, "Aunty hauwa amma kema kinsan Aisha tafi kyau ko? Kawai bana son ranki ya ɓaci ne shi yasa nafi son Fatima, amma Aisha kullum tunaninta nakeyi, sai na tuna ƙanwata ce". Hassan yana hararan Aisha yace, "wallahi fatima tafi kyau, wannan ka dubi kanta fah ƙato ne, dama chanje akayi ita aka bawa Aunty hauwa, aka bamu baby Fatima, amma idan baka son baby fatima nikan Aunty hauwa ina sonta, idan ta girma zan aure ta ko"? ya faɗa yana shafa gashin baby fati. "Insha Allahu kowa wanda yake so za'a bashi ya aura", inji Aunty hauwa data faɗa tana hararan Ummi da wasa tana murguɗa baki. Hararanta Ummi tayi sannan ta jawo hannu na tace, "rabu da Aunty hauwa, tunda Hassan yace yana son baby Fati zamu mishi kamu, kai kuma Allah zai baka taka wacce tafi Aishan mu kyau sosai, amma Aisha ƙanwar kace, kai zaka aurar da ita ma a wanda kaso idan ta girma", ummi ta faɗa tana jan mu baya domin su Aunty hauwa su tafi. Ta window Aunty hauwa ta turo kanta tana dariya tace, "Ummi duk abinda Allah fa ya hukunta wallahi bawa bai isa chanjawa ba, saboda haka kibar abinda yafi sanin ɗan'adam, kibar komai a hannun ubangiji, nidai ina tare da ra'ayin ƴaƴana har abada, jinina kuma mahaɗin jinin Adda na dana fi so sama da uwar data kawo ni duniya ne, saduwar alkhair Adda na", ta faɗa tana ɗaga mana hannu dukan mu. Tunda muka koma parlour Ummi ta zauna tayi shiru, ganin haka yasaka na tafi jikinta na kwanta nayi shiru, gefe ɗaya kuma Hassan ne suke ta faɗan su shida Aisha akan wallahi ta daina ruɗin kanta Fatima tafita kyau nesa ba kusa ba, ita kuma tana ta mishi tsigalan ae shiɗin tafi shi kyau, ya taso zai mareta nayi sauri na tare shi da hannuna, hararana yayi ya koma ya zauna, don Hassan duk iskanci idan na kalle shi yana bari, wanda kowa yana mamakin hakan da mukeyi a tsakanin mu, haka nima duk abinda nakeyi idan yace nabari toh nabar abin kenan har abada, haka duk abinda nake so idan ya nuna yana so toh na bar mishi, haka shima komai nake so ya bar mun kenan, sai dai hali kawai da yazo daban daban, amma muna son junan mu ba kaɗan ba. Rayuwa babu wuya a wurin ubangiji, har yau muke shirin rubuta SSCE, wanda lokacin muke daf da cika 16yrs nida Hassan, inda Aishan mu kuma zata cika 11yrs, a lokacin kuma tana jss 1 a FGGC Bauchi, haka muka dage da karatu nida Hassan. Aunty hauwa kuma bai daɗe ba suka bar ƙasan inda Uncle Abdallah ya samu lecturing a saudi, a wani university mai girman tarihi, bai samu matsalan tafiya da iyalan shi ba, tunda babu wuya suka bawa Aunty hauwa aiki a cikin school ɗin, so Aunty Fadila bata wani tayar da hankali ba, sun tafi da kusaɓ six month yazo ya ɗauke ta, daga lokacin kaman an tsayar da haihuwa a gidan su, don ko sau ɗaya basu sake haihiwa ba, amma Uncle Abdallah bai wani tada hankaliba, shidai ya gode Allah kullum yake cewa da samun Fatima, Allah ya raya mishi su kullum addu'an shi. Kuma har zuwa lokacin mun ɗauka da gaske Aisha iyayen mu ɗaya da ita, don har Narabi muke zuwa hutu a matsayin gidan iyayen mijin Aunty hauwa, kuma Baban aminin Abban mu, kuma Abba ya saka mu tun muna yara kullum mukayi sallah mu dinga yiwa aminin shi kuma Baban mu, Baba Umar addu'a, kuma duk iya son gulmar ka bazaka taɓa gane Abba ko Ummi sun nuna banbanci tsakanin mu da Aisha ba, don yadda Abba yake nuna mata so to ko mu baya mana irin shi, don duk abinda Aisha tace a gidan shi akeyi, shi yasa kullum suna cikin faɗa ita da Hassan. Abba london ya kaimu domin yin degree ɗinmu, ni Accounting na karanta, inda Hassan ɗina kuma yace shi Barrister yake so ya zama, saboda dukkanmu art class muke a secondry school, hakan yasa kowan mu ya zaɓi course ɗin da yafi sha'awa, ni nayi accounting ne saboda tun asali ina son yanda nake ga Abba yana shigan shi na zuwa office, kuma a tsari na nafi son naganni ima aiki a banki, amma Allah bai nufa ba sai na zama malamin makaranta, duk da farko bashi bani a raina, shi kuma dama Hassan Burinshi kenan ya ganshi a tsaye yana shari'a a gaban Alƙali yana baza hamata yana nuna isa,Lol Allah sarki ɗan'uwana, Hussain ya faɗa bayan ya share wasu hawaye da suka zubo mishi, sannan ya ɗago kanshi yana dubana yace, "Hummy dukkan yanayi da kamannin Aisha haka kike, shiyasa tun ranan dana fara ganinki naji tsoron ko Aisha ce ta biyoni, amma daga baya sai nayi tunanin babu yadda za'ayi Aisha ta zauna har yanzu bata girma ba, idan kuma ke Fatimace toh babu yadda za'ayi ya zama kina ƴar shekara 16, domin nasan yanxu duk inda Aisha take tayi 35yrs, Fatima kuma ta kai 27yrs, toh nayi tunanin ke ɗin ƴar Uncle Baba ce ko kuma uncle Auwal, saboda kamaninki da iyayena yayi yawan gaske, duk duniya akwai masu kama iri ɗaya, toh yanayi na ɗabi'un ku fah"? Sai ya juya ya dubi Daddy daya ƙura mishi ido. "Humairah naso idan naga Daddy naga ɗaya daga cikin uncles ɗinane amma sai naga saɓanin hakan, amma duk da haka naji a raina keɗin ƴar'uwatace ko ta ƙauyen su Ummi ko kuma dai cikin garin misau, amma jikina yana bani ke ɗin ƴar'uwata ce ta jini", sunkuyar da kanshi yayi ƙasa yana ajiyan zuciya mai ƙarfi. Ni kuma da sauri na dubi Daddy nace, "Daddy wai hakane? Daddy Dr ɗan'uwa nane"? A ruɗe na jefawa Daddy tambayoyin lokaci ɗaya, shi kuma murmushi yayi yace, "sweet heart sauri da gaggawan na meye kikeyi haka? Mujira muji ƙarshen labarin Dr Hussain, sai suma suji ke ɗin daga ina kike? Kuma ki ɗin ƴar waye"? A razane na tashi na tsaya nace, "nifa Daddy bana son kowa yazama Baba nah sai kai, nifa kaine kaɗai Daddy na", na faɗa una ƙarasawa jikin shi na kwanta ina kuka. Dariya Daddy yayi yana buga baya na yace, "Humairah na waya isa yace ke ba ƴata bace? ae sai na gille misho kai, ni na taɓa ganin inda uba da ƴa suke son junan su ma irin ni dake? Wallahi babu Humairah, keɗin ƴatace ta cikina, wanda nake jin son ta fiye da komai na rayuwar duniyan nan, saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji sweet heart"!. Gaba ɗaya parlourn yayi shiru sai sautin muryan kuka na da yake tashi a hankali, shiru kamar bazai cigaba da magana ba chan kuma sai yayi gyaran murya ya cigaba. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/3, 17:02] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 44📑* *__________📖* Aisha tana da 14yrs muka gama karatun mu muka dawo service a ƙasar mu, babu ɓata lokaci muka taho bauchi wurin parent ɗin mu muka fara service ɗinmu hankali kwance, shekara babu wuya haka tazo har muka shekara guda muka gama. Muna da 22yrs muka dawo gida kowan mu ɗauke da masters ɗinshi, shekaran kuma Aisha ta gama secondry sechool da 1yr kenan, lokacin tana da 17yrs, mundawo Aisha ta samu admission a ATBU, inda zata karanta micro biology, tunda muka dawo Hassan tsamarsu da Aisha ya yi yawan gaske, babu hali ta zauna zakaji ya fara cewa ita da ba'a sonta an barta karatu a nija, haka zatayi ta kuka tana cewa Abba ita ma, dole saidai a fitar da ita waje, amma Abba sai yayita rarrashinta akan tayi haƙuri tayi a gabanshi, da ƙyar zata huce, ni kuma haka kawai na samu kaina da rashin yawan magana, idan har kaji bakina toh Ummi ne ko Abba na, amma Aisha kuma kaman ance ta dinga shige mun, ni kuma ina jan jiki da ita saboda ita ƙanwatace, amma kuma sai wani baƙon *Al'AMARI* yana faruwa dani, babu hali na kwanta sai nayi mafarkinta, kuma duk inda zanga budurwa ko ta nuna mun tanayina, babu wacce zata zo mine ɗine sai Aisha, watarana muna kwance da Hussain a parlourn mu nida shi, da yake side ɗinmu parlour ne da 2bedroom, inda ina amfani da ɗaya shima yana amfani da ɗayan, ina kwance na ɗaura dukkan hannuna na rufe idona kaman mai bacci, kawai saiga Aisha da mugun gudu ta shigo parlourn mu, saɓye da wani shegen wando da ɗan figigin riga a jikinta, sai wani ƙamshin daɗi ta keyi, kawai jin mutum nayi ya faɗo jikina. A razane na miƙe zaune, wanda dole ta ɗago itama ta biyo jikina muka tashi zaune tana rungume da ni, gaba ɗaya notin kaina saida suka neme kuncewa, saboda Aisha yarinyace wanda chest ɗinta yake cike da breast masu masifar girma da ɗaukan hankali, duk yadda naso tureta kasawa nayi, kawai ƙura mata ido nayi ina kallon bakinta yadda take ƙyalƙyala dariya tana duban idona. Ganin yadda nakasa ta ɓuka komai yasa Hassan ya daka mata tsawa yace, "ke kam mahaukaciyar ina ne da zaki rungume mutum ne wai? Don Allah ki ɗaga shi ya samu daman iya tashi, ƙatuwar yarinya kawai wanda bata san ta girma ba". Tashi zaune Aisha tayi amma bata bar jikina ba, tana hararan Hassan ta dube ni fuska a kwaɓe tace, "Yayah Hussain ɗina laifine idan na kwanta a jikin ka? Kaifa yayah nane ko"?, ta faɗa kaman zatayi kuka, riƙo hannun ta nayi na ɗan haɗiye yawon da ban san dalilin shiba, "Aisha yanzu ke kin girma, kuma islamically bai kamata ache kina hawa jikin mu ba yanzu, kinga gaskiya yayah Hassan ɗinki yake gaya miki, ki gyara kinji my dear"! na faɗa mata da yanayi na rarrashi. Amma yarinyar nan ƙara shige mun jiki tayi tana mutsu-mutsu a jikina, dole Hassan ya taso ya figota ya kwaɗa mata mari, kuka iya ƙarfinta ta ƙwala, sannan ta fita da gudu tayi hanyar waje. Cikin ƙarfin hali na dube shi nace, "me yasa ka mareta Hassan"? Tsaki yaja ya koma inda yake zaune yana operating laptop ɗinshi, sai jera tsaki yakeyi, daga baya ya ɗago ya dubeni, "My heart kasan wani abu? Wallahi idan naga Aisha a jikin wani namiji hankalina tashi yakeyi, ni na rasa me nakeji akan ta, bana son naga tana tarayyah da kowani namiji, gashi kullum na kwanta mafarkinta nakeyi, kai infact ma dai bari na gaya maka gaskiya, nifa ji nake kaman ina sonta, shiyasa bana son ta dinga zuwa inda nake, saboda ƙanwata ce, ban taɓa ganin irin wannan masifan ba", ya faɗa kaman zaiyi kuka. A razane na kalle shi, har wani rawa jikina ya keyi, "Hassan baka da hankaline? Kana tunani marar kyau Aisha ƙanwar muce wanda har abada babu aure a tsakanin mu, kuma koda a kwai aure a tsakanin mu kasan ni ya chanchanta na aureta ba kai ba", na faɗa ina ture nawa laptop ɗin da yake ajiye akan table ɗin gaba na, bayan na gyara zamana ina kallon shi. "Hussain amma kai jahili ne, Aisha ƙanwar muce, kuma na gaya maka koda aure tsakanin mu toh nine babbah ni yakamata na aure ta ba kai ba, garama ka daina wannan maganan, kuma kada na ƙara ganin Aisha a jikinka don sai na karya ta", Hassan ya faɗa kaman wani zautacce. "Lallai na yadda baku da hankali, ƙanwar taku uwa ɗaya uba ɗaya kuke muhawaran aurenta a tsakanin ku? Toh wani irin dabbanci ne kukeyi? Nawa ma kuke da har zaku fara maganan aure"? Ummi ta jeho mana tambayan bayan ta ƙaraso cikin parlourn. Cike da kunya Hassan ya gaya mata yadda mukayi amma bawai da nufin muna son Aishan ba, saidai kawai don mu kwatanta hakan ne. Ranta a matuƙar ɓace ta dube mu dukkanmu, wanda ni tun shigowarta na sunkuyar da idona a ƙasa, inajinta tana cewa, "wallahi ko a mafarki na ƙara jin kunyi wannan tunanin toh da Babanku zan haɗaku, idan ba dabbanci ba meya haɗaku da son ƙanwarku uwa ɗaya uba ɗaya? Gaskiya kada na ƙara jin hakan ya faru daga yau a tsakanin ku, ko wanku idan ya tashi aure yaje chan wani wuri ya nemi matar aure amma ba Aisha na bakam, ku biyu mawa zan bayar idan ma da auren kenan a tsakanin ku, bayan duk ɗaya kuke a wurina, kada ku sake hakan", ta faɗa tana duban mu dukkan mu. Turo baki Hassan yayi yana duban Ummi yace, "toh Ummi kija mata kunne wallah ta daina faɗo mana ɗakin mu, kuma ta daina shigewa jikin mu, don ta girma, muma kuma mun girma, ɗon gaskiya dukkanmu aure mike so, gara ta daina chakuɗa jikinta dana mu", ya faɗa yana dubana. Bakin Ummi a buɗe tace, "Hassan yaushe aka yaye ka har kake cewa kana son aure? Tsabar baka da kunya nawa kake Hassan"? "Ahh kaji Ummi dai? Wallahi aure muke so, ke Ummi kinsan irin namu halittan ne? Ni wallah ummi bazan wuce next year ba aure za amun, nifa kullum mafarki nakeyi da Aishan, shiyasa bana son ganinta a kusa dani, kuna ganin kaman bana sonta ne, wallahi Ummi kullum naganta sai naji dama bake kika haifeta ba, da babu abinda zai hanani aurenta", Hassan ya faɗa yana duban Ummin, dama Hassan asalin shi mutum ne wanda baya jin kunya faɗawa su Ummi da Abba komai da ya shafe shi, don ina tuna ranan da yafara mafarki da mace sai da yagayawa Ummi muna zaune a ɗakinta, lokacin duka Ummi ta kai mishi, Abba kuma yace ta daina dukan shi, tunda ya zaɓi gayawa iyayen shi damuwan shi, kawai tana bashi shawaran da yakamata, haka muka tashi muka fita nidai cike da kunyan su Abba ranan. Jin abinda Hassan ya faɗa ya saka Ummi zare ido tana duban shi ta kasa rufe bakinta, ganin haka na dube ta nace, "wallahi ummi nima haka nakeji, don Allah kice ta daina faɗamun jikina, ni narasa ma yanzun me yakawota har tazo ta faɗa mun jikina". "insha Allahu ta daina shigo muku ɗakin ku, yanzu ma tazo muku albishir ɗin zuwan Aunty Hauwa ce, amma kuka kama kuka daka mun auta na, kuma nasan Hassan ne mugun cikin", ta faɗa tana kai mishi ranƙwashi. Gucewa yayi yana dariya, "Ummi toh idan ba wulaƙanci ba, me yasa Aisha bata damu dani ba sai Hissain, tana shigowa fa faɗawa jikin shi tayi, me yasa ni ɗin bata faɗo jikina ba? Shiyasa na duketa saboda ta kiyaye gaba, don bana son ganin ta a jikin ƙattin maza", ya faɗa yana shigewa ɗakin shi da gudu ganin Ummi zata sake kai mishi ranƙwashi. Ajiyan zuciya nayi na mayar da kaina ƙasa ina wasa da wayan hannu na, kusa dani Ummi ta dawo ta zauna, murya a hankali tace, "Babanah! Aisha nina haifeta, bai kamata kubar sheɗan yayi galaba akan ku ba, ku daure ku ya fucheta a zuciyarku, dama akwai wani yayan matar Baba Umar da yace yana son Aishan har yayi magana wa Baban Narabi, amma ganin da mukayi Aisha yariyace, don yana da mata har da yara kusan uku, shiyasa bamu bada haɗin kai ba, don itama Aishan ta nuna bata so, amma idan munga zaku kawo mana tashin hankali wallahi zamu mishi magana ya fito, don ma yanzu baya ƙasan ne, idan ban da ku Aishan rabata za a yi wa ku biyun, ko kuma yayah kuke so ayi"? ta faɗa tana bina da kallo cikin tashin hankali daya bayyana a fuskarta lokaci ɗaya. Hannunta na riƙo cikin nawa murya a hankali nace, "Ummi kiyi haƙuri kada abar Aisha ta auri wanda bata so, ni dai kawai bansan meyasa nake jin ta araina ba, amma Ummi baki tunanin ko an chanja miki ne a wurin haihuwarta? Don wallahi Ummi nifa son aure nake mata, nayi na daure naso wata yarinya da ta nuna mun tana sona amma firr Aisha ta hana zuciyata son kowa sai ita". A razane Ummi take kallona, "Hussain ɗina, Aisha nina haifeta, bakaga irin kamannin da ta keyi dani ba? Babu ɗayan ku da yake kama ni bayan Aisha, wannan ma ae ya isheku ishara". "hakane Ummi kiyi haƙuri, duk sharrin shaiɗan ne, kuma zamu kiyaye kinji, yaushe Aunty Hauwan zasu iso"? Ummi tana murmushi tace, "sun wuce Narabi ne, suna fitowa nan zasu taho, kuma kutashi ku shiryah saboda taji daɗin ganin kun girma, ga Fatima idan ta girma ba sai a haɗaku da ita bama"? Murmushi nayi ina kallon Ummi nace, "Ummi ƴar Fatiman nan wa zai iya jiranta? Maganan gaskiya ae Hassan ya miki ɗazu, mu bazamu wani wuce next year ba zamuyi aure, kawai ki fara shiri ke dai", na faɗa ina dariyan jin kunya. Dariya Ummi tayi sannan ta tashi tafita a ɗakin. Ana idar da sallaɓ la'asar su Aunty Hauwa suka iso, a lokacin Ameer bai wuce 11yrs ba, Fatima kuma bazata wuce 9yrs ba, yaran sunyi wani irin girma da kyau sosai, duk inda sukayi kallon su nakeyi, don wani irin kama da Fatima da Aisha da sukeyi har ya ɓaci, Uncle Abdallah kamo hannun Aisha yayi ya zaunar da ita gefe yana duban ta cike da so kaman shi ya haifeta, yana dubanta yace. "Baby na haka kika girma? Yaushe zakizo mana hutu? Tunda naji Baban Narabi yace wai har mun fara samun surakune, kina son Muhammad ɗin?" Shagwaɓewa tayi ta kwanta a kafaɗan shi tana jijjiga kanta alaman ita bata son shi, ta buɗe baki tace, "Uncle nifa ya mun tsufah, ni nafi son miji irin Yayah Hussain, ni komai irin nashi nake so, don........." sai kuma tayi shiru ta rufe bakinta alaman ta tuna da wani abu, sai kuma tayi sauri ta kalli Ummi da ta zuba mata harara. Dariya Uncle Abddallah yayi yana buga kafaɗanta yace, "kada ki damu baby nah, bazamu taɓa miki auren dole ba, asali ma wanda kike so zamu baki kinji baby nah". Dariya tayi tana kallon uncle Abdallah tace, "koda yayah Hussain ne uncle"? "koda kuwa Yayah Hassan ne", ya faɗa yana mata murmushi. "Abdallah kutashi kuje kuhuta, bana son ka biyewa shirmen Aisha, taya zakana biye mata tana danganta kanta da ɗan'uwanta a aure kuma? Kasan yaran yanzu ba hankali ne da su ba". Dariya uncle Abdallah yayi bayan ya miƙe tsaye yana duban Abba yace, "Yayah kanajina da Ummi baka ce komai ba"? Abba yana kallon shi fuska a murtuƙe yace, "me zance maka naji kuna zuba shiririta kaida auta". Dariya uncle Abdallah yayi ya dubie ni yace, "Hussain idan ka amince ni zan baka auren Aisha don naga babu mai burge ƴata a duniya irinka, tun tana yarinya na lura da hakan, inaga kai ɗin kaine zaɓinta". "Uncle ae idan aure ne toh nine yakamata na auri Aisha, don nine babba kuma ni nake sonta ba Hussain ba, shi bai taɓa cewa kowacce mace yana so ba har yau, ni kuma ina sonta", Hassan ya faɗa yana duban Aisha da take hararan shi. Kallonta Uncle Abdallah yayi yace "wai doughter haka ne"? Turo baki tayi gaba tana hararan Hassan tace, "nikan bana son shi yayah Hussain ne yake burgeni, kuma nagayawa Ummi ni kan idan za'a mun aure yayah Hussain nake so, amma tace babu aure a e tsakanin yaya da ƙanwa", ta faɗa tana kallon Ummin kaman zatayi kuka. Tsawa Ummi ta daka mana da iya ƙarfinta, "ku wace kowa ya tafi ɗakin shi," sannan ta maida kallonta kan Uncle Abdallah, "Bana son haka Abdallah, baka taɓa ganin irin kalan nawa ɓacin ran bako? Haka kawai zaka zo ka ɗaga mun hankali acikin iyalina, kasan ƴan biyu ne su, wa zan bawa........." sai kuma tayi shiru tana dafa kanta, Abba da sauri ya riƙo hannunta, "kanne Ummin su"? Ɗaga kai tayi alaman hakan ne, sai lokacin Aunty hauwa da bata furta ko A ba tun lokacin da aka fara maganan sai yanzu, "Ummi BPn ki har yanzu yana yawan hawan ne"? Ɗaga kai tayi alaman haka ne yana yawan tashi. Cikin tausayawa Aunty hauwa take mata sannu da jiki, sannan uncle Abdallah ya dubi Ummi da murmushi yace, "Adda Allah ya baki lafiya, daga baya sai mu gama maganan mu, don wallahi burin Baba Umar kenan, kawai bai gaya muku bane, amma ni nan yagaya mun, shiyasa banga dalilin da zai sa a hana yara su fahimci su ɗin yayah suke a juna su ba"? Ummi ta ɗago ta bishi da wani irin kallon tace, "haba Abdallah kasan yadda nake son Aisha kuwa? Ni so kake na zama bani da ɗiya ta mace? Bayan ko ita Hauwa ta manta da cewa Aisha ƴarta ce, ta haƙura mun da ita duniya da lahira sai kai yanzu zaka taso da abinda bazai taɓa kasancewa ba, idan nace zan aura mata Hissain toh Hassan kuma fah? Baka tunanin rabewan zumumcin yara nane? Gaskiya kubar maganan nan daga yau kuma anan wurin". "Haba Adda ni baki son haɗa zuri'an ki danawa ne kam? Wallahi Ummi babu abinda nake matuƙar buri irin ace Hussain ya zama miji wa Aisha, amma ke narasa me yasa baki da wannan ra'ayin? Ko dai nice baki son haɗa iri dani"? Aunty hauwa ta ƙarasa faɗa idonta cike da ƙwallah. Runtse ido Ummi tayi ta cije bakinta, a hankali ta dubi Aunty hauwa, "Hauwa wallahi son da nakeyiwa Aisha ban taɓa jinshi kan Hassan da Hussain ba, asali ma tun ranan da na fara tozali da Aisha Allah ya saka mun sonta, toh ta yayah kike ganin ƴar da nake jin kaman ni na haifeta na barta ɗana ya aureta? Kalan watarana ya ƙuntata mata ni kuma bazan iya ɗaukan hakan ba? Kuma idan na amince yayah kike tunanin Aisha zataji na tsawon lokacin da ban barta ta san kece mahaifiyarta ba? Kuma yayah zanyi da Hassan da Hussain? Wallahi dukkansu sonta sukeyi"., ummi ta karasa faɗi tana share hawayenta. "Wallahi kamuwan ubangiji ne Adda, bai kamata ki nemi haramta abinda Allah ya hallata shi tsakanin bayin shi ba, ke yakamata ki danni ɗaya daga cikin su, sai abawa ɗaya, kuma wanda yafi chan-chanta Hussain ne, wanda tun son da ya nuna mata tana jaririya Mahaifinta ya gaya mun Aisha matar Hussain ne, idan sun girma zai haɗa wannan auren a tsakanin su", cewar Uncle Abdallah. Kaman an jeho mu nida Hassan da tun fitan mu muke laɓe muna jin me suke cewa, Hassan da iya ƙarfin shi yace, "Wallahi ni zan auri Aisha, don kawai duk kunfi son Hussain sai kuce shi zaku bawa? Bayan shi ɗin bai taɓa cewa yana sonta ba, kunsan ton yaushe nake sonta"? Ya faɗa kaman zai sha kwalan uncle Abdallah. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/8, 11:01] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 45📑* *__________📖* Rai a ɓace Ummi ta dubi Hassan tace, "Hassan nace bazaka auri Aisha ba, Aisha ƴa tace babu wanda ya isa ya chanja, ko ita hauwan ce ta matsa saidai mu rabu, don wanda yafita iko da ita ya mallaka mun ita duniya da lahira". Duk illahirin jikin Ummi rawa ya keyi, nidai ganin haka sai na razana, don ban taɓa ganin Ummi cikin wannan yanayin ba, saboda hakaɓda sauri na ƙarasa jikinta, hawaye ne yafara zuba mun ina riƙe da hannunta nace, "Ummi na Aisha ƙanwar muce dukkan mu babu mai aurenta, Aisha ma baza tayi aure yanzu ba sai ta gama karatun ta, ita da kanta zata zaɓi mijin da ta keso Ummina, ki kwantar da hankalinki" na faɗa ina share hawayen idon Ummi. "Hakane Aisha ta tabbata zata auri mohd kenan, ƙanin Aunty domin Baban Narabi auren ta kawai yake son ganin, kuma a irin halaccin da ya maku ya kwar da kanshi akan Aisha, ko na rana ɗaya bai taɓa nuna muku ko sa muku ido akan Asiha ba, ya kamata kuma ku daure ka bashi haɗin kai yaga auren Aisha da ran shi", Uncle Abdallah ya faɗa idon shi nakan Abba da Ummi. Girgiza kai Abba yayi alamar maganan Uncle haka yake, sannan ya maida kallon shi kan Ummi yace, "Fatima naso ace kin haƙura da hukuncin Allah kin yarda an sanarwa Aisha cewa bake kika haifeta ba, idan yaso sai a haɗa aurenta da ɗaya daga cikin yaranki, kinga komai yazo mana da sauƙi, tuwo na maina, amma idan kika bari Aisha ta auri wani daban, tou daga ranan ta fita daga ikon mu, kuma ko ba daɗe ko ba jima zatasan bake kka haifeta ba", Abba ya faɗa da muryan rarrashin Ummi. Girgiza kai Ummi ta keyi alamar a'a, bata samu daman buɗe bakinta tayi magana ba kawai muka ga Aisha a tsugunee a gefen Ummi, muryan ta cikin rauni tace, "Ummi idan bake kika haife ni ba waye ya haifeni? Ummi kigaya mun wacece ta haifeni bayanke?" tana jijjiga hannun ummi tana kuka. Runtse idanun ta Ummi tayi da ƙarfi bata furta komai ba, har saida Aisha ta ƙara maimaita tambayanta babu adadi tukun Ummi tace, "Aisha nice nan na haife ki, bakiga kin fi su Hassan kama dani ba? ae nice na haife ki", ta faɗa tana miƙa hannu wa Aisha da nufin ta matso jikinta, amma sai mukaga Aisha ta miƙe ta tsaya, a hankali ta matsa kusa da Uncle Abdallah, hannu ta miƙa ta riƙo nashi, muryanta na rawa tace. "Uncle duk duniya babu matar da nake so sama da Ummi na, amma cikin ƙasan zuciyata kuma babu abinda nake so dagani koji irin ka Uncle, kaida Baban Narabi ina jinku a raina fiye da tunanin wani mai tunani, wataran ina tunanin kaman nafi jin sonka sama da iyaye na", sai kuma tayi shiru tana sheshsheƙan kuka, a hankali ta cigaba da maganan ta. "Uncle kaine ka haifeni ko? Don Allah uncle kace mun ehh kaine, don wallahi Yayah Hussain duk duniya nake jin zan iya aure na rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali", ta ƙarasa faɗi tana faɗawa jikin Uncle Abdallah. Uncle Abdallah ma kukan yake yi bayan ya rungumeta, hala tun rasuwar Baba Umar yana jin bai sake kuka irin na yau ba, hannun ta ya jawo suka zauna, a hankali yafara warware mata komai, tun daga auren iyayenta har haihuwarta, har rasuwar Babanta, har zamanta hannun Ummi. Tashi Aisha tayi fuskanta da murmushi da hawaye, ƙarasawa tayi jikin Ummi ta rungume ummi, sun daɗe a haka sai Asiha ta ɗago tanata murmushi ta dubi Ummi. "lallai Ummi na ke ƴar aljannah ce, dubi irin son da kika mun kamar ke kika kawo ni duniya? Lallai Baba Umar yana kwance a kabarin shi hankali kwance don an nunawa gudan jinin shi kulawa, wallahi ban taɓa maraici ba kuma bazan taɓa ba, idan har ke Ummi da Abba kuna raye, kuma bazan taɓa kukan rashin Baba Umar ba, don kuɗin kune shi," tana murmushi ta sake riƙo hannun Ummi tace, "Ummi na kinsan daɗin da nakeji don naji ba ke kika haifeni ba kuwa"? ta faɗa fuskarta da tsananin fara'a, hakan yasa Ummi ta daina kukanta ta ƙura mata ido cike da mamakin maganan Aishan. "Aisha akwai wani mummunan abu dana miki ne a riƙon dana miki har kike murnan bani na haife ke ba"? Ummi ta faɗa a razane, tashi Aisha tayi ta tsaya tana duban Aunty Hauwa tace, "Aunty duk duniya babu mai zuciyar imani irinki keda Ummi na, ke kika sadaukar dani gareta don ta samu kwanciyar hankali, ita kuma tayi riƙo da Amana ta riƙe tamkar ita ta haife ni, kuɗin iyayena ku ƴan aljannane, zumunci ku ba kowa zaiyi ba, naji daɗi zan auri Yayah Hussain ɗina, Ummi na ta ko ina zata zama mun uwa, bani da matsalan komai a rayuwata, yau zanje wurin Baban Narabi na rungume shi nace mishi ɗan tsohu mai ran ƙarfe", ta ƙarasa maganan cike da farin ciki a fuskarta. "Aisha baki isa ki auri Hussain ba, ni nan ni zaki aura ko kin ƙi ko kinso, saboda ni nake sonki ba Hussain ba", Hassan ya faɗa yana matsuwa kusa da ita. Da sauri Aisha ta matsa kusa dani, "Yayah Hussain ka gayawa yayah Hassan kana sona, kagaya mishi yau ya sani, don ni kai kaɗai nakeso a rayuwana, kuma bazan iya son kowa bayan kai ba", ta faɗa tana riƙo hannuna. Hannu na saka na janye nata, ina duban ta cikin ido nace, "na taɓa cewa ina sonki? Ni har abada ke ƙanwata ce, amma Hassan shi yana sonki, saboda haka shi zaki aura, ni zan jira Fatima ce ta girma". Ihun Aisha ne gaba ɗaya ya firgita kowa da yake parlourn, da guda Aisha ta faɗa jikin Ummi tana cewa, "Ummi ki basu umurni mana Ummi na, kice yayah Hussain shi zai aure ne, dole Yayah Hassan yayi haƙuri, ni ba shi nake so ba", bata jira me Ummi zata ce ta tashi taje da gudu ta rungume Aunty hauwa, murya da ƙarfi tace, "mamie nah!". Runtse ido Aunty hauwa tayi, don Aisha bata taɓa furta mata mamie na ba, kullum Aunty hauwa ta ke ƙiranta, "mamie na kice musu ni yayah Hussain nake so, yayah Hassan yayi haƙuri", ta faɗa tana ƙanƙame jikin Aunty hauwa. Duban kowa Hassan ya tsaya yanayi, chan yace, "naga wanda zai aura miki Hissain ɗin bayan ni nake sonki, wallahi saidai kowa ya rasa daga ni har Hussain ɗin, idan yaso a bayar da ke wa ɗan'uwan kin chan kowa ya rasa a nan", ya faɗa cike da ɓacin rai. Abba ne ya saka kowa ya nemi wuri ya zauna, haka yayita ƙoƙarin kwantar mana da hankali, nidai na danne duk wani abu da nakeji game da Aisha a zuciyata, domin ina son farin cikin mahaifiyata da ɗan'uwa na, amma narasa mai yasa Hassan ya kasa fahimtar komai, kodan shine *ƘADDARAN DA YA RIGA FATA* akanmu? A lokacin Ummi ta nunawa kowa abinda taji tsoro ya faru a tsakanin mu, muryah a raunane tace, "na daɗe da sanin Allah ya saka ƙauna mai girman gaske a zuciyar ƴaƴana akan Aisha, tou su ƴan biyu ne, wa zan zaɓa wa Aisha wa zan bari? Don Allah ku fahimceni, nasan Hussain da irin haƙurin shi, duk irin son da yakeyiwa Aisha zai iya haƙura wa ɗan'uwan shi, amma kuma an shiga hakkin shi, don tun tana baby yake ce mun wannan ne wife ɗina idan muka girma ko? Tou Hassan kuma nasan halin shi ko na rana ɗaya bazai taɓa haƙurawa ɗan'uwan shi ba, kunga kuma Aisha ita hankalinta nakan Hussain ne, ta yayah zaman su da Hassan zai kawo mana farin ciki? Saboda haka nabar mu wuƙa da nama ku warware komai", sannan ta dawo da kanta kan Aunty hauwa tace. "Hauwa kinga dalili na tun farko ko? Bawai bana son mu haɗa ƴaƴanmu aure bane, kawai ina son kwanciyar hankalin Aisha ne fiye da komai, don idan ba tare da Hussain ba bazata taɓa samun nutsuwa ba, shi kuma Hassan ba zai taɓa bamu haɗin kai ba", Ummi ta faɗa tana share hawayenta. Murmushi Uncle Abdallah yayi sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar kowa, "tou ae ina ganin daga Hassan har Hussain mu muka haife su, basu suka haife mu ba, inaga tou babu wanda yafi ƙarfin mu a cikin su, yadda Hussain zai iya haƙuri da farin cikin shi don ɗan'uwan shi ya samu, tou me yasa shi Hassan ɗin bazai iya yiba? Ita fa Aisha ta riga da ta raba gardama, ta nuna Hussain shi ta aminta dashi, tou mai zai hana bazamu bata shiba? Shi kuma Hassan sai yaci girma ya haƙura, Allah zai bashi wacce tafi Aishan idan yayi haƙuri". "Bazan taɓa haƙura da abinda nake so ba, dole ne ma a bani Aisha ko kuma dukkan mu a hana kowa, amma bazai yiwu dukkan mu ku kuka haife mu ba amma zuciyar ku kullum sai tayita karkata kan ɗaya, don nafi kowa sanin dukkanku kunfi son Hussain akaina, shiyasa kuka nunawa Aisha son shi tun tana ƙarama, dama da niyyyanku akan shi shikaɗai ko"? ya faɗa yana hararan inda nake. Tsawa Abba ya daka mishi, muryah a hargitse Abba yace, "na rantse da Allah Hassan babu mai baka Aisha, kuma idan ni na haife ku gobe zamu tafi wurin Baban Narabi a ɗaura auren Hussain da Aisha, domin mu muka haife ka bakai ka haife mu ba, kuma Hissain yafi dattaku da kamala, yafi ka chanchanta da auren Aisha, idan ya maka zafi ka gyara halinka, saboda haka kowa ya tashi ya bani wuri, kuma ku kwana da shirin tafiya Narabi gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya". Duk parlourn babu wanda bai razana da ɓacin ran da Abba ya shiga ba, domin shi mutum ne mai haƙuri da kawaici, daga gani Hassan ya kure shi ne, shiyasa yayi wannan masifan, ganin haka kowa ya tashi yabar musu parlourn, kowa jiki a sanyaye, na miƙe zan tafi Abba yace, "Hussain kaida Abdallah ku tsaya." Duk jikina rawa yake yi, ina tsugune dai-dai ƙafan Ummi, chan naji muryan Abba yana faɗin, "Hussain nasan kai mai haƙuri ne da ƙoƙarin nuna kulawa akan damuwan naka, wanda Hassan yakasa koyi da halinka, kuma a jikina inajin ko bayan raina kaine zaka tsaya mun akan gidan nan, Hussain na baka auren ƴata Aisha, ina son ka riƙe ta da amana tsakanin ka da Allah, kuma bana son kayi gaba da Hassan, don nasan tabbasa sai ya nuna maka, amma kaja girmanka, kuma ku kula da kwanciyar hankalin mahaifiyar ku don bata da Lafiya kada a ɗaga mata hankali da fitina kaji? Jeka Allah yayi muku Albarka". Ummi hannu ta saka tana shafa kaina, amma bata iya cewa komai ba, sai hawayen dana lura yana ta bin fuskanta, kiss na mata a forehead ɗinta sannan na miƙe na bar su a parlourn. Da asuba na tashi na shiga toilet nayi wanka nayi alwala na fito nayi raka'atul fajir, naiƙe zan fita zuwa mosque domin yin sallan asuba, kawai wani irin mummunan ihun Ummi na naji har cikin ƙwaƙwalwar kaina, da gudu na fita nayi hanyar side ɗin Ummi, ina zuwa daidai parlourn ta naga Aunty hauwa ma da Uncle Abdallah da Daddy da sauri sun ƙaraso bakin ƙofan ɗakin Aisha, inda a kasan wurin muka ga Ummi ta faɗi kaman wata gawa, da sauri Abba yayi kanta shida Aunty hauwa, ni kuma nida Uncle Abdallah muka leƙa ɗakin Aisha da yake ƙofan a buɗe. Wani mummunar faɗuwa gaba naji wanda tunda na zo duniya ban taɓa ji ba, wani irin jirine naji yana shirin kaini ƙasa, badon komai ba sai don ganin Aisha ƙanwata, rabin raina kwance gaba ɗaya jini na malalae a jikinta, ban tashi fahimtan komai ba kawai naji ni na zuɓe ƙasa, babu abinda na kara ji sai ihun Aunty hauwa itama tana faɗowa kaina". Dr Hussain yana kawuwa nan ya sunkuyar da kanshi yana zubar da hawaye mai masifan yawan gaske, duk illahirin jikin shi rawa, yana wani kuka ko mace albarka, murya a bayyane yana cewa, "shikenan Aishan mu, Allah sarki Aishan mu". Hummy ganin yanayin da Dr ya shiga ya sakani tafiya inda yake da sauri na rungume kanshi ina kuka nace, "Mutuwa tayi? Aishan dama ta mutune baby? Wayyo baby na kayi shiru don Allah, ina su Ummi"? Na faɗa ina ƙara rungume shi a jikina, shi kuma baiƙi ba ya manna kan shi a ƙirjina yana kuka mai sautin gaske. Gaba ɗaya su Abbi kukan suke shi da su Ummi, faisal ma kuka ya keyi kaman mace, Amaal kuma zuwa tayi ta rungume Ummi tana nata kukan. Jijjiga kai Daddy yake tayi yana faɗin "wannan shine ikon Allah, wannan duniya ƙaramar wurine, ikon Allah humaira wani ƙaddaran ne yake shirin maimaita kanshi kuma, yau kuma mai nake sake ji da gani a rayuwata?" yana kuka ya ƙarasa wurin Dr Hussain ya ɗaga shi daga jikin Hummy, duban irin yadda idon Dr ya koma ya saka shi jawo jikin shi ya rungume shi ƙam a jijinshi yana kuka yana bubbuga bayan Dr. Ni Aunty nice juyawa nayi na dubi miss xerks da ta wangale baki tana shaftara kuka kaman ance mata yau za' a mata auren dole da Hassan nace, "besty zo mu koma nigeria muyi kukan sai mudawo gobe idan Allah ya kaimu muji me yake faruwa ne? Hala ma mum sayyeed da jikar kulu suna ta vibration dom suji me yake wakana, haka muka fita sum sum sum mu ka bar su suna kukan su. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/9, 21:42] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 46📑* *__________📖* Uncle Abdallah kuma da Abba ganin nida su Ummi duk mun suma a wurin sai sukaji hankalinsu yayi matuƙar tashi, jiki na ɓari Abba ya ƙira number Dr su, shi kuma Uncle Abdallah yadda kasan tsohon soja haka jikin shi yake rawa, daga ya dubi Aisha sai yaji kaman yayi ta ihu don tsananin tausayinta da shiga tashin hankali, a zuciyar shi kuma yana ayyana duk wanda yake da hannu a cikin raping ɗin Aisha da akayi wallahi bazai barshi ya sarara ba. Dr su biyu suka zo, da yake Daddy ya gaya mishi case ɗin da yawa, zuwan su gaba ɗaya suka fara aikin ceto rayuwar mu, babu ɓata lokaci nida Aunty hauwa muka farfaɗo, amma Ummi dole suka ɗauketa akayi mota da ita, muna tashi daga ni har Aunty hauwa da gudu mukayi wurin Aisha, zuwa lokacin naga an rufe mata jikinta da bedsheet, ba kaman zuwan mu tana kwance haihuwar uwarta ba, rungumeta Aunty hauwa tayi tana kuka kamar ranta zai fita, nima haka na haɗasu na rungume ina tayata kukan, da ƙyar Uncle Abdallah ya sa muka sake ta, shi ya ɗauketa mukayi hanyar zuwa asibitin Dr Basheer, wato *CITY CLINIC* da yake wannan asibitin su Ummi suke zuwa, muna zuwa asalin babban likitan wato Dr Basheer yayi kan Aisha shi da wasu nurses guda 2, ita kuma Ummi ɗayan Dr sani ya rufu akanta. Ni dai ranan na koma kaman mace, kafaɗan Aunty hauwa kawai na kwantar da kai na sai kuka muke ta rerawa nida ita, daga Abba har Uncle Abdallah kallon mu sukeyi ba tare da sun iya furta komai ba, gaba ɗaya kansu suke ji ya kulle, waye zai shigo har cikin gidan ya iya wucewa har ɗakin Aisha yayi mata wannan mummunan illar ba'a ganshi ba? Gaskiya abun yayi matuƙar ɗaure musu kai, kawai sunyi shiru ne suna jiran farfaɗowar Aisha da Ummi ne kawai, sai su shiga bincike. Ummi bata daɗe ba ta farfaɗo, amma Aisha sai da tayi rabin awa tukun ta farfaɗo, hakan ma tana farfaɗowa suka mata alluran kashe zafi don su samu su mata ɗinkin wurin, domin ba ƙaramin jin ciwo tayi ba, bayan an gama komai su Abba suka bi Dr basheer har cikin office ɗin shi, inda yayi musu bayanin BPn Ummi yayi mummunan hawa, ya kamata a kiyaye abinda zai dinga tayar musu hankali, sannan case ɗin Aisha kuma yayi musu jajen abinda ya faru, sannan ya ce su neme police a cikin case ɗin, don ma abinda ya kamata suyi ne tun farko, wato saida police tukun ya karɓi Aisha, a haka muka wuce zuwa ɗakin da Ummi take kwance idonta a rufe kaman mai bacci, amma kuma ba baccin ta keji ba, kawai tana sauraren kukan da Aunty Hauwa ta keyi ne, wanda ta kejin shi kaman zai fasa mata heart ɗinta. Gefen Aunty hauwa Uncle Abdallah ya zauna yana ta rarrashinta, yana kuma roƙonta da ta je wurin Aishan ta zauna da ita, shi kuma Abba zuwa yayi ya riƙe hannun Ummi, wanda tana jin zuwan shi inda ta ke ta buɗe idon ta a hankali , ƙurawa Abba ido tayi nata idon ma ya fara zubar da hawaye. "kiyi haƙuri Fatima, insha Allahu yanzu zamuje mu miƙawa police case ɗin, kuma ina da tabbacin zasu gano wanda ya shiga har gidan ya aikata wannan mummunan aikin wa Doughter, insha Allahu zamu bi mata hakkin ta", Abba ya faɗa yana jijjiga kan shi alaman abinda yake faɗa babu fashi, hannu Ummi ta miƙo mishi ya ɗaga ta, zama tayi fuskanta ɗauke da wani irin ƙunci, amma sai da tayi ɗan murmushi kaɗan, ido ta ƙurawa Aunty hauwa na zuwa wani lokaci, sannan ta dawo da kallonta kaina da nake tsaye a bakin ƙofan ɗakin tun shigowan mu ina kuka a tsaye a wurin, sannan ta karkaɗa kanta, ta dawo da kallonta kan Abba, hannuta ta ɗaga ta ɗaura a kan saitin zuciyarta, "Abba wani police zaku nema akan wanda yayi fyaɗe wa ƴata? Bayan wanda ya aikata yana cikin gidan da kuke?" runtse ido ta sakeyi hawaye yana zuba a fuskanta da gudun gaske. Da sauri Abba ya dubeta yace, "ban gane me kike faɗa ba Fatima? Kina nufin kinga shigowan wani ne cikin gidan, ko kuma me kike nufi"? Ya faɗa gaba ɗaya hankalin shi a tashe. "Abban su kana tunanin akwai wani daban da zai aikata wannan mummunan aikin bayan ɗanmu Hassan? Tabbas Hassan shi ne yau ya saka hawaye mai zafi da ƙunan xuciyar da bamu san ranan ƙarshen shi ba a rayuwar mu, Hassan yau shi yasaka na kejin kunyar duban idon Abdallah da Hauwa, yake sani jin da wani idon zan dubi Baban Narabi, yayah zanji ranan da Allah ya haɗani da Baba Umar yaji irin saken da nayi na riƙon amanan da ya bani?" kuka Ummi ta saka mai ƙarfin gaske, wanda daga ni har Aunty hauwa ma kukan mu keyi, jiki na rawa Abba ya sake buɗe baki yace. "Fatima ban fahimci me kike nufi ba, shin kinga Hassan ya shiga ɗakin ta ne? Don Allah ki fahimtar dani Fatima, komai ya kulle mun", ya faɗa kaman shima raunin shi zai saka shi zubar da hawayen. Juyawa Ummi tayi ta dubi kowa da yake cikin ɗakin, sannan ta dubi Abba tace, "gamu nan dukkan mu a hallare a ɗakin, shi kaga Hassan a cikin mu? Baka tunanin mai ya hana shi zuwa inda muke? Wallahi jikina ya bani Hassan ne ya aikata wannan mummunan illar wa rayuwar Aisha, domin yayi katanga wa ɗan'uwan shi na auren Aisha, shi kuma a bashi aurenta, kuma nayi alƙawari idan har nono na Hassan ya sha tou na haramta mishi auren Aisha har abada". Waya da sauri Abba ya ɗauko ya shiga dialing number Hassan, wanda dukka layin shin a rufe suke, haka Abba ya ajiye wayan shi jiki a sanyaye, ɗago idon shi yayi ya dubi uncle Abdallah yace, "muje mu miƙa case ɗin zargin Hassan da mukeyi a wurin police" Abba ya faɗa jikin shi yana ta rawa, wani zufah mai azaban zafi yana karyo mishi. Murmushi Uncle Abdallah yayi ya matsar da Aunty hauwa dake lafe a jikinshi ya ƙaraso inda Abba yake, hannu ya dafa a kafaɗan shi yace, "haba Yayah! Kana ganin ni da kaina zan iya shari'a da ɗana ne akan ƴata? Wallahi Allah ya sauwaƙa, nasan koda Baba Umar yana raye bayida abinda zaiyi sama da addu'a da haƙuri, ae Hassan ɗan mune, kuma idan ba rashin godiyar Allah irin namu ba, ta yayah zamuyi shari'a da kai? Don kuwa yin shari'a da Hassan tamkar da kai mukayi, wannan abun mun ɗauke shi a ƙaddaran rayuwar Aisha, kuma wannan shine *ƘADDARA TA RIGA FATA* munyi fatan haɗa aure tsakanin Hussain da Aisha, amma ƙaddaran da ta gifta tsakanin Hassan da Aisha ta saka dole mu haƙura mubar Hassan ya auri Aisha, mudai fatan mu Allah ya bata sauƙi, don ni tun ganin Aisha ban zargi kowa ba sai Hassan, saboda irin kalaman shi da yayi tayi a daren jiya, dama duk hankalina bai kwanta ba, Allah-Allah nake gari ya waye muje Narabi akan maganan auren Hussain da Aisha, toh amma ga abinda Allah ya aiko mana, dole muyi haƙuri". "Idan kai kanaga ka haƙura tou ni ban haƙura ba, dole sai nayi shari'a da Hassan, kuma babu abinda zai hana auren Aisha da Hussain, don abinda yayi bai isa yasa mu chanja ra'ayin mu ba, nayi rantsuwa koda mazan duniya sun ƙare tou har abada Aisha bazata taɓa auren Hassan ba, sharrin shi ya koma kanshi", Abba ya faɗa yana miƙewa don tafiya wurin police. Uncle ne ya ɗauki waya ya ƙira Baban Narabi, a handsfree ya saka, sannan yayi sallama ya gaida Baban, murya a raunane ya shiga zayyanawa Baban abinda yake faruwa, a ɗaya ɓangaren kuma sai, "innalillahi wa'innah ilahir raji'un" Baba yake ta maimaitawa, bayan Uncle ya gama gayawa Baban komai, sai Baban yace ya bashi Abba, nan Uncle ya gaya mishi wayar tana handsfree kowa yana jin shi, gyaran murya Baba yayi sannan yace. "Gambo! Wallahi kaji Allah ɗaya yake ko? Toh idan ka fitar da wannan magana waje har wani daban ma yaji, toh ban yafe maka ba duniya da lahira, daga kai har Fatima sai nayi shari'a daku agaban ubangiji, kuma ban yafewa duk wanda yayi mummunan furuci wa Hassan ba tsakanin kai da Fatima ba, mu ƴan halal ne ba butulu ba, munyi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau, shin idan ɓarawo ne ya shigo gidan yayi mata haka yayah zakuji? Hassan fa mun sanshi mun san kuma shaiɗan ne yafi ƙarfin zuciyar shi ya saka ya aikata mata haka bawai don halin shi bane, saboda haka kubar maganan mun yafe duniya da lahira, kuma Aisha tana gama istibira'i za a yi auren su da Hassan ɗin", Baban Narabi ya ƙarasa maganan cikin dakiyar zuciya, ina jin su nayi sauri na runtse ido na, amma jin muryan Ummi da maganan da ta keyi cikin kuka ya saka ni buɗe ido na ƙura mata shi. "Baba don Allah kayi mun rai, wallahi Hassan idan ya auri Aisha bazan rayuwa ba, duk ranan da aka aira mishi Aisha ranan ni kuma zan koma ga ubangiji na, Baba Hussain na amince ya auri Aisha, idan muka bawa Hassan zai ga kaman yayi nasara ne akanmu, kuma Hassan bayi da halin kirkin da zai riƙe mun ɗiyata cikin mutunci, tunda baiji tausayinta ba ya aikata mata haka, baiji tausayin wani hali mu iyayen shi da ɗan'uwan shi zamu ji ba ya aikata mana wannan mummunan aikin ba, toh bazai samu abinda yake so ba cikin sauƙi, Baba tunda kace baka yafe ba idan munyi shari'a da shi ba ko kuma muka bishi da mummunan fata ba, tou Baba muma kamana adalci mu samu sauƙi a zuciyar mu, ka amince babu aure tsakanin Aisha da Hassan har abada", Ummi ta ƙarashe tana fashewa da kukan da ban taɓa gani tayi irin shi ba. Da gudu Aunty hauwa ta ƙarisa jikinta ta rungume ta ƙam a jikinta itama tana kukan gaske, murmushi Baban Narabi yayi cikin ƙarfin hali yace, "naji Fatima Allah ya muku albarka, ya baku haƙurin jure wannan babban damuwan a zuciyar ku, na amince kubawa shi Hussain ɗin idan bazai damu ba", sannan ya musu sallama ya ajiye wayan. Aisha ba ita ta samu kanta ba sai da tayi sati biyu a asibitin, bayan an sallame mu mun koma gida ne, sai uncle Auwal ya zo tare da Hassan wanda gaba ɗaya duk yabi ya lalace, duk yadda uncle auwal yayi Ummi ta daina kuka da ta ga Hassan amma kasawa tayi, dole saida Mama tazo daga Misau suka haɗu akayita kwantar mata da hankali, da ƙyar ta amince shima da sharaɗin ba zai sake shigo mata side ɗinta ba, hakan ba yadda aka so aka amince, ita kuma Aunty hauwa bayan sati ɗaya suka wuce da uncle Abdallah, haka gidan ya dawo shiru babu daɗi, nine ma dole nake zuwa parlourn Ummi nake ta yata ɗan hira, wanda gaba ɗaya Ummi ta kasa samun lafiya, bata kwana biyu bata kwanta BPn ta ya hau ba, ita kuma Aisha gaba ɗaya ma bata fitowa parlour, kullum tana ɗaki tare da Umma da aka ɗauko ta daga misau suna kwana tare, kuma hakan wataran Umman zata zo tayita yiwa Ummi faɗan yadda ta hana kanta saƙat. Shi kuma Hassan idan mun haɗu da safe da ƙyar yake iya ɗaga ido mu gaisa, nima kuma sai ina jin shi kaman wani baƙo, bana iya sakewa kuma da shi. A haka lokaci yayita tafiya har Aisha ta cika wata uku da faruwan abin, wanda zan iya cewa baifi sau 2 na taɓa ganin ta ba tunda abin ya faru, ana saura kwana uku ta cika wata ukun na ganta tana fitowa a ɗakin Ummi da bata da lafiya tana kwance, ni kuma zan shiga duba jikin Ummin, gaba ɗaya sai danaji zuciyana ya yanke, domin wani irin rama da Aisha tayi babu komai fuskarta sai karan hanci, muna haɗa ido tayi sauri ta sunkuyar da kanta, bata iya ce mun komai ba ta ratsa ta gefe na ta wuce, haka na bita da kallon cike da tausayinta. Ina shiga ɗakin Ummi kuma na samu Umma sai faɗa take tayi mata akan ta daina yawan zama tana wannan kukan, kallon Ummi nayi ganin yadda duk itama ta rame ta fita hayyacin ta kawai sai naji kuka ya zo mun, gaskiya Hassan ya wargaza mana duk wani farin ciki na zuri'ar mu, don Aunty hauwa kullum mukayi waya don taji jikin Umm, kawai kuka zakaji tana yi, wanda ni nakasa fahimtar meye matsalan Aunty hauwa, halin da aka jefa ƴarta ce yake da munta ko kuma halin da Ummi take ciki ne damuwan ta? *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/10, 10:38] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 47📑* *__________📖* Zuwa nayi daff da Ummi na zauna, a hankali na kwantar da kaina a kafaɗanta ina ta share hawaye na, "haba Hussain! Me yasa kai da zaka kwantar mata da hankali sai ya zama kai ne kake tayata kukan? Shin da wanne zataji, da abinda ya faru ko kuma da ciwon da yake damunta"? Umma ta ƙarasa maganan itama tana share hawayen da suke ta zubo mata akan fuskanta. Ranan jumma'a bayan an idar da sallan Azahar sai ga Baban Narabi Uncle sabo ya kawo shi, zama sukayi a parlour aka kawo musu ruwa da abinci, bayan sun gama ya saka a ka ƙira mu dukkan mu harda Hassan muka zo parlourn, kusa da Ummi Aisha taje ta zauna, wanda tun shigowar ta Baban Narabi yake ta zolayanta, amma haka ta kasa bashi amsa, sai ma share hawaye da ta ke ta faman yi, ina zaune kusa da Hassan na sunkuyar da kaina ƙasa, don ni babu hali na dubi Ummi na sai naji kaman nayita kuka, ga gefe ɗaya idan naga Hassan nakan ji wani baƙin ciki da ban san irin shi ba, kaman daga sama naji muryan Baban Narabi ya ƙira sunana, a hankali na ɗago da kaina na ƙura mishi ido. "Hussain wannan tafiyan purposly nayi shine domin kai da ƙanwarka, tun naji ta gama watan nin da musulunci ya yardar mata idan tayi anga tsaftar mahaifanta zata iya aure? Toh Alhamdulillah Aisha bata tare da cikin Hassan ajikinta kuma anyi mata duk test da ya kamata a mata lafiyanta ƙalau, yanzu abu na gaba shine maganan auren ku, wanda ni anawa shawaran ayishi ranan jumma'a mai zuwa, amma idan kuna da wani shawaranku daga kai har iyayenka, tou ina saurarenku", ya faɗa yana maida kallon shi kan Abba da ya sunkuyar da kanshi tunda Baban ya fara magana. Da ƙyar Abba ya buɗe bakin shi yace, "Baba bamuda wani shawara sai wanda ka yanke, ɗari bisa ɗari mun amince Allah ya kaimu wannan rana da rai da lafiya", Abba yana faɗa yaja bakin shi yayi shiru. Gefe ɗaya kuma Ummi ce da Aisha suke ta kuka wanda bansan meye dalilin su ba, wanda ni a tunanina ni yakamata na zauna nayita kukan, tunda macen da na fi so yau an wayi gari ɗan'uwa naafi kusanci dani, wanda ko a ciki tare muka zauna, yayi mata fyaɗe, haba da ne zanji suke tunani? Sunaga zan iya rayuwa da Aisha bayan Hassan yana raye? Kullum da abin zan dinga ganin shi, kuma bazan iya rayuwar aure da Aisha ba duk son da nake mata, a hankali na ɗago kaina na dube su, baki na rawa na fara magana. "Baba kabawa Ummi na haƙuri ta rage irin kukan da ta keyi saboda samun lafiyanta, nidai har ga Allah ba zanji daɗin kullum ina buɗan ido inaga tashin hankali a tare da ita ba, tayi haƙuri don Allah", na samu bakina da chanja abinda nayi niyan faɗa, wanda ina jin tsoron idan na faɗa yayah Ummi zataji a lokacin, kawai nabar wa raina na aikata shi kawai basai na faɗa ba, saboda kada Ummi na ta faɗi abinda bazan iya aiwatar da komai ba. Baban Narabi ne yayita mana nasiha gaba ɗayan mu, wanda Alhamdulillah naga alaman sauƙi a fuskar Ummi na, wanda ganin hakan ya saka ni ajiyan zuciya mai ƙarfi. Bayan sallan la'asar Baba suka wuce Narabi, inda zuwa safiya naga Ummi sun fara shirye-shiryen aure a gidan, daga ɗayan gefen kuma Mama ce tazo daga misau inda Umma suka haɗo suka fara yiwa Aisha gyara na musamman, gida dai naga alaman an rinchaɓe da shiri. Ranan talata wanda ya kasance sauran 3dys auren nagama duk wani shiri da zanyi, zuwa dare hatta mai mashin ɗin da zai zo ya ɗauke ni da Asuba na nema, ana idar da sallan ishaa na wuce parlourn Abba. Tunda na zauna Abba ya maida hankalin shi kaina, sai gaya mun abubuwan daya shafi rayuwar shi kawai yakeyi, zuwa wani lokaci yaje ya ɗauko mum key ɗin gida ya miƙa mun, yana duba na da murmushi yace. "Hussain kaine sanyi idanuna, wannan key na gidana da yake sir kashim road ne na baka shi duniya da lahira, dama na gayawa duk wanda ya kamata su sani, nabawa Ummin ka ɗayan key ɗin wanda tace zuwa gobe zasije suyi jere wa Aisha, wannan kuma nakane, Hussain Allah yayiwa rayuwarka albarka, Allah yasa duk inda kasanya ƙafanka kashiga kaga haske da rufin asiri a rayuwarka, Hussain yadda ka faranta mun ina roƙon Allah yabaka yaran da zasu maka sama da yadda kamun, Hussain duk wani abu da kamun daga ranan haihuwarka har zuwa yanzu har zuwa ƙarshen rayuwarka na yafe maka shi duniya da lahira", duk sai naji kaman nafasa ƙudirina, amma ina bazan iya rayuwa da matar da ɗan'uwa na ya kusance taba, har abada bazan samu nutsuwa da ita ba, rasa abinda zanyi nayi, kawai sai naje na rungume shi na fashe da kuka, abin mamaki duk dauriya da ƙarfin halin Abba, amma sai kawai naji shi yana kuka kaman mace, wanda nayi imani da Allah tunda abin nan ya faru bai samu ya cire abin a ranshi ba sai yau, saboda haka barin shi nayi yayi iya son ranshi, wurin ƙarfe tara na mishi sallama nace zan duba Ummi ne, da ƙyar Abba ya barni nabar parlourn kaman wanda yasan abunda yake mine ɗina. A zaune a bakin gadonta na sameta tana zuba wasu ƴan kunnaye a cikin kid ɗinta, ganina ya saka tayi murmushi, nima maida mata martanin murmushin nayi, a hankali na karasa inda take, hannu na saka na matsar da kid ɗin na zauna a gefenta, ita ma hannu ta saka ta maida kaina kan kafaɗanta. "Ummi nah!" na faɗa bayan na kwantar da kaina da kyau a jikinta, "Autana!" itama ta faɗa tana shafa kaina, da sauri na ɗago da kaina muka ƙurawa juna ido, daga nan mukayi dariya wa junan mu, domin idan taso raha takance mun yayan auta, yau kuma ta ƙirani da autan, wato ta tabbatar yanzu ni autan tane. Murya a hankali nace, "Ummi na ina sonki, kuma bana son na dinga ganin tears a fuskar ki, ummi bana son na dinga ganin wani ya ɓata miki rai ballantana ni da kaina, Ummi duk abinda na miki daga ranan da kika haifeni ki yafe mun". Shafa kaina ta dinga yi a hankali, chan kuma sai naji muryanta tana cewa, "Alhussain, wallahi tun daga haihuwarka har ka koma ga mahalicci na yafe maka duniya da lahira, ina roƙan Allah ya haska rayuwarku kaida ɗan'uwanka, Allah ya kare mun gabanku da bayanku, duk inda kuke a duniya Allah ya tsare mun ku", shiru tayi na wani ɗan lokacin sannan ta cigaba da cewa. "Hussain damuwa ɗayane, me hauwa zataji a zuciyarya? Na hanata xama da ƴarta, na hanata nunawa ƴarta ita ta haifeta, a ƙarshe kuma ga abinda ɗana yayiwa ƴarta, shin haiwa zata iya mantawa da wannan al'amari kuwa? Kullum sai nayi kukan abinda ya faru, ga tsananin kunyar Aisha da nakeji, domin bansan da wani ido Aisha zata dinga dubana da shiba, gashi tun ranan har zuwa yau ta kasa dogon magana da ni, iyakarta gaisuwa shima ba kullum ba Hussain", Ummi ta ƙarasa faɗi tana kuka. Hakan Nayita kwantar wa Ummi nah da hankali kuma na mata alƙawarin zan fahimtar da Aisha komai, amma nafi son Ummin ta kwantar da hankalinta tukun, haka mukayi ta hira har nagaya mata kyautar da Abba ya bani na gida, amma murmushi tayi tace ya gaya mata, hannu na saka a aljihuna na fito da key ɗin na miƙa mata nace ta riƙe mun idan zanje gidan zanzo na karɓi key ɗin, babu wani tunanin komai ta karɓi key ɗin, wurin 11:00 na dare mukayi sallama da ita na fita a ɗakin. Ɗakin Aisha na wuce, inda na sameta suna shirin kwanciya ita da Mama da Umma, bayan mun gaisa dasu nacewa Aishan tazo parlourn ta same ni, na zauna banfi minti 2 ba ta fito da zunbulelen hijabinta, har ƙasa ta tsuguna ta gaisheni, sai naji wani tausayinta kaman na fashe da kuka, a lokacin naji haushin Hassan ya mamaye zuciyata, ban san lokacin da na furta "Allah ya isa tsakanina da kai Hassan", da sauri Aisha ta ɗago idonta ta dubeni, sannan tayi ƙasa da kanta tace Yayah kana kishi a kaina ne? Kana sonane yayah?" duban ta nayi a zuciyata nace wato Aisha har gobe babu abinda ta keso sama da na furta mata ina sonta ko? Murmushi nayi na dubeta a hankali nace, "meye riban idan nace ina sonki bayan wani ya rigani furta yana sonki"?. Murmushi tayi tace, "Yayah aiko raina ne yake shirin fita babu abinda zan so irin naji kalmar ka kace, "Aisha ina sonki, toh bansan da wani farin ciki zan koma ga mahaliccina ba, domin nayi imani da Allah ko ajiye mu gida ɗaya akayi da kai bazaka taɓa aikata mun irin cin amanan da Hassan yayi mun ba", ta ƙarasa faɗi tana share hawayenta. "Aisha ina sonki! Ina sonki!! Ina sonki!!! Amma kinsaka jikina yana sanyi da ke saboda naga kaman kina fushi da Ummi na, wanda gaba ɗaya kin saka ta daina walwala damu irin nada, Aishan mu banji daɗi ba", na ƙarasa ina jijjiga kaina. Matsuwa tayi da rarrafe har kusa da ƙafana fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Yayah nah ko yau Allah ya ɗauki raina burina ya cika, mutumin da na rayu da son shi ya furta mun yana sona sau uku, nagode yayah nah! Nagode yayah nah!! Ummi kuma wallahi tausayinta ne yake saka ni kasa sakewa da ita, saboda Ummi ta nuna mun so sama da abinda ta haifa, amma ɗanta yazo ya cutar dani, shiyasa kullum na dubeta sai naga damuwan abun a kwance a fuskarta, ni kuma sai naji banji daɗiba, kuma ina samun rashin nutsuwa idan na ganta a haka, yayahn mu kuma ni bana so ace Aunty hauwa ce mamana, nafi son Ummin," ta faɗa tana turo bakinta gaba zatayi kuka. Murmushi nayi ina dubanta nace, "tou idan da ba Aunty hauwa bace ta taimaka ta haife ki tou yayah kike tunanin zan furta miki ina sonki"? Buɗe baki tayi tana kare hannunta akai, dariya tayi tace, "nafi son Ummi ta haife ni, ku kuma Auntyn Hauwan". Dariya nayi nace, "tou mun yarda daga yau kece ƴar Ummi mu kuma Aunty hauwa, saboda haka tashi muje muyiwa Ummi albishir ko zata samu yau tayi bacci mai daɗi". Sallama mukayi muka buɗe ɗakin Ummin, lokacin ta fito daga toilet daga gani alwalah ta ɗauro, da gudu Aisha taje ta rungumeta tana dariyanta irin na da tace, "Ummi mun yarda nida yayah na, daga yau kice kika haifeni ni kaɗaina, su kuma Aunty hauwa ce maman su, kinga an raba ko Ummi? Kuma kullum ni kaɗai zakiyi taso". Murmushi Ummi tayi tana duba na kaman tazo ta goyani ta keji, a hankali tace, "Allah yayi muku albarka, tabbas na yadda ki kaɗaice ƴata, kai kuma hussain kaxama surukina saboda haka fita kabawa uwa da ƴarta wuri zasuyi shawara", dariya dukkansu sukayi wanda nima sai da suka sakani nayi bayan hawaye ya cika mun ido, ina dubansu da yadda suka manne da junan su, sai naji kaman kada na tafi na barsu, domin nasan yanzu abu mafi tashin hankali da zasu shiga shine rashina kusa da su, amma kuwa bazan iya buɗe baki nace bazan iya auren Aisha ba, saboda Hassan, kuma bazan iya auren ta ina tunanin Hassan ne yafara kusantar ta kafin ni ba, haka na ɗaga musu hannu alaman bye-bye, na juya zan fita. "Yayah mu!" naji muryan Aisha a hankali ta ƙirani, a hankali na share hawayena na juyo ina duban su, "Yayan mu yau a ɗakin Ummina zan kwana, saboda haka kada kamana sammakon zuwa da sassafe, kabar mu sai mun neme ka", ta ƙarasa tana rungume Ummi, ni kuma kasa ce mata komai nayi tsabar tausayinta, murmushi kawai nayi na juya na fita. Ƙiran sallah asuba ya tashe ni, da wuri naja jaka na wanda kaya na basu da yawa a ciki, saidai dukkan credentials ɗina suna ciki, ɗakin Hassan na buɗe na ganshi a dunƙule yana jin sanyin Ac, rage AC nayi na dube shi na share hawayena, sannan naja ƙofan na fita, ina zuwa ƙofar gate naga bangies mai achaɓa, hawa nayi mukayi gaba dashi. *BARCELONA* Shine inda ya mun na taho, saboda nan ne inda na tabbatar su Abba baza suyi tunanin zuwa na ba, duk da lettern dana bawa bangies nace yabawa Abba nah, nagaya mishi dalilin tafiyana, kuma na basu tabbacin kada ma su fara nema na, don nayi nisa kada su wahalar da kansu. Yana zuwa nan ya ɗago da idon shi da sukayi jaa ya ƙura man shi, nima share hawayena nayi ina duban Daddy da naga shima hawaye yake tayi babu ƙaƙƙautawa, a zuciyana ina jin tausayin Dr nah babu adadi, duk da chan ƙasar zuciyata inajin zafin Aishan tunda ya taɓa furta mata kalmar so, wato ya taɓa son wata kafin ni kenan. Daga nan Dr Hussain ya cigaba da bawa su Daddy labarin haɗuwar shi dani a school da irin alƙawarin da mukayi wa junan mu, ya basu labarin har zuwa tahowa na saudi. "Ikon Allah Daddy ya furta da ƙarfi yana duban Dr yace, *ƘADDARA TA RIGA FATA* shine labarin ka kam Dr, toh yanzu ma jikina yana bani akwai aure kuwa tsakaninka da Hummy? Gaskiya ina tantama Dr" Daddy ya faɗa yana share wani hawayen. Da sauri Abbu ya ɗago yana duban Daddy yace, "kasan shine? Kuma kasan wani alaƙa ne tsakanin shi da Hummyn"? Duk a firgice Abbu ya jeho da tambayoyin wa Daddy. Shima Dr a razane yake duban Daddyn, yana kuma jira yaji me Daddyn zaice. "Kunsan danganta kar dake tsakanin Hummy da Aisha da kuma Hassan ne"? _TOH MAKARANTA KARATUN ƘADDARA TA TIGA FATA KU KASANCE DANI A SHAFI NA GABA DOMIN JIN ME ZATA KASAN CE, MEYE KUMA DANGANTA KAR HUMMY DA HASSAN DA KUMA AISHA, NIDAI BAZAN FASA SANAR DAKU DUNAN BOOK ƊIN BA, *ƘADDARA TA RIGA FATA*_ *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/11, 17:42] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 48📑* *__________📖* Hannu Daddy ya saka ya matso da ni kusa da shi, jiki na rawa na kwantar da kaina a kafaɗan Daddy, duk wani tsoro da firgici ya gama bayyana a fuskana da gangan jikina, don har a zuciyana ina gudun abinda zai sa aure tsakanina da Dr ya haramta, a zuciyana sai addu'a nake Allah yasa Daddy na shine mahaifina, Allah yasa ba riƙo na Daddy yayi ba, a fakaice na maida kallona kan Dr mu, amma dukkan hankalinshi da nutsuwar shi yana kan Daddy, dole na dawo da dubana kan Daddy da naji yana gyaran murya. "Ranan monday na dawo daga office kenan na samu ƙiran wayan Baba nah, inda yace mun duk abinda nakeyi ya bani zuwa gobe da safe na taho Tilde, tambayan shi lafiya nayi tayi amma ya amsa mun da lafiya kawai yana nema nane da gaggawa. Lokacin ina zaune a cikin garin jos, ina da mata ɗaya da yara uku, dukkan su maza, akwai Ahmad wanda shine babban su, sai Aliyu mai bi mishi sai kuma Kabir wanda lokacin ana shayar dashi bai wuce 1yr ba, Ahmad kuma yakai 11yrs, Aliyu kuma yana 6yrs, akwai tazara tsakanin haihuwar yaran mu, wanda lokacin da mukayi aure saida matata tayi 9yrs tukun ta samu haihuwa, don har mun cire rai da samun haihuwar, escuse na ɗauka a wurin aiki na taho Tilde domin halartar ƙiran Baba nah. Bayan mun gaisa da mutanen gidan ne na shige kai tsaye zuwa parlourn Baban mu, bayan gaisuwa da tambayan iyalina na tattaro duk kan nutsuwa na da hankalina na miƙa mishi, don sauraron abinda zai ce mun, gyaran murya yayi sannan ya fara da. "Muhammadu a jiyane surukin marigayiyah ya zo har nan Tilde inda yake sanar dani dukkan abinda yake faruwa da jikarshi ƴar wurin Umar marigayi", anan dai Baba nah yayi mun bayanin dukkan abinda ya faru da Aisha da kuma tambayana ina nan akan bakan zan aure ta ko kuma su barta ta koma karatu? Ajiyan zuciya nayi lokaci ɗaya naji wani irin kwanciyar hankali ya ziyarceni, domin haka kawai Allah ya saka mun ƙaunar Aisha a raina, duk da idan da na haihu da wuri, tou da zan haifi wacce ta kaita, amma ina jin wani irin ƙaunarta a raina, don ko da Baba na ya mun bayanin raping ɗinta da ɗan'uwanta yayi bai sa naji bazan iya aurenta ba, na daiji rashin daɗi, amma kuma Allah yana gani ina son ƴar kyakkyawar yarinyar mai fara'ar nan, babu ɓata lokaci na sanar da Baba abinda yake zuciyana na amince da auren, shi kuma Baba yace mun tou cikin satin nan yake so ayi auren idan yaso daga baya sai ta tare, amma ban ƙi wa Baba ba, na amince kuma na gaya mishi ayi auren da tarewa gaba ɗaya, ina tafiya zanje na sama mata gida a cikin jos ɗin. "Muhammadu bazaka haɗa matanka gida ɗaya bane kake nufi"? Baba ya jeho mun tambayan. Murmushi nayi ina duban shi, "Baba banida ra'ayin haɗa su gida ɗaya yanzu, saboda nasan iyalina bata da haƙuri, kuma ta haifi Aisha zaman su wuri ɗaya zai kawo matsalah, amma nafara ginina, idan Allah yasa na gama shi dukkansu zan haɗa su wuri ɗaya, saboda gidan yana da girman gaske kowa da side ɗinta, inaga hakan zaifi sauƙi", na faɗa mishi fuskana cike da murnan bani Aisha da akayi, gawani daɗi da nakeji da bansan irin shiba, haka nayi sallama da Baba na wuce jos. Gida mai 2bedroom na kamawa Aisha a cikin garin jos, haka sati na zagayowa aka ɗaura auren mu da Aisha, duk yadda naso na samu haɗin kan iyalina mu zauna mu fahimci juna abin yaƙi yiwuwa, don wani irin masifa da tashin hankali ta tayar mun, inda daƙyar iyayenta suka shiga cikin maganan aka samu sauƙin ta, don ta dage dole sai na haɗasu da Aisha, a ganinta idan ba munafurcin namiji ba wai me yasa zan rabasu gida ɗaya, a haka na sanar mata insha Allahu nanda wata shida zanyi ƙoƙarin ganin na gama ginina mun koma gaba ɗaya, tunda dama aikin gidan kaɗan ne ya saura, nan ma ban tsira ba ta fara masifar wai dama ɗayan side ɗin nayi niyyan ƙara aure ne yasaka nayi shi, bayan da nace mata wa Ahmad nayiwa, nidai ganin masifar bana kare bane ya saka na ƙyale ta nabar mata gidan, don ranan aka kawo Aisha daga bauchi, haka na tafi na sallami baƙi ni kuma na wuce gidan Aisha. Aisha nada wata uku a gidana ta fara laulayin cikin ɗan satin da basu fi uku ba, tasha wahalan gaske wanda bata iya aikata komai akanta, dole ta koma Bauchi wurin Umminta, Aisha sai da tayi wata uku da tafiya a cikin na huɗu tukun ta samu sauƙi, lokacin cikinta ya kai 5month, sai lokacin Ummi ta dawo da ita, mukuma muna ta shirin komawa sabon gida, ganin haka Ummi tace tou zasu dawo bayan 2weeks idan zamu tashi su taya Aisha parking. Haka kowa akayi, bayan 2weeks muka koma gidan mu, inda dole saida Ummi ta ɗauko yarinya daga garin misau mai suna buɗɗo tazo ta ke taya Aisha da aiyukan gida, duk yadda Aisha taso suyi zumunci da maman su Ahmad amma firr taƙi suyi, haka dole itama Aishan ta haƙura, kuma gashi har wannan lokacin bata wani iya zama dani tayi hira, saboda har lokacin zuciyarta yana ga Yayan ta Hussain, don idan ina son zama da ita muyi hira tou dole na saku mata labarin Ummi da Hussain, tou ranan zan sha labari kam, ta dinga gaya mun cewa Hussain yayi kaza yayi kaza, wataran kuma zata dube ni tace, "idan na haifi ɗa namiji sunan Yayan mu Hussain zan saka, idan mace ne kuma sunan Ummi na zan saka", idan ta faɗa sai dai na bita da tou don mu zauna lafiya. Aisha tunda cikinta ya shiga wata takwas sai ta fara kumbura, kuma lokacin babu garin Allahn da zai waye bata ɗauko kayan sanyin da muka saya ba ta ware su, zata saka rigan acikin showel ɗin ta ɗaga sama kaman tana wasa da babyn, "Yi shiru babyn Mama, yi shiru baby nah, kana so kaga yayah hussain ɗina ko? Tou yayah hussain ya gudu ya barni, ya gudu yaƙi aure na, amma kai zakaje kanemo mun yayah na, ka kawo shi har gida, idan kaje kace mishi mummyn ka tayi missing ɗinshi sosai, mummy tayi kuka babu adadi, amma na yafe mishi ya dawo ya kula da Ummi da Abba da ni da kai, kace mishi muna son shi sosai", tou ranan zata kwanta tayita kuka. Da ƙyar nake samu na shawo kanta, shima sai na mata wayo nace mata, idan ta haihu lafiya nida ita da babyn mu zamu tafi neman yayah Hussain duk inda yaje, tou ranan zanga farin cikinta haka zata fara mun shirmenta tana cewa, "hmmm muna ganin yayah na zanyi tsalle na chafke shi nace bai isa ba dole sai ya tsaya munyi aure, don bazan taɓa iya ƙarasa rayuwa na babu shi ba", tana gama faɗa kuma zata fara kuka, tana mun rantsuwar wallahi tana sonshi, na mata alƙawari zan nemo mata shi sai na barta ta aure shi. Haka zan bawa kaina haƙuri nace mata idan ta kwantar da hankalinta ta haihi lafiya, ni kuma zan nemo mata yayah ta, kuma zan bar mishi ita ya aure ta, tou zatayi ta mun addu'a da godiya, wanda ni kuma tausayi take bani na rasa wani irin so ta keyiwa Hussain ne?. Cikinta yana cika 9month gaba ɗaya tayi wani irin kumburi, a wannan lokacin kuma Aunty hauwa suka zo da mijinta da ƴarta fatima, a wannan zuwan a Narabi suka sauƙa, bata daɗe ba tazo har jos don ta duba Aisha, ranan duk da ina namiji kuma mijinta da yakamata naji kishin Hussain a raina, amma kuka nayi kaman mace, saboda tausayin da uwar da ƴar suka saka ni, na sako ƙafa zan shiga parlourn Aisha domin mugaisa da Aunty Hauwa kawai sai naji muryan kukan su inda naji Aunty hauwa tana ce mata. "Aisha wallahi ina sonki fiye da komai a rayuwata, don kece abin farin cikina ina dubeki, tou amma girma da darajan Ummi yafi ƙarfin naƙi bata ke, kuma alƙawari nayi bazan taɓa nuna mata cewa nina haife kiba, amma bawai ina ƙinki ba, kuma rashin jina da kikayi game da abinda ya faru wallahi Aisha nafi kowa shiga damuwan abinda ya sameki, domin burina da addu'a na kullum naga na haɗa zuri'a da Adda na, kuma babu wanda ya kwanta mun irin Hussain a raina, wallahi nayi kuka ne saboda inaji ina gani za'a haramta aure tsakanin ki da Hussain, wanda shine burin mahaifinki, amma kiyi haƙuri Aisha wallahi ina sonki sosai sama da komai a rayuwata". Itama Aishan kukan takeyi tana gayawa uwarta irin son da takeyi mata, amma kuma ta tayata addu'a ta daina son Hussain ta so ni a zuciyarta, faɗin haka yasa dukkansu suka fashe da kuka. "Mamie nah wallahi ina so na cire yayah Hussain a zuciyata, domin na faranta wa Baban Ahmad, yayi haƙuri dani sosai amma nakasa, kimun addu'a", ta faɗa tana ƙara rungume uwar. "Aisha babban damuwa na a duniya guda ɗaya ne yanzu ya saura mun, naga Hussain ya dawo cikin mi ya zauna, sannan kuma naga aure ya haɗa shi da zuri'a ta, shiyasa nake addu'ar naga na haɗa shi da Fatima idan ya amince", cewar Aunty hauwa . Raba jikin su Aisha tayi ta turo baki gaba tace, "naƙi wayon ni zan haifawa Yayah Hussain mata, don ni ya chanchanci na zaɓa mishi mata, Mamie ni zan haifa mishi mata, da ina son na haifi ɗa namiji don na saka sunan yayah Hussain, amma yanzu mace nake so, na saka mata Aisha juniour don na bashi ya aura, kuma na saka shi yayi ta mata son da bai mun ba", ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi. Ranan naga soyayyah tsakanin uwa da ƴarta, haka dai na koma ban shigo ba awanann lokacin, sai kusan magrib na dawo muka gaisa. Bayan kwana biyu da zuwan Aunty hauwa Aisha ta tashi da naƙuda mai zafin gaske, wanda tun safen mukayi aisibiti da ita ana ganin haihuwar kaman yanzu amma abu shiru har azahar, dole ta saka na gayawa Umminta da Aunty hauwa, ganin yadda take ta neman su, da yake Ummin suna tare da Aunty hauwa a bauchi, ae kafin la'asar har sun iso Jos, kai hattah Baban Narabi sai da yazo, ranan naga dangi da irin soyayyar da suke nunawa Aisha, don Uncle Abdallah har labour room ya shiga, amma ganin yadda Aisha ta kumbura da kuka ya fito yana a nemo mishi likita ya cirewa ƴar shi cikin, gaba ɗaya hankalin su ya tashi ganin yadda Uncle Abdallah yake zubar da hawaye. Ana ƙiran Dr yace babu komai mujira zuwa 1hr idan bata haihu ba sai ayi mata CS ɗin, amma ya kwantar mana da hankali akan cewa haihuwar fari ne ya jawo haka, bayan sallan ishaa, Aisha ta saka aka ƙirani nazo, hannu ta miƙo mun ta riƙe ni gam-gam. "Baban Ahmad ka yafe mun duk abinda na maka, wanda na sani da wanda ban saniba," hawaye yana bin gefen idonta, kasa magana nayi sai jujjuya mata kaina da nakeyi, Aunty hauwa ce da Ummi da suke zaune a ɗakin suka fara mata magana ta ɗaina irin wannan maganan insha Allahu zata haihu lafiya, haka kowa ma yasha wahalan, murmushi tayi idonta da hawaye ta dube ni. "Ka nemo mun Yayah Hussain ɗina kabashi abinda zan haifa kace ya riƙe mun amana, na bashi duniya da lahira, idan ba shiba bana so ka bawa kowa riƙon babyn, kai da kanka nake so ka riƙe bawai don nafi sonka a kan iyaye na ba, kawai ina son duk abinda zan haifa ya tashi a gaban mu, hannun iyayen shi, saboda duk abinda zai faru da shi ba za ace sunyi sakaci ba, kasan me yasa"?, Ta tambayeni, wanda da sauri na jijjiga mata kaina da idona da yake tsiyayan hawaye, alaman ban sani ba. Murmushi ta sakeyi tace, "Ummi na ta min riƙon da ko Aunty hauwa bazata iya mun ba, ta bani tarbiya da kulan da ko iyayena ba lallai bane su bani, amma abin baƙin ciki lokacin aure na da kai sai naji ɗaya daga dangin Baba na tana cewa, abin tausayi saboda riƙon muguntar da akayi mun da sakaci saboda ni ba ƴar Ummi ba, shiyasa ta bari ɗanta yayi raping ɗina don mugunta, gashi yanzu yarinya ƙarama marainiyar Allah zata ƙare da auren tsohu, ni kuma jin haka ya sa nayi alƙawarin ko bana sonka, zan zauna da kai na maka biyayyah don Ummi na tayi alfahari dani, saboda haka duk abinda zan haifa kai nake so ka riƙe bashi ko kabata irin naka tarbiyan da kulawan, har sai ka samu Yayah na ka danƙa mishi riƙon, don nayi imani da Allah ko mace ne, zai kula da ita bazai iya cutar da ita ba, koda shi kaɗai ne tare da ita ba zai cutar da ita ba", ta ƙarasa tana sauƙe ajiyar zuciya. Kukan su Ummi ne ya ƙaru, ita kuma Aisha ta cigaba da faɗin, "Ummi ki yafe mun, mamie na ki yafe mun, kucewa Yayah Hassan ɗina na yafe mishi duniya da lahira, kuyi haƙuri bawai na hanaku riƙon abinda zan haifa bane, don nasan duk duniya babu wanda zai kai Ummina son riƙewa, amma bana son ƙara ja mata baƙin jini, kawai na amince ke ko mamie na ku riƙe babyn har zuwa 2yrs, sai ku maida riƙon hannun mahaifinta ko mahaifin shi, ku gayawa Yayah Hussain nayi burin sake ganin shi a rayuwata, amma insha Allahu abinda zan haifah zai nemo shi", ta faɗa tana runtse idonta da ƙarfi. Likita ne ya shigo yace mu fita za a shiryata suyi mata CS, domin ga chan Babanta a waje sai faɗa yakeyi, jin haka ya saka na ɗan rankwafa na sumbaci goshinta na mata fatan alkhairi, Ummi da Aunty hauwa ma da ƙyar aka fitar dasu a ɗakin, inda nake jin muryan Ummi tana cewa, " Aisha insha Allah ke da hannun ki zaki raini abinda zaki haifa, kuma insha Allahu tare da abinda zaki haifa zaku nemo yayanki", ta faɗa tana ta kuka. Fitowar nurse ne ya saka mu saurin zuwa inda ta ke, amma bata ce mana komai ba ta wuce da sauri ta ɗauko abu ta koma, chan bayan wasu mintuna sai gata ta fito da yarinya fara sosai a hannunta cikin farin kayan sanyi, da sauri Ummi ta ƙarasa jiki na rawa ta miƙa hannu tana faɗin, "Alhamdulillahi me muka samu? Yayah jikin ƴarmu kuma"? "Baby girl" nurse ɗin ta amsa mata batare da wani rawan jiki ba, murmushi nayi kaɗan dana dubi fuskar ƴar bayan Uncle Abdallah ya ɗago mun yana murmushi yace, "kaga mun ɓarauniya, wato ta sato mun kaman nin ƴata kaf ko"? Ya faɗa yana juyo mun da fuskar ƴar dana kasa miƙa hannu na karɓa, Ummi ce da take ɗan murmushin yaƙe tace, "tace kaidai ka gode Allah da kuka samu wannan baturiyar ƴar ta ɗauko kamanin mu sak ita ma bata ɗauko naku ba", murmushi yayi yana duban Aunty hauwa yace, "Hauwa kishi ne haka da gaggawa? Don kinga wacce ta fiki fari da manyan ido"? Ita dai Aunty hauwa yadda nakasa maida hankali kan ƴar ita ma haka tayi, dole aka miƙawa Baban Narabi da Mama kaltun take zaune a gefen shi. Yana karɓa kuma dr ya fito tare da abokan aikin shi, Hannu Uncle Abdallah ya miƙa mishi yana "sannun ku da aiki Dr, gara ae da akayi aikin, ae kunga uwa da ƴar duk sun huta", ɗaga kai Dr yayi yace, "Tabbas kuwa duk sun huta, domin ita ma Jaririyar ta huta da neman hanyar da zata fito, itama uwar ta huta da rayuwar da muke ciki mai cike da ƙalubale," shiru ya ɗanyi..... chan kuma sai yace, " ina mai bawa ahalin Aisha haƙuri da wannan babban rashi da akayi na wannan baiwar Allahn Aisha, domin a yau Aisha ta amsa ƙiran mahaliccinta, wanda dukkanmu munyi imani da Allah shi muke jira, saboda haka kuyi hakuri, wanda yafi mu sonta ya karɓi abinshi, amma gashi ya bamu madadinta". *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 [9/12, 12:06] Bsty: *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 49📑* *__________📖* ƙuuuu naji wani ƙaran da sai da yaso firgita ni, a razane kowa ya ɗago kanshi ya dubi uncle Abdallah da ya wanke Dr da mari, jikin shi na rawa ya chakomo wuyan rigan Dr yace, "kana hauka ne zaka ce Aisha ƴata ta rasu? Dubi iyaye da kakanunta da har yayunta duk a tsaye babu wanda ya mutu sai ƴata kake nufi? tou bazan yadda ba, komawa zakayi cikin ɗakin ka ɗauko ta mu chanja mata asibiti, ita kaɗai fah yaya Umar ya haifah, wa kake so na gani a madadin ɗan'uwa na"? kuka kuma ya fashe da shi bayan ya gama surutun shi wa Dr, hannu Baban Narabi ya miƙa ya riƙo Uncle Abdallah, sannan ya fara bawa Dr haƙuri, amma Dr bai wani ɗaga hankalin shi ba, yace wa Baban, "Baba ae haka zafin bugun mutuwa yake, mun saba ganin sama da haka ma, mudai addu'an mu Allah ya jiƙan ta da rahama, Allah ya raya abinda ta haifa". Sai lokacin idona ya kuma wurin su Ummi, amma wayam naga babu kowan su daga ita har Aunty hauwa, sai a lokacin naji muryan nurses ɗin suna basu haƙuri akan su ɗaga Aisha su bari a shiryata, nidai yadda kasan gunki haka nake bin kowa da kallo, sai wani bugawa da zuciyana yake yi kaman zai fito, a lokacin na daure naja ƙafana zuwa ɗakin da Aisha ta ke ciki, abunda na iya tunawa ɗaya ne, ina shiga naga gawan Aisha kwance akan gadon, gefe ɗaya wurin kanta kuma Aunty Hauwa ce ta kife tanata kuka a jikin Aishan, Ummi kuma ta riƙe ƙafan Aishan tana kuka tana magana, wanda gaba ɗaya bana fahimtan me suke cewa, ban ƙarasa sanin me ake ciki ba, sai zuwa wani lokaci naji muryan Baban Tilde yana cewa. "Alhamdulillah! Muhammadun ma ya farfaɗo, a dakata yaje yayi mata addu'a", haka naji muryan Baban Tilde akaina. Jin haka ya saka ni da sauri na miƙe zaune, da ƙarfi na furta, "Baba da gaske ne Aishan nawa ta rasu? Ko dai na razana da wuyan haihuwar da take shane nayi mafarkin ta rasu? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ina Aishan ne take Baba"? na faɗa ina miƙewa tsaye. Mutumin da ake ƙiran shi Abban Aisha shine ya saka hannu yana share hawaye ya riƙe ni, a taushashe yace, "kayi haƙuri mohd, Aisha ta amsa ƙiran wanda yafi mu sonta, kayi haƙuri kaje kamata addu'a yanzu za'a sallaceta", yana gama faɗin haka na juya na fita a parlourn, har inda ake shiryata na shiga, sunkuyawa nayi kan gawanta da nufin yi mata addu'a, amma sai zuciyata tayi rauni, kuka na saka ina riƙe da ita, da ƙyar na daure na mata addu'a, ina riƙe da ita naji maganan Aunty hauwa tana kuka, "shikenan Aisha bazamu rayu da ke irin na uwa da ƴarta bake nan har abada, da gaske mutuwa kikayi Aisha?" miƙewa nayi na bar wurin saboda wasu surutai da Aunty hauwa take tayin su babu tsayawa. Kwanan Aisha bakwai da rasuwa kowa ya watse, a ranan kuma akayi sunan yarinyar da ta haifa, wanda taci sunan Aishan, amma mukayi mata laƙabi da Humairah!", dakatawa Daddy yayi da bamu tarihin shi ya ɗago da fuskana da nake ta kuka tunjin lokacin da Daddy na ya fara kuka, ƙura mun ido yayi yana ɗan murmushi yace. "Sweet heart! kece yarinyar da Aisha ta haifa mun, kece farin cikina sama da komai a duniyata, kece farin cikin zama dake ya maye gurɓin baƙin cikin da na shiga a rayuwar baya", sannan ya juya ya nuna mun Dr Hussain yace, "wannan shine ɗan'uwan mamanki da take burin zaki nemo mata shi, gashi kuma kin nemo shin, wanda soyayyah ya shiga tsakanin ki da shi har ta kai ku da tunanin aure, ni dai zan cigaba da baku labarin yadda na reniki, daga baya zamuyi tambayan shin akwai aure tsakaninki da ɗan'uwan mahaifiyar ki? Kuma wanda yayi soyayyah da ita"? Da sauri na juya na dubi Dr mu, duk sai najini a tsorace kada ace babu aure tsakanin mu da baby, amma sai kawai naga ya kashe mun ido ya mun alaman kada na razana, a hankali kuma naga saitin bakin shi yayi alamar furta mun, "I luv u babyn baby"! Murmushi nayi na maida kaina inda Daddy ya cigaba da bayanin shi. Washe garin sunan Hummy su Ummi sukayi shirin tafiya da ita, amma da ƙyar na daure suka ɗauke ta, bayan na ɗaura ta akan cinya na ina duban tsantsan kaman da sukayi da Aisha, wanda har tsoro yake ban, nayi mata addu'a ina kuka kaman zan shiɗe, a haka Babana ya saka hannu ya ɗauke ta ya miƙawa Ummi da ita ma kukan take tayi. Amma abin mamaki lokacin da suka isa bauchi sai Ummi ta ɗauki Humaira ta ɗaura akan cinyar Aunty hauwa, tana dubanta tace, "hauwa bazan tauye ki a karo na biyu ba, ki riƙe ƴar Aisha ko zaki ɗan samu sauƙi a zuciyarki kada abin ya haɗu ya miki yawa, ni kuma zanji da jinyar da yake damuna, don tabbas rashin Aisha wani giɓi ne na lafiya a jikina, inaga banida ƙarfi da kuzari a zuciyata na iya wani abu mai muhimmanci, don idan naji kukar ƴar nan, zai iya tarwatsa mun zuciya na", ta ƙarasa maganan tana share hawayenta. Ita kuma Aunty hauwa bata ƙi ba, haka suka ƙira ni ita da Uncle Abdallah suka gaya mun zasu tafi da Humairah, ban ƙi ba don nima ina maijin tausayin Aunty hauwa ba kaɗan ba, daba don Aisha tace tafi son riƙon Humaira a hannu na ba da babu abinda zai hanani barwa Aunty hauwa, haka naje na musu sallama, na ɗauki makuɗan kuɗaɗe na bawa Aunty hauwa domin sayen madara dasu pampers ko wani abu da zai taso a sayawa Humaira, amma ranan naga kalan masifar Aunty Hauwa da Aisha ke bani labari. Dariya Daddy yayi yana duban Dr Hussain da shima dariyan yakeyi, ni kuma na zunɓuro baki ina kallon Daddy, don babu shakkah nasan halin irin masifar Kaka, don idan tazo dubani kullum sai tayi masifar wai su yayah Ahmad basu da mutunci, har sai Goggo mai raino na tayita bata haƙuri takeyin shiru, wani lokacin ceea zatayi ɗakin su zataje ta tsitstsigale su, nidai dariyanta zan tayi har ta huce, nima dariyan nayi ina duban Daddy da yake tayi kaman ba yanzu ya gama kuka ba. "Aunty hauwa ranan ta balbaleni inda take cewa mai na mayar da ita, ƴar Aishan ne zance zan biya ta ciyar da ita?" daga nan kuma sai ta fashe da kuka tana cewa, "me nayiwa Aisha a rayuwar duniya wanda uwa ta keyiwa ƴarta bayan shayarwa? Duk fa Ummi nane rayi mun hidiman da uwa ta keyiwa ƴarta, gashi Aisha ta bar duniyan ban nuna mata irin nawa soyayyah ba don ina jin kunyar Ummi na, don Allah kabarni na nunawa Humaira irin soyayyar da uwa ta keyiwa ɗiyarta", dole na mayar da kuɗina bayan na zauna na tayata kukan, ina ji ina gani aka tafi mun da sweet heart ɗina. Da ƙyar na daure sukayi 5month da tafiya nabi bayan su, haka naje na musu 2weeks, naji daɗin ganin irin kulawan da Aunty hauwa da ƴaƴanta suke bawa Hummy nah, kai hattah abokiyar zamanta Fadilah da ɗanta ba ƙaramun so sukeyiwa Hummy ba, haka na dawo cike da kewar ƴata. Babu wuya a wurin Allah, hummy tana shirin cika 1yr Aunty hauwa ta gaya mun, ae babu ɓata lokaci nayi shirin tafiya tare da mahaifiyata wanda ta matsa da son zuwa ganin jikarta, ranan da muka isa naji farin cikin da bazan taɓa mantawa ba, domin Sweet heart na samu babu inda bata zuwa da ƙafarta, gashi ko ɗaya bata mun ƙiyuwa, cikin jin daɗi akayi partyn cika shekaranta ɗaya, inda mukayi ta ɗaukan pics da ita, kuma abin sha'awa duk inda na saka ƙafa na yarinyar nan sai ta bini, gashi bakinta ta iya furta, Papa, kaka, Dada, mama, wato uncle Abdallah ne papa, yadda su fatima suke ƙiranshi, Aunty hauwa kaka, ita da Aunty fadila, fatima kuma mama, don firr fati tace itace uwarta, ni kuma abin daɗi wai Dada, tana nufin Daddy, naji daɗin da nakasa ɓoyewa a gaban kowa. Abin haushi da iyalaina suka mun shine ina dawowa nigeria, jikina yana rawa na kai musu pics ɗin Humaira su ganta, amma buɗan bakin maman su Ahmad sai cewa tayi, "kana tunanin cewa ƴaƴana suna da wata chan ƴar ubane? ae sam kada ka fara gigin haɗa su da ƴar matar ka, don kuwa inada labarin bawai ƴar ka bace ƴar matar kane wanda tazo da cikinta gidan nan, domin babu abinda ya haɗa yarana da ƴar ta, babu abinda zai saka mu kalli photon ta chan ta matse muku", tana gama maganan ta bar mun wurin da nake zaune, yaranta kuma suka bi bayanta, ranan nayi kuka kaman raina zai fita, amma haka na bawa kaina haƙuri na shige ɗakina, zuciyana cike yake da tausayin Humaira. Kasa zama nayi a ɗakuna na wuce chan ɗakin Aisha, inda na fara bin ɗakin da kallo, chan kan dressing mirrow ɗinta na ɗauko wani paper na buɗe, kawai sai ganin saƙon da ta bar nagani. "Baban Ahmad don Allah nabaka amanan abinda zan haifa, idan namijine kasaka sunan Yayah Hussain, idan mace ce ka saka mata sunana don tunawa dani, kuma bana son kabada riƙon ta wa kowa idan ba a hannunka ba, bana so taje ko'ina da sunan hutu don gudun abinda ya faru dani kada ya faru da ita, Kagayawa Ummi da Aunty hauwa duk mai son ganinta yazo har inda take ya ganta amma ban amince ka kaita inda suke ba, zumuncin yanzu shaiɗan ya shiga, ina tsoron wani yayi mata illar da nawa ɗan'uwan da nake ganin ciki ɗaya muka fito ya mun, bana so kabari rayi sabo da kowani cousin ɗita, ban yadda da kowa ba banda yayah Hussain ɗina, sannan kada kabar matar ka da yaranta su wulaƙanta mun ƴata ko ɗana, don kullum sai ta furta mun na kawo musu cikin shege gidan su, kona rana ɗaya bana son ta zauna a hannunta, kasama mata mai kula da ita mai hankali dattijuwa, nagode Allah ya musu albarka". A hankali Daddy ya maido da kallon shi kaina yace, "sweet heart kinji tushen da ban barki kin shaƙu da kowa ba, don bin umurni da kuma shawarar mamanki, nima sai naji ina gudun kije wani wurin don kada ki wulaƙanta, kuma ko a gidana ɗana lura basu sonki sqi ban barki da suba, kiyi haƙuri kinji", ya faɗa yana shafah kaina, nima murmushi nayi bayan na mike zaune ina share hawayen ido na nace. "Daddy! amma mummy na da ta rayu dani baƙa ramin so da kulawa zata nuna mun ba, gashi Allah ya amshi addu'anta na nemo mata yayah Hussain ɗinta, kuma shi kona rana ɗaya bai taɓa nufina da niyyan cutarwa ba, kullum ma ƙara nuna mun hatsarin zuwa inda maza suke yakeyi, ashe zuciyar Drn mu mai kyau ne tun asali", na faɗa ina duban Dr da murmushi cike da fuskana. *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻 *°🔘°ƘADDARA TA RIGA FATA°🔘°*      *1442H/2020M.* *AL-MUHARRAM/SEPT.*     ®☄ *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍* _{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_        ```🎐G•W•A🎐``` *_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼 *NA MARUBUCIYA:-* *AUNTY NICE✍🏼* *@wattpad AuntyNice.* *SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-* *NABEELAH ARABI* *NUHU ARABI* Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.* Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.* Bakandamiya:- *GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.* *SHAFI NA 50🔚📑* *__________📖* Shekaran Humairah biyu a hannun Aunty hauwa naje na taho da ita, ranan da zamu dawo na tausayawa Aunty hauwa da uncle Abdallah, domin kaman yara ƙanana, zama sukayi suna kuka kaman ance musu mutuwa tayi, haka na baraso cike da jin tausayin su, Fatima kuma ranan barin gidan tayi har saida na bar gidan tukun ta dawo. Kafin na ɗauko Humairah dama akwai wata goghon mu wanda Allah bai taɓa bata haihuwa ba, ƙanwar mahaifin muce, kuma ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa agidan su Baban mu, mijinta ya rasu, tou ita Baban mu yayiwa magana ta taho domin kula da Humairah, tadawo gidan da kwanaki kaɗan na taho ɗaukan Humairah, muna dawowa na danƙa mata amanan kula da Humaira, amma bawai na sakar mata komai na Humaira gaba ɗaya ba. Idan har na dawo gidan tou zamanta dawowa yake yi inda nake, domin side ɗina sai da nayi mata ɗakin wasanta, babu abinda ban zuba mata ba a ɗakin, duk lokacin da take wurina tou biyeta nake yi muyita wasan tare, wanda hakan baya yiwa matar gidan daɗi, ganin haka ya saka ta rage shigowa side ɗina sai dai idan kwanciya zatayi. Allah ya jarabce ni da son Humairah sama da komai a rayuwata, sannan duk inda zanje hankalina da tunanina yana gareta, shiyasa duk wani tafiya da zan daɗe na daina shi. Humairah na da shekara tara, Allah ya karɓi ran dattijon kirki, wato Baban Narabi",......... Da sauri Dr Hussain ya ɗaga kai ya dubi Daddy a razane yace, "Baban Narabi ya rasu"?. "Baban Narabi ya rasu Dr, mun shiga tashin hankali na rasuwar wannan dattijon, wanda bamu wani daɗe da shiga cikin jimamin rasuwar shi ba, Allah ya sake aiko mana na Baban Tilde, tsakanin su wata uku daidai, don ko takaba mama kaltum bata fita ba Baban mu ya rasu", tsayawa yayi da labarin, saboda ta'aziyan da Abbu da Dr suka fara yi mishi, kuma da alama Dr yaji rasuwar Baban Narabi ba kaɗan ba. "Humaira nada shekara 10 chif-chif akayi auren Fatima da Dr Hassan", ...... Da sauri Dr Hussain ya ɗago yace, "Hassan yayi aure da Fatima"? Murmushi Daddy yayi yace, "yanzu auren su shekara shida kenan, don yanzu haka yaran su biyu, Babban cikin ne, Aliyu haidar, inda akace sunan ka yaci, amma suna ƙiranshi da Haidar, ta biyun kuma sunan Ummi taci, amma suna ƙiranta da Nabeeha, yanzu haka suna zaune a garin Abuja, inda Hassan yake aiki achan, kuma yana da chamber shi na kanshi a chan. Aunty hauwa duk lokacin da tazo nigeria sai tazo tayi kwanaki a wurin Humaira, amma yanzu rabonta da humairah kusan 2yrs kenan, tun zuwanta sunan ƴar su Hassan Nabeeha bata zo ba sai last month, Fatima ma idan tazo tana zuwa ta duba Humaira haka ma Ummin ku, nidai sau kusan biyu nakan ɗauki Humaira muje har misau da bauchi gidan Ummi nakai musu Humaira mu wuni mu dawo, don tana ƙarama sosai ma nakan kaita mu wuni a bauchi mudawo. Kunji tarihi na da Humairah kenan a taƙaice. Shikuma Dr a zuciyar shi yana cewa, "lallai Aisha ba so na mata ba, duba da yadda zuciyata gaba ɗaya ya nace akan humaira, gaba ɗaya inajin ban taɓa son wani abu sama da ita ba, idan na rasa yarinyar nan ban san yayah zanyi na dawo dai-dai ba", ya gama magana da zuciyar shi yana kan binta da kallo. Shawara aka tsayar tsakanin Daddy da Abbu akan dole Dr ya haƙura a je Nigeria wirin Abban shi, domin bazai taɓa yiwuwa a tsayar da magana ba tare da sanin iyayen shi ba, amma firr Dr yace shi bazai koma ba, kuma Humairah ma bazata je wurin Ummin shi ba, idan itama Hassan ya gani yace yana sonta fa?. Murmushi Daddy yayi yana duban Dr Hussain yace, "amma ashe surukina ɗin ragon namiji ne ban sani ba, har kana tunanin akwai wani da zai iya ɓanɓareka a zuciyar Hummy"? Girgiza kai Dr yayi jiki a sanyaye yace, "nidai kawai ina tsoron mu koma Abba yace babu aure tsakani na da Humaira ne, ni nafi son ayi auren a nan tukun a koma chan ɗin". Abbu ne ya gyara zama yana murmushi yace, "Haba ɗana! ae idan babu aure tsakanin ka da Humairah ae tun anan ɗin ma baza mu aura maka ita ba, Aisha ae ba ciki ɗaya kuka fito da ita ba, da ace ciki ɗaya kuka fito da Aisha da babu abinda zai sa ka auri Humairah, tou amma yazo da sauƙi akwai aure tsakaninku, saboda haka ya kamata kaje kaga a wani hali da yanayi iyayenka suke bayan tafiyan da kayi na tsawon shekaru, inaga hakan shine yafi zama dai-dai", Abbu ya faɗa yana bubbuga kafaɗan Dr. Shirye-shiryen tafiyan mu nigeria ne aka shiga fafah, haka muka hallara gaba ɗayan mu sai garin jos, ranan da muka isa mun samu Yayah Kabir ya dawo daga school, oyoyo yaje yayiwa Daddy sannan ya dinga bin kowa yana gaishe su, yana ganina ya ɗaga mun hannu kawai ya wuce cikin gida. Parlourn Daddy duk aka wuce daga nan ni kuma da Ummi da Amaal muka shiga side ɗina, Gaggo nanny na muka samu zaune a parlour tana kallo, da gudu naje inda take na rungumeta, itama babu abinda ta keyi sai murnan ganina, tana cike da mamaki tace, "uwar ɗakina yau kece a ƙasar namu babu notice"? Dariya mukayi dukkan mu dasu Ummi, duk da bawai fahimtar abunda take cewa sukayi ba, sannan na gaya mata tare mukazo da Daddy na da baƙi, jin haka ta fita da sauri tafara haɗa musu abin sha, kafin ta haɗa abinci. Munayin sallah bayan mun hutu Ummi tace mun muje na kaita ɗakin Mama domin su gaisa, da mamaki na kalli Ummi nace, "Ummi bazafa ta kulaki ba, ko Kaka tazo gidan nan har ta tafi basu kulata ita da su Yayah Ahmad, kada muje ta wulaƙanta ki Ummi nah". Haka dai Ummi na ta sakani dole muka je side ɗin Mama, duk yadda nasan Mama da baƙin halin kada wani ya raɓe ta idan ba ita da ƴaƴanta ba, amma abin mamaki Ummi ta mata kwarjini haka ta zauna suka gaisa, inda Ummi take gaya mata ni ƙawar ƴarta Amaal ne, hakan Mama ta daure ta nuna jin daɗinta da zuwansu, bamu ƙara wasu lokaci ba muka koma nawa side ɗin. Waya Daddy yayiwa uncle Abdallah ya sanar mishi da komai daya shafi Dr da Humaira, kuma ya gaya mishi duk mun taho tare, Uncle Abdallah yaji daɗin labarin dawowar Dr Hussain, sannan kuma yace a nemi Abba agaya mishi. Haka Daddy ya ƙira Abba ya gaya mishi labarin komai da kuma zuwan mu, Alƙawari Daddy yayi mishi akan zuwa gobe idan Allahu ya kaimu zai kawo mu har Bauchi. A washe gari mukaje bauchi gaba ɗayan mu, inda muka samu uncle Auwal, uncle Baba, Aunty Fatima da mijinta Hassan da yaransu duk sunzo su, domin tun a jiyan Ummi ta ƙira kowan su ta gaya musu zuwanmu, hattah su Mama da Addagana da Bappan su Ummi duk sun zo, Umma da yake ta daɗe da dawowa gidan Abba saboda yawan rashin lafiyan da ta keyi kawai sai Abba ya dawo da ita gidan, gefen Aisha aka gyara mata ta zauna a wurin. Abin tausayi muna shiga parlourn Abba inda gaba ɗayan su suke zaman jiran isowar mu, da gudu Hassan ya taso yazo ya rungume Drn mu, dukkan su kuka suka saka suna rungume da junan su, da ƙyar ya sake Drn mu ya samu ya ƙarasa gaban Ummin ya tsuguna yana kuka baice mata komai ba, ganin haka itama Ummin ta fara kwanɗa mishi pillown kan kujeran tana kuka tana kwaɗa mishi, ganin baxata daina ba Drn mu ya rungumeta yana kuka, itama rungume shu tayi tana faɗin. "Haba Baba nah! Me na maka haka da zafi na chanchanci ka gujeni irin wannan tsawon shekarun? Katafi kabarni, Aisha ma ta tafi tabarni, da wanne kuke so naji? Kasan zafin rashin Aisha da nayi kuwa? Kasan Aisha ta tafi ta barni bayan bata sake jin yadda dani ba, ta hanani riƙon abinda ta haifa? Kasan zafin rashinka yadda na dinga ji a rayuwata kuwa"? Kuka mai sauti Ummi ta cigaba dayi tana rungume da Drn mu ƙyam a jikinta kaman wani zai ƙwace mata shi. Abba na murmushi yace, "yau ko naga inda ake mun fir ƙarfi? Farko ɗan'uwan shi ya rigani rungume ɗana, na tashi zanji ɗumin ɗana kuwa wannan matar ta rigani, gashi kuma ta gama chin zalin kyakkyawan fatan ɗan nawa da duka, kuma ta hana ni naje inda yake"? Ya faɗa yana matsawa kusa da Drn mu. Da sauri Drn mu ya tashi ya rungume Abba yana cigaba da kuka, da ƙyar ya buɗe baki yana, "Abba ku gafarceni tafiyan danayi na barku, Abba kuyi haƙuri bazan sake ba, nayi laifi bazan sake ba". Jin abinda yake faɗa nayi tsulum nace, "dama ina zaka sake tafiya bayan na chafko ka kadawo gida? ae yanzu zan maka ɗaurin da akeyiwa ragon layyah da karfi bazaka sake tafiya ko'ina ba, amma idan Ummi ta cigaba da kuka kuma zan ɗauke ka mugudu mu ɓuya, tun da nice na nemo ka, bazamu dawo ba har sai Ummi ta daina kukan shagwaɓa", na faɗa ina duban cikin idon Ummi, don kullum nazo gaisheta ko ita tazo ganina ta ringa mun kuka kenan tana tuna Mummy nah, har sai nace mata idan bata daina ba zan daina zuwa wurinta tukun ta daina. Murmushi Ummi tayi ta jawoni jikinta ta rungume ni ƙam, tana bubbuga baya na tana cewa, "ni Fati naga ta kaina da wannan sarkin surutun, tou yanzu yayah zamuyi ƴace ko jika? Wanne zamu kama ne"? Gaba ɗaya parlourn dariya aka fara, inda na dubi Ummi nace, "nifah jikace, don gaskiya bazan yadda da wayon nazama ƴaba, amma ita Aunty hauwa saboda masifarta zan yadda ta zama mun kaka, don idan uwace toh ta dinga masifance ni kenan bani da iko da bakin ramawa, amma ke kam naƙi wayon ni jikace, kuma Dr na ma jika zai zama miki gaskiya", na faɗa ina turo mata bakina gaba. Ranƙwashi na Drn mu yayi yace, "Ummin nawa kike tsagalgalewa"? Dariya dukkan su suka fara inda Aunty fati ta jawo ni jikinta ta rungume tana faɗin, "doughter wato uwar tawa kike cewa mai masifah? Tou bari ta iso zuwa gobe kiga iko da gadaran da zata sauƙe miko, ta hanaki auren ɗanta naga yanda zakiyi kina tsagalgale mana iyayen mu", ........ Tashi nayi da sauri daga jikinta na dubi Uncle Hassan da tunda muka iso yakasa sake wa, saidai idan anyi abu ya share hawaye ya kuma binmu da murmushi, "Uncle Hassan kaji Aunty Fati wai baza a bani babyn baby ba? Uncle kafi kowa kusanci da baby kace mata kabani shi", nafaɗa ina turo bakina gaba. Murmushi yayi ya kamo hannu na na dawo kusa dashi yace, "ki kwantar da hankalin ki uncle babyn baby naki ne ke kaɗai, kuma daga yau na baki shi kyauta, ni zan biya sadaki ma kafin Umma taje tayi kwaskwarima ta ƙwace miki shi, kuma Ummi ni da Aisha ne kaɗai ƴaƴanta, ke kuma jikace ke da baby, Aunty hauwa ce maman Baby, nida Aunty Fati kuma mune iyayenki, ni yanzu Baby ma ɗa yake mun", ya faɗa yana wani ɗaure fuska yana hararan Aunty Fati irin kada ta kawo mana wargi. Tsaki Umman misau tayi ta harari inda Drn mu yake zaune tace, "ni kuwa idan kun kwantar da hankali ku me zanyi da wannan tsohun tuzurun? Mutum saida ya ninka shekarun mijina a duniya kafin ya rasu zan so? Ni ae ko kyauta aka ban Hussaini bana so, kede da kika ga zaki iya kije chan ki ƙarata da sauran majina", .......... Parlourn kowa dariyan maganan Umma akayi, inda aka zauna aka cigaba da hiran bayan rabuwa. Bappan misau ne ya ƙara mana bayani akan hallacin da yake tattare da auren mu da Dr, inda kowa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali, kai wannan rana baxan taɓa mantawa dashi ba a tarihin rayuwata, don kuwa naga zumunci na ƴan'uwan mahaifiyata, don kuwa dukkansu da ƴaƴan su suka zo. Uncle Auwal yana da yara shida Aunty Ummi guda huɗu Affan, Aisha mai sunan mummy nah, Zahra mai sunan Ummi, sai khalifah mai sunan baban su Aunty ummi. Uncle Baba kuma yaran shi guda uku ne, Babban mai sunan Bappah ne inda suke ƙiran shi da Ammar, na biyun kuma mai sunan Baba Umar ne, inda suke ƙiran shi da Khalifah, sai ƙaramar kuma mai sunan Aunty hauwa inda suke ƙiranta da Jiddah, kuma naga alaman ba ƙaramin su Uncle Baba yakeyiwa yarinyar ba, don duk abinda yakeyi zakaji yace na Jeddah ne, duk abinda yaro zai taɓa zaice kubari na jiddah ne, ita kuma yadda kasan Aunty hauwa da faɗa haka ta ke. Washe gari zuwa dare su Aunty hauwa suka iso garin Abuja, da ƙyar suka kwana da safe suka kamo hanyar garin bauchi, da yake jirgi suka biyo da wuri suka iso, don wasu ma basu tashi a bacci ba suka iso. Gdan su Ummi yana da girman gaske, ga guest house mai kusan threebedroom har biyu, Ɗaya aka sauƙe su Ummi da su Abba a chan, ɗaya kuma mutanen misau aka ajiye a wurin, shi kuma Daddy na a ɗakin da yake parlourn Abbaha kuma side ɗin su Drn mu da Uncle hassan, inda ana uncle Baba da Uncle Auwal suka sauƙa, uncle Hassan gidan su suka tafi tare da Drn mu, side ɗin mummy na kuma Umma da su Mama da Addagana suka sauƙa, nidai ƴar lele a ɗakin Ummi na kwana tare da Amaal, amma Amaal da wuri tayi bacci, nida Ummi kuwa kwana mukayi muna hira, rabi gaba ɗaya labarin rayuwar Mummy na take ta bani, wani lokacin ta tsaya tayi kuka, wani lokacin ta girgiza kanta tayi murmushi, har sai wurin 4 na dare bacci ya sace mu. Zuwan Aunty hauwa da Uncle Abdallah wani kukan kuma ya sake tashi, domin ranan na tabbatar Aunty hauwa ba ƙaramin so ta keyiwa iyalan Ummi ba, don daga Uncle Hassan da Drn mu gaba ɗaya haɗa su tayi ta rungume su tana kuka, da ƙyar Bappah ya mata magana ta haƙura tayi shiru, gaba ɗayan su sakata sukayi a tsakiyar su, ita kuma dukka hannayenta suna ɗaure akan su kaman zata maida su cikinta ta keji. Bayan hira da gaisuwa da akayi a tsakani, Abbu yayi wa kowa bayani dangane da abinda ya faru da mu a saudi, da kuma dalilin daya kawo Drn mu yabada labarin shi, da zuwan Daddy na, gaɓa ɗaya kowa saida ya jinjinawa Dr irin son da yake mun, daga baya Bappan misau yayi mana nasiha mai ratsa jiki da kuma yadda da *ƘADDARA* mai kyau da marar kyau, inda yake cewa da babu wanda bai so auren Aisha da Hussain ba, amma ashe babu rabon auren a tsakanin su, gashi kuma da akayi haƙuri itama tayi biyayyah wa iyayenta gashi abinda ta haifa mafi soyuwa a gareta zata auri abinda itama taso sama da komai a rayuwarta, ya cigaba da duban fuskar kowa har ya kawo kan Aunty hauwa, murmushi yayi yace. "Hauwa kinga ikon ubangiji ko? Babu abinda kike so sama da kiga kin haɗa zuri'a da ƴar'uwarki, sai gashi alokacin da kika so Allah kuma bai nufa ba, dama haka iko na ubangiji yake abinda kake ganin shine dai-dai agareka sai kaga wurin Allah kuma ya chanja maka da wani indai har kabar mishi dukkan al'amuranka, gashi yau Hassan ya auri ƴarki ta cikin ki, ga shi kuma Hussain da rawar kai ya tsallaka ya tafi har kan jikarki, don tsabar basu son wani ya kwashe musu iyalen maman nasu duk suka handame a tsakanin su", Bappah ya faɗa yana duban Hassan da Hussain da dariya. Uncle Hassan ne ya buɗe baki yace, "dik wanda yayi zagin kasuwa yasan da wa yake, don tabbasa kaso Fatima ni kuma na ƙwace maka shiyasa kake gugan zana ɗan tsohu", Ranƙwashi Abba yayi mishi yana dariya yace, "mai Bappah zaiyi da zabiyar matarka", dukkansu dariya sukayi, sannan muka shiryah mukaje Narabi mukayi ziyaran ƴan'uwa. Tunda Affan ɗan uncle Auwal ya ƙyalla ido akan Amaal gaba ɗaya ya susuce gashi ba mai yawan magana bane, yadda kasan Uncle Auwal haka yake da shiru, amma duk hankalin shi da idon shi yana kanta, mutsi kaɗan idan za'aje wuri zakaji yace tazo ta shiga motan shi, duk yadda naso na jawota amma fir ya hana, haka dole na haƙura na barsu tare, shi kuma Faisal gaba ɗaya hankalin shi nakan Jedderh autar uncle Baba da yanzu take Ss3, duk wani feleƙe irin nata baya bashi haushi sai bibiyanta kawai yakeyi, ita kuma duk da kyau irin nata amma ganin ɗan balarabe sai wani falli ta keyi, nidai babu ruwana da kowa ta Baby na kawai nakeyi. Daga Narabi tilde muka wuce family house ɗin su Daddy, inda anan muka haɗu da su Yayah Ahmad shida Yayah Aliyu, ganin su yasa Daddy ya tara musu ƴan'uwan shi akayita musu faɗa domin su daina bin halin uwarsu suyi zumunci da ƴar'uwar su ƙwaya ɗaya, haka suka nemi gafaran Daddy dani gaba ɗaya. Duk yadda Daddy yaso zama dani Ummi taƙi mishi, domin shirin auren mu da Dr akeyi cikin satin nan, domin zamu koma school, kuma su Abba sun tabbatar mishi muna gama karatun mu ya tattaro ya dawo gida ya zauna, inda Umma tace idan bai dawo ba kuwa ita zata zo ta ɗauke ni mu dawo, haka yayita murmushi bai ce musu komai ba. Shiri na musamman Ummi na ta ke mun, don watarana inaji Aunty hauwa tana mitan wai Ummi me take so tayiwa ɗanta ne kam? Mallake mata ɗa ne za'ayi irin wannan shiryani da ake tayi"? Dariya Ummi tayi tace, "ɗan nakine dole sai mun kammale kanshi wuri ɗaya, din kada mu mishi laifi ya tattara kayan shi mu rasa kuma wa zai sake dawo mana da shi gida", da sauri na buɗe bakina bayan na ajiye goran tsumin Hajiya Aisha Aliyu Garkuwa mai haɗin gaske da nake sha nace, "Ummi ae duk inda Baby ya gudu zan bishi na tarkato abuna, ina zan bari wasu masu jan kunne su ƙwace mun shi? Kinsan faman danayi da shi akan wata ƴar india mai jan kunne kuwa? Sai da na zama ƴar bariki tukun na kwace abuna, na barta da sakakken baki, ga wasu masu halittan kajin mayu a hotel da in sun ganshi suke lanƙwasa kaman macizai, da kyat na fige mishi zuwa cin abinci inda suke na dage da bashi abinci, hmmm ta ina zanyi saken wannan haɗaɗɗen babyna ɗin ya kuɓuce wani wurin kuma"? Ina rufe bakina Aunty hauwa ta kaimun dundu a bayana, baki a buɗe tace. "anya humaira kinsan ku.ya kuwa? Mufa iyayen shine kika zaƙalƙalewa a gaban mu irin haka? Tou na sake ji kince babyn nan a gabana kiga yadda zan fasa miki baki, ɗan nawa da girman shi zaki na gaya mishi baby sai kace wani Affan". Muryar Baby naji shi da Aunty Fatima da Uncle Hasan suna dariya bayan sun shigo ɗakin Baby ya dawo kusa dani ya zauna yana duban Aunty hauwa yace, "haba Aunty nawa ma nake da baza ace mun baby ba? Gaskiya ni Aunty hauwa babu ruwanki, kawai kibarni a ce mun baby kafin na tsufah, yanzu Hassan ya isa a ƙira shi da baby ne bayan ya zama wani dattijo, har zai aurar da ƴa, nikan kubar mun sweet baby na ta faɗi abinda ta keso, ku toshe kunnen ku". Nidai zunɓura baki nayi ina kallon Aunty hauwa da wutsiyar ido, azuciyata ina Allah-Allah Ummi tace ta tashi ta tafi ta barmu, Amaal kuma sai dariya ta ke tayi ita da Ummi, uncle Hassan ne yace. "Aunty hauwa nima fah ana ce mun babyn nan fa idan babu idon ko" ya faɗa yana duban Aunty fati data buɗe baki tana kallon shi, dariya yayi yace, "ƙarya nayi ne baby luv"? Gaba ɗaya ɗakin dariya aka fara har da Auntyn hauwa, don Aunty Fatima tuɓurewa tayi tana ta rantsuwa tana duban Ummi tana cewa, "wallahi Ummi faɗi yakeyi, bana wani ce mishi Baby, nikan kuce ya bari Hummy fah ƴata ce yayah yake faɗa a gabanta". Dariyanta akayi tayi don gaba ɗaya Aunty Fati bata daina shagwaɓa har yanzu. Ranan friday aka ɗaura auren mu da Dr nah agarin Tilde, inda Baban mu dama ya yi ginin shi mai kyaun gaske a gefen gidan su, zuwa yamma a ka ɗaukoni zuwa garin bauchi, ranan Daddy na ba ƙaramin kuka yayi ba, wanda dayawa sai da suka taya shi kukan, ni kuma nayi kuka domin a ranan na ƙara tausayawa Daddy na rashin mummy na da yayi. A bauchi Aunty hauwa ce ta sauƙi mutane, inda Aunty Fatima da su Aunty Ummi da Aunty Indo ne suka ɗaukoni, kai ranan gaba ɗaya ahalin Baban Narabi ƙannen Kakana duk sunzo, inda duk yadda akayi da Uncle sabo da Uncle Abdallah kada su mun komai ƙi sukayi, domin Mota ko wannen su ya saya mun, domin Daddy na da Ummi da Abba sun cika mun gida na da gadaje masu tsadar gaske, ita kuma Aunty Fatima cewa tayi kada kowa ya sayi kayan kitchen, don itace uwa ita zatayi, lokacin dana leƙa kitchen ɗina kuwa ba ƙaramin kuka nayi ba, domin nikan yanzu bazan iya cewa nayi maraicin uwa ba, dama Daddy bai taɓa barina nayi kukan rashinta ba, yanzu kuma da ya sakewa zuciyar shi yabarni cikin familynta sai naji duniya bani da abinda yafi so. Abin dariya Uncle Hassan da baby suma sukace dole abar musu side ɗin Baby, wai suma zasuyi kayan uba a matsayin su na yayun Mummy, kowa ya ga irin kayan da suka zuba a ciki sai yayi santi, domin ɗaki biyu ne da parlour a side ɗin baby, kuma babu irin kayan alatun da basu zuba a ciki ba. Side ɗina ma parlour ne da 3bedroom, shima babu irin kayan da Daddy na bai zuba ba, nidai gaskiya naga gata a wurin ƴan'uwa na, inda kuma dama anyi zama domin magana su Amaal da Faisal, haka Abbu yace ya bada Amaal wa Affan, amma ya sanar musu sickler ce, haka su Uncle Auwal suka bada Jeedderh wa Faisal, an tsayar da maganan aure har sai Amaal ta gama karatu, ana gama biki washe gari su Abbu suka wuce saudi, inda mukayi kuka nida Amaal kaman ba nan da 1week zamu haɗu ba. Bayan kowa ya watse ne Uncle Hassan ya rako Baby, har parlour na suka shigo, abin dariya ya bani inda Baby yazo "wai ke ƴan mata ki fito ki gaisa da abokai na suna parlour," ɗago da kai nayi na ɗaga mishi kafaɗa alaman bazan fito ba, murmushi yayi ya ɗaga murya da ƙarfi yace, "Uncle Hassan tace bazan fito ba ka tafi saida safe" da gudu na tashi nayi hanyar parlourn ina, "uncle Hassan Allah bance ba, gani na fito", dariya dukkan su sukeyi inda Baby ya fito ta bayana yana ta dariya. Wuri ɗaya suka zauna, inda ban taɓa tsayawa naga irin kamanini su ba irin na yau, domin kayan su iri ɗaya ne, zaman da sukayi ma iri ɗaya ne, gashi dukkan su yau fuskar su ɗauke da farin glass yake, murmushi nayi nace, "uncle kuna kama fa". Dariya yayi ya fara bani labarin lokacin da suke school, yadda yake zuwa yace wa yarinya yana sonta, ranan da ta ganshi da wata sai yace bashi bane ɗan'uwan sa take nufi, kuma basu gane su, hakan sukayi ta ban labarin yarintar su ina dariya, duban uncle Hassan baby yayi yace. "Bros ka tashi ka tafi wurin mama Fatima, domin ni yau aikin furta I luv u ne akaina har asuba, inda hali ka taho mun da maganin ciwon baki, don tabbas yau leɓe ne sai sun kunbura da furta I luv u wa baby da zan tayi", dariya suka saka gaba ɗaya, Uncle Hassan yace, "gaskiya ban mantaba, kasha gaya mun duk daren da kayi aure kwana zakayi kana gayawa mai sa'ar matar ka kalman so". Na ɗauka wasa baby yakeyi, bayan tafiyar Uncle hassan wanka mukayi, ya ɗauko mun wata white rigar bacci, shima kuma white ɗin ya saka, duk muka feshe jikin mu da wasu turaruka masu ƙamshin gaske, haka na zauna a tsakiyar gado inda baby ya umurceni da na zauna, zama shima yayi ya tanƙwashe ƙafan shi irin tadda nayi,don har gwiwarmu suna haɗuwa dana juna. Tun ina ɗaukan abin wasa har na fara karaya da irin kalaman soyayyah da baby yake gaya mun, sannan duk bayan wasu lokuta zai nuna wani wuri a jikina yace, "baby idon ki yamun kyau, baby ƙwayar idonki yafi komai kyau a jikinki, baby ban taɓa ganin kyaun lips irin naki ba, baby dubi kyaun gashinki, ban taɓa ganin mace mai kyaun tsari na halittah ba irin naki," kuma duk inda zaiyi misali da shi sai hannun shi ya kai wurin. Duk yadda nake tunanin zan iya bacci amma kasawa nayi, gaba ɗaya ma sai naji wani hawayene mai masifar yawa yana bin fuskana, a hankali na furta mishi, "ina sonka Baby! Ina sonka baby nerh!!. Rungumeshi nayi da ƙarfi bayan munji an fara ƙiran sallan asuba, ranan gaba ɗaya familyn mu suka zo mun sallama, kowa ya koma inda ya fito, nidai duk inda naga baby sai naji anƴa akwai matar da tayi dace da soyayyan miji kuwa irin nawa? Gaskiya ina son Baby. Da dare haka baby ya ɗauko mana wasu kayan baccin masu ruwan sky blue, gaba kyaun su yafi na daren jiya da muka saka, a daren yau na ɗauka baby zai ci gaba da baiyana mun sirrakan zuciyar shine da baki, ashe nayi kuskure, soyayyar da ya ƙunsheta mai zafin gaske a zuciyar shi ce yau ya sauƙe mun ita a aikace, ranan nayi danasanin irin yadda nayita buɗe bakina ina kwwankaɗan tsumin Aisha Garkuwa da gumbarta da na sha, kai hattah wannan haɗin kazarta da haɗin nasha da kankanan danayi amfani dasu nayi dana sanin amsa a wurin Ummi babu musu na dinga ci. Aunty Fatima nane tazo tayita faman rarrashina ranan, don firr baby ya kasa gane kaina, daga tayi magana tace "haba doughter babyn kine fa", da karfi zan fasa mata kuka nace, "mummy babban mutumin ne zaki ce mishi baby? Na daina ce mishi baby, kawai Baban mutum sunan shi", haka zan faɗa ban lura ba Aunty Fati kuma sai ta ɓingile da dariya tana, "haba babyn baby". Muna gama school akayi auren Amaal da Affan, Faisal da Jeederh, lokacin kuma da ƙyar nake jan cikina wanda yayi nauyin gaske, haka muka zauna a gidan Ummi don firr naƙi komawa namu gidan, don gaskiya bazan iya da fitinar baby ba, don ko duba yanayina bayayi, haka na zauna a wurin Ummi na. Ranan talata na tashi da naƙuda mai matuƙar wahala, wanda dama lokacin Uncle Abdallah sun dawo nigeria da zama, suna zaune a cikin garin jos, haka Ummi ta ɗagawa kowa hankali, babu shiri Aunty hauwa ta tattaro ta taho bauchi, itama Aunty Fatima Ummi bata barta ta huta ba, domin ko arba'in batayi da haihuwar ɗanta ba, amma haka tayi ta ƙiran su, Aunty hauwa tana isowa ko rabin awa banyi ba na haifi ƴan biyu na dukkan su mata. Ummi tana ganin su ta dubi Baby tayi mishi gwalo tace, "mu aka sake zubuwa sak, kai Hauwa nida ke jininmu yana da ƙarfi, ko kuma nace jinina na da ƙarfi, hauwa kika biyo kamanni na, Aisha ta ɗauko mu, Fatima ta biyomu, Humaira ma mu sak, gashi wasu ƴan biyun yauma babu maraba damu kenan". Murmushi Aunty hauwa tayi tace, "waƴannan sun nuna mana so ne fisabilillah, da yake Adda bata haife mu a ƴanbiyu, kan Baba ƙarami ya fito kafin ni ya shiga tsakanin mu da rusheshen kai, sai yanzu Allah ya hukunta Hussain ɗinmu zai haife mu a tare, saboda haka, wannan da ta fi ɗan cikan fuska da kyaun sajen ita ce ni, wato itace *HAUWA'U KULU MAIJIDDAH* wannan mai ɗan dogon hanci da sirirn fuskar kuma kece Ummi na Adda na, itace *FAƊIMATUL ZAHRA'U*" ta faɗa tana dariya. Baby ma dariya yayi yace shikenan babu komai, next time masu kama dani za'a haifa ƴan mazaje a saka musu *ABBA NA DA BABA UMAR* Daɗi Ummi ta keji kaman ita ta haife su, Allah ya gani tana son yara mata, bata haifa amma ga ƴar uwarta da zuriyarta suna ta haifa mata, haka suka koma gida akayiwa yaran wanka, kayan sanyi farare masu kyaun gaske aka saka musu, kowa yazo ya gansu sai yaji kaman ya lashe su. Aunty Fati tana zuwa ta fara santin yaran, haka ta fara cewa ita za ayiwa takwara ita da Mummy na, amma harara ta samu daga Aunty hauwa tace, "har kunfi mune nida Ummi nah"? Haka kowa ya haƙura ymranan suna ƴanbiyu suka ci sunan su Ummi, inda muke musu laƙani da *NASREEN* da *NABEELAH*. _AYAU NAKAWO ƘARSHEN LABARIN BABYN BABY DA HUMMY, WATO *ƘADDARA TA RIGA FATA* INA ROƘON ALLAH KUSKUREN DA MUKAYI ACIKI ALLAH YA GAFARTA MANA, ABINDA MUKE SO KUMA MU ISAR MAI KYAU ALLAH YASA YA SAMU ISA, WANNAN SHAFI NA SADAUKAR DA SHI WA QUNGIYAR *GASKIYA WRITERS ASSOCIATION* ƘARƘASHI JAGORAN CIN BESTY NA *MISS XERKS* GASKIYA BAKI BAZAI IYA FURTA MIKI KALMAR GODIYA DA ƊAWAINIYA DA KIKAYI DANI TUN DAGA FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI BA HAR ZUWA YAU, WANDA SUKE ƘIRANA SUYI MUN GODIYA DA JINJINAWA AƘAN WANNAN BOOK, DA WANDA SUKAYI TA WATSA MUN BOOK ƊIN NA DON YA ISARWA MUTANE NAGODE MUKU SOSAI_ *HUSSAIN 80K* *JIKAR KULU* *DR MOHD ATK PALACE* *AUNTY SIS* *AISHA MUSA BABA* *DA DUK WANDA SUKA MUN POSTING BOOK NAGODE SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI* *ƘAWATA BEBI S DAWAKI* *ZEE YAWALE* *FATI YAWALE* *GODIYA MAI TARIN YAWA A GAREKU* *©AUNTY NICE CE*✍🏻✍🏻✍🏻