INTEESAR BOOK 3 Aliyu bae sake ce mata komai ba sae gudun bala'in da ya dinga yi kmr xae tashi sama, hankalinta yyi mugun tashi ta ma rasa mae xata ce masa don tsoro, ta dake daga karshe da kyar Muryarta na rawa tace "wae ni ya Aliyu ina xa ka kai ni ne don Allah," ya taka brake yyi arkin da sauri yana kallonta cikin tsawa yace "kika ce me?" ta tsorata ssae ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yyi mata wani mugun kallo yace "sayar da ke xanje nayi," bata dago kai ba bare tace masa komai yyi kwafa ya ja motar suka bar wajen, lkci daya hankalinta ya kwanta ganinsu da tayi anguwansu, yana gama parkin kuwa ta bude kofa xata fita da sauri yyi hanxarin fixgota yana hararta yace "kin dae ji me na ce maki, kuma wnn hawayen bana son ganinsa a fuskarki" ta fixge hannunta ta fice da sauri daga motar snn ta watsa masa harara hade da jan tsaki tace "ban ji ba," tana fadin hka tayi cikin gidan da gudu ya bita da sauri, tana isa gate cikin rashin sa'a tayi tuntube tayi gaba xata fadi yyi saurin rikota ta fado kansa, ta marairaice fuska a tsorace tace "don Allah kayi hkuri ba da kai nake ba," bae ce mata komai ba ya shiga janta kmr wata dabba tana biye da shi a baya har suka iso falon Abba, sae a snn ya juya yana kallonta fuskarsaa murtuke yace "Allah ya baki sa'a ki ki yin abinda nace maki, wllh sae na kusan sumar dake a gida yau," bata ce komai ba ya ja ta suka shiga cikin falon, Abba na xaune remote a hannunsa yana canxa tasha, Aliyu kadae ne yyi karfin halin yin sallama ita kam inteesar kasa wa tayi ji tayi hka kawae gabanta na faduwa, ta xauna Aliyu ya xauna gefenta snn ya gaida Abban nasa ba tare da ya kallesa ba, Abba ya amsa bbu yabo bbu fallasa snn ya kalli Inteesar da ta kirkiro murmushi tana gaishesa ya amsa da fara'arsa yana tambayarta ya gidan, ta sunkuyar da kai tace lfya lau Abba, murya can kasa Aliyu yace "ga ta nn Abba na kawo ta," ko kallonsa Abba bae yi ba ya fara magana kmr hka "tambayace kawae xan maki Fateemah, amma gskya kawae nake son ki gaya min kar kiyi min karya ban san ki dakarya ba," tayi shiru gabanta na faduwa tana kalln Abban, ya dan dau lkci snn yace "wae da amincewarki Aliyu xae kara aure?" ji tayi komai nata ya tsaya ta kasa dago kai bare ayi expectn amsa daga gare ta, nn da nn taji hawaye na neman cika mata ido, Aliyu ya kamo hannunta ya hade da nasa a boye, ta gane abinda yake nufi, suka ji muryan Abba na cewa "magana nake fateema kin yi shiru, sharri yyi maki ko?" da ganin Abba kasan ransa a bace yake, da kyar ta iya bude baki ba tare da ta kalli Abban ba tace "eh hka ne Abba da sanina," Abba ya girgixa kai yace "karya kike," tayi kkrin boye hawayenta tace "da gske Abba na sani ni ce nace yyi," Abba yyi shiru yana kallonsu gaba daya daga bisanni yace "to yyi yau, baxan hanaka kara aure ba Aliyu kuma ni kam bbu abinda xan ce maka da ya wuce Allah ya taimaka, snn abu na karshe da nake son na gaya maka shine ka tabbatar kafin kayi auren naka 'ya ta ta fara karatu tayi settle dwn idan ba hka ba wllh sae na wargaxa komai, ka tashi ka ban wuri" bbu ko dar bare damuwa Aliyu ya mike yace "ngd Abba," ya sace kallonta, ita ma kallonsa take hawaye cike idonta da ganinta ta shiga wani yanayi da baxa a iya fassarawa ba ya galla mata harara snn ya fice, Abba yyi shiruyana kallonta snn a hankali ya fara magana"kiyi Hkuri fateema, nayi dana sanin hadaki daAliyu da nayi, kuma ni ban isa hana shi kara aure ba, snn baxan ce kar ki bi mijinki ba amma idan har kin ga baxa ki iya xama gidan ba bayan auren nasa ni nn nace ki tattaro ki dawo gida," kai kawae take gyada ma Abba tana hawaye yyi mata nasiha ssae yana kwantar mata da hankali daga karshe yace ta tashi tashiga cikin gida amma kar ta ce da inna komai tukun, ta mike jikinta a mace tayi masa gdya snn ta fita falon tayi bangaren inna tana kuka ssae, tsaye ta gansa alamar ita yake jira, yana ganin tayi bangaren inna ya daka mata tsawayace "c'mon gida xa mu wuce ina kike tunanin xa ki," ko kallonsa bata yi ba ta saka gudu tayi sashin inna ya bi ta shima da sauri, Kursum da ta fito daga gun inna knn ta bi su da kallo baki bude, saura kiris ya kamata ta afka falon inna tana mayar da numfashi ta fasa ihu tare da xubewa tsakiyar falon, inna dake daki ta fito da gudu tana salati tace "me ya faru?? Daga ina hka?" shi ko ya fixgota a fusace ya shake ta hade da hada ta da bango yana huci yace "don ubanki ina wasa da ke ne?" inna tayo waje da ido snn tayi waje da gudu ta saki kuka cikin daga murya tace "jama'a yau naga ikon Allah xae kasheta gabana, Bukar Bukar ka taho kaga abinda dan ka ke shirin yi da daddaren nn" . Haisam ya karaso da sauri yana kallon inna yace "me ya faru inna," tana kuka wiwi tace "wllh Haisam ina daki na je ajiye kayan da kursum ta gama goge min naji ihu kmr xa a xaga falona, fitowar da xanyi wae sae ganin Aliyu nayi shake da Inteesar yana duka yana buga ta da bango, duk yyi mata kaca kaca ko motsin kirki wllh bata yi yanxu ban san ya ake ciki ba ka taimaka ka kira mun Bukar don Allah," tana kai wa nn ta fashe da wani kukan har da durkushewa kasa, Haisam ya girgixa kai ya shiga falon innar da sauri dai dai bakin kofa ya hadu da Aliyun rike da hannun inteesar yana janta tana kuka tana cewa "wllh ka kyaleni bbu inda xa ni," ya buge mata baki Haisam yace "wae kai wani irin mutum ne Aliyu 4 heaven sake" Aliyu ya watsa masa wani mugun kallo yace "da'alla can get out malam kar na buge ka," inna tayi cikin gida da gudu tana rusa kuka lkci daya tana kwala ma Abba kira, da sauri Aliyu ya ja inteesar suka fice daga gidan tana nonnokewa ya bude mota ya jefata ciki snn ya shige motar ya tada ta, dae dae nn inna ta fito kofar gidan Abba na biye da ita a baya tace "maxa bi shi Bukar ya tada motar," Abba ya girgixa kai cike da takaici yace "kina ma Allah da annabi ki daina daga min hankali a gidan nn baaba wnn wani irin bala'i ne," bae jira mai xata ce ba ya koma cikin gidan ransa a bace. Suna isa gida Aliyu yyi parkin ya bude motar ya fito yana kallnta har lkcin bata daina kuka da take ba ta hade kai da gwiwa, cikin tsawa yace "ko sae na jefar dake waje," taki dago kai bare ta tanka masa, ya fixgota ta fasa masa ihu tana cewa "wllh baxan shiga gidan nn ba ka mayar dani gida," cak ya dauketa ya rufe motarsa tana dukansa bae damu da hkn ba ya shiga gida da ita ya haura sama ya bude dakinsa, nn da nn ta saita kanta cikin muryar kuka tace "ni ka ajiye ni," bae kulata ba ya isa kan gado ya kwantar da ita ta mike da sauri ya turata da karfi ta fada kan gadon snn ya fada kanta, nn da nn ta hadiye kukan da take xuciyarta na bugawa a hankali tace "kayi hkuri ya Aliyu na daina kukan" ya dago yana kallonta da ganinta kasan a tsorace take, ta fara kkrin sauka daga kan gadon ya rikota yace "bbu inda xaki yau nn xaki kwana," kanta ce komai ya kashe wutan dakin, ta fasa masa ihu ya buge mata baki da karfi, ba karamin wahala ya bata ba, don duk sae da ya jagwalgwalata, ganin irin kukan da take da kuma yanda jikinta ke bari duk da bae ma kai ga yi mata komai ba yasa ya kyaleta tare da cewa "ki rufe min baki kar na baki mamaki," ba shiri ta hadiye kukan jikinta na rawa don duk ya tsorata ta, ya rungumota ssae, snn ya dauki wayarsa yyi dialin nmbr safeenah, kmr jira take yana ringin kuwa ta daga, murya can kasa yace "bbyna," ita ma a marairaicen tace "mijina," ya sauke ajiyar xuciya ya daura bakinsa kan gashin inteesar da ta rumtse ido xuciyarta na bugawa, yace "nayi missn naki ssae fa bby, i need yhu safeena," ta danyi dariya tace "matarka fa? Kaje ka sauke need din a kanta mana," ya yamutse fuska yace "me wnn take da shi da xata bani da ya wuce wahala, naki nake so bbyna," tayi dariya ssae snn tace "ka kusa samu dear na, ina amaryartaka," yace "ga ki nn bbynah," nn suka dinga xancen yanda 1st nyt dinsu xae kasance bbu kunya bare tsoran Allah, a hankali Inteesar ta shiga xamewa daga rungumar da yyi mata, ya matseta da karfi ta shiga kokuwa da shi, ya ki sakinta, ya kunna wutan dakin yana kallonta, hawaye ne kwance fuskarta, ta boye fuskar da sauri, bbu yabo bbu fallasa yace "nayi maki wani abu ne kike min kuka don munafurci?" tayi shiru bata ce komai ba har lkcn hawayen da take yaki tsayawa, ya dada rungumeta ya kashe wutan ya ci gaba da wayarsa, suna nn a hka yana ta hirarsa da safeenah har bacci ya dauke Inteesar . Karfe sha biyu da rabi ya kwantar da ita a hankali, snn ya shiga bathroom yyi wanka ya koma wani dakin yyi kwanciyarsa. Da safe taji an watsa mata ruwan sanyi ta farka a tsorace tana kallonsa da mamaki, ya galla mata harara yace "ke kafura ce ina ga ko," bata ce masa komai ba ta sauka daga kan gadon fuskarta a daure tayi hanyar fita daga dakin ya fixgota yace "ina magana xaki fita don baki da kunya," ta hararesa tace "to ca nayi maka banyi sallah bane" ya wara ido ya shaketa yace "ni kike kallo hka, wae me sa kika raina ni hka ne yarinyar nn?" ta girgixa masa kai kmr xata yi kuka tace "kayi hkuri baxan sake ba," yyi kwafa ya saketa yana kallonta tayi hanyar fita da sauri ya daka mata tsawa "ke! Uban wa xae gyara maki dakin?" ta juya tana kallon dakin snn ta dan yi tsaki ta dawo ta fara gyara gadon, ya bude Bathroom ya shiga wanka, tana gama gyara dakin ta fice da sauri tayi hanyar dakinta. Inteesar na jin muryarsa a kasa ta mike da sauri ta isa jikin window tana kallonsa yana tsaye jikin motarsa yana magana da masu gadi, ta juya da sauri hawaye ya cika idonta, jin ya tada motar ne yasa ta juya tana kallonsa har ya bar gidan snn ta dawo gefen gado ta xauna a sanyaye, tana nn a hka bayan fitarsa da kmr minti goma Zainab ta shigo gidan, Zainab ta ajiye mayafinta tana kallon Inteesar da ta kirkiro murmushi tace "lah daga ina kike da safen nn," Zainab tace "wae jiya da kuka xo gida da daddare da ya Aliyu me ya faru" Inteesar tayi shiru tana kallon Zainab snn tace"me aka ce ya faru?", Zainab tace "oho, Abba yace mu taho gida tare ynxu, ya kira Aliyu tun jiya ya ki dagawa," Inteesar tace "to ae baya nn," Zainab ta galla mata harara tace "to ina ruwana, Abba ca yyi mu taho gida ynxun nn da ke," Inteesar ta girgixa kai cikin confusion tace "to ki kira ya Aliyun ki fara gaya masa," Zainab ta bude baki tana kallonta tace "iyye sae na kirasa xa mu tafi," Inteesar tace "to ae bae sani ba," da mamaki Zainab tace "Ahh lallai," snn ta juya tace "sae anjima," Inteesar ta bi ta da sauri tace "ki tsaya don Allah Zainab," Zainab xa tayi magana wayar dake gaban madubi na Aliyu yyi ring, Inteesar ta karasa gaban madubin tana kallon wayar a tunaninta Safeena ce, ta daga wayar ta kara a kunne bata ce komai ba, "kina jina, idan kika kuskura kika fita gida ba tare da izinina ba xaki sha mamaki, just dare me, ki ga" yana kai wa nn ya katse kiran, ta juya tana kallon Zainab ta marairaice tace "yace kar na fita Zainab," ko kallonta Zainab bata yi ba tayi hanyar kofa, Inteesar ta bi ta da kallo har ta fice. Da yamma tana kwance abun duniya ya isheta tun tean data sha da safe bata sake cin komai ba ta rasa me ke damunta, jin an bude kofar downstairs ya sata mike da sauri a tunaninta Zainab ce ta kuma dawowa, ta xauna gefen gado tana jiran shigowartata, kamshin turarensa da taji yasa ta gane shi ne, ta koma ta kwanta a hankali tana kallon kofar dakin, ya tura kofar dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta, bata ce masa komai ba, ya tabe baki yace "wa ya shigo gidan nn daxu?" tayi kmr bata ji sa ba ya daka mata tsawa "ba da ke nake ba," xata yi magana taji ana kiransa da darlin, ya juya da sauri yace "srry bby, magana nake da wnn ballagaxar," Inteesar tamike tsaye da sauri tana kallon safeenah da ke lekota, ta karaso bakin kofar tanai ma safeenah wani irin kallo snn tace "karuwancin ne har sae kin biyosa gida don rashin sanin ciwon kai, ke kam kin banu banxa kawae sha sha sha," bata rufe baki ba Aliyu ya sauke mata mari ya fixgota ya jefar kan gado yana huci ya nuna ta da dan yatsa yace "ki shiga hankalinki wllh, don kika sake ce mata karuwa sae na illata ki, dabba kawae" ta sulalo kasa daga kan gadon ta fashe da kuka ssae tace "Allah ya isa ban yafe maka ba mugu kawae mara....." wani wawan marin ya sake kai mata hade da buge mata baki da karfi yana huci nn da nn sae ga jini, ta fasa ihu a gigice, safeena ta dafe kanta tare da sauke ajiyar xuciya tana yatsine fuska tace "kai bby ban cika son hayaniya ba wllh, muyi abinda ya kawo mu na bar nn plss," ya ce "srry bby," snn ya kamahannunta suka fita daga dakin tana ma Inteesar wani irin kallo tana murmushi, kuka Inteesar ta dinga yi kmr ranta xae fita ta hade kanta da gwiwa, tana nn a hka suka sake bude kofar dakin suka shigo, taji yace "nan fa bby?" Safeenah ta dan yatsine fuska snn tace "yauwa nn yafi dear, nn din nake so can bae yi min ba,". Aliyu yyishiru yana kallon safeenah, ta dan matso kusa da shi ta yi masa fari da ido tace "mun gama da wnn, kuma ni bna son irin paint din nn, mu jedear na fara jin yunwa," tana fadin hka ta juya xata fita daga dakin ya riko hannunta a hankali yace "meyasa baki son wancan dakin bby?" ta yatsine fuska tana masa wani irin kallo tace "can bai yi min ba nn nake so," ya juya yana kallon Inteesar da har lkcn ke kuka a hankali kanta kife a gwiwanta, ya maida kallonsa ga safeenah yace "to na bar maki dakina, ni sae na koma wancan," ta xaro masa ido tace "No! Ni wnn dakin nake so," yyi shiru yana kallonta, Inteesar ta mike tsaye ta dauki Hijab dinta ta sa ta ciro flat shoe dinta shima ta sa snn tayi hanyar fita, duk suka bi ta da kallo har ta iso inda suke tsaye tabi ta gefensa xata fita ya fixgota, "ke? Gidan ubanwa xaki," ta galla masa harara da jajayen idonta tace "gidan ubana xani," yace "ko?" tace "eh," ya aketa ya gyada kai yana murmushin mugunta yace "to tafi," cikin kuka tace "ni wllh sae na tafi," ya daka mata tsawa ya fixgota yana kallonta yace "ae shine nace ki tafi na gani," ta fashe da kuka ta xube wajen tana kiran Abbanta, safeenah ta dafe kanta tare da jan dogon tsaki tace "gosh! kaga nifa Hydar ban cika son hayaniya ba wnn abu hka sae kace ina kindergarten, don Allah ka taho muyi abinda ya kawo mu ka mayar da ni gida yau fa xan fara gyaran jiki" Inteesar ta mike tsaye da sauri tana mata wani mugun kallo tace "da'alla fice min daga daki rahama ya shigo, banxa da ke kawae jahila" Safeenah tayi wani dariya tana taunar cingam din yan iska tace "ae sae dae ki kira wani gun da dakin ki amma ba nn ba, don dis is myn, kuma kika sake ce min jahila wllh sae na kusan illataki kmr yanda mijinki ya gaya maki daxu, don wnn karan ba sae ya dukan min ke ba, ni da kaina xan nakade ki, ki san cewa ni ba sa'ar uwarki bace bare......" bata rufe baki ba Inteesar ta sauke mata tagwayen mari masu rae da lfya nn da nn fuskarta ya koma ja don axaba, ta dafe kuncinta a gigice tana kallon Aliyu da ya jingina jikin bango rungume da hannayensa yana kallon Inteesar da mamaki tace "wat? She slapped me Hydar" Inteesar tace "ae kadan ma kika gani," bata jira me Aliyu xae ce ba tayi kanta, inteesar na ganin hka ta fasa ihu a tsorace tayi hanyar bathroom, safeenah ta fixgota ta buga ta da bango ta shaketa tana huci snn ta shiga dukanta kmr an aikota Aliyu yyi kansu da sauri ya fixge safeenar ya watsa mata mari ya buga ta da bango yana huci yace "don ubanki kasheta xakiyi ne," Safeena tayo waje da ido tana kallonsa da mamaki, Inteesar ta sulale kasa gabanta na faduwa tana kallonsu, Safeenah ta girgixa kai ta fashe da kuka tana kallon Aliyun, ya saketa ya dafa bango tare da sauke ajiyar xuciya, can ya dawo gabanta a hankali yace "meyasa xaki kulata Safeenah baki ga yarinya bace warce bata san ciwan kanta ba, bbu abinda ta sani nn da kike ganinta she's just a kid," Inteesar ta mike tsaye tace "ku dae ne baku san ciwon kanku ba amma ni nasan ciwon kai na," Aliyu ya bude baki da mamaki yana kallonta, tayi hanyar bathroom da sauri xata shige ya bita ya fixgota a fusace, ta fasa masa ihu tare da durkushewa a kasa tace "wayyoo Abbana," ya durkushe shima da sauri gabanta yana kallonta yace "me ya faru?" ta dago tana kallonsa kmr xata yi kuka tace "to ba kai bne xa ka doke ni . Aliyu yyi kwafa ya mike tsaye, ita ko ta ja da baya daga xaunen da take tana goge hawayenta, ya juya yana kallon Safeena dake hawayen takaici xae yi magana ta juya da sauri ta bar dakin yaji ta bude kofar dakinsa ya gane jakarta xata dauka a ciki ta bar gidan, ya juyo yana kallon Inteesar da ta bi ta da harara, ya sa kafa ya haureta yace "xan babbalaki a gidan nn wllh idan kika yi wasa," ta mike tsaye da sauri tayi tsaki can ciki ta koma kan gado ta xauna tana ci gaba da share hawayen fuskarta, danna bell din gidan da aka yi yasa ya juya ya fita daga dakin dae dae lkcn da Safeena ma ta fito daga dakinsa rike da handbag dinta, yace "haba bby ina kuma xaki?," ko kallonsa bata yi ba ta fara sauka daga stairs, ya bi ta da sauri yana kiran sunanta,tsaye suka ga Hajiya a falon tana kare ma ko ina kallo fuskarta a tamke, ya juya da sauri ya koma dakin Inteesar, tana nn yanda ya barta ya karasa gabanta yana kallonta ya kama hannunta ta fixge tana hararansa tace "meye hka," ya buge bakinta ya fixogata ya bude bathroom ya tura ta ciki snn ya kulle da makulli ya cire makullin yasa a aljihu, kofar ta shiga bubbugawa tana kuka, ya fice daga dakin ya sauka downstairs da sauri, tsaye yaga safeena kusa da Hajiyan tana mata magana tana kuka, ko me take ce mata oho, ya karaso yana kallonsu Hajiyar dake ta faman huci tayi hanyar stairs kmr xata tashi sama, ya juya yana kallon safeenar yace "me kika gaya mata," ta galla masa harara tace "meye baxan gayamata ba," yace "haba safeenah kin san fa ina sonki kuma dae kinga abinda na mata daxu a kan rashin kunyar da ta maki,yarinyar ce bata jin magana wllh ban san yanda xanyi da itaba," tace "dnt tell me dat kai dae kace ka fara sonta kawae,idan ba hka ba yarinyar dake mugun tsoranka kmr mutuwalkci daya xata rainaka hka idan ba wani abun ya shigatsakaninku bane kana xuwa gurinta da daddare karban sweet tunda dae kai a wnn bangaren baka da maraba da maye," yace "ya salam, haba safeena wllh bbu abinda ke shiga tsakaninmu me take dashi da xata bani, baki yrda dani bne, wllh Abbana ne yasa ta rainani hka ke ma kinsan ba wasa da ita nake ba," safeena taki cewa komai sae tabe baki da tayi, ko minti biyar ba ayi ba Hajiya ta sauka tana huci tace "kaban mamaki Aliyu ban xaci hka daga gareka ba," sae kuma ta fashe da kuka "ni dama nasan cika bakin naka na kwana biyu ne sae sun juya min kanka, na shiga uku ni Aisha," safeenah tace "no Hajiya shi ba ruwansa ae bae yi supportn din ta ba, har dukanta ma sae da yyi amma hkn bae sa ta daddara ba, ina ga kmr a gida ake xugata" Hajiya kmr xata hadiye xuciya don bakin ciki tace "to na shiga dakin ban ganta ba kuma ai," Aliyu yace "nima na shiga ynxu nace ta tafi gida ban ganta ba," Hajiya tace "xata ko ci ubanta shegiya tsinanniya, daxu fa a gabana Alhaji yace xainab taje tace ta dawo gida taki dawowa, ita ta samu gidan hutu ko to wlh ba gidan dana ba don ubanta kuma idan Allah ya yrda baxa ki shigo ki sameta a gidan nn ba Safeena," safeena tayi murmushi tace "to Hajiya naji ddin jin hkn," Hajiya tace "to ya shirye shirye safeena, kin xo ganin Aliyun ne, shi me ya hanasa xuwa" safeena tace "ehh dama yace na xo na xabi dakin da nake so ne, kuma nace wanda take ciki ne yyi min," Hajiya tace "to ae shknn sae yasa ta fiffito da kayan nata, abinda ma ba samunta xaki yi a gidan ba ae Alhaji ya nuna kawae ta dawo gida" Aliyu ya juya ya koma sama ya shiga dakin nata, ya ciro makulli ya bude kofar bathroom din, ta mike tsaye a tsorace da ganinta kasan kuka ta ci, ya karaso yana kallonta ya galla mata harara yace "uban me aka maki munafuka," ta girgixa kai a tsorace xata yi magana suka ji muryarsu alamar suna haurowa sama, ta shiga yarfe hannu tana hawaye tace "wayyo tsoro nake ji xata dawo," ya juya yana kallon kofar dakin, yaji safeenah na cewa "bari mu je dae ki gani Hajiya" da sauri Aliyu ya rufe kofar bayin ya sa makulli ya koma baya ashe tana dab da shi ya bugeta tayi baya xata fadi yyi hanxarin rikota ya rungumeta, taboye fuskarta a kirjinsa tana kuka a hankali har wani rawajikinta yake, su Hajiya suka bude kofar dakin suka shigo safeena na cewa "ban ma duba bathroom din ba wllh," Hajiya tace "ehh duk sae mu duba ynxu," xamowa Inteesar ta shiga yi daga jikinsa ya bita ya riketa yana mata wani mugun kallo, a hankali cikin muryar kuka tace "tsoro nake ji," ya mike tsaye ya dagota jin suna bude drawers dinta yasa ta girgixa masakai taki mikewa tsaye, taka kafarta yyi yana mata mugun kallo ba shiri ta mike har tana bugesa makullin hannunsa ya fadi, yasa kafa da sauri ya take amma duk da hka sae da yyi kara,ta toshe bakinta a tsorace tana harharde kafa ta rikesa tace "wayyo ya Aliyu fitsari xanyi," . Safeenah tace "ina ga kamar fa da mutum a bayin can," Hajiya tayi shiru tana kallon bayin snn ta karasakusa da bathroom din ta murda kofa ta ji shi a rufe, tana kallon safeena tace "a rufe yake ma," safeenah ta karaso ita ma ta murda taji shi a rufe, ta sa kunne ko xata ji motsi, Hajiya tace "to wae ma ina Aliyu yyi ne ban gansa ba," Aliyu ya tsura ma kofar ido yana kallo, ita ko Inteesar sae yarfe hannu take hawaye na bin kuncinta tanabubbuga kafa a kasa a hankali, har gobe ita dae tasan baxata daina tsoron Hajiyar nn ba, suka ji Safeenah tace "bari naje naga ko kofar iri daya ce da na dakinsa na dauko tasa makullin," Inteesar ta dafa sa a tsorace tace "nashiga uku wayyo Abbana," har wani bari jikinta yake, ya riketayana kallonta yace "xaki sha mari, idan baki rufemin baki ba," ta sa hannu ta toshe bakin jikintana rawa, hajiya kuwa na ta bude buden drawersdin dakin tana ta xage xage ita kadae harsafeena ta shigo rike da makullin, Hajiya tace "kinsamu," safeena tace "eh iri daya ne, bari mu budemu ga, munafuka kila tana ciki," Inteesar ta kamohannunsa hawaye ya gama wanke mata fuskamuryarta na rawa kmr mae rada tace "ya Aliyuwllh fitsari xanyi," ya jawota yana kallonta yashiga xuge mata xip din skirt dinta, ta rike skirt din da sauri tana xaro ido, ya galla mata harara murya can kasa kasa yace "ba fitsari xaki yi ba," ta girgixa masa kai sae kuma ta gyada kan da sauri kmr wata wawuya, ya xuge mata gaba daya Zip din ta rike hannunsa da sauri tana xaro ido, suka ji Safeena na kkrin saka keyn cikin kofa, ta rungumesa tana kuka a hankali tace "ya Aliyu wllh dukana xasuyi tsoro nake ji," shima ahankalin yace "ae gwara su doke kin ni da kaina ma xan bude masu kofar idan sun kasa," ta shiga girgixa masa kai cikin tashin hankali tace "A'a don Allah kayi hakuri ka kai ni gidanmu yau Abba dama yace na dawo," safeena dae na ta kiciniyar bude kofar Hajiya na taya ta, a hankali Aliyu ya bi skirt dinta da ya shiga xamewa daga jikinta da kallo har ya sauka kasan bayin, ya tsura ma laps dinta da kafafuwanta ido, don tsabar tsoro bata ma lura da hkn ba ganin wani irin kallon da ya shiga mata yasa ita ma ta kalli inda yake kallo, ta durkusa da sauri tace "na shiga uku," ya dagota, nn da nn yanayinsa ya canxa tace "wayyo Abbana......" a hankali kmr wan mashayi yace mata "ae baxa su iya budewa ba tunda ba makullin bane dnt...." bae karasa abinda xae ce ba ya shiga kissin dinta kmr xae cinyeta, ta shiga turasa da karfi suka xube kasa, bata san lkcin da ta fasa wani ihu a tsorace ba jikinta na rawa. Safeenah ta juya da sauri tana kallon Hajiya tace "ba nace maki tana ciki ba" Hajiya ta shiga buga kofar da sauri tana cewa "don ubanki fito ki bar gidan nn kar na kasheki shegiya munafuka, gidan da na yafi karfinki wllh" a tsorace cikin kuka ba tare da ta shirya ba tace "kiyi hkuri mumy xan....." buge mata baki Aliyu yyi da karfi ya mike tsaye yana kallonta ya sa kafa ya haureta, ta toshe bakinta ta koma baya da sauri hawaye na cigaba da bin kuncinta, safeenah tace "Hajiya kawae mu kira kafinta ne ya balla kofar don ba budewa xata yi ba," a fusace Hajiya tace "to wae ina Aliyu ne, ya xo ko xae iya ya bude don wllh wllh yau sae ta bar gidan nn don ubanta," safeena ta ciro waya tace "bari na kirasa," yana jin hka ya ciro wayarsa da sauri ya kashe, safeena tace "kinji tsiya wae a kashe yake," nn Hajiya da safeena suka dinga xaginta suna cewa ta bude kofar ta xo ta wuce gida kar su balla su kasheta, ita dae bata ce komai sae kukan da take yi a hankali, shi ko Aliyu na tsaye sae kallon kofar yake yana girgixa kai, sun kai kusan minti goma a dakin suna abu daya daga bisanni suka bar dakin Hajiya nacewa "ae yau da ta kwana gidan nn gwara gidan ya babbake, bari muje mu samo kafinta ya cire kofar kawae, shi kuma Aliyu don tsabar wlknci ficewa yyi ya bar gidan ga yar iska ta xo" Safeena tace "ni wllh Hajiya tsoro ma Aliyun nn yake bani," yana ji sun fita daga gidan gaba daya ya juya yana kallon Inteesar da ta xama kmr wata marainiya ya daga hannu xae xabga mata mari ta fasa ihu sae kuma ya fasa, ya fixgota yana mata mugun kallo yace "daga yau kika sake bara min wnn shegen bakin naki kmr na xaki a gidan nn sae na cire maki hakora wawiya kawae," yana kaiwa nn ya bude kofar ya fice ya bar ta nn durkushe tana kuka, direct gun mai gadi ya nufa yace "kar ka bude ma kowa gate ya shigo gidan nn, snn kar ka bari ta ciki ta fita" mai gadi yace "to yallabae, snn ya shiga motarsa ya bar gidan shima, hka Inteesar ta yini tana kuka ranar gashi mai gadi yaki barin ta fita, tsoranta daya kar su Hajiya su dawo, cikin ikon Allah kuwa bata ga sun dawo ba, har ta kwanta ranar Aliyu bae dawo gidan ba. Yau tana xaune ita kadae abun duniya ya isheta rabonta da Aliyu tun ranar da Hajiya ta xo gidan aka yi wnn draman gashi yau kusan kwana uku, budewar kofar dakinta yasa ta mike a raxane don ynxu ba karamin tsoron gidan take ba, Zainab ce ta karaso tana kallon Inteesar tace "wae dama ashe aure Aliyu xae yi Inteesar," jikin Inteesar yyi sanyi kmr lkcn ta fara jin xancen, tayi shiru bata ce komai ba, ganin Zainab ma tayi shiru yasa tace "wa ya gaya maki," Zainab tace "yau Abba ke gaya ma Inna wae ashe ma saura sati daya, tun safe inna ke kuka tana tsine tsine a gidan wae xamanta ya xo karshe a gidan," Inteesar ta xauna gefen gado bata sake cewa komai ba, Zainab tace "in ni ce ke Inteesar wlh baxan xauna gidan nn ba, infact na gama auren ma gaba daya, duka duka watanku nawa da auren ko three month fa bae cika ba," budewar kofar dakin yasa suka juya da sauri suna kallon waye, Aliyu ne ya shigo dakin yana ma Zainab wani irin kallo, nn da nn hanjin cikinta ya kada. . Zainab ta dauki mayafinta gabanta na faduwa ta kalli Inteesar tace "na tafi inteesar, inna tace na xo nace maki ki hada kayanki tana nn xuwa," tana kai wa nn ta juya ta dake tana kallonsa tace "ina yini yaya," bae tanka mata ba sae dae har lkcn kallonta yake, ta bi ta gefensa xata wuce ya cakumota ya watsa mata mari cikin tsawa yace "daga yau, na sake ganin shegun kafafunki cikin gidana wllh sae na ji maki," kuka ta fashe da tace "ni me nayi maka xaka mareni hka wlh sae na gaya ka da Abba," wani marin ya kai mata snn ya fixgota ya shiga janta har suka fita daga gidan, ita dae Inteesar bata ce komai ba sae kifa kanta da tayi kan gado tana kukan da bata san dalilinsa ba, suna isa gate Aliyu yace mamaigadi "kar ka sake barin yarinyar nn ta shigo gidan nn," mai gadi yace "to yallabae," snn ya jefar da ita waje ya rufe gate din ya koma cikin gida. Washegarin ranar da daddare Inteesar na gaban madubi ta fito daga wanka knn tana shafe shafenta gaban madubi wayarsa dakegunta yyi ring ta duba ta gane nmbrsa ce dayan, ta daga yace "ina jiranki downstairs," da kmraxa ta je ba sae kuma ta dauki Hijab dinta har kasa ta sa snn ta sauko downstairs yana xaune remote a hannunsa, yana daura idonsa kanta ya daka mata tsawa "ke daga yau kika sake sa irin wa innan hijaban a gabana sae na ci ubanki daga ke har hijabin, wawuya kawae get out," ganin bbu alamar wasa tattare da shi ya sa ta koma sama ta sa kayan barcinta mai dan mutunci don dama xani kadae ne jikinta snn ta sa gashinta cikin net ta sauko kasa fuskarta a daure, kallo daya yyi mata ya dauke kansa yace "ga kayanki nn ki kwashe su gabana," ta tsura ma akwatinan da ya nuna mata ido snn ta dake tace "na me," ya galla mata harara yace "na xubar wa, c'mon kin xo kin kwashe su gabana ko sai na bata maki rae" ta girgixa kai tana kkrin mayar da hawayenta tace "na yafe bana so, ka kara mata a nata," tana fadin hka ta juya da sauri ta koma sama, ya bi ta da kallo, kan gado ta fada ta fashe da kukan takaici tana data sanin kin bin Zainab da tayi ranan, don dae ko hauka yake baxae je yace xae daukota ba, Aliyu ya cuceta ya walakantata bakin cikin ta daya ynxu ya raba ta da budurcinta, hka ta kwana ranar tana abu daya. Washegari da safe ya shigo dakin yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "ki shirya anjima xa a raka ki registration na Jamb," yana kai wa nn ya juya xae fita ta mike da sauri tace "bbu inda xa ni wllh," ya juya yana mata wani mugun kallo yace "to sae me, me xa a fasa mutuwan ko hisabi, kar Allah yasa kije din jaka kawae" ta fashe da kuka tace "ni a jaka bace wllh, ka jira jaka na nn shigowa nnba da ddewa ba," ya karaso cikin dakin ya kwashe ta da mari ta fasa ihu tana kiran Abbatace "Allah ya isana ban yafe maka ba wlh mugu kawae," juyawa yyi ya fice daga dakin da sauri ta mike jikinta na rawa ta shige bathroom ta rufe da key. Karfe sha biyu saura taji ana ring din Bell, ta sauko gabanta na faduwa don tasan Aliyu baya danna bell, ta karaso kusa da kofar tana lekan ko waye, wani mutumi ta gani tsaye, ta ki bude kofar tace "waye," yace "ina yini madam, Yusuf ne, oga Hydar ne ya aikoni waexamu je registration da ke yau, shi yana buzy," tace "kaje kace masa ban xuwa," bata jira me xae ce ba ta koma sama abunta, da daddare Aliyu ya dawo gidan direct dakinta ya nufa ta hada tea knn xata sha, duk da ba karamin tsorata tayi ba amma ta dake bata nuna ba, kuma taki dago kanta, ya karaso inda take ya fixgota cikin tsawa yace "wani sako kika bada a kawo min daxu," ta shiga kikkifta ido a tsorace tace "ni ka kyaleni wllh," ya jefar da ita ya fice daga dakin ta bi sa da harara, ko minti biyar ba ayi ba ya dawo rike da belt, ta fasa ihu a tsorace ta mike tsaye tace "na shiga uku, wayyo Abbana," ya fixgota ya shaketa yana huci yace "na rantse da Allah idan baki kama kanki a gidan nn kinsan da wanda kike xaune ba sae na sumar dake watarana" yana kai wa nn ya buga ta da bango ya fice daga dakin, hka ta kwana kuka da ciwon kai ranan, Da safe yana fita ita ma ta shirya xata bar gidan amma mai gadi yaki bude mata gate ta dinga rusa masa kuka tana rokansa ya bude mata gate amma yace "to ko yau sae da yallabae ya kara jaddada min cewar kar na bari ki fita," ta fashe da kuka abun tausayi ta kasa cewa komai, kmr daga sama taji Muryar inna da karfi tana cewa "salama alekum, kin tabbata nn ne gidan kursum" . Inteesar na jin muryar inna ta fasa kuka tana kallon gate din, inna ta shiga bubbuga gate din tana cewa "lah nn ne kursum ga muryarta nn naji, a bude mana" Mai gadin yace "waye wnn," inna ta bude baki tace "nashiga uku amar ya waye? Waye ke min wnn tambayar," Inteesar tace "malam ka bude mata kakata ce fa," mai gadi yace "ko ma wacece yallabae yace kar na bude ma kowa gate," cikin daga murya inna tace "yau naga jaraba waye wnn kuma" kursum tace "mai gadi ne," inna tace "mai gadi? To ya ci ubansa ba a gaya masa ko ni wacece bane ni da gidan jikokina xae hana ni shiga," kursum ta fashe da dariya inna tace "ke ban san shashanci fa," sae kuma ta shiga kiran Inteesar," cikin kuka inteesar tace "Na'am inna yaki bude gate din," a fusace inna tace "yau ni naga jarababben dan iska gate din ta ubanka ce ko ko, kaji min mutum," dariya ma abun yaba mai gadin inna tace "shi Aliyun yana ina," Inteesar tace "oho nima ban sani ba," inna ta shiga buga gatedin da karfi tana duddura ma mai gadi xagi,shi dae yana xaune sae shan rakensa yake inteesar tace "wae kai wani irin mutum ne baka jin ka bude mata gate ne ka maida mutane mahaukata," inna tace "ki rabu da shege, kursum maxa kira min Bukar," kursum ta karbi wayar ta kira Abba ta mika mata tace "Bukar Bukar gani gidan Aliyu wani kato yahanani shiga, na kai awa biyu tsaye cikin rana Bukar," Abba yyi murmushi yace "to ae umarnin da aka basa knn baaba ku koma gida kawae," cikin kuka inna tace "kambu, Al'quran bbu inda xani sae ya bude min gate don uwarsa," nn ta shiga jijjiga gate din kmr xata cire tana tsine ma mai gadi, maigadi yyi tsaki ya ciro dan wayansa ya kira Aliyu "oga ga wata tsohuwa nn ta xo ta cika anguwa wae sae an bude mata gate," Aliyu yyi dariya yace "karka kuskura," snn ya katse kiran mai gadi ya mike yana fito ya shige dakinsa. Inteesar taji kmr ta shakesa ta karasa kusa da gate din tace "inna Aliyun ne fa yace kar ya bude maku wlh, ku tafi gida kawae ba budewa ae yi ba," inna ta yo waje da ido tace "me? To wllh bbu inda xani ina nn har sae an bude min gate din," cikin kuka take maganar, kursum kuwa sae dariya take har da faduwa,inna ta nemi dakali ta xauna tana sharbe majina, tace "ae yau bbu abinda xae hanani shiga gidan nn wllh sae na shiga" Inteesar ta gaji da tsayuwa ta shiga, ciki lkci lkci ta kan fito ta tarar suna nn, sae tausayin innan ya cika ta taji kmr ta dinga ihu don takaici lallai Aliyu ya cika mara mutunci, duk irin yanda ta lallaba inna ta tafi kin wucewa inna tayi, har aka kira azahar inna na nn xaune kursum ta gaji ta kama hanyar gida inna ta rakata da xagi, shegiya kawae ni ba mutum bace kuma ban san ciwon jikina ba sae ke ko, ganin har kusan karfe hudu inna na nn a xaune yasa inteesar ta fito da ruwa tana kallon mai gadi tace "don Allah don annabi malam ka dan bude gate din sae ka mika mata ruwan nn wllh tsohuwace," da kamr baxae tashi ba sae kuma ya mike ya karbi ruwan da take mika masa ya dan bude gate din yana lekota yace "ga ruwa kaka," ta mike tsaye tana kallonsa da shirin masifa ko me ta tuna sae kuma tafasa, ta karaso kusa da gate din kmr xata karbi ruwan ta bangajesa da karfi ta shige gidan da gudu. Me inteesar xata yi idan ba dariya ba, ta durkushe kasa ta dinga dariya kmr cikinta xae kulle, mai gadin ya bude baki yana kallon inna dake huci tace "don buhun ubanka ni xaka hana shiga gidan jikokina, mugu katon bnxa kawae, wllh baka sameni lkcn ina Rahmatu ba da yau bbu ubanda xae hanani faffala maka mari dan iska," Inna na kai wa Aya ta yi hanyar garden kmr xata tashi sama tana huci Inteesar ta bi ta da sauri tana ci gaba da dariya tace "ba nn bane hanyar shiga inna," Mai gadin ya sauke ajiyar xuciya yana bin inna da kallo, bae taba ganin tsohuwa da karfi hka ba, har suka shiga falo Inteesar bata daina dariyar da take ba inna ta hade rae tace "ke ni fa ban san tsiya meye abun dariya a nn, wlkncin da katon can yyi min ko me" kan Inteesar tace komai inna ta rike haba baki bude tace"A'aah bene kuma cikin gida ni Rahmatu naga abinda ya ishe ni," Inteesar tace "kuma shi xaki hau muje daki ba," inna tace "ni ina xan iya," inteesar na dariya ta ja ta suka haura sama tana mitan kafafunta na ciwo, sae da inna ta fara sllh snn Inteesar ta kawo mata abincin da ta dafa kmr dae tasan inna xata shigo gidan daga karshe, inna aka xauna aka bubbude kafa tana ci tana xagin mai gadi da Aliyu, sae da inna ta gama cika cikinta snn Inteesar ta xaga da ita ko ina na gidan har dakin Aliyu sae da suka shiga, inna sae washe hakora take tace "ashe dae xan ga wnn rana da xan taho gidan jikokina ni rahmatu, ae Bukar bae yi ba, ni ban san meyasa yake min hka ba gidan jikokina ma ya hanani xuwa sae da ixininsa sae kace ubana, daba dan hka ba ae sae na dawo nn ma gaba daya gani ga ku, ni dae ynxu 'ya yana nake son gani duk da bamu san gawan fari ba, xan so naga yayanku da Aliyu," Inteesar dae bata ce komai ba a xuciyarta tace Allah shi kyauta na Haihu da Aliyu, inna ta juya tana kare mata kallo tace "wae ni ya naji shiru ne har ynxu Inteesar ga fadila can da ciki, anya kuwa bakwa shan abu yaran nn, barin ke, nafi tausaya maki don shegen yaron nn kai ki xae yi ya baro ki" Inteesar ta hade rae tayi gaba ta barta nn tsaye, inna ta bita a baya tana cewa "to ni dae banga abun bata rae ba a nn daga fadan gskya" suna komawa daki inna ta xauna ta hade rae tana kallon Inteesar tace "ki maxa ki hada kayanki tafiya na xo yi dake dama, wae ashe gantalallen yaron nn aure xae yi ban sani ba," sae kuma ta fashe da kuka tace "sakayyar da xae mana kenn, wllh sae ya baki takardar ki ba rasa masoya kika yi ba," Inteesar tayi shiru da mamaki tana kallon inna kmr ba ita ba kuma mai son ganin ya'yansu, inna ta gama ta mike ta koma kan gado tace "bari na dan runtsa kafin nn kin gama hada kayanki," Inteesar dae bata ce mata komai ba har ta fara bacci, ta kalli agogo ta ga biyar ya gota ta mike a sanyaye ta shiga kitchen tana tunanin abinda inna ta gama gaya mata ynxu, to ynxu knn hada kayan nata xatayi gaba daya su koma gida, jikinta ba kwari ta shiga girka mata tuwan shinkafa da miyar vegetable don tana da kayan girkin gaba daya a deep Freexer, sae kusan Maghrib ta gama komai snn ta koma daki tayi wanka tayi alwala ta fito ta tada inna tayi sllh, karfe bakwae da rabi ta shigo ma da inna abinci inna tace "uban wa yace kiyi girki mu da xamu bar gidan ynxu, kin gama hada kayan naki" ta hade rae tace "to inna ki ci abinci dae tukunna mana," inna ta sauko tace "Atoh don xaman ki ya xo karshe a gidan nn yyi ta xama da amaryar tasa, wae in tambayeki wnn me sa kayan 'yar bbyn mai kaman xabiyar nn ce xae auro," Inteesar ta gyada mata kai kawae, inna tayi kwafa tace "xasu ci ubansu," snn ta fara kai loman tuwo, a tare suka gama cin abincin da inna ta kwashi kwanukan ta kai kitchen ta shiga wanke wanke ta gama ta fito knn Aliyu ya shigo gidan, suna hada ido ta dauke kanta da sauri tayi hanyar stairs yana yatsina fuska yace "wa yace kiyi girki da kifi a gidan nn, kinga ina son jin warin kifi?" tayi masa wani mugun kallo ta haura sama ta bar sa nn tsaye, ko da ta koma ta tarar inna na shafa'i da wutr, ta shiga bayi ta wanke baki snn ta fito ta xauna gaban madubi tayi shafe shafenta ta saka kayan barcinta ta kwanta don tayi isha, inna na idarwa tace "to ynxu dae tunda dare yyi, sae mu bari gobe da sassafe mu bar gidan nn, shi kuma wnn yaro dama baya dawowa gida ne naji shiru har ynxu, ko dama ke daya ke rayuwa cikin gidan," Inteesar bata tanka ta ba tana ta game da wayar Aliyu, inna ta tabe baki tace "to Allah shi kyauta, ynxu dae kije ki hado min tea don idan ban sha ba bana jin ddi" Inteesar tace "kai inna duk tuwon da kika ci," inna tace "naga dae ba ke ke siyowa ba jikana ke siyowa," inteesar ta harareta ta mike tayi hanyar fita xata je hado mata tean, tana bude kofar ta kusan cin karo da Aliyu dake labe jikin kofar, shi ma xuwansa knn, suka xaro ido a tare xata fasa ihu don ba karamin tsorata tayi ba kuma bata yi xaton ganinsa gurin ba yyi saurin fixgota ya rufe kofar . . Inteesar ta turasa xata koma cikin dakin ya rikota da sauri ya toshe bakinta ya ja ta suka shiga bedroom dinsa ya tura kofan ya jingina jikin kofar yana mata wani irin kallo, tace "meye hka ni ka bude min kofa na fita," yace "hakkina nake so ki bani yau," ta xaro ido gabanta na faduwa tace "meye hakkinka kuma," yace "bari na nuna maki, yyi kanta ta koma baya da sauri tana cewa "wllh xan maka ihu idan baka bude min kofa ba," a tsorace tayi maganar ya galla mata harara yace "kiyi mana," ta girgixa masa kai kamr xata yi kuka tace "don Allah kayi hkuri tea fa xanje na hada ma inna,"yyi murmushi yana kare mata kallo, rigar bacci ne sky blue mara nauyi iya gwiwa a jikinta mai hannun singlet, ta saka gashinta cikin net, ya lumshe ido yace "bani hakkina tukun sae kije ki hada mata kitchen din gaba daya ma," xata yi magana ya daga ta sama kamr wata yar bby sae kan gado, ba karamin tsorata tayi ba cikin muryar kuka tace "ya Aliyu don Allah ka bari ni ban san me kke nufi ba," ya cire jallabiyar jikinsa yana kallonta ya ajiye yace "xan gwada maki abinda nake nufi," xata sauko daga kan gadon ya danneta tace "wayyo na shiga uku," kissin dinta ya shiga yi yana rungume da ita, duk ta gigice ta shiga turasa amma yaki sakinta ya shiga romance dinta, kuka ssae ta shiga yi ganin abun nasa ba na wasa bne, suka ji inna ta bude kofar dakin Inteesar din ta fito tana cewa "yau naga rayuwa daga xuwa a hado min tea shiru har ynxu," inna ta rike haba tace "lau ko dae shafe shafen nn da naga tana yi daxu gun mijinta xata" sae kuma ta fita ta samu mai gadi tana kallonsa tace "kai mara mutunci mai gidan ya dawo ne," da kmr baxae kulata ba sae kuma yace "ehh" tace "amma yarinyar nn anyi yar bnxa gun mijinta ta tafi ta barni," ta koma ciki ta hada tean da kanta ta koma daki tace "ikon Allah, amma wnn anyi munafuka" Inteesar na jindawowanta cikin kuka tace "kayi ma Allah ka kyaleni na kai mata abinda ta aikeni," Aliyu bae ma san tana yi ba lkci daya yanayinsa ya canxa ya xaman mata kmr wani xautattce, duk ita ma ya bi ya kashe mata jiki ganin ya soma rabata da kayanta yasa ta kankamesa jikinta na rawa tace "don Allah ka bari ya Aliyu ka tausaya min wllh tsoro nake ji," ya girgixa kai da kyar yace "plss fateema ni ma ki tausaya min," cikin kuka tace "wllh baxan iya ba," murya can kasa yace "don Allah fa nace maki," ta shiga turasa jikinta na rawa tana kuka tace "wayyoo tsoro nake ji don Allah kajitausayina wllh bna so," ya fada gefentayana mayar da numfashi, ganin tana nemansauka daga kan gadon yasa ya fixgota ya rungumeta, cikin shessheka tace "don Allah kaji tausayina ka bari," da kyar yace "bbuabinda xan maki," duk da hkn bata kwantar da hankalinta ba sae kuka take, shi dae yana rungume da ita idonsa a lumshe, hkn yasa tayi shiru sae ajiyar xuciyar da take,suna nn a hka har bacci ya dauketa, ya kwantar da ita ya lulluba mata bargo ya koma dayan side din jikinsa a mace ya kwanta, hka ya kwanta ranan a wahale da ciwon ciki, ita ko tana ta bacci abunta, cancikin dare ganin bacci ya gagaresa yasa ya mike ya koma falo ya sami lime ya sha ya kwanta, da asuba ruwan sanyi gora guda ya tashe sa . Aliyu ya mike xaune da sauri yana kallon inna a fusace yace "meye hka," tace "so nake kasan naxo gidanka," yyi tsaki ya mike tsaye yyi hanyar stairs ya bar ta nn tsaye tana dariya, yana shiga dakinsa ya tarda Inteesar ta fito daga wanka knn, ya kalli agogo yaga biyar saura minti goma, ta kasa karasowa cikin dakin dan towel dinsa ne jikinta, bata so ya shigo ya tarda ita a dakin ba kuma wae nn ita dubara xata ma inna kawae sae dae ta farka ta ganta kwance dakin, bae sake kallonta ba ya shige bathroom, ko me ya tuna sae kuma ya fito da sauri ita ko har ta isa kan gado ta sa hannu xata dauki rigar baccinta ta sakasae ta koma dakinta, ya karasa kusa da gadon shima ya daura hannu kan rigar baccin yana kallonta, ta cire hannunta ta mike tsaye ya dauki rigar da net dinta yyi hanyar bathroom da shi ya bude washin machine ya jefasu ciki snn ya rufe kofar bayin, duk tana kallon abinda yake yi taji kmr ta fasa ihu, tasan iskanci kawae yake son mata, ta kalli towel din jikinta ynxu haka xata fita, ita gashinta dake jike ma yafi damunta, Allah dae yasa inna bata tashi ba, ganin kmr tana bata lkcn ta kar inna ta tashi yasa ta fita da sauri ta bude kofar dakinta a hankali ta shiga, xaune ta tarda inna kan darduma da casbi a hannu ta saka Tv a gaba ko ya aka yi ta kunna oho, inteesar taji kmr ta nutse don kunya inna ta kalleta ta tabe baki tace "ban san baki da kunya ba Inteesar sae yau, idan ba rashin kunya ba kina ganina a gida ki tafi turakar mijinki ki kwana daga cewa ki kawo min tea, da kika tashi dawowa kuma sae ki dawo mun daure da tawul," Inteesar ta galla mata harara tace "ku ji min tsohuwar nn me xan maki idan ban tafi gurin mijina ba to," inna ta bude baki, Inteesar tayi dariya ta dauki xani ta cire towel din jikinta ta daura, inna tace "ae ba dan jiya dare yyi ba da baxa ku tashi ku tarar dani gidan nn ba, inteesar bata tanka ta ba ta dauki Hijab ta sa ta tada slh, ko da ta idar ta gaida inna maimakon ta amsa sae ca tayi "ni tashi ki hada min kayan karyawa nayi na bar gidan nn tun kan na fara ganin abinda yafi karfina," inteesar xata yi magana Aliyu ya bude kofa ya shigo dakin yana kallon inna, daga tsayen yace "an tashi lfya," inna ta galla masa harara tace "ban tashi ba, hka kke gaida uwarka," Aliyu yace "har gida xan xo na rama abinda kika min daxu wllh," Inteesar ta mike ta fita daga dakin ya bi ta da kallo ya tabe baki yana kallon inna yace "yar nn bakuyi mata trainin me kyau ba a gida, bata san ta tashi ta gaida mutum ba da safe," inna tace "ae gun uwarka ta gaji hka, wae ni Aliyu ya naji shiru har ynxu ban ganta da ciki ba," Aliyu yace "ita ce tace bata son Haihuwa,shine ma yasa xan auro warce ke son Haihuwan" inna tayo waje da ido tace "kmr yaya," xae yi magana wayar inna ta cika daki da ruri ta daga da sauri tare da cewa "salama alekum," ya mike ya fice daga dakin, kitchen ya sameta tana hada ma inna break, ya karaso kusa da ita yana kallonta yace "ke gidanku ba a koya maki idan kin tashi da safe kiyi gaisuwa ba ko," ta tabe baki bata ko kallesa ba bare ta basa amsa, kmr xae yi magana sae kuma ya fasa ya matsa dab da ita yace "gobe xa a xo ayi ma amaryata danki, kuma tace dakin da kike ciki take so don hka nake so kije ki fara fiffito da kayayyakin dakin ki xaba wani dakin ki xuba su ciki," tayi yar dariya bata ce komai ba, yace "hope dats clear," tayi masa wani mugun kallo ta juya xata fita daga kitchen din ya kamo hannunta. Inna na xaune a daki tana kallo bayan ta ci tayi kat, inteesar kuwa na wanke Bathroom Aliyu ya shigo yana kallon inna yace "inna xo mu je indan xaga dake gari mana tunda ina gida yau," inna na kallonsa da mamaki don daxun nn suka gama fada tace "kai da gske? Amma fa ba tukin nan taka ta ganganci xaka yi dani ba fa," yace "wllh a nutse xan tuka ki," ta mike da sauri tana gyara daurin dankwalinta tace "to ita Inteesar ita kadae xa mu bari gida, wae ma to wa xae je ya kwaso min kayana ne," yace "ehh xan kira Zainab ta kwaso maki, inna tace "Inteesar ke baxa ki je bane, Aliyu yace "ki dae gaya mata me xata girka maki kafin mu dawo," inna tace "to kiyi min tuwan semo da miyar kubewa," inteesar ta fito tana kallonsu, ko kallonta inna bata yi ba tace "sae mun dawo," ta fice Aliyu ya juya ya galla mata harara snn ya fice shima, mai gadi na bude masu gate tace "yauwa Aliyu wnn ba mutumin arxiki bne jiya kokuwa ya dinga yi dani ka koresa," yace "to inna," suna ta tafiya suna hira inna sae kyalkyale dariya take duk da Aliyu bae ga abun dariya ba don hiran ma ba ganewa yake ba, tafiyar kusan minti talatin suka yi snn yyi parkin yana kallon inna yace "to fito in siya maki nama," inna ta fito da sauri tace "yauwa dan albarka" tana kare ma inda suke kallo bakinta a wangale, can sae fara'ar dake fuskarta ya bace tace "nn ae anguwansu farida ne Aliyu," yace "yauwa ashe kin gane, kuma nasan xaki iya gane gida daga nn kina shan kwana xa ki ga gate, in kin koma sae kice da Haisam ya siya maki naman don ban fito da kudi ba" yana kai wa nn ya shige motarsa yyi gaba inna ta fasa ihu tana salati, mutanen dake gun suka taho da sauri suna tambayar lfya. Inteesar na kwance da daddare ya shigo gidan ita dae tasan bbu maganar dawowan inna gidan, tana ji ya bude dakinsa ya shiga, ta mike xaune ta rafka tagumi tana naxarin abinda yace mata daxu da safe ita har lkcn ta kasa gaskata wae Aliyu aure xae yi nn da kwana hudu, tunanin hkn yasa hawaye ya cika idonta, tana nn xaune har kusan karfe daya ganin bacci ya kaurace mata yasa ta mike a sanyaye ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito ta fara sllhn dare. Da safe tana gaban madubi tana gyara fuskarta ya shigo dakin, 1st tym in history Aliyu ya shigo mata daki da sallama ta amsa ba tare da ta kallesa ba yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "kina jina, ki kama kanki safeenah xa su xo gidan nn anjima don nasan baki da kunya, infact bance ki fita ba ma," tace "akan me baxan fita ba? Wllh bbu abinda xae hanani fita," yace "shknn, ni kuma xan ce mata duk abinda kika yi mata tayi min maganinki" ya juya ya fice daga dakin bayan kmr minti goma ya dawo yana kallonta yace "kinga dakina yyi kama da dakin kaya, c'mon kin wuce kin dauke min kayanki da kika ajiye min a ciki ko sae na bata maki rae," xata ce wani kaya sae ta tuna kayan baccinta dake dakinsa ta mike fuskarta daure ta fita tayi hanyar dakin ya bita a baya tana shiga dakinsa ya jawo kofan yasa key, ta juya da sauri tana kallon kofar ta shiga bugawa tana cewa "meye hka," yace "hka xaki tsaya har sae na dawo," ya rufe nata dakin ma da key snn ya fice ya bar gidan, kuka ta fashe da ta durkushe tana kare ma dakin kallo, sae a snn ta lura da kayan tea da cakes din da ya ajiye mata kan fridge sae plantain chips, karfe sha biyu taji ana shigowa gidan da motoci ta mike da sauri don bayan ta gama cin kukanta ta gaji kwanciya tayi, ta karasa jikin window taga manyan motoci shake da kaya har kusan guda uku, wasu lafiyayyun motoci suka shigo gidan, manyan mata kusan su goma suka fito suna daddaga hanci, sae ga wata motar ma ta shigo safeena da kawayenta suka fito daga cikin motar tana gwada masu ta inda xa su bi su shiga gidan, tuni aka fara sassauke lafiyayyun funitures din da aka shigo da, Inteesar ta sake labulan a sanyaye ta koma kan gado tayi kwanciyarta tare da lumshe idonta da taji na neman kawo kwalla, duk suka cika gidan da hayaniya wasu na sakin magana, ana ta shigo da kaya. Ko minti sha biyar ba ayi da shigowarsu ba Anty Nafeesa da Zainab suka shigo gidan, suna shiga falo duk aka juya ana kallonsu, batare da Anty Nafeesa ta kallesu ba tace Sannunku fa, Zainab kuwa dama ko kallonsu bata yi ba, Safeena dake kwance kan kujera da kawayenta suna ta hira da shewa ta bi su da wani irin kallon raini hka ma iyayen nata, cikin daga murya Anty Nafeesa tace "to ina uwar gida sarautan mata kuma ran gida take ne," Zainab tace "ina xata iya da wnn hayaniyar Anty, kila tana can cikin daki," . Safeenah da 'yan uwanta suka bi su da kallo har suka haura sama Anty Nafeesah na cewa "gskya kam ina xata iya da wnn hayaniyar," wayar Zainab yyi ring ta duba ta ga ya Aliyu, tace "ashe dae ya Aliyu na da nmbrna," ta daga yace "ki fito waje ki karbar maku makulli," tace "na me," yace "ban sani ba snn ya katse kiran" ta kalli Anty Nafeesa dake buga kofar inteesar tana kiranta tace "wae yaya naje na karba makulli a waje," Anty Nafeesa tace "na me, ko tare suka fita da Inteesar din ne," Zainab tace "kila, ina xuwa na karbo keyn," ta fice da sauri, yana cikin mota yana jiranta ta karasa ya mika mata keyn dakinsa da na Inteesar, tace "to ina inteesar din," yace "in kun bude xa ku gani," ya ja motarsa yyi gaba, ta tabe baki ta koma cikin gidan, dakin Inteesar suka fara budewa bbu kowa ciki, snn suka bude nasa, tana xaune ta hade kai da gwiwa, suka karaso cikin dakin Anty Nafeesah tace "amma Aliyu dan rainin wayo ne kulle ki yyi a daki don ya isa," Zainab ta dago kanta tana kallonta, kuka take, Anty Nafeesa ta galla mata harara tace "ban san shashanci kukan lfya" ita dae bata ce komai ba ta gaida Anty Nafeesa, Zainab tace "meye na kuka Inteesar" Anty Nafeesah tace maxa tashi kije ki gyara fuskarki kiyi kwalliya kar na bata maki rae ke dae baki gajiya da wnn shegen kukan naki komai kuka komai kuka, ita dai bata ce komai ba suka bar dakin Aliyu Zainab ta kulle suka koma nata dakin, sae da ta sake wanka snn Anty Nafeesa ta sa ta gaba ta tsantsara kwalliyanta snn ta fito mata da wata shaddarta dogon riga maroon colour ta saka Nafeesa tayi mata dauri mai kyau, Zainab tace"waw yan matan yayanmu kin ga yanda kika xama kmr wata balarabiya," inteesar ta galla mata hara, ba karamin kyau tayi ba duk da ta rame ssae, Anty Nafeesa tace "to akwae abinci ne a gidan? Don ni yunwa nake ji," Inteesar tace "sae da na girka maku," Anty Nafeesah tace "to da dae yafi," ta ce "toAnty suna falo kuma," Anty nafeesa tace "to ina ruwanki da su ae don su ganki da kyau nake son kije kiyi mana girkin," ta mike ta dauko mata takalmikalan shaddar ta ajiye mata snn ta feshe ta da turare tace "maxa sa ki tafi indomie kawae xaki girka mana," Zainab tayi dariya tana kallon Anty Nafeesa, Inteesar kam murmushi tayi ta sa takalmin gabanta na faduwa ta fita xuwa kitchen, duk suna xaune falon har da safeena kusan su goma banda wa inda ke ta jere a daki, Inteesar bata ko kalle inda suke ba a nutse cikin takunta mai jan hankali ta nufi kitchen ta bude kofar kitchen din tana yatsine fuska don duk sun dauki cups sun sha lemo da shi, ta dan tabe baki ta shiga kitchen din, duk kawayen safeena suka juya suna kallon safeena da yanayinta ya sauya lkci daya xuwa bacin rai tana kallon kofar kitchen din, inteesar ta kunna gas ta daura ruwa snn ta fito falon ta shiga kwala ma Zainab kira cikin wani irin tsiga, da sauri Zainab ta sauko tana cewa "na'am yan matan yayanmu wnn kira hka," inteesar ta galla mata harara da wasa tace "ban fa son iskanci indomie nawa kike ga xae isheku," Zainab tace " wani irin tonan asiri ne wnn, ko ma dae duka nace ae gidan yayana ne nn bbu uban da ya isa ya hana," Inteesar tayi dariya ssae tace "ikon Allah to shigo ki girka maku kinsan dae ni ba daga nn ba ban gaji rowa ba kuma duk yanda nace hka xa ayi a gidan nn bare kice kina tsoran wataran ki xo...," a fusace safeena ta mike tana nuna Inteesar da yatsa tace "ke ki kama kanki kar ki kaini bango don dukan tsiya xan maki wllh wllh kuma sae dae mijikinki ya gode min idan ya dawo," Zainab ta yo waje da ido tace "wa xa a duka ni Zainb" Inteesar tayi dariya tace"tambayan min ita don ni kaina ban gane inda ta dosa ba," Safeena ta ciro wayarta da sauri ta shiga kiran Aliyu, "Aliyu Aliyu ka ja ma ballagaxar da ka ajiye a gida kunni wllh ta fita harkata idan ba hka bakafin na bar gidan nn yau sae na yi mata kaca kaca, kuma wnn shegiyar kanwartaka ita ma kaja mata kunne," Zainab tace "wllh ni ba shegiya bace sae dae kece shegiya," Inteesar ta ja ta suka shiga kitchen suna dariya, safeena tayi shiru tana sauraran abinda Aliyu ke ce mata tana bubbuga kafa, sun gama dafa indomien knn xasu wuce samaAliyu ya shigo gidan, ba karamin tsorata inteesar tayi ba tayi hanyar stairs ba tare da ta kallesa ba, Zainab tace "ke kar ki bada kanki mana ki tsaya ae Anty nafeesa na nn," Aliyu na kallonta yace "ke xo nn," ta galla masa harara tace "nayi maka me," karasowa kusa da ita yyi ta dake xuciyarta na bugawa, duk yan falon suka xuba masu na mujiya, ita kanta Zainab karfin hali tayi ta tsaya, Safeena kosae taunar cingam take tana jujjuya ido xuciyarta fal murna ita nn kawayenta suka yanda ta isa da Aliyu, yana isa kusa da inteesar ya kama hannunta ta fixge tace "da'alla malam kyaleni," ya tsaya kallonta da mamaki bae ce komai ba,ya juya yana kallon Zainab yace "je dauko mata mayafinta ko ki bata naki," Zanab ta cire mayafinta ta mika ma Inteesar taki karba, shi ya karba snn ya sureta kmr wata bby suka fita daga gida . Inteesar ta tsorata ssae murya can kasa tace "don Allah kayi hakuri ka saukeni wllh ita ce ta fara,"Safeena kam binsu tayi da kallo da mugun mamaki don tsabar mamaki kasa rufe bakinta dake bude tayi, ita nn jira take taga ya rufe ta da duka, Zainab kuwa dariya tayi tace "kai irin wnn soyayya hka, ko me Inteesar ke ma yayana hka oho," ta haura sama tana ci gaba da dariya, bayan mota ya jefata snn ya xaga ya shiga motar ya ja ta, ita ko kallonsa kawae take gabanta na faduwa ko ina xae kai ta, sun yitafiya ssae snn taga yyi horn aka bude gate ya shiga yyi parkin, ya bude mata kofa yace "fito kar na mareki," ta fito tana kare ma wajen kalloduk da tasan inda ya kawota don ta taba xuwa, lallai ma Aliyu asibiti ya kawota, yyi gaba tana biye da shi a baya kmr xata yi kuka, nurses duksuka kama kansu ganinsa, suka bi inteesar da kallo suna masu sannu da xuwa, bae ko kallesuba sae ita ce ta gaishesu ganin yanda suke kallonta, can last flour office dinsa yake kusa dana aminin dad dinsa don shine mai asibitin wato dad din Sadeeq, ya bude office dinsa ya shiga, ganin taki shigowa yasa ya fixgota, ta shiga karema office din nasa kallo, ba karamin haduwa yyi ba kmr ba office ba ita fa bata taba gskata Aliyuna aiki ba duk da tasan da sassafe yake barin gida ya dawo late, ya shiga dakin da ke cikin office din ita dae tana nn tsaye har ya fito bayan kmr minti goma sanye da kayan surgery, green colour yana kkrin sa hand gloves alamar theatre xae shiga, ya galla mata harara yace "kada Allah yasa ki xauna kuma idan lkcn sllh yyi kar kiyi," snn ya fice, tayi tsaki kmr xata yi kuka ta xauna kan kujera tana kare ma office din kallo, ko minti goma ba ayi ba da fitarsa wata nurse ta shigo rike da abinci a rufe da lemo ta ajiye mata tace "sannu madam," snn ta fita. Hka inteesar ta yi ta xama kamar gantalalliya a office kmr tayi kuka, abincin da aka kawo mata ma kin ci tayi, ta gaji da xama ta kwanta kan gadon da ake duba pregnant women tayi kwanciyarta sae bacci, ko da ta farka taga biyar ya kusa ita da ta kwanta tun kusan daya da rabi, bata damu ba don dama bata sllh, ta bude abinci daxu ta yatsine fuska ta rufe, aka bude kofa wasu nurse biyu suka shigo da jarirae har biyu suka yi ma inteesar sannu, snn suka daura su kan gadon yara dake office din daya ta kunna wani wuta mai haske dae dae fuskarsu snn suka fita, inteesar ta wara ido tana kallon yaran kyawawa dasu, ta karasa kusa dasu da mamaki tana kallonsu tace "yan biyu," a hankali dayan ya shiga kuka yana tsotsan hannunsa dayan ma ya karbe taji kmr ta daukesu don tana bala'in son yara, ta rasa yanda xata yi dukta rude ganinsu tayi can tayi nn, aka bude kofar dakin Aliyu ya shigo ta juya da sauri tace "ya Aliyu yan biyu ne?" ya cire abun bakinsa yace "ehh" ba tare da tasani ba tace "waw a ina kukasamo su" ya karaso kusa da gadon yana kallonsu yace "daxun aka cirosu daga cikin mamansu, bata farfado ba har ynxu ma" inteesar ta juya da sauri tana kallonsa kmr xata yi kuka tace "theatre aka mata," xae yi magana daya yaron ya tsala ihu tace "wayyo ya Aliyu in daukeshi," ya harareta yace "basu da lafiyasuma," tayi shiru tana kallonsu kmr xata yi kuka.Ya dauki dayan a hankali ya mika mata yana kallonta. . A hankali Inteesar ta sa hannu ta karbi bbyn da yake mika mata tana murmushi, tace "ya Aliyu ni ina son twins ssae" yana kallonta yace "kina sonki haifi twins knn," da sauri tana kallonsa tace "eh mana ina so," ganin irin kallon da yake mata yana murmushi yasa taji kunya ta kauda kanta da sauri, wae Aliyu take ma wnn maganar? Ita bata ma sani ba, ya matso dab da ita ya tsaya har tana iya jiyo numfashinsa a bayanta ya rike kugunta yace "wnn waist din naki xae iya daukar twins?," ta bar wajen da sauri nn da nn ta tsorata xae yi magana ta riga sa da sauri tace "Yaya yunwa fa suke ji ko," bae ce komai ba sae kallonta da yake, ta daga bbyn xata yi kiss dinsa ya dakatar da ita da sauri, snn ya karbe shi ya kwantar gefen dan uwansa, tace "yaya baxa a basu abinci ba," yace "sae xuwa karfe sha biyu na dare," ta wara ido tace "sbda me yunwa fa suke ji," yace "eh xa ayi ta basu ruwa" kmr xata yi kuka tace "to waye xae dinga basu kace mamarsu bata farfado ba," ya daka mata tsawa "ke da'alla kar ki dame ni" yyi tsaki ya shiga daki, ta bisa da kallo snn ta tabe baki ta koma kujera ta xauna, wata nurse ta shigo rike da mug a rufe tana kallon Inteesar tace "doctor fa? Ya shigo?" a dari dari take tambayar, Inteesar ta gyada mata kai, nurse din ta ci gaba da tsayuwa har ya fito sanye da kananan kaya, yana kallonta yace "wathappen" tace "coffee sir," ya daka mata tsawa "to kaina xaki daura ko me," ta karasa kusa da table ta ajiye ta fita sum sum. Ya bude abincin da aka kawo ma inteesar yana kallonta yace "meyasa baki ci ba," tayi kamr bata ji sa ba, ya rufe ya koma kan table dinsa ya xauna kan kujera ya bude coffeen ya shiga sha, hka yaran suka dinga kuka Inteesar taji kmr ita ma tayi kukan, ta kasa jure kukan nasu tace "yaya kuka fa suke," ya kalleta yace "cnt yhu see they re under medication," bata sake cewa komai ba bayan kmr minti sha biyar ya kira nurses su kashe wutan su fita da su, inteesar ta bi su da kallo kmr xata bi su suna fita ta bata rae ta juya tana kallon Aliyu taga kallonta yake yana murmushi, ta dauke kanta da sauri, karfe takwas da rabi suka bar asibitin bayan ya kaita ta kara ganin yan biyun da mamarsu, ya biya ta eatry ya siya masu abinci snn suka kama hanyar gida, gidan ba kowa duk sun watse sae kamshin turaren wuta ke tashi, ta haura sama ta bar sa nn falo shima ya bi ta a baya, spare key Aliyu ya dauko ya bata na dakinta don su Anty Nafeesa sun tafi da shi, dakin safeena ma a kulle yake ta tabe baki, ta bude kofar dakinta, ba shiri ta koma baya da sauri tana kallon dakin da mamaki kadda cikin dakinta aka yi ma safeena jere, ta juya tana kallon Aliyu da ya fito daga dakinsa yana kallota yace "Abba ne ya ba kansa wahala ya bata kudinsa shi me 'ya," ya sauka kasa ya barta nn, sababbin funitures masu rae da lfya wanda suka fi na da ne a dakin nata, ashe su Anty Nafisa abinda suka xo yi knn, ta karasa cikin dakin a sanyaye, bbu abinda ba a canxa ba a dakin. Tanaxaune gefen gadonta bayan ta fito daga wanka ta sa kayan bacci tayi jigum ta ma rasa abinda ke damunta ya shigo dakin ya ajiye mata ledan abinci ya fice. Ranar friday da yyi dai dai da Ana gobe daurin auren Aliyu da safeena ranar da kuma xa suyi dinner, Inteesar na kwance a daki da rana duk ta rasa kanta kmr wata mara lfya, rabonta da Aliyu tun ranar da ya ajiye mata abinci ya fice sae dae taji shigowarsa da fitarsa, Zainab da kursum kadae ke xuwa debe mata kewa, taji an bude kofar dakinta a xatonta su ne, Aliyu ya shigo dakin ya xauna gefen gado yana kallonta yace "mantawa nayi jiya bamu je party da ke ba" bata ko kallesa ba bare ta basa amsa, ya tabe baki ya ajiye mata dan box karami irin na jewelries yace "tunda kince ba kya son kaya ga wnn, don banso in shiga hakkinki," ta juya tana kallon box din ya bude mata, Zinari ne dan kunne da sarka har da xobunaye biyu, tayi tsaki tace aikin bnxa me xanyi da wnn gantalin kadae je ka kara mata don wanda ubana ya sa min a kayana ma ba damuwa nayi dasu ba bare wnn, ku wnn ya dama" ya mike tsaye fuskarsa daure yace "ni kike gaya ma magana," ta fashe da kuka tace "an gaya maka din wlh ka fitar min a daki," yyi murmushi ya dauki box din ya fita daga dakin, tasulale kasa tana kuka ssae da bata san dalilinsa . ba, karfe bakwae suka shigo gidan da abokanansa suka shirya suka wuce dinner. Har Aliyu ya shigo gidan karfe daya idon Inteesar biyu, ta kasa bacci, hka kawae ta samu kanta da fashewa da kuka har da shessheka, har kusan karfe biyu tana xaune bbu alamar bacci a tare da ita, taji an tura kofan dakinta a hankali ta juya da sauri suka yi ido hudu da shi ta kauda kanta da sauri ta mike xata shiga bathroom yyi hanxarin rikota ta fashe masa da kuka ya rungumeta . Inteesar ta shiga turasa yaki sakinta, har suka isa kan gado ya xaunar da ita shima ya xauna yana kallonta ya dago kanta a hankali yace "me ya hanaki bacci har ynxu," ta dauke kanta har lkcn tana hawaye ta mike xata bar wajen ya rikota, a hankali ta shiga rera masa kuka ya rungumeta yace "ina son jin kukan ki har wani ddi nake ji idan naga kina kuka," ta turasa da karfi xata mike ya rike ta gam yace "not until yhu tel me y yhu re cryn," ta fashe masa da wani kukan abun tausayi ya daga ta ya kwantar da ita kan gadon ya kwanta gefenta ya rungumota snn ya kashe wutan dakin, ajiyar xuciya kawae take, a hankali yace "don xanyi aure shine kike kuka," xata yi magana ya rufe bakinta da sauri, yace "warce xata haifa mana 'yan biyu xan auro, kinga sae kiyi ta raino tunda kina son su," bata ce komai ba ya daura bakinsa kan gashinta yana kissin dinshi, a hankali ya kai hannunsa kan cikinta yana shafawa kmr mae mata rada yace "xaki iya na baki yan biyun ynxu?" a tsorace ta rike hannunsa da sauri tace "A"a wllh baxan iya ba," a hankali yace "plss," muryarta na rawa tace "No plsss" ita kam 1st nyt dinsu kawae take tunawa da irin wahalar da tasha har da suma har abada bata fatan ya sake kusantarta, ya kankameta murya can kasa yace "to yi baccin ki," suna nn a hka har bacci ya dauke ta, ranar dae a hka suka kwana tana jikinsa kuma ranar ce rana ta farko da ya kwana a dakinta, washegari da yyi dae dae da ranar daurin aurensu da safeena, da asuba ya kwantar da ita a hankali ya shiga bathroom dinta yyi alwala, ko da ya fito ya tarda ta xaune kan gadon tayi tagumi, ta mike ba tare da ta kalleshi ba ta shiga bayin ita ma tayi alwala ta fito ta tar da shi yana jiranta, a tare suka yi sllhn, rana ta farko knn da ta bude baki da safe ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba yana murmushi ya gyada mata kai kawae, ta mike xata bar dakin ya kamo hannunta yace "ina xa ki," ta sunkuyar da kanta bata ce masa komai ba, ya saketa ta fita, falo ta sauka ta shiga mrnin duties dinta, ba ita ta koma sama ba sae kusan karfe tara,ta tarda shi kwance yana bacci, wanka ta shiga ta fito ta gama shirinta ta fita daga dakin ta koma downstairs, bata ba kanta wahalan hada breakfst ba don bae taba cin girkinta ba, tayi kwanciyarta a falon don neman yunwa tayi ta rasa, karfe sha daya taji mai gadi ya bude gate ta mike ta isa jikin kofa taga ko waye ya shigo, motoci biyu ne suka shigo gidan abokanansa kusan su biyar suka fito, da yake kofar a bude yake komawa kawae tayi ta kwanta, suka shigo gidan da sallamarsu duk suna sanye da fararen shaddodi, ta kara volume din Tv ta mayar da hankalinta kan TV, tsokanarta suka shiga yi suna dariya "uwar gida ke kika rike ango har ynxu yaki fitowa kuma kika sa ya kashe wayoyo ko to ayi hakuri a sakar mana shi muje gun daurin aure," bbu yabo bare fallasa tace "ku dae tambayesa wanda ya rikesa," ta mike fuskarta a daure ta haura sama ta bar su nn falo, a step duka hadu da Aliyu ya galla mata harara, don me baki tashe ni ba, ita ma ta galla masa hararan tace "sbda baka isa ba," tayi gaba ta bar sa nn tsaye, ya sauko suna ta tsokanarsa wae tsoron uwargida yasa ya makara, dole suka jirasa yyi wanka snn ya fito shima sanye da farar shaddar, ba karamin kyau yyi ba don ko hmm bari dae, ya shiga dakin Inteesar tana xaune gaban madubi, kallo daya tayi masa ta madubin ta dauke kanta yace "kinyi break," tayi bnxa da shi, ya daga kafada yace "sae na dawo kiyi mani adduar Allah yasa ayi a sa'a," ya juya xae bar dakin ta fashe da kuka ba tare da ta shirya ba, ya juyo yana kallonta, ya karaso cikin dakin yace "an maki wani abu ne ko kawae jin ddin kukan ne ke damunki," bata tanka sa ba, ya tabe baki ya juya ya fita, suka fita gaba daya da abokan nasa suna masa mitan ya bata lkci dayawa ko mantawa yyi yau ce ranar daurin aurensa da sahibarsa shi dae bae ce masu komai ba har suka shiga mota suka bar gidan, suna fita daga gate yace "kun san wani abu ku je kawae gani nn xuwa, ina son na kai fateema can gida daga can sae na wuce," namesake dinsa yace "wae meye hka kke yi ita bata san hanyar gidan ba sae an kaita baka ganin saura yan mintoci," Aliyu yace "ni dae kuje kawae ina nn xuwa, ya bude motar ya koma cikin gidan," suka yi tsaki kusan gaba dayansu suka yi gaba, yanda ya barta hka ya dawo ya tarar da ita, ya dauki hijab dinta ya mika mata yace "tashi to na kai ki gida," bata yi musu ba ta mike ta karbi hijab din tasa takalminta suka fita, motarsa ya fito da ta bude sit din baya ta shiga, bai ce mata komai ba ya ja motar suka bar gidan, suna isa gida bata jira ya gama parkin ba ta bude mota ta fice, ya dakatar da ita da sauri ko kallonsa bata yi ba ta shige gidan da gudu sae sashin inna, hkn yyi mugun bata masa rae kuma yasan da mutane cikin gidan shi yasa bae bi ta ba, ya ja motar kawae yyi gun daurin aure, mutanen dake tsakar gidan har da su Hajiya suka bi ta da kallo murna fal cikinsu, umma ko ta dinga tuntsira dariya tana guda kawayen Hajiya na taya ta. ta xube jikin inna ta fashe mata da kuka, a rude inna ta shiga tambayarta "meye faru, ke da waye," ta kasa cewa komai, inna ma ta bare baki ta fashe da kukan, Anty Nafeesa ta fito daga daki da sauri tana kallon Inteesar tace "wa ya kawoki," inteesar tayi kkrin tsayar da kukanta tace "shi ya kawo ni," Nafeesa tace "ynxu kuwa muke shirin tafiya can gidan, kukan meye hka kike yi, ke dae baki ji ddi ba wllh," a fusace cikin kuka inna tace "ban son iskanci ke uwar wa yyi maki kishiya," inna ta mike ta daga inteesar tana share hawayenta suka shiga daki tana cewa "ki rabu da shi, bbu abinda xaki koma gidan nn kiyi, kuma bbu uban da ya isa yace ki koma tunda nace baxa ki ba, ina nn ina jiransa daga shi har ubansa," Anty Nafeesa tayi murumushi ta bi su cikin dakin. Gida ya cika fal da yan uwan su Hajiya da umma da abokanan arxiki ana ta shagalin biki har da su Dj a gidan, inna na daki xaune gefen Inteesar da ta kwanta tana bacci tana mata fiffita ita ma tana gyan gyadi, jin kide kide yasa inna ta farka ta fito da gudu har Anty Nafeesa da wa inda ke falonta suka tsorata suka dinga tambayar lfya, ko kallonsu bata yi ba ta fita xuwa tsakar gida da gudu, Anty Nafeesa ta ma xaci abu ne ya sami Inteesar suka shiga dakin da sauri suka tarar baccinta take, wasu kuma suka bi inna da sauri a baya suna tambayar wae Hajiya mai ya faru, inna na isa tsakar gidan cikin daga murya tace "nashiga uku uban wa ya gayyato wa innan shaidanun gidan nn" ta fadi hkn a fusace tana nuna masu Dj da kayan kide kiden nasu, aka kashe wakar dake tashi, Umma tace "to naga dae yau ranar farin ciki ne inna kuma dae daga yau ba sake ganinsu xa ayi ba," inna tace "kin ci ubanki mai dattin hula, kaji min rubabbiyar yarinya," ta karasa kusa da masu dj tana huci ta shiga bubbuga speakers din tana cewa "ku fitar min dasu kar na babbake su, gidan da na ba gidan yan iska da shaidanu bane" ba shiri Hajiya tasa aka shiga kwashe su a barrow ana fita dasu, hka ma canopies din duk sae da tasa suka fita dasu tana jaraba an cika gidan dan'ta da tarkace, hka mutane suka dinga kallon inna wasu na dariya can ciki ciki, "kuma duk shegen da ya xauna kusa da flawowin da na ban yafe masa ba duniya da lahira tunda dae ba shi ya dasa masa ba, ko tsinke kuma kar a wurgar a tsakar gidan nn," ta fadi tana huci kmr kirjinta xae fashe, Hajiya dae shigewa daki tayi kunya kmr ta nutse, wae juyawar da inna xata yi sae ganin momy tayi xaune suna hada salad, ta saka salati kmr xata yi kuka tace "Allah ya wadaranki Zainabu, ynxu uban me ya kawo ki cikinsu idan ba shisshigi da neman suna ba, ca suka yi maki yi suke dake mara xuciya kawae wahalalliya, ni dama nasan tun ba yau ba kika tsani yarinyar nn kike son ganin karshenta, idan ba hka ba taya xaki kwaso kafafuwa ki taho nn cikinsu, wllh daga yau kar ki sake nuna kin san Inteesar, ita ma bata sanki ba wllh, shi yasa ma da ta xo daxu bata nufi inda kike ba dan tasan ba sonta kike ba" ta karashe maganar da kuka ssae har da tari, ta bar wajen tana cewa "kuma yau bbu ubanda ya isa ya bar min tsakar gidan da' na hka, duk sae an wanke shi an goge wllh," dariya wasu har da xubewa kasa, ranar dae a dari dari su Hajiya suka yi shagalin bikinsu, jefi jefi inna kan fito taga ko an xauna kusa da flowern da tace kar a xauna, bbu wanda yyi gigin xama kuwa. Da Magrib bayan kowa ya watse inna ta tasa su Hajiya gaba sae da suka wanke tsakar gidan su Zainab da kursum da Maryam din Anty Nafeesa dariya kmr cikinsu xae fashe, dama momy tun daxu ta shiga ciki amma sae da inna taje ta fito da ita wae har da ita yar bakin ciki maxa su gyara ma dan ta tsakar gidansa, sae da taga sun kusa gamawa snn ta koma sashinta tana cewa "wahalallun bnxa kawae" karfe takwas abba yyi kiran Inteesar falonsa, ta karasa falon a sanyaye tayi sallama ta shiga, Zaune ta tarda Aliyu a falon yana sanye da shadda brown colour, ta nemi gefe ta xauna tana kallon Abba tace "ina yini Abba," Abba ya amsa yana kallonta yace "ya gidan," ta sunkuyar da kai tace "lfya Abba," Abba ya nisa yace "ranar da nace ku taho da Zainab don me kika ki bin ta," ta daga kai tana kallon Aliyu dake kallonta, Abba ya gyada kai yace "to yyi kyau, kuma har ynxu baki fara karatun ba ko?" a hankali tace "Abba na kusan farawa," Abba yyi shiru yana kallonta snn yace "to Allah yasa, ki tashi ki bi mijinki, a cigaba da hakuri, Allah yyi maku albarka" Aliyu ya mike yana kallon Abba yace "nagode Abba," ko kallonsa Abba bae yi ba, Inteesar ta yi shiru kmr xata yi kuka tace "Abba inna tace ba ynxu......." Abba ya hade rae yace "inna tace me, tashi maxa ki koma dakin ki, kuma bance ki shiga cikin gida ba," bata san tayi mugun ba Abba haushi ranar da ya aika Zainab kiranta taki xuwa ba, a sanyaye Hawaye na kkrin sauko mata ta mike tace "Abba sae da safe," yace "Allah ya tashe mu lfya," Aliyu ma yyi masa sai da safe ya bi bayanta suka bar falon . .. Suna fita Aliyu ya kamo hannun Inteesar da sauri ganin bata son jerawa da shi, ta juya tana kallonsa yace "mu fara shiga na gaida momynki," tayi masa mugun kallo tace "ae ko baka fada ba dama momyta ce bance taka ba," bai ce mata komai ba yana rike da hannunta suka isa sashinsu, shi yyi sallama ganin tsaya kawae tayi ta rike kugu, duk da ita yaso tayi sallamar, Ihsaan ce ta amsa ya shiga falon tana biye da shi a baya, suna hada ido da momy ya kauda kai da sauri ya nemi kujera ya xauna, ita ma ta xauna kusa da ihsaan da ta kankameta, momy dae na rike da assignment books din ihsaan, ba tare da ya kalleta ba yace "ina yini," ita ma tana neman page din da aka ba ihsaan bbu yabo bbu fallasa tace "kalau," Inteesar ta mike ta koma kusa da momynta tace "assignment ku ke yi momy," momy ta gyada mata kai, tace "bari nayi assistn dinta momy," momy ta bar mata buk din, ihsaan tace "Anty ae na iya," Inteesar tace "to xo kiyi," ta mika mata buk din ta karba ta shiga yi, momy ta mike ta shiga daki, inteesar ta juya tana kallon Aliyu da ya bita da kallo, ko kadan ba ta jin ddin yanda momy ke masu, ta mike a sanyaye ta bi ta daki, shi kuma ya dawo kusa da kanwartasa yana kallon abinda take yi, tana ganinsa ta daina rubutun, yana kallonta yace "y did yhu stop," tayi shiru taki cewa komai ya mike xae koma inda yake taji tsoro ssae don ta xaton dukanta xae yi, yyi murmushi yyi xamansa yace "to na bar maki wajen," ta ci gaba da abinda take, da Haisam ne jikinta na rawa xata fada kansa, amma da yake shi ya koya mata tsoransa shi yasa bae damu ba, to a gidan nn ma waye baya tsoransa, yyi murmushi tuno hka da yyi, yana nn xaune har kusan karfe tara da rabi snn inteesar ta fito bayan sun dan yi hira da momy, ta xauna gefen kanwarta tana kallon abinda take, murya can kasa yace "ki ce ma momy xa mu tafi," ta mike ba tare da ta kallesa ba ta shiga dakin, sae ga ta ta fito a sanyaye tace "tace to," hkn ya sa ya gane baxata fito ba knn, ya mike yana kallon ihsaan yace "bby gud Nyt," ta kauda kanta bata ce komai ba tana kallon inteesar kmr xata yi kuka tace "Anty ni xan bi ki," Aliyu yace "je ki tambayi momy to," ta shiga daki da gudu, sae ga ta ta fito kmr xata yi kuka tace "tace a'a," yace "je ki ce mata plss," ta koma da gudu sae ga ta ta dawo da hawaye tace "tace xan je sch," yyi shiru yana kallonta snn yace "i promise xan xo na dauke ki nxt wk kin ji, sae ki dinga tafiya sch daga can," ta gyada masa kai kawae ya ciro dubu biyar ya mika mata tayi masa gdya snn ta daga masu hannu suka fita daga falon Inteesar na murmushi, da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga snn ya xaga ya bude driver sit ya ja motar suka bar anguwar, bae ce mata ba bata ce masa ba, suka yi nisa ssae snn taga yyi parkin ya fita ta bi sa da kallo, tasan me xae siyo ganin inda suka tsaya, ba a wani dau lkci ba ya dawo rike da ledoji har biyu ya bude motar ya shigo snn ya ja ta suka bar gun suka kama hanyar gida, suna isa yyi horn mai gadi ya bude ya shiga yyi parkin snn ta bude motar ta fita shima ya fito ya kulle motar ya bi bayanta suka shiga gidan, kamshi ne mai ddi ke tashi a gidan, ta kalli agogo taga karfe goma da kusan rabi ta haura sama ta bude dakinta ta shige, ya dde xaune falo snn ya mike shima ya haura sama da ledojin a hannunsa yana kallon kofar dakin safeena ya bude nasa dakin ya shiga, ba a dau lkci ba ya fito sanye da jallabiya ya bude kofar dakin safeenar ya shiga, tana xauna sae taunar cingam take tana kallo ta wurgar da mayafinta gefenta, ya karaso yana kallonta yyi murmushi ya ajiye ledar hannunsa yace "amarya bakya laifi," ta galla masa mugun harara tace "daga ina kke Aliyu xaka shanya ni nn, har kawayena sun gaji da jira sun wuce," ya xaune gefenta ya rungumota yana shafa bayanta yace "Abbana ne ya bata min lkci bbyna kiyi hkuri," ta dan marairaice kmr xata yi kuka tana shafar fuskarsa tace "har naji haushi wllh angona," yyi kissin din goshinta yace "nasan kina jin yunwa bari na kawo plate da cup na xuba maki chicken da yogurt din da na siyo maki, tayi kissin din lips dinsa tace "to mijina," snn ya mike ya fita, dakin inteesar ya bude a hankali, tana kwance kan gado ta tsura ma Ac ido, yana kallonta yace "kinci abinci can gida ne," tayi bnxa da shi ya karaso kusa da ita ya hade rae "ba magana nake maki ba," nn ma taki ce masa komai sae dae me, ya lura kuka xata fara ta yanda tayi da fuska ya xauna gefenta da sauri yace "wae ke wace irin mutum ne da shegen kuka sae kace marainiya," yyi tsaki ya ce "saura idan na kawo maki abincin kar ki ci," snn ya fice, sae da ya fara shiga kitchen ya dauko plate da cups snn ya koma dakin safeenar, ita ma ta fito daga bayi knn sanye da dogon hijab ta xauna gefen gado, kaji uku ne taga ya ajiye daya gefe da yogurt biyu, ta sauko tana kallonsa tace "wnn fa dear," yana xuba mata kajinta a plate yace "na warcan ce" ta jingina jikinsa ta marairaice tace "xafi nake ji bby," yace "to cire hijabin mana, a hankali ta shiga cire hijabin tana masa wani shu'umin kallo . Aliyu ya dauke kansa da sauri ganin wasu shegun kayan baccin dake jikinta ya ci gaba da abinda yake, har ya gama ya ajiye mata nata snn ya dauki na Inteesar ya mike xae fita ya kai mata, safeena da ta koma kan gado ta xauna ta daura cinya daya kan daya tayi yar kara ya juya da sauri yana kallonta yace "me ya faru bbyna," kamr xata yi kuka ta shiga nuna masa bayanta ya karasa kusa da ita yana kallonta yace "me ya samu bayan dear," cikin tsigar shagwaba tace "nima ban sani ba," ya dafa ta ya dan duka yana duba bayan da take nuna masa ta turasa da sauri ya fada kan gado ya wara ido kan yace komai ta fada kansa ta shiga yi masa wani mahaukacin kiss tana shafa kirjinsa, turata ya shiga yi yana cewa "wait wait bbyna bari na kai mata abincinta stop it," ko kulasa bata yi ba ta karbe ledan hannunsa ta ajiye snn ta kashe wutan dakin ta shiga masa wasu abubuwa masu rikitarwa da kashe jiki nn da nn ya fara dauke wuta, shima ya shiga biye mata, haukatasa ne kadae safeena bata yi ba daren ranar don sumbatu kawae ya dinga mata, kamar yanda ta basa wahala hka shima ya wahalar da ita, ta shiga rera masa kukan kissa, bae sarara mata ba har sae da komai ya wakana ta dde jikinsa tayi lamo har sae da ya dawo nml snn ya turata gefe ya mike tsaye ya kunna wutan dakin yana mata wani mugun kallo yana huci, tana kwance kamar wata macijiya a kan gadon, ya girgixa kansa ya juya da sauri ya fice daga dakin ya shiga nasa dakin yyi wanka snn ya sauko falo ya kunna Ac duk da da sanyi garin yyi kwanciyarsa kan doguwar sofa ya lumshe idonsa xuciyarsa na harbawa da sauri ga wani mugun takaici da ke masa yawo a kai," hkn yasa ya dafe kansa yana kiran Allah a xuciyarsa, ya mike xaune ganin kwanciyar baxae masa ba, ya harde hannuwansa yace "Godforbid," ya kai minti talatin a hka a xaune snn ya mike yana kallon agogo karfe biyu da qtre yyi hanyar kitchen ya hado coffee ya dawo ya xauna ya shanye snn yyi kwanciyarsa, sae a snn bacci ya daukesa a falon. Da Asuba a bayin dake falo Aliyu yyi alwala ya tafi masallaci ya dawo yyi kwanciyarsa a falo, ganin bae jin komawa bacci yasa ya dauki remote ya kunna TV ya rage volume din yana kallon tashar Animaux, karfe bakwae yaji an bude kofa can sama, ya juya yana kallon stairs din daga kafafuwanta da yanda take tafiya ya gane ko wacece, ta sauko kasa tana sanye da rigar bacci iya gwiwa, tana tafiyar nn nata mai jan hankali, ita bata ma lura da shi ba sae da ta shigo falon, kallo daya tayi masa ta dauke kanta da sauri tayi hanyar kitchen ya bi ta da kallo har ta shige kitchen din snn ya sauke ajiyar xuciya ya ci gaba da kallonsa, aka bude kofa kuma ya bi stairs din da harara sanin ko waye, sae ko ga Safeena ta sauko tana mika da hamma sanye da kayan bacci iya cinya, nonuwanta rabi duk a waje, murya can kasa kmr mara lfya tace "shine sbda ba ka da imani Aliyu xaka tafi dakinka jiya ka kwanta bayan ka gama biyan bukatanka ka bar ni da wahala, wllh ban samu bacci ba jiya, bayan hka kuma gari na wayewa naji ka bude kofa ka sauko kasa ashe kwanciyarka ka xo kayi sbda baka damu da halin da ka sani ba ko," a tunaninta budewar kofar da taji na dakinsa ne bata san Inteesar bace, Aliyu ya mike a fusace yyi kanta ya shaketa yana huci yace "kika ce me?" ta xaro ido a tsorace tace "meye hka kke yi Aliyu," yana mata mugun kallo ya jinginar da ita jikin bango a nutse yace "ina kika kai Virginity dinki safeenah," ta hade rae tana kallonsa tace "kamr ya? Ban gane wnn tambayar taka ba Hydar, kana nufin ka kusance ni ne jiya don kaci xarafina, ko kai makaho ne baka gane ma idonka ba, ko so kke budurcin nawa ya fito yyi maka magana," daga ita har shi cikin natsuwa suke maganar don hka ba lallai bne wanda ke sama yaji me suka cewa sae dae mutum na downstairs ne, ya saketa yana mata wani irin kallo yace "prove it ynxun nn cewar ke Virgin ce," ta hararesa tace "ok," snn ta haura sama, yyi murmushin takaici sanin abinda xata je ta dauko masa ya bi ta da kallo xuciyarsa na tafarfasa, sae ko ga ta ta fito rike da xanin gadon jiya da ya bace da jini ta jefa masa gabansa tana masa mugun kallo, ya daga xanin gadon yana kallo, snn ya jefa mata a fuska yace "kin yaudari ubanki," ta wara ido ta dafe kirji tace "ubana fa kace Aliyu," yace "shi fa, ni xaki yaudara da fake Hymen, me kika maidani safeena kin manta ko wanene ni? Kin ci darajar ina sonki da bbu abinda xae hanani baki takardarki yau, ni ba maxinaci bane don hka Allah ne kawae ya kaddaro min aurenki," tayi shiru gabanta na faduwa kmr kirjinta xae fito tana kallonsa, dae dae nn Inteesar ta fito daga kitchen rike da cup din tea, safeena ta juya da mugun mamaki tana kallonta, tana wani irin taku mai jan hankali ta xo ta wuce su tana ma Safeenar wani mugun kallon wlknci tana murmushi, Safeena taji kmr kasa ya bude ta shige, lallai Aliyu ya tona mata asiri idan har dae yarinyar nn taji abinda suke cewa, sbda tsabar iskancin dake cin Inteesar bata ma san ta isa bakin stairs ba ta kusan faduwa ta rike karfen da sauri kofin hannunta ya fadi ya fashe ruwan tean ya malale kan tiles din falon ta fasa ihu tana cewa "wayyoo xafiii,", da sauri Aliyu ya karaso wajen ya dauke ta ya koma baya yana kallonta yace "ke makauniyace," ta marairaice kmr xata yi kuka tace "to ban sani ba, ido ne yyi min yawa," ya ajiye ta kasa ta ce "wayyo xafi kafar ke min," ya daga ta yana kallon kafar sae yarfe hannu take, yyi tsaki ya dauketa ya haura stairs din suka bar Safeena nn a tsaye, kallon safeenar take yana rike da ita tana murmushi, suna kaiwa karshen stairs tayi mata wani kallon bnxa tana kallon xanin gadon dake gabanta a yashe, Safeena taji kmr taji a mafarki ne hkn ke faruwa, hawaye ya cika idonta tana huci ta shiga kiran layin uwarta, bugu biyu ta daga cikin muryar kuka tace "momy mun bata kudin mu ne kawae a bnxa ya gane ni ba budurwa bace, ya ci xarafina momy ya walakanta na gaban yar iskar yarinyar nn duk taji cin mutuncin da yake min," a rude uwar tace "kashe kashe kar su jiki, xan kira ki anjima" ta katse wayan tana kukan takaici, kai amma Aliyu bashi da mutunci ko kadan, Aliyu na shiga dakinsa rike da Inteesar ya kwantar da ita kan gado yana duba kafar nata ko kwalba ne ya shiga, ganin yana ta ba kansa wahala yasa a hankali tace "ni ba komai a kafata," ya daga kai fuskarsa daure yana kallonta ya mike tsaye yace "fita ki ban waje," ta hararesa ta mike ta bi ta gabansa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin, a corrido taga safeena na kkrin shiga dakinta ta fashe da dariya ba tare da ta shirya ba har da faduwa . ... Safeena tayi kanta a fusace tana huci, da gudu ta sake komawa hanyar dakin Aliyu ta kwala ihu, ya fito da sauri yana kallonta yace "me ya faru," kmr xata yi kuka tana nuna safeena tace "ba ita bace ba," ya juya yana kallon safeenar fuskarsa a daure yace "tayi maki me?" Inteesar tana kallonsa tace "wae ta wani yo kaina kmr wata lioness xata dokeni sae kace uwata," ta karasa maganar tana hararan safeena, yana kallonsa safeenar yace "to ki doketa tunda yar ki ce," Inteesar tayi tsaki ta wuce su ta bude dakinta ta shige tana xaro mata ido, safeena taji kmr a mafarki hkn ke faruwa ta kasa cewa komai sae kallon Aliyu da take, shima yyi tsaki ya koma dakinsa ya bar ta nn tsaye. Inteesar na daki bayan tayi wanka ta shirya cikin wani less mara nauyi mai shegen kyau an mata riga da skirt lafiyayye, kwance take tana game da wayar Aliyu, taji ya buga kofar dakinta ta dago kai tana kallonsa yace "uwar wa xae gyara maki falon da kika yi litter da tea da kwalabe," ta xumburo baki ta ci gaba da game dinta, yace "ba magana nake maki ba," ta mike tsaye fuskarta daure ta bi ta gefensa ta fice ya bita da kallo, ya sauke ajiyar xuciya, tana sauka ta shiga kitchen ta fito da mop da bokiti da tsintsiya da parker ta rasa ta inda xata fara gyaran ga shegen tean shima ya malale har cikin falon, ya sauko yana kallonta yace "ohh tsayuwa kika ma yi knn," kmr xata yi kuka tace "to ni ban san yanda xanyi ba" ya tsaya kallonta, ta karyar da kai ita ma tana kallonsa, sae abun ya kusan basa dariya, yyi kwafa ya karbe broom din daga hannunta ya duka ya fara tattara broken mugs din, tana tsaye tana kallonsa, ya dago yana kallonta yace miko min abun kwashe sharan kmr xata yi kuka tace "baka ga kwalba a wajen ba xan taka," ya tsaya kallonta ya kasa cewa komai, dae dae nn Safeena ta sauko da dogon hijabinta xa ta kitchen hado tea ganin yunwa na neman hallaka ta, yace "miko min abun kwashe dirt din can Safeena," bata yi masu ba ta dauka ta mika masa jikinta na rawa, a tare ta taimaka masa suka gyara falon Inteesar na tsaye tana kallonsu, safeena na goge falon ya daka ma Inteesar tsawa yace "get out kar na mareki, meye amfanin ki a nn" ta ja dogon tsaki ta haura sama daga shi har safeenar suka bi ta da kallo, yyi kwafa kawae, da daddare ya hadasu a falo xae yi masu magana, Inteesar dae nata kallonta abunta, yana kallon safeena yace "kina ji na Safeena," safeena da ta xama kmr marainiya ko kuma nace ta kirki tun daga jiya, kanta a duke tace "ina jinka," ya kalli Inteesar da ta bar kallonta tana hararanta, yace "kema kina jina," ta yi bnxa da shi ta ci gaba da kallonta, ba karamin daure ma safeena kae abinda Inteesar ke yi yyi ba, lallai xata yi maganin shegiyar nn nn ba da ddewa ba, Aliyu bae damu da bnxan da inteesar tayi masa ba yace "ke kika xo kika sameta a gidan nn safeena don hka ki sani gaba take da ke a gidan nn, bana son wani tashin hankali a gidana ku kame kanku, kar wanda yyi kishi kaina ban aikesa ba, kowa tasa ta fishshesa," ya juya kan Inteesar "ke kuma fitsararriya ki rike fitsararki, ki sani safeena ta girmeki nesa ba kusa ba, ke din yaushe kika balaga ma kika san me duniya ke ciki, yarinya dake sae shegen rashin kunya ki tambayeta shekararta nawa ta fada maki kiji, u had beta respect ur self coz she's nt ur mate, snn girki as frm nxt wk duk every 2dayz xaku ke yi, bana son tashin hankali a gidana i repeat my self kuyi respectn kanku" Inteesar ta mike tsaye tana gyara daurin dankwalinta ta ja dogon tsaki tace "sannu balagaggu, kuma ba girmata ba har haifata Safeena tayi," tayi masu kallon bnxa xata haura sama ya bita da sauri ta saka gudu amma duk da hka sae da ya kamota ya shaketa yace "uban waye sa'anki a nn," ta fashe da kuka tana kiran Abbanta ya jefar da ita kan kujera yana kallon safeena yace "in ta maki ki gyara mata xama ni na sa ki," xata mike daga kan kujerar yace "in kika tashi sae na watsa maki mari," ganin bbu wasa a tattare da shi yasa ta koma tana kuka, yana kallon Safeena yace "kije ki shirya mu siyo abinda kika ce," murna fal cikinta ganin abinda aka ma Inteesar tace "ni a shirye nake," ya ciro makullin motarsa, ta mike ta bi bayansa suka fice daga gidan tana ma Inteesar wani irin kallo tana jujjuya ido. Basu dawo gidan ba sae kusan karfe sha biyu, inteesar na kwance bayan ta gama cin kukanta har lkcn bata yi bacci ba, muryar safeena taji tana cewa "bby ka bari mu shiga ciki mana don Allah ka bari," cikin kissa take maganar, Inteesar ta mike ba tare da ta shirya ba kuma bata san dalili ba ta shige bathroom ta kulle . Yau safeenah ta cika sati uku gidan Aliyu ko sau daya kallon kirki bae taba hadata da Inteesar da ta xame mata jaraba a gidan ba, gashi ba dama tayi mata ko da kwakkwaran kallon bnxa Aliyu ya hau ta da bala'i don yace mata baya so, ta kyaleta kawae yarinyace kuma yarinta ke damunta, bbu yanda Safeena ta iya don tana mugun son Aliyu kmr rayuwarta duk abinda Inteesar tayi mata sae dae ta gaya masa, wani lkcn ya shareta wani lkcn kuma ya samu Inteesar din ya tsoratata ko kuma ya sa ta kuka, shima ta lura ba a son ransa yake yin hkn ba, ko sau daya Inteesar bata taba shiga kitchen tayi masu girki a gidan ba ko da kuwa ranar girkinta ne sae dae Safeena tayi a bisa umarnin da Aliyu ya bata, don ca yyi ta rabu da ita kawae ta dinga girki kullum, littafin girki kadae ne ke taimakonta don bbu abinda ta iya da ya wuce tafasa ruwan xafi, cikin ikon Allah kuwa idan tayi sae ya dan yi ddi da taimakon littafin, ta adana littafinta ssae, iyaka idan ta fito inteesar ta shiga ta dafa indominta ko taliya, ganin rashin amfaninta a gidan yasa Aliyu ya kai ta da kansa tayi registratn din jamb ana saura sati daya a rufe, kila idan ta fara xuwa makaranta xae samu kwanciyar hankali don bata tsinanasu da komai sae tashin hnkli a gidan, wani lkcn yakan yi mamakin ashe yarinyar nn na da baki hka, kuma fitsarewarta lkci daya da rashin tsoran kirkin da take masa yana mugun basa mamaki shi dae ba wasa da ita yake bare yace kuma tunda ya auri safeena bae nemeta ba, gaba daya ta daina tsoransa sae taga yyi kanta xae doketa ta marairaice masa tana kuka, gashi abu kadan sae ta bara masa baki ta fasa masa ihu a gida ba gaira ba dalili, shi kuma yana kyaleta ne kawae sbda Abbansa don ko kadan Inteesar bata gabansa don bbu abinda Safeena ta rage shi da barin a wajen kwanciya shi yasa yake ji da ita, duk da yakan yi murmushi idan ya tuna 1st nyt dinsu da Inteesar, da yanayin da ya shiga da har yau bae ji hkn gun Safeena ba, darajar da Inteesar ke ci kadae a gunsa knn banda hka da bata isa ta taka masa matarsa da yake ji da ba, Safeena kanta na mamakin yanda Aliyu ke share Inteesar duk da iskancin da take xuba masa, ita bbu abinda yafi daga mata hankali ma irin mugun rainata da Inteesar tayi, amma tasan duk Aliyu ne ya ja mata tunda ga irin tonan asirin da yyi mata washegarin ranar da aka kawo ta gidan, wani lkcn takan yi murmshin takaici tace nasan tanadin da nayi maki yarinya kiyi yanda kike so lkcn ki ne ynxu. Ranar da ya kaita tayi registratn din jamb can ya barota ya bata kudin mota ya wuce office, bata bari adai daita sahun ya shigo da ita layinsu ba ta sauka ta basa kudin don yau tana son ta kare ma anguwar kallo tunda dae ba fita take ba, tana isa bakin gate dinsu taga wata yarinya da baxata wuce ta ba rike da wani kyakkyawan yaro a hannunta tana waya, Inteesar ta dauke kanta ganin sun hada ido, yarinyar tace "sannu fa," inteesar tace "yauwa, ngdd," ta danna bell mai gadi ya bude mata ta shiga, taji yarinyar ta burgeta yar kyakkyawa da ita, safeena na kwance a falo da kawayenta ta wucesu tana yatsine fuska ta haura sama, bayan kwana biyu Aliyu ya hadata da driver taje ganin centre dinta, tana dawowa ta sake haduwa da yarinyar a bakin titi ita ma xata karasa layin da kafa tana rike da danta, bayan sun gaisa Yarinyar tace "amma aure kike a gdan nn ko," Inteesar tayi murmushi tace "eh," yarinayr tace "to ya sunanki," inteesar ta gaya mata yarinyar tace "ni kuma sunana Aneesah," Inteesar tayi murmushi tace "to yaron ki fa," yarinyar tace "sunansa Abdush-shakur," Inteesar ta karbi yaron tana murmushi tace "fyn shakur," har suka isa dai dae gidajensu, yarinyar tace "kina da kyau ssae, ina son mu xama kawaye," inteesar tayi dariya tace "to ai kema kina da kyau," Aneesah ta bata wayanta tace "sa min nmbrki to inteesar," Inteesar tace "wllh wayan mijina ne a hannu na ki bari idan na samu waya," Aneesah tace "to mu shiga kiga gidana mana" inteesar ta xaro ido tace "mai gidanki baya nn," Aneesah tace "A'a a Abuja yake aiki sae wkend yake dawo wa," inteesar ta bi ta suka shiga gidanta, gidane babba kmr nasu bbu abinda ya xama bakonta a gidan don duk suna da shi a nasu gidan, har bedroom ta shiga da Inteesar, inteesar ta shantake suka dinga hira kmr da can sun san juna, ta girka masu abinci ta kawo masu dakin suka ci suna ta hira tana ba Inteesar labarae kala kala, Inteesar taji kmr kar ta bar gidan, karfe shidda saura ta rako Inteesar har bakin gate kmr kar su rabu, har shakur ya saba da Inteesar don har da kukansa, wae sae da ta isa jikin gate tukunna gabanta ya shiga faduwa a xuciyarta tace "Allah yasa ya Aliyu bae dawo ba," mai gadi ya bude mata gate ta shiga taga motarsa a parke a garage xuciyarta yyi mugun bugawa da kyar tana jan kafa ta shiga gidan. Bata tarda kowa cikin falon ba tayi sum sum ta haye sama ta bude kofar dakinta a hankali ta shige, xama tayi kan gado ta sauke ajiyar xuciya, jin an fara kiraye kirayen sllh Mahgrib yasa ta mike ta tashiga cire kayan jikinta xata dauki xani ta daura ta shiga wanka don bata sllh taji an bude kofar dakinta, ta tsorata ssae tace "wayyoo Abbana," ta durkushe da sauri tana kare kirjinta da hannunta don undies kadae ne jikinta, ya karaso cikin dakin yana kallonta yace "daga ina kike," taki cewa komai kuma taki dago kanta tana durkushe inda take, ya karasa gabanta ya dago ta ta shiga nonnokewa a tsorace tace "wayyo ya Aliyu ban sa kaya ba," ko kulata bae yi ba ya jinginar da ita jikin bango yana mata wani irin kallo nn da nn yanayinsa ya canxa, duk ta tsure tana son durkusawa yaki barinta ta fashe masa da kuka, ya sauke ajiyar xuciya ya sake ta ya fice daga dakin ta tajawo xaninta da sauri ta shiga wanka, tana fitowa ta gama shafe shafenta ta saka kayan baccinta, ta saka gashinta cikin net ta fita dafa indominta, xaune ta tarda Aliyu a falo safeena na jingine jikinsa suna kallo, ya bi ta da kallo har ta wuce su tana tabe baki ta isa kusa da fridge ta dauki five alive ta bude ta sha ta rufe ta mayar da sauran don bbu mai shan five alive a gidan sae ita, ta juya ta watsa masu harara ta shige kitchen yin abinda ya sauko da ita ya mike da sauri safeena na tambayarsa inda xa sa bae kulata ba ya haura sama ya shiga dakinsa bae dau lkci ba ya fito rike da kwayoyi har uku a hannunsa, bae bari safeena ta lura da komai ba ya shiga kitchen Inteesar na duke cikinta ya hanata sakat, ta mike da sauri ta koma baya a tsorace, bae ko kalleta ba ya dauki cup ya fice, ta dan yi tsaki ta bude tukunyar indomienta tana dubawa, yana fita falo yyi hanyar fridge safeena sae binsa take da kallo, ya juya mata baya ya ciro drink din five alive din da inteesar ta bude ta sha ya xuba kwayoyin a ciki ya rufe ya mayar ya ajiye snn ya fito da hollandia yogurt ya xuba a cup din da ya dauko a kitchen ya rufe ya mayar da sauran a fridge snn ya dawo falo ya xauna gefen safeena yana shan hollandia yoghurt dinsa, Safeena tace "ae da kayi magana na kawo maka shine ka ba kanka wahala," yace "bana son ki ba kanki wahala ne," bata sake cewa komai ba ta kwanta jikinsa tana shafa shi, shi dae idonsa na kan Tv ganin irin abinda take masa yasa ya hade rae yace "stop it am nt in d mood," tayi shiru bata ce komai ba amma bata ji ddin hkn ba don tana jin ddin Aliyu ya iya sa mace ta manta hanyar gidansu gashi yau a matse take, Inteesar ta fito daga kitchen rike da plate din indomienta ya juya yana kallonta har ta isa kusa da fridge ta bude ta ciro Five alive dinta a xuciyarta tana cewa ni da cikina ma ke ciwo, ta dan tabe baki ta rufe fridge din, juyawar da xata yi suka hada ido da Aliyu ya kauda kansa da sauri ta tabe baki ta haura sama, ya sauke ajiyar xuciya har safeena na tambayarsa lfya, bae tanka mata ba yana ta kallonsa har kusan karfe sha daya snn ya mike yana kallonta yace "xanje in kwanta sae da safe," ya haura sama ya bar ta nn xaune, tasan tunda bae nemeta ba yau idan ta kai kanta walakanta ta xae yi, don hka sum sum ta mike ranta bae so hkn ba don tana bukatansa yau ta shige dakinta ranta a bace. Shi kam yana haurawa sama dakinsa ya shiga ya hada coffee yasha don shi mayen coffee ne, snn yyi wanka ya canxa xuwa nyt wears dinsa ya bude kofar dakinsa yyi hanyar dakin Inteesar, xaune ya tarda ta a dakin ta jinginar da kanta jikin gado idonta a lumshe, ya karasa gabanta ya durkusa yana kallonta, ta bude idonta da ya kada yyi jajur a hankali tana kallonsa. . Aliyu yyi murmushi yana kallon cikin idonta ya daura goshinsa kan nata har tana iya jiyo numfashinsa a fuskarta ta lumshe idonta ya dagota ya xaunar da ita kan gado ya dago kanta yana kallonta, a hankali kmr mai rada yace "kina bukatan wani abu ne," kin cewa komai tayi ta koma can tsakiyar gado xata kwanta, bae hanata ba ya barta tayi kwanciyarta snn ya dawo gefenta yana shafa fuskarta yace "to yau baki tsorona" idonta lumshe bata ce komai ba ya dagota ya rungumeta ya shiga kissn din wuyanta yana shafata, da kyar ta turasa muryar ta can kasa tace "ka bari," shima murya can kasa yace "shkkn tunda ba kya so," ya sake ta ya mike ta rikosa da sauri ta fashe masa da kuka, ya rungumeta cikin rada yace "to duk me nayi maki kiyi mani ke ma," xata yi magana ya daura bakinsa kan nata a hankali yace "kiss me," ta lumshe idonta ta shiga kissn dinsa, he could'nt belive it, ya kankameta, ta dauke bakinta daga nasa tana mayar da numfashi kmr xata yi kuka, a hankali ya shiga cire mata kayan baccin jikinta yana kissn dinta, ya shiga romancin dinta kmr xae hadiyeta ita ma lkci lkci takan mayar masa da martani ganin yana neman xautar da ita gaba daya yasa ta kankamesa tana mayar da numfashi tace "plsss" bae tanka ta ba har sae da yaga ta fara kuka snn ya shiga rabata da sauran kayan jikinta, turata yyi ba tare da ya shirya ba, ya fada gefen gado yyi rub da ciki yana mayar da numfashi ta fada kansa tace "no, plss ya Aliyu," duk ta xama kmr wata mara hankali, da kyar ya dago ya rungumota murya can kasa yace "u re nt clean," ta rikesa tana girgixa masa kai tana hawaye ta kasa cewa komai sae mayar da numfashi da take, ya mike da kyar ya fice daga dakin, ta fada kan gado tana kuka a hankali tunda take bata taba shiga irin yanayin da ta shiga ranan ba, ta ma rasa meke damunta kawae, wnn abun dae da take mugun tsoro yau taji take mugun bukata kmr xata yi hauka, ta rasa inda xata sa ranta, ta dukunkune waje daya kmr mai jin sanyi, Aliyu ya bude dakin ya shigo ya karasa kusa da gadon rike da kofi a hannunsa ya dago ta, ta fada kansa tana kuka tace "don Allah ya Aliyu," ya kai mata kofin baki ta dauke kanta da sauri yace "magani ne" ta maida kanta jikinta na rawa ta shiga shan abinda ke kofi, ruwan lime ne, sae da ya tabbatar ta shanye snn ya kwantar da ita ya lulluba mata bargo ta xama kmr wata mara lfya, yaji tausayinta ssae gashi har uku ya xuba mata, da kyar ta samu bacci ya dauketa, snn ya mike ya dauki juice din ya shiga bathroom ya xubar ya fice daga dakin, dakin Safeena ya shiga ya biya bukatansa. Da safe tana wanka ya shigo dakin, ta kasa fitowa daga bathroom din duk da ta gama wani mugun kunyarsa take ji, to wae jiya wani jaraban ne ya sameta ita kam, tunda take bata taba experiance din abinda taji jiya ba, ya gaji da xamansa a dakin ya fice duk da yasan ta gama wankan fitowa ne kadae baxata yi ba gashi ta sa key, yana fita ta fito da sauri ta kulle dakinta da key, tana shiryawa gaban madubi taji muryarsa da safeena can kasa, ta mike da sauri ta bude curtain din window tana kallonsu, tana sanye da wasu shegun matsatsun kaya, ya bude mata mota ta shiga ya xaga shima ya shiga snn ya ja motar suka bar gidan, ta sake labulen ta koma gaban madubinta amma ta samu kanta da kasa yin komai kuma, ta mike ta koma kan gado tayi kwanciyarta tare da lumshe ido, har rana basu dawo ba, hkn yasa ta mike ta dauki Hijab dinta tasa snn ta sa takalminta ta fice daga gidan, mai gadi yace "ina xa ki," tace "bae gaya maka inda da exams yau ba," ya bude mata gate din ta fice tayi gidan Aneesah. . Aneesah tayi farin cikin ganinta ssae ta kai ta har bedroom ranar ma , snn ta kawo mata lemo, Aneesah tace "to ni yaushe kike son na shigo gidan ki kawas," Inteesar ta tabe baki tace "ae ni ba ni kadae bace, ni da kishiyata ce," Aneesah ta yo waje da ido tace "da gske, ke ce ta farko ko ta biyu," Inteesar tace "ta farko," Aneesah ta bude baki tace "shekaranku nawa da auren? Ko don baki haihu bne har ynxu," Inteesar tayi murmushi tace "watanmu biyar knn da aure," Aneesah ta dafata da mamaki tace "kai Inteesar, to dama ba auren soyayya kuka yi bne ko kuwa kinsan ba ke kadai bace," Inteesar tace "kusan auren xumunci aka mana, baya sona bana sonsa," Aneesah tayi shiru tana kallonta snn ta sauke ajiyar xuciya tace "ke xaki koya masa sonki Inteesar namiji fa wawa ne cikin lkci kalilan xaki ga kin mallake abunki sae kace ba mace ba Inteesar," Inteesar ta tabe baki tace "tabdi me xanyi da shi, hanyar jirgi daban ta mota daban, baya shiga harkata bana shiga tasa," Aneesah tace "to amma kuna plannin ne ko," Inteesar tace "kinga ni ki rabu dani da hirar nn, ina shakur?" ba don ran Aneesah ya so ba suka bar xancen suka kama wani hirar, ranar ma a gidan ta ci abincin rana, bata bar gidan ba sae kusan karfe shidda ta shiga ta tarar sun dawo, safeena na kitchen da dan littafinta da take boyewa tana hada masu girki shi kuma yana xaune falo yana kallo, ta hade rae xata wuce sama ya daka mata wani mugun tsawa da ya raxanata ta tsaya daga inda take tana masa mugun kallo ya mike ya karasa kusa da ita fuskarsa daure yace "daga gidan ubanwa kike," ta tabe baki tace "aikena kayi to," bata rufe baki ba ya watsa mata mari ta fasa ihu ta durkushe wajen tana kiran Abba, safeena ta leko tace "haba cweety nace ka rabu da ita yarinya ce bata san ciwon kanta ba tukun yarinta na damunta, meye kuma na dukanta, nasiha ya kamata kayi mata dear," Inteesar ta mike tana kuka tace "don uwarki sae ki xo kiyi min nasihar munafuka kawae jaka" yyi kanta ta fasa wani ihun ta saka gudu ta bar wajen ta haura sama tana ci gaba da rusa kuka kmr xata tsaga gidan, ranar hka taci kukanta ta koshi bbu mai lallashi ta gaji ta kwanta tayi bacci ba tare da ta ci abincin dare ba, karfe goma ya shiga dakin nata, ko wanka bata yi ba bare ta canxa kayanta karewarta ma kasa tayi kwanciyarta, ya daga ta ya cire hijabin jikinta snn ya mayar da ita kan gado yana kallon fuskarta, ya lulluba mata bargo ya kashe mata wutan dakin ya fita. Washegari kin fitowa tayi daga dakinta tana ta xaune har axahar bata karya ba, ya shigo dakin ya tarar da ita xaune kan darduma ta idar da sllh, ta mike ta shige bathroom ta bar sa nn tsaye, yyi tsaki ya fice daga dakin, ranar ma hka suka fita suka barta ita kadae a gidan, taci kukanta ta fito ganin yunwa na neman hallakata ta nemi abinda xata ci, har da na dare ta tanada don ba fitowa xata sake yi ba, Ana gobe xata je ta xana jamb dinta tun safe take ta karatu har kusan sha biyu bata karya ba, ta rufe biology text book din dake hannunta ta fito xuwa falo don neman abinda xata ci a xuciyarta tana cewa inda wnn mutumin kirki ne da ba shi xae koya min abubuwan da na manta a chemistry ba, tayi tsaki ta shiga kitchen ta tarar safeena ta daura girki amma bata kitchen din littafin da take amfani da tana koyan girki na kitchen din a ajiye da alamar tuwon shinkafa da miyar egusi xata yi ganin irin kayan miyan da aka jera a kitchen din ko wanne a cikin dan plate, inteesar ta girgixa kai tace "dakikiya kawae ynxu ina dauke littafin nn bbu abinda xata iya yi a nn," xata daura indomie kawae wata xuciyar tace ta dauke littafin kawae ta boye, ba shiri ta dauke littafin ta ma fasa girkin gaba daya ta fice da sauri ta haura sama a stairs suka hadu da safeena, safeena tayi mata wani kallon banxa tana karairaya, inteesar tayi dariya can ciki ciki a xuciyarta tace "i jez dey laf," ta shige dakinta, safeena na shiga kitchen ta nemi littafi ta rasa ta fito da sauri ta koma sama ta buga kofar dakin inteesar, inteesar ta fito tana gyara daurin dankwalinta a walakance tace "lafiya," safeena tayi mata mugun kallo tace "maxa fito min da kayana kar na nakada maki shegen duka a nn," inteesar tayi dariya tace "meye kuma kayanki," safeena na huci ta kasa cewa komai don wnn ae abun kunya ne a gunta anata tunanin, inteesar tayi tsaki tana yatsine fuska xata rufe kofar safeena ta fixgota ta kai mata mari, ta fasa ihu tace "wayyoo Abbana, wlh sae na rama," safeena ta kai mata wani marin, inteesar ta fasa wani kukan tace "don uwarki me nayi maki xaki dokeni, bnxa kawae dakikiya, karuwa da ke," Safeena tayo waje da ido tace "ni kike ce ma karuwa," Inteesar tace "ance maki din karuwa yar iska, uban waye bae san kinyi karuwanci ba," tayi kan Inteesar ta rufeta da duka dai dai nn Aliyu ya shigo gidan, ya haura sama da sauri da mamaki yana kallonsu ya fixge Safeena a fusace yace "ke jakar wace gari ce" tana huci tace "karuwa fa tace min Aliyu," ya watsa mata mari yace "ta ce maki din, sharri tayi maki, ko bakiyi karuwancin bane. Safeena ta bude baki da mamaki tana kallon Aliyu, cikin tsawa yace "get out kar na taka ki a nn, don uwarki idan kika ji mata ciwo kice baki sani ba ko me? Yar ki ce xaki kamata da duka hka ko sharri tayi maki" tsui tsui Inteesar ta bude dakinta a hankali ta shige tasa key, Safeena da hawaye ya gama wanke mata fuska don takaici ta kasa cewa komai ta juya ta bude dakinta ta shige da sauri, yyi tsaki ya bude dakinsa shi ma ya shiga, dariya Inteesar ta dinga yi kmr wata tababbiya a daki, kai Aliyu bae yi ba ko ke wacece ya disga ki gaban kowa ba komai bane a gurinsa, girkin da Inteesar bata yi ba knn ta ci gaba da karatunta da ta tuna abinda ya faru sae ta fashe da dariya, Safeena kam xamanta tayi a daki bayan ta kira uwarta ta gaya mata abunda ya faru girki kam ta fasa shi har taje takashe gas din ta komo sama, tana xaune tana naxarin abinda uwarta ta gama gaya mata tana murmushin mugunta Aliyu ya shigo dakin ta dauke kanta ya karaso kusa da ita ya xauna yana kallonta cikin lallami yace "haba bbyna, meyasa xaki kulata bayan nace ki daina, i've told yhu times wit out nmbr yarinyar nn ba ishasshen hankali gareta ba wllh, ni kaina tsoro take bani" Safeena ta mike a fusace tace "dnt tell me dat Aliyu, ynxu so nake kawae ka tashi ka maidani gidanmu," ya mike ya kamo hannunta yace "haba safeena wllh ina sonki kema kin san da hka, dukan yarinyar nn da kika yi ynxu baki san xae iya xaman min jaraba ba,"xata yi magana ya saka bakinsa cikin nata ya shiga kissin dinta ya dago kanta yana kallonta yace "yhu knw i luv yhu dear, ki bari ynxu xanje in mata magana," ya xaunar da ita ya fice daga dakin ta bi shi da kallo, ita kam Allah ya daura mata son Aliyu, tayi shiru xuciyarta na tafarfasa tanatunanin abinda xata yi masa taji ddi yau, ta sauke ajiyar xuciya tace "xanyi maganinka kuwa yau," shi kam yana fitaya buga kofar dakin Inteesar ta mike da sauri duk da tasan waye tace "waye," yace "ni kike tambayr waye," tayi tsaki ta koma tayi kwanciyarta, yyi shiru yana kallon kofar snn yyi kwafa ya shiga dakinsa. Ganin mugun yunwan da take ji yasa inteesar ta bude kofar a hankali ta fita xuwa falo, kitchen ta tarda shi tsaye shima yana hada tea ta juya da sauri xata koma ya fixgota, tace "wayyoo ni ka kyaleni," ya cakumota yace "ke kince kunnen kashi gare ki ko?" ta bata rae kmr xata yi kuka tace "ni ka kyaleni" yyi kwafa ya saketa yace "ni nasan maganinki," snn ya fice, itama tean ta hada taxo ta wucesa a falo tana takunta mai jan hankali ya bita da kallo, a dae dae stairs ta hadu da safeena, ta wuceta da sauri kmr mara gskya, safeena dae bata ce mata komai ba ta sauko kasa. Ganin ba girki safeena xata yi ba kuma yasan yyi mata laifi yasa Aliyu ya fita ya siyo masu abinci da daddare, bata nuna masa komai ba ta xauna suka ci abincin bayan ya kaima Inteesar nata, karfe tara tace masa xata je tayi wanka ta barsa nn falo ta haura sama sae da ta fara shiga dakinsa ta bude drawer dinsa ta dauki kwalin wani magani ta cire pills har guda hudu tana murmushi sanin ko na menene ta fice daga dakin ta shiga nata, tana jin ya bude dakinsa ta fito daga nata dakin da sauri ta shiga nasa yace "shine kika bar ni ni daya a falo ko bbyna," ta danyi murmushi bata ce komai ba ta xauna gefensa, ta kalli agogo tace "yau baxa ka sha coffee ba bby," ya duba agogo karfe sha daya saura yace "to kawo min dear," ta mike tana rangwada da shegun kayan baccin dake jikinta tace "ok bby," snn ta fita daga dakin, tana gama hada coffee din ta watsa kwayoyin dake hannunta a ciki tana murmushi ta koma sama ta kai masa, ya karba ya ajiye yace "tnks dear bari sae nayi wanka," tayi kwanciyarta kan gado ya mike ya shiga bathroom yin wanka, tana nn kwance ya fito yyi shirin kwanciya snn ya jawo system ya dan yi danne dannensa snn ya dauki coffee din ya fara sha, sae satan kallonsa safeena take ta gefen ido, a hankali ya dinga shan coffeen har ya shanye ya ajiye cup din, snn yyi rub da cik kan gadon ya kwanta tare da lumshe idonsa, tana ta kallonsa har na kusan minti talatin snn taga ya mike da kyar ya dawo gefenta ya kwanta ya jawota jikinsa, bata hanasa ba ya shiga shafata yana kissn wuyarta, ta fara mayar masa da martani itama, sae da ta bari ya gama ficewa hayyacinsa gaba daya ya xama kaman wani mashayi har wani rawa jikinsa yake yana neman fara aiki snn ta turasa da karfi tace "me kuma xaka yi da karuwa banda abinka," ya kankameta kmr wani tababbe yace "no plss kar kiyi min hka safeena, plsss," tayi dariya ta turasa da karfi ta mike ta saka kayanta tace "aa . . Duk yanda Aliyu ya so Safeenah ta basa hadin kai kememe taki yarda da shi sae dariya take ta tana masa kallon rainin wayo tace "kaje gun warce ba karuwa ba, ni kam karuwace," tunda ta shigo gidan dama ta lura da bbu abinda ke shiga tsakaninsa da Inteesar don kullum ita kadae ke kwana dakinsa sae randa baya bukatarta ne xae hade rae yace tana damunsa ta koma nata dakin, kuma shi da bakinsa ya taba gaya mata baya forcin mace ta kwanta da shi, komin nacinsa gwara ya hakura kuma ta lura da gskya yake fada mata ba karya ba, ta mike tsaye tana karairaye tana kallonsa tace "gud nyt dear," snn ta fice xuciyarta fari tas ae sae dae ya mutu yau, binta kawae yake da kallo ya ma rasa abinda xae ce mata ya mike xaune da kyar ya dafe kansa yana kiran Allah a xuciyarsa, shi daya kadae yasan yanda yake ji a jikinsa, ya ma rasa wani tunanin xae yi, inteesar ta fado masa ya girgixa kai sanin halinta ya koma kan gado ya kwanta yana mayar da numfashi, tsam ya mike kmr wanda aka tsikara ya fice daga dakin ganin yana neman hallaka kansa yyi hanyar dakin Inteesar, tana xaune gefen gado ta kunna bedside lamp chemistry textbook a hannunta tana karatu don gobe xata xana jamb, ta mike da sauri jin an bude kofar dakinta, ta koma da sauri ta xauna ganin Aliyu don dan karamin kayan bacci ne jikinta, gani tayi ya xube tsakiyar dakin, ta mike tsaye da sauri ta dauki xaninta ta daura ta karasa gabansa da sauri ta durkusa tana kallonsa da mamaki, a durkushe kansa yake, nn da nn ta rude kmr xata yi kuka tace "me ya faru ya Aliyu," ya dago da kyar ya riketa, idonsa ya kada yyi jajur da kyar yace "fateema don Allah kar kice kina tsorona yau, i beg u plss ki tausaya min," ta yo waje da ido a tsorace ta mike da sauri xata bar wajen yyi hanxarin fixgota ta fado kansa ya rungumeta yana mata wani irin kallo, kuka ta fashe da a rude tace "na shiga uku, don Allah ka sakeni bana so," muryarsa na rawa yace "baki tausayina fateema," cikin kuka tace "wllh wllh tsoro nake ji ya Aliyu kayi hakuri," ya mike da kyar ya fada kan gadonta ta mike tsaye ita ma ta bisa tana kuka xata yi magana ya jawo ta jikinsa yace "kar ki ce min komai fateema, taimakona xaki yi," bae jira tace komai ba ya shiga rabata da kayanta, duk da rawan da jikinta ya fara yi kmr ana kada gangi bata hanasa ba amma kuka ssae take, ganin da gske ashe yake yasa ta fasa ihu ya toshe bakinta da sauri ta shiga turasa a gigice tana cewa "wayyoo wlh bana so ka bari don Allah nake rokanka baxan iya ba," kuka take kmr ranta xae fita, ya saketa yana mayar da numfashi taga ya mike da sauri yyi hanyar bathroom a nn bakin kofa ya xube kasa ya kasa karasawa ciki, ta mike da sauri ta dawo kusa da shi jikinta na rawa tana kuka tace "kayi hakuri ya Aliyu, gani baxan sake maka kukan ba," cikin tashin hankali take maganar, ya rungumota ta runtse idonta da sauri jikinta na ci gaba da rawa, bata sake hanasa yi mata komai ba kuma tayi kkrin hadiye kukan da take sae ajiyar xuciya, ranar ta ci axaba wajen Aliyu, don bata ga bambancinsa da ranar da ya fara saninta ba, tayi kuka tayi rokan amma Aliyu bae sarara mata ba bae ma san tana yi ba, ya wahalar da ita ssae ba kadan ba, bae kyaleta ba sae da yaga numfashinta na neman daukewa, ya kankameta duk ya rikice mata yana kiran sunanta, sun fi minti goma a hka snn yyi namijin kkrin daga ta ya mayar kan gado, kuka take don tsabar axaba muryarta ma bae fitowa, duk ya rasa yanda xae yi da ita, ya rungumeta abun tausayi ya shiga lallashinta yana bata hakuri, ajiyar xuciya kawae take tana kwance kan kirjinsa duk ta wani langwabe don wahala nn da nn jikinta ya dau xafi, wanka ya fara yi mata snn ya bata magani ta sha, ya kwantar da ita kan gado daga nn bacci ya dauketa wajajen karfe hudu na Asuba. . Da kyar Aliyu ya iya tashi yyi sllhn Asuba, shima duk baya jin ddin jikinsa, har lkcn bacci Inteesar take ya dawo gefenta ya xauna yana kallonta cike da tausayinta, a hankali ya shiga tada ta, ta bude idonta da ya kumbura don kuka a hankali tana kallonsa yace "tashi kiyi sllh, xa ki iya?" ta kauda kanta da sauri bata ce komai ba snn ta mike xaune, ya daura hannunsa a goshinta yaji da xafi, yace "xa ki iya kuwa," bata ce masa komai ba ta mike da kyar gabanta na faduwa ko xata ji irin abinda taji wancan ranar amma bata ji ba sae jiri kawae da take gani ta shiga bayin ya bita da kallo, yana nn xaune ta fito ta fara sllh, tana idarwa, ya dawo kasa kusa da ita ya xauna yana kallonta ta sunkuyar da kanta, yyi murmushi yace "mrning," ta hade rae ta mike xata bar wajen tayi baya xata fadi yyi saurin rikota ya karasa da ita kan gadon ya kwantar da ita, kuka ta shiga yi a hankali ya kwanta gefenta yana kallonta yace "ki fada min gskya fateema, jiya kin ji xafi ne," ta dago kai tana kallonsa don takaici ma kawae sae ta fashe masa da kuka ya dagata suka mike xaune yace "ni bance kiyi min kuka ba," ta turasa cikin kuka ssae tace "tambayata ma kke ko, to wlh daga yau ka sake min irin hka sae na gaya ka da inna" ya rungumeta yana murmushi, ta dinga kuka har da shessheka, a hankali yace "sae kice ma inna nayi maki me," taki cewa komai sae dae har lkcn kuka take, ya kwantar da ita ya rufa mata bargo yace kiyi baccinki, ya koma daya side din ya xauna, nn da nn bacci ya dauketa, yana nn xaune har kusan karfe takwas, yaga ta xabura ta mike xaune ya juya da sauri yana kallonta, ta kalli agogo ta mike tsaye da sauri tayi baya xata fadi ya mike da sauri kan ya karasa kusa da ita har ta buge da bango ta fadi kasa, ta fashe da kuka ya durkushe gabanta da sauri ya dagota, jikinta yyi xafi ssae, ya xaunar da ita kan gado yace "to da ina xaki," tana kallon agogo tace "yau ne exams dina," yyi shiru yana kallonta yace "xaki iya," ta tsaya kallonsa snn tace "kmr ya," yace "naga baki jin ddi ki bari nxt yr kawae, kmr gobe..." bata gama sauraran abinda xae ce ba ta mike ta shige bathroom abinta tana daddafa bango, yana nn xaune ta fito ta shirya, yace "break fst fa," tana rike da chemistry dinta da kyar tace "tea xan sha kawae," ta gane xaxxabi ne ke neman rufeta, da kansa ya hada mata tean ya bata, ta shiga sha, har ta sha rabi ta ajiye sauran snn a hankali tana nuna masa wani calculatn a chemistry textbuk dinta tace "ni na manta wnn formula din," ya karba yana kallo abinda take nuna masa, ya dauki takardar da take calculatns jiya ya shiga solve din mata questn din yana mata explanatn, wai daga kan da xae yi sae ganin ta yyi ta jingina jikin gado tana bacci, yyi shiru yana kallonta, yasan jiya kam bata samu baccin kirki ba, a hankali yace "fateema," ta bude ido da sauri tana kallonsa tace "kace me," yace "ki bari nxt tym kiyi jamb," kmr xata yi kuka tace "ni ka kyaleni, idan baxa ka koya min ba in tashi in tafi," ya daga kafada ya shiga koya mata har ya gama yace kin gane tace eh, ta mike ta sa Hijab dinta ya bi bayanta, sae da ya fara shiga daki ya dauki makullin motarsa snn ya fito ya bude mata motar ta shiga shima ya xaga ya shiga suka bar gidan, hka ta dinga bacci a motar har suka isa, yace "ke baki jin magana nace ki bari wani yr din, ki ci gaba da islamiyya kin ki ko," ko kallonsa bata yi ba ta bude motar xata fita ya mika mata dubu biyu yace xan xo daukarki anjima, snn ya ja motarsa ya wuce, ita kuma ta shiga ciki. A daddafe ta gama exams din don xaxxabi ne ssae ya rufeta, ta fito ta nemi guri ta xauna tana jiransa, jiran minti talatin tayi masa taga bae xo ba ta tsayar da tricycle ta hau abinta ta wuce gida, ko da ta isa gidan bata tarda kowa ba mai gadi yace mata sun fita shi da Safeena, ta tabe baki ta koma ciki tayi kwanciyarta, sae kusan yamma xaxxabin ya sake ta ta sauko kitchen ta dafa indomie ta koma sama abunta ta ci, ba su suka shigo gidan ba sae kusan karfe goma na dare, ya shigo dakin yana kallonta yace "srry fa, mamar Safeena ce bata da lfya shine muka je gidan," ta ja dogon tsaki ko kallonsa bata yi ba ta mike ta bude bathroom ta shige ta barsa nn tsaye, yyi kwafa ya fice kawae. Bayan kwana biyu aka turo mata da scores dinta na Jamb, ya isa har yyi yawa ta karanta Medicine abunta, a falo take gaya masa ranar yyi mata mugun kallo yace "ke ce xaki iya wani karanta Medicine salon na bata kudi na kawae, wae an gaya maki cin tuwo ne," ta galla masa harara tace "to ina ruwanka ka shiga kwakwalwata ne?," ya mike tsaye yana kallonta yace "xan fa babbalaki wataran a gidan nn yarinyar nn," tayi tsaki ta juya ta koma sama tana cewa "ni wllh abba xanje na gaya ka da abba, ina ruwanka da abinda xan karanta, kai wa ya hanaka karanta medicine" Safeena da aka siyo sabon takardar koyon girki ana kitchen ana girki tace "sae hakuri dear, ta xata wasan yara ne medicine din Honey," yana hararanta yace "ke kuma wa yasa bakinki a nan, Bayan sati daya inteesar na kwance ita kadae a daki wajen karfe sha biyu na rana, safeena ma na dakinta waka sae tashi yake kmr xae tsaga gidan, Aliyu ya fita aiki, inteesar ta gaji da kide kiden da safeena ke sa wa gashi ba daman tayi mata magana ta ci ubanta Aliyu baya nn, ta mike ta dauki Hijab dinta ta fita daga gidan, mai gadi yace "oga yace kar na bari kowa ya fita," ta yi shiru tana kallonsa kmr ta shakesa, can dae tace "bae ce maka xan je duba jarabawa bne," mai gadi yace "aa ni bae ce min hka ba," ta galla masa harara ta isa kusa da gate din tace "to sae ka kirasa kaji," ta bude gate din ta fice daga gidan, gidan Aneesah ta shiga, ta tarar tana ta karatun littafin hausa, taji ddin ganin Inteesar ssae tace "kwana da yawa 'yar uwa ina kikaboye gashi ba daman na shiga gidanku,"inteesar tayi dariya tace "ina nn ke dae, ba nace maki xan xana jamb ba," Aneesah tace "ohh hka fa ya scores yyi kyau?" inteesar tace "ehh wllh, shakur fa," Aneesah tace "yana bacci wllh, wae meye sirrin yan mata naga kin kara kyau kinyi haske" Inteesar ta harareta tace "ban fa son cin fuska," Aneesah tayi dariya ssae tace "wllh kuwa da gske, baki duba kanki a madubi ne? ko dae...." inteesarta tabe baki tace "ko dae me," Aneesah tayi dariya tace "oho," ta mike ta kawo mata ruwa da lemo, nn suka dinga hirar rayuwa, ganin Aneesah bata boye mata komai game da rayuwarta yasa inteesar ta bata lbrin nata rayuwan tun bata yi aure ba har ixuwa aurenta da Aliyu, da irin xaman da suke da shi har ya auro safeena, Aneesah tace "tab lallai ba shi da mutunci, kuma Abba bae kyauta maki ba da yyi maki hka da ma Haisam din ne, ke ma da naki ae, taya xaki dinga shiru kina cutar kanki inteesar, na tabbatar da tuni kin gaya Abba irin xaman da kuke da ya raba ku ynxu wllh, to wae ma don me baki son na shiga gidan naku sbda wata safeena, tsoranta kike ko me, shi kuma Aliyun ba kiyi niyar gyara masa xama bne wllh, tab," Aneesah tayi kwafa taji kmr ita ce Inteesar, inteesar tayi murmushi tace "to mu je gidan namu ynxu, ae ya fita office," Aneesah ta mike kmr jira take tace "bari na dauko Hijab," ta wuce sama Inteesar ta bi ta da kallo tana murmushi, ba ajima ba ta sauko sanye da Hijab tana rike da Shakur da kwalban turare a hannunta, ta mika ma Inteesar tace "mum dita ce ta aiko min da turaren nn na dibar maki yana da kyau ssae wlh," Inteesar ta karba tayi mata gdya suka fita daga gidan, inteesar ta danna bell mai gadi ya bude masu gate suka shiga, xaune suka tarar da Safeena da uwarta a falo ta cika ta da kayan drinks da nama sae hira suke suna shewa kmr kawaye, safeena ta bi Aneesah da kallo hka ma uwarta dake kallon inteesar cike da tsana, Aneesah tace "kai amma falonki babba ne Inteesar, nake ga kmr ma yafi nawa," inteesar tayi dariya tace "kai Aneesah kallon tsoro dae kika ma falon nawa," safeena ta mike tana hararan Inteesar tace "falonki? Amma ke jaka ce da kika yi wnn tunanin uban wa ya baki falo," Hajiyarta ta mike tace "wllh kin ban mamaki safeena da har xaki iya xama yarinya karama ta raina ki hka, yaushe kika yi laushi hka safeena, dubi fa kallon da take maki," inteesar tace "to falonki kike son nace da, ni dae naga ko gaban mai gidan kika kira nn da falonki wllh gwale ki xae yi, dama kun saba, ni ko sae na fadi hkn ya xauna" Aneesah ta fashe da dariya, inteesar tace "Atoh ae gskya ne Aneesah, jiya fa daga tace kofarta ya fara samun matsala ya hauta da masifa kmr xae maketa wae ta shigo masa da kofa gidansa ne da xata ce kofarta, bare wnn mae gaba daya wae falonta" dariya Aneesah ta dinga yi ssae, safeena tayi kan Inteesar ta haura sama da sauri ta bar Aneesah nn tsaye, safeena ta cakumi Aneesah tana huci tace "don ubanki me ya shigo dake gidan nn," Aneesah ta ajiye shakur ta watsa mata mari tace "meye hadina dake don uwarki da xaki rikeni hka," haba kan kace komai fada ya kaure tsakaninsu, inteesar ta kasa saukowa don shegen tsoro, da kyar tayi shahada ta sauko ganin dambe suke ssae, safeena dake cin uwarta hannun Aneesah ta fixgo inteesar, uwarta ma ta taho da gudu xata sa hannu Aneesah ta jefar da ita gefe daya ji kke rigijib a kasa, nn inteesar da Aneesah suka hadu suka nakada ma Safeena shegen duka sae ihu take shakur ma na ihu, sae da suka mata laga laga snn inteesar ta ja Aneesah suka haura sama rike da shakur ganin uwar safeena tayi kitchen da gudu, inteesar ta saka key a kofar bayan sun shiga. Ihu safeena ta dinga rusawa a gidan ta dauki wayarta ta kira kawayenta gaba daya su xo wae sae sun kashe Aneesah yau, ita kuma inteesar mijinta baxae ganeta ba, inteesar duk ta tsorata ganin kawayen safeena na ta shigowa gidan, Aneesah kam ko a jikinta, suka dinga bubbuga kofar kmr xasu cireta, inteesar kuka shakur kuka, Aneesah tace "kin ban mamaki wllh inteesar meye abun tsoro a kishiya, ba dole ta maida ki yar ta ba tayi ta duka taga kina tsoranta," inteesar tana goge hawayenta tace "to ko na kira ya Aliyu ne wllh cire kofar xa suyi," ta fashe da kuka tana neman wayar Aliyu dake wajenta. . Inteesar tadauki wayar jikinta na rawa ta shiga kiran Aliyu, dontsabar takaici Aneesah kasa daukar Shakur dake ta tsala ihu tayi, sae kallon Inteesar take kmr ta maketa, Aliyu na daga wayar ta fashe masa da kuka, ya mike tsaye da sauri yace "me ya faru," cikinkuka tace "ko ba Safeena bace wae xata kasheni ta kira kawayenta da yawa a gidan har da mamarta gasu nn xasu cire kofar wae su kasheni," Aneesah ta girgixa kai cike da takaici ta kinkimi danta tayi hanyar kofa xata fita da gudu inteesar ta karasa kusa da kofar ta rikota tace "wayyo so kike su kashemu, don Allah ki bari ya dawo," da sauri inteesar ta cire makullin, Aneesah ta ma rasa me xata ce mata, su safeena har lkcn basu fasa buga kofar da suke suna xage xage ba, Aneesah ta shiga mayar masu ita ma, hka suka dinga xage xage ta uwa ta uba, sum sum inteesar tayi jikin window har lkcn a tsorace take ta tsaya tana jiran shigowar Aliyu, ko minti sha biyar ba ayi ba ya shigo gidan da motarsa, tayi gun Aneesah da ke ji kmr ta cire kofar ta fita suyi ta takare tace "Aneesah ya dawo," Aneesah ta galla mata harara tace "da'allah ja can kin ban waje, kin ban mamaki inteesar," Aliyu ya hauro sama yana kallon safeena da kawayenta kusan su biyar uwarta ma na tsaye cikinsu, wani mugun tsawa ya daka ma kawayen nata yace "b4 d count of 3 duk ku fice min a gida kar na sa a kulle min ku karuwan bnxa kawae yan iska nn din gidan ubanku ne ko na uwarku, kaji min bitches " tuni jikin safeena ya dau rawa, kawayen nata kuwa sum sum suka shiga sauka kasa yana binsu da kallo yana huci, ko kallon uwar safeenar bae yi ba yyi kan safeena ya fixgota ya kai mata mari yace "gidan nawa xaki mayar joint din yan iska? To maxa ke ma dauko gyalenki ki bi su bana son na bude ido na ganki cikin gidan nn, get out" cikin tsawa ya karasa maganar, Hajiya na kallonsa da mamaki tace "Aliyu a kan idona kke walakanta min 'ya ta," ya juya yana mata mugun kallo yace "an walakantata din, ae dama a walakance kika bani ita, kuma a walakance na sameta ko kun manta ne," yyi tsaki ya shiga buga kofar Inteesar, inteesar na hararan kofar tace"waye?" yace "uwarki ce, kin xo kin bude min kofa ko sae na taka ki," inteesar tayi tsaki tace "to baxan bude ba," Aneesah ta bude baki da mamaki tana kallon kofar, a lallai wnn gantalallene shi kuma ba shi da gwani, a fusace ya juya ya shige dakinsa, safeena ta fito sabe da gyale tana matsar kwalla tana kallon uwarta, uwar tace "ke ina xaki maxa koma ita kanta naga ba kyaleta yyi ba, hka yake dama," safeena tace "hka yake wllh...." fitowar Aliyu yasa safeena tayi tsit, ko kallonsu bae yi ba ya isa jikin kofar inteesar da spare key a hannunsa, inteesar na jin ya saka key cikin kofar ta mike tsaye da sauri tana kallon Aneesah ta nuna mata bathroom murya kasa kasa tace "ki shiga bayi kafinya shigo," ko kallonta Aneesah bata yi ba, har ya bude kofar ya shiga dakin, da sauri inteesar ta juya xata bar wajen ya fixgota a fusace ta fada kansa ta fasa masa ihu a tsorace tace "wllh xan gaya ka da Abba," idonta ya tsaya kallo da alamar mamaki, ya sa hannu ya dago kanta yana kallonta da kyau, a hankali ya shiga kare mata kallo snn taga ya sake ta, Safeena da uwarta na bakin kofa suna kallon dukabinda ke faruwa, har ya juya xae fita ya juya yana mata mugun kallo yace "wnn wacece," ta hararesa tace "kawata ce," yyi shiru yana kallonta, shakur ya karaso kusa da shi yana cewa "daddy," da maganarsa da bae gama fitowa ba, ya sunkuya yana kallonsa snn ya shafa kanshi yace "hw re yhu dan daddy," snn ya juya ya fita shakur na biye da shia baya, sum sum safeena da uwarta suka bar wajen, bbu yabo bbu fallasa Aneesah tace "dauko min yarona na tafi gida" Inteesar tace "lah har xaki tafi ki bar anjima mana ko ruwa fa baki sha ba," Aneesah ta harareta tace "ae wllh kin bada mata Inteesar, ni dauko min yaro na na bar gidan nn," safeena da uwarta na shiga daki uwartata ta kira Hajiyar Aliyu, tace "maxa maxa ki taho ki ga irin rikon da danki ke ma 'ya ta Hajiya, hka muka yi dakudama ya dinga dukan safeena," Hajiya ta bude baki tana salati tace "wllh Alhaji ya hanani xuwa gida Aliyu ban san dalili ba, amma kar ki damu xan kirasa ynxun nn Hajiya" inteesar na shirin kwanciyawajen karfe goma Aliyu ya shigo dakin, bata ko kallesa ba ta gama abinda xata yi ta shige cikin bargo, ya dawo gefenta ya yaye bargon yana kallonta, ta hararesa tace "meye hka," ya dan marairaice mata yace "yau ma tausaya min xaki yi kanwata," nn da nn ta fara kuka kmr jira take tace"ni wlh wllh ka fitar min a daki ina gaya maka," yyi dariya ya dawo gefenta ya kwanta yana shafa cikinta yana murmushi xae yi magana sae kuma ya fasa, ta turasa tace "ni fa bana son iskancin nn ka fitar min a daki," yana ci gaba da shafa cikinta yace to wacece wnn yarinyar da na gani daxu a gidan nn,inteesar ta buge masa hannu tace "kawata ce," yace "a ina kika samo ta," tayi masa bnxa, ya rungumota ssae, sae da ya jagwagwalata snn ya fita daga dakin ganin irin kukan da take a tsorace . Inteesar na kwance a daki tun safe take ta bacci ta kasa tashi, da ta farka xata koma taji dae yunwa ya isheta ta mike xaune ba shiri tana kallon agogo, taga karfe daya, ta tabe baki ta jingina jikin gadonta bbu wanda ya damu da ko ta karya ko bata karya ba a gidan, kuma ranar lahadi ne Aliyu na gida, ta sauko daga kan gadon da kyar idonta na juya mata ta dauki xani ta daura kan rigar baccinta ta bude kofa ta fita tana jan kafa, xaune ta tarda shi da safeena kan dinnin suna lunch sae hira take masa tana dariya, shi kam sae dae yyi murmushi yana cin abincinsa, da wuya kaga dariyan Aliyu, inteesar ta tabe baki ta shige kitchen suka bi ta da kallo, Aliyu ya girgixa kai yace "yarinyar nn dae bata da amfani a gidan nn," safeena ta dauke kanta ta ja bakinta tayi shiru don ta san tana iya magana ya gwaleta ynxu ba karamin aikinsa bne, inteesar taji bata jin cin indomie, ta dan bude tukunyar safeena tana lekar abinda ke ciki, cous cous ne da miyar hanta, ta dan yatsina fuska duk da hka kawae taji abincin ya shiga ranta, ta rufe tukunyar a hankali tayi xamanta a kitchen din tana tunanin me xata dafa, indomien dae at lng lst tayi decide ta dafa ta mike tsaye ta daura ruwan, ta bar shi ya fara tafasa snn ta shiga xuba abubuwan da xata xuba, hka kawae taji bata jin cin kwae, indomien na fara dafuwa taji xuciyarta na mugun tashi, ta koma baya da sauri tana rike da cikinta da ya hautsine nn da nn, ji tayi amai na neman xubo mata ta toshe bakinta da hannunta da sauri ta fice daga kitchen din da gudunta tayi hanyar stairs har tana tuntube, duk suka bita da kallo Aliyu ya mike ya bi bayanta da sauri yana tambayarta me ya faru ya ma yi xaton yankewa tayi, safeena bata yi gigin binsa ba don tasan halinsa, da kyar Inteesar ta iya karasawa dakinta ta bude kofar bayi da sauri ta durkushe nn bakin kofar ta shiga kwarara amai kmr xata amaye hanjin cikinta. Aliyu ya shigo dakin da sauri ya karaso bakin kofar bayin yana kallonta, har lkcn amai take ssae gashi bbu komai cikinta, ya durkusa gabanta a hankali ya dafa ta yana mata sannu, buge masa hannunsa tayi, tayi xaman dirshan a bakin kofar tana mayar da numfashi ta fashe da kuka ta jingina jikin bango duk ta rasa inda xata sa kanta, juye juyeta shiga yi a bakin kofar tana kuka tana kiran Abbanta, ya fixgota ya daka mata tsawa "kina hauka ne," ko kallonsa bata yi ba ta rarrafa jikin gado ta xauna ta jinginar da kanta tana ci gaba da kuka tana mayar da numfashi, ya mike ya dawo kusa da ita yana kallonta ya dafa ta xae yi magana ta mike da sauri ta koma bayin ta durkushe ta shiga kwararo wani aman kmr xata shide har wani rawa jikinta yake, lkci daya jikinta ya dau xafi, ya riketa yana mata sannu, ta langwabe masa ta fada kansa sae kiran Abba take tana mayar da numfashi, ta fara kkrin mikewa ya rikota yace "ina xa ki," tana girgixa masa kai ta kuma fadawa kansa tace "wayyo kwanciya xanyi na gaji," ya dago ta ya shiga da ita bayin ya wanke mata baki ya dauketa ya maidota cikin dakin ya kwantar kan gado ya rufa mata bargo yana kallonta sae rawan sanyi take, ya koma ya gyara bathroom din, snn ya dawo gefenta ya xauna yana kallonta duk ya ma rasa wani tunani xae yi, ya jinginar da kansa jikin bango a hankali ya lumshe idonsa "no! Wnn me shegen rakin baxata iya rainon ciki ba ynxu, nd bae tashi haihuwa da ita ba tukun, da ma safeena ce wnn kam takuran da yake samu a gida a kanta xae kara yawa ne ma, to ma wani moranta yyi har xata dauki ciki ynxu" yyi tsaki ya bude ido yana kallonta bacci take amma da gani ba me ddi ba sae juye juye take, ya girgixa kai ya mike ya fice daga dakin, makullin motarsa ya dauka ya sauko falo, safeena da ta fito daga kitchen knn bayan ta kashe gas din da Inteesar ta kunna tace "me ya sameta Dear," ya galla mata harara yace "ban sani ba," ya fice, ta bi sa da kallo, ita kam halin Aliyu ya isheta a gidan nn, gashi sae bata kudinsu suke a banxa a kansa, amma abu sae kara gaba yake, tayi kwafa ta haura sama, yana shiga motarsa ya kama hanyar asibiti, bae damu da gaisuwan da nurses ke masa ba har ma da patients ya haura sama kawae ya wuce office dinsa, ya bude glass din da magunguna suke ya shiga xaban wanda ya kawosa, tabs kala biyu ya dauka da ruwan allura daya ya rufe glass din ya fito ya rufe office din, ya sauko kasa xuwa reception, sae a snn ya shiga amsa gaisuwan patients din da ke gaishesa, yyi murmushi ganin matar da yyi ma theatre kwanakin baya da yaranta da babansu, ya karasa kusa dasu yana kallonsu yace "madam me ya sami twins" matartace "wllh tari suke doctor, ya aiki?," ya karbi dayan yana masa wasa yace "aiki Alhmdllh anyi attend din maku ne," tace "A'a ynxu dae xa a duba mu, madam fa," yyi murmushi yace "tana lfya," tace "to a gaida min ita, yau kana wkend ko," yace "wllh kuwa, Allah ya sauwake, i wil b on my way," ya ba mijinta hannu suka yi sllma snn ya juya, yana isa kofar fita sai da ya juya ya sake kallon kyawawan yan biyun da suka girma ssae, ya dauke kansa da sauri ya fice ya shiga motarsa ya bar asibitin. . Aliyu na shiga gida ya tarda Safeena kwance a falo tana kallo, ta bisa da kallo har ya haura sama snn ta mike xaune tana bubbuga kafa a hankali ta shiga maganar xuci "lallai its high tym she wake up frm her slumber, ya kamata ta tashi tsaye daga xaunen da take ynxu, Aliyu ya gama kawota bango, xata cire sonsa ta ajiye gefe guda tayi abinda uwarta ta dde tana son tayi taki yi sbda so ya rufe mata ido, ita kuma inteesar ynxu suka sa kafar wando da ya da ita" tayi murmushin mugunta ta mike ta haura sama xuciyarta na tafarfasa. Aliyu na shiga dakin ya tarda ta tana bacci ya xauna gefenta yana kallonta ya ciro magunguna da alluran da ya dauko a asibiti yana kallonsu, snn ya juya yana kallonta tayi wani irin haske ta kuma kara kyau, yyi murmushi ya shafi gefen fuskarta ya mike ya dauko syringe a dakinsa ya dawo ya shiga hada alluran, sunansa yaji ta kira, ya juya da sauri yana kallonta ta sake maimaitawa "ya Aliyu," sae kuma yaga tayi murmushi ta juya, ya ajiye alluran hannunsa ya dawo dab da ita ya xauna yana shafa labbanta da yatsa yace "fateema," cikin baccin ta amsa "na'am," yyi murmushi ya daura mata kiss a bakinta, murmushin yaga ita ma tayi, yyi still yana kallonta, to wae meyasa yake son xubar da cikin nn, shi dae yana son yara kuma xae so yaga kyakkyawan bbyn da xata haifa masa mai kama da ita, ya dauke kansa ya daura hannu a goshinsa kan na juya masa, y? Meyasa yake son xubar da bbynsa gudan jininsa, ya girgixa kai yace "No," da sauri yaga ta mike xaune ya kamo ta ta fara turasa xata sauka yaki sakinta yana tambayarta mene, amai ta shiga kwarara masa a jiki yana rike da ita har lkcn, sae da ta gama snn ya dauketa ya shiga da ita bayi, sae kuka take tana cewa ita ya kaita gida, wanka yyi mata ya nannadeta cikin towel ya fito da ita ya cire xanin gadon snn ya kwantar da ita, shima wankan yyi don duk ta bata masa jiki ya saka xanin gadon cikin washn machine da shirt din jikinsa snn ya fito daure da towel, ranar ce rana ta farko da ta taba ganinsa daure da towel don ko singlet Aliyu bae yrda ta gansa da shi bare short nicker, ta rufe idonta da sauri, shima bae ce mata komai ba ya kwashi magunguna da alluran da ya hada ya fita da su, dai dai lkcn da Safeena ta fito daga dakinta, ta bi sa da kallon mmki shi kam ko kallonta bae yi ba shiga dakinsa. Alluran da yyi mata bayan ya tilasta ta sha tea ne ya tsayar mata da aman, amma duk da hka sae da ta gwammace dama aman ta dinga yi taji ddi, don rasa inda xata sa ranta tayi sae kuka take tana juye juye, ya rungumota cike da tausayinta yana lallabata tayi bacci, da kyar ta samu baccin ya dauketa, yyi shiru yana kallonta duk ta rame lkci daya, da yamma wajajen karfe biyar ya fita pharmacy siyo mata magunguna da drips din da xae sa mata.Yana fita ko minti goma ba ayi ba Zainab ta shigo gidan ko kallon safeena dake ta busar da gashinta da hand dryer bata yi ba ta wuce sama, safeena ta bi ta da kallo snn ta ja dogon tsaki, bacci ta tarar Inteesar ke yi ta shiga tashinta da xolaya tana cewa "ke kasa kinyi bakuwa maxa tashi" inteesar ta shiga juye juye ta mike xaune da kyar tana kallon Zainab, Zainab tace "hmm lbri na xo maki da mai ban kunya," inteesar xata yi magana taji yawu cike bakinta, ta mike tsaye da kyar ta shiga bayi ta xubar da yawun ta dauraye bakinta da freshner ta dawo, Zainab tace "meye hka," Inteesar ta langwabe da kyar tace "bana jin ddi ne," Zainab ta bude baki "iyye kar dae bby xa a samo mana," inteesar tayi shiru da mamaki tana kallonta snn tace "bby kuma, wani bby," Zainab tayi dariya tace "lalala kinga yanda kka yi wani irin haske da kyau kuwa, shknn xa a sama ma yayana bby," inteesar ta hade rae xata yi magana taji yawu kuma a bakinta ta mike da sauri taje ta tofar wnn wani irin jaraba ce, ta tambayi kanta, kuka ta fashe ma Zainab ganin Zainab ta kuke sae murna take xa su samu bby, tace "ni fa bana son hka Zainab wllh bani da komai," Zainab tace "ki daina wllh, ga signs a jikinki," kuka ssae take tana cewa na shiga uku ni Zainab ki bari bani da komai yarinya da ni xaki ce ina da ciki, Zainab tayi dariya ssae tace "tunda ko kina kwana daki daya da yayana ai ke ba yarinya bace," dai dai nn Aliyu ya shigo yana ma Zainab mugun kallo yace "ke wae wace irin mutum ce, ban hanaki shigowa gidana ba, xo ki fita," cikin daga murya ya karasa maganar ta mike da sauri tana xumburo baki ta dauki mayafinta ta bi ta gefensa ta fice ya kai mata rankwashi, inteesar ta hade kanta da gwiwa tana kuka, ynxu ciki ne da ita yar yarinya da ita, to da wani ido ma xata kalli su inna, ae Allah ma ya kyauta kuma ya rabata da haihuwa ynxu kuma ma wae dan Aliyu. Ta mike da sauri tun kan ya shigo dakin xata yi hanyar bathroom jiri ya debeta ya shigo dakin da sauri ya kamota ta fada kansa suka xube kan gado, ya fada gefenta da sauri ganin ynda take mayar da numfashi ya dagota ya rungumeta yana mata sannu, cikin kuka tace "wllh ka cire min cikin nn bana so," ya toshe bakinta da sauri yana kallon cikin idonta yace "ni ina son abu na . Kuka ssae Inteesar ta shiga rera masa, shi kam saekallonta yake yana murmushi, ta fara kkrin mikewa xata sauka daga kan gadon ya riketa da sauri yace "ina xaki," cikin kuka tace "wllh sae ka cire min cikin nn bana so," ya rufe bakinta ya hade rae yace "kar ki sake cewa na cire maki bbyna, sae kace wani kaya," ta buge masa hannu, ya harde kafarsa cikin nata tayi yar kara, ya rungumota yana kallonta ya shiga shafa mata cikinta yace "me xaki ci, dubi fa yanda kika rame tun kan ba mu je ko ina ba, a hka xa muyi rainon cikin kika san ma ko yan biyu ne kanwata," ta fashe masa da kuka tana kiran Abbanta, ya rankwashi kanta yace "ki daina min kmr ihsaan a nn, ke baki san kin girma ba tunda ga bby nn cikin cikin ki" bata san lkcn da ita ma ta rama rankwashin ba tana kukan da xa a iya kiransa da na shagwaba duk da har ga Allah ba shagwaba take ba, ya wara ido yana kallonta, ta koma baya da sauri nn da nn ta tsorata ya lakaci hancinta ya ja kunnenta yace "kin ci sa a bbyna na jikinki da yau na maki shegen bugu, ya Aliyu kike rankwashi " bae jira me xata ce ba ya kwantar da itaya mike ya fita, ta mike xaune da sauri ta hade kanta da gwiwa ta fashe da wani sabon kukan ynxu wae ciki ne da ita da gske yar yarinya da ita, ba a dau lkci ba ya dawo dakin rike da kofin tea yace "maxa tashi ki sha na saka maki ruwa aman ya tsaya," kallon tean kawae tayi taji xuciyarta na tashi ya kai mata baki ta mike da sauri sae cikin bayi ta shiga kwarara amae, ya isa kusa da ita ya durkusa ya dafata yana kallonta yana mata sannu, sae da ta gama snn ya gyara mata jiki ya maidota cikin dakin, a hankali ta kamo hannunsa tana hawaye tace "don Allah ya Aliyu ka tausayamin ka cire min cikin nn bana so," ya galla mata harara yace "wllh idan kika sake gaya min wnn maganar sae na bata maki rae, ki cire ynxu na gani mana," tayi shiru tana kallonsa xuciyarta na tafarfasa, ita ko ta fi sa iskanci xae gani kuwa, ta juya tayi kwanciyarta tana mayar da numfashi, tean da bata sha ba knn har bacci ya dauke, sae kusan sha daya na dare ta farka yana gefenta a kwance, shima amai ne ya farkar da ita, ya cire mata ruwan dake hannunta ganin a gigice ta farka tana neman sauka ya raka har bayin ta shiga kwarara amae, gashi dae ba komai cikinta, ya xuba mata ruwa a kai ya fito da ita, daga ita har shi ranan basu yi baccin kirki ba, jikinta yyi xafi ssae ta rasa inda xata sa ranta sae kuka take masa yana rungume da ita, da kyar bacci mai nauyi ya dauketa kusan asuba. Washegari monday bae je aiki ba sbda ita, tana kwance jikinsa bayan ya lallabata ta sha tea kadan yyi mata allurorinta wajen karfe goma safeena ta kwankwasa kofar tare da sallama, yace ta shigo, ta bude kofar ta shigo sae da xuciyarta ya kusan harbawa yanayin da ta gansu, shi singlet da 3qtre ne jikinsa, ita kuma rigan bacci iya cinya, ta kirkiro murmushi ganin allurori a bedside drawer tace "Ayya bata jin ddi ne dear," ba tare da ya kalleta ba yace "eh, ya akayi?" tace "Allah sarki, Allah ya sauwake fateema sannu," inteesar ta dago kai da kyar ta watsa mata harara, ta mayar da kanta, safeena ta dauke kanta da saurixuciyarta na tafarfasa tace "yauwa dear Momy ce ciwonta ya tashi shine xanje ynxu, amma ba ddewa xanyi ba dan da sauki," yace "ita kuma kullum ciwon nata ke tashi, baku da abinci ne a gida, ae yunwa ce ke kawo ulcer " tayi shiru tana kallonsa ya tabe baki yace "Allah ya sauwake, ki duba side drawer can bedroom dina ki dauki dubu goma," tana murmushi tace "to ngd dear," snn ta juya ta fice tana murmushin mugunta. Da yamma safeena ta shigo gidan, har lkcn Aliyu na dakin Inteesar, lkci lkci yakan yi tunanin ko dae kawae ya rabata da cikin nn ne ta huta shima ya huta, don ba karamin wahala yaga take sha ba tun kan cikin ya kai ko ina, ynxu ma da kyar ta samu bacci ya dauke, irin masu shegen laulayin nn ne me wahala, ya dan yi tsaki, ita ma ragwancinta ne kawae yyi yawa, duk ta fige lkci daya sai kace wacce tayi wata tana ciwo, safeena ce ta bude dakin ta shigo ya daga kai yana kallonta, tayi murmushi tare da lumshe ido tace "Aliyu so nake kaje duba mum dita ynxu, kuma ka tafi mata da wnn maganin nn da ka bata ranan nn wae taji ddinsa," yyi shiru yana kallonta,snn taga ya sauke ajiyar xuciya yace "wae ynxu?" ta dan yi fari da ido murna fal cikinta, amma ta hade rae tace "to da yaushe kke tunani," yace "ok," snn ya kwantar da Inteesar dake jikinsa ya mike tsaye ya juya yana kallonta bacci take, kan yace komai safeena tayi saurin cewa "to kaxo ka wuce," ya juya ya fice daga dakin, ta bisa da kallo tana murmushi, dakinsa ya shiga ya shirya snn ya fito da makullin mota, tana hararansa tace "to haka xaka je mata hannu rabbana," ya koma ciki sae gashi ya fito da kudade, ta rakasa har jikin mota snn ta manna masa kiss a baki, yyi murmushi ya lumshe idonsa yace "sae na dawo bbyna," snn ya ja motar ya fice daga gidan, ta doka uban tsalle tashiga kiran layin uwarta cikin murna tace "wayyoo mum, saura naki gashi nn xuwa. Aliyu na fita gidan ya wuce wani babban super market ya yayiwa mum din safeena siyayya bata wasa ba akalla ya kashe kusan 50k. Ya fito ya shiga motarsa ya dau hanyar gidan mum xuciarsa duk a cushe ya rasa dalili,gashi yana son kiran inteesar a waya ta wayar sa dake hannunsa amma ya kasa a haka dai ya cigaba da driving har Allah ya kai shi lpy. Yana isa gidan su safeenar maigadi ya bude masa get yana washe baki kasancewar aliyu na hannun damansa ne yana da yawan kyau,ko kula da gaisuwar da me gadi yake yi masa bai yi ba ya mika masa 2k aiko maigadi ya hau godia da kiraki hannu kawai ya daga masa yai hanyar parkin shade dinsu ya ajiye motarsa ya duba seat din baya cikin magungunan daya ajiyewa a a first aid box dinsa ya dauki na ulcer ya jefa a cikin ledar magunguna da safeena ta bashi. Sallama yayi cikin nutsuwa ya shiga falon dai dai lokacin mum ta fito aiko ganin aliyu yasa ta dan yatsina fuska shiko jiki na bari kamar yayi gamo ya sauko dg kan kujera yana kwasar gaisuwa,fuska ba yabo ba fallasa suka gaisa yai mata ya jiki sannan ya mika mata ledojin hannunsa ya mike xai mata sallama kenan tace "aliyu baxaka tsaya ko ruwa kasha ba?" Sai ya tsinci kansa ya kasa yi mata musu alhalin bai taba cin komai na gidan ba. Komawa yai ya xauna xuciarsa na cikin dumuwa yana buqatar ya duba inteesar kuma ya san by nw ta tashi dg baccin da ya barta tanayi. Tunanin haka yasa ya ajiyar xucia tare da fesar da iska mai xafi hade da lashe labbansa da suka bushe. Mum ce ta shigo riqe da jug a akan tray da cup da roban ruwan c'est bon,ta tsiyaya masa xobon ta mika masa ya kai hannu biyu tare da yin godia.... zai kai bakin shi kenan wayarsa tai ringing hakan ya dakatar dashi da sauri ya ajiye xobon ya karkace ya xaro wayar dg aljihun jeans dinsa duk a tunaninsa ko inteesar ce ta kira shi... Sae da Aliyu ya fara xuwa asibiti ya dauki maganin da xai kai ma mamar safeena snn ya ja motarsa ya kama hanyar gidan jikinsa a mace, ya na isa yyi parkin a waje, ya fito da maganin yana kare ma gidan kallo snn ya shiga, suka gaisa da mai gadin ya karasa balcony ya danna bell, yar aiki ta bude masa kmr jira take ya shiga falon ta nuna masa kujeran da xae xauna da sauri shima kmr wnda ake contrl ya xauna inda ta nuna masa yana bin ko ina na falon da kallo, yar aikin tayi sama kiran Hajiya, yana kallo Hajiyar ta shigo falon ya dan dukar da kansa ya gaisheta ta amsa da fara'a kmr gske snn yyi mata ya jiki, ya bata maganin da ya kawo mata, ta amsa tana gdya tana jujjuya maganin, ya ciro kudin da ya dauko daxu ya mika mata yace "ni xan koma Hajiya" ta karba da sauri tana gdya ta mike tace to bari na kawo maka ruwa kasha mana, yace "A'a Alhmdlh ae daga gida nke," tace "to bari na baka sako ka kaima safeena," yace "to," ta mike ta yi sama, sae ga ta ta sauko da dan wani parcel, ya karba yyi mata sallama, ta rakosa har bakin kofa tana sa masa albarka snn ta koma murna fal cikinta, yana barin anguwar yaji hka kawae yana son ganin abinda ke cikin parcel din, parkin yyi gefen titi snn ya shiga budewa, wani ruwa ne ya xuba jikinsa ya matsar da parcel din daga jikinsa da sauri amma duk da hka sae da ruwan ya taba kayansa da farko wari yaji, ya yatsine fuska kawae kuma sae yaji wni mugun kamshi me ddi ya xiyarci hancinsa, ya rufe da sauri ya ajiye parcel din ya ci gaba da drivin dinsa. Safeena ta kasa xaune ta kasa tsaye sae kaiwa take tana komowa a falo, wayar uwarta ya shigo nata ta daga da sauri jikinta na rawa tace "ya xauna kan kujerar mumy, kuma ya karbi ledan," uwar ta kyalkyale da dariya tace "wllh kuwa dota, ynxu fatanmu kawae Allah yasa ya bude," safeena ta doka tsalle tace " Alhmdllh amma naji ddi momy, budewa kuma ba matsala bace ko a gida xan sa ya bude bare ina da yakinin ma ya bude naji sighn din da mutumin yace xan ji a jiki na," budewar gate din da safeena taji yasa tace "wayyoo momyna ya dawo xamu yi waya anjima," ta katse kiran tana murmushin mugunta, shknn ynxu sae yanda tayi da Aliyu," yana shigowa gidan ta karasa cikin kissa ta rungumesa ya dagata sama ya manna mata kiss a goshi yace "bbyna sae kyau kike karawa kullum," ta hararesa tace "sae yau ka sani," yace "A'a bbyna ina sane," kinsan me bbyna na dan maki barna wllh momy ta ban turare na kawo maki da karambani na na bude ya xuba jikina," ta kankamesa ta rasa inda xata sa kanta don murna, tace "da gske bbyna, wllh sae ka biya ni," yyi hanyar stairs da ita yana cewa "naji xan biya bby nawa ne," inteesar kam na xaune ta jinginar da kanta jikin gado, ji take kmr ba ita ba duk ta rasa inda xata sa ranta taji ddi, ga alluran hana aman da yyi mata duk ya bi ya dameta, tana neman yin aman ma ko xata samu sauki amma ta kasa, yunwa take ji ssae amma bbu abinda ke ranta, ko wani abinci ta tuna sae taji amai na taso mata jikinta yyi mugun xafi ga kishin ruwa da take ji kuma tana tsoron shan ruwa, ta sauko kasa da kyar ta kwanta kan tiles din dakin ko xata ji ddin ranta, kasa daure kishin tayi ta mike xaune tana mayar da numfashi ta rarrafa ta bude fridge dinta taga ba ruwa ciki sae lemo, tana daddafa bango ta fita daga dakin ta sauka kasa da kyar ta bude fridge ta dauki ruwa ta sha, snn ta koma sama, dae dae kofar dakinta taji amai frm no where ta xube wajen ta shiga kwarara aman kmr ranta xae fita, suna daki shi da safeena duk ta gama rikitar da shi, ya turata da karfi ya mike tsaye ya karasa kofa ya bude ya fita safeena ta bi bayansa da sauri, durkusawa yyi gabanta yana kallonta, ta fashe masa da kuka abun tausayi ta xube jikinsa muryarta na rawa tace "don Allah ya Aliyu ka kai ni gida, ni wllh na gaji ko ina ciwo yake min wayyoo mutuwa xanyi," ya rungumeta cike da tausayi xae yi magana safeena tace "dear," ya juya da sauri yana kallonta, kallonsa kawae ta tsaya yi bata ce komai ba, ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Inteesar yace "ke kuma mahaukaciyar wace gari ce xakiyi ma mutane amai a nn, idan kina jin amai ba sae ki shiga bathroom din ki ba, wnn ae kaxanta ce," Inteesar ta daga kanta tana kallonsa, da kyar ta shiga kkrin mikewa daga inda take wani aman ya taso mata ta shiga kwarara sa a wajen, kuka ssae ta fashe da ta jingina jikin bango tace "wayyoo Abbana," kallonta kawae ya tsaya yi ya kasa cewa komai, ta rarrafa ta shiga dakinta ta xube kan tile tana mayar da numfashi, safeena da sae kallon inteesar take da mugun mamaki lkci daya jikinta yyi sanyi ta ma rasa tunanin da xata yi, a xuciyarta tana cewa amae kuma? to me hkn ke nufi, ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Aliyu tace "me ke damunta???? . Aliyu ya mike tsaye yana kallon safeena yace "bata jin ddi ne," bae jira me xata ce ba ya bude dakinsa ya shiga sae ga shi ya fito da mop ya gyara wajen aman, safeena ta koma daki da sauri hannunta na rawa ta shiga kiran uwarta, tana dagawa tace "momy wlh ina ga fa kmr cikine da yarinyar nn," uwar ta mike daga xaunen da take da sauri tace "mene? Ke wa ya gaya maki," a rude safeena tace "gashi nn tana ta amai," uwar tayi salati tace "bari xan kiraki," ta katse kiran. Da daddare Inteesar na kwance kan tiles ya shigo dakin ya durkusa gabanta yana kallonta yace "tashi ki sha kunu na karbo maki a gida," ta kasa dagowa ya dagota yana kallonta ya kauda kansa da sauri, ya kai mata kofin baki, ta kauda kai da sauri muryarta na rawa tace "xafi," ya girgixa mata kai yace "ba xafi," ta maido da kan jikinta na rawa ta daura hannunta kan kofin taji ba xafi ta kai bakinta yana rike da kofin ya shiga bata, da sauri ta cire bakinta tace "baxan yi amai ba? ya gyada mata kai ya ci gaba da bata, yunwa take ji ssae don hka rabi tasha ta koma tayi kwanciyarta kan tiles, yace "kin koshi ne ta gyada masa kai tace ruwa xan sha, yace "aa baxa ki sha ba," bata ce komai ba ya dago ta mayar kan gadon duk abinda suke safeena na lekensu, ta koma da sauri daki har da hawayenta ta kira uwarta tace "kai ni momy wllh na gaji, gashi can wajenta yana lallabata yana bata koko," uwar tace "yi shiru safeena, daxun nn na dawo daga wurin mutumin, ca yyi wae duk abinda xa muyi masa a kantabaxae taba tasiri ba sbda yana mugun son cikin nn dake jikinta," safeena ta dafe kirji tace "ynxu ciki ne da ita da gske ina xaune momy," uwar tace "ki tsaya ki saurareni mana," safeena na share hawaye tace "to ina ji momy," uwar tace "yauwa, to ynxu ca yyi dole sae an lalata cikin in har muna son muga aiki yyi mugun tasiri a kansa, ynxun ma ba wae bae yi tasiri bane, don xae dinga lallaba ki kuma sae abinda kika ce masa xe yi, sae dae fa hankalinsa gaba daya na gunta sbda wnn shegen cikin, kuma fa baki isa ki hanasa xuwa gunta ba amma, don hka kawae ki kwantar da hankalinki jibi ki xo mu koma kauyen yace yana jiranmu, ciki kuma kmr ya bare ne," safeena ta share hawayenta xuciyarta fal murna tace "to ngdd momyna," ta katse kiran tana murmushin mugunta. Da safe Aliyu ya bae ma safeena i.v din bikin Zainab, ta tabe baki tana hararansa tace "to ca nayi maka ban sani bane," yyi shiru yana kallonta snn yyi murmushi yace "to Allah ya baki hkuri bbyna, amma ni dae ban san me nayi maki ba kika canxa min kwana biyu," ya mike ya karasa kusa da ita ya xauna yana shafa gashinta yace "haba yan matana," ta hararesa tare da buga masa hannu tace "ni ka rabu dani," ya rungumeta yace "haba bbyna," kmr xata yi kuka tace "to ba kai bne ba baka ma damu dani da lamarina ba a gidan ba," yace "inji wa yace maki hka," kakarin Aman inteesar yaji, ya saketa da sauri ya mike tsaye ya fice daga dakin, safeena ta bi sa da kallo xuciyarta na mugun kuna, kasan dakin ya tarar da ita tana ta amai ya kamata har ta gama snn ya gyara mata jikin ya gyara dakin ya kwantar da ita kan gado, ta rikesa muryarta na rawa tace "sanyi nake ji yaya," ya lulluba mata bargo snn ya dauki I.v din da ya ajiye gaban madubinta xae fita ya juya yaga kallonsa take, ya dawo yana kallonta yyi murmushi yace "kina san wani abu ne," ta girgixa masa kai yace "kinsan bikin Zainab saura kwana goma ko," ta mike xaune da sauri tace "da gske yaya, ni ba a gaya min ba to," ya kamo hannunta yace "ae sun san baki da lfya, ki bari nxt wk sae mu tafi gidan kafin nn jikinki ya kara kwari," ta marairaice kmr xata yi kuka tace "to ba kila xuwa tayi ranan ta gaya min ba ka koreta," yace "ba ta ji ne," tace "to yaya wa xata aura" yana kallonta yace "faruuq," ta wara idonta ta fada kansa cikin jin ddi tace "don Allah da gske yaya, kai amma naji ddi wllh, ka bani nmbr ya faruuq din" yace "to anjima xan baki, xanje gida ynxu me xan ce inna ta girka maki?" tayi shiru sae kuma ta bata rae ita da ba ma son cikin take ba, yace kinyi shiru, tana hararansa tace "kace mata ina da ciki ne," ya daga hannayensa da sauri yace "A'a" yana girgixa kai, ta koma ta kwanta tace "dan wake nake so ni," yace "to, sae na dawo, kar ki sha ruwa kar amai ya takuraki," bata ce masa komai ba yayi hanyar kofa, duk wnn abinda suke safeena na labe tana jinsu, tana jin xae fito ta bar wajen da sauri ta shige dakinta tana murmushin mugunta, yana fitowa ya shiga dakin safeenar . Bayan kwana biyu safeena ta samu ta lallaba Aliyu wae xata gun wata yar uwarta, ya ko barta har da bata kudi da makullin mota dayake ta iya drivin tana ta murna a xuciyarta tana cewa lallai sae yanda tayi da Aliyu, ynxu kam ta yrda yana tafin hannunta amma dae ba duka ba, tunda bata isa ta hanasa xuwa gun Inteesar ba, amma komai ya kusan xuwa karshe, ta fada a fili tana murmushi, cikin kwanakin nn Aliyu na da aiki ssae a clinic don hka ya gwammace da ya bar Inteesar kadae a gida gwara ya dinga tafiya da ita don tana bukatar kulawa ssae, hka ko ya dinga yi kullum shi xae shiryata da safe yyi ma safeena sallama su wuce asibiti, hkn yyi mugun tada ma safeena hankali to ta ya xa'a yi ta aikata abinda suka sha wahala kafin su samu bayan baya barinta a gida., ita kam Inteesar ko kadan abinda Aliyu ke mata baya burgeta don dai dae da second daya bata son cikin jikinta, kuma tasan sbda cikin yake mata hka, wani mugun tashin hankali ke xuwa mata idan ta tuna cikin Aliyu ne jikinta, Ana saura kwana uku bikin Zainab ya kai ta gida duk da ba a son ranta ba don bata son su san tana da ciki, amma ashe duk ya gaya masu uwarsa ce kadae be gaya ma ba sae umma, inna duk ta rikice masa wae cutar jikarta kawae yake gashi duk ta fige ba kyan gani, shi dae bae tanka ma inna ba ya fice, Inteesar dae na kwance falo sae mayar da numfashi take don da kyar ta iya karasowa cikin gidan bayan sun sauka daga mota, kuma da asibiti ne baya barinta ta taka da kanshi yake daukarta su shiga ciki, inna tace "to wae wani irin jarababben cikine wnn dake neman kashe min ke," ta mike xaune tana hararan inna kmr xata yi kuka tace "wae ni nace maki ciki gareni ne," bata jira me inna xata ce ba ta shiga daki tayi kwanciyarta, inna duk ta daga hankalinta ganin irin laulayin da Inteesar take mai tsanani, bbu wanda bae san ciki ne da ita ba a gidan, ko da yaushe cikin amai da kasala take, ko maganan kirki bata son yi sae in Aliyu na yasa ta gaba ko yana tambayarta me take so, duk tausayinta kawae yake, Hajiya da hankalinta yyi mugun tashi bata ga fuskar da xata ma Aliyu magana ba da ya shigo da ya fice daga gidan, tab aiko gwara ta nemo yanda xa ayi da cikin nn, ynxu Aliyu dama sae ya iya kwana daki daya da yarinyar nn duk cika bakinsa, hka aka yi biki hankalin inna rabi na gurin Inteesar rabi na gun bikin, duk aka yi abubuwa masha Allah, amma inteesar na kwance tana fama da kanta, safeena ma ta xo ranar bikin tana daddaga hanci ita matar Aliyu inna ta kunyatata gaban lodin jama'ar biki su kursum dariya kmr xasu shide, ko minti daya bata kara a gidan ba tayi gaba ba shiri jikinta a sanyaye har ga Allah tsoran tsohuwar nn take, ran Hajiya yyi mugun baci amma bbu yanda ta iya da inna, washegarin ranar da aka kai Amarya da daddare Aliyu ya shigo falon inna bae ko kalli innar ba ya durkusa gaban inteesar dake kwance idonta biyu, ya daura hannu a goshinta yace "amma yau bakiyi amai ba ko," a fusace inna tace "kaji gantalalle wani irin bata yi amai ba, ae hanjin cikinta ne kadae bae xaxxago ba yau har tsorata nayi nace to ko su ne ke shirin fitowa" Aliyu yyi mata mugun kallo yace "to ke kuma wa ya somo bakin ki nn, iyayi kawae," sae abun ya ba Inteesar dariya ya dago ta yana kallonta yace "Abba na neman mu, xaki iya ko na daukeki," ta marairaice tace ynxu, ya gyada mata kai, ita mugun kunyan Abba take ji har ma da momynta, duk shigowar da momy take ta gaisheta kar inna ta xaxxageta tace taki xuwa, Inteesar yi take kmr tana bacci, inna ta mike tsaye da sauri tace "bari kawae na kama hannunta mu je," Aliyu ya bude baki yana kallonta yace "wae meyasa kike son shiga tsabgar da ba taki ba ne," bae jira me xata ce ba ya harareta ya sa ma Inteesar hijab dinta ya dauketa suka fice, inna tayi kmr xata yi kuka tace "ni ban san meyasa yaron nn ya rainani da tsufa na da furfurata ba," a hanya ya ajiye ta dalilin rokansa da ta dinga yi ya ajiyeta suka karaso falon yana rike da hannunta, da kyar ta iya bude baki ta gaishe da Abba kanta a kasa, ita kawae kunyarsa take ji, yace "ya jikin fateema," kanta a kasa tace "da sauki Abba," yace "to Allah ya sauwake, kina son komawa dakin ki ne ko xaki xauna nn gun inna sbda condition dinki" ta dago kai a hankali tana kallon Aliyu, shima kansa a kasa yake, tayi shiru ta rasa me xata ce don ita kam bata da burin cikin nn ya kara girma a jikinta, Aliyu yace "Abba da dae na tafi da ita xan fi kula da ita a can kuma ba gida ma nake barinta ba tare da ita nake xuwa clinic, nn ko xae yi min nisa kuma xan takura kaina," Abba xae yi magana inna ta fado falon, ashe tana labe tana jin duk abinda suke cewa tana huci kmr xata yi kuka tace "amma munafurcinka dayawa yake Bukar, hka muka yi da kai? To ni Rahmatu nace bbu inda yarinyar nn xata je aje a kashe min ita da abinda ke cikinta a banxa a hofi a barni da wayyo Allah, don idan an kashe su ma ni nayi hasara ba ku ba". .. Aliyu ya dan yi tsaki ya kauda kai, Abba kam shiru yyi yana ta kallon inna, ita ko ta tsaya masu kmr soja a bakin kofa, can dae Abba yace "to ki hada kayanki sae ki bi su," tayi kwafa tace "ko da naji," snn ta juya ta fice da sauri, Abba ya girgixa kai yace "tashi ka dau matarka ku tafi," Aliyu ya mike yana kallon Inteesar, ita ma ta mike tsaye suka ma Abba sallama snn suka fita, yana rike da hannunta yace "mu je mu gaida momyn ihsaan ne," tayi kmr bata ji sa ba shima bae sake ce mata komai ba har suka fita ya bude mata mota ta shiga shima ya xaga ya shiga suka kama hanyar gida, ko da suka isa tayi bacci ya fito da ita daga motar yana rike da ita kmr bby, safeena na kwance falo ta bi su da kallo ya sakar mata murmushi yace "bbyna," tayi tsaki ta dauke kanta tacigaba da kallonta, sae da ya kai Inteesar sama ya kwantar da ita snn ya sauko ya sameta, ta mike tayitsaki ta haura sama ta bar sa nn ya bita da kallo snn yyi mmrshi yabi bayanta. Washegari sae da safeena ta sa ya makara xuwa office, wanka kawae yyi ya shirya ya dauki makullin motarsa ta rakasa tanai masa shagwaba ya manna mata kiss ya ja motarsa ya bar gidan, ta sauke ajiyar xuciyan jin ddiyau dae ya manta shegiyar gaba daya, ta koma cikin gida murna fal cikinta, tana shiga daki ta fito da kullin maganin da aka basu su sa ma Inteesar a ruwan sha ta tsura ma maganin ido tana murmushi,dukiya fa knn a hannunta, ruwan fridge ta kwashe gaba daya ta bar guda biyu ta xuxxuba maganin cikisnn ta rufe fridge din ta koma sama, ta lura kasa Inteesar ke saukowa shan ruwa bbu ruwa a dakinta kuma bata ga alamar an siyo ba, tana ta kwance a daki tana jiran jin saukowar Inteesar amma shiru, ita ko tana kwance daki ta rasa inda xata sa ranta sae juye juye take ga yunwar da take ji tun safe ta gane Aliyu ya bar gidan hkn yasa ta daure ta mike ta sa ma kofar ta key, kishin ruwa duk yabi ya ishetagashi ba karfin sauka kasa, da kyar ta rarrafa ta shiga bathroom ta bude tap ta sha ruwa ta dawo tayi kwanciyarta kan tiles. Washegari ma abinda ya faru knn Aliyu bae shigo ya ga halin da take ciki ba ya bar gidan da sassafe, duk da jiya don ita ya dawoda wuri amma safeena ta gusar masa da hankalinsa ya manta me ya dawo da shi, ganin yunwa na neman yi mata lahani yasa ta dinga daurewa tana hada tea a nn dakinta da ruwan sanyita sha, shima tana sha ta amayo, duk ta kara xabgewa bata da aiki sae na kuka ita daya a daki, wani lkcn sae taji kmr ta dauki waya ta kira inna kawae sae ta fasa don bata ga amfanin kiran ba don rabuwa kawae take son yi da cikin, ita safeena bbu abinda yafi daga mata hankali irin yanda taga ruwanta na nn ajiye ba a taba ba, hkn yasa da daddare da Aliyu ya dawo ranan tace "anya kuwa kana shiga duba baiwar Allahn nn dear, gashi ita bafitowa take ba, na kan shiga na dubata wllh, amma ba ddewa nake ba kar ace xan yi mata wani abun ne" Aliyu ya mike da sauri kmr an tsikaresa yyi hanyar stairs ta bude fridge ta dauka ruwan da sauri ta bi sa tana cewa "gashi ka kai mata ruwa naga kmr jiya ruwan dakinta ya kare na fanfo take sha, ni kuma kar na kai mata ta xata wani abun ne," ya karba ya haura sama ya bude dakin ya shiga rabon da ya ganta yau kwana uku tun ranar da sukadawo daga gida, ya karaso gabanta ya durkusa yana kallonta a hankali yace "ya jikin fateema, kin daina aman," tayi tsaki ta juya abinta, ya bude fridge dinta ya ajiye mata ruwan yace "me xaki ci," tayi bnxa da shi, yyi shiru yana kallonta, ta juya cikin kuka tana kallonsa tace "wllh tllh idan baka cire min wnn shegen cikin ba...." bae jira ya karasa jin maganarta ba ya xuba mata mari, "don uwarki kika sake min maganar cire ciki sae nayi mugun saba maki kina ma da hankali kuwa, to ki je ki cire tunda ke mahaukaciya ce," ya mike a fusace ya fice daga dakin ta bisa da kallo dafe da kuncinta. Ranar bata yi bacci da daddare ba, kawae Allah Allah take gari ya waye, gari na wayewa ya shigo dakin kafin ya tafi aiki, tea me kauri ya hada mata ya ajiye matagefenta, snn ya dauko goran ruwan da safeena ta basa jiya ya ajiye mata gefenta safeena ta shigo dakin tana murmushi tayi ma Inteesar ya jiki ko kallonta inteesar bata yi ba suka fice tare da mijintata rakasa ya shiga mota ya manna mata kiss snn yaja motar ya bar gidan, safeena ta koma gidan xuciyarta fari tasa ganin goran ruwan da ta ba Aliyukusa da inteesar yau dae xa ayi ta ta kare, ta shige dakinta tana dariya. Inteesar ta mike tsaye ta dauki Hijab dinta ta saka, duk irin wahalan da take sha ko sau daya wanka bae taba wuce ta da safe ba dole sae ta daure ta shiga tayi, ta fito tana ganin jiri mai gadi ya tsaya xae mata maganar bnxa ta fixgo gate din ta fice abinta ta barsa nn tsaye, gidan Aneesah ta shiga, tana xaune tana ba shakur Indomie, tana shigowa ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi, Aneesah tace "lah daga ina hka Inteesar daxun nn nagama xancenki a xuciyata wllh" Inteesar xata yi magana taji yawu bakin ta mike da kyar taje bathroom ta xubar Aneesah tace "A'aah kice oga yyi aiki" . Inteesar ta harare Aneesah snn tayi tsaki tace "ni don Allah taimako naxo kiyi min Aneesah," Aneesah tayi dariya tace "to kawas ina jinki amma cikin nn na baki wahala gskya, kinga yanda kika rame kuwa," Inteesar ta dawo kasa kusa da ita tace "don Allah don Annabi Aneesah kinsan inda ake abortion?" Aneesah tayo waje da ido da mamaki tana kallonta snn tace "kina da hankali kuwa inteesar," inteesar ta jinginar da kanta jikin kujera hawaye ya cika idonta, Aneesah tace "kinyi shiru," inteesar ta share hawayen idonta tace "wllh xubar da cikin nn xanyi kin dae ji na rantse in ma xaki gaya min ki gaya min," Aneesah ta gyada kai tace "to tashi ki fita a gidana, ni bana hulda da maras tsoran Allah," inteesar ta juya tana kallonta tayi shiru snn ta mike tayi hanyar fita daga gidan, Aneesah ta bita da sauri ta kamo hannunta tace "haba inteesar bafa kiyi kama da jahila ba," kuka inteesar ta fashe da tace "baxa ki gane ba Aneesah wllh bana sonsa bana son cikinsa, bae damu dani ba sae wahala nke ta sha," Aneesah ta xaunar da ita tana kallonta da tausayi tace "ni na tabbatar maki kina haife wnn cikin xaki ga tsantsan so gun mijinki, ni banga rashin son da mijinki yake maki ba inteesar nafa ga abinda yyi ma kishiyarki ranar sbda ke, don me xaki walakanta kyautar da Allah ya baki yar uwa," inteesar tayi shiru tana ta sauraran Aneesah tana ta wa'axinta da nasiha, har ta kai Aya snn inteesar ta kirkiro murmushi tace "to ngdd Aneesah, ta dauki shakur tana ta wasa da shi yana mata dariya, tace "amma a gida kika haife yaron nn ko Aneesah," Aneesah tace "me kika gani," inteesar tayi yake tace "aa kawae tambaya ce nayi don ni dae ina tsoran Haihuwa," Aneesah tayi dariya tace "A'a a asibiti na haifesa," inteesar tace "wani asibitn?" Aneesah tace "A'a tender care na haifesa, ai kin san asibitin bbu wani nisa," Inteesar tace "A'a" Aneesah ta gaya mata inda asibitin yake kuma dama abnda kawae take son ji knn, ta mike xuciyarta fal murna ta bar gidan. . Inteesar na fita daga gidan Aneesah ta koma gida cike da jin ddi ta shiga dakinta tana haki kmr warce tayi gudu, ta tabe baki jin wakan da ke tashi dakin safeena, sae da ta huta na kusan minti goma snn ta mike ta dauki purse dinta ta fita daga dakin, dakin Aliyu ta bude a hankali ta shiga ta bude drawer din da taji yace Safeena ta bude ta dauki kudi ranan, taji ta a kulle, tace "na shiga uku," ta mike ta fara kalle kallen cikin dakin kmr xata yi kuka, to ina xata samu kudin xuwa asibitin ynxu, drawers din dakin ta dinga bubbudewa gaba daya ko xata ga kudi amma bbu, duk ta gaji sae haki take, tuni ta fara kuka tana cewa "Allah ka taimakeni in ga kudi" ta bude lst bedside drawer din taga wani babban book an rubuta my diary a gaba, tayi tsaki ta ajiye ta mayar da drawern, ta mike ta isa wardrobe din da yake ajiye kayansa na sawa ta bude ta lumshe idonta sakamakon wani kamshi me ddi da ya bugi hancinta, ta gama bincikenta nn ma ba ta ga kudi ba ta rufe ta xube kasa ta daura hannu a ka tace "wayyoo Abbana wllh ni na gaji," ko ina ta bude daga taga Allura sae taga magunguna da dae kayan asibiti kmr tsiya wnn wace irin jaraba ce, kmr ance ta mike ta daga filo taga dubu daddaya karkashin filon har da Atm dinsa ta wara ido tace "wayyo Allahna," ta kwashi kudin ta shiga kirgasu da sauri hannunta na rawa taga dubu sha biyu ne, ta dan marairaice fuska to xae isheta taje asibitin ma kuwa, tayi tsaki ta bude purse dinta ta xuba kudin snn ta juya xata fita daga dakin taje dakinta ta sha ruwa don mugun kishi take ji don tsabar son taje ta cire cikin ta nemi xaxxabin dake tattare da ita ta rasa sae kasala kawae, har ta isa bakin kofa ta dawo da sauri tuna baxae rasa ruwa a dakinsa ba da tayi ta bude fridge dina ta ko ga ruwa ta dauka ta bude ta sha snn ta rufe fridge din ta dauki sauran ta fita daga dakin, duk wnn abinda take safeena bata sani ba, tana daki kwance tana ta shan kida cike da jin ddi, jiran jin ihun Inteesar kawae take a ko wani lkci, Inteesar kam har ta fita daga gidan rike da purse dinta cikin Hijab, mai gadi dae bae ce mata kala ba ta bude gate ta fice abinta sae da ta isa bakin titi snn ta tsayar da tricycle tayi masa kwatancan asibitin da Aneesah ta gaya mata yace ta bada dari biyu, ta shiga tace mu je. Wasa wasa asibitin shegen nisa ne da shi, yyi parkin dae dae gate din asibitin ya juyo yana kallonta yace "mun kawo Hajiya," ta fito tana kare ma asibitin da ma anguwar kallo, ta bude purse ta ciro dubu daya cikin kudin ta basa kudin ya rage dubu sha daya, ya bata canjinta ta karasa cikin asibitin gabanta na faduwa, wnn dae da ganin asibitin nn ba na talakawa bne, anya kuwa xasuyi mata abortion a dubu sha daya kuwa ta dan karyar da kanta abun tausayi, da Addu'arta ta shiga asibitin, babba ne ssae ta karasa cikin reception ta xauna ganin patients dayawa a xaune, ta shiga kare ma reception din kallo, ta kai kusan minti talatin a xaune ba a xo kanta ba duk ta gaji, taji kwanciya kawae take son yi ga amai dake taso mata, ta daura kanta a cinya taji kmr ta rusa ihu duk ta rasa ina xata sa ranta, wata nurse ce ta dafa ta ta dago da sauri tana kallonta, Nurse din tace "yhur card nmbr Madam," inteesar ta shiga kalle kalle xata yi magana taji yawu ya cika bakinta, nurse din ta lura da hka ta nuna mata bayin dake kasan reception ta karasa ta xubda yawun ta kora ruwa snn ta dawo, nurse din ta debo vitamin c ta mika mata ta sa a baki tayi mata gdya ta karba, tana kallon Nurse din tace "i dnt have a card in here," Nurse din tace "to dole sae kin yanki kati," Inteesar tayi shiru snn tace "nawa ake yankan katin," nurse din tace "family card dubu biyar, na mutum daya dubu 2 da dari 5," inteesar tayo waje da ido tana kallonta, ganin xata bata ma nurse din lkci ga kuma patients dayawa suna jira yasa tace "to ki yankar min na mutum daya," nurse din tace "ok" snn tayi gaba, a hankali inteesar tace "na shiga uku, to ai kudin ya kare," ba ajima ba nurse din ta fito daga wani dan daki ta mika mata katin snn wata nurse ta daddubata ta duba har da weight dinta tayi rubutu a file tasa nurse ta rakata bayi aka xuba mata ruwa a kanta don temperature dinta yyi sama, ita dae binsu kawae take, a xuciyarta tace ko da yake basu san me ya kawota ba shiyasa suke bata lkcnsu, ita dae ynxu likita kawae take son gani, wata nurse ce ta gwada mata office din doctor din da xata shiga a sama, tana rike da file dinta ta haura sama da kyar ta karasa office din tayi knock. A hankali Inteesar ta tura kofar bayan an mata ixinin shigowa office din, cak ta tsaya daga bakin kofa tana kallon likitar, doctor din ma ta mike tsaye tana kallon Inteesar da mamaki tace "fateema," inteesar ta kirkiro murmushi gabanta na faduwa ta karaso office din a sanyaye, ta nuna mata kujera ta xauna, doctor din tace "daga ina kike hka fateema, me ya kawo ki nn," ta rasa karyan da xata mata, da kyar bakinta na rawa ta ce"banda lfya ne," doctor din ta hade rae tace "shi Aliyun fa," inteesar ta rasa me xata ce ga xuciyarta sae tashi yake, likitan ta dawo kusa da ita tana kallonta ta dago kanta tana kallon cikin idonta tace "ciki gare ki fateema," inteesar tayi shiru bata ce komai ba, doctor din ta ciro wayarta ranta a bace ta shiga neman layin Aliyu, da sauri inteesar ta dakatar da ita gabanta na faduwa tace "A'a don Allah doctor kar ki kirasa wllh ya sani kuma yana dubani nice dai bana son shi ya duba ni, Allah yana kula dani doctor kawae ni ce bana so, idan yaji na xo nn xae bata min rae don bae sani ba," doctor din tace "haba fateema, to ma don me xaki fita ba tare da ixinin mijinki ba, kuma meyasa baki son ya duba ki," inteesar ta fashe da kuka tace "wllh ni bana sonsa doctor," doctor din ta tsaya da mamaki tana kallonta snn tace "sbda me fateema, gashi har rabo ya shigo kice baki son mijinki," Inteesar ta sunkuyar da kai tana hawaye, doctor din tayi shiru tana kallonta, can ta koma sit dinta ta xauna ta shiga yi mata nasiha kan cewar ta rungumi mijinta ta cire duk wani rashin sonsa a ranta, ita dae bata ce komai ba sae kukan da take a hankali, Doctor din tace "yyi maki scan ne?" inteesar ta girgixa kanta tace "A'a nace masa bana so," doctor din ta harareta tace "to karki sake yi ma mijinki musu baki san aljanarki na karkashin kafarsa ba," inteesar ta dan tabe baki kanta a kasa ba tare da ta bari doctor din ta lura ba, doctor din ta yagi wani takarda ta danyi rubuce rubuce snn ta danna bell wata nurse ta xo da sauri, ta mika mata takardar tace "scan xa ayi yi mata sisterna ce," doctor din ta kalli Inteesar tace "tashi ki bita," inteesar ta mike a sanyaye ta bi bayan nurse din har sun kai bakin kofa ta juya tana kallon doctor Maryam tace "don Allah doctor kar ki kirasa wlh xae bata min rae,"doctorn tayi murmushi tace "baxan kirasa ba ki kwantar da hankalinki" bayan kusan awa daya inteesar da nurse din suka shigo da sakamakon a hannun nurse din, ta mika ma doctor maryam ta fita, doctorn ta bude takardar tana dubawa, inteesar dae kallonta kawae take ranta a hade, ba shiri taga doctor maryam ta mike tsaye da sauri tace "waw Ahmdllh, twins 4 Aliyu, Allahu akbar," ta rungume inteesar tace "Allah ya raba lfya kanwata, kinga ma yan biyu ne" inteesar ta sunkuyar da kanta da sauri hawaye ya cika idonta, hka doctorn ta dinga mata surutu cike da murna kmr ita xata haifa ma cikin, ita dae bata ce mata komai ba daga karshe ta hada mata magunguna, da allurori a office dinta ta xuba mata su a leda da takardar scan din tace "to maxa tashi ki koma gida sae ki kai masa takardar scan din, sae ya fada maki yanda xaki sha magungunan yyi maki alluran," Inteesar ta mike da sauri kmr jira take tace "ngdd ssae doctor," har gate doctorn ta rakota snn tayi mata sallama bayan ta kara jaddada mata ta hakura ta xauna da mijinta, ita dae inteesar sae gdya take mata har ta koma ciki snn ta kama hanyar titi inda xata samu tricycle, a cikin wani flower ta watsar da magungun da injectns din dake cikin ledar dake hannunta ta bar takardar scan din kawae, ta isa titi xuciyarta na suya, ta tsayar da tricycle tace "malam don Allah idan kasan ko wani asibiti a nn wajajen ka kai ni," yace "to shigo muje akwae wani can gaba," ta shiga da sauri ya ja machine din suka kama hanyar asibitin, ae ko yan goma ne a cikinta ba yan biyu ba sae ta xubar da su yau wllh . Wani babban Asibitin aka kuma kawota, ta fito tana kare ma asibitin kallo snn tace "nawa xan baka," yace "ki bada ko nawa ne," ta ciro dari biyu ta mika masa tayi hanyar gate din shiga asibitin, gabanta ya shiga faduwa ganin asibitin bana wasa bane don har yafi wanda taje da xu, tana isa reception bata tarar da patients da yawa ba aka xo kanta, nurse din tace "yhur card nmbr madam," Inteesar tace "i dnt have a card in here, nawa ne katin," nurse din tace "family card dubu biyar, na mutum daya dubu uku, na Anti natal, dubu biyu," Inteesar ta ciro dubu uku ta mika mata, matar tace "sunanki fa," inteesar tace "Fateema Aliyu," matar tace Address fa? Da date of birth, Inteesar ta bata fake address da date of birth dinta, matar ta juya ta wuce, ba ajima ba ta dawo ta mika mata katinta snn aka dubata wata nurse ta rakata da file dinta a hannunta xuwa office din doctor, yana xaune yana ta rubuce rubuce farin glass a idonsa, sae da gabanta yyi mugun faduwa don sae taga kmr ya Aliyu barin yanda ya hade rae da tsukekken bakinsa, shima kyau kam ba a magana, ta karasa office din xuciyarta na ci gaba da bugawa ta ajiye masa file din a gabansa ta xauna kan kujera a sanyaye tana kallonsa, yana ta rubuce rubucensa har lkcn bae dago ba, hkn yasa ta dan marairaice a hankali kmr me shirin kuka tace "doctor," sae a snn ya dago yana kallonta yace "srry ina dan abu ne," ya jawo file dinta gabansa ya bude, tana kallonsa a sanyaye tace "don Allah don annabi taimako naxo ka min doctor," ya dago yana kallonta yace "taimakon me fa," nn da nn hawaye ya cika idonta ta rasa me xata ce, yace "tok 2 me mana yan mata, taimakon me kike nema, baki da kudine kika xo a dubaki," ta girgixa kai ta fashe masa da kuka tace "A'a," ya kauda kansa yace "ni karkiyi min kuka a nn, ki fadi abinda ya kawo ki, mijin ki fa?" a hankali muryarta na rawa tace "ni banda miji," ya wara ido yana kallonta yace "wat? Amma kin san kina dauke da juna biyu kuwa," ta fashe da matsanancin kuka tace "ka taimaka min ka tausaya min ka cire min don Allah abinda ya kawo ni knn," yace "kina da hankali kuwa ca aka maki ana xubar da ciki a nn," cikin kuka tace "nasan ka iya doctor, ni taimakona nake son kayi don Allah," ya girgixa kai yace "me ya aike ki kanwata, meyasa kika xabi ki..." da sauri ta katsesa tace "rapin dina aka yi, kuma har yau ba a sani ba a gida," yace "innalillahi wa inna'ilaihi raji'un, to don me baki fada ba a gida" tana kuka tace "ba yrda dani xasu yi ba wlh," yace "to waye yyi maki," tayi shiru kmr me tunanin abinda xata ce nn kuma amai ne ke taso mata, ta daure tace "saurayina ne," yyi shiru yana kallonta, mikewa yaga tayi da sauri shima ya mike, yaga ta toshe bakinta ya bude mata bayi da sauri ta shiga ta fara kwarara amai, yana tsaye gefenta tausayinta ya rufesa ganin yanda take aman kmr xata shide amma bae taba ta ba har tagama ya bata ruwa ta wanke bakinta ta xuba ruwa a wajen ta fito da kyar ta xauna kan kujeran ta kifa kantakan table dinsa abun tausayi, yace "to sae mu ce ma Allah me, wllh ban taba xubar ma mace ciki ba kanwata," ta dago tana hawaye tace "plss ka taimakeni kuma ka fadi nawa xan baka ko ba yau ba xan biyaka don kudin hannuna ya kare," shi dae yyi shiru bae ce komai ba, har dae daga karshe ya mike ya fito gabanta yana kallonta yace "takardar meye a hannunki," ta kalli takardar snn tace "na scan da nayi ne," ya karba yanadubawa snn yace "Mrs Aliyu kuma aka sa," kmr xata yi kuka tace "kunya nake ji, ace bani da miji kuma gani da ciki," bae ce komai ba ya maida idonsa kan takardar yace "ya salam, yan biyu ne ae," ta gyada masa kai tana hawaye, ya koma ya xauna ya dafe kansa, yace "anya kuwa xan iya taimakon nn kanwata, rae biyu fa kuma har kusan 2mnth," ta fashe masa da wani sabon kukan tace "don Allah ka rufa min asiri," ya mike shima da ganin sa kasan jikinsa yyi sanyi, ya bude wani show glass din magunguna ya shiga xaban wasu magani har kala uku, snn ya dawo yana kallonta rike da maganin yace "amma xan maki allura a nn," kai kawae ta gyada masa tana kallonsa ya hada alluran ya juyo yana kallonta tace "ni ba kai xaka min ba ka ba nurse su min," yana kallonta yace "ok ni xan rufa maki asiri, ke kuma ki tona min nawa ko," da sauri tace "A'a wllh," ta bude cinyarta yyi mata snn ya dauko magungunan ya bata ya gwada mata yanda xata sha, tayi ta masa gdya har da kuka, nn dae yyi mata nasiha ssae akan matsalar da ta tsinci kanta a ciki, ya nuna mata ita ce me babban laifi, ita dae hawaye kawae take har yyi mae isar sa, yyi shiru, a hankali tace "to nawa xan biyaka doctor," yyi shiru yana kallonta snn ya sauke ajiyar xuciya yace "bana bukatan komai tunda ba aiki me kyau nayi ba, kawae dae nmbrki xaki bani don Allah," da sauri tace "to xan baka amma a kashe yakesae na koma gida na kunna," ta basa tsohon layinta, snn ta dada masa gdya ssae ya rakata har gate, ya koma, ta shiga ticycle xuciyarta fari tasa kmr an mata albishir da aljanna ta kama hanyar gida da magungunanta. . A gajiye Inteesar ta shiga gida bayan ta biya mai adai-daita sahu kudinsa, xaune ta tar da Safeena a falo tana cin Ayaba da gyada tana kallon American film sae kyalkyale dariya take ita daya kmr tababbiya, bata ko kalli inda safeena take ba ta haura sama da sauri gabanta na faduwa kar ta biyo ta ta ci ubanta, don mugun tsoranta take idan su biyu kadae ne a gida, in ko Aliyu na nn fitsara sae wanda bata tuna ba, dat was den, lkcin da take da lafiya knn, ynxu kam ta kanta take ba ta tsiwa ba, Safeena ta bi ta da kallon mamaki baki bude, dama yarinyar nn bata gidan ashe, shine take ta xaune kmr yar iska tana jiran jin ihunta, to ina ma taje, ranta yyi mugun baci ta kasa cin ayaban gabanta, tunawa tayi cewar tunda ta kwaso rana 1st abinda xata fara bukata shine ruwa, hankalinta ya kwanta tunanin hkn da tayi, to amma Allah yasa a fridge ruwan yake kar taga abinda ke ciki don inda sanyi baxata taba lura da komai ba, inteesar kam na shiga daki ta ajiye magunguna da takardar scan dinta a kan gado, katunan asibitin dama tun a hanya ta watsar da su, ta bude fridge dinta da sauri tana haki xata dauki ruwa ta sha taga bbu ruwa, ta yarfe hannu kmr xata yi kuka to ynxu ya xata yi ga wancan mayyar a falo taje tayi mata duka a bnxa, ta juya xata shiga bayi tasha ruwan ganin bata da wani alternative ta hango goran ruwan da safeena ta ba Aliyu ya kawo mata a bedside drawer, ta karasa da sauri ta dauki ruwan taji shi kmr ruwan dumi, bata damu ba ta kai bakinta xata sha taga abubuwa na yawo a ciki kmr an xuba kasa, idan ma baka kura ido ba baxa ka lura da hkn ba, ta dauki dayan ma tana kallon kasan ruwan ta gansu kwance ta girgije ta ga suna ta yawo, ta yatsine fuska ta isa bathroom dinta ta tsiyaye duka ruwan guda biyu a bath tub snn ta koma daki ta dauko cup ta dibi ruwa a famfo ta sha ta koma ta kwanta a gajiye, a hka bacci mai nauyi ya kwasheta ba tare da ta shirya ba, shafa cikinta da taji ana yi a hankali ne yasa ta bude idonta da sauri suka yi ido hudu da Aliyu xaune gefenta ta shiga kkrin mikewa xaune ya taimaka mata yana kallonta yace "kin ci abinci kuwa don yau na xo duba bbyna ne hope kin shirya?" ta juya ta kalli agogo da sauri taga karfe takwas na dare, mikewa tayi da sauri taje ta xubar da yawun bakinta ya rikota yace "ina xa ki," ta buge masa hannu ya saketa ta karasa bakin kofar bayin ta juya tana hararansa, magungunanta ta gani kan gadon kusa da shi, ta yo waje da ido a tsorace da ganinta kasan bata da gskya, ya tsaya kallonta yace "me ya faru," sanin cewa xae juya ya kalli inda take kallo ne yasa ta tofar da yawun bakinta nn bakin kofa da sauri ta fasa wani raxanannen ihu tana tsalle, har ya juya ya kalli ledan kan gadon kuwa ya mike da sauri ya karasa kusa da ita a rude ya riketa yana tambayarta lfya, jikinta ya dau rawa ta fashe masa da kuka tace "wayyoo cikina ke min ciwo har da kaina," da mugun damuwa yace "cikinki kuma" ta gyada masa kai jikinta na ci gaba da rawa, ya daga ta xae kwantar da ita kan gadonta ta fasa masa ihu a gigice tace "wayyoo ni ka kai ni dakinka, xafi nake ji," duk ta rikitasa ya dauketa da sauri ya bude dakin ya fita, sae kuka kuwa take jikinta na rawa, safeena dake fitowa daga dakinta knn ta bisuda kallo xuciyarta na bugawa "kai wayyoo ddi, ta sha ruwan," ko kallonta Aliyu bae yi ba, ita ko inteesar sae kuka take kmrgske, ya kwantar da ita kan gado bayan ya kunna AC yana kallonta yace "ina kika ce ke maki ciwo," a hankali tace "ya daina, wanka kawae xanyi da ruwan xafi," ya shiga bayinsa da sauri ya hada mata ruwan, yana shiga ta mike har tana tuntube ta fice daga dakin da sauri suka kusan cikin karo da safeena dake labe bakin kofa, safeena ta koma baya a tsorace tayi xaton Aliyu ne, inteesar ta watsa mata harara tace "an dae ji kunya," tayi tsaki ta bude kofar dakinta da sauri ta kwashe magungunan kan gadon ta xuba su cikin handbag dinta jikinta na rawa, tana xuba su ta fice da sauri taga safeena tsaye har lkcn kwakwalwarta a jagule to ko bashi tasha bane, inteesar ta wuce ta ta shige dakin Aliyu, dae dae nn ya fito ya tsaya kallonta da mamaki, xae yi magana ta rigasa "ruwa, amm ruwa naje sha," yana mata mugun kallo yace "get out," ta yi kmr xata yi kuka ya daka mata tsawa "ni kike raina ma hankali ko, fitar min a daki munafuka," tayi tsaki ta juya ta fice daga dakin tare da sauke ajiyar xuciya. Bata samu shan maganin ba ranar da daddare har tayi bacci don ido Aliyu ya sa mata, washegari sunday yana gida yana xaune dakinsa na'ura gabansa, safeena ko na daki kwance abun duniya ya isheta, inteesar ta gama duk abinda xata yi da kyar don xaxxabi ne ssae tare da ita, ta rufe dakinta da makulli ta ciro maganin da likitan ya bata jiya ta debo ruwa a bathroom don har lkcn ba ruwa a dakinta, ta xauna kusa da gado, ta fiffito da magungunan daga kwalayensu ta daddauki yanda yace mata, ta tsura ma kwayoyi shiddan dake hannunta ido, ita bata ma taba ganin irinsu ba, ta rumtse idonta ta xuba su a bakinta ta kora da ruwa da sauri ta hadiye su. TAMMAT ALHAMDULILLAHI.