[17/06, 03:30] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 1&2 Cikin matsanancin kuka take goge hawayen fuskarta saboda ganin halin da kakarta take ciki, gefen hijabinta ta janyo ta goge hawayenta sannan ta ce, " Dan Allah Goggo karki mutu ki barni wallahi nima mutuwa zanyi, kinsan dai duk duniya babu mai so na sai ke kowa ya tsaneni inkika mutu ya kike so nayi da rayuwa ta, dan Allah Goggo ki tashi karki tafi " Goggo dake kwance tausayin Indo ne ya kamata bata yi aune ba taji hawaye na gangaro mata daga idanunta, cikin wahalalliyar murya ta fara magana, " Indo nikam tawa taxo ƙarshe haka Allah ya tsara mana kinsan duk mai rai mammaci ne, zan barki a hannun Allah kuma a hannun Huwaila da kuma mai gari, Indo kowa da kika gani da yanda Allah ya tsara masa rayuwarsa, kuma mutanen da kika ganin kamar basa sanki suna sanki Indo soyayyarki ce da ta rufemun ido yasa ko kaɗan banasan laifin duk kuwa da ke kanki kinsan abubuwan da kikeyi ba dai-dai bane " Tari ne ya sarƙeta sai da ta jima tanayi sannan ya lafa, Indo ruwa ta miƙo wa Goggo tana ɗan ɗaga kanta ta bata ta sha sannan ta janye kofin tana maida Goggo kan fillon da take kwance. Goggo juyowa tayi ta kalli Indo ta cigaba da cewa, " Indo zan bar miki wasiyya ki zama mai haƙuri da tsoron Allah ba ruwanki da abin hannun wani ki riƙe mutumcinki dan Allah Indo ki riƙe maraicinki, ki kiyaye tsokanar da kikeyi da ɗauko magana " Indo jikinta ne ya gama sanyi sannan ta ce, " Yanxu da gaske Goggo mutuwar zakiyi ki barni ni wallahi banasan naji kina faɗan haka " murmushin ƙarfin hali tayi ta ce, " Indon Goggo kenan, maza tashi ki buɗe adaka ta cen ƙasa akwai wani ƙulli ki ɗauko shi zan miki bayaninsu " Indo jiki ba ƙwari ta tashi ta fara binciko ajiyar da Goggo ta gaya mata, cen ƙasan kaya ta hango wani ƙulli ɗaure a ɗankwali ɗauko shi tayi tazo gaban Goggo ta ajiye shi. " Kunce su " cewar Goggo, babu musu Indo ta kwance su wata takarda ta gani a nannaɗe da wasu hotuna guda biyu, jikin takardar rubutune kamar wasiƙa sai kuma wasu zobuna guda biyu na Azurfa da wani agogon maza da alama shima mai tsada ne sai wani towel yello na jarirai, kallan tsaf Goggo tai musu tana goge hawaye sannan ta cewa Indo, " Indo ki adana wannan agurinki ki riƙesu wata rana zasuyi miki rana da alama wannan waɗansu hujjoji ne da shaida amma Allah shi ya barwa kansa sani " Indo kanta ne ya kulle sam bata fahimci abinda Goggo ke nufi da ajiyar wannan kayan ba, bayan ta ɗaure cikin kayanta ta kaisu kamar yanda Goggo ta bata umarni, tana shirin zama Goggo ta ce mata, " Jeki gidan Huwaila kice tazo sai kije gidan Mai gari kice masa jikina ne ya tsananta inasan muhimmamiyar magana dashi " Indo ficewa tayi sukukuku kamar mara lafiya kai tsaye gidan Baba Huwaila ta wuce, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan, Jamilu na bakin rariya yana wanki ya ɗago kai da mamaki yabi Indo da kallo sannan yace, " Indo Sarƙa yau kuma wani salon munafurci kika ƙullo kece yau harda sallama, Allah sa ba wata tsiyar zaki shuka mana ba " fuska ba walwala Indo ta ce masa, " ka ga Jamilu yau ba da masifa nazo ba Baba Huwaila tana ciki " Baba Huwaila ce ta ɗago labule ta ce, " a'a sarƙa rikicin gangan ya jikin Goggon? " ƙasa da murya Indo tayi tace, " wallahi jikin Goggo ya yi xafi yanxu ma cewa tai na kiraki keda Mai gari " Salati Baba Huwaila ta rafka sannan ta ɗauko mayafinta dake saƙale akan ƙaure, Indo juyawa tayi kai tsaye gidan Mai Gari ta nufa, tana tafe a hanya Hanne ta tare mata hanya tana faɗin, " Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya, ke Sarƙa rannan wa kika zubarwa da ƙullin awara agurun Ɗan Bala mai Niƙa? " ta ƙarasa faɗa tana cakumar hijabin Indo da yayi jurwaye, da ƙarfin gaske Indo ta fisge ta ce, " kinsan dai Goggo bata da lafiya bana faɗa sai ta warke amma wallahi ki rubuta ki ajiye baki shaƙen wuya a banza ba bashi kika ɗauka " tana ƙarasa faɗa tana bangaje Hanne ta wuce abinta. Da Sallama ta shiga cikin gidan Mai Gari, da Baraka ta ci karo a tsakar gida wata uwar harara Baraka ta watsa mata batare da ta amsa sallamar Indo ba tana faɗin, " tauraruwa mai wutsiya..., " Indo batabi ta kan Baraka ba ta ce mata, " Mai Gari yana nan " aikuwa kamar ta watsawa Baraka Ruwan zafi a zafafe ta ce, " Idan yana nan Uban me zakiyi mai wato biyo shi kikayi har gida ko? Dama ay antsaigunta mun ance Mai Gari ya taɓa zuwa gurun munafukar Kakarki neman auren ki " Tun daga ƙasa Indo take ƙarewa Baraka kallo sannan ta yatsina fuska ta ce, " Mtsswww me akayi da wani Mai Gari me zanyi dashi ko a ƙafa aka ɗauranshi wallahi sai dai na kwance, Goggo kike cewa Munafuka ko? Wallahi bashi kika ɗauka Allah bawa Goggo lafiya zaki gane baki da wayo " Magajiya ce ta fito daga ɗakinta jin hayaniyar Indo da Baraka tana faɗin, " Wai lafiya mai yake faruwa " Indo ce tai karaf ta ce, " Magajiya Goggo ce ta turo ni gurun Mai Gari shi ne dan na tambayi Baraka take Haushi kinsanta kamar karya haka take " A zabure Baraka taxo kan Indo tana faɗin, " Dan Ubanki nice karyar wallahi ko yau sai na ci Ubanki a gidan nan " Da sauri Magajiya ta shiga tsakani tana tura Indo hanyar waje ta ce, " Jeki cen faɗa yana cen ki je ki sameshi dan Allah karkuyi mana tashin hankali " Indo juyowa tayi tayi ƙwafa sannan ta ce, " Zamu gamu dake kinsan ance sata gidan ɓarawo rance ne " tana gama faɗa tayi tafiyarta ta bar Baraka na ta sababi. Fadar Mai Gari cike take da mutane kai tsaye Indo cen ta nufa, daga gefen wata bishiya ta gefen Mai Gari ta tsaya tana shirin yin magana Musa ya kalleta yace, " To uwar ƴan marasa tarbiyya a tsaye zaki tsaya mana ƙerere zaki tsugunna ki gaida Mai Gari ko sai na fyaɗoki? " guntun tsaki Indo tayi ta ce, " Musa sai ka bari inkasa da kai sannan ka ɗauka ni ba gurunka nazo ba, kuma rashin tarbiyya ay tawa da sauƙi tunda ba haura katanga nake ba " Kunya ce ta kama Musa ba shiru yaja bakinsa ya tsuke dan inya biyewa Indo sai taita bankaɗa asirinsa gaban mutane, Mai Gari ne ya kalli Indo Yace, " Ƴar gatan Goggo me ke tafe dake " ya ƙarasa faɗa yana mata wani malalacin murmushi, kauda kanta gefe tayi tana tsuke fuska ta ce, " Dama Goggo ke san muhimmiyar magana da kai jikinta ne yayi zafi " Cikin zumuɗi Mai Gari yace, " Muje-muje Allah sa muji alheri " mutanen da ke gurun mamaki ne ya kamasu dama maganganu ɗaya biyu suna yawo agari akan cewar Mai Gari san Indo yake amma basu tabbatar ba sai yanxu da suka ga yana rawar jiki akan kiran da Goggo tayi masa. Indo na gaba Mai Unguwa da Mutanensa mutum biyu na biye da ita har suka ƙarasa cikin gidan Goggo, kai tsaye Indo tai musu iso suka shiga ɗakin Goggo. Bayan sun gaisa sunyi mata ya jiki Goggo ta kalle su ta fara magana, " Huwaila duk cikin ƙauyenan banida Aminiya tamkarki ki dubi girman Allah zan bar miki Amar Marainiyar Allah wato Indo saboda ni tawa taxo ƙarshe, Zan raba dukiya ta gida biyu zan baki Rabi ki riƙe agurinki saboda waɗansu ɗawainiya na yau da kullin da zaku dinga yi da Indo, rabi kuma zan ɗamƙawa Mai Gari ya riƙa juyawa har lokacin da Allah zaisa Indo ta samu mijin Aure ayi mata kayan ɗaki dasu " Mai Gari na jin haka wani farin ciki ya lulluɓeshi ko banza yasan zai samu tagomashin arziki saboda yasan Goggo bata da kowa a garin sai Indo kuma tana da tarin gonaki, shanu da dabbobi, Baba Huwaila hawaye ta goge ta ce, " Maryo ki daina faɗin haka cuta ba mutuwa bace " Mai Gari haɗiye murnar sa yayi yace, " Haba Goggo itafa mutuwa sai lokacinka yaxo duk tsananin ciwo idan lokaci baiyi ba sai kiga antashi " Goggo girgiza kai tayi tace, " Haka ne, Mai Gari duk wasu takarduna suna cikin waccen kwabet ɗin zaku samu komai aciki sannan.... " wani irin tari ne ya tirniƙe Goggo kafin wani lokaci har ta fita a hayyacinta, Baba Huwaila ce ke karanta mata kalmar shahada har Goggo ta samu ta biya daga nan rai yayi halinsa. Indo faɗawa kan Goggo tayi tana gursheƙen kuka mai tsuma zuciya, Baba Huwaila ma gefe taja tana goge hawaye na rashin Aminiyarta da tayi, Mai Gari kwallar munafurci ya goge yana basu haƙuri sannan ya miƙe yaje ya buɗe drower da Goggo ta nuna sannu a hankali ya fara ɗebo wasu takardu zuciyarsa fes ya haɗasu gaba ɗaya, ko Baba Huwaila bai bawa ba ya juya har zai fita ya juyo ya ce musu, " zanje in adana takardunnan kafin nan da sadaka asan abinyi, kuma zansa ayi shela na rashin Goggo azo ayi mata sutura akaita gidanta na gaskiya. _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:30] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 3&4 Daga Baba Huwaila har Indo babu wanda yabi ta kan Mai Gari shima kuma ganin a yanayin da suke yasa bai wani jira jin ta bakinsu ba ya wuce gaba Maƙarrabansa na take mai baya, kai tsaye cen gidansa ya wuce domin adana takardun daya karbo. Da sallama ya shiga cikin gidan har zuwa lokaci Baraka bata huce da haushin Indo ba shiyasama da yayi sallamar sama-sama ta amsa masa shima kuma dake zuciyarsa fes take bai tsaya jin mai ya ɓata mata rai ba ya wuce cen turakarsa ya buɗe ƙasan akwati ya ɗaga wata babbar rigarsa ya tura ciki sannan ya fito ya shaida musu rasuwar Goggon Indo, Baraka taɓe baki tayi ta ce, " Allah ya jiƙan musulmi " daga haka sabgar gabanta ta shigayi shima ya fice daga gidan. Kafin wani lokaci tuni rasuwar Goggo ta karaɗe ko'ina kasancewar Goggo mutuniyar kirki ce bata da matsala da kowa idan kaji ta da wani kuwa sai dai idan Indo ce ta yo tsokana, ita kuwa ƙara goma idan za'a kawo mata bazata taɓa bawa Indo laifi ba, amma idan ka cire wannan babu abinda yake haɗata da kowa, hasalima mace ce mai yawan kyauta ko kaɗan abin hannunta bai rufe mata ido ba hakan ne ma yasa koda ɓarna Indo taje tayiwa mutum yana zuwa idan ya faɗa a take zata ɗauki kuɗi ta biya shi abinsa. Wannan ne ya bawa Indo dama take cin karenta babu babbaka take shuka tsiyarta yanda take so tare da ƙawayenta, Zulai, Karime da Saude saboda sunsan muddun da Indo suka shuka tsiyarsu babu wani hukunci da za'a iya yi musu koda su kaɗai suka yo tsokanar suna sanarwa Indo take uwa tai makarɓiya masifar Indo ma kaɗai ta ishe ka. Ƙofar gidan Goggo cike yake da mutane kowa na jimami da ta'ajibi, daga cikin gida kuma maƙota da abokan arzikin Goggo da ƙyar suka cire Indo daga jikin Goggo saboda irin gursheƙen kukan da take yi, duk wanda yake gurun babu wanda bai tausayawa Indo ba duba da irin soyayyar da ke tsakanin Indo da Goggo, wasu daga cikin matan lokaci-lokaci suke share ƙwallar idanunsu saboda tausayinta, a haka har akayiwa Goggo wanka aka fitar da ita aka sallace ce aka miƙa ta gidanta na gaskiya. Baba Huwaila da ƴan uwanta sune suka zauna a ɗakin Goggo suka cigaba da karɓar gaisuwa har aka yi sadakar bakwai, tun ranar da Goggo ta rasu Indo ta zama wata shiru-shiru maganar kirki ma batayi daga ummm sai a'a, ko abinci ma sai Baba Huwaila ta matsa mata take iya shan kunu ko koko ko kayan sadaka bata iya sa komai abakinta, zuwa lokacin da akayi sadakar Bakwai Indo duk ta fige ta rame ta lalace kamar wacce ta kwanta ciwo idan ta ƙeɓe guri ɗaya sai dai taita share ƙwallah musamman idan ta dubi kayan sawar Goggo. Washe garin sadakar bakwai Baba Huwaila ta haɗawa Indo kayanta tsaf acikin jaka da wasu daga cikin kayan Goggo, sauran kayan danginsu gado kwanuka da dai sauransu, Sailu dillaliya tasa aka kira mata gaba ɗaya aka saida su aka bata kuɗin, Indo lokacin da zata bar gidan su tayi kuka kamar ranta zai fita ayanda takeji kamar bazata iya barin gidan ba danma tana tuno wasiyyar da Goggo tai mata amma da ko ƙasa da sama zata haɗe babu inda zata ta gwammace tayi rayuwarta ita kaɗai. Cen wani ɗakin ajiyar shirgi Baba Huwaila ta sa Jamilu ya gyara aka shinfiɗawa Indo tabarmar kaba da ƴar katifarta da ta taho da ita, daga bayan ƙaure ta ajiye jakar kayanta ta koma kan katifar ta rafka tagumi ta zubda hawaye. Ganin haka ba ƙaramin damuwa yasa Baba Huwaila ba, zama tayi a kusa da ita ta dinga lallashinta har ta samu ta shawo kan Indo tai shiru daga ƙarshe har suka ɗan fara taɓa hira. *BAYAN WATA UKU DA RASUWAR GOGGO* Har zuwa lokacin Indo ba ruwanta da sabgar kowa gaba ɗaya ta koma wata saliha da ita hakan ne yasa wasu daga cikin mutanen garin suke murba har suna ganin kamar rasuwar Goggo shi ne silar shiryuwarta bisa shaiɗancin da take shuka musu a baya, wasu kuma sai suka samu ƙofa da kafar yiwa Indo wulaƙanci da cin zarafi yanda suke so. Wata rana Indo na zaune ta gama cin ɗumamen tuwo su Zulai ne sukayi sallama Baba Huwaila na tsakar gida bayan sun gaisheta suka ce, " Baba Huwaila Indo zata ɗiban ruwa? " karaf Indo ta amsa tana fitowa daga ɗakin, " Eh zani zulai, Karime ga bokitina cen ɗauko mun mu tafi " ba musu Karime ta ƙarasa gindin tukwane ta ɗauko bokitin Indo na ɗiban ruwa, saboda gaba ɗayansu babu wanda Indo zata bawa umarni ya tsallake, haka suka jera suna tafe suna ƴan waƙoƙinsu haɗe da hirarraki. A hanyarsu ta zuwa ɗiban ruwa suka haɗu da Lantan da zuwaira su Indo ne a gaba su Lantan na baya, suna cikin tafiya Lantan ta take takalmin Indo aikuwa lokaci guda igiyoyi biyu na jikin takalmin suka tsinke Indo har tana tuntuɓe bisa tsautsayi ta faɗa kan wani dutse ta gurje hannu, cikin jin zafi ta dafe gurin tana faɗin, " wash Allah hannuna " da sauri su Karime suka rufa kanta suna mata sannu, ganin Lantan ta ɗauke kai ko ajikinta yasa Indo ta kalleta cikin jin haushi ta ce, " Ke Lantan bakya ganin abinda kika mun ko sannu bazaki mun ba " Lantan sai da ta kalli Indo sama da ƙasa sannan taja tsaki ta ce, " Hanya kika tare mun nikuma naga bazan iya ba na ƙara miki sauri " tana gama faɗa ta wuce abinta, Indo bin Lantan tayi ta kallo zuwa cen kamar wacce aka tsikara sai ji sukayi ta fashe da dariya, ita kanta Lantan sai da ta juyo tana mamakin jin dariyar Indo, lokaci guda ta tsuke fuska ta yunƙura ta tashi da ƙyar sannan ta nuna Lantan ta ce, " Ni Indo Sarƙa kika gayawa haka, wato sanyin da nayi na wasu ƴan kwanaki yasa har za'aci kashi a kaina, Lantan karki manta ko kura ta rame tafi ƙarfin gawurtattun karnuka " Lantan bata bi ta kan Indo ba ta juya tana mata waƙar habaici ita da Zuwaira suka cigaba da tafiya. Indo iya ƙarfinta ta zage ta tafi da gudu ta baya tai tsalle ta ɗane wuyan Lantan ( _kasancewar Lantan irin dogayen nan ne sosai babu jiki_ ) Lantan ba tai aune ba sai jin Indo tai akanta duk yanda taso sauko da Indo abun ya faskara gashi ta ko'ina duka take kaiwa Lantan, ganin abun bana ƙare bane yasa Zuwaira tai kukan kura ta fara kaiwa Indo duka, su Zulai na ganin haka suka fisgo Zuwaira suna duka nan da nan faɗa ya rabu gida biyu, da ƙyar da suɗin goshi Lantan ta samu ta janyo Indo kasa kusan tare suka faɗi rigija kowa sa maida numfashi yake, Lantan na niyyar kaiwa Indo duka Aykuwa Indo ta ɗau bokin Saude na ƙarfe ta rafkawa Lantan a goshi. Cikin tsananin azaba Lantan ta ƙwala ihu tana dafe gurin har jini ya fara zuba, ihun Lantan ne yaja hankulan su Zuwaira suka dakata da nasu damben cikin zaro ido suke kallon Lantan, ita kuwa Indo ko ajikinta miƙewa tsaye tayi ta fara karkaɗe jikinta ta koma ta ɗebo tsinkakkun takalmanta ta kunto ɗan kwalinta ta ɗauresu ta ɗaura ɗan kwalin ta saƙalosu ta wuyanta, bokitinta ta ɗauka ta kalli su Zulai ta ce, " Inzaku taho kuzo mu tafi inkuma jinyarta zaku zauna shikenan. " tana gama faɗa tayi gaba abinta. Jiki a sanyaye su Saude suka ɗau bokitansu suka marawa Indo baya kai tsaye burtsaten Ɗan Iliya suka wuce. Bayan fitar Indo dama Baba Huwaila shiri take akan zata je gidan Mai Unguwa dan ta same shi da maganar dukiyar Indo dan tunda Goggo ta rasu bai taɓa tunkarar Baba Huwaila da zancen yanda za'ayi da takardun gurinsa da Goggo ta ce araba biyu ba. Lokacin da Baba Huwaila ta ƙarasa gidan Mai Gari cikin sa'a ta same shi a gida, yana ganin Baba Huwaila ya tsuke fuska yana faɗin, " Baba Huwaila ce ke tafe " mamaki ne ya kamata ganin sauyin Mai Gari amma sai ta basar ta ce, " Allah ya baka nasara ni ce dama nazo muyi wata magana ne ni da kai " ɗauke kansa gefe yayi sannan ya ce, " Faɗi inajinki " Baba Huwaila kallan tsakar gidan tayi ta ce, " Allah ya taimakeka amma da mun ɗan zauna ina ganin zaifi " " Bama buƙatar zama saboda akan hanya muke yanzu haka fada zamu aka tsaida mu, faɗi meke tafe dake? " kasancewar Baba Huwaila nada matsalar ciwon ƙafa yasa ta janyo wata kujera ƴar tsugunno ta zauna sannan ta ce, " Dama naxo ne game da gadon Indo waɗannan takardun na gurinka, tunda dama marigayya kan ta rasu ta ce araba biyu abani rabi nayi ɗawainiyar Indo dasu, nikuma na duba naga koda nayiwa Indo wani abu da dukiya ta ba faɗuwa nai ba domin ko nice na faɗi na mutu Maryo zata kulamun da baya na, dan haka na yanke shawarar saida ƴan gonakin da akace abani intura Jamilu gidan Ƙanina dake birni suje ayi ciniki asaiwa Indo gida azuba ƴan haya duk shekara ana karɓar mata kuɗinta, inyaso sauran gonakin gurinka sai acigaba da yi mata noma ana ƙara siya mata kadarori dasu kaga kafin nan da ta samu mijin aure andaɗa tara abun arziki " Mai Gari wata uwar harara ya watsawa Baba Huwaila sannan ya ce, " Kin gama? To ni ban lamunci wannan tsarin da kika zo da shi ba, hasalima ko takardar tsire bazaki samu daga gurina ba bare wata takardar gonaki, ke tsohuwa abinda baki sani ba wannan takardun sun shiga Asusun mabuƙata wai kin ɗauka bansan babu wata alaƙa tsakanin Indo da Goggo bane? Kinzaci banda tarihin Goggo tsinto Indo tayi tun tana jaririya ne? To wallahi maganar nan ma idan ta sake ta kuma fita daga bakinki sai na ƙulla miki baƙin sharrin da sai kinji kamar kibar garin nan " yana gama faɗa ya kaɗa babbar rigarsa yayi gaba ya bar Baba Huwaila zaune mamaki ya mamaye ta. Ganin zaman bazai kaita ba yasa ta tashi ta fice daga gidan ko su magajiya bata yiwa sallama ba, tana tafe tana hawaye har ta ƙarasa gida zamanta babu wuya Indo ta shiga gidan tana ƴar waƙarta, " kujerar tsakar gida gun zama na mata wacce duk ta hauta......." turus tayi ganin Baba Huwaila na sharɓe hawaye da gefen mayafi, sauke ruwan kanta tayi ta ƙaraso gurunta ta tambayeta, Baba Huwaila zayyanawa Indo tayi duk abinda yake faruwa tsakaninta da Mai Gari, amma bata gaya mata cewar Goggo tsintota tayi tana jaririya ba, tana gama ji ta ƙyalƙyale da dariya da mamaki Baba Huwaila ta kalleta ta ce, " Nifa sakarcinki yasa bana san gaya miki maganaganu masu muhimmanci " Tsagaitawa da dariyar tayi ta cewa Baba Huwaila, " Dan Allah Baba Huwaila ki daina zubda hawayenki a banza Ni Indo Sarƙa na Rantse miki da girman Allah Mai Gari sai ya bada takardunan cikin ƙasa da kwanaki ƙalilan, ki barni da shi wallahi sai ya bada su kuma babu wanda zai je ya karɓa da hannunsa zai bayar " tana gama faɗa ta shige ɗaki tana cigaba waƙar, " Ahayye dawo dawayya, dawo masoyiyata dawayya.... " da idanu Baba Huwaila ta rasa Indo dashi tana mamakin maganganunta. *KACOKAN WANNAN SHAFIN NAKI NE MUM AMNASH ( MARUBUCIYAR DAFTA A'IYA💉💊) BARKA DA DAWOWA KWANA BIYU MUNYI KEWA DA FATAN KIN DAWO LAFIYA🥱.* _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:30] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 5&6 Indo har ta shiga ɗaki tai farat ta fito ta ce wa Baba Huwaila, " Yauwa Baba Huwaila nasan yanzu zakiji Sa'ar malam Sani ta kawo ƙara gurinki wallahi karki biye mata Lantan ce ta tsokane ni nikuwa na rama " Jamilu da tun farkon fara maganar Indo ya shigo gidan ya ce, " Munafuka wani abun kika aikata kenan shi ne kike kandagarki tun kafin akawo ƙararki ko? " Zumɓura baki gaba Indo tayi tana ɗauke kai gefe sannan ta ce, " Idan ma ƙarar tawa aka kawo ayba gunka za'a kawo ba " da sauri Jamilu ya ƙaraso gunta yana faɗin, " Rashin kunya zaki mun wallahi zan wanke ki da mari " Da Sauri Baba Huwaila ta katseshi, " Kai wai wane irin azzalumi ne Jamilu? Kullin baka da magana sai ta zaka mareta, to yanxu kai take gayawa ba ni take gayawa ba " Haushi ne ya rufe Jamilu yayi gaba yana cewa, " Indai indo ce ba ƴar goyo bace ina zaune zan jiki idan ta janyo miki wata masifar " yana sa kai zai shiga ɗaki yaji sallama daga ƙofar gida juyawa yayi ya nufi hanyar waje dan ganin mai yin sallamar. Mlm Sani da dogarawan Mai gari ya gani cikin sakin fuska yayi sallama yana miƙa musu hannu dan su gaisa, Mlm Sani Fuska a murtuke ya ce wa Jamilu, " Kai yaro dube mu da kyau ba gaisuwa ce ta kawo mu " Ado ne yayi karaf ya cewa Jamilu, " Shaiɗaniyar gidanku ce ta kusa ɓanɓarewa Lantan ƴar wajen Mlm Sani goshi suna cen gaban Mai Gari yanxu haka ku ake jira kayiwa Kakarka magana yanzun nan ta fito mu wuce " afili Jamilu ya furta, " Ay nasan ruwa baya tsami banza, amma ina zuwa " juyawa yayi cikin gida a bakin ƙofar soro yaci karo da Indo laɓe aykuwa batayi aune ba ya zuba mata ranƙwashi aka yana faɗin, " Almura dama nasan kame-kamen da kikeyi akwai tsiyar da kika shuka ni dama nasan wannan tuban da kikayi tuban muzuru ne bana Allah da Annabi bane " Tun lokacin da Jamilu ya damƙi hannun Indo ta fasa wata uwar ƙara da ihu kamar wacce akewa yankan naman jikinta, Baba Huwaila tun tana zaune take ƙwalawa Jamilu kira jin ihun Indo yaƙi ci yaƙi cinyewa yasa ta taso tana tafe tana masifa. " Wallahi Jamilu ka kiyaye ni da yarinyar nan tunda yarinyar nan ta dawo gidan nan ka sata gaba, yanxu abun har yakai da duka wallahi kaji tsoron Allah ka daina zalintar marainiyar Allah " Tana ƙarasowa Jamilu yayi ƙwafa ya ce, " Wallahi Baba Huwaila na ga alamar tarbiyyar da Goggo tayiwa Indo ita kike niyar cigaba da ɗorata akai " Baba Huwaila daƙuwa ta yiwa Jamilu ta ce, " Gidanku Jamilu, wato wata tarbiyya ta daban muke bawa Indon.... " daga cen bakin ƙofa aka katse Baba Huwaila ana cewa, " Wai zaku fito bane ko sai mun shigo mun ɗauke ta aka " Jamilu ne ya tasa ƙeyar Indo da take ta cika tana batsewa Baba Huwaila na biye da su. Suna fita Ado ya kalli Indo yace, " Maƙira ƙanƙanuwa da ita sai hatsabibanci yarinya kamar jikar Aljanu " Indo harara ta galla masa ta ce, " Idan ni jikar Aljanu ce sai dai inkaina Kakan nawa dan ka fini kama da siffar Aljanu " doguwar bulalar hannunsa ya tsulawa Indo a baya, yana cewa, " Shashasha mara tarbiyya da bata ganin girman manya" dafe baya Indo tayi tana susa saboda yanda bulalar ta shigeta tana shirin magana Baba Huwaila ta ce, " Kai Ado ka fita ido na rufe wallahi karka ƙara taɓa mun yarinya tunda ba wani laifi tayi ba zalincin naka da ake faɗa zaka gwada agabana " Indo da ta gama susar bayan ta ce, " Ƙaleshi Baba Huwaila wallahi shima sai jikinsa ya gaya masa Sarƙa ce fa " haka suka tafi suna yi har suka ƙarasa fadar Mai Gari. Fadar Mai Gari cike take da mutane Lantan na zaune da busassun hawaye anɗaure mata goshinta sai mahaifiyarta Sa'a dake gefe tana ta harare-harare, gefe Iyayen Zuwaira ne sai su Zulai suma da Iyayen su Goggo sallama tayi ta zauna Jamilu ya koma cen gefe yana watsawa Indo Harara, Mai Gari ne yayi sallama sannan ya kalli Indo ya fara magana, " Ke Indo mai ya haɗa ki da Lantan har kika ji mata wannan mugun raunin? " Indo kallan Lantan tayi ta murguɗa mata baki tana ƙwafa, jin tayi shiru yasa Audu ya buga mata tsawa yace, " Indo Magana ake miki " karaf Indo ta ce, " Naga Lantan ɗin ta rigani zuwa mai yasa baza'a fara tambayarta ba sai ni saboda ni aka raina? " Mai Gari kallon Indo yayi ya watsa mata daƙuwa yace, " Ke fitsararriya kalleni kinci gidanku waye ya raina ki anan gurin? Kaga Yarinya mara kunya " Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, " Allah ya baka nasara ya ƙara girma muna tafiya zamu ɗebo ruwa Lantan ta take mun takalmi har na faɗi naji ciwo da nace ta ban haƙuri shi ne ta gayan ba suga nikuwa na bita na rama tunda nima har ciwo ta ji mun, ko ba haka akayi ba Karime? " Karime tai sauri ta amshe zancen, " Eh haka ne ni har cizo na ma Zuwaira tayi garin dambe " Mai Gari ne ya ce, " Ke Lantan haka akayi " Lantan girgiza kai tayi ta ce, " Ƙarya take ni bansani ba na bige ta kawai sai ji nai ta rufe ni da duka shi ne ta ɗauki bokiti ta buga mun kaina, kuma ni ban ji mata ciwo ba.... " karaf Indo ta katse Lantan, " Kuturun uba Allah ya tsine uwar mai ƙarya wallahi Ranka shi daɗe ƙarya take " Tsawa Audu ya buga musu ya ce, " Kai karku maida mutane sa'anninku mana, Ke Indo Ina ciwon da kika ce anji miki? " Indo kamar jira take ta fiddo hannu tana nuna musu gurun data kwaile sannan ta ɗora da cewa, " Kuma wallahi ko yanxu yarinya ta kawo mun raini sai jikinta ya gaya mata " Mai Gari ne ya kalli Indo yace, " Ke Sarƙa kike ko wa? Wallahi idan baki iya bakinki ba zansa a hukuntaki yanxun nan, kuma mai yasa da ta ji miki ciwo baki zo kin kawo ƙara ba kika ɗauki doka a hannu? " " Ay wallahi nasan ko nazo na faɗa ba abinda za'ay mata sai dai ace inyi haƙuri daga haka kuma ta samu guri gaba ma abinda yafi haka zata mun " cewar Indo. Mai Gari Kallon Baba Huwaila yayi yace, " Baba Huwaila zaku biya duk kuɗin da za'a wankewa Lantan ciwo kuma duk maganin da za'a siya ku zaku saya mata, Ke kuma Indo idan na kuma samun makamancin irin wannan wallahi sai jikinki ya gaya miki " Baba Huwaila sunkuyar da kai tayi ta ce, " Na amince zan biya amma itama Lantan aja mata kunne karta kuma shiga sabgar Indo tunda bama sa'o'i bane, yoo banda ma rashin kamun kai ina Lantan ina Indo nawa Indon take ni bana san ma ta kuma takalarta harta kaisu ga haɗa ƙashi haka kawai yarinya ta dinga haɗa jiki da tsohon ƙashi " Sa'a kamar jira take ta ce, " Ahayye ay gwara mu tsohon ƙashi ne ita waya sani ma ko ta gaba da alfatiha ce shiyasa ma ta addabi mutanen gari " Mai gari ne ya buga musu tsawa sannan ya ce, " Banasan shashancin banza da wofin fada ba gurin kace-nace bane Mlm Sani faɗi abinda kake so abiyaku kuɗin magani " Indo sam bata fahimci inda zancen Sa'a ya dosa ba shiyasa ma ko kaɗan bata kawo komai aranta ba. Mlm sani kallan Mai Gari yayi ya ce, " Allah ya taimakeka abani dubu biyar ma sun isa " Indo karaf tai tace, " kambu lallai ma sai kace wacce aka cirewa ƙafa ko hannu zamu biya dubu biyar... " Jamilu daga gefe ne watsa mata daƙuwa shiyasa ta ja bakina tai shiru tana harare-harare, Baba Huwaila kallan Mlm Sani tayi ta ce, " Haba Mlm Sani wane irin ciwo aka ji mata da har zan biya dubu biyar " Sa'a ta karɓe zancen, " Wallahi haka zamu ƙarɓa ko sisi bazamu kankare ba " Indo ɗaga kanta sama tayi kamar mai tunani aikuwa tai farat tace, " Yauwa Allah ya taimakeka Ina kadarorina na gurunka da Goggo ta baka kafin ta rasu to kawai a saida gonar bayan gidan Idi mai Nama dama bata da girma abiya da ita sauran kuɗin ka bawa Baba Huwaila ta ja jari " Wata tsawa Mai Gari ya bugawa Indo ya ce, " Ke baki da mutumci ko? a yaushe Kakarki ta bani wasu takardu? Baƙin sharri zaki ƙullamun " Daga Indo, Jamliu har Baba Huwaila Mamaki ne ya kamasu, lokaci guda aka fara kus-kus kowa da abinda yake tofawa agurin, Baba Huwaila ce ta taɓo Indo ta ce, " Karna ƙara jin bakinki Indo kinji " Indo badan taso ba ta ja baki ta rufe, Baba Huwaila ta cewa Mai Gari, " A gaskiya Ranka shi daɗe dubu biyu zan bayar idan zasu karɓa shikenan idan kuma sun raina na riƙe abuna" Mlm Sani ganin da gaske Baba Huwaila take yasa ya amince gudun kar yayi biyu babu, atake Jamilu ya zaro dubu guda ya basu yace su biyoshi gida su karɓi sauran, haka Fada ta watse kowa yayi nasa gurin. Tun a hanya Jamilu ya rufe Indo da faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kamar zai dake ta har suka je gida, ganin Faɗan yaƙi ci yaƙi ƙarewa yasa Baba Huwaila itama ta fara nata bambamin faɗan, " Wai yanxu Jamilu akan naira dubu biyu ka sa Marainiyar Allah a gaba da masifa kamar ka cinyeta ɗanya, wallahi da nasan haka zakayi daka riƙe abinka tunda kasan dai nafi ƙarfin dubu biyu bare kamana san iyawa " jin irin faɗan da Baba Huwaila take yi yasa ya ɗebi takalmansa ya fice daga gidan, sai da taga ya fita sannan ta sa Indo a gaba da rarrashi tana mata nasiha akan abinda ta aikata ba dai-dai bane. *DA DADDARE* Tun yamma Indo ta zaƙulo wasu kayan Goggo waɗanda aka bata da zummar za'a rage mata su ta dinga sawa, wani zumbulelen farin hijabin Goggo na sallah ta fito dashi fili, ɗaga ƙasan filo tayi ta sasu ciki tana jiran dare yayi, ana sallar Isha'i Indo tayiwa Baba Huwaila sallama dan har saƙo ta barmata idan su Saude sun biyo mata zuwa dandali bazata ba, Baba Huwaila ba ƙaramin mamaki tayi ba najin haka amma sai tayi tunanin ko gajiya ce ta sa Indo zata kwanta da wuri. Cikin dare lokacin ƙafa duk ta ɗauke banda kukan tsuntsaye ba abunda yake tashi, alokacin ta farka daga bacci kayan wajen Goggo tasa ta ɗauko zumbulelen farin hijabin tasa, kwandon kayan kwalliyarta da shafe sati bata buɗeshi ba, ta buɗe ta ɗauko hoda ta zazzaga ta shafe fuskarta, hannu da ƙafafuwa Ludayin miyar Baba Huwaila da tun rana ta ɓoyeshi ta ɗauka ta sa a hijabi, ƴar fitilarta ta ɗauka ta fito daga ɗaki saɗaf-saɗaf ta je wajen bakin ƙofa ahankali ta zare sakata ta fice, kamar Aljana ita kaɗai ce a waje haka ta samu ta ƙarasa bayan katangar gidan Mai Gari ( _Dake gida huɗu ne tsakanin gidana Baba Huwaila da na Mai Gari_) ta kamata ta ɗane ta dirga. A hankali ta ɗaga labulen ɗakin Mai Gari ta shiga ta same shi a kwance baccinsa yake hankali kwance, toshe bakinta tayi tana dariya ƙasa-ƙasa musamman da ta tuna irin muguntar da zata yiwa Mai Gari, sai da tayi ta gama ta koma saitin kan Mai Gari ta zaro ludayin miyar ta dai-dai ci kan sa ta bashi ƙwaaal, azabure Mai Gari ya tashi yana susar gurin baya yaja ganin mutum tsaye cikin fararen kaya. Indo canja murya tayi shigen ta Goggo sannan ta fara magana, " Ni ce Goggo Kakar Indo Sarƙa nazo tafiya kai cen makwancina tunda cin Amana zakayi " Mai Gari cikinsa ne ya juya baiyi aune ba sai ji yayi ɗumi na bin wandonsa, Indo na ganin Fitsari na bin ƙafar Mai Gari ta gimtse Dariyarta ta kuma cewa.....🥱 _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ https://chat.whatsapp.com/HqkJ9DNdj356ipogZ4Sldt GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 7&8 Indo na ganin fitsarin na bin ƙafar Mai gari ta gimtse dariyarta ta kuma cewa, " Bani kaɗai na taho ba da sauran Abokan zamana muke tafe amma na dakatar dasu a tsakar gida domin aikin nawa ne " ɗan ɗingisawa Indo tayi irin yanda Goggo take tafiya tana shirin sake magana Maigari yace, " Ki dubi Allah da Muhammadu Rasulillahi Goggo karki tafi dani wallahi duk abinda kike so ki faɗa Goggo zanyi miki shi " shiru Indo tayi ta nufi hanyar bakin ƙofar ɗakin tana tafe tana ɗingiwa sannan ta ce, " Kaaaaaai karka gaya mana maganar banza ba makawa sai mun tafi da wata gaɓa daga jikinka acikin daren nan domin kaci amanar marainiyar Allah, zaɓi ya rage gareka shin ƙafarka zamun fara cira ko hannunka? Domin mu fatalwa muddun muka ziyarci mutum bama tafiya sai mun bar masa wata shaida " Mai gari kamar wani ƙaramin yaro yana jin haka ya fashe da kuka gwiwa bibbiyu ya tsugunna yana baiwa Indo haƙuri, ganin duk ya firgice ya fita hayyacinsa yasa Indo ta ce, " Munyi maka afuwa mun fasa tafiya da gaɓɓan jikinka, nemi guri ka kwanta kayi rufda ciki zamuyi maka irin alfarmarmu " Tun Indo bata rufe baki ba Mai gari yayi sufa ya kwanta jikinsa banda ƙyarma ba abinda yake yi, ganin ya juyo yana kallonta ta ce masa, " Idan ka kuma kallonmu zamu tafi da ƙwayar idanunka " aikuwa ba shiri Maigari ya sunkuyar da kansa ƙasa, Indo kusurwan bangon ɗakinsa ta kallah ta fara magana ita kaɗai, " Au Marka mai waina shigowa kika yi tafiya da Ɗan naki, ay ya nemi afuwa da kinyi zamanki inkika ce mun kina san ganinsa ba sai mu taho miki da shi ba " gaban Mai gari yankewa yayi ya ƙara faɗuwa jin an ambaci Marka mai waina, shi dai a iya saninsa Mahaifiyarsa ce take amsa sunan Marka mai waina duk cikin ƙauyensu kuma ta rasu wajen shekara guda rabi da suka wuce, juye-juye yake da kai yana san ɗagowa aikuwa Indo na ganin haka ta ce, " Marka mai waina Ƙwaƙulomin idanunsa kinga ma bawa Muzammilu mai Icce ya wuce mana dashi kafin mu ƙarasa tafiya da mutanen da ya kamata mu tsitstsinta acikin daren nan " Mai gari rintse idanunsa yayi gam yana yiwa Indo magiya da ban haƙuri, Indo fakar idon Mai gari tayi ta ɗan sunkuyo ta kuma bashi ƙwaaaal da ludayin miyar hannunta, Mai gari Zabura yayi zai tashi kuma ko me ya tuna da sauri ya koma ya kwanta yana sosa gurin. Indo takawa tayi a hankalin tana faɗin haba Ramma ya kika fara ɗaukan fansa tun bamu tafi dashi cem cikin jinsin mu ba? " Ludayin hanunta ta sa a jikin kofar langalangar ɗakin Maigari ta fara ƙoƙawa ji kake ƙiƙar-ƙiƙar sai ta sa ƙafarta ta fara buga ƙasa zuwa cen sai ta fara wani irin nishi da gurnani hmmmmmm kamar wata rago, duk inda tashin hankali ya kai Maigari yaje cen gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe sharkaf da gumi, wandonsa duk ya fitsareshi da fitsari, zura kanta tayi tsakar gida da ke da hasken farin wata ta hango wani ƙaton buhun geron Mai gari wani murmushi tayi da ta tuno irin mugunta da zata yi masa da shi idan ta kuma dawowa a wani daren, wata sanda ta hango ta zura hannu ta ɗauko tana shigo da ita da sauri ta ɗaga ta makawa Maigari a gadon baya tare da ranƙwala masa ludayin a goshinsa, a zabure ya tashi yana buga ihu da neman ɗauki cikin magiya ya fara magana, " Dan Allah Goggo ku faɗi duk abinda kuke so zanyi muku wallahi kome kuke so zanyi shi ku daina azabtar dani dan Allah kuyimun rai " Indo na daga gurin da take ta fara bubbuga hijabinta kamar mai shirin tashi sama tana wani irin ɗan gurnani, sannan ta ce masa, " Zamu koma makwancinmu amma ka sani zamu ƙara dawowa, zamu baka saƙo idan ka wani gari gobe duk wanda ka gayawa abinda ya faru abakin ranka, tashi ka shige ƙarƙashin gado har sai anyi assalatu sannan ka fito " tun bata rufe baki ba Maigari ya ɗaga zanin gado ya shige ciki dake irin kadon ƙarfen nan ne mai rumfa. Indo fitowa tayi daga ɗakin Mai gari alokacin Baraka ta fito hannunta ɗauke da buta ihun Maigarin da taji ne ya tashe ta, sam bata kawo Maigari bane tayi tunanin ƴan kwamati ne suka kama ɓarayi, mutum ta gani da farin hijabi da sauri taja baya ganin haka yasa Indo ta ce, " bururururu bum bum bum bum kuzo maza ga wata ta fito ku janyota mu tafi da ita " Baraka sakin butar tayi ta koma ɗaki da gudun gaske tana banko ƙofa. Indo na ganin haka ta tsugunna ta fara tafiya da rarrafe tana tafe tana baza ƙasa dan gudun kar aga sawun tafiyar mutum da safe asirinta ya tonu idan zata ƙara komawa. Tun ta da samu ta kama katanga ta dirga take tafe tana waige kamar mara gaskiya, da sauri ta samu ta tura ƙofar gidansu ta shiga buta taci karo da ita a ƙofar ɗakin Baba Huwaila da sauri ta ɗauka ta fara wanke fuskarta da hannuwanta xuwa ƙafarta, tana gamawa ta faɗa ɗakinta kan katifa ta fashe da dariya, Indo dariya take yi harda riƙe ciki sai da tayi mai isarta sannan ta kwashe kayan Goggo ta cusa cen cikin jakarta ta koma ta kwanta. *A CEN GIDAN MAI GARI* Tunda Maigari ya shige ƙarƙashin gado ko motsin kirki ya kasa yi, lokacin da yaji Indo ta buga ƙara tana cewa a tafi da Baraka luff ya ƙarayi gabansa na dukan uku-uku, yanda yaga rana haka ya ga ƙarshen darensa, har akayi Assalatu Maigari kasa fitowa yayi saboda yana gudun kar ya fito ya kuma gamuwa da fatalwar Goggon Indo. Baraka ma na shiga ɗaki ta banko ƙauren ɗakinta ƙarshen gado ta koma tana maida numfashi dan ita a zatonta gamo ne tayi da aljanu cikin dare, fitsarin da bata yi ba kenan har akayi Assalatu. Magajiya jin shirun Maigari yayi yawa bai fito sallar asuba ba yasa ta ƙaraso ɗakinsa tana ɗaga labule, cikin mamaki take bin ɗakin da kallo duk a hargitse ga ƙaramar katifarsa nan ta ƙasa duk a yamutse, tsoro ne ya kamata ganin ba Maigari babu motsinsa, cikin ta'ajibi ta fara magana, " To yau lafiya ni banji motsin malam ba kofa Sallar asuba banji ya fito ba " daga cen ƙarƙashin gado Maigari ne yake ɗan ɗago zanin gadon yana leƙe hango Magajiya da yayi a tsaye yasa ya yunƙura ya fito da ƙyar gaba ɗaya jikinsa yayi tsami, da mamaki tabi Mai gari da kallo tana faɗin, " Lafiya kuwa Malam naga ka fito daga ƙarƙashin gado? " Mai gari basarwa yayi yana murtuke fuska ya ce, " Ke Magajiya banasan shashancin banza da wofi ko a yaya aka samemu sai antambaye mu dalili ne? Ki kama bakink fa naga kwana biyu kinaji da rashin kunya " Magajiya bakinta ta tsuke ta juya zata fita sannan ta ce, " Allah ya baka haƙuri ya huci zuciyarka " Mai Gari yana ganin fitarta ya riƙe ƙugu yana sunkunyawa da alama bayansa ciwo yake masa, sai da ya fara zuro kansa ya leƙa ko'ina sannan ya samu ya ɗauki buta ya nufi hanyar banɗaki. Baraka jin motsin Magijiya a waje ne yasa ta yi ta maza ta fito amma har lokacin bata saki jikinta gaba ɗaya ba, tana nufar hanyar banɗaki ta hango Maigari tsugunne abakin rariya yana kama ruwa, riƙe baki Baraka tayi tana faɗin, " Malam yau me nake gani a idona kaine tsugunne a bakin rariya kana kama ruwa " Mai gari baibi ta kan Baraka ba yana gamawa ya zare wandon jikinsa ya ajiye a gefe ya kalleta ya ce, " Ga wancen kayan ki wanke mun su idan kinyi sallah bari na ƙwaɓo na jikina na haɗo miki da su " Da ido Baraka ta raka shi cike da takaici take kallonsa, banɗaki ta faɗa tana fitowa ta samu ya kawo mata ragowar kayan daya cire ta sameshi tsaye a da bokiti a hannu, juyawa tayi ta kalli kayan wani ɗan bashi-bashi taji yana tashi ta kalli Maigari ta ce, " Wai Malam mai ya samu kayanka ne har kake san a wanke maka su da farar safiyar nan wallahi ni wani bashi-bashi ma naji sunayi " A ƙufule Mai gari ya ce, " Ke saboda baki da mutumci dan na baki wanki har sai na gaya miki dalilin da ya sa na baki wankinsu, ki kiyaye ni fa " yana ƙarasa faɗa ya fa ɗa banɗaki domin wanke jikinsa, mita ta farayi ƙasa-ƙasa sannan ta wuce ɗaki, Mai gari ruwa ya watsa ya wanke jikinsa ya ɗauro Alwala ya koma ɗaki dan gabatar da sallar Asuba. Maigari tunda ya idar da sallah tunanin duniya ya addabi rayuwarsa, tunda ya zauna a ɗaki yake saƙa da warwara musamman idan ya tuna cewar fatalwa tace kar ya sanarwa da kowa abunda ya faru kuma wai zasu dawo gurin sa, tunowa yayi harda fatalwar mahaifiyarsa Marka mai waina da ta Muzammilu mai icce, hawaye ne ya fara gangaro masa na tausayin kansa da yake yi, kansa tun cikin dare banda raɗaɗi babu abinda yake masa hannu ya kai ya shafa gurun sai ji yayi kansa zuwa goshinsa sunyi wasu manyan Ƙullulai, sauran Robb ɗinsa ya ɗauko ya fara bi yana shafawa sannan ya ɗauko hularsa ya saka ya janyo rawaninsa ya ɗaura duk dan gudun kar matansa su gani su fara jefo masa tambaya. Baraka ce ta fito tana gayawa Magajiya irin mugun gamon da tayi cikin dare har fasaltawa Magajiya irin shigar da ta ga aljanar dasu tayi da maganar da aka gaya mata na cewar za'a tafi da ita, Mai gari najin haka cikinsa ya kuma ɗiban ruwa wani irin ƙugi yaji cikin yayi masa, da sauri ya tashi ya tafi banɗaki domin ji yake kafin yaje gudawar da take cinsa zata iya zubowa, daga Baraka har Magajiya binsa sukayi da kallo sai da suka ga ya wuce suka fara kus-kus ƙasa-ƙasa. Baraka ƙarasawa tayi ta far duba kayan da zata wanke ganinsu jiƙe da fitsari da ƴar gudawa yasa ta yafito Magajiya da hannu tana nuna mata, badan ranta yaso ba haka ta fara wanke su cikin ƙyanƙyami, magajiya banda dariya ba abinda take yi tana faɗin Allah ya tarfawa garinta nono ba ita ce da girki ba da tuni ita zata wanke su, Maigari na fitowa ya hau muzurai yana tsuke fuska dan gudun kar su fara tambayarsa yana tafe yana bubbuɗawa har ya ƙarasa cikin ɗakinsa ya rafka uban tagumi. Indo da ƙyar da iya tashi sallar Asuba saboda baccin da yake addabarta tana yin sallar kuwa ta koma ta ƙara kwanciya, ba ita ta tashi ba sai wajen tara saura, wanke idanunta tayi Baba Huwaila ta zuba mata abinci sai da ta ci tayi ƙat tana gama cin abinci ta haɗa kayan wanke-wanke ta wanke su sannan ta ɗau bokitin ɗiban ruwa ta wuce gidan su Karime, a hanya suka haɗu da Jamilu kamar bata ganshi ba haka ta ɗauke kanta zata wuce, fisgota yayi ya riƙe kunnenta sannan ya ce, " Idan kinje ɗiban ruwan dan Allah karki dawo akan lokaci yau inkinje ki cire kan ƴaƴan mutane tunda jiya goshi kike fashewa lantan " ya ƙarasa faɗa yana zuba mata ranƙwashi, da sauri ta fisge tayi gaba tana yimai Allah ya isa. Cikin Arashi aka wani gari da rasuwar wani maƙocin su Indo Malam Haruna mai wankin hula, katangar gidansa ta baya tana jikin ta gidan Maigari lafiya kalau aka kwanta da mutumin ya wayi gari da Amai da gudawa zuwa safiya kafin akaishi asubiti rai yayi halinsa, lokacin da labarin ya isa kunnen Mai gari har ya shirya yana shirin fita fada duk da baya jin daɗin jikinsa amma haka ya daure gudun kar wani ya harbo jirginsa, Maigari na jin mutuwar Malam Haruna wani irin azababban gumi ne ya yanko masa take cikinsa ya karta kafin ya isa banɗaki har ya fara ɓata wandonsa. MORE COMMENTS.......🥱 _ASEELA FANS NASAN ANATA ZUBA EYES TO AMUN UZURI ZUWA SALLAR MAGRIBA._ _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 9&10 Tsoro ne ya kama su baraka musamman da sukaji labarin amai da gudawa ne ya kai Malam Haruna mai icce ƙasa, gasu sunga mijinsu sai zarya yake tun safe, bayan Mai gari ya fito yana tafe tana tamke fuska, ɗakinsa ya koma cen kan katifarsa ya faɗa ki kake rigija saboda gaba ɗaya jikin Mai gari ya saki, Magajiya da baraka ne suka shiga ɗakin duk yanayinsu ya nuna suna cikin damuwa. Guri suka samu suka zauna kallon kallo suka farayiwa junansu anrasa wacce zata fara magana, ɗagowa yayi da kansa ya kallesu yace, " Lafiya kuka zo kuka tsare ni da idanu? " Baraka ce tai ƙarfin hali tace, " Malam ga dukkan alamu yau baka wayi gari da daɗin jikinka ba, shine mukazo muji me yake damunka? " tun kafin ta gama ya fara watsa mata harara sannan yace, " Uban waye yace muku bani da lafiya? Wato duk wani motsina akan idanunku nakeyi ko, ku tashi ku bani guri tun ranku bai ɓaci ba " Magajiya da Baraka haka suka fice suna jin haushin wannan hali irin na mijinsu. Indo gidansu Karime ta biya suka fito suka wuce gidansu Zulai daga nan suka wuce gidan su Saudai suna tafe suna hira Indo sai da ta waiga hagu da dama sannan ta fara bawa su Karime labarin abinda ya faru, aikuwa mai zasuyi ba dariya ba harda hawaye, Zulai ce ta cewa Indo, " Dan Allah Sarƙa inzaki koma ki tafi dani nima ayi Dramer dani " Indo jim tayi sannan ta ce, " Idan kina da farin hijabi sai muje amma fa yau bazan koma ba dan kar ya gano ni bari zamuyi sai ya fara sakin jikinsa tukunna sai muje masa, mu bari zuwa nan da jibi ko gata " Su Saude ma cewa sukayi baza'a barsu a baya ba suma zasu je, Indo wani tunanin faɗa zuwa cen ta saki murmushi ta ce musu, " Gaskiya na fasa kowa ya nemi riga da wano na yadi ko shadda amma fa waɗanda suka muku yawa, nima zan ɗauki na Jamilu insaka kunsan Malam Haruna ne ya rasu inda mukayi shigar maza sai muje a zuwan Haruna ne ya taso da jama'arsa " shawar Indo ba ƙaramin daɗi tayi musu daɗi haka suka cigaba da hira har suka ƙarasa gurin ɗiban ruwan. Bayan sun ɗebo ruwa suna tafe suna hira a hanya Indo tai farat ta ce, " yauwa Zulai muje zan biya ta gidan Mai gari inga halin da yake ciki " ba musu kuwa maimakon duk su wuce gida suka tafi gidan mai gari, a ƙofar gida suka samu Ado tun baya wani lokaci da ya tura agayawa mai gari yana jiransa zuwa sallar jana'izar Malam Haruna, ganin su Indo yasa yaji daɗi cikin sakin murya yace, "a'a Indo ciki zaki shiga ne " caraf ta amshe zance, " eh zamu je gun Magajiya " da sauri yace, " dan Allah idan kun shiga kuce yallaɓai kawai ake jira " Mirmushi su Inso sukayi saboda tuno muguntar da zasuyiwa Mai ugari. Da sallama suka shiga cikin gidan Baraka ciki-ciki ta amsa musu hango ƙofar ɗakin mai gari sukayi labule a ɗafe, kallan juna sukayi suna murmushi. Indo ce ta leƙa ɗakin Magajiya bayan sun gaisa suka ce, " oh magajiya ya haƙurin Mlm Haruna naji ance ya rasu mukace bari muxo mu miki gaisuwa tunda ance tsohon mijin ƙanwarki ce Rabi " nan suka jajanta wa juya Indo ta kalli baraka ta ce, " yooo ni jiya ko da so akayi a tafi da Baba Huwaila nifa a tsakar gida na dinga jin muryar fatalwu suna yawo wai sun fara ɗauki ɗai-ɗai ne duk wanda suka je masa ido da ido ya gansu to shi ne sahu na gaba " _KUYI HAKURI DA WNN BA YAWA_ _FATAN AKHERI GAREKU MASOYA NAGA COMMENTS ƊUNKU INA GDY._ _Ummou Aslam Bint Adam_😉 *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 11&12 Hantar cikin Mai gari ce ta kaɗa take yaji wani azababben gumi ya keto masa cikin zuciyarsa yake faɗin, " Au watalwoyin nan ba gidan nan kaɗai suka xo ba? " Indo kamar tasan mai yake zuciyar Mai gari ta cigaba da cewa, " Gashi nan dake Allah yayi Mlm Haruna yana hanya sun tafi dashi " Magajiya ce tai murmushi tace, " Ke Indo daɗina dake shirme wa yace miki fatalwa tana ɗaukan ran mutum kowa kikaga ya mutu lokacinsa ne yayi " Baraka zaburowa tayi tace, " Barta mana Yaya ay kinsan Sarƙa da mugun baki mu da ke suka ɗauka ma da kowa ya huta da sheɗancin ki " ta ƙarasa faɗa ta watsawa Indo harara. Indo wata shewa tayi ta ce, " Ahayye sai kuma basu tafi dani ba, to ay naji Laure ƴar gidan Mlm Haruna ta ce ta leƙa ta windo ta ga fatalwa ɗaya da fararen kaya a cikin tsakiyar dare " Baraka tsai tayi da tunani tana nazari tunowa tayi da gamon da tayi sai kuma tsoro ya fara kamata, ƙasa tayi da murya tace, " Sarƙa nifa makircinki tsoro yake bani dan Allah da gaske kike Laure ma ta ga fatalwar " tsuke fuska Indo tayi tace, " Au kina nufin ƙarya zan miki Saude ba tare aka bamu labari ba? " Saude tai sauri tace, " Eh man kin tuna ta ce fatalwar ma kamar ta matattun layin nan ce " ba Baraka ba hatta Maigari tsumu yayi a ɗaki, Indo gaba tayi cen ƙofar ɗakin Mai gari ta ce, " Allah ya baka nasara barka da hutawa, dama daga ƙofar gida ne ake sallama da kai za'a sallaci Mlm Haruna " Da ƙyar ya yunƙura ya tashi saboda gaba ɗaya jikinsa ba ƙwari, murya ba kuzari ya cewa Indo, " barka dai, kije ki ce masa muna zuwa " Indo tashi tayi tana ƙarewa Ƙeyar Maigari da goshinsa yanda yake ta ƙyalli, Baraka tunda taji batun Fatalwa ta shiga taitayinta gaba ɗaya jikinta yayi sanyi. Su Indo bokitan ruwa su suka ɗauka suka fice suna gimtse dariyar da ke cin su. Mai gari ta maza yayi ya yunƙura ya fita kai tsaye cen ƙofar gidan Mlm Haruna suka wuce zuwansu keda wuya aka fito dashi, Mai gari haka ya ɗinga nesa-nesa da Makara lokacin sa aka zo tafiya da ita maƙabarta zame jikinsa yayi fiiiit ya gudu gida. Bayan kwana biyu bayan sallar la'asar Su Zulai ne zaune a ɗakin indo suke hira ƙasa da murya Indo tayi ta ce, " Ke Karime leƙa mana tsakar gida kiga Baba Huwaila da Jamilu basa nan? " Karime leƙawa tayi ta dawo ta ce, " Babu kowa " Indo ce ta fara magana, " Yauwa kuna ji na yau da daddare ku shirya zan biyo muku tunda wajen kwana huɗu kenan Mai gari na hutawa, amma wallahi duk wacce ta ɓatamun shiri sai ranta ya ɓaci, kuma kowannen ku ya nemi kayan yayansa namiji ko na babansa ya saka kuma ku baɗe fuskokinku da farar hoda " Saude cikin damuwa ta ce, " Nidai gaskiya Indo banda farar hoda sai ja " Saude ma ta ce, "Wallahi nima haka " Indo janyo kayan kwalliyarta tayi ta yagi leda ta shiga zazzaga musu ta ɗaure ta miƙa musu ta cigaba da cewa, " Kuma kowanne ya taho da ludayin Innarsa " da kallan mamaki suka kalleta ta gyaɗa kai ta ce, " ƙwarai kuwa yanxu dai idan mukaje duk abinda kuka ga nayi kuma kuyi, Ke Karima ay nasan zaki iya kwaikwayon muryar marigayya Mai waina babar mai gari " gyada kai karime tayi Indo ta cigaba da cewa, " Ku kuma duk abinda nace kuyi a lokacin sai kuyi " amsa mata sukayi sannan suka cigaba da tsara yanda zasuyi. Bayan tafiyar su Karime Indo ce ta faki idon Baba Huwaila ta faɗa ɗakin Jamilu cen ƙasan kayansa ta zaluƙo wata Jallabiyyarsa, sum sum sum ta fice tayi nata ɗakin zuciyarta fal farin ciki. A ɓangaren Maigari kuwa a ranar da ya wayi gari da tashin hankalin fatalwa da dare yayi fir ƙin kwana yayi a ɗakinsa ya koma bin ɗakuna, ganin babu abinda ya kuma faruwa ya tattara ya koma cen ɗakinsa da kwana. Cikin dare Indo ce sanye da jallabiyar Jamilu da tayi mata yawa sai jan ƙasa take, hannuwa ma duk sun zazzago saboda tayi mata yawa, wannan karan farin hijabinta ta nannaɗe tayi rawani dashi, a hankali ta tura ƙofa ta dafa katangar gidansu Saude ta dire, ɗakin kwanansu ta leƙa ta lallaɓa ta taso ta, Saude kamar jira take zumbur ta tashi ta shirya suka fice haka suka dinga kama katangu suna biyawa sauran ƙawayen su, daga ƙarshshe suka dangana da gidan Mai Gari. Lokacin da suka shiga ɗakinsa yana kwance bacci yake harda munshari, zagaye shi sukayi Indo ce ta zaro ludayinta daga Aljihu suma sauran cirowa sukayi, kusan lokacin guda suka saita kan Mai gari suna bashi Raaaaaallll. _Ummou Aslam Bint Adam_😉 *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 13&14 Mai gari jin yayi kansa ya ɗaure lokaci guda ga wani irin raɗaɗi da azabar zugi da ya dabaibaye shi, a zabure ya miƙe tsaye saboda ruɗewa da gudu ya ɗane gadon ƙarfen shi yana salati da salallami bisa tozalin da yayi da mugun gamo, Karime hannu biyu tasa ta toshe bakinta saboda yanda dariya ta taho mata Indo ce akan gaba ta fara takowa tana tafe tana zaro harshe tana karkata kai tana wani irin far da idanu, kamar yanda suka ga Indo nayi suma haka suka mara mata baya suna yin irin abinda take yi, Mai gari ilahirin jikinsa rawa yake gumi ne ta ko ina yake keto masa cikin tashin hankali ya ƙara matsawa cen ƙarshen gado yana hakki, Indo wata irin dariyar basawa tayi sannan ta canja murya zuwa ƙatuwar murya irin ta maza ta fara magana. " Mu jinsin Fatalwa muna maraba da zuwanka cikin mu domin a daren nan zaka ƙarasa rayuwarka acikin mu " ta ƙarasa faɗa tana wani irin jijjiga kai. Mai gari baisan lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba yana roƙonsu, " Dan Allah kumun rai ku agaza mun ku gayamun duk abinda kuke buƙata zanyi muku, wallahi ko dukiyata kuka ce zan iya kwashewa duka na baku, nidai ku agaza mun ku daina wahal dani dukan rannan ma da kuka mun har yanxu ban warware ba " ya gama maganar yana goge majinar da take ta tsiyaya tun fara kukansa. Saude ce tayi karaf ta ce, " Ay yanda muka fara azabtar fa kai akanka har sai kan ya ruɓe ya faɗi da kansa sai awayi gari ka mutu " Indo daɗin maganar Saude taji har cikin ranta ta karɓe maganar Saude da, " Ay yanda muka cinyewa Malam Haruna kayan ciki ya dinga amai da gudawa kaima haka zamu fara cin ƙwaƙwalwarka har sai idanunka sun daina gani wuuuuuuuu garaaaraaaaraaaaa " Indo kamar wata ƴar bori haka ta fara wasu irin surutai tana bige-bige, suma su karime haka suka fara yi basu jima ba suka daina yi Indo ta bugawa Maigari tsawa ta fara magana, " Kaaaaaaaai sauko ƙasa ko mu rufta ka ƙarƙashin ƙasa kaida gadon da kake kai " Indo tana rufe baki Maigari ya duro ƙasa ya durƙushe a gabansu, tsakiyar kansa ta kuma daidaita ta bashi ƙwal da ludayi, cikin tsananin azaba Mai gari ya kwarara ihu yana cewa, " Magajiyaaaaaa Barakaaaaaa ku taimaka zasu kashe ni " daga cen ɗakunan su suna bacci suka jiyo ihun Maigidan nasu azabure suka fito kusan lokaci guda suka fito tsakar gida, sai dai daga nesa suka fara hango mutane da fararen kaya, Jin motsin fitowarsu yasa Indo ta ce, " Ku miƙomin Likafanin infara ɗaura masa inmuka gama dashi sai mu koma gun matansa, dama Baraka munyi arba da ita tun zuwanmu na farko " Su Magajiya har gware suke wajen shiga ɗaki da ƙarfin gaske kowacce ta banko ƙofar ɗakinta. Maigari cikinsa ne ya karta jin abinda suka ambata ko alamun gudawar baiji ba sai jin ɗumi yayi yana bin wondonsa, wannan karan kasa magana yayi sai hannuwa biyu da ya haɗa guri ɗaya yana roƙonsu, Zulai ce ta fara magana, " Alfarma ɗaya ce zamu yi maka duk wani kayan marayu da suke hannunka ka tarkata ka mayar musu da abinsu inba haka ba kullin zamu dinga azabtar da kai kafin mutuwarka " Bakin Mai gari har rawa yake ya ce, " Ko yanzu kuka ce a shirye nake na kai musu kayansu nidai kumun rai ku daina azabtar dani " lokaci ɗaya suka fara wata irin dariyar basawa kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka kuma bashi ƙwal ƙwaƙwaaaal da ludaya akai, sannan Indo ta ce, " Kuma a sharaɗinmu duk marayun da ka mayarwa suka ƙi karɓa to wanda suka rasa zamu turo cikin dare ya karɓi abunsa, misali idan babansu ne ya mutu ka kaiwa iyalansa suka ƙi amsa shi mammacin ne zai taso cikin dare ya karɓi abunsa. " banda gyaɗa kai ba abinda Mai gari yake yi gefe ɗaya kuma yasa hannuwa biyu ya dafe kansa yana tsoron jin wani dukan. Indo ce ta buga mai tsawa ta ce, " Tashi ka shige ƙarƙashin gado karmu ganka a waje har assalatu " da rarrafe ya tashi zai shige Indo ta kuma cewa, " Au bayan gari kayi a wando aykuwa zamu sakar maka shi nan gaba ka dinga sakinsa kamar yanda tumaki suke yi " Mai gari juyowa yayi zaiyi magana ta buga masa tsawa da sauri ya shige ƙarƙashin gado yana haki. Kamar yanda Indo tayi a ranar zuwanta na farko yanxu ma haka suka fara tafiya da rarrafe, suna zuwa bakin ƙofar Baraka Indo ta sa hannu ta buga da ƙarfin gaske tana cewa, " Itama ta nan ɗakin wa'adinta ya kusa zuwa na gaba da ita zamu tafi " wucewa sukayi suka je suka kama katangu suka ɗane suka fice daga gidan. Suna fita suka fara tuntsirewa da dariya harda riƙe ciki, daga cen nesa suka ga hasken fitila ƴan ƙwamiti na buga musu tsawa, da gudu wacce ta tafi ta faɗa gidajensu. Washe gari gaba ɗaya jikin Mai gari ya rikice ko motsin kirki ya kasa yi sai sauke wahalallan numfashi yake yi gudawa na fita ba ƙaƙƙautawa, a ɓangaren su Magajiya gaba ɗayansu rasa wanda zai fito sallar asuba akayi sai da gari ya waye sosai har masu tallan Ƴar tsala sun fara kawo musu sannan Magajiya tayi ra maza ta fito tayi alwala Baraka ma lokacin ta samu ta fito tayi alwala amma gaba ɗayansu kowa a tsorace yake, sai da sukayi Sallah sannan suka koma ɗakin Maigari don su ga halin da yake ciki, tun daga tsakar ɗakin suka fara hango Ƙudaje yamama har zuwa ƙarƙashin gado, leƙawa sukayi tsoro ne ya kamasu haɗe da tashin hankali ganin halin da Mai gari yake ciki, janyo shi sukayi suka fito dashi suna zaunar dashi ya tafi ya faɗi yaraaaaf, kuka suka fasa alokaci guda musamman da suka ga idanunsa na tafiya luuuuuuuuuuu kamar yana suma, da sauri suka cire masa kayan jikinsa suka gyara shi, Magajiya ce ta fita ta sanarwa da fadawan Mai gari, da sauri suka bazamo suka xo cikin gidan alokacin Mai gari banda sumbatu ba abinda yakeyi, kurar ruwa aka samo aka shimfiɗa tabarma da filo aka sanya mai gari aciki, kai tsaye aka tura shi aka wuce Asibitin gangare dashi. *MY LVLY SIS INA JIN DAƊIN COMMENTS ƊINKU DAN ALLAH DUK WANDA YAYI COMMENTS RANNAN ZUWA YAU INBANYI REPLAY BA AMUN AFUWA NAYI BUSY NE TYPING ƊINMA KAWAI INA DAGEWA NE, IYA WUYA ANA TARE.*🤸🏼‍♀️🤸🏼‍♀️ _ASEELA FANS HOW MARKET?_🤭😛😛😛 _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 15&16 _KUYI HAƘURI BAN TACE SHI BA_🤭 Lokacin da suka ƙarasa Asibitin gangare Mai gari ya daɗe da daina gane mutane, duk inda tashin hankali yaje su Baraka sun kai cen, Magajiya ce ma take ɗan tausarta tana bata bacci, cikin jin haushin maganar Magajiya ta ce, " Eh ay dama ce Yaya bakida matsala koda Malam mutuwa yayi saboda ƴan matanki biyu duk kin aurar dasu babu ke babu ɗawainiyar marayu, nikuwa fa kina gani Hasiya ko shekara biyar cika ba ga Ɗahiru mai shekara biyu ay dole nayi kuka " ta ƙarasa faɗa tana rushewa da wani kukan, Magajiya maganarce ta bata haushi aykuwa cikin hassala ta cewa Baraka, " Yoooo Allah na tuba ɗa ay baifi ɗa ba yanda kike taƙamar Malam ubansu ne suma su Sadiya ay ubansu ne kuma nida su sai munfi ki jin rashinsa tunda ni da kika ganni tunda jajayen sawu na muke tare da shi sai ke mai shekara shida dashi zaki nunamun san iyawa, gwana ta gwanaye kinfini shaƙuwa da shi ne? " Gama maganar Magajiya kamar ta watsawa Baraka wuta aykuwa atake suka fara cacar baki kowaccensu zuciyarta a wuya, Sai da au Ado suka sasanta sy tukunna, Lokacin da suka isa Asibitin Nurses biyu kawai suka samu aciki Amma likita bai ƙaraso ba kasancewar dama likita guda ɗaya ne acikin asitin sai Nurses da suke taimaka masa, Gado aka bashi su Ado ne sukayi ƙoƙari suka ɗorashi akai Mai gari banda idanu da yake binsu dashi ba abinda yake iya taɓukawa. Dudduba shi suka fara yi sannan suka sa masa ruwa da Allura kafin babban likitan ya ƙaraso yayi masa duk abinda ya dace, cikin Alluran da akayiwa Mai gari harda na bacci domin ya samu hutu dan yanda suka lura kamar gaba ɗaya jikinsa babu ƙwari. A cen ɓangaren Indo bayan da gari ya waye Baba Huwaila shirun Indo taji yayi yawa, ɗakin nata ta bankaɗa tana ƙwala mata kira, Indo cen cikin bacci ta fara jiyo muryar Baba Huwaila tana mata magana, juyi tayi ta ƙara gyara kwanciya tana cewa, " Baba Huwaila dan Allah ki barni na matse kaina har ya fara sarawa tashin da kika mun " Baba Huwaila sakin labulen tayi tana faɗin, " Indo koea rai yayiwa daɗi baya mai shi ba dama tashinki nayi naga hantsi har yayi baki karya ba, idan taki ta kawoki ina zaune zaki neme ni " Jamilu ne ya shigo da sallama jikinsa a sanyaye, ganin yanayinsa yasa Baba Huwaila ta fara tambayarsa, " Kai Jamilu lafiya naga ka shigo mun a saluɓe kamar ɗan autan kunkuru? " Zama yayi akan turmi yace, " Inna Inafa lafiya naje Shagon Iro ina hanyar dawowa naga anwuce da Maigari acikin kurar ruwa ba lafiya da alama ma baya cikin hayyacinsa dan banda sumbatu ba abinda yakeyi, lokacin da su Ado sukemun bayani sai barin wasiyya yake, kai gaskiya jikin Maigari fa sai Allah kawai Inna " Salati Baba Huwail ta rafka tana faɗin, " To Allah gamu gareka rannan munyi rashin Malam Haruna ga kuma Maigari amma kuma cuta ba mutuwa ba " Indo dake kwance tana jinsu cikinta ne ya karta gabanta yau faɗuwa, zumbur ta miƙe tsaye tana mutstsika idanu lokaci guda duk tayi fiƙi-fiƙi, farat sai gata a tsakar gida ba tsammani ta jefowa Jamilu tambaya, " Yaya Jamilu amma dai kaga yana numfashi ko? " hararara ya watsa mata sannan yace, " Idan baya numfashin wani zaki busa masa? " murguɗa baki gefe tayi ta ɗauke kai gefe tana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa duk kuwa da har lokacin gabanta bai daina faɗuwa ba. Suna nan tsakar gida suka ji sallamar Karime da Zulai, Indo na ganinsu ta fara ƙifta musu idanu, gaida Baba Huwaila sukayi da Jamilu sannan suka cewa Indo, " Indo zaki ɗiban ruwa? " karaf Baba Huwaila ta karɓe da, " A'a gaskiya tashinta kenan daga bacci ko karyawa batayi ba..." Indo katse Baba Huwaila tayi, " Baba Huwaila bari naje idan na ɗebo naci abincin " tana gama faɗa ta wuce cen bakin randa ta ɗau bokitinta, hijabinta dake kan ƙaure ta zara ta ɗora akan kafaɗarta suka nufi hanyar fita, Jamilu da tun ɗaukan hijabinta ya bita da kallo yaga iya gudun ruwanta ne ya buga mata tsawa yana faɗin, " Ke rasa kunya haka zaki fita babu mayafi kina tafe da kafa kamar ta balbela " bata jiyo ta kalleshi ba ta tsaya tana gyara hijabinta ƙasa-ƙasa ta ce, " Eh anji tubarkallah maye yaci kansa " tana gama faɗa ta ƙara gaba. Suna fita daga gidan da sauri Indo ta riƙe hannun su Zulai suka zagaya bakin wata bishiyar dalbejiya, sai da ta kalli gefe da gefe cikin ƙasa da murya Indo tace, " Ke Karime kinji me ya faru da Mai gari kuwa? " cikin yanayin jimami tace, " wallahi abinda ya kawo gidanku kenan dan mu samu mu keɓe mu jajantawa juna ni wallahi tsorona ɗaya karya mutu ya rataya a wuyanmu " jikin Indo sanyi ya ƙarayi tsoro ya kuma kamata ta ce, " Wallahi nima haka amma fa gani nake jawai tsurewa ce yayi " Zulai dake gefe ta ce, " Sarƙa ko ludayan da muka dinga ranƙwala masa sun isa su kai Maigari lahira " dariya ce ta taso musu lokaci guda suka dinga ƙyaƙyatawa, suna cikin haka sai ga Saude ta ƙaraso, ɗan tsuke fuska tayi ta ce, " Au wato abunma wulaƙanci ne ko a biyo mun ko ay zan rama " Karime ta galla mata harara tace, " Innarku bata gaya miki munzo akace kinje ansar Nika, shi ne muka biyowa Sarƙa inyaso sai mu biyo ta gidanku " Indo kallansu tayi ta ce, " Kai ni ba wannan ba, ance Mai gari na Asibitin gangare abinda zamuyi kawai muje muga halin da yake ciki sai muce dubiyarsa muka xo, amma wallahi Naji Yaya Jamilu yace baisan fa wanda yake kansa ba " da wannan shawarar ta Indo suka tsaya kai tsaye suka wuce cen Asibiti gurin Mai gari. Lokacin da suka je tuni Mai gari ya jima da bacci, a farfajiyar asibitin suka ci karo dasu Baraka, Indo gurin Magajiya ta nufa sai sa ta gaisheta sannan tayi mata ya mai jiki, Magajiya cikin dattako ta msa mata Baraka dake gefe ta hayayyaƙowa Indo tana faɗin, " To rasa kunya wato ni ban isa ki gaida ni ba ko? " harara indo ta watsa mata ta ce, " Mutumci ay madara tuni kin riga da kin zubar da naki " Indo na gama faɗa ta wuce hanyar da zata sadasu da ɗakin mai gari, Nurses ɗin nan suna zaune suka tahowar su Indo da bokitai, da sauri ta dakatar dasu tana tambayrsu, Indo ba tsoro ta shaida musu dubiyar Mai gari, hanasu shiga tayi suka juya jiki ba ƙwari, sai dai fal zuciyarsu a dagule take. Baraka sai habaici take wa Indo ita kuwa ko a jikinta, har sunbi hanyar fita Indo ta cewa su karime, " kuxo mu zagaya ta bakin window ay bazasu gammu ba " su Indo zagaya sukayi suka je bakin ƙofar da Maigari yake kwance, hangoshi sukayi yayi ɗai-ɗai da alama baccin wahala yake, musu suka farayi a junansu akan cewar Maigari ya mutu wasu kuma suka ce suma bai mutu ba. Dutse Indo ta ɗauka ta ce, " bari mu raba gardama " tana rufe baki ta saita Maigari ta jefa mai dutsen hannunta aykuwa cikin sa'a ta wurga masa dutsen nan akan wani ƙululu dake goshinsa. _Ummou Aslam bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 17&18 _KUYI HKR BAN TACE SHI BA_👏🏻 Mai gari cikin bacci ya ji wani irin raɗaɗin azaba akan kamar wanda aka zabura haka ya miƙe azabure yana kurma ihu, Nurses ɗin da ke waje ne suka jiyo sautin Maigari da sauri suka shigo ɗakin suma su Baraka rufo musu baya sukayi dan suka mai yake damun mai gidan nasu, lokacin da suka ƙaraso ɗakin tuni Mai gari ya daɗe da shigewa ƙarƙashin gado, yana faɗin, " Dan Allah kuyi haƙuri ku mun rai wallahi duk zan maida musu dukiyoyinsu " da farko rasa gurun da Mai gari yake sai ihun sa da ke tashi, ɗayar Nurse ɗince ta ɗan sunkuya ta bankaɗa ƙasan gadon sakamakon hango pan ƙafafun Maigari da tayi sun leƙo, da sauri Maigari yaja da baya yana kuma kurma ihu, Magajiya ce ta zura kanta ta ce masa, " Malam dan Allah ka dinga ambaton Allah, sannu ko jikin ne? " sai da yaga fuskar Magajiya sannan ya saki ransa ya fara magana, " Dan Allah Magajiya karku ƙara nesa dani wallahi sunce kashe ni zasuyi fatalwa ce take bibiyar rayuwa ta " gaba ɗaya Nurses ɗin dariya abun ya basu sai kawai suka maze ɗaya daga cikinsu ta ce, " Ranka shi daɗe ka fito daga gurin nan dai babu wata fatalwa da zata zo gurinka " Maigari sai da ya kalli hagu da dama ya kuma zuro kansa sosai sannan ya yanƙura ya fito da ƙyar yana yana muzurai, kan gado ya hau ya zauna sannan ya kalli Ado dake gefe ya tsuke fuska ya ce, " Kai Ado ina Rawanunmu aka barmu kai ba hula ba rawani mai yake damunku ne? " Ado sosai kansa yayi cikin zuciyarsa yake ayyana ƙarfin hali irin na Maigari yana cikin wani hali yana neman wani rawani, amma sai ya ce masa, " Allah ya baka yawan rai lokacin da muka taho asibiti kana cikin wani yanayi ne babu damar neman Rawani " ɗan jim Mai gari yayi yana tunanin halin da ya tsinci kansa aciki, shafa kansa yayi yaji wasu irin manyan ƙululai sai zugi suke masa, runtse idanunsa yayi cikin jin zafi sannan ya buɗe su, Mai gari ko tunanin mai yayi sai gani sukayi ya zabura yana cewa su Baraka su wuce shi gida zai tafi, Babu yanda Nurses ɗin nan basuyi da Maigari akan ya haƙura ba amma fir yaƙi amincewa, babu yanda su Baraka da Magajiya suka iya haka Maigari ya sasu a gaba suna tafe yana binsu abaya, su Ado kuma su aka bari da tura kura. Indo tun bayan tashin Maigari banda dariya babu abinda sukeyi gudun kar aganosu yasa suka tsutatsuna suna leƙowa da kawunansu, lokacin da sukaji Maigari yace zasu wuce tuni su Indo suka saɗaɗa suka fice daga Asibitin. Mai gari na komawa gida ya sake shiri da rawani, cen ƙasan akwatin ya buɗe ya ɗebo wasu takardu kala-kala, cen wata jaka a saƙale ya ɗauko itama ya dinga ɗebo takardu sai da ya haɗa duk takardun da yake buƙata sannan ya fito tsakar gida ya ƙwallawa matansa kira, cikin gurmamawa sun zo suka rissuna a gabansa gyara tsayuwarsa yayi ya ce, " Kuyi gaggawar kammala aikin gida anjima kaɗan ku sameni a fada " da mamaki suka ɗago cikin haɗin baki sukace, " Fada " Maigari gaba yayi yana faɗin, " ƙwarai kuwa domin yau ko wanne shege zai karɓi takardun gadonsu nima na huta da masifa " ya na gama faɗa yasa kai ya fice. Maigari yana zuwa fada ya aika sanƙira yayita shela yana sanarda Maigari nasan ganin kowa a fada babba da yaro, Lokacin sa yaje wucewa ta gidansu Indo tana zaune tana cin abinci, dariya ce ta taso mata cikin suɓutar baki ta ce, " Shege Maigari anji maza " Baba Huwaila zaro ido tayi ta wurgawa Indo daƙuwa sannan ta fara mata faɗa, ɗauke kai gefe Indo tayi sannan ta ce, " Yauwa Baba Huwaila dan Allah kimun alƙawarin komai nace kiyi zakiyi " da kallon mamaki ta bi Indo zuwa cen ta ce, " Ja'ira wani abun kika aikata ko? " marairace fuska Indo tayi ta ce, " Dan Allah nidai kimun alƙawari zan gaya miki " Baba Huwaila ta ce, " To na miki ina jinki idan baifi ƙarfi na ba " Indo saboda murna tashi tsaye tayi tana rawa harda juyi sannan ta koma ta zauna ta ce, " Baba Huwaila nasan kiran da Maigari yake mana takardun gadona zaije mu karɓa dan girman Allah kice mun yafe yaje ya riƙe, ba dan raina doka ba ma wallahi Baba Huwaila da sai muyi zamanmu " kallon baki da hankalu Baba Huwaila tayi mata sannan ta ce, " Lallai yarinyar nan abunda muke nema amma kuma mun samu dama muce bama so? Har yanxu da sauranki " Indo tsuke fuska tayi ta ce, " Kinsan dai alƙawari kayane kuma kin riga da kin ɗauka, Bba Huwaila kinsan dai ba zanyi abu dan na cutar damu ba " jikin Baba Huwaila ne yayi sanyi ta amincewa Indo, daga nan ta shi sukayi kowacce ta ɗau hijabinta suka kai tsaye suka wuce fadar Maigari da tuni harta fara cika. KUYI HƘR DA WANNAN. _Ummou Aslam Bint Adam_ [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 19&20 _SHIMA KUMUN AFUWA BAN TACE SHI BA_👏🏻 Mai gari na zaune sai waige yake yana hango mutane yake daga ko'ina suna tahowa zuwa fadarsa, daga cen nesa ya hango Indo da Baba Huwaila suna tahowa ajiyar zuciya ya sauke yana kuma leƙen Musataf ɗan gidan Marigayi Malam Sada kasancewar iyalan gidan ne kaɗai bai hango ba, daga cen Yamma ya hango zugar gidan Malam Sada sun taho a karo na biyu ya ƙara sauke ajiyar zuciya, sunkuyar da kansa ƙasa yayi shi kaɗai yana nazari bayan wani ɗan lokaci ya ɗago da kansa bayan kowa ya hallara agurin. Ado ne ya ɗaga wata ƴar lasifa irin wacce masu sayen kayan gwangwan suke yawo da ita ya fara magana, " Assalamu alaikum, barkanku da wannan lokaci na tabbata duk gurin nan akwai iyaye ko yayyen waɗannan yaran da suke mana surutu, ya kamata ku ja kunnensu inba haka ba kowa zai biya kuɗin tara kamar yanda aka saba biya aduk wani babban taro irin wannan " Ado na gama magana harabar gurin yayi tsit sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba, ƙasa-ƙasa mutane ke ƙus-ƙus kasancewar sun jima ba suji Maigari ya yayi wannan gagarumin taron ba, tun lokacin da aka turo musu da tallafin gidajen sauro daga gwamnati, hakan ne yasa kowa yayi tsit ya ya maida hankalinsa ga Maigari, sai dai ganin baby baƙin fuska yasa suka fara wasi-wasin maƙasuɗin taron. Ado miƙawa Maigari lasifika yayi sannan ya koma cen gefe ya tsaya, Maigari ƙara miƙa kansa gaba yayi sannan ya waiga gefe da gefe yana ƙarewa mutanen gurin Kallo, Gyaran murya yayi sannan ya fara magana, " Asalamu alaikum warahamatullahi ta'alawabarakatuhu, Nasan da yawa daga cikinku zasuyi mamakin wannan taro na gaggawa ba tare sanarwa daga baya ba kafin wannan rana, Wannan taro mun yi shi ne domin mu dawowa da wasu mutane daga cikinmu waɗanda aka damƙa mana dukiyoyinsu, gonakinsu, da ƴan kadarorin da ba'a rasa ba " ƴar hayaniya ce ta fara kaurewa agurin ƙasa-ƙasa kowa da abinda yake furtawa waɗanda kuwa suka san da dukiyarsu agurin Mai gari jin suke kamar Sallah saboda murna bakunansu sunƙi rufuwa, Maigari ne yayi gyaran murya hatsaniyar ta ɗan tsagaita sannan cigaba da cewa, " Zamu fara kiran sunayen takardun dallah-dallah ɗaya bayan ɗaya, duk wanda yaji sunan Mahaifinsa ko kakansa ga wanda takardunsu ke gurina sai su miƙe tsaye, zamu ware su guri guda idan mu kammala ware su sai mu ƙara dawowa mu maimaita kiransu ɗaya bayan ɗaya domin mu tabbatar da sahihancin wanda ya amsa dan kar mu bawa wanda ba shi ne mai mallakin gadon ba " Akaro na biyu ƴar hayaniya ce ta ƙara tashi wannan karon Ado ne yayi magana sannan suka dakata. Hannu Maigari ya miƙa aka Yusha'u ya miƙo masa wasu takardu masu ɗan yawan gaske, glass ɗinsa ya ciro daga aljihu sai da ya ɗan goge shi sannan ya sa a idonsa sannan ya fara karantawa kamar haka:- _Muna neman Iyalan Malam Murtala bamaina_ _Sai Iyalan Musa Isa Babandi_ _Ina Iyalan Malam Baharu Rabe_ _Da kuma Iyalan Rakiya Sani Gudidi_ _Sai Iyalan Inno Gwadabe Kunkuru_ _Ina Iyalan Muttaƙa Bala Shinkafi_ _Sai kuma Iyalan Maryo Hashimu Nadabo_ Gaba ɗaya waɗanɗa Maigari ya kira ne suka miƙe tsaye banda Indo da sunkuyar da kai kasa tana dariya harda hawaye, ita gaba ɗaya ma Maigari Dariya yake bashi yanda taga kwana biyu duk ya fige ya lalace kamar wanda yayi jinya, wani tunani ne ya faɗo mata aykuwa ta kuma sunkuyar da kai cikin zaninta tana kuma tintsirewa da dariya, Baba Huwaila haushi ne ya fara kamata cikin jij takaicin Indo ta shureta da Kafarta tana kifta mata ido alamun tayi shiru, suna cikin haka Suka ji Maigari ya cigaba da cewa, " Iya karku kenan waɗanda haƙƙinku yake kaina ko? Dan banasan sai daga baya wani yace mun ga zance ga magana " cikin zumuɗi da azarɓaɓi suka amsa, " Eh mune gamu " Ƙare musu kallo Maigari yayi yana daɗa leƙensu cikin kallan ƙurulla, dawo da idanunsa yayi cen wajen taron jama'a, cen lungu agefen Baba Huwaila ya hango Indo suna haɗa ido ta ɗauke kai gefe kamar bata ganshi ba, cikin jin haushi Mai gari ya cewa Indo, " Ke Sarƙa kinci ƙaniyarki ke bakiji na ambaci sunan Goggonki bane kika yi shiru kika ƙi tashi? " Indo ɗan tsuke Fuska tayi sannan ta ce, " Allahbya taimakeka ya baka yawan rai naji mana, kawai dai bari nayi ka sallamesu tukunna sai inyi maka magana saboda akwai saƙon da Goggo ta gayamun ta ce ingaya maka acikin Mafarki na " dirar maganar Indo dai-dai tayi da faɗuwar gaban Mai gari, wata irin zufa ce ta yanko masa take cikinsa yayi wata irin kartawa, amma gudun kar agane halin da yake ciki yasa ya maze ya tsuke fuska ya ce, " Ke Sarƙa banasan sakarcin banza da wofi kinji, ni zaki gwadawa sheɗancin ki " ita ɗinma ƙara tsuke fuska tayi ta ce, " Ranka shi daɗe kasan dai bazanyi maka ƙarya ba, har tace mun ma wai na gaya maka sirrinku kai dasu na dare karka sake ka furtawa kowa " A karo na biyu cikin Maigari ne ya sake kartawa tuni zufa ta rufe shi, da hannu ya goge gumin fuskarsa sannan ya ce, " To to to, to shikenan Allah ya kyauta makwancin " Indo dariya ce ta ciyo ta amma gudun kar mai gari ya ramfo ya yasa ta gimtse bakinta. Maigari kallan mutanen da ke tsaye yayi ya fara da na farkon da ya kira sunan Mahaifinsa, wasu takardun gona guda uku ya ciro sannan yace, " Ku ɗan dakace ni zuwa wani lokaci saboda takardarku ta huɗun mun saida ta mun tura kuɗin Zariya ana noman rake da shi, lokacin da amfanin gona yayi kyau zamuyi muku magana " karɓa suka dinga yi suna godiya har yazo kan kusa da takardun Indo miƙa masa takardunsu guda biyu yayi sannan ya musu shanunsu guda biyu anturasu kiwo cen garin rogo su da wani ƙaninsa kafin damina ta sauka. Rufa'i ɗan gidan Malam Muttaƙa kallan takardun yayi tsaf sannan ya cewa Maigari, " Allah ya baka yawan rai bayan da mahaifina ya rasu dai nasan takardu biyar aka baka amma naga ka bamu guda huɗu shanu kuma kace suna kiwo? " ɗan duburburcewa Maigari yayi sannan ya ce, " Ai ita ɗayar itama saida ita mukayi mun tura kuɗin cen garin Daura ana mana noma riɗi da ita, idan albarka ta bayyana yabanya tayi kyau ai kuma zaku ga alama " tsuƙe fuska Rufa'i yayi yan ƙunƙuni ƙasa-ƙasa, Maigari zaburowa yayi ya rufeshi da faɗa, " Kaga tsageran yaro zai kawo mana raini cinye maka dukiyarka zanyi da nayi niyyar cinye maka zaka samu sauran wannan ne, jama'a kuna gani fa dan Allah kuga yaran zamani da rashin kunya " Aikuwa Maigari na gama magana akayowa Rufa'i caaaaaa akansa kowa da abinda yake faɗa, ganin haka yasa ya wuce ya koma mazauninsa ya zauna. Maigari ne ya kalli gurin da Indo take aikuwa kamar jira take ta miƙe tsaye tana faɗin, " Gani Ranka shi daɗe nasan ni zakayiwa magana " Jamilu dake gefe kallon Indo yayi tundaga ƙasa har sama, takaici ne ya rufeshi musamman da yaga yanda cen ƙasan hujabinta ya wani nannaɗe wanda da za ka ja shi yafi haka tsayi, takalmanta ya gani a cikin sangalalin hannuwanta ta zuzzurasu kamar wani zai ɗauke mata, cikin jin haushi yayi tsaki yana ɗauke kai gefe. Indo kuwa ko ajikinta bata san ma yanayi ba, Maigari ne ya ce mata, " Ke Sarƙa wazai karɓi takardunki ke zan damƙawa ko Baba Huwaila? " Indo ɗan jim tayi sannan ta ce, " A'a Allah ya baka yawan rai daga ni har ita bazamu karɓi waɗannan takardun ba, ka riƙe ka adana mun agurunka nan da wani lokaci Baba Huwaila ta karɓar mun " Mai gari ji yayi kamar ta watsa mai ruwan zafi musamman da ya tuni gargaɗin da fatalwa tayi masa akan lallai dole ya bawa kowanne maraya haƙƙinsa, cikin masifa ya fara mata magana, " Ke Sarƙa rashin mutumcin naki yazo har kaina, to ni bazan riƙe agurina ba zan baku su idan kunga zaku riƙe to inma watsarwa zakuyi ku kuka sani, Baba Huwaila kina ina? " Baba Huwaila dake gefe ta amsa, " Ranka shi daɗe ayni banda abinda faɗa tunda haƙƙi na yarinya ne kuma tace ka riƙe agurunka " girgiza Kai Mai gari yayi ya ce, " Sai yanxu na fahimci haɗin bakinku wato kema zaki cigaba da ɗaure mata gindi kamar yanda....." Maganar Maigari maƙalewa tayi tunowa da yayi karyaje ya faɗi magana mara daɗi akan Goggo cikin dare su kuma yi masa ba daɗi, basarwa yayi ya kalli Jamilu ya ce, " Kai Jamilu zo karɓi " Jamilu bai musa ba ya miƙe ya karɓo takardun Indo ya koma ya zauna. Indo kallon Maigari tayi ta ce, " Allah ya taimakeka a cikin Mafarki Goggo ta cemun ko na ƙarbi takardun nan sai ta maidasu da kanta dan haka wallahi ni babu ruwana tunda nace maka bazan karɓa ba " Maigaru sak yayi kamar wanda ruwan jikinsa ya ƙare, amma gudun kar mutane su fahimta sai ya basar ya fara rufe taron, bayan rufe taron ya sallami kowa daga gurin, haka masu takardu ahhanu suka juya guda zuciyarsu fak farun ciki, sauran mutane kuwa sai mita suke akan an ɓata musu lokaci. Lokacin da suka koma gida Jamilu faɗa ya fara yiwa Baba Huwaila akan tana biyewa Indo, daga baya kuma ya dawo kan Indo itama yana mata faɗa kamar ya cinyeta ɗanya, Ɗakin Baba Huwaila ya shiga ya ɗauko wata jaka yasa takardun aciki ya ɗaga katifar gadon Baba Huwaila ya sa aciki, duk abinda yake faruwa akan idanun Indo murmushi tayi acikin zuciyarta ta ce, " Aykuwa a yau takardunan sai sun koma gurun Mai gari " jim tayi kamar mai nazari kome ta tuna ta sauri ta shuru ta kalminta ta fice Jamilu na ƙwala mata kira ko ta kanshi bata biya ba, kai tsaye cen Zangon malam Idi ta nufa wajen shagon Malam Muddasiru mai likkafani. *_YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING, INA GODIYA DA WANCEN COMMENTS ƊIN ALLAH YA BAR ƘAUNA❤️❤️❤️._* _Ummou Aslam Bint Adam_😉 *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 21&22 _MAI ZAFAFA KINYO BELINKU YAU NA TACE SHI🤣_ Lokacin da Indo taje shagon Malam Muddasiru mai likkafani sai da ta tsaya daga bayan shagon ta kunto bakin zaninta ta cire wata maƙalalliyar ƴar ɗari biyunta da ta koma kamar tsumma, da Sallama ta shiga shagon cikin sakin fuska yace, " Wai yau Sarƙa ce a shagona ya Baba Huwaila? " Bakin Indo har kunne sai yashe baki take kamar gonar Auduga cikin kulawa ta ce, " Baba Muddasiru ina wuni " Malam Middasiru mamaki ne ya kamashi ƙarara wai yau shi Sarƙa ke cewa Baba har tana gaida shi, cikin sanyin jiki ya amsa da, " Lafiya ƙalau Sarƙa ya gida? " da sauri ta amshe da, " Lafiya ƙalau Baba Huwaila ma tana gaisheka " cikin jindaɗi yace, " Madallah ina amsawa " Indo ɗan jim tayi zuwa cen ta ce, " Baba Mudassiru dama zuwa nayi siyan likkafani na ɗari biyu " xaro idanu yayi yana kallanta yace, " Likkafani Sarƙa waye ya mutu? Kuma wa ya turo ki? " ganin halin da ya shiga ba ƙaramin dariya ya bata ba, aikuwa sai da tayi mai isarta sannan ta ce, " Ba wanda ya mutu, kawai dai wani aiki aka bamu a makarantar boko wai zane ne za'ayi akai sai a ɗinka da baƙin zare " Ido ya zura mata kamar bai yarda da maganar Indo ba, amma da yaji tace aiki Malaminsu ya bata sai ya amince, cikin mita ya fara magana. " Yanzu banda shashanci a rasa da wane yadi za'a bawa yara aiki sai sittirar mamaci, shima malamin duk bokonsa dai ƙarshensa wannan farin yadin " Tashi yayi ya ɗauko mata wani guntu da baifi rabin yadi ba yace, " Ungo riƙe wannan ki bani ɗari biyun amma kusan kyauta na baki tunda kuɗinsa ya fi haka " Indo cikin Murna ta amsa tana zabga masa godiya. Abinda Malam Muddasirru bai sani ba rabon Indo da makarantar boko to fara jinyar Goggo yau kimanin kusan wata huɗu kenan, wucewa tayi gida zuciyarta fal da farin ciki, kafin ta ƙarasa tuni ta sokeshi a ƙugunta tana tafe tana ƴar waƙarta harta shiga gida, kai tsaye ɗakinta ta wuce taje ta ɓoyeshi a cen ƙasan adakarta. Mai gari na gama ganin watsewar jama'a shima ya lallaɓa ya ƙarasa gida saboda ba jin daɗin jikinsa yake ba ƙarfin hali ne kawai ya yi dan ya sauke nauyin da fatalwa ta ɗora masa. Bayan la'asar liƙis wajen doshin magriba wata danƙareriyar mota baƙa wuluk da gilashinta baƙi baka iya gane wanda yake ciki ce tayi parking a ƙofar gidan Mai gari, daga bayan motar aka fara buɗewa a hankali, wata dattijuwar mata ce ta zuro ƙafarta sanye da wani tsadajjen takalmi ruwan zaiba da ɗigon ja, kafin ta ƙarasa fitowa wani matashi ne ya buɗe wajen mazaunin Driver, tun kafin ya ziro ƙafarsa kamshin turarensa ya fara zagaye harabar gurin, cikin nutsuwa ya dai-daita ƙafarsa yana sannan ya sauko da ita bisa doro ƙasa, Mahaifiyarsa ce ta fara fitowa tana ƙarewa yanayin garin kallo, murmushi ta saka musamman da ta kalli wata kwatuwar bishiyar Mangwaro dake kallan gidan Maigari, tunowa tayi da ƴanmatancin su da irin gararanbar da suka sha, wasu ƴan mata biyu ta hango a ƙasan bishiya sun ɗaga kansu sama da alama kallan mai ciro musu mangwarn suke suna jiran faɗowarsa, Fahad dafa murfin ƙofar yayi ya fito daga cikin motar yana kallan yanayin tsarin garin yana ɗan yatsina fuska. Daga cen gefen su Zualai ne ke wa Indo magana saboda ganin ta shanyasu tun tsayuwarsu mangwaro biyu kawai ta jefo musu. " Sarƙa tun ɗazu fa muke jiranki wallahi munsan dama sai kinsha kin ƙoshi zaki jefo mana " Indo siɗe ruwan mangwaron hannunta tayi cikin masifa ta ce, " Wallahi Saude ke da mayya ce da sai dai aga gawata ta faɗo " cikin jin haushi Saude ta ce, " Amma ai ba haka mukayi da ke ba " Fahad kallan gurin yayi yana ƙarewa ƴanmatan kallo yana ɗan yamutsa fuska, jin maganar Indo yasa shi ɗan ɗaga kai ya kalli gurin amma ko alama baiga mai maganar ba, Mahaifiyarsa ce ta kalleshi ta ce, " Fahad kaga yanda ƴanmata nan suke tsinkar magwaro muma fa haka mukayi muna ƴan mata " Jinjina kai yayi yace, " Mommy meye abin birgewa dan Allah a hawa bishiya " murmushi tayi ta ce, " Kai rainon birni ne bazaka gane ba, mu ƙarasa gurunsu Yaya " ta ƙarasa faɗa tana wucewa gaba. Indo sai da ta kusa shanye Mangwaron ta wurgoshi tana cewa su Zulai, " Zulai ku taɓa wannan wallahi kamar Binta siga kunji zaƙin tsiya kuwa? " saukowar Mangwaro yayi dai-dai da tahowar Fahad take faɗo jikinsa, ruwan mangwaro duk ya ɓata gaban farar shaddar Fahad " Ko kaɗan su zulai basu lura mangwaro kan Fahad ya sauka ba sai ganinshi sukayi ya tsaye yana kallan bishiyar, cikin ƙasa da murya Saude ta ce. " Sarƙa sakko kiga wani wasu ƴan Birni harda motarsu wallahi irin ta cikin shirin kallon kaset ɗin nan da muka gani a gidan kallo " Indo ta gefen wani reshe ta leƙo da kanta aikuwa tana ganinsa ta saki baki dan ganin kawun saurayin, da sauri da dirgo tana kafeshi da kallo, shi ɗinma cikin takaicin yake binta da kallo tun daga ƙafarta da babu takalmi har zuwa kayan jikinta da suke kowanne kalarsa daban, takalmanta ta dake saƙale a gwiwar hannunta ta ciro tana kaɗesu ƙurar takalmin sai baɗe fuskar Fahad take, bata ma bi ta kansa ba ko me Indo ta tuna sai kuwa ta juya aguje tana cewa. " Jama'a kuzo wallahi ƴan wasan kwaikwaiyo ne suka sauka a gidan Maigari " su Zulai najin haka suma suka rufa mata baya saboda irin shigar da suka ga waɗannan baƙin sunzo dashi dole sai ƴan wasan kwaikwaiyo tunda agunsu suke ganin irin wannan ƙatuwar motar. Fahad takaicin duniya ne ya isheshi yama rasa abinda zaiyi tun tuni ya nunawa Mommy bayasan zuwan ƙauyen amma ta takura masa sai gashi tashin farko ga abinda ya biyo baya, Mommy kallan ɗan nata tayi taga yanda ya kwaɓe fuska kamar zaiyi kuka ta ce. " Sorry My Son kasan fa yaran karkara sai a hankali ba lallai ma sun lura da abinda sukayi ba, baka ji ma me suka tafi suna faɗa ba " yana shirin magana ya hango zugar yara sunyo caaaa sun tunkaro gurinsu suna faɗin, " Yau zamuga su Ali Nuhu da Adam A Zango " _TOFA WANNAN KARAN ZAN ƘOƘARTA NAYI LITTAFIN SOYAYYA DUKDA NAYI GUDA ƊAYA A BAYA *TSANTSAR BUTULCI* INA MASU MUN GORIN LITTAFIN ALJANU NAKE YI🤣🤣🤣 KO ZAI BADA CITTA KUWA? ƘILA KUJI SHI DABAN DAN NI NAFI GANE LITTAFIN SU *MARWAN*👽 da *ASEELA*👹 AMMA YANXUN MA A KAFTA🤸🏼‍♀️🤸🏼‍♀️🤸🏼‍♀️ MEYE HARSASHENKU AKAN FAHAD DA INDO MAI GAYYAR JAMA'A._🤣 *ASEELA FANS YAU KU ZAN BAWA HAƘURI BANIDA CAJI*🤭 _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 23&24 Mamaki ne ƙarara ya bayyana akan fuskar Fahad cikin ɓacin ran jin kalmomin da suka faɗa ya kalli Mommy yace, " What Mommy kina jin me suke faɗa kuwa? Do i look like Hausa actor? Wai wannan wanne irin ƙauye ne haka " Mommy dariya ce fal bakinta amma gudun karta ƙara tunzura ɗan nata tace, " Haba Son don't mind them na gaya maka su fa yaran ƙauye suna da tazara mai nisa tsakaninsu dana birni, So mind your Business inba haka ba su maida kai abun tsokana " tana ƙarasa faɗa ta wuce gaba ta shiga gidan Mai Gari, fuska a haɗe shima yabi bayanta saboda bashida wani zaɓi. Da sallama suka shiga cikin gidan Maigari alokacin Mai gari na kwance abakin bishiya anyi masa shimfiɗa yana ramakon bacci, salamarsu su Fahad ce ta tashe shi kamar a mafarki haka ya riski muryar ƴar uwar tashi. Cikin murya ya tashi zaune yana faɗin, " Yau manyan baƙi garemu haka wa nake gani kamar Mejidda? " murmushi ɗauke akan laɓɓanta ta amsa, " Yaya ba gizo bane nice nake tafe tare muke da Fahad " Juyawa yayi ya kalli Fahad dake cika yana batsewa yace, " Kai ƙaniyarka Fahad ne ya girma ya zanƙale haka? Zo nan mana kake wani raɓewa sai kace wani baƙo " Fahad yaƙen dole ya aro ya yafawa fuskarsa ya ƙarasa gefen Maigari ya zauna sannan yace, " Ina Wuni? "Maigari da kallan mamaki ya kalleshi yace, " Mejidda wai yaron nan ba shine ɗan ƙanƙanin nan da mukaje lokacin Magajiya nada tsohon ciki ba? " Kallan Fahad tayi taga yanda ya kuma tsuke fuska ta ce, " Eh shine Yaya lallai baka manta fuskarsa ba " " Haba ya za'ayi na mantashi ja'iri muskili amma halin nashi ya ragu ko" cewar Maigari. " Yaya ay Fahad sai abunda ya ragu dan miskili ne kaganshi nan yanxu ma wasu ƴan mata ne daga zuwanmu suka ɓata masa jiki da mangwaro " Inji Mommy. Murmushi Maigari yayi yace, " kaga kazo a sa'a daga zuwa har ka samu matar aure " da sauri Fahad ya ɗago da kansa ya wurgawa Maigari mugun kallo. Su Magajiya ne suka ƙaraso cikin murna suna lale marhabun da sannun da zuwa, suna zama kamar ance su kalli bakin ƙofa gaba ɗaya sai gani sukayi yara cunkushe a bakin ƙofar gidan Maigari wasu daga cikin yaran har kokawa suke, da mamaki Maigari ya kallesu ya buga musu tsawa yace. " Kai meke tafe daku lafiya? " Kallon kallo suka farayi a junansu daga cen baya Sahabi ya kutso ya fito gaba yace, " Allah ya taimakeka Sarƙa ce tace mana ƴan wasan kwaikwayo sun kawo ziyara gidanka shi ne muka zo ganinsu, ance harda na namiji hine muke musu da Ɗayyabu shi yace Ali Nuhu ne nikuma nasan ba mai zuwa gurinka sai Adam A Zango " Maigari tsuke fuska yayi yace, " Kai banasan shashancin banza da wofi ku tafi ku bamu guri " Indo dake shigowa soron gidan Maigari batasan me ake ciki ba, tana shiga Lami ta ce, " Amma Sarƙa ki sake hali ashe babu wasu ƴan Wasan kwaikwayo " Cikin jin haushin ƙaryatata da Lami tayi Indo ta shiga tsakar gidan Maigari tana faɗin, " Ke Lami angaya miki kowa maƙaryaci ne kamar ke, idan ba ƴan wasan kwaikwayo ba su waye suke zuwa a wannan hirgegiyar motar, ba gasu agefen Maigari ba ko waɗannan kece a zaune? " tunda ta fara magana kan Fahad na sunkuye a ƙasa saboda gaba ɗaya ransa yakai maƙurar ɓaci, Indo duk wannan masifar da takeyi hannunta riƙe da wani makeken Magwaro da bata jima da fara sha ba, ƙudaje sai zagayeta suke yi amma ko ajikinta. Indo dan ganin sai ta tabbatar da gaskiyarta yasa ta ƙarasa kusa da Fahad tana cewa. " Dan Allah Ɗan dirama ka gaya mata ziyara kuka kawowa Maigari tunda hine hugabanmu, ƙarasowar Indo gurun Fahad yasa Ƙufaje suka biyota suka kuwwa, cikin kyankyami, jin haushi da ɓacin rai Fahad ya fisgo tattararren hujabinta, aikuwa ji kake daɓass tayi zaman ƴan bori a gabansu, Indo na shirin magana Fahad ya kifeta da wani zafaffen mari cikin ƙunan rai ya fara mata magan. " U r very stupid, ke wacce irin Dabba ce mara hankali? " Indo kafeshi tayi fa ido tana kallonsa saboda gaba ɗaya ranta yayi mugun ɓaci, tunda take acikin Garin gangare babu wanda ya taɓa mata abinda yayi mata a yanxu, cikin jin haushinta ya tsartar da yawu gefe sannan ya miƙe tsaye ya cukwikwiye Indo acikin hijabinta ya ƙarasa bakin ƙofa, sauran yaran na ganin ya dunfarosu kowa ya ranta ana kare saboda marin da yayiwa Indo ba ƙaramin tsorasu yayi ba, sai da yaje bakin ƙofa ya wurga Indo kamar wata kaza ya juyowarsa ko ta kanta baibi ba. Yana shigowa ya hangi butar Maigari ya ƙarasa ya ɗauka sannan ya wanke hannunsa ya koma ya zauna yana huci, kallansa Mommy tayi ta fara faɗa, " Kai Fahad maiyasa ka fiye zafin zuciya ne? ko me yarinyar nan tayi aisai kayi mata uzuri baka ganin da ƙarancin shekaru atattare dasu, wallahi abu ɗaya ne yasa ban tsawatar maka agabansu ba saboda na tabbata suka ga na maka faɗa ko ƙofar gida ka fita ka zama abun tsokana agurinsu, bare kuma ka fita zaga gari " Kwaɓe fuska yayi ya ce, " Mommy har wani fita zanyi nifa idan naga da takura sai na wuce gida inyaso gobe Yahaya yazo ya tafi da ke " Mai gari daƙuwa yayi masa yace, " Kai gidanku, nabi takurawar da gudu ba hula, kaga babu inda zakaje sai kun gama kwanakin da ta ɗebo muku " murmushi Mommy tayi ta ce, " Ay Yaya gobe ma zamu wuce, amma Yaya lafiya naga duk kayi wani iri ga alamun raunuka nan akanka ko dai wani abu na faruwa ne? " Maigari kwallah ce ta ciko mai idanu ya ce, " Babu komai Mejidda ciwo ne dai naji " Mommy sam hankalinta bai kwanta ba shiyasa ta kuma tambayar ɗan uwan nata, " Yaya ciwo da me kaji ciwon? " Baraka dake gefe tace, " Wallahi wata irin jarabta ce aka jarabcemu da ita, fatalwa ce take zuwa har gida tana yiwa Malam Lahani, rannan har mu tace zata haɗa damu " Fahad shi da Mommy suka ce, " Fatalwa kuma, dama akwai wata fatalwa ne " Magajiya ta cigaba da cewa, " Wallahi kusan kullin sai tazo mana yau fa sai da Malam ya kwanta a asibiti saboda tashin hankali da raunin kansa " Mommy Nuna ƙulalan Maigari tace, " Wannan ciwon ma fatalwarce ta ji maka shi? " Maigari da gabansa ke faɗuwa yace, " Wannan da kika gani hannunta ne yayi mun wannan ƙulalen amma Dan Allah mu bar magana, cigaba da yinta kamar ina ƙara kusantar mutuwa ta ne " Ganin yanda duk ya firgice yasa Mommy ta shiga tausayin ɗan uwan nata, cikin sigar tausayi ta ce, " Zamu bar maganar amma ka gayamun yaushe fatalwar take zuwa " cikin zumuɗi yace, " Tsakar dare ne " jinjina kai Mommy tayi suka cigaba da hirar yaushe gamo. Indo tunda Fahad ya jefarta ƙasa baƙin ciki ne ya cika ta, batayi aune ba sai ji tai hawaye na zuba daga kuncinta, yara ne suka fara taruwa suna yiwa Indo waƙa, " Sarƙa taci Mari, Sarƙa taci mari, Sarƙa taci mari bakinta ya ja mata " Indo tashi tayi jiki ba ƙwari sai su Karime ne suka rakata har cikin gida. Da kuka Indo ta shiga cikin gida, ba Baba Huwaila ba hatta Jamilu sai da mamaki ya kamashi, cikin tashin hankali Baba Huwaila ta fara jefo musu tambaya, Saude ce ta basu labarin abinda ya faru aikuwa Jamilu mai zaiyi ba dariya ba, da farko Baba Huwaila cewa tayi zata je taji akan me zai marar mata yarinya. Jamilu ne ya ce mata, " Wallahi Baba Huwaila kije bakisan ba'aiyiwa irin waɗannan masu kuɗin haka ba, yana haɗawa keda ita ya kaimu cen policestation arufe ku " Baba Huwaila najin haka tsoro ya kamata ta shiga rarrashin Indo tana bata haƙuri. *CIKIN DADDARE* Indo ce cikin shigarta da ta saba ta fararen kaya, wannan karan har ɗan ƙaramin tulun Baba Huwailata ɗauka ta tura wannan ƙyallen likkafanin aciki sannan ta nufi gidan Maigari. Kamar yanda ta saba ƴar katangar ta kama ta haye, kai tsaye ɗakin Maigari ta nufa cen kan gado cikin bargo ta hangoshi aikuwa tana zuwa batayi wata-wata ba ta ɗaga hannunta iya ƙarfinta ta ranƙwala masa aka, cikin azaba Fahad ya tashi firgigit saboda ludayin ba ƙaramin shigarsa yayi ba. Indo tun kafin ya tashi tsaye tsoro ya kamata amma sai ta basar ta fara wani buga ƙafa ɗaya tana baza farin hijabinta, fuskarta bajau tasha hoda sai zaro mai idanu take, tana wani jijjiga kai sannan ya jefo mai tukunyar nan tana cewa, " KAINE RABONMU NA GOBE SAI DAI A WAYI GARI DA GAWARKA A YASHE " Fahad da haushi ya gama cika shi da sauri ya ƙarasa gurunta ya kifeta da mari. 🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *INDO SARƘA FANS ANCE RANA DUBU TA ƁARAWO.... KUJE KU KARƁO INDO YAU TA SHIGA HANNU.* _AKWAI SABON LITTAFIN SABUWAR MARUBUCIYA MAI SUNA *HATSABIBI BOKA DAMGAS* SALON LABARIN NA DABANNE BAZAN CE KOMAI BA AMMA KU TARA ZAKU GANI DA IDANUNKU, KU DAKACE SHI NAN DA ƊAN WANI LOKACI NIDA ITA ZAMU FARA MUKU POSTING._ _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 25&26 Indo cikin jin zafin marin tace, " Kuturun karen nan ka mari fatalwa? Wallahi sai ɗauki rayuwarka daga yanxu zuwa safiya kuma..." Indo bata ƙarasa magana ba Fahad ya kuma kifeta da wani marin cijin kausashshiyar murya yace, " Ke wace ce kuma daga ina? Waya turo ki kika zo kina azabtar da bawan Allah da sunan Fatalwa? " Indo tsuru tayi gabanta ya fara dukan uku-uku ilahirin jikinta karkarwa yake yi cikin ƙarfin hali ta ce, " Ni ƴar mutum biyu ce jikar mutum huɗu, kuma wannan marin da Wallahi bakaci banza ba, daga jiy zuwa ni akayiwa wannan marin " da ƙarfin gaske Fahad ya damƙo wuyanta yana huci. Indo azaba ce ta isheta ba shiri ta janyo hannunsa da gantsara masa uban cizo, da sauri ya riƙe hannunsa yana faɗin, " Auwwtchh " Indo na ganin haka ta fita da gudu kamar ɗan biri haka tabi katanga ta ɗane ta dirga, Fahad rufa mata baya yayi amma kafin yaje tuni ta sauka daga kan katangar, Maigari dake ɗakin Magajiya ƙarar gudun su Fahad ne ya tashe sakancewar dama baccinma rabi da rabi yakeyi, Fahad babu tsoro a tattare dashi ya yaje soron gidan ya fara ƙoƙarin buɗe sakata, yana fita wayam ya gani ba mutum babu alamarsa, guntun tsaki yaja sannan ya tura ƙofar gidan ya koma ciki. Yana shiga ɗaki cen ƙasa ya hango wani abu a ƙasa haskawa yayi da fitila ya hango wani takalmin indo dana sai farin likkafin data jefa masa, tsugunnawa yayi yana duba takalmin yana jujjuyasu sannan ya koma cen kan katifar ya zauna yana nazari. Lokacin da Indo ta dira batai wata-wata ba da gudu ta faɗa cikin gidansu, kai tsaye ɗakinta ta shige tana sauke ajiyar zuciya, jikinta banda karkarwa ba abinda yake. Tana nan sai ji tayi anhaske ta da fitila, a zabure ta juyo tana ɗauke numfashi, cikin alamar tuhuma yace, " Ke daga ina kike acikin tsohon daren nan? " Indo zuru tayi ta rasa wacce amsa zata bawa Jamilu. Cikin tsawa ya ce, " Zaki gaya mun ko sai jikinki ya gaya miki daga ina kike nace? " turo baki gaba tayi sannan ta ce, " Gidan Maigari... " A hassale ya katseta, " Maigarin ƙanin ubanki ne ko na uwarki da zaki je gurinsa da tsohon daren nan ubanme kikaje yi gidansa? " Indo shiru tayi bata tanka masa ba, Jamilu hassala ya daɗae kai tsaye ɗakinsa ya nufa yaje ya ɗauko belt, yana shigowa ya rufe Indo da duka ta ko'ina, Indo ihu take kamar wacce ake zarewa rai, Baba Huwaila dake bacci sama-sama ta fara jiyo ihun Indo azabure ta tafi tana salati da salallami, Baba Huwaila ce ta shiga ɗakin ganin abinda Jamilu yakeyi yasa ta fashe da kuka tana dukansa tambayar ba'asi. Sai da jikin Indo ya gaya mata sannan Jamilu ya dakata da dukanta, cikin huci ya zayyanewa Baba huwaila dalilin dukanta, ita kanta jikinta ne yayi cikin jimamin maganar Jamilu ta ce, " Indo saboda Allah yanxu abinda kika aikata kinyi dai-dai kenan, meye haɗinki da wani Maigari? Wallahi nima a wannan karan bazan goyi bayanki ba. " Indo cikin kuka ta ce, " Nifa Wallahi babu wani abu antsakaninmu kawai zuwa nake tsorata shi..." Tas Indo ta kwashe yanda sukeyi da Maigari ta gaya musu har zuwa yanda sukayi da Fahad, Baba Huwaila dariya take harda hawaye shi kansa Jamilu duk yanda ya kai ga tsuke fuska da sai da ya murmusa sannan ya kaiwa Indo rankwashi yace. Sheɗaniya shakiyya wato shiyasa naga rigata ajikinki, waye yace ki ɗaukarmun kaya? Wato kece kika sa Maigari zugewa har ya fara maidawa da marayu kayansu, gaskiya na yarda Indo ke sarƙa ce ni kinfara bani tsoro ma wallahi" Murmushi Indo tayi sannan ta yakice hijabin jikinta ta ajiye, gaba ɗaya ta sharɓa uban gumi Jamilu ne ya fice daga ɗakina yana ƙara jinjina shu'umanci irin na Indo. Indo tare da Baba Huwaila suka wuce cen ɗakinta tana tafe tana dariya. *A CEN GIDAN MAIGARI* Fahad na zaune yana nazarin yanda zaiyi ya ɓullowa lamarin yarinyar nan dan ya lura abin nata da rainin hankali, murmushi yayi lokacin da ya kalli takalmin ya tuna gadar zaren da zai kulla mata. Fahad tashi yayi ya fita tsakar gida yana zarya kamar mai neman wani abu, daga ƙofar ɗaki ya hango Maigari na leƙowa cikin zuciyarsa dariya ce ta kamashi, Maigari ta maza yayi ya zuro kai ya cewa Fahad. " Kai Fahad bazaka koma ɗaki ba sai fatakwar nan ta kuma dawowa ko? " Fahad haushi ne ya kamashi ganin duk girman Maigari amma wai ƙaramar yarinya tana neman raina masa hankali, ɗaki ya shige abinsa ya bar Maigari yana bin bayansa da kallo. *WASHEGARI* Bayan gari ya waye Fahad ya samu Maigari bayan aun gaisa yace, " Kawu dama inasan anjima atara mun mutanen garin nan akwai abinda nake sanyi amma bana buƙatar atuhumeni saboda na ganno sirrin fatalwar da take zuwa tana tsoratar da kai " A zabure Maigari ya miƙe tsaye yace, " Kai ɗan nema kar kazo ina zaman zamana ka jazamun masifa, wallahi ka fitar sabgar Fatalwar nan dan na lura ku ƴan birni kanku rawa yake" Fahad ɗauke kai gefe yayi bai tankawa Maigari ba har ya gama maganganunsa ya ƙara gaba. Bayan wani lokaci Maigari ne yasa su Ado suka dinga yawo suna ƙara gayyatar mutane bayan sallar Azahar, kowa da abinda yake faɗa sai dai mutane da dama ba wanda ya nuna goyon bayansa ga zuwa gurin taron. Bayan wasu daga cikin tsararun mutane sun taru Fahad ne tsaye fuska ba walwala ya kallesu yana sallama kamar me raɗa, da zumuɗi suka amsa masa suna sauraron ji daga gareshi, sai da ya ɗauki ƴan mintuna sannan ya fara magana. Wannan taron ban tarashi domin komai ba sai dan inbada cigiya, ina buƙatar sannin waye me wannan takalmin daga yanzu zuwa nan da bayan la'asar, zan bawa duk wanda ya gayamun waye mai takalmin nan tukwicin naira dubu ɗari biyu " hayaniya ce ta fara tashi sama-sama kowa da Abinda ake faɗa, Fahad ne yayi gyaran murya ya cigaba da cewa. Ina buƙatar hujja gamsassa nasan dai takalmin na mace ne kuma akwai hujjar da inna gani zan gane wacce take da mallakin wannan takalmin " Indo kallan tsaf tayi masa sannan tayi murmushi, daga cen gefe ta ɗaga hannu, kallanta yayi cikin mamaki ya gyaɗa kai alamar ta fito, da idanu ya bita yana wani nazari domin gani yake kamar yaso yasa fuskarta. Tana fitowa gaban jama'a ta kalleshi ido cikin ido ta ce, " Nasan Mai takalmin amma dubu ɗari biyu tamun kaɗan kuɗin tukwici" Da mamaki kowa ya zurawa Indo ido shi kansa Fahad mamaki ne ya kamashi, jinjina kai yayi ya ce, " Faɗi duk abinda kike buƙata na miki alƙawari zan cika miki " Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi kamar mutuniyar kirki sannan ta ɗago ta ce, " So nake kayi sati biyu acikin garin nan, kuma wannan kuɗin ka maidasu su zama naira dubu ɗari biyar " _Ummou Aslam Bint Adam_😉 [17/06, 03:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ BAYAN ƊAN HUTUN DANA ƊAUKA YANZU NA DAWO🌚 BARKANMU DA SALLAH DA FATAN KOWA YAYI SALLAH LAFIYA, INA MUKU FATAN ALHERI.🥰 27&28 Fahad Jim yayi saboda Allah ya sani ba zai iya ƙara koda kwana uku a wannan ƙauyen ba bare kuma sati guda, Indo kamar ta so ta gano lagwan Fahad ta ɗauke kai gefe tana murmushin gefen baki, kallan sa tayi ta tsuke fuska ta ce. " Naji kayi shiru inbazaka iya ba zan wuce dan ina da Abinyi " Da sauri Fahad ya ɗago da kansa yana kallon saboda yanda tayi maganar cikin izza da ƙasaita kai ka ɗauka wata isashshiyar budurwa ce take magana, ɗan karka kansa yayi gefe yana jinjina kansa saboda kusan tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa gaya masa haka, guntsun zaki ya ja sannan ya ce. " Bazan iya sati a cikin baƙin ƙauyen nan naku ba, while zan iya ƙara miki kuɗi akan yanda kika buƙata but karki wuce yau banji wani issue ba, ki tabbatar da kin haɗo da ɗayan warin takalmin " Indo bakin zaninta ta kunto ta ciro gyaɗarta marau sai da ta ɓare ta watsa ta a baki, tana ci tana tauna kamar ba zata bawa Fahad amsa ba ta, maida ƙullin gyaɗar tayi jikin zaninta ta ɗaure sannan tayi taku biyu ta kalleshi ta ce, " Kamar yanda na gaya maka ina da abinyi idan har bazaka ƙara sati ba to shikenan, kuma ƙauye dai naga asalin kowa ƙauye wanda ma basu da ƙauye ba birgewa sukayi ba " sauran gyaɗar hannunta ta watsa baki ta cigaba da tauna " Fahad haushi ne ya kamashi saboda irin maganganun da Indo ta gaya masa, basarwa yayi saboda ya lura idan ya biyewa Indo sai ta zubar masa da mutumci a idanun jama'a. Ɗauke kansa yayi daga kallanta ya ce, " Shikenan ba buƙatar hakan kije na gode " Indo zuciyarta fes saidai a ɓangare ɗaya ƙirjinta banda lugude ba abinda yake dan gani take kamar fahad zai gano ta. Wasu tafka-tafkan tsofaffun sifas ɗin Jamilu ne saƙale a ƙugunta da ta ɗaure su da mayafinta, cikin halin ko inkula ta kunce su ta fankama abinta a ƙafa, Fahad haushin Indo ne ya rufe a fili ya ja gudun tsaki ya kuma ɗauke kai gefe. Gabaɗaya mutanen gurin ido suka zubawa Indo kowa yana mamakin ƙarfin hali irin na Indo, ƴan matan garin kuma suna mamakin yanda Indo ta tsaya take iya gayawa Wannan kyakykyawan Ɗan birnin magana, ta ɓangare guda kuma suna ganin wautar Indo da taki amincewa da buƙatarsa alhalin tasan wannan Mai takalmin ga kuma maƙudan kuɗin da yace zai bayar. Su Zulai na gefe guda suna ƙus-ƙus da alama zancen Indo sukeyi akan takalmin Lami ce tace wa Zulai. " Zulai ni takalmincen sai yayi mun kama da naccgff Sarƙa ko dai nata ne take wa Ɗan birni basaja? " Zulai da tasan halin Indo idan akaji magana daga gurinta ta fito ta ce, " Oho waya sani yanda kika ganshi nima haka na gani " Lantan abokiyar ƴar tsamar Indo tayi karaf ta ce, " Ke Zulai wallahi kinyi asara yanzu Sarƙa kike tsoro saboda kina gudun karta yankaki ɗanye, ai nasan komai sarai wannan takalmin Sarƙa ne mu za'a rainawa hankali " Zulai ta watsawa Lantan harara ta ce, " Kanki ake ji keda bakya tsoro ai gaki nan a tabonta a goshinki " Suna cikin haka Indo ta ƙaraso gurin sai da ta ƙare musu kallo sannan ta tsare su da ido ta ce, " Magana ta akeyi ko " Lantan ɗauke kai gefe tayi Zulai ta ce, " Indo gaba tayi ta koma bakin bishiya ta zauna tana sauraron abinda Fahad zai ce. Fahad kallonsu yayi ya ce, " Bayan ita babu wanda yasan mai takalmin nan? So idan babu kowa zai iya tafiya " kamar masu jira haka suka dinga wucewa zugwi-zugwi, wasu daga cikinsu tsaki suke suna ƙananan maganganu. Fahad na nan zaune wata dabara ta faɗo masa, murmushi yayi a fili ya furta, " Dole mu shirya tafiya gida yau hakan ne zai bani damar kama duk wacce take shuka tsiyar nan " Indo dake cen bakin bishiya a zaune tunanin irin muguntar da zata yiwa Fahad kafin ya tafi dan ta fanshe marinta, tana nan zaune Fahad ya tako cikin nutsuwa kamar bazai tak ƙasa ba, sai da ya wuce ta ta harari bayansa a fili take, " Yana tafe yana ƙwanbare baya kamar Allon Malam Barau mai tsangaya " BA LALLAI NA DINGA POSTING KULLIN BA SABODA ASEELA FANS MA SU SAKONI GABA🤣 GA WANDA BAIJI BARI BA SO KAWAI SAI YANDA TA KAYA. _BINT ADAM CE_😉🌚 *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 29&30 Fahad yaji sarai abinda indo ta faɗa har yayi gaba kamar bazai juyo ba sai kuma ya dakata ya jiyo ya kalleta, indo basarwa tayi kamar ba ita tayi maganar ba sai ma ta fara waƙar, " Ahayye sha madarar lilo..." waƙar take yi har ƙarshenta tanayi tana taunar gyaɗarta tana gyaɗa kanta, girgiza kai Fahad yayi ya wuce yana mamakin fitina irin ta wannan yarinyar. Indo na zaune su Zulai suka ƙaraso gurinta suma zama sukayi a gefenta, Indo na ganinsu ta watsa sauran gyaɗar a baki ta cinye, Zulai ce ta ce, " Sarƙa saboda kin ganmu zaki cinye sauran gyaɗar? " Indo kamar jira take ta ce, " Ni banma ga ƙarasowarku ba sai yanzu, to idanma na cinye ba tawa bace " Saude ta ce, " kedai kawai kice kin cinye amma ba maganar baki ganmu ba " Indo shiru tayi bata tanka musu ba, tashi sukayi zasu tafi ko me indo ta tuno da sauri ta ruƙo hannun Zulai ta ce, " Yauwa ƙawaye na ina zaku ne? " Saude ta ce, " Zamu tafi munga kamar bakya buƙatar zaman mu " Tasowa tayi ta shiga tsakiyarsu tana saƙala hannuwanta akan kafaɗarsu ta cigaba da cewa. " Saude kunsan me nake so? " Kamar masu jiranta suka ce, " A'a sai kin faɗa " " Wallahi tun ɗazu nake tunanin irin abunda zanyi wa wannan ɗan birnin na fanshe marin da yamun amma na rasa ku kawo wata dabarar " cewar Indo. Zulai tayi karaf ta ce, " Sarƙa kinsan Lantan taso gane kece me takalmin nan ɗazu har tambayata tayi " cikin halin ko'inkula Indo ta ce, " To ai da kun bata amsa inyaso taje ta faɗa masa wallahi dai-dai nake da zamaninta tasan karnmu da ita baya kyau " Saude ta ce, " Gaskiya Sarƙa tsoro nake ji kinga fa yanda mukayiwa Mai gari baiji da daɗi ba, kawai kiyi haƙuri tsoro nake karmu jawa kanmu ruwa, haka kawai a kamamu a tafi damu birni gurin ƴan sanda " Tunda Saude ta fara magana Indo ta kafeta da ido cikin masifa ta ce, " Da haƙurin ya mutu sadakar nawa kika bani, dama na lura tun cen ke matsoraciya ce, ki barshi bana gayyarki kuma wallahi idan asirinmu ya tonu ko bake bace kece, aikin banza ni wallahi bana tsoron mutum sai Allah, ba ƴan sanda ba Allah sa gun ƴan itace za'a kaimu " Indo na ƙarasa maganar taja hannun Zulai zasu wuce, Saude jiki a sanyaye tabi bayansu tana bawa Indo haƙuri. Indo zuciyarta ƙal saboda dama tasan su Zulai bazasu watsa mata ƙasa a ido ba, cen ƙofar gidansu indo suka ƙarasa akan dandamalin ƙofar gidan suka zauna, Zulai ce ta kalli Indo ta ce, " Wai Indo ya akayi kika bar takalminki gidan Mai gari kodai tarko suka ɗana miki? " Indo jim tayi kamar mai nazari sannan ta bawa su Zulai labarin abinda ya faru tsakaninta da Fahad, dariya suke harda riƙe ciki. Itama dariyar take sosai suna nan zaune Jamilu yazo ya wucesu ya samesu suna wannan dariyar, jikinsa ne ya bashi wannan zaman nasu ba abin arziƙi zasu ƙulla ba, har ya kusa shiga gida ya juya fuska a tsuke ya ce. " Ke kizo muje zan aike ki " Biris Indo tayi kamar bataji Mai ya ce ba ta cigaba da ƙyaƙyata dariyarta, Saude ce ta ce, " Sarƙa ana miki magana " Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, " Waye yake kirana ni banji an ambaci suna na ba ai " Jamilu ƙarasowa yayi ya zuba mata rankwashi yace, " Ni ne nake kiranki " A zabure ta miƙe tana sosa kai harara ta watsawa Jamilu tana murguɗa baki ta ce, " Wallahi ka daina cin zalina idan ba haka ko..." Jamilu ya katse ta, " Idan ba haka ba me? Ramawa zakiyi? " ƙeya ta juya masa tana ɗan girgiza jiki kamar me jiran kaɗan ta fara dambe, Jamilu kallan Indo kawai yayi takaicin ta ne ya kamashi, juyawa yayi ya wuce ciki ya na faɗin, " Zaki shigo gida zaki mun bayani " Indo ta ce, " Idan na shigo karka barni da rai " Zulai ce ta cewa Indo, " Sarƙa dan Allah ki daina yiwa Jamilu wannan abun, duk garin nan anshaida baida abokin faɗa, ni wallahi har cikin zuciyata nake jin ƙaunarsa dama yace yana sona " Da sauri Indo ta juyo tana kallan Zulai cikin mamaki tafara tafa hannuwa tana salati, Zulai waigawa tayi tana duba hanya taga babu mai ganinsu, ƙasa tayi da murya ta ce, " Ke Sarƙa meye dan nace inasan Jamilu " Da sauri Indo ta fisge hannunta da Zulai ta dafa ta cikin zallar tsoro Indo ta ce. " Zulai ashe kin koma ƴar iska ban sani ba? Wallahi mun raba hanya babu ni babu ke tun kafin Goggo ta rasu ta ce mun duk wanda yace yana sona ɗan iska ne ashe kema kina cikinsu? Kuma wallahi ina shiga zan gayawa Baba Huwaila kuma ko ƙofar gidan nan karki ƙara zuwa " cikin zulai ne ya ɗuru ruwa tsoro da fargaba suka kamata sai yanzu take ganin abinda ta faɗa ba dai-dai bane, ita ta ɗauka ba laifi bane dan kace kanasan mutum saboda taji Yasiran gidansu ta ce tanasan Muɗɗafa, cikin tsoro ta janyo Indo tace. " Dan ALLAH Sarƙa kiyi haƙuri ni bada wata manufa na faɗi haka ba, naji rannan Yasiran gidanmu tace tanasan Muɗɗafa shima ya ce yana santa kuma Innarmu bata mata faɗa ba " Sototo Indo tayi har Zulai ta gama magana sannan ta ce, " Wato agun Yasira kika koyi iskanci ko to wallahi ni babu ruwana, mu gidanmu ba ƴan iska bane daga yau babu ni babu ke " Indo na gama magana ta tura ƙauren gidansu ta shige ta bar su Zulai a tsaye. Zulai duk ta firgice da ka kalleta zaka gane tana cikin tashin hankali, kallan Saude tayi ta ce. " Saude wallahi bansan meyasa na faɗawa Indo inasan Jamilu ba " Saude jiki a sanyaye tace, " Zulai kema me ya kaiki ni kaina Innarmu ta ce duk wanda yace yana sona ɗan iska ne amma wai yau da bakinki kike faɗa " Zulai ƙasa tayi da murya ta ce, " To amma bazaki gayawa kowa ba ko? " Saude shiru tayi kamar mai nazari sannan ta ce, " Amma wallahi kika ƙara ko nima na daina hurɗa da ke " daga haka rankayawa sukayi suka wuce gida Zulai kamar wata mara lafiya. Fahad na zuwa gidan Mai gari Fuska ba walwala ya kalli Mommy ya ce, " Mommy ya kamata muzo mu wuce saboda yanzu aka kirani a waya ina da wani uzuri " Mommy kamar taso ta fahimci Fahad amma sai tai tunanin Fahad bai saba ƙarya ba hasalima baya shiri da maƙaryaci, murmushi tayi ta ce, " Ɗan gidan Mommy ko gajiya kayi da garin namu? " Girgiza kai yayi ya ce, " A'a kawai dai ina da wani uzuri ne " Mommy ta ce, " To shikenan bari muzo mu fara shiri amma mu da gida sai dare " Shiru yayi saboda yasan Mommy ta faɗa ne dan bataso tafiyar yau ba. Mai gari taje ta samu ta sanar dashi ta ɗebo kudi masu ɗan dama ta bashi, haka matansa ma tayi musu alheri sannan suka fara shirin tafiya. Lokacin da Indo ta ƙarasa cikin gida kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, jiki ba ƙwari taje ta zauna ta zuba uban tagumi, Baba Huwaila ce ta fito daga ɗaki ta ƙarewa Indo kallo ta ce. " Indo lafiya naga kin zuba uban tagumi ko wani abun kika aikata kafin ki shigo gidan? " A sanyaye Indo ta ɗago ta ce, " Baba Huwaila kafin Goggo ta rasu ta ce mun duk wanda yace yana sona ɗan iska ne? " Baba Huwaila ta ce. " Eh, waye yace yana sanki? " Indo sai da ta leƙa ɗakin Jamilu ta hango labulensa a sauke yake sannan ta ce, " Wallahi Zulai ce tace tanasan Jamilu nikuwa nayi mata tas dan nace ko gidanmu karta ƙara zuwa " Baba Huwaila zama tayi kusa da Indo zata fara magana Jamilu ya fito daga ɗaki. " Tana ganinsa ta ɗauke kai gefe takowa ya farayi cikin zuciyarta tace, " Jibeshi wani soɓoɓo mugu azzalumi " Jamilu takowa yayi yazo har kusa da Indo ya zauna juyo da ita yayi, yasa hannunsa ya haɗa hannuwanta biyu ya riƙe cikin shammata ya zuba mata rankwashi, so take ta fisge hannunta ta kasa ga azabar rankwashi. Tamke fuska yayi sosai ya kalleta ya ce, " Indo rainin da kuka min keda sauran shaiɗanun ƙawayenki har ya kai haka? " Baba Huwaila da sauri ta fisge hannun Indo ta rufe Jamilu da faɗa. " Meye laifinta aciki ita tace tana sanka ko ƙawarta? Saboda zalinci ko Jamilu? Wallahi ka fita harkar yarinyar nan idan ba haka ba ranka zaiyi mummuna ɓaci, da ka samu akace ana sanka ma har wani kyau gareka da zaka tsaya zaɓen budurwa, Ina laifin Zulai yarinyar arziƙi " Haushi ne ya kama Jamilu ya ce, " Ai duk tsiyar da Indo take shukawa ku kuke ɗaure mata, ni me zanyi da ƙawayen Indo? Inrasa wacce zanyi soyayya da ita sai ƙawayen Indo tir Allah ya tsareni " yana gama faɗa ya tashi ya fice daga gidan. Cikin faɗa Baba Huwaila ta ce, " Ka zauna ruwan ido har ka rasa wacce zatayi da ka sakaran banza sakaran wofi meye aibunsu " juyowa tayi ta kalli Indo ta ce, " Goge hawayenki kinji Indo na, ita kuma Zulai karki daina kulata ai ba kowa ne idan yace yana sanka ya zama ɗan iska ba, idan mutum yace zai taɓa ka shine ɗan iska " Sai a lokacin Indo ta fahimci abinda Baba Huwaila ta sanar da ita. *INA KUKE MASOYA LITTAFIN WANDA BAIJI BARI BA BOOK2 YA KAMMALA, KAMAR YANDA NA GAYA MUKU BOOK1FREE NE, DA NAIRA 100 ZAKI KARANTA BOOK2 ƊINKI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKI BIYA NAIRA 100 DA SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624* _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [26/06, 19:42] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 31&32 Goge hawayen idanunta tayi ta miƙe ta shiga ɗakin Baba Huwaila, kan gado ta faɗa tayi rufda ciki tana nazarin irin abinda zata shukawa Fahad dan ta fanshe abinda yayi mata, kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta fito ta shuri takalmanta ta fice, Baba Huwaila kallanta tayi tana girgiza kai a fili ta furta, " Oh nidai na godewa Allah, Allah ka shiryamun Indo ko yaushe yarinyar nan zatayi hankali? Yarinya harta fara ƙirgen dangi amma babu saurayin kirki da ta taɓa tsaida ta " Jamilu da ya shigo gidan ya riski maganar Baba Huwaila ya ce, " Yaushe zatayi hankali bayan ku kuke ƙara sangarta yarinya, idan kuka cigaba da tafiya a haka to wallahi sai an aurar da ƴan matan garin nan gaba ɗaya idan tayi kwantai ma nemi wani tsohon mu bashi,Tsohon ya raka da ita " a hassale Baba Huwaila ta ce. " Bakinka ya faɗa kanka sakarai, kai Jamilu ka fita harkar yarinyar nan to bari kaji Indo ko mai mata bazan bawa ba bare kuma tsoho cen sai dai idan kai zaka auri tsohuwa kai da kullin cikin ruwan ido kake " Jamilu bai tankawa Baba Huwaila ba ya shiga ɗaki ya ɗauko jakarsa har yazo tsakiyar gida ya ce, " Baba Huwaila zan wuce na canjowa Indo Uniform dan na gaji da ganinta da wannan tsangalallen wandon kamar mai shirin tsallaka ruwa, kuma wallahi wannan karan bazan laminci rashin zuwa makarantar da batayi ba, ace yarinya a sati baifi ta je makaranta sau ɗaya ko biyu ba kuma ana kallanta, shiyasa gata nan da kwakwalwa kamar ta kifi babu tsiyar da take tsinanawa a makarantar " Indo dake ɗakin tayi farat ta fito tana riƙe da ƙugu ta ce, " Wallahi badai ni ce mai kwakwalar kifi ba kuma daga yau wallahi na daina zuwa makarantar tunda ba ta Allah da Annabi bace " ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki, da sauri Jamilu ya zabura zai juya gurinsa Baba Huwaila ta dakatar da shi, cikin jin haushi ya ce. " Wallahi karki bari na kamaki kuma makaranta babu fashi mu zuba nida ke mu gani " yana gama faɗa bai jira cewarsu ba ya fice. Baba Huwaila ƙarasawa tayi gurin Indo ta ce, " Indo ina rabaki da rashin kunya Jamilu fa kamar yaya yake a gurinki, kinga dan ina hanashi ne amma wata rana ya kamaki bana kusa wallahi zai miki dukan tsiya " Zumɓurar baki Indo tayi ta ce, " To bakiji me yace ba, wai nice mai Kwakwalar kifi " Baba Huwaila ta dafa Indo ta ce, " Kyaleshi ya faɗa ne kawai amma ba wata kwakwalwar kifi da kike da ita, Keda zaki hadda ce mana izifi sittin " Murmushin jindaɗi Indo tayi ta faɗa ɗaki ta koma kan katifa, har zuwa wannan lokacin nazarin abinda zata shukawa Fahad takeyi. Indo bata jima a kwance ba tayi wani nazari lokaci guda ta bushe da wata irin dariya, tun tanayi a hankali har ta fara kyakyatawa harda riƙe ciki, Baba Huwaila ɗagowa tayi tana kallan Indo da mamaki sannan ta ce, " Indo karfa harsashen mutane ya tabbata akanki da suke miki take da ƴar uwar Aljanu, banda haka ke kaɗai ki dinga ɓaɓɓaka dariya sai kace mai hauka sabon kamu? " Indo kuma tuntsirewa tayi da dariya ta kalli Baba Huwaila ta ce. " Baba Huwaila ba komai amma bari naje gidansu Zulai na dawo " Indo bata jira cewar Baba Huwaila ba ta shuri takalmanta zata fita, ɗakinta ta faɗa cen cikin fanteka ta buɗe ta ɗauko wani ɗan mukulli ta ɓoyeshi ta fice, wani ɗan ɗaki dake jikin ƙofar shiga gidan Baba Huwaila ta buɗe banda Ɓeraye da gafiya babu komai a ɗakin sai wasu ƙananan buhunhunan gero da sauran kayan amfanin gona, Indo na shiga ɓerayen suka fara guduwa ramukansu. Cikin sa'a ta sa dutse ta buga wata ƙatuwar gafiya take ta mutu, fita tayi da sauri taje ta ɗauko magen Baba Huwaila a soro ta ajiyeta ta samu wani tsohon zanin Baba Huwaila ta yayyaga shi ta ɗaure ƙugun magen kamar wani ɗan biri, sauran igiyar ta ɗaure a jikin kofa ta fita taje ta ɗaure jelar Gafiyar da sauran tsumman sannan ta koma ta kunto magen, acikin wani tsohon buhun ta jefa gafiyar ita kuma magen ta sata a cikin hijabinta, idan kaga Indo zaka rantse aikenta akayi. Janyo ɗakin tayi ta rufe mukullin taje soron gidansu ta ɗaga dutse ta ajiye tana gudun kar ta shiga gida asirinta ya tonu, lokacin da indo ta wuce Jamilu na zaune da Abokinsa Hassan kamar mutuniyar kirki haka ta wuce su, Jamilu mamaki ne ya kamashi ganin irin tafiyar nutsuwar da Indo take yi, sai dai acikin zuciyarsa daɗi yaji a tunaninsa faɗan da yayi mata ne yasa ta fara nutsuwa. Kai tsaye Indo gidan Mai gari ta nufa taci sa'a babu mutane sosai yawanci masu wucewa ne, sai da ta faki ido sannan ta ɗane bishiyar kofar gidan Mai gari, murmush tayi musamman da taga motar su Fahad na ƙofar gidan. Ta hau bishiyar babu jimawa taga Fahad ya fito da waya akunne da alama waya yakeyi, jikin motar ya jingina ya bawa bishiyar da Indo take kai baya, a hankali indo ta fito da gifiyar cikin Buhu ta fara zurota tana riƙe da igiyar, sai da ta kawota kusa da dai-dai ƙeyar Fahad sannan ta fito da magen nan itama ta fara zurota, Magen nan na hango gafiya tayi wani kukan kura ta kai mata cafka a dai-dai lokacin Indo ra saki Gafiyar da magen hannunta ta faɗa kan kafaɗar Fahad, kusan tare suka sauka kan Fahad gafiyar da magen, take magen ta fara yagar gafiyar da faratanta tana haɗawa da wuyan Fahad. Banda ihu ba abinda Fahad yake yana faɗin, " Help ! Help " ihun Fahad yayi dai-dai da fitowar su Momy, Indo dake saman bishiya banda dariyar ƙeta ba abinda takeyi, tana tsaka da dariya taga Fahad ya faɗa gidan Mao gari da gudu, a hankali ta furta. " To idonsa ya rufe baida Mommyn bane? " tana gama faɗa ta kuma ƙyaƙyatawa da dariya. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [06/07, 18:06] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 33&34 A tsorace duk suka bi bayan fahad da kallo ko zasu ga wani abinda ya sashi gudu amma basu ga komai ba, Mommy hankali tashe ta juya tana ƙwalawa Fahad kira, Mai gari ma rufa mata baya yayi suna kiran Fahad amma ko ƙurarsa basu gani ba, suna shiga gidan a cen ƙuryar ɗakin Mai gari suka hango Fahad yana ta karkaɗe-karkaɗen riga, Mommy saurin dafa shi tayi ta ce, " Fahad lafiyarka me yake faruwa ne " Kafin Fahad yayi magana Maigari ya ce, " Wallahi ni dama nasan tunda ya taɓosu bazasu ƙyaleshi haka ba, Haba Malam fatalwa wasa ce? Ba yan da banyi ba dan inja kunnenka kaƙi ita fa fatalwa ba ruwanta da ɗan birni ko ƙauye " Jiki a sanyaye Mommy ta ce, " Yaya kana nufin fatalwa ce tasa Fahad wannan abun? " Fahad da baƙin ciki ya kamashi kamar zaiyi kuka yace, " Mommy wallahi bazan ƙara dawowa garin nan ba, mage ce fa ta kama ɓera akaina Mommy..." saboda takaici kasa ƙarasa maganar yayi Mommy mamaki ne ya kamata ta ce, " Mage ta kama ɓera akanka Fahad? Shi ɓeran ya akayi ya hau kanka? " Fahad jin maganar Mommy yayi kamar anwatsa masa ruwan zafi, furzar da iska yayi ya nunawa Mommy wuyansa, Hannunta Mommy ta kai gurin ta ga yanda shatin yaƙushin mage ya fito a wuyansa gurin har yayi ja, Sannu Mommy ta fara jera masa yana amsawa da ƙyar, Mai Unguwa kallan Fahad yayi yace, " Kai Fahad ka tabbata mage ce tayi maka haka ba fatalwa ba? " Cikin jin haushi Fahad ya ce. " Dan Allah ka daina mun maganar wata fatalwa, naga jiya-jiya nace maka wata yarinya ce zaka take zuwa tana raina muku hankali " Maigari shiru yayi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya ce, " Amma wallahi ka bani kunya Fahad magence kake yiwa wannan ihun da tsalle kamar zaka suma, kudai yaran birni sakalci yayi muku yawa " Fahad ƙara tsuke fuska yayi ya ce, " Muje Mommy muyi mu bar garin nan " Mommy gaba tayi Fahad na biye da ita a baya. Lokacin da su Mommy suka shiga gidan Maigari Indo sakkowa tayi tana dariya, wajen motarsu taje ta fara leƙawa tana duddubata,gurin morrior taje ta tsaya tana ƙarewa fuskarta kallo, muryar Mommy ta jiyo tana cewa, " Ai dama Fahad tun yana ƙarami babu abinda yafi tsoro kamar magane shiyasa inasan kiwonta akan dole na haƙura " Indo acikin zuciyarta ta ce, " Alƙur'an da nasan haka ne acikin motar na zura masa magen naga abinda zaiyi mutum sai shegen iyayin tsiya " Fahad na ƙarasawa ko magana bai yiwa Indo ba yasa hannu ya ja hijabinta ya janye ta gefe saboda gabaɗaya ransa a ɓace yake, Mommy ce ta kalleta ta ce, " Ƴan mata kwalliya ake kallo a mudubi? "Indo washe baki tayi ta ce, " Ai banmayi kwalliyar ba sai zani dandali anjima " Mommy tsai tayi ta kafe Indo da kallo tana ƙarewa fuskarta kallo, hatta muryarta jinta tayi kamar tasan mai irinta Fahad ne ya katse mata tunani da, " Mommy ki shigo mu tafi " Mommy jakarta ta zuge ta ɗauko dubu ɗaya ta miƙawa Indo ta ce, " Ƴan mata ya sunanki? " Indo daɗi ne ya kasheta tayi farat ta ce, " Sunana Indo " Murmushi Mommy tayi ta ce, " To maza ki tafi gida ki gaida Innarki a daina wasa a hanya" Indo hannu biyu ta sa ta karɓi kuɗin tana zabga godiya,Maigari ne ya ce, " Maza Sarƙa a wuce gida " Indo gefe ta ja Mommy ta buɗe mota ta shiga tana yiwa Maigari sallama amma har lokacin waigen Indo take da zubin tafiyarta " Indo na hango motarsu Fahad ta fara tafiya ta tsaya tana ƙare musu kallo har suka ɓacewa ganinta, A guje ta sheƙa gida tana karya kwana sukayi karo da Jafaru Ɗan gidan Malam Isa ya karɓo markaɗen gasarar koko da mahaifiyarsa take na siyarwa, gaba ɗaya gasar ta ɓata musu jiki shi da Indo, cikin fargaba da tsoro ya ɗora hannun aka yana cewa, " Yau na shiga uku Indo kinja mun wallahi bazan yarda ba sai kin biyani " Wani Uban ashar Indo ta ƙunduma ta ce, " Wallahi Jafaru idan duk ƙauyen nan gatanka ne bazan biya ba tunda ai gware mukayi ba da sani na na bige ka ba, meyasa da kaga na taho baka matsa ba? Ji yanda ka ɓatamun jiki wallahi sai anwankemun hijabi na " Isa da takaici ya kamashi ya shaƙo wuyan Indo ya ce, " Sarƙa wallahi bazaki rainamun hankali ba dole Baba Huwaila ta biya ni, yarinya sai tashen rashin ji kamar jikar sheɗanu " Indo fisge hijabinta tayi ta ce, " Wallahi Isa ka iya bakinka idan ba haka zan shuka maka tsiya " Cikin jin haushi Isa ya kife Indo da mari ya ce, " Ni zaki kawowa iskanci Sarƙa duk abinda nayi miki aike kika ja " Indo bokitin ƙullin ta sura da sauri ta juyewa Isa sauran ƙullin akai ta kifa masa bokitin acikin kansa sannan ta zura aguje, Isa banda lalube ba abinda yakeyi yana tafe yana kurma ihu ga ƙulli ya shigar masa idanu, yana tafe Audi ya taho akan mashin yayi ciki da Isa. Audu da Isa cen gefe suka faɗi kowa na maisa ajiyar zuciya, Audu salansa ce ta danne masa ƙafa cikin azama ya ture mashin ɗin gefe, Isa kuma kurjewa yayi a cinya da hannuwansa sai kansa da ya dinga buguwa da bokiti, mutane ne suka taru agurin suka fara ƙoƙarin kai musu agaji. Indo gida ta faɗa da gudu tana haki acen ƙofar ɗakin Baba Huwaila ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, Baba Huwaila dake tuƙa tuwo ɗagowa tayi ta ce, " Indo wata maganar kika ƙara ɗaukomun ko? " Indo har lokacin bata daina sauke numfashi ba ta ce, " Baba Huwaila wallahi ba abinda nayi kawai gware mukayi da Isa " gyaɗa kai Baba Huwaila tayi ta ce, " Nasan za'a rina tunda ga jikinki nan ya nuna, ki tashi kije kiyi wanka ki gyara jikinki " Indo zumɓurar baki tayi ta ce, " Gaskiya sai dai na wanke ido na, yamma fa tayi sanyin magariba ya fara sauka " Baba Huwaila riƙe haɓa tayi tace, " Indo yanzu Allah rayuwa zata yiwu haka rabonki da wanka yau kwana nawa? Idan ba mantawa nayi ba kusan kwana huɗu kenan kullin sai dai ki wanke ido a haka zaki samu saurayi? Kibar ganin ina kareki agurin Jamilu dan kar ya samu lagonki ne yasa bana goyon bayanki, wallahi idan baki tashi kin tafi bayi kinyi wanka ba ina gama kwashe tuwon nan da kaina zan kamaki inwanke ki tass" Indo kamar jiran Baba Huwaila take ta dire zancen tayi karaf ta ce, " Cabdijam, Alƙur'an bazaki mun wanka ba sai kace wata yarinya " Baba Huwaila Murmushi tayi saboda tasan dama zasuyi haka da Indo, tsuke fuska tayi ta ce, " To ki tashi ki tafi idan ba so kike na miki da kaina ba " Indo tunawa tayi da kuɗin da Mommy ta bata da sauri ta ce, " Yauwa Baba Huwaila kinga kuɗin da Baƙin Maigari suka bani " ta ƙarasa maganar tana nunawa Baba Huwaila dubu ɗaya. A tsorace Baba Huwaila ta dafe ƙirji ta ce, " Ke Indo ki rabani waye ya baki wannan kuɗin ince dai ba namiji bane? " Indo na shirin magana sai ga Jamilu ya shigo cikin gidan yana shiga babu wanda yayiwa magana, kai tsaye hannun Indo yaje ya damƙa yayi hanyar waje da ita, da sauri Baba Huwaila ta miƙe tana cewa. " Kai Jamilu ya kake figar mun yarinya kamar kaza ina zaka kaita? " Fuska a tsuke Jamilu ya ce, " Megari ne ya turo ana kiranta shine zan miƙa musu ita " " Amma Jamilu bantaɓa tunanin ƙiyayyar da kakewa Indo ta kai haka ba, yanxu idan ka miƙa ta wato ko kasheta za'a ayi kai ba ruwanka, to sakarmun hannunta idan kai bakasan girman amana ba nina sani kakar yarinyar nan hannu da hannu ta damƙa mun ita, ka ɗauka saboda ƙasa ta rufe mata ido zan ci amanarta ne, yarinya marainiya gaba da baya " Da ƙarfi Jamilu ya saki hannun Indo ya ce, " To shikenan Wallahi daga yau zan tsame hannuna akanta gaba idan ta kashe mutum duk yanda za'ayi mata sai ayi, Allah ina gabda tafi ya gurinsu Baffa ina dalili yarinya ta buwayi kowa a gari " Baba Huwaila ƙasa tayi da murya ta ce, " Haba Jamiluna karmuyi haka da kai mana, indai Indo ce zan ja mata kunne kaji, yanzu bari na rufa mayafina muje gurin Maigarin " Baba Huwaila kwashe sauran tuwon tayi ta ɗauko mayafinta suka ranka gurin Maigari, Indo kamar mutuniyar kirki tayi shiru sai kallan mutane take ɗai-ɗai. Lokacin da suka je fadar Maigari kusan cike take da mutane, Baba Huwaila da Indo guri suka samu suka zauna Maigari kallan tsaf ya karewa Indo sannan yace, " Sarƙa ungo wannan, Ja'ira mai siffar Aljanu yarinya ƙarama sai hatsabibanci, dubi yanda kikayiwa mutanen nan " Maigari ya ƙarasa faɗa yana nuna su Isa dake gefe. Baba Huwaila na shirin magana Indo tayi karaf ta ce, " Saboda duk garin nan ni aka tsana su baza'a tuhumesu ba sai ni? " Maigari kallan Ɗan jummai yayi yace, " A gyara mata zama " yana rufe baki Ɗan Jummai ya fara zabgawa Indo bulala ta ko'ina, tun tana ihu har ta gaji ta yanke jiki ta faɗi, Ɗan Jummai na shirin zabga masa bulala Indo tayi wani kukan kura mai haɗe da kuwwa ta fisgi bulalalar hannun Ɗan Jumma ta fara zuba masa tun ƙarfinta. Wani irin hargitsatsen yare takeyi tana ihu haɗe da kai duka har kan sauran mutane, Maigari na ganin haka ya fara ja baya yana maƙalewa jikin kujerarsa, lamarin Indo ba ƙaramin tsoro ya bashi ba cikin zuciyarsa yake faɗin, " Anya yarinyar nan bata da aljanu ko dama su suke sata take wasu abubuwan na hatsabibanci..." tunaninsa ne ya maƙale lokacin da yaji saukar bulala a tsakiyar kansa, take yaji kansa ya ɗaure musamman da yake kan nasa har zuwa lokacin akwai sauran ciwon dukan ludayin da Indo tayi masa, yana shirin magana yaji tana ta tafka masa bulala ta ko'ina a zabure Maigari ya miƙe ya bi hanyar gida yana gudu babbar riga tana taɗe shi har kusan adungure yake yi, kafin wani lokaci tuni gurin ya hautsine mutane kowa ya fara takai-takai. _INJI RUWAN COMMENTS🥴🥴🥴🥴 IDAN NAJI ƊIF NIMA NAYI ƊIF NA FARA *ANYA BAIWA CE?* MASU SIYA HAR SUN FARA TAMBAYA TUN KWANAKI, NA DAKATA NE ZUWA BAYAN SALLAH INSHA ALLAH IDAN NAGA BA COMMENTA SHIKENAN🤒🤒🤒🤒 FATAN ALHERI AGAREKU🌚🌚🌚🌚_ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [10/07, 16:36] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 35&36 Duk inda Maigari ya shefa ƙafarsa ya ɗauke Indo ce take ɗora tata haɗe sa zabga masa bulala, ba ita ta ƙyaleshi ba har sai da ta raka Maigari har soron gidansa, da gudu ta juyo kamar Mai hauka sabon kamu haka ta dawo ta cigaba da kaiwa sauran mutanen da suka rage duka ta ko'ina,Baba Huwaila dama tun lokacin da ta ga Indo ta warci bulala ta haɗa takalmanta a hannu ta fara ɗingisawa tabi hanyar gida, duk abinda yake faruwa Jamilu na zaune a gefen bishiya yana kallan Indo takaicin duniya ya kamashi. Indo lura tayi da mugun kallon da Jamilu yake aika mata, jinin jikinta tasha a ganinta tana ganin kamar ya harbo jirginta, wani tunani tayi kawai ta fara wani kurma ihu tana kai duka, har ta ƙarasa gurin Jamilu tana zuwa barayi wata-wata ba ta ɗaga dorinar ta zabga masa a jikinsa, sosai bulalar ta shigeshi idanunsa ne suka kaɗa jawur saboda ɓacin rai. Da sauri ya fisgo hannun Indo har tana faɗuwa ƙasa, bulalar hannunta ya karɓa har ya ɗaga zai zuba mata sai yayi wani tunani ya sauke hannunsa, jan hannunta ya farayi suka nufi hanyar gida.Banda ihu da tsalle-tsalle babu abinda Indo take yi amma cikin zuciyarta ƙirjinta sai dukan uku-uku yake saboda tasan yau kashinta ya bushe. Mutanen da suke warwatse agurin juyawa sukayi suka fara kallan Indo da Jamilu har suka fara ɓacewa ganinsu, wasu daga cikin masu tsegumin har sun fara mara musu baya domin ganin ƙwaƙwaf,lokacin da su Indo suka ƙarasa gida Baba Huwaila na zaune tana maida numfashin wahala, da ƙarfin gaske Jamilu ya rufe ƙofar Baba Huwaila na ganinsu ta fara magana. " Jamilu maza turata ɗaki ka rufeta ka tafi gidan Malam Sadi ka kirawo shi yayi mata ruƙiyya,wallahi ni dama na daɗe jikina yana bani yarinyar nan akwai mutanen nan akanta amma idan nayi magan sai kace iskanci ne kawai, duba fa ka..." Maganar Baba Huwaila ce ta katse lokacin da taga Jamilu ya riƙe hannuwan duka biyun yana zabga mata bulala ta ko'ina, indo banda ihu da neman taimako ba abinda take yi. Kafin Baba Huwaila ta yunƙuro ta zo ceton Indo jikinta duk yayi ruɗu-ruɗu, cen gefe ya wurgar da ita sannan ya fara magana cikin ɓacin rai, " Daga yau munsa ƙafar wando ɗaya dake tunda iskancin naki ƙara gaba yake, haka kawai zaki maida mutane ƴan iska kin raina kowa iskancin naki har ya fara kaiwa kan manya da mutanen gari, ba aljanu ba Allah sa bishiyar bulukiya ce akanki, kuma daga yau idan na kuma jin wani yayi ƙararki wallahi sai kin banbance aya da tsakuwa " nunata yayi da ɗan yatsa ya cigaba da cewa, " Ku buɗe kunnenki ki saurareni da kyau, a gobe basai an ɗauki kwanaki ba zaki fara zuwa makaranta yanzu zan ƙarɓo miki uniform ɗinki nasan Musa baida saɓa alkawari, daga aike sai makaranta ko ɗiban ruwa na yafe miki idan kuma na kuma ganin ƙafarki a waje sai na ɓallata biyu, karyaki zanyi inkarya banza da wofi " Indo ɗago da jajayen idanunta tayi sai da ra murguɗa masa baki ta watsa masa harara ta ce, " Wallahi idan ka karya ni biyu nima sai karya huɗu " Jamilu da sauri ya bige bakinta ya ce. " Wato bakinki baya mutuwa ko? Baki da kunya ko? To ki saɓa ɗaya daga cikin abubuwan dana gindaya ki gani zaki gane kurenki " yana gama faɗa ya juya zai fita cikin ƙasa da murya Indo ta ce, " Allah ya isa mugu azzalumi kuma wallahu sai na rama " karaf a kunnen Jamilu juyowa yayi ya ce, " Karki fasa Indo duk abinda yake kanki zan sauke miki su " Yaran da suke ɗafe a jikin katanga ne suka fara ihu suna yiwa Indo waƙa. " Sarƙa taci duka wooo, ashe Aljanun ƙarya ne wooo, gashi jikinta yayi tsami wooo, kuzo mu sosa mata wooo, kuzo mu shafa mata wooo..." Jamilu zuciyarsa fes ya fice yasan ko ba komai yaran nan zasuyita tsokanar Indo tunda gashi har sun fara yi mata waƙa. Baba Huwaila tun lokacin da Jamilu ya fara magana shiru tayi saboda ta lura da ransa a matuƙar ɓace yake tasan yau takai Jamilu bango, Baba Huwaila bata taɓa tsammanin Indo Aljanun ƙarya tayi sai yanzu da Jamilu ya zane Indo taji tana neman ceto, tana shirin yiwa Indo magana ta hango Indo ta suri wani dutse ta jefawa yaron da ya fara mata waƙa a goshinsa tana cewa. " Uwarka Tasallah itace taci duka kuma wallahi duk shegen da ya kuma maimaita waƙar nan sai naci uwarsa " Ihun yaron ne ya karaɗe gidan ga jini na zuba a gashinsa, take sauran yaran sukayi shiru kamar haɗin baki suka sauka daga katangar, Indo komawa tayi ta zauna tana rafka uban tagumi kamar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa. Baba Huwaila riƙe haɓa tayi jiki a sanyaye ta dafa Indo ta ce, " Indo yanzu kullin kinfi san ayita kai ƙararki gurun Maigari ko? Yanzu daga wajen wata ƙarar taki muke kike ɓige da zane mutanen yanzu kin fasawa ɗan mutane goshi, Indo ya kike nayi? Kinfisan kullin Jamilu ya dinga dukanki kamar Jaka? " Indo cikin takaici ra ce. " Baba Huwaila bakyajin waƙar da suke mun kuma kawai sai insaka musu ido su rainani wallahi ni ba wanda ya isa ya gayamun ba daɗi " Baba Huwaila ƙwafa tayi ta ce, " Ai shikenan Indo hausawa suka ce Jiki magayi tunda haka kika ga yafi miki " Indo ɗauke kai gefe tayi tana ƙara jin ba daɗi a zuciyarta, tunani kawai take ta wace hanya zata rama cin kashin da Jamilu yayi mata a idanun yara. BAYAN WANI LOKACI Baba Huwaila ce tsaye agurun Indo tana mata magana cikin lallashi, " Yanzu Indo haka zaki zauna da yunwa tun ɗazu kici abinci kinƙi, wa yace miki ana zuciya da abinci? " Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, " Baba Huwaila wallahi ni bazanci abincin nan na rantse kuma bazan karya rantsuwa ta ba " Jamilu ne ya shigo gidan hannunsa ɗauke da ledar Uniform ɗin indo ya riski maganar da sukeyi da Baba Huwaila. Uffan bai furta ba ya wurgawa Indo ledar Uniforma ɗinta ya ce, " Gashi nan sai ki kwana da shirinki a gobe insha Allah zan gama miki komai..." yana cikin magana sallamar da akeyi a ƙofar gida ce ta katse shi, cikin ƙosawa yasa hannu ya dafe goshinsa yana furta, " Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un " yana nan tsaye yaji ankuma rafka sallama ana cewa. " Salamu Alaikum idan ba'a amsa ba zamu shigo da kanmu, aike ne daga fadar Maigari yace ko aka ne mu ɗauko yarinyar nan Indo " Cikin takaici Jamilu ya ce, " Basai kun shigo ba zamuje fadar da kanmu " Jamilu na gama magana ya kalli Indo fuska a murtuke ya ce, " Sai ki tashi mu tafi baƙar munafuka kike sinne kai ƙasa kamar mutuniyar kirki " Shiru Indo tayi bata tanka masa ba ta yunƙura ta tashi jikinta na mata tsami, Indo da Jamilu suna gaba Baba Huwaila na biye dasu a baya har suka ƙarasa fadar Maigari. Kamar ɗazu ne yanzu ma fadar cike take sai dai yanzu fuskoki gaba ɗaya a tamke suke babu alamun wasa har shi kansa Maigari, da ƙarfin gaske Jamilu ya ƙarasa ya dunƙufar da Indo agaban Maigari ya koma gefe ya zaune.Maigari tun daga ƙasa ya fara ƙarewa Indo kallo sai da ya kai har tsakiyar kanta sannan ya ce, " Gaki ƴar ƙanƙanuwa wacce batafi na haɗeki da hannuwa na biyu na karye ki ba amma sai sheɗanci da hatsabibanci fal kanki, mu zaki kawowa iya shege ko? Sarƙa iskancinki har kaina yazo da sauran mutanena kamar ni da girmana da darajata zakiyi aljanun ƙarya ki dinga duka ko? Yanzu kin fashe kan ɗan gidan Shafa laifin me yayu miki? Sarƙa raini ne yasa kike haka ko iskanci ne? " Indo shiru tayi kamar bataji mai yace ba sai da ya buga mata tsawa sannan ta ce, " Ranka shi daɗe dama ni kullin ai ba'a bani dama ta ne amma ai ansan haka kawai bazan fasa masa kai a banza ba da wani dalili ba, kuma ai nima..." Tsawa Maigari ya ƙara buga mata ya ce, " Ke akwai abokin wasanki anan gurin? Rashin kunya nace kiyi mana ba tambayarki nayi ba? " ɗauke kai gefe Indo tayi ta ce, " Aini ba rashin kunya nayi ba bayani kawai nakeyi..." Maigari ne ya katseta da cewar, " Ya isa haka, Baba Huwaila zaku kai yaron nan kyamis sannan akwai aikin horo da za'a bawa Indo tayi na tsawon kwana bakwai tun safe har yamma, kullin zata dinga share fadar nan sau biyu a rana kuma ruwan gidana kullin sai ɗebo ta cika ko'ina na tsawon mako guda, Zaki dinga ɗebowa Mati ɗan wajen Shafa ruwan wanka kullin kina yiwa uwarsa cefane ke duk aikin da Mati yakeyi zuwa nan da sati guda " Baba Huwaila ce ta kalli Maigari cikin sanyin murya ta ce. " Allah ya baka yawan rai munji duk bayananka zamu biya duk abinda za'a kashe amma ataimaka a ragewa Indo waɗannan ayyukan sunyi mata yawa ko a gida bana bata rabin wannan aikin " Shafa da ke gefe tana cika tana batsewa tayi karaf ta ce, " Eh, da yake ba ɗanki ko ƴarki aka jiwa ciwo ba ko? Dole ki nemar mata rangwame yanzu da antsokanewa Ɗana idonwa gari ya waya? " Maigari fuska ba walwala ya ce, " A dakata banasan cecekuce,Indo taci mutumcin masarauta dole mu hukuntata saboda masu tunani irin nata su hankalta, dole tayi abubuwan dana lissafa mata kuma Allah sa inkuma jin wani ya kawo mun ƙararta,Akwai Bulala goma da Ɗan Jummai zaiyi miki yanzu kai Ɗan Jumma a hukuntata " Maigari gama Ɗan Jummai ya taso ya fara zubawa Indo bulala amma ko motsin kirki batayi bare tayi Ihu, dan a ganinta idan ta kuma kuka agaban mutane da sauran yara ba ƙaramin raini zai ja mata ba, Hatta Jamliu yayi mamakin jarumtar da Indo tayi saboda kowa na faɗar bulalar Ɗan Jummai musamman waɗanda suka taɓa laifi aka hukuntasu, manya ma kuka sukewa bulalar Ɗan Jummai bare yara, idanun Indo ya kaɗa yayi jawur amma ko ɗigon ƙwalla babu a idonta. Maigari gyara zama yayi ya cigaba da cewa, " Ga mai irin tunanin Indo wannan ya zama izina agurinsa, idan muka samu waninya aikata makamancin haka nasa hukuncin sai ya ninka nata, Indo zata fara gudanar da aikinta daga gobe da ƙarfe bakwai na safe saɓawa umarninmu hukunci ne mai tsanani, idan babu mai magana zaku iya tafiya mun sallami kowa " Jamilu ne ya ɗaga hannu alamar yana da magana, Maigari gyaɗa masa kai yayi sannan Jamilu ya ce, " Allah baka yawan rai ba wai ina nema mata rangwamen aikin bane, amma ya zatayi da zuwa makaranta? " Mai gari wani kallo ya watsawa Jamilu sannan ya ce. " Duk faɗin garin nan kowa yasan ya zuwa makarantar Indo yake, idan taje sau ɗaya sai ta shafe wata bata koma ba, saboda min bata horo za'a ɓullo mana da haka? " Jamilu furzar da iska mai zafi yayi ya ce, " Wata makarantar zan canja mata da zan mayar da ita makarantar Rimaye inda nake koyarwa yanzu haka har Uniform na ɗinka mata " Maigari ya ce, " Ai abun yazo da sauƙi tunda ma bata fara zuwa ba sai ka bari idam ta kammala aikin sai ta fara zuwa, kwana bakwai ai kamar yau ne,idan babu mai wata maganar xaku iya tafiya " sannu a hankali mutanen gurin duk suka watse. Baba Huwaila,Jamilu,Indo da au Shafa tarkatawa sukayi suka wuce chemist domin duba kan Mati, duk abinda akayi masa Jamilu ne ya biya ana gama duba yaron Baba Huwaila da Indo sukayi gida Jamilu ko ta kansu baibi ba ya wuce sabgar gabansa. WASHEGARI Tun bayan sallar asuba Indo bata koma ba ita kaɗai take ta saƙa da warware abinda zata shukawa Jamilu dan ta huce abinda yayi mata kafin ta koma kansu Maigari, wata dabara ce ta faɗo mata saboda jin daɗin shawarar data yanke har sai da ta dinga ƙyaƙyata dariya ita kaɗai, sai da tayi Mai isarta sannan ta koma ta kwanta tana jiran lokacin, gari ne ya fara wayewa Jamilu tana ta shirin tafiya makaranta, cen ƙasan kayanta ta fara lalubawa har ta ciro wata waƙunanniyar Bireziyar da suka taɓa siya ta gwanjo, ita dasu Zaliha suka taɓa siya naira Ashirin -ashirun ita bata taɓa sawa ba tana jin kunya kar Baba Huwaila ta lura tayi mata magana, soketa tayi a ƙugunta kamar ba komai a jikinta ta koma ɗakin Baba Huwaila ta zauna tana tsammanin futowar Jamilu ya yiwa Baba Huwaila sallama. Ta zauna ba jimawa Jamilu ya fito tsaf dashi yasha wani farin yadi mai ɗison baƙi sai zabga ƙamshi yake, dama Jamilu ba daga nan ba akwai tsafta kwasai-kwasai dashi, Baba Huwaila na daga kwance tayi masa fatan alheri Indo fuskarta wasai ta gaida shi, ahi kansa sai da yayi mamakin yanayin Indo, dan ya lura tana cikin nishaɗi, har ya kusa bakin ƙofa wayarsa ta fara ringing tsayawa yayi domin ya cirota daga aljihu, cikin hanzari Indo ta ciro maƙalalliyar Bra ɗin gurinta wani ɗan guntun Gum ta manna ajiki ta fice ta sabi bokiti kamar mai ɗiban ruwa, lokacin da taje wucewa ta wajen Jamilu yana tsaye yana waya, da sauri ta manna masa ita a bayansa har tayi gaba ta juyo tana masa sannu, mamaki ne ya kama Jamilu shi dai yasan badai Indo ta bigeka har ta juyo ta baka haƙuri ba amma da ya tuno zamam fadar da akayi sai yayi tsammanin taji faɗan da akayi mata ne, yana gama wayarsa ya fice. Jamilu tafe yake zashi makaranta, amma abinda ya bashi mamaki yanda yaga ɗalibai da sauran ƴan mata suna masa dariya idan ya gifta suwani lokacin harda manyan ma, Jamilu haka ya ƙarasa makarantar da yake koyarwa shigarsa keda wuya Ɗalibai aka dinga zinɗensa wasu na nunashi a fakaice suna tuntsirewa da dariya. FATAN ALHERI🥰🥰🥰🥰🥰🥰 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [11/07, 14:50] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 37&38 Yana hanyar shiga staff room yaji wasu ɗalibai sun ce, " Kunga Malam Jamilu da bireziya " suna gama faɗa suka kwashe da wata irin dariya,Jamilu sarai yaji abinda suka faɗa fuska a tsuke ya juyo gurinsu ya ce, " Me kuke faɗa? " Kunya ce ta kamasu haɗe da tsoro dukda sun san bashi da yawan dukan ɗalibai amma yana da matuƙar kwarjini a idon ɗalibai, cikin jin tsoro suka ce, " Babu komai Malam " fuska ba walwala ya ce, " Ku wuce Class " tun bai gama rufe baki ba suka juya sumi-sumi suka wuce, gabaɗaya Jamilu jinsa yake wani iri shi kaɗai yaji duk ya tsargu musamman yanda yaga anatayi masa dariya, cikin Staff room ya shiga gaisawa sukayi da sauran Malaman sannan ya nemi kujera ya zauna, maganganun ɗaliban nan ne suka fara dawo mai aka dudduba jikinsa ya farayi ko zai ga abinda yaji ɗaliban sunce amma ba abinda ya gani, yana nan zaune wani ɗalibi ya shigo, cikin ladabi ya tsugunna ya ce, " Malam lokaci ya shiga " gyaɗa masa kai kawai yayi, jiki ba ƙwari Jamilu ya miƙe zai nufi hanyar fita da sauri Malam Sani yayi farat ya ce, " Malam Jamilu dakata meye wannan a bayan rigarka? " Gaban Jamilu ne ya yanke ya faɗi da sauri ya juyo ya ce, " Malam Sani wani abu ka gani? " Malam Auwalu sai a lokacin ya ɗago da kansa ya ɗagowa yayi tozali da Bra ajikin rigar Jamilu, Malam Sani tasowa yayi ya dafa kafaɗar Jamilu ya fisgemasa yaƙunanniyar Bireziyar da Indo ta manna masa, nuna masa ita yayi sannan ya ce, " Kai kuwa Malam Jamilu ya akayi haka ta faru? Saurin me kake baka lura ba har ka saƙalo da wannan tsummar abar " Jamilu zaro idanu waje yayi yana ƙarewa Bra kallo, Malam Sani miƙo masa yayi yana cewa, " Gaskiya Allah ya taimakeka da baka shiga da wannan abar ajikinka ba da na tabba sai sun saka maka suna " Jamilu ɗagata yayi cikin ƙyanƙyami cikin suɓutar baki ya furta, " Indo ce tabbas Indo ce da wannan iskancin " Malam Sani da mamaki ya ce, " Wace Indo kuma? Kana tunanin saka maka akayi " gyaɗa kai yayi yace, Ɗakina ni kaɗaine ko Baba Huwaila sai tayi kwana da kwanaki bata shiga ba bare Indo, lafiya kalau na shirya to kana ganin a ina zan samu wannan a jikina? " shiru Malam Sani yayi sannan ya ce, " To kai wacce hujja gareka da zaka ce ita ce " shiru Jamilu yayi yana jan guntun tsaki sannan yace, " Bani da wata hujja amma nasan ta yanda zan ɓullowa lamarin " Yana gama magana ya wurgar da ita agefe zai fice da sauri Malam Auwalu yace, " Dawo Malam Jamilu ka sauyawa abarnan guri, kasan halin yaran nan yanzu ɗaya na zuwa idan ya gani zai je ya gayawa sauran sai kaji sun ƙirƙiri wani zancen daban " Jamilu ƴan yatsu biyu yasa a ɗauketa wata leda ya gani a gefe a ɗauka yasa aciki ya ɗaure ya wurgar ta window, yana wurgarwa ya sa kai ya fice kai tsaye aji shida ya nufa dan gabatar musu da darasin turanci. Lokacin da Indo ta fice daga gidan dariya take harda riƙe ciki, kai tsaye ɗiban ruwa ta tafi tana tafe tana ƴan waƙe-waƙenta har ta ƙarasa bakin rijiyar, lokacin da taje bakin rijiyar ba mutane sosai Mutum biyu ta samu agurin, gefe ta koma ta zaune kamar mutuniyar kirki haka ta tsaya a gefe har suka gama ɗiba itama taje ta ɗibata bar gurin, kai tsaye gidan Maigari ta nufa da sallama ɗauke a bakinta ta shiga babu wanda ta yiwa magana Indo ta juye ruwa acikin garwar ruwa,haka Indo ta dinga ɗiban ruwa tana kaiwa har ta kusa gamawa, a sawunta na ƙarshe harta juye zata juya ta fita Baraka ta ƙwala mata kira da Indo kamar bazata amsa ba Maigari da ya shirya tsaf ya fito ya ce, " Ke Sarƙa ba kiranki akeyi ba? " Fuska a haɗe Indo ta juye ta cewa Baraka, " Gani meye kike kirana " Baraka zuciyarta ƙal ta kalli Maigari ta ce, " Malam dama wankin kayan yaran nan ne da nawa ya taru nace ko inhaɗa mata taje bakin rijiya ta wankesu " tun kafin Maigari yayi magana Indo tace, " Ƙundun ubancen wallahi babu uban da ya isa ya sani wanki ai ni ba baiwa bace " Maigari daƙuwa ya yiwa Indo yace, " Ƙaniyarki Indo rashin kunya zakiyiwa mutane? " Baraka ce ta karɓe maganar tana cewa, " Rashin tarbiyya zata nuna mana kasan sai mutum ya samu tsatso mai kyau yake tasowa da tarbiya, ƴar iskar yarinya mara tarbiyya " Maigari na shirin tsawatarwa Baraka Indo kayi karaf ta ce, " Wallahi ni ba ƴar iska bace sai dai ke " Baraka batayi wata-wata ba ta ɗauke Indo da mari, Indo na jin zafin mari ta cukumi wuyan Baraka suka fara kokawa, Maraka ta girmewa Indo nesa ba kusa ba shiyasa ta kusa yiwa Indo dukan tsiya, jin zafin duka ne yasa Indo ta gantsarawa Baraka cizo da sauri baraka ta saki Indo cikin jin azaba. Gabaɗaya huci suke kowanne ya galabaita, Baraka cikin kumfar baki ta cewa Indo, " Ai dama duk inda shege yake sai ya nuna hali, shiyasa duk cikin ƙauyen nan kika fita zakka kinfi kowa sheɗanci wayasan irin tsiyar da aka shuka kafin a kawoki duniya " Indo cikin jin haushi ta ce, " Nice shegiyar? " Baraka har tuntuɓen harshe take ta ce, " Ƙwarai idan kina tantama kije ki tambayi waccen tsohuwar, ki tambayeta alaƙarki da Goggo zata gaya miki yarinya kamar ƙanwar a sheɗan daga wannan sai wannan " Jikin Indo ne yayi sanyi tana shirin magana Maigari ya rufe Baraka da faɗa, " Ke Baraka baki da hankali ne wayace ki gaya mata wannan maganar kuma..." Baraka katse shi tayi, " Malam Ƙarya nayi idan ƙarya nayi taje ta tambaya waye Ubanta? Su waye iyayenta? Dama ai tsintacciyar mage bata mage " Indo jiki ba kwari ta juyo ta fito kai tsaye gida ta wuce tana tafe tana nazari sai yanzu wasu daga cikin maganganun mutane suke faɗo mata arai, sautari idan sukayi faɗa da wasu suna jefa mata kalmar Tsintacciyar Mage..." Tana tafe tana hawaye har ta ƙarasa gida kamar mara laka a jika haka ta nemi bakin ƙofa ta zauna tana rafka uban tagumi, Baba Huwaila ta lura da yanayin da Indo ta shigo da shi itama gefe ta samu ta zauna ta ce, " Sannu Indo na kinji wallahi nasan wannan aikin da Maigari ya ɗebar miki ya miki yawa amma kiyi haƙuri komai lokaci ne " hawaye ne ya ƙara gangarowa Indo sanna ta kalli Baba Huwaila ta ce, " Baba Huwaila su waye Iyayena? Wane ne Babana? " Baba Huwaila jin maganar Indo tayi kamar saukar aradu, cikin duburburcewa ta ce, " Bangane ba Indo wani abu akace miki " Gyaɗa kai tayi ta ce, " Gayamun akayi kuma nasan tunda maganar ta fito akwai wata a ƙasa " Baba Huwaila dakewa tayi cikin zuciyarta tanajin ba daɗi amma gudun kar Indo ta fahimci wani abu ta ce, " Iyayenki Allah yayu musu rasuwa tun kina jaririya " Indo zuwa lokacin zuciyarta ta bushe banda wani ɗaci ba abinda take ji a zuciyarta ta cewa Baba Huwaila, " A ina dangin mahaifana suke " take wani tunani ya ziyarci zuciyar Baba Huwaila tabbas dama tasan dole wata rana allura zata tono garma shiyasa tun Goggo na da rai taso agayawa Indo matsayinta, ajiyar zuciya Baba Huwaila ta sauke sannan ta ce, " Indo ko gajiya kikayi da zama agurina shine kike mun waɗannan tambayoyin " Indo ba alamun wasa a tattare da ita ta ce, " Ko ɗaya Baba Huwaila, inasan ki gayamun tsakaninki da girman Allah su waye Iyayena kuma a ina dangin Mahaifana suke, ko da baki gayamin yanzu ba nasan duniya zata gayamun tunda a yanzu ma anfara yimun bita " Tausayin Indo gaba ɗaya ya mamaye zuciyarta take taji hawaye na niyyar zubo mata, fakar idon Indo tayi ta goge hawayenta sannan ta ce, " Indo girman Allah yafi komai, tsakanina da Allah Indo bansan su waye Iyayenki ba bansan kuma dangin Mahaifanki ba, abinda na sani Goggo tazo dake cikin garin nan tun bakifi wata biyu ba, ita kuma Goggo ƙawata ce tun muna ƴan mata aure ne ya rabamu daga baya kuma bayan mijinta ya rasu ta dawo cikin ƙauyen nan, ta cemun ta tsinceki tun kina jaririya a bakin wata kasuwa dake cikin garin da take, kasancewar bata taɓa haihuwa ba yasa ta ɗaukeki ta sanar a gidan Maigarin garin, daga baya ta ɗauki ruƙonki ya dawo hannunta gaba ɗaya, lokacin da tazo da ke garin nan kowa yasan ke ba yarta bace saboda a shekarun Goggo ta wuce haihuwa, kuma nan garin da kike gani shine garin Iyayenmu gabaɗaya, shine babban dalilin da yasa kowa yasan ke ba jininta bace saboda duk munsan Goggo bata taɓa haihuwa ba, amma Allah ya sani Goggo tana ƙaunarki har cikin zuciyarta kamar ita ta haifeki " Baba Huwaila dakatawa tayi ta goge hawayenta ta cigaba da cewa, " Indo amma ban gaya miki wannan maganar saboda ki sawa ranki damuwa aranki ba " Indo hawayen Idanunta ta goge ta ce, " Baba Huwaila a ina dangin Goggo suke? " wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce. A yanzu daga ni har ita ba wasu shaƙiƙanmu da suke raye kusan duk sun mutu, sai wani ɗan uwanta da yake cikin garin kaduna wanda suke ɗan maza zar shima tun shekaru biyu baya na daina jin labarinsa, dama kuma agurinta nake jin Labarinsa " Indo miƙewa tsaye tayi ta ce, " Baba Huwaila a taƙaice dai bani da kowa wanda zan nuna na ce wannan shaƙiƙina ne? " Baba Huwaila itama miƙewa tsaye tayi ta dafa kafaɗar Indo tace, " Kina da kowa mana tunda kina dani " girgiza kai Indo tayi ta ce, " Baba Huwaila bansan gawar fari ba idan aka wayi gari babu ke fa " Jim Baba Huwaila tayi tabbas tasan maganar Indo akan hanya take da sauri ta cewa Indo, " Ga Jamilu nasan zai riƙeki har abada " Indo girgiza kai tayi ta ce, " Baba Huwaila wannan ba hujja bace, a yau basai gobe ba zan shiga duniya innemo dangina, idan ma ni shegiya ce shikenan zan cigaba da rayuwa acikin mutanen sa basusan asalina ba " Baba Huwaila kuka ta fashe dashi ta ce, " Indo dan Allah karki mun haka, akan Idonki Goggo ta bani amanarki idan kika mun haka zan kalli kaina amatsayin maciya amana " Indo murmushin yaƙe tayi ta ce, " Karki damu baba Huwaila duk inda zanje bazan aikata wani abun muni ba kina nan insha Allah wata rana zan dawo gareki, idan kuma shirun yayi yawa to ƙila ta Allah ta kasance " Indo na gama magana ta sa kai ta nufi hanyar waje Baba Huwaila fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [13/07, 19:21] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 39&40 Indo jin kukan Baba Huwaila take har cikin zuciyarta, runtse idanunta tayi tana jin wani iri acikin ranta, bayan Goggo babu wacce ta shaƙu da ita take jin ƙaunarta har cikin zuciya kamar Baba Huwaila, shashsheƙar kukan Baba Huwaila ne ya dawo da ita daga ɗan guntun tunanin da ta shiga, juyowa tayi ta ɗan kalleta take guntun hawayen da take maƙalewa ya gangaro saman kumatunta, jiki a sanyaye ta sa kai ta fice daga gidan, Baba Huwaila na ganin fitar Indo ta fashe da wani irin matsanancin kuma mai taɓa zuciya, Baba Huwaila yunƙurawa tayi da ƙyar ta ɗan ɗingiso ta fara takowa zuwa ƙofar gida, dube-dube ta shiga yi babu Indo babu alamarta. Wani sabon kukan ne yazo mata haka ta cigaba da share hawayenta, wani tunani ne ya faɗo mata kai tsaye ta wuce gidan Maigari tana tafe ko kallan gabanta bata yi, tana shiga cikin gida ko sallama ta kasa furtawa saboda yanda take sauke ajiyar zuwa, Magajiya ce ta tare da tambaya jin an ambaci sunan Baba Huwaila yasa Maigari fitowa saboda yasan dama za'a rina..." Maigari ganin yanayin Baba Huwila ba ƙaramin sanyaya masa jiki yayi ba, jiki ba ƙwari Maigari ya fara watso mata tambaya, " Lafiya Baba Huwila me yake faruwa " Baba Huwaila majina ta fyace sannan ta ce, " Allah ya baka yawan rai suna korar mun Indo, ta tafi ta barni bansan inda ta tafi ba " da mamaki Maigari ya ce, " Su waye suka koreta kuma ina ta tafi? " Baba kwashe yanda sukayi da Indo tayi sannan ta ɗora da cewa, " Ba yanda banyi da yarinyar nan akan ta sanar dani waɗanda suka gaya mata maganar nan amma taƙi dan Allah ka taimaka ka baza mutane a nemo min ita yanzun nan ta fito daga gida amma na nemeta sama ko ƙasa na rasa " wata gwauruwar ajiyar zuciya Maigari ya sauke cikin zuciyarsa yake hamdala da Indo bata sanar da Baba Huwaila Baraka ce ta gaya mata ba, nunfasawa Maigari yayi sannan yace, " Ashsha gaskiya lamari baiyi daɗi ba amma bari na fita nasa su Ado su fita ciki da wajen ƙauyen nan Insha Allah zasu dawo da ita, karki ɗaga hankalinki Baba Huwaila wannan ba abin damuwa bane kinsan shaƙiyancin Sarƙa yanzu haka ma gwada ki kawai takeyi " girziga kai Baba Huwaila tayi ta ce, " Kai gaskiya jikina yana bani Indo ba wasa take mun ba tunda duk abin Indo bata taɓa gwada mun irin wannan wasan ba " Maigari ya ce, " Insha Allah yanzu zasu nemo ta " kusan tare suka fito da Baba Huwaila tare suka ƙarasa fadar Maigari inda su Ado suke, sanar da su akayi abinda yake faruwa take suka ɗauki ƙananan lasifiku suna shelar ɓatan Indo. Indo na fitowa gyara wuyan hijabinta tayi ta kunto bakin zaninta dubu ɗayan da Mommy ta bata ta ciro, da sauri ta fara tafiya kai tsaye hanyar tasha ta nufa, tana tafe tana duba mota kowacce tazo acike take har ta kusa ƙarasawa bakin tasa taga wata motar Bus ta taho, da sauri Indo ta tsayar da ita tana faɗin, " Kano ne? " da sauri kwandastan ya ce, " Kano mukayi ƴan mata " buɗe mata murfin ƙofar akayi Indo ta kama mota ta haye, tana hayewa Driver ya bawa motarsa wutasuka wuce kai tsaye motarsu ta wuce garin Kano. Baba Huwaila na komawa gida sai a lokacin ta tuno da wayarta da sauri ta ɗauki wayar ta shiga gidan Malam Musbahu, Ɗan wajen Malam Musbahu ta bawa wayar ta sashi ya nemo mata lambar Jamilu ya kira mata, karɓa yayi ya kira mata tana fara shiga ba jimawa Jamilu ya ɗauka. Ko amsa sallamarsa batayi ba cikin tashin hankali ta fara magana, " Jamilu kana ina maza kazo Indo ta ɓata dan Allah kazo yanzun nan " murmushin takaici Jamilu yayi ya ce, " Haba Baba Huwaila kawai saboda kinsan yarinyar nan acikin zuciyarci sai kuma ta dinga ɗaga miki hankali, ba gaira ba dalili. Kinsan dai shaiɗancin Indo sarai ba wanda baisan halinta ba kima kwantar da hankalinki kina zaune zata dawo saboda..." Cikin hassala Baba Huwaila ta katse shi, " Jamilu idan ban isa da kai ba shikenan ina nuna maka gabas kana rintse ido kafin sanin wacece Indo ne? Idan bazaka zo ba shikenan " Baba Huwaila na gama magana bata jira cewar Jamilu ba ta kashe wayar gabaɗaya.Jamilu kira ya ƙarayi amma Baba Huwaila bata ɗauka ba sallama tayiwa matar Malam Musbahu ta koma gida jiki ba ƙwari. Su Indo basu jima da tafiya ba wasu fasinja suka tsayar da motar mutum biyu ne suka hau sunna shiga suka ga Indo zaune akan kujera, da mamaki suka kalleta Malam Bala ya ce, " Sarƙa yau kece a mota ina zuwa haka ina kuma kika baro Baba Huwaila? " Indo ta fahimci su Malam Bala basu fahimci komai game da ita ba, ɗauke kai gefe tayi tace, " Aikena akayi birni " cikin mamaki Lauwali yace," Birni fa Sarƙa Ina Jamilun da Baba Huwaila zata turaki har Kano? " hararara Indo ta watsa mai tace, " Ni ɗin bazan iya zuwa ba kenan ina kano ina Kura, kudai bakwa gani ku ƙyale " gaba ɗaya baki suka ja suka tsuke saboda sun san idan suka biyewa Indo sai ta tsinka su agaban mutane, motar ce tayi tsit ba magana suka cigaba da tafiya. Jamilu sanar da Principal yayi kiran da akayi masa na gaggawa daga gida, sanin Jamilu mai himma ne kuma baya wasa ko kaɗan a ɓangaren aikinsa yasa yana tambaya Principal bai tuhumeshi ba, tafe yake yana sauri kamar zai tashi sama har ya ƙaraso gida, yana zuwa gida Baba Huwaila ta fashe masa da kuka tana bashi labarin yanda sukayi da Indo, dukda ba wani shiri suke da Indo ba amma maganar ta matuƙar girgiza shi, takalmansa ya shura ya fice daga gidan domin nemo Indo. Tafiya sukayi mai nisa sannan suka shigo cikin garin kano, motarsu na zuwa Unguwa uku su Lauwali suka sauka, Bala ne ya juyo ya cewa Indo, " Sarƙa kina ganin Hanya ko? Kinsan fa cikin gari daban yake da karkara " Gyaɗa masa kai kawai Indo tayi saboda tun lokacin da ta fahimci sun shigo cikin gari gabaɗaya taji zuciyarta ta ƙara mata ba daɗi, ji take kamar ta dakatar da motar ta koma garinsu, tana ta tunane-tunane har motarsu ta ƙarasa Kano line, yawancin mutanen da Indo ta samu da wanda suka sameta aciki duk sun sauka, Kwandastan ne ya kalli Indo yace, " Ya ƴan mata har yanzu ba'a inda zaki sauka bane? gaskiya sai dai mu saki a mota dan bazamu ƙarasa Ƴan kura ba " Indo muzurai ta farayi tana ƴan dube-dube bata bashi amsa ba, Kallanta Kwandastan yayi ya ce, " Sakko ga mota cen Ungo Talatin ki basu zasu ƙarasa da ke " Jiki ba ƙwari Indo ta karɓi kuɗin ta sauka tana sauka kuwa suka bawa motarsu wuta. Indo tsaye take motoci da ƴan Adaidaita sahu sai wucewa suke, wasu suyi mata horn wasu kuma su wuce, tsaye take kusa da wasu mata ɗaya tana ƴan shekaru dan Aƙalla zatayi shekara arba'in da uku ba, ƴar matashiyar budurwae batafi shekara ashirin ba, suna nan tsaye wani Mai Napep yazo ya tsaya a gabansu, babbar macen ce ta ce, " Medile " gyaɗa kai yayi ya ce, " Ku duka ukun? " Matar ce ta kuma cewa, " A'a mu biyu ne amma bansani ba ko ita cen tayi " tana magana tana taunar cingam ƙas ƙas ƙas, Mai Adaidaita sahun ne ya kalli Indo yace, " Kema cen kikayi? " Indo samun kanta tayi da gyaɗa kai, Mai Adaidaita sahun ya ce, " Kuɗinku ɗari da hamsin-hamsin " ba ko tantama matar tace, " Preety shiga muje " wacce aka kira da Preety shiga tayi Indo na ƙarewa yanayin shigarta kallo, matar ce tabi bayan Preety sannan Indo ta shiga. Tunda suka fara tafiya matar da taji ana kira da Aunty take ta ɗan jan Indo da hira, amma Indo sai dai tace Ummm ko uuummmm-uuummm, tafiya sukayi me ɗan nisa suka ƙarasa Medile, Auntyn Preety ce ta tsaida ɗan sahu suka sauka itama Indo sauka tayi ta miƙa masa ɗari biyu ya bata hamsin, akan Idonta su Preety suka tsallaka titi suka shiga wani layi, awannan lokacin ne taji anfara kiraye-kirayen sallar Azahar, Indo banda kalle-kalle ba abinda takeyi juyawa tayi ta fara tafiya batasan inda take jefa ƙafarta ba, tafiya tayi Mai nisa sannan ta nemi bakin wata bishiya ta zauna tana hutawa,wata me wake da shinkafa ta hango kiranta tayi ta sayi ta nera ɗari saboda yanda taji cikinta yake mata ƙugi, kafin wani lokaci tuni ta cinye tas.A cen nesa ta hango famfo ƙarasawa tayi ta tara hannunta ta sha sannan ta ɗaura alwara ta shinfiɗa ɗan kwalinta tayi sallah, tana nan zaune ita kaɗai take nazarin inda ta dosa, bata taɓa tsammanin haka a rayuwarta ba wata irin ƙwallah ce ta zubo mata da ta tuno Baba Huwaila, yanda take nan-nan da ita akan taci abinci amma wai yau ita da kanta ta nemi abinci har ta siya da kuɗinta, hawayen fuskarta ta goge ta tashi ta karkaɗe ɗan kwalinta ta ɗaura aka sannan ta cigaba da tafiya. Indo tun tana tafe tana hutawa ta gabatar da sallah har ta fara gajiya ga duhun dare ya farayi, daga Medile zuwa Tukuntawa Indo tayi zaryar hanyar yafi sau biyu, gabaɗaya ta galabaita ga gajiya ga tunanin inda ta dosa a haka tana tafiya har dare ya tsala, wani shago ta hango arufe da alama Provision ne, ƙarasawa tayi ta shiga cikin rumfar ta zauna a gefe ta takure guri ɗaya, gabaɗaya idonta ya bushe babu alamar bacci acikinsa, banda kukan karnuka babu abinda yake tashi, tana nan tsugunne ta ga wasu matasa su Biyu sun fito daga wani layi dake kallan gurin da take a tsugunne, hasketa ɗaya yayi da fita ɗayan yace, " Kai Boss wa nake gani kamar cika agurun cen " wanda aka kira da Boss yace, " Ai ba kama bace Uzee wata ƴar shilar muka samu " suna gama magana suka ƙarasa cikin rumfar, Indo na ganinsu jikinta ya hau tsuma miƙewa tayi tsaye, ɗaya daga cikinsu ne yace, " Ƴan mata ke kuwa lafiya me kikeyi da tsohon daren nan agurin nan? " Indo jiki a sanyaye tace, " Daga Kura nake ni baƙuwa ce " Kallan juna sukayi zuciyarsu ƙal sanna Boss yace, " Zamu taimaka miki tunda kina mace zaman gurun nan bai kamace ki ba" Indo sam bata yarda dasu ba duba da yanayin shigarsu, girgiza kai tayi ta ce, " A'a nagode zuwa safiya zan nemi gurun zama " Kallan juna suka ƙarayi suna ƙifta ido da sauri Uzee ya fisgi hannun Indo, ganin haka yasa ta ƙwalla ƙara domin neman taimako, a zafafe Bosa ya kifa mata mari kafin ta ɗago ya ƙara kifeta da wani marin, hannunsa ya sa ya shaƙi wuyanta har sai da ta fara kakarin amai idanunta sun firfito, sakinta yayi ya zaro wata wuƙa a ƙugunsa yana nuna mata sannan yace, " Idan kika kuma yimun Ihu sai na kasheki na kashe banza a gurun nan " WAYYOOOOOO JAMA'A KUJE KU CETO INDO, MAMAN NASEER INDONKI NA CIKIN WANI YANAYI🥴🥴🥴🥴🥴 NASO NAYI MUKU YAFI HAKA BANA SAMUN CAJI SOSAI NE☹️ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [14/07, 13:56] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 41&42 Indo wani irin yawu ta haɗiya na wahala Uzee ne yake janye da hannunta suna gaba Boss na biye dasu a baya, Indo jikinta banda karkarwa babu abinda yakeyi gumi ta ko'ina sai keto mata yake, tafe take tana ɗan waigen Boss a tsorace gudun kar cutar da ita, wannan karan ma juyowa tayi cikin kuka ta ce, " Dan Allah ku taimaka kuyi haƙuri karku cutar dani wallahi ni marainiya ce " daga bayanta Boss ne ya buga mata uwar tsawa yace, " Allah sa ke ƴar wahainiya ce ba maraniya ba idan kika ƙara magana sai na sa miki kaifi " daga haka Indo bata ƙara magana ba tafi sukayi ɗan nisa sannan suka hango ƙyallin fitila wasu mutane ne suke tunkaro su da alama kamar ƴan bijilanti ne, da sauri suka faɗa wani lungu Uzee ya ce, " Ga wasu mutane cen idan kika sake kikayi abinda zasu gane kina gurin kinga waccen wuƙar sai mun huda wuyanki da ita " Uzee na gama magana Boss ya sawa Indo wuƙa a wajen wuyanta, Indo ba magana banda gyaɗa kai babu abinda takeyi.Suna nan tsaye har mutanen nan suka zo suka wuce a lokacin Indo ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta tashi, banda ruwan hawaye babu abinda takeyi. Sai da ƴan bijilantin nan sukayi nisa sannan su Boss suka fito daga lungun suka cigaba da tafiya, basu ƙara tafiya mai nisa ba suka fita kan titi tsallakawa sukayi suka shiga wani layi a bakin wani ƙaramin gida suka tsaya, Boss ne yasa mukulli ya buɗe gidan ya fara wucewa, Uzee jan hannun Indo yayi zasu shiga cikin shammata ta gantsara masa cizo a hannu, yana jin azaba ya saketa yana ɗan kwalla ƙara, da gudu Indo ta juya ko kallan gabanta batayi bisa tsautsayi tana fita titi wata mota ta kawo kai ta bigeta, atake Indo ta sulale ta faɗi a gurin tana sauke numfashi da kyar, su Boss da suke biye da ita a baya suna ganin haka suka dakata da sauri suka koma dan gudun asirinsu ya tonu. Mutanen dake cikin motar mace da namiji ne, da sauri suka fito daga motar da ganin wacce suka bige, Indo dukda tana cikin mawuyacin hali yunƙurin tashi take tana nuna musu hanya, jini na ɗiga daga goshinta murya a hankali take faɗin, " Dan Allah ku taimaka mun zasu cutar dani " Namijin ne ya kalli gurin da Indo take nunawa amma sam baiga komai ba, macen ce ta kama hannun Indo ta ce, " Sannu kinji " Namijin ne yace, " Dear ya zamuyi da yarinyar nan? " wacce ya kira da Dear ta ce, " Ɗaukanta zamuyi Sweet dan bazamu barta acikin wannan halin ba, da alama tana cikin firgici tunda har yanxu ba ta jikinta take ba " wanda aka kira da Sweet yace, " Bari na ɗaure mata kanta da ɗan kwalin nan ko jinin ya rage zuba, da sauri ta janyo ɗan kwalin Indo ta fara ɗaure mata kai, tana gamawa suka ja hannun Indo zasu sa ta a mota, tirjewa Indo tayi ta ce, " Dan Allah karku cutar da ni wallahi ni marainiya ce " da mamaku suka kalli juna macen ta ce, " Look at this gal, munyi miki kalar macuta ne? Idan bakyasan taimakanmu you can go " ta ƙarasa magana tana buɗe murfin motar sannan ta cigaba da cewa, " Sweet zo mu wuce " kallan Indo yayi yace, " Kinfi san mu barki agurin nan " Indo girgiza kai tayi kwalla na zuba daga idonta, buɗe mata kofar baya yayi jiki ba ƙwari Indo ta shiga ya rufe shima ya shiga sannan ya bawa motarsa wuta. Basuyi wata tafiya mai nisa ba suka shiga wani layi, a wani madaidaicin gida sukayi parking, jakarta ta zuge ta ɗauko mukulli sannan ta fito ta buɗe gidan, dawowa tayi ta buɗewa Indo mota sannan ta leƙa ta ce masa, " Sweet bari na shiga da yarinyar nan sai muji ya za'ayi da ita " leƙo kansa yayi ya ce, " Ok Dear, amma ina ganin ko asibiti zamu kaita " Yatsina fuska tayi ta ce, " A cikin duhun daren nan wane asibiti zamu kaita? kasan dai ko mun kaita asibiti sai sun ce mu taho da Police, tunda dai jinin ya tsaya da zuba mu bari zuwa safiya sai mu kaita ayi mata check up " murmushi yayi ya ce, " Ok Allah ya kaimu " yana gama magana bata jira cewarsa ba ta wuce gaba Indo na biye da ita a baya. Lokacin da suka shiga gidan shiru ba wani ɗaki ta buɗe mata ta ce, " Shiga kafin na dawo " Indo a hankali ta taka ta shiga jiki ba kwari ga wani irin ciwo da kanta yake mata, guri ta samu ta zauna tana ƙarewa falon kallo, ba laifi Falon ya ƙayatu ga wasu luntsuma-luntsuman kujeru, bayan fitar Dear daga wata ƙofa taji anturo ƙofa anfito, wata mata ta hango mai jiki ta nufo gurinta, itama matar da mamaki take kallan Indo har ta ƙaraso gurinta ta zauna kan kujera, kallan Indo tayi taga yanda fuskarta da alamaun jini, dubanta ta ƙarayi da kyau sannan ta ce, " Yarinya sannu kinji " Indo gyaɗa kai tayi ta kuma sunkunyar da kanta ƙasa, kallan matar tayi taga kamar ta santa tunowa tayi da inda suka haɗu,cikin zuciyarta ta tuno itace matar nan da taji wannan matashiyar budurwa na cewa Aunty, suna nan zaune sukaji anturo ƙofa anshigo.Da murna matar nan ta fara magana, " Oyoyo oyoyo, barka da zuwa mutanen Kaduna, Matar Minista kece tafe da daren nan? " cen gefen matar ta zauna tana ajiye katuwar jakarta, ɗora kafaɗarta tayi akan ta matar sannan ta ce, " Wallahi Aunty munso dawowa da wuri so sai wani uzuri ya tsaida Nasir " kallonta ta ƙarayi tace, " Tun safe nake sa ran ganinki naji shiru har na fidda rai, Matar minista kinga yanda kikayi shar kuwa? " murmushin jindaɗi tayi suka cigaba da hira dan sam sun manta da wata Indo dake gefe a zaune, Matar minista ce ta ce, " Aunty muna tafe mun kusa ƙarasowa mun bige yarinyar cen amma naga jinin ya daina zuba, ko zuwa safiya akaita asibiti " Aunty leƙawa tayi tana kallan Indo tana tunanin inda tasan fuskarta, cikin muryar tausayi ta ce, " Allah sarki Allah ya kaimu, gata very young and she is so cute ƴan mata ya sunanki? " Indo ta ce, " Suna na Indo " kallan juna sukayi suka tuntsire da dariya sannan matar tace, " Wane irin wani Indo ana zaune ƙalau, daga yanzu duk wanda ya ƙara tambayarki kice sunanki Humaira " wannan karanma Indo gyaɗa kai tayi, Aunty tashi tayi tace, " Bari na ɗora miki ruwan wanka kiyi wanka ki kwanta zuwa safiya musan abinyi, ni sai nake ganin kamar nasan fuskarki ma " Indo ta ce, " Ɗazu tare da ku muka hau Adaidaita sahu " Da Aunty ta juyo ta ce, " Tabbas anyi haka " tana gama faɗa tayi gaba, da ƙarfi matar minista ta ce, " Aunty nima ki ɗora dani dan jikina gaba ɗaya ciwo yake saboda gajiya " tana gama magana ta tashi ta ɗauki jakarta ta shige wani wani ɗaki aka bar Indo zaune tana mamakin mutumci da karramawar waɗannan bayin Allah. Ba'a ɗauki lokaci ba Aunty ta dawo cikin falon ta koma mazauninta na da ta zauna tana ƙarewa Indo kallo, acikin zuciyarta take yaba kyawun fuska da kwantaccen gashinta irin na fulani, bayan wani lokaci matar minista ce ta fito taje ta juye ruwan wanka ta faɗa toilet,bata jima ba ta fito ta wuce su Indo, Aunty ce ta juyewa Indo ruwan wanka da kanta ta kamo hannun Indo ta rakata har banɗaki sannan ta juyo, Indo a hanakali rake komai saboda har zuwa lokacin kanta banda sarawa ba abinda yakeyi, itama bata jima ba tayi wanka ta fito tana tafe tana dafa kanta. Ruƙota Aunty tayi ta wuce da ita cen ɗakinta wata ƴar doguwar riga mara nauyi ta ɗaukowa Indo ta miƙa mata sannan ta ce," Ki saka wannan ki cire na jikinki idan kin gama ki fito falo sai ciki abinci kisha ko Paracetamol ne " Indo amsa mata tayi sannan Aunty ta fito, ba'a jima ba Indo ta sa doguwar rigar ta fito ta koma gurin da ta zauna da farko ta rakuɓe, a dai-dai lokacin Aunty ta shigo hannunta ɗauke da kofun Tea ɗayan hannunta farfesun kayan ciki ne acikin plate, cen tsakiyar Falon Aunty ta kai mata ta ce, " Humaira taso ga abinci ki saki jikinki kamar nan gidanku ne, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki kinji? " Indo tasowa tayi ta ce, " To Aunty nagode Allah saka da alheri " Aunty gyaɗa kai tayi tana murmushi, biredi ta miƙowa Indo sannan ta wuce cikin ɗakinta, Indo zama tayi ta fara cin abinci sai da taci tayi ƙat ta ƙoshi sannan ta kwashe kayan ta kai, hanyar da taga Aunty ta shigo da kayan abincin nan ta bi ta shiga cikin kitchen ta ajiye ta dawo ta koma ta zauna, dawowarta ba da jimawa ba Aunty ta shigo da magani ta bawa Indo da ruwa ta shanye, Aunty juyawa tayi ta koma ɗaki ta ɗan jima kafin ta fito har indo ta fara gyangyaɗi, tashinta tayi suka shiga ɗakinta. Katifu ne manya guda biyu ɗakin banda zabga ƙamshi babu abinda yakeyi, ɗaya daga ciki Aunty ta nunawa Indo ita kuma ta haye guda ɗaya, Indo katifar ta hau tana mamakin taushi da laushin wannan katifa, kwanciya tayi babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita duba da yanayin gajiyar da tasha awunin ranar, bargo Aunty taja ta rufe Indo saboda yanda taga Indo ta takure guri ɗaya da alama sanyin AC ne yayi mata yawa, Aunty ta jima akan Indo tana murmushi ita kaɗai tasan abinda take ayyanawa game da Indo, hannu tasa ta shafi fuskarta tana shafa cukurkuɗaɗɗen kitson Indo da har tsagarsa ta haɗe, afili ta furta, " Yarinya nan idan ta goge sai tafi su Preety kawo haske " komawa tayi ta kwanta itama ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita. WASHEGARI Tun da asuba Indo ta fara ganin ƴan mata kala-kala kyawawa dasu, azuciyarta take mamakin duk yawansu ace ƴaƴan Aunty ne, bayan tayi sallah bacci ta ƙara komawa ba ita ta tashi ba sai wajen ƙarfe takwas na safe.Indo na fitowa taga kusan ƴan mata biyar zaune a falo tana shigowa har ƙasa Indo ta tsugunna ta ce, " Ina kwananku? " kallan junansu sukayi lokaci guda suka kwashe da dariya wasu daga cikinsu har suna tafawa, Matar Minista ce ta fito a lokacin itama kan kujera ra samu ta zauna, Indo ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba amma sai ta basar ta juya ta gaida matar minista, fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa tana mata ya jiki, Ƴar ƙwai ce ta kalli matar minista ta ce, " Matar minista saukar yaushe kefa kamar fataken dare haka kike " Wayarta ta ɗauka tana dannawa sannan ta ce, " Kjiya muka sauka lokacin duk kunyi bacci, kuma ni kinsan bana harkar ƙananan ƙwari " taɓe baki ƴar ƙwai tayi tace, " Ko tare kuke da magen? " Sanin rainin hankalin ƴan gidan yasa ƴar minista ta tsuke fuska ta ce, " Eh tare muke kuma bance kowacce yarinya ta taka ta ba " sanin halin matar minista yasa ba wanda ya tanka mata kowa ya cigaba da harkar gabansa, Aunty ce ta haɗo musu breakfast suka cikin girmamawa Indo ta gaida Aunty, fuska ɗauke da fara'a ta amsa tana mata ya jiki. Haɗuwa sukayi suka karya sannan sukayi wanka, matar minista da Aunty ne suka kai Indo wani private hospital dake Zoo raod, ɗinki akayiwa Indo a goshinta danma bataji wani ciwo sosai ba sai magunguna da aka bata sannan aka basu wasu ƴan dokoki da zata bi domin samun ɗorewar lafiyarta, tun bayan da suka dawo Indo ba abinda takeyi daga wanka sai dai taci abinci tasha magani ta kwanta. Cikin abinda baifi sati guda ba Indo ta murje tayi haske har wata ƙiba tayi ga wuyanta wasu garaye da suka fito mata, abu ɗaya ne yake damunta kullin idan ta cewa Aunty zata tafi sai tace mata tayi haƙuri ta zauna jikinta ya ƙara samun sauƙi, Indo ba ƙaramin damuwa ta shiga ba ga wasu ɗabi'u data fuskanta daga ƴan matan gidan, idan wannan tayi tafiya sai tafi kwana uku ko huɗu bata dawo ba kuma Aunty ba abinda take ce musu sai ma addu'a fatan alheri da take musu. Satin Indo Biyu ta ɗauketa ta kaita saloon aka gyara mata kai da wankin ƙafa, daga nan kasuwa suka shiga ta lodowa Indo atamfofi da leshina a ƙalla sunfi kala goma, kai tsaye shagon telansu da yake musu ɗinki ta kai masa tana yi masa bayanin ɗinkin Indo, kallanta kawai yayi ya fahimci size ɗin Indo daga nan gida suka wuce agajiye saboda yanda suka sha tafiya. Bayan kwana biyu suna zaune gidan ba kowa daga Aunty sai Indo kayan ɗinkin da aka amso mata ta ɗauko ta miƙawa Indo ta ce, " Humaira yau zamuyi baƙi inasan kije kisa kayan nan dan baƙin suna hanya sun kusa ƙarasowa banasan suzo su ganki ba gyara, Indo zuciyarta ɗaya taje tayi wanka ta saka kayan da Aunty ta bata riga da sike ɗin leshi ne orange mai ratsin green, kayan ba ƙaramin karɓarta sukayi ba, ita kanta da ta kalli kanta a mudubi sai da tayi mamakin kyaun da tayi, Aunty ce ta gyara mata kai ta tazo mata gashinta har gadon baya sannan ta ɗaura mata ɗan kwali, masha Allah duk wanda yasan Indo abaya da zai ganta da kyar zai ganeta, ta gama shiryawa kenan sukaji sallama anshiga cikin gidan, fuskar Aunty wasai ta amsa tana musu barka da zuwa tana musu iso cikin falo, Maza ne guda biyu baza'a kirasu da dattawa ba kuma baza'a kirasu da yara matasa ba, aƙallah zasuyi shekara Arba'in zuwa Arba'in da biyar ba, zama sukayi suka gaisa da Aunty sannan ta fita cen ɗakin da Indo take ta ɗebo drinks ta bata sannan ta ce, " Ungo ki shiga ki kai musu kuma bance ki tsugunna har ƙasa ki gaishesu ba akan kujera zaki zauna sannan kice ina wuninku, idan kuma sun tambayeki sunanki kice sunanki Humaira banasan gidadanci, wannan da kike gani na gaban da ya fara wuce ciki Honourable ne ba ƙaramin alheri zaki samu nima naci arziƙi ba, wuce ki tafi ba daga shigarki zaki taso ki fito ba " Indo karɓa tayi har ta yo gaba ta juyo ta ce, " Aunty Ina mayafina " Aunty harara ta watsa mata ta ce, " Wuce ni ki tafi acikin gidan har wani mayafi zaki yafa " Indo gaba tayi ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, ajiye musu tayi ta koma kan kujera kamar yanda Aunty ta gaya mata, ganin girman mutanen yasa ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, " Ina wuninku? " muryar Indo ba ƙaramin ratsa tsakiyar kansa tayi ba, kasa amsawa yayi sai ɗayan da suke tare ne ya amsa mata jin muryar mutum ɗaya ya amsa ya sa Indo da kanta karaf suka haɗa ido, ƙara ɗauke kanta ƙasa tayi tana wasa da ƴan yatsunta. Ajiyar zuciya Honourable yayi sannan ya ce, " Cutie ya sunanki " Indo batasan me yake nufi ba da farko bata zaci da ita yake ba sai da ta ɗan ɗago taga ita yake kallon sannan tace, " Sunana Humaira " runtse idanunsa yayi tunda yake bai taɓa haɗuwa da yarinya da muryarta take masa amsa kuwwa kamar yarinyar nan, ƙara lumshe idanu yayi ya ce, " Humcy sunanki yamun daɗi " Indo shiru tayi bata ce Uffan ba sun ɗan jima a haka sannan Aunty ta shigo tana shigowa Indo ta tashi ta fita, Honourable kallan Aunty yayi ya ce, " Hajiya ina kika samo yarinyar kamar wannan " dariya Auntua tayi ta ce, " Haba Honourable aini gidan nan duk kalar da kake so ina da ita " Honourable sunkuyowa yayi ya ce, " Amma naga yarinyar kamar tana da kunya ko farin shiga ce? " Itama ƙasa tayi da murya ta ce," Ɗanya shakaf ce fa batafi shekara goma sha uku zuwa sha biyar ba " Honourable dariya yayi ya ce, " Irinsu nake so amma wannan da ita zan tafi dama zuwa yamma nake san tafiya Abuja ina sa wani meeting kwana biyu ne kawai zamuyi " Aunty daɗi taji har cikin ranta amma sai ta basar ta ce, " A'a Honourable yarinyar nan fa farin shiga ce " Honourable hannu yasa a aljihu ya ciro bandir biyu na ƴan dubu-dubu sannan yace, " Ai so nake a barmun ita ta zama tawa ce ni kaɗai, ga wannan ayi cefane dasu " Dubu ɗari biyu ya ajiyewa Aunty ya miƙe tsaye yace, " Hajiya ta fito yanzu kawai mu wuce dan bani da enough time " gaba ya wuce Abokin tafiyarsa na take masa baya, Aunty daɗi taji kamar ta buga tsalle, ɗakin da Indo take ta shiga wata ƴar ƙaramar akwati ta ɗauko ta miƙawa Indo tace ungo wuce maza zakiyiwa Alhaji rakiya Abuja zaku tafi saura kiyi masa gardama duk abinda ya umarceki kiyi masa kinji me nace miki? " Indo fuska ta kwaɓe hawaye ya ciko idanunta ta ce, " Aunty Abuja fa? Dan ALLAH kice su Aunty Preety su raka shi wallahi tsoro nake ji " wata razananniyar tsawa ta buga mata Indo har sai da ta ja da baya sannan ta ce, " Su Preety ɗin bayinki ne da zasu dinga fita suna nemowa kina zama kina ci, zaki wuce ko sai na ci miki mutumci? Kuma wallahi karki bari ya kawo mun ƙararki " Indo tana hawaye ta ɗauki jakar ta fice, tana fita ya buɗe mata mota ta shiga Aunty sai zabga Addu'a, Indo na shiga Honourable yaja motarsa suka bar unguwar, kai tsaye guest house ɗinsa ya wuce da ita dake Unguwar Nassarawa GRA. WASA FARIN GIRKI🤒 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [15/07, 19:10] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 43&44 Aunty gida ta koma ya ɗaga kuɗin tana shinshina su cikin shewa sa jindaɗi ta ce, " ALLAH ya kawo mun fara mai farar aniya wannan yarinya da goshi take tashin farko dubu ɗari biyu inaga sunje Abuja sun dawo wayasan alherin da zata samo mana, haka kawai da yarinya zatayi mana baƙin ciki " tana gama magana ta faɗa ɗaki domin ɓoye kuɗin gurin Honourable. Tun da Indo ta shiga motar Honourable tayi kicin-kicin ta haɗe fuska, ya lura sarai da yanayin Indo cikin zuciyarsa yake faɗin, " Yarinya zama ki ware ne munyi tarayya da irinki ba a dadi kuma tuni sun bada kai bori ya hau, nasan ta inda zan ɓullo miki hmmmm yaro man kaza " da wannan tunane-tunanen suka ƙarasa cen gidansa dake Unguwar Nasarawa GRA, tun bayan fitowarsu daga gidan Aunty sukayi sallama da abokin tafiyarsa ya aikeshi kai wani sako acen unguwar Kabuga,shi kuma ya wuce da Indo gidansa, katafaren gida ne na alfarma mai ɗauke da ƙawatattun furanni masu ban sha'awa, a harabar gidan ya yi parking ɗin motarsa cikin takunsa na ƙasaita ya taka ya fito, zagayowa yayi ya buɗewa Indo ƙofa yana faɗin, " Cutie na fito mu watsa ruwa kafin zuwa anjima mu wuce " Indo watsa masa harara tayi ta ce, " Amma wallahi kaidai anyi ƙaton banza, angaya maka ƴar iska ce da har zan bika cikin gida " Tun da Indo ta fara magana ya kafeta da kallo, tunda yake mu'amala da mata babu macen da komai nata yake burgeshi kamar Indo, sam maganganunta basu ɓata masa rai ba sai ma bin bakinta da ya dingayi da kallo harta dire maganar da takeyi " yawu ya haɗiya sannan ya tako kusa da ita, hannunsa ya kai ya shafi fuskarta da sauri ta matsa tana janye jikinta, lumshe ido yayi na ɗan sakanni ya buɗe sannan ya ce, " Haɗuwata dake na ƴan wasu mintuna yasa na tsinci kaina cikin wani irin baƙon yanayi, tabbas ke ɗin ta daban ce acikin mata,dan Allah karki aikata abinda kike shirin aikatawa domin na lura kina ƙoƙarin bijiremun,idan kika aikata hakan ba ƙaramin illa zaiyi mun ba domin bazan iya jure rashinki ba " duk wannan maganganun da Honourable yakeyi Indi zuba masa ido tayi tana ƙare masa kallo har ya gama, sannan ta ɗora da cewa, " Cab ashe dama alhazawan birni haka kuke ƴan iska ne? Wallahi ko ka mayar dani ko nayi maka ihun kwarto " murmushin gefen baki yayi ya ce, " Haba Humcy kar mu fara ja'inja dake tun bamuje ko'ina ba, karfa ki manta Abuja fa zamu " taɓe bakin Indo tayi ta ce, " Kai ka jiyo ko uwar Abuja ne bazani ba " mamaki yake sosai bai taɓa zaton Indo na doguwar magana haka ba, wani tunani yayi yaga idan ba dabara yayiwa Indo ba babu yanda za'ayi suyi tafiyar nan lafiya ƙalau ba tare da asirinsa ya tonu ba, kallan Indo yayi ya ce, " Duk naji abinda kika faɗa gaya mun yanzu me kike so inyi miki? " Indo daɗi taji har cikin ranta zuciyarta ɗaya ta ce, " Ka mayar dani gidan Aunty " Honourable ya ce, " Ki dai ƙara tunowa bayan nan bakyasan komai? Kuma kin tabbata idan na mayar da ke ba abinda zatayi miki? " Take gaban Indo ya faɗi idanunta ne suka ciko da ƙwallah, sunkuyar da kanta ƙasa tayi ta ce, " Ka buɗe mun gida kawai na tafi ko na haɗu da dangina tunda ta sanadin haka na baro gidanmu " Baba Huwaila ce ta faɗo mata a rai take taji wani kuka yazo mata, sai da tayi mai isarta sannan ta goge hawayenta, Honourable ya fahimci tana cikin damuwa fuskar tausayi ya sauya ya ce, " A ina zaki nemi dangin naki? Dama ba'a gurunsu kike ba " Indo share hawayenta tayi ta gaya masa wacece ita da dalilin zuwanta gidan Aunty da abinda ya fito da ita, cikin zuciyarsa yake faɗin, " Wannan shi ne tsuntsu daga sama gasashshe " amma a fili sai yace, " Ayya karki damu na fasa mayar da ke gurin Hajiya zan taimaka miki har ki nemo danginki, zanje gidajen rediyo da kafafen yaɗa labarai na kai cigiya kinji " Abinka da wanda ya fika shekaru ba'a ɗauki lokaci ba Honourable ya yiwa Indo dabara,tuni ta aminta da zancensa. Honourable ya fahimci Indo ba abinda ta sani a harkar ilimin boko na addinma bai gama tabbatarwa ba, kallanta yayi ya ƙara ƙasa da murya ya ce, " Daga yanzu ki ɗaukeni tamkar mahaifinki bazan cutar da ke ba, idan zaki dinga kirana kice Honey shi Honey yana nufin Babana da turanci " Indo gyaɗa kai tayi tace, " Nagode Honey " Honourable har cikin zuciyarsa daɗi yaji ya ce, " Cutie muje ciki ki zauna na shirya sai mu tafi amma sai munje Abuja akwai aikin da zai kaini cen mai muhimmanci " Zuciya ɗaya Indo ta taso tabi bayan Honourable har suka shiga cikin falon.Ƙayataccen falo ne na alfarma mai ɗauke da manyan kujeru na alfarma,duk inda Indo ta sanya ƙafarta akan carpet nitsewa takeyi sakin baki tayi tana ƙarewa falon kallo, ita daina iya saninta tunda take a duniya bata taɓa koda mafarkin irin wannan falon ba, sai gashi yau ta ganshi a zahiri ajiyar zuciya ta sauke tana shaƙar iska mai daɗin shaƙa, kujera ya nuna mata da hannu ya ce, " Zauna Cutie na bari na hau sama na sauko " Indo a ɗan tsorace ta dafa kujerar ta hau ta zauna tana ƙara ƙarewa falon kallo. MU KOMA KURA Jamilu da su Ado haka suka karaɗe ciki da wajen ƙauyen amma babu Indo babu alamarta, Tun Jamilu yana ganin kamar wasa ne abun har ya fara bashi tsoro,kafin wani lokaci tuni labarin ɓatan Indo ya zagaya ko'ina na cikin garin, masu murna nayi saboda gajiya da halin Indo masu jimami nayi, Baba Huwaila banda kuka babu abinda takeyi musamman da labari ya risketa na cewar anduba ko'ina babu Indo babu alamarta,shi kansa Jamilu ya shiga damuwa da kansa ya je cikin gari yakai report gurin ƴansan saboda lamarin ba ƙaramin tsoro ya basu ba. Washegari haka fadar Maigari ta haɗu ana jajintawa Lauwali ne ya ƙaraso gurin bayan ya gaida Maigari,Laminu ne yace, " Lauwali ya mukaji da abinda ya faru " Lauwali gyara zaman jakarsa yayi ya ce, " Wani abu ne ya faru bayan tafiyata jiya-jiya fa na tafi Kano " Maigari ya ce, " Yarinyar nan Indo ce ta ɓata annemeta sama ko ƙasa babu ita ko labarinta babu wanda ya samu " Lauwali yace, " Dawowa ta fa kenan zan wuce nace bari na ƙaraso mu gaisa da ranka shi daɗai, amma ban fahimci wace Indo ce baku gani ba? " Laminu ya ce, " Sarƙa fa ta wajen Baba Huwaila tun jiya da ta fita ba wanda yaji ko da labarinta " Lauwali jim yayi sannan ya ce, " Sarƙa fa jiya tare da ita muka tafi motarmu ɗaya da ita, tace mana Baba Huwaila ce ta aiketa garin Kano " gaba ɗaya gurin salati suka ɗauka Maigari ne ya ƙara tsuke fuska ya ce, " Kai Lauwali bama san maganar banza Indon ka gani a motar Kano? " cikin tabbatarwa ya ce, " Ƙwarai kuwa nida Malam Bala muka ganta yanzu haka yana cen Kano zai yo sarin robobi amma xuwa yamma zai dawo, idan kuna tantama bari na kirashi a waya kuji " Lauwali ya ƙarasa magana yana zaro waya daga Aljihunsa, Lambar Malam Bala ya kira yasa a speaker bayan ya ɗauka sun gaisa ya ce, " Malam Bala jiya wa muka gani a mota da zamu tafi Kano? " daga cen ɓangaren Malam Bala yace, " Sarƙa mana ko yau ma kun haɗu da ita a mota? " Lauwali yace, " Ka ga nan Ƙauye hankalinsu duk a tashe yake wai Indo ta ɓata " da sauri Malam Bala yace, " Au Baba Huwaila batasan ta tafi kano bane? " Lauwali ya ce, " Wallahi basu sani ba " daga haka katse wayar yayi ba tare da ya ƙara ji daga bakin Malam Bala ba. Maigari Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, " Amma yarinyar nan anyi shakiyiya haka kawai ta tashi hankulanmu muna zaune ƙalau, kai Ado maza jeka ka kiramun Baba Huwaila " Maigari na rufe baki Ado ya tashi ya nufi gidansu Indo, lokacin da saƙon kiran Maigari ya isa kunnen Baba Huwaila da sauri suka fito ita da Jamilu a tunaninsu ko labarin Indo aka samu, suna ƙarasawa zama sukayi suna jiran ji daga gurin Maigari. Maigari kallan Baba Huwaila yayi ya ce, " Ansamu Labarin Indo a..." da sauri ta katseshi, " Alhamdulillahi Ranka shi daɗe a ina" Maigari ya cigaba da cewa, " Lauwali ya sanar damu jiya da zashi Kano mota ɗaya suka hau da Indo " Cikin tashin Hankali Baba Huwaila ta ce, " Kano fa Lauwali? Indon tawa ce ta tafi Kano? " Lauwali ya ce, " Ya wuce wai Baba Huwaila tunda da idona ga Indo kuma mun riga ta sauka ma " Baba Huwaila bata ƙarasa jin maganar Lauwali ba ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,Jamilu wani iri yaji har cikin zuciyarsa dafa Baba Huwaila yayi cikin sigar lallashi ya fara bata baki yana tausarta, ganin ta ƙasa daina kukan yasa Jamilu ya tasheta suka wuce gida tana tafe tana hawaye,Baba Huwaila ba ƙaramin tausayi ta bawa su Maigari ba. Lokacin da suka ƙarasa gida Jamilu haka ya dinga tausarta yana bata baki, harta fara tsagaitawa da kukan sai da ya lura ta fara dawowa nutsuwarta sannan ya ce, " Baba Huwaila dan Allah ki kwantar da Hankalinki kinsan fa kina da hawan jini yanzu idanzu Kawu suka ji labarin halin da kike ciko bazasu ji daɗi ba, ki kwantar da Hankalinki ni zan je Kano na nemo miki ita " da sauri Baba Huwaila ta dafa ƙafar Jamilu ta ce, " Sai dai mu tafi tare idan angano ta mu dawo tare " cikin dabara ya ce, " Haba Baba Huwaila idan muka tafi tare ai bazan nemota lungu da saƙo ba tunda kinsan dai Kano girma gareta, a gidan Kawu zan sauka duk yanda ake ciki zaki zan kiraki a waya " Baba Huwaila gyaɗa kanta tayi cikin jindaɗi tace, " Jamilu idan kayi mun haka ka gama mun komai Allah yayi maka albarka " Tausayin Baba Huwaila ne ya kamashi cikin zuciyarsa yake mamakin irin ƙaunar da Baba Huwaila take wa Indo, gani yake da Goggo na raye haka ta faru baisan me faru ba,ɗagowa yayi ya ce, " Ameen ya rabbi Baba Huwaila " wani hawayen ne ya ƙara zubo mata gefen mayafinta tasa ta goge ta ce, " Allah ya jiƙan Aminiyata da tana raye bansan wane hali zata shiga ba, Allah ya bayyana mun ke Indo incika Alƙawarin da na ɗauka " Jamilu amsawa yayi sannan ya tashi ya shiga ɗakinsa, saman katifa ya kwanta yana tunanin halin da zai ɓullowa Baba Huwaila dan ya lura idonta rufe gashi ya ce zai je ya nemo Indo, afili ya furta, " Yanzu da nace zani Kano nemanta ta ina zan fara? " shi kaɗai ya zauna yana jerowa kanta tambayoyin da rasa amsoshinsu. Indo tana zaune tana ƴan kalle-kallenta har Honourable ya sauko sanye da dakakkiyar shadda ruwan toka, tunda ya fara takowa ƙamshin turerensa ya mamaye cikin falon, yana ƙarasowa wani kwarjini ya yiwa Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi ta cigaba da wasa da ƴan yatsunta, yana ƙarasowa ya ce, " Cutie na Afuwan kina ta jirana ko? " Indo girgiza kai tayi bata masa komai ba, hanyar waje ya nufa ya ce, " Zo mu wuce inajin sai mun biya ta Resturant munci abinci ko? " Indo bata ce masa komai ba yana gaba taba biye dashi a baya, mota ya buɗe mata ta shiga tana shiga shima ya zagaya ya shiga ya figi motar tuni dama Maigadi ya riga da ya buɗe masa gate. Kai tsaye Tarauni suka wuce Resturant ɗin HINDAT CHIPS&CHEKEN RESTURANT haɗaɗɗen gurin cin abinci ne na ƴan gayu da masu kuɗi, Honourable yana gaba Indo na biye da shi, ɗan siririn mayafinta saƙale yake akan kafaɗarta suna shiga kujera suka ja suka zauna, Indo a fakaice take ƴan kalle-kallenta List aka kawo musu Honourable ya zaɓi abinda za'a kawo musu. Sanye yake cikin ƙananan kaya waɗanda suka ƙara fito da zallar kyawunsa mai ɗauke da zallar haba da kamalarsa, kamar kullin fuskarsa babu walwa zaune yake yana latsa wayarsa, a hankali wayarsa ta fara ringing tana fitar da amo mai sanyaya zuciya, sai da wayar ta kusa katsewa sannan da ɗauka cikin murya zaratan maza, da sauri Indo ta juya tana kallan mai amsa wayar saboda muryarda ba ƙaramin amsa kuwwa tayi mata cikin dodon kunnenta ba, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa kallonsa take har ya ƙarasa wayar, Hanourable kallanta yayi ya ce, " Cutie na ga abinci ankawo mana " adai-dai lokacin ya ƙarasa waya ɗagowar da zaiyi karaf idanunsu suka haɗu da juna, kauda kansa yayi kamar bai ganta ba, Indo juyawa tayi ta fara cakalar abinci amma rabin hankalinta yana kan kyakykyawan saurayin, lokacin da ya lura da indo ta daina kallansa ɗagowa yayi ya zuba mata sexy eyes ɗinsa yana ƙare mata kallo,kansa ne ya kulle gani yake kamar yasan fuskarta amma a yanda yasan waccen bata kai wayewar wannan ba, to me haɗinta da wannan mutumin da yake kiranta da Cutie, yana ganin zata ɗago ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar bai damu da abinda sukeyi,Kiran wayar Honourable akayi har lokacin Indo tana kallansa saurayin take tantama take wai wanda ta sani ne ko kuma wani me kama da shi suna haɗa ido ya tsuke fuska yana watsa mata harara, Haonourable tashi yayi ya ce, " Humaira bari naje na amsa waya na dawo " Honourable har yayi gaba Indo tace, " Honey nidai kazo mu tafi " rass gaban Fahad ya faɗi, jiki a sanyaye ya ɗago kai yana kallon Indo saboda yanda yaji muryarta farin sani, Honourable juyowa yayi ya ce, " Cutie karki damu yanzu zamu tafi " gyaɗa kai Indo tayi tana sunkuyar da kai ƙasa,Fahad tashi yayi zai fita wayarsa ce ta faɗi ya tsugunna ya tattarata, har ya wuce cikin sanyin murya Indo tace, " Fahaaaad " har yayi gaba ya tsaya cak ɗan juyowa yayi kallon tsana ya bita da shi yana ƙarewa shigar jikinta kallo, wucewa yayi yana jin zuciyarsa na masa wani irin zafi, yana fita motarsa ya shiga wayarsa ya ɗauko ya nemo lambar Maigari, saving ɗinta yayi da Kawun kura kira yayi tana shiga ya ɗauka. WHATSAPP FANS COMMENTS YAYI ƘARANCI☹️☹️ WATTPAD KU CIGABA DA GASHI🌚🌚 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [17/07, 17:59] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 45&46 Da sallama Maigari ya ɗauka fuska a sake, Fahad gaida Maigari bayan sun gaisa cikin dabara ya ce, " Kawu dama wata makaranta akesan buɗewa ta kangararrun yara marasa ji, to hukuma ta bada umarnin a ɗauki list ɗin adadin yaran, amma yara mata kawai suke ɗauka shine nace a nan Kura ko kuna da yarinyar da ta fitineku ko yara mata? " Maigari kamar jira yake ya ce, " Allah ya yanke mana wannan masifar Fahad dama yarinya ɗaya ce ta addabemu kuma mun wayi gari ta ɓata, wata yarinya na nan doguwa da ka taɓa marinta bayan zuwanku " Fahad wata hargitsatstsiyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, " Shikenan Kawu nagode..." da sauri Maigari ya katseshi, " Amma Fahad babu wani alheri da zamu iya samu bayan wannan? Nufina ko ɗan wani hasafi haka " Fahad fuska ba walwala ya ce, " Gaskiya babu Kawu agaida mutanen gidan " bai jira cewar Maigari ba ya kashe wayar gaba ɗaga, yana gama wayar Honourable ya hango zai giftashi wata wayar ce ta ƙara shigo masa ɗauka yayi ya fara magana, bayan sun gaisa da wanda ya kira wayar suka shiga hira cikin hirar tasu yake faɗin, " Kai Abokina ina zaka gani Allah ya ne yayi mun gyaɗar doguwa na haɗu da wata baƙauyiyar yarinya, ai ko zaka ganni sai na gama sha'anina yanzu haka yau Abuja zamu wuce da ita " amsa aka bashi daga cen ɓangaren sannan suka cigaba da magana ba jimawa sukayi sallama,duk wayar da Honourable yake yi akan kunnen Fahad yayi ta zuciyarsa na wani irin zafi ya kunna motarsa ya bata wuta da gudun gaske ya bar gurin,Honourable gyara babbar rigarsa yayi ya shiga ciki a lokacin tuni Indo ta gaji da zama, bata wani ci abincin kirki ba shima ko rabin plate bai ci ba ya sallami masu resturant ɗin sannan suka wuce, Indo sai wurga Idanu take ko Allah zai sa ta ga Fahad amma ko mai yanayinsa bata gani ba, kai tsaye Mustafa ya kira a waya yace su haɗu a Airport yaje ya karɓi motarsa shi kuma zai wuce Abuja. KURA Shirye yake tsaf cikin shigarsa ta Shadda coffee agogon hannunsa yake ɗaurawa,Baba Huwaila na daga tsaye tana ta yi masa fatan samun nasara da dacen ganin Indo,Jamilu sallama ya yiwa Baba Huwaila ta rakoshi har ƙofar gida tana yi masa Addu'a, tana ganin yayi nisa ta share hawayen idanunta ta juya cikin gida, Jamilu motar Kano ya tara tafiya suke amma gabaɗaya acikin tunani yake da nazarin ta inda zai ɓullowa lamarin ɓatan Indo. ABUJA Lokacin da suka sauka garin Abuja Magriba ta kawo kai,SUWAIT HOTEL acen suka yada zango ɗakinsu ƙayatacce ne mai ɗauke da kayan alatu kala-kala, Honourable zaune yake a gefen gado yana cire babbar riga, Indo zaune take akan kujera one siter miƙewa tayi zata fita ya ce, " Cutie ina zaki haka? " cikin yanayin gajiya ta ce, " So nake na kama ruwa " murmushi yayi ya ce, " Ga Toilet nan muje na rakaki ki watsa ruwa " da mamaki Indo ta ce, " Honey kaine zaka rakani na watsa ruwan? " Honourable tunowa yayi da suɓutar bakin da yayi, cikin wayancewa ya ce, " Ina nufin na rakaki bakin banɗakin ki shiga ki watsa ruwa " Indo gyaɗa masa kai tayi cikin nuna yarda da abinda ya furta, matsawa yayi kaɗan tana biye da shi ya nuna mata Toilet ɗin, shiga tayi a ɗarare saboda yanda taga yanayin gurin tunda take bata taɓa taka ko makamancin wannan gurin ba, tsaye tayi ta rasa gurin da zatayi fitsari daga ƙarshe ta yanke shawarar tsugunnawa a ƙasa tayi abinta, famfo ta kunna tayi tsarki ta ɗauro alwala, tana fitowa ta sameshi zaune daga ahi sai singlet da gajeren wando, yi tayi kamar bata ganshi ba ta wuce ta fara duba jakarta ko zata samu babban mayafin da zata iyayin sallah da shi, duk cikin kayanta matafi ɗaya ne sai kayan sawarta shawara ta yanke ta ɗauki babbar rigar Honourable ta yafa kamar mayafi ta tayar da sallah,ajere ta rama sallar la'asar da magariba bayan ta idar ta fara Addu'ar Allah ya cika mata burin abinda ta fito nema,Baba Huwaila ce ta faɗo mata take ta fara zubda kwalla musamman da ta san halin Baba Huwaila da sa abu arai, kuka take harda shashsheƙa tanajin inama ta koma ta cigaba da zama da Baba Huwaila,agefe ɗaya tunowa tayi da irin gorin da Baraka tayi mata,wani sabon kukan ne ya ƙara zuwar mata,Honourable ne ya tako a hankali ya tsugunno gurinta ya dafa kafaɗarta ya ce, " Haba Cutie kukan me kike yi? Me zai dameki kina tare da Honey? " Indo janye jikinta tayi sannan ta ce, " Gaskiya Honey ka ɗaukeni daga gurin nan ka kaini gidan rediyo ka kai musu cigiya " a fakaice Honourable ya ɗan yamutsa fuska sannan ya ce, " Haba Cutie nace miki ki ɗaukeni tamkar mahaifinki kina tunanin zan cutar da ke ne? " Kafin Indo ta bashi amsa sukaji nocking a bakin ƙofa Honourable ne ya buɗe, abinci ne aka kawo musu tun daga bakin ƙofa Honourable ya karɓa ya ajiye, dawowa yayi gurin Indo alokacin ta ajiye Babbar rigarsa ta ɗauki mayafinta ya yafa ta koma cen gefe ta takure,kusa da ita ya zauna har suna iya jin numfashin juna ɗan matsawa Indo tayi gabanta na faɗuwa, kamo hannunta yayi ya ce," Haba Cutie ki bani haɗin kai mana akan abinda bai taka kara ya karya ba muyita kewaye-kewaye " ƙara matsawa yayi ya cigaba da cewa, " Zakiji daɗin haɗuwarmu domin Allah kaɗai yasan alherin da zaki samu agurina, idan har kika amincemun a yau ba sai gobe ba zan mallaka miki tsadaddiyar mota, kuma sai..." Indo ce ta katseshi tana fisge hannunta daga cikin nasa tana ƙyaƙyacewa da wata irin dariya, Honourable murmushi yayi a tunaninsa maganarsa ce ta faranta ran Indo har yana tsammanin yayi nasara akanta,cikin zuciyarsa ya ke faɗin, " Yarinya ai nasan za'a rina waɗanda suka fiki taurin kai ma mun buga dasu kuma sunyi biyayya..." wata sabuwar dariyar tata ce ta ƙara katse masa tunaninsa, kallanta yayi da mamaki ganin tana ta ɓaɓɓaka dariya ba kyaakykyautawa ga wani irin juya idanu da takeyi kamar mai yin fari,yana shirin yin magana zumbur Indo ta miƙe tsaye tana ƙwambare ƴan yatsunta tana cigaba da dariya haɗe da zare idanu tana kalle-kalle. Cikin Honourable ne ya kaɗa tsoro ya fara kamashi yana daga zaune ya fara ja da baya,Indo taku uku ta ƙara ta ɗanyi baya da shi girgiza kanta ta farayi take ɗan kwalinta ya fita gashin kanta ya ware cikin wata irin murya ta fara magana, " A yau basai gobe ba zamu fyeɗeka tabbasa hanjin cikinka dashi zamuyi kalaci wuuuuuuuuuuuu gurururu kai ku kwantar mun da shi " Honourable najin ance a kwantar dashi a zabure yaja baya tumbinsa banda rawa ba abinda yakeyi, cikin tashin Hankali ya ce, " Humaira dan girman Allah kiyi haƙuri wallahi bansan haka kike ba,tsautsayi ne da sharrin shaiɗan..." Wawan Ihun da Indo ta kwara ne ya katse shi wani irin gumi na daɗa kaiyo masa, tsaye tayi ta dira kan plate ɗin abincin da Honourable ya ajiye take abincin ya watse a tsakar ɗakin,ɗaukan ɗayan Plate ɗin tayi ta ƙaso gurin Honourable ta juye masa a ka sannan ta fara nunoshi da plate ɗin tana cewa, " Idan kanasan ka fanshi kanka sai ka cinye farantin nan idan ba haka ba sai mun daddatseka " jiki na rawa Honourable yace, " A dai canjamun wani abun amma ina ni ina iya cinye plate hukuncin yayi tsauri..." kafin ya rufe baki Indo tsalle tayi tun iya ƙarfinta tana dira ta buga masa Plate ɗin a saman kansa, wani irin Ihu Honourable ya kwara ya faɗi cen gefe yana maida numfashi, Indo dariya ta sa ta cigaba da cewa, " Kuzo mu farke ƴaƴan cikinsa ku bawa ƴaƴanmu su cinye " yana daga kwance ya fara ja da baya yana ɗaga hannu alamar roƙo, Indo wani tsallen ta buga ta haye saman gado ta fara kwaso fulallika da zanin gadon tana jefawa Honourable,ilahirin jikinsa banda rawa babu abinda yakeyi tunani yayi kawai akan yaje ya murɗeta yasa abu ya ɗaureta, yunƙurawa yayi ya tashi yana tunanin ta inda zai fara kamo Indo, a gefe ɗaya kuma yana fargabar taɓa shi karta masa illah,Indo kamar ta shiga zuciyarsa tana ganin tashinsa jikinta ya bata da sauri ta sauka daga kan gadon ta kurma wani uban ihu haɗe da tafiya da gudu taba fisgo Plasma Tv dake jikin bango, tana ɗaukota ta hau zaro ido tana kalle-kalle wata irin dariya ta fashe da ita ta buga Television ɗin a ƙasa, da sauri Honourable ya ja baya yana dafe ƙirji Tv stand ɗin ta fizgo ta jefawa Honourable da sauri ta fisgo wayar jikin Tv da ƙarfin gaske, ihu tayi ta fara buɗe baki kamar mai shirin kai cizo ta fara shauɗawa Honourable bulala ta ko'ina. KUYI MANAGE DA WANNAN SABODA RASHIN CAJI🤒 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [18/07, 18:28] Ameera Adam: *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 47&48 Honourable banda tamola da soshe-soshe babu abinda yakeyi,yanasan yayi ihu domin neman agaji yana tsoron abinda zai janyo hankulan mutane har su fahimci abinda yake faruwa,sanin shi waye da matsayinsa yasa ya ja bakinsa ya rufe banda roƙo da hannu babu abinda yakeyi,domin yasan muddin yayi ihu har aka kawo masa ɗauki ko yaƙi ko ya so sai labarinsa ya fita duniya musamman da ɗaukan abu da yaɗashi a waya bashi da wuya,yana tsaka da wannan tunanin yaji Indo ta ɗaure masa ƙeya da wayar Tv, wata uwar ƙara ya saki yana dafe ƙeya haɗe da hawayen wahala,cikin tashin hankali ya fara buga ƙasa da tafin hannunsa yana cewa, " Dan Allah Humaira kiyi haƙuri kimun rai karki illatani wallahi komai kike buƙata zan yi miki shi " Indo juya idanunta tayi ta kuma kallan gefe da gefe sannan ta kalli Honourable ta ce, " Bazamu barka araye ba sai mun farke hanjin cikinka mun cinye saboda ka taɓo ƴar sarkin Aljanun farisa,hukuncinka mai tsanani ne " Kamar ƙaramin yaro Honourable hawaye ne yake bin fuskarsa cikin tashin hankali yace, " zan iya mallakar da dukiyata akan rayuwata amma dan Allah kumun afuwa wallahi sharrin sheɗan ne kuma ba halina bane..." da sauri Indo tayi sufa ta faɗa kan katifa tana cizgarta, Honourable cikin zuciyarsa yace, " Yarinyar nan ashe annoba ce na ɗaukowa kaina bansani ba amma..." yana tsaka da tunani Ya ga Indo ta ɗaga katifar gadon ta jingineta, da gudu ta nufi wajen ƙofa tana wani irin jijjiga kai sannan ta fara cewa, " Zamu buɗe ƙofa mu gayyato sauran dakarun Aljanun domin mu sanmusu hanjin cikinka " Indo ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin buɗe ƙofar, da sauri Honourable ya rarrafo lokacin jikinsa duk yayi tsami ga shatin bulala ruɗu-ruɗu ajikinsa, cikin magiya ya fara roƙon Indo, " Ku yiwa Allah da Annabi kuyi haƙuri dan Allah karku tonamun asiri wallahi ni babban mutum ne a ƙasar nan,muddin labarin nan ya fita kashina ya bushe " Indo wani irin layi tayi irin na ƴan shaye-shaye kamar zata faɗi cikin shammata ta kaiwa Honourable duka da ƙafa a ƙirji,ji kake ƙwal ƙeyarsa ta bugu da center table.Wani irin yuuuu yaji kansa ga wani irin zugi da yake ji dama gurin da ta buga masa plate har ya fara tashi,cen ya faɗa gefe yayi ɗai-ɗai yana sauke ajiyar zuciya,Honourable gabaɗaya ya gama laushi magana yake amma da kyar ake iya jin abinda yake faɗa, wani kukan kura Indo tayi sa gudu ta ɗauko jakar kayanta ta fara kai duka ta ko'ina, tana ƙarasawa gurin Honourable ta dinga jibga masa iya ƙarfinta tun yana iya magana har ta kai saidai ya dinga girgiza kai daga kwance,miƙewa tayi ta ƙara ƙwallah ƙara sannan ta faɗi a cen gefe tunda ta faɗi bata ƙara motsi ba,Honourable a hankali ya juya kansa gefe ya hangota gefe warwas jiki ba ƙwari ya yunƙura ya ja jiki jikin bango yana maida numfashi. Bayan wasu mintuna Indo ce ta yunƙura a hankali ta tashi zaune cen gefe ta hango Honourable har lokacin yana jikin bango,kallan ɗakin ta farayi da mamaki take bin ko'ina da kallo miƙewa tayi tsaye da sauri Honourable ya ja baya,a ɗan tsorace Indo ta kalleshi ta ce, " Honey lafiya me ya faru ne? " Honourable girgiza kai yayi gabaɗaya ya jeme idanunsa sunyi zuru-zuru murya ƙasa-ƙasa ya ce, " Ba komai Humaira " Indo ƙara kallan gurin tayi sannan ta ce, " Amma ai naga gurin kafin nayi bacci ba haka bane nidai tsoro nake ji dan Allah mu bar gurin nan ka azo acutar damu, naga duk anfarfasa abubuwa " Da sauri Honourable ya ce, " Yanzun nan kuwa yanzu zamu tafi kwaso kayanki " Indo zuciyarta fes ta juya ta fara neman ɗankwalinta da mayafinta, jakarta ta ɗauko ta ajiye ta ce, " Ka tashi mu tafi dan Allah Honey muje gidan rediyon ka kai cigiyar " Honourable bai ce uffan ba ya yunƙura jiki ba ƙwari babbar rigarsa kawai ya ɗauka ya zura ya nufi hanyar fita, har ya ja ƙofa ya tuna bai saka sauran kayansa ba, agurguje yasa kayansa ko saka babbar rigar baiyi ba ya waurgar da ita gefe, ko hularsa bai ɗauka ba wayarsa ya ɗauka ya wuce fuskarsa murtuk ba fara'a suka fice,Indo cikin zuciyarta banda dariya babu abinda takeyi.Key ɗin ɗakinsu Honourable ya bawa ma'aikata yace musu zaije ya dawo,lokacin da suka fito tuni anyi sallar Isha'i motarsa ya ɗauka ya fara shawagi dasu a titi shi tunaninsa ɗaya inda zai kai Indo,gashi bayasan Matarsa tasan yana cikin garin Abuja,gabaɗaya tsoron Indo yake ko motsi yaga tayi zai zabura yaja gefe,wata dabara ce ta faɗo masa kallan Indo yayi ya ce, " Humaira muje gurun cin abinci daga nan sai muje gidan Rediyon " Ita ɗinma yunwa take ji da sauri ta amsa masa " kai tsaye wani resturant suka wuce, shigarsu ba wuya aka kawo musu list Honourable ne ya zaɓar musu ba jimawa aka cika musu gabansu da Abinci, sun fara ci ba jimawa Honourable ya fara wayar bogi tashi tsaye yayi ya cewa Indo, " Humaira ina zuwa zan amsa waya " Indo ko ajikinta ta gyaɗa masa kai, Honourable na fita da sauri ta shiga motarsa ya bata wuta da gudun gaske ya bar gurin. Indo gama cin abinci tayi tana ta jiran Honourable ya dawo amma shiru,tun tana jiransa harta fara gajiya kwashe kwanunka gabanta ma'akanta sukayi hamma take ta zabgawa tana leƙensa,mutanen da suke gurin duk sun watse wasu ma sunzo sun tafi, gajiya tayi da zama ta tashi zata fita da sauri ɗaya daga cikin ma'aikatan yayiwa Indo magana, " Hajiya zaki tafi baki sallamemu ba " da mamaki Indo ta ce, " Bangane ban sallameku ba? " Murmushi yayi ya ce, " Ina nufin baki bada kuɗin abinci ba " Indo gyara tsayuwa tayi ta ce, " Tare nake da Honey shi zai biya ya fita yin waya waje bari na duba shi " kusan tare suka fita dashi Indo na fita ta nemi motar Honourable sama ko ƙasa, wani mutum ta gani jikin motarsa da alama zuwansa kenan bai daɗe da zuwa ba, da saurinta ƙarasa gurinsa ta ce, " Dan Allah Malam baka ga motar Honey ba ɗazu ya fito waje ya ce mun zai amsa waya " Indo na rufe baki taga anturo ɗayan murfin ƙofar cikin masifa wata kyakykyawar mata ta fara magana, " Malama lafiya me ya kawoki gurun mijina, ƴan iska kawai da kunga maza kun dinga kwarkwasa kenan, zaki matsa daga gurin nan ko sai na ci mutumcinki " Cikin tsiya Indo tace, " Allah ya kiyaye me zanyi da wannan buhun alabon ko maza sun ƙare wallahi bazan aureshi ba " tana gama faɗa ta matsa cen gefe tana dube-dube aikuwa matar ta cigaba da bambamin faɗa sai da mijinta ya rarrasheta, kallanta yaron Mai resturent ɗin yayi yace, " Hajiya mufa ba wani Honey ke muka sani Honey ya gudu ya barki cen ku kuka sani, mudai kuɗinmu zaki bamu " ya ƙarasa magana yana matsawa kusa da Indo, Idanunta ne suka ciko da ƙwallah sannan ta ce, " Wallahi Malam ni baƙuwa ce daga Kura nake kuma bansan kowa agarin nan ba Honey ne ya taho dani " Kallan sheƙeƙe yayi mata yace, " Lallai ashe kema ƴar hannu ce muje kiyiwa Hajiya Bayani " yana gama magana auja juya cikin resturent ɗin daga wani ɓangare, matar na zaune a hakimce kan kujera ɗan risinawa yayi yai mata bayanin Indo tun daga farko har ƙarshe, kallan tsaf tayiwa Indo sannan ta ce, " Lallai yarinya kin rainawa kanki Hankali wallahi ba Honey ba ko Uban Honey ne ya kawoki Abuja sai kin biyani kuɗi na " kallan sa tayi ta ce, "Abinci nawa aka haɗa musu? " Cikin girmamawa yace, " Abinci dubu Huɗu da ɗari biyar ne " _INDO FANS HOW MARKET🤣🤣🤣_ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [19/07, 08:53] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* *ASSALAMU ALAIKUM BARKANKU DA WANNAN LOKACIN DA FATAN KOWA YANA LAFIYA,INA MUKU FATAN ALHERI MASOYA ALLAH YA BAR ƘAUNA,JIYA NA MANTA BAN SANAR DA NA TAFI HUTUN SALLAH BA AMUN AFUWA,KAR AMANTA DA KABARBARI DA ADDU'O'I ALLAH YA DATAR DAMU AMEEN.* *ZAN CIGABA DA SANADIN RAGON LAYYA INSHA ALLAH,MASU WATTPAD SU DUBA TA CEN XASU SAMESHI COMPLETE,LITTAFIN BA SABO BANE TUN LAST YEAR NA RUBUTA SHI KAWAI NA DAWO DASHI NE YANZU.* INA MUKU FATAN ALHERI DA FATAN ZA'AYI SALLAH LAFIYA😉 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [29/07, 18:21] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 49&50 Wani murmushi mai ɗauke da manufar lallai yarinya bakici nanin ba Hajiya mai abincin tayi sannan ta tsuke fuska kamar bata taɓa dariya ba tace, "Ke dube ni nan ki gani kinga na miki kalar wacce zaki rainawa hankali? To tun muna magana cikin mutumci ki bani kuɗi na idan ba haka ba na haɗaki da ɗaya daga cikin yarana ki kaishi inda Honey yake "Indo zuru-zuru tayi ta rasa abinda yake mata daɗi cikin marairaicewa ta ce. "Wallahi kinganni Hajiya a garin nan babu wanda na sani Honey kawai na rako daga nan yace zai kaini gidan rediyo cigiyar iyayena shine muka zo cin abinci nan ni kuka bansan guduwa zaiyi ba " Dariya Hajiyar tayi ta ce, "Honeyn Ubanki ne da bazai nuna miki hali irin na maza ba " Indo tayi ta farat tace,"Eh, kamar uba haka na ɗauke shi amma dan Allah kiyi haƙuri ko gurin da zan kwana bani da shi " ƙare mata kallo Hajiya tayi taga irin tsukakkun riga da siket ɗin dake jikin Indo sannan ta ce, " Kai Allah wadaran naka ya lalace, banda lalacewar zamani yanzu wai ƴar ƙanƙanuwar yarinyar kamar ke har kinsan shiga Abuja ki raka ƙasurgumin ƙato wai honey,tunda uba kika ɗaukeshi sai ki kirashi yazo ya biyani kuɗi na,har namijin bariki zaki ce kin ɗaukeshi uba" Indo tsumu tayi babu amsa banda raba idanu babu abinda takeyi, saboda ta ma rasa ta ina zata nemarwa kanta mafita daga gurin wannan mai abincin. Cen ƙasa Hajiya ta nunawa Indo tace, " Ga guri cen ki zauna har ki nemar mum kuɗina idan Honey yaji shiru ai dole ya biyo sahunki" Indo cikin zuciyarta take tunanin anya kuwa Honourable zai dawo saboda irin dukan da tayi masa,wani murmushi ne ya ƙwace mata da ta tuna sanda ta ɗaurewa Honourable ƙeya da wayar talabijin,rabonda tayiwa wani irin wannan gigitaccen dukan tun zuwan da suke yiwa Maigari,ƙauyensu ne ya faɗo mata da Baba Huwaila tunawa tayi da a gida take da tuni tana cen kwance akan katifarta,hawaye ne ya zubo mata cikin zuciyarta take addu'ar Allah ya cika mata burinta. A ranar da Jamilu ya shigo cikin garin Kano Unguwar Hotoro ya sauka gidan wani kawunsa Kawu Umaru ɗan Baba Huwaila na biyu ne,duk abinda yake faruwa haka ya sanar da shi da manufarsa ta shigowarsa cikin gari,ba ƙaramin damuwa suka shiga ba jin halin da Baba Huwaila take ciki ta sanadin barin Indo daga gida. Washegari da safe Kawu Umaru suka shirya kai tsaye gidan rediyon Freedom da Rahama suka je suka bada cigiyar Indo da yanayin kamaninta tare da adireshin gurin da za'a sameta idan anganta da lambar waya,daga nan gidan talabijin na Abubakar rimi (ARTV) suka wuce nan ma aanarwarta suka bayar tare da wani tsohon hotonta,dana nan gida suka wuce Jamilu har lokacin ji yake kamar ya rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa ne,bai taɓa zatan Indo zata shiga ransa kamar yanzu ba sai gashi rashinta na neman hargitsa rayuwarsa,a ɓangare ɗaya kuma damuwar Baba Huwaila ba ƙaramin ɗaga hankalinsa take ba. Honourable tunda ya cilla motarsa a kan titi ya bata wuta, da farko yaso ya canja Hotel,amma sai yayi tunanin sabon da sukayi da ma'aikatan kuma sun san waye shi ga irin ɓarnar da Indo ta tafka musu,yana komawa ɗaki ya sake ya sanar musu da abinda ya faru tare da alƙwarin biyansu kuɗin duk abinda aka lalata musu,yana shiga ɗakin da ya sake faɗawa kan gado yayi cikin gajiya saboda gabaɗaya jikinsa tsami yake da dukan da Indo tayi masa, afili ya furta," Shegiyar yarinya haka kawai zata illatani kai amma fa wannan aljanu nata ƴann azaba ne..." Maganarsa ce ta katse sakamakon kiran wayarsa da ya shigo,Numaber Hajiya Medile ya gani kauda kai yayi da guntun tsaki kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka murya ƙasa-ƙasa. "Hello Hajiya ya akayi ne?" daga cen ɓangaren Aunty ta amsa, "Allah ya taimaki Honourable ai tunda naji shiru nace labari yasha bam-bam" a daƙile yace, "Eh labari kam yasha bam-bam Hajiya " daɗi ne ya kama Aunty tace,"To gaskiya Alhaji sai ka ƙaromun toshi,Ni banji motsin ƴar tawa ba ko bata kusa ne? " Fuska a tsuke yace," Ai dama bazaki ƙara jin motsinta a kusa dani ba, ashe mahaukaciya kika haɗani da ita bansani ba?Yarinya ta dinga dukana a ɗaki kamar wani ƙaramin yaro yanzu jikina yayi tsami banda ciwo babu abinda yake mun " salati Aunty ta sa sannan tace, " Duka fa Honourable Au haka Humaira zata yi maka bani ita a wayar zanci ubanta maza bani ita " guntun tsaki Honourable yayi yace, " Na kaita wanu Resturent na baro ta acen bazan iya da ita ba,sai ta ɓatamun suna ta zubar mun da kimata zan miki transfer na 1million ki share zancenta kawai" cikin rawar Murya Aunty tace, " To to bari na turo maka da Account Number yanzun nan " Bai tanka mata ba ya katse wayar afili yake furta, " Lallai wannan mata akwai mahaukaciya babu ruwanta da halin da yarinyar take ciki idan siyar da ita ma nayi shikenan ita dai burinta ka bata kuɗi " yana gama magana ya tashi ta faɗa toilet domin watsa ruwa. Har kusan ɗaya na dare Indo na zaune tun tana zaune har ta fara gyangyaɗi,lokacin yaran Hajiya sun gama haɗa komai sun fara shirin tashi,Hajiya ce ta ɗakawa Indo duka a cinya tace, " Ke sai ki tashi mun tashi zamu rufe gurin" murje ido Indo tayi tana ɗan dube-dube sannan ta ɗauki ɗan figigin mayafinta,fitowa sukayi daga gurin aka rufe daga haka kowa ya fara kama gabansa yana tafiya makwancinsa,Hajiya ce ta kalli Indo tace, " Tunda na ganki zuciyata ta tsinke da mamaki saboda irin ƙanƙanta shekarunki,kiyiwa kanki faɗa wannan rayuwar da kika ɗaukarwa kanki ba me ɓillewa bace,tun wuri tun lokaci bai ƙure miki ki koma gaban iyayenki,kike na yafe miki kuɗin abincin amma idan halinki ne wata ran sai kinyi dana sanin abinda kike aikatawa " Hajiya na gama magana ta shiga motarta ta bata wuta ta wuce abinta. Indo ta fahimci sarai inda maganar Hajiya ta dosa wani irin kuka ne ya ƙwace mata,durƙushewa tayi agurin tayi mai isarta sannan ta tashi ta cigaba da tafiya batare da tasan inda take cilla ƙafafuwanta. Tafiya tayi mai nisa har sai da ta fara gajiya tsirarun mutane kaɗan-kaɗan ne sai motoci kaɗan da suke wucewa wani layi ta shiga ta cigaba da tafiya har ta ƙarasa ƙofar wani gida,Masallaci ta gani a gefensa da fanfo ruwa ta tara hannunta ta sha sannan ta taka ta hau kan interlock ɗin ƙofar gidan ta tsugunna,ta kurewa tayi aguri ɗaya saboda ɗan sanyi-sanyin da ke ratsa jikinta,kanta ta tusa cikin cinyoyinta babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita. Ƙarasowarsu amota ke da wuya fitilar motarsa ta haske bakin gate ɗin,yana shirin danna horn ya hango mutum tsugunne a bakin gate,a hankali ya danna horn wanda shi ya tashi Indo daga wahalallan baccin da take yi badam jin daɗi ba, a zabure ta miƙe ta matsa gefe ƙarasowa yayi da mota daga kusa da mazaunin Driver aka zuge glass ɗin motar aka fara magana, " Ke ƴanmata lafiya me kikeyi anan da tsohon daren nan?" Indo murza ido tayi ta ce wallahi bani da kowa a garin nan wani mugu ne ya gudu ya barni " kawai sai ta rushe da kuka. Kafin su bata amsa maigadi ya leƙo ta window sa yana musu barka da zuwa,da sauri ya zagayo ya buɗe musu ƙofa matar ce ta kalli Indo tace, " Biyomu ciki " suna shiga mutumin ya ce, " Wannan ba ganganci bane daga ganin yarinya kice ta shigo mana cikin gida?" " Idan ka lura akwai damuwa tattare da yarinya nan,idan bamu taimaka mata ba dole wasu zasu taimaketa watakila ta faɗa hannu na gari ko akasin haka, mu fara jin daga bakinta inyaso zuwa safiya sai musan abinyi " jinina kai yayi ya shiga da motar ciki. Indo kamar wacce ƙwai ya fashew a ciki haka ta fara takawa ta shiga cikin gidan,dukda ba yau ne karanta na farko shiga cikin gida mai kyau ba amma ko a mafarki bata taɓa tsammanin zata taka guri irin wannan ba " parking ɗin mota sukayi a parking space sannan suka tako gurin da indo take. Suna shirin yin magana wani matashi ya taho da gudu yana faɗin, " U are highly welcome my Momma "ya ƙarasa faɗa yana rungume matar da ke tsaye,Indo mamaki ne ya kamata ta kafeshi da kallo gabanta har faɗuwa yake take jikinta ya hau rawa,dukan bayansa matar tayi ta ce," Yaseer wai meyasa kullin baka girma ne ko sai nayi sirika tukunna " cikin murmushi yace, " Momma almost two months kenan fa rabonda na saki a idona kuma Daddy bai gayamun zai je ɗauko ki ba,kawai yace yau kar nai bacci idan ya dawo zaimun suprise " tunda ya fara magana Indo ta kafeshi da kallo tana mamakin zuwansa Abuja,cikin zuciyarta take maimaita sunan Yaseer da taji Momma ta faɗa har take tunanin ya akayi Fahad ya koma Yaseer?, Momma ce ta katse mata tunani ta ce, " Ai ni nace kar Daddynka ya sanar da kai dan nasan rigimarka ka dinga takuramun da tambayar yaushe zamu ta so " juyawa yayi da niyyar yiwa Daddy magana idanunsa suka kai kan Indo dake gefe cikin mamaki yace, " What a Beautiful Momma ina kika samo wannan " ya ƙarasa magana yana nuna Indo. Indo cikin zuciyarta ta ce, " Kut wai wannan yana nufin bai sanni bane? Ko bai taɓa ganina ba? " _CAKWAKIYA_🤪 *ASSALAMU ALAIKUM ƳAN UWA KAMAR YANDA NA SANAR DA KU ZANYI LITTAFIN GASA MAI SUNA SHAFAFFU DA MAI,A DA WAKILAN GASAR SUN BADA UMARNIN KOWA YA SAKI LABARINSA AMAN DAGA BAYA SUN CANJA TSARIN AKAN RANA-RANA NE INSHA ALLAH LABARI NA SAI NAN DA KWANA HUƊU ZAI SAUKA,DAN ALLAH KU TAIMAKA MUN DA SHARE KUMA AKWAI RANAR ZAƁE ZASU BAMU LINK MU BAKU KU MASOYA ZAKU SHIGA KUYI MANA VOTE DAN ALLAH KU NUNA ƘAUNARKU GARENI TA HANYAR ZAƁEN LITTAFINA NGD.* _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [05/08, 18:29] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 51&52 Momma kallan Yaseer tayi ta ce, "Haba Yaseer waɗannan tambayoyin ai ka bari mu shiga gida mu huta" murmushi ya yi yana sosa ƙeya amma har lokacin satar kallon Indo yake, ita kuwa sai sunne kai take kamar mutuniyar kirki. Cikin gida suka shiga kai tsaye ta wani ƙaton falo suka shiga, Indo kanta ne ya juye saboda yadda ta ga falon ya ƙayatu. Wani irin sanyi ne yake ratsa ta gashi duk inda ta jefa ƙafarta jinsu take cikin lintsumammun carfet. Wani tunani Indo tayi cikin zuciyarta take ayyana anya ba gidan ƴan yankan kai ta zo ba kuwa, tana tsaka da tunani Momma ta kalleta ta ce, "Daughter ga guri zauna" Indo sam bata fahimci me akace ba tun da taji kalmar zama ta san tayi guri akayi mata, banda kalle-kalle babu binda take yi. Suna nan zaune mai gadi ya shigo da manyan akwatunan yana dire su ya juya, a cen gefe Indo ta rakuɓe ta zauna Alhaji ya zauna a kujera ya kalli Indo ya ce, "Yarinya meye sunanki?" Indo ta samu kanta da cewa,"Suna na Humaira" Momma ta ce, "Masha Allah suna me daɗi ashe mamana ce" Indo murmushi tayi tana sunne kai ƙasa. Daddy ya ce, "Ke kuwa me ya fito da ke a tsohon dare nan bakya tsoron hanya?" Indo ras gabanta ya faɗi tanasan ta sanar da su gaskiya, amma tana tsoron karsu mayar da ita kura saboda taci alwashin bazata koma ba sai ta nemo inda iyayenta suke. satar kallon Yaseer tayi cikin zuciyarta ta ce, "Idan kuma ya gaya musu gaskiya fa?" ɗayar zuciyar ta ce,"Ke wannan fa ba shi bane baki ga wannan yafi haske ba? Kuma wannan yafi ruwan mutumci. Cikin suɓutar baki ta ce, "To kodai ƴan biyu ne? Amma jiya ba a kano kika ga Fahad ba?" Ji sukayi Indo tayi shiru Momma ta ce, "Mamana muna so muji me ya fitar da ke da kina mace gaki da ƙarancin shekaru" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, "Ni ƴar gudun hijira ce, antarwatsamu nida iyaye na kowa ya kama gabansa, ni da wasu ƴanmata muna zaune a gidan wata mata tana taimaka mana da abinci ashe ba dan Allah take yi ba, kwatsam rannan sai tayi mana sababbun ɗinkuna ashe haɗamu zatayi da wasu alhazawan birni, wasu daga cikinmu sun karɓi tayin da aka musu mu kuma shine muka gudu" tsoro ne ƙarara ya bayyana a fuskar Momma da sauri ta ce, "Ina ne gidan matar?" Tsoro ne ya kama Indo take ganin kamar asirinta zai tonu, saboda muddin aka je gidan Aunty zata ce basu daɗe da haɗuwa ba, ita kuwa ta fito da alwashin nemo inda iyayenta suke, dabara ce ta faɗo mata ta ce, "Ai matar a kano take, kuma dama gidan da take na haya ne, a ranar da muka taho nan a ranar ta tashi shine ta cewa shi Honey idan mun koma ya kirata zata bashi address ɗin inda ta koma." Kallan juna suka yi cikin haɗin baki suka ce, "Waye Honey kuma?" Indo ɗan tsorata tayi musamman yadda taga tsoro ƙarara a fuskarsu, dake wa tayi ta basu labari tiryen-tiryen har zuwan ta gurin mai abinci, tausayinta ne ya kamasu a lokacin suka fahimci a rashin ilimi a tattare da ita. Daddy ne ya ce, "Yanzu dare ya yi haka mu barwa zuwa safiya idan Allah ya kaimu, idan mun fita zaki gane hotel ɗin?" Indo ta ce, "Gaskiya bazan gane ba, kaina duk ya juye" Yaseer ya ce, "Amma Daddy..." Daddy ya katse shi da, "A'a Son Mommynka na buƙatar hutu mu barwa zuwa safiya" Yaseer ne ya bi wata hanya ya fara ƙwalawa Baba Mariya kira amma shiru ko motsinta babu, Mommy ce da kanta ta riƙe hannun Indo tabi hanyar da ita suka fara ƙwanƙwasa ƙofa, basu daɗe ba Baba Mariya ta fara tambaya, daga cen ɓangaren Momma ta ce, "Baba Mariya buɗe nice, baƙuwa na kawo miki" da sauri ta buɗe ƙofar tana murje idanu, ganin Momma a katse ya sa ta washe baki tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa saukar yaushe" Murmushi Momma tayi ta ce, "Da daren nan muka sauka Baba Mariya, ga yarinya na kawo miki" Baba Mariya ta ce, "To shikenan Hajiya, ƴanma shigo muje" Indo kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka ta fara takawa ta wuce ciki" tana shiga Momma tayi musu sallama ta koma falo lokacin Yaseer baya nan, kai katsaye ɗakinta ta wuce a gajiye. Indo na shiga ta nemi guri ta rakuɓe a gefe sai raba idanu take, tana bin ɗakin da kallo. Baba Mariya ce ta katse ta da faɗin, "Ƴanmata ya sunanki ne?" Indo ta ce, "Suna na Humaira" Baba Mariya ta ce, "Wai ashe tsohuwa ce, shiyasa ina arba dake na fara jin yunwa" Indo murmushi tayi kawai ta ƙarewa bangom ɗakin kallo da ya ke ta walwali, Baba Mariya ta cigaba da cewa, "Ga katifa nan ki kwanta mana tsohuwa" Indo cire mayafinta tayi ta haye kan katifa ta kwanta. WASHEGARI Baba Mariya duk ta gama aikace-aikacen da ta saba, har wanka sunyi ita Indo sannan ta haɗa musu kayan breakfast ta kawo musu ɗaki, sai da suka ci suka yi ƙat har sun fara taɓa hira suka ji Momma na ƙwala musu kira, da sauri suka fita cikin girmamawa suka gaishe ta. Zuwan su falo ke da wuya sai ga Yaseer ya shigo sai zabga ƙamshi yake sanye yake da Ash ɗin shadda mai ɗauke da aikin baƙin zare, kansa sanye yake da baƙar hular hannunsa da ɗaure da wani tsadadden agogo. Indo na ɗago kai suka haɗa ido take gabanta ya yi wani irin mummunan faɗuwa, Yaseer kallanta yayi yana murmushi yana shirin magana Indo ta ce, "Ina kwana?" muryarta wani irin amo tayi masa mai ratsa kunnuwa wanda yayi dai-dai da bugun ƙirjinsa, ƙaƙalo murmushi ya yi ya ce, "Lafiya ƙalau Humaira ya gajiya" wani tsautsayi ne ya kwasheta ta ƙara ɗago idanunta zata amsa karaf suka ƙara haɗa ido, ba ƙaramin kyau yayi mata ba musamman murmushin sa da yake ƙarawa fuskarsa kyau, cikin sanyin murya ta ce, "Ba gajiya" Ƙarasawa yayi ya rungumo Momma yana faɗin, "Morning my Habeebty ya gajiyar hanya" Cikin jindaɗi Momma ta ce, "Lafiya ƙalau Habeebee har anshirya?" ɗagowa ya yayi ya ɓata fuska kamar zaiyi kuka cikin marairaicewar murya ya ce, "Momma ya na iya zan tafi Office, da su wasu ne da sun ɗaga mun ƙafa na yau kaɗai amma ina" Momma ta ce, "Haba Yasee idan ka fita gabaɗaya awa nawa zakayi indai nice har sai ka gaji da gani na" ɗan jinjina kai yayi yana kwaɓe baki kamar ƙaramin yaro sannan ya ce, "Shikenan Momma sai na dawo" Yaseer har yayi gaba Momma ta ce, "Yaseer Idan ka samu lokaci zan aikeka akwai siyayyar da zaka yiwa Humaira" da sauri ya juya yakai kallonsa gurin Indo ya ce, "Ok Momma babu damuwa" yana gama faɗa ya fice daga falon, Ajiyar zuciya Indo ta sauke, ga wanda ya lura da ita zai fahimci rashin nutsuwar da take ciki. Momma ce ta kalli Indo ta ce, "Humaira ni da Alhaji mun tattauna akan zamu riƙe ki tsakani da Allah, kuma zamu taimaka miki wajen nemo iyayenki indai suna raye, ina fatan kema zaki zauna da mu zuciya ɗaya kamar yadda muka ɗaukeki ki ɗaukemu kamar iyayen da suka haifeki shi kuma Yaseer ki ɗauke kamar yayanki, wannan Baba Mariya ce tana da jikoki biyu amma sunje gida mai aikinmu ce, ki girmamata ki bata girmata dan banasan raini" Indo gyaɗa kai tayi cikin farin ciki ta ce, "Nagode Hajiya Allah saka da alheri, Allah jiƙan mahaifa" Momma taji daɗin addu'ar taji ta ce, "Daga yau karki ƙara kirana da Hajiya yadda Yaseer kikaji Yaseer na kira da Momma kema haka zaki dinga faɗa" Indo a kunyace ta ce, "To Momma" shiru ne ya biyo baya Indo ta faɗa nazari, kamannin Yaseer ne suke ƙara dawo mata kan ƙwayar idonta. A gefe ɗaya Ayyano Fahad tayi cikin zuciyarta take faɗin, "Kai wannan lamari akwai ɗaurewar kai, gaskiya baxai yuwu ace mutum ɗaya bane tunda halinsu ma ba ɗaya ba, Fahad bashi da mutumci ga shegen iya yi. Shikuwa Yaseer da ganin kalarsa ta masu mutumci ce?" cikin suɓutar baki a hankali ta ce, "To ko ƴan biyu ne?" karaf taji Momma ta ce, "Humaira magana kike ko akwai abinda kike so? Karfa kiji kunya ta ni ƴa na ɗaukeki" Indo murmushi ta ƙirƙo ta ce, "Ba komai Momma dama cewa nayi a miƙa godiyata gurin Alhaji" Momma ta ce, "Zaiji insha Allah, ni bari na ƙarasa ciki" tana gama faɗa ta tashi ta nufi hanyar sashenta. Baba Mariya ce ta cewa Indo, "Tsohuwa ki saki jikinki mutanen gidan nan fa basu da matsala, nima dai kinganni mai aiki ce amma warkan da ni" Indo dariya tayi ta ce "To shikenan Baba Mariya". A ƁANGAREN SU JAMILU Tun yana zaman jiran kira daga gidajen radiyo har zaman ya fara damunsa, kullin sai dai suyi waya da Baba Huwaila yayi ta kwantar mata da hankali. Ana cikin haka har sai da suka shafe kwanaki babu alamun Indo daga gurin aiki tun suna ɗaga masa ƙafa har suka fara masa magana, yana shirin tafiya ya samu transfer daga hukumar aikata, anyi masa canjin aiki zuwa makarantar sakandire ta maza dake cikin Sa'adatu rimi dake dake cikin garin Kano, ba shiri ya haɗa kayansa ya koma Kura. lokacin da Jamilu ya gama zayyanewa Baba Huwaila yadda suka yi a kano kuka ta fashe masa da shi, sai da tayi mai isarta ya lallasheta sannan ya sanar mata da sauyin aikin da ya samu. Tayi murna ƙwarai daga baya kuma tayi tsalle ta dire, tace atabau sai dai su ɗunguma su koma kano. Jamilu mamaki yayi sosai, shi dai a saninsa Su Kawunsa sun jima suna yaƙi akan Baba Huwaila ta koma gurinsu da zama amma ta shafawa idonta toka taƙi yarda, a yanzu rana tsaka ta ce su koma Kano, da farko kamar ya yi mata maganar amma da ya tuna a wannan lokacin ta zama hukuma sai rarrashi sai kawai ya share maganar. Wayarsa ya ɗauka ya kira Kawu ya sanar da shi yadda sukayi da Baba Huwaila, farin ciki sukayi sosai sannan suka ce su haɗa kayansu zasu taho da mota su ɗauko su gabaɗaya. BAYAN SATI BIYU Indo ta murmure ta murje ta zama ƴar gida, har wata ƴar ƙiba tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa, tun tana baƙunta tana jin nauyin su har ta saki jikinta da su. Daddy ne ya ɗauko mata mai koya mata karatun islamiyya da boko, Momma ce ta kawo wannan shawarar acewarta idan aka saka Indo a ba tare da lesson ba zai yi wuya ta dinga fahimtar karatu cikin sauƙi.Wani ustaz aka ɗauko yake zuwa yana koya mata karatun addini da safe sai wani Teacher da yake zuwa bayan sallar la'asar yana koya mata karatun boko. Indo ta fahimci Yaseer sun sha matuƙar bambam da Fahad, mutum ne mai barkanci da fara'a uwa uba sauƙin kai. haka zai biye mata kamar ƙaramin yaro suyi ta hira Indo na bashi tatsuniya, wani lokacin idan yaga Indo tayi zuƙuɗum tana tunani dan ya kawar mata da damuwa har ɗaukanta yake su tafi stores suyo siyayyar tarkacen kayan zaƙi dangin su alewa chocolate da sauransu. A wannan lokacin abu ɗaya zuwa biyu ne yake damun Indo, wani lokacin haka zata zagaya cen Garden ta sha kukanta san ranta, wani lokacin kuma cikin dare idan Baba Mariya na bacci, abu na farko idan ta tuna rashin asalinta shi yake ɗaga mata hankali domin takan zauna ta dinga gayawa kanta wannan kalmar ta, "KAYAN ARO BAYA RUFE KATARA" duk jindaɗin da zaka samu indai za'a ce baka da asali na banza ne domin ko ba daɗe ko ba jima ALLURA ZATA TONO GARMA. Abu na biyu su Baba Huwaila ita da Jamilu, kodayaushe tana tunanin halin da Baba Huwaila take ciki wani lokacin idan kewarsu ta dameta sai dai ta fashe da kuka, wata rana tana garden a durƙushe tana kuka Yaseer ya tsaya yana sauraron yadda take rera kuka, sai da tayi mai isarta sannan ya zauna a gefe yana tambayarta abinda yake damunta. Sai da ta share hawayenta sannan ta ce, "Ba abinda yake damuna kawai Iyayena na tuno" tausayinta ne ya kama shi har cikin ransa ya shiga lallashinta daga nan ya fara aikin nasa na barkwanci, lokaci ɗaya ya mantar da Indo damuwar da take ciki. Tun daga ranar yake samar musu lokaci yana suna zama shi da ita yana bata labari ita kuma ta yi masa tatsuniya. Ya ma Indo ta fito daga ɗakinsu lokacin yamma tayi, cen garden ta nufa saboda ta duba filin motsa jikinsa bayana nan, ta san indai bayacen a wannan lokacin yana garden a zaune. Kamar yadda tayi tsammni hango shi tayi ta bayansa a kan kujera da alama waya yake dannawa kuma yayi zurfi cikin abinda yake yi, Indo tsinken tsintsiya ta zaro ta tafi a hankali tana zuwa, ta fara zana masa a cikin kunnensa. Da sauri ya zabura a tsorace har yana jefar da wayar hannunsa ta faɗi cen gefe, Indo ƙyalƙyalewa tayi da wata iriyar dariya irin ta tsokana tanayi tana tafi da hannunta, batayi aune ba taji ya kifeta da wani irin azababben mari har sai da ta kusa faɗuwa, da sauri ta dawo cikin nutsuwarta tana dafa jikin bango. Da mamaki ta ɗago ta kalleshi hannunta riƙe da kumatunta, tana shirin yin magana ya nuna ta da ɗan yatsa fuska a tsuke ya ce, "Ki shiga nutsuwarki banasan hauka da rashin hankali irin naki idan ba haka ba zan banbance miki aya da tsakuwa wawiya, ko cikin karnuka ke shashar karya ce" yana gama faɗa ya tsugunna ya ɗauki wayarsa ya fice daga gurin ya bar Indo riƙe da kumatu. TO FA FANS KU KAFTA🤸🏻‍♀️ *KUMUN AFUWA NA JINA KWANA BIYU DA KUKA YI INSHA ALLAH NA DAWO DA ZAFINA AMMA GOBE BAZAKU SAMU POSTING BA, KU TAYANI DA ADDU'A INA DA EXAMS GOBE IDAN ALLAH YA KAIMU.* KUMA INA JIRAN NAJI RUWAN COMMENT🤓 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [10/08, 17:26] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 53&54 Indo tsaye tayi kamar wacce aka zarewa laka a jiki, jiki a sanyaye ta juyo tana bin hanyar da ya nufa da kallo, gangarowar hawayenta zuwa kan tafin hannunta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, sautin muryarsa ce ta cigaba da yi mata amsa amo cikin dodon kunnenta, maganarsa ta ƙarsh ita tafi tsaya mata a rai, "Ko cikin karnuka ke shashar karya ce" da gudu ta fice daga gurin kai tsaye ɗakinsu ta wuce, tana shiga ta faɗa kan gado ta rushe da wani irin matsanancin kuka. Sai da tayi mai isarta ta goge hawayenta a fili ta fara magana kamar zautacciya, "Ya Yaseer meyasa zaka yi mun haka? Kasan ba haka halinka yake ba zaka yaudare ni da barkwancinka?" kamar an tsikareta ta miƙe tsaye a zabure take wani tunani a faɗo mata haɗe da tsoro a fili ta ce, "Ina tunaninki ya tafi da zaki sakankance masa ko kin manta halinsa lokacin da yaje garinku?" sai kuma ta zauna gefen katifar tana cewa, "Kenan Fahad yaudarata yayi? Me nayi da zai kirani karya?" take ta tuno haɗuwarta da shi a kano a gurin cin abinci. Cikinta ne ya karta tsoro ya kamata afili ta ce, "Nashiga uku yanzu idan ya gayawa Momma ya zata ɗauki abun" sai kuma ta ce, "Amma ai na gaya mata yanda muka haɗu da Alhaji" ɗayar zuciyar ta ce, "Idan ya sanar da su asalinki fa" a nan indo tayi shiru kanta ya kulle ta rasa bakin magana, amma gaba ɗaya tsoro ya addabi zuciyarta a kowanne lokaci tsammanin kiran Momma take, a gefe ɗaya kuma taci alwashin fita daga sabgar Yaseer indai ba gaisuwa ce zata haɗa su ba. Yana fita daga gurin ɗakinsa ya wuce yana huci da ƙarfi ya banka ƙofar, yana shiga ya dunƙule hannunsa ya kaiwa bango duka yana furzar da iska mai zafi. Wani tunani yayi da sauri ya fice daga ɗakin ya wuce ɗakin Momma, yana shiga ya fara ƙwala mata kira. Da sauri ta fita a hargitse saboda jin kiran da yake mata tasan ba na lafiya bane, tana fitowa ta ce, "Son lafiya wannan kiran haka" fuskarsa murtuk babu walwala ya ce, "Momma magana akan waccen yarinyar ne" Momma zama tayi akan kujera ta nuna masa gefe ta ce, "Zauna nan, me Humairan tayi maka?" zama yayi yana sauke ajiyar zuciya yace... Da daddare su Indo na zaune a ɗakinsu Momma ta shiga, cikin girmamawa Indo ta rissina ta gaishe da Momma, Zama tayi a bakin gadonsu ta ce, "Humaira yayanki ya kawo mun ƙararki wai kinyi masa rashin kunya, banasan raini kuma banasan ya ƙara kawo mun ƙararki nan gaba" Tun da Momma ta fara magana jikin Indo yayi sanyi cikin zuciyarta take faɗin, "Meyasa Yaseer zaiyi mun haka? Dama lumbu-lumbu yayi mun? Aikuwa anyi ɗaya babu ƙari indai nice" a fili Indo ta ce, "Insha Allah Momma haka bazata ƙara faruwa ba zan kiyaye" murmushi Momma tayi ta ce, "Yauwa Humairan Momma" ta faɗa tana ɗora hannunta akan kafaɗar Indo sannan ta tashi ta fice daga ɗakin, Indo ta jima tana jin ranta babu daɗi daga ƙarshe ta yanke shawarar yanke alaƙarta da Yaseer. Washegari da yamma bayan angama yiwa Indo lesson tana zaune agurin tana duba abinda aka koya mata, daga bayanta taji kamar an jefo mata ƙaramin dutse a tsorace ta juya, ganin babu kowa yasa ta ci gaba da harkar gabanta. A karo na biyu taji ankuma jefo mata dutsen miƙewa tayi ta fara haɗa takardunta, ta nufi hanyar falon batayi aune ba ta taji ya ce, "Kamota nan" Indo ihu ta saki tana watsar da takardun hannunta, saboda tsoro jikinta sai karkarwa yake. Dariya Yaseer yayi yana nuna ta da ɗan yatsa ya ce, "Matsoraciya! matsoraciya! Nima na rama abin da kika mun rannan" Indo tsuke fuska tayi ta ce, "Ya Yaseer dan Allah ka bari bana so" tana gama faɗa ta kwashe takardun ta shige falon. Da mamakin abin da tayi masa ya bita da kallo amma sai yayi wani tunani yake ganin kamar ko tana cikin yanayin da bata buƙatar haka, amma ko kaɗan ransa bai so haka ba. Ya jima a tsaye sannan ya wuce ɓangarensa fuska ba walwala. Lokacin da Indo ta shiga ɗaki kan katifa ta faɗa tana lumshe idanu, wani irin nishaɗi take ji acikin zuciyarta. Fuskar Yaseer ce take mata yawo acikin ƙwayar idanunta, ɗagowa tayi tana murmushi a fili ta furta, "Yaseer kenan..."motsin ƙofar ne ya katse mata maganar da ƙoƙarin furtawa, Baba Mariya ce ta shigo tana faɗin, "Tsohuwa ana hutawa" Indo ta amsa mata, Baba Mariya zama tayi gefen katifa ta fara jan Indo da hira. Tun daga ranar Indo ta fara wasan ɓuya da Yaseer ko sun haɗu a hanya gaisuwa ce kawai take haɗasu, ko da ya ja ta hira sai dai ta bashi amsa sama-sama ko ta ce masa zata shiga ɗaki tana da abinyi. Tun abun baya damun Yaseer har ya fara damunsa sai yayi niyyar yiwa Indo magana sai kuma ya fasa dan bayasan duk wani abu da zai ɓata mata rai ko ya takurata, amma matakin da ya ɗauka na barazanar sanya rayuwarsa cikin wani hali. Wata rana Indo na zaune a garden zaune a kan kujera da alama tana cikin damuwa, Idanunta a rufe suke daga gefen idanunta hawaye na gangarowa. Ya jima a tsaye yana kallonta yana jin babu daɗi a zuciyarsa, duk ɗigon hawayenta ɗaya dai-dai yake ya bugawar numfashinsa, zuciyarsa ta kasa sukuni kamar zata hudo ƙirjinsa, Indo na daga zaune kamshin turerensa ne ya fara fusgar numfashinta, a hankali ta sauke ajiyar zuciyar tana juya ƙwayar idanunta da suke rufe, wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta amma ko buɗe idonta batayi ba saboda kar Yaseer ya fahimci ta san da zuwansa. Murmushi Yaseer yayi saboda ya fahimci sarai abinda Indo take nufi, handkee ɗinsa ya ɗauko ya ɗora mata a dai-dai fuskarta yana cewa, "Ki goge hawayenki bana buƙatar ganin su" Sautin muryar Yaseer yayi dai-dai da bugawar ƙirjinta, jiki ba ƙwari ta buɗe darara-dararan idanunta karaf suka haɗo. Da ƙyar ta samu sukunin sauke ƙawar idanunta ƙasa haɗe ta miƙa hannu ta karɓi handkee ɗin ta fara goge fuskarta, lumshe idanunta tayi saboda daɗin kamshin turaren da take shaƙa sannan ta miƙa masa. Janyo kujera yayi ya zauna yana fuskantar Indo ya watsa mata manyan idanunsa, Indo ji tayi duk da tsargu ta fara wasa da zara-zaran ƴan yatsunta, Yaseer kallanta yake cikin murmushi saboda yadda yaga duk ta dubur-duburce. Indo ɗago da kanta tayi suka ƙara haɗa ido da sauri ta kauda kanta gefe tana ƙoƙarin miƙewa, Yaseer ƙafarsa yasa ya tokare hanyar da zata bi yana murmushin gefen baki, Indo cikin wata iriyar murya ta ce, "Ya Yaseer ni ka bani guri zan shiga ciki" Daidaita nutsuwarsa yayi cikin nutsuwa ya ce, "Idan naƙi fa?" Indo turo baki gaba tayi ta ce, "Nidai ka matsa zan wuce" Yaseer tsuke fuska yayi cikin wata iriyar murya ya ce, "Ki koma ki zauna" da sauri Indo ta kalleshi suna haɗa ido a zuciyarta ta ce, "Wallahi shi ne" jiki a sanyaye ta koma ta zauna. Yaseer murmushi yayi ya ce, "Matsoraciya kinji tsoro ne?" Indo ɗauke kai gefe tayi ta ce, "Ni ai bana tsoron kowa sai Allah" tun da ta fara magana ƙwayar idansa na kan ɗan bakinta sannan ya cigaba da cewa, "Humaira me yasa kike neman wahalar da rayuwata?" da sauri ta kalleshi tana mamakin maganganunsa. Ya ci gaba da cewa, "Na rasa laifin da nayi miki da kike share ni kina azabtare da ruhina, kin daina hira dani kin daina bani tatsuniyarki mai daɗi ko kinasan na kai ƙararki gurin Momma?" Indo wani kallo ta watsa masa cikin zuciyarta ta ce, "Kai ƙara na nawa kuma? Banda ƙara ta da ka kai wata zaka kuma kaiwa" a fili ta ce, "Ba komai" Yaseer ya kuma jefo mata tambaya, "Humaira ni ne bakyasan na dinga raɓarki?" da sauri Indo ta kalleshi tana girgiza kai, murmushin gefen baki yayi sannan ya ce, "To idan bakyasan na kai ƙararki ki daina yi mun waɗannan sababun halayen naki" Indo hannunta ta sa a baki murya a sanyaye ta ce, "To na daina Ya Yaseer" shima murmushi yayi ya ce, "Gaskiya ban alama ba dan banga kinyi mun murmushi ba" da sauri Indo ta rufe fuskarta tana dariya, Yaseer dariya yayi daga nan suka cigaba da hira cikin farin ciki. Tun daga wannan lokacin Yaseer da Indo suka ɗinke suka koma kamar yadda suke a baya, duk lokacin da Yaseer ya dawo daga gurin aiki bayan ya huta zasu zauna ya ƙara yiwa Indo bita akan karatun da akayi mata na ranar, bayan sun gama karatu sai ta zubo musu ruwan tea suna sha suna hira, Yaseer da Indo sunyi matuƙar shaƙuwa Momma har mamakin wannan shaƙuwar tasu take, duk lokacin da gurin aiki suka tura Yaseer wani garin idan zaiyi kwana biyu sai Indo tayi ta jin wani iri saboda damuwa, bata da sukuni ko walwala sai Yaseer ya dawo. Indo sosai take fahimtar karatun da ake koya mata hakane yasa Daddy ya nemi wata private school mai suna Al-manar Collage yayi mata registration, makarantar haɗe take da islamiyya wuni suke tun bakwai na safe sai biyar na yamma suke dawowa. Kullin idan yaseer zai tafi aiki shi yake sauke Indo a bakin gate, da yamma kuma driver ne yake ɗaukota ya dawo da ita. A jss1 aka saka Indo saboda a yanayinta tayi girma a ce tana primary school, duk da haka malaman da suke zuwa biya mata karatu suna zuwa shiyasa karatun baya bata wahala sosai, a wannan lokacin ne Jikokin Baba Mariya su biyu suka dawo hakan ne yasa aka warewa Indo nata ɗakin da toilet ɗinta aciki. Lokacin da su Indo suka cinye first term a result ɗin ta ita ta ɗauki ta goma sha bakwai acikin su talatin, gabannin zasu koma school Lubna ƴar ƙanin Daddy tazo karatun jami'a nan garin Abuja, a gurin Momma zata zauna har ta gama karatunta na shekara huɗu. A ɗakin Indo Momma ta sauke ta hakan sam be yiwa Lubna daɗi ba dan tana ganin kamar an ƙasƙantar da ita ne agurin wacce bata kaita gata ba. Bayan Momma ta fita daga ɗakin su Indo Lubna a ya mutse ta kalli Indo ta ce, "Ke! Kamar kece mara asalin nan wacce muka ji labarin kece ƴar gudun hijara ko" Indo ji tayi kamar an buga mata guduma a ka, take idanunta suka kaɗa sukayi jawur, haɗiye ɓacin ranta tayi ta ce, "Eh nice, ke kuma wace ce?" Lubna taku biyu tayi tana watsawa Indo wulaƙantaccen kallo sannan ta ce, "Ni ƴa ce ga Alhaji Nasir ƙanin mai gidan nan, a taƙaice zan iya ce miki nan gidanmu ne" Indo cikin halin ko'in kula ta ce, "Ok, hakan yayi" tana gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin. Tana fita kai tsaye garden ta wuce tun kafin ta ƙarasa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sai da tayi mai isarta sannan ta ji sanyi a zuciyarta. A hankali ta furta, "Me yasa na zaɓarwa kaina wannan rayuwa? Anya bazan koma gurin su Baba Huwaila ba?" ɗaya daga cikin tsagin zuciyarta ya ce, "Idan kin koma kina da abin da zaki goge wannan mugun tabon da kike da shi?" shiru tayi ta rasa bawa kanta mafita, gabaɗaya ji tai zaman gidan Momma ya fita daga ranta, ta jima a gurin tana saƙa da warwara sannan ta taso jiki ba ƙwari ta koma ciki. Bayan kwana biyu su Indo suka koma makaranta, sai dai yanzu gabaɗaya bata sakewa saboda Lubna ta matsa mata, kodayaushe cikin faɗa mata magana take Indo ta rasa wannan dalili na tsangwamar da Lubna take mata, wannan dalilin ne yasa ko yaushe tana falo idan yamma tayi bayan ta gama karatu sai ta wuce garden ta zauna, idan ta gaji da kaɗaicin sai ta tafi gurinsu Baba Mariya tayi zamanta suyi ta hira. A yadda Indo ta lura Lubna batasan alaƙarta da Yaseer shiyasa ta fara takatsantsan dan gujewa abin da zai sa taci mata mutumci, dan ta lura rashin mutumci da wulaƙanci yafi komai sauƙi a gurin Lubna. Duk wanda ya san Indo a baya ya ganta yanzu sai yayi matuƙar mamakin irin sanyin da tayi, ta koma wata shiru-shiru mara san magana zagin wulaƙanci babu irin wanda Lubna bata yiwa Indo, sai dai ta ji ta da kunne idan ta ga maganar zata ɓata mata rai sai ta tashi ta bar mata gurin. Duk ranar da Lubna ta ga Yaseer da Indo a zaune guri ɗaya suna hira to a ranar sai tasan yadda tayi ta takalo Indo da faɗa, dan ta samu ta zage tas. A haka rayuwa ta cigaba da cuɗawa Indo har suka shafe wani lokaci tare. Wata rana suna zaune suna a falo Yaseer ya shigo, yana shiga Lubna ta kalleshi tana sauke ajiyar zuciya, ba ƙaramin kyau Yaseer yayi mata ba, tana shirin magana ya ce, "Humaira ɗauko mayafi ki rakani shopping" take annurin dake ɗauke a fuskar Lubna ya ɗauke, a fakaice Indo ta kalli Lubna murmushin mugunta tayi a cikin zuciyar, ɗan yamutsa fuska tayi ta ce, "Ya Yaseer Assignment fa gareni kuma banyi ba" Kwaɓe fuska yayi kamar ƙaramin yaro ya ce, "Minti nawa zamuyi mu dawo ba fa daɗewa zamuyi ba, Lubna kema taho mu tafi" Lubna kamar jira take ta ce, "Ok, muje kawai Yaya" Indo haushi taji ba haka ta so ba amma cikin rashin damuwa ta koma jikin kujera ta kwanta, harara ya watsa mata ya ce, "Bazaki ba ko?" Dama haka Indo take so a hankali ta miƙe kamar ranta bai so ba ta wuce ɗakinsu, acen ɗakin tana shiga Lubna ta fara yadda habaici tana faɗin, "Nan gani dai nan bari duk cusa kan mutum bazai taɓa amsa sunan ɗan danginmu bane?" Indo bata kulata ta ɗauko mayafinta ta fito daga ɗakin tana fitowa tuni Yaseer har ya shiga mota su yake jira, Lubna haushi ne ya kamata rashin kulawar da Indo tayi mata, Indo ta fito baranta Lubna ta sa mata ƙafa ta baya cikin tsautayi Indo ta zame ta faɗi, kanta ne ya bugu da bango ya fashe wani irin zafi Indo taji cikin azaba ta ƙwalla ƙara, da sauri Yaseer ya fito daga mota yana zuwa ya ɗaga hannu ya zabgawa Lubna mari. Cikin tsananin ɓacin rai ya rufeta da faɗa, "Ke wacce irin mara hankali ce, ina kallan duk abin da ya faru komai akan idona akayi yi shi, ashe haka kike ban sani ba?" Ba Lubna ba hatta Indo sai da ta tsorata da ganin yanayinta, ganin yadda jini yake fita daga goshinta yasa ya ƙarasa gurin da Indo take kwance, kanta ya tallafo yana zame ɗankwalinta da sauri ya fara ƙwalawa Momma kira, Lubna na tsaye kamar mutum-mutumi riƙe da kumatu, wani irin huci Lubna take furzarwa cikin ɓacin rai ta juya ta bar gurin, har ta je tsakiyar falo Momma ta ƙaraso gurin Yaseer tana tambayarsa abin da yake faruwa. Tun kafin Yaseer yayi magana Momma ta zaro ido ganin abin da ya faru da Indo, da sauri ta kama ta suka saka ta a mota, hijabinta ta ɗauko da sauri ta shiga motar suka wuce asibiti. Wani Private hostipital suka kaita da sauri Nurses suka shiga bata kulawar da ta kamata, ba'a ɗauki lokaci ba suka mata ɗinki a gurin suka naɗe da bandaji. Momma na gefe zaune kan kujera tana ƙarewa Indo kallo, Idonta ne ya kai kan wani baƙin tabo dake gefen kan Indo, kamar rowa haka yake me ɗan girma sai dai shi baƙiƙƙirin yake, a hankali ta furta, "Allah me iko" tana shirin magana, Yaseer dake tsaye jikin gadon Indo ya shafa gefen kansa ya ce, "Momma kin ga irin abun kanmu akan Humaira" Momma kallan kan Yaseer tayi babu ko tantama iri ɗaya ne sak, mamaki ɗauke akan fuskarta ta ce, "Ikon Allah kenan" suna cikin haka Wayar Momma ta fara ringing ɗauka tayi daga cen ɓangaren aka amsa mata, sun ɗan jima suna waya sannan suka yi sallama. Kallan Yaseer tayi ta ce, "Su Mommy suna tafe gobe idan Allah kaimu ita da Fahad" Kamar ƙaramin yaro ya buga tsalle ya ce, "Yess sooo, Allah ya kaimu goben" duk abinda yake faruwa Indo tana bacci saboda allurar baccin da akayi mata. YAU DAI NA WANKE KAINA KO NAYI TYPING DA YAWA🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈 NASAN HAR KUN GAJI DA JIRA☹️☹️ KWANA BIYU BANA ZAMA WALLAHI, NAGA ADDU'O'INKU DAGA WHATSAPP, WATTPAD ZUWA FACEBOOK. INA GDY ƘWARAI ALLAH BAR ƘAUNA MUTANEN WATTPAD HAR KUNYARKU NK JI SBD SAƘWANNINKU RUBUTUTU🙈 INA JIRAN COMMENTS✋🏻🤠🤚🏻 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [11/08, 18:15] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 55&56 Indo ba ita ta farka ba sai gabannin magriba a hankali ta buɗe idanunta, ɗan zugi taji a kanta ta ɗan runtse ido , Momma ce ta taimaka mata ta tashi zaune. Kusan tare suka dinga jera mata sannu, a hankali Indo take ansawa. Yaseer ne ya kira likita ya zo ya ƙara duddubata sannan ya rubuta mata magunguna ya basu sallama suka wuce gida. Lokacin da suka je gida a falo duk suka zube kasancewar su Baba mariya basu san da abin da ya faru ba sai a lokacin, cikin tashin hankali take tambayar Momma abinda ya faru. Momma ta ce, "Ɗazu ina ɗaki Yaseer ya kirani ina zuwa na ganta kwance..." gabaɗaya abin da Yaseer ya gaya mata shi ta sanarwa da Baba Mariya, sosai ta jimanta abin cikin zuciyarta ba ƙaramin haushin Lubna taji ba saboda ita kanta ba ƙaramin wulaƙanci Lubna take mata ba ita da jikokinta, tana cikin wannan tunanin Momma ta fara ƙwalawa Lubna kira. Ba'a ɗauki lokaci ba Lubna ta shigo falon fuska a tsuke, gefe ta samu ta zauna ta ce, "Momma gani" Momma ɓata rai tayi ta ce, "Lubna me humaira tayi miki kika yanke mata wannan hukuncin?" shiru Lubna tayi ta sunkuyar da kai ƙasa, cikin ɓacin rai Momma ta ce, "Ba magana nake miki ba Lubna me yasa kika yi mata haka?" turo baki gaba Lubna tayi ta ce, "Ban sani bane fa na taɗe ta shi ne ta faɗi" Momma ta ce, "Lubna banasan rigima ko tashin hankali yanzu ki bata haƙuri" da sauri Lubna ta juyo tana kallan Momma da mamaki ta ce, "Inbata haƙuri fa Momma? Wannan ƴar gudun hijrar zan bawa haƙu..." a hargitse Yaseer ya katseta cikin tsawa ya ce, "Keeeeeee" ba Lubna ba hatta Momma sai da ta tsorata da jin tsawar da Yaseer ya buga mata, Yaseer har huci ya ke ya nuna Lubna cikin fusata ya ce, "Ko ba yanzu ba idan na kuma jin kin ƙara ce mata ƴar gudun hijira sai na ɓata miki rai" Lubna harara ta watsawa Indo ta ce, "Ya Yaseer akan wannan abar kake yi mun tsawa ɗazu fa har mari na kayi" a zafafe Yaseer ya ce, "An mareki idan baki rufen baki ba zan tattataka ki a gurin nan" Lubna zaro ido tayi ba ƙaramin tsoro Yaseer ya bata ba, Momma ce ta ɗaga hannu ta ce, "Yaseer ya isa haka banasan hayaniya, ke Lubna banasan rashin kunya kai kuma Yaseer banasan ka ƙara shiga sabgar yaran nan" Yaseer amsawa Momma yayi sannan ya tashi ya fice yana watsawa Lubna harara. Lubna shiru tayi zuciyarta na suya saboda irin abin da Yaseer yayi mata a gaban Indo, Momma ce ta riƙe Indo ta rakata har ɗakinsu sannan ta fito, Momma na fitowa Lubna ta shiga cikin ɗakin tana shiga ta watsawa Indo harara ta ce, "Yarinya kin janyowa kanki masifa wallahi tunda kika nemi shiga rayuwa ta" Indo da har lokacin kanta zugi yake bata bi ta kan Lubna ba ta ja filo ta kwanta tana lumshe idanu. Momma tunda ta koma sashenta take safa da marwa sai kaiwa take tana komawa, abu ɗaya ne yake ta mata yawo a zuciyarta hoton wannan tabon na kan Indo shi kaɗai yake yi mata yawo a zuciyarta, wayarta ta ɗauko ta fara lalubo hotunan da ta ɗauka na Indo lokacin da take bacci. Zooming ɗin hotonta ta farayi sai tana ƙare mata kallo, kamanin Indo gizau suka fara yi mata take ta fara wani irin tunani da mamakin irin tabon gadon ƴaƴansu a jikin Indo. Da daddare suna zaune da Daddy bayan sun gama cin abinci, tun yamma abin yake cin Momma a zuciyarta. Suna tsaka da hira Momma ta ce, "Daddyn yara nikam wani abu na gani yau me ban al'ajabi" tattaro nutsuwarsa yayi ya ce, "Momman yara wane abu ne wannan?" gyara zama tayi cikin nutsuwa ta ce, "Bayan mun kai Humaira Asibiti sai a lokacin na lura wani tabo a saman goshinta irin naku" da mamaki Daddy ya ce, "Bangane irin tabon mu ba? Yi mun ƙarin bayani" wayarta ta ɗauko ta kamo hoton Indo ta ce, "Irin tabon kanku wanda kuke gada daga Alhaji Baffa" da sauri ya karɓi wayar yana ƙarewa hoton Indo kallo. Babu ko tantama irin tabonsu ne kuma a dai-dai gurin da nasu yake hatta yanayin girmansa haka na Indo yake. Mamaki abun ya bashi sosai ya ɗago ya ce, "Tabbas irin tabonmu ne sai dai bana ganin yarinyar nan daga cikinmu take, tunda munsha banban ta fannin zamantakewa. Idan kin tuna yarinyar nan ta ce mana iyayenta ɓata sukayi har Allah ya kawota garin nan, kuma kinga duk cikin ahalimu babu wanda ya rasa wani iyali daga cikinmu" jinjina kai Momma tayi ta ce, "Haka ne amma ko yaushe na kalli yarinyar nan inajin wani abu acikin raina ko dam saboda bantaɓa..." Hannunsa ya ɗora akan bakinta ya ce, "Shiiiiii banasan jin haka daga gareki, kin tuna alƙawarin da kika ɗaukar mun?" murmushi Momma tayi ta gyaɗa masa kai sannan suka cigaba da hira. Washegari tun safe su Baba mariya suke ta shirye-shirye da gyare-gyare Momma da Lubna ne suke girki ita kuma Indo Momma ta ce ta huta saboda ciwon da yake jikinta, tana kwance akan kujerar Falo wayar Momma ta fara ringing da sauri Indo ta ɗauka BLOODY Indo taga anrubuta akai da sauri ta kaiwa Momma, tana ganin number da murmushi a fuskarta ta ɗauka tana faɗin, "Mutanen Kaduna kwana biyu ansaka ni a kwandon shara" daga cen ɓangaren aka amsa mata sannan ta cigaba da cewa, "Alhamdulillah yanzu haka baƙi gareni su Mommyn Fahad ne zasu zo anjima dan sun kusa zuwa ma" Indo dake ƙoƙarin fita daga kitchen cikinta ne ya karta gabanta ya yanke ya faɗi, a sanyaye ta taka ta fice daga gurin. Gabaɗaya Indo ta rasa nutsuwarta fargabarta ɗaya kardai ace Fahad ɗin da ta sani ne zai zo da Mommy, ƙirjinta ne ya buga take tsoro ya kamata a hankali ta furta, "Na shiga uku shikenan asirina yau zai tonu, Allah ka duba ni" kai tsaye cen gurin da ta saba zuwa ta zauna yanzun ma cen ta nufa wato garden, zama tayi ita kaɗai tana tunanin rayuwa da makomarta muddin su Momma suka gano gaskiyar labarinta, hawaye ne ya ciko mata idanu ta sa hannu ta goge, ta ɗan jima a gurin sannan ra tashi ta koma cikin gida, a falo ta samu Yaseer yana ganinta ya sakar mata murmushi ya ce, "Humaira yau ina cikin farin ciki saboda yau My ciwon kai zai zo tare da Mommy" Indo murmushin yaƙe tayi ta ce, "Nima ina cikin farincikin yau dai zanga Yaya Fahad" daɗi yaji har cikin ransa ya ce, "Anya idan kika ganshi zaki gane shi kuwa? Amma bari zanyi miki suprise" murmushi tayi ta wuce cikin ɗakinta, kan gadonta ta faɗa ta rasa me yake mata daɗi a zuciyarta. BAYAN WASU AWANNI Mommy da Fahad tuni sun ƙaraso zaune suke a falon Mommy sai hira sukeyi ana dariya, kowa ya gansu yasan suna cikin farin ciki.Indo tun lokacin da taji buɗewar gate da shigowar mota tayi tsumu kamar wacce aka zarewa laka. ta shi tayi ta ɗauki litattafanta da dadduma ta nufi gurin karatunta, amma ga wanda zai ƙarewa yanayin Indo kallo zai fahimci irin tashin hankalin da take ciki, ko da aka zo yi mata lesson ɗin ba abinda take fahimta. Suna gama karatun ta wuce cen garden sai dai abu ɗaya ne ya ɗan faranta mata rai Assignment ɗin da malamin ya bata ta cinye su duka, yadda malamin yake ƙara ƙarfafa mata gwiwa ba ƙaramin birgeta yake ba, lokacin da ta ƙarasa garden zama tayi tana kallan tsuntsayen da suke gurin. Tana nan zaune sama-sama ta fara jiyo magana daga bayanta da alama waya akeyi cikin wayar taji ana cewa, "Ok, amma waɗannan kayan na riga da nayi signing akansu kar abari su fita batare da sani na ba" da sauri ta juya, hango shi tayi tana tafe yana waya abinsa hankali kwance, har ya kusa ƙarasowa gurinta sannan ya kammala wayar, tasowa tayi da murmushi ta ce, "Ya Yaseer kaga na cinye Assignment ɗin jiya kasan dai kamun alƙawarin Chocolate" ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa littafin Lesson ɗinta, watsa mata muguwar harara yayi a zafafe ya fisgi littafin ya keta shi gida biyu sannan ya watsa mata a fuska, dogon tsaki ya ja sannan ya juya ya bar gurin. Indo kamar gunki haka ta daskare agurin take gabanta ya faɗi ƙirjinta ya hau bugawa, wannan karan neman hawayen tayi ta rasa zuciyarta har ɗaci take saboda ɓacin rai, take zuciyarta ta bata wannan Fahad ne ba Yaseer ba. Tattara takardunta tayi ta wuce cikin gida daga cen bayanta taji anƙwalla mata kira, tana juyawa ta hango shi fuska ɗauke da murmushi takowa yayi ya ƙaraso ya ce, "Da naso naui fushi da ke amma zuciyaya ta azalzaloni naji ba zan iya ba, su Mommy sun zo amma ko kizo ki gaishe su" sai a lokacin Indo ta tabbatar wa da zuciya cewa lallai wancen ne Fahad, murmushin ƙarya ta ƙirƙiro ta ce, "Haba Ya Yaseer ya za'ayi naƙi zuwa na gaishe su bari nayi su huta kasan sun sha hanya suna buƙatar hutu" Hankali da sanin yakamatan Indo na matuƙar birgeshi murmushi yayi ya ce, "Eh haka ne, amma yanzu kizo muje ku naji Momma ma na tambayarki agun Lubna" gaban Indo ne ya yanke ya faɗi ta tattaro nutsuwarta ta ce, "Ok, bari na kai littafina ɗaki" sai a lokacin ya kai idanunsa kan yagaggun littafin Indo da mamaki ya ce, "Humaira ya akayi littafinki yayi haka" rasa abin cewa tayi, dabara ce ta faɗo mata ta ce, "Ina zauna a garden ƙadangare ya faɗo to garin zan gudu bansani ba na gaya littafin" gyaɗa kai yayi ya ce, "Ki dinga lura sosai, ki je ki ajiye ina jiranki" Indo wucewa tayi kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki taje ta ajiye ta dawo suka wuce ɓangaren Momma. Suna shiga kan Indo a ƙasa ta tsugunna ta gaishe da Mommy, Mommy kallanta tayi cikin murmushi ta amsa daga cen gefe Fahad ta hango yana danna waya, har ta miƙe Yaseer ya ce, "Humaira baki gaishe da Brother ɗina ba" Indo na ɗago kai suka haɗa ido da Fahad ya watsa mata harara, cikin daburburcewa ta gaisheshi kamar bazai amsa ba murya cen ciki ya amsa da, "Lafiya" Indo miƙewa zatayi Momma ta dakatar da ita da faɗin, "Ina zaki Humaira bakya ganin ga Lubna nan a zaune ki zauna mu ci abinci mana" Indo komawa tayi ta zauna banda gumi babu abin da takeyi, Lubna dake gefe sai watso mata harara take. Shiru Indo tayi su Mommy sai hira suke cikin hirar ne taji Mommy na gayawa Momma a cikin satin za'a kai kuɗin aure da sa rana na Fahad gidan su budurwarsa Rufaida, sosai Momma taji daɗi cikin farin ciki tace, "Ai ni kuwa Mommy tuwona mai na zanyi saboda Yaseer ya gayawa Daddy shi Humaira yake so idan ta gama karatu" Zaro idanu Lubna tayi cikin tashin hankali, kafin Mommy tayi magana tuni Fahad ya ce, "What? Momma kina nufin wannan abar zai aura?" Canza fuska Momma tayi ta ce, "Fahad bansan ka da wannan ɗabi'ar ba, bawa baya taɓa gujewa ƙaddararsa kasancewarta ƴar gudun hijira bazai hana mu haɗa zuri'a da ita ba" Indo gabanta sai dukan uku-uku yake, gabaɗaya tayi zuru-zuru. Fahad ne ya watsa mata wulaƙantaccen kallo ya ce, "Kiyi haƙuri Momma ba rashin kunya xanyi miki ba, amma gaskiya bana bada goyan bayan Yaseer ya auri wannan ƴar kunamar, kai ni inada shakku akan ingancin lafiyarta sabo..." cikin ƙaraji Yaseer ya ce, "Stop! Bana buƙatar ƙarajin waɗannan miyagun kalaman naka" murmushin takaici Fahad yayi ya ce, "Ok, banyi mamaki ba saboda soyayya ta rufe maka ido" Mommy sai a lokacin ta ce, "Fahad wai ko itace maganar da ka ce idan mun zo zamuyi?" Momma da kanta ya gama kullewa ta ce, "Fahad kasan wani abu akan Humaira ne?" Fahaf gyaɗa kai yayi ya ce, "Indo ake kiranta a garinsu ba Humaira ba..." ALLURA ZATA TONO GARMA🤒🤒🤒🤒 FATAN ALHERI GAREKU SAI NAJI COMMENTS🥰 WATTAP KUYI HKR SBD RASHIN REPLAY NA COMMENTS ƊINKU😉😉 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [12/08, 18:11] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ DAN GIRMAN ALLAH DUK WACCE TA KARANTA SHAFIN NAN TA BI WANNAN LINK ƊIN👇🏻👇🏻 TA DANGWALAWA *MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)* SAI KUYI *SUBMIT* SHIKENAN, DAN ALLAH KARKU BANI KUNYA MASOYA👏🏻👏🏻 https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSfU5hK-9VjsISvD_EeweRZj-ivTJBN-qNJFmVU3Y8N0uWe51g/viewform 57&58 Maganar Fahad ce tayi dai-dai da ɗagowar kan Indo, cikin tashin hankali ta kafeshi da dara-daran idanuwanta da suka kaɗa sukayi jawur. Mommy da sauri ta kalli Fahad ta ce, "Indo kuma Fahad? A ina kasan yarinyar nan ba yan ance iyayenta ba ƴan nahiyar nan tamu bane?" murmushin takaici Fahad yayi ya ce, "Ta dai yaudare ku ne da haka amma Indo shine ainihin sunan da ake kiranta" Yaseer ne ya furzar da Iska mai zafi cikin takaici ya ce, "Ka ga dan Allah karka wargaza mana gida, idan ka san babu abinda ka sani game da Humaira ka ja bakinka ka tsuke" Tamke fuska Fahad yayi zaiyi magana Momma ta ɗaga hannu tana faɗin, "Bana buƙatar hayaniya ko cecekuce, Fahad kaji tsoron Allah ka sani idan ka ɓoye mana bazaka ɓoyewa ubangijinka ba. Ka sanar da mu abin da ka sani, amma ina ƙara sanar da kai muddin na bincika naga ƙarya kake ranka zaiyi mummunan ɓaci" Fahad jinjina kai yayi ya ce, "Momma nayi tsammanin farat ɗaya ke da Mommy zaku gasgata abin da na faɗa, sai gashi na ga shakku a cikin idanuwan ku" Mommy cikin tsuke fuska ta ce, "Fahad ina tsammanin nida Momman ku babu abokin wasan ka, ƙarin bayaninka muke nema ba dogon sharhi ba" Lubna dake gefe zuciyarta fes taji cikin sigar zuga ta ce, "Ni dama wallahi tun ranar da na fara ganinta jikina ya bani bata da gaskiya munafuka mai ƙwala-ƙwalan idan..." a hargitse Yaseer ya watso mata tsawa take ta tsuke bakinta tana watsawa Indo harara. Fahad ne ya ci gaba da cewa, "Yarinyar nan sunanta Indo kuma ƴar garin Kura ce acen take zaune da iyayenta" Mommy da sauri ta ce, "Kura fa kace fahad?" Fahad gyaɗa kai yayi sannan ya ce, "Kema kin santa Mommy sai dai wataƙila baki gane ta bane, zan kira Kawu yanzu a gaban ku ya jadaddar da abinda nake faɗa muku" Fahad na gama faɗa ya ciro wayarsa ya kira lambar Maigari, kiran farko da yayi ba'a ɗauka ba sai a kira na biyu Maigari ya ɗauka bayan sun gaisa Fahad ya ce, "Kawu dama tambayarka zanyi anga yarinyar nan kuwa Indo wacce ka ce mun ta ɓata kwanaki?" Maigari ya ce, "Ina fa Fahad har kwanan gobe bamuji labarinta ba, kai tsohuwar da take riƙonta ma ta koma cikin garin Kano gurin ƴaƴanta, kasan yarinyar nan hatsabibiya ce yanzu haka tana cen ta shiga duniya tana addabar wasu, mudai tun da Allah ya rabamu da alaƙaƙai taje cen ta ƙarata" murmushin gefen baki Fahad yayi ya ce, "To Kawu an same ta" da sauri Maigari ya ce, "Kai yaron nan banasan shaƙiyanci, yau sama da wata nawa da ɓatan wannan sheɗaniyar yarinyar sai yanzu zaka ce mun an ganta" Fahad ya ce, "Kawu kasan bana maka irin wannan wasan, wallahi anganta" tattaunawa suka cigaba da yi daga ƙarshe sukayi sallama. Mommy kafe Indo tayi da kallo sosai take ganin yanayin kamar tasan kamanninta, Momma ce ta kalli Fahad ta ce, "Dan ka kira waya wannan bazai tabbatar mana da cewar ita ce wacce kuke magana akanta ba" Fahad tamke fuska yayi ya kalli Indo ya ce, "Ke ki buɗe baki kiyi magana kece Indo ko ba ke bace?" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi bata ce komai ba, buga mata tsawa Fahad yayi ya ce, "Ba magana nake miki ba?" Indo fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya. Gabaɗaya falon shiru yayi banda shashsheƙar kukan Indo babu abinda yake tashi, Lubna yatsina fuska tayi ta ɗauke kai gefe cikin zuciyarta fes kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, Yaseer jin kukan Indo yake har cikin ransa lokaci-lokaci yake furzar da iska mai huci, Momma ce tayi ƙarfin halin yin magana ta ce, "Humaira shin abinda Fahad ya faɗa gaskiya?" Indo goge hawayen Idanunta tayi ta gyaɗa kai muryarta na rawa ta furta, "Eh Momma! Gaskiya ne abin da ya faɗa" Yaseer ji yayi maganar Indo kamar saukar aradu a tsakiyar kansa, da sauri ya ɗago ya kalleta yana mata wani irin kallo mai wuyar fasaltuwa, suna haɗa ido da ita ta sunkuyar da kai tana jin babu daɗi a zuciyarta, wani irin abu ne ya tokare ta Momma cikin ɓacin rai haɗe da mamaki ta kalli Indo ta ce, "Humaira dama duk abin da kika gaya mana ƙarya kike? Yanzu a ƙananan shekarunki har kin iya tsara zance irin wannan? Meye ribarki ta barin gaban iyayenki? Kina tunanin akwai mutanen da zasu maye miki gurbinsu ne? Gaskiya kin bani mamaki" Indo rushewa tayi da wani irin matsanancin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraronta, Yaseer dukda yana cikin jin haushin haushin Indo hakan bai hanashi jin kukanta na ratsa jijiyoyin jikinsa ba, Lubna taɓe baki tayi ta ce, "Ai dama bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage bata mage, Allah ya tonu asirinki sai ki bi wani sarkin ba wannan ba" wannan karan Yaseer bai dakatar da Lubna ba saboda bashi da hujjar kare Indo, sunkuyar da kansa ƙasa yayi yana jin ɗaci a zuciyarsa. Indo sai da taci kuka mai isarta sannan ta tashi ta ƙarasa gaban Momma ta tsugunna ta ce, "Dan Allah Momma kiyi haƙuri ki yafeni akan ɓoye muku ainihin labari na da nayi, tabbas nayi kuskure amma dan Allah karkuyi mun mummunar fahimta. Babu ko tantama a maganar Fahad tabbas ni ƴar garin Kura ce kuma a cen muka taɓa haɗuwa da Fahad da Mommy lokacin da suka je gidan Maigarin garinmu, na taso a garin Kura gurin wata baiwar Allah da ta riƙeni tun ina ƙarama har na fara girma, daga baya Allah karɓi rayuwarta na koma hannun Aminiyarta da zama, sai dai inda Fahad yake tunani nan ne gidanmu sam ba mutanen gidan ne asalin mahaifa na ba..." Indo gabaɗaya ta kwashe labarinta ta basu har tahowarta garin Kano da yadda ta ƙwaci kanta agurin samarin da suka biyota, zuwa gidan Aunty da haɗuwarta da Fahad a resturent har zuwa tahowarsu garin Abuja da dalilinta na zuwa ƙofar gidansu ta zauna." Indo na rufe baki Daddyn Yaseer ya shigo jiki a sanyaye saboda yaji duk abinda Indo take faɗa, zama yayi a kan kujera Indo ta cigaba da cewa, "Tabbas nasan zamana a gidan nan yazo ƙarshe, amma ko da zan tafi zan shiga duniya ne domin naci alwashin bazan koma gurin Baba Huwaila ba har sai na nemo ainihin iyaye na, Momma da Daddy tabbas kun nuna ƙauna da hallaci agareni Allah ya saka muku da mafificin alheri, Ya Yaseer tabbas ka nuna mun kulawa ka ƙaunace ni ba zan taɓa mantawa da kai a shafin rayuwata ba, Allah ya baka wacce ta fini Ubangiji ya dauwamar da kai cikin farin ciki kamar yadda a kullin kake ƙoƙarin faranta min rai." Indo na zuwa nan ta goge hawayen Idonta ta miƙe tsaye ta ci gaba da cewa, "Na barku lafiya Allah ya sada fuskokinmu da alheri" ta ƙarasa faɗa tana tunkarar bakin ƙofa, Cikin muryar damuwa Daddy ya ce, "Dakata Humaira! Baza ki bar gidan nan ba ki shiga duniya ba, domin muddin mukayi haka Allah bazai barmu ba. Idan Allah ya kaimu gobe gabaɗayan mu zamu ɗunguma zuwa garin Kura domin nemo inda wannan Baiwar Allah ta koma a garin Kano, na tabbata a faɗin ƙauyen baza'a rasa sanin inda ta koma ba, zamu je gurinta bayan mun sameta akwai hukuncin da ya kamata mu ɗauka" Indo jiki babu ƙwari ta juyo ta ce, "Amma Daddy..." katseta yayi da, "Wuce ki tafi ɗaki banasan musu" Indo labulen ɗakin ta ɗaga ta fice wani irin kuka na taso mata, Lubna tsuke fuska tayi saboda bataji daɗin hukuncin da Daddy ya yanke ba, Daddy ne ya kalli Fahad ya ce, "Allah yayi maka Albarka Fahad Allah ya ƙara haɗa mun kanku" Mommy da Momma jiki ba ƙwari suka amsa da Ameen. Lubna tashi tayi fuuuu ta fice daga ɗakin ta nufin ɗakinsu da niyyar cashewa Indo, tana fita Yaseer yabi bayanta sannan Fahad ya mara masa baya. KUYI MANEJI SBD RASHIN CAJI *MASU TAMABAYATA LINK INSHA ALLAH GOBE DA ƘARFE TARA NA DARE ZA'A SAKI NAMU ZUWA TARAN DARE NA RANAR ASABAR, INA FATAN ZAKU BANI HAƊIN KAI TA HANYAR DANGWALA MUN VOTE, A WANNAN NE ZAN GANE ZALLAR SOYAYYAR DA KUKE YI MUN.* _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [17/08, 12:57] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 59&60 Indo tana shiga ɗakin su ta faɗa kan katifa ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, sosai take kuka tun ƙarfinta saboda wani irin zugi da raɗaɗi da zuciyarta take mata, Baba Huwaila ce ta faɗo mata take taji zaman su Yaseer ya fice mata daga ranta, tana nan kwance taji shigowar Lubna amma kasancewar halin da take ciki ya sa bata bi ta kanta ba dukda irin baƙaƙen maganganun da Lubna take gaya mata. Lubna na cikin magana Yaseer ya shigo cikin ɗakin fuska babu walwala, tana daga kwance ƙamshin turarensa ne ya bugi hancinta wanda yayi dai-dai da bugawar zuciyarta, ƙarasowa yayi daf da ita ya zuba mata manyan idanunsa wanda yayi dai-dai da ɗagowar Indo karaf suka haɗa idanu, da ƙyar ta samu sukunin janye ƙwayar idonta hawaye na ci gaba da gangarowa. Yaseer kallan tsaf ya yiwa Indo cikin wata irin murya mai ya ce, ''Humaira me yasa kikayi haka? Kinbani mamaki meyasa zaki yi mana ƙarya alhalin mun ɗaukeki zuciya ɗaya tsakaninmu da Allah? Na tsani maƙaryaci bana mu'amala da mayaudari, bantaɓa tsammanin zan samu makamancin wannan daga gareki ba, amma bamu kika yiwa ba kanki kika yiwa" yana gama maganar ya juya ya fita zuciyarsa tana suya. Lubna zuciyarta ƙal saboda farin cikin abin da Yaseer ya yiwa Indo, sai da ta leƙa ta tabbatar da Yaseer ya fita ya ƙaraso gurin Indo ta ce, "To anyi walƙiya mun ganki sai a bi wani sarkin, da ansamu guri har ana shuka iya shege ansamu gidan daɗi har anmurje ancanja kala, dole a koma ƙauye a ci gaba da cin tuwon dawa" Indo ɗagowa tayi kamar zata yiwa Lubna magana, amma sai ta ɗauke kai bata tanka mata ba. Lubna ba haka taso ba sai ta kuma cewa, "Ƴar gudun hijira ashe ƴar kwararo ce yooo ƴar kwararo mana tunda ba'asan asalin mutum ba" Indo ba ƙaramin ciwon maganar Lubna taji ba, ɗagowa tayi ta kalli Lubna murya a shaƙe ta ce, "Lubna kina yawan shiga gona ta karki bari ki take shukokin da suke ciki, a kullin ina ƙara gargaɗarki da ki kiyayeni har yanxu bakisanni ba bakisan wacece ni ba" Lubna shewa tayi harda tafa hannu ta ce, "Yooo dama ta ina zan sanki ƴar kwararo wayasan iskancin da tsohuwarki ta shuka har ta jefar da ke, tunda gudun abin kunya ne yasa ta jefar da ke a titi..."maganarta ce ta maƙale lokacin da Indo ta tsinke ta da wani irin azababben mari, kafin ta ɗago Indo ta ƙara wanke ta da mari. Hannu biyu Indo ta sa ta shaƙe wuyan Lubna ta turata jikin bango tana buga kanta da shi, idanun Lubna ne ya furfuto wani irin tari ya sarƙe ta. Dukda haka Indo bata saurarawa Lubna ba, ƙara tsaurara riƙon wuyan Lubna tayi har numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa. Sai Lubna ta galabaita Indo ta sake ta ji kake yaraf ta faɗi a wahalce tana jan numfashi da ƙyar, Indo tsugunnawa tayi kusa da Lubna da sauri Lubna ta ja baya tana haɗa hannuwanta guri ɗaya alamun roƙo, Indo bata saurare ta ba ta ce, "Tun da kika zo gidan nan ban taɓa shiga harkarki ba saboda nan gidan a Humaira nake, karki bari na zo miki a INDO SARƘA bazaki ji daɗin haɗuwarmu ba." tana gama faɗa ta koma kan katifa ta janyo fulo ta shiga tunanin rayuwa. Lubna ba ƙaramin tsorata tayi da Indo ba, abin da ya hanata guduwa rashin ƙwarin jikin da ƙarancin numfashi, tana jin ta fara daidaita ta miƙe da sauri ta fice daga ɗakin a guje, bata tsaya ko ina ba sai cen falon Momma lokacin Daddy ya koma nashi falon. A hargitse Lubna ta shiga falon tana haki hannu riƙe da wuya, tun kafin su tambayeta ta fara magana, "Momma wallahi zata kashe ni ba zan ƙara kwana a ɗakin ba wallahi kasheni zata yi" da sauri Momma ta ce, "Wace zata kashe ki" da sauri Lubna ta ce, "Humaira ce wuya na ta shaƙe mun" zaro ido sukayi suna kallan wuyan Lubna da yayi ja ga shatin hannun Indo a jiki, Yaseer ne ya shigo ya riski maganar da sukeyi ya ce, "What? Yarinyar nan tana da hankali kuwa?" Mommy ta ce, "Kafin mu yanke hukunci me ya haɗaku da ita" shiru Lubna tayi daga baya kuma ta fara kame-kame" Yaseer har ya juya zai fita Momma ta ce ya je ya kira mata Indo, hakan daɗi yayi masa saboda shima dama gurun nata zai je, yadda Lubna ta barota haka yaje ya sameta . Yana shiga daga bakin ƙofa ya ce, "Saboda ɗan uwana ya tona asirinki shine zaki huce akan ƙanwata? Kar kiga ina bata rashin gaskiya idan kukayi faɗa badan bana ƙaunarta bane, ina ƙaunar ta fiye da yadda kike tsammani saboda ita ɗin ƴar uwata ne ta jini, duk yadda kike tunanin kanki agurina baki kaita ba" Maganganun Yaseer ta yake furtawa dai-dai suke da da saukar guduma a tsakiya kan Indo, kalmar da tafi tsaya mata arai, "Ina ƙaunarta fiye da yadda kike tsammani saboda ita ɗin ƴar uwata ce ta jini, duk yadda kike tsammanin kanki a gurina baki kaita ba!" wani irin abu ne mai nauyi da ɓacin rai ne ya turniƙe zuciyarta take taji wani irin hawaye mai zafi na zuba daga idanunta, ɗauke kansa gefe yayi ya ci gaba da cewa, "Ka tashi kije Momma na san ganinki idan kin ga dama" yana kawo wa nan ya fice daga ɗakin. Indo kifewa tayi ta kuma rushewa da matsanancin kuka sai da tayi mai isarta, sannan ta fice zuwa kiran da Momma take mata. Fuskarta tayi jawura idanuwanta sun kumbura, gefe ta samu ta zaune murya a dakushe ta ce, "Momma gani" Momma ba ƙaramin tausayin Indo taji ba amma tasan duk irin laifin da Lubna zatayi mata bai kamaci ta shaƙe wuyanta ba saboda guri ne mai matuƙar hatsari, Mommy ce ta katsewa Momma tunanin da take yi ta ce, "Humaira me ya haɗaku da yayarki Lubna" Indo da zuciyarta ta gama bushewa ta ce, "Ba komai Mommy" Momma ma tambayarta tayi amma gabaɗaya babu wanda ta gayawa abin da ya faru, duk yadda sukayi da Indo sai dai tace musu babu komai, daga haka faɗa Momma tayi musu sannan ta ce su tashi su bata guri, a tsorace Lubna ta bi bayan Indo tana fargabar karta ƙara yi mata abinda tayi mata ɗazu. Indo ji take zuciyarta kamar ana hura mata wuta, tana shiga ɗakinsu hijabinta ta ɗauko ta saka ta fice daga ɓangarensu Lubna bata iya furta mata komai ba sai binta da tayi da ido, Indo kai tsaye bakin gate ta nufa tana zuwa ta buɗe kofa ta fice daga gidan, mai gadin baiyi gigin hanata ba saboda yasan matsayin Indo a gidan sai dai mamakinsa ɗaya da ya ga ta fita ita kaɗai kuma a ƙafa, tafiya take tana jefa ƙafarta ko kallan gabanta batayi saboda ɓacin rai. Har ta kusa zuwa titi taga ansha gabanta da mota ɗagowa tayi da niyyar masifa ta hango shi zaune cikin mota fuska ba walwala. Idanunsa na kallan titi ya ce, "Ki shiga mu koma gida" cikin tsiwa Indo ta ce, "Bazan koma ba" tana faɗa ta ci gaba da tafiya da sauri ya kuma shan gabanta ya ce, "Idan baki shiga ta lallami ba zaki shiga ta ƙarfin tsiy" a fusace Indo ta ce, "Idan na koma me zanyi maka? Wai me kake so dani ne ka barni na tafi mana" Fahad murmushin takaici yayi ya ce, "Alƙawari na ɗaukarwa kaina sai na kaiki har garinku badan haka ba da duk inda zaki je bazan hanaki ba, idan Lagos ki nufa bazan hanaki ba nan ne dai ƙarshen garuruwan da riƙaƙƙun ƴan duniya suke zuwa, ko ki shigo ko na ɗauke ki na saka ki" guntun tsaki Indo tayi ta ci gaba da tafiya bata tanka masa ba. Fahad fitowa yayi daga mota ya fisgi hannun Indo ya buɗe mota ya wurga a ciki kamar wata kayan wanki, shiga motar shima yayi ya bata wuta suka wuce gida, horn yake kamar zai tashi sama da sauri mai gadin ya buɗe masa suka shiga ciki, yana parking tun bai ƙarasa ba Indo ta fito fuska a tsuke, yana fitowa Yaseer yana ƙarasowa gurin ya ce, "Brother daga ina kuke?" Fahad ya nuna Indo a yatsine ya ce, "Wannan abar ce zata gudu na dawo da ita" Yaseer kallan Indo yayi cikin jin haushi ya ce, "Ashe dama haka halinki yake ban sani ba? Saboda su Momma sunyi miki faɗa shine zaki gudu, tir da wannan ɗabi'ar taki ashe Allah ya taimake da na kwasarwa kaina ƙaddara" ƙarasa kalaman Yaseer yayi daidai da ɗagowar kan Indo da wata irin murya ta ce, "ƘADDARA? Ya Yaseer ni kake kira da ƙaddara" a zafafe ya ce, "Yadda kunnenki yaji" yana gama faɗa ya juya ya koma ɓangarensa. Indo cikin ƙunan rai ta itama ta juya ta wuce sashen su. Indo saboda ɓacin rai yadda ta ga rana haka ta ga dare kwana tayi tana kuka haɗe da dana sanin zuwanta gidansu Yaseer, a ɓangaren ɗaya kuma tana jin wani irin abun game da Yaseer sai dai ta rasa gane wane irin abu ne, tabbas tana jin haushin yadda Lubna take shigewa Yaseer amma ta rasa dalili. Ƙarin takaici da haka ra faru har yana ƙara nuna mata muhimmancin Lubna a gurinsa. A daren ranar Daddy ya sanarwa da Momma akan su shirya, da safe zasu tafi garin Kura domin miƙa Indo hannun iyayenta da basu haƙuri akan tahowar da tayi ba tare da izininsu ba. Washegari da safe gabaɗaya suka shirya Indo tunda taji maganar tafiyarsu gabanta yake faɗuwa, ɗaurewa tayi tana ambaton sunan Allah a zuciyarta. Mota biyu suka ɗauka Daddy, Momma, Mommy, a mota ɗaya Fahad na driving ɗinsu, Lubna, Indo suna mota ɗaya Yaseer na Driving ɗinsu. Lubna na zaune a gaban mota sai zabga surutu take da iyayi, Yaseer ban da ummm ba abinda yake amsa mata da shi, Indo kuwa zabga tagumi tayi cikin tunani tana kallan titi. Yaseer da ya gaji da surutun Lubna parking yayi cikin tsukewar fuska ya ce, "Lubna tashi ki koma baya" turo baki tayi ta ce, "Yaya kayi haƙuri dan Allah" tsawa ya guga mata ya ce, "Ki fice ki koma baya nace ko, yarinya sai shegen surutu kamar aku fice mun" Lubna jiki ba ƙwari ta fita ta koma baya haushi fal zuciyarta, saboda wannan ba ƙaramin wulaƙanci Yaseer yayi mata ba, haka ta dinga cika tana batsewa a fakaice tana watsawa Indo harara. Tun daren ranar da zasu je Kura Mommy ta kira wayar Maigari ta sanar da shi game da zuwansu, duk wani shiri na tarbar. baƙi Maigari ya sa matansa sunyi. Bayan wasu awanni Motocin su Yaseer suka ƙarasa cikin garin su Indo, suna zuwa ƙofar gidan Maigari yaran garin suka fara dafifin zuwan kallon motar ƴan birni, Indo kallan ƙauyen nasu take tana jin wani irin farinciki a zuciyarta, hawaye ya fara gangarowa daga idanunta, juyawa tayi zata nufi hanyar gidansu da sauri Fahad ya damƙi hannunta yana watsa mata mugun kallo, bata ƙara ƙoƙarin tafiya ba suka ƙarasa cikin gidan. Shinfiɗa akayi musu a ɗakin Maigari cikin murya shi da iyalansa suka tarbi su Mommy. Bayan sun gaisa Maigari ya ƙurawa Indo ido sannan ya ce, "Amma Indo kedai anyi sheɗaniyar yarinya, kamar fitar tusa haka muka nemeki muka rasa, anya kinyiwa Baba Huwaila adalci? Ashe sheɗancinki ba iya taɓin aljanu bane?" Indo harara ta watsa Maigari ta ɗauke kai gefe. MASHA ALLAH INA GODIYA DA KULAWARKU, CAJINE BANA SAMU SHIYASA KUKA JINI SHIRU, YAU DAI NA CIKA ALƘWARAI🥺🥺🥺🥺 FATAN ALHERI GAREKU.❤️ ALHAMDULILLAH NAYI NASARAR LASHE GASA INA GDY GA ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI MASOYA BAZAKU LISSAFU BA ALLAH YA BAR ƘAUNA.❤️ INA JIRAN COMMENTS✋🏻🤠🤚🏻 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [18/08, 18:18] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 61&62 Maigari daƙuwa ya yiwa Indo ya ce, "Kinci gidanku ja'ira mara lissafi. Ashe har yanzu kina nan da wannan halin naki na rashin ɗa'a? Haka kuke zama da ita tana shuka muku tsiya? Rabona da ɗaga murya kamar haka har na manta" Mommy murmushi tayi ta ce, "Yaya ai yaran namu sai addu'a" Daddy ne yayi gyaran murya ya ce, "Yaya dama wata muhimman magana ce tafe damu kamar yadda aka fara yi maka ita a waya" Maigari gyaɗa kai yayi ya ce, "Na fihimta dangane da Sarƙa ko" Yaseer kallan Maigari yayi ya ce, "Kawu wane irin Sarƙa Humaira dai" Maigari wani kallo ya watsawa Yaseer ya ce, "Kai bana iya da wani ƙaƙalallan suna ba, ni da Sarƙa muka san Indo ba wani Humaira" Daddy ya ci gaba da cewa, "Mun zo nan gabaɗaya ne domin mu miƙa yarinyar nan hannun maruƙanta" Maigari ya ce, "Ehto! Wani hanzari ba gudu ba, ita fa wannan mariƙiyar tata ta koma birni da zama gidan ɗanta" Indo a zabure ta ɗago, tana kallon Maigari. Cikin faɗuwar gaba ta rushe ta kuka tana faɗin, "Ranka shi daɗe dan Allah ina suka koma yau na shiga uku" Maigari haushi Indo ta bashi a hassale ya ce, "Kinci ƙafar gidanku, da kina san nasu kika gudu kika barsu, kaji ja'ira mu zaki gwadawa kinibibi?" Daddy ne ya ce, "Allah ya huci zuciyarka Yaya yanzu ya za'a mu gana da ita wannan baiwar Allah?" Maigari ya ce, "Akwai wani yaro Hafizu Abokin Jamilu ne sai dai insa a kirawo shi ya yi mana jagora" Ajiyar zuciya Indo ta sauke tana jin sauƙi a zuciyarta, saboda ko ba komai ta san zatayi samu kwanciyar hankalinta ta huta da zaman gidan su Yaseer. Maigari tashi yayi ya leƙo tsaka gida ya aiki Ɗansa Saminu, sannan ya koma ya zauna. Zama sukayi gurin yayi shiru kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyaraa, bayan wani lokaci sai ga Hafizu ya dawo tare da Saminu.Sai da ya gaishe da su Daddy sannan ya ce, "Allah ya taimakeka ance kana kirana ina fatan dai ba wani laifin nayi ba?" Maigari gyara zama yayi ya ce, "Kano zakayi mana jagora gidan da Baba Huwaila ta koma, waɗannan bayin Allahn sune suka dawo da Sarƙa. Zamu kaisu su miƙata a hannunta" da sauri Hafizu ya ɗago yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, har ya kai ga Indo dake zaune cikin doguwar rigar jar atamfa ta yane kanta da jan mayafi, cikin mamaki ya bin Indo da kallo ya ce, "Ranka shi daɗe Sarƙa ce ta koma haka, Allah ya baka yawan rai karadai ace Indo yawon duniya ta shiga..." da sauri Yaseer ya buga masa tsawa ya ce, "Kai Malam ka iya bakinka kayi abin da ya kawo ka kawai" Hafizu sosa kai yayi ya ce, "Ayi haƙuri nayi mamakin yadda Sarƙa da ganɗame rana ɗaya, naga ta murje shar kamar..." Maigari ya katse shi, "Kai Hafizu ka manta a inda kake ne?" da sauri Hafizu ya ce, "Tuba nake ranka shi daɗe" shiru ne ya biyo baya Daddy ya katse shirun da, "Yaya idan ba damuwa ko zamu iya tafiya yanzu?" Maigari ya ce, "Eh zamu iya tafiya tunda ga Hafizu, kai Hafizu ina fatan baka da wani uzuri yanzu" Hafizu gyaɗa kai yayi sannan suka tashi gabaɗaya suka fito daga gidan Maigari. Su Maigari mota suka shiga gabaɗaya suka ɗunguma suka nufi hanyar Kano wajen su Baba Huwaila. BAYAN AWA ƊAYA Tiryen-tiryen haka Hafizu ya dinga kwatantawa su Daddy hanya har suka ƙarasa unguwar Hotoro, a ƙofar wani madaidaicin gida sukayi parking sannan suka firfito su Momma ne suka fara shiga cikin gidan da sallama, wata mata ce ta tarbesu wacce batafi sa'ar su Mommy ba ta musu barka da zuwa. Ɗaki ta shigar da su bayan sun gaisa Mommy ta ce, "Ba mu kaɗai bane muna tare da baƙi suna waje, munzo da wata muhimmiyar magana da so samu ace Maigidan yana nan" Matar mai suna Hajiya Usaina ta ce, "Eh yana ciki amma shiryawa yake bari ayi masa magana, amma ina fatan babu matsala saboda bangane fuskokinku ba" Momma ta ce, "Mu tafe da yarinya Humaira wacce Baba Huwaila take riƙon ta a baya, mun dawo mata da ita ne kuma mu tattana a tsakaninmu" da sauri Hajiya Usaina ta ce, "Kardai ku ce mini Indo? Kai amma yau Baba Huwaila da tayi farinciki, bari nayi mata maga..." kafin ta rufe baki taji Mai gidanta ya shigo yana magana, gaishe shi su Mommy sukayi sannan Hajiya Usaina ta sanar da su dalilin zuwan su Momma. Farinciki sosai yayi da sauri ya fita ƙofar gida wajen su Maigari yayi musu Iso zuwa babban falonsa, Hajiya Usaina fita tayi ta nufi ɗakin Baba Huwaila ta sanar mata da zuwan su Mommy, Baba Huwaila saboda sauri har kusan faɗuwa tayi. tana shiga falon ta fara dube-dube amma bata ga Indo ba, kallan Hajiya Usaina tayi ta ce, "Usaina bantaɓa zaton zakiyi mun irin wannan wasan ba, ina Indona take..." da sauri Indo ta taso ta rungume Baba Huwaila cikin shagwaɓa ta ce, "Baba Huwaila wai ni ɗin ce baki gane ba?" Baba Huwaila ɗagowa tayi tana ƙarewa Indo kallo ta ce, "Indo kece kika koma haka? Indo Allah sa ba wata rayuwa kika sauya ba kika zama uwar mata haka? Yanzu Indo dama zaki iya tafiya ki barni kullin cikin tunanin halin da kike nakeyi" Momma murmushi tayi ta ce, "Baba Huwaila ki zauna zaki samu duk bayanin da kike tambaya a gurinmu" Kafin Baba Huwaila tayi magana Alhaji ya shigo ya ce, "Yauwa ki shigo da su cikin falona muna cen gabaɗaya" yana juyawa Hajiya Usaina ta yiwa su Mommy jagora har cikin falon Alhaji, Baba Huwaila riƙe take da Indo tsam kamar wani zai kwace mata ita. Zama sukayi a karo na biyu suka ƙara gaisawa, Baba Huwaila sai a lokacin ta lura da Maigari. Gaisawa sukayi tare da tambayar mutanen garin Kura, ruwa da lemuka aka zuɓe musu kala-kala. Indo na lafe a jikin Baba Huwaila ita kuwa Lubna sai yatsina take tana watsawa Indo harara a fakaice, kamar wacce aka zabure ta da sauri Indo ta ɗago ta ce, "Baba Huwaila ina Ya Jamil?" Baba Huwaila ido ta zubawa Indo tana mamakin yadda Indo ta iya magana cikin nutsuwa, daɗi sosai taji tayi murmushi ta ce, "Yayanki Jamilu yanzu ya fita amma ba jimawa zai dawo" Indo cikin wata irin muryar shagwaɓa ta ce, "Wallahi nayi kewarsa Baba Huwaila ni kaɗai idan na zauna sai nayi ta tunaninsa, wai har yanzu yana nan da muguntar sa?" Gaban Yaseer ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, saboda yadda yaji Indo ta ambaci sunan Jamilu har ji yayi ransa na masa wani irin ɗaci" Baba Huwaila ta ce, "To Indo bakya nan wa zai zalinta dama ai iya shegensa yasa yake zalintarki, shima bayan tafiyarki baki halin da ya shiga ba" Indo zuciyarta ɗaya ta ce, "Allah sarki Ya Jamil ashe haka yake sona sosai? Wallahi har ja matsu na ganshi" Baba Huwaila ta ce, "Muna nan zaki ganshi" Yaseer fesar da iska yayi mai zafi yana sunkuyar da kai ƙasa. Daddy ne ya gabatar da kansu sannan ya sanar dasu dalilin zuwansu, da abin da suka sani akan Indo da yadda ta basu labarin tarihinta da asalin da duk abinda Baba Huwaila ta sanar da ita. Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya ce, "Lallai Allah ya taƙaita wahala kuma Addu'a tayi tasiri, mun godewa Ubangiji da yarinyar nan ta faɗa hannu na gari. Allah ya tsare ya ƙara shirya mana zuri'a, tabbas Indo tayi ƙuruciya amma mungode Allah, da Allah ya kawo lamarin cikin sauƙi. Kai kuwa Fahad Allah ya saka maka da mafificin alheri, tabbas kayi ƙoƙari kuma hakan da kayi shine dai-dai" su Daddy ba ƙaramin daɗin maganganun Alhaji suka ji ba, Baba Huwaila ce ta kalli Fahad ta ce, "Amma kuwa wannan yaro Allah ya saka maka da mafificin alheri da kayi sanadiyyar dawowar Indo ta, tabbas duk abinda Indo ta sanar da ku gaskiya ne kuma nima yanzu yan ƙara muku haska akan abin da ta sanar da ku" Baba Huwaila na zuwa nan Jamilu yayi sallama yana shigowa cikin falon. Cikin girmamawa ya gaishesu ƙur Yaseer ya kafeshi da kallo, har ya juya zai fita Baba Huwaila ta ce, "Jamilu ina zaka zo nan kaima ayi da kai man, kaga ƙanwarka Indo ta dawo" Zaro Ido Indo yayi yaja wani irin numfashi sannan ya sauke shi da ƙyar cikin wata Irin murya ya ce, "Indo ina kika tafi kika barmu" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi tana wata irin dariya sannan ta ce, "To Ya Jamil ba gani andawo dani ba" Maganar Indo har tsakiyar kansa ta riskeshi mamaki ne ƙarara bayyane akan fuskarsa jin yadda Indo take magana, wai yau har shi take cewa Yaya. Koma yayi ya zama cen jikin bango yana fuskantar Indo, A fakaice Yaseer sai watsawa Jamilu harara yake yana jin wani irin haushi a zuciyarsa. Baba Huwaila ce ta cigaba da cewa, "Tun ranar da Indo ta so tafiya nayi niyyar nuna mata wani abu da bata san da shi ba, wanda Goggo ta bani saura kwana biyu ta rasu. Ta ce mun kar insanarwa da Indo matsayinta har sai bayan Aurenta kuma a lokacin ya dace na ɗauko wannan abun na damƙa mata shi da ƙarin bayani. A lokacin da ta nunamin zata tafi na ɗauka wasa take mun saboda bata taɓa mun irin wannan maganar ba, lokacin da ta fita nayi niyyar na kiranta na miƙa mata kayan da Goggo ta bani, daga nan mu ɗunguma zuwa gidan Maigari domin mu san abinda zai aiwatar ga wanda ya tono da wannan maganar sai dai ban sameta ba" Baba huwaila janye Indo tayi daga jikinta ta ce, "Bari na je na kwaso muku kayan na saukewa kaina nauyi, saboda ban sani ba ko ina da ikon ganin lokacin auren Indo ko akasin haka, tun da daga ni babu wanda yasan da wannan kayan ko Jamilu bai san da su ba" Baba Huwaila na gama faɗa ta fice daga falon, gabaɗaya shiru sukayi banda ƙarar fanka babu abinda yake tashi a ciki. Baba Huwaila shigowa tayi hannunta ɗauke da wata baƙar leda, zama tayi ta kwance ledar ta fito da wasu ƙananan kayan harirai ta ce, "Wanaan riga da siket da kuke gani Goggo ta ce mun sune a jikin Indo lokacin da ta tsince ta, tare da wannan shawul ɗin. ajiye su tayi a gefe ta ɗauko wata ƴar mitsitsiyar azurfa ta zobe da ɗan kunne tare da abin hannu ta ci gaba da cewa, "Wannan ɗan kunne sune suke jikin kunne Indo, sai zobenta da ɗan awarwaronta." suma ajiyesu tayi a gefe ta kuma zaro wasu tsofaffun hotuna guda biyu ta ce, " Ga kuma waɗannan hotunan ta ce mun acikin pampars ɗin Indo ta same su" suma ajiyesu tayi a gefe ta ciro wata ƴar duƙunƙunanniyar takarda ta ce, "Wannan takardar itama ta ce a cikin pampars ɗinta take sai dai ta jiƙe har wasu daga cikin lambobin lambar wayar da aka rubuta sun goge" Alhaji kallan karɓar kayan yayi ya fara miƙawa Daddy, tunda Baba Huwaila ta fara fito da kayan Mommy da Momma jikinsu yayi sanyi hoton jiki Daddy ya hango da sauri ya miƙa hannu ya ce, "Alhaji bani hoton nan mu gani wa nake gani a jiki kamar hoton Khaleel" yana rufe baki Momma ta ce, "Bani Muga wannan Azurfar" Daddy na ƙarewa hoton kallo ya fara jinjina kai a fili ya furta, "Ashe harsashen da nake bai tashi a banza ba, tabbas Humaira ke jinimu ce Allah ya dawowa da Khaleel Ɗiyarsa Aisha" A KAFTA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ SHIN A HARSASHEN KU SU WAYE IYAYEN INDO A CIKI???? MU HAƊE A COMMENTS🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [18/08, 18:26] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BANYAR WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 61&62 Maigari daƙuwa ya yiwa Indo ya ce, "Kinci gidanku ja'ira mara lissafi. Ashe har yanzu kina nan da wannan halin naki na rashin ɗa'a? Haka kuke zama da ita tana shuka muku tsiya? Rabona da ɗaga murya kamar haka har na manta" Mommy murmushi tayi ta ce, "Yaya ai yaran namu sai addu'a" Daddy ne yayi gyaran murya ya ce, "Yaya dama wata muhimman magana ce tafe damu kamar yadda aka fara yi maka ita a waya" Maigari gyaɗa kai yayi ya ce, "Na fihimta dangane da Sarƙa ko" Yaseer kallan Maigari yayi ya ce, "Kawu wane irin Sarƙa Humaira dai" Maigari wani kallo ya watsawa Yaseer ya ce, "Kai bana iya da wani ƙaƙalallan suna ba, ni da Sarƙa muka san Indo ba wani Humaira" Daddy ya ci gaba da cewa, "Mun zo nan gabaɗaya ne domin mu miƙa yarinyar nan hannun maruƙanta" Maigari ya ce, "Ehto! Wani hanzari ba gudu ba, ita fa wannan mariƙiyar tata ta koma birni da zama gidan ɗanta" Indo a zabure ta ɗago, tana kallon Maigari. Cikin faɗuwar gaba ta rushe ta kuka tana faɗin, "Ranka shi daɗe dan Allah ina suka koma yau na shiga uku" Maigari haushi Indo ta bashi a hassale ya ce, "Kinci ƙafar gidanku, da kina san nasu kika gudu kika barsu, kaji ja'ira mu zaki gwadawa kinibibi?" Daddy ne ya ce, "Allah ya huci zuciyarka Yaya yanzu ya za'a mu gana da ita wannan baiwar Allah?" Maigari ya ce, "Akwai wani yaro Hafizu Abokin Jamilu ne sai dai insa a kirawo shi ya yi mana jagora" Ajiyar zuciya Indo ta sauke tana jin sauƙi a zuciyarta, saboda ko ba komai ta san zatayi samu kwanciyar hankalinta ta huta da zaman gidan su Yaseer. Maigari tashi yayi ya leƙo tsaka gida ya aiki Ɗansa Saminu, sannan ya koma ya zauna. Zama sukayi gurin yayi shiru kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyaraa, bayan wani lokaci sai ga Hafizu ya dawo tare da Saminu.Sai da ya gaishe da su Daddy sannan ya ce, "Allah ya taimakeka ance kana kirana ina fatan dai ba wani laifin nayi ba?" Maigari gyara zama yayi ya ce, "Kano zakayi mana jagora gidan da Baba Huwaila ta koma, waɗannan bayin Allahn sune suka dawo da Sarƙa. Zamu kaisu su miƙata a hannunta" da sauri Hafizu ya ɗago yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, har ya kai ga Indo dake zaune cikin doguwar rigar jar atamfa ta yane kanta da jan mayafi, cikin mamaki ya bin Indo da kallo ya ce, "Ranka shi daɗe Sarƙa ce ta koma haka, Allah ya baka yawan rai karadai ace Indo yawon duniya ta shiga..." da sauri Yaseer ya buga masa tsawa ya ce, "Kai Malam ka iya bakinka kayi abin da ya kawo ka kawai" Hafizu sosa kai yayi ya ce, "Ayi haƙuri nayi mamakin yadda Sarƙa da ganɗame rana ɗaya, naga ta murje shar kamar..." Maigari ya katse shi, "Kai Hafizu ka manta a inda kake ne?" da sauri Hafizu ya ce, "Tuba nake ranka shi daɗe" shiru ne ya biyo baya Daddy ya katse shirun da, "Yaya idan ba damuwa ko zamu iya tafiya yanzu?" Maigari ya ce, "Eh zamu iya tafiya tunda ga Hafizu, kai Hafizu ina fatan baka da wani uzuri yanzu" Hafizu gyaɗa kai yayi sannan suka tashi gabaɗaya suka fito daga gidan Maigari. Su Maigari mota suka shiga gabaɗaya suka ɗunguma suka nufi hanyar Kano wajen su Baba Huwaila. BAYAN AWA ƊAYA Tiryen-tiryen haka Hafizu ya dinga kwatantawa su Daddy hanya har suka ƙarasa unguwar Hotoro, a ƙofar wani madaidaicin gida sukayi parking sannan suka firfito su Momma ne suka fara shiga cikin gidan da sallama, wata mata ce ta tarbesu wacce batafi sa'ar su Mommy ba ta musu barka da zuwa. Ɗaki ta shigar da su bayan sun gaisa Mommy ta ce, "Ba mu kaɗai bane muna tare da baƙi suna waje, munzo da wata muhimmiyar magana da so samu ace Maigidan yana nan" Matar mai suna Hajiya Usaina ta ce, "Eh yana ciki amma shiryawa yake bari ayi masa magana, amma ina fatan babu matsala saboda bangane fuskokinku ba" Momma ta ce, "Mu tafe da yarinya Humaira wacce Baba Huwaila take riƙon ta a baya, mun dawo mata da ita ne kuma mu tattana a tsakaninmu" da sauri Hajiya Usaina ta ce, "Kardai ku ce mini Indo? Kai amma yau Baba Huwaila da tayi farinciki, bari nayi mata maga..." kafin ta rufe baki taji Mai gidanta ya shigo yana magana, gaishe shi su Mommy sukayi sannan Hajiya Usaina ta sanar da su dalilin zuwan su Momma. Farinciki sosai yayi da sauri ya fita ƙofar gida wajen su Maigari yayi musu Iso zuwa babban falonsa, Hajiya Usaina fita tayi ta nufi ɗakin Baba Huwaila ta sanar mata da zuwan su Mommy, Baba Huwaila saboda sauri har kusan faɗuwa tayi. tana shiga falon ta fara dube-dube amma bata ga Indo ba, kallan Hajiya Usaina tayi ta ce, "Usaina bantaɓa zaton zakiyi mun irin wannan wasan ba, ina Indona take..." da sauri Indo ta taso ta rungume Baba Huwaila cikin shagwaɓa ta ce, "Baba Huwaila wai ni ɗin ce baki gane ba?" Baba Huwaila ɗagowa tayi tana ƙarewa Indo kallo ta ce, "Indo kece kika koma haka? Indo Allah sa ba wata rayuwa kika sauya ba kika zama uwar mata haka? Yanzu Indo dama zaki iya tafiya ki barni kullin cikin tunanin halin da kike nakeyi" Momma murmushi tayi ta ce, "Baba Huwaila ki zauna zaki samu duk bayanin da kike tambaya a gurinmu" Kafin Baba Huwaila tayi magana Alhaji ya shigo ya ce, "Yauwa ki shigo da su cikin falona muna cen gabaɗaya" yana juyawa Hajiya Usaina ta yiwa su Mommy jagora har cikin falon Alhaji, Baba Huwaila riƙe take da Indo tsam kamar wani zai kwace mata ita. Zama sukayi a karo na biyu suka ƙara gaisawa, Baba Huwaila sai a lokacin ta lura da Maigari. Gaisawa sukayi tare da tambayar mutanen garin Kura, ruwa da lemuka aka zuɓe musu kala-kala. Indo na lafe a jikin Baba Huwaila ita kuwa Lubna sai yatsina take tana watsawa Indo harara a fakaice, kamar wacce aka zabure ta da sauri Indo ta ɗago ta ce, "Baba Huwaila ina Ya Jamil?" Baba Huwaila ido ta zubawa Indo tana mamakin yadda Indo ta iya magana cikin nutsuwa, daɗi sosai taji tayi murmushi ta ce, "Yayanki Jamilu yanzu ya fita amma ba jimawa zai dawo" Indo cikin wata irin muryar shagwaɓa ta ce, "Wallahi nayi kewarsa Baba Huwaila ni kaɗai idan na zauna sai nayi ta tunaninsa, wai har yanzu yana nan da muguntar sa?" Gaban Yaseer ba ƙaramin faɗuwa yayi ba, saboda yadda yaji Indo ta ambaci sunan Jamilu har ji yayi ransa na masa wani irin ɗaci" Baba Huwaila ta ce, "To Indo bakya nan wa zai zalinta dama ai iya shegensa yasa yake zalintarki, shima bayan tafiyarki baki halin da ya shiga ba" Indo zuciyarta ɗaya ta ce, "Allah sarki Ya Jamil ashe haka yake sona sosai? Wallahi har ja matsu na ganshi" Baba Huwaila ta ce, "Muna nan zaki ganshi" Yaseer fesar da iska yayi mai zafi yana sunkuyar da kai ƙasa. Daddy ne ya gabatar da kansu sannan ya sanar dasu dalilin zuwansu, da abin da suka sani akan Indo da yadda ta basu labarin tarihinta da asalin da duk abinda Baba Huwaila ta sanar da ita. Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya ce, "Lallai Allah ya taƙaita wahala kuma Addu'a tayi tasiri, mun godewa Ubangiji da yarinyar nan ta faɗa hannu na gari. Allah ya tsare ya ƙara shirya mana zuri'a, tabbas Indo tayi ƙuruciya amma mungode Allah, da Allah ya kawo lamarin cikin sauƙi. Kai kuwa Fahad Allah ya saka maka da mafificin alheri, tabbas kayi ƙoƙari kuma hakan da kayi shine dai-dai" su Daddy ba ƙaramin daɗin maganganun Alhaji suka ji ba, Baba Huwaila ce ta kalli Fahad ta ce, "Amma kuwa wannan yaro Allah ya saka maka da mafificin alheri da kayi sanadiyyar dawowar Indo ta, tabbas duk abinda Indo ta sanar da ku gaskiya ne kuma nima yanzu yan ƙara muku haska akan abin da ta sanar da ku" Baba Huwaila na zuwa nan Jamilu yayi sallama yana shigowa cikin falon. Cikin girmamawa ya gaishesu ƙur Yaseer ya kafeshi da kallo, har ya juya zai fita Baba Huwaila ta ce, "Jamilu ina zaka zo nan kaima ayi da kai man, kaga ƙanwarka Indo ta dawo" Zaro Ido Indo yayi yaja wani irin numfashi sannan ya sauke shi da ƙyar cikin wata Irin murya ya ce, "Indo ina kika tafi kika barmu" Indo sunkuyar da kai ƙasa tayi tana wata irin dariya sannan ta ce, "To Ya Jamil ba gani andawo dani ba" Maganar Indo har tsakiyar kansa ta riskeshi mamaki ne ƙarara bayyane akan fuskarsa jin yadda Indo take magana, wai yau har shi take cewa Yaya. Koma yayi ya zama cen jikin bango yana fuskantar Indo, A fakaice Yaseer sai watsawa Jamilu harara yake yana jin wani irin haushi a zuciyarsa. Baba Huwaila ce ta cigaba da cewa, "Tun ranar da Indo ta so tafiya nayi niyyar nuna mata wani abu da bata san da shi ba, wanda Goggo ta bani saura kwana biyu ta rasu. Ta ce mun kar insanarwa da Indo matsayinta har sai bayan Aurenta kuma a lokacin ya dace na ɗauko wannan abun na damƙa mata shi da ƙarin bayani. A lokacin da ta nunamin zata tafi na ɗauka wasa take mun saboda bata taɓa mun irin wannan maganar ba, lokacin da ta fita nayi niyyar na kiranta na miƙa mata kayan da Goggo ta bani, daga nan mu ɗunguma zuwa gidan Maigari domin mu san abinda zai aiwatar ga wanda ya tono da wannan maganar sai dai ban sameta ba" Baba huwaila janye Indo tayi daga jikinta ta ce, "Bari na je na kwaso muku kayan na saukewa kaina nauyi, saboda ban sani ba ko ina da ikon ganin lokacin auren Indo ko akasin haka, tun da daga ni babu wanda yasan da wannan kayan ko Jamilu bai san da su ba" Baba Huwaila na gama faɗa ta fice daga falon, gabaɗaya shiru sukayi banda ƙarar fanka babu abinda yake tashi a ciki. Baba Huwaila shigowa tayi hannunta ɗauke da wata baƙar leda, zama tayi ta kwance ledar ta fito da wasu ƙananan kayan harirai ta ce, "Wanaan riga da siket da kuke gani Goggo ta ce mun sune a jikin Indo lokacin da ta tsince ta, tare da wannan shawul ɗin. ajiye su tayi a gefe ta ɗauko wata ƴar mitsitsiyar azurfa ta zobe da ɗan kunne tare da abin hannu ta ci gaba da cewa, "Wannan ɗan kunne sune suke jikin kunne Indo, sai zobenta da ɗan awarwaronta." suma ajiyesu tayi a gefe ta kuma zaro wasu tsofaffun hotuna guda biyu ta ce, " Ga kuma waɗannan hotunan ta ce mun acikin pampars ɗin Indo ta same su" suma ajiyesu tayi a gefe ta ciro wata ƴar duƙunƙunanniyar takarda ta ce, "Wannan takardar itama ta ce a cikin pampars ɗinta take sai dai ta jiƙe har wasu daga cikin lambobin lambar wayar da aka rubuta sun goge" Alhaji kallan karɓar kayan yayi ya fara miƙawa Daddy, tunda Baba Huwaila ta fara fito da kayan Mommy da Momma jikinsu yayi sanyi hoton jiki Daddy ya hango da sauri ya miƙa hannu ya ce, "Alhaji bani hoton nan mu gani wa nake gani a jiki kamar hoton Khaleel" yana rufe baki Momma ta ce, "Bani Muga wannan Azurfar" Daddy na ƙarewa hoton kallo ya fara jinjina kai a fili ya furta, "Ashe harsashen da nake bai tashi a banza ba, tabbas Humaira ke jinimu ce Allah ya dawowa da Khaleel Ɗiyarsa Aisha" A KAFTA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ SHIN A HARSASHEN KU SU WAYE IYAYEN INDO A CIKI???? MU HAƊE A COMMENTS🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ƊAN ƊANO DAGA LITTAFIN SIRRIN MU* Yadda kake tunanin rayuwa ba haka take ba,da lokota da dama kana iya gane SIRRIN wasu, Amma wani lokaci naka SIRRIN dake bibiyar Rayuwarka wahalar gane masa kake,Yau Uban daya haifesa ya kawosa Duniya shine da gansa ya masa sharri,Shi ne ya saka za'a kai shi gidan yari,Matar da yafi so fiye da komai nasa,wacce ta zame masa Uwa,Uba,Yaya,Ƙanwa,Aboki yau itace Mahaifinsa ya kwanta da ita har ta ɗauki cikinsa,Kuma yanzu shine ake cewa shi yay mata CIKIN,da me zaiji? Da nakasar da take damunsa?ko kuma da BAƘON YANAYIN daya tunkaro sa?Wannan SIRRIN MU ne bai kamata ace kowa ya jishi ba,SIRRIN MU ne nida mahaifi na,SIRRIN MU ne nida Matar da nakeso, SIRRIN MU ni da Aljanun da suke tare da ita. _JAMA'A WANNAN MARUBUCIYAR CE DAI WACCE TA NISHAƊANTAR DAKU A LITTAFIN *MOON* DA *UNCLE NE* GA KUMA *THE NEW EMIR* SBD NIN DAƊIN MASOYA YASA SAI TA GAMA PART ONE ZATA FARA SAKINSA WANDA ZATA NA BAWA ƳAN *VIP* POSTING 2 KULLUM A RANA ƳAN *NRML GRP* KUMA POSTING ƊAYA A RANA NASAN KUSAN *NIMCYLUV* TAURARUWAR MARUBUCIYA MAI TASHE😂 ZAKU IYA PAYMENT TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0116886423 Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 400 for nrml grp 600 for vip Nima AMEERA ADAM na shiryar tsaf domin karanta littafin *SIRRIN MU* [19/08, 18:53] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 63&64 Gabaɗaya kallo ne ya koma kan Daddy, da mamaki su Baba Huwaika suka bi shi da kallo, Alhaji na shirin magana Baba Huwaila ta ce, "Kai yaro kada kamun alaye, ban fahimci ƴar Khaleel ba?" Momma ta ɗago ta ce, "Allahu Akbar kabiran tabbas Safna ta samu labarin nan yau ko bacci bazata iya runtsawa ba, dama tun da na ga taɓon dake kanki Humaira nake ta wasu wasi a zuciyata, ashe ke ɗin jinina ce" Da mamaki Fahad ya ce, "Momma wai me yake faruwa ne kun sa mu a duhu? Wai kuna nufin Aishan Aunty Safna dai tamu wacce a ka sace?" Daddy ya ce, "Ƙwarai kuwa Ya zama dole na tunasar da ku alaƙarmu da Humaira idan kun manta" Indo dake kwance akan cinyar Baba Huwaila ta taso tana bin su Momma da kallo, Momma ware mata hannu tayi ta ce, "Zo Humaira ta" sororo tayi kamar bazata tashi ba, amma sai ta yunƙura da kyar ta ƙarasa gurin Momma da sauri Momma ta rungumota tana fashewa da kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta ce, "Gabaɗayan mu babu wanda baiji ɓatanki ba Humaira, ashe Allah zai ƙara sada fuskokinmu" sai a lokacin Mommy ta ce, "Tun ranar da na fara tozali da ke naji wani yanayi a jikina, tabbas ina ganinki sai da gaba na ya faɗi kuma tashin farko Safna ce ta faɗo mun, saboda wasu abubuwa da na gani masu fasalin na Safna" Alhaji ɗan gidan Baba Huwaila yayi gyaran murya ya ce, "Alhamdullahi ga dukkan alamu faɗuwa ce tazo dai-dai da zama, amma har yanzu kanmu a cikin duhu yake muna buƙatar ƙarin haske, kuma bazamu gasgata abin da kuke faɗa ba dole sai munyi arba da su waɗannan mutanen da kuke magana akai" murmushi Daddy yayi ya ce, "Alhaji kenan! Ai da zamu riƙe Humaira to da bamu tako tun da garin Abuja mun kawo ta ba, kuma ko da acen muka gano cewar Humaira ƴar mu ce to zamu zo nan, domin karamcin ku agurinmu bazai taɓa musaltuwa ba" Baba Huwaila ta ce, "Nikam har yanzu ban gama gasgata maganar ku ba, kawai dai so kuke ku raba ni da Indo" Baba Huwaila na zuwa nan ta rushe da kuka tana faɗin, "Allah ya jiƙanki Goggo, mutuniyar ƙwarai, ta ƙaunaci Indo fiye da tunanin mai tunani. Ta gaya mun babu irin bincike da cigiyar da bata kai ba, amma ba'a samu mutum ɗaya da ya ce ya san ko da makamancin Indo ba. Ta sha tsangwama da ƙyara kala-kala Maigari kai ne shaida, ina ce har sai da ka sanya doka akan Indo sannan lamarin ya daidaita, amma rana ɗaya ku ce mun wai Indo ƴar ku kai jama'a, ina murna Indo na ta dawo kuke neman rabani da ita." Momma tausayin Baba Huwaila tayi saboda ga daga maganganunta zaka fahimci irin ƙaunar da take yi wa Indo, kuma ko ita da bata wani daɗe da Indo ba sai da taji babu daɗi lokacin da suka ɗauko hanyar dawowa da ita ga mariƙanta,bare kuma Baba Huwaila da suka kwana biyu da Indo. Momma kallan Baba Huwaila tayi ta fara mata bayani a nutse. "Baba Huwaila ita wannan Safna da kika ji muna maganar ta Ƙanwata ce ita take bi na uwar mu ɗaya ubanmu ɗaya, ni na riƙeta da hannuna har muka aurar da ita, duba da yanayin da kike ciki ba lallai ki amince da abin da na faɗa ba, amma akwai hotunanta a wayata idan kina buƙatar gani sai ki duba ki gani da ta jikin wannan hoton da kika bamu" Daddy ya ce, "Baba Huwaila Shi wannan Khaleel da muke magana, Ƙanina ne uwar mu ɗaya Ubanmu ɗaya kamar yadda kika ji Momman yara ta faɗa nima ahannuna na riƙeshi, kasancewar tare muka riƙesu har suka shaƙu suka fara soyayya, bayan sun haɗa kansu aka tsaida magana mukayi musu aure, amma ki yarda da mu baza mu ƙirƙiri abinda va haka bane" Baba Huwaila jikinta ne yayi sanyi, cikin sanyin murya ta ce, "Idan kuwa haka ne nafi kowa murna da bayyanar Iyayenki Indo, Allah na gode maka aikuwa har garin Kura sai naje, ki nuna mun waɗanda suka yi miki gorin iyaye." Shiru Baba Huwaila tayi sannan ta ci gaba da cewa, "Sai dai nasan ba lallai su bar min ke ba Indo,hakan kuwa ba ƙaramin ciwo zai mun ba" Yatsuna fuska Fahad ya yi ya ce, "Daddy nifa gaskiya ina da ja ya za'ayi a ce Aunty Safna ce ta haifi wannan abar, yarinya kamar ƙanwar Ifritu..." Mommy ce ta watsa masa daƙuwa tana katse shi ta ce, "Gidan ku Fahad wai me yarinyar nan tayi maka ka tsangwameta haka ne? Zan ɓata maka rai idan na kuma jin bakinka" taɓe baki yayi yana ɗauke kai gefe Indo ɗagowa tayi ta ce masa, "Idan ni ƙanwar Ifritu ce sai dai idan kaine Ifritun" Yaseer binta yayi da kallo ganin yadda take kwaɓe baki kamar ba ita ba, uwa uba mamakin tsiwarta yake. Aikuwa kamar ta watsawa Fahad ruwan zafi a hassale ya ce, "Mommy kunji ko wallahi kika bari na kama kinsai na karyaki biyu" Indo miƙewa tayi ta koma ce lungu kusa da Baba Huwaila tana watsa masa harara ta kalli Jamilu ta ce, "Ya Jamil wallahi ka ja maka kunne, ya kuma cewa zai karyani wallahi sai na kuma sa masa mage a riga, matsoracin mage" Su Daddy dariya suka saka Mommy ta ce, "Humaira ya akayi kikasan Fahad na tsoron mage naga gidan Moma babu mage" wata dariya Indo ta bushe da ita sannan ta ce, "Lokacin da kuka zo Kura ranar da zaku tafi nina haɗa masa tarko da gafiya Mage ta maƙale masa a wuya" gabaɗaya ɗakin babu wanda bai sa dariya ba banda Yaseer da yake cika yana batsewa, Maigari murmushi yayi yana riƙe baki ya kalli Indo ya ce, "Sarƙa amma dai ke anyi shakiyyar yarinyar ashe baƙo ma baki bari ba, wallahi lokacin da kika tafi kunne na shiru da kawo ƙara" Jamilu ne ya kalli Fahad da ya tamke fuska saboda abinda Indo ta faɗa ya ce, "Kabi a sannu nasan har yanzu baka san wace Indo ba, ina baka shawara karka shiga harkar ta bana shiri da duk wani mai shiga sabgarta dan ya takura mata" Lubna da ke gefe wani yawu ta haɗiya musamman da ta tuno shaƙar da ta yi mata a ɗakinsu, sai dai wani abu da ya tsaye mata arasa wacce za'a ce ƴar Uncle Khaleel ce sai wannan banzar yarinyar? A fakaice take kallan Indo tana watsa mata harara, tana jan ƙwafa ƙasa-ƙasa. Momma ce ta ciro waya Daddy ya kalleta ya ce, "Me zaki yi?" Momma ta ce, "Zan kira Safna nayi mata albishir" girgiza kai Daddy yayi ya ce, "Karki gaya mata, kawai ki ce mata daga Kano zamu biyo ta Kaduna mu gaisa da su" Momma amsa masa tayi sannan ta kira wayar Mahaifiyar Indo, daga cen ɓangaren aka ɗauka da sallama. Bayan sun gaisa Momma ta ce, "Idan mun gama da Kano zamu biyo ta Nan Kaduna mu gaisa" cikin murna ta amsa mata sannan sukayi sallama. Bayan Momma ta gama waya Daddy ne ya kalli Alhaji ya ce, "Alhaji idan babu damuwa ko zamu zo mu wuce saboda yanayin gari kar lokaci ya ƙure mana" Alhaji ya ce, "Amma da ku bari ku ci abinci mana" Momma cikin zumuɗi ta ce, "Ai mun riga da munci a gidan Yaya" Daddy ya ce , "Alhaju bamu da yunwa amincewar ku kawai muje jira." Alhaji ya kalli Baba Huwaila ya ce, "Baba zaki bimu ko mu je mu dawo" Baba Huwaila tayi karaf ta ce, "Haba Ɗan nan yanzu ko cewa nayi bazani ba ai ka tursasani, ai ƙafara ƙafar Indo" gabaɗaya Falon aka kwashe da dariya. Su Baba Huwaila shiryawa sukayi sannan suka ɗunguma suka ɗauki hanyar Kaduna, Alhaji ne ya ɗauki Baba Huwaila da Indo sai Jamilu, baƙin cikin duniya ne ya cunkushe Yaseer, saboda ya ɗauka Indo motar sa zata ƙara shiga. Har buɗe mata ƙofa yayi amma tayi wucewarta ko kallan gurinsa batayi ba. Lubna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta wuce ta buɗe gaban motar ta shige, Yaseer tun da suka tafi yake tsaki itama Lubna ganin yanayinsa babu walwala yasa taja bakinta ta tsuke, dan ta san gab yake da ya sauke mata kwandon masifa a kanta. Daddy tun a hanya ya ja kunnensu akan koda sun je abi komai a sannu banda garaje dan so yake yayiwa su Aunty Safna suprise. BAYAN WASU AWANNI Suka ƙarasa cikin garin Kaduna, a katafaran wani ƙofar gida suka tsaya suna Horn. Ba'a ɗauki lokaci ba Maigadi ya leƙo ganin Daddy yasa ya buɗe ƙofar da sauri yana musu sannu da zuwa, Su Baba Huwaila sai bin gidan suke da kallo, kallan Jamilu tayi ta ce, "Jamilu anya mutanen nan ba yaudarar mu sukayi ba dan su kawo kawunan mu nan gidan ba, gaskiya akwai lauje cikin naɗi wannan gida kamar ba a ƙasar nan ba" Indo dariya tayi ta ce, "Baba Huwaila wallahi bazasu sayar da mu ba, gidan su Momma ma fa haka yake baki ganshi ba me kyau" Alhaji ya ce, "Haba Baba Huwila da ganin mutanen nan nagari ne bazasu aikata haka ba, ko da yanayin shigar su kika lura ai kinga masu aiziƙi ne." Jamilu watsawa Indo Idanunsa yayi yana mata murmuahi, wani irin nauyinsa ta ji. Take ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da zaren mayafinta, tuni sun shiga cikin gidan Jamilu bai sani ba. Sai da Alhaji ya ce,"To ku fita muje" yana gama faɗa ya buɗe ƙofar ya fita, sannan Baba Huwaila ta buɗe ta taka da ƙyar ta fita saboda yadda ƙafarta ta mata tsami, Indo na ƙoƙarin fita Jamilu ya ce, "Ayusher!" Indo dakatawa tayi ta ɗan waiga dan ganin ko akwai wacce Jamilu yake wa magana, amma bata ga kowa ba. Sai dai maganar sa ta ratsa har jinin jikinta saboda yadda ta ji muryarsa ba haka ya saba magana ba, sunkuyar da kai Indo tayi ta ce, "Ya Jamil dani kake magana?" Jamilu shiru yayi yana kallan Indo, jin yayi shiru ya sa Indo ta ɗago da kai, karaf suka haɗa ido ya sakar mata wani malalacin murmushi. Sannan ya ce, "Ayusher shi ne kika tafi kika barni, bakiyi tunanin zan iya shiga damuwa ba?" Indo ɗagowa tayi tana mamakin jin kalaman Jamilu, sannan ta sunkuyar da kai ta ce, "To Ya Jamil ai gashi na dawo" Jamilu murya a sanyaye ya ce, "Ba gashi zaki ƙara tafiya ki barni ba, kinsan yadda nayi kewarki kuwa?" Indo zuciyar ta ɗaya ta ce, "Ya Jamil dama kana sona amma kake dukana?" Jamilu ya kwaikwayi muryar ta ya ce, "Bakiji bahaushe me yace ba, kaza na taka ɗanta ba dan bata sanshi ba..." Indo na shirin magana Jamilu ya ɗan tsuke fuska ya ce, "Wai ya kuke da waɗancen samarin naga suna min wani gani-gani" Indo zata buɗe baki tayi magana suka ga Yaseer ya tsaya ta bakin murfin motar, fuska a tsuke ya zuro kai ya ce, "Ke Humaira ki fito mu ƙarasa ciki" Indo yunƙurawa tayi zata fita Jamilu ya tsuke fuska ya ce, "Ayusher! Na baki umarnin tafiya ne? Indo komawa tayi ta zauna. Cikin jin haushi Yaseer ya ce, "What? Kai wai kai waye ne naga sai wani zaƙewa Humaira kake?" 🤗🤗🤗🤗 LAMARIN ZAI FARA ƊAUKAN HAZO FA🧐🧐🧐🧐🧐 KUYI HAKURI DA RASHIN REPLAY NA COMMENTS ƊINKU ARADU DUK NABI NA GANI INA GDY😘😘😘😘😘😘😘 ALLAH YA BAR ƘAUNA🥰🥰🥰🥰🥰 MU HAƊE A COMMENTS. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 *ƊAN ƊANO DAGA LITTAFIN SIRRIN MU* Yadda kake tunanin rayuwa ba haka take ba,da lokota da dama kana iya gane SIRRIN wasu, Amma wani lokaci naka SIRRIN dake bibiyar Rayuwarka wahalar gane masa kake,Yau Uban daya haifesa ya kawosa Duniya shine da gansa ya masa sharri,Shi ne ya saka za'a kai shi gidan yari,Matar da yafi so fiye da komai nasa,wacce ta zame masa Uwa,Uba,Yaya,Ƙanwa,Aboki yau itace Mahaifinsa ya kwanta da ita har ta ɗauki cikinsa,Kuma yanzu shine ake cewa shi yay mata CIKIN,da me zaiji? Da nakasar da take damunsa?ko kuma da BAƘON YANAYIN daya tunkaro sa?Wannan SIRRIN MU ne bai kamata ace kowa ya jishi ba,SIRRIN MU ne nida mahaifi na,SIRRIN MU ne nida Matar da nakeso, SIRRIN MU ni da Aljanun da suke tare da ita. _JAMA'A WANNAN MARUBUCIYAR CE DAI WACCE TA NISHAƊANTAR DAKU A LITTAFIN *MOON* DA *UNCLE NE* GA KUMA *THE NEW EMIR* SBD NIN DAƊIN MASOYA YASA SAI TA GAMA PART ONE ZATA FARA SAKINSA WANDA ZATA NA BAWA ƳAN *VIP* POSTING 2 KULLUM A RANA ƳAN *NRML GRP* KUMA POSTING ƊAYA A RANA NASAN KUSAN *NIMCYLUV* TAURARUWAR MARUBUCIYA MAI TASHE😂 ZAKU IYA PAYMENT TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 0116886423 Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 400 for nrml grp 600 for vip Nima AMEERA ADAM na shiryar tsaf domin karanta littafin *SIRRIN MU* [20/08, 19:44] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 65&66 Jamilu furzar da iska mai zafi yayi sannan ya watsa masa manyan idanunsa ya ce, "Kai wane naka dalilin har zaka tsare ni da tambaya?" Yaseer gani yake kamar ma Jamilu ya raina masa hankali, be ƙara bi ta kan Jamilu ba. A karo na farko riƙe hannun Indo yayi ya ce, "Muje Humaira karki ɓata mun rai" wani irin yar taji amma sai ta maze, ba yadda ta iya haka ta bi Yaseer ta fito daga cikin motar. Haushi ne ya turniƙe Jamilu ya yunƙura da ƙyar zuciyarsa na zafi ya fito. Fitowar Indo yayi dai-dai da ƙarasowar Fahad lokacin su Momma tuni sunyi gaba, Kallan Hannun Yaseer yayi ya ganshi saƙale da na Indo, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke fuska a tsuke ya ƙara gurinsu, bai bi ta kan kowa ba ya sa hannuwa biyu yana zare hannuwan Yaseer dana Indo, da mamaki Yaseer ya bishi da kallo ya ce, "Brother meye haka" Fahad juyowa yayi lokacin idanunsa sun rine jawur, wani yawu mai ɗaci ya haɗiye sannan ya juya hannunsa riƙe dana ta.Da sauri Indo ta yunƙura zata cire fusge hannunta ji tayi ya riƙe katamau, cikin muryar ta ta ce, "Wai meye haka ne ka wani riƙemun hannu?" Watsa mata dara-daran idanunsa yayi ya ɗauke kai, cen har lamubu ya bi da ita, a jikin bango ya jingina ta ɗan yatsa ya sa ya nuna ta sannan ya ce, "Kar inƙara ganin kin shigewa ɗan uwana! Ina fatan kin jini, Saboda banasan ki ɓatamin ɗan uwan" yana gama faɗa ya wuya yayi gaba, ai kuwa da sauri Indo ta sha gabansa tana faɗin, "Kambun ubancen! Wallahi bazaka faɗa mun baƙa ka wuce haka nan ba, ni kake cewa zan ɓata maka ɗan uwa? To daga yau wallahi kace masa ya fita harkata" ta nuna shi da ɗan yatsa tana murza su sannan ta ci gaba da cewa, "Idan ba haka ba wallahi sai ya gane kurensa" Murmushi yayi ya fara latsa wayarsa, sannan ya nuna mata ya ce, "Kina nufin kin manta wannan rayuwar da kika yi" Indo zaro ido tayi ganin bidiyon ta da Honourable a resturent sai dariya take, shi ɗinma dariya yake sai dai bata kai ga jin me Honourable zai faɗa ba Fahad ya ce, "Oh! na tayar miki da tsohon tsumi ko? To ai..." Muryar Yaseer suka tsinta cikin ɓacin rai ya ce, "Fahad wau meye kake yi haka ne? Ka janyo yarinya nan gurin su Momma na jiranmu" hawaye ya gani shaɓe-shaɓe a fuskar Indo, da sauri ya ƙaraso yana huci ya ce, "Me kayi mata? Nace kayi mata?" duk a hargitse yake tambayar Fahad. Fahad murmushin gefen baki yayi cikin isa ya ce, "Idan wani abu nayi mata zaka rama mata ne?" Yaseer wani hargitsatstsen kallo ya watsawa Fahad cikin kausashshiyar murya ya ce, "Ka dinga gyara kalamanka fa akan Humaira zan iya yin komai" yana gama faɗa ya sa hannu a aljihu ya ciro Handkee ya miƙa mata, wani banzan kallo ta watsa masa ta juya da gallawa Fahad harara ta wuce abinta, sororo Yaseer yayi ya juya yana yiwa Fahad kallon tuhu sannan ya ce, "Me ka gayawa yarinyar nan akaina?" ɗaga kafaɗa Fahad yayi cikin halin ko'inkula ya ce, "Ka binciki kanka idan kana da wasu munanan halaye to su na sanar mata" yana gama faɗa ya wuce ya barshi a tsaye. Indo na fita taci karo da Jamilu ya kawo kai, da sauri ya ce, "Ayusher me yayi miki?" Girgiza kai tayi ta ce, "Babu komai" badan ya yarda ba ya nuna mata kamar ya amince, cen hanyar da yaga su Mommy sunyi cen suka nufa, kafin su ƙarasa Daddy ne ya fito yana faɗin, "Yaran nan wai ina suka shiga ne?" yana rufe baki yaga tahowarsu gabaɗaya.Bayansa suka bi sannan suka ƙarasa katafaren falon. Wata Farar mata suka hango zaune kusa da maigidanta, ko ba'a faɗa maka ba kana ganinsa kaga daddy zaka fahimci ƴan uwan juna ne, matar bata fi shekara talatin da bakwai ba. Fuskar ta ɗauke da murmushi ta tarbe su, Indo bin matar tayi da Kallo har ta ƙarasa kusa da Baba Huwaila ta zauna, Daddy ne ya kalli Aunty Safna ya ce, "Safna yau nazo miki da wani abu mai girman gaske" da zumuɗi Alhaji Khaleel ya ce, "Na me fa Yaya?" Aunty safna ta ce, "Amma Yaya kafin wannan dan Allah a ina kuka samo ƴar beauty haka, ga kuma Baba baku min bayaninsu ba" KUYI MANAGE ƘARFIN HALI NAI KAWAI NAYI TYPING SBD YAU NAYI BUSY WALLAHI _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [26/08, 16:13] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 67&68 Daddy Murmushi ya yi ya ce, "Safna zumuɗin me kike yi? Ai duk gaggawar asara ta jirayi samu ko?" dariya duka mutanen falon sukayi banda Jamilu, Yaseer da Fahad da suke watsawa junansu harara a fakaice. Daddy ne ya ci gaba da cewa, "Khaleel yau shekara nawa kenan da haihuwar ƴarka Aisha?" Alhaji Khaleel yanayinsa ne ya sauya cikin sigar damuwa. Murya a raunane ya ce, "Yaya nayi matuƙar mamaki da jin wannan tambayar taka" yana rufe baki Aunty Safna ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kukan ta yake ji har cikin ransa, saboda kowacce uwa dole zuciyarta ta sosu a duk lokacin da aka ambaci ɗiyarta wacce rasa, musamman idan ba mutuwa bace wani sanadi ne na daban. A raunane Alhaji Khaleel ya runtse idanunsa shima kamar zai zubar da ƙwalla ya ce, "Yaya wannan maganar da kayi mana kamar ka famo mana da tsohon gyambon da yake damun mu a zuciyar mu, ka gafarce ni Yaya idan maganar nan bata da wani muhimmanci muyi haƙuri mu barta, amma kayi haƙuri idan maganganuna sunyi tsauri." ya ƙarasa maganar idanunsa na cikowa da ƙwalla. Gabaɗaya mutanen falon babu wanda bai tausaya musu ba duba da yanayin da suka ga ma'auratan sun shiga, bisa tambayar da akayi musu. Jamilu cikin zuciyarsa yake faɗin, "Tabbas labarin Humaira tafe yake da sarƙaƙiya da tausayawa, ga dukkan alamu an zalinci waɗannan bayin Allah." Daddy ne ya kalli ɗan uwan nasa ba ƙaramin tausayin su yaji ba, amma sai ya danne ya tsuke fuska ya ce, "Khaleel ban tsammani haka daga gareka ba, na ɗauka zaka iya amsa mini tambaya ta, shin zan sami amsar tambayar ta ko kowa?"Alhaji Khaleel russunar da kai ya yi cikin girmamawa ya ce, "Yaya dan Allah kayi haƙuri. Wallahi a duk lokacin da aka ambaci Ƴar mu Aisha sai inkasa controlling ɗin kaina, amma banyi haka saboda wata manufa ba." Murmushi Daddy ya yi ya yana ƙarajin ƙaunar ɗan uwana nasa a zuciyarsa, saboda irin biyayyar da yake masa kamar shi ya haifeshi, kallan Alhaji Khaleel ya yi ya gyaɗa masa kai sannan ya ci gaba da cewa. " Yaya ina tunanin yau dai shekara goma sha shida da haiihuwarta ." Daddy ya gyaɗa kai ya ce, "Ko ka riƙe watannin ta lokacin da muka rasa ta?" Ɗan jim ya yi yana nazari Aunty Safna murya a ɗan dakushe ta ce, "Yaya ko wata biyu bata cika ba. Muna yin arba'in da kwana biyar ne." tana rufe baki hawaye ya ƙara ziraro mata. Alhaji Khaleel ya gyaɗa kai ya ce, "E h tabbas haka ne" Daddy Jakar da ke hannun Momma ya karɓa ya zaro azurfar Indo tare da kayan da aka tsince ta haɗe da wannan tsohon hoton da aka saka mata a pampers. ɗaga musu ya yi ya ce, "A cikin ku ko akwai wanda zai gane waɗannan kayan?" Alhaji Khaleel a zabure ya miƙe, Aunty Safna ma tashi tayi tsaye bakinta na rawa ta fara nuna kayan tana faɗin, "Ka...ka...kayan...Aisha..." bata ƙarasa magana ba ta yanke jiki ta faɗi a gurin. Da sauri su Momma suka yo kanta tare da Maigidanta, Daddy ne ya bata umarni a ɗebo ruwa a zuba mata, ba musu Fahad ya tashi ya ɗebo ruwa aka yayyafa mata. A hankali ta fara buɗe idanunta, jiki babu kwari ta yunƙura ta tashi zaune. Idanunta ne suka ci gaba da zubar da hawaye ta ce, "Yaya dan Allah a ina kuka samo waɗannan kayan? Tabbas nasan akwai babban al'amari dangane da zuwan nan na ku." Daddy ya ce, "Tabbas Safna akwai babban al'amari, kamar yadda kika yi tsammani. Kinga waccen yarinyar?" ya ƙarasa faɗa yana nuna Indo, da ke zaune cen kusa da Baba Huwaila. Sai raba ido take kamar shege a rabon gado. cikin zumuɗu suka amsa masa, Daddy ya ci gaba da cewa, "Allah cikin ikon sa ya bayyana muku ita. A lokacin da kuka cire tsammani da sake sata a cikin idanun ku..." a hanzarce suka katse shi da faɗin, "Yaya kana nufin waccen ƴarmu Aisha ce?" Dadday murmushi ya yi ya ce, "A iya zama na da ku ban taɓa muku irin wannan wasan ba, dan haka yanzu ba wasa nake muku ba tabbas Humaira ƴar ku ce." tun bai ƙarasa rufe baki ba Aunty Safna ta tashi ta ƙarasa gurin Indo. Rungume ta tayi sosai a jikin ta kamar wani zai ƙwace ta, ta rushe da wani irin matsanancin kukan. Duk dakiya da taurin zuciya irinta Indo sai da ta zubda hawaye. Haka su ma mutanen falon gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi tausayin su gabaɗaya ya kama su, Mai gari sai a lokacin ya yi dariya ya ce, "Ja'ira Sarƙa ƴar nema ji yadda tayi luff, kamar kwailar mage" Maigari dariya ya basu sosai saboda dama ahi mutum ne mai barkwanci. Sai a lokacin Alhaji Khaleel ya ƙaraso ya riƙo kafaɗar Indo, ya riƙota suka koma kan kujera. Indo sai raba ido take tana sunne kai kamar mutuniyar kirki. Lubna sai harara take watsawa Indo a fakaice, Gabaɗaya zuciyar ta a dagule take saboda baƙin cikin ta ɗaya ace wai kusan matsayinsu ɗaya, lokaci-lokaci take furzar da iska tana ƙissima abubuwa acikin zuciyarta. Alhaji Khaleel ɗaga hannuwa sama ya yi ya ce, "Ya Ubangijin sammai da ƙassai ina godiya da ka nuna mini wannan ranar. Tabbas lamarin Ubangiji daban yake, na jima da fidda ran ganin wannan ranar, sai gashi Ubangiji ya nuna ƙudurarsa. Allah na gode maka, Allah mun gode maka da ka bamu ikon cinye jarrabawar da ka jarabcemu har zuwa wannan ranar." kallan Daddy Aunty Safma ta yi ta ce, "Amma Yaya muna buƙatar ƙarin bayani game da yadda akayi kuka samo Aisha" Daddy nuna Momma yayi ya ce, "Auntynki ita zata fara baki labari. Ina ce kinji labarin wata yarinya da muke riƙewa kwanakin baya?" A tare suka gyaɗa kai. Momma ce ta gyara zama ta fara basu labarin Indo tun lokacin da suka ganta a ƙofar gidansu, har zuwan su Momma da tafiyar su garin Kura. Zata ci gaba da magana Daddy ya ce, "Momman yara iya nan kaɗai zaki tsaya, saboda nan ne huruminki sauran ki barwa Baba Huwaila. Kinsan Hausawa sun ce waƙa a bakin me ita tafi daɗi." Baba Huwaila sai a lokacin ta yi magana, "Maganar ka haƙƙun haka take, musamman da yake fage ne na Indo, ko ban da murya dole na gyarata ta yadda za'aji daɗin sauraron ta." miƙe ƙafarta tayi saboda tsamin da tayi mata sannan ta fara basu labari tun daga farkon alaƙarsu da Goggo har zuwa rasuwarta, labarin gwagwarmayar da Goggo ta sha da Indo da irin tswangwamar da aka dinga yiwa musu ta basu, saboda tausayinta har zubar mata da ƙwallar sukayi, a taƙaice dai Baba Huwaila babu abin da ɓoye musu game da Indo, har dalilin tafiyar da tayi wanda shi ne silar faɗawarta hannun su Momma. Jikinsu ne ya yi sanyi da haɗe da tausayin Indo mariƙiyarta. Sai kuma yabawa da jinjinawa da suka yi wa Baba Huwaila da Jamilu, musamman da suka ji irin diramar da suke tafkawa tsakanin Indo da Jamilu. Dariya mutanen falon suke sosai banda Fahad, Yaseer da Lubna dan shi kansa Jamilu da ana maimaita abin da ya dinga faruwa a tsakaninsa da Indo abin ba ƙaramin dariya ya bashi ba, sunkuyar da kai ya yi yana murmushi ƙasa-ƙasa. Alhaji Khaleel ne ya yi murmushi ya ce, "To Jamilu ko ƴar gida za'ayi n? Wannan faɗa na ku kamar Tom and Jerry?" Baba Huwaila zuciyar ta fess ta ce, "Ai kuwa da nafi kowa murna" Wani irin abu ne ya tokare zuciyoyin Yaseer miƙewa yayi da niyyar fita Momma ta ce, "Kai ya zakuyi mana juyin mulki tuni Ɗana Yaseer ya sanar mana da buƙatarsa ta auren Humaira ko ba haka ba Daddyn Yara?" Daddy murmushi ya yi ya ce, "Haka ne amma namu ido ne sai wanda Ƴata Humaira ta zaɓa" Indo na jin haka ta sunne kai cikin jikin mahaifiyarta tana jin wani irin matsanancin kunyar su, Jamilu ne ya saci kallanta ba ƙaramin birgeshi tayi ba, amma mamaki yake wai yau Indo ce take jin kunya. Duk garin su babu wanda baisan Indo ba babu wanda take jin Kunya, karshe har Maigari da su Malam Liman. Mommy ce ta kalli Fahad yake danna waya kamar bai san sunayi ba ta ce, "Ɗana ya ana ta magana kayi shiru." Fuska ba walwala ya ce, "Mommy wannan fagen su ne ni kinsan babu wannan a tsarina" Kamar ya sosowa Mommy abin da yake mata ciwo ta kalli Alhaji Khaleel ta ce, "Daddyn Aseel ina jin fa sai kun fara nemawar ɗana magani nina rasa gane kansa, wai yaron nan ko maganar budurwa bayasan nayi masa. Kuna ji fa yanzu abin da ya faɗa." Daddy ya ce, "Wai Fahad har yanzu kallan ƙaramin yaro kake wa kanka? Yanzu haka fa kana shekara ta talatin ko so kake sai na kaɗa maka ƙararrawa ne?" Indo kamar jira take aikuwa ta kwashe da dariya ta ce, "Kamar gwanjon Ɗan Iya na garin gangare" Maigari ya karɓe zancen da, "Idan bashi da farin jini yazo Kura na haɗa shi da Alawiyya itama ba mashinshini, kunga abinsu fes musha biki" Aikuwa duk inda ɓacin rai yaje Fahad ya kai, kwaɓe fuska ya yi kamar zaiyi kuka ya ce, "Mommy kina jin fa me Yarinyar nan take faɗa, wai har da Kawu ma. Wallahi ko mata na rasa bazan auri ƴar ƙauye ba." ya faɗa kamar me shirin rushewa da kuka. Hira suka ci gaba dayi gwanin birgewa, Indo daga gurin wannan sai ta koma gurin wannan. Daddy ne kalli Ɗan uwansa ya ce, "Khaleel ina yaran nan ne banji motsinsu ba?" Alhaji Khaleel ya ce, "Yaya suna Islamiyya amma babu jimawa zaku ji shigowar su" jinjina kai Daddy ya yi ya ci gaba da cewa. "Khaleel naso na bawa su Baba Huwaila tarihinku. tun daga farko har zuwa ƙarshe amma sai nayi wani tunani. Kamar yadda su Baba Huwaila suka baku labari tiryen-tiryen da bakin su, haka nake so kai ko matar ka ku basu labari game da rayuwarku, har zuwa lokacin da kuka rasa ƴar ku da bayan rabuwar ku da ita." Alhaji Khaleel ne ya gyara zaman ya fara cewa. BANDA BAKIN GODE MUKU MASOYA MASU TAMBAYA KWANA BIYU DA KUKA JI NI SHIRU, FATAN ALHERI GAREKU *AMEERA ADAM FANS GROUP* ❤️❤️ ZUNZURUTUN ƘAUNA GA MUTANENA NA *WATTPAD*❤️❤️❤️🥰🥰🥰🥰 MESSAGE ƊIN KU HAR BA ADADI 😂 INA GDY SOSAI DA KULAWA❤️ ALHAMDULLAH NA WARTSAKE ALLAH YA ƘARE MU DA LAFIYA👏🏻👏🏻 KU SUBURBUƊO RUWAN COMMENTS ANJIMA MU TAFI NEXT LEVEL✋🏻😂🤚🏻 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [09/09, 19:23] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 69&70 Alhaji Khaleel gyara zama ya yi ya fara cewa, "Kamar yadda kuka ji daga bakin ɗan uwa na suna na Ibrahim Khaleel. Asalin iyayenmu fulanin shanono ne, sunan mahaifinmu Baffa Inusa sai ɗan uwansa Baffa Musa amma duka muna kiransu da Baffa, su biyar ne agun mahaifinsu amma su biyu ne agurin mahaifiyarsu da suke Uwa ɗaya uba ɗaya. Mahaifinmu ƴan biyu ne shi da ɗan uwansa kamarsu tayi tsanani har ba'a cika gane su ba sai da tabon gefen kan mahaifinmu wanda muka gada daga gurinsa gashi kuma har kan jikokinsa, Baffa Musa shi ne Hassan sai Baffanmu shi ne Usaini. kasuwanci ne ya kawo mahaifinmu garin Kano tare da sauran ƴan uwansa. A hankali tun yana zuwa ya koma, har ya fara tunanin dawo da mahaifiyarmu garin nan. Da farko ƴan uwanta ƙin amincewa sukayi da kyar suka bari ya dawo da ita, daga haka sai ya koma sai bayan wasu lokatu yake kaiwa ƙauyensu ziyara yaje ya gano ƴan uwansa da Ƴan uwan mahaifi dana mahaifiyarsa, saboda tun kafin mahaifinmu yayi aure Allah ya yi wa iyayensa rasuwa. Haka suka ci gaba da gudanar da kasuwanci har Allah ya sa musu albarka. Mahaifiyar mu sunanta Raliya amma muna kiranta da Goggo, su goma sha biyu agurin mahaifinsu. A gurin mahaifiyarsu kuma ita ce ta fari tana da ƙanne biyar, mahaifinsu yana da mata uku kuma shima ainahinsa ɗan garin shanono ne. Mu biyar iyayenmu suka haifa huɗu maza ɗaya mace. Yaya Sani, Yaya Mubarak, Yaya Haruna, Yaya Halima sai ni. Dukkanmu mun samu ilimin boko da na addini dai-dai misali, kuma har yau har kwanan gobe bamu bar harkar kasuwancin da mahaifinmu ya gina mu akai ba. Dukda mahaifanmu sun tsufa amma har yanzu suna alfahari da haɗin kanmu, kuma muma muna fatan wannan haɗin kai namu ya tafi har ƴaƴa da jikokinmu. Ɗagowa Alhaji Khaleel ya yi yana kallon mutanen falon da kowa ya yi shiru yana sauraronsa sannan ya cigaba da cewa, "Na taso a hannun ɗan uwana Yaya Mubarak shi ya kula da karatuna tun daga farko har ƙarshe, lokacin da na kusa kammala karatuna sai suka janyoni cikin harkar kasuwancin fata da robabin da sukeyi, dukda a lokacin inada sha'awar aikin gwamnati, amma sai na kauda kaina sabida karna saɓawa ƴan uwana, tunda banida kamar su sun ɗaukeni kamar ɗan da suka haifa na cikin su. Kuma a wannan shekarar ne suka buɗe wani babban kamfani na sarrafa maganin sauro, a hankali sai Allah ya albarkaci abun bayan buɗe wannan kamfanin da shekara uku sai suka ƙara tunanin buɗe wani kamfanin tare da gidajen mai guɗa biyu, kuma a wannan shekarar ne Allah ya karɓi rayuwar mahaifiyarmu. Mutuwar Goggo ba ƙaramin ɗaga mana hankali ba tare da mahaifinmu dan ta sanadin haka ne ya jininsa ya hau, tun daga wannan lokacin sai Yaya Haruna ya ɗauki Mahaifinmu ya koma gidansa da zama, komawarsa gidan Yaya Haruna sai suka haɗu da Inna Hafshe wacce ta kasance me aiki ce a gidan. Ba'a ɗauki lokaci ba aka sanarwa da danginka aka ɗaura musu aure, Yaya Haruna ya basu gidansa da yake Unguwar Hausawa. Mahaifinmu yayi aure da shekara guda aka fara maganar aure na da Safna, wacce ta kasance ƙanwa ce a gurin matar Yaya Mubarak, ba'a ɗauki lokaci ba aka tsaida wata bakwai lokaci na zuwa aka ɗaura aurenmu muka tare a nan garin Kano unguwar Gyaɗi-gyaɗi." wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli Safna ya ce, "Ummu Banat na gaji fa ko zaki ci gaba da basu labarin?" hararar watsa ta jefa masa ta ce, "Aikuwa idan ka yarda sai dai idan nima na fara basu labarin daga farkon nawa" ta ƙarasa faɗa tana kashe masa ido ɗaya. Martanin hararar wasa ya mayar mata ya ce, "Wallahi bazai yuwu ba sai dai ki bari na gama kya ɗora" Fahad murmushi ya yi ba ƙaramin birgeshi su Uncle Khaleel suke ba, sun fara girma amma har zuwa wannan lokacin suna bawa junansu kulawa, lumshe idanu yayi yana ƙissima wasu abubuwa a zuciyarsa. Uncle Khaleel ya cigaba da cewa, "Shekarar mu Biyar a Kano muka dawo nan garin Kaduna, sakamakon buɗe sabon Kamfinmu da akayi a cikin garin, kuma ni da Yaya Haruna ne muka dawo sauran ƴan uwana suka ɗora mana alhakin kula da duk wani shige da ficen sa. Har zuwa wannan lokacin Allah bai azurtanmu da samun haihuwa ba, tun Safna bata damuwa har abin ya fara damunta. Haka muka fara shige da ficen neman magani mune daga wannan asibitin zuwan wancen, amma duk inda muka je abu ɗaya ne zasu dubamu suce lafiyar mu ƙalau kawai lokaci ne baiyi ba. Wata matsala da muka fara fuskanta ta yawan ɓarin da Safna takeyi, amma muna zuwa asibiti da aka dubata suka sanar da ni, maganin zubar da ciki take amfani da shi shiyasa cikin jikinta baya zama" A dai-dai lokacin da yazo wannan gaɓar Hawayen da Safna take ɓoyewa ne ya gangaro mata, a hankali ta sa hannu ta fara gogewa. Ɗagowa ya yi ya miƙa mata wani farin kyalle a hankali ya furta, "Kefa kika mun alƙwarin kin daina wannan kukan, a duk sanda muke tada wannan maganar" Kukan ne yake niyyar cin ƙarfin ta sannan ta, "Amma kasan ancutar dani matuƙa" Momma dake cen gefe ta ce, "Haba Safna Allah ma muna masa laifi ya yafe manan bare kuma ɗan Adam, wannan maganar ta riga da ta wuce kuma duk wanda ya cutar da ke Allah zai saka miki" Safna gyaɗa kai tayi tana goge hawayen Idonta. Alhaji Khaleel ya ci gaba da cewa, "A wannan lokacin na shiga tashin hankali mara musaltuwa, kuma abubuwa da dama sun faru idan Safna tazo baku labari zakuji daga gareta, bayan mun samu mun kawar da wannan matsalar da shekara guda, sai Allah ya taimakemu muka ƙara samun wani rabon, har Allah ya sauki Safna lafiya ta haifi ɗanta namiji. Sai dai kash Allah ya yi bame tsawon rai bane,, ranar suna aka sameshi kan gado baya numfashi" Wannan karan ma kukan Safna ne ya tsananta har tana ƴar shasheka, bai ce mata komai ba, sai dai yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa. Ya ci gaba da cewa, "Mun ji mutuwar Muhammad sosai kasancewar yaro lafiyayye, amma ita mutuwa babu ruwanta da me lafiya. Haka gidan suna ya juya zuwa gidan mutuwa akayi ta jimami, haka muka fauwalawa Allah lamuranmu. Bayan faruwar haka da ƴan watanni Safna ta kuma samun ciki shima kuma ta haifeshi lafiya ƙalau, amma wani ikon Allah shima kamar wancen ranar suna ya mutu." Wata nannauyar ajiyar zuciya Alhaji Khaleel ya sauke sannan ya ci gaba da cewa, "A wannan haihuwar da tayi dama likitoci sun sanar damu, hutun da Safna zata ɗauka kafin ta kuma ɗaukan wani cikin, a ƙalla zata yi shekara uku kafin ta kuma ɗaukan wani cikin saboda mahaifarta ta samu hutu. Haka muka barwa Allah lamuransa muka zauna har zaman jiran adadin shekarun da likitoci suka ɗaukar mana, a lokacin ba shawarar da ba'a kawo mini ba akan na ƙara aure amma ban amince ba, amma ban sani ba ko Safna kan Ungulu ta binne mini oho" ya ƙara faɗa cikin sigar zolayawa yana kallonta, gabaɗaya falon ba wanda bai dara ba, Daddy ya ce, "To gasu nan ai ƙila bakinsu ɗaya, inajin Mommyn yara ita ta nuna musu hanya tun da aka ce daga na gaba ake gane zurfin ruwa, kana gani ta kanainaye ta hana bawan Allah ƙara aure, nima kuma gani da Momman yara shiru" dariya suke sosai Mommy ta ce, "Eh mun ji ba komai, haka kawai muna zaune za'a ƙwace mana mazaje ne" Alhaji Khaleel ya numfasa ya ci gaba da cewa. "Bayan shekara Uku sai Allah ya ƙara azurta mu da samun haihuwar ƴa mace, da farko hana taron sunan nayi amma sai nayi tunanin duk abin da Allah ya ƙaddara babu mai iya canza shi, ranar suna yarinya taci suna Aisha haka Momman Yara ta dinga kaffa-kaffa da jarira dan ba kowa ake bawa ita ba, kuma ba'a barinta ita kaɗai a ɗaki. Bisa arashi Safna na falon ƙasa gurin wasu baƙi suna gaisawa, itama Momman yara ta sauka ƙasa wani uzuri, tana dawowa ta nemi jaririya sama da ƙasa ta rasa, cikin tashin hankali ta fito tana sanar da abinda yake faruwa, nan da nan aka rufe gidan aka hana kowa fita, kuma aka ci gaba da dube-dube amma ba jaririya babu alamunta. Sai da aka koma ana duba cikin ɗakin aka fara jiyo motsi a cikin drowa, lokacin Momman yara ce da Safna a ɗakin sai sauran ƙawayenta. Da sauri aka buɗe ga mamaki sai ga yarinya ta faɗo ta sauri Safna ta riƙe ta, wani babban tashin hankali gani sukayi an naɗe kan jaririyar da ɗankwalin Mommyn Yara. a razane Safna ta furta, "Dankwalin Mommyn yara? aka naɗe wuyan ƴa ta za'a kashe ta? Lallai akwai lauje cikin naɗi" da sauri Momma ta karɓi jaririyar sai dai har lokacin numfashinta sama-sama yake fita. *ALHAMDULILLAH AM BACK, INA GDY DA ADDU'ARKU MUTANENA NA WATTAPAD MUCH-MUCH ƘAUNA BA ADADI NA RISKI SAƘONKU NA ADDU'A HAR ƊAZU NAGANSU DA YAWA, MUTANENA NA WHATSAPP MUSAMMAN ƳAN GROUP ƊINA WOLLAH BANDA BAKIN GODIYA A GURINKU SAƘONNINKU BAZASU ƘIRGU BA INA GDY SOSAI ALLAH BAR ƘAUNA ❤️❤️❤️* FATAN ALHERI A GAREKU🙋🏼‍♀️ PLS SHARE GIDA BIYU KAWAI NA TURA SAI WATTPAD _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [13/09, 11:20] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 71&72 Lokacin da Alhaji Khaleel yazo nan a zancen sa, a firgice mutanen falon suka ɗago suna kallonsa. Momma, Mommy, Daddy da Aunty Safna ne basu wani nuna alamun firgici ba, amma kana kallan fuskar Mommyn Yara, zaka fahimci launin fuskarta ya sauya cikin damuwa. A tsorace Fahad ya ce, "Dan Allah Uncle karka kace mini Mommy ce ta aikata wani mummunan abu akan jaririyarku, domin nasan bazata taɓa aikatawa ba." Alhaji Khaleel ya ce, "Fahad kenan! ai duk gaggawar Unguwar zoma ta jira haihuwa. Ka jira ci gaban labarin mana, nasan kowanne ɗan Adam yana matuƙar ƙaunar mahaifiyarsa dan haka sam banga laifinka ba Son. Amma ka sani nina san wace Mommynku ko kwatankwacin haka bazata iya aiwatarwa ba." Wata nannauyar ajiyar zuciya Fahad ya sauke yana lumshe ido, Indo dake gefe cikin tausayin iyayenta ta ce, "Dan Allah Abba wace ta aikata muku haka, Allah idan na gano ta zata gane zakaran da Allah ya nufa ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Kuma sai na koma mata Sarƙa, tunda yanxu na koma Aishatul humaira." Yaseer kafe ɗan bakinta ya yi da kallo yana murmushi haɗe da mamaki, saboda gabaɗaya sanin da ya yi mata bata da hayaniya. Jamilu shima murmushi ya yi da ya tuna wace Sarƙa da shuka tsiya da take yi a baya sannan ya ce, "Ayusher zan tayaki da bada shawara kawai kiyi mata fatalwar me..." tun kafin Jamilu ya ƙarasa faɗa, Indo da sauri ta miƙe tsaye tana sa hannunta a baki alamun yayi shiru, murmushi ya yi sannan ya ce, "Sai kin bani cin hanci amma" ɗaga idanunta sama tayi alamar tunani da sauri ta ce, "Ka tuna dukan da ka mun akan gonar Ɗan Iya?" Jamilu jim ya yi yana nazari saboda ya daki Indo ba adadi, zuwa cen ya ce, "Eh na tuna, wacce kukai masa ɓarna ko?" Yaseer tsuke fuska yana tsaki ƙasa-ƙasa. Indo ta ce, "Yauwa to dama naci alwashin wannan dukan, da akwai abin da niyyar zanyi maka amma yanzu kawai ka fanshi kanka, nima kayi shiru basai ka faɗa sun ji ba" murmushi Maigari yayi ya ce, "Kai jama'a Sarƙa kin daɗe kina shuka tsiya wai Jamilun ma bakya raga masa? Lallai Baba Huwaila kunyi ƙoƙari" Ɗan shiru ne ya biyo baya sannan Alhaji Khaleel ya ci gaba da cewa. "Ganin za'a ɓata lokaci yasa Momman Yara ta fice da yarinya, a lokacin muna gate cikin tashin hankali, bamuyi wata-wata ba muka wuce asibiti. Muna zuwa aka karɓeta aka shiba bata kulawa, kwanan mu ɗaya a asibiti aka sallamemu muka koma gida. Mommyn yara ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, najin labarin ɗankwalinta aka gani naɗe a wuyan Aisha. Banda kuka babu abinda takeyi, Ƴan uwana ne suka zauna muka tattauna sukayi mana nasiha akan kada mu zargi Mommyn yara ko kaɗan, tunda a lokacin da abin ya faru ma ta tafi rakiyar wasu ƙawayenta da sukayi kara suka xo suna. Kuma har yau har kwanan gobe Allah shi ya barwa kansa sanin wanda ya aikata wannan abun. Abin da muka ɗauka kawai duk wanda yake mana wannan abun ba ƙaramin maƙiyinmu bane, kuma Allah shi zai mana sakayya. Haka muka ci gaba da al'amuranmu yarinyar mu na ƙara wayo, gwanin ban sha'awa gata da farin jini duk inda muka je da ita mutane na sha'awar ɗaukanta. Alokacin da ta cika wata biyu cif, idan ka ganta zaka rantse tayi wajen wata huɗu. mun ɗauki soyayyar duniya mun ɗora akan ƴar mu Aisha. Ƙwatsan wata rana da daddare muna tsaka da bacci mukaji harbe-harbe, daga baya sai Ihun maigadin gidanmu muka fara ji. Ta window muka leƙa muka hango mutum biyu sun saka shi a tsakiya ga jini na zuba a gefen kafaɗarsa, muna nan tsaye muka ji anfara buga ƙofar falonmu, bugun ƙofar ne ya tashi Aisha ta fara kuka. A firgice na fara neman wayata domin kiran ƴan sanda, amma akayi rashin dace na barta a falo jikin caji. Ɗaya daga cikinsu ne naji ya ce, "Kai Babba idan bazasu buɗe ba mu doke ƙofar Ƴarinyar kawai akace mu karɓo idan kuma sukayi gardama duk mu kashe su" muna jin haka gabaɗaya tsoro ya kama mu bamuyi aune ba, mukaji sun karya ƙofar falon haɗe sakin harbi. Kallan Safna nayi na ce mata, "Kishiga cikin ɗakin cen zan tsaya akan koda sun shigo ɗakin nan bazasu sameki ba, zan roƙesu alfarma ko kuɗi ne na basu su tafi." cikin firgice ta miƙomin waya tana faɗin, "Bazamuyi haka ba ga wata maza ka kira ƴan sanda" karɓar wayar nayi sai dai kash ba lambar DPO a wayarta, wata dabara ce ta faɗo min na kira wayar Yaya Haruna, sai a kira na uku ya ɗauka na sanar masa. Da hanzari ya kira lambar DPO ya sanar masa halin da mike ciki da adireshin gidanmu, kuma akan dole badan Safna ta so ba na turasu cikin ɗaki ina me gargaɗinta da duk rintsi karta sake ta buɗe ƙofar ta fito, tunda tsakaninmu da ofishin ƴan sandan ba nisa cen sosai, nasan kafin su shiga gurinsu Safna folisawan sun ƙaraso. Safna na kuka haka na rufosu na dawo dakin na tsaya ina jiran ikon Allah. Aikuwa ina nan tsaye har suka samu nasarar karya itama wannan ƙofar suka shigo su wajen biyar, fuskokinsu duk a rufe. Suna shigowa na ce musu, "Dan Allah ku tsaya muyi magana da ku, duk iya kuɗin da kuke buƙata zan baku amma karku ɗaukar mun ƴata" Babban cikin su ne yayi wata dariya sannan ya ce, "Ka ɗauka bamusan kana da kuɗi ba? Munsan kana da amma ƙwandalarka baza mu ɗauka ba, ƴarka ita aka turo mu mu ɗauka idan kuma kuka yi mana gardama zamu kasheku gabaɗaya." shiru nayi ban tanka musu ba wani daga cikin su ya ce, "A ina ka ɓoye uwar da ƴar?" A wannan karanma shiru nayi ban tanka musu ba, banyi aune ba sai ji nayi sun sakar min bindiga a ƙafata, cikin azaba na kurma ƙara ina ambaton sunan Allah, daga cikin ɗakin naji Safna ta kurma ihu tana ambatar sunan, cikin azaba nake ƙara gargaɗinta da karta sake ta fito. Suna jin gargaɗina suna ƙara sakarmin harsashi a gefen kafaɗa ta, cikin tsananin jin zafi na ƙara kurma ihu. Anyi haka babu jimawa sai ga Safna ta fito, hannunta ɗauke da Aisha tana kuka ta miƙa musu ita tana faɗin, "Inda ƴa ce ga ta amma dan Allah karku kashe mini mijina, ina matuƙar ƙaunarsa." Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙarɓe yana murmushi ya ce, "Shikenan fa abin da zakuyi ka tsaya yi mana gardama" Ɗago da kaina nayi na ce mata, "Safna me yasa kika yi haka?" Kafin ta bani amsa Ɗaya daga cikin su ne ya shafo wuyanta yana lashe baki ya ce, "Gaskiya wannan hajar tayi ku wurga min ita ɗakin da ta fito" zan dinga typing ko ba yawa ne sbd bana samun tym idan nace sai da yawa zan jima banyi ba. Kuyi hkr da rashin replay kwana biyu network ke rikeni dan posting ɗin jiya ma da kyar ya tafi. Mommy, mmn naseer, mmn rauda kuna da yawa wallahi naga comments ɗinku na muku replay yaki tafi ina muku fatan alheri. Wattpad ina gdy kulawa🥰 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [13/09, 19:27] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 73&74 A firgice kowa ya kalli Alhaji Khaleel a lokacin daya zo nan a zancensa, murmushi ya yi saboda yadda yaga firjici a idanunsu sannan ya ci gaba da cewa. "Da sauri Safna ta ja da baya tana kare jikinta da hannuwanta, matsawa ya yi kusa da ita yana wani murmushi. A firgice na ɗago na ce, "Ka dubi girman Allah karka taɓa min matata" ko kallona baiyi ba ya fara takawa zuwa gurinta. Cikin tsawa ogansu ya buga masa tsawa yana faɗin, "Kai Ƙusa wane irin kidahumi ne kai? Dama a bajat ɗinmu munyi da wannan harƙallar ne? Wallahi idan ka ɓata mun shiri sai dai wani ba kai ba. Aikin sa kaine kawai nake yadda naga dama, amma aiki ture ina tsayawa akan ƙa'idata" yana gama faɗa ya juya ya fice, sauranma suka rufa masa baya. Suna Fita Safna ta durƙushe a gurin tana wani irin gursheƙen kuka, mai tsuma zuciyar me sauraro. Duk wanda yayi tozali da Safna sai ya tausaya mata, jiki ba ƙwari na janyo jiki dukda har lokacin jini na zuba a jikina na rungumota jikina. Bani da wata mafita ko dabara nima fashewa nayi da kukan, saboda yadda zuciyata take azalzalata akan ƴarmu ƙwaya ɗaya tilo, muna cikin haka muka jiyo jiniyar ƴan sanda a ƙofar gidanmu. Ɗagowa nayi da raunanan idanuna na ce mata, "Why Safna? Meyasa zaki basu ƴarmu kikasan halin da zata shiga?" kafeni tayi da ido kamar wacce bata cikin hankalinta zuwa wani lokacin ta kuma rumgumeni tana rushewa sa wani irin kuka, ban hanata ba saboda nasan yadda tsananin soyayya take tsakanin Ɗa da uwa, kallanta nake ina daɗa jinjina irin zallar soyayyar da Safna take mini, dagowa tayi cikin dakusashshiyar murya ta ce, "Me muka yi musu? Me yasa basasan su ga muna mallaki ɗa ko ƴa a rayuwarmu? Me muka tsare musu? Kuma su waye suke aikata munanan abubuwan nan haka a kanmu?" Murya a naunane na ce, "Har yanxu amsar dana gagara bawa kaina kenan. Gabaɗaya kaina ya kulle bansan wanda zan zarga akan wannan lamarin ba, abu ɗaya na riƙe Allah baya zalinci. Tunda bamu da haƙƙi kuma bamu zalinci kowa ba shi zai saka mana, amma meyasa kika bada Aisha bakya tunanin irin cutarwar zasuyi mata?" hawayen Idonta ta goge ta ce, "Na sanka na tsawon shekaru kuma nayi sabo da kai na tsawon shekaru, mutuwa ita kaɗai zata iya rabani da kai. Kai nagartaccen mutum ne taya zan fifita wacce ko wata uku banyi da ita ba akanka? Kana ganin idan nayi haka na maka adalci? A yadda na fahimta zasu iya kasheka muddin ban basu Aisha ba. Ni kuma ban shirya rabuwa da kai ba, kuma nasan muddin muna tare Allahn da ya bamu ita zai iya ƙara mana wasu masu albarka" tana zuwa nan kuka yaci ƙarfinta, rungumeta nayi a jikinta ina jin wata irin soyayyarta a zuciyata, cikin kuka ta ci gaba da cewa, "Na rubutua lambar wayarmu da taƙaitacen bayani, haɗe da hoto na sa a cikin pampars ɗinta. Nasan ko kasheta sukayi duk wanda ya tsinci gawarta zaiga lambarmu zai neme mu." hawaye ta cigaba da yi sannan ta ɗaga hannu sama ta ce, "Ya Allah kana gani bamu cutar da kowa ba bamu zalinci kowa ba, Allah mun ɗauki wannan lamarin a matsayin ƙaddararmu, Allah ka bamu ikon cinye waɗannan ƙaddarorin da kake jarabtar mu da su. Ya Allah mun dogara da kai ka tsare mana yarinyar mu a duk inda take da tsarewarka, idan ba me tsawon kwana bace Ubangiji ka karɓi rayuwarta cikin sauƙi." tana gama addu'ar mukaji shigowar ƴan sandan, da sauri suka ƙaraso gurunmu suna tambayar yadda abun ya faru, taimaka mun sukayi suka fita dani kai tsaye suka wuce asibiti da gabaɗaya, sai da basu samu nasarar kama ko mutum ɗaya daga cikin ƴan fashin ba. Muna zuwa asibiti suka shiga bamu kulawar gaggawa, zuwan mu babu wuya ɗan uwana suka ƙaraso shida matarsa. Satinmu biyu a asibiti aka sallamomu kuma har wannan lokacin babu labarin Aisha, ƴan uwa sun yi jimami kowa yaji ɓatanta. Safna kullin cikin kuka take da damuwa a lokacin har hawan jini sai da ya kamata, sai a hankali ta fara cire damuwa muka fauwalawa Allah lamuranmu, tun muna sa ran jin labarin Aisha har tafiya ta miƙa muka daina tunanin sake jin labarinta ganinta. Bayan wasu shekaru sai Allah ya azurtamun da samun ƴan biyu duka maza Aseel da Aseem. Ba mu ɗora soyayyarmu akansu ba, saboda suma gani muke a kowanne lokaci zamu iya rasasu. Kuma cikin ikon Allah sai gashi Allah ya raya manasu yanxu haka suna da shekara goma bibbiyu a duniya, tun daga kansu haihuwa ta tsaya mana. Allah da ikonsa sai gashi yau Allah ya nuna buwayarsa, ya dawo mana da ƴarmu a lokacin da muka riga da mun cire rai akanta." Alhaji Khaleel ya ƙarasa faɗa cikin nuna godiyarsa ga Allah subhanahu wata'ala. Gabaɗaya mutanen falon jikinsu ne yayi sanyi, tausayin waɗannan bayin Allahn na ratsa zuciyoyinsu. Ita Kanta Indo tausayin Iyayenta ne ya kamata, Safna da ke goge hawayen ta ce, "Tabbas lamarin Ubangiji da girma yake Allah mun gode maka" Fahad ji yayi ɗan tausayin Indo ya ɗan tsarga masa, tunaninsa ɗaya ya aka ƙare bayan da ƴan fashin suka tafi da ita kuma ya akayi ita da suke Kaduna amma tayi rayuwa a garin Kano, cikin Kanon ma a wani ƙauye da ke garin Kura, Aunty Safna ce ta gyara zama ta ce. Fatan alheri masu comments ina gdy❤️❤️❤️❤️🥰🥰 whatsapp da wattapad har facebook ɗinma ina fatan alheri🥰🥰🥰 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [14/09, 20:00] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 75&56 Aunty Safna gyara zama tayi ta ce, "Da farko suna na Safna Yusuf Bature, asalinmu ƴan garin Zaria ne. Mu biyu ne kawai agurin iyayenmu nida yayata Momman yara, kafin ni sun haifi yara da yawa suna rasuwa sannan ni, iyayenmu sun rasu bayan bikin Momman yara da shekara biyu, sanadin rasuwarsu hatsarin mota sukayi. Nikuma a lokacin ina da shekara goma sha biyu a duniya, rasuwar iyayena yasa na dawo hannun yayata da zama, kuma mijinta ya riƙeni da gaskiya kamar ƙanwarsa. Ina nan ina karatu na har ƙaninsa ya dawo gurinsa da zama, wata shaƙuwa ce ta shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakaninmu, daga baya kuma ta riƙiɗe zuwa soyayya, tun yayyanmu basu fahimata ba har suka fahimce mu, bayan na kamalla karatuna na sakandire sai manya suka shiga maganarmu aka tsaida rana. Lokaci na zuwa aka ɗaura mana aure." Aunty Safna ɗagowa tayi ta kalli mutanen falon da sukayi zuru suna sauraronta ta cigaba da cewa. "Basai na ja ku da nisa ba tunda duk abinda zan faɗa Hubby ya riga da ya faɗa, sai dai abinda ya manta bai sanar da ku ba shine. A ranar da za'a tafi da Aisha ranar Momman yara ta kawo mana ziyara, kuma ta kawowa Aisha Sha tara ta arziki wanda wannan ba baƙonta bane. Saboda duk zuwan da zamuyi gidansu sai ta bani wani abun wanda ta saiwa Aisha, saboda tsananin ƙaunar da take mata. a ranar ne ta zo mata da kaya acikinsu harda zobe da azurfa na jarirai da ta saya mata, tare da wasu riga da siket masu kyawun gaske. Da kanta ta sawa Aisha kayan nan da awarwaron azurfar da ta kawo mata, kuma ba ƙaramin kyau sukayi mata ba. Daddare lokacin da ƴan fashin nan suka zo mana bayan na shiga ɗaki, lokacin da naji sun harbi Hubby wani tunani yazo mun, takarda na samu da biro na rubuta lambar wayarmu da bayanin tursasawar da ƴan fashin sukayi mana, sai hotonmu dake drower mudubi na ciro kati ɗaya na ninkeshi da takardar, na tura mata acikin pampers ɗinta. kafin fitata nayi kuka kamar raina zai fita saboda kowa yasan soyayya irin ta ɗa da mahaifiya" Aunty Safna na zuwa nan hawayenta ya tsananta, sai da ta goge hawaye ta cigaba da cewa. "Ina ji ina gani haka na fita na basu Aisha saboda ceton rayuwar maigidana, zancen da nake muku har yanzu bamusan waye ya aikata mana wannan mugun ƙudurin ba, sai dai abu guda na bawarwa raina koma waye tabbas wannan ba masoyinmu bane, babban maƙiyinmu ne da bayasan farincikinmu. Allah da nashi ikon sai gashi ya dawo mana da ƴarmu cikin ruwan sanyi, tabbas wannan baiwar Allah da ta tsince da ke Baba Huwaila bamu da abinda zamu ce muku, baki bazai iya furta kalmomin godiya ba saboda ɗubin alkairin da kukayi mana. Na jima banga mutane masu karamci kamar ku ba, kuma na jima banga mace mai riƙon Alƙawari kamar ke ba Baba Huwaila, anbaki amanar Aisha dukda ba ran uwar goyonta hakan baisa kin wofantar da ita ko kin azabtar da ita ba, wannan shi ne abinda yayi mana ƙaranci wato riƙon Alƙawari ga dai Aisha a gurinki ba dangin iya bare na Baba amma kinmata riƙo kamar jikarki ta jikinki, tabbas wannan abun a jinjina miki ne Allah ya saka miki da mafificin alheri Ameen" gabaɗaya Falon suka amsa da Ameen. Baba Huwaila ce ta ɗago fuska da ƴar damuwa ta ce, "Ƴata Safna banji daɗin abinda kika faɗa ba, na cewar babu dangin Iya bare na Baba game da Indo. Wallahi tunda nake da Indo bantaɓa jin cewar ita ba jinina bace" Aunty Safna kunya ta ɗan kamata ta ce, "Baba Huwaila ban faɗa da wata manufa amma kowa ya sani Indo takice da Jamilu, Amun afuwa tuba nake" ta ƙarasa faɗa cikin sigar wasa, gabaɗaya dariya aka sa banda Fahad, Lubna da Yaseer da kowa ya sha toka yana muzurai, musamman Fahad da sai furzar da huci yake. Baba Huwaila murmushi tayi ta ce, "To shikenan kin fanshi kanki" Mommyn Fahad ce ta numfasa ta kalli Indo ta ce. "Aisha bari nayi miki bayaninmu dalla-dalla yanda zaki san matsayin kowa a gurinki" Indo gyaɗa kai tayi tana binsu da kallo, suna haɗa ido da Fahad ya watsa mata harara taɓe baki Indo tayi tana murguɗa masa baki a fakaice. Mommyn Fahad ta ce, "Kinga wannna da kike gani Fahad ɗan uwanki ne, nina haifeshi kuma shi kaɗai ne ɗana" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya cika Fahad, gani yake kamar zata rainashi wai har sai anwani gabatar mata da shi kamar uwar mutane, Indo ta lura da yanayinsa har Mommy zata cigaba da magana ta ce, "Amma Mommy gaskiga kamar bake kika haifeshi ba, dan wallahi bashi da kirki sai yayi ta hararar mutane" Da sauri Aunty Safna ta ce, "Aisha gidanku Yayan naki kike gayawa haka" Indo shiru tayi shikuwa sai wani ƙaracin mazu yake. Mommy ta cigaba da cewa, "Yaseer kuma ɗan uwansa ne abokin tagwaitakarsa ne" da sauri Indo ta ce, "Shima ke kika haifeshi" Mommy ta ce, "A'a ga mamansa cen Momman yara" kan Indo ne ya ɗaure Baba Huwaila ta ce, "Amma hajiya dan Allah karkiga na muku shishshigi, naji kince tagwaye ne amma kuma kowa mahaifiyarsa daban, ya abun yake?" Mommy zatayi magana karaf Momman yara ta ce, "Baba Huwaila Yaseer da Fahad tagwaye ne, Fahad ne Hasan Yaseer Usaini, Mommyn yara ita da mijinta Abi suka mun kyautar Yaseer tun lokacin da ta haifesu a asibiti saboda mu Allah bai azurta mu da haihuwa ba, kuma ba yadda banyi da Daddyn yara akan ya ƙara aure amma yaƙi sai da kyar ya auro wata bazawara, shekara biyu da aure suka rabu, kuma itama bata haihu ba. Daga kanta bai ƙara auren wata matar ba, kuma tunda muka samu Yaseer sai damuwar rashin haihuwa da kau daga zuciyoyinmu. Abinda ya sa ma ba'a kiransu da Hassan da Hussaini saboda karsu fahimci cewar ciki ɗaya suka fito, kuma daga ɓangaren mahaifinsu har na mahaifiyarsu, dogon meeting akayi akan duk wanda ya sanar dasu cewar ciki ɗaya suka fito basu yafe ba. Mommyn yara ƙanwar mijina ce wato ƙanwar mahaifin Indo amma wallahi ta zama kamar ƴar uwata ta jini." Fahad da Yaseer kallan juna suka fara yi lokaci ɗaya sukaji Indo ta bushe da wata irin dariya. FATAN ALHERI❤️🥰 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [17/09, 19:47] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 77&78 Da mamaki gabaɗaya juyawa sukayi suna kallanta da mamaki, Fahad ne ya ƙara tsuke fuska ya ce, "Ke meyake damunki ne?" Indo ba kunya ta watsa masa harara ta ce, "Nace maka akwai abinda yake damuna ne? Ina da baki za'a hanani dariya ne..." da sauri Aunty ta katse ta tana bige bakinta ta ce, "Aisha wai yaushe kika raina yayanki haka?" tura baki gaba Indo tayi Fahad yayi gutun tsaki ya ce, "Aunty ki barta dani akan rashin kunya zata mun bayani" Mommyn Fahad ta ce, "Aisha banasan tsiwa kinga Fahad yayanki ne" Yaseer jin ana tayiwa Indo faɗa yasa ya ce, "Brother kaima ka fiya shiga sangar Humaira meyasa ni bata mun haka" Indo dukda fushi take da Yaseer amma taji daɗin yadda Yaseer ya gayawa Fahad, ita kanta ta rasa dalilin da yasa sam basa jituwa da Fahad, ita ta rasaa meyasa yake yawan shiga sabgarta, tana tsaka da wannan tunanin taji Fahad ya ce, "Karka ɓatamun rai Yaseer kasan banasan raini" Alhaji Khaleel ne ya kalli Indo da take cika tana batsewa, sannan ya kalli Fahad ya ce, "My Son ka hukunta ta dan na lura kunnenta baya ji" Maigari wata irin dariya yayi mai ɗauke da manufar har yanzu bakusan wacece Sarƙa ba, sannan ya ce. "Kai Fahadu wallahi karma ka fara tarkarwa kanka dan wallahi duka baya yiwa Sarƙa, idan kuwa ka biye mata wallahi har fitsari a wando sai ta saka ka" Aikuwa lokaci ɗaya mutanen falon suka fashe da dariya, Yaseer dariya yake harda riƙe ciki. Kallan Fahad yayi yana dariya ya ce, "Wa yaga Brother na sakin amalala" Duk inda ɓacin rai yakai Fahad yaje gurin, iya ƙuluwa ya ƙulu kansa ya sunkuyar ƙasa yana furzar da iska mai zafi, ganin zaman bazai kawo masa mafita ba yasa ya miƙe batare da ya tankawa kowa ba ya fice. Sai bayan da suka tsagaita da dariya sannan Mommy ta cigaba da cewa, "Humaira kina da ƴan uwa masu yawa, waɗanda sai a hankali zaki gane kowannensu, ga wata ƴar uwar taki cen wato Lubna, ita ma ƴar yayan mahaifinki ce. Sannu a hankali daga dangin mahaifinki har na mahaifiyarki zaki gane su" Indo murmushi tayi, ita ba bayanin da Mommy tayi ne ya sa ta murmushi ba, yadda ta ga Fahad ya shaƙa ne ya bata matuƙar dariya, suna nan zaune su Aseel suka shigo sanye da uniform ɗin makaranta, suna shigo Aseem ya faɗa kan Momma yana dariya, Indo bin yaran tayi da kallo tana kallon yanayinsu, a fuska ta ɗan lura da yanayin kamar da suke amma bawai kana ganinsu zaka fahimci kamanninsu ba, harsai ka zuba musu idanu. Kallansu ta ƙarayi a karo na biyu tayi murmushi, tana ƙara kallan tabon gefen kansu irin nata da kuma su Yaseer. Gaida mutanen falon sukayi sannan Aunty Safna ta gabatar musu da Indo, maƙaleta sukayi suna dariya daga baya suka ɗagata, suka haye sama domin cire uniform ɗinsu. Domin sai wani murmushi take ita gata babba, idan ka ganta zaka rantse haka take gabaɗaya da nutsuwa. Abinci da abinsha aka gabatar musu suka zauna suka fara ci ana ci gaba da hira, sai da sukaci suka yi ƙat sannan Alhaji ɗan Baba Huwaila, ya sanar musu da komawarsu gida saboda kar dare yayi musu, Alhaji Khaleel ne ya nemi izinin su kwana, amma ya ce sam haka bai dace ba. Aunty Safna da kanta ta nemi izini da a bar mata Baba Huwaila ta kwana biyu a gurinsu, Alhaji bai musa ba kuma da su Momma su kansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba. Su Momma da su Mommy suma tashi sukayi kowa zai koma garinsu, Su Mommy, Alhaji, Mai Unguwa da Jamilu sune suka wuce Kano. Yaseer da su Momma suka wuce garin Abuja, Yaseer yaso ya ɗan keɓance da Indo amma kunyar Iyayensa yasa ya kasa yi mata magana. Jamilu ma haka ya tafi zuciyarsa fal tunanin Indo. Fahad anan ya zauna saboda dama rabi zamansa a Kano yakeyi rabi kuma a Kaduna, saboda wani kamfani da yake kula da dashi na sarrafa takalma da robobi. Baba Huwaila ba ƙaramin kulawa take samu ba ita da Indo, babu abinda sukeyi sai dai su ci abinci suyi wanka su kwanta, Aunty Safna mace ce mai faram-faram da sakin fuska bata da matsala ko kaɗan. Fahad tun bayan tafiyarsu Mommy ya koma cen ɗakinsa, bai cika fitowa ba dan haka ma basa haɗuwa da Indo. Baba Huwaila Satinta biyu ta matsa sai anmayar da ita gida, ba yanda basuyi da ita ba akan ta haƙura ta ƙara ko sati guda ne amma taƙi, kaya suka haɗa mata sha tara ta arziƙi da kayan abinci kala-kala. Ranar da zata tafi gabaɗaya suka ɗunguma zuwa garin Kano, Banda Fahad da ya ce musu sai washegari zai tafi saboda bai gama wani uzurinsa ba. Ya yi haka ne saboda haɗa tafiya da Indo dan lura yarinya na nema fara bashi matsala. Lokacin da suka je Kano tarba akayi musu ta karamci da mutumci, Jamilu bakinsa wasai kamar gonar auduga, sai zanga fara'a yake. Bayan sallar la'asar suka ɗunguma Unguwar Tudun Yola, gabaɗaya har su Baba Huwaila dan su gano gidansu Mommy acigaba da sada zumunci. Mommy ba ƙaramin daɗi taji ba nan ma hira suka baje suna yi, Su Baba Huwaila basu suka koma gida ba sai bayan magriba. Lokacin da zasu tafi Indo da Baba Huwaila rungume juna sukayi suna kuka, sai da sukayi mai isarsu sannan suka saki juna Driver ya ɗauke su ya kaisu gida. Su Indo anan zasu kwana biyu sai ranar Lahadi zasu koma gida kasancewar ranar Juma'a suka zo. Washegari da safe Fahad ya iso garin Kano lokacin baifi ƙarfe goma na safe ba, lokacin da ya shigo gabaɗaya suna Falo sun gama breakfast kenan, yana shigowa ya gaida iyayen nasa suna yi masa ya hanya, su Aseem ne suka maƙale shi kasancewar mutuminsu ne sosai. Indo taɓe baki tayi tana ɗauke kai gefe Aunty Safna na lura da Indo, daƙuwa tayi mata ta ce, "Bazaki gaishe da Yayanki ba?" Turo baki gaba tayi kamar bata so ba tace, "Ya hanya" Kafin Fahad ya amsa Aunty Safna ta ce, "Ƙaniyarki haka ake gaisuwa shashasha kawai" Harara ta watsawa Fahad ta ce, "Ina kwana" Wani murmushi ne ya suɓuce masa, me ɗauke da yarinya har yanzu bakisan waye ni ba, a yatsin shima ya amsa sannan ya ce, "Ungo ga jaka ta nan ki kaimun ɗaki, nasan yayi ƙura ki share ki mun mopping, banasan ɓarna duk abinda kika gani ki barshi a inda yake, idan kin kai ki je bakin gate ki kira mun Rabe" Wani mugun kallo ta wurga masa suna haɗa ido da Aunty Safna ta watsa mata harara, ba shiri ta tashi ta ɗau jakar tana ƙunƙuni har tayi gaba ta juyo ta ce, "Ina ne ɗakin?" da hannu ya nuna mata wata hanya, juyawa tayi ta nufi inda ya nuna mata. Wata irin dariya ce ta suɓucewa Indo ƙasa-ƙasa ta furta, "Wallahi yanda ka sani aiki ban shirya ba kaima ka jira naka" daga bayanta Aunty Safna ta ce, "Magana kike ne" Indo Murmushi tayi ta juyo ta ce, "A'a Ammi kawai nace amma jakar da nauyi" NA GAISHE KU KYAUTA🌚🌚 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [18/09, 14:17] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 75&56 Aunty Safna gyara zama tayi ta ce, "Da farko suna na Safna Yusuf Bature, asalinmu ƴan garin Zaria ne. Mu biyu ne kawai agurin iyayenmu nida yayata Momman yara, kafin ni sun haifi yara da yawa suna rasuwa sannan ni, iyayenmu sun rasu bayan bikin Momman yara da shekara biyu, sanadin rasuwarsu hatsarin mota sukayi. Nikuma a lokacin ina da shekara goma sha biyu a duniya, rasuwar iyayena yasa na dawo hannun yayata da zama, kuma mijinta ya riƙeni da gaskiya kamar ƙanwarsa. Ina nan ina karatu na har ƙaninsa ya dawo gurinsa da zama, wata shaƙuwa ce ta shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakaninmu, daga baya kuma ta riƙiɗe zuwa soyayya, tun yayyanmu basu fahimata ba har suka fahimce mu, bayan na kamalla karatuna na sakandire sai manya suka shiga maganarmu aka tsaida rana. Lokaci na zuwa aka ɗaura mana aure." Aunty Safna ɗagowa tayi ta kalli mutanen falon da sukayi zuru suna sauraronta ta cigaba da cewa. "Basai na ja ku da nisa ba tunda duk abinda zan faɗa Hubby ya riga da ya faɗa, sai dai abinda ya manta bai sanar da ku ba shine. A ranar da za'a tafi da Aisha ranar Momman yara ta kawo mana ziyara, kuma ta kawowa Aisha Sha tara ta arziki wanda wannan ba baƙonta bane. Saboda duk zuwan da zamuyi gidansu sai ta bani wani abun wanda ta saiwa Aisha, saboda tsananin ƙaunar da take mata. a ranar ne ta zo mata da kaya acikinsu harda zobe da azurfa na jarirai da ta saya mata, tare da wasu riga da siket masu kyawun gaske. Da kanta ta sawa Aisha kayan nan da awarwaron azurfar da ta kawo mata, kuma ba ƙaramin kyau sukayi mata ba. Daddare lokacin da ƴan fashin nan suka zo mana bayan na shiga ɗaki, lokacin da naji sun harbi Hubby wani tunani yazo mun, takarda na samu da biro na rubuta lambar wayarmu da bayanin tursasawar da ƴan fashin sukayi mana, sai hotonmu dake drower mudubi na ciro kati ɗaya na ninkeshi da takardar, na tura mata acikin pampers ɗinta. kafin fitata nayi kuka kamar raina zai fita saboda kowa yasan soyayya irin ta ɗa da mahaifiya" Aunty Safna na zuwa nan hawayenta ya tsananta, sai da ta goge hawaye ta cigaba da cewa. "Ina ji ina gani haka na fita na basu Aisha saboda ceton rayuwar maigidana, zancen da nake muku har yanzu bamusan waye ya aikata mana wannan mugun ƙudurin ba, sai dai abu guda na bawarwa raina koma waye tabbas wannan ba masoyinmu bane, babban maƙiyinmu ne da bayasan farincikinmu. Allah da nashi ikon sai gashi ya dawo mana da ƴarmu cikin ruwan sanyi, tabbas wannan baiwar Allah da ta tsince da ke Baba Huwaila bamu da abinda zamu ce muku, baki bazai iya furta kalmomin godiya ba saboda ɗubin alkairin da kukayi mana. Na jima banga mutane masu karamci kamar ku ba, kuma na jima banga mace mai riƙon Alƙawari kamar ke ba Baba Huwaila, anbaki amanar Aisha dukda ba ran uwar goyonta hakan baisa kin wofantar da ita ko kin azabtar da ita ba, wannan shi ne abinda yayi mana ƙaranci wato riƙon Alƙawari ga dai Aisha a gurinki ba dangin iya bare na Baba amma kinmata riƙo kamar jikarki ta jikinki, tabbas wannan abun a jinjina miki ne Allah ya saka miki da mafificin alheri Ameen" gabaɗaya Falon suka amsa da Ameen. Baba Huwaila ce ta ɗago fuska da ƴar damuwa ta ce, "Ƴata Safna banji daɗin abinda kika faɗa ba, na cewar babu dangin Iya bare na Baba game da Indo. Wallahi tunda nake da Indo bantaɓa jin cewar ita ba jinina bace" Aunty Safna kunya ta ɗan kamata ta ce, "Baba Huwaila ban faɗa da wata manufa amma kowa ya sani Indo takice da Jamilu, Amun afuwa tuba nake" ta ƙarasa faɗa cikin sigar wasa, gabaɗaya dariya aka sa banda Fahad, Lubna da Yaseer da kowa ya sha toka yana muzurai, musamman Fahad da sai furzar da huci yake. Baba Huwaila murmushi tayi ta ce, "To shikenan kin fanshi kanki" Mommyn Fahad ce ta numfasa ta kalli Indo ta ce. "Aisha bari nayi miki bayaninmu dalla-dalla yanda zaki san matsayin kowa a gurinki" Indo gyaɗa kai tayi tana binsu da kallo, suna haɗa ido da Fahad ya watsa mata harara taɓe baki Indo tayi tana murguɗa masa baki a fakaice. Mommyn Fahad ta ce, "Kinga wannna da kike gani Fahad ɗan uwanki ne, nina haifeshi kuma shi kaɗai ne ɗana" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya cika Fahad, gani yake kamar zata rainashi wai har sai anwani gabatar mata da shi kamar uwar mutane, Indo ta lura da yanayinsa har Mommy zata cigaba da magana ta ce, "Amma Mommy gaskiga kamar bake kika haifeshi ba, dan wallahi bashi da kirki sai yayi ta hararar mutane" Da sauri Aunty Safna ta ce, "Aisha gidanku Yayan naki kike gayawa haka" Indo shiru tayi shikuwa sai wani ƙaracin mazu yake. Mommy ta cigaba da cewa, "Yaseer kuma ɗan uwansa ne abokin tagwaitakarsa ne" da sauri Indo ta ce, "Shima ke kika haifeshi" Mommy ta ce, "A'a ga mamansa cen Momman yara" kan Indo ne ya ɗaure Baba Huwaila ta ce, "Amma hajiya dan Allah karkiga na muku shishshigi, naji kince tagwaye ne amma kuma kowa mahaifiyarsa daban, ya abun yake?" Mommy zatayi magana karaf Momman yara ta ce, "Baba Huwaila Yaseer da Fahad tagwaye ne, Fahad ne Hasan Yaseer Usaini, Mommyn yara ita da mijinta Abi suka mun kyautar Yaseer tun lokacin da ta haifesu a asibiti saboda mu Allah bai azurta mu da haihuwa ba, kuma ba yadda banyi da Daddyn yara akan ya ƙara aure amma yaƙi sai da kyar ya auro wata bazawara, shekara biyu da aure suka rabu, kuma itama bata haihu ba. Daga kanta bai ƙara auren wata matar ba, kuma tunda muka samu Yaseer sai damuwar rashin haihuwa da kau daga zuciyoyinmu. Abinda ya sa ma ba'a kiransu da Hassan da Hussaini saboda karsu fahimci cewar ciki ɗaya suka fito, kuma daga ɓangaren mahaifinsu har na mahaifiyarsu, dogon meeting akayi akan duk wanda ya sanar dasu cewar ciki ɗaya suka fito basu yafe ba. Mommyn yara ƙanwar mijina ce wato ƙanwar mahaifin Indo amma wallahi ta zama kamar ƴar uwata ta jini." Fahad da Yaseer kallan juna suka fara yi lokaci ɗaya sukaji Indo ta bushe da wata irin dariya. FATAN ALHERI❤️🥰 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [18/09, 14:17] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 79&80 Fahad kallan tsaf ya yiwa Indo yadda ya karanci fuskarta, ya tabbatar da abinda ta faɗa ba shine abinda ta furta ba. Murmushin gefen baki yayi ya kauda kansa gefe, Mommy sai a lokacin tayi magana, "Safna dan Allah ku ƙyalemun yarinya ta sarara keda ɗanki kunsa min ita a gaba, banda aikin da ya sata sai faɗa kuke mata. Aunty Safna ta ce, "Wallahi yarinyar ce na lura nema take ta raina Fahad" Ita dai Indo wucewa tayi hanyar da Fahad ya nuna mata tana zuwa wata ƙofa ta gani, a hankali tasa hannu ta murɗa kofar ta shiga. Tana shiga wani daddaɗan ƙamshi ne ya doki hancinta har sai da ta Lumshe ido, bayan wasu ƴan sakanni ta buɗe su ta ƙarasa cikin ɗakin tana ƙarewa ɗakin kallo. A fili ta furta, "To banda Iyayi me za'a gyara anan bayan ɗakin komai ya gyare yake" Ajiye jakar tayi a gefe ta zuba wani uban tsalle ta faɗa kan katifar, kamar wata ƙaramar yarinya haka ta dinga tsalle tana watsi da kayan dake kan gadon. Ta jima tana tsalle-tsallenta sannan ta dakko ta nufi bakin kan mudubi, tsayawa tayi tana ƙarewa kayan kai kallo, wani ɗan ƙaramin akwati ta gani da sauri ta janyoshi ta buɗe, wasu takardu ta gani buɗewa tayi amma sam bata fahimci ko takardun meye ba. A zuciyarta ta ayyana koma dai na meye tasan masu muhimmanci ne, ɗaga rigarta tayi ta soke su ta mayar da rigarta ta saki. komawa tayi ta gyara gadon da ta ɓatashi. fita tayi daga ɗakin taje ta ɗakko mofa. Lokacin da zata wuce su tafiya takr sumi sumi tana sunne kai ƙasa kamar wata ta kirki, komawa tayi ta goge iya abinda zata iya gogewa ta fice daga ɗakin zuciyarta fes, dan tasan ko a iya haka ta tsaya sai Fahad ya kusa kuka. Ballantana taci alwashin yanda ya tasota a gaba sai ta ƙure masa lamba. Lokacin da ta gama babu kowa a falon dan haka ta wuce bakin gate, lokacin Fahad ya fice daga gidan. Tana ƙarasawa bakin gate bancin Baba Maigadi ta gani, zama tayi akai lokacin ya shiga banɗaki. Yana fitowa ya samu Indo zaune akan benci, murmushi ɗauke akan fuskarsa ya ce, "Hajiya barka da fitowa" Indo ɗan waigawa tayi sai ta tuno da yadda maigadinsu na cen Kaduna yake bata girma, acikin zuciyarta ta ce, "Wayyo Allah! Ina ma su Zaliha na kusa suga yadda nake cin karena babu babbaka" a fili kuma murmushi tayi ta ce, "Yauwa Baba, Dan Allah Baba anan unguwar a ina zan sami kifi soyayye?" Ɗan jim yayi sannan ya ce, "Gaskiya Hajiya da ƴar tafiya sai anje cen titi" kuɗi Indo ta miƙa masa tace, "Gashi na ɗari biyu nake so" juyawa yayi hagu da dama sannan ya ce, "Tuba nake Hajiya amma a ƙa'ida banine me cefane ba, Hashimu Driver ne" Indo bata damu ba ta ce, "To ina Hashimun yake?" Baba maigadi ya ce, "Baya nan sai yamma yake shigowa" ganin zata ɓata lokaci yasa ta ce, "To bari kawai naje na dawo, amma duk wanda ya tambayeka ni kace baka ga fita ta ba" Zaro ido waje yayi saboda jin kalaman Indo, yana shirin magana Indo ta zare sakata ta fice" Indo tafiya ta dinga ti har sai da ta je titi ta siyo kifinta ta dawo, kuma koda ta dawo ta samu babu wanda ya neme ta. Lokacin da ta shiga falon sanɗa ta dinga yi kamar munafuka, wajen ɗakin Fahad ta nufa tana waige-waige. Sama-sama taji muryarsa yana waya yana cewa, "Kinsan dai nace miki ki daina kirana a waya idan har bani na nemeki ba, har yanzu abinda baki fahimta ba nifa ba maganar aure a gaba na yanzu, sai nan da ɗan wani lokaci" yana zuwa nan ya katse wayar. Ji tayi alamun ya shiga Toilet amma dan ta tabbatar sai ta fita ta zagaya ta windown ɗakin sa ta leƙa, da sauri ta koma ta tura ƙofar a hankali ta fara damƙar kifin tana wurgashi guri-guri har bakin gadonsa dan so take yana fitowa yayi arba dashi, wani kan kifi ta ɗauka ta jefa masa kan gado. A hankali ta lallaɓa ta fice daga ɗakin amma sai ta ɗan bar ƙofar ɗakin abuɗe, a bakin ƙofar ɗakinsa ma jajjefawa tayi har zuwar bakin ƙofar shiga falon, wani ta kuma ɗan damƙa a hannunta ta nufi cikin kitchen ta wurgar dasu guri-guri. Leda da takardar kifin ta yayyaga gutsi-gutsi ta wurgata bakin kantangar da tankin gidan yake kai, da yake nan ne kawai babu wayar shocking a jiki. Da sauri ta ƙarasa bakin famfo ta wanke hannunta, tana gamawa ta shiga ɗakin da aka bata wanda shine take kwana, banɗaki ta faɗa tayi wanda ta sako wasu riga da wando fari da baƙi, rigar ta saukar mata har gwiwa sai baƙar hular da ta ɗora akanta, tayi kyau sosai dukda ba wani make up tayi a fuskarta ba. Sabuwar wayarta da aka siya mata ta ɗauka ta fito Falo a ɓangaren dianning ta samu Mommy a zaune tayi mata barka da hutawa, ta wuce kitchen kamar me ɗaukan wani abu. Tana shiga ta fito tana ya mutsa fuska ta ce, "Mommy kuna da mage a gidan nan ne?" Mommy zaro ido tayi ta ce, "Wa? Rufa mun asiri! Ni da Fahad yake tsoronta, tun ina sha'awar kiwonta har na haƙura" Indo da sauri ta fice zuwa bakin windown Fahad, maƙale murya tayi ta fara kukan mage har da ɗan irin gurnanin nan da sukeyi, musamman idan suna faɗa. da sauri taji Fahad ya buɗe ƙofa zai fita itama tayi maza ta koma ciki tana cewa Mommy, "Aikuwa wallahi Mommy inajin mage ta shigo gidan nan, ɗazu na siyo kifi fa na kai kichen wai daga zuwa wanka kinga banganshi ba, kuma gana duk gashi nan an zuzzubar a ƙasa..." Tun bata rufe baki ba suka ga Fahad ya fito daga shi sai gajeren wando, jallabiyarsa maƙale a hammata yana ihu yana cewa. "Mommy! Mommy kina ina wallahi mage ta shigo mun ɗaki dan Allah kisa a fitar mun da ita" Indo dariya ce taso ƙwace mata amma sai ta maze ta ce, "Kai amma Yaya Fahad wallahi ka bani mamaki namiji da kai kana tsoron wata mage" harara ya watsa mata, bai tanka mata ba Mommy ta ce. "Ashe kuwa da gaske ne yanzu fa Humaira take gayamun ta siyo kifi bata ganshi ba" da sauri Fahad ya ce, "Wallahi ta kaishi ɗakina, har kan kifi na gani a kan gadona" Wannan karan saida Indo ta murmusa sannan ta ce, "Muje ka nuna mun daga ina kaji motsinta dan ni bana tsoron wata mage" Indo ta ƙarasa faɗa tana wucewa hanyar ɗakin nata, kamar wani yaro haka Fahad yabi bayanta yanayi yana ɗan miƙa wuya gaba, suna zuwa Indo kanta tsaye ta tura ƙofar ta shiga. Juyowa tayi ta ce, "Daga wajen ina take?" Fahad na maƙale ya nuna ɗan yatsa wajen bakin window yace, "Ta nan haka na ji kuka da motsinta" Indo ɗan tsuke fuska tayi ta ce, "Amma fa sai ka shigo ka ɗan riƙen labulen yadda zan kamata ta ruwan sanyi" Fahad cikin sanɗa ya tako ciki har ya haye kan gadon yaja labule ya riƙe, Indo sunkuyawa tayi tana leƙa ƙasan gadon, wata uwar ƙara ta saki ta nufi bakin ƙofa, kafin ta kai ga fita taji Fahad ya fusgota gefe ya zuba a guje. MASU COMMENTS INA GDY ILOBIYU LODI-LODI😘🥰😘😘😘😘🥰🥰 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [19/09, 18:32] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 81&82 Indo faɗuwa tayi shi kuwa Fahad tuni ya daɗe da barin gurin, kwanciya tayi tana dariya harda riƙe ciki. Sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe ta fito daga ɗakin a guje, kamar wacce ta ga wani abun tsoro, lokacin da ta zo falo Mommy ta hango a ƙofar kitchen, Indo tsayawa tayi tana haki ta ce,"Mommy Ina Ya Fahad ne" Mommy ta ce, "Na ga ya fito da gudu yayi ɗakinki, wai magen ce ta biyoku ne? Humaira Idan bazaki iya ba ki kira Baba Maigadi ya fitar da ita." Indo ta ce, "Haba Mommy magen ce zata gagareni, muna shiga Ya Fahad ya ɓatamun shiri ta shige ƙarƙashin gado, shine ya zubo a guje." Indo ta faɗa tana bin hanyar ɗakinta. Koda ta je kanta tsaye ta buɗe ƙofar ta shiga tana cewa, "Ya Fahad wai dama haka kake da tsoro kana ina?" mamaki ne ya kama Indo da taga ba Fahad ba alamunsa, dariya tayi a fili ta ce, "Dama duk basarwar da hura hancin da yake na banza ne, wai mage ita ƙaton gardi yake wa gudu" tana shirin fita ta ji motsinsa ya fito daga drower kayanta, fuska a murtuke ya ce, "Ke wa kike gayawa haka?" Indo ƙare masa kallo tayi wannan karan ya sa jallabiyarsa sai dai a juye ya sa ta gaba a baya, dariya ta farayi ganin yadda duk yayi wani fiƙi-fiƙi da shi, takaici ne ya kamashi kamar zaiyi mata magana sai kuma ya ƙyaleta, Indo shiru tayi ita ta tsuke fuska ita nan a dole batasan raini ta ce, "Wallahi sai dai ka tsukewa wasu fuska badai ni ba, sai kace bakai ka bangajeni ka zuba a guje ba, shine kazo mun ɗaki ka wani ɗafe drower kamar wani biri ay..." hannu ya sa ya bige mata baki ya riƙe kunnenta da ƙarfi yana murzawa ya ce, "Ki dinga iya bakinki akan rashin kunyar nan taki sai na basa bakinki" Indo duk yadda taso fusgewa ta kasa, sai da ya ga dama dam kanshi ya saketa yana sakinta ta watsa masa harara ta ce, "Chab wallahi ka fasa mun baki dan kuwa ka gane wace Sarƙa, kuma wallahi bazan fitar maka da magen ba kaje ka nemi me fitar maka, kuma Malam ka fice mun daga ɗaki." Ta sauri ya kai hannu da niyyar ya wanketa da mari, amma sai ya fasa ya damƙi gashin kanta har sai da ta saki ƴar ƙara, ƙirjinta sai bugawa yake saboda tsoro amma sai ta dake ta ce, "Ka sakarmun kaina idan ba haka ba wallahi na tada aljanu na kowa a gidan nan bazaiji daɗi ba." Dukda Fahad na cikin fushi bai hanashi yin murmushin gefen baki ba, wani uban ranƙwashi ya sakarwa Indo a tsakiyar ka wanda bata taɓa tsammani ba, sannan ya ce, "Taƙama kike da aljanu ko?" to ki tayar da su bisimillah" Bai ƙarasa faɗa ba yaji jikin Indo ya saki, wata uwar ƙara ta ƙwallah ta yanke jiki ta faɗi. Fahad gaba yayi yana cewa, "Lallai yarinya naki wasa ne, makircin mata wanne ne bansani ba zama ki tashi da kanki" yana gama faɗa ya fice daga ɗakin ko ƙofar ɗakin bai tsaya janyowa ba. Yana zuwa Falo Mommy ta ce, "Fahad zanga ranar da zaka daina tsoron mage, ina ka baro ƙanwar ta ka? Ba ita zata fitar maka da ita ba..." Mommy bata ƙarasa magana ba suka ji ihun Indo tare da jin ƙarar fashewar abu, da sauri suka juya suna kallan ƙofar ɗakin da Indo take ciki, ƙarar fashewar abun yayi dai-dai da fitowar Aunty Safna, tana ƙarasowa ta ce, "Subhanallah ƙarar meye haka?" Kafin su bata amsa suka kuma jin wata ƙarar, da gudu suka nufi hanyar ɗakin dan ganin abin da yake faruwa. Suna zuwa da tsananin mamaki suka fara kallan Indo wacce take ta fashe-fashen abubuwa, hannunta jini ne kaɗan yake zuba, jin motsin mutane ne yasa ta juyo idanunta a juye ta nuna su tana cewa. "Ku fice mana daga ɗakin nan bama buƙatar ganin kowa tun bamu illata ku, ko mun salwantar da rayuwarku ba" Sosai suka tsorata da ganin yanayin da Indo take ciki, Fahad ne yayi ƙarfin halin cewa. "Ke wai baki da hankali ne me yake damunki, dama aljanin ƙaryar da kika ce zakiyi dama ɓarna zakiyi? Bakya ganin yadda kike jiwa kanki ciwo kina hauka ne...?" Cikin tsawa Indo ta ce, "Rufe mana baki, bama buƙatar shirmenka a gurin nan" Fahad da sauri ya ƙarasa gurinta ya fisgo hannunta da niyyar ya janyo ta, daga gurin saboda ƙwalaben da ke zube a gurin. Fahad bai ankara ba yaji Indo ta fuske hannunta haɗe da hankaɗashi jikin bango, cikin jin zafi ya ce, "Auch" Aunty Safna ce ta ƙarasa ta riƙeshi, kallan Indo tayi ta ce, "Ke me yake damunki ne?" da wata irin murya Indo ta ce, "Na gaya muku ku fice ku bamu guri, tun bamu sauke fushinmu akanku ba" Mommy ce ta sha jinin jikinta, dafa Aunty Safna tayi ta ce, "Safna yarinyar nan fa da alama ba ita bace kamar shafar jinnu ne a jikinta." Aunty Safna zatayi magana Fahad ya ce, "Ina zuwa" Toilet ya faɗa ya ɗauro alwala sannan ya ce Mommy ta miƙo masa ruwa a kofi, babu jimawa Mommy ta kawo masa ya ƙarɓa ya fara karanta ayoyin tsari daga cikin ayoyin Alƙur'ani. Ganin ya fara tunkarota yasa Indo ta fara ja da baya dariya na niyyar kubce mata, yana zuwa yayi bismilla yana mata tofi tare da yayyafa mata ruwan Addu'a, da ƙarfinta Indo ta fara kaiwa Fahad duka sannan ta ƙwallah wata irin ƙara ta durƙushe a gurin babu jimawa jikinta ya saki ta faɗi gefe tana numfashi. Bayan wani lokaci ɗagowa tayi a hankali ta tashi tana dafa kanta, kamar wacce tayi aljanun gaske. Ganin jini a hannunta yasa ta juya tana ƙarewa ɗakin kallo, hango Fahad tayi a gefe ta watsa masa harara a fili ta ce, "Dama rashin imanin naka har ya kai ka fitar mun da jini a jiki, wallahi Ya Fahad ka kiyaye ni tun kafin..." Aunty Safna ce ta katse ta tana mata faɗa, Mommy riƙo hannun Indo tayi suka wuce Falo, fitar su tayi dai-dai da zuwan Family Doctor ɗinsu, ciwukan jikin Indo ya shiga gyarawa haɗe da sa mata magunguna, ita kuwa sai wani basarwa take tana cije baki. Fahad da kansa ya fita ya kira Baba me gadi dasu Badaru, ɗakinsa suka shiga suka fara dubawa sai da suka yiwa komai filla-filla, amma babu mage babu alamarta har cikin toilet suka duba. Share ɗakin sukayi har zuwa falo da duk guraren da Indo ta barbaɗa kifin suka goge, Mommy ce ta fesa turaren ƙamshi ta koma cen gefen Indo ta zaune, Fahad jiki a sanyaye ya shigo falon ya zauna. Shi ba abin da Indo tayi ne yake bashi mamaki ba, tsoronsa ɗaya da su Baba megadi suka duba ɗakinsa da sauran gurare amma ba mage ba alamarta. Mommy ce ta ce, "Habibi lafiya kuwa? Indai jikin Humaira ne da sauƙi sosai, dan munyi waya da Daddynku insha Allah gobe zamu gurin masu magani." Indo gabanta ne ya faɗi, a zuciyarta ta ce, "Na shiga uku karfa su kaini gurin masu riƙiyya asirina ya tonu" amma a fili sa ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Mommy nikam na warke dan wallahi bana ƙaunar shan magani daga na bature har na gida" Fahad taɓe baki yayi ya ce, "Mommy nifa ba wannan ne damuwata ba, babban tashin hankali na da aka duba ba'a ga magen nan ba." Indo murmushi tayi a fakaice da sauri ta ce, "Cab Allah sa ba aljana ka haɗu da ita ba, dan haka ya taɓa faruwa lokacin da ina Kura. Aljanar mage ta shiga gidan su Harisu, shu'umar aljanar magen nan har ƴaƴan gidan ta fara taɓawa" Fahad cikinsa ne ya karta take gumi ya tsatstsafo masa, ita kanta Mommy sai da gabanta ya yanke ya faɗi jin abinda Indo ta faɗa. FATAN ALHERI❤️😘 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [21/09, 12:43] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 83&84 Fahad sosai ya zuba mata ido dan gano gaskiyar abinda ta da faɗa, amma sai ya gagara fahimtar haka a ɗan tsorace ya ce, "Habeebty wai Aljanu na irin haka?" Mommy da har lokacin a tsorace take ta ce, ,"Eh to kasan komai akace aljani lamarin sai Addu'a" Fahad ya ce, "To kuwa zanje inkira Malam Khalid ai basufi ƙarfin ayar Allah ba" Indo ba haka ta so ba, amma dan karsu gano ta sai ta basar. Mommy ta ce,"To Allah ya tsaremu daga sharrinsu" daga haka Fahad tashi yayi ya fice daga falon. Yamma liƙis Fahad ya shigo shi da Malam Khalid, ɗakinsa suka shiga Malam ya zauna ya fara karatu ya jima yanayi, amma babu wani abu da yaji ko ya gani da zai baka shaidar da shafar aljanu a ɗakin, bayani yayi wa Fahad kuma ya gamsu sannan ya sanar da shi zai yiwa Indo ruƙiya. Kai tsaye Fahad ɗakin Indo ya wuce sau biyu kawai ya ƙwanƙwansa, yana shiga ya sameta kwance a kan katifa sanye da wata doguwar rigar, rigar roba ce dan ta ɗan kamata, kanta ko ɗan kwali babu. Fahad wani abu ne ya tsarga masa baisan lokacin da ya shagala da kallonta ba, sai ji yayi ta ce, "Ya Fahad yanzu kuma me ya kawo ka ɗakina? Ko yanzu ma zuwa zakayi ka dake ni" sai ta nutsuwarsa yayi ya ce, "Ki fito akwai mai ruƙƙiya a falo" Indo ɗan tsorota tayi, da sauri ta ce, "Me ya haɗani da me ruƙiyya ko nice na koma maka magen?" maganar Indo taso bashi dariya amma sai ya kanne ya ce, "Ai da zaki koma magen ma da nafi kowa murna, inɗaukeki inkaiki cen waje na yar ko na huta" yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin. Indo kanta tsaye ta fito itama falon, lokacin da ta ƙaraso Falon Malam Khalid na zaune da sallama, ta shigo falon ta nemi kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fahad da ya shiga kitchen domin ɗebo ruwa a kofi, yana zuwa falon ya bugawa indo tsawa, "Ke! Baki da hankali ne? Wuce ki sako hijabinki" Indo ta ɗan tsorota da yanayin da ta ga Fahad a ciki, amma sai ta shanye tsoronta ta ce, "Ya Fahad ruƙiyar ce har sai na sa wani hijabi meye haɗin aljanu da hijabi na ko..." tun bata rufe baki ba ya tunkaro gurin da take a hassale ya ce, "Zaki wuce ko sai na karya ki a gurin nan" nan take fuskar Fahad tayi jawur jijiyoyin wuyansa duk sun tashi, Indo shiru tayi gabanta sai faɗuwa yake, wannan karan ba ƙaramin tsoron Fahad taji ba. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya ƙarasa gurin ya fisgi hannunta, ya wuce da ita har ɗakinta. Yana shiga ya ce, "Wallahi idan kika kuma fitowa a haka sai na baki mamaki" yana faɗa ya bar gurin ya koma falon. Bayan Fahad ya koma ya ce, "Malam kayi haƙuri kasan lamarin mata sai a hankali ." Malam Khalid ya ce, "Malam Fahad kasan mata sai da lallami, tunda matarka ce ka dinga janta a jiki bare kaga da ƙuruciya, sai kana kauda kai. Yanzu ka je ka lallasota ku fito tare, kasan ko jinnun jikinta zasu iya sata wasu abubuwan" Fahad tashi yayi ya wuce ɗakin yana jin zafin Malam dan ya dangantashi da mijin Indo, sai dainta wani fannin tausayinta yaji da ya tuna aljanin da suke jikinta, yana zuwa ya same ta zaune akan katifa ta rafka tagumi kamar wata mutuniyar kirki, cikin sanyin murya yace, "Ki sako hijabinki ki fito Malam yana jiranki" bata ɗago ta kalleshi ba, itama muryarta a sanyaye ta ce, "Ni ka ƙyaleni na fasa zuwa, a ƙyale aljanun su mun duk abinda zasu mun kowa ya huta, tunda dama ba sona ake ba." bakinta yake bi da kallo da yadda take motsa su, lumshe ido yayi ya girgiza kai. Har zai mata faɗa sai kuma ya tuna maganganun Malam, ƙasa-ƙasa ya ce, "To ni da ba mijinta ba? Meye zan wani lallame ta" sai wata zuciyar ta ce masa, "Amma ko ba komai ƴar uwarka ce ta jini" tsugunnawa yayi gabda ita har suna jin numfashin juna ya ce, "Kinsan mutumin nan saboda mu yazo, idan yaga baki fito ba bazai ji daɗi ba. Kuma wa yace miki bama sanki? Da bama sanki zamu nemo miki mai maganin warakar lalurarki?" Indo ware manyan idanunta tayi ta shagala da ƙarewa Fahad kallo, da yadda yake sarrafa laɓɓansa yake mata magana, cikin zuciyarta take ayyana dama Fahad ya iya tausasa murya wajen kalamai? Amma komai yake mata cikin masifa da hantara." ganin ta shagala da kallonsa yasa hannun saitin fuskarta, yana murza ƴan yatsunsa. Sai a lokacin Indo ta farga wata ƴar kunya ce ta kamata, shi kuwa tsuke fuska yayi kamar zai yi mata magana sai ya tuna, yana mata magana yasan zai iya wargaza komai zata iya ƙin fita. Miƙewa yayi ya ce, "Sauri ki fito yana jiranki" yana fita Indo ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Nan take ɗaya daga sashen zuciyarta ya ce, "Me yake damunki? kin manta waye Fahad? Kawai dan ya tausasa miki harshe na lokaci ɗaya, har zaki fara tunaninsa." guntun tsaki tayi a filinta ce, "Ko meye abin tunani akan wancen oho, dukda kamar su ɗaya da Yaseer amma Yaseer ya fishi komai" tana gama magan ta ɗau hijabi ta fice. Tana zuwa ta hau kan kujera ta ƙame guri ɗaya, Malam Khalid alwala ya ƙara ɗaurowa sannan ya zauna ya fara karatun alƙur'ani. Sai da Malam Khalid ya shafe awa ɗaya cif amma ko motsi baiga Indo tayi ba, kallan Fahad yayi ya ce, "Malam Fahad muje inasan magana da kai" Malam na gama maganar ya nufi bakin ƙofar, da sauri Indo ta ce, "Malam angama ruƙiyyar zan iya tafiya?" Malam yace, "Eh! Zaki iya tafiya" Indo kamar dama jira take tun bai rufe baki ba, ta tashi zata wuce sashenta su Momma suka fito. Da mamaki suka bi Indo da kallon ganin tasha zumbulelen hijabi, barka da hutawa tayi musu ta wuce ɗakinta. Malan ya gaida su Mommy sannan ya koma suka zauna gabaɗaya, ya fara musu bayani akan ruƙiyyar da aka kirashi yayi. Sai dai sam babu wasu ginnu a jikin Indo, mamaki sukayi suka kawo kuɗi suka bashi tare da yi masa godiya, ya yi musu sallama ya tafi. Mommy ce ta kalli Momma ta ce, "Amma lamarin da mamaki fa" Momma ta ce, "Wallahi nikam banyi mamaki ba idan kika tuna da lamarin da su Baba Huwaila suka bamu, wallahi nifa dama jikina bai bani aljanu bane shaƙiyancin yarinyar nan yawa gareshi" Fahad dake gefe ya ce, "Amma wallahi yarinyar nan data gane kurenta" yana gama magana ya nufi ɗakin, Indo ta cire hijabi kenan Fahad ya ja hannunta ko magana babu, bai dire ta a ko'ina ba sai gaban su Mommy. Aunty Safna ce ta rufe da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Mommy ce ta karɓe zancen cikin lallami da nasiha. Nasiha mai kashe jiki Mommy tayi mata tare da nuna mata illar kwaikwayon abinda takeyi, sosai jikin Indo yayi sanyi nadama ƙarara ta hau kan fuskarta. Su Mommy sun lura da haka ita kanta Aunty Safna ba ƙaramin daɗi taji ba, ganin yanayin da Indo ta shiga na nutsuwa. Fahad kallan Indo yayi ya ce, "Allah sa dai ta ɗauki faɗan da akayi mata, dan Allah Aunty ji yadda take sunne kai kamar ta kirki" Aunty Safna ta ce, "Kaima dai ka faɗa Fahad, wai a haka Yaseer yake so da wannan sakarcin nata" Indo zumɓurar baki tayi gaba ta ce, "Dan Allah Ammi ku daina faɗa a gaban Ya Fahad karya rainani" Indo ba ƙaramin dariya ta bawa su Mommy ba, Aunty Safna ta ce, "Wane raini kuma bayan shi ya fara saninki a lokacin da kike ƴar ƙauyenki, ba yanzu da kike waye ba. Ai wallahi kome kika zama yanzu Ɗana Fahad ne sila" Fahad kansa murmushi yayi, ko ba komai ya samu abin gori nan gaba, Indo kamar zatayi sabida takaici. Mommy ta ce, "Rabu da su Humaira, kice asalin kowa ma ai ƙauye. Kuma cen ɗinma ai a gida kike tunda kin rayu da Kawunki Maigari" Indo kamar wata yarinya ta yiwa Fahad gwalo, sannan ta ce, "Yauwa Mommy naji kince Maigari ɗan uwanku ne, amma banji kun gaya mun alaƙarku da shi ba rannan" Mommy ta ce, "Mahaifinsa da Mahaifin abokan wasa suke, lokacin da Mahaifinmu zaizo garin saida ya yiwa mahaifin Maigari tayin zuwa amma yaƙi, sai wani zuwa da Mahaifinmu yayi suka taho tare, har dai Allah ya sa shima yayi tunanin dawo da iyalinsa garin nan. Amma shi Mahaifinsa sai ya fara safarar kaya yana kaiwa garin Kura, har aminci ya haɗasu da Maigarin wancen lokacin. Humaira labarin yana da tsayi a takaice dai Maihafin Maigari ya zamu zama a wancen garin kuma mutum ne me amana, da tsoron shiga haƙƙin wani. Lokacin da Maigarin wancen garin ya fara wata jinya, sai yayi sanarwa tare da saka sojojin masarauta, ya sa hannu akan ko da bayan ransa Mahaifin Maigari, shi zai cigaba da mulkarsu saboda tausayinsa da amanarsa. To kinji yadda akayi, banda ma zumuncin yanzu ya zama yadda ya zama, dama duk cikin ƴan uwana ba yabon kai ba nafi su ƙoƙarin zumunci, kuma da har zuwa Kura muke muna zuwa mu shafe watanni a cen. Ni da kike gani a cikin garin da kikayi rayuwa babu inda bansani ba, idan na fara baki labari sai mu kwana anan." Indo ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Taɓ amma wallahi Maigari nasha da ƴan ƙauyen nan sam be ɗauko halin mahaifinsa ba, zalinci a cikin mutumin nan kamar..." da sauri Mommy ta ce, "Gidanku Humaira" Fahad yayi karaf ya ce, "Ku barta ta faɗa dan ni kaina wani zuwa da mukayi inaji wasu mutane na zaginsa, wai ya cinye wata gonar gadonsu" Aunty Safna ta ce, "Ƙaniyarka ana kwaɓar ƙanwarka kana kuma sakin bakinka" Fahad dariya yayi ya tashi zai shiga ɗakin, Indo ta ce." Ai wallahi nina saita shi sai da ya mayar musu da dik gonakinsu" da mamaki ta fara suka kalleta, gyaɗa kai Indo tayi basu labari tun daga lokacin da aka damƙawa Maigari takardunta, da ɓadda kamar da sukeyi ita ƙawayenta. Hatta ludayin da suka dinga ranƙwalawa Maigari sai da ta faɗa da umarnin da suka bashi akan ya mayar wa da mutane dukiyarsu. Fahad duk gimtsewar da yakeyi sai da ya dinga ƙyalƙala dariya, su Mommy dariya suke harda hawaye sai da suka tsaida, Mommy ta ce, "Dama Humaira ke kika rikitamu ɗan uwa lokacin da muka je" Indo dariya tayi ta ce, "Mommy nima ai Ya Fahad tasoni yayi saura kaɗan asiri na ya tonu, wallahi da ya kamani da na kaɗe dan ƴan garin nan sai mun tofin Allah tsine" Fahad me zaiyi banda dariya, Aunty Safna ta ce, "Ikon Allah wato mu duk shakiyancin ƙuruciya da mukayi muna yara, bamu kama ko rabinki ba Humaira. Allah ya ƙara shirya mana ku gabaɗaya." gabaɗaya suka amsa da Ameen, suna nan zaune Daddy mahaifin su Fahad ya shigo hannuwansa riƙe da su Aseem, zama sukayi suka cigaba da hira cikin barkwanci. Alhaji Mahmud Lamiɗo shine ainihin sunan Mahaifin su Fahad, asalinsa Fulanin daura ne. Sai dai kakanni da iyayensa a buɗi ido ya gansu a cikin garin Kano, Iyayensa sun rasu bayan haihuwar su Fahad babu jimawa, Su uku ne rak a gurin iyayensa. Shine babba sai ƙannensa mata biyu, Alhaji Mahmud ɗan kasuwa ne saboda baiyi wani zurfi a karatun boko sosai ba, Allah ya bunƙasa kasuwancinsa har ƙasashen waje yana fita sarin kaya. Mutum ne mai matumci da karamci gashi da zumunci da taimakon marasa ƙarfi, uwa uba gashi da alheri da sakin fuska. MU KOMA LABARI Kwanan su Indo biyu suka wuce garin Kaduna, wannan karan ma ba tare da Fahad suka wuce ba, saboda wani uzuri da zai gabatar kafin komawarsa. Indo ji tayi kamar ta je ta ajiye masa takardar da ta ɗauka, amma sai kawai ta share har suka koma. Makaranta me kyau Mahaifinta ya nemar mata idan tare da direban da yake kaita, yana dawo da ita. Wannan karan a JSS3 aka sakata tare da ɗaukan malam da suke yi mata lesson a gida, makarantar su Indo haɗe take da islamiyya basu suke dawowa gida ba, sai gabanin magriba. Wannan dalilin yasa koda Fahad ya koma basu cika wani haɗuwa ba. Indo batasan yadda akayi Yasir ya samu lambarta ba, amma kodai mene ne tasan a gurin Momma ya ƙarɓa, Indo tun tana fushi da Yasir har ta sakko suka cigaba da mutumci, kamar yadda Indo ta ɗauka tunda har yau Yasir bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba. Wata ranar Asabar Indo na cikin garden Yasir ya kirata a waya, sun shafe awa guda suna waya banda murmushi babu abinda take, wani lokacin sai dai ta tuntsire da dariya, kome Yasir ya gaya mata ta miƙe tsaye tana murna harda tsallenta. Dun abinda takeyi Fahad na tsaye yana kallanta wani ƙululun takaici ne ya rufeshi, Bai ankara ba yaji tace, "Wallahi nima nayi missing ɗinka Ya Yasir, amma kasan me zaka siyo mun idan zaka zo?" Kafin Yasir yayi magana Fahad ya ƙaraso a zafafe ya fusge wayar, kasheta yayi gabaɗaya fuska a tamke yace, "Ƙaramar yarinya da ke har kin iya soyayya ko? Shi kansa Yasir ɗin zamu gauraya dashi, zanga wanda zai ƙara baki waya yanzu" Indo batasan lokacin da hawaye ya fara zubar mata a fuska ba, da gudu tabi ta gefensa ta wuce ɗakinta. Iska mai zafi Fahad ya fesar ya wayar a aljihu ya bar gurin. AKWAI ƘURA🙊🤣😂 KUYI HAƘURI DA KURAKUREN CIKI. WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA ƳAN GROUP ƊINA NA *AMEERA ADAM FANS GROUP* DA MUTANENA ƳAN AMANA TA *WATTPAD* _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 85&86 Aunty Safna na falo Indo ta shiga falon da gudu, da ido ta bita da kallo har ta shige ɗaki. Bata bi ta kanta ba saboda tasan wataƙila ita da Fahad ne, faɗansu kuwa bata shiga dan baya ƙarewa daga wannan sai wannan. Fahad ɗaki ya shiga banda zarya babu abinda yakeyi, wayar ya ciro daga aljihu ya kunna domin ya shiga ciki yaga abinda take shukawa, sai dai password ɗin da yaci ƙaro dashi ne ya dakatar da shi. gwada lambobi ya farayi amma babu wacce tayi dai-dai, sai yayi tunanin bari ya sa 1234 yana sakawa ta buɗe. yana shiga cikin gallery ɗinta ya shiga ɓangaren camera, banda hotunanta dana su Aseem babu komai, whatsapp photos ya duba nan yaci karo da hotunan Yaseer ne birjik, har sai ɗaiɗaikun hotunan Jamilu, da wasu tsurarin ƴanmata wanda da alama ƙawayenta na makaranta ne.Da sauri ya fita ya koma cikin Whatsapp ɗinta, Ya Yaseer ya gani da sauri ya shiga, baiga wata doguwar hirarsu banda gaisuwa, sai kuma Assignment da take rubutawa take tura masa sai ya koya mata. fita yayi ya koma cikin lambar Jamilu da yaga anrubuta, Abokin Faɗa. Yana shiga ya fara duba hirarsu wacce rabi Voice note ce ba typing ba, ɗaya bayan ɗaya ya fara buɗewa yana saurara. Yawanci hirar tasu ta ƴar tsama ce sai wani lokacin gaisuwa ce, wani lokacin kuma labarin makarantarsu da take yawan bashi. Shima tana tura masa Assignment da yake koya mata, amma abin da ya dagula zuciyar Fahad da kodayaushe zaiji Jamilu na cewa Indo yayi missing ɗinta, wasu Voice note da ya ji Jamilu da Indo sunyi ya kunna su yafi a irga wanda Jamilu ya ce, "Ayusher yaushe zaki zo mana hutu ne?Saboda na nayi missing ɗin tsiwarnan taki" Indo ta ce, "Ya Jamil dama wai kana sona amma da sai kayi ta dukana" Jalimu ya ce, "Ayusher meyasa kika tambayeni?" Indo murmushi tayi ta ce, "Naga Baba Huwaila ce kawai take so na duk faɗin ƙauyen nan, bayan har kaini kake gurin Maigari ya dokeni" Jamilu ya ce, "Ayusher ni kuwa nake sanki! Bazan taɓa fasalta irin ƙaunar da nake miki ba. Amma lokaci na gabda zuwa da zan sanar dake abinda ya daɗe yana cimun tuwo a ƙwarya. Kina da Saurayi kuwa" Gaban Indo ne faɗi, murya a sanyaye ta ce, "Ya Jamil ba kai kake hanani kula kowa ba bayan su Zulai duk da samarinsu, kace har ansa ranar su." Jamilu ya ce, "Ai ba a ƙauye nake nufi ba, ina nufin anan Kaduna" da sauri Indo ta ce, "Cab bana kula kowa, bare mugun nan Ya Fahad yana nan ina zai barni na kula kowa" Gaban Jamilu ne ya faɗi amma sai ya basar ya ce, "Kintuna dai a ƙauye abinda ya taɓa faruwa da Hansa'u ko? To karki yadda ki kula kowa da sunan soyayya, idan lokacin yayi ni zan gaya miki, ko kuma na samo miki miji mai hankali kuma ɗan gayu ko bakya so?" Indo kunya taji kamar yana ganinta ta rufe fuska sannan ta ce, "To ya Jamil, amma karka samo mun mai mugunta kamar kai, kuma kyakykyawa nake so kamar kai ko wanda ya fika " ba ƙaramin dariya ta bawa Jamilu ba, Saboda ya lura har yanzu da sauran yarinta a kan Indo, yace "To shikenan ai dai-dai ke zan samo miki" sun jima suna hira sannan sukayi sallam. Fahad ba ƙaramin shaƙa yayi ba, kashe wayar ya ƙarayi sannan ya koma kan katifarsa ya kwanta. Bayan Magriba su Indo na zaune gabaɗaya suna cin Abinci, Fahad ya shigo da kofi a hannu da alama tea yake sha, Bayan ya zaune Indo miƙewa tayi zata bar falon Aunty Safna ta ce, "Humaira wai me akayi miki kike ta ɓata rai kamar wacce taci kashi?" Indo kamar jira take nan take idanunta suka ciko da ƙwalla, murya na rawa ta kalli Fahad ta ce, "Haka kawai ina zaune Ya Fahad ya karɓe mun waya, kuma waya muke da Ya Yaseer nasan yanzu haka ya neme ni bai same ni ba" Fahad ɗan zaro ido yayi wato ita bata ma kunyar faɗar wayar da take yi, har take jimamin kar Yaseer ya kira bai samu ba. Yana cikin tunani Aunty Safna ta ce, "Da abinda kikayi dan ruwa baya tsami banza" ganin angoyi bayan Fahad yasa Indo bata ƙara magana ba ta wuce ɗakinta. Tunda Fahad ya karɓi wayarta bai bata ba. Kuma itama bata tambayeshi ba, sai bayan wasu watanni sannan ya bata wayar tare da canza mata layi, da kamar bazata karɓa ba ta karɓe abarta tana watsa masa harara.Tun daga lokacin Indo bata kuma shiga sabgar Fahad, shi ɗinma bai cika shiga sabgarta ba. Sai dai duk wani moshi da Indo takeyi akan idonshi takeyi. BAYAN SHEKARA BIYU Watarana Indo ta dawo daga makaranta da yamma liƙis, tana shigowa kamar a mafarki ta hangoshi zaune akan kujera da waya a hannunsa yana dannawa, cikin bazata gabanta yayi mummunar faɗuwa. Dukda shi ba fari bane amma ba ƙaramin canjawa taga ya yi mata dukda batafi wata shida rabon da tayi tozali da shi ba, kyawunsa ya ƙara fitowa har wata ƴar ƙiba taga ya yi. cikin murna ta jefar da jakarta gefe ta zuba da gudu kamar zata rungumeshi sai kuma ta tsaya, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce, "Ya Jamil kaine! Wow dama zaka zo amma ko jiya a waya baka gaya mun ba, ina My Baba Huwaila wallahi nayi missing ɗinku gabaɗaya, Ya Jamil ka ga yadda ka ƙara kyau kuwa" tana faɗa ta ɗan taɓe baki ta cigaba da cewa, "Inama yadda ka ƙara kyau haka ka daina mugunta amma ina wallahi nasan halinka yana nan, Yauwa ya wajensu Zulai yanzu ƴaƴanta nawa?" Kafeta yayi da kallo, wani abu na tsarga masa cikin jikinsa. Ganin ya tafi duniyar tunani yasa Indo ta hura masa iska a fuska, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu Ayusher wacce tambaya kikesan na fara amsa miki?" ya ƙarasa faɗa yana harɗe hannuwa a ƙirji. Tura baki gaba tayi cikin shagwaɓa ta ce, "Ni duka zaka amsa mun" Murmushi yayi ya ce, "To ko zan amsa miki sai kin cire Uniform ɗinki kin huta tukunna" ɗan ɓata fuska tayi zatayi magana ya sa ɗanyatsansa akan laɓɓansa, sannan ya ce, "Kinsan dai bansan..." da sauri Indo ta karɓe zancen da, "Banasan musu, kedai Allah ya yi ki da kunnen ƙashi taurin kai kamar mutanen farko." gabaɗaya suka kwashe da dariya, Jamilu ya ce, "Shiyasa nake missing ɗinki Sarƙar Baba Huwaila yanzu gidanmu duk ba daɗi saboda bakya nan" Indo ta ce, "Ai nasan kashedin ka kenan shiyasa tuni na haddace shi." Duk abinda yake faruwa Fahad dake cen jikin mota yana jinsu kuma yana ganinsu, takowa yayi fuska a haɗe ya ce, "Ke! ba daga makaranta kika dawo ba, wuce ki shige ciki banasan sakarci" Indo ta ce, "Ya Fahad rabin raina na gani, kasan kuwa yadda nakeji da Ya Jamil kuwa? Tagwayen Baba Huwaila wasu ke kiranmu dan Allah ka barmu muyi hirar yaushe gamo" Jamilu wani irin daɗi yaji har cikin ransa, ko ba komai yasan Indo ta bashi babban matsayi. Fahad jin maganganun Indo yayi kamar saukar aradu, yana shirin magana Jamilu ya ce, "Wuce cikin gidan, kinsan banasan rashin kunya..." da sauri Indo ta kuma karɓe zancen da, "Kinsan dai banasa rashin kunya, dan wani lokacin kamar ɓeran birni haka kike" Jamilu murmushi yayi ya taka ya ɗauko mata jakarta ya miƙa mata sannan Indo ta wuce. Fahad sai lokacin ya bar gurin yabi bayan Indo suka wuce ciki, Jamilu yaji ba daɗi sosai dan idan duba alaƙar da ke tsakanin Indo da Fahad sai ya ga kamar zai rasa ta gabaɗaya, dan duk mai hankali yaga abinda Fahad yakeyi yasan Zallar kishi ne yake sashi. Alhaji Khaleel yaji daɗin zuwan Jamilu akan lokaci dukda bai sanar dashi dalilin kiran da yayi masa ba, kafin zuwan nasa. Da daddare suna zaune shi da Fahad,Jamilu da Mommy ya ce. "Nasan zakayi mamakin jin kiran da nayi maka! Jamilu dalilin da yasa na kiraka ba komai bane sai dan na damƙa amanata ta agurinka, saboda na yaba da hankali da nutsuwarka, na tabbata ko bayan rayuwa ta bazaka ci amana ta ba, zaka riƙe hannu bibbiyu tsakaninka da Allah " Tunda Mahaifin Indo ya fara magana gaban Fahad yake lugude jikinsa har rawa yake, wani irin gumi ne yake keto masa dikda Ac dake cikin falon. Alhaji Khalil ya cigaba da cewa. "Ban yanke wannan shawarar ba sai da muka tattauna da ƴan uwana, kuma suma ba ƙaramin dadi suka ji ba, danma basa ƙasar da su zasu tattauna da kai ba ni ba. Haka Kawunka Alhaji mun sanar da shi komai kuma yayi farin ciki sosai, sai dai mun roƙi alfarmar karya sanar da kai dan nafisan naji komai daga bakinka." fuskarsa ce ta sauya cikin damuwa ya cigaba da cewa, "Sai dai bansan ya zaka ɗauki lamarin ba zaka amince ko bazaka amince ba shine damuwa ta" a firgice Jamilu da Fahad suka ɗago da kai suna kallan Alhaji Khalil a yayin da ya dire a zancensa. Hmmmm wallahi akwai ƙura bari nayi nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ Naga bakya comments sosai 😥 kuyi haƙuri mu raka dan littafin yazo ƙarshe. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [24/09, 13:08] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 85&86 Aunty Safna na falo Indo ta shiga falon da gudu, da ido ta bita da kallo har ta shige ɗaki. Bata bi ta kanta ba saboda tasan wataƙila ita da Fahad ne, faɗansu kuwa bata shiga dan baya ƙarewa daga wannan sai wannan. Fahad ɗaki ya shiga banda zarya babu abinda yakeyi, wayar ya ciro daga aljihu ya kunna domin ya shiga ciki yaga abinda take shukawa, sai dai password ɗin da yaci ƙaro dashi ne ya dakatar da shi. gwada lambobi ya farayi amma babu wacce tayi dai-dai, sai yayi tunanin bari ya sa 1234 yana sakawa ta buɗe. yana shiga cikin gallery ɗinta ya shiga ɓangaren camera, banda hotunanta dana su Aseem babu komai, whatsapp photos ya duba nan yaci karo da hotunan Yaseer ne birjik, har sai ɗaiɗaikun hotunan Jamilu, da wasu tsurarin ƴanmata wanda da alama ƙawayenta na makaranta ne.Da sauri ya fita ya koma cikin Whatsapp ɗinta, Ya Yaseer ya gani da sauri ya shiga, baiga wata doguwar hirarsu banda gaisuwa, sai kuma Assignment da take rubutawa take tura masa sai ya koya mata. fita yayi ya koma cikin lambar Jamilu da yaga anrubuta, Abokin Faɗa. Yana shiga ya fara duba hirarsu wacce rabi Voice note ce ba typing ba, ɗaya bayan ɗaya ya fara buɗewa yana saurara. Yawanci hirar tasu ta ƴar tsama ce sai wani lokacin gaisuwa ce, wani lokacin kuma labarin makarantarsu da take yawan bashi. Shima tana tura masa Assignment da yake koya mata, amma abin da ya dagula zuciyar Fahad da kodayaushe zaiji Jamilu na cewa Indo yayi missing ɗinta, wasu Voice note da ya ji Jamilu da Indo sunyi ya kunna su yafi a irga wanda Jamilu ya ce, "Ayusher yaushe zaki zo mana hutu ne?Saboda na nayi missing ɗin tsiwarnan taki" Indo ta ce, "Ya Jamil dama wai kana sona amma da sai kayi ta dukana" Jalimu ya ce, "Ayusher meyasa kika tambayeni?" Indo murmushi tayi ta ce, "Naga Baba Huwaila ce kawai take so na duk faɗin ƙauyen nan, bayan har kaini kake gurin Maigari ya dokeni" Jamilu ya ce, "Ayusher ni kuwa nake sanki! Bazan taɓa fasalta irin ƙaunar da nake miki ba. Amma lokaci na gabda zuwa da zan sanar dake abinda ya daɗe yana cimun tuwo a ƙwarya. Kina da Saurayi kuwa" Gaban Indo ne faɗi, murya a sanyaye ta ce, "Ya Jamil ba kai kake hanani kula kowa ba bayan su Zulai duk da samarinsu, kace har ansa ranar su." Jamilu ya ce, "Ai ba a ƙauye nake nufi ba, ina nufin anan Kaduna" da sauri Indo ta ce, "Cab bana kula kowa, bare mugun nan Ya Fahad yana nan ina zai barni na kula kowa" Gaban Jamilu ne ya faɗi amma sai ya basar ya ce, "Kintuna dai a ƙauye abinda ya taɓa faruwa da Hansa'u ko? To karki yadda ki kula kowa da sunan soyayya, idan lokacin yayi ni zan gaya miki, ko kuma na samo miki miji mai hankali kuma ɗan gayu ko bakya so?" Indo kunya taji kamar yana ganinta ta rufe fuska sannan ta ce, "To ya Jamil, amma karka samo mun mai mugunta kamar kai, kuma kyakykyawa nake so kamar kai ko wanda ya fika " ba ƙaramin dariya ta bawa Jamilu ba, Saboda ya lura har yanzu da sauran yarinta a kan Indo, yace "To shikenan ai dai-dai ke zan samo miki" sun jima suna hira sannan sukayi sallam. Fahad ba ƙaramin shaƙa yayi ba, kashe wayar ya ƙarayi sannan ya koma kan katifarsa ya kwanta. Bayan Magriba su Indo na zaune gabaɗaya suna cin Abinci, Fahad ya shigo da kofi a hannu da alama tea yake sha, Bayan ya zaune Indo miƙewa tayi zata bar falon Aunty Safna ta ce, "Humaira wai me akayi miki kike ta ɓata rai kamar wacce taci kashi?" Indo kamar jira take nan take idanunta suka ciko da ƙwalla, murya na rawa ta kalli Fahad ta ce, "Haka kawai ina zaune Ya Fahad ya karɓe mun waya, kuma waya muke da Ya Yaseer nasan yanzu haka ya neme ni bai same ni ba" Fahad ɗan zaro ido yayi wato ita bata ma kunyar faɗar wayar da take yi, har take jimamin kar Yaseer ya kira bai samu ba. Yana cikin tunani Aunty Safna ta ce, "Da abinda kikayi dan ruwa baya tsami banza" ganin angoyi bayan Fahad yasa Indo bata ƙara magana ba ta wuce ɗakinta. Tunda Fahad ya karɓi wayarta bai bata ba. Kuma itama bata tambayeshi ba, sai bayan wasu watanni sannan ya bata wayar tare da canza mata layi, da kamar bazata karɓa ba ta karɓe abarta tana watsa masa harara.Tun daga lokacin Indo bata kuma shiga sabgar Fahad, shi ɗinma bai cika shiga sabgarta ba. Sai dai duk wani moshi da Indo takeyi akan idonshi takeyi. BAYAN SHEKARA BIYU Watarana Indo ta dawo daga makaranta da yamma liƙis, tana shigowa kamar a mafarki ta hangoshi zaune akan kujera da waya a hannunsa yana dannawa, cikin bazata gabanta yayi mummunar faɗuwa. Dukda shi ba fari bane amma ba ƙaramin canjawa taga ya yi mata dukda batafi wata shida rabon da tayi tozali da shi ba, kyawunsa ya ƙara fitowa har wata ƴar ƙiba taga ya yi. cikin murna ta jefar da jakarta gefe ta zuba da gudu kamar zata rungumeshi sai kuma ta tsaya, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce, "Ya Jamil kaine! Wow dama zaka zo amma ko jiya a waya baka gaya mun ba, ina My Baba Huwaila wallahi nayi missing ɗinku gabaɗaya, Ya Jamil ka ga yadda ka ƙara kyau kuwa" tana faɗa ta ɗan taɓe baki ta cigaba da cewa, "Inama yadda ka ƙara kyau haka ka daina mugunta amma ina wallahi nasan halinka yana nan, Yauwa ya wajensu Zulai yanzu ƴaƴanta nawa?" Kafeta yayi da kallo, wani abu na tsarga masa cikin jikinsa. Ganin ya tafi duniyar tunani yasa Indo ta hura masa iska a fuska, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu Ayusher wacce tambaya kikesan na fara amsa miki?" ya ƙarasa faɗa yana harɗe hannuwa a ƙirji. Tura baki gaba tayi cikin shagwaɓa ta ce, "Ni duka zaka amsa mun" Murmushi yayi ya ce, "To ko zan amsa miki sai kin cire Uniform ɗinki kin huta tukunna" ɗan ɓata fuska tayi zatayi magana ya sa ɗanyatsansa akan laɓɓansa, sannan ya ce, "Kinsan dai bansan..." da sauri Indo ta karɓe zancen da, "Banasan musu, kedai Allah ya yi ki da kunnen ƙashi taurin kai kamar mutanen farko." gabaɗaya suka kwashe da dariya, Jamilu ya ce, "Shiyasa nake missing ɗinki Sarƙar Baba Huwaila yanzu gidanmu duk ba daɗi saboda bakya nan" Indo ta ce, "Ai nasan kashedin ka kenan shiyasa tuni na haddace shi." Duk abinda yake faruwa Fahad dake cen jikin mota yana jinsu kuma yana ganinsu, takowa yayi fuska a haɗe ya ce, "Ke! ba daga makaranta kika dawo ba, wuce ki shige ciki banasan sakarci" Indo ta ce, "Ya Fahad rabin raina na gani, kasan kuwa yadda nakeji da Ya Jamil kuwa? Tagwayen Baba Huwaila wasu ke kiranmu dan Allah ka barmu muyi hirar yaushe gamo" Jamilu wani irin daɗi yaji har cikin ransa, ko ba komai yasan Indo ta bashi babban matsayi. Fahad jin maganganun Indo yayi kamar saukar aradu, yana shirin magana Jamilu ya ce, "Wuce cikin gidan, kinsan banasan rashin kunya..." da sauri Indo ta kuma karɓe zancen da, "Kinsan dai banasa rashin kunya, dan wani lokacin kamar ɓeran birni haka kike" Jamilu murmushi yayi ya taka ya ɗauko mata jakarta ya miƙa mata sannan Indo ta wuce. Fahad sai lokacin ya bar gurin yabi bayan Indo suka wuce ciki, Jamilu yaji ba daɗi sosai dan idan duba alaƙar da ke tsakanin Indo da Fahad sai ya ga kamar zai rasa ta gabaɗaya, dan duk mai hankali yaga abinda Fahad yakeyi yasan Zallar kishi ne yake sashi. Alhaji Khaleel yaji daɗin zuwan Jamilu akan lokaci dukda bai sanar dashi dalilin kiran da yayi masa ba, kafin zuwan nasa. Da daddare suna zaune shi da Fahad,Jamilu da Mommy ya ce. "Nasan zakayi mamakin jin kiran da nayi maka! Jamilu dalilin da yasa na kiraka ba komai bane sai dan na damƙa amanata ta agurinka, saboda na yaba da hankali da nutsuwarka, na tabbata ko bayan rayuwa ta bazaka ci amana ta ba, zaka riƙe hannu bibbiyu tsakaninka da Allah " Tunda Mahaifin Indo ya fara magana gaban Fahad yake lugude jikinsa har rawa yake, wani irin gumi ne yake keto masa dikda Ac dake cikin falon. Alhaji Khalil ya cigaba da cewa. "Ban yanke wannan shawarar ba sai da muka tattauna da ƴan uwana, kuma suma ba ƙaramin dadi suka ji ba, danma basa ƙasar da su zasu tattauna da kai ba ni ba. Haka Kawunka Alhaji mun sanar da shi komai kuma yayi farin ciki sosai, sai dai mun roƙi alfarmar karya sanar da kai dan nafisan naji komai daga bakinka." fuskarsa ce ta sauya cikin damuwa ya cigaba da cewa, "Sai dai bansan ya zaka ɗauki lamarin ba zaka amince ko bazaka amince ba shine damuwa ta" a firgice Jamilu da Fahad suka ɗago da kai suna kallan Alhaji Khalil a yayin da ya dire a zancensa. Hmmmm wallahi akwai ƙura bari nayi nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ Naga bakya comments sosai 😥 kuyi haƙuri mu raka dan littafin yazo ƙarshe. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [24/09, 13:08] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 83&84 Fahad sosai ya zuba mata ido dan gano gaskiyar abinda ta da faɗa, amma sai ya gagara fahimtar haka a ɗan tsorace ya ce, "Habeebty wai Aljanu na irin haka?" Mommy da har lokacin a tsorace take ta ce, ,"Eh to kasan komai akace aljani lamarin sai Addu'a" Fahad ya ce, "To kuwa zanje inkira Malam Khalid ai basufi ƙarfin ayar Allah ba" Indo ba haka ta so ba, amma dan karsu gano ta sai ta basar. Mommy ta ce,"To Allah ya tsaremu daga sharrinsu" daga haka Fahad tashi yayi ya fice daga falon. Yamma liƙis Fahad ya shigo shi da Malam Khalid, ɗakinsa suka shiga Malam ya zauna ya fara karatu ya jima yanayi, amma babu wani abu da yaji ko ya gani da zai baka shaidar da shafar aljanu a ɗakin, bayani yayi wa Fahad kuma ya gamsu sannan ya sanar da shi zai yiwa Indo ruƙiya. Kai tsaye Fahad ɗakin Indo ya wuce sau biyu kawai ya ƙwanƙwansa, yana shiga ya sameta kwance a kan katifa sanye da wata doguwar rigar, rigar roba ce dan ta ɗan kamata, kanta ko ɗan kwali babu. Fahad wani abu ne ya tsarga masa baisan lokacin da ya shagala da kallonta ba, sai ji yayi ta ce, "Ya Fahad yanzu kuma me ya kawo ka ɗakina? Ko yanzu ma zuwa zakayi ka dake ni" sai ta nutsuwarsa yayi ya ce, "Ki fito akwai mai ruƙƙiya a falo" Indo ɗan tsorota tayi, da sauri ta ce, "Me ya haɗani da me ruƙiyya ko nice na koma maka magen?" maganar Indo taso bashi dariya amma sai ya kanne ya ce, "Ai da zaki koma magen ma da nafi kowa murna, inɗaukeki inkaiki cen waje na yar ko na huta" yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin. Indo kanta tsaye ta fito itama falon, lokacin da ta ƙaraso Falon Malam Khalid na zaune da sallama, ta shigo falon ta nemi kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fahad da ya shiga kitchen domin ɗebo ruwa a kofi, yana zuwa falon ya bugawa indo tsawa, "Ke! Baki da hankali ne? Wuce ki sako hijabinki" Indo ta ɗan tsorota da yanayin da ta ga Fahad a ciki, amma sai ta shanye tsoronta ta ce, "Ya Fahad ruƙiyar ce har sai na sa wani hijabi meye haɗin aljanu da hijabi na ko..." tun bata rufe baki ba ya tunkaro gurin da take a hassale ya ce, "Zaki wuce ko sai na karya ki a gurin nan" nan take fuskar Fahad tayi jawur jijiyoyin wuyansa duk sun tashi, Indo shiru tayi gabanta sai faɗuwa yake, wannan karan ba ƙaramin tsoron Fahad taji ba. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya ƙarasa gurin ya fisgi hannunta, ya wuce da ita har ɗakinta. Yana shiga ya ce, "Wallahi idan kika kuma fitowa a haka sai na baki mamaki" yana faɗa ya bar gurin ya koma falon. Bayan Fahad ya koma ya ce, "Malam kayi haƙuri kasan lamarin mata sai a hankali ." Malam Khalid ya ce, "Malam Fahad kasan mata sai da lallami, tunda matarka ce ka dinga janta a jiki bare kaga da ƙuruciya, sai kana kauda kai. Yanzu ka je ka lallasota ku fito tare, kasan ko jinnun jikinta zasu iya sata wasu abubuwan" Fahad tashi yayi ya wuce ɗakin yana jin zafin Malam dan ya dangantashi da mijin Indo, sai dainta wani fannin tausayinta yaji da ya tuna aljanin da suke jikinta, yana zuwa ya same ta zaune akan katifa ta rafka tagumi kamar wata mutuniyar kirki, cikin sanyin murya yace, "Ki sako hijabinki ki fito Malam yana jiranki" bata ɗago ta kalleshi ba, itama muryarta a sanyaye ta ce, "Ni ka ƙyaleni na fasa zuwa, a ƙyale aljanun su mun duk abinda zasu mun kowa ya huta, tunda dama ba sona ake ba." bakinta yake bi da kallo da yadda take motsa su, lumshe ido yayi ya girgiza kai. Har zai mata faɗa sai kuma ya tuna maganganun Malam, ƙasa-ƙasa ya ce, "To ni da ba mijinta ba? Meye zan wani lallame ta" sai wata zuciyar ta ce masa, "Amma ko ba komai ƴar uwarka ce ta jini" tsugunnawa yayi gabda ita har suna jin numfashin juna ya ce, "Kinsan mutumin nan saboda mu yazo, idan yaga baki fito ba bazai ji daɗi ba. Kuma wa yace miki bama sanki? Da bama sanki zamu nemo miki mai maganin warakar lalurarki?" Indo ware manyan idanunta tayi ta shagala da ƙarewa Fahad kallo, da yadda yake sarrafa laɓɓansa yake mata magana, cikin zuciyarta take ayyana dama Fahad ya iya tausasa murya wajen kalamai? Amma komai yake mata cikin masifa da hantara." ganin ta shagala da kallonsa yasa hannun saitin fuskarta, yana murza ƴan yatsunsa. Sai a lokacin Indo ta farga wata ƴar kunya ce ta kamata, shi kuwa tsuke fuska yayi kamar zai yi mata magana sai ya tuna, yana mata magana yasan zai iya wargaza komai zata iya ƙin fita. Miƙewa yayi ya ce, "Sauri ki fito yana jiranki" yana fita Indo ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Nan take ɗaya daga sashen zuciyarta ya ce, "Me yake damunki? kin manta waye Fahad? Kawai dan ya tausasa miki harshe na lokaci ɗaya, har zaki fara tunaninsa." guntun tsaki tayi a filinta ce, "Ko meye abin tunani akan wancen oho, dukda kamar su ɗaya da Yaseer amma Yaseer ya fishi komai" tana gama magan ta ɗau hijabi ta fice. Tana zuwa ta hau kan kujera ta ƙame guri ɗaya, Malam Khalid alwala ya ƙara ɗaurowa sannan ya zauna ya fara karatun alƙur'ani. Sai da Malam Khalid ya shafe awa ɗaya cif amma ko motsi baiga Indo tayi ba, kallan Fahad yayi ya ce, "Malam Fahad muje inasan magana da kai" Malam na gama maganar ya nufi bakin ƙofar, da sauri Indo ta ce, "Malam angama ruƙiyyar zan iya tafiya?" Malam yace, "Eh! Zaki iya tafiya" Indo kamar dama jira take tun bai rufe baki ba, ta tashi zata wuce sashenta su Momma suka fito. Da mamaki suka bi Indo da kallon ganin tasha zumbulelen hijabi, barka da hutawa tayi musu ta wuce ɗakinta. Malan ya gaida su Mommy sannan ya koma suka zauna gabaɗaya, ya fara musu bayani akan ruƙiyyar da aka kirashi yayi. Sai dai sam babu wasu ginnu a jikin Indo, mamaki sukayi suka kawo kuɗi suka bashi tare da yi masa godiya, ya yi musu sallama ya tafi. Mommy ce ta kalli Momma ta ce, "Amma lamarin da mamaki fa" Momma ta ce, "Wallahi nikam banyi mamaki ba idan kika tuna da lamarin da su Baba Huwaila suka bamu, wallahi nifa dama jikina bai bani aljanu bane shaƙiyancin yarinyar nan yawa gareshi" Fahad dake gefe ya ce, "Amma wallahi yarinyar nan data gane kurenta" yana gama magana ya nufi ɗakin, Indo ta cire hijabi kenan Fahad ya ja hannunta ko magana babu, bai dire ta a ko'ina ba sai gaban su Mommy. Aunty Safna ce ta rufe da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Mommy ce ta karɓe zancen cikin lallami da nasiha. Nasiha mai kashe jiki Mommy tayi mata tare da nuna mata illar kwaikwayon abinda takeyi, sosai jikin Indo yayi sanyi nadama ƙarara ta hau kan fuskarta. Su Mommy sun lura da haka ita kanta Aunty Safna ba ƙaramin daɗi taji ba, ganin yanayin da Indo ta shiga na nutsuwa. Fahad kallan Indo yayi ya ce, "Allah sa dai ta ɗauki faɗan da akayi mata, dan Allah Aunty ji yadda take sunne kai kamar ta kirki" Aunty Safna ta ce, "Kaima dai ka faɗa Fahad, wai a haka Yaseer yake so da wannan sakarcin nata" Indo zumɓurar baki tayi gaba ta ce, "Dan Allah Ammi ku daina faɗa a gaban Ya Fahad karya rainani" Indo ba ƙaramin dariya ta bawa su Mommy ba, Aunty Safna ta ce, "Wane raini kuma bayan shi ya fara saninki a lokacin da kike ƴar ƙauyenki, ba yanzu da kike waye ba. Ai wallahi kome kika zama yanzu Ɗana Fahad ne sila" Fahad kansa murmushi yayi, ko ba komai ya samu abin gori nan gaba, Indo kamar zatayi sabida takaici. Mommy ta ce, "Rabu da su Humaira, kice asalin kowa ma ai ƙauye. Kuma cen ɗinma ai a gida kike tunda kin rayu da Kawunki Maigari" Indo kamar wata yarinya ta yiwa Fahad gwalo, sannan ta ce, "Yauwa Mommy naji kince Maigari ɗan uwanku ne, amma banji kun gaya mun alaƙarku da shi ba rannan" Mommy ta ce, "Mahaifinsa da Mahaifin abokan wasa suke, lokacin da Mahaifinmu zaizo garin saida ya yiwa mahaifin Maigari tayin zuwa amma yaƙi, sai wani zuwa da Mahaifinmu yayi suka taho tare, har dai Allah ya sa shima yayi tunanin dawo da iyalinsa garin nan. Amma shi Mahaifinsa sai ya fara safarar kaya yana kaiwa garin Kura, har aminci ya haɗasu da Maigarin wancen lokacin. Humaira labarin yana da tsayi a takaice dai Maihafin Maigari ya zamu zama a wancen garin kuma mutum ne me amana, da tsoron shiga haƙƙin wani. Lokacin da Maigarin wancen garin ya fara wata jinya, sai yayi sanarwa tare da saka sojojin masarauta, ya sa hannu akan ko da bayan ransa Mahaifin Maigari, shi zai cigaba da mulkarsu saboda tausayinsa da amanarsa. To kinji yadda akayi, banda ma zumuncin yanzu ya zama yadda ya zama, dama duk cikin ƴan uwana ba yabon kai ba nafi su ƙoƙarin zumunci, kuma da har zuwa Kura muke muna zuwa mu shafe watanni a cen. Ni da kike gani a cikin garin da kikayi rayuwa babu inda bansani ba, idan na fara baki labari sai mu kwana anan." Indo ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Taɓ amma wallahi Maigari nasha da ƴan ƙauyen nan sam be ɗauko halin mahaifinsa ba, zalinci a cikin mutumin nan kamar..." da sauri Mommy ta ce, "Gidanku Humaira" Fahad yayi karaf ya ce, "Ku barta ta faɗa dan ni kaina wani zuwa da mukayi inaji wasu mutane na zaginsa, wai ya cinye wata gonar gadonsu" Aunty Safna ta ce, "Ƙaniyarka ana kwaɓar ƙanwarka kana kuma sakin bakinka" Fahad dariya yayi ya tashi zai shiga ɗakin, Indo ta ce." Ai wallahi nina saita shi sai da ya mayar musu da dik gonakinsu" da mamaki ta fara suka kalleta, gyaɗa kai Indo tayi basu labari tun daga lokacin da aka damƙawa Maigari takardunta, da ɓadda kamar da sukeyi ita ƙawayenta. Hatta ludayin da suka dinga ranƙwalawa Maigari sai da ta faɗa da umarnin da suka bashi akan ya mayar wa da mutane dukiyarsu. Fahad duk gimtsewar da yakeyi sai da ya dinga ƙyalƙala dariya, su Mommy dariya suke harda hawaye sai da suka tsaida, Mommy ta ce, "Dama Humaira ke kika rikitamu ɗan uwa lokacin da muka je" Indo dariya tayi ta ce, "Mommy nima ai Ya Fahad tasoni yayi saura kaɗan asiri na ya tonu, wallahi da ya kamani da na kaɗe dan ƴan garin nan sai mun tofin Allah tsine" Fahad me zaiyi banda dariya, Aunty Safna ta ce, "Ikon Allah wato mu duk shakiyancin ƙuruciya da mukayi muna yara, bamu kama ko rabinki ba Humaira. Allah ya ƙara shirya mana ku gabaɗaya." gabaɗaya suka amsa da Ameen, suna nan zaune Daddy mahaifin su Fahad ya shigo hannuwansa riƙe da su Aseem, zama sukayi suka cigaba da hira cikin barkwanci. Alhaji Mahmud Lamiɗo shine ainihin sunan Mahaifin su Fahad, asalinsa Fulanin daura ne. Sai dai kakanni da iyayensa a buɗi ido ya gansu a cikin garin Kano, Iyayensa sun rasu bayan haihuwar su Fahad babu jimawa, Su uku ne rak a gurin iyayensa. Shine babba sai ƙannensa mata biyu, Alhaji Mahmud ɗan kasuwa ne saboda baiyi wani zurfi a karatun boko sosai ba, Allah ya bunƙasa kasuwancinsa har ƙasashen waje yana fita sarin kaya. Mutum ne mai matumci da karamci gashi da zumunci da taimakon marasa ƙarfi, uwa uba gashi da alheri da sakin fuska. MU KOMA LABARI Kwanan su Indo biyu suka wuce garin Kaduna, wannan karan ma ba tare da Fahad suka wuce ba, saboda wani uzuri da zai gabatar kafin komawarsa. Indo ji tayi kamar ta je ta ajiye masa takardar da ta ɗauka, amma sai kawai ta share har suka koma. Makaranta me kyau Mahaifinta ya nemar mata idan tare da direban da yake kaita, yana dawo da ita. Wannan karan a JSS3 aka sakata tare da ɗaukan malam da suke yi mata lesson a gida, makarantar su Indo haɗe take da islamiyya basu suke dawowa gida ba, sai gabanin magriba. Wannan dalilin yasa koda Fahad ya koma basu cika wani haɗuwa ba. Indo batasan yadda akayi Yasir ya samu lambarta ba, amma kodai mene ne tasan a gurin Momma ya ƙarɓa, Indo tun tana fushi da Yasir har ta sakko suka cigaba da mutumci, kamar yadda Indo ta ɗauka tunda har yau Yasir bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba. Wata ranar Asabar Indo na cikin garden Yasir ya kirata a waya, sun shafe awa guda suna waya banda murmushi babu abinda take, wani lokacin sai dai ta tuntsire da dariya, kome Yasir ya gaya mata ta miƙe tsaye tana murna harda tsallenta. Dun abinda takeyi Fahad na tsaye yana kallanta wani ƙululun takaici ne ya rufeshi, Bai ankara ba yaji tace, "Wallahi nima nayi missing ɗinka Ya Yasir, amma kasan me zaka siyo mun idan zaka zo?" Kafin Yasir yayi magana Fahad ya ƙaraso a zafafe ya fusge wayar, kasheta yayi gabaɗaya fuska a tamke yace, "Ƙaramar yarinya da ke har kin iya soyayya ko? Shi kansa Yasir ɗin zamu gauraya dashi, zanga wanda zai ƙara baki waya yanzu" Indo batasan lokacin da hawaye ya fara zubar mata a fuska ba, da gudu tabi ta gefensa ta wuce ɗakinta. Iska mai zafi Fahad ya fesar ya wayar a aljihu ya bar gurin. AKWAI ƘURA🙊🤣😂 KUYI HAƘURI DA KURAKUREN CIKI. WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA ƳAN GROUP ƊINA NA *AMEERA ADAM FANS GROUP* DA MUTANENA ƳAN AMANA TA *WATTPAD* _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [24/09, 13:08] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 87&88 Fahad bakinsa sai motsi yake kamar zai tari kawun nasa da tambaya, amma sai ya danne ya juya kai gefe. Jamilu jiki a sanyaye ya ce, "Abba in sha Allah zanyi bakin ƙoƙarina wajen ganin na riƙe wannan amana taka, dukda bansan wacce irin amana bace." Alhaji Khaleel ya ce, "Na buɗe sabon kamfanina a garin Kano, kamfanin leda ne da takalma shiyasa na yanke shawarar damƙa maka amanar sa, saboda da Kawunka zan damƙawa amma sai ya nuna mun gwara na sameka tunda shi baiyi zurfi a karatu ba, dan yana gudun kar a samu matsala dan haka kai zan mallakawa ragamarsa amma bansani ba zaka amince kuwa saboda kaima ma'aikaci ne, banasan na shiga haƙƙinka idan kana ganin babu damuwa.Karka ji kunyata idan har da takura ka mun bayani" Wata gwauruwar ajiyar zuciya Fahad ya sauke har sai da ta fito fili, Alhaji Khaleel murmushi yayi saboda ya fahimci sarai inda Fahad ya dosa, Jamila gyara zama yayi ya ce, "Abba ina matuƙar godiya da wannan karamci agareni, kuma insha Allah ba abinda zai gagara Allah ya sa albarka ya taya mu riƙo" gabaɗaya suka amsa da Ameen, sai lokacin Fahad yayi murmushi ya ce, "Malam Jamilu ina taya murna Allah ya taya riƙo" Jamilu ya amsa cikin sakin fuska, bayanin yadda abubuwan suke ya ɗan fara yiwa Jamilu yadda zai gane, sannan suka ɗan taɓa hira daga nan kowa ya kama gabansa. Washegari Jamilu ya koma sai dai gabaɗaya baiso ba ji yake kamar ya tafi ya bar wani ɓangare na jikinshi, ita kanta Indo taji ba daɗi saboda ba ƙaramin shaƙuwa sukayi da Jamilu ba, dukda dai kafin ya tafinma sai da sukayi faɗa ita, dalilin Faɗansu kuwa. Jamilu na zaune a harabar gidan Indo ta fito da wani kofi, cike yake da ƙanƙara. Kujera ta janyo ta zauna ta fara sha, Jamilu kallan kofin ya yi ya ce, "Ayusher me yasa bakyaji ne" Indo kauda kai gefe tayi ta ce, "Wallahi dama nasan sai ka yi magana, wai kai Ya Jamil meyesa bakasan duk wani abu da zanji daɗi?" Jamilu tamke fuska yayi ya ce, "Har yanzu bakida da kunya ko?" Harara ta watsa masa tana juya idanu haɗe da murguɗa ta ce, "Rashin kunya nayi maka sai dai in tsarguwa kayi..." kafin ta ƙarasa Jamilu ya bige bakin ya ce, "Inajin kafin na tafi sai na fasa wannan bakin naki, dan naga har yanzu hankalinki da saura" Idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Wallahi Ya Jamil da hankali na, idan ma banida shi ai sai idan a gurinka na koya..." da sauri ya kuma bige mata baki wannan karan ba ƙaramin zafi taji ba, hawayen da take maƙalewa ne ya sauko tashi tayi sai da tayi nisa da shi ta juyo ta ce, "Wallahi banyafe ba mugu kuma sai na gayawa Baba Huwaila" tana gama faɗa ta zuba da gudu. Jamilu murmushi ya yi a fili ya ce, "Wato Sarƙa har kwanan gobe Sarƙa ce, bazata taɓa sake hali ba. Rashin kunyar nan na nan." Lokacin da Jamilu yaje gida ba ƙaramin daɗi Baba Huwaila taji ba, kiran Mahaifin Indo sukayi suna yi masa godiya, har akan tagomashi da ya haɗowa Jamilu da zai tafi. Ba ƙaramin kyautata musu yake ba dan kayan abinci kafin wannan ya ƙare zai turawa Jamilu kuɗi a sayi wani. Bayan wasu ƴan kwanaki an buɗe kamfani cikin ƙudurar Ubangiji komai ya fara tafiya yadda ya kamata. Mahaifin Indo mota ya bawa Jamilu ƴar madaidaiciya ma kyau, kuma dikda wannan cigaba da Jamilu ya samu bai bar aikin koyarwarsa ba, Zumunci mai ƙarfi ne ya shiga tsakanin waɗannan gidajen guda biyu. Indo sun fara jarrabawar Waec ana ta shirin Candy kuma a shekarar ne zasuyi saukar Alkur'ani, Indo ta ƙara zama budurwa ta kuma wayewa kamar ba ita ba. Sai dai akace idan ka shekara dubu baka ga mutum ba, idan kun haɗu tambayeshi wani abun ba halinsa ba, halin Indo na tsokona da abinda ba'a rasa ba yana nan.Yanzu a cikin dangin Mahaifi da mahaifiyarta babu Wanda bai santa ba, sai dai ba kowa ta cika shiga sabgarsa ba, saboda har a lokacin gani take ita ba ƴar wasu bace, dukda tana ƙaunar iyayenta amma har lokacin tafi jin kanta kamar yadda take ada ƴar ƙauye, shiyasa bata cika shiga sabgar cousin ɗinta na dangin Mahaifinta ba, saboda ta lura wasu daga cikinsu suna da ɗaga kai, musamman ƴan ɗakin su Lubna. Wasu Ƴaƴan abokin mahaifinta mutum biyu ne suka nuna suna santa, amma sam basu kwanta mata ba, da suka matsa mata sai ta ce sai tayi candy ko zata fara kula samari. A ɓangarenta da Yaseer kuwa ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba, kusan duk dangin kowa yasan da shaƙuwarsu, dan ita kanta Indo ta yarda son Yaseer yayi nisa a zuciyarta.Sai dai har zuwa wannan lokacin bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba, hakan ne yasa itama Indo take nuna kamar bata fahimci inda ya dosa ba, A ɓangaren Jamilu shima ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba, sai dai ko kaɗan Indo bata tsammanin soyayya daga gurinsa, tafi danganta hakan da shaƙuwa. Kuma Jamilu ya barwa zuciyarsa akan sai Indo tayi Candy koda zai sanar mata da kalmar soyayya, dan idan ya tuna abinda zai sanar mata gabansa har faɗuwa yake, saboda Alasan abokinsa ya taɓa tarar ta tun a ƙauye yace yana santa, tun daga ranar Indo ta daina ganin mutumcin shi sai ma ta koma ce masa Ɗan iska. Shi kansa Yaseer wanan hukuncin ya yanke, na sai Indo ta yi Candy zai sanar da Ita, kuma ya gabatarwa da manyansu maganar aurensu. Fahad a har kullin yanasan nunawa Indo kulawar da zata fahimci yana ƙaunarta, amma wani tsagi na zuciyarsa na ƙaryata wannan tunanin, kuma yana ganin kamar raini ne zai ƙara samun gurbin zama a tsakaninsu, tunda dama tuni Indo ta riga da ta raina shi. Wata mata na gani a cikin duhun bishiyoyi, fuskarta ɗauke da niƙab. A gaggauce ta ce, "Hadari da kyar na samu lambarka, dan Allah aikin wata yarinya zan baka, akwai adireshin gidansu dana makarantarsu a jikin takardar, banasan a samu matsala kawai ku kashe ta. Na turo muku Million biyu dan Allah banasan a samu matsala." Hadari ƙarɓa yayi yana murmushi ya ce, "Baki da damuwa Hadari baya jagwal, ki baza kunne nan da ƴan awanni zakiji sanarwar mutuwarta." da sauri ta bar gurin saboda batasan ta samu matsala. Su Indo sun fito daga makaranta Direbansu ta hango, da sauri ta ƙarasa tana yiwa ƙawayenta sallama. Tana shiga mota wasu mutane da ke cikin wata baƙar mota suka rufawa motar su Indo baya, sai da suka fara barin cikin mutane waɗannan mutanen suka sha gaban motar su Indo. cikin tashin hankali Direban motar yake bin motar da kallo, Indo jikinta banda rawa babu abinda yake yi, mutum biyu ne suka fito daga motar hannunsu ɗauke da bindiga. cikin fargaba direban ya ce, "Humaira ya zamu yi?" Indo tace, "Mu gudu kawai, bani wayarka na kira Daddy." bata rufe baki ba suka ɗaga bindiga sama suna sakin harbi. Wayarsa babbar ya ɗauko ya miƙowa Indo, sai dai kash tana kira babu kuɗi a ciki. Da sauri ta miƙa masa cikin kiɗima ta ce, "Ba kuɗi musty, ba kuɗi" ƙaramar wayarsa me madanne ya miƙa mata, wanda alokacin tuni har sun ƙaraso wajen motar su Indo. Da sauri ta danna lambar Mahaifinta wanda yayi daidai da buɗe murfin ƙofar, da sauri indo ta tura wayar cikin aljihun wandon uniform ɗinta. Ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya fisgo Indo yana kifeta da mari, da sauri Musty ya fito ya fara roƙonsu, wanda yayi dai-dai da ɗaukan wayar da Alhaji Khalil yayi, kiran da Indo tayi masa. "Dan Allah maigida kuyi haƙuri kuyi mana rai" Mutumin da baka ganin komai a fuskarsa, sai ƙwayar idonsa ya ce, "Ɗan samari ba gurinka muka zo ba, mun zo ɗaukan wannan yarinyar ne" Jin maganar nan ba ƙaramin ɗaga hankali su yayi ba, Musty ya ce, "Dan Allah ku haɗa dani dan idan na koma bansan me zan cewa mahaifinta ba, wallahi bazan taɓa fita ba. Idan kuma kuɗi kuke so ko nawa ne Alhaji zai bayar..."Tun bai rufe baki ba mutumin ya sakar masa harbi a ƙafa yace, "Ga shaida nan na bar masa dan na rage masa wahalar nema, dan idan ba'a ganku ba gabaɗaya ɗauka za'ayi tana raye mukuma kwangilar kisa aka bamu" yana gama faɗa ya fisgi hannun Indo tana ihu, Musty durƙushe yake yana ɗaga hannu alamun a taimaka masa, yana ji yana gani suka tasa ƙeyar Indo a mota suka tafi da ita. Musty na nan wani me mashin yazo wucewa ya ganshi tsugunne cikin jini, da sauri ya ƙarasa gunshi dan ganin halin da yake ciki, Musty hanya ya dinga nuna masa yana cewa, "Ka taimaka sun tafi da ita" mutumin tambayarsa ya yi, a take Musty ya bashi labarin abinda ya faru, taimaka masa yayi ya sashi a mota, sannan ya fita cen gurin mutane yayi yekuwar mutane suka taho suka ɗaukeshi suka wuce da shi asibiti. Alhaji Khalil duk abinda yake faruwa akan kunnensa, sakamakon kiran da Indo tayi masa da wayar Musty bata katse ba. Jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali, kiran wayar yake amma ba'a ɗauka ba. Da sauri ya kira Lambar Director ɗin makarantar su Indo, dan tsammaninsa a makaranta ne abinda ya faru. Saboda ruɗewa ya manta da lambar Musty ce aka kirashi, amma yana kiran Director ya shaida masa tuni ɗalibai sun jima da tafiya. Da sauri ya katse ya kira lambar kwamishinan ƴan sanda ya sanar da shi halin da ake ciki, Kwamishina cewa yayi ya tura masa lambar da aka kirashi da ita, zasu bibiyu sahun gurin da suke. Alhaji Khalil tura masa lambar yayi sannan ya fita daga cikin office ɗinsa, ya nufi ofishin Kwamishina dan ƙara jaddada masa. Gudu yake kamar zai tashi sama har a ƙarasa, lokacin da yaje tuni har sun fara tracking ɗin lambar kuma sun tura jami'ansu suna bibiyar sahun makasan da suka tafi da Indo. Mutanen da suka ɗauki Indo wata hoda suka shaƙa mata, nan take jikinta ya saki ta faɗi ƙasa ba numfashi. Tafiya suka yi me ɗan nisa kamar zasu bar garin, sannan suka shiga cikin wani ƙasurgumin daji, basu wani shiga cen ciki ba sukayi parking ɗin motarsu. Zuwan su babu jimawa Indo ta fara farkowa, Ɗaukkota sukayi kamar wata ƙaramar yarinya, a ƙasa suka wurgar da ita zafin buguwar da taji yasa ta ƙarasa wartsakewa. A zabure ta miƙe zaune tana ja da baya nan take ta tuna abinda ya faru da ita, idanunta ne suka ciko da ƙwallah, haɗa hannuwanta biyu tayi cikin roƙo ta ce, "Ku dubi girman Allah kuyi haƙuri karku cutar dani" Hadari dake cen gefe da yake ƙarewa Indo kallo, ji yayi ta matuƙar birgeshi har zuciyarsa, takowa yayi har gabanta ya tsugunna a gabanta yana ƙarewa laɓɓanta kallo, tana ƙarasa magana yasa ɗan yatsansa a laɓɓanta, sannan ya ce, "Yarinya kwangila aka bamu mu kashe ki, daba dan haka ba dana ƙyaleki amma ba wannan alƙwari, na yaba da kyawunki ƙwarai." Indo girgiza kai ta farayi ta ce, "Duk wanda ya baku wannan kwangilar bansan me na tsare masa ba, tun ina jaririya yake farauta rayuwata ashe har yanzu baza'a barni na huta ba?" Sunkuyar da kai tayi ta ce, "Ku kashe ni kawai, saboda nasan ko baku kasheni yanzu ba dole zasu kasheni. Amma dan Allah inasan idan kun kasheni, ko da da daddare ne ku kai gawa ta ƙofar gidan Mahaifina ayi mun sutura, karku barni dokar daji dan Allah" Indo ta ƙarasa faɗa cikin karaya. Hadari jikinsa ne yayi sanyi ba yau ya saba irin wannan aikin ba, amma lokaci ɗaya yaji tausayin yarinyar ya kamashi, ganin yanayinsa yasa ɗaya daga cikin yaransa ya ce, "Haba Megida karfa ka ɓata mana harka... " tun kafin ya ƙarasa magana Hadari ya sakar masa harbi a ciki take ya faɗi ko shurawa baiyi ba. Indo zaro ido tayi tana rushewa da kuka, Hadari hannu yasa ya tayar da Indo tsaye yace, "Bazamu kasheta ba zamu tafi da ita ƙasar nijar tunda a cen zamu yada zango, ni zan aureta..." be kai ga rufe baki ba suka ji motar ƴan sanda, suna shirin shiga mota su gudu suka fara sakar musu harbi, mutum biyu ne suka gudu aka kama mutum uku, amma a cikin wanɗanda aka kama harda Hadari. Indo banda kuka babu abin da take yi, kamata sukayi suka saka a mota, suma su Hadari aka tasa ƙeyarsu zuwa Headquarter ƴan sanda. Alhaji Khalili bai sanar da Mahaifiyar Indo ba saboda yasan nan da nan hankalinta zai tashi, idan ba'ayi sa'a bama hawan jininta yana iya tashi. Sai dai ganin su Indo basu dawo ba yasa ta kira wayar Musty amma a kashe, wayar mijinta ta kira ta sanar dashi, a lokacin nuna mata yayi kamar bai san me yake faruwa ba, ya ce mata zai kira Director makarantasu. Bayan ƴan mintuna ya ƙara kiranta ya ce mata akwai abinda aka zaunar da ɗalibai ake musu, jikinta a sanyaye ta amsa amma wani tsagi daga cikin zuciyarta ya kasa amincewa da maganar mijinta, sai dai batasan ta ƙaryata shi yasa bata musa masa ba. Amma tasan idan har akwai wani muhimman abu da za'a tsaida ɗalibai tun kafin ranar Director yake buga takarda, kowanne ɗalibi ya kaiwa iyayensa. Fahad ne yazo ya same ta cikin jimami bayan ya tambayeta take sanar da shi abinda yake faruwa. Mukullin motarsa ya ɗauka ya nufi makarantar su Indo, domin ya ji ba'asin da za'a zaunar da yara har doshin magriba batare da sanin iyayensu ba. Sai dai yana zuwa ya samu makatarantar a rufe ko megadinta baya nan, da sauri ya kira lambar Kawunsa a nan yake sanar da shi abinda yake faruwa, tare da jan kunnensa akan karya sanarwa da Mahaifiyarta abinda ya faru. Kai tsaye Fahad cen Headquarter ƴan sandan shima ya wuce hankali a tashe, Su Indo kuwa sai wajen ƙarfe takwas na dare suka ƙarasa Headquarter, lokacin da mahaifinta ya ganta ba ƙaramin farinciki yayi ba, ita kanta Indo rungume shi tayi ta rushe da kuka, cikin kuka ta ce, "Daddy wai me nayi musu da basa so na? Meyasa basa san suga ina rayuwa da Iyayena? Daddy me na aikata masu ne?" kukanta ne ya tsananta fuskarta tayi jawur, tausayinta ne ya kama Fahad saboda ya rasa me ta tsare musu da tun tana cikin tsuma take fuskantar barazana daga garesu, sai dai babban farin cikin da yayi da Allah yasa aka kamasu, yasan ko ba komai zasu faɗi wanda ya sasu wannan mugun aikin. Mahaifinta ƙara riƙeta yayi idanunsa na cikowa da ƙwalla, yasan shi dai duk tsawon rayuwarsa bai taɓa aikatawa wani mugun abun da zai yi masa sakayya da irin wannan abun ba.Godiya ya yi wa Allah, da Allah yasa aka kama waɗannan masu mugun aikin kuma a yanzu ne zai san waye wannan babban maƙiyin nashi. Kallan Indo ya yi ya ce, "Ina Musty fa?" Indo ta ce, "Tun kafin su tafi dani suka harbe shi" A razane ya ce, "Yana ina yanzu?" Bata bashi amsa ba yaji ankirashi a waya, yana ɗauka aka sanar dashi asibitin da Musty yake da halin da yake ciki. A hanzarce yasa Fahad ya wuce da Indo gida, sai dai razanar da tayi yasa taƙi sakin Mahaifinta dan yanzu ma gani take idan sun tafi wani abu zai iya faruwa dasu. Ya lura da halin da Indo take ciki, cikin lallashi ya ce, "Humaira ba abinda zai faru kinji, kinga ankama su kuma in sha Allah ƙarshen matsalar tazo." Bakin ta na rawa ta ce, "Daddy a gabana suka harbi Musty, kuma a gabana suka kashe ɗan uwansu, nima fa sunce kasheni zasu yi" Fahad ne ya riƙo hannunta cikin tausayi ya ce, "Bazasu kashe ki ba kinji, zo mu wuce gida." Indo kamar wata ƙaramar yarinya, haka ta bishi suka shiga mota sai juye-juye take har suka ƙarasa gida. Lokacin da Daddy yaje asibiti Musty bacci yake saboda Alluran da akeyi masa, ansamu nasarar ciro harsashin kuma har angyara ƙafar annaɗe da bandeji. Duk abinda ya kamata Alhaji Khalil ya biya sannan ya kira Ƙanin Mahaifin Musty ya sanar dashi, kasancewar Musty maraya ne. kafin wani lokaci ƴan uwan Musty sun cika asibitin. Bayan kwana biyu jikin Musty yana ƙara samun sauƙi sosai, Da farko Mahaifiyar Indo cewa tayi sai dai Indo ta haƙura da zuwa makarantar, bayan da Daddyn Indo ya gaya mata abinda ya faru. Sai dai Daddy yayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta ɗan samu nutsuwa, duk ranar da Indo take da Jarrabawa Fahad ne yake kaita, ya jira ta gama ya dawo da ita gida. Su Hadari fir suka ƙi faɗar wanda ya saka su Kashe Indo sai da suka ji wahala tukunna suka faɗa, a lokacin Alhaji Khalil na gida Kwamishina ya kirashi zuwa cen Headquarter. Bayan yaje ya saurari abinda su Hadari suka faɗa a razane ya ce, "Hajiya Safiya fa? Hajiya Safiya dai matar ɗan uwana?" ana cikin haka Ɗan uwansa Yaya Haruna tare Ɗansa Muhsin suka zo, Ɗan uwan nasa na zuwa ya ce, "Khalil kace mun sun faɗi wanda ya tura su waye dan Allah? Wanne azzalumin ne?" Alhaji Khalil kunyar Yayansa yake yace matarsa ce, Kwamishina ne ya karɓi zancen da, Sunce Hajiya Safiya ce ta sasu kuma har Video lokacin da take basu kwangilar suka nuna mana, tare da kwanan watan ranar da taje ta same su a mazauninsu, Kwamishina ya ƙarasa faɗa yana nuna masa bidiyon wayar Hadari. A razabe Mahaifin Lubna ya ce, "Safiya tawa kai ƙarya ne, a rasa wa za'ayiwa sharri sai Iyalina? Gaskiya da sake bazai yuwu ba." _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 83&84 Fahad sosai ya zuba mata ido dan gano gaskiyar abinda ta da faɗa, amma sai ya gagara fahimtar haka a ɗan tsorace ya ce, "Habeebty wai Aljanu na irin haka?" Mommy da har lokacin a tsorace take ta ce, ,"Eh to kasan komai akace aljani lamarin sai Addu'a" Fahad ya ce, "To kuwa zanje inkira Malam Khalid ai basufi ƙarfin ayar Allah ba" Indo ba haka ta so ba, amma dan karsu gano ta sai ta basar. Mommy ta ce,"To Allah ya tsaremu daga sharrinsu" daga haka Fahad tashi yayi ya fice daga falon. Yamma liƙis Fahad ya shigo shi da Malam Khalid, ɗakinsa suka shiga Malam ya zauna ya fara karatu ya jima yanayi, amma babu wani abu da yaji ko ya gani da zai baka shaidar da shafar aljanu a ɗakin, bayani yayi wa Fahad kuma ya gamsu sannan ya sanar da shi zai yiwa Indo ruƙiya. Kai tsaye Fahad ɗakin Indo ya wuce sau biyu kawai ya ƙwanƙwansa, yana shiga ya sameta kwance a kan katifa sanye da wata doguwar rigar, rigar roba ce dan ta ɗan kamata, kanta ko ɗan kwali babu. Fahad wani abu ne ya tsarga masa baisan lokacin da ya shagala da kallonta ba, sai ji yayi ta ce, "Ya Fahad yanzu kuma me ya kawo ka ɗakina? Ko yanzu ma zuwa zakayi ka dake ni" sai ta nutsuwarsa yayi ya ce, "Ki fito akwai mai ruƙƙiya a falo" Indo ɗan tsorota tayi, da sauri ta ce, "Me ya haɗani da me ruƙiyya ko nice na koma maka magen?" maganar Indo taso bashi dariya amma sai ya kanne ya ce, "Ai da zaki koma magen ma da nafi kowa murna, inɗaukeki inkaiki cen waje na yar ko na huta" yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin. Indo kanta tsaye ta fito itama falon, lokacin da ta ƙaraso Falon Malam Khalid na zaune da sallama, ta shigo falon ta nemi kujera ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fahad da ya shiga kitchen domin ɗebo ruwa a kofi, yana zuwa falon ya bugawa indo tsawa, "Ke! Baki da hankali ne? Wuce ki sako hijabinki" Indo ta ɗan tsorota da yanayin da ta ga Fahad a ciki, amma sai ta shanye tsoronta ta ce, "Ya Fahad ruƙiyar ce har sai na sa wani hijabi meye haɗin aljanu da hijabi na ko..." tun bata rufe baki ba ya tunkaro gurin da take a hassale ya ce, "Zaki wuce ko sai na karya ki a gurin nan" nan take fuskar Fahad tayi jawur jijiyoyin wuyansa duk sun tashi, Indo shiru tayi gabanta sai faɗuwa yake, wannan karan ba ƙaramin tsoron Fahad taji ba. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya ƙarasa gurin ya fisgi hannunta, ya wuce da ita har ɗakinta. Yana shiga ya ce, "Wallahi idan kika kuma fitowa a haka sai na baki mamaki" yana faɗa ya bar gurin ya koma falon. Bayan Fahad ya koma ya ce, "Malam kayi haƙuri kasan lamarin mata sai a hankali ." Malam Khalid ya ce, "Malam Fahad kasan mata sai da lallami, tunda matarka ce ka dinga janta a jiki bare kaga da ƙuruciya, sai kana kauda kai. Yanzu ka je ka lallasota ku fito tare, kasan ko jinnun jikinta zasu iya sata wasu abubuwan" Fahad tashi yayi ya wuce ɗakin yana jin zafin Malam dan ya dangantashi da mijin Indo, sai dainta wani fannin tausayinta yaji da ya tuna aljanin da suke jikinta, yana zuwa ya same ta zaune akan katifa ta rafka tagumi kamar wata mutuniyar kirki, cikin sanyin murya yace, "Ki sako hijabinki ki fito Malam yana jiranki" bata ɗago ta kalleshi ba, itama muryarta a sanyaye ta ce, "Ni ka ƙyaleni na fasa zuwa, a ƙyale aljanun su mun duk abinda zasu mun kowa ya huta, tunda dama ba sona ake ba." bakinta yake bi da kallo da yadda take motsa su, lumshe ido yayi ya girgiza kai. Har zai mata faɗa sai kuma ya tuna maganganun Malam, ƙasa-ƙasa ya ce, "To ni da ba mijinta ba? Meye zan wani lallame ta" sai wata zuciyar ta ce masa, "Amma ko ba komai ƴar uwarka ce ta jini" tsugunnawa yayi gabda ita har suna jin numfashin juna ya ce, "Kinsan mutumin nan saboda mu yazo, idan yaga baki fito ba bazai ji daɗi ba. Kuma wa yace miki bama sanki? Da bama sanki zamu nemo miki mai maganin warakar lalurarki?" Indo ware manyan idanunta tayi ta shagala da ƙarewa Fahad kallo, da yadda yake sarrafa laɓɓansa yake mata magana, cikin zuciyarta take ayyana dama Fahad ya iya tausasa murya wajen kalamai? Amma komai yake mata cikin masifa da hantara." ganin ta shagala da kallonsa yasa hannun saitin fuskarta, yana murza ƴan yatsunsa. Sai a lokacin Indo ta farga wata ƴar kunya ce ta kamata, shi kuwa tsuke fuska yayi kamar zai yi mata magana sai ya tuna, yana mata magana yasan zai iya wargaza komai zata iya ƙin fita. Miƙewa yayi ya ce, "Sauri ki fito yana jiranki" yana fita Indo ta lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Nan take ɗaya daga sashen zuciyarta ya ce, "Me yake damunki? kin manta waye Fahad? Kawai dan ya tausasa miki harshe na lokaci ɗaya, har zaki fara tunaninsa." guntun tsaki tayi a filinta ce, "Ko meye abin tunani akan wancen oho, dukda kamar su ɗaya da Yaseer amma Yaseer ya fishi komai" tana gama magan ta ɗau hijabi ta fice. Tana zuwa ta hau kan kujera ta ƙame guri ɗaya, Malam Khalid alwala ya ƙara ɗaurowa sannan ya zauna ya fara karatun alƙur'ani. Sai da Malam Khalid ya shafe awa ɗaya cif amma ko motsi baiga Indo tayi ba, kallan Fahad yayi ya ce, "Malam Fahad muje inasan magana da kai" Malam na gama maganar ya nufi bakin ƙofar, da sauri Indo ta ce, "Malam angama ruƙiyyar zan iya tafiya?" Malam yace, "Eh! Zaki iya tafiya" Indo kamar dama jira take tun bai rufe baki ba, ta tashi zata wuce sashenta su Momma suka fito. Da mamaki suka bi Indo da kallon ganin tasha zumbulelen hijabi, barka da hutawa tayi musu ta wuce ɗakinta. Malan ya gaida su Mommy sannan ya koma suka zauna gabaɗaya, ya fara musu bayani akan ruƙiyyar da aka kirashi yayi. Sai dai sam babu wasu ginnu a jikin Indo, mamaki sukayi suka kawo kuɗi suka bashi tare da yi masa godiya, ya yi musu sallama ya tafi. Mommy ce ta kalli Momma ta ce, "Amma lamarin da mamaki fa" Momma ta ce, "Wallahi nikam banyi mamaki ba idan kika tuna da lamarin da su Baba Huwaila suka bamu, wallahi nifa dama jikina bai bani aljanu bane shaƙiyancin yarinyar nan yawa gareshi" Fahad dake gefe ya ce, "Amma wallahi yarinyar nan data gane kurenta" yana gama magana ya nufi ɗakin, Indo ta cire hijabi kenan Fahad ya ja hannunta ko magana babu, bai dire ta a ko'ina ba sai gaban su Mommy. Aunty Safna ce ta rufe da faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Mommy ce ta karɓe zancen cikin lallami da nasiha. Nasiha mai kashe jiki Mommy tayi mata tare da nuna mata illar kwaikwayon abinda takeyi, sosai jikin Indo yayi sanyi nadama ƙarara ta hau kan fuskarta. Su Mommy sun lura da haka ita kanta Aunty Safna ba ƙaramin daɗi taji ba, ganin yanayin da Indo ta shiga na nutsuwa. Fahad kallan Indo yayi ya ce, "Allah sa dai ta ɗauki faɗan da akayi mata, dan Allah Aunty ji yadda take sunne kai kamar ta kirki" Aunty Safna ta ce, "Kaima dai ka faɗa Fahad, wai a haka Yaseer yake so da wannan sakarcin nata" Indo zumɓurar baki tayi gaba ta ce, "Dan Allah Ammi ku daina faɗa a gaban Ya Fahad karya rainani" Indo ba ƙaramin dariya ta bawa su Mommy ba, Aunty Safna ta ce, "Wane raini kuma bayan shi ya fara saninki a lokacin da kike ƴar ƙauyenki, ba yanzu da kike waye ba. Ai wallahi kome kika zama yanzu Ɗana Fahad ne sila" Fahad kansa murmushi yayi, ko ba komai ya samu abin gori nan gaba, Indo kamar zatayi sabida takaici. Mommy ta ce, "Rabu da su Humaira, kice asalin kowa ma ai ƙauye. Kuma cen ɗinma ai a gida kike tunda kin rayu da Kawunki Maigari" Indo kamar wata yarinya ta yiwa Fahad gwalo, sannan ta ce, "Yauwa Mommy naji kince Maigari ɗan uwanku ne, amma banji kun gaya mun alaƙarku da shi ba rannan" Mommy ta ce, "Mahaifinsa da Mahaifin abokan wasa suke, lokacin da Mahaifinmu zaizo garin saida ya yiwa mahaifin Maigari tayin zuwa amma yaƙi, sai wani zuwa da Mahaifinmu yayi suka taho tare, har dai Allah ya sa shima yayi tunanin dawo da iyalinsa garin nan. Amma shi Mahaifinsa sai ya fara safarar kaya yana kaiwa garin Kura, har aminci ya haɗasu da Maigarin wancen lokacin. Humaira labarin yana da tsayi a takaice dai Maihafin Maigari ya zamu zama a wancen garin kuma mutum ne me amana, da tsoron shiga haƙƙin wani. Lokacin da Maigarin wancen garin ya fara wata jinya, sai yayi sanarwa tare da saka sojojin masarauta, ya sa hannu akan ko da bayan ransa Mahaifin Maigari, shi zai cigaba da mulkarsu saboda tausayinsa da amanarsa. To kinji yadda akayi, banda ma zumuncin yanzu ya zama yadda ya zama, dama duk cikin ƴan uwana ba yabon kai ba nafi su ƙoƙarin zumunci, kuma da har zuwa Kura muke muna zuwa mu shafe watanni a cen. Ni da kike gani a cikin garin da kikayi rayuwa babu inda bansani ba, idan na fara baki labari sai mu kwana anan." Indo ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Taɓ amma wallahi Maigari nasha da ƴan ƙauyen nan sam be ɗauko halin mahaifinsa ba, zalinci a cikin mutumin nan kamar..." da sauri Mommy ta ce, "Gidanku Humaira" Fahad yayi karaf ya ce, "Ku barta ta faɗa dan ni kaina wani zuwa da mukayi inaji wasu mutane na zaginsa, wai ya cinye wata gonar gadonsu" Aunty Safna ta ce, "Ƙaniyarka ana kwaɓar ƙanwarka kana kuma sakin bakinka" Fahad dariya yayi ya tashi zai shiga ɗakin, Indo ta ce." Ai wallahi nina saita shi sai da ya mayar musu da dik gonakinsu" da mamaki ta fara suka kalleta, gyaɗa kai Indo tayi basu labari tun daga lokacin da aka damƙawa Maigari takardunta, da ɓadda kamar da sukeyi ita ƙawayenta. Hatta ludayin da suka dinga ranƙwalawa Maigari sai da ta faɗa da umarnin da suka bashi akan ya mayar wa da mutane dukiyarsu. Fahad duk gimtsewar da yakeyi sai da ya dinga ƙyalƙala dariya, su Mommy dariya suke harda hawaye sai da suka tsaida, Mommy ta ce, "Dama Humaira ke kika rikitamu ɗan uwa lokacin da muka je" Indo dariya tayi ta ce, "Mommy nima ai Ya Fahad tasoni yayi saura kaɗan asiri na ya tonu, wallahi da ya kamani da na kaɗe dan ƴan garin nan sai mun tofin Allah tsine" Fahad me zaiyi banda dariya, Aunty Safna ta ce, "Ikon Allah wato mu duk shakiyancin ƙuruciya da mukayi muna yara, bamu kama ko rabinki ba Humaira. Allah ya ƙara shirya mana ku gabaɗaya." gabaɗaya suka amsa da Ameen, suna nan zaune Daddy mahaifin su Fahad ya shigo hannuwansa riƙe da su Aseem, zama sukayi suka cigaba da hira cikin barkwanci. Alhaji Mahmud Lamiɗo shine ainihin sunan Mahaifin su Fahad, asalinsa Fulanin daura ne. Sai dai kakanni da iyayensa a buɗi ido ya gansu a cikin garin Kano, Iyayensa sun rasu bayan haihuwar su Fahad babu jimawa, Su uku ne rak a gurin iyayensa. Shine babba sai ƙannensa mata biyu, Alhaji Mahmud ɗan kasuwa ne saboda baiyi wani zurfi a karatun boko sosai ba, Allah ya bunƙasa kasuwancinsa har ƙasashen waje yana fita sarin kaya. Mutum ne mai matumci da karamci gashi da zumunci da taimakon marasa ƙarfi, uwa uba gashi da alheri da sakin fuska. MU KOMA LABARI Kwanan su Indo biyu suka wuce garin Kaduna, wannan karan ma ba tare da Fahad suka wuce ba, saboda wani uzuri da zai gabatar kafin komawarsa. Indo ji tayi kamar ta je ta ajiye masa takardar da ta ɗauka, amma sai kawai ta share har suka koma. Makaranta me kyau Mahaifinta ya nemar mata idan tare da direban da yake kaita, yana dawo da ita. Wannan karan a JSS3 aka sakata tare da ɗaukan malam da suke yi mata lesson a gida, makarantar su Indo haɗe take da islamiyya basu suke dawowa gida ba, sai gabanin magriba. Wannan dalilin yasa koda Fahad ya koma basu cika wani haɗuwa ba. Indo batasan yadda akayi Yasir ya samu lambarta ba, amma kodai mene ne tasan a gurin Momma ya ƙarɓa, Indo tun tana fushi da Yasir har ta sakko suka cigaba da mutumci, kamar yadda Indo ta ɗauka tunda har yau Yasir bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba. Wata ranar Asabar Indo na cikin garden Yasir ya kirata a waya, sun shafe awa guda suna waya banda murmushi babu abinda take, wani lokacin sai dai ta tuntsire da dariya, kome Yasir ya gaya mata ta miƙe tsaye tana murna harda tsallenta. Dun abinda takeyi Fahad na tsaye yana kallanta wani ƙululun takaici ne ya rufeshi, Bai ankara ba yaji tace, "Wallahi nima nayi missing ɗinka Ya Yasir, amma kasan me zaka siyo mun idan zaka zo?" Kafin Yasir yayi magana Fahad ya ƙaraso a zafafe ya fusge wayar, kasheta yayi gabaɗaya fuska a tamke yace, "Ƙaramar yarinya da ke har kin iya soyayya ko? Shi kansa Yasir ɗin zamu gauraya dashi, zanga wanda zai ƙara baki waya yanzu" Indo batasan lokacin da hawaye ya fara zubar mata a fuska ba, da gudu tabi ta gefensa ta wuce ɗakinta. Iska mai zafi Fahad ya fesar ya wayar a aljihu ya bar gurin. AKWAI ƘURA🙊🤣😂 KUYI HAƘURI DA KURAKUREN CIKI. WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA ƳAN GROUP ƊINA NA *AMEERA ADAM FANS GROUP* DA MUTANENA ƳAN AMANA TA *WATTPAD* _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 85&86 Aunty Safna na falo Indo ta shiga falon da gudu, da ido ta bita da kallo har ta shige ɗaki. Bata bi ta kanta ba saboda tasan wataƙila ita da Fahad ne, faɗansu kuwa bata shiga dan baya ƙarewa daga wannan sai wannan. Fahad ɗaki ya shiga banda zarya babu abinda yakeyi, wayar ya ciro daga aljihu ya kunna domin ya shiga ciki yaga abinda take shukawa, sai dai password ɗin da yaci ƙaro dashi ne ya dakatar da shi. gwada lambobi ya farayi amma babu wacce tayi dai-dai, sai yayi tunanin bari ya sa 1234 yana sakawa ta buɗe. yana shiga cikin gallery ɗinta ya shiga ɓangaren camera, banda hotunanta dana su Aseem babu komai, whatsapp photos ya duba nan yaci karo da hotunan Yaseer ne birjik, har sai ɗaiɗaikun hotunan Jamilu, da wasu tsurarin ƴanmata wanda da alama ƙawayenta na makaranta ne.Da sauri ya fita ya koma cikin Whatsapp ɗinta, Ya Yaseer ya gani da sauri ya shiga, baiga wata doguwar hirarsu banda gaisuwa, sai kuma Assignment da take rubutawa take tura masa sai ya koya mata. fita yayi ya koma cikin lambar Jamilu da yaga anrubuta, Abokin Faɗa. Yana shiga ya fara duba hirarsu wacce rabi Voice note ce ba typing ba, ɗaya bayan ɗaya ya fara buɗewa yana saurara. Yawanci hirar tasu ta ƴar tsama ce sai wani lokacin gaisuwa ce, wani lokacin kuma labarin makarantarsu da take yawan bashi. Shima tana tura masa Assignment da yake koya mata, amma abin da ya dagula zuciyar Fahad da kodayaushe zaiji Jamilu na cewa Indo yayi missing ɗinta, wasu Voice note da ya ji Jamilu da Indo sunyi ya kunna su yafi a irga wanda Jamilu ya ce, "Ayusher yaushe zaki zo mana hutu ne?Saboda na nayi missing ɗin tsiwarnan taki" Indo ta ce, "Ya Jamil dama wai kana sona amma da sai kayi ta dukana" Jalimu ya ce, "Ayusher meyasa kika tambayeni?" Indo murmushi tayi ta ce, "Naga Baba Huwaila ce kawai take so na duk faɗin ƙauyen nan, bayan har kaini kake gurin Maigari ya dokeni" Jamilu ya ce, "Ayusher ni kuwa nake sanki! Bazan taɓa fasalta irin ƙaunar da nake miki ba. Amma lokaci na gabda zuwa da zan sanar dake abinda ya daɗe yana cimun tuwo a ƙwarya. Kina da Saurayi kuwa" Gaban Indo ne faɗi, murya a sanyaye ta ce, "Ya Jamil ba kai kake hanani kula kowa ba bayan su Zulai duk da samarinsu, kace har ansa ranar su." Jamilu ya ce, "Ai ba a ƙauye nake nufi ba, ina nufin anan Kaduna" da sauri Indo ta ce, "Cab bana kula kowa, bare mugun nan Ya Fahad yana nan ina zai barni na kula kowa" Gaban Jamilu ne ya faɗi amma sai ya basar ya ce, "Kintuna dai a ƙauye abinda ya taɓa faruwa da Hansa'u ko? To karki yadda ki kula kowa da sunan soyayya, idan lokacin yayi ni zan gaya miki, ko kuma na samo miki miji mai hankali kuma ɗan gayu ko bakya so?" Indo kunya taji kamar yana ganinta ta rufe fuska sannan ta ce, "To ya Jamil, amma karka samo mun mai mugunta kamar kai, kuma kyakykyawa nake so kamar kai ko wanda ya fika " ba ƙaramin dariya ta bawa Jamilu ba, Saboda ya lura har yanzu da sauran yarinta a kan Indo, yace "To shikenan ai dai-dai ke zan samo miki" sun jima suna hira sannan sukayi sallam. Fahad ba ƙaramin shaƙa yayi ba, kashe wayar ya ƙarayi sannan ya koma kan katifarsa ya kwanta. Bayan Magriba su Indo na zaune gabaɗaya suna cin Abinci, Fahad ya shigo da kofi a hannu da alama tea yake sha, Bayan ya zaune Indo miƙewa tayi zata bar falon Aunty Safna ta ce, "Humaira wai me akayi miki kike ta ɓata rai kamar wacce taci kashi?" Indo kamar jira take nan take idanunta suka ciko da ƙwalla, murya na rawa ta kalli Fahad ta ce, "Haka kawai ina zaune Ya Fahad ya karɓe mun waya, kuma waya muke da Ya Yaseer nasan yanzu haka ya neme ni bai same ni ba" Fahad ɗan zaro ido yayi wato ita bata ma kunyar faɗar wayar da take yi, har take jimamin kar Yaseer ya kira bai samu ba. Yana cikin tunani Aunty Safna ta ce, "Da abinda kikayi dan ruwa baya tsami banza" ganin angoyi bayan Fahad yasa Indo bata ƙara magana ba ta wuce ɗakinta. Tunda Fahad ya karɓi wayarta bai bata ba. Kuma itama bata tambayeshi ba, sai bayan wasu watanni sannan ya bata wayar tare da canza mata layi, da kamar bazata karɓa ba ta karɓe abarta tana watsa masa harara.Tun daga lokacin Indo bata kuma shiga sabgar Fahad, shi ɗinma bai cika shiga sabgarta ba. Sai dai duk wani moshi da Indo takeyi akan idonshi takeyi. BAYAN SHEKARA BIYU Watarana Indo ta dawo daga makaranta da yamma liƙis, tana shigowa kamar a mafarki ta hangoshi zaune akan kujera da waya a hannunsa yana dannawa, cikin bazata gabanta yayi mummunar faɗuwa. Dukda shi ba fari bane amma ba ƙaramin canjawa taga ya yi mata dukda batafi wata shida rabon da tayi tozali da shi ba, kyawunsa ya ƙara fitowa har wata ƴar ƙiba taga ya yi. cikin murna ta jefar da jakarta gefe ta zuba da gudu kamar zata rungumeshi sai kuma ta tsaya, murmushi ɗauke a fuskarta ta ce, "Ya Jamil kaine! Wow dama zaka zo amma ko jiya a waya baka gaya mun ba, ina My Baba Huwaila wallahi nayi missing ɗinku gabaɗaya, Ya Jamil ka ga yadda ka ƙara kyau kuwa" tana faɗa ta ɗan taɓe baki ta cigaba da cewa, "Inama yadda ka ƙara kyau haka ka daina mugunta amma ina wallahi nasan halinka yana nan, Yauwa ya wajensu Zulai yanzu ƴaƴanta nawa?" Kafeta yayi da kallo, wani abu na tsarga masa cikin jikinsa. Ganin ya tafi duniyar tunani yasa Indo ta hura masa iska a fuska, lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu Ayusher wacce tambaya kikesan na fara amsa miki?" ya ƙarasa faɗa yana harɗe hannuwa a ƙirji. Tura baki gaba tayi cikin shagwaɓa ta ce, "Ni duka zaka amsa mun" Murmushi yayi ya ce, "To ko zan amsa miki sai kin cire Uniform ɗinki kin huta tukunna" ɗan ɓata fuska tayi zatayi magana ya sa ɗanyatsansa akan laɓɓansa, sannan ya ce, "Kinsan dai bansan..." da sauri Indo ta karɓe zancen da, "Banasan musu, kedai Allah ya yi ki da kunnen ƙashi taurin kai kamar mutanen farko." gabaɗaya suka kwashe da dariya, Jamilu ya ce, "Shiyasa nake missing ɗinki Sarƙar Baba Huwaila yanzu gidanmu duk ba daɗi saboda bakya nan" Indo ta ce, "Ai nasan kashedin ka kenan shiyasa tuni na haddace shi." Duk abinda yake faruwa Fahad dake cen jikin mota yana jinsu kuma yana ganinsu, takowa yayi fuska a haɗe ya ce, "Ke! ba daga makaranta kika dawo ba, wuce ki shige ciki banasan sakarci" Indo ta ce, "Ya Fahad rabin raina na gani, kasan kuwa yadda nakeji da Ya Jamil kuwa? Tagwayen Baba Huwaila wasu ke kiranmu dan Allah ka barmu muyi hirar yaushe gamo" Jamilu wani irin daɗi yaji har cikin ransa, ko ba komai yasan Indo ta bashi babban matsayi. Fahad jin maganganun Indo yayi kamar saukar aradu, yana shirin magana Jamilu ya ce, "Wuce cikin gidan, kinsan banasan rashin kunya..." da sauri Indo ta kuma karɓe zancen da, "Kinsan dai banasa rashin kunya, dan wani lokacin kamar ɓeran birni haka kike" Jamilu murmushi yayi ya taka ya ɗauko mata jakarta ya miƙa mata sannan Indo ta wuce. Fahad sai lokacin ya bar gurin yabi bayan Indo suka wuce ciki, Jamilu yaji ba daɗi sosai dan idan duba alaƙar da ke tsakanin Indo da Fahad sai ya ga kamar zai rasa ta gabaɗaya, dan duk mai hankali yaga abinda Fahad yakeyi yasan Zallar kishi ne yake sashi. Alhaji Khaleel yaji daɗin zuwan Jamilu akan lokaci dukda bai sanar dashi dalilin kiran da yayi masa ba, kafin zuwan nasa. Da daddare suna zaune shi da Fahad,Jamilu da Mommy ya ce. "Nasan zakayi mamakin jin kiran da nayi maka! Jamilu dalilin da yasa na kiraka ba komai bane sai dan na damƙa amanata ta agurinka, saboda na yaba da hankali da nutsuwarka, na tabbata ko bayan rayuwa ta bazaka ci amana ta ba, zaka riƙe hannu bibbiyu tsakaninka da Allah " Tunda Mahaifin Indo ya fara magana gaban Fahad yake lugude jikinsa har rawa yake, wani irin gumi ne yake keto masa dikda Ac dake cikin falon. Alhaji Khalil ya cigaba da cewa. "Ban yanke wannan shawarar ba sai da muka tattauna da ƴan uwana, kuma suma ba ƙaramin dadi suka ji ba, danma basa ƙasar da su zasu tattauna da kai ba ni ba. Haka Kawunka Alhaji mun sanar da shi komai kuma yayi farin ciki sosai, sai dai mun roƙi alfarmar karya sanar da kai dan nafisan naji komai daga bakinka." fuskarsa ce ta sauya cikin damuwa ya cigaba da cewa, "Sai dai bansan ya zaka ɗauki lamarin ba zaka amince ko bazaka amince ba shine damuwa ta" a firgice Jamilu da Fahad suka ɗago da kai suna kallan Alhaji Khalil a yayin da ya dire a zancensa. Hmmmm wallahi akwai ƙura bari nayi nan🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ Naga bakya comments sosai 😥 kuyi haƙuri mu raka dan littafin yazo ƙarshe. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 87&88 Fahad bakinsa sai motsi yake kamar zai tari kawun nasa da tambaya, amma sai ya danne ya juya kai gefe. Jamilu jiki a sanyaye ya ce, "Abba in sha Allah zanyi bakin ƙoƙarina wajen ganin na riƙe wannan amana taka, dukda bansan wacce irin amana bace." Alhaji Khaleel ya ce, "Na buɗe sabon kamfanina a garin Kano, kamfanin leda ne da takalma shiyasa na yanke shawarar damƙa maka amanar sa, saboda da Kawunka zan damƙawa amma sai ya nuna mun gwara na sameka tunda shi baiyi zurfi a karatu ba, dan yana gudun kar a samu matsala dan haka kai zan mallakawa ragamarsa amma bansani ba zaka amince kuwa saboda kaima ma'aikaci ne, banasan na shiga haƙƙinka idan kana ganin babu damuwa.Karka ji kunyata idan har da takura ka mun bayani" Wata gwauruwar ajiyar zuciya Fahad ya sauke har sai da ta fito fili, Alhaji Khaleel murmushi yayi saboda ya fahimci sarai inda Fahad ya dosa, Jamila gyara zama yayi ya ce, "Abba ina matuƙar godiya da wannan karamci agareni, kuma insha Allah ba abinda zai gagara Allah ya sa albarka ya taya mu riƙo" gabaɗaya suka amsa da Ameen, sai lokacin Fahad yayi murmushi ya ce, "Malam Jamilu ina taya murna Allah ya taya riƙo" Jamilu ya amsa cikin sakin fuska, bayanin yadda abubuwan suke ya ɗan fara yiwa Jamilu yadda zai gane, sannan suka ɗan taɓa hira daga nan kowa ya kama gabansa. Washegari Jamilu ya koma sai dai gabaɗaya baiso ba ji yake kamar ya tafi ya bar wani ɓangare na jikinshi, ita kanta Indo taji ba daɗi saboda ba ƙaramin shaƙuwa sukayi da Jamilu ba, dukda dai kafin ya tafinma sai da sukayi faɗa ita, dalilin Faɗansu kuwa. Jamilu na zaune a harabar gidan Indo ta fito da wani kofi, cike yake da ƙanƙara. Kujera ta janyo ta zauna ta fara sha, Jamilu kallan kofin ya yi ya ce, "Ayusher me yasa bakyaji ne" Indo kauda kai gefe tayi ta ce, "Wallahi dama nasan sai ka yi magana, wai kai Ya Jamil meyesa bakasan duk wani abu da zanji daɗi?" Jamilu tamke fuska yayi ya ce, "Har yanzu bakida da kunya ko?" Harara ta watsa masa tana juya idanu haɗe da murguɗa ta ce, "Rashin kunya nayi maka sai dai in tsarguwa kayi..." kafin ta ƙarasa Jamilu ya bige bakin ya ce, "Inajin kafin na tafi sai na fasa wannan bakin naki, dan naga har yanzu hankalinki da saura" Idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Wallahi Ya Jamil da hankali na, idan ma banida shi ai sai idan a gurinka na koya..." da sauri ya kuma bige mata baki wannan karan ba ƙaramin zafi taji ba, hawayen da take maƙalewa ne ya sauko tashi tayi sai da tayi nisa da shi ta juyo ta ce, "Wallahi banyafe ba mugu kuma sai na gayawa Baba Huwaila" tana gama faɗa ta zuba da gudu. Jamilu murmushi ya yi a fili ya ce, "Wato Sarƙa har kwanan gobe Sarƙa ce, bazata taɓa sake hali ba. Rashin kunyar nan na nan." Lokacin da Jamilu yaje gida ba ƙaramin daɗi Baba Huwaila taji ba, kiran Mahaifin Indo sukayi suna yi masa godiya, har akan tagomashi da ya haɗowa Jamilu da zai tafi. Ba ƙaramin kyautata musu yake ba dan kayan abinci kafin wannan ya ƙare zai turawa Jamilu kuɗi a sayi wani. Bayan wasu ƴan kwanaki an buɗe kamfani cikin ƙudurar Ubangiji komai ya fara tafiya yadda ya kamata. Mahaifin Indo mota ya bawa Jamilu ƴar madaidaiciya ma kyau, kuma dikda wannan cigaba da Jamilu ya samu bai bar aikin koyarwarsa ba, Zumunci mai ƙarfi ne ya shiga tsakanin waɗannan gidajen guda biyu. Indo sun fara jarrabawar Waec ana ta shirin Candy kuma a shekarar ne zasuyi saukar Alkur'ani, Indo ta ƙara zama budurwa ta kuma wayewa kamar ba ita ba. Sai dai akace idan ka shekara dubu baka ga mutum ba, idan kun haɗu tambayeshi wani abun ba halinsa ba, halin Indo na tsokona da abinda ba'a rasa ba yana nan.Yanzu a cikin dangin Mahaifi da mahaifiyarta babu Wanda bai santa ba, sai dai ba kowa ta cika shiga sabgarsa ba, saboda har a lokacin gani take ita ba ƴar wasu bace, dukda tana ƙaunar iyayenta amma har lokacin tafi jin kanta kamar yadda take ada ƴar ƙauye, shiyasa bata cika shiga sabgar cousin ɗinta na dangin Mahaifinta ba, saboda ta lura wasu daga cikinsu suna da ɗaga kai, musamman ƴan ɗakin su Lubna. Wasu Ƴaƴan abokin mahaifinta mutum biyu ne suka nuna suna santa, amma sam basu kwanta mata ba, da suka matsa mata sai ta ce sai tayi candy ko zata fara kula samari. A ɓangarenta da Yaseer kuwa ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba, kusan duk dangin kowa yasan da shaƙuwarsu, dan ita kanta Indo ta yarda son Yaseer yayi nisa a zuciyarta.Sai dai har zuwa wannan lokacin bai taɓa furta mata kalmar soyayya ba, hakan ne yasa itama Indo take nuna kamar bata fahimci inda ya dosa ba, A ɓangaren Jamilu shima ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba, sai dai ko kaɗan Indo bata tsammanin soyayya daga gurinsa, tafi danganta hakan da shaƙuwa. Kuma Jamilu ya barwa zuciyarsa akan sai Indo tayi Candy koda zai sanar mata da kalmar soyayya, dan idan ya tuna abinda zai sanar mata gabansa har faɗuwa yake, saboda Alasan abokinsa ya taɓa tarar ta tun a ƙauye yace yana santa, tun daga ranar Indo ta daina ganin mutumcin shi sai ma ta koma ce masa Ɗan iska. Shi kansa Yaseer wanan hukuncin ya yanke, na sai Indo ta yi Candy zai sanar da Ita, kuma ya gabatarwa da manyansu maganar aurensu. Fahad a har kullin yanasan nunawa Indo kulawar da zata fahimci yana ƙaunarta, amma wani tsagi na zuciyarsa na ƙaryata wannan tunanin, kuma yana ganin kamar raini ne zai ƙara samun gurbin zama a tsakaninsu, tunda dama tuni Indo ta riga da ta raina shi. Wata mata na gani a cikin duhun bishiyoyi, fuskarta ɗauke da niƙab. A gaggauce ta ce, "Hadari da kyar na samu lambarka, dan Allah aikin wata yarinya zan baka, akwai adireshin gidansu dana makarantarsu a jikin takardar, banasan a samu matsala kawai ku kashe ta. Na turo muku Million biyu dan Allah banasan a samu matsala." Hadari ƙarɓa yayi yana murmushi ya ce, "Baki da damuwa Hadari baya jagwal, ki baza kunne nan da ƴan awanni zakiji sanarwar mutuwarta." da sauri ta bar gurin saboda batasan ta samu matsala. Su Indo sun fito daga makaranta Direbansu ta hango, da sauri ta ƙarasa tana yiwa ƙawayenta sallama. Tana shiga mota wasu mutane da ke cikin wata baƙar mota suka rufawa motar su Indo baya, sai da suka fara barin cikin mutane waɗannan mutanen suka sha gaban motar su Indo. cikin tashin hankali Direban motar yake bin motar da kallo, Indo jikinta banda rawa babu abinda yake yi, mutum biyu ne suka fito daga motar hannunsu ɗauke da bindiga. cikin fargaba direban ya ce, "Humaira ya zamu yi?" Indo tace, "Mu gudu kawai, bani wayarka na kira Daddy." bata rufe baki ba suka ɗaga bindiga sama suna sakin harbi. Wayarsa babbar ya ɗauko ya miƙowa Indo, sai dai kash tana kira babu kuɗi a ciki. Da sauri ta miƙa masa cikin kiɗima ta ce, "Ba kuɗi musty, ba kuɗi" ƙaramar wayarsa me madanne ya miƙa mata, wanda alokacin tuni har sun ƙaraso wajen motar su Indo. Da sauri ta danna lambar Mahaifinta wanda yayi daidai da buɗe murfin ƙofar, da sauri indo ta tura wayar cikin aljihun wandon uniform ɗinta. Ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya fisgo Indo yana kifeta da mari, da sauri Musty ya fito ya fara roƙonsu, wanda yayi dai-dai da ɗaukan wayar da Alhaji Khalil yayi, kiran da Indo tayi masa. "Dan Allah maigida kuyi haƙuri kuyi mana rai" Mutumin da baka ganin komai a fuskarsa, sai ƙwayar idonsa ya ce, "Ɗan samari ba gurinka muka zo ba, mun zo ɗaukan wannan yarinyar ne" Jin maganar nan ba ƙaramin ɗaga hankali su yayi ba, Musty ya ce, "Dan Allah ku haɗa dani dan idan na koma bansan me zan cewa mahaifinta ba, wallahi bazan taɓa fita ba. Idan kuma kuɗi kuke so ko nawa ne Alhaji zai bayar..."Tun bai rufe baki ba mutumin ya sakar masa harbi a ƙafa yace, "Ga shaida nan na bar masa dan na rage masa wahalar nema, dan idan ba'a ganku ba gabaɗaya ɗauka za'ayi tana raye mukuma kwangilar kisa aka bamu" yana gama faɗa ya fisgi hannun Indo tana ihu, Musty durƙushe yake yana ɗaga hannu alamun a taimaka masa, yana ji yana gani suka tasa ƙeyar Indo a mota suka tafi da ita. Musty na nan wani me mashin yazo wucewa ya ganshi tsugunne cikin jini, da sauri ya ƙarasa gunshi dan ganin halin da yake ciki, Musty hanya ya dinga nuna masa yana cewa, "Ka taimaka sun tafi da ita" mutumin tambayarsa ya yi, a take Musty ya bashi labarin abinda ya faru, taimaka masa yayi ya sashi a mota, sannan ya fita cen gurin mutane yayi yekuwar mutane suka taho suka ɗaukeshi suka wuce da shi asibiti. Alhaji Khalil duk abinda yake faruwa akan kunnensa, sakamakon kiran da Indo tayi masa da wayar Musty bata katse ba. Jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali, kiran wayar yake amma ba'a ɗauka ba. Da sauri ya kira Lambar Director ɗin makarantar su Indo, dan tsammaninsa a makaranta ne abinda ya faru. Saboda ruɗewa ya manta da lambar Musty ce aka kirashi, amma yana kiran Director ya shaida masa tuni ɗalibai sun jima da tafiya. Da sauri ya katse ya kira lambar kwamishinan ƴan sanda ya sanar da shi halin da ake ciki, Kwamishina cewa yayi ya tura masa lambar da aka kirashi da ita, zasu bibiyu sahun gurin da suke. Alhaji Khalil tura masa lambar yayi sannan ya fita daga cikin office ɗinsa, ya nufi ofishin Kwamishina dan ƙara jaddada masa. Gudu yake kamar zai tashi sama har a ƙarasa, lokacin da yaje tuni har sun fara tracking ɗin lambar kuma sun tura jami'ansu suna bibiyar sahun makasan da suka tafi da Indo. Mutanen da suka ɗauki Indo wata hoda suka shaƙa mata, nan take jikinta ya saki ta faɗi ƙasa ba numfashi. Tafiya suka yi me ɗan nisa kamar zasu bar garin, sannan suka shiga cikin wani ƙasurgumin daji, basu wani shiga cen ciki ba sukayi parking ɗin motarsu. Zuwan su babu jimawa Indo ta fara farkowa, Ɗaukkota sukayi kamar wata ƙaramar yarinya, a ƙasa suka wurgar da ita zafin buguwar da taji yasa ta ƙarasa wartsakewa. A zabure ta miƙe zaune tana ja da baya nan take ta tuna abinda ya faru da ita, idanunta ne suka ciko da ƙwallah, haɗa hannuwanta biyu tayi cikin roƙo ta ce, "Ku dubi girman Allah kuyi haƙuri karku cutar dani" Hadari dake cen gefe da yake ƙarewa Indo kallo, ji yayi ta matuƙar birgeshi har zuciyarsa, takowa yayi har gabanta ya tsugunna a gabanta yana ƙarewa laɓɓanta kallo, tana ƙarasa magana yasa ɗan yatsansa a laɓɓanta, sannan ya ce, "Yarinya kwangila aka bamu mu kashe ki, daba dan haka ba dana ƙyaleki amma ba wannan alƙwari, na yaba da kyawunki ƙwarai." Indo girgiza kai ta farayi ta ce, "Duk wanda ya baku wannan kwangilar bansan me na tsare masa ba, tun ina jaririya yake farauta rayuwata ashe har yanzu baza'a barni na huta ba?" Sunkuyar da kai tayi ta ce, "Ku kashe ni kawai, saboda nasan ko baku kasheni yanzu ba dole zasu kasheni. Amma dan Allah inasan idan kun kasheni, ko da da daddare ne ku kai gawa ta ƙofar gidan Mahaifina ayi mun sutura, karku barni dokar daji dan Allah" Indo ta ƙarasa faɗa cikin karaya. Hadari jikinsa ne yayi sanyi ba yau ya saba irin wannan aikin ba, amma lokaci ɗaya yaji tausayin yarinyar ya kamashi, ganin yanayinsa yasa ɗaya daga cikin yaransa ya ce, "Haba Megida karfa ka ɓata mana harka... " tun kafin ya ƙarasa magana Hadari ya sakar masa harbi a ciki take ya faɗi ko shurawa baiyi ba. Indo zaro ido tayi tana rushewa da kuka, Hadari hannu yasa ya tayar da Indo tsaye yace, "Bazamu kasheta ba zamu tafi da ita ƙasar nijar tunda a cen zamu yada zango, ni zan aureta..." be kai ga rufe baki ba suka ji motar ƴan sanda, suna shirin shiga mota su gudu suka fara sakar musu harbi, mutum biyu ne suka gudu aka kama mutum uku, amma a cikin wanɗanda aka kama harda Hadari. Indo banda kuka babu abin da take yi, kamata sukayi suka saka a mota, suma su Hadari aka tasa ƙeyarsu zuwa Headquarter ƴan sanda. Alhaji Khalili bai sanar da Mahaifiyar Indo ba saboda yasan nan da nan hankalinta zai tashi, idan ba'ayi sa'a bama hawan jininta yana iya tashi. Sai dai ganin su Indo basu dawo ba yasa ta kira wayar Musty amma a kashe, wayar mijinta ta kira ta sanar dashi, a lokacin nuna mata yayi kamar bai san me yake faruwa ba, ya ce mata zai kira Director makarantasu. Bayan ƴan mintuna ya ƙara kiranta ya ce mata akwai abinda aka zaunar da ɗalibai ake musu, jikinta a sanyaye ta amsa amma wani tsagi daga cikin zuciyarta ya kasa amincewa da maganar mijinta, sai dai batasan ta ƙaryata shi yasa bata musa masa ba. Amma tasan idan har akwai wani muhimman abu da za'a tsaida ɗalibai tun kafin ranar Director yake buga takarda, kowanne ɗalibi ya kaiwa iyayensa. Fahad ne yazo ya same ta cikin jimami bayan ya tambayeta take sanar da shi abinda yake faruwa. Mukullin motarsa ya ɗauka ya nufi makarantar su Indo, domin ya ji ba'asin da za'a zaunar da yara har doshin magriba batare da sanin iyayensu ba. Sai dai yana zuwa ya samu makatarantar a rufe ko megadinta baya nan, da sauri ya kira lambar Kawunsa a nan yake sanar da shi abinda yake faruwa, tare da jan kunnensa akan karya sanarwa da Mahaifiyarta abinda ya faru. Kai tsaye Fahad cen Headquarter ƴan sandan shima ya wuce hankali a tashe, Su Indo kuwa sai wajen ƙarfe takwas na dare suka ƙarasa Headquarter, lokacin da mahaifinta ya ganta ba ƙaramin farinciki yayi ba, ita kanta Indo rungume shi tayi ta rushe da kuka, cikin kuka ta ce, "Daddy wai me nayi musu da basa so na? Meyasa basa san suga ina rayuwa da Iyayena? Daddy me na aikata masu ne?" kukanta ne ya tsananta fuskarta tayi jawur, tausayinta ne ya kama Fahad saboda ya rasa me ta tsare musu da tun tana cikin tsuma take fuskantar barazana daga garesu, sai dai babban farin cikin da yayi da Allah yasa aka kamasu, yasan ko ba komai zasu faɗi wanda ya sasu wannan mugun aikin. Mahaifinta ƙara riƙeta yayi idanunsa na cikowa da ƙwalla, yasan shi dai duk tsawon rayuwarsa bai taɓa aikatawa wani mugun abun da zai yi masa sakayya da irin wannan abun ba.Godiya ya yi wa Allah, da Allah yasa aka kama waɗannan masu mugun aikin kuma a yanzu ne zai san waye wannan babban maƙiyin nashi. Kallan Indo ya yi ya ce, "Ina Musty fa?" Indo ta ce, "Tun kafin su tafi dani suka harbe shi" A razane ya ce, "Yana ina yanzu?" Bata bashi amsa ba yaji ankirashi a waya, yana ɗauka aka sanar dashi asibitin da Musty yake da halin da yake ciki. A hanzarce yasa Fahad ya wuce da Indo gida, sai dai razanar da tayi yasa taƙi sakin Mahaifinta dan yanzu ma gani take idan sun tafi wani abu zai iya faruwa dasu. Ya lura da halin da Indo take ciki, cikin lallashi ya ce, "Humaira ba abinda zai faru kinji, kinga ankama su kuma in sha Allah ƙarshen matsalar tazo." Bakin ta na rawa ta ce, "Daddy a gabana suka harbi Musty, kuma a gabana suka kashe ɗan uwansu, nima fa sunce kasheni zasu yi" Fahad ne ya riƙo hannunta cikin tausayi ya ce, "Bazasu kashe ki ba kinji, zo mu wuce gida." Indo kamar wata ƙaramar yarinya, haka ta bishi suka shiga mota sai juye-juye take har suka ƙarasa gida. Lokacin da Daddy yaje asibiti Musty bacci yake saboda Alluran da akeyi masa, ansamu nasarar ciro harsashin kuma har angyara ƙafar annaɗe da bandeji. Duk abinda ya kamata Alhaji Khalil ya biya sannan ya kira Ƙanin Mahaifin Musty ya sanar dashi, kasancewar Musty maraya ne. kafin wani lokaci ƴan uwan Musty sun cika asibitin. Bayan kwana biyu jikin Musty yana ƙara samun sauƙi sosai, Da farko Mahaifiyar Indo cewa tayi sai dai Indo ta haƙura da zuwa makarantar, bayan da Daddyn Indo ya gaya mata abinda ya faru. Sai dai Daddy yayi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta ɗan samu nutsuwa, duk ranar da Indo take da Jarrabawa Fahad ne yake kaita, ya jira ta gama ya dawo da ita gida. Su Hadari fir suka ƙi faɗar wanda ya saka su Kashe Indo sai da suka ji wahala tukunna suka faɗa, a lokacin Alhaji Khalil na gida Kwamishina ya kirashi zuwa cen Headquarter. Bayan yaje ya saurari abinda su Hadari suka faɗa a razane ya ce, "Hajiya Safiya fa? Hajiya Safiya dai matar ɗan uwana?" ana cikin haka Ɗan uwansa Yaya Haruna tare Ɗansa Muhsin suka zo, Ɗan uwan nasa na zuwa ya ce, "Khalil kace mun sun faɗi wanda ya tura su waye dan Allah? Wanne azzalumin ne?" Alhaji Khalil kunyar Yayansa yake yace matarsa ce, Kwamishina ne ya karɓi zancen da, Sunce Hajiya Safiya ce ta sasu kuma har Video lokacin da take basu kwangilar suka nuna mana, tare da kwanan watan ranar da taje ta same su a mazauninsu, Kwamishina ya ƙarasa faɗa yana nuna masa bidiyon wayar Hadari. A razabe Mahaifin Lubna ya ce, "Safiya tawa kai ƙarya ne, a rasa wa za'ayiwa sharri sai Iyalina? Gaskiya da sake bazai yuwu ba." _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 89&90 Kwamishina gyaran murya ya yi ya ce, "Alhaji dan Allah ka saurareni ka bamu haɗin kai, dan sun faɗi haka bashi zai nuna cewar da gasken hakan bane. Bincike shi zaiyi aikinsa mu tabbatar da me gaskiya, mara gaskiya mu miƙashi Kotu..." a hassale Yaya Haruna ya ce, "Kana zargin Iyalina a matsayin mai laifi kuma ka ce na kwantar da hankalina, sam ni ban yadda da wannan maganar ba. Kai Mhusin tashi mu tafi." Muhsin da tun da yaji sunan mahaifiyarsa a ciki yake muzurai, yana harare-harare ya miƙe ya bi bayan mahaifinsa. Har ya kusa zuwa ƙofa Kwamishina ya ce, "Alhaji karka manta ita hukuma tana amfani da hujja ne, zan turo yara su binciki matarka, ba ma ita ba ko da kai ne bincike ya biyo ta ka kanka ina fatan zaku bamu haɗin kai." Yaya Haruna ji yayi kamar anwatsa masa ruwan zafi, saboda masifa jikinsa har rawa yake ya juyo ya ce, "Na amince idan kuka same ni ko iyalina da laifi duk hukuncin da ya dace kuyi mun, idan kuma yaran nan ƙazafi sukayi mata wallahi sai ɗauki mataki." ya juya fuuu ya bar ofis ɗin Alhaji Khalil na ƙwala masa kira, amma ko waige baiyi ba. Kwamishina murnushi ya yi ya ce, "Alhaji karka damu, idan da sabo mun saba da ganin irin haka harma fiye da haka. Ka ƙyaleshi na ɗan lokaci zai sakko kasan ko waye aka gaya masa irin haka, zai shiga irin wannan yanayi amma ka bari bincike shi zai fayyace mana komai." Alhaji Khalil ya ce, "Yallaɓai ina tsoron kar wannan dalilin ya wargaza farincikin dangina, wallahi ina matuƙar ƙaunar ƴan uwana banasan zumuncinmu ya ruguje." Kwamishina ya ce, "Abokina sai fa ankauda ƴan uwantaka da sanayya, idan ba haka ba za'ayi kitso da kwarkwata." ajiyar zuciya Alhaji Khalil ya yi ya ce, "Haka ne Abokina, Allah ya iya mana" Kwamishina ya ce, "Amin, zan tura yarana su gayyato mana Hajiya Safiya, kuma zamu tsaurara bincike akai" tattaunawa suka ƙarayi sannan suka yi sallama da Kwamishina ya wuce gida. Lokacin da yaje gida ya sanarwa da Aunty Safna maganar da su Hadari suka faɗa, jikinta ne ya yi sanyi cikin kuka ta ce, "Ni kuwa me nayi wa Safiya da zata aika haka agareni? Me na tsare mata a rayuwa?" Lallashinta ya dinga yi har ya samu ya lallasheta, ta daina kuka sannan ya kira sauran ƴan uwansa ya sanar da su halin da ake ciki. A cen gidan Alhaji Haruna ƴan sanda tuni sukayi dirar ɗango, da gaske suke yasa Alhaji Haruna ya ce zai ɗauki matarsa ya kai ta da kansa. Hajiya Safiya banda muzurai babu abin da take yi. Hankalinta bai ƙara tashi ba sai da suka ƙarasa tayi tozali da su Hadari, ana tambayar Hadari ya tabbatar da ita, har da lambar wayarta ya shaida musu a wayarta da kwangilar da ta basu, daga ƙarshe ya nuna musu alert ɗin kuɗin da tayi musu wanda ga sunanta nan, ɓaro-ɓaro da lambar bankinta. Lokacin da abin yake faruwa Fahad da Alhaji Khalil sun koma headquater, a gabansu duk yake faruwa. Alhaji Haruna ne ya buga mata tsawa jin antamabaye tayi shiru. kamar munafuka haka ta fara raba idanu tana motsa baki amma ta kasa magana, a hassale ya miƙe kamar zai doke ya ce, "Wai ba magana nake miki ba? Kece kika basu umarnin kashe Humaira?" girgiza kai tayi ta ce, "A'a ƙarya suke mini" Hadari yayi karaf ya ce, "Ke lallai matar nan ni zakiyiwa latsi, wallahi ko kwalba haka ta ganni ta ƙyale a iya sharri" Kwamishina ya ce, "Idan ba ke bace, ya akayi kikayi musu alert?" tsugunnawa Hajiya Safiya tayi ta ce, "Dan Allah Alhaji ku gafarceni wallahi sharrin sheɗan ne..." kafin ta rufe baki Alhaji Haruna ya ɗauke ta da mari ya ce, "Keda Sheɗan ɗin na ɗura muku ashar, kisa akashe mun ƴar ƙanina ki ce sharrin sheɗan ne?" da sauri Alhaji Khalil ya riƙe ɗan uwansa yana bashi haƙuri, Yaya Haruna banda huci babu abinda yake yi, cikin huci ya ce. "Wallahi sai an hukuntaki annamimiya makira" Muhsin da ke gefe haushin mahaifiyarsa ne yaji ya kamashi, wani irin kallo yake jifanta da shi mai wuyar musaltuwa. Da ƙyar Kwamishina ya sallami Alhaji Khalil tare da ƴan uwansa, lokacin da zai tafi ya kalli Mahaifiyar su Lubna ya ce, "Kuma wallahi ni da ke har abada kije na sake ki saki uku" Hajiya Safiya rushewa tayi da kuka amma ko waigenta baiyi ba, Fahad banda harara babu abinda yake wurga mata. Daga nan Headquater kai tsaye kotun Addinin musulunci aka miƙa su Hadari da Hajiya Safiya, Yaya Haruna da kanshi ya ɗauki lauyan masu ƙara. ya yinda Hajiya Safiya ta ɗauki lauyanta, su kuwa su Hadari basu da lauya dan haka Alƙali yace sai dai su kare kansu. Su Lubna da sauran Ƴaƴan Alhaji Haruna gabaɗaya basu ji daɗin abinda mahaifiyarsu ta aikata ba, Lubna sai yanzu take jin wata irin kunyar Indo, babban tashin hankalinta Yaseer ne, tunda ta san tunda cen ma Yaseer ba santa yake ba ta Indo yake bare yanzu da haka ta faru. Cikin lokaci ƙalilan duk ta rame ta bushe ta lalace kamar wacce tayi laifi, sai abu na gaba da idan ta tuna yake hana ta bacci shine hukuncin da za'a yankewa mahaifiyarsu, gashi tun ba'aje ko'ina ba mahaifinsu ya sauwaƙewa mahaifiyarsu. Waɗannan tunane-tunane ne suka haɗu suke dagula lissafin Lubna, wanda bacci ma ya ƙauracewa idanunta. Wata ranar Laraba ce aka zauna aka fara sauraron ƙarar su Indo, kotun cike take da mutane aka aka shigo dasu suka tsaya gurin mazaunin masu laifi, magatakarda ne ya karanta ƙunshin tuhumar sannan Alƙali ya kalli su Hadari ya ce, "Kai meye sunan ka?" Hadari ya ce, "Sunana Salihu amma anfi sanina da Hadari" Alƙali ya ce, "Shin kaji ƙunshin tuhumar da ake muku" Hadari ya ce, "Naji ya me shari amma a taimaka ayi mana afuwa wallahi sharrin sheɗan ne" ɓangaren Hajiya Safiya Alƙali ya koma ya tambayi sunan ta ta ce, "Sunana Safiya Alhasan" Alƙali ya ce, "Shin ko akwai dalilin da ya sa kika aika a kashe ƴar mutane? Idan akwai kotu tana sauraren ki" Hajiya Safiya ta kalli Indo dake cen a zaune kusa da mahaifiyarta ta ce, "Ya me shari'a bani da wani dalili face ƙyashi, hassada da baƙin ciki da suka ruɗeni. Kasancewar mun taso gari ɗaya kuma unguwa ɗaya da Safna, sai ya kasance makarantarmu ɗaya kuma ajinmu ɗaya da ita. Safna tana da ƙwazo da ƙoƙari yadda har makarantar mu ya kasance ansan da ita, kafin zuwanta duk ajinmu dama na girmesu dan haka gabaɗaya sai suke tsorona, duk abinda na faɗa basa iya ƙetarewa kuma duk abinda na gani agunka nace ina so zan karɓa baka isa ka tanka ba. Kwatsam sai aka kawo Safna ajinmu, tun daga zuwanta na fara nuna halina akanta amma sai taƙi amince da shi, saboda bata da tsoro ko kaɗan kuma girmana baisa ta ji shakkuna ba. Ganin haka yasa sauran ƴan ajinmu suka fara daina tsorona, daga baya ma sai gabaɗaya ƴan ajinmu suka rainani, tun daga lokacin tsanarta ta ɗarsu a zuciyata. Sai kuma ƙoƙarin da take da shi duk lokacin da akayi jarrabawa ita take zuwa ta ɗaya, ni kuma kusan nice ta ƙarshe ta biyun ƙarshen aji. Wata rana munyi faɗa da ita, dan kuwa ni na takali faɗan kawai sai ta mun gorin ƙoƙari nikuwa na lakaɗa mata duka, aikuwa tana guduwa ta samu ƴan ajinmu suka fara yi minj waƙar Safiyya ganɗama daƙiƙiya, tun daga ranar sunana yayi fice a makarantarmu, har ta kai ta kawo idan bakace Ganɗama babu wanda zai ganeni. Sai na koma mujiya a cikin makarantar kowa tsokanata yake yi, ana haka har Yayana ya zo ya sanar da shugan makarantar, daga ranar ne na ɗan samu sasaauci. Ana cikin haka sai su Safna suka dawo nan layinmu gida biyu ne kawai ya rabamu da su, a lokacin kuma muna shekarar mu ta ƙarshe a sakandire. A lokacin ina tare da saurayina Sulaiman yana ƙyalla ido da ya ganta, ya daina zuwa gurina dana matsa masa da tambaya ya kwatanta mun ita, tare da cewa ya faɗa tarkon ƙaunarta. Ba ƙaramin tashin hankali na shiga a lokacin ba, amma sai mahaifiya ta tausheni tare da nusar dani wataƙila dama ba mijin aurena bane. Wata rana da yamma na fita naci karo da Safna tana zance da Khalil, tunda na ƙyalla ido akanshi naji duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar shi, a ranar dashi na kwana a raina ko baccin kirki banyi ba, tunani na dinga yi yadda zan samu na samu koda lambarsa ce amma na kasa. Sai dabara ta faɗo mun akan na ƙulla ƙwawance da Safna ko na samu ta saki jiki dani na samu lambarsa a gurinta. Shiryawa nayi naje gidansu na sameta muka gaisa fuskarta ba walwala, kasancewar kowa yasan ba shiri muke da Safna, sunkuyar da kai ƙasa nayi na nemi alfarma da mu aje wannan rashin jituwar da muke gefe ɗaya mu cigaba da rayuwa kamar kowa, amsa mun tayi daga haka na fara nuna soyayyata ga Safna a fili wanda a zuciyata ba haka bane, ita kanta Safna da farko ƙin sakin jiki tayi da ni, sai daga baya ta saki jikinta muka cigaba da ƙawancenmu gwanin sha'awa..." Alƙali ne ya ƙatse Hajiya Safiya sannan lauyoyi suka cigaba da fafatawa, daga ƙarshe Alƙali ya ɗaga shari'ar zuwa goma ga watan gaba, sati biyar kafin komawarsu.Hajiya Safiya da su Hadari aka tasa ƙeyarsu gidan yari, haka kotun ta tashi mutane na Allah wadai da hali irin na Hajiya Safiya. A yau ne su Indo suka zana jarrabawarsu ta ƙarshe, murna gurinta tare da sauran ɗalibai ba'a magana. Kuma tun safiyar ranar Yaseer ya tura mata saƙwanni kala-kala na soyyaya, kuma a ranar ne ya da Daddynsa abinda ke tsakaninsa da Indo, Daddy ba ƙaramin farinciki yayi ba, a take kuma ya kira ƴan Mahaifin Indo ya sanar dashi, shima ba ƙaramin daɗi yaji ba nan take ya kira sauran ƴan uwansa ya sanar dasu. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 89&90 Kwamishina gyaran murya ya yi ya ce, "Alhaji dan Allah ka saurareni ka bamu haɗin kai, dan sun faɗi haka bashi zai nuna cewar da gasken hakan bane. Bincike shi zaiyi aikinsa mu tabbatar da me gaskiya, mara gaskiya mu miƙashi Kotu..." a hassale Yaya Haruna ya ce, "Kana zargin Iyalina a matsayin mai laifi kuma ka ce na kwantar da hankalina, sam ni ban yadda da wannan maganar ba. Kai Mhusin tashi mu tafi." Muhsin da tun da yaji sunan mahaifiyarsa a ciki yake muzurai, yana harare-harare ya miƙe ya bi bayan mahaifinsa. Har ya kusa zuwa ƙofa Kwamishina ya ce, "Alhaji karka manta ita hukuma tana amfani da hujja ne, zan turo yara su binciki matarka, ba ma ita ba ko da kai ne bincike ya biyo ta ka kanka ina fatan zaku bamu haɗin kai." Yaya Haruna ji yayi kamar anwatsa masa ruwan zafi, saboda masifa jikinsa har rawa yake ya juyo ya ce, "Na amince idan kuka same ni ko iyalina da laifi duk hukuncin da ya dace kuyi mun, idan kuma yaran nan ƙazafi sukayi mata wallahi sai ɗauki mataki." ya juya fuuu ya bar ofis ɗin Alhaji Khalil na ƙwala masa kira, amma ko waige baiyi ba. Kwamishina murnushi ya yi ya ce, "Alhaji karka damu, idan da sabo mun saba da ganin irin haka harma fiye da haka. Ka ƙyaleshi na ɗan lokaci zai sakko kasan ko waye aka gaya masa irin haka, zai shiga irin wannan yanayi amma ka bari bincike shi zai fayyace mana komai." Alhaji Khalil ya ce, "Yallaɓai ina tsoron kar wannan dalilin ya wargaza farincikin dangina, wallahi ina matuƙar ƙaunar ƴan uwana banasan zumuncinmu ya ruguje." Kwamishina ya ce, "Abokina sai fa ankauda ƴan uwantaka da sanayya, idan ba haka ba za'ayi kitso da kwarkwata." ajiyar zuciya Alhaji Khalil ya yi ya ce, "Haka ne Abokina, Allah ya iya mana" Kwamishina ya ce, "Amin, zan tura yarana su gayyato mana Hajiya Safiya, kuma zamu tsaurara bincike akai" tattaunawa suka ƙarayi sannan suka yi sallama da Kwamishina ya wuce gida. Lokacin da yaje gida ya sanarwa da Aunty Safna maganar da su Hadari suka faɗa, jikinta ne ya yi sanyi cikin kuka ta ce, "Ni kuwa me nayi wa Safiya da zata aika haka agareni? Me na tsare mata a rayuwa?" Lallashinta ya dinga yi har ya samu ya lallasheta, ta daina kuka sannan ya kira sauran ƴan uwansa ya sanar da su halin da ake ciki. A cen gidan Alhaji Haruna ƴan sanda tuni sukayi dirar ɗango, da gaske suke yasa Alhaji Haruna ya ce zai ɗauki matarsa ya kai ta da kansa. Hajiya Safiya banda muzurai babu abin da take yi. Hankalinta bai ƙara tashi ba sai da suka ƙarasa tayi tozali da su Hadari, ana tambayar Hadari ya tabbatar da ita, har da lambar wayarta ya shaida musu a wayarta da kwangilar da ta basu, daga ƙarshe ya nuna musu alert ɗin kuɗin da tayi musu wanda ga sunanta nan, ɓaro-ɓaro da lambar bankinta. Lokacin da abin yake faruwa Fahad da Alhaji Khalil sun koma headquater, a gabansu duk yake faruwa. Alhaji Haruna ne ya buga mata tsawa jin antamabaye tayi shiru. kamar munafuka haka ta fara raba idanu tana motsa baki amma ta kasa magana, a hassale ya miƙe kamar zai doke ya ce, "Wai ba magana nake miki ba? Kece kika basu umarnin kashe Humaira?" girgiza kai tayi ta ce, "A'a ƙarya suke mini" Hadari yayi karaf ya ce, "Ke lallai matar nan ni zakiyiwa latsi, wallahi ko kwalba haka ta ganni ta ƙyale a iya sharri" Kwamishina ya ce, "Idan ba ke bace, ya akayi kikayi musu alert?" tsugunnawa Hajiya Safiya tayi ta ce, "Dan Allah Alhaji ku gafarceni wallahi sharrin sheɗan ne..." kafin ta rufe baki Alhaji Haruna ya ɗauke ta da mari ya ce, "Keda Sheɗan ɗin na ɗura muku ashar, kisa akashe mun ƴar ƙanina ki ce sharrin sheɗan ne?" da sauri Alhaji Khalil ya riƙe ɗan uwansa yana bashi haƙuri, Yaya Haruna banda huci babu abinda yake yi, cikin huci ya ce. "Wallahi sai an hukuntaki annamimiya makira" Muhsin da ke gefe haushin mahaifiyarsa ne yaji ya kamashi, wani irin kallo yake jifanta da shi mai wuyar musaltuwa. Da ƙyar Kwamishina ya sallami Alhaji Khalil tare da ƴan uwansa, lokacin da zai tafi ya kalli Mahaifiyar su Lubna ya ce, "Kuma wallahi ni da ke har abada kije na sake ki saki uku" Hajiya Safiya rushewa tayi da kuka amma ko waigenta baiyi ba, Fahad banda harara babu abinda yake wurga mata. Daga nan Headquater kai tsaye kotun Addinin musulunci aka miƙa su Hadari da Hajiya Safiya, Yaya Haruna da kanshi ya ɗauki lauyan masu ƙara. ya yinda Hajiya Safiya ta ɗauki lauyanta, su kuwa su Hadari basu da lauya dan haka Alƙali yace sai dai su kare kansu. Su Lubna da sauran Ƴaƴan Alhaji Haruna gabaɗaya basu ji daɗin abinda mahaifiyarsu ta aikata ba, Lubna sai yanzu take jin wata irin kunyar Indo, babban tashin hankalinta Yaseer ne, tunda ta san tunda cen ma Yaseer ba santa yake ba ta Indo yake bare yanzu da haka ta faru. Cikin lokaci ƙalilan duk ta rame ta bushe ta lalace kamar wacce tayi laifi, sai abu na gaba da idan ta tuna yake hana ta bacci shine hukuncin da za'a yankewa mahaifiyarsu, gashi tun ba'aje ko'ina ba mahaifinsu ya sauwaƙewa mahaifiyarsu. Waɗannan tunane-tunane ne suka haɗu suke dagula lissafin Lubna, wanda bacci ma ya ƙauracewa idanunta. Wata ranar Laraba ce aka zauna aka fara sauraron ƙarar su Indo, kotun cike take da mutane aka aka shigo dasu suka tsaya gurin mazaunin masu laifi, magatakarda ne ya karanta ƙunshin tuhumar sannan Alƙali ya kalli su Hadari ya ce, "Kai meye sunan ka?" Hadari ya ce, "Sunana Salihu amma anfi sanina da Hadari" Alƙali ya ce, "Shin kaji ƙunshin tuhumar da ake muku" Hadari ya ce, "Naji ya me shari amma a taimaka ayi mana afuwa wallahi sharrin sheɗan ne" ɓangaren Hajiya Safiya Alƙali ya koma ya tambayi sunan ta ta ce, "Sunana Safiya Alhasan" Alƙali ya ce, "Shin ko akwai dalilin da ya sa kika aika a kashe ƴar mutane? Idan akwai kotu tana sauraren ki" Hajiya Safiya ta kalli Indo dake cen a zaune kusa da mahaifiyarta ta ce, "Ya me shari'a bani da wani dalili face ƙyashi, hassada da baƙin ciki da suka ruɗeni. Kasancewar mun taso gari ɗaya kuma unguwa ɗaya da Safna, sai ya kasance makarantarmu ɗaya kuma ajinmu ɗaya da ita. Safna tana da ƙwazo da ƙoƙari yadda har makarantar mu ya kasance ansan da ita, kafin zuwanta duk ajinmu dama na girmesu dan haka gabaɗaya sai suke tsorona, duk abinda na faɗa basa iya ƙetarewa kuma duk abinda na gani agunka nace ina so zan karɓa baka isa ka tanka ba. Kwatsam sai aka kawo Safna ajinmu, tun daga zuwanta na fara nuna halina akanta amma sai taƙi amince da shi, saboda bata da tsoro ko kaɗan kuma girmana baisa ta ji shakkuna ba. Ganin haka yasa sauran ƴan ajinmu suka fara daina tsorona, daga baya ma sai gabaɗaya ƴan ajinmu suka rainani, tun daga lokacin tsanarta ta ɗarsu a zuciyata. Sai kuma ƙoƙarin da take da shi duk lokacin da akayi jarrabawa ita take zuwa ta ɗaya, ni kuma kusan nice ta ƙarshe ta biyun ƙarshen aji. Wata rana munyi faɗa da ita, dan kuwa ni na takali faɗan kawai sai ta mun gorin ƙoƙari nikuwa na lakaɗa mata duka, aikuwa tana guduwa ta samu ƴan ajinmu suka fara yi minj waƙar Safiyya ganɗama daƙiƙiya, tun daga ranar sunana yayi fice a makarantarmu, har ta kai ta kawo idan bakace Ganɗama babu wanda zai ganeni. Sai na koma mujiya a cikin makarantar kowa tsokanata yake yi, ana haka har Yayana ya zo ya sanar da shugan makarantar, daga ranar ne na ɗan samu sasaauci. Ana cikin haka sai su Safna suka dawo nan layinmu gida biyu ne kawai ya rabamu da su, a lokacin kuma muna shekarar mu ta ƙarshe a sakandire. A lokacin ina tare da saurayina Sulaiman yana ƙyalla ido da ya ganta, ya daina zuwa gurina dana matsa masa da tambaya ya kwatanta mun ita, tare da cewa ya faɗa tarkon ƙaunarta. Ba ƙaramin tashin hankali na shiga a lokacin ba, amma sai mahaifiya ta tausheni tare da nusar dani wataƙila dama ba mijin aurena bane. Wata rana da yamma na fita naci karo da Safna tana zance da Khalil, tunda na ƙyalla ido akanshi naji duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar shi, a ranar dashi na kwana a raina ko baccin kirki banyi ba, tunani na dinga yi yadda zan samu na samu koda lambarsa ce amma na kasa. Sai dabara ta faɗo mun akan na ƙulla ƙwawance da Safna ko na samu ta saki jiki dani na samu lambarsa a gurinta. Shiryawa nayi naje gidansu na sameta muka gaisa fuskarta ba walwala, kasancewar kowa yasan ba shiri muke da Safna, sunkuyar da kai ƙasa nayi na nemi alfarma da mu aje wannan rashin jituwar da muke gefe ɗaya mu cigaba da rayuwa kamar kowa, amsa mun tayi daga haka na fara nuna soyayyata ga Safna a fili wanda a zuciyata ba haka bane, ita kanta Safna da farko ƙin sakin jiki tayi da ni, sai daga baya ta saki jikinta muka cigaba da ƙawancenmu gwanin sha'awa..." Alƙali ne ya ƙatse Hajiya Safiya sannan lauyoyi suka cigaba da fafatawa, daga ƙarshe Alƙali ya ɗaga shari'ar zuwa goma ga watan gaba, sati biyar kafin komawarsu.Hajiya Safiya da su Hadari aka tasa ƙeyarsu gidan yari, haka kotun ta tashi mutane na Allah wadai da hali irin na Hajiya Safiya. BAYAN SATI BIYU A yau ne su Indo suka zana jarrabawarsu ta ƙarshe, murna gurinta tare da sauran ɗalibai ba'a magana. Kuma tun safiyar ranar Yaseer ya tura mata saƙwanni kala-kala na soyyaya, kuma a ranar ne ya da Daddynsa abinda ke tsakaninsa da Indo, Daddy ba ƙaramin farinciki yayi ba, a take kuma ya kira ƴan Mahaifin Indo ya sanar dashi, shima ba ƙaramin daɗi yaji ba nan take ya kira sauran ƴan uwansa ya sanar dasu. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [02/10, 19:30] Omu Aslam Bint Adam✍🏼: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 91&92 Murna sosai suka yi da jin wannan maganar kowannensu sa albarka ya dinga yi da Allah san barka, Lokacin da Indo taci karo da saƙon Yaseer wani irin daɗi taji a ranta, bayan ta gama karantawa lumshe idonta tayi tana ƙara maimaita saƙon nasa a zuciyarta. Tana cikin wannan yanayin kiran Yaseer ya shigo wayarta, zaro idanu tayi kamar tana gabansa sai kuma taji wata irin kunyarsa ta kama ta, kamar bazata ɗauka ba har kiran ya kusa katsewa ta ɗaga ta kara a kunnenta, cikin sanyin murya ta ce, "Hello Ya Yaseer" daga cen ɓangaren ya amsa da, "Hi ƙalbi" runtse idonta tayi tana murmushi, sannan ya cigaba da cewa. "Yau na sauke dakwon da na daɗe ina yi na tsawon shekaru, a duk lokacin dana tuna bakya tare dani zuciya da ruhi kan shiga firgici, akan kar wani yayi mun shigar sauri sai gashi yau Allah ya bani ikon gabatar da soyayyar da na jima inayi miki, Humaira bantaɓa ƙaunar wata a duniya kamar yadda nake ƙaunarki ba, a kullin zuciya ta azalzalata take akan na gabatar miki da soyayya ta, da ƙyar nake iya lallashinta har muka kawo tsawon wannan shekarun tare, ki taimaka ki amshi soyayya ta ko na samu sauƙin abinda yake mun yawo a cikin zuciyata, karki hukunta ni da abinda bazan iya ɗauka ba domin tabon bazai taɓa gogewa a zuciyata ba." maganganun Yaseer ba ƙaramin nutsar da zuciyarta yayi ba, haka kawai ta samu kanta cikin farinciki. Wasu tsuntsaye ta ƙurawa kallo dake cikin garden ɗin amma sam hankalinta na wani guri daban, jin tayi shiru yasa Yaseer ya ce, "Humaira! Zaki iya hukuntani ta inda kika ga dama, amma dan Allah ki furta mun kalmar kina sona" ya ƙarasa faɗa a raunane kamar me shirin yin kuka. Firgigit Indo ta dawo da hankalinta kanshi, murmushi tayi tana jin ƙaunarsa na fisgar zuciyarta cikin wata irin murya ta ce, "I love you too Ya Yaseer" sai kuma tayi ɗif saboda tunowar da tayi da alƙawarin da ta yiwa Jamilu, ihun murnarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa, a gaggauce ta ce, "Ya Yaseer ina zuwa" bata jira cewarsa ba ta katse wayar da niyyar kiran Jamilu ta sanar da shi abinda ke faruwa, saboda Allah ya sani zuciyarta tayi nisa a soyayyar Yaseer, bazata iya ƙin furta masa kalmar so ba. Kamar almara tana katsewa kiran Jamilu ya shigo wayarta, fuskarsa da yanayin damuwa ya ce, "Ayusher da wa kike waya tun ɗazu ina kira busy" da kamar ta ce masa Yaseer ne, sai ta tuna yadda yake nuna bayajin daɗin yawan wayar da takeyi da shi, basarwa tayi ta ce, "Ya Jamil masu yi mun Congratulations ne fa" sai a lokacin ya saki muryarsa bayan sun gaisa yayi mata congrats sannan yace. "Ayusher!" yanayin yadda ya ambaci sunanta ne ya faɗar mata da gaba, tare da jin wani yar tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta. Jamilu ya cigaba da cewa. "Na shafe tsawon shekaru ina dako tare da ɗaukar nauyin abinda zuciyata ce kawai zata iya ɗaukansa, ba dare ba rana koyaushe addu'ar zaɓin Allah nake tare da fatan Allah ya cika mun burina, kunnuwana sun kurumce ta yadda banajin daɗin sautin muryar kowacce mace sai ke" a zabure Indo ta zaro idanu haɗe da dafe ƙirji amma bata ce komai ba, ya ci gaba da cewa. "Idanuna sun makance! Bana ji bana gani idan ba sauke ƙwayar idanuwa nayi akanki ba, tun kina ƙarama nake lallashin zuciyata akanki saboda kinyi yarintar da bazaki iya ɗaukan kalamaina ba. Nasan duk wanda ya tambayeki halina kalmar mugu, itace kalma ta farko da zaki fara gaya masa daga cikin halayena, saboda gani kike a duk duniya babu wanda ya tsaneki sama da ni. Ko kaɗan ba haka bane! Duk abin da kika ga inayi ina yinsa ne saboda tarbiyyantar da ke akan abinda ya dace, bahaushe ya ce kaza na taka ƴaƴanta badan bata sansu su ba... Ina matuƙar ƙaunarki Humaira dan Allah karki juyomun da martanin da zuciyata bazata iya ɗauka ba, dan Allah karki wargaza saƙar da na daɗe ina saƙawa a zuciya, ki taimaka ki furta kalmar ina sanka ko zuciya ta samu saƙin azalzalar da take mun." tun da Jamilu ya fara magana jikin Indo yayi sanyi ta sandare guri ɗaya tana sauraron maganganunsa, tabbas Jamilu ya nuna mata kulawa ya ƙaunace ta a lokacin da bata da kowa, ya riƙeta kamar ƴar uwarsa a lokacin da batasan kanta ba, Jamilu mutum ne me karamci da nuna kulawa uwa uba kyawawan ɗabi'u da riƙon addini, amma ya zatayi da Yaseer da dakon soyayyarsa da take yi na tsahon shekaru? Ta amsa ta ƙaunar Yaseer anya idan ta amsawa Jamilu bata sa yaudara cikin lamarinta ba? Tun da tasan ko addinin kirista bai amince da auren maza biyu ba, bare kuma a addinin musulunci. Amma ta yaya zata bijirewa Jamilu bayan sun gama mata komai a duniya? Da wanne idon zata kalli Baba Huwaila bayan ta furta bazata iya auren jininta ba, jinin nata ma kamar Jamilu da duk cikin jikoki babu wanda take ƙauna kamar shi, kuma duk ƙaunar da take masa amma ta fifita ta akanshi, da duk abinda take aikatawa Baba Huwaila bata ganin laifinta. Tabbas Jamilu ya tsaya mata da gangar jikinsa da aljihunsa, duk irin ɓarna da ta'asar da takeyi shi yake biya, amma dukda haka ta kasa amincewa da soyayyarsa? Anya tayi hallaci kuwa? Jamilu jin tayi shiru yace, "Ayusher! Bazan tursasa miki ba saboda duk abinda kike so shi nake so, idan kinga ban dace da ke ba karki cuci kanki ki fito ki gaya mun" ya ƙarasa faɗa muryarsa na rawa. Idanunta ne suka ciko da ƙwallah, murya na rawa ta ce, "Ya Jamil!" sai kuma ta kasa furta komai, ganin kukan da take ɓoyewa na neman cin ƙarfinta yasa ta kashe wayar gabaɗaya, tana juyawa zata fita daga garden ɗin ta ci karo da Fahad yana tsaye harɗe da hannu a ƙirji, da gudu ta bi ta gefensa ta wuce cikin gida kai tsaye ta wuce ɗakinta, ta faɗa kan gado tana rushewa da matsanancin kuka. Fahad daskarewa yayi a gurin saboda jin maganganun da Indo ta furtawa Yaseer, saboda tun farkon hirarta da Yaseer ya shigo gurin, da niyyar fara sakarwa Indo Fuska kafin ya sanar mata da ƙudurinsa. Ƙafafuwansa ne suka gaza ɗaukar gangar jikinsa saboda yadda yaji kansa yana sara masa, kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka ya taka zuwa ɗakinsa ya haɗa kai da gwiwa. Aunty Safna ba ƙaramin jin daɗin soyayyar Yaseer da Indo taji ba, haka Momma wacce bakinta yaƙi rufuwa. Ganin lamarin na gidane yasa cikin kwana biyu Daddyn Yaseer wato Yayan Mahaifin Indo suka tsayar da maganar auresu, cen gurin Yaya Haruna aka kai kuɗin Indo dubu ɗari da hamsin da sa ranar wata shida. Murna gurin iyayensu abun baya musaltuwa, haka ɓangaren Yaseer ana tabbatar masa da sa ranarsa da Indo ya kira ɗan uwansa, cikin murna ya sanar masa. Lokacin da Yaseer ya sanarwa da Fahad yana kwance wani irin zazzaɓi ya rufeshi, ɗan sakin fuska yayi kamar ba abin da yake damunshi, ya nuna farincikinsa ga ɗan uwan nasa sannan sukayi sallama. Indo tun da ta shiga ɗaki sai da ta sha kuka me isarta sannan tayi wanka ta koma ta kwanta, tun da ta kashe wayarta bata ƙara kunnawa ba, mahaifiyarta ta lura da ƴar damuwar da take ciki da farko tayi niyyar ta tunkareta domin taji matsalarta, amma sai ta bari zuwa kwana biyu dan taga yadda yanayin nata zai sauya. Indo ko da ta ji sa ranarta da Yaseer tayi farinciki amma sai ta rasa da wane ido zata kalli Jamilu, kuma me zata gaya masa? da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita. Baba Huwaila ce zaune tana waya da Aunty Safna, Jamilu ne ya shigo ya nemi gefen Baba Huwaila ya zauna, dariya yaji Baba Huwaila tayi haɗe da guɗa ta ce, "Ayyiriri kai Alhamdulillahi da Allah ya nuna mun wannan ranar, yanzu Indona ce aka sawa ranar aure Safiya? amsa mata akayi daga cen ɓangaren sannan ta kuma cewa. "Allah ya nuna mana da rai da lafiya ina jikar tawa ne banji motsinta ba?" Aunty Safna ta ce, "Tana ɗaki wai kanta ne yake ciwo" Baba Huwaila ta ce, "Ki duba mun ita kafin na kirata a waya" hira suka yi sannan sukayi sallama. Baba Huwaila da murnarta ta ce, "Kai Jamilu yaudai ansaka ranar Indo, mugun bakinka ya koma kanka yaudai Indo ta kusa zama ta Yaseer. Aikuwa Allah ya kaimu da rai da lafiya ranar auren Indo sai nayi rawa na juya" tunda Baba Huwaila ta fara magana kansa ya sara, fuska ba walwala ya ce, "Allah sanya alheri" Sototo Baba Huwaila tayi ta ce, "Au Jamili baƙin cikin naka haka ya shahara akan yarinyar nan, na gaya maka abun daɗi amma sai haɗe fuska kake kamar wanda yaci kashi." Jamilu da yaje har wuya ya ce, "Wai Baba Huwaila me yasa kike haka ne me zan yiwa baƙin ciki, dama haka Allah ya tsara." yana gama faɗa ya tashi zai fice, Baba Huwaila riƙe baki tayi ta ce, "Jamilu bansan lokacin da ka lalace da hassada ba, hassada ta samu gurbin zama a zuciyarka, Anya Jamilu rayuwa zata yuwu haka?" yana jinta har ta gama magana bai kulata ba ya fice ya nufi ɗakinsa kansa na juyawa. Indo sai bayan kwana biyu da sa ranarta da Yaseer ta buɗe wayarta, saƙonnin Yaseer har babu adadi daga text msg har zuwa whatsapp. Replay tayi masa ta whatsapp bayan minti goma sai ga kiransa ya shigo wayarta, ɗauka tayi da sallama murya a sanyaye. Amsa mata yayi sannan ya fara jero mata tambayoyi kala-kala, murya ba walwala ta ce, "Wallahi bana jin daɗi ne Ya Yaseer shiyasa na kashe wayata gabaɗaya" sannu yayi mata daga nan ya ɗan fara janta da hira tun tana ɗan ɗari-ɗari, har ta saki jikinta suka sha hira sannan sukayi sallama. Yamma liƙis Indo na kwance a ɗaki, kiran Jamilu ya shigo wayarta. Wata mummanar faɗuwar gaba taji da ta ga lambar Jamilu, kamar bazata ɗauka ba tayi ta maza ta ɗauka da sallama tayi shiru. Daga cen ɓangaren Jamilu ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya ce, "Ayusher ashe ansa ranarki amma baki gaya mun ba?" Indo shiru tayi ƙirjinta na ci gaba da lugude, Jamilu ya cigaba da cewa. "Ina taya ku murna sosai Allah sanya alkairi Ubangiji ya kaimu lokacin da rai da lafiya, Baba Huwaila ma ta ce ta neme ki bata samu ba" Murya na rawa Indo ta ce, "To zan kira ta" Jamilu ya ce."Maganar da na miki rannan inasan ki binneta tunda bayan ke babu wanda na sanarwa, ina miki fatan alkairi Ayusher a koyaushe". yana gama faɗa ya katse wayar, Indo na jin haka ta cire wayar daga kunne tana rushewa da kuka, ita kam bata san haka cakwakiyar soyayya take ba, meyasa tun tuni Jamilu bai sanar mata ba ko dai zata rabu da Yaseer ne? Wani tsagi na zuciyarta soyayyar Yaseer ce ke cigaba da azalzalar zuciyarta, a zuciyarta take waɗannan kalaman a fili ta furta, "Anya zan iya jingine soyayyar da nake yiwa Ya Yaseer kuwa? Idan na juyawa Jamilu na yiwa kaina adalci kuwa" bata da wannan amsar illa komawa da tayi tai lamo tana shashaheƙar kuka. "Yanzu Fahad ya kake so nayi? Kasan dai mace bata auren maza biyu ko? Tuntuni kasan kana san nata kayi sake har ta fara soyayya da ɗan uwanka? Babu abinda zan iya maka yanzu illa kayi haƙuri haka Allah ya tsara, kasan matar mutum kabarinsa kuma dan Allah karka bari ɗan uwanka yasan da wannan maganar." Mommy ta ƙarasa faɗa cikin lallashi. Fahad miƙewa yayi ya amsa ciki-ciki yana furzar da isaka mai zafi, ya fice daga falon. A ranar ya dawo garin Kaduna dan gani yake zamansa a ko'ina zafi yake masa idan ba a Kaduna ba. Washegari Indo na garden a zaune ta zubawa tsuntsaye Ido, a zahiri su take kallo amma hankalinta ya tafi wani guri daban, Fahad ne ya shigo gurin ya janyo kujera ya zauna suna fuskantar juna, Indo miƙewa tayi zata zauna muryarsa a raunane yace. "Humaira! Dan Allah ki zauna" maganarsa har amsa amo tayi mata a dodon kunnenta, a iya saninta tunda take dashi bai taɓa ambatar sunanta ba, tana tsaka da tunani ya ce. "Dan Allah ki saurareni kuma ina roƙonki da kimin adalci, karki ƙi amincewa da buƙatar da nazo gurinki" Indo Zuba masa ido tayi tana kallo haɗe da mamakin wai yau Fahad ne, yake mata magana cikin tausasa harshe tare da roƙon alfarma agurinta, lallai ta tabbatar abu ne me muhimmanci. Haɗiyar yawu tayi sannan ta ce, "Ina jinka Ya Fahad" Fahad kafeta yayi da kallo ya ce, "Humaira na jima ina ƙaunarki..." A zabure Indo ta miƙe tsaye ko ƙarasa jin kalamansa batayi ba, a ɗan tsorace ta ce, "Ya Fahad kasan me kake faɗa kuwa? Anya ba mantuwa kayi ba?" Fahad cikin nutsuwa ya ce, "Dan Allah Humaira ki amshi soyayya ta Please" ya ƙarasa faɗa yana haɗa hannuwa biyu alamar roƙo. Indo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Ya isa Ya Fahad! Dan Allah da wanne zanji? Wance yace, Shi yace kaima yanzu ka ce mun. Dan Allah ku bar zuciyata ta huta wallahi kaina ba ƙaramin caji ya ɗauka ba, yanzu ya kuke so nayi?" ta faɗa tana zubda ƙwallah, bata jira cewarsa ba ta wuce ciki a gaggauce cikin tsananin damuwa. Fahad dafe kansa yayi yana haɗiyar yawu me ɗaci tare da zabga uban tagumi. Tun daga rana Indo ta fara wasan ɓuya da Fahad, shi kansa Yaseer ya rasa gane kanta. Walwalarta da sakin fuskarta duk ya sauya, ya tambayeta yafi a irga amma babu wata ƙwaƙwƙwarar amsa da take bashi. Haka shima Jamilu tun daga ranar bai ƙara kiranta ba, ko ta whatsapp baya mata magana, ƙarƙari ta tura masa gaisuwa ya bata amsa tare da tambayar iyayenta, bayan wannan babu wata magana da take shiga tsakaninsu. Lokacin da Mahifiyar Indo ta tirke ta da tambaya sai cewa tayi kawai tana jimamin rabuwa da su ne, Aunty Safna sam bata yarda ba amma tasan idan tayi wari dole ta ji. A kwana a tashi ba wuya lokacin komawa su Hajiya Safiya kotu yayi, kamar kullin a yau ma kotun cike take da mutane, iyayen Indo gabaɗaya sun halarci zaman. Shigo da su Hajiya Safiya akayi ita dasu Hadari, fuskarta harta rame tayi baƙiƙƙirin. Magatakarda ne ya gabatar da ƙararsu Sannan aka buƙaci lauyoyin masu ƙara da su kawo hujjoji, Lauyan su Indo ne ya tashi ya ciro wayar Hadari tare da nuna Musty dake kan kujerar marasa lafiya, da sauran shaidun da ya tattara ya miƙawa alƙali. Alƙali karɓa yayi tare da waiwayar Lauyan waɗanda ake ƙara, domin gabatar da sheda da shedun kariya amma yace bashi da wata shaida. Alƙali ya juya gurin Hajiya Safiya yace, "A zaman da ya gabata kin koro bayani dan haka muna sauraronki" Hajiya Safiya ta ce, "Bayan na yi duk yadda zanyi na shiga jikin Safna sai watarana bayan Khalil yazo gurinta, sunyi sallama har ta shiga gida sai nai maza na fito daga soron gidanmu da nake a laɓe, nazo na sami Khalil na gabatar masa da kaina da abinda yake zuciyata. Mamaki ne ya kamashi ganin ni babbar ƙawar budurwarsa amma zanyi mata haka? A take ya kifeni da mari tare da zageni tas ya hankaɗa ni gefe ya buɗe motarsa ya shige, tun daga ranar na ɗauri aniyar yadda su biyun nan suka munana mun, na dinga dasa musu ɓacin ran da har sai yayi silar ajalinsu, ana cikin haka wata rana kakar Safna tayi rashin lafiya sai muka je dubata nida mahaifiya, a ranar Khalil yaje da ɗan uwansa wanda ni kuma a ranar ne Allah ya haɗani da Uban ƴaƴana, ganina da yayi yaji duk duniya babu wacce yake so sama dani, ni kuma har lokacin zuciyata na kan ƙaninsa, amma gudun kar nayi biyu babu yasa na amincewa yayansa. An riga bikina da Haruna sakamakon karatun da Khalil yake yi ba'ayi nasu a wannan lokacin ba, ana cikin haka ba daɗewa sai Kakar Safna ta rasu wacce take riƙonta bayan rasuwar iyayenta, wannan dalilin ne yasa ta koma cen gidan yayarta. Bayan bikin Safna da Khalil sai suka dawo garin Kaduna, anan na cigaba da shige mata kuma duk lokacin da na fuskanci tana da ciki, sai nasan dabarar da nayi na bata ƙwaya tasha cikin ya zube, ana cikin haka har Allah yasa ta haifi Ɗanta namiji da yake Allah yayi sai ya shaƙi iskar duniya, amma ranar suna sai na faki ido na toshe masa hanci har ya mutu, haka nayi tayi mata har lokacin da nasa ƴan fashi suka je suka ɗauki Humaira tana jaririya, ashe basu kashe ba sai gashi ta ƙara bayyana. Bayan dawowarta nayi niyyar sawa a kashe ta amma sai na lura da irin tsaron da suke bata, sai da na bari sun sakankance na aika su Hadari su kashe ta." gabaɗaya kotun hayaniya ta ɗauka sai da Alƙali yayi gyaran murya sannan kowa yayi shiru, Alƙali ne ya yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai tare da horo mai tsanani na shekara uku-uku. Hajiya Safiya kuka ta rushe da shi ƴan uwanta ma suka saka kuka, suna ji suna gani ma'aikatan gidan yari suka tasa ƙeyarsu. Haka kotun ta tashi kowa yana yabawa da hukuncin da Alƙalin ya yanke. Su Lubna sunyi kuka kamar ransu zai fita haka mahaifinsu, ya rungumesu yana jin tausayin ƴaƴansa a zuciyarsa. *KWANCI TASHI ASARAR RAI* Bikin Yaseer da Indo ya zo daga kowanne ɓangarori shiri ake ta hidimar biki, saura sati biyu bikin aka kawo lefen Indo akwati shida. Sun zuba mata kaya sosai gwanin birgewa, ganin bikin ya matso yasa Fahad ya tattara kayansa ya koma Kano, Yaseer duk ya shiga damuwa ganin ɗan uwansa ba walwala, kuma yayi juyin duniya ya gaya masa damuwarsa amma yaƙi, har gwara ɓangaren Indo ta ɗan saki jiki ana mata harkokin gyara jiki, Momma tura Yaseer Kano tayi tasa aka kawo mata Indo gurinta acen take mata gyaran jiki da sauran magungunan da take haɗa mata. Indo ba ita ta koma Kaduna ba sai ana gobe za'a fara biki, Ranar Laraba suka fara shagali, a ranar sukayi Bridal shower, Alhamis akayi Kamu, Juma'a akayi Dinner, Asabar Mother's day. Babban abinda yafi tsayawa Indo a rai rashin zuwan Baba Huwaila, da ta tambayi mahaifiyarta ta ce mata Jamilu ne babu lafiya yana kwance a asibiti. Fahad da ƙyar ya lallashi zuciyarsa yake zuwa guraren Event ɗin, sai dai duk wanda ya ganshi zai fahimci yana cikin matsananciyar damuwa, sosai yake yiwa amarya da ango liƙi kamar babu abinda yake damunsa. Ranar Lahadi ita ce ranar ɗaurin aure, daga gari-gari mutane suka dinga zuwa domin halartar ɗaurin aurenta, gidansu Indo cike yake ta ko'ina da mutane. Tun da gari ya waye Fahad yake aman jini abunda ya ɗaga hankalin iyayensu kenan, raba ƙafa akayi wasu suka tafi asibiti wasu kuma suka wuce gurin ɗaure aure. Ƙarfe goma dai-dai na safiyar ranar aka ɗaura auren Indo akan sadaki naira dubu ɗari, dubbunin mutane ne suka shaida ɗaurin aurenta. Yaseer ne zaune a tsakiyar iyayensa kamar mace banda hawaye babu abinda yake yi, Daddy ne ya gyara zama ya ce, "Assalamu alaikmu, na tabbata gabaɗaya kunsan maƙasudin zamanmu a gurinnan, Yaseer gabaɗaya da kake ganinmu kalma ɗaya ce zamu iya gaya maka wato kayi haƙuri, duk abinda ka gani Allah ya rubuta wani baya auren matar wani, Allah ya rubuta Humaira matar Jamilu ce ba taka ba" Jin wannan kalmar yasa Yaseer ya kuma fashewa da wani irin matsanancin kuka. 🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ NASAN YAU WASU ZASU GA BAƘI NA.🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ JAMIL FANS A FITO AYI CELEBRATIONS😂🤪🤣💃🏻 MAGANAR GASKIYA YAU INA JIRAN COMMENTS🤥 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [30/09, 19:28] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _SHARARRIYAR MARUCIYAR NAN MAI LITTAFIN *SO KO WAHALA* TA ƘARA DAWO MUKU DA WANI ZAZZAFAN LITTAFI MAI SUNA *ƳAR HIZBA* BAZANCE KOMAI AMMA KUNSAN SALON LABARINTA DABAN YAKE, MASOYA KU GARZAYO KAR A BAKU LABARI._ *Alhamdulillah masu buƙatar sabon littafina 🧕ƳAR HIZBA🧕 da zai zo bayan sallah zasu iya biyan kuɗin karatunsu tun yanzu, normal group #200, vip 300, special 400. Za'a tura kuɗin ta wannan Accoun No. ɗin 2083460164 Abubakar Abdullahi Usman Zenith Bank ko a turo katin Waya na MTN ta wannan number 07038826617 ta wannan number za a turo shaida, ta nan za a tuntuɓeni don neman ƙarin bayani.* 93&94 Gabaɗaya falon shiru ya ɗauka banda shassheƙar kukan Yaseer babu abinda yake tashi, tausayinsa ne ya kama mahaifansa cikin sigar lallashi Daddynsa ya ce, "My Son! Kayi haƙuri, Allah ya rubuta Humaira ba matarka bace, abin da mukayi ba munyi domin mu baƙanta maka bane, munyi ne domin nuna hallaci ga waɗannan bayin Allahn, na roƙoka dan Allah kayi haƙuri insha Allah shi zai saka maka da mafi alheri agareka." Yaseer ya ce, "Daddy Humaira ce alkairi a gareni meyasa zaku rabani da ita, meyasa tun farko baku ce Jamilu zaku bawa ba kuka zuba ido kuna ganina ina ta dakon soyayyarta, Daddy zuciyata zafi yake mun bazan iya rashin Humaira ba." Daddyn Fahad ne ya ce, "Yaseer bamasan sakarcin banza da wofi, karka mayar da mu sa'anninka mana muna faɗa kana faɗa, sakarcin banza sakarcin wofi wallahi ranka zai..." da sauri Alhaji Khalil ya katse shi, "Haba Alhaji dan Allah ka yi haƙuri yaron nan yana cikin wani yanayi da dole ya kasa fahimtar abinda aka sanar da shi, kar a doke shi a hana shi kuka mana abun da ciwo fa" Daddyn Yaseer ya taso ya dafa Yaseer ya ce, "My Son bazan hana ka kuka ba, amma dan Allah karka sawa kanka matsananciyar damuwa domun danuwarka damuwa ta ce" Yaseer gyaɗa kai yayi amma shi kaɗai yasan ya abinda yake ji cikin zuciyarsa, miƙewa yayi tsaye ya ce, "Daddy zan wuce gida yanzu" da sauri Daddyn shi ya ce, "Yaseer ka bari mu wuce tare banasan ka fita a wannan yanayin da kake ciki, Alhaji Haruna ya ce, "Ɗana Yaseer abu na ƙarshe da zan roƙi alfarmarka ita ce, karka riƙi yaron nan Jamilu a zuciyarka domin shi a yanzu ma baya cikin hayyacinsa, yana kwance a asibiti baisan abinda yake faruwa ba." Yaseer gyaɗa kai kawai yayi ya fice daga ɗakin Daddynsa na rufa masa baya. A lokacin da ake tsaka da shagali Indo ba ƙaramin kyau tayi ba cikin tsadajjen leshinta baƙi, kowa ya kalli fuskarta zai tabbatar da irin farin cikin da take ciki, sai walƙiya take tasha ado ta ko'ina. Daga wajen harabar gidan maroƙa da makaɗa ne kala-kala suka shigo gidan suna busa tare da shelar ɗaurin aurenta. "Allah ya kawo mu, bikin ƴar gata kuma ƴar dangi, fara mai farar aniya tauraruwa acikin taurari, Aishatu Indo uwar muminai tare da angonta sukari bakai farin banza ba, Ango Jamilu kayi dacen mata Allah ya tsaga da rabonka, babban goro sai magogin ƙarfe Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya Aishatu tare da Angonta Jamilu, ina iyayen Aisha ku fito ku nuna farincikin ƴar dangi, ku nuna mun ƙauna tabbas wannan bikin na ƴar gata ne bantaɓa zuwa bikin ƴar dangi irin wannan ba..." Haka maroƙa da makiɗan nan suka dinga banbaɗanci Abokan mahaifin Indo sai zuwa suke suna zuba musu kuɗi. Kafin wani lokaci take maganar auren Indo da Jamilu ta karaɗa kunnuwa kowa dake gidan, ciki kuwa harda mai gayya mai aiki wato Amarya Sarƙa, lokacin ne Momma ta ja Hannun Indo ɗaki take lallashinta, Indo fashewa tayi da kuka ta faɗa jikin Momma gwanin tausayi, Momma bubbuga bayanta tayi tana lallashinta amma indo banda ajiyar zuciya babu abinda take yi, A hankali ta ɗago ta kalli Momma ta ce, "Momma zuciyata da ruhina Ya Yaseer take so, Momma anya zan iya jure rashinsa kuwa? Me yasa tuntuni Jamilu bai koyar dani sanshi ba sai da ya bari nayi nisa a soyyayar Ya Yaseer zai tarwatsa mun farincikina, Momma ni bana sanshi wallahi bazan iya rayuwar aure da shi ba..." da sauri Momma ta toshe mata baki ta ce, "Kul karna ƙara jin waɗannan kalmomin daga bakinki, kar kuma ki sake ki ƙara furta wata magana mara daɗi akan mijinki, Jamilu ya zama mijinki ba yanda zakiyi haka Allah ya tsara, babu yadda zamuyi dama tun cen Allah ya ƙaddara ke matarsa ce." Jin waɗannan kalaman ba ƙaramin ƙara ɗaga hankalin Indo yayi ba, zuciyarta har zugi take soyayyar Yaseer na ƙara nuƙurƙusarta, jiki a sake ta dafa gado ta zauna Momma lallashinta ta cigaba da yi, sannan ta fice daga ɗakin ta bar Indo a kwance. Wani tunani Indo tayi kamar wacce aka zabureta da sauri ta miƙe zaune ta lalubo wayarta, number Yaseer ta kira amma shiru bai ɗauka ba, ta kira ba adadi amma shiru bai ɗaga ba daga ƙarshe ma da ta kira sai ji tayi wayar a kashe. Tana jin haka ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, tana cikin haka Mahaifiyarta ta shigo ta sameta a wannan halin, har cikin zuciyarta taji kukan da ƴarta ta takeyi, jiki a sanyaye ta ƙarasa bakin gadon ta zauna tana fuskantarta. Indo faɗawa tayi jikin Mahaifiyarta ta ce, "Ammi wai Jamilu ne mijina wallahi banasan sa Ammi..." da sauri Aunty Safna ta rufe mata baki ta ce, "Kul Humaira banasan jin haka daga gareki, Ki buɗe kunne kiji abinda zan gaya miki Humaira, kinsan dai mu iyayenki ne bazamu zaɓa miki abinda zai cutar da ke ba. Kinfi kowa sanin su waye Baba Huwaila kinsan irin hallaci da nuna ƙaunar da suka nuna miki, Jamilu ba shi yasa muka aura miki shi ba, hasalima yana cen kwance ba lafiya, Baba Huwaila ita ta kira mahaifinki da safen nan tana kuka wai Jamilu ba lafiya, yana kwance rai a hannun Allah likitoci sunce zuciyarsa ta buga, Mu dama bamusan Jamilu yana sanki ba da mun sani da tuni mu ɗauki matakin da ya dace, a lokacin ta sanar da mu cewar indai ba'a bashi abinda yake so ba zai iya rasa rayuwarsa. Da farko Baba Huwaila cewa tayi bazata sanar da mu ba, amma ganin yana cikin wani hali yasa ta nemi wannan alfarmar a gurinmu, Humaira yanzu kina ganin ko ba ke ba, da ace muna da wata ƴar bayan ke Baba Huwaila ta nemi alfarmar aurawa Jamilu zamu hanata ne? Humaira ki zama ƴar halak ance ɗan halak shi yake rama hallaci, a yanzu magana nake miki ta ƴa da mahaifiya, umarni ne nake baki da karki bamu kunya karki je gidan mijinki kiyi abinda zaki ɓata rawarki da tsalle. Kinsan dai irin ƙaunar da Baba Huwaila ta nuna miki, tunda ke da bakinki kike faɗa mana. Kinga lalurar da ke damun mijinki, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu kiyi masa biyayya yi nayi bari na bari, nasan dai a iya zamanku kinsan halin Jamilu wanda yake so da waɗanda baya so. Ki kiyaye abunda zai ɓata masa rai kuma yadda kike wa Baba Huwaila ki cigaba karki fasa ke harda sauran ƴan uwansa baki ɗaya." tunda Mahaifiyarta ta fara magana Indo take ruwan hawaye, ita kanta tasan duk abubuwan da Mahaifiyarta ta faɗa haka ne, amma shin babu wanda zai fahimci yadda zuciyarta take mata zugi da raɗaɗi ne? Me yasa bazasu fahimci halin da zuciyarta take ciki ba, kaf cikinsu tasan babu wanda yasan zafin rabuwa da masoyi, cikin hawaye ta kalli mahaifiyarta ta ce, "Amma Ammi meyasa..." Aunty Safna cikin dakiya ta katse Indo ta ce, "Banasan jin komai Humaira, so nake ki zama yarinya ta gari wacce zamuyi alfahari da ke, banasan ko kaɗan a samu matsala daga gurinki. Allah ya albarkaci aurenku ya bada zuri'a ɗayyiba." Auntya safna na gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin, tana fita Indo ta koma gado tayi lamo hawaye na bin idanuwanta. Likitoci cikin gaggauwa suka amshi Fahad suka shiga bashi kulawar data kamata, gwajin farko da likitoci sukayi masa suka tabbatar da zuciyarsa ce take neman bugawa, tashin hankali iyayensa suka shiga nan da nan suka shiga zarya da mamakin yadda akayi har damuwa tayi masa yawa, batare da sun fahimci halin da yake ciki ba. Babu jimawa Likitoci suka shawo kan matsalar ta hanyar allurai da magunguna da suka bawa Fahad, abu ɗaya likitan ya cewa su Daddy shine akwai abinda yake buƙata, matuƙar ba'a bashi ba baza'a samu a shawo kan matsalar ba, idan kuma wani abu ne yake damumsa ayi ƙoƙarin kawar masa da damuwar domin samun sauƙin ciwon nashi. Ranar wunin Indo da daddare Alhaji Haruna ya tara ƴan uwansa, akan su tattauna lokacin da za'a kai Indo ɗakin mijinta, tattaunawa sukayi gabaɗaya suka yanke shawarar nan da kwana uku, za'a je a kwaso kayanta na gidan Yaseer dake Abuja, aje a jera mata a gidan da Mahaifinta ya bawa Jamilu dake Unguwar Tukuntawa a garin Kano. Da wannan shawarar suka tashi daga zaman. Jikin Fahda ba laifi yana samun sauƙi sai dai gabaɗaya ya rame ya lalace, kamar wanda ya shekara yana jinya. A ɓangaren Yaseer duk wanda ya ganshi zai fahimci irin matsananciyar damuwar da yake ciki, danma Momma da Daddyn sa suna matuƙar ƙoƙari, wajen ganin sun jashi a jiki da kawar masa da damuwa. Ya rame sosai yayi fari idanuwansa duk sun faɗa har wata ƙasumba ya tara a fuska, duk dare sai yayi sallah ya kai kukan gurin Ubangiji, akan ya yaye masa damuwar da yake ciki tare da sawa zuciyarsa dangana, tunda yasan a duniya gabaɗaya ya riga da ya rasa Humaira, babu inda yake zuwa daga zaman ɗaki sai ɗaki. BAYAN KWANA UKU Duk wasu shirye-shirye na tarewar Indo ankammala su, angama jera mata komai a gidanta, gidan madaidaici ne mai ɗaki huɗu, kitchen da banɗaki. Gidan dukda ba wani babba bane amma ya tsaru duk wanda ya gani sai ya birgeshi, anzuba mata kaya dai-dai misali haka daga ɓangaren kayan kitchen abin ba'a magana. Ranar laraba su Mommy ne suka taho da Indo garin Kano, lokacin da za'a taho da ita ba ƙaramin Nasiha mahaifi da mahaifiyarta suka yi mata ba, banda kuka babu abin da Indo take yi. Ita kanta Aunty Safna wannan karan sai da ta goge hawaye, ɗan zaman shekara uku zuwa huɗu da tayi da ƴar tata yasa sun shaƙu sosai, sai dai ya ta iya dama dole tasan haka zata faru tunda ƴa mace ƴar gidan wani ce. Jamilu tun bayan da aka ɗaura aurensa da Indo Baba Huwaila da ke gurinsa, sai a lokacin hankalinta ya kwanta. A lokacin Jamilu bacci yake sakamakon allurar baccin da akayi masa, bayan kamar awa biyu da ɗaurin auren buɗe idonsa ya yi, idanunsa sun rine jawur jiki ba ƙwari ya ɗau hannu, ya dafa saitin zuciyarsa da yaji tana yi masa wani irin zugi, idanunsa ne suka ciko da ƙwallah ya buɗe baki ya fara magana dukda muryarsa bata fita sosai. "Baba Huwaila wannan ciwon nawa bazai barni, gani nake kamar rayuwata ta zo..." da sauri Baba Huwaila ta katse shi, "A'a Jamilu ciwonka na tashi ne da yardar Allah, ka kwantar da hankalinka Indo ta zama mallakinka matarka ce halak malak" dukda jikinsa ba ƙwari hakan bai hanashi yunƙurin miƙewa ba, cikin mamaki ya ce, "Da gaske Baba Huwaila?" murmushi Baba Huwaila tayi ta ce, "Da gaske nake Ɗan Jamiluwana" shiru yayi kamar me nazari sai ya ce, "Dan Allah Baba Huwaila karki gayamun haka saboda ciwon da kika ga ina ciki" Baba Huwaila ta ce, "Kasan ni kaifi ɗaya ce Jamilu, bazan gaya maka abinda ba haka yake ba, yanzu haka ranar Laraba iyayenta suka ce zasu kawo ta, gobe talata zasu zo jere mahaifinta ya baka kyautar gida ku zauna a ciki." A zabure Jamilu ya zuro ƙafafuwansa saura kaɗan ya cire ledar ƙarin ruwan da ake sa masa, a dai-dai wannan lokacin Alhaji ɗan wajen Baba Huwaila ya shigo, da murnarsa ya ƙaraso ganin Jamilu a zaune, Baba Huwaila ce ta yi masa bayanin dalilin tashinsa, nan suka shiga yi masa tsiya suna dariya. Tun daga ranar jikin Jamilu yake ƙara samun sauki, hatta likitocin da suke kula da lafiyarsa hakan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba. Su Mommy kai tsaye gidan Alhaji suka sauka lokacin Baba Huwaila na gida, ba ita take zaune da Jamilu a asibiti ba. Tarba akayi musu ta sha tara ta arziki cikin farin ciki dangin Mahaifiyar Jamilu dana mahaifin Jamilu suka karɓe su, gidan su Baba Huwaila cike yake da ƴan uwa kamar dama ansan da bikin Jamilun, Su Mommy damƙa Indo sukayi a hannun Baba Huwaila kafin Jamilu ya ƙara warware su tare a gidansu. Su Mommy basu wani jima ba bayan sun ci abinci, suka yiwa su Baba Huwaila sallama suka wuce gida. Lokacin da zasu tafi Indo ba ƙaramin kuka tayi ba amma duk mutanen gurin babu wacce ta kawo komai a ranta, saboda yawanci haka yake faruwa bisa ga al'adar malam bahaushe. Washegari ƴan uwa kowa ya kama gabansa gida ya rage daga, Baba Huwaila, Indo matar Alhaji da ƴaƴansa, a ranar ne Baba Huwaila ta shirya ta sa Indo ma ta shirya akan zasu je Asibiti ta duba jikin Jamilu, Indo kamar zatayi magana ta fasa dan gani take bazata iya musantawa Baba Huwaila ba, dan babu wani abu data nunawa Baba Huwaila hasalima wata irin kunyarta take ji, shiryawa tayi tsab cikin doguwar rigar atamfa, ta ɗauko hijabinta coffee ta saka ba ƙaramin kyau yayi mata ba. Ga duk wanda ya fahimceta zai fahimci zallar damuwar dake tattare da Indo, hannunta ɗauke da flask suka ƙarasa asibitin ƙirjinta sai dukan uku-uku yake, Baba Huwaila ce a gaba tana biye da ita har suka shiga cikin ɗakin, tana shiga ɗakin idanunta suka sarƙe da juna, faɗuwar gabanta ce ta tsananta take ta sunkuyar da idanta ƙasa ta nemi kujera ta zauna, Baba Huwaila ce ta ce, "To Jamilu ga matarka na kawo maka ta duba ka" kusan lokaci ɗaya suka ɗago da kansu suna kallon juna, wanda da alama kowannensu mamakin jin kalaman Baba Huwaila yayi, a sanyaye Indo ta janye idonta cikin zuciyarta tana maimaita ni Indo wai nice matar Jamilu..." bata ƙarasa tunanin ba Baba Huwaila ta katse ta, "Jamilu ina kawunka ne?" Jamilu da har zuwa lokacin idanunsa na kan Indo ya ce, "Ya fita siyan kati" Baba Huwaila miƙewa tayi ta ce, "Indo ga abinci nan ki bawa mijinki yanzu Allah ya hutar dani, bari naje na duba shi a waje ina zuwa" Baba Huwaila ta ƙarasa maganar tana yin hanyar fita. Bayan ta fita shiru ne ya biyo baya Indo ta cigaba da wasa da ƴan yatsunta, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa ya ce, "Ayusher ba magana?" a hankali ta ɗago idanunta ta ce, "Ina kwana ya jiki?" murmushi yayi yace, "Lafiya ƙalau da sauƙi" shiru suka ƙarayi ya ce, "Yunwa nake ji" Indo bata amsa ba ta miƙe tana tattare hijabinta ta fara zuba masa a plate, kujerarta ta janyo bakin gadon ta zauna ta fara ɗiban abincin zata miƙa masa. Girgiza mata kai yayi sam bata fahimci me yake nufi ba, kallan gefen sa yayi ya ƙara mayar da idanunsa gareta, ta fahimci abinda yake nufi sarai sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa ya ce, "Nan zaki dawo ki zauna Baba Huwaila anan take zama tana bani a baki" ya faɗa cikin shagwaɓa kamar wani ƙaramin yaro. Tsam Indo ta miƙe ta koma cen kan gadon tana ɗan ɗari-ɗari, daga ɗan nesa dashi ta zauna ta miƙo masa. Ƙara noƙewa yayi badan ta so ba ta ƙara matsowa kusa da shi, ta kai masa cokalin saitin bakinsa. Buɗe baki yayi ya karɓa tana ƙoƙa ƙara ɗebo wani abincin ya riƙo hannunta, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da Jamilu ya ɗago ya kalleta, a hankalin ya sunkuyo saitin fuskarta har suna jin numfashin juna, zuciyarta banda lugude babu abinda take yi. KWANA BIYU KUN JINI SHIRU WALLAHI NEPA NE SAI A HANKALI YAUMA ƘUƘEWA NAYI, SAM BANSO LITTAFIN NAN ZAI SHIGA WANI WATAN BA, AMMA BA YADDA NA IYA KANA NAKA ALLAH NA NASHI. NAGODE SOSAI DA KULAWARKU❤️ _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [01/10, 19:31] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _Ina masoyan Real eeshow na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna *KARAGAR MULKI* cikin farashi mafi sauƙi #300 ta wannan account number 2411022356 aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334 ko transfer credit Mtn ko Airtel ta wa'innan numbers ɗin 08108362334 & 08087971440 sena jiku._ 95&96 Sun jima a haka sannan Jamilu ya motsa bakinsa ya fara magana, "Ayusher!" cikin wani irin yanayi ta ɗago ta kalleshi ta kuma sauke idanunta ƙasa, Jamilu ya cigaba da cewa, "Dan Allah kiyi haƙuri" idanun Indo ne suka fara cikowa da ƙwalla ta tsinkayi muryarsa yana cewa, "Nasan zafin rabuwa da masoyi haka nasan bakya so na amma dan Allah kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara" hawayen da ke maƙale a idanunta ne suka sakko, ji tayi kamar Jamilu ya famo mata wani tsohon gyambo dake cikin zuciyarta, yana shirin magana ta ɗebo abinci zata miƙa masa ya ce, "Insha Allah zan riƙe amanarki hannu bibbiyu zakiyi alfahari dani" bata tanka ba kuma bazata tanka masa ba ta kuma miƙa masa abincin saitin bakinsa ya ƙarɓa, daga nan babu wanda ya kuma tankawa kowa da wata kalma haka ta cigaba da bashi abinci yana ci har ya ƙoshi, ruwan tea ta haɗa ta miƙa masa ya karɓa yana sha, ta koma cen kujerarta ta farko ta zauna ta cigaba da wasa da ƴan yatsunta. Jamilu mamakin shirun Indo yake ta gefe ɗaya kuma yana alaƙanta hakan da rashin walwala, musamman idan ya tuna Indo bashi take so ba. Babu jimawa Baba Huwaila ta shigo ɗakin ganin Jamilu yaci abincin sosai murna ta kamata, zama tayi ta ce, "Jamilu yau da yake Indo ce ta baka abinci har ka cinye tas amma da nice da tuni kananan kana mun sanabe, ashe dama ni kakewa wannan sanaben yo tunda ka kwanta ciwo kaci abinci me yawa kamar wannan?" Jamilu yace, "Wallahi abincin ne yayi daɗi Baba Huwaila kuma Ayusher a hankali take bani" Baba Huwaila kallansa tayi ta juya ta kalli Indo bakina sake ta ce, "Oh! Yau naga sanabe da kitifi irin na ƴaƴan zamani, yau Indon kake cewa wata Ayusher? Au Jamilu dama ka iya tausasa Kalamai haka bansani ba, da ka dinga azabtar da yarinyar nan" Jamilu kunya yaji sosai ita kanta Indo sai da taji kunya Baba Huwaila ta lura da haka ta ce, "Au Indo yau ni kike jin kunya? Kai jama'a Allah ya kawo zamani wane dare ne jemage be gani ba" Indo ganin idan ta cigaba da kunyar Baba Huwaila ta dinga mata tsiya, shagwaɓewa tayi ta ce, "Wai Baba Huwaila dama haka kike zuwa ki cikashi da surutu mara lafiya bayasan hayaniya fa" Baba Huwaila ta ce, "Eh to kuma fa maganarki na hanya danma naga jikin nashi yayi kyau ai" daga haka hira suka shiga yi sai yamma liƙis suka wuce gida ita da Baba Huwaila. Jikin Jamilu ya warke garau sai rashin ƙwarin jiki, ranar juma'a likita ya sallameshi suka koma gida cen ɗakinsa ya sauka. Indo na kwance Baba Huwaila ta ce, "Indo ga ruwan wanka cen na sauke je ki sirkawa Jamilu ki kai masa, ɗakinsa da banɗaki a ciki" Indo badan ta so ba ta miƙe ta ɗauki bokiti ta sirkawa Jamilu ruwa ta shiga ɗakinsa da sallama, daga bakin ƙofa ta tsaya ta ce ga ruwan wankanka nan" tana shirin juyawa yace, "Kice Baba Huwaila ta zo ta jai mun banɗakin" ta fahim inda maganar ta dosa dan haka ta watsa masa wani kallo, duk abinda yaga tayi tana masa ne albarkacin idon Baba Huwaila dan tana matuƙar jin nauyinta, da sauri taje ta ajiye masa bokitin a banɗakin ta fito. Tun daga ranar babu wani abu da yake haɗashi da Indo idan ba kawo abinci ko kai ruwan wanka ba, gaisuwa ma idan ba agaban Baba Huwaila ba bata gaisheshi. Baba Huwaila sai ƴan jiƙe-jiƙe take mata tana bata wani tasha da daɗi wani kuma har sai sunyi faɗa take karɓa ta sha, satinsa ɗaya da dawowa Jamilu ya murmure hatta ramar da yayi duk ya cicciko, babu inda baya zuwa ya samu sauƙi sosai. Zuwan Daddy Fahda da Mahaifin Indo biyu kowanne zuwa zasuyi sai sun taho da sha tara ta arziki, hakan ba ƙaramin daɗi su Baba Huwaila suka ji ba. Satin Jamilu biyu da dawowa daga asibiti Baba Huwaila ta ce su tarkata su koma gidansu, Indo sam ba haka ta so ba dan ta sakankance a gidan Baba Huwaila, ba yadda ta iya wata ranar Juma'a Baba Huwaila da Alhaji suka shirya suka ɗauki Indo da Jamilu a mota suka wuce unguwar tukuntawa. Jikin Fahad ya samu sauƙi sosai saidai har zuwa lokacin yana cikin damuwa, ya rame sosai ya ƙara tsayi ga wani haske da yayi sosoi, kallo ɗaya Aunty Safna tayi masa ya bata tausayi duk yadda taso Fahad ya tafi gidanta fir yaƙi, dan dole haka Mommy ta ɗauki Fahad ta wuce dashi gida. A ɓangaren Yaseer shi ɗinma kusan hakan take, tunani shine ya zama abokin hirarsa a duk lokacin da soyayyar indo ta addabeshi sai ya ɗaga waya kamar ya kirata, sai ya gargaɗi zuciyarsa akan tsoron Allah domin yasan koshi ne aka kira matarsa sai inda ƙarfinsa ya ƙare, idan haka ta faru da shi ya gwammaci ya ɗauki mota yayi ta zaga gari, Lubna lokaci-lokaci take kiransa a waya amma yawanci daga gaisuwa shikenan abinda yake haɗasu, wani lokacin ma idan ta kira baya ɗauka tun abin na damunta har ya daina damunta idan ta tuna da abinda ya faru da shi da Indo. Lokacin da su Baba Huwaila suka raka su Indo gidansu nasiha sukayi musu mai ratsa zuciya, Indo tunda aka fara shirin tahowa ta fara ruwan hawaye haka lokacin da zasu tafi rungume Baba Huwaila tayi tana kuka, da kyar ta raba jikinta dana Indo tayi mata sallama suka tafi. Bayan sun tafi Jamilu ne ya dawo gurin Indo ya zauna cikin lallashi ya fara magana. "Ayusher bana jin daɗin yadda kike zubda hawayenki" hannunsa ya ɗora akan fuskarta ya fara goge hawaye, ya cigaba da cewa. "Dan Allah ki daina mun asarar hawayen..." wata uwar harara ta watsa masa lokaci guda taji wani irin haushinsa ya kamata, tunowa tayi da irin lallashin da Yaseer yake mata musamma idan yaga tayi fushi, ƙamshin turarensa ne ya faɗo mata a ɗan ƙaramin ƙyallen da yake bata duk lokacin da ya kawo mata ziyara, guntsun tsaki ta saki ta miƙe ta wuce ɗakin gadonta ta banko ƙofa ta faɗa kan gado tana sakin wani irin kuka. Shima Jamilu take yaji idanuwansa na kawo masa ƙwallah, baiyi aune ba yaji ɗigar hawayensa a kan hannunsa. Dafe zuciyarsa yayi yana cewa, "Me yasa kika mun haka meyasa zaki cutar dani? Me yasa zaki so abinda bashi yake muradinki ba? Tabbas bakimun adalci ba kin cutar dani kin yaudareni yaudara me tsananin mai matuƙar wahalarwa. Allah ka kawo mun mafita Ya Allah kana gani bani na tursasawa kaina ba, Allah ka karkato mun da hankalin matata akaina" haka ya cigaba da surutai idanunsa na zubda hawaye, duk abinda yake faɗa Indo na jinsa ko kaɗan bataji ɗigon tausayinsa ba bare taji zata iya ƙaunarsa a zuciyarta. Sai da ya jima a zaune har yaji zuciyarsa ta ɗan zafin da take masa, tashi yayi ya fice daga gidan a lokacin har magriba ta fara kawo kai. Sai da ya gabatar da sallar magriba sannan ya biya Dadin kowa suya spot dake tsalleken titin unguwarsu, ya siyo musu kaji manya guda uku ya shiga shagon saida drinks ya siyo musu hollandia da fresh milk da sauran lemuka, hannunsa cike da ledoji ya nufa gida. Har ya kusa shiga gida ya ga wani babban provision sanin da ya yiwa Indo na shan zaƙi, yasa ya shiga shagon ya kwaso mata tarkacen alawoyi dasu chocolate, yana zuwa ƙofar gidan yasa mukuli ya buɗe ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, lolacin da ya shiga falon tana zaune duk tayi wani zuru-zuru da alama a tsorace take na rashin ganin dawowarsa. A cikin zuciyarsa yake mamakin yaushe Indo ta fara tsoro yarinya da take bin dare tana haura katanga, wani tunani yayi ɗayar zuciyar ta ce, "Karka manta wancen karan aida ƙuruciya akanta yanzu kuwa tasan ciwon jikinta." kauda tunanin yayi ya zaune tare da zube ledojin ya ce, "Ayusher je kitchen ki ɗauko mata plate" wasa ta cigaba da yi da watarta kamar bata ji shi ba, kallanta yayi ya ƙara maimata abinda ya faɗa sannan ta miƙe ta nufi hanyar kitchen ɗin ya bi bayanta da kallo. Ta canja kayan da tazo da su da riga da siket ne a jikinta yanzu kuma wasu riga da siket ne ƴan kanti a jikinta, da alama basu da nauyi dan ko a gida yana daga ɗaki yanajin Baba Huwaila na mata faɗa, akan ta dinga yawaita saka atamfa a gidan mijinta dan sam Indo bata san kaya masu nauyi shiyasa yawancin kayanta dogayen riguna ne, riga da siket ɗin na roba ne masu baƙi da rashin ruwan madara ba ƙaramin kyau sukayi mata ba, sai hular lilo baƙa ta saƙa da ta sawa kanta irin mai raga-ragar nan. Ba ƙaramin kyau tayi masa ba wani irin tunani ya faɗa wanda har taje ta ɗauko baisan dawowarta ba, baisan lokacin da yayi suɓutar baki ya ce, "Ina ma tana ƙaunata" Indo taji abinda ya faɗa sarai da ƙarfi ta ajiye masa Plate ɗin dan da alama ta lura ya zurma cikin kogin tunani, a zabure ya sauke ajiyar zuciya ya sauke ya janyo ledar kajin ya turawa Indo ya ce. "Ki zuba mana" hannu tasa ta karɓa a dai-dai lokacin hannunsu ya sarƙe da juna, a kasalce ta janye hannunta ta zuba musu dai-dai wanda zasu ci ta ajiye sauran. Tana ajiyewa Jamilu ya ce, "Kai mana sauran cikin firji" Wannan karan a ɗaɗɗare ta miƙe cikin tsarguwa dan ta lura da biyu ya ƙara aikenta, dawowa tayi ta zauna ya ɗauka wata tsoka yayi bismillah tare da miƙawa Indo baki, wani kallo ta watsa masa ta ce, "Meye haka ne wai" tsuke fuska yayi ya ce, "Abinda kika gani, Malama buɗe baki ki ci ina lura dake tun jiya da akace miki zamu tare baki ci abinci ba, inaji Baba Huwaila na miki faɗan cim abinci" murguɗa baki tayi ta ce, "Bazan ci ba dole ne sai naci cikina ko naka dan Allah Malam ka rabu dani banasan..." ƴan yatsunsa biyu yasa ya ɗalle bakinta ya ce, "Kisan irin kalmomin da zaki dinga gaya mun banasan rashin kunya" idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce, "Wai me nayi maka ne Ya Jamil meyasa ko yaushe bakasan farinciki, ka raboni da mai sona kazo zaka dinga azabtar dani wallahi sai Allah ya saka mun" Jamilu yaji ɗacin abinda ta faɗa, tsuke fuska ya ƙarayi ya ce. "Eh naji duk abinda zaki faɗa ki faɗa amma sai kinci abinci" kamar me jira ta fashe da kuka ta ce, "Wallahi bazan ci ba banaci" a yadda yasan Indo da kafiya indai ta kafe kan abu to bazaka taɓa juya ta ba, tausasa murya yayi ya ce, "Nasan bakya sona Ayusher amma dan Allah karki azabtar da kanki da yunwa, banasan Ubangiji ya kamani da haƙƙinki" wani irin kallo tayi masa na ka raina mun hankali, cikin jin haushi ta ce, "Shiga haƙƙi na nawa? kana tunanin yanzu daka sa aka kawo nan ba haƙƙina ka shiga ba?" tana gama faɗa ta rushe da wani irin kuka. Jikinsa ne yayi sanyi nan take nadama ta shige shi, tabbas shi zai isar da saƙon rabo da masoyi tunda ya shiga irin wannan damuwar a kwanakin da ya gabata, tausayinta ne ya kamashi ya miƙe tsaye ya taka zuwa gurin da take zaune. Ɗagota yayi yana riƙe da kafaɗunta yaja da baya ya zauna akan kujera, fuskarta ya ƙarewa kallo nan take ya rungumeta yana bubbuga bayanta kamar wata ƙaramar yarinya, jikinta banda rawa babu abinda yake yi ƙirjinta na bugawa har Jamilu na iya jiyo bugun ƙirjinta, mutsu-mutsu take tana niyyar ƙwacewa amma tsam ya riƙeta yana goge hawaye, sai da yaji ta tsagaita da kukan ya saketa ya ce. "Ayusher me kike so?" Ajiyar zuciya ta sauke ta buɗe baki zata yi magana ya ce, "Amma da sharaɗi sai kinci ki ƙoshi duk abinda kike so zanyi miki" Indo juyawa tayi ta kalli plate ɗin jiki ba ƙwari ta ƙarasa gurin ta tsugunna tasa hannu ta fara ci. Murmushi Jamilu yayi ya koma ya zauna suka cigaba da ci babu mai yiwa kowa magana kamar kurame, sai da suka ci sukayi ƙat sannan ya buɗe hollandia ya miƙa mata, babu musu ta karɓa ta fara sha nan take ta shanye shi tas. Jamilu ya hira ya fara sakowa Indo amma sam fuskarta ba walwala, har ya gama maganarsa bata tanka masa ba. Suna nan zaune aka fara kiraye-karayen sallar Isha'i, miƙewa sukayi shi yayi alwala ya fice zuwa masallaci ita kuma ta ɗaura alwala ta shiga ɗaki dan gabatar da sallah. Jamilu bayan sun idar da sallar isha'i ya samu limamin ya gabatar da kansa a gurin nan suka ƙara gaisawa tare da sauran mutanen da ke gurin , Bayan ya dawo ƙofar gidansa nan ya sa akayi masa sallama da wasu maƙotansa bayan sun gaisa duk ya gabata da kansa agurinsa, musabaha suka ƙarayi sukayi masa Allah sanya alheri tare da fatan alheri, hira suka fara yi Musa maƙocin Jamilu na hannun dama ya ce, "Ango maza wuce ka wuce amarya na jiranka mu nan duk tsofaffun hannu ne" gabaɗaya dariya suka saka Jamilu yayi musu sallama ya shiga gida, yana shiga ya sakawa gidan sakata. Lokacin da ya shiga cikin falon bata nan kai tsaye ɗakin ya tura ƙofa ya shiga, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga da sauri ta durƙushe a gurin daga ita sai towel ɗaurin ƙirji da alama daga wanka ta fito, bakinta har rawa yake ta ce. "Dan Allah ka fita kayana zan sa" tsayawa yayi yaga yadda duk da takure guri ɗaya juyawa yayi batare da ya furta komai yana rintse idanu, cen ɗakinsa ya wuce shima toilet ya faɗa ya yi wanka ya sako doguwar jallabiyya, cen ɗakin Indo ya wuce ya sameta kwance a kan gado ta takure guri ɗaya zama yayi a gafen gadon ya ce, "Ki tashi ki ɗauro alwala muyi sallah" a taƙaice Indo ta ce, "Nayi tawa" shima ya mayar mata da martani, "Nafila zamuyi" bata amsa masa ba ta tashi taje ta ɗauro alwala ta saka hijabi sannan suka gabatar da sallar nafila, ya jima yana kwararo musu addu'a tun Indo na amsawa a zuciyarta har ta gaji tayi shiru sai da ya idar sannan suka shafa gabaɗaya. Yana shirin miƙewa murya a raunane Indo ta ce, "Ya Jamil ɗazu kamun alƙawari." murmushi yayi yace, "Ina zuwa" yana gama faɗa ya fice daga ɗakin kai tsaye ya wuce firji ya ɗebo musu fresh milk da kofuna ya dawo ya zaune, a inda ya barta anan ya dawo ya sameta, zuba musu yayi ya miƙa mata ya ce, "Ki sha wannan idan muka gama sai muyi magana" karɓa tayi tana sha tana ɗan danna waya har suka kammala sha, kwashe kwanukan yayi ya fita da su Indo tun tana jiran dawowarsa har ta gaji ta haye gado ta kwanta. Bacci har ya fara kwashe Indo taji alamar shigowarsa, hasken fitilar ya rage musu sannan ya zagaya ta gefen Indo ya bargon da take ciki ya kwanta. A hankali ta fara janye jikinta yayi karaf ya ce, "Wacce magana kike yi ɗazu" a sanyaye tace, "Dama akan wannan..." ya katse da faɗin, "Akan me" zaro idanu taji saƙon daya fara aika mata. KUYI HKR BAN TACE SHI BA _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 GA TALLAN LITTAFIN SISTER NA😊😊👇🏻👇🏻👇🏻 👑 *KARAGAR MULKI* *MALLAKIN* *REAL EESHOW* _*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_ _Dasunan Allah me Rahama mejinƙai_ *PAGE* 0️⃣1️⃣➡️0️⃣2⃣ *MASARAUTAR MURISHIYOS* babbar Masarauta cemai cikakken iko wadda kaf nahiyar babu wata Masarauta wacce ta kaita kuɗi taƙama izza zalinci da rashin sanin darajar bayinsu sarki idan ya zartar da hukunci dole abi ba'ah jayayya sunada riƙo al'adun su akwai kananun masarautu goma dake ƙarƙashin babbar masarautar wa'inda suke a ƙarƙashinta. Zaune suke da kayan bayi suna cin abinci ɗaya daga cikin ƴammatan ce tace" Maryam muyi sauri mu gama cin abincinnan mu wuce dan naga har rana tayi sosai". "eh wlh muyi sauri Khadija nike nikejiyewa ma karki riski Assultana Fatimah tasa ayimiki hukunci kinsan halinta abu kaɗan zakayi akaika ɗakin duhu". "wlh kuwa nina ƙoshima bara na tafi saboda tsaro". "toh sekin dawo nima bara na ƙarasa na fita". "toh". nan Khadija ta tafi tabar Maryam tana ƙarasa cin abinci tana cikin ci wata mata tashigo tare da cewa"ɗiyata har yau baki tafiba kinsan dai halin masarautar nan daiko damma kina guri me dama-dama ke yi ki tafi da Allah". "toh Ummah". nanta taƙarasa cin abincinta ta tafi part ɗin Assultana Hindu. Cikin sauri ta isa ɓangaren ta tarar da sauran kuyangi wasu na aikinsu wasu kuma sun kammala nata portion ɗin ta wuce wato cikin ɗakin Assultana Hindu samunta tayi wani falo tana waya duƙawa tayi harta idda wayarta sannan Maryam tace"Ina kwana ranki shidaɗe". harar Maryam Assultana Hindu tayi tare da cewa"lafiya ƙlau Maryam tin ɗazu niketa zuba idon ganinki nina ɗaukama bakida lafiya shiyasa bakizo ba". "lafiyata ƙlau ranki shidaɗe makara mukayine". "okay amma kuma tin ɗazu naga uwar bayi tana aikinta". kame-kame Maryam tashigayi kamar kullum hakan yasa Assultana Hindu yin murmushi tace"Allah ya shiryeki kidena wannan makarar ki wuce kifara aikinki". duƙar dakanta tayi tare da yin dariya murmushi itama tayi nanta wuce tashiga gyaran ɗakin. "Salamu Alaikum". "wa'alaiki salam Jakadiya ce". "eh nice uwar bayi yakike". "lafiya ƙlau". "masha Allah dama ba wani abun ne yakawoni ba se akan Maryam tadena tsaya ƙawarta Khadija saboda kinga watarana ba fata akeba karta haɗu da Yarima Ahmad ya ɓatamata rayuwa a banza a wofi yanzu naganta tana tsaye tana jiran Khadija". "to Jakadiya kullum inzata fita senayimata faɗan haka bataji ko ita Khadija batason take zuwa tsayata saboda karta haɗu dashi". "toh ni zan koma kar a nemeni". "nagode sosai Allah yabar zumunci". "Ameen". nan Jakadiya ta tafi koda su Maryam suka dawo sosai Ummansu tayi musu faɗa kan abinda Jakadiya ta sanarmata. Assultana Hindu na zaune taji anbada sanarwar shigowar Jakadiya ɓangarenta bada iso tayi jakadiya ce tashigo jiki na rawa cikin girmamawa tace"barka da hutawa Assultana". murmushin ƙasaita Assultana Hindu tayi dake nuni da itaɗin jinin sarauta ce tace"barka Jakadiya meke tafe dake". duƙar dakai Jakadiya tayi tare da cewa"Sultan ne yace akiraki cikin gaggawa". "toh kicemasa ina zuwa". "godiya nake ranki shidaɗe nabarki lafiya". Jakadiya taƙarasa zancenta cikin girmamawa ta tafi bayan tafiyarta Assultana Hindu ta gyara Alkyabbar dake jikinta ta tafara tafiya cikin takun ƙasaita harta isa babban falonta tadda bayin da zasuyimata rakiya na sunkuye suna jiran fitowarta murmushi tayi tare da yin gaba suka bita a baya har suka isa ɓangaren Sultana a bakin babbar ƙofar suka dakata itakuma ta wuce tashiga. Samun Sultana tayi da Assultana Fatimah se Ashraf dake dake kusa kusa da mahaifiyarshi yana danna waya gefe guda kuma me gayya me aikice Assultana Ummuh Hauwa'uh ke hakince kan wata KARAGA ƙarasawa tayi tare da duƙawa gaban Assultana Ummuh Hauwa'uh cikin girmamawa tace"barka da hutawa ranki shidaɗe". cikin izza dattijuwar matar tace"barka". a ɗan taƙaice waigawa tayi gaban Sultana Abdallah tace"barka da hutawa Sultan gani". "yauwa magana zamuyi me matuƙar mahimmanci". murmushi tayi tare da zama kusa da Assultana Fatima gyaran murya Sultan yayi tare da cewa"ba wani abu bane yasa na taraku ananba face akan Aliyu dole ya dawo yayi aure domin ina matuƙar jin takaici a duniya idan na tuna duk faɗin masarautar nan bani da magaji *KARAGATA* inajin ba daɗi yau da safe bokan masarauta ya dubamun cewa muddum Aliyu ya dawo cikin gobe zuwa jibi za'ah iya samun rabon ɗa namiji kamar yadda aka yiwa Ashraf wato Saɗaka hima haka boka ya umarta dan haka dole sannan idan aka yimasa Saɗaka tasamu ciki za'ah kaita gidan Saɗaka har Allah ya sauketa tabamu yaron tayi nesa da masarautar nan sannan Boka Kiriyanu ya shedamun dakaina zan rife ido in jefa sanda kan Kuyangar daya tsaya ita za'ayi Saɗa kan da ita dan haka dole ya dawo kafin na mutu inason ganin magajin KARAGAR MULKIN masarautar nan". A razane Assultana Hindu ta kalli Sultana murya na rawa zatayi magana Assultana Ummuh Hauwa'uh ta ɗagamata hannu tace"wannan hukuncin yayi ko nima naji daɗinshi dan kana aikin soja sekaƙi aure amma kuma Sultan ɗiyar wa'inne masarautun ne suke neman haɗa zuri'ah da Aliyu gadanga ƙusar yaƙi a wannan shekarar nan ni banga tsarin jadawalinba". "masarautu Shida ne suka aiko da wasiƙa da hotunan ƴammatan na zaɓarmishi ɗiyar Sarki Muhammad wato gimbiya Usaina saboda ɗiyar aminiyar Assultana Fatimah ce kuma yarinyar tanada tarbiyya". "masha Allah ke seki kirawoshi ki sanar dashi". jin wadda Sultana ze aurawa Aliyu gadanga ƙusar yaƙi baƙaramun tashin hankali Assultana Hindu tashiga dakyar ta saita kanta tace"toh shikenan zan sanar dashi". "yauwa kekuma Assultana Fatimah ki aika da wasiƙa Aliyu zeje yaga gimbiya Usaina". cikin ƙissa Assultana tace"toh godiya nike ranka shidaɗe". nansuka tashi kowa yakoma ɓangarensa. Assultana Fatimah na shiga ɓangarenta ta tadda Ashraf yanata zabga uban tsaki ƙarasawa tayi ta zauna kusa dashi cikin kulawa tace"Ashraf wai meyasa bazaka kwantar da hankalinka kabarmun komai a hannuna bane". "haba Mamah tin yaushe nacemiki nafison a kauda wannan tsinanne Aliyun me gadara kina cemun akyaleshi kuma kullum mahaifinmu ƙara nuna banbanci yake akamu kamar bakya gani haba Mamah a wannan karon inyadawo itace dawowarshi ta ƙarshe domin sena zama ajalinsa". "kai da Allah mahaukacin banza bakaji abinda bokan masarauta yace abinda bazan taɓa bari yafaru ba kenan danaga randa Aliyu ze haifi magajin *KARAGAR MULKI* gwara naga mutuwata domin bazan taɓa bari hakan ta faruba koda zan rasa zanin ɗaurawata kuma kai inbanda sakaraine kai ai abinda yasa nabari gimbiya Usaina ina taga wata tarbiyya shiyasa na zuga Sultan a auramishi ita kadena damun kanka ninasan mezanyi wannan karon zakasha mamaki domin sede ayi mutuwar kasko shima in anyimishi Saɗakan itama tahaifi macen". "toh amma Mamah meze hana ki sanarwa da gidansu Usaina dukda Sultan ya hana". "kaifa banza ne ninasan abinda zanyi bara kawai ka wuce gurin iyalinka". tsaki yayi cikin rashin tarbiyya yace"kan wannan KARAGAR banƙi inbata da uban kowa ba ato ko kece wlh".don nikisan ihar inason abu tobawanda ya isayayimin shamakidashi bangabayansaba kokece "banjimekaceba koniceko to sainakƴaleka"ainasan bazaki iyaba yaƙarasa tare da ficewa daga part ɗin ba alamun jin haushi tayi dialing number aminiyarta Gimbiya Kareemah bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa"ƙawata albishirinki". "goro fari tass shaƙamun". "ai ina me tabbatarmiki jibi zakiga wannan yaron mara tarbiyya yazo gurin Usaina". "wow amma gaskiya naji daɗi burika na sun fara cika". nansukayita kulla abubuwansu daga ƙarshe sukayi sallama. Bayan ta kashe wayarta ne Khadijat data gama aikinta tazo wucewa Assultana Fatimah tace"keeeh zonan". jiki na ɓari ta ƙarasa inda take tare da duƙawa murya na rawa tace"gani ranki shidaɗe". "ki kiramun Saratu ". "toh". jiki na ɓari taje ta sanarwa da Saratu cikin rawar jiki Saratu ta nufi ɓangaren Assultana Fatimah ta zube a gabanta cikin izza Assultana Fatimah tace"gurin boka( ba'ah zuwa da wando) zamuje". "toh Assultana Ummuh Fatiman gobe ƙarya suke su ja dake faɗa da aljani bakyau". murmushin jindaɗi tayi tare da cire sarƙar wuyanta tace"ga tukuicinki muje". "godiya nike Allah yaja zamananinki". "Ameen". nan ta rifa alkƴabba cikin sirri sukabi ta ƙofar baya su ka nufi wani guri da yike duk kukoki suna zuwa daidai kukokin suka tuɓe wandunansu sannan suka shiga wata bukka guda ɗaya dake gurin. Zaune suke a gaban boka turnuƙu Assultana Fatimah tace"gaskiya boka wannan karon so nike ayiwa ɗan iskan yaronnan abinda kowa ze zamana ya tsaneshi saboda ya katangemun komai". wata uwar dariya boka turnuƙu ya ɓaɓɓake da ita tare da haɗe rai lokaci ɗaya yace"angama buƙatarki tabiya ungo wannan maganin zebi mata kamar yadda bunsuru kebin awaki zezamana bashi da aiki se shaye-shaye ta yadda sarki da kansa zega be dace abashi sarauta ba balle kuma ya haifi magajin KARAGA". cikin murna Assultana Fatimah tace"gaskiya naji daɗi sosai aidama nasan ina zuwa komai ze daidaita". wata uwar dariya boka yaƙara bushewa da ita sannan kuma baki bari na faɗamiki sharuɗan wannan maganiba kikayi saurin yadda dolene shize tsallaka idan wani ya tsallaka kan wanda ya tsallaka abun zekoma sannan kuma shi wannan magani ba'ah karyashi inko aka karyashi to mutuwa ta tabbata a gareki". "aibama wanda ze tsallaka Saratu zata kula sosai godiya nike boka ka gamamun komai in wannan maganin yayi". taƙarasa zancenta cikin farinciki ta ajemasa kudaɗe masu yawa taƙara da cewa"Saratu kibamu guri na ƙarasa babbar godiya". "toh ranki shidaɗe". tafaɗa tare da ɗaukar magani tafita waje bayan tafita suka shiga masha'arsu seda suka daɗe sannan Assultana Fatimah ta fito tana gyara zane a hanyarsu ta komawa Assultana Fatimah ta kalli Kuyanga Saratu cikin farinciki tace"kiyi ƙoƙari ki zuba maganin nan daidai nayimiki alƙawarin baki dukiya me yawa sannan zan ƴantaki a matsayin baiwata". cikin farinciki tace"godiya nike Assultana Ummuh Fatiman gobe bazan taɓa bari asamu matsalaba". "yauwa haka nikeso". nansuka ƙarasa gida cikin farinciki. Ɓangaren Assultana Hindu ko dakyar take tafiya saboda tashin hankalin da take ciki tana shiga ɓangarenta ta zube akan kujera furzar da iska mezafi tayi bazato taji muryar Maryam tace"ranki shidaɗe sannu da hutawa addu'ah itace maganin komai ki yawaita ambaton Allah idan wata musiba tasameki da Allahumma ajirna fi musibati wa'akalifli khairan minha ". buɗe ido tayi taga Maryam dake tsugunne a gabanta da kayan bayi wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta tasaki murmushi da bata shirya yinsaba tace"nagode Maryam Allah ya albarkaci rayuwarki". "ameen ranki shidaɗe nabarki lafiya". ta tafi kallonta kawai take harta ɓacema ganinta ta sauke ajiyar zuciya tashiga karantawa lokaci ɗaya taji wata nutsuwa ta ratsa zuciyarta ta ɗauki wayarta ta tura text message a mamakinta setaga tana turawa Aliyu gadanga ƙusar yaƙi ya mayarmata sosai tayi murmushi haɗe da cewa"miskilina kana kusa da wayar kenan Allah na godemaka da yaronnan ze dawo Allah yakaimu". nan taita murmushin jindaɗi saboda tana mutuwar son tilon ɗan nata. Jiki a saluɓe kamar wadda kwai ya fashewa a ciki tashiga ɓangarensu kallonta Khadijat tayi cikin tsokana tace"keko Maryam wacce irin tafiya kike kamar wadda aka yiwa gashin kazar kuku aka yimiki dagargaza". waro oily eyes ɗinta tayi waje tare da cewa"ba ruwana niba ƴar iska bace Allah yasa Ummah tajiki kinga ace tin baki tafasaba zaki ƙone ayi a aurar dake musha biki". "hhh ƴar iska wato baƙinciki kike da zamana ko Allah ya shiryeki". "ameen aikinga maga ƙarshen tafasa mudai ƴan cika kaine da ɗan kwali ni babbar aminiya kinga kyabani labari yadda akayimikima". dukan wasa Khadijat takaiwa Maryam ta goce!!!!! *Shimfiɗa yanzu zamu fara wasan Allah idan banga ruwan comments and votes ba sena maida book ɗinnan na kuɗi.* *Dan Allah a tayani share badon na isaba sabida Allah zakiyi koda bana ganinki so nike wannan book ɗin yafi kowanne book nawa zaga duniya.* More votes and Comments More typing Plz share _*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_✍️ 👑 *KARAGAR MULKI* *MALLAKIN* *REAL EESHOW* _*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_ _Dasunan Allah me Rahma mejinƙai_ *PAGE* 0️⃣3️⃣➡️0️⃣4️⃣ Dariya ta kyalkyace da ita tare da cewa"matsoraciya asheke ƙaramar ƴar iskace aini dase inje in sanarwa da Ummah ta sanar da Ummanki kinga sede kawai musha biki". taƙarasa tare da ƙara tuntsirewa da dariya duk sukayi Khadijat tace"au namanta ɗazu masoyinki yace dan Allah insanar dake yana baya gurin zancenku yana jiranki". "amma shine biki faɗamunba yanzu ƙilama ya tafi tinda yaga shiru banje". "wlh mantawa nayi kiyi haƙuri amma ai zeyi wuya idan yabar gurin saboda dazan shigo yike faɗamun". "toh muje ki rakani mugani Allah yasa yana nan domin nayi kewarshi yaufa kwatakwata banganshiba". "toh muje mugani". "toh". suka tafi suna hirarsu har suka isa bayan makarantar bayi tindaga nesa yiketa zabgamata murmushi mayarmata da martani tayi suka ƙarasa gurinsa tare da zama cikin girmamawa Maryam tace da mutumin dake sanye da kayan bayi irinta"ina yini". "lafiya ƙlau gaskiya nayi kewarki da kuma yanzu zan tashi nayi tinanin sarkin mantuwa ta manta da zancena". dariya Khadija tayi haɗe da cewa"Allah ne ya temakeka na tina domin wlh harna manta sarkin soyayya ga gimbiyar taka nan na kawomaka". "godiya nike Khadija naji daɗin kawomun ita da kikayi". "bakomai nidai abinda nikeso dakai ka riƙemun ƙawata amana kamar yadda nasan itama ta riƙemaka amana". "insha Allahu Khadija". "yauwa nabarku lafiya Maryam asha soyayya lafiya". hararta Maryam tayi cikin jin kunya tace"zan dawo na samekine zakiyi jawabi". "najiɗin". tafaɗa tare da tafiyarta . Bayan tafiyarta Muhsin yayi gyaran murya haɗe da cewa"yadai yau nasan gimbiyata fishi akeyi dani ayi haƙuri tuba nike aikin gina gidan Saɗakan Yarimah Zaki mukaje". lokaci ɗaya gabanta ya yanke yafaɗi tace"badai Aliyun masarautar nan ne ze dawo ba". "shine kuwa ze dawo anjuma za'ah saki busar algaitar masarauta me sanar da dawowarshi shiyasa ma duk aiki yashamun kai". sauke numfashi tayi tare da cewa"niko zanso ganin wannan Aliyu gadanga ƙusar yaƙin da kowa na masarautar nan ke zancensa". dariya Muhsin yayi me sauti haɗe da cewa"au kufa baku sanshiba tin tasowarku ko tab ganinshi yafi jinshi domin mutum ne me tausayin na ƙasa dashi ammafa mugun muskiline idan kaganshi zaka ɗauka baida kirki seka zauna dashi zaka tabbatar da baida girman kai ammafa murɗaɗen haline dashi". "to Allah yakaimu naganshi sarkin yabo". "naji yabon gwani yazama dole masoyiyata domin shiɗin na dabanne". taɓe baki Maryam tayi tare da cewa"nifa babban nadaban be wucemun kaiba saboda kaine kaɗai zuciyata idan bata gankaba wuni ɗaya take shiga wani mawuyacin halinda bansan yadda zan iya misaltamaka ba inasonka Muhsin ina ƙaunarka ina fatan mu rayu tare da juna ka riƙemun alƙawari kamar yadda nima na rikemaka". "hmm nagode sosai Maryam ai kema ta dabance masoyiyata abar alfaharina insha Allahu babu abinda ze rabamu tare zamu rayu cikin aminci ki haifamun kyawawan yara kamarki". rife fuska Maryam tayi alamar kunya nansuka cigaba da jifan junansu da kalaman soyayya masu zafi inda ko wanne cikinsu gani yike yafi ɗan uwanshi ƙaunarshi basu suka tashiba se ana kiran Magriba ta wuce ɓangarensu shikuma ya tafi masallaci. Assultana Fatimah na shiga ɓangarenta tace"Saratu ki kula sosai da Allah saboda kinji dai sharaɗin boka ba'asa wando banason asamu matsala". "toh ranki shidaɗe nabarki lafiya". ta tafi tabar Assultana Fatimah cikin farinciki bayan fitarta Ashraf yashiga ba tare dako sallamaba ya zauna tare da cewa"Mamah ina kika shigane Sultan ya aiko a kiraki akwai wani babban albishir daya samemu". "ina gurin samomana ƴanci saboda dawowar wannan mara tarbiyya kuma kwalliya tabiya kuɗin sabulu domin yanzu daka gurin boka Turnuƙu nake yabani tabbacin wannan karon yaronnan bazekai labariba kaidai kawai kasa ido gobe akwai shan kallo ". "kokefa yanzu nasan inada uwa da kintsaya kinata wani yimun abu kamar wata maƙiyata Hauwa'uh fa ciki gareta kiriyanu ya tabbatarmun da Namiji zata haifa yanzu haka ya sanarwa da Sultana yau akwai liyafa a masarautarnan ". "dan Allah dagaske kakeyi wayyo Allah daɗi". "wallahi ai shiyasa ma tinɗazu aketa nemankiba kinacan gurin gal-gal ɗinki kenan". ba tare dataji komai akan abunda ya faɗamataba ta rangaɗa guɗa ta nufi ɓangaren Sultan. Samunsu tayi Jakadiya na yiwa Sultan kirari yanatayimata kyaututuna ƙarasawa tayi cikin farinciki takai gasiwa gurin Assultana Ummuh Hauwa'uh ansamata tayi tare da cewa"gaisheki mejiran gadona Allah ya sauki uwar magajin KARAGA lafiya". "godiya nike Allah yaja zamaninki". takoma ta zauna kusa da Assultana Hindu ta tayata murna Jakadiya zata fita Sultan yace"Jakadiya anjuma inason a jeramub Kuyangi mata gabaki ɗaya wadda takwana ta tashi a cikin masarautar nan banason a rage ko guda ɗaya domin yin hakan ka iya jawa mutumin da aka ɓoye rasa rayuwarsa". "toh ranka shidaɗe za'ayi". "yauwa idan kin gama ki sanar dani zamuzo nida Boka Kiryanu ". "toh ranka shidaɗe". taƙarasa maganarta cikin girmawa ta tafi. Jakadiya bata zame ko inaba se ɗakin uwar bayi samunta tayi tana cin abinci ƙarasawa tayi jiki a saluɓe tace"wash Allah Haire akwai matsala". "tamefa Jakadiya". "Sultan ya umarceni da a jere kuyangi ya kumace seya kashe duk baiwar da aka ɓoye nikuma banason a haɗa dasu Maryam". "hmm to yanzu ya zamuyi hakanan zaki haɗa dasu inba hakaba wata masifar zasu shiga kuma insha Allahu baza'ah ɗaukesu ba". "toh Allah yasa amma dole muyi wani abun akai saboda kinga Maryam nada matuƙar kyau dan kar a zaɓeta ". "toh shikenan bara na kirata tana ɗakinsu Khadija". "yauwa yimaza kinga se a shiryata shikenan semu fita a jerasu". "toh". nanta tafi ɗakin su Khadija ta kirata suka shiryata cikin wasu burma-burman kaya sannan uwar bayi ta hura usur aka jera bayi kowacce tayi ƙasa da kanta Jakadiya kuma ta tafi sanar da Sultana. Tare suka dawo da Sultan da boka Kiriyanu se Jakadiya gani Sultan yayi duk anjerasu hakan yasa yasaki wani ƙasaitaccen murmushi yace"boka yanzu ya za'ayi". "abinda za'ayi shine rife ido zakayi ka jefa sandar nan duk wadda ta tsaya akanta ita za'ah ɗauka ammafa se ankashe hasken gurinnan". "toh shikenan Jakadiya asa a kashe wuta ida zan jefa". jiki a sanyaye jakadiya tace"toh ranka shidaɗe ". nan sarkin ƙira yabada shelar kashe wuta ana kasgewa Sultan ya jefa sanda aka kunna haske kowa nagurin so yike a ɗaukeshi saboda irin dukiyar da zesamu gakuma haɗa shimfiɗa da zeyi da Aliyu gadanga ƙusar yaƙi. Cikin mugun tashin hankali Maryam takalli sandar data tsaya a kusa da ita wasu zafafan hawaye suka zubomata lokaci ɗaya jikinta yashiga tsuma ta ɗaga kai taga kowa ita yike kalla ƙasa tayi da kanta ba zato taji muryar Sultan yace"kifito ". saurin ɗaga kai tayi idanunta yafaɗa kan na Ummanta dake hawaye gani tayi ta ɗagamata kai alamar ta fita jiki a saluɓe ta riƙa jefa ƙafa harta isa gaban Sultan da Kiriyanu ta zube murya na rawa tace"gani". "Jakadiya ayimata wankan madara da safe kafin isowar sarkin gobe a kawota turakata". "toh ranka shidaɗe godiya take". nan ya wuce bayan tafiyarshi Maryam ta rungume Ummanta suka fashe da matsanancin kuka mutane sauran kuyangi ko sun ɗauka kukan farinciki suke hakan yasa aka watse aka barsu daga Jakadiya Khadija Ummanta cikin kuka Maryam tace"Ummah na shikenan rayuwata tagama lalacewa zanzama bani da wata daraja anrabani da Muhsin". shafa bayanta Ummanta tayi taja hannunta suka nufi ɓangarensu sosai take kuka kamar ranta zefita sosai tabasu tausayi Ummanta da daurewa kawai takeyi ce tace"Maryam kidena kuka insha Allahu Allah zefitomana da mafita kidena kukannan insha Allahu sekin auri burin ranki". "taya Ummah ai nikuma tawa ta ƙare wannan wacce irin masarauta ce Allah dangirmanka ka kawomun ɗauki daga wannan iftila'ih daya faɗomun". taƙarasa zancenta tare da ƙara fashewa da matsanancin tashin hankali nansu jakadiya suka shiga lallashinta. Washe gari tana kwance akan tabarmarta taji muryar Jakadiya tana cewa"Harira ina ganin lokaci yayi da zaki sanar da Maryam sirrin da muka daɗe muna ɓoyewa". "a'ah Jakadiya abinda baze taɓa yiwuwaba kenan dan haka kibar zancennan". "to ai shikenan bara na tasheta nasan masu shiryata suna can suna jira". "toh shikenan". Maryam dake kwance tana jinsune a zuciyarta tace"toh wannan wanna irin sirrine da ba'aso nasani dole ko nasani ". tana cikin wannan zancen taji Jakadiya akanta tana cewa"Maryam tashi muje a shiryaki". miƙa tayi kamar me bacci tace"toh Ummah". nanta ta buɗe idanunta da suka ɗan kumbura saboda kuka ta miƙe tafara tafiya jiki a sanyaye har zasu fita daga ɓangarensu sega Khadijat zata shiga itakuma tsayawa Maryam tayi hawaye nabin kuncinta tace"Khadijat dan Allah abinda nikeso dake duk yadda za'ayi ki haɗu da Muhsin ki sanar dashi halin da nike ciki dukda yanzu nasan yaji". "toh shikenan insha Allahu zan faɗamishi". tafaɗa tana hawaye saurin yin gaba Maryam tayi saboda kukan daya tahomata suka nufi wani ɓangare. Wani ƙayataccen ɓangare aka kaita wanda yagaji da haɗuwa suna shiga Kuyangin da zasu shiryata suna shiga Jakadiya ta umarcesu dasu shiryata zataje ta dawo nan ta tafi sukuma suka shiga haɗa ruwan wanka kala-kala na alfarma tashiga tayo wanka tana fitowa suka ƙara haɗamata wani ruwan seda tayi wanka biyar sannan tana fitowa aka bata wani haɗaɗɗen turaren busar da laima ta shafa sannan suka shafeta da mayuka sannan aka shiga tsaramata kwalliya aka sakamata wasu tsadaddun kaya na alfarma sannan aka mayarmata da wata farar alkyabba me ratsin ja wata Kuyanga tace"ranki shidaɗe kalli kanki a madubi". ɗagakai Maryam tayi taga lokaci ɗaya ta canza kamar ba ita dukda tana cikin ɓacin rai hakan be hanata ganin mugun kyan da tayiba tashiga duniyar tinani Jakadiya ta shigo riƙe baki tayi tare da ƙarasawa inda take tace"kai Masha Allah ɗiyata kinga yadda kikayi kyau kuwa". wasu hawayene suka zubowa Maryam dafata Jakadiya tayi tare da cewa"haba ɗiyata karki ɓata kwalliyarman kitaso mutafi". tafaɗa tare da sharemata fuska da tissue Maryam data zama kamar kurmace ta miƙe Jakadiya ta kama hannunta suka nufi ɓangaren dayafi kowanne kyau a cikin masarautar dukda tana cikin ɓacin rai haka taita bin guraren da kallo har suka isa bakin wata katafariyar ƙofa datafi kowacce kyau a ƙofofin da suka wuce suna niyyar shiga aka busa alkyabbar shigowar Aliyu gadanga ƙusar yaƙi masarautar . Lokaci ɗaya gaban Maryam yayi wata muguwar faɗuwa Ashraf na niyyar fitowa suna niyyar shiga wuceshi sukayi binsu yayi da wani shu'umin kallo tare da lace leɓensa kamar baƙin maye yace!!!!!!! *Dan Allah idan kin karanta ki daure ki tayani share fisabilillwh badon niba.* Votes and Comments Plz share _*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_✍️ [02/10, 19:40] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ _Ina masoyan Real eeshow na haƙiƙa kufito ku nunamun ƙauna ta hanyar siyan book ɗina mesuna *KARAGAR MULKI* cikin farashi mafi sauƙi #300 ta wannan account number 2411022356 aiko da shedar biyanka ta wannan number 08108362334 ko transfer credit Mtn ko Airtel ta wa'innan numbers ɗin 08108362334 & 08087971440 sena jiku._ 97&98 Ido ɗaya ya kashe mata ta murtuke fuska ta ce, "Ka bari pls bana so, Yauwa game da abinda ka tambayeni ne" Murmushi yayi ya ce, "Ok, wai tambayar da nayi miki? Ai baki bani amsa ba me kike so nayi miki?" Indo kanta tsaye ta ce, "Kawai ka sakeni" ta faɗa batare da wata damuwa ba. Kallanta yayi yaga ko a jikinta har zuciyarsa yaji ba daɗi sai ya danne ya ce, "Haka kike so?" da sauri ta amsa da, "Eh! Shikenan" ya jefo mata tambaya, "Saboda bakya sona ko?" shiru tayi bata bashi amsa ba. Ya kuma cewa, "Idan na sakeki wa zaki aura Yaseer ko Fahad" idanunta ne suka ciko da ƙwallah bata bashi amsa ba ya ce,"Yanzu yaushe kike so na sakeki" a zabure ta miƙe zaune ta ce, "Ko yanxu ma" Ƙura mata ido yayi yana kallonta kamar bazai magana ba sannan yace, "Ayusher idan na sakeki a yanzu kina ganin na miki adalci, ashe ƙiyayyar da kike mun har ta kai haka? Nasan Yaseer kike so amma bantaɓa tunanin zaki nemi saki da kanki ba tunda Allah S.W.A ya haramta haka"jikin Indo ne yayi sanyi bata ce dashi uffan ba ya cigaba da cewa, "Amma ba damuwa ki bari akwai lokacin zan ɗiba wanda zan baki takardarki, wannan kawai kike so?" shiru Indo tayi batare da ta furta masa komai ba, daga haka juya mata baya yayi, ya fara karanto addu'o'in kwanciya bacci, Indo itama gyara kwanciya tayi ta kwanta sai dai gabaɗaya kowa da abinda yake saƙawa zuciyarsa, daga haka kuma bacci yayi awon gaba dasu. Washegari da safe Jamilu ne ya fara tashi ya haɗa musu breakfast, sai kusan ƙarfe tara Indo ta tashi kai tsaye banɗaki ta faɗa tayi wanka sannan ta shiryo cikin doguwar rigar atamfa Ja, ba wata kwalliya tayi ba amma ba ƙaramin karɓarta atamfar tayi ba. Lokacin data fito falo a lokacin shima ya shigo daga shi sai t-shirt da gajeren wando, Indo basarwa tayi kamar bata ganshi ba ƙamshi take jiyowa daga kitchen tana nan zaune ya ji ya kwaso musu kayan karin kumallo, wayarta ta ɗauka ta shiga whatspp tana duba saƙwannin da suke shigo mata, duk lokacin data buɗe data sai ta dinga baza ido ko zata ci karo da saƙon Yaseer amma ko makamancinsa babu, kashe datar tayi ta shiga cikin lambar Yaseer tun daga farkon tsohon chart ɗinsu take karantawa, sai zabg murmushi take hankalinta yayi nisa sosai, lokacin da Jamilu ya gama kawo musu kayan karin su shayi ya haɗa musu sannan ya ce, "Ayusher ba gaisuwa?" sam bata sanma yanayi ba hankalinta yayi nisa sai da ya ƙara maimaitawa amma ko gezau bata motsa ba, a shammace ya fisgi wayarta ya ce, "Wai wane irin wulakanci ne ina magana kina jina?" yana gama faɗa ya sauke idanunsa akan wayarta yaci karo da wani saƙon Yaseer da ya ce, "I really miss u dear ko bacci bana iya yi sai naji sautin muryarki" Ƙirjin Jamilu ne ya buga ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba, wani irin kallo ya watsawa Indo ita kuwa ko ajikinta ta ce, "Malam ka bani wayata" wata razananniyar tsawa ya daka mata yace, "Bazan baki ba, Uban waye ya baki damar yin hira da wani banza kina ɗauke da aurena akanki" haushi ne ya kamata a hassale ta ce, "Ya Yaseer ɗinne banza wallahi karka ƙara gaya masa haka..." a hargitse ya katse ta, "Na gaya masa daga yau sai yau na kuma ganin wayar a hannunki" yana rufe baki ya buga wayar akan tayals lokaci ɗaya wayar tayi kwatsa-kwatsa ta tarwatse, wani irin abu ne ya soki zuciyar Indo take ta fashe da kuka tana faɗin, "Allah ya isa wallahi kuma bana sanka bana ƙaunarka wallahi sai ka sakeni mugu azzalumi kawai" Kan kujera Jamilu ya koma ya zauna ya dafe kansa wanda yake sara masa kamar zai tsage gida biyu, wani irin zafi yake ji a zuciyarsa ga wani irin jiri da yake neman ɗibansa. Indo na shiga ɗaki ta faɗa kan gado ta fashe da wani irin kuka, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta fara haɗa kaya a gaggauce cikin ƙaramar trolly ɗinta, tana gama haɗawa ta janyo abarta fuskarta ta yi jawur saboda kukan da ta sha. Lokacin da fito Falo yana zaune a inda ta barshi harta zo tsakiyar falon binta yayi da kallo bai tanka mata ba dan yaga iya gudun ruwanta, kai tsaye wucewa tayi ta buɗe ƙofar ta fita harabar gidan da sauri yabi bayanta, yana zuwa ya fisgo hannunta yace, "Ke wai me yake damunki ne, meye haka zakiyi?" cikin zafin zuciya ta ce, "Ina ruwanka da duk ma abinda zanyi ka sake ni Malam infita wallahi bazan zauna ba" ta faɗa tana fisge hannunta tayi gaba. Janyo hannunta ya ƙarayi har sai da ta faɗo jikinsa yace, "Wai baki da hankali idan kinje me zaki ce musu, kuma da izininwa zaki fita" cikin tsiwa ta ce, "Ni kake cewa banda hankali aikasan ba'a mara hankali ɗaya sai dai idan agurinka na koyi haukan..." tun bata rufe ba Jamilu ya ɗauketa da mari cikin wata irin murya yace, "Me yake damunki ne?" Indo sakin baki tayi tana yi masa wani irin kallo kamar wata sakarya, cikin wata irin murya ta ce, "Ni ka mara?" tausayin Indo ne ya kamashi amma ganin tsiwa kwance a fuskar Indo yasa ya kuma tamke fuska yace, "Indai bazaki dinga sanin abinda zaki dinga faɗa mun ba ranki sai ya dinga ɓaci..." Tun bai ƙarasa zancen ba ta ce, "Wallahi wallahi sai na rama ra rantse da girman Allah babu wani ƙato da zai dake ni ya daki banza" Jamilu mamaki ne ya kamashi azuciyarsa yace, "Ashe har yanzu halin Indo na nan?" matsawa yayi kusa da ita yace, "Ni kike kira da ƙato? Bismillah rama kinji ko ba ni zaki mara ba?" wani murmushi Indo tayi kamar wacce aka farantawa rai da ido ya bita da kallo lokaci ɗaya yaji ya tuntsure da wata irin dariya, sakin baki yayi yana kallonta kamar ba ita take sharɓar kuka ba dariya take sosai harda ɗan durƙusawa, sai da tayi mai isarta sannan ta kalleshi fuska a sake ta ce, "Tun da na rantse sai na rama wallahi sai na rama da sannu gaggawar me kakeyi? Bari kaji Ya Jamil wallahi nama fasa tafiya idan zaka fita kabar gidanan a buɗe wallahi babu inda zani, ai bahaushe yace jiki magayi" tana gama faɗa da ƙarfin gwiwarta ta ja akwatinta ta koma cikin gidan, Jamilu tsoro ne ya ɗan ɗarsu a zuciyarsa saboda yafi kowa da wacece Indo indai ta kafe akan abu sai ta aiwatar dashi, bare wani abu ya haɗaku da ita ko ya shekara da faruwa sai ta fanshe abinta, tsoronsa ɗaya baisan wane ɗanyan aiki zata shuka masa ba, gyara tsayuwa yayi yana ayyana a ransa bazai taɓa nunawa Indo tsoron hukuncin da zata yanke ba. Lokacin da ya shiga falon har ta bararraje ta fara cin wainar ƙwai da shayin da ya ajiye musu, bai tanka mata ba ya nemi guri ya zauna shima suka cigaba da karyawa. Tun daga lokacin babu wata doguwar magana data ƙara shiga tsakanin Indo da Jamilu, banda gaisuwa babu abinda yake haɗasu itama sai ta ga dama, washegarin ranar da ya fasa mata waya da yamma ya siyo mata wata sabuwa da sabon layi a ciki lambobi huɗu ne kawai a ciki, daga ta iyayenta sai tashi da ta Baba Huwaila, lokacin da ya bata wayar ko godiya batayi masa ba saboda a ganinta biyanta tata yayi wacce ya fasa mata. A haka suka shafe kwana biyar acikin gidan daga gaisuwa shikenan, Jamilu tun yana ɗari-ɗari da Indo akan furucinta har ya fara sakin jiki dan itama ta saki jikinta kamar ba abinda yake damunta, sai dai har lokacin babu wata kykkyawar mu'amala a tsakaninsu, a ranarsu ta shida da tarewa Jamilu na kwance a kan kujera ya faɗa nazarin rayuwa yaji fitowarwa, ɗagowa yayi ya ganta ta fito cikin doguwar rigar leshi hannunta ɗaya ɗauke da ƙatuwar akwatunta tana janta, tashi yayi zaune yana zurawa sarautar Allah Ido dan a tunaninsa cewa zatayi zata tafi gida, da ƙyar ta dinga jan akwatin tana nishi kamar wacce aka sata dole. Tana tafe tana wata waƙa da Jamilu bai tama jinta a bakin kowanne mawaƙi ba, dan yadda yaji waƙar na fita ba wata isarshiyar ƙafiya da alama Indo ce ta haɗa abarta, sai da ta fitar da jakar har cen gate ɗin gidan kamar Jamilu zai bita sai ya tsaya yaga iya gudun ruwanta dan babu hijabi ko mayafi a jikinta. Yana nan zaune yaji dawowarta tana tafe tana cigaba da waƙarta, duk baiti ɗaya na waƙar na ƙara tsoratar da Jamilu saboda miyagun kalmomin da suke ciki. "In farke cikin hallita, in tsarge hanjin hallita in kama gabana a sauƙi batare da kuskure ba, naci kamar ƙuda ga rashin zuciya amma hakan bazai hanani kwakwale hanjin mutum ba, da sabuwar wuƙata..." haka tayi ta shige da fice tana waƙarta ba kai ba fasali harta faɗa kitchen, hargitsa kayan kitchen ɗin tayi da ƙyar ta samo saitin wuƙaƙarta, sharɓa-sharɓa biyu ta ɗauko da kowanne hannuwanta wani plate ɗinta na tangaran ta ɗora akan sink sai da ta ɗan leƙa Jamilu, taga duk yayi wani zuru-zuru ƙasa-ƙasa taji yace, "Yarinyar nan shirin me take anya ba wani mugun abun take ƙullawa ba" dariya ce ta subce mata ta fara murmushi a hankali, wayarta ta zaro ta fara wayar ƙarya. "Hello eh komai na tafiya dai-dai nan da ɗan lokaci sai dai wani bashi ba" tana gama faɗar haka ta haɗa farantannan ji kake taassss, da gudu ta fito daga kitchen ɗin ta fara kai sara da wuƙa, wani throw pillows ɗinta na kujera ta fisgoshi wani kukan kura tayi ta farke shi da wuƙa abinka da sabuwar wuƙa, nan take ya tarwatse. Jamilu na ganin haka ya ɗan ja da baya yace, "Ke meyake damunki ne..." bai rufe baki ba ta fisgo wani throw pillows ɗin na kusa da wanda Jamilu yake zaune, Jamilu na niyyar magana ta luma masa wuƙa tana cewa, "Zan farke hanjin pillow kafin nazo kan na uban gayya" tana gama faɗa ta wurgar ta buga wani uban tsalle tana ɗaga hannunta me ɗauke da wuƙar sama, kafin ta sauke da gudu Jamilu ya zuba a guje ya banka ɗaki da gudu. Indo dariya take harda riƙe ciki da sauri tabi bayansa tana cewa, "Yau idan ban farke ka ba hankalina bazai kwanta ba" tana shiga Jamilu ya rafka Ihu yana cewa. "Dan Allah Sarƙa karki farkeni ko me kike so zanyi miki" SU JAMILU YAU ANMANTA DA AYUSHER AKE CEWA SARƘA🤣🤣🤣 KUYI MALEJI DA WANNAN🤥 _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [03/10, 19:15] Ameera Adam: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share *INDO SARƘA*🤸🏼‍♀️ *BY* *AMEERA ADAM* *FOLLOW ME @WATTPAD* _*AmeeraAdam60*_ GARGAƊI BAN YARDA WANI YA SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. _*WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA DUK MAI SUNA AISHA😉🥱 NAMESAKE WHERE ARE U🤭*_ 99&100 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Indo bata saurareshi ba ta ci gaba da kaiwa iska suka da wuƙa tana cewa, "Gwara na kawo ƙarshen komai kowa ma ya huta, yadda na farke hanjin filon nan sai na farke hanjinka." Jamilu cen saman gado ya ɗare ya janyo ƙaton bargo ya kare da shi yana yiwa Indo magiya" sun ɗan jima a haka sannan Indo ta tunkaro shi gadan-gadan, daga cen ƙofar gida suka ji ana bubbugawa da ƙarfin gaske Indo ce ta juya ta fara takawa har zuwa falo, Jamilu na ganin tayi gaba ya diro daga gado cikin shammata ya fita a guje banda haki da gumi babu abinda yakeyi, Indo daga bakin ƙofar falon ta tsaya tana ƙyalƙyala dariya, bugu ake kamar za'a ɓalle ƙofar har Jamilu ya ƙarasa bakin ƙofar ba'a daina bugawa ba, sai da ya tsaya ya ɗan saita nutsuwarsa amma dukda haka kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana cikin wani hali, sai gumi yake yi ta ko'ina ga hakin da yakeyi. A hankali ya zare sakatar gate ɗin ya fita, maƙocinsa Malam Inuwa ya gani wanda gidansa yake jikin gidansu Indo, saita nutsuwarsa yayi ya miƙa masa hannu suka gaisa yana ɗan ƙoƙarin kawar da yanayin da yake ciki, Inuwa ya ɗan fahimci wani abu sai yace, "Malam Jamilu muna zaune da Iyalina muka fara jiyo ihu sama-sama, da farko na so na share amma kuma bisa ga koyarwar addininmu daya nusar damu haƙƙin maƙotaka, nace bari nazo naji ko lafiya? " Jamilu duburburcewa yayi ya ce, "Am dama ai dama muna ɗan wasanni ne irin na masoya to bamu zaci sautin na fita waje ba" Malam Inuwa sam bai yarda da abinda Jamilu ya faɗa ba amma sai yace, "Ah lallai haka ake san irin wannan soyayya, kasan dake katangarmu ɗaya ana iya jin hayaniya idan akayi magana da ƙarfi "murmushin yaƙe Jamilu yayi ya ce, "Ai fa dama haka ne" cikin zolaya Malam Inuwa yace, "Zan turo madam nima tayi course muma mu dinga wasan farke-farken" Jamilu dariya ya sa saboda ya lura da Malam Inuwa tun tariyarsa mutum ne me barkwanci, Jamilu yace. "Amma sai ka biya dan ba'a aikin banza a Kano, yauwa anjima dama zata shigo su gaisa kasan gajiyar biki bata samu ta leƙa maƙota ba" hira suka ɗan taɓa sannan sukayi sallama. Jamilu yana hirar ne amma gabaɗaya fargabarsa ɗaya idan ya koma me zasu ɗora a gaba shi da Indo, wata zuciyarce tace. "Ka zauna Indo taga makwancinka dama ya lafiyar kura bare taci nama, Indo bata ga makwancinka bama yaya bare kuma ka bada kai bori ya hau" juyawa yayi ya shiga ciki yana zuwa yabi falon da kallo, ko'ina tsaf ta share shi kamar ba falon da aka farke fulillika ba. Motsinta yaji a kitchen a zabure ya juya hangota yayi tana ta mayar da kayan ɗaya bayan ɗaya, mamaki ne ya kamashi idan tana wani abun kamar me aljanu dan ko da za'a ce masa aljanu gareta bazai musa ba, saboda guraren da ta dinga hawa tana sauka a ƙauye. Komawa yayi kan kujera ya zaune ba jimawa ta fito daga falon hannunta ɗauke da kofin tea guda biyu, fuskarta sai murmushi take idan ka ganta sai ka rantse wani kyakkyawan albishir akayi mata, cen ƙasa gujera ta zaune ta ajiye nata shayin ta miƙa masa nashi sannan ta koma ta zaune, karɓa yayi yana binta da kallon tuhuma bayajin Indo zata iya kashe mutum amma yana tsoron sharrin zuciya karta kaita ga halaka shi. Ajiye kofin shayin yayi yana kallonta bai tanka mata ba, ita kuwa ta ɗauko remote ta kunna kallo tana shan shayi tana kallo. Sakkowa yayi ƙasa ya zauna ya ce, "Ayusher wai meyasa kike wasu irin abubuwa idan kikayi wani abun kamar me aljani..." wani kallo ta watso masa tun bai rufe baki ba ta katse shi. "Bishiyar Bulukiya ce akaina" Jamilu yace, "Ba magana nazo ki gaya mun ba, zuwa nayi muyi magana cikin masalaha. Yanzu kina ganin abinda kikayi ya dace kenan? Kina gani ashe duk ihun neman agajin da nakeyi maƙota na ji na" cikin halin ko'inkula tace, "Kai ka so" Jamilu yace, "Wallahi duk abinda zaki faɗa ba yin kaina bane ina ƙaunarki inasanki soyayyar da bantaɓa yiwa wata ƴa mace ba, Ayusher meyasa bazaki fahimci zallar soyayyar da nake miki ba shin laifine dan na ƙaunace ki? Kuskure dai nasan nayi da tuntuni ban furta miki ba har kika fara soyayya da wani, amma idan kin duba duk wasu alamomi na nuna miki inasanki ina ƙaunarki na tabbata ko Yaseer baya miki soyayyar da nake..." a hargitse ta dakatar da shi tana ɗaga hannunta. "Ya isa dan Allah! ina cikin nishaɗi da farinciki dan Allah karka tarwatsa min ɗan guntun farincikin dana samu yanzu, har inmutu nasan babu namijin da zai so ni ya nuna mun ƙauna da kulawa kamar Yaseer. Jamilu zaman mutum uku kawai nake a gidan saboda sun isa dani ko ba kai ba suka ban wani da ban sani ba, matuƙar umarni ne zan musu biyayya. Ina zaman Baba Huwaila sai iyayena amma banda wannan bana sanka bana ƙaunarka kuma bazan taɓa sanka ba." ta ƙarasa faɗa hawaye na bin fuskarta. A duk lokacin da zata gaya masa irin waɗannan maganganun suna damunsa amma yana mata uzuri saboda yadda silar aurensu ta kasance, sai dai wannan karan ba ƙaramin ɗacin magangnunta yaji ba, kallan fuskarta yayi yana san haɗa ƙwayar idonsa da nata dan ya tabbatar da abinda ta faɗa cikin ƙwayar idont, amma hakan ya gagara, haɗiyar yawu yayi me ɗaki ya tashi ya fice daga gidan gabaɗaya. Tun daga wannan lokacin Jamilu yake ƙoƙarin ganin ya kyautata mata koda bazata soshi ba, satinsu biyu fa tarewa ya koma bakin aikinsa hakan ne yasa zamansa a gida yayi ƙaranci idan ba weekend ba, duk yamma idan zai dawo sai ya tahowa da Indo wani abun ɗan na motsa baki musamman kayan zaƙi da yake yasan tafi mu'amala dasu. Indo ta leƙa gidan maƙotansu baifi gida biyar ta shiga ba ta gabatar musu da kanta, yawancinsu yaran matane daga me haihuwa ɗaya sai me haihuwa biyu. Wata maƙociyarsu ce da ake kira da Maman Hibban ita ce me ƴaƴa uku kuma da alama duk ta ɗan girmesu, cikin sakin fuska suka gaggaisa bata jima ba ta koma gidanta. Bayan kwana biyu suma da kaɗan da kaɗan suka shigar mata daga haka babu wanda ya kuma shiga gidan wani a cikinsu, ahaka rayuwa ta gangara dasu Indo har ta shafe wata huɗu a gidan Jamilu, ba yadda batayi da Jamilu ba akan ya barta taje Kaduna amma fir yaƙi, gidan Baba Huwaila ma gabaɗaya zuwanta uku, gidansu Mommy ma zuwanta biyu kuma duk tare da Jamilu suke zuwa ya kaita da yamma, wajen ƙarfe tara na dare yaje ya ɗaukota su wace gida duk zuwan da sukeyi basu taɓa haɗuwa da Fahad ba, tayi masa mitar ya barta taje Kaduna da Abuja amma ya hanata tun abin na damunta har ya daina damunta ta saki jiki ta cigaba da rayuwa. Sai dai har zuwa waɗannan watannin babu wani zama me daɗi da sukeyi, gabaɗaya Jamilu ya rame ya bushe idan ka ganshi sai ka rantse jinya yasha, duk lokacin da zaije gun Baba Huwaila sai ta sashi gaba da tambayar abinda yake damunsa amma ya ce mata babu komai har ta daina tambayarsa. A Ɓangaren Yaseer duk yadda yaso yakice soyayyar Indo abun ya gagara, sai dai a hankali yake jin yawan tunaninta na raguwa daga zuciyarsa, kuma har lokacin bai daina miƙawa Ubangijin kukansa akan ya yaye masa matsanancin halin da yake ciki ba, ana cikin haka Lubna da ƙanwarta Ihsan suka dawo gidan su Yaseer yayyansu Lubna suka koma gidansu Indo, kasancewar Mahaifinsu yayi tafiya gida ba kowa. Zaman Lubna a gidan Momma a hankali ta fara shiga rayuwarsa dukda da farko yana shareta, amma bata gaza ba har ya fara sauraronta suna zama suna hira, lokaci-lokaci har ɗaukanta yake suna zuwa shopping. Shima Fahad ya warware babu wani ciwo da yake damunsa sai dai har lokacin bai mayar da jikinsa ba. Fahima ƴar Cousin ɗin Daddynsa ce tasu tazo ɗaya da Fahad sosai, har mamaki take yadda mutane suke faɗar murɗaɗɗen halin Fahad, ya ɗauke ta kamar ƙawarsa itama haka tana da ilimin addini dana boko dai-dai misali, ta karanci fannin lafiya tana aiki a wani ƙaramin asibitin kuɗi anan garin Kano, Mommy ce ta samu Daddynsu da maganar Fahad da Fahima shi kansa Daddy yaji daɗi amma sai ya tambayeta ko yara suna san juna, Mommy tace. "Daddyn yara naga yaran nan sun shaƙu amincewa soyayyar su bazai wuya ba" Daddy yace, "Haka ne Allah ya tabbatar mana da alheri, zan samu Fahad da maganar idan sun daidaita kansu sai na samu Sunusi da maganar" Mommy ba ƙaramin daɗi taji ba cikin zuciyarta take addu'ar Allah ya daidaita tsakanin Fahad da Fahima. Jamilu na zaune a office ɗin malamai, Malam Isa ya kalleshi yace, "Abokina duk wanda ya sanka a da, da yanzu zai fahimci zallar rashin kwanciyar hankalin da kake ciki, kaga yadda ka rame ka lalace kuwa? Na tambayeka har na gaji amma kace babu abinda yake damunka yanzu rayuwa zata yuwu haka? Ka tuna fa ciwon zuciya ya taɓa barazanar kamaka amma kullin baka da aiki sai tunani har rafkanwar shiga ajin ɗalibai kake" Jamilu ya ce, "Malam Isa ina cikin damuwa wallahi" Isa yace, "Malam Jamilu ai ko baka faɗa ba wanda ya sanka kallo ɗaya zai ma ya fahimci haka" Jamilu yace, "Malam Isa nayi aure amma aurena tattare yake da ƙalubale da tashin hankali, hatta girki sai ta ga dama take mun har na fara wani tunani saboda karna cutar da ƴar mutane, tunda bansan halin da zan jefa ta ba idan ni nayi haƙuri da haƙƙina ina azumi ita fa? Kaga kar azo ayi abunda babu daɗi saboda babu wani farinciki da muke ciki daga ni har ita a cikin gidan nan..." gabaɗaya Jamilu ya kwashe labarin sa da Indo tun daga farko har ƙarshe har irin ƴar tsamar da sukeyi da ita a ƙauye da bayan tariyarsu. Malam Isa murmushi yayi yace, "Malam Jamilu wannan ƙaramar matsala ce ai" da mamaki yace. "Bangane ba Malam Isa" Malam Isa yace, "Wallahi ita kanta tana sanka kuma zaka gaya mun nan gaba indai ka ɗau shawarar da zan baka, kasan meyasa wancen yafi tafiya da zuciyarta, kasan macen tunaninta kamar na yara yake dan haka kaima sai ka mayar da kanka kamar ƙaramin yaro, ya siye zuciyarta da kulawa tarairaiya, daɗin kalamai kasan mata ba wuya ka saye zuciyarsu da wannan, kuma ka dinga ɗaukanta lokaci-lokaci kuna fita yawon shaƙatawa a hankali zaka ga ta fara rage duk abubuwan nan da take yi maka, amma wani hanzari ba gudu ba" da sauri Jamilu ya Kalli Malam Isa zaiyi magana Malam Isa ya cigaba da cewa. "Duk waɗannan abubuwan ka fara ajiyesu a gefe har sai ka bari ta fara zurfi a sanka" guntun tsaki Jamilu yayi ya ce, "Wane so Malam Isa yau fa mun tafi wata biyar da aure tuntuni bata so ni ba sai wani zaman da zamu ƙara nan gaba?" Jamilu ya faɗa cikin damuwa. Malam Isa ya ce, "Haba Malam Jamilu kamar ba Namiji ba, yanzu abinda nake so da kai sai ka jajirce kacire duk wani abu da zaka ji yazo maka zuciya, dan ka daidaita rayuwar aurenku. Idan kaga tana zaune tsiri wayar ƙarya kai dan ka nuna da gaske kake ko ni ka kirani sai kayi kamar wayar gaske kakeyi da budurwa, idan ka dawo daga aiki da yamma gabannin magriba ka sheƙa wanka ka fice, kai abincinta ma ka rage ci idan ka samu ta tambayeka kace unguwar da kaje kaci acen, kuma idan dare yayi ka daidaici lokacin bacci yayi" Malam Isa ɗagowa yayi ce, "Wai intambayeka tare kuke kwana ko daban-daban" Jamilu yace guri ɗaya muke kwana" Malam Isa yace, "Yauwa to idan kaga ta kwanta ɗauki waya ka fita amma karkayi nesa da ɗakin, ka hau wayar ƙarya ka zuba kalamai yadda zata ji ka, ka shafe kamar minti biyar zuwa goma sannan ka dawo ɗakin ka kwanta. Amma fa da farko zaka ga barazana karka damu a hankali zaka ga ta fara damuwa har ta fara sakkowa" Jamilu yace, "Nagode ƙwarai Malam Isa, amma bakasan wace Aisha ba nasanta da taurin kai ƙwarai" Murmushi Malam Isa yayi ya ce, "Malam Jamilu kenan mace fa duk girmanta duk tsufan mace ce, ba'a sakewa tuwo suna" Jamilu ya daɗe yana ɗaukan darasi agun Malam Isa har lokacin tashi yayi. Yamma liƙis ya shiga gidan lokacin Indo na kwance kan doguwar kujera tana karanta littafin MARWAN (Littafin Ameera Adam) taji shigowarsa, a ɗan tsorace ta juya saboda labarin da take karantawa cike yake da bantsoro, sanye take da T-shirt sai gajeren wando iya gwiwa tana kallansa ta ɗauke kai gefe tana cigaba da harkarta, a zatonta zaizo gurinta ya mata magana kamar yadda ya saba ta ga ya wuce ɗakinsa, ya jima a ciki da alama wanka yayi ya fito sanye da singlet da gajeren wando, ruwan tea kawai ya zuba ya hau kujera ya zauna yana danna waya ya kara a kunne cikin salon kashe murya yace. "Hello, barka da yamma ina fatan banyi laifi ba?" shiru yayi ya ɗan saci kallon Indo da yaga ta ɗanyi wani jim, sannan ya cigaba da cewa. "Ok ba damuwa ai ko yanzu kika ce nazo aguje zanzo amma dai ataimaka abarni nayi magriba tukunna" Indo ya kuma kallo a fakaice yaga yadda tayi kicin-kicn ta tsuke fuska har abun yaso bashi dariya, tashi yayi ya cigaba da wayar ƙaryar har ya shige ɗakinsa ya laɓe daga ƙofa yana leƙen yanda zatayi. Indo na ganin shigewarsa ta tashi zaune tana cewa, "Ƙundun uba mutumin nan badai budurwa yayi ba" Jamilu na ganin haka ya ɗan ɗaga murya da ƙarfi yace, "I love you my baby" ƙirjin Indo ne ya buga kujera ta koma ta zauna jaɓar ganin zaman bazai kaita ba ta tashi ta shige ɗaki.Bayan sallar magriba tana zaune a ɗakinta ya shigo cikin galalleliyar shadda sai zuba ƙamshi yake, da biyu dama ya shigo dan taga shigar da yayi zai fita, cen gaban mudubi yaje ya ƙara fesa wani turaren yana nan tsaye wayarsa ta fara ringing, da sauri ya ɗauka yace, "Ina hanya karki fushi" yana katsewa ya fice daga ɗakin, tun bai ƙarasa falo ba Indo ta biyoshi cikin masifa tace, "Wai da wacce shegiya kake waya a gabana kuma ina zaka" wani kallo ya watsa mata har cikin ransa baiji daɗi ba a fili ya ce, "Karki ƙara zaginta saboda tana bani farinciki kuma babu ruwanki da inda zani" yana maganar ya fice. Indo saboda takaici kuka ta rushe dashi ta haye kujera ta ƙudura a ranta saita zauna taga dawowarsa. Jamilu tun da ya fita ya rasa gurin da zashi saboda bai saba fitar dare ba, yawo ya dingayi a mota har wajen ƙarfe tara da rabi na dare sannan ya shigo gida, Indo tun tana jiransa har bacci yayi awon gaba da ita ƙarar shigowarsa ce ta tasheta, yana ganinta yayi kamar be ganta ba zai wuce ta sha gabansa ta ce, "Daga ina kake?" fuska a tsuke yace, "Aikena kika yi, malama karki dagula mun farincikin da nake ciki da baƙin ciki" ya raɓa ta gefenta ya wuce ɗaki, kayansa ya cire ya haye kan gado ya kwanta yana nan kwance Indo ta shigo ta kwanta, sai da yaga kwanciyarta ya miƙe ya fara waya kamar yadda Malam Isa ya gaya masa sannan ya dawo ɗaki ya kwanta, yana jin Indo tana ta shassheƙar kuka tausayinta ne ya kamashi kamar ya rarrasheta sai kuma ya basar kamar be ji ta ba ya juya mata baya, yana jinta tun tana kuka har bacci yayi gaba da ita. Juyawa yayi ya haska fuskarta yaga duk ta kunbura bargo ya janyo ya rufesu ya tofesu da addu'o'i shima bacci yayi awon gaba dashi. Tun daga ranar Jamilu ya sauyawa Indo kamar ba shi ba a haka har suka shafe wata biyu a wannan yanayin, ga wani irin kishinsa da yake nuƙurƙusar zuciyarta dan ta gama yankewa kanta hukuncin Jamilu aure zaiyi, gefe ɗaya kuma wata irin kulawa da take san bashi amma sam babu dama, ta rasa wa zata gayawa har tayi niyyar gayawa Mahaifiyarta taga idan ta faɗa ma ba lallai su yarda ba tunda sunsan dama cen ba san Jamilu take ba, Jamilu ya lura da halin da take ciki har ramar da tayi ba ƙaramin damunsa tayi ba, dan wani zuwa da sukayi gurin Baba Huwaila har hannunka me sanda ta dinga yi musu, dan a tunaninta Indo laulayin ciki take, Indo duk ta rame tayi zuru-zuru ko abincin kirki bata ci har olsarta ta tashi ga wani irin zazzaɓi me zafi daya rufeta, lokacin da ciwon ƙirji ya kamata ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, da kansa ya haɗa mata ruwan shayi ya sameta a ɗakin duƙunƙune cikin bargo, yakice bargon yayi ya riƙota ya zaunar da ita ya dinga bata tana sha da kaɗan-kaɗan har ta shanye. Magungunan daya siyo mata ya ɓallomata ya bata tasha bayan wani lokaci ya kamata ya kwantar ya rufa mata bargon, zagayawa yayi ya kwanta ya rungumota yana jin yadda jikinta yayi zafi sosai, zazzaɓin jikinta sai cikin dare ya sauka zuwa safiya jikinta yayi sauƙi sosai. Washegarin ranar asabar ce Jamilu bashi da aiki wuni yayi yana bawa Indo kulawa, mamaki ne ya kamata sosai kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, haushi ɗaya ne ya kamata idan ta tuna Jamilu na soyayya da wata.Da daddare sun fara shirin kwanciya wayar Jamilu ta fara ringing ɗauka yayi ya fita daga ɗakin, Indo ji tayi zuciyarta na zafi hayewa fado tayi ta fashe da wani irin kuka, Jamilu bai jima ba ya shigo ɗakin ya sameta tana rera kuka me tsuma zuciya. Tausayinta ne ya kamashi haurawa yayi gadon ya zauna kusa da ita yace, "Ayusher me yake damunki" wani takaici ne ya kuma rufeta wato ma baisan me ya mata ba kuma rushewa tayi da kuka, janyota yayi jikinta yana bubbuga bayanta ya fara lallashin har ta tsagaita da kukan sannan yace, "Me yake damunki Ayusher ji yadda kika rame ko abinci bakya ci" Indo goge hawayenta tayi ta ce, "Ya Jamil meyasa yanzu baka sona baka kula dani ka tsaneni wai har wata ta fini a gurinka, baka farantamin sai dai waccen dan Allah ya Jamil meyasa ka koma haka?" ta ƙarasa faɗa tana hawaye wani farinciki ne ya lulluɓe Jamilu yace, "Naga bakya sona Ayusher shiyasa na samo wata" janye jikinta tayi daga jikinsa ta ce, "Ka rabu dani to sai ka zauna ita" janyota yayi jikinsa yace, "Ai nida ke mutu ka raba, duk wacce zata zo ma a bayanki take" Indo bata tanka masa ba ta cigaba da ruwan hawaye ganin yadda hankalinta ya tashi yasa Jamilu ya warware mata duk plan ɗin da suka haɗa shi da Malam Isa, kunya ce ta kamata Jamilu ya dinga mata dariya. Da wata irin murya yace, "Ayusher har yanzu baki bani amsar tambayata ba" wata kunyarsa ce ta kamata ta tura kanta cikin jikinsa tana murmushi, ɗago da fuskarta yayi yana ɗaga mata gira sannan ya furta. "Ina ƙaunarki Ayusher kuma bazan daina ƙaunarki ba" runtse ido tayi tana ƙasa da murya tace, "I LOVE U YA JAMIL!" waro ido waje Jamil yayi yana mamakin jin kalamanta ganin haka yasa ta janyo bargo ta rufe fuskata, dariya Jamilu yake ta farinciki sosai jin sa yake kamar wani sabon mutum, janyota yayi jikinta yana ƙara zubar mata da kalaman soyayya, nan take hirar ta fara sauya salo cikin salon faranta zuƙatan masoya wanda da alama a wannan lokacin Jamil zai tabbata cikakken angonsa. Bayan wani lokaci Jamilu ne ya janyo bargo ya rufawa Indo tare manna mata kiss a goshi, a hankali yace, "Allah yayi miki albarka Ayusher" kunyarsa taji ta rufe fuska ta ce, "Ameen ya rabbi" tashi yayi yaje ya haɗa musu ruwa sai da yayi wanka sannan ya dawo ya taimaka mata ya rakata ƙofar toilet ta shiga, zai biyota da sauri ta banke ƙofar shida ita suka sa dariya lokaci ɗaya. Da asuba Jamilu ne ya fara tashi ya fara tashin Indo yaji jikinta da ɗumi kamar me zazzaɓi, da ƙyar ta tashi bayan ya idar da alwala tashiga ta gabatar da tata alwalar ta koma dadduma ta gabatar da sallar asuba, bayan ta idar kafin su koma bacci sai da tasha paracetamol sannan suka koma bacci yayi awon gaba dasu. Da safe Jamilu ne ya haɗa musu komai na breakfast bakin Jamilu yaƙi rufuwa sai wani nan yake da indo, ita kuwa dama yaya lafiyar kura sai zuba iya shegenta take san ranta. Jamilu sabon hutu ya ɗauka agurin aiki sai da yayi sati biyu a gida ana shan amarci sannan ya koma badan san ranshi ba, Indo har wata ƴar ƙiba tayi ta kwanciyar hankali cikin ƴan kwanakin Jamilu ya ƙara mantar da ita duk wasu abubuwa da suke damunta, haka itama ta rungumi mijinta da farko ne take jin kunyarsa musamman da ta ga wasu zafafan baƙin abubuwa da yake mata, a ranta har take mamakin ashe shima ɗan gari ne amma a haka idan ka ganshi zaka ɗauka da zaka sa hannuka a bakinsa bazai tauna ba a fannin soyayya, ashe abun ba haka bane. Yaseer da Lubna sun ƙara haɗa kansu har iyaye sun shiga maganarsu, haka shima Fahad Mommy nayi masa magana ba'a ɗau lokaci ba ya samu Fahima da maganar dama kuma ko Mommy batayi masa magana ba, yana da niyyar tunkararta ya sanar mata da saƙon dake cikin zuciyarsa dan yayi sake a baya baiji da daɗi ba. Gabaɗaya lokaci ɗaya aka tsayar da ranar biki akan wata bakwai saboda wani course da Fahima zatayi, da wata huɗu akayi niyyar sawa wannan dalilin yasa aka kaishi watanni bakwai. BAYAN WATA BIYU Indo ce ke fama da ciwon ƙirji komai taci sai zafin ƙirji da yake damunta, tun ciwon baya damunta har ya kai ko abinci zata ci ta dinga fargaba. Wannan dalilin yasa Jamilu ya ɗauketa zuwa asibiti saboda zarginta yake da samun tagomashin alheri, suna zuwa gwajin farko aka tabbatar da Indo na ɗauke da ciki na sati bakwai, murna gurin Jamilu bakinsa har baya rufuwa ita kuwa gani take kamar ba haka ba, suna kan hanya zasu wuce gidan Baba Huwaila ta kalleshi tace, "Ya Jamil wai cikin haihuwa irin mutane nake dashi" dariya yayi saboda har gobe idan sakarcinta ya motsa sai ta nuna hali, kallanta yayi ya ce, "In tambayeki mana" ta ce "Ina jinka" ya ce, "Mijinki irin na mutane ne ko babyn roba" ta gane sarai inda maganarsa ta dosa dukan wasa ta kai masa ta ce, "To gani nan dai dan gani nake kamar baida wani ƙwazo" da sauri ya taka birki ya ce," Mun fasa zuwa gidan Baba Huwaila muje gida na nuna miki ƙwazon nawa" dariya ta kwashe dashi ta ce, "A'a wallahi da wasa nake" a haka suka ƙarasa suna hira har suka je gidan. Suna zuwa Indo ta ɗafe Baba Huwaila da sauri Jamilu ya ce, "Keeeee wai meyake damunki ne? Bakisan yanayin da kike ciki yanzu ba?" shewa Baba Huwaila tayi ta ce, "Ahayye! Allah na gode maka Jamilu wai yau kai ne baka san motsin Indo, duniya yayi ke muje ciki karya isheni da kitifi sai kace akan matarka aka fara samun ciki" Indo turo baki gaba tayi ta ce, "Ni ce miki nayi ciki gareni" kiran wayar Jamilu akayi yana ɗauka da sallama Malam Isa yace, "Malam Jamilu lafiya yau baka shigo makaranta ba" Jamilu yace, "Wallahi Madam ce ba lafiya na kaita asibiti" Malam Isa yace, "Ayya Allah bata lafiya amma fa da alama shawarata tayi aiki to idan Allah ya raba lafiya ayi mun takwara" Jamilu dariya yayi yace, "Shegen kaya baka da dama sai Allah ya kaimu gobe idan na shigo" daga haka sukayi sallama. Wata kulawa ta musamman Indo take samu agurin Jamilu, Baba Huwaila tunda ta fahimci Indo nada ciki farinciki ya kamata bakinta har kunne a haka har cikinta yakai wata takwas shida, wanda hakan ne yayi dai-dai da lokacin bikin Yaseer dan anƙara na Fahad da wata biyu saboda karatun Fahima. Da farko Jamilu yaso hanata zuwa amma Baba Huwaila ta nuna sam bazai yuwu ba, saboda tunda aka kawo Indo bataje gida ba sai dai iyayenta su kawo mata ziyar, badan ya so ba haka ya sai musu ticket ɗin jirgi suka wuce garin Abuja acewarsa bazai iya barinta ta tafi ita kaɗai ba, tafiyar ma basu tafi ba sai ranar da za'a yi kamun amarya da Ango. Lokacin da suka je kowa kallon Indo yake yadda suka ga tayi ƙiba tayi kyau cikin jikinta ya fito sosai, Lokacin da suka haɗu da Yaseer gaisawa sukayi kamar wani abu bai taɓa shiga tsakaninsu ba, haka Jamilu dasu Fahad faram-faram suka gaisa suka shiga hada-hadar biki, kwanasu uku suka tarkato suka dawo garin Kano. BAYAN WASU WATANNI Cikin ikon Allah, Allah ya sauki Indo lafiya ta haifo Ɗanta namiji mai kama da Jamlu sak sai dai hasken farta da ya ɗauko, wani ikon Allah sai ga gefen kansa ɗauke da tambari irin na kan Indo. Murna gurin ƴan uwa da Abokan arziƙi baya musaltuwa daga asibiti gurin Baba Huwaila aka wuce da ita, dan tace babu inda Indo zata agurunta zata zauna, hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa iyayen indo ba. Ranar suna jariri yaci sunan marigayi mahaifin Jamilu wato, Muhammad suna kiranshi da Abulkhairi anyi taro gwanin birgewa daga cikin waɗanda suka zo suna harda Maigari dasu Zulai, a lokacin Zulai ƴaƴanta biyar Saude kuma ƴaƴanta uku biyu sun rasu, anci ansha a taron sunan daga nan kowa ya kama gabansa. Kafin Indo tayi arba'in aka fara bikin Fahad da Fahima ranar da aka ɗaura auren Fahad Indo sukayi arba'a a washegarin ranar Indo ta wuce garin Kaduna gurin iyayenta yawon arba'in. BAYAN SHEKARA BIYAR Indo ce laɓe a jikin labule ta ga wucewar Jamilu cikin toilet, da sauri ta fito tana dariya ƙasa-ƙasa dan tasan muguntar data shirya masa mukulli tasa ta rufe ƙofar, Jamilu na shiga banɗaki bayan ya cire kayansa har ya fara saɓa sabulu yaji wani kuka daga sama, ɗaga kan da zai yi sama ya hango macizai biyu a saitin kansa, wata uwar ƙara ya ƙwalla ya fara fusgar ƙofa dan ya buɗe amma ya kasa ga macizan sai zaro harshe suke, dariya Indo take harda riƙe ciki sai da tayi mai isarta sannan ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar ta koma kan gado da gudu ta zauna. Da sauri taje ya buɗe ƙofar ya fito fuskarsa duk kumfa wannan karan Indo dariya take harda hawaye, yana murje ido yace, " Hala ke kika ƙullamun?" cikin dariya ta ce, "Wallahi ramawa nayi ka tuna abinda kuka mun rannan kaida su Abulkair, Lah kalleka fa yadda ka fito namiji da kai wai kake tsoron macizai" girgiza kai yayi ya juya yace, "Allah ya shiryeki Sarƙa haihuwa biyu amma har yanzu halinki na nan" yana shiga ya fisgo macizan robar ya watso waje. Indo kwasarsu tayi ta tafi falo acen ta samu Hanan ƴar shekara ɗaya da Abulkairi mai shekara biyar suna wasa, ta zube musu kayan wasansu. Rayuwa mai daɗi aka cigaba da gudanarwa a gidan Indo da Jamilu haka gidajen su Yaseer, matar Fahad ta haifi Ƴa mace me sunan Momma ana ce mata Ilham matar Yaseer kuma namiji ta haifa aka sa sunan Dadddyn Lubna suke kiransa da Aslam, haka suka cigaba da rayuwa gwanin sha'awa. TAMMAT BIHAMDULILLAH🥰 ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN INDO SARƘA DARASIN DAKE CIKI ALLAH YA BAMU IKON ƊAUKA, KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA BAKIƊAYA.👏🏻👏🏻👏🏻 INA MATUƘAR GODIYA GAREKU MASOYA BISA YADDA KUKA JURE BIBIYAR LITTAFIN NAN NA TSAWON WATANNI BABU ABINDA ZANCE MUKU SAI ALLAH YA BAR ƘAUNA, WATTPAD, WHATSAPP DA FACEBOOK INA MATUƘAR GODIYA FANS NAJI DAƊI SOSAI YADDA KUKA JURE ASHA RUWAN TSUNTSUYE NA, NA YAU DA UPDATE GOBE BABU🤣🤣🤣 MUTANENA NA WATTAPAD MUSAMMAN MASU CEWA" UPDATE SOOOOOOON PLS SIS" IYA WUYA ANA TARE ZANYI MISSING ƊINKU WALLAHI😥😥😥 SAI NA WHATSAPP MASU CIJIYAR "YAU BA SARƘA NE SIS AMEERA INA KIKA SHIGA🗣️" KU DAMA ANA TARE KO BA SARƘA🥰🥰 *FATAN ALKAIRI GA ƘUNGIYATA TA FIRST CLASS WRITER'S☀️*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 AKWAI MARUBUTU DA DAMA DA SUKA BANI GUDUNMAWA BA LOKACI BAZAI BARI NA LISSAFAKU AMMA KUMUN AFUWA, KUNSAN YANAYIN TYPING SAI A HNKL AMMA ZAN MIƘA SAKON GODIYA GA *MARYAM MUHAMMAD SANI (MUM AMNASH)* ALKAIRIN ALLAH YA JE MIKI HAR GADON BARCINKI😘😘😘 KU TARA DANI A SABON LITTAFINA NA JARIRINA👹 LABARI ME TAFE DA BARKWANCI HAƊE DA BANTSORO FREE NE SAI COMMENTS KAWAI NAKE BUƘATA, ZAI FARA ZUWAR MUKU 15/10/2021. SAI LITTAFINA NA *ANYA BAIWA CE* SHIKUMA 200 NE GAME BUƘATA. GABAƊAYA GA ƊANƊANONSU NAN 👇🏻👇🏻 [26/09, 00:43] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *ANYA BAIWA CE?* Na *AMEERA ADAM* _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ FREE PAGE 1 Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce. "Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare" Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, " Tauraruwa mai wutsiya..., Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? " Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, " Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na " ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta. "Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke " ya faɗa cikin son jin labarin. Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, " Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho " Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, " Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa " ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu. Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, " Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya" Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, " Domin rana ɗaya ba'a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba " zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, " Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki " ya faɗa yana yin gaba abinsa. Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, " Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce " kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, " Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba'a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi " yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron. Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, " Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe " tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa. Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, " Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba... " murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, " Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke?? " russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, " Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama, amma dukda haka ba za'a rasa abinyi ba dan ba'a rasa nono a riga, ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ranki shi daɗe " Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, " Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye, Me yake faruwa ne?" Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, " Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu, kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari..." cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, " Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? " Jakadiya ta bata amsa da, " A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk..." Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, " Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, tabbatas dole labari ya ƙara maimaita kansa, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha'i " Jakadiya najin haka ta kuma rissinawa ta ce, " ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci " Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba. Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take, abun duniya gabaɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta. A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya, " Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha " Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, " Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin. " Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka?? " Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce, " Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne?? " cigaba da tankaɗenta tayi ta bawa Jakadiya amsa, " Ni na isa nace banten Sarki yayi ɓurtu, ai hanyar lafiya abita da shekara, meye labari?? Dan nasan bakin ki baya rasa motsi?? " Murmushi Jakadiya tayi ta ce, " Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani, kuma abokin cin mushe ba'a ɓoye masa wuƙa, wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na ɗauke da juna biyu?? Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi " ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya. Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ƙofa tayi sannan ta cewa Jakadiya, " Da gaske kike wannan maganar?? aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata daɗi ba, kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya" Jakadiya ƙara matse bakin zanin ta tayi ta ce, " Ai a bakin wawa akanji magana, wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere, kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba, bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar " Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji daɗin maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani, " Tafasar tukunya bata gefe ɗaya bace, haka nan abinda baki ya ƙulla hannu bashi iya kunce shi, idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haƙiƙa ya taka dutse, Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito kuma ni nan da kika gani na iya taku na" Miƙewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ƙofa sannan ta juyo ta ce, " Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama baƙi, bakinki dai ƙanin ƙafarki kuma harshenki linzaminki " bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan. _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [26/09, 01:58] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *ANYA BAIWA CE?* Na *AMEERA ADAM* _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ FREE PAGE 2 Da daddare Bayan sallar Isha'i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga ta russuna tana cewa, " Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan " Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, " Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare na nemi mafita ba " Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, " Duk abinda kika ce haka za'ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne " Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye. Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba'a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin. Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, " Marduska! Marduska!! Marduska!!! " tana gama faɗa ta buɗe idanunta. Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, " Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki. Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya. Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana, " Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu " Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, " A gafarceni sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza'a sake ba " " Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan " ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani. Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Murduska, " Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba " Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, " Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya " A zabure Fulani Maryama ta ce, " Ban fahimce ka ba Marduska " Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, " Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne mahaifinsa ba Aminullah ba " Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, " Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? " Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa. A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, " Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho " Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, " Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi? " Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafinsa ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala. Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, " Tabbas cikin biyun za'a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar, amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za'a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma" Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, " Bangane mai kake nufi ba? " mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, " Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya..., kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago " Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, " Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi..., Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa " " Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce " Fulani Maryama ta faɗa. Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, " Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za'a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za'a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa " Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, " Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye, akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru " _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 [26/09, 02:13] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *ANYA BAIWA CE?* Na *AMEERA ADAM* _LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._ FREE PAGE 3 Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba." Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, " To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? " " Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba " Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, " Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? " Marduska ya cigaba da cewa, " Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amar dake bibiyar jinin zuri'ar sarki Aminullahi " Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, " Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? " Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, " Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta " Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, " Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara " Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, " Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya..." Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, " Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita..." katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, " Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki " sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, " Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka " Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, " Akwai wasu ɓoyayun al'amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi, ƙarɓi wannan " Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani. " Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri " Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, " Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. " Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, " Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba " Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, " Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne " Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, " Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira " Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, " Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. " " Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani " Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata. Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, " Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu " yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin. Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, " Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba " rissunawa Jakadiya tayi ta ce, " Ina ankare ya shugaba ta " _UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉 👹JARIRINA👹 LABARI DA RUBUTAWA AMEERA ADAM ☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️ *{Home of qualities and trusted writer's of The nation}* https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP GARGAƊI BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA. 1&2 Fuskar Halifa ɗauke da damuwa yace, "Inno gaskiya zuwa gidan Nusaiba da matsala saboda ko kaɗan banasan tayi nesa dani, na shaƙu da matata banasan ko nan da cen taje" Inno ido ta zura masa tana ganin rashin kunyar ƴaƴan zamani ido biyu, kafin tayi magana Goggo ta karɓe zancen da, "Kaji mun yaro da sabuwar salawaitun fitsara ido biyu, mu zaku gwadawa fitsara da rashin kunya? Munga tantabaru ma wajen soyayya yaran yanzu da komai sai sun nuna rashin kunya a ciki" Inno ta ce, "A'a barshi Hansai ya nuna mana ya kusa haɗa kafaɗa da mu, tunda ya kusa ajje ɗa kinga mun haihu shima ya haihu ai mun zama ɗaya da shi, fitsararre mai idanun marasa ɗa'a dubi yadda yake fiƙi-fiƙi saboda ɗiban albarka" Nusaiba da ke gefe ta zumɓuri baki gaba ta ce, "Ni dai gaskiya Inno ku ƙyaleni anan inyaso wani a cikinku yazo ya zauna mun" Nusaiba na rufe baki Goggo ta ce, "La'ilaha'illallahu Muhammada ɗan Abdullahi, Inno kinji ɗibar albarka da yarinyar nan zatayi mana irin ta yaran zamani, kinji Nusaiba ta zaɓi miji akan gidan ubanta, ke dan Ubanki ni zaki nunawa rashin kunya ido biyu, idan ban kwashe miki albarka ba kice bani bace?" Halifa ya ce, "Goggo abun fa bai kai haka ba, saboda Allah zuwa gidan nan yayin haihuwa ba fa dole bane ku barmun matata a gida mana, ina jin ɗumunsu ita da abinda zata haifa amma kunzo sai kwashe mana albarka kuke, a haka zan barta taje wankan gida kuna kwashe mana albarka." Wannan karan Inno ce ta kuma rafka salati ta ce, "Tir da wannan halin naka na rashin ɗa'a amma dai Halifa na kwashe maka albarka, wato jarabar taka ido biyu har agabanmu dan rashin ɗa'a? Wato mu bar maka yarinya inyaso ko arba'in bazatayi ba ka nuna rashin ɗa'a mujita da wani cikin ko?" Halifa hannu biyu yasa ya rafka tagumi saboda tsofaffun ba ƙaramin caja masa kai suke yi ba, cikin damuwa ya ce, "Inno wai dan Allah me yasa kunfiya matsala ne?' Inno daƙuwa ta watsa masa ta ce, "Ubanka Salisu shine me matsala" tashi yayi ya fice daga falon dan yasan indai ya cigaba da biye musu to tabbas zasu hau sama da su. Nusaiba da sauri ta tashi tabi bayan mijinta bisa tsautsayi ta harɗe ta faɗi, nan take ta fara naƙuda ba shiri suka fara ƙwala masa kira, hankali a tashe ya dawo suka kamata suka sakata a mota suka wuce asibiti. Zuwan su asibiti da awa guda Allah ya sauki Nusaiba lafiya ta haifo ɗanta namiji kyakkyawa da shi, Nurse ɗin data karɓi haihuwarce ta fara goge jaririn amma wani abu daya ɗaure mata kai, yadda jaririn ya ƙura mata idanu ba kiftawa har hannu tasa ta rufe masa ido amma ƙir idanunsa a kanta. A haka ta samu ta gama gyarashi da gurin aka sa masa kaya Nusaiba ta rungume abinta suka koma bacci, kafin wani lokaci tuni ƴan uwa sun cika asibitin kowa xai zo hannunsa ɗauke da kullar abinci yake shigowa, gudun hayaniyarsu yasa nurses suka hanasu shiga ɗakin da Nusaiba take saboda karsu hanata bacci. Bayan wani lokaci, Nusaiba ce ta tashi gabaɗaya yunwa takeji cikinta kamar anmata yasa, batasan da kawo abincin da akayi tana bacci ba dan haka ta ƙwalawa Nurse kira, tana zuwa tace ta kira mata su Inno da sauri ta fita ta sanar musu da saƙon Nusaiba, su Inno tare da sauron ƴan uwa ne suka shigo ɗakin fuskarsu ɗauke da farinciki, wasu daga ciki ne suka ɗau jaririn, Nusaiba a shagwaɓe ta ce, "Inno yunwa fa nake ji ku haɗa mun ruwan tea" Inno ita goggo da ƙarfinsu suka nufi wajen kullar amma tunkafin su buɗe sukaci karo da tsottsatssen ƙashi da wanda aka taune, suna buɗe ƙatuwar kular abinci yace ɗaukeni inda kuka ajiye. Ledar ƙaton buredin ma cen ƙarƙashin gado suka hangota, da alama anciye biredin iskar fanka ce ta tura shi cen ƙasan gadon, mamaki ne ya kamasu amma babu wanda ya magantu a cikinsu, Inno ce ta ɗakko flask ɗin shayi shima ta jishi shafal ba komai a ciki, a hassale ta fara magana. "Yau naga rashin ɗa'a ido biyu, ni za'a gwadawa ɗiban albarka. Waye ya cinye abincin da shayin gurin nan?" Goggo ta ce, "Gane mun hanya yarinya ta haihu madadin taci ta ƙoshi wasu sun cinye" Da mamaki Mahaifiyar Nusaiba ta ce, "Inno duka abincin aka cinye? To Nusaiba ko kinci abinci ɗazu?" Nusaiba ta girgiza kai, Inno ta ce, "Banda rashin ɗa'a Nusaiba duk cinta ai bazata iya cinye cooler uku ta abinci ba, maza kiramun masu fararen kayan cen gabaɗaya sai na kwashe musu albarka, yara sai rashin ɗa'a da ɗiban albarka." Mami mahaifiya Nusaiba ta nufi mazaunin Nurses ɗin ta kira suka taho tare dan su a tunaninsu wani abun ne ya samu Nusaiba, suna zuwa Inno ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta ce, "Ina kuka kai abincin gurin nan saboda ɗiban albarka yarinyar nan ko loma ɗaya batayi ba, idan sha'awa ya baku basai ku tambaya a baku ba amma zaku nuna mana halin rashin ɗa'a?" kallan juna suka farayi kamar haɗin baki suka ce, "Wane irin abinci ana zaune ƙalau kamar wasu mayunwata" Goggo kulolin ta janyo tana cewa, "Gasu naga ɗazu ke kika taya ni shigo da wata" ɗan zaro Ido sukayi suka ce, "Duka abincin cikin kular aka cinye" Inno ta ce, "Kiji mun shakiyyan yara marasa ɗa'a tambayarmu ma kuke yi, wallahi ko ku fito dashi ko na ɗebe muku albarka" Ɗayar nurse ɗin ce ta ɗan fara ɗaukan zafi ta ce, "Iya wai me kuka ɗauke mu ne saboda kuma muna ma'aikatan jinya duk wata ƙura aka ɗebo sai a watsa mana..." Inna a hassale ta katseta. "Amma kedai wannan yarinyar anyi maras ɗa'a wallahi idan baki rufen baki ba zan kwashe miki albarka" ganin abun na nema zama faɗa Mami ta sasanta tare da yin waya gida akan a ƙara kawo musu wani abincin. A yammacin ranar aka sallami Nusaiba ita da Jaririnta, tun a asibiti ake taƙaddama akan zaman Nusaiba a gidan ita Mami ma shiru tayi saboda yadda su Goggo suka ja'ina da Halifa amma fir yaƙi yarda. A hassale Goggo ta ce, "Rakiya wai dole sai mun bi ta yaron nan ne? Shi da ita duk jikokinmu ne me zamu zauna muna bi ta tasu, ni idan ya bari idanma bai bari ba zan ɗauke ta na wuce gurina da ita." Inno sheƙeƙe ta ce, "Hansai au ke zaki tafi da Nusaiba? Wallahi bazan yarda da wannan ɗiban albarkar ba nice na haifi Uban Nusaiba nafiki iko da ita" Goggo ta ce, "Rakiya wallahi baki isa ba nina haifi uwarta kuma ance uwa mafi uba koda uban sarki ne" Inna ta ce, "Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji, wallahi baki isa kizo mun da wannan rashin ɗa'ar ba, ninan gurina zan wuce da ita." Halifa ne ya shigo yaji yadda suka fara hawa sama a tsakaninsu dukda sun kasance ƴan uwa kuma aminan juna, Halifa ya fahimci sarai inda maganarsu ta dosa yace,"Nifa gaskiya babu wanda zai ɗaukarmun mata wai magana ɗaya ayita yinta har a asibiti ina dalili" nan da nan sukayo caaa akansa Mami ce ta raba musu gaddama ta ce, "Inno dan Allah kuyi haƙuri ku bar masa matarsa tunda har yace bayasan taje gida wanka, shawara ɗaya zan bayar gabaɗaya kuje ki zauna mata ai ina ga hakan yayi?" gabaɗaya sun aminta da shawarar Mami, Inno ta ce. "Hansai kinga gwara da akayi hakan dan kinsan ni yanzu bana iya aiki a bakin wuta, na dinga kula da aikin cikin gidan kina ɗora garwan wankan, wankan mejego da jaririnta idan ba haka ba kar naxo na aikata rashin ɗa'a" Goggo ta ce, "Eh kuma fa hakane Rakiya kinga zamanmu bibbiyunma zaifi." Da wannan shawarar suka tarkata zuwa gida tare da ƴan uwa da abokan arziki. A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, "Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da daren nan" ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta. A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, "Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani a daren nan" tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta. _OUM ASLMA BINT ADAM_😉