[5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah SWT da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin Allah yasa yadda na fara rubuta wa lafiya in ga ma lafiya Allah yasa ya zama Silar shigar mu Aljanna, Ameen. 𝖄𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖉𝖎𝖓𝖐𝖞 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏&𝟐 Tun daga nesa kake jiyo tashin kiɗa layin da kiɗan ke tashi na bi Gidaje ne na Alfarma jere reras Wani Mansion ne Babba ya tsaru iya tsari daga ciki ki ɗan ke tashi Mutane ne cike da gidan Mata ne kawai suke ta kai kawo, da gani kasan Biki ake yi. Daga can cikin gidan shima mata ne dan kam dan sunfi na ciki yawa ma sai maza ƙalilan da suke fita. Wasu mata ne suke zaune a gefe suna Hira daga zancen wane sai na wani ɗaya daga cikin su ce ta Chanja topic ɗin hirar tasu "Ni har Tausayin yarinyar nan nake ji duk ƴan uwan ta an sunyi Aure, ace har maza ma saura ita kaɗai" Sai wata tace "Hajiya Kenan komai lokaci ne ba gashi nata yazo ba" "Haka ne kuma, ita ma yar uwar ta haka ta da ɗe bata yi ba Amma duk da haka bata kai ta da ɗe wa ba ba" "Ai ita tayi karatu saɓanin su ana gama secondary sukayi Aure, Ga ba shi ya wuce ba yanzu ƴaƴan ta biyu fa, To Allah Ya sa mu dace " "Ameen dai" suka cigaba da zancen wasu. ✫✫✫✫✫ Ƴan mata ne cike a ɗakin wasu na shirya wa wasu na hira ɗaya daga cikin su kwalliyar ta tafi ta kowa kyau a gurin zaune akan gado da waya a hannun ta da alamu kira take yi tsaki ta ja "Wai me akayi Miki ne tun ɗazu kin ishe mu da tsaki, ko kin fasa ne" ta faɗa cikin zolaya Harara ta balla mata "Me zan fasa, Gaskiya da alama har yanzu baki san yadda Zaid yake a wurina ba, Kinga Anisa nake ta kira bata picking rabo na da ita tun ranar Ladies Night ko lafiya, taimaka ki kira min ita" "Ke ma kin san lafiya amma da ba lafiya ba da ti ni ta ishe mutane da waya kin san Rashin lafiyar ta bari in kira" ta ɗau wayar ta ta fara kira. Kallon ta tayi "Kinji nima tana ringing amma bata ɗa ga wa bari in sake trying maybe bata kusa da wayar sake kira tayi, Ta kashe kiran fa da alamu tana gani kenan" wata ce a cikinsu ta fara magana "Ku kuka damu da ita musamman ke zata ɓa ta miki rana shekara nawa ana jiran ta zo sai yanzu da ta zo zata fito da wannan abin, Please ki ƙyale ta kar ki ƙara kiranta ai Kin yi ma da nice tun yaushe zan ƙyale ta" "Ke ko matsala ta dake faɗa baki iya bin abu a sannu ba, ai sai ki tsaya muji uzirin ta Koh" "Ai bata da wani uziri kawai dan taga tana ji da ita ne da yawa, ai ta kira tace ga abinda yasa sai kiran ta kuke ku kuma" Masifa tayi ta yi suka gaji da bata amsa suka yi shiru ✫✫✫✫✫ Tsaya take a backyard Waya take amsa wa da alam abinda ake faɗa mata a ciki ba daɗin shi take ji ba "Me kake cewa? Me kake so faɗa Innalillahi wainnaillaihir rajiun" ta kashe wayar cikin gidan ta koma da sauri Zuwa tayi ta ja ta gefe ra ɗa mata magana tayi a kunne da sauri ta kalle ta ba abinda ya fita a bakin ta sai "Innalillahi wainnaillaihir rajiun" shine abinda take ta maimaita wa..... ✯ Wacece wannan da ta damu da ita haka? ✯ Me bata ɗa ga kiran ta? ✯ Mai aka faɗa mata wanda ya razanar da ita? 𝙺𝚞 𝚍𝚊𝚒 𝚔𝚞 𝚜𝚊𝚗𝚌𝚎 𝚍𝚊𝚗𝚒 𝚍𝚊𝚗 𝚓𝚒𝚗 𝚊𝚖𝚜𝚘𝚜𝚑𝚒𝚗 𝚠𝚊𝚍𝚊𝚗𝚗𝚊𝚗 𝚝𝚊𝚖𝚋𝚊𝚢𝚘𝚢𝚒𝚗 #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯✍️ ᴋᴀᴍᴀʀ ʏᴀᴅᴅᴀ ɴᴀ ғᴀᴅᴀ ᴀ ғᴀʀᴋᴏ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛs ʏᴀᴡᴀɴ ᴛʏᴘɪɴɢ ᴋᴜᴍᴀ ʏᴀᴡᴀɴ ᴘᴏsᴛɪɴɢ ɪɴ ʙᴀ ʜᴀᴋᴀ ʙᴀ ᴋᴜᴊɪ sʜɪʀᴜ😌😌😌. ғʀᴇᴇ ʙᴏᴏᴋ ɴᴇ ᴀᴍᴍᴀ ɪɴ ʙᴀ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛs ᴢᴀɪ ᴢᴀᴍᴀ ᴘᴀɪᴅ🤸 Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2l Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1 Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑&𝟒 Yan ɗaurin Aure ne suka fara dawowa abinda ya faru a gurin ɗaurin Auren aka fara sanar wa ƙananan magana ne suka fara tashi abinda ya fara jan hankalin jama'a kenan. Wasu matasa ne suka shigo ransu a bace ɗaya daga cikin su ne ya fara magana "Ina take" "Ka bari mu shiga ciki mana sai ayi maganar a sirri" "Gwara ayi a nan ɗin, ko an yi sirri sai ta fito ai" Wata mata ce ta fito daga ɗa ki kallon su tayi "Ai sai ku zo mu ku faɗa mana Koh, ku wuce muje ciki" "Haba Aunty" ɗa ga masa hannu tayi "Ya isa, Ku kama hanya Ku shige" duk shige wa suka yi itama bin bayan su tayi. Abin nema ya samu nan aka fara ƴan maganganu mara sa kan gado sai da yan ɗaurin Auren suke ta shigowa anan suka ji cewa an fasa Auren kuma dama wasu sun sanar yadda ne basu yi ba, ba da ita aka ɗaura ba nan aka fara cece ku ce.. ✫✫✫✫✫ Daga ɗa kin Mami kuwa ta haɗa kan duk ƴaƴa maza na gidan "Me ya faru aka fasa ɗaurin Auren" "Ban taɓa tunanin mutumin banza Hooriyah zata kawo ba, Iyayen nasa ma mutanen banza ne wallahi, Mami suna zuwa fa suka yace baya sonta a gaban mu aka ɗaura Auren sa da wata fa" "Babu wani dalili da suka bayar kawai an fasa Aure" "Da farko fa cewa suka yi Basu san da zaman ta ba ga wadda yace zai Aura sai da muka kusa faɗa Sannan" "Kuma Abin baƙin cikin ma wannan yarinyar ya Aura ya take da suna ma" ya juyo yana kallan su alamar su yake tambaya "Yaya Anisa ce ba wata ba" "Anisa? wace Anisa? Wadda na sani?" "Ita fa Anty, wai ita zata yaudari Hooriyah duk yadda suke" "Saboda Anisa ya fasa Aure Hooriyah duk daɗewar da suka yi" "Duk ba wannan ba ya kamata a boye mata kar ta ji wannan zancen kun san halin ta" "Abdul jawwad ka tattara iyalin ka sannan ka haɗa da ita ku tafi gidan ka yanzu" "Mami zancen duniya baya ɓu ya ina tabbatar miki izuwa yanzu ta sani" "Kayi abinda nace kawai, ba lallai ta sani ba, ku kuma ku tashi ku tafi" ✫✫✫✫✫ Daga cikin ɗa ki kuwa amarya na zaune ƙawayen ta sai tsiya suke mata ɗaya daga cikin ƙawayen su ne ta shigo kallan su tayi ta ga sai shewa suke tace "Da alama baku san Abinda yake faruwa ba Koh?" Lokaci ɗaya kallo ya dawo kanta kowa na don jin abinda ke faruwa wata ce tayi magana "Bamu sani ba, me yake faruwa?" Ba tare da tunanin komai ba tace "Ba da ita aka ɗaura Aure ba fa" Ruɗewa suka yi da salati wasu na jajanta abin wata ce ta ƙara magana "Kamar yaya kenan, ke Rukayya dama can kin saba karya kawai zaki ɗa ga mana hankali" "Ok haka ma zaki ce kenan to ki je waje ki je zancen da ake tayi kenan, The most worst part of it ma wai Anisa ya Aura, Kamar Anisa" "Wace Anisa kike nufi?" "Wadda kika sani mana" Amarya ce ta tashi da sauri gurin wadda aka kira da Rukayya tayi "Da gaske an fasa Aure na, ba'a ɗaura ba kika ce" "Da gaske nake wallahi" "Innalillahi wainnaillaihir rajiun Allahumma ajirni fi musibati" shine kawai abinda ta faɗa sai ki kake ta faɗi. ✫✫✫✫✫ Kowa kan Amarya ya rufa ganin ta suma fridge ɗin cikin ɗakin ta buɗe ruwa ta ɗauko tana kokarin buɗe shi ta zuwa mata Rukayya ce tayi ƙarfin halin magana "Mun shiga Uku ta mutu" sai ta fice da gudu. ✫✫✫✫✫ Yawancin mutanen duk suna zaune a na jajanta lamarin sai ganin ta akayi ta fito daga Corridor ɗin ɗakunan da suke "Aunty! Aunty!! kuzo Hooriyah ta mutu" shine abinda take faɗa Aunty ce ta kalle ta a raza ne "ta mutu fa kika ce" da sauri ta shige Corridor ɗakunan buɗe kofar ɗa kin tayi duk sun ru fu a kanta "Da gasken ta mutu kenan" Khalil ne ya shigo ɗakin gurin da take a kwance yayi Aunty ce ta rike masa hannu tana kuka "Karka ce min yayar ku mutu in ta mutu Nima Binta zan yi Khalil" "Aunty kiyi Hakuri bari in duba ta" cika shi tayi duba ta ya fara yi "Tana numfashi amma da alama tayi dogon suma, mu tafi Asibiti kawai zaifi" "Alhamdulillah, Allah mun gode maka" shine abinda suke ta faɗa ɗaukar ta yayi ya fice a mota ya saka ta mazaunin driver ya koma Sadik ne ya zauna a gefen mai zaman baza suka fice Mami Da Aunty da Wasu daga cikin yayan ta suka cika mota biyu suka bi su. ✫✫✫✫✫ ⁎𝔸𝕤𝕚𝕓𝕚𝕥𝕚⁎ An karɓe ta da gaggawa aka shiga da ita ɗa ki neman gurin zama suka yi ana jiran tsammani. Bayan wani lokaci Doctors ne suka fito daga ɗakin daya daga cikin su ce ta yi magana "Ta farfaɗo, tana buƙatar hutu zuwa anjima zaku ganta" "Masha Allah, Allah ya kaimu" Office ɗin Khalil suka nufa dan jiran lokacin da za'a ce su shiga. Bayan awa biyu Nurse ce ta zo tace su zo zasu iya ganin ta gaba ɗayan su ɗakin suka nufa har bakin ɗakin ta kai su sannan ta wuce. ✫✫✫✫✫ Gidan Biki ya koma tamkar gidan mutuwa kowa yana zaune ji gum-ji gum kaɗan daga cikin su ne suke ta kaiwa da kawo wa wasu har sun fara hara mar ta gida tunda abinda ya kawo su an gama ba'a yi ba ga amarya ba lafiya tana asibiti. Wasu kuma sai sanar wa wadanda basu zo ba suke kar su zo anfasa Auren. ✫✫✫✫✫ Tunda ta farfaɗo take kuka Aunty ce take lalla shin ta "Kiyi hakuri Hooriyah haka taki ƙaddarar ta zo ki daina kuka" "Aunty ya za'ayi na daina kuka Kawar wadda na fifita fiye da kowa ita ta Auri Zaid wanda nake so fiye da tsammani kuma ta sani basu duba halin da zan shiga ba, suka yaudare Ni, ina zan daina kuka Aunty" "Wanda yayi hakuri yana cin ri ba, ki ƙarbi ƙaddara kiyi Hakuri Allah zai baki wanda ya fi shi Insha Allah.... #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 ✷Wai wace Wannan Anisa? Me yasa suka shiga ɗimuwa jin ita ya Aura? Ku cigaba da biyaya ta ɗan jin wace Anisa🤸 Please Share & Comments 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓&𝟔 𝕳𝖆𝖗 𝖞𝖆𝖓𝖟𝖚 𝖋𝖆 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖉𝖎𝖓𝖐𝖚 𝖎𝖓 𝖇𝖆 𝖍𝖆𝖐𝖆 𝖇𝖆 𝖎𝖓 𝖙𝖆𝖋𝖎 𝖍𝖚𝖙𝖚🙄😌 𝕯𝖆𝖒𝖆 𝖓𝖆 𝖌𝖆𝖏𝖎 𝖉𝖆 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖉𝖎𝖓🤣🤣🤣 ᴍᴜᴛᴀɴᴇɴ ᴀᴍᴀɴᴀ ᴍᴀsᴜ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛs ᴅᴀ ʀᴇᴀᴄᴛɪɴɢ ᴋᴜ ᴄɪɢᴀʙᴀ ᴅᴀ ɢᴀsʜɪ ɪɴᴀ ᴊɪɴᴅᴀᴅɪɴ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛs ᴅɪɴ ᴋᴜ, ʟᴏᴠᴇ ʏᴏᴜ ʟᴏᴅɪ ʟᴏᴅɪ😍❤️❤️❤️ ᴡᴀɪᴡᴀʏᴇ ღ Alhaji Harith Yahaya Mai kanwa shine cikakken sunan sa, haifaffen garin Kano ne, sunan Mahaifinsa Yahaya Bala mai kanwa ya samo sunan ne tun daga mahaifinsa da yake sana'ar Siyar da kanwa sunan sai ya bi shi. Malam Yahaya yana da mata guda ɗaya Karima da ƴaƴa Uku Namiji ɗaya sai Mata biyu, Safiyya da Bilkisu. Sun jajirce akan yaran su duk da ba wani kuɗi ne dasu ba Sai dai rufin asiri. Harith yayi karatun sa a ABU Zaria. Yayi Aure Yana da mata guda ɗaya amma har yanzu Allah bai basu haihuwa ba yana matuƙar son matar sa Aseeyah. Mace ce mai hakuri shiyasa bata ce musu komai sai dai ta sha kukan ta, takurawar da ƴan uwan sa suke mata da gori ne ya sa ya yanke shawarar ƙara Aure ya Auri wata matar Hafsa. Iyayensu sun daɗe da rasuwa shi yasa suke abinda suka ga dama tunda shi kaɗai ne ɗan uwansu kuma shine Babba. Gaba ɗaya sun yi Aure Safiyya ta na da Ƴaƴa Biyar duk mata sai Bilkisu kuma ƴaƴa biyu Mace da namiji. Hafsa irin matan nan ne da basu da ɗaukar raini basa barin ta kwana in an faɗa musu a lokacin zasu rama tunda ya aure ta ake jiran haihuwa amma shiru kake ji. Hafsa tana girmama Aseeyah tana yi mata biyayya sun haɗe kansu kamar ba kishiyoyi ba suna zaman su lafiya. Yan uwansa sun so fara yi mata abinda suke wa Aseeyah Amma ta taka musu burki tun daga lokacin suka yi tsit Aseeyah ma ta samu sauƙin abin. Fara ta kura masa suka yi ya ƙara Aure tunda waɗannan basa haihuwa amma ya murje idon sa yaƙi karawa tunda ga lokacin sai suka zuba musu ido. Bayan Shekara da Auren sa sai ga Aseeyah da ciki ƴan uwansa sun so goran tawa Hafsa amma sun san hali tsitt kake ji ba wanda yayi magana. Tare da Hafsa aka raini cikin Aseeyah har ya kai lokacin Haihuwa Aseeyah ta haifi ƴan biyu duk maza ranar suna yara suka ci suna Yahaya da Huzaifa. Yahaya ana kiransa Amir, Huzaifa kuma Anwar. Ko yaye su bata yi ba ta kuma sake samun ciki ta haifi namiji Ahmad Shekarar Ahmad biyu Hafsa ta samu ciki bayan ta haihu aka saka masa Abduljawwad. shekaru sun ja Alhaji Harith ya cika da yara ƴaƴan sa goma, Aseeyah tana da shida maza huɗu mata biyu, Hafsa kuma huɗu maza biyu mata biyu. Yahaya da Huzaifa ne manya sai Ahmad sai Abduljawwad bayan shi sai Aseeyah da Hafsa sun ƙara Haihuwa tare tsiran wata biyu ne, Aseeyah ce ta fara haihuwa sai Hafsa, Aseeyah ta haifi A'ishah (Hooriyah) da Saudat. Hafsa kuma ta haifi Hauwa'u. Sai da aka da ɗe sannan Hafsa ta haifi Sadiya da Ibrahim Khalil tsiran su shekara biyu ne. Aseeyah kuma tun daga kan ƴan biyu bata ƙara haihuwa ba sai da suka shekara goma sannan ta haifi Muhammad kuma shine ɗan auta a gidan. Suna cewa Aseeyah Mami ita kuma Hafsa Aunty. ✫✫✫✫✫ Hooriyah ta tashi ne a hannun Aunty duk wani gatan duniya ta bata ta fifita akan ƴaƴan ta ko laifi tayi in dai tana gaban Aunty ta tsira. Zaman su suke lafiya ƙalau ba lallai ka gane wannan ɗan wannan bane sun basu tarbiyya tare sun kula da su. Hooriyah Yarinya ce mai son jama'a kowa nata ne bata da abokin faɗa, duk anyi wa ƴan uwanta Aure yanzu daga ita sai Muhammad auta ne suka rage a gidan. Tayi karatun ta tun daga nursery har secondary a Nigerian Turkish, Yanzu tana karatu a B.U.K tana Level Four, Final Year ɗin ta. 𝐁.𝐔.𝐊 𝐔𝐧𝐢𝐯𝐞𝐫𝐬𝐢𝐭𝐲, 𝐊𝐚𝐧𝐨. A 360 ta shigo cikin makarantar har tana neman bi ge wani parking tayi tarkacenta ta tattara ta fito tana duba waya kira ta shiga yi "Kun ƙara so, ya shigo" banji answer da aka bata ba sai tace "Ok Gani nan Nima" ta kashe wayar da sauri ta ƙara sa cikin class ɗin ta tarar ba kowa sai students wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hamdala ta shige ciki. ✫✫✫✫✫ Theater Cike take ɗan kam da dalibai kowa ya nutsu baka jin komai sai wata zazzaƙar murya tana bayani daga jin Muryar kasan mamamlakin ta ya haɗu. Kyakkyawan Saurayi ne a tsaye*" wata Matashiya ce ta shigo ajin a saurin ta "How dare you Zaki Shigo min aji bayan kin san you are late, Out of My Class" idon ta ne ya ciko da kwalla da sauri ta juya ta fice. Lecture ɗin sa ya cigaba kamar ba abinda ya faru.. 𝑌𝑎𝑛 mata biyu ne zaune a cikin theater kowa ya fita su kaɗai ne suke hira "Ni fa banji daɗin abinda yayi wa wannan yarinyar da safe ba, abin yana damu na tun ɗazu" "Ita ma da tasan hali me ya Kaita shigowa, ba gashi yayi Disgracing ɗin ta a banza ba" "Ta so muje ko zamu ganta" "Me zamuyi mata" "Koya mata lecture ɗin yau mana, baki ga inda tayi abin tausayi ba wallahi" "Ai sai kije kiyi ta yi, Ni ba inda zaki saboda neman suna Koh" "Ni sani tunda ba zaki ba" ta tashi ta fice "Ai sai kiyi ta yi, ko ina sai an sanki mtwsssss" ta faɗa bayan taga ta fi ce ✫✫✫✫✫ Zaune ta ke a bayan theater fuskar ta tayi wani iri alamu kuka ta sha taɓa ta akayi da sauri da juyo dan ganin waye ganin bata san ta ba sai ta juya "Hope ba abinda ya ke damun ki" ta faɗa gyaɗa mata kai tayi guri ta nema ta zauna kusa da ita "I'm A'ishah Hooriyah and you" "I'm Anisah" "Wow! nice name, me yasa kika shiga bayan kin san kin makara" "i thought bai zo ba" "Can we be friends?" ɗago wa ta yi ta kalle ta "Karki damu in baki so shikenan, Amma dan Allah ki bani Chance na koya miki lecture ɗin yau karki ce a'a please" "Mai yasa sai Ni zaki koya wa?" "Kece bakya nan aka yi, kuma bana so kiyi missing" ɗauko handout ɗin tayi nan ta fara koya mata. Nan da nan Anisah ta gane cigaba da jan ta da hira tayi har sukayi exchanging Contacts. Da suka gama lectures ɗin ranar tace tazo ta rage mata hanya amma taki nan suka yi sallama ta tafi. #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages😍🤍 Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1 Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟕&𝟖 𝖄𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖋𝖆𝖆 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ Anisa Rabi'u Sada shine cikakken sunan ta haifafiyar garin Katsina suna zaune a Funtua, Mahaifiyar ta ƴar garin Kano ce, ta haɗu da mahaifin Anisah a Kasuwa lokacin da take gurin Babanta, yaron ɗan Abokin baban ta ne, basu daɗe da haɗuwa ba akayi musu Aure. ya tafi da ita Katsina, Allah ya albarka ce su da samun ƴa suka saka mata suna Anisa. Watan Anisa goma Allah Yayi wa mahaifin ta ras Sun dawo garin Kano ne bayan Rasuwar Mahaifin da shekara ɗaya suna zaune a Mandawari, anan tayi primary da secondary ɗin ta jefi-jefi tana zuwa Katsina gurin dangin Babanta. Tunda mamanta ta ɗauke ta suka dawo Kano da zama suka tsane ta sun cire ta daga sahun ƴaƴan su tunda abinda ya haɗa ya raba, ko taje sai su ringa nuna basu santa ba, ba sosai take zuwa wajen su ba, kuma suma basa zuwa. *Kun san dai yadda abin yake in ka rasa iyaye, ƴan uwa please mu gyara in Allah ya karɓi wani daga cikin ku please ku rin ga jan ƴaƴan su a jiki a daina watsar da su kamar ba'a san su ba. Allah yasa mu dace yasa muyi kyakkyawar ƙarshe. Ameen* Anisa yarinya ce mai ha zaƙa bayan sun gama secondary ta fitar da ran cigaba da Karatu basu da shi, ƙawar tace ta sanar mata ana bada scholarship mai zai hana ta nema tunda tana da hazata kuma duk taci exams ɗin ta. Tayi shawara da mahaifiyarta ta amince sai ta nemi scholarship, cikin ikon Allah yasa ta samu ta fara karatun ta a B U K har suka haɗu da ita... ✫✫✫✫✫ Tun daga lokacin Hooriyah da Anisah suka zama ƙawaye bata da wadda ta fita a cikin ƙawayen ta, ko a gidan su an san labarin Anisah amma basu taɓa haɗu wa da ita. matsalar Anisah ta zama tata komai ita take musu tana tausaya musu sosai, ta zama kamar ƴar gidan su kullum ita take maida Anisah gida, duk wata tasa Daddy'n ta kawo musu kayan abinci, in ana yi mata magana abinda take yayi yawa sai tace musu "Allah ne ya haɗa wannan ƙaunar ba mai iya raba ta" "ba kwa jin Tausayin su ne?" ita ce amsar ta kullum a gurin wanda yayi mata magana. Hooriyah ta nace Anisah sai taje gidan su, Anisah ta shirya Weekend da basu da lecture taje, bata yi tunanin kuɗin su Hooriyah ya kai haka ba, raina kanta tayi da Ajin ta, Kamar Hooriyah ta zauna kula ta gaskiya tayi mamaki. Tun da ta koma gida take bawa Maman ta labarin gidan su Hooriyah har sai da ta gaji sannan ta daina bata. Sun cigaba da ƙawancen su har yafi na da dan yanzu ita ma Anisah tana zuwa gidan su sosai. #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1 Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟗&𝟏𝟎 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ Zaune suke a palour cards ne a gaban su suna dubawa "Khalisat ya kamata a fara raba IV's ɗin nan Kinga saura sati biyu kar muzo muji kunya" "Nima tunanin da nake kenan ko gobe mu fara,bari Hooriyah ta ƙara so muji yaushe take da time mu fara fita" "Yanzu sai mun jira zuwan ta, kawai ki ɗauko mota mu tafi gidan su" "Mu bari ta ƙara so kawai, Ni ban fiya son driving ɗin nan ba, amma ita bata jin zuwa ko ina driving baya mata wahala" "Allah ya kawo su lafiya, amma da mun tafi mu tsara da wuri yadda zamu gama da wuri" "Let me call her, in ba su taho ba kawai sai mu tafi" "Hakan ma yafi" Wayarta ta ɗauka ta kiranta ta fara yi a handsfree ta saka ta "Amarya ba kya lefi, ko in kashe ɗan masu gida, ya akayi?" "Kin fiye zolaya, ba abinda akayi, kuna ina" "Gamu a cikin street ɗin ku, mun kusa ƙara so wa" "Ok sai kun ƙara so" ta kashe wayar "Da tini kin samu wahala mun tafi bayan suma ga su nan" "Su ƙara so ɗin dai" duba cards ɗin ta cigaba Sallama suka yi suka shigo neman gurin zama suka yi "Hala dai Mommy bata nan" "Ba kiga gidan kaca-kaca ba, ai kenan kin san bata nan" "Wai harda Amaryar da saura sati biyu Aure amma bata iya gyara gu ba" "Sarauniyar tsafta ai sai ki gyara, Ni ba wannan ba cards ne ya kawo shine nake tunanin ko gobe mu fara rabo" "Zumuɗin me kike saura sati biyu fa, gobe fa muna da lectures sai dai ko jibi" "Me tayi na zumuɗi, kar mu manta da wani a ce bamu da kirki gwanda kowa yazo,Ai da gobe da jibin duk ɗaya Allah ya Kaimu" "Ameen dai" Miƙa musu cards ɗin suka yi suka cigaba da dubawa. Sunyi rabon kati lafiya an gama lafiya har an fara shagalin biki anyi Ladies Night ranar Alhamis juma'a da Rana aka ɗaura Aure da daddare dinner sai Ranar Asabar yini da kai Amarya. ✫✫✫✫ Tafiya ta ke yi tayi kyau cikin less ɗin ta babu kwalliya ko ɗigo a fuskar ta amma tayi kyau sosai buɗe motar ta tayi ta shiga Da sauri Zainab ta riƙe murfin motar "Haba Hooriyah ya zaki tafi ke kaɗai bayan kin san kece best friend ɗin ta ai kamata yayi kina motar amarya" "Kin san bana son harka irin haka Koh?, Abokan Ango su riƙa yi maka kallon raini" "Sai aka ce Miki duk irin su ɗaya kowa da halin sa, dan anyi mana a wani gurin ai ba lallai ayi mana a nan ba, Kin san AndulFatah yana da kirki ai sai muyi wa Abokansa shaidar ma ai na gari ne" "In kina son Abu kin dinga kare shi kenan, in na biku inyi Yaya da mota ta? Wa zai maida Anisah gida? Kin san Mama bata barin ta kaiwa dare" "Ni zan tuƙa motar in zamu dawo sai ki maida ta gida sai ki wuce" "it's okay" fitowa tayi ta mika mata key ɗin motar "Take care, sai mun haɗu, ki kula da Anisah please" "ok karki damu" ta wuce "Mtwsssss sai kace wata yarinya kullum a kula da Anisah, kamar wata jaririya" motar ta kulle ta koma ciki gurin su, idan sun gama sai su tafi. Zaune suke a cikin Mota suna jiran Ango da Abokinsa su tafi "Kinga irin abinda bana so, an zo an shanya mu bacin basu gama shirya wa ba" "kiyi hakuri ayi masa uziri mana kin san mutane ne suka riƙe shi amma da tini mun tafi" "Mene amfanin ake biki ba'a ga Amarya ba, ni in ana biki na da wuri zanje kowa ya zo akan idona" "Ce Miki akayi zasu tafi, Allah dai ya Kaimu lokacin in zaki iya" buɗe motar akayi Ango ne ya shigo da abokin nasa "Me ya farunaga duk kunyi shiru" "Gata nan faɗa takeyi kun daɗe, harda cewa ranar bikin ta kowa a gaban ta zaizo" dariya suka saka gaba ɗayan su "Hooriyah ayi mana afuwa mana, Wannan tsohon tuzurin ne ya ɓata mana lokaci, Ya kamata kaima kayi Auren nan fa" "Kaima yaushe ka fita daga sahun tuzuran, Ni ma dai ina ganin na kusa Auren nan dan na samu matar Aure yau"........✍️ #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1 Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟏&𝟏𝟐 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ "Haba, a ina take" "Gata a kusa dani, amma da alama sai kun taya Ni campaign" "Ba sai mun taya ka campaign ba ma zaka samu shiga Insha Allah" dariya yayi, Ita da yake yi don ita ko ƙala ba tace Ba balle ta ɗago chatting ɗin ta take yi "Allah yasa" Tunda suka je yake liƙe da ita duk inda zata yana bayan ta kamar jela har aka tashi daga bikin. Fito wa suka yi daga ciki Zainab ta kalla "ina key ɗina Kinga anyi Isha'i ya kamata mu koma gida, zan ajiye Anisah a gida" "Ai tare da ke zamu koma, yadda muka zo tare" wani banzan kallo ta watsa masa ɗauke kanta tayi daga gare shi, Zainab ce tayi magana"gashi za'a mai da ke gidan su Khaleesat ɗin ba sai mu haɗu a can ba sai ku tafi" "Ai daga nan zamu rabu, na gaji sosai wallahi" "Mu yanzu yaya zamu yi in kika tafi da motar a me zamu koma" "Da zamu taho ai baki yi wannan bayanin ba, kuzo sai in rage muku hanya sai mu wuce" "Ai ko baki isa ba, ki samu za'a kai ki Sannan kice A'a" juya wa tayi gurin su Khaleesat "Khaleesat kizo ku saka baki ta biku mana, ma haɗu acan sai ta karɓi Motar" "Kin san in ta nace akan abu sai tayi ki bata key ɗin sai mu tafi tare tunda ku biyu ne, Babe ka shiga gaba sai mu zauna da su a baya Koh" "Ya ma fi ai, dan wannan ƴar darun in ta nace sai tayi Abinda take so" suka saka dariya "Ungo Key ɗin ki, Gobe ma Rana ce" ta miƙa mata "Yafi dai, Good Night bazan shigo da wuri ba gobe, Anisah muje koh" "To, Sai da safe" mota suka shiga suka tafi. Maida kallon sa yayi kan Ango "Wallahi Auwal ka kwafsan ban so haka ba gashi sun tafi ko number ta nan karɓa ba" "Haka yafi maka, Kabi komai a sannu mana" "Nabi mu tafi Koh" Mota suka shiga duk suka tafi. Washegari kamar yadda ta faɗa bata zo da wuri ba sai bayan La'asar tazo bayan sun gaisa waje ta fito ta zauna bata daɗe ba sai ga Anisah tazo a kusa da ita ta zauna "Anzo ɗaukar Amarya fa" "Sai sun dawo, ba zuwa zan yi ba daga baya naje" "Haba dai, wai me yasa kike haka ne" "Minti nawa ne a je an dawo" jayayya suka yi tayi daga ƙarshe dai ta haƙura ta tashi ta bita suka fito compound ɗin gidan Duk masu zuwa gidan Amarya sun fito dan Amarya har ta shiga Mota ma Rukayya ce ta ƙara so gurin su"Khaleesat sai neman ki take yi amma dai zaki je Koh" ɗaga mata kai tayi kawai "Amma dai ba'a motar ki zaki ba dan Allah, muje tare mu dawo tare" kallon ta Kawai tayi ta wuce "Yau ciwon ya tashi Kenan, kin dame ta ne Koh" "Eh, da kin zuwa tayi sai da kyar ta tashi" "Allah ya Kyauta, amma in Hooriyah tayi Miki wani abin kamar ki dake ta, muje Koh" Buɗe mota tayi ta shiga kawai ta rufe suma shiga suka yi Basu dade ba suka tafi sun kai Amarya ba jima wa suka taho bayan Ango yazo. Har compound ɗin gidan aka dawo da su buɗe kofar yazo yi taji ta a lock kallon sa tayi "Malam buɗe min mana" "Zaid nake, magana zamu yi ba zata wuce ta ten mins ba" "Nidai Sunana Zaidul Haifaffen Kano Sunan Mahaifina Alhaji Sulaiman Former Senator Muna zaune a Nasarawa GRA Cikin Kano. Abokina ya Bani labarin ki kuma na ƙarbi number ki a Gurin amarya, na ganki kuma ina sonki Kuma Insha Allah Auren ki zan yi ki bani dama, zan kira ki please karki ki ɗagawa" kallon banza ta watsa amsa "Sai ka buɗe min Kofar na fita Koh" "Sorry Queen, sai na kira" ya buɗe mata motar, tsaki taja tayi ficewar ta. "Naga kin daɗe" suka haɗa baki gurin faɗa "ba komai, muje muyi musu sallama mu tafi"ciki suka shiga suka yi musu sallama Mommy sai godiya take musu sunyi wa ƴar ta hallaci sun cika ƙawaye motar ta ta shiga su kuma driver ya ɗauke su suka tafi. A hanya ne take sanar da Anisah Abinda Ya faru tayi murna sosai kuma ta bata shawarwari. Sai da ta kaita gida sannan ta wuce tana shiga a palour ta zube Aunty ce ta fito daga ɗakin ta kallon ta tayi "yaushe kika shigo" "Yanzun nan Wallahi, Aunty ya gida" "Ai na zata sai anjima zaku dawo, Alhamdulillah" "A'a angama biki zaman me zamuyi, bari in shiga ciki na gaji" "Sai kin fito amma ki huta sai ki fito kinji" "Tohm Aunty" ta tashi ta shige ciki. Wanka tayi ta saka kaya sallah tayi sannan ta kwanta.......✍️ Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1 Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟑&𝟏𝟒 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ Tana tashi da safe da kiran sa ta fara cin karo sai ƙorafi yake ta kashe waya jiya Ita dai shiru tayi masa, sunyi waya da amarya sai da sukayi faɗa akan me zata bashi number ta da kyar ta haƙura. Tun daga lokacin kullum shine cikin kiran ta safe, rana, dare wani lokacin ta ɗaga wani lokacin kuma ta share, shi kuma bai taɓa fushi ba ko ya kira bata ɗaga ba zai ƙara kira ne. Anisah kullum tana mata faɗa ta kula shi amma taki. Duk lokacin da suka yi waya da Khaleesat tayi ta nacin ta kula shi yana damun su amma sai ta nuna bata san wa take magana akai ba. ღღღ Zaune take a palour gaba ɗaya hankalin ta yana kan littafin hannun ta exams take da ita gobe tana duba wa, sallama akayi Amsawa tayi ba tare da ta kalli mai sallamar ba "ka wani maƙale daga waje kamar ba gidan ku ba ka shigo mana, ke kuma Har yanzu dai Kina nan da halin ki Koh? baki chanja ba" ɗagowa tayi sai taga Aunty Safiyya ƙanwar mahaifin su "Mama Barka da zuwa, Ashe kece na zata su Hauwa ne Wallahi, ku ƙara so ku zauna" ta tashi "Bari in kawo muku ruwa" "bashi nazo sha ba, ina su Uwar taki" ɗauke kai tayi daga kallon ta, tana jin Haushin zagin iyayensu da take yi in tazo daure wa tayi tace "Sun fita suna" "Dama gurin ki nazo ba gurin su ba, sai ki nemi guri ki zauna ai" dawo wa tayi ta zauna inda ta tashi "Gashi nan yayan ki ne kinsan kuma kin sun rabu da matar sa, gashi nan ku sasanta nan da ƙarshen wata a daura muku Aure tunda kunyi kwantai kinki Auru wa duk ƙannen ki sunyi Aure" a firgice ta kalle ta "Yaya Salisu zan kai wa Daddy a matsayin mijin Aure? waye bai san halin sa ba" "Kince Yaya, Ashe kinsan da alaqa a tsakanin ku sannan kina zancen hali, wane Hali zaki yi zance, ke da zai rufa Miki asiri ya aure ki" "Mama ba Rashin kunya zan Miki ba, Amma gwara na mutu ban yi Aure ba dana Aure dan shaye-shaye mai neman mata ko ke baya girmamawa balle wani" ta ƙarasa faɗa tana zabga masa harara"Mama in Baki da wani abin cewa zan shiga ɗaki inada exam gobe" "Ai ban san kin zama haka ba Hooriyah ina Miki magana kina min rashin kunya, duk halin Hafsa kin kwashe a cikin ki, bari iyayen naki suzo inji kosu suka ɗaure Miki gindin Rashin kunya" tashi tayi ta wucewar ta ɗaki masifarta ta cigaba da yi "Auu tafiya ma kike yi ina miki magana kenan" ɗan nata ne yace "Mama kinga Abinda nake guje miki kenan shi yasa nace kar muzo gashi yarinya ƙarama haihuwar yau tana faɗa Miki magana a banza, ai sai ki tashi mu tafi tunda ta gama faɗa Miki magana" "Ai na gama yi maka komai Dole kace mu tafi, kai in ba Nan gidan nazo nayi jan ido ba ina kake tunanin za'a baka Aure bayan Wannan baƙin hallin naka da kake da shi, ai sai naci mutuncin iyayen nata sannan zata amince babu inda zani ina nan har sai sun dawo" tashi yayi yana magana "Ai sai kiyi ta zama, in sun dawo sai mai da ke gida, Ni na tafi" yayi ficewar sa. Cigaba da zaman jiran su tayi har bayan magariba sannan suka dawo ta kare musu tasss sun sha Masifa har da gori Aunty ta so ramawa amma Mami ta hana ta sai da tayi ta gaji sannan ta tafi. Around 10:00PM Zaune suke a palourn Daddy Aunty ta gama sanar masa abinda ya faru wayar sa ya janyo kira yayi "Kizo yanzu ki sameni a Palour na" shine kawai abinda ya faɗa ya kashe wayar, ba jimawa sai gata nan neman guri tayi kusa da kafar Aunty ta zauna "Daddy Barka da dare, ya aiki" "Alhamdulillah, Kin san abinda kika yi baki kyauta ba Koh, Kanwata ce kinsani" "Nasani Daddy kayi hakuri ba dason raina haka ya faru ba" "Allah ya kiyaye gaba, Zan baki nan da ƙarshen satin nan ki fito da miji kafin ta dawo".......✍️ Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages Arewa Books: https://arewabooks.com/fatimaintisar1 Wattpad: https://wattpad.com/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟓&𝟏𝟔 𝖄𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖋𝖆𝖆 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ A razane ta ɗago ta kalle shi "Daddy" ɗaga mata hannu yayi "ya isa haka bana son jin komai, tashi ki tafi" jiki a sanyaye ta tashi ta tafi. Aunty ce ta fara bashi hakuri "Daddy'n su ba haka ya dace kayi ba, a hankali zaka yi mata" "Hakan ne zaifi, in ta dawo kawai an mata miji kar wata Maganar ta tashi duk da ƙanwata ce" "Allah ya Kyauta" "Ameen" Mami ta ce miƙewa tayi "Bari in tafi, Allah ya tashe mu Lafiya" Ameen suka ce ta fice. Tunda ta koma ɗaki take kuka sai da taci kukanta ta koshi sannan ta tashi Alwala tayi sai tayi sallah a Gurin ta kwanta ba ita ta tashi ba sai asuba. Da safe sunyi waya da Anisah ta sanar mata abinda ya faru da yamma sai gata ta zo ɗaki suka tafi A nan ta ƙara sanar mata da abinda ya faru "Hooriyah zaki bi shawara ta" "Ai saboda haka na kira ki, wallahi kaina ya kulle na rasa yaya zan yi" "Ki amince da Zaid kawai" Wani Kallo ta watsa mata "Waye Zaid" "Ya kike min wani kallo kamar baki san shi ba, Bari in tafi tunda kin fara halin naki" ta tashi da sauri ta riƙo ta "Yi hakuri zauna muyi maganar" zama tayi "ke kika jiyo, indai shawara kike nema wallahi ki amincewa Zaid Kinga mutumin kirki ne abokin Auwal ne" Riƙe baki tayi "Iyyye ashe har kin san shi haka, har kin san yana da hakuri" "Ni fa bana son irin haka, wallahi zan tafi nazo kuma kina wani zance" tashi tayi ta fice, dage kai tayi "Innalillahi, itama zata gudu bata bani shawarar arziki ba" da sauri ta mike ta bi bayan ta a palour ta same ta suna magana da Aunty "Taso mu koma mu gama maganar please" Aunty ce ta kalle ta Sannan tace "Ayi maganar a gaban mu mana" "A'a Aunty sirri ce" tayi dariya "Anisah Meya haɗa ku" "Ba wani abu bane Aunty, bari inje" "Babu inda zaku, ku zauna, Meya haɗa ku" "Wallahi ba abinda ya faru Aunty bari kiji" nan ta sanar mata da zancen Zaid. Sallati Aunty tayi "Amma ban taɓa tunanin baki da hankali ba Hooriyah sai yau, Muda muke neman mafita amma kin san da yaron nan ai da sai ki faɗa masa" "Aunty Ni bana sonsa" "kin ba shi dama ne da har zaki ce bakya son sa, in dai na isa dake daga yau in ya kira ki dinga ɗagawa ki bashi dama, muga abinda Allah zai yi kafin ta dawo" nan ta ringa yi mata faɗa daga ƙarshe har Mami sai da ta kira ta faɗa mata tace sunfi kusa. (Nima dai haka na gani kunfi kusa ba ruwan Mami😂) Tunda ga lokacin ta fara sauraren sa inya kira tana ɗagawa ta saurare sa ya nemi ta bashi da ma yazo ta amince yazo har sun daidai ta. 𝐓𝐰𝐨 𝐌𝐨𝐧𝐭𝐡𝐬 𝐥𝐚𝐭𝐞𝐫 Soyayya suke yi tsaftattciya babu algus a cikin ta yana sonta tana son shi yanzu ita gani take bayan Iyayen ta babu wanda yake da mahimmanci a gurin ta sai shi kusan ko yaushe suna maƙale da juna ta waya indai baizo ba. Maganar ta yi nisa dan har manya sun shiga ana shirin kawo kuɗi. Gidan shiru kamar ba kowa sallama tayi ta shiga ganin babu kowa a palour yasa ta fita part ɗin Daddy tayi shiga tayi a nan ta tarar da su ba sallama ba komai ta hau cewa "Ashe nan kika taho kika bar gida shiru, sai Anzo anyi sata kiyi ta rantsuwa bake bace, ina ita Aseeyar take" "A'a Safiyya Ashe kece a tafe shigo ciki mana, Yaya taje dubiya" "To Naji, sai ki tashi ki bamu guri zanyi magana da ɗan uwana" dafe kai yayi "Wai Dan Allah Safiyya mai yasa ba zaki san Annabi ya gamu ba?, Meyasa kike musu haka ne? Wai ba gaba suke da ke ba Matana ne fa" "Yaya babu mai mutunci a cikin su duk sun bata yara da rashin tarbiyya" Aunty ce ta tashi ta fice "Ai gwara ki fita inyi magana da shi" sai kuma ta rissina. "Yaya Ina wuni, da fatan na sameku lafiya" "Ba gashi kin gani ba, Meya kawo ki" "Yaya maganar Hooriyah da Sulaiman ce ta kawo Ni har yanzu naji shiru baka ce komai ba" "To me zance Miki, bayan diban Albarkar da kika yi, Kuma maganar Sulaiman karki ƙara yi min ita nan da sati biyu zan karɓi kuɗin Auren Hooriyah, ina fatan shikenan sai ki tafi" ya faɗa a fusace.........✍️ Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages Arewa Books: fatimaintisar1 Wattpad: fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟓&𝟏𝟔 𝖄𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖈𝖔𝖒𝖒𝖊𝖓𝖙𝖘 𝖞𝖆𝖜𝖆𝖓 𝖙𝖞𝖕𝖎𝖓𝖌 𝖋𝖆𝖆 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ "Yaya maimake nufi in bar maka gida, saboda nazo ina son Sulaiman ya auri Hooriyah dan zumunci mu ya ƙaru amma kake korata, ai shikenan" ta tashi hawaye shaɓe shaɓe a fuskar ta, jin bai ƙara cewa komai ba yasa ta fice. Kara dafe kan yayi ya gaji da matsalar ƙannen nan nasa sun girma amma basu san sun girma ba kullum sune da matsala gwara ayi auren yarinyar nan kowa ya huta in sunga ba kowa ai sa haƙura cigaba da saƙawa da warwara yayi tayi. Bayan sati biyu an kawo kuɗin Auren Hooriyah tare da saka rana nan da ten weeks kowa sai murna yake. ☆(❁‿❁)☆ Kwance take tana hutawa basu daɗe da dawowa daga gidan Khaleesat ba shirin biki suke tayi har sun fitar da Anko kira ne ya shigo dubawa tayi ganin bata san number ba yasa ta ajiye bata ɗauka ba ƙara kira aka yi bata daga ba katse wa yayi aka sake kira nan ma kin ɗagawa tayi maimakon mai kiran ya haƙura sai ya cigaba da kiran. Turo kofa akayi "Wai Anisah ba ƙarar wayar ki nake ji bane" "Ita ce Umma" "To ba zaki ɗaga ba ne ko yaya" "Ban san waye yake kira bane" "Baki ɗaga ba ina zaki san me kiran" "In an ƙara na daga Umma" fice wa tayi kamar jira aka ta fita wani kiran ya ƙara shigowa ɗaga wa tayi tare da sallama "Wake magana" "Ashe duk halin ku ɗaya tsiwa, to ba wani bane Zaid ne" "Uhmmmmm ya kaje gida, har ka sauke ta kace" "Eh, dama cewa zanyi in ba damuwa ina so gobe inzo zamu yi magana dake" "Masha Allah, Ni kuma? Ok mu haɗu a gidan su Hooriyah" "Eh ko ban kai ba, Ba da ita zanyi magana ba dake zanyi maganar sirri ce" dariya ta saki "Ni na isa ince baka kai ba, Angon Bestie guda ai ka wuce haka, ok a ina zamu haɗu" "A'a nasani ko zaki ce hakan sai in faɗa mata, gidan ku zanzo" "Haɗa mu faɗa zaka yi kenan" "Ok Allah ya kaimu" "Ameen" "Ai ban isa haɗa hanta da jini faɗa ba" haka sukai ta raha har ya kashe. Bayan ya kashe ne take sanar da Umma tace Allah ya kaimu. 𝑾𝒂𝒔𝒉𝒆𝒈𝒂𝒓𝒊 Bayan La'asar tana zaune sai ga kiran sa ɗagawa tayi "gani a kofar gida" shine abinda yace ya katse kallon Ummanta tayi "Umma bari inje " "Sai kin dawo" ta tashi ta fice. Tsaye yake a jikin motar sa ya sha gayu gaisawa suka yi sannan yace "Da yake ba daɗewa nazo nayi ba magana zamu yi ta fahimtar juna please" "Ok inaji, Allah yasa ba wani laifin tayi ba" "Ba akan ta bane, Anisah" "Tunda na ganki na fara sonki amma nayi nauyin baki ban sanar da ke ba har aka kai kuɗi, Maganar gaskiya bazan iya haƙura da ke ba shiyasa na yanke shawarar sanar da ke, Auren ki nake so nayi da yaudarar ki zanyi ba" A kiɗime ta kalle shi bata san lokacin da ta fara zabga masa harara ba daga masa hannu tayi "Dakata Malam na gaji dajin shirmen ka, Ban taɓa tunanin baka da hankali ba sai yau, baka san yadda nake da ita bane da zaka zo min da wannan shashancin?" "Ban taɓa tunanin maganar da zaka zo yi ba aiko wani ya faɗa zaka yi haka ƙaryata wa zan yi" "kaga nan" ta nuna masa hanya "ka mike ta straight ka koma inda ka fito" ta juya zata shige "wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, dan Allah ki amince min" "Da dawa kake rayuwar, mtwsssss" ta shige da sauri. Umma ce ta ce "Ya na ganki haka wata iri" "Ba komai" ta shige ɗaki, tashi tayi ta bita "Ke Anisah me yayi miki, ya naga kina kuka" "Umma Ashe da gaske ne ana yaudara" "Meya faru ne kina sani a duhu Anisah" nan ta faɗa mata duk yadda suka yi da Zaid, Riƙe baki Umma tayi "Ke da muke neman kiyi Aure yanzu Allah ya kawo miki miji har gida shine kike gudun sa, saboda wata" "Umma saura wata biyu bikin su fa, Amma saboda cin amana ji abinda yace fa" "Amma ban taɓa tunanin lusara na haifa ba sai yau" kallon ta tayi "Umma" "Karki ce min komai Anisah, shekarar ku nawa kuna tare bata taɓa tunanin hada ki da wani nata ba tace ya Aure ki, yan'uwanta nawa ne suka yi Aure kuna tare ai da sai tace wani a cikin su ya nemi ki, Allah ne ya kama ta shiyasa na ɗora wa wanda zata Aura sonki" "Umma duk yadda nake da Hooriyah amma da abinda zan saka mata kenan, Ni duk wannan abinda kika lissafo bai dame Ni ba" "Ni kuma so nake kiyi Aure Anisah kullum girma muke ƙarawa, in na mutu yaya zakiyi, kin san dangin mahaifin ki ba ƙarbar ki zaki yi ba" "Umma a bar maganar nan, wallahi ko daɗin ji babu" "Ai ko dole muyi ta, Ai shi yazo bake kika je ba" "Ke dole ma ki Aure shi, zan sanar da dangin mahaifin ki yaje can su tattauna" zaro ido tayi "Haba Umma Muda zamu rufe maganar nan kar muji kunya Hooriyah ce ba wata ba" "Uwar ki ce, bari kiji indai Ni na haife ki sai kin Aure shi" ta tashi ta fice. Kuka ta Daɗa fashe wa da shi. Tun da ga lokacin ta zama wata iri ta kashe wayar ta gaba ɗaya ko fita ta daina Zuwan Hooriyah biyu tace bata da lafiya. Ya dawo kusan sau Uku amma taƙi fita, A karshe gurin Ummanta yazo suka yi magana tace ya kawo Kuɗi indai da gaske yake yayi na'am da maganar ta kuma yace zasu zo a Weekend da zai tafi ya bata kuɗi. (𝙷𝚊𝚓𝚒𝚢𝚊 𝚄𝚖𝚖𝚊 𝚊𝚗 𝚓𝚒 𝚔𝚞𝚍𝚒🤣😂) Ta yiwa dangin mahaifin ta waya ta sanar musu Anisah ta samu miji zasu zo neman Aure Ranar Asabar. An kawo kuɗi An saka rana ɗaya Da Hooriyah za'a daura tun tana tsoro har ta saki jikin ta, komai da ita ake yi na hidimar biki itama daga ɓangaren su Ummanta tana yi mata har aka zo ɗaurin Aure Babu wanda ya sani a sirri suka yi aka gama.......✍️ Bari mu koma labari Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Follow My Pages Arewa Books: fatimaintisar1 Wattpad: fatimaintisar1 Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟏𝟗&𝟐𝟎 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚✯ ✫✫✫✫ An sallame su daga asibiti bayan Magariba lokacin da suka dawo ragowar mutane kaɗan ne duk an watse sai Yan gidan su da basu tafi ba kowa sai sannu yake mata.Zama tazo yi Aunty ce ta riƙe hannun ta"Tashi mu shiga ciki ki huta" tashi tayi ba dan taso ba suka shiga cikin ɗakin wayar ta ta janyo zata kunna Aunty tayi saurin karɓe wa "Me zaki yi da ita" "Kunna wa zanyi mana" "Kwanta ki huta sai gobe zaki kunna" "Aunty bazan da ɗe ba zan kashe Anisah kaɗai zan kira please" "Har kina da lokacin kiran wata Anisah kenan yarinyar da taci amanar ki" "Ai kinji kashe ɗin doctor yace karki zauna da damuwa shine zaki kira ta, ta ƙarasa kashe ki, kwanta maza" kwanciyar tayi gyara mata bargo tayi ta kashe wutar ɗakin ta fice. Fitar ta baifi da minti biyar ba ta tashi zaunawa tayi ita fa har yanzu bata Yarda zasu iya cin amanar ta ba mutan en data fifita akan kowa tana ƙaunar su tsakani da Allah amma sunci amanar ta "Ya Allah dama mafarki nake, bazan iya jurewa ba, Ya Allah kasa min dangana" haka tayi ta maganganu ita kaɗai. ₍ᐢ⑅•ᴗ•⑅ᐢ₎♡ 𝗚𝘂𝗿𝗶𝗻 Ɗ𝗮𝘂𝗿𝗶𝗻 𝗔𝘂𝗿𝗲🤸 Bayan An daura Aure Mutane sai zuwa suke gurin Ango yin Allah ya sanya alkhairi, Yawancin mutane basu gane an Chanja sunan Amarya ba Abokansa ne na kusa suka gane Auwal ne ya janyo shi gafe "How Comes, Naji an canja sunan Amarya" "Zan maka bayani daga baya" kawai yace ya tafi. Sallamar mutane suka ƙara sa yi sannan ya suka tafi gidan su Amarya... 𝐆𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐬𝐮 𝐀𝐦𝐚𝐫𝐲𝐚... Amarya ta sha kwalliyar ta tayi kyau kamar ba gobe suna zaune a ɗaki tare da ƴan uwanta sai bata gayyaci ƙawaye ba kwata kwata. Yan uwansu sai san Barka ake mata ta Aure Mai kuɗi ba'a daɗe da ɗaura Aure ba ango yazo aka sha hotuna suka tafi. Basu jima da tafiya ba sai ga su Rukayya sun zo su biyar shigowa suka yi ba sallama ba komai sai cewa Zainab tayi "Ina Amaryar take" wata tsohuwa ce tana daga zaune tace "Ke ko ƴar nan lafiya kike mata wannan kiran" "Baba ba gurin ki muka zo ba gurin Maciya Amana muka zo" inji Khaleesat. Kallo kansu duk ya dawo. Tana daga ɗaki ta jiyo su gaban ta ne ya yanke ya faɗi "Innalillahi wainnaillaihir rajiun, na shiga Uku Ni Anisah, na janyo wa kaina matsala" tashi tayi ta fito gurin su "Ya na ganku a haka ku shigo ciki mana" Wani kallon banza Rukayya ta watsa mata "Ba zama ya kawo mu ba, ke in banda abinki ai kin san munfi ƙarfin zama anan Koh" "Ke dan Allah baki ji kunyar abinda kika yi ba, ki rasa wa zaki ci Amana sai Hooriyah yarinyar data taimaka Miki, kin san dukkanin mu munfi ƙarfin kula ki amma saboda da ita muka kula ki ta fifita ki akan kowa da komai amma kika Aure mata wanda zata Aura" "Ki rubuta ki ajiye sai Allah ya saka mata ko badaɗe ko ba jima, sai anjima" suka juya zasu tafi tsohuwar ɗazu ce ta ƙara magana "Yaran nan bamu gane inda Maganar taku ta dosa ba, ku dawo kuyi mana bayani" "Tsohuwa ki kama kanki, wadda muka bawa sako ka gane inda muka dosa, ita da Uwarta zasu iya yi muku bayani dalla dalla" Zainab ce mai wannan jawabin suka yi fice War su. Baki ta kama sai ta kalli Anisah "Ai sai ki yi mana bayani kamar yadda suka ce Koh" juyawa tayi ba tare da tace komai ba ta shige ɗaki. "Ke ai Sai kiyi mana bayani Koh" ta faɗa tana kallon Umma "Iya ƙyale su ina ganin bata suka yi, Anisah da bata da Ƙawa ko ɗaya, Sharri ne kawai dan anga tayi Aure kinsan halin mutane" "To Allah ya sawwaka". Nan aka fara tsegumi ƴan unguwa wanda suka san su Zainab suna ta magana Amma Umma tayi biris tace basu san su ba dan Haka a boye ake maganar. Bayan magariba aka kai Amarya ɗakin ta gida ne na Alfarma aka kaita nan fa zance ya ƙara tashi da gaske Auren cin amana tayi tunda aka ga gida wasu sai cewa suke basu taɓa ganin ta tana zance ba Amma gashi Auri Mai kuɗi. Nan aka dawo ana ta zancen ta. ✦✦✦ Bayan Kwana Uku Kwance take akan cinyar Mami kalba take mata a hankali kuma tana mata nasiha Aunty ce ta shigo "Har kin dawo, ashe ba daɗe wa zaki yi ba" "Ina zan dade na bar ƴar lele ba lafiya" dariya suka yi gaba ɗaya "Aunty ai Naji sauki, Ya hanya" "Ai haka ake so, Hanya Alhamdulillah, Fasa kwana nayi nace gwanda in dawo kawai" "To Masha Allah, ai na zata sai gobe" "A'a Wallahi" "Naji daɗi da kika rungumi ƙaddara gashi har kin ware" "Aunty ai hakan yafi min, Abinda kafi so sai kaga ba alkhairi ne a Rayuwar ka ba" "gaskiya Hakane, To Allah ya baki wanda ya fishi" "Ameen ya Allah"tashi tayi tace bari ta shiga ciki ta huta. Tunda aka fasa Auren Mama take sintiri Sulaiman yazo su sasanta tunda ta rasa wanda zai Aure ta duk ta zama wata iri duk sanda Mama zata zo sai ta taho da mutane wai a ganta ta rasa wanda zai Aure ta kuma taki yarda da ɗan uwanta wannan abinda da take mata ne yasa ta yanke shawarar komawa gidan Yaya Abduljawwad da zama ba tare da ƴan uwan su sun sani ba. Tayi shawara da su Aunty kuma sun amince da Yamma zata tafi. ( ̄▽ ̄)~* Zaune suke a Palour ita da Auwal tunda abin nan ya faru kullum jikin jajjanta wa suke yanzu ma maganar suke Khaleesat ce tace "Wallahi Abban fadil kunyar Hooriyah nake ji ina zan iya zuwa gidan su" "Da wane ido zan kalle ta Ni nayi ta convincing ta kula Zaid da kyar ta amince amma ya watsa mana kasa a ido" "Duk kunyar ta da zaki ji ai baki kaini ba, kawai ki kirata muji tana ina mu bata hakuri, Ni fa duk laifin na nake gani da banzo da Zaid gurin Biki ba ai ba zasu haɗu ba har haka ta faru" "Bari in gwada in ji ko zata ɗaga dan bana tunanin zata ƙara kula Ni" wayar ta ta ɗauko ta kira anci Sa'a tana kusa da wayar ɗagawa tayi wata nauyayyar ajiyar zuciya Khaleesat ta sauke "Ummu Fadil ya da haka, baki da lafiya" shine abinda ta faɗa "Ai dole in Sauke ajiyar zuciya Hooriyah na zata bazaki ɗauki waya ta ba" "Me kika yi min haka da zafi" "in munzo kyaji, yaushe zamu same ki a gida" "Yaushe kika fara tambayar appointment in Zaki zo gurina" "Sorry, mu bar zancen wasa yaushe kike gida" "Kizo ko anjima ne, amma karki kai yamma zan fita" "Ga amsa ta nan ta fito zaki fita, sai munzo" ta kashe wayar. "Ga ba shi ba da kika kira ta, tashi ki shirya mu tafi" tohm tace ta shiga ciki. Bayan Azahar suka zo sun samu tana nan bayan sun gaisa suka yi ta bata hakuri akan abinda ya faru tace ba komai basu suka janyo ba nan take sanar da Khaleesat yau zata koma gidan yaya Abduljawwad da zama......✍️ Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books: fatimaintisar1 Wattpad: fatimaintisar1 #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟏&𝟐𝟐 𝐌𝐮𝐭𝐚𝐧𝐞𝐧 𝐀𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐜𝐨𝐦𝐦𝐞𝐧𝐭𝐬 𝐝𝐚 𝐫𝐞𝐚𝐜𝐭𝐢𝐧𝐠 𝐈𝐧𝐚 𝚐𝚘𝚍𝚒𝚢𝚊✯ 𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝐝𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐇𝐨𝐨𝐫𝐢𝐲𝐚𝐡 𝐅𝐚𝐧𝐬 ❣ 𝐊𝐮𝐲𝐢 𝐲𝐚𝐫𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐤𝐞 𝐬𝐨 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐢. 𝐌𝐮𝐜𝐡 𝐊𝐚𝐮𝐧𝐚❤❤❤ ✫✫✫ Bayan magariba ta shirya tsaf shi kaɗai take jira yazo su tafi tun yamma tace zata tafi yace ta jira shi shiyasa duk a ƙage take su tafi sallama akayi da sauri ta amsa "Kai Hooriyah, duk azarbaɓin tafiyar ne" inji Aunty dariya Khalil ne ya sheke da dariya "Allah Sis kin cika zumuɗi, sai kace wadda baki taɓa zuwa ba" "Ba zaka gane bane, amma na gaji da zama anan" "Gwara in tafi kafin gobe tayi taxo ta saka Ni a gaba, Aunty ko ƙara kiran sa sanyi" "Tunda yace ki jira shi ai zai zo Koh" "Wa ake jira ne" cewar Yaya Abduljawwad "Har Naji daɗi" sallama yayi ya shigo "Wai wa ake jira" "Ga ta nan kai take jira tun ɗazu" inji Mami, Khalil ne yace "Yaya Kasan tun ɗazu ta gama haɗa kaya kamar ta tashi sama take ji ta tafi" ya saka dariya. Gaisawa suka yi da su Mami sai ya shige part ɗin Daddy sai gurin tara ya fito lokacin har ta kwanta a Palourn Khalil ne ya tashe ta "Ashe har kin yi bacci" "Tunda kaƙi fitowa shiyasa na kwanta, dan kaga ina son zuwa sai wulakantani kake" "Ni na isa in wulakanta ki, ta shi mu tafi" tashi tayi tana yiwa su Mami sallama suka fice Khalil ne ya ɗauko mata akwatin ta har baƙin mota ya rako su yana ta tsokanar ta wai ta guje su "Allah Khalil ka raina Ni da yawa" "Ni na isa in raina Yaya ta, yaushe zaki dawo" "Tun ban tafi ba har ka fara tambaya, sai nan da wasu watanni" "Kin san zanyi missing ɗin ki da yawa" "Da yake gida ɗaya muke Koh, yaya muje Ni ya ishe Ni da surutu, Kanin Good Night ka gaida Adeel da Mama sa" "Zasu ji, har kin gaji da Ni, ku gaishe da mutan gidan" "Tohm" tace, rufe musu kofar yayi yana cewa "Yaya sai da safe" "Allah ya tashe mu Lafiya" yace yana kunna motar suka tafi... Baifi minti talatin ne ya kaisu gidan suna shiga gaisawa kawai suka yi tana ta yi mata tsiya ta saka ta girki kuma bata zo da wuri ba. Kare kanta tayi tayi da taga abin nata bana ƙare bane sai tayi shigewar ta Ɗaki ta kyale ta. Dan in ta zauna sai su kwana tana mita. Duk cikin matan yayanta sunfi shaƙuwa da ita Sajidah tana da hakuri bata da hayaniya shiyasa tasu yazo ɗaya. Bayan Sati Biyu Lafiya ƙalau suke zaune bata da wata matsala yanzu shirye-shirye koma wa makaranta take yi. Tun Asuba da ta tashi bata koma Bacci ba break fast ta haɗa musu duk da akwai masu yi amma tace ita zata yi bayan ta gama ta shiga ɗaki wanka tayi Shirya wa tayi Sea green Abaya ta saka da mayafi Golden tayi kyau sosai. Fito wa palour tayi nan taga duk sun fito suna zaune a dinning ita kaɗai suke jira "Wow, Masha Allah irin wannan kyau haka, wannan ai sai ki rikita maza, Tabarakkalah" "Anty Sajeedah Kenan ina abin yake, Good Morning" Kujera taja ta zauna Yaya ta kalla "Yaya Good Morning" "Morning" Su Fudail ne Suka gaishe ta Amsawa tayi tana karɓar Batool a hannun Sajeedah karya wa suka fara. Da Sauri-Sauri tayi ta gama ta mike "na tafi, sai na dawo" "Allah ya kiyaye hanya, Ki duba kan TV stand ki ɗau key" "Ok Thank you" "Sai kin dawo" Tohm tace tana fice wa. 𝐁𝐔𝐊 𝐔𝐧𝐢𝐯𝐞𝐫𝐬𝐢𝐭𝐲 𝐊𝐚𝐧𝐨. Shigowar ta makarantar kenan Parking tayi ta fito Kicibis suka yi "Sorry Sir" "Barka" "Ahhh Bakomai, Barka kadai" "Ashe haka abu ya faru Allah ya baki wanda ya fishi" Ameen tace tayi saurin Wuce wa. Binta yayi da kallo. Tafe take tana tunanin Ashe kowa ya san abinda ya faru amma da tasan haka ne da bata dawo makarantar ba kowa kallon wata iri yake mata kenan. ❥❥❥ Knocking ƙofar akayi Kallon kofar yayi "Come in" ya maida kansa kan abinda yake yi. Wanda yake ƙwanƙwasa kofar ne ya shigo neman guri yayi ya zauna "Zaaheed kai dai ba zaka Chanja hali ba Koh" "Me kuma nayi ne" ya faɗa ya ɗagowa "Ya wuce, kasan menene" "Ya za'a yi na sani, Ni da ba sanin gaibu nake ba" "Matsala ta da kai kenan, Da gaske ne fa zancen da muka ji" "Wanne daga ciki?" "Na Ba'a yi Auren A'ishah Harith ba, yau ma har mun gaisa da ita" "Dan kun gaisa da ita Shine yake nufin bata da Aure" "A'a baka gama jin zancen ba, ai har jaje nayi mata dan na tabbatar" dafe kai yayi "Wallahi Naseer ka shiga uku, gulma kamar mace" "Ai dama kace haka, Ni da nake so kaima kayi Auren nan" "Dan Allah wannan lokacin Karka ƙi faɗa mata kana son ta karta suɓuce" "Da ai kai kasa nace ina son nata Koh" "A'a Ni dai shawara ce na baka, karka yi sake sai anjima" Tinani ya shiga yi akan maganar tasa dan gaskiya tunda ya fara ganin ta yaji yana son ta bai taɓa kamu wa da ƙaunar wata ba sai ita, Dole ya nemi mafita kafin wannan damar ta ƙara kufce masa... **** Zaune suke a cafeteria hira suke tabawa Khaleesat ce tayi tsaki Zee ce tace Lafiya "Waccan Banzar na gani wallahi" "Kace kema kinyi mugun gani" inji zee "Wai wace ne haka" cewar Hooriyah "Wace wadda ta wuce Anisah mana" Ruky ta faɗa. Zaram ta miƙe "Ina zaki kuma" ba tare da tace komai ba ta fice. "Abinda na guda kenan shi yasa ban faɗa ba wallahi" "Bari inje inga ina tayi" Cewar Khaleesat, Karɓar Fadil tayi ta bita. Can ta hango ta zaune a cikin Mota Karasa wa tayi ta buɗe shiga tayi sannan tace "Meyasa kika taho, ai bai ka mata ki taho ba" "Me zanyi in ban tashi ba nayi Wa kaina Alkawarin babu Ni babu ita, ko inuwa ɗaya bana son mu zauna" "Abin ba daɗi amma da baki nuna kin ganta ba" "Ai bata isa zuwa inda nake ba" "Allah ya Kyauta" "Ameen". Hira ta ringa janta da shi har ta saki jiki Bayan wasu mintina suka fito suna da wata lecture..... ✰✰✰ 𝐸𝑚𝑖𝑟'𝑠 𝑃𝑎𝑙𝑎𝑐𝑒 𝑨𝒃𝒖𝒋𝒂. Motoci ne suke shigo wa cikin masarautar a tsare suke tafiya basu tsaya ko ina ba sai baƙin fada nan suka yi parking Buɗe kofar Motar ba faɗe yazo yayi "Allah ya ja zamanin yarima Barka da dawowa yarima" shine abinda fadawan suke ta faɗa Kusan minti ɗaya sannan Aka zuro ƙafa sai da ta ɗau wasu seconds sannan aka sako ɗayar kafar fito wa yayi gaba ɗaya Tunda ga Kallon Kafar sa Kaɗai Kasan Mamamlakin ta ya haɗu dogone ba shi da ƙiba sosai Kyakkyawa ne abin farko in ka gansa zaka yi tunanin Balarabe ne ya haɗu, ɗaga musu hannu kawai yayi ba tare da yace komai ba Cikin fadar suka shiga cikin takun izza... **** **** **** Zaune take akan kilishi ta kishingiɗe a cikin ɗaki ita kadai Kofar aka ƙwanƙwasa izinin shigowa ta bayar buɗe wa akayi aka shigo Amintacciyar Hadima ta ce zube wa tayi a ƙasa "Ranki ya daɗe Barka da Rana" "Barka kadai" tace cike da izza "Me yake faruwa a cikin gidan" "Ranki ya daɗe ʏᴀʀɪᴍᴀ mai jiran gado ne ya dawo, daga gani kuma ya samu lafiya" A zabure ta mike "Mai kike nufi da ya dawo, Jiya ma sai da muka yi magana da mai Martaba amma bai Sanar mun da dawowar sa ba".............✍️ 𝐄𝐧𝐝 𝐎𝐟 𝐁𝐨𝐨𝐤 σɳҽ Alhamdulillah Anan na kawo ƙarshen Book One sai mun haɗu a Book Two zan tafi hutu sai bayan sallah Idan Allah SWT ya Kaimu bayan Sallah Zamu cigaba. Tafiyar mai nisa ce.. Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya duba wannan WhatsApp channel ɗin https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books: fatimaintisar1 Wattpad: fatimaintisar1 #𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Please Share & Comments 🙏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸ℍℝ𝔸𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Ina yiwa ƴan uwa musulmai Barka da sallah da Fatan munyi Sallah Lafiya Allah ya karɓi ibadun mu yasa muna cikin ƴantattun bayi Ameen بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟐&𝟐𝟑 ———————————————————————————————————————— *Gidan Amarya* Soyayyar su suke zuba wa basu da damuwar komai tun tana jin ɗari-ɗari har ta saki jiki da shi zaman su suke lafiya ƙalau. Buɗe motar tayi ta fito cikin gidan ta shiga tass yake ba abinda yake tashi sai kamshi ba kowa a cikin palour sama ta haura. Zaune yake a palour aiki yake yi a system, a hankali ta fara tafiya har ta isa inda yake baiji shigowar ta ba. Rufe masa ido tayi,dafe idon yayi "Be cika min ido mana aiki nake fa" Dariya ta ƙyalƙyale da ita "Ya akayi ka gane Ni ce" "Ai nasan babu mai wannan aikin sai ke" Dariyar ta cigaba da yi tana dawowa kusa da shi zama tayi a jikin sa "Kin tsorata Ni da yawa Habibty" "Sorry Noory, Har ka dawo" "Eh, Babie ya makarantar" "Alhamdulillah duk ba daɗi ina ta kewar ka" "Ba gashi kin dawo ba, fatan babu abinda ya faru" "A'a babu komai, Kasan yau na haɗu dasu Hooriyah" "Amma dai baki kula su ba Koh, dan nasan suna ta jin haushin mu" "Ban kula su ba, in na kula su ai sai suyi min duka ko zasu hu ce Haushin" "Innnnnnaaaaaa dako munyi Shari'a dasu kawai su dakar min mata, Ni fa ko sunan su bana son kina ambata haushi nake ji" "An dai na daga yau ranka ya daɗe" anan ta cigaba da zama tana kallon sa yana aiki kiran sallah ne ya tashe su ɗaki suka yi yayi alwala ya fice ita Kuma ta shiga wanka tana fito wa tayi sallah ta tashi zata fice Wayar tace tayi ƙara dawowa tayi ta ɗauka ganin Ummanta ce take kira "Umma na ina wuni" "Fatan kuna zauna lafiya ba wata matsala" "Babu Matsalar komai wallahi, lafiya ƙalau muke zaune" "Masha Allah haka nake son jin, dan Allah ki bishi sau da ƙafa kar a samu matsala" "Babu abinda zai faru Umma, yana sona fa" "Allah yasa dai" "Ameen" nan suka cigaba da hirar su cikin nishaɗi da walwala. *To dama ina za'a samu saɓa ni tunda yanzu kuka yi auren, har yanzu amarya ce fa😌* ★★★ Bata dawo gida ba sai Kusan Magariba Sajeedah ce kaɗai a palourn duk yaran basa nan neman guri tayi ta zauna tana yi mata ya gida ta amsa da lafiya lau "My Only Anty Ina su Fudail" "Yau kuma shakiyanci kike ji kenan sun fita da Abban su" "Ba shakiyanci bane ba, kin san babu ya ke Babu ke ba kishiya, Shine basu jirani ba" "Ai ko shi in ya faɗan haka nasan zolaya ce, Kun fi kusa da shi ai" "Shikenan sa wasa, kin san in na faɗi Abu kamar shi ya faɗa Koh" Nan take bata labarin abinda su Khaleesat suka yi ranar biki da suka je gidan su Anisah "Kai amma basu kyauta min ba da sun sanar da Ni zasu ai sai nayi abinda yafi nasu" galala tayi tana kallon ta "Ke dana kawo wa ƙara in sunzo kiyi musu faɗa" "Wane irin faɗa za'a yi musu, ai kamata yayi da suka je sunci ubanta, ko ta gane Shayi ba Ruwa bane" "Chabbbbb Ni dai banji daɗi ba wallahi, in tani ne ma da basu je ba" "Ni Ko sun min dai-dai, da sun sanar dani dana raka su, dan Duka zamuyi mata wallahi" "Abin naki babba ne gwanda da baki sani ba"Bari in tafi ɗaki. Tashi tayi ta shige ɗaki bata fito ba sai da taji hayaniyar yaran sun dawo. Fito wa tayi ta ringa yi masa mita bai jira ta dawo sun tafi tare ba. Hakuri ya bata yana ce mata baisan zata ba da ya jira ta amma ta bari next time sai suje da kyar ta yarda. Zaman cin abincin suka yi bayan sun gama gurin yaran ta koma tana ta yi musu wasa sai gurin shabiyu ta fito shima dan Sajeedah ta saka yaran suyi bacci ta koma ɗakin ta sallah daren ta tayi tun lokacin sai ta dau Kur'ani ta fara tilawa bata kwanta ba sai gurin uku. ♥♥♥ Zaune suke a cikin fada tsitt ba ka jin komai sai ƙarar AC hayaniya ce ta fara tashi daga waje wani bafade ne ya fita dan dubawa bai jima ba sai gashi ya dawo "Allah ya taimake ka Yarima ne dawo" yayi mamakin jin Yarima ne ya dawo Jiya ma fa sunyi waya amma bai sanar da shi ba, ɗazu ma yayi waya da likitan sa shi ma bai faɗa masa ya taho ba *"Me kake jira da ba zaka shigo da shi ba" da sauri ya miƙe zai fita sai gashi ya shigo fadawa suna ta masa kirari Gurin Sarki yazo ya gaishe shi tare da mutanen Fada bai daɗe ba ya tashi yayi musu sallama yana ficewa daga fadar. ⍟⍟⍟⍟ ⍟⍟⍟⍟ ⍟⍟⍟⍟ "Tabbas Ranki ya daɗe ya dawo chan na hange shi ya shiga Fada" "Bai mutu ba kenan" Shiru ɗakin yayi na yan Mintina Wata Harara ta wurga wa Hadimar da sauri ta mike jikin ta na ɓari "A huta Lafiya" tace ta fice da Sauri tsaki taja tashi tayi ta fara zaga ɗakin magana ta fara "Yanzu yaron nan bai mutu ba kenan, yana raye, kuma ya dawo Fada" "Dole ya koma inda ya fito tunda bai mutu ba"......✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/CmyP8hlqbHtGyhdQ7FVc2w 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟒&𝟐𝟓 ———————————————————————————————————————— Part ɗin sa ya nufa ya tarar da komai tass kamar yana nan Toilet ya shiga yayi wanka fito wa yayi ya shirya bai zauna ba hanyar fita yayi Fadawa ne guda Uku A gurin saurin taho wa gurin sa suka yi ɗaya daga cikin sune yace "Ranka ya daɗe fita zaka yi" Eh kawai yace musu ƙara magana ya cigaba da tafiya biyo da suka yi a baya "bani makullin ba tare da kowa zan fita ba" yace musu. Kallon juna suka yi "Ranka ya daɗe Mai martaba yace kar a bar ka kai kaɗai ka fita" wuce wa yayi zuwa gurin motar kawai yayi cikin izzah ba tare da ya ƙara ce musu komai ba. ✿✿✿✿ ✿✿✿✿ ✿✿✿✿ Kano Nigeria. Buɗe gate mai gadi yayi parking yayi Fitowa yayi daga motar da sauri ta ƙara so kusa da shi Kyakkyawa ce sosai Doguwa ce amma ba sosai ba dan ba za'a kira ta gajeriya ba, Magana ta fara yi masa "Tun ɗazu nazo ina jiran ka" Kallon banza ya watsa mata sannan yace "Mai zan Miki da kike jirana? Na faɗa miki Bana son irin haka Koh, Kizo kiyi ta jirana sai kace wadda take bina bashi" "Kawai zuwa nayi mu gaisa, in ganka ko naji daɗi a raina" cewar ta. Shiru yayi mata cigaba da yi masa magana tayi "Har yanzu baka gama yarda da irin son dana ke maka ba Yah Zaaheed, naga kamar kana tantama akan haka" "Noor In kin gama surutun kya iya tafiya gidan ku, na gaji da jin maganganun nan naki" wucewar sa yayi, riƙe baki tayi tace "Au haka kace, Chabbbbb ai ko baka isa ba, dole kaji abinda zan faɗa" fuuuu ta wuce ta bi shi. A palour ta tarar da shi tare da wata babbar Mace suna Magana Juyowa tayi ta kalle ta sai tace "Noor dama ba tafiya kika yi ba" Noor ce ta bata amsa da "Eh Mommy dama shi nake jira ya dawo" "Ai gashi nan ya dawo, sai Kizo"cewar matar da aka kira Mommy Ɗagowa yayi ya ɓalla mata Harara ba tare da Mommy ta lura ba da Sauri ta ɗauke kanta daga kallon shi "Ai Mommy Tafiya gida ma zanyi kawai" "Saboda me zaki tafi Bayan gashi ya zo" "Baƙuwa nayi yanzu tayi min waya" "Ahhh ya kamata ki ganta gaskiya" Tace tana tashi "Kya gaida Hajiya in kinje gida" "Zata ji Insha Allah, Mommy kya yi wa su Kausar Sallama bazan koma Gurin su ba" Tohm tace ta haye sama Kallon ta maida kansa ko zai kalle ta amma taga ba ta ita yake ba tashi tayi jiki ba ƙwari zata fice yace "Idan kika sake zuwa nema na gidan nan sai ranki ya ɓaci, wai Ni sa'an ki ne" Ba tare da tace masa komai ba tayi ficewar ta. ╰╮o( ̄皿 ̄///) (╯-_-)╯╧╧ Noor ce Zaune a gefen gado kuka take ta rusa wa turo ƙofar ɗakin aka yi Babbar Mace ce daga gani Maman tace Kamar su ɗaya Zama tayi kusa da ita "Yaushe kika dawo Noor?" inji matar da ta shigo Hawayen Fuskar ta Share sannan tace "Ban daɗe ba, naga ba kya Palour shiyasa na shigo ɗaki kawai" "Yauma ya ɓata Miki ran kenan" Shiru tayi ba tace mata komai ba, cigaba da mata magana tayi "Na rasa wace irin zuciya gareki Noor?, Yaron nan ya nuna baya sonki ba sai ki ƙyale shi ba amma kin nace sai shi, wai shi kaɗai ne namiji a duniya ne?" "Mommah kin san duk Duniya ba wanda nake so sai Yah Zaaheed tun ina ƙarama nake son shi, na rasa me nayi masa da baya sona ba" "Mommah ina da wata makusa ne a jiki na ɗaya tsane Ni" "Ba ki da shi" juya wa tayi ta Maida Kallon ta gare ta "Noor" "Na'am" "Da zaki ji Shawara ta da tuni kin ƙyale Zaaheed, duk da ɗan ƴar uwa ta ce. A cikin samarinki da kike kulawa ki bawa wani dama, Zaaheed bashi da niyyar Aure, kuma ko yana da niyyar Aure ba Auren ki zaiyi ba ya riga da ya tsane ki" "Mommah" ɗaga mata hannu tayi "Karki ce min komai, ki fara Tunani akan wannan maganar" ta tashi ta fice............✍️ Jiya an samu Typing Errors da yawa mantawa nayi Banyi editing ba sai daga baya na lura. Tun cikin Azumi nayi typing ɗin ne Afuwan😰 Posting zai koma Monday, Wednesday & Friday sai Rana ɗaya a Weekend in na samu dama Insha Allah. Kamar yadda muke yi kafin A fara Azumi. # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟔&𝟐𝟕 ———————————————————————————————————————— Tagumi ta zuba ta lula duniyar tunani zunbur ta miƙe gaban dreesing mirror ta tsaya kallon fuskar ta tayi sai kuma ta ja wayar ta Number tayi dailing ta fara Kira ringing biyu aka ɗaga "Aunty Barka da Rana" "Barka dai, Kwanwas naji Muryar ki kamar kinyi kuka, ko baki da lafiya ne?" aka faɗa daga cikin Wayar "A'a Ba komai, Yaya yana gari?" "Baya nan" "Ok gani nan zuwa" ta kashe wayar Jaka ta ɗauko ta ɗauki Key ɗin Mota da wayar ta ta fice, a Palour ta tarar da Aliyu yana zaune magana ta fara yi masa "Yaya in Mammah ta sauko kace mata nake gidan Aunty" "Meya faru? Na ganki haka" "Ba komai, na tafi" ta fita da sauri ❦❦❦❦ ❦❦❦❦ "Yah Zaaheed sannu da zuwa" cewar Aliyu ƙanin sa Yauwa kawai yace masa ya tashi ya haura sama bin sa da kallo yayi kawai. Ɗakin Mommy ya shiga waya take yi Zama yayi yana jiran ta gama wayar. "Ba zaka huta ba ne?, Daga aiki fa ka dawo" "Mommy please ki daina turon yaran nan a matsayin na Aure su" Yace mata. Kallon shi tayi da kyau "Saboda ta zo gurin ka shikenan ba zaku gaisa ba" "Mommy ita Yarinyar nan ba gaisuwa ce take kawo ta ba" "To mene yake kawo ta? Faɗa min inaji" Shiru yayi sai kuma yace"Mommy bari in tafi in huta" "Nemi guri ka zauna" tace masa Guri ya nema ya zauna. Nisawa tayi sannan tace" Zaaheed na gaji da zaman ka haka ba Aure, kowa yana Aure amma banda kai" "Mommy Insha Allah nan bada jimawa ba zanyi Nima" "Ko yaushe haka kake cewa, ko sai bayan rai na zaka yi ne" ta share hawayen da ya zubo mata, da sauri ya sauko kasa ya zauna kusa da ita yana riƙe hannun ta "Kukan ki Azaba ne a gare Ni, dan Allah ki daina Insha Allah zan yi Aure nan bada jima wa ba. Mommy zan cika Miki burin ki ba zaki mutu ba sai Kinga ƴaƴa na In sha Allah" "To naji yaushe zaka kawo matar, indai da gaske kana son farin ciki na" "Nan bada jimawa ba Insha Allah" "Allah yasa" tace tana shafa Kansa Waye ZAAHEED ??? Wace NOOR ??? Alhaji Yusuf Shine sunan mahaifinsa matar sa Ɗaya Hajiya Sa'a Ƴaƴa biyu Allah ya basu a duniya duk maza Zaaheed shine babba sai Ƙanin sa Al-Ameen. Hajiya Sa'a tana son Mace amma Allah bai bata ba. ƙwanwar ta ɗaya a duniya Habiba suna son junan su ko yaushe suna tare da juna har Allah yayi wa mahaifansu rasuwa ta dawo gurin ta da zama har tayi Aure. Habiba tana da yara Uku biyu Mata ɗaya Namiji, Amina ce Babba ana ce mata Khairat, sai Aliyu, sai ƴar Auta wadda taci sunan Mommy Sa'adatu ana ce mata Noor. Tunda aka yaye Noor Mommy ta karɓe ta. Noor yarinya ce kyakkyawa bata da hayaniya bata da rawar Kai, sun taso tare da ƴaƴan ta har sai da ta gama secondary school sannan ta koma gidan su a Lokacin Zaaheed yana US karatu. Zaaheed yayi karatun sa a US tun daga Degree har Doctoring Degree duk a US sai da ya gama sannan ya dawo Nigeria ya tarar ƙannen sa duk sun girma bayan dawowarsa ba daɗe wa Noor ta nuna tana son sa amma yayi biris kamar bai san tana yi ba da farko ta so ƙyale shi amma sai ta kasa. In Mommy'n tayi masa maganar Aure sai ya hau neman hanyar da zai guje wa maganar yanzu yana da shekaru 35 a duniya Lecturer ne a B.U.K. Shine dalilin da yasa Mommy duk ta damu yayi Aure......✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan Follow My Pages Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/Lg8RQ7S5NfX6fSmnSkRA79 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟐𝟗&𝟑𝟎 ———————————————————————————————————————— 𝒁𝑨𝑨𝑯𝑬𝑬𝑫 Tunda yaga Mommy'n sa na son tada hankalin ta akan Auren ya yanke shawarar yi wa Abiee'n su waya baya ƙasar yana India ya sanar da shi. Ringing wayar take yi ba'a ɗaya ba har ta katse bai ƙara bin kiran ba yasan maybe Yana meeting ƙyale shi yayi yasan zai kira sa bayan Hour ɗaya sai gashi ya kira shi Bayan sun gaisa ya fara sanar da shi dalilin kiran "Abiee dama sanar da kai zan yi na samu Yarinyar da zan Aura" "To Masha Allah, a ina take" cewar Abiee "A nan Kano take, ɗaliba tace" "Alhamdulillah, Ƴar gidan wace?" "Ƴar Alhaji Harith mai Kanwa" "Harith mai Kanwa dana sani" "Dama ka san shi ne Abiee?" "Na sanshi shekaru da daɗewa, wacce daga cikin su" "A'isha" yace "Masha Allah, Zan nemi Contact ɗin sa in sanar da shi kafin na dawo" nan suka cigaba da maganar Mommy tayi murna da jin zancen saboda zamuɗi bata jira dawowar Abiee ba ta sanar wa ƴan uwa aje a nemo masa Auren kar a samu Matsala wani ya riga su. Abiee ne tuntube shi sannan ya turo musu number Daddy'n su Hooriyah tunda ya sanar da shi zai turo masa baƙi ya basu dama suzo Ranar Asabar. Ranar Asabar bayan La'asar suka je bayan ƴan gaishe gaishe suka sanar da shi abinda ya kawo su yaji daɗi sosai dan Yasan Zaaheed tun da daɗewa yaron kirki ne nan ya amince yace a turo shi... ♡♡♡ ♡♡♡ ✭✭✭ ♡♡♡ ♡♡♡ A bangaren Hooriyah komai yana tafiya dai-dai yanzu bata da wani damuwa ta fawwalawa Allah komai ta ɗauki ƙaddara sai tayi two weeks bata je gida ba sai dai suyi waya dasu Mami kowa so yake ya faranta mata suna zaune lafiya da Aunty Sajeedah. Tunda Aunty Sajeedah tace mata Yayan ta na neman ta take jin wani iri sau uku tana attempting tafiya side ɗin sa sai ta kasa ta rasa dalili har aka idar da Sallah bata je ba. Turo kofar ɗakin aka yi "Yanzu dama ba kije kiran da yake Miki ba, kina zaune a inda na barki, maybe ko Sallah ma baki yi ba" "Har anyi salla?" "Tun ɗazu gani nayi ba kya Palour kuma shima bai dawo daga Masallaci ba nasan kina ɗaki baki je ba" "Tsoron Zuwa nake, kawai ji nake gabana na faɗuwa" "Allah yasa ba Su Mami ne suka ce na koma gida ba, wallahi bana son Komawa" "Ke da baki je kinji mene ba har kinyi hukunci" "Amma ke zaki rakani gaskiya, in yace in koma Dan Allah ki sa baki ya barni" "To naji, tashi kiyi salla" Jiki ba ƙwari ta tashi ta nufi Toilet Alwala tayo tazo ta tada Sallah bayan ta idar ta kalle ta "Tashi muje Koh" "Jeki zanzo daga baya" Rau tayi da ido sannan tace "Amma ai ba muyi haka da ke ba My Aunty" "Haba Hooriyah sai abu kike kamar ƙaramar yarinya ko Fudail ba zai yi haka ba" Bata rai tayi da kyar ta lallaɓata ta tafi ita kuma tayi gurin yaran ta" ✿✿✿✿ ✿✿✿✿ Zaune ta same shi yana karanta Jarida Sallama tayi ta nemi guri ta zauna a ciki ya answer bai ce mata komai ba. kana ganin ta kasan a tsorace take sai da tayi gurin minti Goma sannan yace "Sai yanzu kika ga damar zuwa kenan" "A'a naga an kusa tada sallah ne Shiyasa na zauna sai da nayi Sallah sannan na taho" Jinjina kai kawai yayi "Daddy ne yace gobe kije yana son ganin ki" "Shikenan abinda nake gudu ya tabbata" take faɗa a ranta "Me kike gudu?" Ya jefo mata tambaya, da sauri ta lalle shi "yaya ba magana nayi ba" "Magana ce akan Auren ki ba wani abu ba, karki saka wa ranki damuwa, Dan har Iyayen yaron sunzo sun tambaya kuma Daddy ya basu dama" A firgice ta kalle shi ɗan bata taɓa kawo maganar Aure a ranta ba ta riga data soke shi a rayuwar ta ba zata ƙara kula kowa ba balle har a samu damar yi mata Abinda Zaid da Anisah suka mata magana ta fara yi masa "Yanzu Yaya har zaku iya ƙara bawa wani dama kuce yazo gurina, kun manta abinda su Zaid suka min dududu wata nawa da har zaku manta" "Ni a ganina ba zaku ƙara bawa wani dama yazo gurina ba"ta faɗa Muryar ta na rawa........✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Jiya nace zanyi posting amma ban samu dama ba ɗan Yayana ne Allah yayi masa rasuwa Allah ya jikan shi ya gafarta masa tare da Al'ummar Musulmi baki ɗaya👏 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan Follow My Pages Arewa Books: https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/6, 2:06 PM] Fatima Zahra Intisar: https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟏&𝟑𝟐 __________________________________________________________________ Tausayin ta ne ya kama sa duk sai yaji babu daɗi da Daddy ya sani sun fara tuntuɓar ta kafin ya amince magana ya fara mata cikin kwantar da murya "Daddy ne ya yanke shawarar, Kiyi haƙuri ki bi umarnin sa kinji Allah yasa haka yafi alkhairi, Yace gobe in Allah ya kaimu kije" magana zata yi masa yayi saurin ɗaga mata hannu "Hooriyah ya isa haka tashi kije da safe sai ki shirya in sauke ki kafin in tafi aiki" Tohmm kawai tace ta tashi ta fice. Da safe Gurin goma ta gama shirin ta tana zaune jiran sa da ganin ta kasan tana cikin damuwa yana gamawa suka fice Yana sauke ta ko shiga cikin gidan bai yi ba ya tafi sai ya dawo zai shigo. 💫💫💫💫 💫💫💫💫 💫💫💫💫 Cikin Gidan ta shiga ba kowa a Palour da alamun mutanen gidan duk suna ɗaki basu fito ba Motsin da taji a kitchen ne yasa ta nufar gurin Mai Aiki ce kaɗai a ciki tana ta kai kawo "Baaba Barka da Safiya, Ina su Aunty?" Tace mata "Kece tafe da safiyar nan, Barka kadai, Mami tana Bangaren Alhaji, Aunty kuma tana Ɗaki bata daɗe da shiga ba" ta bata answer. "Thom idan sun fito kice musu ina cikin ɗaki" cewar Hooriyah "Insha Allah zan sanar musu" ta faɗa mata, wucewa ciki tayi. Ɗakinta ta nufa shiga tayi ta nemi guri ta kwanta bata jima ba ta tashi waya ta ɗauko kira ta shiga yi ringing biyu aka ɗaga gaisawa suka yi "Na zata ba zaki ɗa ga ba ai, ya fadil?" "Ashe kin san laifin naki, Fadil yana nan qlau" cewar Khaleesat "Anjima zan shigo" "Kinzo gida yau kenan, Ashe kina son Goge laifin naki" "Ban daɗe da zuwa ba, mun kwana biyu bamu gaisa ba, sai na shigo" "To Allah ya kawo ki lafiya" "Amin, sai anjima" ta kashe wayar. Tashi tayi ta fito palour ta samu sun fito suna zaune da alamu ita suke jira itama zama tayi ta fara gaida su "Ashe Da wuri ya kawo ki" Aunty ta faɗa "Ehh Da zai fita muka taho tare inya dawo yace zai shigo" "Ai Yayan ku baya fashin zuwa kullum sai yazo" "Bari mu baku guri, in kun gama kizo za muyi magana" cewar Aunty "Insha Allah" 🤙🤙🤙 Zaune take a gaban Daddy magana ya fara mata: "Da fatan Ya sanar dake abinda yasa na kira ki" "Eh Daddy" "Na ba shi dama yazo ku ga juna Lecturer ne a makarantar ku yace anan ma ya ganki, Mahaifinsa Abokin na ne a da" "Daga yanzu zuwa kowane lokaci zaki iya ganin kiran sa" "Allah ya bani ikon yi maka biyayya" kawai tace "Amin, Allah yayi Miki Albarka, Ni zan fita in kin shiga ki sanar da su" "Ameen Daddy, tohmm sai ka dawo Allah ya tsare Hanya" Ameen yace ❉❉❉❉ ❉❉❉❉❉ ❉❉❉❉ ABUJA Zaune suke ita da wata budurwa daga gani kasan ƴar ta ce kamar su ɗaya ranta a ɓace daga ni kasan wata maganar suke yi wadda bata jin daɗin ta "Ammi na faɗa Miki ba tun yau ba ki ƙyale su kinki, Ni banga amfanin abinda kike yi ba" "Husna nace ki ƙyale ni dasu, wai kamar ni a ce zai dawo ba'a sanar min ba, sai na Kashe shi kowa ya huta" ta faɗa tana yin kwafa "Ammi baki haife shi ba, mahaifiyarsa na raye ba mutuwa tayi ba, dan zai dawo dole sai an sanar da ke?. Ki daina irin furucin nan kar wani yaji ya zame mana matsala, Ɗan uwan mune fa, wallahi bana jin dadi in kina faɗin zaki kashe shi" "Husna Ni kike faɗa wa waɗannan maganganun?, Na kira ki ne dan ki kwantar min da hankali amma kinzo kina faɗa min wasu maganganu marasa daɗin ji" "Tashi ki fice min daga nan" ta faɗa tana nuna mata Hanyar fita "Ammi ban fadi wata magana dan na ɓata Miki rai ba, Kiyi haƙuri in na faɗi abinda bai Miki daɗi ba" "Ba zaki fitan ba kenan?, To Ni bari in bad Miki ɗakin" ta faɗa tana ƙoƙarin mike wa, da sauri ta tashi ta fice mata a ɗakin. Ta rasa me yake damun mahaifiyar nan tata da komai na gidan sai an sanar mata in ba'a faɗa mata ba ta Ringa ƙorafi "ya kamata in fara binciken mene dalili" take faɗa cikin zuciyar ta............✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/9, 4:10 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟑&𝟑𝟒 _______________________________________________________________________________________ Tana barin gurin Daddy ta nufi ɗakin Aunty suna zaune a Palour'n ta da Mami "Magana dama zamu yi dake Hooriyah" Mami ta faɗa mata "Mami inaji" "Yayan ku ya faɗa Miki Maman ku Safiyya tazo?" A rikeɗe ta kalle ta gumi na keto mata "Tazo? Me tazo yi kuma?" "Tabbas Ta ƙara zuwa, Maganar Auren ki da Sulaiman ce ta kawo ta, tace ba zata taɓa haƙura ba har sai kin Aure shi. In Kuma ba ki Aure shi ba dole kiyi Aure a kankanin lokaci" "Sulaiman kuma Mami? Ai na zata an gama maganar, Mami ya zata ce haka bafa ita take riƙe Ni ba" "A gurin kine ta wuce amma ita a gurin ta tana nan, Kuma ta taso da ita" shiru tayi Aunty ce ta cigaba da magana "Hooriyah wannan yaron da yazo Indai na gari ne ki amince masa kafin ta ƙara dawowa" "ki bashi dama kinji"Aunty ce tayi Maganar "In Sha Allah Aunty zan bi duk abinda kuka zaɓa min, Allah ya sa Haka ne yafi Alkhairi" "Ameen, yanzu ki huta Kafin Yayan ku ya dawo ku tafi" cewar Mami "Ina so Zanje Gidan Khaleesat bayan La'asar mun daɗe baku haɗu ba" "Khaleesat yarinyar kirki Last week ma ta shigo ai, Allah ya kaimu" Aunty ta faɗa "Bama ta faɗan tazo ba, Amin" "Ai nasan ba lallai ta sanar Miki ba" Miƙe wa tayi tana cewa"Bari inje in taya Baaba Aiki" "Ke da zaki huta kyau tafi wani aiki, kije kiyi hutawar ki anjima muyi hirar yaushe gamo" inji Aunty Dariya ta saka sannan ta ce "Bari dai in taya ta daga baya mayi hirar, nayi missing girkin Baaba" ta faɗa tana ficewa. Kitchen ta nufa gurin Baaba ta tarar har ta kusa gama Girkin hirar yaushe gamo suka shiga yi tana miko mata abu kawai ta ringa yi in ta buƙata bayan ta gama girkin tayi mata wanke-wanke da kyar ta yarda cewa tayi ta huta ita da ba zuwa take yi gidan ba yau kuma tazo ai sai ta huta ba tayi ta aiki ba. Bayan Sun gama suka sha hirar su da su Mami sai da Uku ta wuce sannan ta shirya ta nufi gidan Khaleesat. A gidan Khaleesat ma Hirar su suka sha har bayan Isha tana gidan sai da Yaya ya kira sannan ta koma gida Fadil har kuka yayi da zata tafi. Tana shiga gida sallama kawai tayi dasu Mami suka tafi sai faɗa yake tayi dare Bacin yasan ba ita kaɗai zata tafi ba. ✨☆★✨☆★✨☆★✨☆★✨ Bayan Kwana Biyu da zuwan ta gida ya kira ta ya mata bayanin kansa a taƙaice kafin ya zo. Taji ya kwanta mata a rai amma taki amince masa har sai yazo ta Ganshi. 𝗔𝗿𝗼𝘂𝗻𝗱 10:00 𝗣𝗺 Saukowa take daga bene waya take duba wa Palour'n shiru alamun duk yaran sunyi bacci Sajeedah ce kaɗai zaune take kallo zama tayi kusa da ita "Aunty Sannu da Hutawa" "Yauwa, Har kin sauko" "Eh Wlh, Har na kwanta nace bari in zo muyi magana kafin kiyi bacci" "Maganar me zamuyi" "Zaaheed da Daddy ya turo shi ne yace zaizo Ni na rasa yadda zanyi" "Eennyyeeh ashe da gaske yake ya shirya in fara shirin Biki" "Joke apart Aunty" "Kawai kice yazo mana, mene a ciki kawai sasantawa za kuyi musha Biki" "Gani nake kamar shima yaudara ta zaiyi Indai yazo" "Ai baizo ba Koh Balle ki yanke masa hukunci, ki bari yazo sai mu yanke masa hukunci" "Zan sanar da shi" Nan tayi ta bata shawarwari tana ƙara mata wayar mata da kai akan Rayuwa har 12 suna palour sai da Yaya ya sauko sannan kowa ya nufi ɗaki. Ko da ta shiga ɗaki bata kwanta ba salla tayi sannan tayi Addu'a Allah yayi mata zaɓin Alkhairi. 💦◆◇💦◆◇💦◆◇💦◆◇💦 𝟑𝐫𝐝 𝗔𝘃𝗲𝗻𝘂𝗲 𝗔𝘀𝗼𝗸𝗼𝗿𝗼, 𝗔𝗕𝗨𝗝𝗔. Zaune suke a palour su biyu Tsit sai ƙarar A.C ne kaɗai ke tashi shi da wani Babban Mutum ne a zaune a ƙalla zai kai Shekaru 65-70 Fari ne qal kamar Balarabe da gani magana suke mai muhimmanci nisawa yayi Sannan ya cigaba da cewa "ARSHAD ina ganin nan zaka dawo da zama, jikin nan kamar bai gama warke wa ba" "Papi na warke zan iya zama a can Insha Allah" wanda ya kira da Arshad ne ya bashi answer "Bana son kana zama kai kaɗai a gidan tunda mahaifiyar ka ba lafiya ne da ita ba, ba lallai ayi maka komai da kake so ba" "A'a Papi na fison in zauna a can, ina son gano wanda ya saka min guba ne, nasan tunda na tashi yanzu yana son haɗa wani abun kuma"............✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/14, 10:30 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I *🌙MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙* We shine all over the world https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟓&𝟑𝟔 __________________________________________________________________ Ta sanar da shi duk lokacin da ya shirya zai iya zuwa bayan sati ɗaya ya zo. Bayan La'asar ya kira ta gashi ya ƙara so. Sajeedah ce tayi wa maigadi waya ya kaishi guest room mayafi ta saka ta nufi guest room ɗin. Zaune yake yana Facing ɗin Ƙofa Tayi mamakin ganin sa sosai shanye wa tayi bata nuna ba ko a fuska guri ta nema ta zaune nesa da shi gaisawa suka yi cikin mutuncin nan ya fara magana "Nasan kinyi mamakin ganina duk da baki faɗa ba" "Kamar yadda kika sani sunana Zaaheed Lecturer ne a BUK nasan duk kin san wannan" nan yayi tayi mata bayanin sa Ita dai nata ji ne dan har yanzu mamakin sa take daga Ehh sai A'a take bashi answer wani zubin tayi masa shiru, bai jima ba yace mata zai tafi ta raka shi har bakin motar sa sai da ya tafi Sannan ta shige ciki. 💣💥 A palour ta tarar da Sajeedah zaune tana yiwa Fudail aiki zama tayi kusa da ita ta rafka tagumi tun shigowar ta tana lure da ita yanayin ta ya chanja Fudail ta tattara wa Littafin sa tace ya shiga ciki zata zo su ƙara sa aikin "Meya faru na ganki haka" "Aunty Lecturer mune fa, gaskiya Ni ba zan iya ba bashi da mutunci ko na kwabo" "To sai me dan Lecturer kune" "Wlh Aunty ko Lecture zaiyi ya dinga bata rai ga rashin mutunci Ni gaskiya da kyar in zan iya Auran sa" "In da ya sake fuska yanzu da yazo zaki kula shi ne cewa zakiyi yafiya kula ƴanmata ya kame kansa ma bai tsira ba" "Sai Kiyi ta yi ai, karki sake yayanki yaji wannan Maganar balle har ta kai kunnen Daddy dan nasan ranki ne zai ɓaci" "Yanzu kuma sai inyi shiru a cuceni, ba shi da mutunci ko na sisi Wallahi ban taɓa baki labarin abinda yayi wa Anisah ba, one minutes after ya shiga class ta shigo amma korar ta yayi yana faɗa mata magana" "Anisah daban ke daban" dafa kafaɗarta tayi sannan ta cigaba da cewa "ki dai bashi dama har yanzu ki na da chance in Kinga halin shi ɗaya ne dana makarantar sai ki sanar da Daddy" "Ai shikenan, amma" "Amma me kuma kiyi shiru kawai" Kwanciya kawai tayi a kujerar ba tare da ta ƙara ce mata komai ba Befi sau biyu zuwa uku yayi yana zuwa ba aka kawo kuɗi sai dai waya da kullum yake kiranta ba fashi duk da har yanzu cewa take bata sonsa amma tana ganin zata iya Auren sa. An saka Biki six Months ya kama bayan sunyi Graduation da wata biyu za'a yi bikin. 💕 ✿★ ❤️ ✿★💕 Shirye-shiryen exams suke duk sun zama busy itace last exam da zasu yi sun gama makaranta basa son su samu matsala ga bikin Hooriyah da yake ta matsowa saura Three months. Sun yi exams lafiya suka gama lafiya anyi Graduating sai jiran results kuma. ⋇⋆✦⋆⋇ 💫 ⋇⋆✦⋆⋇  𝗡𝗢𝗢𝗥 Tana barin gidan bata nufi ko ina ba sai gidan yayar ta Khairat ta nufa ɗaki ta nufa ta ajiye jakar ta ɗakin Khairat ta shiga ta same ta tana waya jira tayi ta gama sannan tace "Ya gida Yaaya, ina su Hidaya naji gidan shiru" "Suna islamiyya basu taso ba" ta bata answer tana Hararar ta "Yanzu ke Noor ba zaki hakura da Zaaheed ba Kenan, ya nuna baya sonki amma kinki hakura. Yanzu muka gama waya da Mommy tace kiyi zaman ki Anan har sai ta nemi ki"tsaki taja tana tashi "Haba Yaaya ya zaki ce haka shi ya fara nuna yana sona tun muna yara amma kawai yanzu yace ya fasa Bacin yasan irin yadda nake son shi" Tsawa ta daka mata har sai da ta firgita "rufe min baki Shashasha wadda bata kishin kanta kawai" ta ce tana shiga Toilet Anan tayi ta zama har ta fito ta fice daga ɗakin ba tare da ta kalle taba. Sai da ta gaji dan kanta Sannan ta fito ta bata hakuri. A gidan tayi zaman ta bata zuwa ko ina sai makaranta. Tunda taji ankai kuɗin Zaaheed hankalin ta yake a tashe ta rasa inda zata saka kanta tana matuƙar kaunar sa gani take in ba shi ba zata iya rayuwa ba kullum Neman Hanyar da zata Raba Auren take kafin ayi mutane ta ɗauka ayi mata bincike akan Hooriyah amma sun kasa samun wani naƙasu na ta kowa yabon ta yake tana cikin wannan yanayin ta samu Labarin an taɓa fasa Auren ta ranar ɗaurin Aure ango yace ya fasa......✍️ 🏃💨 Anya burin Noor zai cika na mallakar Zaaheed? 👻💕 Ya Rayuwar Anisah take kuwa? 👀📝 Hooriyah zata Auri Zaaheed? Duk waɗannan Answers ɗin suna nan tafe... # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/17, 9:48 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟕&𝟑𝟖 ____________💅_____________ Dole ta nace wa wadda ta sanar mata an fasa Auren Hooriyah sai ta raka ta gidan matar data sanar da ita da kyar da siɗin goshi ta amince tace su shirya suje gobe. Washegari Da sassafe ta tashi ta shirya saboda kar ta makara Shaɗaya nayi ta fice ko sanar da Yaayar ta bata yi ba tayi tafiyar ta lokacin da taje gidan su ko tashi bata yi ba nan tayi ta lallaɓa ta tashirya suka tafi sai mita take ta fiya azarbaɓi Bayan sun gaisa ta ɗora da cewa "Hajiya wannan da kika ga munzo da ita ita ce da zata Auri Zaaheed ƴar uwar sa ce wanda zai Auri Hooriyah yanzu amma ya yaudare ta" "Ayyaahhh ashe ke zai Aura da" cewar matar Jinjina mata kai kawai tayi sai wani kallon banza take watsa wa gidan tana ɓata fuska. Matar ce ta cigaba da cewa "Uhmmmmm, Ni nan da kike gani na ƙanwar mahaifin ta ce, ɗana naso ta Aura amma ubanta yace ba zata aure shi ba, shiyasa nace duk inda naji zata yi aure sai na ɓata Auren don ɗana kaɗai ya dace ta aura tun tana yarinya nayi masa tanadi sai yanzu da ta girma ace ba za'a bashi ba ba zai taɓa yiyuwa ba" Ido Noor ta zaro "ƙanwar mahaifin ta fa kika ce" "Ehhhhhh ko baki ga kama bane" "mun gani Wallahi, Amma kika zaɓi sanar mata da wannan maganar"cewar ƙawar Noor ɗin "Ba ita ba duk wanda zai Auri Hooriyah sai na faɗa masa an taɓa fasa Auren ta ranar ɗaurin aure" Shiru suka yi sai can Noor ta cigaba da cewa"So muke duk wanda yazo tare da Ni Ko ba dani ba Indai yace daga gurin Zaaheed ne kice masa cikin shege tayi asirin ta ya tonu aka fasa Auren, ke kuma ba zaki iya kin fadar gaskiya ba kike tonawa" "Kamar ya kenan ƙarya kuke so inyi gaskiya ba zan iya wannan ba" "Zamu biya ki ko nawa kike so indai zaki faɗi haka" Washe baki tayi taji maganar kuɗi"kace Nima na kusa zuwa Hajj, nasan abinda zan ƙara bayan haka. yaushe zasu zo" inji Aunty Safiyya "ko wane lokaci daga yau zuwa kafin auren, kema burin ki zai cika sai ta Auri ɗanki Nima in Aure shi" Buɗe jakar ta tayi raffer kuɗi ta fito da shi ta miƙa mata "ga wannan mu zamu tafi, so min taɓi ne Indai kika yi abinda muke so zaki samu ninkin su" Karɓa tayi tana ta godiya ta raka su har kofar gida suka yi tafiyar su. Tunda suka tafi take irga kuɗin bakin ta yaƙi rufuwa sai murna take ●○◌ ●○◌ "Arshad tunda ka nace Allah ya tsare ka kawai zance" Amin yace sai kuma yace"Bari in tafi kar suga na daɗe" yana faɗa ya tashi sallama suka yi. Fitowa yayi daga cikin gidan motar sa ya shiga key yayi mata ya fice daga cikin gidan.A hankali ya cigaba da tukin bai nufi ko ina ba sai fada tunda ya shigo ya kula fadar Tsit take Ba mutane da yawa bai kawo komai a ransa ba ya gangara zuwa part ɗin sa Ba kowa a bakin part ɗin na sa ma shiga yayi nan ma ba kowa sai da yaje kofar da zata sada shi da ɗakuna nan ya ga me tsare gurin wuce wa yayi har ya kusa ƙara sawa ɗaki sai kuma ya juyo ko me ya tuna tsaya wa yayi ya fara tambayar wanda yake gurin "Ina suke naga ba kowa" "Yarima Hajiya ce ta suma tun ɗazu suna can" "Ta suma kuma? bata da lafiya ne?".............✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/18, 7:35 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟑𝟗&𝟒𝟎 __________________________________________________________________________________________ "Haka dai ake ta faɗa Yarima" "Tun yaushe ta suma ba'a sanar dani ba?" "To nidai bana ce ba" "Amma naji ance" da sauri ya juya batare da ya jira Abinda zai ƙara faɗa ba duk da nisan dake tsakanin su a ƙafa ya tafi. Kofar part ɗin nata cike da Hadimai Suna ganin shi suka hau gyara masa yana shigewa. A zaune kan gado ya tarar da ita gefan ta mai martaba ne sai doctors guda biyu mata Mai martaba ya kalla sannan yace masa "Me ya faru da Ammi aka ce ta suma, dama bata da lafiya ne baka faɗan ba?" "Ba abinda ya faru Arshad" matar da ke zaune ta faɗa A bazata yaji ta bashi answer hankalin sa ya dawo da shi kanta gaba ɗaya sai yace"Ammi kin warke yanzu kina iya magana kina jin abinda nake faɗa" ya faɗa yana riƙe hannun ta kuka na kufce masa "Na warke Arshad, matso kusa dani" Matsowa yayi ya rungume ta. Hannu tasa tana share masa hawayen Fuskar. Waye Yarima Arshad??? 💦💥🤍 Tana dire ta a gida sai ta wuce gidan su Zaaheed maimakon gidan Khairat a cikin bedroom ta tarar da Mommy'n su Zaaheed gaishe ta tayi "Ohhh Noor kin guje mu ko zuwa bakya yi" "Mommy makaranta ce ta boye ni yanzu ma wani labari naji nace sai na sanar da ke bazan ɓoye miki ba" "Me ya faru kuma Noor" "Akan matar da Yah Zaaheed ya kawo ne" Bata rai tayi don ta tsani a kawo wata banzar magana akan Matar da Zaaheed zai Aura "Noor kenan duk ana ta zuwa ana faɗan zasu maganganu amma ba zan saurare su ba nace, inaji ke kuma me ya faru kika zo?" "Wallahi Mommy yah Zaaheed yana cikin Matsala Indai ya Auri Yarinyar nan bata da tarbiyya ko kaɗan" Nan ta sanar da ita komai har da ƙarin ƙarya "Innalillahi wainnaillaihir-rajiun, anya Noor ba ita ba ce Yarinyar kirki ce fa wannan, Innnnaa gaskiya ba ita ba ce" "Wallahi Mommy ita ce ban sanar da kowa ba sai da nake har gidan matar na tabbatar ta ƙara da ce min ƙanwar mahaifin Hooriyah ce" "A ina take" "Bata da nisa sosai" "Bari in ɗauko mayafi ai zama ban ganni ba inje in tabbatar da kaina" tace tana miƙewa zuwa ɗaki. Dariya Noor ta kwashe da ita bayan wucewar ta "Tunda kunki bari na Aure shi ta lallami ai yanzu na Aure shi ta tsiya yah Zaaheed nawa ne Ni kaɗai banda ko wacce mace" Fitowar Mommy ce ta saka ta yin shiru"tashi mu tafi Koh" cewar Mommy da sauri ta tashi suka fice. 🌟🌟🌟 🌟🌟🌟 🌟🌟🌟 A kofar Gidan Aunty Safiyya tayi parking motar kallon Mommy tayi sannan tace "Mommy mun ƙaraso" "Nan ne" Ehh tace tana fito wa daga motar shiga ciki suka yi a tsakar gida suka tarar da Aunty Safiyya maraba tayi musu tace su shiga daga ciki palour ta kaisu ta kawo musu ruwa Sannan ta zauna "Hajiya sannu da zuwa" "Sannun mu" "Wannan Maman Zaaheed ce tazo jin gaskiyar lamarin" cewar Noor Washe baki ta ƙara"Sannu dai Hajiya" Shiru Mommy tayi bata answer mata ba Noor ce ta cigaba da cewa"ki sanar da ita ba hira ba sauri muke" "Toh toh" nan ta sanar da ita kamar yadda Noor ta faɗa mata "Kiji tsoron Allah karki mata sharri "Ƴa tace fa Hajiya kina ganin zan mata sharri? To kije duk inda zaki ki tambaya ki ji wannan Labarin za'a sanar Miki ɓoyewa suke kawai ba sa so a sani" nisawa tayi sannan ta cigaba da cewa "Ba zan rufe miki ba har zubar da ciki ta taɓa yi" Salati Mommy ta saka tana rufe baki "Amma shine suka liƙa masa Ita sun san bata da tarbiyya" "Innnnaa ba zai yu ba, Noor tashi mu tafi" tana miƙewa da sauri. Zuciyar Noor fess dan daɗi dan tasan Aure ba zai yi ba angama wannan kuma. 🌞 Kaikawo take yi a palour buɗe Kofar aka yi gaba ɗayan ta tajuya "Gwara daka ƙara so, dan yanzu nake shirin ƙara kiran ka" "Me kuma ya faru kin ɗagan hankali ina cikin meeting" "Maganar Auren Zaaheed ne an fasa dan bazan yarda ɗana ya Auri ƴar iska ba" "Kamar ya? Wace ƴar iskar?" "Ita yarinyar da kake nema masa Aure "Wallahi Alhaji ba zai Aure ta ba Hauka ake yarinya har ciki ta zubar amma su ɓoye mana" "Calm down mana ki tsaya a kira su muji dalilin daya sa suka ɓoye mana wannan babban al'amarin" "A kira su? Tsoron su ma ake ji kenan, ai kawai an fasa" wayar ta ta janyo number ta lallubo ta dana kira "Wa kuma zaki kira?" Buɗe baki tayi zata bashi answer aka Ɗaga kiran "Kana ina" tace wa wanda ya answer kiran "Kazo yanzu ina jiran ka a palour" ta faɗa tana katse kira................✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/19, 4:00 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟏&𝟒𝟐 ________________________________________________________________________________________ Kaikawon ta cigaba da yi ba jima wa sai gashi ya turo Kofar Palour ganin su a tsaitsaye ya tsorata shi ƙara so wa yayi ko zama baiyi ba tace "Na soke Auran ka da wannan Yarinyar "Mommy me Hooriyah tayi miki?" "Sai ta min wani abu zan soke Auran?, Na samu labarin bata da tarbiyya ne har ciki ta zubar" "Innalillahi wainnaillaihir-rajiun, ciki kuma Mommy ciki dai dana sani?" "Ehh shi cikin, kuma suka ɓoye mana, kasan ma an taɓa fasa Auren ta?" "Mommy masan wannan" "Kasan da shi amma ka tafi neman auren ta ba bincike, shine dalilin da yasa wancan mijin ya gudu yace ya fasa" "Mommy Abiee fa yasan mahaifin ta kowa ya mata shaidar arziki a makaranta babu ruwan ta da kowa, amma ce min aka yi Ƙawar tace ta yaudareta ta Aure shi" "Kabar wani zagaye zagaye kawai an fasa Aure kirata ka sanar mata" "Wait haka kawai zamu kira su muce mun fasa haka ake yi, bayan mu muka je neman Auren, baku da hankali ne" cewar Abiee "Nasan Hooriyah ba zata aikata wannan laifin ba, in ma ta aika ta Abiee Ni Ko a haka inason ta zan iya Auren ta" "Ku bari mu kira su muji gaskiyar lamari da dalilin kin faɗa mana" "Abiee ta sanar dani, kuma Nima tun kafin ta faɗa min na Sani an fasa auren ne saboda ƙawarta ta Aure shi" "Wallahi Indai baka bar Maganar yarinyar nan ba zan tsine maka, haka kawai ka janyo mana jaraba a gida" "Waya sanar dake ma wannan zancen" "ƙanwar mahaifin ta ce ta sanar dani ba wani ba" "Ƙanwar Mahaifi kai ina sai dai wata, amma wace ƙanwar mahaifin ce zata so a fasa auren ƴar danuwan ta" Nan ta sanar dasu yadda suka yi da Aunty Safiyya "Tirkashi" shine abinda Abiee kawai yace Da sauri Zaaheed ya ce"Wallahi Abiee ƙarya take matar nan maybe ma bata san ta ba" "Kai a ina Kasan haka" "Jiki na ne ya bani haka Abiee amma Bari in kira ta in tabbatar" "Ba sai ka kira ta ba ma. Gwara in sanar da kai kasani Ranar Friday za'a ɗaura maka Aure kowa ya huta. A bar zancen Hooriyah take ko wa, ohhho kai ka kasani" "Aure kuma Mommy? Dawa?" "Ehh Aure da Noor ina ce ƴar Uwar ka ce tafi baren nan da kake jajiɓo mana" "Amma" ɗaga masa hannu tayi tana ƙara bata rai "Dakata Zaaheed kai ka haife mu ko mu muka haife ka da ba za muyi maka umarni ba, na gama magana tashi ka bani guri" Tashi yayi ya fice. Nan tayi ta famfa Abiee har sai da ya kira gidan su Hooriyah aka sanar da su sun fasa Auren. 💥🌟✨ Sun shiga matukar rudani jin an ƙara fasa Auren kuma sun ki sanar musu dalili ga gobe za'a kawo lefe ba shiri Daddy ya nemo Abduljawwad ya sanar da shi neman layin Hooriyah ya shiga amma baya samu sai ya yanke shawarar kiran Sajeedah ta haɗa shi da Hooriyah. Aiki suke ta yi gobe za'a kawo lefe duk matan Yayyen ta suna gidan Tun safe wayar ta ta ɗauko missed Call gurin ashirin kuma duk Zaaheed kiran sa tayi baiyi picking ba kawai ta ƙyale shi maybe Yana lecture ne. Sajeedah ce ta shigo "Nan kika dawo kuma" "Eh na gaji ne hutawa zanyi sai na fito" "Yayan kine ya ke ta kira wai ya kira baki ɗaga ba yace in haɗa ki da shi" "Banga kiran ba ma, To Allah yasa lafiya" "Gashi ki kira shi" ta faɗa tana miƙa mata wayar zama tayi kusa da ita "Ina ta kira ba kya ɗagawa" "Yaya banga kiran bane" ta bashi amsa "Zaaheed ya kira kine" "Eh" "Yaushe? Ba abinda yace Miki" "Missed Call kawai na tarar Yaya" "Shikenan, inya kira karki ɗaga kinji Koh" "Tohmm" tace masa ta katse kiran. Tashi tayi ta miƙa wa Sajeedah wayar ta dawo ta zauna tana sanar da ita abinda yace "Saboda me zaice karki ɗaga" "Aunty bai sanar min ba" "Kawai ƙyale shi in ya kira ki ɗaga sai kice baki ɗaga ba" Suna cikin maganar sai ga kira yana shigowa Sajeedah ce tace "Wa yake kira" Janyo wayar tayi ta duba sai tace mata "Zaaheed ne, ga yaya yace kar in ɗaga, ban san meyasa ba" "Ɗaga kawai ki rabu dashi yasan kin ɗaga" "Kar yaji yayi faɗa fa" "Ki ɗaga kawai ai ba sani yayi ba sai dai in ke zaki faɗa masa" "Bama zan faɗa masa ba Insha Allah" tace tana daga wa muyar mace taji maimakon ta Zaaheed ɗin "Ana ta Murna an samu ɗan Masu kuɗi za'a Aura Koh? "Please wace?" "Bashi yasa na kira ki ba, kin san Zaaheed ya fasa Auren ki?" "Kamar ya?" "Auuuuu Ashe bai sanar da ke ba to bari in sanar da ke ya fasa Auren ki, ranar Friday zamu yi Aure da shi" Wayar ce ta fadi daga hannun ta abinda yaja hankalin Sajeedah da take wa Batool wasa ajiye Batool ɗin tayi tana tashi da Sauri ƙara so wa kusa da ita tayi tana dafa ta sai kuma tace mata "me ya faru kuma?" "An kuma fasa Auren Innalillahi wainnaillaihir-rajiun" kawai tace mata tafiya tayi luuuuuuuu ta faɗi sumammiya.....................✍️ Wasssh na gaji 😂 inga ruwan Comments da Like Much Kauna mutanen Amana😍✨ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/21, 12:27 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟑&𝟒𝟒 ___________________________________________________________ 𝐍𝐎𝐎𝐑 Tana daga cikin ɗaki take jiyo hayaniyar su abinda yaja hankalin ta kenan ta fito a bakin ƙofar ɗakin Mommy ta tsaya tana jinsu jin maganar Zaaheed ya Aure ta aka yi ya sata daka tsalle da yake tana nesa dasu basu jiyo ba da sauri ta shige ɗakin ta tana murna wayar ta ta ɗauko rasa wa zata fara faɗa wa wannan Albishir ɗin tayi sai daga can tayi dailing number ta kira ringing uku ta ɗaga "Bestie Albishirin ki" ta faɗa da sauri ba tare da ko sun gaisa ba "Goro" aka bata amsa daga can "Ranar Friday ɗaurin Aure na" tace cikin zumuɗin ta "Da gaske, wa zaki Aura?" "Wallahi yanzu ake sanar dani, Masoyi na mana" "Kina nufin Zaaheed, But How comes?" "Eh shi" nan ta kwashe labarin komai ta sanar mata "Kai amma bestie kin iya makirci" "Bawan nan ba shawara nake so ki bani" "Wace irin shawara kuma bayan kin samu abinda kike so ɗaurin Aure kawai ya rage" "Da saura fa, so nake Ni in sanar mata ya fasa auren ta tunda shi yaƙi amma na rasa wace hanya zanbi in faɗa mata" "Baki da number ta?" "Allah ya kiyaye me zanyi da number ta" "Bari kiji wata shawara..." Faɗa mata shawarar tayi "Wow amazing, banyi tunanin wannan Bama" "Gashi yanzu na sanar dake" "Bari inyi sauri kafin ya fice" "Ok sai na jiki" ta katse wayar Ajiye wayar tayi tana miƙewa dan ta aiwatar ta abinda ƙawarta ta sanar mata Part ɗin Zaaheed ta nufa baya palour sai wayar da kawai ta gani ɗauka tayi ta koma cikin gidan ɗakinta ta nufa sun card ɗin sa ta cire ta saka a wayar ta ta ɗau nata ta saka masa komawa tayi ta ajiye masa wayar tasa ta koma ɗakin ta number Hooriyah tayi ta kira bata ɗaga ba ƙara kira tayi nan ma bata daga ba ta kira ya kusa sai ashirin ganin ba'a ɗaga ba yasa ta ajiye wayar ta shiga wani abin baifi awa biyu ba sai ga Hooriyah ta kira sai da ta bari ta katse sannan ta kira ta sanar mata tana gama faɗa mata tayi dariya sai tace "Mayya abi wani kuma ba dai Yah Zaaheed ba dan nawa ne" "Nan da Friday na zama tashi ya zama nawa, Daɗi kashe Ni, yanzu da banbi wannan hanyar ba sai dai ya subucemin Allah na gode maka" ta faɗa tana sakin wani malalacin murmushi. Da sauri ta tashi maida masa sim card ɗinsa sai ta dawo ta zauna Aunty Safiyya ce ta faɗo mata a rai "Ya kamata inje in sallami matar nan kar ta tona asirin ba'a ɗaura ba" ta ce tana tashi. Yanzu ma Palour'n ba kowa dan haka ficewar ta tayi bata sanarwar Mommy ba. Gidan Aunty Safiyya taje sallame ta. Gida ta nufa dan ta huta sai ta fara shirin biki kuma... 💥💫 H̶O̶O̶R̶I̶Y̶A̶H̶ Sajeedah hankalin ta tashi yayi rasa abinda zata yi tayi sai can shawara ta faɗo mata kwantar da ita tayi buɗe fridge tayi ruwa mai sanyi ta ɗauko tana kwara mata shiru bata motsa ba hankalin ta ƙara tashi yayi ƙara kwara mata ruwan tayi atishawa ta saka tana buɗe idon ta nan abinda ya faru ya dawo mata Kuka ta saki riƙe ta Sajeedah tayi tana bata haƙuri "Aunty shima ya fasa da gaske Koh?" Shirun da Sajeedah ta mata ne ya sata ƙara cewa "Ni kuma yawa ƙaddarar Kenan, sai anzo Aure sai suce sun fasa" "Ki daina faɗin haka mana, shi ya faɗa Miki ne?" "Wata ce kuma cewa tayi ita zai Aura ranar Friday" "Kiyi shiru kar yayanki yazo ya ga kina kuka bayan yace karki ɗaga kiran sa" "Ashe abinda Yaya ji kenan yake son ɓoye min, baya san tashin hankali na Aunty Nima bazan tayar masa da hankali ba Insha Allah zan dau Ƙaddara ta" "Nace ki daina faɗin haka, Kiyi shiru ko yazo kar ki nuna masa kin ji sai muji abinda zaice" kai ta gyaɗa mata "Yauwa tashi ki wanke fuskar, by now Yana Hanya kar yazo" Toilet ta shiga ta wanke fuskar powder Sajeedah ta miƙa mata "me zanyi da ita?" "Goge Fuskar zaki yi ko sai ya gane kin ji" Karɓa tayi ta goge fuskar. Fita Sajeedah tayi ba jima wa sai gata da kwalli miƙa mata tayi tana cewa "ungo saka har yanzu ana ganewa kinyi kuka" Sakawa tayi badan ranta yaso ba. Sauka kasa suka yi dan kar a zargi wani abin kuma...............✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟓&𝟒𝟔 ___________________________________________________________________________ Aminu Abubakar Muhammad (Arshad) shine Cikekken sunan shi Haifaffen Garin Abuja ɗa ɗaya tilo da Allah ya bawa Mahaifiyar sa shekarar sa Talatin da Biyar a duniya yana da ƙane guda biyu mata ƴaƴan Kishiyar Ummi'nsa. Kyakkyawa ne ajin Farko tsayawa kamanta muku kamarsa ma ɓata lokaci ne. *𝐾𝑎𝑟𝑠ℎ𝑒 𝑛𝑒 𝑎 𝑔𝑢𝑛 𝑘𝑦𝑎𝑢 𝑘𝑢 𝑎𝑦𝑦𝑎𝑛𝑜 𝑑𝑢𝑘 𝑘𝑦𝑎𝑛 𝑑𝑢𝑛𝑖𝑦𝑎 𝑘𝑢 𝑎𝑧𝑎 𝑚𝑎𝑠𝑎 𝑦𝑎 𝑘𝑎𝑖 ℎ𝑎𝑟 𝑦𝑎 𝑘𝑢𝑠𝑎 𝑤𝑢𝑐𝑒𝑤𝑎😂💔* Alhaji Abubakar Muhammad Sarki mai ci a garin Abuja Matan sa Biyu Hajiya Abeedah ita ce Uwargida Ba ƴar Nigeria bace a Saudiyya take ya Aure ta suka dawo Nigeria ɗa ɗaya ta haifa Arshad daga shi bata kuma haihuwa ba. Yana ce mata Ammi. Abeedah bata da matsala kowa nata ne a gidan bata da abokin faɗa. Shekarar Arshad Goma a duniya Sarki ya ƙara Aure ya auri Hajiya Kareema sai da ta shekara Biyar da aure Sannan Allah ya bata haihuwa ta haifi Asma'u Husna sai ƙanwar ta Zainab tun daga lokacin haihuwa ta tsaya a gidan ba wacce ta sake haihuwa. Kareema ƴar uwar sa ce da Akwai ɗagawa da girman kai bata son raini ga ta tsani Abeedah bata shiri da ita ko tafiya take ta hango Abeedah chanja hanya take dan kar su gaisa taso Aurar Abubakar tun kafin ya haɗu da Abeedah amma yaƙi sai daga baya ya Aure ta. Yayi karatun sa ƙasar Indai inda ya karanci medicine yana aiki a National Hospital Abuja. Babban likita ne da ake ji da shi a Asibitin suna jin daɗin aiki da shi. Tun yana ɗan shekara Ashirin Ammi ta kamu da lalura rana tsaka ta daina ji ta daina magana sun shiga tashin hankali Babba nan aka fara neman magani amma shiru an fita da ita daga kasar maimakon samun sauƙi sau larura ta ƙaru ta daina gani gaba ɗaya. Haƙura suka yi da Asibiti suka koma gida ana yi mata addu'a amma shiru bata warke ba. Tun daga lokacin komai nashi ya tsaya shi yake wa Ammi'nsa duk wani abu sai masu aikin ta da suke taya shi bashi da lokacin kowa aikin da yake yi ma ajiye sa yayi har sai ta warke. Ƴanmata da yawa suna kawo kansu ya Aure su wasu kuma Iyayen sune suke kawo su tun yana sauraren su har ya daina Sarki ya kira shi yayi masa faɗa amma yace shi duk basu yi masa ba basu da tarbiyya a karshe sarki ya goya masa baya duk lokacin ɗaya kawo wadda yake so yaga zai iya zama da ita yayi Aure. Komawar sa India wani ne a cikin gidan ya zuba masa guba a abinci yaci yasha wahala sosai Kamar bazai rayu ba har sai daya tafi India jinya. Wannan kenan. 𝔸𝑵Ɩ𝘚𝔸Η Rayuwa tayi mata zafi ga ciki ga rashin mutunci kala-kala da ya fito da shi da duk baya mata sai yanzu halin sa mara kyau yake fito wa. Wani lokacin ko makaranta baya barin ta taje a haka dai aka ƙara sa lokacin Graduation da kyar ya barta taje yanzu bashi da aiki sai zancen zai ƙara Aure kullum zancen sa kenan zai samo wadda ta fita komai ga Ummanta ba lafiya ya hana ta zuwa duba ta ko ta faɗa wa iyayensa sai suce Aure dan hakuri ne kowa haka yake yi basa ganin laifin sa kwata-kwata komai yayi dai-dai ne a gun su suna matuƙar ƙaunar sa. Tun safe ake kiran ta daga unguwar su tazo jikin Ummanta yayi tsanani sai kiran sunan ta take yanzu ma zaune take a palour ta buga uban tagumi kira ne ya shigo wayar da Sauri ta daga ganin ƴan unguwar tasu ne bansan abinda ake faɗa mata ba kawai ta zaro ido tana cewa "Ta mutu fa kika ce, Innalillahi wainnaillaihir-rajiun, na shiga Uku"...................✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟕&𝟒𝟖 __________________________________________________________________________________ Wayar ce ta faɗi kasa faɗa wa tayi ragab akan kujerar hawaye ne ya fara zubo mata surutai ta fara"Umma ta rasu, Ummana fa itace ta rasu" neman wayar Tata ta fara yi a kasa ta ganta number Zaid tayi dailing yana ɗagawa tace "Allah ya isa mugu ka cuceni ka hanani zuwa Duba Ummata gashi har ta rasu banje ba" wani kukan ne ya ƙara kufce mata ajiye wayar tayi ba tare da ta kashe ba bedroom ɗin ta ta nufa mayafi da key ɗin Mota ta ɗauko rufe gidan tayi ta fice a guje. Hanyar babu kowa dan haka ta samu damar sharara gudu san ranta ƙatuwar trailer ce ta taho itama gudu take sharara wa kanta tayo gadan-gadan kafin ta farga Ta kauce mata har tayi gaba da ita. ✨😍✨ A bangaren Hooriyah kuwa kwanciyar ta tayi a palour Sajeedah ta shiga kitchen cigaba da taya su aiki. Yana shigowa gidan ya san ta sani amma ya basar tashin ta yayi zama tayi tana ƙaƙalo murmushi "Yau da wuri ka dawo" ƙoƙarin rufe damuwar ta sake yi "Sannu da zuwa Yaya" "Yauwa, ɗauko mayafinki zamu je gida" "Yaya gida kuma, ai ba sai mun wahalar da kanmu zuwa gida ba dan ku sanar da Ni na riga da na sani" ta faɗa tana aro jarumta dan kar ya gane tana cikin tashin hankali "Kin sani fa kike ce" gyaɗa masa kai tayi "Eh Yaya Aunty ma ta sani, kaga babu maganar muje gida wahalar da kanmu na ɗauki ƙaddara Allah yasa haka ya zame min alkhairi" Jikin sa ne yayi sanyi jin abinda ya fada tashi yayi ya barta a gurin Kitchen ya nufa inda yaji hayaniyar su aiki ya tarar da su suna tayi Sajeedah yayi wa alamu ko ta sanar da su ta girgiza kai "An fasa Auren ku daina wahalar da kanku, abinda baku yi ba kawai ku barshi" yace musu kawai Gurin lokacin ɗaya hankulan su ya dawo kansa "An fasa fa kace?" Suka haɗa baki gurin faɗa... 💥💥💥 Tunda ta samu Labarin farkawar Abeedah hankalin ta yake a tashe waya take ta yi amma anki ɗagawa ta rasa yadda zata yi sai zuwa ake yi mata murna sai yanzu ta samu damar kebe wa amma anki ɗaga kiran. 💦💦💦 Rungume ta shima yayi har gurin minti goma sannan ya cika ta maimarta ba ne yayi gyaran Murya "Abeedah muna son jin abinda ya faru dake" sarki ya faɗa "Zan sanar wa Arshad sai ya faɗa muku" ta fadi tana ɗauke kanta. Tunda ta farka haushin shi take ji gani take kamar ya Aure ta bata da mai bata amsa ta sai Arshad shiyasa take so ya basu guri tayi magana da ɗanta Jinjina kai yayi sai kuma ya kalli waziri yace masa "A sanar da kowa gobe karfe goma suzo fada ina neman su, Allah ya ƙara Afuwa" yana gama faɗa suka fice Har dare yana tare da ita da hadimai tana son suyi magana amma ta kasa cewa su fita su basu guri sai haƙura tayi. sallah ce kaɗai take fitar da shi gani yake kamar in ya fita kafin ya dawo ta koma yadda take ada. Washegari Zaune suke a fada kowa na family ya hallara Abeedah kawai ake jira ta fara magana ƙasa ta ƙara yi da kanta tana share hawayen ta Yana Zaune a kusa da ita ƙara Riƙe hannun ta yayi yana magana "Ammi ki daina kuka, ki sanar mana abinda aka yi miki dan Allah, ance kin sani ya kamata ki sanar mana ko zamu fita daga rudanin nan" Magana ta fara kamar haka: ᴡᴀɪᴡᴀʏᴇ Ranar wata Laraba da safe ina zagaye kamar yadda nake yi kowane lokaci naji Habiba tana waya a bayan garden kasa kunne nayi na saurari maganar da take faɗa "So nake a kashe miji na, kasan nayi ƙoƙarin zama da shi na tsawon shekarun nan, kuma karka manta a dasawa sarki sona a saka tsanar matar sa da ɗansa a zuciyar sa yadda ina gama takaba zai Aure Ni" dan jimm tayi tana jiran amsar da ake bata sai kuma ta cigaba da cewa "Ai ita bai damu da itaba kamar Abeedah daga ita har ƴaƴan nata ba wani sonsu yake ba kaga bani da matsala da su, in na shiga zan saka ya sake ta" Jin abinda take faɗa yayi matuƙar tayar mata da hankali ai bata jira ta gama maganar ba a fusace ta hau cewa "Yanzu yadda muke da ke Habiba abinda kike min kenan? Duk yadda da amanar da na baki? Habiba bani da kamar ki duk gidan nan amma sakayar da zaki nuna min kenan" A firgice ta juya ba tare da ta kashe wayar ba dan bata yi tsammanin wani yana jin ta ba "So kike in cigaba da zama a ƙarƙashin ki ba cigaba kullum sai ci baya, kin san ina son mijin ki amma kika sa aka Aura min Hakimi. Sarki nake so ba Hakimi ba kin sani" "Dan shi kike so shine zaki yi wannan abin? Ai ko sai kowa yasan abin nan" ta ce tana saurin juya wa da sauri ta shaƙo wuyan ta "Ba sai kin ƙara magana ba sannan zaki tona min asiri? ɗan naki ma da kike tutiya da shi raba ku zanyi kowa ya huta" ta faɗa ta sakar mata wuya tare da wucewar ta Ɗaki Nima na koma da zummar idan Arshad ya shigo in sanar masa amma tunda ya shigo nake kokarin yin magana na kasa. Shine abinda ya faru tun daga nan na daina ji kuna ta zargin Kareema bata da laifi ko kaɗan nasha bibiyar rayuwar ta inga ko tana wani abu mara kyau amma ban taɓa kamata ba kawai faɗa ne da yayi mata yawa. **** Share hawaye ta tayi bayan ta gama basu labarin kowa jinjina lamarin yake matar da take simi-simi bata da hayaniya ba ruwanta da kowa ko faɗa ba tayi amma itace da wannan aikin. Mijin ta ne ya mike da sauri jikin sa sai tsuma yake yi inda take ya nufa yana ɗauke ta da mari Sannan ya cigaba da cewa "Amma kin cuceni kin ɓata sunan gidan mu, Aure na da ke ya ƙare. Bari Ni in fara Kashe ki kafin ki kashe ni"ya faɗa yana shaƙo wuyan ta...................✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟒𝟗&𝟓𝟎 ———————————————————————————————————————— Sarki ne yayi masa magana da kyar ya sake ta sai kakari take duk ta shiɗe ruwa aka bata ta sha tana ta nishi "Me yasa kika yi wannan laifin" Sarki ya jefo mata Tambayar "Bayan kasan yadda nake sonka tun kafin kayi Auren fari, nayi ƙoƙarin danne san da nake maka in zauna da wanda ka Aura min amma na kasa ƙawata ta bani shawarar bin malaman za'a samo kanka har ka amince ka Aure Ni wallahi ranar da taji ina waya ranar ne na biyu dana kirashi jin zata tona min asiri yasa nace ya rufe bakin ta amma sai ya kurmantar da ita ya makanta ta na tsoro ta ƙwarai da lamarin tunda na gane ba Aure na zaka yi ba na tuba na ƙyale ta ban ƙara neman wani abu a gurin saba. Dan Allah ku yafe min" "Wane tuba, kin cuceni ana ta zargi na, kuma ai Nima ke kika zo 𝒕𝒂𝒏𝒂 𝒃𝒊𝒏 𝒎𝒂𝒍𝒂𝒎𝒂𝒊 𝒅𝒂𝒏 𝒕𝒂 𝒓𝒂𝒃𝒂 𝒎𝒖 Ni kuma na tada hankalina na daina kula ta Ashe karya kike" Kareema ta faɗa kamar zata dake ta "Ni kuma?" "Eh ke din zan Miki karya ne" Kareema ta ƙara faɗa tana huci "Dama ance rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tame kaya, Sharrin Shaidan ne yasa na faɗa Miki haka Amma Abeedah mutuniyar kirki ce na sani kawai dan ku rabu ne yasa na faɗa Miki haka" ta faɗa tana rushewa da kuka "Kuyi hakuri na tuba, Abeedah ki yafe min dan Allah" ta faɗa tana tasowa zuwa gurin Abeedah hannunta tazo kamawa zata riƙe Arshad ya buge shi "Me kuma zaki yi mata" ya faɗa yana tsareta da ido Kwarjini taga yayi mata ƙasa tayi da kanta "Haƙuri zan bata kawai" "Ki bata daga inda kike ko wani abin zaki ƙara yi mata" "A'a Arshad dan Allah ka bata hakuri wallahi nayi nadama" Papi ne yayi gyaran Murya (𝒎𝒂𝒉𝒂𝒊𝒇𝒊𝒏 𝑨𝒎𝒎𝒊 𝒏𝒆) "duk abinda ya faru ya riga da ya faru Allah yasa bata yi kisan ba, Abeedah ki yafe mata munji Uzurin ta sai ayi mata Alfarma tunda bata kai ga aikata laifin ba, Allah ya yafe mana baki ɗaya" "Alhaji dole ayi mata hukunci" cewar Hakimi "Papi nakasar da Ammi da tayi kuma ya tafi a banza?" Cewar Arshad "Duk wanda aka yi wa laifi kaga an bashi hakuri to an cuce shi ne, ba ga sakayya nan Allah ya mata ai bata Auri Abubakar ɗin da take so ba" "Allah ya yafe mana baki ɗaya" cewar Ammi Da Amin aka yi ta amsawa Da kyar aka lallashi Hakimi ya haƙura ba sai anyi hukunci ba amma ya sake ta sai cewa yake sai anyi mata hukunci Ta inda yaji daɗi bashi da zuri'a ko ɗaya da ita. Kamar jira mutane suke su gama zaman zancen ya fara zagaye gidan Mutane sai Allah wadai suke yi mata, wadda ta riƙe ki amana tun shekaru da yawa ita zaki cuta. 🅩🅐🅐🅗🅔🅔🅓 Tunda Mommy'n su ta yanke wannan hukuncin yake jin ba daɗi Baya son Noor ko kaɗan kallon kwanwa yake yi mata Kulle kanshi yayi a ɗaki ya daina cin abinci dan Mommy'n ta gane baya son Noor Amma ta masa banza ta nuna bata san abinda yake ba ganin ba mafita bace yasa shi yanke shawarar tunkarar ta ya sanar mata shi baya sonta taje ta nemi dai-dai da ita. Bayan La'asar ya shirya ya nufi gidan su Noor yana zuwa ko ciki bai shiga ba yasa maigadin su yi masa sallama da ita ciki ya shiga a palour ya tarar da Mummy ita kaɗai gaishe ta yayi sannan yace "Hajiya ana sallama da Noor a waje" "Sallama kuma?, Su Waye? Basu san Gobe ne Auren ta ba" "Ai Angon ne yazo yana waje" ya faɗa yana washe baki sai kace wanda aka bawa Kujerar Hajj😂💔 "Zaaheed ɗin mai yasa bai shigo ba" "Hajiya cewa yayi sauri yake" "Je kace masa gata nan zuwa" "Tohm Hajiya Allah ya ƙara girma" ya faɗa da Sauri yana ficewa Tashi tayi ta shiga ɗakin Noor tana zaune a kan gado waya take yi ganin Mom ne yasa ta katse kiran kana ganin ta kaga Amarya an fara gyaran jiki ta ƙara yin wani kyau ga kamshi sai tashi yake a jikin ta Mummy ce tace "Kizo Zaaheed ne yazo yana jiran ki" "Mummy Zaaheed ɗina, gani nan zuwa" ta faɗa tana tashi Drawer ta buɗe ta ɗauko Hijab sakawa tayi ta fice jikin ta sai rawa yake 𝐾𝑒𝑑𝑎 𝐴𝑛𝑔𝑜 𝑘𝑜 𝑎𝑚𝑖𝑛𝑐𝑒𝑤𝑎 𝑏𝑎𝑖𝑦𝑖 𝑏𝑎 𝑘𝑖𝑘𝑒 𝑔𝑦𝑎𝑟𝑎𝑛 𝑗𝑖𝑘𝑖 𝐻𝑎𝑏𝑎 𝑁𝑜𝑜𝑟 𝑑𝑖𝑛 𝑚𝑢 𝑦𝑎 𝑧𝑎𝑘𝑖 𝑏𝑎𝑑𝑎 𝑚𝑢🤣🤣🤣😂😂 A tsaye ta tarar da shi jikin Motar sa ransa a dagule tafiyarta ta gyara tana takun jan Aji Muryarta ta ƙaryar "Yayana, Habiebie 🤍 yaushe kazo? Me yasa baka shiga daga ciki ba?" A fusace ya ɗago yana Nuna ta da yatsa " Ke Noor Ba wannan ne ya kawo Ni ba ki dakata, zuwa nayi na faɗa miki ki sanar musu kar su sake su Ɗaura Auren nan dan sai kinyi dana sani tunda aka raba Ni da Hooriyah babu wata mace da zata same ni yanzu" ya faɗa yana watsa mata wani kallon banza tare da shigewa motar sa yayi tafiyar sa. Sagadee ta bishi da kallo zuciyar ta kamar zata fito Aa koma cikin gidan... 𝑯𝑶𝑶𝑹𝑰𝒀𝑨𝑯 A bangaren Hooriyah kuwa Depression ne mai tsanani ya kamata ba Abinda yake ɗaga mata hankali sai jin wai har ciki ta zubar shiyasa aka fasa Aure na farko ita da ko riƙe hannun namiji bata taɓa yi ba Indai ba Yayyun ta ba duk wanda yayi mata sharrin nan bazata yafe masa ba ya shafa mata tabon da ba zai taɓa goguwa ba. Bata tabbatar da tana son Zaaheed ba sai yanzu bata da aiki kullum tana cikin damuwa magana ma sai Sajeedah ta saka ta a gaba take yi ga kusan kullum sai ya kira ta Shiyasa ta kashe wayar tunda Auren shi saura kwana Uku. Tattarawa tayi take gida tayi musu kwana biyu ko zata samu sauƙin abinda take ji amma sai yafi da ƙaruwa dole ta dawo Gidan Sajeedah. Anyi wa Abduljawwad Transfer zuwa Abuja a gurin aiki kuma dole a cikin satin zai koma Dan haka suka fara Shirin tafiya Hooriyah kuma ta shirya zata koma gida ganin halin da take ciki yasa yace zai ɗauke ta su tafi can ko zata manta da abinda ya faru bayan wani lokaci ta dawo. Da farko Daddy kin yarda yaso yi Mami da Aunty ne suka yi ta lallaɓa shi da kuma ganin halin da take ciki yasa ya amince suka tafi........................✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟏&𝟓𝟐 ___________________________________________________________________________ Around 9:00 Pm Cosgrove Smart Estate, Wuse, Abuja. Anan aka sauke su gida ne Mai kyau da Bedrooms guda biyar sai palour da kitchen kowanne ɗaki da Toilet ɗin sa suna shiga kowa ɗaki ya nufa wanka da sallah Tayi tana kwanciya ta huta. Washegari Gyara gidan suka yi suka chanja abinda ba za'a rasa ba Su biyu suka yini sai gurin La'asar Sannan Yaya da yaran suka dawo bayan La'asar suma shiryawa suka yi zawa shopping da Park zaman gidan ba daɗi duk da a Kano ma ba fita suke ba. 💥💦 Duk da an hana yi mata Hukunci tana cikin wani yanayi Sashe aka ware mata a cikin gidan kowa tsoron zuwa gurin ta yake kar ta cutar da shi tunda wadda ta yarda da ita ma ta cutar da ita. Mutum ɗaya ce ta yarda zata iya zuwa kullum da safe tayi mata aiki ta dawo. Bata da aiki sai kukan nadama wanda ba abinda zai yi mata. Kwana Uku tayi a Sashe da safe wadda ke zuwa yi mata aiki tazo a kwance ta tarar da ita jijjiga tayi amma shiru hakan yasa ta fito da sauri. Da akwai Fadawa guda biyu a ƙofar sashen suna tsare ta. Ganin ta suka yi arikice "Ta suma, kuzo ku gani ko zaku iya dubata" "Ki yayyafa mata ruwa mana zata tashi" ɗaya daga cikin su ya faɗa "Na yayyafa mata" itama ta Bashi amsa "Sai ki haƙura ai" yace yana ɗauke kansa da cigaba da abinda yake Wuce su kawai tayi cikin gidan ta nufa "Ta suma kuzo ku taimake ni" Yawan ci mutane sun firgita dajin zancen nata dan sun gane wa take nufi, Kowa tsoron shiga sashen yake "Wai ba zaku ƙara so ba ne kuga halin da take ciki?" Da kyar aka samu mutum biyu suka bita suna zuwa ta raka su har ɗakin datake ɗaya ce ta duba ta salati suka ji ta saka tana cewa "Kamar fa ta mutu" "Ta mutu" wacce ke kula da ita ta maimata "Ban tabbatar ba, Amma bari mu sanar a ciki" Nan suka fita suka sanar a ciki. Likita ne yazo ya duba ta ya sanar musu ta mutu. Mutuwar ta doki mutane da yawa bayan Azahar aka kaita gidan ta na gaskiya. *Allah yasa mu cika da Imani, Amin* Jikin Ammi ya ƙara warware wa tana jin sauƙi shirun da take yawan yi ne yake damun sa saka ta yayi dole sai ta shirya sun fita. A sirrance suka fice daga cikin gidan ko Mai martaba basu sanar wa ba hadiman tane kawai suka san sun fita suma sai da aka ja musu kunne kar a san sun fita. ✨💫 Jabi Lake Mall, ABUJA. Tafe suke da Sajeedah "Aunty Bari in duba ko akwai wani turare da nake ta nema ban samu ba" "Ok sai kin dawo" Thom tace mata juyawa tayi tana nufar wurin Turaren. Duba su ta fara can ta gano wanda take nema "Yes shine" ta faɗa tana ɗan yin sauri zuwa gurin karo tayi da wani abu ɗagowa tayi dan ganin menene Mutum ta gani tsaye a gaban ta. Tafe suke shida Ammi Hira yake ta yi mata kiran sa aka yi a waya ɗaga wa magana yake yana tafiyar ji yayi karo da wani abu a fusace ya ɗago Arba yayi da kyakkyawar Budurwa da sauri tace masa "I'm sorry, I didn't know that would happened" "Kamata yayi ki ringa kallon hanya in kina tafiya ba waige-waige ba" "You should stop answering calls when you're walking sir" itama ta bashi amsa tana wucewar ta Ammi Bata lura da abinda ya faru ba kawai giftawarta ta gani taɓa shi tayi "Wace wannan kuma" "Ammi ban san ta ba, bige Ni tayi" "Ba abinda ya same ka dai" ta faɗa tana duba hannun sa Hannun ta ya riƙe yana cewa"Ba komai Ammi" 🌟💕 Tunda suka koma gida yake wa Ammi zancen Yarinyar da suka haɗu dazu ta birge sa a nemo masa ita duk inda take. Hakan yasa Ammi ta sanar wa Sarki aka shiga neman ta da kyar aka samo information akan ta. 𝑍𝐴𝐴𝐻𝐸𝐸𝐷 A bangaren Zaaheed kuwa kamar yadda Mommy'n su ta sanar haka ne ya faru Ranar Juma'a bayan Idar da Sallah aka ɗaura masu Aure da Noor Kowa mamakin Auren yake ba sanarwa Amarya Noor sai murna take ta mallaki Zaaheed ɗin ta shagalin su suka yi har dare lokacin da aka zo daukar amarya dan kukan da amarya take in za'a Kaita gidan miji Noor ko kwalla bata yi ba. ABUJA Zaune yake a gurin aiki kira ya samu daga Office ɗin MD da Sauri ya tafi dan jin menene Mutane biyu ya tarar a Office ɗin MD gaisawa suka yi sannan MD ya fara magana "Abduljawwad waɗan nan mutanen da kake gani gurin ka suka zo daga Masarauta, suna so ka bi su za kuyi magana" "Amma sir..." "Babu komai ka bi su" "Tohmm" yace masa kawai jikin sa a saɓule zuciyar sa cike da wasi-wasi suka tafi. Isar su Fada sun nemi sanin wace Hooriyah ya sanar da su komai na rayuwar Hooriyah har fasa Auren ta da aka yi da dalili da kuma sharrin da aka yi mata. Suma suka sanar da su Yarima ne ya ganta kuma yana sonta da aure in sun shirya su ko a cikin satin za'a yi...... .....................✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/27, 2:32 PM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/InjFDl8g9KiCk5F8oos5Yz 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟑&𝟓𝟒 ______________________________________________________________________________________ 𝙰𝙽𝙸𝚂𝙰𝙷 A bangaren Anisah Bata san wanda yake kanta ba an yanke mata ƙafa guda ɗaya kwanan ta Uku sannan ta farfaɗo babu kowa a gurin ta har Lokacin da aka kira mijinta aka sanar da shi cewa yayi Allah ya ƙara mata ita ta fita bai sani ba dangin Mahaifinta da suka zo daga Katsina ne suka zauna da ita komai suke mata tayi nadamar gudar su lokacin da take da dama da badan su ba yanzu babu mai kula da ita ga wadda ta dogara da ita ta rasu watan ta guda a asibitin sannan aka sallame ta. Lokacin da suka koma gida Zaid baya nan sai wata suka tarar a gidan sai a waje suka jira shi ɗan hana su zamar mata a palour tayi Anisah sai kuka take ita da gidan ta amma wata banza ta hanata shiga sai gurin Magariba sannan ya dawo sun sanar da shi an sallame ta ne ta dawo kuma sunga wata a ciki ya sanar dasu Aure yayi ita sai dai ta koma BQ dan ciki yanzu na amaryar sa ne babu yadda ta iya dan yanzu bata da wani muhimmanci a gurin sa haka ta koma can da zama Wulakancin da yake mata yafi na da ga nasa gana matar sa ✨🦋 ɴᴏᴏʀ A bangaren Noor kuwa abubuwa rincaɓewa suka yi bata taɓa tunanin haka ba tayi tunanin zata same shi da sauƙi tun daren da aka kawo ta bata Ganshi ba ko inda take bai zo ba kuma Taji shigowar sa washegari kafin ta tashi har ya bar gidan ita kaɗai tayi zaman ta har gurin sati sannan suka haɗu tayi ta yi masa magiya tana bashi haƙuri ya nuna bai San tana yi ba yayi tafiyar sa duk ta rame damuwa tayi mata yawa. Ga Mommy'n ta tun washegarin da aka daura Aure tabar Ƙasar shi kuma tun ranar da aka kawo ta ya turo mata text message duk abinda ta gani ita ta jawo wa kanta tunda baya sonta kar ta sake ta faɗa wa mahaifiyar sa inba haka ba a bakin Auren ta Shiyasa tayi shiru bata faɗa wa kowa ba. Zaune take ta buga Uban tagumi Khairat ce take ta sallama ƙara so wa ciki tayi taɓa ta tayi tana cewa "Lafiya na ganki haka sis" A firgice ta ɗago "Lafiya lau ina su Hidaya" ya bata amsa "Suna makaranta baki da lafiya ne?" "Lafiya ta kalau me kika gani" ta faɗa tana yin murmushi "Ba komai" zama tayi kusa da ita nan ta cika mata gaba da kayan ciye-ciye har Dare tana gidan sai da ta fito zata tafi tace "Ni tunda nazo ban ga Yaya ba ko baya nan ne" "Ya fita gurin aiki bai dawo ba" ta faɗa tana sosa ƙeya dan itama yau kwanan ta biyu bata Ganshi ba "In ya dawo kya ce ina gaishe shi" "Zai ji Insha Allah ki gaida su Hidaya da yaya" "Zasu ji, ki koma ciki" Tohmm tace tana shigewa tare da ɗaga mata hannu har ta fice 💦💥🤍 Sunyi da shi zai sanar da Iyayensu daga nan saji komai Shatara ta arziki suka haɗa masa da farko kin karɓa yayi sai da kyar ya karɓa gida aka maida shi maimakon Office da daddare ya kira Daddy ya sanar da shi ce masa yayi zaiyi tunani ya nema sa daga baya. Har kwana biyu Daddy bai kira ba Gashi shi kuma kullum sai an kira shi daga Fada yanke shawarar kiran shi yayi nan yace zai shigo Abuja gobe sa tattauna bayan yazo suka tattauna da daddare ya koma. Bayan kwana biyu mutane daga Fada sunzo neman Aure An basu An saka daurin auren sati biyu suka tafi. Khaleesat kawai aka sanar wa sai ƴanuwan ta na cikin gida ko su Aunty Safiyya ba'a sanar wa ba dan kar a sake samun matsala. Duk wannan abin da ake ba'a sanar mata ba suna tsoron kar tace shima yaudarar ta zai yi shiru suka yi in an ɗaura taji kawai. Sajeedah taso ta sanar mata amma yaja mata kunne dan haka tayi shiru. Ko da taga Daddy yazo bata kawo komai a ranta ba tayi tunanin har ya fara missing ɗin su ne ya biyo su. Two Weeks Later🔥 Kano💦 Masallacin cike yake da Jama'a mai shela ne yake ta sanar wa "An ɗaura Auren Aminu Abubakar Muhammad da A'ishah Harith Yahya akan Sadaki Naira Dubu ɗari Biyu" kawai yake ta faɗa..................✍️ Wai ina Aunty Safiyya ne da Sulaiman ɗin ta 😜😂 shagali💃 # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Yau dai nasan na gama burge readers Hooriyah'n ku ta zama amarya 💃 sai a haɗa min Party🤸 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/29, 10:23 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟓&𝟓𝟔 _______________________________________________________________________________________ ᴀᴜɴᴛʏ sᴀғɪʏʏᴀ Kwance take a Palour tana bacci Sulaiman ne ya shigo a guje "Umma! Umma!!" Yana kwalla mata kira tashi tayi "Har yanzu Sulaiman ba zaka yi hankali ba ne? Kana gani bacci nake ka tashe ni, Ko Sallama baka yi ba, kai dai ba zaka shiryu ba ina ta maka fafutukar neman Auren Hooriyah ko zaka yi hankali" "Baki kalli abinda ake haska wa bane a TV?" "Ni kasan ba kallon nan nake so ba da ita da babu duk ɗaya a gurina, me yake faru wa a garin kuma?" "Ba abinda ake a gari, Yaya kuma bai sanar dake komai ba" "Ni mun kwana biyu bamu yi waya dashi ba ko gidan banje ba, Meya faru a gidan" "Yanzu aka daura wa Hooriyah Aure da Ɗan Sarkin Abuja shi kaɗai ake haska wa a TV wllh" "Wace Hooriyah'n, Hooriyah tamu dai" "Umma wadda kika sani mana, ta gidan yaya" "Ban gane Aure ba Sulaiman Aure wanda na sani?" "Shi Umma" "Kace ɗan gidan wa" "Ɗan Sarki" "Dan Sarki kuma? A ina ta samo shi? Kai kuma da zaka aure ta fa?" "A Abuja da suka tafi mana. Wallahi Umma bari in nuna Miki a facebook na gani yanzu naki yarda ina shiga gidan Abdul naga ana haskawa ko zama banyi ba na taho sanar dake" "Kan Uba Ni yaya zaici amana yayi mata Aure bai sanar dani ba, sai faɗi tashi nake yi dan ka Aure ta, ita kuma matar nan algunguma aiko ita ma sai nata Auren ya mutu" ta faɗa tana miƙe wa "Wace Mata Umma?" "Ba ruwan ka" tace tana shiga ɗaki mayafi ta ɗauko tana ce masa "Ka jira Ni yanzu zanje in dawo" "Ina zaki kuma" ya tambaye ta "Auren wata zanje kashe wa" ta faɗa tana fice wa da sauri Gidan Noor ta nufa dama ta sa an nemo mata shi saboda irin wannan rana a buɗe ta tarar da gidan tana zaune a palour kamar kullum da tagumi ba sallama ba komai kawai ta banka kai tana cewa "Ashe kin san Hooriyah wani zata Aura shiyasa kika shirya wannan manakisar?" "Kamar ya kenan? Ce miki aka yi ina da Haɗi ne da ita" ta ce tana watsa mata wani kallo "Ban sani ba, kamar yadda Sulaiman ya rasa Hooriyah kema sai na kashe miki naki auren" "Ai aure na mutu ka raba takalmin kaza, ke a wa da zaki raba wannan auren" ta faɗa tana jin kanta On top Nan suka cigaba da musuyar yawu tare da tonawa kansu asiri kowa tana sai ta ɗau mataki. Turo Kofar Palour akayi a firgice Noor ta kalli kofar bata yi tsammanin kowa zaizo gidan a wannan lokacin ba shigowar Zaaheed ne ya sata shiga tashin hankali addu'a ta fara a ranta Allah yasa baiji abinda suke tattaunawa ba ƙara so wa kusa da su yayi sannan yace "Kin kyauta Noor kije gida na sake ki, ke kuma kije ke da Allah shi zai mata sakayya akan sharrin da kika yi mata" Ko a jikin Aunty Safiyya dan haka take so, Noor ce ta ɗora hannu aka tana cewa "wallahi Yaya ba abinda kake tunani bane ka tsaya nayi maka bayani" Ko Ni takan ta baiyi ba ya shige ɗakin sa juyo wa tayi gurin Aunty Safiyya "Allah ya isa na muguwa kin kashe min Aure" Dariya ta saki "ai dama nayi alƙawari indai Sulaiman bai auri Hooriyah ba kema sai na raba ki da Auren ki, anyi biyu babu kenan dan bazan dau asara ni kaɗai ba" Taho wa tayi kanta gadan-gadan da sauri taja baya "Allah ya kiyaye da ina yarinya ma banyi wannan rayuwar ba balle yanzu da girma na, aje aji da idda da gabzar gidan Baba" ta faɗa tana hararar ta tare da fice wa ranta fesss ko banza itama ta rasa mijin sun zama ɗaya da Sulaiman bata zame ko ina ba sai gidan su Hooriyah. Lokacin data isa gidan babu kowa shiru gidan a palour kawai ta zauna tana jiran mutanen gidan su fito bata wani jima ba sai ga Aunty ta fito daga ɗakin ta zama tayi tana Facing ɗin ta fuskar ta fess bata nuna komai ba "Safiyya yau kece a gidan namu da rana tsaka" "Nice kamawa tayi zuwan, da fatan wanda nazo gurin sa Yana nan" "Yaje ɗaurin Aure bai dawo ba" "To bari in jira ya dawo" ta faɗa tana hararar Aunty. Ita ma tashi tayi ta bata guri dan tun lokacin da suka samu labarin ita ta raba auren Hooriyah take jin ba daɗi a lokacin taso Daddy ya barta taje mata da ƴan sanda an kama ta amma yaƙi, bata da lokacin raba hali yanzu ga ƴan ɗaurin Aure da zasu dawo kar a shigo da ɓaki taji kunya dan Safiyya ko a jikin ta indai abin kunya ne. Har bayan Uku tana zaune jiran shigowar Daddy amma babu shi babu alamar sa ga matan gidan yau iskanci suke ji ko ruwa ba'a kawo mata ba tashi tayi ta ƙara duba ƙofa a karo na barkatai ko zasu shigo sai ga ƙarar Horn ɗin su wata bahaguwar ajiyar zuciya ta sauke fita tayi ta tsaya a ƙofar palour yadda yana shigowa zaici karo da ita suyi Maganar da zasu yi ta wuce suna parking ya hango ta bai kawo komai a ransa ba ya fito ya ƙara so kusa da ita "Yaya sannu da dawowa tun ɗazu nake jiran dawowar ka" ta faɗa tana tsugunawa ƙasa "Ina wuni, fatan mun same ku lafiya" Shi abin ma dariya yaso bashi Safiyya da ko abu tazo nema bata tsuguna wa ta gaishe sa amma yau har da tsuguna wa "Tashi mu shiga daga ciki Koh" ya faɗa yana wucewa Dariya Khaleel dake kallon su ya kwashe da ita Abduljawwad ne ya juyo yana cewa "lafiya" "yaya wani abin dariya na gani, Aunty Safiyya ce da durkusawa yau dan zata gaida Daddy" "Ina ruwan ka, in ta hango ka fa ga jama'a tazo tayi ta rashin mutunci, ka wuce muje" ya faɗa yana nuna masa hanya. Sim-sim ya shige girgiza kai kawai yayi shima ya bishi. A cikin palour kuwa Aunty Safiyya ce zaune a ƙasa Daddy yayi yayi da ita yau ta hau kujera amma taƙi tace gaba yake da ita yana sama tana sama ai ba zai yiwuwa ba dole ta bashi girman shi {😂😝} "Yanzu yaya sai ka Aura wa Hooriyah wani bare bayan kasan Sulaiman yana sonta" ta faɗa tana share kwalla Kallon ta ya sake yi shi ya rasa abinda zai faɗa ma tun da ya shigo take share masa hawaye can sai yace "Ke yanzu Safiyya baki ji kunyar zuwa gida na ba, har da wani zancen Sulaiman kike?" "Yaya dan zanzo gidan ka sai inji kunya sai kace wadda tayi wani abu" cewar Aunty Safiyya "Bari kiji yau duk abinda kika yi wa Hooriyah an sanar min na sharrin da kika yi mata, na ɗauka ko wani kika ji ya fadi haka zaki yi masa faɗa Hooriyah ƴar kice amma baki ɗauke ta a matsayin dana ɗau Sulaiman ba. Ki tashi ki bar kin gida bana son na ƙara ganin ki balle ƴaƴan ki a cikin gidan nan" A firgice ta kalle shi dan bata yi tsammanin abinda tayi zai dawo kunnen sa ba "wallahi Yaya ba haka bane Sulaiman na matuƙar son Hooriyah, sharrin Shaidan ne kayi haƙuri nayi nadama" "Haƙuri! Safiyya hakuri kike so nayi to bazan haƙura ba ki bar min gida yanzu" ya fada yana fita daga Palour. Ji take kamar ta kurma ihu ko zata ji sassauci a zuciyar ta bata yi tsammanin zai samu Labarin ita ta rusa auren ba gashi yanzu ta Auri wanda basu taɓa harsashe ba ina zata saka kanta ita Safiyya dama shine yake taimaka mata yanzu yace babu shi babu ita Sulaiman ba wani abin arziki yake yi mata ba shima wani lokacin ita ke taimaka masa. Da kyar ta tashi ta nufi gidan ta dan ji take kamar zazzaɓi ya kama ta. *Dama Hausawa sunce in zaka gina ramin mugunta ka gina shi dai-dai da kai. yanzu wa gari ya waya?* 💫💦🖤 ABUJA Sajeedah ce ta turo ƙofar ɗakin a kwance ta tarar da ita tashi tayi ta zauna ganin Sajeedah ce ta shigo da sauri ta ƙara so kusa da ita rungume ta yi bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba tana jin tausayin ta sosai. Ɗago ta tayi daga jikin ta ganin fuskar ta da hawaye yasa ta ce mata " me ya faru Aunty?, Ko wani ne ya mutu?" "Kukan daɗi nake Hooriyah, Yau dai Allah yayi Hooriyah Aunty ta zama Amarya" ta faɗa tana share hawayan "Amarya kuma, like how?" "Yes kamar yadda kika ji" "Ban gane ba Aunty" "Zaki gane ne soon, ki shirya zamu bi Flight ɗin 6 zuwa Kano, gobe zamu dawo" ta fadi tana tashi tazo buɗe Ƙofa ta ƙara ce mata "Kano kuma? Kuma gobe mu dawo" "Kin fiya tambaya fa, ki bari in munje zaki ji komai ai" # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ [5/31, 10:01 AM] Fatima Zahra Intisar: ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟕&𝟓𝟖 Second to the last Page ———————————————————————————————————————— A bangaren Kareema kuwa ƴaƴan ta ta zaunar su bata shawara yadda kowa zai yarda da ita a gidan a daina zargin ta Shawara ta gari suka bata ta fara zama da kowa lafiya a gidan ba tashin hankali. 🤍💥🖤 Suna sauka daga Airport direct gidan Daddy suka yi gidan cike yake da ƴan uwan ta da matan yayyanta da ƙannen ta gaisawa suka yi ta shige ciki ba wanda yayi mata Allah ya sanya alkhairi dan duk sun san bata sani salla tayi ta kwanta ba jima wa sai ga Khaleesat ta kira ta sun daɗe suna waya sannan ta katse cigaba da kwanciyar ta tayi dan babu abinda zata yi. Gurin goma sai ga Aunty ta shigo sai a lokacin suka gaisa dan da suka zo bata nan ita da Mami suna part ɗin Daddy. Ce mata tayi tazo inji Daddy sai da taji wani iri dan indai ba magana nace mai muhimmanci Daddy baya yin ta da daddare sai da safe tashi tayi suka tafi. A palour ta tarar da duka Yayyan ta da Mami suna gurin Daddy gaishesu su tayi bada ɓata lokaci ba Daddy ya fara magana da cewa "A'isha" "Na'am Daddy" Tunda taji ya kira sunan ta ta faɗa kanta a ƙasa "Menene matsayi na a gunki" ya faɗa Maganar taji ta wani iri amma ta daure ta amsa da "Daddy Kaine Mahaifina" "A'isha na zaɓa miki kuma kika karɓe shi Allah bai yi za'a yi auren ba yanzu ma mun ƙara zaɓa miki wani har mun Aurar da ke yau" Wani dumm taji kanta yayi "Aure Daddy yace sun min fa" Waye Mijin? Sulaiman mana zuciyar ta ta bata "kai ina Daddy ba zai taɓa aura min Sulaiman ba" ta bawa kanta amsa ji tayi Daddy ya cigaba da cewa "A'isha kibi mijin ki sau da ƙafa, kinga duk ƴan uwan ki kowa yana zaune lafiya a gidan sa kece babba acikin su amma sai yanzu Allah yayi naki auren kar inji kar in gani A'isha" Nan su Mami da Aunty ma suka yi mata nasiha Yayyan ta ma haka. Ta yiwa Daddy alkawarin zama da duk wanda suka zaɓa mata a matsayin miji. Washegari Ba wani taro suka yi ba ƴanuwa da abokan arziki ne kawai suka zo sukuku ta yini tana ɗaki sai da rana ne ta fito da aka kira ta da yamma aka shirya amarya da duk wanda yake son zuwa ta sha kukan rabuwa da su. Tsaya wa faɗa muku tsarin gidan ma ɓata lokaci ne kyawun sa da tsaruwar sa ɗakin ta aka kaita dan Ammi tace a barta gobe sa so gaishe ta yanzu ta huta. A nan gidan Amarya suka kwana washegari zasu yi bikin su a nan da safe suka shirya ta suka kai ta gurin mai martaba sannan aka wuce da ita gurin Ammi suna tare da Mommy da wasu daga cikin matan gidan sun karɓe su an musu tarba ta mutunci sun dau Amanar ta da alkawarin kula da ita. Da rana yini suka yi da daddare aka yi dinner dole anan dangin amarya suka ƙara kwana ba dan sun so ba washegari da safe suka wuce, ita kadai suka bari har lokacin bata san waye mijin ba. 💃💥🥰 Bai shigo gidan ba sai ranar da daddare tunda aka ɗaura auren ya bar gidan ko dinner da suka yi bai je ba iya mata kawai suka yi kayan su. Yana shigowa direct part ɗin Ammi yayi ba abokin daya rako shi bashi da abokan ma balle su rako shi bata palour sai hadimar ta kawai ya tarar shiga yayi nasiha tayi masa sosai tare da addu'a har kwalla sai da yayi duk da ba barin gidan zai yi ba part ɗin sa yana gidan sai da ta kore shi sannan ya tafi. Zaune ya tarar da su a ɗaki ita da su Husna ne Sannu da zuwa suka yi masa sai Zainab ta cewa "Yauwa Yaya dama kai muke jira mu tafi, sai da safe" Raka su yayi yana kulle kofar ya dawo tana nan zaune alwala ya sata tayi salla raka'a biyu suka gabatar,addu'a mai tsaho suka yi ta neman alkhairi da samun zaman lafiya da haduwar kai a tsakaninsu sannan ya waiwayo ya kama kanta ya karanto addu'ar da annabin rahama ya koyar da mu '' *Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wa a uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi*'',da salatin annabi ya rufe musu suka shafe tare. Noor Bata nufi ko ina ba sai gidan su Zaaheed kuka ta sawa Mommy wai ya sake ta bata san laifin da tayi masa ba. Mommy waya ta ɗauka ta kira shi yana zuwa ya sanar mata da abinda yaji suna tattaunawa da Aunty Safiyya Salati Mommy ta saki tana cewa "Yanzu dama Noor ke kika kitsa abin nan duk irin ƙaunar da nake Miki amma kika yi haka" "Mommy wllh Sharrin Shaidan ne baza sake ba ki bashi hakuri ya maida Ni dan Allah" "Kinci gidan ku Noor ai ko Zaaheed bai sake ki ba ni nace ya sake ki, baki kyauta ba Noor kika sa na daga hankali na har sai da aka fasa Auren" Nan tayi ta mata faɗa da taga kamar ba ɗauka take ba tace ta shirya ta koma gidan su. Sati ɗaya da haka Mommy ta samu Abiee da maganar a nemo wa Zaaheed Auren Hooriyah ta yarda yanzu ya aure ta, ta gane ba laifin ta bane nan yake sanar da ita bakin alkalami ya bushe yau satin ta ɗaya da aure. Sai da Zaaheed yayi gurin shekara yana jinyar rashin Hooriyah da kyar ya samu wata Rukayya ya aura ita ma student ɗin sa ce tare suka yi Graduating da Hooriyah ta daɗe tana sonsa amma yaƙi amince wa duk da bata kai Hooriyah ba amma ya haƙura haka ya Aure ta tana da ladabi da biyayya yarinyar bata da rashin ji. Noor kuwa tunda Mommy'n ta taji abinda tayi ta ɗauke mata wuta babu ruwan ta da ita ga gida ɗaya suke kwana su tashi amma bata shiga harkar ta ko ta gaishe ta bata amsawa gurin wata biyu suna haka da Abban su yaga ba zasu shirya ba ya Aura mata ɗan Abokin sa Junaid. Junaid dan shaye-shaye ne na gaske dan har Cocaine yana sha idan ya bugu ya kamata ya zane dama shi ba sonta yake ba dan kawai kar ya musa wa mahaifin sane ya sa ya aure ta ta sha wahala a gidan sa Daga baya Auren ya mutu tayi nadamar abinda tayi ga Zaaheed ya mata nisa ko gidan su taje Mummy da kyar take kula ta. 🤍💥🖤 Five Months later Zaman su suke lafiya ita da mijin ta ba wanda yake jin kansu ko saɓani suka samu anjima zasu sulhunta kansu ba tare da wani yaji ba Sajeedah tana leƙo mata lokaci lokaci sau ɗaya taje gidan Yaya. Bata taɓa zuwa Kano ba kullum tana masa naci amma sai yace ba yanzu ba sai wani lokacin haka ta haƙura sai dai suyi waya. Kareema kuwa Tunda aka kawo Hooriyah ta zama ta gurin ta, Tsakani da Allah take sonta jinta take kamar su Husna so take duk laifin da tayi wa Ammi ya goge saboda kyautatawar da take wa Hooriyah dan tana sonta Addu'ar ta ta karɓu dan Ammi ta yafe mata tuntuni yanzu zamansu suke lafiya ba wani kishi sai dai dan kaɗan da ba za'a rasa ba. Ko abu Hooriyah take so kai tsaye take tambayar ta dan tana jin nauyin Ammi ba komai take tambayar ta ba kowa a gidan yana son Hooriyah bata da matsala da kowa..................✍️ # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️ ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ https://chat.whatsapp.com/L3tt0Q6Zcqe3eeCa3cXcAG 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 𝙰𝙽𝙳 𝚆𝚁𝙸𝚃𝚃𝙴𝙽 𝙱𝚈 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷 тԋє ɯɾιтєɾ σϝ *ʂιʅαɾ ɯαყα* 𝗔𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗪 ♡ ԋσσɾιყαԋ ♡ Follow My WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I بسم الله الرحمن الرحيم 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷✍️ 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝟓𝟗&𝟔𝟎 ________________________________________________________________________________________ Anisah Tunda ta rasa ƙafa take halin wuya watan Amaryar sa shida da Aure mahaifin sa yayi accident ya rasu ya shiga tashin hankali sosai bayan anyi rabon gado ƴan fashi suka shigo duka suka yi musu suka tafi da kuɗi da Amaryar sa. Ya rasa idanun sa gaba ɗaya biyun. Sai daga baya suka gane ita ce ta turo su da kyar aka kamo su aka kulle. Ga Mommy su ba iya kula da shi take ba tsufa ya kamata dole dai sai Anisah ce take kula da shi kullum sai yayi kukan kuntata mata da yayi bayan yayi aure ga neman Hooriyah da yake ruwa a jallo ya bata haƙuri ko zai samu sauƙin Ƙaddarar da take ta afka masa. Aunty Safiyya Ta shiga rayuwa mai wahala da kunci Sulaiman ɗin da take yi wa fafutukar neman Aure ya guje ta tunda bata da abinda zata bashi yanzu da kyar aka shawo kan Yaya ya yafe mata kowa yaje gurin sa sai yace babu shi babu Safiyya in suka dage sai ya sanar musu da abinda tayi duk ƴan uwa duk wanda yaji abinda tayi sai yace ba ruwan sa sai da ta Ringa haɗawa da ƴan unguwa wajen zuwa neman yafiya Sannan ya haƙura. ✨💕✨💕✨ Two Years Later Abubuwa da yawa sun faru ciki harda zaman Arshad Sarki, Mai martaba ne yayi murabus tsufa ya kama sa ya kamata ya huta duk da baya so haka suka tilasta masa ya karɓa. Allah ya albarkace su da ƴan biyu masu kama dasu lokacin watan sa biyu da zama Sarki, ɗaya kamar Hooriyah sak komai nata ta ɗauko ɗayar kuwa kamar ta ɗaya da Arshad mai kama da Hooriyah aka saka wa Abeedah ita kuma mai kama da Arshad suka sa mata A'isha yana so tayi halin Hooriyah, Abeedah suna kiran ta da Minha ita kuma A'isha suna ce mata Mirha yanzuwatan su Uku a duniya. Sun taɓa haɗuwa da Zaaheed a Abuja yaje wani meeting ita kuma sun fita Arshad lokacin bai zama Sarki ba anan yake sanar da ita sun rabu da Noor da abinda ya faru da shi ta tausaya musu matuƙa har ya haɗa ta da matar sa suka gaisa ta gane ta sarai lokacin da yace yana sonta har zuwa ja mata kunne tayi akan ta fita a harkar Zaaheed ashe itace matar sa a yanzu taji kunya lokacin da ta tina abinda tayi tace mata ba komai ya wuce ai. 💦✨💦✨💦✨ A shirye take cikin atamfa riga normal doguwar riga, tayi lite make up feshe jikinta da turaruka masu dadi tayi, ta daura dankwalinta bayan ta gyara gashinta kai azabar santsi ta hadeshi da ribbom madaidaici, haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar, ba qarya ta mata kyau matuqa, motsi ta jiyo a palour tasan shine ya dawo, cigaba da tsaya wa tayi gaban madubin ba tare da ta zauna ba, turo ƙofar aka yi harshen nata ya tabbata Shine ya dawo tsayawa yayi yana kallon ta dan tayi masa kyau sosai ƙaraso wa Yayi ta rungumeta ta baya "Kinyi kyau sosai" ya rada mata a kunne Murmushi ta saki "Barka da dawowa, ka dawo lafiya My" ta faɗa muryar ta ƙasa-ƙasa "Zanyi missing ɗin ki in kika tafi, anya ba zaki fasa tafiyar nan ba" "Haba sai kace wadda ba zata dawo ba, Just ten days fa zan yi in dawo" ta faɗa a shagwaɓe "Yayi nisa Habibty, ko One week kika yi ya isa" "Sau ɗaya fa naje Kano tunda nazo Abuja, Mi Amor ka taimaka Please" ta faɗa tana juyo wa tare da kama kunnen ta, shiru yayi mata an ta cigaba da cewa "Allah zan faɗa wa Ammi da Mommy ince ka hana tafiyar" ta faɗa tana diddire ƙafa Zaro ido yayi yana cewa"Ammi fa a'a sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya dawo mun daku lafiya" "Ameen ya Allah, muje kayi wanka" ta faɗa tana wuce wa Toilet. Binta yayi a baya... Washegari Jirgin Asuba tabi suka nufi Kano ita kaɗai sai Mirha da Minha sai hadimai guda Uku ta tafi. A gidan ta dake Aminu Dabo Road ta sauka gida ne mai kyau da ya tsaru in ka shiga ciki sai ka zata ba'a Nigeria kake ba. Ko su Mami bata sanar musu da zuwan ta ba bayan La'asar ta shirya ta nufi gida sunyi murna sosai dan rabon su da ita anfi shekara sai gurin Sha ɗaya ta tafi. Da safe gidan Khaleesat taje ta ƙara haihuwa tana son ganin Baby kafin ta koma goma ma a can tayi mata anan ne Khaleesat take ƙara bata labarin halin da Anisah take ciki. "Wllh Hooriyah Rayuwar Anisah Abun tausayi yanzu bata da kowa, danaje na ganta sai da nayi mata kuka tana halin rayuwa" cewar Khaleesat Nisawa tayi sannan tace"Allah sarki Anisah, yaushe ya kamata muje gurin ta kafin in koma" "Duk lokacin da kika shirya amma ki fara sanar wa mijin ki sannan mu tafi" "Bani da matsala da shi Khaleesat ko da yamma in kin shirya ma je" "Allah ya kaimu bari in sanar da Abban Fadil kar ya dawo bama nan" ta faɗa tana ɗauko wayar ta kiran sa tayi ta sanar masa. Hira suka cigaba da yi anan ne ma take sanar da ita bikin Zee ƙawar su daya rage saura kwana Ashirin tayi mata murna sosai. Ko da suka je gidan Anisah sai da tayi musu kuka ganin halin da suke ciki duk kyan nan na Zaid yanzu babu ya zama wani iri Maman sa sai kuka take duk da bata taɓa ganin Hooriyah ba sai yau tana jin labarin ta a gurin su da halin da suka saka ta. Bata taɓa tsammanin haka zai faru da Anisah ba da tini itace a wannan Rayuwar. ta yafe wa kowa a cikin su duk laifin da suka yi mata Allah ya yafe musu baƙi ɗaya. Da zata tafi tayi musu kyauta sosai da alkawarin zata ringa turo wa ana kula da su koda bata zo ba. Tako ina rayuwa tayi mata dai-dai. A kullum gode wa Allah take daya bata miji kamar Arshad samun irin sa a wannan zamanin sai an tona gani take tafi kowa Sa'ar Miji a duniya. Ko yaushe yana jin matsalar ta baya son kukan ta ko gani yayi bata da lafiya shima zaka same sa sukuku kamar shine mara lafiyar. Taje duk gidan ƴanuwan ta har gidan Aunty Safiyya sai da Daddy ya tilasta mata zuwa. Kwanan ta goma cif ta koma Abuja dan tayi missing ɗin mijin ta. Tammat Bi Hamdulillah🥰🔥 Godiya Ga Allah SWT daya bani Ikon Kammala wannan Littafin. Ya Allah ka tsare mu da cin amanar wanda suka aminta damu Allah ka haɗa mu da Abokai na gari👏 Saƙon godiya zuwa ga Hooriyah fans, Fateyzahraah Fans group & WhatsApp Channel Allah ya bar Kauna Allah ya haɗa mu a Aljanna Firdaus💋 Nagode da Kauna da Kulawa. Nainarh Kd, Nanameera, Aunty Amal, Ummeta Sannun ku da ƙoƙari😍 Saƙon Jinjina ga Ammi Hisham Aunty Amal Aunty 40 Issy's Cuisine Ummi's Makeover Zarah Chouchou Babyn Daddy Fauziyya Hashim Lubabatu Muhammad ~Shukura Her Xcellency Dama waɗanda ban lissafo ba Sannun ku da ƙoƙarin Comments da Like Nagode ƙwarai. Ku kasance sani bayan Sallah da sabon Littafi na mai suna *Sune Silar Ƙaddara* Paid Book ne.💕 Nice dai takun nan Fatima Intisar Abdulhadi ◎Fateyzahraah◎ Thank You So Much💋 # 𝙵𝙰𝚃𝙴𝚈𝚉𝙰𝙰𝙷𝚁𝙰𝙷👯 Masu son Hooriyah daga Farko zasu iya Following WhatsApp Channel ɗin nan https://whatsapp.com/channel/0029VaOeCGv42DcbctBrce2I Follow My Pages Arewa Books:https://www.arewabooks.com/u/fatimaintisar1 Wattpad: https://www.wattpad.com/u/fatimaintisar1 09047574404 WhatsApp Only Comments & Share Fisabillah🥰👏 𝔽𝔸𝕋𝔼𝕐ℤ𝔸𝔸ℍℝ𝔸ℍ✍️