*H I Y A A M* Page 1 Bright pens More pages on ArewaPen. Ku yi searching sunan littafin za ku samu. Yota/001 Bari na yi amfani da wannan damar na yi miki godiya Yaɗɗo am, kina daga cikin alherin da media ta bani, Ubangiji Ya cika miki muradanki ya raya miki zuri'a Falmata 😂Every time I see you, I see you as family, even though you're the one I love. You'll always be my favorite person, Yaɗɗo, and my best friend forever. Even if I’ve never said it before, I can proudly shout it to the world through a loudspeaker: you're so special to me. Daga farko har ƙarshe wannan littafin sadaukawa ce a gare ki Jikar Nashe. Dedicated to NAZEEFAH SABO NASHE. Fans ɗinta zanga adadin capacityn da za ku nuna mini a tafiyar HIYAAM. NOTE: A baya ban taɓa faɗa ba, a yanzu na ce, duk wanda ya sake ya yi mini amfani da littafi a YouTube Shari'a zata rabani da mutum in sha Allah, ban fara ba sai dana samu Copyright. Ta kowacce fuska kar a juya mini littafi. MY WORDS: Wani labari da zai yi dai-dai da abin da kuke buƙata wani labari ne dana fara rubutawa tun 2/5/2025 bani da tabbacin zai muku amma ina da yaƙinin ba za ku yi danasanin karantawa ba. Duk abin da ya yi dai-dai da rayuwar wata ko wani ayi mini lamunin cewa bincike ne ya kawo haka, ƴar jarida daku nake a yi mini afuwa, iyayen ƙasa ayi mini afuwa da masu ruwa da tsaki abin da kukai makkuwa ne na dawo dashi, idan kina sake da addu'a ko tarbiyya ba ki wahala ki zo mu sasanta lamarin tare. Iyaye mata wanda suka riƙe responsibilities na gida wannan ma naku ne. Ƙirƙira ce amma labarin ƙabilar da za ku ji da wasu abubuwan masu kama da almara duk gaske ne, kawai na yi ƙari kaɗan akan wasu kuma zuwa gaba zan faɗa. THANK YOU: Kafin na fara zan godewa marubutan da suka taimaka mini wajan haɗa information waje guda, na sha wahala na kasa sukuni akan tattara bayanai ganin kar a baku abin da hankali ba zai ɗauka ba. Marubuta sun mini ƙoƙari tabbas, Lubnasufyan, Sumayya takori, Zuwairiyyah Adamu gerie, Autar manya, Mai dambu, MeerahGee thank you all sun mini ƙoƙari wajan tattara bayanai da ganin na kammala komai. BRIGHT PENS: Dear Ayushercool na gode sosai my zizi Zee Kumurya Allah Ya baku aljanna ina son ku sadidan yan'uwana abokan🤭... Da na ce ba zan rubutu ba sai 2027 sune suka tasoni gaba😄. My pple YOTAWA dangina duniya da lahira Allah ya sakawa jama'ar Young talented writers association wannan page ɗin naku ne. _Bisimillahir Rahmanir Rahim_ A ƙa'ida a kuma tarihi, maza ne kawai suke yin aiki a gidan, sun tsani mata basa son su sam, suna ganin alaƙa da matan da suka ƙetare iyaka daka waje zuwa cikin gidan, kamar zai zama tubalin rusa dukkan wani al'ada, tsafi, ƙarfin ikon da sukai shekara da shekaru suna ginawa, domin kyautata goben da har yanzu suke zaman jiran ganinta. Kakanninsu ne suka damƙawa iyayensu, bayan sun cinye wa'adin da ƙaddara ta shimfiɗa wanda kowanne mai numfashi a ƙirji yake rayuwa tare da zanen tasa ƙaddara, mai kyau ko akasin hakan, sai suka tattara ragamar komai suka damƙawa ƴaƴansu, wanda ƙarfin iko, isa, izza, jinin ƙifaɗin dake gudana a jikinsu ya zarce waɗanda suka shuɗe. Sun rayu akan mafarki, sun wanzu da tsoron da mafarkin ya saka musu, wanda kuma shine zai zame musu jagoran da zai sanya su samu haske a cikin duhun da suke. A bisa wannan tsoran suka zartar da hukunci na ma'aikatan da za su dinga hidima a cikin TAJMAHAR. Jadawalin maza kusan 150 ne masu aiki kowacce rana, safe da yamma. Suna amfani da maza ne, domin kafin haihuwarsu an sanar musu mace ita zata zama hujjar rarrabuwar kan su gabaɗaya. Kamar kullum yau ma ma'aikatan sun yi layi a babbar ƙofar da zata fitar da su daka cikin Tajmahar, jerin maza ne, sanye da kaya iri ɗaya wanda ke bawa wanda ya kalle su, tabbacin uniform ne.Kowanne akwai numbersa a jikin rigarsa, duk wanda zai fita akan caje shi domin tabbatar da bai yi sata daga ciki ba zuwa waje. Zuciyarta ce ta cigaba da bugawa a ƙirji, wanda ya haifarwa da jikinta amsar yanayi, duk ƙoƙarinta ta kasa daurewa, a kullum da wannan tsoron take shigowa Tajmahar kuma take fita, Allah yana tarfawa garinta nono wajan fita salin alin. Sanda binciken yazo kanta numfashita ne ya ɗauke tsaf, kamar wacce wa'adinta ya yi a sa'ilin zufa na yanko mata a duk wata ƙofa da Ubangiji ya halitta a kyakkyawan jikin da wahala ta gama muzanta shi, zuwa siffa ta daban, siffar da ita kanta tsoran kallonta take yi a madubi, bata sha'awar ganin ma. "No 089" aka nanata kiran sunanta. Cikin hanzari ta ƙarasa tana shanye tsoran da ya gama cinye dukkan zuciyarta sai rawar ɗari take yi, a zuciyarta take furta; “Allah ya cece ta yau ma”. Aka fara caje ta, aka cire hular kanta domin tabbatar da babu komai a ciki, aka tarar da santalelen kanta daya sha ƙwal kwabo babu tsoruwar suma ko guda ɗaya sai ƙyalli yake. Bayan an duba aka mayar da hular kan nata, aka caje har cikin takalminta har zai sallame ta, sai ya lura da ƙirjinta kamar ya tasa, tunaninsa ko wani abu mutumin ya sato, zato ko tsammani balle hasashe bai taɓa kawo masa ita ɗin macace ba, tunda ta fara aiki har kawo yanzu da sunan namiji take amsawa “TERSEER”. Ya yi mata kallon tsaf kamar zai cinye ta a dake ya furta "089" Sannu a hankali ta jinjina kai alamar amsawa. "Cire rigarka, umarni nan take" Ta ji umarnin har tsakiyar kanta, kamar an sanar mata da ranar mutuwarta, ƙoƙarin magana take yi, amma ta kasa, muryarta zata fallasa sirrinta na jinsin ƴa mace, ya sake yi mata tsawa "Terseer 089!" Fafur taƙi cire rigar, sauran ma'aikatan da basu fita ba, suka fara yi mata ban baki akan ta yi abin da aka ce, domin a cikin abu biyu za'ayi ɗaya, ko ta rasa ranta nan take, ko dai ta tabbata a cikin kurkukun “GBANDE AONDO” "Guards! Guards!" "Umarnin kira nan take......!" Cikin ƙaramin lokaci dukkan wasu Guards da suke tsaron ƙofar suka bayyana, aka zagaye ta. Babban cikinsu ya ce "Wannan mutumin ya yi sata, akwai kaya a ƙirjinsa, a ƙwace a yi masa bulala hamsin a kore shi" "Kashina ya bushe!" Ta furta a zuciyarta. Kokawa suka shiga yi da ita, sai dai kasancewar ta macace ita dole ta bada kai bori ya kar boka, bugun zuciyarta ya tsananta lokacin da suka zare rigar wata razana suka yi tare da yin baya, nan take kuma iska ta fara tashi a wajan, arba da halittun ƙirjinta na ɗiya mace da suka yi a lokacin ya fi komai muni a tarihin masarautar Tajmahar, wani abu ne da ko a mafarki ba'a taɓa tunanin zai faru ba, rashin sani ga Guards ɗin, domin bayyanarta zanannen labari ne tun iyaye da kuma kakanninsu har zuwa yanzu. Ta saka hannu wajan kakkare tsaraicin ƙirjinta, hawaye na taruwa a cikin idanunta. Bayyanar abin da ya faru ya zama abu me sauƙi, kamar wutar daji a cikin Tajmahar, kafin ka ce wane aiki, Shugaban da kan shi da jama'arsa sun ƙarasu wajan, ya shiga bin kowa da idanu, yana ɗora idanunsa a kanta, jikinsa na matsanancin rawa da ɓari ya yar da sandan dake hannunsa ya zube a gabanta wajan ƙafafuwanta ya furta "Lale, barka da zuwa uwata, barka da zuwa Mamaa, barka" ya ce da rawar ɗari. Allah Subhanahu wata'ala shi kaɗai ake bautawa, ita musulma ce mene ya haɗata da abin da suke yi? Su waye su ɗin? Mene hakan? Me kalma Uwata, da Mamaa suke nufi a tattare da ita? Ta shiga girgiza kai "Bani bace, bani bace" ta faɗa a sanyaye, jikinta na rawa "Mun fi shekaru muna dakwan zuwanki Mamaa, kar ki yi fushi damu, ki albarkaci wannan masarautar, an ce, kalmar ki ɗaya na iya sauya mana rayuwa, ki yi furuci akai na Mamaa, ki buɗe bakinki Mamaa, ki yi..," "Ban kasance wacce kuke nema ba"Ta rushe da kuka "bani kuke jira ba.... Nan da nan suka fara rawa da kiɗe-kiɗe hatta Shugaban rawa ya fara cikin waƙe yake maganar "Kece ruhinmu Mamaa, kece gatanmu Mamaa, abar bautarmu kece Mamaa, kece" Suka shiga watsa mata wasu abubuwa aka. Sham ya ce "Mu fara tabbatarwa ita ɗin ce, an bamu haske na yadda za mu gane Mamaa, an baka umarnin kasancewa da ita a dare ɗaya, idan ka samu nasarar keta budurcinta, to ba ita ce Mamaa ba, idan alƙalaminka ya gaza keta budurcinta to tabbas Mamaa ta bayyana a wannan karon" Jin haka ya saka ta mance da tsaraicin ƙirjinta dake bayyane, ta saki hannunta ta juya zata fara gudu ya ce "A ɗakkota, akai ta kyakkyawan gadon da nake kwajin budurci domin tabbatar da zuwan Mamaa, ku kasance a bakin ƙofa, idan kuka ji ihu to na samu budurcinta, sai a fara tunanin yadda za mu kashe ta, idan kuka ji shiru baƙin hayaƙi ya bayyana, to Mamaa ta bayyana, sai mu shirya inda zamu ajjiyeta mu dinga yi mata bauta" duk yadda ta yi ƙoƙarin kiran sunan Allah ta kasa, komai nata ya kunce ta durƙushe a wajan, wani badakaren mutum ya zo ya saɓa ta a wuya ya nufi da ita cikin ɗakin Shugaba. Ya ajjiye ta ya fito, Shugaban ya shiga jama'ar wajan sun fi ɗari suka tsaya a bakin ƙofa ana dako, tare da sauraro zuƙata cike da fatan Allah Ya sa ta kasance MAMAA ABAR BAUTA wace suke jira tsayin shekaru. *** H I Y A A M. Littafin Haleeym Ana Daada. Jerin kalmomi guda biyar kawai ta samu zarafin rubutawa a cikin fejin littafin dake hannunta, idan ta irga haruffa a jimilance a yau ta samu ƙarfin zuciyar rubuta harafai har Talatin cif, saɓanin baya da iya HIYAAM kawai take rubutawa a tsayin kwanaki talatin har yinin yau kenan, kalmar da a yanzu bata san me take nufi ba, bata san bigirin da zata ajjiye ta ba, ta ci karo ne da ita a cikin mafarkan data saba a kullum. Ta shiga juya biron hannunta, tana tunanin da zuciyarta, da tambayar kanta a hikimance. "Zan zama marubuciyar kuwa?Zan iya rubuta abin da nake ji yana mini yawo a cikin kaina wanda baya barin ƙwaƙwalwata samun nutsuwa? Wanda yake gallabar zuciyata..Haka rubutun yake dama?" Ta ja numfashi ta sauke. "Haka kowacce marubuciyya take ji?" Sai ta sake ɗora biron akan takaddar akaro na babu adadi, wannan karan ma haƙarta bata cimma ruwa ba, duk yadda ta saƙa zaren labarin daka farko har ƙarshe, data zo rubutawa komai yake daburce mata, ta kasa. "Wataƙila bani da basirar zama marubuciya" Ta furta a fili cike da sangarta da shagwaɓar da take jin kamar da ita aka haife ta, luuu ta ja manyan idanunta ta lumshe su, saboda iskar bishiyar darbejiyar dake kaɗata, wacce ta kasance zaune a ƙasanta saman tabarma. Sai kuma ta saki dariya me sauti. "Ƙila rabon zama ƴar jarida ya daƙusar dani daga kasancewa marubuciya, irin shahararrun marubutan nan da suke tashe, amma ba masu rubutun lalata tarbiyya ba" Idan zaman banza ne da rashin abin yi ya riga ya gama zama a jikin Ana, hankali kwance cike da sabon nishaɗi ta juya bayan littafin nata, ta fara rubutu sannu a hankali. "Sunana Ayshatul-Haleeym, da yawan mutane basu san asalin sunana na Aysha ba, irin sunan Nana Aysha Matar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Ban san ina Babana ya samo sunan ba, a kaf danginmu na uwa da uba babu wata mai suna Aysha....Au dangin Babanmu basa son mu na manta ban faɗa muku ba, bayan Aysha, ana kirana da Haleeym irin sunan ƴan gayu, duk da ni talauci ya ɗaurawa iyayena riga, bayan Haleeym ana kirana da ANA. Sunan Mamata INNTI, wanda ya amsa sunan uba a gare ni ana ce masa DAADA, Muna zaune a garin Kano, a cikin local Government ta Municipal, a wata unguwa da ake kira da Kankarofi. Mu biyar ne a wajan Iyayenmu, haka Innti ta haife mu duk da Talaucin da take fama dashi, amma masu kuɗi yara biyu kawai suke haifa, Babban yayanmu ana ce masa BABBAN YAYA, bayan shi ta haifi tagwaye duk maza Yaa Jaheed da Yaa Jadid, amma nafi son Yaa Jadid, saboda shi yana taje mini kaina, yana yanke mini farce, shima Yaa Jaheed ina son shi saboda yana da kirki, yara uku kenan, sai mu da muka kasance ƴan auta, tagwaye ne muma, dani da mahaɗita, rana ɗaya aka haife mu, bamu san waye babba ba, Innti ta ce bata cikin hayyacinta ta haifo mu, don haka kowa babba ne. Sunan abokiyar haihuwata IFTIHAL, wasu na ce mata Iftin Innti, ni kuma Shalelen Innti Itama sunanta Aysha, ni ANA ita IFTI... Sai ta dakata daga rubutun tana bin jerin kalmomin da bata san yaushe ta rubuta ba, ba tare data san hakan shi ne tubalin zama marubuciya a gare ta ba, baiwar kalaman da suke fitowa daka ƙasan zuciya na zahiri. Iskar ta cigaba ta kwasarta dara-daran idanunta ya fara lunshewa alamar bacci. "Ina da ƙanin uba, amma fa shi ɗan daudu ne, ana kiran shi da suna Sukunbiya, don Allah ba sunan kifi ne haka ba? Bala sunansa na gaskiya... Sai kuma Yaa Sam, abokina aminina kuma yayana maƙocinmu ne, kyakkyawa ne sosai yana da grey eyes amma talaka ne irinmu, wasu da yawa suna cewa wai saurayina ne, bayan babansa ya yi masa zaɓen matar aure, kuma ni bana son ma ya zama mijina. Ina son namiji kyakkyawa,bani da burin daya shige na auri kyakkyawan namiji a duniya, fari, dogo, mai zubi da tsarin halittar Ubangiji, irin kyawun da bana damuwa ko da na Aljanu ne, talaka ne, gurgu ne, ko da me cutar ƙangamau ne (Hiv) muddin kyakkyawa ne ajin ƙarshe, irin kyawun mazan novel to zan aure shi, ko da ace zai dinga gutsirar naman jikina yana soyawa tare da cinyewa ne, kai ni ko da maye ne ina so. Wannan shine ra'ayi da tsarin ANA.... Bacci ne ya ci ƙarfinta a daf da lokacin da limamin Masallacin unguwarsu ke ƙwalla kiran sallar la'asar, haka ta cusa littafin a rigarta ta ɓingire wajan ta fara bacci. * 1500 / 1700. TIVLAND NA FARKO Sau tari ana cewa, idan masifu suka yi yawa a inda kuke, yin ƙaura tare da yin nisa shine yafi zama alheri, a kwanakin baya na faɗa muku asalin su waye Tiv, na san kuma kun fahimci daga ina iyaye da kakanninku suka samu tushe, Hausawa sukan ce, Tushiya masomin dawa, haka kuma kowa ya bar gida, gidan zai bar shi. Mun samu matsin rayuwa, na rashin doka, bamu da shugaba ko wanda suke jagorantarmu, kowa yana cin gashin kan shi ne, mun yi imani da Akombo fiye da yadda kuke tunani, mun wayi gari cikin fari da talauci, har muka yanke shawarar yin ƙaura, ashe Akombo ya yi fushi me tsanani damu, hakan yasa komai ya rikici mana. Muka ɗauki hanya me nisa. A cikin wannan shekarar a hanyarmu ta yin ƙaura saboda yawan jama'a sai aka rabu kashi da kashi, kowanne rukuni suka kasance Ahhali guda, kamar yadda muma muka kasance iyali ɗaya ta hanyar kaka ɗaya daya haifi iyayenmu, ni na fito daga ɓangaren Ikur ɗan'uwana ya fito daga ɓangaren Imande, ma'ana babana shine Ikur babansa kuma Imande, muka tashi dangi biyu a bisa jagorancin kakanmu. Mun yi wannan ƙaurar saboda yawan jama'a, da kuma neman ruwa da kuma Dazuzzuka sai ƙasar da za ta iya yin noma. Akan hanyarmu ne wa'adin mutuwar kakanmu ya yi, dare ya tsala babu gida gaba, babu baya, muna tsakiyar daji ne. Mun yi kukan rashi sosai, domin shine muke gani matsayin Dattijon da yake jagorancin Ikur da Imande. A cikin wannan daren muka fara shirin bikin jana'izar kakanmu, muna yara amma har yanzu ina hango yadda al'amarin ya faru. Aka haɗa ganye da ruwa da ƙasa, aka fara watsawa gawar kakanmu tare da wasu kalamai na tsafi, an lulluɓe shi da farin yadi. Ba'a ɗauki minti biyar da fara wannan tsafin ba, mu kaga kakanmu ya miƙe saman ƙafafuwansa, na ɗauka idan mutum ya mutu shikenan tashi ta ƙare, bisa ga mamakina sai na ga gawa ta miƙe da ƙafafuwanta tana tafiya, haka muka dinga binsu gawa na tafe muna bayanta ana kiɗa da waƙe, har zuwa inda aka haƙa ramin, kakanmu na zuwa zai shiga cikin kabarinsa, sai mu kaga ya tsaya cak, wani baƙin hayaƙi na fita ta cikin idanunsa, wanda alama ce na cewa, yana son bayar da saƙo ne kafin ya kwanta a cikin kabarin nasa, wanda zai zama gidansa na ƙarshe, sai idan dalili ya zama babban dalili za'a iya tayar da shi ya bamu haske akan abin da ya shige mana duhu muka kasa samun mafita mai ɓullewa. Ya yi shiru daga basu tarihin kakansa, ya dubi ƙananun yaran da suke gabansa, basu fi shekara biyar biyar ba, sai namiji da ba zai fi shekara biyu ba a cinyarsa ya yi luf yana bacci. Yana shafa kan wata mace ya ce "Na san kuna son jin me kakana zai ce ko a lokacin?" Suka jinjina masa kai alamar "eh" Ya ɗora da; Ikur da Imande, muna tsaye muna kallon kakanmu, Iyayenmu na kallon mahaifinsu suna sauraro daga gare shi. Cikin abin da bai gaza daƙiƙo ba, gawar kakanmu ta buɗe bakinta cikin damuwa da murya irin ta kuka da tashin hankali, ta ce “Haƙiƙa kun karya dokar Akombo, bala'i da masifu za su faɗo muka, ba za ku taɓa samun sauƙi ba, har sai UWA MAMAA ta bayyana, zata bayyana ɗauke da TSAV, kalmarta ɗaya waraka ce a tattare daku, albarkarta ceto ce a wajanku, kada ku neme ta, ita da kanta zata kawo kanta inda kuke, domin bata kasance ɗaya daga cikinmu ba, tana wata uwa duniya, wata nahiyar ta daban, kar ku neme ta, zata zo har inda kuke ta same ku, duhu da iska,da baƙin hayaƙi da kukan Akombo shi ne zai baku shaidar cewa, MAMAA tazo, kalmanta shi ne misali na biyu, babu yankan shakku a duk wani furucinta, harshenta bala'i ne ga ƴan'uwanta, ku kuma haske da tabarraki ne a gare ku, idan kun samu MAMAA kar a yadda a kuskura ta kasance da ɗa namiji, balle ta ɗauki ciki, MAMAA tsarkakkiya ce, na san Ikur da Imande da maitar mace. Akwai alama ta uku da zata sake bayyana zuwan MAMAA, idan an yi mata gwajin budurci, Alƙalamin ba zai taɓa shiga jikinta ba, babu wani daya isa ya amshi kimar MAMAA, zaku sadaukar da budurcinta ne zuwa ga Akombo, Tsav ɗinta zai cece ku” "Kaka mene Akombo da Tsav?" Anum ta yi tambayar cikin rashin fahimtar tarihin kakan nasu na zamanin daya shige. Ya dubi Anum ya ce "Anum, Akombo yana nufin ikon ruhaniya da aka gada daga kakanni, yana warkar da cuta, kariya daga bala'i, gano me laifi, warware rikicin dangi a taƙaice Akombo shine haskenmu da muka yi imani da shi Anum. Tsav shi ne ikon sihiri mugun iko a al’adar Tiv. Ana danganta shi da Mayu, masu shan jini, masu cutarwa ta ɓoye ana cewa Tsav yana cikin jinin mutum ko ruhinsa. Ba kowa ke da Tsav ba masu Tsav suna iya, haddasa cuta, kashe mutum a ruhaniya, rikitar da al’umma hakan na faruwa ta harshensu, a kalamansu" Ya cigaba da basu labarin asalinsu; Bayan mun kammala sauraran Kaka, yana gama faɗa ya faɗa cikin kabarinsa muka binne shi. Muka cigaba da nausa tafiya a tsakiyar daren har muka samu yada zago a gaɓar wani ƙogi. A lokacin Itayo daga ɓangaren Imande shine ya amshi jagorancin tafiyar. A hannunsa akwai ganye da aka ɗaure da zare,da ƙasa a ƙaramar ƙwarya, da ruwa daga kogi. Ya durƙusa a wajan yana duba ƙasa kamar me nazari cikin girmamawa ya ce “Ba mu mallake ku ba” ya faɗa a hankali. “Ku ne kuke riƙe mu.” Ya ɗauki ɗan gishiri ya zuba a ƙasa. Ya shafa ruwa a ganyen, ya ɗora su a gefen wuta. Murmushi mu kaga yayi, akan hadayar da ya yi wa Akombo. Itayo ya ce "Akombo ya yarda da zamanmu a nan, bai amince da zubda jini ba, duk wanda ya karya doka bala'in Akombo zai saukar mana, don haka a kiyaye kun ji?" Ikur da Imande sun yanke shawarar a zauna a nan, saboda ruwa mai yawa, mun samu ƙasa me laushi da albarka ga kuma sauƙin noma. Aka kafa tanti Ikur suka keɓe haka Imande, muna murna mun samu makoma me kyau muna tsaka da bacci, wata mummunar masifa ta afko mana, wanda ya haddasa mana rashin mutane wajan ashirin a cikinmu, farmakin da ƙabilar Jukun suka kawo mana. 1976. TIVLAND. Shigowar Dooshima ne da sauri ya dakatar da Kaka daga Tarihin da yake bawa jikokinsa na asalinsu wanda yake bin tarihin shekara-shekara na abin da komai ya faru, tunda daga asalin Tiv har zuwa yanzu da yake shekarar da sukai ƙaura a 1500/1700. Kaka ya bi ɗansa Dooshima da idanu, shima kallon mahaifin nasa yake kafin da hanzari kuma ya ce "A ɓoye mata da ƙananun yara" "Ɓoyewa? Dooshima lafiya?" Kaka ya tambaya da tsoro saboda gudun wani bala'in da Akombo zai jefo musu. Anum na ɗan juya fararen idanunta masu kyau da tsari irin na mahafinta Dooshima. Dooshima ya kalli Kaka ya ce "Sojoji ne, sune sukai mana ƙawanya kar su sake kashe mu, kamar yadda Junkun suke bin mu kowacce farar asuba su kashe mu" "Na rantse da Akombo babu abin da zai faru da dukkan jinin Ikur alƙawarina ne wannan, ka hanzarta ɓoye yaran nan yanzu" Anum ta ce "Kaka me ya saka za'a ɓoye mu?" Ya shafa kan ta cike da damuwa ya ce "Za mu iya rasa ku a yau ɗin nan Anum ɗin kaka, jeki wajan Babanki ya ɓoye ki kin ji?" Rashin yadda ya bayyana a tattare da Anum, ita a dole sai ta fita taga Sojojin da ake magana akai. Haan ne ya shigo hannunsa ɗauke da baka da kibbau, yana ganin ɗan'uwansa Dooshima ya furta "ka shirya?" "Zan ajjiye Anum da Jarumi" Tashin hankali ya wanzu a saman fuskokinsu, tsoro suke ji da gaske, sun ɗauka sun samu ƴancin kai bayan zuwan turawan Biritania, amma hakan duk ya tafi a busar sarewar Audu. Haan ya furta "Yaushe za mu daina fuskantar matsi da rikin ƙabilanci, anya ba za mu yi magana da gawar Kakanku ba Ortyom?" Kaka ya ce "Ba za mu daina shiga masifa ba, har sai MAMAA ta bayyana wacce za mu samu TSAV a tattare da ita, dole sai ita" Cikin gwaranci Anum ta ce "Kaka yaushe Mamaa zata zo?" "Yau ne, gobe ne, jibi ne ko gata, wannan shekarar, wannan zamanin ko sai bana raye ban san yaushe ne Mamaa zata bayyana ba, amma komai daran daɗewa Uwa Mamaa zata zo, kuma za ta cece mu" ƙarar Kibbau suka ji, da sauri Haan ya yi waje yana kare ƙofar shigowa gidan duk da a tsakiyar dokar daji suke a gaɓar kogin da bashi da suna. Da hannu ɗaya Dooshima ya saɓa Anum a kafaɗa, ya saka hannunsa ya ɗauki yaron dake wajan kaka yana bacci ɗan wajan Haan. Can cikin gidan ya shiga wajan wani ramin ƙasa inda suke ɓoye mata da yaran, Anum na kuka da ihu haka ya dannata cikin ramin ya ɗauki Jarumi ya saka mata a cinya, ya mayar da ƙofar ya rufe tare da ƙaton dutse, cak ya tsaya yana goge hawayen idanunsa bayan ya zubawa ramin ido, yana jin kukan Anum dake ratsa kunnunwansa, babu tabbacin zai sake sanyata a cikin idanunsa. Ya ɗaga kai sama ya ce "Na bar Anum da Jarumi a hannunka Akombo, an yi maka laifi har yanzu Uwa bata bayyana ba, waɗannan ɗin yara ne ka kula dasu Akombo" yana faɗin hakan ya fice da sauri yana tushe kunnunwansa daga jin kukan Anum ɗinsa. *** Mafari. 11/8/2025. KANKAROFI/ KANO MUNICIPAL. Kankarofi na daga cikin tsofaffin unguwanni da ke cikin birnin Kano. Tana cikin Kano Municipal LGA. Yammacin ranar Asabar ne wanda ya yi dai-dai da Shaɗaya ga watan takwas, shekara ta dubu ashirin da ashirin da biyar, kasancewar watan Nuwamba ne, farkon shigowar sanyi ya saka iska me daɗi da sanya nutsuwa take kaɗawa a lungu da saƙo na cikin garin, har zuwa unguwar Kankarofi da mutane shige da fice. Ƙarar ihunta ne ya ja hankalinsu zuwa ga ƙasan bishiyar da take kwance tana bacci a saman tabarma, ba ihun ke basu mamaki ba, face yadda take kiran sunan Anum da dukkan ƙarfinta zufa na yanko mata, bayan sunan Anum har sunan jarumi take kira. "Kar ku bar su a ramin nan, shikenan za'a kashe Anum na shiga uku, Anum, Anum... Wanda yake alwala ya juyo ya kalle ta, sai ya girgiza kai ya ce "Ina fa'ida a baccin La'asar daman, ba dole mutum ya yi mugun mafarki ba, tai ta bacci kamar kasa haba" Matar dake ta tsinke zogale da ya yi kore shar saboda rani, ta ajjiye zogalen tare da zuba tagumi sannu a hankali kuma take bin yarinyar dake ƙwance wacce bata fasa kiran sunan Anum da Jarumi ba da kallo, can ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Tashe ta daga baccin nan Jaheed" ya ajjiye butar hannunsa. Tsaye ya yi a kanta, fuskarta ta yi sharkaf da zufa ta kuma yi ƙyalli ya saka ƙafa yana shurinta a hankali Ya ce "Ana" Jadid ya kalli Jaheed yana dariya ya ce "Wannan uwar baccin, da shegen nauyin bacci kake wa wannan kiran Jaheed?" "Wallahi takaici ne ya kamani, wannan ihun kamar mahaukaciya sabon kamu har ina" Jadid ya ce "Ko kuma sabuwar amaryar da ake shirin sawa a lalle ba, zaune zaka tashe ta, idan ba haka ba, ba tashi za ta yi ba". Duk yadda Jaheed ya yi ƙoƙarin tashin Ana kasawa ya yi, ya juya ya kalli mahaifiyarsu data mayar da kai zuwa ga aikin tsinke zogalen ya ce "Innti taƙi tashi, anya lafiya?" Bata kalli Jaheed ba ta miƙe zuwa inda Haleeym ke bacci da sambatun kiran sunan Anum da Jarumi, ta zubawa kyakkyawar fuskar yarinyar idanu kamar tana karantar yanayin da take ciki, ta fara kiran sunanta. "Ayshatul Haleeym!" Ta nanata "Ana, Haleeym" Sallama ya yi a nutse cikin kamala ya shigo gidan, amma duk basu san ya shigo ba, ya jima tsaye hannunsa cikin aljihu ya watsa idanunsa akan fuskar Ana ganin yadda Innti ke ta kiran sunanta amma ko motsi ba ta yi. Ya juya zuwa bakin rijiya, ruwan da ya gani a cikin bokici ya ɗakko tare da ƙarasuwa wajan da suke, duk suka matsa shi kuma ya ɗaga bokicin ya sheƙa mata ruwan. Ruwan sanyin da aka kwarara a jikinta ya haddasa mata farkawa daga nauyayyen baccin yamman daya ɗauke ta, ta shiga mustsikka manyan idanunta, ƙoƙarin komawa take yi ta kwanta tana surutai irin magagin baccin nan wanda bai gama sakin mutum ba, daman gata da nauyin bacci. A fusace ya ɗauke ta, ya dire a wajan. Ganin ta tsaya akan ƙafafuwanta ya saka ya juya ya zauna akan Benci yana duba agogo. Littafin dake rigarta ya faɗo ƙasa "Wayyo Anum, ki yi shiru kin ji jikalle" cikin magagin baccin ta sake furta hakan idanunta na lunshewa jikinta na zubar da ruwan daya kwara mata saboda yadda ta ishe su da ihun ana saka Anum da Jarumi a cikin rami, garin kayan takaicinta ta kwasuwa kanta mutanen ɓoye ita kaɗai ta sani sai Allah, yin duniya ta tashi daga bacci amma fafur taƙi sai mimmiƙe hannu take. Daga gefe aka ce "Wai uwar wace Anum ɗin nan, da kika cika mana gida da kiran sunanta a cikin baccinki? Ƙawarki ce ko?" Jadid ya girgiza kai ya ce. "Ko kuma ta yi rigima da wasu, suka biyo yammaci wajan shaƙe wuyanta wallahi" "Babu mamaki" in ji Jaheed. Sai kuma ya miƙe yana kakkaɓe yadin da yake jikinsa da furta "Duk hankalina ya tashi, na ɗauka Shalelen Innti aka kawo wa hari, gashi na rasa jami'in la'asar dole a gida zan gabatar na yi na koma shago yanzu" "Kar ka sake ka yi mini sallah a gida" Innti ta furta a sanyaye idanunta zube akan yarinyar da aka tayar daga bacci. Sai ɗacin rai take yi tana kukkumbura kamar wata kububuwa, fuskar nan na ƙyallin kyakkywar baƙar fatarta ga shatin tabarma da ya yi mata zane a kumatu Jaheed ya ce "A gafarce ni Innti" Ya furta yana ficewa daga cikin gidan. "Mutum yana baccinsa me daɗi kawai sai a katse shi fisabilillahi? Kun san me nake gani?" Jadid da Innti suka zuba mata idanu, wanda ya tashe daga baccin kuwa har yanzu ko tari bai yi ba, bai ma sake kallon inda take tsaye ba, tuni ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar hannunsa daya kunce. Ta juya ta kalli Jadid suna haɗa ido ta murguɗa masa bakinta, ta kalli Innti ta ce "Innti wanne me tsautsayin ne ya tashe ni?" "Gashi can" Jadid ya bata amsa yana nuna bayanta. Ta juya zata fara masifa idanunta ya sauka akan Baban yaya, nan take ta ji zufa na karyo mata duk da iskar bishiyar darbejiya dake kaɗawa tana bada yanayi me daɗi. Ta haɗiye yawon baccin daya tarar mata a baki. Ta nufi tabarmar zata zauna ta ji kamar daga sama ya yi gyaran murya. Sai ta kwaɓe fuska ta ce "Nifa aka zalunta bance komai ba, kun san a tarihin gidan nan ko Tv ta wasa ba'a taɓa yi ba, balle ta gaske ɗan kallon nan dake saka nishaɗi ba'ayi, kowa keyboard ce a hannunsa, shikenan na samu ana haska mini film a cikin baccina sai a tashe ni saboda mugun abu? Yanzu ba lalle na sake yin wannan sa'ar ba, gashi ina son sanin yadda ƙarshen abu zai kasan da rayuwar Anum data Jarumi...," bata ƙarasa maganar ba, ta miƙe a zabure ta yi cikin ɗaki ganin Babban yaya ya ciro darbejiya tasan tsaf zai zane ta, ba imani ne dashi ba wallahi ga mugun abu. Ganin ta shige cikin ɗakin ya nufi hanyar waje, bai jima da shigowa ba tun safe amma har zai sake ficewa. "Tafiyar kenan?" Inji Innti. Ya jinjina kai alamar "Eh" "Allah Ya tsare hanya Babban yaya, kar ka yi dare don Allah bana son kaiwa daren nan ka ji ko?" Jiki a sanyaye ta yi furucin. Bai amsa ba, ya saka kai ya fice. "Babban yaya kike cewa kar ya kai dare? Shine fa babba a gidan nan, babban wa magajin uba ne Innti a ɗan raga masa" Hararar wasa ta yi masa kafin ta fara ƙwalla kiran sunanta. "Ana kika bari na shigo ba ki fito kin ɗauki buta a gidan nan kin yi sallah ba, mai rabani dake sai Allah ki cigaba da saka ni kumfar baki a gidan nan" Ita kam tuni ta yi nisa a tunanin da take yi, game da rayuwar mutanen da aka haska mata a cikin baccinta, waɗanda bata san su waye ba, ƙilama basa duniyar, domin rayuwar da taga sunayi irin ta labaran almara ne da hikayoyi da kuma da tsuniyya, koma yaya ne, ita a Film ta ɗauke shi, kallon ya yi mata daɗi sosai, domin taga abubuwan daba kowa ne ya san dasu ba. "Jadid shiga ka fito mini da yarinyar nan" Fit ta fito daga ɗakin, kai babu ɗan ƙwali sumar kan nata a hargitse gashi tubarakallah kamar Buzuwa har ƙasan wuyanta baƙa suɗik da ita. "Ki cigaba da shiga banɗaki babu kallabi Ana, in sha Allah sai na saka Babban yaya ya aske mini rabin sumar nan taki, kamar wata Bunzuma" babu abin da take so sama da sumar kanta cikin sauri ta fusge hular kan Jadid ta kifa a nata kan. Ta yi cikin banɗakin Ya ce "Kika shafa mini kwarkwata a hula na daina koya miki komai, me kama da chocolate" "Yaushe ka fara yin halitta ne Jadid?" Ya ce "A gafarce ni Innti, fatar Ana ce ke bani mamaki wallahi, ko mai take shafawa ne?" Innti ta ce "Sai ka tambayi Babban yaya, domin naga kalarsu iri ɗaya ce ko shine yake sammata man da take shafawa, bata da kuɗin siyan mai" Jadid ya yi saurin yin shiru jin ta sako Babban yaya a lamarin nasu. Ganin ya yi shiru ya saka ta ce "Kasha maganinka ne?" Ya ce "E, saura na dare in sha Allah" "To, Allah Ya sa kaffara ne Jadid" Ganin ta fito da gudu daga cikin banɗakin ya saka suka juya suna kallon ta, ta saka hannu ta tushe hancinta ta ce "Wanne ƙazaminne ya gundura mana kashi a ruɓaɓɓen banɗakin nan sai uban wari, kana gani ka san kashin gardi ne wallahi" Jadid ya ce "Waye gardin? Babban yaya? Bari ya shigo gidan zai ji komai in sha Allah" Tsuke fuska ta yi, bata sake magana ba ta cigaba da ɗaura alwala cike da nutsuwa da tarbiyyar da Innti ta ɗora yaranta akai. *** “Labaran rana, a ranar 25–26 Disamba 2025, Amurka ta kaddamar da harin sama da ake kira da airstrikes a yankin arewa‑yammacin Najeriya, musamman jihar Sokoto. Wannan aiki ya kasance tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya Harin ya shafi sansanonin ƴan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State (ISIS)musamman irin waɗanda ake kira Lakurawa a yankin. Sojojin Amurka sun yi amfani da makamai masu daidaitaccen GPS daga jiragen sama masu iko da na teku, inda suka kaddamar da harbe‑harbe kan manufofin da aka gano suna da alaka da ISIS. Babu cikakkun bayanai kan adadin mutane da suka mutu, amma gwamnati ta ce an kashe ƴan ta’adda da dama. Harin ya faru ne da yardar gwamnatin Najeriya ta wancan lokaci. Me rahoto Ahlam Abdallah Zango, mita 116 BRIGHT FM” Cigaba da sauraron Redion ya yi yana murmushi cikin nutsuwa da kamala. “An saurari rahoton tsaro daga abokiyar aiki Ahlam Abdallah Zango. Yanzu za mu koma ɓangaren wasanni, me rahoto Anees Adeel Yakasai" kashe Redion ya yi ya ajjiye a gefe ya ɗan murmushi tare da kallon ta ce ya ce "Madam" "Na'am Abban Mufeed" Ya furta "Ina jin daɗin yadda kika taimaka mini muka tsaya kai da fata wajan cikawa Ahlam burinta na zama ƴar jarida". "Abban Mufeed, Ahlam amana ce a gare mu, kafin mahaifinka ya rasu kai ya bawa wasiyyar kulawa da Ahlam, a matsayina na matarka dole ne na tayaka kulawa da ita, da wannan wasiyyar, ka duba muryar Ahlam ce muke saurara ni da kai a Redion yanzu haka" ta ce tana riƙe hannunsa. "Ba iya ni dake ba, duka garin Kano suna sauraron Amanata, ita ɗin Golden voice ce" Idanunsa ya kawo ruwa, sai kuma ya ce "Ni tana ina ne ma? Wani labari na ji ɗazon nan ta zo na faɗa mata amma sai ta bada abin sadaƙa" cikin tsokana Jiddah ta ce "Haba ranka ya daɗe uban Mufeed, yayan Ahlam mijin Hawwa'u a gaza mana" Daidai nan Ahlam ta fito tana gyara hular kanta, bata gama dawowa daidai daga baccin da take ba, Mufeed ya je ya uzzura mata ganin yayanta ya saka ta zauna cikin shwagaɓa ta ce "Yaya kaga Mufeed ko?" "Babu ruwan Yaya, ki faɗawa babarsa" Cikin sauri Jiddah ta miƙe tsaye ta ce "A'a sun fi kusa, harshe da haƙori kunga hanyata" ta haura sama tana musu dariya. Engineer ya ce "Na biyo hanya na ci karo da taron mata, har zan shige na tuna ina da suda a gida, na tambayi meke faruwa aka ce wata kishiya ce ta ɗauki jaririn amayar mijinta ta cilla a ruwan zafin..," ko gama bata labarin bai yi ba, ta zabura ta miƙe duk da hannunta ɗaya da yake shanye ta ce "Yaya wacce unguwa ce don Allah" Ya ce "Kawo abin sadaƙa" Cikin shwagaɓa ta ce "Ina son ka, sosai da sosai yayana abin alfaharina, you're my 001" "Daɗin baki, babu komai da haka kike yin nasara akai na. A Gandun Albasa ne" Ɗaki ta koma, ta ɗauki jakar kayan rahotanni cikin sauri ta fice tana waving yayanta. Ya lumshe idanunsa ya ce "Allah Ya tsare" *** Jifanta ake yi da duwatsu yara sun taru maza da mata ana kallon yadda take durƙushe, tuni yaron da aka kama shi da ita acikin lungun yana taɓa mata ƙirji ya gudu. "Nifa gwara da asirinta ya fito fili, ba zata zauna ta ɓata mana yara ba, uwa uba gata mayya dole ne tabar mana cikin rugar" bata fahimtar me suke cewa, wani irin kartawa cikinta yake mata saboda saɓar yunwa. Fincikota aka yi da ƙarfi. Jamila ta ce "Babu mamaki ita ta cinye jaririyar Zabba'u tun tana ciki. Wannan ai irin masifa ne" Rinannun idanunta kawai Batty ta ɗago tana binsu da ido da ƙyar ta ce "E ni mayya ce, amma wallahi bani na ci jaririyar Zabba'u ba, daman Zabba'u bata da ciki ƙarya kawai ta yi muku. Ga cikinta nan lafiya lau babu alamar ɗa ya taɓa zama a ciki, kayan cikinta gwanin sha'awa" Jamila ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Wannan wacce kalar masifa ce ai dole ki bar rugar nan kafin ki cinye mu gabaɗaya" tusa ƙeyarta suka yi zuwa gidan me gari. *** Ganin Shida ta kusa ya saka ta ɗan ƙara saurin da take yi akan nada, kanta a ƙasa tana tafiya cike da nutsuwa kamar kazar da ƙwai ya fashewa, addu'a take yi Allah Ya sa Babban yaya bai dawo ba, yanzu sai ya haɗa mata Malaman jikinta. Daga can nesa ta ji an ce "Ifti" cikin sauri ta juya. Zaune ta hango shi a ƙasan bishiya, shi da abokansa suna ta faman karta hayaƙin taba na tashi, ya ɗan ya fito ta da hannunsa ta ƙarasa "Na'am Dadaa" ta amsa tana durƙusawa. Ya dube ta sosai yana sake zuƙar tabar yana busawa a gefe ya ce "Ina Ana na ganki ke ɗaya?" Ta ce "Ana na gida, kitso na je na yi" "To nawa kika samu a can?" Ta ware hannunta, yaga curarriyar ƴan dubu guda biyu, ya kwashe kuɗin yana faɗin "Jeki gani nan zuwa gidan, hanzarta Ifti, kar Ana ta biyo sahunki" Kan ta ƙasa hawaye na cika idanunta ta ce "To Dadaa" Bayan ta yi gaba, wani Dattijo wanda a ƙalla zai yi shekaru 62 bakinsa fal goro da ƙaton tumbin daya kwanta masa, ya saɓa babbar rigar jikinsa ya ce "Kar ka ce mini ɗiyar wajanka ce wannan?" Dadaa ya bushe da dariya yana juyawa wajan kallon Ifti ya ce "Alhaji Baita, kar dai ka ce baka san ƴar taka ba, ai Tagwaye ne su, Ayshatul-Ana, da Ayshatul-Ifti, wannan Ifti ake ce mata, ta gidan kuma Ana, yarana ne" "Ka ce kawai dukiya na gida a ajjiye" In ji Alhaji Baita. Ya ɗora da "Ina da shawara, Miliyan goman dana saka na caca, kai kuma ka saka keken ɗinkin matarka, yanzu na ƙara miliyan goma akai ya zama miliyan ashirin, ina son ka saka Ifti ma'ana Iftihal a cikin cacar, idan ka ci zan baka miliyan ashirin kash, idan na ci, zaka bani Iftihal.... *H I Y A A M* Page 2 Bright pens Yota/001 Dedicated to Nazeefah Sabo Nashe Bai sani ba ko yana da gwaggwaɓar riba a sanya ɗiyarsa Ifti a cikin cacar, idan ma ya barta mene amfaninta da kuma tasa ribar, banda galaulawar kula da ita, shi ƴaƴa mata a marasa amfani yake kallon su, bai taɓa saƙawa a ran shi suna da wata rana a wajansa ba. Gwara ya sata a cacar ya ciyo Miliyan ashirin a kanta, bashi da wata asara. "Zan saka Ifti a cacar na ci Miliyan ashirin, ita kuma Ana zan kai ta wajan wani Alhaji da zata dinga kwana a can yana bani kuɗi" Ya yi zancen a ƙasan zuciyarsa. "Idan bai ci cacar ba, hakan yana nuni da cewa zai damƙa Ifti a hannun Alhaji Baita?" "Ko kuma aikin gida zata dinga masa, tunda matansa huɗu yana haddace dasu a kan shi" ya yi shiru yana nazari, me gobe zata haifar. Ifti ta yi ƙanƙanta da auren Alhji Baita ya yi mata tsofa tuƙuf, to me zai yi da ita? Bashi da masaniyyar yadda rayuwar Ifti zata kasance idan tsohon ya mallake ta a caca, domin mutum ne me shekaru 62 a duniya, kaso ɗaya daga cikin haƙoransa duk a cinye suke, sauran kuma goro ya yi musu ado da lalle, sun yi jawur ko magana ya yi warin goro ke fita, ƙoƙofin gidansa, kulle suke da mata huɗu cif, yaransa, da jikokinsa kamar gyaɗa saboda azabar yawan da suke dashi. Haka gidansa yake, kamar rayuwar bariki. "Ka saka Iftihal a cacar nan da Alhaji Baita ya yi maka ta yi, kana kallon yadda ka haɗa zumunci da talauci dai" cewar Ɗahe yana cilla kartar a ƙasa da murmushin ƙeta Ƙwarai da gaske, Daada da talauci kamar tagwaye ne, suka fito daga mahaifa guda, ko dai yaga bayan talaucin nan, ko kuma shi talaucin yaga bayan Daada ya kai shi zuwa inda ba'a dawowa idan anje. Ganin Daada ya yi shiru, yana ta jan sigarin hannunsa, ya ajjiye kartar da suke bugawa, ya saka Malam Ɗahe miƙa hannunsa zuwa kafaɗar Daada ya jijjigata, alamar tabbaci akan shawarar da yake basa, wacce babu zamba cikin aminci a tattare da ita ya ɗora Da "Ka saka a ranka, ɗiyarka ce jarinka" "Amfaninta kenan" Ya nanata yana jinjina kai, alamar tabbacin maganarsa ga Daada. "Su yara mata dukiya ne, kadarar rufawa kai asiri, ka amince ka saka Ifti a cikin cacar nan, sai ka ga ta ciwo maka maƙudan kuɗaɗe kuma yanke talauci wlh" Garba ya riƙe zancen daga wajan Malam Ɗahe, yana sake yi wa Dadaa ingiza me kantu ruwa wajan sanya ɗiyarsa mai hankali da nutsuwa da kamala, kyau da tsarin halitta. Dadaa ya yi shiru yana tunani, idan abin da yake buƙata ne a zuciyarsa, bai shige kuɗi masu ɗumbin yawan da zai iya sake dulmiya su a cikin cacar ya sake cin ninkin su ba, yana son kuɗi fiye da duk wani abu da yake cikin wannan duniyar, ƙamshin jaka guda kaɗai dagula masa lissafi yake yi balle yaga fara ƴar shehu, mulmulalliyar dubu ɗaya, ko notikan kansa basu kunce ba, da ƙyar yake iya hattama nutsuwarsa ya daidaita zuciyarsa gudun murna da zumuɗi kar su yi masa illar da zai gaza ganin bayan dubu ɗayan. Ya dube su, yana nazari. Yana buƙatar lokaci,lokacin da zai tantance mene yafi muhimmaci a gare shi, a tsakanin ɗiyarsa Iftihal da dukiyar da ake magana akan ta, sai ya nutsu, yadda zai tantance Me ake nufi da zuri'a ta ƴaƴa mata, Me ake nufi da arziƙi masu rufin asiri. "Ina buƙatar lokaci" Ya furta yana miƙewa tsaye. "Wanne lokaci kuma kake buƙata, ƴa dai taka ce, kana da iko da rayuwarta, kamar yadda miliyan ashirin ɗin nan suke jiranka" "Malam Ɗahe, a bani lokaci, bari zan je na dawo sai mun haɗu zuwa tsakiyar dare ko safiya ko kuma war haka yammacin nan" Wani irin maƙetacin murmushi Alhaji Baita yake wanzar dashi a fuskarsa, murmushin da indai a kaga ya yi a cikin abu biyu ne za'a samu guda, wanda ya zama zakarar gwajin dafi. Ko dai budurwar zuciyarsa ta hango masa kyakkyawar matashiya wacce zai huta ya more tsofansa a jikinta, ko kuma an yi masa batun caca, me kawo ruwan kuɗi. Musamman da idan ya rufe idanunsa yake hasaso tsanain kyawun fuska irin na Iftihal Da faffaɗan ƙugunta,wannan mazaunan daya zauna das, ta cikin hijabin daya kwanta a bayanta ya hango hakan. Yabi Daada daya shige ya bar wajan da kallo, tare yin kwana ya ɗauke idanunsa yana kallon Garba ya ce "Garbati" Cikin rawar jiki Garba ya amsawa Alhaji Baita da murmushi a fuskarsa "Ni kaɗai na ga yarinyar nan ƴar wajan Daada, ko kaima ka ganta don Allah?" "Alhaji wai Iftihal kake nufi? Daman baka da labarin tagwayen yaransa, Ana da Iftihal? Ai kaf unguwarsu babu yara masu kyawun ɗiyoyin Daada" Garbati ya shiga labartawa Alhaji Baita bayani akan su Ana da Iftihal "Ita wacce ta shige ita ce Iftihal ana ce mata Ifti, ɗayar ta gida kuma sunanta Haleeym ana ce mata Ana, kyawawa dasu" Wani yawo ne ya taro a ƙasan maƙoshin Baita cike da zalama ya ce "Kasan da yarinyar nan baka taɓa bani labarinta ba?" "Alhaji tuba nake, na gansu ƙanana ne yanzu fa suke aji uku na Sakandire" "Irin waɗannan sabbin ƙinƙisar nake so, a ganin farko yarinyar nan ta dagula mini lissafi sai tsiyaya nake ta yi ta ciki" Garbati ya shanye mamakinsa, wajan yin amfani da tafin hannunsa zuwa bakinsa ya rufe, ya sauke muryarsa a ƙasa kamar wanda wani zai ji me zai faɗawa Alhaji Baita ya ce "Ko zaka ƙara miliyan goma akan ashirin ɗin nan, yadda za mu samu damar shawo kan Daada ya afka cikin cacar, ina da yaƙini kai zaka lashe tunda ka fisa iya yin wasan nan nesa ba kusa ba, idan ka cinye sai ka yi gaba da ƴarsa ka more abinka, amma wani hanzari ba gudu ba, ka rufe ƙofofin gidanka, kar wankin hula ya kai mu zuwa dare, babu abin da ya rage maka na jerin ɗakuna huɗun nan sai dai ka haƙura" da wani irin yanayin da yake nuna Alhaji Baita yaje ƙarshe, irin wa'adin da ba zai iya tausasa zuciyarsa har ya gamsar da ita akan ta yi haƙuri da Ifti ba, ya ce "Sai na buɗe ƙofa ɗaya, ka ga an samu sarari zaman Iftihal a ciki ko?' Ya yi furucin yana kallon Garbati. Caraf Garbati ya ce "Wannan ma ya yi" *** Duk yadda Ifti ke sauri kar Babban yaya ya rigata cimma isa gida kamar yadda idanunsa ya nuna gargaɗi a gare ta, tafiya take yi cikin ɗan karsashin da ya yi mata saura a matsagaicin jikin nata, ta na yi tana juyawa ko Daada ya biyo bayanta, sai taga babu komai dake biye da ita sai ƙurar iskar bazarar dake tashi, a haka ta dinga bin jigin bango tana gujewa kwatocin lungun data shigo cike da taka tsantsan, kamar bangon da take bi zai tsake ta shige ciki, tana karyawa lungun da zai kai ta gida, tun a bakin hanyar ɗaya lungun wanda ya kasance yana da mahaɗa biyu ta hango shi yana tafiya, kamar baya son takawa, idan ya cire ƙafa ɗaya sai ya mayar da ɗaya, hannunsa duka biyun ya adana su cikin aljihun wandonsa, hular tsakin daya saka ya ɗan karkatar da ita zuwa gefe guda a kan. Buɗewar farar manyan idanunsa, da yadda ƙwayar idanun ta juya a cikin gurbinta, ya bawa Ifti tabbaci yake bata akan zai ci ubanta idan ya rigata ƙarasawa cikin gidan. Sai ta ƙarawa tafiyarta sauri, wuf kamar iska ta ƙarasa shigewa da gudunta tana haƙi. "Ass... Assalamu alaikum" "Wannan gudun ke kuma na mene? Gudu kina ɗiya mace haba ƴar albarka irin arziƙi a bari don Allah" Innti ta faɗa bayan ta amsa sallamarta. "Wallahi Babban yaya na gani" Ta ce da ƙyar tana juya idanunta, sai kuma ta zare hijabin jikinta ta rataye saman igiya tare da ƙarasawa kusa da Innti dake bakin murhu tana tuƙa towon masara. "Barka da gida Innti, kawo na ƙarasa miki aikin ki wuta kin ji uwata?" Innti ta girgiza kai ta ce "Jeki abinki ki huta ƙasan bishiya kafin a kira sallar magariba ku tafi makarantar dare ko" "Allah sarki uwata, Ubangiji Ya yi mini arziƙin da za ki huta, Allah Ya kula mini dake Sahibata" murmushi kawai Innti ke yi. "Mutuniyar abin ƴar haka ne? Innti kawai kika gani a taskar gidan ashe?" Cewar Jadid "Tuba nake Yaa Jadid" Ta ce tana ƙarasawa ƙasan bishiyar da yake zaune saman tabarmar da Ana ta yi bacci akai, labari sosai Ifti ta shiga bawa Jadid suna tafawa kamar ba yayanta ba. "Sannu da dawowa yaya" Suka haɗa baki ita da Jadid wajan faɗa suna daidaita nutsuwarsu, jinjina masu kai kawai ya yi sanda ya shigo ɗin, a hankali kuma ya durƙusa daidai inda Innti take yin aiki yana ɗan lumshe idanunsa saboda hayaƙi, ta juyo ta kalle shi, shima ya ɗan kalle ta, da body language ya yi mata magana sai ta ce "Sannu da hanya yaya, kaga ka riga Jaheed shigowa yau, shima na san yana hanya duk inda yake, wataƙila bai kammala sallamar mutane ba, tunda uban gidan nasa ya ce kamar ya yi tafiya shi kaɗai ne a katin yau" Shiru Babban yaya ya yi. Da nutsuwa kuma ya miƙe ya shige cikin ɗakinsu, wanda suke kwana su uku a ciki. "Innti wai ina Mahaɗita ne?" "Wai Shalelen Innti?" Maganar Jaheed ta riga shi shigowa cikin gidan, ya ƙarasa maganar sanda yake durƙusawa a kusa da Innti cike da ladabi ya ce "Sannu da aiki Innti" cikin kulawa ta amsa masa "Yanzu nake maganarka yaron kirki" "Sai gani ɗan halak yaƙi ambato" "Ma sha Allah, Allah Ya yi muku albarka ya kare ku daga dukkan sharri da abin ƙi" "Amin" Da ita suka amsa. "Innti wai ina Mahaɗita?" "Sannu kashin awakai, tana cikin ɗaki kin san yau da miskilanci ta tashi, gashi ana abokin gaban nata, ƙato da kwat" inji Jadid. Dariya sosai Jaheed ya yi kafin ya ce "Tuwo da miyar kuka" Duk kiran da Ifti ke yi wa Ana ƙin fitowa ta yi, sai da aka kira sallar magariba sannan ta fito tana kame fuska taƙi yi wa kowa magana, tana shirin ɗaukan buta ta ji an zabga mata ranƙwashi a kanta, zafi da raɗaɗin da ta ji ya sauka har tsakiyar ƙwaƙwalwarta, yatsun ƙafafuwanta suka shiga rawa da kakkarwa, jikinta ya dinga tsuma kamar ya watsa mata ruwan sanyi, da wani irin rawar jiki ta ɗago har wani ruwa ne yake kwanciya a cikin manyan idanunta wanda suka samu surki da wata zaiba, blue- blue haka cikin idanun Ana suke, kodayaushe kamar an yi mata ado da kwalli haka suke nuna wa, saboda wani ɓaki siriri daya zagaye ƙasan idanunta da saman idanun wanda ya ƙarawa ƙwayar girma wai da aniyya, girmansu ya yi daidai da tsarin zagayyiyar fuskarta. Ganin Babban yaya tsaye da buta a hannunsa ya saka ta yi sak.Curarriyar girarta ta tattare waje guda. Ta kafe shi da idanun da lokaci ɗaya suka fara surkawa, gefenta ya bi ya shiga banɗaki abinsa ba tare daya sake bi ta kanta ba, Ana tabi hanyar da yabi da kallo. Ruwan daya taro a cikin kwarmin idanunta ta haɗiye su, tare da mayar dasu ta hana su zuba a saman fuskar da babu tabo ko guda. Butar ta saki ruwan ya mamale ta shige ɗaki abinta, sai da duk suka fita zuwa masallacin su uku, kana ta fito kanta babu kallabi ta shige banɗaki, a bakin banɗakin ta yi addu'a ta shiga. Alwala ta ɗaura ta yi sallah a sakar gida kusa da Mahaɗinta wato, 'Ifti'. Bayan sun idar sun yi azkar wanda Innti take nanata musu muhimmancinsa, sukai sabuwar shimfiɗa aka saka Tuwon a babban faranti da ruwa a babban kofi wanda ake sha ɗaya bayan ɗaya. Ana sai tsinewa Tuwon albarka take yi, wanda takaicin ya saka ta miƙe ta shige ɗaki bacci ya ɗauke ta. Ɗabi'ar zuri'ar Innti ce, cin abinci a faranti ɗaya tare da iyalanta, safe, rana da dare. "Innti, Daada ya amshi kuɗin kitson dana bawa Mahaɗita ta siyo taliya ƴar murji" "Daada?" Jaheed da Jadid suka maimaita. Ita dai Innti ba ta yi magana ba, kalmar Daada kawai ya tsayar da bugun zuciyarta na wani lokaci, a ƙarƙashin tsayuwar bugun zuciyar, ta nemo fargaba da tashin hankali, zullumin abin da zai biyo baya, akan abubuwa da suka riga suka shuɗe ya sakata tsame hannunta daga cikin jerin hannu huɗun da yake faranti, biyar cif idan aka haɗa da nata hannu. "Ifti, kici abinci ki bar Ana kawai, samu ne wanda yafi rashi ɓarna, ganin Tuwon ya saka take wannan, da Allah bai hore na ɗora tukunyar bafa?" Ifti za ta yi magana, yatsun Babban yaya daya motsa ya saka ta yi shiru. Har akai sallar issha'i Ana na bacci, da ƙyar ta miƙe ta fito kan nan babu ɗan ƙwali gashi sumar ta mimmiƙe kamar sabon kamu, bata kitso bata son dukkan wani tashin hankali da zai saka a taɓa mata kai, kamar me gyambo a kan, suka zuba mata idanu, Babban yaya kallon ta kawai yake yi ya ƙudurce abin da zai mata idan ta shiga banɗakin babu kallabi, Innti ta tsaya da tatsuniyar da take basu, da labarin iliya ɗan me ƙarfi. Ana ta nufi banɗaki bayan taja ruwa a rijiya, a magagin bacci take ko addu'ar shiga banɗaki ba ta yi ba, tana saka ƙafafuwanta cikin banɗakin, ta yi arba da me kama da ita kwabo da kwabo zaune a banɗaki ta zuba mata manyan idanunta. Da fari ta ɗauka Ifti ce, sai ta tuna yau ba kaya iri guda suka saka ba, Ana ta murza idanunta, sai taga matar itama ta murza nata idanun, ta ɗauka ko bacci take yi har yanzu, tana a duniyar mafarki ne wataƙil Sai ta girgiza kanta sumar ta baje. Nan take matar itama ta girgiza kanta. Wani gigitaccen ihu Ana ta saki sanda ta tabbatar gamo ta yi a banɗakin, ta zube a wajan a sume babu numfashi a ƙirjinta. Babban yaya, ya riga su miƙewa, taku ɗaya biyu dugwayen ƙafafuwansa suka ƙarasa dashi banɗakin,a bakin ƙofa yaga Ana bata motsi, ya zuba mata idanunsa da suke iri ɗaya sak da nata kafin ya saka hannunsa ya ɗakko ta zuwa harabar gidan. Salati Innti ta fara a gigice tana ɗaukan carbi, cikin rikicewa Ifti ta fashe da kuka, Jaheed da Jadid suka rufu a kanta suna kiran sunanta. Hijabin Innti dake gefe Babban yaya ya ɗauka ya zurawa Ana, a zuciyarsa ya dinga addu'a yana tofa mata, da yayyafa mata ruwa a fuskarta zuwa wuyanta sosai Ajjiyar zuciya ta sauke me ƙarfi. Sai kuma ta zabura tana sambatu da surutai, suka danne ta suna sake yi mata addu'a a haka har ta dawowa daidai. "Yau naga abin da ya ishe ni, sau nawa zan ce ki dinga saka kallabi a kan ki Ana?" Inji Innti tana riƙe haɓa. Jaheed ya ce "Babu mamaki gamo ta yi" "Idan gamo ta yin ma ai da sauƙi muddin basu shafe ta ba, yarinya ce da shegen taurin kai da miskilancin jaraba kamar matar kuturu, ƙila ko addu'a ma ba ki yi ba" Wata uwar harara ta watsawa Jadid. Ya ce "Oh, hararata ma kike?" Ya juya yana kallon Innti ya ce "Anya Innti Shalelenki ce wannan ko wata ce daban?" "In sha Allah ita ce. Tashi maza ɗiyar albarka ki yi sallah ki ci abinci kin ji Shalelen Innti" Ana ta miƙe kamar ka ce mata ƙyat ta gudu saboda tsoro, ta marairace fuska ta ce "Mahaɗita rakani banɗakin don Allah?" "Ai ya zama dole rabin jiki" Ifti ta ce tana miƙewa, bayan ta yi alwala ta yi sallah yin duniya aka yi taci abinci amma taƙi a haka bacci ya ɗauke ta, bayan ta shiga ɗaki Ifti baccin itama ta yi, Innti dake tsaye a ɗakin ta bisu da kallo, a hankali ta zauna gefen katifar da rabi duk ya cinye, kallon fuskar Ana take yi, kyawun fuskarta tsoro yake bata, wannan tsoran shine yake cin zuciyarta, wannan tsoran shine yake damunta, dashi take kwana take yini, wannan tsoron shine yake hanata sakin jiki da fitar Ana, shine yake hanata sakin jiki da barin Ana ta yi ƙawaye, wannan tsoron shine yake sawa bata barinta fita waje. Ta ja numfashi me ɗauke da damuwa da yawa, na makomar yaranta, da tarbiyyarsu. Ta jima tana yi musu addu'a sosai ta shafa musu sannan ta fice daga cikin ɗakin. Sannu a hankali suka juya a tare, Ifti da Ana, suka rungume junansu cikin bacci. Basa iya bacci sai sun yi wannan rungumar kamar ibada, wannan numfashin junan. Shine ke riƙe da zuciyoyinsu. Ɗakin mazan ta shiga ta tarar Jaheed ya yi bacci, Jadid riƙe da azkar, Babban yaya na duba wata waya a can gefe wajan shimfiɗarsa, ma kwanci biyu ne a ɗakin. Jadid da Jaheed, sai ta Babban yaya. "Jadid" Ya ce "Na'am, wani abin zan miki Innti?" Ta zuba masa idanunta wanda suke faɗar abubuwa da yawa a hankali ta ce "Magani" "Kasha maganinka na dare?" "Ina cin abinci na sha ai Innti" Ta ce "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara lafiya" "Amin Ya Allah, Allah ya ja kwana Innti" Ta yi masa murmushi. "Yaya" ta kira sunan Babban yaya. Fararen idanunsa sune suka fara shiga cikin nata kafin kyakkywan duhun fatar fuskarsa, ya yi jim ta ce "Zo, ka saman a waje" tana fita ya bi bayanta a nutse A tsaye ya sameta tsakiyar hasken wata, haskensa da yake nuna cewa ya shiga 14 ko 15. Ya durƙusa har ƙasa cike da ladabi. "Yaya, kai ne Babba bana son yi maka faɗa a cikinsu shi ya sa na rabu da kai, kar ka sake ranƙwashi Ana a tsakiyar kanta, ita macace tarbiyyar mace akwai wahala a wannan matakin bana son ka yi mata sabon duka, idan ya zama dole gwara ka ɗauki bulala ka zane ta akan ranƙwashi nan ka ji?" Ya jinjina kan shi alamar “Eh" Dubansa ta yi da kyau bata san me ya sa shurunsa ke ninka maganarsa ba, yana yaro kamar karsashinsa yafi haka. Hannunsa ta riƙo cikin nata ta damƙe, ajjiyar zuciya ya sauke saboda wani daɗi da nutsuwa da ya ji, ya ɗauki hannunsa ya ɗora a nata. "Hausawa suka ce babban wa magajin uba, ina jiye maka kula da tarbiyyar Ana zuwa ɗakin miji idan haka zaka dinga mata, na san kana da zafin zuciya wacce a lokutan baya har tsoro nake ji, na ji da ɗabi'arka ta sauya. Ka yi haƙuri Yaya ka sake haƙuri watarana sai labari, za kaga babu Ana babu Iftihal duk suna ɗakin mazajensu, kaima kana tare da matarka wataƙila da yara, be patient yaya" "Har Ana? Itama auren kenan za'a mata?" Ya shiga zance a zuciyarsa ransa kuma ya ɓaci nan take. Ta ce "Saboda lafiyar idanunka, ya kamata ka kwanta don Allah, kar na leƙo naga kana wani aikin na daban kuma yaya" Tsoro Innti take ji! Taka tsantsan take yi! Tana ƙoƙarin tilasta musu yin bacci, bayan dole sai sun farka kamar kullum. Ya sake bata tabbacin zai kwanta ta hanyar jinjina mata kansa kana ya miƙe ya koma ɗakinsa. Tsakar gidan ta dawo da zama hannunta riƙe da carbi zuciyarta sai bugawa take yi, na rashin sanin dalili gashi bata jin bacci sam, kamar wacce akai wa farraƙu dashi, tunawa ta yi tana da ɗinki sai ta ɗakko atamfar da almakashi ta fara yankawa. Tana zaune Yaa Jaheed ya fito hannunsa riƙe da waya zai nufi ɗakin su Ana. Innti ta ce "Jaheed me za ka yi a ɗakinsu a yayin da suke bacci" ya yi sak sai ya ce "Ana zan bawa wayar ne Ana nemanta" kallon wayar ta yi har za ta yi magana kuma ta fasa. Ta miƙe ta amshi wayar shi kuma ya juya zuwa ciki. Kamar me jiran wayar haka Innti ta samu Ana zaune akan katifar ta ɗora kan Iftihal a cinyarta tana shafa kanta a hankali, idanunta yana kallon sama ta yi shiru. "Shalele me ya farkar dake yunwa ko?" Sai ta girgiza kai a hankali cikin sautin muryarta mara ta ce "Sumar kaina Innti don Allah kar Babban yaya ya aske mini na san halinsa da ƙeta wani lokacin, ina son sumar kaina ba zan samu mijin aure me kuɗi da kyau ba idan bani da gashi wallahi" "Oh! Wannan kyau da kuɗi Ubangiji ya sa ya zame miki alheri Aysha. Wani kyawun masifa ne" Ta ɓata fuska kaɗan "Ki yi mini addu'a kawai Sahibarmu, addu'arki kaifiyance. Yanzu da Daada yana da kyau sosai irin na mazan novel da Zainab Alƙali take karantawa a redio wallahi da wani takaicin nasa bai sarƙi zuciyarki ba, da ya shigo kinga kyakkyawan mijinki ko yunwa kike ji za ki mance" Innti bata san lokacin da ta yi murmushi ba ta ce "Au yanzu idan na ganshi bana farincikin kenan Shalele" ta ce tana ɗan jingina da ƙofar yin hira da Ana na sata nishaɗi yana ƙara mata son yarinyar. "Nifa ban taɓa ji kince masa I love you ba, kinga Miftaa na cikin littafin Allah Yana gani matarsa kullum sai ta ce masa I love you, shi ma ya faɗa mata ai soyayya duniya ce Babarmu" "Oh really?" "Wallahi Innti" "Allah Ya kula mini da rayuwarki Shatuna, Ubangiji Ya miki zaɓi da mafi alheri ke da ƴan'uwaki gabaɗaya. Riƙe ana nemanki a waya" wayar ta bata ta amsa ita kuma ta juya zuwa inda take yankan atamfa. Sannu a hankali ta manna wayar a kunnenta tana lumshe idanunta, shima shirun ya yi saboda gabaɗaya ya ji hirar da suke yi da Innti. Ciki ciki tana kumbura fuska ta ce "Hello..... "Assalamu Alaiki" Muryarsa me cike da kamala ta sauka a kunnenta ajjiyar zuciya ta sauke tana jingina da bango. Bai jira ta amsa ba ya ce "Me kike buƙata?" Shiru taƙi amsawa. "Nanaah....." Ya kirata da sunan da yake kiranta, madadin ta amsa sai ya ji kamar tana ɗan shessheƙar kuka. "Nanaah mene?" "Ni yaushe zaka dawo kuma ka ƙi kirana sai yanzu" Ya yi jim yana jin damuwarta na sauka a ransa kamar ba zai ce komai ba sai ya ce "To ni da ba kyakkywa ba mene za ki ƙwarzaɓi ranki don ban dawo ba?" Bai bari ta amsa ba ya ɗora da "Ba zan dawo ba, ki faɗa mini me kike so zan aiko miki dashi, idan kinga dama ki yi ta yin rashin kunya Nanaah. Kina faɗawa Innti ke handsome kike so" "To kai ma ka ɗan fara shafa man bilitin mana, kana saka kaya masu kyau ni kawai.....," Cikin tsawa ya ce "Heee queit!" Yana faɗa ya kashe kiran gabaɗaya ta ji tsawar har cikin kanta tabi wayar da kallo tana tura bakinta gaba zuciyarta kuma ta ji babu daɗi. *** Ahlam na zaune a parlour tana bawa yayanta labari na rahotan da ɗazo da taje ɗauka, cikin sanyin muryarta me ɗauke da wani 'sounds' wanda duk ƙarshen harafi sai ka ji kamar tana fitar dashi da sauri ne. Tana da ƙin-ƙina sosai a saman harshenta, wata baiwa ta Ubangiji muddin akan aikinta ne ko karatun Alkur'ani bata yin ƙin-ƙinar. "Yaya wai me kishiya ta ɗauki abokiyar zamanta ne? Wasu mutanen basu da imani da tausayi sam a cikin lamuransu yaya" Ya murmusa kawai ya ce "Ahlam me kika gano ne?" Cikin damuwa ta ce "Yaya ɗazo da naje ɗaukan rahoto, wata ce mijinta ya yi mata kishiya, yanzu kishiyar ta haihu sai ta ɗauki jaririn ta saka shi a cikin ruwan zafi, kar kaso kaga babyn gabaɗaya ya saɓule" Engineer ya ce "Subuhanallahi!" "Babu kyan gani, da ƙyar bai mutu ba" Anty Jiddah dake zaune kusa da mijinta tana sauraran hirar yaya da ƙanwa cikin raunin murya da damuwa irin ta uwa ta ce "Ai wasu matan basu da imani, wannan ya fita daga kishi ya koma hauka ya kamata hukuma ta shiga cikin lamarin a bi mata haƙƙinta, ban san yaushe ne mutane za su yi hankali ba a wannan rayuwar, kodayaushe wa'adinmu ƙarewa yake, yanzu zaka mutu, yau ne, gobe ne bamu sani ba, da muna da masaniya wataƙila mu yi hankali da wasu abubuwan rayuwar" Ahlam idanunta ya cika da hawaye muryarta na rawa ta ce "Anty abin baƙin ciki mijin yace muddin tai ƙarar kishiyar zuwa hukuma a bakin aurenta, duk wanda ya shigo cewa ake yi ruwan zafi jaririn ya faɗa, mace ɗaya ce abin ya faru akan idanunta ita ce wacce ta fito da maganar ta fara hawa iska kamar wutar daji, da ƙyar ta bani haɗin kai na yi Recorded muryarta, kuma na ga hakan ma babu fa'ida kar na saka a Redio na yi sanadin aurenta, auren fari ne" "Allah buwayi gagara misali, Allah mun tuba. Zata iya sauya miji amma ɗanta fa?" Ahlam ta kalli Anty Jiddah. "Bari kawai Anty, ina ganin goge recorded ɗin zan yi, kar tsautsayi ya saka na turawa News editor" Alhaji Abdallah ya dubi Ahlam cikin nazari da tunani da nutsuwa ya ce "Amma wannan kamar opportunity ne kika samu da za ki moving level ɗinki a gidan rediyon naku, nasan kece kika fara samun rahoton jaririn, ya kamata ki kai musu" "Yaya... "Yaya ina jin tsoro ne" Ta fashe da wani irin raunataccen kuka, jikinta har rawa yake yi nan da nan hankalin yayan nata ya tashi, ya dawo kusa da ita yana riƙota da kulawa, ganin yadda shanyayyen hannunta ɗaya ya fara rawa shi kaɗai. "Tsoron me kuma kike Ahlam, ki tuna ina tare dake a koyaushe dukkan abin da kike buƙata ko kike so zan miki, ke ƴar jarida ce, matakin farko a fara aikinki, ki tuna daga shigarki kika samu award a 2024, ina ganin wannan labarin zai iya sawa ki samu wani award ɗin a ƙarshen shekarar nan, ki ƙarfafa zuciyarki, ki cire tsoro, daman kun saba ɗaukan kasada, tsoro ko ja da baya bana ɗan jarida bane, wannan mafarkinki ne, burinki ne, ba daga sama kika samu aikin ba, karanta kikai, karatunki ya kai ki wannan matakin, kar ki sare kin ji?" "Idan na yi mata sanadin igiya uku fa? Idan na yi sanadin aurenta a gidan mijinta fa?" Ya yi jim, sai ya ce "Hakan ba zai faru ba" "Idan ya faru fa? Zaka aure ta?" Anty Jiddah kallon Ahlam kawai take yi tana girgiza ƙafarta hannunta rungume a ƙirjinta ta cije leɓenta, zafi da ɗanɗanon da ta ji ya shiga cikin bakinta, ya bata tabbacin ta datse leɓen da haƙoranta, ta jiwa kanta rauni ne. Miƙewa ta yi da murmushin data ara ta shimfiɗa a fuskarta ta ce "ƴar gatan yaya rigima ake ji yau, ni dai mu kwana lafiya" Abdallah ya bi bayanta da kallo har ta shige cikin part ɗinsu kafin ya sauke nauyayyiyyar ajjiyar zuciya yana kallon ta Ya ce "Ki je ki kwanta, kinga gobe da wuri za ki tashi, idan na kunna rediyo ina son na ji wannan rahoton daga cikin golden voice ɗinki" rarrashinta ya dinga yi har ya rakata ɗakinta ta je ta kwanta tana tunanin yadda ta bar jaririn matar a saɓule tas ko asibiti anƙi kai shi. A daren ta turawa Editor recorded ɗin tana son amincewa daga wajansa *** Tsaye ta yi a gaban room ɗin hotel ɗin cikin shigar after dress data ɗora a saman kayan jikinta, ta rufe fuskarta da face mars. Babu jimawa aka buɗe ƙofar da fararan idanunsa ya bita da idanu kafin ya yi baya wajan bata waje ta shige ciki. "Na fara gajiya da wannan mu'amalar, ni ba matarka ba ni ba budurwa ba nama kasa gane ina muka dosa. Yaushe ne zaka daina yi mini barazana jikina ya fara gazawa" Jallabiyar jikinsa ya zare ya zago ta bayanta ya rungumeta yana ɓalle after dress ɗin ya ce "Kin samu abin da kike so, nima dole ki bari na yi yadda nake so, tunda nine na kai ki matakin da kikai kai. Don haka quiet ki haɗiye duk wani complain ki bani farinciki a nan" ya ce yana nuna mata gadon ɗakin. "But sir.... "But what? Fitowa kike so na yi na ce ba ki cancanta ba, ko kuma ba karantar ɓangaren kikai ba, ko kuma ana daƙile wasu ne saboda ke" Sai ya girgiza kai da faɗin "I'm not in the mood ne sir" yana shafa fuskarta ya ɗan murmusa kaɗan "Never mind, zan dawo dake mood yanzu" yana faɗin hakan ya kashe hasken room ɗin *** Cikin dare Ana ta dinga firgita saboda gamon da ta yi a banɗaki ta hana Ifti bacci sam, sai ta dinga rungumeta tana mata addu'a kuma taƙi kiran Innti bata so ta dame ta. Har kusan 1:36 na dare Innti na zaune a tsakar gidan tana yankan ɗinki. Garam! Sautin bugowar ƙofarsa ya bayar a cikin kunnenta, addu'a ta fara idan ka shiga tsoro da firgicin gamuwa da wata halitta ta Ɗan'Adam. Jin bata ji motsin shi ba, ya saka ta juya a hankali bayan ta ajjiye yadin landin ɗin da take saita kafaɗa zata yanka, zumbur ta miƙe tsaye, a tsakanin miƙewa da tsayuwar bugun zuciyarta na wani lokacin ba zata lissafa wanne ya zarce wani ba. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta furta a gigice da sautin daya cika gidan ganin Daada tsaye a tsakiyar gidan zigidir haihuwar uwarsa, idan ya miƙe tsaye sai ya sake yanke jiki ya faɗi yana layi da tangaɗi, ko irin ɗan kamfan da maza suke sawa babu a jikinsa, bata san tun yaushe ya kasance tsirara ɗin ba, wandonsa da zabgegen tazugen wandon da yake lilo har ƙasa, ya yi amfani dashi wajan ɗaure wuyansa da tunanin al'aurarsa ya rufe, furfurar kan shi da wacce hazo ya ƙara masa sun yi haɗin gwiwa wajan sake fito da tsofan nasa. Sambatun giyar bata sake shi ba, a cikin can tsakiyar kan shi jijiyoyin da suke sarrafa tunanin Ɗan'Adam, su sanar da ƙwaƙwalwa halin da gangar jiki take ciki, sune suke aikinsu a tattare da Daada, ya ɗauka har yanzu yana cikin ɗakin Tani suna aikata abin da suka saba. Wani mokaɗe kwankwaso yake yi yana tura shi gaba zuwa bawa. "Tani ke duniya ce, Tani zumata, me zaƙi, Tani kin fi reza kaifi, Tani kinfi Innti amfani da garɗi!" Jerin baitocin waƙar duka a kunnen Babban yaya da Ana dake ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fito waje, cikin sauri Babban yaya ya saka headphone a cikin kunnensa yana juya zaibar idanunsa zuwa shimfiɗar su Jadid da Jaheed, yaga bacci suke yi ɗaya ya yi filo da hannun ɗaya, abin mamaki hannunsu damƙe dana juna a haka suke yin baccin A gigice Innti ta nufi ƙofar ɗakinsu Ana tun kafin ta fito, karo suka yi. "Ana" "Na'am" ta faɗa a hankali. "Me za ki fito yi cikin daren nan?" "Innti na kasa ganin film ɗinsu su Anum da Jarumi a ɗaki, zan kwanta ƙasan bishiya ne" "Ƙasan bishiya?" Ta ce da mamaki "Ana anya ba zan kwana ina faɗawa Ubangiji lamuranki ba?" Innti ta maimaita tana buɗe mata idanu. "A daren nan? Bakya tsoron mutanen ɓoye ashe ba ki ɗauki darasi a banɗaki ba Ana?" Ta zubawa Innti manyan idanunta masu saƙar baƙi kamar me son karanto gaskiyar maganar Innti a fuskar tata. "Koma cikin ɗaki" Da ƙyar ta ce "Bari na sha ruwa" "Aysha!" Ta kira sunanta a tsawace jikinta ya fara bayar da ita wajan amsar rawar da zuciyarta take yi mata ganin tamboɗan Daada na ƙara ƙaimi, ya kwanta a ƙasa yana wasu abubuwa kamar wanda yake tare da mace wajan auratayyar aure. Macen ce, da macen yake tare. Tani ce ke yawo cikin kansa! Tura Ana cikin ɗakin ta yi,ta janyo ƙofar ta ɗaure da igiya kana ta dawo tsakar gidan. "Menene? Me ya sa ta hanaki fita" Ifti ta tambaya tana murza idanunta, Ana taƙi magana sai waje guda data kafe da kaifafan idanunta, Ifti zata sake yin magana suka jiyo ihu da kururuwar Innti, a kiɗime Ana ta miƙe ta fara jijjiga ƙofar haka ma Ifti amma sun gagara buɗewa saboda ta rufe su ta waje, suna jin yadda Daada ke ɗaukan Innti yana bugata da ƙasa. Ihunta ya farkar da Jadid da Jaheed daga bacci, Babban yaya duk da ya saka abu kunnensa bai hana shi jin kukan ba, gabaɗaya kwantattun gargasar ƙirjinsa suka mimmiƙe reza ce a hannunsa yana yanke wata waya, bai san yadda aka yi ya dunƙule hannunsa ba, sai jini ya gani yana tsiyaya daga cikin tafin hannunsa, raɗaɗin zuciyarsa yafi na yadda rezar ta kekketa masa hannu, idanunsa kamar zasu zazzago ƙasa saboda tsabar yadda suka buɗe. Jadid kuka ya saka yana kiran sunan mahafiyarsu, ashe suma ta rufe su ta waje da kwaɗo.... *H I Y A A M* Page 3 Bright pens Yota/001 Stay blessed as always; Nazeefah Sabo Nashe A gigice Innti ta miƙe tsaye ganin yana shirin yi mata tsirara a tsakar gidan, cikin tashin hankali da kiɗima tana ja da baya da wani irin tsoro Ta ce "Ka dubi girman Allah Daada...," yana layi da tangaɗi ya ce "Wata can a waje wacce ba matata ba, ta iya bani komai da Ubangiji Ya yi mata na ɗiya mace, sai ke da kike ƙarƙashin ikona, za ki mini iyaka da jikinki? Jikin da nake maleji dashi, jikin dashi da babu duk uwarsu ɗaya, wai gayyar ta ahoo. Tani da muke dadiro ta fiye mini ke sau dubun du bata wlh Innti" Ciki maye yake furta hakan, yana tangaɗi a tsakar gidan ya yi tik haihuwar uwarsa, zafi da raɗaɗin da zuciyar Innti take yi, kamar ana rura wutar ƙona biredi haka nan take jin yayyafin wutar azaba na dirar mata a cikin zuciyarta, ance mace ta gari ni'ima ce. Ashe miji na gari ma rahma ce. "Ta ina zan iya mu'amala da kai a tsakiyar tsakar gida? Ta ina zan iya mu'amala da kai a lokacin da kake a buge, na barasar da ka sha? Ta ina zan iya, Daada ta ina zan iya" "Ta yadda Tani take mini" Amsar daya bata ya tabbatar mata cewa, zancen zuciya ne ya fito fili, ta san ya yi mata targaɗe a yatsunta na dama, amma ciwon da yake ji mata a zuciya a kullum, a koyaushe yafi rauninka da yake samun gangar jikinta, wahala mudu ce, ba'a taɓa sabo da ita, tarbiyya fa? Yaranta take ji. Yaranta biyar! Ta sassauta muryarta zuwa ƙasa sosai, da tana da iko na toshe kunnuwanta daga daina jin sautin muryoyi huɗun da suke tashi, suna kiran 'Innti' suna kiranta, da ta yi hakan, amma bata da sa'a sam ta gaza. "Shikenan, na fahimta" Ta furta a sanyaye tana tsayawa a gabansa, ba tare da shikenan ɗin ta zama “Everthing” ba, ba tare da “Everything” ɗin ya zama “Solving” ba ko da ya zama, baya nufin abubuwan zun shuɗe, sun jingina zuwa ga kalmar "Ending“ ba balle a samu “Happiness” "Mu shiga daga ciki mu yi magana, saboda kunnuwan zuri'arka Daada, akwai Babban yaya, Jadid, Jaheed, Iftihal da Ana, zan yi dukkan abin da kake so, umarninka biyaya ne a gare ni, amma ka tuna mune makarantar waɗannan halittu biyar ɗin mune allon kwaikwayonsu" "Za ki bani abin da Tani take bani?" Ya furta yana layi tana riƙo shi ita kuma zuwa gabanta, idanunta cike da hawaye. "Ko ban baka ba, zan yi iya ƙoƙarina na faranta maka" Ya ɗan suɗe leɓansa da harshensa. "Gaskiya Tani duniya ce, ita kamar kankana ce me abin alheri, ke kuma tamƙar murhun gasa nama ce saboda azabar zafi Innti" "Ya Rabbi!" Innti ta furta a ƙasan zuciyarta, domin ta fahimci abin da gurɓatattun kalmominsa suke nufi. Ta cire kallabin kanta ta ɗaurawa Daada a ƙugunsa wajan suturta al'aurarsa, kana ta riƙe hannunsa suka nufi ɗaki, suna zuwa bakin ƙofa ya saka mata ƙafa nan take ta yanke jiki ta faɗi akan hannunta, ya shiga taka mata ruwan ciki tana kuka da ihu da kiran sunan Allah, har numfashinta ya fara ƙoƙarin tsayawa, can kuma ya shiga sheƙa mata amai me azabar wari a fuskarta, sai da ya amayar mata da duka barasar daya sha kafin ya tsallake ta ya shige cikin ɗaki abinsa ya zube a ƙasa yana rufda ciki sai bacci, cikin sa'a ya shiga mafarkai da Tani. *** A hankali take juyi saman makeken gadon nasu, ƙirar royal bed tana sanye da kayan bacci ruwan huda, amma idanunta ya gaza ɗaukan bacci ko kaɗan balle ta runtsa kamar kowanne me rai da ke bacci a wannan lokacin.Motsinta ne ya yi yawa, ya saka shi ɗan juyowa daga bayan daya bata kaɗan. "Madam" ya kira sunanta a sanyaye yana me kallon ta Ta kasa amsawa sai lumshe idanunta kawai da ta yi. "Ya aka yi? Mene Madame?" Engineer ya tambaya yana tashi zaune tare da miƙa hannunsa ya kunna hasken kusa dashi yana ƙarewa fuskarta kallo sosai. "Yanayin garin? Damuwa? Ko buƙatar kai da kai Jiddo?" Sai ta ɗan girgiza masa kai kawai alamar babu ɗaya daga ciki. "Kar ki ce mini ban canka ba?" A sanyaye ta ce "Eh" Sai ya ɗan birkitota saman cinyarsa yana kama hannunta ɗaya ya riƙe cikin nasa. "Kamar Abdallah zai fi kowa sanin halin Jiddah, shikenan faɗa mini mene ya hana idanunki runtsawa ya kuma hana zuciyarki sukuni har haka?" Sannu a hankali ta juyo da fuskarta zuwa kan tasa, ta zuba masa idanunta masu cike da buƙata, wanda hakan ya nuna ta bugun zuciyarta da yadda ƙwayar idanunta take nuna alamar buƙata. Ta sauke numfashi "Akan Ahlam ne fa" Ya ɗan yi jim na nazari "Ahlam?" Ya faɗa a zuciyarsa. "Ahlam!" Wannan karan a fili ya furta. Ta ce "E, akan ta Yallaɓai" "Ta miki wani abu ne?" Sai ta yi shiru ta kasa bashi amsa "Tear out, me ta yi miki?" Sai ta girgiza masa kai, tana aro murmushi ta aza a saman fuskarta "Ko kallon banza Ahlam bata taɓa yi mini ba, balle saɓani ya shiga tsakanina da ita, yarinya ce me nutsuwa da sanin ya kamata, ba kowa ne zai yarda ita rainonka bace, tun kafin mu yi aure kake kulawa da tarbiyyarta, a dalilinta ka aure ni domin tana ganin saboda ita ne kaƙi aure, na yarda she's talkative, wannan kuma a dalilin aikinta ta zama kamar aku" "Baby nada surutu sosai" Ya furta yana murmushi. "Kar ki mini shiru, bani labari sauyin yanayin na lokaci guda" Jiddah ta kalli mijinta, shima kallon ta yake yana murmushi kamar wanda ya riga ya san abin da zata furta ta hanyar karantar yanayin fuskarta da kyau. "Me zai hana ta goge recorded ɗin matar can ta yi, tun kafin a saka a Redio?" Ya ce "Me ya sa?" "Saboda gujewa matar shiga matsala, ina tausaya mata ƙwarai, a budurwa ya aure ta, kuma tashin ƙauye ce, mene zai faru aurenta ya mutu ta dalilin Ahlam? Ina Ahlam zata kai hakƙin matar? Mutane da yawa ba za su fahimci akan aikinta take yi ba, wasu ma za su ga saboda ita bata da aure ne ya saka ta yi mata ƙyashi na farraƙa na matar" Ya girgiza kai "Wannan bai zama hujja ba" "Engineer!" Ta kira shi da sunan da mutane suke kiran shi da mamaki a fuskarta. "Wannan bai zama hujjar da za'a tauyasawa matar nan ba? Aure fa Engineer?" "Auren fa" Ya ce yana ɗage mata girarsa biyu. "Faɗa mini wani abu Hawwa'u , idan na yi aure, sai wata mace ta yi wa Mufeed haka ya za ki ji raɗaɗin abin a zuciyarki? Idan daka side ɗina na nuna kar ki ɗauki mataki ya raɗaɗin zai ruɓanya kan shi a zuciyarki?" Sai ta yi masa shiru. "Adalci take nema wannan yarinyar, wanda kuma shine ya yi ƙaranci a wannan zamanin a cikin al'ummarmu, da shuwagabanni, da jami'an tsaron, a kowanne ɓangare ba'a fiya samun adalci ba, ban ce duka ba, yawanci. Human rights ce zata iya bi mata haƙƙinta ba tare da fargaba ba, ko kuma WRAPA (Women’s Rights Advancement and Protection Alternative) ƙungiya ce dake kare hakƙin mata da yara, taimakon shari’a (legal aid) Yaƙi da auren dole, duka, da cin zarafi. Idan rayuwar ɗanta ya salwanta bata da tabbacin dana da wani ƙwan na haihuwa, zata iya sauya miji idan ƙaddararsu ba za ta zo ɗaya ba, amma zuri'a Rahma ce Jiddah" Ya ɗan lakaci hancinta "Da ina da iko da tuni na shiga maganar, amma tunda baby tana da dama me ya sa zamu daƙushe ta? Ita ƴar jarida ce, bana son tun yanzu ta kafa aikinta akan tsoro, dole zata fuskanci ƙalubale, amma idan ta yi haƙuri komai zai shige, da ɗan jarida, da lauya da marubuci suna da hanyoyin daya haɗa su, na san wasu za su iya yi mata bazarana kuma da yawan lokaci matsoraci ake yi wa, ina son wannan karan ma ta yi abin da za'a bata award a girmamata ko hakan zai rage mata raɗaɗin zuciyarta musamman akan nakasarta" Ta sauke ƙarfaffar ajjiyar zuciya a hankali. "Na fahimta Engineer, daman saboda halin da Ahlam za ta iya shiga ne ya sa na damu" Bai magana ba sai murmushi kawai yake. "To dariyar ta mece?" "Taki mana" Ta ce "Ni kuma?" Ta nuna kanta da yatsarta zuwa fuska. "Na san matata, kar ki ce mini ban fahimci cewa akan abin da Ahlam ta ce mini bane" "Ahlam? Ta ce maka?" Yadda ta yi maganar da yadda ta kira sunan Ahlam kamar a lokacin ne ta taɓa jin sunan. "Yes, saboda ta ce zan auri yarinyar idan aurenta ya mutu saboda ita?" Ta buɗe baki za ta yi magana ya yi saurin ɗora yatsarsa akai ya ce "Shhhh, mu kwanta" yana faɗin hakan ya jata zuwa jikinsa suka kwanta. *** Batty kasa runtsawa ta yi a wannan daran, bata tsoron a gaban kowa ta ce ita mayya ce ita da Innarta, bata sani ba ko ana yarda da ita ko akasin hakan, tunda mayen gaskiya ba zai fito ya nuna kan shi ba. Taja idanunta da sukai laushi ta lumshe su, a hankali bacci ya fara ɗaukanta tana daga zaunen da take. "Hiyaam.... "Hiyaam.... "Hiyaam!" Haka ta ji wata kamilalliyar murya na shiga cikin kunnenta, muryar me taushi ce, da nutsuwa da kamala, sautin me muryar yana nuna neman agaji domin murya ta nuna a wahale yake, bata me yake nufi da Hiyaam ba, suna ne, ko kalma ce, ko sunan wani gari bata da tabbacin me yake buƙata. Yana cikin duhu a kuma ɗaure yake da wasu igiyoyi. A hankali ta fara tafiya zata ƙarasa inda yake domin ya juya mata baya ne bata ganinsa. "Hai Batty, kai yaro Batty" muryar Gana ta ratsa cikin kunnenta, a ɗan firgice ta farka daga baccin da ɗan jujjuya kanta ko za taga mutumin sai ta fahimci mafarki take yi. Yau bata yi mafarki da Innarta ba sai da wani bawan Allah. Gana dake tsaye ta kalli Batty ta ce "Tashi ki je maza ga Saleh can a bayan bukka yana jiranki na ganshi da ƙunshin leda a hannunsa, maza tashi Batty ki je" Sai ta ɗan turo bakinta gaba cikin yanayin ƙuruciya ta ce. "Saleh ƙirji yake matse mini Yaaye, kuma ina jin zafi sosai" "To don ubanki da yake matse miki ƙirji ba abin daɗi yake kawo miki ki laƙume ba" Batty kallon Gana kawai ta yi idanunta da ya yi damshin hawaye, hasken fatar fuskarta sai ƙyalli yake ta cikin aci balbal ɗin da Gana ke haske ta dashi. "To idan kina bani abinci kuma ina shan kindirmon nagge ba zan ji yunwa ba. Kuma ki faɗa mini su waye suka shigo rugarmu suka kashe jama'a suka tafi da wasu har da Innata aka kashe saboda taƙi shiga wani addinin daba Musulunci ba. Yaaye ina son yin karatu sosai ki saka ni a bokoko don Allah" "Ƙaniyarki da karatu, bokokon a wuta da Allah Ya tsinewa masu makarantar bokoko kike so? Za ki shige ki samu Saleh ko sai na ɗaure ki a turke" ta girgiza kai a hankali tana haɗiyar zuciya don bata son kwanan cikin dabbobi. Sosai take fargabar zuwa wajan Saleh tsoro yake bata ma. Har ta yi gaba ta dawo ta ce. "Kin san mutanen da suka shigo rugar Yari? Idan kin sani ki waɗe mini su Allah sai na cinye kurwarsu tunda suka yanka mini Innata. Kuma ki faɗa mini kin san mene Hiyaam? Idan abinci ne ko kayan daɗi ki bani kin ji" Gana ta ce "Na boni, na sani yana wajan Saleh. Kuma duk ranar da kika kuma cewa Innarki mayya ce sai na yanka ki a gidan nan, tunda Baffanki ba lafiya gare shi ba" Batty ta yi wa Gana ƙuri da ido. "Saboda kar a ce kema mayya ce tunda ke ƙanwar Innata ce ko?" Sai ta washe bakinta tana lumshe idanunta ta ce "Idan aka tambaye ni kam zan faɗe musu gaskiya" Zangarniyyar kara ta ɗakko ganin haka ya saka Batty zabura tana zura yatsarta a baki ta fara tsotsa ta yi waje. Gana ta fara tunanin dole ta raba Batty da rugar Yari tun kafin taja mata masifa. Idanunta lumshe tana tsotsar yatsa a bakinta jikinta sanye da kayan saƙi na Fulani farare tas, hatta ƙarfta sarƙa ce da wuyanta, fararan ƙafafuwanta a bayyane a haka take tafiya har ta ƙarasa inda Saleh ke laɓe yana jiranta. Yana ganinta ya washe bakinsa sosai ya ce "Masoyiyata Batty ki yi murmushi mana ko zan ji daɗi haba Batty" ta kau da kai zuwa gefe guda tace "Ni dai mu kunce, na daina kulaka kuma ba zaka sake taɓa mini ƙirji ba, tunda ka fara taɓa mini suke zama kamar balo wacce ka taɓa kawo mini daka je birni" Saleh ya gyara tsaiwa ya ce "Yanzu ma biredi da lemo ja na ruwa na kawo miki Batty duba kiga" "Ce Allah rantse in ji" "Da gaske nake duba" Hannu ta miƙa zata amsa ya yi baya da hannun ya ce "To bani na taɓa kaɗan kin ji? Gana da kanta ta ce na dinga yi" shiru ta yi alamar tunani sai ta ce "Amma sau ɗaya ko?" Ya kada bakinsa wajan faɗin "Kayya Batty, Gana fa Innarki ce ta san ba zan cece ki ba ki buɗe kawai kuma ni zan aure ki" da sauri ta ce "A'a walle, ɗan boko nake so kyakkywa dogo wanda zai dinga goyani yana shillani" "To na ji buɗe mini" Tattare rigar ta yi sama jikinsa har rawa yake yi wajan yin abin da ya saba na taɓe mata matasan ƙirji, data fara jin zafi yaga zata gudu sai ya manneta da bangon ya shiga murzawa da ƙarfi ihu ta saka ta fashe da kuka tana yarfe hannunta. "Wayyo... Wayyo shikenan ya cire mini kindirmona wayyo kindirmona na barinkaɗi na lalashe" Gana na jinta ta yi iska da ita, addu'a take yi dama zai lalata mata rayuwa a wajan ta wuta da bala'in yarinyar. Dan haka ta ɗauki niyya gari na wayewa zata fice da Batty daga rugar Yari. *** Sun daina jin kukan Innti! Sun daina jin sautin muryarta! Sun daina jin hargagin Daada! “Mene ya faru?” Jadid, Jaheed, da Iftihal suka shiga tambaya a ƙasan zuciyoyinsu, banda Yaya wanda tunda ya yi ƙasa da kan shi bai ɗago ba, bai kuma motsa ba, ya gaza sakin rezar data murmushe a tafin hannunsa, jini sai zuba yake kamar a lokacin rana ta take. Ƙirjinsa ne ya shiga harbawa da yi masa rawa, wani abu ya tsaya masa a ƙahon zuciyarsa, baya ko motsi. "Suma ta yi" cewar Jadid. Sai ya durƙushe a wajan da jikinsa da bashi da ƙwari saboda lalurar dake damunsa, hawaye na bin farar fuskarsa. Jaheed daskarewa ya yi daka tsayen da yake jinin jikinsa ya daina gudana na wani lokaci, idan akwai wani abu da ake kira da tsoro, sun riga da sun gama shiga, tsoran rasa Innti shine abin da zai wa zuciyoyinsu wahalar ɗauka, ba balle ƙwaƙwalwarsu ta yarda zasu iya rasa ta. "Ka kira sunanta, zata amsa" "Ba zata amsa ba" Jadid ya bawa Jaheed amsa nan take yana riƙe kan shi. "Babban yaya!" Suka kira sunansa a gigice ganin jini na zuba a hannunsa, bai ji kiran ba, saboda ya shiga cikin tunaninsa ne sosai,kama hannunsa da suka yi ne ya dawo dashi cikin zahiri. Ya kalli Jadid da Jaheed, ya dubi hannunsa da suka riƙe, fararen idanunsa da suka rine da ja ya buɗe musu sosai, curarriyar girarsa na haɗewa waje guda. "Babban yaya hannunka" Ya sake buɗe musu idanunsa. Sai suka yi saurin sakinsa, daya motsa idanunsa ya basu tabbacin umarni yake basu da su je su kwanta jikinsu a sanyaye suka koma shimfiɗarsu tare da kwanciya. Shima kallonsu kawai yake yi, ganin da gaske ba za su yi bacci bane ya saka shi miƙewa tsaye, ya ɗauki bakin rigarsa ya yi musu firfita, duk yadda sukai ƙoƙarin juyawa suka gagara, saboda wata iska me daɗi data ratsa fuskokinsu, wacce basu taɓa jin irinta ba, nan take ta mantar da su abin da ya faru da halin da Innti take ciki, wani nauyayyen bacci ya ɗauke su. Babban yaya ya ja numfashi ya cika bakinsa da iska ya fesar, sannu a hankali ya zare rigar jikinsa duhun fatarsa me ɗaukan idanu ta bayyana, da yawan lokaci jikin mutum na yin ɗumi amma koyaushe sanyi ne a jikinsa idan tsautsayi ya saka ka raɓo da jikinsa, sai ka ji kamar ka taɓa ruwa me sanyi ne don haka ba kasafai yake gogayya da mutane ba. Sumar kan shi har ƙasan wuyansa. Baƙa suɗik da ita, idanunsa da surkin blue blue sak irin na Ana komai da komai. Jikin bango ya zubawa idanu, a hankali ya matsa sai bangon ya buɗe masa ya fice, yana zuwa tsakar gidan yaga Innti kwance a ƙasa babu numfashi ya durƙusa dab da ita yana kallon ta sosai, tamkar zai mai data ciki saboda soyayyar uwa haka yake ji a ƙirjinsa. Ta cikin idanunsa ya hango ƙashin hannunta daya goce, ga jini nan yana gudana a wajan, sai daya fara saka ta nauyayyen bacci kafin ya yi bisimillah a zuciyarsa ya shafi hannun, tsananin azaba ya saka Innti firgita zufa ta jiƙe mata jiki amma iskar da yake hura mata ta baki ya hanata farkawa ko yunƙurin motsa bakinta, ya saka farin zare wajan naɗe hannun ya shafa mata magani, kana ya saki hannunta. Shi kaɗai yake iya ganin zaren kuma. Haka yaja yatsunta sukai ƙara ya daidaita musu zama, sai ya miƙe tare da Innti a hannunsa ya tsallake Daada ya kwantar da ita saman katifar ɗakin kafin ya miƙe ya fita. Har zai fice waje, ya ji sautin kukan Ifti, tabbas ita ce, yasan Ana ba zata taɓa kuka ba, suna da saɓani ta nan. Kamar walƙiya ya ratsa ƙofar ya shige, Ifti na durƙushe tana rera kuka da muryarta da bata fita sosai saboda kukan data sha. Ana kuma na tsaye jingine da bango ta zubawa waje guda ido, yana hango yadda jikinta yake rawa da kakkarwa idanunta kamar su fita waje, jijiyoyin kanta sun yi reras a saman goshinta sai fuskar numfashi take yi. Babban yaya ya motsa. "Yaya" Ifti ta kira sunansa. Da sauri ta miƙe ta nufi wajansa tana riƙe shi "Mene ya samu Innti? Me Daada ya yi mata, yaya mun shiga uku idan muka....," Bai bari ta ƙarasa ba ya saka hannunsa ya shafi kanta yana mata tattausan murmushi. Ajjiyar zuciya ta shiga saukewa sanda ya bata tabbacin Innti lafiya ƙalau take."Me ya sa Daada yake dukan mahaifiyarmu? Me ya sa yake shan giya? Me ya sa yake zuwa wajan karuwa, haka kowanne mahaifi yake Yaya?" Ta sake fashewa da kuka. Jikinta har wani ɓari yake. "Innti ta ce za mu yi aure watarana, muma haka mijinmu zai dinga yi mana? Ya dinga shigowa gida tsirara babu tufafi a jikinsa?" Bashi da amsoshinta, daman shi bai taɓa amsa ko tambaya ɗaya ba a rayuwarsa idan ya shige tambayoyin jarrabawa, iya su kawai. Zata sake yin magana ya ɗora yatsarsa a saman ƙaramin bakinta alamar "Ya isa" Sai ya matsar da bakinsa dab da fuskarta ya hura mata iska, nan take idanunta ya fara lunshewa jikinta ya saki murus ta yi kamar zata faɗi ya taro ta a tafukan hannunsa tare da kwantar da ita ya lulluɓe mata jikinta. Ganin baccinta ya yi nisa ya saka shi juyawa zuwa inda Ana take tsaye, tunda ya shigo ɗakin ko yatsar hannunta bata motsa, ya matsa dab da ita yana ɗan kallonta taƙi yadda ta kalle shi, tana da taurin kai kafiya da zuciya, tana da sauƙin hali da shiga rai kamar kuɗi, da daɗin zama da baiwa ta karatu, bata taɓa shiga sabgar mutane. Ya saka hannunsa ya juyo da fuskarta. Sai a lokacin ta kalle shi da blue eyes balls ɗinta, sai wani haske ya fita kamar magic. Da idanunsa ya yi mata alamar "Menene?" Sai yaga ta yi murmushi, har dimples ɗinta suka lotsa ta lumshe idanunta gashin idanun suka bi fatar wajan kwanciya suma. Kuka ya dace ta yi kamar sauran ƴan'uwanta, amma sai yaga akasin hakan, suna da kamamceceniyya na hali, shi da ita. A hankali ta dube shi ta ce "Babban yaya ka je ka kwanta" Ɗas! Yatsunsa suka bada sautin magana "Ke kuma fa?" Haka ƙarar ta bayyana. "Bana jin bacci" Sai yaga tana ta murmushi jikinta ya shiga rawa sosai, ya sani idan zai kwana a tsaye yana hura mata iska ba zata taɓa ɗaukanta ko aiki a jikinta ba, sai ya kama hannunta kamar tana jira ta lumshe idanunta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi tana sakin wata ajjiyar zuciya, duk yadda take ƙoƙarin taga hawaye ya fita a idanunta amma ya ci tura, wani irin raɗaɗi na azaba ƙirjinta yake yi mata. Gani take idan suka rasa Innti sai tafi kowa shiga damuwa a wannan duniyar. "Ya......yaaaa" ta kasa magana. "Zafi ƙirjina yaya.... "Ka danna mini ƙirjina" Ta faɗa a rarrabe, jikinta na kakkarwa. "Ba zan iya taɓa ƙirjinki ba Shalelen Innti" Haka numfashinsa ya bata amsa, ganin da gaske ƙirjinta ciwo yake yi ya jata jikinsa ya rungumeta daga tsayen da suke, tafin hannunsa ya ɗora a bayanta ya dinga shafawa har sai da ya ji ta yi gyatsa ciwon ya faɗa mata. Tana jikinsa ta ce "Kamar na mutu, bana son Daada, bana son ganinsa" ta rufe idanunta da ƙyar numfashinta na sarƙewa ta ce "Ko dai ba babanmu bane?" Yaya ya yi mata shiru. "Ɗan iska ne fa, yana zuwa wajan karuwa" "Iskanci yake yi da Ta....," Bai bari ta ƙarasa ba, ya danna jijiyar wuyanta sai ta tafi luu ya yi saurin rungumeta, bai san me ya sa yake jin soyayyar Ana fiye da komai ba, banda Innti mahafiyarsa ce, wani lokacin har tsoro yake kar soyayyar Ana tafi ta Innti yawa a ƙirjinsa, yana ƙoƙarin dannewa kar ya nuna fifiko ita da mahaɗinta, shi ya saka yafi hukunta Ana fiye da Iftihal ɗin. Ya ɗan sumbaci goshinta kana ya kwantar da ita kusa da ƴar'uwata ya yi musu addu'a shima ya fice daga cikin ɗakin ta jikin bango. Ya zauna a tsakar gidan, iska na kaɗa shi tana tafiya da duk wata damuwa dake ƙasan zuciyarsa, bayan ya lumshe idanunsa na wani lokaci, sai ya ji sanyin jikinsa ya yi masa yawa, iskar ma haka, ga wani haske dake shigar masa ido sosai, sannu a hankali ya buɗe ido, ya shiga ƙarewa wajan ido, ba tsakar gidan Innti bane, tsakiyar dokar daji ne, gefen ƙoramar dake gudana a wajan. Cikin bacci Jadid da Jaheed suka ji muryar Innti tana kiran sunan su, a hankali suka buɗe ido, bakinsu ɗauke da addu'ar tashi daga bacci. "Innti?" Jadid ya furta a hankali "Har an kira sallah kuna bacci? Wannan baccin na magani da mene ban saba ganin irinsa ba" Jaheed ya miƙe zaune. "Ban san ya aka yi mukai nauyi ba yau" "To ku tashi, kar ku rasa jam'i" Ta faɗa tana miƙewa tsaye, kaɗan kaɗan hannunta yake mata ciwo, gefen fuskarta a kumbure haka ta fita, ta dubi Iftihal ta ce "Ana bata fito ba?" Kafin Iftihal ta yi magana Ana ta fito daka cikin banɗaki kan nan babu ɗankwali, Innti ta yi sak ganin kan Ana kamar bishiya saboda tsabar yawa da tsayi, Iftihal ma kallon Ana take yi da mamaki a fuskarta. "Allah Ubangiji ka shirya mana zuri'a, Ubangiji ka shirya mini Aysha, da asubar nan ki shiga banɗaki babu kallabi kamar kuntacciya, haba Ayshatuna, me ya sa kike so na dinga yaƙi da baki akan ki ne, haka ki kaga ƴar'uwarki na yi? Kin manta abin da ya same ki ne jiya a cikin bayan gida?" "Fitsari nake ji sosai Innti" "Sai ya ba ki damar fitowa haka? Ki raba kan ki da Aljanu Ana, ina rabaki da Aljannu" "Ni ina ruwana da wasu Aljanu" ta faɗa tana kumbura baki Innti ta ce "Au haka kika ce?" "Nifa Innti zan so ganin Aljanun ma idan akwai, ko matar dana gani kawai mafarki ne, babu wasu Aljanu a duniya, kuma Innti ki yi shela, masu yi mana kashi da asuba kamar masu cikin fara don Allah su daina" kasa magana Innti ta yi idan ta biyewa Ana bata san wacce kalma zata iya amfani akan yarinyar ba. Ganin ta yi shiru ya saka Ana ta yi murmushi tana kashe idanunta "Allah Ya yi mini arziƙi na kai ki Umara da Hajji Sahibarmu abar ƙaunarmu walwala da jin daɗinmu idan bake babu gida lantarkin gidanmu baya goya marayu na karya miki ɗan kwali Babarmu" Murmushi Iftihal ta yi tana kallon mahaɗinta gabaɗaya ita babu Daada a lissafinta, gashi ita kuma a duniya tana masifar son mahaifinta yarinya me nutsuwa bata da hargagi ko ɗaya, saɓaninta ɗaya da Ana, ita Ana data saka ƙafa waje dukkan farincikinta zai kau ta haɗe fuska bata buƙatar kowa sai iya su kawai, miskila ta bugawa a mujalla a rubuta taurin kai da kafiya akwai barkwanci amma. Iftihal yawan fara'a da murmushi duk wanda ya yi mata magana babu ruwanta, she's so friendly to everyone. Akan wannan matsalar har daina magana suke yi na minti biyar, Ana tana ganin kaf duniya Iftihal kawai take da ita matsayin ƙawa, idan kuma tana kula wasu shikenan sun ƙwace mata nutsuwar zuciyarta masifar kishin yan'uwanta gare ta. Dai-dai nan Babban yaya ya fito yana gyara zaman Jallabiyar jikinsa, ya dubi Innti jin tana maganar Aljanu, kana ya dubi Ana, Innti ta yi mamakin ganinsa domin data shiga ɗakin baya ciki, dai-dai nan ma Jadid da Jaheed suka fito, Babban yaya ya yi waje suka bi bayansa. Alwala Ana ta yi haka Iftihal daman tuni Innti ta yi, a tsakar gida sukai sallah bayan sun idar sukai azkar suka ɗora da tilawar Kur'ani. Innti ta kunna wuta ta fara ɗora ɗumamen tuwon da suka yi jiya, gaban Ana sai faɗuwa yake kar dai ɗumamen za su ci yau ma, sun manta da abin da ya faru jiya banda Ana da Innti da Babban yaya.Abin yana zane a zuciyoyinsu raɗau. Suna idar da karatun, Iftihal ta fara share tsakar gidan, Ana kuma ta fara wanke-wanke. Ƴan mazan na dawowa suka fara nasu aikin, Jaheed jan ruwa a rijiya ya cika ko'ina, Jadid na zaune yana karatun Alqur'ani saboda bashi da lafiyar yin aiki. Babban yaya kuma ya haɗa kayan Innti dana Ana dana Iftihal ya wanke tas ya shanya, Jaheed ya wanke nasa dana Jadid. Bayan sun gama kowa ya yi wanka ya shirya weekend ne, Babban yaya sai 11 zai tafi farm center, Jaheed kuma sai 12 zai je shago Ana da Iftihal kuma babu makaranta. Suna zaune a tsakar gidan iska na kaɗawa gwanin sha'awa, sun shimfiɗa tabarma a ƙasan bishiya suna jiran Innti ta kawo musu ɗumamen tuwon. Ana ta miƙe ta nufi ɗaki babu jimawa ta dawo hannunta ɗauke da waya tana ta murmushi a fuska Jadid ya ce "Yau kuma kin tashi daga mafarkin zama marubuciya kin ɗauki burin Iftihal na zama ƴar jarida Allah Ya shirya mutum muna ganin ta kanmu a gidan nan" murmushi kawai ta yi masa bata ce komai ba. "Muna ɗaukan rahoto kai tsaye daga gidan rediyon Innti, me rahoto Ayshatul-Haleeym Ana" "Ƴar jarida kika zama yau?" Ta kashewa Jaheed idanunta. "Yaya Jaheed, me zaka iya cewa akan ɗumammen tuwon da Innti take yi yau?" Yana murmushi sosai ya ce "Ɗumammen tuwo duniya ne, ba'a bawa yaro me ƙiwa" Ta juya idanunta ta koma kan Iftihal ta ce "Mahaɗita ke mene ra'ayinki?" Iftihal na murmushi ta ce. "Kai mahaɗita, ɗumame akwai daɗi" Tun kafin ta ƙarasa kan Jadid ya ce "Kina zuwa inda nake zan kwarfeki, da wasu idanunki kamar na mage wasu koraye" A hankali Babban yaya ya juya nasa idanun da suke blue akan Jadid sai kawai ya ɗauke yana cigaba da danna waya. Ana ta koma kan Innti ta ce "Hajiya Inntinmu ta gargajiya, me za ki ce akan wannan ɗumamen da kika yi mana yau don Allah" "Allah Ya cika miki burikanki na alheri Aysha, ya shirya mini ke". Ta lumshe idanunta kamar yadda ta saba kamar me jin bacci can ta buɗe su akan Babban yaya tana ƙarasawa kusa dashi. "Babban yaya magajin uba, me zaka ce kai kuma" Kamar ba zai motsa ba, sai kuma ya ɗago kan shi ya sauke mata fararan idanunsa masu launi a cikin nata, bai san me ya sa ba, sai ya ji murmushi yana shirin suɓuce masa, ya kawar da kan shi zuwa gefe guda. Duk yadda Innti taso Ana ta ci tuwon fafur taƙi ci, ta tsani tuwo kamar mutuwa. Bayan sun gama ci, Innti ta samu Yaya a cikin ɗakinsu ta ce "Yaya, Ana taƙi cin abinci fa tun jiya, na rasa yadda zan yi mata" Ya jinjina kai, bayan ta fita ya miƙe shima ya fita zuwa waje, babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke da leda, ya ɗauki kwano ya saka tuwo da miyar ya shiga ɗakinsu Ana, ita kaɗai ce Ifti ta fita aike zuwa maƙota. Ya zauna saman ƙafafuwansa irin zaman raƙuma ya ja kwanon gabanta, tun kafin ta yi magana ya zura yatsunsa ya ciro tuwon ya saka mata a baki, ta ɓata fuska haka ya dinga bata tuwon a bakinta da hannunsa ganin kamar za ta yi amai ya wanke hannunsa ya miƙa mata ledar, indomie ta gani dafaffiya tun kafin ta yi magana ya fice daga cikin ɗakin yana rufe idanunsa. Daman tun asubar fari Daada ya fice nasa waje, su kaɗai ne a gidan. *** Ƙuri ta yi wa jaririn da yake kwance jikinsa kamar kwando saboda saɓulewa da ya yi, bata iya taɓa shi an baɗe masa jiki da wani garin magani. A hankali ta kai hannunta zuwa fuska ta share hawayen idanunta, bata taɓa ganin aure irin wannan ba, ko da ta taɓa gani nata yana da tarin bambanci, mijin ya aureta amma kamar kishiyarta ce ke riƙe da igiyoyin auren, da ƙuruciyarta da komai amma baƙincikin aure da zaman kishiya ya sako rayuwarta gaba, haihuwa ta yi ko kunun kanwa wannan bai ga cikinta ba, balle ƙaurin da ake yi wa me jego. Ɗan kara kunnenta ta yi sai ta ji numfashin babyn na fita da ƙyar. Labulen ɗakin aka ɗago yana daga tsaye ya ce "Wato Maryama ba za ki je ki hana me rahotan can sakawa ba, wallahi Allah muddin ta saka a bakin aurenki makira munafuka" kasa motsi Maryama ta yi, jikinta ɗanye ne sosai abarka da farar mace ta sake yin fari shar kamar mara jini a jika, gefe da gefen fuskarta duk gashi ne kwance haka ma girarta kyakkywa ce sosai bata shige 21 ba gabaɗaya. Cike da tsoro ta ce "Ai ban santa ba, bani na faɗa mata ba. Kar ka sake ni don Allah wallahi za'a iya kashe ni a gidanmu" Da hargagi ya ce "Ai gwara su kashe ki tunda gashi za ki jazamin shiga masifa da zarar hukuma ta ji na kaɗe har ganyena" Wacce take gefensa ta yi ƙwafa "Malam burinta ba a rufe ni na bar gidan ya zama daga kai sai ita, na faɗa maka ba ƙaunata take yi ba, da zaka sake ta da yafi" sai ya yi mursisi da idanu saboda yana ƙaunar tarayya da ita "A'a bata kai ga haka ba, ki duba duk ayyukan gidan nan Maryama ce ke yi miki idan ta bar gidan yaya kenan" Wani irin malalacin kallo ta watsa masa "Na fahimci kamar son ta kake, bana hanaka ce mata Maryama ba idan ba zaka ce ƴar aiki ba kawai ka yi shiru kaima fa Malam jarababbe ne" tusa ƙeyarsa ta yi suka fice daga ɗakin. Maryama ta bisu da idanu tana fashewa da kuka a hankali ta ce "Ubangiji ka kawo mini mafita ta alheri" *** NIGER/MINNA. Jihar Niger tana Arewa ta Tsakiya (North Central Nigeria). Ita ce jiha mafi girma a faɗin ƙasa wanda babban birninta ya kasance Minna, suna maƙwabtaka da Zamfara, Kebbi daka Arewa, sai Kaduna, FCT Abuja daga Gabas, sai kuma Kogi, Kwara daga Kudu, Benin Republic daga Yamma. Akwai mabanbanta mutane a jihar Niger zuwa Minna, Nupe a ɓangaren Bida, Lavun, Agaie. Sai Gwari/Gbagyi daka ɓangaren Suleja, Tafa, Minna. Sai Hausa Fulani a yankin Kontagora, Rijau, Wushishi, haka sauran ƙabilun kamar Kamuku a yankin Mariga, sai Kambari a yankin Agwara, sai Basa a yankin,Katcha haka kuma Dukawa a yankin Borgu. Niger na daga jihohin da suka fi kabilu haɗuwa a Najeriya. BIYA. Wani yanki ne a Nijer ƙauye ne sosai, wanda mutanen ƙauyen suka dogara da Noma, farauta da kiwo sana'ar hannu, suna da ɗan yawa gasu da soyayyar juna ta mutunci. "Wai har yanzu bata sauka bane?" Lami ta yi tambayar tana kai komo hannunta riƙe da zaninta saboda tashin hankali. Jin an yi mata shiru ya saka ta sake cewa "Sadiatu, magana nake yi" "Kika ce me Lami?" Sadiatu ta yi maganar tana ɗago labule daga ɗakin da take ta fito fuskarta babu walwala saboda damuwa. Lami ta ce "Har yanzu bata juye bane?" "Sai dai Allah Ya saukar da alheri, ban taɓa ganin naƙuda irin wannan ba Lami, abu tun jiya? Har hantsi ya fara kawo kai?" Sadiatu ta faɗa idanunta cike da hawayen halin da Kulu take ciki, suka yi jingum jingum. "Ai Malam ne da kalar tasa masifar, a kira me karɓar haihuwa amma bafur yaƙi ba dole ba" Sadiatu ta ce "Kin san shi da kafiya kamar kuturu haka yake". "Ai har gwara kuturu dashi" "Gafaranku dai" Suka ji an yi sallama daga bakin ƙofa. "Maraba lale da Gana, yau kece a tafe?" Cikin fara'a da walwala Gana ta ce "Wallahi, ai tafiyar dole ce shi ya sa na yi babu sanarwa" ta ƙare maganar yanayin fuskarta yana sauyawa zuwa damuwa can kuma ta juya a fusace ta ce "Ba za ki shigo ba ƴar kusun uwa, munafuka makira me ido a tsastsaye, mahaukaciyar banza da wofi" Lami da Sadiatu suka shiga leƙawa zuwa bayan Gana domin ganin dawa take sai suka hangota tsaye rakuɓe da jikin katanga. Tana zazzare idanu, tare da murza gashin kanta dake tufke tana wasa dashi, sai murmushi take yi tana girgiza kai da nunna abu a sama, ita kanta bata san me take yi ba, ba kuma tana yi saboda hauka bane bata son ganin matan gidanne "Au wai Batty ce, ince dai lafiya yaushe ta fara hauka kuma ni ƴar nan?" Gana ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce "Ina lafiya? Ai Baffan Batty ne ya ce a dawo da ita gabanku, wataƙila za ta yi hankali, ta dage sai an sata a makaranta" mamaki ya wanzu a fuskokinsu. "To ina Fulani ina zuwa wata makaranta, arna ne kawai suke zuwa bokoko, ya yi mini daidai ai" "Wata sabuwa ni Lami" ta sake faɗar haka Gana taja kujera tana zama. "Me ta yi ne? Me ya sa Baffan Batty ya ce a kawo ta Biya wani abu ta aikata a can yarin?" Cikin fillatanci Gana ta ce “Ko Batty woni jokka waɗude jango mo, sabu ɗum jokkaare makko.” ma'ana a yaren Biya ana nufin “Batty ce ta fara ɗauko masa zance, ai iskanci ne ke tuka ta.” Lami ta shiga salati "Na boni, me ta ɗakko?" "Zuwa ta yi ake taɓa mata matasan ƙirjin saboda iskaci, shi ya sa shekarunta be ɗakko ba, zuciyarta ta ɗakko nan da nan ƙirji ya haye" Sadiatu ta girgiza kai kawai. "Yanzu ni da aka kawo mini ita nan na yi yaya da ita? Salon ta dinga ɗaukar mini zance, Biya fa ba kamar can yari bace" Gana ta ce "haka za ki haƙuri Lami" Sai ta juya ta kalli Batty wacce kanta yake sama tana ta murmushi, a nutse yarinyar take sosai, idan ka ɗauke ƙuruciyar dake addabar kanta kayan saƙi na fulani ne a jikinta an ɗaure sumar kanta kamar alkaki. "Shai Baffan daya turo ta nan me za'ayi mata? Kiwo zata dinga yi ko farauta?" "Idan an samu me son ta a bayar da ita sadaƙa" sai a lokacin ta ɗago dara-daran idanunta ta zuba akan Gana tana jin duk abin da suke cewa, da sauri kuma ta faɗo cikin gidan, a hankali kuma ta kalli Sadiatu, ba ita take kallo ba, jinin da yake gudana a jikinta yana kai kawo take kallo, da kuma kwantaccen kitsan da yake cikinta, ta zubawa cikin idanun sai ta hango dafaffiyar masarar da Sadiatu ta ci ɗazo wacce bata gama narkewa ba, wani irin numfashi ta fuska idanunta yana rinewa saboda ja da kuma abin da ya motsa mata, tana ta kallon abin da yake yawo a ƙasan ƙafafuwan Sadiatu. Kafin su yi magana sun jiyo kukan jariri cikin sauri Sadiatu ta nufi ɗakin Gana kuma ta ce "Waye zai haihu?" "Kulu ce" "A'a tubarakallah ma sha Allah, kulu Allah ya yi kenan" Gana ta ce tana washe bakinta. Suna zaune aka gyara jaririn mutane suna ta yi wa Kulu murna haihuwar da har ta fitar da rai da ita. Gana ce ta shiga cikin ɗakin tana ƙifta idanunta, bayan ta ɗauki jaririn da yake fari tas ƙato dashi, sai motsa baki take, can dai ta miƙe tana faɗin "Allah Ya raya Kulu sai mun dawo raɗin suna, sannu kin ji haihuwa me daɗi" Kulu na murmushi Ta ce "Yaya Gana har za ki shige?" "Wallahi, Batty na kawo ai" Tana faɗin hakan ta laso bakinta kamar za ta yi magana sai ta haɗa da kurwar jaririn ta yi sauri ta fito. "Gana tsaya mu yi magana" "A'a Sadiatu, zan dawo ai in sha Allah" Ta faɗi hakan tana ficewa, sai data je waje ta tsaya ta ƙulle kurwar a bakin zaninta.... *H I Y A A M* Page 4 Bright pens Yota/001 *"A resilient heroine;* Nazeefah Sabo Nashe Ganin rana ta buɗe ya saka ta ƙara ɗaure bakin zaninta inda ta ƙulle kurwar jaririn tana tafe tana juyawa har ta ɗauki hanyar shiga rugar Fulaninsu da ake cewa Rugar Yari, idanun nan nata jajur babu kyan gani sai motsa bakinta take, tana yin tiƙar baki. Daga can cikin gidan Kulu na zaune da jaririn a hannunta sai murmushi take yi yau Allah ya azurtata da samun ɗa, bayan shafewar wasu shekaru da aurenta, mai rai baya fida tsammani a rayuwa, a wajan Kulu har ta cire rai da ganin jininta a duniya, banda gorin haihuwa, dana kishiya da kuma dangin miji, ana kiranta da juya babu kalar cin kashin da bata gani ba. Duk tafiyar minti guda sai ta juya ta kalli jaririn da zuwa yanzu ta kwantar dashi akan ka katifa. "Kulu kallon yaron ya isa haka" In ji Sadiatu Murmushi ta yi can kuma ta ce "Yaa Sadiatu ji nake kamar ba daka cikina ya fito ba, me zan yi na nuna wa Ubangiji godiyata daya share mini hawayena? Yau ni na haihu? Ɗana na kaina nake gani a gabana?" Sadiatu ta ce "Haka Allah yake ikonsa" "Haka ne Yaa Sadiatu" Sannu a hankali ta juya ta sake kallon jaririn sai taga kamar numfashinsa baya tafiya yadda ya kamata, ba kamar sanda ta haife shi ba, ta dinga kallonsa gabanta na faɗuwa, jinin jikinta na daskarewa saboda tsabar fargaba da zullumi, bata son dukkan abin da zai gitta a jikinsa da sunan ciwo ko wata damuwa, a hankali ta ja numfashi ta fesar, sai kuma ta miƙa hannunta ta ɗauke shi, sharf haka ta ji jikinsa ya saki, yana wani ƙanƙandarewa, ƙwayar idanunsu ta yi fari tas tana kallon sama. "Na shiga uku, Yaa Sadiatu duba mini yaron nan kamar bashi da lafiya, wayyo Allahna" jikinta ya ɗauki rawa da wani irin kakkarwa na fargaba. "Ki nutsu Kulu, shawara ce ta shige shi" da ƙarfi Kulu ta ce "Shawara?" Kulu ta maimaita a kiɗime. Sai kuma ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye ta ce "Ba haka na haife shi ba..," ta kasa ƙarasawa "Da cikakkiyar lafiya yazo duniya" ta furta a lokaci guda tana fashewa da kuka sosai. Sadiatu taga sauyi sosai a tattare da jaririn amma bata so ta ruɗa Kulu cikin kulawa ta ce "Haba Kulu, shikenan Ubangiji baya jarabtar bawa? Na faɗa miki shawara ce ba wani abu ba, yara kuma suna yi, bari na fitar dashi waje yanzu zan aika a amso mini magani" ta faɗa tana miƙewa tsaye, bata son rawar da jikinta ya ɗauka ya ankarar da Kulu cewa ba lafiya ba, don haka cikin sauri ta fice da jaririn tana sallallami a zuciyarta. Batty dake rakuɓe tana wasa da wani zakara data kama tana fiffige gashin jikinsa yana cara da kuka amma duk basu ji ba, ganin jini na fita a jikin zakaran ta yi saurin rungume shi kamar mutum yunwa ke ƙoƙarin zautar da ita. Da sauri ta zubawa Sadiatu manyan idanunta da nan take suka sauya daka fari zuwa ja, ba Sadiatu take kallo ba, jinin dake gudana a jikinta shi take bi da idanunta guda huɗu, jikinta ya ɗauki rawa, sai ta yi saurin yin ƙasa da idanunta zuwa ƙafafuwan Sadiatu ta zubawa kurwar Sadiatu dake yawo a ƙasan ƙafafuwan idanu, idan ta yi kamar zata kame kurwar sai ta fasa, cikin hanzari ta yi cilli da zakaran ta fice daga cikin gidan ta fara tafiya idanunta na shigewa ciki ya yi jajur bata ganin ko gabanta, sai data nausa ta shiga cikin gonaki kafin ta samu gefen wata ƙorama da ruwa ke gudana a wajan ta zauna, zanin Fulanin dake jikinta ta ɗan kuntu kaɗan sai ga baƙar leda ta bayyana, ɗanyen barkono ne a ciki jajur dashi, ta saka fararan hannunta ta ɗamki barkonon ta watsa a bakinta ta shiga taunawa kamar zata ci babu, sai data kusa cinye sannan ta ji abin ya faɗa mata a hankali. “Baffana, Innata ku cire mini abin nan bana so bana so a cire mini bana so” ta ce a hankali. Tana yi tana ƙoƙarin yage kayan jikinta. Sai kuma ta kwanta a gefen ƙoramar tana sakin wani irin kuka mara sauti tare da shura ƙafafuwanta tana riƙe cikinta. Idan ta tuna mutanen da suka shigo har rugarsu suka yanka Innarta wani irin abu take ji yana yawo a ƙirjinta, burinta na son yin karatun boko yana ƙaruwa a ranta. *** Yana daga zaunen da yake a saman kyakkyawar kujerar ofis ɗinsa tana ɗan juyawa dashi cike da nutsuwa ya ɗaga kai ya kalle ta kafin ya ce "You again? Na ɗauka na kawo ƙarshen matsalarki? Ina nufin zuwa yanzu ba ki da wata damuwa akan aiki?" Murmushi ta sakar masa tana ɗan juya jikinta da kwainane ta ce "Kasan buƙata haifar kanta take yi sir, kuma sai ina da buƙata zan zo wajanka tunda ka sabar mini?" Ta ƙasan idanunsa yake kallon ta ya yi shiru alamar yana sauraranta.Sai ta yi ƙasa da murya ta ce "Akan recorded ɗin dana tura maka ne wanda Ahlam ta yi, kuma ni ce wacce zan gabatar dashi a labaran rana. Labarin me kyau ne idan aka cire sunan Ahlam a matsayin wacce ta kawo labarin aka maye gurbinsa da nawa zan samu ƙarin ɗaukaka sosai Sir, zan ƙara farin jini a idanun mutane kuma kasan an kusa taron ƙarshen shekara zan iya samu award, shine requesting ɗina" "Amma kin san wannan labari ne me kyau da zai ƙara kawo mana audience a gidan rediyon nan, daga zuwan Ahlam kawo yanzu kin san muhimman labaran data kawo ake saka sunanki a madadinta saboda kawai ki samu ɗaukaka da fashion. Shekara nawa da kafa gidan rediyon nan wanne irin Appointment letter ne bamu turawa Sayyadi Baffa ba, amma ko sau ɗaya daga Office ɗinsa na Hisba Shari'a ba'a taɓa responding ba, amma tun wani program da Ahlam ta yi akan rigingimu addini da ake da Malaman Ɗari'a da jama'ar Shi'a sau ɗaya ya amshi gayyatar ta ɓoyayyiyar hanya, madadin a tura Ahlam ke aka tura, ban san ta ina ya fahimci cewa ba Ahlam bace sai office ɗinsa suka cancelled program ɗin ma, last last ma ashe bada shi za'ayi hirar ba da yaronsa ne. Kin ja mana asara babba, da Ahlam ta yi hira da Sayyadi Baffa Allah kaɗai ya san mabiyan da Bright Fm zata samu da irin ɗaukakar da yarinyar za ta yi" Cikin sigar damuwa ta ce "Ka kwantar da hankalinka sir zan nemo Sayyadi Baffa zan yi program dashi a wannan gidan radiyon" wani kallo ya yi mata na kamar bata san me take ba, a baki kawai take jin Sayyadi Baffa ɗin, ko Hisba bata da ikon shiga balle Office ɗinsa. "Kar ki wahalar da kan ki, kamar yadda bai taɓa shiga kowacce kafar yaɗa labarai ya yi magana ba, to ke ba ki isa ki saka shi ba, duk wa'azinsa da yake yi har gidansa ake zuwa a ɗauka" "Ok fine. Yanzu yaya ake ciki?" Sai ya miƙe tsaye ya zago inda take yana kallon ta a tsanake. "Kenan a kamilalliyar ƴar jarida ake kallonki duk wannan uban rawar kan da kike dashi da yadda kika gama rabawa manya jikinki saboda kawai ki samu damar program dasu" murmushi ta yi kawai tana jin yadda ya ɗan rungumeta ta baya yana hura mata iska a kunne ta yi saurin jan numfashi. "Sir..... "Can I?" Idanunta a lumshe ta kasa motsi muryarta na rarrabewa ta ce "What?" "Kiss you" "Can I kiss your lips?" Ta fara gajiya amma kuma tana buƙatar cigaba da ɗaukaka a matsayinta na ƴar jarida ta jinjina kai. Kissing ɗinta ya fara na wani lokaci kafin ya sake ta ya yi baya ya ce "Approved" "Thank you sir" "Amma da sharaɗin za ki saman a hotel yau mu kwana ko?" Ta yi ɗan jim sai ta ce "Amma me zan ce a gida?" Ya ce watsa mata harara "Ɗan jarida ai yafi kowa iya tsara zance. Ki nemi abin faɗa kawai ko ki ce dutyn dare ne dake suwa safiya, ita Ahlam ki mance da ita bata biyo layin ɗaukaka ba" har zata fita ya ce "Taken ki, hankaka me da ɗan wani naka, idan kin zo hotel ɗin haka za ki ce ina da shadols da yawa" "Ok sir" ta faɗa tana ficewa. *** A hankali take takawa kamar bata son shiga ciki, sanye take da abaya purple wacce take da feshin stones daya kasance baƙi, ta yi rolling kanta da baƙin mayafin abayar, hannunta ɗaya riƙe da jakarta da wayarta, ɗaya hannun maƙale a wajan hammatarta wanda ya kasance shanyayye. Addu'a ta yi kafin ta sako ƙafafuwanta cikin reception ɗin BRIGHT FM. Wanda a ƙofar shiga aka rubuta da babban haruffa da golden colour da feshin milk. “BRIGHT FM 116 KANO” "Bulala hamsin ta makara" Ta ji an furta a bayanta, cikin murmushin da baya taɓa barin kyakkyawar fuskarta ta murmusa kaɗan cike da ladabi tana yin baya kaɗan ta ce "Baba driver ina kwana" ya washe baki ya ce "Lafiya lau Alam" "Alarm?" Ta faɗa tana marairace fuska. Ya ce "Sunan naki ne na ƴan gayu, akwai wahalar furtawa a saman harshe musamman wajan irinmu tsofaffi wallahi" Ta lumshe idanunta ta buɗe, har ƙirji ta ji ƙamshin turarensa ya saukar mata, kafin sannu a hankali ta ji takun tafiyarsa ya ratsa ta gefenta ya shige, sai ta ji kamar ya shige da komai nata ne, nutsuwa, farinciki, da sauran kuzarin daya ragu a jikinta komai ba. Idan ta ce komai, tana nufin everything! "Barka da shigowa MD" Ta ji Baba driver ya faɗa, bata da tabbacin ya amsa, domin a karkashinsa ta san tuni ya yi kwana ya shige sashin da yake. Idanunta ya ɗan yi rau-rau wani ruwa na kwanciya a cikinsu, idan akwai abin da take da rauni ko yake nuna saurin gazawarta, bai shige kuka ba. Ko fitar hawaye daga cikin idanunta. "Ahlam ne baba" sai ta ɓata fuska. "Idan ka ce Alarm kana nufin abin agogo" Baba ya ce "Ba ki da sunan gaskiya ne?" "Akwai, Haleemah" Ya ce "kice kakata ce, bari na ce tsohuwa" "To shikenan, na gode baba" Ta furta tana jan ƙafafuwanta zuwa ciki, kai tsaye sashin sashen Labarai (News Department) ta dosa, office ɗin Director of News ta fara shiga, ta yi sa'a yana zaune yana duba wasu ayyuka a computer gabaɗaya ya tattara hankalinsa zuwa ga abin da yake yi . "Sai yanzu?" Ya furta a hankali. "Sir, na tashi da ciwon kai ne" "Opps, wish you a very quickly recovery" "Thank you, Sir" "Zauna mana, have a seat please" Jin shiru kuma bata zauna ba, ya sanya a karon farko ya ɗago idanunsa da suke cikin farin glasses ya zuba a saman fuskarta kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce. "Ahlam" "Na'am" "Nemi waje ki zauna, ya akai?" A sanyaye ta ja kujera ta zauna, yau ɗin ba kamar yadda ya saba ganin karsashi a jikinta ya ruske ta ba, sai ya ji a ran shi tabbas akwai damuwa, duk da ɗabi'arta ce zuwa gaida kowa a gidan rediyon muddin ta shigo. "Kin yi shiru? Kamar da matsala ko?" "Sir, akan rahoton dana tura maka jiya ne" "Oh; Yes, na duba komai ya yi kyau kin yi aiki me kyau kuma me muhimmaci, ni kaina hankalina ya tashi dana saurara ban yi ƙasa a qwiwa ba na tura shi bayan na tace komai" ya ce yana yin baya da juya kujerar. Ahlam ta fiddo idanunta wajan faɗin. "Ina ka tura shi Sir?" "Editor-in-Chief, is there any problem?" Shiru ta yi har zata miƙe tsaye ta ce "Sir ka gyara zaman tea cup ɗin zai iya faɗuwa ya zube maka a ƙafa, idan ka ƙone ai muna cikin wani hali" kallon cup ɗin ya yi sai ya kalle ta. "Babu wani faɗuwa....," bai ƙarasa faɗa maganar ta tsaya masa ta dalilin rikitowar cup ɗin da shayin zuwa ƙasa, Ahlam ta hangame baki cike da tsoro ta yi baya tana faɗin "Sannu sir, bari na...," "Hold on please Ahlam, ki faɗa mini gaskiya ya akai kika san cup ɗin zai faɗi da shayin? Da faɗar da kikai ko minti uku ba'ayi ba ya kifo mini a ƙafa" kai ta shiga girgiza wa da alamar jarumta a tattare da ita ta ce "Kawai na faɗa ne bana nufin hakan" Wani kallo ya yi mata wannan shi ne karo na uku tana musu a gidan rediyon nan yana faruwa wani abu kamar camfi "kina nufin bakya tsafi?" Ta girgiza kai sai kuma ta yi saurin tashi tsaye ta yi masa godiya ta fita, cikin sassarfa bata ganin ko gabanta ta nufi office ɗin Editor-in-chief, tana ƙoƙarin yin corner ta ji ta yi ƙaro da ƙirjin mutum, a kiɗime ta yi baya tana rarraba idanunta, tare da dafe goshinta, ya tsaya cak daga tafiyar da yake yi yana juya idanunsa a kanta, wacce take biye dashi ce ta yi siririn tsaki wajan furta "Kin fita daga cikin hankalinki ne da za ki dinga tafiya anyhow, duk yadda zuciya ta raya miki kamar a filin gidanku?" Ahlam ta zubawa Yusraah idanunta, kamar da biyu take mata faɗan, kamar bata lura cewa abin da ya faru unexpected ne ba, ba da gangan ta yi ba, ta ya ya zata tsara buge mutumin daya girme mata, ya zama sama da ita a gidan rediyon, yake sama da kowa ma. Dukkan su ai suna ƙarƙashinsa ne, a ƙasan MD suke shi kuma yake ƙasan Founder, kamar bata lura shima ya yi mata rauni da buɗaɗɗan ƙirjinsa ba, ko ita Yusraah bata gani ne, bata kuma fahimta. "I'm very sorry Sir" Shine abin da ya suɓuce daga cikin bakinta, ba tare data lura daya jima da barin wajan ba. "Ga iyayi ga nakasa, a dole sai an ɗaukaka wai, mu zuba mu gani ni dake babu wani cigaba da za ki kawo wanda zai iya moving level ɗinki daga yadda kike ɗaukaka sai dai ki ga ana yi wallahi" "Yussy, ai ban ɗauka kina halitta ba" Yusraah ta ce "Kar ki mini rashin ɗa'a yanzu na miki illa" Ahlam ta yi murmushi tana cije bakinta tana kallon Yussy ta ce "Bayan rashin aji dake ɗawainiyya dake ashe hadda rashin ilimin addini ne ke damunki Yussy." "Ni kike faɗawa haka" "Na faɗa miki ki saka mini gas idan za ki iya, wacece ke da za ki fara mini ihu a saman kaina, da faɗan zan ji ko da muryarki dake neman tarwatsa dodon kunnena, maganar nakasa da kike, na yarda ina da nakasa, amma nakasata bata taɓa zama kasawa a gare ni ta zama hujjar zama raunin Ahlam ba, kina ji kina kallo da wannan nakasar Ahlam zata kafa tarihin da har abada Yusraah bata kafa ba, kuma ki faɗawa me sama cewa bai iya halitta ba, ƙarshe kenan" Tana faɗin hakan ta shige office ɗin Editor-in-chief ta bar Yussy tsaye shanye da baki."Kamar fa daƙiƙiya take ƙoƙarin haɗani da kalmar, kan uba, yaushe tazo gidan rediyon?" Ta saka hannunta a baki tana ciza sai kuma ta yarfe hannun, ba zata taɓa zuba idanu Ahlam ta shigo ta fita farin jini ko ƙoƙari a cikin BRIGHT FM, Radio ba, wacece Ahlam yaushe ta fara koyan aikin? Ta tuna ranar data fara zuwa gidan rediyon, ranar data saka idanunta akan Ahlam sai ta ji kamar wacce zata kawo ƙarshen farin jininta a gidan rediyon ce tazo. Tabbas ta tuna, ta tuna komai. Daga office ɗin HR ta fito sukai karo a hanya "Sunana Ahlam Abdallah Kurmi, matashiyar ƴar Jarida me koyan aiki yau na fara aiki" Ta ce da golden voice ɗinta tana kallon Yussy, wacce ta yi tsaye tana kallon ta, bafa mata ƴan jarida ne bata saba gani ba, ana yawan yin mata masu koyan aiki, kuma ta dalilin Yussy suke barin BRIGHT FM ɗin. Sai dai me? Akwai bambanci. Tarin bambancin dake tsakaninsu da Ahlam, a suffa, kyawun sura, nutsuwa da kamala, da zallar kyau irin na kanuri. Da farko, muryarta ita ta fara ruɗa Yussy, irin muryar dake hawa da kowanne kalar program a gidan rediyon, News, interview, Boardcast, kowanne kalar abu muryar Ahlam zata ɗauka. Hakan ya bawa Yussy tabbacin Ahlam za ta yi nasara na shiga kowanne kalar program, ita kuma za ta yi ƙasa ne. Hujjar farko daya zama dalilin tsanarta da Yussy ta yi, hujjar da bata zama ƙwaƙƙwara ba, bata zama dalili babba ba. Tana da kyawun da za'a so ta, sai dai tana da tabbacin ko kallo bata ishe MD ba, kamar yadda burin Yusraah shine maza matar MD ɗin. Sai ta kalle ta sheƙeƙe ta watsar, tana taunar chewing gum, ƙas ƙas ƙas ƙas. Al'amarin da ya yi wa Ahlam zafi kenan. "Ina fatan na samu ƙawa, wacce zata koya mini abubuwa da ya kamata na sani game da aikin daya kawo ni ko?". "Sai da bana abota da nakasasshe, da zan ba ki shawara da kin koma gida kin ɗauki roba ki bi sawun mutanen gefen titi, amma wannan aikin bana mutane masu nakasa bane irinki" ta faɗa tana watsawa Ahlam harara, har zata juya sai kuma ta tsaya ta ce "Yusraah Yassar Yakasai, shine sunana, matashiyar ƴar jaridar da ake ji da ita" Tana faɗin hakan ta juya tana rangaji kamar wacce zata bi iska ta yi sama, siririya ce sosai, irin masu shafaffan ɗuwawun zaman nan, ga ɗamammun kaya da take son sakawa, wanda ke fitar da jemammen kwankwason nata a fili, zanƙaleliya ta ita tana da yalwar ƙirji da kyan fuska sosai Ahlam sai ta fito da hannunta data ɗan rufe da mayafi, ta kasance me duhun fata, irin me hasken nan sosai da akewa laƙani da 'Chocolate colour' Bata da tsayi can, kuma ba gajeriya bace, tana da kakkuran jiki ko'ina a murje kamar ita ta zaɓin yadda zata kasance, abu uku dake fito da asalin kamarta da Kanuri shine, manyan idanunta farare tas, sai jajayen laɓɓanta wanda suke koyaushe kamar ta shafa musu lips lamp peach kuma. Hannun daya shanye take ta kallo, yatsun hannun wani yafi wani, wani dogo wani gajere, sai ɗan kaifi da suka yi, wanda ya kasance manuniyya shine ya yi zabgege a ciki, sai fatar hannun da ta yi yaushi da tattare waje guda, bata taɓa iya motsa hannun yana maƙale kodayaushe, da hannu guda take yin komai na rayuwa, wanda ya zama na damanta, bata samun gazawa na yin abu. To ai ita ma ba haka aka haife ta ba. Kamar cutar ƙyanda ta yi. "Baby na kusa rasa ki, fara ce ke sosai, ƙyandar nan da kikai ta saka kin yi baƙi" Cewar Engineer. Yussy ta sauke ajjiyar zuciya bayan Ahlam ta shige cikin office ɗin Editor-in-chief, ta yi ƙwafa tana bin bayan MD zuwa office ɗinsa. TJ ya kalli Ahlam ya ce "Golden voice ya akai ne?" "Sir, na je wajan Director of News akan batun rahoton dana tura masa jiya da daddare, shine ya ce ya turo maka ai" "Rahotan matar da aka ƙonawa jinjiri?" Cikin rawar murya Ahlam ta ce. "Yes Sir, shi nake magana" "Ok ya akai Golden voice?" "Sir Tj akwai matsala ne akan rahoton, ina buƙatar a dakata wajan ɗora shi, kar a gabatar dashi Please don Allah sir Tj" Ya yi baya ya ce "A dakata?" Ta ce "E, don Allah" "Na riga na turawa News editor, zai wahala idan ba'a kammala ba, domin a labaran 12 za'a saka shi, sai dai ki je can ki duba muga...," bai ƙarasa faɗa ba, ta yi saurin miƙewa jikinta na rawa ta fita ta nufi office ɗin News editor, a hanya ta haɗu dashi, tun kafin ta ƙarasa ya dinga yi mata kyakkyawan murmushi yana lumshe idanunsa tare da daidaita tsaiwarsa yana jiran zuwan nata, daman wajanta zashi sai kuma gata tazo. "Baby ya aka yi?" Ya furta kamar yadda Engineer yake faɗa, sai ta kwaɓe fuska idanunta ya yi rau rau muryarta na rawa domin bata so ya dinga ce mata baby sam. "Shikenan, Ahlam" Ya ɗan matsa kusa da ita yana jin numfashinta na sauka. "Anees, rahoton dana turo yana ina? Ka cire a cikin rahotanni da za'ayi ina cikin matsala ne sosai Please" "Problem?" Ta jinjina masa kai. "11:52 fa baby" Anees ya faɗa yana duba agogon hannunsa. "News Anchor tana studio yanzu haka, ki yi haƙuri ki bar shi baby, ai labari ne me kyau" "Na shiga uku" Shine abin data samu zarafin faɗa tana jingina da jikin bangon. Anees ya ɗan matsa kamar zai riƙe hannunta daga bayansa ya ji an furta "Kana iya ɗaukanta zuwa hotel, nan bai zama dandalin yin iska ci ba" kafin su juya tuni ya bar wajan, ƙirjin Ahlam sai ɗagawa yake yi kamar wacce Asthma ɗinta ke ƙoƙarin tashi, ta dinga riƙe ƙirjinta, bata san zirga-zirgar da MD yake yi yau ɗin nan ba, tana lura sai shige da fice suke yi shi da Official & Professional department, tare da Events & Outside Broadcasts (OB) Unit. "Anees ka taimaka mini, idan aka saka abin nan ina cikin matsala ba zan yafewa kaina ba, ka taimaka mini" Anees ya zuba mata idanunsa da sukai ɗan laushi da kalaman da MD ya jefe shi da su, da ƙyar ya iya cewa "Baby bana shiri da Yussy kin riga kin san hakan" "Yussy ce zata gabatar da labaran?" Ya ce "Yes, Zainab Alƙali bata shigo ba" Ta sulale a wajan tana dafe kanta, daidai nan messenger ya shigo da sauri yana faɗin "Golden voice kin yi baƙuwa a reception" bayan messenger tabi tana zuwa ta hango matar, wacce kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci Bafullatana ce, da kuma ɗanyen jikin dake tattare da ita na haihuwa. Tana ganin Ahlam ta zabura tana durƙushewa ta ce "Ki taimaka mini kar ki saka abin nan a iska yabi duniya, ki taimaki igiyar aurena kar a sake ni, idan ya rabu dani wallahi yanka ni za'a yi a gida, ki tausaya wa rashin gatana nasan ke macace, ba za ki so na wulaƙanta ko aurena ya mutu ba, na haƙura na bar komai a wajan Ubangiji don Allah kar ki saka na roƙeƙi" baya da baya Ahlam ta fara ja, jikinta na rawa da kakkarwa ta juya a guje zuwa studio wanda aka rufe ko'ina gudun kar iska ta shiga, tuni Yussy ta shirya komai gabatarwa kawai ya rage, tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ta ji an buga mata uwar tsawa a firgice ta juya idanunta ya sauka akan Md ɗin. *** Ƙafarsa ta ɗora ɗaya kan ɗaya idanunsa zube cikin farin glasses da kaya na shan iska a jikinsa, ƙasaita kamala da ilimin zamani da gogewa ta shiga cikin manyan mutane ya gama zama a jikinsa. Labarai yake kallo a Aljazira girman parlourn kaɗai abin kallo ne. Wayarsa ce ta fara ƙara alamar shigowar kira ya juya kaɗan, sai ya miƙa hannunsa me ɗauke da gargasa zuwa kunnensa ya gyara zaman Bluetooth. "Indabawa ya ake ciki?" Ya furta a tausashe yana sake lumshe idanunsa. "Abin da kake jira ne, Government house ta fitar da sabbin forms na ɗaukan matasan da suka kammala University babu aikin yi, an fitowa da tsarin Allowance for the other students da basu samu Form na aikin ba da za'a dinga musu shi monthly" ya yi jim. Indabawa ya ce "Kana jina?" "Wane ya akai wannan buƙar ga Shugaba? Wa aka bawa damar rabawa local government forms ɗin da Reps?" "Actually ban sani ba, amma kai aka bawa duka forms ɗin ta hannunka za su fita" sai a lokacin ya saki ajjiyar zuciya ta samu nutsuwa ya ce "Ina ga abin da za'ayi, zan ɗan rabawa rukuni sai ku bawa familys naku, za'a sanar a Internet dama ga masu son aiki su je Government house a tantance aiki ne kyau ga wanda suka kammala University suka fita da first class, sauran aikin zan sanarwa da Kalido yadda za'a tsara, ba za'a raba ko ɗaya ba, duk me buƙata siyar masa za'ayi, idan mata ne a tura su office ɗin P.A na, idan sun ji jarrabawar da ya yi musu sai a basu" "Yadda ka ce haka za'ayi, Allah Ya taimake ka, na hannun daman Shugaba ƙasar taku gwamnati taku" ɗan murmusawa kawai ya yi kafin ya kashe kiran. *** Iftifal ce ke tafiya daga aiken da Innti ta yi mata na karɓo kuɗin adashi, tun daga nesa ta hango majalisar dasu Daada suke zama, kamar koyaushe yana zaune suna karta sai busa sigari Daada yake yi yana fesarwa tazo dab dasu ta durƙusa har ƙasa tana wasa da yatsun hannunta da suke farare tas abinsu. "Ina yininku?" Ta ce a sanyaye da murya me laushi. Alhaji Baita ji ya yi wani abu ya yi masa zillo ya tsarga masa, kamar tsohon maye haka ya shiga suɗe bakinsa yana washe haƙoransa masu jan goro, nan da nan ya rasa nutsuwarsa sai riƙe wando yake yi. "Lafiya lumi Iftihal, unguwa za'a ne?" Garbati ya amsa mata yana zungurin Alhaji Baita. Jinjina kai kawai ta yi, shi kuma Alhaji Baita ya karkace yana zaro kuɗi sabbin ƴan dubu dubu har dubu biyar ya ɗauka ya bawa Ifti. "A'a Baba, na gode" "Ke Iftihal amshi, don ubanki" Ta ji muryar Daada. "Daada Innti ta hana mu amsar kuɗi wajan wanda bamu sani ba, babu kyau ta ce" Alhaji Baita ya ce "Ayya ayyya, ban ji daɗi ba nine ba ki sani ba Alhaji Baita? Abokin mahaifinki ne ni ƴar nan" "Wallahi ban sanka ba" Ta faɗa a tsorace, tsawar da Daada ya yi mata ita ce ta saka ta amshi kuɗin tana yin godiya kana ta miƙe ta tafi. Bayan ta shige Garbati ya ce "Daada kaga irin arziƙin da yake tattare da yara mata? Wallahi ko sabon gari ka kai su, ka kama musu shago kaga yadda za'ayi taruruwar tayin su, kamar nama a miya haka Ana da Iftihal za su zama, ka amince da wannan cacar Dada" Daada ya numfasa yana kallon Alhaji Baita, kafin ya ce "Baita ka tabbatar Miliyan ashirin zaka saka a wannan cacar? Ka tabbata ko?" "Haba Daada, ba ƙaramin mutum bane ni, kaf unguwar nan waye kullum ake miya da nama a gidansa idan ba ni ba? 20 Millions ne cash" Daada ya shiga lissafin dokin Rano, rayayye da matacce, hango kan shi cikin daula da arziƙi yake, hango yadda zai gina tangameman gida, ya siya mota da abubuwan mure rayuwa, yadda zai ƙara aure ya ajjiye mata har huɗu, ga Tani a gefe biyar cif kenan. "Na amince, na amince" "Na amince wallahi, da gaske na amince" "Ka amince dame?" "Na amince da saka Ayshatul-Iftihal, Ifti a cikin cacar, ina da yaƙinin ni zanci" wani irin shu'umin murmushi Garbati ya yi ya juya ya kalli Alhaji Baita kafin ya ce "Sai a yi komai a rubuce ai" Suka ɗakko takadda kowa ya yi rubutu. "Ni Alhaji Baita na saka Naira miliyan ashirin a wannan cacar, idan Daada ya ci, zan bashi kuɗin, kamar yadda sharuɗan cacar yake" Shima Daada ya rubuta. "Ni Daada, na amince da saka ƴata Ayshatul-Iftihal Ifti, a cikin wannan cacar, idan Alhaji Baita ya ci, zan mallaka masa ƴata Iftihal da hannuna" Aka saka kwanan wata, da saka hannun kowa dana shaidu suka tsayar da ranar da za'ayi wasan kamar yadda aka tsara. Da saurin daya rage a jikinta ta nufi gidan nasu, kanta a ƙasa tun kafin ta ƙarasa ta hango shi tsaye ya harɗe hannunsa a ƙirji, milk ɗin shadda ce a jikinsa ta haska farar fatarsa ya ɗora zanna bukar a kan shi, sajen gefe da gefen fuskarsa sun yi kwance yana da tsayi da buɗewar ƙirji babu alamar wasa a tattare dashi. Ta durƙusa har ƙasa ta ce "Yaa Sam, ina yini" Daga sama har ƙasa yake kallon ta ya yi shiru har sai data sake maimaita kanta. A hankali ya ce "Lafiya" ya faɗa da ƙyar. "Bari na faɗawa Ana ka dawo, ƙila bata sani ba....," bata ƙarasa faɗa ba, ta hangu su, su huɗu jere sanye da Jallabiya a jikinsu suna tafe suna rangaji da yarfe hannu zuwa gefe, sai karairaya suke yi kamar babu ƙashi a jikinsu, babban cikinsu ya saka ɗankwalin atamfa wajan ɗaure ƙugunsa dashi ya rataya baƙar jaka a kafaɗa, suna tafe suna hira sai su yi shewa su tafa. Ganin haka ya saka ta yi saurin cewa "Yaa Sam bari na shiga na kira maka ita yanzu yanzu" ta yi saurin shigewa ciki gudun kar su same ta. Yana ganin sun ƙarasu ya shige gidan dake kusa da gidansu Ana abinsa. Ana na zaune tana duba ɗinkin da Innti ta yi tana mai yaba rigar wajan faɗin "Gaskiya ɗinkin nan ya yi kyau Innti, irin shi za ki yi mini da ƙaramar sallah kin ji uwata" "Allah Ya nuna mana Indo, yasa muna raye" "Innti ga Baba Bala nan" Iftifal data shigo ta faɗa a ruɗe, kamar walƙiya haka Babban yaya ya shige ɗakinsu. "Gafaranku dai" Suka furta a tare suna shigowa cikin gidan, Ana da Iftihal suka yi saurin komawa waje guda, Innti ta amsa da "Allah yai mana" Suna shigowa tsakiyar tsakar gida, suka yi shewa "Ahayye... Riiiii" suka game kwankwaso waje guda ana karya kai gefe guda. Hakan ya faru bayan ido biyu da sukai da rigar Maman Innti dake shanye a igiya. "Yaya ga abar fa" Ƴar Beauty ya ce yana saka dariya Ya maƙale hannu a kafaɗa kamar mai shan inna yana tauna cimgam ƙas ƙas. "Sai dana fito naga wannan na tuna ashe tsirara na fito" wanda aka kira da yaya ya faɗi hakan "Kai Yaya, haka maza suka ƙare miki kallo a hanya ashe?" Cewar Abar ƙauna. Sukunbiya ya rangwaɗar da kai. "Bari kawai, shi ya sa na jini tantsan tantsan, ba tsiya ba arziƙi ki ce a ɗaiɗaice na fito" ƙas ya faɗa yana bada sauti. Tiƙa-tiƙan maza ne, wanda akewa laƙabi da ƴan daudu suke maganar a tsakaninsu. Ita dai Innti ɗinkinta kawai take yi. Ƴar Beauty ya kalli Sukunbiya ya ce. "Yaushe duniya ta yi tunbuɗi na fitar da sabbin ƙinƙisa a gidan nan Yaya?" Sukunbiya ya ce "Ke uwar gane gane, ƴaƴana ne su fa, ɗan yayanka ai ɗanka ne bana son haka" "Baba Bala ina yini" "Kinga yini akan ki Ana, ni za ki kalla ki kira da Bala, ina mace ƴar'uwarki ta ina na yi miki suffa da namiji, shi yasa bana son shigowa cikin gidan nan wallahi aikin kawai" Ana ta tura baki gaba ta ce "Ai shi ya sa naga nono a ƙirjinka, wallahi mugun duka ne baka ci ba, da sauri zaka dawo asalin namiji ina faɗa maka" Iftihal ta buɗe baki da mamakin Ana. Innti ta ce "Ana, wacce magana ce haka?" "Innti ki bari na faɗa masa gaskiya, sai ya dinga yawo yana zubar mana da rigar mutumci, waye zai aure mu idan yaga ƙanin babanmu ɗan daudu ne, ni da nake burin auren kyakkywan miji, kuma kin san kyakkywan maza yawanci masu kuɗi ne" Innti ta kasa magana. Ana ta murguɗa baki ta ce "Wallahi walakiri ba zai maka da kyau ba idan ka mutu a haka, jibgarka za'ayi kamar jaki, ai sai ka auri namiji ƙarshen daudu kenan" Bala Sukunbiya ya ce "Ni kike faɗawa haka? Kamar a bakin Daada wallahi, sai na ja miki masifa za ki san kin yi da watsastse" Caraf Ana ta ce "Kaga watsewa a kan ka, da kai da Daada duk ku kaga duhu, wlh sai na yi addu'a in sha Allah nono ya fito maka har ciki, wai Sukunbiya?" Sai ta sheƙe da dariya "Mahaɗita yau miyarmu da Sukunbiya za'ayi" takaici ya kama Sukunbiya. Sai ya yi ƙwafa kawai. "Daɗin ciwo nishi, inda me maka sannu" Inji Ƴar Beauty. Caraf Abar ƙauna ya amshe da faɗin. "Ni dai ki yi sauri yaya, ina da aikin suyar waina zani yinin suna kuma, kar a yi mini asarar haɗuwa da ƙawayena masu capacity" "Heeee riii" suka sake saka shewa da haɗe kwankwaso waje guda abinsu. Sukunbiya ya ce "Daman kuɗin adashi na kawo gashi, ina neman alfarma a bani zubi na gaba, saboda bikin ƴar aminiyata za'a yi" Ya ranƙwafar da hannu wajan miƙa mata kuɗin, ganin Innti bata amsa ya dire kuɗin ya ce "Na rasa ta cewa, wai uwar gulma ta yi cikin shege, sai aron rigar mamakin za ki bani zani suna yau, naga size ɗinmu ɗaya dake matar Daada, kema dai tubarakallah" Abar ƙauna ya riƙe zancen da faɗin. "Kallabi tubani, wai anwa uwar kwarto fyaɗe ya ce mama riƙe mini wando ina zuwa" "Riiiii!" Suka sake yin shewa. "Ya naga kina mini kallon hadarin kaji, abin fa duk the same me, wai Ali ya ga Ali" Cewar Sukunbiya. Innti ta ce "Bala ka yi haƙuri, bana bada kayan sawata, kar ka sake mini haka" Ya riƙe haɓa ya ce "Oh ni Sukunbiya abin zubawa a miya, ina ruwan gayyar tsiya arna a idi abin arziƙi bai amshe ni ba ni dai kam" Ƴar Beauty ya ce. "Yaya muje don Allah, na ji kamar al'adata ce take bin ƙafafuwana, muje muje ni" Suka rankaya tare da ficewa suna sakarwa Innti habaice-habaice ita dai bata kula su ba. "Mahaɗita Yaa Sam ya dawo fa" "Me ƙarya?" "Ɗan aljanna, yana waje ma" Cikin sauri ta zura hijab ɗinta, rabon data fita waje har ta manta makaranta ke fitar da ita, kuma kwana biyu bata je kwata-kwata. Sanda ta fita bata same shi a waje ba, sai ta shiga gidansu ta tarar da Mama zaune tana suya gyaɗa ta ce "Barka da yamma mama?" Mama na dariya ta ce "Ana manya, muddin naga ƙafafuwanki a gidan nan mutuminki ne ya dawo, yanzu ya fita yana shagonsu na waje ai" murmushin kawai Ana ta yi ta nufi waje, a bakin shagon ta tsaya tana bubbugawa, yana jinta bai amsa ba, ta gaji ta bugawa ta leƙa sai taka ya miƙe tsaye yana gyara rigarsa ya fito. "Yaushe ka dawo?" Ya dube ta tsam ta grey eyes ɗinsa ya sake yin fresh fuskarsa na ɗaukan ido sai ya ce "ban sani ba" "Au sorry faɗa muka yi ne? Naga ka yi fari ko bilitin ɗin ka fara ne, ina yini ya hanya?" Bakinta kawai yake kallo. Ƙafarta ya kalla yaga takalminta ya lalace sosai kafin ya ce " kin rame" Kamar me jira ta shawagaɓe masa fuska blue eyes ɗinta ta juya ta ce "To ba kai bane" "Ni?" Ya nuna kan shi da yatsa. "Baka sake kirana a wayar Yaa Jaheed na duk na damu" A kasalance ya ce "Ban niyya ba" Sai ta fara yarfe hannunta tana shirin yi masa kuka abin da ba ɗabi'arta ba, ya tsuke kyakkyawar fuskarsa ya ce "Kar ki mini banso" sai ta yi ƙasa da kanta kawai. "How many times zan ce ban son shawagaɓar nan Nanaah?" Ita dai ba ta yi magana ba, ya ce "Muje" Ta ce "Ina?" "Siyar dake" *** A gurguje Gana ta shige cikin bukkarta tana sakin assabari, ajjiyar zuciya ta sauke kafin ta sunkuya ƙasan ƙaramin gadonta ta janyo wani kasko ta fito da baƙin ƙyalle a hankali ta kuntu gefen zaninta ta ciro ƴar tsokar kurwar jaririn ta ɗaure da baƙin ƙyallen, sai kuma ta saka a cikin kaskon ta zura cikin wata kwarya ta rufe. Wani kwano ta ɗakko me ɗauke da mai fal ciki, ta saka yatsa ta lashi man a bakinta tana jin garɗi da daɗin man na ratsa cikin kunnuwanta saboda daɗi "Allah ka sake haɗani da mai maiƙo a jiki kamar Hansai, wayyo daɗi wayyo daɗi" Ta sake laso man ta kai bakinta. "Kamar na sayarwa da Alhaji kurwar nan, kamar na yi watanda a kanta" ta fara tunani. Sai kuma ta ɓata fuska sosai "Ina son kuɗin kuma" Can ta yi tsaki ta ce "Ina son jaririn ma" *** A bakin shagon Ana ta tsaya Yana Sam kuma na can gefe yana yin waya hannunsa cikin alijuhu yana daga inda yake yana hangota. Ita bata saba tsayuwar shagon katin nan ba, gashi ko ta kira sunan Jaheed ba ji zai ba. A cikin cunkoson wajan ta ji an zura hannu ana shafo ta, sai ta yi banza ta sake jin an shafo bayanta cikin sauri ta juya idanunta na rinewa ta kalli yaron ta ce "Ajjiyar me ka yi a jikina da kake shafani, ɗan iska ne kai? Uban me kake nema?" Gabaɗaya mutanen wajan suka juyo suna kallon Ana, kamar basu taɓa ganin mace ba sai a kanta musamman yadda take juya manyan idanun nan nata, sai ya ce "Ni za ki wa sharri?" Tai wani irin luu da idanunta kamar za ta yi bacci ta buɗe su akan shi, fuskarta ta haɗe ta watsa kamilallun idanunta akan shi. "Ashe ban ji sanda kake taɓa ni ba" Ta sake faɗa kamar bata son magana. Wani ya ce "Ke yarinyar nan me zai taɓa a jikin naki, ko dai ba ki ji dai-dai bane?" "Me namiji yake taɓawa a jikin mace?" Caraf yaron ya ce "Sharri ma take yi mini" Wani irin haske ne ya bayyana a idanun Ana ya sauka akan yaron jikinta har wani irin rawa yake yi ta ce "Ban taɓa yi wa wani sharri ba, ban yafe ba ɗan iska kawai, in sha Allah sai kaga abin da zai same ka" Wani irin ɗaci take ji a maƙoshinta, ta tsani a ƙaryatata, ta sani a nemi cin zarafinta, gata da wata baƙar zuciya da riƙe abu a rai "Kake cewa na maka sharri?" Ta runtse idanunta, ta sake ware idanun wannan hasken me kama da magic ya sake sauka akan yaron "Zaka gani" Ganin abin na neman zama rigima aka ce yaron ya tafi zuwa wani kantin, ita kuma ta cije a wajan jikinta sai kakkarwa yake yi. Yaron na ƙoƙarin juyawa kawai ya faɗi a wajan yana murɗewa idanunsa suka kakkafe, cikin sauri ta kalli yaron domin itama ta tsorata sosai sai ta juya caraf wani ya riƙe hannunta ya ce "Mayya ina za ki bayan ki kama yaron mutane shine za ki gudu?" Da rashin fahimta Ana take kallon cikin idanun mutumin ranta ya sake ɓaci ta rasa abin cewa, da alama yau bata da sa'a. Wani ya ce "Daman ta ce zai gani" "Kuma zai ga abin da zai same shi" in ji wani. Mutumin ya ce "Bidiri kashin rana da kiɗa, gashin nan tun ba'a yi nisa ba ta kame shi" Nan da nan wajan ya cika ana faɗin. "Mayya ce Mayya ce" Mene kuma mayya? Wani abu ne hakan da bata san dashi ba har ake jifanta dashi? Gabaɗaya sai ta rasa fahimta ta zama confused lokaci guda, ta haɗiye wani abu mai ciwo a ƙirji taƙi barin ruwan daya taru a cikin idanunta zuba, wanda ya sake sawa idanun nata suka sake zama manya. "Ni ba mayya bace, me na yi masa?" "Ai wallahi babu inda za ki sai kin tsallaka shi" cewar yayan yaron daya ƙarasu. Jaheed bai san meke faruwa ba, domin ko da wasa bai taɓa tunanin Ana zata fito ba, balle har ta ƙarasu kantin nasu. "Kul, kurwata kur ina faɗa miki" mutumin ya sake furtawa yana jefa wa Ana harara "Idan kun su ko kashe ni, babu wanda ya isa na tsallaka yaron nan, ku kuka san wata mayya kamar wani man shafawa aikin banza" sannu a hankali Yaa Sam ya ƙarasu wajan saboda hayaniyar da ta yi yawa, kuma ya hango Ana a tsakiyar mutanen, ya dubi mutanen kaf ya kalli Ana sai ya ce "Menene?" Cikin rawar murya ta ce "Wai ni ce Mayya zai na tsallaka yaron nan" "Mayya?" Yaa Sam ya nanata sunan a ƙasan ranshi. Sai ya kalli mutanen wajan ya ce "Kun yi kuskuren fahimta, ba ita bace" Yayan yaron ya ce "Wallahi sai ta tsallaka ƙanina sau uku, ko mu ƙone ta da taya a wajan nan a rage iri, wato a bari ta tafi gida, idan yaso ta cinye shi a can ko?" Ana ta kalle shi sosai. "Idan baka ƙona ni baka cika ɗan halak ba" Yaa Sam kallon ta ya dinga yi Daman ana cin mutum ne? Ganin al'amarin ya zama babba ya saka Yaa Sam sassauta murya yana kallon Ana Ya ce "Tsallaka shi, ki goge shakkun ransu" Sai a lokacin ne ruwan idanunta ya yi kamar zai sauka da sauri ta haɗiye hawayen ta ce "Kaima kallon mayyar kake mini? Wallahi tallahi sai dai su kashe ni amma ba zan taɓa tsallaka shi ba.... *H I Y A A M* Page 5: Six Worlds Around Me Bright pens Yota/001 “I pray that Allah grants you Jannah together with your parents.” Nazeefah Sabo Nashe. Page ɗin yau naku ne, Rabi'ahtu Achadu Fulani gal tare da Hiyaam book channel Allah Ya saka muku da alheri ya biya ku da Aljanna. "Ko duka garin nan gatanki ne, wallahi sai kin zo kin tsallaka yaron nan ya tashi, mayyar banza mayyar wofi masu cinye kurwar mutane a duhu" wani irin kallon gefen hagu ta yi wa yayan yaron ta ce "Bani da gatan daya shige na Allah da kuma mutanen shidan da suke tare dani, maita kuma kai ne mayen bani ƴar gidan Innti ba" Yadda take furucin a hankali ɗaya bayan ɗaya, da yadda idanunta sukai jajur wajan sauya launi amma taurin zuciya ya hanata zubar da hawaye zai tabbatar wa duk wanda yake wajan ranta ya kai maƙura wajan ɓaci. A nutse ta sake juya idanunta akan Yaa Sam, kafin ta mayar da ganinta kan yaron dake kwance har yanzu, sai ta yi baya kaɗan tana ƙoƙarin juyawa ta bar wajan. Caraf wani dattijo ya riƙe gefen hijabinta yana faɗin "Guduwa za ta yi" Ana kallon Dattijon ta yi, sannu a hankali ta kalli gefen hijabin nata inda ya riƙe mata. Runtse idanunta ta yi, ƙirjinta yana yi mata wani irin nauyi kamar an saka mata dutse a ƙirjin, wani zafi-zafi take ji haɗe da yaji-yaji. Ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Ina ganin darajar furfura ko bata mahaifina bace, ka cire hannunka a jikina Baba" Dattijon ya ce "Rashin kunya za ki mini?" Ya ɗora da "Ke anya ke kuwa mutum ce? Ban taɓa ganinki a wannan unguwar ba, ko irin ƴan iskan yaran nan ne masu barin gaban iyaye zance su biyo saurayi har unguwarsu?" Takaicin da ya yi mata yawa a zuciya tana jin kamar ta yi bindiga saboda yadda take jin wata wuta na rura kanta a cikin zuciyarta sai ta ka da bakinta ta ce "E, ita ce. Ka sake ni" "Waye ubanki a unguwar nan?" Ta ce "DAADA" Sunan ya fita ta cikin sirriyar muryarta mara son hayaniya da ihu ko kaɗan bata so. "Kan uba! Wannan tantirin tsohon shine uban naki? Me caca da garta kike nufi?" Cewar wani matashi, da ya yi maganar yana riƙe haɓa saboda tsananin mamakin daya cisa. A wannan karon Ana watsa firgitattun idanunta ta yi akan matashin, idanun da tunda take bai taɓa fita daga hayyacinsa irin yau ba, kanta wani irin ciwo yake mata yana juyawa tana jin kamar zai rabe mata biyu. A tausashe ta ce "E, shine ubana" "Babangida wai Daada me shan barasa yana yawo tsirara a kwararo idan dare da ya yi kake nufi? Me bin matan banza yana aikata aikin banza dasu, kamar yadda ya kasance ɗan banza? Wannan shine uban yarinyar nan?" Kai tsaye Babangida ya bashi amsa da "Wallahi shine, ai Daada ɗaya ne unguwar nan" ya tuntsire da dariya ta mugunta. Kallon tsana Dattijon yake bin Ana dashi kafin ya sake ta yana ɓata fuska kamar yaga kashi ya ce "Sannu ƴar nan, na tayaki baƙinciki da kuma takaicin samun mahaifi irin wannan, ashe yana da yarinya data girma har haka yake aikin banza da wofi a gari babu kunya babu tsoran Allah? Ashe yana da zuri'a mace yake bin manta banza? Yarinya kin yi kyawun ɗan maciji, kyawun da kike dashi ya tashi a banza ya kuma tafi a banza, babu uban arziƙi da zai yadda ɗansa ya aure ki domin baki kasance tsatson arziƙi ba" Babangida ne ya ce "Gaskiya kam baba" "Abin ya muku yawa wai shege da hauka, ke maita, Ubanki Dattijon banza, ƙanin ubanki wanda Allah Ya tsinewa me shigar mata" Sai a lokacin ne wasu azababbun hawaye masu masifar zafi da raɗaɗi suka kwace mata tare da bin kyakkyawar fuskarta suna sauka da gudu saman kumatunta, cikin sauri ta saka bayan hannunta ta goge su. Ba'a taɓa bin Ana bashin magana. Saboda haka ta kalli Dattijon ta ce "Na gode Allah da baka da gidan wuta balle na Aljanna, Ubangiji shike fitar da iri daga matacciyyar shuka, kuma shike raya wannan irin har ya zama ganye kore shar wanda kowa yake birge shi, na yarda ubana yana shan giya, yana caca, amma ƙazafin bin mata da kukai masa Allah shine zai mana sakayya daku, ban taɓa jin tsanar shi ba, soyayyar da nake masa ce ta saka kai tsaye nace muku shine ubana, babu wanda ya isa ya saka na sauya sunana daga nasa" Za su yi magana Jaheed daya rufe shagon ya ƙarasu wajan, idanunsa zube akan shalelen Innti ya dube ta tsaf kafin ya ce "Meya fito dake?" "Au ɓoye ta kuke yi saboda mugun iri ce ko?" Jaheed ya kalli Babangida ya ce "Sai dai ban fahimce ka ba" Babangida ya ce "Borin kunya daman da hauka ake naɗe shi, yaron mutane ta kama" "Kar ka sake ce mata Mayya!" Furucin Yaa Sam ya fito a nutse a tausashe yana bubbuɗe grey eyes ɗinsa zuwa waje. "Na faɗa a saka kaina gabas a yanka, wallahi ni dai kurwata kur nafi ƙarfinta" Cikin zafin rai da raɗaɗin kalaman Babangida da yake jifan Ana dasu wanda kai tsaye suke sauka a zuciyarsa suna kartar naman dake sarrafata ya nuna shi yana tattare hannun rigarsa ya ce "Ka yi kuskuren jifanta da wannan kalmar wallahi sai na maka illa mutumin banza da wofi, yunwa duk ta cinye muku yara babu mamaki ma olser gare shi, shine za ku zo kuna ihun banza bara a kufai" ganin da gaske Yaa Sam naushin Babangida yake shirin yi ya saka Jaheed saurin matsawa gabansa yana faɗin "Ka yi haƙuri ka rabu dashi Yaa Sam. Ana dai ba mayya bace kuma banda Innti ta hana mu faɗa da mutane wallahi yau da ya ɗauki kashinsa a hannu babu wanda ba ɗan iskan kan shi bane, da ita mayya ce da mune farkon waɗanda zata fara cinyewa I'm telling you this" "Kuma da mayyar ce me zan yi da naman mummunan mutum irinsa jiki duk basir da sanyi ya yi masa illa" Jaheed ya ce "Gaya masa dai tawan" Yaa Sam ya juya ya kalli Jaheed sai ya mayar da idanunsa akan Babangida ya ce "kuma wannan maganar shari'a ce zata rabani da kai, tunda ko mugun abu kukai iya da tsinanne sa ido wa jama'ar unguwa" Cikin shakku dattijon ya dubi Yaa Sam yana nuna shi da yatsa ya ce "Wannan ba ɗan gidan Malam Usmanu bane? Shi Usmanun ya barka kaka mu'amala da zuri'ar Daada?" Ko inda dattijon yake Yaa Sam bai kalla ba. Jaheed da ya shiga mamaki da takaicin fitowar Ana ya dube ta a hankali ya ce "Me ya fito da Shalelen Innti?" Ta ji shi sarai amma ko motsi ta kasa yi balle ya yi tunanin zata ɗago ta kalle shi har ta bashi amsar da kunnuwansa suka mace wajan jiran jin abin da yake faruwa, shi dai a tunaninsa da iya lissafin ƙwaƙwalwarsa a shekarun nan ɗaiɗai har shekaru goma sha Bakwai, tun daga haihuwar tawayen Innti, Iftifal da Ana, tun daga rainonsu zuwa girma idan kaga Ana ta fito waje a cikin biyu ko uku akwai ɗaya, babban dalili zuwa makaranta, boko, Islamiyya sai ta dare, dalilin dake bayan neman ilimin shine kiran Yaa Sam idan ya dawo gari. Wannan sune. Ƙawaye bata dasu, sau tari ta kan ce; "Duniyoyi shida ne ke zagaye da rayuwata, ina jin sanyi daga kowacce kusurwa Innti" Zata ja numfashi a hankali ta sauke manyan idanunta na sauyawa zuwa yanayi na ruwa, ruwan dake ƙara musu nagarta da kuma sahihin kyau, wanda yake sake fitar da kalarsu na “sexcy eyes” bata fiye kallon mutane da wannan suffar idanun ba. Babban mutum kawai take iya kalla dasu kai tsaye ta ji ta yi na'am da kallon har ranta. Da wannan nauyin zuciyar take riƙe hannun Innti da Iftihal musamman a ƙasan bishiyar dake ƙara musu ƙaunar juna saboda sanyinta. "Innti ni kaɗai nake jin idan na rasa ku kamar Ana ba zata iya rayuwa ba? Ina jin kamar nima wa'adina zai zo ɗaya da naku ne, zan jure komai, zan haƙura da komai, zan fahimce komai, zan yarda da komai, a cikin komai ɗin nan banda ku...," Ta lumshe idanunta ta ɗora da, "A cikin komai ɗin nan ban da rashinku a duniyata, kune ƙawayena, aminaina na cikin zuciyata, farinciki da walwalar Ana" A irin wannan lokacin Iftihal ke damƙe hannun Ana ƙam hawaye na sauka a saman fuskarta ta ce "Ita kanta mutuwa na san za ta yi mana halarci mahaɗita, zata ɗauke mu ne tare, dani dake da Inntinmu, yadda muka zo duniya a rana ɗaya, a kusan daƙiƙa ɗaya, a mahaifa ɗaya, daga cikin nagartacciyar uwa ɗaya, ina roƙan Allah ya amshi rayukanmu su yi wa'adi ɗaya tare da uwar data kawo mu duniya" Ita kanta Innti wannnan ranar ta rabuwa kashe ta take yi tun kafin mutuwarta, tana rayuwa da mutuwa da tunanin rabuwa dasu watarana dole. Idan ta tuna su yarana sai ta ji ta mutu, idan ta tuna su mata ne sai ta sake yin wata mutuwar, idan ta tuna dangin mahafinsu sake macewa take yi, babban dalilin dake sawa ta ji ta zama matacciyya shine; halin mahafinsu Daada. Bayan macewar tana farfaɗo wa da ƙarfin zuciya da shauƙin tuna cewa akwai, wani jigo a rayuwarsu bayan ita. Akwai garkuwarsu. Suna da Babban yaya a tare dasu tabbas..... Ta yi nisa cikin tunaninta Jaheed ya sake maimaita mata tambayar "Mene ya fito dake Ana?" Bata iya bashi amsa ba, saboda yadda ƙirjinta ke ɗagawa tana jin wani zafi da raɗaɗi kiranta da mayya, kalmar da bata san ma'anarta ba, bata kuma san me take nufi ba. Tambayar duniya Jaheed ya yi mata ganin kamar zata haɗiye zuciya ya saka Yaa Sam ya yi gyaran murya ya ce "Ka barta" "Shikenan, amma....," Bai ƙarasa faɗa ba, su kaga yaron ya miƙe a guje yana ihu ya yi lungun gidansu yana faɗin "Cikina, yunwa....yunwa zata kai ni lahira" Babangida ya yi saurin ɗauke kai jiki a sanyaye, haka dattijon ma ya bar wajan. Jaheed ya ce "Bari na koma shago Yaa Sam" Yaa Sam ya jinjina kai. A hankali ya juya tare da bin bayan Ana ganin ta yi gaba ya ce "Madam, takalmin fa?" Sak ta yi sai kuma ta juyo a nutse bata yarda ta kalle shi ba, ta fito da kuɗin hannunta ta miƙa masa. Yatsun hannun Sam ya bi da kallo ganin wasu kwantatun gargasa kwance a kowacce gaɓa ta yatsun hannunta, sun yi kyau sosai gwanin sha'awa. Ya san nufinta da baƙar zuciya saboda ya ce ta tsallaka yaron shi ne ya gogawa kan shi laifi. "bata son kuɗin ta fasa siyan takalmin kuma" haka yanayinta ya nuna. Sai ya tattara ya yi watsi da ita tare da yin gaba duk yadda yaso ya yi magana da ita. Ita ma gida ta nufa zuciya ba daɗi. Ana bata san abin da take ji a zuciyarta ya yi ƙarfin da zai saka ta rasa sukunin zuciya ba, sai da ta ji kamar damshin hawaye a saman fuskarta, a hankali ta miƙa hannunta zuwa ga zagayayyiyar fuskar tata, ba hawayen bane domin ƙarfin abin bai kai girman da zai saka ta zubar da hawaye a banza ba. Amma me ya sa yake cin zuciyarta har haka? Bata sani ba, amma hakan baya rasa nasaba da yadda aka aibata mata uba a gabanta. "Me ya sa zan ji zafi har haka? Me ya sa zan ɗauki lamuran Daada na ƙwarzafi raina da shi na hana zuciyata sukuni?" Ita da zuciyarta suke wannan taɗin, tana cilla ƙafafuwanta ba tare data san inda suke samun masauki ba, ta ji zafi tabbas. Ta kuma ji raɗaɗi tabbas. Bata san ta ƙarasu ƙofar gidansu ba, sai data na ƙoƙarin shigewa ta yi gaba ba tare data sani ba ta ji an yi saurin riƙo hannunta. Bata firgita ba, saboda dakkakiyar zuciyarta sometimes, rigima kuma a jininta kawai take. "Daga ina? Yaushe kika fara haka?" Idanunta ta watsa a saman fuskar Jadid ta dube shi na wani lokaci kafin ta tabbatar a ƙofar gida take ta raɓa ta gefensa ta shige. Wani abu na musamman dake sanyaya zuriyar Ana ganin abin data fi so a rayuwa. Yanzu ma tana ɗora idanunta akan Innti da Iftihal ta ji ta nemi dukkan damuwar data cushe mata a tsakiyar ƙirji ta rasa. Iftihal ce ta kalle ta kafin ta ce "Mahaɗita ko dai mu tattara ki kawai ki koma gidansu Yaa Sam?" "Da kin duba mini, ko babu komai zan huta da cin arne da kwat. Ya kike Mahaɗita?" Iftihal ta ce "Ba lafiya ba, bani da lafiya" A ɗan rikice Ana ta dafe ƙirjinta saboda wani azababben bugawa da ya yi mata, wani tsoro ya lulluɓe ilahirin ƙofofin zuciyarta, idan ba ta yi ƙarya ba, har wani zazzaɓi ta ji ya fara saukar mata. "Mene ya same ki? Me kike so? Ina ke miki ciwo, mene damuwar?" Yadda ta rikice kawai Iftihal ke kallo tana jin wata sabuwar soyayyar abokiyar haihuwar tata yana sake samun gurbi na musamman a zuciyarta. Idanunta ya kawo ruwan hawaye ta sake tabbatar idan bata raye Ana zata samun bugawar zuciya, yanzu ma idanunta ya zama kamar ba nata ba, jikinta sai faman rawa da kakkarwa yake yi. "Ayshatul-Haleeym!" Innti ta kira sunanta da ƙarfi tana jijjigata, amma tuni ta fara rasa nutsuwarta daidai lokacin Babban yaya ya shigo cikin gidan shi da Jadeed tsayawa suka yi, Jaheed ya dubi Ifti, Babban yaya kuma Ana da ake jijjigawa ya zubawa kasalallun idanunsa masu kyau. "Shalelen Innti... Ana.... Ayshatu....." Innti ta faɗa a gigice. "Babban yaya duba mini ita, Yaa Jadid ɗebo mini ruwa me sanyi a randa ka ji" A kiɗime Jadid ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ko dai aljanu ne suka shaƙe mata wuya, ko ta yi faɗa da wasu ne?" Bata iya bashi amsa ba, gabaɗaya ta rungumeta a jikinta bata taɓa ganin girman yaranta, Iftifal fashewa da kuka ta yi tare da durƙushewa a wajan ta riƙe hannun Ana gam a cikin nata, cikin kuka take faɗin "Ki yafe mini mahaɗita, ba zan sake ba, ba zan kuma yi miki irin wannan wasan da zuciyarki zata kasa ɗauka ba, ki yi haƙuri" sai a lokacin Babban yaya ya fahimci abin da yake faruwa da kuma dalilin shigar Ana halin da take ciki, wato a kowacce haihuwar tagwaye akan samu mugu ɗaya da zai dinga gallazawa ɗayan, Iftihal ba mugunta take wa Ana ba, amma tana raunata zuciyar yarinyar da soyayyarta, jin cewa Ifti babu lafiya ya saka Ana fita daga hayyacinta. A hankali ya durƙusa dab da fuskar Ana ya miƙa yatsun hannunsa guda biyu na tsakiyar ya shafi fuskarta kaɗan kafin a hankali ya sauke a gefen ƙirjinta ya danna a nutse. Ajjiyar zuciya ta sauke me nauyi jikinta ya saki a jikin Innti bata motsa ba, bacci ya ɗauke ta a nan jikin mahafiyarsu. Innti ta dubi Iftihal ta ce "Iftihal.... "Na'am, Innti" "Shin ba ki aminta da son da Ana ke miki bane? Ba ki yarda cewa zata iya rasa ranta idan bakya duniya ba? Ba ki yarda ba ko?" "Na yarda Innti, wasa nake mata" Innti ta ce "Wasa? Wasa da rayuwarta ko zuciyarta? Bari na faɗa miki za ki iya yi mata wannan wasan, wasan da har abada zai iya rabaki da ita, kar ki kuma na faɗa miki" Cikin kuka da murya a raunace har ta fara dashewa ta ce "Na tuna Innti, ki yafe mini don Allah ba zan kuma ba in sha Allah" "Shikenan, Allah Ya yi muku albarka gabaɗaya, Ubangiji Ya duba gabanku da bayanku ya tsare kima da mutuncinku" "Amin" Iftihal da Jadid suka amsa. Babban yaya ɗaki ya shige abin shi ba tare da ya ce komai ba, Jadid ya yi shiru ya zubawa Innti idanunsa kamar me buƙatar wani abu. Suna ta zaune har Ana ta farka, ko data farko ta manta da abin da ya faru ta ce "Gaskiya daga yau kullum a cinyarki zan dinga bacci uwata, kin ji laushi? Ubangiji Ya yi mini arziƙin da zan saka ki ji daɗi ki huta ki daina jin tuwo kwata-kwata, ki ce amin" Girgiza kai kawai Innti ta yi tana amsawa da "Amin" a zuciyarta. A hankali ta ja idanunta ta lumshe tana jin fresh air ɗin wajan na sake saukar mata da nutsuwa, abubuwa da yawa take son yin tunani akan su, na farko yadda zata rayu har abada ita da Innti da Iftihal, na biyu tunanin rayuwar mutanen da take gani a cikin baccinta, ta rasa dalilin da ya sa take mafarki dasu, ta rasa su waye, bata kuma iya hango haɗinta dasu ba. “MAMAA? UW?” ta furta a sanyaye domin sai a lokacin ma sunayen ya faɗo mata. Abu na uku alaƙarta da Daada ta rasa tudun dafawa domin har yanzu ta kasa gasgata cewa, shi ɗin mahafinsu ne, bai dace da uba ba sam. Tattara maganar ta yi waje guda ta watsar. Ta juya ta kalli Innti ta kalli Iftihal sai ta ce "Ni dai ku dinga saka ni a addu'a, Allah Ya bani miji kyakkyawa ko da maye ne shi" Ta yi maganar hankalinta kwance. Iftihal murmushi kawai ta yi. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Innti ta zabga uban salati tana riƙe haɓa. Kafin ta ce "Ubangiji Ya miki zaɓi da mafi alheri a rayuwarki daku duka gabaɗaya ya nisanta ku daga abin ƙi, Allah Ya rabaku da auren maye. Maita babu daɗi" Ana ta yi shiru saboda tuna dramar ɗazo da aka yi da aka ce mata mayya. Jadid ya ce "Daman gata nan kamar kazar mayu saboda rashin kuzari, tatsa ɗaya zai mata ya suɗe abin shi, ji jaraba wai maye?" Idanunta a lumshe ta ce "Allah idan na auri mummunan miji zan iya haɗiyar zuciya, ina son abu me kyau, ina son kyakkyawan miji ko Aljani ne...," bata ƙarasa faɗa ba Babban yaya ya fito yana kallon ta, itama kallon shi ta yi ƙwayar idanunsu suka shiga cikin na juna ya ɗauke kai yana yin waje abin shi. "Innti kin gama ɗinkin atamfar nan?" "Wanne ɗinki? Abin duniya duk ya daman bayan kin ce ya yi kyau kin fita daga nan na rasa meke faruwa dani, komai ya lalace gashi yanzu atamfar jama'a ta yi kaca-kaca" Miƙewa ta yi ta nufi inda taga atamfar tana ɗauka ta tuntsire da dariya ta ce "Daman abu ya fiya kyau masifa ne, Allah ya kyauta" *** Bayan ya kammala gyarawa wani wayarsa da ta ci screen ya ajjiye sannu a hankali ya zubawa gefe guda idanu, ya ɗan girgiza kai sai asalin kamannin da yake dashi na zubi da labarabawa suka fara bayyana, yana tsoron wannan sauyin yanayin a cikin jama'a kar su dinga gudunsa, shi kan shi bai san meke faruwa da rayuwarsa ba, tsakanin baƙar fatar da farar fatarsa me sheƙi da ɗaukan idanu wacece asalin halittarsa? Ya miƙe a hankali ya shiga takawa ya ƙarasa jigin bango madubin dake maƙale ya kalla, daya kalli fuskarsa shi da kan shi ya ji tsoron ace shine wannan domin kyawun fuskar ya yi masa yawa, kyawun da zai zame masa bala'i ne. Waye shi idan ya ɗauke cewa shi Babban yaya ne? Ya tattara maganar ya watsar yaje ya zauna saboda gajiya da yunwa tunda uban gidan nasa ko kwabo har yanzu bai bashi ba. Bacci ne ya ɗauke shi a wajan. Babu jimawa ya ji iska na kaɗa shi, sanyin ruwa na ratsa jikinsa ga ƙarar tsuntsaye na tashi alamar yana cikin daji ne. Ya buɗe idanun, bai san alaƙar da yake da ita a wannan wajan ba, bai san me ya sa yake zuwa nan ɗin ba. Numfashi ya ji yana sauka a fuskarsa kafin ya gama buɗe idanunsa ya ji siriyar murya ta shiga kunnensa an ce. "Kaɗo.... Ya yi saurin janye fuskarsa, sai ta kuma matso da tata har goshinta na sauka a nasa, ta washe fararan haƙoranta masu kyau ta ce "Kai kaɗo ne ko? Kai kyakkywa ne zaka zo a yi mana aure irin wanda ake yi?" Nan ma bai magana ba sai kallon ta kawai da yake yi, ya zame kaɗan ya yunƙura ya tashi sai a lokacin yaga ɗanyen barkonon data yatsar a wajan. "Wayyo Allah, kana da kyau kai kyakkywa ne, amma baka da lafiya shi ya sa baka da kuzari" Ya yi mata shiru. "Me kake yi a nan? Kai ma ɗan gidan Moddibo ne? Ina naggenka? Ina Innarka ta mutu ko tana raye? Kuma kai ma kana ganin kayan cikin mutane? Mutum nawa ka taɓa ci? Ka taɓa fita maitar dare? Wa aka taɓa cewa ka kawo aci? Kai kaɗai kake kama kurwa ko haɗin gwiwa kuke yi?" Tambaya take ta yi masa daga wannan zuwa wannan, shi kuma ya juya mata baya. Ɗan zabura ya yi kaɗan jin ta cakume shi sai ta yi baya. "Innalillahi!" Ta lumshe idanunta "Jikinka laushi kamar burudin da Saleh yake bani idan ya taɓa ƙirjina" Sannu a hankali ya juya ya kalle ta, don tsayi tana da tsayi amma bata kai Anarsa tsayi ba, kyau kuma bai san waye yafi wani ba, wannan akwai surutu kamar aku, ana kuma maganarta a sanyaye take kuma babu ƙuruciya a tattare da Ana magana cikin hikima take yi. Ana ta zama budurwa completely, wannan yanzu take girman. "Baffana makaho ne, amma sarai da idanunsa Yaaye ce ta makantar dashi saboda ta kasa cinye shi, ta ɗora masa lalura ita a tunaninta duk ban sani ba, ta manta muddin mayu suka kama mutum idan ɗan'uwansa ya gani yana gane tambarin mayen" ganin ko tari bai ba, ya saka jikinta yin sanyi ta ce "Laa kaɗon baya magana Allah Sarki" Ta zuba tagumi ta tallafi haɓarta. "Ka dinga shan ruwa sosai zaka samu kuzari da ruwan zogale ka saka madara a ciki *** BRIGHT FM REDIO. Ta gefen ido ya sake watsawa Ahlam wani irin miskilin kallo wanda yake nuna kin rainawa kan ki hankali. Ita kam gabaɗaya jikinta wani irin rawa yake yi yana ƙoƙarin bada ita, da yadda tsoron MD ɗin ya bayyana ƙarara akan fuskarta, ta kasa ɗago kai ta kalle shi, gashi zuwa yanzu tasan Yussy ta fara karanta labaran, gashi bata son ta saka auren matar can a cikin matsala. A hankali ta ɗago kai kamar zata kalli fuskar MD ɗin sai kuma ta yi saurin mayar da idanunta zuwa gefensa, ta shiga kame jikinta da tattauna laɓɓanta wanda ta gama jiƙasu da yawon bakinta ba tare data sani ba. A iya tsayin lokacin data shafe a BRIGHT FM ɗin bata taɓa kallon cikakkiyar fuskarsa ba, bata da wani dalilin da zata kama wanda zai zama hujjar ƙin kallon fuskar ta MD. Kawai dai tana da yaƙinin bata da alaƙa dashi da dukkan abin da ya mallaka a ciki har da fuskar da zuwa ke janta wajan kala, ko zata iya yango bambancin da yake tsakaninsa da sauran maza, wanda ya saka shi irin wannan ƙifaɗin da jin kai har haka. MD da yake tsaye kamar an dasa shi wayarsa kawai yake dannawa, yatsunne kawai suke operating wayar, amma duk wani motsi na Ahlam yana ankare dashi, tare da sanya su cikin ma'adanan sirrin shi. "Don Allah....," Ta kasa yin maganar a lokacin daya ɗago idanunsa ya watsa a saman fuskarta, jiran abin da zata ce yake yi, sai kawai yaga ta fashe da kuka ta haɗe kai da jikin ƙofar Studio ɗin jikinta na wani irin ɓari tana girgiza kai, a firgice kuma ta juya tare da zubewa a wajan ta haɗe hannunta biyu waje guda ta ce "Sir don Allah, don girman ka tsayar da Yussy daga karanta labaran nan, na shiga uku idan ta karanta na kaɗe har ganye na" da ƙyar take yin maganar ma. "Bana son matar nan ta rasa igiyar aurenta akan son raina, akan son ɗaukakata don...," "Baby mene haka? Get up please" Anees ya furta yana ƙarasawa wajan idanunsa ya rine saboda ɓacin rai da ganin yadda Ahlam ta durƙusa a gaban MD ta zama wulaƙantacciya a wajan mara gata. Girgiza kai ta yi ta ce "Ya zan yi Anees?" "Wataƙila idan na durƙusa za'a fi fahimtata" Anees ya ce "Ba dole sai kowa ya fahimci ki ba baby, saka labarin nan baya nufin tsayuwar rayuwarki, wani ko wata basu isa su yi miki abin da Ubangiji bai ƙaddara ba" Hannu Anees ya miƙa zai ɗagota ganin yadda shanyayyen hannunta yake ta rawa shi kaɗai, shi dai sosai yake jin tausayin Ahlam har ƙasan zuciyarsa ba tare daya san wani dalili ba. Kafin ya saka hannunsa Md ya yi baya kaɗan da waya kare a kunnunsa Ya ce "Idan room zaka kama mata a hotel bani da damuwa, Bright Fm bai zama dandalin ƴan iska na mamajos ba Please" Daga Anees har Ahlam wani abu suka ji ya tokare musu a maƙoshi ya tsaya waje guda, wani irin duhu kawai Ahlam take gani, ta rasa dalilin daya saka MD yake mata kallon ƴar iska ko kuma me buɗewar ido, bata san abin daya taka ba da yake jin ko a gaban Ubangiji zai iya maimaita wannan kalaman masu muni a gare ta dama rayuwarta gabaɗaya. Ko dai ya taɓa kamata tana aikata abin da ba shikenan ba? Ko wani namijin ya taɓa gani ya rungumeta, ko ya sumbace ta, ko kuma kamata ya taɓa yi turmi da taɓarya? Tana buƙatar sanin dalilin wannan ƙazafin wanda yake shirin rusa mata dukkan farincikin rayuwarta. Mijinta take wa tanadin kanta, jikinta na wanda Allah ya bawa ita ne matsayin mata Da ƙyar ta miƙe tsaye, kanta a ƙasa daidai nan Yussy ta fito daga Studio kuma ya yi wa'adi da lokacin da HR ya ƙarasu wajan. HR ya ce "Na je office ɗinka baka nan, so you're here ashe. Na ji kana kirana?" "HR daga yau kar ka sake ɗaukar mana shirmammun mutane a gidan rediyon nan, waɗanda basu san komai ba sai shirme da tsoro, wanda basu da wani amfani sam" Cikin girmamawa HR ya ce "In sha Allah" MD ya juya a hankali, Yussy ma ta yi wa Ahlam wani irin ƙasƙantaccen kallo kafin da sauri tabi bayan MD tana riƙe masa hannu da faɗin "MD yaushe aka mayar da taron?" Ahlam tabi bayansu da kallo, ta dubi yadda shafaffen ƙugun Yussy ke mannewa ita a dole murguɗa shi take yi, sannu a hankali kuma ganinta ya sauka akan hannun Yussy da yake cikin na MD. "Ɗan iska akwai" Ahlam ta furta a sanyaye tana jin cewa daman ɗan iska ne kawai ke yi wa wasu kallon ƴan iska. Da ƙyar Anees ya rarrashe ta suka nufi office ɗinsa tana ta murmushi tare da juya manyan idanunta, bayan sun shiga office ɗin ya ja mata kujera ta zauna. "Anees" "Na'am baby" A hankali ta ce "Anees ina buƙatar ɗaukaka a aikin jarida kota wacce hanya ce, ina buƙatar na samu ɗaukaka ko hakan zai saka Yussy ta daina yi mini kallon da take yi mini na wacce ba zata iya ba, ina son nunawa duniya nakasa ba zata taɓa zama kasawa ba" ta ƙare maganar a hankali tana yin ƙasa da kanta saboda kallon da Anees yake mata. Shiru ne ya biyo baya, tun tana jiran ta ji amsar da Anees zai bata har ta gaji ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita tana ƙoƙarin buɗewa Ta ji ya ce "Ahlam" Cak ta tsaya kuma bata juya ba, tana jin sanda ya miƙe ya tsaya a bayanta ya ce "Wata ɗaukakar masifa ce, ki yi addu'ar samun abin da yafi zame miki alheri. Aikin jarida ba abu bane me sauƙi, yanzu kika fara ba balle ki fahimci me nake son faɗa miki ba. Amma ɗaukaka ga ɗiya mace hatsari, kar ki damu da abin da Yussy ke miki, ki mata uzuri na wani lokaci kin ji?" A hankali ta jinjina kai ta ce "Thank you Anees" "Bari na ajjiye ki a hanya nima tafiya zan" Office ɗin ya rufe fuska fito tare, tunda ta fito Baba driver yake mata kirari irin wanda ya saba. "Allah Ya taimaki Golden voice, maƙiyanki fadawanki an buga dake an barki sarauniyar murya ta Bright Fm gabaɗaya" Ta murmusa ta ce "Duk ni kaɗai Bana?" "Haka za'a ganki a bar ki, bangon sigari kowa ya jingina dake sai ya lasa Wallahi" Anees ne ya ciro walet ɗinsa ya ce "Wannan kirarin ya zama dole na biya" Jiki na rawa Baba driver ya saka hannu ya amshi kuɗin yana faɗin "Sarauniya sai da Sarki, Allah Ya baka Golden voice ka ji" "Amin Ya Allah, Amin Ya rabb" Anees ya furta cikin sauri yana lumshe idanunsa, cikin sauri Ahlam ta kalle shi sai ya yi saurin kashe mata ido ya yi waje. Ta saman bene MD ya hango shigar Ahlam cikin motar Anees har suka fice sai kawai yaja siririn tsaki yana mai da sunglasses ɗinsa zuwa saman fuskarsa. *** Ya murmusa kaɗan ya ce "Giɗaɗo ikon Allah masu Gwamantin da kan su, to ya ake ciki ne?" Wanda aka kira da Giɗaɗo ya gyara zaman shi a nutse fuska a kame cike da kwarjini ya ce. "Barde, Gwamnati ai taku ce" Barde ya jinjina kai yana faɗin "Shi ya sa naga nine na hannun daman Gwamna. Na ji abin arziƙi na offers data fito daga hukumar Ma'aikata ta Jiha, kuma dai kai ne Kwamishinan ilimi, dole na yi kamun ƙafa da akai" Giɗaɗo ya buɗe fararan idanunsa ta cikin glasses ya kalli Barde kamar ba zai magana ba, sai ya ce "Mun tattauna da Indabawa jiya, an ware naku da za ku bawa iya family ɗinku, Offer ɗin me kyau ce, hatta salary duk da ba'a kammala yanke nawa za'a bada ba. Waɗanda za'a bawa Allowance ma daban suke. Don haka za'a dinga siyar da Offer ɗin akan dubu ɗari uku, ba zamu rabawa yaran talakawa a aikin banza ba, ba sanin darajar ilimin sukai ba duk sune ƴan iskan gari" Barde ya ce "Allah mutumina? Shi ya sa nake yinka ba, masu Gwamanati da kan su" Giɗaɗo ya miƙe tsaye yana gyara zaman suit ɗin jikinsa wacce ta yi masa kyau sosai. "You're not nice Barde. Zuwa anjima zan shige Qatar dani da Madam, wai tana buƙatar hutun sati biyu ne kawai a can" "Dole Madam ta huta da yawa, kuɗi yazo Alhaji" taɓe baki Giɗaɗo ya yi, mutum ne me ji da kan shi uwa uba ilimi da izza professor matakin ƙarshe kuma Dr. Suka ɗan fito harabar babban wajan. Barde ya ce "Yanzu airport zaka shige kenan Giɗaɗo?" "Nop, ina da meeting da Kwamishinar kuɗi, domin tattauna batun gina sabbin makarantu a jihar. 2 weeks zan yi na dawo akwai zama a Executive Council Majalisar zartawa" Sallama suka yi ya shiga bawan haɗaɗɗiyar motarsa driver ya ja shi. *** Tsoro ya hana Batty komawa gida saboda bata san wanne irin hukunci za ta yi mata ba na zuwa gaɓar kogi da take yi, tana tafe tare da wawwaro idanunta hannunta riƙe da sanda jikin nan babu kayan arziƙi sai kayan Fulanin dake jikin, kanta a buɗe babu kallabi, gashi dare tuni ya kawo kai. Cikowar mutane ta gani ga kiɗe-kiɗe na tashi akwai samari maza da mata da kuma ƙananun yara, cikin sauri ta washe jerarrun fararen haƙoranta cikin jin daɗi da nishaɗi ta ƙarasa wajan, wasu Ƴan'mata ne suke rawa a tsakiya ana musu kiɗa ga wasu samari na yi musu liƙi, Batty ta shiga girgiɗa kai saboda bata taɓa jin nishaɗi da kiɗa irin wannan ba. Wuf ta faki idanun jama'a ta shige wajan tare da kutsawa tsakiyar matan dake rawa, rawa ta shiga yi tana girgiza tare da yin fari da idanunta da wani irin salo yadda take rawar kamar wacce ta saba da yin rawar dandali. Kafin wani lokaci matasan rugar Biya sun rufe Batty ana yi mata liƙi ta ko'ina. Mado, ɗan gidan Moddibo shugaban rugar shine ya tako a hankali shi da abokansa ya tsaya a gaban Batty yana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, yarinya ce sosai akan yadda ya san matan birni, amma a rugar Biya tuni ta isa shiga ɗakin miji. Tunda da yawansu a gidan miji suke irgar dangi, duk da itama bashi da tabbaci ko ta fara. Kuɗi ya fara watsa mata a jiki, Batty ta ɗauka yin rawar abin arziƙi ce ta shiga banƙaro ƙirji ana malƙwasa har Mado ya gama yi mata liƙin. Cak ta tsaya daga rawar saboda ƙwayar idanunta daya hango mata kasasshiyar kazar daya gama ci ko gama narkewa a cikinsa ba ta yi ba, ta rufe ido ta buɗe tana sake hango komai da yake cikinsa har da fura da nonon daya sha. Cikin sauri ta biyo bayansa yana cewa "Kaɗo, kaɗo hai kaɗo" Mado ya tsaya a inda yake yar Batty ta ƙarasu wajan tana zuwa wajan ta ce masa "Nima ka bani kazar da kaci" Da mamaki yake bin bakin maganar da kallo na rashin fahimta. "Har da fura da Nonon" Ta sake kashe shi da mamaki da faɗar Fura da nono. Mado ya numfasa ya ce "To" "Amma sai gobe ko?" Ta girgiza kai ta ce "A'a yunwa nake ji, tun safe ban ci abinci ba, ko kazar ce ka bani" Ya ce "Ya akai kika san na ci naman kaza?" Dariya ta ƙyalƙyala ta ce "Wai ma, gata nan ina kallonta gwanin sha'awa ka siya mini" Ya share maganarta, domin a shirme ya ɗauki zancen Batty babu mamaki taga lokacin da yake ci ne, tunda a nan ya siya ɗin. "Me kike da ba ki ci abinci ba har kawo shigowar dare?" Ta yi shiru sai kuma tadai "Yau aka kawo ni nan gidan Ƙanin Baffana, kuma matansa basu bani abinci ba, ina can baƙin kogi ina wasa ni ɗaya da ruwa sai barkono ɗanye da na ci in faɗa maka" Mado ya buɗe ido ya ce "Subuhana, harkokin kuma?" Sai kawai ta jinjina masa kai tana murmushi. "To, ina ne garinku?" "Rugar Yari" "Me ya sa aka kawo ki nan?" A hankali ta ce "cewa akai wani kaɗo yana taɓa mini ƙirji wai nono ya fito mini" Da wani irin mamaki da tashin hankalin surutun yarinyar Mado ya buɗe baki ya rasa ma me zai ce, tashin farko tsoro maganar ya dinga bashi, yanzu kuma ita ɗince take bashi tsoron ba wani ba. "Kuma da gaske ne?" Ta juya idanunta na rashin fahimta Ta ce "Me ɗin?" "Shi kaɗon ya taɓa?" Ta jinjina masa kai. Ya ɗaure fuska babu wasa ya ce "Allah sai ya saki a wuta yarinya, kike buɗe masa jikinki ko? To me ya taɓa ɗin? Me kike ji?" Kai tsaye ta ce "Nono ya taɓa, zafi na ji" Mado ji ya yi zufa na yanko masa ta ko'ina a jikinsa. Batty ta ce "Kai ma idan sai ka taɓa zaka bani kazar na buɗe ka taɓa kaɗan, sai ka siya mini abinci shima kaɗon abinci yake siya mini, saboda a gida ba'a bani komai. Bana cin komai sai duka da azabar zagi da kiwo, shine shi kuma yake.....," hannu ya ɗaga mata fuska a ɗaure ya ce "Ya isa" Ya ciro kuɗi ya bata ya ce "Duk abin da kike so ki mini magana amma duk sanda na ji labarin kin sake buɗe jikinki sai na yanka ki" Batty ji ta yi kamar fitsari na bin ƙafafuwanta, kisa? Irin kisan da aka yi wa Innarta? Me ta yi masa? Ko shima me sace nagge ne? Jikinta ya yi sanyi ta amshi kuɗin shi kuma ya yi gaba abin shi. Tsire ta siya me zafi ta ci ta sha ruwa kafin ta ɗauki hanyar gida hankali ƙawance. Sanda ta shiga a waje ta same su Kulu nata kuka saboda jikin yaronta da ya yi zafi sosai baya ko numfashi, an rasa abin da yake damunsa Sadiatu sai banbaki take yi amma taƙi shiru. Gana na zaune gefe tana yin kaɗin Audiga. Babu wanda ya kula da Batty har ta shige ƴar bukkar da aka bata tana shiga ta yi kwanciyar babu jimawa bacci ya ɗauke ta me nauyi ko sallah ba ta yi ba. Cikin bacci ta fara wani irin mugun mafarki wanda bata taɓa yin irinsa ba, ita sam bata mafarki. Wani waje ne babba, yana kama da gari gudu ko masarauta, bata taɓa ganin girman gari da jama'ar garin da suke wata kala ba irin waɗannan mutanen da take gani a gabanta. Bata san mene ya kawo ta garin ba, tana cikin tafiya kawai ta ji an kamata an ɗaure da sarƙa an sanyata a cikin jerin matan da aka kama, sai muzurai take wani babban tashin hankalin ma, ganin yadda ake kwantar da mace a tsakiyar filin wajan ana rabata da budurcinta su yi mata kaca-kaca, kamar masu neman wani abu jikin matan, idan suka amshi budurcin nan take suke kashe yarinya su cillata ruwa ko a bawa dabbobin da suke wajan su cinye. Batty ji ta yi fitsari na bin ƙafafuwanta, ita bata san ma'anar yadda ake danne mace ƙato ya hau kanta ba, kuma namiji ɗaya ne yake yin wannan ta'asar yadda yarinya ke kuka da ihu yake bawa Batty tabbacin ko ma me ake yi tabbas abu ne me ciwo da azaba. Ta fashe da wani irin matsananci kuka tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige ko kuma ta mutu kafin azo kanta. Mutumin ne ya ce "Ko duka matan duniya za su ƙare ba za mu saurara sai UWA MAMAA ta bayyana ta cece mu daga halaka, sai ABAR BAUTA ta bayyana" Jin abin da ya ce ya saka Batty fashewa da kuka da ƙarfi ta ce "Do Allah idan akwai ɗiyar data san sunanta UWA MAMAA ta fito, walle bana son abin nan da ake yi kowa" Daga daga cikin dakarun wajan ya zube a ƙasa yana ɗaga hannu ya ce "Ya shugabana shin babu wata alama da za'a iya haska mana yadda za mu UWA cikin sauƙi haka?" "Akwai" "Sanar dani Shugabana" Ya shaƙi iskar wajan, yana wani irin ɗaci da raɗaɗi da yake cin zuciyarsa, ya dubi yarinyar dake kwance cikin jini har yarinya idan ya lissafa ya lalata budurcinta mata kusan arba'in kenan amma har yanzu haƙarsa bata cimma ruwa ba, da ƙyar ya ce "Akwai wasali UKU da aka bamu na farkon sunanta, a ciki ɗaya akwai wasalin daya fara da sunan UWA MAMAA shine kawai" Farinciki ya kama duka jama'ar wajan. "Ka bamu sunayen wasalin?" A hankali cikin taƙama ya ce "Akwai A akwai F da H" Ajjiyar zuciya Batty ta sauke jin babu wani wasali da ya yi iri ɗaya da BA tunda sunanta BATTY ne sai ta samu nutsuwar zuciya. A haka aka dinga tambayar sunansa aka dinga ware wanda farkon sunansu ya yi ɗaya, a nan ne Batty ta hango wata mata a cikin babban keji da ƙaton ciki a jikinta tana kuka da ihu tana kiran Batty tare da yi mata alama ta gudu ko kuma dai tazo ta taimaka mata. Daidai nan kuma layi yazo kan Batty. "Ya sunanki?" Ta ce "Batty" A hankali ya maimaita sunan "Batty" Tun kafin ya yi magana ta ce "Amma na gaskiya Fatima ne kuma mayya ce ni.... *H I Y A A M* Page 6: Haunted by Blood Bright pens Yota/001 “You are a blessing, and I pray happiness never leaves your side.” Nazeefah Sabo Nashe A firgice ta farka daga mummunan mafarkin data afka a cikinsa, wani irin nishi take yi numfashinta yana yin sama ƙirjinta na ɗagawa, kaf-kaf kuma haka duka ilahirin jikinta ya shiga rawa da kakkarwa zufa sai yanko mata take yi, ta kasa buɗe idanunta saboda tsoran daya gama gigita mata nutsuwarta tunanin abin da ya faru da inda taga kanta ya tsayar da tunanin ƙwaƙwalwar Batty cak waje guda. Ta jima a haka kafin ta saki wata iriyar ƙara me firgitarwa tana yin baya tare da kakkare jikinta tana ganin kamar mutanen zuwa za su yi su kamata. "Ƙarya nake yi, ba sunana Fatima ba" Gabaɗaya ta ruɗe ta fita daga hayyacinta "Bani ce wacce kuke nema ba, don Allah kar ku bari ya yi mini abin nan bani ce ba" da wani irin sauri aka ɗaga assabarin bukkar tare da shigowa ciki, Lami ce ta haske fuskar Batty sai taga kamar ba Batty ɗin ba, lokaci guda ta sauya ga fuskarta ta yi jajur sumar kanta ta kunce ta hargitse kamar mahaukaciya sai ihu take yi tana karta faratanta a jikinta jini na fita a duk inda ta saka farcen hannun nata haka jini yake fitowa. Baya Lami ta yi da sauri ta ce “Kai ni kam na shiga uku, mun lalace ƙwarai!” Dikko ya girgiza kai cike da damuwa ya ce "Batty, kai yaro Batty meke damunka?" Ya yi furucin cikin sarƙewar murya domin shi kan shi jikinsa rawa yake yi saboda tsoron yanayin yarinyar daya gama gitta masa zuciya. A hankali ta ɗago kanta tare da buɗe rinannun idanunta, ganin yadda idanun ya yi wani irin jaa ya firfito waje kamar bana mutane ba, ya saka cikin Lami juyawa ta yi saurin saka hannunta ta dafe cikin ta ce "Ko dai Batty nada iska Dikko?" "Bana jin haka daga gare ta Lami" Sai ya yi gaba daidai inda Batty ke durƙushe shima ya durƙusa a wajan ya saka hannunsa ya kama hannunta cike da nutsuwa da kulawa ya ce "Mene ya samu ɗiyar nan?" Baki ta buɗe za ta yi magana sai suka ji kukan mage ya cika ɗakin, wani irin kuka mara daɗin ji wani amon sauti na fita, tuni fitsari ya cika wandon Lami jikinta sai rawar ɗari yake yi. "Yi magana Batty menene?" Wannan karon ma madadin sautin muryar Batty ɗin ya fita sai kukan mage ya sake karaɗe wajan, kafin kuma tif su ji ƙarar saukar abu a gadon bayan Dikko, wani irin hantsilawa Lami ta yi tare da yin allandugure ta kifa, zanin jikinta ya yi gefe guda bata tsaya ɗauka ba ta yi waje fitsari na bin cinyoyinta, a hanya ta haɗu da Sadiatu data fito da sauri tana kiran Dikko ta faɗa masa cewa Allah Ya yi wa yaron Kulu rasuwa, suna haɗuwa da Sadiatu a hanya ta yi gefe zata shige ɗakinta. Sadiatu ta ce "Lami yaron Kulu ya koma" Kafin Lami ta yi magana sun ji yo ihun Dikko daga cikin bukkar Batty wani tsalle suka yi tare da rungume juna suna salati da ƙarfi, suna rungume da juna Dikko ya fito a guje yana faɗin ya shiga uku zata kashe shi ta cinye masa hannu, tun kafin ya ƙarasa fitowa Lami da Sadiatu sun rugasa ƙarasawa cikin bukkarsa kafin ya ƙarasu sun rufe yana ganin haka ya yi kwana ya nufi ɗakin Kulu wacce take rusa kukan rashin jaririnta. Yana zuwa ya tarar itama ta rufe ɗakin nata, sai kawai ya fashe da kuka ya kama bukkar Kulu ya haye saman bukkar, yana hawa kamar an ce ya juya suka yi ido huɗu da wata baƙar mage jibgegiyya da ita idanunta jajur sai haki take yi tana zaro harshe waje. Cak numfashin Dikko ya tsaya a ƙirjinsa daga nan bai sake sanin abin da yake faruwa ba. Dikko na fita daga bukkar Batty sai ta yi saurin miƙewa tsaye idanunta rufe ta fito farfajiyar gidan shiru babu kowa, sannu a hankali ta dinga takawa har ta isa banɗaki ganin babu me ganinta ya saka ta tsugunawa waje guda ta cure jikinta, tana daga durƙushen ta fara wata kalar rawa da girgiza ta kafe yatsun ƙafarta a ƙasa tana kartar ƙasa dasu, a hankali halittar jikinta ya fara sauyawa zuwa suffar mage bata ɗauki lokaci ba, ta koma wata baƙar mage me jajayen idanun ta yi tsalle tare da haure kewayen banɗakin ta yi waje abin ta. Tafiya magen take yi hankali kwance da idanunta na huɗun take cin karo da kurwar jama'a dake yawo a duniya a cikin sakaliyar daren. Dake yawanci sai dare yayinda gangar jikin mutum ke kwance yana samun nutsuwa a wannan lokacin ne kuma kurwa take tashi ta shiga duniya ta dinga yawo, wannan dalilin ya saka idan ka haɗu da mutum a zahiri sai ka fara tunanin kamar ka san shi, kuma ka rasa inda ka taɓa ganinsa. Hakan ya faru ne dalilin kurwarku data haɗu da daddare a hanya. Wasu kuma na cewa Ruhi ne yake tashi yabar gangar jiki. Tunda Batty ta yi arba da Mado ta ji ranta ya biya, domin yana da kitse sosai jininsa da namansa masu kyau ne za su yi daɗi a baki. Wannan dalilin ya saka ta biyo dare ko za ta iya cimma burinta a wannan karon, wannan ne lokaci na farko da take jin ba zata iya haƙura da abin da take ji ba akan Mado ba. Har cikin gidan Moddibo ta kutsa kai cikin sa'a ta samu ɗakin Mado ta haye rufin ɗakin ta shiga rera masa kuka a cikin kunne mara daɗin ji saboda wani amo da yake fita a ciki "Mado... Mado... Mado..." Haka magen ta dinga kiran sunansa. A firgice Mado ya farka jin abin ya yi kamar a mafarki, ya zabura ya miƙe tsaye yana juyawa ya ci karo da Moddibo yana tsaye, Mado ya nufi wajan mahaifinsa yana faɗin "Baka ji ba?" Ya girgiza kai. "Baka ji kukan mage ba?" "Sunana na ji ana kira" Moddibo ya kalli Mado, a wannan lokacin da Mado ya nutsu zai iya hango ƙwayar idanun Batty a cikin idanun Moddibo zai fahimci Batty ce bawai mahaifin nasa ba. Moddibo ya miƙa hannu kamar zai riƙo Mado sai kawai ya kai hannun zuwa wuya Mado ya shaƙe masa wuya, Mado ganin Mahafinsa ne sai bai shiga ramawa ba, ya dinga kokawar ƙwace kan shi amma ya kasa, sai da aka kai Mado ƙasa baya ko motsi kafin Moddibo ya bar ɗakin daidai nan magen ta yi sauri ta fice daga cikin gidan gabaɗaya. Sama-sama ya ji ana kiran sunansa, gabaɗaya jama'ar gidan sun cika ɗakin Mado saboda ihun daya dinga yi, a hankali ya buɗe idanunsa sai yaga ƙannensa da sauran ƴan'uwansa, salatin da ya ji ana yi ne da tofin da ake yi masa da sautin muryar Moddibo ya saka Mado ƙoƙarin juyawa amma ya kasa saboda kasalar data saukar masa a jiki, ga wuyansa daya kumbura. Sai ya mayar da idanunsa ya lumshe. *** Bayan sallar issha'i duk suna zaune a ƙasan bishiyar da Iftihal ta shimfiɗa musu babbar tabarmar da suka saba zama akai wajan cin abinci da hira. Jadid da Jaheed na zaune suna hira sai Iftihal data gama jera musu kwanikan da aka kwasa tuwo da miya a ciki haɗe da babban tire da babban jug, Innti na saman darduba tana azkar. Jadid da yake ta jin sauyin yanayin da yake tabbatar masa ciwonsa zai tashi yaja idanuna ya lumshe a ƙasan zuciyarsa yana addu'ar Ubangiji ya sauƙaƙa masa wannan jarrabawa ya kawo masa da sauƙi. Babban yaya ne ya shigo ciki hannunsa ɗaya cikin aljihu ɗaya kuma riƙe da wayarsa farar Jallabiya ce a jikinsa wacce tabi fatar jikinsa ta kwanta yana da buɗaɗɗan ƙirji tsayi da faɗi a tsaye yake sosai, bai saka hula ba, sai kyakkyawar sumar kan shi data bi fatar wuyansa ta kwanta sai ɗaukan idanu take. Sun san dole zai yi sallama duk da basu ji ba, amma haka suka haɗa baki wajan amsawa. Ya nemi waje ya zauna. Iftihal ta ƙarasu inda yake ta durƙusa har ƙasa ta ce "Barka da dare Babban yaya, ya aiki?" A nutse ya dubi Iftihal kafin ya ɗan lumshe idanunsa, gargasar idanunsa suka sauka a fatar idanun nasa ya sakarwa Iftihal murmushi. Ta ce "Babban yaya za mu fara exam ta shiga Ss 1 a makaranta gobe" Ya zuba mata ido, sai ya miƙa hannunsa kaɗan ya riƙe nata ya ɗan matse kasan Alamar "I wish you all the best" Cikin jin daɗi ta ce "Thank you Babban yaya" Wajanta ta koma ta zauna, Babban yaya kuma idanunsa ya dinga juyawa yana neman inda zai hango Ana amma bata tsakar gidan. "Ƴan'matan Innti ana ta girma wasa-wasa daga secondary school sai University sai kuma aure, ina ka gane mini fuskar tagwaye a ɗakin miji? Musamman ke" ya ƙare maganar yana kallon Iftihal. Iftihal ta ce "Kai Yaa Jaheed, aure kuma?" Ya ce "Shi fa, ai kece bakya damun mu da maganar saurayi ko miji. Ita kuma tattabara kullum maganar Allah ya bata kyakkywan miji take yi koda maye ne ba ruwanta" "Ko kuma Aljani ba" cewar Jadid. Babban yaya ya watsa ƙwayar idanunsa a fuskar Jadid jin ya ce Alljani sai ya ɗauke kai. Innti data kammala azkar ta ce "Ƙuruciya dangin hauka, mazan yanzu ya ka ƙare dasu balle ka dinga yi wa kan ka mummunan alkaba'i? In sha Allah mazaje nagari Ubangiji zai muku tukuci dasu, kuma za ku samu mataye na gari da za su zame muku abin alfahari. Bani da addu'a wacce ta shige taku" "Muna godiya uwar arziƙi irin albarka, Allah Ya yi mana arziƙin da za ki ji daɗi a duniya Babarmu" Ta ce "Arziƙi na tsoran Allah in sha Allah" Iftifal ce ta ce "Innti shalele bata fito ba?" "Ƙyale Ana kin ji Iftihal miskilancin ne ya motsa tun ɗazo take ta ƙunci, kin san an yi tuwo" suka kwashe da dariya abin su. Ɓata fuska Iftihal ta yi ta ji itama abincin ya fita a kanta tunda mahaɗinta haka zata kwana da yunwa, gashi yau ta fahimci akwai abin da yake damun Innti taƙi nuna musu ne. "Innti nima na ƙoshi, bari na jira ki yi mana tatsuniya kawai kafin na kwanta" Innti ta zubawa Iftihal idanu kafin ta numfasa zuciya babu daɗi murya a karye ta ce "Ina son ku dinga haƙuri da abin da kuka samu kuke dashi a rayuwa, ni ba kowa ba, ban banda ajjiya ba, ba'a bani ba, bamu da wani gata ɗaya shige na Ubangiji. Ku dinga haƙuri da abin da kuka samu wasu suna nan a daren ko tuwon basu samu ba, mu hakan ni'ima ce a gare mu kin ji?" Iftihal ta jinjina kai ta ce "Kece gatanmu a nan duniya Innti, bamu da haufi akan kulawarki, ba kuma takaicin cin tuwon nake ba, ina samu kaina da rashin sukunin zuciya idan naga mahaɗita tana cikin damuwa ki yi haƙuri" "Mahaɗinki halinta dabanne da naki, ta fiki jarumta da taurin zuciya, ki barta da masifar son da take miki da Inntinta ta gargajiya, wannan soyayyar da take mana ita ce jarrabawarta" Murmushi Iftihal ta yi ta ce "Ban san ya zata yi ba idan na yi nisa da ita" Jaheed ya ce "In sha Allah brothers za ku aura tagwaye, da suka fito ciki guda suma" "I hope so bro..... Jadid ya ɗan yatsuna fuska ya ce "Turawan zamani, daman a Government school ana koyar turanci har haka Innti?" Innti ta ce “Education is a gift; muddin ɗalibi yana da fahimta, they can achieve anything. Kuma ya danganta da koyarwar Malami" "Innti ni dai kece Malamata, kowa yana jin daɗin koyarwarki kafin ki daina teaching" Abinci suka fara ci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da soyayyar juna, a ƙa'ida idan suna cin abinci babu wanda yake yin magana har su kammala. Yanzu ma haka ne, Babban yaya ne ya fara kammalawa ya ɗauki ruwa ya sha yana kammala sha Ifti ta ɗauka ta sha, sauran ma duk suka sha, bayan sun wanke hannunsu tas Ifti ta kwashe kayan ta ajjiye wajan da suke ajjiye marasa kyau. Akan shimfiɗar suke zaune ta fara yi musu tatsuniya kamar yadda ta saba me cike da hikayoyi da alamar, bayan ta kammala zata tambayi kowa abin da ya koya na darasi daga tatsuniyar. A hankali ta ɗaga kai ta kalle su, zuciyarta cike da fargaba da kuma soyayyar yaranta, an ce dukkan yaran da suka yi nasara a rayuwa, akwai jajirtattun iyaye a bayansu, ita a rayuwar yaranta ita kaɗai ce tsaye a bayansu, ita ce ta ɗauki responsibilities na uwa, kuma ta haɗa tana uba, ta sake ɗaukan ɗawainiyyar dangin uba, bata gajiya da dukkan ɗawainiyyar dake kanta ta sake haɗawa dana dangin uwa. Ta dubi hannunta babu komai sai farcen sosa, bata da komai sai dattin alijuhu. A ƙarƙashin tsoron daya cukukuye zuciyarta harɗa bauɗaɗɗan halin Ana, yarinya ce mafi soyowa a ranta, yarinyar da take matuƙar so fiye da sauran. A ƙarƙashin wannan son, ta koyi yadda zata sarrafa shi ba tare da mahaɗin haihuwarta ta gane ya haddasa mata damuwa ba, a madadin ta nuna soyayyar Ana a fili sai ta danne tsaf. Ita ce ma wace tafi Addabawa da faɗa a ciki. Gyaran murya ta yi gabaɗaya suka kalle ta, kaifafan idanunsu masu huda zuciyarta da ƙauna ne ke kallon ta. "Ina sake tuna muku ku ba kowa bane a duniya, ba kowa bane a dangin mahaifinku, ku iya talaucinku, ku ɗauke ranku tsam daga kan abun wani, ku yi rayuwa da abin da kuke dashi, watarana sai labarin... Ko ba yau ba, ko ba yanzu ba, za ku ji daɗi za ku zama kune masu ƙarfafa wasu da taimakon su, kun ji me ma ce ko?" Murmushi Jaheed ya yi cikin ladabi ya ce "Idan hadda ce wannan da tuni mun sauke mun sake ruɓanya saukar sau shurun masaƙi uwar arziƙi. Kalamanki kai tsaye umarni ne ba kawai wa'azi ba. Mu masu biyayya ne a gare ki, Allah Ya bamu ikon kulawa dake" nauyayyiyar ajjiyar zuciya Innti ta sauke, tana jin dole ta sake zage damtse tare da humɓasawa akan sana'ar da take saboda yaranta musamman matan. Yanayin fuskar Jaheed ya sauya zuwa damuwa kafin ya ce "Bana son arziƙin da zan yi wanda Daada zai amfana dashi..," Marin da Innti ta ɗauke Jaheed dashi ne ya hana shi ƙarasa faɗar abin da yake ƙwarzabar zuciyarsa, ya yi saurin dafe kuncinsa da hannun dama idanun ya yi jajur duk da duhun dare ya yi ba'a ganin fuskarsa balle cikin idanunsa. Raɗaɗin da ƙonar marin da Jaheed ya ji ya sauka a zuciyar abokin haihuwarsa Jadid, shima runtse idanun nasa ya yi a hankali kuma ya miƙa hannunsa ya ɗora akan na Jaheed Alamar rarrashi. "Dukkan arziƙin da ɗayanku zai samu wanda mahaifinku ba zai amfana dashi ba nima ya zama haramiyata, bana buƙata bana muku addu'ar ku samu, ƙwara mu zauna cikin babu ko ƙasa za mu ƙwaba mu dinga ci saboda yunwa na aminci da hakan" da ƙyar take maganar tana jin raɗaɗin marin da ta yi wa Jaheed yana sauka a ƙasan zuciyarta yana cinta. Ta yi saurin yin ƙasa da kanta tare da goge hawayen da yake zuba daga cikin idanunta. Ta ɗora da "Hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, ko baku ƙaunaci Daada a Matsayin uba ba, ba za ku hana duniya faɗar cewa ku ƴaƴansa bane. Ko muguwar kalma ɗaya daga cikinku ya yi masa, ko ina raye ko bana yare ko akan idanuna ko a bayan idanuna wallahi tallahi ban yafe ba, biyayya a gare shi umarnina ne, shi mijina ne, garkuwata kuma uban ƴaƴana, duk yadda zai kai da addaba mini ko aibata ku, haka zan cigaba da yi masa addu'a, haka kuma kullum cikin addu'oinku umarni ne akan ku yi masa addu'a" a karo na farko Jadid ya kalle ta. Ya ce "Innti rawar zata sauya zani ne?" Muryarsa shima a raunace take sosai "Kin san kallon da jama'a suke yi mana akan Daada? Kin san raɗaɗin da muke ji a cikin zuciyarmu? Kin san yadda muka sha bambam da sauran yara a duniyar nan?" Ya runtse idanunsa yana jin yadda komai baya yi masa daɗi, yana ƙoƙarin fidda rai da rayuwa me tsayi yana da yaƙinin ciwon nan ba zai bar shi ba. A fusge ya ce "Innti mutane basu da adalci, sun kasa yi mana adalci cewa, bamu da laifi ko saka hannu a cikin al'ummaran Daada, ya za mu yi ne? Ya za mu yi da ranmu, a wajanki kawai muke jin iska me daɗi, a wajanki muke samun inuwar da za mu raɓa mu ji sa'ida. Na karaya na fara karaya ina tsoron in ji cewa kamar ba mu yi sa'ar uba ba....," "Jadid!" Ta dakatar dashi da ƙarfi ta hanyar kiran sunansa, ya yi ƙasa da kan shi a hankali yace. "Ki yafe mini Innti kar ki yi fushi damu, ke kaɗai muke da ƙwarin gwiwar buɗe ba ki mu faɗawa halin da zuciyarmu take ciki, ina tsoron kar matsalolin Daada ya yi wa'adin ɗaya daga cikin zuri'arki, dauriya kike, na sani na san da wannan Innti shiru bashi ne ba" Ta zubawa Jadid idanu, sai yanzu ta lura da sauyawar da ya yi, wanda ya ci tun a jiya ta gane saboda bata da wasa wajan fahimtar yanayin yaran nata. Ta ja numfashi ta sauke ta kasa cewa komai sai ƙirjinta da ya yi mata nauyi, wani abu ya tsaya mata. Wayar Jaheed ce ta fara ƙara alamar shigowar kira, number wanda ya gani ce ta saka shi yin murmushi, murmushin daya saka Jadid sauke ajjiyar zuciya me nauyi ko babu komai ganin abokiyar haihuwarsa cikin farinciki ya sauƙaƙa masa ciwon da yake ji a jikinsa. "Mutumin rigimammiya ne" "Yaa Sam?" Inji Iftihal tana dariya. "Haysaam, kin canka masoyiya" Jaheed ya bata amsa, yana miƙa mata wayar ya ce "Jeki kai mata, na san dai ita yake nema" Iftihal ta amshi wayar da hannu biyu cike da ladabi ta juya zuwa ɗakin nasu. "Wannan wayar da suke yi da Haysaam da Ana babu damuwa a cikinta dai ko? Kun san irin maganganun da suke yi a tsakaninsu?" Jadid ya ce "Babu in sha Allah, hirar dai ba zata shige ta masoya ba idan ta yi ƙamari" "Soyayya? Sonta yake yi?" Yadda Jaheed ya yi tambayar ya bawa Jadid dariya ya ce "Kusanci idan ya yi yawa tsakanin mace da namiji ai soyayya ce kawai, wata rigimar da Shalelen Innti Babban yaya da Innti sai shi Haysaam ɗin kawai ne suke tanƙwara mana ita, kafirin taurin kai kamar matar kuturu da iyayin tsiya kamar jikar ƙaruna. Ga yauƙi kamar kuɓewa" Innti ta girgiza kai tana murmushi ta ce "Allah Ya shirya ka Jadid ya shirya mini zuri'a baki ɗaya, ka je ka sha maganinka ka kwanta haka nan" Kamar zai ce mata maganin ya ƙare sai kawai ya yi shiru ya miƙe tare da cewa "Mu kwana lafiya Sahibata" ta jinjina masa kai. Jaheed miƙe ƙafafuwa ya yi yana bawa Innti labarin shago, gabaɗaya ya mance da abin da ya faru na sharrin da aka yi wa Shalelen Innti. Babban yaya daman kamar baya wajan, wayarsa kawai yake dannawa ba tare daya san mema yake yi dannawa ɗin ba, tunaninsa kamar ba nasa ba, hatta shi ɗin jinsa yake kamar ba shi ba. Sai ya dinga gani ko ji a ran shi cewa; yana da bambanci da ƴan'uwansa. Bambancin da yake sake nisanta shi da al'umma, baya samun nutsuwa muddin zai jisa a cikin mutane. Wannan rayuwar jejin da yake tsintar kan shi a ciki idan ya yi bacci tafi masa daɗi. Iftifal da fara'a ta shiga ɗakin tana saukar da ganinta a shimfiɗarsu, domin ta ɗauka mahaɗinta ta jima da yin bacci.. turus ta yi ganin Ana zaune a ƙasa a inda ta yi sallar issha ko tashi ba ta yi ba, ta zubawa waje guda idanu. Har Ifti ta ƙarasu inda take ta tsuguna bata sani ba, alamar ta yi nisa cikin tunaninta. "Ana!" Ta kira sunanta da ƙarfi. Tana jijjigata kafaɗunta biyun. "Tunanin me kike yi mahaɗita?" A hankali taja manyan idanunta ta lumshe su bata jima ba ta ware su a fuskar Ifti ba tare da ta ce komai ba. Ajjiyar zuciya Ifti ta sauke a sanyaye ta ce "Ba damuwa Daada kika sakawa ranki ba ina fata rabin rai?" "Daada....? Yadda ta yi furucin da yadda ta ambaci sunan Daada zaka ɗauka bata taɓa jin sunan ba sai a lokacin. Furucin da Ana ta yi ya daskarar da jinin jikin Ifti da wani irin sabon tashin hankali ta ce "Kin san me kika ce? Kin san abin da kalmominki ke nufi?" Ana ta girgiza kai ta ce "A'a" "Waye Daada? Da gaske ban waye shi ba?" Iftihal ta ce "Ina tunanin Sunanki Ayshatul-Haleeym Ana Daada, wannan sunan da yake maƙale da sunanki kamar rai da ajali, wannan sunan da idan babu shi ba ki gama zama cikakkiyar ƴar sunna ba, wannan sunan da zai ta bibiyarki har yaranki da za su amsa sunan jikokin Daada.. wannan Daada mahaifinki" Ana ta bubbuɗe idanunta kafin ta juya ƙwayar idanun ta ce "Oh! Idan na fahimta wannan mutumin mai dukan matarsa, wannan dai mutumin me shigo mana gida tsirara cikin talatainin dare, hakazalika wannan mutumin me bin manta banza wanda yake da karuwa me suna Tani, wannan dai mutumin me yin caca shi kenan nufi? Shine Daadan da kike magana akai?" "Ana!" "Iftihal.... Ta kira sunanta itama cikin sanyin muryarta mara son hayaniya da rashin ɗaukan raini. "Ana mahafin naki kike faɗawa haka? Babu kyau fa ki tuna abin da Innti take faɗa mana akan Daada. Ni dai ina son Daada ina matuƙar son shi sosai a cikin zuciyata" Ana ta sake ware idanunta da mamaki ta ce "Kai haba? Shine mahaifin nawa kenan ashe?" Iftihal bata iya bawa amsa ba. Ana ta ɗan cije lips a hankali ta ce "Kuma kin taɓa ji na saka muku baki idan kuna batu akan shi? He's never been headache wallahi" "Kinga Iftihal, za ki iya son Daada har ƙarshen rayuwarki idan kin so, amma ba'a tilasta Ana yin abin da ba ta yi niyya ba. Idan ba ki ba sani ba, bari yanzu ki sani. Mahaifin Ana ya jima da rasuwa tun tana cikin Innti" Tana faɗin hakan ta miƙe zata je ta kwanta cikinta na yi mata wani irin ciwo saboda azababbiyyar yunwa, amma data ci tuwo ta gwammace ta kwana da ƴar gusau. "Yaa Sam ke kiranki a waya" Wayar ta amsa fuska ba walwala ta kara a kunne da wannan sanyin muryarta ta ce"Uhm... Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Yaa Sam ya sauke tun ɗazo yana jin yadda take surutu na masifa saboda ta yi niyya. "Dawa kike?" Ta yi masa shiru ta yatsar fashi. Shirun da yake azabtar da zuciyarsa wanda baya so baya buƙata shi ta yi masa. Ba zai jure sai ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya sake fesar da numfashi da ta ji sautinsa ya shiga kunnenta ya saukar mata a zuciya, ta ƙanƙame wayar tana lumshe idanunta tana jin wani abu yana yi mata motsi a ƙirjinta. "Nanaah" Ta yi masa shiru wannan karon ma. "Zan koma Lagos gobe idan rai ya kai mu, naso ganinki kafin hakan ta kasance kin ji?" Sai ta yi shiru tana sake saka ƙarfi wajan riƙe wayar da kyau, Lagos ke ta yi mata kai komo a kunne, ba yau ta saba jin sunan Lagos a bakin Haysaam ba, ba yau bane kawai, wannan bai zama na farko ba, babu tabbacin zai zama na ƙarshe. Akwai wani abu da take ji game da sunan Lagos, da duk sanda ya furta a kunnenta, menene shi? Menene abin? Bata sani ba, ko wuƙa aka saka a wuyanta akan sai ta faɗi me take. Tabbas sai dai a ɗauki ranta. "Na....... Ya kasa ƙarasa kiran sunan nata. Kamar yadda ta yi shiru shima shirun ya yi, duk wani bugun zuciyarta yana tafiya daidai da bugun tasa zuciyar. Ta ɗauka ya kashe kiran sai ta ce "Yaa Sam..... "Na'am" "Zaka tafi dani? Ka tafi dani Please" ta ce kamar za ta yi kuka "Nanaah, ya zan tafi dake garin da babu dangin uwa balle na uba, ke ba matata ba?" Ta ɗan narke masa ta cikin wayar "To ba sai ka ce ƙanwarka bace ni, ka yi maganin munafukai ko?" Ya yi jim sai kuma ya ce "A baki kike jin Lagos Nanaah, ba irin garinku Kano bane, kuma inda nake ɗaki ɗaya ne da Banki suka bani, ko zan dinga kwana dake muna using one bedroom?" "E, na yarda nikam" "Ba za ki ji komai ba, mu kwana tare?" A hankali ta ce "Me zan ji to?" "Think dear, yi tunani ko?" "Na yi, ba zan ji komai ba" Sai kawai ya share ta, yaja matsagaitan idanunsa ya lumshe. "Yaa Sam" "Nanaah" "Kai za ka ji?" Ya ɗan murmusa, sautin murmushin nasa ya saka ta sakin nata kyakkyawan murmushin da zuciya ke ayyana masa kamar ya ji ɗumin bakinta ne a fuskarsa. "E, zan ji" ya bata amsa. "To faɗa mini me zaka ji ɗin, na ji ko nima zan ji irin shi mu yi anko ni da kai abokina" “Abokina” ya maimaita sunan a ran shi. "Please Yaa Sam, say it" "Zan faɗa, not now" Ta ce "Sai yaushe?" "Sanda Shalelen Innti ta girma" "Yaa Sam.. Yaa Sam... Ƙit ya kashe wayar. Bayan ya kashe wayar juyi kawai yake yi a saman ƴar yaloluwar katifarsa, yaja idanunsa ya lumshe ya sake buɗe su, ya ƙara rufe su ji ya yi zuciyarsa na yi masa motsi. Ya zai yi ne? A aboki ta ɗauke shi Madam, kuma kamar she's too young ta fahimci abin da yake ji, wata ƙilama ita bata jin komai ma. Yaushe ya san Ana ne? Kamar zai iya tuna sanda ya ganta? Idan ya rufe ido tsaf zai ga tarihin daya shuɗe akan Ana Sanda ya fara ganinta a duniya. *** Rediyo take saurara amma taƙi tsayar da hankalinta waje guda, daga ta danna nan sai kuma ta danna nan cikin sa'a takai inda ake maimaicin labarai. Ta yi shiru tana saurara. Sai ji an ce "Wannan kenan. A yau ne wani rikicin kishi tsakanin matan Malam Sani dake Gandun Albasa ya barƙe, barƙewar data tashi barƙewa ta haɗa da jaririn da aka haifa wanda yake a shaƙi iskar kwana ɗaya a duniya, inda kishiyar Maryama wato uwar gida ga Malam Sani ne suna Talatuwa ta yi juyin waina a tanta da jaririn Maryama a ruwan zafin, kai ka ce kaza ake shirin figewa wajan yin tagomashin arziƙi a baki" me yin labaran ta ɗan yi shiru ta ɗora da; "Duk yadda gidan rediyon bright Fm yaso ganawa da Maryama abin ya faskara, ga abin da ya faru a taƙaice daga bakin wanda idanunsu ya gane musu" Muryar wata mata aka sako tana kuka sosai ta ce "Ban taɓa ganin azababben kishi fara fa'ida irin wannan, akan idanuna ta ɗauki jaririn amaryar ta cilla a ruwa, Talatuwa ta yi haka ne da gayya da tunanin hukuma ba zata ɗauki mataki ba, sun auro yarinyar suna gallaza mata hatta mijin bayan Talatuwa yake bi shi ya hana Maryama ta kai ƙara. Alkur'anin Allah akan idanuna komai ya faru" Ɗif aka ɗauke muryarta. "To daman kowa ya sai rariya ai ya san zata zubda ruwa, Allah kasa mufi ƙarfin zuciyarmu. Me rahoto Yussrah Yassar Yakasai" Sai aka ɗan sako take da muryar namiji a background sound ana faɗin "Labaran rana kuka Saurara daga bakin Yussrah Yassar Yakasai....," bata bari ya ƙarasa faɗa ba ta yi cilli da rediyon hankali tashe ta fito tana faɗin "Malam malam fito ka ji muryar Asabe a rediyo ta yi bayani dalla dallah mun shiga uku Malam" fitowa ya yi daga ɗakinsa domin shima yanzu yaga ma ji ya kalli Talatuwa data rushe da kuka daidai nan Maryama ta fito tana kuka sosai "Malam na rasa ɗaya ya rasu na shiga uku, an kashe mini yarona" A fusace ya ce "To allahamdulilah da hakan ma, maza tattara kayanki da gawar ki fice mini a gida na sake ki saki uku cif kar na sake ganin me kama dake. Ba za ki ja mini masifar zaman gidan yari ba billahi" Cak kukanta ya tsaya ta zubawa Malam ido jikinta duka rawa da ɓari yake yana zata da gawa cikin daren nan? Ina za ta yi? Ba zata iya komawa gidansu ba, ta shiga uku. "Ka tausaya mini Malam na yarda ka sake ni amma kabar ni na zauna a gidan nan don Allah, na shiga uku. Ka tuna ɗan nan na kane ko jana'iza ayi masa" Talatuwa ce ta shiga ta ɗakko jaririn a hannu, Malam ya shiga jan Maryama tana turjewa sai da ya kai ta bakin ƙofa Talatuwa ta ajjiye mata gawar ƙasa suka ja ƙofa suka rufe babu ko mayafi a jikin Maryama. *** Juyi kawai Ahlam take yi a saman gadon dakinti, ta ɗauki a ƙalla awa ɗaya da daƙiƙo a haka tana juyin da bashi da amfani, idan ta yi niyyar bacci baya samo, maganganun MD da suke neman saka mata ciwon zuciya kawai take tunawa a cikin kanta, ga matsalar baiwar Allah da bata san halin da take ciki Bama, ga matsalar Yussy da kanta. "Na shiga uku! Ko dai bani da rabo ne a aikin jarida?" Ta saka hannu ta dafe kanta. Da sauri ta miƙe zaune tana faɗin "No! Ba zai yiwu ba, dole na ɗaukaka akan aikina, ɗaukaka nake so ko ta wacce fuska wacce zata saka tauraruwar Yussy ta disashe" ta saka tafin hannunta wajan goge hawayen idanunta, shanyayyen hannunta ta kalla. "Ko nakasata ce silar komai? Ko ita ce ta hanani ɗaukaka ni Ahlam?" Sannu a hankali ta miƙe tsaye bayan ta sakko daga kan gadon, safara da marwa ta shiga yi a cikin bedroom ɗinta. "Anees" ta kira sunan. Wayarta ta ɗauka ba tare data duba lokacin kiran ba, idanunta rufe ta fara neman number. Kira biyu ta yi ba'a ɗauka ba, ana ukun aka ɗauka sai aka yi shiru. "Hello.... Babu martani. "Hello... Nan ma shiru sai ta ce "Anees, akwai matsala ina buƙatar taimakonka Please" babu raddi ko numfashi balle sauti a ɓangaren Anees ɗin. Wayar ta ciro daga kunnenta tana ƙoƙarin sake kira, da firgici ta yi baya tana zaro ido ganin number MD ta makawa kira a cikin daren. *** Wajejen gotawar uku da kwata na dare, Innti na zaune saman laddumar da ta yi lafila hannunta riƙe da carbi tana azkar. Ta jima zaune iska na kaɗata. Hannunta ta ɗaga sama bayan ta ajjiye carbin da karyayyiyar murya me raunin gaske, buɗaɗɗiya me cike da buƙatu a wajan Ubangiji ta ware hannayenta wajan furta. "na sani Ubangiji, ina da masaniyar babu abin da zai faru da rayuwar bawa face abin da ka ƙaddara masa, na amshi jarrabawata da hannu bibbiyu, burina, fatana addu'ata akan ƴaƴana ne da mijina. Mijina shine gatana ƴaƴans sune farincikina, Ubangiji ka shirya mini zuri'a, ka shirya mini su. Allah ka haɗa su da alherin da yake cikin wannan duniyar, ka nisanta su da sharrin dake cikinta.. Allah ga autata nan Ubangiji ka shiga cikin rayuwar Ayshatul-Haleeym, ka shirya mini ita, ka shirye ta ka tausashi zuciyarta, ka cire mata zafin zuciya da taurin kai. Ka daidaita tsakaninta da mahafinta" taja ajjiyar zuciya me ƙarfi ta sauke ta ce "Mijina... Wani irin hawaye masu zafin gaske ne suka shiga sunturi a saman fuskarta, jikinta ya shiga rawa da ɓari a wahalar ce ta shiga faɗin. "Mijina Ya Allah. Ya zan ce bana son mijina? Gyara naka ne, shiriya taka ce, Allah ka shirya mini mijina ka dawo dashi hanyar tsira kar ya koma gare ka cikin wannan mummunan tufar, bana riƙon shi a raina bana jin zafinsa. Allah ka dawo dashi kan tafarki madaidaici, ka kiyaye masa alƙalaminsa daga aikata mugun abu akan kowacce ɗiya mace ko don tsoron dawowa gare ka. Ko don tarihin zuri'arsa.....," Bam! Ta ji ƙarar buɗe ƙofar da ya yi ya shigo, wata faɗuwar gaba ta saukar mata. Kafin ta yi yunƙurin matsawa ta ji saukar ita ce a gadon bayanta, azaba, raɗaɗin da bata taɓa jin irinsa ba ya saka ta saki wata ƙara haɗe da kiran sunan Allah. Daman niyyar tashi take yi saboda nishin da ta ji a ɗakin samarin yaranta wanda babu tantama Jadid ne ciwonsa ya tashi, ciwon ƙodar da yake fama dashi. Ƙarar da ta yi na farko ya fito da Jaheed daga cikin ɗaki dai-dai lokacin ma Ana ta fito ta kafe Daada da ido, yau ma tik yake haihuwar uwarsa babu kaya a jikinsa. Jaheed na ƙoƙarin janye Innti, Daada ya sake ɗaga icen hannunsa ya sake makawa Innti a gadon bayanta. A hargitse Jaheed ya nufi Daada zai ture shi. "Idan ka sake hannunka ya sauka akan mahafinka zan maka Allah Ya isa Jaheed. Mahafinka ne" Cak Jaheed ya tsaya jikinsa na wani irin rawa da ɓari hawayen daya cika idanunsa ya shiga bin fuskarsa ya durƙushe a wajan. "Daada ka yi haƙuri, ka ji tsoron Allah ka tuna mu da Innti amana ce a gare ka, matarka ce. Kar hakkin Innti ya bimu har gidan aurenmu" Iftihal ce ta furta hakan bayan ta fito daga ɗakin. "Daada ka tuna faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, dukan mata rashin adalci ne, idan ya zama tura da bakin riga ake dukan su, haka Mu'allim ya ce mana. Muna son ka muna kwaɗayin rayuwa da kai, kar ka kashe mana Innti" kallon Ifti ya yi zai kai mata duka sai ya tuna yarjejeniyar cacar da yake kanta, zai samu miliyan ashirin cif saboda ita, don haka a yanzu ita kallon kuɗi yake mata. Ya kalle su sama da ƙasa kafin ya ce "Na tsani haihuwa, me ya saka ta saki jiki duk ta haife ku kamar wata dabba, uwarku bata da amfani ita da dabba ɗaya suke a wajena. Jaka ce, daƙiƙiyya mara amfani" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Iftihal ta furta tana fashewa da kuka, tana jin kamar zuciyarta ce zata fito waje. Daada ya sake kallon Innti take durƙushe ya ce "Wallahi Tani ta fita armashi da garɗi, ta sani bana son haihuwa me ya saka ta haife ku har haka? Ku duka tsinannu ne ba za ku yi albarka ba. Allah wadaran....," a zabure Innti ta miƙe tana girgiza kai kafin ta ce "Kar ka aibata mini zuri'a Daada, kar furucinka ya zame musu Harshen wuta, ka yi wa girman Allah Daada...," bai bari ta ƙarasa ba ya ɗauke ta da mari ya nuna ta da manuniyya "Na faɗa, Allah Ya tsine musu dake dasu gabaɗaya, zuri'ar da bata da wani amfani kema ba ki da amfani bare su, sai sun watse sun bi duniya. Allah ya tsine musu, Allah ya farraƙu gabaɗaya na huta" "Allah Ya tsine maka dai Daada da kai da Tani Allah Ya tsine muku" muryar Ana ta sauka akan kunnuwansu.... *H I Y Y A M* Page 7: Abbaa, Save Me Bright pens Yota/001 Stay blessing as always FALMATA. Wani irin ɗauke ta da mari Innti ta yi, kafin Ana ta dawo hayyacinta ta sake sauke mata wani lafiyayyen mari a ɓarin dama na ƙuncin kyakkyawar fuskar yarinyar. A firgice kuma ta ce "Allah Ya shirya ki Allah kai bani yarinyar ka shirya mini Ayshatuna" ta ɗora "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Salatin Innti ya karaɗe cikin gidan har zuwa maƙota. Jikinta yana wani irin rawa ta sake durƙushewa a wajan ta kasa furta komai saboda yadda laɓɓanta suke rawa a saman bakinta. Da ƙyar ta ɗago kai ta kalli Ana, ta ɗauka za taga fuskar yarinyar cikin damuwa da tsoron kalaman data jefi mahaifin nata dasu, sai taga saɓanin hakan a tattare da ita. Babu tsoron, babu ladama ko guda dake mintsinin zuciyar Ana. Kamar ma ta shirya furta da wasu zantukan da suka fi na baya muni. Sharr hawaye ya sako a idanun Innti. Da rawar ɗari kamar jonin wutar lantarki haka Jaheed ya zame kusa da Innti da rawar murya cike da rauni ya ce "Mun shiga uku.... "Kuka kike Innti? Hawaye kike fitarwa?" Ya yi furucin muryarsa na rawa tana kakkatse masa a maƙoshi saboda tsananin tsoro da tashin hankalin yau mahafiyarsu ke zubar wa da ƴar data haifa hawaye, duk da ta san hawayenta azaba ne a gare su, musamman ga Ana ɗin da take da busasshiyar zuciya, ba zata jure ba idan sun yi haƙuri wajan kawar da kai daga ƙaddararsu. Ƙaddarar da Ubangiji ya zaɓa musu yake son ganin su a cikinta. Jadid ma riƙo hannun Inntin ya yi a cikin nasa yana kallon ta, a sanyaye kamar an watsawa kifi gishiri ya ce "hawaye kike zubarwa akan kalaman Daada? Kar ki yi kuka Innti, kar ki yi baƙin ciki don Allah" girgiza kai ta shiga yi a hankali tana ƙoƙarin dakatar da Jaheed daga goge mata hawayen idanunta. Ta riƙe su da ƙarfi ta ce "Ana.... "Ka ji furucin da Ana ta yi? Ka ji me ta ce akan mahaifinku?" Ta ja numfashi me zafi ta yi feshin shi a gefen fuskar Jadid, da sauri ya yi ƙasa da kan shi yana kiran sunan Allah, hucin numfashinta ya bashi yaƙinin gwargwadon yadda zuciyarta ke ɗaukan ɗumi akan al'amuran Daada. Gashi wata haƙar na neman kai su ga rijiya madadin ganin ruwa, Ana na ƙoƙarin zame musu wata jarrabawa me wahalar gaske musamman ga Innti gama dukkan su gabaɗaya. "Jaheed, Jadid" ta kira sunayensu "Me ya sa ɗabi'un shalele yake da tawaya da naku? Me ya sa komai naku ya yi hannun riga da nata? Bafa ta san kuskure ta yi ba" "Kuskure?" Ana ta faɗa tana wani irin lumshe manyan idanunta da suke gajiye da al'amuran gidan nasu ga raɗaɗin marin da Innti ta yi mata amma ko gezau ba ta yi ba, daman ita bata taɓa saka ciwon kan Daada a matsayin lalurarta ba, bata taɓa takaici akan abubuwan da yake yi na gurɓata musu suna ba. Da yawan lokaci tana cewa "Matsalolin Daada nasa ne, haka kuma damuwarsa tasa kawai bata Ana ba" yanzu ma take tsaye tana fuskantar Daada wanda ya yi mutuwar tsaye da jin furucin da ko matarsa bai taɓa hasasowa zata jefa masa su ba, balle ɗiyar daya haifa. A hankali ta saka hannunta guda ɗaya ta ɗora a saitin ƙirjinta, ji take kamar zuciyarta ce take kekketa fatar ƙirjin tana ƙoƙarin ratso ƙirjinta ta fito waje. Bakinta ta ware tana ƙoƙarin cewa wani abu sai ta ji kamar ya tsaya mata, ta haɗe laɓɓanta waje guda ta taune su, taja idanunta ta lumshe su, idanun da shi kan shi Daada suke bashi ciwon kai a rayuwa. Da ƙyar ta iya cewa ta kalli Iftihal wacce take ta sharɓar kuka sosai. Da rashin fahimtar ma'anar kukan Ana ta ce "Me na ce ne?" "Tsoro nake ji mahaɗita, tsinewa Daada kikai" cewar Iftihal tana ƙanƙame jikinta. Ana ta juya ta ce "Shine me? Daadan na farko ne da ba za'a iya tsine masa ba? Babu abin da zai faru sai hukuncin Allah" ta ƙarasa kusa da Iftihal ta ce "Ta ya kike tunanin bakin dake shan giya, jikin dake ɗaukan zunubi da Iskanci dana cin zarafin matarsa da ƴaƴansa don ya tsine mana zai yi tasiri akan mu? Wannan mutumin ko ledar pure water ya tsinewa babu abin da zai same ta, balle mu da muke tare da albarkar Innti" ƙuri Iftihal ta yi wa Ana da idanunta masu rauni da suka cika da tausayin Ana ɗin matuƙa saboda taurin kanta. Murmushi kawai Ana ta yi, tana ƙoƙarin riƙe kanta daga jirin dake ɗaukarta. Sai ta ɗan daƙune fuska ta ce "Rabin rai" "Na'am Rabin rai" Iftihal ta amsa a sanyaye "Smile for me, ki yi murmushi saboda ni" ta shafi fuskarta "Kawai ina son ki ne Ana, ina jin kamar ba zan iya rayuwa ba idan babu ke a gefena" Ana ta ware blue eyeballs ɗinta kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa, ta kafe Iftihal da ido sai kallon ta take yi kamar zata mayar da ita ciki, a hankali kuma take shafa fuskarta ta ɗauki lokaci a haka kafin ta sauke ajjiyar zuciya saboda ƙwarin gwiwar data samu sanda ta fahimci nutsuwa a tattare da Iftihal, wani irin sarawa kanta yake mata gefe guda kamar me shirin tafiya da ganinta ko kai ta lahira. Durƙusawa ta yi daidai inda Innti take zaune cikin sanyin murya da confidence ta ce "Na ɗauka za ki bani tukucin kalamaina ne Innti ta hanyar yi wa cikina alheri da abinci kar na kwana da yunwa. Ciwon kai na ke ji sosai a tattare dani" Innti ta yi mata shiru sai kallon ta kawai take yi kamar bata fahimci me take faɗa ba. A hankali Ana ta ce "Na yafe abincin, ko albarka ki saka mini da addu'ar samun kyakkyawan miji ko Aljani ko maye..," Kyakkyawan marin da Innti ta ɗauke Ana dashi hagu da dama a karo na biyu shine ya hanata ƙarasa faɗar abin da ta yi niyya, ta yi baya tare da yin zama raƙuma ta dafe kuncinta tare da zubawa Innti idanunta masu kaifi da haske. Cikin zafin nama Innti ta ce "Har kike da kalmomin tara ta dasu bayan kin yi wa mahafinki rashin ɗa'a. Ba haka na ba ki tarbiyya ba, ba abin da na nuna muku kenan ba Aysha. Me ya sa don me ya sa?" Ta kalli Babban yaya da yake jingine da jikin bango yana kallon gefe guda kamar baya tsakar gidan abubuwan da suke faruwa suke wakana ɗin. "Ko dai ina da tawaya wajan gina tarbiyyar Aysha ne Yaya?" "Me ya sa kamar bakya so na ne Innti?" Ta faɗa da rawar murya Bata farfaɗo ba wasu kalaman na Ana suka sake cakar zuciyar Innti da yi mata wani irin rauni me zurfi. Da rawar murya Ana ta ce "Naga kamar bakya so na ne, a tunanina abin ƙwarai na yi ai, abin azo a yaba. Taya kike tunanin zan jure ganin ana cin mutuncinki da na dinga ganin haka gwara na bar muku duniya, gwara na bar wa mijin naki duniyar" "Kept quiet Aysha!" "Ki bari na faɗa Innti,naga kamar kin fi son mijin naki akan yaran naki, naga kamar ya fimu muhimmaci a rayuwarki. Ko babu komai muna saka ki farinciki, muna sawa ki yi alfahari damu, muna sawa ki ji mu yaranki ne da suka fito faga cikinki" ta juya ta kalli Daada da yake tamboɗe ta nuna shi da yatsa ta ce "Shi ɗin wanne hakƙi naki ya sauke, mene abu ɗaya da ya yi miki wanda kike jin ya cancanci amsa sunan miji da uba?" Innti ta juya ta kalli yaran nata gabaɗayansu ta ce "Ta ce wai na bata amsa?" Duk suka zubawa Innti ido ban da Ana. "Me ya sa ba zan so wanda ta silarsa na samu alarbarkatattun yara irinku ba?" Wani irin murmushin takaici Ana ta yi tana sake watsa idanunta akan Innti kafin ta girgizar kai ta yi baya tana ƙoƙarin zubewa a wajan saboda ciwon da kanta ke yi mata. "Uhm... Uhm haka ne" Sai ta ce "Mashayi, ɗan giya, me fifita karuwarsa akan ki, me aibata yaranki, me yi mana fatan mu farraƙa, ɗan caca irin shi kike so, kike ƙauna har haka a ranki?" "Innalillahi! Aysha;.... "Ki so mijinki Innti, ni kinga ubana nan" Ta nuna Babban yaya dake tsaye ya rungume hannunsa a ƙirji idanunsa sun yi jajur ilahirin jijiyoyin kan shi sun fito sosai a saman goshinsa dukkan wata gargasa da Ubangiji Ya halitta a jikin Babban yaya sai data mimmiƙe daga fatar jikinsa, ya dunƙule hannayensa hagu da dama har wata power ta tashi a damtsen hannunsa buɗaɗɗan jikinsa me ɗauke da gaɓoɓi suka gama bayyana. Wani abu ya tsarga masa lokacin da Ana ta kira shi da sunan uba, mahaifi wani irin responsibility ta ɗora masa na kulawa da ita, bai mata alƙawari ba, amma yana da tabbacin zai amsa mata, zai bata dukkan wata kulawa da uba yake bawa ƴarsa. Ji ya yi zuciyarsa tana rarrabewa wani abu yana shiga cikinta. "Daga yau Babban yaya shine Abbaana, shine ubana, da sunansa zan dinga amfani har abada idan ya zama dole na yi amfani da sunan namiji a jikin sunana kenan" Sai a lokacin ta ji kamar numfashinta na season a ƙirjinta yana kakkatse mata. "Ki so mijinki Innti, ina fatan soyayyar da kike masa ba zata ja rauninki zuwa ga tsine mana ba kamar yadda mijinki ya yi....," a hankali ta ce "You're my world Innti" Buɗe baki Innti ta yi zata hau kan Ana da faɗa sai ta yi saurin sauya harshe daga faɗan zuwa addu'a a zuciyarta ta shiga yi; "اللَّهُمَّ اهْدِ قَلْبَهُ، وَأَصْلِحْ حَالَهُ، وَاجْعَلْهُ مِنَ الْبَارِّينَ بِي، وَاغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ. Ma'ana. (Ya Allah ka shiryar da zuciyarta, ka gyara halinta, ka sanya ta cikin masu biyayya gare ni, ka gafarta mata ka yi mata rahama). Juyawa Ana ta yi itama da niyyar barin wajan. Sai ta yanke jiki ta faɗi a wajan. Yunwar da ta ci ƙarfinta da ciwon da gefen kanta ke yi mata ne ya haddasa mata hakan. Kafin ta miƙe zaune Daada ya saka ƙafa ya taka mata ruwan cikinta, tsananin zafi da azaba sai gani sukai fitsari yana bin ƙafafuwanta a hankali ta zubawa Daada ido, kallon da yake nuna tsoro da mamakin kiran shi da Uba. Kafin numfashinta ya ɗauke ta miƙa hannunta da ƙyar zuwa ga Babban yaya ta ce "Zan mutu Abbaa ka ɗauke ni" "Cikina Abbaa.... Bata iya ƙarasa faɗa ba saboda wani duka da Daada ya kai ruwan cikin Ana a karo na biyu daidai lokacin da numfashinta ya tsaya. Da wani irin fitar hayyaci Babban yaya ya saka haƙora wajan datse harshensa jikinsa na tsuma da kakkarwa ya yi kan Daada ya saka hannunsa guda ɗaya ya damƙo wuyan Daada ya ɗage shi sama, ƙafafuwan Daada suka fara lilo a ƙasa, wata sabuwar kururuwa Innti ta yi saboda abin da bata taɓa zato bane ya faru. "Yaya mene haka, ubanka ne mahaifi ka sake shi, muddin nina ɗauki cikinka wata tara, na shayar da kai nono wallahi idan baka sake shi ba ban yafe maka ba, ya zama na ƙarshe a rayuwa da za ka yi tunanin taɓa jikin mahaifinka" Babban yaya bai ko kalli Innti ba jikinsa kamar an jona masa wutar lantarki haka yake tsuma, ya manne Daada da jikin bango wanda ya fara hango kabari kafin ya yi cilli dashi zuwa gefe guda. A gigice kuma cikin wani slow ya yi kan Ana da yana durƙushewa akan ƙafafuwansa ya yi zaman raƙuma ƙoƙarin magana yake yi ya kasa sai laɓɓansa da suke rawa da wani sounds dake fita ta cikin gurnaninsa. Rabon da su ji sautin muryarsa ta fita har haka sun mata, yadda yake ƙoƙarin kiran sunan Ana kamar yadda ya sama idan yaso ya saka Innti saurin yin baya tana dafe ƙirjinta. Tashin hankali da tunanin Iftihal zata rasa Ana ya kasa ɗaukan zuciyarta ta yanke jiki ta faɗi cikin sauri Jaheed ya taro ta jikinsa yana kiranta. Kakkar haka laɓɓansa da harshensa suke masa rawa ya zubawa fuskar Ana ido a cikin saman kan shi ya ji ya kira sunanta da ƙarfin gaske. "Shettyyy... Da wani irin slow Babban yaya ya rungumota jikinsa gabaɗaya yana bubbuga fuskarta yadda Jaheed ya wanzu yana kiran sunan Iftihal. "Jini... Jini a jikin Ana" Jadid ya ce a firgice shima zuciyarsa na ƙoƙarin tsayawa da aiki jikinsa na wani irin rawa da kakkarwa idanunsa na ƙaƙƙafewa. "Na rasa yarana na rasa aminai na" Gabaɗaya neman ficewa daga hayyacinta Innti take shirin yi saboda tashin hankali. Tsam kuma Babban yaya ya rungume Ana a jikinsa, gashi jikin nasa sanyi sosai kamar na maciji idanunsa suka rikiɗe tare da yin blue sosai wani haske na fita daga cikinsu sai girgiza kai yake yi. Ya rasa abin yi a nutse ya saka tafukan hannunsa wajan riƙo fuskarta yaga babu alamar numfashi a tattare da ita babu alamar tana jin shi, babu alamar akwai rai a jikinta. Da wani irin rawar jiki data zuciya ya manna bakinsa a goshinta ya sumbace ta. Daidai lokacin Haysaam dake ta sallama ba'a amsa masa ba ya faɗo cikin gidan, Jallabiya ce a jikinsa ash wacce tabi farar fatarsa jikinsa ta kwanta bai iya tsayawa tambayar mene ya same ta ba ya kalli Jaheed ya ce "Jeka ka tashi Mas'ud ya ɗakko napep ɗinsa yanzu" yana faɗin hakan ya sunkuya ya sunkuci Ana a jikinsa ya yi waje da ita. Daidai nan Iftihal ta farka tana fasa wani irin gigitaccen ihu da kiran sunan Ana. Daada da yake numfashi da ƙyar yana riƙe wuyansa da yake jin kamar ya kumbura ya yi baya yana faɗin "Allah Ya sa ta mutu na huta, daman sun yi mini yawa ai ba zata taɓa albarka ba, Innti duka yaranki ba za su taɓa yin albarka ba, tsinannu ne" Babban yaya ne ya miƙe yana tattare hannunsa ya nufi hanyar ficewa daga cikin gidan. “MURAAD” cak ya tsaya bai juya ba saboda baya son taga sauyin da ya yi "Muraad ka dawo mini da Shalele da ƙafafuwanta, Muraad ka dawo da ƴarka" "Itama ta bashi Shetty kenan? Ta yarda shine uba kuma mahaifin Anarta?" Ya yi jim. "Muraad" "In sha Allah" ya ce a taƙaice a karo na biyu bayan kiran sunan Ana da ya yi. Yana faɗin hakan ya saka kai ya fice yana ɗan ranƙwafar da kan shi abinka da dogo Yana fita ya tarar har an fito da Napep ɗin, Mas'ud ba zai iya kai su ba, don haka Yaa Sam ne ya shiga gaba Babban yaya ya zauna a baya rungume da Ana suka tafi asibiti mafi kusa. Jaheed ya koma gida. Emergency aka amshi Ana babu ko biyar a hannun Babban yaya, kuɗin da Haysaam ya tanada domin tafiya Lagos dasu a gobe sune ya fito dasu ya bayar aka siyo kayan aiki dasu, suka jira a reception su kuma. *** KANO/ MAITAMA SULE GRA BAFFAS ESTATE. An sanya sunan unguwar MAITAMA SULE ne domin girmama fitaccen ɗan siyasar Kano, Yusuf Maitama Sule wanda aka fi sani da Dan Masanin Kano. Ya kasance babban ɗan siyasa, jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma mutum mai daraja a tarihin ƙasar. Saboda irin gudummawar da ya bayar, aka sanya masa wannan yanki mai daraja. Maitama Sule GRA yana cikin sabbin yankunan birnin Kano. Yana kusa da manyan hanyoyi da wuraren gwamnati Tsarinsa na “GRA” (Government Reserved Area) yana nufin an tsara shi ne musamman domin manyan mutane da attajirai tare da masu faɗa a ji na faɗin Jihar Kano. Gidajen MAITAMA SULE GRA mafi yawansu manyan mansions masu tsada ne wanda aka yi su da arziƙi bada kuɗi ba. Duplex da gidajen zamani Filayen suna da girma sosai (ba kamar tsofaffin unguwanni ba) Yawancin gidaje suna da: CCTV tsaro na sirri,lambuna (gardens) a matsayin arziƙi ana ɗaukanta matsayin unguwar masu kuɗi sosai (elite area) Mazauna sun haɗa da: ƴan kasuwa masu arziƙi ƴan siyasa manyan ma’aikatan gwamnati. Farashin gida ko haya a nan ya fi yawancin unguwanni tsada. A cikin jerin estate dake Maitama sule Baffas Estate daban yake, gida ne da aka yanki gininsa na musamman tsarinsa komai ya bambanta da sauran, an yi masa ado da zane irin na gidan sarauta wanda bai san asalin BAFFA ba, zai ɗauka iyalinsa da shi kan shi jinin sarauta ne madadin sanin da aka yi masa na kasancewarsa Babban Malamin Addinin Musulunci dashi da zuri'arsa. Mabiyin Izala (Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa lqamatis sunna) Ta dalilin SHEIKH HAFIZZ HAFIZZ BAFFA jama'ar da suka koma ɓangaren Izala suna da matuƙar yawan gaske al'amarin daya kawo ruɗu da ceceku ce tsakanin bambanta Addinai al'amarin daya yi ƙamari kenan yaja hankalin mabiya Shi'a (Shi'a Islam) a wani wa'azi da ya yi ya ya taɓo su, ya yi musu caccakar da taɓa har ƙasar Iran. Sheikh Hafizz Hafizz Baffa bai yi zaton girman abin ya kai har haka ba. Sai da aka wayi gari an kashe Sheikh Hafizz Hafizz Baffa, kisan da ba'a san su waye ba, tun daga lokacin har kawo yanzu, an kashe shi tare da babbar ƴarsa a kan hanyarsu ta zuwa Qatar. Sai jaririnta guda biyu ne suka tsira, wanda a ranar ne kuma ta haife su ba tare data san me ta haifa ba, aka yi mata yankan ragu aka ƙune Sheikh Hafizz Hafizz Baffa. Wannan jinin dake jikin Diyanah, jini ne da har abada ba zai taɓa fita daga zuƙatan BAFFAS FAMILY ba. Wannan jinin shine abu na farko da yake cin zuciyar mutumin da bai taɓa buɗe baki ya yi kukan rashin DIYANAH HAFIZZ HAFIZZ BAFFA ba. Ba tsoran jinin yake ba, domin ya yi imani da Ubangijin Al'arshi kowanne rai zai ɗanɗani ɗacin dake cikin zare rai daga gangar jiki, ya yi imani da Allah da kuma ƙaddarar dake zane a rayuwar kowanne bawa. Baya tsoron dukkan abin da zai faru dashi muddin Ubangiji ne ya ƙaddaro masa. "Wani rai ba zai sake salwanta ba ta dalilin Baffas Family, zai raini jinin DIYANAH HAFIZZ HAFIZZ BAFFA da soyayya da kulawa, zai ƙarar da rayuwarsa, shekarunsa wajan ingata jinin Diyanah Hafizz Hafizz" Ya ɗora da "Zai danne feelings da emotions ya manta cewa shi namiji ne, ya manta daɗin daya taɓa ji sau ɗaya a rayuwarsa" Shine abin da zuciya take faɗa masa a koyaushe. Daman zuri'ar daya samu da Diyanah Hafizz Hafizz Hafizz Baffa unexpected ne, ba zai iya tuna yadda ma komai ɗin ya kasance ba, shuɗewar shekara goma sha Bakwai kenan cif, a cikin shekarun 17 ɗin zai ware kwana ɗaya kawai, a wannan daren juma'ar ya kasance da Diyanah Baffa, kyakkywar yarinya fara tas kamar ita ta zaɓi yadda kyawunta zai kasance, ko a cikin daren ita ce wacce taja ra'ayinsa ita ce wacce komai nata ya yi tasiri a jikinsa ba'a zuciyarsa ba, daga wannan daren kuma sai komai ya lalace ya rasa kan shi a matsayin ɗa namiji ta dalilin hatsarin motar daya samu wanda yaja aka yi masa aiki a mararsa. Sai ya zama dashi da mace basu da bambanci sai na suna da suffa. Daga ranar ne kuma SAYYADI BAFFA ya fara kallon kowacce mace a suffar Garzali. A hankali take sakkowa daga steps ɗin benen fuskarta ɗauke da yalwar murmushi tana sanye da atamfa ruwan ƙasa me zanen ɗawisu ta ɗora Jalbab a saman a atamfar wanda ya saukar mata har ƙasa hannunta ɗaya riƙe da counter tana tafe idanunta na kallon direction ɗaya tana sake faɗaɗa murmushinta wanda yafi maganarta yawa a koyaushe a haka har ta kammala sakkowa daga saman benen tana nufar kujera me cin mutum biyu ta zauna bakinta ɗauke da Bisimillah. "Barka da sakkowa Hajiya Umaimah" juyawa ta yi a nutse ta kalle shi, kamar ba zata ce komai ba sai ta jinjina kai "Kana ta jira a downstairs Alhaji Sadi?" Ta ce a tausashe tana mai gyara zaman nata sosai. Ya jinjina kai yana murmushi ya ce "Bai zama damuwa ba zaman ai Hajiya Umaimah nasan uzuri ne ya zaunar dake a can saman, ni abin kari ma nake jira a nan" ɗan ɗaga kai ta yi sai taga gabaɗaya 11:12 na safiya ta sake yin murmushi can ya ce "Gidan shiru yau ɗin" A nutse ta sake cewa "Nadiyah Baffa ce babu lafiya" Alhaji Sadi ya buɗe idanunsa cike da damuwa da tsoron jin abin da ya samu Nadiyah ɗin, dukkan wata damuwar da zata sake bawa Baffa damar shiga ƙunci baya son ta, yana jin kai tsaya damuwar Sayyadi Baffa ne na sauka a zuciyarsa tana haifar masa da rashin kuzari da walwala. Ya dubi Hajiya Umaimah a nutse ya ce "Nadiyah fa?" "Nadiyah Sayyadi Baffa" ta bashi amsa. "Ikon Allah, mene ya same ta har haka? Ban taɓa jin ta yi lalura har ta kwanta ba, dama dai Diyanah ce wannan tana da laulayi" baya Hajiya Umaimah ta yi tana ɗauke kanta zuwa gefe kamar bata ji me yake cewa ba, a hankali ta ce "Ya za'ayi da lamarin Ubangiji Alhaji Sadi? Ciwo ai waraka ce" shima ɗin jinjina kai kawai ya yi ya ce "Mun je nema wa Liman aure kamar yadda ya buƙata, to my surprise basu bamu matsala ba iyayen yarinyar akwai karamci sosai da alama" "Allah Ya sa ba ƴar ƙananun mutane Liman ya ɗakko mana ba" yadda ta yi maganar tana neman wajan zama kai tsaye ya bawa Alhaji Sadi mamaki ya juya ya kalle ta na wani lokaci sai bai ce komai ba, ya mayar da idanunsa kan Umaimah ya ce "Sun amshi kuɗin, an kuma saka rana nan da watanni biyar masu zuwa" "Allah Ya nuna mana, ya sa abokiyar zama ce" Hajiya Umaimah ta furta a sanyaye tana lumshe idanunta, bawai haka tasu ba, ba kuma hakan ta buƙata ba, yaronta namiji guda ɗaya tal a duniya ta yi masa buri da kwaɗayin auren ƴa gidan manyan mutane, wacce ubanta yake wani a garin nan a Jihar ko a ƙasar bakiɗaya. Sai gashi ya ɗakko wacce tsabar takaici bata iya tsayawa ta tambayi wacece ita ba, balle ta san ƴar wacece. "Ina so a yi mini iso wajan Baffa" "Baffa...." Umaimah ta maimaita "Sayyadi Baffa kake nufi?" Cikin sauri matashiyar yarinyar dake zaune taja idanunta ta lumshe su, ji ta yi duk wani raɗaɗin zuciyarta ya kau, nauyin da ƙirjinta yake mata ta ragu wani sanyi da nutsuwa na saukar mata a jikinta ta dalilin kiran sunan Sayyadi Baffa da aka yi. Ta ɗauke kai gefe guda tana murmushi duk sun lura da hakan suka share. Alhaji Sadi ya ce "Ina son ganawa dashi ne" da mamaki Umaimah ta dube shi kafin ta ce "Babu shi aka je neman auren na Liman daman Alhaji Sadi?" "E, daga ni sai Sheikh Nurain da Malami da Alhaji Huzaifa Abdallah muka je tafiyar ai" "Na ɗauka girma da ƙimar Baffa suka duba wajan amincewa da batun auren Liman? Ashe dai kawai.....," cikin sauri ya dakatar da Hajiya Umaimah da faɗin "Mu bamu wadatar mu nema wa Liman aure ba sai dole akwai Baffa a ciki tafiyar? Ko mu ƙima da mutuncin ne bamu dashi? Sayyadi Baffa ɗa ne kawai a wajan Sheikh Hafiz Hafiz Baffa, mu kuma ƙannnen Sheikh Hafizz ne idan kika ɗauke Alhaji Huzaifa da yake yayanki, kenan duk wata martaba da kike tunanin Sayyadi Baffa na da ita sai data fara shafar mu kafin ta ruski inda Sayyadi Baffa yake" Hajiya Umaimah kallon shi kawai take yi ganin yadda ya juya mata manufarta a fili. "Alhaji Sadi ko dai kana son faɗa..," ya katse da faɗin "Babu abin da zan faɗa miki Hajiya Umaimah wanda ya shige ce miki an bawa ɗanki Liman auren yarinyar da yake so" Ta jinjina kai da girmamawa ta ce "Na gode" Alhaji Sadi ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin barin haɗaɗɗan parlourn ƙasan da ya gama gajiya da haɗuwa wanda shine main parlour na kowa da kowa. "Barka da Safiya uncle" kamilalliyar muryarsa ta riga shi zuwa "Yawwa Mu'allim kana gida ashe?" Hannunsa ɗaya cikin aljihun wandon shaddar jikinsa sai ƙamshi yake da nutsuwa da kulawa ya ce "Ina hutawa ne" "Ga Liman nan ya tura maka Buzu" Uncle ya faɗa da sigar zolaya a fuskarsa Mu'allim yaja idanunsa ya lumshe bayan ya zauna a kujera ya rungume hannunsa a ƙirji bai fahimci maganar Alhaji Sadi ba a gajarce ya ce "Buzu kuma Uncle?" Uncle Sadi ya ce "E, kuɗin aure muka kai masa yau ɗin nan, nan da wata Biyar za'ayi auren Liman fa" Mu'allim ya jinjina kai yana ciro wayarsa a cikin Aljihu a tausashe ya furta "Ahky yana da budurwa daman har ake maganar Nikkah?" Uncle Sadi ya buɗe hannayensa wajan faɗin "Yanzu da ta yi wari ba gashi kowa ya ji ba? Sai fatan Allah Ya sa Albarka" "Sayyadi Baffa yana sashensa ne?" "Ya je Da'awa" Mu'allim ya bashi amsa. "Wanne gari? Wacce ƙasar?" Gabaɗaya suka juya a tare suna kallon Azizah wacce tun ɗazo laɓɓanta suke rawar tambayar son sanin inda Sayyadi Baffa ɗin yake, gida ɗaya suke rayuwa dashi, amma ta kusa wata ko fi bata sanya shi a idanunta ba, ko motsinsa bata ji. Babu ma wanda yake jin motsin Baffa ɗin daga Nadiyah sai Diyanah sai kuma Mu'allim Hafiz Baffa ɗin. Makomar baikonsa da yake kanta take son sani sama da shekaru Biyar amma babu wani cikakken lamarin da zai iya bata tabbacin zata zama mata a wajan shi, zata zama uwar da zata cigaba da kulawa da rayuwar yaransa Nadiyah Sayyadi Baffa da Diyanah Sayyadi Baffa, tana son ta maye gurbin murgayiya matarsa Diyanah Hafizz Hafizz Baffa, wacce a tunaninta rashin Diyanah ɗin a rayuwarsa shine ya hana shi aure. Damuwarta ɗaya ce, yana son ta? Yana jinta a ran shi kamar yadda itama take jin idan yaƙi aurenta za ta yi silar ɗaukan rayuwar duk wacce zai aura a matsayin mata. Ko kuma yana jin kamar ya tsufa ya girma da auren ne saboda tagwayen yaransa da suka zama Ƴan'mata? Ta sani Dattijo ne shi, amma irin su ne ake kira da Suger Daddy. Babbar hujjar dake sawa Azizah ta ji ta karaya da komai yadda tunda take zaune a gidan sama shekaru biyar bata taɓa ganin kamannin Sayyadi Baffa na, hatta ƙwayar idanunsa kodayaushe suna cikin glasses ne, ko a photo babu kamarsa, duka gidajen t.v da suke ɗora Wa'azinsa live ko recording babu kamanninsa. "Na shiga uku" "Maganin shiga uku Allah" Hajiya Umaimah ta bata amsa tana watsa mata harara ta gefen ido. Mu'allim ya ce "Wajan Nadiyaah da Diyanah kawai zaka san inda Baffa ya je uncle" "Bari na je wajan nasu daman zan duba jikin Nadiyah Sayyadi Baffa, sai na ji bayani a can" Mu'allim ya miƙe yana nufar sashin mahafiyarsa ya ce "Laba'sa Uncle" daga nan Uncle ɓangaren yaran Sayyadi Baffa ya nufa *** Da ƙyar ta samu shigowa Bright Fm ɗin yau idanunta a kumbure saboda kukan da ta yi a dalilin cire sunanta da aka yi aka saka na Yussy, gashi labarin ya hau iska sai positng ake yi a social media bayan Yussy ta ƙirƙiri photon Malam Sani da Maryama da Talatuwa sai jaririn a Ai. Mutane nata sharing suna jinjina mata wasu a dalilin hakan suke following page ɗinta. Ahlam ta yi kuka ta ji raɗaɗi da ƙuncin zuciya sai da ta yi kamar ta ajjiye aikin. Da ƙyar Engineer ya saka ta a gaba kamar yarinyar goye yana lallashinta kafin ta haƙura ta janye. Program ne da ita amma bata da nutsuwar yi, dole Anees ya karɓeta ta hanyar amsa tambayoyin masu saurare da sanya musu waƙoƙin nishaɗi, mutane da yawa Golden voice kawai suke tambayarsa sun fi jin daɗin muryarta a program ɗin. Bisa dole ta amsa. "Mita 116 kuke sauraro, Bright Fm Redio mitar zamani tashar zamani...," Sai ta numfasa "Me sauraro barka da rana, barka da wayewar garin yau. Golden voice ɗinku ke tare daku a daidai wannan lokacin, kuma zan cigaba da kasance daku har zuwa lokacin da abokiyar aikina zata amshe ni..." Nan ma ta sake yin shiru, Anees ya zuba mata idanu yana murmushi. "Ehmn. Ko ina kake, ko zaka, ko me kake yi ka tabbata ka kasance da Golden voice domin mu yi nishaɗi tare, mu ilimantu a tare. Kiran farko dawa muke tare?" Daidai lokacin da Ahlam ke yin program ɗin Anees ya saka a live mutane sai ganin kyakkyawar fuskarta suke. Daga gefe guda shima wayarsa me ƙirar Tap tana hannunsa a hankali ya numfasa kaɗan kafin ya juya ya kalli na kusa dashi ya ce "Wacece ita?" "Ahlam Abdallah Kurmi sunanta tana aiki a Bright Fm Rd" Ya ɗan yi jim can ya ce "Ina son ganinta, a nemo mini ita immediately" "Yes sir" *** 1976. TIVLAND. Da ƙyar Dooshima ya danne zuciyarsa saboda sosai kukan Anum ɗinsa wacce yake so fiye da kowa da komai a duniyar yake hargitsa masa lissafi, idan ka cire Anum Jarumi shine abi mafi soyowa a zuciyar Dooshima idan yana buƙatar kasancewar su a raye dole ne ya ɓoye su kamar yadda aka saba wannan gudun tsira da ran a duk sanda Sojoji sukai musu wannan zuwan na bazata. Ya saka hannunsa ya share zufar dake bin fuskata yana kokarin mayar da hawayen idanunsa. Yana zuwa ya tarar Kaka baya harabar wajan sai ya nufi ƙofar gidan da suka ɗan zagaye. A ƙofar ya tarar da ɗan'uwansa Haan hannunsa riƙe da kibbau, daga can ɓangaren ya hangi iyalan Imande. Ikur da Imande family ɗaya ne, kaka ɗaya ne ya haifi iyayensu. Kamar yadda Kaka ya haifi Dooshima da Haan haka a ɓangaren Imande mahaifinsu ya haifi Terhemba da Uji, da Kaka da Ityo uba ɗaya ne ya haife su, duk da sun fito daga ciki guda amma kowa yaja iyalinsa ya raɗawa iyalin sunan da suke ganin ya dace dasu. Akwai bambanci hali da ɗabi'a a bayyane, Imande sun kasance masu son zuciya da zafin rai, suna da mugata tare da ƙetar dasu kan su basu san adadinta ba. Wannan dalilin ya saka suke da burin ganin duk abin da zai zo na samu da ci-gaba ya fito daga ɓangaren Imande kawai banda iyalan Ikur. Wajan ya ɗauki shiru sai kaka ne ya dubi Sojojin da fahimta da nutsuwa ya ce "Kuna ganin tsoron da kuke ƙoƙarin sakawa zuƙatanmu zai saka ku samu abin da kuke so ne? Mun rasa rayuka masu yawa saboda ku, ku bari mu yi rayuwa yadda muke so" Wani soja ya ce "Naga kamar kana da fahimta Dattijo, ƙarasu nan mu yi magana" "A'a Kaka kar ka ƙarasa" Kaka ya juya ya kalli Dooshima sai ya yi murmushi me kamala ya ce "Na yi imani da Aondo, babu abin da zai faru Dooshima" Haan ne ya ce "Kaka suna ƙoƙarin kawo mana sauyi ta hanyar hana mu amfani da Addinin gargajiya ((Traditional beliefs)" Kaka ya ce "Haan!" "A gafarce ni Kaka, Aondo ya bayyanar mana da UWA MAMAA mu huta" Sojan ya ce "Ba cutar daku za mu yi ba, sauyi za mu kawo muku wanda zai taimaki rayuwarku, a cikin jeji kuke rayuwa babu ilimi, baku da addini guda ɗaya da za ki ce shine kuke bi, ina so ku amshi addinin Yesu Almasih, a kafa muku gari a sanya masa suna, a gina muku makarantu, da kasuwanni na ƙawa da jin daɗin rayuwa, a baku dama na shigowa sabgar siyasa a ware muku yanki guda tare da wakilcin mutum ɗaya da zai jagorancin dukkan ƙabilar Tiv" Uji daga ɓangaren Imande ya ce "Mutum ɗaya da zai mulki jama'ar Tiv? Kenan bamu da ikon yin abin da muke so sai bisa sahalewarsa? Ka bamu hujjar da zamu yadda" babu wasa a fuskar Sojan ya ce "A shekarar 1976, Najeriya tana ƙarƙashin mulkin soja, bayan kisan shugaban ƙasa Murtala Mohammed. Wannan ya kawo sauye-sauye da dama, ciki har da: Ƙirƙirar sabbin jihohi Inganta tsarin mulki da gudanarwa rasirin gwamnati ya ƙara shiga cikin yankunan karkara, ciki har da Tivland, har daku ƙabilar Tiv ɗin" "Bamu yarda ba, bamu amince ba" Dooshima ya yi furucin saboda wasu kuskure daya hango. Akwai soyayya mai girman gaske tsakanin Imande da Ikur family. Sai Uji ya ce yana buƙatar magana da shugaban sojojin, suka je gefe guda tare da yin magana. Bayan sun kammala sojan ya kalli Dooshima ya ce "Ina son na nuna maka komai a bayyane na tsarin da muke son kawo muku ka biyuni mu je" Dooshima ya juya ya kalli Kaka da Haan. Dooshima ya ce "Zan je, ka kula mini da Anum kafin na dawo, ka riƙe ta ita da Jarumi a wajanka ɗan'uwa Haan" Haan ya ce "Aondo na tare da kai" Dooshima motar sojojin ya shiga ta “trucks, jeep” wacce suka zo da ita saboda hanyoyi basu da kyau akwai “dirt roads” Suna tafiya Terhemba ya kalli ɗan'uwan nasa da suke uwa ɗaya uba ɗaya Uji ya ce "Kamar kun ce wani abu da sojojin nan ko?" Uji ya ce "Ka yi tunani Terhemba, idan za'a sake fitar da mulki a Tiv Imande sune mafi cancanta, muna buƙatar hakan idan Dooshima yana nan, ba zai bari mu samu cigaban zamani ne, na yi abin da ya kamata" "Me ka yi?" Terhemba ya tambaya da tsoro. Sai Uji ya buɗe hannunsa ya ce "Na siyar da Dooshima, na siyarwa da sojoji shi matsayin Bawa" daidai nan wata iska ta karaɗe wajan da wani ihu da gurnani mara daɗin ji, iskar na lafawa suka fara ganin mutane na faɗuwa ƙasa matattu fiye da mutane 20. A tsoron Kaka ya ce "An sake yin abin kuskure wannan bala'in ba zai lafa ba zai UWA MAMAA ta bayyana" ya juya da sauri ganin gidansu na rushewa yana shigewa ciki. "Anum Jarumi, suna ciki" Haan ya faɗa a gigice yana nufar ciki da sauri Kaka ya riƙe shi ya ce "Sai haƙuri amma mun rasa su" ***A hankali take juya kanta da ya yi mata nauyi tana fuskar numfashi da ƙyar ƙoƙarin tashi take yi amma kamar an saka dutse an danne ta haka take ji, kamar me shayar da yaro haka take ji ana sha mata Nono wata zufa ta wanke mata jikinta, ilahirin jikinta ciwo suke mata gabar an saka abu an mata dukan tsiya ga wani irin sanyi da gaɓɓanta sukai mata. Duk yadda take ƙoƙarin buɗe ido da dakatar da abin da yake faruwa da ita ta kasa, ji ta yi ba zata iya tashi ba, an danne ta sosai ta kowanne ɓangare a jikin nata. "Ayshatu" ya kira sunanta yana kunna hasken ɗakin asibitin da take ƙwance. Sai ya yi turus ganin zanin jikinta a bankaɗe sai motsi take amma ta kasa buɗe idanunta. Babban yaya ya koma gida balle ya kira shi shine muharraminta sannu a hankali ya fara takawa zuwa inda take ya ranƙwafa kaɗan ya ce "Nanaah" a hankali ta buɗe idanunta ta sauke ganinta akan Haysaam ɗin. Luu taja idanun ta lumshe su. Hannunsa ya saka me taushi a saman goshinta ya share mata zufar wajan ya gyara mata zanin jikinta ita kuma ta tsora masa ido, kamar me son gano wani abu a fuskarsa sai ya ɗan kashe mata ido yana ja baya saboda har zuciyarsa kallon ta ke saukar masa da wani irin yanayi. A hankali ya ji ta ce "Yaa Sam" "Na'am, menene ina ke miki ciwo?" Ta girgiza kai sai kuma ta nuna masa tsakiyar ƙirjinta ta ce "Ina Anum da Jarumi? Ina aka kai Dooshima Abban Anum?" Ganin ya yi shiru ta sake kallon shi ta ce "Da gaske Anum ta rasu ne.... Haysaam ya yi jim ya ce "Su waye haka?" Sai ta yi masa shiru tana tuna abin da ta ji bayan mafarkin da ta yi, a cikin mafarki Babban yaya ne ta gani yana sha mata ƙirji... Today's HIYAAM sponsor is Annoor Foods your trusted choice for healthy and delicious food. Kamfanin da suke haɗa garin ɗan wake, garin funkasu, garin kunun Aya, Zobo mix yaji dakan hannu. Duk garin da mutum yake zai biya Rabin kuɗin delivery ne mu mu biya rabi. Kayan ANNOOR FOODS, ingantattu ne masu kyau da tsafta. Ku tuntuɓi wannan number. 09075181211 HIYAAM dama ce ga masu Business da za su yi sponsoring mu kuma mu tallata musu kayansu har zuwa facebook. Ga duk me buƙata ya yi magana a wannan number 08164069385 *H I Y A A M* Page 8: Tajmahar Palace Bright pens Yota/001 "No one be like you" Nazeefah Sabo Nashe Ganin ta zuba masa idanunta masu tasiri a jikinsa da zuciya ya sake ɗan ranƙwafawa ya share mata zufar fuskarta yaja hancinta kaɗan ya ce "Na ɗaga ki ne ki yi breakfast?" Sai ta girgiza masa kai kaɗan tana lumshe idanunta ƙirjinta na ɗagawa sama-sama da sauri ta buɗe ta ce "Yaa Sam ciwo nake ji" Da damuwa ya ce "A ina?" "Nan" ta nuna masa mararta. "Sosai take mini ciwo, ina jin ciwo Yaa Sam" Ya yi jim cike da tausayi yana jin duk wani pain da Ana take ji a zuciyarsa kamar tare suke raba damuwa da raɗaɗin, duk farincikin da yake ciki muddin ya yi arba da fuskarta ya hangi damuwa zai ji bashi da saurin wani farinciki. "Sorry jerryna" ya faɗa a tausashe da laushin muryar nan tasa me cike da nutsuwa da kamala, ganin yadda take ta zufa ya saka ya ɗan miƙa bakinsa kaɗan ya hura mata iska yana me share mata zufar ita kuma sai bin fuskarsa take yi da kallo tsinin hancinsa tafi kalla fiye da komai, da yawan lokaci shi da kan shi Haysaam yana mamakin irin kallon da Ana take binsa dashi, ta haddace ”Anything and everything” da yake fuskar tashi. "Ka yi brush?" Ta ce a hankali. Sai ya tsaya ba tare daya kalle ta ba "No, ya akai?" Ya bata amsa after a few seconds. Taja ido ta lumshe su "Na ji warin bakinka ne" Ta ce tana kakkafe shi da manyan idanunta sai kuma yaga tana murmushi da lumshe idanunta alamar wasa take masa "Uhm, tashi ki yi breakfast" "Ka fasa tafiya Lagos ɗin?" "No" ya ce a gajarce bayan ya ɗagota zaune. Tana ta kallon shi kafin ta ce "Zaka dani?" Ya ji me ta ce, sai ya share ya ce "Me za ki ci kafin ki sha maganin?" Ta yi ƙasa da kanta bata ce komai ba, baya ya yi kaɗan ganin tuni lokacin shigowar likita ya yi ma, yatsu biyu ya saka ya ɗago haɓarta abin da bai zata ba ya gani, kuka take yi kuka mara sauti sai hawaye ne suke zuba daga cikin idanunta suna sauka a fuskarta a hankali. "Nanaah.... "Jerry" taƙi amsawa. "Menene? Jikin ne ? Ban son kukan banzan nan" "Bana son mijin Innti, bana son ganinsa Yaa Sam ka tafi dani na zauna a wajanka ka ji" Ganin da gaske take yi sai ya saka yatsu biyu yana goge mata fuska, sosai su Ana suke cikin talauci, wannan shi ne karo na farko kuma daya taɓa ɗora hannunsa a jikinta laushin da taushin fuskar Ana ya ɓaci, kodayake bai ci ya yi mamaki ba, sabulun wankanta, man shafawarta, turaran fesawa duka Haysaam ne ya ɗauke responsibilities ɗinsu. "Shikenan, fara cin abincin" "Fitsari nake ji" ta ce tana kumbura fuska. "Ok. Na kai ki toilet ɗin kenan?" Sai ta yi saurin juyowa ta dube shi, ya ɗaga mata gira. "To kai ni" ta ce tana bubbuɗe idanunta yana miƙewa da tattara hannun Jallabiyarsa kafin ya yi aune ta miƙe ta shige toilet ɗin tana sakin ƴar ƙara "Auchhii" *** Tsit cikin dajin ya ɗauka babu ƙarar komai sai ta tsuntsaye da suke kuka a saman bishiyoyi. Daji ne me duhun gaske da hatsari wanda yake da wahalar fahimta kai tsaye. Daga gefe guda kuka ne yake tashi daga muryoyi daban-daban, kai tsaye muryoyin sun nuna alamar gajiyawa da wahala da gazawa da gangar jikinsu ya yi. A hankali ya fito daga cikin rumfar da suka kafa ta ƙawa da hutawa, cikin nutsuwa da gadara yake taka ƙafafuwansa da suke cikin wani kyakkyawan takalmi baƙi a ƙasan wajan. Kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka fahimci bai haɗa hanya da imani a zuciya ba, fari ne irin farin nan mara shiga ido, sumarsa har baya baƙa suɗik da ita, sick pack ɗinsa a bayyane yake yana ɗan motsawa ƙirjinsa yake fara rawa. Ash ɗin riga ce a jikinsa armless wacce ta saka rabin ƙirjinsa bayyana. Daga gefen wuyansa rubutu akai da zane na baƙi inda aka rubuta Triplets-T, iya wannan ne ya bayyana sauran riga ta rufe su. Yana fitowa sauran yaran suka mimmiƙe tsaye daga sabgogin da suke yi. Ɗaya daga cikinsu ne ya kalli wanda ya fito ya ce. "Ya kamata mu bar wajan nan soon fa" Sannu a hankali ya juya ya kalli wanda ya yi maganar ya ce "Kana bani umarni ne?" Sai ya girgiza kai. Ya ce "Akwai matsala ne Oga Hunter shi ya sa" Wanda aka kira da Hunter ya saka hannu wajan zare glasses ɗin idanunsa ya jim for a while kafin ya numfasa ya ce "Zaman nan ɗin akwai nishaɗi na ganin korayen tsirre, takura ɗaya ce babu sararawa, dole mu yi haƙuri tunda muna under control na T.T.T ne, sai an cika aikinsa za mu tafi" Jago ya fesar da numfashi can ya ce "Triplets-T, sa baka da dariya sai hamma, uban mazaje maganin mara kunya. Hunter yanzu ya ake ciki ne?" Sai ya ɗaga kafaɗa alamar rashin sani. Ya cigaba da takawa har zuwa inda tarin jama'ar suke, yawancinsu Fulani ne, manoma da makiyaya sai ɗaiɗaiki. A gaban wata dattijuwar mata ya zauna yana kallon ta wacce ta gama fita daga hayyacinta bata iya buɗe idanunta sama-sama haka numfashinta yake fita. Ya zaro chigger daga alijuhunsa ya saka leta ya kunna yana fesar da hayaƙin a fuskar matar. Ya muzar kaɗan. "Dattijuwa to ya? Are You in or out?" Ya zuƙi tabar ya fesar kafin ya ce "Kina da rayuwar ƴanci a gaba idan kikai mana yadda muka so, bama buƙatar ko kwabo don ba mu yi kama da ɓarayin jama'a ba. Abu ɗaya mukai requesting, ki fita daga cikin Addinin Musulunci, kina fita daga Muslunci za ki samu rayuwa me kyau da tsaf a tattare damu" Tana daga ƙwancen ƙirjinta na ɗagawa ta tofa masa yawon cikin bakinta wanda da ƙyar ta tattaro shi, laɓɓanta ya tsage yana zubar da jini ta ce "Allahu ahad, Allah ɗaya ne, kuma shine ya turo mana da Addinin Musulunci ta hannun Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, mabiya addinin Islama sune akan daidai muna kan daidai" ya miƙa hannunsa zuwa kan fuskarsa ya lakato yawon bakinta data tofa masa. Ya murmusa kaɗan ya ce. "While......... Sai ya juya zuwa bayansa ya ce "Jago, wai ta ce ba zata fita daga addinin musulunci ba, me ya kamata a yi?" Wanda aka kira da Jago yana tattare belt ɗin wandonsa bayan ya fito daga wani lungu da wata yarinya wacece ya ci mutuncinta ya barta a wajan ya saki dariya. "Hunter wannan hukuncin yana hannunka ai, me girma Triplets-T ya bar komai a wajanka har zuwa sanda zai shigo ciki" Hunter ya kalli matar ya ce "Hajju kin ji fa? Try your best kina da last chance na kasancewarki a raye, fita daga Muslunci ko rayuwa me kyau" "Allah ɗaya ne, bashi da abokin tarayya, bai haifa ba, kuma ba'a haife shi ba, shine ya samar da Addinin Annabi Isah ɗan Maryama, kuma a bayan Addinin Yesu, ya kawo mana Addinin Musulunci, Addinin ƙarshe, Annabin ƙarshe, zamanin ƙarshe. Na shirya mutuwa akan addinina, ban san dalilinku na san raba mu da addininmu ba, ko ma mene idan addu'ar Ubangiji Ya hana ku cimma burinku, Allah Ya wulaƙantaku, Allah Ya ɗaukaka Muslunci da Musulmai" ta faɗa da wata murya me cike da alfahari jikinta na ƙara samun ƙwarin gwiwa tana jin babu wani mutum daya isa ya rabata da Addininta. Hunter ya yi baya kaɗan, a hankali ya ɗora hannunsa a daidai gaban wandonsa ya janyo shi kaɗan, har ana iya ganin ƴar kwantattun sumar mararsa ya shiga rawa da juyi kaɗan, idan ya ɗan tura gaba sai ya yi baya. Yana rera wata waƙar Square. Jago dake gefe ya shiga murmushi yana rungume hannunsa. Sannu a hankali ya daina rawar ya kalli Jago ya ce "Wa'azi take mana fa Jago, zaka jure ji ne ko yaya?" Jago ya ce "So boring gaskiya" Nan da nan Hunter ya haɗe fuska kamar bashi ya gama waƙa ba, a wannan lokacin duk wanda ya kalli fuskarsa sai ya girgiza ya ji gabansa ya faɗi ya ji kuma kamar ya saki fitsari a wando. Ya durƙusa gaban matar, ya zuba mata fararan manyan idanunsa kafin ya zaro wata kaifaffar wuƙa a ƙugunsa me kama da zarto, ganin hakan ya saka mutanen da suke ɗaure suka fasa gigitaccen ihu, suna rungume na kusa dasu, ƙafa ɗaya Hunter ya saka ya danne kan matar ya saita wuyanta daidai maƙogaranta ya shiga yanka wuyanta, zillo take jini na feshi ta wuyanta, bata gushe ba tana ambaton Allah da kalmar shahada tare da yin kaffa tare da shure-shure har rai ya yi halinsa. Yau sun kashe mutane wajan goma akan ƙin fita daga Musulunci, da yawansu kuma waɗanda aka kashe Fulani su gaba da baya. Jago ya ce "Ga wata fara kyakkyawa can, ko za'a kiwatawa Triplets-T ne ita?" Hunter ya juya ya kalli yarinyar wacce ta ƙurawa gawar mahafiyarta idanu sai ya girgiza kai ya ce "No need, ba layinsa bane, ya dai bada umarnin duk matan da suke wajan ko ba'a kashe su ba, a tabbatar sun san namijin a gun nan so idan kana ra'ayinta go ahead" Jago ya ce "Kai baka da ra'ayi ne ?" Hunter ya tattare girarsa biyu ya ɗage zuwa sama kafin ya ce "Tawa tana can duk runtsi zam koma gare ta, Ayshatuna matar Hunter yaron T.T.T. na hannun damar Triplets-T" yana faɗin hakan ya koma cikin rumfar daya fito. *** TAJMAHAR PALACE. Shirun da masarautar ta ɗauka na yau na musamman nan, ba sai an yi shela an faɗawa mutum wani abu na musamman yana faruwa ba, duba da yanayinsu manyan jami'an masarautar da suke tsaye tun daga gate na farko har zuwa na huɗu. Masarautar Tajmahar ba kawai masarauta ce ba, duniya ce gudu ta musamman, masarautar da take da iko da zartarwa, masarauta ta zamani da kayan ƙawa. Ginin golden ne da ita me haske da ɗaukan idanu tun daga sama an rubuta TAJMAHAR PALACE. Doka ce aka saka tun satin daya shige, an rufe shiga da fitar mutane, idan kana cikin Tajmahar kar ka fara yunƙurin fita, idan kana waje kar ka yi tunanin shigowa ciki, wannan umarni ba iya na jama'ar garin bane, hatta hadimai, bayi, barori, da ƴan majalisa na fada umarnin ya hau kan su, ba iya su ba, hatta jinin Tajmahar wannan ƙararrawar umarnin ta hau kan shi. Tor Tiv ne kawai me yin yadda yasu a daidai wannan lokacin. Sannu a hankali ya fito daga ɓangarensa, yana taka ƙafafuwansa kamar baya son taka su, duk inda ya ɗora ƙafarsa ɗaya sai ya ɗan jira, da yawan lokaci wannan izzar da gadara bata biya damunsa ba, sai ya sako ƙafarsa zuwa Tajmahar, jinin Tajmahar ya ƙara sanar dashi waye shi, matsayinsa da abin da yake jira. Farar fatarsa me ɗaukan ido sai sheƙi take yi ta dalilin wuyan da yake sakkowa daga gashin wuyansa yana sauka a fatar wuyansa tare da sakkowa jikinsa. Garden za shi, har ta gilma ya ɗan ja ya tsaya, ya ɗauki lokaci yana kallon waje guda kafin ya juya zuwa inda ya ganta zaune ɗaure da sarƙa a jikinta. Jikinta duk ya farfashe jini na zuba a jikinta, gashin kan nan nata a diddige, wannan shine karo na uku yana ganinta, dukkan bayin Tajmahar ai ba'a nan suke ba, me ya sa aka fito da wannan waje ne? Miƙewa ta yi a hankali ta fara tafiya duk inda ta taga jini take bari shaida. Har zai shige sai ya dubi wani badakare, cikin sauri badakaren ya yi ƙasa da kan shi sai kuma ya ce "Umarninka biyayya ne Madaki" Wanda aka kira da Madakin ya juya ya cigaba da tafiya yana jin bugun zuciyarsa na ƙaruwa. Tun kafin ya kai waje ake yin ƙasa da kai tare da rusunawa har ƙasa, a haka ya shige hadaɗɗan garden ɗin yana shiga ya ƙarasa kan wata kujera wacce take a kwance ya bi kan kujerar ya kwanta idanunsa na kallon saman masarautar Tajmahar ɗin. *** Duk da sanyin safiya ne wajejen 11:30 bai hana su jeruwa a majalisar da suke zama koyaushe suna sana'ar tasu ta karta ba. Su wajan biyar ne yanzu ma, Alhaji Baita, Daada, Ɗahe sai Garbati na ƙarshen kuma Sadisu. Tsofaffi ne masu iyalai da kuma shekaru sai dai sun lalata tsofan su wajan son abin duniya da kuma aikata saɓo. Daada ne rangwamen shekaru a cikin su. "Daada ko dai kana jin tsoro ne?" Garbati ya yi furucin yana daidaita zaman shi tare da kallon katin kartar dake hannun Daada. Yau ne suke yin cacar da Daada ya saka Iftihal a ciki, don haka wasai Daada yake jin zuciyarsa yana hasaso kan shi nan da mintina biyar ko goma ya zama mamallakin Naira biliyan Ashirin cif. Sai murza raguwar katin daya rage a hannunsa yake me alamar Square 2 sai ya jinjina kai Ya ce "Garbati me kake ci na baka na zuba?" Cikin sauri Garbati ya ce "Ɗoki da zumuɗi mana" "Muje zuwa" Alhaji Baita ya furta yana cilla Square 1. Bayan ya saka ya dubi Daada ya ce. "Zagayenka ne abokina" ganin alamar nasara a tattare da Daada sai ya yi murmushin daɗi da farinciki Ya ce "Nasara tawa ce" "Ina maka fatan samun ta" In ji Alhji Baita ya yi masa raddi Daada ya cilla Triangle 1 . Sai ya rasa juyinsa don haka ya yi hold on. A tunaninsa Alhaji Baita bashi da sauran katuna ya yi murmushin jin daɗi ya ce "Na rasa katina, na yi nasara" ya fara miƙewa tsaye da shirin ɗaukan jakar. "Last card!" Alhaji Baita ya faɗa yana ajjiye katin hannunsa, Daada babu yadda zai yi yana ji yana gani Alhaji Baita ya saka katin kuma ya yi nasara. Zufa ta shiga yankowa Daada a kowanne ƙofa na gargasar jikinsa. Ba wai murnar kuɓutar da ƴarsa yake yi ba, baƙincikin rashin samun miliyan ashirin ɗin ita take ƙoƙarin ganin bayansa a yanzu. "Kuɗina ya dawo, kuma na ci yarinyarka a caca Daada, ba tare da kowa ya ji ya gani ba, ka shirya ƴarka ka kawo mini ita gidana a matsayin yarinyar da na ci a caca finally" ya faɗa da murna yana tattara kayan. Daada ya kalli Alhaji Baita da jajayen idanunsa na makakku ya ce "Kutumar, kana nufin ka tafi da miliyan ashirin ɗin kuma na baka yarinyar da nake kallo matsayin jari? Ai da na baka Iftihal gwara na kama mata hayar shago a sabon gari ta dinga samar mini kuɗi, daman na jima da wannan burin" "Ka yi ƙarya, ka kuma kwana da yunwa Daada" Alhaji Baita ya miƙe tsaye yana kallon Garbati ya ce "Ɗakko mini yarjejeniyar nan Garba" cikin sauri ya fito da ita, Alhaji Baita ya amsa ya nunawa Daada. Ya ce "Wasan WHOT wasa ne na haramci wanda idan jami'ai suka ji za su kama mu, kaina talaka kai zaka dauwama a wajansu bani da asara ni kam. Ina baka shawara bakinka a laikum ka je ka fito mini da ita" "Na baka Iftihal a matsayin me?" Cikin isa da izza Alhaji Baita yana dariya ya ce "A matsayin yarinyar da na ci a caca" Dadda ya haɗiye wani abu me ɗaci a maƙoshi yana ayyana yau har Innti ta shiga uku a wajansa. "Na ji, ina nufin aurenta za ka yi ko me? A matsayin me za'a kaita" "Ko a matsayin mene baka da ruwa da tsaki, zan dinga hutawa ne a jikinta ba wani abu ba" Kallon Alhaji Baita kawai Daada ya yi kafin ya juya ya bar wajan. "Kar ka manta" Cewar Alhaji Baita "A daren nan za'a kawo ta bani da haƙurin jira na gama kaiwa geji" WHOT wasa ne na katuna da ake yi domin nishaɗi ko gasa, inda mutane ke ƙoƙarin ƙare katunansu kafin sauran ƴan wasa, wasu na ce mata wasan karta wasu caca suke kiranta dashi a turance kuma ana kiranta da WHOT. Wasu na yi domin nishaɗi wasu kuma suna saka kadararsu na abin da suka mallaka a ciki. Idan ka yi nasara ka ciyo abin da ba ka yi tunani ba, idan ka yi rashin sa'a za'a cinye abin da ka saka. Kamar yadda Daada ya saka ɗiyar cikinsa a cacar kuma aka yi nasarar cinta. Hukuncinta a shari'a ya bambanta, Idan ana yin Whot da kuɗi (caca)Wannan yana shiga cikin abin da ake kira Maysir. A Musulunci, an haramta caca a fili haramun ce ta kowacce siga kamar yadda dalilai suka zo a cikin Alkur'ani mai girma, caca tana haddasa rikici da rigimar da zata iya yin wa'adin ran wani, tana hana ibada akan lokaci wasu basa yi, tana cin dukiyar mutane ba bisa ƙa'ida ba. Duk kuɗin da mutum ya samu a Whot ko ya mallaki wani abu, ba zai taɓa zama halak ba, waɗannan abubuwan sun zama haram a gare shi. Wasu kuma Malaman suka ce, Whot idan ana yi da sigar nishaɗi suka ce babu haramcin muddin bata hana mutum ibada ba, wasu kuma suka ce makruh ne (ba a so), saboda tana iya kai wa ga yin cacar yana iya ɓata lokaci. Kamar zai tashi sama haka Daada ya nufi hanyar gidansa sai surfa bala'i yake kamar zai ciro bakinsa ya ajjiye a ƙasa. Bugo ƙofar da ya yi ya saka zuciyar Innti bugawa da ƙarfi, salati ta saki saboda tsabar yadda take tsoron ganinsa ko shigowarsa cikin gidan. Yana shigowa Iftihal na fitowa daga cikin ɗaki sanye da uniform zata tafi makaranta. Jikinta na rawa ta durƙusa ta ce "Ina...," Bata ƙarasa ba ya sakar mata wata uwar tsawa da faɗin "Gidan ubawa za ki da safiyar nan?" Kanta a ƙasa dukkan jikinta rawa da ɓari yake yi saboda tsananin tsoron daya gama ratsa mata zuciya bata taɓa jin tsoron wata halitta a duniya sama da halittar dake tsaye a gabanta ba, bata taɓa jin tsoron wani ba kamar yadda take tsoron mahaifinta Daada. Maganarsa faɗuwar gaba take haddasa mata, ko tari ya yi sai ta saka hannu ta dafe ƙirjinta domin ji take kamar zuciyarta ce zata faɗo ƙasa ta cikin ƙirjinta ba tare data shirya hakan ba. "Ke don ƙaniyyarki munafurci kika koya irin na uwarki? Mugun abu take koya muku ashe?" Ta girgiza kai a hankali ta ce "A'a Daada... "Makaranta zani muna exam ne" A hargitse ya ce "Dake da makarantar da uniform ɗin makarantar, da Malaman, da wacce ta saka ki makarantar Allah ya yi wadaranku tsinannu marasa amfani a duniya har ma da lahira, duk wani mugun abu kuma gama lashe shi a nonon uwarku" Wani irin runtse idanu Innti ta yi idanunta sun yi jajur ta kasa motsi, idan cin mutuncin Daada ne ta saba amsar shi a koyaushe a gaban yaran nata. Babu ranar banza ita ta rasa yadda wannan ƙiyayyar ta samo asali da tushe. Kamar ba haka yake ba, kamar kuma haka ɗin yake tun fil'azal. Ta fuski numfashi da ƙyar ta tuna kamar ta tuna. Zata iya tuna dalilin faruwar komai. "Bana son haihuwa Innti, bana son zuri'a Innti ban shirya mata ba, yara basa ɗaya daga cikin abin da yake birge duniyar Daada. Daga wannan cikin kar ki ƙara sakin jiki wajan ware ƙafa ki ɗauki ciki, shima wannan ɗin bana murna dashi, kuma ba zan ɗauki alhakin kulawa dashi ba na faɗa miki" Wannan sune kalaman shi na farko, lokacin data samu cikin Babban yaya ne, tun bata san me zata haifa ba a lokacin cikin yana watanni bakwai ne dab da zuwa duniya yaso zubar dashi ma, haƙarsa bata cimma ruwa ba. Tunda aka wayi gari da labarin cikin komai ya sauya komai ya zama labari. Zata iya tuna raddin data yi masa ma a lokacin. Kamar cewa ta yi "Daada ƴaƴa ai Rahma ne baka san me jin ƙan ka ba" "Assalamu Alaikum" Sallamar da aka yi ya katse ta daga tunanin abubuwan da suka shige, wata sabuwar faɗuwar gaban ce ta sake ruskarta. Uwar mijinta ce da kuma yayar mijin da ƙanwarsa. "Ina yini Emama?" Wani irin gatsine wacce aka kira da Emama ta yi ta dubi tukunyar da Innti ta dafa taliya ƴar murji jallof wacce ta ji ganyen albasa sai ta riƙe baki ta ce "Babu shakka ashe abin da nake ji na cewa kin shanye Daada gaskiya ne, ya tare a gindinki ke da yaranki har taliya kuke dafawa da wannan sanyin hantsin?" Innti ta kalli tukunyar tana mamakin shi Daada ne ya ce shi ya yi cefanen ko me? Sama da shekaru rabon da taga sisin kwabo nashi? Duk abin da yake dashi ko ya mallaka ya tafi a caca. Taliyar fa Haysaam ne ya kawo da saffafe ya ce su dafa a kai wa Shalale asibiti daga baya ma ya kira ya ce ya siya mata Rufaida da Shawarma. Shine za su azabtar da zuciyarta da wani baƙin cikin na dangin miji? Ita kam tana tunanin da ƙyar idan takaici da baƙin cikin namiji bai yi ajalinta ba. Ƙoƙarin magana take yi Baba ta kalli babbar ƴarta me suna Hanna ta ce "ke jeki juyo mini taliyar nan a faranti gabaɗayanta kin ji" "To Emama" Hanna ta faɗa cikin sauri. "Wallahi Emama Daada ya zama mijin tace a gidansa, komai ya samu yana gidan wannan matar data zame mana bala'i. Haka jiya dana biya ta wajan abincin Bala yake bani labarin cin mutuncin da wannan me suffar Aljanu ta yi masa, Ana" Emama ta riƙe haɓa ta ce "Ba shakka iskancin yarinyar nan da rashin kunyarta haka ya bunƙasa?" Daada dai ya yi shiru yaƙi cewa komai. "Liya ki daina suffanta ƴata da Aljanu" Kau! Daada ya ɗauke Innti da wani irin mari yana nuna ta da manuniyya ya ce "Ahir ɗinki. Ke kuma......" Ya juya kan Iftihal da take ta rusar kuka ya ce "Daga yau na haramta miki zuwa makaranta, kuma zuwa dare ki shirya akwai inda zamu dani dake" "Ba mu yi haka dakai ba, duk abin da za ka yi don Allah na roƙe ka sbd Allah ka tsaya iya kaina. Kar ka rusa goben yarana na sadaukar da komai saboda su yi karatu" "Wacce gobe? Har wata gobe suke dashi a nan? Ai indai cigaba ne a rayuwa sai dai su yi na me haƙar rijiya. Har abada yaranki ba za su taɓa zama wasu ba a rayuwa tunda suka fito daga cikinki" Kuka Innti ta fashe dashi tana wani irin fidda numfashi da kiran sunan Allah, yadda take kuka haka ma Iftihal ke kuka ta rarrafa wajan Daada ta riƙe ƙafafuwansa ta ce "Muna da buruka a karatunmu Daada za ka ji daɗi ta dalilinmu, kar ka bari mafarkina na zama ƴar jarida ya rushe, kar ka bari mafarkin Ana na zama marubuciya ya zama tarihi mun rayu akan mafarkanmu da burinmu don Allah kar ka tarwatsa mana su" ƙafa ya saka ya shure ta ya nunata da yatsa ya ce. "Har wani mafakar kike dashi?" Ya yi ƙwafa "Ni na riga na saka ki a caca kuma rashin sa'ar uwarki ta shafe ki wacce taja mini asara babu kuɗin kuma aka ciki" Cak! Numfashin Iftifal ya tsaya a ƙirjinta dumm haka ta ji wani abu yana mata amo a kunne kallon Daada kawai take yi da kallo na rashin fahimta. "Ka.. saka..ni a caca Daada?" Ta yi maganar a rarrabe tana dafe ƙirjinta. "La shakka kuma an ciki zuwa dare zan kai ki gidan Alhaji Baita, ban sani ba ko auranki zai yi ko kuma dai ajjiye ki zai yi kawai a gidan" 'Alhaji Baita?' ta maimaita sunan ba wannan tsohon bane me baki duk dauɗa wanda goro ya gama cinye masa haƙori har wata tsotsa ce take gani a bakin wannan Alhaji Baitan mai ciki kamar name shirin haihuwa shi ne za'a kaita gidansa a matsayin me? "Na shiga uku Daada ka yi mini rai" Ta fasa wani gigitaccen ihun daya saka Jadid dake kwance tun ɗazo saurin runtse idanunsa ya saka hannu ya dafe kai, fitowa yake son yi daga ɗaki abu ya ci tura saboda nauyin da jikinsa ya yi masa ga tashin zuciya da hakki da ƙyar yake iya buɗe idanunsa. A hankali hawayen da suka cika masa idanu suka silalo ta gefen idanunsa. "Allah ka ɗauki raina ko zan huta da ganin kuncin dake zuciyar Innti da ƴar'uwana" "Ka aurar dani idan kana buƙatar hakan amma Daada don Allah kar ka kai ni gidan mutum nan mutuwa zan yi, kar ka saka ni a caca. Ka duban girman Allah ka tuna mu jininka ne, ƴaƴanka ne ka tuna mu amana ne a gare ka watarana Ubangiji zai tambaye ka. Ka ji tsoron haɗuwa da Ubangiji Daada wallahi muna son ka muna ƙaunarka kai mahafinmu koyaushe muna jiran sanda zaka dawo mana da soyayyar da muke maka" ya ɗauke kai zuwa gefe bai ce komai ba. Emama ce ta kalle shi bayan ta tattara wasu kayan miya data gani a wajan ta ce "Zuwa na yi a siyar da rabin gidan nan a bawa Liya kuɗin zata tafi Saudia aikatau" "Wanne gidan?" Innti ta faɗa tana buɗe jajayen idanunta da ƙyar saboda faɗuwar gaba. Ta ɗora da faɗin "Kar ku siyar da gidan nan don Allah, idan Babban yaya ya tashi aure a nan zai zauna bamu da komai ku tausaya mana don Allah" Emama ta ce "Gidana ne sai an siyar shi Muradun ɗin aure aka ce za'a bashi? Wani ɗan iskan uba ne zai bawa wannan mara lakar ɗiyarsa? Da wacce sana'ar zai yi auren?" "Emama, wannan gidan gidana ne bawai na Daada ba, ki tambayi Daada ki ji" tana faɗin hakan ta shiga ɗaki tana dafe saitin zuciyarta dake mata ciwo da raɗaɗi. "Ohho dai. Ke kuma tashi aikatau na samo miki a wani gida, ko na kwana biyu ne ki yi kafin akai ki can gidan Baita ɗin, ba zan ɗauki wannan fitsarariyyar da zata iya ja mana bala'i a gidan jama'a ba" ta saka hannu ta fusgi Iftihal za su yi waje Daada ya ce "Kin san Baita bashi da mutunci fa?" "Ka bashi uzurin shirya yarinyar ake yi" Tana faɗin hakan ta fice daga gidan suka nufi titi napep ta shiga ta ce masa Maitaima Sule Baffas Estate kai tsaye. Bayan fitar su zama Innti ta yi ta dinga kuka har sai da ta yi me isar ta tana kukan tana cewa. “Rabbanaa hab lanaa min azwaajinaa wa dhurriyyaatinaa qurrata a’yunin waj‘alnaa lilmuttaqeena imaamaa” (Surah Furqan: 74). Ta ɗora da faɗin. “Allahumma ihdihi wa-shrah ṣadrahu lil-ḥaqqi, Allahumma habbib ilayhi al-īmāna wa zayyinhu fī qalbihi, wa karrih ilayhi al-kufra wal-fusūqa wal-‘iṣyāna, waj‘alhu minar-rāshidīn.” Ma’ana: “Ya Allah, Ka shiryar da shi, Ka buɗe ƙirjinsa ga gaskiya, Ka sanya ya so imani Ka yi masa kwalliya da shi a zuciyarsa, Ka tsanar da shi da kafirci, da fisqanci, da saba wa Allah. Ka sanya shi daga cikin masu samun shiriya.” Wani irin numfashi take fitarwa me ɗauke da ciwo tattare da damuwar da ta yi shekaru a cikinta ba tare data buɗewa kowa cikinta ba. Idanunta na buɗewa da lumshe ta ce “Allahumma aslih lī zawjī, wa aslih līhi, waj‘alhu qurrata ‘ayni, waj‘alnī qurrata ‘aynih.” ta ɗan ja idanunta ta lumshe su. Sama-sama ta ji kakarin amai tana fitowa taka Jadid ne ke kwara amai gabanta kuma ya faɗi ganin yadda fuskarsa ta kumbura sosai da ƙafafuwansa da hannayensa. Bayan ta wanke masa baki da fuska ta ce "Ina maganinka?" "Ya ƙare" ya ce da ƙyar. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Shimfiɗa ta yi masa ya kwanta ta dinga kallon shi tasan da ƙyar idan ba dialysis za'ayi wa Yaa Jadid ɗin ba. "Babu komai, Allah duk abin da ka yi daidai kuma na amsa. Bari na ɗakko kuɗin adashin nan na jama'a siya maka magani kafin aje asibiti idan Allah ya hore mana" ko data miƙe ta nufi ɗaki tana zuwa inda take adana kuɗin jama'a na adashi taga babu komai kusan dubu ɗari biyu da hamsin an kwashe *** BIYA. Batty na rakuɓe a cikin bukkarta ta yi shiru tana kallon saman rufin wajan idanunta ya yi jajur saboda tsananin azabar da take jin tana yunƙuro mata, bata taɓa jin kanƙarar maita na mata yawo a ciki irin yau ɗin ba. A hankali ta juya ta kalli inda ta ajjiye kurwar Mado data kamo a jiya data fita maitar dare. Miƙewa ta yi a hankali ta isa wajan randar ruwan dake ɗakin, randar ta yi sanyi sosai ta miƙa hannu zuwa ƙasan randar ta buɗe wani ɗan ƙyalle idanunta ya sauka akan ƴar tsokar kurwar data kamo ta zubawa kurwar idanu tana jin kamar ta ci kamar kuma hakan ba dai-dai bane ba. Wasu hawaye ne suka shiga sakkowa daga cikin idanunta ta mayar da kurwar ta ajjiye. Wata baƙar leda ta ɗakko barkono ne ɗanye shar a ciki haka ta dinga damƙa tana kaiwa baki tana ci ga hawayen a zama na cika idanunta bayan ta gama ci abin da take ji ya ɗan lafa mata sai ya miƙe ta fito zuwa tsakar gidan turus ta yi ganin jama'a fal ta manta yaron Kulu ya rasu. Sadiatu ta ce "Batty kin fito ne?" Ta jinjina kai alamar "Eh" "To jeki waje wajan yara muna amsar gaisuwa ne" nan ma ba ta yi magana ba kanta a ƙasa cike da nutsuwa ta fito sumar kan sai ɗaukan ƙyalli na dauɗa take yi a haka ta nufi waje cikin sa'a ta samu yara sa'aninta suna ta wasa tana zuwa ta shiga tsakiya aka fara wasa da ita. Kamar an ce ta ɗaga kai ta hango cikin Shatu fal wainar gero har da albasa bata gama narkewa ba.Caraf ta ce "Sammin wainar geron kin ji" Shatu ta fiddo ido ta ce "Wa ɗin?" "Ke, gashi nan kin ci wainar gero" "Laaa ha'ilallah wallahi kin cinka waina na ci" Gabaɗaya yaran suka zagaye Batty. "Ni me ma ce?" "Rogo da gyaɗa" ta bawa Hawwa amsa. Wani irin daɗi da murna ya kama yaran su basu taɓa sanin ana sanin me mutum ya ci ba sai yau. "Ni ki faɗa mini me na ce to" Ramu ta yi tambayar a hankali tana kallon Batty cike da tsoro. Batty ta zubawa cikin Ramu idanu komai da komai dake cikin Ramu na kayan ciki tana gani, daman duk wani maye da kallo ɗaya yake kallon ka tsirara musamman idan babu dafa'i a jikinka. Madadin Batty taga abin da Ramu ta ci sai taga hanjin cikinta ya motse kuma ya yi kore. Ɗauke kai ta yi zuwa gefe guda ta ce "Ai ba ki da lafiya, ga hanjinki nan ya ta mushe ya yi kore ki nemi magani idan ba haka ba za ki mutu wallahi ina faɗa miki" Fashewa da kuka Ramu ta yi tana riƙe cikinta. "Na shi gangaɗi" ta faɗa gigice. Su Shatu ne suka dinga bata haƙuri har ta yi shiru juyi kaɗan tana dafe da cikinta tana jin kamar hanjin nata ne zai fito ta cikinta. Shatu ta ce "Kin zama ƙawarmu daga yau za ki dinga faɗa mana me muka ji kin ji ko?" "To za ku dinga sam mini?" "E, sosai ma. Ya sunanki?" "Batty me gani har hanji" Hawwa ta dafe ƙirjinta ta ce "Laa wallahi haka ne gashi nan ta hango hanjin Ramu" Hira suka fara yi Batty ta shiga cewa "Ita fa ta kusa fara cin mutane tana shan wahala, ta taɓa shan man wani da babarta ta zuba mata man a cikin abinci akwai daɗi sosai. Kuma tana ganin jinin mutum da kayan cikinsa ita fa har mage tana iya zama" suka fashe da dariya suna jin abin kamar alamar. Bayan sun gama hirar la'asar sakaliya ta koma gida tana ta zuba idanun a bata abinci amma shiru. Sai ma hira suke yi "Ai Kulu haƙuri ya zama dole, kinga samu kinga rashi amma hakan yin Allah ne. Yanzu fa mutuwar fuju'a ake yi babu ji babu gani ana ta zuba" Lami dake ta wanki ta ce "Wallahi Sadiatu al'amarin har tsoro ya bani sosai" Ita dai Batty jinsu kawai take ta san wannan mutuwar da ake yi rabinta mayu ne sanadi. Mutane za su ga ana ta rasuwa irin mutuwar abin mamaki nan, daga ciwon kai sai ace wane babu ko ciwon ciki, ko kuma mutum da lafiyarsa da komai sai aji ya yanke jiki ya faɗi shikenan sai tashin lahira. A cikin wannan watan ne na dab da babbar sallah Mayu suke sharafi a cikin watan ne suke yanka duk wanda suka ɗaure kurwarsa da niyyar shagalin babbar sallah. Don haka duk wanda yake fama da jinya ta Mayu a irin wannan watan Allah ne kaɗai me tsallakar dashi sai idan ya dage da addu'a da neman tsari da taimako. Miƙewa ta yi ta sake shiga bukkarta, kurwar Mado ta ɗakko ta riƙe a hannunta sosai ta nufi hanyar rafi tana addu'ar Allah ya sa yau ma taga kyakkywan Kaɗo har mafarkinsa ta dinga yi tana isa ta haƙa rami a gefen rafin ta adana kurwar a ciki ta shiga wasa da ruwa can kuma ta fashe da kuka lokacin data tuna kisan gillar da akai wa Innarta A can gidan Moddibo suna zaune a tsakar gida, suna ta amsar baƙin da suke zuwa duba Mado. Wani ihu suka ji Mado ya kwarara yana faɗin "Wayyo ga ruwana zai cinye ni ga kifi nan, ruwa ne zai tafi dani" A razane suka shiga ɗakin suna masa sannu. Hanne ta ce "Moddibo anya ba iska bace ta kama Mado? Wanne irin ruwa zai tafi dashi ana zaune ƙalau Moddibo?" Moddibo ya ɗan taɓa jikin Mado ya ce "Kuma jikin sanyi ƙalau. Bari zan kira me ruƙiyya in sha Allah sai a yi masa a gani" "To da dai yafi" Hanne ta ce tana yin takumi. *** Aikin yamma ne da ita yau bayan ta kammala shiryawa ta fito hannunta riƙe da jaka da damuwa ta bayyana sosai a tattare da ita. Engineer na zaune a parlour shi da matarsa Jiddah ta ɗan durƙusa ta ce "Barka da yammaci Abba" saboda da yawan lokaci tana bin bakinsu Mufeed wajan kiran Engineer da Abba. Itama ta yi imani da Allah bata da wani uba bayan Engineer ɗin nata. "Baby an fito kenan?" "E, Abba. Anty Jiddah sannu da aiki" Jidda ta murmusa ta ce "Yawwa babyn mijina" murmushi kawai Ahlam ta yi. Ya ɗan kalle ta sai kuma ya ce "Wannan baby hijab ɗin baya miki kaɗan ne a jiki Ahlam?" Ta dubi Hijab ɗin, abaya ce a jikinta me ɗan faɗi ruwan ƙasa sai ta ɗauki hijab ta saka madadin mayafin abayar. "Idan akwai kuskure a shigar zan je na sauya Abba" "Matsayin naki ne ya sauya daga yadda kika sani. Ahlam na taɓa miki maganar fitar da mijin aure har na yi tunanin wannan yaron na wajan aikin ku ko son ki yake yi. Yama sunan nasa?" Kanta a ƙasa ta ce "Anees ne" "Good, Anees" Ya ɗan ɗaga filon kujera ya ciro kuɗi bandir bandir ya damƙa mata ɗaya ya ce "Wannan kuɗin na gani ina so ne naki dana amsa da safe. Ke da kan ki kika bani damar zaɓar miki mijin da nake ganin zai iya kulawa da nake. Nasan komai na zartar a rayuwarki ba za ki yi mini musu ba, ba za ki ce a'a ba. Daga ni har ke marayu ne, amma ke ba za'a taɓa miki kallon maraici ba, dukkan abin da zai zo ya tuna miki ke marainiyya ce bana son shi Ahlam ɗina. Na bada ke, na bada aurenki ga mijin daya kwanta mini kuma ina da yaƙinin ba zai cutar dake ba baby" Sak Ahlam ta yi tana juya kuɗin a hannunta jikinta ya yi sanyi ba damuwarta waye mijin ba, saboda ba soyayya ce a ranta ba, cikar burinta shi ne gaba da komai a rayuwarta. Tambayoyin zuriyarta bai shige zai barta aiki ba? Ba zai tauye mata rayuwa wajan hanata zuwa aiki ba? Ya san cewa ita nakasasshiya ce? Waɗannan tambayoyin sune suke damunta a yanzu. "Baby " da ƙyar ta ce "Abba ba zan tambaye ka waye ba, ba kuma zan bijire maka ba, na amshi abin da ka zaɓa mini na san ba zai taɓa cutar dani ba" Sai ta ɗan yi shiru tana mai da murmushi. "Ya san ina da nakasa Abba?" "Ya san abin da ba ki sani ba don gane da rayuwarki ma Ahlam. Matsalolin suna bibiyarki wanda ni ban san su ba, ya ɗauki ɗamarar yaƙi da wannan matsalolin ne" "Amshi nan.... Ya sake damƙa mata wasu kuɗin ya ce "Sadakinki an ɗaura aurenki a sanda suka kawo kuɗin baiko, ni ba zan iya wannan ba tsarina daban shi ya sa na buƙaci ɗauren auren daga baya a yi maganar tafiyarki" Ji ta yi kamar Engineer ya saka igiyoyi ya sarƙafe rayuwarta da ita ne, komai ya tsaya mata. Yana nufin yanzu ita matar aure ce? Yana nufin igiya uku ke ɗaure da rayuwarta. An yi mata ɗaurin da sai hanata sakewa da zai kawo mata matsala a cikin burinta? Ta rufe ido ta buɗe yafi sau shurin masaƙi wajan tabbatar da abin mafarki ne amma da alama gaske ne. Wata faɗuwar gaba ta ruske ta, aikinta shine gaba da komai, ɗaukarta shine burinta. Ta yi aure bata cimma komai na rayuwa ba, Yussy ta samu sararin yi wa ƙaddararta dariya? Girgiza kai ta shiga yi wajan faɗin "Impossible.... "... menene impossible ɗin? Auren ko kuma mijin Ahlam Abdallah Kurmi?" Sai ta ƙirƙiri murmushin ta ce "A'a Abba" "Kina farinciki?" "Sosai. Na gode sosai my 001 madakina" "Nima na gode ƙwarai my happiness" Wani abu ya caki zuciyar Jiddah ta yi saurin shaƙar iska ta fesar tana jifan Ahlam da wani irin kallo. Kishin yarinyar kamar ya kashe ta dannewa kawai take yi for more than a years yanzu ya fara cin ƙarfinta sosai. "Tashi ki je a kiyaye kula wasu samarin tunda dai kina da naki zaɓin Baby Ubangiji ya yi miki albarka ya sa tafiyarmu ta yi nisa" "Amin na tafi" "Allah ya tsare Kakata" inji Jiddah. Fita ta yi ɗauke da addu'ar fita daga gida a bakinta tana buɗe gate ɗin gidan ta fice sai taga mota daga can nesa kai tsaye ta yi gaba bata tsaya ba. Me motar ya sake kunnawa ya yi horn yasha gabanta, tsayawa ta yi tana ƙoƙarin yin masifa wanda ya buɗe motar ya saka gabanta faɗuwa ta yi saurin yin ƙasa da kanta jikinta duka ɓari yake yi. Ta cikin glasses ɗin idanunsa ya zuba mata ido yana daga kishingiɗen da yake a kujerar motar tasa.... *H I Y A A M* Page 9: The Secret Bright pens Yota/001 I can repeat it again, this book dedicated to Nazeefah Sabo Nashe. AUTAR MANYA: Thank you so much na gode da ƙoƙarinki Allah Ya saka da alheri Ubangiji Ya bar zumunci. Ta cikin motar ya ɗan sake ware idanunsa kaɗan ya kalli yadda take tsaye a waje tana rarraba idanu. Kamar zai yi mata shiru sai ya ɗan duba agogon dake hannunsa sai yaga lokaci yaja yana kuma da abin da zai yi. A nutse yana kame fuskarsa ya dube ta ya ce "Are you getting into the car, or will you keep standing outside, looking around like someone who has something to hide?" Yadda take kallon nasa sai yaga kamar bata fahimci me yake cewa ba, ya danna mata horn da ƙarfi sai ta yi saurin sakin ajjiyar zuciya saboda ɗan firgitar da ta yi duk ta kasa samun sukuni da nutsuwar zuciya. Ta ɓata fuska ta ce "Me kace ne?" Ya yi mata ƙuri da ido sai kuma ya ce "cewa na yi za ki shigo motar ne ko za ki tsaya a waje kina rarraba ido kamar mara gaskiya?" Sai ta tura bakinta gaba kaɗan itama ɗin ta makara ƙwarai da gaske, amma a yau ɗin sai ta ji bata samu ƙwarin gwiwar shiga motar ba, ta kuma rasa dalili, ba zata yadda saboda auren da yake kanta bane bata jin hakan. Kai bama shi ɗin bane, aure ai ba zai iya shata mata layi da abin da ta zaɓa kuma take so ba. Sai ta taka sannu a hankali ta buɗe murfin motar ta shiga kanta a ƙasa, bayan ta shiga da sallama ta zauna taja murfin ta rufe. A kunne motar take sai ya fara driving da hannu guda ɗaya hannun kuma yana shafa gemun fuskarsa yana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci yake juyawa yana kallon ta. Sai ta ɓata fuska tace "Allah ban shirya mutuwa yanzu ba, ka kalli gabanka ka yi driving a nutse please" A kasalance ya ce "Nima hakan take baby" "Shine kake ta kallo na?" Ya ɗan ɗaga shoulders alamar rashin damuwa da furucinta ya ce "Wataƙila da bana kallon naki shine zai yasar damu a titi, but trust me baby, ki yarda dani baby kallon fuskarki ke bani energy a jikina kin ji ko?" Ta yi masa shiru saboda faɗuwar gaban da take ji ta yi kaɗan ta kwanta a jikin kujerar. Shiru ne ya ratsa cikin motar lokacin da ya ɗauki titin da zai kai shi Bright Fm ɗin tasu. "Ahlam..... "...Tell me something please!" "Kamar me kenan a something ɗin?" Ya sake shafo sajensa ya ce "Me kike ji yau?" Ya ɗora da "Ina nufin wanne irin farinciki kike ciki yau ɗin nan, domin na san a jerin shekarun da kika ruska a rayuwarki yau ɗin zata iya zama ta musamman a gare ki kamar dai nima haka nake ji yau ɗin" ya nuna tsakiyar ƙirjinsa alamar nuna kan shi. Ta yi shiru alamar nazari da tunani, tunani ta fara saboda kamar wani aiki ya sata wanda ba ta yi niyya ba ko kuma bata san dashi ba, ta fara processing da ƙwaƙwalwarta wajan haƙaito anahin abin da zai iya zama na musamman a yau ɗin a kuma rayuwarta. "Aure?" Sai ta yi saurin girgiza kai a ranta ta ce "No, impossible" Wannan aure ba zai zama na musamman a wajanta ba, wannan auren dai ba zai zama abin da zata rubuta shi a history na rayuwarta ba, auren da Engineer da Anty Jiddah ne kawai suka san dashi, suka san waye mijin ma? Sune suke ɗoki da zumuɗin yau ta zama matar aure, matar wanin da bata waye shi mene halinsa da ɗabi'unsa. Ita fa ko sunan shi ma bata buƙatar ji ɗin, tana son ta ƙarfin dole ta fuskanci matsalarta kuma ta yi maganinta. Ƙaddarar cimma burinta bata san ina zata tsaya ba, bata kuma san ina zata kaita ba. A fusge taja numfashi bayan ta lumshe idanunta tace. "Bani da wata rana ta musamman" "Bana jin akwai wani abu special.... "Really.... Da gaske kike?" Ta dude shi kawai ba tare da tace komai ba. Ya murmusa "Ni ina da, ina jin akwai ta" Ya sake jan gemunsa "Ina jin ƙamshin zama ango, ina kusantar rayuwar aure da amarci" Dam! Gabanta ya faɗi ta yi saurin cewa "Anees!" Yadda ta kira sunansa da ƙarfi ya saka shi juyawa ya kalle ta suka haɗa ido sai ta yi saurin ɗauke fuska ganin ya kashe mata ido ɗaya. "Yes baby, soon zan tare da matata in sha Allah. Aure zan yi ko na ce...," "Stop..... Ta yi saurin dakatar dashi tana taro ƙirjinta da take jin kamar zuciyarta ce zata yanko ƙirjin ta fito, bata fatan ace abin da take hasashe ya zama gaskiya. Sarai ta san mahaukacin son da Anees yake yi mata amma babu haka a lissafinta ya shi ya sa ma bata bashi fuska ba, kar ta wahalar da zuciyar ɗan mutane a banza. "Ahlam" Ya kira sunanta a tausashe ya ɗora da faɗin "wannan satin za'ayi Annual Media Excellence 2025. Shagalin karrama ma'aikatan kafafen yaɗa labarai na shekara ta 2025. Kina expecting karramawa ne a wannan shekarar ne kikai da za'a iya baki wani award, wanne kalar award kika hasashe za ki samu a taron?" Jikin Ahlam har rawa yake yi ita gabaɗaya ta mance da taron da ake yi duk ƙarshen shekara wajan bada karramawa ga ƴan jaridun da suka fi kowa hazaƙa. A wannan shekarar ne kuma take son nunawa Yussy cewa za ta iya, zata nuna mata nakasa ba zai zama kasawa ba. "Allah Ya bawa me rabo sa'a Anees" "Amin. Allah Ya sa ki samu Outstanding Journalist Award a ɓangaren mata baby" Maganar award da taron da Anees ya yi ya sake saka Ahlam cikin damuwa, a hankali ta ciro wayarta saboda wani program da zata fara gabatar tana buƙatar bincike sosai. Data ta kunna, ta shiga Chatgbt ta fara bincike a hankali take dubawa, sai idanunta ya sauka akan wata kalma da bata taɓa gani ba, kuma ta kasa fassara ma'anar ta. "Kwagh" shine kalmar sai ta sake tambaya, mene fassararta wanne yare ne wannan? Nan take ya bata amsa da "Tana nufin Almara a harshen Tiv, wanda yana cikin harsunan Bantu/Congo" A hankali ta furta "TIV?" Anees ya juya ya kalle ta, sai ya yi murmushi ya cigaba da driving domin shima bai san mene Tiv ɗin ba. Ta samu kanta da buƙatar son sanin mene Tiv. Chatgbt ta sake tambaya ta ce "Mene Tiv?" "Tiv wata kaɓila ce a Nigeria, sun fito daga yankin da yake kusa da Kamaru" Taɓe bakinta ta yi, a hankali kuma ya fice daga cikin application ɗin bayan ta karanta, haka kawai kuma kalmar Tiv da son sanin su waye su ya shiga yi mata yawo a cikin kanta. Har suka ƙarasa Bright Fm bata sake cewa komai ba, saboda abubuwan da take ji sun fi ƙarfin ta faɗe su. Parking Anees ya yi a harabar gidan rediyon ganin Ahlam ta fito tana ƙoƙarin amsa kira ya ɗan yi gaba saboda akwai aikin da zai yi a ciki. Da murmushi ta amsa kiran ta ce "Zainab Alƙali" Ta cikin wayar Zainab Alƙali ta ce "Golden voice, ya naga har yanzu ba ki shigo ba ko ba ki da duty ne yau?" Cikin jin daɗi ya ce "Kin ganni a haraba yanzu zan shigo reception. Shegiya ki ce yau akwai labari, wanne littafi kika samo za ki fara karanta mana Besty?" Zainab Alƙali ta yi dariya. "Ke dalla ki shigo ciki tukunna" "Please bama ƴar haka" "Ban wani duba littafin ba, amma naga sunan wai ko INUWAR GIGINYA. Akwai labari ki ƙarasu ciki" "Ok....." Cewar Ahlam. Kashe wayar ta yi tana ƙoƙarin juyawa taga mutum tsaye a gabanta yana ɗan zazzare idanu "Malam lafiya ya zaka tsaya mini a gaba kamar ka haɗiye taɓarya?" Ya ƙura mata jajayen idanunsa yana watsa mata wani irin malalacin kallo zata tafi ya ce "Kece Ahlam Abdallah Kurmi?" Ta ɗan dube shi kaɗan "Yeah, ni ce ya aka yi?" Ya jinjina kai ya ce "Ƴar jarida fa Golden voice?" Siririn tsaki taja saboda ta fara gajiya da rainin da wayon da yake yi mata. Duk ni ce. Malam ka faɗi mene matsalar aiki ne dani a ciki kuma ka tsayar dani waje guda" ya yi baya yana murmushi da ɗaga kai. "Relex..... Relex.... Relex" "Ina nufin wacce ta saka labarin matar da aka ƙonawa jariri fa?" Ya tambaya. "Ni ce, kana da matsala ne?" "Eh babba ma" ya bata amsa. Kafin ta ce komai ya ciro wata lafiyayyiyar wuƙa a ƙugunsa tana wani irin sheƙi ya yanki Ahlam da ita a hannunta ta fasa wani gigitaccen ihu ta yi baya ya sake yi mata wani lafiyayyen yanka a wuyanta ya ce "Hukuncin ɓatawa mahafinmu suna" Yana faɗin hakan ya juya a guje ya fice daga cikin wajan. Wani gigitaccen ihu Ahlam ta kurma tana dafe wajan da hannunta, jini tuni ya wanke mata wuya da rigarta har jiri ya fara ɗaukanta, ta kasa motsi ta ƙanƙame wajan da hannunta tana jin kamar ranta ne zai fita idan jininta ya ƙare, kai tsaye rayuwarta aka nema, rabata da duniya aka so yi ta ƙarfin gaske akan case ɗin da bata da laifi a kan shi. "Wayyo wuyana, don Allah taimaka mini zai kashe ni, Anty Jiddah, yayana, wuyana" da ƙarfin gaske take kiran sunayen nasu. Sannu a hankali yake murza ɗan Bluetooth ɗin hannunsa daga inda yake tsayen, waya yake yi don haka dukkan attention ɗinsa yana ga wayar da yake yi ne. A hankali ya ce "Ki fita daga maganar nan, kin san bana shiga sabgar kowa bana son raini at all" Ya yi shiru alamar saurare can ya nisa ya ce "Zan sake faɗar the same abin da na ce, babu ruwana ok?" Wanda yake wayar dashi zai sake magana MD ya yi saurin dakatar dashi da faɗin. "Hold on....." Ya kashe wayar tare da saurare na ihun da yake ji tun ɗazo, ya juya idanunsa sai kuma ya ɗan taɓe bakinsa tabbacin bashi da ruwa da tsaki akan me ihun da dalilin ihun. Addu'arsa ɗaya ce, kar hargagin ya saukar masa da ciwon kai mara tushe. Amma me? Takalmi macen daya gani da jaka a yashe sune abu na farko daya ja hankalin nasa. "Wace wannan?" "Ta kuma rasa wajan yin taɓararta sai a nan? A gidan rediyonsu? Ta ɓata musu suna?" Gently ya fara tafiya hannunsa ɗaya cikin aljihu, idanunsa cikin glasses wanda ya amshe shi ya yi daidai da faɗin fuskanta me ɗauke da zagayayyen sajen daya kwanta. Yana isa idanunsa ya sauka akan ta tana durƙushe jini na zuba daga wuyanta gashin kanta ya tarwatse a bayanta kamar zautaciyya. MD yaja numfashi ya sauke sbd bai yi tsammanin ganin jini ba, ya kuma fahimci wacece tunda ga Id card ɗinta nan a yashe. Bayan ya ƙarasa ya ɗan miƙa ƙafarsa kaɗan yana zungurinta. A gigice Ahlam tace "Don Allah kar ka kashe ni, nifa matar aure ce, ko tarewa ban yi ba. Kar ka cutar dani" Idanunta ya faɗa a kan shi, sai ta miƙe tsaye da ƙyar tana layi idanunta na shanyewa, a firgice ta ƙarasa kusa da MD ta miƙa hannunta ta damƙi nasa ta ce "Na san ni da kai bama shiri, amma kar ka bari na mutu saboda jin haushina da kake, bana son na mutu banga ƴaƴana ba, yau aka yi mini aure ko mijin ban sani ba, wayyo yaya za su kashe ni" Ta sake damƙo MD ta ce "ka taimaka mini ka kira mini yayana, wallahi bana son na mutu, ina da buri akan aikina, ina da burin ganin na ɗaukaka ina da burin naga na haihu na tara zuri'a masu yawa" da ƙyar take yin maganar saboda fitar hayyaci. "Help me..... "Please!" Ta ce cike da raunin murya. Taɓe bakinsa kawai ya yi ganin ta sulale zata faɗi a wajan ba numfashi ya saka hannunta ya riƙo nata, ɗaukarta ya yi gabaɗaya ya sakata a cikin motarsa, daidai nan Baba driver yazo wajan ya ce "Yallaɓai ina zaka?" Hannu MD ya ɗaga masa alamar babu buƙata. Baba driver har ya juya ya ji MD ya ce "baka ji ba?" Sai Baba driver yaja ya tsaya "Na'am, ka ce wani abu ne?" A nutse MD bayan ya shiga mota ya ɗan murza key ya ce "Ka faɗawa officer muna buƙatar police a cikin Bright Fm right now" "Police? Ƴan sanda fa Yallaɓai?" "In sha Allah" cewar MD. Yana faɗin hakan yaja motar a guje ya bar cikin gidan rediyon. *** "Mita 119 bright Fm kuke so sauraro. Au yau ne hukumar ma'aikatar ilimi ta jiya ta sanar da sabon tallafi da gwamnati ta fitar ta ƙarƙashin hukumar, inda za'a ɗauki adadi ɗaliban jami' kimanin mutane dubu ɗaya aikin Gwamnati, tare da bada tallafi ga wasu. Za'a fara tantance ɗaliban a ranar Litinin me zuwa, ɗaliban zasu taho da takardun makaranta wanda dama ta iya wanda suka fita daga first class ne" sai aka ɗan dakata da maganar aka sako taken gidan rediyo. "Labaran Duniya" muryar na namiji ya fito. "Daga gefe guda, wasu da ba'a san ko su waye ba, suna shiga rugar Fulani tare da yi musu kisan gilla, bayan kisan suna tattare kan jama'ar su yi gaba dasu, an fasa Fulani adadin da ya kai 75. Duka ina jami'an tsaro da gwamnati suke ake wannan abin? Aka ce, kowa ya ji daɗin gemu bai ka maƙoro ba. Ahlam Abdallah Kurmi ke tare daku" A hankali ya kashe radiyon tare da yin baya ya lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa na bugawa sosai, tun rahotanni da ta yi jiya da daddare ne sai yau aka saka. Ya numfasa ya ce. "Ba wani bayani akan yarinyar ne?" Wanda aka tambaya ya ce "Akwai, Ahlam Abdallah Kurmi sunanta, amma asalin sunan shine Haleemah, iyayenta sun rasu tare zaune a wajen yayanta Engineer Abdallahi. Shine ya tsaya mata tun daga primary har zuwa secondary da jami'a, karatu me kyau ta yi a makaranta me tsada a ɓangaren aikin jarida. Tana da ƙoƙari da jajircewa a aikinta, amma a nutse take, bata da hayaniya tana da kamun kai, ba irin sauran da suke mata aikin jarida bane. Sir i wonder why kake son ganinta, is there any problem da ba zaka iya sharing ɗinsa dani ba?" Ya ware idanunsa, kallon yaron kawai ya yi ta cikin glasses ɗin idanunsa ba tare da ya ce masa komai ba. A ɓangaren Maryama a wannan dare a tasha ta kwana, mutane sai kallonta suke yi, wanda tana da tabbacin kallon mahaukaciya suke yi mata, ƙudaje suna ta binta saboda jinin haihuwar daya ɓata mata jiki, zuciyarta ta yi mata wani irin nauyi a ƙirjinta, ko kuka ta kasa idanunta ya bushe sai yawo take yi da gawa a hannunta wacce ta ɗan fara wari. Mutane na ganinta suke matsawa zuwa gefe. A hankali taja jaririn ta ƙanƙame a ƙirjinta sai a lokacin ta samu damar sakin wani irin raunataccen kuka me cin zuciya, ta yi ta gama ta lallashi kanta ta faki idanun jama'a ta ajjiye gawar a gefen kwata dake tashar ta tashi da sauri ta bar wajan tana dafe ƙirjinta. *** Ana ce kwance a gadon asibitin da take, ta yi shiru idanunta a rufe tana sauraran bugun zuciyarta daya ruɓaya fiye da yadda take ji a lokutan baya, a hankali ta miƙa hannunta zuwa saitin zuciyar da nufin ta danne ta da tafin hannun, sai ta ji haƙarta bata cimma ruwa ba, tamƙar tana saƙa ne zaran baya data tufke yana warware kan shi. A dalilin bugun dake ratso ƙirjin yana haɗawa da hannun da take ganin ta ɗora da nufin bata kariya. A kowacce daƙiƙa ta shigewar lokaci ƙara nisanta zuciyarta da Daada take yi, nisan da take murna dashi domin da gaske bata buƙatarsa a rayuwarta, ace da uba ake gado, ita kam bata yarda da wannan gurɓatacciyar kalmar ba, bata yi believing da ita ba, kuma bata jin ko nan gaba da abada zata yarda cewa da uba ake ado har ta bawa jimilar muhalli nada ban a zuciyarta. Da Innti take yin ado, ita ce sahibarta abar adonta, abar ta ɗauki abu ta yi shelan irin tarin soyayyar da take yi mata, sau tari ta kan rasa sanin adadin soyayyar da take yi wa Innti da Mahaɗinta, soyayyar kunnen doki ce, kowanne ba zata iya shaƙar wadataccen numfashi ba idan babu shi.... Bayan su sai waye next? Yaa Jadid, da Yaa Jaheed jaruman yayyinta a ɓangaren uba kuma Babban yaya shi ne ubanta shine abu mafi ƙauna a ranta a ɓangaren maza. Shine duniyar Ana. Bayan su sai wa zata saka a lissafin nata?" “Haysaam" "Yaa Sam..... Ta faɗa a fili tana sakin lallausan murmushi. Motsin da ta ji ya saka ta buɗe gajiyayyun idanunta wanda sukai laushi saboda ciwo da galabaitar da zuciyarta ta yi saboda tunanin 'future life' ɗinsu ita da Iftihal. "Abbaa" ta kira sunan a tausashe tana faɗaɗa murmushinta. Kallon ta ya yi na wani lokaci, jikinsa sanye da sabbin kaya wanda sukai masa kyau sosai, ya ɗan sake yin fresh, lallausan sumar kansa da take har baya ta dinga ɗaukan idanu a nutse ya ƙarasa ya zauna daidai kanta ya zuba mata ido, ita ɗinma kallon shi take yi da manyan ƙwayar idanunta jin shiru ya saka ta miƙa hannunta ta riƙo nasa ta ce "Abbaa... "Abbaana" Ya ɗan buɗe ido bai magana ba. "Ina ka je? Tun jiya baka dawo ba in ji Yaa Sam" bai bata amsa ya juya idanunsa alamar "Kina jin ciwo?" Ta ji ya furta da silent voice ɗinsa me sanyi a cikin shurunsa da maganarsa ta body language. Ta jinjina kai lokaci ɗaya ta ce "Eh" Ya zauna kusa da ita ya damƙe hannunta dake cikin nasa ya shafa gefen kanta ya zuba mata ido alamar saurare. Ana ta ce "Abbaa ka yi mini alƙawarin ba zaka zama irin mijin Innti ba, ba zaka dinga cutar da matarka ba, da yaran da Allah zai baka, ka yi mini alƙawarin zaka dinga sakawa yaranka albarka daga cikin yaran na zama ɗaya daga ciki, ka zama babana ni na riga na zama ƴarka Abbaa. Zan yi addu'a Ubangijin Ya yi mini yalwar arziƙi na siya maka gida babba mu koma can ka yi aure ka buɗe babban shago a Farm center. Ina son ka Abbaa kaina hope ɗina, kai na nake gani na ji ka cike mini gurbin uba, ina ƙaunarka Abbaa" Ya shafa goshinta alamar "Idan ba Ubangiji ba, waye zai maka kyautar ɗa babu aure?" Ta washe masa jerarrun fararen haƙoranta. Ya shafa hannunta tabbacin "Idan Ubangijin Ya ara mini rai da kuma dama, zan cike miki duka gurbin da kika rasa, In sha Allah" "Da gaske kake Abbaa?" Ya jinjina kai alamar "Me kike buri a rayuwa?" "Na yi rayuwa daku ta har abada, naga na zama cikakkiyar marubuciya idan na kammalawa karatuna, idan Allah ya yi mini arziƙi na kai ku hajji da umara na siya muku gida, na dinga ajjiye kayan abinci akai akai" "Kayan abinci?" Ta matse hannunsa a nata tana jin relief yana sauka a gangar jikinta yana samar mata da nutsuwar zuciya. "E. Saboda kada mu ji yunwar da muka rayu a cikinta, kada mu sha wahalar rayuwa My Abbaa" Ya ce "Na fahimta" Ƙuri ya yi mata da nasa idanun dake nuna maganar "Ba ki yi maganar aure ba?" In seconds yaga mood ɗinta ya sauya, damuwa ta maye gurbin walwalar wani abu ya tukare ƙirjinta ya tsaya mata tana jin ya yi mata nauyi. "Kodayake you're still my baby" Ta yi murmushi "I'm always been your baby" "Your favourite daughter" Sai ya sumbaci goshinta yana faɗin "In sha Allah!" hanyar fita daga ɗakin ya nufa da ƙarfi ya ji ta ce "Abbaa" jikinsa na rawa ya juya yana tambayar mene sai ta ce "Ina son ka Abbaa" Girgiza kai ya yi ya fita cike da karyewar zuciya da tunani kala-kala a ransa ya nufi titi neman me napep ya ɗauke su zuwa gida. Haysaam. Yana zaune a cikin ofis ɗin likitan ya zuba masa ido tare da sauraran abin da yake cewa cike da zallar nutsuwa da fahimta. Dr ya gyara zama ya ce "Wannan yarinyar Allah ne ya yi tana da sauran kwana Sam, ga binciken da muka yi abin da ya nuna" ya tura files ɗin gaban Sam ya ɗora da faɗin. "Bincike ya nuna ta samu tabo a mahaifarta dalilin dukan da akai mata, wanda a turance muke kiran matsalar da SCAR wani gurɓataccen nama ne da jiki ke ƙirƙira bayan rauni ya warke. Idan aka samu duka, ita kuma ta samu Scar a MAHAIFA (uterus) wanda zai haifar mata da miscarriage, ko ta samu wahala wajan samun ciki, wahala wajan saduwa. Zubar jini mai yawa (internal ko external bleeding) don haka disvirging nata zai wahala, kamar yadda ɗaukan ciki zai mata wahala. Wannan serious issue ne Haysaam, yana da kyau duk wanda zai nemi aurenta ya san da wannan matsalar Please" Wata zufa ce ta shiga tsastafowa Haysaam ta tsakiyar goshinsa, ya yi shiru bayan ɗora kan shi da ya yi a saman table ɗin dake gaban likitan, jikinsa duka rawa yake yi kamar an watsa masa ruwan ƙarƙara wanda ya yi daidai da lokacin hunturu ƙofofin da suke lulluɓe gargasar jikinsa, ya yi shiru. "Haysaam.... Likitan ya kira shi da kulawa. "Naga ka damu da Chocolate girl ɗin nan, ka yi haƙuri kowa da ƙaddararsa, ka dai ja mata kunne akan wasan banza ko don lafiyar jikinta" Haysaam ya kasa magana, dr ya dafa ƙafaɗarsa "A kula sosai da jikinta, a faɗawa wanda zai aure ta" a hankali Sam ya ɗago kan shi ya watsa rinannun idanunsa a fuskar Dr a kasalance ya ce "Ina son maganar nan ta zama sirri, kar yarinyar ta ji haka mahaifin yarinyar ka bar ta daga ni sai kai" Dr ya buɗe ido da mamaki "Amma ta ya ya wannan matsalar zata zama sirri, bayan dole ta yi aure ta zauna a gidan mijinta?" Haysaam ya ce "Dole ta zama sirri Dr " "Ok tell me how? Tayaya...... "Saboda ni ne mijin, ni zan aureta" ya nuna kan shi da yatsa "What!" Dr ya furta da sauti na zallar mamaki. "Haysaam baka yi mini kala da wanda hankalinsa ya bar jikinsa ba, kana son sadaukar da lafiyarka saboda ita ne?" A ɗan harzuƙe Sam ya ce "Ok Kamal, Ka faɗa mini ya kake so ayi, ya kake so yarinyar ta fahimci rayuwarta zuwa nan gaba? Wannan ba zai zama hujja kaɗai ba, bai zama hujjar da zaka gina na cewa na yi Sacrifices ba, idan sadaukarwa zan yi mata nawa ke buƙatar hakan, na je gidan gyaran hali, ko gidan karuwai, ko gidan marayu zan iya ruskar matan da zan iya zaɓa na yi Sacrifices akan su" sai ya yi baya kaɗan ya taka a hankali zuwa gaban Dr Kamal ya ce "Wannan daban yake, dalilin ma daban na, is difference Kamal ina fatan zaka fahimta" Dr Kamal ya ce "Matsalar soyayya?" "I did say it..... "You don't need to say it ai dama, baka buƙatar ka ce ma, your action shows. Soyayya kaɗan ke rufe idanunta mutum ya gaza gane gaskiya, ta ya zaka auri yarinyar da zaka iya ƙare rayuwarka babu haihuwar ko kuma ka ƙare rayuwar ba tare daka taɓa saninta a matsayin mace ba?' ƙuri Sam ya yi da jajayen idanunsa akan fuskar Kamal. "Ai ya zame maka dole ka kalle ni, ba zan ɗauki wannan rubbish ɗin ba, akan wannan yarinyar ko farcen da zaka sosa jikinka wallahi sai ka neme shi ka rasa, ka ɗauki responsibilities ɗin daba naka ba, ka ɗora wa kanka kazar tsaba haka za ta yi ta binka. Kai ne suttura, kai ne kayan abinci, kai ne kayan ƙyale ƙyale na mata. Babban takaicin ma, yadda ta fito daga maragurbin gida, kallon turɓaya nake mata, gidan da basu da tarbiyya ko ta misƙala zarratan........," "Kau.... Kau!" Haysaam ya ɗauke Dr Kamal da wasu maruka lokaci guda, wanda ƙarfinsu ya bada wani irin sauti. Ya dafe kunci yana kallon Haysaam ya ce "Mari?" "Marina ka yi akan yarinyar can fa Haysaam?" "Zan iya yi maka fiye da mari akanta. Sai dai wannan marin ya sha bambam da tunaninka. Rayuwarta kake kallo kawai, mahaifinta kake dubawa kawai, baka san wacece ita da irin tarbiyyar data samu ba" A zafafe Kamal ya ce "Tarbiyya banza da wofi, tarbiyya idan irin ta gidansu ce Allah Ya tsine mata, ko kyauta za'a bani auren mace a gidan nan banga uwar da zan yi da ita ba. Har shine kake da zafin zuciyar marina akan ta?" Da wata irin zafin zuciya shima Sam ya yunƙuro kan Kamal ya ce "Kasan zafi da raɗaɗin da yake cikin muzanta ɗiya mace? Idan maganar tarbiyya kake akaso ɗari na tarbiyyar yarinyar nan kaso talatin nawa ne, kashi hamsin na babarta kashi ashirin na Yaa Marwaan" "Matse muku ta yi kai dasu, amma alamu yana nuna shaiɗaniyya ce alaƙarka kai da ita babu alheri tunda har ka iya marina akan ta" wani irin huci su biyun suke fitarwa kamar masu ganin hanjin juna, fuuuu kuma Sam ya juya. "Kazo ka bani kuɗin treatment ɗin da na yi mata don ubanka ni ba bawa bane" cewar Dr Kamal yana ɗaga murya amma ko ta kan shi Sam bai bi. Ko da ya fito daga ofis ɗin sai daya tsaya ya samawa kan shi nutsuwa ya saita fushinsa kafin ya ƙarasa room ɗin da take ciki a nutse abin shi Bacci ne ya ɗauke ta tana rungume da hannunta a ƙirji kanta a tsakiyar katifar gadon gashin ya barbaje numfashinta na sauka a ƙirjinta a hankali tana sakin ajjiyar zuciya kamar wacce ta yi gudun tsira da rai. Haysaam ya jima tsaye a kanta ya zuba mata idanunsa a cikin jinya take amma sosai ta yi masa kyawun gani a cikin idanunsa. Yaja nasa idanun ya lumshe yana haƙaito lokacin, da ranar daya fara sanyata a cikin idanunsa, ranar daya fara ganinta. Wata ranar talata ce, da farar safiya ya fito sanye da fararan kaya wanda suka kasance uniform, ranar da zai rubuta jarrabawar ƙarshe a Rumfa College lokacin yana Sakandire. Yana tsaye ya zubawa gefe guda ido yana lissafin yadda zai taka a ƙafa daga nan Kankarofi zuwa Rumfa College ɗin. Murmushinta ya ji, murmushinta ya fara ji ya sauka a cikin kunnensa, idan ba zai mata ba abu biyu daya gani a tattare da ita bayan murmushinta shine yatsun hannunta, wanda ta yi amfani dasu wajan riƙe tsinke tana yin zane na haƙa rami za ta yi ƴar carafke ake cewa, bai ba gama sanin sunansa ba. Kasancewar ɗaukewar ruwan sama kenan, wanda yana daga cikin abin da ya saka shi yin latti a makaranta. Bayan yatsun hannunta sai sumar kanta wacce aka rabata gida biyu aka tufke. Babu takalmi aƙafar kamar yadda ya lura da koɗewar kayan jikinta. Bai mata magana ba, ya nufi shigewa ta ƙofar gidansu a sama ya ji ta ce "Ramina... Wayyo ka rufe mini ramina" Ya ji wannan karaɗin, ya ji slow voice ɗinta. "Ƴaƴana na wasa suna ciki, wayyo ni" Cak ya tsaya a wancan lokacin ya juya ya kalle ta, bashi take kallo ba, hankalinta yana kan abin da take ƙorafin ya yi mata ɗin. "Ƙazama" abin da ya furta kenan. "Ba ƙazama bace ni, mahaɗita nake jira ta fito mu yi wasa shine ka cike mini ramina" Sai ya dakata gabaɗaya fuska a tsuke ya ce "Tashi a nan wajan" Sanda ya fara ganin ƙwayar idanunta sai da ya yi tasbihi a cikin ransa, ba ƙwayar ido ce bai saba gani ba, hasken daya fito daga cikin nata ya shiga nasa shine abin da bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa, bayan hasken shine manyan da ƙwayar idanun nata suka kasance dashi, sai kuma shuɗiyar kala madadin baƙa. "Idan ba ƙazami ba, wake wasa a turɓaya?" Ita dai kallonsa take yi, kallon da bata taɓa tsayawa ta yi wa wani ba, idan aka ɗauke ƴan gidansu. "Kana da kyau" "You're very handsome" Ya ji kyau ɗin, ya kuma yi mamakin fitar turanci daga cikin bakinta. Miƙewa ta yi tsaye sai ya lura jikinta ya girme wa shekarunta, ya kuma lura da yadda take ƙyanƙyamin turɓaya kamar ma akwai abin da ya fito da ita daga cikin gidan. Ya nisa yace "Ina takalmanki? Kallabinki?" "Suna gida" bata bari ya sake yin wata maganar ba ta shige cikin gidansu a nutse. Motsin da ta yi a saman gadon ya tilatsa Haysaam dawowa daga tunanin abin da ya shuɗe, gani ya yi tana jujjuya kanta zufa na yanko mata a goshinta sai ya ranƙwafa kaɗan ya kalle ta, har numfashinta na sauka a saman fuskarsa. "Nanaah.... Nanaah..." "Kai na.... "Kaina Yaa Sam zai cire" Da farko ya rasa abin yi, domin yana avoiding duk abin da zai haɗa shi da ita wanda yake a haramce. Amma alaƙar shi da Ana tafi ƙarfin haka, mu shi da kan shi shaiɗan zai ji kunyar kunno kan shi cikin su. Hannunsa biyu ya ɗauka ya ɗauki kanta ya ɗora a cinyarsa ya ɗora tafin hannunsa yana murza kan nata. Babu jimawa ta sauke numfashi tare da buɗe idanun. "Nagode" Ta ce a sanyaye. Ya yi mata ƙuri da ido. "Ya jikin naki?" "Allahamdulilah" Ya jinjina kai ya ce "Sakko muje" "Lagos?" Harara ya watsa mata ya ce "Ba za ki raba kan ki da zuwa Lagos ba?" Sai ta ɓata fuska taƙi cewa komai. Rufaida fura ya ɗakko ya saka cokalin ya nufi bakinta ya ce "Sha tukunna sai mu yi magana" ƙin kula shi ta yi. "Niko?" Ta yi shiru. Sai ya mayar da furar cikin rubar, ta ƙasan ido take kallon shi sai ta ce "Zan sha fa" Yana jinta ya share sai daya kammala tura saƙo da keyboard ɗin wayarsa ya sake ɗebo furar ya nufi bakinta, ta buɗe ƙaramin bakin ya shiga bata, idanunta a cikin nasa, kamar yadda shima yake kallon ta. Murmushi ta yi masa, shima ya sakar mata murmushin, ta lumshe idanunta shima yaja idanun ya lumshe. Idanu ɗaya ta kashe masa, a hankali yaja idanunsa na dama ya kashe mata. "Yaa Sam ɗina" ya murmusa ya ce "Nanaata" "Na ƙoshi" Tissue ya ɗakko ya ɗora hannunsa a kanta ya ɗan matso da ita ya shiga goge mata bakin, bayan ya kammala ya ɗauki hijab ɗinta da Babban yaya ya kawo ya saka mata. Sauran furar ya fara sha shima yana cikin sha Babba yaya ya shigo. Kallonsu ya yi su biyun babu wanda ya yi wa magana ya kwashi kayansu zuwa waje. Sakkowa ya yi ya miƙa mata hannunsa ta saka nata a ciki suka nufi fita daga asibitin suna zuwa waje Yaa Sam ya yi saurin sakin hannun Ana. Napep suka shiga Ana da Yaa Sam na baya, Babban yaya a gaba suka nufi Kankarofi. *** Ta shafe awanni huɗu a bakin ruwan, tun tana saka rana zata sake ganinsa har ya fitar da rai. Hannunta ta miƙa kaɗan ta share hawayen da yake bin fuskarta a sanyaye ta ce "Yau ma kaɗo bai zo ba, ina kaɗona? Yana ina?" Taja idanunta ta lumshe a raunace ta ce "Innata..... "Su waye suka kashe mini Innata?" Ta fashe da kukan halin maraican da take ciki. *** YARI. Yau tunda Gana ta tashi, sai ta tashi da wata kalar maita kamar ta ci babu ga ranar rugar yau a buɗe take ta rasa inda zata saka kanta ta ji daɗi, idan ta juya nan sai ta yi karta da haƙori idan ta sake juya sai ta karta haƙori idanunta ya yi jajur har barkono ta watsa a bakinta ɗanye jawaur dashi amma ƙanƙarar maitar bata lafa ba. Burin da ta ci na samu kuɗi ya rushe ta shiga ɗakinta can uwar ɗaka taja ƙofa ta rufe, inda take ajjiye kayan tsafinta ta sunkuya ta ɗakko ta zaro wani baƙin ƙyalle ta ciro wata ƴar ƙaramar aba, mai kama da tsokar nama ta dunƙule a hannunta ta shiga surutai yana yafa jan yadi, nan take sai ga kurwar jaririn Kulu ta koma ɗanshila wanda ba'a jima da ƙinƙishewa ba. Ta kwantar dashi ta murɗe kan ta yi cilli dashi kamar idanunta za su faɗo waje, ta cilla shi cikin ruwan zafi ta fiffige gashi ta ɗora sulale da jini-jini a jikinsa ta dinga ɗauka tana ci tsabar masifar da ta yi mata yawa. "Wayyo.... Wayyo daɗi, naman jariri akwai Musulmin daɗi wallahi" Soyawa ta yi tana gamawa ta juye a ƙaramin filast ta tsiyaye man soyar a ƙaramar roba. "Naman jariri yafi kowanne daɗi, dashi da tayin da ba'a haifa ba. Inama Kulu ta sake haihuwar wani. Oh ni Gana ina zanga wani jinjirin yanzu da zan ci? Waye ke da ciki?" "Gafaranku dai" "Allah yai mana" ta amsa sallamar tana buɗe ƙofa ta fito waje. Washe baki ta yi ta ce "A'a wa nake gani kamar Hindatu" "Ni ce rana tsaka Gana" Gana ta ce "Lale maraba da Hindatu" Ta shimfiɗa assabari a gefen inuwa ta ce "Yada zango mana Hindatu, jiyan nan kika faɗo mini a rai nace muna maƙwabta amma ba zumunci walle kunya ta yi mana yawa" Hindatu ta ce "Bari ke dai Gana, surfe da casa ne ya azo ni gaba. Yanzu ma ina zaune ina taɗin zuci na ji ƙamshi ta saman kanta shine na leƙo nima ayi dani, ko me gidan ya yi miki tsaraba" Gana ta zubawa Hindatu ido na wani lokaci kafin ta ce "kayya, Ƙamshin man ƙuli dana soya da albasa kika ji. Bari na kawo miki ruwa da abinci ko?" Miƙewa ta yi ta zuba mata wake da gero da ƙuli ta ɗauki man data soya jaririn Kulu dashi ta kelaya saman abincin ta ajjiye mata ta kawo ruwan tulo me sanyi a kofi ta ajjiye. "Bisimillah Hindatu" "Hadda wahala haka Gana?" Bakinta har dalalar da yawo yake tsabar kwaɗayi ta fara cin abincin. "Gana wai ni kowa ina Batty ana ta raɗe-raɗin yaro hura mata iskar balo a ciki shi ne kika ɗauke ta, wasu ma sun ce saboda uwarta bata raye kin kasa riƙe marainiyyar Allah" Gana ta fashe da kuka tana kunce bakin zani ta ce "Na shiga uku kuma ni Gana, duk ɗawainiyyar da nake da Batty babu wanda ya yaba sai yanzu da jarrabawa ta same ni? Yadda naga Saleh yana turmushe Batty a zaure da murje ƴan ƙirjinta Allah Ya nuna mini Annabi. Ki faɗa mini da ban ɗauki matakin ɗauke Batty ba ai da tuni ya hura mata iska a ciki mun shiga uku. Da uwar uwar Batty dani nono ɗaya muka sha fa?" Hindatu ta ce "Sai haƙuri, mutane akwai su da gadon zancen wasu. Gana kin ji abincin nan inda ya yi daɗi? Ban taɓa jin man ƙuli da daɗi irin wannan ba, ko nama aka bani ba lalle ya yi daɗin wannan man ba" Gana ta yi murmushi ta fara tunanin yadda zata sawa Hindatu ƙanƙarar maita ta yi maganin shegen kwaɗayinta. Ta ce "Naman ma ina dashi, kuma idan kikai biyayya ma irin wannan kullum dashi za ki ci abinci na rantse" Hindatu ta waro ido waje ta ce "Don Manzo?" "Taso muje na ba ki nama da wani man" cewar Gana tana miƙewa tsaye ta yi cikin ɗakinta zumbur Hindatu ta miƙe tare da bin bayan Gana tana tafe tana riƙe zani da suɗe yatsun hannunta tana tunanin kakarta ta yanke saƙa daman ta biyu ta shigo gidan.... Littafin HIYAAM na kuɗi ne akan 1500. Muna tsarin discount akan mutanen farko da suka fara payment, daga book 1 2 3 za su biya 1k kacal. Wannan Discount ɗin ana kammala free pages an rufe. Mutanen farko da suka fara payment na HIYAAM za su biya 1k kacal ne. Idan mukai limit da yawa za mu yi Hiyaam a WhatsApp ne, idan ba'a samu limit ba, za'ayi a Telegram da ArewaPen. Kana da ikon siyawa ƙawayenka, ko ka yi sponsoring wa jama'a domin Allah ko kuma a tallata maka business ɗinka. Wannan tafiyar sabuwa ce, baku taɓa cin karo da ita ba. 0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S Shaidar biya. 08164069385 ko 08082101373 A yi weekend lafiya. *H I Y A A M* Page 10: The Girl Wagered Away Bright pens Yota/001 Distance means so little when someone means so much. May Allah watch over you wherever you are. NAZEEFAH SABO NASHE. Mun yi chapter 14 a ArewaPen. Turus Gana ta tsaya a bakin ƙofar tana nazari sai kuma ta juya da murmushi ta ce "Hindatu ina ganin ki bari zan shigo na kawo miki, tunda har man ya yi miki daɗi" a zuciyarta kuma ta ce "Sai na ba ki ƙanƙarar maitar ki ji idan maitar daɗi gare ta shasha" ta yi furucin haɗe da yin gatsine tana me haɗawa da ƙwafa a lokaci guda. * MD a baƙin ƙofar room ɗin da aka ajjiye Ahlam ya tsaya ya harɗe hannayensa a ƙirji zaka rantse da Allah ba sashin dasu Ahlam da nurse ɗin yake kallo ba. Hawayen azaba ne kawai yake fita daga cikin idanun Ahlam yana bin kumatunta. Nurse dake riƙe da kayan Treatment ta ce "Sannu Golden voice" "Kin sanni ne?" Ahlam ta furta da ƙyar tana cije laɓɓanta da yarfar da hannunta sbd zafi Nurse ta ce "E. Bake ce Ahlam Abdallah Kurmi ba, me yin dandalin nishaɗi program ɗin samari da ƴan mata a Bright Fm? Ina bibiyar shafinki na Facebook da Tiktok" duk da a cikin halin ciwo Ahlam take sai ta ji wani irin farinciki mara misaltuwa bata taɓa tunanin zata je wani waje a nuna an santa ba a dalilin aikinta na jarida, sai ta ji wani irin courage da confidence sun haɗe mata waje guda, ga wani hope data samu a furucin Nurse. Ta ɗan yi yaƙe ta ce "Thanks" "Muke da godiya ai Golden voice" ta faɗa da zumuɗi na farinciki "Idan an kammala treatment ɗin sai ku ƙarasa hirar taku ko?" Cewar Dr yana riƙe almaƙashi a hannunsa. Shiru Nurse ta yi ita kuma Golden voice ta kalli Dr a hankali cikin ƙasa da murya saboda har lokacin jini ke zuba a wuyanta ta ce "Sister ko za ki ara mini wayarki na yi vedio sai ki tura mini ta WhatsApp?" Cikin sauri Nurse ta ce "da gudu ma, Golden voice guda yadda nake mutuwar son programs ɗinki babu wanda bai san sunanki ba a bakina musamman ƴan gidanmu" wani yalwataccen murmushi Ahlam ta saki cike da jin daɗi da alfahari ta ce. "Ai har photo za mu yi, zan yi inviting naki zuwa shirin dandalin nishaɗi sister" "A wannan rana har party zan haɗa a gida" Tana faɗin hakan ta cire password ta miƙawa Ahlam wayar. Sun ɗauka wani nata zata kira ko gidansu zata sanar wa tsautsayin daya sameta. Sai su kaga akasin hakan, domin camera ta buɗe ta saita a kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka ta shiga faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Kamar yadda kuka sani sunana Ahlam Abdallah Kurmi matashiyar ƴar jaridarku wacce aka fi sani da Golden voice. A yau na tashi da babbar jarrabawa a sanadin aikin jarida, shigowata Bright Fm kenan wani ɗan balaja'u riƙaƙƙen ɗan daba ya kawo mini hari, wanda rayuwata ya nema kai tsaye Allah Ya kiyaye ni, ban san me na yi masa ba, amma ya yi iƙirarin ganin bayana kuma yace saboda rahotan matar da aka ƙonawa jariri ya yi mini haka. Kai ɗan'daba idan kana jina ka saurare ni da kyau, ni ƙadangaren bakin tulo ce ban fito ba sai dana shirya, aikin jarida yanzu na fara ko da kowa shi ne silar barina duniya ba zan tsagaita ba sai na cimma burina, yadda ka yi mini abin nan ka sake rura wutar abin, sai an ƙwatar wa matar nan haƙƙinta idan ma ubanka ne ya sa ka yi mini abin. Na gode jama'ata a tayani da addu'a hakan ma alamun nasara ne da ɗaukaka, zan zo muku da cikakken bayanin abin da ya faru da matar. Har kullum Golden voice ce taku" Tana kammala vedion ta miƙawa Nurse wayar ta ce "Na gode sister " "Babu komai. Allah Ya cigaba da tsare wa" cewar Nurse ɗin "Wayyo yayana, zan mutu wayyo Anty Jiddah" ta cigaba da ihu da yarfe hannunta saura kaɗan likitan ya fashe da dariya. Dukkan kuma abin da yake faruwa akan idanun MD baya ko motsi daga ƙarshe ma, juyawa ya yi yabar cikin room yana amsa kiran wayar da ake ta yi masa a lokacin. Treatment aka yi mata da allurai da drip Allah Ya taimaka yankan babu zurfi a jikinta * "Kan uba amma annarka uwar dukiya a gidan nan, Allah ka bamu mu taɓa, wasu sukan ce arziƙi kashi baka kwana dashi ba, sai ka tashi dashi. Kamar gidan ƴan Film" Tunda Emama ta shigo Baffas estate ta kasa yin shiru da bakinta saboda sambatu ganin daular gidan girma da arziƙinbgidan masu Jiha da juya wasu rassuna na ƙasashe. Gidan da ake ado da addini da taƙama da Musulunci gidan cikakkun mabiyan Izala (Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa lqamatis sunna). Ganin babban parlorn da ake ajjiye baƙi babu kowa sai su ya saka Emama zungurin Iftihal ta ce "Kalli gida ɗan ubansu, ba irin na gidanku ba wanda uwarku ta ja mana jarfa, ai Allah Ya isa tsakaninmu da Innti sau cikin carbi gantalalliyya matsiyaciyya" Iftihal ta runtse idanunta daga zaunen da take tun ɗazo ta ƙanƙame jikinta waje guda, wasu hawaye masu zafi suka shiga bin fuskarta. Idan ta buƙaci lallashin kanta da zuciyarta da zarar ta tuna wai an sakata a caca Alhaji Baita ta cita sai ta ji tsakanin rayuwarta da mutuwa babu tazara, walwala da farinciki sun sake nesanta kan su da ita. Iya rumbun cikin Alhaji Baita tsoro yake bata, balle ta kalli cikin bakinsa, gashi bata ma san ya kalar gidansa yake ba, babban abin da yake mata yawo a kanta bai shige rashin sanin aurenta zai yi ko kuma farkarsa zata zama a gidan? Tana cikin wannan tunanin Emama ta ce "Idan kina so a soke batunki da Alhaji Baita ki yi ƙoƙarin sace zuciyar wani namijin a gidan nan, ko me gidanne ma. Ina nufin magajin gidan, idan hakan bata faru ba, da zarar kinga an ajjiye kuɗi ki yi wuf ki saka su a hammata ko cikin wando ko cikin hular kan ki, su basa jin kuɗin a iska suke ganinsa ina faɗa miki. Ɗan raguye-raguyen abinci da nama duk ki haɗo kan su ki juye a leda ki kawo mini har gida. Ke ko wani ne ya nuna yana buƙatarki ki amince" sai ta yi saurin rufe bakinta ta ce "Asstagafirullah! Nan gidan malamai ne na manta ba za'a samu me bin mata ba" ita kaɗai take da surutunta ci kan ki Iftihal bata iya cewa ba. Ina zata iya magana? Bayan ƙirjinta ya jima da yi mata nauyi yana rinjayar zuciyarta, ji take kamar zuciyar ce zata tarwatse gabaɗaya ta huta. "Assalamu alaikum" Wata kyakkyawar yarinya ta yi sallama ba tare data shigo ba. "Maraba waye?" "Zan iya shigowa?" "Bisimillah" Shigowa ta yi ta gaishe da Emama ta ce "Mamy ta ce ku shigo ɗaya parlorn" "To to to babu laifi, ke tashi muje" tana faɗin hakan ta juya abinta. Emama ta ce tana kallon Iftihal dayin gaba. Iftihal bata san ya aka yi ta iya miƙewa ba, balle tasan yadda aka yi ta iya taka ƙafafuwanta taje bakin ƙofar kamar yadda bata san mene ya tsayar da ita a wajan ba. Ta ji ƙamshi na dukan hancinta ta kuma ji ƙwayar idanu na bin jikinta wanda ya sake sakar mata da lakar dake riƙe da gadon bayanta zuwa ƙafafuwanta. Idanunta rufe kamar yadda ƙofar zuciyarta yaja ya rufe bata san kuma mene ya haddasa mata rawar ɗari ba, gabaɗaya ta yi baya ta nemi zubewa a wajan. "Ki bi a hankali ko?' Ta ji sautin muryarsa ya sauka a kanta. Ta buɗe idanunta da ƙyar ganinta ya sauka a farar fuskarsa me ɗauke da nutsuwa da kamala, nutsuwarsa kaɗai ta isa ta nuna yadda ibada ta zauna masa domin ta tabon sallah nan a tsakiyar goshinsa, wanda hakan ya tuna mata da nata tabon ta miƙa hannu kaɗan ta shafi nata tabon hakan ya saka ya kai dubansa ga nata. "Ma sha Allah" Ya ce a fili yana bin gefenta ya shige. Iftihal ta ƙarasa ta zauna kanta a ƙasa ta ce "Ina yini?" "Allahamdulillah" Mamy ta amsa da kulawa. "Ita ce me aikin?" "E Hajiya ita ce kamar yadda kika nuna yarinya kike buƙata itama bata shige 17 ba" "Age mate ɗin Nadiyaah da Diyanah ce ashe ma" Mamy ta furta a fili kafin ta ce. "Shukràn alaiki. Waɗanda za ta yi wa aikin sa'ointa ne. Zata dinga musu breakfast, lunch da dinner. Ina ga iya lunch ne dinner bai wani dame su ba. Sai mahafinsu idan ya dawo" idanunta akan azkar ɗin hannunta take yin maganar. Da kamala a tare da ita. Emama ta ce "Duk zata iya babu assha" "Makaranta ta?" "Na'am........? "Bata zuwa makaranta ne?" Caraf ta ce "Lahaula bokoko a wuta? Ai tuni suka yi mata korar kare bata fahimta sam a karatun data samu mijin aure za'a yi mata" Daidai nan ya sake shigowa parlourn cikin sabuwar shiga wagambari ya saka ruwan sararin samaniya wanda ya kwanta a jikinsa ya ɗora hula me kyau ta zauna a sumar kan, bayan ya sake yin sallama ya nemi waje kusa da Mamy ya zauna. Mamy ta kalli Iftihal lokaci guda ta ji yarinyar ta shiga zuciyarta. "Ok. Per month kuke son salary ɗinta ko per year or daily? Wanne a ciki" Emama ta zazzaro idanunta waje. Mamy ta ɗauki a ƙallla minti uku tana duba azkar kafin ta ce "duk wata za'a dinga bata dubu ɗari da hamsin in sha Allah, ki je ita zata dawo gida anjima ko?" Sallama Emama ta yi musu ta tafi. Bayan tafiyarta aka nunawa Iftihal wani kitchen daban da zata dinga aiki a ciki. Mu'allim ya dubi Mamy ya ce "Baffa be sanar dake garin da yaje da'awa ba ne Mamy?" Kai kawai ta girgiza. Bai sake cewa komai ba, domin ya lura itama Mamyntasa bata da ra'ayin cewa wani abu a yanzu ɗin. Don haka sai ya tattara nutsuwarsa wajan jan idanunsa ya lumshe yana sauraran kiran Liman duk da babu tabbacin zai kira shi a yanzu ɗin kamar yadda ya ce. Kasa haƙuri ya yi ya dubi Mamy ya ce "Mā ismuhā?" (Ya sunanta)" A hankali ta juya ta watsa masa fararan idanunta ta ce "kana da business da ita ne Mu'allim?" "Mamy kika sani ko a haɗa bikina dana Akhy" azkar ɗin hannunta ta ajjiye ta kalli jaridar dake saman table ta miƙa hannunta tare da faɗin "Nāwilni" (Miƙo mini" ya ɗauki jaridar ya miƙa mata yana rusunar da kai gefe cike kuma da ladabi. "Mamy don Allah...," ta yi saurin katse shi da faɗin "Ina ga kamar ka san hanyar shiga kitchen ko Al'ameen?" Ya ɗan cire hularsa yana shafa kai bai sake magana ba, ya nufi saman bene Mamy ta bishi kallo har ya shige a hankali ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya me nauyi. Tana tsaye a gaban haɗaɗɗan madubin dake cikin bedroom ɗin tana yin rolling da mayafin abayar hannunta, silver ce irin wacce bata da nauyi a jiki tabi jikinta ta kwanta. A hankali ta ɗan yatsuna fuska saboda ciwon dake ɗarsarta har yanzu. Daga bayanta aka ce "Ukhty ina zaki ne?" Nadiyaah ta juya ta kalli Diyanah dake kwance saman kujera wacce take jikin gado, kayan shan iska ne marasa nauyi a jikinta sai data gama ƙare mata kallo ta ce "Abinci" "Yunwa nake ji..... Taja idanunta wanda suke sak irin na mahaɗinta ta ce "Sosai nake ji Ukhty" Diyanah ta sakko daga saman kujerar ta ce "Muje na tayaki girkin ko noodles ce" "Noodles dai?" In ji Nadiyaah. "Yeah. Kin yi waya da Baffa?" Girgiza kai kawai ta yi alamar a'a tana sake jan idanunta wajan lumshe su. Diyanah ta kama hannunta suna ƙoƙarin fita aka yi knocking cak suka tsaya. "Assalamu alaikum" a tare suka amsa sallamar. Ya ɗora da "Ina neman izinin shigowa wajanku" Diynaah na shirin tambayar waye Nadiyaah ta rigata da faɗin "Khālī Al'ameen, Mu'allim" "Bisimillah..." Ya buɗe ƙofa ya shigo. Gabaɗaya suka miƙa masa hannunsu alamar musabaha suka gaisa ya ce "Baffa fa?" Nadiyaah ce ta ce "Ya dawo ne? Ban ji Ƙamshinsa ba, jikina bai bani Baffa am yana kusa damu ba" Mu'allim ya girgiza kai ya ce "Bai dawo ba, ina tambayar ko kun san garin da yaje da'awa" Nadiyaah ta ce "Ask Ukhty Diyanah" tana faɗin hakan ta fita. Diyanah ta ce "Ban san sunan garin ba, amma dai garin babu sauƙi suna da wahalar sha'ani ya ce, koyaushe za'a iya jin dawowarsa a wayar da mukai dashi jiya" sai ta ɗan ɓata fuska kuma ta ce "Wait, meye ne kake nemansa har haka?" Mu'allim ya harareta kafin ya ce "kuɗin aure zai kai mini ne in sha Allah" "Oh really?" "Yeah.... In sha Allah" "Allahumma barik, wace matar her name?" "Ban san sunanta ba for now" Da rashin fahimta Diyanah ta ce "Are you kidding me? Taya hakan zai faru?" Ya ɓata fuska ya ce "Ƙaddara. Yarinyar tana kitchen ɗinku, please ki sama mini sunanta da number waya har ma da address me gabaɗaya nake so a yi, rana ɗaya za'ayi bikinmu da Akhy Liman" sai Diyanah ta rage tafiya kaɗan ba tare data ce komai ba suka sauka ƙasa. Gidan babu hayaniya sanda suka sakko Mamy bata nan sai Nadiyaah da Azizah wacce take ta yi wa Nadiyaah magana tana amsata jifa-jifa yaran basa shiri da Azizah tunda suka ji ita zata auri Baffansu, suna ganin kamar age mate suke da Azizah a nasu tunanin,kuma bata dace da Baffa ba, infact basa buƙatar Baffansu ya yi aure idan akwai abin da Nadiyaah da Diyanah suka tsana suke yin kuka a kan shi sosai da kwanciya ciwo, su ji ance Baffa am ɗinsu zai yi aure, wani irin mugun son shi suke yi da kishinsa mai tsanani, kishin da ya kamata ace murgayiya mahaifiyarsu ita za ta yi wannan kishin, sai ta tafi ta bar musu suke damawa. Suna ganin abin kunya ne a gare su ace Baffa am ɗinsu ya yi mata kuma har ta haifi baby, ta haifi little sis or brother. Basu da sani da cewa, shi Baffa da kan shi baya ra'ayin auren, uwa uba bashi da lafiya ta kasance da mace a dalilin hatsarin da ya taɓa yi shekarun baya. Baya jin feelings na kowacce mace, kamar yadda bai taɓa ganin kyawun ko wacce ɗiya mace a idanunsa ba, babu wata mace data taɓa burge shi a rayuwa. Diyanah ko Azizah bata kalla ba ta shige Kitchen tana shiga aroma ɗin girki na shiga hancinta, ta ƙarasa idanunta akan Iftihal ta ce "sannu da aiki sister?" Cikin sauri Iftihal ta durƙusa ta ce "Barka da yamma" sosai Diyanah ta ji rashin jin daɗi ta ɗagota ta ce "Ki bar durƙusawa babu kyau. Sunana Diyanah Sayyadi Baffa. Kefa?" Ta ce "Iftihal, sunana Iftihal" "Ma sha Allah. Kin kammala ne?" Iftihal ta ce "Eh Anty" "Who's Anty abeg? Call me by my name" zuba mana abincin a babban plate with 2 spoon me and Nadiyaah than you, Nadia bata cin abinci da spoon irin Baffa am ce "A'a nikam Allahamdulillah, bari na zuba muku" Diyanah gefe kawai ta koma ta zubawa fuskar Iftihal ido, bakyau ne ke bata mamaki ba, itama kyau gadon nasu gidanne, amma ta rasa me take kallo a fuskar Iftihal. "Kina wacce unguwa ne?" A hankali ta ce "Kankarofi" sai Diyanah ta buɗe ido ta ce "Ya rabb, tun daga can sannu sister. Give me your number so that muke gaisawa lokaci zuwa lokaci" murmushin da ake kira da yaƙe kawai Iftihal ta yi ta ce "Bani da waya, sai dai ya yayana idan kina so" wani irin rashin jin daɗi ya wanzu a zuciyar Diyanah ta ce "Ba damuwa saka mini" wayarta ƙirara iPhone 15 ta miƙawa Iftihal ta ce "Saka mini number tasa, ki kira yanzu ki faɗa masa sunana ya yi saving" Bayan ta saka number Yaa Jaheed nan take kira, abinka da talaka wanda yake nema ya ɗauka customer ne tuni ya ɗauki kiran ya ce "Hello...." A hankali muryarsa ta sauka a kunnen Diyanah ta yi shiru tana saurare. "Yaa Jaheed ni ce Iftihal" "Masoyiyyar" ta ce "Na'am" "Kina ina? Wayar wacece wannan kika kira da ita?" "Wani gida Yaa Jaheed ka yi saving number nan ka ji" ta cikin wayar ya ce "Bangane ba, number wanne ƙaton kika samu da za ki ce na yi saving? Ya sunansa Tanimu ko? Wayar ma na san rakani kashi ce yasin, to ba zan saka number nan a Vivo ta me capacity ba" Murmushi kawai Diyanah ta yi, Iftihal kuma ciro wayar ta yi a kunnenta tana jujjuyawa ta kalli Diyanah ta ce "Ya sunanta?' "IPhone 15" "Kan uba IPhone 15, masoyiya wayar waye wannan maza bashi a barsa kar ki fasa ki ja mana masifa muna lallaɓa rayuwarmu" a hankali ta ce "In sha Allah. Ka yi saving ka saka Diynaah" a fili ya ce "Wow, sunan larabawa ne, Diynaah wa kar Innti taga number ta ɗauka lalacewa na yi na fara kula ƴan'matan Kano" Diynaah ce ta amshi wayar ta ce "Ahky Jaheed ka saka Diynaah Sayyadi Baffa" ji ya yi komai nasa ya tsaya cak, Sayyadi Baffa kamar fa babban malamin da ake tutiya dashi a Kano da Nigeria bakiɗaya. "To. In sha Allah" ya amsa a saɓule yana kashe kiran. Aka ce da Iftihal ko ta bar abincin za'a iya a sarar shi ta tabi dashi gida, da farko taƙi amma data tuna yanayin gidan sai ta tattara abincin da nama fal da kayan fruits. Lokacin ana kiran sallar issha ne, sai da ta yi sallah kafin nan. Da ƙyar Mamy ta lallaɓa Iftihal akan Mu'alim ya kawo ta gida. * Tunda suka dawo gida Engineer yake ta jera mata sannu, ita kuma sai langwaɓe masa take yi da kukan shagwaɓa. "Kin gani ko baby? Ai na faɗa babu inda ba'a san Golden voice ba a faɗin Kano, ina da tabbacin sai kin zama babbar ƴar jaridar da za'ayi ko yi da ita wacce zata shiga kundin tarihi kuma ta zama abar tunawa. Wannan ma ɗaukaka ce kuma ta ɓangarena ba zan bari abin da akai miki ya tafi a banza ba, tunda naga gidan rediyon taku ba ta yi yunƙurin komai ba" Ahlam ta ce "Abban Mufeed, ni wannan abin ya yi mini daɗi duk da ya cuce ni daya ɓare mini baki gida biyu ai daya cuce ni ya cuci masu ƙauna ta wallahi" Engineer ya ce "Kuma da ya cuci mijinki ma" sai ta yi saurin sauya maganar da faɗin. "Zan koma gidan matar na yi hira da ita, zan ɗora hirar a wani sabon program ɗinmu na MU FARKA MATA" cikin jin daɗi da nuna goyon baya ya ce "A'a ka da ki koma gidan nan baby, haka kawai su danne mini ke su yanka na shiga uku" ta ɗan murmusa kaɗan ta ce "Uhm" "Be careful my love ok?" "By the grace of God" Miƙewa ta yi ta musu sai da safe ya shige ɗakinta, wayarta ta ɗakko ta kunna cikin sa'a tana shiga WhatsApp taga Nurse ɗin ta tura mata vedion, kai tsaye ta shiga Facebook ta yi positng vedion da caption ɗin. "Beging a Journalist isn't easy" cikin ƙaramin lokaci ta tara comments ɗin mutane sama da dubu biyu wanda kusan duka rabinsa jaje suke yi mata da ƙara mata ƙarfin zuciya da confidence, bata taɓa tunanin haka aka santa a social media ba sai yau ɗin nan. Ta shiga tambayar kanta kenan muryarta bata tafi a banza ba? Kenan duk ƙoƙarin da take yi bai shuɗe a banza ba, sannu a hankali take jin nutsuwa na sauka a zuciyarta, nutsuwar data haɗo mata da wani wish and hope, suka cure waje guda tare da zama big dream ɗinta na rayuwa, hakan ya sake tunatar mata da burinta na ɗaukaka a duniyar aikin jarida, ba zata taɓa manta wulaƙanci da cin mutumcin da Yussy ta yi mata. Ko kalaman data jefe ta dasu bata buƙatar tunawa, balle ita kanta Yussy ɗin. Sai dai me? Abin ya zame mata kamar yadda a duk sanda ta runtse idanunta ko kuma tazo kwanciya bacci sai maganganun sun dawo cikin kanta, sun maimaita kan su. Hakan ɗin ce ta kasance a yanzu ma, ji ta yi kamar a daidai wannan lokacin ne komai ke faruwa tsakaninta da Yussy muryarta ta ji tana sauka a kunnenta. "Ai Ahlam ko za ki ƙarar da duk abin da kika mallaka ba za ki taɓa bin layin dana bi ba, balle ki huce ni. Na ba ki shawara ba ki ɗauka ba, zan sake ba ki a yanzu wataƙila ki yi aiki da ita zuwa gaba sai ki gode mini" a wancan lokacin Ahlam na tsaye fitowar ta kenan daga office ɗin Editor-in-chief taje kai masa wani labari data samu akan hanyarta ta zuwa gidan rediyon, lokacin tana matsayin News Gatherer, sai ya nuna labarin bai yi ba, ba balle ya samu ƙarbuwa ba. A lokacin har kuka ta kusa yi saboda baƙinciki labarin wani dattijo ne da ya yi wa yarinya ƴar 3 years fyaɗe, amma saboda bata ɗauki rahoton murya ba ya yi watsi da ita. "Sir wallahi yanzu labarin nan ya faru babu wata gidan jarida da suka wallafa ko gidan rediyon da suka sanar, Bright Fm ce zata zama ta farko ka yarda dani akan idanuna aka kama dattijon" wani kallo ya yi mata irin na bata isa ba, yaushe ma ta shigo aikin? "Look Ahlam, bawai da ka muke watsa labarai ba, abu muke na ilimi wanda mutane za su yarda dashi. Idan muka yi saken da aka saka wannan labarin mutane da yawa za su daina sauranmu" cikin rawar murya ta ce "Sir don me ya sa za su daina?" A taƙaice ya ce "Saboda ƙarya ce tsantsa a rahoton naki" Jiki a saɓule ta miƙe tare da ficewa daga cikin ofis ɗin, hawayen daya ciki idanunta ya tilasta mata tsayawa a wajan tana share su da shanyayyen hannunta, a daidai lokacin ne kuma ta ji sautin dariyar Yussy shine ta ɗora da wancan maganar ta sake faɗin. "Ki koma ki nemi tabarma da roba ki fara zaman bakin titi Ahlam, trust me za ki samu sadaƙa sosai. Nakasassu basu da wata sana'a ai bayan wannan. Amma kinga aikin jarida?" Sai ta yi shiru tana cije lips ɗinta da kallon Ahlam na wani lokacin. "Za ki ji fa kamar muguwar shawara nake ba ki, ki saka a zuciyarki ni me son ki ce, idan kuma kika tilasta a wannan sabgar to haƙarki ba zata taɓa cimma ruwa ba, babu inda za ki je a aikin jarida, ki duba kamar haka.....," Ta nuna ofis ɗin da Ahlam ta fito, tare da nuna rahotannin da suke hannunta ta ce "Haka ce zata dinga faruwa dake daga nan har a kore ki daga aikin jarida wallahi" Wani irin murmushi Ahlam ta saki bayan ta gama goge hawayen kallon sama da ƙasa ta yi wa Yussy ta ce "Ashe kina tara sani da Allah Yussy, ashe kin san me gobe zata haifar ko?" Cikin sauri Yussy ta ce "Ke kam gobenki ai ta jima da bayyana a idanun jama'a" A wannan karan ma murmushi Ahlam ta yi ba ta ce komai ba ta yi gaba.Har ta tafi ta ɗan tsaya ta ce "Yussy ki rubuta ki ajjiye in sha Allah muryar Ahlam sai ta kare duniya ba iya jihar nan ba, ba iya ƙasar nan ba, duniya gabaɗaya. Na yi miki alƙawarin sai muryar Ahlam ta hanaki bacci Yussy, idan kin shirya na shirya shege ka fasa" tana faɗin hakan ta yi gaba abinta. *Ajjiyar zuciya Ahlam ta sauke bayan ta gama tuna kaɗan daga cikin wulaƙancin da Yussy take ba, ta dubi hannunta dake maƙale a fili ta ce "Kai ina, Impossible wannan hannun ba zai taɓa hanani cimma burina ba" duk abin da zai faru tana buƙatar samun Outstanding Journalist Award. Sai ta fara tunanin wanne irin abu za ta yi in few days da zai saka ta samu wannan Award ɗin? Ta runtse idanunta ta sake buɗe su. "Think Think..... "Ahlam think" Wayarta ta ɗakko ta kira Anees tasan yana da night duty bai yi bacci ba yanzu ba. Bayan ya ɗaga kiran ta cikin wayar ya ce "Baby ya jikin naki?" Da nutsuwarta ta ce "Da sauƙi" "Ma sha Allah. Akwai wani abu ne?" Ta sauke ajjiyar zuciya "Anees" Calmly ya ce "Na'am" "Kana ganin idan na yi Interview da Sayyadi Baffa zan iya samun karramawa ta musamman?" Anees ya yi shiru domin a bazata ya ji maganar tata. "Ka yi shiru" Ya ce "Wa kika ce baby?" "Sayyadi Baffa" Wani ƙarfaffan numfashi yaja a ƙirji ya fesar mata dashi ta cikin wayar, da ƙyar ya ce "Kin taɓa ganinsa ne? Kina da hanyar da za ki ganshi har ki yi Interview dashi? Hakan ba mai yiyuwa bane baby, ki sauya idea ba za ki taɓa samun dabar yin hira da Sayyadi Baffa ba" jikinta na wani irin rawa da ɓari cikin karyewar murya kamar za ta yi kuka ta ce "Don me ya sa? Shi ɗin ba mutum bane?" Anees ya ce "Of course mutum ne, amma ba gamagarin mutum ba, to cut the conversation short da ace hira da Sayyadi Baffa abu ne me sauƙi to da tuni Bright Fm ta yi hakan. Daga nan jiharmu da ƙasar babu wata gidan jarida daya taɓa yin hira dashi wallahi Allah, mutumin da ko ganinsa ba'a taɓa yi ba, saboda taka tsantsan irin nasa" shiru Ahlam ta yi domin ita Sayyadi Baffa shine target ɗinta akan shi ta ɗora duka hope ɗinta. A hankali ta ce "Amma Anees mene dabarar hakan da yake ɓoye kan shi? Na ji ance kamar yana da raya ko?" "Nima a haka na ji wai yana tagwayen yara amma babu tabbaci, domin babu wanda ya taɓa ganinsu. Kin ɓaro aiki babba baby" "Uhmmm" ya ji taja numfashi ya yi saurin lumshe idanunsa yana sosa ƙirjinsa a nutse "Trust me Anees zan yi shira da Sayyadi Baffa, zan zama ta farko zan ɗaga Bright Fm da hirata da Sayyadi Baffa ka yi mini addu'a" "Best of luck baby, ki yi a hankali kuma" "I will.... Definitely" Ta sake cewa "Anees, I'll make my words" "Idan ya tabbata haka ne daga Bright Fm za ki shige Special training opportunity NIJ Lagos, kina kammala sai BBC yin attachment" idanunta ya cicciko da hawaye cikin rawar murya ta ce "da har abada bani da bakin yi wa Ubangiji godiya daya ƙaddara mini cikar burina ina raye ina kallo, maƙiyana za su kalli ɗaukakata babu yadda suka iya, Anees bani da burin daya shige na ganni a BBC ko VOA" cikin ƙasa da murya ya ce "Za ki cika burinki da yardar Allah baby" Ta ce "Allah Ya sa. Good night" "I love you... I so much love you Ahlam" Ƙit ya ji ta kashe wayar ya yi murmushi yana ajjiye wayar shima. A hankali kuma ta shiga tunanin kalmar Tiv dake mata yawo a cikin kanta da zuciya. **Tana tsaye a harabar masarautar jikinta sanye da wani ƙyalle da kuma wasu ganye manya, manyan mutane maza da mata sun kewaye ta suna mata kirari da kuka tare da roƙo da magiya, ga wani kaɗe-kaɗe da suke yi. Da rawar ɗari ta ce "Su waye ku? Me kuke buƙata a wajena, ina ne nan waye kawo ni nan wajan" ta shiga tambayar su, da alama basa jin hausa koma suna ji alamun hakan bai nuna a tattare dasu ba, ita sai taga kamar ma naman mutane suke ci. Wani daga cikinsu ne ya zube a ƙasa daidai ƙafafuwansa ya ce "Kakanninmu sun shuɗe suna zaman jiranki, Iyayenmu sun tafi da baƙinciki rashin ganinki, mun rasa rayuka da dama saboda ƙin bayyanarki, mun rasa dukiya mun rasa ƙarfi da iko, mun shiga cikin fushin Akombo. Ki cece mu MAMA ki dawo mana da kima da martabar TAJMAHAR, kece UWA MAMA a gare mu" A kiɗime ta yi baya ta ce "Wallahi bani bace, ni ban san wata uwa mama ba, sunana Ahlam ku rabu dani bani bace wallahi" ihu da kuma kawai take yi "Subuhanallahi baby ke da waye haka?" Engineer ya shigo cikin ɗakin da gudu yana riƙe ta ganin yadda take fusge fusge tana cewa ba ita bace ihunta ya cika gidan nasu. "Abban Mufeed anya ba za'a haƙura da aikin nan na Ahlam ba, mijinta me rufin asiri ne zai iya kulawa da ita, na fara jin tsoro gaskiya" girgiza kai Engineer ya yi yana rungume da Ahlam tare da tofa mata addu'a yana jin yadda ta ƙanƙame shi kamar ance za'a ƙwace ta daga wajansa sai numfashi da ajjiyar zuciya take saukewa. "Sannu kakata, tsofan ne ya motsa?" Da ƙyar ta yi maganar saboda wani abu daya tsaya mata ganin yadda Abban Mufeed ya rungume Ahlam. Ahlam ta ce "Tsoro nake ji Anty Jiddah" "Baby ko za ki haƙura da aikin nan?" Engineer ya ce "Hawwa'u Ubangiji baya jarabtar bawa sai ace yabar abu? Sakaci ne irin na yaran zamani wataƙila haka ta kwanta babu alwala balle addu'a ba dole mutum ya dinga mugwayen mafarkai ba" ya duba lokaci ya ce "Zan tafi masallaci kar na makara ki tashi ki yi alwala ki tabbata kin yi lafila tare da azkar" Anty Jiddah ta ce "Baka jin firgitar da na yi ba, har cikina ne ya juya na ɗauka ko biyota aka yi har gida" Bayan mijinta tabi suka fita a tare Ahlam ta yi shiru tana tuna mafarkin da ta yi. * Sanda Mu'alim ya sauke Iftihal akan corner ɗin unguwarsu bata jira sun yi magana ba, shi ɗinma da yake ƙoƙarin cewa wani abu sai ya samu rashin kuzarin tanka ta, ya fahimci tsoro da firgici a tattare da yarinya, bai san dalili ba, kamar yadda bai san wani abu na musamman da ya fusgi ra'ayinsa akan ta, ya ji ta yi masa, ya kuma gamsu ta yi ɗin, ya ji ta cancanci ta zama Mrs Al'ameen Hafizz Baffa, mata a wajan Mu'alim. Kamar ma bata taɓa shiga mota irin wannan ba idan ka ɗauke batun napep yana kallon yadda take takawa a hankali har ya isa corner. A hankali ya sauke gilashin motarsa ya ɗan leƙa, shi kamar ji ya yi ta ce "My Mu'alim" daidai lokacin itama ta juyo suka haɗa idanu sai ya jinjina mata kai alamar ta shige ciki. Ashe dai kiran nasa ta yi, ba kira na baki ba, kira dake tsakanin zuciya da zuciya. Ya ɗauki lokaci kafin ya iya kunna motar ya yi reverse ya bar Kankarofin gabaɗaya ya nufi Maitama Sule, da zumuɗin ƙara ganinta. Kamar mara gaskiya haka Iftihal ta shiga gidan nasu da sallama suka amsa mata, a cikin muryoyin da ta ji babu ta mahaɗinta cikin damuwa ta shiga rarraba idanu ta kalli Innti ta ce "Ina mahaɗita Innti?" A sanyaye ta ce "Tana ciki, sai yanzu Iftihal?" "E, ya gida Sahibarmu? Ya aiki da jikin mahaɗita?" Innti ce ta miƙa hannunta wajan riƙo hannun Iftihal ta zaunar da ita kusa da ita ta ce "Ita kam da sauƙi naga, Yaa Jadid ne jikin nasa sai godiyar Ubangiji, wankin ƙoda yake buƙata, babu kuɗi wajena na kuma rasa mafita da abin yi, ɗazo ma jikin tsoro ya bani, ganin yarona na sha wahala ga abu bane me sauƙi da zuciyata zata jure" "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Iftihal ta faɗa tana runtse idanunta, another banger, another problem. Su kam me rayuwa take nufi da tasu rayuwar ne. A hankali ta ce "Innti kuɗin dashi, ki ari kuɗin dashin mana tunda daman Baba Bala za ki bawa ɗauka, zai yi miki lamunin rance zuwa ki samu ko?" Innti ta yi shiru domin bata son tace an sace kuɗin, babu ɓarawo a yaranta kai tsaye za su ce Daada ne "Rabani da Bala ɗiyar arziƙi, Bala fa? Tabɗim" Iftihal ta zubawa Yaa Jadid dake kwance idanu kan shi a kan cinyar Innti tana masa addu'a da firfita da mafici. Da rawar muryar sosai jikinta na rawa Iftihal ta ce "Ko za ki siyar da kan kekenki sai a nemi ciko?" "Wanne keken? Kan nan ko dubu goma ba zai yi ba, asara ce siyar dashi, kuma dashi nake amfani me hamsin ɗari ina mana abin da ya sawwaƙe na kai wa baka, ga mai atamfar can da ɗinkin ya lalace tana ta sintiri na rasa mene ya lalata ɗinkin lafiya ƙalau na kammala" Iftihal ta fashe da wani irin kuka jikinta na rawa ta kasa cewa komai, Yaa Jaheed ma shirun ya yi yana lissafin rayuwa da inda zai iya samu kuɗi akai ɗan'uwan nasa asibiti, duk inda ya yi tunani sai yaga a rufe hanyar take babu sauƙi ko kaɗan a lamarin. Hatta ogansa na wajan aiki ya tambaya yace babu kuɗi a wajansa A daidai wannan lokacin kuma Ana ce a cikin ɗaki zaune ta rungume hannayenta a ƙirji idanunta rufe, sai ka ɗauka bata da rai sannu a hankali ƙirjin nata ke ɗagawa. Tunani take yi ita da zuciyarta, wacce hanya za ta bi wajan ƙwatuwa Innti haƙƙinta, da matsayinta? Wanni littafi da Zainab Alƙali ta karanta ne ya faɗo mata, ta tuna yadda matar takai mijinta ƙara ofishin ƴan Hisba, har aka hukunta mijin akan kuskuren da ya yi, hukunci irin wanda Shari'a ta tanata. A fili ta ce "Ina ne ofishin ƴan Hisba a nan? Ina zan samu kuɗin mota?" Ita kam ko a ƙafa ne zata iya zuwa muddin zata samu ganin jama'an hisbar. Sallama ake ta rafkawa a ƙofar gidan sai Babban yaya wanda yanzu ya shigo ya miƙe domin ganin waye, yana fita ya yi turus ganin Alhaji Baita, kallo ɗaya ya yi masa ya kawar da kai, ba ɗabi'ar zuri'ar Innti bace raina na gaba don haka a ladabce ya gai da Alhaji Baita cikin kamilalliyar muryarsa wacce sai a lokacin Baita ya taɓa jinta. "Yawwa nace ina Ayshatul-Iftihal ɗin? Na biyo sawu ne na gaza haƙuri naga har war haka ba'a kawo ta gidana ba, kamar yadda muka yi da Daada" Da rashin fahimta Babban yaya ya juya idanunsa alamar "Wacce Aysha? Wanne gidan kuma?" A fusace Baita ya ce "kai bana son shiririta uban naku bai baku labarin ya saka Iftihal a caca ba, kuma nine wanda na yi nasara, idan baka da labari yanzu ina baka, akan naira miliyan ashirin ya saka Iftihal a caca, kuma nine wanda ya yi nasara na riƙe kuɗaɗena, kuma na ci yarinya. Ka shiga ka fito mini da ita yanzu mu shige, tun safe nake jiƙe-jiƙe a takure nake ta ciki, banda yayyu babu abin da nake yi. Yau ranar hutawa ta ce Allah ya kashe ya kuma bani" Babban yaya ji ya yi komai ya tsaya masa ya kuma daina fahimta, ya kalli Alhaji Baita sama da ƙasa, iya haƙorinsa kaɗai tayar masa da zuciya yake yi, ga cikinsa kamar an yi masa ajjiyar yara goma, ko kuma wanda mayu sukai masa ajjiya. "Yanzu ita Iftihal kaza ɗauka?" Haka kallon Yaya ya bawa Alhaji Baita raddi. Alhaji Baita ya ce "A rubuce wannan take" Sai ya yi baya kaɗan ya jinjina kai alamar "Tana ciki, jeka ɗauke ta" abu kamar wasa yaga Alhaji Baita yana ƙoƙarin shigewa cikin gidan da sauri ya saka hannunsa ya tura shi baya da wata kakkausar muryar data motsa zuciyar Baita saboda kwarjinin da take dashi ya ce "Ashe girman biredi ne kawai da kai, baka da saiti har haka? Bari na faɗa maka gaskiya, yadda kukai cacarku babu wanda ya sani haka yanzu zaku ƙare ta iya ku. Muddin ina numfashi kuma ɗan halak ne ni wallahi Iftihal ta haramta a gare ka, ni kaina da kake ganina ɗan wahala ne ni, rashin sanin waye ni zai saka ka yi maganar nan....," bai ƙarasa faɗa ba ya ji an ɗauke shi da mari, kafin Babba yaya ya dawo hayyacinsa cike da ƙonar rai Yaa Jaheed ya wankawa Alhaji Baita mari, ya rama marin da Daada ya yi wa Babban yaya, da gudu kuma ya arce cikin gidan. Alhaji Baita ya kalli Daada ya ce "Ashe yaranka basu da tarbiyya?" Daada ya ce "Ina suka ganta daman? Ko wani ya faɗa maka suna da ita?" Sai ya juya kan Babban yaya ya ce "Kai kuma muddin kai ba ɗan shege bane, bada cikinka uwarka ta shigo gidana ba, ka yi gigin hana shi tafiya da ita mu gani, sakarai wawa tasono hanci duk majina, kana tafiya kamar mace lusari. Ai tunda ka fito daga cikin Innti babu yadda za'ayi ka zama wani abu a rayuwa, babu yadda za'ayi ka yi nasara a rayuwa sai ka lalace ka zama annoba wa jama'a, dukkaku lalatattu ne billahi" saboda tsananin ɓacin rai idanun Babban yaya har wani rawa suke bayan firfitowa waje da sukai jijiyoyin kan shi suka mimmiƙe, sai yanayinsa ya fara sauya da sauri ya fice daga cikin gidan gabaɗaya. Daada ya kalli Baita ya ce "Jira na fito da ita" A can cikin gidan kuma bayan Yaa Jaheed ya shiga a guje bai iya tsayawa a wajansu ba, ɗaki ya shige kai tsaye ya rufe ya fashe da wani irin matsanancin kuka, wai Iftihal aka saka a caca? Har lusari bagidajen mutumin na iƙirarin zai huta da ita. Ji yake yi kamar ya haɗiye zuciya ya huta. "Sannu ƙaunata ba dai jikin bane ko?" Cewar Iftihal tana kallon Ana. A hankali ta lumshe idanunta cikin sanyin murya ta ce "Yaa Sam ya ce zai zo kuma shiru" murmushi Iftihal ta yi kafin ta ce "Allah dai ya nuna mana wannan rana" Da rashin fahimta ta juya idanunta ta ce "Heee, wacce rana?" Harara Iftihal ta watsa mata kafin ta ce "Kinga wacce na yi aiki a gidansu yau" ta nunawa Ana picture ɗin Nadiyaah da Diyanah ta yi status dashi, a tunaninta Diyanah ɗince. Ana ta zubawa photon Nadiyaah idanu musamman idanunta a hankali ta ce "Idanunta manya masu kyau dasu" sai kuma ta taɓe bakinta. Iftihal itama zubawa idanun ido ta yi a fili ta ce "Tubarakallah ma sha Allah kam dasu" "Kina ina fito don uwarki wannan mara amfanin a duniya, wannan wacce ta yi asarar haihuwa duniya da lahira wannan mara rabon, sai kun farraƙa in sha Allah" muryarsa kaɗai tsayar da numfashin Innti da yaranta yake idan ka ɗauke Ana da Babban yaya. Wani irin masifar tsoron Daada suke yi kamar sun ga mala'ika. Jikin Iftihal na rawa ta miƙe tsaye, ana kam ko motsi ba ta yi ba, domin hargagin zautaccen mutumin nan ya daina zama damuwarta. Ɗaki Daada ya shige yana sababi. Ana ta kalli Iftihal sosai ta ce "Wai meye kike rawar ɗari, kifa daina saka damuwar bugaggen mutumin nan akan ki. Wallahi idan ba haka ba, watarana sai ya zama ajalinki sai ya kashe ki da baƙinciki ya rabaki da duniya. I'm telling you ki share shi" Da wani irin ƙarfi da firgitacciyar murya Iftihal ta ce "Mahaɗita na shiga uku, a caca Daada ya saka ni, yanzu haka gidan Alhaji Baita zai kai ni, ni Daada ya saka a caca kuma an yi nasara akan shi. Ya hanamu zuwa makaranta a sanda zamu rubuta jarrabawa ta shiga SS1. Burinmu ya rushe Ana, mafarkanmu sun zama tarihi Ana, ba zan taɓa zama ƴar jarida ba, ba za ki taɓa zama marubuciya ba. Ya ce zai tsine mana idan muka je makaranta ko a bayan idanunsa ne" zumbur Ana ta miƙe jikinta duka rawa da ɓari yake idanunta na lumshewa yana ƙaƙƙafewa numfashinta na ƙoƙarin tsayawa ta futar da kalmar bakinta a wahalce "Kan uba, uban kuturu ya yi kaɗan balle na makaho, wallahi bai isa ya hanani zuwa....," Kafin ta ƙarasa Innti ta saka bayan hannunta ta make mata baki, nan take leɓenta na ƙasa ya fashe, da wani irin yanayi na sarewa da macewar zuciya daga abin da take so Ana ta ce "Innti duka? "Me ya sa bakya so na ne Innti......" Ta kasa ƙarasawa "Saboda mijinki kike wannan?" Jajur haka idanun Innti ya yi gashi sun ƙanƙance tare da shigewa ciki tana wani irin haki da dafe ƙirji ta ce "Saboda duk abin da zuciya ta raya miki ne Nanaah, wallahi akan idanuna ko bayansa, ina duniya ko bana duniya kika bijirewa Daada, ki kai rashin biyayya a gare shi ban yafe ba, ban yafe muku ba duka. Mahaifinku ne yana da iko da hakan, duk abin da ya zartar akan ki ya zartu babu haufi. Mene don ya saka Iftihal a caca? Haka tunaninsa da lissafinsa ya bashi, hakan yake ganin shine dai-dai. Idan ƙaddararta ce hakan babu yadda za mu yi sai dai mu yi mata addu'a Ubangiji ya bata haƙuri da juriya ya sanya mata salama ko?" Cike da takaici da baƙincikin da ya yi mata yawa a zuciya take faɗin hakan "A'a.... A'a Innti" Iftihal ta ce tana ƙanƙame jikinta da rusa wani irin firgitaccen kuka ta ce "Ba ruwan ƙaddara, idan ma akwai ta, Daada ne ya zaɓa mini wannan muguwar ƙaddarar da kan shi. Don Allah kar ki bari ya tafi dani, Innti ke uwa ce kin san ɗaci da raɗaɗin hakan, kin san zafin dake cikinsa. Wallahi idan Daada ya tilasta zuciyata zata iya bugawa. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku, ki taimaka mini Sahibata" Ana ma fashewa da kuka ta yi taje ta rungume Iftihal ta sumbaci goshinta da kuncinta ta riƙo hannayenta ta sumbata. "I promise you in dai ina raye babu inda za ki, idan dole sai kin je zani a madadinki, za'a maye gurbina dake, ki zauna da Innti ko ƙaddarar ce ni na shirya mata, ni na amshi ƙaddarar" kuka suke yi sosai sun ƙanƙame juna. Innti sulale wa ta yi a wajan, ta kasa fitar da hawaye balle kuka ta yi hooking ma gabaɗaya bata sam meke yi mata daɗi ba, bata hayyacinta balle ta lura da suman da Yaa Jadid yake yi. Daidai ne Daada ya fito suna ganinsa suka ƙanƙame juna, Ana ta dafe hannun Iftihal ta ce "Daada zani a madadin Mahaɗita zan bika" kallon tsaf ya yi mata sai ya ce "muje" Ya miƙa mata hannunsa, hannun ta kalla sai ta miƙa nata zata ɗora akan nasa kenan ya cafke hannun ya fito da sabuwar reza ya kama tafin hannunta ya shiga tsaka hannun, wani ihu Iftihal ta kurma, ihun daya dawo da Innti daga hayyacinta ta miƙe ta ce "Daada! Mene haka ka sakar mini ƴata" "Kina matsowa a bakin aurenki wallahi" Cak ta tsaya, ta zubawa jinin da yake tsiyaya daga hannun Ana yana sauka a ƙasa, Ana ko motsi ta kasa kamar yadda ko tari ta kasa, ta kafe Daada da manyan Idanunta, sai daya kammala rubuta sunan Daada a tafin hannunta sannan ya fusgeta ya cillata a wani ɗaki me masifar duhu ya rufe ya saka ɗan makulin a alijuhu da ƙarfin gaske kuma ya shiga jan Iftihal tana tirjewa haka ya jata har ƙofar gida inda Alhji Baita yake tsaye yana sake shanye haɗin tsumin da ya yi, duk da wannan robar ya sha kusan roba goma ta tsumin maza. "Gata riƙe ta ku tafi" Daada ya ce yana tura Iftihal waje yaja ƙofa ya rufe.... *H I Y A A M* Page 11: The Price of Betrayal Bright pens Yota/001 NAZY's KITCHEN me abincin ƴan gayu, duk wani nau'in ƙwalam da maƙwalashe, da kayan jiƙa maƙoshi da fita kunya za'a samu a wajanta. 08033748387 Iftihal ji ta yi kamar ana jan zuciyarta daga cikin ƙirjinta, ta kasa kuka sai haɗiyar zuciya idanunta rufe haka Alhaji Baita ya damƙi hannunta ya riƙe yana washe bakinsa. Daada ya kalle ta yana nunata da yatsa ya ce "kuma wallahi kika sake kika bar gidansa sai na tsine miki albarka kin bi duniya, gargaɗi nake miki" har ya rufe ƙofar ya buɗe takanas domin ya yi mata wannan gargaɗin. Bata san me yake cewa ba, balle kuma ta fahimta, cikin wani irin farinciki da jin daɗi Alhaji Baita ya zura hannu a aljihu ya damƙo kuɗi ya bawa Daada yana godiya tare da jan hannun Iftihal sukai gaba hankalinsa kwance. * BIYA. Juyi take kamar macijiya a cikin bukkarta ta kasa bacci Idanunta sun yi jajur saboda tsananin azabar da take ciki, idan ta runtse idanunta sai ta buɗe da sauri, zuciya ke kai komo na son tilasta mata cinye Mado, tana ƙaunar ɗanɗana zaƙin naman mutumin da ita ce ta yi farautarsa, ta kama shi, ta danne ta kuma soya, saɓanin lokutan bayan da ake yin haɗin gwiwa da ita wajan kama kurwa tun kafin ta kai adadin lokacin da take a yanzu. Zuciyarta ke rarrabewa tare da cure mata a ƙirji idan ta tuna kamar akwai rashin kyautawa a abin da take shirin yi ɗin a yau. A nutse ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar bukkar tana leƙawa sai taga dare ya tsala amma akwai hasken watan dake haske sararin subuhana da Ubangiji Ya halitta. Tana cikin wannan halin ne ta ji kukan mage da wani irin sautin da har abada ba zata taɓa mance shi ba, wani irin faɗuwar gaba ya ruske ta, haɗe da wani irin firgitaccen yanayi me kama da tsoro. Jin wannan kukan masifa ne a gare ta, kuma babban bala'in da zai iya sakawa a yi mata korar kare a rugar Biya ɗin. Har inda Batty ke tsaye magen da ƙarasu baƙa da ita jibgegiyya sai huci take yi tana zare manya manyan Idanunta, ta raɓa ta gefen Batty ta shige zuwa cikin bukkar. "Batty, zo nan ciki Batty" Ta ji muryar Gana na kiranta da sautin da ita kaɗai zata iya jinsa. Jiki a matuƙar saɓule Batty ta ƙarasa inda Gana take tsaye wacce ta dawo asalin suffarta ta mutane. Kanta a ƙasa cikin rawar murya ta fara ƙoƙarin gaisar da Gana, da azama ta ɗaga mata hannu ta ce "Bana buƙata, ki bani kurwar Mado da kika kama, ita na biyo sawu" Batty ta ware ido tana kallon Gana da rashin fahimta. "Kurwar da kika kama ta Mado na ce ki azo mini ita na shige yanzu" a hankali Batty ta shiga ja da baya tana girgiza kai wasu hawayen tsoro suka shiga bin fuskarta. A tsorace ta ce "A'a.... A'a ki bar Mado a raye......."Na roƙe ki, zan sakar masa kurwarsa" Gana ta ce "Ai wallahi sai na yanka kurwar Mado, sai na yi watanda da ita a irin wannan lokacin tunda har kika riga kika kamata" sosai ƙafafuwan Batty suka shiga rawa da kakkarwa suna ƙoƙarin gaza ɗaukan gangar jikinta, wani irin nauyi ta ji sun yi mata, kamar yadda ta ji wani rikitattaccen yanayi yana saukar mata tare da shirin rikita lissafin dake riƙe da rayuwarta, idan lissafinta ya cika cif da cif, Gana zata cinye Mado a zuwan ita ta cinye shi, duk sanda me afkuwa ta afku asirin dake lulluɓe ya bayyana ita za'a zubawa jakar tsaba kaji su bita, kamar yadda a baya ta yi mata tuggun daya saka zaman rugar Yari ya fi ƙarfinta, kamar yadda a dalilinta ne ya rayuwarta taso lalacewa duk da har yanzu bata da amsar da ƙwaƙwalwata ke tambayarta na ma'anar rushewar rayuwa ko gurɓacewarta. Ta ɗauka kishiyar uwa, a rubuce a haka lissafin yake itama uwa ce? Balle matar da take wa kallon jininta madadin uwa, ƙanwar mahafiyarta da suka sha nono guda, innarta ta saki nono Gana ta kama, shine take yi mata rashin kyautawa. Zuciyarta ta ji tana sake tsagewa da fargabar halin Gana ta durƙushe a wajan tana haɗewa hannayenta biyu alamar roƙo kafin da ƙyar ta iya buɗe laɓɓanta da suka bushe ta ce "Ki yi mini afuwa, ki mini rai kar ki kashe Mado, yana da kirki mutumin arziƙi ne....," bata ƙarasa maganar ba Gana ta saka ƙafa ta shure Batty ta hantsila baya. "A irin wannan lokacin da nake jin kamar na ci babu kike cewa na bar Mado? Ƙanƙarar data yunƙuro mini na yi yaya da ita kuma?" "Kici barkono, zata lafa miki" "Abin da nake ji yafi ƙarfin na ci barkono, ya yi kaɗan ya lafa mini, ki gwada kama kurwa ki bata wahala daga ƙarshe ki danne ki yanka kici za ki faɗa mini daɗin da yake cikin hakan" ƙuri haka Batty ta zubawa Gana ido, tana ta lissafi a zuci, idan Gana ta ɗauke kurwar Mado za'a wayi gari babu mado a duniya, ita kuma ba zata iya zama silar wa'adin wanda ya yi mata alheri ba rayuwa. Da ƙyar da wani irin nauyin zuciya dana jiki Batty ta buɗe baki wajan tambayar Gana. “Mi waawi ƴamde maa, Yaaye?” (Zan iya tambayarki Yaaye?) tana kiran Gana da sunan Yaaye wani lokacin wanda yana nufin ƙanwar uwa a Fulatancin Kontagora, ko kuma Gwaggo. Gana ta dubi Batty ba tare da ta yi magana ba. Cikin rawar murya ta ce "Me ya sa Inna ta zaɓe ni ta bani maita? Me ya sa taga nice fi dacewa na zama mayya a kaf zuri'arta? Yaaye mene maita do Allah waɗe mini?" Ta saki wani kuka "Me ya sa muka zama mayu ni dake? Da kuma Inna? Baffana ma yana yin maita ko shi ba maye bane ba.... Me ya sa?" "Yaaye ki waɗe mini batun gaskiya" Cikin fusata Gana ta ce "Sai ki matse mini bakina na faɗa miki, ko kuma ki je kabarin Innar taki ki haƙe ki tambaye ta batun maitar ta amsa ki muga idan zata iya" A ruɗe ta ce "Bani da ƙarfi, ni ba babba bace ba zan iya haƙo kushewar Innata ba, da zan iya taso ta daga kabarinta da a yau ba zan kwanta bacci ba sai na ji amsar tambayoyin da kaina yake mini, sai ta amsa mini abin da nake girma dashi yana addabata da ci mini nan ɗina" ta nuna saitin ƙirjinta hawaye na cigaba da zuba daga cikin idanunta ta ƙanƙame ƙafafuwan Gana. "Ni mayya ce na yarda, na yarda wallahi na yarda na amince" Ta runtse idanunta ƙirjinta na buɗewa yana yi mata wani irin bugu "Amma bana so, Yaaye bana son maitar nan, don Allah ki kai a cire mini bana iya bacci, bana son ganin kayan cikin mutane da abubuwan da suke ci, da jinin da yake gudana a jikinsu. Ki taimaka mini kar a sake korata daga wannan rugar idan gaskiya ta bayyana a bayan ƙaryar da muke rufe wa. Tsoro nake ji, fargaba nake ji, damuwa nake ji, tashin hankali nake ruskar kaina a ciki. Yaaye ki cire mini maitar nan bana so, ba zan iya cin mutum ba. Na shige su na lalashe." Ta rusa wani irin gigitaccen ihu ta faɗi a ƙasa tana birgima da riƙe cikinta. "Wayyo ni Batty me gani har hanji na shiga uku na barinkaɗi" Ganin tana shirin janyo hankalin jama'ar gidan ya sanya wuf Gana ta ɗauke kurwar Mado dake cikin wani tulo ta fice daga cikin gidan. Abin ka da rugar Fulani basu da ƙofa tuni ta bar unguwa tana yin tuƙar baƙi da ƙifta idanu, zuciyarta fal murna zata ci wata kurwar me zallar tsokar nama a jikinta. Batty ta jima tana birgima da ihu da kuka tana kirin sunan Innarta da bata duniyar, ba ƙaramar azaba maitar kenan bata ba, da wata wahalar da bata saba da ita ba. Bayan ta yi me isarta ta miƙe tsaye tare da fitowa daga bukkar ta ɗan kewaye, cure jikinta ta yi waje guda tana rawa da juyi da katantanwa da surutai a hankali jikinta ya fara sauyawa zuwa kuliya baƙar ƙirin Idanunta mai matsagaicin ja ta yi shiru tana kallon rufin bukkokin Sadiatu, Kulu da Lami sai ta Dikko. Ɗaya daga cikin abin da ke bawa maye farinciki da jin daɗi shine maitar dare, bawai su fito su kama kurwar mutum ba, suna bin saman rufin gidajen jama'a wajan hana su bacci, da sanya musu tsoro da firgici wannan abin kuma yana ƙarfafa zuciyar maye yana jin daɗinsa sosai da sosai. Tsalle ta buga ta hau rufin bukkar Dikko ta fara wani irin firgitaccen kuka me ban tsoro da keta zuciya da wasu-wasi idan ta yi tsalle sai ta dire, yanayin kukan kuma kamar me kiran sunan Dikko da Sadiatu a ƙarƙashin wannan kukan har da fitowar siririyar dariyar da za ka ji kamar kukan jariri. A wannan lokacin Sadiatu ce ke da kwana tana shimfiɗar Dikko yana mitar su irin ta ma'aurata. Sadiatu ta kalli Dikko a kaikaice ta ce "Malam kai ko nauyi baka ji sai ka dinga mitar anƙi sauraranka wajan baka haƙƙi?" Fuska a haɗe ta yi mgnar Dikko ya daƙune fuska ya ce "Sadiatu bafa tsofa na yi da neman haƙƙina ba ko? Me ya sa kuke mini haka ne wai ni?" "Malam abin ne babu tsari" Ya miƙe zaune daga shirin riƙota zuwa jikinsa tana ja baya ya ce "Neman haƙƙin nawa ne babu tsari, ko faɗar Ma'aiki da ya ce ku jewa matanku a sanda kuke buƙatarsu? Wai ko dan jahilci na kara kaina a kanku ne kuke ganin abin a hagunce?" Sadiatu ta ce "To yanzu Malam me kake nufi?" "Abin da duk kike nufi shi nake nufi" Ta juya ta ɗan kalle shi ya girma sosai amma har yanzu bai daina ƙulafucin tarayya da mace ba, da wannan ke saka a samu zuri'a da sai yafi kowa yawan ƴaƴa a rugar Biya. "Sanyi fa duk ya yi maka illa" Wani irin kaikaitaccen kallo ya yi mata a fusace ya miƙa hannunsa ya damƙi ƙirjinta ɗaya daya koma ya yi bacci a binsa. "Ai shi ya sa naga ke tsaf kike, ko tinkiyoyin da nake kiwo da nagge naga mashayarta haka nasan ta tashi daga aiki ne balle mace" Wani irin takaici ya cika zuciyarta ta ce "Naga yadda saman yake haka ƙasan naka yake" ya watsa mata uwar harara yana cire makarin jikinsa ya ce "Kuma a hakan nake neman haƙƙina, ki cinye ko kwaɗa ki sha kin ji" Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye hannunsa riƙe da wandonsa ya nufi bukkar Kulu yazo daidai tsakiyar gidan ya ji wani irin kuka. Ana cewa "Dikko.... Dikko.... Dikko.......... Kar kar haka jikinsa ya ɗauki rawa da ɓari ya shiga jujjuya kai ya kasa yin ko da kiran sunan Allah ne. Yana ɗaga kan shi sama sukai idanu huɗu da Batty data zama mage, sai yaga tana zaro harshe, daya rufe ido ya buɗe sai yaga kamar dariya take yi. Shi dai ya san baya jin fitsari amma sharkaf ya jiƙe jikinsa da fitsari ya saka hannu yana tare zubar shi. Yana shirin juyawa ta yi tsalle ta dire a saman kan shi. Wani gigitaccen ihu ya kurma yana kiran "Lami... Sadiatu.... Kulu" Kamar haɗin baki Lami da Kulu suka rufe bukkarsu, Sadiatu na shirin rufe bukkar Dikko ya kwasa da gudu yana yin cilli da wandon ya bangaje Sadiatu ya shige ciki. Ganin magen na nufo bukkar ta saki nata ihun, sakin ihun ya yi dai-dai da sakin kukan magen idanu rufe Sadiatu ta afka kan Dikko tana faɗin. "Malam gani, sauke hakƙin naka" "Ki cinye na bar miki" Ya ce yana ƙanƙame al'aurarsa domin ita ce a fili kuma gani yake kamar watanda magen zata yi da ita idan ta samu kafa babu mamaki haihuwa ta yi take neman kalace. * Tunda Daada ya fice bayan ya damƙa Iftihal a hannun Alhaji Baita sai ya tafi sharholiyarsa sai wajan 2 na dare ya shigo, yadda ya bar Innti ta yi zaman ƴan bori haka ya dawo ya same ta, babu inda yake motsi a jikinta sai zuciyarta da take aikin bugawa a tsakiyar ƙirjinta, duk wani bugu da take mata ciwo ne, ciwon ba sabo bane ya kasance mafi girma a raunikan data samu a baya, wannan karan raunin zuciyar har girma ya ƙara, ya yi ruwa yana neman fashe mata, a wannan lokacin bata da maraba da matacciyya, a kullum macewa take yi da tashin hankali, tana sake farfaɗo wa da tunanin makomar yaranta. Ta ji sautin muryar mace bayan ta Daada, al'amarin daya ruɓayan ciwon dake ƙasan zuciyarta, wutar dake ci da kanta. Ta haɗa zufa tar da yin sharkaf ta ƙanƙame hannunta. A hankali bakinta ke motsawa tana faɗin "Allah ka shirya mini mijina, Allah ka shirya mini mijina, Ya Allah ina son Daada ka dawo dashi hanyarka ta tsira ka ganar dashi abin da ya zama kurma da makaho a kan su. Allah ka kula mini da zuri'ata ka kula mini da bayana. Ka shirya mini mijina Ya Allah" "....Shalale" ta ce a fili cikin daƙushewar murya "Allah ka sassauta mini zuciyarta" Bata da wani says akan Iftihal ta san definitely za tai wa Daada biyayya ko da hakan na nufin tsayuwar numfashinta. Tsoran Innti ɗaya kada Alhaji Baita ya rusa rayuwar ƴarta ta gurɓatacciyar hanya, Allah kuma ya sanya wa matan Alhaji Baita tausayin Ifti su kula da ita da jikinta. Motsin data ji ya saka ta buɗe idanunta, sai ta ji zuciyarta a rarrabe adaddin rabuwar kusurwar duniya gida huɗu, gabas, yamma da gudu sai arewa. A kowacce kusurwa labari ne wanda babu amsa, damuwa ce wacce bata da magani. Dum! Haka taji wani sauti ya sauka a tsakiyar kanta sai data saka hannunta ta dafe ƙirjinta ta fahimci bugun zuciyarta ne haka. Mace ta gani ta fito daga cikin ɗakinta zuwa tsakar gidan kai tsaye ta je cinyar Daada da yake zaune haihuwar Emama. Ko a faɗa ko ba'a faɗa ba, tana da tabbacin ita ce TANI matar da yake mu'amala da ita. Ta runtse da ƙarfi. Burin Innti a lokacin bai shige ta nemi ganinta ta rasa ba, fata take da addu'a dama ace ita makauniyya ce da wataƙila ba za taga wannan ƙazantar ba. Sun ma mance tana tsakar gidan masha'arsu kawai suke yi. Bata san zuciya na numfashi ba, balle har a ji numfashin sai yanzu. Hucin abu take ji yana saukar mata da wani irin soft ɗumi, a hankali ɗumin ke narkewa yake zama gumi wannan yanayin shine numfashin zuciyarta. Har lokacin kuma Yaa Jadid a sume yake ba tare da hankalinta ya kai kan shi ba. Inama take da hankalin a yanzu balle ta fahimta? Shi kuma Yaa Jaheed tunda ya fice bai dawo gidan ba, kamar yadda shima Babban yaya bai dawo ba, ta san damuwa da tashin hankali ne ya haddasa musu hakan, rana ta farko da suka kai biyun dare a waje yau. Tun tana daure suratan da suke yi da ihu har zuciyarta ta karaya a gigice ta saka hannunta bibbiyu ta rufe ƙofofin kunnuwanta jikinta na rawa da ɓari da wani irin kakkarwa ta sake zubewa akan ƙafafuwanta tana fashewa da matsanancin kuka a lokacin data gama tabbatar wa sun yi nisa a abin da suke domin ga muryar Daada nan yana faɗin "Tani kin fi Innti inganci, kina da garɗi kamar Dabino, Tani ke duniya ce, da a bani Innti gwara a bani irin Tani dubu, wayyo rayuwa Tani ke duniya ce" itama Tanin raddi take yi masa da kalaman da baki ba zai faɗa ba, tana jin sanda sukai ƙara a tare suka saki ajjiyar zuciya lokaci guda. Bayan shigewar lokacin da ba zata iyakance su ba, taga sun miƙe suna shirin shiga ɗakinta da zafin nama ta miƙe tana kallon Daada. "Ka yi komai a waje ƙazantar da ban gani ba tsafta ce, amma ka daina kawo mini karuwarka cikin gidana ka daina Daada" Daada ya ce "Ana da Iftihal sune karuwar ba Tani ba" "Da izinin Ubangiji ba zanga wannan ranar ba. Addu'ata zata cigaba da bibiyarsu" "Ni kike cewa karuwa?" Tani ta faɗa tana buɗe idanunta. "Au ba ki san sunanki bane da za ki yi mamaki don na kira ki dashi? Ai duk macen da take bin mijin aure ba mijinta ba bata da wani suna daya shige wannan. Ina mai jan hankalinki akan ki ji tsoron Allah, ki tuna kema macace, haƙƙina zai biki wallahi" "Tunda kika kira ni da karuwa sai na tabbatar na miki aikin karuwanci kafin na bar gidan nan. Masoyi ina son second round a ɗakin matar nan inda kuke yin sunna" Daada ya ce "Faɗa taki cikawa tawa" Ta ɗora da faɗin "ka ce ta dafa mana ruwan zafi kafin mu tsane mu fito" nan take ya bawa Innti umarnin dafa ruwan zafi. Akan Idanunta suka shige cikin ɗakinta tana jin zuciyarta na narkewa da rabewa gida biyu, ɗakin aurenta? Inda suke raya sunna a nan ya ja Tani a ciki. Ta shiga uku me Daada yake nema ya zama? Me yake nema da ita? Abu biyu ne yake riƙe da ita, bata ƙaunar kalmar saki ta gifta a tsakaninsu daman fa kamar igiya ɗaya ke riƙe da ita, ya yi mata ɗaya lokacin cikinsu Jadid, ya sake yi mata wani sanda ta ɗauki cikinsu Ana. Tana duba goben yaranta. Bata san surutan jama'ar gani, bata da wani confidence na kai wa Emama ƙararsa goya masa baya take yi a koyaushe. Aurenta da Daada ya zame mata auren zobe, bata da inda zata idan ta rabu dashi tunda auren zumuncin ne, rufin asirin kowacce mace ɗakin mijinta. Tana shaƙar takaicin ɗa namiji da baƙincikin dangin miji. Ana cewa komai namiji ya yi ado ne, ba'a tunanin hali jini yake bi. Inama Allah zai fitowa da Ana miji ta aurar da ita ta bar gidan tun kafin ya rusa mata rayuwa kamar yadda ya yi wa Iftihal. Tana tsaye taga Babban yaya ya fito daga cikin ɗakinsu abin ya girgiza ta bata san yaushe ya shiga ba, data lura dashi sai taga kamar bashi ba, taga kamar idanunsa bana Muraad ɗinta ba, data ci-gaba da kallonsa sai taga kamar gashi ne ya mimmiƙe a jikinsa har ya zame masa riga data sake kallon yatsun hannunsa sai taga kowanne yatsa ya ruɓanya kan shi sau biyar a tsayi. Ɗago kai ta yi suna haɗa ido taga ya yi mata kyakkyawan murmushi kuma ya zubawa ƙofar ɗakin da Daada ya cilla Ana a ciki idanu yana girgiza kai. SHEKARUN DA SUKA SHIGE A BAYA. YEARS AGO. Ana ta ƙwala kiran sallar magariba a lokacin tana zaune kan dakalin ƙofa da cikinta da ya yi kimanin wata huɗu kanta babu ɗan kwali. Yau ɗin da fara'a ya shigo gidan ya juya ya kalle ta da kulawa sai ya girgiza kai ya ce "Na fahimci a kwana biyun nan ba ki da aiki sai zaman kan dakali kuma dab da magariba kike wannan ɗabi'a" ta kalle shi kawai sai ta ce "Zaman yana mini daɗi ne sosai" Ya jujjuya kan shi kafin ya ce "duk faɗin tsakar gidan ki rasa wajan zama sai dakalin ƙofa? Gaki da juna biyu ga kai a buɗe" Ta yatsuna fuska ta yi tamiƙe da ƙyar tana nufar murhu shimkafa ƴar Hausa ta tace tana jin yana ta mita shi kaɗai kamar zai ari baki amma bata ce ci kan ka ba. Bayan ta gama tace shinkafar ta mayar ta turara, ruwan da tatar da yake azabar turiri ta nufi bakin rariya dashi. Kafin ya yi magana ta zubar da ruwan a wajan tsananin azabar ya saka fuskarta haɗa zufa. Ya yi zumbur ya ce "Subuhanallahi! Ya za ki zubar da ruwan zafi a bakin rariya da irin wannan lokacin madadin ki tsahirta ya sha iska ba kyau" "Ina ake zubar da ruwan zafi idan ba bakin rariya ba masoyi?" Ya kalle ta sai ya girgiza kai ya ce "Allah Ya kyauta" *Back. Iskar da ta ji an kaɗa mata ya dawo da ita tunaninta, kafin ta yi magana ya fice daga cikin gidan gabaɗaya. Fargabar rasa igiyar aurenta ya saka Innti ɗora ruwan zafi a wannan lokacin. Sai yanzu take sanin anahin inda take samun ciwon sanyi (Infection) idan Daada ya ɗauke mata ƙafa da zarar ta fara amfani da maganin sanyi na haɗin shayi da Maman Haysaam ke bata, wanda take siya a wajan BloomHer Wellness ingantaccen haɗin maganin sanyi ne da ake tafasa shi kamar shayi, sha ɗaya ka yi masa zaka san ka sha maganin sanyi tsaftacce ne, iya ƙamshinsa abin sha'awa ne, tana aikawa ko'ina cikin ƙanƙanin farashi, Maman Haysaam har maganin sanyin ƙashi take bata. Duk sanda ta sha haɗin shayin na sanyi wasai take jinta, amma da zarar Daada ya raɓeta sanyinta zai dawo ashe a wajansa take kwasa shi kuma a wajan Tani yake ɗauka. Ruwan ya yi zafi ta juye a tukunya. A tare suka fito manne da juna suka shige banɗaki zuciyar Innti na ayyana mata ta ɗauki ruwan zafin ta kwara musu gabaɗaya. Sukai wanka suka fito, daga nan suka fara buɗe ƙofar shaiɗanci, wajan busa sigari da yin wasan karta. "Mijin Innti" Cewar Tani sai ya watsa mata harara. "Zan miki rashin kirki Tani ki daina haɗani da wannan salamatun matar na faɗa miki" Tani ta ce "Ina da shawara, me zai hana ka kamawa Ana shago a cikin gari irinsu ake ya yi a wannan zamanin, tunda kaga yadda cacarku da baita ya kasance, ni zan dinga kai wa manyan mutane tallanta mu dinga samun kuɗi da ita, yarinyar ba ƙaramar kasuwa za ta yi ba" Daada ya numfasa. "Kina ganin hakan me yiyuwa ne daman shiga cacar da na yi da Iftihal a wajanki na nemi shawara?" Ta maka masa duka "Me zai hana shi yiyuwa? Kafin kama ɗakin za'a fara bata wasu magunguna, za'a koya mata makirci, salon ƙwace ɗa namiji, da salon tafiya da yaudara" "Shi ya sa nake son ki gidan albarka, ko ni zan iya koya mata ina da sauran magungunan dana ba ki jiya bari na ɗakko na danne ƴar banza a bata" Innti ta ce "Wallahi ƙarya ne, idan kun isa na zama ƴar albarka" wani wawan mari ya yi mata ya saka ta a cikin ɗaki da ƙarfi ya rufe ta a a ciki. Maganin ya ɗakko da suka kasance masu ƙarfi, ya buɗe ɗakin ya shiga tana kwance bata cikin hayyacinta Tani ta riƙe ta suka tuttula mata maganin ta ce "Yarinyar ta zama budurwa ma. Ka ce basu fi 17 ba" "Jikinsu ne me fushi amma yara ne su fa" Ta ce "Ina yara a nan duba ka gani" Ta faɗa tana yaye masa rigar Ana har zuwa ƙirji, sanda idanun Daada ya yi arba da ƙirjin Ana har yawu ya haɗeye, duk da yana ƙoƙarin haramtawa kan shi hakan. "Ka dubi ƙirjinta ai wannan ta riƙa sosai a gida ta zama riƙaƙƙiyyar kuɓewa, idan baka yarda ba duba" ta ce tana haska masa ƙirjin Ana ta fitila, duk tsalle tsallen Daada da yadda yake shigewa lungu da zarar magariba ta yi yana tarfa yaran jama'a da laƙume musu baiwarsu gane ganensa bai taɓa gano masa lafiyayyen ƙirji irin wannan ba, wani abu ya ɗarsu a ransa wanda yake kokawa dashi a hankali ya kai hannu kamar zai shafo su sai ya yi saurin janye wa ya ce "Muje waje" * Tun 7 saura Yaa Sam ya shirya cikin farar shadda me kyau ya ɗora a saman kan shi, ya yi kyau sosai nutsuwa da kamalarsa ta fito, sai ƙamshi yake yi. A nutse ta dube shi ta ce "Har ka shirya? Gashi ban kammala abin kari ba, ko zaka jinkirta?" Ya duba lokaci, sai ya girgiza kai alamar tafiya zai. "Yanzu a can gidan Gwamnati za'ayi muku interview ko ma'aikatar ilimin?" "Both, wasu a Government house wasu ma'aikatan ilimi" ya faɗa a nutse yana gyara zaman hular kan shi tare da juya grey eyes ɗinsa. "Allah Ya taimaka ya bada sa'a, Allah Ya sa ka samu aikin nan ko zaka mure da ilimin da ka yi ko?" "Amin" ya ce yana ficewa daga cikin gidan. * Washegari da safe a gurguje Ahlam ta shirya cikin kamilalliyar shigarta duk da still tana jin raɗaɗin ciwon amma burinta yafi ƙarfin ta tsaya sanya ta ci sa'a Engineer baya nan ta nufi waje tare da tarar napep ta ce Hisba headguater zai kai ta don Allah ita kaɗai. Ya ce "To hajiya amma drop za ki biya" "No problem" Suna isa ta biya shi kuɗinsa ya dinga godiya ita kuma ta shiga cikin babban headguater ɗinsu tana addu'ar fatan alheri wa kanta. * GANDUN ALBASA. Yana tsaye inda ya yi parking motarsa ya jingina bayansa da jikin motar idanunsa cikin glasses kamar koyaushe, farar single ce a jikinsa data kama shi sosai, sai jeans wanda ya dace da rigar jikin nasa, ya ɗora p.cap a kan shi yana ɗan kaɗa key ɗin motar dake hannunsa. Wanda ke kusa dashi ya ce "Seriously idan na ce kana da problem baka yadda dani, yanzu kalli yadda kake ɓata time ɗinka akan wasu ƙazaman mutane" ya yi maganar yana jan siririn tsaki tare da hurgawa MD uwar harara, duk abin da yake yi ta wutsiyar idanu MD ke kallon shi. Ganin yadda ya yi masa banza ya masshe shi ɗan banza ya saka Anwar yin ƙwafa ya ce "Amma dai ka san ni ba ɗan banza bane da zaka je har office ka ɗakko ni ka yi tunanin zan zauna free time muna shan iskar gari, iskar ma mu rasa ta shan ko'ina sai ta Gandun Albasa for God sake" yadda ya yi maganar shi kaɗai shi kaɗai ya sake bawa kan shi amsa da "Are You deep?" "Ubanka kake so na yi maka Anwar?" Ya ce a slow voice Anwar ya zare glasses ɗin idanunsa ya ce "Kar ka faɗa mini mun fito don kawai muzo ƙofar gidan dattijon nan mu kalla mu koma?" Taɓe baki kaɗai MD ya yi cikin husky voice ɗinsa ya ce "Anwar idan ba zaka iya jira ba you can go please, ba kyauta na ɗakko ka ba aiki za ka yi mini na kuɗi officer" "Aikin kuɗi" A daƙile MD ya ce "Yeah" Kafin Anwar ya yi magana dattijon ya fito bayan ya yi musu sallama ya ce "kune kuke sallama dani?" MD ya yi shiru sai Anwar ne ya ce "Mune baba". Wanda aka kira da Baba ya ce "To lafiya dai? Naga baƙin fuskoki ne ban waye ku ba" MD ya ɗan yunƙuro ya ce "amm ina jin lafiya ba zata kawo mu gidanka ba, tunda baka da wani abu da kake na business ɗin da zamu zo gare ka. More especially daya kasance ina tare da mai uniform ɗin police" a gadarance ya ce "Ina ɗanka daka aika shi ya yi kisan kai? Ka fito mana dashi mu shige station" a rikice ya ce "Ɗana? Kisan kai fa ka ce yaro?" MD ya dubi kan shi sosai jin ya ce masa yaro kafin ya tsuke fuska ya ce "Kasan me nake magana akai. Ɗan'daban yaronka daka tura shi ya kashe ma'aikaciyarmu saboda ta saka rahotan abin da matarka ta yi wa amarya" Baba ya ce "Assha assha yaro ban san zancan ba, ban san anyi ba wallahi" Anwar na daidaita tsayuwarsa ya ce "Kana nufin ba kai ne ka tura ɗan'daban Bright fm ba?" Cikin kiɗima da gigita baba ya ce "Wallahi bani bane, ni bani da yaro namiji ma, balle na samu saurayin ɗa ka tambayi maƙota ka ji. Wallahi ban san an yi ba, ban aika kowa ba, na san har zuciyata ban ji daɗin abin da yarinyar ta yi ba saboda ɓata mini suna zai yi kuma wataƙila azo har gida aka me mini matata. Amma ban tura kowa yin wannan ɗanyen aikin ba ka yarda dani" Anwar ya hura iska kaɗan daga cikin bakinsa yana karkaɗa ƙafa ya numfasa ya ce "Baba ka yi haƙuri kana under suspect ne, ba zaka iya cire zarginmu akan ka ba. Ka yi haƙuri za mu tafi dakai domin yin bincike, idan gaskiya ta wanke ka shikenan" jikin Baba duka rawa da ɓari yake saboda tsoro "Na shiga uku ku yi mini yawan rai, bana son abin da zai kai ni wajan ƴan sanda" Ya haɗe hannu bibbiyu yana bawa Anwar haƙuri, Anwar ya nuna Md ya ce "Wannan zaka bawa haƙuri bani ba, case ɗinsa ne" Tun kafin Baba ya yi magana Md ya buɗe mota ya shige ciki, kafin kace wane aiki jama'a sun taro a wajan ana yamaɗiɗin an kama Malam Sani saboda abin da suka yi wa amaryarsa na rashin kyautawa shi da uwar gidansa, da uwargidan ta ƙonewa amaryar jariri saboda ta haifi ɗa namiji ita kuma tana baƙinciki bata taɓa haifar namiji ba, mutane sunga rashin kyautawar hakan. Gashi amaryar me haƙuri da nutsuwa da biyayya. Zance ya isa har kunnen Talatuwa uwar gidan Alhji Sani ta dinga danna ashar wai ƴan unguwar sun zama munafukai sun wa mijinta shunan ƴan sanda a kama shi. * Ahlam ta jima zaune a reception na Hisba amma babu wanda yabi ta kanta miƙewa ta yi ta nufi wajan wani da yake sanye da uniform ta ce "Sannu da aiki ya ƙoƙari" Ya ɗan dube ta kaɗan ya ce "Aiki Alhamdlh" "Sunana Ahlam Abdallah Kurmi matashiyar ƴar jarida a Bright Fm" ta ƙare maganar tana nuna masa ID card ɗinta. "Alfarma nake nema idan zan samu, kusan na ce taimako ma ɗan'uwa idan zan samu" Ya ce "Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi? Har na zama ɗan'uwa. 3 minutes da suka shige a ban sanki ba kike" murmushi ta yi masa ta ce "Mu ƴan jarida kowa namu ne" ya jinjina kai "Ok me kike buƙata yanzu?" "Appointment, na interview da Sayyadi Baffa" wani irin buɗe idanunsa ya yi da mamaki ya zuba mata ido daga sama zuwa ƙasa.. ya kasa cewa komai. "Ko baka ji ba?" "Na ji. Kin zo da abin da ba za ki taɓa samu ba yarinya. Ki yi haƙuri ki nemi wani" girgiza kai ta yi Idanunta na ciccikowa da hawaye ta ce "ka taimaka mini, wallahi interview dashi shine kaɗai hope ɗina. Ko numbersa ce a ka bani zan yi magana dashi, idan kuma yana nan ka yi mini iso a wajansa" Mukhtar ya ce "Hajiya ko mu da muke tare dashi numbersa bai taɓa shiga wayarmu ba, balle wasu. Ki yi haƙuri ki koma, ko kuma ki yi Interview ɗin dani kawai" a sheƙe ta kalle shi da kyau. "Yaushe zan gashi?" Mukhtar ya ce "Babu rana" "Me ya sa babu rana a ganinsa? Help me" "Muma ba ganinsa muke ba, bata wannan ƙofar yake shigowa ba, ba kuma tanan yake fita ba. Za mu iya yin fiye da watanni 8 bai saka mu a idanunsa ba, muma haka. Maganar da nake yi miki baya gari yaje da'awa ne" Ahlam ta riƙe kai tana sakin numfashi. Kamar ta zunduma ihu haka take ji a ranta murya a karye ta ce "Na gode" tana ƙoƙarin fita daga headquarter ɗinne daga jerin motoci wajan huɗu sun shigo ciki, motoci na alfarma da tsari wani irin sanyi ta ji yana saukar mata a zuciya da farinciki gani take buƙatarta ce zata biya, har ranta ta ji cewa Sayyadi Baffa ne ya dawo. Bayan sun yi parking wani da jikinsa yake a buɗe yaje da sauri ya buɗe bayan motar dake tsakiya, hakan ya saka Ahlam buɗe ido, madadin taga ƙafar namiji sai taga farar ƙafa ta fito sanye da takalmi me tsini wanda yake da igiya, a hankali kuma wacce take cikin motar ta fito tana sanye da abaya me kyau ta yi rolling kanta shigar Larabawar ya amshi fatar jikinta da kyau ta shagala da kallonta da yadda aka mara mata baya, har bata san ta shige ba, sai data dawo tunaninta taga babu kowa a wajan, idanunta ya sauka akan ɗan card ɗin daya faɗo ta ɗauki card ɗin ta saka a jaka duk da bata san na mene ba ta yi gaba. Bright FM ta yi zuciyarta a cunkushe da damuwa, tana tunanin shi kenan babu wani award da za'a iya bata a wannan taron. * A can Kankarofi Yaa Jaheed ne ya fara shigowa shine kuma ya fara ganin halin da Yaa Jadid yake ciki, a gigice ya ɗauki ruwa ya dinga shafa masa, fuskarsa ta kumbura sosai da hannunsa da ƙafa cikin ikon Allah ya farfaɗo, sai ya farfaɗo da wani irin masifaffan ciwon kai da zazzaɓi ya shiga yin amai mara kyan gani. Yaa Jaheed ya buɗe Innti ganin halin da Jadid yake ciki ta fara salati Idanunta cike da hawaye, duk wani abu da take tunanin tana dashi ya ƙare bata da komai ta rasa tunanin da za ta yi. Yaa Jadid ya riƙeta "Innti mutuwa zan yi ki yafe mini" "Yaa Jadid ba zaka mutu ba, zaka samu lafiya in sha Allah zanga aurenka da yaranka da izinin Allah za ka ji daɗin rayuwa kaima" ta faɗa tana rungume shi zuwa jikinta. Jaheed ma ya durƙusa wajan riƙo hannun abokin haihuwar tasa. Suna zaune Babban yaya ya shigo idanunsa wasai wannan karan kamar kuzarin jikinsa ba irin na baya bane. "Kada ka buɗe ɗakin nan Babban yaya" Innti ta faɗa ganin ya nufi ɗakin da Daada ya rufe Ana a ciki, baya son musu da Innti kamar yadda baya buƙatar barin ƴarsa a ciki. "Ban san wanne kunne gare ku ba, ba zaku taɓa barin bakina ya zauna lafiya ba, na yi yaƙi da kai Yaya na yi da ƙannenka? Na faɗa muku maganar Daada da abin da ya yi dole ku yi biyayya akai muddin kuna son na zauna lafiya daku. Ba zan taɓa yafe muku ba idan kuka bijire masa wallahi" wani abu Babban yaya ya ji ya sauka a ƙirjinsa, ya haddasa masa wani irin ciwon kan daya fara gani dishi-dishi. Damuwa da takaicin rayuwarsu da bai taɓa yi ba shine yake yi a yanzu. "Innti haka za mu yi rayuwa?" Cewar Yaa Jaheed "Allah yana sane da komai, zai shiga cikin lamuranmu ya kawo mana tallafi in sha Allah" Yaa Jaheed ya ce "A samu abu a bawa Jadid" Ta kalli Jaheed ɗin tana shafa kan Jadid ta ce "Bani da komai sai hukuncin Ubangiji Yaa Jaheed" Gently ya shigo cikin gidan yana takawa a hankali da nutsuwa da kamala sai ƙamshi yake yi irin ƙamshin turaren marasa shi ɗin nan, excuse ya ɗauka a wajan wanda yake bi layi akan zai dawo gida yaga ƙanwarsa bata jin daɗi. Da murmushi ta ce "Haysaam?" "Na'am" ya amsa yana kallon Jadid dake cinya, kafin ya ɗauke idanunsa ya durƙusa ya gaishe shi ya ce "Jikin nasa ne kuma?" "Shine Haysaam amma da sauƙi Allahamdulilah" Ya jinjina kai a gajarce ya ce "Allahu ya bashi lfy" suka amsa da amin. Jaheed ya gaisar da Haysaam shi kuma Yaa Sam sukai musabaha da Babban yaya, sanyin hannun Babban yaya ya bawa Yaa Sam mamaki sosai. "Mutuniyar tana cikin ɗakin can tun jiya Daada ya rufe ta" Bai magana ba ya miƙe ya nufi ɗakin zuciyarsa na tafasa da ace Daada bashi da alaƙa da Ana wallahi da yau babu me ƙwatar shi a duniya sai Allah. Wanne irin uba ne shi wai? Ƙafa ya saka ya daki ƙofar ta buɗe. Tana kwance tsananin azaba ya saka ta yi fitsari a wajan idanunsa ya fara kawar wa gefe saboda rigar jikinta da take yaye, babu ko halfvest a jikinta balle rigar Mama. Ya saka yatsu biyu ya rufe mata jiki ya zubawa fuskarta idanu yana jin wani abu na buɗewa a ƙirjinsa tare da harba masa fiye da adadin tafiyar lokaci, ta yi masa kyau a yanayin baccinta ko suman, a karo na farko ya rusketa a yanayin da bai taɓa ganin wata ƴa mace a duniya ba. "I'm very sorry Jerry" Ya san zata ji haushinsa idan ya bata labarin yadda ya ganta, amma zai adana wannan maganar har zuwa lokacin daya dace ya faɗa. "Nanaah" Ya furta silently yana ɗan bubbuga gefenta bata motsa ba, ya kai fuskarsa dab da datata ya buɗe bakinsa ya shiga hura mata iska a fuska ya yi using yatsu biyu wajan goge mata zufar fuskarta. "Yaa Sam.... "Yaa Sam ka tafi dani, zan bika zani" Shine abin da ya ji tana faɗa cikin mawuyaci hali. "Zani dake in sha Allah, ba zan koma Lagos ba sai dake Nanaah, open ur eyes" Ta buɗe Idanunta suka kalli juna, ta ɗauka mafarki take yi miƙe a gigice ta riƙo hannunsa ta shiga tattaɓa shi ta koma kan fuskarsa ta shafa. Ya yi saurin riƙe hannun nata ya ce "Stop, Haysaam ne ba Aljani ba" Yana furta hakan Babban yaya ya sako kai cikin ɗakin da sauri Ana ta miƙa masa hannunta ta ce "Abbaa" Ya riƙo hannunta cikin nasa ta miƙe tsaye jikinta duka rawa yake yi da ɓari ganin haka ya ɗan jata gefensa ya rungume yana shafa kanta. "Bari na je, kizo gida ki saman" Haysaam ya furta yana juyawa, yana jin kamar ya ɗauki Ana ya tafi da ita gabaɗaya. Babban yaya ne ya lallaɓata ta yi wanka ta sauya kaya ta sha maganinta ba tare data ci abu ba. Tana zaune ya ware mata tulin sumar kanta fuskarta babu walwala ko kaɗan, taƙi tambayar Iftihal kuma rashin Iftihal ya jefa ta a cikin wannan yanayin, tana jin kamar zuciyarta ce zata buga amma ta yi alƙawarin ba wanda zata tambaya ita zata nemo ta da kanta in sha Allah. Ya ware kanta ya je mata shi ya raba gida biyu ya tufke, ya cire mata farce tare da kakkarewa ganin tana lumshe idanunta kamar za ta yi bacci. Ya zuba mata narkakkun idanunsa da suke sauya kala kafin ya saka yatsu biyu ya juyo fuskarta zuwa daidai tasa ya ja idanu ya lumshe alamar "Tashi kije ɗakinku" ta girgiza kai tana damƙe hannunsa ta ce "Zan kwanta a nan" ta nuna masa cinyarsa tana gyara kwanciyarta ta cure jikinta gabaɗaya a cinyarsa. Innti mayafi ta zara ta nufi gidan uwar mijinta Emama wacce take tare da yaranta Hanna da Liya da Bala Sukunbiya. * A tsorace Iftihal ta kwana a gidan Alhaji Baita, bai yi mata komai ba amma idan ta yi bacci sai dai ace bacci ɓarawo da yake sace mutane ba tare da saninsu ba, ta wanzu tana kuka da kiran sunan Ana da Innti. Babban abin da yake bata tsoran da gidan tunda ta shigo ake surfa masifa da bala'i wanda bata san su waye masu yin hakan ba, ta fahimci babban gida ne yadda take jin motsin mutane da hayanayi kamar gidan bariki. Ta yi kuka har ta rasa hawayen yi, banda kashe kai babu kyau a addinin musulunci da tuni ta bar wannan duniyar da babu daɗi a cikinta balle farinciki. Da ƙyar ta tashi ta yi sallar asuba, bata san a yaya ta yi sallar ba duk da ta yi ƙoƙarin aro jarumta da nutsuwa ta sakawa zuciyarta amma ta kasa. Addu'a ma kallon gabas kawai take yi tana da yaƙinin Ubangiji ya san me take so kuma me take fata wato mutuwa. 8:00 aka shigo kawo mata abin kari wata mata ce ta kalli Iftihal ta ce "Ga abin kari, yau ranar kice tunda tun jiya aka kawo ki nan. Amma mai gidan ya labarta mini bai riga ya angwan ce ba sai yau" ko inda take Iftihal bata kalla ba. "Sunana Jummai kowa ya bini ya huta wanda ya ƙini ya wahala. Ni ce uwar gidan Baita ina da yara goma cif, akwai Marka me zaman kanta, ƴata ce tana da gida a gidan nan amma zaman kanta take yi, akwai Lamratu tana siyar da wiwi, sai Kasko shi kuma cikakken ɗan'daba ne. Ni kuma ni ce sirrin Baita na san abin da babu wanda ya san dashi. Baita yana da adadin yara talatin cif da ɗaya, amma cikon ta ɗayan bata duniya, tana raye bata raye bamu sani ba, amma sama da shekaru goma sha bamu san inda take ba. Baita yana da kuɗin da ni kaɗai ce na sani sai mutanen da yake mu'amala dasu, kuɗinsa bana Allah da Annabi bane, sanin inda ya samu kuɗinsa daidai yake da sanin wannan jihar da ruguza manyan mutane masu faɗa a ji. A fili shi ɗan caca ne kuma dillalin gidaje. A ɓoye shi cikakken ɗan....." Cikin tsawa ya ce "Jummai!" Da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce "Har ka shigo? Ka shanye haɗin maganin?" Ya murtuke fuska ya ce "Na shanye ya yi ƙarfi da yawa amma shi ya sa na shigo babu shiri ba zan iya jurewa zuwa dare ba gsky" Wata uwar shewa Jummai ta yi ta ce "Gaske, sai da kai uban Marka da Kasko kace yau zaka raya dare akan Buzu aikin jama'a zai yi kyau an bawa jiki abin da yake buƙata tsayin shekaru" ya ɗan murmusa cike da taƙama yana shafa rumbun cikinsa ya kalli Jummai "Kina da matsala uwar Kasko, ki bari na fara hutawa ai wannan yarinyar da biyu na shiga caca akanta, ga sabga ga aiki yanzu dai jeki ki fara ɗora ruwan zafi ki kuma kawo mini jan ƙyallen nan da zan tare zubar jinin a jikinsa na aiki" "Hankaka kake mai da ɗan wani naka, bawa mara gaskiya, gaskiya azurta wanda bashi da farcen sosai saka soyayyar wanda ya zama mujiya a idanun jama'a. Nasan matsalarka zaka iya ware ɗan iskan bakin nan naka ka cika gidan nan da ihu har maƙota su ji, ga yaranka a tsakar gida suna ji" ya sutale rigar jikinsa ya fara zare tazuge ya ce "Ki faɗawa yaran idan suna ra'ayi su leƙo su gani, mazan amma. Matan kuma babu ƴar iskar da bata taɓa sanin namiji ba. Marka ciki nawa ta zubar? Ke duk gantallu ne sau nawa basa kwana a gida har a ɗakina na tarfa Zainaba da wani yaro" ya ɗora da "Maƙota kuma ko sun ji babu abin da za su iya tuni mun ɗinke bakunansu. Jeki" Jummai ta ce "Haka ne. Yarinyar Allah Ya ba ki juriya, kwaɗayin ubanki ya ja miki wahala" Tana ƙoƙarin fita Iftihal ta yi saurin riƙota ta ce "Don Allah don girman Allah ki taimaka mini ban taɓa yin magana da wani namiji ba balle kwana ɗaki ɗaya, wallahi tsoran mutumin nan nake yi ki tausaya mini ki cece ni" wani irin kallo Jummai ta yi wa Iftihal Idanunta na juyawa ta ce "Akan idanuna ya yi da ƴarsa me kike tunanin ke zan miki?" Ta ture hannun Iftihal ta yi waje abin ta. Baita ya rufe ƙofar ya tuɓe yana lashe gefen baki ya yi kan Iftihal..... *H I Y A A M* Chapter 12: When Innocence Bleeds Bright pens Yota/001 "A sister to share secrets with, laugh with, and trust forever." Nazeefah Sabo Nashe su Falmata Ceo NAZY's KITCHEN. Kamar kodayaushe yara sun cika a dandali suna harkokinsu. Batty dake gefe guda ta kalli Shatu ta ce "Yau ma kika ci abu ba ki bani ba ko Shatu?" Far Shatu ta yi da Idanunta cikin wani irin nishaɗi da jin daɗin yau zata ƙure Batty da take cewa tana gani har hanji. "Batty in manshe ki tambaya?" Batty ta murmusa ta ce "Ingizo ta ina jinki" Shatu ta ɗan gwame numfashi ta yi ƙasa da kanta kamar me son yin raɗa ta ce "Yau me na ci waɗe mini, idan kin yi daidai ina ba ki abin daɗi walle Allah" Batty ta kalli cikin Shatu sannu a hankali kuma ta fara murmushi domin fura da nono ne Batty tasha sai kwaɗon zogale da tumatur wanda suke cikin har yanzu basu gama narkewa ba. "Kin yi shiru ko ba ki sani bane Batty?" Batty ta girgiza kai a hankali sannan ta ce "Na sani. Kin sha kindirmo me zafi a jikin nagge, shai aka dama miki fura da wani kindirmon, ɗanɗanon bai gushe a bakinki ba kika ɗauki kwaɗon zogala kika ci da tumatur na gona. Shatu nima ina so ki bani yunwa ina ji, cikina ciwo yake yi mini" "Laaa....laaaa....laaaa" shine kawai abin da Shatu take iya cewa saboda wani mahaukacin daɗi da ta ji yau ma Batty ta faɗi abin da ta yi kari dashi ta lumshe idanunta ta buɗe su tarwai akan Batty ta ce "Daga yau sunanki bokanya, a dinga ce miki karaba kin ji kyakkyawar Batty?" Da rashin fahimta Batty ta ce "mene bokanya? Da kuma karaba?" "Muna da ƴan'uwa a binni, Innata ta taɓa zuwa dani kin san su suna yin kallo a wani abu. Sai aka saka mana wani kallo a ciki na ji ana cewa bokanya da karaba" Shatu ta labarta mata kafin ta muskuta ta ce "Zo kiji" Batty ta ɗan matsa, Shatu ta kara bakinta a kunnen Batty ta ce "Kawai ki dinga bada magani, da yin asiri sai mu tara kuɗi sosai mu siyi nagge da yawa su dinga haihuwa muna samun ƴaƴa" Batty ta kalli Shatu ta ce "Ina zan samu maganin?" "Ke muna da ganyayyaki har da su rai ɗore su tunfafiyya. Ki yadda dani Batty zan dinga kawo miki mutane, idan mun samu kuɗi sai mu shiga kasuwar yamma ya kika gani?" Ta yi narai narai da fuska cike da tsoro da rashin gamsuwa. Da tsoro a tattare da ita ta ce "Idan aka gano ni mayya ce fa?" Shatu ta ce "mene mayya kuma? Daga yau sunanki bokanya karaba. Za ki lulluɓa ganye a jikinki, a shafa miki bayan tukunya a fuska ana shigowa sai ki ce "Bokayan karaba tana muku maraba meke tafe dakai ko ke, me kake so mene damuwarka kuma? Hahaha" Ta ɗora da "Sai ni bokanya karaba me gani har hanji kuma me abin mamaki hahaha" Batty ta sauke ajjiyar zuciya "Amma wannan ya zama sirri tunda mun zama ƙawaye ko? Daga yau zan dinga ce miki mutuniyar" "Ke kuma masoyiyar" inji Shatu. "To mu ƙulla kar ki ciki amanata ki sauya ƙawa, kinga daman ni bani da yaya bani da ƙanwa bani da kowa sai Yaaye kuma ta tsane ni ta saka an kore ni daga rugarmu ta Yari don taga Innata ta mutu" kamar wasa sai ta hau kuka wiwi har da majina tana murza ƙafa da yarfe hannunta ta narke gabaɗaya. Shatu ta saki baki tana kallon ta, da yawan mutane idan suna kuka muni suke yi, akasin hakan wani irin kyau Batty ta yi mata tana kuka tana shigar da leɓenta na ƙasa tare da tsotse shi ruf kuma take rufe idanunta, dogwayen gashin idanun da suka kwanta sai su bi fatar idanun su lafe gwanin sha'awa. "Ba za ki ce na yi shiru ba?" Ta yi furucin cikin raunin murya. "Ki yi shiru masoyiyar" "Na yi mutuniyar. Ina Ramu?" "Laa ba kin ce daman hanjinta ciwo yake ba? Tana can ta kwanta lalura abin tausayi ko za ki ke duba ta?" Batty ta girgiza kai "Ki faɗawa Innar Ramu ta kai ta wajan Bokayan karaba zata samu waraka" Shatu ta ce "To" "Hawwa fa?" Wani irin hangame baki Shatu ta yi ta ƙanƙame idanu kafin ta ce "Don ki ji aure za'a yi mata, a kwarkwaɗa aka kamata da Iro yana mata maɗe shine Baffan Hawwa ya ce aure zai yi mata, daman ko a dandali idan Hawwa na rawa Iro ne yake mata manne, to duk wanda yake manne a dandali alama ce ta yana son ka, shine take ta kuka wai tsoro take ji ni kuma na ce bata da wayo dama ni ce za'a yi wa auren kullum na dinga girki da share gida na gyara bukkarmu idan gari ya waye na gaida mijin sai na dawo gidanmu, da sassafe na koma gidan mijin, kuma ya dinga kawo mini tsaraba na dinga cin abinci ina ƙoshi sosai" Batty ta yi shiru tana tunani da nazarin maganar Shatu kafin ta nisa tace "Idan akai auren a gidanku kake kwana?" Shatu ta ɗan jujjuya taga ba kowa cikin raɗa ta ce "Daga safe zuwa yammaci kana gidan mijin idan almuru ya yi sai ka tafi gidan Baffanku saboda babu kyau zama waje guda da namijin shaiɗan ke shiga tsakani Inji Innarmu sai kiga an yi miki maɗe a yi miki iskar balo ki mutu" Batty ta haɗe fuska Ta ce "Ce Allah?" "Na rantse masoyiyar" "To na yarda mutuniyar" Shatu ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta "Muje wajan Innata ta ba ki abinci ki yi kari" ta kama hannun Batty suka nufi gidansu. * Tsoron daya gama rikitowa duniyar Iftihal ya gama razanar da ƴar nutsuwar da ta yi mata saura, da kekketa zuciyar data riga ta gama macewa da rauninkan da ƙaddara ta wanzar mata dashi ta haɗaɗɗan rubutun daya samu waje,a inda ba'a rubuta ƙarya na abin da Ubangiji ya wanzar a rayuwar bawa a allon Lauhil Mahfouz. Wannan tsoran ya ɗauke ganinta na wani lokaci kamar yadda wannan tsoran ya saka fitsari sakin kan shi daga cikin mararta, ta jiƙe sharkaf. A firgice ta ce "Na shiga uku....," sai ta kasa ƙarasa maganar saboda wani abu daya tukare mata maƙoshi ko numfashi ta gagara ja da saukewa, hatta iskar dake cikin daƙin a gurɓace take shaƙa, da ɗan ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta lallaɓa tana jan jiki zuwa inda Alhaji Baita yake tsaye ya riƙe ƙugunsa tare da zuba mata ƴan iskan idanunsa masu ɗauke da manufofi da yawa. Tana ƙarasawa inda yake ta haɗe hannayenta biyu alamar neman alfarma, alamar dake nuna ƙasƙanci da karayar zuci ta ce. "Idan na ce ka ji tsoron Allah na san na makara, sai dai an ce fazzakir fa'innal zikira tamfa'ul mu'uminun" Ya kalle ta ya ce "Ka tunatar domin tunatar wa tana amfanar Musulmai" ya ƙare da shafa tsakiyar jikinsa daya kwanta ya zame masa kaya. Ji ta yi ɗan raguwar hope da confidence ɗin da suke rage mata sun yi nasu waje ta kuma neme su ta rasa su. A tsakanin mutuwa da rayuwa bata san a wanne ɓangare ta fi ƙarfi ba a yanzu, tana buƙatar ta rayu saboda Mahaɗinta da kuma Innti sai taurarinta Yaa Jaheed da Yaa Jadid da Babban yaya. Tana buƙatar rayuwa ko zata zama silar shiryuwar Daada, ita kam tana son mahaifinta sosai, so mara algus mara kuma wa'adi, idan ta rayu, za ta yi rayuwa ne da wannan soyayyar ko da bai sauya halinsa ba, idan kuma ta mutu zata mutu ne da begen babu shi a tsaginta a yanzu haka kuma har zuciyarta ta yafe masa dukkan wata musgunawa da ya yi wa rayuwarta. Ta kalli Baita ta ce "Me kake buƙata a wajena?" Ya ɗan gwame numfashi da ƙoƙarin sarrafa nutsuwar dake shirin kwance masa yace "ke nake buƙata, ki saki jiki kuma ki tsayar da zuciyarki waje guda. Ki kuma zama jaruma" Ta ɗan dube shi. "Yes, ni mabuƙaci ne a ƙalla zan iya buƙatarki sau biyar haka a rana" A kiɗime ta ce "Ba zan iya ba, ban ma san mene buƙatar ba, ba zan jure ba, ba kuma zan iya sakin jikin nawa ba ban ma san me kake nufi da kalamanka ba. Duk abin da za ka yi Bisimillah na san Ubangiji yana kallo yana kuma ji ya kuma fini sanin abubuwan da suke yawo a zuciyarka. Duk abin da ya same ni ƙaddarata ce, Innti ta ce bawa baya taɓa shige ƙaddararsa, faman ƙaddarallahu haƙƙa ƙadirihi. Ba wani abu da zai samu bawa face abin da Ubangiji ya hukunta masa" tana faɗin hakan ta yi ƙasa da kanta ilahirin jikinta rawa da ɓari yake yi kamar an jona mata hutar lantarki. Idan abin da Iftihal take ji a yanzu shine daidai bai shige zaucewa da ta yi kamar tunaninta ya yi ƙaura a jikinta, ta amince da ƙudurin Baita, amma zuciyarta ta gaza ɗaukan tashin hankalin da yake neman kunno kai cikin rayuwarta... "Tashi ki cire kayanki" "Ba zan iya ba" ya buɗe ido sosai. Sai kuma ya ce "Ni ina da hannaye har biyu" Ganin da gaske kayan yake shirin cire mata ya saka ta riƙe hannunsa a ƙyamace ta shiga girgiza masa kai, "kalle ni" rashin sanin rashin kallon nasa shine fa'ida a gare ta aka yi rashin sa'a ta ɗago ta kalli cikin tsakiyar idanunsa, a hankali komai ya shiga warware wa a kanta jikinta ya saki, komai nata ya tafi ya barta babu abin da ya yi mata saura sai tunaninta da raɗaɗin zuciyarta, Allah take kira da Innti da kuma Anarta, abokiyar haihuwarta wacce suka gama tsara kalar rayuwar da za su yi tare daga kan girma, karatu, cigaban da za su kawowa rayuwarsu. "Ban san me kake shirin yi mini ba" ta ce da ƙyar Idanunta na tsiyayar da hawaye daga gefen fuskarta, ta ƙarasa buɗe idanun da ya yi mata nauyi a fuskarta, ta dubi yadda ya yi mata tsaye a saman kanta, baƙi ne shi sosai, yana da buɗaɗɗan jiki da kuma ƙaton tumbin da yake fara shaida zuwan shi waje, sai jajayen idanunsa da suke manyan gaske wanda yake rambaɗa musu farin ƙwallin da bata san na menene ba. Dole ta shaida kamannin mutumin daya zama silar rusa duniyarta. Ya gyara tsaiwa yana washe mata bakinsa da faɗin "Ki kwantar da hankalinki, abin da zan miki shine abin da kowacce mace ake mata idan ta girma idan an yi mata aure, budurcinki zan ƙarba saboda kin kwanta mini, dalilin daya saka na saka miliyan ashirin saboda makwaɗaicin ubanki ya faɗa cikin cacar na kuma yi sa'ar gaske ya sakaki ni kuma na yi nasara, daman nasara a jinin Alhji Baita take Ƴan'mata. Sai kuma buri na biyu yi, wanda idan na aikata zan samu biliyoyin kuɗi, wani sirri ne da ko matana basu taɓa sani ba, sai abu kaɗan dana shaidawa matata kuma uwargidana wato Jummai, macace azzalumar gaske, mun haɗu da ita a yawan da nake yi na gari-gari har muka yi aure, tana shan taba, sigari, tana kawalcin mata da niyyar samar musu aikin yi sai a buƙe da safarar su zuwa ƙasar waje, ko kuma ta siyar dasu kamar yadda ake siyar da bayi a zamanin baya, ina yi mata aiki na rufe bakin iyayen yara dama su kan su yaran, duk abin da aka ce musu ba za su taɓa bijirewa ba, iyayen kuma ba za su taɓa neman yaransu ba har abada, idan kin ga sun yi magana to na lahira ne ya dawo" Ya ɗan murmusa yana durƙusawa daidai kan Iftihal da take kwance kamar gawa saboda sakin da jikinta ya yi babu abin da yake motsi a jikinta sai Idanunta da laɓɓanta, kallon shi kawai take yi da fuskar dake nuna tashin hankalin daya gama mamaye rayuwarta da zuciyar dake ƙuntacce a tsakiyar ƙirjinta. Fat! Fat! Haka zuciyarta ke bugawa, bugun da take jin kamar zata yaye fata bakwai dake lulluɓe da ita ta fito zuwa sarari. Ya miƙa hannu kaɗan ya shafi fuskarta ya ce "Sorry fa. Kina ganina kamar bagidajen ƙauye ko irin mutumin ƙawayen da yake da kuɗi amma babu ilimi?" "...... haka kike tunani ko? You have to think gaskiya ni da kaina tsoran kaina nake yi" Ta lumshe idanunta ta buɗe a kan shi. "Yeah; when it comes to money gaskiya bani da imani ne ko kaɗan akan hakan. Na yi niyyar na zauna dake ki dinga bani nishaɗi kina ɗebe mini kewa da hutawa a jikinki, haka nan kike birgeni fa Ƴan'mata. Ranar dana fara ganinki aka shaida mini ko biyu ne nazo na buga ƙasa, kuma ƙasa ta shaida mini naso sauya ƙudirina zuwa kan uhm" Sai ya ɗan murza goshinta alamar tunani, a hankali ta dinga girgiza kai jikinta ya shiga rawa, idan wani abu ya samu mahaɗinta ba zata iya yafewa kanta ba, duk da cewa basu san wacece babba ba a cikinsu, amma tuni ita ta ɗauki girma, Ana da kanta take cewa "Haƙurinki dabanne mahaɗita, kece yayata zan iya kallon ki a matsayin Innti a lokacin da babu Innti a kusa dani, ke yayata ce ta" Ƙoƙarin tashi take ta kasa idanunta na zubar da ruwan hawaye ta ce "Karka taɓa mini Anata, ita ɗin rayuwata ce kar ka...," Ya yi saurin ɗora yatsarsa ɗaya a saman laɓɓanta ya ce "Shhhh, duk yadda nake son abu idan na duba naga taurarina dana mutum bai zo ɗaya ma ina haƙura dashi. Ki kwantar da hankalinki babu ruwana da ita" Ajjiyar zuciya ta sauke a wahale alamar relief. Ya ɗora da; "Bayan matata Jummai na auri Karime, a kanta kuma na buƙaci zama abin da nake a yanzu, me kuɗi kuma bagidaje kuma hatsabibi sirrin manyan ƴan ƙasar nan. Fulani, ita ce sunan aljanar data aure ni a jerin Jinnul Ashqie na mata, ita ta bani umarnin sai na fara kwanciya da ƴata da take shekara shida a haihuwa, ƴar gidan Karime ce, sunanta Anisa, kaf cikin yarana tafi kowacce kyau ita ce fara kamar ka wanke hannu ka taɓa, tun tana yarinya bata da rigima tana da haƙuri gata da farinjini, na taƙaita miki kaf yarana ba wacce nake so sama da Anisa. Sai dai kin san wani abu?" Iftifal ta kasa magana sai kallon shi kawai da take yi zuciyarta na rarrabewa. "Anisa na wata shida na yi mata fyaɗe, kuma na tsafa ce ta, ita ce take bani kuɗin da nake dasu a yanzu, har gobe ina kukan rashinta akanta kuma zuciyata taƙeƙashe, yarana duk suka zama kangararru, Jummai ta yi kawalcin mata, Marka babbar ƴata ce, taƙi aure zaman kanta take yi, tana shigowa da duk namijin da ta yi niyya kuma ta fita dashi, ni ne da kaina na gyara mata ɗakin, sai Lamratu tana siyar da wiwi itama bata da kunya ba'a taɓa ta a zauna lafiya kowa ya shiga gonar ta ni da kaina nake saita masa hanya, sai Kasko namiji ne shi. Bari na bar ki haka abubuwan da za ki ji zuwa gaba zai iya sanadin rayuwarki a yanzu, ni kuma ina buƙatarki da kuma aikin da zan yi akan ki" "Don Allah.....," sai ta kasa magana saboda hawaye da bugun zuciya. "Innti ta ce duk namijin daya kaɗaita na mace tana ɗaukan ciki, duk macen da ta yi ciki kuma tana rasa ƙimarta a idanun Ubangiji da jama'a, ban san me take nufi da kaɗaita ba sai yanzu, don Allah ka tausaya mini ka kashe ni kafin ka ci mutuncina" ta shiga girgiza kai a razane "Ba zan iya ba, da gaske ba zan iya ba, zuciyata zata iya bugawa idan kaci zarafina. Innti ta ce girma da martabar mace gidan mijinta" Alhaji Baita ya yi shiru yana tunani. "Nice. Gaskiya Innti ta cika uwa ta gari ta baku biyayya iya iwarta she's a good mother" "Ka aure ni. Na yarje maka ka aure ni daka aikata ba daidai ba dani, gwara na zama matarka ba zan iya saɓa umarnin Innti na ƙin biyayya ga Daada ba, da tabbas na gudu daga gidan nan. Ina son Daada sosai da sosai wallahi ina matuƙar ƙaunar mahaifina. Wacce ta kashe kanta ta mutu kafura da tuni na raba kaina da wannan duniyar. Don Allah ka aure ni ka ceci martaba da kimar ɗiya mace, ka ceci tarbiyyar Innti Please" "I can't do it". Ya jinjina kai "Ba zan iya wani auren ba, wannan sharaɗin Fulani ne da kanta" Yana faɗin hakan ya yi kanta wani irin gigitaccen ihu ta saka tun bai fara yi mata komai ba, bata da ƙarfi don Allah kuka take tana kiran sunan Allah da Innti da Anarta, dukkan wasu ƴan gidansu sai data kira su, hatta Diyanah da bata da wata alaƙa sai data kira sunanta, jikinta na waia irin rawa da ɓari da kakkarwa saboda tsananin tsoran daya gama raza zuciyarta ta wanzu a gaɓɓan jikinta, ta ƙanƙame jikin da ƙarfi wanda ya saka Baita jan uban tsaki ya ce "Don ƙaniyarki ba za ki buɗe jikinki ba sai kin ɓata mini aiki? Kin san girman aikin da yake gabana ba, idan ba ni ba, babu mai iya yin aikin nan sai an je can kusa da Tajmahar" bata hayyacinta tuni tun kafin ya shiga jikinta firgitar da ta yi ya ɗauke ji da ganinta, bata taɓa tunanin irin wannan yana wanzuwa a tattare da mace da namiji ba sai yau, ita tausayin Anarta take yi, Ubangiji kada ya ƙaddara mata wannan abin. Yin duniya ya yi abin da yake so na shiga jikinta abu ya gagari kundila, sai daya zura yatsarta sai kuma ya yi cak yana nazari. Kafin ya ce "Lalle uwarku Innti ta iya maganin ƴan iska, amma na yi mamaki fa" Ganin bashi da cikakken lokaci ya miƙe daga kanta ya ɗakko wani hayaƙi ya bunka a ɗakin ya ƙarasu daidai inda take ya kara hayaƙin a al'aurarta wani irin tsuma naman jikinta ya shiga yi, ta zaro harshenta waje ta datse har bata san haƙoranta sun nutsa cikin harshen na sai da jini ya fara fita, azabar hayaƙin ce kuma ta saka ta farfaɗo daga suman da ta yi. Ajjiye hayaƙin gefe ya yi ya sake kwantar da ita kamar matacciyya a wajan, sai daya fara tura yatsarsa jikinta ya ji ta saki ƙara tana zabura sannan ya ce "Good!" Ya janyo wani jan ƙyalle ya ajjiye a daidai gabanta, ya kalli jan zakarar dake gefe guda me rai sai ɗaga kai yake sama an ɗaure shi da igiya. Sosai da sosai Alhaji Baita yake haɗa zufa, wannan karan ma kasa yi ya yi yaja siririn tsaki ya ɗauki wata reza dake gefe babu tausayi babu imani ya saka rezar a gaban Iftihal ya yaga fatar wajan, wata kururuwa data amsa dukan gidan Iftihal ta saka, a zabure cikin fitar hayyaci ta damƙo wuyan Alhaji Baita ta kafa masa haƙora a wajan tana me kiran sunan Ana da Innti, har tafi kiran sunan Ana ma akan mahaifiyarta daidai nan ta sake wani irin ihu ta datse bakinta numfashinta ya tsaya cak. Wani numfashi Alhaji Baita ya yi yana sakin murmushi da ihu da kururuwa yana kiran sunan Jummai, Allah ya taimaka yaran gidan babu kowa sai matan nasa. Jini ya zuba akan ƙyallen ya zare, ya miƙa hannunsa ya damƙo zakaran bai jira komai ba ya murɗe wuyan zakaran ya cike ya ajjiye uwar jikin a gefe, ɓare bakin zakaran ya yi ya tara jinin budurcin Iftihal ya zuba a jikinsa, nan take daga kan zakaran har uwar jikin suka ɓace ɓat daga ɗakin, ya samu nutsuwa da gamsuwa ya miƙe ya faɗa kan katifa sai baccin daya rasa tantance na wahala ne ko kuma da farinciki da nutsuwa? * Emama dake zaune a tsakar gidan tana juya ruwan shayi daya sha madara da milo ga soyayyiyar doya gefe ta kalli Innti ta ce "Ina ganin masifa da bala'i ni Emama, wai da kika zo mini gida da maraican nan uban me kike so na yi miki bayan kin riƙa da kin gama mini da yaro, ban taɓa sanin ke na haifawa Daada ba billahil azim sai yanzu, ya zama mijin tace baya jin maganar kowa sai taki, yanzu me kike nema? Ci sha, magani suttura duka ya ɗauke muku da yaranki saboda rashin godiyar Ubangiji kike nuna rashin gamsuwa da hakan ko?" Hanna yayar Daada ta ce "Kina fa gani Emama mu da gidan ɗan'uwanmu amma bamu da mutumcin da matar nan za ta yi girki ta kawo mana" Liya da take ƙarama a cikinsu ta kalli Innti a sheƙe kamar kashi ta ce "Ai wani auren zumuncin sam bai yi ba, banda iyayenki sun rasu ai dana ce musu Allah Ya isa da suka ƙaƙabawa Daada ke" Innti ta ce "Liya iyayena me suka yi miki? Me na yi muku da zafi ne wai har haka? Shi Daada ya ce ya ɗauke mana buƙatunmu?" "La'ilaha ilallah kun ji munafuka ko? Kai wasu surukan akwai mugwaye azzalumai, a haka aka auro ki da? Wannan ƙugun a gidan uban wa kika same shi idan ba gidan yayana ba? Akan idanunmu kika dafa ƴar murji" Idanun Innti ne ya ciko da hawaye ƙirjinta na ɗagawa ta saka hannunta ta dafe ƙirjin ta kasa cewa komai, da ƙyar ta ce "Allah shine shaida, me ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo. Jikin Yaa Jadid ne ya tashi kuma alamu ya nuna wankin ƙoda yake buƙata, an sace mini kan keken ɗinkina yau da safe na rasa kuɗin dashin jama'a bani da komai hatta abin da za mu kai bakinmu bamu dashi wallahi. Emama don Allah ki taimaka akai yaron nan asibiti na baro shi a cinyar ɗan'uwansa yana ta suma kece kakarsu basu da wani a duniya bayan mahafinsu sai ke. Ki tausaya kada na rasa yarona don Allah" ta fashe da wani irin kuka tana durƙushewa a wajan zuciyarta sai bugawa take yi. Hanna ta ce "Kan uba an sace kan keke ko dai kin siyar a yawon bin bokaye da mallake Daada? Wai har da kuɗin adashi ma kamar" Liya ta buƙa tsalle da tafi ta ce "Bala ba a wajanta yake yin adashi bane wai Yaya?" "A wajanta ne. Har da kuɗinsa kenan?" Cewar Hanna tana riƙe haɓa. Murya a karye aka ce "Me nake ji haka babu daɗin ji wai arne da yin asuwaki, yaya ne ya akai kuma" Liya ta juya ta kalli Sukunbiya daya shigo yana yarfe hannunsa da murya a karye ya dire kayan cefanan hannunsa yana faɗin "Wash ƙirjina, me haihuwar fari a farin shigar shayarwa ta ce wash ƙirjina. Liya ya akai wassafa mini a gajarce do Allah" Liya ta ce "Bala wai kuɗin adashinku na wajan Innti aka sace kuma ƙarya take yi yawon malamai ta yi da kuɗin wallahi" "Kuturun uba, da fari Liya wuta balbal da sunan da kika kira ni, idan ba za ki iya cewa Sukunbiya ba ki ce ke. Me nake ji haka wai kwarto ya yi wa uwarsa fyaɗe ya ce me nake jin haka, billahil azim ba zata saɓo ba, ba'a isa a cinye mini kuɗin da nake ganganɗawa zan buɗe wajan cin abinci ba, duk inda suke dole ne a fito dasu ni za'a yaudara? A ci amana" sai ya fito da waya ya kira wata number ana ɗagawa ya ce "Ahhayyyye cas" Daga cikin wayar aka ce "Cas mutuniyar ya aka yi ne?" Muryar Abar ƙauna ce a wayar "Ki biya ki ɗakko ƴar Beauty tare da polices zuwa gidanmu na gado, ni za'ayi wa hau ni za'a yi wa bariki, ni za'a ciwa kuɗin adashi ina daku a raye a duniya" ya ƙare maganar da yarfar da hannu a gefe can kuma ya saka hannun ya tallafo ƙirji yana karya wuya. Abar ƙauna ya ce "Ni na rasa ta cewa yaya Sukunbiya wai uwar gulma ta yi cikin shega, ai dangi guda zan haɗo tunda abin na jinsi ɗaya ne" yana faɗin hakan ya kashe waya Hanna ta ce "Ai nasan abin babu sauƙi dama matuƙar Sukunbiya yazo" "Wai mayya da kaɓar haihuwa, ban ci nanin ba nanin ba zata cini ba, bikin ƴar aminiyyata za'ayi aka fasa shine zan buɗe restaurant da kuɗin amma matar nan zata kunyatani a idanun duniya" Liya ta saki dry "Kar ka kuskura ka yarda Bala" Wani irin kallo ya cillawa Liya sai ya je ya ɗakko tsinke ya miƙa mata ya ce "Cire abin da yake miki kama dana namiji a jikina da kike kirana da Bala ba kunya da tsoron Allah" girgiza kai kawai ta yi tai dariya. Juyawa Innti ta yi zata fita ya yi saurin miƙa hannu zai riƙe ta, ta yi saurin ɗaga hannunta ta kwaɗa masa mari ta ce "Mara ta ido fitsararre kawai....," bata ƙarasa maganar ba Hanna ta ɗauke Innti da mari. * A nutse ya duba agogon dake maƙale a tsintsiyar hannunsa, yaga lokaci yaja yamma ta kawo kai tun yaushe suke wajan nan? Gashi ko mutum ɗaya ba'a yi wa Interview ba, sai dai a dinga kiran mutanen da aka ga dama. Ya saki siririn tsaki tare da miƙewa ya ƙarasa wajan mutumin ya ce. "Wai What's going on here? Tun safe muna wajan nan, kune kuka kira mu bawai mu ne muka kawo kan mu ba. Idan yaudara ce abin ai gwara mu sani mu cire rai" wanda yake zaune akan kujera ya juya ya kalli Yaa Sam "Shine zaka zo kana mana ihu a saman kai saboda rashin kunya? Shi talaka duk inda yake sai ya nuna halinsa ne?" Yaa Sam ya tattare baƙar ƙirarsa ya cure waje guda yana fito da idanunsa waje ya kalli mutumin sosai cikin turanci ya ce "Kuma wannan talakan yasan limit ɗinsa ya kuma iya talaucinsa, yana da zuciyar nema. Gwamnati ta neme mu, ita kuma Gwamnati ta kowa ce, haƙƙinta ne yin abin da take yi, tunda mune muka kafa gwamnatin. Kuma wallahi a shirye nake da shiga rediyo na faɗi irin wulaƙancin da kukai mana. Ai na haddace sunanka tsaf a kaina" Jin furucin Yaa Sam ya saka mutum miƙa hannunsa ya ce "Have a seat, muga ducoment ɗin naka?" Ya miƙa masa ya shiga dubawa, a hankali ya ɗago kai ya kalli Yaa Sam ganin tun daga kan primary school har University result ɗinsa masu kyau ne, irin wanda ake buƙata. "Ina zuwa" Ya ce yana miƙewa gefe ya koma ya kira waya yana ɗagawa ya ce "Sir an samu exlty irin ducoment ɗin da kuke so, har bangaren karatun na Accounting. Ka faɗawa wanda ya ce sai siya ya bada 3 millions a cire sunan Haysaam a ɗora na yaronsa, ko kuma ya tafi akan sunan na Haysaam" ya yi jim. Can ya ce "Sure sir, ok I'll in sha Allah" Few minutes ya dawo ya kalli Haysaam ya ce "Malam Haysaam, zuwa gobe ka dawo da za'a yi maka takadda na offer later congratulations" Sak Haysaam ya yi yana kallon mutumin, wani irin hamadala yake yi a zuciyarsa, ashe yana da rabon cin muriyar karatunsa? Ashe iyayensa za su ji daɗi tun suna raye? Ashe zai samu kuɗin da zai kula da Ana? Sai samu kuɗin da zai auri yarinyar da yake mutuwar so da ƙauna kamar numfashin shaƙarsa. Ya zame ya yi sujudur shukràn kana ya tafi yana hamdala. * A can rugar Biya a gidan Moddibo, Mado ne kwance jikinsa ya rikice babu yadda yake jikin ya ɗauki zafi rau kamar gaushin wuta saboda zafi, sai sambatu yake yi yana faɗin "Ga kura nan ga doki nan, za su kama ni ga wuta nan tana bini gata nan zata cinye ni" Malamin da aka kira ya girgiza kai yana zubawa Mado dake kwance idanunsa rufe ido, kaya ne a jikinsa irin yadin nan me kyau da aka goge masa jikinsa aka saka masa. Moddibo ya nisa ya ce "Ka gani Malam Horo, ɗazo jikin gwanin sha'awa sanyi ƙalau har aka bashi kindirmo ya ɗan sha amma duba ka gani yadda ya rikice lokaci guda" Malam Horo ya ce "Sannu Mado, sannu ka ji. Allah yo jam tan" ya faɗa yana taɓa Mado “Malam Hooro, too aljannu’en ngari natti dow ɓandu Mado naa?” Horo ya yi shiru yana kallon Mado da nazari ya kalli yadda yake zabura da surutai marasa ma'ana. "Sune, abubuwan da yake yi duk sharrin Aljanun ne, za'ayi masa Ruƙiyya idan Allah Ya so za su bar jikinsa. Sannu Mado, Allah yo jam tan" jakar kayansa ya buɗe ya ɗakko wata kwalba me ɗauke da maganin zafi ya ajjiye a gefe, sai dogon carbi irin me guda dubu ɗin nan ya ce "ku riƙe shi da kyau, babu mamaki shaiɗanun jinnu ne ke addabar shi da bibiyar rayuwarsa" Mado ya ƙurawa Malam Horo ido kamar ya buɗe baki ya sace masa bashi da wata iska kar ya yi masa ruƙiyya amma babu bakin magana, suka riƙe shi Malam Horo ya shaƙa masa man zafin cak numfashin Mado ya tsaya na wani lokaci, saboda yadda maganin ya ratsa ƙwaƙwalwarsa ya gigita mata lissafi, jikin ya ƙara birkicewa ya fara fusge fusge da wani irin numfashi yana samƙamewa. Moddibo ya riƙe shi gam ya ce "Sai kun tafi inda kuka fito, ku bar jikin bawan Allah ina faɗe muku tun tuni amma kun manshe ni ɗanbaza ko? Ga Malam Horo nan gare ku ai" tsananin azaba ta saka Mado riƙo hannun Moddibo da kyau yana fidda wani irin numfarfashi, Malam Horo ya saka hannunsa a goshin Mado ya danne ya fara addu'a yana tofa masa, ba'ayi minti biyu da danne goshin ba, Mado ya yi wata fusga da salati da ƙarfi jikinsa ya saki alamar rai ya yi halinsa. Malam Horo ya ce "Allahamdulilah bacci ya ɗauke shi kar a tashe shi sai ya farka da kan shi, idan ba haka ba za'a samu matsala" "A'a Malam Horo idan Allah Ya so babu me tashin shi. Mun gode miyyeti masin" sallama ya yi musu ya fita, Moddibo kuma ya fito daga bukkar Mado ya saki assabari ba tare daya san gawa ya rufe ba. * Tunda ya shigo gidan yake surfa masifa kala-kala. Girgiza kai kawai ta yi kafin ta ce "Yanzu shi ya ce maka aurenta zai yi ko me? Me yake dashi da zai ɗakko wa kan shi maganar aure? Ji nake a can Lagos ɗin ba wani aikin kirki yake ba Masinja ne shi a bankin" Ya ka da baki wajan faɗin "Ai na ga take takensa, ko yana da halin yin ban lamunce masa auren ƴar mashayin mutumin nan ba, mara kunya fitinannen mutum. Haka jiya akan idanuna ya shige da wata shiryayyiya. Ba zan iya haɗa iri dashi ba" ita dai abin da take yi ya cigaba da yi. Dai-dai nan ya sako kan shi cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, gogaggen yadi ne a jikinsa daya sake fito da kwarjininsa, sai ƙamshi yake fitarwa dawowarsa kenan daga Interview ya shiga ya yi wanka. Baba ya ce "ka shigo a dai-dai" Kallon mahaifin nasa ya yi ba tare da ya ce komai ba. "Yaushe zaka koma can Lagos ɗin?" Haysaam ya kalli Baba sai ya yi shiru "Magana nake ka tsare ni da ido?" "Sai na haɗa kuɗin mota in sha Allah" Baba ya dube shi ya ce "Nawa ne zuwa Lagos ɗin?" A ɗan taƙaice ya ce "Ya danganta" "To Allah Ya taimaka ya yi muku albarka. Bance kar ka taimaki yarinyar ba, amma rai na baya mini daɗi ganinka da ita, yanzu ɗan mutum ake kiwo ba dabba ba, ka lura" Yaa Sam ya yi kamar bai fahimta ba da kamala a tattare dashi ya ce "Wacece?" "Ladidi yama sunan yarinyar?" Caraf Walid ya ce "Ana sunanta Baba" Yaa Sam ya juya ya kalli Walid sai yaron ya yi saurin yin ƙasa da kai. "Ka kawo mini abinci shago" yana faɗin hakan ya fice zuciyarsa babu daɗi. Shagon nasa da yake jikin ɗakinsu ya nufa, yana jin baba yana faɗin shi sam bai ga amfanin karatun Haysaam ba, an ƙare karatu babu aiki, ganin takaddar ƙosai yafi faranta masa akan takardun Sam. Kwanciya ya yi a katifar ɗakin ya lumshe idanunsa ya rufe fuskarsa da hula yana jin Walid ya shigo shagon ya ajjiye masa abinci. Yaron ya dinga kallon ledar dake ajjiye kamar ya ɗakko sai ya fasa. Yana ta kwance tunani ya yi masa yawa a zuciya ya ji alamar an buɗe ƙofar an shigo, bai motsa ba kuma bai buɗe idanunsa ba, har ta ƙarasu gefen wajan ta durƙusa kanta a ƙasa yana jiran ya ji ta yi masa magana amma shiru. A hankali ya cire hular ya buɗe gargasar idanunsa tare da kallon inda take daf dashi, tun kafin ya yi magana ta rushe masa kuka, ya san yadda take ƙoƙarin danne rauninta bata bari aga gazawarta kukanta sai ya riƙe ta shi "Nanah....... Ta kasa amsawa sai ta kifa kanta a cinyarsa ta sakar masa wani irin kuka me raunata zuciya, yaja idanunsa ya lumshe su yana jin zuciyarsa na buɗewa. Bai sake magana ba sai ɗora hannunsa da ya yi a saman kanta. Ganin kukan zai iya haddasa mata ciwo a hankali ya ce "Enough, daina kukan hakan" "Yaa Sam...," "Shhhh" ya katse ta wajan ɗora yatsarsa a bakinta ya zaunar da ita kusa dashi ya janyo kwanon abincin ya buɗe, banɗashen gurasa ne ya ji mai da ƙuli an yayyanka masa ita. "Muga hannunki?" Ta nuna masa bai gamsu da tafin hannun ba ya tanƙwashe ƙafarsa tare da saka kwanon a tsakiya ya shiga ɗakko gurasar yana bata a baki shima yana ci, idan ya bata sai ya saka a nasa bakin. Ya sake ɗakko ya miƙa mata har ta saka a bakinta ta turo ta faɗo hannunsa ta ce masa "I'm full" ya ɗan kalle ta anutse. "Kuma kika fara sata a bakinki?" Ta ɗauke kai "To ba sai ka cinye ba kar a yi asarar abincin" ya kalli gurasar duk yawon bakinta kamar ba zai magana ba sai kuma Ya ce "Abin baka zan ci jaririyar Innti?" "Yap. Ai ni na ci fa" "And.......?" Ya ɗora da "I mean who are you to me?" "Uhm mmm ba budurwa ba, ba mata ba, hmm ƙawarka ce ni, I'm your friend" girgiza kai kawai ya yi yarinyar da a haihuwar awaki ya yi jika da ita maybe. "Miƙo mini ledar can" tana juya ya cillar gurasar a bakinsa ya cinye tas. Ledar ta ɗakko Apple ne guda ɗaya a ciki sai Yougurt da Biscuits biyu. "Ina gurasar bani abata na cinye" bai kalle ta ba ya miƙa mata Yougurt ɗin bayan ta kafa baki tasha ya miƙa mata hannunsa ta ce "ba siya mini ka yi duka ba Yaa Sam?" Bai tanka ta ba ta dire masa Yougurt ɗin tana ajjiye ya miƙa mata Apple ɗin daya ciro a bakinsa sai ɓata rai take yi bai bi ta kanta ba, ya ɗauki Yougurt ɗin ya sha ya sake miƙa mata, karɓa karɓa suka dinga yi har ta ce ta ƙoshi ya rufe ya ajjiye. "Oya tashi ki koma gida kar Abbaa ya neme ki" ta yi shiru "Nanah..... "Ina ganin Abbaa a cikin mafarkina ta wata siga sai ya dinga ce mini shi mijina ne. Innti bata gida Mahaɗita ma haka" ya yi jim. "Ina Iftihal ɗin ta je ta bar ki?" Kwanciya ta yi a gefe tana hamma "Mijin Innti ne ya sakata a caca, wai zai ci miliyan ashirin shine Alhaji Baita ya ci cacar aka bashi Mahaɗita, Innti ta ce koda wasa na je gidan xan haɗu da fushinta, kuma kar na faɗa maka" ta ɗan yatsuna fuska tana jujjuya kai ya saka hannunsa ya riƙe kan, zafi sosai ya ji ita kuma ta zuba masa ido har bata san lokacin data ɗora kanta a cinyarsa dake miƙe ba. "Abin dai sai ita da mijin nata, i told Iftihal Daada shi zai zama ajalinta but she refused to understand that" tana faɗin hakan ta rufe idanunta ruf babu jimawa ya ji saukar numfashinta alamar bacci ya ɗauke ta. Ya dinga kallon fuskarta ta torchlight ɗin daya kunna ya ja numfashi ya sauke ya ji ta mirgina a hankali ta shige can ƙurwar ɗakin tana riƙe hannunsa sosai a cikin nata, ya wanzu yana kallon ta sosai, yana sake tuna ƙuruciyarta da ta yi akan idanunsa ya ɗan ranƙwafa goshinsa ya sauka akan nata a hankali ya mayar da idanunsa kan laɓɓanta.... *H I Y A A M* Page 13: The Night of Reckoning Bright pens Yota/001 Sending you lots of love, my Pixie 😘NSN the great NAZY's KITCHEN Ya jima yana kallon fuskarta me cike da rauni, ƙuruciya da rashin mafita goshinsa yana shafar nata, a hankali ya janye goshin nasa sai kuma ya sake ɗorawa ya sumbaci goshinta da kulawa kafin ya gyara mata kwanciya ya miƙe tare da fita daga cikin shagon nasa, a dakalin gidansu Ana ya zauna ya yi shiru yana harɗe hannu a ƙirji. *** A karo na biyu ta sake ɗago kanta daga kan t.v da take kallo, ta juya kaɗan ta kalle shi sai taga ya harɗe ƙafarsa ɗaya kan ɗaya hannunsa ɗaya riƙe da hot coffee yana sha. "Liman ko baka ji me na ce maka bane?" Bai ɗago kai ba, sai ajjiye cup ɗin da ya yi a center table ya ce "Me kika ce Umaimah?" Wani irin kallo ta watsa masa me cike da gargaɗi kafin ta mai da hankalinta gabaɗaya gare shi ta ce "Ina magana akan yarinyar da zaka aura wacce Alhaji Sadi suka je kai maka kuɗin auren, auren da tunda Baffa yaƙi zuwa kai kuɗin jikina ya bani akwai matsala a tattare dashi bawai baki na yi maka ba Allah Ya tsare" ta ƙarasa maganar tana sauya yanayin fuskarta. Wanda aka kira da Liman kallon ta kawai yake yi, ya ji me ta ce kuma zai iya maimaita kalaman da Umaimah ta ce, amma ko za'a saka masa wuƙa ba zai ce ga abin da take son nuna masa ba. Sai ya zaɓi yin shiru akan bata amsa. "Ya zama last time da zan sake maimaita kaina akan batun nan Liman" Ya numfashi ya ce "Me kika ce ne?" Ta dube shi ta ce "Ina magana akan yarinyar ne" Da rashin fahimta ya ce "Who?" "Why are you answering my question with a question ne Liman? Yarinyar da zaka aura wacce aka kai sadakinka gidansu, ina buƙatar ka kawo mini ita na ganta da kaina" da wani irin yanayin na rashin jin daɗi Liman ke kallon Hajiya Umaimah yafi seconds sha biyar kafin ya iya cewa "Umaimah ina jin I already told you that the girl is visually impaired, so I can’t bring her to Baffas Estate by myself.” da mamaki tace "She's visually impaired? Mugunta zan mata ko naman jikinta zan dinga yanka ina ci da zaka wani sauya mood kana ce mini wani visually impaired, au daman da gaske kake makauniyya zaka aura Liman? Kana da cikakken hankali kowa? Me ya sa kai ɗin nan abin da ka yi ra'ayi kawai kake mana a cikin gidan nan? Haka kaga Mu'allim yana yi ne?" Liman ya miƙe tsaye fuska a kame, Hajiya Umaimah ta ce "Zauna ban gama magana ba" daga tsayen ya kalle ta sai ya yi kamar ba zai zauna ba a hankali kuma ya yi baya tare da sake zama akan kujerar daya tashi akai ya fara kallon wani direction daban. "Zan sake magana, ina fatan ta zama ta ƙarshe ina son ka kawo mini ƴarinyar nan gidan nan, domin ba zaka auri wacce zan zo ina kasa nuna ta a dangi ba. Ban ma dai gama gamsuwa da uban nata ba, ƴar waye? Matsayin mahaifinta, mene matsayin karatunta? Ƙasashe nawa ta je? Ta je Saudia? Musaɓaka nawa ta ci, ta Jiha ko ta ƙasa? Sau nawa tana sauke Alkur'ani?" Ya yi jim a daƙile ya ce "Ba ko ɗaya" Murmushi Azizah ta yi ta ce "Stop beating around the bush Liman, ka fito ka ce ƴar talakawa kawai zaka aura, duk kewaye-kewayen naka da gujewa ƴaƴan ƴan'uwa sai ka ƙare akan ƴar talakawa haba Liman?" Tunda ta fara magana yake binta da wani irin masifaffan kallo yana sauke numfashi akai-akai idanunsa sukai jajur ya dunƙule hannunsa dake masa rawa. Hajiya Umaimah ta ce "Ga dukkan alamu Azizah, ki yi shiru kar ya kawo mana duka naga yana rawar ɗari" Azizah ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya "Ko burkutu yake sha ai bai isa ya taɓa ni ba balle ke Umaimah da kika haife shi ko?" A hankali ya ce "Bata da iyaye a haka kuma nake son ta" "Kutumar uba, marainiyya zaka aura?" Daidai nan wanda ya sako ƙafarsa cikin parlour ya tsaya cak kamar wanda aka yi wa umarnin hakan, ƙafar ta daɗe a yadda ya ɗage ta cikin wani kyakkyawan farin takalmi na saƙi me ɗauke da gashin ɗawisu daya kwanta, sannu a hankali kuma ya shiga yin baya da ƙafar hakan ya bawa wanda yake tare dashi tabbacin ya fasa shiga gidan a yanzu. Ya yi tsaye akan ƙafafuwansa hannunsa ɗaya ya juya shi zuwa bayansa ɗayan kuma ya ɗora a saman goshinsa ya saka yatsu biyu yana murza tsakiyar goshinsa idanunsa a lumshe suke, kamar yadda zara-zaran gashin idanun suka bi fatar wajan suka kwanta, iya idanun daman kawai ake iya gani a fuskarsa da zarar ya saka glasses suma ya yi wa jama'a rowar ganinsu, ilahirin gargasar jikinsa sai data mimmiƙe wani irin sanyi ya shiga ratsa farar fatar jikin nasa, yaja numfashi da saukewa sau babu adadi. Babban yatsarsa na ƙafa sai rawa yake yi shi kaɗai hakan ya faru ne a dalilin zagin da Azizah ta yi a daidai sanda Sayyadi Baffa yake sako kan shi cikin parlourn. Fuskarsa ta rikiɗe ta yi jajur laɓɓansa yana wani irin rawa da ɓari, a cikin zuciyarsa ya furta “A’udhu billahi minash-shaytanir-rajim” yana kame jikinsa da kyau cike da kulawa ya ɗora da; “Allahumma ighfir li wa lahum wahdina sawaa’as-sabeel” ya maimaita a zuciya. Ya ɗauki a ƙalla minti guda tsaye yana addu'ar nemawa Azizah gafara wajan Ubangiji da kuma tsari da neman afuwa wajan Allah akan jin zagin da ya yi. Bai san wacece ta yi zagin ba, bai ɗauki murya ba kamar yadda bai damu da sani ba, ba murya kowa ya haddace ba, yadda jikinsa ke rawa ya sake tabbatarwa Mu'allim akwai matsala. Juyawa ya yi yabar sashin gabaɗaya baya mistake a sauke ƙafa sai ya cire ɗaya yake ɗora ɗaya saboda nutsuwa. Ta ƙofar baya yabi har zuwa babban sashin da yake mallakin Sayyadi Baffa, a nan ƙofa Mu'allim ya ja ya tsaya yana cewa "Allah ya huci zuciyar Baffa, ya ƙarawa Baffa lafiya" Wannan karan ko zarafin jinjina kai bai samu ba, ya buɗe ƙofa da yatsu biyu, sai da ya yi addu'ar shiga ɗaki kafin ya saka ƙafarsa da Bisimillah ya shiga zuwa ciki. Mu'allim ya juya kai tsaye cikin gidan ya shiga idanunsa ya sauka akan Azizah dake zaune har yanzu ita da Hajiya Umaimah saboda Liman ya fita. "Ukhty Azizah me ya sa kike son yi mana zagi a gidan nan ne? Wa kika ji yana yi?" Ta ce "Mu'allim ban fa san na yi ba?" Al'ameen ya watsa mata fararan idanunsa "Ko?" Ya tambaya cike da takaici. "To a kunnen Baffa kikai, kuma ya ce ko wacece ya bata minti ashirin ta bar gidan nan, yana da tabbacin ba zuri'ar Hafiz Hafiz Baffa ce da aikata wannan saɓon ba" wani irin sandarewa Azizah ta yi, sunan Baffa ya saka zuciyarta bugawa da matsanancin farinciki har ta kasa ɓoyewa ta faɗaɗa murmushinta tare da lumshe ido ta buɗe. "Da gaske Baffa ya dawo? Yana cikin gidan nan Please Mu'allim ka nema mini iso wajansa, don Allah ina kamon ƙafa da kai" "Allahumma yahdiki. Is like kamar ba ki fahimci me nake cewa ba ko Ukhty Azizah?" "No, na ji. Na san bai sanni ba, ka rufa mini asiri idan ya tambaya ka ce baƙuwa ce kuma ta tafi, sai ka nema mini izinin ganin nasa Please" Mu'allim ya dinga kallon ta ya rasa abin da zai ce mata, yaushe ma zai sake ganin Baffa balle ya nema mata izini a wajansa, shi ɗin wa ma? a hankali ya juya ya nufi part ɗin Mamy yana jin gajiya na saukar masa a jikinsa saboda driving da ya yi daga airport zuwa gida, ba kowa Baffa yake son ya dinga driving jikinsa ba, baya son damuwa, rawar kai a komai, yana buƙatar mutum me nutsuwa da kamala da kuma taka tsantsan, baya son stress ko hayaniyar da ta saka mutum ya yi driving kamar bashi da nutsuwar sanin me yake, hakan yana saukar masa da ciwon kai me tsanani, ciwon kan da baya buƙatar shi ko kaɗan, wata baiwa ce ko kuma haɗuwar jinin da ya yi yawa tsakaninsa da yaransa, muddin ya kwanta ciwo sai Nadiyaah da Diyanah Sayyadi Baffa sun kwanta, shi ya sa yake kulawa da jikinsa da duk abin da zai shafi lafiyarsa ɗin baya wasa dashi. A ƙarƙashin wannan dalilin ya ware mutane biyu da ya yi na'am da nutsuwarsu, duk da a hakan ma cike yake da yi musu gargaɗi da wa'azin babu kyau wasa da kowanne irin rai da Ubangiji ya wanzar a duniya. Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa wato Mu'alim, sai kuma wani babban yaron shi a ɓangaren aikin Hisba me suna Ansar Khamal Khashim. A wannan dawowar ma tun kafin su taso Ansar ya kira Mu'alim ya sanar masa, yana airport ɗin jirgin nasu ya sauka, bashi da tabbacin ko sun yi nasara akan Da'awar da suka je yi bashi kuma da ƙwarin gwiwar tambayar Baffa sai Ansar. Ansar ɗin kuma tun a airport suka rabu dashi. Sanda ya shiga part ɗin Mamy bayan ya yi sallama sai daya jira izinin shiga daga bakin Hidaya bisa umarnin Mamyn da kanta. A nutse ya sako kan shi cikin parlourn nata da yake ta ƙamshi, bakinsa ɗauke da sallama. Hidaya ce kawai zaune hannunta da riƙe da Mi'ata Hadith tana karantawa. Ya nemi waje ya zauna. Cikin sauri Hidaya tace "Ahky Mu'alim yaushe zaka kai ni shan Ice cream ɗin, ka yi mini alƙawari fa, shi alƙawari kaya ne cika shi wajibi ne" Ya dubi ƙanwarsa, wacce take yanayi da late Hafizz Hafizz Baffa, cikin kulawa ya ce "Zan kai ki Hidaya in sha Allah, but not now" "Than, when?" Sai ya yi ƙasa da muryarsa domin gani yake a hakan Baffa yana takura da maganar da suke yi. "Baffa is back, da zarar ya ji labarin ina ɗaukan ki zuwa wajan shan Ice cream mun kaɗe a gidan nan, kinga ke little sis ce autar gidan nan, kuma amanar Hafizz Hafizz Baffa, kenan Baffa ba zai taɓa yi miki faɗa ba" Hidaya ta yi shiru tana kallon Mu'allim cikin rashin fahimta ta ce "Baffa baya faɗa ai Akhy" "And who told you that? Bakya nan ya kwakkwaɗawa Liman mari, wata ƙara da ihu da ya yi wa Liman sai da kowa ya firgita a gidan, don Allah Hida mu ajjiye shan Ice cream a gefe zan siyi na kawo miki, ni aure zan lallaɓa Baffa ya nema mini please?" Ta washe fararan haƙoranta masu kyau ta ce "Idan baka kawo mini ba, I'll go and tell Baffa everything kana zuwa wajan Ice cream" Mu'allim ya dafe goshinsa yana murzawa ya ce "Ya rabb, ke ba'a sirri dake ne Hidaya?" "Ka rasa dawa zaka yi sirri sai da Hidaya Hafiz Hafiz Baffa? Baka san halinsu ɗaya da Nadiyaah Sayyadi Baffa ba? Ai Baffa yana jin komai dake faruwa a gidan nan ta wajan Hidaya da Nadiyaah da Diynaah tas ma kuwa" "Sannu da fitowa Mamy" Mu'allim yace yana bata girma wajan miƙewa, ta nemi waje ta zauna idanunta akan Mu'allim, tana sanye da baƙar Jallabiya me kyau ta yi rolling kanta da mayafi a nutse ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, hannunta riƙe da counter da azkar. "Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa" Mu'allim ya ɗaga kai ya kalli Mamy bayan ya amsa cike da kulawa da rashin sakin fuska ta ce "Zaryar me kake wajan nema na haka?" Ya yi ƙasa da kan shi na wani lokaci. Kan shi a ƙasa ya ce "Akan yarinyar nan ne" "Yarinya?" Ta maimaita a fili ta ɗora da "Wacce yarinya? Wani abu ne ya faru?" "Mamy akan Iftihal yarinyar da aka kawowa su Nadiyaah da Diynaah aiki, da gaske ina son yarinyar nan sosai a cikin zuciyata tun kallon farko da na yi mata na yaba da hankali da nutsuwar da take dashi. Sunanta Iftihal na gaskiya Aysha, a unguwar Kankarofi suke, na sake komawa na yi bincike akan ta sosai" Ta ɗan gyara zama kafin ta ce "Ina fata binciken da ka yi ya yi daidai da tsarin matan da Baffa ya ɗora ku akai wanda suka dace da zama surukan Baffas family. Ba ƴar ƙananun mutane bace" "E, gaskiya su talakawa ne sosai Mamy" "Shine me? Kuɗi da talauci mutum ke yin su ko Ubangiji? Mutumci da tarbiyyar gidansu nake magana akai" Ya yi jim, domin binciken da ya yi ba mai daɗi bane akan gidansu, binciken da shima sai da ya hana shi bacci, da ace yarinyar bata tsaya masa ba, tabbas zai iya haƙura da Iftihal amma me? Ko idanu ya rufe ita yake kallo, idanunta, fuskarta, komai nata sune suke masa gizau a cikin idanunsa. Da wannan muryar tata me sanyi da kamala. Mamy ta ce "Uhm? Ina jinka?" Ya girgiza kai, "Mamy ban saba ƙarya ba kin sanni akan gaskiyata ko za ta yi ajalina. Da ina da iko da fara yi miki ƙarya to zan fara a yau ne, a dalilin Iftihal. Mutanen unguwar sun ce mahafinta yana shan giya, yana yin caca, kawai dai ba mutumin ƙwarai bane, mahaifiyarta tana da ilimi sosai ta taɓa koyarwa a makarantar gwamnati kafin sabuwar gwamnati tazo ta sauya ma'aikata. Ta basu tarbiyya sosai, komai na rayuwarsu ita ce. Suna da ƙanin uba sunansa Bala amma ɗan daudu ne.....," tun kafin ya ƙarasa ta ɗaga masa hannunta tana miƙewa tsaye cikin rawar ɗari da kakkarwar jiki ta ce "Auzubillahi! Ka bincika komai kaga komai, amma baka gamsu ba sai ka faɗa mini? Tun a can unguwar tasu ya kamata ka ajjiye soyayyarta. Irin wannan jinin da tsatson zaka kawo mana cikin zuri'ar Baffas? Al'ameen ka haukace ne me yake going ta cikin kanka daka kasa controlling zuciyarka" Sai ta yi baya kaɗan tana salati. Ba tare data juya ta kalle shi ba ta ce "Karka kuskura Baffa ya ji wannan maganar hukuncin da zai maka na san ba zaka iya ɗauka ba. Zai nemi wata can cikin matan da suka amshi musulunci ya ɗaura maka aure da ita ne for sure" jikin Al'ameen ya dinga rawa ya zamo daga kan kujerar ya ɗora ƙafafuwansa a ƙasa, idanunsa sukai jajur duk da acn dake cikin parlorn zufa ce ke wanke masa fuska. "Mamy don Allah.....," "Kar ka roƙe ni Mu'allim, tashi ka fita" Ya ce "Ki yi haƙuri. Amma Mamy tarbiyya daman ta iyaye mata ce, yau da mahaifiyarta ke aikata abin da mahafin nata ke yi wallahi ba zan sake ɗaga maganar ba" wani uban kallo ta yi masa, a karan kanta zata iya barin Mu'allim ya auri yarinyar itama ta yi mata, amma hakan ya saɓa dokar ahhalin Baffa. Zai ja musu ƙasƙanci ne a idanun jama'a. Wannan maganar ma ba zata bari Hajiya Umaimah ta ji ba. Ta juya ta kalli Hidaya ta ce "Da kika je kitchen kinga baƙuwar me aikin nan tazo yau ɗin nan?" "A'a Mamy, bata zo ba" "Good, ta bar aikin daga yau ɗin" ta nemi waje ta zauna fuska babu walwala "Ko auren za ka yi ma ai ka haƙura a fara na Baffa, tunda na ji Malami ya ce yau za'a saka rana" Hidaya sai kallon Mamy take yi sai ta ce "Mamy zani wajan Anty Diynaah ta yi mini ƙarin karatu" ta jinjina kai ta fice. Al'ameen da ƙyar ya iya jan jikinsa ya fice zuwa nasu part ɗin, ɓangarensa da yake kusa dana Liman ya shiga babban ɓangare ne me kyau yana shiga ya zube a ƙasa yana riƙe kai. *** Ruwan daya sauka akan fuskarta shine ya sakata sauke ajjiyar zuciya me ƙarfi, ta ɗan juya kanta kaɗan da ya yi mata nauyi, sannu a hankali ta miƙa hannunta ta ɗora saman ƙirjinta daidai saitin zuciyarta da take bugawa da ƙarfin gaske. Laɓɓanta a bushe ga wani irin ciwo da kan yake mata bata iya ko buɗe ido balle taga mutanen da suke kanta. Ta ware bakinta da take jin ya bushe mata sosai tace "Yau dai da gaske bani da lafiya mahaɗita, ban san me yake mini ciwo ba, amma ko ma mene Alhamd gaki a kusa dani, na san ciwon da kan shi zai ji kunyar kamani akan idanunki" ta yi shiru sai ta miƙa hannunta. "Ki ɗora ni a cinyarki mahaɗita, ki rungume ni a jikinki ina jikin kamar Innti ce ina son ki danne mini ƙirjina ki hana zuciyata fitowa" Jummai ta yi wa Iftihal ƙuri da idanunta, yarinyar ta yi fari fat saɓanin jiya, ga jini sai zuba yake yi a jikinta tunda Baita ya yi mata aika aika. Jummai ta juya kaɗan taga Baita shimfiɗe a saman gadonsa ya ɗora hannunsa a saman cikinsa sai bacci yake yi yana sakin munshari. Hannu ta saka ta maka masa dukan daya saka shi buɗe ido da miƙewa tsaye, ganin Jummai sai ya yi siririn tsaki ya ce "Uwar Kasko ya kai ne?" "Ya akai kake tambayata? Sakko ka kalli ɓarnar da ka yi wa yarinyar nan Baita" Alhaji Baita ya kalli Jummai sai ya juya ya kalli inda Iftihal take kwance, ya ƙurawa ƙirjinta idanu ganin da ƙyar take iya jan numfashi da saukewa. "Jummai ke sanda na amshi budurcinki ya kike a lokacin? There's nothing serious, pain ne kawai a bata magani" Jummai ta girgiza kai ya ce "Wannan pain ɗin bana iya budurci bane, hadda na zuciya. Ka faɗa mini ka yi aiki a kanta ne?" Sai ya jinjina kai na wani lokaci. "E, na yi mana. Kalli can kiga Jummai" Juyawa ta yi sai taga sabbin daloli bandir bandir, kamar kuma bayan su akwai saura. "Au har kuɗin sun samu shine babu labari? Daman ai saboda aikin nake tausayin yarinyar idan kuma ka yi ai shar dani" Baita ya watsa mata wani lalataccen kallo ya ce "Macuciyya uwar Kasko da Marka. Ki ɗauki yarinyar nan ki mata wanka yanzu zan dawo domin har yanzu a sama nake jin kaina" "Kasan aiki kuɗi nake, bari na yi mata yanzu na dawo mu tsadance, akwai wasu magungunan ma"ya ce "ki haɗu mini dasu". Fita waje ta yi, shi kuma ya yi shirim yana danna waya, wata number ya kira ana ɗagawa ya ce "Ranka ya daɗe, Allah Ya taimake ka. Aiki ya kammalu a ɗakin da na ce ka ware, yanzu kana shiga zaka ga zakara me abun mamaki" shiru ya yi alamar saurare ya ce "Ka bada Biliyan goma ya wadatar ai kai ne, dole mu tsaya maka a komai, idan aka kafa ai damu ake komai. Thank you Sir na gode" Ya kashe kiran yana sakin murmushi. Jummai ta dawo tana kallon Iftihal dake cikin jini, yarinyar sai surutai take ita kaɗai tana cewa Ana ta rungumeta, ji take yi kamar ana fusgar naman jikinta, ji take yi wata wuta na rura kanta a fatar jikinta, ƙoƙarin buɗe baki take yi wajan yi wa Ana bayanin irin ciwon da take ji, amma ta kasa. Jummai ta tattare hannu ta ɗago Iftihal sama wani gigitaccen ihu Iftihal ta saki tana zabura jini na sake ɓalle mata ta cakume Jummai tana kafa mata haƙori a hannu saboda wani irin raɗaɗi da take ji a ƙasanta. Jikinta ya ɗauki zafi sosai kamar gaushin wuta. Ta shige banɗaki da ita a cikin wani ƙaton ruwan zafi ta saka Iftihal, daga nan kuma bata sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi da wata sabuwar azabar data ninka ta baya. Ɗis haka idanunta ya buɗe ya kumbura sosai kamar zai faɗo, Baita ta gani a kanta yana yi mata abin da ya yi jiya, ta yi masa ƙuri da idanunta, deep down na zuciyarta sunan Allah kawai take kira jikinta ya saki zuciyarta ta tsaya, daga nan numfashinta ya ɗauke bata sake sanin inda kanta yake ba saboda tashin hankali. Yadda azaba ta sumar da ita, haka wata azabar ta sake farkar da ita. Ɗakin shiru, ba iya ɗakin ba, kusan duka gidanne shiru, Ana take son gani, Anarta take buƙatar kwanciya a jikinta, ta san dole raɗaɗin da take ji a zuciyarta zai ragu, ta shiga kiran sunan Allah guda ɗari babu ɗaya, cikin hukuncin Allah ta samu zarafin yunƙura wa ta miƙe zaune, ta ɗauki hijabin data gani a gefe ta saka, ya saukar mata har ƙasa jikinta ko wando babu, ta shiga daddafawa ta miƙe, taga kuɗi da yawa ta saka hannu ta ɗauki dubu ɗaya, da taimakon Ubangiji ta fito tsakar gidan, tas kamar an share, har zata fice sai taji wata ƙara da ɗan ihu daga gefen ɗakin da take tsaye, ɗaki da akaf mutanen gidan har matan Baita hatta Jummai babu wanda ya taɓa shiga, kodayaushe a rufe yake, yanzu bata san mene ya saka ya zama a buɗe ba. Taja ƙafafuwanta a hankali ta nufi ɗaki ta buɗe ta shiga, sandarewa ta yi kanta ya sara gabanta ya yi mummunan faɗuwa, wata ƙaramar yarinya ta gani tsaye cur an kafeta, tana kyautata zaton Anisa da Baita ya bata labari ce. "Anisa?" Iftihal ta kira sunanta, madadin Anisa ta amsa sai ta shiga ambaliyar kuɗi ta cikin bakinta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Duk wani kira da Iftihal ta yi wa Anisa kuɗi ke zuba, cikin ƙaramin lokaci kuɗi ya taru sosai. Ta shiga ƙarewa ɗakin kallo sosai, da sauri ta juya ta fita jiri na kwasarta haka ta samu zarafin bin wani lungu ta fice daga unguwar. Ina zata je? Ba zata iya komawa gida ba a wannan halin da take ciki ba, tana buƙatar ganin Ana akwai abin da take son faɗa mata akan Alhaji Baita, amma gidan a yanzu ya haramta da ita. Ta tsayar da me napep da ƙyar ta shiga ta ce masa "Mai taɓa sule, Baffas estate zai kaita, please ka kaini har bakin gate ɗin Baba driver ka ji?" "In sha Allah yarinya" yace yana jan napep ɗin zuwa kan titi hankali kwance. Iftihal taja jikinta kaɗan ta kwanta jikin kujerar napep *** Yana zaune a saman dakalin yana danna wayarsa ya ji motsi kusa dashi, a hankali ya ɗaga kan shi zuwa gare ta, ya watsa mata idanunsa masu laushi, sai yanzu take farkawa. "Anji daɗin katifata irin bacci haka" Ta ɗan dube shi kamar za ta yi magana kuma sai ta yi shiru, idanunta ya yi wani irin jirkicewa fuskarta a haɗe babu walwala da wata sanyin murya ta ce "Abbaa yazo?" Haysaam ya girgizar kai ya ce "Jaheed dai" "Abbaa bai zo nema na ba?" "Sure, ai kamar baya nan fa" Ana ta juya manyan idanunta wanda sannu a hankali suke sake rinewa, ta ɗaga hannunta wajan dafe ƙirjinta ya ce "Ya akai? Ciwo yake miki ƙirjin?" Ta yi tsaida idanunta akan Yaa Sam bata kuma sake masa magana ba ta shige cikin gidansu, sallama ta yi ta shiga Jaheed dake ta aikin kuka ya tusa Jadid dake cinyarsa yana suma ya amsa mata. Da wani irin rawar jiki idanunta na firfitowa ts durƙushe ta riƙo hannun Yas Jadid ta ce "Masoyi, don Allah ka tashi haka nan, ka daina wannan ciwon, ina jin fiye da abin da kake ji, idan na tuna kuna kusa dani sai na ji duk wani ciwona ya yafi. Haba nawan" Jaheed ya share hawayensa ya ce "Masoyiyar jeki gidan Emama ki kira Innti kar Jadid ya mutu bata nan, nima mutuwa zan yi idan ɗan'uwana baya raye a duniya wallahi" "A'a......." Ta shiga girgiza kai, gabaɗaya Ana bata san me take ji a ranta ba, tana jin ciwo tabbas, tana jin raɗaɗi tabbas, idan taga sunan Daada a tafin hannunta ji take kamar ta cire hannun ta yar, babu wani abu data tsana a duniya fiye da Daada da kuma hannunta, ta ɗauki alƙawarin goge wannan sunan ta kowacce hanya. "Abbaa fa?" Jaheed ya ce "Ban san ina yake ba" Bata sake magana ba, ta miƙe tare da yin waje bata ganin ko gabanta, kamar wacce ta yi wani mugun abu duk inda ta shige sai taga ana kallon ta, a haka ta isa gidan Emama tana shiga ta same su suna cin shinkafa da miya da nama ga lemo a gefe. Daga tsayen ta ce "Sannu Emama, Innti fa?" Liya ta ce "Ke don uwarki a haka uwarki ta koya miki yadda ake gaida na gaba dama?" Tana saukewa Ana ta ce "Ke don uwarki a haka uwarki ta koya miki yadda ake yi wa mutum gyara dama?" Liya ta juya ta kalli Hanna da wani irin mamaki ta ce "Ni yarinyar nan take zagi da mayar wa da magana Hanna? Ni yaushe aka haifi Ana?" Hanna ta ce "Ki bar shegiya da idanu irin na Aljanu, mugun duka za mu yi mata wallahi" Ana ta juya sosai sai ta saki dariya ta ce "A haba? Ƙarya kike wallahi Hanna, sai dai mu daku kuma kar ki yi kuskuren taɓa Ana, don wallahi ko wannan bugaggen yayan naku a yanzu ya ce zai taɓa ni sai ya san ni ƴar wahala ce, sai ya san ni cikakkiyar ƴar halak ce gaba da baya. Idan kina ganin ƙarya ne bisimillah try me za ki gani a fayyace" Liya ta miƙe tsaye tana yin ɗamara, cikin azama Ana ta cire hijabin jikinta ta cire ɗankwali ta yi ɗamara, gashinta da Babban yaya ya yi mata gida biyu dasu suka sauka har baya, wasu kwantattun suma ne daga gaban goshinta masu ɗaukan idanu, gefe da gefen fuskarta sumar ce ta kwanta gwanin sha'awa. "Ƙashi ɗaya ne dani, idan kun fasa baku haifo cikin Emama ba dukanku" Kanta suka yo, Hanna ta shaƙe wuyan Ana, Liya kuma ta shiga jan gashin kan Ana. Idanun yarinyar ya yi jajur jijiyoyin kanta suka firfito waje, wani ihu da kururuwa Ana ta yi saboda azama ta kai wa nonon Hanna cafka ta matse, azaba ta saka Hanna sakin wuyan Ana, tana sakinta Ana ta juya ta buga Liya da ƙasa da wani irin ƙarfi daya zo mata, idanunta rufe ta shiga dukan Liya da naushi ta fasa mata baki. Hanna ta ɗakko taɓarya zata makawa Ana a kanta ta ji an kwarfeta ta baya, ta yunƙura zata miƙe ta sake jin an kwarfeta ta zube a wajan wanwar a ƙasa. "Innalillahi, Muraad uban me ya kawo ka cikin gidana? Kashe mini ƴa za ka yi?" Babban yaya bai ko kalle ta ba, ya ciri wayar caja daya gani a tsakar gidan ya shiga zararawa Hanna tana ihu da birigma ya farfasa mata jikinta, ganin ta yi laushi ya kalli Ana yaga har yanzu tana kan Liya hannu ɗaya ya saka cak ya ɗauke Ana, ta ɗauka Hanna ce da ihu ta juya zata dake ta ya yi saurin riƙo hannunta. "Abbaa....," ta ce da rawar murya. Rungumeta ya yi sosai yana jin tana sauke ajjiyar zuciya, ya ɗauki ɗan kwalin ya saka mata ya zura mata hijab, idanunsa zube cikin ƙwayar tata idanun. "Abbaaa... "Ina ka je na dinga nemanka..," "Shhhh" ya ce yana ɗora yatsarsa a bakinta alamar ta yi shiru yana ta shafa kanta. Emama ta ce "Shegu haihuwar asara, uwar taku tana can wajan police sun garƙame shegiya a can" dam! Zuciyar Ana data Yaya ta buga lokaci guda, cikin sauri ya riƙe hannunta suka fice daga cikin gidan Emama. *** BIYA. Shatu na gaba Innar Ramu na biye da ita, ta riƙo Ramu a hannunta a haka suke tafiya, har suka shiga cikin dajin sosai kafin suka isa inda bukkar take. Innar Ramu ta ce "Shatu kin tabbatar me bada magani ce? Yama sunanta kika ce mini jiya da yammaci?" Shatu ta murmusa sosai ta ce "Bokayan karaba sunanta" Ta ƙarasa jikin bukkar a hankali ta ce "Muna gaisuwa zuwa ga karaba, muna muki jinjina yake bokanyan rugar Biya da kanta gamu" Daga cikin bukkar Batty ta kumbura murya ta ce "lalle, ga Ramu da Innarta, ga Shatu ƴar rakiya, ga ciwo nan da mutuwa suna binki Ramu, ga lahira nan dab dake Ramu" Ramu ta ƙanƙame Innarta tace "Inna kin ji ko mutuwa zan yi, daman na faɗa miki Batty ta ce bani da lafiya kin ƙi yadda dani gashi yanzu bokanya karaba ta faɗa sai ki yarda" "Yanzu Bokanya mene abin yi?" Batty ta maƙale murya "Kin san ciwon Taifot? Shine yake damun Ramu hanjinta ya fara taɓowa yana fashewa kuma shikenan. A samu tafashasshen gayen zogale ko neem (dogon yaro) ta dinga shan ruwan akai akai sai a dinga yi mata surace, in sha Allah zata samu waraka magani sadidan daga wajan Bokayan karaba" Innar Ramu ta ce "Na gode sosai, na gode Bokayan karaba mene kuma abin sadaƙa" Batty ta yi shiru ta rasa me zata ce, cikin sauri Shatu ta ce "Dubu uku ake bata ai" jikin Innar Ramu na rawa ta ɗauki kuɗin ta tura ta ƙasa, ta riƙe Ramu suka tafi. Suna tafiya Shatu ta yi wuf ta faɗa ciki ta ce "Mutuniyar.... "Na'am, masoyiyar" Batty ta amsa tana cire ganyen kanta ta ce "Wash Masoyiyar yunwa nake ji sosai wallahi" Cike da damuwa Shatu ta ce "Yau ma su Lami basu sammiki abinci ba? Suke barinki da yunwa haka?" Batty ta jinjina kai ta ce "Ai don fara cin mutane ba, da sai na lashe kurwarsu tas. Jira nake kaɗo ya dawo mu yi aure irin wanda za'ayi wa Hawwa tunda kin ce mijin mutum yana bashi abinci" Shatu ta ce "Sosai ma. Amma waye kaɗo?" "Wani fari, dogo kyakkywa, me gashi a gefen fuska, me suma har wuyansa shine mijina shi nake so ba Saleh ba, kyakkywa ne sosai don ki ji" shiru suka yi, Batty ta lumshe idanunta tana hasaso yadda taga mutumin. "Ya sunansa?" "Kaɗo..... "Ke sunan gaskiya za ki waɗe mini?" Sai Batty ta watsa hannunsa alamar rashin sani. Daidai nan Hawwa ta ƙarasu da sauri tana hakki ta ce "Ke Shatu maza zo, Mado ne ya mutu gashi can an cika a gidan Moddibo ana ta kuka, duka abokan Mado na birni sun zo har da Sambo" jikin Shatu ya ɗauki rawa, domin tana da alaƙa da gidansu Moddibo. Jikin Batty ma ya ɗauki rawa sosai da ɓari hawaye ya ɓalle mata a fuska ta ƙanƙame jikinta tana jin kamar ta fasa wani irin gigitaccen ihu haɗe da birigma. "Wallah bani na cinye shi ba, bani bace...," Hawwa ta ce "Batty me kika ce?" Cikin sauri Shatu ta ce "Babu komai, mu je mu gani" Batty taƙi yadda ta je gani take kamar asirinta ne zai bayyana. Sanda suka je, shirin yi wa Mado jana'iza ake yi, Shatu ta hangi Sambo yana alwala a hankali ta ce. "Laa ashe da gaske dai Hawwa take yi?" Idanun Sambo akan abin da yake yi ya ce "Da gaske me?' "Da gaske ka zo binne Mado" Ya ɗago idanunsa a hankali, ganinsa ya sauka akan Batty, ya ƙura mata idanunsa da suka sha farin ƙwalli ya jima yana kallon ta kafin ya zame idanunsa ya ce "E, babu jimawa" Shatu ta ce "Allah sarki, ya aiki kuma?" "Kazo da Lemo da biredin yau ma?" Kafin ya ce komai Batty ta ce "Nima ka bani idan ka zo dashi, zaka bani ko yaya ne ko?" Sambo ya sake juyawa ya kalli Batty can ya ɗauke kai yana miƙewa ya ce "Ina dawowa" A hankali Batty tabi bayansa da kallo. *** Anty Jiddah ce ta tura handle ɗin ƙofar ɗakin Ahlam magana za ta yi sai ta fasa, ta zubawa bayan Ahlam idanu ganin yadda faffaɗan waist ɗinta ya zauna a riga da skirt ɗin data saka, ya yi mata wani irin kyau sosai atamfar, ta murza ɗauri na gaban goshi, fat fat haka ƙirjin Anty Jiddah ke bugawa. Sai ta ƙirƙiri murmushin dole ta ce "Golden voice da kanta, kwaliyyar tarbar mijin ce har yanzu bata ƙare ba?" A hankali Ahlam ta juyo idanunta ya yi jajur saboda kukan da ta yi, ba ta yi kwaliyya ba, amma skin ɗinta ta yi fresh ta goge hannunta ɗaya maƙale a hammata. "Kuka kike Ahlam?" "Kuka akan me subuhanallahi!" Ta ƙarasa tana kama Ahlam zuwa jikinta ta ce "Haba kakata, mene abin kuka a aure? Na ɗauka za ki fi kowa farinciki, kin san a duniya bayan ganin kin samu nasara akan aikin ki, babu abin da Engineer yake so irin ya ganki a ɗakin mijinki. Haba Hali dubu, kakata ta kaina ya isa haka daina kukan" Ahlam ta narke tana shagwaɓe fuska ta ce "Anty Jiddah wanene shi? Ki faɗa mini ko sunansa ne, Allah tsoro nake ji bana son fita, bana son auren, na amince saboda Yaya ne kawai, fargaba da faɗuwar gaba nake ji idan na tuna ina da aure. Burina, farincikina, nasarata duk za su rushe fa Anty Jiddah, ɗaukakar da nake son yi fa?" Anty Jiddah ta share mata hawaye ta ce "Haba Babyn yaya, aure ai ni'ima ce kuma ba zai hanaki cimma burinki ba, idan bakya son ran yaya ya ɓaci maza tashi ki sami mijinki yana parlour" da rawar ɗari Ahlam ta ce "Yazo ne? Innalillahi!" Anty Jiddah ta fashe da dariya tana sake fesawa Ahlam turare, taja hannunta suka sakko ƙasan bene daga nan Anty ta juya. Yana tsaye a tsakiyar parlourn, ya bata baya sanye yake da yadi kaftan brown wanda ya haska fatar jikinsa, ya ɗora wula a saman kan shi, hannunsa ɗaya sanye cikin aljihun wandonsa. Kan shi a sama ya zubawa photon Ahlam dake manne idanu baya ko ƙiftawa. Ya ji sanda ta tsaya a bayansa nesa dashi, kamar yadda gabanta ke faɗuwa haka shima nasa yake yi, bai sani ba ko zata amince masa, zata karɓe shi a matsayin mijinta, ya aureta ba tare da amincewarta ko neman soyayyarta ba. Amma bashi da iko da kan shi, kamar yadda bashi da control da zuciyarsa akan soyayyarta. She loves her so much. Sannu a hankali ya shiga juyawa zuwa inda take, wata ajjiyar zuciya ya sauke sanda ya ɗora idanunsa a kanta, a yanayin da bai taɓa ganinta ba. Kanta yana ƙasa bata son ya juyo ba, bata san ya ƙarasu inda take ba. Sai nunfashinsa ta ji yana sauka a fuskarta. Kadin ta yi motsi ya zaga hannunsa biyun zuwa bayanta daidai ƙugunta ya ɗora ya janyota kaɗan ya sakata a tsakiyarsa. Wani irin rawa jikinta ya fara. "Assalamu Alaiki Halimatul Sadiya..... "Hello my Ahlam Abdallah Kurmi.... "Fine baby, my wife" Ahlam ta sandare ta kasa motsin kirki zuciyarta ta fara gaza ɗaukan yanayin, tsigar jikinta ya shiga tashi, dum haka take jin saukar muryarsa kamar dalma kamar kuma ruwan sama, ta kasa yadda da abin kunnenta yake jiye mata a yanzu ɗin. "Mrs Asad.... "Matar MD da kanta" Ya saka yatsu biyu ya ɗago kanta, idanunta da yake zubar da hawaye ta watsa akan fuskar Md wani abu na cakin zuciyarta. "Md ne mijina?..... "Md yaya ya aura mini? Me Md zai yi da ƴar iska matsoraciyya? Anya Md take gani?" A zuci take wannan maganar jikinta duka rawa yake ta kasa furta komai, ji take kamar ba Ahlam ba, yau ita Md kewa dariya? Bata dawo daidai ba ta ji ya jata jikinsa ya rungumeta kaɗan, ta rasa dalilin daya hanata hana shi, ko yatsa ta kasa motsawa ta yi wani irin hooking gabaɗayanta. Ya sumbaci goshinta ya riƙo hannunta ya ce "Let's go..... "Mu je" ya jata suka fita har inda ya yi parking motarsa ya buɗe mata tare da sakata, ya zagaya ya shiga. Tafiya suka yi me tsayi hannunta yana cikin nasa, ta kasa motsi, ta kasa magana, ta kasa daina zubar da hawaye. Daidai Napep na tsayawa a bakin gate ɗin daidai lokacin da motar Md ta ƙarasu, aka buɗe masa gate ya shiga, itama a dai-dai lokacin ta sako ƙafafuwanta da babu ko takalmi a cikin makeken gidan. Md ya buɗewa Ahlam ƙofa ya riƙo hannunta, Ahlam kuma ta juya sai kallon wacce take tsaye dafe da cikinta ta kasa motsi take yi. Ya ja hannun Ahlam zuwa babbar ƙofar shiga gidan daidai nan Mu'allim ya fito saboda saƙon Mamy da zai amso, na magani, idanun Nadiyaah ke ciwo sosai tun jiya sun jajur. Mu'allim ya dakata. "Finally, ni ne wanda ya fara ganinta" in ji Mu'allim Md ya kalli Mu'allim ya yi shiru. "Ahky Liman, Allah Ya sa Albarka ashe staff ɗinka ka ɗakko, wannan ai na sha ganinta a Bright Fm idan na je wajanka, Am right?" Md ya ce "Al'ameen, ina zaka by this time?" "Nadiyaah Sayyadi Baffa zan amsowa magani a asibiti wajan family Doctor" "Sayyadi Baffa?" Ahlam ta maimaita a zuciyarta, Md yaja hannunta zuwa ciki shi kuma Mu'allim ya yi gaba. Har yazo daidai inda take bai lura ba, sai da ya ji ta cakume shi kamar daman wani take jira, ya ɗago kai gabansa ya faɗi ya ce "Iftihal? Me kike a nan wajan?" Bata iya buɗe ido, bata ko ware laɓɓanta ta kifo jikinsa, nan take kuma jini ya ɓalle mata, a firgice ta ce "Ana....... "Ana, kai ni wajan Ana zani gida" Laɓɓanta ne kawai ke motsawa idanunta a rufe suke. "No bari na kai ki asibiti" Ta damƙe hannunsa tana girgiza kai "Don Allah ka kai ni wajan Mahaɗita don..... Gabaɗaya jinin ya ɓata shi, ya sunkuce ta gabaɗaya ya saka a mota suka nufi Kankarofi. Ana ta kira magariba sanda ya isa, ya ci sa'a Babban yaya yana shirin shiga Masallaci, suka gaisa cikin kulawa, Mu'allim ya yi wa Muraad bayanin komai, har yadda yake son Iftihal ya shirya aurenta, Yaya ma ya yi wa Al'ameen bayani har batun cacar, nan take ya ce zai biya miliyan ashirin ɗin a bawa Alhaji Baita, zai turo Mahaifinsa gobe a ɗaura masa aure da Iftihal ɗin. Yaya ya yi na'am da hakan sukai exchanging number. Ya ɗauki Iftihal a hannunsa zuwa gida, Innti ta dawo gida da ƙyar bayan alƙawarin da yaya ya yi zai biya Bala Sukunbiya kuɗinsa. Sanda Innti taga Iftihal bata san lokacin ta saki wani irin kuka ba, ta riƙe Babban yaya jikinta na wani irin rawa da kakkarwa kamar mazari. "Na shiga uku Yaya, me na aikata wa Iftihal? Me yake damuna ne, me ya sa nake biyewa Daada wajan saɓon Ubangiji? Ba haka na yi niyya ba, abin da nake niyyar yi daban abin da nake aikatawa daban, ina jin kamar narasa kaina yaya. Na yi asara a matsayina na uwa, na yi saɓon Ubangiji" Wani irin kuka take yi har da shassheƙa, idanunta kamar za su fito waje. "Na rusa rayuwar yarana, wani ciwo nake ji a ƙirjina Yaya" gam yaya ya rungume Innti a jikinsa idanunsa sun yi jajur wani irin ruwa ya taro a cikinsu ya kasa cewa komai. Ana ƙuri haka ta zubawa Iftihal ido, zuciyarta na buɗewa haka ƙirjinta, idanunta na soyewa na rashin sanin dalili ko hawaye ya kasa fita daga cikinta. Wanka Innti ta yi wa Iftihal ta gasa mata jikinta, data duban jikin yarinyar bata san sanda ta sake sakin wani ihun ba tana rungume Iftihal. Ta bata magani ta kwantar da ita bacci ya ɗauke ta. Cikin dare Iftihal ta riƙe Ana saboda a jikin Ana ɗin take, ta shiga bata labarin abin da Baita ya yi mata, ta ɗauki wani abu ta damƙawa Ana a hannunta. Ana ko tari bata yi sai ƙanƙame Iftihal kawai ta yi a jikinta. Wajejen ƙarfe uku na dare ya banko ƙofar ya shigo, hannunsa riƙe da kwalbar giya yana layi da tangaɗi, kamar yadda ya saba yau ma ɗin tsirara ya shigo, yana shigowa gaban Innti ya yi mummunan faɗuwa. Tana zaune akan ladduma tana istigifari, jin shiru ya saka Innti juya wa dam! Ƙirjinta ya buga jikinta na wani irin rawa da ɓari ta miƙe tsaye, ganin Daada ya gurfana a gaban Ana ya yaye rigarta yana ƙarewa ƙirjin yarinyar idanu, maganganun da sukai da Alhaji Baita yake tunawa, ya faɗa masa hanyoyin da zai bi idan yana so ya yi kuɗi ya shahara ya nemi duniya, dole sai ya kasance da Ana. "Daada!" Ta kira sunansa da ƙarfi. "Innalillahi raji'un mene haka?" Kafin ta ƙarasa ya saka hannu ya damƙo ƙirjin Ana da suke tubarakallah, bata saka rigar mama saboda ciwon ƙirji take yi. Duk abin da yake faruwa akan idanun Iftihal data farka ta yi sallah ta dinga yi wa Daada addu'a domin har zuciyarta tana ƙaunarsa. "Innti ina son na kasance da Ana" ya sake faɗin "Zan kasance da Ana a wannan daren ina kwaɗayinta, zan yi arziƙi idan na kasance ta" Kau! Kau! Kau! Kau! Innti ta jerawa Daada maruka huɗu a fuskarsa lokaci guda, tana wani irin huci ta ce "Wannan ya zama na ƙarshe, hatta Iftihal ba zata koma inda ta fito ba, idan ka shirya na shirya shege kafasa" ya ji zafin marin har wuta ya gani. "Muddin ina raye sai na kusanci Ana!" A firgice Iftihal ta fito daga ɗauki ta yi wa Daada wani irin kallo, hijabi ne a jikinta wanda ta yi sallah, duk irin masifar da ake Ana bacci take sosai. Ga wani duhu a tsakar gidan babu nepa, "Sai na kusanci Ana!" Shine ya dinga yawo a zuciyar Iftihal. Yadda ta kasance me shegen tsoran duhun dare da abin da yake cikinsa, hakan bai hanata fitowa tsakiyar tsakar gidansu ba, ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa tana jan wani irin ƙarfaffan numfashi daga baki ya sauka a ƙirjinta, jiki na rawa ta zube a ƙasa bayan ta kalli gabas ta yi Sujjada ta ɗago, hannunta ta miƙa zuwa sama idanunta na kallan sararin samaniya gangar jikinta na fuskantar Alƙibila cikin sarƙewar harshe ta fara magana. "Allah Ya tsinewa babana, Allah ka yi sanadin mutuwarsa yau, Ubangiji ka haɗa shi da ajalinsa a cikin daren nan, idan ya yi tsayin rai, Allah ka hana babana jin daɗin rayuwa, ka yi masa farraƙu da farincikinsa, Allah ka sanya babbar mota tirela ta yi awon gaba dashi yadda ko ƙashinsa ba za'a gane ba, Allah ka sanya bilo inci goma ya faɗuwa babana a kan shi idan yana bacci, Allah ka haɗa babana da ƴan daban da za su sassara naman jikinsa, Allah ka ɗorawa babana ciwon zuciyar da zai ajalinsa, Allah ka hana babana shiga Aljanna, ka yi masa iyaka da walwala, farinciki, da jin daɗin rayuwa...," bata ƙarasa faɗa ba, Daada ya sunkuci Iftihal baya ganin ko gabansa bai zarce ko'ina ba sai cikin rijiya, cumdum haka ya cilla Iftihal a cikin rijiyar..... *H I Y A A M* Page 14: The Visitors Bright pens Yota/001 I Dedicated this book to you Pixie. Kasa motsi Innti ta yi saboda wani abu daya tsaya mata a ƙirji, ya daki zuciyarta ta kasa ko jan numfashi saboda tashin hankalin ganin yadda Daada ya cila Iftihal a cikin rijiya. Numfashinta ya shiga kakkatsewa jikinta ya ɗauki rawa idanunta rufe ta fasa wata iriyar ƙarar data farkar da Ana daga bacci ɓarawo daya ɗauke ta. Da ƙyar ta buɗe idanunta, ta miƙa hannunta zata taɓo Iftihal saboda numfashinta data daina ji yana sauka a fuskarta, wayam babu Iftihal. Ta juya domin ganin ina ta Iftihal take, sai taga ashe a tsakar gida bacci ya ɗauke ta, bayan ta samu ta yi bacci, ita kuma Innti ta kira ta, kiran daya saka bata koma ɗakin ba. "Mahaɗita.... Ta kira sunanta da muryarta me sanyi, sai ta yunƙura ta miƙe tsaye, ita da fari ihun Innti a mafarki ta ji shi, sai ta ɗauka ko Anum ce? Tana ƙoƙarin shiga ɗakin Innti ta sake sakin wani ihun tana faɗin "Ka cilla mini yarinya a rijiya Daada, shikenan ka kashe mini Iftihal" Dam! Ƙirjin Ana ya buga da matsanancin ƙarfi, sai Idanunta ya fara dishi-dishi tun kafin ta tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji, da wani irin sauri ta juya taga Innti a tsakar gidan wajan bakin rijiyarsu. Ta juya ta kalli Daada da ya yi baya yana sake tangaɗi ya ce "Au duk gargaɗin da na yi mata bata jiba shine ta dawo mini gida? Ni zata jawa jarfar Alhaji Baita? To ga sakamakonta nan" Ya yi shaƙuwa yana fashewa da dariya. "Innti ai tunda kika haifi yara ba za ki taɓa jin daɗi a wajena ba, tun a cikin Muraad na faɗa miki ki tsayar da haihuwa kikai burus dani, kullum sai dai ki dinga haihuwa kamar akuya? Bani da ra'ayi ƴaƴa bani da burinsu" Innti bata da lokacin tsayawa ta ji surutan Daada sai ta juya da sauri zuwa ɗakin yaran "Yaya, Jaheed ku fito..... "Muraad kana ina?" Jikinta duk rawa yake yi. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Ta ce tana dafe ƙirjinta tana jin kamar zuciyarta ce zata faso ƙirjinta saboda nauyin da ta yi a ƙirjinta da kuma yadda take buga mata tare da yi mata motsi tana fitar da wani irin numfashi. "Innti...., Ta kasa maganar tana ƙanƙame jikinta da tsoran yin tambayar da tsoran abin da za ta ji. Idanunta kamar za su faɗo saboda wani irin girma da suka yi suka zazzago Ana ta ce "Ina mahaɗita? Ina take? Akwai abubuwan da take faɗa mini wanda bata kammala ba ta yi bacci, Innti ki nuna mini mahaɗita tana ina?" Innti ta kasa amsa Ana, sai kurma ihun sunan Babban yaya take yi da Jaheed. A firgice Jaheed ya fito sanye da Jallabiya, ya bar Jadid a cikin ɗaki. Jaheed ya kalli Innti. Ya ce "Innti lafiya? Wani abu ne ya faru?" Ya ce a tsorace "Ya cilla Iftihal a cikin rijiya... "Ya saka mini yarinya a rijiya" Ta fusgo Jaheed zuwa gabanta ta ce "Jaheed na shiga uku, na shiga uku, na kashe ƴata da hannuna na rasa Iftihal, na rasa yarinya me haƙuri da biyayya" ta matse kafaɗunsa ta ce "Ina Yaya? Ina Muraad yake Jaheed" He can't believe it, ya ji me Innti ta ce tabbas, ya kuma san bata ƙarya, ya rasa dalilin da hujja na rashin yadda cewa Daada ya cilla masoyiya a rijiya, Iftihal ɗinsa? Abokiyar wasan shi. Ya yi cak ya kasa motsi, ya ƙurawa Innti idanunsa da sukai wani irin juyawa a karo na farko. Ganin shima kamar ya rasa kan shi ya saka Innti matse kafaɗunsa ta ce "Jaheed ina Yaya? Iftihal a rijiya, kar na rasa Ayshatuna" "Babban yaya baya ɗaki" "Innalillahi!" Tana dafe kanta. Jaheed ya nufi rijiyar ta yi saurin riƙe shi tana girgiza kai. "Kar ka shiga Yaa Jaheed, ba zaka iya ba, rijiyar akwai zurfi, kar na rasa ku gabaɗaya" ta furta tana haɗiyar zuciya. Jaheed ya ce "Innti jinkirin zai saka wani abu ya faru, sai yaushe za mu jira?" "Mu jira hukuncin ubangiji" Ana tunda ta ƙurawa rijiyar idanu bata ko ƙiftawa, ko numfashi ta gagara ja da saukewa. Da wani irin yanayin tashin hankali idanunta rufe ta nufi rijiyar tana ambaton sunan Iftihal, ganin Ana na shirin faɗawa rijiyar ya saka Innti riƙota ta matse ta a jikinta. "Wallahi mutuwa zan yi idan na rasa mahaɗita, ki bari na shiga zan ceto ta, na miki alƙawarin babu abin da zai same ni, ki yarda dani Innti. Zan iya kamar yadda Abbaa zai iya" wani surutai take babu kan gado a ciki, idanunta rufe jikinta ya ɗauki rawa. Innti ta girgiza kai tana sake riƙe ta. "Yaya ina ka shiga? Kana ina Muraad" Innti ta ce da nauyin zuciya, duk irin kukan da Innti take yi babu maƙocin daya shigo, hatta Yaa Sam da yake kodayaushe idanu biyu Allah bai nufe shi da jin abin da yake faruwa a gidansu Ana ɗin ba, Salati kawai Innti ke yi ta ƙanƙame Ana ta shiga kokawa da ita ganin yarinyar na shirin ƙwacewa, daga cikin ɗakima jikin Yaa Jadid ya rikice. *** TAJMAHAR PALACE. Masarautar ta yi shiru sai kukan tsuntsaye da sauran nau'in dabbobin da suke ciki, girma da faɗin masarautar ya kai a yi kwantance da masarautar Tajmahar a cikin jerin masarautun da suka africa, ba lokacin bayi bane, amma har yanzu Tajmahar suna bautar da jama'a kamar sune suka halicce su, yawanci kuma sun fi ɗora tsananin dokar tasu ne akan mata, suna siyan bayi mata daka ko'ina, musamman suke ranar kasuwar bayi a naɗa shugaban bayi ya je ya siye duk matan da aka kawo kasuwar, a cikin farashi me tsananin tsada. Akaf cikin Tajmahar, babban part guda shine ya zama daban, komai na part ɗin daban, tsarin fari da ash ne, sai ya zama very different da sauran kuma yafi ɗaukan idanu saboda tsarin shi Yana zaune akan kushin ya ɗan tanƙwashe ƙafafuwansa, daga shi sai three qauter, duk da farin fatar jikinsa da yadda take ɗauke idanu, wani sahihin fari na burge wa, bai hana gargasa kwanciya a saman cinyarsa ba, ta lulluɓe fatar sai sheƙi take yi baƙa suɗik da ita. Babu riga a jikinsa, A hankali ya miƙa hannunsa idanunsa rufe ya ƙaro gudun acn, bai san me saka shi dawowa Tajmahar a dai-dai irin wannan lokacin ba, da alama kafin ya fita sai ran kowa ya ɓaci daga ciki kuma har dana Mai girma Deborah. Yaja numfashi ta cikin bakinsa ya cika bakin da iska ya fesar a hankali. Wannan karon ma yana ji ana sake knocking ƙofar da za'a shigo haɗaɗɗan ƙaramin parlourn nasa da yake hutawa ya yi burus. Wayarsa ce ta shiga haske, saboda baya son ringtones a silent take kodayaushe kuma a DnD. Number Tor Tiv ya gani da ya yi saved da "World" kiran ya katse a karo na farko. Aka sake kira, ya miƙa hannunsa kaɗan ya shafi screen ɗin wayar ya saka a hands free, dakakkiyar muryar Tor Tiv me cike da iko da izza ta ratsa cikin kunnensa. "Idan ba ka yi haka ba, ai ba zan kalle ka matsayin jinin Tajmahar ba, jinin Imande, zuciyar Imande, ƙaunar Uji" A hankali ya sake sauke ajjiyar zuciya saboda muryar abin da yafi ƙauna a zuciyarsa ta ratsa cikin wannan zuciyar dai. "Our next Tor Tiv, Me Tajmahar gabaɗaya" "World..... Ya ce a kasalance. "No agreement, my prince" Tor Tiv kuma Uji ya yi saurin tare shi da faɗar hakan, babu hayaniya cikin muryar shugaba, a nutse take cikin zallar iko da isa da kuma izza na jinin mulkin Tajmahar dake gudana a jinin jikinsa yana kwaranya a zuciyarsa. Bai sake cewa komai ya yi shiru. "Me ya samu Madaki yake hargagi a sashin Mai girma Deborah?" Madaki ya ji tambayar da aka yi masa, wato har an kai maganar zuwa fada gaban Shugaban Tajmahar? To shi duka duka, da Tor Tiv ɗin, da kingmakers, ciyamomin fadar, da dattawan cikinta akwai me zummar tarar shi ne ya masa wannan birkitacciyar tambayar bai ɗaure mutum ya saka shi a kurkuku ba, shi kan shi Tor Tiv yana da zummar tambayarsa ne kawai ta cikin wayar ba fuska da fuska ba. Yi masa wannan shirman tambayar daidai yake da sabon tashin hankali a Tajmahar. Sai ya ɗan yatsuna zagayayyiyar fuskarsa me ɗauke da kwantaccen saje me laushi da kyawun gani. "Ina son barin Tajmahar" Shine abin da ya fita daga cikin bakin Madaki kamar baya son yin maganar, ya saka hannu ya tura gashin gaban goshinsa zuwa baya. Tor Tiv ya yi shiru, don baya jin zai sake bawa Madaki damar barin Tajmahar masifun da suke bibiyarsu kaɗai sun isa. "Za ka iya banda yanzu" "World amma....," bai ƙarasa faɗa ba, Tor Tiv ya kashe kiran gabaɗaya da ita kanta wayar. Wani abu ya caki zuciyar Madaki, tsigar jikinsa ta shiga tashi tana mimmiƙewa da zubewa a farar fatar jikinsa, ya tsani hakan baya son hakan, wannan shi ne ƙarshen raini kashe waya mutum waya a fuska. Ajjiye wayar ya yi, ya miƙe tsaye yana saka kyakkyawan takalmi a cikin farar ƙafarsa, fuskarsa kamar zai ce ya shiga uku haka ya nufi ƙofar fita daga cikin sashin nasa, yana fitowa ƙofar farko gabaɗaya sojojin da suke gadin ƙofar suka yi saurin zubewa akan ƙafafuwansu, kan su a ƙasa, ko numfashi da suna da iko da kan su ba za su iya jan shi ba, da sassarfa yake tafiya, saboda kuzarin da ya yi wa jikinsa yawa, ba'a ganin fuskarsa sosai saboda gashin daya kwanto masa, a jinin jikinsa yake jin Tajmahar, amma deep down akwai abin da yafi Tajmahar muhimmaci a zuciyarsa a yanzu, ji yake kamar ana kiransa ana jan zuciyarsa zuwa wani waje daban, wani waje me muhimmaci. Fada ta jima da tashi, don haka kai tsaye sashin Shugaba Tor Tiv Madaki ya nufa, daga shi sai gajeren wandon da yake jikinsa buɗaɗɗan jikinsa na motsawa, sojojin ko inuwar Madaki basa kuskuran gani balle shi da kan shi Madaki, ya fito a suffar da ba kowa ke ganinsa da ita ba, kamar yadda ba kowa ne ya san ya shigo cikin Tajmahar ɗin ba. Madaki yana middle of the age ne, amma arziƙi da gata haɗi da gidan sarauta, da sangartar da aka nuna masa, sun buɗe masa jiki sosai ya zama fiye da age ɗin nasa. Yana zuwa ƙofar da aka rubuta TOR TIV da manyan haruffa yaja ya tsaya. Wani soja ne ya kira Tor Tiv ya ce "Shugaba, ga gudan jinin Tajmahar a ƙofar Tor Tiv da kan shi" ta cikin wayar da wata kasalalliyar murya Tor Tiv ya ja numfashi "Kar a bar shi ya shigo" Yana faɗin hakan ya ƙare da wani sauti na fitar hayyaci. Duk yadda ka kai da jin kan ka muddin Tor Tiv bai baka damar shigowa sashin ba, dole ne ka haƙura ko waye kai. Madaki ya juya zuwa can gefe, jikinsa ya ɗan fara ɗaukan rawa. Kamar ance ya ɗago kai sai yaga matar daya taɓa gani an fito da ita daga sashin Tor Tiv jikinta ɗaure da sarƙa, ya ware kasalallun idanunsa ya cigaba da kallon yadda ake janta kusan duk kayan jikinta a yayyage yake. Can wani waje da ake ajjiye dabbobi suka cillata sojojin kana suka juya. Ya ɗan taɓe jajayen laɓɓansa yana zura na ƙasa a cikin bakinsa ya tsotsa, kamar zai shige sai ya nufi wajan, da wannan karsashin nasa. Yana zuwa ya yatsuna fuska wajan ya yi datti da yawa, duk da ko tsinke babu. Yana shiga ya ganta ya rakuɓe tana cirar ciyawa tana ci kamar mahaukaciya, ya zuba mata maganaɗisun idanunsa kafin ya saka yatsu biyu ya murza A gigice ta ɗago kai, cike da tsoran ko wajan Tor Tiv za'a sake mayar da ita, ta shiga girgiza wa Madaki kai tana ja baya kamar ma tsoran mutane take yi. Ya durƙusa inda take ya dinga kallon yadda fatar jikinta take duk shatin duka, faratanta ma duk an cire su. "Ka tafi, ka tafi ka bar nan ba zan koma ba" a tsorace take maganar tana girgiza kai da wani firgice ta ce "Kar ka mayar dani.... "Bana so, ba zani ba" Ya buɗe idanunsa, a karo na farko daya taɓa tsayawa da wata baiwa a cikin Tajmahar har ta ji muryarsa, murya a shaƙe da slow ya ce "Wacece ke?" Da sauri itama ta ce "Wacece ke?" "Ina nufin sunanki?" Itama ta ce "Ina nufin sunanki?" "Huh!" Ya fesar da iska me zafi. Ya jima yana binta da kallo kafin ya taɓe bakinsa ya miƙe ya bar wajan. Yana barin wajan kuma aka fara kuke-kuke, yana ji bai bi ta kai bai ba, bashi da wani ra'ayi sosai akan Tajmahar ɗin. Gashi kuma shine namiji guda ɗaya wanda ya zama magajinta. Kukan da ake yi ya saka shi miƙewa daga saman lafiyayyen gadon da yake kwance, mata guda uku suna yi masa tausa, ya sakko ƙafarsa, ɗaya ta miƙo masa rigar bacci ya saka, ɗaya ta shiga rufe masa botiran rigar, da wata sabuwar izza ya shiga takawa wajan bakin ƙofarsa ya fita zuwa wani part ɗin duk a ɓangare guda. Yana shiga yaja ya tsaya ya kalli wacce ke shimfiɗe a ƙasa kafin ya yi magana ace "She's died, ta mutu mun rasa ta itama" Ɗaya yarinyar ta girgiza kai ta dawo kusa dashi ta riƙe shi ta ce "Yaushe Uwa Mamaa zata bayyana? Bana son na mutu kamar yadda Zizi ta rasu, yaushe Mama zata zo?" Yaja idanunsa ya rufe. "Terhemba, kana gani dai kana ji komai dake faruwa?" A hankali ya ce "Mun ta ganin masifa kenan har sai Uwa Mamaa me ɗauke da Tsav ta bayyana a Tajmahar, Mama yaushe za ki zo?" *** "Abbaaa..... Ana ta daddage ta kurma ihun kiran sunan Abbaa, bisa mamakin Innti sai Babban yaya ya fito daga cikin ɗakinsu, yana tafiya a hankali idanunsa zube akan Ana wacce ya ji kiran da take masa yana fusgarsa, a nutse ya mayar da ganinsa kan Innti yana juya ido. Kafin ma ya yi tambaya Yaa Jaheed yace "Daada ya cilla Iftihal a cikin rijiya" wani zaro ido Yaya ya yi waje yana yin baya kamar zai koma ɗaki a guje ya taho ya faɗa cikin rijiyar, daidai lokacin Yaa Sam ya shigo shima cikin shigar bacci, idanunsa bai gama buɗewa ba, ya kalle du ɗaya bayan ya ce "Jaheed meke faruwa ne? Ko jikin Jadid ne?" Jaheed ya kasa magana sai rawar jiki yake yi. "Ai hukuncin bijirewa umarnina da ta yi kenan, tana fitowa kuma zata goma gidan Alhaji Baita. Idan ta yi rai a cikin rijiyar kenan" nan take Yaa Sam ya fahimci abin da yake faruwa, ya saurin leƙa rijiyar baya ganin komai saboda duhu amma yana jin motsin ruwa. Ya runtse idanunsa ya shiga addu'ar Allah Ya sa Iftihal ta fito lafiya, ya san kusancin dake tsakanin zuciyoyi biyu idan Ana ta rasa Iftihal akwai matsala, idan Iftihal ta rasa Ana nan ma wata sabuwar matsala ce. Ana na jikin Innti, da alama tsoron kallon rijiyar ma suke yi, Jaheed da Yaa Sam suna wajan rijiyar suna leƙawa, Daada kuma na tsaye sai surutan iska yake. Yaa Sam na ƙoƙarin cilla igiya a cikin rijiyar sai ga Babban yaya ya fito, goye da Iftihal yana fitowa ya saka hannunsa wajan kunce rigar jikinsa wacce ya yaga ya yi amfani da ita wajan goya Iftihal, da hannu ya yi alamar a bashi tabarma, Jaheed ne ya ɗakko ya shimfiɗa, shi kuma ya kwantar da Iftihal akai, kallo ɗaya ya yi wa Iftihal ya ɗauke kai ya miƙe ya ce yana zuwa kar wanda ya taɓa ta, cikin ɗakinsu ya shiga, Ana kasa biyayya ta yi wa maganar Abbaa ta yi saurin nufar Iftihal ta zauna tare da janyota jikinta ta rungumeta sosai tana sauke wata wahalliyar ajjiyar zuciya. Sanda Yaya ya shiga ɗakinsu ya mance da Jadid ya zube akan ƙafafuwansa, gabaɗaya jijiyoyin dake kwance a goshinsa suka firfito, ya zaro harshensa ya haɗe da haƙoran sama dana ƙasa ya datse su da ƙarfin gaske har sai da ya ji ɗanɗanon jini a bakinsa, gabaɗaya jikinsa rawa da ɓari yake yi, baki yake son ya buɗe ya saki kuka sai ya yi saurin ɗora hannunsa a bakin yana girgiza kai dukkan wata jijiya da Ubangiji yake halitta a jikin mutum sai data jikin Yaya ta bayyana, idanunsa ya zama kamar ba nasa ba, ya yi wani irin ja kamar gaushin wuta, ya kasa zubar da hawaye. Jadid ya ji sautin tashin hankalin da Babban yaya ya shiga, amma ba zai iya motsa ko hannunsa ba shima ɗin. Ana ta sake rungume Iftihal tana sauke ajjiyar zuciya, tana jin wani abu mai kama da relief yana sauka a jikinta sannu a hankali. A hankali ta shiga faɗin "Mahaɗita" "Sannu Mahaɗita, in sha Allah kin bar gidan mutumin nan, idan ya zama dole zani ni" "Kema babu inda za ki, babu wanda ya isa ya sake saka mini ƴa a caca ko waye shi" Cewar Innti tana riƙe hannun Iftihal gam a cikin nata Yaa Sam ya yi wa Iftihal ƙuri da idanu zuciyarsa na bugawa. "Sahibarmu tashi Mahaɗita mu koma ɗaki" Daada dake gefe ya ce "Ba dai ɗaki ba, wannan yarinyar sai ta bar gidan nan yanzu" wani irin ƙasƙantaccen kallo Innti ta yi wa Daada, bata ma da lokacin yi masa raddi. Ta juya kan Iftihal ta ce "Indo,Aysha" Sai taga bata motsa ba. Yaa Jaheed ya ce "Ki danna mata ƙirjinta ko ta sha ruwa a cikin rijiyar ina tunanin haka" Kamar yadda ya ce ɗin, ta saka hannu biyu ta danna ƙirjin Iftihal ta yi har sau uku amma babu ruwan daya zuba daga cikin bakinta ko hancinta. Ƙirjin Innti ya buga ta zubawa fuskar Iftihal idanu, sai taga ta yi mata kyawun da bata taɓa gani ba, fuskarta wasai alamar babu wani tashin hankalin da yake cin zuciyarta, alamar babu wani ciwo ko raɗaɗin da yake damun gangar jikinta. Wani haske fuskar yarinyar ke yi, me ɗauke da annuri. Ta kira sunan Allah a zuciyarta. "Iftihal ɗita, Ayshatuna, Indota... "Sannu Iftin Innti, sannu da jiki" ta ce tana sake riƙota sosai Ana ta ce "Ta farka ne? Ya ba ta yi motsi ba?" Sai ta ɗaga hannun Iftihal tana ɗagawa ya koma inda yake sharaf. "Ta karye a hannu" ta sake faɗin "Hannunta ya karye" da sabon tashin hankali ta faɗi hakan jikinta na rawa ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta. A gigice take girgiza Iftihal tana kiran sunanta. Yaa Sam ya jima da fahimtar abin da yake faruwa, zuciyarsa ta fara rawa na tsananin tausayin Ana ya juya wajan saka hannu yana share hawayen da suka cika masa idanu. Jaheed ko ƙafa ma ya kasa ɗagawa yaja ya cake yana kallon Iftihal kamar zai kira ta amsa masa. Innti ce ta kira Ana tare da faɗin "A'a, bacci take yi kar ki tashe ta kuma ki batta" "Bacci take yi?" Ana ta maimaita sai ta lumshe idanunta da faɗin "To nima zan yi bacci a kusa da ita, Innti nima bacci zan" Babban yaya ne ya fito ya shiga takawa a hankali, fuskarsa babu walwala kamar ya ce ya shiga uku, wayar daya mance da ita a cikin alijuhunsa ita ce take ta haske, alamar shigowar kira Allah Ya sa a silent take, kuma irin wayar nan ce da ruwa baya kassara su. Bai bi ta kan wayar ba, ya janyo wani zani dake saman igiya, yana zuwa ya durƙusa dai-dai in da Iftihal take kwance a cinyar Ana, ya miƙa hannu zai ɗauke ta. Ana ta girgiza kai ta ce "Ka barta a jikina Abbaa" Bai kalli ko fuskar Ana ba, balle idanunta ya sake miƙa hannu zai ɗauki Iftihal da ƙarfi Ta ce "Abbaa..... "Ina jin kamar zuciyata ce kake janye wa, bar ta a jikina don Allah Abbaa bar mini ita" Sannu a hankali ya janye hannunsa ya zubawa waje guda idanu, da sauri kuma ya miƙa hannunsa ya zare Iftihal daga wani irin riƙo da Ana ɗin ta yi mata, ganin tana shirin bin Iftihal ya saka Yaa Sam ya yi saurin riƙe ta suka shiga kokawa zata ƙwace. Yaya ya kwantar da Iftihal saman tabarma, ya shiga yin addu'a a hannunsa ya tofa a tafin hannunsa ya shafi idanun Iftihal zuwa fuskarta, ya yi ƙasa da kan shi ya sumbaci goshinta, ya riƙe hannunta sosai kamar kar ya cika alamar ban kwana, ya jima cikin wannan yanayin, ya sake sumbatar goshinta daidai nan hawayen daya cika idanunsa ya sakko a saman fuskarta, a hankali ya ja zanin ya lulluɓe ta gabaɗaya. "To me ya sa kake rufe ta haka Yaya?" Jaheed ya ce yana girgiza kai domin shima bai fahimci abin da yake faruwa ba. Ana ta ce "Ya ce bacci take yi, Innti ma ta ce bacci take yi, nima zan kwanta ka rufe ni Abbaa" ta sake yunƙurin ƙwacewa daga hannun Yaa Sam. Miƙewa Innti ta yi ta matsa kusa da Babban yaya ta ce "Meke faruwa?" "Allah Ya yi mata rahama...., Sai Babban yaya ya kasa ƙarasawa ya miƙe gently yana ɗan ja baya ya nufi inda Yaa Sam yake a hankali ta wata laushin murya me cike da kasala, kwarjini da haiba ya ce "Allah Ya ji ƙan Ayshatul-Iftihal" Dam! Ƙirjin Innti ya buga da ƙarfi ta ce "Ta rasu ne Muraad? Na rasa Iftihal?" Ya jinjina mata kai a hankali. Cak Ana ta tsaya daga kokawar ƙwace kanta da take yi, ta ƙurawa gawar Iftihal idanu, bata ko blinking eyes ɗinta, ta san mutuwa tabbas, ta san yadda mutane suke faɗar raɗaɗin mutuwa, kuma ta san idan an mutu ba'a taɓa dawowa, mutuwa ɗaya ce, tafarkinta yana da yawan gaske, ita dai wannan mutuwar me raba uwa da ɗanta tun yana ciki, wannan mutuwar me ɗauke uwa ta bar jariri a cikin jini, wannan mutuwar mai ɗauke miji ta bar mata da ƴaƴa, wannan mutuwar me ɗauke uwa ta bar yaranta cikin maraici da kewa ta mahaifiya, ita ce me raba soyayya da iyakance jin dadi lokaci guda, ita ce me saka mikin da baya taɓa gogewa sai ya yin da naka lokacin ya yi, ita dai-dai wannan mutuwar me raba masoya, me raba mutum da arziƙinsa na duniya. Irin wannan mutuwar Mahaɗinta ta yi? To a cikin rijiyar ta rasu a cikin ruwa data kasa shaƙar numfashi? Ko kuma wani abu ne ya daki kanta a lokacin da Daada ya cilla ta rijiyar? Ita wanne irin bacci ne me nauyi ya ɗauke ta wanda bata taɓa yin irinsa ba har ya cilla mata rayuwarta a cikin rijiya? Ina Abbaa yake a lokacin, Innti me take a lokacin? Ta yi wata iriyar shaƙuwa ta zubawa ƙawar Iftihal, ita sam bata yadda gawa bace ba. That's meana Daada ya kashe mata mahaɗinta kenan? Ya raba su? Ita tana duniya ita kuma zata tafi lahira? Me ya sa Iftihal za ta yi mata haka? Duk soyayyar da take yi mata? Da ƙaunar da take nuna mata? Ta ɗauka ita da kanta mutuwa za ta yi mata halacci da alkunya wajan ɗauke idanunta daga kan danginta more especially Mahaɗinta? Ta ina zata fara rayuwa without her? Without Iftihal, itama mutuwa za ta yi. Da ƙyar ta juya kanta ta zubawa Daada idanu, gabaɗaya ƙwayar idanunta ta jirkice ta shiga bin da Daada da kallon da ita kanta bata san dalili ba. Sai ta yi murmushi ta ce "Yaa Sam" "Uhm" kawai ya iya cewa. Tana ta murmushi ta ce "Ka cikani ganinta kawai zan yi na tabbatar ta rasu ɗin ka ji?" Yaa Sam yaƙi sakinta, Abbaa ne ya miƙo mata hannunsa, ganin hakan ya saka Yaa Sam sakinta kamar wacce ƙwai ya fashewa a haka take takawa, tsoron ganin abin da zuciyarta ta kasa ɗauka shine ya hanata yin sauri. Tana zuwa ta durƙusa a gaban gawar Iftihal ta miƙa hannunta wajan yaye fuskarta, ta zuba mata idanunta na wani lokaci. Ta juya ta kalli Babban yaya ta ce "I told Iftihal ai, sai Daada ya zama ajalinta, sai ya rabata da duniya, sai takaicin Daada da mugun halinsa ya kai ta zuwa lahira. Now..," sai ta yi murmushi tana shafo fuskar Iftihal da hannunta. "Abbaa..." Ta kira sunan Babban yaya ya matsa ya ɗora hannunsa a kafaɗarta ta ce "Mijin Innti ya kashe mini wacce muka fito ciki ɗaya da ita, muka zauna a mahaifa ɗaya ita, muka fito duniya a rana ɗaya, Mijin Innti ya rabani da ƴar'uwata, ƙawata, aminiyyata, abokiyar faɗa da wasana. Abbaa ya zan yi?" Ta sake shafo fuskar Iftihal ta ce "Ina so na mutu nima Abbaa ina son na bi mahaɗita, ina son na je inda Anum da Jarumi suke, ina son na je inda Iftihal zata tafi yanzu Abbaa" Innti ji ta yi surutan Ana suna dukan tsakiyar kanta, kamar ana mata shocking a cikin ƙwaƙwalwarta haka take ji, kanta ya yi mata nauyi ta saka hannu ta dafe ƙirjinta. As a mother, ya kamata ta ji baƙinciki, ta kuma zubar da hawaye na rashin Iftihal, madadin hakan wani abu me nauyi da girma da ciwo ta ji ya tsaya mata a ƙirjinta ya danne mata zuciya. Ana ta girgiza kai "Abbaa kar ka binne mini Mahaɗita, ni ina son ganinta haka nan, zan zauna da ita" Shifa ko motsi yaya kamar an yi masa dolen yi ni ne, da ƙyar ya iya matsawa kusa da Ana sosai ya ɗora bakinsa a kunnenta yana dafa kanta ya ce "Shetty" a hankali ta ce "Abbaa" "Pray for her" ya ce silently. "To Abbaa" ta kalli Iftihal sai ta ce "To me zan ce? Mece addu'ar? Ya ake yi?" Yaa Sam ya ce "Anything, ki yi mata" Bata kalli Yaa Sam ba idanunta akan fuskar Abbaa gabaɗaya ya ɗora goshinsa a saman nata ya riƙe kanta. "Ni ban iya ba" Da ƙarfi kuma ta ce "Allah Ya ji ƙan ki Mahaɗita, Allah Ya yi miki gafara, Ubangiji Ya saka miki tun a nan duniya, Ubangiji Ya duba kawaici da haƙurinki, yadda kika so mijin Innti ina addu'ar Ubangiji Ya hana shi sukuni da soyayyarki bayan bakya duniya" a hankali ta miƙe tsaye tana murmushi Babban yaya ya miƙe ta yi saurin riƙe hannunsa ta ce "Abbaa ina jin tsoro sosai" Gam ya riƙe hannunta sai ta fara gani dishi-dishi ta miƙa hannunta ta shafo fuskar Babban yaya da take ganinta a wata suffa ta daban a hankali ta ce "Waye kai? Ina Abbaa?" Ta runtse idanunta, Babban yaya da yake riƙe da ita ya shafi fuskarsa sai ya ji suffar da baya so a san da ita, ita ce ta bayyana a idanun Ana. Ana ƙoƙarin sake buɗe idanu take ta kalli mutumin amma ta kasa. "Abbaa kana ina, bana gani, nima mutuwa zan yi zan bi mahaɗita Abbaa" faɗawa jikin Babban yaya ta yi dai-dai lokacin da numfashinta yake tsayawa a ƙirji, tana faɗowa jikinsa ya haɗe hannunsa biyu ya rungumeta ya ɗora fuskarsa a wuyanta domin baya son kowa yaga yanayinsa. Da wata kamilalliyar murya ya ce "I'm sorry Mamaaa... Daidai nan Jaheed ya yake jiki shima ya faɗi babu numfashi zuciyarsa ta kasa ɗaukan mutuwar masoyiyarsa. *** BIYA. Taron jama'a ne masu ɗauke da jajayen kaya sama da mutane ashirin a ƙarƙashin bishiya cikin tsakiyar daren, layi bayan layi ake binsu da jini ana basu umarnin sha, ko da aka zo kanta ta zubawa jinin idanu ta yi kamar ba zata amsa ba. Sai kuma ta amsa ta shanye, suna gama sha suka hau kan wata dabba kamar jirgi ta tashi dasu zuwa sama. A firgice ta farka daga madadin da take yi, lokacin ana ta kiran sallar Asuba ne. Hindatu ta yi shiru tana zabga uban tagumi da tuna mafarkin, wannan shine karo na uku tana mafarki, na farko ta yi mafarki an bata ɗanyen nama kyauta aka ce ta ci, kuma ta cinye, na biyu ta yi mafarki tana ɗaure rago da akuya. Yau kuma mafarkin shan jini ta yi. Abin duniya ya addabi Hindatu ta rasa wa zata faɗawa, da Gana kawai suke kirki a unguwar. Har gari ya yi haske tana zaune. "Hinde, yau an ɗauke miki sallah ne?" Da raunin murya ta ce "A'a malam" "Sai ki fito kar mukutarinta ya shige ko?" Ta miƙe tana saka hijabi ta fito, wani ihu ta kurma sanda ta yi arba da kayan cikin Malam a sarari, da jinin da yake gudana a jikinsa. Ta dafe ƙirji tare da rarraba idanu. Malam ya ce "Lafiya kike wannan ihun?" Hindatu ta kasa magana kamar zata zauce ganin yadda kayan cikin Malam ke ta motsi, a guje ta juya zuwa ɗaki tana rufe idanunta. *** BAFFAS ESTATE. 9:00 na safe. Baffas estate ya yi shiru baka jin motsin komai da kowa, tun bayan dawowar Sayyadi Baffa, tun daga kan ma'aikatan gidan zuwa jami'an tsaro, da jama'ar gidan kowa cikin taka tsantsan yake yi, sun jaddada komai na abin da zai iya zamewar su matsala a gidan. Hidaya ce ta kalli Diynaah wacce take sakawa Nadiyaah maganin ciwon idanu ta ce "Mamy ta ce an saka ranar auren Ukhty Azizah da Baffa, wai za'ayi musu aure tare" Cak Diyanaah ta tsaya daga abin da take yi, Nadiyaah ma Idanunta da ya yi jaa ta watsa akan Hidaya kafin ta ce "Waya ya tsara haka?" Hidaya ta ce "Mamy tace Abba Malami ne, wai dole Baffa ya yi aure wai kuma ya auri Azizah" "Ya Rabbi!" Cewar Diyanaah. Nadiyaah ta yi ƙasa da kanta hawaye ya cika idanunta jikinta ya shiga rawa ta kalli Diyanaah ta ce "Baffaa am zai yi aure?" "Shikenan Baffa zai yi aure mu dinga jin kunya a cikin abokanmu a dinga cewa Baffa ya yi aure? Kuma sai a haifa mana ɗan ƙani?" Diyanaah itama fashewa ta yi da kuka sosai suka haɗu waje guda suka dinga kuka, nan da nan jikin Nadiyaah ya ɗauki wani irin zafin zazzaɓi daman kwana biyu ba lafiya ce da ita ba, da sauri Diynaah ta ɗauki wayarta ta nemo number Baffa data saka masa Baffa am. Ta dinga kira baya ɗauka a kira na uku ta ji ya ɗauka ya yi shiru na ce wani lokaci. "Baffa am" ta kira sunansa da soyayya me ƙarfi dake huda zuciyarta ta ce "Nadiyaah babu lafiya Baffa..," Ƙit ya kashe wayar bai bari ta ƙarasa faɗa ba. Ta kwantar da Nadiyaah. Ta ce "Ukhty ki narke sosai, ki ce wa Baffa bakya son auren za ki mutu muddin ya ce zai yi aure kin ji" Diyanaah ta fi Nadiyaah wayo sosai, kamar yadda Diyanaah ta ɗakko sunan mahafiyarta, haka Nadiyaah ta ɗakko sanyin halin mahafiyarta, kamar yaran ɗaya sak. Tun kafin ya shigo suka ji alamar zuwan nasa ta ƙamshin da yake sanar dasu, jin hakan ya saka Nadiyaah rufe idanunta, ta ƙofar daya saka aka yi tsakanin shashinsa dana yaran nasa ya shigo, kyakkywar farar Jallabiya ce a jikinsa, fara sol da ita babu zanen komai a jikinta, sai wani sassanyan ƙamshi na musamman daya cika ɗakin tun sako ƙafarsa da ya yi zuwa ciki, jerarrun yatsun ƙafarsa Diynaah ta fara sauke idanunta akai, taja numfashi ta sauke, zata buɗe murya a ko'ina ta nuna wannan bawan Allan ta ce shi ne mahafinta farincikinta, irin uban da ake taƙama dashi da kuma tutiya. Asalin fatar Baffa ba zaka iya tantance ta turawa ce ko Larabawa ba, jin Nadiyaah babu lafiya ya saka ko rawanin da yake sakawa a kan shi bai samu dama ba, kan shi babu komai ya shigo cikin bedroom ɗin bayan ya samu izinin shigowa daga bakin Diyanaah. Sumar ƙan shi baƙa ce sosai, a cuccure take ta yi gado gado ta murmuɗe ta saka har ƙasan wuyansa, wata tayo gaban goshinsa, akwai ratsin jaa a sumar gaban goshinta. Baffa a tsaye yake sosai a saman ƙafafuwansa, cike da kuzari, izza, mazantaka taƙama da ilimin addinin da yake dashi, uwa uba kwarjini, haiba da salon nasa ra'ayin, har wani yellow yellow fuskarta take yi tsabar haske kyau wajan Sayyadi Baffa ba'a magana, duk kyan da yaransa suke dashi ko kwatan nasa basu ɗauka ba. Ya yi tsaye hannunsa ɗaya riƙe da ƙaramin carbi, ɗaya hannunsa yana zagaye a bayansa ya zubawa Nadiyaah idanunsa. "Barka da shigowa Yaa Baffa" Cewar Diyanaah tana yin ƙasa da kanta. Ya juya launin ƙwayar idanunsa a kanta da wata kalar nutsuwa da yanayin da yake nuna magana kai tsaye yake mata da "Kar ki sake ɗora photo a Social media Diyanaah Sayyadi Baffa" cikin sauri ta ce "In sha Allah Baffa" A jikinsa ya ji zai wahala ciwon idanun Nadiyaah idan ba Kambun baka bane. Ya ƙarasa ya zaune kusa da ita, jikinta zafi sosai don haka ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata. Nadiyaah ta girgiza kai ta ce "Baffa am, don Allah Baffa kar ka yi aure, idan ka yi aure zan iya mutuwa, za'ayi mana dariya ace mahafinmu ya yi aure, kuma har a yi mana ƙani" jin abin da ta ce ya saka su waro idanu sai kuma yaja idanuna ya lumshe, kishin mahaifiyarsu suke yi wacce bata raye ma. Diyanaah ta ce "E, Baffa. We're 17 years fa, ai tun muna ƙanana za ka yi aure ba yanzu ba, kuma duk wacce ka aura zata rabamu da kai. Muna son ka Baffa don kar ka yi aure" Ta zame zuwa ƙasa cikin sauri ma Nadiyaah ta sakko suka jeru a gaban Sayyadi Baffa. Da wani irin kuka me narkar da zuciyarsa suka ce "Kuma muma idan mukai aure, matarka tana haihuwa mu muna yi? Ka tausaya mana Baffa,bama som ka auri kowa" Diyanaah ta ce "Ukhty ba kin ce ana aure a aljanna ba, kinga sai Baffa ya yi aure da Ammie a can aljanna ko? Please Baffa" Kuka suke yi sosai, gani suke babban tozarci ne ace mahafinsu ya yi aure a age ɗinsa, Shugaban Hisba da kan shi, shi da yake gujewa mu'amala da mata baya saka so a tsarin rayuwarsa, duk wata mace Garzali ce a idanunsa. Ya dubi yadda suke kukan kamar za su rasa rai. Ya miƙe a nutse ya riƙo hannayensu, a hankali ya sumbaci kumatun kowacce kafin ya juya ya bar ɗakin nasu. Sanda ya fito direct babban parlornsa ya nufa saboda tun jiya yake ganin shigowar saƙon Mu'allim, sai ya bashi izinin zuwa, yana shiga yaga Mu'allim tare da Liman zaune, jin zuwan Sayyadi Baffa ya saka su miƙewa tsaye kan su a ƙasa? "Barka da zuwa" Suka ce a tare, ba tare daya kalle su ba ya nemi waje ya zauna. Shiru shiru babu wanda ya yi magana, a hankali ya ɗaga kai ya kalle su, ya juya ya kalli Liman a nutse Gaban Mu'allim sai faɗuwa yake yi, ya ɗan zunguro Liman "Liman Please, ka faɗa masa" Liman ya kalli Mu'allim sai bai ce komai ba. Baffa ya harɗe ƙafa idan ya kalli wannan sai ya kalli wannan. A nutse ya miƙe zai fice. Mu'allim ya ce "Na samu matar aure ne Baffa, a unguwar Kankarofi, sunanta Aysha......," ya ɗauke labarin komai har abin da Babban yaya ya ce ya faɗawa Baffa ya ɗora da "Baffa Please, ko dan ciro yarinyar daga faɗawa wani hali ka amince na aure ta, wallahi ina son ta da gaske. Amma idan ka ce a'a shikenan" Baffa ya yi shiru bai ce komai. Liman ya ce "Ka taimaka Baffa" Ya juya ya kalli Liman, juyawa ya yi sai da ya je bakin ƙofa ya yi musu yanayin da yake nufin "Ka shirya mota ina fitowa yanzu" wata ajjiyar zuciya Al'ameen ya sauke cikin sauri ya rungume Liman yana faɗin "Finally.... Allahamdulillah!" "Congratulations" "Thank you Akhy Asad Hafiz Hafiz Baffa Jazakalla bil khair" Cikin ƙaramin lokaci Malami ya zo da sauran ƴan'uwa. Liman ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda domin har dashi za'a je ɗaurin auren na Mu'allim. Sanda ya fito Hajiya Umaimah ta ce "Zai wahala idan matar Asad ƴar arziƙi ce, kina ganin Baffa yaƙi zuwa neman auren Liman gashi zai je na Mu'allim. Kuma ka tabbata ka biya ta gidansu yarinyar ka kawo mini ita, tunda wancan zuwan bana nan tazo" shi dai bai ce komai ba ya fice. Malami ya shigo yana faɗin. "To yanzu ya ce baikon ma an warware baya son auren, when he's ready zai yi magana, bai duba cewa Azizah ƙanwar Hajiya Umaimah bace ba, kalli abin da ya yi" Hajiya Umaimah ta ce "Malami me nake ji kana faɗa ne haka?" Yana gyara babbar rigarsa ya ce "Baffa ya fasa auren Azizah an warware baikon" Kafin ta yi magana Al'ameen ya shigo cikin farar shadda me ɗauke da babbar riga da hula kana ganinsa kaga ango ya ce "Baffa ya fito, baya jira kun san dai ko?" Yana faɗin hakan ya fice. Asad ma ya yi waje abinsa. Wata baƙar mota Baffa ya shiga me duhun glasses shi ɗaya a Baya sai Al'ameen matsayin driver, Malami da sauran suka shiga motar Asad ya shiga yaja. Suka nufi Kankarofi. Sanda suka isa suka tarar da unguwar a cike da jama'a, Al'ameen ya sake jin daɗi wato ma an san da zuwan nasu gashi an yi taron ɗaurin aure. Liman ya fito yana ɗan duba lokaci domin yau suna da taron ƙarshen shekara na ƴan jarida. "Ina ne gidan"? Al'ameen ya ce "Gashi.....," bai ƙarasa faɗa ba yaga an fito da makara Babban yaya ne a gaba shi da Yaa Sam suna riƙe da Gawar Iftihal. *H I Y A A M* Page 15: She ran away Bright pens Yota/001 I dedicated to her. Pixie ceo NAZY's KITCHEN. Liman ma sak ya yi ganin an fito da makara da gawa a ciki daga gidan da Mu'allim yazo neman aure, ya yi baya kaɗan yana ƙoƙarin basu waje cikin sauri jikinsa na matuƙar rawa da ɓari Mu'allim ya tari gaban Babban yaya da Yaa Sam, ya kasa magana sai kallon makarar yake a zauce yana riƙe kan shi. Yaa Sam ne ya samu ƙwarin gwiwar kallon Mu'allim a hankali ya ce "Lafiya dai ko?" "No, aa". Shine kawai abin da Mu'allim ya iya furtawa. Liman na tsaye yana kallon su. "Mene ya faru?" "Sunana Al'ameen Hafizz Hafizz Baffa, ni ne wanda ya nemi auren Iftihal a wajan yayanta Muraad, kuma ya bani izinin zuwa da iyayena domin ɗaura auren a yau ɗin duka" da ƙyar yake haɗe laɓɓansa wajan yin maganar, tsoro yake ji sosai, ba tsoron mutuwa yake yi ba, tunda ya san raɗaɗi da ɗacinta, ya san yadda take saka kaɗaici da mayar da mutum maraya abin tausayi. Ya rasa mahaifinsa Hafizz Hafizz Baffa, yana jin duk wani rashi da za'ayi wa mutum a bayan ta iyaye take. Bai sani ba, amma ya samu kan shi da tsakanin tsoron abin da zuciyarsa ke raya masa, da fargabar jin wanda yake cikin makara ɗin. Yaa Sam ya juya kaɗan. Tsakanin Yaa Sam da Babban yaya aka rasa mai tankawa Mu'allim maganarsa sbd tsoro. "Yawwa, na ce zan iya wa Baffa magana?" "Allah Ya wa Iftihal rasuwa jiya da daddare" "What!" Mu'allim ya ce da ƙarfin gaske. Hakan ya janyo hankalin Malami da yake jingine a jikin mota, shima yana mamakin cikar da aka yi a unguwar ta Kankarofi ɗin. Jin sautin muryar Mu'allim ya saka Malami ƙarasawa wajan ya kalle su ya ce "Menene?" "Abba, wai cewa sukai ta rasu" Ya runtse idanunta numfashinsa na kakkatse masa a ƙirji ya ce "I couldn't believe, wai ce mini sukai ta rasu, wai ta mutu, ko dan kar su bani aurenta ne? Ko ban cancanci zama mijinta bane? Ko ina da wani aibu ko mummunan hali ne Abba?" Abba Malami ya riƙo Mu'allim, Liman ya ƙarasu yana dafe kafaɗar Mu'allim ya ce "Please Al'ameen, ka nutsu" "Ahky Liman ya zan nutsu? Jiya nina kawo Iftihal gidan nan da kaina, kuma yau sai ace ta rasu? Ai data rasu da na ji hakan a jikina da kuma zuciyata. Aurenta ne kawai basa son bani. Me ya sa ba ku faɗa musu ni jinin Hafiz Baffa ne, ni ɗaya daga cikin zuri'ar Sayyadi Baffa bane, bani da mugun hali" idanunsa ya yi jajur jikinsa na rawa, Liman ya saka hannunsa ya riƙo shi sosai da ƙoƙarin janye shi domin ya basu waje a yi mata sallar Jana'iza kamar yadda addini ya tanadar. Abba Malami ya kalli Mu'allim ya ce "Dawa kukai magana a jiya ɗin Al'ameen?" Ya nuna Babban yaya ya ce "Yayanta" Abba Malami ya kalli Yaya ya ce "Bawan Allah mene gaskiyar magana? Yarinyar da Al'ameen ya kawo mu domin nema masa aurenta ne ta rasu ko wata ce a cikin gidan daban?" Kallon su kawai Babban yaya yake yi, zuciyarsa ta masa nauyi laɓɓansa sun bushe. Da wani irin yanayi kuma ya ce "Eh" "Ina nufin da gaske ta rasu jiya da daddare" "Mene ya same ta? Jinya ta yi?" Yaa Sam ya ce "Tana da mutanen ɓoye ne, ta fito zata banɗaki shine suka tashi ta faɗa cikin rijiya, sanda aka shiga ceto ta, already ta rasu a cikin rijiyar, ka yi haƙuri, tunda har yayanta ya amince da auren to kamala da mutumcinka ya kai har ya yi yawa, ai babu wanda bai san sunan Baffas family ba" "Abba ban yadda ta rasu ba, ba Iftihal bace ta rasu. Don Allah Yaa Muraad ka bani auren Iftihal, wallahi ina son ta zan kula da ita sosai" Babban yaya baya buƙatar sabon tashin hankali da hayaniya, duk abin da zai saka ya yi magana a yanzu baya buƙata, a birkice yake jin kan shi sosai. Ya juya kaɗan ya kalli Yaa Sam ya kalli Jaheed dake baya yana riƙe da hannun makarar sai mahaifin Haysaam. "Ku ajjiye makarar ya gani" sannu a hankali suka sauke makarar a ƙasa, jikin Mu'allim na rawa ya durƙushe a wajan da farar shaddarsa ta angwanci, ya miƙa hannunsa kaɗan ya yaye likkafanin. Kyakkyawar fuskarta me cike da annuri ce ta fara yi masa sallama a cikin idanunsa. Ita ɗin ce dai, yarinyar da zuciyarsa ta so a lokaci guda, son da yake jin ba zai sake samun wacce zai yi wa irinsa ba. A hankali ya ja idanunsa ya lumshe, da tunanin mafarki ne, da tunanin zai farka ya ji shelar an ɗaura musu aure, da tunanin zai farka ya ji ta amsa sunan Mrs Al'ameen Hafizz Baffa. Ya buɗe idanun da ƙyar da nauyin zuciya ya ce "Allah Ya yi miki rahama Aysha, Allah Ya ji ƙan ki, Ubangiji Ya sa mutuwa hutu ce a gare ki, Allah Ya haskaka miki makwancinki" Luu idanunsa suka fara lumshe. Liman dake tsaye shima yana kallon fuskar yarinyar domin tabbas ita ya gani sanda suka zo shi da Ahlam gidan. "Take heart" Ya ce yana ɗan bubbuga kafaɗarsa. Ya ja likkafanin ya rufe mata fuska, Liman ya ɗago shi tsaye yana miƙawa ya faɗa jikin Liman shi kuma ya yi saurin rungume shi cike da soyayya yana bubbuga bayansa. Abba Malami ya juya zuwa motar da Sayyadi Baffa yake ciki, ya yi knocking ya ɗauki wajan 10 seconds a tsaye kafin a sauke glasses ɗin ƙasa, yana kishingiɗe a bayan motar idanunsa rufe, farar shadda ce a jikinsa, ya zagaya scarf a samanta wanda ya sake fito da martabarsa ta kasancewarsa shugaban Hisba, malamin addinin Islama, me zuwa yaɗa Musulunci gari-gari, ƙasa ƙasa yana yin da'awa. Kamar kodayaushe ya yi rawani a fuskarsa, hatta idanunsa ya saka su cikin glasses ba zaka taɓa sanin wanene ba, hannunsa riƙe da ƙaramin littafi yana dubawa, ɗaya hannun ƙaramar counter ce yana tasbihi da ita. Luf luf haka gargasa ta lulluɓe farar fatar hannunsa, ba zaka taɓa kallon Sayyadi Baffa ba ka ɗauka ya yi shekarun da suke jingine da rayuwarsa, jikinsa gabaɗaya bai nuna shekarun ba. Ba kuma zaka taɓa yadda ya haifi tagwayen yara mata masu shekaru har sha bakwai ba. Abba Malami ya yi ƙasa muryarsa ya ce "Yarinyar da aka zo nemawa Al'ameen aurenta Allah Ya yi mata rasuwa, yanzu haka Jana'izarta za'ayi ba, shine ka ga taron jama'a" A nutse ya juya kamar zai kalli Malami sai ya fasa, ya ajjiye azkar ɗin hannunsa bai ce komai ba ya ɗauke kai. Abba Malami ya juya zuwa inda aka ajjiye gawar za'ayi Jana'iza, jama'a duk an hau jam'i ana jiran liman, Mu'allim da Liman suna sawun gaba. Malami ya san Baffa ba zai taɓa fitowa ba. Bisa mamaki sai ya ji saukar kamilalliyar muryarsa me cike da kamala da zallar kwarjini ta sauka a kunnen ɗaruruwar jama'ar da suka samu jana'izar Iftihal. A kabbarar da ya yi ta farko wajan ya yi tsit, muryar Sayyadi Baffa na dukan kunnawansu suka samu kan su da yin wata sabuwar nutsuwa bayan wacce suke ciki. Shi da kan shi ya yi wa Iftihal sallah, kuma ya sunkuya aka ɗauki makara dashi aka saka a mota, ya koma cikin motarsa. Babu wanda ya san waye shi, amma muryarsa na tunawa jama'a da babban malamin nan. Wato Sayyadi Baffa. Sai suka yi tunanin ko wani ne yake kwaikwayon Sayyadi Baffa ɗin. Bayan an kai Iftihal, Baffa ya buƙaci a kira masa mahafiyarta zai mata gaisuwa. Babban yaya ya shiga gidan yaga taron jama'a sosai, daman Jadid na asibiti duk da likitocin sun ƙi taɓa shi sai an kawo kuɗi, Ana kuma tunda ta yanke jiki ta faɗi a jikin Babban yaya har yanzu bata farko ba, tana ɗakin su Babban yaya a kwance ita kaɗai. Innti da kanta ta buƙaci kar a tonawa Daada asiri, duk wanda ya ce shi ne ya cilla Iftihal a cikin rijiya bata yafe ba. Tunda ta yi wannan furucin ko tarinta ba'a sake ji ba, bata ko motsi idanunta rufe zuciyarta ta yi mata wani irin nauyi a cikin ƙirjinta, tunaninta ya rarrabu, ga rashin Iftihal, ga halin da Ana take ciki ga tunanin inda zata samo kuɗin da za'ayi wa Jadid wankin ƙoda, Babban yaya ya buga ko'ina rancan kuɗi ba'a samu ba. Haka Jaheed bashi komai, Yaa Sam ma babu kuɗin a hannunsa wannan ya zama babban dalilin daya saka Innti cewa bata zaman makoki, har wasu suka fara ɗan zancen wai babi abin da za'a bawa masu zaman makokin ne na abincin ci da sadaƙa. Babban yaya ya ƙarasa kusa da ita dab da kunnenta hankali ya ce "Za'a yi miki ta'aziya" Ta juya ta kalle shi sai ta ce "A ina ne?" Da yatsarsa ɗaya ya yi mata nuni da waje. "Maman Haysaam ina zuwa" "A'a babu komai ai" Tare suka jera kamar ƙawaye ita da Yaya yana riƙe da hannunta, jikinta sanye da hijabi kanta a ƙasa, domin bata yadda ta ɗago kai ba. Ta ja ta tsaya kaɗan sai ya ce "Yana cikin mota, babban mutum ne shi" ta ɗaga idanunta ta kalli Yaya kamar za ta yi magana kuma ta fasa, ta ƙarasa jikin motar kanta a ƙasa. Abba Malami ne ya fara yi mata ta'aziya ta jinjina masa kai kawai tana ɗora hannu a ƙirjinta. Mu'allim da yake kwance a jikin Liman ya ɗago da ƙyar ya ce "Ya ƙarim haƙurin Iftihal? Ubangiji Allah Ya yi mata rahama ya kyauta makwancinta" Shima ta jinjin masa kai alamar ta gode. Za ta juya kenan, daga cikin motar ta ji kamilalliyar muryarsa me cike da nutsuwa da haiba da wani zallar kwarjini ya ce "Rabbi rahamhuma" ya ɗora da faɗin; إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ، أَعْظَمَ اللَّهُ أَجْرَكُمْ، وَأَحْسَنَ عَزَاءَكُمْ، وَغَفَرَ لِمَيِّتِكُمْ، وَأَلْهَمَكُمُ الصَّبْرَ وَالسُّلْوَانَ. Ma'ana: "Lalle mu na Allah ne kuma gare Shi za mu koma. Allah Ya ƙara muku lada, Ya kyautata ta'aziyyarku, Ya gafarta wa mamacinku, kuma Ya ba ku haƙuri da juriyar wannan rashi" a hankali ta ɗago ta kalle shi, sai taga hankalinsa yana kan azkar ɗin hannunsa, ba zata iya magana ba, ko yaya ta buɗe baki sai ta ji kamar zuciyarta ce zata fito waje, sai ta jinjina kai ta juya. "Ga wannan ayi sadaƙa, wataƙila ba za mu samu damar dawowa ba" ta dubi kuɗin, sam ba ta yi niyyar amsa ba, amma data tuna ciwon Jadid sai ta saka hannu biyu ta amsa ta nufin cikin giani. Daada yana ganin abin da yake faruwa da kuɗin da aka bawa Innti ya yi zumbur ya miƙe ya nufi cikin gidan, kamar zai kifa saboda saurin da yake. *** Abba Malami ne ya amshi driving ɗin, saboda Mu'allim har yanzu baya cikin hayyacinsa tun bayan suman da ya yi a can maƙabarta sanda ake saka Iftihal a gidanta na gaskiya. Liman yana buƙatar zuwa wajan Ahlam domin ya yi mata text akan zashi, a kuma yau za'ayi Annual Media Excellence Awards 2025. Ban da an ɗan jirkinta da tuni an yi ɗin. Yana buƙatar ya tafi tare da ita. 2:05 ya ƙarasu unguwar Kurmi a hankali ya yi parking da motarsa a harabar gidan Engineer Abdullah Kurmi, ya jima yana kallon wajan kafin ya ɗauki wayarsa ya yi masa text na zuwan nasa. Sai da ya shafe minti wajan goma ta fito tana cika tana batsewa, fuskarta babu walwala ko kaɗan, a hakan ma sai da Anty Jiddah ta ce zata haɗata da Engineer sannan ta saka wani dakakken lace wanda Engineer ya yi mata da kansa, ta yafa mayafin da ya yi dai-dai da lace ɗin, abinka da Kanuriya wani irin sassanyan ƙamshi me sanya nutsuwa ne yake tashi a jikinta. Tun kafin ta ƙarasu ya zubawa fuskarta idanu yana kallon dukkan wani moving da jikinta yake yi, a hankali yaja idanunsa ya lumshe zuciyarsa na buɗewa da tsananin ƙaunarta me girma. "Rest of my life.... Ya furta a ƙasan zuciyarsa. "My beloved wify" ya ce sanda take buɗe murfin motar ta shiga ta zauna kanta a ƙasa, ta shiga wasa da fingers ɗin hannunta, gabanta na faɗuwa. Ya miƙa hannunsa ya riƙo nata ya ɗora a cinyarsa da rashin kuzarin jiki ya ce "Do you want me to greet you?" A kumbure ta ce "Ina yini Liman?" "What!" Ya ce yana bubbuɗe idanunsa, don mai tsammaci ko da wasa ta ji sunan ba. "Say it again" Ahlam ta yi masa banza. Ya murza tsakiya tafin hannunta ya ce. "Say it again, again again and again" Wani irin takaici ke kama Ahlam kamar ta daddage ta ƙunduma masa ashar haka take ji a ranta, duk irin rashin mutuncin daya dinga yi mata? Da wulakanci kala-kala? Shine zai zo yana mata wani abu kamar wani ɗan iska ko wanda ya sha wata ƙwaya ta daban? Me ya sa sometimes maza masu data ido ne? Most of them akan mace? Ta yi ƙwafa kawai tana share shi. Ya ɗan matsa hannunta da yake cikin nasa kaɗan yana matsar da fuskarsa dab da tata, kwantaccen sajensa ya shafi gefen fuskarta. Yar yar haka ta ji tsigar jikinta yana tashi. "Ɗan is.....," Saurin saka hannu ta yi wajan rufe bakinta, saboda subucewa da kalmar ta yi a bakinta. Md ya jinjina kai ya ce "Ɗan iska" "To kai ma ba ce mini kake ƴar iska ba, kullum kana aibata ni da hattarata a cikin jama'a, kana mini kallon mara kamun kai ni da Anee..," bai bari ta ƙarasa faɗar sunan Anees ba ya yi saurin ɗora yatsarsa a bakinta ya ce "quiet" ta tura masa bakin. "To mene tsakaninki dashi da har kike kiran shi in the middle of the night? Haka daman kike? Kiran wani ƙatoto a tsakiyar dare eh?" Ta murguɗa masa baki ta ce. "Abin da yake tsananinka da Yussy, shine yake tsakanina da Anees da kake magana" Ya yi poiting ɗin kan shi da yatsa ya ce "Kike haɗani da ƴar iskar nan?" Ahlam ta waro ido, ta ce "Oh! Ƴar iska ce?" A daƙile ya ce "Halimatu!" Yanayin kiran da ya yi mata ya saka ta shiga hayyacinta sai kuma ta fashe da kuka tana ɗora kanta a cinya ta ce "Haka kawai kamar wata wacce ta rasa saurayi sai ka sallaɓo kamar ɓarawo ka nemi aurena, without my knowledge, ina na taɓa jin wannan gadara da ikon? Ina kuma aka taɓa yin haka? Bayan kowa ya san ka tsane ni baka so na, wulaƙantani kake saboda kaga ni marainiyya ce kuma ina da naƙasa, komai a Bright Fm sai ace ban iya ba sai Yussy, duk ƙoƙarina, haka ina ji ina gani ake cire sunana a saka na Yussy duk don na haɗiye zuciya na mutu kuma burinku bai cika ba" ta sake sautin kukan jikinta duka rawa yake yi. "Har da cewa wai Anees ya ɗauke ni ya kai ni hotel, ko ka ɗauka alaƙar dake tsakaninka da Yussy ita ce muke yi da Anees? Anees kawai yana taimakona a aiki ne, yana fahimtata da bani shawara. Me na yi maka haka da zafi har kazo ka nemi aurena don ka baƙanta mini, ai na san cusguna mini kake da ainiya" ta ɗago fuskarta sharkaf da hawaye ta haɗe hannunta biyu da me lafiya da maƙalallen ta ce "Please, ka sake ni..," Wata tsawa Md ya daka mata ta yi saurin runtse idanunta ta ce "Ni dai bana son ka, ka sake ni don girman Allah, ina da buri akan aikina yadda ake mini kallon wulaƙantaciyya, nakasasshiya, wacce yin bara ne ya dace da ita, na ci burin sai na nemawa duk wani me nakasa ƴan cinsa" "Please Liman, ka sake ni" Idanunsa da suka sauya kala ya zuba mata, yana mamakin yadda ta ƙware a zuba surutu don bai yi expecting nata haka ba. A hankali ya ce "Kike cewa na sake ki?" Ta yi masa shiru. "Saboda ba ki son yadda nake son ki ba, yadda nake nake faɗa akan ki ba, har kike da courage na kallon idanun Md ki ce wai na sake ki? Wacece ke Please? Who are you?" Ahlam ta ce "To ni bana son ka?" "Than, kalli cikin idanuna ki faɗan haka" Ta murtuke fuska ta ce "Idanun duk kwantsa" Md ya ware ido, ya miƙa hannun to make sure haka ɗinne ko a'a, bai yadda ba, ya buɗe madubin motar yaga idanunsa fresh farare tas dasu. Ya shammace ta ya riƙo ta, zata ƙwace gabaɗaya ya fusgota ta faɗa jikinsa ya rungumeta sosai a ƙirjinsa. Ya ɗora bakinsa a kunnenta, ya hura mata iska kaɗan, kafin ya yi kissing ƙasan kunnen. "Wannan na rashin kunya ne" Ya sake kissing kumatunta ya ce "Wannan na hana zuciyata sukuni da tunaninki ne" Ya yi kissing tsinin hancinta ya ce "Na kishin Anees ne wannan" Sai ya jirkituta cinyarsa, jikinta duka rawa yake yi da ɓari saboda taɓa jin hakan ba iyaka cin rayuwarta. Ya dinga kallon bakinta da yadda laɓɓanta suke rawa, ya yi baya kaɗan yana lumshe idanunsa, hannunta ɗaya ya riƙe ya ɗora lips ɗinsa a nata. Slowly ya yi kissing na ƙasan sosai. "For all the love I have for you" Ya ja hancinta kaɗan ya ce "Ina son ki Halimatul Sadiya, ina son ki Ahlam ɗin yaya, ina son Babyn yaya, ina son Golden voice. Ina son ki tun ranar dana fara ganinki Ahlam, na zuba idanu ne naga yanayinki da tarbiyyarki, duk abin da nake miki tsakanin kishin Anees ne ya ja, domin da ace na furta ina son ki ko bakya so na, yake shige miki ko ban karya ɗan mutane ba, jikinsa zai faɗa masa. Sannu a hankali na fahimci kema kina ra'ayina. Kar ki mini musu ke kin sani nima na sani, Yussy kuma bani da business da ita, ina barinta ne ta yi abin da taga dama akan idanunki saboda na kunna ki, kuma Alhamd ina yin nasara" ya yi shiru yana sassauta riƙon da ya yi mata, kanta a ƙirjinsa tana rera masa kuka ya shafa kanta kaɗan ya ce "Ni ba zan tauye ki akan aikinki ba, zan barki duk abin da kike so ki yi muddin bai saɓawa koyar war musulunci ba, zan tayaki aiki wajan cimma burinki" Cikin sauri ta ce "Za ka yi inviting Sayyadi Baffa na yi Interview dashi don Allah?" Md ya yi shiru yana kallon ta. Ta daki ƙirjinsa ta ce "Please Liman" A hankali ya ce "Ƙarewa ki ce Asad Hafiz Baffa" ya ɗora da "Ba zan miki ƙarya don ki so ni ba, Md ne ni a Bright Fm, Bilal ne Founder a Bright Fm, shine me rediyon, kuma muddin yana nan Sayyadi Baffa ba zai taɓa zuwa nan ba, ke ko bashi bane i don't hakan zai faru, even Nadiyaah da Diyanaah ba ki da zarafin hira dasu" ya kalli cikin idanunta yana goge mata hawaye ya ce "Tunda kika amsa sunan Mrs Asad Hafiz Hafiz, dole ki yi Interview da Sayyadi Baffa" Ahlam ta ce "Yaushe?" "Not now" Ta zame a jikinsa ya tayar da motar ya jata suka fice daga cikin gidan gabaɗaya. *** Bayan azahar jama'a duk suka watse a gidan Innti, da an shigo an yi gaisuwa mutum yake komawa gida. Jaheed ta bawa kuɗin aikin da za'ayi Jadid a asibiti ta ce ya je ya zauna kusa dashi, saboda kada a shigo ba'a same ta ba daman shi ai namiji ne, gwara ya saba da jinyar ɗan'uwansa tun yanzu. Ita ta kewa Jadid komai, hatta wanka da alwala idan ciwon ya tashi, bata jin nauyinsa kamar yadda shima yake jin bashi da kamar Innti a duniya kuma uwa ce, labulen sirrinsa ce. A hankali ta miƙe tun bayan dawowarta daga waje babu wanda ta cewa komai, komai da idanu take binsa dashi. Duk yadda zata faɗi raɗaɗin da take ji a zuciya ba kowa zai fahimce ta ba, nauyin da zuciyarta ta yi mata ita kaɗai ma sai ta saka ta jinya, ga tijarar da Daada ya yi a cikin jama'a akan kuɗi, Emama tazo ta tusa. "Wai ai ita ce ta kai Iftihal gidan masu kuɗi, kuma idan Innti ta bata kuɗin sadaƙa za'ayi" Hanna ta ce "Ta ina kike zaton zata ba ki kuɗi, tana kallo mugun abin da take jifanmu dashi, da kuma Daada ya fara komawa kanta, gashi nan ƴarta ta faɗa rijiya ta mutu" "Ai shi sharri kan me shi yake bi, kuma alhaki ɗan tsako ne" ita kanta ko karin maganar bata gama iyawa ba. Innti da idanu kawai take bin su dashi, bata ko tari. Maman Haysaam ta ce "Haba bayin Allah, wanne irin tozarci ne wannan? Ɗiyar cikinta ta rasu saboda baku da lissafi ku dinga binta da waɗannan munanan malaman? Shi ɗan'uwan naku me ya tare mata da har zata yi asiri saboda shi? Wallahi baiwar Allan da tana jin shawara ta da tuni ta jima da kashe aurenta ta rungume ƴaƴanta ta rufawa kanta asiri. Banda gantalallen ɗan'uwan naku yana yi mata yadda yake so, saboda tunanin tana masa biyayya ko wani dalili nata can mara tushe, ai tuni Innti ta sha kwana ta zama abar data zama. Jaheed yana shago, duk wata ana masa albashi ko babu yawa ne, Muraad yana zuwa farm centre ko babu yawa dai yafi zamam gidan, matar nan tana koyarwa a makaranta, tana ɗaukan albashi, ga ɗinki ta na yi, ga ƙananun sana'a ta hannu da mata suke yi. Ita kenan faɗi tashi wajan ganin ta rufawa kanta asiri bata bar yaranta cikin yunwa da datti ba. Motsi kaɗan sai ya sace kuɗi ya shiga caca, komai na Innti a sace yake a wajan ruɓaɓɓan mutumin can, ga shegen bin mata kamar uwa ɗaya ta haife su da ɗan taure, tunda ta daina koyarwa ta shiga matsin lamba, ga ciwon Jadid dake lashe kuɗi, ɗaukin nawa kika taɓa kawo mata a matsayinki na uwar mijinta, kuma jininta? Wanne tallafi kikai mata?" Maman Haysaam ta ƙare maganar tana miƙe tsaye idanunta na zazzagowa kamar zata hau iska jikinta sai rawa yake. Daada ne ya ɗaga hannu zai mare ta, Emama ta riƙe hannunsa ta ce "Rabu da ita" "Basshi ya taɓa ni, wallahi da sai na masa sanadin da zai koma bakin titi da yin bar" Ta juya kan Emama ta ce "Ke kuma ba wayo kike dashi ko dabara ba, tunda ga ƴaƴa mata nan kina dasu, tun a nan duniya za ki fara ganin HUKUNCIN ALLAH, Saboda kin riga da kin zama INUWAR GIGINYA mara tsoran Allah da son zuciya, a halin da matar nan take ciki ga yaro can a asibiti ba'a san ina kan shi yake ba, shine nan kuka wanko jiki a baku kuɗi, daman ba jana'iza ta kawo ku ba. Jarrabawa ce kawai irin ta aure amma Innti ba tsaran Daada bace in sha Allah farincikin da kuke baƙincikin ta yi kuna ji kuna gani za ta yi yaranta za su zama zama abin sha'awa ga jama'a. Ƴan wahala kawai" Tana faɗin hakan ta saka kai ta fice, zuciyarta na yi mata raɗaɗin rashin hankalin jama'a. Suma ɗin juyawa suka yi tare da ficewa. Daada ya kalle ta ya ce "ƴar daba kika kawo mini cikin gidana ashe bani da labari? Har tana iƙirarin zata sabauta ni ko?" Ya jinjina kai, yau fes yake cikin hayyacinsa tsaye akan ƙafafuwansa ya ce "Ina jin igiya ɗaya ta rage tsakanin auren da bashi da wata ma'ana a wajena, face ni na rufa miki asiri kamar yadda mahaifinki ya nema ko?" A hankali ta ɗago ta kalle shi, ta zuba masa rinannun idanunta bata ce ci kan ka ba. Ya ce "Tunda babu abin da za ki yi dani kuma kina da wanda zai iya aurenki, ki je na sawwaƙe miki. Nima yau zan yi sabuwar amarya. Na yanke sauran igiyar da ta yi saura" yana faɗin hakan ya juya ya fice da takun isa da ƙasaita. Ta zubawa bayansa idanu, a hankali ta ɗora hannunta a ƙirji ta danne sai kuma ta saki yalwataccen murmushi. Duk abin da yake faruwa Babban yaya yana ɗakinsu kusa da Ana wacce har yanzu babu inda yake motsi a jikinta, kanta a cinyarsa yana shafa sumarta a hankali hannunsa ɗaya ya damƙe nata hannun dashi. Bai sani ba, amma ya samu kan shi da hamdala bayan sakin da Daada ya yi wa Innti ɗin, ya ji wani sanyi na musamman, ya ji relief na musamman a zuciyarsa yana sauka a hankali, hakan ya yi masa daɗi shi ya shirya, daga Ana har Innti yana da inda zai kai su da baza su ta gayyara ba. Yana wannan tunanin Jaheed ya kira shi a waya, ya zubawa wayar ganin number da baya so a kira shi da ita yana yawo a screen ɗin wayar bayan katsewar kiran na Jaheed, ya kuma fahimci filashin daman Jaheed ɗin ya yi masa. Don haka numbers ya kira kai tsaye yana ɗagawa Ya ce "An fito da Jadid yanzu daga wankin ƙodar" Babban yaya ya yi shiru for a while Sai kuma ya kashe kiran. Innti na zaune har yanzu ta kasa motsi, ita da kanta bata san meke damunta ba, duk abin data furta kusan zata iya cewa ba shine ainihin abin da yake mata yawo a zuciyarta ba, carbi kawai take ja tana istigifari, a ranar sai da suka saukewa IFTIHAL Kur'ani ita da Yaya da Jaheed, ta san da idanun Ana biyu ita kaɗai zata iya sauke Kur'anin da kanta cif. A nutse ya shigo cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama, ƙamshinsa me sanyi ya mamaye tsakar gidan, yana sanye da yadi me laushi ash colour ya ɗora a akan shi. Ya durƙusa ya ce "Ina yini ya ƙarin haƙuri?" "Allahamdulillah Haysaam" ta ce da ƙyar. Ya yi shiru kan shi a ƙasa, ta dube shi ta ce "Ya aka yi ne Haysaam?" "Daman Offer ɗin aiki da gwamnati ta raba Allah Ya yi na samu, yanzu ma daga can ma'aikata ilimi nake, an sake tantance mu wajan Hamsin akwai wani interview da za mu ke Abuja, wannan kuma shine Finally Interview da za mu yi, shine na ce a tayamu da addu'a mu tsallake idan da rabonmu" Innti ta ce "Khairan in sha Allah Haysaam, Allah Ya taimaka ya basa sa'a isa rabo ne" Ya ce "Amin Ya Allah" "Amma yaya bai san da Offer ɗin ba, link aka cike ko e-mail ne? The offer is still available?" Ya girgiza mata kai kafin ya ce "A Redio aka sanar, kuma masu first class" "Yaya ma first class gare shi. Babu rabo ina maka murna ƙwarai da gaske. Yau za ka tafi?" "Nan da 2 days masu in sha Allah" "Ma sha Allah" ta ce a nutse. Ya yi jim kafin ya ce "Nanaah ta farko?" Da hannunta ta yi masa nuni da ɗakinsu yaya, ya miƙe gently hannunsa ɗaya cikin aljihu da nutsuwarsa ya ƙarasa cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, bai da tabbacin ko Muraad ya amsa, ya yi cak a bakin ƙofa ya zuba musu ido, Ana na jikin Yaya ya rungumeta kanta a ƙirjinsa yaja idanunsa ya lumshe, ƙirjinsa na ɗagawa a hankali, alamar shima bacci yake yana jingine da bango, Yaa Sam ya harɗe hannayensa a ƙirji idan ya kalli Babban yaya sai ya kalli Ana, sai kuma ya kalli yadda take rungume a jikin yaya, ya ɗan runtse idanunsa, ai yayanta ne, bai kuma ci ya ji abin da yake ji a yanzu ba. Ya jima yana kallon su kafin ya juya ya fice daga ɗakin ya yi wa Innti sallama jikinsa a sanyaye, zuciyarsa ta yi masa nauyi. *** BIYA. Batty na zaune a bakin gaban ruwan ta yi shiru tana wasa da ruwan da ƙafafuwanta data saka a ciki, idanunta ya kaɗa ya yi jajur kamar an wasa mata gaushi a cikinsu, barkonon da take ci idan ƙanƙarar maitar ta motsa a ƙare bata san kuma inda zata samu wani ba, ta yi kuka sosai da birigma duk a gaɓar kogin ita kaɗai idanunta suka kumbura. Daga bayanta ta ji an dafata cikin sauri ta juya sai taga Shatu ce, wata ajjiyar zuciya ta sauke tana jan numfashi ta ce "Shatu kin bani tsoro, ki ce na yafe miki" Shatu ta marairai ce fuska ta ce "Shatu kika ce mini fa? Haba mutuniyar, ba masoyiyar?" "To ai ki maitata ce ta motsa, bani da lafiya bana jin daɗi, mutum nake son ci Shatu" Shatu ta waro idanu waje ta ce "Ke Batty mutum fa, ai ba'a cin mutum wallahi" "In ji wa? A na ci Mado ma cinye shi akai, ba mutuwa ya yi ba, kurwarsa aka kame wlh" Jikin Shatu a sanyaye tana kallon Batty ta ce "Shatu ya ake cin mutum to? Mece maitar nan, a ina take ɗakko ki nuna mini ita" Batty ta girgiza kai idanunta ya kawo ruwa ta yi saurin goge hawayen ta ce "Nima ban san mece maita ba, amma kafin a kashe Innata, ita ce ta bani maitar, ina jin ƙanƙarar maitar na mini yawo a ciki babu daɗi Shatu. Kekam kin ji daɗi Innarki ba'a kashe ta ba, kuma tana son ki, ana ba ki amince da yawa, kina yin wanka kina sauya kaya, ina jin kamar ina wari fa" ta yatsuna fuska ta ce "Shanshanani fa ki ji Shatu wari nake yi, ɗoyin dauɗa nake" Shatu ta girgiza kai cike da damuwa. "To yanzu wa za ki ci? Ke kika ci Mado?" Batty ta ce "A'a Yaaye ce ta cinye Mado, ai ni ban taɓa cin kowa ba, amma an taɓa yankawa an soya an bani na ci" sai ta yi saurin kara bakinta a kunnen Shatu ta ce "Kuma wallahi naman mutum akwai daɗi" "Ce Allah Batty? Nima zan ci" Yanayin Batty ya sauya ta ce "A'a, ai ba kyau tunda ke ba mayya bace babu ruwanki, kuma idan kika je gidan mutanen da ba ki sani ba, aka ba ki abinci kar ki ci, kar ki yi kwaɗayi Shatu, idan kikai mafarki ana ba ki ɗanyen nama ki ci, to kar ki ciki, idan ba haka ba, kina ci watarana za ki wayi gari kina kallon kayan cikin mutane. Ki dinga addu'a kina neman dafa'i na sharrin mayu" Ita dai Shatu bata ce komai ba, domin kamar almara haka take kallon abin, bata ma san mene maita ɗin ba, ta kuma gaza gane maganar Batty. Sai ta ce "Jiya da daddare na ganki Batty, ina kika je?" "Maitar dare. Nima ai na ganki a jiyan wajan ƙarfe uku na dare kin fito shan ruwa a kogi" Shatu ta zaro ido ta ce "Ni ɗin?" "E, nima ai kin ce kin ganni haka ne?" Shatu ta ce "Ni a mafarki na ganki fa" "Zahiri ne, da babu Dafa'i a jikinki wallahi da tuni na kama kurwarki Batty, ki daina kwanciya da ƙishirwa, idan mutum yana jin ƙishirwa kuma yaƙi shan ruwan har ya kwanta bacci, to kurwarsa bata jurewa, tana tashi cikin dare duk inda ruwa yake ta nema, a wannan tafiyar tana haɗuwa da kurwa kala-kala, muma mayu muna fitowa, kuma duk kurwar da babu Dafa'i a jikinta nan take ake kame ta, madadin mutum ya farka da lafiya kamar yadda ya yi kwanta sai ya tashi cikin jinya. Shatu duk mutuwar da ake yanzu ta farat ɗaya wallahi mayu ne da yawa, sharrinmu yana da yawan gaske" Idanun Batty ya kawo ruwa ta ce "Shatu ke kamar jinina ce bana son na rasa ki, zan ba ki magani sosai, idan kina tare da maye a cikin gida ko maƙwafta ne ku, muddin kikai wannan wallahi sai dai maye ya ganki ya barki, daga ƙarshe ma ko inuwa ɗaya ba zai iya haɗawa dake ba. Ki samu Igiyar yaɗiya, sai ki bubbuga da dutse, sai ki samu sassaƙin maɗaci amma da dutse ake sassaƙe wa, ba da adda ko gatari ba, ko magirbi ba. Ki haɗa su waje ɗaya ki zuba a babbar roba ko ƙwarya sai a zuba ruwa akai, sai ki samu ɗanyen tafarnuwa ki zuba a ciki, sai ki rufe ruwan, ya yi awa ashirin da huɗu ki dinga sha kina wanka, idan mayen a cikin gidanku yake ki dinga wankan safe da yamma, idan a maƙwafta ne da yamma kawai za ki dinga yi, ba maye ba ko Inna Badakuwa ce nan gani nan bari Shatu sai ta Allah bata mutum ba" Shatu ta yi shiru tana sauraran Batty. A hankali ta miƙe ta ce "Bari na koma cikin gari kar Innata ta ji shiru" Batty ta jinjina kai kanta a ƙasa. *** BAFFAS ESTATE. Tunda ta zauna a hadaɗɗan parlourn kanta a ƙasa yake, tana jin yadda idanu wajan huɗu suke kallon ta, Azizah, Hajiya Umaimah sai kuma Mamy, da Hajiya Kaltum ƙanwar Hajiya Umaimah. Mamy ta kalli Ahlam a hankali ta ce "Allah Ya nuna mana lokacin Nikkah da alheri, ya saka mutuwa ce zata raba tsakaninki da Liman" ita dai bata iya cewa komai ba, kanta yana ƙasa abinta. Liman ne ya kame fuska ya ce "Amin Mamy" Ta miƙe tana faɗin "Idan zata tafi ka yi mini magana Please Asad" nan ma ya ce "I'll" Azizah zuciyarta a cunkushe tabi bayan Mamy da kallo ta ce "Mikirar mace, wallahi ina zargin idan ba ita ta rusa aurena da Baffa ba, kuma wallahi indai ina raye Baffa bashi da wata mace a duniya sama dani" Hajiya Kaltum ta ce "Ko ba Hajia Ni'ima ba? Ai na jima da fahimtar kamar tana da saka hannu a ƙin auren Baffa, hatta hatsarin Baffa wallahi ita nake zargi ke har mutuwa Hafiz Baffa ma ina saka ran ita ta tsara komai, saboda ta samu gado me yawa, ba tana taƙamar zaratan yaranta maza har biyu ba, ga ƴar auta Hidaya da late Hafizz Hafizz Baffa ya ɗauki son duniya ya ɗora a cikinta tun kafin ma yaga zuwanta duniya, da yana raye aka haife ai ƴar kallo za ki zama a gidan" Hajiya Umaimah girgiza ƙafa kawai take yi, ba tare da ta ce komai ba. Liman ya kalli Hajiya Kaltum ya ce "Is this the right time da za ku yi wannan maganar? Haba Ummy" ta kalle shi. "Ni na mance wai matarka ka kawo ashe Liman. Ke yama sunanki kika ce ɗazo?" Kanta a ƙasa ta ce "Ahlam sunana" "Ke dilla bana son iyayi, sunan gaskiya" Slowly Ahlam ta ɗago kai ta kalli Azizah, shigar alfarma ce a jikinta wuyanta ya sha daham, ta yi kamar ba zata yi magana ba sai ta ce "Halimatu sunana" Azizah ta taɓe baki "Hajiya Halimah kenan ko?" "No" kawai Ahlam ta ce. Azizah ta ce "Kan uba, uban mene no?" "Ina nufin ko airport ban taɓa zuwa ba, ban kuma san ranar zuwana ba, amma ina da rufin asiri dai-dai gwargwado in sha Allah" Hajiya Umaimah ta ɗago kai ta kalli Ahlam sosai, taga gabaɗaya lace ɗin jikinta bai fi 150k ba, ɗan kunnen ba gold bane, ta kalli hannunta a maƙale da ya yi yaushi ta taɓe bakinta ta ce "Ok, ashe ke nakasasshiya ce?" Wani abu ya daki zuciyar Ahlam ta ɗago a hankali ta kalli Liman sai ya yi saurin runtse idanunsa yana ɗauke hawaye ya fara cika idanunta. Azizah ta ce "Disable kenan ko?" Hajiya Kaltum ta ce "Ko shi ya sa daga zuwa neman aure aka ɗaura auren? Wannan ai dole Liman ya auri lafiyayyiyar mace gsky" "Let's go" Liman ya miƙe yana riƙo hannun Ahlam, bai jira ya koma part ɗin Mamy ba, yana da tabbacin ma likita ne yake duba Mu'alim itama tana wajan Al'ameen ɗin. Suna shiga mota Ahlam ta fashe da wani irin raunataccen kuka, wanne irin aure ne wannan, tun kafin ta shiga? Ba zata iya ba, gwara ta nemi ɗaukaka a aikinta akan wannan zaman na aure, babban gida ne sun fi ƙarfinta. Ta kowacce fuska, Liman ya kasa ce mata komai sai hannunta daya riƙe. Wajejen 8:00 na dare ya sake dawowa ya ɗauke ta, zuwa wajan awards, sabuwar Abaya ya saka me masifar kyau, shi da kan shi ta yi masa kyau, lokacin da suka ƙarasa event ɗin ya cika sosai, ta riga shi fitowa suka hadu da Zainab Alƙali suka yi ciki, Anees tun daga nesa yake mata murmushi ta yi ƙasa da kanta. Waje suka nema suka zauna da Zainab Alƙali, Yussy sai ƙwainane take, ta saka wasu shegun kaya, ɗuwawunta ko motsi ba ya yi ya haɗe da bayanta ya shafe. Zainab Alƙali ta zunguri Ahlam Ta ce "Ga mutuniyar fa, yau sai Allah" Murmushi kawai Ahlam ta yi hankalinta akan wayarta, ta samu kanta da yin research akan TIVA. Zainab Alƙali ta ce "Ke kawai nake jira a bawa award na tafi" Ahlam ta ce "Wa fa?" "Wawa" cewar Zainab Alƙali. "Kefa kin san dole sai an ba ki award, akaf Bright Fm waya kai ki kawo news tell me?" "Uhm" Aka ci aka sha. A hankali aka fara bada awards kamar daga sama suka ji an ce "Zainab Alƙali ta samu Rising Star in Journalism” wani irin buɗe baki Zainab ta yi, Ahlam ta rakata ta amsa. Aka kira wata Binta Baba aka bata na "Most Promising Reporter" Me bada award ɗin ya ce "Award ɗinmu na ƙarshe me taken,Outstanding Journalist Award, wato Lambar Yabo ta fitaccen ɗan jarida. Wannan award zai je zuwa ga, ga" A tare Yussy da Ahlam suka miƙe. Md daga nesa yana ta kallon Ahlam yana murmushi, domin tun kafin yau ya san ita ce, haka ma Anees. Deep down na zuciyarta bugawa yake sosai. Daga sama ta ji an ce "Zuwa ga Yussrah Yassar Yakasai" A tare Md da Anees suka miƙe tsaye da faɗin "What!" Yussy na murmushi ta je ta amsa cike da farinciki friends ɗinta sukai ca A ɓangaren maza aka bawa Md da Anees. Dishi-dishi haka Ahlam take gani ta miƙe ta yi waje tana fashewa da wani irin kuka. Tana tsaye ta ki an sakar mata dariya da ihu ana mata Vedio. Yussy ta ce "To ya akai Ahlam?" "Yanzu za ki yadda ni ba sa'arki bace? Za ki yadda na fiki ta kowacce fuska? Za ki yadda ki ɗauki shawarar dana ba ki na ɗaukan roba ki bi layin mabarata? Ki haƙura da aikin jarida, bana irinku bane, ba za ki iya ba wallahi" Billy ta ce "Wai Yussy daman wannan ce me yin ƙasa dake tana ɗaukan footstep ɗinki? Ashe naƙasa ma gare ta" "Wallahi fa Billy, kuma ya zama na farko na ƙarshe da zan ganki tare da Md domin nawa ne, mijina ne in sha Allah. I'm sorry fa, ga Outstanding Journalist Award da sunan Yussrah Yassar Yakasai, yau kam bacci ai babu shi a cikin idanunki na sani wallahi" Suka sheƙi da dariya Yussy ta ce "lose....," Bata ƙarasa faɗa ta ji an ɗauke ta da mari a hagunce, Md na sauke hannunsa Anees ya sake sharara mata wani marin ya ce "Ke Yussy har kina da zummar faɗawa yarinyar da nake so magana? Waye bai san da yadda kika samu Award ɗin ba, waye bai san halinki ba, award indai ta hanyar da kika samu ne bana fatan baby ta samu irinsa" Md ya kalli Yussy sama da ƙasa ya ce "Ya zama last time da za ki yi wa matata haka, ni sa'anki bane zan iya saka ki a gidan yari har ƙarshen rayuwarki, texci no garage" Yussy jikinta na rawa ta ce "matarka? "Yes, Mrs Asad Hafiz Hafiz Baffa" Yana faɗin hakan ya riƙo hannun Ahlam yana sanyata a cikin mota, suman tsaye Anees ya yi, ji kamar bai ji daidai ba, yau yake shirin faɗawa Ahlam komai na yadda zuciyarsa ke son ta, ya faɗa wa family ɗinsa shi kawai suke jira. Yussy kamar ta haukace Sanda Md ya kai Ahlam gida ya jima yana rarrashinta kafin ta yi masa murmushi ta ce "Nothing fa, ya shige ai" Ya ce "Da gaske kike har zuci?" Ta jinjina kai. "Ok kiss me idan haka ne" Ta shawagaɓe fuska "Ai ban iya ba" "Ni na iya, come closer" Ya riƙota yana kallon fuskarta ta yi masa murmushi ta miƙa hannunta zuwa sajensa ta shafa kaɗan ta ce "Ina son Liman" "Ina son Asad Hafiz Hafiz Baffa" Ta sake shafar lips ɗinsa ta ce "Ina son Md ɗina" Wani shock ya kama Md, domin bai taɓa expecting hakan ba, ya san tana son shi, amma bai kawo hakan ba nan kusa, ya dinga kallon ta, ta ce "Ka fasa kissing ɗin?" "No, I'll try ban iya ba" Kafin ta yi magana, ya ɗora bakinsa a nata ya shiga kissing ɗinta, cikin sa'a ta shiga yi masa nata kissing ɗinz few seconds ta zare jikinta ta ce "I'm very sorry Md please" "Sorry? Na mene?" Ta ce "Just, za ni Abuja please" Ya ce "Me za ki a Abuja?" "Wajan Antynmu, kwana biyu zan" Ya girgiza kai ta ce "No, ki bari zan kai ki" "A'a don Allah, da Yaya zamu kuma gyaran amarci za'a yi fa" ya dinga kallon ta. "Am going to miss you Leemah, ya zan?" "You can call me, and nima zan yi kewarka ai" ya jinjina kai ya lumshe idanunsa. "Ka amince?" "Sure, Allah Ya tsare hanya" Sai ta yi saurin rungume shi, hawaye na cikowa a idanunta, ya yi holding nata back" Sallama sukai ta shiga cikin gida, ƙarfe 2 na dare ta gama haɗawa duka wasu ID cards nata, atm, wayarta, computer da komai ta saka a cikin jaka, ta yi ɗan note a paper ta ajjiye. Tana da duka maƙulan gidan ta buɗe ta fice, har kuma ta fice daga cikin gate ɗin me gadi yana sharata bacci bai sani ba. Ta kalli gidan ta ce "I will be back, zan dawo da nasarar da za ka yi farinciki yaya, zan dawo da nasarar da Yussy bata isa ta yi mini dariya ba, zan dawo matsayin cikakkiyar ƴar jarida" ta goge hawayenta. "Zan dawo, dawowar da zata bani nunawa Md so na gaskiya, son da zai yi alfahari dashi, soyayyar da Yussy bata isa ta shiga cikinta ba" ta nemo number Md ta yi masa text da "I'm sorry sweetheart.... "I will be back soona or later" *** Washegari ya kama juma'a, Jadid ya dawo gida ya nemi warware sai jinyar zuciya na rashin Iftihal, gashi har lokacin Ana bata farka ba. Suka shirya suka nufi masallacin juma'a, Yaya, Jaheed da Jadid, daga nan suka ƙarasa kabarin Iftihal wajan yi mata addu'a. Lokacin Innti ta yi alwala ta yi sallah ta leƙa ɗakinsu Yaya ta kalli Ana, ta shafi fuskarta tana sumbatar goshinta a hankali. Innti ta jima tana azkar da yin addu'a ga Iftihal da Ana, ta dinga addu'a Allah Ya bawa Ana haƙuri da juriya Allah Ya bata dangana. Sallah ta fara, tana cikin sallar kuma su Yaya suka dawo, waje suka nema suna jiran su yi mata sannu da gida, sun san tana jimawa a Sujjadar ƙarshe amma wannan jimawar ya yi yawa. Jaheed ya ce "Sahibarmu a roƙa damu" Jadid ya yi dariya sosai shima ya ce "addu'ata duka taku ce ai" Jaheed ya ce "Kai ni Innti?" "To ai abin da zata ce na faɗa, ni dai ki roƙa mini ko a mafarki ne na dinga ganin Iftihal" Suna ta barkwanci. Babban yaya yana zaune sai kallon Innti yake yaga hannunta ya ɗan lamƙwashi ya miƙe da sauri ya dafata, yana dafata yaga ta faɗi, jini ta hanci da bakinta hannunta riƙe da farar takadda, da biro daga can gefe. "Innti...!!!" Suka kira sunanta. "Ta rasu" shine abin da yaya ya ce yana ɗora kan shi a ƙirjinta ya ƙanƙameta jikinsa ya shiga wata iriyar rawa da kakkarwa da ƙarfi ya ce "Don Allah Innti, Anarki, ni ɗaya ba zan iya kulawa da Ana ba" daidai nan Ana dake cikin ɗaki ta fasa wata iriyar ƙara ta ce "Abbaaa.... *H I Y A A M* Page 16: Last FP Bright pens Yota/001 Note: Akwai sanarwar a end of the page. As I said, littafin HIYAAM daga farko har ƙarshe sadaukarwa ne zuwa ga Nazeefah Sabo Nashe. Luv u all d tme😘 Wannan shafin naki gabaɗaya Maman Fati, alkairin Allah Ya kai miki har gadon baccinki😊 "Abbaaa!" Ana ta sake ƙwalla ƙiran sunan Babban Yaya a karo na biyu daga cikin ɗaki. Dukkansu kasa motsi suka yi, balle a samu wanda zai iya shiga ɗakin da Ana take wajan duba abin da yake faruwa da ita a ciki ɗin. Babban Yaya har yanzu kan shi yana ƙirjin Innti hawaye na fita daga cikin idanunsa yana sauƙa a hankali, rawar da jikinsa yake yi ta tsananta, ya kuma kasa amsa tarin tambayoyin da Jaheed da Jadid suke masa. Jaheed ne jiki na rawa ya ce "Ta ya Innti za ta rasu ta bar mu a lokacin da muke tsananin buƙatarta a kusa damu?" Ta girgiza kai ya ce. "Innti bata rasu ba, wasa ma take yi" "Jaheed kuma mutuwa ta rasa wa za ta ɗauka sai Sahibarmu? Anya ta mutu kuwa?" Cewar Jadid, jikinsa duka rawa yake yi. "No, mu za mu riga Innti rasuwa fa" Wata ajjiyar zuciya mai ƙarfi Jadid ya sauke, abin da Jaheed ya faɗa ya saka ya ji wani irin relief na musamman yana sauka a zuciyarsa da jikinsa, tashin hankalin da ya nemi rikito masa ya ji ya ɗan yaye kaɗan. "Allahamdulillah!" Ya ce cikin sanyin murya. Suka zubawa Babban Yaya idanunsu na jiran furucin cewa Innti tana numfashi, Innti tana raye a duniya, kuma za ta cigaba da numfashinta cikin ƙoshin lafiya da farinciki, za ta cigaba da rayuwa, rayuwar da zai ba ta taɓa ganin cigaban da suka samu a tasu rayuwar, rayuwar da zai ba ta damar ganin sauyin da suka samu, za ta ɗauki Yaƴa da jikokinsu in sha Allah. Babban Yaya ya jima a yadda yake, da ƙyar yake iya jan numfashi da sauke wa, wani irin azababben ciwon kai na musamman tare da zazzafan zazzaɓi suka saukar masa a lokaci guda. Tunda ya taɓa zuciyarta ya ji ba ta aiki, ya taɓa hannunta shima baya bugawa ya san Allah Ya ßauƙi rayuwar Innti a ranar juma'a, a kuma Sujjadar ƙarshe, ga azkar da Kur'anin da ta karanta nan a gefe guda kusa da kanta Ya shiga tambayar kan shi, ya aka yi Innti ta rasu? Mene ya zama silar mutuwarta? Jini ta hanci da bakinta, ko guba Daada ya sa mata. Ban da idanun su Jaheed, da yadda za su firgita babu abin da zai hana shi tashin gawar Innti ta faɗa masa silar mutuwarta. Sannu a hankali ya zame jikinsa daga nata, ya kwantar da ita a saman laddumar ya ja Hijab ya rufe ta. "Babban Yaya Innti?" Yaya ya juya ya kalle su da nutsuwa da fahimtar daya arowa zuciyarsa da jikinsa, ba don bai firgita ko ya zauce ba, sai don a yanzu shine wanda suke kallo a matsayin Innti ɗin, dole ya zama jarumi. Ya riƙo hannayensu cikin ƙasa da murya wacce take fita da ƙyar ya ce "Na san ku Musulmai ne, kuma dukkan cikakken musulmi an san shi da imani da Allah, tare da Mala'iku da mazanni, tare da imani da ƙaddara me kyau ko kasin hakan. Duk wanda bai yadda da ƙaddara ba, kai tsaye yana faɗa da Ubangiji ne, kuma imaninsa yana da rauni" ya yi jim kafin ya ɗan rufe idanunsa, fishaa kuma ya buɗe su. "Jaheed, Jadid mun rasa Innti kamar yadda muka rasa Iftihal, kar ku yi kuka, domin yinsa yana saka mamaci cikin azaba, kar ku yi baƙin ciki, domin wanda ya halicci Innti shine ya ɗauki ranta, rayuwarta a wajansa ta fi wacce take yi a wannan gidan. Za ku iya cewa Allah don me ya yi muku haka? Idan ba Ubangiji ba, wane zai ɗauki ran uwa kuma ya ɗauki na ƴa a taƙin lokaci? Kuna da ikon question ɗinsa akan hakan? Ya kamata mu yi farinciki, Iftihal ta yi shahada, ta rasu a cikin ruwa, Innti ta rasu yayin da take ganawa da ubangijinta, ranar juma'a kuma" Ya ɗan fesar da iska "Akwai raɗaɗi tabbas, akwai ɗaci, ciwo ne kuma a zuciya ta tafi ta bar mu dashi. Mu yi mata addu'a, kar ku yi kuka, idan ya zama dole ku zubar da hawaye" kallon Babban Yaya kawai suke yi, sun ji me ya ce kuma sun gamsu, amma tambayar da suke da ita, yaushe za ta sake dawowa rayuwarsu a karo na biyu a matsayin uwa mahaifiya? Suna son sake fitowa daga cikinta, su sake rayuwa da ita. "Bango ya faɗi Yaya" cewar Jadid. Ya ɗora da "Ni ya kamata na mutu ba ita..," "Shhha, ita Ubangiji ya yi niyya, domin ya gwada imanin da muke dashi, babu lokaci ina son a yi mata sallah a kaita gidanta yau" Gabaɗaya zuciyoyinsu sun yi nauyin gaske, wani abu mai girma ya danne musu kirji, Jaheed da Jadid suka nemi hawaye suka rasa a idanunsu, rawa da kakkarwa da wata tsuma kawai jikinsu ke yi, basa ganin ko gabansu, su ka ji kamar basu taɓa walwala ko farinciki a duniya ba, komai ya ƙare. Wata sabuwar rayuwa suke hangowa, tare da wata sabuwar ƙaddara me girman gaske. "Jeka faɗawa Maman.... Jadid ya gane me Babban Yaya yake nufi, kamar an zare masa lakar jikinsa ya nufi gidansu Haysaam. Yaya ya miƙe ya nufi ɗakinsu. Yana shiga ya ja ƙofa ya rufe, wanwar ya faɗi a ƙasa ya dinga haɗawa jikinsa da bango, baya son yin ihu saboda kar su gane ya karaya ko kuma su yake hanawa kuka. Ya saka haƙori wajan datse harshensa, idanunsa suka zazzago, ya ji wa kan shi rauni a harshe. "Innti me ya sa? Za ki tafi ki bar Ana? Ke da kanki kike faɗin yadda take damuwa da ku ko kanta bata damu dashi ba, ke da kanki kike faɗar taurin kai da rigimarta, Innti ba zan iya da rigimar Ana ba, ba zan iya ɗaukan wannan nauyin ba, Abbaa ba zai iya kulawa da Ana ba, ba tare da kina a kusa damu ba, Innti ba zan iya faɗawa Ana cewa bakya duniya ba, wallahi ba zan iya ba, ta ya zan rufe mata wannan maganar? Ta ya zan iya wannan?" "Abbaaa.... Ya ji muryar Ana ta kira shi da wannan sanyin nata, da wannan silent voice ɗin nata Ya juya kaɗan, sai ya ga har yanzu ba ta farka ba, amma sai kiran sunansa take yi. A hankali ya ja jikinsa ya matsa kusa da ita, sai ya ji tana surutai. "Abbaa kaga Iftihal ko, Abbaa wai ba za ta yi wasa dani ba da Innti za ta yi, Abbaa ka ga sun tafi sun barni suna mini dariya, Abbaa kalli kaya iri ɗaya zan saka. Nima ka siya mini irin kayansu ka ji" "No" ya ce cikin sauri yana girgiza kai. "Ba za ki saka irin wannan kayan ba, ba yanzu ba, ba nan kusa ba in sha Allah Shetty" ya riƙota jikinsa gabaɗaya ya rungumeta sosai kamar zai mayar da ita ciki ya sake haifar ta haka yake ji, wata sabuwar soyayyar Ana ce me zafin gaske ta shiga huda zuciyar Yaya, wani irin hope, da wish tare da dreams me girma ne suka shiga yawo a cikin zuciyarsa. Dole ya ɗauke Ana ya kaita inda ake buƙatarta, inda za ta yi farinciki da jin daɗi, amma ba za ta iya farinciki ba idan babu Iftihal da Innti a cikin rayuwarta. Dole ya shafe mata tunaninsu gabaɗaya a cikin kanta da zuciyarta, ta yadda za ta mance ta yi rayuwa dasu. Saboda nutsuwar zuciyarta zai yi hakan. A hankali ya sumbaci goshinta, ya sake sumbatar gefen kuncinta, a nutse ya zura yatsun hannunsa guda biyar cikin nata ya haɗe su gam. "Rayuwarki ta zama tawa, Abbaa ya zama naki ke ɗaya, zan sadaukar da komai nawa saboda ki yi farinciki, sbd ke" ya yi shiru yana kallon fuskarta me kyau Ya ɗora fuskarsa a saman tata ya ce "Ina fatan ba zan zama mai laifi a gareki ba a sanda kika tuna matsayin Innti da Iftihal a rayuwarki, ina fatan ba za ki guji Abbaa ɗinki ba. Rayuwata taki ce Shetty, ina rayuwa dominki ne a gidan nan shettyyy" Ya ƙanƙameta for a while. A hankali ya kwantar da ita, ya miƙe ya nufi wajan wata jakarsa ya ɗakko turare ya dawo gabanta, ya haɗe hannayensa biyu sai ga wuta ta kama ya saka turaren, ya fara shaƙa mata, cikin fitar hayyaci ta fara tari sosai ƙirjinta na ɗagawa sama, jikinta ya ɗauki rawa ta shiga girgiza, da ƙarfi ta yi ihu sai kuma ta kira sunan Allah, maganarta ta ƙarshe shine ambaton sunan Iftihal da Innti. Jikinta ya ɗauki zufa ta wanke mata fuska ya miƙe ya fice. Yana fitowa Maman Haysaam da shi kan shi Yaa Sam da wasu matan maƙota suna shigowa cikin gidan, Maman Haysaam ta fashe da kuka tana salati. Da aka sanar da Daada ƙin zuwa ya yi, sai Emama da Liya da Hanna ne suka shigo, suna fashewa da kuka. "Baiwar Allah, mace mai haƙuri da kawaici Allah Sarki Innti" a cikin wannan lokacin Jaheed da Jadid da Yaya suka sauƙewa Innti Kur'ani tare da Yaa Sam daya zama kamar jininsu. Babban yaya da kan shi ya yi wa Innti wanka, ƙamshi sai tashi yake a jikinta, ya sha kuka saboda duk inda ya juya jikin Innti, shatin dukan Daada ne. Ya zubawa ƙasan cibiyarta idanu, saboda zanen wani tambari daya gani, ya rasa kuma wanne tambari ne wannan? Ya wanke ta tas, ya shirya ta, da aka zo tafiya da ita sai ya samu kan shi da riƙe gawar ya kasa saki, da ƙyar Yaa Sam ya zame hannun Babban yaya. Jaheed tun bayan maganar Babban yaya ko tari ya kasa, idanunsa ya bushe gabaɗaya bai san me yake ji a ransa ba. Bayan an yi mata sallah, sanda aka binne Innti Jadid ya yanke jiki ya faɗi a jikin Babban yaya babu numfashi haka Jaheed. *** Asuba a tasha ta yi wa Ahlam, ta shiga motar da za'a kaita zuwa Banue state. Ta yi kuka har ta gaji idanunta sun kumbura sosai, amma taja ji this is the only way, da zata iya samun damar cika burinta, zata samu damar amsa sunan cikakkiyar ƴar jarida kuma ƴar gwagwarmaya. Ta san Engineer dole zai yi baƙinciki, amma tana hango farincikin da zai yi idan ya ganta ciki matsayin da za ta taka. "Liman?" Ta ƙira sunansa a hankali tana dafe ƙirjinta, ta so Md, ta ƙaunaci Md, kuma tana fatan rayuwa dashi ta har abada, za ta dawo tabbas. Ta lumshe idanunta, tana sauraran waƙar “Im coming home" tare da binta a hankali. 6:00 motar ta ɗaga tare da barin tashar, Ahlam ta ji kamar rayuwarta ta bari a kano kacokan, dukkan wani farinciki da jin daɗi sannu a hankali ta ji suna yin ƙaura a jikinta. Yana daga bakin ƙofar hannunsa riƙe da casbaha ya ce "Wai Jiddah tashin baby ne haka?" Daga cikin ɗakin Anty Jiddah ta ce "Abban Mufeed, Ahlam bata ɗakin fa" "What?" Ya ce yana shigowa da sauri. Aunty Jiddah ta ce "Wallahi, shigo ka tayani ganin ikon Allah, har banɗaki bata ciki fa" Engineer ya shiga duddubawa, ya fita waje ya shiga kiran sunan Ahlam amma shiru, duk inda suke expecting ganinta bata nan. Da aka mira me gadi yana duba gate ya ganshi a buɗe, gaban Engineer ya faɗi, hankalinsa ya tashi sosai. "Abban Mufeed ko dai kidnapers ne suka shigo suka ɗauke Ahlam, da za ta kwanta bacci sai da ta yi mini sai da safe fa. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Engineer ya ce "Kidnapers?" Ya girgiza kai "Kuma su ɗauki iya baby kawai? Duk mutanen gidan sai ita kawai?" "Abin ne da ɗaure kai, amma ka ƙira Asad ka ji, ko suna tare da ita da" ya kalle ta ya ce "Jiddah, kin san me kike nufi, by this time ki ce wai Ahlam na tare da wani? Gabaɗaya yaushe aka idar da sallar Asuba ne?" Ta ce "Naga mijinta ne, ba abin mamaki bane" Ance ba'a ƙin ta mutum sai ya juya zuwa cikin gidan kai tsaye ɗakinsa ya shiga ya nemi inda ya ajjiye wayarsa, number Md kuma Liman ya nemo, a ringing ɗin farko ya ɗauka kamar me zaman jiran ƙiran ya ce "Wify, ina kika ajjiye wayarki kika ɗauki tasa?" Jin hakan ya saka Engineer dafe kan shi da ƙyar ya ce "Asad, Engineer ke magana" Liman ya yi ƙasa da murya ya ce "Afuwan Yaya, good morning ya hanya?" "Allahamdulillah. Nace Ahlam fa?" "Ahlam" Liman ya maimaita a kan harshe, ya kuma kasa bawa Engineer amsar tambayar da ya yi masa domin bai fahimta ya san by now shi da ita ai suna tare a hanyar Abuja. Engineer ya ce "Asad, why? Ai ka bari a yi bikinmu me ya sa zaka ɗauki yarinya ka tafi da ita? Har ta kwana a wajanka, this is wrong" again, Liman shiru ya yi saboda wani shock da tsoro kuma da ya ratsa masa cikin zuciyarsa. A hankali ya ce "Wajena?" Ya ɗora da "ta ce za ku je Abuja, har ta nemi izinin tafiya a wajena, Yaya ya zan ɗauke ta ta kwana a wajena, bayan a gida nake rayuwa ban taɓa yi nini a hotel ba. I thought ma ita ta kira da lambarka" Engineer ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" "Lafiya menene ya faru?" "Asad, bamu da yan'uwa a Abuja, ba mu da kowa a Abuja, asalinmu ƴan Maiduguri ne, a sanadin boko haram muka rasa ƴan'uwanmu, Ahlam ba ta da kowa da za ta ziyarta idan ma akwai suna rayuwa ba mu san ina suke ba, Ahlam ita ta rage mini, nima ita kawai nake da ita, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ko wani abu ya faru ne wanda ban san dashi ba? An shigo har gida an sace mini baby, su waye wannan? Me ta yi musu? Ina baby take yanzu wanne hali za ta shiga ne don Allah?" Liman ya yi shiru. A hankali ya ce "Bari na zo gidan Yaya" Ya kashe wayar. Engineer da ƙyar ya ja jikinsa zuwa cikin gidan ya zauna saman kujera kan shi a ƙasa, wasu hawaye masu zafi suka shiga bin fuskarsa, duk yadda yake tunanin abin da fasalta shi a zuciyarsa ya kasa fahimtar cewa she run away from the house, zuciyarsa ta cunkushe ta shiga buga masa. Anty Jiddah ce take sakkowa daga saman bene wajan faɗin "Engineer ga abin da Ahlam ta bari akan gadonta, tabbas gudawa ta yi, amma yarinyar nan ba ta kyauta mana ba, idan auren ne ba ta so me ya sa ba za ta faɗa ba, sai ta ɗauki hanya ta gudu ta bar gida? Haka aka ba ta tarbiyya ko haka shine mafita a gare ta, ina za ta? Ina take fisabilillahi?" Ya amsa takadda har biyu, ɗaya an saka sunan Yaya a jiki ɗaya kuma Liman, wanda yake nuna tabbacin bashi da ikon dubawa balle ya karanta. A hankali ya buɗe tasar ta fara karantawa inda ta fara rubutun da; "Yaya zan tafi ba tare da yadda da izininka ba, saboda na san ba za ka amince mini ba, kai ba kawai Yaya bane a wajena, kai ne uwa kuma uban da nake gani ƴan'uwana gabaɗaya. Ina son ka sosai ina gudun ɓacin ranka, na kuma amince da auren da ka yi mini saboda ina son Asad sosai Yaya, zan kuma dawo gare ku a kai ni gidansa na aure na yi rayuwa kamar yadda kowacce take yi a gidan mijinta. Ina da buri sosai akan aikina, ina son aikin jarida Yaya ina jin ƙaunar aikin a jinin jikina, ina son na kawo sauyi a harkar jarida musamman a ɓangaren mata Yaya. An yi taron karrama ƴan jarida ban fuskanci komai ba sai baƙinciki da baƙinciki, na yi kukan da zuciyata ta kusa samun matsala, ban taɓa takaicin nakasar da nake da ita ba sai yau. Na tafi Yaya, zan dawo a lokacin dana amsa sunan ƴar jarida cikakkiyar, zan dawo idan na samu ɗaukakar da nake fata, zan dawo da abin mamaki kuma bazatar da duniya za ta yi mamaki da ita. Kar ki yi mummunan tunani a kaina, zan tsare kaina da mutuncina ba zan taɓa yin abin da zai taɓa ƙimata da taka ba. Ka yi haƙuri Yaya ka yafe mini kuma ka yi mini addu'a, ka bawa mijina haƙuri ka rarrashe. Ahlam Abdallah Kurmi" Tun kafin ya gama karantawa idanunsa yake zubar da hawaye, ya ji kamar ya samu matsala da zuciyarsa da kuma jikinsa, ya yi shiru yana sauraran bugun da zuciyarsa take. Aunty Jiddah ta saki salati tana fashewa da kuka. "Ahlam me ya sa za ki mana haka, duk irin abin da za ki fuskanta ba gwara kin zauna kusa damu ba?" Muryarsa mai sanyi ta sauka a cikin parlourn yana yin sallama, shine na farko sai Mu'allim da yake bayansa, hannunsa manne da kanuna yana sanye shadda mai ruwan duhu data amshi jikinsa sosai ya rame ya sake haske. Liman kuma tattausar Jallabiya ce a jikinsa wacce ta yi kwance a fatar jikinsa, tunda ya je masallaci Baffa ya ja su jam'i ya dawo gida ya ji wannan tashin hankalin kasa motsi ya yi, da ƙyar ya iya faɗawa Al'ameen, duk da Al'ameen ɗin babu lafiya shine ya yi ƙoƙarin yin driving nasu zuwa. "Barka da asuba" cewar Mu'allim yana miƙawa Engineer hannu su ka yi musabaha ya gaida Anty Jiddah. Liman kasa magana ya yi "Gashi, saƙon da ta bar maka" Liman ya amsa ya buɗe, shima a nutse ya fara dubawa da; "To my one and only Zauj, Mr Asad Hafiz Hafiz Hafiz. Na rubuta maka wannan a lokacin da bani da wani zaɓi bayan abin da nake jin zan aikata shi ne daidai. Na rubuta maka wannan a sanda zuciyata ta cika da so da ƙaunarka, yes, ka fahimci ina son, kusan kai ne confidence ɗina a Bright Fm, ina tsintar kaina cikin tsananin kishi idan na ganka tare da Yussy... Na maka ƙarya na ce zan ji Abuja haƙiƙanin gaskiya ba mu da kowa a can, na yi haka ne kar na tafi da haƙƙinka na fita ba tare da izininka ba. Abin da Yussy ta mini zai iya saka mini ciwon zuciya, na kasa haƙura na kuma kasa mancewa. Na ji sanarwa BBC a jiya da Hausa France International RFI suna neman wani sabon tarihi da za su wallafa a ranar Hausa ta duniya, na tafi zuwa ga neman abin da zai dace da su, ina da tabbaci za su buƙata kuma duniya za ta san dani a wannan rana, ta HAUSA INTERNATIONAL DAY. Wallahi Liman i so much love you, I love you with all my heart and soul, I love you to the Extra Liman. Zan kare maka kaina da mutuncina, za ka same ni yadda kowanne miji yake samun matarsa, ba zan taɓa kallon wani namiji a bayanka ba, ina fatan kafin na dawo zaka soyayyata a cikin zuciyar danginka, ina fatan daga nan har na dawo na tsaya a gabanka mijina ba za ka taɓa kallon wata mace da irin kallon da kakewa Halimatul Sadiya ba. A ranar dana dawo a wannan rana ba zan kwana gidan kowa ba, sai gidan mijina Mr Asad Hafiz Hafiz fa, a gadonsa zan kwana rungume a jikinsa. I love You Md, Liman, Asad. I'll be back sooner or later bye. Ur wife Ahlam" Ya naɗe takaddar ba tare da ya ce komai ba, wannan shirun kuma har gwara ya ce wani abu ko babu yawa. Engineer ya ce "ka yi...," "No need Yaya, i can wait for her" Ya yi shiru yana jan numfashi da sauƙewa yana jin zuciyarsa ta yi masa nauyi sosai. "Bani da wata mata a duniya sama da Halimatu, zan jira ta, zan jira ta jira na iya adadin da za ta ɗauka kafin ta dawo Yaya" "Amma Asad...., "No please, na fahimci uzurinta, akwai wauta da ƙuruciya a tattare da ita. Ka yi addu'a za ta dawo da nasarar da take fata, ina addu'ar Ubangiji Ya sa ta je a sa'a. Ni na san ba za ta iya jurewa ba tare da ta yi notifying ɗina ba, zan jira ranar daga sanda ta neman a sannan zan yi tracking numberta zan bita zuwa inda take" ya yi ƙasa da kan shi a hankali ya miƙe tare da kama hannun Al'ameen da yake jingine da jikin Liman ɗin yana riƙe da hannunsa ya ce "And please, kar ka yi cigiyarta, saboda tana da ɗaukakar da zuwa gaba zai iya taɓa ɗaukakar data samu. Thank you Yaya" Engineer yana jin tausayin kanshi, amma ganin Liman ya ji kamar shi ne abin tausayi, yana son Ahlam sosai yana ƙaunarta Allah ya bashi haƙuri da juriya kawai. Anty Jiddah ta kawowa Engineer shayi ya ce "Ga tea ɗin" "Bana jin yunwa Hawwa'u" Ta yi shiru na wani lokaci. Wayarta ce ta fara ringing, ganin sunan matar abokin mijinta ya saka ta ɗauka ta ce "Firdausi ina kwana ya kwanan yaran?" Ta cikin wayar Firdausi ta ce "Alhamdlh Jiddah, daman akan maganar ƴar aikin da kika ce kina so ce, ga wata an samu, ba su jima da zuwa Kano ba, wai ƴar gudun hijira ce daga Barno shine na ce bari na kira ki" Jiddah ta yi jim ta juya ta kalli Engineer ta ce "Firdausi zan kira ki zuwa anjima, amma batun aikin nan kamar na fasa ɗauka fa, idan na yanke shawara za ki ji ni in sha Allah" kashe wayar ta yi, ta shiga lallashin Engineer daya lumshe idanunsa yana ta kokawa da numfashinsa ya kasa jure rashin Ahlam a kusa dashi. Wayarsa ya ɗauka ya kunna data ya shiga page ɗinta ko zai ga ta yi update na wani abu, madadin hakan sai ya ga vedion Ahlam ne tana kuka sosai kanta a ƙasa, wacce ta yi posting ta saka caption na. "Ƴar jarida Ahlam Abdallah Kurmi, a wajan taron ƙarshen shekara na karrama ƴan jaridu. Tana yin kuka saboda bata samu award na Outstanding Journalist ba" Vedion ya je viral, ya samu a ƙalla viewes wajan 5M. Ga sharing da comments kamar hauka, ya miƙe da ƙyar yana shirin fita daga gidan ya yanke jiki ya faɗi a tsakiyar parlourn. *** TIVLAND 1976 Haan ya kasa yadda da maganar da Kaka yake yi na cewa sun rasa Anum da Jarumi. Ya yi cikin gidan da sauri, har lokacin iska me ɗauke da guguwa na tashi yana ɗaukan mutane sosai. Sanda ya shiga sai ya ga cikin inda su ka yi gininsu a gaɓar kogin ya tsira ya shiga yana duba inda Dooshima ya ɓoye Anum da Jarumi. Cikin sa'a ya ga ramin ƙasan ya buɗe, daga Anum har jarumi babu me numfashi a ƙirji haka ya ɗaƙƙo su yana kiran sunan Kaka da ƙarfin gaske, kwantar da su aka yi a gefe aka shiga yi musu magani. Anum ta riga farfaɗowa a gigice ta shiga girgiza Jarumi tana kiran sunansa, wata soyayya ce me ƙarfin gaske a tsakaninta da Jarumi, soyayyar da ko iyayensu basa yi wa hakan. Kaka ya sauke numfashi ya ce "Uwa" "UWA MAMA kina ina? Ki kawo mana ɗauki ki, maganarki muke jira, furucinki muke jira" Haan ya ce "Kaka anya ba za mu fita neman uwa mama ba? Yaushe za mu jira zuwanta? Yaushe za ta zo garemu? Tana ina? Tana kusa da mu ko tana nesa da mu? Tana duniya ko ba a haife ta ba? Ya kamaninta suke Kaka?" Kaka ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce "Haan, ba a faɗa mana suffarta ba, haruffan sunanta kwai aka bamu, sunan Uwa Mama za a iya samun a haruffan A, ko H, ko F, Mama tana ɗauke da Tsav ne, Tsav wani tsohon tunani ne na gargajiya a al’ummar Tiv wanda yake da alaƙa da:bikon asiri, sihiri, ƙarfin ruhaniya,ko wata baiwa da ake ganin mutum yana da ita ta ɓoye. A fahimtar gargajiyar Tiv: ana ganin wasu mutane suna da “Tsav” a jikinsu wanda zai iya ba su ikon yin abubuwa na al’ajabi ko cutarwa, waɗannan mutane su kan su basu son suna da wannan baiwar ba, wannan baiwar ita mu Tubabe muke so da buƙata" Haan ya ce "Yanzu kaka yaya za mu yi?" "Dole mu jira bayyanar Uwa mu roƙi Aondo ya kawo mana ita, bana son Akombo ya sake yin fushi damu Haan, wannan shine" Dare ya yi, cikin dare suka farka da wani sabon tashin hankali, gabaɗaya gonakin da suke noma a ciki wuta ta kama a cikinsu, komai ya ƙone tas, ga gawarwakin mutane da suka gani zube. Sati ya shuɗe haka watanni babu Dooshima babu labarinsa, hankalin Anum ya tashi sosai, kaka ne ya shafe mata tunanin Dooshima tas kanta da zuciyarta, ta mance ta dinga kallon Haan mahaifin Jarumi a matsayin nata uban. Sojoji suka dawo, a wannan lokacin babu tashin hankali. Suka kalli kaka suka ce "Ya muke ciki daki ne?" Kaka ya ce "Mun amince da sauyin da za ku kawo mana, ina roƙan Aondo ya baku damar dawo mana da Dooshima da aminci" Sojan ya ce "Dooshima? Bai dawo ba?" "Kun sake shi ne?" Sojan ya kalli Haan ya ce "Me zai saka mu riƙe shi? Baya wajanmu, tun a lokacin ai mu ka saka a kawo shi kan iyaka damu" Uji da Terhemba suka kalli juna. A 1976 aka sake ƙafa tsarin Mulki na TOR TIV aka naɗa Kaka matsayin shugaban Tubabe. Wannan mulkin ya baƙanta ran Imande family sosai, aka yi shagali akai Swange dance Kwagh-hir (wasan kwaikwayo da al’adar Tiv) Tsarin Tor Tiv, ba sai ka mutu ba, akwai adadin da ake ɗauka a yi juyin mulki zuwa wani family, don haka Imande suka matso ƙwarai mulkin ya ƙare daga hannun Ikur family. Kaka ya mutu, nan take aka ɗauki muƙami aka bawa Terhemba. Haan yana ɗaya daga cikin dattawan masu zartarwa duk da haka ya zama ɗan kallo, ya bada shawara akan yadda Terhemba ya fara sawa na kawo masa mata yana lalata budurcinsu akan neman Uwa Mama da yake. Jarumi yana da shekaru goma a duniya, ya fara kulawa da Tor Tiv da dukkan zuciyarsa, duk rikicin da za a kawo musu yana ɗaya daga cikin jaruman da suke kare tubabe. Ya zama zakaran gwajin dafi wajan faɗa da wasa da kibbau, yana da sha'awar wasan ruwa, kodayaushe yana gefen ruwa ƙafafunsa a ciki, ga wata soyayyarsa da aka ɗorawa jama'a, duk inda aka ce ga Jarumi nan sai an cika. Murmushinsa ya fi maganarsa yawa sosai. Watarana aka wayi gari rikicin manoma da makiyaya ya ɓarke, Jarumi ƙoƙarin kare al'ummar Tiv yake, koda wasa baya taɓa zubar da jini, ko Fulani ya gani yana basu hanya. Rikicin ya yi tsanani domin jar da Junkun a kawo musu hari. Bayan komai ya lafa jikinsa duk jini ya nemi Anum ƙasa da sama ya rasa babu ita babu alamar ta, ba ƙaramar ɓarna Fulani sukai musu ba. Jarumi ya yi kukan rashin Anum ya sake zama shiru shiru a wannan lokacin kuma dukkan Tiv suka amshi addinin kiristanci, aka fara daina gargajiya mutane suka fara zuwa cuci, aka gina makarantu da kasuwanni. Amma duk da haka wasu ba su daina gargajiya ba, kamar yadda ba su watsar da tsafi ba. A wannan lokacin Terhemba da Uji da Haan su ka yi tafiya, sanda suka tashi dawowa babu Haan sai gawarsa da ta ƙone sun yi tsari kuma shi kaɗai ne ya rasu. Maraici kota ina ya rufe jarumi. Shekarar 1976 tana da muhimmanci sosai a tarihin yankin Tiv. Najeriya a 1976 A lokacin soja ne ke mulkin Najeriya. Shugaban ƙasa shi ne Olusegun Obasanjo (bayan mutuwar Murtala Muhammed a Fabrairu 1976).Babban Abin Da Ya Faru a 1976 1. Local Government Reform (Gyaran Ƙananan Hukumomi) A 1976 gwamnatin soja ta yi babban gyara: an ƙarfafa ƙananan hukumomi, an tsara shugabancin gargajiya, an ba sarakuna rawar hukuma. A yankin Tiv: an ƙara ƙarfafa matsayin: Tor Tiv da kuma: Tiv Traditional Council. Ba a kafa Benue State ita kaɗai ba tukuna. A lokacin: Benue-Plateau State ce. Sai a 1991 aka raba: Benue State da Plateau State Benue ta zama jiha mai zaman kanta Inda Tiv sukai rayuwa ya zama River Benue. *** Sannu a hankali take juya kanta da yammacin, mafarkin da ta yi a yau na rashin Anum ya sake saka mata nauyin zuciya. Da ƙyar ta buɗe idanunta da suka kumbura sosai, kwananta huɗu kenan a haka, hakan ya yi daidai da kwana uku da rasuwar Innti. "Abbaaa" ta ce a hankali tana yi masa murmushi me kyau, domin a fuskarsa ganinta ya sauka, kanta a kan cinyarsa yana gyara mata sumar kan da a kullum baya rabuwa da gyara mata. Jadid ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Finally, gudan jinin Abbaa ta farka" sai ta masa murmushi. Jaheed da yake ta firfita wuta idanuna cike da hayaƙi yana ƙoƙarin dafa taliya ya ce "Sannu da turmushe wa Abbaa cinya" Ana ta miƙe a hankali ta kalli Abbaa shima kallon ta yake, ta tsorawa cikin idanunsa ido sai ta shagwaɓe fuska ta ce "Abbaa wai haka?" Ya girgiza kai ya ce "Ko goyo kike so zan miki shi har ki sake yin wani baccin" Jadid ya kasa dauriya ya ce "Ba ki tambayi Iftihal da Innti ba" ta yi shiru alamar tunani zuciyarta ta buga da gaske kanta ya sara ta ɗan rirriƙe kanta ta ce "Su waye haka?" Su ka yi shiru suna kallon ta, Jadid ya juya yana share hawaye. Sai ta juya idanunta ta ce "Nifa ban san so ba, Allah da gaske" Daidai nan Yaa Sam ya yi sallama yana ganinta zaune kusa da Babban Yaya ya ja idanunsa ya lumshe yana jan numfashi da saukewa. Su Jaheed suka gaishe shi, idanunsa akan Ana ya amsa. Ta gaishe shi ya ce "Ya jikin nakin?" Ta juya idanunta ta ce "Abbaa wai ya jikina bani da lafiya ne?" Bai amsata ba, bata da sukuni yanzu komai ta ce Abbaa. "Ya ƙarin haƙuri kuma?" "Waye ne ya rasu kuma? Daada? Allah Ya sa shine ya mutu Allah Ya sa babu shi a raye" Babu wanda ya san meke faruwa da Ana sai Abbaa gabaɗaya ya shafe mata tunanin Iftihal da Innti. Yaa Sam ya yi musu sallama ya fita Ana ta yi kwanciyarta akan cinyar Abbaa yana ƴan wakoƙinta deep down tana jin kewa me zafin gaske, tana jin kamar bayan ita akwai wasu daban da suke tattare da ita. Jaheed ne ya yi musu girki suka ci, da dare ya yi a ɗaki ɗaya suka kwanta, Jaheed da Jadid shimfiɗa ɗaya, Ana tana shimfiɗar Babban Yaya ta shige jikinsa sai bacci take. Idanunsa biyu, suna haka Daada ya shigo a yadda ya saba shigowa, duk suka farka har Ana ta fito. "Ki shirya gobe zan kai ki wajan Alhaji Baita, a madadin ƴar'uwarki dana saka a caca, ya ce dole sai na biya shi" Ana ta sheƙi da dariya ta ce "Ko ba biya ba" Ta san cacar, fresh komai yake kanta matsayin Innti da Iftihal da kasancewar su a gidan duk ta mance bata ma san so ba. Daada yayo kanta Abbaa ya shiga tsakiya, shi dai ya san yana ɗora hannunsa akan Daada tsaf za'a ɗauke shi babu rai, kuma hukuncin zai hau kan shi, duk abin da zai raba shi da Ana baya so. Kuma har yanzu yana riƙe da umarnin Innti akan Daada. "Muddin kaga ban bawa Baita ita ba, ka ɗauka bana raye a duniya ne wallahi" Sannu a hankali Ana ta fara tuna irin makamancin wannan maganar da ya yi a baya. Rawar da zuciyarta take yi, ya haddasa wa jikinta amsar ta yin da zuciyar ke yi masa. “kuɗi ya fi mini komai akan ta, farincikin da nake ciki idan na ga jaka guda, ya fi mini kallon ta, matsayin ɗiyar cikina, ba ita ba, hatta uwarta zan iya sadaukar da ita muddin za a cika lalitata da kuɗi wallahi” Sannu a hankali, maganganun suka shiga dawo mata tare da kai komo a cikin kanta. Suna yi wa ƙwaƙwalwarta tuni! “Bani da ko sisi, ina kuma buƙatar sulalla na gaji da zama da dattin aljihu, na shiga caca, na kuma yanke shawarar sanya Ayshatul-Iftihal a cikin cacar, idan na ci za ta cigaba da rayuwa a gidan nan, akasin hakan na sadaukarwa da Alhaji Baita ita akan cacar” Sai ta ji daren na yi mata nisa, tuna cewa Alhaji Baita ya bawa shekaru Sittin baya. Kaddarar wasu mutanen na zuwa cif da cif kamar sune suka zanawa kansu taswirar rayuwar, tun daga farko har ƙarshe fari tas take, kamar yadda rayuwar Nadiyaah ta kasance, komai na rayuwarta kamar ita ce da kanta ta zaɓawa kanta yadda za ta wakana. Wasu kuma raba dai-dai suke yi, daga farko farinciki irin mai mantar da mutum wani abu kan iya faruwa dashi na ƙaddara, sai daga baya reshe ya juye zuwa mujiya, kwatankwacin rayuwar Ahlam Abdallah Kurmi. Wasu mutanen kamar dare biyu haka rayuwarsu take ciki saboda ƙaddarar da ta yi musu ƙulli, babu farinciki ko kaɗan kamar yadda ta kasance a rayuwar; ANA. Wasu mutanen kuma gabaɗaya ƙaddararsu a baibai ba su fahimci kansu ba, balle su fahimci ƙaddararsu har su yi maganinta. A ɓangaren Batty hakan lissafin yake a rigar Biya gidan Dikko. Ta ɗaga jajayen idanunta cikin ƙunci da raɗaɗin zuciya ta ce "Allah Ya nuna mana gobe, ko gawata ko ta Babana..," Sai ta yi shiru. "Ko ta Alhaji Baita" Gabaɗaya suka kalle ta banda Yaya. Bayan sun koma bacci, wannan sanyin da yake ratsa jikin Yaya shine ya fara, ya yi iya ƙoƙarinsa wajan hana hakan faruwa amma ya kasa. Sannu a hankali sanyin ruwan kogin ke ratsa jikinsa alamar baya tare da Ana a yanzu ɗin. Itama data farka bata ganshi ba, babu kowa sai ita, fresh tunaninta ya dawo ta ƙwala kiran sunan Innti da Iftihal a gigice, ta dinga kuka da ihu ta bigirma ta rarrashi kanta. Hijab ta ɗauka ba ta ganin ko gabanta ta shiga Napep ta ce Hisba Headguater. Tana zuwa ta kalli wani mutum ta ce "Shugaban ƴan Hisba nake son gani" Ya kalle ta sosai, yarinya ce bata fi 17 years ba. Ya ce "Baya nan ki bada bayanin abin da kike so za a sanar dashi ko?" Ana ta girgiza kai ta ce "Matsalata ai bata ƙananun ma'aikata bace, shugaban Hisba ɗin nake son gani da kan shi, akwai abin da zan faɗa masa wanda sirrina ne, kuma na yi masa wasu tambayoyi" ya dinga kallon ta da mamaki yace "Ikon Allah, ƴar ke ɗin nan ce kike da matsala, ko auren dole za a yi miki?" Wani irin jirkitaccen kallo Ana ta yi masa. "Malam ba wasa na zo ba, keep a joke aside please. Ina shugaban Hisba ɗinku yake?" Ya ce "Me kike buƙata a wajansa?" "Ƙarar mahaifina na kawo. Ina so ya kawowa rayuwata ɗauki, kamar yadda ka ce haka ɗinne, auren dole za a yi mini kuma bana so, domin ni ba matar tsoho bace, ina so ya shiga tsakanina da mahaifina. Ni na yarda zan yi aure idan ana buƙatar hakan, amma idan shugaban Hisba ɗin naku ya amince zai aure ni. Auren rufin asiri kafin na samu wanda nake so" ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya har ta juya ta dawo tace "Oops, ka faɗawa shugaban Hisbar taku, na kawo ƙara idan bai ɗauki mataki ba, dukkan abin da ya samu da faru da rayuwata shine sila kuma shine sanadi, ga number wayata" Ta bada number Yaa Jaheed. Tana fita ya saki dariya kawai ya cilla number a bakinsa ya taune tas. *** BIYA. Yana kwance bakin ruwan yana rawar ɗari hannunsa dafe da ciki da kan shi, idanunsa rufe ruf dasu. Gabaɗaya hankalinsa yana kan Ana da tunanin halin da take ciki, ko yatsarsa ya kasa motsawa. Ya yi namijin ƙoƙarin ɗago hannunsa ya ware takaddar da Innti ta rubuta kafin ta rasu, kyakkyawan rubutunta ne ta ce "Yaya ban sani ba ko za ku dawo ku same ni, zuciyata ta yi mini nauyin dana kasa tantance abin da yake damuna, idan na tuna na yi saɓon Allah wajan yin biyayya ga Daada sai na ji kamar zuciyata za ta fashe. Na sani babu biyayya ga mutum wajan saɓa wa Ubangiji, amma na biyewa Daada mun aikata son rai. A jiya na sake jin wa'azi,"Lā ṭā‘ata li makhlūqin fī ma‘aṣiyatil Khāliq." Ma'ana: "Babu biyayya ga wani halitta idan biyayyar za ta jawo saɓa wa Mahalicci." Yaya ya zan yi da hakƙin Iftihal, na yi lafila na roƙi zaɓin Ubangiji, ina da yaƙinin ya amsa kuma ya gafarta mini. A yau da safe na fahimci ina yi wa Daada biyayya ne saboda ban san wacece ni ba, bani da alaƙa dashi ta kusa ko ta nesa balle ta jini, ina tunanin tsoron gaskiya ta bayyana ku tambayi wacece ni ko asalina, ban sani ba, kuma zai iya korata ya ƙwace mini ku" Sai ta yi sakin layi ta ce "One day I may die without saying goodbye to you but I'll never forget to say thank you, because you hold most lovely part of my life. Ina rubutu wannan a lokacin da tunanina ya dawo na san wacece ni, ina tsoron na sake mancewa, zan tafi da raɗaɗin sabon Ubangiji da na yi, Yaya an ce; Ana biyayya ga mutane ne a cikin abin da ya dace da shari'ar Allah. Idan umarninsu ya saɓa wa umarnin Allah, to a ƙi bin umarnin cikin ladabi da hikima, domin biyayyar Allah ita ce tafi kowace biyayya. Muddin ina raye kuma na cigaba da mance kaina zan ta aikata saɓon Ubangiji wajan yi wa Daada biyayya, na riƙo zaɓin Ubangiji" Ta sakin layi. "Na bar maka Ana duniya da lahira, ta amsa sunanta da naka, Aysha Muraad Ana. Ka kula mini da ita don girman Allah Abbaa, asalina ba musulma bace, daga baya na musulunta. Sunana.... Sunana.... Sunana" Ta rubuta sunana sau wajan biyar kafin tace "Sunana ANUM" "Laaa kaɗo, ka dawo kai ne?" Muryarta Batty ta sauka a cikin kan shi, ya yi saurin rufe idanu yana damƙe hannunsa. "Ina ta nemanka shine ka gudu ka barni, ko kana tsoran na cinye ka ne? Ni fa mayya ce" Babban Yaya ya yi wa Batty shiru. Ta washe bakinta ta ce "Kyakkywa ne kai, kalli gashin fuskarka me kyau, kuma kana wanka kullum kana ta ƙamshin abinka ko?" Ta miƙa hannu ta shafin kwantaccen sajen gefen fuskarsa "Innalillahi, laushi" ta faɗa tana yin saurin ɗauke hannunta ta ce "Kai" Ta zungure shi, ko motsi bai ba, "baka magana?" Ta zabga uban tagumi "Allah sarki kurma ne, sunana Batty" Ya yi mata burus sai ta sunkuya dai-dai fuskarsa ta zaro harshe ta ce "In cinyeka na lashe ka" harshenta ta taɓa tsinin hancinsa. *** Suna zaune da yawa. Ɗaya daga ciki ya ce "Idan mu ka yi wasa Sayyadi Baffa zai ɓata mana sabuwar gwamnatin da muka kafa, ya zama dole mu ɗauki mataki akan shi, kamar yadda muka ɗauka akan Hafizz Hafizz Baffa, a shekarun baya shi da ƴarsa Diyanaah Hafiz Hafiz Baffa, ba za mu zuba idanu ya rusa mu ba, kuma dole adadin musulmai a ƙasar nan ya yi ƙasa, kun san ba za su taɓa zaɓar Jonathan ba, suna da kishin musulunci" a hankali ya numfasa kafin ya ce "Ba iya Baffa ba, hatta Major sai mun ɗauki matakin gaske a kan shi, za su iya zame mana matsalar gaske a tattare da tafiyar nan?" A hankali ya jinjina kai kafin ya ce "Ya batun wannan maganar da aka yi?" Madubi ya ce "Tana nan, an gama jadawalin su ɗari ne cif Yaranka ya daɗe" ya yi shiru. "A faɗawa Baita ya rufe bakin jama'a daga abin da yake shirin faruwa a garin nan" Madubi ya ce "An gama" *** Al'amarin ya yi wa Ana zafi, ga rashin Abbaa, su Jaheed kuma idan sun fita nema sai dare suke dawowa gida. Ta ɗauki ciki takadda ta rubuta tarihin rayuwarta tas, komai da komai har batun Iftihal da Innti. Ta ɗora da "Wannan saƙon naka ne shugaban Hisba, na zo baka nan wannan takaddar ta zama shaida, rayuwata idan ta lalace akwai saka hannunka, kuma kai ne sila, ka zo ka aure ni kafin mahaifina ya rusa rayuwata, babu isasshen lokaci, duk wanda ka cewa gidan Daada a unguwar Kankarofi ya sani ga number wayar Yaya nan" ta ninke takaddar ta sake komawa Hisb Headquarter, cikin sa'a ta samu Ansar ya bata haƙurin Shugaban baya nan, amma zai bashi in sha Allah" Cikin rashin sa'a da saurin da Ansar yake yi, sai ya saka takaddar cikin jerin wasiƙun da aka riga aka karanta su a ofishin Baffa. Sanda ta dawo gida dare ya yi kuma kai tsaye ɗakin Yaa Sam ta shiga ta same shi yana ta tattare kayan da zai tafi interview da su, ta durƙushe a wajan ta fashe masa da kuka kamar ranta zai fita ta ce "Yaa Sam ina Abbaa, ban ga Abbaa ɗina ba. Daada ya ce zai kai ni gidan Alhaji Baita ba zan jure ba" "Nanaah, za ki iya aurena?" Yaa Sam ya yi furucin lokacin da take durƙushe a cikin shagon nasa a tsakiyar daren. Kasa magana ta yi, ba ta da zaɓi face abin da ya zaɓa mata. "Nanaah........... Ya kira sunanta da ƙyar ganin ta ƙi tashi ya saka hannunsa wajan ɗagota tsaye, ƙafafuwanta rawa suke sosai tana ƙoƙarin sake zubewa a wajan, sai ya taro ta ya jinginata da jikinsa ya tallafo haɓarta yana kallonta da nasa rinannun idanun wanda suke raba pain ɗin a tare ya ce. "Tun da ba ki da wani saurayi give me a chance, ki bani dama na zama mijinki Nanaah, ki bani dama" a hankali take kallon shi ta kasa cewa komai, ta rasa kalma ko ɗaya a bakinta. Ya cure girarsa ya ɗage ɗaya ya ce "Na sani, na sani kalma ta soyayya ba ta taɓa kilmawa a tsakaninmu ba, amma ina jin soayyarki a zuciyata bani da ƙwarin gwiwar faɗa miki tunda na san mene burinki. Ki bani haɗin kai wajan tallafar rayuwarki na aure ki, ko zuwa gaba idan kin samu wanda kike so sai na sawwaƙe ko?" Ta yi masa ƙuri da idanunsa. "Amma kai abokina ne, Yayana kuma" A nutse da kamewa ya ce "Kuma mijinki zuwa gobe da yamma, ki amince mini" "Amma ni bana sonka da aure fa" "Wannan ba zai zama matsala ba, idan ina sonki wadatar, kuma I will keep my promise na sakinki idan kin samu wanda kike so ko?" Kamar ta yadda kamar bata yadda ba. "Da gaske kake?" Ya jinjina kai tare da faɗin "Yeah. In sha Allah" "Na amince Yaa Sam" "Dame?" Ya tambaya a hankali yana jin wani sanyi yana lulluɓe jininsa tare da saukar masa da kasala a jikinsa. "Da auren naka" A tsayin shekarun da ya yi da ita bai taɓa sha'awar riƙe ko da hannunta bane, ko da ya riƙe bai riƙe da wata manufa ba, da gaske kallon jinjira yake mata kamar yadda yake yawan ce mata "My ƙwailata" ko kuma "Jaririyar babarta" ya ji akasin hakan a yanzu, har bai san yaushe ya taka kusa da ita ba, balle ya san yaushe ya jawo ta jikinsa ya rungume ba, sai jin goshinsa ya yi a saman nata numfashinsa na sauka a saman fuskarta ta watsa idanunsa cikin nasa itama. Da rawar murya ya ce "Ni talaka ne Nanaah, amma zan fifitaki za ki yi farinciki a tare da wannan talakan, a tare dani, mudin kin kasance tare dani. Ki mini alƙawarin za ki jira ni, ki mini alƙawarin za ki saurari dawowata?" Idanunta cike da hawaye ta ce "Na yi maka Yaa Sam, zan jira ka" Yana ta kallon idanunta ya ce "Adadin yaushe jiran naki zai ɗauka Nanaah?" Jikinta ne ya saki saboda ta san shi kaɗai ne hope ɗinta tsanin da za ta cika burinta laɓɓanta na rawa ta ce "Adadin sanda zan koma ga Ubangiji Yaa Sam, ina nan ina jiranka ba zan ƙarya alƙawari ba, zan ta jiranka ka dawo da wurwuri ka ji ko?" "In sha Allah" ya ɗora da; "Rufe idanunki" ta yi kamar ba za ta rufe ba, sai kuma ta ja idanun ta rufe. Iska ta ji ya wura mata a kunne tare da kiran sunanta tun na yarinyarta “Jerryna" sai kuma ta ji alamar saukar laɓɓansa akan nata, jikinta ne ya shiga rawa jin abin da ba ta taɓa tunani ba, ba ta ma kawo shi cikin kanta ba. Kissing ɗinta yake slowly yana riƙe da ita, idanunta lumshe hawaye na tsiyaya. Ya sake ta yana murmushi "Na samu aiki, Interview zani, da an gama zan dawo a goben in sha Allah kin ji my wife to be" Kallon shi kawai take yi kafin ta juya ta koma gida. Jaheed na ta rarrashinta yana cewa Abbaa neman aiki ya tafi. Bayan gari ya hawaye Jaheed ya fita shago Jadid ya je wajan inda ya samu aiki. Tun safe take sunturi a gidan Maman Haysaam har yamma babu labari. Daga ƙarshe Walid ne a gigice ya shigo yana cewa an tare motar ɗaliban University da suka tafi Interview Abuja a hanya, an ƙone motar tas da mutanen cikinta su wajan ɗari kuma duka zaratan maza. Ana ta yanke jiki ta faɗi. Sanda ta farka a wani ɗaki a ganta daban kuma dare ya yi, ta shiga juyawa tana tunanin Ina ne nan ɗin? Muryar Daada ta ji yana cewa "Ai Baita na samu damar ɗauke yarinyar, tunda ka bani ƙalanin da zan yi arziƙi ai an gama burina na zama attajiri" Ya yi shiru sai ya ce "Ba dai ka ce dana amshi budurcinta shikenan ba?" "Gwara ka kashe ni ko ka yi mini aure da ka aikata mini abin da kake niyya" a kiɗime ta faɗi hakan tana saka hannu wajan kakkare ƙirjinta. "Ko ka siyar dani matsayin baiwa, na san zaka samu abin da kake so Daada" Ƙafafuwanta ne suka gaza ɗaukan gaggar jikinta, ta kalli kwalbar dake hannunsa wacce ta tabbatar ta giya ce, ta sake kallon wani jan zare da kan zakaran dake ajjiye an buɗe bakinsa, da ƙyar ta fusgi numfashi wanda ya kasa sauka a maƙoshinta hatta iskar dake cikin ɗan ƙaramin ɗakin a gurɓace take shaƙarta, ganin yana tunkaro ta idanunsa sun yi jawur saboda azabar buguwar da ya yi da yadda abin da yake ji yana addabar sa tsayin kwanaki da suka gabata da zuciyarsa ta fara kwaɗaita masa ƴar cikin nasa, wannan rana ta zame masa ranar da zai jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, ko ma ya ce tsuntsaye uku masu lafiya. Ya ɗan laso gefen bakinsa yana kallon ta da miskilayen idanunsa masu tasiri. "Zan cika buri na ne a kanki tun da wancan damar ta shige ni Ana, ni ubanki ne ba zan taɓa cutar dake ba, ko na raɓe ki babu damuwa ai, kuɗi zan samu, kuma kema zan saka ki ne a turɓar arziƙi, rayuwar da muka yi baya zata zama tarihi, za ki zama sarauniya, me isa da kuma iko. Zan ƙirƙirar miki wata sabuwar duniya wacce babu kowa a cikinta daga ni sai ke, sai daula da farinciki irin wanda arziƙi ke samar wa kowa" ya ɗaga kwalbar ya tuttula abin da ya yi saura a ciki "ƙyasss" ya saki wata ƙyasa me warin data saka ta saurin ɗauke kanta zuwa gefe, ya kusantoto yana me ƙarewa surar jikinta kallo ban da ƙirjin da ta saka hannu ta kare. Ya miƙo hannunsa zai riƙota ta yi saurin zillewa zuwa gefe. "Na tsaneka Daada....," Ta kasa ƙarasa sauran maganar da ta yi niyya saboda wani abu daya tukare mata a tsakanin wuyanta da maƙoshinta ta kasa yin koda ƙwaƙƙwarar numfashi wajan da kuma saukewa. A hankali ta ɗago kanta wanda suka rine da ja asalin blue eyeballs ɗinta ya rine baka ganin komai a cikinsu wanda ya shige tsana me munin gaske, damuwa wacce bata da magani, kaɗaici wanda babu wani mutum da ya isa ya cike mata gurbin kaɗaicin da take ji yana mamaye ilahirin ƙofofin zuciyarta yana sauƙa a gangar jikinta. Ta watsa masa rinannun idanun ta ce. "Wai me kake nema dani ne Daada, me ya sa ka ɗakko ni daga gida ka kawo ni nan?" Ya ɗora hannunsa ɗaya a ƙugunsa yana sake bin sassan jikinta da kallo. Murya ba ta fita ya ce "Kin kwanta mini na kuma kwaɗaito dake, ki bani haɗin kai" "Haɗin kai?" Ta maimaita a raunace raunin daya shiga rarraba zuciyarta in to peaces ba tare data sani ba. "Haɗin kai na mene?" Ta sake nanata tambayar a karo na biyu. "Na sanki a matsayin ɗiya mace.....," "Ka ɓata mini rayuwa kenan?" Ta yi saurin tare numfashin da tambayar da ita kanta ta kusa jikkita mata tunani. "Ubana ya yi mini fyaɗe ko kuma me?" Ta ƙara ruɓanya masa tambayar, bai gama tattaro abin da zai ce ba, duk da bashi da abin cewa ya sani ɗin face cimma burinsa wanda yake tsaye a kan shi kai da fata, ya ji ta jefe shi da wata tambayar. "To idan na samu ciki fa?" Ta yi wani irin murmushi ta sakin numfashi, numfashin daya saukar mata har zuwa fuska. "Cikin ubana? Ubana ya yi mini ciki?" "Eh, Yes." Ya bata amsa sai kuma ya ce "Kin ga is normal thing a wannan zamanin, ni zan nema miki mijin aure idan hakan kike gudu, ɗan kuma mata nawa ke haihuwa suna yar da babyn a ƙwata ko bola ko dai a cilla shi a masai ko kuma a murɗe masa kai" "Anya kai ne ubana ne na jini? Kai ka haifan" "ANA!" Ya kira sunanta da ƙarfin gaske. Ita kanta sai a lokacin ta san cewa ita ta yi wannan furucin ta dai ji saukar maganar ne kamar zubar ruwan sama, kamar yadda zuciyarta ke gudu daidai da gudun ruwan, daidai kuma da bugawar lokacin daya sauya komai ya lalata komai daga cikin komai ɗin har da abin da ubanta yake buƙata a gare ta. Duk da bashi da ƙarfi haka ya tattaro abin da ya yi masa saura a jikinsa ya raromota zuwa gare shi, ta yi saurin durƙushewa a wajan tana faɗin. "Ka ji tsoron Daada, ka da ka lalata mini rayuwa, Yaa Sam nake jira zai aure ni, ya ce zai aure ni zai tafi dani. Ka ji tsoron Allah Daada...," Rikitowar da ya yi jikinta ya saka numfashinta ɗaukewa cak, idanunta ya rufe ruf babu abin da take gani sai duhu da ƙucin dake lulluɓe da zuciyarta. Wani ihu ta kurma saboda wani irin raɗaɗi da azabar da ta ji a zuciyarta kafin ya cimma burinsa, wanda ya tilasta mata dawowa daga tunanin hirar da suka yi da Yaa Sam a daran jiya, a haukace ta saka ƙarfi wajan ture Daada daga jikinta, ta yi nasarar hakan ta miƙe a lokacin da idanunta ya sauka akan wasu wuƙaƙe biyu da suke gefe, shima Daada ya ga wuƙaƙen kamar ya san abin da take shirin yi ya miƙa hannunsa, a kusan tare kowanne daga cikin su ya ɗauki wuƙa ɗaya, ta ja ta tsaya ita ko ganinsa da kyau ba ta iya yi ta fita daga cikin hayyacinta. "Gwara na kashe ki da ki hanani abin da na yi niyya" ya yi kanta da wuƙa yana zuwa ta ɗaga wuƙar ta luma masa a ciki daidai lokacin da itama ya caka mata wuƙar a ciki suka yi rakas, lokaci guda suka faɗi gefe jini yana malala a ɗakin, shi ko motsin kirki bai yi ba, saɓanin ita data motsa kaɗan ta shiga ƙiran sunan Allah da salati fuskarta ɗauke da murmushi da kuma hawayen da suke fitowa daga cikin idanunta a hankali kuma ta shiga lumshe idanun lokaci guda komai nata ya tsaya cak. LAST FREE PAGE. ƘARSHEN SHAFIN KYAUTA NA LITTAFIN HIYAAM. Idan kana son cigaban labarin, kana son shiga paid group. Za ka biya 1k kacal ta wannan account ɗin. 0116886423 Union bank Na'ima Sulaiman S Ko kuma 8164069385 Opay Na'ima shu'aibu Sulaiman. Duk account daba na Na'ima ba, to ba na littafin HIYAAM bane ba ruwana. Ka tura shaidar biya ta wannan number. 08164069385. NOTE. Littafin HIYAAM book 1 2 3 ne. Free ɗin nan ba wai book 1 bane, an cire pages ɗinne a cikin book 1. Littafin HIYAAM 1500 ne, daga yau zuwa 1 ga watan July muna tsarin discount akan 1k kacal. Muna shiga 2 ga wata ya koma 1500. Bani da ducoment ongoing ne, me buƙatar ducoment ya jira a kammala. Kuma 2k ne in sha Allah. Idan an yi payment da yawa a WhatsApp za mu yi paid book ɗin, idan ba'ayi ba, a Telegram za yi. Akwai tsarin posting a AREWAPEN. Ku yi searching sunan Littafin ku yi following account ɗina domin samun notification idan an yi update. Ina fatan za ku bani haɗin gwiwa ku biyo ni a wannan littafin babu danasi a siyan shi in sha Allah. Duk abin da kake zato akan shi ba haka bane. Follow me. Bright pens na godiya har kullum. KEEP READING HIYAAM 2026 BOOK. Sai mun haɗu daku a paid group.