*HAYATIY حياتي* 1/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-1 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing🤭*_ Wata yarinya ce ƙarama da ba zata wuce Shekara biyu zuwa uku ba aduniya ba tare da wani matashin saurayi da aƙalla zai kai shekaru goma sha biyu zuwa uku,sanye da uniform,tarin kayan wasa ne birjik gaban su kai kace shagon kayan wasa aka tara,ban da dariya ba abun da yarinyar ke yi ganin yayan nata ya tashi tsaye yana ta rawa, "Anything you need yes I'm your guide. I only wanna keep you satisfy. I just wanna be there for you.." Waƙar da yake ta yi mata kenan ita kuma tana jin dadi tana ƙara kyalkyalewa da dariya. Cikin Tsamin Muryarta na yarinta ta ce, "Yaya." Sai kuma ta yi shiru. Ganin shirun nata yasa shi matsawa kusa da ita tare da fadin, "Na'am HAYATIY." Ta kama kunnensa kan ta raɗa masa ,"Ina Shon Yayana." Kallonta ya yi kan ya ce, "Nima ina son HAYATIYna,ina ba za ki bar sona ba?" Ta girgiza kai alamar "Eh" Ya ce, "To HAYATIYN waye?" Dariya ta yi kan ta ce, "Ayatin Yayane." "SUHAIL, SUHAIL ba ka ji na ne ? Za ka makara fa ka zo ka tafi skul." Cewar Momah da ke kitchen "Naam Momah da HAYATIY zan tafi nikam yau bana so ta yi kuka." Da sauri Momah ta fito domin sarai ta san halin SUHAIL kan SUHAILA zai yi mafiyin hakan ma. "Ka yi hakuri ka ga za ta ji yunwa kuma kai karatu za ka yi,wai ma ka manta alƙawarin da ka ma HAYATIY ne? Ba ka ce za ka yi karatu ka yi kudi kamar Abu ba kuma ka sata a makaranta ta zama Likita? In baka je skul din ba ta ya za ka mai da HAYATIY likita?" SUHAIL ya kalli kanwar ta shi da tun da aka fara maganar ta zuba mi shi ido duk da kasancewar ba ta ma san me suke faɗa ba, murmushi ya sake mata kan ya ce, "Momah Hayatiyna likitace kuma ni zan biya mata da kai na natafi byeebyeee.". Hannu ya ɗaga mata yana kokarin fita ganin tana kokarin fara kukane ya sa shi saurin fita yana goge hawaye. In da sabo Momah ta saba duk sanda SUHAIL zai tafi skul da kuka suke rabuwa da SUHAILA ,shi yana yi ita tana yi. Shaƙuwar SUHAIL da SUHAILA na matuƙar ba mutane mamaki hatta iyayen na su ma. Lokacin dawowar SUHAIL na yi za ka ga SUHAIL tsaye abakin get bata san Lokaci ba,kuma bata ma iya dubawa ba amman lokaci indai na dawowan SUHAIL ne SUHAILA ta sani . Kamar kullum tsaye take bakin get cikin mintuna kadan kuwa sai ga mota ta shigo SUHAIL ne da drive ,"Oyoyo Yaya,Oyoyo,Yaya,Yayan Ayati Oyoyo." Tsalle take tana waƙa. Yana fitowa ya rungumeta tare da faɗin, "Oyoyo HAYATIYna Daukanta ya yi su ka shige cikin gida ban da washe baki da dariya ba abun da SUHAILA ke yi. Da Sauri SUHAIL yaje ya canja kaya ya dawo falo da ya aje HAYATIY ,Hajiya Kaka ce ta kalle shi cikin gyatsina baki, "Kai SUHAILU ince wai ba ka da Lokacin kan ka sai na Yarinyar nan ne? Duk kunbi kun shagwaba 'Ya" HAYATIY ce ta ɓare baki za ta yi kuka jin abin da kaka ke faɗa da kuma kallon da take Mata. Nan da nan SUHAIL ya bata rai ya dau HAYATIY yana, "Kaka mun bar kukaki wallahi tunda zaki samun HAYATIY na kuka,ni ba ruwana da ke kuma bana kulaki." Duk da kasancewar SUHAIL ƙarami amman ya ɗauki HAYATIY tamkar rayuwarshi haka ita ma, gata ƙaramar Yarinya sosai amman in tayi wani abun kan SUHAIL sai asha mamaki. Hatta barci SUHAILA bata taba yi sai jikin SUHAIL,haka ma abinci in ba shi zai bata ba ba ta taba ci Akwana atashi SUHAILA ta ta ƙara girma baki ya dade budewa hakan yasa Dady yanke shawarar sata a primary school haka kuwa akayi SUHAIL ya ce sai school din da yake ba yadda ya iya haka aka sata yana Jss2 SUHAILA na Nursery 1 Kullum SUHAIL sai ya raka SUHAILA aji ya mata wasa kan ya tafi na shi, lokacin tashin su kuwa nayi yake ɗaukota ya dawo da ita ajinsu. In anaso aga fada da bacin ran SUHAIL to ko zagine ayiwa SUHAILA bare kuma ataba lafiyarta. Baya taba wasa da karatun SUHAILA domin tana primary, lokacin yana Ss class abun yan secondry yake koya mata ,abun mamaki SUHAILA na ɗauka sosai fiye da zaton kowa. Har ya gama school amman ya koma domin ya ce shi ba zai bar SUHAILA kadai tana tafiya sai ya jira harta gama kan su shiga jami'a tare Wasa wasa Abu ya fahimci cewa in Bai mai da SUHAILA makarantar kwana ba SUHAIL ba zai ci gaba da karatu ba, kamar yadda ya fada,hakan Aka yi ba da son ran Momah da Abun ba amman sun raba su domin ci gabansu duka. Daga SUHAIL har SUHAILA sai da suka yi ciwon rabuwa sosai kamar ba za su rayu ba. Tunda ta tafi Kullum ban da video call ba abun da suke in ba ta aji,dan dole Abu ya nemi izinin bai wa SUHAILA waya cikin makarantar domin sun lura cewa rayuwar 'ya'yan nasu tamkar gudace a gangar jiki biyu. SUHAIL ya gama karatun shi kuma har ya samu aiki ya yin da SUHAILA ke JSs3 Ta dawo gida domin hutu, sunyi jarabawa. Tun daga kofar get kamshi ya fara dokar hancinsa ,Wani irin numfashi ya yi tare da sake murmushi azuciyarsa ya ke fadin, "Tabbas Kanwata ta dawo gidannan." Ita ma da ke kichen tana girki yana shigowa falon kamshin turaren jikin sa ne ya fara dukan hancinta, Shagwabe fuska tayi sannan ta fice aguje tana faɗin, " Yayana." Juywar da zai yi ta Ƙara Shagwabe fuska tare da tsayawa cak tana kallon shi. Murmushi ya sake mata,tuni ta kawar da kai tare da faɗin , "Ni fushi na ke kuma Ni ba zan ƙaraso ba ka ƙara so ni,kuma ka bani hakuri." Kasancewar ya san halin ƙanwar tasa sarai ya sa shi ƙarasawa gareta cikin sauri. Yana zuwa ya durkusa tare da rike kunnuwansa, "Am so sorry Rayuwata,kar ki ci gaba da fushi dani kin ji ko?ko ki na so inyi kuka ne?" Idanunta ne suka fara cika da hawaye tamkar za ta yi kuka. Da sauri ya miƙe tare da rungumeta,nan da nan ya birkice cikin sauri ya ce, "Rayuwata me ya same ki? Me aka miki? Kar ki zubarmun da hawayenki kinji dan Allah faɗamun kar kiyi kuka." Cike da Shagwaba take maganar, "Ni to ban ce yayana ya kama kunne ba kuma wayace ya kama ni bana so bana so yayana." Ƙarasa Maganar ta yi cikin muryar kuka. Fara share mata hawayen ya yi kan ya ce, "amman ba na hana rayuwata kukan nan ba? Kuma ai ke ki ka ce ki na fushi dani na miki laifi shi yayan ba a hukunta shi ne?" "Ummm to ba kai ne ka ƙi zuwa ɗaukana ba? Kuma ka san yau zan dawo daga skul ka tafi office dinka." "To kiyi hakuri kin ji,na so zuwa aiki ne dole sai dani kuma kema Kin san ba zan so barinki ke ɗaya ba shi yasa na tura drive,yanzu dai muje yunwa nake ji ina kewar girkin Rayuwata." "Tam muje,kuma sai ka cinye duka ni." Murmushi ya sake mata kan ya ce, "To muje." Riƙe Hannunshi ta yi sai da suka je har falo ta zaunar da shi kan ta ce, "Ka jirani ina zuwa karka tashi fa." Dariya kawai ya yi mata ba tare da ya ce komai ba Sinasir ne hadadde da vegetables soup ya ji hanta ta ta zuba mi shi a plate tana kai wa Ya ce, "Wooooo Rayuwata gaskiya zanci sosai." Ta shagwabe , "Ummm umm Zan dai baka sosai bude bakin tom." Ba gardama ya bude domin yasan ba ƙaramin abu bane yanzu Suhaila ta fara kuka. Ba shi take ta yi yana cewa ya koshi zata turɓune fuska da niyar fara kuka. Sai da ya cinye biyu ras kan ya ce, "Yawwa Alhamdu Lillah yanzu saura rayuwata tun da dai Yayanta ya koshi ko?" "Ummmm,Ummm ni na koshi bana jin yunwa,Momah ta dafa mun doyana na ci." Ɓata rai ya yi, "ban yarda ba na san halinki ai sarai ki ci abincinnan ko mu ɓata." Yana gama maganar ya ƙara bata rai tare da ɗaukan wayarsa. Fuskarshi ta juyo da ita gabanta a sanyaye ta ce, "Zan ci kaji yayana bani." Murmushi ya sake , "Yawwa ɗiyar albarka buɗe bakin." Yana ba ta ɗaya ta tashi ta gudu,haka ya bita suna zagaya ɗakin tana dariya yana dariya yana bata ahaka har ta ci abincinnan. Sallamar Momah ne ya katse su "Ai shikenan yanzu Kuma andawo rigima zata ci gaba." Kawar da kai SAHLA ta yi cike da Shagwaba. SUHAIL ya yi Murmushi tare da fadin, "Momah Sannu da fitowa." "Yawwa SUHAIL ,kai dai ba ka gajiya da halin HAYATIYN ka ko?" SUHAILA ta taɓe baki, "Umm Ai dai Yayana ne ba yayan Momah ba kuma Yayana ne ni ka dai." Ta ƙarasa maganar tana kallon Yayan nata, wanda murmushi kawai ya sake mata. Momah ta ce, "SAHLA kwana nawane? Tabbas na kusa haifawa SUHAIL kani very soon Kyakkyawa ba mai kama da ke ba." Kallon Yayan na ta ta yi cikin sauri ta rungume shi tana, "Ka ce kai Yayana ne ka dai kuma ka cewa Momah ni ba mummuna ce ba ka ji Yayana,ka faɗa mata ni ce ka dai kanwarka ni ka fi so kuma ba ka son kowa." Maganar take tana dukan girjinsa can kuma ta fara kokarin kuka. Da sauri SUHAIL ya ce, "Ni Yayan Hayatiy na ne ita Ka dai ba kowa, kuma HAYATIY na kyakkyawa ce ta fi duk matan duniya kyau ni anya ma Ba ke ce sarauniyar kyau ba?" Washe Baki SUHAILA ta yi tare da yi wa Momah gwalo, "Yayana ne ni ka dai ba kowa." Murmushi Momah ta yi har aranta tana jin dadin yadda 'ya'yan nata ke nuna tsantsan so da kaunar juna amman duk ran da ta tuna cewa Tabbas watarana dole sai SUHAIL ya rabu da SUHAILA , SUHAILA ta rabu da SUHAIL ji take ranta sam Babu dadi dariyar su ne ya katse mata tunani , "Umm Yaya ka goyani kaji." "Aa Hayatiy Yanzu fa kin girma kun wuce goyo." "Ummm,ummm,ummm wallahi sai ka goyani ko sau ɗayane." Hawaye ne ke kokarin zubowa Momah tai saurin tare su ba tare da ta bari 'ya'yan nata sun fahimta ba,,sum ta shige ɗaki ta sha kukanta son ranta. _*Ko miye dalilin kukan Momah?*_ SUHAIL kuwa goyata ya yi suna ta zagaye gidan ban da dariya ba abun da SUHAILA ke yi. Ni shi yake ya ajiyeta saman kan wata farar mota. "Hayatiy na gaji kin yi nauyi fa, tsabar shan Madara da chocolate ko? Dan dai Wannan na san ba dai abinci ba." "Ni abinci ina ci fa yaya." "To rantse in da gaske ne." Subulewa tai daga kan motar sai da ta ja gemun shi kan ta ce, "Umm umm ni ba kyau rantsuwa Yaya ya hana ni." Ta shige cikin gidan da gudu. Bin ta shima ya yi yana dariya. Tana shiga ta zabga wata ƙara. A firgice SUHAIL ya Karasa cikin gidan......... _*A ci gaba ko a tsaya??*_ *More comments more typing* 08103080717 Urs Xayyeesherthu *HAYATIY حياتي* 2/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-2 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing🤭*_ A guje SUHAIL ya ƙaraso, SUHAILA kuwa tuni ta fara kuka, "Yaya Ɓera,ɓera a kafata, kafata ya hau." Ta ƙara fashewa da kuka. Mai SUHAIL zai yi ban da dariya. "Hayatiy ki rasa me za ki ma kuka sai ɓera dan kawai ya hau mi ki ƙafa? Cizon ki ya yi?" Ya ƙara kyalkyalewa da dariya. Ɓata rai ta yi ta kalle shi kan ta fara dukan shi a kirjin shi. "Yaya, ni ka ke ma dariya? Ni ka dai na mun dariya, na ce ka bari kuma ba ruwana ma da kai." Ta fada tana ƙara dukan kirjin shi. "Wash wayyo Allah kirjina." SUHAIL ya faɗa yana gyatsine fuska. Da sauri SUHAILA ta ɗago, "menene Yaya? Zafi ya ke ma? Sorry na daina kaji ko? Sorry." Ta fada tare da tashi a jikin sa. Da sauri SUHAIL ya tashi yana mata gwalo Ƙarasawa falo ya yi. Ita ma ta bi shi da gudu tana, "wayo kamun ko yaya? Kuma zan rama nima ai." Kaka ce ta fara magana "Ke Salamatu yayan na ki kike ma rashin kunya? Oh ni Jikar Ubana wannan wace irin yarinyace." Kallonta SUHAILA ta yi kan ta ce, "Kaka ni ba salamatu ce ba,kuma ai ba yayanki bane ." SUHAIL ya ce, "Hajiya kaka yaushe ki ka ji tamun rashin kunya?" "Aa bata ma ba SUHAILU Ni na zageka ma kaji,ai yar gwal bata laifi." Cewar Kaka tana gyatsina baki. Tashi SUHAIL ya yi tare da riƙe ma SUHAILA hannu suka fita domin ya san sarai nan da anjima Kaka zata iya sa SUHAILA kuka. "Mtseww, oh Ni ina ganin salabe Aduniyar nan, yara kamar Masu rayuwa da ran juna ba dama ataɓa ɗaya,muje zuwa ai dole zaku rabu kije can kima mijin naki shirme da shagwabar banza,bari uban naku ma ya dawo walllahi aure zan sa ya miki." Karaf a kunnen SUHAILA Tsayawa ta yi cak. SUHAIL ya ce, "HAYATIY muje kinji rabu da kaka." Buɗe bakin da zata yi kawai sai kuka, "Yaya kana ji wai za arabani da kai,wai aure zata sa Abou ya mun? Yaya ni bana son auren ba zan yi ba,ka fadawa Kaka kar arabani da kai, Yayana ni nace bana so, bana so wallahi,ni ba zan yi auren ba." Shiɗewa ta yi nan da nan numfashinta na kokarin ɗaukewa. Wani irin kira da SUHAIL ya yi ma SUHAILA ne yasa kaka da Momah saurin fitowa tare da ƙarasowa gare su. "HAYATIYNA ba za amiki na fada miki ba za arabani da ke ba,kinji kar ki tafi ki barni,nima bana son rabuwa da ke,wasa kaka ta ke miki, kaka ki fada mata wasa ki ke mata kinji bana so wani abu ya samu Hayatiy na." Cikin ruɗun yanayin da kaka taga SUHAILA ya sa ta saurin faɗin, "SUHAILATU wasa na ke miki wallahi wallahi aradun Allah, na rantse ba za kiyi auren ba,ba zan fada mi shi ba." Kuka kaka ta fara harda majina _Duk tsitar da kaka ke yiwa SUHAILA aranta ba wadda ta ke so kamar ta, Amman tace shagwabar ta ce ke bata mata rai._ A hankali numfashin SUHAILA ya fara dawowa kallon yayan nata ta Yi, "Ina ba za ka bar ni ba?" Fuskar ta ya shafa tare da sake murmushi, "Alƙawari ba zan ba HAYATIY na ba,da ke zan rayuwa yar uwata." Ita ma Murmushin ta sake kan ta kalli kaka ta murguɗa baki. "Kuma daga yau na daina kulaki ma." Kaka ta yi guntuwar dariya, "Yo ni indai zaki rayu baki kulani ba ai ba komai bane in kika mutune nasan nima zan iya binki SUHAILATUta." Dariya Momah tai kan ta ce, "To dai Yanzu Alhamdu Lillah mai yaya ta dawo seti, SUHAIL ka tafi masallaci SUHAILA ki zo muje muyi sallah da kaka." "Tab, tab ni dai ba zan yi sallah da kaka mai majinar kuka ba, yaya ina tare za muyi waje?" Dagata yayi kan ya rike mata hannu, "eh muje Rayuwata." Juyowa ta yi tanama kaka gwalo, "hee tsohuwa tayi kukan majina." "Yar baɗo zan kamaki ai." Sallah su ka yi tare kan SUHAIL ya ƙara mata karatu tayi. """""" Zaune suke zasu ci abincin dare duka haɗawa aka yi, Abou ,Momah, kaka, SUHAILA, SUHAIL domin tare suka saba ci. SUHAILA na zuwa ta ɗane cinye SUHAIL , "Yaya ina jin yunwa." Kaka tai karaf ta ce, "wallahi har tausayin SUHAILU na ke inn SUHAILATU ta dawo gidannan bai da sukuni kamar jinjirar kuliya yake kiwo." SUHAILA ta shagwabe fuska, "Abou Ka ga kaka ko? Yau sai mun masifa tana ta yi,kuma ina Yayana ne ba nata bane ita ma anemo mata yayanta." Murmushi kawai Abou ya yi. Haka aka ta fama da SUHAILA duk da tace tana jin yunwa amman da kyar ta ci kaɗan hakanma ta ga Momah na gunne. A jikin SUHAIL SUHAILA tai barci sai da ya kaita ɗakinta ya mata addu'ar ya shafa mata, kan ya fita adakin shi ma yaje ya kwanta. Washe Gari SUHAIL zai wuce masallaci dakin SUHAILA ya shiga barcinta take hankali kwance murmushi ya yi kan ya durkusa dai dai kunnenta a hankali ya ke faɗin, "HAYATIY HAYATIY HAYATIY." Kiran na ukun ta Amsa " *Alhamdu Lillahil- lazi Ahyana ba'adama Amatana wa ilaihin nushur* Murza ido tayi tana kallon yayan nata. "Oya Aje ayi alwala ayi sallah, kiyi wanka, sannan kisa kayan sport dinki Kan na dawo." "Ok Yaya." Ta fada tare da nufan toilet din. Kan SUHAIL ya dawo kuwa har SUHAILA ta shirya cikin kayan sport din ta ja mai ratsin fari rigace da kuma wando har ƙasa dai dai jikinta,sai wata farar hula akanta mai adon stons ba ƙaramin kyau ta yi. Shi ma yana dawowa haka ya shigo cikin shigar kayan sport din sak irin na SUHAILA. Tsayawa ya yi tare da ɓata rai, "hijabin fa?" "Yaya ba sai nasa ba fa ni bana son hijabinnan damuna yake." SUHAIL ya ƙara bata rai , "wuce ki dauko hijabin kisa nace." Ganin yadda yake mata maganar yasa ta san ba wasa tuni ta ɗauko tasa. Karamin farin hijabine iya kafadarta ya tsaya. Kallonta ya yi kan ya sake murmushi, "Yawwa Yar lukutar HAYATIYNA Kin fi kyau a haka." "Ni unmm umm, morning Yaya." "Morning Hayatiy,Da gaske fa muje kan gari ya yi haske, ke ba cin abinci ba ma narasa dalilin wannan kibar ta ki,ina ga dai madarace ke huraki." Maganar yake suna fita. Gudun suka fara abinsu a hanyar su na dawowa gida SUHAILA ta kafe. "Yaya Walahi ni na gaji sai dai ka goyani." "Hayatiy awaje muke fa taya katuwa da ke zan goyaki sorry tashi mu karasa kinji." Bajewa tayi akasa tana bubbuga kafa, "ni ai yayana kuma ba ruwana da kowa,ni ka goyani yaya ni na gaji ba zan iya ba, yaya ka goyani." SUHAIL ya ce.... *_more comments more typing_* 08103080717 Urs xayyeesherthu *HAYATIY حياتي* 3/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda ku ke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-3 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing🤨*_ _*kamar yadda na fada more comments more typing*_🤨 "HAYATIY ki na ganin mutane sun fara fitowa fa so ki ke ata kallomun?" "E in ni ba ruwana da kowa ni a gayoni." Durkusawa ya yi gabanta haka ta hau bayan nan har suka ƙarasa gida, labari yake ba ta ita ko tana ta kyalkyalewa da dariya. Shigan su gida suka ci karo da Abou. "Morning abou," cewar SUHAIL. "Morning Abou, "Cewar SUHAILA. Da murmushi afuskar ta shi ya amsa da , "MORNING oll, amman SUHAILA kin girma fa ya kamata abar goyonnan haka kin ji Ummina,ga ki katuwa kar ki sa wa Yayanki ciwon kirji, ko ki na so ya yi ciwo ne." Shagwabe fuskar tai kamar za ta yi kuka, "Aa abou bana so yaya ya yi ciwo, in ya yi ni ma zan yi." Murmushi Abou ya ƙara sakewa , "Yawwa Ummina to kin ga kin girma yanzu dan haka yaya ya daina goyaki." Kokarin sauka ta fara a bayan tana, "Abou an daina daga yau ni, ta kalli yayan nata kan ta ce, "Yaya Sorry ba za ka yi ciwon kirji ba kaji." Murmushi kawai SUHAIL ya yi mata. "Yawwa maza ku shiga kuyi break, SUHAIL kar ka makara a office." Hada ba ki su ka yi da fadin, "Ok Abou." Kan suka shige cikin gida. Momah ta fito daga kitchen tana, "Yawwa ga kayan break din ku cen falo." Sai da ita ma su ka gaisheta kan su ka nufi abincin. Kamar kullum dai da kyar SUHAILA ta ci kaɗan. Ɗaki SUHAIL ya koma domin canja kaya ya tafi office. Sai da ya kammalawa sawa kan SUHAILA ta shiga. "Yaya, ka tuna labarin littafin *JAMEEL* da na baka,wan da _xayyeesherthou_ ƙawata ta rubuta?" Ya girgiza kai alamar eh. "Yawwa to faɗamun mai Jawahir ke faɗa ma Yayanta in Yayi wanka zai fita." SUHAIL ya yi murmushi kan ya dago kwalban turaren shi ya ce, "Yayana kullum cikin kamshi ya ke,aduk san da ka yi ado indai baka sa turare ba ina tabbatar maka da cewa adonka bai cika ba,kuma ni kai ba Yayana bane." Ya karasa maganar yana kallonta. SUHAILA ta ce, "Yawwa to nima Yayana kullum cikin kamshi yake,har ma ya fi na Jawahir ko?" Dariya ya yi kan ya amsa da , "Eh mana Hayatiy." "Tam Ni bani in fesama da kaina." Miƙa mata ya yi, aiko ta fashe shi tsaf. "Tam byeebyeee Hayatiy ki kulamun da kan ki kinji." Bata rai ta yi kamar za tayi kuka. Ya matso kusa da ita tare da zaunar da ita gefen gadon, "menene zo ki faɗamun kinji HAYATIY." "Ni yayana zan bi,ni ba zan zauna agidan ba." SUHAIL ya ce, "tashi kije ki canja kaya to." Tsalle tayi kan ta rungume yayan nata, "ina son ka yaya, na gode." Da gudu ta fita ta nufi ɗakinta. Wata pitchen daguwar riga ta sa, mai adon golden, da gyalenta ko kwalliya babu afuskarta amman ba ƙaramin kyau tayi ba,ban da kamshi ba abun da ke tashi. Falo ta sami Momah da kaka. "Momah,kaka mun tafi officen din Yayan HAYATIY byeebyer." Ta fita aguje. Kaka ta ce, "Oh ni Salamatu wannan 'Ya subutul subutul kamar doyar turawa ko ina sai sunje tare ne wai." Dariya Momah ta fara tana, "Hajiya daman akwai doyar turawa?" "Yoo eh mana gata kun ajiye agida." Da guda ta karasa SUHAIL ya ce, "in kika fadi ba zan ɗaga ki ba dai nikam." Ya ƙarasa maganar yana bude mata kofar motan. Sai da ta shiga ya shigo kan ta ce, "Yasin ina faɗuwa kuka zan ma ai." " Ni kuma inta dariya ina Lutiya a kasa ba." "Yaya nice lutiya ko? Ai zan rame,na kusa ramewa ma duka shikenan kuma bar kulani." SUHAIL ya ce, "Sorry Hayatiyna wasa ina miki mun shirya yanzu ko?" Shagwabe fuska ta yi, "Umm umm ni sai ka ce mun Anty Hayatiy to." "Iyee ni ba zan fada ba,ai na baki hakuri." Bata rai tai tamkar za ta yi kuka, "ni ka ce mun Anty,na ce ka ce mun Anty, Ni Antyn Yayana ce." SUHAIL ya yi murmushi, "To sorry Antyn Yayanta." Wage baki tayi kamar an mata albishir ta daga hannu yawwa mu tafa Yayana. Miƙa mata hannun ya yi suka tafa duka suna dariya Dadi take ji yau ta zama Antyn Yayanta. Haka har suka isa office. Zaune take tana ta kallo awayar Yayan nata da yin hotuna shi kuma yanata aikin sa. "Yaya" ta kirashi. "Naam Hayatiy menene?" "In ka tashi office zamu saloon awanke Mun kai?" "Oh na tuna fa kam eh bari in ƙarasa aikin nan ina so ma muje a miki lalle ko?" Murmushi ta yi ta amsa da "eh" Har ya ci gaba da aiki ta ƙara kiransa. "Yaya" "Naam." "Dagaske in kayi aure zaka mantani zaka daina sona?" Tashi ya yi akujerar da yake ya dawo daf da ita kan ya rike hannunta ya ce........... 08103080717 Urs xayyeesherthou😘 *HAYATIY حياتي* 4/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-4 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing*_ "HAYATIY, mutum zai iya mantawa d kan sa?" Ta girgiza kai alamar Aa. Ya ƙara gyara zama kan ya ci gaba da magana, "kamar yadda mutum ba zai iya mantawa da kan shi ba,haka nima ba zan iya mantawa da ke ba,domin ke ce RAYUWATA, ina son ki kanwata,ina matukar so da kaunarki zan iya sadaukar da farincikina domin na ki, zan iya juran duk wata wahala na duniya domin rayuwarki ta inganta, ina son ki, zan ci gaba da son ki kuma ba zan daina ba,yar uwata kuma rayuwata." SUHAILA ta ce, "Yaya Amman Askul yan class din mu sun ce matar yaya na kwacewa kanne shi gaba-daya ya daina son su,yaya ni kam ina tsoro kar kayi aure kaji ina ba za ka yi ba,zamu ta zamanmu agidanmu tare ko?" Murmushi ya yi kan ya ce, "Ko da ace zan yi aure ba zan taba iya rabuwa da kanwata ba,bare kuma in auro wadda zata rabamu,to ma wai taya za a iya cire rayuwar mutum a jikin sa ne? SUHAILA ba ki san kece rayuwata ba? Duk wani abu da zai taba ki tamkar zai taba mun rayuwa ne, banji cewa zan rayu idan babu amman tabbas na zabi kiyi rayuwar lafiya da Farinciki fiye da kaina, ba zan yi aure ba,banjin cewa zan iya so ko kuma ba wata 'ya mace aduniya kulawa, lokaci na da ma kaina gabaɗaya bayan ke,dan haka kiyi murmushi kinji Hayatiyn Yaya." Murmushin tai tare da fadin, "Yayana nawane ni kadai yayana ne Ni ɗaya ba kowa." Waƙar da ya saba mata tun yarinta ya fara tana ta dariya. "Anything you need yes I'm your guide. I only wanna keep you satisfy. I just wanna be there for you.." "Thank you yaya, Yayana ya fi na kowa aduniya." *WACECE SUHAILA? SANNAN KUMA WANENE SUHAIL?* Ku biyo dan jin takaitaccen tarihin wannan ahali mai albarka. SUHAIL Da SUHAILA 'Yaya ne ga Alhaji Muhammad,,attajiri dan kasuwa. Tare da Matarsa Hajiya A'isha lecturer ce a jami'a. Dukkaninsu mazaunan garin Abuja ne. 'ya'yansu biyu jal aduniya daga SUHAIL sai SUHAILA suna matukar son 'ya'yannan nasu fiye da misali. Shakuwace mai ban mamaki cike da al'aji tsakanin SUHAIL da SUHAILA domin tun haihuwarta aduniya, hatta sunan SUHAILA, SUHAIL ne ya raɗa. A yanzu SUHAIL ya gama karatunsa yana aiki a asibiti ya yin da SUHAILA ke kokarin shiga Ss1 kamar yadda ya furta tun suna kanana shi zai dau dawainiyarta inta girma hakan kuwa akayi domin shi ke biya mata komai na karatunta a yanzu,haka kuma burinsa na zamanta likita kamar shi na daf da cika domin kuwa makarantar da take na science kuma tsarin makaranta ana karatun secondry sannan ana na fannin health ne da zaran ta kammala ss1 ,2 da 3 tamkar jami'a yake. Ba zata fito ba sai da takardar zamanta malamar asibiti. Inda matsalar take Momah da Abou na matukar tsorata da shaƙuwar SUHAIL da SUHAILA ,Abou kan iya daurewa yayin da Momah kan zubda kwalla. Tabbas akwai wani boyayyen sirri da suka barwa junansu sani. Amman komin daɗewa komai zai bayyana ku ci gaba da kasancewa dani. Hajiya Kaka kuwa mahaifiyar Abou ce kasancewar ita ma shine ɗaya danta tillo aduniya tun da mahaifinsu ya rasu hakan yasa shi dawo da ita gidan.. Suna rayuwarsu cikin Farinciki da kaunar juna. Wannan kenan Ci gaban labarin. Karfe uku dai dai suhail ya bar office domin Kai SUHAILA wajen wanke kai.... *Shin kun san cewa akwai gasa ta musamman kamar yadda aka yi a littafin SAI NA AURI MARUBUCI?? tabbas na ƙara shirya awannan littafin domin sanya gasa tare da cire best commeters domin karramasu tare da basu certificate watakil agaba kuji wata kyautar mai zuwa ta musamman🤩 Hayatiy littafine na musamman awajena wanda ya juri karantawane kadai zai fahimta,ku ci gaba da kasancewa dani masoyan asali🥰💃ina yinku lodi lodi, best commeters loading........* 08103080717 Urs xayyeesherthou 😏😏Free Novel ne dan haka ina bukatar comments In kin San bakya karantawa kuma ba kya sharhi goggo dan Allah kar ki shiga domin ko kin shiga zan tsigeki wallahi😑tabbas https://chat.whatsapp.com/IpsParMb6dOBXLpns86N2u *HAYATIY حياتي* 5/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-5 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing*_ _*Kumin Addua dan Allah😰🙏ina bukatar adduoin ku*_ Ko da suka je shiga tayi ya jirata a waje gaban motar yana kallon shagon saloon din kamar mai gadi ko kau da kai baya yi. Cikin 30minit kuwa ta fito. Da gudu tazo ta rugume yayan nata tare da fadin, "Yaya gobe daman weekend ba office sai ka kaini lallen da kitso ko?" Murmushi ya yi kan ya ce, "eh mana Hayatiy,yanzu dai shiga mota mu yi gida." "Ok Yaya." Suna shiga ta fara kokarin cire gyalen. Kallonta ya yi, "Hayatiy menene haka?" Taɓe fuska ta yi tana faɗin, "Yaya ba ka ga gashin ba nunama zan yi fa." "Oh ni kam to bari muje gida mana Hayatiy." "Aa ni, nace aa yanzu za ka gani kan muje in kyan ya ragu fa?" "To mu gani." Cewar SUHAIL. Cire ɗankwalin ta yi ta na, "ka ga ni, yaya ya yi kyau? Ka ce ya yi kyau kaji,kar ka ce bai yi kyau ba ni." Bude baki ya yi, "iyeee Hayatiy kin ga yadda kan ki ya yi kyau kuwa gashin ya kara tsayi da sheƙi,ga kamshi,umm lallai kanwata ashwariyace da na sani ma ashwariya aka sa miki ko?" Dariya ta yi kan ta ce, "Tab Ni dai ba ashwariya ce ba, Hayatiyn Yaya ce." Dan tsokaci ****Masu bukatar sanin shelarun Hayatiy da na Yayanta kuyi hakuri ganin na fadi shekarun su tun na yarinta yasa ni mantawa ayanzu. Amman tabbas a yanzu SUHAIL na da shekara asharin da hudu. Yayin da Hayatiy ke da shekara goma sha uku aduniya. Hayatiy farace kyakkyawa dai dai gwargwado sannan tana da jikin girma, daga kiba har tsayin, suma kuwa sai dai ace ma sha Allah domin wasu ma in ba tai magana ba ace balarabiyace. SUHAIL ma fari ne sol kamar yadda Hayatiy take dogo mai suffar fulanin asali domin shi kam baya da kiba, SUHAIL kyakkyawa ne ajin farko. Da ka ga SUHAIL ka ga Hayatiy za ka ga tsantsar kama ta bayyana. ******* Ci gaban labarin. Momah zaune tana kuka a bakin gado kamar yadda ta saba. Abou ne ya shigo tare da fadin, "Haba Madam wai yaushe za ki bar kukan nan ne? Shin ba za muyi imani da wannan ƙaddarar bane? Kar ki manta fa shi Allahn da ya Hallicce su ya fi mu son su, addu'a ce kadai za ta mana magani domin ba abun da ya fi karfin Allah,abu mara yuhuwa atunanin mu shi agun Allah ba komai bane,kuma na san yana sane da mu shi zai mana magani." Da sauri Momah ta karasa tare da rungume mijin nata, "Abou ba kan mu nake ji ba yadda rayuwar su zata kasance nake ji,bana tunanin wanininsu zai iya rayuwa batare da wani ba,wallahi ina jin tsoro,ina jin tsoro lokaci tafiya yake kamar wasa shikenan fa." Ta ƙara fashewa da kuka. "So ki ke su dawo gidannan su fuskanci halin da muke ciki ko? Kina so tun yanzu ahalinmu ya rushe ko? Haba A'isha ,Haba ni nasan me ki ke ji aranki amman ki tuna yanzu wannan sirrin na bayyana komai zai ruguje,muyi hakuri mu zubawa sarautar Allah ido na tabbatar Allah baya ɗaurawa bawa abun da ba zai iya ba, kamar yadda lokaci keta kara karatowa hakama baza mu fasa kai kukanmu ga Allah ba." Sallamar SUHAIL ne yasa Momah saurin goge hawayen da ke fuskarta. Abou ya ce, "yawwa ka da ki bari su fahimci komai,domin ko Hajiya taji wannan lamarin mun kaɗe." Murmushin dole Momah ta ƙakalo ta ce, "In sha Allah." "Momah, Momah Yaya ya kai ni saloon." "Iyee Hayatiyn Yaya kyau kenan." Juyawa tayi ta kalli yayan nata, "yaya muje muyi wasanmu to kan dare ya yi,yau kai za arufe wa ido bani ba." SUHAIL ya ce, "Naki wayon yanzu dai bara na aje jaka amman ki tabbatar ke za arufewa fuska, in kin kamani tabbas yau za ki sha chocolate da madara." Tsalle ta fara tana murna. Abou ya ce, "Daga kai din har SUHAILA ban san yaushe za ku girma ku bar wasan nan ba dai." SUHAIL ta ce, "Abou yau fa harda kai da momah Please." Ta karasa maganar kamar za ta yi kuka. Kasancewar da duk tare suke irin wannan wasan. Da sauri Momah ta ce an gama , "Hayatiyn Yaya." Abou ya kalli Momah ta sake mishi Murmushi tare da fadin, "kadan dai Abou domin farincikinta,kaga rabon da muyi wasa tare tun kan ta tafi skul." Shi ma Murmushin ya yi tare da fadin ok. SUHAIL ne ya dawo da wani farin gyalle tare da daurawa hayatiy afuskarta. Ita kadai suka bari a tsakiyan falon. Ta ce, "1,2,3 start." Fara dubi dubi tayi afalon tana kokarin kamosu sai ta zo zata rike wannan sai wannan ya gudu, ban da dariya ba abun da suke suna kiranta "HAYATIY." "Yaya,ka fito in kamaka kaji tunda Momah da Abou sun ki, Yaya ka fito kai ina son kamawa, momah ,abou kuma ku fito.".. Taji shiru sun daina dariyar kuma sun daina kiran sunanta. Wani irin ƙara da SUHAILA ta yi...... Urs Xayyeesherthuo *HAYATIY حياتي* 7/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-6 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing*_ *Rudun da ke cikin labarinnan ya wuce tunanin mai tunani, wanda ya jure bibiya shi kadai zai fahimta👌* Ji tayi an ɗauketa cak. Da sauri ta fara kokarin fisgewa tana son bude idanunta. Tana budewa mai zata gani, SUHAIL ne Abou,Momah suna ta yi mata dariya. Taɓe fuska ta yi kamar za ta yi kuka, "Abou ina na ci kuma za a siyomin chocolate dina ko?" Momah ta ce, "Ni dai da Ɗana muka cinye, dan haka Abou ni da SUHAIL za asiya mana chocolate." SUHAIL ta ce, "Aa Abou ka ce ni za ka siyawa kaji kar ka siya masu,zan sam ma su kadan kaji." Murmushi Abou ya yi, "An gama Ummyna zan siyo miki da yawa kinji.". Tsalle ta fara tana yiwa SUHAIL da Momah gwalo. Abou ya ce, "SUHAIL ka fito da mota muje ShopRite in siyowa Ummyna abincin ta." Ba musu SUHAIL ya dauko mota. Momah da Kaka kawai aka bari a gida. SUHAIL ke driving a gaba Abou zaune agefe tare da SUHAILA a cinyarsa taki yarda ta zauna ita kadai. Suna isa SUHAILA ta ga ball Washe baki tayi yawwa Abou gobe weekend ball zamu buga agida asiya mana ball da kayan ball din harda naka, dana kaka da momah ,da yayan HAYATIY ka ji. Haka kuwa akayi kowa sai da aka siya mai kayan ball hatta kaka harda ta kalma. Chocolate kuwa ba adadi,kala kala ba wanda ba kwasowa SUHAILA ba. """"""Washegari. Bayan SUHAIL sun dawo daga gudun da suka saba. SUHAILA ta dinga bin kowa daki tana ba shi kayan ball din sa yasa. Ta ce ba xa ayi break ba sai anyi ball an gama. Kuma kakace gollarsu ita da SUHAIL team din su ɗaya. Momah da Abou na su ɗaya mai gadi ne gollansu. Hatta mai gadi sai da tasa shi sa kayan ball dinnan. Tana kai wa kaka kuwa ta ce , "Tab SUHAILATU wallahi bani sa kayan kafurannan haka kawai ina nan yau ko gobe in mutu a kafira? Kin ci gidan ku, ba abun da zai sani sa kayan kafirai yan iska, ki ga ni da wando, Subhannallah ni jikar ubana mudi, ki rufani ki sayani ni ba er iska bace." Ta karasa maganar tana taɓe baki. SUHAIL ta shagwaɓe fuska, "Kaka kiyi hakuri kinji ni kisa, ba fa kayan yan iska bane kayan yan kwallone dan Allah ki sa kaka ball nake so mu yi fa yau." "Taɓɗinjan ashe yau mudi mai niƙa zai dawo duniya ya sake ni kan ya koma lahira, ball ki ki kace ko bole? To aradun Allah na rantse rantse rantse tse bani sa wangq kayan yan iska banyi iskanci tun a kauye ba sai a birni? So ma ki ke ayi tanbaɗeɗe dani ko?" Ganin kaka ba ta da niyar sa kayan yasa SUHAILA bajewa a gun tana bori harda kukanta hawaye shabe-shabe, "kaka wallahi ni ki sa na ce kisa,kuma in ba ki sa ba ba ruwana da ke nama daina kawance da ke,kuma Wallahi gobe ma zan mutu tunda bakya so na." Kaka na jin maganar mutuwa ta zare ido. "Iyee? SUHAILATUta? Rufamun asiri ta shi kije zan sa kayannan yanzu yanzu kuwa." """"Momah ce ke kokarin sanya kayan ball din nata. Abou ya fito sanye da na shi, murmushi ya sake mata tare da fadin, "kin ga yadda ki kai kyau kuwa Hajiya, kuma Madam dina? Gaskiya SUHAILA ta kyauta ko ba komai kin mun ado na musamman." Hararshi tai tare da fadin, "irinnan wato da bana ma ko?" "A'a ni na isa ince haka." Karasowa gare shi tayi tare da fadin, "Ogana, tabbas zan komai domin farincikin SUHAILA kam a yanzu ji nake duk wannan abubuwan da muke na karshe ne, ban jin cewa zamu sake rayuwa irinta yanzu nan da yan kwanaki." Abou ya ce, "ba ke ba,ko ni zan yi komai dan farincikin SUHAILA ko da kuwa dukiyar da na tara kaf zata ƙare ne sanadin ta, inna tuna hakan zan ji dadi arayuwata, amman nasan rayuwa za ta yi matukar mana wahala batare da 'ya'yan nan biyu ba,su din tamkar haske ne da ke kara haskaka rayuwarmu a kullum, amman kin san miye?" Momah ta kalle shi tare da girgiza kai alamar "aa." "Inna tuna Allah ne kadai kan iya jarabtar bawan sa na kan ji dadi araina." Momah ta ce, "hakane kam Alhamdu Lillah, na san Allah na tare da mu." Riƙe hannun Abou ta yi suka fita tare. SUHAILA da SUHAIL sun tsaya bangare guda. Momah da Abou ma haka. Kaka kawai ake jira domin har mai gadi ya tsaya abangaren su Abou SUHAIL ta kalli SUHAIL. "Yaya, ina so yau mu cinye Abou da Momah, mu ci su goma fa kasan Ba iya ball su ka yi ba." Abou ya ce, "tabbas yau za ki ga iya ball domin sai mun ci ku ashirin ma ba goma ba, ko ba haka ba madam?" Ya ƙarasa maganar yana kallon Momah. "Sosai ma Ogana, zamu basu mamaki ai." Fitowar kaka ne ya dakatar da su. Abou da Momah , SUHAIL basu san sanda suka tintsire da dariya ba. SUHAILA kuwa harda faduwa akasa. Gabadaya yanayin kaka ya chanja ga gajeran wando ka katuwar rigar ball gabadaya yawo take acikin kayan. Takalmin kuwa ko daure igiyar batai ba Wata irin tafiya take tamkar wanda ya yi kashi awando domin takalmin ba karamin nauyi ya mata ba. Kallonsu ta yi tare da wage kafa kan ta ce, "Oyaaaaaa boleeeeeeee." _hhhhhhhh kaka za abuga ball_ Urs xayyeesherthou *HAYATIY حياتي* 8/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*SADAUKARWA*_ _SADAUKARWA GARE KU YAN UWAN KWARAI,BA ZAN IYA MIKU SO KAƊAN BA FARIDA MUSA (SWEERY) ZAINAB SALIHU (SARAUNIYAR KANAWA), ASMA'U ABUBAKAR (JASMEEN) REAL NANA AISHA,HAUPHA,MANAB/YAR BABA,JANNAT M NASIR,RAHMA SABO USMAN,HANNA MUHAMMAD SUHANA._ _*Ku yi yadda kuke so da littafinnan daga farko har karshe naku ne,son so fisabillah🌹*_ PAGE-7 _Bismillahir-rahmanir-rahim_ _*Gajeran Labari ne, dan haka pages din za su rinka zuwa guntu-guntu amman duk da hakan yawan comments yawan typing*_ SUHAILA ce ta damƙe dariyar tare da fadin, "Kaka ke fa golarmuce ni da Yayana, ke zaki dun ga tare ball in su Abou sun turo kar su cinyemu,kinji." Kaka ta ce, "oh na gane aiko ba za su taba cinyemu ba SUHAILATU afara kawai." Gwananin sha'awa cike da nishadi tare da fara'a afuskar dukka ahalinnan suka fara buga ball din. Abou na kokarin zura kwallon raga caraf Kaka ta bararraje agun ta tare tare da fadin, "aradu kunyi kadan sai mun cinye kwallon yau dinnan." haka aka ta fama d kaka harda rungumar ba, mai gadi kuwa ya washe baki tuni SUHAIL ya wurga ya cinye masu. Daga karshe dai 3/0 aka tashi SUHAILA da kaka sai dariya ana yiwa su Abou gwalo. Hoto suka dunga yi, kowa dariya da ka gan su zaka san Farinciki na mussaman ya ziyarci zukatansu. Momah ce ta kasa daurewa sai kuka . Da sauri SUHAILA ta karasa gun Momah ta fara goge mata hawaye, "Momah na, menene ya sa ki kuka? Ba kya so mu ci ne? Tam kiyi hakuri kinji ni kam mun bar ma ku cin dan Allah ki daina kuka ki daina in kina yi nima zan yi." Ta karasa maganar tana fashewa da kukan ita ma. Da sauri Momah ta rungume ta, "SUHAIL ba zan iya rayuwa ba bu ku ba dan Allah kar wanin ku ya bar ni." Abou ne ya yi saurin datse batun Momah da fadin, "Madam me ya kawo maganar rabuwa kuma? A tunani ban ji wani abu zai iya rabamu ban da ƙaddarar rayuwa, Ummyna kuyi shiru kinji ,Momahnki kukan farinciki take." Jikin kowa dai ya yi sanyi amman sai da Abou ya san yadda ya yi ya kawar da tunanin komai azukatansu. "Ummyna yunwa muje muyi break na san yanzu komai ya kammala ." Rike hannun yayanta ta yi suka shiga cikin gidan duka tare. Bayan sun gama break ne Abou ya yi gyaran murya tare da fadin, "Yawwa Ummyna daman ina so ki dawo karatu gida, ki bar boarding ki koma day,tun da daman can rashin barin yayanki ya sa dole muka turaki can kuma Alhmdu Lillah yanzu ya kammala har aiki yake, saura ke, zaki dawo gida na gama magana da Pcn ku kuma ya fahimta ba ma da matsala a yanzu." Dasauri ta tashi tare da rungume Abou, "Thank you, Abou, thank you so much،ina sonka daman na fi son zaman gidan ya fi dadi." Murmushi ya yi, "to yanzu ga shi anyi an gama, kullum in yayanki za shi Office zaina sauke ki, lokacin tashi ma inya dawo sai ya daukoki ko?" Kiss ta ma Abou kan ta kara cewa, "Thank you Abou." Ta dawo gun SUHAIL tare da ja mi shi gemu, "Yayan Ayati za ka kai ni ko?" "Dole na in ban kai Hayatiy ba wa zan kai?" Tsalle ta fara tana murna. "Yaya anjima zamu lallen da kitson ko?" "Eh in sha Allah،muje amiki kifi Hajiya kaka kyau." Kaka ta taɓe baki, "Yo tun da dai Ba gani zai ba ai kuta fina kyan, ba zan yi kishi da lutiya ba, Tunda Malam har ya mutu bai taba son lutaye ba." "Yaya ka ga Kaka ko? Ka ce mata ai nima kuma zan rame, kuma ina na fita kyau?" SUHAIL ya ce, "tabbas ana maganar indiyawa wake na hausawa yan Nigeria." SUHAIL ta kyalkyale da dariya tare da yi ma kaka gwalo . SUHAIL na kokarin magana kenan jini ya fara zuba daga bakin sa. Aman jini. Wani irin firgita SUHAILA ta yi..... Urs xayyeesherthou *HAYATIY حياتي* 14/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ *PAGE-8* Da sauri Momah ta tashi ta ɗibo ruwa da audiga tare da tallafawa SUHAIL ya daga kan sa sama. SUHAILA kam suman zaune ta yi, ban hawaye ba abun da ke sauka a idanunta ya yin da ta kurawa Yayan nata ido. Cikin ikon Allah Jinin ya daina zuba, da taimakon Momah da Abou. Hajiya kaka ma kuwa sake ido tayi kawai tana kallon abun al'ajabi,amman da ka ganta za ka fahimci cewa a tsorace take. Murmushi SUHAIL ya yi tare da dagowa ya kalli SUHAILA, yana bude hannayen sa alamar ta zo. Da sauri ta karasa tare da rungumesa a lokacin sautin kukanta ya fara fita. Cikin lallashi ya fara shafa bayanta yana, "Hayatiyna ba komai bane fa, sorry kinji." Abou ya ce, "SUHAIL ya aka yi hakan? Shin ma hakan me ke nufi ne wai?" Murmushi SUHAIL ya yi yana, "Abou ban san dalili ba wallahi amman na fi tunanin normal ne ba matsala watakil zafin rana ne ya janyo mun hakan." "Uhumm uhumm Yaya ni ban yarda ba,ni bana so,ba na so jininka yana zuba, ka daina bari yana zuba ka ji." Cewar SUHAILA. "To Hayatiyn Yaya, Smile ." "Ummm umm ni ba zan yi ba sai ka mun alƙawari, promise?" Ta karasa maganar tare da nuna mai hannunta. Rike hannun nata ya yi kafin ya ce, "Yes Promise In sha Allah HAYATIY." "Na gode Yayana,ina sonka,kar ka daina sona kaji." "Ina sonki HAYATIY ba zan daina sonki ba kinji." "Ku dalla kun dameni da surutan banza to waye bai son yan uwansa daman? Ku mana shiru kullum maimaita magana daya agun." Cewar Kaka. SUHAILA ta kalli Yayanta, "Yaya ka ga kaka ko, ni bana kulata fa." "bar Hajiya kaka kishi take da haushin rashi tashi kiga muje in kai ki gidan lallen kinji Hayatiyna." "Uhumm uhumm, Yaya ni na fasa tunda baka da lafiya." Zaro ido ya yi. "Iyee? Waye ce miki ban da lafiya? Lafiyana Lau muje in kai Ama Hayatiy na Ado ta Kara fin Hajiya Kaka kyau." "Yaya Allah ba zani ba ni,mu zauna agida na fasa."ta karasa maganar tana shirin kuka. Zama ya yi yana, "Shikenan amman kan ki ba zai zauna haka ba,dauko kayan kitsonki in miki." Da sauri ta tashi tana tsalle tare da kai wa yayan nata kiss. Wani karamin kid ta dauko na kayan kitsonta. _duk da kasancewar SUHAILA ta fara girma amman hakan bai sa an daina yi mata kitson yara mai kyalkyali da adon beat ba, abun mamakin anan shine sanadin SUHAILA ,SUHAIL ya iya kitso, aduk san da za akaita kitso da kuka suke rabuwa hakan ya sa shi cewa zai mata kamar wasa kuwa gashi ya iya yi mata kalaba da twistin , kitso biyunnan da yake mata kuwa shi ke kasancewa akanta ko Bata gida,ko da ba shi zai mata ba cewa take ita irin kitson yayanta za amata, SUHAIL ya zabi murmushin SUHAILA fiye da komai, hakan yasa baya taba gajiya da duk wani abu nata_. Abou, Momah,da kaka kuwa inda sabo sun saba hakan yasa ba wanda ya kulasu. Tana ɗaukowa ta dire gabansa tana, "Yaya daman ka dade baka mun kitson ba fa." ...... Urs xayyeesherthou *HAYATIY حياتي* 15/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ *PAGE-9* _*Ashe Hayatiy na da fans haka ban sani ba🤔wato laɓewa kukai, godiya sosai da soyayyar ku gareni😍, Xayyeesherthou na maku so tamkar wanda SUHAIL ke ma SUHAILA😂kun yarda ai ko? Tabbas da gaske son so fisabillah*_ _*Masoyan gaskiya ba sa fushi su kan juri jira komin rintsin dadewa🤩😘*_ Kama gashin ya yi, ya kitse mata shi tsaf da kalaba. Sai da suka gama kan ya jera mata beat din. Abun ka mai gashi, ban da sheki ba abun da kan keyi,ba karamin kyau kitson ya yi ba SUHAILA ta kalli Momah, "Momah ku cewa Yaya Thank you,kuma ku ce kitsona ya yi kyau kunji." Murmushi su ka yi duka. Kan Abou ya ce, "Gaskiya kitson Ummyna ya yi kyau." "Thank you, Yayan Ayati, tunda ance dole mu gode." Cewar Momah. Kaka ta ce, "Tab ni da tsidigu kai kamar farantin hausawa." "Uhum uhumm Yaya Ka ga Anty Kaka ko? Zan daina ce mata Anty fa." "Yoo ki daina mana bakina ya huta da tsugudidin ki ai." Kallon yayan nata ta tsaya yi. "Sorry RAYUWATA kin san Halin Hajiya Has dinnan dai na nan kuma duk dan nace bana sonta ne,ta shi mu ta fi abun mu." Rike mata hannu ya yi suka fita tare yana bata labari. Zama su kai ta gefen flowers wani bangare guda da akama ado tare da jerin kujeru biyu da dan table,wanda wajen ya kasance aduk san da SUHAIL za su yi karatu ko hira su kan fito nan su zauna. Ban da tashin kamshin flowers ba abun da ke tashi agun. Rike mai hannu tai gam kan ta ce, "Yaya." "Naam Hayatiy." "Inna mutu za ka yi kuka?" "Ke kin fi so ki mutu ki bar ni aduniya ni daya?" "Aa." Ta fada cikin sanyayyar murya ,tana girgiza kai,tamkar za ta yi kuka. "Ace Allah zai bani damar zaban rayuwar daya acikinmu,zan zaɓi rayuwarki SUHAILA,ina so ki rayu,ina so kiyi farinciki, na dauki alkawarin sadaukar da kaina in dai zaki rayu a ko ina, ina so ace ko bana duniya ki kasance cikin farinciki,ina so ace ko bana duniya ki zama abun kwatance ga rayuwar al'umma,ina so ki girma ki taimaki al'umma ta fannoni daban daban,ina ji araina cewa ke wata,ke wata ce ta mussaman aduniyar nan, ba zan so ace anyi gaggawar rasaki ba." "Yaya ni to bana so na rayu in babu kai, ba zan iya ba, ni bana so, wallahi bana so, yaya in ka mutu nima mutuwa zan yi,dan Allah mu rayu tare kuma mu mutu tare,ina sonka yaya, ina so na rayu da kai kaine rayuwata." Karasa maganar tayi tana kwantawa a kirjin sa. Bayanta ya fara shafawa yana maganar. "Na yarda ni ne rayuwarki kamar yadda kece rayuwata,hakan yasa Kasancewar ke da matukar muhimmanci agareni SUHAILA,ina sonki fiye da kaina,bana jin cewa da kwai abun da zan so aduniya fiye da ke, murmushin ki ka dai kan iya sani farinciki,to ina ga shi Farincikin naki bakiɗaya?" "Uhum Yaya ni ka min alƙawari cewa zamu rayu tare." "In ban rayu da rayuwata ba to dame zan rayu? In sha Allah zamu rayu tare har karshen numfashin Hayatiy." Kara kyankyame shi tai tana fadin, "Thank you Yaya,ina sonka." Wasa-wasa hoton SUHAILA ya kare ta koma makaranta amman day ba boarding ba, SUHAIL ke kaita kuma ya daukota akullum. Safiyar yau gaba-daya jikin SUHAILA ba kwari. "Yaya ni kamar kar inje skul din." "HAYATIY! Saboda me? Ban san ki da haka ba fa kuma bana so yanzu ki fara muje kinji ga chocolate dinki." Murmushi tayi ta karbi chocolate din tare da fadin, "Thank Yayan Anty Hayatiy." Dariya ya yi yana, "lallai fa Antyn YAYANTA ." suna isa skul kamar kullum har ta tafi ta dawo tare da yi masa kiss afuska. "Bybyee Yaya,Miss you,ka kulamin da kan ka kaji ina sonka." Har ta kara tafiya ta dawo. Asanyaye ta ce, "dagaske ina son ka yayana kaji." Murmushi ya yi, "nima da gaske ina don ki Hayatiy,miss u more." Sai da ta shige class kan ya wuce office. Karfe goma cif gaban SUHAIL ya fara faduwa yana bugawa cikin sauri, ba wadda yake tunawa sai Hayatiy. Keyn motarshi ya dauka kawai azuciyarsq yana jin bukatar ganin kanwarsa yanzu. Kiran wayar da akai mai ya tsaida shi. Daga skul din su SUHAILA ne. Kara wayar da zai akunne aka ce, "Sorry to say sir, SUHAILA...... *DOMIN SHIGA GROUP DINA YI MUN MGN TA WNN NUNBER 08103080717* Urs Xayyeesherthou https://facebook.com/groups/589074325850132/ *HAYATIY حياتي* 18/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ *PAGE*-10 _*Wannan fejin nakune Hayatiy Fans Group,Cute Na Fans Group kuyi yadda kuke so da shi*_ _*Muje zuwa akwai kallo😊, boyayyun masoya kun fi na bayyane yawan gaske,tabbas ina yinku aduk in da kuke😘 Xayyeesherthul-humaerath na maku so ba na wasa ba*_ _*Abi link domin shiga facebook group dina hilis an AMANAN XAYYEESHERTHOU😩*_ Anyi Admitting dinta a asibiti da ke cikin skul." Wani irin jirine ya fara ziyartar SUHAIL nan da nan hankalinsa ya fara gushewa fita ya yi kawai cikin sauri ya nufi motarsa. Figarta ya yi cikin sauri masu gadi sai da suka firgita ganin hakan domin kowa yaga yanayin da SUHAIL ya bar asibitin yasan ba lafiya ba. Tuki yake kawai cikin sauri batare da ya lura da titin ba. Yana isa skul din fannin asitin ya yi kawai tafiya yake kawai amman hankalinsa sam baya jikinsa kan ya karasa ya ciro wayarsa tare da kirin Abou. Abou na amsawa ya ce, "SUHAILA." Daga nan bai kara fadin komai ba. Daga nan Abou ya fahimci cewa akwai matsala gida ya nufa kawai tare da dauko Momah. Kuka Momah ta fara a motar tana fadin, "Shikenan asirin mu zai tonu zai tonu wallahi, meyasa,wai meyasa abunnan zai bayyana yanzu ne, na shiga uku, wallahi ba zan iya rayuwa babu SUHAILA ba kasani." Ta kara fashewa da kuka. Abou driving din sa yake kawai ba tare da yace komai ba illa radadin da zuciyar sa ke yi masa. Momah ta ci gaba da magana, "dagaske Farincikin gidanmu ya zo karshe, gwandamun mutuwa da wannan rayuwar ba zan iya ba, na fadama ba zan iya ba,duk boye sirrin nan da muke ayau yazo karshe komai yazo karshe, komai zai tarwatse,farinciki ya tafi SUHAILA in ta tafi tamkar SUHAIL ya tafine nasani shikenan Abou zan mutu .* "Haba,haba Aisha ki faɗi Alkairi ko kuma kiyi shiru,wannan abun mun san da shi kuma fil azal mun san dole komin daren daɗewa zai bayyana fatanmu kawai Allah ya dubemu,sannan ya ba mu ikon cin jarabawar nan,muyi godiya ga Allah mu kara A kullum domin yana tare da mu." SUHAIL na shiga likitan ya tare shi domin suyi magana. Sam gaba-daya ya kasa zama kuma ya kasa nutsuwa. "SUHAIL ka saurareni rayuwar SUHAILA na cikin haddari babba fiye da tunaninmu duka, ko zan iya sanin sunan maganin da take sha akullum?" Cewar Doctor Umar. SUHAIL ya shiga rudani domin sam bai san wani magani da SUHAILA ke sha fa. Dafa kan shi ya yi can kuma sai ya fara tuno lokacin da Momah ke bin SUHAILA tana fadin tazo ta sha maganin. "Yaya ka ga Momah ko? Kullum da safe sai ta bani wani magani ni bana so ka ce mata lafiyata kalau." A lokacin SUHAIL tunaninsa bai basa ya bincika ya ji maganin miye ba domin ya san SUHAILA da kin magana. Muryarsa na rawa yake fadin, "sai dai Momah suna hanya,amman dan Allah kar ka ce mun SUHAILA ta mutu ko zata mutu,ka faɗamun meke damunta ko ma miye ni zan yi indai zata rayu,in za a iya cire rayuwata asa mata doctor ka cire kasa mata domin ba zan taba iya numfashi ba tare da SUHAILA ba." Da mamaki likitan ke kallon shi. "Kar ka ce mun ba ka san meke damun SUHAILA ba? abun da mamaki to a Gaskiyar lamari ko da kai baka da masaniya iyayenku sun sani, SUHAILA tun tana jinjira alamu ya nuna tana da matsalar wata cuta wadda tana girma cutar ke girma ajikinta sannan duk sanda cutar ta fara bayyana zata konar da jinin da ke cikinta ne kaf haka kuma babbar matsalar itace ba za mu iya mata magani ba har sai wannan cutar ta girma kamar yadda girmanta hadarine ga rayuwar SUHAILA haka ma ciretan domin kuwa za ai yi wuyar samun mutum da zai bada abubuwan da muke da bukata koda da kudine kuwa.* Wata irin gigitacciyar zuface ta fara ketowa SUHAIL. "Doctor ka mun rai ka faɗamun koma miye ni zan yi na fadama zan iya komai kan SUHAILA,ka faɗamun likita." "Akwai bukatar diban jini mai yawa ajikin wani domin sanya mata, sannan kodarta ma ta tabu ana da bukatar dasa mata koda, gwanda koda zamu iya samu cikin sauki amman jinincan da kaji na ambata ba karamin matsala bane domin da yawa muke bukata indai munyi nasarar cire mata wannan ciwon aka sanya jinin tare da kodar akwai yuhuwar ci gaba da rayuwarta ammab bana da tabbaci Allah ne kadai masani." "Na aminci jini na dayane da SUHAILA na san zai mata kodar ma acire kada ka damu da rayuwata ko da ace zan mutu garin hakan kayi damuwata kawai SUHAILA ta rayu kuma kamin alkawarin ba za ka sanar da Abou ko Momah ba, ina so hakan ya kasance sirri tsakanina da kai SUHAILA ta rayu,rayuwarta tamkar tawace." "SUHAIL ka nutsu ka saurareni wannnan abun fa ba wasa bane akwai haddari tattare da shi duka kayi hakuri amman ba zan iya ba." Rike hannun likitan ya yi yana fadin, "Dan Allah kar ka mun haka,ka taimaka ka ceto mun rayuwar ,rayuwata yana da matukar mahimmanci ko nawa ka ke so nayi alƙawarin zan bada. Momah da Abou ne suka shigo cikin firgici. "Doctor Umar ina SUHAILA? Ya jikin nata? Don Allah ka ce mun da sauki." Cewar Momah. Kan doctor ya yi maganar wata nurse ta shigo nishe take ta ma rasa abun fadi, da kyar ta iya cewa, "Doctor SUHAILA ta mutu." Daidai lokacin SUHAIL ya fadi wajen.... *OYAAA HAYATIY FANS KUZO MUYI GAME DINNAN, SHIN KUNA GANIN HAYATIY TA MUTU KO TA RAYU? SUHAIL YA BADA RAYUWARSHI DAN TA TA KO KUWA ABARTA TA MUTU? KO ANEMO WANI?* 08103080717 URS XAYYEESHERTHUO https://facebook.com/groups/589074325850132/ *HAYATIY حياتي* 19/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ *PAGE-11* _*INA KUKE ?🤣NA CE INA KUKE? MASOYAN HAYATIY? OYAAA KI HITO KU RAGARGAJE DA GUNTUN FEJINNNAN*_ Kokarin tallefe SUHAIL doctorn ya yi cikin sauri , zaunar da shi gefe ya yi kan ya nufi dakin da SUHAILA take, Momah da Abou suka bi bayansa SUHAIL kuwa ban da ajiyar zuciya ba abun da yake. SUHAILA kuwa gata kwance ba numfashi. Kallonta doctorn ya yi tare da fadin, "Subhannallah lallai lamarin SUHAILA ya zarce tunanina." Abou ya ce, "Doctor da gaske kana nufin SUHAILA ta mutu?" Nan take Momah ta fadi sumammiya awajen. SUHAIL ne ya ja jikin sa yana dafa bango har ya isa dakin domin jikin sa sam ba kwari. Yana shiga ya karasa gadon da SUHAILA take ya kwanta ajikinta tare da fadin, "HAYATIY, shin da gaske kike daman zaki tafi ki barni? Da gaske kike kin fi so ki rigani barin duniya? SUHAILA na fada miki kece rayuwata, dan Allah kada ki tafi ki barni, kada ki tafi,ina sonki SUHAILA na ce miki ina sonki ba zan iya rayuwa ba in babu ke, kece rayuwata dan Allah kar ki mun haka ki dawo mu rayu tare kin manta alƙawarin da ki ka mun ne? HAYATIY ki tuna alƙawarin mu zamu rayu tare dan Allah kar ki mun haka ki dawo mu rayu." Fashewa ya yi da kuka yana kara kwanciya ajikinta. Ban da fadin Innalillahi-wa inna-illaihir-raji'un ba abun da abou ke yi domin ga Momah can assume SUHAILA ma kwance ,haka SUHAIL hankalin sa ya bar jikinsa. Ban da sambatu ba abun da yake yi. Daga karshe bai san lokacin da wani irin barci ya kwashe shi jikin SUHAILA ba Momah kuwa anfita ita adakin an kaita na hutu domin ana sa ran farfadowarta a cikin mintuna kadan. Kamar cikin mafarki SUHAIL ya fara jin numfashin SUHAILA tana kiransa a hankali. Afirgice ya farka da mamakinsa kuwa tana numfashi amman bata kiransa. Da gudu ya fita yasanar da Doctor,da mamaki kuwa doctor ya tarar SUHAILA na nunfashi. SUHAIL ya rike hanun doctorn tare da fadin, "Umar dan Allah ka taimakeni koda ni ba zan rayu ba SUHAILA ta rayu acire koma miye nawa asa mata kuma kamin alkawarin cewa ba zaka sanar da su abou ba." Ba yadda doctorn ya iya domin ya san shaƙuwar SUHAIL da SUHAILA hakan ya sa shi amincewa domin yin wannnan aiki mai tattare da babban hatsari. Batare da su Abou sun sani ba aka fara shirin aiki SUHAIL yasa hannu nan take aka shigar da SUHAILA da SUHAIL dakin opretion . Momah na farkawa ta kalli Abou, "Ka ga ni ko? Wai da gaske SUHAILA ta mutu? Da gaske ne? Dan Allah ka ce mun karyane Abou kaji, shikenan asirinmu ya tonu Farincikin ahalinmu ya tarwatse zan mutu nima nasan mutuwa zan yi kawai." "aa Aisha kiyi masu addu'a duka , wannan ƙaddarar mu ce kuma kada ki yi sako wa Allah gode masa ya kamata mu kasance masu yi akullum." Shigowar doctor ne ya katse su yana fadin, "Abun mamaki abun al'ajabi SUHAILA na raye kuma in sha Allah ayau zamuyi maganin wannan lalura tata domin yanzu haka anyi nisa wajen yi mata aikin." Tashi Momah tayi ta zaune tare suka furta. , "Alhamdu Lillah Allah mun gode ma." Abou ya ce, "to doctor SUHAIL fa yasani?" Doctor ya yi shiru can kuma ya ce, "E,e yana ma tare da ita yanzu haka." Abou ya kalli Momah" yanzu abu mafi mahimmanci shine muyi alwala muyi sallah domin nuna godiyar mu ga Allah daman na fada miki Allah na tare da mu kuma shi zai yi mana magani,kinga komai yazo cikin sauki ko?" Murmushi kawai ta yi tana mai jin dadi aranta. Zuwan Wani Attajiri ne ya tsaidasu tare da fadin , "Dan Allah ko kai ne Alhaji Muhammad?" "Eh" Abou ya amsa cike da mamaki. Murmushi wannan Attajirin Ya yi kan ya ce, "Na san za ka yi mamakin ganina ko? Amman kafin nan ina Suhaila? Ina fatan tana cikin koshin lafiya? Dan naji ance sanadin ta kukazo asibitin nan." Wani irin kallo Abou da Momah suka ma juna. Niko nace anzo wajen. Cikin dimuwa Momah ta ce, "Shikenan dukkan komai zai bayyana rayuwa ta fara juya mana baya." Ta karasa maganar tana faduwa ƙasa. Attajirin ya ce," .... *†Ahito awasa kwakwalwa,shin wannnan mutumin waye?sannan kuma meke shirin faruwa?†* 08103080717 Urs xayyeesherthuo *HAYATIY حياتي* 28/09/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ *PAGE-12/13* _*HAKURI MAI YAWA GAREKU MASOYA😫BANA DA LAFIYA NA KASA TYPING,NA GODE DA KULAWAR KU GARENI*_ _*DOMIN KU KADAI MY GROUP MEMBERS INA YINKU HAYATIY FANS GROUP MUJE ZUWA*_ "Banzo dan tada maku hankali ba ko wani abu, nazo ne domin tunatar da ku cewa tabbas wani cikin dangin SUHAILA na raye." Momah ta Bude baki. "Dangin SUHAILA Kamar ya?,Ban Fahimta ba, Dangin SUHAILA fa." Murmushi ya yi kan ya ci gaba da magana. "Sosai kuma kada kuyi Mamakin Hakan,Nine na rubuto komai na jikin takardar kuma duk labarin SUHAILA Gaskiya ne ba ƙage ko kadan,kar kuyi mamaki innace maku agabana ɗanku ya dauketa kuma ina lura da komai da ke wakana agidanku." Abou ya ce, "Ikon Allah kenan." Murmushi wannan dattijon ya yi kan ya ce, "Ina SUHAIL? Ina bukatar ganinsa cikin gaggawa domin da kwai maganar da zamu tattauna da ku duka ayanzu tana da matukar muhimmanci." Kan Abou ya yi magana SUHAIL ya fito daga dakin operation,ya jima da farkawa amman kasancewar ba yaso su Abou su fahimci komai ya tsaya har sai da ya gama dawowa hayyacinsa. Ganin Iyayen nasa ne yasa shi kakalo wani murmushi yana karasowa garesu a hankali . Attajirin ne ya yi murmushi tare da kallon shi yana fadin, "madalla da kai ɗana, madalla da kyawun dabi'u irin naka,in babu damuwa Ina so mu samu waje mu zauna domin tattaunawa." Kallon Abou SUHAIL ya yi da alamar tambaya. Murmushi Abou ya yi tare da fadin, "SUHAIL kar ka damu muje mu zauna zaka fahimci komai in sha Allah." Bangaren da mutane ke zama domin ganin likita suka nufa kasancewar darene ba kowa. Attajirin ne ya fara jawabi kamar haka, "Kamar yadda kuka sani kuma na sani SUHAILA tamkar haske ce ga rayuwar duk wanda take tare da shi,banzo da niyar kwace maku ita ba, illa sanar da ku wacece SUHAILA, bazan manta da ranar da kuka samu SUHAILA ba domin ni na aje maku ita, kan nan ina so ku sani cewa SUHAIL Ne Mijin SUHAILA akwai bukatar daura masu aure cikin gaggawa,SUHAILA 'Yace ga Wani Hamshakin mai kudi kuma Attajiri mai suna Muhammad Sa'id wanda bai da dangi face matarsa Ramla da cikin da ke jikinta, kwatsam abokan kasuwanci tare yaransa suka haɗa baki domin hallakasa tare da matarsa dan su kwashe wannan arzikin,sunyi nasarar kashe Muhammad Sa'id ya yin da matarsa ta tsere da cikin da ke jikinta aranta tasa cewa ko da ba za ta rayu ba tana son yarta tazo duniya kuma ta rayu kamar kowa,kar kuji mamaki innace maku ni ba BIL ADAM bane." Abou, Momah da SUHAIL suka tsaya kallon juna cike da Mamaki. Ya ci gaba da magana, "Kada ku tsorata kuma kada ku sa komai aranku domin ni banzo dan cutar da ku ba koda wasa, yayin da Mahaifiyar SUHAIL ta samu damar tserewa yayin da ta gama jigata ba mai taimakonta sai Allah domin daji ta shiga wanda ba ta san gabansa ba bare bayansa, alokacin Allah ya kawoni ta tsaka da nakuda,na matukar tausaya mata, hakan yasani taimakonta har ta haihu sannan ta fada mun dukkan abun da ya faru a karshe ta bani mukudan kudaden da kuka tsinci suhaila tare da su,kuma wa innan kudaden ko kwata ga arzikin Mahaifin SUHAILA bai kai ba,in manta ba ajikin takardar nan na sanar da ku cewa yarinyar ta jigata sosai kan tazo duniya akwai bukatar ta ga likita,wanda shine musabbabin ciwon nan da ya kamata har da yau akai mata aiki,ina sane da bawa likita ya dubantan da kuka yi har zancen cewa aboye ws SUHAIL, ni ba Mutum bane kamar yadda na sanar da ku hakan ya sani fidda SUHAILA awannan dajin yayin da mahaifiyarta ta rasu,kuma na kawota wancen asibitin ba wai dan bana Sonta ba,illa nasan cewa ba zata iya rayuwa cikin Jinsin da ba nata ba,in ma ta iya to tabbas na kwareta,sannannake so ka auri SUHAILA ba illa tamkar garkuwa take arayuwarka,kai ne mafi dacewa tayi rayuwa da shi hakan yasa ba wanda ya ganta illa kai domin da kai tafi cancanta ku rayu tare, lokaci ya yi, lokacin da zanxo ne Yayi domin suhaila tana matuƙar so da kishinka, abu daya ke tarwatsa mata tunani cewa ku yan uwan junane,dan haka na san kai ma kana sonta ka ma fi kowa sonta aduniya ,abu daya nake so kumin kada ku taba bari SUHAILA ta san cewa ita ba yarku ba ce,ina so ya kasance kun nuna mata cewa SUHAIL ne ba danku ba,domin nuna mata cewa ku ba iyayenta bane tamkar barazanace ga rayuwarta har ma da taku,ina so wannan sirrin ya kasance iyaka ni da ku." Numfasawa Momah tai ya yin da Abou ya tafi dogon tunani. *WAIWAYE* Wata rana juma'a da afkuwar Jarabawa tare Alkairi ya kasance duk ga wannan ahali Momah ce rangaranga ba lafiya,ban da jini ba abun da ke gangarawa daga jikinta bakin asibiti kasancewar basa da kudin aikin da za ayi mata. Abou zaune gabanta ya yi tagume ya rasa abun fadi ban da hawaye ba abun da ke kwarara a idanunsa. Yanayin da SUHAIL keta zagaya asibitin. Kwatsam ya ga jaririya cikin ciyayi tana kuka gefenta wata tsimmace tare da takarda. Ihu SUHAIL ya yi tare da fadin, "Abou ga Babyn Momah anan bata mutu ba." Dasauri Abou ya ƙaraso mai zai gani jaririyace abar tausayi ban da kuka ba abin da take,tausayinta yasa shi saurin mantawa da damuwarsa tare da daukanta,abun mamaki sai ga makudan kudi da wata farar takarda sun fado kasa. Takardar abou ya fara karantawa "Wannan 'ya amanace ga duk wanda ya tsince ta,kuma wannan kudaden Mallakinta ne,sannan ya hallarta ga duk ahlin da suka tsince ta zasu iya rayuwa da su kuma rayuwa mai inganci, alƙawari daya kada abari ta zubda hawaye mara dalili ita din amanace,akaita asibiti aduba lafiyarta domin ta sha azaba kafin zuwa duniya,bata da suna amman kuna da damar sanya mata suna, kuma tabbas watarana ina zuwa." Alokacin Abou ya daga hannu sama tare da godiya ga Allah domin kuwa an samu warakar Momah cikin sauki ga kuma ɗiya da suke da matukar bida. Nan da nan Abou ya biya kudi aka fara yiwa Momah aiki nan take. Yayin da SUHAIL ya kyankyame SUHAILA duk da yunwar ds take ji nan take ta daina kuka madara abou ya siyo da kan shi ya bata tasha sosai har ma tai barci. Ko da Momah ta farka Abou ya mata bayani tayi farinciki ds hakan sosai,abu daya ne ya dameta sanar da su ciwon SUHAILA da likita yayi sun san cewa SUHAIL na sani za a shiga matsala domin bashi kadai ba su kansu Allah ya jarabesu da matuƙar kaunar SUHAILA. Madara aka ci gaba da bai wa SUHAILA har girmanta. Ya yin da Abou ya fara juya wannan dukiyar da tai sanadin arzikinsa. Tunda Momah ta haifi SUHAIL duk cikin da ta samu sai ya zube. Wannan har ya kai wata biyar shima ya zube wanda yazo da hadari ina bukatar mata aiki ajuya mahaifiyar tare da wankin ciki,amman basa da halin wannan. Ci gaban labari... Attajirin ya ci gaba da magana, "Ina maku fatan Alkairi." Daga wannan maganar ya bace. Ya yin da SUHAILA ta farka.... *SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI FARU?* Urs xayyeesherthuo *HAYATIY حياتي* 1/10/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ PAGE-14 *HAYATIY FANS🙏NA SAN KUNA HAKURI AMMAN DAN ALLAH KU KARA WANNAN FEJINMA GUNTU NE KAWAI NAYI NE DANKU KU CI GABA DA MUN ADDUA ALLAH BANI LAFIYA DA IKON YI MAKU MAI YAWA* SUHAIL ta fara kira abakinta. "Yayana,Yaya Ka zo ka ji, Yaya ka zo." Tana Maganar tare da mika hannunta idanunta arufe. Likitanne ya yi saurin zuwa ya sanar da su domin SUHAIL yaje suhaila ta farka. Ko da ya shigan ma shi kawai take kira. Saurin karasawa gareta ya yi tare da riƙe hannunnata. Nan take ta bude ido tana fadin, "Ina Sonka Yayana,ba zan iya rayuwa ba in babu kai kar ka tafi ka barni kaji." "Nima Ina Sonki SUHAILA,ina kaunar ki,kece Farinciki na kinji." "To ba ka ce ba zaka tafi ka barni ba." "Ina so na rayu da ke kuma bana son in tafi in barki kinji Hayatiy na, yanzu ki bar surutu haka kinga ba kya da lafiya." Kwanan SUHAILA biyar aka sallameta a asibiti. Tsantsar So da Kauna tare da tausayin SUHAILA ya kama su fiye da,babbar matsala da damuwarsu a yanzu shine yadda za a tinkari SUHAILA da maganar Auren SUHAIL. Zaune suke afalo Abou ya fara magana . "Yawwa daman ina son magana daku, SUHAIL kayi girman da dole akwai bukatar fadama kai wanene ,bana so ko fatan na bar duniya ba tare da na sanar da kai sirrin da muka binne shekara da shekaru ba." Nan Abou ya kwashe duk abun da ya faru da SUHAILA ya mai da shi ga SUHAIL. Hawaye ta fara ta tashi ta karasa gun yayan nata tare da rike masa hannu tana , "Yaya kayi Hakuri kar ka yi kuka kaji, Dan Allah kar ka yi kuka, nikam na bar ma Abou da Momah kyauta har ma da Kakata, Yayana ina sonka kar ka ce zaka bar mu kaji sorry." Ta fashe da kuka tana rungumarsa. SUHAIL ma ya rungumeta yana murmushi, "Shikenan ai ni ban yi kukan ba kinyi ina zan yi kuka kin bani aron Abou da Momah Oyaaa smile HAYATIY." Ya fada yana share mata hawaye. Murmushi tai ta ce, "Umm ba Aro ba na baka kyauta kaji." Kumatun ta ya rike yana, "Thank you Hayatiyn Yaya,amman kin san miye? Zan yi kuka in baki yarda da wani abu ba." Shagwabe fuska tai tana, "Yaya Kar ka yi kuka ni bana so kar kayi kaji,kar ka yi fadamun zan yarda ni bana so ka yi kuka." Rike hannunta yaiy tare da tashi, "Zo muje muyi magana sirrine bana so Momah da Abou su ji." Murmushi Momah da Abou ,tare da kaka su ka yi lokaci guda kasancewar sun san maganar da SUHAIL zai ma SUHAILA. Gwalo tai wa kaka tana, "Ba dai za ki ji me za mu ce ba." Kaka ta ce, "Yoo me za ku ce da ya wuce maganar doyar turawa." Suna fita wajen dai da suka saba zama domin tattaunawa suka nufa. "Hayatiy kina son Yayanki?" Ta girgiza kai alamar eh "Zaki iya Auren Yayanki?" Wani irin faduwar gaba SUHAILA ta ji Nan da nan hawaye ya fara zubo mata. SUHAIL ya ce.... *ME KUKE GANI SUHAILA TA AMICE KO KUWA A'A?* *XAYYEESHERTHUO* *HAYATIY حياتي* 3/10/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ *PAGE-15* *SADAUKARWA GAREKU HAYATY FANS GROUP❤️* *AMEENATOU YAR KAKA YANA HANYA IN SHA ALLAH KU GYARA ZAMA🥰* "Hayatiy in bakya sona ki fada kinji,ba zan miki dole ba kuma ba wanda zai miki dole domin zabinki shine Farincikin ki."ya karasa maganar yana share mata hawayen da ke fuskarta. Dagowa tai ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai,cikin sanyayyar Muryarta ta ce, "Ni Yaya Ina so,kuma ni Bana son kowa." Murmushi SUHAIL ya yi, "Hayatiy indai wannan maganar zata sa ki takura tare da jin kunyata. To kawai abari in nemo miki Anty." Bata rai tayi ta dago tare da shagwabe fuska, "Yaya ni bana so, bana so, Ni ni ni kadai ka ke so,kuma ni kadai za ka..... Sai tayi shiru. Suhail ya ce, "Karasa Mana." "Uhum,uhumm , uhumm ni." Ta fada tana kokarin tashi. Dasauri ya rike hannunta yana, "ni sai kin fada ko nai fushi." Cikin shagwaba ta ce, "Yaya hannuna zafi ka sake mun zan zauna kaji." Sake mata hannun ya yi yana, "Sorry Hayatiy." Kamar zata tauna sai kuma ta tashi ta zura aguje har taje kofar falo kan juyo, ta ce, "Yayana Zan Aura." Ta shige ciki da gudu. Murmushi SUHAIL ya yi yana hamdala aran shi yake fadin, "Tabbas SUHAILA ce rayuwata in ba ita ba zan iya komai ba,ina sonki HAYATIY." Tana shiga ta dane cinyar Momah tana dariya. SUHAIL ya biyo baya yana, "zan kama ki ai." Abou ya yi gyaran murya kan ya ce, "To yanzu sai akiyaye, ina tunanin mu bari SUHAILA ta karasa karatunta kan afara maganar aure." SUHAIL ya fara sosa kyeya,yana so ya yi magana amman ya kasa. Kaka ta kalleshi. "To fa akwai magana tunda kaga ya fara sosa kyeya kamar kunkurun karkara." Abou ya kalli SUHAIL kan ya ce, "Meya faru in hakan bai ma ba ka fada." Ya ci gaba da sosa kyeya , "um Um Abou daman Wai,in da Haline Ayi Yanzu." Kaka ta ce, "yoo ga magana nan ta fito ai daman nasani kuna ganin shi da ido kamar gurjiya." Murmushi kawai Abou ya yi kan ya ce, "Shikenan ba matsala ku fara shirin biki nan da sati in sha Allah, tunda angama gina sabon gidan can ma." Ba karamin dadi SUHAIL ya ji aranshi ba domin gani yake in aka ja bikinnan za a kwace mi shi Rayuwarshi. ,,,,Nan da nan aka fara shirin biki ba kakkautawa ya yin da Momah ta dauke SUHAILA agidan ta maidata gun kawarta domin gyarata. Kullum SUHAIL ban da kewar SUHAILA ba abun da ke damunshi itama haka,ba yadda suka iya haka sukayi hakuri domin hatta wayarta Momah ta kwace ta ce baza su hadu ba har sai ranar daurin Aure. Wasa-wasa akwana atashi yau ta kasance ranar daurin auren SUHAIL da Hayatiy. Ya gama shirin shi tsaf za a tafi daurin aure ya wuce dakin Hayatiy. Ganinta ya yi bakin gado zaune tayi shiru tana ganinsa ta tashi da sauri ta rungumeshi. Zaunar da ita ya yi kan shima ya zauna. "Yaya Da gaske kai ne mijina? Da gaske kai zan aure? Zamu rayu har karshen rayuwa,ina sonka Yayana ka mun alƙawari ba za ka rabu dani ba dan Allah,dan Allah kaji." Ta karasa maganar tana kuka. "Hayatiy ina sonki fiye da tunani ko zatonki,ina so inyi rayuwa da ke fiye da kowa afadin duniyarnan kullum ina fada miki kece rayuwata da gaske hakan ne ba wasa ba,kimun alƙawari za ki kulamun da kanki duk rintsi duk wuya,ki rikemun mutuncinki da kimarki na 'ya mace ina miki so fiye da zaton kaina." "Yaya nima ina sonka kuma ina so mu rayu tare,ina sonka sosai ba kadan ba,ko nama laifi karka rabu dani kaji,ina sonka." "Ko da bana duniya zuciyoyinmu na san suna tare kuma zasu kasance cikin farinciki, Kanwata, rayuwata,kuma farincikina, haka kuma matar da nake burin aure ina matukar kaunarki Hayaty." Ta kara rungumeshi, " nima ina matuƙar kaunarka Yayana kaji,na fi kowa sonka aduniya kuma ni kai yayana ne kadai ba na kowa ba,yayan Hayaty ne ko?" Taji shiru. Ta kara magana, "Yaya ina kai nawane Ni kadai ko?" Har yanzu dai shiru. Ta fara shagwabewa zata yi kuka, "Yaya kamun magana zanyi kuka fa,ina kai yayana ne ni kadai?" Ta fara jijjiaga shi ba alamar motsi atattare da SUHAIL, kuka ta fara tana, "Yaya ka fadamun kace Ni ƙanwar kace ni kadai kar kace kadaina sona dan Allah,ina sonka kaji,yaya kadai na wasannan kamun magana,ni kamun magana, ka tashi kamun magana kaji." SUHAIL ya bingire kan gadon ba numfashi kuma ba motsi Innalillahi-wa inna-illaihir-raji'un _*dukkan mai rai mamacine*_ Dukan kirjinsa ta fara tana, "Dan Allah yaya ka mun magana ,bana so,na ce ma ni bana so kumun magana dan Allah,zan yi kuka,wallahi kuka xanyi yaya ka tashi,nq ce ka tashi." Gani tai bai da alamar magana ko motsi Wata irin kara tai da sai da ta kauraye gidan kaf "Yaya ka tashi,ka tashi dan Allah, kwanciya ajikin sa tai tana kuka." Tuni jini ya fara fita ta hanci, da bakin . Momah ce ta fara shigowa sannan yan biki abayanta SUHAILA ta dago tana. "Momah dan Allah kicewa Yaya ya tashi bana son wasannan ni bana so,wallahi ina son yayana, Kuma shi nawane ni kadai." Wani irin jirine ya Fara ketowa Momah. SUHAILA kuwa nan take ta fadi sumammiya. *DOMIN SHARHI KO TSOKACI KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER,08103080717* Urs xayyeesherthuo *HAYATIY حياتي* 9/10/2021 *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° *https://www.facebook.com/106494781436168/* _*XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*_ _(Mrs Ɗangote)_ _*HAYATIY:* Labari mai cike da tsantsar Soyayya, Amince tare da Sadaukarwa,sarƙakiya mai ban mamaki_ _*PAGE-16*_ 🔚🔚🔚🔚🔚🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙🔙 _Allah ya yi,Labari mafi gajarta acikin arubutuna na littafi,kuma littafi na daban🥲 dole inyi kukan rabuwa da Hayatiy domin mun saba😂🤚amman ya muka iya da kaddarar rayuwa? Suhail ya dauke abar shi_ _*Albishir ku mun murna an mun takwara Aysha ana kiranta Xayyeesherthuo🤚😂kar kuyi mamaki innace kamarmu daya da little Xayyeesherthuo*_ [10/9, 5:28 PM] Xayyeesherthul-humaerath: Farkawa barci ta yi cikin shesshekan Kuka, tana fadin, "Momah kina gani Yaya bai mutu ba ni na ce miki bai mutu ba, Yaya ka tashi." Sautin Kukanta yasa Momah,Abu da SUHAIL suka fito atare cikin gaggawa. Suna shiga dakin SUHAIL ta rugume tana shekar kuka, "Yaya Dan Allah kar ka mutu kaji,ina sonka,inka mutu binka zan yi nikam." Ta kara fashewa da kuka. Rugumeta ya yi yana, "Oh Sorry,kiyi shiru kinji ba zan mutu ba,in Sha Allah zan rayu da Hayatiy na,yanzu fada mana me ya faru?" Cikin Muryar kuka ta ce, "To ba kai ne,na yi mafarki ka mutu ba." Daga Momah har Abu murmushi kawai su ka yi. SUHAIL ya ce, "To ai mafarki ba gaskiya bane,yanzu ba gani kina gani na ba,maza je kiyi addua ki kwanta." "Uhum,uhumm ni Yaya Ka mun alƙawari ba za ka mutu ka barni ba,kaji,ina sonka,ina sonka Yaya." SUHAIL ya ce, "Nayi alƙawari in sha Allah to je ki kwanta." "Uhum yumm ni aa." Momah ta ce, "miye haka kuma? Ba gashi ba? Maza je ki kwanta." Kuka ta fara gani take inta tafi ta kwanta yayan nata zai mutu da gaske. "Yaya Muje Falo mu zauna kaji,ni bana jin barci kuma ba na son Zaman dakinnan, Ni bana so ka mutu,ba zan yi barci ba,ni na daina Barcin ma." SUHAIL ya ce, "To muje." Momah za ta yi magana Abu ya dakatar da ita da ido kawai su ka fice. Ranar kuwa Barcin da SUHAILA ba tai ba kenan ko ta fara cikin sauri zata farka ta kalli Yayanta tare da sake mi shi murmushi. Washegari kuwa kowa ya sheda daurin auren SUHAIL da SUHAILA. Anyi shagalin biki na rana daya ba tashin hankali mai ciki da kayatarwa [10/9, 5:50 PM] Xayyeesherthul-humaerath: An kai Amarya gidanta kowa ya watse daga SUHAIL sai SUHAILA. Daga mata mayafin fuskarta ya yi tare da fadin, "Alhamdu Lillah tsarki ya tabbata ga ubangijina da ya hallaci wannan tauraruwar tawa." Daga hannunta tai tare da rufe fuskar ta tana dariya. "Laaa Hayatiy na jin kunyar Yaya ba za ta bari ya ga kwalliyarta ba,to bara inje waje inga na wasu." Shagwabe fuska tai cikin sauri ta sauke hannayen nata riko hannun yayannata tai cikin sanyayyar murya ta ce, "Yaya bana so ka kalli kowa,ni kadai za ka na kallo ni ce kawai ka ke so kaji, zan ma duk abun da ka ke so kar ka kalli wata in ka kalli wata zanyi kuka." Ta karasa maganar hawaye na zuba daga idanunta. Dawowa yaiy ya zauna ya fara goge mata hawayen kan ya ce, "Waya ce miki zan kalli wasu bayan kanwata? Kina tunanin kona kallesu za su min kyau ne kamarki? Ko kwatan yanayinki bana taba gani afuskar wata mace,kanwata tafi kowacce kyau aduniya,kuma ta fi kowacce mace iya murmushi aduniya,ki mun murmushin kinji,ki daina mun asarar hawayenki ina jin zafin hakan har cikin raina Hayatiy." Murmushi tayi tare da kwanta a kirjin yayan nata. "Yawwa goog gurl." Cewar SUHAIL ya na shafa bayanta. "Uhumm ni Yayana ya fi na kowa,ina son shi,ina alfahari da shi,kuma ni ina kishinsa bana so kowa ya so mun shi,shi nawane ni kadai,Yaya kace ni kai nawane ni kadai kaji." Kara rungumeta ya yi kan ya ce, "Wayace Yayanki ba naki bane? Yayan HAYATIY ne ita kadai ba kowa,Oyaa yanzu mu tashi muyi sallah mu ci kazarmu ko?" "Uhumm uhumm ni ba zan ci kaza in ba." "Sai fa kinci ." Ya fada yana rikota suna saukowa agadon. Ko da su ka yi sallah suka idar da kyar SUHAIL ta ci naman nan sau biyu. Nan take kuwa ta bingire da Barcin karya jikin Yayan nata. Murmushi ya yi azahiri ya ce, "Ayyah Hayatiy ta gaji ko kayan Barcin bata sa ba bara in gama insa mata." Kara lumshe ido tai domin ko kadan bata so ya fahimci idonta biyu. Haka ya gama canja kaya ya sa mata har ya kwantar da ita tana ji,kan tai barci. *Rayuwar Farinciki ta haskaka wannan sabon ahali ta kowanni fanni domin kuwa SUHAILA na samun kulawa fiye da na da wajen Yayanta* [10/9, 6:17 PM] Xayyeesherthul-humaerath: Bayan Wata Shida, SUHAILA ce ta fito da tsohon ciki tana tafiya da kyar, "Yaya,Yaya kana ina? Ni kazo ka goyani, wallahi na gaji da nauyin cikinnan kazo ka goyani ni humm." SUHAIL da ke ta typing a system dinsa ne ya dago tare da fadin, "Hayatiy yau abun yazo kainan yanzu dan Allah wa zan goya tsakanin abu uku,Cikin Jikin naki? Kibar taki? Ko kuwa zallan ke din?" Zama tai agun za ta fara kuka, "To wa ya maidani haka,ina Yayanane? To ni wallahi ka karbi cikinka ma bana so." Ta fara kuka. Tasowa ya yi ya durkusa gabanta, "in karba in kaiwa wata ta haifamun kenan?". Da sauri ta ce, "Aa ni bar mun abuna kuma ka bar kallona, ka bar ma kulani." Dariya SUHAIL ya yi, "To naji kin san dai ba wadda zan kai ma ko,yanzu fadamun abun da kike so muje mu siyo." "Uhimm chocolate ni ina so." "Bayan shi fa?" Cewar SUHAIL. "Yhum sai Yayana kawai ina so." Rike hannunta ya yi yana kokarin taimaka mata ta tashi. "Yayanki ai daman naki ne bana kowa ba ko? Ya karasa maganar tare da kai mata kiss." Dariya ta yi, "zan rama ai." Akwana atashi har cikin SUHAILA ya kai haihuwa ta sulubo er ta ta mace. An sanya mata Aisha ana kiranta Xayyeesherthuo _*Hhhh Fans kumin murna Hayatiy ta mun kara ysn*_ Bayan ta haihu ta karasa karatunta nan take SUHAIL ya nema mata aiki a asibiti , Little Xayyeesherthuo kuwa har ta fara zuwa skul,kar kuji mamaki innace ma ku da ni take kama,hhh lol. SUHAIL kuwa dukafa ya yi wajen nemawa SUHAILA hakkin mahaifinta da aka danne batare da kowa ya sani ba,sai da ya yi kokarin kwato komai kan ya tara aka sanar da SUHAILA gaskiyar komai Duk da cewa hakan ya tabata amman bata damu ba kasancewar ta tare da SUHAIL. Murmushi ta yi tana fadin, "Yaya Allah kan iya kashe wasu arayuwarmu sanan ya Turo mana wasu muyi rayuwa tare domin sune mafi cancanta ga rayuwarmu Ina sonku Momah,Abu,Yaya,Hajiya Kaka." Suhail ya ce, "Ina alfahari da ke Hayatiy na Allah karawa rayuwarki albarka." Suhaila ta ce, "To Yaya Agoyani." Kallonta suka yi duka kan suka sa dariya. Little Xayyeesherthuo ta zo da gudu, "Aa ammier ni Abhie zai goya." Alhamdu Lillah💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 I'm Done💃💃💃💃💃 Ya Allah in nayi kuskure acikin littafinnan ka yafemun🙏 Godiya mai yawa gareku Masoyana🤩 ina maku so fisabillah. Feel free in kina bukatar magana dani ki dau numberta 08103080717 Masoyan boye da na zahiri tabbas duk ina yinku over🤩 AMEENATOU YAR KAKA is loading 💯 ku shirya kwasan dariya amman paid book ne in kin karanta MATAR POLICE da KUCHAKAR KISHIYA ba sai na ce komai ba kun san salon ai😂🤚 mu tare a Aminatu daure ku siya naki tun wuri. Urs Xayyeesherthuo