*HASKEN CIKIN DUHU💋* *My dearest fans,To everyone who held on to light… even when darkness whispered louder. This is for u, Duhu na iya zuwa, amma haske ya san hanya✨🥺💃* To the woman who guides me, Na'ima Sulaiman Nimcyluv. Your words teach me, your actions shape me. Kamar haske ne a cikin duhu, ba kawai kina gaba na ba, kina cikin zuciyata. Na gode. For your wisdom, for your strength, and for never letting me lose my way, thank u marh🥺❤️. HASKEN CIKIN DUHU Nanameera, YOTA/23. *Tubman Boulevard, (First Liberian civil war.)* *December 1991, Monrovia* Sansanin ECOMOG, 2:34am. Daren yaƙi ne, ba dare na hutu ba. Wutar da ta tashi tana cilla ƙyaftin haske a cikin duhun da ya ƙi tausayawa. Sama ta cika da ƙura da ƙamshin jini, gurnanin masu rai da kukan marasa ƙarfi yana gauraye da karar bindiga da fashewar bama-bamai. Kamar ƙahon ƙarshen duniya ne ke busawa. Gajimare sun rufe wata, kamar shi ma yana nadamar kallon wannan azaba. Gwanaye da marasa ƙarfi, duka suna fadowa ƙasa ɗaya. Abin da ya rage daga dare shi ne sanyi, tsoro da ƙamshin ɓarna, alamar cewa duniya bata da tausayi ga mai rauni. General Khal B. Musa ya ɗaga idanunsa yana kallon sararin samaniya wadda tayi wani irin baƙi, sauke idanunsa ƙasa ya yi yana jin ƙarar harbin bindiga wanda ke tashi daga hannun damansa. Dafe saitin zuciyarsa ya yi yayinda ya zuciyarsa ta tuno da wani abu, wani abu wanda yake a muhimmanci a gare shi fiye da komai, wani abu wanda ya kasance rauninsa. Abokinsa Colonel Bashir dake gefensa ya dafa shi cikin sanyin murya ya ce"tana cikin aminci in sha Allah" ɗago idanunsa wanda suke kamar garwashi saboda tsabar jan da suka yi ya yi ya zuba masa, kafin a hankali ya shiga buɗe laɓɓansa, sai dai kafin ya kai ga furta wata kalma suka ji wata mummunar ƙara, ƙara she ta fashewar nakiya, wadda ta tashi tare da ƙarar ɗaruruwan mutanen da suka sake rasa rayukansu. "Kar kaje!, bamu da issheshen harsashi, wait!" Khal B. Musa bai ko juyo ba ballantana ya saurari abin da abokin nasa ke faɗa masa, sai da ya yi ɗan nisa dashi yana tafiya toward direction ɗin da nakiyar ta fashe ya juyo gabaɗayansa yana kallonsa ya ce cikin wata murya mai amo “Ban zama soja domin tsira da kaina ba,” ya ce. “Na zama soja domin kare waɗanda basu da ƙarfi.” Daga haka ya juya ya cigaba da tafiya yana taka duwarwatsun dake cikin sansanin. Duk yanda harbe harben bindiga ke tashi hakan bai hana Khal B danna kansa cikin gidan ba, duk da kuwa ya san ba lallai bane ya fito da ransa, kasancewar babu wadatattun kayan aiki a wajensa. Harbi ya sakarwa wani daga cikin yan ƙungiyar NLEP, nan take ya faɗi ya mutu, ya ƙarasa inda wata ma'aikaciyar jinya ke kwance cikin jini, gefenta wani ƙaramin yaro ne, wanda daga gani tana ƙoƙarin ceton rayuwarsa ne, a fusace Khal B ya ɗago da niyyar sake wani harbin sai dai kafin ya yi wani yunƙuri harsashi ya zo ya fasa ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa. Durƙushewa ya yi a wajen yana dafe inda aka harbenshin, duk da haka bai sare ba, ya sake yunƙurawa a karo na biyu, sai dai shima ɗan ta'addan bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake sakar wani harbin, wanda kuma kai tsaye ya dira a cikinsa, baya ya yi cikin wani fim yanayi, azaba na shigarsa ta ko'ina, ya lumshe idanunsa hawaye ya gangaro gefen fuskarsa, hotonta yake gani a cikin idanunsa. Tunanin halin da take ciki yake yi. “Ka dawo da wuri, nafison na haihu a gabanka, ka dawo Yallaɓai!” Yaji sautin muryarta cikin kunnuwansa, tamkar yanzu take faɗa masa maganar. Bakinsa na wani irin rawa numfashinsa na kakkatsewa ya ce “Jidderh!... Jidderh!” Cak! Numfashinsa ya tsaya, idanunsa suka rufe, wanda ke alamta cewa tabbas rai ya yi halinsa, he died!. *Nigeria, Asokoro district hospital,* 3:45am. Mummunar bugawa zuciyarta tayi, tayi saurin dafe ƙirjinta, wani irin abu taji yazo ya tokare mata a maƙoshi, a hankali ta miƙe daga kwancen da take, ta kai hannunta ta janyo wani ɗan ƙaramin bedside enlargement ta zubawa idanu, wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri akan fuskarta, daidai lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin. Bata ɗago kanta ba, domin bata ma san an shigo ba, hankalinta na kan abun da tafi da so da ƙauna duk duniya. Dafata taji an yi wanda hakan ya sanya ta ɗago runannun Idanunta. "Kiyi haƙuri Jidda, ko dan abin da ke cikinki" Faɗawa jikinta tayi tana sakin wani raunataccen kuka, "Khalid Hajiya!, Khalid ya dawo Hajiya!, banason na haihu baya nan, ya yimin alƙawarin shine zai zauna dani har na haihu!, ina jin akwai abin da ba daidai ba Hajiya!. Tabbas akwai abin da yake faruwa, inason ganinsa" Ajiyar zuciya babbar matar tayi, har sannan tana riƙe da Jidda ta ce"Khalid yana nan lafiya klao, kuma zai dawo gareki in sha Allah" Kasa maganata tayi sakamakon wani irin murɗawa da mararta tayi, ta riƙe hannun matar gam kamar zata ɓalle hannun, Ganin haka ya sanya matar ɗago fuskarta a kiɗime ta ce"Hauwa'u, lafiya?, ko dai haihuwar ce?" Girgiza mata kai kawai ta dinga yi, ta yi saurin zameta daga jikinta ta tashi ta fice da sauri, not too long ta dawo tare da likitoci, nan da nan suka yi kanta, iyaka wahala tasha wahala, sai wajejen ƙarfe 4:50am sannan Jidda ta haihu, ɗago mata shi likitar tayi tana murmushi ta ce"me ki ka haifa" Jidda murmushi kawai tayi, hawaye na biyo kan kuncinta, ta kalli abin da ta haifa ɗin, tana murmushi tana hawaye a lokaci guda, hawayen dake nuni da kamar furucin "na gama aikina" ne ya fito daga idonta kafin ta lumshe su har abada. Rayuwa ta fito daga cikinta, ita kuma ta koma cikin duhu mai nutsuwa. _HASKEN CIKIN DUHU_ *35yrs Later* Play imperial lounge, Adetokunbo Ademola Cres, Wuse 2, Abuja. 2:35am. Tamkar rana haka wajen yake, gabaɗaya wajen kiɗa ke tashi, mata da maza masu ji da kansu sai harkarsu suke, daga can gefen wata kujera yake tsaye idanunsa a lumshe hannunsa riƙe da class cup mai ɗauke White house wine a ciki, yana sipping a hankali, Sanye yake cikin wasu Versace light blue, wajen sai tashin ƙamshin turaren Clive Christian No.1 yake, rollex ɗin hannunsa ya kalla sai kuma ya yi ɗan tsaki ya ajiye glass cup ɗin, car key ɗinsa ya ɗauka ya nufi hanyar fita daga club ɗin. “ina zaka je bayan ba'a tashi ba?" Wani matashin saurayi ya yi maganar hannunsa riƙe da glass cup na giya, ɗaya hannun kuma riƙe da wata budurwa yar siririya tana sanye da wata yar ƙaramar riga wadda ta kama mata jiki sosai. Ganin bai bashi amsa ba ya sanya ya kai hannu zai taɓa shi, janye jikinsa ya yi yana yi masa wani irin kallo, ɗan tsaki abokin ya yi ya ce"calm down, muje a ƙara maka one cup mana" “Gida zan je” Ya yi maganar yana juyawa, da idanu kawai Faisal ya bishi sai kuma ya taɓe baki. Dare ne sosai, babu abin da ka ke ji sai sautin karnuka da kuma kide-kide wanda ke tashi daga nightclub ɗin, wata Lamborghini Aventador black colour ya buɗe ya shiga, ya ɗauki two minutes cikin motar kafin ya yi bismillah ya cilla motar kan babban titi, yayyafi ake yi, kasancewar lokacin weathern damuna ne, time to time yake furzar da iska daga bakinsa a haka har ya ƙarasa titin Kwame Nkrumah cikin Asokoro. A bakin wani mansion ya yi parking, ya yi jim kaɗan kafin ya danna horn, a hankali kuma gate ɗin ya fara zugewa da kansa, sai da ya buɗe duka sannan ya zura hancin motar kai tsaye. Ya Salam! Gidan ya tsaya cikin natsuwa da izza, an zagaye shi da katanga mai tsawo, mai haɗa aesthetics da security wuri guda. Babbar ƙofa ce take jagorantar shiga, inda armed security guards ke tsaye prepared 24/7. Inside the compound, akwai wata lush and serene garden da ke kara wa wurin kyau da kwanciyar hankali. Fitilu na zamani suna haskaka hanya, yayin da bishiyoyi da furanni ke busar da iska mai daɗi, kamar wani Presidential retreat. The main building rises elegantly, windows made of reflective glass, baranda mai faɗi da fentin bango mai sulɓi. A bakin entrance ɗin gidan ya yi parking, ya buɗe motar ya fito, bai ko kalli securities ɗin dake gaisar dashi ba ya shige cikin gidan. Kai tsaye main parlon na gidan ya shiga, waje ne wanda yake spacious and tastefully furnished, da Italian leather sofas, manyan tagogi masu gilashi da ke barin haske ya ratsa ciki. Akwai chandelier mai sheƙi da ke walƙiya daga saman cealing, Zanen bangon wallpaper ne na zamani. Big flat-screen TV yana manne a bango, da sound system masu ƙarfi, kamar a cinema. Komai yana nuna luxury, class, and quiet power. Tsaye ya sameta tana kai kawo cikin parlon ko ba'a faɗa maka ba kasan akwai abin da ke damunta, tana jin shigowarsa ta juya da sauri tana kallon direction ɗin da yake, wata babbar Mace ce, wadda ba zata shige shekaru 47 ba, fara ce tass kuma mai kyau, da idanu kawai ya kalleta sai kuma ya juya zai bar wajen “Zayyad!” Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, a hankali ta taka har inda yake tana masa wani irin kallo ta ce “daga ina ka ke?” bai bata amsa ba, hasalima ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe, ganin da gaske ba amsa mata zai yi ba ya sanya ta sake cewa “rayuwar daka zaɓama kan ka kenan?, haka kake son ka rayu?, ka zaɓi aikata ɓarna akan abin da yake daidai, haba Zayyad!, meyasa?, why?” Wannan karan a raunace take maganar, idanunta sun cika da hawaye, ajiyar zuciya ya sauke yana jin idanunsa na wani irin lumshewa sakamakon giyar da yasha, “Zayyad!” Ta sake kiran sunansa. Juyowa ya yi ya zuba mata idanu, kafin a hankali ya buɗi bakinsa ya ce “Mommah nayi wani abun ne kuma?, meyasa kodayaushe ki ke son ki dinga shiga rayuwarta?, just leave me abeg” ya faɗa yana haɗe hannayensa waje guda. Bai kuma sauraren abin da zata ce ba ya nufi stairs yana tafiya da sauri da sauri. Da idanu kawai ta bi shi har ya ɓacewa ganinta, hawayen da suka samu damar zubowa kan kuncinta ta sanya hannu ta share sannan ta nufi stairs ɗin itama. Kiran sallar asuba na farko ta tashi ta shige toilet ta ɗauro alwala, sallah ta zauna tayi tana kuma roƙon Allah ya yewa Zayyad abin da ke damunsa, kiran sallahr da taji an fara yi ya sanya ta tashi ta fice daga ɗakin kai tsaye kuma apartment ɗinsa ta nufa. Knocking tafara yi duk da tasan ba lallai bane ya jiyota, dan haka kawai ta tura ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ko'ina tsaf yake, sai tashin ƙamshi parlon ke yi, system ta hanga kan table a buɗe sai kuma can ɗin coke ajiye a gefe, da alama bai daɗe da barin wajen ba. Bedroom ɗin ta tura ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Tsaye ta sameshi yana shafa turaren Clive Christian No. 1, sanye yake da wata coffee ɗin jallabiya kansa sanye da hula wadda bata hana gashin kansa bayyana ba. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye kafin ta ce “Ashe ka tashi?” Gyaɗa mata kai ya yi ba tare da ya juyo ba, bata sake ce masa komai ba ta ja ta tsaya a wajen, sai da ya kammala abin da yake sannan ya juyo yana kallonta, murmushi ta sakar masa ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce“Mommah” fuskarta a sake ta ce “Zayyad” wayarsa ya ɗauka gefen drawer yana kallonta ya ce “masallaci” jinjina kanta tayi ta ce"Tom a dawo lafiya" tare suka fito daga ɗakin, ya tsaya a parlon ya ɗauki wani mukullin mota ya zura a aljihu, da idanu kawai ta bisa bata ce masa komai ba. Koda suka fito corridor babu kowa tayi hanyar daƙinta shi kuma ya yi hanyar ƙasa. Masallacin gidan ya shiga ya gabatar da sallar asuba sannan ya fito, wayarsa ce ta fara ringing ya kalli screen ɗin sai kuma ya yi ƙaramin tsaki, parking lot ɗin gidan ya nufa, yana zuwa ya buɗe wata Lexus jeep black colour ya shiga, ya yi warming motar kafin ya fara tafiya kan kwalta ɗin dake shinfiɗe a gidan. Sauke curtains ɗin daƙin tayi ta koma gefen gado ta zauna, “Ina zai je da asuba?” Ta tambayi kanta, sai dai babu wanda zai bata amsar tambayar tata, koda kuwa ace Zayyad ɗin ne. *Transcorp Hilton, Maitama, Abuja* A compound ɗin luxury hotel ɗin ya yi parking ya fito, cikin hanzari ya shige ciki, zaune ya hangeshi akan ɗaya daga kujerun dake restaurant ɗin wajen, ƙarasawa ya yi ya zauna yana kallonsa amma bai ce komai ba. “Wai ya ake ciki ne?, jiya kace zaka dawo amma muka ji shiru, yarinyar nan fa yar manya ce itama, amma sai wulaƙantata ka ke” Taɓe baki Zayyad ya yi ya ce“ina ruwa da ko yar gidan wace?, kawai naji ban shirya bane, that's the reason why na tafi, beside ma ana dole ne?, ni nace a kawomin ita, kuma naji nafasa, menene abun damuwa anan?” yana gama fadin haka ya mike tsaye yana shirin barin wajen. Tashi shima Faisal ya yi yana kallonsa ya ce “Yanzu me ka ke nufi?” “Nafasa” Ya ce a takaice. Sai kuma ya juya ya bar wajen, yana tafiya cike da izza da taƙama. Ɗan siririn tsaki Faisal yaja kafin ya ce“ka yiwa kanka” daga haka shima ya bar wajen. Kai tsaye mota ya koma ya nufi hanyar Asokoro, dan daman abin da ya fito dashi kenan. Around 6am ya dawo gida, kai tsaye ɗakinsa ya shige, yana zuwa ya faɗa gado dan bacci ne sosai a idanunsa. Ƙarfe 10:34am ta shiga knocking kofar ɗakin nasa, kasancewar bashi da nauyin bacci ya sanya ya tashi zaune yana yatsune fuska, ko kallon inda ƙofar take bai yi ba, duk da yaji irin bugun da ake yi ya tashi ya shige toilet yana tafiya a sanyaye. Gajiya tayi da tsaiwa ta bar jikin ƙofar tana tura baki, daman tasan hali shiyasa ko kaɗan batason Mommah ta aikota tashin sa. Tana tsaye jikin bango ya buɗe ɗakin ya fito, sanye yake da wata polo t-shirt sai cargon 3-quater wanda ya tsaya dai-dai gwuiwarsa, parlon ya ɗauki ƙamshin mayataccen turaren Clive Christian No. 1, ɗan lumshe idanu tayi sannan ta buɗe, budurwa ce wadda ba zata shige 18-19yrs ba, tana da haske amma ba can ba, jikinta sanye da wata simple gown mai duwatsu, cikin nutsuwa ta ce"Big bro Mommah na kiranka" kamar ba zai magana sai kuma ya yi mata alama da tazo da hannunsa. Murɗe mata kunne ya yi a nutse ya ce “Duk ranar da ki ka sake zuwa kina yimin irin wannan bugun mahaukatan sai na ɓalla miki hannu” rau rau tayi da idanu kamar zata yi kuka ta ce“to idan an yi maka magana ai baka ji, kuma nasan ka tashi fa” taɓe baki Zayyad ya yi wanda ya kasance ɗabi'arsa ya sake kunnenta sannan ya yi hanyar waje, da gudu ta ƙaraso gabansa ta zura hannunta jikin nasa ta riƙe shi, ta gefen ido ya kalleta amma bai ce mata komai ba. Zaune ya hangeshi kan sofar idanunsa maƙale da glasses yana duba wata jarida dake hannunsa, sakin hannunsa Nayla tayi ya ƙarasa kusa da shi, zama ya yi gefensa ya ɗora kansa akan cinyarsa. Ajiye jaridar hannunsa ya yi ya shafa kansa yana murmushi ya ce “Zakina ya aka yi?” Fuska a kwaɓe ya ce“babu komai Dad, kawai bana jin daɗi ne” ɗago fuskarsa ya yi yana taɓa jikinsa ya ce a ɗan kiɗime “faɗamin wani abu na damunka?, ko akwai abin da ka ke so?, idan akwai kawai ka faɗamin, ko bakason aikin asibitin?, idan baka so sai ka barshi ba damuwa bane, ni banason naga ɓacin ranka ko damuwarka ka sani” Mommah dake ƙarasowarta parlon kenan ta kalli Dad sai kuma ta girgiza kanta. Zama tayi kujerar dake facing nasu murya a sanyaye ta ce “Yanzu Yallaɓai wannan abun shine daidai?, Zayyad ka ke tambaya idan baya son abin da zai taimaki rayuwarsa?, idan bai yi aiki da ilimin da ya yi ba mai zai yi?, shashanci kake son ya cigaba da yi?” Lokaci ɗaya annurin fuskar Dad ya ɗauke, ya zare glasses ɗin idanunsa yana kallonta ya ce “Khadijah me ki ke nufi?, na barshi ya wahala?, ko baki ji yana cewa baya jin daɗi ba?, dole dan ya yi karatu sai ya yi aiki?, akwai abin da ya nema ya rasa ne?” “Faɗa mata dai Yallaɓai, ban san menene abin da take nufi da yaron nan ba, har nawa Zayyad yake da za'a dinga takurawa rayuwarsa?, akan me?” Wata ƙatuwar mata tayi maganar tana sakkowa daga stairs ɗin benan, sanye take cikin wani ubansu lace maroon colour ɗinkin boubou, ko ba'a faɗa maka ba kasan kuɗi ya yi biyayya a jikinta. Kallonta Mommah tayi sai kuma ta ce“duk da haka Ummi Zayyad ya girma, ya kamata ace ya daina irin wannan abubuwan da yake, kina gani fa baya kwana cikin gidan nan, idan ma ya yi niyyar kwanan baya shigowa sai tsakiyar dare sannan zai dawo, kuma a buge, mutum nefa shi!" Mommah tayi maganar fuskarta na nuna zallar damuwar da take ciki. Zama Ummi tayi kan sofa tana murmushi ta ce “Yaran zamani kuma, sannan Zayyad ai ba yaro bane, koma ina yaje ya kwana na tabbata ba zai cutu ba, dan Allah ki dinga ɗauke idanunki akan wasu abubuwan” murmushin takaice Mommah ta yi, bata sake cewa komai ba. Tashi Zayyad ya yi ya ɗauki car key gefen mahaifinsa ya yi hanyar waje. “Ka gani ko, fita zai yi ba tare da an san inda ya tafi ba” “Khadijah!” Dad ya ce a ɗan tsawace, kallonsa Momma tayi bata ce komai ba ta miƙe tsaye. Kusan karo suka kusa ci dashi yana ƙoƙarin fita shi kuma yana shigowa, ko kallonsa Zayyad bai yi ba ya yi hanyar compound ɗin gidan, da idanu Khalil ya bishi sai kuma ya shigo parlon bakinsa ɗauke da sallama. Durƙusawa ya yi ya gaida Dad nasu sannan ya yi hanyar upstairs, wani shegen kallo Ummi ta watsa masa kafin ta ce“Kai kuma daga ina kake?" Ɗan shafe ƙeyarsa ya yi yana murmushi ya ce“Ummi naje gidansu Mahmood nefa nan baya” “Shi gidansu Mahmood ɗin ne idan zaka fita ba zaka iya sanar da mutane ba?" Dad ya yi maganar idanunsa zube akansa, sunkuyar da kansa ya yi murya a sanyaye ya ce“I'm sorry Dad, ban sakewa” taɓe baki Dad ya yi ya ce“Ka san abin da kake yi, maza je ka shirya ina jiranka” toh kawai Khalil ya ce sannan ya juya ya bar wajen. Kallon hanyar da Khalil ya bi tayi sai da taga ya shige sannan ta juyo tana kallon Dad ta ce“irin wannan ya kamata ka dinga yiwa Zayyad, ka daina nuna masa soyyaya irin wannan, ka daina fifitashi cikin ya'yanka” tashi tsaye shima Dad ya yi a fusace ya ce “Na daina nuna inason Zayyad ki ka ce?, kenan na nuna na tsaneshi?, kina son duniya ta zageni, kinason a dinga buga labarina a gidan jaridu!, kar na nuna na damu da Zayyad. To bari kiji muddin ina numfashi duk wani abu wanda Zayyad yake so sai nayi masa shi, kuma babu wanda ya isa ya takurawa rayuwarsa muddin ina raye, u better know what u're doing!”. _A cikin wannan duhu, wani haske yana ƙoƙarin bayyana... Amma shin zai samu damar haskaka zuciyar da ta riga ta ƙone?_ HASKEN CIKIN DUHU# Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU💋* Chapter 02 Nanameera, YOTA/23. _Even when darkness takes over your life, there’s always a light, you just have to find it._ Mommah ta bi shi da kallo sai dai bata ce komai ba, badan bata da abun faɗa ba, sai dan tasan faɗar bashi da wani amfani. Tsaki Dad ya yi ya juya ya fice daga parlon gaba ɗaya, Mommy da ke zaune ta taso tazo gabanta, dafata ta yi tana ɗan murmushi ta ce“Khadijah, ki daina ɗaukan abu da zafi irin haka, idan bai so Zayyad ba wa zai so?, duk abubuwan da yake masa akan gaskiyarsa yake, ki daina nuna kamar bakya jin dadin hakan” ɗan murmushin takaici Momma tayi kafin ta ce “Nifa Mommy ban ce kada ya nuna yana son ɗansa ba, daman ai kowane uba dole ne yaso ɗansa, amma wlh abin da yake yiwa Zayyad it's too much, yaushe zai yi hankali?, yaushe zai zaunar dashi ya dinga masa faɗa?, sai dai ni kullum nayi?, kuma idan ma nayi faɗan a gabansa zai nuna ni ce ban yi daidai ba, zai goyi da bayan ɗansa. Haka yake son ya cigaba da rayuwa?, kuma sannan ki ce na daina damuwa, amanar Allah ce fa” shiru Mommy ta yi can kuma ta ce“shikenan, Anjima idan Zayyad ya dawo zamu zaunar dashi mu yi masa faɗa ba sai Yallaɓai ya ji ba okay?” jinjina kai Mommah ta yi ta ce “tom Allah ya kaimu”. *Maitama, Abuja* 1:55pm Zaune yake kan sofa yana danna wayarsa, time to time yana ɗan murmushi. Fitowa tayi tana sanye da wata riga ta atampa hannunta riƙe da ice-cream, ta zauna tafara shan ice-cream ɗinta ba tare data kalli inda yake ba “Nimra” Ɗagowa tayi ta ɗan kalleshi kafin ta ce“yes” yanda tayi maganar irin in i don't care manner ya ƙara ƙona masa rai, ya ajiye wayar hannunsa still looking at her eyes ya ce“hala baki san ina zaune a parlon nan waiting for u ba ko?” ɗan ɗaga kafaɗa tayi bayan ta lashe cokalin hannunta ta ce“nasani mana, ba kaga nazo na zauna ba, hira zan taya ka ai, but I think u're doing something” cikeda rainin hankali ta yi maganar still kuma bata kalleshi ba. Miƙewa ya yi a fusace yana kallonta ya ce“ke wace irin mata ce wai?, kinsan kuwa abin da ki ke yi?, kinsan darajar auren dake kan ki kuwa?, kin je islamiyya ma kuwa?” a fusacen itama ta miƙe tsaye tana masa wani shegen kallo cikin ɗaga murya ta ce “stop raising ur voice at me, ka daina min shouting aka, ni ba yar ka bace, kuma ni ba ƙanwarka bace, ni ba irin wadda zan tsaya kana gaya min maganar da kaga dama bace, I'm ur wife. Aure nake ba wai wahala ba, saboda haka kada ka sake cewa zaka yimin faɗa idan kuma ba haka ba...” “Idan kuma ba haka ba me?” “Then definitely I'll show you the other side of me” Ta ratsa ta gefensa ta bar parlon tana tafiya kamar zata tashi sama, da idanu kawai Farooq ya bita sai kuma ya girgiza kansa. Kamar ya bita sai kuma ya fasa, wayarsa ya ɗauka ya yi waje. Nimra na shiga ɗaki tafaɗa kan luxury bed ɗinta ta fashe da kuka, wace irin ƙaddara ce wannan? har zuwa yaushe zata cigaba da zama da wanda bata so? meyasa za'a mata haka? meyasa Daddy zai barta cikin duhu wanda zai iya kai wa da yin ajalinta?. Sake fashewa da wani sabon kukan tayi dan shine kawai abin da zata yi taji sanyi a ranta. Tana nan kwance har after one hour sannan ta tashi ta shiga toilet, wanka ta sake yi ta shirya cikin wata Abaya Black colour wadda ta haska farar fatarta sosai, ta fito bayan ta ɗauka car key ɗinta. Kai tsaye makeken compound ɗin gidan tayi, ta buɗe wata Accord maroon colour ta shiga, tayi horn mai gadi ya buɗe mata gate tayi waje a guje. Tana tafiya a hanya taga kiransa sai ta share, sau uku Farooq na kiranta daga ƙarshe ta saka wayar a dnd ta cigaba da tuƙinta hankali kwance. *Mararaba, Nassarawa state* Orange Market, 2:05pm. Hadari ya mamaye sama, gajimare ya rufe rana tamkar dare ne ke kokarin sauka kafin lokaci. Iska tana kadawa da ƙarfi, tana daga tarkace, leda da ƙura cikin iska. Orange Market ya cika kamar kullum, masu sayar da kayan lambu, 'yan kasuwa, da masu hayar kaya sun baza komai a kasuwa, amma idan ka kalli fuskokinsu zaka fahimci hadarin ya fara tayar da hankali. Thunder yana tsawa daga can nesa, lightning na haska saman ginin katako da zinc, fitattun shagunan roba da kayan miya suna rawa a ƙarƙashin iska. A cikin wannan hayaniya, take tafiya, yarinyar da ba zata shige shekaru sha bakwai, sanye da uniform wanda suka ɗan gaji, riga da siket mai ɗan duhu, ta fito daga layin gefen kasuwa. Hannunta riƙe da tsohuwar jaka mai ɗinki iri-iri, books ɗinta na tsalle-tsalle a ciki saboda hanyar ba daidai ba. Iska tana kadawa tana haɗa gashinta a fuska, sai ta share da yatsunta cike da ƙura. She's walking fast, ta ratsa cikin kasuwar, tana matsawa tsakanin masu siye da masu sayarwa, tana ƙoƙarin kai gida kafin ruwan sama ya biyo. Tsohuwar tabarma da aka shimfiɗa a gefen hanya ta keta, yara suna tsalle cikin laka suna dariya, amma ita bata tsaya ba, zuciyarta na cike da damuwa. Thunder ya sake tsawa, hadari na kara kumbura, amma ta ci gaba da tafiya cikin kasuwa, kafarta na nutsewa cikin laka, idanunta a lumshe da fatan zata isa gida lafiya kafin sama ta ɓalle da ruwan sama. Cikin wannan tunanin ta ƙarasa unguwar Kabayi inda nan ne gidansu yake, wani gida wanda ya kasance uncompleted, tun daga nesa ake hango tsurar bulon dake gidan, domin babu ko siminti a gidan, ta ƙarasa tana tafiya da sauri, tura ƙofar gidan tayi wadda ta kasance tsohuwa sosai, Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, tsakar gida ne mai faɗin gaske, sai dai babu interloke ko tiles, sai malalen siminti wanda duk ya farfashe. A hankali ta ƙarasa inda ɗakuna uku suke, zaune ta samesu suna dan taɓa hira, cike da ladabi ta sunkuya ta gaishesu cikin murya mai haushi. Ɗaya daga cikin matan wadda take sanye da mayafi ta kalleta fuskarta ɗauke da fara'a ta ce“Har kin dawo?” gyaɗa mata kai tayi daga durƙushen da take, ɗaya matar wadda ta wani haɗe rai ta ce“gidan ubanki ki ka tsaya sai yanzu za ki dawo daga makarantar?, kina tsayawa a ina ne?” cikin ɗaga murya tayi maganar, yarinyar ta shiga girgiza kanta muryarta na rawa ta ce“Ban tsaya a ko'ina ba Umma, teachern mu ne bai tashemu da wuri ba yau” “Sai da an yi magana kina da abun kare kanki, wannan makarantar sai kin daina zuwanta nan kusa wlh, tashi ki bani waje, kuma yanzu ki fito ki yi wanke wanke, kafin anjima nayi magana ki ce makaranta za ki tafi, ina ga makaranta, Al huda huda” ta ƙarashe maganar tana zabga mata wata uwar harara. Tashi tayi jiki a sanyaye ta shige ɗakin wanda ya kasance nata, wani empty ɗaki ne, babu komai a cikinsa sai wata tsohuwar tabarma da bargo wanda ya gaji da tsufa akai, daga can ɗaya side ɗin kuma wani Ghana must go ne, black colour da alama a nan ne take ajiyar kayanta. Ƙarasawa ciki tayi ta zare hijabin jikinta, nan take tarin gashin dake kanta ya baje, ɗan tsaki tayi sannan ta sake ɗaureshi da wani yanki. Tana gamawa ta miƙe tsaye, hijabin ta linke sannan ta fito daga ɗakin ta nufi inda kayan wanke wanken suke, duk da basu da wani yawa. Sai da ta ɗebi ruwa a wata baƙar roba ta zauna sannan tafara dube-dube, sai dai duk iya dubanta bata ga abin da take neman ba, hakan yasa ta tashi ta ƙaraso inda mahaifiyartata ke zaune ta ce a hankali “Umma babu Omo” “Kin ga irinta ko?, to komai sai dai ni nayi, ubanta bashi da hali sai Zuciya da kakkafi, kina gani dai yanzu Omon da za'a yi wanke wanken ma babu cikin gidan, shi ya saka ƙafa ya fita, ita kuma ba zata yi neman kuɗi a rufawa kai asiri ba, sai dai taje makaranta, idan an yi magana ubanta ya ce zai yiwa mutum wa'azi.” ta ƙare maganar tana kallon Hajiya Jinjin dake gefenta. Ɗan murmushi matar ta yi ta buɗe jakarta ta zaro ɗari biyar, ta miƙa mata ta ce “Tashi ke ji ki siyo Omon kin ji” Karɓar kuɗin ta yi sannan ta tashi ta shige ɗaki, wani hijab na tayabo ta zuro maroon colour daga gani kasan ya daɗe amma kuma tass dashi a goge, ta zura slippers ɗinta tayi waje tana tafiya cike da nutsuwa. Sai da ta fita sannan Hajiya Jinjin ta ce“Wannan faɗan da ki ke ai bashi da amfani Rahmatu” tsaki tayi ta ce“ba zaki gane halin da nake ciki a gidan nan ba, nagaji, ni ban fita nayi sana'a ba, ita ma yar ya hanata sana'a, bashi da hali sai kifaɗi, yarinyar kamar wannan ya ce wai sai taje makaranta, yaƙi ya aurar da ita ballantana na saka rai da samun wani abu daga wajen mijinta. Je bi yarinyar nan, ji sura, ji kyau amma duk a banza, kullum sai gantalin bokon da ba zai amfaneta ba, yanda ki ka san ubanta ƙaruna ne haka take ji da zuwa makaranta” girgiza kai Hajiya Jinjin tayi ta ce“To wai har yanzu shi Malam Habu ɗin bai barta ta yi ko talla ba?, yara kamarta zaki dinga gani suna talla gwanin sha'awa suna rufawa kansu asiri, idan aurenta ya tashi da me za'a yi?” Caraf ta amshe ta ce“Kin gane inda matsalar take ashe, ba zai bari ba, taurin kai ya yi masa yawa, ko zan mutu akan faɗa masa ba zai yarda ba, gani yake ma kamar tsanar yarinyar nan nayi” taɓe baki ta yi ta ce“Ai ko wannan ba rayuwa ba ce, a cikin wannan halin kanada yarinyar ai ka nuna mata hanyar samun taro da sisi, Yarinya da girmanta amma tana zaune sai dai komai a yi mata” “Idan muna da abin yi mata ɗin kenan, sai dai komai dai ta rasa, kullum haka yake zaunar da ita a wajen nan yana mata nasiha mara amfani, ita kuma tana faman gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa” Dafata ta yi ta ce“Calm down, haƙuri za ki yi, cikin kissa zaki yi masa magana, kefa mace ce, kisan yanda zaki jawo hankalinsa ya gane abin da ki ke nufi, amma tashin hankali ba zai miki magani ba, tun da kin san halinsa” jinjina kai Rahmatu ta yi ta ce“Tom, zan gwada sa'a ta, amma halin Malam...” murmushi ta yi ta zaro wata sabuwar dubu ta miƙa mata ta ce“Ki riƙe wannan a hannunki, Allah ya rufa asiri, nima jiya saurayin Maryam ya zo ya bata kuɗi him shine na karɓe” washe baki Rahmatu ta yi tana dariya ta ce“Kinga harkar arziki, kai Allah ya ƙara arziki, Nagode, Nagode Hajiya, yanzu da a ce nima yar nan tana da mashinshinin ai da ba haka ba, to ita wai Allazi boko” Murmushi kawai Hajiya Jinjin tayi, daidai nan tayi sallama ta dawo gidan, har sannan kuma garin a haɗe yake da hadari, ƙarasawa wajensu ta yi ta tsuguna cike da ladabi da miƙa mata canjin, girgiza kai Hajiya ta yi ta ce“Riƙe a hannunki, kema kya kashe” shiru ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce “A'a nagode” “Munafuncin banza, za ki tashi anan wajen ko sai na kwaɗeki, baƙin hali irin na ubanki” tashi tayi ta koma inda ta haɗa kayan wanke wanken jiki a sanyaye, murmushi Hajiya ta yi ta ce“Ai daidai kenan, hakan ma wata tarbiyyar ce” “Yo tarbiyya ko munafurci?” Ita dai tana jin su bata sake cewa komai ba ta cigaba da wanke wankenta,a zuciyarta tana karatun haddarta dan anjima zata bayar. ****Around 5:45pm take tafe a hankali, sanye take da wani hijabi Ash colour wanda ya rufeta ruf, ko ƙafafunta baka gani, tafiya take tana sake ɓoye littafan hannunta gudun kada yayyafin da ake ya jiƙa mata su. Namiji ne tsaye jikin wani bango jikinsa sanye da wasu kaya wanda suka matseshi sosai, kansa ya yi wani irin aski wanda kana gani zaka iya faɗar kowane shi, fuskarsa duk tabbai na yanka da ɗinki, hannunsa riƙe da ledar gyaɗa yana cillawa a baki yana taunawa. Tun da ta hangoshi gabanta ya yanke ya faɗi amma ta dake, da sauri tafara tafiya tana shirin shige shi ya juyo yana kallonta ya ce “Kut, duk jiran naki da nagama shine za ki zo ki shigeni? Haba my love” cak ta tsaya amma bata juyo ba, ya tako har inda take, ban da warin wiwi babu abin da yake, ga tsami na rashin gyara, tayi saurin ɗauke numfashinta tana runtse ido. “Ummusalma!” Aka kira sunanta a tsawace. Juyowa ta yi ta kalli mai kiran nata sai kuma ta sunkuyar da kanta, wani babban mutum ne mai kamala zai iya kai wa 55yrs ɗin nan, yana sanye cikin wani yadi mai sauƙin kuɗi, kansa ɗauke da hula. Fari ne tas kuma kyakkyawan bafulatani, sai dai rashi ya ɓoye asalin kyawun nasa. Ƙarasowa gabanta ya yi, ya kalleta, sai kuma ya juya ya kalli Bashir dake tsaye, ɗan sunkuyar da kansa ya yi yana shafa ƙeya ya ce“Barka da Yamma Dad” bai amsa maganarsa ba, sai cigaba da kallonsa da ya yi kamar mai son gano wani abu. Juyawa Bashir ya yi ya bar wajen, girgiza kai Malam Habu ya yi sannan ya juyo yana kallonta. Sunkuyar da kanta tayi yayyafin na dukanta, bai ce mata komai ba ya kama hanyar gida, ganin haka ya sanya Ummusalma min bayansa tana tafiya da sauri. A tsakar gidan ta sameshi ya naɗe hannayensa yana kai da komo, tana shigowa ya juya yana kallonta cikin faɗa da kuma hargagi ya ce“Wanene wannan? Menene haɗinki dashi? Me ki ke tsaye kina yi dashi Ummusalma?” girgiza kanta ta shiga yi bakinta na rawa ta ce“wlh Abba ban kula shi ba, kawai kullum sai ya dinga yimin magana, bana kula shi, shine Umma ta ce idan na sake shigewa yana yimin magana sai ta zaneni” “Kaji annamimiyar yarinya, ni nasan inda ma ki ke zuwa ballantana nasan da waɗanda ki ke gamuwa? Ni za ki yiwa sharri? Ke ki ji tsoron Allah” Rahmatu ta yi maganar hannunta riƙe da buta da alama daga banɗaki ta fito. Kallonta Malam Habu ya yi sai kuma ya kalli Salma ya ce“Babu ruwana da abin da aka ce miki, amma ki sani duk ranar dana sake ganinki da wani sai kin gwammace kiɗa da karatu, banason shashancin banza. Ilimi na aika ki ki yi ba wannan rashin albarkar ba, kar na sake gani...” Daga haka ya juya ya bar wajen, sai a sannan Salma ta ɗago Idanunta tana kallon inda ya bari, Rahmatu ta zabga mata uwar harara sannan ta dire butar a gabanta ta bar wajen. Da gudu Salma ta ƙarasa ɗakinta tana zuwa ta faɗa kan tabarma ta fashe da kuka, to ita mene laifinta? Akan me za'a dinga yi mata faɗa irin haka?... *Asokoro, Abuja,* 6:22pm. Horn ɗin mota ya ɗan yi ƙara a bakin gate, nan da nan maigadi ya buɗe kofa da girmamawa. Black tinted Benz ɗin ta shigo cikin harabar gidan kai tsaye kuma ƙofar entrance na gidan tayi parking.Tana zaune a baya, ta sauke wayarta daga kunne, idonta na kallon window, kamar bata jin daɗin dawowa gida amma ba ta da choice. Gashinta a gyare, simple packing amma classy, fuskarta babu kwalliya mai yawa, natural beauty ɗinta ya sake bayyana.Sanye take da wani fitted trouser mai launin navy blue da white top mai sauƙi amma expensive, sai wata gold chain mai sauƙi a wuyanta, da wristwatch ɗin designer. Ta ɗora wata kimono black colour akai, idanunta sanye cikin shades glasses. Fitowa tayi daga motar ta ɗan ƙarema katafaren mansion ɗin kallo sai kuma ta nufi hanyar da zai sadata da cikin gidan, tana tafiya cike da izza da kuma tarin nutsuwa. Babu kowa a main parlon na gidan kasancewar yammaci ya yi kowa yana apartment ɗinsa, kai tsaye stairs ɗin benan ta nufa, tana gama hawa ta yi hanyar nata apartment ɗin, sai dai kafin ta ƙarasa ta tsaya, shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi hanyar ɗakin Mommy. Tura ƙofar ta yi ta shiga ba tare da sallama ba, zaune ta hangesu kan kujera da alama labari take bawa Mommy, ƙarasawa ta yi ta zauna kan ɗaya daga luxury sofas ɗin dake zagaye da ɗakin “Oh my god!” She said. Murmushi Mommy ta yi ta ce“An ɗebo wahala ko?, da tashi ki ka yi ko wanka ki yi kya samu sauƙi” bata ɗago ba, sai ma sake kwanciya da tayi akan kujerar tana lumshe idanunta. Taɓe baki Nimra ta yi ta ce“lazy girl” sai a sannan ta buɗe idanunta ta zuba mata, kamar zata yi kuka ta ce“saukar yaushe?” tayi maganar tana tashi tsaye. Ɗan murmushi Nimra ta yi ta ce“ban jima ba, kuma tafiya zan yi” jinjina kai Mufeeda ta yi, ta ɗauki handbag ɗinta tana cewa “Ina mijinki?” “Yana gida” ta ce a taƙaice, ɗan cute smile Mufeeda ta yi ta ce“My regards to him please, na ɗan jima ban ganshi ba” Toh kawai Nimra ta ce sannan ta cigaba da danna wayarta, Mufeeda ta kalli Mommy ta ce“lemme take shower Mom” gyaɗa mata kai ta yi ta ce“Idan kin gama make sure kin ci abinci, nasan halinki” langwaɓar da kai ta yi ta ce“Sure Mom” daga haka ta fice daga ɗakin, sai a sannan Mommy ta juyo tana kallon Nimra ta ce“Kin dai ji nafaɗa miki” kamar zata yi kuka ta ce“Naji fa Mommy”... ****Mufeeda na fita suka kusa cin karo da Khalil wanda shigowarsa kenan, murmushi ya sakar mata ya ce“Shagwaɓa princess, school ɗin ne?” gyaɗa masa kai ta yi, ya ce“ohya je ki huta, zuwa anjima muje yawo” “Really Bro?” Gyaɗa mata kai ya yi ta ce“Awwwn, bari naje na shirya” daga haka tayi hanyar apartment nata da ɗan sauri. No.34 Wuse 2, Abuja. Zaune yake cikin katafaren office, hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa, buɗe ƙofar office ɗin aka yi ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Zama ya yi kan kujera har lokacin Zayyad bai ɗago ba, ɗan tsaki ya yi ya ce“Ni zaka wulaƙanta? Wai kai menene matsalarka ne?” “You” Zayyad ya faɗa still looking at his phone. Ƴar dariya Ahmad ya yi kafin ya ce“Then karka sake kirana a waya, kuma nima ba zan kira ka ba, kowa ya yi rayuwarsa” kashe wayar hannunsa ya yi ya ɗago yana kallonsa, sanye yake da wata suit black colour wanda suka yi masa kyau, fuskarsa da kamala kamar ba wancan Zayyad ɗin ba. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sai kuma ta miƙe tsaye ya ɗauki car key ɗinsa ya yi hanyar waje yana faɗin “Sai ka kwana anan” Girgiza kai Ahmad ya yi sai kuma ya tashi ya biyo bayansa, a parking lot ɗin babban asibitin ya sameshi yana ƙoƙarin shiga motarsa. Dafashi Ahmad ya yi, Zayyad ya juyo ya zuba masa idanu yana kallonsa. “Yanzu ina zaka je?” “Club” ya ce ba tare da ya kalleshi ba, shiru Ahmad ya yi sai kuma ya ce“kenan kullum sai kaje club? Sai yaushe ka shirya daina wannan rayuwar ne friend?” ɗan murmushi Zayyad ya yi ya dafa kafaɗarsa ya ce“You can't understand” “Ai daman ba zan taɓa ganewa ba, har abada kuwa, amma kasani wannan ba rayuwa ba ce, watarana zaka yi danasani” harɗe hannayensa ya yi a ƙirji ya zuba masa idanu yana ji yana masa masifa, sai da ya gama tas sannan Zayyad ya juya ya shige mota ya figeta da gudu ba tare da ya bawa Ahmad amsa. Girgiza kai kawai Ahmad ya yi sannan ya ƙarasa gaban tasa motar ya shige ya bar asibitin. Around 9pm ya yi shiga gidan, zaune ya yadda Nayla tana danna wayarta tana ganinsa ta taso ta rungumeshi tana dariya, janyeta ya yi a jikinsa fuskarsa a haɗe ya ce“Kin raina ni ko? Ina Mommah” dariya ta sakar masa ta ce“A'a fa big bro, dan nayi maka welcome back?. Mommah nasama, kuma tana jiranka nasani” “Yen yen” Ya faɗa yana taɓe baki, tuntsirewa ta yi da dariya tabi bayansa ganin ya yi hanyar sama. Kai tsaye apartment ɗin Mommah ya nufa, ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya hangeta kan sofa tana danna system ɗin gabanta, ƙarasawa ya yi ya zauna kusa da ita. Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da abin da take, Nayla dake tsaye ta kalleta ta ce“Mommah ga Yaya fa” kallonta ta yi ta ce“Me zan yi masa to?” yanda tayi maganar ya sanya Nayla yin shiru ta juya ta fice daga ɗakin. Sai da taga ta fita sannan ta rufe system ɗin dake gabanta ta ɗago ta kalleshi, gani tayi yana kallonta. Bata ce masa komai ba ta tashi ta shige kitchen nata, not too long ta fito hannunta riƙe da tray, a gabansa ta ajiye masa sannan ta shige bedroom ɗinta. Kamar jira yake ya gyara zamansa ya shiga buɗe warmers ɗin, lafiyyayiyar White rice ce, wadda taci kayan haɗi sai ɗaukar ido take, ya sake buɗe ɗaya warmer ɗin mai ɗauke da miya wadda taji nama sai ƙamshi take. Plate ya ɗauka ya yi serving kansa sannan ya yi bismillah ya fara cin abincin dan daman yunwa yake ji. Tsaye take cikin toilet ɗin hannunta riƙe da wayarta lokaci zuwa lokaci tana kallon screen ɗin wayar, kiran data gani ya sanya tayi saurin ɗagawa murya can ƙasa ta ce“Eh ya ci, nasan ya ci” daga ɗaya ɓangaren aka ce“Ki tabbata dai ya ci, idan ba haka ba aikin zai tashi a banza”... # HCD # Light within the darkness # Nanameera 08106608363 *HASKEN CIKIN DUHU💋* Chapter 3: Behind Her Silent Tears Nanameera, YOTA/023. Maitama, Abuja. Zaune take kan royal bed ɗinta, tana sanye da wata sleeping dress doguwa wadda ta tsaya iya gwuiwarta, hannunta na dama riƙe da bubble tea tana sipping a hankali, idanunta zube cikin system ɗin gabanta inda take kallon dramar Lee jae wook ta dear hongrang, sosai take jin daɗin kallon tana ɗan murmushi. Turo ƙofar ɗakin a kayi, ya shigo yana sanye da wasu pyjames White colour idanunsa sanye da glasses wanda ya kasance medicate ne, harɗe hannayensa ya yi a ƙirji ya zuba mata idanu, sarai Nimra taji shigowarsa amma ta share, ganin bata ɗago ba ya sanya Farooq takowa har inda take zaune, zama ya yi gefen gadon ya janye system ɗin gabanta. Sai a sannan ta ɗago ta kalleshi fuskarta babu walwala “Madam ina kika je babu tambaya?” Ya faɗa fuskarsa a sake, shiru Nimra ta yi, can kuma ta ce“Naje gidanmu ne, ko sai na tambayeka dan zan je gida?” ɗan murmushin takaici Farooq ya yi ya ce“A'a, tunda baki saba da hakan ba” taɓe baki tayi, ta sanya hannu zata ɗauki system nata. Sake janyewa ya yi ya ce“Yunwa nakeji madam, I need food” “But akwai maid, why not kace ta dafa maka abinci?” Farooq kallonta kawai ya yi, sai kuma ya girgiza kansa bai ce komai ba. Tashi tayi daga zaunen da take ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ya bita da idanu yana jin wani irin zafi can ƙasan zuciyarsa. Yana nan zaune har ta buɗe ƙofar ta shigo after 20mins, maid ɗin bayanta ta bawa hanya ta dire ɗan ƙaramin tray ɗin kan table sannan ta juya ta fita. Kallon tray ɗin ya yi, tea flask ne sai kayan shayi, milk, Milo, bounvita, da kuma sugar. Daya plate ɗin kuma slices sponge cake ne acikin sai kwalbar Nutella a gefe. Zama tayi ta ja bargo tana cewa“you can manage this, coz it's already late, good night” daga haka ta rufe jikinta da lallausan duvet ɗin. Kallonta Farooq ya yi sai kuma ya kalli tray ɗin, wannan zai ci matsayin abinci sunan yanada mata? Haka zai cigaba da rayuwata da ita? Tayaya?... Washegari da sassafe ta tashi ta shirya cikin Abaya wadda ita ce kayanta koda yaushe, tayi rolling mayafin rigar sannan ta fito parlon. Zaune ta sameshi kan sofa yana karatun Alqur'ani, ta kalleshi sau ɗaya ta ɗauke kai “Zan tafi” Tafaɗa tana shafa lip gloss a bakinta, ajiye Alkur'anin ya yi ya tashi yana kallonta ya ce“lemme drop u” ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“then idan ka kai ne, zaka dawo ka ɗaukeni ne?” gyaɗa mata kai ya yi sannan ya shige ciki, taɓe baki ta yi a ranta ta ce“kamar na saka shi” tana nan tsaye har ya fito cikin wani yadi blue black wanda ya yi masa kyau sosai, ya kalleta ganin yanda take kallonsa ya ce“ko dai nayi miki kyau ne?” kallonsa ta yi da lulu eyes ɗinta amma bata ce komai ba, da hannu ya nuna mata hanyar waje ya ce“muje” ta ɗauki jakarta dake kan kujera tayi waje tana tafiya a hankali. **** Cikin hanzari yake taka stairs ɗin benan yana sakkowa idanunsa kan rollex ɗin hannunsa, a dining area ya hangesu kasancewar safiya ce kowa yana cin abinci. Ƙarasawa ya yi ya ɗan yi hugging Dad yana murmushi ya ce“Morning Dad” shafa kansa Dad ya yi ya ce“Ɗan gidan soja ka tashi lafiya?” jinjina kansa ya yi ya ce“Alhamdulillah” daga haka ya gaida Mommy da Mommah. Kallonsa Mufeeda ta yi ta ce“Big bro jiya ban ganka ba” harararta ya yi ya ce“to yanzu kin ganni sai ki cinyeni” murmushi ta yi ta ce“Ni na isa na cinye Favourite ɗin Daddy, da an ciremin subsidy a gidan nan” Dariya duk suka yi, ya kalli Daddy ya ce“Dad I'm off” “To where?” Cewar Momma, langwaɓar da kai ya yi yana kallonta ya ce“My own Momma, nifa ba yaro bane, ko Nayla ce zata fita da safe ai ba'a tambayeta ina zata je ba, asibiti zan je fa” taɓe baki ta yi ta ce“to sannu Babba, irin wannan daɗewa da aka yi da haifarka” Dad ne ya katseta ta hanyar faɗin “leave ur Mom je ka kawai, kuma idan kana buƙatar wani abu ka sanar dani, duk da dai nasan kuɗi ba matsalarka bane, coz kama fini” sake hugging nasa ya yi ya ce“ni na isa nafi Dad kuɗi, bayan shi yake bani” dariya duk suka yi ya yi hanyar fita daga gidan. Tashi shima Dad ya yi yana kallon Nayla ya ce“kiyi sauri ki gama, Khalil zai kara ki makaranta” murmushi ta yi ta ce“Daddy nafa ƙoshi, so nake kawai na ganni a school” "Su Nayla a University” Mufeeda tafaɗa tana dariya, kallonta ta yi sai kuma ta kwaɓe fuska ta ce“Mommy kin ganta ko, sai kace wani girmana tayi” riƙe baki Mufeeda ta yi ta ce"sannu yarinya, au ni sa'arki ce?” tsaki Mommy ta yi ta ce“Mufeeda ranki zai ɓaci fa, ki fita hanyar yarinyar nan” girgiza kai tayi bata ce komai ba ta tashi ta bar wajen. Mommah ta ce“sauran idan kin je ki tsaya shashanci, karki mai da hankali akan karatun ki” gyaɗa mata kai Nayla ta yi ta ce“Zan yi Mommah, kuma ban faɗawa Yaya Zayyad zan fara zuwa school ba” “Idan kin faɗa masa me zai yi miki?” “Sai ya ƙaramin kuɗi Momma, yana da kuɗi dayawa wlh, kuma ma nasan Aunty zata bani kuɗi” Shiru Momma ta yi sai kuma ta ce“with Aunty?” cike da son surutu Nayla ta ce“wata ce, mun taɓa zuwa wajenta tare da Yaya daya kai ni Magic land, she's so beautiful wlh, kuma tana da kirki fa” murmushi Mommy ta yi ta ce“Ki ce In-lawa ɗinmu ce” gyaɗa mata kai Nayla ta yi sai kuma ta ce“Allah yasa ya aureta Mom, zaku ganta, ta burgeni” “Zaki shige ki tafi ko kuma zancen zaki ci gaba dayi?” Mommah tafada tana kallonta, turo baki ta yi, ta ɗauki slice ɗin cake ta saka a baki sannan ta bar wajen tana cewa “Goodbye Mommy, Goodbye Momma” Girgiza kai Mommy tayi tana murmushi ta ce“Nayla kenan” murmushin itama Momma ta yi ta tashi tana cewa“Bari naje na shirya dan kar Hajiya A'isha tazo tana jirana” jinjina kai Mommy ta yi ta ce“Aikuwa dai, ya kamata ace ma kun je da wuri, Allah ya sanya Alkhairi, ya nuna mana ranar auren yaran nan haka. Musamman Zayyad” Murmushi Momma ta yi ta ce“Aikuwa, daman Inason magana dake akan haka, bari dai naje na dawo” “Tom, a dawo lafiya” cewar Mommy. ****Zaune yake cikin office ɗin nasa, ya kishingiɗa da kujerar da yake kai, idanunsa a lumshe. Gabaɗaya ya gaji da surutun nata, dafe kansa ya yi ya buɗe idanunsa yana kallonta ya ce a hankali “Angel” murmushi ta yi tana kallonsa ta ce“Na'am Bae” yanda tayi maganar ya sanya shi tashi zaune sosai ya zuba mata idanu yana kallonta. Fara ce tas kuma kyakkyawa, tana da siririyar fuska da pointed nose bakinta ɗan ƙarami yasha Avon lipstick, sanye take da wata t-shirt fara sai tomy skirt baby pink, kanta ɗaure da jersey veil pink, babu kwalliya a fuskarta amma tayi wani irin siritaccen kyau. Hannunta ya riƙe cikin nasa yana murmushi ya ce“baki gajiya da surutu ne?” waro idanunta ta yi ta ce“in dai kai nake yiwa bana gajiya Bae” “Saboda me?” Ya yi maganar fuskarsa a sake, murmushi ta yi ta ce“Just because I love you, i can't do without you Bae” jinjina kansa ya yi ya ce“my cute Angel, she don love me” dariya tayi ta kai hannunta fuskarsa ta shafa cute beard ɗinsa, ɗayan hannun nasa ya sanya ya janye nata daga fuskarsa ya ce“tashi muje na mayar dake gida” langwaɓar da kai ta yi sai kuma ta ce“har ka gaji dani?” girgiza kansa ya yi ya ce“Idan baki so zauna till down” yanda ya yi maganar ya sanyata dariya ta girgiza kanta ta ce“Ni ba yanzu zan tafi ba to, ina nan har sai ka tashi” jinjina kansa ya yi, daidai lokacin aka buɗe ƙofar office ɗin, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai, ya juya ya fita. Taɓe bakinta ta yi sai kuma ta ce“Wai mene matsalar Ahmad ɗin nan ne? Ni wlh bana son shi” "Nima bakya sona kenan!” Ya faɗa yana janye hannunsa daga nata, girgiza kanta tayi ganin yanda ya haɗe rai lokaci guda ta ce“A'a fa, ina sonka mana, kai ma kasani ina sonka” “Idan har zaki ce baki son jinina ai nima baki sona, ko kin manta Ahmad cousin ɗina ne? Koma ba haka ba he's a friend of mine so you have to respect him, but in front of me ki ke cewa bakya son shi” ya ƙare maganar yana harararta. Shiru tayi for some seconds sai kuma ta ce“I'm sorry to” Ya ɗauke kansa, ta sake maimatawa. Sai da faɗa sau uku sannan ya juyo ya kalleta. “Tashi na maida ki gida” “Ni tare zamu kwana fa” Taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“Look, I'm not in that mood today, I can't! I Just can't” girgiza kai tayi ta ce a shagwaɓe “Amma ni ai ina so” ɗauke kansa ya yi zata sake magana ya ce “Aneeserh” Jin yanda ya kira sunan nata ya sanyata yin shiru, ta tashi tana kallonsa ta ce“Sai anjima” “lemme drop you” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a ka barshi aiki ka ke ai, zan tafi da kaina” taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“daman kin fito da mota ne?” Aneeserh ta ce“A'a I'll call my driver don't worry” jinjina mata kai ya yi ya ce“Okay then, bye” gyaɗa masa kai tayi kawai ta juya ta fice daga office ɗin yabi bayanta da kallo. Tana fita Ahmad ya shigo fuskarsa a haɗe ya zauna bai ce komai ba, kallonsa Zayyad ya yi sai kuma ya taɓe baki ya ɗauki wayarsa yana dannawa. “Wai yanzu haka zaku ci gaba da wannan yarinyar?” Ɗago kansa ya yi ya ajiye wayar kan table in a serious tone ya ce“Me kuma tayi maka?” “Kwata-kwata babu tarbiyya a tare da yarinyar nan, ba kuma tada kamun kai, a haka zaka aureta ka kai ta gidanka matsayin mata?” ɗan murmushi Zayyad ya yi ya dafashi ya ce“Mr man, calm down, mene laifin Aneeserh? Mene tarbiyyar da ita bata da? Me tayi ba daidai ba?” a ɗan fusace Ahmad ya ce “Oh, you're questioning me? Duk abubuwan da take baka gani kenan? Kalli irin shigar da take yi tana fita” ɗaga masa hannu ya yi ya ce “Heyy! Calm down mana, me shigar ta tayi? Ina ruwanka da life style ɗinta? Ni nakesonta kuma zan zauna da ita a haka so you don't need to be worry” jinjina kai Ahmad ya yi ya ce“Haka ne, babu abin da ya dameni, ka aureta, amma ai kaje islamiyya kuma kasan abin da yake dai dai daba dai dai ba, duk da kai ma takewar kake, sai hali yazo ɗaya daman ake iya zama waje ɗaya, da kai da ita duk ɗaya” a fusace Zayyad ya tashi tsaye yana harararsa ya ce“Na take gaskiyar ina ruwanka? Mene naka a ciki? Ahmad! Ahmad! Ka bar ganin ina raga maka wlh idan ka ƙureni ba zaka ji da daɗi ba” tashi shima Ahmad ɗin ya yi yana kallonsa ya ce“Ai ba sabon abu bane, ka wulaƙantani, kayi duk abin da kake ganin zaka yi Zayyad, wlh bazan fasa faɗa maka gaskiya ba!” Zayyad haɗe hannayensa ya yi alamar roƙo ya ce“To malam Ahmad wanda yasan gaskiya, Zayyad baya buƙatar gaskiyarka, ka riƙe a barka dan Allah” murmushin takaici Ahmad ya yi ya ce“Haka kace?” “Eh, haka nace” Ahmad bai sake cewa komai ba ya juya ya bar office ɗin, tsaki Zayyad ya yi sannan ya koma ya zauna. After two minutes ya tashi ya ƙarasa inda fridge ɗin office ɗin yake ya buɗe, wata bottle ɗin Red snow wine ya ɗauko ya dawo ya dire kan table ɗin, ya koma ya ɗauko wani ɗan ƙaramin glass cup. Zama ya yi kan kujera ya tsiyaya giyar ya kai bakinsa yana sipping a hankali, sai da ya sha cup 2 kafin ya ajiye ya jingina da jikin kujerar ya lumshe idanu yana jin komai na saukar masa. Kabayi, Nassarawa state. 4:50pm Durƙushe take gaban kurfotin time to time take jan tsaki, tun ɗazu take abu ɗaya gawayin yaƙi kamawa, gashi ita kaɗai ce a gidan, tashi tayi tana tunanin inda zata samo ledoji dan yanzu duk ledar da mutum ya taɓa a jiƙe zai jita. Da sallama ya shigo gidan hannunsa riƙe da wata leda, ciki ciki ta amsa ya ajiye ledar hannunsa yana kallonta ya ce“Lafiya ki ke zarya?” cikin kunfar baki ta ce“To ba dole nayi zarya ba, tunda ni ce baiwa da komai zan yi, nafi awa ɗaya ina tsugune gurin wuta taƙi kamawa, ko yaron da zan aika ya samon garwashi ko leda babu, ita kuma waccen sarkin iyayin ta shige ta tafi makaranta” girgiza kai ya yi cikin sanyin murya ya ce“Yarinyar data tafi neman ilimi ita kike cewa mai iyayi? Daman neman ilimi iyayi ne?” “To menene idan ba iyayi ba? Tunda bata da halin yin karatun? Sai ana buga buga” Umma Rahmatu ta bashi amsa, ɗan murmushi ya yi ya ce“Allah ya fito dake daga wannan duhun da ki ke ciki, Allah ya kawo haske” Umma ta ce“Ameen, Allah ya kawo mana Hasken cikin duhu dan nima nagaji da wannan masifar”... Zaune suke cikin makarantar tasu, kowa hannunsa riƙe da Alkur'ani mai girma, dan lokacin angama ƙari. Addu'a malamin ya yi musu ya tashe su dan lokacin gefen magriba ne, sai da kowa ya tashi daga kan tabarmar sannan ta tsuguna ta naɗeta dan daman kullum ita take wannan aikin, bayan tagama ta shiga gidan da suke arowa ta mayar musu. Tana fitowa ta ganshi tsaye hannunsa riƙe da jakarsa, ta kalleshi ta ce“Sai da safe Malam” “Ummusalma” Taji ya yi kiran sunanta. Juyowa ta yi ta kalleshi ta ce“na'am malam” takowa ya yi inda take yana kallonta ya ce“Daman inason magana dake ne” shiru tayi sai kuma ta ce“Malam lafiya?” murmushi ya yi ya ce“bakomai Ummusalma, kawai daman Inason nafaɗa miki wata magana ne” gyara tsaiwarta ta yi ta ce“Tom, ina ji malam” shiru Malam Yusuf yayi na ɗan lokaci kafin ya ce“Wato Ummusalma na daɗe da wani abu a cikin raina, tun kina yar ƙaramarki halayenki suke burgeni, kuma naji ina da kwaɗayin ki zama matata idan har babu damuwa. Ina son ki yarda dani Salma, ki karbi soyayyata saboda Allah” wani irin abu Salma taji ya tsaya mata a ƙirji, so kuma? Malam Yusuf? Tuni hawaye suka wanke fuskarta, tabbas lokacin da zata daina zuwa makarantar nan ya yi, domin Abbanta ba zai taɓa lamuntar haka ba. Bata ce masa komai ba ta juya ta bar wajen tana tafiya kamar zata faɗi saboda sauri. Da idanu Malam Yusuf ya bita sai kuma ya yi murmushi “Sai na mallakeki matsayin mata in sha Allah”... Ana kiran sallahr Magrib ta shigo gidan, tsugune ta samu Abbanta yana alwala Umma kuma durƙushe inda take girki, cikin ladabi ta ce“Sannu da hutawa Abba” sai da ya idar da alwalar sannan ya kalleta ya ce“Ummusalma ina kika tsaya sai yanzu?” da sauri ta ce“Yau ba'a tashemu da wuri bane Abba shiyasa” ƙare mata kallo yayi ta sunkuyar da kanta. “To shiga ki je ki ajiye jakar ki zo kiyi alwala” to kawai ta ce sannan ta shige ɗakinta, ita kuwa Umma Rahmatu ta bisu da kallo tana taɓe baki. Bayan sallar isha'i yana zaune a ɗakinsa ta buɗe labule ta shigo, kallonta ya yi har ta ƙaraso gabansa ta zauna ta ce“Abba gani” ajiye Qur'anin hannunsa ya yi yana kallonta sosai cikin natsuwa ya ce“Meke damunki Salma? Faɗamin?” girgiza kanta tayi ta ce“Babu komai Abba” ɗan murmushi ya yi ya ce“karki damu faɗa min, ni mahaifinki ne, sannan kuma abokinki, duk abin da yake damunki ni za ki faɗawa, to karki ji nauyi na faɗamin ” Ɗora kanta tayi akan cinyarsa ta fashe da wani raunataccen kuka, shiru Malam Habu ya yi yana jin hawayenta na sauka akan wandon yadin jikinsa, shafa kanta kawai ya yi bai hanata kukan ba, dan bai san dalilinta nayi ba. Sai da tayi mai isarta sannan tafara sauke ajiyar zuciya, tana jin zuciyarta wasai. Ganin na nutsu ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“To yanzu faɗamin mene ne?” goge hawayen fuskarta ta yi ta ce“Abba Inason naga Ammina, Inason ganinta Abba” ɗan murmushi ya yi ya ce“Kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo Salma?” girgiza masa kai ta yi ya ce“To Amminki ta bar duniya Salma, kinga baki da damar ganinta, amma kina da damar yi mata addu'a” wasu tagwayen hawayen suka sake biyo kuncinta, da kansa ya goge mata yana murmushi ya ce“Kin girma amma kina kuka ko? Ki daina to. Ki nutsu ki cigaba da karatunki Allah ya yi miki albarka” jinjina kanta ta yi ta ce“Ameen Abba” shafa kanta ya yi ya ce“tashi ki je ki ci abinci ki kwanta” gyaɗa masa kai ta yi sannan ta tashi ta fice daga ɗakin. A tsakar gida ta hangi kwanon abincin nata ta ƙarasa ta buɗe, shinkafa da wake ce da manja, ta ɗauka ta shiga ɗakinta. “Ummusalma! Ummusalma” Fitowa ta yi daga ɗakin da sauri tana faɗin “Na'am Abba” baƙar leda ya miƙa mata yana cewa“Na manta ban baki ba” hannu biyu ta sanya ta karɓa sannan ta juya ta koma ɗakin. Tana shiga ta buɗe ledar, gunduwar kifi sukunbiya ce a ciki, ta yi murmushi tana jinjina ƙarfin hali irin na Abbanta, koda ba shida kuɗi amma yana da zuciyar faranta masu. ****Rahmatu ta kalleshi ganin ya yi shiru bai ce komai ba, ta sake cewa“Malam kayi shiru” tashi ya yi daga kashingiɗan da yake ya kalleta sosai ya ce“Rahmatu kin san me ki ke faɗa kuwa? Na cire Ummusalma daga makaranta ta koma talla akan titi haka ki ke so?” girgiza kanta ta yi ta ce“A'a, A'a fa Malam, baka gane abin da nake nufi bane. Ba wai nace Salma ta daina zuwa makaranta ba, amma ta daina zuwa ɗaya, ko bokon ce tunda ba wani amfanin zuwan yake mata ba” girgiza kansa ya yi ya ce“Shekarar ƙarshe take, kuma cikin zangon ƙarshe shine ki ke so ta bar makarantar? Saboda wani ƙuduri naki?” shiru ta yi ya sake cewa “Rahmatu na tambayeki shin akwai abin da bana yi muku ne? Duk abin da yake na dole ina ƙoƙarin ganin nayi muku daidai ƙarfina, meyasa ki ke saka son zuciya cikin al'amuranki?” “Amma Malam...” Ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu. Shiru tayi tana kallonsa ya ce“Dan Allah Rahmatu ki rabu dani, gobe inada aikin gini da wuri Inason na kwanta” takaici ne ya isheta ta tashi ta fice daga ɗakin. “Allah ya kyauta” Malam ya faɗa yana girgiza kai... Daren ranar rabi da rabin bacci Salma ta yi, maganar Malam Yusuf ta tsaye mata arai, tunanin yanda gobe zata shirya taje makarantar take. Tana jin an fara kiran sallar asuba ta tashi ta fito tsakar gida, da hasken farin kwai kasancewar akwai wutar NEPA a lokacin, ta ɗauki buta ta shige banɗaki. Tana fitowa ta tsuguna nan wajen tayi alwala sannan ta koma ɗaki, tana ji Abbanta ya fito ya yi alwalar shima amma ban da Rahmatu. Tana idar da sallar asuba ta zauna tana bitar karatunta har wajen ƙarfe 6:30am. Bayan ta gama ta tashi ta gyara ɗakinta sannan ta fito tsakar gida, tsintacciya ta ɗauka ta hau shara gudun kada ta makara a makaranta. Tana gamawa ta haɗa wanke-wanke tafara, tana cikin yi ya fito daga ɗakin, ta tashi ta je har inda yake ta gaishes shi. Da fara'a ya amsa ya kalleta ya ce“baki jin sanyi Ummusalma?” ɗan murmushi ta yi ta ce“Ai Abba banason na makara ne shiyasa” jinjina kai ya yi ta tashi ta koma ta cigaba da abin da take, gani tayi ya ɗebo kayan gininsa ta kalleshi ta ce“Abba da wuri zaka fita aikin?” gyaɗa mata kai ya yi yana zaro wuƙar siminti ya ce“Eh, aikin yini zan yi, to gara naje da wuri. In sha Allah zan samu na baki kuɗin jarrabawar idan na dawo” Salma ta ce“Tom Abba, Allah yasa” takalmin ya zura ya ce“Idan babarki ta tashi ki ce mata na ajiye kuɗi a gefenta ta sarrafa ayi abinci, sai na dawo” “Allah ya tsare Abba” ta ce masa, ya amsa da Ameen sannan ya fita ya bar gidan. Ƙarfe 7:40am tagama shiryawa, ta fito tana kallon Umma dake dama kunu ta ce“Umma zan tafi” a fusace ta ce“To Al huda huda, sai kin dawo, tun da makarantar ta ubanki ce da bazaki tsaya ki karya ba” sunkuyar da kai Salma ta yi sai kuma ta ce“Umma ai zan makara, ki ajiyemin sai nadawo zan sha” taɓe baki ta yi ta ce“Allah ya taimaka” Salma ta fita daga gidan, da idanu Umma ta bita ta ce “Kinibabbiya” A ƙofar gidansu suka haɗu da Fateema yar ajinsu, murmushi ta yi tana kallonta ta ce“Candy tamu” murmushi Salma tayi har sai da beauty point ɗinta ya Loma ta ce“Fatima kin tashi lpy?” Fatima ta ce“Lafiya klao beauty, mu tafi kar mu makara” to Salma ta ce sannan suka jera suna tafiya suna hira gwanin sha'awa. Suna shiga aji Malam Dawood ya shigo hannunsa riƙe da wata takarda, tsit ajin ya ɗauka ya fara kiran sunaye, sai da ya gama tas sannan ya ce wanda duk bai ji sunansa ba ya koma gida ya karbo kuɗin da ake binsa” tashi Salma ta yi tana kallon Fatima ta ce“na tafi, duk abin da aka yi ki biyo ki faɗamin kinji ” murmushi Fatima ta yi ta ce“Tom shikenan”. Sallama ta yi ta shigo gidan, zaune ta hangi Umma ta zuba uban kunu a kofi tana haɗawa da ƙosan dake gabanta. Da mamaki take kallonta har ta ƙaraso ta zauna kan ƙofar ɗakinta, Umma ta ce“ke kuma lafiya?” “Umma korarmu aka yi fa” Dariya ta yi ta ce“Allah shi ƙara, maganinki ai kenan, kuma in sha Allahu kin bar makarantar nan kenan” haɗe rai Salma ta yi sai kuma ta ce“To fa Abba ya ce idan ya dawo anjima zai bani kuɗin daman” harararta Umma ta yi ta ce“Idan ya samo ba, ke ko tausayin uban naki ma bakya yi, ya yi ta fama yana buga buga yana magiya a bashi aiki, amma ke ba zaki yi zuciya ki dinga neman kuɗi ba” tura baki ta yi tana cewa“Kuma ai idan nagama makaranta nafara aiki zan gina masa gida, zan kuma kai shi makkah” ta yi maganar cike da wawta da yarinta. Taɓe baki Umma ta yi ta ce“To ayi mugani idan tusa zata hura wuta, kuma in sha Allah ba zai samo ba, naga ta tsiya” shiru Salma tayi hawaye na biyo fuskarta. “Sai ki tashi ki cire kayan ki zo na aike ki gidan Hajiya Jinjin” tashi Salma ta yi daidai lokacin aka yi sallama daga waje, amsawa ta yi wasu maza suka shigo. Tashi tsaye Umma tayi, Salma ta dinga gwalalo idanu tana ganin yanda aka ɗauko Abbanta ɗaukan yara. Akan tabarmar da Umma ke zaune aka shinfiɗeshi, da gudu Salma ta ƙarasa gabansa tana kuka ta ce“Abba meya sameka? Me ya samu ƙafarka?” “Yana cikin aiki ne a sama ya faɗo shine ƙafarsa ta karye” Fashewa da kuka Salma tayi, Umma Rahmatu ta ɗora hannunta aka tana faɗin “Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, mun shiga uku” girgiza kai ɗaya daga cikin mazan ya yi ya ce“sai haƙuri, amma an kira mai ɗori an ɗora shi, sai fatan Allah ya bashi lafiya” daga haka suka juya suka fice daga gidan. Salma Kuka kawai take tana kallon Abbanta wanda idanunsa suke a lumshe da alama an yi masa har da allura ne, ta kalli Umma ta ce“Umma kin ga ko? Kalli Abbana Umma, mun shiga uku” harararta Umma ta yi ta ce“Ai duk kece sanadi, domin da badan shegiyar makarantar da ki ke ba da bai fita da safen nan ba, kin cucemu wlh” ta ƙare maganar tana sharar hawaye, girgiza kai Salma ta yi tana kuka ta ce“. HCD# 08106608363, Nanameera. *HASKEN CIKIN DUHU💋* Chapter 4: When Hope Fades Nanameera, YOTA/23. “A'a Umma, wannan ƙaddarace, haka Allah ya rubuta, da ace nasan idan Abba ya fita zai gamu da wannan masifar wlh dana haƙura da zuwa makarantar, dana hana shi fita, sai dai ban isa na hana abin da Allah ya rubuta faruwa ba, kuma...” Salma ta sake fashewa da wani kukan, harararta Umma ta yi ta ce“Rufa min baki anan, munafuka, ai yanzu kin ji daɗi, naga da uban da zaki koma makarantar, nagani” Komawa kusada Abbanta ta yi ta zauna tana kallonsa hawaye na biyo fuskarta, ita kuwa Umma ɗaki ta shige tana cigaba da masifa kamar Salma ce wadda ta sanya ya karye. Abacha road, Mararaba. 5:45pm. Compound ne mai kyau sosai, Yana ɗauke da flats biyu, dukkansu neat and modern. Gidan yana da spacious compound, akwai parking space sosai. Fence ɗinsa high ne da strong gate, yana bada security and prestige. Flowers da small trees sun zagaye gidan suna ƙara masa kyau da fresh look. Gidan ya haɗu, perfect for comfort and peace of mind. Zaune take kan veranda idanunta maƙale cikin glasses gabanta system ne na companyn Apple, tana dannawa a hankali, gefenta wani glass cup ne mai ɗauke da milk shake a ciki tana sipping a hankali. Horn ɗin motar ya sanyata ɗagowa, babbar mace ce ba zata shige shekaru 50 ba, tana da haske, bafulatana mai tsagu a gefen fuskarta, sai kana ganinta kaga kuɗi da kuma arziki. Ɗauke idanunta ta yi ta cigaba da kallon abin da take yi, a parking space ɗin gidan ya yi parking sannan ya fito, matashin namiji wanda ba zai haura shekaru 34yrs ba, shima kyakkyawan bafulatani ko ba'a faɗa maka ba kasan wannan matar ita ce Mahaifiyarsa. Yana zuwa veranda ɗin ya nemi kujerar dake facing nata ya zauna. “Mami” Ya faɗa kamar zai yi kuka, ɗago kanta tayi tana kallonsa sai kuma ta ce“Al-ameen ka dawo?” gyaɗa mata kai ya yi yana ƙoƙarin ɗaukan cup ɗin gabanta, harararsa ta yi ta ce“Oh daman kai ka ajiye?” langwaɓar da kai ya yi bayan ya ɗauki cup ɗin, ya kai bakinsa ya sha sannan ya ajiye yana murmushi ya ce“nagaji ne wlh” ɗan taɓe baki ta yi tana kallonsa ta ce“Tashi ka bar nan ni sai warin magani kake” tuntsirewa ya yi da dariya yana kallonta, wanda hakan ya sanya ita ma ta yi dariyar ta miƙe tsaye yana cewa “Daman magani wari yake Mami?” Banza tayi masa ta cigaba da abin da take, shima bai jira amsarta ba ya nufi entrance na gidan. Kai tsaye ɗakinsa ya shige yana duba agogon hannunsa “Oh god!” Ya faɗa yana girgiza kai. A gefen luxury bed ɗin nasa ya zare suit ɗin jikinsa sannan ya yi hanyar toilet. Ana kiran sallar magrib ya sakko daga upstairs, tsaye ya samu Mami tana jera warmers a dinning table. Kallonsa ta yi ta ce“Ina kuma zaka je?” murmushi ya yi ya ce“Mami masallaci zan je, daga nan kuma zan biya gidansu Mubarak” “Sai ka dawo” tafaɗa ba tare da ta kalleshi ba. Kusan karo suka yi tana ƙoƙarin shigowa, baya ya yi yana cewa“wai yaushe zaki yi hankali ne?” “Gobe” Tafaɗa cike da tsiwa, Al-ameen bai sake bi ta kanta ba ya yi gaba abinsa, da harara ta bishi sannan ta shiga parlon tana kiran sunan Mami. Asokoro, Abuja. Da daddare around 8pm Momma ta shigo ɗakin, zaune ta samu Mommy tana magana da Mufeeda, tana ganinta ta ce“Ai nayi tunanin ma kin manta ne” girgiza kai Mommah tayi tana zama kan sofar ta ce“A'a wlh, na tsaya ƙarasa aiki ne kafin na fito” jinjina kai Mommy ta yi, tana kallon Mufeeda ta ce“Tashi ki je zamu yi magana” to ta ce sannan ta tashi ta fice daga parlon. Gyara zama Mommy tayi tana kallonta ta ce“Ina jin ki Khadijah” numfasawa Mommah ta yi sai kuma ta ce“Daman akan maganar Zayyad ne, naga ya girma yanzu, ya kamata ace an fara maganar aurensa ko hakan zai saka ya yi hankali” jinjina kai Mommy ta yi ta ce“Nima nayi wannan tunanin Allah ne bai nufeni da yi miki maganar ba, to amma yanzu ya ki ke ganin za'a yi?” shiru Momma ta yi na wasu sakwanni kafin ta ce“Ni da nace ko Fatiha ya nema, yarinyar Adda Maryam” shiru Mommy ta yi sai kuma ta ce“Hajiya Maryam taku?” gyaɗa mata kai Mommah ta yi, Mommy ta yi murmushi ta ce“Hakan ma ya yi sosai, yanzu tayaya za'a haɗasu?” murmushi Mommah ta yi ta ce“Wannan ba zai gagara ba, idan nace Zayyad yaje ya ganta tabbas zai je” jinjina kai Mommy ta yi ta ce“To shikenan, ayi hakan, ki samu kiyi magana dashi” tashi Mommah ta yi tana cewa“Tom Shikenan, bari naje na sameshi tun yanzu” “To, Allah ya jisshemu Alkhairi”. Da Ameen Mommah ta amsa sannan ta fice daga ɗakin. Tashi Mommy ta yi ta shige bedroom nata, wayarta ta ɗauka ta shiga danna kira, sai da tayi ringing sau uku sannan aka ɗaga, Mommy da ranta ya gama ɓaci ta ce “Ina ki ka shige ne?” Daga ɗaya ɓangaren wata mata ta ce“Kaga uwar gida a gidan Colonel Idris, matar soja, wlh ina can gurin Yallaɓai ne” shiru Mommy ta yi tana ayyana abin da zata ce, matar ta sake faɗin “Hello, Hajiya kina jina kuwa?” numfashi Mommy ta sauke sannan ta ce“Akwai matsala Hajiya, abubuwa na gab da lalacewa” cikin tashin hankali matar ta ce“Subhanallahi, me kuma ya sake faruwa?” girgiza kai Mommy ta yi ta ce“Maganar bata waya bace, gobe idan Allah ya kaimu zan zo gidan naki sai kiji abin da ake ciki” shiru matar ta yi can kuma ta ce“To Allah ya kaimu, ina nan ina jiranki” To Mommy ta ce sannan suka yi sallama ta kashe wayar. Zama tayi gefen gadonta tana saƙe-saƙe a ranta. Momma na fita ta samu Nayla na ƙoƙarin shiga ɗakin Zayyad. “Zaki je takura masa ɗin?” Langwaɓar da kai ta yi tana cewa“Wlh Mommah ba takura masa zan yi, assignment ɗina nakeson ya yimin” “Ku kuka sani dai” cewar Momma tana barin wajen. Tura ƙofar ɗakin ta yi ta shiga, shiru taji parlon babu alamar mutum sai tv dake kunne tana faman aikinta. Taɓe baki Nayla tayi sai kuma tayi hanyar bedroom ɗinsa, turus Nayla tayi, tayi baya tana toshe hancinta. Zaune yake kan kujera idanunsa zube kan marble Coffee table wanda yake ɗauke da bottle na wine da kuma cigarette kwali guda, sai shisha wadda yake zuƙa a hankali, hayaƙi sai tashi yake. Shigowar Nayla ya sanya shi ɗago idanunsa yana kallon inda yarinyar ke tsaye, tuni hawaye suka wanke fuskarta, sai girgiza kanta take hannunta bisa bakinta. Zare shishan ya yi daga bakinsa ya kashe, sannan ya tashi daga zaunen da yake, da gudu Nayla ta juya ta bar ɗakin, ya bita da idanu sai kuma ya yi hanyar toilet kawai. Wanka ya yi sannan ya fito ya gyara gashinsa sai sheƙi yake, ya shirya cikin wasu Burberry dark blue, ya sanya Gucci vandaner akansa ya feshe jikinsa da mayataccen turaren Clive Christian No.1 nan da nan ɗakin ya ɗumame da ƙamshi, ƙarasawa yayi ya kwashe komai dake kan table ɗin ya mayar dasu inda ya saba ajiyewa, sannan ya ɗauki car key ɗinsa da wayarsa ya fito kai ba zaka ce shine wanda ya gama shaye-shaye ba, he look quite and gently man. A corridor ya tsaya ya yi ɗan jim sai kuma ya yi hanyar ɗakin matan gidan. Tura ƙofar parlon ya yi bayan ya yi sallama wadda ba lallai a ji ba. Zaune take kan sofa idanunta zube kan system ɗin gabanta tana game, sanye take da wata Gucci oversized sweatshirt sai Celine wide pants, gashin kanta wanda yake ƙyalli ta yi parking ɗinsa a tsakiya, she looks elegant. Tana ganinsa ta rufe system ɗin tana murmushi ta ce“Welcome Yaya” kallo ɗaya ya yi mata ya yi hanyar bedroom ɗin Nayla yana faɗin “How are you doing” “Fine Yaya” Mufeeda tafaɗa tana mai da hankalinta kan kallon da take. Can ƙarshen gadon ya hangeta ta cure jikinta waje ɗaya fuskanta cikin tsakiyar ƙafafunta tana shassheƙar kuka a hankali. Kasa ƙarasowa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar idanunsa harɗe a ƙirji yana kallonta. Above 5mins yana nan tsaye kafin ya ƙarasa cikin ɗakin yana tafiya a hankali, a gefen bedside drawer ya zauna yana kallonta, Hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta. Zabura Nayla tayi ta sauka daga gadon tana girgiza kanta, tashi Zayyad ya yi yana kallonta ya ce“Lil sis” “A'a Yaya, banaso, ni ka tafi, ka tafi dan Allah” tayi maganar tana sake rushewa da kuka, ɗan murmushi ya yi ya ƙarasa gabanta tana ƙoƙarin barin wajen ya riko hannunta, hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen daya cika mata fuska yana murmushi ya ce“Guduna kike yi? Kina cewa na tafi Nayla?” girgiza kanta tayi tana cigaba da kukanta. Sakin hannunta ya yi yana murmushi ya ce“anyway, sai anjima” daga haka ya juya ya bar ɗakin, durƙushewa tayi a inda take tsaye tana cigaba da kuka. Ashe daman abun nasa har ya kai haka? Yayanta kuma a cikin gidansu?. Zayyad na fita ɗakin Daddy ya nufa, zaune ya sameshi a parlon suna magana da wani Soja a waya, zama yayi kusada shi ya ɗauki remote ya can ja tasha zuwa Bollywood inda suke haska film ɗin Mohenjodaro. After some minutes Dad ya kalleshi yana ajiye wayar hannunsa ya ce“Har ka fito?” gyaɗa masa kai Zayyad ya yi, ya ajiye remote ɗin hannunsa ya juyo yana kallon Daddy ya ce“Dad inason zan yi tafiya ne” shiru Dad ya yi sai kuma ya ce“Ina kenan?” murmushi ya yi ya ce“Maybe London zan je, nagaji da zaman nan wlh, kwata-kwata bana jin daɗi” dafashi Daddy ya yi ya ce“Duk yanda kake so haka zaka yi Zayyad, ni ba zan takura maka ba, idan ka tsayar da ranar tafiyar sai ka min magana” sosai yaji daɗi a ransa shiyasa yafi son magana da Dad fiye da kowa, dan koda yaushe yana goyon bayansa, babu yanda za'a yi ya ce ga abin da yakeso ba'a yi masa shi ba. Tashi ya yi ya ce“Tom, duk yanda ake ciki I'll let you know, zan ɗan fita” jinjina kai Daddy ya yi yana kallonsa cike da so da ƙauna ya ce“Tom a dawo lafiya”. Zayyad ya fice daga sashin yana tafiya cike da isa da kuma taƙama. Wuse 2, Abuja. Kwance take akan gado tana danna wayar hannunta taji ana knocking ƙofar ɗakin “Yes, coming” Tafaɗa ba tare data ɗago ba. Buɗe ƙofar ɗakin aka yi wasu yan mata guda biyu suna shigo, muryar waɗanda taji ya sanyata tashi zaune tana kallonsu baki buɗe, sanye take da wata riga Dior blouse sai chanel tweed skirt, ta ɗaure gashin kanta da hermès scarf, sosai tayi kyau abin ta, duk da babu makeup a fuskarta amma ta saka eyeliner a idanunta ta kuma saka lip gloss a bakinta. Harararta Khairiyya tana cewa “why are you staring at us?” ɗan murmushi Aneeserh ta yi tana kallon Hibba dake tsaye ta ce“Have a sit mana Beb” wani banzan kallo Hibba ta watsa mata tana cewa“Sai kin ce min na zauna zan zauna?” tuntsirewa tayi da dariya ta ce“To sai kiyi ta tsaiwa ai” ta juya tana kallon Khairiyya ta ce“I thought ai da wasa kike fa” Khairiyya ta ce“A'a da gaske muke fa, mun je transcorp tun jiya da tuni mun shigo sai muka fasa kuma tunanin ko Dad yana nan” murmushi ta yi ta ce“sarkin tsoro to me zai yi muku? Bayanan ma” girgiza kai Khairiyya tayi ta ce“A'a kamarya mai zai yi mana? Kin san dai halinsa ai” Tashi tayi tana cewa “Ke dai kin fiye tsoro kawai” daga haka ta nufi inda fridge yake, coke mai sanyi ta ɗauko musu guda biyu ta haɗo da cups. A ƙasa ta ajiye sannan ta koma kan gadon ta tankwashe ƙafafunta tana kallon Hibba ta ce“Manyan mata, Hibba naga kina wani ƙara jiki mene sirrin ne?” ɗan murmushi ta yi ta ce“Ke matsalata dake kenan, kamar ya ina ƙara jiki” “Tana nufin taga kin sauya” cewar Khairiyya tana ƙoƙarin buɗe coke ɗin hannunta. Harararta Hibba ta yi ta ce“To nima ban sani ba” dariya Aneeserh ta yi ta ce“Shikenan, idan tayi tsami ma ji” “Ba ma zata yi ba. Wai kuwa Aneeserh ina Zayyad?” Hibba ta tambaya tana kallonta. Aneeserh dake danna wayarta ta ce“Yana nan wlh” Hibba ta sake cewa “Ɗan girman kai da jin kai” Aneeserh ajiye wayar hannunta tayi tana kallon Hibba ta ce“To bari kuma. Girman kan me ya yi miki? Kinga Hibba banason ana taɓa min miji rai zai ɓaci” tuntsirewa da dariya suka yi a tare Khairiyya ta ce“Wai miji, abokin rayuwarki dai kawai” Aneeserh ta ce“Like how? Bangane ba” “Aneeserh mene baki gane ba? Cewa nayi abokin rayuwarki ne shi ba mijinki ba, domin ba lallai bane ya aureki” wani mugun kallo Aneeserh ta watsa mata tana cewa“Haka yace miki ai ko? To bari kiji Zayyad shine mijin aurena, in har na tashi aure to Zayyad zan aura” jinjina kai Hibba tayi ta ce“Muma shine fatanmu, Allah yasa ya aureki” “Ai ma kamar ya aureni ne” Khairiyya ta buɗi baki zatayi magana wayar Aneeserh ta shiga ringing, ɗaukan wayar tayi sai kuma ta saki wani murmushi tana kai wayar kunne “I'm outside, ina jiranki” Taji muryasa. Numfasawa ta yi ta ce“Tom gani nan” daga haka ta kashe wayar, kallonsu Khairiyya ta yi ta tashi daga kan gadon tana faɗin “To ni dai saurayina yazo kuma zan bi shi, idan anan zaku kwana ne to” harararta Hibba ta yi ta ce“Tunda ke kaɗai ce mai saurayi wanda zai zo ya ɗaukeki ko?” ɗaga kafaɗa Aneeserh tayi tana cewa “Ni na sani”. Cikin mintuna kaɗan tagama shiryawa cikin wata riga doguwa wadda ta tsaya iya gwiuwarta, ta gyara gashin kanta sai sheƙi yake, wayarta ta ɗauka tana kallonsu ta ce“Ya kuka ganni” tafaɗa tana juyawa. Murmushi Hibba ta yi tana cewa“Kin yi kyau yarinya kamar bake ba” sosai Aneeserh taji daɗi jin sun yabeta ta tabbata haka Zayyad ɗinta zai yabeta idan ta fita. Koda suka sakko ƙasa babu kowa a ƙaton parlon hakan yasa suka yi waje a bin su. A bakin gate ɗin gidan ta hangi motarsa Lexus jeep, ta ƙarasa tana tafiya cike da kwarkwasa. Front seat ta buɗe ta shiga tana kallonsa ta ce“Sorry Bae I keep u waiting” tayi maganar a shagwaɓe. Murmushi ya yi ya ce“Kin yi kyau” dariya Aneeserh tayi tana cewa “Thank You, ina zamu je?” “Transcorp” ya faɗa yana yiwa motar key. ****Ranar Saturday da yamma suna zaune a parlon suna hira ya shigo, Tashi Nayla ta yi ta bar parlon ba tare da ta kalleshi ba. Murmushi Mommy tayi tana kallonsa ta ce“Wai meya haɗaka da mutuniyar?” girgiza kansa ya yi yana zama kan sofa ya ce“nothing kawai shirmenta ne” Mommy ta ce“Nayla uwar rigima ita har yanzu autar bata barta ba” Mufeeda dake zaune kan kujera tana danna waya ta ce“Wlh Yaya Nayla taba da kai, kullum fa sai tayi kuka har can dare bata yin bacci” shiru Zayyad ya yi bai ce komai ba, Mommy ta kalleshi sai kuma ta kalli Mufeeda ta ce“But kin tambayeta me aka yi mata? Ko a school ne ake ɓata mata rai?” girgiza kai Mufeeda tayi ta ce“Babu wani a school da ake ɓata mata rai fa Ita dai tasan abin da ya dameta, kuma nafaɗa mata zan faɗawa Daddy idan ya dawo daga Paris” Tashi Zayyad ya yi ya bar parlon suka bi shi da kallo. Kai tsaye apartment ɗin su Naylan ya shiga, ya buɗe ɗakinta amma bata ciki, fitowa ya yi ya shiga apartment ɗin Mommah. Zaune ya hangeta kan kujera hannunta riƙe da handout tana karatu, ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya ƙarasa ciki, Zama ya yi kan sofa tayi saurin tashi tsaye ta haɗe takardunta tana shirin barin wajen “Nayla” Zayyad ya kirata da kakkausar murya. Cak ta tsaya amma bata juyo ba, ya tashi ya ƙarasa gabanta, juyo da fuskarta ya yi yana kallonta saurin shigewa jikinsa tayi tana sakin kuka. Tsaf ya rungumeta jikinsa yana shafa kanta, sai da yaji tayi shiru sannan ya ɗago kanta yana goge mata hawayen ya ce“I'm sorry” cikin shassheƙar kuka ta ce“Dan Allah Yaya kadaina, wlh it's totally haram, ka daina kaji” numfashi ya furzar still looking at her ya ce“shikenan, muje ki rakani” hannunta ta miƙa tana cewa“then promise me you won't do it again” Lulu eyes ɗinsa ya zuba mata sai kuma ya ce“Then u didn't trust me?” girgiza kanta tayi ya ce“Alright muje”. “Maganar me kuke yi naji ana ba'a yarda ba?” Suka ji maganar Mommah akansu, juyowa Nayla ta yi tana cewa“Chocolate nace ya siyomin shine ya manta fa Mommah” taɓe baki Momma tayi tana faɗin “I see” daga haka ta kalli Zayyad wanda ke tsaye ta ce“Zayyad Inason magana da kai” “Tom Mommah bari naje nadawo” “Kaje Ina?” tafaɗa tana tsare shi da idanu, komawa ya yi ya zauna yana murmushi ya ce“Na tuba” harararsa ta yi sannan ta zauna tana kallon Nayla ta ce“Madam yi tafiyarki” tura baki Nayla tayi sannan ta fice daga ɗakin. Gyara zama Mommah tayi tana kallonsa ta ce“Daman Inason nayi maka magana ne akan batun aurenka domin naga kamar kai hakan baya gabanka ma” langwaɓar da kai ya yi ya ce“Mommah aure kuma? Har yaushe nayi girman da zan bar gabanku?” baki buɗe Mommah ke kallonsa kafin ta ce“Zayyad ka fita a idona, idan baka yi aure yanzu ba sai yaushe ka shirya yi kenan? Sa'anninka duk sun ajiye iyali amma kai ka zauna kana faman shashanci. To bari kaji kafin mahaifinka ya dawo ka fitar da matar aure, idan kuma babu to ni na fitar maka” shiru Zayyad ya yi yana kallonta ganin how serious she's. Ta ce“Sannan kana sane da Adda Maryam batada lafiya ban ji kace zaka je dubata ba” Zayyad ya ce“Eh mun yi maganar da Ahmad, maybe gobe zan je in sha Allah, bana son shiga garin nan traffic ya yi yawa wlh” harararsa ta yi ta ce“To ka fasa zuwa kaji, shi Ahmad ɗin da kullum yake tawowa daga can bai ce komai ba sai kai” “But Mommah shi ya saba da zaman can daman, garin gabaɗaya mutane sun yi masa yawa, tafiyar mintuna ashirin amma idan baka yi sa'a ba sai ka yi awa, suna fama” tashi Mommah tayi tana cewa“Sannu wanda baya fama” dariya Zayyad ya yi sannan shima ya miƙe yana cewa“Zamu je tare ne?” girgiza kai tayi ta ce“A'a ni naje, amma idan zaka tafi ku tafi da Nayla taga Fatiha” okay ya ce sannan ya juya ya fita, ita kuma ta koma kitchen dan cigaba da abin da take. Kabayi, Mararaba. Da salamma ta shigo gidan hannunta riƙe da wata ƙatuwar cooler, sanye take da hijabi yadin ɗan Abba coffee colour wanda ya tsaya iya gwuiwarta sai wata doguwar rigar yadi baƙa a jikinta, zaune ta hangeshi kan tabarma ta ƙaraso gabansa tana kallonsa ta ce“Sannu Abba ya ƙafar taka?” madadin ya bata amsa sai taga hawaye na zuba akan idanunsa, rikicewa Salma tayi cikin tashin hankali take faɗin“Abba meya faru? Kafar ce? Kayi hakuri Abba” ta ƙarashe maganar hawaye na biyo fuskarta. Malam Habu kallonta kawai yake har sannan hawaye bai daina zuba daga idanunsa ba, girgiza kanta tayi tana cewa“Dan Allah Abba kayi hakuri Allah zai yaye maka” yatsansa ya sanya ya goge hawayen dake idanunsa cikin sanyin murya ya ce“Ummusalma ba wai ina kuka bane saboda Allah ya jarrabeni, A'a ina kuka ne saboda nagaza a matsayina na mahaifi, na gaza. Na kasa kare rayuwarki, har yau ta kai kina fita talla domin sama mana abin da zamu ci, Ummusalma wane irin ubane ne? Sam ban cancanci zama mahaifi ba, nagaza!” girgiza kai Salma ta shiga yi tana kuka ta ce“Dan Allah ka daina faɗar irin haka Abba, tabbas ka ubane wanda kowace ƴa ke fatan samun kamarsa. Ka tsaya kai da fata wajen ganin ka kare mutuncina, duk da bakada hali hakan bai sa nayi kuka akan wani abu ba, Abba ka cancanci yabo, wlh ban taɓa ɗaukar dan nafara fita sana'a gazawarka bane, ƙaddarace. Haka Allah ya tsara mana, kuma malam ya faɗa mana ba'a iya gujewa ƙaddara, saboda haka ka daina damun kanka Abba, fatanmu Allah ya baka lafiya” Malam Habu kallonta kawai yake yana sake godewa Allah cikin ransa daya bashi Ummusalma a matsayin Ƴa, jinjina mata kai ya yi ya ce“Allah ya yi miki albarka, ya kula da rayuwarki, ya haɗaki da masu sonki tsakani da Allah” da Ameen ta amsa sannan ta tashi ta shige ɗakinta. Gab da Magriba ta shigo gidan hannunta riƙe da leda, zaune ta sameshi inda yake ta zauna gefen tabarmar tana cewa “Wash Allah!” Kallonta ya yi amma bai ce mata komai ba, ganin coolern da tayi yasa ta ce“Allah dai yasa Salma kin siyar da lemon nan kafin ki ka dawo” Salma dake kunna wuta ta ce“Eh Umma na siyar sauran leda biyu ne ya rage, to kuma inason na dawo wajen Abba tunda ke bakya nan shiyasa ban siyar ba” taɓe baki Umma tayi ganin idon Malam Habu ta ce“Da kin tsaya kin siyar ɗin me zai cijeshi a gida, ke wai uwar kinibibi” shiru Salma tayi bata ce komai ba, Umma ta tashi ta buɗe cooler, lemon tsamiya ne mai sanyi guda biyu ta ɗauko ta dawo ta zauna, miƙa masa leda ɗaya tayi tana cewa“Gashi kai ma ka jiƙa maƙoshinka” kallon ledar lemon ya yi sai kuma ya kalleta, amsa ya yi ya ajiye gefensa, ita kuwa tafasa na hannunta tafara sha. Around 8pm tana zaune kusada Abbanta yana mata ƙari wani yaro ya shigo yana cewa “Salama alaikum wai Salma tazo” Wata irin faɗuwar gaba Salma ta ji, ta saci kallon Abbanta taga ya ɗago yana kallon yaron ya ce“In ji wa?” komawa ɗan ya yi, bayan minti ɗaya ya shigo ya ce“Wai in ji wani” shiru Abba ya yi Umma da fitowarta kenan daga banɗaki ta kalli yaron ta ce“kai je kace masa to, gatanan” juyawa ɗan ya yi ya fita, Salma ta ɗago tana kallonta. Fuska a hade ta ce“Kin bar mutum a tsaye ba zaki je kiga kowane ba” Salma marairaice fuska tayi ta ɗago ta kalli Abbanta taga ba ita yake kallo, sake kallon Umma ta yi ta ce“To ai ni ban san wane ba Umma” a fusace Umma ta ce“To zauna sai kin san wane sannan ki tashi” Jiki a sanyaye Salma ta tashi ta shige ɗakinta, Hijabinta na ɗazu ta ɗauko ta saka, ta zura slippers ɗinta dake Kofar ɗakin tayi waje tana waigen Abbanta. Turus tayi a ƙofar gidan nasu ta dinga kallonsa kamar idanunta zasu faɗo. “Ummusalma”. # HCD Nanameera, 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU 💋* Chapter 05: The Visit That Cut Deep Nanameera, YOTA/023. Malam Yusuf ya kira sunanta, Salma da ta daskare a wajen tana kallonsa ta ce“Malam!” murmushi ya yi yana gyara tsaiwarsa ya ce“Na'am Ummusalma kin ganni a gidanku ko?” Salma da har sannan mamaki ya isheta ta gyaɗa masa kai. Numfasawa ya yi sannan ya ce“Daman naga kwana biyu baki zo makaranta bane, dana tambayi ƙawayenki sai suka ce Abbanki ne ya ƙarye shine nace bari nazo na duba shi” ɓoyyayiyar ajiyar zuciya Salma ta sauke, ta ƙirƙiri murmushi ta ce“Allah sarki, aikuwa yana ciki bari naje na masa magana” gyaɗa mata kai ya yi sannan ta juya ta shige gidan nasu. Tunda ta shigo Umma ke kallonta har ta ƙaraso gabansu, tsugunawa ta yi tana kallon Abbanta ta ce“Abba daman malaminmu ne na islamiyya yaga kwana biyu bana zuwa shine aka faɗa masa baka da lafiya yazo ya duba ka” jinjina kai Malam Habu ya yi ya ce“Allah sarki, to ce masa ya shigo” to ta ce sannan ta tashi ta fita. Umma ta taɓe baki ta tashi ta koma wajen wuta inda take ta kokawar gama abincin dare. Tsaye Salma ta same shi cikin bango, muryarta a sanyaye ta ce“Malam ya ce ka shigo” murmushi ya yi ya ce“To masha Allah, muje” daga haka ta koma ciki ya bi bayanta. Sosai Malam Habu ya yi farin ciki da zuwansa har wajen ƙarfe tara yana gidan suna hira, shirin inda ranka na freedom Radio da aka fara ya sanya Malam Yusuf miƙewa yana murmushi ya ce“Allah ya ƙara sauƙi ya kiyaye gaba” jinjina kai Abba ya yi ya ce“Ameen Malam Nagode sosai, Allah ya bada lada” Ameen Malam Yusuf ya ce sannan ya juya ya fice daga gidan ba tare da ya sake ganin Salma ba, wadda tun bayar shigowarsa ta shige ɗakinta ta cigaba da karatun da take. Washegari daya kasance Lahadi da wuri Umma tagama dafa zoɓonta, dan ranar an fi ciniki dayawa, around 10am Salma ta fito daga ɗakinta tana sanye cikin wata doguwar riga ta atampa mai kyau kuma a goge, ɗinkin riga da skirt, ta sanya hijabi sister colour wanda ya tsaya iya gwuiwarta babu komai a fuskarta sai kwalli wanda ta sanya a idanunta amma tayi kyau tamkar tayi kwalliya farar fatarta sai sheƙi take. Kallonta Umma tayi sai kuma ta ce“Ke ko ɗan jambakin da ake sakawa ba zaki dinga sakawa ba? Kika sani ko Allah yasa acan ki dace da wanda zai aureki?” tura baki Salma tayi tana wasada fingers ɗinta bata ce komai ba, taɓe baki Umma ta yi tana cewa“Au mahaukaciya ma kika mayar dani, ina magana kin yimin banza” a sanyaye Salma ta ce“Umma nifa banaso” “Ai daman ke duk wani abu da zai kawo mana cigaba bakya fatansa ya za'a yi ki so?. Ni zo ki shige karki ɓata mana lokaci” ƙarasowa Salma tayi ta buɗe ƙatuwar cooler da lemo da ruwan yake ciki. “Sauran ki ce zaki dawo baki siyar ba, yau ba fita zan yi ba zan zauna da uban naki. Kayan dubu biyar da ɗari uku ne, sauran ki dawo ki cemin baki gane ba” Salma ta ce“To Umma ban ci abinci bafa” wangale baki Umma Rahmatu ta yi tana cewa“Wato duk wanda ya ji ya ce na hanaki abinci saboda ban haifeki ba. Ni na hanaki cin abinci? Ga ragowar shinkafar da aka dafa jiya nan, mu ma ita muka ci da awara, kuma ga naki can ki ɗauka” Salma bata ce komai ba ta juya ta koma inda Ummar ta nuna mata. Murfin da aka rufe farantin ta buɗe, shinkafa da wake ce sai awara guda uku akai. Ta zauna kan kujerar dake wajen tayi bismillah tafara cin abincin. Tana cikin ci yaron dake ɗaukar mata coolern yazo Umma ta juyo tana kallon inda take ta ce“Salama abincin ne ya gagara ki cinye? To maza tashi ku tafi kar masu siya su ragu” ajiye farantin tayi ta tashi ta ƙarasa inda randar ruwa take ta buɗe ta wanke hannunta. Sannan ta wanke bakinta ta dawo inda Umman da yaron suke, ɗaukar coolern ya yi suka fita tana cewa“Sai mun dawo” “Allah ya tsare ya bada kasuwa”. Abacha road, Mararaba. Girgiza kai Al-ameen ya yi yana kallonta ya ce“A'a Mami, u need to rest fa, fitar da kike shine ya haifar da wannan ciwon, ya kamata ace kin zauna kin huta koda na kwana uku ne” Mami wadda take sanye da wata Egyptian Abaya Black colour tayi rolling mayafin abayar akanta tana murmushi ta ce“Al-ameen dole na tafi wlh, bazan iya zama ba ka sani ban saba ba. Tunda dai Allah yasa nasamu sauƙi to kawai gara na tafi na samu ƙarfi” fitowa tayi hannunta riƙe da handbag ƴar ƙarama tana kallonta ta ce“Mami muje kar nayi missing lecture” harararta Al-ameen ya yi ya ce“To babu inda zata je, shige ki kama gabanki” turo baki tayi tana kallonsa ta ce“Yaya da Mami fa nake, to idan ban tafi da ita ba da wa zan tafi?” “Yaya Ahmad ya tafi dake” “Tun ɗazu fa ya tafi, yanzu ai ya kai Abuja ma” murmushi Mami tayi ta riƙe hannunsa ta ce“Sorry son, bazan daɗe ba” “Mami promise?” Jinjina kai tayi ta ce“Yeh” “Alright, Allah ya kiyaye” “Ameen” tafaɗa sannan tayi waje Fatiha tabi bayanta. Sun yi nisa Fatiha ta kalleta ta ce“Mami ɗazu naji Yaya yana cewa wai su Nayla zasu zo?” murmushi Mami ta yi ta ce“Eh haka Khadijah tace min a WhatsApp, but ban sani ba ko za su zo ɗin” Fatiha ta sake cewa “To Mami u have to call them, inason na tabbatar” Mami da idanunta ke kan titi ta ce“As if wajenki zasu zo ko?” dariya Fatiha tayi tana cewa“Wlh Mami Inason ganin Sis ne, i missed her alot, rabon da na ganta fa tun a Makka kwata-kwata basa zuwa” girgiza kai Mami ta yi ta ce“Ba laifin Khadijah bane kinsan General ba ko'ina yake barinsu suje ba, so shine inda ake samun matsalar, Nima kuma ayyuka sun yimin yawa bana samun damar shiga Abujan” Jinjina kai Fatiha tayi daidai sanda aka zo inda zata sauka ta ce“Tab, aikuwa idan tazo zamu yi yawo” Mami ta ce“Tunda ke kece ƙafar yawo ba” murmushi Fatiha tayi ta ɗauki handbag ɗinta ta buɗe motar ta fita tana ɗaga mata hannu. Maitama, Abuja. Around 8am ya tura ƙofar ɗakin, kwance ya sameta cikin duvet bata da alamar tashi daga bacci. “Nimrah! Nimrah” A hankali ta shiga buɗe idanunta ta janye duvet ɗin jikinta tana kallonsa, gyara zamanta tayi ta jingina da fuskar gadon fuskarta babu walwala ta ce“Amma akan me zaka tasheni daga bacci?” tayi maganar kamar zatayi kuka, Farooq dake tsaye gefenta ya ce“Gani nayi har time ɗin tafiyarki school zai shige but banga kin tashi ba, sannan gashi nima da wuri zan fita but banga breakfast ɗina ba” “Yanzu saboda breakfast ɗinka ka tasheni a bacci? Akan me? Shikenan banida yancin da zan kwanta na huta a cikin gidana? Duk maids ɗin gidan nan ka rasa wadda zata dafa maka abinci sai dole ni?” Farooq kallonta kawai yake dan yanzu lamarin nata ya daina bashi mamaki. Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce “Kenan ina matsayin mijinki banida right ɗin da zan saka ki kimin breakfast ko?” “As far as akwai masu aiki da zasu iya yi maka to wlh bakada shi. Ni nagaji da wannan rayuwar wlh, nagaji da takurarka, akan me zaka kawoni gidanka ka dinga azabtar dani? Wlh bazan iya ba!” ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka. Tsananin mamaki ya sanya Farooq sakin baki, shi da ta yiwa laifi bai yi kuka ba sai ita ce mai bakin kuka? Girgiza kansa ya yi kawai ya juya ya fice daga ɗakin gudun kada zuciya ta ɗebeshi ya illata yar mutane. Da harara ta bishi sai kuma ta koma ta cigaba da kwanciyarta hankali kwance. ****Babbar mace ce zaune kan royal sofa dake zagaye da parlon, tana sanye da wata embroidery atampa ruwan zuma ɗinkin riga da zani, baƙa ce saidai kana ganin fatarta kasan hutu ya zauna. Girgiza kanta tayi tana kallonsa bayan ya gama maganar da yake ta ce“Yanzu ni da kake faɗamin me zan yi akai? Sanda nake faɗa maka ka saurareni? Akan me yanzu zaka dinga kawomin complains? Ƴar ƙanwarta nace ka aura amma ka watsamin ƙasa a ido kace kai ba zaka aureta ba wayayyiya kakeso. Da me kayi tunani da wayayyiyar mace? Zata dinga maka biyayya, ai sai dai kai ka bita wlh, sai ka bari idan mahaifinka ya dawo wanda ya yi ruwa da tsaki saboda tasa buƙatar shima yasa ka auri yarsu ka faɗa masa. Amma ni ka cireni daga sabgar gidanka Farooq” Farooq wanda ke zaune kujerar dake facing tata ya kalleta sai kuma ya girgiza kai a hankali ya ce“Amma Mama...” dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce“Farooq babu abin da zaka faɗamin na yarda, ka aureta saboda haka dole ka zauna da ita a duk yanda take, ka koyi juriya da haƙuri” “Mama i know I made a mistake but dan girman Allah karki hukuntani da haka, wlh nagaji da halayen Nimrah, nagaji Mama, bazan iya cigaba da jure irin abubuwan da take yimin ba, dan Allah Mama” murmushi Mama ta yi ta ce“To yanzu Farooq me kake so nayi?” numfasawa ya yi yana gyara zamansa ya ce“Dan Allah Mama ki kirawota nan gidan kiyi mata magana ko zata rage wasu abubuwan, Mama tunda muka yi aure da Nimrah ban jin ta dafamin abincin ya yi sau uku, bata da lokacina, sannan batasan maganar da zata faɗamin ba a matsayina na mijin da take aure, kwata-kwata batada tarbiyya” “Thank god daga fuskanci haka da kanka Farooq, babu yanda ban yi ba akan kabar maganar aurenta amma ka ƙi, bayan kasan tun asali yarinyar nan ba sonka take ba, Babanta ya mata dole ta aureka. Ni nasan babu wani farin ciki da zaka samu daga gareta, saboda haka ni yanzu shawara ɗaya zan baka, idan kaga zaka ɗauka to ka taimaki kanka, idan kuma yanzun ma zaka sake watsi da maganata sai kayi”. Farooq ya ce“Bazan sake wannan wawtar ba Mama just tell me” “Ka ƙara aure!”. ****Mommah ce tsaye ƙofar ɗakin Nayla tana kallon yanda take rolling mayafi kamar batada laka, tsaki tayi ta ƙaraso ɗakin ta kama fuskarta ta yi mata rolling ɗin tana cewa“Kinsan dai halin Yayanki kinaso ya yi miki faɗa ne yasa ki ke abu kamar bakida laka ko?” murmushi Nayla tayi tana kallon madubi ta ce“Wow Mommah nayi kyau?” harararta Mommah ta yi ta ce“Zaki tsaya tambayar kin yi kyau ko kuma shigewa zaki yi ki tafi” langwaɓar da kai tayi ta ɗauki handbag ɗinta ta yi hanyar waje tana cewa“Bari naje gurin Yaya nasan shi zai ce nayi kyau”. A corridor suka ci karo dashi, sanye yake da wata dakkakiyar shadda Madam gezner ash colour, ɗinkin ya yi matuƙar yi masa kyau, ya ɗora hular zanna mai aikin ash itama, sai tashin ƙamshin turaren Clive Christian No.1 yake, murmushi Nayla ta saki tana cewa“Wow, My handsome brother” taɓe baki ya yi ya ce“Kyaji dashi” haɗe rai tayi ta kalli Mommah wadda fitowarta kenan ta ce“Mommah kina gani nace yayi kyau shine ya gwaleni ko?” murmushi Mommah ta yi ta ce“Ni ina ruwana da sabgarku kuma?” shiru Nayla tayi bata sake cewa komai ba tayi hanyar downstairs. Ƙaraso gabansa Momma tayi tana kallonsa ta ce“Dan Allah Zayyad karka je kayi abinda bai kamata ba, kasan dai halin Adda” murmushi ya yi ya ce“Shiyasa zan tafi da headphone saboda nasan irin faɗan Mami” murmushin itama Momma tayi ta ce“Allah ya baka sa'a, ka gaishesu” jinjina mata kai ya yi sannan ya yi hanyar downstairs shima. A compound ya samu Nayla idanunta zube kan flowers ɗin dake wajen sai tashin ƙamshi suke. Matarsa ya ɗauko yazo inda take daga cikin motar ya ce“Sai nace miki ki zo mu tafi?” murmushi tayi ta buɗe front seat ta shiga. Basu fi 10mins da fara tafiya ba ta kalleshi ta ce“Yaya bamu zo ba?” Banza Zayyad ya yi mata ya cigaba da tuƙin da yake, kwaɓe fuska tayi ta ce“Yaya I'm asking you fa” tsaki yayi idanunsa bisa titi ya ce“Kina iya sauka ai” bata sake cewa komai ba ta juya tana kallon hanya, rabonta da Nassarawa har ta manta. Tunda suka shigo Mararaba-Nyanya Expressway Zayyad yake tsaki the traffic is to much, yana ɗaya daga abinda ya sanya baya son zuwa Nassarawa saboda wannan cunkuson. A ƙalla sun kai kusan 20mins kafin su samu su shige, kai tsaye kuma Abacha road ya nufa. Around 1:05pm Ya yi horn a bakin gate ɗin gidan, mai gadin dake zaune kan benci ya taso ya buɗe masa. Yana gama parking Nayla ta fito ta rungume Fatiha wadda ta tawo da gudu sanda taji horn ɗin mota, kallonsu kawai Zayyad ya yi sai kuma ya yi hanyar entrance ɗin gidan. Da sallama ya shiga parlon, Zaune ya hangeta kan kujera 2 seater idanunta zube kan wayarta tana dannawa. Tana ganinsa ta ajiye wayar tana murmushi, zama ya yi kan sofa muryarsa a sanyaye ya ce“Ina yini Mami” wani banzan kallo ta watsa masa, daidai lokacin da Ahmad ya fito daga kitchen hannunsa riƙe da mug na tea. Murmushi ya yi yana kallonsa ya ce“Nayi tunanin ai fasa zuwa kayi” girgiza kai Zayyad ya yi har lokacin idanunsa na kan Mami wadda ta haɗe rai, kallonta Ahmad ya yi sai kuma ya yi murmushi dan daman yasa za'a rina. Nayla ce suka shigo parlon da Fatiha sai dariya suke, zama tayi kan kujerar da Zayyad ke kai ta ce“Mami ina yini” taɓe baki Mami tayi tana kallonta ta ce“Lafiya, kema sai yau kika ga damar zuwa ko?” sunkuyar da kai Nayla tayi dan tasan halin faɗan Mami. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin Ahmad ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin “Mami dan Allah ki yi haƙuri, yanzu ba gashi sun zo ba” Harararsa Mami ta yi tana cewa“Da yake kai ne wanda ka yi laifin dole ka bada haƙuri” ɗan murmushi Zayyad ya yi yana kallonta ya ce“Dan Allah Mami kiyi haƙuri, Allah ya baki haƙuri”. “Haƙuri ka ke bani Zayyad? Okay saboda ka raina min hankali ya sanya ka ke bani haƙuri kenan? Yanzu ni banida ƙima ko daraja a gurinka da zaka zo inda nake ko? Ban isa ba. Kenan da ace Yaya tana da rai haka zaka dinga wulaƙantamu kana nuna bamu da wani matsayi a gurinka, to bari kaji ko kana so ko baka so dole a faɗa a ce mu ƙannen mahaifiyarka ne uwa ɗaya uba ɗaya. Kuma baka da waɗanda suka fi mu duk duniya wlh. Amma mune yan iska ko nace ni ce yar iska ban isa kazo inda nake ba da sunan ka zo gaida ƙanwar mahaifiyarka banida wannan matsayin, amma da ace a dangin su Hajara abu ya faru da tuni kaje saboda ita kana ganinta da gashi, bakomai rayuwa ce” Mami ta ƙarashe maganar tana haki. Ahmad ne ya kalleta ya ce“Calm down Mami kar wani abun ya sake samunki dan Allah” tasowa Zayyad ya yi ya dawo kujerar da take zaune, hannunta ya riƙe a sanyaye ya ce“Dan Allah Mami ki yi haƙuri, nayi laifi but ba zan sake ba in sha Allah. Ki yi haƙuri saboda girman Allah kinji” fashewa tayi da kuka tana cewa“Zayyad ba wai dan wani abu nake maka faɗa ba, sai dan hakan ya zame mana dolene, Yaya ta riƙemu yanda ya kamata, a lokacin da muka rasa iyayenmu, duk wani abu da uwa ke yiwa ɗa ita tayi mana, ta aurar damu, yanzu Zayyad idan muka bar rayuwarka ta cigaba da tafiya a haka kana ganin zata yafe mata? Mun kyauta mata kenan? Mun bar abin da ta haifa yana cikin rayuwar da bata dace ba. Kasani kai maraya ne wanda ya rasa iyayensa a lokacin da aka haifeshi, rayuwarka abun tausayi ce, madadin kayi abinda ya kamata sai ƙanin mahaifinka ya gurɓata tarbiyyarka da sunan soyyaya. Kowa ya sani Idris yana sonka yana tausayinka amma ba hakan ke nufi ba zai dinga maka faɗa ko kuma ya gyara maka abu ba, ya kamata ka yiwa kan ka faɗa kasani girma kake yanzu ba baya kake komawa ba” Shiru Zayyad ya yi haka kawai yaji hawaye na zubo masa akan fuskarsa, da gaske Bashida Iyaye, shi marayane irin marayan da kowa ke tausayinsa. Goge masa hawayen Mami ta yi tace“You don't need to cry Zayyad, abin da kake buƙata shine ka sauya rayuwarka, ka samarwa da kan ka haske wanda zai fitar da kai daga cikin wannan duhun mu kuma zamu tayaka da addu'a” murmushi ya yi a sanyaye ya ce“Nagode sosai Mami, kuma in sha Allah zan yi duk abin da ki ke ce, kiyi haƙuri” murmushin itama tayi ta ce“Bakomai Allah ya yi maka albarka” Daga haka ta kalli Fatiha da Nayla wanda suke zaune ta ce“Ku tashi muje kitchen a ƙarasa abincin” tashi Nayla tayi da sauri tana faɗin “Mami kiyi zamanki nida Fatiha sai muyi na iya girki ai” murmushi Mami ta yi ta ce“Yaushe Auta ta iya girma bansani ba? Mu je dai na tayaku” daga haka ta tashi tayi hanyar kitchen ɗin suka bi bayanta. Ahmad da tun ɗazu ke tsaye ya zagayo ya zauna kusada Zayyad yana kallonsa ya ce“Tashi muje sama” taɓe baki Zayyad ya yi ya ce“To wajenka nazo da zaka ce wani muje sama” tuntsirewa da dariya Ahmad ya yi yana cewa“Kai daɗina dakai ba'a maka gwaninta, to sai kayi ta zama ai” tashi Zayyad ya yi ya nufa saman yana cewa“Sai mutum ya bari idan nace ya yi min abu ya yi” daga haka ya haye saman abinsa, da idanu Ahmad ya bishi sai kuma ya yi murmushi ya cigaba da shan tea ɗinsa. Around 4:50pm suna zaune cikin ɗakin Fatiha Mami ta shigo, kallonsu ta yi ta ce“Har yanzu hirar bata isheku ba?” murmushi Nayla tayi ta ce“Mami inason naje Orange market kafin mu tafi, ki ce Yaya Zayyad ya kaimu” Murmushi Mami ta yi ta ce“Shikenan ku shirya bari nayi musu magana, daga nan sai ku yo mana cefane” ihu Nayla ta saki ta kanƙame Fatiha tana cewa“Wayyo Allah na zan ga gari” dariya Fatiha tayi ta ce“To ki zauna ihu yamma ya sake yi a tashi daga kasuwar” da gudu Nayla ta shige toilet tana cewa“Da nayi asara kuwa”. Zaune Mami ta samesu Ahmad sai hira yake masa, ta kalleshi ta ce“Son ko zaku je Orange market dasu Fatiha sai su yo min cefane” Toh Ahmad ya ce sannan ta juya ta fita. Ƙarfe 5:15pm suka fito compound ɗin, Zayyad ya kalli Nayla wadda ke faman murmushi ya ce“Ke koma ciki” turo baki tayi ta ce“Ai fa Mami ce tace ku raka mu” taɓe baki Zayyad ya yi ya buɗe motar ya shige gefen mai zaman banza. Murmushi Ahmad ya yi ya shiga driver seat yana cewa“Kayi wani saurin zama anan” “Eh cause ni ba drivenku bane ai” dariya Ahmad ya yi ya ce“Allah ya yaye maka” Zayyad bai ce masa komai ba ya yi commenting karatun Alkur'ani a motar, wanda hakan ya sanya su Nayla suka yi shiru dan dole. Ahmad ya yiwa motar key suka nufi hanyar orange market. *HASKEN CIKIN DUHU💋* Chapter 06: When destiny came in disguise Nanameera, YOTA/23. Around 5:30pm ne, rana na kokarin shige wa cikin hazo, Iska tana kadawa da ƙanƙanin sanyi, tana ɗauke da ƙurar gawayi da tururin abinci daga kan tanderun masu talla. Orange Market ta cika sosai da jama'a kasancewar ranar Lahadi ne ko'ina kabi cike yake da hayaniya da motsin mutane Shaguna sun cika har da ƙofofin su, 'yan kasuwa na ta waƙa da kiran sayarwa, "Fresh tomatoes! Dankalin turawa! Fruit ɗin sabo!" Murya na hadewa da kukan yara da tattausar dariyar mata yan talla masu soyayya. Fitilun titi na haskawa sannu a hankali, suna ba wa kasuwar wata kalar launin rawaya da ke rikita ido, Jama'a na yawo da buhuna a kafaɗa, wasu na cin abinci a bakin masu sayar da masa da soyayyen dankali. Tsaki Zayyad ya yi ganin yanda traffic ya yi yawa a cikin kasuwar, kasancewar lokacin gefin magriba ne, kasuwar ta hargitse masu siye da siyarwa sai kai komo suke, Yayinda iska ta yawaita cikin kasuwar sakamakon kwantaccen hadarin daya ɓuya cikin gajimare. Kashe karatun motar Zayyad ya yi yana kallon Ahmad ya ce“Nifa duk sanda na shigo Mararaban nan ina jin wani irin yanayi, yanda kuke iya rayuwa a nan yafi bani mamaki fiye da Chemistry” Ahmad da ke kallon motocin da suke gabansa ya ce“Nima kuna bani mamaki yanda ku ke iya rayuwa ba tare da tunanin wasu ba, ai ita rayuwa kowa da irin tasa kuma duk inda Allah ya nufa dole nan ne inda zaka rayu” yanda ya yi maganar ya sanya Zayyad murmushi ya ce“To mene abun fusata kuma?” “Wane ya ce maka haushi naji?, ai kana da right ɗin ka faɗi abin da yake ranka” harararsa Zayyad ya yi bai ce komai ba ya shiga danna wayarsa. Tamkar wanda aka ce ya juya haka ya kalli side ɗinsa daga cikin motar, Zaune take kan wani bencin tana ware ledar ruwan dake hannunta, daga gefenta wasu matane su biyu sai kuma namiji guda ɗaya. Da murmushi a fuskarta ta buɗe ƙatuwar coolern gabanta ta zaro ledar lemon tsamiya guda biyu ta saka cikin ledar data buɗe ta miƙawa matar gabanta. Amsa tayi tana murmushi ta ce“Allah ya yi albarka” murmushi Salma ta yi ta ce“Ameen Mama” daga haka ta bar wajen, ta juya ta sake karbar kuɗin ɗaya mutumin. Lemon zobo ta ɗauko ta miƙo masa sai dai kafin ya amsa ya suɓuce daga hannunta ya faɗi ƙasa nan take ledar ta fashe lemon ya tsiyaye a gefen wajen. Samun kansa ya yi da yin murmushi a fili ya ce“Allah shi ƙara” kallonsa Ahmad ya yi sai kuma ya ce“Kai dawa?” banza Zayyad ya yi masa ya cigaba da kallon yarinyar, Ahmad ma ya kalli wajen, Salma kamar zata yi kuka ta kalli mutumin ta ce“Yi haƙuri Baba” girgiza kai mutumin ya yi cikin sanyin murya ya ce“Bakomai yarinya” ta sake ɗauko wani zobon ta miƙa masa, a zuciyarta tana tunanin yanda zata yi da Umma idan taje gida. Ɗago kanta tayi cikin rashin sa'a suka haɗa idanu da ita, a fili kuma yanda zata ji ya ce“Da kin nemi sana'a mai ma'ana kin yi kin bar wannan sayar da lemon” Salma da ranta ke a ɓace ta kalleshi ta ce“Duk sana'ar da ba haramun bace ai bata zama mara amfani ba, ko an faɗa maka agogo ne kaɗai ke faɗa mana gaskiya?” ta ƙare maganar tana murguɗa masa baki. Tuntsirewa da dariya Ahmad ya yi ya ce“ka samu daidai da kai” haɗe rai Zayyad ya yi yana kallonta ta cikin motar ya ce“And who are u?” Salma ta ce“Ni ba kowa bace, kuma ba yar gidan kowa ba, amma nan gaba kasan irin maganar da zaka faɗawa mutum domin baka san halin wani ba” daga haka ta ɗauke kanta tana kallon wani wajen daban. Shiru Zayyad ya yi haka kawai ya samu kansa da kasa sake faɗar wata maganar, kawai ya juya yana danna wayarsa daidai nan suka samo hanyar shigewa. Suna barin wajen Ahmad ya kalleshi ya ce“Kaga abin da nake faɗa maka ko? Ba kowa zaka yi ma abu ya rabu da kai ba, kuma koda hakan na nufin kafi ƙarfinsa” tsaki Zayyad ya yi ya ce“Ni banida lokacin tsayawa ina magana da wannan yarinyar daga ganinta kasan tana rayuwane a cikin duhu, Bama tasan kanta ba” “Oh really?.” Ahmad ya faɗa yana kallon Zayyad, banza ya yi masa, Ahmad ya sake faɗin “But you have to know that ba kowane haske ke zuwa daga chandelier ba. Wani hasken na iya zuwa daga titin Orange market.” Zayyad kallonsa kawai ya yi ta gefen ido, sai kuma ya kalli wajen daidai sanda iska ta kaɗa ya lumshe idanunsa. Murmushi Nayla tayi tana kallon Fatiha dake tsaye gaban mai sai da Alayyahu tana yanka mata ta ce“Nifa wani abun kwaɗayi nakeson siya” Fatiha ta yi dariya ta ce“Kamar me kenan?” juya idanu Nayla ta yi alamar bata sani ba. Ta kalli gefenta nan ta hango ana miƙawa wata mata sumammen zoɓo mai sanyi, “I got it!” Tafaɗa da ƙarfi tana dafa Fatiha, kallon inda take nunawa Fatiha tayi ta ce“Wai lemon can kike so?” gyaɗa mata kai Nayla ta yi, Fatiha ta ce“Ki bari idan mun je gida sai muyi, muje mu siya zoɓon” girgiza kai Nayla tayi ta nufi wajen mai siyarwar. Babu yanda Fatiha ta iya haka ta biyo bayanta. Salma take zaune tana ɗan kalle kalle ta amsa sallamar Nayla. “How much?” “Hundred Naira each” murmushi Nayla tayi dan ta burgeta ta ce“Okay bani guda biyar” to kawai Salma ta ce, sannan ta zaro baƙar leda tafara zuba zoɓon a ciki. Nayla ta ce“Oh ashe ba iya zoɓo bane” “Eh akwai Tamarin ma” “Haɗa min har da shi sai ki bada na 1k” Okay Salma ta ce sannan ta cigaba da zuba mata. Nayla ta kalli Fatiha dake tsaye kamar statue ta ce“Tyha bani 1k” zaro dubu ɗayan tayi a jakarta ta miƙa mata, Kallon kuɗin Nayla ta yi sai kuma ta ce“ƙara min wata” Fatiha ta sake bata ba tare da ta tambayi dalili ba. Salma nagama zubawa ta miƙawa Nayla, Amsa tayi tana murmushi ta ce“Thank you dear” daga haka ta miƙa mata duka 2k ɗin. Kallon kuɗin Salma ta yi sai kuma ta ce“Amma ba haka bane kuɗin ai, naga 2k kuma 1k ne kuɗina” Nayla na murmushi ta ce“Yeh i know, baki nayi” girgiza kai Salma ta yi ta miƙo mata tana cewa“A'a ki bar shi Nagode” murmushi Nayla ta yi ta riƙe hannun data miƙo mata ta ce“I insist” “Kinga in zaki amsa ki amsa ana baki kuɗi kina wani baki so, as irin kinfi ƙarfin nan nashi” Fatiha tayi maganar tana kallon Salma fuskanta a haɗe. Jan hannunta Nayla ta yi tana cewa“Ayyah sister mene haka, isn't good fa” tsaki Fatiha tayi ta juya ta bar wajen, haka kawai taji Salman bata mata. Girgiza kai Nayla ta yi kamar zata yi kuka ta ce“I'm sorry on her behalf dear” daga haka ta juya ta bar wajen itama. Komawa Salma ta yi ta zauna ta sanya hannunta ta share hawayen daya zubo mata. Sun fara tafiya Nayla ta kalli Fatiha ta ce“Abin da kika yi ba daidai bane Tyha, bakyau yiwa ɗan adam irin haka. Ke kina gani kinsan ƙaddarace ta sanyata a wannan rayuwar, kalleta mai kyau kuma ga ilimi bugu da ƙari daga ganinta tanada tarbiyya” “And so what? Ke bakisan halin yan matan kasuwar nan bane shiyasa kike wani cewa haka, duk yan iska ne wlh. Dan kin ganta da kyau to Allah ne kaɗai yasan abin da take aikatawa, haka suke, iyayensu ke aikosu kasuwa da sunan suna talla, amma s zahiri da sana'ar ta kawosu ba, suna zuwa ne kawai dan su haɗu da zama, ayi abin da bai dace ba” Fatiha ta ƙarashe maganar tana yin tsaki. Shiru Nayla ta yi sai kuma ta ce“Yaya Zayyad wai haka?” shiru ya yi mata ba dan bai ji kiran da tayi masa ba, sai dan bashida interest akan hirar tasu. Nayla ta sake cewa“Yaya I'm talking to you fa, amma ka shareni” ba tare da ya juyo ba ya ce“Mene ne?” madadin ta bashi amsa sai ta mayar da idanunta kan Ahmad dake tuƙi ta ce“Yaya wai haka ne? Ni ban yarda da abin da Fatiha tafaɗa ba” murmushi Ahmad ya yi ya ce“Hakane Auta, but not all of them, wasu ba hakan bane, wasu ƙaddarace take kawosu kasuwar. Wata zaki ga mahaifinta ta rasa, wata kuma mahaifiya, wata kuma suna rayen amma basu da yanda zasu yi dasu, rayuwar Mararaba ba kamar ta Abuja bace, anan akwai ƙalubale dayawa. Wasu duhu ne ya cika rayuwarsu, kuma basu sami wanda zai nuna musu haske ba, basu samu wanda zai fitar dasu daga wannan ƙangin ba. Saboda haka babu yanda za'a yi ace duk macen dake sana'a cikin kasuwa ƴar iska ce” kamar zatayi kuka ta ce“Allah sarki, abun tausayi Yaya, nikam wannan duk inda take mutuniyar kirki ce, kuma bata rasa haske ba, daga ganinta ita kanta Hasken wani ce”. Murmushi Ahmad ya yi ya ce“Daɗina da auta kaifin tunani” tayi dariya bata ce komai ba har suka ƙarasa gida. ****Tafiya take a hankali tana tunane tunanen cikin ranta, duk rin horn ɗin da ake yi Salma bata ji ba, dan gabaɗaya zuciyarta bata wajen, Wani mutumi dake kusada ita ne ya yi mata magana yana cewa“Ku yaran nan meke damunku? Idan ya bigeki ai ubanki ya siya magani” sai a sannan ta juyo tana kallon motar ƙirar Accord mai launin baƙi. Parking mutumin ya yi ya fito daga motar yana nufo inda take tsaye, a sanyaye ya ce“Me kike tunani?” sunkuyar da kanta tayi cikin cool voice ɗinta ta ce“Dan Allah kayi haƙuri” murmushinsa mai kyau ya yi ya ce“Bakomai, Allah ya kiyaye. But ina zaki je?” ya yi maganar cike da kulawa. “Mamana ta aikeni gidan ƙawarta” agogon hannunsa ya kalla, around 6:30pm ne ya ɗago ya kalleta ya ce“Okay, ina ne wajen? Can I help you?” Salma tayi saurin cewa “A'a nakusa zuwa ma ai, dana zagaya wannan layin ne” murmushi kawai ya yi ya ce“Alright sai kin dawo” murmushin itama tayi ta ce“Nagode” daga haka tabi ta gefensa ta shige. Da idanu ya bita yana murmushi sai kuma ya koma motarsa ya tada ya bar wajen. Salma na shan kwana ta tsaya tana dafe ƙirji, sosai mutumin ya bata tsoro a fili ta ce“Waya sani ma ko ɗan yankan kai ne” daga haka ta cigaba da tafiya dan tana hango gidan Aunty Maryam ɗin. ****Murmushi Mami tayi tana kallonta ta ce“Kenan ta burgeki daga ganinta?” jinjina kai Nayla ta yi ta ce“Mami ko ke kika ganta sai ta burgeki, she's cute kuma daga gani tayi karatu, can you imagine Mami har turanci ta iya?” Jinjina kai Mami tayi tana murmushi ta ce“Allah sarki, to Amma mene ya saka take talla a kasuwa?” watsa hannu Nayla tayi alamar bata sani ba. Fatiha dake kallonta tun ɗazu ta ce“Ke kina da matsala wlh, kinga Mami duk ta damu akan wata wadda bata sani ba” harararta Nayla ta yi ta ce“To ina ruwanki dani? Ni nace kiji tausayinta ne?” “Allah ya tsareni da jin tausayin ƴar talla fitsararriyar banza” “Fatiha!” Mami ta kira sunanta a tsawa ce. “Don't ever try it again” A sanyaye ta ce“In sha Allah Mami” tashi Nayla ta yi ta ce“Ni bari na ɗauko lemona ma nasha, nasan yanzu ya sake yin sanyi” daga haka ta tashi ta shige kitchen. Cup guda biyu ta ɗauko kowanne ta zuba leda ɗaya na lemon wanda ya sake sanyi aciki sannan ta ɗauko ta fito. Mami ta samu zaune inda ta barta, ta miƙa mata daya tana cewa“Mami test it please” amsa Mami tayi tana dariya sanin halin Nayla. Without second thought kuma ta kai lemon bakinta. Lumshe idanu Mami tayi dan bata yi tunanin zai yi mata daɗi haka, sai da ta shanye tas sannan ta ajiye empty cup ɗin kan table tana cewa“Gaskiya Ya yi daɗi, na daɗe ban sha lemo mai daɗin wannan ba. A ina take a Orange market ɗin?” gyara zama Nayla ta yi bayan ta shanye nata itama ta ce“Kinji ko Mami? Ni dama daga ganinta nasan abunta zai yi daɗi wlh. A bakin titi take zaune kusada masu sai da abinci, kinga yanda ake layi kuma Mami?” Jinjina kai Mami ta yi ta ce“Allah sarki, aikuwa idan nashiga kasuwar zan biya na siya watarana” sosai Nayla taji daɗi jin yanda Mami ta yabeta. Ita kuwa Fatiha sai taɓe baki take duk da tanason tasha lemon ko dan taji abinda suke yiwa kwazozoton. Ana fara kiran sallar isha'i suka sakko daga saman, Mami ta kallesu sai kuma ta ce“Naga ka saka hula ina zaka je?” murmushi Zayyad ya yi ya ce“Mami dare nayi, tafiya zamu yi” haɗe rai Nayla tayi lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke. Taɓe baki Mami ta yi ta ce“Amma ai ka tsaya ku ci abinci ko? Ko kuma tafiya zaku yi da yunwa?” Zayyad ya ce“Mami ni dai wlh I'm full, Alhamdulillah” “I see. Idan kai ka ƙoshi ita ai Nayla zata ci abinci” ta ƙare maganar tana kallon Nayla, gyaɗa mata kai tayi ta ce“Eh Mami ni yunwa nake ji, kuma na daɗe ban ci tuwo ba ni dai sai naci abinci” harararta Zayyad ya yi ta gefen ido. Mami ta ce“Saboda haka sai ka jirata ita taci abinci, kai kuma Allah ya ƙara ƙoshi” murmushi Ahmad ya yi ganin yanda Zayyad ya yi da fuska kamar zai saka ihu. Ya dafa shi yana faɗin “Baba let's go, mu koma daman ban gama da kai ba” wani kallo Zayyad ya watsawa Ahmad ɗin sannan ya juya ya koma saman. Mami ta bishi da harara. “Mami ki ce ya barta ta kwana mana” Fatiha tayi maganar kamar zata yi kuka. Shiru Mami ta yi mata ta tashi ta shige kitchen dan ta duba girkin da take. Tasowa Fatiha tayi ta dawo gefen Nayla ta riƙe hannunta tana faɗin “Dan Allah ki kwana mana” murmushi Nayla ta yi ta ce“Yaya won't let me, ba zai barni ba nasani” tsaki Fatiha tayi ta ce“But sai kiyi pretending a zuwan baki da lafiya, kinga sai ya tafi ya bar ki” “As if bakisan he's a medical doctor ba ko?” shiru Fatiha ta yi sai kuma ta ce“To ya zamu yi?” girgiza kai Nayla ta yi ta ce“Nima bansani ba, but wlh inason na kwana, banason komawa Abuja, nan yafi daɗi” Shiru Fatiha tayi tana tunanin hanyar da zasu bi Nayla ta kwana a Mararaba. Can ta tashi ta shige kitchen Nayla ta bita da idanu. Daidai nan aka fara knocking ƙofar parlon, tashi tayi ta buɗe dan Mami ta rufeta, shigowa ya yi yana sanye da wani yadi mara kauri, da gudu tafaɗa jikinsa tana faɗin “Masoyiii” Rungumeta Al-ameen ya yi yana dariya ya ce“Masoyiya ashe kin zo” gyaɗa masa kai tayi tana sakinsa ta ce“Muna nan da Yaya tun rana, but ban ganka ba ina kaje?” murmushi Al-ameen ya yi yana zama a kujera ya ce“Ina clinic wlh, Abubuwane suka yi yawa shiyasa” zama tayi kusa da shi tana faɗin“Then ka yadani ko Masoyi? Ba kira babu saƙo ko dai kayi sabuwar budurwa ne?” girgiza kansa ya yi ya ce“Duk mai son ganin rigima yazo wajen Autar Mommah, wane ya faɗa miki haka? Ke dai kika yada masoyinki bani ba, you left me” ya faɗa yana marairaice fuska, Tuntsirewa tayi da dariya tana cewa“Kaga fuskarka kamar wani Baby taɓ” lumshe idanunsa ya yi ya ce“I'm so tired wlh” Rau rau tayi da idanu ta ce“Ayyah Masoyi tashi kaje kayi wanka kazo kaci abinci Mami tagama” Tashi Al-ameen ya yi yana cewa“Ina Yaya Zayyad ɗin?” “Suna sama da Yaya Ahmad” jinjina kai Al-ameen ya yi ya ce“To bari naje na shirya nazo mu sha hira” langwaɓar da kai tayi ta ce“Bayan tafiya zamu yi” “Da daren nan? Why not ku bari sai gobe?” “Yaya ba zai bari ba, ni nasani” shiru Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“Bari dai ina zuwa” daga haka ya haye upstairs. Zaune suke kan dinning table ɗin kowa yana cin abincinsa banda Al-ameen wanda ya zubawa plate ɗin idanu, sau biyu Mami na kallonsa tana ganin yanda ya yi shiru kamar yana tunani, sanda ta ɗago idanunta ana ukun ne ta ajiye spoon ɗin hannunta tana faɗin “Al-ameen” Shiru bai amsa ba, alamar hankalinsa ma baya wajen, Nayla dake kusa da shi ce ta taɓa shi ta ce a hankali “Yaya, Mami na magana” sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta. Da mamaki ta ce“Lafiyarka? Me kake tunani?” numfasawa ya yi ya ɗauki spoon ɗin kan abincin ya fara kai tuwon semovitan da miyar agusi wadda taji nama bakinsa. Mami bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincinta. Ahmad ne ya kalli Zayyad wanda ke faman danna waya ya ce“Wai ba zaka ci abincin ba? Ko bakason tuwon?” “Wai Ahmad meyasa kake yimin haka? Ina ruwanka dani?” ya faɗa yana harararsa, duka Ahmad ya kai masa yana cewa“Banza ni dan nayi maka abin arziki” “But ai already tell you banason abun arzikin naka, kana wani yin abu kamar na Allah a gaban Mami. Mami can you imagine yanda Ahmad ke dakamin tsawa a Abuja, babu kalar zagin da baya yimin” Ya ƙare maganar yana kallon Mami. Murmushi tayi ta ce“To kayi hakuri, ni yanzu nace kaci abinci” Zayyad spoon kawai ya ɗauka ya yi bismillah sannan ya kai tuwon bakinsa, ya lumshe idanunsa jin yanda miyar tayi wani irin daɗi, daman Mami ba dai iya girki ba, that's why some years back yake zuwa takanas kawai dan ya ci abincinta. Basu gama cin abincin ba sai wajen 8:30pm Zayyad ya tashi ya haye sama da sauri, wanke bakinsa ya yi sannan ya fito yana kallon Ahmad dake tsaye a corridor “Why not ku kwana Zayyad?” “I will not” ya faɗa yana sauka kasa. Taɓe baki Ahmad ya yi sai kuma yabi bayansa. Zaune ya samu Nayla ta shirya sai tura baki tayi, Mami ta ce“Allah ya tsare hanya, make sure idan kun je gida ka kirani” Jinjina kai ya yi ya ce“In sha Allah Mami, mun gode Allah ya ƙara girma” Ameen ta ce sannan ta kama hannun Nayla wadda ta fara hawaye suka yi waje. Turus suka yi a veranda ganin yanda ruwan sama ke zuba kamar da bakin kwarya, wani murmushi Nayla da Fatiha suka saki, suna rike hannun juna. Mami ta ce“Ikon Allah, that's means sai dai ku bari sai gobe” daga haka takama hannun Nayla suka koma ciki as if abinda take jira kenan. Zayyad tsayawa ya yi a wajen kamar statue, yanzu ya za'a yi ya kwana anan? Ba zai iya kwana ba tare da ya sha giya ba. Yaya zai yi kenan?. Ya runtse idanunsa yana jin wani irin yanayi, ko menene ya sanya ya bari sukai magrib anan ma Ohho. Ahmad komawarsa ciki ya yi dan yasan halin Zayyad, a parlon ya samu Nayla sai dariya take bayan tayi wurgi da jakarta a ƙasa. Al-ameen da bai fita ba yana dariya ya ce“Ki bari ya shigo ya ganki kina dariya ya kwaɗeki” Sake fashewa tayi da wata dariyar tana faɗin “Kaga yanda yaya ya haɗe rai kuwa? Ai nikam naji daɗin ruwan nan, Yaya zo ka bani labari” ta ƙare maganar tana zama kan sofa. Zama shima Al-ameen ya yi yana kallonta ya ce“Labarin me zan baki Auta?” murmushi ta yi ta ce“Koma menene just kabani labari” gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce“Ɗazu gab da magrib ina ƙoƙarin dawowa gida na haɗu da wata yarinya. Ban san meyasa ba amma kawai naji tayi min, ke infact ma ni nasamu matar aure” gyara zama Nayla ta yi ta ɗora hannayenta duk biyu kan kumatunta tana kallonsa daga gani tana jin daɗin labarin. Jin ya yi shiru yasa ta ce“Yaya ka cigaba” murmushi ya yi ya ce“Tana da kyau kuma tanada hankali, ta burgeni sosai” “Wannan wace mai sa'ar ce da har Al-ameen ɗin dana sani ya ce yana sonta, ko dai halin zaka gwada mata?” cewar Ahmad yana murmushi. Girgiza kai Al-ameen ya yi ya ce“No be joke Yaya, wlh da gaske ta shiga zuciyata, tunda muka rabu nake tunaninta” “And what's her name, a ina kuma take?” Girgiza kansa ya yi ya ce“Ban sani ba nima, a bakin titin Kabayi muka haɗu, tana tafiya ina faman horn bata ji ba” shiru Ahmad ya yi can kuma ya ce“Al-ameen kai ɗin dana sani ne kake cewa kaga yarinya a Kabayi, kai ɗin? Karka yaudari ƴar mutane” girgiza kansa ya yi ya ce“Ba zaku gane ba, wlh da gaske nake, babu wata yaudara a tattare dani” Fatiha dake zaune ta ce“Taɓ, kawai sai ka auri yar Kabayi kasa friends ɗina suna min dariya” Harara ya watsa mata kafin ya ce“To uwata, hanani tunda ke zaki zauna da ita, ƙawayenki ɗin banza” tashi tayi tana yin hanyar upstairs ta ce“Allah ba zaka aureta ba” da idanu suka bita Nayla ta ce“Barta Masoyi cigaba da bani labari” Al-ameen ya ce“Ai shikenan abin da ya faru fa” Nayla ta ce“To yanzu yaushe zamu je tare na ganta?” Dariya ya yi ya ce“Nima bansan inda zan sake ganinta ba, ban san gidans ba, bansan sunanta, kawai fuskarta nasani” da mamaki Nayla ta ce“To yanzu a ina zaka sake ganinta Yaya?” murmushi ya yi ya ce “Idan har ƙaddara tana nufin mu sake haɗuwa to nasan definitely zan sake ganinta sooner or later” tafi Nayla ta shige yi tana cewa“Yaya kaga yanda ka yi maganar with so much courage kamar a movies?” murmushi kawai ya yi ya ce“Da gaske?” Nayla na gyaɗa kai ta ce“Da gaske Yaya, in sha Allah zaka sake ganinta, ina a jikina ita ɗin taka ce” jan kumatunta ya yi ya ce“My Clever Auta”. 2:30am. Kwance yake kan makeken royal bed ɗin, sai juyi yake, kwata-kwata bacci ya ƙi zuwar masa. Gajiya ya yi da kwanciyar ya tashi zaune, wayarsa ya janyo ya shiga WhatsApp kai tsaye kuma Aneeserh ya yiwa magana, ya tura mata da sallama, tana online sannan hakan yasa tayi masa reply da “Bae, ba kayi bacci ba har yanzun?” Text ya tura mata da Eh, ta sake cewa “But why?🥺” Murmushi Zayyad ya yi ya tura mata da text “Nima bansani ba, kawai bana jin daɗi ne” Aneeserh dake kwance kan gadonta taga message ɗin nasa ya shigo. Tashi ta yi zaune ta sake masa text “Kaje club ne?” A'a ya tura mata ta sake cewa “But you have to, meya hanaka zuwa?” Zayyad bai bata amsa ba ya ajiye wayar kan gadon ya zura slippers ɗin dake bakin gadon ya buɗe ɗakin ya fito. Ko'ina tsit yake dan ko kukan karnuka ba'a ji, sauka ƙasa ya yi kai tsaye kuma ya shige kitchen dan ƙishirwa yake ji. Buɗe fridge ya yi ya zaro bottle ɗin ruwan, zai rufe yaga wani glass jug mai ɗauke da wani abu kamar tea. Daukowa ya yi sannan ya rufe fridge ɗin, ya yi jim yana kallon jug ɗin sai kuma ya ɗauko wani cup ya tsiyaya abinda ke ciki, a hankali kuma ya yi bismillah ya kai bakinsa. Lumshe idanunsa ya yi saboda sanyi da kuma tsamin tsamiyar daya ji, sai dai ya shanye tas sannan ya sauke kofin yana sakin ajiyar zuciya. Samun kansa ya yi da sake tsiyayar lemon a karo na biyu ya sake shanyewa, sai a sannan ya yi gyatsa ya mayar da jug ɗin inda yake sannan ya ɗauki ruwan ya fito. Yana dawowa ya ajiye ruwan kan bedside drawer ya koma ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukeshi. # HASKEN CIKIN DUHU 08106608363, Nanameera. HASKEN CIKIN DUHU Chapter 07: Endless Trials Nanameera, YOTA/023. Washegari wajejen ƙarfe 10:30am Salma na zaune kan kujera a tsakar gidansu tana ƙullin zoɓo Umma ta fito daga ɗakin, daga inda take ta kalleta ta ce“Amma dai kina ganin yanda garin nan yake ko Salama? Ba zaki yi da jiki ba ki gama ki zo ki shige” Salma wadda zuciyarta ke wani gurin ta ɗago ta kalleta, a sanyaye ta ce“Umma daman cewa nayi ko zan je makaranta naga abin da ake yi” riƙe haɓa Umma ta yi ta ce“Au ashe daman baki cire maganar wannan gantalalliyar makarantar daga zuciyarki ba? To sai kin dawo tunda kyauta zasu miki karatun, shi kansa uban naki daya ɗoraki akan wannan turbar ya haƙura ya saki tunda dai bashida yanda zai yi, dangin naci da gaddama” ta ƙare maganar tana zabga mata uwar harara. Sunkuyar da kai Salma tayi hawaye ya shiga sakkowa kan fuskarta, daka mata tsawa Umma ta yi tana cewa “Zakiyi ki gama ki tashi anan gurin ko sai ranki ya ɓaci” Goge hawayen nata tayi ta cigaba da ƙulla zoɓon. Tsaki Umma ta yi ta koma ɗaki tana faman sababi, Malam Habu dake zaune kan tabarma yana sauraren duk abin da ke faruwa ya kalleta amma bai ce komai ba. Zama tayi ɗan nesa dashi tana cewa“Haba yarinya kamar mayya idan ta kama abu, wannan makarantar ko ta uwarta ce sai haka” “Rahmatu!” Abba ya kira sunanta cikin ɗaga murya. Kallonsa ta yi ya ce“Kiyi duk abin da zaki yi amma karki sake taɓo mahaifiyarta, domin bata duniyar” a fusace ta ce“Au ashe? Sai kace min kishin matacciyar matarka kake, tsintacciya matarka” tuni jijiyoyin kansa suka mimmiƙe idanunsa ya yi wani irin kaɗawa ya kalleta ya ce“Ki iya bakinki, domin wannan furucin naki zai iya kai ki ga halakar da baki taɓa tsammani ba!” ganin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya Umma Rahmatu yin shiru. Tashi ta yi ta fice daga ɗakin a fusace, tsaye ta samu Salma ta jingina da bangon ɗakin hawaye sai shatata yake akan kuncinta. Umma ta ce“Kin bar wajen nan kin je kin shirya ko dai ranki ya ɓaci?” Salma wadda ta tsaya tana jiran fitowarta ta shige ɗakinta. Wata doguwar rigar yadi ta saka dan daman tuni tayi wanka, ta sanya hijabi ruwan ƙasa wanda ya tsaya iya gwuiwarta, fuskarta ta fito sosai cikin hijabin. Goge idanunta ta sake yi sannan ta fito daga ɗakin kai tsaye ta nufi inda coolern lemon nata yake, daidai nan kuma yaron dake ɗaukar mata lemon ya shigo. Ɗauka ya yi sannan tabi bayansa suka fita daga gidan, Umma ta bita da harara. Tafiya suke amma idanunta a rufe dan kuka take, sai da suka zo bakin titi sannan ta buɗe idanunta tana goge hawayen daya gama ɓata mata fuska. Tsaye yake jikin motarsa Accord yana sanye da wasu sport wear blue ƙafarsa sanye da sneaker black sai safar ƙafa fara, daga ganinsa kasan daga wani wajen yake. Ganin tana goge hawaye ya sanya shi tsallako titin ya zo gabanta, Salma ta kalleshi a lokacin da take ƙoƙarin sake rufe fuskarta, “Hi dear” Shiru yaji tayi masa ya sake maimatawa kuma bata amsa ba, girgiza kansa ya yi ya ce“Ayyah meya faru? Me aka yi miki?” “Babu komai” Tafaɗa tana yin gaba, da idanu kawai Al-ameen ya bita har ta tsallaka titin ta nufi hanyar Orange market ɗin. Numfasawa ya yi sannan ya koma inda motarsa take ya shiga kai tsaye kuma hanyar gida ya nufa. Maitama, Abuja. Turo ƙofar ɗakin tayi ta shigo, zaune yake kan sofa idanunsa kan system ɗin gabansa yana dannawa cike da nutsuwa. Sanye take da wata Abaya maroon colour ta ɗaure kanta da veil ɗin Abayar. Fuskarta fresh babu kwalliya sai lip gloss data sanya. Zama tayi kan kujera tana kallonsa ta ce“Yau ba zaka fita aiki ba?” yana cigaba da danna system ɗin ya ce“Uhn, ba zan je ba, akwai inda zan je ne” shiru tayi can kuma ta ce“Anjima around 2 inason zan fita, akwai wani get together da zamu yi da old friends ɗina” rufe system ɗin Farooq ya yi ya ɗago yana kallonta, murmushi taga ya yi ya ce“Alright Allah ya kaimu” “Ameen” Nimrah Said, sai kuma tafara danna wayarta. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin Farooq ya ce “Nimrah” “Na'am” “Inason magana dake, ki ajiye wayar hannunki” ɗago dara daran idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce“But I'm hearing you ai” Farooq ya ce“Eh nasani, amma inason ki bani hankalinki ne ba wai kawai ki saurareni ba” Tayi shiru sai kuma ta ce“Okay then, Ina ji” ta ajiye wayar akan table. Numfasawa Farooq ya yi kafin calmly ya ce“Kinsan dai irin abubuwan dake faruwa a cikin gidan nan, ba sai na tsaya ina sake faɗa ba. Duk da daman zaman aure ya gaji haka, amma abubuwan yanzu they're getting worth, I can't endure it, saboda haka na yanke shawarar na ƙara aura, kinga kema kya samu lokacin kanki kuma na daina shiga rayuwarki kamar yanda ki ke yawan faɗi. So that's it, in sha Allah nan bada nisa ban zan sake aure” Tsaye yaga Nimrah akansa, tana yi masa wani irin shegen kallo, ta girgiza kanta tana dariya kuma tana cije baki at the same time. Tafa hannayenta ta yi sai kuma ta ce a fusace “Aure! Aure? Aure kake cemin zaka yi Farooq? Kana ganin har ka isa kayi aure? Ni zaka ƙarama kishiya. Na rantse da girman Allah baka isaba. Kayi kaɗan Farooq kai ɗin banza, wlh baka isa kayi aure ba as far as Ina numfashi. To kai awa kuma? Wato ka mayar da Nimrah yar iska wadda batasan me take ba, sai na bari kayi aure. Hmmmm...!” Nimrah ta ƙare maganar tana wani irin huci, Farooq kuwa kallonta yake da mamaki dan bai yi tunanin haka daga gareta ba. Zagaye ɗakin ta shiga yi tana gyaɗa kai tana sauke numfashi. Can kuma ta sake dawowa gabansa a fusace ta ce “Kai wlh ma kayi kaɗan kazo gabana kana faɗamin zaka ƙara aure. Wlh Farooq ka gama samun farin ciki a gidan nan, sai na tayar maka da hankalin da baka taɓa tsammani ni, I'll make u regret what you have said now” Daga haka tayi hanyar fita daga ɗakin, sai kuma ta dawo, dube dube ta shiga yi amma bata samu komai ba, idanunta ya kai kan system ɗinsa dake ajiye kan kujera. Wawurarta tayi ta buga da ƙasa tana wari irin huci, tashi tsaye Farooq ya yi yana bin ta da wani irin kallo. Ganin ta nufi hanyar kitchen ya sanya ya bita da sauri kafin ta shiga ya sha gabanta. “Ka matsa min hanya na shige ko kuma nayi maka abin da ba zaka taɓa mantawa dani ba” girgiza kai Farooq ya yi ya jawota jikinsa yana faɗin “Nimrah are you okay?” Ture shi tayi tana masa wani irin kallo idanunta har rufewa yake ta ce“are you asking me? To ban sani ba! Nace ban sani ba Farooq! Kuma na rantse sai na zame maka masifar da bazaka iya da ita ba, sai na zame maka duhun da zaka gagara gano haske. Sai na balbala maka wutar masifa acikin gidan nan. Kuma zaka gani” ta ƙare maganar tana nuna shi da yatsa, kafin ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata tashi zama. Furzar da numfashi Farooq ya yi dan koda wasa bai yi tunanin haka daga gareta. Me hakan ke nufi? Kenan tana sonsa? Ya girgiza kansa lokaci guda a fili kuma ya ce “Impossible” Nimrah na fita ɗakinta ta shiga, car key kawai ta ɗauka ta juya tayi waje. A corridor suka kusa cin karo, ta zabga masa wata uwar harara sannan tayi hanyar fita daga parlon. Da idanu kawai ya bita ganin ko mayafi bata ɗauka ba, Allah ne kaɗai yasan inda ta nufa yanzu. Abacha road, Mararaba. 12:24pm Tsaye take a parlon tana sanye da wata rigar atampa ɗinkin doguwar riga, ta ɗora veil wanda ya yi matching da atampar a kafaɗarta. Ƙarasowa wajen Fatiha tayi tana kallonta “I'm gonna to miss you sis” rungumeta Nayla ta yi tana faɗin “Same to me. Yaushe zaki zo Abuja?” waro idanu Fatiha tayi ta ce“Gidanku securities sun yi yawa, duk inda ka gilma sai kaga soja” harararta Nayla ta yi tana murmushi ta ce“To ai babu abin da zasu maki, Ni dai ki saka rana ki zo sai kiyi mana ko 2weeks ne” taɓe baki Fatiha tayi ta ce“Naji, amma sai dai idan zaki zauna anan kema kiyi 2weeks ɗin” Ta langwaɓar da kai tana faɗin “Yaya ne ba zai barni ba, beside ma inada lecture yau kin ga nayi missing” jinjina kai Fatiha tayi daidai nan suka sakko daga upstairs ɗin. Sanye yake wasu ƙananun kaya, t-shirt fara sai trouser blue colour, ya yi kyau abinsa. Mami na murmushi ta ce“Fatan dai kaji abin da nafaɗa maka?” jinjina kai Zayyad ya yi ya ce“Naji Mami, kuma in sha Allah zan yi. Sai mun sake zuwa” taɓe baki Mami tayi tana faɗin “Till next year kenan” girgiza kai ya yi yana murmushi ya ce“A'a Mami, in sha Allah zuwa next week ma zaki iya ganina” “Allah yasa” ta ce tana maida idanunta kan Nayla. “Auta sai yaushe kuma?” Nayla da idanunta ya fara kawo kwalla ta tawo da sauri ta shige jikin Mami tana sakin kuka, shafa kanta tayi tana cewa“Ya isa, zan zo da kaina har Abuja na ɗaukoki, daina kukan” ta ƙarashe maganar tana goge mata hawayen. Zayyad taɓe baki ya yi ya ce“Idan taɓarar zaki cigaba dayi zan kama gabana” tura baki tayi tana sakin hannun Mami ta ce“Zan yi missing naki Mamina” jan kumatunta tayi ta ce“Nima haka Auta” daga haka ta kalli Zayyad ta ce“Yaya mu je to” gaba ya yi Ahmad yabi bayansa, ta riƙo hannun Fatiha wadda taja gefe tana hawaye ta ce“Muje ki rakani sis” daga haka suka yi hanyar fita daga parlon. Kuka sosai Fatiha tayi ganin da gaske tafiya Nayla zata yi, kai kace ta shekara ne a gidan, Itama Naylan sai faman koke-koken take. Tsaki Zayyad ya yi ya shiga motarsa ba tare da ya cewa kowa komai ba suka ga ya tashi motar, da wani irin Speed ya bar gidan dan daman mai gadi ya daɗe da buɗe ƙofar. A tare duk suka kalli inda ya bari, Ahmad daya san hali ya yi murmushi ya ce“Yayi tafiyarsa kin san baya jira” goge hawayen Nayla tayi tana kallon Mami ta ce“To yanzu wane zai kai ni gida Mami?” Fatiha ta ce da sauri“Sai ki sake kwana abin ki, idan ya so ranar Saturday sai Yaya Ahmad ya tafi dake” shiru Nayla tayi, tanason ta sake kwana amma kuma tana gudun faɗan Daddy, domin idan har ya ji bata je school ba for the whole week sai ranta ya ɓaci” langwaɓar da kai tayi Mami ta ce“A'a ki bari ranar Friday banida aiki dayawa a office idan nadawo sai na kai ki da kaina” Gyaɗa kai Nayla tayi, Fatiha ta ja hannunta tana faɗin “Muje ciki” . Da idanu kawai Mami ta bisu tana murmushi, ta kalli Ahmad ta ce“Wai ina Al-ameen tun safe daya fita ban ganshi ba” “Maybe ya tsaya wani wajen, amma bai dawo ba” Girgiza kai ta yi ta ce“Allah ya shirya” Ameen Ahmad ya ce sannan ya yi hanyar entrance ɗin gidan. Tafiya yake yana tsaki shi kaɗai, gabaɗaya traffic ɗin Mararaba ɓata masa rai yake. Ganin babu alamar sauƙin abun ya sanya ya ɗauki hanyar orange market kawai ya bi ta cikin kasuwa. Tafiya mintuna biyar ya yi cikin kasuwar nan ma ya tarar da wani traffic ɗin, Dukan sitiyarin motar ya yi yana faɗin “Oh god!” Jingina ya yi da kujerar motar yana kallon yanda titin yake a haɗe. Gajiya ya yi da zama a motar ya zaro kwalin cigarette ya zari guda ɗaya. Ya kunna da lighter ya fara busar da hayaƙi, nan da nan motar ta cika da hayaƙin tabar. Zuge glass ɗin motar ya yi ta inda hayaƙin zai samu damar fita, kamar an ce ya ɗago suka yi ido biyu da ita, tana zaune kan benci ta zuba uban tagumi, sake kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da zuƙar tabar hannunsa. Salma kuwa girgiza kai tayi, aranta tana tunanin wannan wane irin mutum ne. Sai da ya shanye tsinke biyu sannan ya bari haka, ya feshe motar da air freshener nan da nan ta ɗauke ƙamshi kamar ba ita ce wadda ke warin taba ba. Mouth listener ya ɗauka ya feshe bakinsa ƙamshi mai daɗe ya game ko'ina. Ganin kamar ba zai samu tafiya ba har wajen ƙarfe 1 na rana ya sanya ya buɗe motar ya fito. Cikin tafiyarsa ta izza ya ƙarasa gabanta hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa, kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce “Ina zan iya samun eatery nan?” Ɗago dara daran idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ɗauke idanun ta ce“Nima ban sani ba, babu ma” Kallonta kawai Zayyad ya yi can kuma ya ce“Duk cikin kasuwar nan babu inda zan iya samun abinci mai tsafta?” “Ni ban sani ba ko akwai ko kuma babu, ga masu abinci can ni su nasani” ta ƙare maganar tana kallonsa. Kallon inda ta nuna masa ya yi sai kuma ya girgiza kansa yana taɓe baki ya ce“Bazan iya cin wannan abincin ba” kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta ce“To sai ka haƙura” daga haka ta ɗauke idanunta daga kansa ta maida hankalinta wajen titi. Ganin yanda tayi masa ya sanya abun ya so bashi haushi a ɗan fusace ya ce“Amsa kike bani wannan ko kuma rashin kunya kike yimin?” da mamaki Salma ta sake kallon shi, me tayi masa? Ta tambayi kanta. Ganin bata bashi amsa ba ya sake ƙular dashi ya ce “Heyyy Yar tallah, har ni zan dinga miki magana kina ɗaukemin kai?” Salma da ranta ya fara ɓaci ta kalleshi ta ce“Eh naji ni yar tallah ce, amma ba wadda batasan darajar kanta ba take shaye-shaye ba” ta ƙare maganar tana galla masa harara. Baki buɗe Zayyad ke Kallonta ganin yanda yar ƙaramar yarinya ke gasa masa magana. Ya ce“Ke ni kike faɗawa wannan maganar?” Salma ta ce“Nafaɗa maka ɗin, kai wane?” ta ƙare maganar tana tashi tsaye, ta riƙe ƙugunta tana kallonsa. Zayyad da ya ji kamar ya maketa ya sake cewa“Wato na fuskanci baki da tarbiyya, iyayenki basu nuna miki yanda ake girmama na gaba ba ko?” da hannunta ta nuna shi tana faɗin “Kar ka kuskura ka sake sako iyayena babu abin da ya haɗaka dasu, da ni kake maganarka ka tsaya anan idan ba haka ba...” “Me zaki yi?” kafin tayi magana mai kantin dake wajen ya kalleta ya ce“Haba Salma wannan ba halinki bane, ana miki kallon mutuniyar kirki?” a sanyaye ta ce“Baba kawai zuwa ya yi yana zagin iyayena, to me nayi masa?” Kallon Zayyad ya yi ganin yanda ya wani haɗe rai, mutumin ya ce“Haba Alhaji, daga ganinka baka yi kama da wanda zaka tsaya kana sa insa da yarinya irin wannan ba, kayi haƙuri dan Allah” Jinjina kai Zayyad ya yi yana ɗan murmushi ya kalleta ya ce“Okay, idan kina da rabon wahala watarana zamu sake haɗuwa. A sannan zan nuna miki ko wanene ni” daga haka ya juya ya bar wajen yana tafiya a zafafe. Da idanu kawai suka bi shi har ya shige mota, Mai kantin ya girgiza kansa yana kallonta ya ce“Kiyi a hankali Salma, irin waɗannan mazan haɗari gare su. Sunada ɗaurin gindi a ko'ina” hawayen daya zubo kan fuskarta ta goge tana cewa“In sha Allah Baba, ni daman tunda naganshi naji tsoro wlh” girgiza kai ya yi ya koma shagonsa yana cewa “Allah dai ya kyauta” Salma ta koma ta zauna ta sake zuba tagumi. **** Zaune suke kan royal sofa ɗin dake zagaye da ƙaton parlon, Daddy ne da kuma wani abokinsa General Kabeer daya zo gidan suna magana, turo ƙofar parlon aka yi suka ɗaga kai a tare suka kalleshi. Da sauri ya tawo yana zuwa ya rungume Daddy yana murmushi ya ce“Sai yau ka dawo?” Girgiza kai Daddy ya yi yana shafa kansa ya ce“Tun jiya nadawo Zayyad, an cemin kun je Mararaba, banason na takura maka shiyasa ban kiraka ba” janye jikinsa Zayyad ya yi yana cewa“Okay, I see. Yanzu nadawo nima lemme take shower” Sai a sannan ya kalli abokin Baban nasa yana murmushi ya ce“Good afternoon sir” murmushin shima ya yi ya ce“Afternoon dear, Ya kake?” “Alhamdulillah” Zayyad said, jinjina kai ya yi ya ce“Masha Allah, Allah ya yi albarka” Ameen kawai ya ce sannan ya juya ya fita daga parlon. Numfashi Daddy ya sauke sai kuma ya kalli General ya ce“As a said before” “Zayyad ne ya girma haka?” Jinjina kai Daddy ya yi yana murmushi ya ce“Yeh, shine, kaga ya girma sosai ko?” gyaɗa kai General ya yi ya ce“Gaskiya dai, ya kamata ace kun haɗa shi da mata ya yi aure” shiru Daddy ya yi can kuma ya ce“I think so general, but kasan halin yara, i didn't know weather he prepare or not” girgiza kai General ya yi yana cewa“Ya kamata a masa, idan ma bai shirya ba sai yanzu ya shirya. Idan babu damuwa Daughter ta dawo daga USA last week sai ya je ya ganta, idan sun daidaita sai a yi auren a shige gurin” Murmushi fal fuskar Daddy ya ce“Wow,Masha Allah, aikuwa in sha Allah anjima zan yi masa magana, kuma zai je ya ganta” Jinjina kai General ya yi ya ce“Tom Allah ya bada iko”. Zayyad na fita ɗakin Mommah ya shiga, bai ganta ba sai ƙarar plate daya jiyo a kitchen hakan yasa ya ƙarasa ciki, tura ƙofar ya yi ta juyo tana kallonsa. “Zayyad kun dawo?” Jingina ya yi da jikin bangon kitchen ɗin ya gyaɗa mata kai kafin ya ce“Eh Mommah, nadawo” shiru tai can kuma ta ce“Ina Nayla?” “Tana can” ya ce a takaice, da mamaki Mommah ta ce“Bangane tana can ba, mun yi waya da Adda da safe tace min zaku tawo tare anjima, to me ya hanata dawowa?” Zayyad ya ce“Bataso ta tawo ne, tana ɓatamin lokaci nd kinsan Momma bazan iya jiranta ba, so shiyasa nayi tawowa ta, idan taga dama a kawota” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Tana son ubanta ya ɗagamin hankali ne ya sanya bata tawo ba ko? Bari zan kira Yayar”bai ce mata komai ba ya juya zai bar kitchen ɗin “Zayyad” Juyowa ya yi yana kallonta ya ce“Na'am” “Zamu yi magana da kai anjima, akwai abin da nakeson mu tattauna” shiru ya yi sai kuma ya ce“Okay Allah ya kaimu” daga haka ya fice daga kitchen ɗin. Ajiyar zuciya Mommah ta sauke aranta tana tunanin ko zai yarda??. ****Ko gama parking ɗin motar bata yi ba, ta buɗe ta fito tana tafe tana kuka, a babban parlon ta samu Daddy wanda ya dawo daga raka abokinsa, sai Mommah da Mommy dake zaune kan kujera, Mufeeda na tsaye jikin stairs tana danna wayarta. Kai tsaye wajen Daddy ta nufa tana sake fashewa da wani sabon kukan, da mamaki yake kallonta kafin ya ce“Ke lafiyarki? Me aka yi miki” durƙushewa tayi a wajen madadin ta bashi amsa ta cigaba da rera kukanta. Daddy da bayason ya yi magana ayi masa shiru ya ce a tsawace “Baki ji ina miki magana ne?” cikin shassheƙar kuka ta ce“Daddy nagaji, nagaji da zama gidan Farooq, I'm so tired wlh. Daddy Aure zai ƙara, Daddy Aure zai yi fa” da mamaki ya kalleta sai kuma ya ce“Shi Farooq ɗin ne ya ce miki zai ƙara aure?” tana rage sautin kukanta ta ce“Eh Daddy, yanzu abin da ya gama cemin kenan, kuma ya ce ban isa na hana shi ba, nace zan faɗa maka ya ce wai ka wanene, ko nafaɗa maka sai ya aikata har cewa ya yi ko B. Musa ne zai dawo duniya ya hana shi ba zai fasa ba kuma...” Dakatar da ita Daddy ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, ya fara zagaye cikin parlon, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, ya jinjina kansa. Aƙalla ya ɗauki ya kusa 5mins kafin ya ce “Then definitely I'll show him my true colour, zai gane wanene Idris B. Musa, ba shi kaɗai ba har ubanshi ya saka a matsala!” daga haka ya fice daga parlon da sauri kamar zai tashi sama. Nimrah goge hawayenta ta shiga yi dan ko babu komai tasan Daddy ba zai bar shi ya yi auren ba. Mommah ta kalleta ta ce“Nimrah! Nimrah!” Kallon Mommah ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Ki cigaba, wato saboda kinsan halin mahaifinku ya sanya ki ka zo da wannan maganar ko? Kina tunanin idan aurenki ya mutu wani ya yi asara?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Wlh Mommah ba ƙarya nake ba, haka ya ce min, kuma har zagina ya yi. Mommy dan Allah ƙarya nayi?” ɗan murmushi Mommy ta yi ta ce“How could i know? Amma dai nasan halin Farooq” Goge hawayenta tayi ta tashi tana cewa“Wlh ba sharri nayi masa ba” daga haka tayi hanyar upstairs abinta. Mufeeda dake tsaye ta bita da kallo, sai da taga ta bar wajen, sannan ta dawo parlon tana kallon Mommah ta ce“Wlh Mommah sharri take masa, Farooq ba zai zagi Daddy ba” girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Nasani Mufeeda, Nimrah bata jin magana, duk abubuwan da nake faɗa mata basa shiga kunnenta”. Numfasawa Mommy ta yi ta ce“Rannan fa da tazo sai da muka yi magana, amma shima Farooq ɗin da laifinsa” “Koma da laifinsa ai itama da laifinta, ya za'a yi kina zaune gidan miji baki masa biyayya? Haka taga mu muna yi? Da haka muke ai da ma kai labari? Amma zata ci ubanta wlh” Daga haka Mommah ta tashi ta haye sama. Da idanu kawai Mommy ta bita sai kuma ta ce“Allah ya kyauta”. **** Tafiya take tana jan ƙafarta dan ba ƙaramin gajiya tayi ba, lokacin kusan ƙarfe shidda na yamma ne, hayaniya tayi yawa a hanya, yara sai kai komo suke wasu da uniform na islamiyya wasu kuma da kayan gida. A haka har ta ƙaraso ƙofar gidansu, burki taja ta tsaya tana binsa da kallo, fuskarta ɗauke da mabayyanin mamaki. Tasowa ya yi daga kan dakalin da yake ya ƙaraso gabanta yana murmushi. “Hi dear” Ta tsinkayi muryarsa. Shiru ta masa tana binsa da kallo har sannan, shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce“Sorry baki sanni ba ko? I'm Al-ameen Jameel Giwa, I'm a physician doctor, ina aiki a clinic ɗin Mom ɗina, Dad ɗinmu ya rasu at least 10yrs yanzun, Ina zaune a Abacha road, Shikenan” yanda ya ƙare maganar yana watsa hannu ya sanyata ɗan murmushi, Kallonta Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“And baki faɗamin ko ke wace ba, ko sunanki ma bansani ba” Salma shiru tayi masa can kuma ta ce“I'm Salma Abubakar, ina zaune da Abbana da Ummana, Ammina ta rasu tun ina ƙarama” girgiza kansa ya yi cike da tausayi ya ce“Allah sarki, Abun tausayi, Allah ya jiƙanta” Salma da idanunta suka fara kawo ruwa ta ce“Ameen Nagode” agogon hannunsa ya kalla sai kuma ya ce“Magrib ya kusa Salma, kuma naga kamar daga wani wajen ki ke, tunda naga gidanku shikenan bye” shiru tayi sai kuma ta kama hanyar gida, juyowa ta yi taga har sannan yana tsaye yana kallonta “Sake zuwa zaka yi?” Ta tambaye shi. Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi, ta juya ta shige gida abin ta. Ajiyar zuciya Al-ameen ya sauke sannan ya fara tafiya toward direction ɗin motarsa yana jin wani irin sanyi a ranshi. Da sallama ta shiga gidansu, ta ƙarasa kan tabarmar da sauri ganin yanda yake ƙoƙarin gyara ƙafartasa.. “Abba...” ta faɗa a raunace. Shafa kanta Malam Habu ya yi hannunsa na rawa, hawayen azaba na zuba daga cikin idanunsa. Magana yake son ya yi amma ya kasa, tashi Salma tayi ta yaye labulen ɗaki tana kiran sunan Umma, sai dai shiru taji da alama ma Ummar bata cikin gidan. Dawowa tayi ta zauna tana kallon ƙafar tasa wadda duk ta kwaɓe sai ruwa take, hawaye na zuba kan fuskarta. Cikin kuka ta riƙe rigarsa tana faɗin “Sannu Abbana, Allah ya baka lafiya Abba, Allah ya rabaka da wannan ciwon, innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, Astagfirullaha wa'a tubu ilayk” Tana nan zaune tana wannan kukan Umma Rahmatu tayi sallama ta shigo gidan, da mamaki take Kallonta ta ajiye ledar hannunta tana rataye mayafinta kan igiya ta ce“Yau kuma wani sabon kinibibin kika samu na koke koke? Ba zaki bar shi ya ji da abin da yake damunsa ba?” Ɗago kanta tayi tana kallonta ta ce“Umma mu kai Abba asibiti ƙafarsa ruwa yake Umma, ina ga mai gyaran nan bai gyara ya yi ba, zo kiga Umma” “Iko sai Allah, ke a rayuwarki baki son kiga mun zauna lafiya? Wato ɗan kuɗaɗen da muke samu yanzu shine sai kin san yanda ki ka yi aka kashewa ubanki su ko? To wlh kin ji kaɗan, naji wani iskancin banza. Duk wadanda suke karyewa yake gyara basu ce bai iya ba sai ke gwana” Girgiza kai Salma tayi ta ce“A'a Umma wlh wannan daga gani da zafi, kuma ya ɗaure ciwon ya kamata a kwance aga yanda yake” a fusace Umma ta ce“Ke wace irin shashasha ce? Kin taɓa ganin inda aka kwance karaya a gida? To ba'a yi kai tsaye sai dai a kira mai gyaran ya kwance” tashi tsaye Salma dan daman da hijabinta a jikinta, ta ce“To Umma bari naje na kira shi” Taka mata tsawa Umma ta yi ta ce“Kaga yarinya? Dawo ki kunna min wuta na ɗora abinci ni, ki barwa safiya a kira mai gyaran” Jiki a sanyaye Salma ta tsaya, ta saci kallon Abbanta taga idanunsa a lumshe sai kuma ta ɗauki ledar gawayin tayi hanyar inda suke girki. ****Da gudu ta fito daga ɗakin, tana ihu ta buɗe dakin da take kwance tana kiran “Salma! Salma! Ummusalma, fito kiga, innalil lahi wa ina ilayhi raji'un” Salma da batada nauyin bacci ta buɗe idanunta tana kallon Ummarta ta ce a kiɗime“Umma meya faru ki ke kirani da tsohon daren nan?” Kamo hannunta Umma tayi suka fito daga ɗakin tana kuka ta ce“Muje kiga Salma, min shiga uku” ban da faduwa babu inda ƙirji Salma ke yi, har suka shiga ɗakin. Ganin Abbanta a zaune yasa ta sauke wata ɓoyyayiyar ajiyar zuciya, Umma ta ƙarasa inda yake tana kallonsa ta ce“Salama kalli, Ƙafar Mahaifinki tsuntsa take Salama,Wlh tsutsotsine a ƙafarsa, inaga ta ruɓe Salama!” # HCD # Light within the darkness # Nanameera. 08106608363 *HASKEN CIKIN DUHU💋* Chapter 08: Strings Attached Nanameera, YOTA/023. Dafe ƙirji Salma tayi ta nufi ɗakin Baban nata da gudu, zaune ta sameshi, idanunsa a rufe sai gumi ne ke keto masa duk da ba lokacin zafi bane, durƙushewa tayi akan gwiwoyinta hawaye na zuba daga kan fuskanta, da gaske tsutsotsine a ƙafar Babanta, ɗora hannunta tayi aka ta fasa wani razanannen ihu, Umma dake tsaye kansu ta ƙaraso tana kuka itama ta ce“Mun shiga uku Salma, meya sami Babanki?” tashi Salma tayi tana cewa“Umma bari na kirawo mai gyara ya duba masa” daga haka tayi hanyar waje, da gudu Umma ta bita ta riƙo hannunta tana cewa“Ina zaki je a daren nan? Sai dai koma menene mu bar wa safiya ai” fashewa da kuka Salma tayi tana girgiza kanta, Umma bata ce komai ba ta kama hannunta suka koma ɗakin, agefen mahaifinta ta zauna tana gursheƙan kuka, Malam Habu wanda yake jin wata irin azaba na ratsa shi ya shafa kanta alamar rarrashi, ɗago kanta tayi ta kalleshi taga yanda idanunsa suka yi wani irin jaa sun kuma kumbura, cikin kuka ta ce“Abba kayi haƙuri, laifina ne, Ban samo kuɗi da wuri mun kai ka asibiti ba, Kayi haƙuri Abba...” Ta ƙare maganar tana riƙe hannunsa, girgiza kai kawai Malam Habu ya yi dan ya garara furta koda kalma ɗaya, Umma ta zuba uban tagumi tana tunanin abin da zasu yi gobe. Suna nan zaune dashi har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba, Salma ta tashi tana kallon Ummar ta ce“Yanzu sun fito sallahr asuba Umma, bari naje na tawo dashi” Bata jira cewar Ummar ba kuma tayi waje da sauri. Buɗe ƙofar gidan nasu tayi tafara tafiya, Babu wasu mutane a hanya sai dai ɗaiɗaiku masu zuwa masallaci, a haka har ta ƙarasa ƙofar gidan Malam Audi mai gyaran. Tsayawa tayi tana ɗan tunani sai kuma ta kwankwasa ƙofar, sai bayan mintuna biyar sannan aka zo aka buɗe, matar ta kalleta da mamaki, Salma ta ɗan sunkuya ta ce“Ina kwana” “Lafiya klao wacece?” a ɗan rabe Salma ta ce“U... Daman Abbana ne wanda Babansu Lawan ya yi masa gyaran karaya ƙafar take ciwo, to shine nazo na kira shi yaje ya gani, ƙafar Tsutsa take” shiru Matar tayi tana kallon Salma can kuma ta ce“Allah Sarki Allah ya bashi lafiya, Malam yaje Masallacin gangare, sai dai ko ki je can ki neme shi” Toh kawai Salma ta ce sannan ta juya ta bar ƙofar gidan tana tafiya da sauri da sauri. Da sauri ta tashi daga kan dakalin data zauna ganin an fara fitowa daga masallacin, hangoshi ta yi yana tawowa ta yi saurin ƙarasawa gabansa tana kallonsa. Da mamaki yake kallonta kafin ya ce“Lafiya Ummusalma?” Salma ta ce“daman Abbana ne bashi da lafiya, ƙafarsa tana ciwo har tsutsa take” ta ƙare maganar tana hawaye, cikin tashin hankali ya ce“Subhanallahi, muje nagani” daga haka ya yi gaba tana bin sa a baya. Girgiza kai ya yi bayan ya gama kallon ƙafar Abban, ya kalli Salma wadda ke tsugune gefe tana hawaye, sannan ya kalli Umma wadda ke tsaye hannunta riƙe da kofi, jin bai ce komai ya sanya Salma ta ce“Meya samu Abbana?” numfasawa ya yi kafin ya ce“Ɗorin da aka masa ne ya goce kuma ba a lura ba ballantana a sake ɗora shi, yanzu sai dai a kai shi asibiti” ɗora hannu aka Umma ta yi ta shiga girgiza kanta tana cewa“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una, mun shiga uku” tashi Salma ta yi ta riƙe hannunta tana kukan ita ma ta ce“Ki yi haƙuri Umma, Allah zai bashi lafiya, zamu kai shi asibitin” janye hannunta ta yi ta koma bakin ƙofa tana sake rusa ihu, to yanzu ina za su sami wani kuɗin kai shi asibiti??. **** 4:35pm. Murmushi Mami ta yi tana ci gaba da yanka lettuce ɗin gabanta ta ce“To me za ki je yi a Orange market ɗin?” Nayla dake tsaye gefenta tana ɓare maggi ta ce“Lemon nan nakeson na siyo Mami” Mami ta ce“Okay, ki bari ko zuwa gobe idan Allah ya kai mu sai muje tare” murmushi Nayla ta yi ta ce“Yawwa Maminmu, shiyasa nake sonki wlh” girgiza kai kawai Mami ta yi tana murmushi. Turo ƙofar kitchen ɗin ya yi ya shigo yana kallonsu, Nayla ce ta juya ta kalleshi sai kuma ta ce“Masoyi ina zaka je haka?” girgiza kansa ya yi kafin ya ce“Zo ki ji” daga haka ya fice daga kitchen ɗin, ajiye ledar maggin ta yi dan daman ta gama ɓarewa, ta wanke hannunta jikin sink sannan ta fita, Mami ta bi su da idanu. Zaune ta same shi kan sofa yana danna wayarsa, ta zauna gefensa tana murmushi ta ce“What's going up Masoyi?” ajiye wayar ya yi kafin ya ce“unguwa nake son ki rakani” shiru ta yi tana kallonsa kafin ta ce“Ina zamu je?” “Idan ba zaki rakani ba shikenan tashi” langwaɓar da kanta tayi ta ce“kuma sai na ce ba zan raka ka ba masoyi? Lemme take shower” murmushi ya yi ya ce“To agwagwa je ki yi” murmushin itama ta yi sannan ta tashi daga wajen ta nufi hanyar upstairs. Asokoro, Abuja. Tunda Daddy ya fara magana Zayyad ke kallonsa, ganin irin kallon da yake masa ya sanya Daddy cewa “anything wrong Zayyad?” Girgiza kai kawai ya yi yana danna wayarsa ya ce “Nothing Dad, ina jin ka” Gyaɗa kai Daddy ya yi sannan ya ci gaba da fad'in “As i said before, kaga muna da kyakkyawar alaƙa da General Kabeer, kuma na san shi, na san halinsa, bashi da matsala, na tabbata Family nasa ma basu da matsala. Inason ka je ka nemi yarinyar Zayyad, ka gani idan ta yi maka sai a san abin yi, amma idan har ka ga bata maka ba to ba za'a takura maka ba, ka daure ka je ka ji son” numfasawa ya yi kafin ya ce“Don't worry Dad, I'll.” murmushi Daddy ya yi ya ce“that's why u're always been my favorite” murmushin shima ya yi ya ce“Tanc you Daddy” daga haka ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin barin parlon ya ce“In sha Allah gobe zan je kamar yanda ka buƙata” jinjina kai Daddy ya yi ya ce“Allah ya kai mu, when u're free inason ka yi magana da wannan yaron Farooq, cause ba zan iya tsayawa ina magana dashi ba” okay kawai Zayyad ya ce sannan ya fice daga parlon. Kai tsaye apartment ɗin Mommah ya nufa, ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama wadda ba lallai bane mutanen dake cikin parlon su ji. Zaune ya hangeta kan kujera tana danna wayarta hankali kwance, ya ƙarasa ciki yana kallonta kafin ya ce “Kee!” A ɗan firgice ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, ya zabga mata harara kafin ya ce“Karki kuskura ki kai dare a cikin gidan nan, ki tattara duk abin da ki ka san kin zo dashi ki koma gidanki or else...” ya ƙare maganar yana mata wani irin kallo, bai kuma saurari abin da zata ce ba ya yi hanyar bedroom ɗin Mommah. Da kallo Nimrah ta bi shi kafin ta fashe da kuka, akan me zai ce mata ta koma? Tashi tayi ta ɗauki wayarta ta fice daga parlon ta nufi ƙasa wajen Mommy. Kamar zai yi kuka ya ce“Yanzu kuma abin da za ku dinga yimin kenan? Dad ya ce naje naga yar gidan general, kuma yanzu Mommah ki ce wai mu daidaita da Fatiha? Wannan yar ƙaramar yarinyar, sa'ar Nayla ce fa Mommah” da mamaki Mommah ta kalleshi sai kuma ta ce“When ku ka yi magana da Dad ɗin ka?” “Yanzun fa” Taɓe baki ta yi ta ce“anyway, dan ka je ganin wadda ya ce hakan ba zai hana nima ka ji maganata ba, ni bana son auren ya'yan abokan nan a zo ana faɗa ce faɗa ce irin na Nimra, Amma nasan Fatiha sosai, yar yayata ce fa” “But Mommah...” Katse shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu tana ci gaba da jera kayanta da aka kawo daga wajen guga a press ta ce“Ni fa nagama magana, sai dai idan kana son nuna min iyakata ne” Zayyad ya bita da kallo kawai ganin yanda ta ɗaure fuska kamar ba ita ba, duk abin sa baya son ɓatawa Mommah rai hakan ya sa ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce“Shikenan Mommah, I'll” ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Allah yasa” “But Mommah smile man” ya ƙare maganar yana ɗan murmushi. Kallonsa ta yi tana harararsa ta ce“As if kana son ganin ina murmushin” waro idanu ya yi ya ce“Mommah idan ban so murmushin ki ba nawa zan so?” taɓe baki ta yi ta ce“Ni tafi ka bani guri ban son daɗin baki” ya sha kansa ya yi yana cewa“Amma Mommah yunwa nake ji, yau baki bani abinci ba, gaba ɗaya kin daina son ɗan ki” kallonsa ta yi ganin yanda ya marairaice fuska ya sanya ta yi murmushi ta ce“Shikenan, mu je parlon na baka” juyawa ya yi ya fita ta ƙarasa rufe press ɗin sannan ta fito. Bai ga Nimrah a parlon ba, ya kalli Mommah wadda ta yi hanyar kitchen ya ce“Kar na dawo na tadda yarinyar nan a gidan nan Mommah, wallahi zan ɓata mata rai” Mommah ta ce“Zayyad ka mata magana da kanka, Nimrah bata ji, narasa in da take koyan halayen nan, ko me za'a faɗa mata ba zata yi ba” kwafa ya yi ya ce“Ina zuwa” daga haka ya nufi hanyar fita daga parlon “Abincin fa?” “Idan na dawo zan ci Mommah” **** Ajiyar zuciya Farooq ya sauke yana kallon Zayyad ya ce“Ni ban san yanda zan faɗa maka ba wlh, i can't explain it, Nimrah bata son zama dani Zayyad, Ni ban isa na faɗa mata magana ta ji ba, idan ban yi sa'a ba sai ta haɗa min da masifa, she's always shouting, ban san yaushe ta zama haka ba. Saboda na kawo ƙarshen waɗannan matsalolin nace zan sake aure, amma idan kaga irin abin da Nimra ta yimin sai ta baka mamaki, can u imagine har system ɗina ta fasa min? Na tabbata da ta samu dama sai ta iya dukana, sannan ta sanya ƙafa ta fito without my consent, daman wannan abu ne wanda ta saba yi, ba zan san zata fita ba ba zan san dawowarta ba, ya za'a yi rayuwa ta ci gaba da tafiya a haka?” Zayyad dake zaune kusa da shi idanunsa maƙale cikin wasu shade glasses ya jin jina kansa ya ce“Daman shiyasa na neme ka, inason na san inda matsalar take. Karka damu, an jima Nimrah zata dawo nd duk abin da ta sake yi maka just tell me. And one thing kar ka fasa ƙara aure, ka samu wata ka aura” murmushin jin daɗi Farooq ya yi ya ce“Tom na gode sosai Allah ya ƙara girma” Zayyad ya miƙe yana ɗaukan car key ɗinsa ya ce“Shikenan see you later” Farooq ya bashi hannu suka gaisa kafin ya bar transcorp ɗin. Tun da ya fito yake kallonta har ya ƙaraso inda ya yi parking Lexus ɗinsa, sanye take da wata riga wadda ta tsaya iya gwuiwarta gashin kanta a buɗe ta gyara shi, fuskarta ta ci ka da kwalliya, kwata kwata bata gansa ba, dan hankalinta yana wajen ƙawayenta wadanda suma suka ci uwar kwalliya, taɓe baki Zayyad ya yi ya shige motarsa ba tare da ya kulata ba, ya daɗe a motar kafin ya yi mata key ya bar wajen. Ana kiraye-kirayen sallar magriba ya shigo gidan, zaune ya same su duk a parlon suna hira, kallo ɗaya ya yi musu ya mai da hankalinsa kan Nimra wadda tana ganinsa ta sake riƙe Mommy, a fusace ya ce“ke zo nan” kallon Mommy ta yi sai kuma ta kalli Mommah ganin ba ma ita take kallo ba. Tashi tayi ta ƙarasa in da yake tsaye, Zayyad ya ƙare mata kallo kafin ya ce “Wato ke baki da hankali ko? Ke mahaukaciya ko? Yaushe ki ka koyi irin wannan halin na dabbobi? Yaushe ki ka lalace har haka Nimrah? Who's behind all of this? Who changed you? Da suwa ki ke mu'amala? Me ki ka ɗauki aure! Tell me!” Tuni hawaye suka fara wanke mata fuska cikin kuka ta ce“Yaya cewa fa yake zai ƙara aure, na rantse da Allah in dai ina numfashi Farooq bai isa ya auri wata ba idan ba haka ba wallahi tallahi sai na...” Ta ji saukar maruka har biyu a both checks nata, suman tsaye Nimrah ta yi, tun da uwarta ta haifeta ba'a taɓa mata irin wannan dukan ba, infact ma bata san mene ne duka ba. Da dafe kuncinta tana sauke ajiyar zuciya dan kukan ma ya gagareta, shiru Parlon ya ɗauka ganin yanda idanun Zayyad suka kaɗa, yana dadewa bai yi faɗa irin haka ba, ana dadewa bai shiga sabgar shirmen ya'yan gidan ba. Ya gyara tsaiwarsa yana ci gaba da kallonta ya ce “And this is the first nd the last warning da zan yi miki, ki koma gidan mijinki kuma ki zauna lafiya, tun da ba wani ya ce ki yarda ki aure shin ba, ba dole aka miki ba! Duk ranar dana sake jin kin dawo gidan nan saboda wai wani abun ya haɗaku wallahi sai kin gane baki da wayo, sai kin san wane Zayyad! Shashasha kawai mara hankali” Ya juya ya fice daga parlon kamar zai tashi sama. Sai da ta ga ya fita sannan ta zube a ƙasa ta fasa ihu tana sake shafa check ɗinta ko ya fashe. Mommy ce ta taso ta zo inda take ta kamo hannunta cikin rarrashi ta ce“Ya isa haka Nimra, tashi” Sake fashewa tayi da kukan ta rungume Mommy tana cewa “Mommy ba'a sona a gidan nan, ki kalla fa Yaya marina ya yi a kan Farooq, he slapped mommy, kuma ya ce sai na koma gidan Farooq, wayyo Allahna, ni wlh gara na mutu” Mommah ce ta taso tana kallonta ta ce“Tashi ki shige ki shirya! Kar ki bari na sake miki magana, idan kin so ki bari ya dawo ya tarar dake a gidan nan” daga haka ya yi hanyar upstairs kamar zata tashi sama, da idanu Mommy ta bita sai kuma ta kama hannun Nimra ta ce“tashi mu je kin ji” Nimra ta mike tsaye har sannan hannayenta na kan fuskarta tana kuka. Mararaba, Nassarawa. Tafiya take a hankali tana ɗan shassheƙar kuka, idanunta har sun gaji da kumburi saboda irin kukan da ta yi, maganganun likitan ne suka shiga dawo mata daya bayan ɗaya “Tabbas sai dai a yanke ƙafarsa, domin gaba ɗaya ta riga da ta ruɓe, wannan shine dalilin daya sanye ake cewa a kawo mutum asibiti idan karaya ta same shi. Dole yanzu sai an yi masa aiki, sannan domin yin wannan aikin ana buƙatar kuɗi kimanin Naira dubu ɗari huɗu, zaku je ku biya zuwa gobe in sha Allah za'a yi masa aikin, idan ba haka ba gaba ɗaya ƙafar zata ruɓe ne” Salma ta ja dogon numfashi, bata san sanda ta zauna gefen titin ba ta kifa kanta tana sake rushewa da kuka, a ina zasu sami waɗannan kuɗaɗe? Ko dubu hamshi basu da ita ballantana wadannan kudaden da tun da take a rayuwarta bata taɓa ganinsu ba. Ta ina zata fara? Ya za'a yi ta bar Abbanta a haka?. Waɗannan tunanin sune suka sanya ta kasa daina kuka tun safe take yawo daga nan taje nan, babu inda bata zaga ya ba daga Orange market zuwa cikin Kabayi ba tare da tasan inda ta nufa ba, yunwa, ƙishiwa, gajiya duk sun haɗe mata, she wish a ce ita ce wadda ƙafarta ta samu matsala ba Abbanta ba, ina ma ranar bai fita ba, ina ma ranar bata zo ba, sai dai ƙaddara ta riga fata, tana nan zaune har wajejen ƙarfe 11 na dare, sahun mutane ya fara ɗaukewa, daman tun mutanen kasuwar Orange market kowa ya kama gabansa, kasa ci-gaba da zaman tayi hakan yasa ta kwanta a wajen tana cure jikinta waje guda, duk sanyi da kumar raɓar damunar data gama sauka a wajen. Around 11:43 na daren wata mota ta yi parking daidai gabanta, hasken da taji an dallareta dashi ya sanya ta runtse idanunta ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, mutumin dake cikin motar ya ƙura mata idanu, a ransa ya ce “what a beautiful girl” a fili kuma ya yi murmushi ya kashe motar ya sakko ƙasa. Karasowa gabanta ya yi ya tsuguna dai dai tsayinta, numfashin mutum da taji kusa da ita sosai ya sanya ta buɗe idanun, zabura ta yi sai kuma ta yi baya tana girgiza kanta, daga gani a tsorace take. Ɗan murmushi mutumin ya yi a ƙalla zai kai shekaru kusan 40 ya ce a nutse “Nutsu kin ji yarinya, ba cutar da ke zan yi ba” Salma kallonsa kawai take, ƙoƙarin tashi take sai dai yunwar da take ji ta hanata yin kwakwaran motsi, ya tashi tsaye har sannan idanunsa akanta ya ce “Me ki ke yi cikin daren nan?” A sanyaye ta ce “Abbana ne yake asibiti shi ne aka ce na je na samo kuɗin da za'a yi masa aiki, shi ne Ummana ta ce na je na samo” ta kare maganar tana shassheƙar kuka, ɗan murmushi ya yi kafin ya ce “Allah sarki, shikenan zo mu je sai na baki kuɗin” shiru Salma ta yi tana kallonsa sai kuma ta girgiza kanta ta ce “A'a ni” Hannunsa ya sanya a aljihu ya zaro wata id card ya ce “I'm Barrister Tareek Mohd, ki yarda dani ba zan cutar dake ba” Salma kallonsa kawai ta yi, a lokacin bata da wata buƙata wadda ta shige ta samo kuɗin da za'a yi wa Abbanta aiki, hakan ya sa ta gyaɗa masa kai a hankali ta ce “Duka zaka bani kuɗin?” Ta yi maganar cike da yarinta, murmushi ya yi ya ce “Har ma na ƙara miki wani kin ji” tashi tayi a hankali ta ƙaraso inda yake tsaye ta ce“To sai ka dawo dani?” nan ma ya gyaɗa mata kai, jin jina kanta ta yi ta ce“To mu je ka bani” ajiyar zuciya ya sauke sai kuma ya buɗe mata back seat yana kallonta ya ce“Zauna” ta sake duban cikin motar kafin ta shiga ta zauna tana kallonsa, rufewa ya yi ya buɗe driver seat ya shiga ya tada motar da wani irin Speed ya bar wajen.. # HCD # Nanameera 08106608363. https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t HASKEN CIKIN DUHU Chapter 09: The unfinished rescue Nanameera, YOTA/023. Tun da ya fito daga ɗakin yake bin su da kallo, he just can't believe abin da idanunsa ke gani, how? Ɗan tsaki ya yi sai kuma ya nufi hanyar upstairs na hotel ɗin ba tare da ya sake bi ta kansu ba. Tsaye Salma ta yi bakin ƙofar ɗakin ta kasa shiga ciki, juyowa ya yi yana kallonta ganin irin kallon da take wa ɗakin ya ce “Shigo mana” Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce “A'a ka barni a nan kawai” Dafe kansa ya yi ganin zata wahalar dashi ya sa ya ce“To ya za'a yi ki tsaya a nan har na baki kuɗi? Ki shigo ko baki yarda dani ba?” shiru ta yi na wasu mintuna kafin ta shigo ɗakin tana tafiya a sanyaye. Gefen gado ya nuna mata da hannu ya ce “Zauna ina zuwa” Kallon wajen ta yi amma bata zauna ba, ya juya ya shige toilet ya barta nan tsaye. Above 10mins kafin ya fito jikinsa sanye da bathrobe, daga gani wanka ya yi. Kallo ɗaya Salma ta yi masa ta ɗauke idanunta, haka kawai ta ji bata son zaman ɗakin, ta juya ta nufi hanyar fita ba tare da ta ce masa komai ba, cikin hanzari ya bi bayanta yana cewa “A'a cutie lafiya? Me aka yi miki?” Girgiza kanta ta yi ta ce “Tafiya zan yi ni” Shiru Tareek ya yi can kuma ya ce “But i promised u ko, nace zan biya miki kuɗin aikin Abbanki” “To ni bana so, ba zan iya ci gaba da zama ina ganinka haka ba, it's totally haram, kai ba muharramina bane, ni tafiya zan yi, kawai ka bani kuɗin” Salma ta ƙare maganar hawaye na kawowa idanunta, daga sama har ƙasa ya kalleta kafin ya ce “Then ki zauna na saka kaya, sai mu je na cire kuɗin a bank na baki, kin ga bani da cash” Tura baki ta yi kafin ta nemi waje nan kan tiles ta zauna tana cewa “Zan jiraka a nan” Kallonta kawai ya yi da alama tana da matuƙar wayo, bai sake cewa komai ba ya ƙarasa wajen dressing mirror ya fara shiryawa, yana gamawa ya sanya singlet da 3-quater ya dawo inda take zaune, tashi tsaye ta yi tana bin sa da kallo kafin ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe fuskarta tana cewa “Ni ka rufe jikinka babu kyau, kuma...” Bata yi aune ba taji ya rungumeta gaba ɗayanta a ƙirjinsa, a matuƙar razane Salma ta buɗe idanu ta fara ƙoƙarin kwace kanta amma ya ƙi sakinta. Duk irin kokawar da ta dinga yi ƙin rabuwa da ita ya yi, kasancewar ba karfinsu ɗaya ba, kuka ta sanya ta sakar masa cizo a gefen hannu, zafi da kiɗimar cizon ya sanya ya saketa yana yarfe hannunsa. Da gudu ta yi waje kamar mahaukaciya. Ta kusa kai wa ƙarshen ɗakunan ta ji an janyota, wani razanannen ihu ta saki ya yi saurin toshe mata baki, ƙoƙarin kwace kanta ta shiga yi amma sam ya ƙi bata dama, sai a sannan ta gane wancan mutumin ba ma riƙeta ya yi ba, dan wannan kwakwaran motsi ta gagara yi, ga ƙamshin turarensa daya gama cikata, da kyar take jan numfashinta. Suna tsaye a wajen Tareek ya ƙaraso wajen yana kallonsu, a fusace ya ce “Kai malam uban me ka ke da yarinyar nan? Ko baka san ni na kawota nan ba?” Bata san sanda ta sake ƙamkameshi ba, tana ɓoye fuskarta a faffaɗan ƙirjinsa, tsananin tsoro ya riga da ya gama cikata. Janyeta Zayyad ya yi daga jikinsa ya juya ya kalli mutumin dake maganar. Kallo ɗaya Tareek ya masa ya juya ya bar wajen dan ya san shi farin sani, duk ba ba lallai bane shi Zayyad ɗin ya gane shi, amma duk wanda ke shiga transcorp ya san Zayyad. Juyowa ya yi yana kallon Salma wadda ta sake riƙe gefen rigarsa har sannan tana shassheƙar kuka, tsaki ya yi ya fizge rigarsa yana harararta. A hankali ta ɗago idanunta wanda suka kumbura ta kalleshi, ɗan ja da baya ta yi dan ta gane fuskarsa, shi ko Zayyad gaba ya yi ya bar ta tsaye a wajen. Kalle kalle Salma ta shiga yi ganin babu wani ɗaki wanda yake a buɗe ya sanya ta bi bayan Zayyad ɗin, a ƙofar room 404 taga ya tsaya, ya saka key ya buɗe ƙofar ya shiga, tana ganin haka itama ta shige da saurin tana sauke ajiyar zuciya. Tsaye ta sameshi tsakiyar luxury room ɗin, ko ina tsaf yake sai sassanyan ƙamshi ne ke tashi wanda ke haɗewa da Ac dake kunne yana bada wani irin amintaccen yanayi. Ɗan ja da baya tayi ganinsa a gabanta dan bata san sanda ya ƙaraso ba, Yana mata wani shegen kallo ya ce “Munafuka, daman daga ganinki na san ke ba ƙaramar yar iska ba ce” Da sauri Salma ta kalleshi, gani ta yi ita yake kallo har sannan ransa a haɗe fuskarsa babu walwala, tura baki ta yi tana ɗauke kanta ta ce “Ni ba yar iska ba ce wallahi, kar ka sake ce min haka” Wani irin shegen kallo Zayyad ya yi mata kafin ya ce “Oh karuwa ce kenan? Tun da har kina iya baro Nassarawa ki biyo namiji Abuja, daman kin fi ƙarfin yar iska” Tuni hawaye suka wanke fuskarta, ta sanya hannunta tana sharewa ta ce “Ni ba karuwa ba ce wallahi, Ni kuma ba yar iska ba ce, ka daina zargina da abin da ban aikata ba, Babu kyau hakan wallahi, kuma Allah sai ya sakamin” A fusace ya ce “Yimin shiru a nan, idan ba karuwa ba me ki ke yi a hotel? Idan ba iyayenki basu baki tarbiyya ba me za ki zo yi a nan? Wane ma ya kawo ki Abujan? Nawa ya biya ki?” Zama dirshan Salma ta yi a ƙasa ta sake rushewa da wani sabon kukan, har da birgima a ƙasa. Da mamaki Zayyad ke Kallonta ganin yanda take ihu tamkar ya yi mata wani abun, sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya ce “Da ban yi miki komai ba shine za ki zauna kina min kuka?” “Ni ba yar iska ba ce wlh, kuma ni ba karuwa ba ce, sai dai idan kai ne ɗan iskan, to mene kai ma ya kawo ka hotel ɗin da daddare!” Ta ƙare maganar ta ci gaba da kukanta, duk yanda ta bawa Zayyad dariya ƙin nunawa ya yi, in a serious tone ya ce “Ai ko ni ɗan iska ne cikakke ma, kuma yanzu zan nuna miki” Daga haka ya ɗagota yana ƙoƙarin cire hijabin dake jikinta, wani irin ihu Salma ta saki, jikinta ya fara rawa, tana girgiza kanta ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan sake ba, da wasa nake maka, kai ba ɗan iska ba ne” Ko saurarenta Zayyad bai yi ba ya ci gaba da rabata da hijabin jikinta, sanda ya samu damar cirewa kusan shiɗewa Salma ta yi, domin tun da aka haifeta wani namiji bai taɓa ganinta irin haka ba. Doguwar riga yadi ce a jikinta, kanta babu dankwali, kitsonta wanda ya sakko har kafaɗunta sune suka zame mata kamar ɗankwali. Runtse idanunta ta yi tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, Zayyad daya mutu wa kallon gashin kanta ya ma manta da abin da yake shirin yi, gyara zamansa ya yi ya ci gaba da kallonta. Jin ya tsaya ya sanya Salma ɗago kanta tana kallonsa da idanunta da suka kumbura, ganin bai ce komai ba ya sanya ta ɗauki hijabinta ta mayar ta mike tsaye har sannan tana shassheƙar kuka ta yi hanyar fita daga ɗakin. Babu yanda bata yi da kofar ba amma ta ƙi buɗewa ta juyo da niyyar yi masa magana amma ta ga wayam babu shi babu alamunsa. Gajiya ta yi da ƙoƙarin buɗe ƙofar ta zauna a wajen ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana ci gaba da koke kokenta. Sai bayan one hour sannan ya dawo parlon, ya ƙarasa bakin ƙofar yana kallonta, ya ɗauki wasu sakanni a a wajen kafin ya ɗago kanta, ganin bacci take yi ya sanya bai tasheta ba, ya ɗauketa ya kai har kan gadon ɗakin ya kwantar da ita, Ac ɗakin ya kashe sannan ya rufa mata duvet ya kashe hasken ɗakin ya fito parlon ya yi zamansa yana danna wayarsa. Maitama, Abuja. Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo ɗakin, zaune ya hangeta kan sofa tana sanye da riga da wando ta ɗaure kanta da jersey veil, idanunta maƙale kan wayarta tana hira da wata friend ɗinta. Kallo ɗaya ta yi masa ta mayar da kanta kan wayarta ta ci gaba da dannawa, gefenta Faruk ya zauna yana murmushi ya kalleta ya ce “Morning love” Ɗago dara daran idanunta ta yi ta zuba masa, a sanyaye ta ce“Morning” Faruk ya sake cewa “Kin tashi lafiya?” “Alhamdulilah” Nimrah replied. Jinjina kai ya yi, parlon ya ɗauki shiru na wasu mintuna kowa da abin da zuciyarsa ke saƙawa, can kuma ya sake kallonta ya ce “Idan an jima zamu je gida wajen Mama” Ajiye wayar hannunta ta yi kan cinyarta ta ce “Did something happens?” Girgiza kai Farok ya yi ya ce “Nothin, kawai zamu je mu gaisar da ita ne” Ɗan taɓe baki ta yi kafin ta ce “Allah ya kai mu” “Ameen” Faruk ya ce. Ɗaukan wayarta ta yi ta miƙe tana ƙoƙarin barin parlon ta ce “Breakfast ɗin ka yana dinning” Murmushi ya yi ya ce“Thank u love” Nimra bata ce masa komai ba ta buɗe ƙofa ta fita. **** “Yanzu General saboda Nayla ta je gidan Adda shi ne abin laifi? Me za'a yi mata a gidan?” General Idris dake zaune kan sofa ya kalleta ya ce “Kin ji na ce miki za'a mata wani abun? Kawai na ce Nayla ta dawo gida, bana son ta sake kwana a Nassarawa, that's it” Tashi Momma ta yi bata ce komai ba ta fice daga parlon kamar zata tashi sama, Daddy ya bita da idanu kafin ya taɓe baki ya maida kansa gurin newspaper ɗin dake gabansa. Kai tsaye ɗakinta ta nufa, tana zuwa ta ɗauki wayarta dake ajiye kan gado ta zauna tana kallonta, ta ina zata fara kiran Mami ta ce a dawo da Nayla? Me yasa General yake haka akan yayansa? Tsaki Mommah ta yi kafin ta yi dialing numbern Zayyad. Ringing biyu ta yi kafin ya ɗauka Mommah ta ce “Zayyad kana ina ne?” Daga ɗaya bangaren Zayyad ya ce “Wani abu ya faru Mommah?” “Just answer my questions Malam” Mommah ta yi maganar a ɗan fusace. Numfasawa ya yi yana kallon Salma dake zaune can ƙarshen gado ta cure jikinta waje guda ya ce “Na ɗan fita ne, but yanzu zan dawo gida” Shiru Mommah ta yi can kuma ta ce “Kayi sauri ina jiranka to” Okay ya ce sannan ya kashe wayar. Ya tashi tsaye yana ƙoƙarin sanya agogonsa ya ce “Idan kin gama sai ki tashi ki koma gida” A sanyaye ta miƙe tsaye, ta gyara hijabinta tana ci gaba da kallonsa. Car key ɗinsa ya ɗauka ya nufi hanyar waye ta bi bayansa. Sai da ya tsaya a reception ya basu key ɗin ɗakin sannan ya yi waje, kai tsaye parking space ya nufa, yana zuwa ya buɗe motar ya shiga, tsayawa ta yi a wajen tana kallonsa har ya gama warming ɗin motar. Dan tsaki ya yi ya sauke glasses yana kallonta ya ce “Idan baki shirya tafiya ba sai ki ci gaba da tsaiwa anan” A hankali ta buɗe backseat ta shiga ta yi zamanta, ta mirror ya kalleta ya ce “Kin sakko daga nan ko sai ranki ya ɓaci, did I look like ur driver?” kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta buɗe motar ta fito ta dawo front seat ta zauna tana tura baki. Bai sake ce mata komai ba ya yi reverse ya bar transcorp ɗin, Sun fara nisa ya yi parking daidai wani keystone bank ya sauka ya shiga ciki, Ita dai Salma sai bin sa take da kallo har ya ɓacewa ganinta. Sai bayan 15mins sannan ya fito daga bankin ya dawo motar da wata yar jaka, a back seat ya ajiye sannan ya shiga motar ya ɗauki hanyar Mararaba. Ƙarfe 10:23am ya yi parking a bakin titin Kabayi, ya kalleta ganin yanda take kallon hanyar, hannunsa ya sanya ya ɗauko jakar daya shigo da ita ya miƙa mata, amsa ta yi tana kallon jakar ya ce “here it's 1m naira, sai ku biya kuɗin aikin nasa, Allah ya ƙara sauƙi, but you have to be careful, not all the glitters are gold” Wasu hanwaye ne suka fara sintiri kan fuskarta wanda ta kasa tantance na farin ciki ne ko akasin haka, ta kalleshi muryarta na rawa ta ce “Na.. Nagode sosai, Allah ya biya maka buƙatunka, yanda ka taimakeni kai ma Allah ya taimaki rayuwarka, Nagode sosai Yaya Yad” Taɓe baki Zayyad ya yi kafin ya ce “Yaushe har ki ka yi hankalin da ki ka ce min Yaya? I'm not ur Yaya, saukar min a mota” Ɗan murmushi Salma ta yi har sai da beauty point ɗinta suka loma, ta buɗe motar ta sauka tana ɗaga masa hannu, samun kansa ya yi shima da ɗaga mata hannun ta yi hanyar cikin Kabayi tana tafe tana waiwayensa, sai da ya daina hangota sannan ya ja motar, ya so zuwa wajen Mami sai kuma ya fasa tunawa da kiran Mommah kawai ya nufi hanyar Abuja. Sai da tayi nisa sannan ta tuna da Abbanta na asibiti, kawai ta yanke shawarar ƙarasawa gida ta sauya kaya tun da ta riga da tayi wanka, tun da ta fara shiga layinsu mutane ke kallonta, ta sunkuyar da kanta dan babu abin da ta tsana a rayuwarta sama da kallo, a ƙofae gidansu ta hangi mutane sun ɗan taru, kuma duk maza, a sanyaye ta ƙarasa ƙofar gidan bata cewa kowa komai ba ta shige gidan gabanta na faɗuwa. Turus tayi a tsakar gidan ganin Ummarta zaune gefen mutum wanda aka rufe shi da likkafani kamar gawa sai rusa kuka take, Hajiya Jinjin dake gefenta sai rarashinta take. Baba Asabe ce ta hangota ta ce “Ga ma yar tasa nan ai” Duk suka ɗago suka kalleta, Umma ta taso ta ƙaraso wajen ta riƙe hannunta kuka na kokarin kwace mata ta ce “Ina ki ka je Salama? Salama ina ki ka je Babanki ya dinga nemanki? Salama daga ina ki ke?” Kasa bata amsa Salma ta yi sai ma zame hannunta daga nata da tayi, ta nufi inda aka kwantar da gawar, zubewa tayi gaban gawar hannunta na rawa ta shiga buɗe likkafanin, zabura ta yi ta saki likkafanin tana yin baya. Ƙarasowa Umma ta yi ta dafata tana kuka ta ce “Kin gani ko Salama, Abbanki ya tafi ya bar mu, ya mutu Salama, ba zamu sake ganinsa ba” Girgiza kai Salma ta shiga yi, ta ma kasa kuka sai ajiyar zuciya take saukewa. Tana kallon gawar babanta ta ce “Meyasa Abba? Ba nace maka ka jirani ba? Ba nace zan samo kuɗin da za'a maka aikin ba? Me yasa za ka yi fushi? Me yasa zaka tafi ka bar ni Abba? Kai ma baka sona? Abba dan Allah ka tashi, na samo kuɗin da za'a maka aikin fa, na dawo dasu Abba. Karka mutu ka barni, dan Allah Abba, Ammina ma ta tafi shine kai ma zaka tafi ka barni? Duk baku sona daman? Ka yimin magana Abba! Ka tashi Abba! Dan girman Allah Abba ka tashi, na haƙura da makarantar fa Abba! Ka tashi na ganka, ka buɗe idanunka” Salma ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ta ɗora kanta kan gawar Abbanta tana jijjigashi, ganin hakan ya sanya mutane aka riƙeta, masu ɗaukar gawa suka shigo dan daman ita ake jira ta ganshi, Salma na ganin za'a fita da Abbanta ta fincike jikinta ta tashi da gudu ta bisu, tana kai wa soro ta yanke jiki ta faɗi a wajen Sumammiya. # HCD # Nanameera 08106608363. https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t HASKEN CIKIN DUHU Chapter 10: The Cost of Being Alone Nanameera, YOTA/023. Ranar Alhamis aka yi sadaƙar ukun Malam Habu, babu mutane a gidan kasancewar ba dangi ne dashi ba a Kabayi yasa a ka yi addu'ar a masallaci. Ɗage labulan ɗakin ta yi tana kallonta, zaune take ta jingina da jikin bango wanda yake cement ne kawai ba tare da an yi paint ba, idanunta a lumshe yayinda hawaye yake gangarowa gefen idanun, shiru Umma ta yi ta zuba mata idanu tana kallonta. Sallamar da aka yi ya sanya Salma buɗe idanunta, Umma ta sauke labulen tana amsa sallamar, Hajiya Jinjin ta ƙaraso tsakar gidan wanda yake a ɗan jiƙe kasancewar an yi ruwa da safe, Umma ta kalleta tana cewa “Au Hajiya kece da yammar nan?” Numfasawa ta yi ta ce“Wallahi Rahmatu, ya ƙarin haƙuri?” Umma ta ce “Alhamdulillahi, shigo ciki mana” To ta ce sannan ta ƙaraso ɗakin, tana shigowa Salma ta gyara zamanta tana kallonta ta ce a sanyaye “Ina yini” Sai da ta zauna sannan ta ce “Lafiya klao Salama, ya ƙarin haƙuri” Salma ta ce “Alhamdulillah” Shiru ɗakin ya ɗauka, ganin kamar suna son yin wata magana ya sanya Salma ta tashi tana kallon Ummarta ta ce “Bari naje ɗakin Abba” To kawai Umma ta ce, ta juya ta fice daga ɗakin tana tafe a sanyaye. Sai da ta fita sannan Hajiya Jinjin ta kalli Umma Rahmatu ta ce “Yanzu ya za'a yi ne?” Numfasawa Umma ta yi kafin ta ce “Nima shine ban sani ba Jinjin, kuɗaɗen bansan me zan yi dasu ba? Ko gwala-gwalai zan siya na ɓoye?” Ɗan murmushi Hajiya Jinjin ta yi ta ce “Ke daɗina dake rashin basira, idan ki ka siya gwal sai ki ci gaba da zama a haka? Ita ma Salmar a haka zata zauna?” Umma ta ce “To me zan yi mata dan Allah? Ko bar ta zan yi da waɗannan maƙudan kudaɗen?” Dafata Jinjin ta yi ta ce “Ai ba haka za ki yi ba, fito da kuɗin nan zaki yi a kasafta su, ita ma yarinya ki bata nata, kema ki ɗauki kasonki” Girgiza kai Umma ta yi ta ce “Na bawa Salma kuɗi? Haba Hajiya, ba zan iya ba wallahi. Ai ita bar ta kawai ta ci gaba da sana'ar zoɓonta, wannan kuma idan Allah ya kawo mata mijin aure ma yi buƙata tun da dai yanzu babu ran Malam” Wani irin kallo Hajiya Jinjin ta yi mata, ta jin jina kanta tana cewa “Eh lallai baki san rayuwa ba Rahmatu, baki san mutuwar miji ba” Tagumi Umma ta yi ta ce“Ni da mijina ya mutu ai kuwa nasan mutuwar miji, kin san ko tsohon mijina fa naji mutuwarsa” Gyara zama Jinjin ta yi tana kallonta sosai ta ce “Kin ga ki fuskanci abin da yake gabanki, wannan kuɗin ki fito dashi, ki bawa Salma rabi” Zumbur Umma ta miƙe tsaye tana kallon Hajiya Jinjin ta ce “Ai ko wannan ba abu bane mai yiwuwa, akan me zan bata wannan dukiyar? Ko ubanta bai taɓa ganin kuɗi mai yawan wannan ba, ballantana ita” ta ƙare maganar tana sauke numfashi. Tsaki Jinjin ta yi ta ce “Ke daɗina dake bakya cin ribar zance, ki zauna ki ji abin da zan ce miki” “Ai maganar taki ce naji bata zama ba ce, wannan zance kamar babu kai” Umma ta faɗa tana ƙoƙarin zama. Sai da ta zauna Hajiya Jinjin ta dafata ta ce “Kin san me yasa na ce ki bawa Salma wannan kuɗin?” Umma ta girgiza kai tana gwalalo idanu. Gyaɗa kai Hajiya ta yi ta ci gaba da fad'in “Saboda Salma ita ce jarin ki yanzu, tun da har ta iya samo waɗannan maƙudan kudaɗen to abar ki tattalata ce, dole ki fito da kuɗi ki kashe mata, ki siya mata kaya na gani na faɗa, ki siya mata mayuka masu tsada, a siyo kayan mata a bata tasha. Ni kuma nasan inda za'a dinga kai ta, wallahi sai kin yi mamakin arzikin da zaku samu, dan irin su Salama maza ke so, yarinya ƙarama kuma mai abun arziki” Tun da ta fara magana Umma ke kallonta kamar zararriya, duk da bata wani damu da Salma ba amma ba zata iya yiwa rayuwar yarinyar haka ba. Ganin ta yi shiru ya sanya Hajiya cewa “Naga kin yi shiru?” Nannauyan numfashi Umma ta sauke kafin ta ce “Gaskiya wannan maganar ta ki ba mai yiwuwa ba ce ba Hajiya, Salma fa? Ba zan iya ba gaskiya” Ta ƙare maganar tana girgiza kanta. Baki buɗe Hajiya ke kallonta kafin ta yi shewa tana faɗin “Eh lallai Rahmatu, sannunki! To wallahi za ki yi babban danasani, tunda har tafara gane tabi namiji ya bata kuɗi to wallahi ba zata zauna ba. Idan ma baki ɗorata a hanya da kan ki ba, to kina zaune zata dinga ficewa abinta, ke wata rana ma wallahi idan ta tafi ba zaki sake ganinta ba. Kin ga kin yi asara, Gara ma kin san inda take idan ta samo ku dinga rabawa” Shiru Umma ta yi ta tafi tunanin maganar Hajiya Jinjin, Above 5mins kafin ta sake girgiza kanta tana cewa “Gaskiya ba zan iya ba Hajiya, ba zan iya ba! Salama ba zata taɓa tafiya yawon duniya ba, kuma wannan ma ai kyauta aka bata” “Kina da tabbacin kyautar aka bata? Wane ya faɗa miki zata samu wanda zai bata kuɗi kyauta a Abuja? Kuma a otel? Ke bama haka ba, kwana fa ta yi acan, nan aka yi an ganta a bakin titin Kabayi wani ya direta a zundumemiyar mota, har tana ɗaga masa hannu” Hajiya Jinjin ta ƙare maganar tana kallon Umma da kyau. Shiru Umma ta sake yi, can kuma ta ce “Duk da haka, koma ta aikata nasan saboda Babanta ne, yanzu ba zata sake ba” Tashi Hajiya Jinjin ta yi tana cewa “To ai shikenan, Ni bari na shige, Allah ya rufa asiri” Ita ma Ummar miƙewa ta yi tana cewa “Tom ki gaida gida, duk yanda ake ciki zan leƙo ki in sha Allah” riƙe haɓa ta yi tana cewa “Ke kuma da ki ke takaba?” taɓe baki Umma ta yi ta ce “Dan ina takaba idan fita ta kamani ba zan yi ba?” Girgiza kai Hajiya Jinjin ta yi suna fitowa daga ɗakin. Salma dake share tsakar gidan ta tsaya tana riƙe da tsintsiyar. “Hajiya Salama ƴar Abuja” Sunkuyar da kai Salma ta yi tana sake danasanin bin mutumin da tayi, ganin yanda ta yi ya sanya Hajiya cewa “Ke bafa wani abun na ce ba, ba ki yi laifi ba karki damu” Salma da tuni hawaye suka kawo idanunta ta share da hannunta tana gyaɗa kai. Umma kallonta kawai ta yi bata ce komai ba, Hajiya ta yi hanyar soro tana cewa “Allah ya bamu Alkhairi” “Ameen ki gaida gida” cewar Umma. Ganin ta fita ya sanya Umma kallon Salma ta ce “Ki ajiye tsintsiyar nan ki koma ciki, ban da gulma ina abun sharar yake a nan?” Daga haka ta ɗauki buta ta yi hanyar banɗaki, da idanu Salma ta bita sai kuma ta dire tsintsiyar ta shige ɗakinta, tana zuwa ta kwanta kan tsohuwar tabarmar dake shinfiɗe a ɗakin, ta fara kuka a hankali, har sannan zuciyarta ta kasa yadda Abbanta ya rasu, gani take kamar zai dawo idan magriba ta yi, sai dai yau gashi har an kwana uku babu shi babu dalilinsa, ya tafi kamar yanda Amminta ta tafi ta barta, sun tafi sun bar ta cikin duhu wanda Allah ne kawai zai iya kawo mata HASKE domin ta gane in da rayuwarta ta dosa.. Abacha road, Mararaba. 5:45pm. Da gudu ta shigo parlon tana dariya, Mami dake zaune kan sofa tana danna system ta ɗaga ido ta kalleta, girgiza kanta ta yi ta ce “Ke da wa kuma?” Kafin Nayla ta ce komai ya buɗe ƙofar parlon, da gudu ta faɗa gefen Mami tana cewa “Mami kin gansa ko, Save my Mami” Ƙarasowa ya yi yana shirin jan hannunta Mami ta zabga masa wata uwar harara, ya yi baya yana sosa ƙeyarsa. “Me ta yi maka Al-ameen?” Kwafa ya yi kafin ya ce “Wai Mami yarinyar nan muna tafe ta kusa sakawa muyi hatsari, wallahi sai ranta ya ɓaci” ɗagowa ta yi daga jikin Mami ta ce “Mami wai dan na ce masa akuya kar ya kaɗeta shine sai ya dake ni” Kallonsa Mami ta yi ta ce “Saboda kai shashasha ne ya sanya zaka buge rai kuma an maka magana shine zaka daketa? To zo ka daketa!” Ta ƙare maganar a ɗan fusace. Girgiza kai Al-ameen ya yi bai sake cewa komai ba ya yi hanyar upstairs, sai da ya kusa kai wa ƙarshe ya juyo yana kallonsu ya ce “Yaya Ahmad bai dawo ba Mami?” “Ga ganshi ne to?” Ta bashi amsa, murmushi kawai ya yi ya juya bai sake tankawa ba. Tashi Nayla ta yi tana ɗaukan ledar da ta shigo da ita ta ce “Bari na ƙarasa haɗa kayana, sai yaushe Fatiha zata dawo ne Mami?” agogon ɗakin ta kalla kafin ta ce “Tana hanya, maybe ma ta tsaya shegen surutu ne” Murmushi Nayla ta yi ta ce “Ai gobe tare zamu tafi Abuja” Mami ta kalleta tana murmushi ta ce “Inji wa?” “In jini man” Girgiza kai kawai Mami ta yi tana murmushi, Nayla ta haye sama tana tafe tana waƙar kizz denial ta Terminator. Bayan sallar isha'i suna zaune a daki, Nayla na ƙarasa linke kayanta tana zurawa cikin ƙaramar trolley ɗin Fatiha wadda aka bata, Mami ta buɗe ɗakin ta shigo, kallonsu ta yi ganin yanda suke hira abin su. Ta zauna gefen gadon ta ce “Gashi kuma zaki tafi bamu samu an je Orange market ɗin ba” Langwaɓar da kai Nayla ta yi ta ce a shagwaɓe “Ayya, shikenan ai, dan Allah Mami idan kin je ki ce ina gaisheta” “Wa kenan?” Cewar Fatiha, kallonta Nayla ta yi ta ce “Salma mana, Mami sai kin ganta wallahi zata burgeki, tana da kirki, ga hankali kuma kyakkyawa da ita” murmushi Mami ta yi ta ce “Kuma ita take siyar da lemon?” Gyaɗa kai Nayla ta yi ta ce “Me sef I'm so surprised Mami, kin ganta kuwa, maybe dai wani abun ya faru” “Allah sarki, shiyasa duk yana yin daka tsinci kanka ake cewa ka godewa Allah. Ta bani tausayi duk da ban ganta ba” “Mami wallahi ba wata abar tausayi ba ce ba fa, kawai Nayla ce ta iyayinta, irin fa yaran kasuwar nan ne masu buɗewar ido” Fatiha ta yi maganar tana hararar Nayla. Mami ta ce “Kin santa ne da zaki bada shaida a kanta?” Girgiza kai Fatiha ta yi Mami ta ce “To kar na sake jin irin wannan rashin hankali, sai ka ce baki je islamiyya ba?” shiru Fatiha ta yi gudun faɗan Mami. Nayla kuwa ta sake cewa “Yawwa kar ki manta Mami sunanta Salma” Tashi Mami ta yi ta ce“Tom ba zan manta ba in sha Allah, ku kwanta da wuri, da safe zamu shige kar mu yi rana” Okay Nayla ta ce suka mata sai da safe sannan ta juya ta fita. “Banza kawai” Fatiha ta faɗa tana harararta, murmushi Nayla ta yi ta ce“Naji ɗin, Ni wallahi da ace zata yarda da Yaya Zayyad ya aureta” “Amma ban tabbatar da baki da hankali ba sai yau Nayla, wannan yar ƙananun mutanen zai aura? Mutun mai class kamar Yaya Zayyad? You are kidding right?” Girgiza kai Nayla ta yi ta ce “No be joke fa, seriously nake magana wallahi, tana da hankali” Tashi Fatiha ta yi ta ce “Tsayawa magana dake bashi da wani amfani wallahi” Daga haka ta fice daga dakin tana buga ƙofar. Murmushi kawai Nayla ta yi dan ita ba komai ne yake ɓata mata rai ba, kuma babu ruwanta da abin da mutum zai ce ta dauki niyyar faɗawa Yaya Zayyad wannan maganar koda zai daketa. Wuse 2, Abuja. A hankali ta turo ƙofar ɗakin, da sauri ta wurgar da wayar hannunta ta tashi zaune tana gyara duvet ɗin jikinta. Wata kyakkyawar mata ce wadda ba zata shige 47yrs ba, kana ganinta kaga riƙaƙƙiyar yar boko, ƙarasowa dakin ta yi ta kunna haske tana murmushi ta ce “You haven't sleep Aneeserh?” Marairaice fuska Aneeserh ta yi tana kallon matar wadda take matuƙar kama da ita ta ce “I will Mom” Zama ta yi gefen gadon tana kallon ta ta ce “Akwai wani abun ne?” Girgiza kai Aneeserh ta yi, matar ta tashi still looking at her ta ce “Ki kwanta sai da safe” Daga haka ta nufi ƙofa, tana shirin fita ta ji ta ce “Mom sai yaushe Dad zai dawo ne?” Sakar handle ɗin ƙofar ta yi tana kallonta ta ce “Maybe next week, baku yi magana dashi ba ne?” Girgiza kai Aneeserh ta yi ta ce “Last two days muka yi magana dashi, but I didn't ask him” Mom ta ce “Then u should call him tomorrow” jin jina kai ta yi ta ce “okay ma, good night” Murmushi Mom ta yi ta ce “Good night baby” har ta juya sai kuma ta ce “Au zan manta, ba lallai bane gobe ki tashi ki sameni, i have alot to do at office z and kuma zan je transport wajen Uncle” Gyaɗa kai Aneeserh ta yi ta ce “Okay Mom, I'll take care of my sef don't worry” “Sure Baby?” Aneeserh ta gyada mata kai tana murmushi, okay Mom ta ce sannan ta juya ta bar ɗakin. Ajiyar zuciya Aneeserh ta sauke sannan ta koma ta kwanta ta janyo wayarta, Khairiyya dake kan video call ta kalleta ta ce “Ni kin ga nagaji da wannan, kawai ki zo transcorp mana” Girgiza kai Aneeserh ta yi ta ce “Mom gobe zata je can ɗin, ba zani ba gaskiya” tsaki Khairiyya ta yi ta ce “Idan aka yi sallar Asuba ba sai ki komo gida ba, ni muna nan ni da su Feedy” Shiru Aneeserh ta yi can kuma ta ce “I'll not, bacci zan yi yau” harararta ta yi ta ce “Bacci za ki yi ko kuma kin shirya wayar dare da Zayyad?” taɓe baki Aneeserh ta yi ta ce “Ke baki sani ba, kwana biyu ma bamu yi shiri sosai ba, ko kulani baya yi” waro idanu Khairi ta yi ta ce “For what reason kenan?” Daga kafaɗarta ta yi ta ce “I don't know, kawai yana banza dani ne, kin san wani lokacin girman kansa ya yi masa yawa” Murmushi ta yi ta ce “Da yake kula ki ma kenan, wai yaushe zaku yi auren?” numfasawa Aneeserh ta yi ta ce “Idan Dad ya dawo zamu yi maganar sai a ke gidansu” “And who told u daga gidansu budurwa ake zuwa?” Murmushi Aneeserh ta yi ta ce “Silly me, anyway I go talk to Zayyad tomorrow” “Better” Khairiyya ta faɗa kafin tayi cutting kiran. Washegari ko da ta tashi bata tarar da Mom ba, shiryawa ta yi cikin wasu riga da wando ta yi rolling jersey veil akanta, ta ɗauki school bag nata ta yi waje. Tana cikin driving taga kiransa, ta samu gefe ɗaya ta yi parking kafin tayi answering call ɗin, daga ɗaya bangaren Dad ya ce “Daughter” Shagwaɓe fuska ta yi kamar tana gabansa ta ce “Dad i dey missed you alot, come back please” Murmushi ya yi daga nasa bangaren ya ce “My poor neeserh, in sha Allah on Monday zan sauka a 9ja” Waro idanunta ta yi tana murmushi ta ce “Dad are u serious?” Dad dake kan layi har sannan ya ce “Yeh, just wait for me my baby girl” Aneeserh da murna ta isheta ta ce “Okay Dad am, I'll, sai ka dawo” Murmushi ya yi ya ce “Akwai wani abu ne?” Aneeserh ta langwaɓar da kanta kafin ta ce “Dad i dey broke those days wallahi” Daga ɗaya bangaren Dad ya ce “But why u didn't tell me neeserh? Saboda wa nake neman kuɗin? Karki sake irin haka?” murmushi ta yi ta ce “Okay First love, I'll not” “Zan saka miki 1m a keystone naki, ya isheki?” Aneeserh ta yi dariya ta ce “My one and only Dad, thank you” Murmushi ya yi jin dariyarta ya ce “Haka nakeson jin ki koda yaushe kina farin ciki kin ji” Aneeserh ta ce “Idan ina da kai Dad ai ba zan taɓa kuka ba, driving nake zani school I'll call u later” Dad ya ce “Okay love, bye” Daga haka ya yi cutting kiran. Kallon screen ɗin wayar tayi tana sake yiwa Allah godiya daya bata Dad a matsayin mahaifi, he's always behind her happiness, ajiye wayar ta yi sannan ta ci gaba da driving ɗinta. Kabayi, Mararaba. Zaune take kan kujera a tsakar gida tana tsince wake, Umma na zaune kan tabarma tana yanka sallad wani yaro ya yi sallama ya shigo, yana wasa da tsolon rake ya ce “Wai Salma ta zo” Kallonsa Umma ta yi sai kuma ta ce “Kace tana zuwa” Salma dake sunkuye ta ɗago ta kalli Umma kafin ta yi magana Ummar ta ce “Tashi ki je ki ga wane” Kasa motsi Salma ta yi, ta tafi tunanin wanda ke nemanta. “Baki ji bane Salama?” A sanyaye ta tashi ta shige ɗakinta, wani hijabi maroon colour ta ɗauko ta saka, ta fito ta zura takalmanta ta nufi hanyar waje “Sauran ki wulaƙanta mutum” Salma ta juyo ta kalleta sai kuma ta juya ta ci gaba da tafiya. Tsaye yake jikin motarsa, yana sanye da wata dakkakiyar shadda royal blue, idanunsa maƙale da shades glasses, da matukar mamaki Salma ke kallonsa yayinda shi kuma yake sakar mata murmushi. “Kai ne?” # HCD # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 11: Between Grief and Promises Nanameera, YOTA/023. Kyakkyawan murmushi ya sakar mata yana sauke glasses ɗin idanunsa, ganin irin kallon da take masa ya sanya ya girgiza kansa still smiling ya ce “Rufe bakin mana” kunya ce ta rufeta, ta sanya hannayenta duk biyun ta ɓoye fuskarta. Girgiza kai Zayyad ya yi yana murmushi shima ya ce“Kin gane ni?” langwaɓar da kanta ta yi a sanyaye ta ce “Yaya Yad ya zan manta ka?” Zayyad ya gyara tsaiwarsa yana cewa“Sai ki mantani mana, wait idan baki mantani ba ina ki ka sanni?” wani kyakkyawan murmushi ne ya kwace mata, ta Jinjina kanta ba tare da ta ce komai ba. Shiru wajen ya ɗauka iskar damuna mai ɗauke da danshi tana kaɗawa a hankali. Furzar da numfashi ya yi kafin ya sake kallonta ya ce “Ya jikin Abba?” Shiru Salma ta yi lokaci ɗaya hawaye suka kawo kurmin idonta, da mamaki Zayyad ke Kallonta, a nutse ya ce “Lafiya dai?” Kasa bashi amsa ta yi, sai kawai ta fashe da kuka, ƙarasowa gabanta ya yi ya zuba mata idanu, a hankali ya sanya hannunsa yana janye hijabin data rufe fuskarta dashi, sake rufe fuskar ta yi tana ci gaba da kukanta. Ya yi tsaye wajen yana kallonta, ganin ta ƙi yin shiru ya sanya ya ce “Ina miki magana kina ji na?” Bata basa amsa ba, dan ko ɗago fuskar bata yi ba, ya girgiza kansa ya ce“shikenan tun da ba za ki faɗa min ba sai an jima” daga haka ya juya yana komawa in da motarsa take. “A'a Alhaji ina za ka je? Dawo mana, me ta ƙo faɗa maka?” Zayyad wanda yake tsaye riƙe da handle ɗin mota ya juyo dan ganin wanda yake magana. Umma ce tsaye kusa da Salma ta lulluɓe jikinta da mayafi sai rarraba idanu take, tun daga sama har ƙasa Zayyad ya kalleta, fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin bai ce komai ba ya sanya Umma sake cewa “Salman ce sai addu'a, tun da baban nan nata ya mutu shikenan bana gane kanta, ko abinci ma ba tsayawa take ta ci ba, to babu mai daɗi” Da mamaki Zayyad ke Kallonta, Sai kuma ya kalli Salma wadda har sannan ke kuka, ya gyara tsaiwarsa kafin ya ce“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, yaushe ya rasu?” Umma ta sake langwaɓewa kamar abar tausayi muryarta har rawa take ta ce“Wallahi yau a kayi kwana uku, To da yake baban nata ba wasu dangine dashi a nan kusa ba ya sanya baka ga jama'a ba, Yanzu ni ce uwarta ni ce ubanta” Shiru Zayyad ya yi for some seconds can kuma ya ce“Allah ubangiji ya jiƙansa ya sa ya huta, ya kyautata namu zuwan” a sanyaye Umma ta ce “Ameen” Shiru wajen ya ɗauka Umma sai bin sa take da kallo, Zayyad ya juya ya koma motarsa, Umma ta dinga leƙensa tana son ganin abin da yake yi. Dawowa ya yi hannunsa riƙe da wrappers na 1k guda uku ya miƙawa Umma yana cewa “Gashi a yi sadaƙa” Jikin Umma Rahmatu na rawa ta amshi kuɗin tana cewa “To...To Allah ya ƙara buɗi... Allah ya biya buƙata” Zayyad bai ce komai ba, ta kalli Salma ta ce can ƙasa “Sai kin shigo” Daga haka ta shige gida da sauri. Takaici da baƙin ciki ya sanya Salma sake fashewa da wani sabon kukan, Shiru Zayyad ya yi ya kamo hannunta a hankali, saurin fizgewa ta yi ta janye hijabin fuskarta, idanunta caɓa-caɓa da hawaye ta ce “Ni...Ni karka sake taɓani” Jin jina kansa ya yi ya ce “Ni magana zan miki, meyasa Abba ya mutu?” Salma na kuka ta ce“Sanda na dawo sai na tarar an kawo gawarsa, Abba bai jirani na dawo ba ya mutu ya barni, Ni na daina kulashi” Sosai ta bashi dariya amma ya dake, A nutse ya ce“Bayan ya mutum za ki ce kin daina kula shi? Addu'a za ki dinga masa kin ji” gyaɗa kanta ta yi tana share hawayenta. Agogon hannunsa ya kalla ya ce“Koma gida to, sai na sake zuwa” sake gyaɗa masa kai ta yi ta juya ta shige gidan. Numfasawa Zayyad ya yi kafin ya juya ya shige motarsa ya bar ƙofar gidan. Salma na shiga ta tarar da Umma zaune kan tabarma sai lissafa kuɗaɗe take, har ta rufe jin taku da taga Salma ce kuma sai ta buɗe, ƙarasowa Salma ta yi ta zauna gefenta. Hannu Umma ta miƙo mata, Salma ta kalleta da mamaki dan bata gane me take nufi ba “Ina abin da ya baki?” Baki buɗe Salma ke kallonta, a ɗan tsawace Umma ta ce“Ko baki ji ina magana ne? Ina kuɗaɗen daya baki?” A sanyaye ta ce“Umma ni babu abin da ya bani fa” waro idanu Umma ta yi ta ce“Ni za ki yiwa ƙarya? Na tabbata ya baki kuɗaɗe kema kamar yanda ya bani” Salma na hawaye ta ce“Ni wallahi bai bani ko biyar ba, Ni ba kuɗinsa nake so ba” riƙe baki Umma ta yi ta ce “Eh lallai! To shi me yake so idan ba kyan ki ba? Ke bana son tsirfa fa! So nake na aurar dake, Kuma dole ki ci kuɗin samari” Tura baki Salma ta yi ta tashi ta shige ɗaki da sauri, da idanu Umma ta bi ta sai kuma ta yi tsaki tana cewa“Shashasha wadda bata san inda yake mata ciwo ba, har irin wannan attarijin ya zo wajenki ki ce wai ba kuɗinsa ki ke so ba? Ni dama bari ya yi na gama takaba ya aureni” Ta ci gaba da ƙirga kuɗaɗenta. Koda ta shiga ɗaki kwanciyarta ta yi kan tabarma tana kuka ita kaɗai, ba'a fi mintuna goma ba Umma ta shigo ɗakin tana kallonta ta ce “Zan fita, Ki zo ki ci gaba da girkin nan” Da mamaki Salma ta ɗago ta kalleta, a sanyaye ta ce“Umma wadda take tabaka ai bata fita” “To uwata hanani fita! Na ce hanani” ta ƙare maganar tana zabga mata uwar harara. Shiru Salma ta yi dan bata da abin sake cewa, Umma ta juya ta bar ɗakin. **** A hankali ya buɗe ƙofar parlon yana murmushi ya ce“Shigo Mama” Shigowa ta yi tana sanye da wata atampa glitter, ɗinkin riga da zani, Ta yafa veil wanda ya hau da atamfar, hannunta riƙe da jaka. Zama ta yi kan ɗaya daga cikin royal sofa ɗin dake zagaye da parlon. Farooq na murmushi ya ce“Bari na kirata” daga haka ya nufi hanyar upstairs. Koda ya shiga ɗakin zaune ya hangeta tsakiyar gado idanunta zube kan system ɗin gabanta tana murmushi abin ta, Da mamaki yake kallonta ya ƙarasa gaban gadon a zaune gefenta a hankali ya ce “Love” Ɗago idanunta ta yi ta kalleshi, murmushi ya sakar mata kafin ya ce“Guess what?” langwaɓar da kai ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Just tell me” Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“Mama na downstairs” shiru Nimra ta yi can kuma ta ce “Shine baka faɗa min ba?” Farooq ya ce“Yanzu ai gashi na faɗa miki” Rufe system ɗin gabanta ta yi ta sauka kan gadon, toilet ta shige dan riga da wando ne jikinta. Bata ɗauki lokaci ba ta fito, wata atampa ɗinkin riga da skirt, ta ɗaure kanta ta ɗan yi simple kwalliya a fuskarta kafin ta baro ɗakin. Koda ta sakko downstairs Mama kawai ta samu zaune kan sofa tana danna waya, ƙarasowa ta yi ta zauna kujerar dake facing ɗinta a nutse ta ce“Ina yini Mama?” murmushi Mama ta yi ta ce“Lafiya klao Nimra ya gida?” “Alhamdulilah” Nimra ta ce sannan ta tashi, kitchen ta nufa ta haɗo drinks a tray ta kira wata maid ta ɗauko mata, a gaban Mama aka ajiye tray ɗin, tana ɗan murmushi ta ce“Mama ki sha ruwa, Me za'a dafa miki?” Girgiza kai Mama ta yi tana murmushi ta ce“A'a ba sai kin wahalar da kan ki ba, Ai baki san zan zo ba, Ba sai kin yi girki ba” Murmushi kawai Nimra ta yi ba ta ce komai ba ta koma kitchen ɗin. Ƙarar door bell ne ya fito da ita daga kitchen ɗin, duk a tunaninta Farooq ne ya dawo. Turus ta yi bayan ta buɗe ƙofar tana kallonta da mamaki, Tsaki Deejah ta yi ta ce“Dalla matsa min hanya ni” wani irin Ihu Nimra ta saka ta rungumeta tana dariya ta ce“Welcome Bestie” Tureta Deejah ta yi ta ce“Ba wani Bestie, abin da kin manta dani? Yaushe rabon da ki zo in da nake? Ke kin yi aure ko?” langwaɓar da kai Nimra ta yi ta kama hannunta suka shiga ciki tana cewa “Ya Uk ɗin?” “Alhamdulillah, Ai kin yi missing yarinya” Dariya Nimra ta yi, Daidai sanda suka zo parlon. Kallo ɗaya Deejah ta yiwa Mama dake zaune kan kujera ta ɗauke kanta, Hannunta Nimra ta ja tana mata alama data gaisheta. Harararta Deejah ta yi kafin ta kalli inda Mama take daga tsaye ta ce “Good afternoon Ma” Murmushi Mama ta yi ta ce“How are you yarinya?” “Alhamdulilah” Deejah ta faɗa, Mama ta Jinjina kanta bata sake cewa komai ba. Deejah ta kalli Nimra ta ce“Ni zan shiga ciki sai kin shigo” daga haka ta yi hanyar upstairs, Mama ta bita da idanu. Taɓe baki Nimra ta yi sanin halin Ƙawartata ta koma kitchen dan ƙarasa abin da take. Asokoro, Abuja. Zaune suke cikin katon parlon, Mami na kallon Mommah dake mata bayani tana jin jina kai, Mommah ta ci gaba da fad'in “To kinji abin da ya faru Adda, na rasa yanda zan yi da Zayyad, kwata-kwata General baya son laifinsa, ban isa na ce ya yi ba daidai ba sai ya nuna ɓacin ransa. Zayyad duk ya sake lalacewa, sai sanda ya ga dama fa yake shigowa yanzu” Numfasawa Mami ta yi ta ce “Idan haka ne zan yi magana da General kuwa, ya daina lalata masa tarbiyya da sunan tausayi da soyayya, Abubuwan Zayyad sun yi yawa, Ahmad ya ce min har giya yake sha, wace irin rayuwa ce wannan?” Mommah ta girgiza kai kafin ta ce “Wallahi Adda idan kin ga yanda nake fama sai kin tausayamun, Zayyad baya so gaskiya, tunda ya dawo daga Uk komai na sa ya lalace, ya je ya yi rayuwa da mutanen banza, Babu irin club ɗin da bai sani ba. Allah ne kaɗai ya san irin abubuwan da yake yi ma a ɓoye” Dafata Mami ta yi ta ce“Ki ci gaba da haƙuri Khadijah, Karki manta Zayyad amana ne a wajenmu, Allah ya rufa asiri ma da kece ki ke auren Idris. Ke ce matsayin Mahaifiyarsa, Kece ki ka shayar da shi, ke yake wa kallon uwa. Saboda haka ki dage masa da addu'a da naiman taimako kuma ci gaba da masa faɗa koda a ce baya so, watarana sai Allah yasa ya ji” Goge hawayen daya zubo mata ta yi tana sauke numfashi ta ce“Haka ne Adda, Kodan Yaya dole nayi iya ka kokarina, domin ta kula damu, Ta bamu tarbiyya, Haƙƙine a kaina na kula da rayuwarsa, Allah ya shiryesa” Ameen kawai Mami ta ce parlon ya ɗauki shiru koda da abin da yake tunani. “Khadija ku kula da rayuwarku, ki zauna lafiya da mijinki, na saka kin auri Idris ne saboda mu sake samun kusanci. Idris ƙanin mijina ne uwa ɗaya uba ɗaya, duk wani halin kirki da Khalid yake da shima yana da shi, Duk da ya fi Khalid zafin zuciya amma nasan yana da halaye na gari, Ki yi hakuri, Ki zauna lafiya da mijinki, Dan Allah Khadijah” Mommah ta sake share hawaye tunawa da maganar da Marigayiya Jidderh ta faɗa mata lokacin data auri General. Kallonta Mami ta yi ganin tana sharar kwalla ta ce “Haba Khadijah, kuka ai ba magani bane, Addu'a za ki dinga mata” ɗora kanta ta yi kafaɗar Mami tana sake fashewa da kuka ta ce “Dole nayi kuka Mami, Yaya ta tafi ta barmu, Ta tafi ta bar Zayyad a lokacin da yafi buƙatarta fiye da komai, Wallahi tausayi yake bani Yaya, Yana cikin wani hali, yana cikin duhu wanda Allah ne kawai zai kawo masa hasken rayuwa. Ina ma Yaya tana nan” Rufe mata baki Mami ta yi tana girgiza kanta ta ce“Ki daina cewa haka, Allah ya san da hakan ya ɗauke ranta. In sha Allah komai zai zama tarihi, Duk yanda duhu zai mamaye waje wata rana sai haske ya bayyana, ina ji a jikina Zayyad zai samo HASKEN CIKIN DUHUnsa nan ba da jimawa ba” Mommah ta jin jina kai ta ce“I hope so” **** Jinjina kai kawai Zayyad yake yana saurarenta amma gaba ɗaya ta ishesa, hannunta ta kamo kamar zata yi kuka ta ce“Yaya I'm talking fa” ɗago lulu eyes ɗinsa ya yi ya zuba mata kamar zai fasa ihu ya ce“Dan girman Allah Nayla ki rabu dani, I'm tired wallahi” turo baki ta yi ta janye system ɗin gabansa tana cewa. “Kwana nawa bana nan amma ko missing ɗina baka yi, Kuma na zo ina maka magana shi ne ka ke ce min haka?” Girgiza kansa ya yi ya mike daga kan gadon yana cewa“An jima ma yi magana, tashi ki tafi” kallonsa ta yi sai kuma ta ajiye system ɗin ta miƙe ta fice daga ɗakin tana buga ƙofa da ƙarfi. Da idanu ya bita sai kuma ya taɓe baki ya nufi toilet abin sa. Ana kiran sallar la'asar ya fito sanye da wata dakkakiyar shadda milk colour, sai ƙamshi turaren Clive Christian No. 1 yake, kai tsaye parlon Mommah ya nufa, Babu kowa a parlon don haka ya shige bedroom ɗin kai tsaye. Zaune ya same su da Mami suna hira, Ya tsaya daga bakin ƙofar yana kallonsu bai ce komai ba. “Ina kuma zaka je Zayyad?” Lumshe idanunsa ya yi kafin ya ce “Zan ɗan fita ne, but ba zan daɗe ba. Mami ku jirani please” Harararsa Mami ta yi ta ce“Naƙi na jira kan, Ahmad na zuwa zamu tafi, idan mun yi dare kai zaka mayar damu Zayyad?” gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce“Wallahi zan kai ki har Abacha road” Ta taɓe baki kafin ta ce“To ka yi sauri dai” Jinjina kansa ya yi sannan ya juya ya bar dakin. A corridor suka ci karo da Khalil wanda shigowarsa gidan kenan, Ya kalleshi ya ce “Yaya unguwa zaka je?” Zayyad na nufar downstairs ya ce“Uhm” Khalil ya bi shi da idanu ya ce“A dawo Lafiya” “Allah yasa”. Cikin Maitama gidan yake, ƙaton gida mai ɗauke da securities da sojoji, gidan Babban soja kamar General Kabeer. A compound ɗin gidan ya yi parking dan already an san da zuwansa. Ya yi jim a motar kafin ya ɗauki wayarsa ya yi dialing wata number. Ringing ɗaya aka ɗauka a nutse ya ce “I'm outside” Cikin cool voice ɗinta ta ce“Ka shigo ciki tom” okay kawai ya ce sannan ya kashe motar ya fito. Cike da nutsuwa da tagama tsarata take tafiya har ta ƙaraso tsakiyar parlon. A sanyaye ta ce“Ina yini” Sai a sannan ya ɗago kansa ya kalleta. Kyakkyawar budurwa ce wadda ba zata shige 22-23yrs ba, baƙa ce doguwa mai siririyar fuska, da ka ganta kaga baƙar shuwa. Zama ta yi kujerar dake facing wadda yake kai a nutse ta ce “Fatan ka zo lafiya?” Zayyad ya ce “Alhamdulilah ya ki ke?” lumshe idanunta ta yi ta ce“Ina nan klao, Ya su Mommah?” Sosai ya yi mamaki jin ta ambaci sunan Mommah sai bai nuna ba ya ce ”Tana nan klao” Ta sake cewa“To idan ka koma ka gaida min dasu” shiru parlon ya ɗauka can kuma ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin “Dad ya ce na zo na gan ki daman” Ɗan sunkuyar da kanta ta yi ta ce “Eh Nima haka Daddyna ya ce min, And kuma na ganka ka kwanta min, ban sani ba ko nima nayi maka?” ɗan murmushi Zayyad ya yi ya ce “In sha Allah” Ta yi murmushi bata ce komai ba. Ganin lokaci na tafiya ya sanya ya miƙe tsaye, tashi itama ta yi tana kallonsa ta ce “Naga ka tashi?” Zayyad ya ce “Mum na jirana ne, Zan dawo in sha Allah” Murmushi ta yi ta ce“Tom Allah ya dawo da kai lafiya” Zayyad ya ce Ameen Sannan ya nufi Kofar fita daga parlon. “Jidda, Ba dai har ya tafi ba?” Juyowa ta yi tana kallon wadda ke magana kafin ta ce “Eh Mummy, Wai ana jiransa ne” Shiru ta yi can kuma ta ce“Tom sai ku yi waya ai” murmushi Jidda ta yi ta ce“Eh Mum, Kuma wallahi yanda na gashi a hoto ma sai naga yafi haka kyau a zahiri” riƙe haɓa Mummy ta yi ta ce“Ikon Allah, To sai ki faɗawa General ɗin idan ya dawo, a yi abin da ya kamata nan da 1 month a ɗaura aure” da gudu ta tafi ta rungume Mummy tana murmushi ta ce“Shiyasa nake son ki mummyna”. Kabayi, Mararaba. Gyara zama Hajiya Jinjin ta yi tana kallon Umma ta ce“To yanzu ya ki ka yi?” Umma dake zaune gefen kujera ta ce“Sai na kwatanta masa gidana, Kin ga kuwa a mota zundumemiya” shewa Jinjin ta yi ta ce“Kin yi kyan kai ta gurina, Ai dama ba'a wasa da irinsu” Umma ta ce“Ai yanzu dana gama wannan takabar sai Aure” tuntsirewa da dariya Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Au ke yanzu sai ki yi aure? Taɓ!” Da mamaki Umma ke kallonta sai kuma ta ce“To Hajiya tun da na samu wanda ya ce yana sona me zan yi idan ba aure ba?” Da hannu ta yi mata alama da ta kawo kunnenta, Umma ta miƙa mata ta faɗa mata wata magana. Shiru Umma ta yi jiki a sanyaye ta ce “Ni kuma Hajiya da girmana?” tsaki ta yi ta ce“To har yaushe ki ka yi girman da zaki ce haka? Mu ma duk harkokin da muke kenan, kafin tsufa ya cimmaka ka yi abubuwa dayawa” Jinjina kai Umma ta yi ta ce“Kuma fa haka ne, na yarda da maganganunki, Haka ma za'a yi. To yanzu maganar ita kuma Salama fa?” Hajiya Jinjin ta yi dariya kafin ta ce “Dana faɗa miki ai baki yarda ba, To bari ki ji kin ga yanda aka fara sallamar nan da ita gara ki bar ta, idan ba haka ba Wallahi kina nan zata dauko abun kunya” Jinjina kai Umma ta yi ta ce“Nima na fuskanci haka wallahi, Yanzu dai bari na koma, idan Allah ya kawo wannan mutumin na je na masa magana idan yana so” girgiza kai Jinjin ta yi ta ce“A'a ai ba'a shiga dawa dan ƙarya, Yanzu dai ki tashi mu je gidan naki, akwai abin da zan aikata” Zumbur Umma ta mike tana cewa“Mu je to, A yi ta ta ƙare wallahi!”. # HCD # Light within the darkness # Nanameera 08106608363. https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 12: “Not Meant for Me” Nanameera, YOTA/023. Tuntsirewa da dariya Ahmad ya yi yana kallonsa ya ce“To ka yi zamanka mana, Dole sai ka rakamu?” wani shegen kallo Zayyad ya watsa masa, Ya kalli Mami dake tsaye suna magana da Mommah ya ce “Mami let's go” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Alright” Ta kalli Mommah tana murmushi ta ce“Ki kula sosai Khadijah sai mun sake shigowa” Jinjina kai Mommah ta yi ta ce“Tom Mami, Idan kuma na riga ki zuwa shikenan” murmushi kawai Mami ta yi ta nufi in da Zayyad ya yi parking ride ɗinsa, Tana ƙoƙarin shiga motar General ya fito daga tasa motar. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta tana faɗin “Barka da dawowa” Babu yabo babu fallasa ya ce“Kuna lafiya?” “Alhamdulilah” Mami replied. Ta shige motar abin ta, Fatiha ce ta kalli Nayla dake riƙe da hannunta ta ce“Sake ni kar Yaya Zayyad ya tafi ya bar ni” langwaɓar da kai Nayla ta yi ta ce“Tom ku gaida gida, Dan Allah kar ki manta ki cewa Salma ina gaidata idan kun je Orange market” Harararta Fatiha ta yi ta ce“You Are mad” Daga haka ta nufi motar. Backseat ta shiga ta zauna kusa da Mami, Zayyad da Ahmad suka shiga front seat, Ya ja motar a nutse Momma da Nayla na daga musu hannu. Sun yi nisa sosai Mami ta kalli Zayyad ta ce“Kana tafiya a hankali mana” ɗan murmushi ya yi yana kallonta ta mirror ya ce“Mami ba fa zan yar dake ba, Ina sauri ne saboda ka da nayi dare” Harararsa ta yi ta ce“Da nufinka a daren nan za ka juyo Abuja?” Gyaɗa mata kai ya yi ta ce“To baka isa ba, Sai dai ka bari sai gobe. Idan kuma baka da wajen zama ne sai naji” numfasawa ya yi a sanyaye ya ce“Inason zan yi magana da Dad ne idan na dawo” “Koma wace magana ce sai ka bari sai gobe Zayyad” Mami ta faɗa tana danna wayarta, Shiru Zayyad ya yi amma tabbas ba zai iya kwana a Mararaba. Sai wajejen ƙarfe 8 na dare sannan suka isa gidan, Da idanu Mami ta kalleshi ganin bai fito daga motar ba. “Sai da safe Mami” Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi. Girgiza kai kawai ta yi ta ce“Allah ya tashe mu lafiya” Ta yi gaba abin ta dan tasan tun da ya yi haka ba zai taɓa kwanan ba. Kallonsa Ahmad ya yi ya ce“Banza kawai” Fuska a ɗaure Zayyad ya ce“Malam saukar min a mota” ƴar dariya Ahmad ya yi kafin ya ce“Daɗinta dai nima Allah ya hore min ina da mota, Da yau an gama tsinkani” Daga haka ya buɗe motar ya fita. Da harara Zayyad ya bisa sannan ya yi reverse ya bar ƙofar gidan. Har ya dauki hanyar komawa Abuja sai kuma wata zuciyar ta ce masa ya je ya ga Salma, Bai san me yasa ba haka kawai ya ji yana son sanin halin da yarinyar ke ciki. A ƙofar gidansu ya yi parking, Ya ɗauki a ƙalla 2mins kafin ya hango wani yaro yana tafe. Sai da ya bari ya ƙaraso sannan ya fito daga motar yana kallonsa ya ce “Kira min Salma a gidan nan boy” To kawai yaron ya ce sannan ya tura ƙofar gidan ya shiga. Babu wani haske a tsakar gidan dan babu wuta, Salma na zauna kan tabarma ta ɗora kanta a cinya yaron ya ce “Wai ana sallama da Salma” Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da idanunta wanda suka kumbura tsabar kuka, Murya bata fita ta ce“Ka je ka ce bata nan” “Da bakya nan kina gidan Ubanki ne hala, Kai je ka ce gata nan zuwa” Umma data fito daga banɗaki ta yi maganar hannunta riƙe da buta. Juyawa yaron ya yi fita, Ta ƙaraso wajen tana kallonta ta ce“Kin tashi kin fita a gidan nan ko sai ranki ya ɓaci shashasha wadda bata sanmu da arziki” Sake fashewa da kuka Salma ta yi ta tashi ta shige ɗakinta, Hijabi ta ɗauko ta fito ta yi hanyar waje tana tafe tana kuka. Tsaye ta same shi jikin motarsa yana danna wayarsa a nutse, Tsayawa ta yi tana kallonsa, Cikin shassheƙar kuka ta ce“Gani” Sai a sannan Zayyad ya ɗago kansa ya kalleta. Maida wayar ya yi aljihu ya ƙaraso har gabanta har tana jin hucin numfashinsa, A nutse ya ce “Meya faru?” Banza ta yi masa ta ɗauke kanta, Ya sake tambayarta nan ma taki bashi amsa, A ɗan zafafe ya ce “Keee! Ni nake miki magana ki na ji na? Who are you?” Ya ƙare maganar yana riƙe fuskarta, Fizge hannunsa ta yi daga fuskarta tana harararsa ta ce “Ina ruwanka dani? Me ka zo yi gidanmu?” Mamaki ta bashi ya ce“Oh tambayata ki ke me nazo yi gidanku? Ina gidan ya ke?” Salma goge hawayen fuskarta ta yi cike da tsiwa ta ce“Kai ka sani koma ka ganshi ko baka ganshi ba, Ina son na faɗa maka wata magana kar ka sake ƙoƙarin kai hannunka jikina dan ni ba yar iska ba ce, Sannan kar ka sake zuwa gidanmu ka ji na faɗa maka!” Kasa magana Zayyad ya yi ya tsaya yana kallon ikon Allah, Tun da yake a rayuwarsa babu wata macen data taɓa tsayawa gabansa ta faɗa masa makamanciyar wannan maganar, Ko yar gidan wace ita, Sai ka shi yarinya yar ƙarama ta tsaya tana gasa masa magana. Jin ya yi shiru ya sa ta ɗan saci kallonsa ta ga still ita yake kallo, murguɗa baki ta yi sai kuma ta sake cewa “Idan ka ji haushi kar ka sake zuwa in da nake, Ballantana ka bawa Ummana kuɗi, Babu ruwanka da rayuwarmu, Kana ji na?” Tamkar tana magana da dutse haka Zayyad ya yi mata, Sai kawai ta fashe da kuka tana cewa “To ni banason kana zuwa gidanmu, Ummana ta ce sai ta kai ni wajen maza kuma saboda ka zo ne, Kar sake zuwa in da nake dan girman Allah” Taɓe bakinsa ya yi bai ce mata komai ba ya juya ya shige motarsa ya ja ya bar ƙofar gidan, Tamkar yana tafiya da rayuwarta haka Salma ta ji, ta tsurawa motarsa idanu har ta daina hangota. Zubewa ta yi ƙasa ta fashe da wani sabon kukan, Tabbas bata ji tana son daina ganinsa ba, Amma bata san ta bar gidansu a kai ta wani waje, Gara Ummarta ta ga babu wanda yake nemanta ko hakan zai saka ta rabu da ita. A sanyaye ta shigo gidan tana tafiya kamar wata mara gaskiya, Umma Rahmatu dake zaune kan tabarma har sannan ta kalleta ta ce“Zo ki bani abin da ya baki” Wasu sabbin hawaye ne suka fara zubowa kan fuskarta ta kalli Umma ta ce“Ni babu abin da ya bani wallahi” Tafe hannaye Umma ta shiga yi tana cewa“La'iha illalahu Muhammadu Rasulullahi Na shiga uku Ni Rahmahtu, Abin da Jin jin take faɗa min gashi ya fara zama gaskiya” Ta ƙare maganar tana yin kan Salma, Rufeta ta yi da duka tana cewa “Zaki fito min da abin da aka baki ko kuma sai na kasheki a gidan nan” Salma ko ban da kuka babu abin da take, ba dan zafin dukan ba, Sai dan zafin maganar da Ummar ke mata. Sai da gaji dan kanta sannan ta rabu da ita, Ta shige ɗaki tana banbamin masifa. Kwanciya Salma ta yi a tsakar gidan tana ci gaba da kukanta kamar ranta Zai fita. Asokoro, Abuja. A bakin entrance na gidan ya yi parking ya fito daga motar ya yi cikin gidan yana ɗan tafe a zafafe. Zaune ya samu Daddy a parlon yana karanta news, Ganin yana shirin wucewa ya sanya Daddy ya ce*Zayyad Zo nan” Bai ce komai ba ya dawo ya zauna kan kujera, Kallonsa Daddy ya yi ganin yanda jijiyoyin kansa suka tashi fuskarsa ta yi wani irin jaa, A matuƙar Dame ya ce “Meya faru? Me aka yi maka?” Sauke ajiyar zuciya kawai ya yi ba tare da ya bawa Daddy amsa ba, Daddyn ma bai sake tambayarsa ba dan yasan halinsa idan ya yi fushi ba ya magana. Sun ɗauki kusan 5mins a haka kafin Daddy ya ce “Daman maganar yarinyar General Kabeer ce da ka je ka gani, Inason na sani idan ta yi maka” Tashi ya yi ya ce“Ta yi Daddy, Duk abin da ka yanke shikenan” Murmushi Daddy ya yi ya ce“To Alhamdulillah, Daman mun yi magana dashi, In sha Allah zuwa gobe sai a je a kai kuɗi da kayan saka da rana” Okay kawai Zayyad ya ce sannan ya nufi upstairs abin sa, Daddy ya bisa idanu sai kuma ya sauke ajiyar zuciya. Yana shiga ɗaki ya zare agogon hannunsa ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi. “Bana son ka sake zuwa ƙofar gidanmu, Ummata ta ce zata kai ni wajen maza kuma saboda ka zo ne, Dan girman Allah kar ke sake zuwa in da nake” Ya runtse idanunsa tunawa da kalamanta, Haka kawai ya ji ya damu sosai, Tsaki ya yi ya kashe showern ya saka bathrobe ya fito. Pyjames ya ɗauka white colour ya sanya ya feshe jikinsa da turare ya kwanta. Washegari Maitama, Abuja. Tun da ya fara magana take kallonsa ba tare da ta ce komai ba, Sai da ya kai ƙarshe sannan ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Go straight to the point Faruk ka daina min wannan kwana kwanan” ɗan murmushi ya yi sanin halinta ya ce“Nimrah kenan, yanzu duk wannan bayanin dana yi miki baki gane ba?” Nimra dake haɗa tea ta ce“Ni ban fahimci abin da ka ke nufi bane” Numfasawa ya yi ya ce“As i said before Mama ta saka aka nemi yarinyar, To kuma an riga da an samu matsaya, But yarinyar bata da matsala fa, In sha Allah za ku zauna lafiya” Nimra bata san sanda ta saki mug ɗin hannunta ba, Tea ɗin ciki ya zube a wajen. Tashi ta yi tana kallonsa ta ce“Kana nufin za ka aureta ne ka kawota nan gidan as ur wife?” A nutse ya ce“Eh mana in sha Allah” Girgiza kanta ta yi ba ta ce masa komai ba ta bar wajen, Ya bi ta da idanu yana mamakin shirun nata ya tabbata ba haka kawai ba. Tana shiga ɗaki ta ɗauki wayarta, Dialing numbern Deeda ta yi, ringing ɗaya ta ɗauka, Nimra da numfashinta ke up and down ta ce “Ki na ina Dee...?” Deeda dake zaune parlon gidansu ta ce“Ina gida, Lafiya na ji muryaki haka?” Nimrah ta ce “Come to my house please” “Alright I'm on my way” Nimra ta katse kiran, ta zaune gefen gado tana tunanin irin tashin hankali da za ta yi wa Faruk. **** Nayla ce tsaye bakin ƙofar ɗakinsa, Ta tura baki ganin har sannan bai buɗe mata ba, Kamar zata yi kuka ta sake cewa “Yaya Mommah ke kiranka fa” Zayyad dake zaune kan sofa idanunsa a lumshe hannunsa riƙe da bottle ɗin Red snow wine ya kalli ƙofar, Tun da tafara bugun yake jin ta ya yi mata banza. Gajiya Nayla ta yi ganin tana shirin yin late a school ya sanya ta bar apartment ɗin nasa. A dining area ta samu duk yan gidan, Mommah na ganinta ta ce“Kin zauna magana ko?” kamar za ta yi kuka ta ce“Ko buɗe min ƙofa ma bai yi ba kuma nasan yana ji na wallahi” Daddy dake zaune ya ce“Ku rabu dashi naga kamar ransa a ɓace yake” Kallonsa Mommah ta yi ta ce“Me aka masa?” “I don't know but tun jiya na fuskanci akwai abin da aka masa, nd kin san halinsa right” Taɓe baki Momma ta yi ta ce“To Allah ya kyauta". Mommy ta ce“But at least ya kamata a yi magana dashi ko?” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“A'a idan ya gama fushin nasa a yi magana dashi” Murmushi Mommy ta yi ta ce“Allah ya shirya Zayyad” Mommah ta sauke nunfashi ta ce“Ameen ya rabbi” **** Da idanu kawai Salma ke bin Ummar ganin yanda take ta fama haɗa kaya, Fitowa ta yi riƙe da bakko tana kallon Salman ta ce“Ki tashi ki ɗauko hijabinki zamu shige” a sanyaye ta ce“Umma ina zamu je?” Harararta ta yi ta ce“Sai dake zan yi” Tashi Salma ta yi ta shige ɗakinta. Jakar kayanta ta buɗe ta ɗauko hijabi, wani ɗan ƙaramin hoto ne ya fado daga jikin Hijabin, Ɗaukan hoton ta yi, a hankali ta shiga shafa hoton hawaye na zubowa kan idanunta. She wish Ammina na raye, tasan babu yanda za'a yi irin waɗannan abubuwan su dinga faruwa da ita, Sai dai babu yanda ta iya. Ɗaukan hoton ta yi ta riƙe a hannunta ta sanya hijabi sannan ta fito. Tsaye ta samu Umma, Ta kalleta ta ce“Shige mu je” Gaba Salma tayi Umma na bin ta a baya. Suna fitowa ta sanya kwaɗo ta rufe gidan sannan suka nufi hanyar fita daga Kabayin. Abacha road, Mararaba. Girgiza kai Mami ta yi tana kallon Ahmad ta ce“Yanzu shi General ɗin shi ne ya ce zai saka ya auri ƴar abokinsa?” Jinjina kai Ahmad ya yi kana ya ce“Ni Gara haka wallahi Mami, Saboda dama bana son sa da wannan yarinyar Aneeserh, gabaɗaya tarbiyyarta bata min ba” Shiru Mami ta yi sai kuma ta ce“Ikon Allah, a ina yarinyar take?” Gyara zama Ahmad ya yi ya ce“Yar wata minister ce, batada kunya wallahi, But wanda an ce sunan Marigayiya ne da ita Jiddah” Mami ta ce“Tom Allah yasa haka ne mafi Alkhairi, ya basu zaman lafiya” Ameen Ahmad ya ce sannan suka ci gaba da wata hirar. Murmushi Hajiya Jinjin ta yi tana ci gaba da yankan salak ɗin gabanta ta ce“To shikenan sai kin dawo” Umma dake tsaye tana gyara mayafi ta kalleta ta ce“To Allah ya dawo dani lafiya” Ta kalli Salma dake zaune waje ɗaya gefen kujera ta ce“Ke kuma ki zauna lafiya sai Allah ya dawo dani” A sanyaye Salma ta ce“To Umma, Allah ya dawo dake lafiya” Ameen ta ce sannan ta fice daga ɗakin, Hajiya jinjin ta tashi ta bi bayanta. Da idanu Salma ta bi su sai kuma ta zuba tagumi tana tunane -tunane cikin ranta. Asokoro, Abuja. Yammaci ne lokacin, Around 5pm ya tura ƙofar garden ɗin, Zaune ya hangi Daddy kan kujera gabansa a cike da kayan marmari yana ci a hankali, Ƙarasowa Zayyad ya yi ya zauna kujerar dake facing tasa, Murmushi Daddy ya yi yana kallonsa ya ce“Ango” Ɗan murmushi Zayyad ya yi kafin ya ce“Dad!” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“An kai kayan auren sai fatan Allah ya kaimu da rai da lafiya” Ameen kawai Zayyad ya ce sai kuma ya yi shiru. Above 5mins babu wanda ya ce komai a cikinsu, Can Zayyad ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin “Dad daman Inason zamu yi wata magana da kai” Gyara zama Daddy ya yi yana kallonsa sosai ya ce“Ina jin ka” Numfasawa Zayyad ya yi kafin ya ce “Daman ina son takardun Companyn na Khal B. Idan babu damuwa” Shiru Daddy ya yi for some seconds sai kuma ya ce “Did something happens?” Girgiza kai Zayyad ya ce “Not at all Dad, Kawai ina son amfani dasu ne” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Anyway, Zuwa gobe in sha Allah zan saka a kawo sai na miƙa maka” Murmushi Zayyad ya yi ya ce“Thank U Daddy” Shima Murmushi ya mayar masa yana kai Apple bakinsa. Miƙewa tsaye ta yi tana girgiza kanta daga ɗaya ɓangaren aka ce “Yanzu mene abin yi?” Numfasawa Mommah ta yi ta ce “Dole a san abin yi, Ba zai taɓa yiwuwa ba! Ki cewa Malam ina nan zuwa in sha Allah” Murmushi ɗaya matar ta yi ta ce“Daɗina dake kina yin abin da ya kamata, Shikenan sai kin zo” Katse kiran Mommah ta yi, Ta buɗe press ta ɗauko mayafi ta ɗauki handbag ɗinta ta bar ɗakin dan ba ta ga ta zama ba, Dole ne ta je ta san abin yi. # HCD # Light within the darkness # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 13: Nowhere Feels Like Home Nanameera, YOTA/023. Kusan sati ɗaya kenan da tafiyar Umma Rahmatu kuma har yanzu bata dawo ba, Gabaɗaya Salma ba jin daɗin zaman gidan take ba, Koda yaushe sai dai ta zauna ita kaɗai tana tunane-tunane. Wasu lokutan kuma su zauna tare da Khadijah ɗiyar Hajiya Jinjin tana bata labarin irin rayuwar da ake a Abuja. Yau ma kamar kullum suna zaune cikin ɗakin Khadijah gefen katifa tana ɓarar gyaɗa ta kalli Salman ta ce “Anjima zan bar gida fa, Ko za ki rakani?” Girgiza kai Salma ta yi a sanyaye ta ce“A'a ina jiran Ummana ta dawo mu koma gida, Ina son na ci gaba da zuwa makaranta” Taɓe baki Khadijah ta yi ta ce“Ikon Allah, Ai sai ki yi ta zama a nan ke kaɗai, Ko ki samu Ummana ta samar miki wani alhajin yanda ki ke farar nan kuɗi zasu dinga baki ba kaɗan ba wallahi” Shiru Salma ta yi maganganun Abbanta suka shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya, Ta sunkuyar da kanta kawai. Tashi Khadeejah ta yi dan lokacin guraren la'asar ne ta fice daga ɗakin, A tsakar gida ta samu Hajiya Jinjin tana sharar, Ta kalleta ta ce“Umma wai yaushe Ummar Salma zata dawo?” Ajiye tsintsiyar Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Mene naki na son sani?” Girgiza kai Khadijah ta yi ta ce“Babu komai fa, Kawai dai inason sani ne, Na ce mata ta zo mu tafi Abuja tare wai ba zata je ba ita Ummar ta take jira” Jin jina kai Hajiya ta yi kafin ta ɗaga labulen ɗakin tana cewa“Salma, Salma” Fitowa Salma ta yi tana kallonta ta ce“Umma gani” “Ki shirya ku tafi tare da Khadijah mana” Zaro idanu Salma ta yi, Ganin ta yi shiru yasa Hajiya ta ce“Ko baki ji ba?” Sunkuyar da kanta ta yi tana cewa“A'a Hajiya ni bana son zuwa wallahi, Ummana zan jira” Taɓe baki Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Tun da ta ce miki dawowa zata yi?” Tura baki Salma ta yi bata ce komai ba. Khadijah da take son Salman ta bita ta kalleta ta ce“Da zaman da zaki yi ke ɗaya ba Gara ki bini ba Salma?” Maƙe kafaɗa Salma ta sake yi ta ce“Ni A'a” Ta yi maganar a shagwaɓe. Shiru Khadijah ta yi, Hajiya Jinjin ta ce“Ke shige ki yi wanka ki zo ki tafi ki bar wannan” To kawai Khadijah ta ce ta ƙarasa inda bokiti ke ajiye ta ɗiba ruwa ta yi hanyar banɗaki. Harararta Hajiya Jinjin ta yi ta ce“Sai ki nemi waje ki dawwama a nan, Kuma sai ki samu wanda zai dinga ciyar dake, Tun da nasan kina da labarin ubanki bai bar miki komai ba!” Shiru Salma ta yi har sannan kanta yana sunkuye, Hajiya Jinjin ta shige ɗaki ta barta nan tsaye. A hankali ta sanya hannunta tana goge hawayen da suka zubo kan kuncinta. Above 10mins tana tsaye a wajen har Khadijah ta fito daga wanka, Ta kalleta bata ce mata komai ba ta shige ɗaki. Hanyar waje ta nufa dan daman akwai hijabin Khadijah jikinta, Kai tsaye kuma ta nufi cikin Kabayi in da zai sadata da gidansu. Asokoro, Abuja. Murmushi Momma ta yi tana kallonsa ta ce“Yanzu yaushe zaka je Companyn? Ko kai fa Zayyad, Ka amshi girman daya zo maka ka daina shashanci dan Allah” Langwaɓar da kansa ya yi yana bayan ya yi sipping tea ɗin dake hannunsa ya ce“Tom Mommah, Na zama serious yanzu shikenan kin ji daɗi?” Gyaɗa masa kai ta yi tana kallonsa fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce“Irin daɗin dana ji ba zai faɗu ba Muhammadu, Kai dai Allah ya yi maka Albarka” Murmushi ya yi ya ce“Ameen Mommah na” “Yanzu when zaku haɗu da Ahmad ɗin?” Tashi tsaye ya yi kafin ya ce“Ai yanzu ma zan je Mararaban in sha Allah, Sai mu yi maganar acan” Mommah ta ce“Yawwa to gara hakan, Ka gaida min da Mami ka ce ina nan zan zo mu yi maganar” “Maganar mene Mommah?” Ya faɗa yana ɗaga mata gira, Harararsa ta yi tana murmushi ta ce“Gulma to ba zaka ji ba, Tafiyarka” Langwaɓar da kansa yayi yace“Idan na je na tambayi Mami na san ita zata faɗa min” Jin jina kai Mommah ta yi ta ce“Ta faɗa makan kun fi kusa” Fita ya yi daga ɗakin yana murmushi. Ta sauke ajiyar zuciya tana sake godewa Allah, a kwanakin nan Zayyad ya nutsu sosai, Ko fitar dare baya yi, da wuri yake kwanciyarsa daya tashi kuma ya tafi asibiti. A main parlon ya tarar da Daddy da Mommy suna magana, Tana ganinsa ta saki murmushi tana faɗin “Babban mutum an fito?” Gyada mata kai ya yi, Daddy ya ce“Ina kuma zaka je?” Murmushi Zayyad ya yi ya ce“Zamu yi magana da Ahmad ne, Ba daɗewa zan yi ba Dad” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Ya maganar Jidda kana zuwa wajenta kuwa?” kwaɓe fuska ya yi ya ce“But Dad me zan je nayi? Tana kirana a waya ina amsawa, So kwana biyu kuma I'm very busy shiyasa” Daddy ya kalleshi sosai sai kuma ya ce“But at least ya kamata a ce kana zuwa kuna gaisawa ka ji” Kofa ya nufa yana ɗagawa Daddy kai. Da idanu kawai Daddy ya bi sa sai kuma ya yi murmushi, Sai da ya fita sannan ya juyo da ganinsa wajen Mommy yana cewa “Zayyad ya fara hankali gaskiya, Shiyasa nake ce muku ku rabu dashi da kansa zai gane ya girma” Ɗan murmushi Mommy ta yi ta ce “Ai kam dai gaskiya, Dan ko Khalil ya ce min yana abin da ya kamata a asibiti saɓanin kwanakin baya” Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya ce“Allah abun godiya, Allah ya ƙara shirya mana ya'ya” Murmushi Mommy ta yi ta ce“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”. Yana shirin shiga motarsa wayarsa ta fara ringing, kallon screen ɗin ya yi ya ɗaga ya kai kunnensa, daga ɗaya ɓangaren ta ce “Bae” “Uhm” Ya bata amsa kamar mai ciwon haƙuri. Tashi zaune Anisa ta yi a shagwaɓe ta ce “Where are u ne?” Buɗe motarsa ya yi ya shiga yana cewa “Like how Anisa? Ina nan mana” “But you left me, why are u ignoring me?” Anisa ta yi maganar cike da damuwa. Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya ce “Nothing serious, Kawai I'm busy ne shiyasa, But zan zo anjima idan na dawo” Ba dan ranta ya so ba ta ce “Alright, I'll wait for you” Jin jina kai ya yi kamar tana gabansa ya ce “Okay” “Love you bae” “Same” Ya faɗa a taƙaice sannan ya kashe wayar. Ajiyar zuciya Anisa ta sauke ta sauke wayar tana kallon screen ɗin, Feedy dake gefenta ta ce “Baki ga kamar Zayyad ya sauya ba?” “I think so” Anisa ta faɗa a matuƙar dame. Taɓe baki Feedy ta yi kafin ta ce“Maybe fa ya samu wata ne shi ne yake miki hanya hanya, Kin san halin maza irin su” Girgiza kai Anisa ta yi ta ce“Zayyad ba zai taɓa yimin haka ba na rantse miki. Kawai dai he has been busy ne kamar yanda ya ce, Kuma nasan tun da ya ce zai zo zai zo ɗin” Jinjina kai Feedy ta yi ganin yanda Anisa ta koma ta ce“Shikenan kwantar da hankalinki, Yanzu ki tashi ki yi wanka ki tafi gida” Numfasawa ta yi kafin ta ce“Eh daman yanzu zan tafi coz Daddy ya je Kano kuma nasan Maybe yanzu ya dawo, Ina son ya sameni a gida”. Okay Feedy ta ce tana danna wayarta, Anisa ta tashi ta shige toilet ɗin hotel ɗin. **** A hankali ta shiga tura ƙofar ɗakin, kwance ta hangeta can ƙarshen gado ta yi ruf da ciki. Ta ƙarasa a hankali ta zauna gefenta “Jiddah” Saurin ɗago kanta ta yi, Ta tashi zaune tana jan ɗankwalin Abayar jikinta ta ce “Na'am Mum” “Na something wrong with you Jiddah?” Murmushi ta yi tana kallon Mum ta ce “Babu komai fa Mummy, I'm fine, Kawai bacci nake ɗan ji” Girgiza kai Mummy ta yi ta ce“Ko zaki ɓoyewa wani abu ban dani Jiddah, Saboda ni na haifeki. Na lura tun da aka fara maganar aurenku da Zayyad ki ka sauya, Akwai wata matsala ne? Ko baki son sa?” Girgiza kai Jidda ta yi, Ta tashi ta dawo kusa da Mamarta ta ɗora kanta bisa cinyarta kawai sai ta fashe da kuka. Da matuƙar mamaki Mummy ke kallonta, Ta shafa kanta murya a sanyaye ta ce “Ki daina kukan nan dan Allah Jiddah, Kar wani abun ya sameki, Tashi ki faɗa min meke faruwa?” Kasa magana Jiddah ta yi sai kuka take a hankali, Sosai Mummy ta damu gudun kada wani ciwon ya tayar mata, Sai da ta gaji dan kanta sannan tafara sauke ajiyar zuciya a hankali. Ɗago kanta Mummy ta yi ta zuba mata idanu, Sunkuyar da kai Jidda ta yi Mummy ta ce a nutse “Hauwa'u” Muryarta na rawa ta ce “Na....Na'am Mummy” “Faɗa min abin da yake damunki, Idan auren Zayyad ne baki so ki sanar dani, Tun da magana bata yi nisa ba a fasa, Koda an ɗaura auren ne ana iya fasawa. But ki daina wannan kukan bayan kin san condition ɗinki, Dan Allah karki saka mu a matsala” Hannunta ta sanya ta goge hawayen da suka sake zubo mata. Cikin cool voice ɗinta ta ce “Babu komai Mummy, Kawai nafara kewarku ne, Sai nake jin daman ba'a fara maganar auren nan ba” Murmushi kawai Mummy ta yi sanin halin Yar tata ta ce “Ba zaki sanar dani ba kenan? Anyway, Ki tashi magrib ya kusa za ku je shopping ke da Kausar” Langwaɓar da kanta ta yi ta ce“Ayyah Mum ta je ita kaɗai mana, Wallahi ƙafata ciwo yake min” Shiru Mummy ta yi tana kallonta, Ganin haka ya sanya Jidda sunkuyar da kanta tana murmushi. Tashi Mummy ta yi ta ce“Ki shirya nafaɗa miki, Bana son ku yi dare, Sannan make sure da ruwan zafi ki ka yi wanka, Ki saka kaya mai nauyi okay?” Gyaɗa kanta ta yi Mummy ta juya ta bar ɗakin. Sai da Jidda ta ga ta tafi sannan ta sake fashewa da wani sabon kukan ta kwanta gefen gadon tana rera abin ta, Ita kaɗai ta san masifar da take ciki yanzun. Mararaba, Nassarawa. A buɗe Salma ta ga ƙofar gidan nasu, Mamaki ya isheta, Daman Umma ta dawo kenan bata faɗa mata ba? Me yasa zata kai ta gidan Hajiya Jin jin ajiya? Ko dai wata matsalar ta faru? Ita kaɗai ta dinga sake saƙe a ranta. Ganin tsaiwar Tata bata da amfani ya sanya kawai ta saka kanta cikin gidan bakinta ɗauke da sallama. Turus ta yi ganin wasu yara guda biyu mace da namiji a tsakar gidan suna wasa, Ita dai tun da take a rayuwarta bata taɓa ganin yaran ba. Ta sake sallama ganin kamar ba'a ji ba. Wata mata ce ta fito daga ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi ta ce “Wa'alaiki assalam, Maraba” Salma da mamaki ya gama cikata ta ƙirƙiri murmushi ta ce“Ina yini?” Matar wadda ta kasance mai sakin fuska ta ce“Lafiya klao” Shiru Salma ta ɗan yi can kuma ta ce“Ina Umma take?" Da mamaki matar ta ce“Wace Umma?” Salma ta ɗan yi shiru kafin a sanyaye ta ce“Matar gidan nan, Naga an buɗe gidan nan to inaga ta dawo. Daman kayana nazo ɗauka” Girgiza kai Matar tayi ta ce“Ikon Allah, To ina ga ko gidan kusa da shi ne, Amma ni ce matar gidan nan, Yau kwananmu huɗu da tarewa, siyansa mukayi” Mutuwar tsaye Salma ta yi tana kallon matar, Gaba ɗaya tunaninta ya kwance, Ta kasa gane in da matar ta dosa. Wane gidan suka siya? Yaushe? A hannun wa? Ganin ta yi shiru ya sanya matar ta ce“Ki shiga maƙotan nan ko nan ne gidan, Amma nan gidan babu wata Umma” Salma bata sake cewa komai ba ta juya ta fita daga gidan tana tafiya a sanyaye. Har ta kai bakin titin Kabayi bata sani ba, Dan tafiya take amma gaba ɗaya tunaninta da hankalinta sun yi ƙaura daga gangar jikinta, Maganganun matar ne kawai ke yawo cikin kanta, Sai saƙawa take tana warwarewa. Ta rasa ta inda zata fara haɗa tunaninta, Bata yi aune ba taji zubar ruwa akanta, Dan ko kaɗan idanunta basu gane mata hadari ba, Ta ci gaba da tafiya a hankali har ta ƙarasa gidan Hajiya Jinjin. Tsaye ta sameta tsakar gida tana tara kayan ruwa, Khadijah kuma na gyara ɗaurin ɗankwali dan ruwan ba sosai yake zuba ba. Ko sallama Salma bata iya yi ba haka suka ganta tsakar gidan kamar an jefota. “Au ai nayi tunanin zuciya ki ka yi, Ki ka kama gabanki” Hajiya Jinjin ta yi maganar tana kallon Salma, Khadijah ce ta ce“Ina ki ka je ke kuma?” Murya na rawa Salma ta ce “Um...Umma dan Allah ina Ummata take? Ina ta je? Yaushe zata dawo? Naje gidanmu naga wasu mutane a ciki, Kuma sun ce basu santa ba, Ki faɗa min yaushe zata dawo?” Salma ta ƙare maganar hawaye na sintiri kan fuskarta. Shiru Hajiya Jinjin ta yi tana kallonta, Can kuma ta ce “Au da gidan naku ki ka tafi kenan? To ai bari ki ji ke da wannan gidan sai dai a lahira idan ana shigarsa. Saboda Rahmatu ta siyar dashi, Ba iya shi kaɗai ba duk wani abu da ki ka sani na cikin gidan ta haɗa dashi ta siyar, Ta kuma tattara kuɗaɗen da sauran waɗannan kudaden na wajenki ta bar garin nan, Tana can ta buɗe sabuwar rayuwa ta samu miji zata yi aurenta. Cewa tayi zata kore ki ni nan na ƙi bari na ce ta kawo ki na riƙe ki, Idan Khadijah zata tafi ku dinga tafiya tare Abujan, Gara ma ki nutsu ki san me ki ke yi! Yanzu babu wani Abu naki ko na ubanki, Kuma kin sani cewa ubanki bashi da wani dangi a garin nan zuwo ne ba'a san daga inda yake, Haka itama mahaifiyar taki, Haka suka zo kamar korarru!”. # HCD # Light within the darkness # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* https://chat.whatsapp.com/GSEDyyyzuMm3woohSiin9W?mode=ac_t Chapter 14: Rescued by Fate Nanameera, YOTA/23. Hajiya Jinjin ta ƙare maganar tana zabga mata wata uwar harara, Ba Salma kaɗai ba har Khadijah sai da ta kalli mahaifiyarta, Koda wasa bata yi tunanin Umma Rahmatu tafiyarta ta yi ta bar Salma ba, Duk zatonta taje ta dawo ne kamar yanda ta faɗa. Salma kasa cewa komai ta yi, Sai bin ta take da kallo, Hajiya Jinjin ta ja hannun Khadijah suka shige ɗaki. Sai a sannan Salma ta fashe da wani irin raunataccen kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, Yanzu ina zata je? Wa zata kalla taji daɗi? Da wa zata yi rayuwa? Babu dangi babu ƙawaye babu wanda tasani a rayuwarta, Ina zata nufa??. Ta durƙushe a tsakar gidan ba tare da ta damu da jiƙewarsa ba tana ci gaba da kuka. Ta ɗauki mintuna a wajen kafin Khadijah ta fito daga ɗakin sanye da mayafi ta ci uwar kwalliya, Ta ƙaraso gabanta kamar ta shigeta sai kuma ta ce “Da kin zo mun tafi tare Salma, Tun da babu in da zaki je yanzu” Ɗago kanta Salma ta yi ta kalli Khadijah sai kuma ta girgiza kanta bakinta na rawa ta ce“Ni ba zan je ba” “Kin gwammaci ki dinga yawo a gari Salma?” Khadijah ta tambayeta. Kafin ta bata amsa Hajiya Jinjin ta fito daga ɗaki tana kallonsu ta ce“Ke shige ki tafi abin da ke gabanki dare nayi, Ke kuma ki tashi ki bar gidan nan tun da ba za'a yi abun arziki dake ba wallahi ba zan iya ciyar dake ba, Ƴata ma bata zauna ina ciyar da ita ba ballantana ke da babu abin da ya haɗani dake!” Ta ƙare maganar idanunta kan Salma. Girgiza kai Khadijah ta yi duk sai ta ji bata ji daɗi ba, A sanyaye ta ce“Umma ki bari mana, Zata tashi” Harararta Hajiya Jinjin tayi ta ce“Kin shige kin bar gidan nan ko sai ranki ya ɓaci kema” Tura baki Khadijah ta yi ta fice daga gidan tana waiwayen Salma. Sake daka mata tsawa Jinjin tayi Salma ta tashi jikinta na rawa ta yi hanyar ɗakin da suke. “Akwai abin da ki ka ajiye a nan ne da ki ke nema?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Abuna zan ɗauka” Daga haka ta shige ɗakin, Bata fi minti biyu ba ta fito har sannan kuka take tayi waje jiki a sanyaye, Hajiya Jinjin ta bita da harara sai kuma ta yi tsaki ta ce“Gayyar tsiya!” Yayyafi ake har sannan, gabaɗaya babu mutane a bakin titin Kabayin kasancewar dare ya fara yi kowa ya kama gabansa, Cikin wannan yanayi take tafiya a hankali jikinta na wata irin rawar sanyi, Tafiya kawai take ba tare da ta san inda ta nufa ba, Batasan kowa ba, Bata san ko ina ba, Babu wani wanda zata ce wannan danginta ne balle taje gidansu. Gajiya ta yi da tafiyar ta nemi dakalin wani gida ta zauna tana mai da numfashi, Zuwa sannan ko kukan ta gagara yi sai ajiyar zuciya take saukewa akai akai. Abacha road, Mararaba. Leƙo kansa ya yi yana kallonsa ya ce“Yanzu ka kwana ka ke ganin asara? Ba gobe sai mu tafi tare ba” Zayyad dake danna wayarsa ya ce“Look ba zan iya kwana ba, Yanzu fa ba wani dare ne ya yi ba, And kuma nayi wa Anisa alƙawarin zamu haɗu” Da mamaki Ahmad ya ce“Anisa kuma? Meya haɗaka da Anisa Zayyad?” Ɗago kansa ya yi ya kalleshi bai ce komai ba. Ahmad ya girgiza kansa kafin ya ce“But kasan abin da kake ba dai dai bane right? Bayan an saka ranar aurenka da wata matar amma ka ci gaba da kula wata, Kuma kasan ba aurenta zaka yi ba” Tsaki Zayyad ya yi sannan ya ce“Zaka fara ko? To ba wani abun zan je yi wajenta ba zan faɗa mata gaskiya ne, Sai ka kwantar da hankalinka” Murmushi Ahmad ya yi dan ba ƙaramin daɗi ya ji ba ya ce“Ai dole hankalina ya tashi, Shikenan ka je amma dan Allah daga bata haƙurin kar ka sake wani abu” Kallon sheƙeke Zayyad ya masa kafin ya ce“Wani abu like how?” Girgiza kai Ahmad ya yi yace“Calm down, Ka gaida Mommah da Nayla” A can maƙoshi Zayyad ya ce“I'll” Ahmad ya janye kansa daga motar yana ɗaga masa hannu, Zayyad ya yi reverse ya bar ƙofar gidan. Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke sai kuma ya girgiza kansa, Ya juya ya shige cikin gida. Yana kan titin Orange market wani irin ruwa ya kece, Yanda ruwan yake zuba da matuƙar yawa ya sanya ba zai iya ci gaba da tafiya ba, Ya nemi gefe ɗaya ya yi parking yana ɗan tsaki a hankali. Idan da abin da Zayyad ya tsana a rayuwarsa bai shige zubar ruwan sama ba, Gaba ɗaya ya ji baya jin daɗin zaman motar. Kwalin cigarette ya ɗauko ya kunna da lighter ya fara zuƙa yana furzar da hayaƙin a hankali, Yana nan zaune sai da ya shanye tsinke uku kafin ya haƙura ya jingina da jikin motar yana jin yanda ruwan yake zuba kamar da bakin ƙwarya. Kamar wanda aka tsikara haka ya buɗe idanunsa, Haka kawai ya ji ta faɗo masa a rai, Kallon agogon hannunsa ya yi yaga karfe 8 har da 12 na dare, Ya sauke ajiyar zuciya sai kuma ya kunna motar ya ci gaba da tafiya, Yana zuwa bakin titin Kabayi ya tsaya yana kallon hanyar, Ko ina a jagwalgwale yake ya ɗan yi tsaki kafin ya danna motar cikin layin, A ƙofar gidansu ya yi parking ya yi shiru yana kallon gidan kafin ya sakko daga motar, Zuwa sannan kuma ƙarfin ruwan ya ragu sai yayyafi a hankali. Tsayawa ya yi yana tunanin yaron da zai samu ya kira masa ita sai ga wani mutumi ya tawo daga hanyar masallaci hannunsa riƙe da carbi. Da mamaki Zayyad ya kalleshi dan iya saninsa babu namiji a gidan, Mutumin ya tsaya shima yana mamakin ganinsa a ƙofar gidansa. Ƙarasowa ya yi suka gaisa kafin Zayyad ya ce“Sannu Malam" Mutumin ya yi murmushi ya ce“Yawwa Alhaji, Lafiya dai?” Zayyad ya ce“Salma nake kira yarinyar nan gidan?” Ya faɗa yana nuna kofar gidan, Shiru mutumin ya yi sai kuma ya ce“Allah sarki, Ai ko sun tashi, Dan yanzu ni ne a gidan na siya a hannun wata mata”. Sosai Zayyad ya yi mamaki amma ya ce“Allah sarki, Ko kasan in da suka koma?" Girgiza kai ya yi ya ce“A'a wallahi ban sani ba, Dan ban ma taɓa ganinsu ba” Jinjina kai Zayyad ya yi ya sake bashi hannu suka gaisa ya ce“Tom Nagode sai an jima” Murmushi mutumin ya yi ya ce“Nima haka, A sauka lafiya” Zayyad ya juya ya shige motarsa yana mamakin al'amarin. Har ya fito titi tunanin maganar da mutumin ya faɗa masa yake, To ina suka koma? Me yasa bata sanar dashi ba? Taɓe bakinsa ya yi tunawar ba wata alaƙa ba ce tsakaninsu ballantana har ta sanar dashi abin da suke ciki. Saurin taka burki ya yi, Ya tsaya yana kallon ikon Allah, fitilun motar ya kunna ya dallaresu da idanu, Hannayensu suka saka suka shiga rufe fuskarsu. Maza ne su uku sai mace guda ɗaya, Tsaki Zayyad ya yi a fili ya ce“Nonsense” Daga haka ya kunna motarsa yana ƙoƙarin barin wajen ya ji ihun yarinyar, Har zai shige sai kuma ya tsaya. A hankali ya fito daga motar yana kallon in da suke, Gaba ɗaya sun yi rumfa sun saka yarinyar a tsakiya sai ihu take, Ya ƙarasa gabansu ya jawo rigar ɗaya daga cikinsu. Juyowa suka yi duka, Da alama ma duk a buge suke, Yarinyar na ganin haka ta ɗago fuskarta. Da wani irin mamaki Zayyad ke Kallonta, Ita kuwa ko lura da waye ma bata yi ba, Ta rufe fuskarta tana ci gaba da kuka har sannan, Hannunta ɗaya ya riƙe ganin tana ƙoƙarin guduwa. Ta sake fashewa da kuka tana ƙoƙarin kwace hannun nata, Ji tayi an janyeta gaba ɗaya ya riƙeta sosai har sannan idanunsa na kansu. Tsaki mutumin ya yi ya kawo hannunsa yana shirin kwaceta, Murɗe masa hannu Zayyad ya yi ya saki wani razanannen ihu yana yarfe hannu, Ji ka ke ƙas wanda ke alamta cewa ya ƙarya masa hannun, Saurin ja da baya sauran suka yi, Ya hankaɗashi yana masa wani irin shegen kallo. Durƙushewa ya yi a wajen yana birgima ya riƙe hannun da ɗayan hannun, Salma data gama tsorata ta sake ƙamkameshi tana sakin wani irin kuka, Jan hannunta ya yi ya koma in da ya yi parking motarsa ya buɗe front seat ya sakata sannan ya zagaya ya shiga motar shima, Bai ko kalli in da take ba ya ja motar ya ci gaba da tafiya. Sai da suka shigo garin Abuja around 9:20pm sannan ya samu gefen titi ya yi parking jin yanda take kuka a hankali. Furzar da iska ya yi daga bakinsa jin yanda take neman damunsa ya ce“Ko kimin shiru ko kuma ki saukar min a mota” A matuƙar razane ta ɗago kanta tana kallonsa, Ya kalleta fuskarta ta yi caɓa caɓa da hawaye da majina, Girgiza kanta ta shiga yi ƙoƙarin yin magana take amma kukan da take ya hanata. A nutse ya ce“Yau kuma mene ya haɗa ki da maza?” Shiru ta yi masa tana ci gaba da kukanta, Sosai ransa ya ɓaci dan ya tsani ya yiwa mutum magana ya ƙi bashi amsa. Ya sanya hannunsa ya jawota har suna iya jin nunfashi juna murya a dake ya ce“Baki ji me nace miki bane?” Madadin ta bashi amsa sai kuma ta faɗa jikinsa ta fashe da wani sabon kukan, Shiru Zayyad ya yi jin yanda ta zagaye hannayenta a jikinsa gabaɗaya ta ɓata masa gaban riga da majina da hawaye. Shiru Zayyad ya yi yana kallonta, Ta ɗauki lokaci mai tsawo tana kukan kafin ta fara sauke ajiyar zuciya a hankali, Sai a sannan ya shafa kanta ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“Ya isa haka, Yi shiru kin ji” Yanda ya yi maganar ya sanyata sake fashewa da wani sabon kukan, Ta rufe fuskarta a ƙirjinsa. Murmushi ya yi ya ce“Oh dan na baki haƙuri shi ne ki ka ci gaba?” Ta yi shiru bata ce masa komai ba. Ganin ta yi shiru ya sanya ya leƙa fuskarta ya ce“To sakeni mana” Kunya ce ta rufeta, Ta yi saurin ɗaga shi ta koma gefe tana sunkuyar da kanta. Girgiza kai kawai Zayyad ya yi ya gyara zamansa yana kallonta ya ce“Now tell me what happened? Me ki ke yi a waje da daddare? Meya samu gidanku?” Saurin kallonsa ta yi hawaye na sake zubowa kan fuskarta “Kar na sake tambayarki” Turo baki ta yi, Cikin shassheƙar kuka ta ce“Ummana ce ta tafi ta barni, Ta siyar da gidan, Yanzu banida kowa kuma ban san inda zan je ba. Shi ne na fito titi na haɗu da waɗanda mutanen suka ce zasu samar mini gidan da zan dinga yin aikatau sai na dinga kwana acan, Kuma shi ne suke...” Kuka ya sake kwace mata. Shiru Zayyad ya yi ya zuba mata idanu, Can kuma ya ce“A saboda ke yarinta da wawta ya miki yawa ya sanya ki ka yarda da wasu maza za su samar miki aiki a cikin dare?, Stupid!” Ya ƙare maganar yana harararta. Ɗan kallonsa ta yi sai kuma ta ɗauke kanta tana kuka ta ce“To ya zan yi ni? A ina zan zauna? Dole na yarda dasu” Jinjina kansa ya yi ya ce“Eh kam dole ki yarda dasu, To sannunki, Kin yi ƙokari” Ya yi siririn tsaki sannan ya tada motar suka ci gaba da tafiya. A cikin compound ɗin gidan ya yi parking bayan an buɗe masa ƙaton gate ɗin gidan, Ita dai Salma sai bin ko ina take da kallo as if her life defend on it. Sauka ya yi daga motar ya zagayo inda take ya buɗe yana kallonta ya ce“Idan kin gama kallon sai ki sakko” Sosai ta ji kunya sai kai ta tura baki ta sakko daga motar, Mayar da ƙofar ya yi ya rufe sannan ya nufi hanyar entrance na gidan, Duk in da taga Zayyad ya yi ita ma nan take yi. Kai tsaye ɗakin Nayla ya shiga, Zaune ya sameta tsakiyar gado tana sanye a wasu riga da wando marasa nauyi kanta sanye da hular Chantilly tana danna system ɗin gabanta. Tana ganinsa ta rufe system ɗin tana murmushi ta ce“Yaya ka dawo?” Zama ya yi gefenta ya ce“Ƴar ƙanwata na dawo, Ya school?” Sakar baki Nayla ta yi tana kallonsa jin yanda yake mata magana kamar ba shi ba. Ta yi murmushi ta ce“Alhamdulilah Yaya, Daman ina da Assignment ɗan Allah zaka yimin?” Jinjina kansa ya yi ya ce“Bring it out” Sauka ta yi daga kan gadon tana murmushi ta nufi dresser ɗinta, Handout ɗin ta ɗauko da kuma plain sheet ɗin ta kawo masa, Karɓa ya yi ya ce“Shikenan zan yi miki zuwa da safe” Dariya ta yi ta ce“Shiyasa nake sonka Yayana Thank you” “Have a seat, let's talk” Ya faɗa yana nuna mata gefensa, Zama ta yi ta ɗora hannayenta kan cheeks ɗinta ta ce“Ina ji" Numfasawa ya yi kafin ya ce“Daman na kawo sabuwar baƙuwa ne, Zata dinga aiki a gidan nan, abin da nakeso dake da safe ki je apartment ɗin Maids ki ce musu su ce su suka zo da ita, Su zo wajen Mommah su kawota, But for now Inason ta kwana tare da ke” Waro idanunta ta yi sai kuma ta ce“Yaya ni zan kwana da maid ɗin kuma? Na kai ta dai ɗakinsu Habiba ta kwana” Girgiza kansa ya yi ya ce“Nan nakeson ta kwana” Tura baki Nayla ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Shikenan tana ina?” Da hannu ya nuna mata parlon sannan ya tashi ya ce“Mu je ki ganta” Tashi ta yi tabi bayansa suka fita daga ɗakin. Tsaye suka sami Salma ta juya musu baya hannunta rufe kan fuskarta da alama wani sabon kukan take. “Keee!” Zayyad ya kirata daga inda yake tsaye, Juyowa ta yi ta sauke hannunta tana kallonsa hawaye na bin fuskarta.. “Salma!” Nayla ta kira sunanta da mamaki, Zura mata idanu Salma ta yi can kuma ta gano inda ta taɓa ganinta, Da mamaki Zayyad ke kallon Nayla kafin ya ce“Then u know her?” Gyaɗa masa kai Nayla ta yi ta ce“Na santa Yaya, Na santa a Mararaba, Ita ce wadda nake baka labari fa, Ina ka santa Yaya? A ina ka samota?” Nayla ta jera masa tambayoyin, Ɗan tsaki ya yi ya ce“Zaki nutsu ko kuma za ki ci gaba da tambayar?” Shiru ta yi tana kallonsa ya kalli Salma ya ce“Mahaifinta ne ya rasu, So tana buƙatar taimako shiyasa na kawota nan gidan. But tun da ma kin santa shikenan komai ya zo da sauƙi, Ku zauna tare zuwa da safe sai ki je ki yi introducing ɗinta gurin Mommah” Nayla da jikinta ya yi sanyi ta ce“Tom yaya in sha Allah” Jan kumatunta ya yi ya ce“Good gal, Sai da safe” Daga haka ya juya ya bar parlon, Salma ta bi shi da kallo. Kamo hannunta Nayla ta yi tana cewa“Zo mu shiga ciki Salma”. Koda suka shiga ɗakin ta nuna mata gefen gado tana cewa“Zauna kin ji” Zama Salma ta yi Nayla ta zauna gefenta fuskarta a kwaɓe kamar zata yi kuka ta ce“Allah sarki, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Salma. Ki yi haƙuri kin ji” Ta ƙare maganar tana dafata. Duk yanda Salma ta so ɓoye hawayenta kasawa ta yi, In dai an yi maganar Abbanta to sai ta zubar da hawaye, tana goge hawayenta ta ce“Ameen Ya Allah, Nagode sosai” Ɗan murmushi Nayla ta yi ta ce“Ki bar min godiya, Na dinga bada labarin ki. Amma yanzu tashi ki yi wanka ki sauya kaya” Bata jira cewarta ba ta shige toilet. Salma na toilet ta ji ana knocking ƙofar, Saurin wanke fuskarta ta yi ta fito sanye da towel ta nufi kofar duk a tunaninta Nayla ce, Dan taje kawo mata abinci. Turus ta yi ganin wanda yake tsaye, Ta kalleshi taga kallonta yake, Saurin kallon jikinta ta yi sai kuma ta saki wani irin ihu, Saurin yar da ledar hannunsa ya yi ya rufe mata baki, Ƙoƙarin kwace bakinta ta shiga yi yaƙi sakinta ya ƙarasa shiga ɗakin ya rufe ƙofar. Sai a sannan ya saketa yana mata wani kallo ya ce“Baki da hankali ne?” Durƙushewa ta yi wajen ta fashe da kuka kamar wanda aka mata wani abun. Tsaki ya yi sannan ya jawo kanta yana kallonta ya ce“Wani abun nayi miki?” Cikin shassheƙar kuka Salma ta ce “To ai babu kyau ganin tsirarar mutum!”. *Second to the last free page, HASKEN CIKIN DUHU isn't free it's ₦700 via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay, evidence via 08106608363, Ki biya ki karanta cikin salama❤️* # HCD # Light within the darkness # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU💋💋* Chapter 15: Exiled With the Mad Nanameera, YOTA/023. Wani irin kallon kin zama mahaukaciya ya yi mata kafin ya ja dogon tsaki, Bai sake bi ta kanta ba ya juya ya buɗe ƙofar ɗakin, Tsaye ya ga Nayla tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ita ma. Ta kalleshi bai ce komai ba ya ratsa ta gefenta ya bar parlon gaba ɗaya, Da idanu kawai ta bi shi sai kuma ta girgiza kanta ta shige ɗaki. Durƙushe ta samu Salma har sannan kuma shassheƙar kuka take, Da sauri Nayla ta ƙarasa gabanta cikin tashin hankali ta ce“Lafiya Salma? Meya faru?” Shiru Salma ta yi ba tare da ta bata amsa ba, Ta miƙe tsaye ta koma toilet ɗin. Da idanu Nayla ta bita tana mamakin abin da ya sanyata kukan, Tana nan zaune har Salma ta fito amma wannan karan jikinta sanye da hijabinta, Duk da kasancewarsa a jiƙe. Tashi Nayla ta yi tana kallonta ta ce“Ya zaki saka hijab jiƙaƙƙe?, Bari na baki kaya” Ita dai Salma ba ta ce komai ba ta ja ta tsaya a wajen. Press Nayla ta buɗe ta ɗauko mata wata sleeping dress mara nauyi. Miƙa mata ta yi Salma ta karɓa sannan ta koma toilet ɗin, Bata jima ba ta fito bayan ta sauya zuwa rigar baccin wadda ta yi mata kyau sosai. Murmushi Nayla ta yi tana riƙe hannunta ta ce “Wow kin yi kyau sosai, Zo ki ci abinci” Ɗan murmushi Salma ta yi tana ci gaba da kallon Nayla. Sakin hannunta ta yi ta ƙarasa in da ta ajiye tray ɗin data shigo dashi, Ta buɗe, White rice ce wadda ta ji vegetables sai miyar kwai, Ta yi serving ɗinta sannan ta ajiye a ƙasa. Kallon Salma dake tsaye har sannan ta yi ta ce “Common zo ki ci abinci” Bata yi musu ba ta ƙaraso inda Nayla take, Ta zauna kan rug ɗin. Tura mata plate ɗin Nayla ta yi ta ce“Yawwa ki ci abincin kin ji sai ki kwanta” Gyaɗa mata kai kawai Salma ta yi. Nayla ta tashi ta koma kan gado taja system ɗinta tana ci gaba da kallon da take, Ganin haka ya sanya Salma sakin jikinta ta sanya hannunta cikin abincin bayan ta yi bismillah ta ɗiba ta kai baki, Lumshe idanunta ta yi saboda daɗin da abincin ya yi mata, Ga kuma yunwa wadda ta dameta, Ta shiga tauna abincin a hankali cike da nutsuwa. Bayan mintuna goma ta gama cin abincin, Ta tsince wadda ta zubar a gabanta cikin empty plate ɗin sannan ta tashi tana riƙe da plate, Kallon Nayla ta yi wadda hankalinta ke kan system sai murmushi take a sanyaye ta ce “Ina zan ajiye plate ɗin?” Ɗagowa Nayla ta yi ta kalleta sai kuma ta yi murmushi ta ce“No don't worry bar shi a nan, Ki je toilet ki wanke bakin ki ki zo ki kwanta dare ya yi” Toh kawai Salma ta ce sannan ta ajiye plate ɗin gefen tray ɗin ta nufi toilet. Koda ta dawo kwance ta samu Nayla ta kashe system ɗin, Ta kalleta ta ce “Zo ki kwanta mana” Shiru Salma ta yi tana kallon Nayla, Wata irin zuciya gareta da har zata bari wadda bata sani ba ta kwana gefenta? Ikon Allah. Salma ta yi maganar cikin ranta, Nayla ta sake murmushi ta ce“Feel free fa, I'm ur friend ki zo ki kwanta nasan kin gaji” Ɗan murmushi Salma ta yi sannan ta ƙaraso wajen gadon, Daga ɗaya side ɗin ta kwanta a hankali kamar me tsoron gadon, Ganin bata ja duvet ɗin ba ya sanya Nayla ta rufa mata ta ce“Sai da safe” “Allah ya tashemu lafiya” Salma said. Washegari da wuri Salma ta tashi, Ta duba gefenta bata ga Nayla ba. Tashi ta yi ta hau gyara gadon dan daman already ta riga da ta yi sallah tun asuba, Tana gamawa ta ɗebi kwanukan jiya ta fito parlon. Da mamaki Mufeeda ke kallonta tana sanye da sport wears da alama daga gurin sport take, Ganin irin kallon da take mata ya sanya Salma rissinawa ta ce “Ina kwana?” “Lafiya lao” Mufeeda ta amsa mata, Sai kuma ta shige nata bedroom ɗin, Da idanu kawai Salma ta bita sai kuma ta tsaya tana tunanin ina zata kai kayan hannunta. Ganin irin kallon da Mommah ke mata ya sanya ta langwaɓar da kai ta ce“Wallahi Mommah, Sai kin ganta zata baki tausayi, Tana da kirki sosai, I know her before” Taɓe baki Momma ta yi ta ce“Ni ba wannan ya dameni ba Nayla, Cewa na yi shi Zayyad ina ya santa? Kuma ina ya ganta har ya kawota cikin gidan nan?” Nayla ta ce“But Mommah kin san wane Yaya Zayyad ba, Koda a ce yana aikata abubuwan da ba daidai ba amma kin san halayensa, Ya ce min ya ganta ne a hanyar Mararaba some mens trying to rape her, Shi ne ya taimaketa” Jin jin kai Mommah ta yi ta ce“And you believe it?” “Absolutely ma” Numfasawa Momma ta yi ta ce“Anyway, Idan haka ne ai babu buƙatar ta zauna cikin maids kawai ku zauna tare har sannan Allah zai kawo mafita” Murmushin jin daɗi Nayla ta yi ta ce“That's our Momma! Thank you so much” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Raba ni da shirme, Ki tashi ki je ki kira min Zayyad ɗin” Toh Nayla ta ce sannan ta tashi ta ɗauki veil ɗinta ta ɗora akanta ta yi waje da sauri. A hankali Salma ke tafiya cikin corridor ɗin, Sai bin kowace ƙofa take da kallo, Kamar daga sama ta ji an ce “Kee!” Tsabar yanda ta tsorata sai da ta saki tray ɗin hannunta, Plate ɗin ya tarwatse a wajen, Haka ma ragowar abincin dake cikin food flask ɗin. Ta juya jikinta na rawa dan ganin wnada ya kira sunan nata. General ne tsaye cikin ƙananun kaya t-shirt fara sai wando na uniform. Ƙura mata idanu ya yi yana kallonta kamar mai son gano wani abu, A rikice Salma ta ce “In... Ina Kwana?” Bai amsa bata ba, Haka kuma bai bar kallonta ba, Ita kuwa duk sai ta tsargu ta sunkuyar da kanta hannunta na ɗan rawa, “Daddy” Ta tsinkayi muryarsa, Zayyad ya yi maganar yana rufo ƙofar apartment ɗinsa. Sai a sannan Daddy ya ɗauke kansa daga kanta ya maida gun Zayyad bakinsa ɗauke da murmushi ya ce“Na'am ka tashi?” Gyaɗa masa kai Zayyad ya yi lokacin da idanunsa suka sauka kan Salma wadda ke tsaye ɗan nesa da Daddy. “Ina zaka je yanzu?” Daddy ya sake tambayarsa. Ɗauke idanunsa ya yi daga kanta sannan ya ce“Company nake son zuwa, An kawo takardun?” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Eh, An kawo, An jima idan ka dawo sai mu yi magana” Okay Zayyad ya ce. General ya sake kallon Salma sai kuma ya juya ya bar wajen. Sai a sannan Zayyad ya ƙaraso in da looking in to her eyes ya ce “Mene haka?” Rau rau ta yi idanu hawaye na kwanciya cikin kurmin idonta ta ce“Babu komai” Taɓe baki Zayyad ya yi sannan ya ce“Wane ya sanya ki ɗauko wannan kayan?” Girgiza kai Salma ta yi ta ce“Babu kowa, Ni ce na ɗauko” “Uwar iya ko?” Ya faɗa yana ɗaure fuska, Shiru ta yi ba ta ce komai ba ya sake kallonta ya ce “And this is the last warning da zan yi miki akan ina magana ki min shiru, You get it?” Muryarta na rawa ta ce “Ka yi haƙuri ba zan sake ba” Kafin ya yi magana Nayla ta ƙaraso wajen tana kallonsa ta ce“Yaya Momma na kiranka” Okay ya ce mata sannan ya juya ya bar wajen, Ta kalli Salma ta ce“Meya faru?” Girgiza mata kai Salma ta yi sai kuma ta ce“Babu komai, Kawai na yarda kaya ne" Ta ƙare maganar tana nuna mata inda tray ɗin yake. Murmushi Nayla ta yi ta ce“Ayyah ai babu komai, Mu je kawai masu aiki zasu kwashe” Salma ta kalleta, Gyaɗa mata kai Nayla ta yi ta ce“Mu je” Daga haka ta kama hannunta suka bar gurin. Tun da ta fara magana yake kallonta har sai da ta yi shiru dan kanta, General ya ce“Hajarah ban gane ba, Go straight to the point” Numfasawa ta yi tana kallonsa ta ce“Wallahi Yallaɓai da gaske nake maka, Abin da nake nufi shi ne ni wannan yarinyar ban yarda da kawota gidan nan ba. Akan me? Gaskiya a sauya wannan al'amarin” Da mamaki General ya ce“And what's the matter? Kin santa ne?” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a ban santa ba, Amma haka kawai naji ban yarda da ita ba, Kuma wallahi tun da na ce haka akwai wani abu a tattare da ita, Shiyasa nake son a yi wa tufkar hanci tun yanzu.” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Shikenan zan yi magana da Khadijah” “Au yanzu har sai ka yi magana da ita kafin ka yanke hukunci? Ai shikenan” Daddy bai ce mata komai ba ya tashi ya fice daga parlon, Ta bishi da kallo sai kuma ta taɓe baki. ****Murmushi Zayyad ya yi ya ce“Amma ai Mommah u trust ur son right?” harararsa ta yi ta ce“Duk da haka a have to know Zayyad, Saboda rayuwar yanzu, Ina iyayenta? Ko ance sun mutu ita bata da wani dangi? Ko na uwa ko na uba?” “Mommahhhh!...” Haɗe rai ta yi ta ce “Ko me zaka ce sai dai ka ce amma dole na sani kafin na fara riƙonta” Shafa sumar kansa mai uban yawa ya yi kafin ya ce “Shiyasa ni na ce kawai ta zauna cikin maids, Kin ga da babu wannan tambayoyin” Murmushi Momma ta yi tana girgiza kanta ta ce“Kakarta ka maidani ko? Ai shikenan” Dariya ya yi ya ce“A'a Mommah ni na isa” Taɓe baki ta yi, Sai kuma ta gyara zamanta ta ce“Look ya kamata a fara shirye-shiryen bikin na, Ka ga sauran 2weeks fa” Langwaɓar da kansa ya yi ya ce“To Mommah ai kune da shirye shirye ba Zayyad ba” Wani kallo ta yi masa daya sanya ya yi murmushi ta ce“Zan samu na je Mararaba sai mu yi magana da Mami” Okay ya ce sannan ya tashi yana kallonta ya ce“Zan je Company na dawo” Murmushi ta yi ta ce“Tom Allah ya tsare ya kiyaye hanya” Ya ce Ameen Sannan ya juya ya bar parlon. 10:23pm Cikin ƙungurmin daji ne, Babu gida gaba babu gida baya, Sai tarin bishiyu masu tsayi da kuma ciyayi, Babu abin da ke tashi cikin dajin sai ƙarar ihu da iface-iface na dabbobi da kuma wasu halittu. Saman wani tsauni mai mugun tsayi ake iya ganin hasken jar fitila, Hayaƙi na tashi da kuma dariya mai ban tsoro, Wani ƙaton mutumi ne zaune kan wani buzu, jikinsa babu kaya sai ɗan fante wanda ya rufe al'aurarsa baƙar fatarsa sai sheƙi da kyalli take, Ko ina na jikinsa guru ne da kuma layoyi, Gaba ɗaya fatarsa a zane take da wasu irin zanuka, Wasu wajejen dabbobi ne aka zana wasu kuma rubutu aka yi da wani yare wanda ba hausa ba haka na ba kuma turanci ba. Gashin kansa ya yi tudu tamkar ya sanya hula saboda yawa, Jikinsa ban da tashin ƙarni da wari babu abin da yake. Daga gefensa wata mata ce zaune tana sanye da hijabi ruwan ƙasa ta zuba masa idanu tana sauraren abin da zai ce. Wata irin dariya mai kashe kunnuwa ya saki, Ta sanya hannayenta ta ɗan toshe kunnenta ba tare da ya ganta ba, Ya washe bakinsa haƙoransa masu azabar datti suka bayyana, Cikin ɗaga murya ya ce “Kun yi sake! Kun yi sake, Baku yi abubuwa yanda na sanar muku ba! Kun kauce hanya” Muryar matar na rawa ta ce “Ka taimakemu ya kai boka mai cikakken iko, Ka duba lamarin mu, Kar ka bari asirinmu ya tuno” Sake tuntsirewa da dariya ya yi, Lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai ya buga gashin hannunsa a ƙasa kafin ya ce“Ai tun da kin zo ki ɗauka buƙatarku ta biya, Wane yake muku tsawon shekaru idan ba ni ba? Ko akwai wani wanda yake baku taimako idan ba ni ba?” Ta girgiza kanta ta ce “Babu kai ne abin dogaranmu, Kai ne mai share mana duk hawayen mu, Kai ne wanda ka ke taimakonmu akan duk abin da ya taso” Ya sake sheƙewa da dariyar jin dadi sai kuma ya ce “To yanzu ma zan taimake ku. Zan yi muku abin da zaku yaba dashi, Dake da ahalinki duk suna ƙarƙashin kulawata saboda haka damuwa ba taki ba ce! Wannan matsalar ta kau kuma nayi maganinta. Tabbas zaki yi dariya, Zaki dawo nan ki sameni ki faɗa min yanda abubuwa suka kasance” Ta yi murmushin jin daɗi kafin ta ce “Shiyasa har abada ba zamu taɓa bijire maka ba, Muna tare da kai, Kai ne wanda ke samar mana da farin ciki. Hajiya na yi maka godiya” Ya bushe da dariyar mugunta wadda ta cika ko ina na dajin. **** Ranar Lahadi wanda ya kama Salma ta kwana shidda a gidan suka shirya dan zuwa gidan Nimrah. Mommah ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana kallonsu ta ce“Sai kun yi yamma ko?” Nayla dake shafa lip gloss ta ce“Yanzu fa zamu fito Mommah” Mommah ta kalli Salma wadda ke zaune gefen gado jikinta sanye da hijabi ta ce“Ke naga baki yi kwalliyar ba?” Kafin ta yi magana Nimrah ta ce“Wallahi Momma nayi mata magana wai ita bata so, Wai ko ɗankwalin Abayar ba zata yafa ba sai dai ta saka hijabi” Murmushi Mommah ta yi ta ce“Haba Salma tashi kin ji ki shirya ku tafi, Baki son ki ga kin yi kyau?” Sunkuyar da kanta ta yi ta ce“Tom Mommah” Nayla ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da eye liner ta ce“Let me help you” Shiru Salma ta yi ta tsaya ta yi mata lining ɗin sannan ta shafa mata lip gloss, Wani irin kyau ta yi fatarta ta sake fresh saboda ɗan hutun data samu. “Damsel” Nayla ta ce tana murmushi, Shiru Salma ta yi. Nayla ta ce“Ki cire hijabin kamar wata me takaba” ɗan murmushi Salma ta yi sannan ta zare hijabin. Wata black Egyptian Abaya ce a jikinta mara ado da yawa, Nayla ta ɗauki pin ta yi mata rolling mayafin, Sosai ta yi kyau kamar wata balarabiya. “To ko kefa” Mommah ta faɗa tana murmushi, Sunkuyar da kai Salma ta yi tana murmushi. Nayla ta ɗauko handbags guda biyu ta miƙawa Salma black colour ɗin ita kuma ta ɗauki union ɗin dan ita ce kalar Abayarta. Amsa Salma ta yi ta riƙe sannan ta tashi tsaye, Nayla ta ɗauki wayarta a gefen mudubi ta ce“Let's take a pictures” Daga haka ta fara ɗaukansu hotuna da videos, Ita dai Salma ban da murmushi babu abin da take. Sai da Mommah ta musu magana sannan Nayla ta bari suka fito daga ɗakin. “Ku gaisheta” Mommah ta ce bayan sun fito parlon, Okay Nayla ta ce sannan ta kalli Mommy dake zaune ta ce“Ko za'a kai wa Aunty Nimra Saƙo?” Girgiza kai Mommy ta yi ta ce“A'a jiya na bawa Khalil ya kai mata ai, Ku gaishemin da ita” Toh Nayla ta ce sannan ta kalli Mufeeda dake tsaye ta ce“Muje mana” Harararta Mufeeda ta yi ta ce“Idan naƙi fa?” Nayla bata tsaya bata amsa ba, Ta kama hannun Salma suka bar parlon. A compound ɗin gidan suka haɗu da General wanda ya fito daga garden, Tun daga nesa yake kallon Salma har ya ƙaraso gabansu. Nayla ce ta fara cewa “Daddy sai mun dawo” Jin jina mata kai ya yi ya ce“Allah ya tsare” “Ina yini?” Salma ta faɗa tana sunkuyar da kanta, Kallonta kawai ya yi amma bai amsa ba ya yi gaba abin sa. Da idanu kawai Nayla ta bi shi amma bata ji daɗin abin da ya yiwa Salman ba, Ta kalleta ganin har sannan kanta a sunkuye, Hannunta ta kama ta ce“Muje kin ji” Jiki a sanyaye Salma ta bi bayan Nayla suka shiga motar. Mufeeda ce a driver seat sai Nayla a gefenta Salma kuma ta shiga back seat. Duk hirar da suka dinga yi uffan bata ce musu ba, Dan gaba ɗaya ba daɗi take ji ba. A haka har suka ƙarasa Maitama gidan Nimra. General na shiga parlon ya samu Mommah da Mommy suna hira, Sannu da zuwa suka masa bai amsa ba ya yi gaba yana faɗin “Khadijah ina son magana da ke” Da mamaki Mommah ta kalleshi, Mommy ta ce“Lafiyarsa kuma?” Taɓe baki Momma ta yi ta ce“Kin san halinsa, Bari na je na ji ko mene ne” Okay Mommy ta ce. Mommah ta juya tabi bayansa. Tsaye ta sameshi tsakiyar parlon sai kai komo yake, Ta tsaya daga gefe ta ce“Yallaɓai gani” “Ina son yarinyar nan ta bar gidan nan yau ba sai gobe ba!” Da mamaki Mommah ke kallonsa sai kuma ta ce“Wace yarinya kenan? Wai Salma ka ke nufi?” A fusace Daddy ya ce “Wace ta zo gidan nan idan ba ita ba? Ina son ta bar min gida a yau kar na sake ganinta” Mommah da hankalinta ya ɗan tashi ta ce “But for what reason? Me ta maka General? Akan me zaka ce sai ta bar gidan nan?” Daddy ya ce “Amma ai kana sane da cewa nan gidana ne ko? To na ce ta bar shi, Ko tayi min wani abu, Ko bata yimin ba wannan duk ba damuwarki ba ne. Abin da na ce shi ne kawai ta bar min gida!” Tuni ran Mommah ya fara ɓaci itama, Ta kalleshi ta ce “Idan har bata yi maka wani abu ba to babu dalilin da zai sanya ka ce sai ta bar gidan nan, akan me? Ni ban gane irin wannan halayen naka ba, Me ta tsare maka? Yarinyar idan ba kamawa ta yi bama sai ka shekara baka ganta ba, Gaskiya da sake!” Jin jina kai Daddy ya yi ya ce“Okay, shikenan, Idan kina ganin za ki iya ki bar ta cikin gidan nan Khadijah, Na dawo da daddare na sameta a cikin gidan nan” Daga haka ya yi waje yana tafiya kamar zai tashi sama, Biyo bayansa Mommah ta yi, Sai dai kafin ta cimmasa har ya kai parlon ɗaga murya ta yi ta ce “Wallahi muddin baka faɗa min abin da yarinyar nan ta yi maka sai idan ni da ita duk mu bar gidan!” Cak ya tsaya a in da yake, Mommy dake zaune ta tashi tsaye tana kallonta da mamaki. Juyowa Daddy ya yi ya kalleta sai kuma ya ce“To ki gwada barin ta cikin gidan nan ki ga, Ba ke ba har ya'yan da ki ka haifa sai kun fita kun bar gidan nan!” Mummunar bugawa zuciyar Mommy ta yi, Ta kalleshi a kiɗime ta ce “Yallaɓai kana hayyacinka kuwa? Lafiya ka ke? Kasan me ka ke faɗa?” A fusace Daddy ya ce “Idan kema za ki shiga ciki ne to Allah ya baki Sa'a” Turo ƙofar parlon suka yi, Suka shigo a tare da Mamaki suke bin su da kallo Khalil ya ce “Lafiya?” Mommy ce ta ce“Tambayesu dan Allah Khalil, Ban gane abin da yake faruwa ba, Ku tambayesu ku ji” Zayyad idanunsa kan Mommah suka sauka ganin yanda take tsaye jikin stairs fuskarta ta yi jajur da alama ba ƙaramin ɓata mata rai a ka yi ba. A nutse ya ƙarasa gabanta yana kallonta ya ce“Mommah lafiya? Meke faruwa?” “Zayyad nagaji da halin mahaifinku, Akan me zai ce sai yarinya ta bar gidan nan, Duk yaran da suke zuwa su zauna babu wadda ya taɓa yi ma magana sai yanzu dan wannan ta zo, Akan me” Kallonta Zayyad ya yi da mamaki ya ce“Wace yarinyar aka ce ta bar gidan nan?” “Salma” Mommah ta faɗa. Juyowa Zayyad ya yi ya kalli Daddy wanda ke tsaye har sannan yana huci, Gabansa ya dawo ya ce “But Dad why? Me ta yi?” “Kawai bana son zamanta cikin gidana Zayyad! Ta bar gida yau ba sai gobe ba” Shiru Zayyad ya yi yana nazarin kalaman Daddy, Khalil ya ce“Amma Daddy me Salma ta yi maka? Yarinyar da ko fitowa ba yi take ba?” Daka masa tsawa Daddy ya yi ya ce “And who are you Ina magana kana saka min baki?” Shiru Khalil ya yi Mommy ta kalleshi ta ce“Kar na sake jin bakin ka anan” Ta maida idanunta kan General ta ce “Haba Yallaɓai dan Allah ka yi haƙuri mana, Idan ma wani laifin ta yi maka ai sai ka faɗa a saka ta baka haƙuri” Daddy ya ce “Ni da gidana na yanke hukunci kuma dole sai ta bar gidan nan!” “Unfortunately babu inda zata je Daddy! Sai dai ka yi haƙuri!” Zayyad ya yi maganar yana kallon Daddy, Da wani irin mamaki Daddy ya kalleshi sai kuma ya ce “Ni ka ke cewa haka Zayyad? Ni ka ke faɗawa babu inda zata je?” Cikin dakkakiyar murya Zayyad ya ce “Eh Dad, Salma na gidan nan babu inda zata je, Idan ta yi maka wani abun ne to zan mata magana, But she can't leave this house like this” Tafa hannu Daddy ya yi sai kuma ya ce “Weldone! Ka yi kokari Zayyad! Ka kyauta, A matsayinka nawa ka ke cemin ba zata bar gidan nan ba?” “A duk matsayin daka ɗaukeni a haka nayi maganar Daddy, Salma ba zata bar gidan nan ba in dai Zayyad yana nan, Idan ka ga ta bar gidan nan to sai dai idan bana cikinsa, Domin ba Mommah ta kawota ba ni ne na kawota cikin gidan nan, Idan kuma ban isa ba sai ka faɗa min naji!” “Zayyad...!” Ɗagawa Mommah hannu ya yi, Still looking at Daddy ya ce“And that's my decision!” Daga haka ya juya ya fice daga gidan. Da idanu duk suka bi shi, Daddy ya yi sak a wajen can kuma ya yi kwafa ya juya ya fice shima. Mommah juyawa ta yi ta koma sama, Gurin ya rage daga Mommy sai Khalil da har yanzu yake mamakin abin da Zayyad ya yi. Ko da Mommah ta koma apartment ɗinta zama ta yi kan sofa ta fashe da kuka, Dan ta tabbata wannan abun da faru ba lallai ya tsaya iya nan ba. **** Around 5pm suka fito daga gidan, Nimra ta kallesu ta ce“Daga can zaku dawo nan ko gida zaku yi?” Girgiza kai Nayla ta yi ta ce“Gida zamu shige, Mommah ta ce kar mu yi dare” Okay Nimra ta ce sannan ta shiga motarta ita da Mufeeda, Salma da Nayla kuma suka shiga wadda suka zo da ita. Suna fita ƙofar gidan yana ƙarasowa, Parking tasa motar ya yi ya fito ya ƙaraso inda suke, Sauke glasses Nimra ta yi ya kalleta ya ce “Da kun jira na kai ku” Babu yabo babu fallasa ta ce“No, Thanks” “Ina yini Yaya Farooq?” Murmushi ya yi yana kallonta ya ce“Lafiya klao Feeda ya karatu?” “Alhamdulilah” Mufeeda ta bashi amsa. Motarsu Nayla ya ƙarasa tana murmushi ta ce“Yayanmu” Jan kumatunta ya yi ya ce“Ka ga yar autar gidan Daddy, Ya school ɗin?” lumshe idanu Nayla ta yi ta ce“Ina nan ina fama Yaya” Jinjina kai ya yi ya ce“Allah ya taimaka, Wannan ƙawarki ce?” ya yi maganar yana nuna Salma wadda ta juya kanta. Taɓa ta Nayla ta yi ta juyo suka yi ido huɗu da Farooq. Da mamaki ya ce “Ummusalma!” Waro idanunta ta yi sai kuma ta ce“Doctor ina yini?” Murmushi ya yi ya ce“Lafiya klao Alhamdulillah, Yaushe ki ka zo Abuja? Ya ƙarin haƙuri?” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Ban jima ba, Alhamdulillah” Jin jina kansa ya yi ya ce “Allah ya jiƙansa da Rahama” A tare suka ce Ameen, Ya ce“Sai kun dawo” Okay Nayla ta ce sannan ta yiwa motar key dan tuni su Nimra suka yi gaba. Sun fara tafiya Nayla ta ce“Ina ki ka san Yaya Farooq?” Tana wasa da fingers ɗinta ta ce“A asibitin da muka kai Abbana, Lokacin shi ne ya duba mu” Nayla ta ce“Au ho, Allah sarki” Salma bata ce komai ba ta jingina da jikin kujerar motar ta lumshe idanunta tana jin mutuwar Abbanta na dawo mata sabuwa. ****Da sallama ya shiga parlon, Zaune ya sameshi kan sofa idanunsa sanye da glasses yana kallon system ɗin gabansa. Ƙarasawa Zayyad y yi ya zauna gefensa, Rufe system ɗin General ya yi ya mai da idanunsa kan Zayyad ya numfasa kafin ya ce“Sorry for what happened kaji, Raina ne ya ɓaci” Girgiza kai Zayyad ya yi a sanyaye ya ce“No Dad I'm the one suppose to apologize, Sorry for what I did” Dafashi Daddy ya yi yana murmushi ya ce“Ba komai ya shige, Allah ya yi maka albarka” Jin jina kai Zayyad ya yi ya ce“Ameen Daddy, Thank you” envelope ɗin gabansa ya ɗauko ya miƙawa Zayyad yana cewa “Ga takardun Company ɗin” Karɓa Zayyad ya yi ya ɗan buɗe sai kuma ya mayar ya rufe ya ce“Tom, Allah ya ƙara girma” Ameen kawai Daddy ya ce, Zayyad ya tashi yana kallonsa ya ce“Sai da safe” “Okay, Allah ya tashemu lafiya” Daddy ya amsa masa, Juyawa ya yi ya bar ɗakin daddy ya bisa da idanu sai kuma ya girgiza kansa.. Ɗakin Mommah ya shiga, Zaune ya sameta gefen gado tana danna wayarta, Zama ya yi kusa da ita ya ce“Barka da dare Mommah” Ajiye wayar hannunta ta yi ba tare da ta amsa ba ta ce“Zayyad ya ku ka yi da General? Na kira Mami na ce Salma zata koma can sai ta riƙeta” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“No need fa Mommah, Mun yi magana da Daddy, So let bygone be bygone zata ci gaba da zama a gidan nan” wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce“To Alhamdulillahi, Halin General ne sai shi” Jin jina kai Zayyad ya yi ya ce“Sai haƙuri, Ina su Naylan suke ne?” Girgiza kanta ta yi ta ce“Har yanzu basu dawo ba” Tashi ya yi ya ce“Okay bari naje bacci nake ɗan ji” To kawai Mommah ta ce ya juya ya fita. Bai daɗe da fita ba suka shigo, Mommah ta kalli Nayla ta ce“Amma sai da na ce kar ku yi dare ko Nayla?” kwaɓe fuska ta yi ta ce“Wallahi bamu san dare ya yi ba fa” Harararta Mommah ta yi, Ta kalli Salma ta ce“Kin gaji ko? Tashi ki yi wanka sai ki ci abinci” Toh kawai Salma ta ce dan ta gajin da gaske ta tashi ta fice daga ɗakin. “Zayyad! Zayyad! Zayyad!” Motsa ƙafarsa ya yi, Kamar zai yi kuka ya ce “Mommah ki barni bacci nake ji fa” Tuntsirewa da dariya ya ji an yi, A firgice ya farka daga baccin da yake, Ya tashi zaune yana ƙarewa ɗakin kallo, Kallon Mommah ya yi wadda ke tsaye kansa sanye da Abaya, Ya langwaɓar da kai ya ce“Mommah ki bar ni na kwanta mana” Murmushi mai kyau ta yi kafin ta ce “Baka son ka bi ni in da zan kai ka? Zaka ji daɗi sosai fa” Shiru ya yi yana kallonta sai kuma ya ce“To ki bari sai gobe mana” Dariya ɗan yi ta ce“Ai ba zai yiwu bane, Kawai kai dai taso” Ta miƙo masa hannunta. Girgiza kansa ya yi sai kuma ya kama hannun, Ɓat ta ɓacema ganinsa, A hankali kuma ya ji kamar wani abu nashiga jikinsa tun daga kansa har zuwa yatsun ƙafarsa, Ya saki wata irin razananniyar ƙara sai kuma ya fashe da dariya. Da gudu Nayla ta shigo ɗakin tana kallonsa ta ce “Lafiya dai Yaya? Ka tsoratani” Wani irin kallo Zayyad ya shiga yi mata sai kuma ya sake tuntsirewa da dariya yana nuna ta da hannunsa. “Yaya Zayyad! Yaya mene haka wai?” Bai bata amsa ba, Sai dariya ya ke kamar wani zarrare. Juyawa Nayla ta yi ta fice daga ɗakin, Bata jima ba suka dawo tare da Mommah, Tana ƙarasowa ɗakin taji kamar an soki zuciyarta da wani abu, Ta tsaya cak, Nayla ta kalleta sai kuma ta ce “Mommah mu je mana” Toh kawai ta ce sannan tabi bayanta suka shiga bedroom ɗin nasa, Zaune suka sameshi yana wasa da yatsun ƙafarsa, Mommah ta ƙarasa gabansa tana kallonsa ta ce“Zayyad!” Zabura ya yi ya sauka daga kan gadon yana mata wani irin kallo ya ce “A'a ni ba zan dawo ba, Ba zan dawo yanzu ba, Wallahi ba zan dawo ba” Daga haka ya nufi waje da gudu, Tashi ta yi cikin tashin hankali tabi bayansa. Sai dai har ya kai main parlon na gidan, Khalil ne yaga yana gudu ya yi saurin tare shi yana cewa “Yaya lafiya? Ina zaka je?” Ture shi Zayyad ya shiga yi yana cewa“Ni a'a ku rabu dani ba zan dawo ba” Da mamaki Khalil ke kallonsa Dai dai nan Mommah ta ƙaraso parlon, Hannunsa ta rike ya fincike. Ta shiga jijjigashi tana cewa“Kai lafiyarka? Meya sameka?” Tuntsirewa da dariya Zayyad ya yi ya kwace hannunsa daga rikon da Khalil ya yi masa ya zauna nan kan tiles yana nuna Momma yana wata irin dariya, Hayaniyar da suka ji ya sanya suka fito, Daddy ya ƙaraso parlon yana kallon Zayyad dake wata irin dariya har sannan. Mommah na ganinsa ta ƙarasa gabansa ta rike shi tana cewa “General duba meya samu Zayyad? Ka ga bai san me yake ba wallahi” Da mamaki Daddy ya ƙarasa gabansa, Ya dafashi. “Kai naga kana dariya...kai ɗan yaron nan, Meke damunka na baka maganiiii, Ka sha paracetamol...” Zayyad ya dinga maganar yana taɓa Daddy, Sosai gaban Daddy ya fadi ya ɗago idanunsa yana kallon kowa dake parlon. Mai da kansa ya yi yana kallon Zayyad ya ce “Kai mene ne haka? Tashi ka je ka kwanta” Ture shi Zayyad ya yi kawai suka ga ya fashe da kuka, Salma da fitowarta kenan ta ƙaraso in da yake da gudu, Tsugunawa ta yi gabansa tana kallonsa ta ce “Me aka yi maka Yaya Zayyad? Mene ne?” “Ita ce! Ita ce ta haukatashi! Wallahi ita ta haukatashi!” Mommah ta fadi maganar tana nuna Salma da yatsa, Ɗagowa Salma ta yi ta kalleta da mamaki dan bata gane in da maganar tata ta dosa ba, Mommy ta tafa hannayenta tana cewa “Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una, Mun shiga uku, Ta haukata yaron mutane, Zayyad! Zayyad!” Daddy kallon Salma ya yi sai kuma ya shaƙe wuyanta kamar zai rabata da ranta ya ke cewa “Ke me ya yi miki haka? Daga taimako? Akan me za ki haukatashi?” Salma ta dake jin nunfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta ta shiga girgiza kanta, Magana take son yi amma irin riƙon da Daddy ya yi mata ya hanata, Da gudu Nayla ta ƙaraso wajen tana ƙoƙarin janye hannun Daddy ta ce “A'a Daddy na rantse ba ita ba ce, Salma ba ita ba ce, Babu abin da ta yiwa Yaya Zayyad dan girman Allah kar ka kasheta” Hankaɗeta Daddy ya yi, Mommy ta ƙaraso wajen tana kallonsa ta ce“General cikata kaga” Wurgi ya yi da Salma, Ta faɗi kan tiles, Ta saki wani irin ihu mara sauti tana riƙe wuyanta. Kallonsa Mommy ta yi ta ce“Za'a tambayi Zayyad idan har ita ce to tabbas zai faɗa” Mommah na kuka ta ce“Ai wallahi ma ita ce! Ita ce ta haukatashi” Girgiza kai Mommy ta yi ta ce“Idan ita ce zai faɗa da kansa, Sannan kuma dole su bar gidan nan daga ita har shi” Girgiza kai Nayla ta yi ta ce“A'a Mommy, wallahi Babu in da zasu je!” Wani wawan mari Mommah ta sauke mata, Tana kallonta ta ce“Idan na sake jin bakinki anan sai na tsine miki albarka” Rufe baki Nayla ta shiga yi tana girgiza kanta wasu zafafan hawaye na zubowa kan fuskarta. Sunkuya Mommy ta yi gaban Zayyad ta dafashi a nutse ta ce “Kai ka san wane ya yi maka wannan abun? Wane ya aiko ku jikinsa?” Tuntsirewa da dariya Zayyad ya yi yana girgiza kansa, Mommy ta haɗe rai kafin ta ce “Ko ku faɗa ko na kashe shi tare da ku" Langwaɓar da kai ya yi kamar zai yi kuka ya ce“A'a kar ki mana haka zamu faɗa wallahi” Jinjina kai Mommy ta yi ta ce“Ku faɗa a gidan nan wane ya aika ku jikinsa?” Hannunsa na rawa ya nuna inda Salma take a tsawa ce ya ce “Ita ce! Ita ce ta sakamu” Sai kuma ya fashe da kuka. Ɗora hannu aka Salma ta yi ta shiga girgiza kanta dan ko kalma ɗaya ta gagara fita daga bakinta. Nayla da Mufeeda suman tsaye suka yi a wajen, Mommah ta yi wani irin kukan kura ta cafki Salma ta shiga dukanta ko ta ina. Mommy ce ta janyeta ta ce“Khadijah!" tsam Mommah ta bari ta ja baya tana huci, Mai da idanunta kan Zayyad ta yi ta ce“Yanzu sai ku bar gidan nan” To kawai ya ce sannan ya tashi har sannan yana dariya, Ƙarasawa inda Salma ta ke ya yi bai yi wata wata ba ya saɓeta kamar kaya ya ɗorata a wuyansa. Duk irin ihun da take bai sa ya sauketa ba, Sai dariya yake yana cewa “Ashe ma bata da nauyi, kilo 3 ce wannan za ki sha paracetamol....” Ya sheƙe da dariya, Matsa masa hanya Mommy ta yi ta ce“Kuma koda wasa kar ku sake dawowa gidan nan” Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin “Eh...Eh... Ba zamu dawo ba, Zan kai ta tasha paracetamol....” Daga haka ya fice daga parlon da gudu, Nayla ta yanke jiki ta faɗi haka ma Mommah, Ko da Zayyad ya fita compound ɗin gidan sojoji ƙin barinsa suka yi, Ya fashe da kuka har sannan Salma na kafaɗarsa ya ce“Ni ku bar mu mu tafiyarmu...” Daddy ne ya fito yana kallon su ya ce“Leave him" Juyowa Zayyad ya yi ya jin jina masa kai ya ce“Sai da kai Oga...” Sannan ya yi waje a guje... _Akwai waɗanda suka haukace, ba saboda rashin hankali ba, amma saboda duniya ta kore su da gaskiyarsu. Akwai waɗanda suka zamo duhu, ba don ba su da haske ba, amma saboda rayuwa ta yanke igiyar da ke riƙe da su. Kuma akwai waɗanda suka ci gaba da rayuwa, amma kowace rana cikin damuwa suke, suna ɗauke da abin da ba zai taɓa faɗuwa a baki ba._ _Kaddara ba ta tambayar shirinka. Sharri ba ya jira shiryawarka. Suna zuwa ne lokacin da zuciya ke jin daɗi, sai su kwashe komai su ce maka: “Daga yau, ba kai ne ba.”_ To wa zai tsaya ya gyara gaskiya idan kowa yana jin tsoron shaidar ta? *Shin mene ne gaskiyar al'amari?* *Wane Zayyad? Wa ce Salma?* *Wace ƙaddara ce ta haɗa su?* *Wane zai zama HASKE a CiKIN wannan Duhun?* *Ina dangin Salma suke?* *Wane ya haukata Zayyad?* *Shin zai samu lafiya ko kuma shikenan zai ci gaba da zama a mahaukaci?* *Wace irin rayuwa zasu yi bayan barin su gida* *Wane General Idris B. Musa?* *Duka zaku samu amsoshin tambayoyinku a cikin ci gaban littafin nan na HASKEN CIKIN DUHU, Wanda yake na kuɗi akan Naira ₦700 kacal, Payment via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay sai shaida ta wannan numbern 08106608363, Nanameera.* _Ki biya ki karanta cikin aminci✌️😍_ # HCD # Light within the darkness # Last free pages # Nanameera 08106608363. Rate me. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 16: Kindness become a risk Nanameera, YOTA/23. A hankali ta juya ta kalleshi ganin yaja da baya, Ya tsaya cak yana kallon hanya. Tun bayan fitowarsu suke tafiya bayan ta samu ya sauketa da kyar, Tafiyar kawai suke yi ba tare da ta san inda zasu nufa ba, Bata san kowa ba, Bata san inda ya kamata ta kai su ba, Ina zasu je?. Ta sauke nunfashi sannan ta kalleshi ta ce a sanyaye “Muje mana” A madadin ya tafi sai kawai taga ya nemi waje ya zauna, Ya ɗora kansa bisa gwuiwoyinsa. Da mamaki Salma ke kallonsa sai kuma ta kalli hanya, Babu kowa sai ɗaiɗaikun motoci da suke shigewa sakamakon dare daya riga da ya yi sosai. A hankali ta durƙusa gabansa tana kallonsa ta ce “Ka tashi mu tafi Yaya yad, Dare yana yi” Kallonta ya yi da daradaran idanunsa wanda suka yi jajur dasu, Bai ce komai ba taga ya ɗauke kansa yana kallon wani wajen, Goge hawayen daya wanke fuskarta ta yi sannan ta sake cewa “Dan Allah ka tashi mu tafi kaji” Ko kallonta bai yi ba, Shiru ta yi tana kallonsa, A ƙalla ta ɗauki mintuna biyar, Can ya fara jin shassheƙar kukanta. Ɗago fuskarsa ya yi yana kallonta, Sosai Salma ke kuka ya tashi tsaye ba tare da ya ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya. Da sauri itama ta tashi sannan tabi bayansa suka ci gaba da tafiyar da basu san inda suka nufa ba. Hadari ne ya haɗo, Sararin samaniya ta yi wani irin jaa, Iska ta shiga kaɗawa da wani irin ƙarfi, Ƙura ta yawaita a ko ina. Sosai gaban Salma ya faɗi, Ta kalli Zayyad wanda ke tafiyarsa babu ko waiwaye, Yanzu idan ruwan nan ya sakko ya zata yi? Ina zasu je? Bata gama wannan tunanin ba yayyafi ya fara sauka, Da gudu Zayyad ya dawo baya ya riƙe gefen rigarta, Kallonsa kawai ta yi tana jin wani irin matsanancin tausayinsa, Muryarta na rawa ta ce “Yaya yad mu yi sauri kar ruwa ya dakemu” Bai ce komai ba, Dan daman tun bayan barinsu gidan bai sake magana ba, Sai dai ya shiga girgiza kansa a hankali. Cikin ikon Allah ruwa mai ƙarfi ya fara sauka, Zayyad ya riƙe Salma sosai jikinsa na wani irin tsuma. Rasa abin yi Salma ta yi, Ta shiga ƙarewa hanyar da suke kallo, Ita kanta ba zata ce ga inda suke ba. Da alama dai sun fita daga Asokoro da daɗewa, Hanyar kuma ta yi mata kama da hanyar komawa Mararaba. Wata tsohuwar container irin na masu cajin waya ta hanga, Ta ƙarasa wajen Zayyad na biye da ita. Tura ƙofar ta yi ta ganta a buɗe, Sai dai duk ƙura da tarkace ya cikata. Juyowa ta yi ta kalli Zayyad a sanyaye ta ce “Cikani to” Banza ya mata kuma bai cikatan ba, Hannunta ta sanya ta janye nasa hannun daga jikinta, Ya ɗago idanunsa ya kalleta amma bai ce komai ba. Shiga cikin container ta yi, Ta sunkuya tana kallon ƙasan, Hannunta ta sanya duk biyun ta fara share wajen. Duk yanda take jin ƙura na damunta bai sa ta bari ba sai da tattare sharar waje ɗaya. Warware ɗan kwalin dake kanta ta yi, Ta shimfiɗa a ƙasan ya ɗan mamaye wajen kasancewar yana ɗan girma. Numfasawa ta yi sannan ta fito daga ciki, Bata samu Zayyad ba, Gabanta ya wani irin faɗuwa, Cikin tashin hankali ta shiga duba ko ina, Shassheƙar kuka ta jiyo daga bayan container ta ƙarasa tana tafiya a hankali, Zaune ta sameshi gefen container ya rufe fuskarsa da hannayensa yana kuka a hankali. Wata ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ƙarasa gabansa, Murya can ƙasa ta ce “Yaya yad” Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake sunkuyar da kan nasa, Hannunsa ta rike tana cewa “Zo muje na gyara maka wajen” Fizge hannunsa ya yi yana ɗauke kansa, Kamar zata yi kuka ta ce“Please mana” Kafin ya yi magana aka saki wata tsawa mai firgitarwa, Ganinsa ta yi a tsaye ya riƙeta sosai jikinsa na rawa, Sai a sannan ta fuskanci ruwan yake tsoro. Bata ce komai ba ta nufi container, Da kyar Zayyad ya shiga ciki domin ta masa kaɗan, Ta zaunar dashi kan ɗankwalin data shimfiɗa sannan itama ta zauna a gefe, Takure jikinsa ya yi waje ɗaya yana motsa bakinsa a hankali, Duhu ya hanata sakat domin ita a rayuwarta ta tsani duhu, Tun tana ƴar ƙarama Abba ke siya mata fitila saboda duk dare bata iya zama sai da fitila, A hankali ta fara hawaye yana tunanin yanda zata yi. Bayan mintuna biyar ta sake kallon Zayyad, Duk da bata hango fuskarsa amma ta fuskanci gyangyadi yake. Sosai ya bata tausayi cikin rawar murya ta ce “Yaya Zayyad, Bacci zaka yi?” Gyaɗa mata kai taga ya yi, Ta sake kallon inda suke zaunen, Wajen ya yi musu kaɗan su kwanta sannan kuma ba son zamanta dashi take waje ɗaya ba tun da shi ɗin ba muharraminta bane. Ganin babu yanda zata yi ya sanya ta ce“Zo ka kwanta anan” Ta ƙare maganar tana dafa cinyarta, Ta cikin duhun ya kalleta sai kuma ya ƙaraso a hankali ya ɗora kansa bisa cinyarta, Ya cure jikinsa waje guda ya rufe fuskarsa da hannayensa nan da nan kuma bacci ya ɗaukesa. Zubar ruwan ce ta yawaita, Ƙara ta cika ko ina, Ɗigar ruwa ta fara ji akanta, Ta ɗaga idanunta dan ganin ta inda ruwan ke zuba. Bata ga komai ba sai dai ruwan bai daina zuba ba, Da alama container a ɓule yake wannan shi ne dalilin daya sanya babu komai a ciki. A haka ruwan ya ci gaba da zuba kan Salma ta yi shiru tana tunanin halin da rayuwarsu zata shiga, Ta ina zata fara rayuwa da mahaukaci? Ya zata yi da Zayyad? Babu wanda ta sani nasa ballantana ta kai shi wajensa, Itama babu wani nata ballantana taje in da yake. Da wannan tunanin Salma ta kwana a zaune har gari ya waye. A hankali ya shiga buɗe idanunsa, Kalle kalle ya dinga yi, Ya tashi zaune yana kallonta. Idanunta a rufe suke da alama bacci ne ya ɗauketa a zaunen da take, Ƙura mata idanu ya yi yana kallonta, Can kuma ya kai hannunsa fuskarta. Buɗe idanu Salma ta yi tana kallonsa, Ta ɗan ja baya, Hannunta ta sanya ta murza idanunta still looking at him. Gani ta yi ya ƙara kawo hannunsa fuskarta, Ta tashi tsaye kamar zata yi kuka ta ce “Mene haka?” Cikin zafin nama shima ya tashin, Kansa ya bugi da jikin langa-langar, Ya dafe kansa yana kwaɓe fuska, Kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta fita daga container. Kallon ko ina ta dinga yi, Ɗaiɗaikun motoci da babura na shigewa, Iska mai sanyi da danshin ruwa na kaɗawa a hankali, Ta lunshe idanunta tana jin nutsuwa na saukar mata. Ta fi minti biyar a tsaye kafin ta buɗe idanunta, Tsugune ta hango Zayyad yana rike da wani kare sai taɓa jikinsa yake. Ƙarasawa wajen ta yi, Ta tsaya a kansa ba tare da ta ce komai ba.. “Baka da lafiya, Meke damunka? To bari daina kuka zan baka magani” Abin da yake cewa karen kenan, Gegen hannunta ta sanya ta share hawayen daya zubo mata. Ganin ba daina maganar zai yi ba ya sanya ta ce a sanyaye “Yaya Zayyad” Ɗaga mata hannu ya yi ya ce “Haba nurse baki ga ina da mara lafiya ba, Ki bari sai na gama dashi sannan mana haba!” Salma ta girgiza kanta, Wato duk rayuwarsa a asibiti ce take dawo masa. Komawa wajen container ta yi ta zauna ta zuba uban tagumi, Tunanin abin da zasu ci ne ya dameta, Gashi bata da komai, Ko ya zasu yi?. Tana nan zaune har taga ya tashi ya rabu da karen ya yi tafiyarsa, Ya dawo inda take ya zauna a ƙasa yana kallonta. “Ka bashi maganin?” Ta faɗa tana kallonsa. Jinjina mata kai Zayyad ya yi, Wajen ya yi shiru can kuma taga ya tuntsire da dariya. Kamar zata yi kuka ta ce “Me ka ke wa dariya?” Bai bata amsa ba, Ya ci gaba da dariyarsa yana girgiza kansa. Can kuma ya haɗe fuska kamar ba shi ba, Cikin kakkausar murya ya ce “Bazan dawo ba! Ni ki bar ni anan Mommah! Ina son zama anan, Zan duba marasa lafiya nefa” Da mamaki Salma ke kallonsa jin ya ambaci sunan Mommah, A hankali Memory ɗin jiya da daddare ya shiga dawo mata fresh cikin kwakwalwarta. “Ita ce ta haukata shi! Ita ta rabamu dashi, Azzaluma, Macuciya, Muguwa, Daga taimako? Sai ki raba shi da hankalinsa, Allah ya isa tsakaninmu dake! Kin cucemu!” Salma ta runtse idanunta, Ta shiga girgiza kanta tana kuka tamkar yanzu Mommah ke faɗa mata wannan kalaman. Tabbas babu abin da ta masa, Ita ta sani bata cutar dashi ba, Sai dai bata san wace ƙaddara ce ta sanya ya zaɓeta a matsayin wadda ta masa asiri ba. Akan me? Me yasa sai ita? Ga Nayla ga Mufeeda ga Mommah ga Mommy, Ya bar kowa ya zaɓeta. Saboda bata da gata, Saboda ya taimaketa. Ta sake rushewa da wani sabon kukan, Shiru Zayyad ya yi da zantuttukan nasa ya zuba mata idanu ganin yanda take kuka, Tashi ya ya ya ƙarasa gabanta. Hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce “Meke damunki? Bari zan baki magani” Ture shi ta yi ta tashi ta shige cikin container. Ɗankwalinta ta ɗauko ta yafa sannan ta fito. Can ta hangeshi yana kwasar ledoji, Ta ƙarasa wajen ɗago kansa ya yi yana kallonta duk ya ɓata fuskarta da ƙasa hannunsa cike da tarkacen ledojin pure water, Murmushinsa mai kyau ya sakar mata ya ce “Ga magungunan na samo muje na baki, har da paracetamol” Takaici da baƙin ciki ya sanya Salma doke hannunsa, Gaba ɗaya ledojin suka zube. Ta nuna shi da yatsa ta ce “Ka bar wannan haukan ka shige mu tafi” A tsawace shima ya ce “Ni ne mahaukacin? Kin san wane ni? Ni Zayyad ki ke cewa mahaukaci?” Bata ce masa komai ba, Ta juya ta nufi hanyar titi, Ganin haka ya sanya ya biyo bayanta. Tafiya suka ci gaba da yi, Suna tafe yana sata magana, Duk abin da ya gani a hanya sai ya tsaya ya tsinta, Idan ta yi masa magana sai ya ajiye. Wasu lokutan kuma yana ɗan surutansa a haka har suka shigo cikin Mararaba wajejen ƙarfe 10:00 na safe. Ta dinga kallon garin tamkar ta shekara rabonta dashi, Rasa inda zata je tayi, Ko taje gidan Hajiya Jinjin? Zata taimaketa? Ta tambayi kanta. Tafiya taga Zayyad ya fara yi, Tayi saurin bin bayansa sai da ta cimma masa sannan ta kalleshi ta ce “Ka daina yin gaba kana bari kar ka je ka ɓata” Banza ya mata, Itama bata sake cewa komai ba suka ci gaba da tafiya. A bakin orange market ta tsaya, Ya dinga kallon kasuwar kamar mai tunanin wani abu. Wata mai siyar da abinci ya hanga tana zuba miya kan farar taliya, Ya ƙarasa wajen ya tsuguna yana kallonta kamar idanunsa zasu faɗo. Sai da ta gama zuba miyar sannan ta kalleshi ta ce “Malam me za'a baka?” Shiru Zayyad ya mata, Ta sake maimata tambayar. Ganin bai da niyyar bata amsa ya sanya ta ce a fusace “Kai Malam Idan ba siya zaka yi ba ka tashi ka bani waje kaji” Salma ce ta ƙaraso wajen bayan ta hangeshi tsugune dan bata san ma sanda ya bar kusa da ita ba tana can tunani. Hannunsa Salma ta kama tana cewa “Yaya Zayyad tashi daga nan” Miƙewa ya yi ya kalleta sai kuma ya nuna mata abincin.. “Yunwa ka ke ji?” Salma ta tambaye shi murya a sanyaye. Gyaɗa mata kai ya yi har sannan idanunsa na kan abincin. Wasu sabbin hawayen taji sun fara zubo mata kan fuska, Itama yunwar take ji, Duk da ta saba jure yunwa amma tasan shi ba zai taɓa jurewa ba. Gashi bata da kuɗi balle ta siya masa abinci, Numfasawa ta yi sai kuma ta ce“Muje zan siya maka a wani wajen”Daga haka ta riƙe hannunsa suka bar wajen. Kai tsaye inda take zama siyar da lemo ta nufa, Akwai wata mai abinci a wajen wadda suka ɗan saba. Tana zuwa ta samu Sa'a matar ta fito ta ƙarasa tana murmushi suka gaisa, Matar ta ce “Salama kwana dayawa kin daina fitowa” A sanyaye Salma ta ce “Wallahi Mama Abbana ne ya rasu shine ya saka” Girgiza kai matar ta yi ta ce “Allah sarki Allah ya jiƙansa da Rahama” Da Ameen ta amsa sannan ta yi shiru tana tunanin ta in da zata fara dan sam roƙo ba ɗabi'arta bane. Ganin ta yi shiru ya sanya Matar ta ce “Lafiya dai Salma?” Numfasawa ta yi ta ce “Daman inason zan miki wanke wanke ne sai ki bani abinci dan Allah Mama” Shiru matar ta yi can kuma ta ce “Tom shikenna, Daman kayan sun ɗan taro je ki yi Salama” Sosai Salma ta ji dadi ta tashi ta shiga shagon nata ta kwaso kayan da za'a wanke, Zayyad na tsaye daga waje har sannan yana bin ta sa kallo duk inda ta yi. Sai da ta haɗo komai sannan ta kalleshi ta ce “Zauna akan bencin nan” Ta ƙare maganar tana nuna masa wani benci. Bai ce komai ba kuma bai zauna kan bencin ba ya ci gaba da tsaiwarsa yana kalle kalle abinsa. Itama bata sake bi ta kansa ba, Ta fara wanke-wanken. Bata fi mintuna ashirin ba ta kammala wanke duk kayan ta mai da komai inda yake sannan ta fito. Murmushi Matar ta yi ta ce “Ywwa Salma sannunki da ƙoƙari” Daga haka ta ɗauko leda ta zuba mata abincin, Amsa Salma ta yi tana godiya sannan ta bar shagon tana kallon Zayyad wanda ya biyo bayanta. Can ƙasan Kabayi ta samu inda babu mutane sai filaye ta zauna kan wani bulo tana kallonsa ta ce “Ga abincin” Ƙarasowa ya yi ya ajiye ledojin hannunsa a gefe sannan ya amsa ledar abincin, Ganin yanda yake kokawa da ledar ya sanya ta amsa ta buɗe masa.Ganin hannunsa duk datti ya sanya ta fasa pure water hannunta da Matar ta bata ta wanke masa hannun sannan ya fara cin abincin. Tass ya tashi da abincin dan daman ba wani yawa gare shi ba, Bayan ya gama ta miƙa masa ragowar ruwan ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya. Basu daɗe a wajen ba ta tashi tana kallonsa ta ce “Mu tafi” Bai ce mata komai ba kuma bai taso ba, Sai ma kwanciya da ya yi kan yashin wajen yana lumshe idanunsa. Dawowa ta yi tana ci gaba da kallonsa da mamaki ta ce “Ka taso mu tafi mana” Ba zaka taɓa ɗauka da Zayyad take magana ba dan ko inda take bai kalla ba. Ganin ba tashin zai yi ba ya sanya ta haƙura ta nemi gefe ɗaya ta zauna ta zuba uban tagumi. Tana nan zaune har aka fara kiran sallahr azahar, Ta tashi daga zaunen da take ta ƙarasa wajen wata buga-buga data hanga gefen wata gona ta samu ledar pure water ta buga ruwan a ciki sannan ta matsa gefe ta gabatar da alwala. Tana gamawa ta dawo inda yake kwancen har sannan yana bacci ta gyara mayafin jikinta ta yi sallahrta a wajen. Koda ta idar zama ta yi ta shiga addu'oi kala kala tana neman Ubangiji ya kawo mata mafita. Zayyad ya shiga buɗe idanunsa a hankali yana ɗan surutansa, Ya tashi zaune yana dafe kansa, Juyi ya dinga yi shi kaɗai kan tarin yashin kafin daga bisani ya saki wata ƙara, Salma ta taso da sauri tana kallonsa ta ce “Lafiya? Mene ne?” Bai bata amsa ba, Sai ma tashi da taga ya yi yana shirin barin wajen, Da sauri itama ta tashin ta riƙo rigarsa tana cewa “Ina zaka je? Mene ne Yaya Zayyad? Ko abincin zaka sake ci?” Bai bata amsa ba sai huci da yake ta yi, A hankali kuma ya fizge hannunta daga jikinsa ya fara tafiya. Sake bin sa Salma ta yi ta cakumeshi hankalinta a matuƙar tashe ta ce “Ka faɗa min mene ne? Ba zan bari ka tafi wani wajen ba Wallahi!” A fusace ya juyo ya shaƙe wuyanta da duk hannayensa guda biyu, Nan da nan idanunta suka firfito waje, Hawaye ya dinga zuba daga cikinsu. Ta sanya hannunta tana ƙoƙarin rikeshi amma ta kasa, Wani bango ya hanga ya shiga janta har wajen bango yana zuwa ya gwara kanta da jikin bangon sannan ya saketa, Salma ta faɗi ƙasa Sumammiya kanta na zubar da jini, Bai ko kalleta ba ya juya ya bar wajen yana tafe kamar zai tashi sama. # HCD # Light within the darkness # Salmerh # Zayyad # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 17-18: "Where Did You Leave My Heart?" Nanameera, YOTA/023. Danshin ruwan da taji akan fuskarta shi ne ya farkar da ita, Ta shiga buɗe lumsassun idanunta a hankali tana ƙarewa wajen kallo. “Sannu yarinya, Sannu” Salma ta kalli wanda ke maganar tana ƙoƙarin tashi zaune, Wani ɗan dattijon mutum ne hannunsa riƙe da ledar pure water, Ganin bata ce komai ba ya sanya ya sake cewa “Daga ina ki ke? Ina iyayenki?” Kalle kalle ta shiga yi sai kuma ta miƙe tsaye cikin tashin hankali ta kalli mutumin ta ce “Dan Allah Baba ƙarfe nawa yanzu?” Tashi ya yi daga durƙushen da yake ya zaro keypad daga aljihunsa ya ɗan danna sai kuma ya ce “Yamma ta yi sosai, Ƙarfe 5:46pm” Dafe kanta tayi saitin inda ya fashe, Ta runtse idonta saboda yanda take jin zafi. “Ya kamata ki je asibiti yarinya Allah ya tsare gaba” Mutumin ya faɗa yana ƙoƙarin barin wajen, Da sauri tabi bayansa tana faɗin “Babba dan Allah baka ga wani mutum anan ba? Wani fari kamar mahaukaci” Girgiza mata kai ya yi ya ce“A'a yarinya ban ganshi ba” Shiru Salma ta yi tana jin bugun zuciyarta na ƙaruwa, Ina ya tafi?. Juyawa ta yi ta koma in da take kwance, Ɗankwalinta ta ɗauka ta yafa sannan ta bar wajen. Yawo sosai Salma ta dinga yi cikin gangaren Kabayi amma bata samu Zayyad ba, Wanda ya gashi ma bata gani ba. Ana kiraye-kirayen sallar magriba ta samu wani dakali ta zauna, Fashewa ta yi da kuka baƙin ciki, Gaba ɗaya bata san yanda zata yi ba, Ga yunwa ga ƙishirwa, Ga Zayyad ya ɓata bata ganshi ba. Ta ina zata fara? “Laa Salma!” A ɗan firgice ta ɗago kanta, Da mamaki suke kallon juna kafin Khadijah ta yi murmushi ta ce “Daman kina nan? Me yasa bana ganinki?” Tashi tsaye Salma ta yi tana kallon Khadijah amma bata ce komai ba. “Na ganki haka ko baki da lafiya ne?” Khadijah ta sake tambayarta, Kuka Salma ta fara yi ba tare da ta ce komai ba. Kamo hannunta Khadijah ta yi tana girgiza kanta ta ce “Yi haƙuri Salma, Nima ban ji daɗin abin da ya faru ba, Na so a ce Ummana ta bar ki kin ci gaba da zama a gidanmu” Salma goge hawayenta ta shiga yi tana jan numfashi ta ce “Babu komai Khadijah, Ai kona zauna a gidanku dole wata rana zan bar shi, Kaddarata kenan, Tun da Abbana ya riga da ya mutu shikenan ai” Sosai jikin Khadijah ya yi sanyi, Taɓa jikin Salman ta yi ta ji zafi, Ta janye hannunta ta ce “Kin ci abinci?” Girgiza mata kai Salma ta yi, Ta buɗe hand bag ɗin hannunta ta ɗebo kuɗaɗe, Dubu ashirin ta kirga sannan ta miƙawa Salma. Amsa ta yi tana kallonta, Khadijah ta ce “Ki dinga cin abinci kin ji” Girgiza kai Salma ta yi ta zari dubu ɗaya daga cikin kuɗin ta miƙawa Khadijah sauran tana cewa “A'a wannan ma ya isheni ai” Harararta Khadijah ta yi ta ce “Nasan da hakan kuma na baki ai, Ki riƙe a wajenki zai miki amfani” Shiru Salma ta yi tana kallon kuɗin can kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Nagode sosai, Allah ya biya ki” Khadijah ta yi murmushi ta ce“Ameen Salma, Bari naje kar na rasa abin hawa” Toh kawai Salma ta ce, Khadijah ta juya ta bar gurin. Jujjuya kuɗin Salma ta dinga yi tana tunanin yanda zata yi da su. Zayyad ne ya ƙara faɗo mata a rai, Ta gyara riƙon kuɗin sannan ta bar wajen tana tafe da sauri. Kai tsaye Orange market ta nufa, Ta dinga yawo cikin kasuwar amma Allah bai haɗata da Zayyad ba, Gajiya ta yi ga yunwa data isheta, Idanunta har rufewa suke saboda tsabar azaba. Dubawa ta yi ta ga duk masu abincin kasuwar sun tashi, Haka ta bar kasuwar tana tafe kamar zata faɗi. A bakin titi ta sami wani mai gashi Gurasa, Ta ƙarasa gabansa ta siya ta ɗari biyar, Wani kanti a gefe ta shiga ta amso ruwa pure water sannan ta ci gaba da tafiya. ***Ban da kuka babu abin da take har ta dawo inda suka zauna ɗazu da Zayyad saboda wajen kamar yafi mata tsaro, Inuwar mutum ta hanga zaune kan yashi ya tankwashe ƙafafunsa, Da gudu ta ƙarasa duk da yanda take jin jikinta. Turus ta yi a kansa tana kallonsa, Wasa yake da tarin ƙasa da yashin wajen, Idan ya haɗa sai ya wargaza yana yi yana yan maganganu. Sakin ledar hannunta ta yi ta durƙusa gabansa tana kallonsa, Ɗago kansa shima ya yi ya kalleta sai kuma ya yi murmushi, Fuskarsa tass da ita kamar bashi ba, Duk yanda take jin tsoronsa haka ta dake ta ce “Ina ka tafi? Me yasa zaka yi tafiyarka?” Shiru ya yi mata Sai dai bai ɗauke Idanunsa daga kanta ba, Zaman dirshan Salma ta yi akan yashin sai kawai ta fashe da wani irin kuka. Bin ta da kallo ya dinga yi ganin yanda take kukan kamar ranta zai fita, Tashi ya yi ya ɗauko ledar bayansa ya miƙo mata, Ɗago kanta ta yi ta kalli ledar sai kuma ta kalleshi, Karɓar ledar ta yi ta cillar da ita gefe sannan ta ci gaba da kukanta. Kwaɓe fuska Zayyad ya yi sai kuma ya ɗora kansa akan cinyarta ya fara kukan shima. Tsit Salma ta yi ta ɗago kanta tana kallonsa, Kuka sosai yake yi tana jin zubar hawayensa kan cinyarta, Ji ta yi jikinta ya yi sanyi ta ɗago kansa a hankali ta ce “Ka daina kuka ya isa” Gyada mata kai ya dinga yi kamar ƙaramin yaro, Ta sanya hannunta ta goge masa hawayen sannan ta ce “Shikenan nima nayi shiru kai ma ka daina kuka Yaya Yad, Amma nan gaba kar ka sake tafiya wani wajen ka barni” Bai bata amsa ba, Sai kawai ya tashi, Ta bishi da idanu tana kallon abin da zai yi. Ledar data yar ya ɗauko sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, Da kansa ya buɗe ledar, Shinkafa da miya ce a ciki har da salad, Ta kalleshi da mamaki ta ce “Ina ka samo abinci? Wane ya baka?” Bai bata amsa ba, Ya ɗauko ledar pure water dake bayansa ya fasa, Hannunta ya kama ya fara wanke mata kamar yanda ta yi masa ɗazu. Ta dinga kallonsa tana murmushi mai haɗe da hawaye, Sai da ya gama tsaf sannan ya tura mata ledar gabanta. Gefen hannunta ta sanya ta share hawayenta sannan ta yi murmushi ta sanya hannunta cikin ledar, Ɗiban abincin ta yi ta kai baki bayan ta yi bismillah, Ya dinga kallonta tana cin abincin har ta gama. Murmushi ya yi sannan ya jawo wata ledar ya shiga buɗewa yana cewa “Yanzu sai na baki magani ki sha, Ki kwanta” Ya yi maganar yana jin jina kansa, Buɗe ledar ya yi taga duk tarkacen ledojin pure water, ledar biscuits, ledar chocolate har da robar lemo. Salma bata san sanda ta fara hawaye ba tana shassheƙar kuka a hankali, Ɗago kansa ya yi ya kalleta yana ɗaura wani zaren tabarma jikin robar lemon ya ce “Ki bar kuka yanzu zan baki magani” Wani irin tausayinsa ta ji ya rufeta, Ta janye ledar daga gabansa, Kafin ta yi magana ya ce “Ina zaki kai min magungunan, Daga asibiti fa nake” Shar hawaye suka sake zubowa kan fuskarta, Cikin shassheƙar kuka ta ce “Ajiye maka zan yi” Zai sake magana ta fito da ledar Gurasar data siya. Murmushi ya yi yana kallonta ya ce “Mommah Abinci ki ka siyo min?” Gyaɗa masa kai ta yi still crying ta ce “Eh, Kaci, Sai ka bani maganin” Jinjina kansa ya yi sannan ya amshi ledar daga hannunta, Buɗewa ya yi ya leka sai kuma ya ture yana haɗe fuska, Ta kalli ledar sai kuma ta kalleshi ta ce “Mene ne? Ko baka so” Tura baki ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce “Ni ba irin wannan ba, Mene wannan?” Ɗan murmushi ta yi ta ce “Gurasa sunanta, Yana da daɗi fa, Ni na siya maka ko baka son abincin hannuna?” Ta ƙare maganar da damuwa akan fuskarta. Kallonta kawai Zayyad ya yi sai kuma ya sake karɓar ledar ya ɗora kan cinyarsa ya sanya hannunsa ya ɗauko slice na gurasar ya kai bakinsa. Lumshe idanunsa ya yi yana murmushi ya ɗauko wata ya sake kai wa baki, Salma kallonsa kawai take tana murmushi mai ɗauke da hawaye. Sai da ya kusa cinyewa sannan ya kalleta, Harararta ya yi sai kuma ya ce “Ke mene ne ki ke kallona ko kin sanni ne?” Girgiza kanta kawai ta yi tana murmushi ta ce “Ni ban sanka ba” Ya gyaɗa kansa ya ce “Yawwa to dai, Ni bana son kallo.” Salma dai bata ce komai ba sai kallonsa take, Tas ya cinye gusarar ya miƙo mata ledar yana cewa“Amshi nan ki je ki ɓoye” juya ledar ta yi sai kuma ta ce“Ledar zan ajiye kuma?” A fusace ya ce “Ko ba zaki ajiye bane? Ni abokin wasanki ne?” Shiru Salma ta masa, Ya tashi tsaye ya shiga zagaye a filin sai kuma ya dawo, Shaƙe mata wuya ya yi ta baya, Ta sanya hannunta duk biyun tana dukan nasa hannun. Cikin kakkausar murya yake cewa “Ni abokin wasanki ne ina miki magana zaki min banza, Kin ga ina miki wasa? Ko mahaukaci ki ka ɗaukeni!” Dakyar Salma ke numfashi, Ta ci gaba da dukan hannunsa, Ƙin cikata ya yi ya sake takure hannunta a wuyanta, Idanunta suka fara firfitowa. Kamar daga sama taji wani mufini na magana, Ya ƙaraso wajen ganin yanda Zayyad yake durƙushe, Taɓa shi ya yi ai kuwa ya saki Salma ya shaƙe nasa wuyan. Dafe wuyanta ta yi tana sauke wani wahalallen numfashi, Sai dai ganin yanda Zayyad yana ƙoƙarin raba mutumin da numfashinsa ya sanya ta tashi tsaye, Ihu ta saki ta ƙarasa gabansu. Rirriƙeni Zayyad ta yi tana kuka ta ce “Dan girman Allah Yaya Zayyad ka bari, Ka dawo cikin hankalinka mana, Ka rabu dashi” Hannu ɗaya ya saka ya hankaɗata ta fadi ƙasa sannan ya mai da hankalinsa kan mutumin yana sake matse hannunsa. Duk yanda ta bugu a ƙasa hakan bai hanata sake yunƙurawa ta tashi ba, Ta sake nufarsu ganin yanda idanun mutumin suka yi, Dukan Zayyad ta shiga yi tana bashi hakuri amma sam ya ƙi saurarenta, Ta yi baya ta zubawa sarautar Allah ido, Can kuma ta sake nufarshi da sauri. Dagewa ta yi ta sakar masa ciwo a gefen ciki zafi da kiɗimar daya shiga ya sanya ya saki wuyan mutumin ya dafe gefen cikinsa. Tafiya mutumin ya yi ya fadi ƙasa ya riƙe wuyansa yana sakin numfashi dakyar, Da gudu ta ƙarasa wajensa tana kallonsa ta ce “Sannu Baba, Tashi ka gudu kar ya sake biyo ka” Muryarsa bata fita ya ce “Mahaukaci ne daman?” Gyada masa kai kawai ta yi tana hawaye. Ya girgiza kansa ya ce “Meyasa ba zaki kai shi asibiti ba, Ina iyayensa?” A sanyaye ta ce“Zan kai shi Baba, Ka tashi ka tafi kar ya sake dawowa kaga babu mai cetonmu” Dakyar mutumin ya tashi ya bar wajen yana tafe jiki babu kwari, Salma ta maida idanunta kan Zayyad wanda ke tsaye har sannan yana kallon gefen cikinsa. A mugun tsorace take dashi dan ba ƙaramar shaƙa tasha ba, Gani ta yi ya maido idanunsa inda take, Gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Tashi tsaye ta yi tana kallonsa a firgice ganin ya fara tawowa, Da gudu ta juya ta bar wajen, Yana ganin haka shima ya bita da gudun. Zagaye suka dinga yi cikin filin, Har da shiga gonar mutane, Cikin rashin sa'a ta daki wani dutse ta bige ƙafa, Durƙushewa ta yi a wajen ta runtse Idanunta. Kallon ɗan yatsan ta yi taga yana jini ta matse da hannunta tana jin wata irin azaba. Dariyar data ji ya sanya ta juyo tana kallonsa, Zaune ta gansi yana tuntsira dariya yana girgiza kansa. Ɗauke kanta tayi daga kallonsa ta tashi ta fara tafiya a hankali, Sai kawai taga shima ya tashin ya sake biyota. Ihu ta saka ta kwashi gudu ta take ƙafar duk da azabar da take mata. Suka ci gaba da zagaye cikin filin, Gajiya ta yi ta tsaya, Cak shima taga ya tsaya yana nunata yana dariya. Kuka ta fara yi tana kallonsa ta ce “Kaga Yaya Yad ka rabu dani, Ni ka daina bina wallahi, Bana so” Tuntsirewa ya yi da dariya har da tafa hannu. Ta goge hawayenta sai kuma ta juya ta bar gurin, Ganin shima ya ci gaba da tawowa ya sanya ta sake ɗiba da gudu. Zayyad kuwa tsayawa ya yi yana dariya yana girgiza kansa, Can kuma ya juya ya koma inda suke zaune. **** Asokoro, Abuja. Turo kofar dakin ta yi a hankali, Zaune ta hangeta gefen gado ta zuba uban tagumi, Ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso ciki. A gefenta ta zauna tana kallonta ta ce “Khadijah” Ɗago kumburarrun Idanunta ta yi ta kalli Mami, Kawai ta rungumeta tana fashewa da kuka. Ita kanta Mami dauriya kawai take hawaye suka shiga bin fuskarta, Sun ɗauki lokaci a haka kafin ta janye jikinta daga nata tana kallonta ta ce “Ya isa haka, Ki yi shiru, In sha Allah za'a gan shi” Cikin shassheƙar kuka Mommah ta ce “Yaushe Mami? a ina za'a ga Zayyad? Mami ya haukace fa, Ta haukata shi daga taimako” Mami ta ce “Karki damu in dai an ganshi ai da sauki, General ya saka a baza hotunansa a Abuja, Ai duk inda yake ba zai shige nan ba. Zayyad ba zai ɓata ba in sha Allah” Jinjina kai Mommah ta yi ta ɗauke kanta tana kallon gefe ta ce “Wallahi Mami nayi nadama, Nayi dana sanin yarda da yarinyar nan, Babu kama wallahi” Numfasawa Mami ta yi ta ce“Duk da haka kema kina da laifi, Akan me zaku bari ya bar gidan nan da sunan ya haukace? Korarsa fa kuka yi. Koda Zayyad ya haukace at least ya kamata a ce an bar shi a gidan nan an duba lafiyarsa, Akan me za'a koreshi daga gidan ubansa?” Cike da damuwa ta ce “Mami ai dole sai ya bar gidan a sannan, Haka aka ce in dai har ya fadi wanda ya masa asiri to sai dai ya bar gidan, Shiyasa” Tsaki Mami ta yi ta ce“Ai shikenan sai ku yarda da wannan maganar” Mommah zata yi magana aka buɗe ɗakin aka shigo, Kallonsu ya yi sai kuma ya ce “Mami dare nayi” Kallon agogon hannunta ta yi sai kuma ta ce “Tom Ahmad gani nan” Okay ya ce sannan ya kalli Mommah wadda ke hawaye, Bai sake cewa komai ba ya juya ya fice daga ɗakin. Numfasawa ta yi sannan ta sake maida idanunta kan Mommah ta ce “Ni zan tafi dare nayi, Duk yanda ake ciki sai mu yi waya, Amma a tabbata an samo Zayyad” Toh kawai Mommah ta iya cewa, Mami ta tashi ta fita daga ɗakin dan Mommah ba fita zata yi ba drip ne a hannunta. A corridor ta sami Ahmad ya yi shiru daga gani wani abun yake tunani, “Ahmad” Mami ta kira sunansa. Ɗago kansa ya yi ya kalleta da idanunsa wanda ruwa yake a kwance ya ce “Na'am Mami” A sanyaye ta ce ”Muje” Okay ya ce sannan ya fara sauka daga stairs ɗin, Har ta nufi stairs ɗin sai kuma ta juya ta buɗe ɗakin ta shiga. Babu kowa a parlon hakan yasa ta shige bedroom ɗin kai tsaye. Zaune ta hangeta tsakiyar gadon ta cure jikinta waje ɗaya sai shassheƙar kuka take. Numfasawa Mami ta yi sannan ta ƙarasa ta zauna gefen gadon still looking at her ta ce “Auta” Ɗago fuskarta wadda ta yi caɓa caɓa da hawaye ta yi ta kalli Mami, Girgiza kai Mami ta yi ta ce “Ki daina kukan nan mana Nayla” Kamar Mami ta turata haka ta sake rushewa da wani sabon kukan. Mami ta riko hannunta cikin sanyin murya ta ce “Kuka ba zai magani ba Nayla, addu'a zaki dinga yiwa Yayanki In sha Allah za'a gan shi” Cikin shassheƙar kuka ta ce “Mami Yaya Zayyad fa ya haukace, Mami yayana ya haukace, Kuma wallahi ba Salma ce ta haukata shi ba sharri aka yi mata. Duk su Mommy sun ƙi yarda dani, Salma bazata aikata haka ba” Goge mata hawayen Mami ta yi ta ce“Ko ita ce ko bata ita ba ce Allah zai bayyana Nayla, Allah zai kawo hasken da zai warware komai, Gaskiya bata taɓa ɓuya saboda haka bana son kina wannan kukan ki tashi ki yi wanka ki ci abinci kin ji” Jinjina kanta kawai ta yi amma ba dan tana jin zata iya tashin ba. Mami ta sauka daga kan gadon ta ce “Be a good girl kin ji Nayla, In sha Allah idan na dawo zan tafi dake” To kawai Nayla ta iya cewa tana goge hawayenta. Mami ta juya ta bar ɗakin. Sun ɗan yi nisa Ahmad ya kalleta ya ce “Any news Mami?” Girgiza kanta ta yi tana kallon titi ta ce“Ko kaɗan Ahmad, Ban gane in da suka dosa ba gaba daya, I'm bit confused yanda general zai bar Zayyad ya fita a gidansa. Wannan ba daidai bane!” Furzar da iska Ahmad ya yi yana ci gaba da kallon titi ya ce“I think so Mami, Duk da ban san yarinya ba amma ina jin kamar ba zata yi haka ba, Yanda suke faɗa fa sa'ar Nayla ce, Tayaya mai shekaru irin na Nayla zata yi tunanin haukata mutum kamar Zayyad, And idan ma ta haukatashin wace riba take da? Dama cewa aka yi tana son aurensa sai nace” Mami ta girgiza kanta ta ce“Bar sharrin duniya Ahmad, Za'a iya haɗa baki da ita koda ba ita ce take da desire na haukatashin ba. Wannan ba zamu yanke hukunci kai tsaye ba, Amma duk abin da ya faru bai dace General ya bar shi ya fita a gida ba tunda har ya san bashi da hankali, Amma in sha Allah za'a ganshi cause sun saka matakan tsaro sosai” Ahmad ya ce“Allah ya sa hakan, Amma Abin yana bani mamaki Mami, Wai Zayyad ya haukace, How?” Numfasawa Mami ta yi ta ce“Kaddararsa kenan, Allah ya bashi ikon cinyeta ya dawo dashi gida lafiya”. Ahmad ya ce Ameen sannan ya maida hankalinsa kan tuƙin da yake. **** Tafiya take kamar mara gaskiya tana leƙen inda yake, Har sannan yana zaune kan yashin yana wasa dashi. Ta ƙaraso tana kallonsa hannunta riƙe da takalmanta, Zama ta yi can nesa dashi tana kallonsa. Ya ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya tuntsire da dariya, Gyara zamanta ta yi tana gani ko tashi zai yi sai taga ya yi kwanciyarsa nan ƙasa yana ci gaba da dariya. Ita dai Salma kallonsa kawai take, Ta yi shiru tana tunanin yanda zata yi, Ba zata ci gaba da zama dashi a haka ba, Kuma bata san inda zata kai shi ba. Babban abin da ya dameta daya kasance basu da wajen kwana, Ga yanayi na damuna. Tana wannan tunanin ta ga ya tashi daga kwancen da ya yi, Ya dawo inda take ya zauna yana bin ta da wani irin kallo, A ɗan tsorace ta ce “Mene ne...?” Langwaɓar da kansa ya yi ya ce“Nurse Mommah ce acan gurin zata tafi dani kar ki bar ta” Ji tayi gabanta ya faɗi ta kalli inda yake nuna matan amma bata ga komai ba, Sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta yi sai kuma ta ce “Babu kowa fa, Ka kwanta dare ya yi” Maƙale kafada ya yi ya ce“To kema ki kwanta ni ba bacci zan yi ba” Murmushi ta yi ta ce“To zan kwanta kai ma ka kwanta” gyaɗa mata kai ya yi ta gyara ɗankwalinta ta kwanta kan yashin duk da sanyin da wajen ya ɗauka. Lumshe idanunta ta yi don daman mugun bacci take ji nan da nan kuma ya ɗauketa, Ƙura mata idanu Zayyad ya yi yana kallonta can kuma shima ya kwanta ya rufe idanunsa. Can cikin bacci taji kamar ana taɓa fuskarta, Ta buɗe Idanunta a hankali, Inuwar mutane ta kalla, Ta tashi zaune tana ja da baya, Kallon mutumin dake tsaye a kanta ta yi, Ya saki murmushi haƙoran suka bayyana duk da duhun da wajen yake da cikin kakkausar murya ya ce “Ummulsalma kenan, Ba zaki iya gujewa ƙaddararki ba, Dole ki ci gaba da zama da wannan mahaukacin domin ke ce hasken rayuwarsa, Ke ce wadda za ki fito dashi daga cikin duhun da yake, Baki isa ki sauya wannan al'amarin ba, Saboda haka ki shirya kalubale kala kala anan gaba, Ba'a fara komai ba Salma, Baki fara ganin komai ba cikin abubuwan da zasu faru nan gaba daga ƙarshe kuma zaki yi farin ciki, Zaki ji dadi sai dai wani abu zai zo da zai yanke wannan jin daɗin...!” # HCD # Light within the darkness # Yaya Yad # Salma # Nanameera 08106608363 For more information contact me. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 19-20: "Stay with me" Nanameera, YOTA/023. Mutumin ya ja dogon numfashi ya sauke kafin ya ci gaba da fad'in “Nasan kina da haƙuri to ki ƙara, Kina da tausayi to ki ƙara, Akwai abubuwan da zasu faru wanda baza su miki daɗi ba amma dole ne ki yi haƙuri sannan kuma ki jure kowace irin wahala, Tabbas lokaci zai zo komai zai shige kamar ba'a taɓa yin sa ba!” Ɓat mutumin ya ɓacewa ganinta, Juyi ta shiga yi daga kwancen da take, A firgice ta tashi zaune tana dafe ƙirjinta wanda yake bugawa da ƙarfi, Kallon wajen ta dinga yi tana tunanin abin da mutumin ya ce mata. Daman ba gaske bane mafarki ta yi? Salma ta tambayi kanta, Ganin babu kowa a wajen ya sanya ta sake gazgata hakan, A hankali ta juya Idanunta kan Zayyad. Bacci yake har sannan ya cure jikinsa waje guda da alama sanyi yake ji, Mayafin kanta ta ware ta tashi ta ƙarasa inda yake kwancen ta tsuguna ta rufa masa mayafin. Ajiyar zuciya ya saki yana mai gyara kwanciyarsa ya ci gaba da baccinsa hankali kwance, Numfasawa Salma ta yi sannan ta tashi ta koma in da take ta zauna tana ci gaba da tunane tunane. ****Zaune ya sameta ta zuba uban tagumi, Ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido ba tare da ya ce komai ba. Ganin irin kallon da yake mata ya sanya Salma kallonsa itama a sanyaye ta ce “Mene ne Yaya yad?” Langwaɓar da kansa ya yi bai magana ba, Ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta ta ce“Ka zauna a nan naje na siyo mana abinci” Miƙewa ya yi yana karkaɗe ƙasar jikinsa, Ta kalleshi sai kuma ta ce “Ka zauna yanzu zan dawo fa” Maƙale kafaɗa ya yi still looking at her, Salma ta sauke nunfashi sai kuma ta yi gaba shima ya bi bayanta. Duk inda suka shige sai an kallesu dan lokacin safiya ce yara sai tafiya makaranta suke, Ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya tana tunano sanda ita ma take zuwa makarantar, A duniyar Salma idan da abin da tafi ƙauna to karatu ne, Burin rayuwarta taga tana zuwa makaranta ta tara ilimi mai yawa, Sai dai rayuwa kowa da ƙaddararsa ita rashin karatun shi ne ƙaddararta. Ihun da taji ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, Da sauri ta ƙarasa wajen ganin Zayyad ana kokawa dashi da wasu yara. Sosai jama'a suka fara taruwa ya riƙe kwalar rigar mutumin ya ƙi saki, Ta cikin mutane ta kutsa ta shiga inda suke, Kallonsa ta yi ta ce “Mene ne haka Yaya Yad sake shi mana” Ko kallonta Zayyad bai yi ba sai ma sake riƙe shi da ya yi, Salma ta kalli tarin jama'ar dake wajen ta matsa kusa da shi sosai ta ce “Ka sake shi ko na tafi na bar ka ba zaka sake ganina ba” Kallonta ya yi da idanunsa wanda suka yi wani irin jaa, Ta jinjina masa kai alamar tabbatar da abin da ta faɗa. Hankaɗa mutumin ya yi ya faɗi ƙasa a wajen, Ya juyo yana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, Ja da baya kowa ya yi aka dara masa hanyar ya yi shigewarsa hannunsa duk biyun bisa ƙugunsa kamar mace. Girgiza kai Salma ta yi sannan tabi bayansa, Sai da suka ɗan yi nisa sannan ta kalleshi ta ce “Idan kana shaƙe wuyan mutane zan daina tafiya ko ina da kai, Ba'a shaƙe wuyan mutum ko kana son ka yi kisa ne?” Cak ya tsaya da tafiyar da yake ya kalleta kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“Ni abokin wasansu ne to?” Sosai ta yi mamakin furucin nasa ta ce “Me suka yi maka to faɗa min” Harararta Zayyad ya yi ya miƙi hanya ba tare da ya amsa maganarta ba, Ta girgiza kanta sannan tabi bayansa. Orange market suka je, Ta tsaya gaban masu suyar masa tana kallonsa ta ce “Na siya maka waina?” Girgiza mata kai ya yi ta ce“To me zaka ci?” Ledar biscuit ɗin hannunsa ya nuna mata, Ta amshi ledar ta juyata sannan ta ce“To zan siya maka” Daga haka ta ƙarasa wajen masu suyar wainar, Sai da ta siya masu wainar sannan ta dawo inda yake tana kallonsa ta ce“Tsaya a nan naje na siyo maka biscuit ɗin a shagon can” Ta ƙare maganar tana nuna masa shagon dake gefen hannun hagunta. Daga haka ta yi gaba, Biyota taga ya yi ta tsaya ta ce“Ba zaka jiranin ba?” Gyaɗa mata kai ya yi ta ce“Tom muje”. Tunda ta shiga shagon yake kallonta, Salma da bata lura dashi ba ta miƙawa mai kantin kuɗi ta faɗa masa abin da zai bata, Kamar daga sama taji an ce “Salma!” Da mamaki ta juyo dan ganin wanda ke kiran sunanta, Sakar baki ta yi tana kallonsa shi kuma ya yi mata murmushi. A nutse ya ce “Rufe bakin mana” Kunya ce ta rufeta ta sanya hannunta ta rufe fuskarta, Dariya mara sauti Al-ameen ya yi kafin ya ce“Ina ki ka tafi na daina ganinki? Naje gidanku aka ce wai kun tashi meya faru Salma?” Numfashi ta sauke kafin ta ce“Abbana ne ya rasu shiyasa, Ni yanzu ma banida gida ai” Da mamaki ya ce“Kamarya baki da gida, A ina ki ke kwana kenan?” Ɗan murmushin yaƙe ta yi ta ce“A waje, Ina dai neman inda zan zauna ne” Shiru Al-ameen ya yi yana nazarin kalamanta, Da gaske babu wasa ko ƙarya a ciki, Sai dai mamaki ya ishe shi daman yarinya mai shekaru irin nata zata iya wannan rayuwar? “Sai anjima” Maganar Salma ta dawo dashi daga tunanin da yake. Girgiza kansa ya yi a sanyaye ya ce “Why not ki zo gidanmu Salma, Mami na da kirki zata riƙe ki kamar ya” Wani irin abu taji ya tokare mata a ƙirji, Zuwanta gidansu Zayyad ya faɗo mata a rai. Hawaye yaga tana yi ya girgiza kansa a ruɗe ya ce“A'a Salma yi haƙuri idan hakan ya ɓata miki rai, Idan baki so ba sai kin zo gidanmu ba” Goge hawayenta ta yi cikin shassheƙar kuka ta ce“Nagode sosai da niyyar taimakona amma ba zan iya zuwa gidan kowa ba, So nake na samu inda zan dinga aiki ana biyana na samu na kama mana gida” Al-ameen ya ce“Au bake kaɗai ba ce?” Saurin kallonsa ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“Ni kaɗai ce mana” Jinjina kansa ya yi ya ce“Shikenan yanzu kamar nawa ki ke ganin zai isheki ki kama gidan?” Kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta ce“Nima ai ban sani ba fa” Ɗan murmushi Al-ameen ya yi ganin yanda ta yi da fuska ya ce“Alright, Zaki jirani a nan yanzu na dawo?” Numfasawa ta yi sai kuma ta gyaɗa masa kai. Murmushi ya yi ya nuna mata bencin dake wajen ya ce“Oyah sit I'll be back right” Jin jina kanta kawai ta yi ya juya ya bar kantin. ****Tana nan zaune har bayan mintuna talatin kafin Al-ameen ya yi parking motarsa ya fito, Ƙarasowa ya yi yana murmushi ya ce“Sorry na bar ki kina jira” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Har na gaji kuma Jakar hannunsa ya miƙa mata ya ce“Nasan zai iya isarki ki kama gida har na shekara biyu, sauran kuma sai ki siya abinci, Iya ka abin da nake da shi kenan Salma, Duk mun zuba kuɗin a company” Bata san sanda ta fara hawaye ba, Ta girgiza kanta cikin shassheƙar kuka ta ce“Har abada ba zan manta da abin da ka min ba Yaya Al-ameen, Idan na samu dama zan saka maka in sha Allahu, Allah ya biya ka” Lumshe idanunsa ya yi ya ce“Ameen Salma” Ya miƙa mata wani kwali yana murmushi ya ce“Ki rike wannan wayar a hannunki na dinga kiranki” Amsar kwalin wayar ta yi ta shiga jujjuya shi sai kuma ta ce“Tom in sha Allah Yaya” Murmushi ya yi ya ce“Tom Allah ya sake haɗa fuskokinmu” Gyaɗa masa kai ta yi still smiling ta ce“Ameen ya rabbi” Daga haka ta tashi daga zaune da take ta ɗauki ledojinta ta yi gaba tana tafe tana waiwayensa. Sai da ya ga ta nufi hanyar Kabayi sannan ya sauke ajiyar zuciya ya koma in da ya yi parking motarsa ya shiga. Tafiya kawai take tana dube-dube a hanya ko Allah zai haɗata da Zayyad, Sai dai iya dubanta bata gansa ba har ta ƙarasa inda suke zaune kwana biyun nan. Zaune ta sameshi ya kifa fuskarsa a tsakanin cinyoyinsa, Da sauri ta ƙarasa gabansa ta dire ledojin hannunta da jakar kudin tana murmushi ta ce “Yaya yad ɗago kaga, Na samar mana kuɗi zamu je mu siya gida” Banza ya yi mata bai ɗago kansa ba ta sake masa magana, A fusace ya ɗago ya hankaɗeta daga kusa da shi, Da mamaki Salma ke kallonsa ganin yanda idanunsa suka yi wani irin ja jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, Jiki a sanyaye ta sake nufo shi muryarta na rawa ta ce “Yaya Yad, Mene ne haka?” Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa. Ta sake matsawa daf dashi kamar zata yi kuka ta ce“Meyasa ka ke fushi dani to?” Ɗauke kai Zayyad ya yi yana kallon gefe, Salma ta yi shiru sai kuma ta janyo kansa gaba ɗaya ta ce“Yaya Yad ɗinaa, Ka yi haƙuri kaji, Na siyo maka biscuit ɗin fa” Kallonta ya yi sai kuma ya sake ɗauke kansa yana magana ƙasa ƙasa, Girgiza kai Salma ta yi ta janyo ledar da tazo da ita ta buɗe. Biscuit ɗin ta ɗauko ta miƙa masa tana murmushi, Kallon ledar ya yi sai kuma ya kalleta, Ta gyaɗa masa kai tana murmushi, Ya sanya hannunsa ya karɓi biscuit ɗin sannan ya ce “Da kin siyo mana ki ka bar mu a tsaye, Shi wannan likitan da kike magana dashi ai na sanshi” Sai a sannan ta gane dalilin fushin nasa, Ta yi murmushi ta ce“A ina ka san shi?” Farke ledar biscuit ɗin ya yi ya ɗauki ɗaya ya kai baki sannan ya ce“Na taɓa masa allura” Salma ta girgiza kanta dan ta gane zancen soki burutsu yake ta ce“Tom shikenan kaci biscuit ɗin zan je na dawo” Gyaɗa mata kai ya yi ta tashi ta ɗauki jakar da Al-ameen ya a bata ta bar wajen, Ta yi nisa sosai ta ji ya ƙwala mata kira ya ce “Kar ki daɗe ki bar mu” Murmushi ta yi ta ɗaga masa hannu sannan ta juya ta ci gaba da tafiya, Shi kuma ya mayar da hankalinsa kan abin da yake. Yawo Salma ta dinga yi cikin Kabayi, Har wajejen ƙarfe 12pm tana tafiya daga nan taje nan, Daga ƙarshe kawai ta yanke shawarar zuwa gidan Hajiya Turai ƙawar Ummarta. Da sallama ta shiga gidan, Babu kowa tsakar gidan sai tarin datti da kayan wanki dan daman Hajiya Turai gwanar ƙazanta ce, Sai da ta yi sallama sau biyu kafin ta ɗaga labule ta fito, Da mamaki take kallonta kafin ta ce “Wa nake gani kamar Salma?” Murmushi Salma ta yi ta ƙaraso ciki ta tsuguna ta gaisheta, Cikin fara'a ta amsa tana cewa “Daman kina nan Salama?” Jinjina kai Salma ta yi ta ce“Eh, Umma ina nan, Daman zuwa nayi na tambayeki” Hajiya Turai ta ce“To Salama shigo ciki” Daga haka ta nufi cikin ɗakin, Tsaf ɗakin yake saɓanin tsakar gidan, Salma ta zauna gefen kujera ita kuma Hajiyan ta shiga cikin kitchen, pure water mai sanyi ta ɗauko ta kawo mata sannan ta zauna tana cewa “Ina jin ki Salama” Numfasawa Salma ta yi kafin ta ce “Umma daman ina son ki haɗani da waɗanda zan samu gida a wajensu na haya ina son na kama na dinga zama a ciki tunda Ummana ta tafi ta bar ni” Shiru Hajiya Turai ta yi na wasu sakwanni kafin ta ce“Ke kaɗai zaki zauna Salama?” Salma ta gyada mata kai a hankali, Numfashi ta sauke kafin ta ce“Kuma a garin nan?” Nan ma Salma ta gyada kai, Girgiza kai Hajiya Turai ta yi ta ce“A'a garin nan ba zai miki ba ki zauna ke kaɗai a gida Salma, Kin san dai yanayin tarbiyyar nan, Ni a ganina ki bar garin nan kamar zai fi miki” Shiru Salma ta yi tana tunani, Ita dai Hajiya Turai ta tsaya tana kallonta can ta ce“To Umma idan na bar garin nan ina zance?” Gyara zama Hajiya Turai ta yi ta ce“Yawwa ƴar gari, Akwai wani gidan haya dana sani zaki iya zuwa can ki zauna. Ɗaki ɗaya ya isheki” Salma ta kalleta kafin ta ce“A wane gari ne Umma?” Hajiya Turai ta ce“Cikin Kaduna ne” Salma ta kalleta ta ce“Umma bai yi nisa ba, Ban san kowa ba a can” Murmushi Hajiya Turai ta yi ta ce“Shi ne zaki rayu ba tare da wata matsala ba Salma, A nan kowa ya sanki, Zama ke kaɗai a gidan haya zai sanya idanun mutane ya koma kan ki, Amma idan ki ka bar gari babu wanda ya sanki” Salma ta yi shiru tana tunani, Tabbas abin da Hajiya Turai ta faɗa mata shi ne zai fi dacewa da ita. Bayan wasu mintuna ta ce“Tom Umma na yarda zan ɗauki shawararki” Jinjina kai ta yi ta ce“Yawwa Salamatu, Yanzu ki yi wanka dan naga kamar da datti jikinki sai na baki kayan Fati ki saka” Godiya Salma ta yi, Ta tashi ta shiga ɗaki. **** Abacha road, Mararaba. Taɓe baki Mami ta yi hannunta riƙe da glass cup mai ɗauke da smooth ta kalli Fatiha ta ce“Haka aka ce miki?” Cikin shassheƙar kuka Fatiha ta ce“Wallahi haka ne Mami, Ni daman tun da naga yarinyar nan naji bata kwanta min ba. Babu yanda ban yi da Nayla ba amma ta kafe ai mutuniyar kirki ce. Ni ban san ma in da Yaya Zayyad ya samota ba!”. Mami ta ce“To kin san gidansu ne a nan ɗin?” Girgiza kai Fatiha ta yi ta ce“Ni ban sani ba Mami, Sai dai ko ita Nayla”. Ahmad ne ya ce“Ni fa nagane yarinyar, Ranar da muka je Orange market ita ce ta masa rashin kunya, But I don't know what comes over his mind da har suka sake haɗuwa ba har ma ya kai ta gidansu” “Ba sonta yake ba?” Al-ameen ya yi maganar yana saukowa daga stairs, Kallonsa Mami ta yi sai kuma ta ce“Haka ya ce maka? Zayyad ne zai ce yana son yarinya yar middle class kamarta” Numfasawa Ahmad ya yi ya ce “That's what I'm thinking too Mami, Zayyad fa baya ƙaunar yarinya mara aji, Duk yaran da zaki ga yana dating dasu ya'yan manya ne kamarsa, I'm just confused wallahi” Fatiha ce ta yi saurin cewa“Wallahi ni fa yaya ina ganin da gaske aikota aka yi ta haukata shi, Tun da ba zai rasa maƙiya ba” Mami ce ta ce“Ni ku bar wannan maganar dan Allah, Ɗazu mun yi waya da Khadijah ta ce an baza securities za'a gan shi soon, Har hoton yarinyar an baza” Al-ameen ne ya kalli Fatiha ya ce“Kina da pic ɗin yarinyar, Ni ban santa ba” Ya ƙare maganar yana zama kan kujera, Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta janyo wayarta akan table ta shiga gallery, WhatsApp pictures ta shiga ta yi scrolling kafin ta zo kan hoton wanda yake ita da Nayla ne. Miƙa masa ta yi tana cewa “Give it a look Ya Al-ameen” Amsar wayar ya yi, A firgice ya tashi tsaye yana sake kallon hoton “Salma!” Maganar ta kufce masa, Kallonsa duk suka yi, Ahmad ya ce“Lafiya?” Kasa basu amsa ya yi sai sake kallon hoton yake as if his life defend on it, Fatiha ce ta ce“Ka ganta ko yaya, wallahi ta yi kama da yan leƙen asiri daman” Shi dai Al-ameen bai ce komai ba, Ya sake taɓa daya hoton wanda take ita kaɗai ta yi murmushi, Girgiza kansa kawai ya shiga yi, Ahmad ya taɓa shi ya ce “Kai me ya dameka? Ka santa ne?” Gyaɗa masa kai ya shiga yi, Ahmad ya gyara zamansa yana kallonsa sosai ya ce“A ina? Wace ce ita?” Ajiye wayar Al-ameen ya yi ya ce “Yaya Na santa fa, Ita ce yarinyar da nake ce muku ina sonta, Sunanta Salma.” Da mamaki Ahmad ya ce “Ita ce wadda ka ce kaje gidansu baka sameta ba?” Ya jinjina kansa, Mami ta ce“To yanzu ina zamu sameta, Tare suka fita da Zayyad so definitely ita tasan inda yake” A ruɗe Al-ameen ya ce“Nifa i didn't understand wallahi, Yaya ko ɗazu fa na ganta” Miƙewa tsaye Ahmad ya yi yana kallonsa ya ce“A ina? Yaushe? Zaka gane inda ka ganta?” Kafin yayi magana Mami ta ce“Ahmad ku je tare, Bari na kira Khadijah na sanar da ita” Shi dai Al-ameen kallonsu kawai yake, Mami ta yi dialing numbern Mommah, Kira biyu ta amsa tana zaune gefen gado kusa da General wanda ke kwance hannunsa maƙale da drip a sanyaye ta ce“Mami ina yini” Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Khadijah yarinyar da ake magana a kai Al-ameen ya ce ya ganta ɗazu, Ki sanar da General a turo jami'an tsaro sai a samu a duba duk cikin Mararaban” Kafin Mommah ta yi magana General ya tashi zaune dan wayar a handsfree take. Duk yanda jikinsa yake hakan bai hana shi magana ba, Ya ce “A ina ya ganta? Kar ku ɗauki wani mataki yanzu zan turo jami'ai” Daga haka ya tashi fizge drip ɗin hannunsa ya yi sannan ya yi waje, Da idanu Mommah ta bi shi, Mami ta katse kiranta. Mai da Idanunta kan Ahmad ta yi ta ce“Ku je tare dashi Ahmad” Okay ya ce sannan ya kama hannun Al-ameen wanda ya zama kamar statue suka nufi hanyar waje. **** Hajiya Turai ta rakota har soro tana cewa“Duk yanda ake ciki idan kin je ki sanar dani Salma” Gyaɗa mata kai Salma ta yi ta ce“Tom Umma in sha Allah zan kira ki, Sai an jima” Suka sake sallama sannan ta fito daga gidan, Gaba ɗaya hankalinta ya yi kan Zayyad dan haka ta dinga sauri har ta fito titi. Motocin sojoji ta dinga gani suna shigewa convey ya cika ko ina na unguwar, Yara sai kallo suke, Haka kawai taji jikinta bai yarda da motocin ba hakan yasa ta ƙara sauri dan taje ta isa ga Zayyad. Koda ta dawo wajen zaune ta sameshi da wasu yara suna ta faman wasa sai dariya yake, Asalin kyansa ya sake bayyana. Ƙarasawa ta yi tana murmushi, Yana ganinta ya tashi yana dariya ya ce “Naga kin sauya fata” Ya ƙare maganar yana kallon hijabin dake jikinta, Murmushi kawai ta yi ta ce“Wanka nayi, Kazo mu tafi kai ma sai kayi” Girgiza kansa yayi ya ce “Ni banaso ba zan yi ba” Langwaɓar da kanta ta yi ta ce“Haba kai kuwa, Baka son kayi kyau kai ma ka sauya fata irin nawa?” Shiru ya yi ta sake cewa“Shikenan tawo mu tafi tun da baka so” Sai a sannan ya saki murmushi sannan ya ƙaraso, Hannunta ta miƙa masa ya riƙe sannan suka fara tafiya. Hira ya dinga yi mata duk da bata gane inda zancen nasa ya dosa a haka har suka ƙaraso bakin titi. Wani gidan wanka ta gani ta kalleshi ta ce “Kana son ka ci gaba da bina?” Gyada mata kai ya yi kamar ƙaramin yaro, Ta ce“To mu shiga nan ka yi wanka kaji Yaya Yad ɗina” maƙale kafada ya yi, Ta saki hannunsa ta ce“To ka yi tafiyarka kar ka sake bina” Daga haka ta juya ta ci gaba da tafiya. Bin ta ya yi da idanu sai kuma ya tsaya, Sai da tayi nisa sannan ta waigo ta hangeshi tsaye in da ta bar shi, Numfasawa ta yi sai kuma ta ci gaba da tafiya. Bayan two minutes ta sake juyowa sai dai bata ganshi ba, Da mamaki ta dinga kallon inda take hangensa da, Kawai ta dawo wajen, Dube dube ta shiga yi amma bata ganshi ba, Nan da nan hawaye suka fara sauka kan fuskarta. Ta dinga kiran sunansa tana kuka kamar itama na neman zarewa. Kamar daga sama taji dariyarsa, Ta juyo ta kalleshi, Dariya sosai yake ya riƙe ƙugu, Ba zaka taɓa ɗauka mahaukaci bane, Da gudu ta ƙaraso gabansa kawai ta rungumeshi tana sakin kuka. Shi dai Zayyad tsayawa ya yi yana kallonta, Bayan wasu sakwanni ta ɗago kanta har sannan da hawaye a fuskarta cikin kuka ta ce“Yaya Yad ka bani tsoro, Kar ka sake yimin irin haka dan Allah” Kamar daga sama ta ji ya ce “Ba tafiya zaki yi ki bar ni ba Mommah?” Girgiza kanta ta yi ta ce“Wasa fa nake maka, Ba zan taɓa tafiya na bar ka ba” “Alƙawari?” Zayyad ya faɗa a nutse yana miƙo mata tafin hannunsa. Gyaɗa kanta ta yi tana hawaye ta ɗora nata hannun ta ce“Eh nayi maka alƙawari ba zan taɓa barinka ba Yaya Yad, Zan zauna da Kai a duk yanda ka ke” Ya saki dariya yana tafa hannu, Itama murmushin ta yi sannan suka ci gaba da tafiya, Napep ta tsayar musu ta ce tasha zai kai su, Sannan suka shiga, Basu yi nisa ba suka iske tarin motoci da babura duk a cunkushe, Sojoji sai yawo suke a tsakanin kowa ce mota ana cajesu, Salma ta kalli Zayyad wanda ke kallon tit yana dariya abin sa, Ta sunkuyar da kanta tana hawaye dan tasan shikenan yanzu za'a rabata dashi, Ta sake kallonsa taga ya ƙura mata ido, Ta sakar masa murmushi hawaye na biyo kan fuskarta. # HCD # Light within the darkness # Yaya Yad # Salma # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 21-22: The mask of generosity Nanameera, YOTA/23. Girgiza kai Salma ta yi ta kalli Zayyad wanda ke kalle-kallensa ta sauke nunfashi sai kuma ta kalli mai Napep ɗin ta ce“Baba sauka zamu yi” Ba tare da ya juyo ba ya ce“Haba yarinya da kin ɗan jira, Yanzu zasu gama aikinsu, Ƙarshe wani mai laifin suke nema” Salma bata saurareshi ba ta kalli Zayyad ta ce“Sauka muje Yaya Yad” Kallonta ya yi sai kuma ya kwaɓe fuska kamar zai yi kuka ya ce“Ki bar ni anan Mommah, asibiti fa zan je” “Idan mun sauka zan kai ka asibitin sauka na ce” Daga haka ta kama hannunsa suka sauka daga Napep ɗin, Ta cikin motoci suka ratsa suka bar titin. Tafiya kawai suke Zayyad na bin ta amma fuskarsa a haɗe babu wata walwala. Sun yi nisa da titi yaja ya tsaya, Juyowa ta yi ta kalleshi ta ce“Muje mana” Ɗauke kansa ya yi yana kallon gefe, Ta dawo gabansa ta ce“Muje mana yamma nayi” Banza ya yi mata, Ta ja hannunsa ya fizge, Baki buɗe take kallonsa sai kuma ta ce“Yaya Zayyad kana son mu kwana anan ne? Common let's go mana” Ba zaka taɓa ɗauka da Zayyad take magana ba dan ko kallonta bai yi ba. Gajiya ta yi ta dawo bayansa ta dinga tura shi kamar mota yana turjewa, Daga ƙarshe ta sake shi tana haki. Neman waje ya yi ya zauna, Salma ta kalli Hanya ganin jama'a na shigewa sosai ta tsuguna gabansa muryarta na rawa ta ce “Dan girman Allah Yaya ka zo mu tafi kaji, Zan siya maka chocolate fa”. Kallonta kawai ya yi, Ta gyaɗa masa kai ya sake ɗauke kansa alamar zancen sam bai masa ba, Furzar da numfashi ta yi sannan ta sake cewa “To zan siya maka biscuit da alawa” Wannan karon ko arzikin kallon bata samu ba, A karo na barkatai ta sake cewa “Okay zan kai ka wajen Mommah” Da sauri ya kalleta ta gyaɗa masa kai, murmushi ya yi ya tashi har da kaɗe jikinsa ya yi gaba ya bar ta a tsugune. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta tashi ta bi bayansa. ****Sojoji biyu ne suka tsaya gaban Napep ɗin, Ɗayan ya ɗora hannunsa samanta yana kallon drivern ya ce“Baba tambaya muke” Mai Napep ɗin ya ce“To Yallaɓai Allah yasa na sani” Wani hoto ya zaro ya nuna masa ya ce“Kaga ɗaya daga cikin waɗannan?” Sake wara idanunsa ya yi kan hoton Zayyad da Salma wanda aka haɗe waje ɗaya. Ya ɗago ya kalli sojan sai kuma ya sake sunkuyar da kansa, Kenan dalilin daya sanya yarinyar ta ce sauka zasu yi kenan? To laifin me suka yi? Kamar mahaukaci ne ɗayan ai. “Baba kana ji” Maganar sojan ta dawo dashi daga tunanin daya tafi, Ya ɗago kansa yana kallonsa. “Ka gansu ne?” Sai kawai ya girgiza kansa a sanyaye ya ce“Ban gansu ba Yallaɓai, Ni babu wanda na ɗauko ma” Sojan suka kalli juna sai kuma ya gyaɗa kai ya ce“Alright” Daga haka ya yi gaba yana yi wa ɗayan signal da hannu. Sojan ya kalli mai Napep ɗin sai kuma ya ce“Get down Baba” Mai Napep ɗin ya sauko ƙasa jikinsa na rawa ya ce“Wani abun ya faru Yallaɓai? Wallahi ban gansu ba” cakumeshi ya yi ya fara tafiya dashi, Ya dinga magiya yana cewa bai gansu ba amma bai saurareshi ba, A gaban wata Hilux white colour ya tsaya, Ɗaya daga sojojin dake tsaye jikin motar ya buɗe ƙofar, General ne zaune kan kujera sanye da uniform na sojoji idanunsa maƙale cikin glasses black, Sojan ya sara masa sannan ya ce “Sir gashi, An ce an gansu a Napep ɗinsa amma ya ce basu shiga ba” General ya ɗago kansa ya kalleshi, Ajiye wayar hannunsa ya yi ya fito daga motar ya ja kwalar rigar mai Napep ɗin duk da shekarunsa, Fuskarsa a haɗe babu alamar annuri ya ce “Hey mr man! Ina suke?” Jikinsa na wata irin tsuma muryarsa na rawa ya ce“Wallahi wallahi ban gansu ba, Ban san su ba. Ni babu wanda na ɗauko” Jinjina kai General ya yi sai kuma ya sake shi, Ya kalli sojan ya ce “Ku je dashi duk abin da ya kamata a yi masa har sai sanda ya faɗi in da suke” Sake sara masa ya yi ya ce“Okay Sir!” Sannan ya ja wuyan mutumin, Kuka ya fara yi yana cewa“Dan Allah Yallaɓai ku rabu dani wallahi ban san su ba” Babu wanda ya sauraresa a cikinsu a haka aka shige dashi mota. **** Around 6:00pm suka iso tashar, Zayyad ya kalleta kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, Ƙarasawa ta yi tana tambaya motar Kaduna, Dakyar ta samu shima drivern ya ce ba zai tafi ba sai bayan sallar magriba, Haka kuwa aka yi suka zauna suna jiransa, Ta siyawa Zayyad abinci ya cinye tas dan ita ta ci abinci gidan Hajiya Turai. Ana idar da sallar kuwa motarsu ta tashi zuwa Kaduna, Basu yi nisa ba Zayyad ya fara jin bacci, Kasancewar a kusa da ita yake ya sanya ya ɗora kansa gefen kafaɗarta nan da nan bacci ya ɗaukeshi, Ita kuma ta ci gaba da kallon hanya tana jin kamar tafiya ce wadda ba zata sake dawowa Mararaba. Tana jin kamar wata sabuwar ƙaddarar ce take shirin kai ta Kaduna, Sai dai ta yarda kowace kaddara ce zata iya jureta muddin zata zauna tare da Zayyad. ****Ana idar da sallahr Isha'i suka shigo gidan, Mami na zaune kan sofa tana danna wayarta. Ganin jikinsu a sanyaye ya sanya ta ce “Ya ake ciki? An same su?” Zama Ahmad ya yi kan sofa ya lumshe idanunsa yana cewa“A'a Ba'a same su ba, Amma an samu wanda suka hau napep ɗinsa” Shiru Mami ta yi can kuma ta ce“Ina yake to?” Al-ameen dake tsaye ya ce“General ya saka an tafi dasu, But you know what Mami ba lallai bane a samesu wallahi” Wani banzan kallo Mami ta watsa masa wanda ya sanya shi sunkuyar da kai, Sannan ta ce“A saboda kai ne ka ke nemansu ko kuma ka san inda suke ba” Girgiza kansa ya yi ya ce“Allah ya huci zuciyarki Mami, Ni fa kawai faɗa nayi” “Eh shi faɗar, Get out from my side Malam!” Al-ameen bai sake cewa komai ba ya nufi stairs yana tafiya da sauri, Kai tsaye ɗakinsa ya shige ya zauna gefen drawer yana tunani, Can ya zaro wayarsa a aljihu ya ɗan juyata sai kuma ya shiga phone, Wasu lambobi ya rubuta ya tsaya yana kallon screen ɗin wayar above 2mins kafin ya danna kiran ya saka a speaker. Ringing ta dinga yi har ta gama ba'a ɗaga ba, Ya sake kallon screen ɗin yana mamakin rashin ɗagawar tata. Sake kira ya yi nan ma har ta katse ba'a ɗauka ba kawai ya haƙura ya yi cilli da wayar kan gado sannan ya tashi ya shige toilet. A can ɓangaren Mami tabi Al-ameen da kallo sai kuma ta numfasa ta ce “Na something wrong with this boy, Akwai abin da yake ɓoyewa” Jinjina kai Ahmad ya yi ya ce“I think so Mami, Dan ma baki ga yanda ya dinga behaving ba a wajen, Gaba ɗaya ma fa ba son a gansu yake ba” Girgiza kai Mami ta yi ta ce“Duk abin da yake ɓoyewa ma zai bayyana ne sai dai idan ba Al-ameen bane” Ɗan murmushi Ahmad ya yi ya ce“Mr talkative kenan, Wallahi Mami hankalina ba a kwance yake ba, Ko wane hali Zayyad yake, I dey missed him a lot” Jiki a sanyaye Mami ta ce“In sha Allah yana nan lafiya a duk in da yake” “Allah ya yarda” Ahmad replied. **** Iskar damina ta dinga tashi a hankali, tana ɗauke da ƙanshin ƙasa mai ɗumi da busasshiyar ƙura. Gajimare sun mamaye sararin samaniya, sun ɓoye komai sai ɗan ƙyalli daga fitilun motar da ke yanke duhun da gajimare suka lullube. Motar da suke ciki tana tafe a hankali kamar ta san cewa akwai wani sirrin da ke boye a gaba. Salma na zaune a gefen taga, hannayenta rungume a kirjinta, idanuwanta na kallon wajen amma ba ta ganin komai. Ruwa kadan-kadan yana soma bugu a gilashin taga, Ta ɗan kai dubanta wajen. Hankalinta ba a kan tafiyar bane, sai akan abin da ke gabanta a Kaduna. A inda rayuwarta za ta canza, ko dai da alheri… ko kuma ta faɗa cikin duhun da ba ta san yadda za ta fito ba. Ta juya kallonta ta kalli Zayyad wanda ke gefenta, Wanda a duniya kewa kallon mahaukaci, Sai dai ita a gurinta ba haka bane, Shi ɗin ƙaddararta ne yanzu, Shi ne kadai wanda ke da ikon kareta, ko halaka ta. Tunanin hakan ya haifar mata da wani irin yanayi a lokaci guda. Zuciyarta na bugawa da ƙarfi, tana tambayar kanta: "Me zai faru idan suka gane cewa muna tare? A kan me suke nemansa bayan su ne suka koreshi? Me ke shirin faruwa ne?. Wata iska mai ƙarfi ta buso, ta ɗan jijjiga motar kaɗan. Ta runtse idonta, tana jin kamar ana kiranta da wata murya daga cikin duhu. “Ki dawo,” zuciyarta ta furta, “ki koma inda kika fito.” Sai dai hakan ba mai yiwuwa bane, Babu koma baya. Domin suna gab da shigowa Kaduna Kaduna, Kamar mafarkin da ba za ta iya farkawa daga cikinsa ba. “Kin yi shiru,” Ta tsinkayi muryar Zayyad wanda ya tashi ɗan mintuna da suka shige. “Kina tsoron inda zamu je ne?, Mommah fa zamu gani” Ta kalli fuskarsa, wadda take a kwaɓe Sai dai akwai wata shaida ta ciwo da ɓoyayyen gaskiya. Sai ta ɗaga kai a hankali, ta ce da ƙasa-ƙasa, “Ban san abin da ke jiranmu a can ba.” Ya yi murmushi mara annuri, yana cigaba da kallon titi. “Mommah na can tana jirana Allah sarki, Ko ta sha paracetamol ɗin?” Wata forked lightning ta fito a sararin sama, tana haska hanya na ɗan lokaci. Wani karan tsuntsu da ba a san ko daga ina ya fito ba ya kara. Motar ta ci gaba da tafiya, kamar zuciyarsu biyu na ɗanɗana wani abu iri ɗaya: Tsoro, fata, da tambayoyin da babu amsa a yanzu. Ana kiraye-kirayen sallar asuba suka isa tashar a Kaduna, Tsayawa motar ke da wuya kuma passenger suka fara sauka, Salma ta kalli Zayyad wanda yake bacci gefen kafaɗarta, Ta kai hannu ta taɓa Fuskarsa. Buɗe idanunsa ya yi yana mitsitsika fuska, In a very cool voice ta ce “Mun zo Yaya yad” Kalle-kallen motar ya yi sai kuma ya fara ƙoƙarin sauka daga motar, Ganin yana shirin tureta ya sanya ta ce “Bari na ce maka!” Yanda ta yi maganar in a serious tone ya sanya ya tsaya yana kallonta, Salma ta ce“Daman haka ake fita waje?” Shiru ya yi ta sauka daga motar ba tare da ta ce masa komai ba, Sauka shima ya yi yana kalle kalle. Gefe ta samu ta tsaya, Zayyad ya kalleta sai kuma ya ce“Mommah kawo na riƙe miki jakar” Kyakkyawan murmushi ta yi sai kuma ta ce“Ka bar shi na gode” Harararta ya yi ya ce“Dan ma zan riƙe miki, To sai ki yi ta yi” Girgiza kai kawai Salma ta yi dan ta gane abun nasa ne ya motsa. Ganin kowa na kama gabansa ya sanya ta yi shiru tana kallon mutane ɗaya bayan ɗaya, Wani benci ta hanga daga gefe, Ta kalli Zayyad sai kuma ta ce “Zo mu zauna” Wani banzan kallo ya yi mata kafin ya ce“Ba zan zauna ɗin ba, Ko an faɗa miki ni zama nake yi, Ni soja ne to” Ko saurarensa Salma bata yi ba, Ta ja hannunsa suka ƙarasa wajen, Zama ta yi ta zauna dashi kusa da ita, Ya dinga kallonta amma bai ce komai ba. Ta zuba uban tagumi tana jiran gari ya fara wayewa ta sanda inda suka yi. Suna nan zaune har gari ya fara wayewa, Haske ya game ko ina, Rana ta fito sosai dan da alama Kaduna na da zafi fiye da Abuja. Tashi ta yi tana kallon Zayyad wanda ya yi zaman dirshan a ƙasa yana haɗe haɗen shirgi. Wasu mutane ta hango zaune kusa da wani kanti da mai shayi a wajen ta ƙarasa tana tafe a hankali, Sai da tayi sallama suka amsa sannan ta ce “Dan Allah a ina zan samu dillalan gidaje, Ina son kama haya ne?” Mutanen suka kalli juna kafin na tsakiyarsu ya ce“Wallahi nan dai bamu sani ba yarinya sai dai ko ki yi gaba” Ta yi shiru sai kuma ta ce“Tom Nagode” Ta juya ta fara tafiya. “Baki ji ba” Salma ta juya ta kalli mutumin dake mata magana, Wani ɗan magidancin mutum ne, Fuskarsa sai sheƙi take yana murmushi ya ce“Naga kamar kina neman taimakone ko?” Kamar jira take ta ce“E, Baba wallahi daman ni baƙuwa ce a garin nan na zo da ɗan uwana to ina nema mana gidan da zamu zauna ne” Ya jinjina kai sannan ya ce “Allah sarki, Daman naji kin yi magana acan ne shi ne nace bari na taimakeki, Akwai wani ɗan uwana da yake harkar idan babu damuwa sai na haɗa ki dashi” Ajiyar zuciya Salma ta sauke cike da fara'a ta ce “Ai ko Nagode sosai Baba, Wallahi ka taimakeni dan daman tunanin yanda zan yi nake” Mutumin ya ce “Allah sarki, Babu komai ai yiwa kai ne, Ana son taimako ai. Mu je sai na kira miki shi” Toh Salma ta ce sannan ta koma inda Zayyad yake, Dakyar ya tashi suka dawo wajen mutumin tana murmushi ta ce“Yi haƙuri Baba na tsayar da kai” Girgiza kansa ya yi ya ce“Assha yarinya, Babu komai muje” Daga haka ya yi gaba suka dinga bin sa a baya. Suna fitowa daga cikin tashar Zayyad ya ja ya tsaya, Ta kalleshi sai kuma ta ce “Muje mana Yaya yad, Kana ganin za'a rakamu” Banza ya yi mata ya ɗauke kansa, Mutumin ya juyo ganin ya ɗan yi nesa dasu, Dawowa ya yi yana kallonta ya ce“Lafiya dai yarinya?” Jiki a sanyaye ta ce“Babu komai Baba daman ya ƙi tafiya ne” Kallon Zayyad ya yi sai kuma ya ce“Bawan Allah muje mana” Ko kallo bai ishi Zayyad ba dan bai juyo ba. Salma ta kalleshi murya can ƙasa ta ce “Mu tafi mana ko baka son ganin Mommah?” Juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce “To abinci zan ci fa” Salma ta ce“To ba sai ka faɗa min ba, Bari na samu kanti na siya maka” Da sauri mutumin ya ce“A'a yarinya ba sai kin kashe kuɗinki ba, Gidana nan kusa ne mu je sai mai ɗakina ta dafa muku” Girgiza kai Salma ta yi ta ce“Baba kar na saka ka wahala, Gara dai na siya masa” Ya ce“Babu wata wahala ai yiwa kai ne” Murmushi ta yi ta ce“Tom An gode Allah ya saka da Alkhairi” Daga haka ta kalli Zayyad wanda ke bin su da kallo ta ce“Muje gida sai a baka” Bai musu ba ya yi gaba abin sa, Salma ta sauke ajiyar zuciya sannan tabi bayansa. Ƙarfe 6:56am suka isa ƙofar gidan, Wani gida na ƙasa mai ɗan faɗi, Ya kalleta ya ce“To yarinya bismillah” Murmushi Salma ta yi sannan ta yi gaba ya bita a baya. Da sallama suka shiga gidan, Salma ta tsaya a tsakar gida tana riƙe da hannun Zayyad gudun kada ya yi wani abun, Mutumin ya shiga cikin ɗaki yana kiran sunan Abu. Bai daɗe ba ya fito tana biye dashi, Wata farar mata mai ɗan jiki, Da murmushi ta kalli Salma sai kuma ta ce “Sannu Yarinya shigo mana” Durƙusawa Salma ta yi ta gaisheta, Ta amsa da fara'arta sannan ta ce“Shigo ciki kin ji” Salma ta kalli Zayyad sai kuma ta ce“A'a Mama zamu zauna a nan bani kaɗai ba ce” Matar ta ce“A'a shi ya je ɗakin Malam ya zauna mana” Mugun kallo Zayyad ya mata kafin a tsawace ya ce “Ke ɗin banza! Baran je ba ɗin” Saurin rufe masa baki ta yi da hannunta tana girgiza kanta, Ya doke hannunta ya ci gaba da fad'in “Ke wace to, Ba zan je ba nace! Nonsense kawai, Haba” Kallon kallo aka dinga yi a wajen, Salma da kunya ta isheta ta sunkuyar da kanta. Matar ta kalli mijin nata ta ce a hankali “Malam lafiya kuwa?” Kafin ya yi magana Salma ta ce “Ku yi haƙuri dan Allah, Baya jin daɗi ne shiyasa yake haka” Numfasawa Mijin ya yi ya ce“Bakomai Allah ya bashi lafiya” Salma ta ce“Ameen” Ɗaki matar ta shiga ta ɗauko musu tabarma ta ce“Tun da ba zai yarda ba ga waje ku zauna” Murmushi Salma ta yi ta ce“Tom Mama mun gode” Daga haka ta kalli Zayyad ta ce“Muje to” Daga haka tayi gaba, Da harara ya bita sannan yabi bayanta. Can gefen tabarmar ya zauna ya dinga wasa da zaren tabarmar. **** Wajejen ƙarfe 10am ya shigo gidan, Zaune suke kan tabarmar bayan sun yi wanka, Zayyad yana sanye da wata t-shirt onion colour ya yi tsaf dashi, Ya ƙaraso gabanta yana murmushi ya ce“Yawwa nazo dashi taso muje ku yi magana” Tashi Salma ta yi tana gyara hijabinta ta ce“Tom muje” Daga haka ta kalli Zayyad wanda shima ya miƙe tsaye, A hankali ta ce “Ka zauna yanzu zan dawo” Ko saurarenta bai yi ba ya riga su nufar hanyar fita daga gidan, Mutumin mai suna malam Habu ya yi murmushi ya ce“Amma ya kamata a nema masa magani, Babban mutum kamar wannan” Jiki a saluɓe Salma ta ce“Eh In sha Allah Baba za'a yi” Toh ya ce sannan ya nufi wajen shima. Tsaye suka samu Zayyad ya riƙe ƙugu kamar mace sai zagaye mutumin yake, Salma ta yi shiru tana kallon ikon Allah da alama kwana biyun nan haukan nasa gaba yaƙe ƙarawa. Malam Habu ne yace“To gata nan ita take neman gidan” Mutumin mai suna Malam Sammani ya kalli Salma fuskarsa cike da fara'a ya ce“Allah sarki Barka da zuwa yarinya” Murmushi ta yi ta ce“Yawwa Baba fatan mun same ku lafiya” “Alhamdulilah, Ya yimin bayanin komai, kuma akwai gidaje a ƙasa yanzu. Idan ba zaki damu ba muna iya zuwa dake mu ga gidan dan tun da ya faɗa min irin wanda ki ke so na ce to tabbas zai miki” Cike da murna Salma ta ce“Ai ko naji daɗi sosai Baba, Mu je dan Allah” Tom ya ce sannan ya kalli Malam Habu ya ce“Ai tare zamu je ko?" Jinjina masa kai ya yi ya ce“Eh mana tare zamu je, Idan ta kama zasu dawo nan ai kaga basu san hanya ba” Murmushi kawai Salma ta yi tana jinjina halin kirki irin na Malam Habu. Napep suka tsayar ita da Zayyad suka shiga ciki, Malam Habu da Malam Sammani suka yi zaman gefe, Zayyad kallonsu kawai yake time to time yana zubar da yawu, Salma ta dinga kallonsa amma bata ce masa komai ba gudun abin da zai yi a haka har suka ƙarasa unguwar. Koda suka sauka daga Napep ɗin sai da suka ɗan yi tafiya kafin su ƙaraso ƙofar wani gida, Gida ne mai kyau na bolon siminti ya sha fenti ash colour, Ginin zamani wanda ya tsaru sosai. Salma ta dinga kallon gidan haka ma Zayyad, Malam Sammani ya kalleta yana murmushi ya ce “To ga gidan fa nan Hajiya, Wannan gidan yana da kyau sosai kuma na zamani ne ga kwari” Salma ta jinjina kanta still smiling ta ce“Eh kam gashi nan Baba, Kuma ɗakuna biyu ne?” “Eh mana ai buɗe miki za'a yi ki gani” Cewar Malam Habu, Salma ta ce“Tom Baba Kuma nawa?” Kallon kallo suka yi sai kuma ya ce“Ai tun da kece kuma kin ga ina ganin ƙimar wanda ya kawo ki to kawai ki bada Naira dubu ɗari uku, Sannan na shekara biyu ake biya saboda tsaro” Shiru Salma ta yi tana kallonsa, Sai kuma ta kalli Malam Habu ta ce a sanyaye “Baba wannan kuɗin yayi yawa ai, Ni wanda bai kai wannan kuɗi ba nake so” Girgiza kai Malam Habu yayi ya ce“Ai kin san yanzu yarinya gidajen ne suna wuta, Kuma kin ga nan babbar unguwa ce, Amma tun da an yi haka Malam Sammani ka bar mata a dubu ɗari biyu da hamsim kaga sai ta baka duba ɗari biyar na shekara biyun” Girgiza kai Malam Sammani ya yi ya ce“Ai fa sauƙi na muku saboda kai, Amma wallahi har naira dubu ɗari huɗu na bada hayar gidan nan, Saboda haka mai gidan ya bani” Malam Habu ya dafa shi cikin kwantar da murya ya ce“Duk da haka ka daure ka rage mata, Kaga baƙuwa ce” “Ai hakan ba zai yiwu bane, Saboda ka san gurin nan ajiya aka bani nake dillanci yanda aka masa kuɗi haka zan bayar nima ba kayana bane, Idan kawai kun ga bai yi to ku je ku sami wani” Shiru wajen ya ɗauka na wasu sakwanni kafin Malam Habu ya kalli Salma ya ce“Kawai haƙuri Salama mu koma gidana a samo wani” Girgiza kanta ta yi jiki a sanyaye ta ce “A'a Baba ba za'a yi haka ba kawai zan bashi kuɗin” Cike da damuwa Malam Habu ya ce“A'a kamar ya yi miki yawa” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Kar ka damu Baba, Tun da na samu ragowar kuɗin da zan siya abinci ai shikenan” Daga haka ta sauke jakar hannunta, wrapper shida na yan dubu-dubu ta ciro sannan ta miƙa masu, Malam Sammani ya amsa ya jujjuya ya ce“Ai ba ma sai na ƙirga ba tun da a manne suke” Malam Habu ya ce“Tom yanzu sai a buɗe mata gidan ai” Jinjina kai Malam Sammani ya yi ya ce“Ai tun da an biya kuɗi kuma to kamar ta shiga gida ta gama ne” Ya ƙare maganar yana lalube a aljihunsa, Above 2mins kafin ya ce“Subhanallahi ai ko na baro wallet ɗin mukullayen nawa a gida” Girgiza kai Malam Habu ya yi ya ce“Kash, Yanzu sai kaje ka ɗauko kenan?” Gyaɗa masa kai ya yi, Salma ta ce“To ai babu komai sai mu jiraka a nan” Sosai ya ji dadi ya ce“To to shikenan, Kaga Malam riƙe kuɗin nan idan na dawo da maƙulli sai a ƙarasa ciniki” Kafin Malam Habu ya yi magana Salma ta yi saurin cewa“Ai ba sai ka bada riƙon kuɗin ba kawai ka tafi dashi ka ga ma ai ka ajiye a gida” Girgiza kai ya yi ya ce“A''a yar nan kuɗi ba abun yarda bane, Ƙara naje na zo da makulli a buɗe miki gida ki shiga sannan na amsa” Salma ta yi murmushi ta ce“Ni ai na yarda daki Baba, Babu komai wallahi ka je dashi kawai” Malam Habu ya ce“Tun da ta yarda kawai kaje muna nan zamu jiraka” Tom kawai ya ce sannan ya mayar da kuɗin aljihu ya juya ya nufi titi. Malam Habu ya kalli Salma dake tsaye ya ce“To ki samu gefe ki ɗan zauna kafin ya dawo” Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Tom Baba” Daga haka ta koma kan dakali ta zauna tana kallon Zayyad wanda ke zaune can nesa da ita yana maganganu shi kaɗai. Malam Habu ya kalleta ya ce“Amma ya kamata ki nema masa magani, Ba'a barin mutum irin haka” Ya ƙare maganar idanunsa zube akan Zayyad cike da tausayawa. Numfasawa Salma ta yi sannan ta ce“Daman ina son mu nutsu ne sai na fara neman maganin, Ai zai dawo daidai ko Baba?” Malam Habu ya ce“Eh mana in sha Allah zai warke tas, Idan kun huta akwai wani malami dana sani yana bada maganin irin wannan lalurar sai na raka ku can” Salma ta ce“Ai ko da naji sosai Baba. An gode Allah ya saka maka da Alkhairi yanda ka mana” Girgiza kansa ya yi ya ce“Babu komai Salama ai yiwa kai ne”. Murmushi kawai ta yi sannan ta maida idanunta kan Zayyad tana kallon duk abin da yake. Sama da awa ɗaya suna jiran Malam Sammani amma shiru bai dawo ba, Gaba ɗaya sun gaji, Malam Habu ya miƙe daga zaunen da ya yi kan takalmansa ya ce“Ko wani abun ya tsare shi?” Salma dake zaune a gajiye ta ce“Ina ga amma ya daɗe sosai” Wayarsa ya zaro ya danna sai kuma ya sake kallonta ya ce“Kin ga har an fi awa ɗaya da tafiyarsa, Ko dai na bi shi ne?” Saurin gyaɗa masa kai ta yi dan bata da burin daya shige ta ji ta a zaune a gida. Ta ce“Eh Baba, Kawai sai ka amso mana muƙullin ma” Gyara zaman wular kansa ya yi ya ce“Gashi rana tafara yi sosai, Bari na yi sauri na dawo ku samu ki shiga gidan. Ki kula dashi sosai dan Allah” Ya ƙare maganar yana kallon Zayyad, Salma ta ce“In sha Allah Baba sai ka dawo” Tom ya ce sannan ya bar wajen. Salma ta kalli Zayyad wanda ke zaune ya takure waje ɗaya, Tashi ta yi ta koma inda yake ta zauna kan takalmanta tana kallonsa ta ce “Ka gaji ko?” Gyaɗa mata kai ya yi da sauri ta ce“Yi haƙuri yanzu zai dawo kaji” Zayyad bai ce mata komai ba ya kifa kansa bisa gwuiwoyinsa Ita kuma ta dinga kallonsa. Suna nan zaune har kusan azahar babu Malam Habu babu Malam Sammani, Ta gaji da zama ta tashi tsaye, Har sannan Zayyad na zaune ko ɗagowa bai yi ba. Zafin rana duk ya dameta dan lokacin rana ta gama buɗewa. “Mommah ruwa” Zayyad ya faɗa bayan ya ɗago fuskarsa, Tsugunawa ta yi gabansa ta ce a sanyaye “Yunwa ka ke ji?” Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Ni zan sha ruwa kuma zan ci abinci” Numfasawa Salma ta yi sai kuma ta tashi tsaye tana kalle-kallen unguwar, Wani provision ta hango yana opposite gidan, Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Zayyad ta ce“Bari naje can na siyo maka ko biscuit ne kaji...” Bai bari ta gama maganar ba ya miƙe tsaye, Ta girgiza kanta kawai dan ta gane nufinsa ta yi gaba yana biye da ita. Da sallama ta shiga kantin, Mutumin ciki wanda ya kasance matashi dan Zayyad zai girmeshi ya amsa, Naira dubu ɗaya ta miƙa masa ta ce ya bata biscuit da ruwa, Ya zuba mata a leda ya miƙo mata. Amsa ta yi tana shirin juyawa ya ce “Hajiya na ce idan jiran matar gidan nan ki ke ai ba yanzu zata dawo ba” Da mamaki Salma ke kallonsa kafin ta ce“Matar gida kuma? Ni ai babu wadda nake jira, Wane gidan?” Mai kantin ya ce “Wancen gidan mana da naga kuna zaune a ƙofarsa” Salma ta yi murmushi sai kuma ta ce“Au ho, Ai gidan da muka kama haya ne” Shiru ya yi yana kallonta, Ganin haka ya sanya ta ce“Ko baka gane ba? Wancan gidan fa, Jira ma nake a kawon maƙullin gidan na shiga” Mai kantin ya ce“Kuma shi wancan gidan ɗin?” Gyada masa kai Salma ta yi ya ce“Ikon Allah, Ɗazu fa matar gidan ta fita taje unguwa kin ga nan ta bada maƙullin gidan ta ce idan mijin ya dawo a bashi” Da wani irin mamaki Salma ke kallonsa kafin ta sake cewa“Amma ai bata nan, Ni wani mutum ne ya bani shi haya fa” Kafin mutumin ya yi magana wani ya shigo cikin shagon yana kallonsa ya ce “Yawwa Auwal bani maƙullin” Da sauri mai kantin ya ce“Yawwa to Kinga mai gidan nan” Ya faɗa yana nuna mata mutumin dake tsaye, Salma kallonsa ta dinga yi kamar idanunta zasu faɗo. Shi ko mutumin ya ce“Lafiya dai Auwal?” “Wai wasu ne suka bata hayar gidanka yanzu sun je kawo mata maƙulli tun wajejen 10:30am take zauna a ƙofar gidan” Auwal ya faɗa. Da mamaki mutumin ya ce“Haya? Kuma gidana?” Jinjina masa kai Auwal ya yi, Mutumin ya juyo ya kalli Salma wadda ta kasa gane inda suka dosa ya ce“Su wane ne? Sannan kuɗi ki ka basu?” gyaɗa masa kai ta yi a sanyaye ta ce “Eh, Mutumin ya ce Naira dubu ɗari uku ne kuɗin hayar shekara kuma sai dai na bada na shekara biyu, Kuma na bada” “Danƙari! Ke ya aka yi ki ka basu kuɗin ki kin san su ne?” Salma ta kwashe labarin duk abin da ya faru ta basu, Mai gidan ya Girgiza kansa cike da damuwa ya ce “Ai ko sun damfareki, Ƙarya suke miki, Sun ga ke yarinya ce shi ne suka cuceki. Wannan ba gidan haya bane, Gidana ne muke zaune da matata” Silalewa ƙasa ta yi ta faɗi kan tiles, Tuni hawaye suka wanke fuskarta, Ta dinga Girgiza kanta kamar zararriya, Magana take son ta yi amma sam ta ƙi zuwa bakinta. Kawai ta sanya hannayenta duk biyun ta toshe bakinta tana sakin wani raunataccen kuka. # HCD # Ya Yad # Salma # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 23-24: Fury's price Nanameera, YOTA/023. I would like to take this opportunity to thank my beloved ones💞, book lovers, and all my followers wherever they are. I am truly grateful and appreciative. May Allah keep us together always, Nanameera heart you 💕❤️. Mutumin ya kalleta ganin yanda take kuka yasa ya ce“Haƙuri zaki yi, Haka mutane suke, Kawai ya yi amfani da yardar ki ne ya cuceki” Cikin kuka ta ce“Wallahi koda wasa ban yi tunanin zai cuceni ba, Mutumin kirki ne sosai” Auwal ya ce“Ai fa haka suke, A fuska kamar na Allah amma idan kaga irin cutar da zasu yiwa mutum sai abun ya baka mamaki”. Mai gidan ya girgiza kai sannan ya maida idanunsa kan Salma ya ce“Yanzu ki tashi ki daina wannan kukan, Ni zan taimakeki” Ta ɗago kumburarrun Idanunta ta kalleshi sai kuma ta ce“A'a ni bana so, Banason kowa ya taimakeni wallahi” Sosai ta bashi dariya ya girgiza kansa ya ce“Kina tsoron kada nima na cuceki, Ba zan cutar dake ba, Sunana Hashim a nan nake aure ina da mata ɗaya da ɗa ɗaya, Bari na kirata a waya ta dawo sai ku shiga gidan” Ya faɗa yana zaro wayarsa daga aljihu, Salma kallonsa kawai take. Duk wannan abun da ake Zayyad na tsaye gefe yana zaro idanu, Ya kalli wannan sai ya mayar da kallonsa ga wani, After 5mins mutumin ya sauke wayar yana kallonta ya ce“Na kirata yanzu za ki ganta ta dawo” Salma na share hawayen fuskarta ta ce “An gode Allah ya saka da Alkhairi” Ameen kawai ya ce sannan ya nemi benci ya zauna. Suna nan zaune har bayan mintuna ashirin matar ta sauka daga Napep, Fara ce mai kyau babu laifi hannunta riƙe da wani ƙaramin yaro wanda ba zai shige 4yrs ba, Ta karaso kantin tana kallonsu, Hashim na ganinta ya miƙe yana murmushi ya ce “Har mun gaji da jira” Langwaɓar da kai ta yi ta ce“Afuwan dan Allah Abu, Wallahi ban samu mai Napep da wuri bane, Ina baƙin?” Ta ƙare maganar tana kallonsa, Da hannu ya nuna mata Salma dake zaune a ƙasa ta yi wujiga-wujiga da ita, Ta ƙura mata idanu tana kallonta har sai da Hashim ya ce “Maryam lafiya dai?” Girgiza kanta ta yi a hankali, Ta saki ɗan murmushi ta ce“Sannunki da zuwa” A sanyaye Salma ta gaisheta, Matar ta kalli Zayyad wanda ke tsaye kamar an dasa shi ta ce“Sannu Yallaɓai” Idan bango ya yi magana to tabbas Zayyad ma ya amsawa Maryam, Ta kalli mijinta wanda tun ɗazu ya lura Zayyad ɗin nada matsala, A sanyaye ta ce “Muje to” Okay kawai Hashim ya ce sannan ya kalli Salma ya ce“Taso Ummusalma” Miƙewa ta yi suka yi gaba ta kalli Zayyad wanda bai motsa ba ta ce“Muje mana” Ko inda take bai kalla ba, Ta girgiza kai kamar zata yi kuka ta ce“Kaga dai na gaji, Ka zo mu tafi nace” Nan ma shiru ya sake mata, Ta yi tsaki ta fice daga kantin ba tare da ta sake bi ta kansa ba. Auwal ne ya kalle shi ya ce“Ka bisu mana” “Kai dallah rufe mana baki ko mun kula ka?” Kamar daga sama Zayyad ɗin ya yi maganar, Da mamaki Auwal ke kalonsa dan bai yi tunanin mahaukaci bane, Ya ce“Allah ya baka haƙuri” Wata uwar harara Zayyad ya zabga masa, ya taɓe baki wanda yake ɗabi'arsa sannan ya fice daga kantin. Babban compound ne mai ɗauke da yan shuke-shuke na zamani, Ko ina a tsaftace ko ba'a faɗa maka ba kasan matar gidan tana da tsaf sosai, Hashim ne ya kalli Salma ganin ita kaɗai ya ce “A'a ina dan uwan naki?” Salma ta ce“Yana waje ya ƙi shigowa ni kuma nagaji ba sai ya yi ta yi ba” Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Hashim bai ce komai ba ya buɗe gate ɗin ya fita, Ita kuma Salman tabi bayan Maryam dake kiran sunanta. Zaune ya sameshi kan wani dakali ya tara duwatsu a gabansa yana jifa dasu ɗaya bayan ɗaya yana dariya, Hashim ya ƙarasa gabansa ya ce “Baka gaji ba duk da haka? Ka tashi kaje kayi wanka ka ci abinci mana” Zayyad ya ɗago dara-daran idanunsa ya yi wa Hashim wani kallon sheƙeke sai kuma ya ci gaba da jefa dutsen da yake, Da mamaki Hashim ke kallonsa yana tunanin ko dai baya jin magana ne, dan haka da ƙarfi ya ce “Bawan Allah ka tashi muje” Wata irin tsawa Zayyad ya daka masa yana cewa “Kai wane irin mahaukaci ne, Baka ga muna aiki bane zaka shigo mana kai tsaye, Ya'yan talakawa kawai!” Hashim kasa rufe bakinsa ya yi, Ya dinga kallon Zayyad kamar ya samu tv, Kodai yana da matsala? Amma how? Wannan babban mutumin a ce yana da matsala, Ganin abun na son fin ƙarfinsa ya sanya ya koma cikin gidan domin ya tambayi Salma. Babu kowa a Parlon sai tashin ƙamshi da yake, Ɗan ƙaramin yaron na zaune kan kujera one seater idanunsa zube kan tv yana kallon wani cartoon da ake haskawa a MBC 3, A nutse ya ce “Khalil” Juyowa yaron ya yi ya kalleshi sai kuma ya ce“Na'am Abu” “Ina Amminka?” Cikin siririyar murya irin ta yara ya ce“She's inside the kitchen Abu” Jinjina kai kawai Hashim y yi sannan ya nufi kitchen ɗin, Tsaye ya sameta gaban cooker tana juya stew, Ya girgiza kansa sannan ya ce “Maryama sarkin ƙoƙari har yaushe ki ka fara haɗa abincin?” Juyowa ta yi ta kalleshi kafin ta yi ɗan murmushi ta ce“And who told you yanzu nafara haɗa abincin? Already fa ina da stew na, Kawai ina warming ne” Jinjina kansa ya yi ya ce“I see” ta kalleshi kawai ta yi murmushi, Shiru ya ɗan yi can kuma ya ce“Ina Salma take? Ɗan uwan nan nata yaƙi shigowa fa, Yana zatunka wanda ban gane kansu ba” Maryam da ke ɗauko food flask daga kwali ta ce“Tana ɗaki maybe ma wanka take, Meya hana shi shigowa? Naga babba ne sosai” Hashim ya ƙaraso ya janyo mata flask ɗin ganin tsayinta ba zai kai ba sannan ya ce“Eh babba ne, Daga gani ma zai girmeni, But yanda yake magana abun ya bani mamaki” Sai da ta amshi flask ɗin sannan ta ce“Okay bari na kirata, Ko baya son shigowa gidan mutane ne, Sai ya zauna a daƙinka na balcony ai” Hashim ya ce“Okay je ki kirata please, Eh idan baya son mutane ba” To kawai ta ce sannan ta rage gas ɗin ta juya ta fice daga kitchen ɗin. A Parlon ta samu Khalil har sannan yana kallo, Ta girgiza kanta kawai ta shige ɗaki. Tsaye ta samu Salma tana ƙoƙarin mai da hijabinta bayan ta fito daga wankan, Maryam ta yi murmushi ta ce“Haba dai ba sai ki kirani na baki kaya ba Salma?” Salma sunkuyar da kanta kawai ta yi, Maryam ta juya ta fita daga ɗakin ita kuma ta bita da kallo. Bata jima ba ta dawo hannunta riƙe da wata Abaya black colour, Ta miƙawa Salma tana cewa “Ki saka wannan sai ki fito, Kin ga ɗan uwanki ya ƙi shigowa Abu ya ce yaji yana wasu zantuka” Amsa ta yi sannan ta ce“Tom Aunty, Bari na zo na tawo dashi” Okay Maryam ta ce sannan ta sake fita daga dakin, Salma ta ware Abayar mai stones a jiki ta sanya. Mayafin Abayar wanda yake babba ta yafa, Nan da nan ta dawo hayayyacinta duk da ta rame sosai amma har yanzu kyawunta bai gushe ba. Ta fito parlon tana tafiya a sanyaye, Zaune ta sami Maryam da Khalil yana ta mata surutu. Tana ganin Salma ta sauke shi daga jikinta tana cewa “Yawwa Salma, Je ki ki tawo dashi” Toh kawai ta ce sannan ta nufi hanyar fita daga parlon. Dube-dube ta shiga yi tana neman in da yake, Can ta hangeshi zaune a ƙasa yana ɗiban ƙasar yana zubawa cikin rigarsa, Da sauri ta ƙarasa tana kallonsa ta ce “Mene haka ka ke yi?” Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce“Nurse tayani kwashe maganin nan, Na tawo a hanya ya zube” Takaici ne ya isheta, Ta tsuguna ta tankaɗe hannunsa ƙasar ta zube, Ta zazzage ta cikin rigarsa tana masa wani mugun kallo ta ce “Wai kai ba zaka yi hankali ba? Kana ganin kowa yana kallonka, Ka daina wannan shirman, Da an yi magana ka ce daga asibiti ka ke, Asibiti zaka je, Magani zaka bawa mutum, Wane zai amsa, Ka tashi mu tafi ni” Tun da ta fara maganar yake kallonta kamar idanunsa zasu faɗo, Sai da ta yi shiru sannan ya sauke nunfashi kawai taga ya fashe da kuka. Rikicewa ta yi ta riƙe hannunsa ta ce “Mene ne? Ka yi shiru ni ce ba zan sake maka faɗa ba” Ci gaba ya yi da kukansa kamar ƙaramin yaro, Salma gaba ɗaya ta ruɗe, Ta sanya hannayenta duk biyun tana share masa hawayen ta ce “Ba na ce ka yi shiru ba, Kayi haƙuri ba zan sake ba” Babu yanda ba tayi da Zayyad ba amma ya ƙi yin shiru, Ta nemi waje ta zauna a ƙasan ta zuba masa idanu tana kallonsa, Tuni hawaye suka wanke mata fuska itama. Suna nan zaune har bayan mintuna goma, Hashim ya ƙaraso wajen yana kallonsu da mamaki “Salma lafiya? Meya faru ku ke kuka?” Hashim ya yi tambayar yana kallonsu. Cikin shassheƙar kuka ta ce “Yaƙi yin shiru Yaya, Ka ce masa ya daina kuka ba zan sake masa faɗa ba wallahi” Hashim da bai gane kan zancen ba ya ce“wane? Shi mene ne ya sanya shi yake kuka?” “Saboda nayi masa faɗa shi ne yake kuka, Kuma na bashi haƙuri ya ƙi yin shiru, Ka ce ya tashi mu tafi” Hashim ya kalli Zayyad a sanyaye ya ce“Taso mu tafi gida” Zayyad ya miƙe tsaye jikinsa duk ƙasa ya ƙarasa gaban Hashim yana ci gaba da kukansa, Shi dai Hashim kallonsu yake kamar soko ya riƙe hannun Zayyad suka fara tafiya. Ganin haka ya sanya ita ma ta taso ta biyo bayansu. A compound ɗin gidan suka tsaya ya kalleshi ya ce“Mene ne yasa ka ke kuka? Ai ƙaddara ta riga fata, Ka yi haƙuri dan Allah” Shi dai Zayyad kukansa kawai yake bai ma san me Hashim ɗin ke cewa ba. Maryam ta fito tana kallonsu ta ce“Lafiya dai? Salma meya faru?” Tana goge hawayen fuskarta ta ce“Babu komai Auntie, Dan Allah a ina zan kai shi ya yi wanka ya shirya?” Hashim ya ce“Kawai je ki ciki zan kai shi da kaina” Salma ta ce“To Yaya, Amma ko ka yi masa magana ba lallai ya amsa ba, Bashi da lafiya ne” Sai a sannan Hashim ya ɗan fahimta ya jinjina kansa kana ya ce“Tom shikenan shiga ciki, Kema ki daina kukan” Ta ce to sannan ta shiga ciki Maryam na biye da ita.. **** Zaune take kan carpet ta zuba tagumi tana kallon abincin gabanta, Maryam ce ta fito daga ɗaki ta dinga kallonta da mamaki ta ce “Salma meya hanaki cin abincin?” Shiru taji ko amsawa bata yi ba, Babu ma alamun tana jin abin da take cewa. Ta tsuguna a gabanta ta dafata ta ce “Salma!” A ɗan firgice ta kalleta sai kuma ta ce“Na'am Auntie” “Lafiya tunanin me ki ke yi?” Maryam ta tambayeta, Girgiza kanta ta yi ta ce“Babu komai Auntie” Maryam ta kafeta da idanu, Ganin haka ya sanya Salma sunkuyar da kanta, Ta ce“Tell me what's going on dear? Ke dawa? Me ki ke tunani?” Fashewa ta yi da kuka, Ta sanya gefen mayafinta tana rufe fuskarta, Maryam ta dinga kallonta sai kuma ta ce“Ba zaki sanar mini ba ya sanya ki ke kuka? I'm i not ur sister?” Salma ta girgiza mata kai tana shassheƙar kuka ta ce“Aunty Yaya Zayyad bai ci abinci ba, Kuma kuka yake har yanzu, Naje wajensa ya ƙi kulani” Maryam ta yi shiru can kuma ta ce“Shi ne yasa ki ke kuka? To ai Abu zai bashi abinci, Baki ga yana wajensa ba tun ɗazu na kai masa abinci nasan yanzu ma ya ci, Don haka kema ki cinye naki” Gyaɗa mata kai kawai Salma ta yi amma bata daina kukan ba, Maryam ta tashi tsaye ta fice daga Parlon. Tsaye ta samu Hashim ya yi shiru kamar mai tunani, Ta ƙarasa kusa da shi, Ta ce “Abu lafiya? Me ka ke tunani?” Kallonta ya yi sai kuma ya numfasa ya ce “You know what Maryam, Wannan mutumin bashi da hankali fa, Jikina duk ya yi sanyi Maryam, Look at him babba mutum matashi mai shekaru kamar nasa, Ke daga ganinsa kin san ba'a wahala yake ba. Da akwai hutu sosai a tare dashi, Duk inda yake ɗan manya ne” Maryam ta girgiza kanta cike da damuwa ta ce“Tun sanda ku ka shigo nayi noticing haka, Allah ne kaɗai yasan abin da ya sameshi, But I think zan tambayi Salma zuwa dare ta faɗa min abin da ya same shi, Bai yi kama da dan uwanta ba” “To ko mijinta ne?” Hashim ya faɗa, Maryam ta girgiza kanta ta ce“Bana tunanin haka gaskiya, saboda kai da ka ganta kasan yarince ƙarama, Bana jin ta yi shekaru ashirin wannan. Dole akwai abin da ya fito dasu daga gida” Hashim ya jinjina kansa kafin ya ce“Haka ne, But a ganina bai dace ki tambayeta ba, If she wish zata faɗa miki da kanta” Maryam ta yi shiru na wasu sakwanni kafin ta ce“Shikenan duk yanda ka ce sai a yi hakan, Yanzu zaka fita ne?” Girgiza kansa ya yi ya ce“A'a gaskiya, Kawai zan haƙura sai gobe, Kin san ma next week zan shige Abuja” Maryam ta haɗe rai kamar ba ita ba ta ce“Yanzu dan Allah har yaushe ka dawo daga Abujan da ka ke shirin komawa? Baka son zama a gida koda yaushe sai ka dinga tafiya kana barina” Dariya ya yi ya ce“Rigima dai irin taki Maryam, Ke zama ki ke a gidan? I thought kina zuwa school kullum, Beside ma kin san Abujan nan aiki nake zuwa da nima ba zan je ba, Amma kullum ki dinga korafi” Turo baki ta yi ta ce“Ni dai wallahi ka bari ba yanzu ba” “Wai cewa nayi gobe zan tafi ko jibi?” Ya faɗa yana kallonta, Ɗauke kanta ta yi ta ce“Koma yaushe ne bana so ka dinga nesa dani, Gaba ɗaya sai na dinga ji na a cikin duhu wallahi” Ya jinjina kansa kafin ya ce “Uhm, Sai ki nemo Haske ai” Hannunsa ta kama cike da so da ƙauna ta ce“And then u're my light, Kai ne HASKEN CIKIN DUHUN nawa ai” Hashim ya lumshe idanunsa yana jin so da ƙaunar matar tasa na ƙaruwa cikin ransa, Ya ja kumatunta ya ce“Me too Maryama, Kece Haske a cikin duhuna, Tun ranar da Malam ya aura min ke abubuwa dayawa suka sauya a rayuwata, Inason ki, Ina sonki sosai” Maryam ta rasa abin cewa kawai ta rungumeshi tana dariya. **** Asokoro, Abuja. Da sallama ta shigo ɗakin hannunta riƙe da tray na abinci, Zaune yake kan gadon ya jingina da jikin bango idanunsa a lumshe. Mommy ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a kan table sannan ta zauna gefen gadon tana kallonsa a sanyaye ta ce “Yallabai” General ya buɗe idanunsa wanda suka yi jajur dasu, Mommy ta dinga kallonsa cike da tausayawa kafin ta ce “Ya kamata ka rage damun kan ka, Kana ganin yanda bp ɗinka yake ta hawa, Kada ka jawo mana wata masifar bayan wadda muke ciki dan Allah” General ya yi mata wani kallo, Ya gyara zamansa sosai kafin ya ce “Hajara ki ka ce na bar tada hankalina? Na kwantar da hankalina? Zayyad baya gida over a week shi ne hankalina zai kwanta. Yaron nan Amana ne a wajena ke kin sani shi ne baya nan Ban san halin da yake ba ki ke cewa na daina damuwa. To Hajara ta ina zan daina damuwa? Ta ina hankalina zai kwanta? How?” Mommy ta girgiza kanta ta ce “Ba fa nace kar ka nuna damuwarka bane, But you have to calm down, At least ka daina wannan zaman kana tunani, Kasan yanayin lafiyarka fa Yallaɓai, Duk abin da ake saboda kai ne, Yanzu idan wani abun ya sameka ai mune a cikin tashin hankali, Kaga saboda haka ya kamata ka sassautawa kanka, In sha Allah Zayyad yana hannu nagari” Numfasawa General ya yi ya ce“Hajarah dan Allah tashi ki fita” Mommy ta kalleshi sai kuma ta ce“Yanzu saboda nayi maganar...” ”I said get out!” Ya faɗa a ɗan tsawace, Tashi tayi jiki a sanyaye ta fice daga dakin. Parlon Mommah ta shiga dan yanzu ba zaman main parlon take ba, Zaune ta sameta kan sofa ta yi shiru da alama tunani take dan tun bayan ɓatan Zayyad bata da abin yi sai shi. Mommy ta karasa ta zauna kujerar dake kusa da ita ta ce “Khadijah” Mommah ta kalleta dan bata san sanda ta shigo ba ta ce“Na'am, Ashe kece” Mommy ta ce“Kema kina nan kina tunanin kenan” Numfasawa kawai Mommah ta yi cike da damuwa ta ce“Wallahi bana iya bacci Mommy, Damuwa tayi min yawa, Kullum da Zayyad nake kwana dashi nake tashi, Idan wani abun ya samu rayuwarsa ba zan yafewa kaina ba, Jidda ba zata taɓa jin daɗi ba” Hawaye Mommy ta fara yi tana kuka ta ce“Kowa ya damu sosai, Allah sarki Jiddah, Mace mai halin kirki, Wallahi hankalina a tashe yake, Allah ya dawo da ɗan nan gida Lafiya, Allah ya sanya yana hannu nagari, Duk wanda ya yi masa wannan mugun abun Allah ga ganshi kuma ka san shi ka hukuntashi, Allah ka nuna mana shi mu ganshi” Mommah ta girgiza kanta itama tana hawayen ta ce “Ai shi Allah ba azzalumin bawansa bane, Duk wanda ya aikata wannan abun ya san kansa, Kuma Allah ba zai bar shi ba, Ko nan kusa ko nesa sai Allah ya yi hukunci domin baya barin zalunci” Mommy ta ce“Wannan haka yake, Wannan yarinyar ita da Allah, Ko su wane suka sakata aikin Allah masani” Mommah ta ce“Akwai Allah ai”. **** Tun da tafara magana Jiddah ke kallonta taba taɓe baki, Tana yin shiru ta gyara zamanta daga kwancen da take ta ce“Kin gama?” Amrah ta kalleta ta ce“What do you mean by nagama?” A hasale Jidda ta ce“Duk abin da ki ka ɗauka haka nake nufi Amrah, zantukanki basu da wani amfani a gareni” Amrah ta girgiza kanta ta ce“Jiddah ki ji tsoron Allah, Ki sani duk wanda ki ka cutar Allah ba zai bar ki ba, Koda ace babu wnada ya gani ai kin san Allah baya bacci, Kuma yana sane dake!” “And who told you bansan me nake ba? Ko kin fini sanin Allah ne Amrah? Ko kin san abin da nasani ne, Ina ruwanki dani ma” Amrah ta ce“Ki yi duk abin da ki ke ganin zaki yi Jiddah, But you have to know akwai ranar danasani, Mene ribarki idan kin cutar da ɗan Adam, Cutarwa mafi muni, Kin san girman abin da ki ka aikata kuwa?” Sauka daga gadon ta yi ta riƙe ƙugunta tana yi mata wani banzan kallo ta ce “Let me tell you something Amrah, Idan kin ga dama ki fita daga nan ki je ki sanarwa da kowa, Ni na haukata Zayyad! Ni Jiddah ni ce na haukatashi kuma wallahi ko yanzu ya dawo daidai sai na sake haukatashi! Zayyad ba, Ba zai taɓa samun jin daɗin rayuwa ba sai dai idan bana numfashi wallahi!” # HCD # Zayyad # Salma # Jiddah # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 25-26: Shadows of the past Nanameera, YOTA/23. Amrah ta dinga kallon Jiddah da mamaki, Ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Ba zan taɓa tona miki asiri ba Jiddah, Amma ki sani akwai ranar dana sani, Duk abin da ki ke ɓoyewa akwai ranar da zai fito kowa ya gani, Akwai ranar da zaki yi nadamar abubuwan da ki ka aikata.” Daga haka ta fice daga ɗakin tana buga ƙofar da ƙarfi, Da idanu Jiddah ta bita har ta ɓacewa ganinta, Ta sulale ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka. Koda Amrah ta fita parlon Mummy ta samu zaune kan sofa tana danna wayarta, Tana ganinta ta ce “Ba dai har zaki tafi ba Amrah?” Dan murmushi ta yi ta ce“Eh Mummy magrib ya kusa tafiya zan yi, Kar Daddy ya nemeni” Mummy ta jinjina kai sai kuma ta kalli bayanta ta ce“A'a ina Jiddahn? Ko har yanzu kukan take?” Amrah ta girgiza kai ta ce“Ai tana sama Mummy, Mun yi sallama naga har yanzu bata saki jikinta bane” “Allah sarki, Na rasa yanda zan yi da Jiddah da wannan damuwar, General ya ce min ana ta binciken yanda za'a samo shi, Amma ta ƙi kwantar da hankalinta” Mummy ta ƙare maganar fuskarta cike da ɗumbin damuwa. Amrah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce“Nima ina ta faman rarrashinta Mummy, Kuma naga kamar ta fara haƙura. In sha Allah za'a gan shi” Mummy ta ce“Allah yasa Amrah, Dan ina tsoron kar ciwonta ya sake tashi” Amrah ta ɗan yi murmushi sannan ta ce“In sha Allah Mummy, Sai anjima” “Okay, Ki gaisar da Mamanki kin ji” “Zata ji in sha Allah” Amrah ta yi maganar tana nufar hanyar fita daga parlon. Tana ƙoƙarin buɗe motar ta Suhaila ta ƙaraso wajen, Ta kalleta tana murmushi ta ce “Aunty Amrah har za ki tafi?” Jinjina kai Amrah ta yi ta ce“Eh Suhaila, Dare zai yi” Suhaila ta jinjina kai ta ce“Haka ne kuma, To ki gaida Yaya Tee” Murmushi Amrah ta yi ta ce“ Iyye! Wato ko kunyata baki ji ba?” Suhaila ta rufe fuskarta da fararen hannayenta tana murmushi ta ce“Kai Aunty Amrah, I'm just kidding fa” Amrah ta gyaɗa kai tana mata wani kallo ta ce“Sannu to, Oyaa shiga gida ni my friend” Suhaila ta tuntsire da dariya wanda ya ƙara fito da kyanta tana matuƙar kama da Jiddah amma ita fara ce saɓanin Jiddah data kasance baƙa, Amrah ta shige motarta tana cewa “See you next time” Bye bye Suhaila ta yi mata sannan ta nufi hanyar shiga gida tana tafe kamar zata faɗi saboda siranta. **** Kaduna, 5 days later. Maryam ta fito daga parlon tana kallon Salma dake zaune gefen wata bishiya tana wankin kaya, Ta ƙaraso wajen tana cewa “Yanzu sai da ki ka yi wankin nan? Ba sai ki bari idan Abu ya dawo a haɗa a kai wanki ba?” Salma dake matse wata rigar Zayyad ta ɗan yi murmushi ta ce“A'a Aunty ai gara na wanke kin ga babu abin da nake” Maryam ta girgiza kai ta ce“Da dai kin haƙura, Wai ina Zayyad ne naga ban ganshi ba?” Salma ta ce“Aunty ya fita waje fa, Kin ga har yau ya ƙi kulani ko ɗazu da nayi masa magana banza ya yimin” Maryam ta yi murmushi ta ce“To ke ki rabu dashi mana, Maybe baya son kula kin ne” Haɗe fuska Salma ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Amma Aunty baya kulani fa, Kuma babu abin da nayi masa ai” “To gaya min meyasa ki ke jin ba daɗi? Kina son yayanki har haka Salma?” Salma ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“Ni fa kawai na damu ne tun da ban yi masa komai ba ai, Kawai ya daina kulani” Maryam ta ɗan yi murmushi ta ce“Anyway ki bari ya shigo sai nayi masa magana” Sosai Salma taji daɗi ta ce“Yawwa Aunty. Ina zaki je ne?” “Khalil zan ɗauko a school naga biyar ya shige, Kin san halinsa yanzu sai ya fara min kuka” Murmushi Salma ta yi ta ce“Ai ko dai, Dana gama ai da sai na raka ki, Amma ki dawo lafiya” “Allah yasa Salma” Daga haka ta nufi hanyar gate. Salma ta ci gaba da wankinta tana ɗan tunane-tunane, Duk da yanda take jin daɗin zamansu gidan Hashim. . Tana shanya kaya ya buɗe gate ɗin ya shigo, Sanye yake da wasu English wears riga t-shirt sai wando na jeans kansa a gyara ba zaka taɓa cewa mahaukaci bane, Salma ta dinga kallonsa ganin ko inda take bai kalla ba ya buɗe ɗakinsa ya shige. Ji ta yi jikinta ya yi wani irin sanyi, Ta ƙarasa shanyar sannan ta ɗauke bokitan. Wanke hannunta ta yi a tap sannan ta nufi ɗakin daya shiga, Tura kofar ta yi ta hangeshi zaune gefen ƙaramin gadon ɗakin, Hannunsa rike da wani zare yana ta wasa dashi, A hankali ta ƙarasa gabanshi ta zauna gefen gadon tana kallonsa ta ce “Yaya Yad” Banza ya yi mata kamar ba dashi take ba, Ta sake kiran sunansa nan ma ya yi mata shiru, Ta sauko daga kan gadon ta tsuguna gabansa tana leƙan fuskarta ta ce“Yaya Zayyad ka yi hakuri kaji” Ko motsi Zayyad bai yi ba ballantana ta saka rai da yaji abin da ta ce, Hawaye ya fara kawowa Idanunta muryarta na rawa ta sake cewa “To ka faɗa min me nayi maka? Ka yi haƙuri kaji ba zan sake ba ai nace, Ka yi haƙuri dan Allah” Ci gaba ya yi da wasa da zarensa babu alamar zai kulata, Sai kawai ta fashe da kuka ta yi zaman dirshan a ƙasa, Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake ɗauke kansa. Ta dinga kuka kamar ranta zai fita, Lokaci zuwa lokaci yake ɗago kansa ya kalleta sai kuma ya sake mayarwa kan zarensa, Tafi minti goma tana kukan amma bai yi magana ba. Salma ta tashi ta nufi hanyar waje sai dai kafin taje bakin ƙofar ta yanke jiki ta fadi tana sakin wata razananniyar ƙara. Da sauri ya kalli inda take ya hangeta zube kan tiles bata numfashi, Tashi ya yi ya ƙarasa wajen ya tsuguna yana kallonta. “Keeee Mommah! Ke ki tashi mana, Ki tashi na ce miki” Zayyad ya fadi maganar yana jijjigata, Shiru babu alamar Salma na jin abin da yake cewa dan ko motsi bata yi ba, Ya ɗagota gaba ɗaya yana kallonta ya ce “Ki tashi mana, Ba kin ce zaki kai ni wajen Mommah ba, Ki tashi mu tafi nace” Ya dinga faɗar maganar a mugun tsorace, Ganin da gaske Salma ba tashi zata yi ba kawai sai ya fashe da kuka, Ya zauna akan ƙafafunsa tana riƙe cikin hannayensa har sannan ya shiga kuka kamar ƙaramin yaro, Yafi 5mins yana kukan kafin ya ƙara ɗagowa ya dinga dukan fuskarta yana cewa “Ba nace ki tashi ba, Ki tashi ke, Ki tashi mu tafi” Tuntsirewa da dariya ya ji an yi, Salma ta buɗe idanunta tana kallonsa, Saurin sakinta ya yi ta tashi zaune tana sheƙa dariya kamar zararriya, Zayyad ya dinga kallonta da mamaki, Can kuma ya ce “Ke Mahaukaciya ce ne?” Yanda ya yi maganar ya sanyata sake fashewa da wata dariyar, Ta riƙe cikinta tana nuna shi da yatsa ta ce “Hooooo nayi masa wayo, Gashi nan ka yi kuka kai ma” Shi dai bin ta kawai yake da kallo dan har sannan bai gane in da zancen nata ya dosa ba. Ta ɗora hannayenta duk biyun bisa fuskarta tana kallonsa sosai ta ce “Meyasa ka yi kuka? Ko kana tsoron Mommah ta mutu ta bar ka?” Zayyad ya kalleta sai kuma ya ɗauke kansa, Hannunsa ta janyo tana murmushi ta ce “Ai yanzu ka haƙura ko Yaya yad ɗina?” Ya ƙura mata idanunsa masu kaifi, Sake waro nata manyan idanun ta yi ta kalleshi sai kuma ta ƙifta masa idanun ta ce“Mene ne? Me ka ke tunani, Ka faɗa min baka so na mutu?” Tashi ya yi tsam daga zaunen da yake ya nufi hanyar waje, Cikin hanzari ita ma ta miƙe ta biyo bayansa tana cewa “Yaya yad! Yaya Yad! Ka tsayani mana” Turus ta yi ganinsa tsaye jikin shanyar da tayi yana faman kwashewa, Duk wadda ya ciro sai ya yi wurgi da ita a ƙasa, Da sauri ta ƙarasa yana ƙoƙarin yar da wata riga ta rike tana kallonsa ta ce“Mene ne haka? Ka bari” Banza ya yi mata ya fizge rigar ya yi jifa da ita, Tafiya ta yi tana kwasar kayan da yake zubarwa tana kwashe wasu yana zubar da wasu, Gajiya ta yi ta zuba a bokiti ta ƙaraso inda yake a fusace ta ce “Wannan wane irin abu ne wai? Kasan wahalar dana sha na wanke kayan ka ke zubar min, Ina ruwanka da kayana?” Bai ko kalleta ba sai da ya watsar da duk kayan a ƙasa, Ta kalli kayan sai kuma ta sake kallonsa, A zafafe ta cafki kwalar rigarsa tana mitsi-mitsi da idanu na masifa ta ce “Wallahi sai ka kwashe min kayana ai ni ba baiwarka ba ce, Tun da kai duk abin da aka yi maka ba zaka gani ba. Wallahi sai ka kwashe min kayana” Kallona hannunta dake riƙe da rigarsa ya yi sai kuma ya kalleta, A fusace ya fizge hannun ya shaƙi wuyanta idanunsa suka sauya kala a take, Ya riƙe maƙoshinta kamar zai rabata da ranta. Kasa numfashi Salma ta yi, Idanunta suka firfito waje, Hawaye ya dinga zubowa kan fuskarta, Sai da ta fara kasa motsi jikinta ya fara saki sannan ya yi jifa da ita tamkar kayan wanki, kanta ya daki karfen jikin balcony ta faɗi ƙasa Sumammiya. Juyawa ya yi ya fice daga gidan kamar zai tashi sama. Bayan mintuna goma sha biyu Khalil ya buɗe ƙofar gate ɗin, Sanye yake da uniform ɗinsa na islamiyya da jakarsa goye a bayansa, Maryam ce ta shigo tana cewa “Da ka ke saurin sai ka zo gida ba gashi...” Maganar ta tsaya a maƙoshinta sakamakon Salma data hanga kwance a ƙasa, Khalil ya dinga kallonta da idanunsa, Da sauri ta ƙarasa gabanta tana cewa “Salma lafiya? Me ki ke a nan?” Jinin data gani kwance a ƙasa ya sanya taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa, Ta tsuguna tana kallonta hankali a tashe ta ce “Salma! Salma! Salma!” Maryam ta shiga kiran sunanta da ƙarfi, Ganin bata motsi ya sanya hankalinta ya ƙara tashi, Ta ɗago kanta tana cewa “Salma tashi mana, Meya faru, Ke Salma!” Tashi ta yi ta buɗe jakarta ta shiga kiran lambar Hashim, sai dai lambar gaba ɗaya bata shiga, Sau uku tana kira amma duk babu wanda ya shiga. Ta ajiye wayar ta fita da sauri, Mai Napep ta samu yana shirin barin layin,Ta ce ya zo ya taimaka mata zata kai wata asibiti. Da sauri ya kashe napep ɗin ya fito suka shigo gidan, Shi ya taimaka mata suka ɗauki Salma aka sakata cikin Napep ɗin suka nufi asibiti. Wani private asibiti suka je, dan a nan insurance ɗinsu yake, Da farko ƙin karɓarta suka yi sai da ɗan sanda, Dakyar Maryam ta roƙesu sannan suka amsheta, Bayan sun yi mata dressing aka kai ta ɗaki suka saka mata ruwa. Maryam zata yi gefenta tana kallonta, Khalil ma na zaune gefenta sai kallon Salma yake yana matsar kwalla, Maryam ta kalleshi ta ce “Ka daina kuka ka ji, Zata samu sauƙi” Cikin kuka ya ce “Ammi Auntie Salma ta tashi, Tsolo ina ji ni” Ya yi maganar cike da yarinta, Da hannu Maryam ta yi masa alama da ya zo, Ya taso ya dawo jikinta. Zaunar tayi kan cinyarta ta rungumeshi tana cewa “Ai zata tashi, Baka ga doctor ya dubata ba kayi shiru kaji yaron kirki” Gyaɗa mata kai kawai ya yi yana sauke numfashi ya yi lamo a jikinta. Ana kiran sallar magriba kiran wayar Hashim ya shigo wayarta, Lokacin tana zaune gefen Salma wadda har sannan take bacci, Ɗaukan wayar ta yi daga ɗaya ɓangaren Hashim ya ce “Na dawo gida ban ganku ba lafiya dai?” Maryam ta sauke nunfashi sannan ta ce “Abu Salma ce bata da lafiya muna asibiti” “Subhanallahi, Wane asibiti?” Maryam ta ce “Muna Emar clinic” Okay ya ce sannan ya kashe wayar, Maryam ta sauke wayar tana kallon Salma wadda take sauke numfashi dakyar, Tunanin abin da ya sameta take yi, Ko garin yaya ta fadi haka Allah masani. Mai da Idanunta kan Khalil ta yi wanda ya yi bacci a wajen har sannan uniform ne a jikinsa, Tashi ta yi ta shige toilet ɗin dakin ta ɗauro alwala, Ɗankwalinta ta shimfiɗa dan daman hijabi ne a jikinta ta gabatar da sallar, Tana idarwa wayarta ta fara ƙara, Ɗauka ta yi ganin Hashim ne, Bayan ta ɗaga ya tambayeta inda suke ta faɗa masa, Ba'a fi mintuna biyu ba ya shigo ɗakin. Gaban gadon ya ƙarasa yana cewa “Garin Ya ya haka ta faru?” Maryam dake ɗaura ɗankwalinta ta ce“Wallahi nima ban sani ba, lafiya na fita na bar ta a gidan naje ɗauko Khalil a school kawai muna dawowa sai na ganta kwance a ƙasa kanta a fashe kuma babu kowa a gidan nayi ƙoƙarin kiranka wayarka kuma not reachable shi ne na fita na samu mai Napep na kawota asibiti, But I don't know what happened” Hashim ya sauke nunfashi sai kuma ya ce “Ina Zayyad?” Maryam ta ce“Ban gashi ba, Bama ya gidan fa sanda muka fito, ko yanzu ka ganshi?” Girgiza kai Hashim ya yi ya ce“Babu kowa a gidan ko yanzu, kuma ban ma gan shi a Kofar gida ba” Maryam ta yi shiru tana tunani can kuma ta ce“Allah yasa dai ba wani gurin ya yi ba to” “Ameen” Hashim ya faɗa, Doctor ne ya shigo ya kallesu ya ce“Ya mai jikin?” “Da sauki Alhamdulillah” Hashim ya bashi amsa, Sake dubata ya yi sannan ya kalli Hashim ya ce“Yawwa oga ka sameni a office” Okay Hashim ya ce sannan ya fita shi kuma ya bi bayansa. Doctor ya kalli Hashim bayan ya zare glasses ɗin idanunsa ya ce “Garin ya ya aka yi mata haka? An shaƙe wuyanta ya yi yawa wanda har ya kusa sanadiyar rasa ranta” Da mamaki Hashim ya ce “Shaƙe wuya kuma doctor? Ita Salman?” Jinjina kai likitan ya yi ya ce“Eh, Sannan bayan haka ta fadi da kanta sosai, Saboda haka a dinga kula gaskiya. Ga wasu magunguna a siya mata su, Idan ta farka kuna iya tafiya gida” Okay Hashim ya ce sannan ya amshi takardar, Ya ɗan duba sai kuma ya miƙawa likitin hannu suka gaisa sannan ya tashi ya fita. Ɗakin ya koma ya samu Maryam zaune tana danna wayarta, Tana ganinsa ta ajiye wayar tana cewa “Ya ake ciki?” “Wai shaƙeta aka yi, Amma wane zai shaƙeta?” “Shaƙewa kuma? Salma ɗin?” Hashim ya gyaɗa mata kai, Shiru Maryam ta yi can kuma ta ce”To ko dai faɗa suka yi da Zayyad? Amma ai naga kamar baya kulata” Kafin Hashim ya yi magana Salma ta buɗe idanunta tana sauke numfashi a hankali, Khalil ya yi saurin cewa“Ammi kin ga ta tashi” Daga Hashim har Maryam kallonta suka yi a tare kuma suka ce “Kin farka?” Salma ta gyaɗa musu kai tana sauke numfashi, Ƙarasawa Maryam ta yi ta zauna gefenta ta kama hannunta tana cewa “Sannu Salma, Sannu” Salma kasa cewa komai ta yi ta lumshe idanunta wasu hawaye suka shiga zubowa gefen fuskarta, Hashim ne ya ƙaraso wajen yana kallonta ya ce“Sannu Salma” Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta gyaɗa masa kai. **** Around 9pm suka shigo gidan, Kasancewar lokacin ana sanyi ya sanya unguwar shiru babu kowa. Babu kowa a compound ɗin amma an mayar da shanyar kayan, Hashim ya tsaya yana kallonsu ya ce”Ku shiga ciki bari na nemo Zayyad” Okay kawai Maryam ta ce sannan ta kama hannun Salma da Khalil suka shiga ciki, A parlon suka zauna Maryam ta kalli Salma ta ce”Tashi muje ki yi wanka sai ki ci abinci ki sha magani” Toh kawai Salma ta ce sannan ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin da take kwana. Sai da tayi wanka sannan ta fito tana sanya da wata doguwar riga da Maryam ta bata, Zaune ta samesu suna cin abinci. Ta ƙarasa tana tafiya a hankali, Hashim ne ya kalleta ya ce “Salma sannu” Ɗan murmushi ta yi duk yanda bata jin daɗin jikinta ta ce“Yawwa Yaya” “Zo ki ci abinci” Maryam ta faɗa tana jawo plate, Jollof rice ce wadda taji kayan haɗi sai kamshi take ta zuba mata, A gefe ɗaya Salma ta zauna ta dinga cin abincin a hankali, Ko rabi bata ci ba ta ajiye, Maryam ta kalleta ta ce “A'a lafiya dai naga kin ajiye?” Kamar zata yi kuka ta ce“Na ƙoshi Auntie” Girgiza kai ta yi ta ce“A'a dai Salma, Da kin cinye” “Wallahi Aunty na ƙoshi sosai” Magungunan ta miƙo mata ta ce“Ohya sha maganin sai ki je ki kwanta” To kawai ta ce sannan ta amsa ta buɗe, Ruwa ta miƙo mata ta ɓalli maganin ta sha ta kora da ruwa. Ganin ta ajiye ledar ya sanya Maryam ta ce”To ki je ki kwanta ki huta” Tom kawai Salma ta ce duk da yanda take son ta ga Zayyad amma ta miƙe “Salma” Taji muryar Hashim ya kirata, Juyowa ta yi tana kallonsa ta ce“Na'am Yaya” “Ina son magana da ke” Tom ta ce sannan ta dawo ta zauna, Maryam ta kalleshi ta ce “Amma ai da ka bari sai da safe ko Abu” Girgiza kansa ya yi ya ce“Yanzu nakeson maganar ai” Shiru Maryam ta yi dan bata saba jayayya dashi ba, Salma ta koma ta zauna ta yi shiru, Hashim ya dinga kallonta kafin ya gyara zamansa ya maida hankalinsa sosai ya ce “Salma zan tambaye ki abu ina son ki faɗa min gaskiya” Toh ta ce kanta a ƙasa, Ya numfasa sannan ya ce “Su waye ku Salma? Wane Zayyad a wajenki? Me yasa ake nemanku a Abuja?” # HCD # Yaya Yad # Salma # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 27-28: “I will never forgive him” Nanameera, YOTA/023. Kallonsa Salma ta dinga yi ba tare da ta ce komai ba, Maryam ta kalleta sai kuma ta kalleshi a sanyaye ta ce“Abu ka kyaleta mana, Tun da kamar bata san ta faɗa” Girgiza kai Hashim ya yi yana mai da idanunsa kanta ya ce“But she have to, Ina son sanin gaskiya” Numfasawa Maryam ta yi sannan ta ce“Duk da haka kar a takura mata kaga...” “Mu ba laifi muka yi ba, Kawai mun bar garin ne, Da gaske ne daga Abuja muke amma babu wanda muka yiwa laifi” Salma ta faɗi maganar kanta a ƙasa. Hashim ne ya gyara zamansa ya ce“Idan haka ne meyasa ake nemanku a Abuja Salma? Har pictures ɗin ku suke yawo, Mene ne alaƙar da ke tsakaninki da Zayyad?” Shiru ta yi na wasu mintuna sannan ta sauke ajiyar zuciya, Ta fara basu labarin abin da ya faru. Babu abin da ta ɓoye musu tun daga farko har ƙarshe. Ba Maryam kaɗai ba har Hashim sai da ya yi hawaye, Salma ta sunkuyar da kanta tana shessheƙar kuka ta ce“Wallahi ban haukata shi ba, Ban san yanda ake haukata mutum ba, Kuma ko zan haukata kowa ba zan taɓa haukata wanda ya taimakeni ba. Amma sun kasa yarda dani, Sun ɗora min abin da ba zan iya ba, Rayuwa kawai nake amma ji nake daman na mutu na huta. Ta yaya zan iya ci gaba da rayuwa da Yaya Zayyad a irin wannan yanayin? Ya zan yi dashi? Sai abun nasa ya yi sauki sai ya dawo sabo, Wallahi na rasa yanda zan yi!” Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka, Tashi Maryam ta yi ta dawo kusa da ita ta kama hannunta tana hawaye ta ce “Ki yi haƙuri Salma, Komai zai shige in sha Allah, Babu yanda za'a yi ku dawwama a haka, Tabbas an cutar da ke, Sun cutar da rayuwarki. Kin yi ƙarama da ɗaukan wannan nauyin, Ki yi haƙuri kin ji” Rungume Maryam ta yi tana sakin wani kuka mai tsuma zuciya, Hashim ya girgiza kansa yana goge hawayen daya zubo masa. Shiru parlon ya yi kowa da abin da yake tunani cikin ransa. Hashim ne ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin “Ki yi haƙuri ki bar kukan nan haka, Duk da ban san Zayyad ba amma naji ya bani tausayi, Mutum kamar sa mai hankali wannan ba ƙaramin jarabawa bane, Amma akwai abin da ba daidai ba, Duk wanda ya yi masa haka ba ƙaramin maƙiyinsa bane, Kuma dole akwai shirin daya sanya aka yi haka. Amma in sha Allah komai zai zo da sauki” Tana jikin Maryam ta ce“Na sani Yaya, Duk da ban san wanda ya aikata masa haka ba amma akwai abin da ya sanya aka yi hakan, So nake nafara nema masa magani ya samu ya dawo daidai, Wallahi tausayi Yaya Zayyad yake bani” Hashim ya ce“Kar ki damu in sha Allah za'a fara nema masa magani, Abin da ban gane ba shi ne haukan nasa na asibiti ne ko kuma na gida ne” “Ni a ganina tun da asiri ne mu je dashi gida wajen Malam mana, Sai ya duba shi ya dinga masa addu'a da taimako mu ga abin da hali zai yi” Maryam ta yi maganar jiki a sanyaye, Jinjina kai Hashim yayi ya ce“Haka ne, Gobe idan Allah ya kai mu sai muje duka gidan” “Allah ya kaimu lafiya” Hashim ya kalli Salma ya ce“Sannan mene ne ya sameki ɗazu?” Salma ta goge hawayen dake kwance kan fuskarta sannan ta ce “Yaya Zayyad ne ya shaƙemin wuya, Saboda nayi masa magana” Da mamaki Maryam ta ce“Shaƙe wuya kuma? Daman haka yake?” Gyaɗa mata kai Salma ta yi kana ta ce“Eh, Idan nayi masa abu yana shaƙe min wuya kamar na mutu da kyar yake sakina. Kuma shi ne na bugu da jikin ƙarfe” Hashim ya girgiza kansa ya ce“Ayyah ki yi haƙuri kin ji, In sha Allah zai samu lafiya” Ɗan murmushi ta yi ta ce“Ameen Yaya, Nagode muku sosai Allah ya saka muku da Alkhairi, Yanda ku ka kula damu Allah ya bamu ikon biyan ku” Hashim ya ce“Ameen Salma, Tashi ki je ki kwanta” Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta bar parlon, Sai da ta tafi sannan Hashim ya mai da hankalinsa kan Maryam ya ce“Allah sarki, wace irin rayuwa muke ciki ne yanzun?” Maryam ta ce“Abu na tsorata sosai, Wallahi mutane basu tsoron Allah, Har a haukata mutum ba komai ba ne” Hashim ya ce“Haka ake yi, Akan abin duniya sai a raba mutum da ransa ma gaba ɗaya, Sai dai kawai Allah ya shirya mu” “Amma Abu baka ganin akwai saka hannu cikin mutanen gidan nasu? Ni ban yarda dasu ba wallahi” Maryam ta yi maganar a dame, Ɗan murmushi Hashim ya yi sannan ya ce“Ya za'a yi yan uwansa su masa asiri? Ai ba zai yiwu ba” “Ba yan uwansa ba, Baka ganin wannan Mommy ɗin da ta ce matar ubansa, Wadda ta sanya aka koresu, Akwai alamun rashin gaskiya a tare da ita” Hashim ya yi shiru yana tunani, Maryam ta sake cewa “Saboda babu yanda za'a yi ta ce a koreshi idan har bata da mugun nufi akan sa, Kasan fa matan uban nan, Kwata kwata ba imani gare su ba, Wallahi ni ita nake tunanin ta yi wannan abun” Girgiza kai Hashim ya yi ya ce“Kin ga wannan duk bashi da amfani a garemu, Koma wane ya yi masa haka ai zai je ya tarar da ubangijinsa koda a ce ba'a gane shi anan duniya ba, Abin da ya dame mu yanzu shi ne a sama masa lafiya ya dawo hayyacinsa” Maryam ta kwaɓe fuska ta ce“Duk da haka, Idan ya dawo daidai Wallahi sai na saka shi ya nemo wadda ta masa asiri an ɗaureta dan wannan rashin imani ne” ta ƙare maganar kamar zata yi kuka. Murmushi Hashim ya yi sanin halinta ya ce“Daɗina da ke naci, Ki yi haƙuri dan Allah” Tashi ta yi tana ƙoƙarin kwashe kayan abincin ta ce“To ba zan yi naci ba, Ka kai Khalil ɗaki dan Allah ka ga ya yi bacci” Okay Hashim ya ce sannan ya tashi ya ɗauki Khalil wanda yake kwance kan 3 seater ya nufi hanyar ɗakinsa dashi. Koda ya fito bai samu komai a parlon ba, Kawai ya nufi waje. Ɗakin Zayyad ya shiga, Ya hangeshi can ƙarshen gado ya cure jikinsa waje ɗaya sai faman rawar sanyi yake, Da sauri Hashim ya ƙarasa kan gadon yana kallonsa ya ce “Zayyad lafiya? Zayyad!” Ganin bai bashi amsa amsa ya sanya ya hau kan gadon ya riƙe shi, Wani irin zafi mai tsoratawa yaji a jikinsa hatta numfashinsa hucin zafi yake, Hankali tashe Hashim ya ce “Baka da lafiya ne Zayyad? Meya sameka?” Babu abin da Zayyad ya ce masa, Daga karshe ma janye jikinsa ya yi daga nasa ya tashi ya fice daga ɗakin yana tafiya kamar zai fadi, Cikin gidan ya nufa Hashim ya bi bayansa yana kiran sunansa, Tsaye ya samu Maryam bayan ta fito daga kitchen ta kalleshi ganin yanda jikinsa ke rawa ta ce “Zayyad lafiya?” Kafin ya yi magana Hashim ya shigo parlon yana kiran sunansa, Turus ya yi ganin Zayyad tsaye tsakiyar parlon yana kalle-kalle, Hashim ya ƙaraso gabansa ya riƙe shi yana cewa “Meya sameka Zayyad? Mene ne?” Ture shi ya yi ya zube ƙasa yana sakin wata ƙara, Salma na tsaye jikin press tana linke hijabi taji ƙara, Fitowa ta yi da sauri dan taji muryar Zayyad. Tsaye ta same su sunyi cirko-cirko suna kallonsa, Salma ta ƙaraso da sauri ganin yanda yake kuka kamar ƙaramin yaro, Bata san sanda ta tsuguna gabansa ba ta dafashi tana cewa “Yaya mene ne? Me aka maka?” Ɗago kansa ya yi da sauri ya kalleta sai kawai taga ya rungumeta yana kuka yana cewa “Mommah! Mommah! Ba zan bi ki ba, Ba zan tafi ba, Ki bar ni anan ni, Tsoro nake ji” Ya dinga maimaita maganar yana Girgiza kansa, Kallonsa suka dinga yi, Salma ta gyara zamansa ta rikeshi sosai duk da yanda ya yi mata nauyi, Ta dinga karanta masa duk addu'ar da ta zo bakinta tana tofa masa, Hashim ma ya durƙusa ya dafashi yana yi masa addu'a, Sun ɗauki mintuna sama da goma kafin ya fara daina maganar amma har sannan jikinsa bai bar ɓari ba, Salma ta dinga hawaye tana girgiza kanta. Maryam kuwa tsayawa ta yi jikin bango sai kuka take. Sai da ya fara sauke numfashi Hashim ya kalleta a nutse ya ce“Bari na maida shi ɗaki” Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin janyeshi daga jikinta, Zabura Zayyad ya yi ya sake ƙanƙameta yana magana ƙasa-ƙasa, Salma ta kalli Hashim cikin shessheƙar kuka ta ce “Yaya ka bar min shi” Hashim ya ce“Salma ya yi miki nauyi, Kuma na ai ba muharraminki bane” Girgiza kanta ta yi tana sake rikeshi ita ma ta ce“Dan Allah ka bar shi, Ai Allah ya ga zuciyata, Bashi da lafiya ne” Shiru Hashim ya yi yana kallonsu ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, Neman kujera ya yi ya zauna yana kallon Maryam ya ce“Zauna mana” Fashewa ta yi da kuka shige ɗakinta da sauri, Hashim ya bita da idanu sai kuma ya sauke numfashi. Bayan awa ɗaya Hashim ya kalleta ganin kamar bacci yake yasa ya ce“Ya yi bacci ne?” Leƙa fuskarsa ta yi sai kuma ta gyaɗa masa kai, Hashim ya taso ya ce“To bari na mai da shi ɗakinsa” Hashim ya dafa shi jin jikinsa ya yi sanyi kalau ya ce a hankali “Zayyad” Shiru yaji alamun bacci yake sosai, Ya ɗago shi sai dai nauyin Zayyad ba ƙarami ba ne, Dole ya sake shi yana haki ya ce “Tabarakallah, Salma na kasa ɗaukansa” Salma ta ce“To yaya kawai ka bar shi a nan idan ya tashi sai ya tafi da kansa” Hashim ya ce“To shikenan, Ke tashi ki je ki kwanta” Langwaɓar da kai ta yi ta ce“A'a ka bar shi a nan” Girgiza kai Hashim ya yi ya ce“Salma dare ya yi, Kuma kema baki jin daɗi ki je ki kwanta ni sai na zauna dashi anan ɗin” “Dan Allah Yaya ka bar ni nima, Wallahi ba zan iya tafiya na bar shi ba, Ka bar ni anan” Ta ƙare maganar hawaye na sauka kan fuskarta, Ganin ta dage ya sanya Hashim ya rabu da ita, Ya nemi kujera 3 seater ya kwanta ita kuma ta jingina da center table tana kallon Zayyad dake bacci a hankali, Sai kusan ƙarfe 2:00 na dare sannan bacci ya ɗauketa ita ma. **** Abuja. Cikin sanɗa ta tashi daga kan gadon tana kallonta. Bacci take hankali kwance, Ta ɗauki wayarta kan drawer sannan ta fice daga dakin tana tura ƙofar a hankali. Corridor ta fito tana ɗan kalle-kalle, Sai da ta tabbatar babu kowa sannan ta tsaya ta shiga danna wayarta, Number ta yi dialing ta fara ringing sai dai har ta katse ba'a ɗauka ba, Ta sake danna kiran ta mayar kunne, Sai da ta kusa tsinkewa sannan aka ɗaga ta yi ƙasa da murya ta ce “Ina ki ka shiga ina kiranki?” Daga ɗaya ɓangaren aka ce“Ke bacci nake yi, mene ne?” Sai da ta ɗan kalli corridor ɗin gaba ɗaya sannan ta ce “Ko za ki fito mu je yanzu?” Daga ɗaya ɓangaren ta kalli screen ɗin wayarta sai kuma ta ce “Kina ganin za ki iya fitowa yanzun?” Jinjina kai ta yi ta ce“Daddy baya nan, Mummy Kuma bacci take, zan iya fitowa” “What about Suhaila?” “She already sleep fa, Babu wanda yake ido biyu, Ki zo muje yanzun” Ta gyaɗa kai bayan ta tashi daga kan royal bed ɗin ta ce“Shikenan ki fito gani nan” Okay ta ce tana ƙoƙarin katse kiran ta ce “Oh wait, Ki zo ki ɗaukeni ba zan iya fitowa da mota ba” Okay ta ce mata sannan ta yi cutting kiran ta ajiye wayar, Jidda ta sauke wayar tana kallon screen ɗin. Dare ya yi sosai amma hakan ba zai hana ta aiwatar da abin da take so ba, Ta juya ta koma ɗakinta da sauri domin shiryawa. Ko da ta fito cire takalmanta ta yi gudun kada su yi ƙara ta sauka daga benan tana tafiya cikin sanɗa, Koda tazo main parlon na gidan duhu ta gani domin duk an kashe light ɗin wajen, Ta samu ta buɗe ƙofa ta fice da sauri, Ta ƙofar baya inda babu securities da yawa ta bi, A bakin gate ɗin ta samu sojoji guda biyu suna tsaye riƙe da bindigu, Suna ganinta suka washe baki suna faɗin “Madam kin fito?” Gyaɗa musu kai ta yi ta ce“Zan je na dawo ba zan daɗe ba bana son magana” Sara mata suka yi a tare suka ce “Yes Mah!” Jidda ta yi murmushi sannan suka buɗe mata gate ɗin ta fice da sauri. Bata fi 2mins a tsaye ba wata Accord black colour ta yi parking a gabanta, Ta sauke glasses ɗin motar tana kallonta. Sai da ta kalli both right and left side nata sannan ta nufi motar ta buɗe ta shiga, Sauke ajiyar zuciya ta yi ta kalleta ta ce “You Are not serious Bibi, mene ne abin fargabar?” Tsaki Jidda ta yi ta ce“You won't understand Meema, Idan Mummy ta ganni ban san me zance ba, I can't explain anything to her” Taɓe baki Meema ta yi ta ce“Ashe baki shirya ba” Daga haka ta yi reverse suka bar titin. **** Around 4:45 na asuba ta yi parking motar, Ta kalli Jidda dake gefe ɗaya ta yi shiru ta ce “Kin dai ji abin da aka ce ba? You have to calm down, Komai na tafiya yanda aka tsara” A matukar dame Jiddah ta ce“But how? Ba zan iya ba Meema, Wallahi hankalina bai taɓa tashi irin na yau ba, Ni ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba idan har ban aiwatar da abin da nakeso ba, i can't get peace Meema” Meema ta girgiza kai ta ce“To shikenan za ki ci gaba da cutar da kan ki kenan? Jiddah idan ciwonki ya tashi kin san ba daɗi za ki ji ba ko? Kuma zaki ɗaga hankalin duk wani mai son ki, Ki bi komai a sannu, Za ki yi nasara in sha Allah” “Zuciyata ba zata taɓa daina min ciwo ba har sai sanda naga bayan Zayyad wallahi, Ba zan taɓa kwantar da hankalina ba har sai na ganshi a tagayyare a rayuwa, Ba zan samu sukuni ba sai har na wulaƙanta rayuwarsa ta inda duk wanda ya san shi zai daina mu'amala dashi, Duk wanda yake son sa zai tsaneshi, So nake ya rasa zaman lafiya, So nake ya zama tamkar kare Meema! So nake rayuwarsa ta zama abun kyama, Ya rasa jin daɗin rayuwa ya gwammace mutuwa akan rayuwa!” Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Dafata Meema ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce“Ki daina irin wannan tsanar Jiddah, Ki yi haƙuri dan Allah, Duk abin da ya shige ki bar shi kawai. Na sani kina da buƙatar ki ɗauki fansa amma duk da haka ki daina irin waɗannan kalaman, Ki yi hakuri” “Na yi haƙuri fa ki ka ce Meema! Na yi haƙuri? Wallahi ba zan iya ba, Sai na ɗauki fansar abin da ya yimin,Yanda ya tozarta rayuwarta sai na tozarta tasa. Yanda ya mayar dani abar tausayi sai na mayar dashi abin tsana, Wallahi ba zan taɓa yafe masa ba Meema, Ba zan iya ba” Rungumeta Meema ta yi itama tana kukan ta ce“Duk da haka ba zan bar baki haƙuri ba, Na sani akwai buƙatar ki ɗau fansa kuma nima ina bayanki amma ki cire damuwa daga cikin ranki, Tun da duk abin da ki ka shirya yana kasancewa” Dakyar ta samu Jiddah ta daina kukan, Ta ce“Ki je kada Mummy ta tashi” Toh kawai ta ce sannan ta sauka daga motar ta nufi gidansu. Koda ta shigo parlon bata samu kowa ba ta haye sama tana tafiya a hankali, Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakinta taji saukar Muryar Mummy “Jiddah!” Sai da gabanta ya faɗi amma ta dake ba tare da ta juyo ba ta ce“Na'am Mummy” “Ina ki ka je? Ya jikin naki?” “Na ɗan sauka ne, Na je kitchen” Mummy ta yi shiru tana kallonta can kuma ta ce“Naji muryarki a haka ko dai jikin ne?” Girgiza mata kai Jiddah ta yi ta ce“A'a Mummy na ji sauki, I just need to rest” Numfasawa Mummy ta yi ta ce“Okay ki je ki kwanta but make sure you perform ur salat” Gyada mata kai kawai ta yi sannan ta buɗe ɗakin ta shige, Mummy ta tsaya tana kallon wajen can kuma ta girgiza kai ta nufi hanyar downstairs. Jiddah na shiga ɗakin ta mayar da ƙofar ta rufe ta jingina da jikin kofar tana sauke wani irin wahalallen numfashi, ta fi 2mins a wajen kafin ta ƙarasa cikin bedroom ɗin, kwance ta sami Suhaila har sannan baccinta take, Ta zame mayafin abayar da ke jikinta ta nufi hanyar toilet, Alwala ta yi sannan ta fito ta sanya ladduma ta gabatar da sallar asuba sannan ta zauna ta yi addu'o'in data saba ta yi azkar sannan ta koma ta kwanta. **** Washegari da sassafe Mummy ta shigo ɗakin, kwance ta samesu har sannan, Ta girgiza kanta sannan ta tashe su. Mummy ta kallesu ta ce “Daddynku ya dawo kuma fita zai sake yi ya ce a kira ku” Suhaila ce ta fara tashi tana mitsitsika idanunta ta ce“Daman ina son magana dashi” Daga haka ta tashi ta shige toilet dan ko sallar asuba bata yi ba, Mummy ta ƙurawa Jiddah idanu ganin yanda take numfashi da kyar ta ce “Jiddah jikin ne?” Girgiza kanta ta yi ta ce“Babu komai fa Mummy, Kawai ban samu bacci bane sosai” Mummy ta dinga kallonta wanda ya sanya ta sunkuyar da kanta, Mummy ta ce“Tashi ki je wajen Daddynki” Gyaɗa kanta ta yi sannan ta sauko ƙafafunta daga kan gadon tana cewa“Mummy ina zai je ne?” Ta yi maganar kamar zata yi kuka, Mummy ta harareta ta ce“Ba kina da baki ba? Je ki tambayeshi” tura baki Jiddah ta yi sannan ta ƙarasa sauka daga gadon ta zura slippers ɗinta ta nufi hanyar waje tana tafiya kamar iska zata hureta. A hankali ta tura kofar parlon bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta hangeshi kan sofa ya naɗe ƙafafunsa idanunsa maƙale da glasses, Yana ganinta ya saki murmushi ya wara mata hannayensa. Da gudu ta tafi ta rungumeshi tana dariya ta ce “Daddy!” Ta yi maganar ya shagwaɓe, Shafa kanta ya yi ya ce“Hauwa'u, Ya jikin naki?” Ɗora kanta ta yi a ƙirjinsa tana cewa“Babu sauki Daddy, Duk nagaji” Ɗago kanta ya yi ya ce“Mene ne yake miki ciwo yanzu? Ina ne?” Ganin yanda ya ruɗe ya sanya ta yi murmushi har sai da beauty point ɗinta suka loma ta ce“Daddy baka san wasa ba, I'm just kidding fa, Naji sauki sosai” Jan kumatunta ya yi ya ce“But you scared me Jiddah, Kar ki sake haka kin ji” Ta gyaɗa masa kai ta ce“I'll not Daddy, Ina zaka je?” Murmushi ya yi ya ce“Yawwa Baby, Fita zamu yi da General” Shiru ta yi tana kallonsa da idanunta masu girma, Ya kalleta ya ce“Ki daina damun kan ki in sha Allah za'a gan shi nan kusa, muna ta ƙoƙari a kai” Cikin shessheƙar kuka ta ce“Daddy bana iya bacci, Hankalina ya kasa kwanciya, Dan Allah a nemo shi Daddy, Wallahi zan aure shi ko a haukan” Shafa kanta ya yi ya ce“Ki daina kukan nan, Daman za ki aure shi in sha Allah, Amma ki bar damun kan ki kar wani abun na daban ya sameki” Gyaɗa masa kai ta yi still crying ta ce“But Daddy...” Hannunsa ya ɗauka kan bakinsa ya ce“Shiiii...” Shiru ta yi tana goge hawayen fuskarta, Suhaila ta buɗe ɗakin ta shigo da gudu ta ƙaraso ta ce“Daddy welcome back” Zama ta yi gefensa ta riƙe hannunsa tana murmushi, Juyo da fuskarsa ya yi ya shafa kanta ya ce“Auta” “Daddyna, I dey missed you alot” Murmushi ya yi ya ce“Same dear, Ya school ɗin” “Not too bad, Amma nagaji” Girgiza kai General ya yi sannan ya ci gaba da musu hira.. **** 6 days later, Kaduna.. 5:00pm Fitowa Salma ta yi daga kitchen tana kallon Maryam ta ce“Auntie nagama fa” Maryam da ke Ƙoƙarin cirewa Khalil uniform ta ce“Tom Salma je ki duba Zayyad ko ya sha rubutun” Salma ta nufi ƙofa tana cewa“Ni na san bai ma sha ba wallahi” Maryam ta yi murmushi tana cewa“Duk da haka duba dai” Tura ƙofar dakin ta yi ta same shi zaune kan tile ya yi tsit yana tunani, Ƙarasawa ta yi ta zauna kusa da shi tana cewa “Yaya Yad ɗina” Ɗago kansa ya yi ya kalleta, Ta janyo ledar rubutun nasa ta buɗe, waro idonta ta yi tana kallonsa ta ce“Yanzu shi ne baka sha ba?” Ɗago kansa ya yi ya harareta sai kuma ya ɗauke kansa, Dauko ledar rubutun ta yi ta fasa bata ce masa komai ba riƙe fuskarsa ta buɗe bakinsa ta fara bashi, Sai da ya shanye tas sannan ya juyo ya kalleta, Murmushi ya ga ta yi masa ya ɗauke kansa yana kallon gefe. Tashi Salma ta yi ta fice daga ɗakin dan daman kwana biyun nan ba magana yake ba. **** Girgiza kai mutumin ya yi ya ce“Yanzu me ki ke so a yi?” Matar da ke zaune gabansa ta ce“Kawai A yi abin da ya dace boka, Ni bana son ya samu salama, Bana son ya dawo da hankalinsa, So nake ya yi haukan da za'a dinga kama shi ana ɗaurewa, So nake ya yi haukan da zai kai shi ga halaka, Bana son ko da wasa ya dawo hayyacinsa, Wanda yake tare dashi ma bana son ya samu nutsuwa a rayuwarsa. So nake a ɗaiɗaita rayuwarsa, A kwance masa ragowar tunaninsa, Ya manta da rayuwarsa ta da, Ya ƙare rayuwarsa akan bola, Ko kuma ya yi hatsari mota ta markaɗeshi akan titi, Bana son ko labarinsa na sake ji, Kawai a kashe shi ta kowace hanya, Ita kan ta yarinyar da ke tare dashi ina son a ɗaiɗaita rayuwarta a sanya mata tsanarsa cikin ransa, Idan kuma baka ba zai yiwu ba to kawai a kasheta ita ma!” _An kusa gama book 1 and book 2 isn't free it's ₦700 via 7041901078 Hauwa Adamu lawan opay evidence via 08106608363, Ki biya domin ki karanta cikin kwanciyar hankali_ # HCD # Yaya Yad # Salma # Nanameera 08106608363.. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 29-30: In his absence Nanameera, YOTA/23. Mutumin da take iƙirari da boka ya bushe da wata dariyar mugunta, Ya kalli gefensa na hagu ya yi shiru can kuma ya yi gyaran murya yana kallonta ya ce“Ki ɗauka duk abin da ki ka nema an yi miki, Zaki sha mamakin abin da zai faru, Zaki yi dariya, Zaki ji daɗi...” Jinjina kanta ta yi cike da jin daɗi ta ce“Nagode boka, Allah ya ƙara maka tsawon rai ya baka abin da ka ke buƙata, Allah ya...” Wata razananniyar tsawa ya daka mata wadda ta sanya ta firgita, Ya haɗe mummunar fuskarsa mai ban tsoro kamar bai taɓa dariya ba ya ce“Kar ki sake kira mana Allah a nan, Muke yi ba Allah ba!” Cike da gamsuwa ta gyaɗa kanta ta ce“Wannan haka yake, Ku ne masu taimakonmu” Bokan ya sheƙe da wata dariya yana busa ƙahon hannunsa. **** Washegari da safe Mommah ta shigo parlon, Zaune ta sami general kan sofa yana danna system ɗin gabansa, Sauke numfashi ta yi sannan ta ƙarasa ta zauna gefensa, Ɗago idanunsa wanda suka nuna zallar gajiya ya yi ya zuba mata yana kallonta, Mommah ta kalleshi sosai sai kuma ta ce “Yallabai baka samun bacci ji idanunka, Kar fa wani ciwon ya sameka” Lumshe idanu General ya yi ya buɗe sannan ya ce“Ya zan yi Khadijah? Bana iya baccin ne, Gaba ɗaya bana jin daɗi, Idan na rufe idanuna Zayyad nake gani, Tunaninsa ya hana ƙwaƙwalwata samun nutsuwa, Ba zan taɓa daina damuwa ba sai ranar dana sake saka shi cikin idanuna” Mommah ta sauke numfashi tana jin damuwar na sake dawo mata sabuwa, a hankali ta ce“Ka yi haƙuri Yallaɓai, ni kaina bana iya bacci saboda tunanin Zayyad, ban san inda zamu same shi ba, Ban san halin da yake ciki ba. Ko yana cin abinci ko baya ci, ko yana samun inda zai kwana ko baya samu, hankalina a tashe yake, dan girman Allah General ku sake saka sabon bincike a samu a dawo da Zayyad, dan Allah ka yi haka, Wallahi ina jin kamar zan mutu idan na tuna baya kusa damu, ka taimaka mana dan girman Allah general, dan Allah...” Rungumeta general ya yi abin da ya daɗe bai yi ba, Ta yi lamo akan ƙirjinsa tana shessheƙar kuka, Shafa kanta ya yi yana sauke numfashi a hankali. Sun ɗauki lokaci a haka har sai da ya ji ta yi shiru sannan ya a nutse ya ce “shikenan ki kwantar da hankalinki, in sha Allah zan saka a sake sabon bincike, za'a baza securities da police in sha Allah za'a samo shi nan kusa, in dai yana cikin Nigeria to nayi miki alƙawarin dawowa dashi” Mommah ta jinjina kanta har sannan bata ɗago ba ta ce”Tom Allah ya baka sa'a general” General ya ce“Ameen” Mommah ta yi shiru tana jin wani irin abu na yawo cikin ranta, maganganun Zayyad suka dinga dawo mata, yanda yake murmushi da yanda yake son taɓe baki, ranar da zai tafi London tafiyarsa ta farko, ranar ta kasance Monday ya shirya cikin kayansa ƙananu wanda suka masa kyau sosai duk da lokacin akwai yarinta a tare dashi, ya tsaya jikin corridor yana kallonta. Ta sakar masa murmushi ganin yanda ya kwaɓe fuska ta ce“Lafiya dai ɗan rigiman Daddy?” Zayyad ya taɓe bakinsa ya ce“Mommah bana son na tafi na bar ki, ina son ki Momma” Mommah ta ja kumatunsa tana murmushi ta ce“nima ina son ka ɗan gidan Mommah, zan yi missing ɗinka, ko da zaka fasa zuwa ne?” Girgiza kansa ya yi “Ina son ki Momma, But ina son nayi karatu sosai, Daddy ya ce yana son ya ga na zama doctor” Mommah ta sake murmushi tana gyara masa gashin kansa ta ce“Ai shikenan tun da ka zaɓi karatu, Sai ka je ka zauna kai kaɗai baka ganina” Daga haka ta sake shi ta juya, Sai da taje kofar ɗakinta sannan ta juyo ta kalleshi, Sosai ya ƙura mata idanu ta gyaɗa masa gira kana ta ce“Mene ne?” da gudu ya tawo ya rungumeta yana cewa “Mommah bana son na bar ki, nafison kullum na dinga zama kusa da ke. Idan bana ganinki tsoro nake ji Mommah, dan Allah kar ki bar ni Mommah”. Wani irin kuka ne ya kwace mata, General ya kalleta fuskarsa babu walwala ya ce“Khadijah ba nace zan saka a ci gaba da nemansa ba?” cikin kuka ta ce“Naji Yallaɓai, kawai na tuno shi ne, ranar daya fara tafiya London, Ya ce baya son ya ga baya ganina, Ban taɓa tunanin Zayyad zai yi nisa dani irin wannan ba. Domin a yanzu ban san in da yake, ban san wace irin rayuwa yake ba, Kuma duk wannan laifina ne, I'm the one behind everything” Girgiza kai General ya yi idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, muryarsa bata fita ya ce“Ki daina cewa haka, Baki da laifi, Ni ne wanda yake da laifi cikin wannan lamarin, ni na jawo duk abin da ya faru. Da ban bar Zayyad ya tafi ba da yanzu haka bata faru ba, Ni ne na saka ya tafi kuma ni zan dawo dashi in sha Allahu” Daddy ya ƙare maganar cike da ƙarfin gwuiwa. **** Tsaki Mufeeda ta yi tana kallon Nayla wadda ke yafa mayafin abaya ta ce“To ke wane ya faɗa miki?” Ba tare da ta juyo ba ta ce“Yaya Khalil” Mufeeda ta yi shiru tana kallonta can kuma ta ce“Kuma da gaske yake?” Sai a sannan ta juyo ta zuba mata gajiyyun idanunta kamar zata yi kuka ta ce“Amma kin san ɗakin yaya khalil ai, So kindly go and ask him stop bothering me please” Nayla ta ƙare maganar tana ɗaukan school bag ɗinta, harararta Mufeeda ta yi ta ce“To kar Allah yasa ki faɗa ɗin, Kuma ba zan je na tambayar ba” Ko kallonta Nayla bata yi ba ta nufi hanyar kofa ta fice daga ɗakin, Mufeeda ta bita da wani banzan kallo sai kuma ta yi tsaki. Koda Nayla ta sakko ƙasa bata samu kowa ba, Ta kalli dining area ɗinsu wanda yake wayam babu kowa saɓanin da, Da akoda yaushe yake so lively, Rabon da a taru a parlon aci abinci tun kafin tafiyar Zayyad. Ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta juya ta nufi ƙofa, Tana ƙoƙarin shiga motarta Khalil ya kira sunanta, Ta fasa bude handle ɗin ta juya tana kallonsa. Sanye yake da sport wear hannunsa riƙe da ƙaton ball, Nayla ta dinga kallonsa har ya ƙaraso gabanta. “School ɗin za ki tafi?” Khalil ya tambayeta, Gyaɗa masa kai ta yi dan yanzu ba wani magana take ba, Ya sake cewa“Ko zaki jirani sai na yi dropping ɗin ki daman akwai maganar da nakeson mu yi dake” Girgiza kanta ta yi ta ce“A'a Yaya sai dai idan nadawo muyi maganar kai fa baka shirya ba, ni kuma zan iya yin late idan na tsayaka kuma lecturern mu bashi da kirki” Harararta Khalil ya yi ya ce“To tafin” Daga haka ya juya ya bar wajen, Buga ƙafarta ta yi a ƙasa sannan ta biyo bayansa tana tura baki. **** Kaduna. 4:30pm Maryam ta yi murmushi ta ce“To yanzu dai idan kin je kar ki zauna dan Allah” Salma dake tsaye sanye da hijabi ta ce“In sha Allah Auntie, Ina amso maganin zan dawo gida” Maryam ta ce“Kamar gaske ba, Kar ki zauna hira wajen Umma dan Allah kin ga dai jiranki nake” Toh kawai ta ce sannan ta fice daga parlon. Zaune ta hangeshi gefen flower ya yi shiru, Ta ƙarasa tana kallonsa ta ce“Yaya Yad” Ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya ɗauke kai, Salma ta yi murmushi ta ce“Au ba zaka kulani ba?” Shiru ya yi mata, Ta rausayar da kanta kamar abin tausayi ta ce “Shikenan na tafi na bar ka ba zan sake dawowa ba” Daga haka ta nufi gate shi kuma ya bita da idanu. Ganin babu mai Napep a layin ya sanya ta yanke shawarar zuwa titi tafara tafiya a hankali kanta a ƙasa, Har ta kai bakin titi bata haɗu da Napep ɗin ba, Ta tsaida wani ta ce unguwar rigasa zai kai ta, Ya amsa sannan ta shiga, Juyowar da zata yi ta ga Zayyad yana ƙoƙarin shigowa shima. Da mamaki ta kalleshi sai kuma ta ce “Kai meyasa ka biyoni?” Ko kallonta bai yi ba ballantana ya bata amsa, Mai Napep ɗin ya ce“Hajiya tare ku ke ne?” gyaɗa masa kai ta yi ya sake cewa“To kuɗinki ɗari biyu da hamsim” Toh kawai Salma ta ce sannan ya ja napep ɗin suka fara tafiya. Har suka je unguwar Zayyad bai ce ƙala ba duk yanda ta dinga masa hira, Wata maganar idan ta yi ya kalleta wata kuma ko arzikin kallon bata samu. Bayan sun sauka daga Napep ɗin ta kalleshi ta ce“Yanzu daka biyoni na biya maka kuɗin mota da me zamu koma gida?” Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa, Ta haɗe rai ta ce “Baka ji na ne?” Yanda ta yi maganar cike da tsiwa ya sanya ya juyo ya sake kallonta, Bata yi aune ba kawai ta ga ya ɗauketa sama ya fara tafiya da ita, Zabura ta yi duk da layin ba mutane sosai ta dinga cewa ya sauketa amma ya yi mata banza. Har dukansa ta dinga yi tana mintsininsa amma kamar ba shi takewa ba, Bai sauketa ba sai da suka je kofar gidan Malam, Yana zaune kan tabarmarsa sai wasu maza guda biyu. Da mamaki ya dinga kallonsu Salma kuwa fashewa ta yi da kuka, Malam ya kalleta bayan ta zauna ya ce“Lafiya dai Ummusalma? Mene ne ya sanya ya ɗauko ki?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Malam baya jin magana shi, Kawai dan nace meyasa ya biyoni shi ne ya ɗaukeni yana tafiya dani Na ce masa kuma ya daina min irin haka” Malam ya Girgiza kansa sai kuma ya mayar da idanunsa kan Zayyad wanda ke tsaye har sannan a sanyaye ya ce “Babban mutum zo ka zauna mana, Muhammadu mai babban suna” Kallonsa Zayyad ya yi sai kuma ya ƙaraso ya zauna gefen tabarmar ya juya musu baya, Malam ya Girgiza kansa kawai ya kalli Salma ya ce“Ki daina yi masa magana idan ki ka ga yana irin haka kin ji” Tom kawai ta ce, Malam ya sake cewa“Rubutun ki ka zo karɓa?” Gyaɗa masa kai ta yi kana ta ce“Eh Auntie ta ce ka gama” “Eh na gama, Ki shiga ciki wajen Ralma ki amsa” Tom kawai ta ce sannan ta tashi ta shige gidan, Zayyad ya dinga bin ta da idanu. Koda ta shiga gidan bata wani daɗe ba ta amso rubutun ta fito, Zaune ta sameshi daga shi sai Malam yana masa karatu, Dan haka kawai ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana jiransu. Sai da ya gama tsaf sannan ya kalleta ya ce“Kin karbo?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh na karbo Baba” Ya ce“Tom shikenan a tabbatar yana sha kuma ana yi masa turaren, Ki gaishe da Maryam ɗin” “Tom Baba an gode Allah ya saka da Alkhairi zasu ji” Daga haka ta mike tsaye tana kallon Zayyad ta ce“Ka taso mu tafi to" Babu musu ya mike ya zura takalmansa ta sake yiwa Malam Sallama sannan suka bar kofar gida. Around 5:40pm suka shigo gidan saboda yanda ya dinga sakata magana a hanya, Ta shige ɗakinsa ita kuma ta yi cikin gidan. Zaune ta sami Maryam tana danna wayarta, Tana ganinta ta ajiye wayar tana cewa“Ai nace na ɗauka sai gobe zaki dawo” Dariya Salma ta yi ta ce”Kai Auntie gobe kuma, Ai ba mu daɗe ba, Umma nata yi mimi hira fa haka na taso dan naji kin ce kar ta dafa” Maryam ta taɓe baki ta ce“Haka fa, Ina Zayyad ɗin?” “Ya shiga ɗakinsa, Ni wallahi kar ya sake cewa zai bini wani waje" Salma ta ƙare maganar kamar zata zunduma ihu, Murmushi Maryam ta yi ta ce“Ai na leƙo naga baya nan nace to ke ya bi, Wani abin ya yi miki acan?” Labari Salma ta bata Maryam ta yi dariya ta ce“Zayyad kenan, maganin ki, Ba ke na cewa ki dinga fita a sabgarsa ba, Amma kin ƙi yarda, Ai gashi nan kina shan wahala a banza” Marairaice fuska Salma ta yi ta ce“To Auntie ya zan yi dan Allah, Kawai fa gani nayi ya biyoni” Maryam ta ce“Ba wannan ba, Nasan daman dole zai iya bin ki Amma ki daina kula shi idan ki ka ga ya miki banza sau ɗaya” Salma ta langwaɓar da kanta ta ce“To kuma sai ya dinga shareni” “To mene ne dan ya share kin?” Salma ta kalleta sai kuma ta yi shiru, Maryam ta yi murmushi ta ce“Ko dai akwai wani abun a ranki Salama?” Da sauri ta kalleta sai kuma ta ce “Auntie ban gane ba” harararta Maryam ta yi ta ce“Kin gane abin da nake nufi, Ko dai baki son Zayyad ya daina kula ki?” Salma sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba, Maryam ta sake cewa“Ba zaki faɗa min ba?” Muryarta na rawa ta ce“Ni fa babu komai Auntie” “Tom Allah yasa, Tashi mu ƙarasa aikin nan ya ce ana idar da magriba zasu zo” Tom kawai ta ce sannan ta miƙe tsaye ta zare Hijabin da ke jikinta, Doguwar rigar atampa ce a jikinta ɗinkin A-shape ba mai kama jiki ba. Ta nufi kitchen ɗin bayan ta ajiye ledar rubutun. Ana kiraye-kirayen sallar magriba ya buɗe gate ɗin ya shigo yana cewa“Bismillah shigo ciki” Shigowa ya yi bakinsa ɗauke da sallama, Hashim ya mayar da gate ɗin ya rufe yana kallon abokin nasa ya ce“Finally dai ka zo gidana” Murmushi Mukhtar ya yi ya ce“Ai kam dai na huta da mita, ka shigo Kaduna baka ƙaraso gidana ba to yau dai gani” Dariya Hashim ya yi ya ce“Naji ɗin muje ciki” Sun kai balcony Zayyad ya buɗe kofar ɗakinsa ya fito, Duka suka kalleshi Hashim ya ce“Babban yaya ina zuwa?” Da hannu ya yi masa nuni da waje sannan ya yi gaba, Mukhtar ya sake kallonsa Hashim ya ce“Muje mana” Okay ya ce sannan ya shiga parlon, Babu kowa a cikinsa amma komai na abinci an gama jera shi, Suka zauna Hashim ya fara zuba masa abincin. Sun ɗan jima suna hira sannan Maryam ta fito suka gaisa, Ta nemi waje ɗaya ta zauna tana danna wayarta, Ana fara kiran sallar isha'i suka tashi kai tsaye kuma masallaci suka nufa, Koda suka dawo Zayyad na zaune jikin bishiya ya yi kamar koda yaushe, Suka kalleshi sai kuma suka shige. Tunda suka shigo parlon yake bin ta da kallo tamkar idanunsa zasu faɗo, Salma data fito daga kitchen ke tana ƙoƙarin shigewa ta ga irin yanda yake kallonta ya sanya ta ɗan durƙusa murya can ƙasa ta ce “Ina yini” Da sauri Mukhtar ya amsa yana murmushi, Ta shige ɗakinta ya ci gaba da bin ta da kallo, Hashim ya ɗan yi murmushi sai kuma ya ce“Yallabai! Yallaɓai!!” A ɗan firgice Mukhtar ya juyo sai kuma ya ɗan yi dariya yace“Afuwan na tafi tunani ne” Hashim ya jinjina kansa kawai dan ya lura da abin da yake wa. **** Karfe 8pm ya bar gidan, Hashim ya raka shi sannan ya dawo gida, Zaune ya samu Maryam tana koyawa Khalil karatu, Ya zauna kan kujera yana kallonsu ya ce “Oh my goodness, wallahi nagaji sosai” Ɗago kanta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce“Har ya tafi?” “Eh mana, ai yau zai koma a Abuja shiyasa” Hashim ya bata amsa, Gyaɗa kanta ta yi tana mayarwa da Khalil books ɗinsa cikin jaka dan sun gama aikin ta ce“Sai kallon Salma yake kamar ya samu tv” Hashim ya yi murmushi kana ya ce“Kema kin lura ashe” Miƙawa Khalil jakar ta yi ta nuna masa hanyar bedroom sannan ta ce“Sosaima, Har sai da ya bani haushi ba'a son irin wannan kallon haramun ne” Hashim ya gyaɗa kansa ya ce“Tom Malamata ki yi haƙuri a maimakonsa” Taɓe baki ta yi ta ce“Tun da kai ka yi laifin” Girgiza kansa yayi ya ce“Ai ko bani nayi laifi ba dole ne na bada haƙuri dan kada ran Amminmu guda ya ɓaci” Murmushin da bata yi niyya bane ya suɓuce mata, Ta kalleshi ta ce“Baka rabo da abin dariya Abu, Yanzu ba wannan ba ni ina son muyi magana da kai” Gyara zamansa ya yi yana kallonta sosai ya ce“Ina jin ki” “Baka ganin ya kamata akai Salma makaranta, tunda ta gama secondary school ɗinta kawai sai a sama mata takardu ta ci gaba da zuwa University ɗinta kafin muga abin da hali zai yi” Hashim ya jinjina kansa ya ce“ i think so fa, Ya kamata ta ci gaba da karatu cause she's to small bai kamata a ce karatunta ya yanke daga nan ba, Kuma daga dukkan alamu tana da ƙoƙari” Maryam ta yi murmushi ta ce“Yawwa hakan ma za'a yi, in sha Allah gobe idan na fita zan iya Malama Rabi magana naji yanda za'a a samar mata takardun” “Tom shikenan, Allah ya kai mu” Ameen kawai ta ce sannan ta tashi tana hamma ta ce“Yau bacci nake ji, ni dai da wuri zan kwanta” Tashin shima ya yi ya ce“Nima ai hakan” Ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta bata sake cewa komai ba ta nufi bedroom ɗinta yana biye da ita. Washegari da yamma Salma ta shirya domin karbo rubutun Zayyad, Har ta fita tsakar gida sai kuma ta dawo ta shige ɗakinta. Jakar da kuɗinta yake ta buɗe ta zari wrapper na yan dubu-dubu sannan ta yi waje, Maryam na kwashe shanya ta kalleta ta ce “Salma karki dade dan Allah ki dawo da wuri da an gama masa” To kawai ta ce sannan ta fice daga gidan, Tsaye ta sameshi kan dakali ya yi shiru kamar mai tunani, Ta ƙarasa gabansa tana murmushi ta ce“Yaya Zayyad” ɗago kansa ya yi ta ce“Zo ka rakani” maƙale mata kafada ya yi ta langwaɓar da kanta ta ce“Dan Allah mana, Jiya ba rakani ka yi ba” “Ba zamu je ba ɗin” Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. Salma ta ce“Zan siya maka abun daɗi ba, har da riga zan siya maka” Ya kalleta amma bai ce komai ba, Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Da gaske fa nake, Taso ka ji” Ta mika masa tafin hannunta, Kallon farin hannun nata ya yi sai kuma ya ɗora nasa akan natan ya miƙe tsaye, Ta saki murmushi wanda ya fito da zallar kyanta ta ce“Ko kai fa Yaya Yad”. **** Maryam na zaune a parlon taji ana bugun ƙofa, Ta tashi ta fito tana cewa waye, Jin ba'a yi magana ba ya sanya ta sake cewa waye, nan ma ba'a ce komai ba. Ta yi tsaki sannan ta ƙarasa ta buɗe kofar tana cewa “Ana cewa wane kuna jin...” Cak maganar ta tsaya a maƙogaronta sakamakon sojojin data gani kusan guda goma tsaye a bakin ƙofar, Baya taja da sauri suna danno kai cikin gidan without even ask for a permission. Zagaye gidan suka yi, Wasu a waje wasu kuma a ciki sai a sannan ta gane yawansu yafi yanda take tunani. Muryarta na rawa ta ce“Yallaɓai lafiya?” Babu wanda ya kulata a cikinsu, Suka shiga har cikin bedrooms ɗinta suka dudduba, Maryam ta dinga bin su da idanu tana jin gabanta na wani irin faɗuwa dan bata san laifin data aikata ba. Hashim ne ya dawo hannunsa riƙe da ledar salad wanda daman shi ne ya fitar dashi, Ganin tarin jami'an tsaro a ƙofar gidansa ya sanya ya saki salad ɗin ba tare da ya sani ba, Ya ƙarasa cikin gidan da saurinsa sai dai ya yi turus ganin Maryam tsaye ta rufe fuskarta sojan ya sai ta mata bindiga a saitin kanta yana cewa “Zaki faɗa ko ba zaki faɗa ba? Ina suke nace!” Da gudu ya ƙarasa gabansu yana Girgiza kansa ya ce“Yallaɓai su wa ake nema? Mu ba masu laifi bane” Wani soja ne ya fincikeshi ya durƙusar dashi ƙasa ya dasa masa bindiga a tsakiyar ka ya ce “Kana motsawa sai na fasa kan ka da bindiga” Fashewa da kuka Maryam ta yi tana girgiza kanta, Aka buɗe gate ɗin gidan suka shigo, General ne sanye cikin uniform sai kuma General Kabeer abokinsa shi ma sanye da uniform ɗin, Suka dinga bin gidan da kallo kafin general ya ƙaraso inda suke, sara masa suka yi duka, ya jinjina masu kai Sannan ya ƙurawa Hashim idanu.. Da hannu ya yi wa wani soja alama ya sara masa sannan ya juya ya fice ba'a fi 2mins ba suka shigo tare, Zabura Hashim ya yi ya dinga nuna shi da yatsa yana son kiran sunansa amma mamaki ya hana shi, Ya tako har in da suke ya rusunawa general, Murya a dake general ya ce “Shi ne?” Gyada masa kai ya yi kana ya ce“Eh Yallaɓai su ne, nan ne gidan” “Mukhtar!” Maryam ta faɗa tana zaro idanu waje.. _Book 1 ya kusa karewa and book 2 isn't free it's ₦700 via 7041901078 Hauwa lawan Adamu Opay evidence via 08106608363 Nanameera_ # HCD # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 31-32: The price of togetherness Nanameera, YOTA/023. General ya kalleta sai kuma ya mayar da kansa gurin Hashim, Hannunsa ya sanya ya ɗago fuskarsa muryarsa a dake babu alamar wasa ya ce “Where are they?” Girgiza kai Hashim ya yi muryarsa na rawa ya ce“ban san inda suke ba, ban san su wane ku ke magana akai b...” Maganar ta tsaya cak saboda yanda general ya daki bakinsa da kan bindigar hannunsa, Hashim ya durƙushe yana sakin ƙara, kuka Maryam ta saka tana ɗora hannu aka, General ya gyara tsaiwarsa hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa ya kalli Mukhtar ya ce“Are you sure?” gyaɗa masa kai ya yi ya ce“absolutely sure sir, jiya na gansu cikin gidan nan” Furzar da iska general ya yi sai kuma ya juya a fusace ya damƙi maƙogaron Hashim fuskarsa a haɗe yana zaro idanu ya ce“Don't ever let me ask you again, Ina suke?” Hashim da ke numfashi dakyar gumi sai keto masa yake ya sake girgiza kansa a karo na biyu muryarsa bata fita ya ce“ka yarda dani, ban sani ba yallabai” Sakinsa general ya yi yana jinjina kansa ya ce“Okay, yayi ka yi ƙokari” Daga haka ya juya yana kallon sojojin da suke tsaye, Da hannu ya yi musu alama dasu tawo dasu sannan ya juya ya fice daga gidan. Salma ta dinga kallon ƙofar gidan dama wajen unguwar ganin yanda ta zama tamkar ƙaramin barikin sojoji. Ta rufe bakinta da hannunta ganin sanda general ya fito daga gidan, bayan mintunan da basu shige biyu ba sai ga Hashim da Maryam sojoji sun fito dasu, Tuni hawaye suka wanke fuskarta ta juya ta kalli Zayyad wanda tun da suka shigo siririn layin yake kallonsu. Cikin sa'a kuma idanunsa ya sauka akan general da ke ɗaga waya, ƙura masa idanu ya yi sai kuma ratsa ta gefenta yana shirin fita, Da sauri ta jawo shi murya can ƙasa ta ce“Ina zaka je?” Da hannu ya yi mata nuni da su Hashim da ake ƙoƙarin shiga mota dasu, Khalil wanda dawowarsa daga makaranta kenan sai ihu yake yana riƙe da gefen rigar Maryam. Salma ta fashe da kuka ta riƙe shi sosai ta ce“Ba zamu iya taimakonsu ba, ka yi hakuri yaya Zayyad” Fizge hannunsa ya yi ya sake nufar wajen layin, Da ƙarfi Salma ta jawo shi, ta rikeshi sosai tana kuka kamar ranta zai fita, tureta ya sake yi a karo na uku sai dai wannan karan ƙin yarda ta yi, ta rungumeshi sosai ganin yanda yake ƙoƙarin kwace mata ya sanya ta fashe da kuka, Ba tare da wani tunani ba kuma ta haɗe bakinsu guri ɗaya a kokarinta na son ganin ya bar wajen, kamar yanda ta yi tunani haka ne ya kasance, Zayyad ya juyo yana zaro idanu ganin bakinsa Salma cikin nasa, Ita kuwa ta rufe idanunta har sannan kuma bata cire bakinta daga cikin nasa ba. After 2mins ta sake leƙa wajen layin sai taga wayam babu kowa sai wasu tsirarin sojoji da basu shige uku ba suna sintiri a bakin gidan, A hankali ta janye bakinta daga cikin nasa tana sauke numfashi, Zayyad kallonta kawai ya dinga yi sai kuma ya kwaɓe baki, Hannunsa ya sanya akan lips ɗinsa ya shafa sai kawai taga ya fashe da kuka. Kallonsa ta shiga yi ganin ya yi zaman dirshan a ƙasa, ta tsuguna tana kallonsa sai dai ta kasa ce masa komai dan gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, koda wasa bata taɓa tunanin zata iya aikata irin haka ba, Sai dai ta riƙe irin wannan abun ne sakamakon kallon da take tashar zee world da mbc a finanin India, bata yi tunanin abun yana aiki da gaske a zahiri ba sai gashi ta gwada kuma ya yi a gaske. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce“Dan Allah Yaya Zayyad ka tashi mu tafi, har yanzu suna nan bana son su kama mu" Kukansa ya ci gaba da yi babu alamar ma yana sauraronta, Ta dinga jan hannunsa daga tsayen da take tana kuka. Cizo ya kawo mata ta yi saurin janye hannunta tana cewa“Cizona zaka yi kuma?” Ya dinga kallonta ta ja baya tana gyaɗa kanta ta ce “Shikenan ai sai ka yita zama, tun da duk abin da nake maka baka gani, ka tsaneni baka sona, baka tausayina, baka ganin yanda nake shan wahala. Tun da kafi son ka bi iyayenka kaje ka tafi dasu ɗin, nima zan haƙura na ci gaba da rayuwata ni kaɗai, zan manta da kai, daga yau kai ma ka manta dani...” Ta kasa ƙarasawa saboda kukan da take, tsallake duk ledojin da suka zube ta yi ta juya ta yi tafiyarta. Zayyad ya dinga kallonta ganin da gaske tafiyar take kuma bata ko waiwaye, Ya ɗauke kansa yana ci gaba da kukansa. Tafiya ta dinga yi tana kuka kamar zararriya, Daga ƙarshe ma ta nemi wani dakali ta zauna tana rusa ihu kamar sanda Abbanta ya rasu, Ko sharrin da aka mata akan Zayyad bai sakata cikin tashin hankali ba irin wannan, Ko wane hukunci za'a musu? Daga taimako General ya saka an tafi dasu, Allah ne kaɗai yasan irin halin da zasu shiga yanzu. Salma ta sake fashewa da wani sabon kukan na rashin madafa da abin yi, ƙirjinta ya yi wani irin nauyi ta dinga sauke numfashi da kyar, tunani ta shiga yi na abin da zata yi yanzu. Cikin kuka ta ce “Nashiga ukuna, yanzu ya zan yi? Wayyo Allahna...” Ta sake fashewa da wani sabon kukan, tunanin ta je ta sanar da gidansu Maryam ta yi dan haka ta miƙe tsaye tana share hawayenta da mayafin hannunta sannan ta ci gaba da tafiya wasu hawayen na sake zubowa. Tafiya ta dinga yi a ƙasa dan tama manta da cewa akwai kuɗi a jikinta, Har ta kai unguwar rigasa wajejen gefin magriba, Malam na tsugune ƙofar gida yana yin karatu ya hangota tsaye tana kallonsu, Sallamar ɗalibansa ya yi sannan ya ta ƙaraso, zama ta yi tana gaishe shi ya amsa yana cewa “Babban mutum zauna mana” Salma ta juya da sauri dan ganin wanda yake nufi,baki buɗe ta dinga kallon Zayyad wanda ke tsaye hannunsa riƙe da ledojin data zubar, bai ko kalleta ba ya nemi gefen malam ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa ya ajiye ledar hannunsa bisa cinyarsa. Malam ya dinga kallonsu can kuma ya ce“Ummusalma lafiya?” Sai da ta ɗan yi jim kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce“Baba daman wani abu ne ya faru...” Malam ya sauke numfashi bayan ta gama bashi labarin duk abin da ya faru, ya jinjina kansa fuskarsa babu alamun ɗimuwa ko tashin hankali ya ce“Allah alhakamu, ai na tabbata ba wani abun zasu yi musu ba, idan sun tambayesu ba'a samu biyan buƙata ba zasu sake su” Salma ta girgiza kanta cike da ɗimbin damuwa ta ce“A'a Baba wallahi a tsorace nake, kar su cutar dasu aunty Maryam, hankalina ya kasa kwanciya” Ɗan murmushin manya Malam ya yi kana ya ce“Ummusalma kenan, ai ita rayuwa mutum baya gujewa ƙaddararsa, tun da har kin san waɗanda suka ɗaukesu to ai shikenan. Dawo dasu ba abu bane mai wahala, yanzu kawai ke ku shiga gida sai ku zauna” Salma ta dinga kallon malam tana jinjina halin kirki irin nasa, duk da yanda aka tafi da yarsa a kansu hakan bai sa yaji ba zai iya taimakonsu ba. Ta girgiza kanta muryarta na rawa ta ce“A'a malam wallahi ba zan iya zama a cikin gidanka ba, tsoro nake ji zasu ya dawowa a kowane irin lokaci, kawai na zo na sanar da kai halin da ake ciki ne amma tafiya zamu yi” Malam ya girgiza kansa cikin dattako ya ce“ashsha! Ai ba wani abu bane dan kun zauna a gidana, daman gidan nan gidan baƙi ne. Sai ku yi zamanku babu damuwa ummulsalma amma yanzu idan ku ka tafi ina zaku je? Shin kin san wani gurin ne?” Murya a sanyaye Salma ta ce“bamu san kowa ba Baba, kawai zamu tafi ne yanda Allah ya haɗa mu dasu Aunty Maryam haka zai sake haɗamu da mutanen kirki in sha Allah, amma duk sanda muka samu dama zamu zo domin duba su, zamu dawo watan wata rana” Malam ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“shikenan tun da kina ganin haka shi ne mafi kwanciyar hankali, amma ina da wata magana guda ɗaya” “Ina jin ka Baba” Ya ɗan numfasa kafin ya sake cewa “wato Ummulsalma kin san shi a rayuwa komai zaka yi kana duba addininka da kuma al'adarka, kuma kin san a addinan ce kasantuwarki da Zayyad a haka ba abu bane mai yiwuwa. Shi ba ɗan uwanki bane dan haka bai zama muharraminki ba, ba zai yiwu ku ci gaba da rayuwa a haka ba” Salma ta kalli Malam sai kuma ta ce“Eh Baba amma ai ka ga babu yanda zamu yi ne, shi baya cikin hayyacinsa ba zan tafi na bar shi ba. Sannan ma ba shi da kowa ballantana na kai shi gurinsu, nima kuma banida dangi da zan je mu zauna a can, dole ta sanya nake tafiya ko ina da Yaya Zayyad na tabbata shi ɗin ƙaddarata ne” “To idan haka ne meyasa ki ka ƙi bari ya bi mahaifinsa?!” Tamkar saukar aradu haka taji tambayar ta Malam, ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“saboda na riga da na saba dashi Malam, bana son na daina ganinsa, kuma na tabbata idan suka gan shi ba zasu bar ni dashi ba. Shiyasa ba zan iya barin su tafi dashi ba, shi kaɗai nake gani naji daɗi banida kowa sai shi malam” Ta ƙare maganar tana kallon Zayyad wanda ya yi shiru abin sa. Malam ya yi shiru for some minutes yana nazarin kalamanta, har sai da ta ɗago ta kalleshi, ganin yanda ya yi shiru ya sanya ta sake sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Gyaran murya ya yi kafin ya fara cewa “kenan baki son rabuwa dashi? Kuma kina ganin kin shirya rayuwa dashi a kowane irin hali?” Gyada masa kai ta yi ta ce“eh, na yarda zan rayu dashi ko da daɗi koda wahala, idan har yaya Zayyad ya zame mini kaddara to nasan ba zan iya guje masa ba. Dan haka na yarda zan kasance a kusa dashi a kowane irin yanayi” Malam ya jinjina kansa kana ya ce“Masha Allah, to idan haka ne mafita ɗaya ce ta rage muku daga ke har shi” Salma ta ji gabanta ya faɗi ta dinga fargabar wata irin mafita ce wannan domin ba zata taɓa yarda a ce mafitar ita ce rabuwarta da Zayyad ba. Malam ya ce“Idan har kina son ki ci gaba da zama tare da Zayyad to mafita ɗaya ce ita ce ki aureshi...” With so much shock Salma ke kallon malam bakinta ya kasa rufuwa sai zaro idanu take, bakinta na rawa ta ce “a'a... a'a Malam, aure fa? Aure zan yi da yaya Zayyad? Ba zan iya ba Malam, wallahi ba zan taɓa iya aurensa ba!” Malam ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce“kenan baki shirya rayuwa dashi ba, idan har da a ce kina son rayuwa dashi to ba zaki kasa aurensa ba, domin Allah bai haramta hakan ba, kina da damar da zaki iya aurenshi, idan har kin amince ni zan ɗaura muku aure a yau ba sai gobe ba” Ban da girgiza kai ba abin da Salma ke yi, hawaye kuwa tamkar an buɗe famfo haka ya dinga zubowa kan fuskarta, ta kalli Zayyad wanda ke kallonta ganin yanda take kukan, sai kuma ta sake mai da Idanunta kan Malam a karo na biyu ta sake cewa “Ba zan iya ba Malam, ina yiwa yaya Zayyad kallon yaya ne a gareni, ba zan taɓa iya aurensa ba, ba zan iya ba Malam dan Allah ka yi hakuri” Malam shiru ya yi yana bin ta da kallo, ya juya ya kalli Zayyad wanda ya yi jigum sai kwaɓe fuska yake yana kallon Salma, wajen ya ɗauki shiru na wasu daƙiƙu kafin ya numfasa ya ce“Ba zan miki dole ba Ummulsalma, idan har kin ce baki son Zayyad to babu yanda za'a yi na tirsasaki, kina da damar zaɓar wanda ki ke son ki yi rayuwar aure dashi ko a yanzu ko kuma nan gaba. Amma ki sani idan har baki auri Zayyad ba to ba zaki sake tafiya wani gurin dashi ba! Sai idan ki yi tafiyarki ke kaɗai, shi kuma da kaina zan mayar dashi har gidansu domin ba zan bari ku yi zaman haramci ke dashi ba” Fashewa da kuka ta yi ta kifa kanta kan cinyoyinta ta shiga rerashi tamkar karatu, Malam bai sake cewa komai ba ya kalli Zayyad jin an fara kiraye-kirayen sallar magriba ya ce“Babban mutum tashi mu je masallaci” babu musu Zayyad ya tashi har sannan yana riƙe da ledojinsu, Malam ya kalleshi ganin yana ƙoƙarin tafiya dasu ya ce“a'a ajiye kayan muje mu dawo” girgiza kansa ya yi ya sake ƙanƙame ledar, Malam ya ce“ajiye nace mana” tura baki ya yi sannan ya dire ledojin ya yi gaba Malam ya Girgiza kai sannan ya bi bayansa, Salma ta bisu da idanu tana zubar da wasu hawayen. **** Mommah ta dinga kallon Nimra ganin yanda take faman kuka ta ce“kin yimin shiru ko sai ran ki ya ɓaci?” sake fashewa ta yi da kukan tana buga ƙafarta, Mommah ta girgiza kai Sai kawai ta tashi ta bar parlon, Nimra bin ta tayi da kallo, sai kuma ta tashi tabi bayanta da sauri tana ci gaba da kukan, tura ƙofar ɗakin ta yi ta hangi Mommah zaune gefen gadon ta yi tagumi, da sauri ta ƙarasa ta faɗa jikinta tana sake rushewa da wani sabon kukan, Mommah ta girgiza kanta ta ce “Yanzu me ki ke so nayi Nimrah?” Cikin kuka ta ce“dan Allah Mommah ki faɗawa Daddy, wallahi ba zan iya zama da kishiya ba Mommah, wallahi ba zan iya ba” ta ƙare maganar tana sake ruƙunƙumeta. Mommah kallonta ta dinga yi kafin ta ce“ Nimra kenan, shi zama da kishiyar mene a cikinsa? Mu duk ba haka muka zauna da kishiyar ba? Ke uwarki ma ita ce ta zo a kishiyar” ɗagowa Nimrah ta yi fuskarta ta yi caɓa-caɓa da hawaye ta kalli Mommah ta ce“Momma ai ke kina zaune lafiya da Mommy, wallahi ba zan iya rayuwa da kishiya ba, ba zan iya sharing mijina da wata ba mommah” Janyeta daga jikinta ta yi ta ɗago kanta tana kallonta sosai ta ce“Na ce ki kwantar da hankalinki kin ƙi, tun ɗazu nake baki haƙuri amma kin ƙi, ya zan yi miki?” cikin shessheƙar kuka ta ce“to mommah ya zan yi?” Gyara zama Mommah ta yi ta ce“Yawwa kina ji, ki kwantar da hankalin ki, idan har kin iya riƙe mijinki kin kuma san martabar kan ki to koda ya yi aure babu abin da zai sameki, just calm down, ki koyi yanda ake iya magana Nimrah,ki daina saurin fushi sannan ki daina gaddama, sannan ki koyi yanda ake wa miji biyayya. Idan har ki ka riƙe waɗannan abubuwan to babu abin da zai taba ƙimarki a gurin mijinki” Nimrah ta sanya hannunta ta goge hawayenta sannan ta ce“tom amma Mommah idan suka yi aure daina son Uwar gidansu suke, shikenan na zama banza” Ɗan murmushi Mommah ta yi sannan ta ce “Nimra kenan, Ni yanzu a gidan nan wa ake bawa girma?” Shiru Nimrah ta yi Mommah ta ce“talk mana” A sanyaye ta ce“Mommy mana” jinjina kai Mommah ta yi ta ce“good, yanzu kin gane abin da nake nufi ko? Idan har kin iya riƙe mutuncinki to babu yanda za'a yi a raina ki, saboda haka ki daina ɗaga hankalin ki akan wai Faruk zai ƙara aure, just leave him, ke dai ki ci gaba da kyautata masa” Nimrah ta gyaɗa kanta wasu sabbin hawayen na sake sakko mata ta ce“tom Mommah zan yi yanda ki ka ce, amma zuciyata zafi take min” ta ƙare maganar tana sake faɗawa jikinta, rungumeta Mommah ta yi ta dinga shafa bayanta a hankali ta ce“ya isa haka, stop crying kin ji Nimrah, zan taya ki da addu'a in sha Allah” Nimrah kasa daina kuka ta yi, har after 5mins kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kuka a hankali, Mommah ta yi shiru tana jin kukan ɗiyar tata har cikin ranta. **** A tare suka fito parlon, Mommah ta dinga kallon general ganin yanda yake safa da marwa cikin parlon, a sanyaye ta ce“lafiya dai Yallaɓai?” kallonta kawai ya yi amma bai ce mata komai ba, Ta mai da Idanunta kan Khalil wanda suka shigo tare ta ce“Ibrahim meya faru?” Satar kallon general ya yi yaga hankalinsa baya kansu sannan ya ce“an je gidan dasu Yaya Zayyad suke ne...” “an same shi?” Mommah ta yi saurin katse shi, girgiza kansa ya yi a hankali ya ce“ba'a same shi ba, amma an tawo da mutanen da suka riƙe su, an yi an yi dasu su fadi in da suke amma sun ƙi” wani irin abu taji ya tsaya mata a ƙirji, ta ɗago idanunta wanda suka sauya kala ta kalli general, sai kawai ta fashe da kuka ta juya ta koma sama da sauri. Nimrah ta bita da idanu sai kuma ta kalli general, jiki babu kwari ta ƙarasa gabansa muryarta na rawa ta ce“daddy dan Allah a samu a dawo dashi, duk mun damu” general kallonta kawai ya yi sai kuma ya gyaɗa mata kai dan baya jin zai iya magana ma, ta juya ta nufi hanyar fita daga parlon ba tare da ta sake cewa komai ba.. Tura ƙofar ɗakin ya yi jin shessheƙar kukanta, zaune ya hangeta gefen sofa sai kuka take ya ƙarasa a hankali ya zauna gefen drawer yana kallonta. Above 5mins kafin ya furzar da numfashi cikin sanyin murya ya ce “Kukan na mene ne? Baku son hankalina ya kwanta, dame zan ji?” “Tambayata ka ke yallaɓai? Baka san dalilin kukana ba? Shikenan ai” Kallonta ya yi sai kuma ya ce“i know but you have to calm down, Ina kan bincike akan yanda za'a samu yaron nan ya dawo, kin san yanda na damu? Kin san a irin tashin hankalin da nake ciki Khadijah? Ya kamata ki tausayamin” “Ni ban ce baka kokari ba, nasan kana yin iya bakin ƙoƙarinka, but you have to put effort into it, Ina son naga Zayyad wallahi” Mommah ta yi maganar hawaye na sakkowa kan fuskarta, Hannunta general ya kama ya riƙe cikin nasa cikin nutsuwa ya ce“shikenan, yanzu dai na saka an kamo min waɗanda suka zauna dasu, ina sha Allah nan bada jimawa ba za'a gan shi” “To tun da ba'a gansu ba mene ne amfanin kamasun? Me zaka musu?” General ya ce“i'll deal with them har sai sun faɗi in da suka kai su” **** Salma na nan zaune har gari ya fara yin duhu, a wajen ta yi sallar magriba, ta dinga jiransu amma shiru ga wata yunwa da take ji kamar ta ci babu. Sai da aka idar da sallar isha'i sannan suka dawo, Malam ya dinga kallonta da mamaki har ya ƙaraso wajen, “Shiga kaje gida yanzu zan shigo” Ya ƙare maganar yana kallon Salma ya ce“au baki tafi ba?” Ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, ya sake kallon Zayyad dake tsaye har sannan ya ce“muje ciki” “Idan har aurena da Yaya Zayyad shi ne zai bani damar ci gaba da rayuwa dashi to na aminci zan aureshi, na yarda Baba, amma dan girman Allah kar ka rabani dashi...” # HCD # Salma # Yaya yad # Nanameera 08106608363. *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 33-34: A twist of fate Nanameera, YOTA/023. Malam ya juyo yana kallonta, kuka take sosai kamar zata shiɗe, ya girgiza kansa cikin natsuwar data gama ratsa shi ya ce“ba zan yarda da wannan amincewar taki ba, domin yanda ki ke kuka ya nuna ba so ki ke ba, kina ganin kamar an miki dole ne. Ni kuma ba zan taɓa yi miki dole ba Ummulsalma, saboda haka ki yi tafiyarki shi ma zan mayar dashi ga iyayensa” Durƙushewa ta yi a ƙasa cikin shessheƙar kuka ta ce“dan Allah Malam kada ka rabani dashi, ba ina kuka bane saboda na amince, ina kuka ne saboda tunanin abin da zai je ya dawo. Malam idan auri Yaya Zayyad a yanzu ba tare da yardarsa ba, duk ranar daya dawo cikin hayyacinsa zai iya cewa bai yarda ba. To ya zan yi Malam?” Numfasawa Malam ya yi yana kallonta cike da tausayawa, ya ɗan yi jim kafin ya ce“idan har kina ganin akwai damuwa to kawai a haƙura, ki yi tafiyarki ko kuma ki bini na mayar daku gidansu” Ɗago kanta ta yi da sauri ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a malam ba zan iya komawa gidansu ba, kasheni zasu yi. Na yarda zan auri Yaya Zayyad kuma zan zauna dashi a kowane irin yanayi” Malam ya dinga kallonta yana nazarin kalamanta kafin ya furzar da iska daga bakinsa“shikenan ki shiga ciki zuwa gobe da safe sai a ɗaura auren ku tafi” Tashi ta yi daga durƙushen da take ta ce“malam ba za'a iya ɗaurawa yanzu ba mu tafi? Bana son na sake kwana a garin nan” malam ya yi shiru can kuma ya ce“to tunda haka ne shiga ciki ina zuwa” to kawai ta ce sannan ta nufi ƙofar gidan, har ta shiga soron ya kira sunanta, ta juyo bayan ta amsa ya ce “kar ki ce musu wani abu akan su Maryam, kawai ki yi shiru” toh kawai ta ce sannan ta shige cikin gidan. Ya kalli Zayyad da ke tsaye kamar statue yace“mu je ka rakani" langwaɓar da kai ya yi sannan ya yi gaba Malam yana biye dashi. Koda ta shiga gidan kowa na ɗakinsa saboda ɗan sanyin da ake, ta nufi ɗakin Ummar Maryam, sai da tayi sallama sannan ta ɗaga labulen. Umma dake zaune gefen kujera ta ce “a'a Salma ke ce da magribar nan?” Sai da zauna sannan ta ce“Eh Umma, nazo wajen Malam amsar wa Yaya Zayyad rubutu shi ne na shigo” “Malam ɗin baya nan kenan?” Girgiza mata kai ta yi ta ce“A'a na ganshi cewa ya yi na ɗan jira shi zai je ya dawo” Umma ta jinjina kanta ta ce“Eh to sai ki jira shi” Daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin. Ba'a fi minti biyu ba ta dawo hannunta riƙe da plate ta ajiye gaban Salma ta koma ta zauna. Shinkafa da wake ce wadda taji salad da yaji a gefe, Salma ta yi murmushi ta ce“Umma ai na ƙoshi fa” wani kallo ta yi mata tana taɓe baki ta ce“naga kin rage min ko kaɗan ne sai ranki ya ɓaci” langwaɓar da kai Salma ta yi ganin yanda Umma ta haɗe rai ya sanya ta ɗauki spoon ɗin kan abincin ta yi bismillah ta fara ci. **** Jiddah tsayawa ta yi da folding mayafin da take tana kallon Suhaila, ganin irin kallon da take mata ya sanya Suhaila ta ce“baki yarda bane wai?” babu yabo babu fallasa Jiddah ta ce“na yarda mana” Suhaila ta yi murmushi sannan ta ce“Auntie Jidda kenan, ni nasan baki yarda ba wallahi” taɓe baki Jiddah ta yi ta buɗe press ta ajiye mayafin sannan ta ce“ni kin isheni da magana, ki fita please” Turo baki Suhaila ta yi ta ce“kai Auntie, Mummy ce fa ta ce nazo na kira ki” “but I'm doing something ai, ki ce ina zuwa” Suhaila ta ɗan kwaɓe fuska sai kuma ta ce“to ni na tafi, kuma ba zan sake dawowa ba ma” daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin. Jiddah ta sauke numfashi ta ci gaba da folding kayan nata har ta gama sannan ta zauna gefen gadon, dafe saitin zuciyarta ta yi jin yanda take mata wani irin zafi, ta tashi ta nufi hanyar toilet tana tafiya a hankali. Jikin sink taje ta zubawa mirror idanu, hannunta ta kai ta taɓa ƙashin da ya yi mata sarƙa a wuya, hawaye ya fara zuba akan fuskarta “Ba zan bar shi ba, I'll definitely take my revenge” Jiddah ta yi maganar cikin shessheƙar kuka. Amai ne ya tawo mata ta sunkuya da niyyar ta yi sai dai madadin ta ga aman sai taga jini na fitowa daga bakinta, ta dinga aman jinin har da guda-guda. Sai da ya daina fitowa sannan ta kunna tap ta wanke bakinta, idanunta ya yi wani irin fari ta ɗago kanta hawaye na ci gaba da bin fuskarta. “Jiddah! Jiddah! Jiddah” Muryar Mummy ta daki kunnuwanta, da kyar ta sauke numfashi sannan ta wanke fuskarta ta nufi hanyar fita daga toilet ɗin, tana buɗe ƙofar Mummy ta dinga kallonta kafin ta ce “lafiyar ki klao?” She just nodded her head dan bata jin zata iya magana, ta nemi kan sofa ta zauna tana sauke numfashi. Mummy ta ƙaraso gabanta ta dafata a sanyaye ta ce“Jiddah! Jiddah!” In a very cool voice ta ce“na'am Mummy” ”tell what wrong with you? Kar ki ce zaki min karya ko kuma ki ɓoyemin abin da ke damunki, I'm ur mother, baki da wadda zaki faɗawa matsalarki sama dani Jiddah. Saboda haka just tell me the truth” Yanda Mummy ta yi maganar ya sanya jikinta ya yi sanyi, ta ɗago runannun idanunta ta kalleta amma ba ta ce komai ba. Mummy ta zauna gefenta ta janye hannayenta duk biyun ta rike cikin nata ta ce“Jiddah kin san na damu dake ko? Kin san bana son abin da zai taɓa ki ko? But why ba zaki bar ni na huta ba? Ina lura da ke tun lokacin da aka ce Zayyad ya ɓata baki sake samun kwanciyar hankali ba. Jiddah yau idan ciwonki ya tashi sai nafi kowa shiga tashin hankali kin san da haka? Kina jin mahaifinki ya ce suna iya bakin ƙoƙarinsu kuma zasu samo shi, amma kin ƙi yarda, kin ƙi kwantar da hankalinki. Me yasa Jiddah!? Baki son ganina cikin kwanciyar hankali ne?” Madadin ta amsa duk maganganun Mummy sai kawai ta faɗa jikinta tana fashewa da wani raunataccen kuka, rungumeta Mummy ta yi tana jin yanda take kuka kamar ranta zai fita, above 5mins kafin ta fara sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kukan ta ce “Ki yi haƙuri Mummya, hankalina ya kasa kwnaciya ne, dan Allah ki tayani da addu'a ji nake zuciyata kamar zata fashe, ƙirjina nauyi yake min Mummy, idanuna...” ta kasa ci gaba da maganar saboda sabon kukan daya tawo mata. Mummy ta dinga kallonta jiki a sanyaye, sai kuma ta girgiza kanta muryarta kamar mai shirin fashewa da kuka ta ce“shikenan Jiddah tun da ba zaki iya faɗa min damuwarki ba zan taya ki da addu'a, Allah ya yaye miki abin da yake damunki, ya bar ki da alherin rayuwa a duk yanda yake. Amma ki sani idan har ki ka cutar da kan ki ba zan taɓa yafewa kaina ba, kuma ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba” Daga haka ta janyeta daga jikinta ta tashi ta fice daga ɗakin, Jiddah ta dinga kallon Mummy kamar ta je ta sameta ta sanar da ita duk abin da yake damunta, sai dai hakan ba abu bane wanda zai taɓa yiwuwa ba!. Ba zata taɓa iya faɗawa Mummy wannan damuwar ba sai dai ta bar ta cikin ranta har ta yi ajalinta. Ta sulale ƙasan tiles tana sake rushewa da wani sabon kukan... Mummy na fita ta tsaya a corridor tana goge hawayen daya zubo kan farar fuskarta, “Hafsa!” Taji muryar General Kabeer ya kirata, muryarta na rawa ta ce“Na...na'am..” Takowa ya yi har in da take ya dinga kallonta da mabayyanin mamaki kafin can ya ce“lafiya? Kukan me ki ke yi?” “Dan girman Allah general ku sake tsaurara bincike akan neman Zayyad, dan Allah ku dawo dashi ko na samu hankalin ƴata ya kwanta, idan har wani abun ya sameta ba zan iya rayuwa ba...” ta ƙare maganar kuka na kwace mata, General Kabeer ya dinga kallonta sai kuma ya ce“ku mata meyasa mentality ɗinku iri daya ne? Kema zaman kukan ki ke saboda tana yi kenan, kun san irin neman da muke masa? Kun san abubuwan da muka jingine kawai saboda bincike akan inda ya shiga? Tun da har aka ce za'a dawo dashi ba shikenan ba, Please Hafsa ki daina biyewa magana ta yara, in sha Allah nan bada jimawa ba Zayyad zai dawo kuma za'a fita dashi domin samar masa da lafiya, so you don't need to be worry dan Allah, idan kuma kinason depression ya kama ki ne to” General ya ratsa ta gefenta ya nufi downstairs, da idanu kawai Mummy ta bishi sai kuma ta yi hanyar nata dakin har sannan kuma bata daina kukan ba. **** Mami ta girgiza kanta ta ce“ba haka ya kamata ayi ba, wannan abun da general yake ba shi ne daidai ba, akan me zai je ya ɗauko mata da ɗanta da mijinta saboda an ce an ga su Zayyad a gidan? Idan kuma ƙarya ake fa? Koma a ce gaske ne tunda shi bai gansu a gidan ba ai babu hujjar da zai sa a kamasu” Mommah ta sauke numfashi ta ce“to me zan ce Mami? Bai ma bani listening ear ba, kin san dai halin general ba'a sauya masa ra'ayi ko nayi magana baya ɗaukanta mai amfani” Mami ta yi tsaki ta ce“zama da Idris ko ƙaddara! Yanzu mene ne abin yi?” Mommah ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“Ni da cewa nayi ko muje gidan Malam Barau a ɗan taya da addu'a Mami ko a samu a ganshi” Mami ta ɗan yi murmushi ta ce“idan har addu'a ce to kawai mu yi anan ni bana son harkar malaman nan” toh kawai Mommah ta ce parlon ya ɗauki shiru kowa da abin da yake sakawa cikin zuciyarsa. Mommy ce ta buɗe ƙofar ta shigo tana sanye da wani ubansu lace mai azabar kyau ɗinkin boubou ta ɗaura ɗankwalin lace ɗin ta yafa mayafi sai tashin ƙamshi take daka ganta ka ga matar manya. Har ta zauna akan sofa babu wanda ya ce wani abu ta yi murmushi tana kallon Mami ta ce“Afuwan hajiya sanda ki ka shigo ina wanka” sai a sannan Mami ta kalleta ta ce“Ai babu komai, Mun sameku lafiya?” Mommy ta ce“Lafiya Alhamdulillah ya yaran?” “Suna nan klao” Mami ta faɗa sai kuma ta yi shiru, jinjina kai Mommy ta yi ta maida idanunta kan Mommah wadda ta rame sosai kamar ba ita ba ta ce“daman zamu je gurin waɗanda aka kamo ne daga Kaduna, shi ne nace ko kema zaki je?” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“a'a ba zan je ba, bana son haɗuwa da kowa wallahi” Mommy ta yi shiru can kuma ta ce“Da dai kin daure mun je, kin ga ko wata tambayar ce kya yi musu” Mommah ta sake girgiza kanta ta ce“a'a fa kawai ku je, wallahi bana son ganin kowa, ko magana wahala take min” Mommy ta numfasa sai kuma ta ce“tom shikenan, Allah ya shige mana gaba sai mun dawo” “Amin, Allah ya tsare” Amin ta ce sannan ta nufi ƙofa, Sai da ta fita sannan Mami ta kalli Mommah ta ce“why ba zaki bi su ba?” “Mami bana son ganinsu, bana son ina tunawa da wasu abubuwan, babu wanda yanzu nake fatan nagani sama da Zayyad” Mami ta ce“Idan har kina son ganin Zayyad to tabbas zaki so ganin waɗanda suka gan shi, ko babu komai zaki tambayesu halin da yake ciki” Kallonta kawai Mommah ta yi amma bata ce komai. **** Kaduna, Unguwar rigasa. Ana idar da sallar isha'i aka ɗauren Salma da Zayyad akan sadaki naira dubu hamsin wanda Malam ya biya, koda suka dawo gidan tana zaune kan ladduma bayan ta idar da sallar isha, Malam ya sanya aka kirata tsakar gida, fitowa ta yi ta tsuguna muryata a sanyaye ta ce“Baba gani” Kallonta ya yi sai kuma ya ce“Alhamdulilahi, an ɗaura aurenki da Muhammad yanzun nan, ga kuma sadakin ki” ya miƙa mata kuɗin hannunsa. Hannunta na rawa ta amsa sai kuma ta sunkuyar da kanta, Malam ya sake cewa “Ku bari da safe sai ku tafi” Salma ta ɗago ta kalleshi, bata son musu dashi haka kuma bata jin zata iya kwana a cikin gidansa dan a kowane lokaci ana iya zuwa nemansu. Ta girgiza kanta muryarta na rawa ta ce“dan Allah Malam ka bari mu tafi yanzu, wallahi bana son sake kwana anan” Ganin yanda ta damu sosai ya sanya ya jinjina kansa ya ce“shikenan Ummulsalma, zan bari ku tafi amma bana so ku yi nesa damu sosai, yanda idan wani abun ya faru zan sani” Salma ta ce“Tom Baba, ina Yaya Zayyad ɗin?” “Yana waje, ki tashi ki je ki mata sallama sai ki zo ku tafi” Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta koma ɗakin Umma, Sallama ta yi mata da niyyar cewa gobe da safe zata dawo Umma ta ce“tom sai kin dawo ɗin, ki gaishesu” tom ta ce sannan ta juya ta fita tana jin wani iri. Bata samu malam a tsakar gidan ba dan haka kawai ta fice ƙofar gidan. Tsaye ta same shi da Zayyad yana yi masa duk da ba ganewa yake ba. Yana ganin ta fito ya juya ya kalleta ya ce“yanzu daga nan ina zaku je?” girgiza kanta ta yi ta ce“nima ban sani ba Baba, tunani nake” Malam ya ce“to idan haka ne zan haɗa ku da wani wanda ya san wajen gari sosai sai ya kama muku haya a can ku zauna” Salma ta ce“Tom Baba an gode Allah ya saka da Alkhairi” Ameen kawai ya ce sannan ya zaro wayarsa ya danna kira, bayan sun gama waya da mutumin ya ce masa gashi nan zuwa ya koma ya zauna yana kallonta ya ce“zauna kema” Gefe ɗaya ta samu ta zauna, ya yi gyaran murya ya ce“Ina son na tunatar da ke wasu abubuwane, Ummulsalma ki sani yanzu ke matar aure ce, matar auren kuma ga wanda bai san inda hankalinsa yake ba. Na aura miki shi ne saboda addini ya yarda idan har wanda zai yi auren ya ga ya yarda zai iya zama da ɗayan a haka, kamar yanda ki ka yarda zaki zauna dashi da haukansa. Dole ki gane akwai banbanci da wadda take auren mai hankali da kuma wadda take auren wanda bashi da hankali, duk da ina masa fatan samun lafiya nan kusa dan abubuwansa sun fara raguwa, amma ki sani dole sai kin yi haƙuri, dole sai kin jure, dole sai kin ɗauke kan ki akan abubuwa dayawa wanda zai aikata. Sannan duk da bashi da hankali wajibi ne a gareki ki yi masa biyayya kamar yanda addini ya bada umarnin mace tabi mijinta, nasan kina da halin kirki sannan kuma kina da sauƙin kai amma ki ƙara, ki zama macen kwarai ga mijinki, sannan har abada kada ki taba cewa zaki yi masa gori wannan shi ne babban abin da yake lalata zamantakewar aure, ki ɗauka duk abin da kika yi masa dolenki ne kuma haƙƙinsa ne da yake kan ki, Da haka nake miki fatan samun albarka a rayuwar aurenku, Allah ya fitar da ku daga matsalar da ku ka shiga, ya bashi lafiya” Cikin shassheƙar kuka Salma ta ce“Amin Malam, Mun gode sosai, Allah ya biya ka da gidan aljanna, in sha Allah ba zan taɓa yin abin da zai zama cutarwa a gare shi, zan zauna dashi komai tsanani kamar yanda na yi alƙawari” Ya jin jina kansa cikin jin daɗi ya ce“Allah yasa Ummusalma” Amin kawai ta ce sannan ta yi shiru tana tunani cikin ranta, Suna na zaune har wajen 8:30na dare sannan mutumin ya zo, bayan Malam ya yi masa bayani ya ce to su zo su tafi, Sallama suka sake yi da Malam ya rakosu har bakin titi sannan suka tsaida Napep tana ɗaga masa hannu, shima ya ɗaga mata hannun yana yi mata Allah ya tsare mai Napep ɗin ya ja motar, Zayyad ya dinga leƙen Malam fuskarsa a kwaɓe kamar zai fashe da kuka. **** Maitama, Abuja. “Wato mahaukaciya ma ka ɗaukeni ina maka magana ka yimin banza ko Farouk? Saboda kaga ina rabuwa da kai ya sanya ka ke min kallon wadda ban san me nake ba ko? Dan kaga na sakko da kaina ko?” Nimrah ta jera masa tambayoyin tana sakkowa daga stairs ɗin, Faruk ya tsaya cak yana kallonta amma bai ce komai ba ta sake cewa “Shikenan ka je kayi aurenka, ba dai aure bane kaje kayi amma na rantse maka da Allah sai dai ka sakeni yanzu kuma ba sai an jima ba. Wallahi sai dai ka sakeni Farouk! Ka sakeni na ce maka!” Ta ƙare maganar tana shaƙar kwalar rigarsa, Ban da kallonta babu abin da Faruk yake, dan shi gaba ɗaya lamarinta ma tausayi yake bashi. Ya janye hannunta daga jikinsa ya ce“bari mana Nimra, wane irin abu ne wannan?ke ba zaki taɓa barina na samu peace of mind ba kenan, kin dinga takurawa rayuwata kenan” “Takura, ai to bari kaji baka ga komai ba cikin abin da zan yi maka muddin ka ce sai kayi auren nan Faruk, wallahi ba zan bar ka ka samu kwanciyar hankali ba koda da na second ɗaya ne!” Girgiza kansa kawai ya yi sannan ya juya ya nufi hanyar main parlon, da gudu ta biyoshi ta riƙe masa riga cikin kuka ta ce“Dan girman Allah Faruk kar ka sake auren nan, ba gashi muna zaman lafiyarmu ba? Ba na daina duk abin da nake ba? Ka yi haƙuri ka bar maganar auren nan dan Allah” Sosai ta tashi tausayi ya kamo hannunta muryata a sanyaye kuma cikin nutsuwa ya cw“Nimra nima ba wai ina son dole-dole sai na ƙara aure bane, wallahi idan da a ce ta ni ne kin isheni daga nan har lahira, amma wannan auren umarnin Mama ne, kuma ba zan iya tsallake umarninta ba. Dan Allah ki tayani yin wannan aikin kin ji, kar ki sare min gwiwa, farin cikinki shi ne nawa Nimra!” Zare hannunta ta yi daga cikin nasa, ta girgiza kanta tana hawaye sai kawai ta koma sama da gudu tana kuka, da idanu kawai ya bita, ya sauke numfashi sannan ya juya ya fita. **** Tun da suka shiga gurin Mommy ke faman kai kawo har sai da aka ce su shiga su gansu, babban ɗaki ne mai ɗauke da sofa guda uku sai carpet da curtains. Maryam ta dinga kallon Mommah ganin yanda take kama da Zayyad sosai, ƙarasawa suka yi suka zauna kan sofa sojoji na tsaye a kansu. Mommy ce ta kallesu cike da masifa ta ce“Ku yanzu baku ji kunya ba? Aje har garinku a tawo daku saboda kun bawa masu laifi matsuguni, ban da ma rashin sanin abin da ya kamata ya za'a yi ku ga mace da mahaukaci sannan ku bar su a gidanku? Wannan sai dai idan daman can daku a haka haɗa baki aka haukata shi, bari General ɗin ya zo!” Tun da ta fara magana Mami ke kallonta amma bata ce uffan ba, Maryam kuwa kuka kawai take dan tasan shikenan ɗauresu za'a yi daga taimako, sai dai can ƙasan ranta tana fatan kada su Zayyad su shiga wani hali. Tashi Mommy ta yi tana kallon su Mommah ta ce“Ba zan iya ci gaba da zama cikin ɗakin nan ba, wallahi zuciyata zata iya tarwatsewa!” Daga haka juya ta fice kamar zata tashi sama, Mommah ta bita kallo sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. Tashi ta yi ta ƙarasa har gaban Maryam, ta zauna ta kamo hannunta cikin wata irin murya mai matuƙar rauni ta ce “Na san ke uwa ce, ko ba uwa ba ce ke mace ce, nasan kin san zafin rashin ɗa, na san kin san abin da mahaifiya ke ji a lokacin data rasa ɗanta. Bana iya bacci, bana iya cin abinci, bani da kwanciyar hankali, a koda yaushe tunanin halin da ɗana yake nake, zuciyata ta gagara samun sukuni. Da nace ba zan zo ba, amma Yayata ta yi insisting ɗina akan nazo. Tun da na ganki naji na samu gwarin gwuiwa, naji tamkar naga Zayyad, domin na san ba zaki faɗa min abin da ba shi ne ba. Dan Allah dan Annabi ki faɗa min ina Zayyad ya ke? Ina zan samu ɗana? Ki faɗa min dan Allah...” Maryam ta dinga kallon Mommah tana jin wani irin tausayinta, hawaye na zubowa akan fuskarta ta ce“ # HCD # Salma # Zayyad # Nanameera 08106608363.*HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 37-38: Her heart's last anchor Nanameera, YOTA/023 Arewabooks @Nanameera08 Malam ya dinga kallonts da mamaki sai kuma ya jinjina kansa ya ce“shikenan tun da haka ki ka zaɓa, ba zan raba ki dashi ba, Allah ya baku zaman lafiya, zan tafi, ta Yi gobe ki ganni idan Allah ya yarda” tashi Salma ta yi tana goge hawayenta ta ce“tom malam, Nagode Allah ya saka da Alkhairi ya ƙara girma” Amin kawai ya ce sannan ya nufi hanyar ƙofa yana ɗan jan carbin hannunsa. Salma ta bi shi da idanu har sannan hawaye bai bar zuba kan fuskarta ba. Sai da taga ya tafi sannan ta je ta rufe ƙofar ta koma cikin ɗakin, kwance ta same shi ya yi ruf da ciki, ta ƙarasa ta zauna gefen katifar muryarta na rawa ta ce “ka yi haƙuri Yaya Zayyad, in sha Allah zaka je ka ga Mommah nan kusa amma kawai ina tsoron a rabani da kai ne, bana son su ɗauke ka” Shiru ya yi mata duk da yana jin abin da take cewa, ta sunkuyar da kanta tana shessheƙar kuka ta ce“ni bana son na zauna ni kaɗai, bani da kowa yanzun sai kai idan suka tafi da kai shikenan ba zan sake ganinka ba. Kuma babu wanda na sani, sai dai na dinga rayuwata ni kaɗai, tsoro nake ji Yaya Zayyad” Ta ɗago ta sake kallon bayansa, ganin ba magana zai yi ba ya sanya ta tashi ta fice daga ɗakin ta koma nata ta zauna tana ci gaba da kukanta, sosai taji kewar Abbanta, taji kamar yau ne ya mutu ya bar ta, taji ina ma Umma Rahmatu bata siyar da gidansu ba su koma ta zauna, da a ce bata siyar da gidan ta ƙarasa tarwatsa ragowar rayuwarta ba da har yanzu suna zaune tare da daɗi ba daɗi, da Zayyad ba zai shigo rayuwarta ba, ballantana har a yi mata sharri mafi muni a rayuwa, da bata fara jin tana sonsa ba. Sai dai duk wadannan abubuwan ba laifinta bane, kaddarace ta zo mata a haka, kuma ta yi alƙawarin duk runtsi duk wahala zata zauna tare da Yaya Zayyad koda a ce shi baya sonta, zata zauna dashi kodan taimakon da ya yi mata, ba zata taɓa gazawa ba. Amma shi zai sota?? Salma ta tambayi kanta, sai kawai ta sake fashewa da wani sabon kukan ta kwanta kan simintin ɗakin ta ci gaba da rera kukanta. Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya turo ƙofar dakin ya shigo, zaune ya sameta kan ladduma tana sanye da hijabi da alama sallah ta idar. Ta dinga kallonsa har ya zauna ɗan nesa da ita, muryarta na rawa ta ce“Ko zaka ci abinci Yaya?” kamar ba zai magana ba sai kuma ya gyaɗa mata kai a hankali. Ajiye carbin hannunta ta yi ta tashi tana shirin fita daga ɗakin taji ya ce“Ni waina nakeso” juyowa ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce“wainar masa?” ya sake gyaɗa mata kamar dangin ƙadangaru, dawowa ta yi ta buɗe jakar da kayanta ke ciki, naira dubu daya ta ɗauka a kuɗin da malam ya bata ta juya tana kallonsa ta ce“tom bari naje na siyo maka” daga haka ta nufi ƙofa dan tasan ba amsawa zai yi ba. Koda ta je bakin titin kalle-kalle ta dinga yi ganin yau gurin kamar an sauya shi babu jama'a kodan sanyin da ake ne ya sanya dan ko unguwar ma babu tarin jama'a kamar da. Ƙarasawa ta yi bakinta ɗauke da sallama ta miƙawa yaron matar kudi, ba'a fi 2mins ba aka miƙo mata ledar wainar ta amsa sannan ta juya, tana fara shiga layin nasu taji horn ɗin mota, ganin yana shirin bigeta ya sanya ta ja ta tsaya, parking y yi a wajen ya fito yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce“afuwan na ɗan takura miki ko?” Salma ta kalleshi amma bata ce komai ba, Ya girgiza kansa ya ce“na ganki ne a wajen mai waina shi ne nace bari na zo mu gaisa Salma Candy” Da sauri ta kalleshi a ɗan tsorace ta ce“a ina ka san sunana?” “Salma kenan, sanin sunanki ba abu bane mai wahala, anan unguwar na san sunanki" Salma ta dinga kallonsa ba dan ta yarda da abin da ya ce ba dan ita ta san kaf unguwar nan babu wanda ya santa tun da babu gidan wanda take shiga, haka zalika kuma babu wanda ya san ana kiranta da Candy, suna tun na makaranta. Jin ta yi shiru ya sanya ya ce“kar na takura miki, idan babu damuwa ina son ki bani lambar wayarki sai mu yi magana, ko ki min izini na ƙarasa gidanku idan ya so sai mu yi magana” Wani irin kallon ka zama mahaukaci ta yi masa sannan ta taɓe baki cike da tsiwa ta ce“Su wadanda suka faɗa maka sunan nawa basu ce maka ni matar aure ba ce? To kar ka sake tsayar dani akan hanya, ni matar aure ce yanzu haka mijina yana gida shi ne ma ya aikeni” Aliyu ya ɗan yi murmushi sai kuma ya ce“yara ma sun iya ƙaryar cewa suna da aure? Ke Salma ke ce mai aure? To ai ko duk jikina kunnene ba zan taɓa yarda ba, kin ɗauka auren abun wasa ne? Shi mijin naki ne zai zauna a gida sannan ke ya aike ki da daddare, to idan har haka ne auren bashi da amfani yin sa, ballantana ma baki da wani aure amma nan ba da jimawa ba zaki yi shi in sha Allah” Harararsa Salma ta yi ta ce“Ba sai ka aure nin ba mu gani” Daga haka ta juya ta ci gaba da tafiyarta, ganin ya biyota ya sanya ta dinga wani irin sauri har sai da ta yi tuntube ta faɗi, ledar ta fadi gefe guda. Da sauri ya ƙaraso wajen yana kallonta ya ce“subhanallahi sannu kin ji, tashi” “Ba za'a tashi ɗin ba, ina ruwanka dani mugu kawai!” Ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, tsayawa ya yi yana kallonta sai kawai ya yi murmushi dan ba ƙaramin burgeshi ta yi ba, ta tashi ta ɗauke ledarta ta ci gaba da tafiya. Bin bayantan ya ci gaba da yi har sai da yaga taje ƙofar gidan, ta zaro key ta sakawa ƙofar. Shiru ya yi yana tunani, To ko dai da gaske matar auren ce? Girgiza kansa ya yi a fili ya ce “No impossible, ko da a ce haka ne ba zan bar ki ba, sai na mallakeki a matsayin mata Salma, ke ce irin matar dana daɗe ina nema, tabbas sai na mallakeki, ko da hakan na nufin zan sha wahala ba zan haƙura da ke ba!” Aliyu ya ƙare maganar idanunsa zube akanta har ta ƙarasa buɗe ƙofar gidan ta shiga ta kuma rufo ƙofar. Rufe gidan ta yi gaba ɗaya sannan ta nufi cikin dakin, zaune ta sami Zayyad a parlon ya yi jigum yana tunanin daya saba, ta ajiye ledar ta tsuguna tana ƙoƙarin kwancewa ta ce“Yaya ga wainar” kallonta kawai ya yi sai kuma ya zamo ya sakko ƙasa, ta tura masa robar gabansa sannan ta tashi ta shige kitchen, pure water ta ɗauko masa ta dawo ta ajiye masa gefe ta nemi can gefen kujera ta zauna. Zayyad ya dinga taunar wainar kamar magani bai fi rabi ya ci ba ya tashi ya ɗauka robar ya dire a gabanta sannan ya nufi hanyar ɗakinsa. Salma ta dinga kallon robar sai kuma ta juya ta ga babu shi babu alamunsa, sai kawai ta ɗauka dan daman bata ci abincin dare ba ta hau cin wainar, bayan ta gama ta maida robar kitchen ta wanke hannunta sannan ta dawo parlon, neman guri ta yi ta zauna can kuma ta tashi ta shiga ɗakinta ta kwanta. **** Kwaɓe fuska ya yi sannan ya ce“Mommah sai yanzu ki ka zo ki tafi dani?” gyaɗa masa kai ta yi kana ta ce“Eh Zayyad ka yi haƙuri da tafiyar da nayi na bar ka kaji, ba zan sake ba” ya marairaice fuska ya ce“To ni ai bana so na biki” “Baka son ka dinga ganina Zayyad?” Ya girgiza kansa ya ce“Ina so mana, to ai ke ce ki ka tafi dani, kuma ki ka bar ni” murmushi ta sake yi sannan ta ce“tom ka yi hakuri ba zan sake barin ka ba, tawo mu tafi” ta miƙo masa tafin hannunta. Kallonta ya yi ta ɗaga masa gira sai kawai ya ɗora nasa hannun, Sai dai tamkar walƙiya haka ya nemeta ya rasa s firgice kuma ya farka “Mommah! Mommah!” Ya dinga kallon dakin da mamaki, tashi tsaye ya yi sai kuma ya nufi ƙofa, zaune ya hangeta ta ɗora kanta jikin kujera tana bacci, ya ƙarasa muryarsa na rawa ya ce“Salma! Salma!” Cikin magagin bacci ta buɗe idanunta, ta ɗago kanta ta kalleshi da idanunta da basu gama buɗewa ba ta ce“Yaya mene ne?” “Gida zan je, ina son naje gida Salma, wajen Mommah zan je, ina son naje na ganta, ina son ganin Daddy, ki zo mu tafi gida kin ji” Bata san sanda ta miƙe tsaye ba tana kallonsa ta ce“Yaya meya faru? Kasan me ka ke faɗa kuwa?” Jinjina mata kai ya yi sannan ya ce“Nasani mana, ni ba mahaukaci bane, I'm Zayyad B. Musa, na gane wane ni fa, ki zo mu tafi gida” Matsawa ta yi daga kusa da shi tana girgiza kanta ta ce“A'a wallahi ba zan yarda ba, ba kai bane, kai Yaya yad ɗina ne, ba kai ne wancan Zayyad ɗin ba, ba zan yarda da kai ba” Kallonta Zayyad ya dinga yi da mamaki, ganin yanda ta ruɗe ya sanya ya ce“Ke baki gane ni bane? Ni ne fa Zayyad, ina son naje gida” Fashewa ta yi da kuka tana ci gaba da kallonsa ita ma ta ce“a'a ban gane ka ba, ba kuma zan taɓa ganeka ba, sai safiya ta yi na kira malam sannan” daga haka ta shige ɗakinta da gudu ta rufo ƙofa, daman tsautsayi ne ya sanya ta sake fitowa. Ƙarasowa ya yi ya dinga buga ƙofar yana kiran sunanta amma sam taƙi buɗe masa, gudun kada ya ɓalla ƙofar ya sanya ya koma ya zauna kan kujera yana tunanin abubuwa dayawa, wane irin mugun mafarki ne wannan ya yi?? Ya girgiza kansa sai kuma ya tashi ya koma ɗakin da yake, banɗaki ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito nan parlon ya fara gabatar da sallar nafila. Gari na fara wayewa ya tashi ya koma jikin ƙofar ya ɗan buga a hankali ya ce“Salma! Salma ki buɗe ƙofar kin ji” Salma ta sake takure jikinta a ƙarshen ɗakin tana shessheƙar kuka a hankali, ya fi 5mins yana kiran sunanta amma bata amsa ba, sai kawai ya bar wajen ya koma yana shirin zama a kujera pillow ya fado ƙasa, ɗaukoshi ya yi yana shirin mayarwa yaga wani bunch of keys ya kai hannunsa ya ɗauka, da sauri ya juya ya koma jikin ƙofar ya zura key guda ɗaya cikin Sa'a kuwa yana murɗawa kofar ta bude, Zabura ta yi ganin ya shigo ta tashi tsaye tana girgiza kanta ta ce“kak...ka bari...ka bari ba kai bane, ni ba kai nake so ba! Sai naje na faɗawa Malam” Daga haka ta tawo da sauri tana shirin ficewa ta gefensa, hannu ɗaya ya sanya ya jawota, ganin tana ƙoƙarin zamewa ya sanya ya riƙeta tsam a ƙirjinsa, ƙoƙarin kwacewa ta shiga yi amma sam ta saka samun damar haka sai kawai ta fashe da wani raunataccen kuka ta yi luf a ƙirjinsa, shiru ya yi yana sauraren yanda take kuka kamar ranta zai fita, ya dinga patting bayanta a hankali har sai da yaga ta fara yin shiru, ɗago fuskarta ya yi yana kallonta ya ce“Ya isa haka, tare zamu je wajen Malam ɗin” Salma janye jikinta ta yi daga nasa ta fice daga dakin da sauri, ganin haka ya sanya Zayyad yabi bayanta shima.. A tsakar gida ya sameta ta tsaya sai kuka take, tsayawar shima ya yi ɗan nesa da ita, ya zuba mata idanu hannayensa harɗea ƙirjinsa. Ganin ba shiru zata yi ba ya sanya ya koma cikin gidan ya rabu da ita, Around 9am ya fito sanye cikin wasu English wears onion colour ya ɗora rigar sanyi a kai dan ba ƙaramin sanyi aka tashi dashi ba. Tsaye ya sameta har sannan sai rawar sanyi take, Muryarsa a nutse ya ce “ki zo ki yi wanka sai muje gidan Malam ɗin” juyowa ta yi ta kalleshi da fuskarta wadda tayi kaca-kaca da hawaye sai kuma ta ce“Ni ba wanka zan yi” Shiru y yi yana kallonta kafin ya numfasa ya ce“shikenan muje” daga haka ya ƙaraso wajen ya sanya key ya fara unlocking ƙofar gidan, takalmanta kawai ta zura sannan tabi bayansa dan har ya fita daga gidan, ya mayar da ƙofar gidan ya rufe sannan kalleta ganin yanda ta tsaya ya ce“muje mana” Gaba ta yi yana bin ta a baya har suka je bakin titi, da kansa ya tsayar da mai Napep ɗin ya ce ta faɗa masa unguwar dan bai sani ba, suka yi ciniki dashi sannan suka shiga. Har suka je gidan babu wanda ya ce da wani uffan a tsakaninsu, Da kanta ta shiga har cikin gidan bayan ta yi sallama Umma ta samu tsaye tana kwashe kaya ta gaisheta sannan ta ce“Baba baya nan?” Umma ta ce“a'a yana nan kin san yau ana sanyi ne, to yana cikin ɗakin soro” Tom kawai Salma ta ce sannan ta juya jiki a sanyaye ta nufi soron, bakinta ɗauke da sallama ta shiga ɗakin. Malam na zaune kan carpet yana jan carbi, yana ganinta ya gyara zamansa da mamaki ya ce“Ummulsalma ke ce da safiyar nan?” “Eh Baba, Da Yaya Zayyad muka zo” Salma ta yi maganar a sanyaye, ɗan leƙa bayanta Malam ya yi sannan ya ce“ina yake?” “Yana waje bari na kira shi” Tom kawai Malam ya ce ta tashi ta fita, after 1min suna dawo tare, tun da ya shigo malam ke kallonsa ya nemi gefe ɗaya ya zauna cikin kamilallyar muryarsa ya ce“Malam ina kwana?” Malam ya kalleshi sai kuma ya kalli Salma, Ta gyaɗa masa kai muryata na rawa kamar mai shirin fashewa da wani sabon kukan ta ce“Malam ba Yaya Zayyad ɗina bane, bashi bane, ya sauya malam. So yake ya tafi ya barni malam, baya sona!”girgiza kai Malam ya yi ya ce“Ya isa haka tashi ki je gida” bata sake cewa komai ba ta tashi ta fice daga ɗakin, Zayyad ya bita da kallo sai kuma ya ɗauke idanunsa. Malam ya ɗan yi shiru na wasu sakwanni kafin ya ce“Zayyad!” “Na'am Baba” Malam ya jinjina kansa ya ce“Alhamdulilahi, Allah alhakamu, Allah ya ƙara maka lafiya” Zayyad ya kalleshi ya ce“Amin malam, amma dan Allah meya faru? Nayi wani mafarki mai ban tsoro, a cikin mafarkin na sanka kuma dana tashi sai naga duk abin da yake cikin mafarkin akwai shi a zahiri, da gaske ba'a Abuja nake ba, ina son naje naga Mommah” Malam ya Girgiza kansa sannan ya ce“Allah sarki, wato Zayyad duk abin da ka gani cikin mafarkinka ba haka bane, a zahiri ya kasance babu wani ruɗani” Ya dinga kallon Malam kamar idanunsa zasu fito kafin ya ce“da gaske ne nayi hauka malam? Duk abubuwan da suka faru gaskiya ne kenan?” jinjina masa kai Malam ya yi ya ce“wannan haka yake, amma yanzu tun da ka dawo hayyacinka to Alhamdulillahi daman shi ne abin da muke fata kuma ya tabbata, sai ka dage da addu'a domin duk wannan sharrin shaidanu ne, ba dan ma kana da riƙon addini ba da Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru” Hawaye ne suka shiga sintiri kan fuskarsa, bakinsa na rawa ya ce“D...da gaske na bar iyayena malam?” gyaɗa masa kai kawai ya yi, Zayyad ya ce“ina son naje gida, ina son na tafi malam, tafiya zan yi, Ina son naga Mommah da Daddyn, na san hankalinsu ya yi matuƙar tashi, tafiya zan yi Malam” Malam ya yi shiru can kuma ya ce“Tabbas kana da bukatar ka tafi Zayyad, domin iyaye daɗi garesu, kodan a sako su Maryama ma zan so ace ka koma a gida, amma ita Salma ina tsoron zuwanta can saboda kada su cutar da ita” Zayyad ya ce“Salma, ai ba da ita zan tafi ba Malam, kawai tafiya zan yi ni kaɗai, ku zauna da ita idan ya so duk abin da kama sai na dinga aikowa dashi daman Daddy ba son zamanta yake acan ba” Da mamaki Malam yake kallonsa sai kuma yace“A'a Zayyad, matarka ce ita, saboda haka duk in da zaka je ka tafi tare da ita, kuma ka kareta kamar yanda ta kare ka, ka kula da ita kamar yanda ta kula da kai, ko da a ce iyayenka sun nemi su ɓata mata kai ne zaka nuna musu muhimmancinta a gareka, idan har suna son ka to ba zasu ƙi ta ba” Shima Zayyad kallon mamaki ya dinga yiwa Malam kafin ya ce“ai ba matata ba ce Malam, kawai dai na ganta a hanya ne tana neman taimako na taimaketa shi ne na kai ta gidanmu har haka ta faru, babu aure tsakanina da ita, ni an saka min ranar Aure da ƴar abokin Daddyna” Malam ya Girgiza kansa ya ce“Ashsha mantawa nayi ban faɗa maka ba, domin ta zauna tare da kai bata son wani abun ya sameka ta yarda ta aureka a haka ni ne wanda na biya sadakin” “Aure kuma? Da Salma ɗin? Wannan yarinyar Malam?” Jinjina masa kai Malam ya yi, Zayyad ya girgiza kansa ya ce“a'a malam, Salma ta yi yarinta da aure, ba zan iya aurenta ba” “Amma ita ta aureka Zayyad kuma dole ka zauna da ita” Malam ya yi maganar in a serious tone. Sunkuyar da kai Zayyad ya yi dan yana ganin girman Malam sosai, Malam ya ce“Ko da wasa ka da ka taɓa cewa zaka rabu da yarinyar nan, domin ita ɗin ƙaddararka ce, tana sonka duk da yarintar ta, kar ka ce zaka watsa mata ƙasa a ido dan girman Allah Muhammad” Shiru Zayyad ya yi duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi ya ɗago kansa yana kallon Malam ya ce“In sha Allah ba zan barta ba. Amma ina ga ta zauna anan idan naje sai na dawo na ɗauketa” Malam ya ce“wannan ma ba wani abun bane, amma koda zaka tafi to ba wannan satin ba Zayyad, inason ka zauna da ita ka fahimceta. Sannan ka sanar da ita da kanka cewa zaka dawo ka ɗauketa, domin tun jiya da na fahimci samun sauƙinka nace zaka koma gida take kuka, kada ka tafi yanzu ka bar ta” Shiru ya yi yana nazarin kalaman Malam can kuma ya sauke numfashi ya ce“tom in sha Allah duk yanda ka ce hakan za'a yi Malam” Murmushin jin dadi ya yi ya ce“Yawwa Allah ya yi maka albarka, Amin” Da Amin shima ya amsa sannan Malam ya sake cewa“Muje ciki ka gaida matan gidan” Toh ya ce sannan ya miƙe ya fito daga dakin malam na biye dashi suka shiga cikin gidan. Farin ciki ba kaɗan ba Umma tayi da samun lafiyarsa, bayan sun gama gaisawa suka koma ɗaki aka kawo musu abin karin kumallo, Salma kuwa zama tayi kamar mara lafiya sai kwnaciya ko abinci ta ƙi ci.. **** Abuja. Mommah ta yi murmushi tana kallon Maryam ta ce“Dan Allah da zarar kun sauka ki kirani” Maryam ta gyaɗa kanta tana cewa “Tom Mommah, in sha Allah muna sauka zaki ji waya” jin jina kanta ta yi sannan ta kalli Hashim dake riƙe da Khalil ta ce“A sauka lafiya to” Murmushi ya yi sannan ya ce“Mun gode sosai Allah ya saka da Alkhairi ya ƙara girma” Mommah ta ce Amin tana kallon Khalil ta ce masa“Ko zaka zauna anan?” girgiza kansa ya yi ya ce“gida zan tafi” Mommah ta ce“ai shikenan na daina baka sweet” ɗan murmushi yaron ya yi sannan ya ce“ai nasan zaki bani saboda kina da kirki sosai” duka suka yi dariya, Suna nan tsaye har aka fara sanarwa cewa jirgi zai tashi, Maryam ta kalleta ta ce“Tom Mommah sai Allah ya sake haɗamu” “Kar ki manta Maryama” “Har abada mommah” Daga haka suka juya suka nufi cikin jirgin tana ɗaga musu hannu, sai da ta daina hangosu sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta koma in da suka yi parking motoci sojoji na biye da ita, basu bar cikin airport ɗin ba har sai jirginsu Maryam ya tashi i zuwa Kaduna, Mommah ta sauke numfashi tana yi musu addu'ar samun nasara, kafin drivern ta ya ja motar suka bar cikin airport ɗin gaba ɗaya. _Sauran kaɗan fa book 1 ya ƙare, make ur payment mana ,7041901078 Hauwa Adamu lawan opay evidence via 08106608363 Nanameera_ # HCD # Salma # Zayyad # Nanameera 08106608363 *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 35-36: When healing meant separation Nanameera, YOTA/023. “Tabbas Mama naga Zayyad, kuma na zauna tare dasu, amma yanzu ban san inda suke ba. Domin na tabbata Salma idan taji an ce an zo an tafi damu to baza bari su ci gaba da zama ba. Mama da gaske kina son Zayyad kuma? Domin ban ga alamun wannan soyyayar a tare dashi ba” Mommah ta dinga kallon Maryam, can kuma ta ce“ina sonsa mana, shi ɗin ɗana ne, akan me ba zan so shi ba? Babu wanda ya kai ni son shi duk duniya” Maryam ta girgiza tana ɗan murmushi ta ce“amma kina son shi ki ka bari aka lalata rayuwarsa? Kina son shi ki ka bari aka koreshi daga gidan ubansa? Mama duk da ban san wasu abubuwan ba amma na tabbata akwai abin da ba daidai ba cikin rayuwarsa, wallahi Mama akwai sakaci cikin lalacewar rayuwarsa, akwai rashin kula daga wajen iyayensa. Domin naga hakan a tare dashi” Mommah fashewa ta yi da kuka, Maryam ta dafata itama tana hawaye ta ce“amma ki yi haƙuri idan na ɓata miki rai Mama, a tare da Zayyad babu kulawa daga iyaye, musamman mahaifiya” Tashi tsaye Mommah ta yi tana tafiya a hankali, muryarta cike da damuwa ta ce“nagaza! Ban kula dashi yanda ya kamata ba, ashe kowa nagane bani na haifeshi ba. Ya zan yi? Kaddara ta sanya na auri Idris da badan haka ba babu abin da zai samu rayuwarsa...” Mami ce ta rufe mata baki tana girgiza mata kai, fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikin Mami tana cewa“nagaza Mami, Yaya Jiddah ba zata yafe min ba. Ba haka ta rainemu ba Mami, bai dace a ce na bar ɗanta ya shiga wani hali ba a rayuwa. Amma na kasa tsawatarwa, ya zan yi Mami? Ya zan yi...” Ta kasa ƙarasawa saboda kukan da yaci ƙarfinta, Maryam dake zaune ta kalli Hashim da mamaki dan bata gane inda zancen nasu ya dosa ba. Kenan ba ita ce mahaifiyarsa ba?, Ganin yanda take kuka ya sanya ta miƙe ta ƙarasa gabanta, Dafata ta yi tana jikin Mami ta ce “Ki yi haƙuri, ban san haka ba da ba zan yi maganar ba, nayi tunanin kece ki ka haifeshi, ashe ba haka bane. Ki yi haƙuri dan Allah” Mommah ta ɗago fuskarta wadda hawaye ya gama wanketa ta ce“babu abin bani haƙuri, kin faɗi gaskiya, gaskiyar dana daɗe ban ji an faɗa min ba, kin ganar dani abin da na daɗe ina tunaninsa, tabbas ban yi kama da mahaifiyarsa ba” ta maida idanunta kan Mami ta ci gaba da fad'in “Da nasan haka zai faru, dana bari kin riƙe shi a lokacin da ki ka nema. Sai dai nayi tunanin idan muka haɗu dani da ƙanin mahaifinsa zamu fi kasance iyaye gare shi, ashe ba haka bane. General ya lalata komai, yayinda ni kuma na taya shi, mun yi tunanin nuna masa soyyaya shi ne abin da zai saka ya ɗauka mune iyayensa na asali, saboda haka muka fifitashi fiye da kowa, bama son ɓacin ransa. Sai dai ashe ba haka bane, ashe makamin tarwatsa rayuwarsa muka ɗauka, a lokacin dana fara gane haka nayi kokarin fahimtar da General sai dai sam yaƙi saurarata ya ci gaba da yi masa duk abin da yake so, koda a ce abun ba shine mafi dacewa dashi ba. Duk da nakasa sakawa a daidaita rayuwarsa amma ina taya shi da addu'a, wallahi ban so rayuwar Zayyad ta kasance a haka ba, ban so hakan ba!” Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye na biyo fuskarta. Girgiza kai Mami ta yi ta ce“Baki da laifi Khadijah, kin yi iya bakin ƙoƙarinki, wannan abin da ya faru kaddara ce. Kuma idan da wanda yake da laifi to general ne bake ba, ki daina ɗaurawa kan ki abin da baki aikata ba. Kin so Zayyad ba kaɗan ba, kin kula dashi a lokacin da yake karkashin kulawarki. Duk abin da ya faru ya faru ne a sanda ya fara girma, dan haka ba laifinki bane” Mommah ta sanya hannunta ta goge hawayen da yake ƙoƙarin sakkowa wuyanta ta ce“amma ai Mami kowa laifina yake gani, babu yanda za'a yi na goge wannan tunanin daga zuciyoyin mutane” “Ko kaɗan babu wanda zai zargeki, wannan laifin namu ne duka, kowanenmu yana da alhaki akan abin da ya faru. Jiddah bata cancanci haka ba, soyyaya ta rufe mana idanu mun kasa fahimtar abin da ya kamata mu yiwa Zayyad, mun cutar da rayuwarsa ta hanyar da bamu fahimci hakan ba, ki daina cewa ke kaɗai ki ka yi Khadijah kowa yana da nasa laifin!” Mommy ta ƙarasa maganar tana shigowa cikin ɗakin, da mamaki suka dinga kallonta dan babu wanda ya yi tsammanin shigowar Tata, ta ƙaraso gabansu ta dafa Mommah tana hawaye ta ce“wannan duk laifinmu ne, ba iya ke kaɗai ba, nima tamkar mahaifiyarsa ce, ina son Zayyad yanda ba'a tsammani, wallahi ko bacci bana iya yi” Kuka sosai suka dinga yi, dakyar Mami ta basu haƙuri suka yi shiru, Maryam ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mommah ta ce “Ki daina kuka Mama, nayi miki alƙawarin dawo miki da Zayyad gida, idan har Allah ya hukunta komawata gida. Na tabbata ba zasu yi nisa damu ba, ni kuma zan dawo dashi gareki a kowane irin hali” Da sauri Mommah ta kalleta, ta kama hannunta bakinta na rawa ta ce“Da..da gaske za ki dawo min dashi? Da gaske Zayyad zai dawo gida? Ina son na ganshi” Maryam ta ɗora nata hannun a saman nata ta gyada mata kai ta ce“Nayi miki wannan alƙawarin Mommah, zan dawo miki da Zayyad har gida” Da sauri Mommah ta rungumeta ta ɗago sannan ta ce“Idan ki ka min haka ba ƙaramin daɗi zan ji ba. Dan Allah ki dawo min dashi” Maryam ta ce“In sha Allah Mama, da zarar an sake mu zan dawo miki da Zayyad” “Yanzu zan yiwa general magana a sake ku” Mommy ce ta yi saurin cewa“Idan an gama bincike kenan” Kallonta kawai Mommah ta yi amma bata ce komai ba. Mami ta ce“Muje to” dakyar Mommah ta saki hannn Maryam tana juyowa suka fice daga ɗakin, sojojin suka sake shigowa. **** Ƙarfe 9:00 na dare suka shiga cikin gidan, Salma ta dinga kallon ko ina na gidan, parlon ne guda ɗaya a ciki da kitchen da banɗaki sai bedroom guda biyu a ciki, gidan da haske dan akwai wuta a unguwar. Ya kalleta ya ce“to ni zan koma, duk yanda ake ciki zaki jini” Toh kawai Salma ta ce, ya juya ya fita. Hannun Zayyad ta riƙe tana cewa “Yaya yad muje ciki” kallonta ya yi sai kuma ya kwace hannunsa ya shiga cikin parlon. Zama ya yi kan kujera ya zuba uban tagumi, koda Salma ta shigo kallonsa ta dinga yi kafin ta ce“Ka tashi ka shiga ciki kaji, zan je na siyo mana abinci” ko kallonta bai yi ba ballantana ta saka ran da yaji abin da ta ce, Salma ta yi shiru sai kuma ta ajiye ledojin hannunta ta juya ta fita. Sai da ta saka key ya wajen gidan sannan ta nufi hanyar titin da suka biyo dan wajen akwai tarin kantina a wajen, koda ta zo babban titin tsayawa ta yi tana kallon tarin motocin dake shigewa, ta yi shiru tana tunanin abin da zata siya masu, juyawa ta yi ta hango wata mata tana suyar wainar masa, wajen an cika sosai da motoci. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nufi wajen direct. Ganin tarin maza a wajen ya sanya ta tsaya daga baya tana leƙensu, tana nan tsaye har bayan 5mins sai taga wani yaro ya zo gabanta yana miƙa mata ledar ya ce “wai gashi” Kallon ledar ta yi sai kuma ta kalli yaron ta ce“mene wannan ɗin?” “wancan ne ya ce a kawo miki” Ya faɗa yana nuna mata wajen wata mota glk white colour, matashin saurayi ne da ba zai shige 34yrs ba tsaye jikin wata glk white colour, yana sanye da wata dakkakiyar shadda milk colour ya ɗora hula akansa, idanunsa maƙale cikin shade glasses. Salma ta kalli wajen sai kuma ta kalleshi ta ce“to ai ni ban siya ba, ka mayar masa” daga haka ta matsa daga wajen, ganin mutanen sun ragu yasa ta ƙarasa wajen, matar tana ganinta ta amshi kuɗin ta zuba mata dan daman tun ɗazu take ganinta. A wata roba ta zuba mata sannan ta saka a leda ta miƙa mata, Salma ta amsa sannan ta juya ta bar wajen ba tare da ta sake kallon inda mutumin yake ba. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidan taji an ce“da kin bani minti ɗaya domin nayi miki magana” Da mamaki ta juyo tana kallon wanda ke mata maganar, wannan mutumin ne na wajen mai sai da waina, ta dinga kallonsa amma ba ta ce komai ba. Ya ɗan gyara tsaiwarsa yana murmushi ya ce“Sunana Dr Aliyu Ahmad, ko zan san naki sunan?” Salma ta dinga kallonsa kamar ta samu tv sai kuma ta ce“Sannu amma ni matar aure ce” daga haka ta juya ta ƙarasa murɗa key ɗin ta shige gidan ta rufo ƙofar. Aliyu ya dinga kallon ƙofar sai kuma ya yi murmushi wanda ya fitar da asalin kyansa ya jinjina kai ya ce“okay” Sannan ya juya ya shige motarsa. Koda Salma ta shiga tsayawa ta yi jikin ƙofar ra dinga sauke wani wahalallen numfashi dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Above 2mins kafin ta ɗaga ƙafarta ta ci gaba da tafiya. Zaune ta sami Zayyad in da ta bar shi, ta ƙarasa ta ajiye ledar tana kallonsa ta ce“Har yanzu baka tashi ba Yaya?” ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake ɗauke kai, ta ɗan yi murmushi ta ce“sauko mu ci abinci” Buɗe robar ta yi dan babu faranti a gidan, ta zauna tana kallonsa ganin ko motsi bai yi ba ta ce“ka sauko mana" ta ƙare maganar kamar zata fashe da kuka, saukowa ya yi ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa. Ta tura masa robar ta ce“kaci sai ka rage min” taɓe bakinsa ya yi sai kuma ya tura mata robar yana harararta, murmushi Salma ta yi ta ce“just eat, idan ka ƙoshi sai nima naci” Banza Zayyad ya yi mata bayan 2mins ta ce“to idan ba zaka ci ba sai na cinye na barka” daga haka ta yi bismillah ta fara gutsurar wainar ta dangwali miyar har ta kai wajen bakinta sai kuma ta miƙo masa tana cewa “ka ci” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ture hannunta, ya sanya hannunsa ya dauki wainar ya saka a bakinsa ba tare da ya dangwali miyar ba. Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta saka wadda ta gutsura a bakinta ta shiga taunawa a hankali. Haka ua dinga cin wainar ba tare da miya ba har suka cinye. Salma ta ɗauke robar ta kai kitchen ɗin sannan ta fito tana kallonsa ta ce“tashi kaje ka kwanta Yaya Zayyad” Ko musu bai yi mata ba ya tashi ya nufi inda yake ganin kamar ɗaki ne ya shiga, katifa ce kawai a dakin ya yi kwanciyarsa a kai ba tare da ya lura da wani abun ba. After 2mins Salma ta shigo ɗakin, kallonsa ta dinga yi ganin har bacci ya ɗaukeshi sai kawai ta yi murmushi ta juya ta fita. Ɗaya ɗakin ta shiga babu komai shi a ciki, ta shimfiɗa ɗankwalin kanta ta yi kwanciyarta sai dai sam bacci yaƙi zuwa idanunta, ta dinga tunanin irin rayuwar da zasu yi yanzu. Washegari around 9am ta fito tsakar gidan ta hangeshi zaune ya yi tagumi, jiki a sanyaye ta ƙarasa wajen dan ta fuskanci kwana biyun nan gaba ɗaya ya sauya, baya magana, kuma ba zai yi abu irin na mahaukata ba sannan ba zai kula kowa ba. Salma ta dafashi ta ce“Yaya Zayyad” ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya sake ɗauke kansa, ta tsuguna gabansa fuskarta cike da damuwa ta ce“Ka faɗa min me aka yi maka Yaya yad ɗina? Ko ni ce?” taɓe baki ya yi, sai kuma ya ce“Mommah gida zani” Ji tayi jikinta ya yi wani irin sanyi, ta ɗan yi shiru ta haɗa nutsuwarta sannan ta ce“to zan kai ka, bari naje na siyo mana abinci” “Zan biki” Ya yi maganar kamar ƙaramin yaro, murmushi ta yi ta miƙo masa hannunta, kamawa ya yi ya miƙe ta ce“muje to” ya ɗan yi murmushi sannan suka fita daga gidan. **** Sai kusan azahar sannan suka dawo gidan, ta kalli Zayyad wanda yake rike da ledoji ta ce“muje ka tayani aikin” bai ce komai ba ya ƙarasa parlon ya dire ledojin. Ajiye nata ta yi itama sannan ta ce“muje kitchen na zuba kayan sai mu dafa abinci” “Ni nagaji” Ya faɗa yana zama a ƙasa, murmushi kawai ta yi ta ce“tom bari nayi da kaina tunda ba zaka tayani ba” daga haka ta fara ɗiban ledojin tana shigewa dasu, ya dinga bin ta da kallo daga ƙarshe ya nemi waje ya kwanta.. Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin gidan har na tsawon wata guda, zuwa sannan abubuwan Zayyad sun yi sauƙi sosai, ko kaɗan baya Abu irin na mahaukata. Haka zalika kuma baya yin irin na masu hankali, babu abin da yake sai dai ya ci abinci ya kuma kwanta. Amma kullum cikin kiran Mommah yake, idan abun ya motsa sai ya daina kulata, ranar daya bushi iska kuma ya yi mata magana, kuma har zuwa sannan General bai saki su Maryam ba, sai dai sun yi sabo mai yawa dasu Mommah dan kusan kullum sai ta zo ta gansu. Biyoshi ta yi ganin yana shirin fita ta ce“magana fa nake yi” Juyowa ya yi ya kalleta sai kuma ya ce“mene ne kuma? Me ki ke so yanzun?” “so nake ka saki yaran nan daka kamosu, basu da wani laifi, kuma basu san inda Zayyad yake ba” Wani kallo General ya yi mata sai kuma ya ce“kuma kawai dan sun ce haka sai na sake su ko? Wai Khadijah me ki ka ɗauki Zayyad ne? To bari ki ji ni ba zan bari wani abun ya sameshi a banza ba” “Mene ne abun da zai same shin bayan wanda ya same shi? Kamata ya yi ka mayar da hankali akan nemansa ba wai ka tsaya kana kamo mutanen da aka ce maka sun ganshi ba. Dan Allah ka sake su, idan ya so sai a haɗa baki dasu idan sun sake zuwa inda suke a rike su har kazo” General ya yi shiru yana nazarin maganarta can kuma ya ce“ina da abun yi yanzu, idan na dawo sai muyi maganar” numfasawa ta yi dan taga alamar zai iya yarda ta ce“tom shikenan Allah ya dawo da kai lafiya” Ameen ya ce sannan ya sauka daga stairs ɗin, Momma ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai a fili ta ce“Allah ka bayyana shi” **** Salma ta dinga kallonsa ganin yanda yake shan rubutun ta ce“Yaya yau kuma ji ka ke da shan maganin?” harararta ya yi ya ce“Na kula ki?” murmushi ta yi tana ɗauraye kayan ta ce“ba ruwana” ko kallonta bai yi ba sai da ya shanye rubutun jarkar tas. Ya tashi ya koma ciki ba tare da ya ce mata komai, ita ma bata sake bi ta kansa ba ta ci gaba da wankin da take har ta kammala. Zaune ta sameshi kan kujera ya yi shiru kamar mai tunani, ta girgiza kanta sannan ta ce“tunanin me ka ke yi?” ta ƙare maganar tana zama a ƙasan kujerar da yake. Shiru ya yi mata, ta ɗago daradaran idanunta tana kallonsa ta ce “Ka faɗa min abin da ya dameka, dan Allah Yaya Zayyad ka daina wannan damuwar. Bana son ganinka cikin damuwa kaji” Ba zaka taɓa cewa da Zayyad take ba, Sai kawai ta fashe da kuka. Kallonta ya dinga yi amma bai ce mata komai ba, ta tashi ta nufi hanyar daƙinta. Koda ta shiga ɗakin faɗawa kan katifa ta yi ta fashe da wani sabon kukan, da gaske Zayyad bai damu da ita ba, amma ita ta damu dashi fiye da komai a yanzun. Sai da aka kira sallahr la'asar sannan ta fito daga ɗakin, bata same shi a parlon ba, kuma bata damu ta ganshi ba. Kawai ta nufi cikin kitchen, spaghetti ta ɗauko guda ɗaya ta ɗauko tukunya ƙarama ta fito tsakar gida, ɗan ƙaramin kurfotin dake tsakar gidan ta kunna sannan ta ɗora ruwa ta koma ciki. After 20mins ta fito ta samu ruwan ya tafasa ta kakkarya taliyar ta zuba sannan ta nemi waje ta zauna, sai da taliyar ta dahu sannan ta tace ta ɗauka ta koma kitchen. Taliyar ta zuba ta saka manja ta ɗauko robar yajin ta dawo parlon. Ko loma biyu bata yi ba y shigo ta kalleshi ta ce“Yaya na zubo maka abincin?” Shiru yayi mata, ta tashi ta shige kitchen ɗin. Bata jima ba ta fito hannunta riƙe da wani plate ɗin ta ajiye a gabansa sannan ta koma ta zauna ta ci gaba da cin nata. Har ta gama ci bai ɗauki abincin ba, ta mai da plate ɗin kitchen sannan ta fito tana kallonsa ta ce“Ko baka son wannan?” “Mommah zani” Girgiza kanta ta yi ta ce“Ba nace zan kai ka ba? Ka zauna ka ci abincin amma” tashi ya yi ya shige ɗaki ba tare da ya ce komai ba. Salma ta bi shi da kallo hawaye na zubowa kan fuskarta. Ɗaki ta shiga ta ɗauko hijabinta ta saka ta fice daga gidan tana kuka. Unguwar rigasa ta nufa, zaune ta hangi Malam kan ladduma da ɗalibai a gabansa suna ɗaukan karatu. Tsayawa ta yi ɗan nesa dasu ta rufe fuskarta da hijabinta tana kuka. Tasowa Malam ya yi dan ya ganeta ya kalleta ya ce“Ummulsalma lafiya?” cikin kuka ta ce“Yaya Zayyad ne Malam, ka zo muje ka gan shi dan Allah” ta ƙare maganar tana sake fashewa da wani kukan. Malam ya ce“subhanallahi, menene ya same shi?” “Baba ka zo muje ka gani da kan ka dan Allah” Shiru ya yi sai kuma ya ce“shikenan muje” daga haka ta yi gaba yana biye da ita. Bakinsa dauke da sallama ya shigo parlon, ta kalleshi ta ce“yana cikin ɗaki malam” tom kawai ya ce sannan ya nufi ɗakin, ƙararin numfashinsa yaji ya sanya ya ƙarasa da sauri yana kallonsa ya ce “Muhammad! Muhammad!” Kasa magana Zayyad ya yi saboda yanda numfashinsa ke hawa da sauka, tsugunawa ya yi ya dafa shi ya ce“me yake damunka Muhammad?” muryarsa na rawa ya ce“Ba...Baba... Momma! Mommah Baba” Salma dake tsaye bakin ƙofa ta fashe da kuka tana kallonsu ta ce“ka gani ko malam, kullum haka yake cemin. Kullum baya kulani, sai ya dinga cemin zai tafi ya bar ni, malam ka gani dai a gabanka, Yaya Zayyad baya son zama dani Baba, baya sona Baba...” Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani kukan, ta sulale ƙasa kan siminti. Girgiza kai Malam ya yi cike da tausayinta, ya mayar da idanunsa kan Zayyad a hankali ya ce“Wajen Mommahn ka ke so ka koma?” gyaɗa masa kai Zayyad ya yi yana hawaye ya ce“zan ga Mommah malam, ina son naga momma dan Allah” jin yanda ya yi magana cike da hankali ya sanya Malam ya dafa shi ya ce“shikenan Zayyad zaka je gida in sha Allah, ni nayi maka wannan alƙawarin, amma yanzu ka zauna lafiya kaji” Gyaɗa masa kai kawai ya yi, Malam ya sake cewa“kar ka sake ɗaga hankalinta kaji?” nan ma ya gyaɗa masa kai, Malam ya numfasa ya ce“bari naje gida, da safe in sha Allah zan zo” Zayyad ya lumshe idanunsa bai ce komai ba. Tashi Malam ya yi ya ƙarasa bakin ƙofar ya kalli Salma dake faman kuka ya ce“taso ki biyoni” daga haka ya fita daga dakin, tashi tayi tabi bayansa tana kuka kamar ranta zai fita. A tsakar gida malam ya tsaya, Salma ta tsaya ɗan nesa dashi tana shassheƙar kuka, Malam ya kalleta sai kuma ya girgiza kansa ya ce“ki yi haƙuri ki daina wannan kukan Ummulsalma, ina son zan yi magana da ke ta fahimta” Rage sautin kukan nata ta yi amma bata ce komai ba, Malam ya kalli sararin samaniya wadda gajimare ya rufeta ya ɗan yi jim sannan ya ce “wato Ummusalma abin da na fahimta shi ne Zayyad ya fara dawowa natsuwarsa, saboda haka a yanzu babu abin da yake buƙata sama da danginsa, musamman mahaifiyarsa. Saboda haka akwai buƙatar a mayar dashi gareta, ko hakan ya saka ya dawo nutsuwarta hankalinsa ya dawo, sannan su Maryama ma su dawo gida, idan Allah ya kai mu gobe ni da kaina zan zo na ɗaukeshi na mayar dashi garinsu” Durƙushewa ta yi akan gwiwoyinta ta haɗe hannayenta waje guda bakinta na rawa kuma cikin kuka ta ce“D...dan girman Allah, dan soyyayar da ka kewa Annabi Muhammadu(S.A.W) kar ka rabani da Yaya Zayyad malam, idan har ka mayar dashi ba zan sake ganinsa ba Malam, ba zan sake magana dashi ba. Ba zai dake kulani ba Malam, Amma ni ina son Yaya Zayyad, ina son zama dashi, ina ganinsa tamkar wani bangon wanda yake kareni. Ina ganinsa tamkar Abbana, kuma Yayana, domin shi ne wanda ya taimakeni a sanda na rasa kowa nawa, dan Allah dan Annabi malam kada ka rabani dashi, kada ka mayar dashi gida, wallahi ba zan sake kawo maka ƙararsa ba, ka yi hakuri ka barni dashi...” Ta kasa ci gaba da maganar saboda yanda numfashinta ke sarkewa, Malam kallonta ya dinga yi yana jin wani irin tausayinta, duk da yarintar ta amma tana sonsa sosai. Ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce“Ummulsalma kina son Zayyad har haka? Kin yarda zaki zauna dashi koda a ce shi baya son ki?” “Na yarda malam, na yarda wallahi, zan zauna da Yaya Zayyad koda zai dinga yankar naman jikina na yarda zan zauna dashi, domin shi ne Haske dana daɗe ina nema a cikin duhu, Shi ne HASKEN CIKIN DUHU na Malam!” _Book 1 ya kusa karewa fa, amma har yanzu baki yi payment, to ki yi maza maza ki yi payment via 7041901078 Hauwa lawan Adamu Opay evidence via my number 08106608363 Nanameera, a yi payment kafin lokaci ya ƙure_ # HCD # Light within the darkness # Nanameera 08106608363 *HASKEN CIKIN DUHU* Chapter 39-40: Book 1 End Nanameera, YOTA/023. Unguwar Rimi, Kaduna state. Saturday, 8:30am Hasken sun rays ɗin daya shigo ɗakin shi ne ya sanya ya buɗe idanunsa dan direct hasken kan fuskarsa ya sauka, ya tashi zaune yana mitsitsika idanunsa. “Morning love” Ɗago idanunsa ya yi ya kalleta, wata kyakkyawar mace ce tsaye tana sanye da sleeping dress doguwar riga mai sulɓi wadda ta tsaya dai-dai gwuiwarta, baƙaƙen ƙafafunta suka fito sosai sai glowing suke. Tana da siririyar fuska da manyan idanu kamar zasu fito, bakinta mai ɗan fadi ya yi daidai da fuskarta. Ta sakar masa murmushi wanda ya bayyanar da wushiryar da ke tsakanin haƙoranta na gaba, hannunsa ya miƙa ya kamo nata ya jawota gefensa, zama ta yi tana murmushi ta ce“Yau ka yi bacci dayawa fa” jan kumatunta ya yi ya ce“but why u didn't woke me up?” langwaɓar da kanta tayi ta ce“Ayyah gani nayi kamar ka gaji shiyasa na barka ka huta tun da yau Saturday” taɓe bakinsa ya yi ya janye duvet ɗin da ke jikinsa ya zura ƙafafunsa kan floor yana cewa“amma ai zan fita” tashi ta yi tana kallonsa ta ce“tom ka shirya nima daman ina so naje na gaida Hajiya” “Not today” Ta ji ya furta sannan ya shige toilet, kallon ƙofar ta dinga yi sai kuma ta girgiza kanta ta juya ta bar ɗakin. Tana tsaye jikin dining tana jera warmers ya ƙaraso wajen, da sauri ya amshi wani jug daga hannunta yana murmushi ya ce”let me help you ko Beb” Turo baki ta yi cike da shagwaɓa ta ce“ai kana gani duk nagama ayyukana baka ce zaka tayani ba sai yanzun?” Dungure mata kai ya yi yana cewa“ke kin fiye rigima ai daman” Dafe gashinta ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kai Noorie daga wasa?” kujera ya ja ya zauna sannan ya ce“madam ni yanzu nake ji, serve me please” plate ta ɗauko ta buɗe warmer, fried irish potato ne wanda ya yi jar suya ta zuba masa sannan ta buɗe ɗayan ta saka masa wainar kwai, ta tura masa gabansa sannan ta shiga haɗa masa tea. Ganin yanda take masa hira ya sanya ya ce“Kar ki ci ka min sugar” Da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce“Ni kuma ka ke tunawa Noorie?” Girgiza kansa ya yi ganin yanda ta haɗe rai ya ce“i'm sorry Madam” Tura baki kawai ta yi ta miƙo masa mug, sannan ta ja kujerar da ke gefensa ta zauna. Da kansa ya jawo mug ɗin ya raba musu shayin sannan ya miƙa mata. Karɓa ta yi tana murmushi ta ce“Good samaritan!” harararta ya yi ya ce“i'm i ur mate?” “Ayyah dan nace maka yaron kirki?” “Iyyeh! Ni ne yaron naki?” Ta marairaice fuska ta ce“to Babba, babban mutum, mijina abin alfaharina, Noorie na abin ƙaunata, Zakina mai tare min faɗa” Kyakkyawan murmushi Aliyu ya yi ya girgiza kansa yana juya cokalin cikin tea ɗin ya ce“Zakiyyana, Thank you baby” Lumshe idanunta ta yi ta ce“Ni zan gode maka Noorie” ta faɗa tana ɗora hannunta akan nasa, matse hannun ya yi sannan ya ci gaba da shan tea ɗinsa. **** Ƙarfe 11:00 na safe ta tura ƙofar ɗakin, zaune ta sameshi kan sofa yana danna system ɗin gabansa. Ta ƙarasa ta zauna gefensa cikin cool voice ɗinta ta ce“wai baka shirya ba? Ni fa sauri nake doctor” kwaikwayon irin maganarta ya yi ya ce“yanzu zan shirya Madam” tuntsirewa ta yi da dariya ta ce“ni ka daina tsokanata” sai da ya rufe system ɗin ya miƙe sannan ya ce“nima ki daina min rigima. Ki je ki jirani nan da 1pm sai mu fita in sha Allah” Kallonsa ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kawai zan yi gaba sai ka tawo, ni sauri nake naje gurin Hajiya” Babu yabo babu fallasa ya kalleta ya ce“to ba zaki tafin ba sai kin jirani” Daga haka ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, tura baki ta yi sannan ta juya ta bar ɗakin. Turo kofar dakin ya yi ya tsaya yana kallonta ya ce“Taso mu tafi” banza ta yi masa, ya ɗan yi murmushi sannan ya taka har gabanta, kan drawer ya zauna ya leƙa fuskarta. Ganin babu alamun dariya ya sanya ya ce“ko nayi tafiyata ne?” idan gadon da take kai ya amsa ta tabbas ita ma ta amsa maganarsa. Ya tashi yana murmushi ya kama hannunta ya ce“sorry i kept you waiting gani nayi fitar mu da wurin bashi da wani amfani shi ne na ɗan tsaya na ƙarasa wasu abubuwa but sorry” Ɗago idanunta wanda suka yi jajur ta yi ta kalleshi muryarta na rawa ta ce“ka... kawai baka son naje gurin Hajiya ne shiyasa, tun ɗazu na lura da abin da ka ke nufi, akan me zaka hanani zuwa wajenta? Ko kai kaɗai ta haifa ban da ni” Aliyu ya dinga kallonta amma bai ce komai ba, ta tashi ta gyara zaman mayafinta wanda da ta sake shi sannan ta ɗauki wayarta gefen madubi ta nufi hanyar waje ba tare da ta sake bi ta kansa ba. Numfasawa ya yi sai kuma ya juya ya bi bayanta, Har suka yi nisa bata ce komai ba ta juyar da kanta ma sai kallon hanya take, gyaran murya ya yi idanunsa zube kan titi shi ma ya ce“Nifa ba wai bana son ki je wajen Hajiya ba ne, kar ki fassara ni. Kawai ɓacin rai ne bana so” Ta gefen ido ta kalleshi amma bata ce komai ba. Hannunta ya kamo ya riƙe yana matsawa a hankali ya ce“shikenan I'm sorry dear” ɗago idanunta ta yi ta kalleshi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“ni ba haushi naji ba” Yana sauka daga flyover ya ce“oh really?” Ɗauke kanta ta yi bata bashi amsa ba shima kuma bai sake mata magana ba har suka ƙarasa GRA ɗin. Babban compound ne mai ɗauke da part guda uku, kowanne part daidai yake dana ɗan uwansa, ya yi parking motarsa a tsakiyar compound ɗin sannan ya kalleta, girgiza kansa ya yi ganin yanda ta yi shiru kamar mai tunanin wani abu. Ya ɗan yi murmushi ya ce“don't be afraid, okay?” jinjina masa kai ta yi sannan ta buɗe motar ta sauka. Bayan ya rufe motar ya dawo side ɗinta ya naɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce“ina zamu fara shiga?” kallonsa ta yi sai kuma ta ce“sai ma ka tambaya, wajen Hajiya mana” ya ce“okay let's go” daga haka ya kama hannunta, ita dai Zakiyya kallonsa ta dinga yi amma ta kasa ce masa komai. Sallama ya yi sannan suka shiga parlon, da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce“laaa yaya sannu da zuwa” murmushi ya yi ya ce“auta ina Hajiya?” “tana sama bari na kirata” Okay ya ce ta juya ta gudu ta yi upstairs, kallon Zakiyya ya yi ya ce“zauna mana” to ta ce sannan ta zauna kan 2 seater ya zauna a gefenta. After 5mins sai gata ta dawo ta zauna tana ci gaba da danna wayarta, “Maama ina take?” Ɗago kanta ta yi ta kalleshi ta ce“Yaya gata nan ta ce min tana zuwa” ko rufe baki bata yi ba suka jiyo ƙarar taku,da sauri ya mayar da idanunsa ga benen. Wata mata ce ta shiga sakkowa fara tas da ita daka ganta ka ga Aliyu ko ba'a faɗa maka ba kasan ita ce mahaifiyarsa, tana da jiki amma ba can ba. Zakiyya ta sunkuyar da kanta tana jan fingers ɗinta, kallonsu ta dinga yi sai kuma ta nemi kujera ta zauna, Aliyu ya ce“Barka da rana Hajiya” Babu yabo babu fallasa ta ce“Ya kuke?” Aliyu ya ɗan kalleta sai kuma ya ce“Alhamdulilah” Zakiyya ta ɗago kanta muryarta na rawa ta ce“ina...ina yini Hajiya?” kallonta ta yi ta ce”lafiya kalao, kina lafiya?” “Alhamdulilah Hajiya” Hajiya ba ta sake cewa komai ba ta miƙe tana kallonsa ta ce“toh ku gaida gida” daga haka ta shige ta koma sama abin ta. Sosai jikin Aliyu ya yi sanyin duk da daman yasan hakan zata iya faruwa, ya juya ya kalli Zakiyya yaga tana goge hawaye daga idanunta. Kasa magana ya yi sai kawai ya miƙe, kallon Maama ya yi yaga ta taɓe baki. Ya tashi muryarsa a dake kamar babu komai ya ce“tashi muje wajen Inna” miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta yi waje, yabi bayanta. Tsaki Maama ta yi a fili ta ce“ƙaryar banza” **** Kallonta ya yi ganin yanda taja ta tsaya, ya ce“muje mana” muryarta na rawa ta ce“a...a'a doctor kaje zan jiraka anan” haɗe ransa ya yi ya ce“innar ce ba zaki gaisar ba? Okay ya yi kyau” daga haka ya nufi cikin parlon, sauke numfashi ta yi sannan tabu bayansa jiki a sanyaye. Koda ta shiga parlon tsaye ta sameshi Inna har ta fara bashi labari sai murmushi yake. Durƙusawa ta yi a hankali ta ce“Inna ina yini?” “lafiya” Cewar inna tana mayar da idanunta kansa, Aliyu ya kalleta ganin yanda ta yi sak sai kuma ya kalli Inna ya ce“mene haka kuma?” A fusace ta ce“ban sani ba, tambayata ma kake? To ubanka ne, saboda ka mayar damu yan iska gantalallu ya sanya har wani kawo mana ita gida ka ke, wato kowa ma ya gani baka ji abin da aka ce maka ba. To kaje ka ci gaba kuma bari uban naka ya dawo wallahi sai an yita ta ƙare, ba zamu ci gaba da saka maka idanu kana abin da ka ke so ba, zama da juya ko masifa, duk sai ka tsofe a haka babu ya'ya to wallahi baka isa ba, dole sai ka yi aure” Wani irin kallon ya dinga yi mata sai kuma ya ce“to daman ana dole ne Inna? Bana son auren dan girman Allah ki daina min irin haka, ba ma sai na sake zuwa inda ki ke ba” “Kar ka zo kada Allah yasa ka zo, ai daman ta shanyeka ita da iyayenta matsiyata. To bari kaji wallahi mun fi ƙarfinka, kuma ba zaka ci gaba da zama a haka da juya ba, shekara 6 ko ɓari ta kasa yi, to wallahi baka isa ba! Kaji ma na gaya maka” Girgiza kai Aliyu ya yi sannan ya ce“ wai mene ne matsalar ku Inna? Ba dai matata ba ce? To ni babu wani auran da zan sake!” Cikin kunfar baki ta ce“to yimin rashin kunya! Na ce zageni saboda juyat matarka da bata da amfani! Ka zageni na ce!” Ƙarar rufe ƙofar da suka ji ya hana shi magana, da sauri ya bi bayanta, can ya hangota tana tafe tana sauri, yabi bayanta da sauri ya sha gabanta. Fuskarta a rufe da mayafin abayar jikinta sai kuka take kamar ranta zai fita, hannunta ya kama ta fizge tana girgiza kanta, saurin riƙeta yayi kawai ya rungumeta ta sake fashewa da wani raunataccen kukan, dafa bayanta ya yi yana jin yanda hawayenta ke zuba kan ƙirjinsa, ya sauke numfashi ba tare da ya ce komai ba. After 2mins ya ja hannunta suka ƙarasa wajen motarsa ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan ya zagaya ya shiga shima ya yiwa motar key suka bar gidan. Sun yi nisa sosai ya sami gefe ɗaya ya yi parking jin yanda take kuka kamar ranta zai fita, kallonta ya dinga yi yama kasa ce mata komai, can dai ya yi ƙarfin halin cewa “Zakiyya, ki yi hakuri dan Allah, kar ki damu da abin da Inna ta ce, dan Allah ki yi haƙuri” Cikin shassheƙar kuka ta ce“ka kai ni gida” ya yi shiru sai kuma ya ce“a'a gida zamu tafi, gobe na kai ki” Cikin kuka ta ce“dan Allah... Dan Allah Aliyu idan ba so ka ke zuciyata ta buga ba ka kai ni gidanmu” Ganin tana kukan kamar zata shiɗe ya sanya ya ce“okay” ya juya ya ci gaba da driving ɗin. **** Salma ta dinga kallonsa amma bata ce komai ba, ɗan haɗe ransa ya yi ya ce“wannan kallon fa na mene?” saurin rufe fuskarta ta yi da hannunta tana dariya, ya girgiza kansa sai kuma ya ci gaba da yankan salak ɗin da yake, tashi ta yi ta shiga kitchen bata daɗe ba ta dawo hannunta riƙe da plate wanda ta zuba shinkafa da wake, gabansa ta zo ta ajiye ganin ko rabin yankan bai yi ba ta karɓa tana cewa“ni Yaya bani baka iya ba” taɓe baki ya yi ya ce“zaki sake cewa na taya ki” murmushi kawai tayi sannan ta ƙarasa yankan salak ɗin ta tashi ta koma kitchen, wankewa ta yi sannan ta dawo dashi ta zuba kan abincin ta tura masa gabansa. Kallon plate ɗin ya dinga yi sai kuma ya ce“ke ba zaki ci ba?” Girgiza kanta ta yi ta ce“a'a ba zan ci ba ni, sai su Aunty Maryam sun zo, ta ce min suna hanya” Taɓe bakinsa ya yi sannan ya ce“okay” daga haka ya gyara zamansa ya yi bismillah ya fara cin abincin. Kan kujera ta koma ta zauna ta ɗora hannunta kan kumatunta ta zuba masa idanu, Yau sati biyu kenan bayan samun sauƙinsa. Suna zaune lafiya dashi yanda yake kula da ita abun har mamaki yake bata, he's always behind her happiness, koda wasa bai so yaga ɓacin ranta, bayan kwana biyu suke zuwa gidan Malam yana sake bashi rubutu, kuma su Maryam sun dawo dan zuwansu gidan biyu. Yau ma sun ce zasu zo saboda za'a yi maganar sauya gidansu da kuma tafiyarta makaranta, Salma ta sake lumshe idanunta tana sake godewa Allah daya bata Zayyad a matsayin miji, duk da yarintarta amma ta fuskanci abubuwa dayawa akansa, bashi da yawan surutu amma yana da kulawa fiye da ƙima, sannan kuma yana da halin kirki amma idan ya so. Ɗago kansa ya yi yaga yanda take kallonsa kamar ta samu tv, ajiye spoon ɗin ya yi ya ce“Idan ki ka cinyeni sai ki daina kallona” sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi, tasowa ya yi ya dawo kusa da ita, hannunta ya riƙe cikin nasa in a very cool voice ya ce“faɗa min meyasa ki ke yawan kallona?” Salma ta kalleshi hawaye na kawowa idanunta ta ce“kawai ina son ganinka ne Yaya Zayyad, idan ina kallonka sai naji tamkar ina da komai a rayuwa. Idan kana kusa dani kewar iyaye da yan uwa tana ragar min sosai. Bana son ka yi nisa dani tsoro nake ji Yaya” ta ƙare maganar hawaye na biyo fuskarta, Zayyad ya dinga kallonta kafin ya numfasa ya ce“ki daina shirme Salma, kin ga yanzu kin girma har aure ki kayi, sannan kuma makaranta za ki fara zuwa be wise man, ko kin fasa zama likitan?” Murmushinta mai kyau ta yi ta ce“ina so mana Yaya, ina son na zama likita saboda na taimaki mutane, ba zan bari wani ya mutu ba in dai ina da halin taimaka masa, sannan idan zan yiwa mutum aiki zan yi masa koda a ce bai kawo kuɗin ba, sai daga baya ya biya” Zayyad ya jinjina kansa ya ce“saboda me to?” “sabo...saboda... Saboda da a ce an yiwa Abbana aiki kafin mu kawo kuɗi da yanzu bai mutu ya bar ni ba, da yanzu ban zama marainiya ba, da yanzu ina zaune tare dashi, da ban rasa kowa ba...” Hawaye ya dinga zubowa kan farar fuskarsa, sosai jikinsa ya yi sanyi, ya sanya hannunsa ya goge mata hawayen sannan ya ce“ba haka bane, ita mutuwa lokaci ce, idan har kuma ya yi to babu makawa sai mutum ya tafi, koda a ce kun kawo kuɗin, ko da a ce an yi masa aikin sai ya mutu domin iya lokacin da zai yi a duniya kenan, dan haka ki daina irin wannan tunanin kin ji” Gyaɗa masa kai ta yi cikin shessheƙar kuka ta ce“Yaya Zayyad!” “Ummulsalma!” Ta kalleshi sai kuma ta yi shiru, ɗago haɓarta ya yi ya ce“talk mana” girgiza kanta ta yi tana murmushi mai haɗe da hawaye ta ce“babu komai fa, i just want to talk to you” “Go ahead” Girgiza kanta ta yi kafin ta ce komai ta ji ana buga ƙofa. Tashi ta yi da sauri ta fita ya bita da idanu. Rungume Maryam ta yi tana dariya ta ce“oyoyo Auntie Maryam” dariya ita ma ta yi ta ce“to ɓallani Salma” sakinta ta yi tana dariya, ta ɗauki Khalil ta ce“Aboki i dey missed you amma kwana zaka yi?” Girgiza mata kai ya yi ya ce“ni ba zan kwana ba” harararsa ta yi ta ce“sai ka kwanan” daga haka ta nufi cikin ɗakin Maryam na biye da ita. Da sallama ta shiga ya miƙe yana kallonsu ya ce“sannunku da zuwa” Maryam ta zauna tana cewa“Yawwa yaya Zayyad, ina yini?” “Lafiya kalao ya gida? Ina Hashim?” Ya jera mata tambayoyin, Maryam ta ce“Alhamdulilah, Ya fita amma idan zamu tafi zai zo” Zayyad ya jinjina kansa sannan ya tashi ya shige ɗaki, Salma ta ajiye musu ruwan data ɗauko tana cewa“Auntie zamu je gidan malam ɗin?” harararta ta yi ta ce“ba zan je ba ɗin” murmushi ta yi ta ce“haba my sweet Auntie, shinkafa da wake fa nayi miki” da sauri ta ce“haba?” Salma ta ce“wallahi har da salak da yaji mai daɗi na daka” Murmushi Maryam ta yi ta ce“to zuba min mana, zamu je to” tuntsirewa da dariya Salma ta yi ta ce“Hajiya Aunty Maryam” daga haka ta nufi kitchen Maryam ta girgiza kanta tana dariya. Koda ya shiga ɗakin waje ya nema ya zauna ya yi shiru yana tunani, time to time Mommah take faɗo masa a rai, ya gama shiri next week zai je Abuja ya ganota idan da hali sai ya tafi har Salman, ya numfasa sai kuma ya kwanta kan katifa ya lumshe idanunsa. **** Jiddah ta sake ƙasa da muryarta ta ce“yanzu ina yaron yake?” daga ɗaya ɓangaren aka ce“yana can mana, bashi da lafiya ne shi ne yasa suka kirani fa, idan zaki samu dama ki fito gidanmu yanzun” Jiddah ta sauke numfashi ta ce“Meema bana son wani abu ya sameshi, Meema ina son ɗana, kin sani ai” daga ɗaya ɓangaren Meema ta ce“that's why yasa na ce ki zo Jiddah, ina son ki ganshi domin shima yaron yayo missing ɗin ki, sai kin ganshi abun tausayi” Jiddah ta ce“shikenan wait for me zan tambayi Mummy na ce zan zo gidanku sai muje” Okay Meema ta ce sannan ta kashe wayar. “Jidda!” A firgice ta juyo ganin Mummy ya sanya jikinta ya yi sanyin, cikin rawar murya ta ce“Mumm... Mummy na'am” hawaye taga tana yi, ta ƙaraso wajen da sauri ta riƙeta tana cewa“subhanallahi! Innalil lahi, Mummy meya faru?” silalewa ta yi ta faɗi a ƙasa ta fashe da wani raunataccen kuka, Jiddah hankalinta idan ya yi dubu to ya tashi, ta durƙusa ta riƙeta tana kuka ita ma ta ce“Dan girman Allah Mummy ki daina kuka, ki faɗa min me aka yi miki, dan Allah ki daina kuka” Muryarta na rawa ta ce“Jiddah! Jiddah! Jiddah!” cikin tashin hankali ta ce“Mummy ki yi haƙuri dan Allah” “Jiddah ɗa? Jiddah ina ki ka samu ɗa? Jiddah ban gane ina ki ka dosa ba, kimin bayani kafin zuciyata ta buga dan Allah” Tashi Jiddah ta yi ta fara takawa a hankali, jikin window ɗin ɗakin ta tsaya tana hango can ƙasan gidan, cikin shessheƙar kuka ta ce“Ki yi haƙuri Mummy, na kasa, ban san da wane ido zan kalleku bane, ba zan iya ba, Mummy mema zan ce muku? Ba laifina bane!” Mummy data zo gabanta ta dafata cikin kuka ta ce“Kenan da gaske ne abin da naji? Jiddah kina da ɗa? Yaushe haka ta faru ni mahaifiyarki ban sani ba? Yaushe Jiddah!” Juyowa ta yi ta kalleta da runannun idanunta ta ce“A lokacin da nayi nesa daku Mummy, A lokacin dana zamana banida mai faɗa min daidai da rashin daidai, a lokacin da ku ke tunanin kun tura ni domin samun ilimi. Mummy shi ne dalilin komai! Shi ne dalilin kamuwa da ciwon zuciyata! Shi ne dalilin rugujewar farin cikina! Mummy da gaske na samu ciki kuma na haihu sannan na ɓoye ɗan gudun ku gane...” ta kasa ci gabawa saboda kukan da yaci ƙarfinta, ta zube ƙasa gaban Mummy tana rera kuka. Kallonta kawai ta dinga yi tana jin ƙafafunta kamar ba'a jikinta suke ba, ta buɗe bakinta dakyar ta ce “Jiddah! Wanene ya yi miki haka? Wanene sanadin wannan cikin! Ki sanar dani dan Allah” Muryarta na rawa ta ce“Shi ne Mummy...shi ne wallahi, Shiyasa na tsaneshi! Shi ne Mummy...” “Shi wane? Shi wane” Cikin wata iriyar muryar mai nuna zallar ƙiyayya ta ce“Zayyad ne! Zayyad ne Mummy, Shi ne...” Da wani irin tashin hankali Mummy ta kalleta, hannunta bisa ƙirjinta ta ce“Ji... Jiddah me ki ka ce? Jiddah...” Wani irin ihu Jiddah ta saka ganin Mummy zube a ƙasa a sume, ta dinga jijjigata tana kuka ta ce”Dan Allah Mummy ki tashi, Mummy ki buɗe idanunki, nashiga ukuna Mummy, wallahi ba zan bar shi ba, daman zan ɗauka mataki amma ki tashi! Dan Allah ki buɗe idanunki...” Jiddah ta dinga kukan cikin fitar hankali. **** Maryam ta dinga kallonta tana murmushi, kwaɓe fuska ta yi ta ajiye liner ɗin ta ce“Auntie meyasa ki ke min dariya?” Maryam ta girgiza kanta ta ce“a'a ni babu dariyar da nayi miki ci gaba da kwalliyarki” Salma ta kalleta sai kuma ta ci gaba da lining ɗin da take tana kallon ɗan ƙaramin madubin da yake hannunta ta ce“kuma ai nayi kyau, Yaya Zayyad nake yiwa kwalliya, Malam ya ce na dinga faranta masa rai” Maryam ta jinjina kanta still smiling ta ce“Ai ko kin kyauta, ki dinga yi masa” murmushi ta yi ta ce“To auntie nayi kyau?” Maryam ta kalleta tun daga ƙasa, wata Egyptian Abaya ce a jikinta baby pink, ta saka veil ɗin rigar a kanta ta sake shi kawai madadin rolling, fuskarta fresh babu kwalliya sai liner data saka a idanunta da kuma zagayen bakinta, she looks quite and elegant, Maryam ta ce“irin wannan kyau haka Amaryar Zayyad” rufe fuskarta ta yi tana murmushi a shagwaɓe ta ce“auntie Maryam ban so” “muje ni” Ta buɗe bakinta zata yi magana taji ana knocking ƙofar gidan, Salma ta ce“ko wane kuma?” “Je ki buɗe mana sai kiga” Okay kawai ta ce sannan ta fito parlon ta wuce wajen, tana buɗe ƙofar ta ce“au Yaya kai ne...” sai kuma ragowar maganar ta maƙale saboda waɗanda idanunta ya gani, ta yi saurin barin jikin ƙofar tana girgiza kanta, Shigowa Mommah ta yi sai kuma General. Ya dinga kallon gidan kafin ya mayar da idanunsa kan Salma, sunkuyar da kanta ta yi tana hawaye ya shiga takawa cikin isa har inda take. “Daddy!” Muryar Zayyad ta daki dodon kunnensa, ɗago kansa ya yi ya kalleshi da sauri ya ƙaraso ya rungume shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya General ya sauke ya ɗago shi ya matse kafaɗunsa yana murmushi mai tafe da hawaye ya ce“son! Zayyad kai ne, kana lafiya?” ya shiga tattaba jikinsa a ruɗe, murmushi kawai Zayyad ya yi sai kuma ya sake rungumeshi muryarsa a dakushe ya ce“Daddy!” Yanda ya yi maganar cikin wani irin raunin zuciya ya sanya Daddy fashewa da kuka ya ce“ka yafeni, I fell, I fell Zayyad!” Ɗagowa ya yi ya kalleshi ya ce“stop saying that Daddy” daga haka ya juya yana kallon Mommah wadda ke tsaye tana kallonsa kamar statue. Da gudu ya tafi ya faɗa jikinta, Mommah ta ƙamkameshi sai kawai ya fashe da kuka, rauninsa gaba ɗaya ya bayyana a jikin wadda kewa kallon mahaifiya. Ita kanta kukan take, kowa ya dinga kallonsu a wajen cike da tausayawa. After some minutes ta ɗago shi tana taɓa shi ta ce“Zayyad! Zayyad! Da gaske kai ne? Meke damunka, zo mu tafi gida, muje Zayyad” Murmushi ya yi ya sanya hannunsa ya share mata hawayen ya ce“babu komai Mommah I'm feeling better now” girgiza kanta ta shiga yi tana kuka ta ce“ka zo mu tafi, kazo mu tafi dan Allah” ta dinga jan shi. Hannunsa ya sanya ya riƙe nata ya ce“Mommah wait! yanzu zamu tafi” ci gaba ta yi da jansa tana cewa“jirgin mu yana can yana jiranmu muje kaji” Ya kalleta amma bai motsa ba, juyowa ta yi taga ya Girgiza mata kai, sakin hannunsa ta yi ta ce“Ba zaka bini ba ne? Ba zaka tafi ba Zayyad? Ina som muje gida, ka zo mu tafi dan Allah, ko baka sona yanzun?” “Mommah!” Ya kira sunanta hawaye na kawo idanunsa, juyawa ya yi ya kalli Salma wadda ke tsaye ta zuba musu idanu hawaye sai zuba yake akan fuskarta kamar an buɗe famfo. Da hannu ya yi mata alama da ta zo, ta ƙaraso tana tafe kamar zata faɗi. Kallonta Mommah ta yi amma bata ce komai ba, ya kamo hannunta ya yi shiru yana kallon fafaren yatsunta, jan numfashi ya yi ya sauke sai kuma ya ce“Salma zan...” “Yaya Mommah tana son ta ganka, zan jira ka kaje ka dawo, zan zauna wajen Aunty Maryam, nasan ai ba zaka daɗe ba ko? Zan fara zuwa makarantar ma kaga...” “Salmaaaa!....” Ya kira sunanta yana matse yatsunta, hawayene suka sake zubowa fuskarta ta ce“na'am Yaya, ba zan yi kuka ba fa, ai zaka dawo ko?” “Zayyad!” Mommah ta kira sunansa, kallonta kawai ya yi sai kuma ya mayar da kansa wajen Salman ya numfasa amma bai ce komai ba, ta dinga kallonsa ganin yanda ya yi shiru ya sanya ta ce“ko tare zamu tafi? Ni bana son naje gidanku Yaya” “Son jirgi na jiranmu kaji” Cewar Daddy ganin yanda ya yi shiru bai ce komai ba. Gyaɗa masa kai kawai yayi sannan ya motsa bakinsa muryarsa a raunace ya ce “Salma nasan kin bani kulawa, kin soni, kin taimakeni da kuɗinki, da lokacinki, da lafiyarki, kin zauna dani a halin da ba kowace mace ce zata iya zama da namiji ba. Kin bani kulawa tamkar daman can kin saba dani, duk da yarintar ki bai saka kin Gaza ba, na so na zauna da ke, naso na saka miki da Alkhairin da ki ka min, naso na baki kulawa irin wadda ki ka ban, sai dai...” “Sai dai me Yaya? Babu komai fa, ai kai mijina ne, kuma kaima ka taimakeni a lokacin da nake buƙata, dan haka duk abin da nayi maka tamkar dole ne a wajena, bana son ka gode min, ai muna tare zan ci gaba da faranta maka har ƙarshen rayuwata. Yaya Zayyad ka san me? Ina sonka! Ina sonka Yaya! Tun ranar dana fara ganinka naji na kamu da sonka, ban san taya ba amma tabbas kai ɗin na daban ne, ashe ƙaddara zata haɗa mu, ashe zan zama matarka. Ina jin nafi kowace mace Sa'a a duniya dana sameka, Yaya ina sonka wallahi ina sonka!” Zayyad ya kasa magana sai girgiza mata kai yake a hankali, Maryam dake kallonsu ta share hawayenta tana jin jikinta ya yi wani irin sanyi, Salma ta bata tausayi sosai, Zayyad ya sauke numfashi a karo na barkatai kafin ya ce “Nagode miki Salma, Thank you for everything, your time, your care, your love, I'll never forget you in the rest of my life, those memories zan ci gaba da ajiye su, zan ci gaba da tunaki har abada. Zaki ci gaba da zuwa makaranta, zaki zama likita kuma ki taimaki masu neman taimako, zan tabbatar da wannan burin naki ya cika” Salma dinga kallonsa ta kasa gane abin da yake nufi, ta kasa gane in da zancensa ya dosa, Ita dai tasan idan ya tafi zai dawo, ba zai barta ba tana da wannan tabbacin. Abin da ya sanya a tafin hannunta shi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, ta kalli hannunta, wata well folded paper ce, ta ɗago ta kalleshi sai kawai taga ya Girgiza mata kai ya sannan ya ce “Zan tafi Salma, ban so haka ba amma babu yanda zan yi, zan koma ga iyayena da kuma yan uwana, I'm sorry to say na sake ki saki ɗaya, I'm sorry Salma, zaki ci gaba da zama wajensu Maryam, ki yi karatu kin ji, one day I'll be back to you, but as for now zamu rabu. Naso na aureki sai dai ina da matar da aka zaɓa min kuma ita zan aura nan bada jimawa ba, thank you, ba zan taɓa manta abubuwan da ki ka min ba, zan kuma dinga miki addu'a a kullum. Sannan ina son na faɗa miki idan kin samu miji ki yi aurenki Salma, kuma ki zauna lafiya da mijinki, ki so shi kamar yanda nake da tabbacin zai so ki, domin kin cancanta a soki, I'm sorry kin ji. Allah ya haɗa kowa da Alkhairin rayuwarsa, good bye Salma, sai anjima!” Ya saki hannunta ya juya ya bi bayan Mommah, kallonsa ta dinga yi tana jin kamar yana tafiya ne zuciyarta da nutsuwarta, can kuma ta fasa wata irin ƙara, tabi bayansu, Maryam ta biyota da gudu. Tsaye ta ganta gabansa ta rike rigarsa tana wani irin kuka mai raunata zuciyar duk wani mai sauraro, da sauri Maryam ta ƙaraso wajen ta riƙeta tana janyeta daga jikinsa, sai dai irin riƙon da ta yi masa ya sanya ta kasa janyeta, cikin gunjin kuka ta ce “A'a Yaya! A'a! Kar ka tafi ka bar ni dan girman Allah, ka ji tausayina, wallahi ba zan taɓa ɓata maka rai ba, zan yi duk abin da ka ke so, dan Allah kada ka sakeni! Ka da ka yi nesa dani, Idan ka tafi ka bar ni mutuwa zan yi Yaya! Wallahi mutuwa zan yi...” Wani soja ya zo ya janye hannunta da ƙarfi, Maryam ta rungumeta itama tana kuka kamar ranta zai fita, Zayyad ya kalleta sai kuma ya shige mota kawai, Salma ta saki wani ihun tana ƙoƙarin bin su, amma Maryam ta riƙeta tsam tana girgiza mata kai. Cikin kuka da fitar hayyaci ta ce“Auntie tafiya zasu yi fa, da gaske tafiya zai yi ya bar ni, Auntie ki cikani na bi shi dan Allah, ina son Yaya Zayyad, Auntie ki barni! Ki bar ni Auntie! Ki daina riƙeni...” Maryam ta kasa cikata, haka tana ji tana gani motocinsu suka dinga tafiya daga layin ɗaya bayan ɗaya, Salma ta dinga jin kamar ƙarshen rayuwarta ne zai zo, ta fara ganin wani irin hazo cikin idanunta kafin daga bisani jikinta ya yi wani irin sanyi, ta fadi ƙasa Sumammiya. **** Kallonta ya dinga yi sai kuma ya ce“me ki ke nufi Zakiyya?” tana kallonsa ta ce“i mean ba zan dawo ba Aliyu! Ba zan ci gaba da zama da kai ba! Ni ba zan taɓa samar maka da ɗa ba, kuma iyayenka da danginka ba zasu taɓa sona ba! Zan zauna wajen Auntyna, kaje kawai! Ka nemi wata Aliyu. Ka yi aurenka dan Allah ka auri wadda zata haifar maka ɗa, idan ta haifi mace ka saka mata sunana...” ta juya ta shige cikin gidan da gudu. “Zakiyya! Zakiyya! Zakiyya..” Ya yi kamar zai bita sai kuma ya tsaya, ya sauke numfashi sai kuma ya juya ya koma mota, da niyyar da dare sai ya dawo ya lallaɓata. Wayarsa ce ta dinga ringing ganin sunan da yake kan screen ɗin ya sanya ya ɗauka, daga ɗaya ɓangaren aka ce “Wai kana ina ne?” Aliyu ya ce“ina unguwar rigasa I'm coming” Mujaheed ya ce“okay, but wait meya sameka naji muryarka haka?” Aliyu ya ce“idan na ƙaraso kaji” okay kawai ya ce sannan ya yi cutting kiran. Salma ta shiga buɗe idanunta tana ƙarewa ɗakin kallo, tashi zaune ta yi ta dinga kallon gidan sai kuma ta miƙe tsaye tana cewa “A'a Yaya Zayyad! Ba zaku tafi ku bar ni ba wallahi! Sai na biku!” Maryam da ke cikin kitchen taji kamar muryar mutum ta ce“Salma” Salma ta kalli hanyar kitchen ɗin sai kuma ta girgiza kanta da gudu kuma ta fice daga parlon, buɗe ƙofar gidan ta yi ta ɗebi gudu ta nufi hanyar titi. Koda Maryam ta fito ta dinga kallon parlon ganin babu Salman data bari kwance, ta shiga duk ɗakunan amma bata ganta ba, tsakar gida ta fito sai dai ganin ƙofar gidan a buɗe ya sanya taji jikinta ya yi sanyi, ta koma da sauri ta ɗauko wayarta ta shiga kiran lambar Hashim. Koda Salma ta zo titi motoci sun cika dan yammaci ne, bata ko kallon gabanta ta nufi tsakiyar titin da niyyar tsallakawa, Cikin rashin sa'a wata mota ta yi sama da ita sannan ta faɗo ƙasa kanta ya bugu da kwalta nan take jini ya fara zuba, cikin tashin hankali ya yi parking ya fito, mutane duk aka taru ana kallonta jininta sai malala yake akan titin, wani ne ya ɗago fuskarta, Aliyu ya ɗan ja da baya sai suka ya ce“innalil lahi wa ina ilayhi raji'un! What i did!?” Wanda ya ɗagotan ne ya tattaɓata sai kuma ya ce“wannan ai ta mutu, ta mutu wallahi!” *Alhamdulillah anan na kawo karshen book 1, sai mun haɗu a book 2 wanda yake na kuɗi ne akan ₦700 kacal, via 7041901078 Hauwa lawan Adamu Opay, evidence via 08106608363 Nanameera* # HCD # Betrayel # Nanameera 08106608363