[12/16, 11:09] 08080966571: *HASASHENA* BISMILLAHIR- RAHMANIR-RAHIM *GARGADI*:Wannan labari mai suna a sama kagaggen labari ne, da ba shafi wata ko wani ba. An yi shi ne kawai da ilmantarwa, fadakarwa da kuma nishaɗantarwa. Idan kin /ka ji wata halayya da ta yi daidai da ta ki/ka arashi ne kawai. *TSOKACI*: Labarin *HASASHENA* Labari ne na wata jarumar da take hasashen duk namijin da ya kara aure, to matarshi ta gida ta gaza ne, ko kuma ta wajen ta fi ta gidan komai. Shi ya sa lokacin Bashir ya zo neman auranta, a matsayin mata ta biyu, ta rika jin za ta ci karenta babu babbaka, za ta more rayuwar aurenta, za ta ja zarenta yadda take so. Ta rika jin ba sai an fada ba, ta yagawa matarshi ta gida ta ko wane bigire. Sai dai bayan auran ta riski abubuwa da yawa. Da har ta gwammace kida da karatu. *HASASHENA* *Page 1* Mallakin Khadija S Mohd Daga inda nake kwance na ji karar rufe kofa, wannan ya sa na yi saurin duba agogon wayata, takwas saura na safe ya nuna. Zumbur! Na mike hade da ficewa zuwa falona, lokaci daya kuma na yaye labulen tagata da zai hasko min tsakar gidan. Tsaye take cikin riga da siket na lace mai launin ja da digon bakin fulawa, hade da kwalliyar zare mai ruwan gold. Dinkin ya zauna a jikinta daram, daurin dankwalinta das ya zauna a kan goshinta, gilashin da ta manna ba ƙaramin kawata mata fuskarta mara wadatacciyar kwalliya ya yi ba. Karamar purser ce baka a hannunta, wacce ta yi daidai da bakin dogon takalmin da ke kafarta. Sabe take da Ramla yarinya yar kimanin watanni takwas a kafadarta, yayin da daya kafadar ta sagala bakin gyalenta. Wannan ita ce kishiyata Sakeena wacce kowa ya fi sani da Maman Khalil. Na kai dubana akan yaranta biyu, da suka fito fes cikin uniform din makaranta, Khalil shi ne babba, wanda yanzu zai kai shakaru 7, sai Affan mai shekaru 5. Na kuma kai kallona a kan maigidan namu, a lokacin da yake saka mata keys din kofa a cikin posern da ke hannunta. Sanye yake cikin manyan kaya farare tas, wadanda aka yi wa kwalliya da bakin zare, takalman kafarshi da hula, su ma sun kasance launin baki da fari. Sosai kyawunsa ya fita a cikin kayan, yayin da kuma suka boye shekarunshi. Fuskarsu kawai za ka kalla ka fahimci suna cikin walwala da farin ciki. Na sake labulen a lokacin da na ga ya nufo bangarena, lokaci daya kuma na fada kitchen hade da goge farantan da ni kaina ma ban san dalilina na goge su ba. Don zuciyata cike take fam da kishi hade da danasanin auran mijin wata. Na tuna yadda wasu kawayena da ƴan'uwa suka rika jimami, lokacin da aka ce zan auri mai mata. Amma ni a lokacin ban ga wani abun jimami ba,tun da ni ce amarya. An cewa kuwa sabo ya fi tsoho, koda sabon kashi ne. Shigowarshi ne ya sanya ni juyawa hannuna rike da plate da ƙaramin towel. "Kin tashi lafiya?" Ya tambaya lokacin da yake kallon kwayar idona. Bakina ya yi nauyi, ba zan iya furta komai ba, dalilin da ya sa kenan na daga kaina alamar "Eh" Matsowa ya yi daf da ni, hade da amshe plate din da ke hannuna da towel din ya aje a kan carbinate. Ya janyoni zuwa jikinshi wanda ya gauraye da kamshin turarenshi, na matarshi da kuma yaranshi. Jikina ya gama mutuwa, dalilin da ya sa kenan na kasa aikata komai fa ce jin yadda yake shafa bayana alamun lallashi. Tsawon mintuna biyu ya dago ni hade da saka kwayar idonshi cikin nawa. " Idan akwai wata matsala don Allah fada min?" Girgiza kai na kuma yi, don kuwa idan na ce zan bude baki, kukana ne zai fita a maimakon magana. "Ina sonki Khadija." ya fada hade da kama kafaduna duk biyun. Hawayen da nake ta boyewa tun dazu suka gangaro zuwa kan fuskata. Hannu ya kai yana share min hawayen. "Bana son kuka, zan tafi office kar in makara, idan na dawo za mu yi magana." Kai na kuma dagawa, a lokacin da nake share hawayen. Ina kallonshi ya fice, ko rakiya kofar falo ma bai samu ba. Sai da na ji fitar shi sannan na fito zuwa falo. Dankwalina na tuge, lokaci daya kuma na tura yatsuna cikin gashin kaina ina sosawa ba don yana min kaikayi ba. "Anya kuwa wannan ba shi ne kuskure ma fi girma da na yi a rayuwata ba na auran mijin wata?" A zuciyata na yi maganar, a zahiri kuma kwantawa na yi kan doguwar kujera ta, hade da kallon P. O. P da ya kawata rufin falon nawa Kawata Samira ce ta fado min a rai, hakan ya sa na yi saurin tashi, na nufi bedroom da zummar dakko wayata in kirata. Sakon dana taras ne ya dakatar da ni daga kiran Samiran "Kin gama kukan" abin da na gani kenan, na dan murmusa a hankali, na mayar mishi da amsa. "Na kusa dai" "Hhhh! Shagwababbiyata" "Smile" abun da na tura mishi kenan "Ina yi miki wani abu mara dadi ne Khadija?" duk da ba na ganin fuskarshi a lokacin na san ba alamun wasa a tare da shi "Me yake so in ce to?" na tambayi kaina. "kana nunawa matarka so da kulawa sosai, sannan matarka ta cika duk wasu sharudda da mace ta gari ya kamata ta cika. Sannan ka yaudareni da aka aureni bayan ka san kana samun duk wani farin ciki a wurin matarka. Haka yake so in fada mishi?" na kuma tambayar kaina. " Ba ka yi min komai ba, bana jin dadi ne idan duk kuka fita, kuka bar ni kadai." Na tura mishi. " Sorry Deejahna, kamar yadda na yi miki alkawari kina cika shekara daya zan nemar miki aiki sha Allah." "Ina godiya Alhajina." "Bukatata ku zauna lafiya cikin aminci ke da abokiyar zamanki. Maman Khalil mutuniyar kirki ce." "Ka san da haka me ya sa ka aure ni, kullum kana cikin yabon matarka" A badini na yi maganar a zahiri kuma tura masa sako na yi kamar haka. "In sha Allah za ka yi alfahari damu." "Me za ki yi min da rana?" ya canja salon hirar. "Me kake so?" "Tuwon shinkafa miyar kuka" ya kuma turowa da sako. Na zazzaro ido cike da mamakin sakon na shi, ina maimaita " Miyar kuka kuma!" "an gama ya Hajj" na tura mishi "Na gode" "Uhhhh! Na ce ba, yau fa ba ni ce da kai ba, ba matsala ko?" " Ba komai, ki yi kamar yadda na ce" "Ok" na kuma yi mishi reply Tsawon mintuna biyu bai turo wani sakon ba. Hakan ya sa na kira Samira. "Kawata!" ta fada da alamun muryar bacci, ajiyar zuciya na sauke kafin na ce "Yar gata, bacci ma kike yi?" "To me zan yi, yau ba ni ce da duniyar ba." ta ba ni amsa. "Samira! (na kira sunanta a sanyaye kafin na ce) ina ma ni ce ke" "Me ya faru?" ta yi saurin tambaya "Aka raba mana gida da abokiyar zamana, kin ga duk kazantar da ban gani ba, tsabta ce." ta amsa ta "Hmmm! Ke babu fa wani sauki wlh, ya fi ma ana ganin idon na ki, wani abun ba za a yi shi ba. Saboda Hausawa sun ce ganin ido na hana cin kai. Amma ba a ganin idonki sai abin da kika gani." "Duk da haka Samira" na tare ta "Ba za ki gane ba Khadija, amma ni kam da za a hade mu da ita gaskiya da na so, ko ba komai zan rika ganin motsinta. Kin ga kishi da jahilar mace, sam bai yi ba, ba karamar artabu nake sha ba, baƙin asiri a wurinta ba a magana. Kuma ke ma dai kin sani, kina ganin har gida na dawo jinya. " Kai na jinjina a hankali ba tare da na ce komai ba, saboda tun kafin in yi aure na san irin yadda Samira ke shan fama da kishiyarta, har auran aka so rabawa amma Allah bai nufa ba. Sau uku Samirar na samun ciki yana zubewa, kuma an ce wai duk siddabarun kishiyarta ne. Duk dai an ce wai mai kishiya ba ya ciwon Allah. Amma tabbas kishiyar Samira tana da baƙin asiri. Wayar na yanke, hade da mikewa na nufi kitchen ina ta bitar miyar kuka "Ya zan fara miyar kuka ta yi dadi ne? Duk cikin koyon girkin da na yi don zan zo gidan kishiya, ban ko yi miyar kuka ba, don gani nake kamar yanzu ba a yayinta. Lokacina na bata shi ne kaf wajen koyon girkin zamani" A zuciyata nake maganar a lokacin da nake tsaye cikin kitchen kamar na kayar da suruka. Komawa na yi bedroom din inda na yasar da wayata. Kawata Badiyya zan kira, na san yadda ta kware gurin cin tuwo miyar kuka dole ta san yadda ake yin mai dadi. Wayar na fara ringing ta daga "Ke ni ki bude baki, ki yi min magana sosai" Na yi maganar cikin muryar fada. "Ki fadi me kike so ki fada ina jin ki?" ita ma ta ban amsa. "Turo min yadda ake miyar kuka, da kayan hadinta yadda za ta yi dadi fa." Ina jin yadda ta yi yar dariya mai sauti, ganin ba ta da niyyar tsayawa na ce "Idan kin gama dariyar ina jiranki, sauri nake yi." katse wayar na yi hade da debo shinkafar tuwo na fara wankewa. Kamar mintuna uku, wayata ta yi haske alamar sako ya shigo, da sauri na bude sakon ina karanta yadda Badiyya ta rubuto min yadda ake miyar kuka. Ban gama karanta sakon ba kiranta ya shigo "Sakon ya shigo?" "Eh" na ba ta amsa "Shi ne ba za ki gode ba?" "Kar fa ki dame ni don kawai kin koya min miyar kuka" Dariya ta kuma yi kadan, kafin ta ce "Wai ina littafin koyon girkinki?" Tabe baki na yi kamar tana kallona, kafin in ce "Ai wallahi in fada miki tun na zo gidan nan tsawon wata biyu, ban taba yin girkin da ke cikin littafin can ba ko sau daya." "To me ya faru?" ta tambaya. "To duk ba haka tsarin gidan da abincin gidan yake ba. Shi ya sa ma ban gwada zan yi ba. Gara ma ranar can dana gidan ba kowa na gwada yin wani abu, na manta ma sunanshi ban iya ci ba wallahi, na faki ido na zuba a bola. Ko ban iya ba ne, ko kuwa dai haka yake ba dadi oho?" Wata dariyar ta kuma saki, hade da fadin "Amma ke ba sai ki zo da na ki sabon salon ba" "Ina jin tsoro Badiyya, in yi bai yi dadi ba, kin ga ai na fado kenan." "Wlh kam. Ga shi ba ke kadai ba, zama da kishiya akwai kalubale Khadija. Gara ma ke, abincinki kike yi ke kadai. Amma mu masu gabadaya muke tantancewa. Yau yara su ce kin yi basu koshi ba, jibi su ce babu dadi. Citta su ce ba ki gama da wuri ba. Kullum da sabuwar tsirfa." Haba na rike kamar tana kallo na, kafin na ce" Wato tukunyar dai tare ta tafasa? " " Wlh kam. Don yanzu haka raina bace yake, kiranki ne ma ya dan warware ni. Yaron can Abbah sarkin gadara, shi ne yake yi min abin da ba na jin dadi, kai tsaye ki ji shi a kitchen dina yana min bincike, kuma ba damar in yi magana, Sai ace wai yaro ne in yi hak'uri zai bari" Cikin sigar lallashi na ce "ki yi hak'urin to, komai zai wuce sha Allah." "Allahu Ya sha" ta amsa, kafin mu ka yi sallama. Duk jikina a mace, ashe haka aure yake, ko wanne da irin kalubalenshi, ba masu kishiyar ba, ba wadanda suke su kadai ba. Kanwata Yusrah da take ita kadai ma a gidan miji, ita ma da tata matsalar. Haka na ci gaba da tattauna kalubalen da zuciyata, lokaci daya kuma Ina aikin tuwona. Matar J [12/16, 11:29] 08080966571: *HASASHENA* *Page 2* *MATAR J* Tun da na gama miyar shiga goma fita goma zan yi a kitchen din sai na bude tukunya na dauki ludayin na dangwala a hannuna na lashe, abun ka da ban taba gwada yi ba so dai nake in tantance, kar Ogan ya ci ya raina min. Tuwon ne dai ya yi tauri da yawa ba kamar yadda mamana take yi ba, shi ba mai tauri ba, kuma ba mai taushi ba, yana nan a tsakiya dadin ci. Amma ni nawa aka jefi kato ba abin da zai hana bai ji ciwo ba. "To me ya sa?" Na tambayi kaina. Kiran layin Ummata na yi " Ummah!" na fada bayan na yi sallama hade da gaishe ta "Na'am" ta amsa "Tuwon shinkafa na yi, ya yi tauri bai yi irin naki ba" Na ta fi kai tsaye akan abin da nake so "To ba sai ki dakko littafin da kike rubuta kalolin girki ba, ki duba yadda za ki gyara" Shiru na yi, ina tuna yadda take jin haushin littafin koyon girkin can nawa, lokaci daya kuma Ina tuno yadda take fada "Aikin banza da wofi, kullum kina like da TV wai koyon girki, idan za ki tsaya ki koyi abu a zahirance ki tsaya ki koya, wannan rubutun ba inda zai kai ki ba, ni dai kika sanya aka zageni a kan ba ki iya girki ba, sai Allah ya saka min." Haka take cewa duk lokacin da nake rubuta yadda ake wani girkin a TV ko a media " Kai Umma, yanzu fa kin san ba kamar da ba ne, idan ban iya wannan abinci zamanin ba akwai matsala wallah, mazan yanzu yan zamani ne ba Yan gargajiya ba" Haka nake ba ta amsa. "Wane namiji ne zai siya miki kayan girkin da kike rubutawa? Wani ma bai ko taba jin sunansu ba, sannan wane namiji ne zai rika siya miki kaza kina rarike cikinta kina tura dankalin turawa da su hanta da koda? Wane namiji zai tsaya siya miki kwai kina dafawa kina dode duwawun kaza? Sannan wane namiji zai fita tun safe ya dawo da yamma ki aje mishi cake ko wani burodi can da danyen tumaturi? " A duk lokacin da ta fadi haka dariya nake yi, a zuciyata ina fadin "Ba ganewa za ta yi ba." Ashe dai ni ce ba zan gane ba. "Kin ji me na fada dai ko?" ta katse min tunanina "Eh" "Yauwa" Ta yanke kiran Fita batun tuwo na yi, na gyare kitchen dina fes kamar ban yi aiki a ciki ba. Wanka na shiga, bayan na fito na shimfida sallaya don sallahr azahar. Bacci ne cike da idona, don haka a kan sallayar na kwanta bayan idar da sallahr. Bacci kuma ya yi awon gaba da ni. Cikin baccin ne na ji kwankwasa kofa. A firgice na tashi na nufi kofar Khalil ne tsaye cikin kayan shan iska na yara, kamshin turarensu na yara da turaren mamarshi tuni ya cika kofar tawa. "Khalil, kun dawo ne? Me ya faru?" cikin muryar bacci na jero mishi tambayoyin. "Momyna ce ta ce idan kin rage abinci wai ki san mana kafin ta girka mana" Hannu na kai cikin sauri na murje idanuna don gasgata mafarki nake yi, kodai gaske Tuwona mai taurin can zan ba ta? Matar da ko ruwan zafi ta dafa sai ya yi dadi. Shi ya sa bana son ba ta abincina, ina jin tsoro ta rika min kallon ban iya girki ba "Zo ka zauna, sai in daukar ma kada ka baras ko" na yi maganar hade da jawo hannunshi zuwa cikin falon sosai. Komai bai ce ba, ya biyo ni. Babban tire mai kyau na dakko, na jera abincin da gorar ruwa daya, sai fruit salad mai sanyi. "Mu je ko" Na fada a daidai lokacin da na zo wurinshi Wannan karon ma bai yi magana ba "Wannan yaron tun wuri miskili ne" Na fada a zuciyata ina kare mai kallo, cikin mulmulallan jikinshi da ke nuna yana samun kulawa a ko wane fanni. "Assalamu Alaikum" na yi sallama a falonta hannuna rike da tiren abincin. "Amarya shigo mana, na fito wanka ne" Daga cikin bedroom nata ta yi maganar bayan amsa sallamar tawa. Daure take da towel iya gwiwa, jikin nan kamar na tarwada, iya inda na gani ban ga kurji ko alamar tabo ba. Haka kalar fatarta mai wahalar fassarawa ta fita sosai gwanin sha'awa. Don ita dai ba za a ce mata fara ba, kuma ba baka ba. Kamshin nan da kullum yake like da dakinta yana nan, na rasa wane irin turare take amfani da shi kamar maye. Ni kaina yanzu dana shiga dakin nata sai in yi awa daya kamshin bai bar ni ba Idan kuwa ta taba kudi, ko mijina ya kwana a dakinta ya dawo dakina, to har ya bar dakina kayan da ya shigo dasu ba zasu bar kamshinta ba. "Tuwo fa na yi miyar kuka" na fada ina murmushi "Ai shi yaran nan suka fi so ma, haka Babansu ma" ita ma cikin murmushin ta yi maganar "Je ka dakko min plate a kitchen Khalil" Ta fada tana kallonshi "Bar shi ya huta bari in kawo miki" Na fada hade da mikewa. Ta yi saurin riko ni "Wayyoh! Rufa min asiri, wallahi ban isa ba, ke da Khalil din duk zauna na hutashassheku" Kafin in yi magana tuni ta fice cikin sauri daga dakin. Na bi bayanta da kallo, wanda yake dauke da faffadan kwankwaso. A zuciyata na ce "Ko yaushe nawa kwankwason zai bude kamar na ta oho" "Wallahi Ramla ce ba lafiya, na biya asibiti shi ya sa ban dawo da wuri ba. Na ce Baban yaran nan yau ma ya shiga kwanonki" . Maganarta ta katse min tunanina. Murmushi kawai na yi, ba tare da na ce komai ba, lokaci daya kuma Ina kallon yadda take warware tuwan daga cikin leda zuwa kan tsabtataccen plate din gabanta Hankali kwance take cin tuwon har da santinta wai ta fi son tuwo ya yi tauri haka. A zuciyata na ce koma ba ki so ya kika iya haka nan za ki sassakeshi. Na mike tsaye hade da taba jikin Ramla da ke bacci "Zazzabin ma ya sauka, Allah ya sawake, bari in je daki" "Amin, na gode amarya na hadaki da aiki," "A'a ba komai wallahi, sau nawa ni kina shan wahalar aikinki ki zubo min in cinye." Dukkanmu muka yi karamar da dariya a daidai lokacin da nake fita daga dakin. "Wannan mata wane kalar mai da sabulu take wanka da shi ni Khadija?" Na fada a daidai lokacin da nake ficewa daga bangaren nata "Ga inda ya kamata in bata lokacina nan, wajen koyon sabulu da turare na je na bata shi a koyon girkin kasashen waje." A zuciyata na yi maganar hade da jan tsoki ina jin haushin kaina. Saman kujera na fada raina yana min babu dadi, Horn din da na ji ne ya sanya ni mikewa da sauri na nufi bedroom don na san maigidan ne ya dawo. Kuma fuskata ko mai ban shafa ba, bare ta kai ni ga kwalliya, shi ya sa faka-faka na yi kwalliyar hade da shiryawa cikin riga da siket na atamfa. Ina tsaka da Fess turare na ji knocking kofa a hankali, wannan ya tabbatar min da shi ne. Na fito cikin yauƙi, a zuciyata ina kiyasta yadda zan tare shi, irin tarar da kullum yake korafin ban yi mishi, yau dai ita zan yi mishi. Ganin hannunshi rike da Khalil ya sanya ni ja baya kadan, saboda na san ba zai so in rungume shi gaban yaron ba. Da murmushi a kan fuskarshi ya ce "Wata biyu da aure amma har yanzu kin kasa sakin jiki da ni, to sai yaushe?" Ban yi magana ba, illa kokarin danne kunyar da take taso min da na yi hade da fadin "sannu da zuwa" "Ban amsa ba ni wallahi" Ya fada cikin muryar shagwaba, hade da kankace idanunshi a kaina. Ba zan iya jurar kallon ba, dalilin da ya sa kenan na raba shi na wuce zuwa dinning table "Ki sauke min abincin a kasa" A kasan na aje mishi, na koma na zauna a kujerar da ke fuskantarshi. Ya daga hannayenshi sama yana kallona. Ni ma kallonshi nake kafin in gano me yake nufi. Mikewa na yi, na cire mishi babbar rigar da yar ciki, na aje a kan majinginar kujerar dinning. Sannan na zuba mishi tuwon hade da fruit salad. Rike hannuna da ya yi ne ina kokarin tashi ya sa na dakata ina kallonshi. "Ina za ki je? Ba za ki ci abincin ba ne?" "Zan ci" na amsa shi "To Bismillah mana" Na juya kan Khalil wanda hankalinshi kaf yana kan tv na ce "Khalil ba za ka ci tuwon ba kai?" Kai ya jinjin alamar eh. Yadda na ga Abbansu na dan murmushi, na fahimci ya ji dadin tayin da na yi wa Khalil din, haka muka rika ci tuwon a nutse hade da yin yar hira. Shi ma dai cewa ya yi na yi mishi tuwon da ya fi so mai tauri. Ban sani ba ko suna karfafa min gwiwa ne, ko kuma dai da gaske irin shi suke son oho. Bayan ya idar bedroom ya shiga, ni kuma na shiga tattare kayan da muka ci abincin na shigar kitchen. Daga nan kuma na bi bayan shi. Lokacin da na isa ya fito daga toilet da alama brush ya yi. Dalilin da ya sa mu ka hadu a tsakiyar dakin "Ina Khalil din?" ya fara tambaya ta "Yana falo" na amsa shi. "Ok" ya fada lokaci daya yana gyara hannun rigarshi Tare mu ka juya zuwa falon, sai dai babu Khalil, da alama ya tafi wurin Mommynshi "Ta shi mu je ki rakani wajen Auntynki in kara duba Ramla, in wuce ina da meeting karfe hudu" "Ka je kawai" na amsa shi "Me ya sa?" "Ba komai" "To idan ba komai tashi mu je" "A'a fa" na ce ina gyara kwanciyata a kan 3sitter "Ko ki tashi, ko in daga ki, wallahi sai a gabanta zan aje ki." Ban motsa ba kamar yadda ban yi magana ba. Ji kawai na yi ya yi sama da ni, hakan ya sa na fara dariya hade da kokarin sakkowa, amma ban samu damar yin hakan ba har zuwa lokacin da muka isa kofar sashinta. Na dire kasa ina dariya, shi ma dariyar yake a haka muka kwankwasa kofar falon nata. Khalil ne dai ya bude mana kofar, yayin da ita kuma Gimbiyar ke zaune a daya daga cikin kujerun falon Wando da riga ne a jikinta masu kalar ja, wandon iyakarshi gwiwa kamar skin tight yake, sai kuma rigarshi mai hannun vest da kwalliyar fulawa mai kyau a jikin rigar, cif kan kwankwasonta rigar ta tsaya, kuma ba ta matseta da yawa ba. A gabanta laptop din ta ce take daddanawa, ganinmu ne ya sanyata dagowa tana murmushi, idanuwanta a kan mijinta. Lokaci daya ta mika mishi hannu tana murmushi. Shi ma hannun ya mika mata fuskar shi dauke da murmushi, suka yi musabiha kamar dai wasu abokai. "Ya jikin Ramla?" ya tambaya a lokacin da yake kallon Ramlan da ke zaune a kan kekenta na yara "Da sauki sosai" Ta ba shi amsa ita ma tana kallon Ramlan. Hancin yarinyar ya ja, ita kuma ta wangale mishi baki. "Zan wuce office, ina da meeting karfe hudu, akwai wani abu ne?" "Babu, amma me kake so da dare?" "Abu mara nauyi, don kanwarki ta cika min ciki da tuwo" Murmushi ta yi "Ta kyauta kuwa" "Zan tafi. Waye zai raka ni?" "Wacce ta rakoka nan" Ta yi saurin fada, babu alamar wata damuwa a kan fuskarta. Gardama sosai muka shiga yi, daga karshe dai na mike hade da bin bayanshi. Bayan ya daidaita a mazauni ne ya kalleni idanuwanshi a kankance "A ba ni bye- bye" Na janye fuskata a kan tashi ina siririn murmushi "Sarkin kunya." ya fada Ban yi magana ba, sai dai na mayar da kallona kanshi, a lokacin da na ji ya kama hannuna yana murzawa "Ba zan daina fada miki ba Khadija, ina sonki, akwai abubuwa masu nagarta da yawa a tare da ke, na san ke ba ki sansu ba, amma ni na san da su" Shiru na yi ina mamakin bakin ganga irin nashi, kullum yabon matarshi yake, sau tari ma idan na yi abu sai ya ce wance ba haka take yi ba. "To idan haka ne me ye nawa yake burgeshi, kodai ya fada ne kawai don ya ji dadi? Ni wani lokaci ma rikita ni suke yi shi da matarshi, in rasa ina ne gabansu" A zuciyata na yi maganar a zahiri kuma kallonshi kawai nake yi, ba tare da na yi niyyar magana ba Juya hannun nawa ya yi, yana kallon bayan hannun kamar mai son gano wani abu. Ganin ina niyyar janyewa ne ya sa shi kai hannun nawa a bakinshi ya sum bata a hankali. Tare muka lumshe idanu, ya saki hannu hade da murza key din da ke jikin motar. Na ja baya a hankali hade da rufe mishi kofar, sai da ya fice na dawo dakina, zama na yi zuciyata cike da sake-sake. Ni dai ba zan ce bama zaman lafiya ba, amma na san abubuwa ba su zo mun yadda na tsara ko nake hasashe ba. Kodayake yanzu aka fara tafiyar, kila rawar ta canja a gaba. Matar J✍🏻 [12/16, 11:56] 08080966571: *HASASHENA* *Page 3* A tsarin gidan shi ne, ranar da miji zai bar ɗakinki, ke za ki yi abincin dare, sai ya ci sannan ya baro dakin. Don haka yau Maman Khalil za ta miko min Abbansu Khalil, shi ya sa tun da na idar da sallahr isha'i na shirya cikin (English wears) da suka yi matukar karbar jikina. Ni ma yau so nike in burgeshi, in nuna mishi ni ma fa duk abin da matarshi ta iya na iya kuma zan iya. Riga da wando ne, masu kalar ruwan madara, wandon dogo ne har kasa bai kamani sosai ba, rigar guntuwa mai siririn hannu da ta zauna kan kwankwaso na. Na kama gashina na matse da ribbon mai kalar far. Na dawo falo na kame ina jiran dawowarshi. Ba jimawa kuwa na ji horn din shi, Ina jin lokacin da maigadi ya bude mishi, shi ya sa na yaye labulen windown falona ina kallon shi, har shige part din matarshi. Zaunawa na yi, zaman jiran tsammani, na san dai ba zai wuce awa daya a can ba. Sai dai sama da awa biyu, ban ji duriyarshi ba. Duk yadda na so danne zuciyata abun ya ci tura. Saboda yadda ya dade din, bai taba dadewa haka ba, bayan kuma ba aikinta ba ne. Haka kuma idan aikin ta ne ba ya jimawa a wurina yake fita, Sometimes ma Idan ya dawo Sai ya leka bangarenta, sannan ya taho nawa, koda kuwa a dakinta zai kwana. Amma ni yanzu ga shi har goma saura bai shigo ba turare sai fesawa nake da gyara powder amma shiru har na gaji. Ba abun haushi irin ka yi abu don mutum kuma bai gani ba. "Allah ma ya kara min! Da na auri saurayi babu abin da zai hada ni da wannan takaicin. Duk inda yake da abin da yake yi hankalinsa dai yana kaina. Amma yanzu yaransa sune farko sai uwar yaransa kafin ni in biyo baya." Kai karshen tunanina ya yi daidai da jin karar bude gate, Sai kuma na ji tashin motarshi, wannan ya tabbatar min da fita suka yi. Na ja tsoki hade da mikewa zuwa doguwar kujera na kwanta. Raina a matukar ɓace Tun ina tuna banza da wofi har bacci ya dauke ni. A cikin bacci na ji kamar ana jan kafata, dalilin da ya sa kenan na bude idanuwana a hankali cikin yanayin bacci na zubasu a kanshi. " Da ace ɗana ne, da kawai mari masu zafi zan wanke fuskarshi da su" A zuciyata nake saka wannan amma a zahiri, kuma lumshe idanuna na yi. "Bacci kike yi?" "A'a rawa nake yi" a zuciyata na kuma yin maganar. Amma a zahiri ko idona ma ban bude ba, bare ya yi tunanin zan ba shi amsa. Ina jin shi ya wuce wurin abincin da na shirya mishi, na yi amfani da damar wajen kallon agogon da ke falona, karfe shadaya saura. Wani gululu ya tsaya min a kirji duk kwalliyar da na yi, ta tafi a banza kenan bai gani ba. Mikewa na yi cikin yanayin bacci na nufi bedroom "Daga karshe dai na ga kwalliyar" ya fada a daidai lokacin da ya mike tare da nufo inda nake Da sauri na shige bedroom, amma sai da ya cimma ni "Ba za ki cire wannan kwalliyar ba, kin yi kyau kuma na yaba, na gode sosai" "Ba za ki ce komai ba?" ya tambaya ganin ba ni da niyyar magana "To me zan ce?" "Abin da ke ranki." "Ai babu komai" ina kokarin zama gefen gado na yi maganar. Shi ma zaman ya yi kusa da ni "Ki yi hakuri, wallahi Affan ne ba lafiya muka kai shi asibiti" Ai dama na san tatsuniyar gizo ba ta wuce koki. Kullum cikin hidimar yaranshi da ta matarshi yake. Ni kuma ko oho. Ko yaushe ma Affan din ya dawo oho. Saboda tun last week ya je hutu gidan kawar Mamanshi, daga can ake kai shi makaranta, a kuma dakko shi "Allah ya ba shi lafiya" Na yi maganar daidai lokacin da nake kwanciya. Don gaskiya na kasa dannewa. A yanayinsa na ga kamar bai ji dadin yadda na karbi abun ba, ta hanyar nuna halin ko in kula, amma ni bai dame ni ba, don gaskiya na fara gajiya da yadda yaranshi da kuma matarsa ke shiga lokacina. Bayi ya shiga, ya yi wanka, na dauka ba zai neme ni ba, sai kuma na ga ya yi hakan, duk da ni ban bayar da hadin kai dari bisa dari ba. Don har zuwa lokacin zuciyata zafi take yi. Ni ce na tashe shi zuwa masallaci sallahr asuba. Ni ma kitchen na shiga bayan na idar da sallah, doya na fere, yam balls nake son yi. A nutse nake yin aikina duk da dai bana jin dadin zuciyata Don ma Bashir mutum ne da ya san mace, sosai ya tafiyar da kashi saba'in cikin dari na damuwata a daren jiya. Sai dai yadda har yanzu da agogo ya nuna karfe bakwai na safe bai fito daga sashenta ba, kuma yana dawowa masallaci ya shiga bangaren nata. Yana kara tunzura min zuciya. Ni ba haka yake yi min ba. Yana shigowa ya dade 30mns. Wani lokacin ma sai ya yi shirin office kafin ya leko ni "Kai!!!" Na ji an fada a bayana, da sauri na saki cokalin da nake kwashe yam balls din cikin Mai, lokaci daya kuma na zabura bayan na saki siririyar kara Da sauri ya rike ni yana dariya "Wallahi kin faye tsoro, to waye zai shigo har nan ya ba ki tsoro idan ba ni ba?" "To dana san waye zai shigo din zan tsorata ne." Na ba shi amsa ina harararshi cikin fuskata mai nuna alamun shagwaba. "Uhhhhhhh! Kamshin dadi" ya fada yana bubbude hancinshi An yaba kaza mika, ta ce ga cinya Sai na ji kaina ya yi fadi, kamar kitchen din ba zai daukeshi ba. "Maman Khalil ta tashi ne?" "Eh" ya ban amsa a lokacin da yake tsoma dunkulalliyar doya cikin kwai cike da kwarewa "Ka iya girki fa" "Maman Khalil ta koya min abinci da yawa ai, da ta tare muke shiga kitchen lokacin aiki bai yi min yawa ba" "Ai fa" na fada a zuciyata a zahiri kuma cewa na yi "Ta kyauta" "Zan dubo Affan ne, in bar ma kitchen din a hannunka?" "Eh je ki dubo shi, zan kula da komai" "Na gode" A corridor muka hadu da ita, hannunta rike da lunch box guda biyu ta fito daga kitchen. Sanye take cikin farar doguwar riga da aka yi mata a don duwatsu masu kyau. Kamshinta mai dadi da kama jiki har yanzu yana manne da ko ina na dakin nata gami da jikinta "Barka da safiya amarya, Allah ya sa ba hukuntani kika zo yi ba, jiya da yau duk na rike miki miji." Cikin murmushi take maganar lokaci daya kuma tana tafiya zuwa ainihin falonta "Yarona na zo gani." Ni ma cikin dariyar karfin hali na yi maganar. Yaran sanye cikin kayan makarantarsu gwanin sha'awa, dalilin da ya sa kenan ma na fitar da wayata na yi masu hotuna, don gaskiya sun burgeni tana kokari wajen gyara yaranta. "Wai har Affan din ma makarantar zai je?" Na yi tambayar ina kallonta "To ya matsa sai ya je, shi ne Babanshi ya yi masu wanka ya shiryasu" Ta fada a lokacin da take ba Affan magani. "Kenan tun dazu da ya shigo yaranshi yake shiryawa" na yi maganar a zuciyata, saboda ganin ba abin da nake zargi ba ne, duk lokacin da zai zauna a dakinta, kawai ji nake soyayya suke yi. Tare muka fito da ita bayan ta gama shirinta da yaranta. Hannuna daya na yi amfani da shi na bude wa yaran mota suka shiga Bayan ta daidaita zamanta ne na dora mata Ramla a kan cinyarta. Na dan ja kumatun yarinyar ina fadin "Ki yo min tsaraba." ta wangale bakinta mai dauke da hakora hudu, kamar ta ji abin da na fada. "Ki dauketa ta zauna da ke?" Cikin tsokana ta yi maganar "Ashe zan biyo ki yau" Mu ka yi dariya dukkanmu lokaci daya kuma ta murza kan mota cikin kwarewa ta yi hanyar fita. Mamaki na yi sosai ganin yadda ya gyare kitchen din tsab kamar dai ni ce na gyara shi Ina mamakin irin saukin kanshi, da kuma yadda yake yanke shekarunshi su daidaita da nawa idan muna tare. Alhaji Bashir Balarabe Ruma, dan asalin jihar Katsina ne a karamar hukumar Batsari kuma a kauyen Ruma. Mutum ne mai saukin hali, iya mu'amala da juriya a kan duk abin da ya sa gaba. Yana da ilmi mai zurfi a ko wane bangaren sannan ya kan yi amfani da ilmin nashi ta hanyar da ta dace. Yana aiki da ma'aikatar fansho ta kasa, sannan yana kasuwanci na sayi da sayarwa, bugu da kari babban manomi ne a kauyensu. Shekarunshi zasu kai arba'in zuwa da daya in da yake da yara uku biyu maza sai mace daya wacce matarshi Sakeena ta haifa mishi. Mace mai kokarin boye damuwarta, iya zama da mutane kawar da kai hade da kawaici. Tana da ilmi sosai musamman na addini, don har yanzu Sakeena na zuwa Islamiya Asabar da kuma Lahadi, a ilmin zamani kuwa tana da degree ne a bangaren education, tana matsayin vice principal a Wata makarantar private da ke cikin garin Abuja. Ita ma yar asalin garin Ruma ce, kila shi ya sa wani lokaci nake ganin kamar suna kama da mijinta. Alhaji Bashir Ruma, dogo ne mai matsakaicin jiki, sannan yana da hasken fata da take nuna irin jin dadin da yake ciki, yana da matsakaicin gemu da saje wanda ya zagaye fuskarshi ya kuma kara mata kyau da cikar haiba Tsagenshi na rumawa wato biyu-biyu a gefen kunnensa ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba. Ita ma Sakeena haka yanayin jikinta yake, duk da yar kibarta mai ban sha'awa ta kan rage tsawon nata. Yanayin hasken fatarsu daya da mijinta, zanen fuskarsu ma daya, bambancin kawai nata ya fi fita sosai da kuma yi mata kyau. Ni kaina zanen nata burgeni ya ke sosai, yaranta uku babu wanda ba a yiwa zanen ba. Su ma sosai zanen ya yi musu kyau. Musamman Ramlah Yau dai wannan ranar tawa ce don kuwa Bashir wunin ranar zuwa masallaci ne kawai ke fitar da shi, saboda koda su Maman Khalil suka dawo bai yi cikakken mintuna talatin tare da su ba. Ga shi yaran babu wanda ya zo part dina, har suka wuce Islamiya. . Maganar irin farin cikin dana tsinci kaina a wannan ranar ma ba zai misilti ba. Na rika jin, ina ma ace kullum hakan ne ke faruwa. ina ma ni kawai ce da Bashir , lallai dana mori rayuwar amarcina, na aje tarihi mai yawa kuma mai dadin bayarwa. Karfe takwas na dare na fito cikin kwalliyata dana tabbatar za ta ja hankalin mijina. Riga ce mai laushi baka, ta wuce gwiwa kadan tana da siririn hannu, yau so nake in ba shi mamaki. Sai da na tabbatar ko ina dake bangaren nawa ya yi fes ga kamshi mai dadi mara hawa kai. Sai dai me? Yana dawowa masallaci ya zarce bangaren Gimbiyar tashi. Yau ne, gobe ne har goman dare bai shigo ba, ɗan baccin ma da nake yi da, idan haka ta faru yau kam kwata-kwata na kasa yi, zuciyata tafasa kawai take yi, ina kuma shirya irin yadda zan nuna mishi bacin raina. Matar J ✍🏻 [12/16, 12:06] 08080966571: *HASASHENA* *Page 4* Duk yadda na kumbura fam ina jiran shi, lokacin da ya shigo sai na ka sa aiwatar da komai, idan ka dauke zumbure-zumburen baki da na rika yi. Kila shi ya sa komai bai ce ba, ya nemi makwancinsa. Hakan kuma ba karamin kara bata min rai ya yi ba. Shi ya na yi kuka mai yawa kafin bacci ya yi awon gaba da ni. Da safe ma haka nan nai ta ayyuka rai babu dadi, ya kuma lura da hakan sai dai sam bai tambaye ni ba, ni ma kuma na shareshi A haka muka gama kwanakinmu biyu tare da shi, ya koma dakin gimbiyarsa. Ranar da ya koma ɗakinta, zaune nake a gaban TV da misalin karfe biyar na yamma , Sai dai hankalina sam baya gurin TV din. Shawarar yadda zan bullo wa matsalata nake yi. Kila wani zai ga ba abun damuwa ba ne, amma ni gaskiya ni yana ci min rai,, kamar kashin wuya haka ya tsaya min. Yau da yake a dakinta yake, tun 10am da ya leko ni bana jin ma ya yi 10mns masu kyau ya fita har yanzu ko keyarsa ban kara gani ba. Kila ko don ya ga ina fushi ne oho. Idan ma haka ne ai kamata ya yi ya lallashe ni, ba wai ya yi banza da ni ba. "Mtswww!" na ja dogon tsoki, lokacin da na tuna yadda yake sintiri ɗakinta, idan har yana dakina ne to ka'ida ne ya ziyarci matarshi sau uku a rana koma fiye. Amma ni yau sau daya na samu ya leko ni. "Gaskiya dole in yi mishi magana tun kafin matsalar ta girmama" Na fada a zuciyata hade da gyara zamana. Lokaci daya kuma wayata na janyo hade da kiran Badiyya. Cikin sa a kuwa ta daga. Muka gaisa, sannan na shiga kora mata abun da ke damuna. Cikin rashin jin dadi na ce "Kawata kar ki ce na faye korafi, amma wlh auran nan ya fita a kaina. Haka auran mai mata yake ne? Daga wannan problems din sai wannan?" Cikin salon kwantar da hankali Badiyya ta ce "Haka zaman aure ya gada Khadija, musamman mu masu abokiyar zama, don haka hakuri za ki yi, wadanda suke su kadai ma haka suke fama. Kuma na sha fada miki hakan ai." Cikin dacin zuciya na ce "Nawa ya zo daban Badiyya, abin da na sani Amarya mai irin kwanakina bai kamata ace ta fara fuskantar irin abin da nake fuskanta ba, kiri-kiri fa yake nuna son matarshi a gabana. Ni na ma rasa dalilin da ya sa ya auro ni" Yanzu kam gajeruwar dariya ta yi hade da fadin "Kauna mana ta sa ya auro ki" "Gaskiya ban yarda ba, shi dai kawai ya auro ni don ya rika bata min rai" na ba ta amsa. Kafin ta ce wani abu na kuma na cewa "Wai kin ga matarshi kuwa Badiyya, wlh kyakkyawa, wayayya ta sha boko ta koshi, Sai kin ganta komai na ta a can-a can" Wata dariya ta kuma yi kafin ta ce "To da ya kike son ganin ta? Wata mummuna kucaka?" "Ni dai abin da na dauka kawai shi ne amarya dole ta fi uwargida da wasu abubuwan, kuma miji ya fi son ta. Ba haka muke karantawa a littafi ba. Uwargida mai baƙin hali, Sai a auro amarya ta kwace gida?" Yanzu kam dariya ta yi sosai, kafin ta ce "Khadija tawa, au dama haka shi ne HASASHEN KI? to bari ki ji, rayuwar auran novel daban, ta zahiri ma daban, sau nawa za ki ga uwargida mummuna ko mai bakin hali, amma kuma mijinta sonta yake ba ya son laifin ta, sau nawa kuma uwargida ke korar amarya? Ke dai sa a dai kawai." Buga kofar ne ya dakatar da ni ba Badiyya amsa, na ce mata" Yi hakuri ina zuwa." na yi maganar hade da yanke kiran. Lokaci daya kuma shiga bedroom da sauri, soson powder na dauka hade da shafawa a fuskata na kara fesa turare sannan na fito. Khalil na gani tsaye a lokacin da na bude kofar Wani haushi gami da takaici suka tokare min wuya duk zatona Babanshi ne. "Momyna ce ta ce ki zo" ya fada tun kafin in tambayeshi Kamar ba zan ce komai ba, Sai kuma na ce na ce 'jira ni, ina zuwa"na kai karshen maganar hade da komawa cikin daki, na dora ƙaramin farin Hijab a kan bakar rigar da ke jikina. Hannunshi a cikin nawa muka shiga falon hade da sallama. Kishingide yake cikin kaya kamar na sports masu kalar light blue , wandon ya dan wuce gwiwa kadan, sai riga mai yankakken hannu. Ita kuma gimbiyar bakin wando ne dogo har kasa, kasan wandon ya dan bude kadan, can saman wandon daidai kwankoso duwatsu ne masu kyau aka yi ma wandon kwalliya dasu. Sai farar rigar T- shirt mai budadden gaba. Wanda rabin kirjinta duk a waje yake. Ko hasadun iza hasadun ba zai ce ba ta yi kyau ba. Kishin ta sosai ya kama ni, wannan zukekiyar mace a gaban mijina, to ni me zan nuna mishi? Don kayan sun karbeta sosai, sun fito mata da surar jikinta, musamman manyan hips nata masu daukar hankali. Ramla na dauka hade da neman guri na zauna, bayan na gaishesu. A zuciyata kuma cewa nake "Ko me ya sa suka kira ni?, wani lokaci sai in ga kamar da gayya suke min abubuwa" "Dama zamu fita ne idan babu abin da kike yi" Ta yi maganar hankalinta a kaina Na dakata da yi wa Ramla wasa "Zuwa ina?" "Store. Kin san bikin kanen Baban Khalil sati biyu masu zuwa ne, ya kamata mu je siyayya kafin lokaci ya kure" Kamar in ce ba zan je ba na ji, don da alama sai da suka gama tsara komai sannan aka neme ni, ni dai na zama yar kallo ko me sai dai in ji ana yi, ko in gani. "Wai haka auran mai mata yake?" na yi tambayar a zuciyata Amma a zahiri sai na nuna kamar dama na san da maganar bikin, ba a bakinta ne na fara ji ba. Na ga alamar ni ma sai na fara dagewa "Je ki shirya to, ni ma bari in shirya kafin ki fito" "To" na fada lokacin da na mike hade da aje Ramla a kan cikin Babanta, da yake kishingide yana jin maganarmu. Kamar bai san damu ba, saboda ko sau daya bai sanya mana baki ba Tsawon minti uku na rasa kayan da zan sanya, daga karshe dai zabina ya fada a kan doguwar rigar shadda mai ruwan toka (light ash) ta sha aiki daga sama har kasa Ni kaina bayan na saka rigar dana kalli kaina a madubi sai da na ba kaina maki mai yawan gaske. Musamman daurin dankwalina ture ka ga tsiya da ya zauna das a kan goshina, jelar kitsona daya na zaro na saketa a kan dogon wuyana Na dora sarkata ash mai tafe da agogo da zobe, farin mayafi da takalmi na yi amfani dasu, sai farar karamar jaka mai doguwar igiya. Humrah kawai na shafa, na nufi bangaren Maman Khalil Ita ma cikin riga da siket take na Lace mai kalar coffee, ta nada daurin dankwali na zamani, wuyanta, sanye da wata tafkekiyar sarka mai hade da yan hannu da zobuna. Gaskiya ta yi kyau, sai na ga ma kamar ta fi ni, kasancewar ita kayan sun fitar mata da dirinta sosai. Ni kuwa a sama ne kawai rigar ta dan kama ni. Hotuna yake mata, wani ita da Ramla da yaran, wani kuma ita kadai. Ganina ne ya sanya shi juyowa yana fadin "Wow! Wow!! Wow!!! Wannan amaryar tawa ta yi kyau Maman Khalil, ba ta taba yin kyau ma irin na yau ba, kalleta ki gani" Juyowa ta yi tana dariya sosai, babu alamar damuwa a kan fuskarta ta ce, "Lallai Abban Khalil, wallahi ka yi na kudinka. Wato ba ta taba kyau ba irin na yau, me kake nufi to?" "Nufina ba kwa kwalliya sai zaku fita" "Kenan duk kwalliyar da nake a baya ba kwalliya ba ce, kuma ban yi kyau ba, haka nan yake cewa na yi kyau" zancen zuci daga gare ni kenan, a, zahiri kuma yaƙe nake yi, gani nake kamar ya ci kin fuska a gabanta Ita kuma Ido ta zaro hade da kallona kafin ta ce "Kin ji me ya fada kuwa?" Ban yi magana ba illa murmushi kawai da na yi. "Kana nufin har ni?" ta tambayeshi cikin sigar shagwaba "Ban da ke" Ya yi maganar da muryar rada. Tuni kishi ya kasheni a inda nake zaune. Dalilin da ya sa kenan na Mike tare da nufar kofa. "Ina kuma za ki je?" Ya yi saurin dakatar da ni "Guri zan ba ku, ku yi soyayyarku da kyau" Na yi maganar a zuciyata Amma a zahiri tsayawa na yi ina kallonshi Da alama ya harbo jirgina, don haka sai ya share yana fadin "Zo in yi maku hoto mana kafin ku tafi" Ban yi gardama ba, na je ya yi ta mana hoton kala-kala wani da yara, wani ni da ita, wani kuma ni kadai. "Alhamdulillahi! Allah na gode maka da ka ba ni ahli kyawawa masu lafiya" Haka yake ta fada a lokacin da yake mana hoton. Ni ce na dauki Ramla lokacin da zamu fita, kuma har a cikin store din ni ce nake rike da ita. Yayin da Sakeena ke zabar kaya masu kyau da tsada Lace kala biyu, shadda biyu sai atamfa kala daya. Gyale kala biyu, hijab daya sai takalma da sarkoki, dukkansu iri daya ne. Sannan ta koma bangaren kayan yara, nan ma ta zabi masu kyau da tsada. A ka yi total ta biya, sannan aka rako mu dasu har mota. Ni dai mamaki nake yi hade da tambayar kaina "Dama haka ake yi ne? Kudin ma ba za a ba ni nawa ba in sayi abun da nake so sai dai a ba wata, ya suke son mayar da ni kamar wacce ba ta da ra'ayi ne?" Har muka isa gida magana kawai nake, amma hankalina baya tare da ni, ni ma so nake ya zama ina cin gashin kaina, bawai gashin wata ba, ya kamata kuma in magantu a kan hakan. Muna isa gida bangarena na wuce, ko kyalle ban dauka ba, kuma ban tayata shigarwa ba, tun da dai ta ce ta ji ta gani, ai shigarwar ma ba zai gagareta ba. Wanshekare misalin bakwai da rabi na ji buga kofa. Ita ce na gani tsaye da ledar kayan da muka siyo jiya. "Zan tafi gurin aiki ne, na yi magana da tela zai zo ya karbi kayan nan ya dinka, sai ki ba shi measurements naki." "OK." Na fada hade da amasar kayan, lokaci guda kuma ina gaisheta. Wata leda ta miko min "Ga sauran kayanki nan" "OK to na gode" Ta kuma zuge karamar jakar da ke hannunta, kudi ta zaro hade da kirgawa. "Yauwa! Wannan ragowar canjinki ne na siyayyar da muka yi jiya" Na kuma sanya hannu na karba, tare da fadin "na gode" Aje kayan na yi hade da kara bude su ina kallonsu daya bayan daya, sun yi kyau kam sosai musamman lace din, ta iya zabe. Kudin da ta ba ni ne na kirga, dubu tara da dari da hamsin. Wani lokaci na kan rasa kan matar nan, kamar dai tana zaune da ni tsakaninta da Allah da kuma zuciya daya. Wani lokaci kuma in ga kamar munafurci ne irin na mata. Koma dai menene na kusa fashe kwan in ga zahirinshi. *MATAR J* [12/16, 14:10] 08080966571: *HASASHENA* *Page 5* Misalin karfe goma na safe kuwa sai ga telan ya iso, tape ya ba ni, na rika auna duk inda yake son na auna, yana rubutawa sannan ya tafi. Gidan ya kasance shiru sai ni kadai da bacin raina, saboda ko yau da safe Abban Khalil ya shigo bai ba ni fuskar da zan yi mishi korafi ba. Ya dai dan yi romancing nawa sama-sama ya fice, saboda ana ta kiranshi a waya, alamar ana jiranshi. Maman Khalil kam sai 2pm ta dawo kamar, kullum tun da ta shige part din ta da yaranta kuma ban kara jin duriyarsu ba. Abban Khalil kuma sai gab magriba ya dawo, shi ya sa bai shigo dakina ba sai 9pm, yadda na hade fuska ya sanya bai jima ba ya fice. Haka zaman ya ci gaba da gudana, ni da shi sama-sama, yayin da Maman Khalil ke ta shirin biki. Atoh ta ke shiri mana, ni shirin me zan yi, ban san kowa ba, kowa kuma bai sanni ba. Ni ko waya ba ma yi dasu, ita kam kullum suna kan waya, idan ma ba ta kira ba, su kam za su kira. Ni kuma sai idan Abban Khalil ya kira su, aka yi sa a muna tare ya ba ni mu gaisa. Ranar Alhamis muka isa garin Ruma da misalin karfe biyar na yamma. Gidanmu na Ruman muka fara sauka, komai a gyare. Flat dinmun a jere yake ba kamar na Abuja ba da ya kasance kowa da bangarenshi. Babu wani tarkace a cikin dakin, idan ka dauke kayan amfani da mutum zai bukata a ko wane lokaci. Babu aikin da mu ka yi lokacin da muka isa, idan ka dauke wanka da cin abinci, Sai kuma jefi-jefi da mutane ke shigowa suna mana sannu da zuwa. Da yawansu kuma ƴan'uwanta ne, da kuma ƴan'uwan Abban Khalil da suke danyen ganye. Karfe takwas na dare ta yi min maganar zuwa cikin gida (Gidan iyayen Bashir) Na gaji sosai, kamar in ce ta je, amma tsoron baki ya sa na bi ta. Saboda tun da muka zo din ma ba hutawa mu ka yi ba, wannan ya fita wannan ya shiga. Don ma ni ba mu saba sosai ba, iyakata dasu gaisuwa sai su wuce wajen Maman Khalil. Koda muka shiga cikin gidan ma dai gaisuwar ce kawai, ita kuwa tun da ta aje ni dakin mamar mijinmu ta yi cikin gida kasancewar babban gida ne, ban sake ganinta ba sai da na sanya aka nemota saboda baccin da ke ci na. Da kyar na isa gida, dama mijin ba nawa ba ne, don haka baccin gajiya kawai na hau yi. Safiyar juma'a aka tashi da aikace-aikace kasancewar za a yi walima da yamma. Maman Khalil kam ba zama, komai ita ce a kan gaba, duk wani abu da ake so ko shawara da ita ake yi, duk abin da ake nema to ita ake tambaya, idan ma yi za a yi sai ta bayar da izni. Ni kuwa kallonta kawai nake yadda take ta kaiwa da komawa ba tare da gajiwa ko kosawa ba. Kamar ba ita ce matar Bashir Balarabe Ruma ba, matar nan mai tsantsar tsabta kula da kanta da kuma yaranta Matar nan da take zaune a daki mai A. C da fankacecen gado mai dauke da lumtsumemiyar katifa ba. Matar nan mai hawa mota da daura zannuwa masu tsada. Matar da idan ka yi mata kallo daya sai ka ga kamar ba za ta iya kwana rufin kasa ba. Ko mu'amala da ƴan kauye ba, irin haka ba Amma ta manta duk wadancan abubuwan ta zage da ita ake ta dorawa ana saukewa babu wani girman kai. Duk da dai asalinta yar garin ce hakan ba zai hana ta bambanta kanta da wasu ba da wata ce. Abin da na fahimta shi ne sosai take da fada a dangin mijin nan, abu ne mai matukar wahala kafin in samu fada kamar tata balle ma in wuce ta. Idan kuwa har na kasa samun hakan, to gaskiya a bazance zasu rika kallona. Sannan ba zan yi wani tasiri ba. Saboda ko yanzu din ma iyakaci na da su gaisuwa, amma wata shewa da tattaunawa duk da Maman Khalil ne "Kai!" Na fada hade da dafe kaina. Sosai akwai aiki a gaba, ta ina ma zan fara ne? Kokarin janyo hankalin mijina Karbar 'yancina ta yadda zan rika cin gashin kaina Kafa fadata a zuciyar mijina ta yadda ni ma kominshi zan rika sani, haka komai zai yi in sani ya kuma yi shawara da ni Ko Neman fada a wajen dangin mijina. "Cikin wadannan da wanne zan fara ne?" Na yi maganar a hankali ina kallon mutanen cikin gidan da suke ta sabgoginsu cikin farin ciki da annashuwa. "Wallahi duk macen da ta yi aure, kuma ba ta da kishiya to kamar tana kan gadon mamanta ne a kwance" Na kuma fada a zahiri. Ai tarin kalubale yana ga macen da ta auri mai mata, ni ban san haka abun yake ba, ai da ban je fa kaina a ciki ba, sai in samu saurayina mai dan rufin asiri in aura mu je mu zauna hankali kwance, duk inda yake me yake hankalinshi na kaina. Kodai ya dakko wata daga baya na san zuwa lokacin na yi mata fintinkau, kamar yadda Maman Khalil ta yi min. Misalin karfe biyar na yamma duk an hallara a farfajiyar gidanmu, a can za a yi walimar Rumfuna ne manya guda shida, jere da kujeru gwanin sha'awa. Kowa ka kalla fuskarshi cike da annuri, da yawan mutanen da ke gurin hijabai ne manya a jikinsu wasu ma har da nikab. Ina jin dalilin da ya sa kenan Maman Khalil ta siya mana hijabai. Zaune nake kusa da Maman Khalil kominmu irin daya, Ramla na kan cinyata su Khalil kuwa suna gurin Babansu. Karewa jama'ar gurin kallo nake yi Maganar gaskiya mutanen garin sun burgeni, akwai su da kara iya mu'amala da rikon addini, son zumunci, uwa uba ilmi zamani dana addini. Ashe al'adarsu ce hakan shi ya sa Maman Khalil ita ma duk ta hadasu. Babu abin da ke burgeni irin yadda kowannensu maza da mata, yaro da babba fuskarsa ke dauke da zanen biyu-biyu (11-11) a gefen kunensu, wasu kuma a kan kumatunsu . Sai na ji kamar ni ma in je in zauna a yi min, in shiga layinsu, na rika ji na daban, kamar wata gayyar sodi. Zanen ba ƙaramin karbinsu ya yi ba, kamar ma shi ne ke kara masu kyau, don gaskiya jama'ar garin Ruma kyawawa ne, ni tun da na zo ban ga wani, wanda muninshi ya kai muni ba Tubarakhallah. Mun sha wa'azi kam da nasiha a kan zaman aure masu ratsa zuciya. In da aka zayyano hakkin namiji a kan matarsa da hakkin mata a kan mijinta. Darajar aure da kuma bambanci da ke tsakanin ibadar matar aure da wacce ba ta da aure. Ana kiran sallahr magriba aka tashi daga walimar wasu ma duk a gidanmu suka yi sallah. Bamu samu damar komawa cikin gida ba, saboda gajiya ga kuma baki har da wadanda zasu kwana a gidanmu. Hatta Amaryar ma da tawagar kawayenta a gidanmu zasu kwana. Kila shi ya sa Abbansu bai samu damar kebewa da ni ba, kasancewar ni ce mai girki. Ni ma na ji dadin hakan, ko ba komai na dan huta. Gari na wayewa Maman Khalil, ta kuma ja na zuwa cikin gida, maganar gaskiya na gaji, kan dole na bi ta. Ni kam ba zan iya wannan zirga-zirgar ba. Sam ban saba ba. Yadda na ga ana ta hada-hada ina raɓe kamar kareriya ya sanya ni kutsa kai cikin su, ni ce daka kayan miya wanke-wanke, yan kananun aiki dai sai in karbe in yi. Kuma sai na ga hakan yana masu dadi. Har wasu sun fara sakin jiki da ni. A zuciyata na ce "ashe haka abun yake, to ai shi kenan, za mu ci gaba da jarabawa" Shawara ce dai ba da ni ake yi ba, sai dai Maman Khalil. "Ko yaushe ni ma za a fara shawarar da ni oho? Ko yaushe zan zama kamar ita?" Wadannan duk tambayoyi ne da ni ba ni da amsarsu. Ban san kuma ranar samun amsar tasu ba Haka muka ci gaba da hidimar biki cikin farin ciki da annushuwa, ranar Juma'a aka daura aure, misalin karfe hudu na yamma aka raka amare dakin su, daga can kuma aka wuce dinner, bamu dawo gida ba dai sai kar 11pm na dare. Safiyar Asabar kuma Maman Khalil ta ja nigidansu mu ka wuni, don gobe Sunday za ta wuce abuja. Na ga karamci kam, na yarda Katsinawa na kara, saboda na ganta da idona ba labari ba. Mahaifiyar Sakeena zam Sakeena, da alama halayenta kaf ta dakko, akwai karamci da kawaici, duk abin da ta ba Maman Khaleel ni ma sai da ta ba ni. Haka mu ka wuni gwanin daɗi cikin ƴan'uwanta, babu kyara ko kallon banza. Ban taba tsammanin haka daga gare su ba, saboda tun ban saki jiki da su ba, har sai da suka sanya na saki jikin dasu. Abin da na fahimta tana da kyakkyawar alaka da kowa. Sam ba ta da girman kai. Sai da aka yi sallahr magriba muka dawo, bayan mun yi sallahr isha'i, na taya ta hada kayanta, Sai, wajen 10pm ɗai muka kwanta. Asubar fari kuma Abban Khalil ya kai ta Katsina, daga can ta hau motor Abuja. Sai kuma na ji gidan shiru babu dadi, kaɗaici ya yi min yawa, in kwanta in tashi, ban warware ba sai da Abban Khalil ya dawo gida. *Matar J* [12/16, 14:16] 08080966571: *HASHENA* *Page 6* Tun ina jin rashin dadi gami da tafiyarta, har na warware, na rika cin duniya ta da tsinke. Ji nake kamar kar mu koma Abuja mu yi zamanmu a nan, sosai yake ba ni kulawa da yin duk wani abu da nake so. Duk da dai a rana sai ya yi waya da matarshi da yaranshi ya kai sau goma, tana fada mishi wai sun yi kewarshi, shi din ma haka yake fada masu. Ni kuma ga kishi sai zuciyata duk ta baci, daurewa kawai nake yi, wani lokaci kuma na kasa daurewa har sai ya gane a fuskata amma baya nuna ya gane. Haka dai muka kwashe sati biyu a Ruma kafin muka fara shirin komawa gida Abuja. Tarkace masu yawa maman mijina ta ba ni wai in kaiwa Maman Khalil abin da take so ne, haka ma daga gidansu aka aiko da sako wai in kai mata. Ya na iya, haka na runguma mu ka yi sallama da su na dakko hanyar kano ni da mijina, inda zamu kwana a kanon da safe mu bi jirgin karfe hudu zuwa Abuja. Shi ɗaki ya kama a hotel, yayin da ni kuma na nufi gidanmu, wanda shi ne karon farko na zuwana bayan aurena. Na sha tarba kam, kowa murnar ganina yake, sannan kowa cewa yake na canza jikina ya yi kyau duk da dai ban yi wata kiba ba. Ni kam sai baki na washewa, sincerely speaking na ji dadin zuwa gida, wani irin farin ciki nake ji mara misultuwa. Ban samu damar keɓewa da Ummata ba sai karfe goma na dare. Hira muke sosai, da yawan hirar kuma a kan zamantakewar yau da kullum ce. Cikin nuna kulawa ta ce "To ya zamanku a Abujan, in ce dai ba wata matsala ko?" Matsalolina da nake fuskanta suka rika yawo a cikin kwakwalwata, ina tantance wadanda suka cancanta in fada. Da wadanda bai kamata in fada ba. Wata zuciyara gargadina take yi da kar in fada, aure wata uku kacal ace na fara kawo matsala gida "Ya ya dai?" Ta katse min tunani na "Ba komai " na amsa a hankali saboda har zuwa lokacin ban yankewa kaina hukunci ba "Fada min gaskiya, ba a boye matsala karama, domin daga karamar ne take zama babba" Na kai hannu hade da shafa fuskata, lokaci daya kuma na gyara zamana. Ina fuskanta, hade da tace maganarta, gaskiya ne matsala daga karama take farawa, kafin ta zama babba "Ni ban san me zan ce ba, yadda za ki fahimta" Na yi maganar hade da rufe bakina dalilin hammar da na yi. "Ki fada min komai zan fahimta." ta amsa ni Na ɗan ja siririn tsaki "Ni lafiya lau muke zaune da ita, tsawon wata uku da mu ka yi tare ko mugun kallo ba ta taɓa yi min ba." "To shi fa mijin naki?" Umma ta yi saurin tambaya "Shi ma haka" Na ba ta amsa "To me ye damuwarki?" Ta yi tambayar hankalinta a kaina "Umma dama haka auran mai mata yake?" ni ma na tambayeta ina kallonta Ita ma kallona take, ba ta yi alamar magana ba, wanda hakan ya nuna min tana neman karin bayani a gurina ne "Ki gode Allah da ba ki auri mai mata ba Umma wallahi duk yadda kike ganin kina da matsaloli a gidan auranki ke kadai to basu kai ace kina da kishiya ba. Ni kam na yi danasanin auran mai mata " "Ni ki fada min matsalar, ba zagaye-zagaye ba" "Umma sam ba ni da ƴancinkaina, sai abin da matarsa ta ce, ba a shawara da ni sai dai in ga ana yi, ke ko wani abu zai min sai ya biyo ta hannun matarsa, yana tare da ni amma hankalinsa na gurin matarsa da yaransa, ke kam dai na zama kamar wata tunkiya a garken awaki. Ko dama haka ake yi? " Na rufe maganar da tambayar ta, lokaci daya kuma ina tabe bakina. Umma ta ɗan murmusa kadan, murmushi dana kasa gane dalilishi Kafin ta ce "Ki yi duk yadda za ki iya ki zama kamar ita, sannan ki yi hakuri, ba da gaggawa ake taka matsayi mai girma ba, kafin ta zama haka sai da ta kwashe tsawon shekaru, kin ga kuwa ke da kike da kika zo jiya, ba ki isa ki zama kamar ita ba. Ki bi komai a hankali " " Kin ga Umma hatta danginshi sai abin da ta ce, wurin bikin nan duk shawara da ita ake yi" Ta kalle ni da alamun damuwa kafin ta ce "Duk wannan kar ya dame ki, a hankali za ki iya zuwa matakin da take, kila ma ki wuce ta. Abin da kike bukata kawai shi ne kyautatawa, girmama na gaba da ke. Sannan girmama kowa. Da tsayawa matsayinki, ba ruwanki da yawan tsegumi ko gulma. Babu girman kai, Sai girmama kai. " Shiru na yi hade da nazarin maganganun Ummana, tabbas wadannan sune abubuwan da Maman Khalil ta rike, babu dadi babu kari. Saboda kowa bai raina ta ba, kuma ba ta raina kowa ba. Haka muka rika tattaunawa, har bacci ya dauke ni. Cikin bacci na rika jin hayaniya da karar taɓa abubuwa. A hankali na bude idona, wanda bacci bai isa ba, kasancewar jiya bacci bai dauke ni ba sai wajen uku saura na dare. Saboda hirar da mu ka rika yi da Umma. Ko bayan hakan ma na dade ina nazarin duk wasu maganganu da ta fada min Duk abin da Hasashena ya ba ni, sabanin haka na taras, yayin da Umma ta kara tabbatar min da cewa Hasashen nawa gaibu ne, ba lallai abin da na Hasaso ya kasance gaskiya ba, kamar yanzu ma. Ni abin da na dauka shi ne, a matsayina amarya, to zai kasance hankalin mijina yana kaina, zai tarairayeni, zai ji da ni, kamar dai yadda na sha fada tun farko. Amma me ya sa ban samu wannan ba? Kodai ni ce ban iya tarairayar miji ba? "Wannan ba gaskiya ba ne." na ba kaina amsa, hade da yunkurawa na tashi zaune a kan katifar. "Me ye bana mishi? Ina mishi komai, bana barin kazanta ko datti a ko ina. Ina kiyaye ganinshi da jin shi. Girki ma na dage sosai nake kokari, duk da dai ni kaina na san ban kamo kafar Maman Khalil ba a nan bangaren" Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, a bayyane na fadi "Mata ce kamar mayya, komai ta iya, ni ban taba ganin mace irinta ba" Jin almar za a shigo dakin ne ya sa na yi saurin yunkurawa na daga net din ina kokarin fita. Maryam ce kanwata "Aunty ashe ma kin tashi, dama Ummanmu ce wai in zo in tashe ki" "Na tashi" na ba ta amsa, lokaci daya kuma muka fita tare Bayan na idar da sallah, daukar tsintsiya na yi, na, share gidan fes, sannan na shiga kitchen inda Umma ke saka danwake "Tsawon wata uku kenan ban ci danwake ba Umma ba" Na fada hade da janyo karamar kujera na zauna gefenta, tare da fara saka danwaken a cikin tukunya. "To me ya sa, ba kwa yi ne?" "Ni dai ban taba yi ba, ban sani ba ko Maman Khalil ta na yi" "Oh kowa girkinsa yake yi" Kai na jijjiga alamar Eh. "Kina ji na?" Umma ta yi maganar hade da dakatawa daga saka danwaken alamar maganar na da muhimmanci. "Allah ya hada ki da kishiya mai wayo, wacce ta san kanta" Na yi saurin kallonta alamun ina neman karin bayani. "Magana ta gaskiya, shi ne akwai aiki a gabanki, kafin ki taka matsayin da kishiyarki take kai yanzu." Ta dan tsagaita, yayin da ni kuma nake bubbuga kumfar danwaken da ta taso. "Natsuwa za ki yi, ki gano a ina gazawarta take, sannan ban da kwaikwayo, ya zama ke ma kin zo da naki sabon salon da zai zama bako a gurin mijinki. Wannan shi ne kawai" "Me kike nufi da haka?" Na yi tambayar a lokacin da nake tsame danwaken "To me kuma kike son in fada miki, komai sai an yi miki dalla-dalla ne?" "Haka ya kamata a rika yi, musamman a kan macen da za a kai gidan kishiya." Na yi maganar a zuciyata, a zahiri kuma murmushi na yi, ina yaba alkunya irin ta iyayenmu, wato komai sai su bamu shi a dunkule, yayin da muka warware za mu samu abubuwa da yawa masu muhimmanci. Duk da wani lokaci mu kan warware abun ba daidai ba, ya fi ace an warware mana shi ta yadda za mu fahimta. Ni na raba danwaken na sanyawa kowa, ni ma na ja na wa, ci nake amma kuma bitar maganar Umma nake yi. Zuwa karfe takwas gidan shiru sai ni, kanwata Maryam da take zana min lalle, Sai kuma Umma da ke ta faman hada min tsaraba. Hira muke da Maryam a hankali wacce da yawan hirar a kan kannenmu ne, Sai kuma Yusrah, daya kanwar tawa da take aure a Kaduna. Ita kam ta jima da aure, saboda ta ma riga ni auran, tun mahaifinmu na da rai aka yi mata aure, ni kuma sai da na kammala NCE. Zuwa karfe biyu, na fita shar da ni, kamar yau ne za a kai ni gidan miji, kunshina ya yi kyau, haka ma kitson da Umma ta yi min zanen kwance, ya fito da fuskata fayau. Doguwar riga mai ruwan madara na saka, na zagaye fuskata da dankwalin rigar ina jiran zuwan Abbansu Khalil Ba jimawa kuwa ya iso, bayan sun gaisa da Umma ya yi mata ihsani, mu ka yi sallama, sai Airport. Matar j [12/16, 20:12] 08080966571: *HASASHENA* *Page 7* Karon farko da na fara shiga jirgi a rayuwata, amma kuma ba na ɗoki, murna ko farin ciki. Hasali ma raina a bace yake, komai baya min dadi, ji nake kamar in ce a tsaya in sauka. Shi kanshi na ga ya fahimci hakan, duk da komai bai ce ba, idan ka dauke hannuna da yake cikin na shi yana murzawa a hankali. Duk bacin ran nawa, na san baya rasa nasaba da yadda nake tunanin yau Maman Khalil za ta amshe min miji, na san yau za ta fanshe duk wasu kwanaki da ya yi a wajena. Gaskiyar Ummanmu ne, Maman Khalil mace ce mai matukar wayo, iya mu'amala da zaunawa a rai. Ta san yadda ake tafiyar da miji, da yi mishi abin da zai tsaya mishi a kwakwalwa da zuciyarshi. Sosai nake tausayin kaina, idan na tuna irin kalubalen da ke gabana. "Tea or coffee?" Ma'aikaciyar jirgin ta yi min magana cikin wani irin turanci da take yi ma Tajweedi Shiru na yi, na kasa gane me ta fada a kalmarta ta biyu, ta fari dai na san tea ne, kuma ai kullum ma sai na sha shi. Don haka sai na yi saurin cewa "Coffee" da irin sallon da ta furta. Cikin yan dakikai, aka kawo mana abin da muka bukata Tea mai kauri na ga an mikawa Abbansu Khalil,, yayin da ni kuma aka mika min abu baki. Na kurba a hankali, hade da kallon Abbansu Khalil, shi ma ni yake kallo, da alama yana son ganin reaction dina ne Idanuna na dauke daga kan fuskarshi, zuwa wani bangaren, na rufe idanuna gam sannan na hidiye abin da na kurba. Gudun kar in yi abun kunya na rika sipping abun kamar magani. Da kyar na sha rabi, na aje sauran. Ina danasanin rashin cewa a ba ni tea dan gida. Misalin biyar muka sauka Abuja Saukar mu ke da wuya na hango Maman Khalil sanye cikin wani hadadden leshi mai ruwan goro Dinkin riga da siket ne, ya zauna jikinta das, ta sha sarka da yan kunne masu kyau da tsada. Eye glass din da ta sanya ya kara mata kyau sosai, idan dai kwalliya ce to Maman Khalil kam ta iya sai madalla. Yaran ma fes dasu cikinsu kaya masu kyau da tsada Tun daga inda take tsaye take aikawa mijinta sakon murmushi. Shi ma hankalinshi duk yana kanta, kamar ya ture mutanen da ke gabanmu ya isa gareta Tuni kishi ya turnekeni, zuciyata ta yi kunci, raina ya dagule, ji nake kamar in dora hannu a kai, in yi ta zumduma ihu. Gaskiya babu abin tashin hankali a gurin mata irin ka ga mijinka da wata, kuma ace mallakinsa ce,, musamman irin su Maman Khalil,, kishi da irinsu ma bala'i ne. Yaransa ne suka fara isa gareshi a guje cike da tsantsar farin ciki, shi ma cikin farin ciki yake dagasu, hade da yi masu tambayoyi, har zuwa lokacin da ya isa gurin Maman Khalil da ke tsaye ta na murmushi. Na yi tunanin zasu rungume juna, sabanin haka hannu ta mika mishi suka gaisa hade da fadin, bayan ya dauki Ramlah "lale marhababika da bangon gida, kowa ya yi kewarka, Alhamdulillahi da ka iso lafiya jarumina" Murmushi dauke a fuskarshi ya mayar mata da amsa "Na yi kewarku sosai uwargidana ke da yara, na yi farin ciki da na same ku lafiya" Na yi tsaye sororo da kaya a hannu, ina kallon yadda suke fadawa juna yanayin da suka shiga da ba sa tare Kamar ma sun manta ina gurin, dalilin da ya sa kenan na mika hannu na karbi Ramla, don sai wangale min baki take yi, hade da daga hannuwa alamun tana son in dauketa. Haka nan nake son yarinyar, ina jin kamar 'yata ta cikina haka nake jin kaunarta. Gaba ya zauna shi da matarsa, yayin da ni da yara muka zauna a baya. Ita ce ke tukin cikin kwarewa, yayin da suke ta hirarsu cikin nishadi, da alama sun manta da ni, don kuwa ko sau daya ma basu saka ni a hirar ba, ni ma kuma ban shiga ba. Ni da yara kawai muke tamu hirar. Bayan mun iso gida, na nuna mata tsarabarta da aka ba ni in kawo mata, ni kuma na dauki tawa na yi sashena. Hade da ajiyar zuciya na zauna, kan kujerar, kaina ma har ya fara ciwo, saboda tsananin kishi. Kwankwasa kofar ne ya sa na mike da sauri, na yi zaton Abbansu Khalil ne. "Ga shi in ji Aunty a kawo miki." Wata yarinya bakuwar fuska ta fada, shekarunta ba za su wuce sha uku, zuwa sha hudu ba. "Na gode." Na fada hade da mika hannu na karbi babban tiren. Tuwon semo ne da miyar egusi da ta sha kifi da ganda, ga ganyen ugu, gaskiya a ido ma kawai akwai burgewa bare a baki. Sosai na saki jiki na ci tuwon, na sha ruwa. Sannan na mike na shiga kakkabe dakina saboda kurar da ya yi Har sha biyun dare na kasa bacci, zuciyata saka min abubuwa marasa dadi kawai take yi Tana hango min Abbansu Khalil da Maman Khalil cikin jin dadin da baya misultuwa. "Mtswwww!" Na ja siririn tsaki, hade da mikewa zaune, ni dai yanzu da za a ce in koma budurwa, to gaskiya zan zabi auran miji mara mata, na yadda wata ta biyo bayana, amma dai ni in zo a farko. Yanzu da ace ni ce farko, da ba ruwana wata ce zan bari cikin kalubale. Yanzu ga shi tun da muka dawo ban kara ganinshi ba, ko a waya ma bai kira ni ba. Na so kiranshi, amma kuma ina tsoron kar ta ga kamar na shiga huruminta "Kai jama'a! Kai da mijinka, amma kira a waya ma ya zama damuwa." na yi maganar tare da mikewa na shiga toilet don rage marata Wasa-wasa ban yi bacci ba sai biyu saura, shi ma cike da mafarkai kala-kala. Dalilin da ya sa kenan na tashi da matsanancin ciwon kai, har tashin zuciya nake ji. Da kyar na dafa indomie da tea na sha, na koma na kwanta. Cikin bacci na ji ana jan kafata. Da alamun yanayin bacci na bude I danuwana hade da dorasu a kan fuskarshi. Sanye yake ciki yadi ruwan kasa mai laushi, dinkin manyan mutane, ga kamshinshi da na matarsa na fita a jikinsa. Haushi yake ba ni sosai, ko kunya tun jiya yana manne da matarsa, ko leko ni ya kasa yi sai yanzu karfe sha daya na safe. Mayar da idona na yi hade da lumshesu, ina jin wani daci a zuciyata. "Amaryata, ya gajiyarki, fatan kin tashi lafiya?" Ya yi maganar daidai yana zama saitin kaina. "Ban tashi ba, ya dameka ne? Ba dai ka dawo wajen babbar masoyiyarka ba?" na yi maganar a zuciyata, a zahiri kuma ban ce komai ba. Bargon ya yaye hade da kwantar da fuskarshi a kan kirjina "Ba kya ji ne?" "Ina ji, na tashi lafiya" Na yi maganar tare da kokarin ture sa. "Jikinki zafi" "Eh bana jin dadi ne tun jiya" "Ban sani ba, sannu, kin samu magani ne?" "Eh na sha paracetamol" "Sannu to, gajiyar hanya ce kawai, na so leko ki jiya ai, ni ma na gaji ki yi hakuri" "Amma gajiyar ai ba ta hanaka hawa gado ba" na kuma yin maganar a zuciyata Amma a fili na ce "Ba komai." "Zan je wurin aiki" "Allah ya kiyaye hanya" "Amin" ya fada a lokacin da yake kokarin tashi. Sai da ya sumbaceni a wuya da hannuna sannan ya ja min kofar ya fice. Na sauke ajiyar zuciya mai sauti Allah ya sani ina son mijina, ina kuma son kasancewa da shi a ko wane lokaci Amma kuma ba damar hakan, ya zama ma kamar ƴarmin ake yi. Wunin ranar dai haka na yi shi da zazzabi, komai karfin hali kawai nake yi. Maman Khalil kam har daki ta zo, ta kawo min tsarabar da aka ce in kawo mata, ni ma na kai mata tawa tsarabar. Jin tsoron abin da zai faru da dare ne ya sa na kira Abbansu Khalil a kan ya taho min da maganin zazzabi. Tun da ya shigo nake jiran ya kawo min maganin amma shiru, ga kuma zazzabin ya kara tsananta. Har karfe goma bai shigo ba, ni kuma na ki kiransa. Paracetamol na kuma sha na kwanta Tun da na zo duniya, ban taba jin matsanancin zazzabi irin wanda na ji a daren nan ba , ban taba tunanin za a wayi gari da ni ba. Kuma a daren ne na fi yin nadamar auran mijin wata, da mijna ne ni kadai, da ko mutuwa zan yi, zan mutu ne a hannunshi, amma wannan kam sai dai da safe su zo su samu gawata. Jiya ma ko leke bai lekoni ba, bare a yi batun magani. Hade da sallama ya turo kofar, kamshinsa ya daki hancina sai na ji zan yi amai. "Morning Dear!" Ya fada a lokacin da yake matsa kafafuna. Bakina cike yake da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji, hakan ya sa na yunkura, na mike zuwa toilet din bedroom nawa ba tare da na yi magana ba. Bi na ya yi kamar bindi, har na zubar da yawun na koma cikin dakin hade da zama gefen gado. "Har yanzu jikin ne?" ya tambaye ni hade da cire hijabin da ke jikina yana taba jikin "Subhanallah! Sannu, wannan kam sai dai asibiti, bari in yi wa Maman Khalil magana ta sauke ki." Na bi bayanshi da kallo bayan ya fita, ni duk haushi yake ba ni, ina gidanmu ya yi ta yi min dadin baki ya auro ni, kamar a duniya babu sauran wanda yake so sai ni. Amma ga shi tun da na shigo nake ganin bambanci, sannan baya ma nuna shi yana yin wani abu da bai dace ba. Tare suka shigo da ita, tana sanye cikin doguwar riga ja, da adon fulawa fara, kamar kullum dai ta yi kyau, kamar ba ta da wata matsala. "Sannu Auntyn Ramla, ya jikin?" "Da sauki." na amsa mata "Bari in taimaka mata ta shirya sai mu je asibitin, ka je gurin aikinka ba damuwa " Ta yi maganar hade da kallonsa. "Ok, to ki kula." "zan kula, kar ka damu da wannan" "Allah ya ba ki lafiya, sorry" ya yi maganar tare da kallona cikin yanayin tausayawa. Ita ce ta taimaka min na shirya, sannan muka fita. Duk wani zirga-zirga a asibitin ita ce ta yi, har sai da ya rage ganin doctor kawai zan yi, sannan ta wuce gurin aikin ta, bayan ta ba ni 10k a hannuna. Bayan gwaje-gwaje dai an gano ina dauke da ciki wata biyu, sai kuma malaria. Ban baro asibitin ba sai karfe biyu, kasancewar dama bamu je da wuri ba. Ganin motarta a harabar gidan ne ya tabbatar min da ta dawo. Yarinyar da har yanzu ban san wacece ba, ita ce ta bude min kofar bayan na kwankwasa. Kasancewar maigadin baya nan. Matar J [12/16, 20:28] 08080966571: *HASASHENA* *Page 8* Ina shiga Ramla na fara dauka da ke koyon tafiya a falon. "Kin dawo? Na kira layinki ba a daga ba,." Cewar Maman Khalil a lokacin da take fitowa daga kitchen "A gida na manta ta." na ba ta amsa ina kokarin zama "Aiko kin tashi hankalin Abbansu Khalil, har asibitin ya je, aka ce kuma kin taho" Shiru na yi komai ban ce ba, saboda ni haushinshi nake ji. Asibitin ma bai iya kai ni sai matarshi. Idan da ace daya daga cikin yaranshi ne ba lafiya, shi zai kai su. "To ya jikin?" ta katse min tunanina "Akwai sauki sosai, malaria ce." na amsa ta "To Allah ya sawake." ta yi maganar hankalinta a ka wayarta da bakuwar yarinyar can ke mika mata. "Eh, ta dawo, ta manta wayarta a gidana ne." ta dan yi shiru, Sai kuma na ji ta ce "Malaria ce aka ce" "OK" ta kuma fada, hade da yanke kiran ta ce min "Ya ce ki dauki wayarki zai kira ki" Yanzu ma ban bi ta kan maganar tata ba na ce "Akwai ɗan abun tabawa kuwa?" saboda sosai wata irin yunwa nake ji "Ba za a rasa ba, bari a yo miki kala" Zobo ta kawo min da dambun nama ya ji kayan hadi sosai. Muna taba yar hira ina ci da zobon har na cinye, na kora maganina, sai na dakko filon kujera na aje a kasa na kwanta, ba da dadewa kuwa bacci ya dauke ni. A cikin bacci na ji muryar Abbansu Khalil yana fadin "Ya jikin nata?" "Da sauki." Ta ba shi amsa "Sosai saukin, na kira wayar ba ta daga ba." "Ai ba ta koma ɗakin ba ma, bacci ya dauke ta" ta amsa shi "Na manta ban ba ku kudin zuwa asibitin ba." "Ai na ba ta wasu kudi a wurina, ban sani ba ko sun ishe ta." "Na gode miki Sakeena, Allah ya saka miki da alkairi kina bin duk wata hanya da zan samu kwanciyar hankali. Da ace du mata za su su yi koyi da irin halinki to da ko wane gida an zauna lafiya. Sannan babu wata mace da za ta tsoraci kishiya." Na dan bude idona, don so nake in ga yanayin fuskarta, irin wannan yabo da ta sha. Da alama tun sa'adda ya fara maganar murmushi take yi har zuwa lokacin da ya kai karshe. Ga ni na yi ta matso dab da shi, hade da kama hannayenshi biyu suna fuskantar juna "Abban Khalil ni ce zan gode ma, in yi ma addu'ar fatan alkairi a ko wane lokaci. Zaman lafiyar gida miji ne ke samar da shi, ba ka wulakantani ba ka juya min baya ba, ba ka watsar da lamarina dana yarana ba, ba ka canja ba daga yadda na sanka ba. Wai don ka yi aure, sabanin wasu mazan da kan nuna yaransu da matansu duk basu da wani sauran amfani a wajensu, saboda sun yi sabon aure." Sai kuma na ga sun yi hanyar bedroom rike da hannun juna. Na karasa bude idona ina bin kofar da kallo,, zuciyata tana daci, kishi mai zafi ya taso min. " Me zai faru a ciki?" Ita ce tambayar da nake wa kaina Ji nake kamar in fada cikin dakin ba tare da sallama ba. Na sauke ajiyar zuciya mai nauyi tare da yunkurawa na mike dakyar zuwa bangarena. Alwallar sallahr la'asar na yi, don kuwa a lokacin karfe hudu da rabi na yamma. Bayan na idar da sallahr na kwanta kan sallaya, babu abin da yake min dadi, haushin kowa da komai nake ji, wannan kuwa ba ya rasa nasaba da har zuwa lokacin Abbansu Khalil na bangaren Maman Khalil bai leko ni ba. "Ya Allah ka rangwanta min wannan kishi." Na yi maganar a hankali hade da gyara kwanciyata a kan sallayar. Daidai lokacin kuma aka kwankwasa kofata, na mike jiki ba ƙwari na nufi kofar. Duk yadda na so in saki fuskata na kasa, time da na bude na gansu tsaye, ko farantin hannun Maman Khalil ban amsa ba, na juya ita ce ta je kan dinning ta aje min tana kara tambayata "Ya jikin!?" "Da sauki" Na fada a hankali Rashin ganin fuska ya sa ta fice, ba tare da ta kuma cewa komai ba. "Deejanah!" ya kira sunan a hankali cikin salon da yake tunani zai kashe min jiki A maimakon hakan ji na yi kamar in mike in yi ta kwasheshi da mari sai na ga bakinsa yana jini. "Deejah!" Ya kuma kiran sunan hade da matsowa kusa da inda nake zaune ina karkada kafa rai bace kamar yaki ya rigani kofar gida. Janyo ni zuwa jikinsa ya yi, yana fadin "Sorry yau kuma me na yi, irin wannan fushi haka?" Na kwace jikina hade da ja baya, ina kallonsa cikin ido rai bace "Ni na gaji da zama a tsakaninku ku biyun nan,don Allah ni ka mayar da ni gida. Ka san kana son matarka ba za ka iya hadata da kowa ba, me ya sa ni ka auro ni?" Kallona yake mai cike da alamun mamaki. Ganin ba shi da niyyar magana na ci gaba "Tun da muka dawo Kano na fada ma ba ni da lafiya, har kiranka na yi jiya a kan ka zo min da magani, amma ba ka siyo min ba, yau din ma asibitin ka kasa kai ni, sai ita ce ka sanya ta kai ni. Na kasa gane kai ne ka auro ni, ko ita ka auro ma ni. Da duk wata hidima tawa ita ce kake ɗorawa. Ita nake aure ko kai, ko dama haka ake yi?" Na yi tambayar hade da kallonsa. Har yanzu bai nuna alamun zai yi magana ba. Shi ya sa na dora " To ka sani, daga yau ban yarda a kara dora wata a kan hidimata ba, kuma sannan duk wani abu da ya shafe ni kai ne za ka rika yi ba ita ba. Abinci ma ka fada mata kar ta kara kawo min idan ba zan iya girki ba, ka je kai ka sawo min a waje amma ba nata ba." Ina gama fadin haka na wuce cikin bedroom,, ba wai don abun da nake son fada sun kare ba, idan zamu kwana to zan ci gaba da lissafi, kawai duk lokacin dana fadi wani abu da nake ganin rashin adalci ne ake yi min, to sai zuciyata ta kuma tunzura in ji kamar in rufeshi da duka. Ko in duddura mishi ashar. Gefen gado na zauna ina fuskantar mirror, kallon yadda fuskata ta zama nake yi saboda bacin rai. Turo kofar bai sanya na waiga ba, saboda na san waye ya shigo, ina kuma jiran in ji da me ya zo, yau kam a shirye nake, idan zaman, to zaman, idan kuma tafiyar, tafiyar. Burina dai ya cika tun da na zazzage rabin abin da ke damuna. Tsaye ya yi yana fuskanta ta, kafin ya ce "A duk abin da kika lissafo daya ne kawai nake ganin shi laifi, wato da kika ce in taho miki da magani ban yi hakan ba. Kuma wlh mantawa na yi..." "Dole ka manta, saboda ba matar sonka ba ce ba ta da lafiya ko yaranka." na katse shi cike da bacin rai. Ya dan murmusa kadan kafin ya ce "Khadija kenan, da ace kin san wacece Maman Khalil da duk ba ki yi wannan fushin ba." "Na sani mana, mace ma fi soyuwa a wurin ka." "Da dai da abokaina suke fada min hada mata biyu ko fiye da haka akwai matsaloli, ban yarda ba sai yanzu. Lokacin da zan aureki 'yan'uwana sai da suka ce, kana zamanka da matarka asirinku rufe za ka je ka dakko wata." Ya dan dakata yana kallona, dana bude baki ina kallonsa cike da mamaki. " Khadija ina sonki, so ba na wasa ba, da ace zan iya ciro zuciyata in ajiye a gabanki, da kin tabbatar da hakan, amma tun da kika shigo cikin nan na fahimci yanzu kin daina yarda da ina sonki. Ba tun yau ba, na fahimci kina da mugun kishi, muddin zan kasance da Maman Khalil sai na gani a fuskarki, kyaleki kawai nake yi in yi kamar ban gani ba. Wannan kuma dalilin ya sanya kike ganin yanzu ba na sonki, ban damu da ke ba, saboda kin sanya kishi a ranki. Komai kankantar abu, Sai ki girman d shi. To amma abin da nake son ki sani Sakeena matata ce kamar yadda ke ma kike matata. Ina da ikon kasancewa da ita a duk lokacin da na so, kamar yadda nake da ikon yin hakan a kanki, raba kwanaki wannan wani adalci ne kawai aka yi maku. Ya kamata ki rage wannan zafin kishin, ki zo mu hadu mu zauna lafiya. " " Ai Basheer muddin irin wannan zaman ne, ba zan amince ba gaskiya, kuma dole in ji ba ka sona, saboda ba ka damu da komai nawa ba. Kullum hankalinka ba a kaina yake ba, a kan matarka yake. Idan kana son zaman lafiya, to kuwa shi ne ni ma in zama mata a gidan nan. Ka rika yin duk wani abu da ya shafe ni da kanka" "Kina ji na ko? zan gina mana zamanmu ne a bisa taimakawa juna ba kowa tashi ta fissheshi ba. Ba ke ce za ki tsara min yadda zan zauna daku ba, ko ita Sakeenar ba ta isa ta tsara min yadda zan zauna da ku ba. Kawai tana bin umarni ne, ko yin abin da zai faranta min, ya kamata ki san wannan. Tun da Sakeena take ba ta taba yin complain a kanki ba, amma ke kullum idonki yana a kanta, me ye wannan? " Zuciyata ta zo min iya wuya, hakan ya sa na mike tsaye tare da fadin " To dama ita a kan me za ta yi ma complain, tun da ka fifitata a kaina, ai ba ta da matsala ni ce mai ita. Ai duk munafurci ne irin na mata take yi ma. " Kuma da kake cewa yan'uwanka sun ce kar ka auro wacce za ta bata ma gida me ya sa ba ka karbi shawararsu ba?" "Ni kike fadawa magana haka?" ya yi maganar yana kallona da wani irin yanayi a fuskarsa da ya tsorata ni. Shiru na yi ban ce komai ba "Lallai yaran zamani, tun da nake da Maman Khalil ban taba fada tana fada ba koda kuwa ita ce mai gaskiya. Shiru take yi sai na gama, ba ta mayar min da martani amma yanzu ga shi nan rashin godiyar Allah irin ta dan'adam na je na auro yar cikina tana fada min magana" Har yanzu dai Maman Khalil ce abakinsa, yaushe zan goge sunanta ne nawa ya zauna? Yaushe zai san ni da ita yanzu duk darajarmu daya? Yaushe zai san cewa ni da ita yanzu babu wani bambanci? "Kar ki kuma kara cewa matata munafuka idan ba haka ba ranki zai fi na yanzu baci, ban san ba ki da kunya ba sai yau" ya katse min tunanin da nake yi, kafin in ce wani abu kuma har ya juya zuwa kofar ficewa daga bedroom din. Tsaye na yi zuciyata tana kuna, ina jin kamar in hada kayana in kama gabana. "Haka dama aure yake kodai nawa ne ya zo da haka?" Daga na yi magana a kan neman yancina sai ya zama tashin hankali,, me ye na fada da ba daidai ba? Ban san lokacin da na fashe da kuka mai sauti ba, lokaci daya kuma na bude kofar na fito zuwa falo. Cikin sa a kuwa na same shi zaune, ya jingina bayansa da kujera kansa a sama da alama ya yi zurfin cikin tunani. "Ka tashi ka koma wajenta, tun da ita ce mai tarbiya, mai kunya. Don Allah ka fita ni ba na son ganinka." Cikin kuka nake maganar "Wannan shi ne zabinki na karshe?" "Shi ne." na ba shi amsa Abun mamaki sai na ga ya mike hade da ficewa daga falon, ko kofar ma bai rufe min ba. MATAR J [12/16, 20:43] 08080966571: *HASASHENA* *Page 9* Bayan fitarshi kuka na saki mai sauti, na yi mai isa ta, har sai da na ji na koshi, kafin na mike na yi alwalar magariba, ban idar da magaribar ba ma aka kira isha'i, shi ya sa kawai na zarce da isha'i har da shafa'i da wutri. Daga nan kuma kitchen na zarce na nemi abin da zan ci, saboda ko abincin Maman Khalil ban bude ba. Bacin ran da nake ji bai hana ni bacci ba, bacci na yi sosai, har sai da ana sallame sallahr asuba na tashi. Na yi alwala hade da yin sallah. Ban wani damu da rashin ganin Bashir ba, tun da dama na rufe kofata, kuma na yi alkawarin ba zan bude ba koda ya buga. Ina kitchen na rika knocking, ta ƴar kofar da ke jikin kofar na leka, ganinshi tsaye da jallabiya ya sa na juya ba tare da na bude kofar ba. Daga shi har matarshi basu ganni ba, har suka fice daga gidan. Yayin da ni kuma na ci gaba da zaman bacin raina Har na fita girkina ban yarda ya kara ganina ba, abin da na fahimta dai yana duk wasu hidimominshi ne a dakin baki, Sai kuma bangaren Gimbiyar ta shi. Saboda hatta matarshi da yaranshi sai da na dauke musu wuta, sau uku tana zuwa bangarena, ganin yadda nake daure fuska ya sanya ta daina zuwa. Zaman kuma haka baya min dadi amma haka nan na daure hade da takure kaina. Lokacin da ta karbi girki, Sai na ga kamar tana min abu da gayya, saboda har wani fita yawo suke yi, su dawo da kaya niki-niki, duk kuma lokacin da suka dawo din za ta aiko min da nawa, ni kuma ban karba, Sai in kora yarinyar da ta aiko da kayan. Kwanaki nan kamar a prison na yi su, sai a lokacin na gane babu abin da ya kai zaman lafiya dadi, ga shi dai ni na hura wutar kuma ta isheni da zafi, maimakon ta kone matsalolin dana hurata don su, sai ma ta kara min wasu matsalolin. Yanzu kam da kaina nake addu'ar Allah ya sa ya dawo dakina yau, kar ya ce zai kara yada zango a dakin baki, idan ya yi haka lallai akwai matsala, ya fi min ya dawo dakina mu ci gaba da fadan, a kan yana wani wuri daban Babu wani amfanin fushi da miji ma idan yana da mata, ko ma ka yi sai ya shareka ya tafi wajen wata. Maimakon ya zama fushin ya kawo masalaha sai ya zama ya barke kofar wata matsalar. Kamar ni yanzu ga shi nan dai na ba abokiyar zamata kofar kara kusantar mijina, yayin da kuma kimata ta ragu a idon abokiyar zamana da kuma mijina. "To wai me ye abun yi ne kuma yanzu?" A fili na yi tambayar hade da gyara tagumin da na yi. "Abun yi shi ne in ci gaba da zama hade da zuba ido, ana fifita wata a kaina?" "Kai! Ina! Sam ba zai yiwu ba" wannan karon a zahiri na yi maganar hade da mikewa tsaye ina zagaye falon. Abokin magana nake nema, amma waye duk wasu yan'uwana suna nesa, wannan ma wani kalubale ne na auran nesa. "To ta ya zan dawo da mijina wajena?" Na kuma yi wa kaina tambayar Shiru ina nazari kafin in dakko wayata, text nake son rubuta mishi. "To me zan ce?" na kuma tambayar kaina hade da bubbuga wayar a hannuna. Duk abin da na fara rubutawa sai in goge, in ga kamar na fado kasa ba nauyi ne ko na yi a mai na lashe. Jin karar bude gate ya sanyani saurin karasawa jikin window hade da yaye labulen. Yaransa ne suka fito a guje zuwa inda yake, yayin da mamansu ta biyo bayansu. Sanye take cikin wani farin cotton material mai laushi, wanda aka yi wa ado da fulawa masu kalar lemon (orange) dinkin riga da siket ya bi jikinta ya zauna, tare da fito mata da kyan dirinta. Kamar ko wane lokaci hannu ta mika mishi, suka gaisa fuskokinsu dauke da murmushi, jakar laptop dinshi ta dauka, yayin da ya bi bayanta suka shige ciki. "Wayyyo Allahna!" Ni kaina ban san a zahiri na yi ihun ba, sai da na ji ana buga min kofa da sauri da sauri, mabanbantan muryoyi na tambayata lafiya?, sannan na san kasassabar da na yi Wiki-wiki na yi da ido ina kallon kofar ba tare da na bude ba, kafin dabara ta fado min, na shiga jan kafata dakyar zuwa kofar na bude. "Lafiya kuwa?" ya yi saurin tambaya ta "Me ka ji?" na mayar masa da tambayar ina tura baki, har zuwa lokacin ina matsa kafata, irin dai a nan koma menene yake. "Ji mu ka yi kin yi kara " Maman Khalil ta karbe maganar "Au! Faduwa na yi, amma ban ji ciwo sosai ba, kafata ce kawai ta dan bugu" na yi maganar hade da juyawa ina dangyasa kafata a hankali, zuwa hanyar bedroom dina, ba tare da na rufe kofar ba Gefen gado na zauna, ina yi wa kaina dariya, jin alamun tafiya kuma sai na hade fuska. Shi ne ya shigo, tsaye ya yi jikin kofar yana kallo na, yadda ban ce komai ba, haka shi ma, ya gaji da tsayuwar ya juya. Da kaina na ba kaina muhawara bayan fitarshi, tsakanin mace yar boko gogaggiya wacce ta san komai, ta kuma iya komai, da kuma kishiya yar kauye wacce ba ta waye ba, ba ta iya komai ba, ba ta kuma san komai ba wacce ta fi dama-dama a wajen zama ne? Haka nai ta kawo points a ka wane bangare ina kuma rugujewa. Jin kiran sallahr magariba ne ya sanya ni mikewa, alwalla na yi tare da hayewa sallayata. Sai da na yi sallahr isha'i sannan na sauka, ina shan tea na ji karar kofa alamar wani zai shigo Dakatawa na yi da shan tea din ina kallon kofar. Sanye yake ciki jallabiya mai ruwan toka, irin mai walkiyar nan, kamshinsa wanda yake gauraye da na matarsa ne suka cika min hanci. Kawar da kai gefe na yi, bayan na amsa sallamar dakyar Kujerar da ke facing dina ya zauna, tare da amsar kofin tean da ke hannuna ya kai bakinsa. "Ya na ji kamar ba sugar?" Shiru ban ce komai ba Labbana ya kama tare da dan jansu "Kina da rikici, zama da ke sai dai ni kawai" Zumbura bakin na yi, tare da kawar da kaina gefe bayan ya sakar min labban. Ci gaba da kurbar tea din ya yi a hankali. Ni kuwa a kasan zuciyata wani farin ciki ne ya cika ni, domin kuwa koda na yi sallah sai da na yi addu'ar Allah ya sa ya dawo dakina yau. "Me ya sa ba ki sanya sugar ba,, ko karewa ta yi?" Daga kai na yi kawai alamar eh "Karewar ta yi?" ya kuma tambaya "Eh" "Shi ne ba ki fada ba?" "A ina zan ganka in fada?" "To ai ke ce kika kore ni?" "Kuma hakan ya ma dadi ai" "Waye ya ce?" "Sai an ce ne, abu da na gani, ni na rasa dalilinka na aurena bayan kana son matarka." "Za ki fara ko? To ke waye ya fada miki ba na sonki?" "Ni ce na gano haka" Wannan karon murmushi ya yi,, ba tare da ya ba ni amsa ba ya dire cup din, hade da shigewa cikin bedroom Sai da na shanye ragowar shayin kafin na bi bayanshi. Sosai al'amarin maza ke ba ni mamaki, yadda Baban Khalil ya tafiyar da ni a daren tamkar ba shi da wata mata sai ni kadai, kamar ba daga gurin wata matar ya fito ba. "Ita ma fa haka yake mata ko?" na yi wa kaina tambayar da tado mini da wani kishi mai maiko, sosai nake jin tukukinsa a zuciyata. Yau kuma dakyar na lallaba bacci ya dauke ni. Da safe na tashi jikina wani iri, ni mai lafiya, ni ba mara lafiya ba, a haka na kammala break fast danwaken fulawa da garin alabo na yi, ya ji kuka da kanwa, ga yajina da ya sha tafarnuwa, na soya mangyadana sai bakin shayi. Bayan nan ban yi komai ba, na koma na zauna don ina jinsa a toilet yana watsa ruwa. Kamar minti ashirin ya fito sanye da jallabiya, abin da ya ba ni mamaki, don na yi tunanin zan ganshi ne cikin shirin aiki. Kamar zai tsaga jikina ya shige haka ya zauna kusa da ni. "Har yanzu fushin ne?" ya yi min tambayar hade da yi min kallon da ya kashe min jiki. Ina mamakin a shekarunsa amma har ya iya irin wannan kallon. Kai na girgiza alamar a'a "Amma shi ne ba ki tashe ni ba, na yi shirya don zuwa aiki. Kalli fa agogo" Ya yi maganar hade da juyar da fuskata ina kallon agogon 8:07am ya nuna. "Maman Khalil ta fita?" "Ban sani ba gaskiya, kila ta fita ina kitchen." Maganar gaskiya ita ce na ji fitarta, ina kuma sane naki tashinsa, so nake ta ji abin da nake ji ni ma, na hana shi ya zo inda nake kan lokaci. "Ok" Ya yi maganar hade da janyoni sosai zuwa jikinsa,, gam ya matseni kamar zai shigar da ni kirjinsa, tsawon mintuna kafin ya sassauta rikon yana mayar da numfashi. Dago kaina ya yi da yake a kan kirjinsa, muka zubawa juna ido kafin daga bisani na lumshe nawa, wanda ya yi daidai da hada bakinsa da nawa. Mun dade a haka, kafin ya janyeni a hankali ya nufi dinning yana tambayar "Me aka dafa min ne?" Shiru na yi, saboda jikina ya yi mutuwar da ko bakina ma ba zan iya budewa ba "Wowww! Na ji ya fada, a lokacin da ya bude flask din ya ga danwake. A lokacin ni ma mikewa na yi da kyar kamar mai koyon tafiya na isa kan dinning din, hade da zuba mishi a bowl na kuma zuba mishi bakin shayin da ya sha kayan kamshi. " Gaskiya yau kin yi min komai, akwai kyauta ta musamman. Ina son danwake sosai, kuma na fi son in ci shi a haka, kamar yadda kika yi, bana son wani tarkacen su cabbage ko kwai. A yadda kakaninmu suka ci haka na fi son in ci shi. Madalla da ke." ya karasa maganar gami da kamo hannuna ya dan matse daga bisani ya manna min kiss. Mu ka yi murmushi a tare. A kasan zuciyata kuma jin dadi nake da ban yi mishi bajintar yanka mishi cabbage dasu tumatur ba, da kuma na kwafsa. A natse muke cin abincin, hade da hira a hankali wadda a cikinta ne ya sako abin da yake son fada min. Gabadaya batun nashi a kan zamantakewarmu ne, ta inda yake nuna min in rage kishi, in zauna lafiya da matarsa. Ni na rasa me yake so in yi, ko so yake in kwanta ta rika takani oho, ni dai abin da na sani shi ne, ba zan taba yarda ya fifita wata a kaina ba. Wannan shi ne matsayata. Matar J✍🏻 [12/16, 20:59] 08080966571: *HASASHENA* *Page 10* Kamar kada Kwanaki biyun nan su wuce haka na ji, saboda mun yi matukar rayasu, na ji ni cikakkar amarya saboda kulawar da na samu, ina ma ace kullum haka nake samu, yau kam da ya koma dakin matarsa sosai nake jin kewa, hatta abinci ma na kasa ci, sai dai in tsakura in ajiye. Ina jin taba kofa na san shi ne ya zo min sai da safe, hakan ya sa na gyara zaman da na san zai ja hankalinsa. Ganin Ramla a hannunshi ga Affan biye da shi, sai na ji raina ya dan sosu, saboda na san abin da na shirya ba zai samu ba. Ga shi tun da Ramla ta ganni take daga hannu alamar in dauketa. Ni ma na yi kewar yarinyar sosai, Allah ya sani jin kaunarta nake yi a jinina kamar ni na haife ta. Fushin da nake yi ne da iyayenta ya shafe ta. Wajen kwana takwas kenan ban rabata jikina ba. Da sauri na mika hannu ina dariya, kawai sai ta fado, don dama ta kosa. Na kankameta a kirjina, kamshin turarenta mai sanyi na yara da kuma na mamanta suka cika hancina. Wani lokaci ina jin kamar in ce mata wai ya sunan turaranki ne, sai dai kuma ina gudun yada kai wai sata dakin kishiya. Na dagata sama ina mata wasa, yayin da Babanta ke tsaye yana kallonmu cikin murmushi, da alama mun burgesa sosai, don har waya ya dakko ya viewing namu. Sosai na mayar da hankalina kan Ramla da ke koyan tafiya, sai in aje abu in ce ta zo ta dauka. Da ta fara takawa sai ta zauna, idan kuwa ta iso, sai in dagata sama ina juyi da ita muna dariya. "Na tafi in ci abinci to, na ga kin manta da zuwana sai yarinyarki" Dariya na yi kafin in ce "To a ci lafiya, zan kawota" "ok." ya fada hade da juyawa Ramla kam ta debe min duk wata kewa da damuwar da nake ciki, wasa muke yi muna ta kyalkyala dariya, har zuwa lokacin da su Khalil suka shigo. Salon hirar sai ya canja, muka koma surutun makaranta, da yawan labarin dai Khaleel ne ke bayarwa, saboda Affan mugun miskili ne. Daga baya na fahimci ya fi Khaleel miskilanci, shi Khaleel kafin kusa saba ne. Misalin tara na dare na ba Ramla tea hade da goge mata jiki na goyata, ba jimawa ta yi bacci, su ma su Affan din duk suka yi bacci. Karon farko da na ji ina sha'awar su kwana a dakina. Shi ya sa na bar su, na nufi bangaren Maman Khalil don kai mata Ramla Na kwankwasa kofar falon hade da sallama. "Wa'alaikissalam shigo." aka amsa sallamar hade da bude kofar. Yarinyar nan ce dai da ban san matsayinta ba. "Tana ciki ne?" Da kai ta amsa min alamar eh. Sai na tsinci kaina da jin kunyar hada ido da ita kuma, rashin kirkin da na yi mata a kwanakin nan akwai kunya in hada ido da ita, muddin na san kunyar. Ina cikin shawarar mikawa yarinyar nan Ramla in juya, na ji takun tafiyarta. Daure take da towel, amma babba sosai, saboda ya sauka har saman kwaurinta, Sai kuma hular wanka, da alama wanka za ta yi, ko kuma har ta yi "Ta yi bacci ne?" Ta yi tambayar hade da murmushi. "Eh." Na ba ta amsa. Kamar in nutse, na san kuma ta fahimci hakan "Su Affan fa?" ta kuma tambaya "Su ma sun yi." na kuma amsa ta kaina a kasa "Wannan kam sai na tayaki dakkosu, sun yi nauyi da yawa" cikin dariya take maganar "Ki bar su kawai su kwana a can." Na yi maganar daidai lokacin da nake kwanto mata Ramla. "Sannu da kokari" "Sai da safenmu" Na fada hade da murmushi a kan fuskata, lokaci daya kuma na fice. Saboda na kosa in fita din, ji na nake yi kamar ina gaban surukata. Sosai nauyinta da kunyarta nake ji, har bana son hada ido da ita, ban kyauta ba yadda na yi mata, tana bakin kokarinta a kaina. Bayan na sanya yaran sun yi fitsari, na gyara masu makwanci a gadona mu ka yi kwanciyarmu. Da safe ma ni na shiryasu, abinci ne dai ba ni na yi ba, ta ce ta ri ga ta yi masu. Gidan sai ya zama gwanin dadi, gaskiya zaman lafiya akwai shi da dadi. Tun da kowa ya watse a gidan na shiga zuwa 12pm na gama komai dakin ya fita fes. Na gaji sosai, hakan ya sa na watsa ruwa hade da shan corn flask na kwanta, bacci mai dadi kuwa ya kwashe ni. Cikin bacci na ji kamar mutum a kaina, dalilin da ya sanya ni bude ido a hankali. Idonshi daya ya kanne, hade da yin siririn murmushi. "Mai ciki?" Da sauri na mayar da idanuna kanshi, cike da mamaki "Waye ya fada ma?" "Likitan da ya duba ki" Komai ban ce ba, na mike zuwa toilet. Wanka sosai na yi hade da alwala, lokacin da na fito zaune yake gefen gado yana taba wayarsa. Humrah na shafa hade da sanya doguwar riga, na zira hijab na kabbara sallah. Bayan na idar ne ya ce "Babu abinci?" Cike da rashin jin dadi na ce "Ban yi ba, saboda ban san za ka dawo ba. Kuma ga shi ba a nan dakin kake ba" "Ni ma ban san zan dawo din ba, haka nan kawai na ji ina son ganinki" Murmushi jin dadi na yi kafin na ce "Na gode" "Me za ki ci yanzu?" "Cornflakes zan sha, kafin in gama abinci" Hannayena ya kamo daga kan sallayar, wannan ya sa na mike a hankali. Saman cinyarsa ya dora ni, tare da zare hijab din da ke jikina. Kanshi ya kwantar a kan kirjina, yayin da hannunshi daya ke kan cikina ya ce "You're not alone yanzun, ki rika cin abinci mai kyau da gina jiki. Sannan yawan aikin nan at this stage bai kamata ba." Kai na jinjina alamar fahimta, yayin da kulawar tashi ta yi min dadi. "Za ki iya zuwa restaurant mu sawo abinci, ko za ki jira in sawo miki" Da sauri na ce zan je, saboda na tabbata Maman Khalil ta kusa dawowa aiki, zan yi matukar farin ciki ta shigo gidan ba ta same ni ba, sannan a kan idonta mu dawo tare da mijinta, ahhh har wani takun kasaita zan yi. Na fita da miji ranar girkinta. Ai da sauri na shirya muka fice, a can din ma haka nai ta shiriritar da shi har la'asar kafin mu ka dawo Har farfajiyar gidan ya kawo ni, ina fita ya juya, sosai raina ya yi min ba dadi, saboda ban ga motar Maman Khalil ba, zuciyata tai ta yi min sake-sake, ta dawo ne ta kara fita, ko ba ta dawo ba, ko kuma motar ta samu damuwa ne? Da wadannan tambayoyin na yi knocking kofarta, yarinyar nan ce ta bude. Cike da girmamawa ta gaishe ni, karon farko da na tambayi sunan ta "Sunana Suwaiba" ta amsa min "Kina ta ya ta aiki ne?" Kai ta jinjina alamar eh "Ta dawo ne?" "A'a basu dawo ba" A cikin zuciyata na ja tsoki hade da juyawa zuwa bangarena. Sai kuma duk na kasa nutsuwa, saboda ba ta saba kaiwa har wannan lokacin ba ta dawo ba. Ko motarta ce ta lalace sha Allah zuwa uku tana gida shi ne ma ta dade. Wayata na dauka hade da dialing lambarta. Ita ce ta fara cewa "Kin ji mu shiru ko?" "Ai kam dai, na ce ko lafiya?" "Lafiya kalau, na biya wani wuri ne, amma ina hanya sha Allah" "To Ma Sha Allah, Sai kin kara so" "To na gode sosai" A tare mu ka yanke kiran, alwalar sallahr la'asar na yi, a kan sallayar na zauna bayan na idar ina taba chat, da ƴan'uwa da kuma kawaye. After 10mns na ji karar motarta, ina zaune a wurin dai na ji an taba kofata alamar ana shigowa. Kofar na zurawa idanu har zuwa lokacin da Affan ya shigo hannunsa rike da bakar leda. Na san ba magana zai yi ba, shi ya sa na karba hade da budawa,, magarya, kurna, aduwa da kuma taura na gani a ciki. "Waye ya ba ka?" "Mamana." ya ban amsa a hankali. "Ta ce ka kawo min?" Daga kai ya yi alamar eh "To je ka, ka ce na gode." Bayan fitarsa na kuma bude ledar ina karewa kayan kallo "Kenan matar nan ta san ina da ciki? Waye ya fada mata?" Shiru na yi ba tare dana amsa tambayar ba, har zuwa lokacin da na lalubo amsar Na san ba mai fada mata sai mijinta. Kenan ni ban da sirri, komai nawa sai ya fada mata. "Mtswww!" na ja dogon tsoki, a bayyane na shiga fadin "Gaskiya ba zan yarda ace ba ni da sirri ba, ace komai nawa kishiya ta sani bayan ni bai fada min komai nata. Allah ya kaimu ya dawo, wannan karon ma zan magantu." Dalilin da ya hana ni zuwa sashenta, Sai ma na mike zuwa kitchen, yayin da na aje ledar tarkacen a kan dining. Aiki nake yi, sai dai raina Sam babu dadi, na kosa ya dawo kamar in sanya igiya in janyo shi. Misalin 6pm kuwa ya dawo, 6:30pm ya shigo bangarena cikin shirin masallaci. Time din hakimce nake a kan kujera ina taba wayata. Da kyar na amsa sallamar da ya yi "Me ya faru na ga kamar ranki bace?" Ya yi tambayar idanunshi a kaina. "in yi magana ka ce bana son zaman lafiya." na amsa shi cikin tabe baki "Ki yi ina sauraronki." "Me ya sa don Allah ba ka son rufe sirrina?" "Sirrinki kuma, me kike nufi?" ya yi maganar hade da tattara duk hankalinsa a kaina. Yunkurawa na yi hade da mikewa zaune na ce "Ni ba ina son tsara ma yadda za ka zauna damu ba ne, amma yana da kyau ka rika boye sirrinkanmu, me ya sa za ka fadawa matarka ina ciki?" "Ni din?" sosai fuskarsa ta canja a lokacin da yake maganar zuwa nuna alamar damuwa "To idan ba kai ba, wa? Ni dai ban taba fada ma wani ina da ciki ba, idan ba ta san ina da ciki ba, me ya sa za ta kawo min wannan?" na karashe maganar hade da dakko mishi ledar da ke kan dinning ina bude mishi. Kallon abin da ke cikin ledar yake kafin ya ce "Yanzu kawai don ta kawo miki wannan shi kenan sai ki yi zargin ni na fada mata kina da ciki? To wai ma me ye don Sakeena ta san kina da ciki? Mayya ce ita da za ta lasheki, kafin ki yi ciki ba ita ta fara ba. Wai me ya sa kullum kike son tayar min da hankali ne Khadija?" Rai bace ya karasa maganar, haka yanayinsa ma ya canja. Ni kaina sai na ji jikina ya mutu,, na kuma yi nadamar maganar da na yi. Kafin in yi wani yinkuri tuni wayar da yake kokarin kira ta shiga Hands-free ya sanya lokacin da ya fara magana " Sakeena!" "Na'am" na ji ta amsa da alamar tsoro. Kila ba ya kiran sunanta kai tsaye haka, Sai da babban dalili "Kina ina?" "ina daki" ta kuma ba shi amsa da yanayin mutuwar jiki a tare da ita "Zo bangaren Khadija ina son ganinki." Bai bari ta bayar da amsa ba ya kashe wayar. Yayin da ni kuma na yi tsuru-tsuru hade da fargabar abin da zai faru. Ko minti daya ba ta hada ba, ta shigo falon nawa. "Ke ce kika ba Khadija wannan?" tambayar da ya fara jefa mata kenan bayan ta shigo, lokaci daya kuma yana nuna mata abun da ke cikin ledar da ya karbe a hannuna. "Eh ni ce" a tsorace ta ba shi amsa, saboda ganin yanayinsa. "A ina kika samu?" "Malama Maryam kawata ce da ta yi tafiya, shi ne da muka biya dazu wajen ta, ta ba yara. , sai na dan debar mata na ga abun marmari ne" Har yanzu a tsorace take maganar "Shi kenan."Ya fada hade da ajiye ledar ya fice ya bar mu a tsaye kowa jiki a sanyaye. Ni dai a bangarena yadda lamarin ya tsaya haka ba karamin dadi ya yi min ba. Yanzu rigimar tsakanin ni da shi ne. Kai barka bante. "Me ya faru?" ta katse min tunanin da nake yi "Ba komai, ya dauka na fita ne wai bayan kun fita" "Au ho!" ta ba ni amsa hade da ficewa. Fitar ta ke da wuya na shiga bubbuga kafafuna, cikin rashin sanin abun yi. "Wallahi idan akwai abin da ya kamata a budewa mata aji a kansa shi ne yadda za su zauna da kishiya. Gabadaya na damalmale komai, na zama sakarya wawiya, ina son cusa kiyayyata a zuciyar mijina da kaina." Hannu na kai na share hawayen da ke bin fuskata. Ni sam ban san haka zama da kishiya yake ba. Ashe dole sai ka iya takunka, idan ba haka ba, Sai a samu matsala. Lallai wannan kalubale ne ga yan'mata masu shirin auran mai mata, kuma suke tunanin cewa, ta gida ta kasa ne, ko an gama yayinta shi ya sa ake son kawo ki, wannan babban kuskure ne muke yi, sai mun shigo kuma zamu gane hakan. Kamar ni yanzu uwargidana ai babu abin da zan nuna mata, kyau, ilmi, hankali, tsafta, girki, kula da miji duk ta iya. Akwai wadanda kuma suke da nakasu, amma kuma dole dai ke amarya ki bi su, kafin ke ma ki zama yar gida. Kamar yadda uwargida ke fuskantar kalubale idan aka mata amarya haka ita ma amaryar ke fuskanta muddin tana da uwargida. Ni dai yanzu ganau ce ba jiyau ba. Na bata darena na gobe kuma Don ya yi fushi irin wanda ban taba gani ba. Matar J✍🏻 [12/17, 06:26] 08080966571: *HASASHENA* *Page 11* Daga sallar magriba zuwa isha'i haka nan na yi su, ba don ina cikin nutsuwa ta ba, tun da na zo gidan, ban taba yin abin da na yi danasani ba irin wannan. Wata zuciyar fada min take yi in gudu gida kawai. Dama ban yi tunanin zai shigo yi min sai da safe ba, Sai ko ga shi bai shigo din ba. Abin da ya kara dama min lissafi, duk soyayyata da bacci, yau dakyar na samu ya dauke ni, shi ya sa na tashi duk ba na jin dadin jikina. Hatta bakina testless ya zama Yanzu abokin shawara nake nema, amma na rasa da wa zan yi ta, Ummana ba na son daga mata hankali, bai kamata ace mu biyu da ta aurar kullum cikin kawo mata Matsaloli muke ba. Ga shi ba ni da wata yar'uwa ko kawa a Abuja bare in fada mata damuwata, don kuwa wannan matsalar ba ta waya ba ce. Saboda gabadaya duk wata basira tawa ta kare, a duk lokacin da na yi kokarin daidaita abu, sai ya kuma lalacewa. Haka na wuni zur ina sake-sake, har zuwa dare, lokacin da nake tsammanin shigowar shi, Sai ko ga shi ya shigo din, amma yanayin da ke kan fuskarshi, bai ba ni damar yin magana ba , dole na janye jikina, kila zai fi bukatar hakan. Haka mu ka yi wadannan kwanakin, gaisuwa ce kawai ke hada mu, ya duba abin da babu a kitchen ya kawo, a haka ya koma dakinta, yayin da ya bar ni da kuka mai cin zuciya. kwanana ya kuma zagayowa. Wannan karon kam, na daura aniyar sasantawa, ba zan yi kasa a gwiwa wajen ganin na yanke wannan fushin na shi ba. Abincin da ya fi so na yi, wato tuwo da miyar kuka. A aljihuna na cire kudi aka sawo min kaza na kawata miyar da ita. Bayan na gama, na fita cikin dogon farin wandona jeans na mata da bakar riga mai guntun hannu, gaban rigar a bude haka ta zauna jikina hade da fitar mini da surar jikina. Dama ga matashin ciki ko ina ya kara cika tubarakhallah Turare mai sanyin kamshin na sanya, bayan na manna kananan yankunne a kunnena. Sosai na yi kyau musamman dana tsaya gaban mirror, cikina dan wata hudu kamar ba shi a jikina saboda yadda cikin yake a shafe. Takwas daidai kuwa ya shigo, abin da ya sanyani farin ciki, duk da babu wata walwala a kan fuskarshi "Sannu da zuwa." na fada a daidai lokacin da yake zama a kan kujera. Bai amsa ba, dalilin da ya kara tabbatar min da har zuwa lokacin dai fushi yake yi sosai. Dukawa na yi a gaban sa hade da dora kaina a kan cinyarsa, na ci gaba da rera masa kuka, saboda ban da komai yanzu sai kukan. Tsawon lokaci yana ji na, bai yi magana ba, ni kuma ban daina kukan ba. Kila gajiya ya yi, kaina ya dago tare da fadin "Shi kenan ya isa" fadin maganar ta shi daidai da mikewarsa ya shige bedroom. Ban yi kasa a gwiwa ba, na bi bayansa ina share ragowar hawayena "Idan kin san kuka za ki yi min, please get outside" ya yi saurin fada ganin na nufi inda yake kishingide Dakatawa na yi, hade da yin kalar tausayi, ni ban karaso ba, kuma ban koma baya ba. Kamar 2mns muna a haka. Kafin ya daga hannunsa hade da yafito ni "Zo nan." Na kuma langabewa sosai na karasa gurinsa. Jikinshi ya janyo ni, hade da kwantar da ni sosai, ina jin yadda kirjinshi ke bugawa da sauri "Khadija ki dawo cikin hankalinki, don Allah kar ki ɓata mana zama. " A sanyaye ya yi maganar bayan ya kwantar da ni akan kirjinsa yana shafa bayana. Ban yi magana ba, illa dai na dago hade share hawayen tausayin kaina, daga bisani kuma na koma na kwanta. "Kina kokwanto ne a kan son da nake yi miki?" Girgiza kai na yi alamar a'a "To me ya sa kullum kike tuhumata a kan na fifita wata a kanki?" "Ka yi hakuri don Allah, sha Allah ba zan kara ba." "Hmmmm!" kawai ya ce kafin shiru ya ratsa tsakaninmu. "Ya kamata in sanar da ke wacece Sakeena a wajena, kuma ki san wacece ita." Ya yi maganar hade da janyeni daga jikinsa, wanda hakan ya nuna mun yana bukatar natsuwata. Ni kaina ma ina son sanin wacece ita, kuma tun farko ma abun da ya kamata kenan in sani ta yadda zan san ya zan zauna da ita. Dalilin da ya sa kenan na tattara hankalina ni ma kaf a kansa ina sauraronsa. "Duk wani namijin da ya samu Sakeena a matsayin mata, to sai dai ya kara aure a matsayin sunnah, ba wai don gazawarta ba." Ya yi maganar idonsa a cikin nawa. "Ni ce zan ba wani labarin hakan, don kuwa ni ma da nake mace kuma Sakeena take matsayin kishiyata, sosai take burgeni da halayyarta, har ina jin ina ma ni ce ita. To bare kuma namiji" a cikin zuciyata nake maganar a zahiri kuma shiru na yi "Wani irin zama ne muke yi da Sakeena mai cike da kauna, sadaukarwa, kyautatawa, kawaici, taimakeninya da kuma fahimtar juna." Ya dan tsagaita hade da kallona, ni din ma shi nake kallo bayan da na rungume hannayena a kan kirjina. "Ko wanne fanni Sakeena kwararra ce, girki, iya mu'amala, tsafta, kwalliya kula da, gida, babu wanda Sakeena ba ta kware ba." "Dangina basu da matsala da ita, ta iya zama dasu da tafiyar dasu yadda ya kamata duk kuwa da yawansu." Jijjiga kai na shiga yi, don ni ma na san gaskiya ya fada. Babu inda ya yi kari. "A yadda muke zaune da Sakeena babu wanda ya taba tsammanin zan yi mata kishiya, saboda ta ba ni komai. Akwai hidimomi masu yawa na gida da ni sam na manta dasu ma ita ce ke yi." Na kuma Jijjiga kai alamar gamsuwa. "Ke hatta matsalolin dangina wani lokaci ita ke magancesu, sai dai in ji an ce an yi ka za, da na ji na san ita ce ta yi." "Eh Sakeena ta same ni da abun hannuna amma ni ma da nata na sameta, na dan ciccibata ne kadan. Babu wani raini ko gori a tsakaninmu, tana da hakuri sosai, zan yi mata laifuka masu yawa, amma ba za ta yi magana ba, ni da kaina wani lokaci nake zaunawa in ba ta hakuri hade da yi mata ihsani da zai sa ta manta da wuri. Babu wanda za ki ji a yan'uwanta ko yan'uwana ya ce ta kai mishi korafina " Hannuna a kan haba nake sauraronsa. " Ban ce miki ba ma fada ba fa, muna yi sosai ma, don tana da zuciya idan aka kureta, ba ta ki a mutu ba. Kin san an ce mai hakuri bai iya fushi ba. " " Wannan haka ne" a karon farko da na yi magana. "Mun sha yin fada, fada sosai, wani lokaci mara dadi da kyan gani ma. Na sha amfani da wannan hannun na mareta, kin san ni ma ina da zuciya da saurin fushi" ya yi maganar hade da daga hannun nasa yana wani irin murmushi. Ido na zaro ina ma sa kallon mamaki "Yes!" ya fada alamar tabbatarwa Shiru na yi komai ban ce ba. Shi ne ya dora da "Da can ni namiji ne mai hange-hange, na yi yan'mata kala-kala masu addini da marasa shi. A lokacin Khalil kawai Sakeena take goyo, ba sai na fada miki halin da mace kan shiga idan ya kasance mijinta yana neman mata ba. To irin wannan halin Sakeena ta shiga, ta rame, ta lalace ta fige yayin da ni kuma hankalina yake a kwance. Ba kunya wani lokaci nake kwana a waje da safe kuma in dawo ina mazurai, wani lokaci ta yi magana wani lokaci ta yi shiru. Sakonnin yan'mata, hotuna, babu wanda Sakeena ba ta kama a tare da ni ba." Ya dan tsagaita hade da kallona, yayin da ni ma shi nake kallo cike da mamaki Sosai na tsorata da abin da yake fada min, don kuwa bai yi kama da wanda zai iya aikata haka ba. Ganin ba ni da niyyar magana ne ya sa ya ci gaba. " Sam! Ba ni da lokacinsu ita da Khalil lokacina daga aiki sai rayuwar dana sanya a gaba, aikin da take ya taimaka mata matuka, saboda ba ta tambayata komai sai idan ni na yi niyya na ba ta. Sai in fi karfin wata ban hada shimfida da ita ba." Ya kuma dago kai ya kalleni, ni ma shi nake kallo cike da mutuwar jiki, yayin da tausayin Sakeena ya kama ni, ni ma nan da Allah ya halatta mishi Sakeenar haushi da kishi nake in gansu a tare ina kuma ace yana tarayya da mata a waje. Kila zan yi ta suma ne kullum. Amma ita baiwar Allah ta jure ta kuma shanye. A hakan ma bai kyale ta ba, Sai da ya hada ta da kishiya wato ni. "Mun sha rikici ba kadan ba, ta matsa lallai sai na sake ta, ni kuma na ki yin hakan, watarana sai ga ta da condom wai gudunmuwa ta kawo min, tun da na ki sakinta, in kare lafiyarta" ya karasa maganar cikin wani kalar murmushi da na kasa fassarawa. Ko motsi ban yi ba, hakan ya sa ya ci gaba "Karon farko a rayuwata da na fara bude baki na zageta,, na ce ta mayar da ni mazinaci, na rika shiga ina fita cikin masifar nade tabarmar kunya da hauka, saboda ai ta sha kama condom din a cikin kayana, sai in ce a office namu ne ake rabawa. Wani lokaci ta ce "Saboda an san halinku, a rasa abun arzikin da za a raba maku sai condom" wani lokaci kuma shiru take yi" Ya sauke ajiyar zuciyar da ke nuna tsantsar nadama a kan fuskarsa " Har na gama bala'ina ba ta ce komai ba, tana zaune a gefen gado hannunta rike da condom, da ta fahimci na yi masifar mai isata, sai ta mike ta aje condom din a aljihun jakar da nake zuwa office ta yi ficewarta. Abin da zai ba ki mamaki shi ne daga karshe dai na yi amfani da condom din da ta ba ni." " Kuma ta gane ka yi amfanin da shi? " Na Jefo mishi tambayar cikin zakuwar jin amsarta. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya ce" Ranar na shigo gida misalin 12 saura na dare , ina toilet na ji alamar ta shigo dakina, lokacin da zan fito sai na sameta hannunta rike da jakata" "Lafiya na tambayeta?" Ba ta yi magana ba illa ta koma gefen gado ta zauna hade da bude gurin da ta sanya condom, sosai gabana ya fadi a lokacin. Ba jimawa kuwa ta zaro ragowar condom din guda uku da ya rage ta ce "Balan-balan ka yi da sauran ko ruwa ka dura kana wasa?" Ta yi tambayar hade da tsare ni da ido. Na fara kame-kamen na ba abokina ne kyauta, sai kawai ta fice daga dakin. Hannuna a kan haba nake kallonsa, yayin da bangare daya nake tausayawa Sakeena, gaskiya ta yi hadiya kamar maciji. Wato kai dai ga mata da miji, su suka san yadda suke zaman auransu, ni dai ina ji a jikina ba zan iya wannan ba. "Irin wannan kalar labarin ba zai kare ba. Ita din jaruma ce. Duk wani abu da zai faru a nan gaba, ba kamar na baya ba ne. Ita a yanzu take jin dadin zama, shi ya sa za ki ga kamar babu wani abu na bacin rai da ake yi mata. To ai ta hadu da abun yafi, abin da yake faruwa yanzu" Ni bakina tuni ya kulle sai ido. Yayin da shi kuma yanayin ya kara canjawa sosai alamar rashin jin dadi, kafin ya ce "Watarana ina tare da sabuwar budurwarta kiran Sakeena ya shigo wayata,, kamar in daga sai kuma na fasa, don sai mu fi wata ba ta kirani ba, idan har zan ga kiranta to na san matsala ce, ni kuwa bana son abin da zai yanke min jin dadina a lokacin. "Ta ci gaba da kira, ni kuma ban daga ba, can sai ga sakon ta kamar haka." _Khalil ba lafiya don Allah ka zo ka kai mu asibiti_" "Na karanta sakon nata hade da aje wayar, na san halinta akwai rudewa a kan ciwon yaro kila ciwon bai yi zafi ba amma duk ta rude. Ban kashe wayar ba haka ban tafi ba." "Da misalin karfe biyar na yamma na fita da Ruky don yi mata shopping kawai na hadu da Maman Khalil da kawarta Rahma na rungume da Khalil yayin da Sakeena ke rike da ledar magunguna..." "Subhanallah!" na yi saurin katse shi, kafin ya yi magana na kuma cewa "To ya ka yi?" "Yadda ba ta min magana ba, haka ni ma ban yi mata ba, suka tare napep, ni kuma na shige mota da Ruky, sosai Rahma ke ta kallona, don har tuntube ta yi saboda kallona." "Dole kam" na yi maganar a sanyaye "Daurewa kawai na yi na shiga gida misalin goma na dare, dole dakinta na wuce. Zaune take kan sallaya hannunta rike da alqur'ani tana karantawa. Ji na yi jikina duk ya mutu don rabon da in dauki Qur'ani da sunan karatu har na manta lokacin. Ni kaina wani lokaci na san ba a kan daidai nake ba. Khalil na nufa da niyyar taba jikinsa, amma kamar fitar kibiya haka na ji Sakeena ta hankade ni gefe, lokaci daya kuma ta zuba min idanunta da ya canja zuwa kalar bacin rai tsantsa, tsana da kiyayyata da kuma kyamata kawai nake hangowa cikin idanun nata." Ya dan numfasa kadan, kafin ya dora da " _Kar ka sake ka taba min yaro Bashir! Sai yanzu ne ka ga sakonmu? Yanzu ne ka tuna kana da yaro? Yanzu ka ji ya kamata ka waiwayi lafiyarshi? Tur da kasancewarka mahaifin Khalil, na tsani zama da kai Basheer na tsaneka, ka fitar min daga daki."_ haka ta rika fada min cikin hargowa mai tattare da bacin rai " Na yi kamar ban ji gargadin nata ba, na nufi yaron a karo na biyu." " Fittt! Na ga ta fitar da sabuwar wuka daga kan mirror, sannan ta tsaya inda yaron yake tana fadin _Wallahi idan ka kuskura ka matso nan sai na farke cikinka_ "Sosai abun ya ban mamaki, saboda na fahimci za ta iya aikata hakan a kwayar idonta Rikici mu ka yi sosai a wannan dare, wanda har ya yi sanadiyyar da na wanketa da mari bayan na yi amfani da karfi wajen karbe wukar hannunta. Karon farko da ta hada kayanta da niyyar yaji" Haka nan na ji idanuna sun cika da kwalla, saboda ina jin daci da zafin abun a zuciyata. Ji nake kamar ni ce aka yi wa haka. Ga mari ga tsinke jaka kenan. "Ai tun farko ya kamata ta yi hakan" na yi maganar cikin kunar rai hade da dauke hawayena. Jikinshi ya janyo ni hade da bubbuga bayana alamar lallashi kafin ya ce "To ai dalilin da ya sa kenan ki ga ina mutunta ba na son bacin ranta, don kuwa duk cikin Yan'uwana ko nata ba na jin wani ya san halin da muke ciki, amma kawarta Rahma ta sani, na san Maman Khalil ta yi kokari sosai wajen shiryuwata, ta hanyar hana idonta bacci don yi min addu'ar shiryuwa, yanzu kuma ga shi na shiryu, rayuwar ba ya ba ta burgeni, har na kuma cin karo da wata abincin ruhin nawa." Ya kai karshen maganar tare da dago kaina, yana yi min wani irin kallo *MATAR J*✍🏻 [12/17, 06:37] 08080966571: *HASASHENA* *Page 12* "Kin san me ya sa na fada miki duk wannan?" Ya yi maganar hade da dago kaina da ke kan kirjinshi Kai na girgiza alamar a'a "Ina son ki sani ko wane da kalar kalubalenshi a zaman aure, idan kika ji na wani, ba za ki iya dauka ba. Sannan da yawa ku 2nd wife din nan bonus kuke samu fa. Uwargida ta gama yi muku duk wani aiki, kila ita ce ta sha wahalar talaucinshi, ta biyu ta ci arzikinshi. Kila ita ta sha wahalar kuruciyarshi ta biyu ta samu dattakonshi"ya tsagaita hade da kallona. Ganin komai ban ce ba ya sa ya ce "Ina sonki sosai Khadija, son da ba zan iya rabuwa da ke ba, kuma ba na son ganin bacin ran ki. Hakan kuma ba ya nufin ba na son Sakeena, bayan so akwai shakuwa irin ta ka dade da mutum din nan . Ki yi hak'uri ke ma za ki ta ka wannan matsayin but a hankali." Kai na jinjina alamar na fahimta "Ina son ki zauna da ni fiye da yadda Sakeena ke zaune da ni." "Ahhh! Karya da ciwo mari da zafi ba zan iya ba, Sakeena bugun da ce, mu kuwa bugun zamani" A zuciyata na yi maganar a zahiri kuma sai na ce "Zan iya yin hakan muddin ni ma za ka rika nuna ni matarka ce" Ido ya zaro cike da mamaki "Yanzun don Allah bana nunawa, cikin jikinki na waye?" "Naka ne, kuma ai anan din ne kawai na san ni matarka ce" na yi maganar hade da tura baki "Za ki fara ko?" "A'a." Na ba shi amsa hade da mikewa a karo na biyu ina fadin "Mu je ka ci abinci." "Me kika dafa min?" "abin da ka fi so" "Tuwo?" ya yi tambayar a lokacin da yake sakkowa daga saman gadon, lokaci daya kuma mu ka jera zuwa falon "Exactly" na ba shi amsa ina murmushi "Kin san kuwa kin iya murmushi, kuma yana kayatar da fuskarki?" Na dakata da zuba mishi miyar ina kallonshi cikin wani murmushi, da kuma wata sabuwar kaunarsa da na ji tana ratsa duk gabobina. Don kuwa maganar ta yi min dadi. "Don Allah jira a haka in yi miki hoto" Maimakon cin abincin sai muka bige da yin hotuna kala-kala, sai wajen goma da rabi mu ka fara cin abincin. Can dare kasa bacci na yi, mamakin labarin da ya ba ni nake yi, na godewa Allah lokacin da na zo ya shiryu don ni ba zan iya juriyar Sakeena ba gaskiya. Yanzu ma ina jin zafi, bare ace presently yake faruwa da ni. Shi ya sa ya iya tafiyar da mace ashe ya ɗan taɓa bude idonshi. Duk irin zafin mace sai idan ba ta shigo hannu Basheer ba,, har mamaki abun ke ba ni, a shekarunsa amma ya iya salo-salo na janye hankalin mace. Wanshekare ma Maman Khalil a gida ta bar Oga, amma kuma ban bari ta tafi da Ramla ba karbeta na yi. Na fahimci tana jin dadi sosai idan na ja yaranta a jikina, abin da ba ta sani ba shi ne, Ita Ramla har cikin jinina nake jin sonta, ko wuni na yi ban ganta ba sai in ji duk na damu, bana gajiya da ita. Bai fita gidan ba sai 12 saura na rana, a lokacin kuwa ina ta hidimar abincin rana Ramla na barci. Dambun shinkafa na yi, ya ji zogale carrot da kayan miya, na soya man gyada hade da daka kuli-kuli da ya sha citta. Na kammala komai a kan tebur sannan na shiga wanka. Doguwar rigar atamfa mai ruwan hoda na sanya, wacce ta sha adon duwatsu tun daga sama har kasa. Sai da na gabatar da sallahr azhar sannan na zauna gaban madubi ina murza mai. Karar bude kofa ya sanyani saurin juyawa, shi ne ya shigo dauke da Ramla "Ta tashi?" "Ina bude kofa ta tashi." "Ka ce dai kawai kai ne ka tayar min da yarinya" Cikin murmushi nake maganar, lokacin daya kuma na katse shafa man da nake ina niyyar daukarta "Wani fresh kike yi fa, Abuja ta karbeki." "Abun kuma har da tsokana" na yi maganar a daidai lokacin da nake shiga toilet don watsawa Ramla ruwa, don ana zafi kadan "Yunwa fa nake ji, ku mata idan kuka yi yara shi kenan duk kulawarku sai ku mayar da ita a kan yaran" cikin zumbura baki ya yi maganar wai shi shagwaba Sosai nake dariya a lokacin da nake yi wa Ramla wanka "To wai kishi kuke?" "Kishin ma ai sai mu yi, tun da na shigo fa hankalinki a kan yarinyar nan yake, kalli kuma kin bar ni tsaye wai kina mata wanka, ki gama ki ce shirya ta za ki yi, to ni a tsaye zan kare kenan?" Na kuma tuntsirewa da dariya "To ba ga shi har an gama wankan ba" Na yi maganar ina dora Ramla a bayana. "To mu je falon ranka ya dade Alhajina" komai bai ce ba ya juya zuwa falon Bayan na zuba mishi Dambun da yake ta santi tun kafin ya ci, kan kujera na koma ina shirya Ramla, rising powder kawai na sanya mata a wuya, na dakko guntun wando na jeans wanda iyakarsa rabin cinya na sanya mata hade da farar singileti. Saboda kayanta rabi duk suna dakina. Sosai ta yi kyau, don haka na dakko waya ina mata hoto, Babanta na kallonmu cike da kauna. Daga bisani shi ma wayar ya dakko yana mana. Sallamar da aka yi ce ta dakatar damu, lokaci daya kuma mu ka mayar da hankalinmu wurin kofar shigowa. Su Khalil ne da Affan suka shigo ko kayan makarantar su ma basu cire ba "Yarana kun dawo?" na tambayesu, ina kallon yadda suke ta ɗokin ganin Ramla kamar sun shekara basu ganta ba "Ehhhh!" suka amsa ba ki daya lokaci daya kuma suna ba Ramlan tsarabar sweet, da biscuit. "To ku mu je kuma ku yi wanka sai mu ci abinci." na dakatar da wasan da suke niyyar farawa "To! Ni bari in je in nemi wurin bacci don ba za ku bar ni in yi bacci ba." Abbansu Khalil ya yi maganar hade da mikewa tsaye daga kan dining din "Dady ina wuni?" yaran suka fada yanzu hankalinsu a kansa. "Sai yanzu kuka ganni?" "Da gaske kana da kishi" cikin dariya na yi maganar, lokaci daya kuma ina tasa keyar yaran zuwa toilet "Ka yi hakuri muna gama wanka zamu fita sai ka y baccinka" na kuma fada wanda ya yi daidai da shigewarmu cikin toilet. Wankesu na yi fes, na murza masu mai mara maiko, su ma na basu guntun wando da vest suka sanya, don su ma akwai kayansu kadan a wajena. Dambun na zuba a babbar kula hade da daukar robar yaji na ce su mu tafi bangaren Momynsu. A kitchen muka sameta tana ta kiciniya, saboda yar aikinta ta je ganin gida, kodayake ko tana nan ma, nata wanke-wanke ne sai mopping da shara, mopping din ma watarana Maman Khalil din sai ta sake. Kullum cikin fada suke da yar aikin, wai ba ta yi mata aikin yadda take so. Ta fadada fara'arta tana kallon yaran cike da kulawa, "Auntyn Ramla ce ta maku gayu?" (Haka yaran ke kirana Auntyn Ramla) Dukkansu suka amsa da "Ehhh" Mika hannu ta yi hade da karbar kular hannuna "Wowww!" ta fada bayan ta bude "Yau kam kin yi babban masoyina aiko zagina za ka yi kuma ki ba ni dambu zan amsa wallahi" Ta kai karshen maganar tata hade da fitowa daga kitchen, tare muka shiga falo da ita A kasa na zauna, hade da kwantar da Ramla a kan cinyata ina warware mata kitson da ke kanta. "Wai wani kitson za ku sake kuma?" ta yi tambayar a daidai lokacin da suka zagaye plate din dambu ita da yaranta suna ci "Eh" "Kuma dai gashin ba fitowa zai yi ba,, irin yadda kuke so din" Dariya na yi kafin in ce "Amma ai ba a cewa Ramla ba ta da gashi kuma, sannan zamu baku mamaki" "Ni ce zan ba ku mamaki, yayeta zan yi" Na yi saurin kallonta hade da dakatawa daga tsifar kan da nake yi ba tare da na ce komai ba "Da gaske gobe zan Yayeta, ta sha da yawa ai" Cikin murmushi take maganar. "Haba don Allah, duka watanta nawa?" " Sha shidda fa" "Har ta yi sha shidda?" "To ki lissafa,, lokacin da kika zo watanta goma ke kuma yanzu watanki shidda" "To ki bar ta ta kai sha takwas mana" na yi maganar cikin maraicecewa Dariya ta yi kafin ta ce "Allah ya isheni haka nan" "Eyyahhh Momy ki bar ta ta kai sha takwas mana" Cewar Khalil da ya cika baki da dambu Muka tuntsire da dariya kafin ta ce "ji shi kamar ya san abin da ake magana a kai" A bangarenta na yi sallahr la'asar, mu ka yi homework da su Khalil sannan na baro bangaren, inda na sanyawa raina ni ce zan yaye Ramla. Kashegari kuwa da ya kama Juma'a sai ga ta da kayan yaye irin su Bobo, kwai, kayan tea, happy hour na yara, pampers ƙaramin flask, biscuit da cheese. "Wannan duk kayan yayen ne?" Na tambaya a lokacin da nake tattabasu Dariya ta yi, amma ba ta ce komai ba "Allah sarki mutanen kauye, wallahi yaransu na ganin rayuwa idan za a yayesu, yaro ya tashi cikin dare yana kuka a mika mishi tuwo ko koko me sanyi, amma ji wai nan duk kayan yaye ne kamar za a bude shago." na yi maganar a zuciyata, a fili kuma sai na ce "Ina za ki kai Ramlan yaye?" "Ba ko ina, dama kawata Rahma ke yayesu to yanzu kuma ba ta nan, suna waje ita da mijinta" "To ni zan yayeta." Waro ido ta yi hade da zuba su a kaina, ba tare da ta ce komai ba. "Da gaske nake fa" "Don Allah ki ji da kanki, yaushe za ki iya da rigimar yaye?" "Ba za ta yi min rigima ba" cikin dariya na yi maganar. Ita ma dariyar take lokacin da take fadin "Don Allah rufa min asiri" "Kin san Allah ni zan yayeta a cire maganar wasa." Kallo na take yi cikin ido cike da mamaki. "Gaske nake fa" "To ai shi kenan, idan ta dameki ai kya maido ta" Murmushi na yi ina tuna shawarar Samira da Badiyya lokacin da na fada masu matsalata, masalaha ta farko da suka ba ni, shi ne in ja yaranta a jikina, in rika kyautata masu, mai ɗa mahaukaci ne, muddin ina hakan, zan saye zuciyar mijina, ta kishiyata da kuma yaran, sannan zai wahala ya rika ganin laifina, dalilin da ya sa kenan nake son fara yi masu bauta, tun da na fahimci muddin ka auri mai mata da yara sai ka zama kamar bawa. Ko ba komai za ka samu karɓuwa wurin miji. Matar J✍🏻 [12/18, 06:38] 08080966571: *HASASHENA* *Page 13* Kamar wasa na dauki yayen Ramla, kuma ba ta yi mini wani rikici mai yawa ba, ranar farko da ta biyu ne kawai mu ka sha rigima, daga nan kuma ta hak'ura, dan rikicin ba yawa. Dalilin ya haddasa karin shakuwarmu da yarinya fiye da baya, son yarinyar da kaunarta ya kuma shiga zuciyata. Komai nake Ramla, duk wani makusanci nawa idan mu ka yi waya sai ya tambaye ta. Musamman Ummana, kanwata Yusrah da kuma Maryam. A bangare daya kuma kimata mutumcina sun karu sosai a idanun iyayenta, musamman Babanta da kullum nake ganin tsantsar kaunata a idonsa. Baya son ya ga ɓacin raina, yanzu zai damu har sai ya ga na warware. Cikin sati daya da yaye Ramla ta warware sosai, babu wata rigima sai wasa. Sosai iyayenta ke mamaki, musamman Mamanta ta kan ce "Ramla ce kawai yayenta ya yi sauki. Babu rigima babu ciwo" Mun shiga sati na biyu da yaye Maman Khalil ta shiga shirin tarar kawarta Rahma. Wacce za ta dawo daga China, wai mijinta ne aka tura aiki can shekararsu biyu. Ni har na kosa in ga wannan Rahma, don kuwa hatta sabon dinki Maman Khalil ta yi masu iri daya, sannan ta yi wa yaran, gidan Rahman an je an share an zuba sabbin furnitures, na rasa irin wannan kalar kawance na amana, babu bakin ciki ko hassada. Ni dai nawa ido, wani lokaci kuma idan ina son yawo sai in bi ta zuwa wani wurin. Ranar kuwa da za su dawo,, wai jirginsu karfe uku zai yi landing. Maman Khalil tun biyu ta kammala komai na abinci aka kai gidan Rahman. Ni ma sai na shirya yarinyata, cikin doguwar riga yar kanti mai kalar purple Amma light, kame gashinta na yi da ribom mai kyau, bayan na yi mata kunshin gargajiya da uwarta ke ta santi, ba ta gajiya da kallon kafar. Karfe biyu da kwata na je bangaren don kai mata Ramla saboda na ga da yaran za ta tafi dukkansu. Amma yarinyar nan fir ta ki bin su, wai sai idan da ni za aje, iya wayo mun yi mata amma ta ki bin su, haka suka tafi suka bar mu a gida. Iskar wajen nake bukata dalilin da ya sa kenan na dakko tabarma na shimfida mana a baranda bayan na aje mata biscuit, cheese da happy Hour. Wasanta take yi sosai, yayin da ni kuma hankalina ya koma kan wayata, ina bibiyar wani group a Facebook. Comment din mutane shi ya fi dauke min hankali, wani ya ban dariya wani ya ban takaici. Karar gate ce ta sanya ni dago kaina hade da zuba mishi ido, cike da mamakin yadda yake takowa a kasa. Wani banbarakwai na ji, saboda ban taba ganinshi ya shigo gidan a kafa ba. Ban dauke idanuna a kanshi ba har ya kara so in da nake zaune "Me ya faru da motar, lafiya?" Na jefa mishi tambayar da ke ci na. "Ina Maman Khalil?" shi ma ya tambaya yana kokarin zama a gefenmu Idan na ce maku raina bai baci ba na yi karya gaskiya. Haka nan na daure na ce "Sun fita" "Tun yaushe kuma?" "Ba jimawa" na kuma amsashi hankalina a kan wayata. Kamar ba zan kara cewa komai ba, sai kuma na kasa jurewa na kara cewa "Ya na ganka a kafa, lafiya dai ko?" Na karashe maganar ina kallon yadda idanunshi ke kam sashen Sakeena, da alama kuma hankalinshi ba ya tare da ni. Siririn tsoki na ja, wanda ya sanya shi juyowa yana kallona Shiru ya ratsa wajen, yayin da na janye duk wata fara'a da ke kan fuskata, na kuma mayar da hankalina a kan wayata sosai, kamar ban san yana wurin ba. A can kasan zuciyata wata irin kuna nake ji, ni a haka rayuwata za ta kare a tsakanin wadannan mutanen biyu, na mayar da kaina tamkar wata baiwa don dai kawai ni ma ya zama tauraruwata ta yi haske, na sadaukar da ra'ayina don kwanciyar hankalin kowa amma ya zama duk a banza. "Anya matar nan ba asiri ta yi masa ba kuwa?" na yi tambayar a hankali wanda labban bakina ne kawai suka motsa. To idan ba aikin asiri ba, ta ya za a ce duk irin kyautata mishin da nake yi, amma ya kasa dakushe koda daya bisa ukun tasirinta a zuciyarshi. Ina kallon shi ya mike zuwa dakina, amma na ƙi bin shi. Kamar 5mns da shigar shi ya rika kwaɗa min kira Dole na mike ba tare dana amsa ba na nufi dakin, ji nake ma kamar ina shiga in rufe shi da duka, sai dai mugun kwarjini yake min daga shi har matarsa, duk yadda na shirya rashin mutunci in yi wa Maman Khalil muna hada ido sai in ji duk na daburce. Na san hakan baya rasa nasaba da yadda ta kame kanta da kuma girmanta, saboda duk iya sharrina da kuma rashin kaunata a kanta karyata in ce ga shi yau ta yi min abu da bai dace ba, idan ma ta yi sai ta ba ni hakuri. Abun da na sani dai kawai shi ne tabbas ta iya rike miji ta ko wane bangare. Kuma gaskiyar Ummata, haka ko wace mace ya kamata ta zama kamar Maman Khalil ciki kuwa har da ni. Saboda hakan ne zai ba ta damar cike duk wani gurbi a zuciyarsa. Sannan a bangaren kishi ma ta zama mai wayo, ta kame miji ta can kasa, ta kyautatawa abokiyar zama, Sanna ta ja girmanta, tabbas kame kai, da girmama shi yana jefa kwarjini a idon abokan mu'amala ciki kuwa har da makiya. Shigata bedroom din ke da wuya, na ji ya janyo ni hade manna ni a kirjinsa, ya mayar da hannayensa a bayana, har zuwa lokacin da bugun zuciyata ya daidaita. Kafin ya dogo kaina, ya zuba min idanunsa da suka canja launi, ba zan iya jure kallonsu a haka ba dalilin da ya sa kenan na lumshe nawa. Bakinsa ya hada da nawa, yayin da hannayensa ke aika min da sakon da ba zan iya jure karbarsu a tsaye ba, dole na fara kokarin janye jikina zuwa gado. Da ya fahimci me nake son yi, da kansa ya kai ni inda nake bukata. Jin kiran sallah bai hana Baban Khalil biyan bukatarsa ba. Cikin dabara na ture shi daga kan jikina, saboda kunnena ya jiyo min alamun tafiyar mutum. Duk da jikina ba kwari hakan, bai hanani yin hanzarin fita falo ba, tare da yaye labulen window da zai sada ni da tsakar gida. Daidai Maman Khalil na shigewa part nata, kafadarta dauke da Ramla. Wannan ya tabbatar min da ita ce ta same mu a yanayin da bai dace ba. Haka nan sai na ji na kasa fita in yi mata sannu da zuwa, kuma ban fadawa Abbansu Khalil matarsa ta yi mugun gani ba. Bakina na kame abu na. Har ya kintsa jikinshi zuwa part dinta, ko ya suka karasa oho. Ni dai ban shiga part dinta ba, kamar yadda ita ma ba ta leko ko kofa ba. Shi kuma gogan bai shigo gidan ba sai takwas na dare. Ya ci abinci hade da yin wanka, bai bar sashena ba dai sai goma na dare Zuciyata nata sake-sake a kan Ramla, wata na fada min in je in dakko ta, wata kuma na hanani, amma sosai ba na ji dadi, ji nake kamar duniyar ba kowa. Wani sanyin dadi na ji, lokacin da ya kara dawowa kafadarshi saɓe da Ramla tana bacci. Sam ban yi tunanin za a kawota ba, saboda idan ni ce Maman Khalil na samu mijina da abokiyar zamana a lokacin da nake ganin kamar ta fita a girkinta, sannan ya kuma komawa dakinta ya ku san shafe awa daya, to yakin ranar ba mai karewa da wuri ba ne, sannan zan karbe yarinyata, in hana yarana zuwa gurinta. Da kansa ya lallabata ta kwanta, sannan ya shafa cikina da ya dan fara fita yana fadin "Na kosa in shigo in sameki da Baby a gabanki fa, za ki yi matukar kyau" Murmushi na yi kafin in ce "Ni kaina ina son ganin wannan ranar, sai dai kuma in tsoron haihuwa" Zaunawa ya yi kusa da ni, hade da kama hannuna cikin sigar kwantar da hankali ya ce " In sha Allah lafiya za ki haihu, kamar yadda Maman Khalil ke haihuwa cikin sauki, ki daina damuwa a kan hakan, saboda kullum ina miki addu'a" Sosai na ji kwarin gwiwa duk da ban yi magana ba. Maganganu masu karfafa gwiwa ya ci gaba da fada min har zuwa lokacin da ya ja min kofa ya fice. Lumshe idanuna na yi cike da jin dadi, ni ma dai yau na rama abun da Maman Khalil ke min, na rike min miji bayan a dakina yake, ban taba tunanin irin wannan ranar ni ma za ta zo ba, ashe dama can sauri nake yi. "Ko ya zuciyarta yanzu?" na yi tambayar a zahiri hade da tashi zaune ina murmushin mugunta. Ya zama dole in karo wasu hanyoyin kissa domin ni ma ya zama mijina ya na yi da ni ba ita kadai ba "Yes!" Na fada da karfi hade da wurga hannayena irin celebration din nan. Koda gari ya waye ma ban ga keyarta ba, ni ma kuma ban leka ba, har zuwa lokacin da Ogan gidan ya zo gaisheni. A lokacin na yi simple kwalliya cikin riga da zane na atamfa, na yi daurin ture ka ga tsiya ina zaune kan kujera ina kallon shirin *Morning to you Nigeria* Kusa da ni ya zauna tamkar zai shige jikina, wannan kuma ita ce dabi'arsa "Ta shi in ga kwalliyar?" abun da ya fara fada kenan bayan na amsa sallamarsa. "Ba ga shi ka gani ba" "Allah sai kin tashi" Na yi kamar ban ji ba Sai ya fara min cakulkuli, dariya nake sosai a lokacin da na zame daga kujerar zuwa kasa, amma bai bar ni ba, har sai da na mike tsaye ina fadin "Sorry na mike ai" Shi ma dariya yake yi sosai a lokacin. "Kin yi kyau, ina masifar son in ga mace ta sanya atamfa ta daura zane, normal zane irin wannan kuma a yi dace ta iya, kai tana tafiya da ni sosai" gama fadin hakan ke da wuya, na ji ya janyo Ni ta baya, hade da dora hannayenshi duk biyun a kan cikina. "Ina sonki!" ya fada daidai saitin kunnena, ban kai ga amsawa ba, ya juyo ni muna fuskantar juna, hannayenshi ya yi amfani da su wajen tallafe fuskata, kafin ya hada bakina da na shi. A daidai lokacin kuma Ramla ta fito daga bedroom cikin yanayin bacci ta zuba mana ido. Da sauri na kwace kaina, hade da nufar inda take. Lokaci daya kuma na daga ta zuwa jikina ina fadin "Yarinyena! Kin tashi" Hankalinta a kan Babanta har na shige da ita bedroom, ina yi mata wanka ya shigo, gefen gado ya zauna hade taɓa wayarshi "Zan je Ruma, ki shirya mu je" ya yi maganar lokacin da nake fitowa daga toilet rungume da Ramla Cike da doki na ce "Aiko na gode, dama Ina ta kewar garin" "Irin kin zauna din nan sosai" Murmushi na yi kafin na ce "Ban zauna ba, amma abubuwa masu dadi sun zauna a kwalkwalwata" Idanunshi ya saka cikin nawa, na yi saurin janye nawa din ina murmushi "Menene abubuwa masu dadi?" "Sirrina ne" na amsa har zuwa lokacin murmushi nike yi "Allah sai kin fada" ya yi maganar hade da kawo min cafka, na yi saurin tashi dauke da Ramla a jikina ina dariya, kai tsaye kan dining na zarce, tea na shiga hada mata. Daidai lokacin ya fito, kai tsaye kuma kofa ya nufa, wayar shi akan kunnenshi, da alama kira yake amsawa. Matar J✍🏻 [12/18, 06:52] 08080966571: *HASASHENA* *Page 14* Yau ma Maman Khalil ba ta yi min sallama ba ta wuce wurin aiki. Na rika hasashen tana jin irin zafin da nake ji ne, ko kuma dai ta yi latti, zan jira ta dawo domin tantance zargina. Mu ka sha baccinmu da Ramla, sai 12pm na shiga kitchen, jalouf din taliya na yi mana da ta ji busasshen kifi da ganyen ogu, Ramla na fara sanya ma wa, kafin na watsa ruwa hade da yin alwalar sallar azhur. Bayan na idar doguwar riga mara nauyi armless na sanya, kafin na zuba abinci ni ma. Cike da jin dadi nake cin abincin. Misalin biyu da yan mintuna motar Sakeena ta shigo. Kamar 30mns da dawowarta na mike zuwa part din nata, hannuna cikin na Ramla. Affan ne ya bude mana kofa, lokaci daya kuma ya mamutsi Ramla, sosai yaran ke son Ramla, tana da farin jinin mutane. A wajen na bar su zuwa cikin falon nata, zaune take tana shan rake "Ƙurmusu!" na yi maganar cikin salon tsokana Dariya ta yi kafin ta ce "Ga naki can cikin fridge, na gaji ne yau sosai" Fridge din na zarce hade da dakko nawa raken na dawo falon. Hira muke yi sosai, a cikin hirar ne take fada min Rahma za ta shigo gobe. Na ce Allah Ya kai mu. A nan na yi sallahr la'asar kafin na koma part dina, saboda na san mijinta yana kan hanyar dawowa. Ban jima da baro wurintan ba kuwa ya dawo. Kashegari da ta kama Friday, ana sakko masallacin juma'a Rahma ta iso, na so ganinta a lokacin da take shigowa, Sai dai lokacin ina sallah. Ina idar da sallahr kuma na yi wa Ramla wanka, na shiryata cikin riga da wando yankanti wandon jeans blue black, da white shirt mai kyau. Ni ma cikin doguwar rigar material rubber na shirya, sosai rigar ta boye girman cikina, duk dama jiki ya sanya ni sosai. Muka fito hannuna cikin nata, cikin sa a main kofar a bude, shi ya sa na saka kai, kaina tsaye Maganar da na ji su na yi ne ta tsayar da ni, hade da rufe bakin Ramla da hannuna don ma kar ta yi magana su ji mu. "Hmmm! Kishiya ko ta kara ce aka yi miki ita wallahi kawata sai kin ga canji, ina hakuri ne kawai game da danne kishina saboda kada girmana ya fadi, amma tabbas ina ganin abubuwa." Mamaki ya kamani da jin kalamanta, "To me take gani?" na tambayi kaina hade da kame habata cike da mamaki. Lokaci daya kuma na mayar da hankalina kansu "Kin ga rawar kan Baban Khalil kuwa? To kamar bai taba hada shimfida da wata mace ba sai ita, koda rana ya shiga bangarenta to bai fita haka nan, ni kuwa nan wani lokacin sai idan ni ce na kusanceni shi" Zaro idon mamaki na yi, "ya a kai ta san Abban Khalil ko da rana baya kyale ni ? Na kuma yi wa kaina tambayar ina kuma mamakin maganarta wai sai idan ita ce neme shi. Ni kuma a can nawa bangaren ina ganin kullum a manne suke da juna, wannan shi ne zargin-zargin. Wato ita kishiya duk inda kika motsa idonta a kanki yake. To idan ba haka ba, ya aka yi ta san wani abu na faruwa tsakanina da Abbansu Khalil da rana, ko don kawai ta kama mu sau daya. " Ko a dakina yake kaf hankalinsa a kanta yake, wani lokaci ko magana muke sai ya kira ni da sunanta" "Ba ke kadai ba Madam, ni ma yana yi min irin wannan suɓutal kalam din, ashe ke ma kina jin haushi." na yi maganar a zuciyata tare da gyarawa Ramla tsayuwa don kar ta gaji ta tona min asiri. "Shi ne ba za ki dakatar da hakan ba?" cewar Rahma cikin zafi "Kawata ba ki san zaman kishi da wayau ake yin sa ba? Ai shi yaƙi ɗan zamba ne. Kuma a haka ma yana kokarin ganin ya daidaita kanmu kawai dai kin san sabon aure murnar ba ta boyuwa." Ta ɗan dakata kafin ta ci gaba "Shi ya sa ni kuma na nuna ban damu ba, ita ma na kame mutumcina da girmana a gurinta, in ji, in yi kamar ban ji ba, in gani in yi kamar ban gani ba, ko ba komai ban bayar da kofar raini ba, na ja girmana." "yarinyar ba ta miki rawar kansu irin na zamani?" tambayar Rahma cikin wata kasalalliyar murya "To ga abu nan dai, abin da na fahimta dai tana da tsananin kishi, haka nan ma sai ta yi ta fushi musamman idan a dakinta yake ya shigo bangarena, ke kwanakin baya ma mun kai sati biyu ko magana ba ma yi, ni ma kuwa na shareta, da kanta ta sakko, da ina biye mata da abubuwa marasa dadi sun faru, don kuwa kishina ma ya fi nata, ina jan girmana ne kawai tare da danne shi " "Ikon Allah ki samu mace da mijinta, kuma har ki nuna wai kin fi ta kishin sa " Akwai alamun mamaki a maganar Rahma "Kuma wayau gareta fa, yanzu ta canja tako, ta janye yarannan gurinta musamman Ramla, to yanzu dai hankalinsa ya kuma komawa wajenta kullum cikin yabonta yake, idan yana yi taya shi nake ba na son ko kadan ya fahimci ina kishi sosai, amma a kasan zuciyata kamar wuta, wai a gabana Baban Khalil ke yabon wata ba ni ba, hmmmm! Wani lokaci sai in yi kuka mai yawa in share hawayena, ko ba komai da karuwar waje gara ta gida." "Ki yi hakuri tun da ma ba ta yi kokarin raba ki da mijin ba, sannan ba ta yi miki rashin kunya, sai a lallaba a tafi haka, ki ci gaba da rike girmanki, yara kuma tun da ba hanyar banza take sanyasu ba rika yi mata kara, ki kuma mika mata su ita ma idan nata sun iso ki kama ki rike hannu biyu." Cewar Rahma cikin sigar lallashi Jin shiru Maman Khalil ba ta yi magana ba sai Rahma ta kuma dorawa. " Kishi kawai yan dabaru ne, kuma kishin cacar baki yanzu an daina shi, kishin neman kudi da yadda za ka zauna da mijin da kuma yan'uwansa ake yi. Kuma wajen wannan kawata bana jin ki, tuni kika kama danginsa kika rike, kina da tsafta, kin iya kwalliya, kin iya girki, kina da jiki mai kyau, kina kula da yaranki, mijinki kina kokari a kan duk abin da ya shafe shi sai dai ko butulci zai yi miki, uwa uba kina da hanyar samun kudi, to me ya rage kawata? " " Hmmmm! " Kawai na ji Sakeena ta iya fada. " Yanzu dai ki kiyaye duk wani abu da zai janyo ki fada ta fada, wannan shi ke zubar da mutunci yarinya ta rika ganin ita din sa'arki ce, kar ki sake ki kai kararta wajen mijinki, duk lokacin da za ki yi maganarta ya zama alkairinta za ki fada. Wannan zai sanya ki kara girma a idonsa." Har yanzu Sakeena ba ta ce komai ba da alama sauraron nasihar kawar tata take yi. " Please calm down kawata haba mana." A wannan karon ziro kaina na yi cikin dabara hade da leka falon, Rahma ce ta sakko daga kan kujerar da take zaune tare da dafa kafadun Maman Khalil cikin sigar lallashi. A yayin da Maman Khalil din ke tsiyayar da hawaye hade da ajiyar zuciya. " Kawata ban samu na zubar da hawayen nan inda za a lalllashe ni ba, bar ni in zubar dasu a gabanki, ke ce za ki lallasheni, ba kuma za ki goranta min ba watarana ba, kirjina yana zafi, wani lokaci ina jin kamar zan mutu idan na ga Baban Khalil na ta rawar jiki zai shiga dakin Khadija. Ko ganinta ne bai yi ba, to ya yi ta tambaya kenan, ko kuma ki ga hankalinsa duk ba ya tare da shi. Ranar ma ce mun ya yi wai zai ba ta motarsa shi kuma ya sayi wata. Ki ji fa ni ciko ne ma zai yi min amma da kyar na samu, shi ma ba duka ba, amma wai zai ba ta motarsa." Ta karashe zancen hade da gyara zama kafin ta dora " Banza na yi mishi a lokacin, sai kuma ya fara kame-kame wai ta yi mata girma, zai dai duba kila ya siyar ya siya mata karama. Ni dai ban ce masa kala ba. Tun zama na da shi bai taba jaraba sai mun mota ba, sai a kan wata da ko shekara ma bai yi da ita ba." Ta karasa maganar cikin kukan da ya ci karfin ta hade da narkar da zuciyar mai sauraro. Ni ma sai na kuma matse bakin Ramla tare da dagata cak mu ka yi waje jikina a mace, saboda da kyar nake jan kafata, Matar J ✍🏻 [12/22, 14:30] 08080966571: *HASASHENA* *Page 15* Jiki a mace na zauna kan kujera hade da sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Shiru na yi na rasa ta ina zan fara tunani, wato ni ina zargin ya fi sonta, ita tana zargin ya fi sona, duk inda kishiyoyi suka hadu to dayan-biyun, kodai wannan ta ji ba ya sonta ya fi son wannan, ko kuma ko waccan ta ji an fi sonta. Ban taba tunanin Maman Khalil tana da damuwa irin haka a kaina ba, wato da hakuri ta fi ni, da kuma iya tako. Ita shirunta shi ne maganarta. Kuma da alama yana gane yaren nata, saboda ko a mafarki bai taba min zancen mota ba, kuma na kara gasgata shirunta shi ne hukuncinta, idan har zai ga ta cika shirun to ya yi ta sintiri kenan zuwa dakinta. Kai namiji sawun keke ba a gane gabanshi. Ni kuma ba na iya shiru ko boye fushina, kuma ya zama dole in koyi wancan dabi'ar tata, ta danne abu ta yadda ba kowa ne zai fahimci kana da matsala ba Ni ma dole in koyi yin shiru da bakina idan ya yi abun da nake ganin rashin adalci ne, saboda dama yawan yin maganar tawa yana rage kimata a idonsa. Kuma da gaske Rahma take yi, yawan kai korafi ko yawan kawo kara yana sa ka sirewa mutum, tun yana kamawa watarana sai ya daina kamawa. Ko ni ya faru da ni, kai tsaye Baban Khalil ya ce ya yi danasanin aurena, wai kullum matarsa tana yabon halina ba ta taba kawo karata ba, amma ni kullum cikin kawo kararta nake, ashe duk salon kissa ne ke hanata yin maganata ko kai karar tawa. Ni ma na karu da wannan. Muskutawa na yi har yanzu jikina a mace yake, cikin tsananin tunani mai zurfi Yanzu dai na fahimci inda nake da rauni, zan kuma gyara. Sannan ni ma dangin mijin ne kawai suka rage min in kama, tun da dai Maman Khalil da kanta ta yadda mijina yana sona, to na daina tayar da hankalina a kan wannan, dama damuwata ko a banzace take kallona, duk da haka zan kara nemo hanyoyin da zan kara rike abuna, ni ma sha Allah sai na zama kamar ita, har ma fiye. A kasalance na nufi kofar saboda kwankwasawar da ake yi. Rahma ce tsaye tare da Maman Khalil Sabanin Maman Khalil, ita fara ce tas, Sai dai ita ma yar gayu ce kamar Maman Khalil, wani kamshi mai dadi na fita daga jikinta "Na zo ganin yarki ne. Tun da kin ki kawo ta" Rahma ta fada cikin dariyar tsokana Ni ma murmushi na kakalo, ina ja gefe, "shiga, ga ta nan, ki ganta, ki bar ta a nan, idan gani ne kawai ba ma fada." Dukkanmu mu ka yi dariya a lokacin da muke zama ni da Maman Khalil, Rahma kuwa Ramla ta nufa da ke ta wasanta a wurin dining "Ma sha Allah! Kawata Ramla ta fi kyau a zahiri, ban da Amarya ta riga ni tabbas da na karbe Ramla na jefata a cikin yan mazan gidana, amma duk da haka ina yi wa Farhan dina riko gaskiya." Ta fada a daidai lokacin da take zama hannunta rike da na Ramla. Mu kam dariya kawai muke yi. " Kunshin nan ya yi kyau fa, nawa za mu biya gara mu fara toshi." "Ga me yi mata nan, ni tun da na haifeta ban taba mata kunshi ba, to ban iya ba, ita kuma kullum cikin yi suke, da ya fita su kuma mayarwa." cewar Maman Khalil tana kallon Rahma Ni kam murmushi kawai nake yi. "Ma sha Allah! Ai kunshi yana da kyau sosai a wajen mace, to ni ma fa nan bana yi, sai in yi shekara biyar ban yi ba." Duk muka dan yi siririyar dariya. Ta kai hannunta hade da shafa kitson kan Ramla, Chuku ne na zanen hausa, ya kamu sosai kan kamar an sudeshi. " Har kitson ma ke ce ke yi?" Jijjiga kai na yi ina murmushi Rike da haba cikin mamaki ta ce" Ke komai kin iya wai?" Wannan karon dariya na yi sosai kafin in ce" Ba fa komai ba. " " To me ye ba ki iya ba? Cewar Maman Khalil tana kallona, kafin in yi magana kuma sai ta dora "Kin iya komai, kamar ba a zamanin kiwa kika zo ba, yaran yanzu bayan rashin kunya babu abun da suka iya, sai kadan ne irinku" Wannan karon ma murmushi kawai na yi Ji nake kamar bugun cikina suke yi, ko kuma dai kishinta ne yau ya ci karfinta. Karar motar Baban Khalil ce ta sanyasu saurin ta shi gabadayansu, Maman Khalil na fadin "Mijinki ya dawo, ga tsarabarku nan ke da yarki, daga Maman Farhan" Ni ma mikewar na yi, hade da karbar ledar na dan leka ciki, tare da yi mata godiyar da na san tabbas ta gamsu na yaba da kyautarta. Gefe ya rabe suka fita, saboda bude kofarsa ya yi daidai da niyyar bude kofarsu su ma. Daga ganin gaisuwar da suke da Rahma ka san an dade tare, akwai kyakkyawar alaka, don kuwa Maman Khalil nan ta barsu tsaye a barandata, ni ma sai na karbi jakar hannunsa, na shige ciki, yayin da na bar su a nan hannunsa rike da Ramla. Ina raka'ar karshe a magriba ya shigo cikin sauri ya yi alwala zuwa masallaci, saboda har an idar da sallahr bai yi ba suna magana da Rahma. Bayan na idar da sallahr isha'i na jera mishi abinci a kasa, kamar yadda ya fi so. Wanka na shiga, bayan na fito na watsawa Ramla ita ma hade da sanya mata rising powder. Pant kawai na sanya mata, yayin da ni kuma na sanya doguwar riga mai yankakken hannu, ba ta da nauyi ta dace da yanayina da kuma yanayin garin, humrah kawai na shafa a jikina. Falo na fito na yi zaman da na fi so, wato in hada bayana da kujera hade da ware kafafuwana, iskar fanka na ratsa ni, a yanzu na fi kaunar irin wannan zaman fiye da ko wane kalar zama. Ramla kwance a kan cinyata ina shafa kanta don ta yi barci a lokacin da ya shigo dakin. "Sannu uwar hudu. Wai don Allah duk iskar fankar nan ta miki kadan sai kin hada da mahuci?" Cikin yanayin mamaki ya yi tambayar. Dariya na yi kafin in yi masa hararar wasa "Wai saboda tsaro, ka ga ko an dauke wuta ba zan sha wahalar tashi zuwa neman mahuci ba ga shi a kusa da ni." "Anya masu scanning din nan kuwa suna gani me kyau? Gaskiya cikin nan naki ba yaro daya ba ne." Dariya na kuma yi hade da shafa cikin "To ai dai scanning din nan ba sau daya mu ka yi ba. Kuma dai duk abu daya yake bayarwa." "To gaskiya kina da girman ciki, sai ka ce za ki haihu yanzu, ko Maman Khalil ma mamakin girman cikinki take yi. A tarihi dai ke ce mace ta farko da cikin farinta ya yi girma kamar daro" Mahucin kusa da ni na dauka tare da kai masa jifa. Ya yi saurin kaucewa yana dariya "Abun da za ka fada kenan ko?" Na karashe maganar ina harararsa. Kafin ya yi magana na dora "Kuma fa ina jin nauyinsa sosai, kai ne ma ka ki barina in je gida ka ga dana huta da wasu hidimomin, tun da na yi aure ma fa zuwana daya, su kuma sun ki su zo mun." Cikin yanayin shagwaba na yi maganar. "Da wannan cikin za ki gidan, kuma duka watanki nawa da auran? Sau nawa kike so ki je gidan a shekara?" "Ni ban ki ba ma kullum in je" Dariya ya yi sosai, kafin ya ce "Ina jin yunwa ina son yin wanka wanne zan fara ne?" "Ka ci abincin sai ka yi wankan idan ka dan huta" "An gama" ya fada hade da cire rigarsa "Yaushe rabon da ki cire min kaya ma wai?" Dariya na yi mai sauti kafin in ce "Ko jiya na cire ma fa, yau kuma gaskiya na ji dadin zama ba zan iya tashi ba." "Ko kuma don yarki na kan cinyarki ba." ya yi maganar cikin tabe baki, lokacin daya kuma ya zauna hade da bude flask din abincin Sababben ne dai, wato tuwo, amma yau miyar ganye na mishi, kuma sosai ya ji dadin abincin saboda yadda yake cinsa hankali kwance. Kodayake shi dai indai abinci na gargajiya ne zai ci shi sosai, kwaben zamani ne bai so. " Ka gama don Allah mu je chemist din Bilya, yarinyata jikinta ba dadi" "Ke ma kin zama Sakeena kenan, da kin ga yaro ya yi shiru sai ku ce ba lafiya. Wannan ma kin fi Maman Khalil. " Gajeruwar dariya na yi "To ai alamun ciwon ne" Shiru ya yi kafin ya ce "Dakinki kamar pharmacy Ko ina duk magunguna, wai yarinya daya ce fa ranar da suka zama biyar, kila sai dai ma'aikatar hada magunguna" Na kuma yin siririyar dariya "lallai ka sanya min ido da yawa, ashe duk kana lura da ni" "Sosai ma kuwa, ko bacci kike hankalinki a kan Ramla, ranar ina kallonki cikin dare da ba ta da lafiya tana bacci har da aje kunnenki a saitin hancinta, na san numfashinta kike ne ma" Dariya na kuma yi sosai "Wai don Allah ka ganni?" Ya dan murmusa kadan "Eh mana, na yi shiru ne kawai, ki daina zafafa soyayya mutuwa ake gudu, tun da dai ta rataya a kan kowa. Ki ki tafi ko ta tafi. Yunkurawa na yi da kyar na tashi, hade da daga Ramla na aje a kan kujera "Idan ta zo babu yadda na iya amma kam tabbas zan ji jiki, kuma ma sha Allah ba yanzu ba, sai na lullube Ramla na kai ta daki, kai har sai na dauki yaranta sha Allah." "Allah ya yarda, ni dai na fada miki ne, ki dan rika ragewa. Ana boye son yaro a barwa zuciya saboda irin wannan son naki sai ya raba kan yara, kiri-kiri kike nunawa." "Ikon Allah! Ni fa ban san ya kake so in yi ba, ina jin ko yarinyar da zan haifa ba zan so ta kamar Ramla ba, ina son yarinyar nan kamar raina wallahi. Allah ne ya dora mun hakan, ba munafurci na kishi ba ko neman gindin zama, wallahi son tsakani ga Allah nake wa Ramla" "Na sani, kuma ina kallon tsantsar kaunarta a idonki, Allah ya saka miki da mafificin alkairi" "Amin" na fada a daidai lokacin da nake shigewa bedroom. Shi ya dauki Ramla a lokacin da muke zuwa chemist din. A can din ma dai Bilya ce mana ya yi zazzabi ne kawai, kuma ya sauka, paracetamol kawai ya bamu. A hanyamu ta dawowa ce na ga mai'awara aiko na sayo mana ni da Maman Khalil. Sosai ta ji dadi a lokacin dana kai mata. Tun da na yi sallahr asuba ban koma ba, kokarin hada mishi break nake yi, don tun dare ya ce min da wuri zai fita. Misalin 7:30am kuwa muka fito tare da shi, hannuna rike da jakarsa ta zuwa aiki. Yayin da ya sha kwalliyarsa cikin blue shadda, hatta hular kansa blue ce, ya fita kamar wani matashin saurayi ko don yau bai sanya babbar riga ba ne oho, amma bana gajiya da kallonsa kwalliyarsa ta yau ta boye shekarunsa. A daidai lokacin kuma Maman Khalil ta fito cikin shirinta na wani blue boyel na mata kamar hadin baki, dinkin doguwar riga aka yi mata sosai dinkin ya karbi jikinta, Cas da ita kamar ba ta haifi yara uku ba. Ina kallon yadda yake ta satar kallonta, take na ji kishi ya kamani dole na yi kokarin dannewa kamar yadda ita ma take yi, don na san ganinmu tare ita ma kishin nata ya motsa. Yanzu kam Kar nake kallonta, tun da na ji sirrinta Da ni ta fara gaisawa kafin ta koma kansa "Barka da safiya Abban yara" Cikin murmushi ya amsa "Barkanki dai Maman Yara, na shiga ai kina wanka." "Eh ina sauri ne zan fita yau, muna da baki" Ya leka cikin mota inda su Khalil suke, ban ji me yake fada masu ba, daga karshe dai ya dago kai hade da tattara hankalinsa a kan Maman Khalil dalilin maganar da take masa. "Kun yi waya da Inna ne da safen nan? Ni na kira wayar ba ta shiga ba." "Ni ban kira ba ma, tun jiya dai da dare Abdul ya ce min akwai sauki." "Eh ni ma Rukayya ta ce akwai sauki sosai, amma ya kamata aje a dubota" "Tun jiya na yanke wannan shawarar, zuwa yaushe kenan?" "Sai mu je ranar Alhamis tun da akwai hutun mid time break, sai mu dawo juma'a" "To shi kenan Allah ya kai mu" "Amin" ta fada hade da shigewa motarta ta fice cikin kwarewar tuki. Sai yanzu hankalinsa ya dawo kaina, tun da muka fito hankalinsa kaf a kanta, amma kuma wai a hakan ita ma complain take yi. Da kyar na danne mugun kishin da yake taso min, na rakashi zuwa gurin motarsa shi ma ya tafi. Bayan na dawo daki kuwa mamaki ne ya kama ni, to wai ni ma yaushe za a rika abubuwa da ni ne? Da alama mahaifiyarsa ce ba lafiya, amma ban sani ba, shi bai fada min ba, kuma daga can ma babu wanda ya fada mij. Ni kamar basu sanyani cikin danginsu ba. "Amma ba komai akwai lokacin da wannan din ma zai wuce, zan yi kokarin samun fada, ai yanzu aka soma wasan." Na rarrashi kaina, saboda raina ya baci sosai da abin da suka min. Kuma ba zan yi mishi magana ba, ina yi zai ce na cika korafi. Da yamma daman ba a dakina yake ba, sai bayan isha ya shigo, bai kuma jima ba ya fita, wai bacci yake ji, zai je ya kwanta. Na ce Allah ya tashemu lafiya, na rungumi yarinyata ni ma mu ka kwanta. Ranar Laraba da safe ne Maman Khalil ke ce min zasu tafi da Ramla, wai Inna ta ce tana son ganinta. Dalilin da ya sa kenan na warware mata kitsonta duk da bai tsufa ba, na canja mata wani kanana me kyau. Kunshi kuwa ba dama in yi wani tun da wancan bai gama fita ba. Sannan na fadawa Baban Khalil ina son ka ji guda hudu idan ba damuwa. Wajen karfe biyu na rana kuwa sai ga kajin, na yi dambun nama da biyu sannan na yi pepesoup din biyu. Har ga Allah daga shi har Maman Khalil haushinsu nake ji, a kan me ba za su fada min cewa Inna ba lafiya ba. Na ma fi jin haushinsa, idan ya dauke ni mata da gaske ai ya fada min mahaifiyarsa ba lafiya. Sannan idan abun na kai da kitso ne ai ya kamata ni ma a tafi da ni, amma hakan goga min bakin jini za su yi ai. Duk da dai na kira Innar na yi mata sannu, amma zuwan ma ai yana da muhimmanci. Da dare haka Ramla ta matsa wai dole sai na yi mata lalle a hannu, ga bacci ina ji amma haka na daure na zauna ina mata lallen. A daidai lokacin ne kuma ya shigo yi min sai da safe. Sai na ji wani haushinsa ya kara kamani, kasa boye bacin raina na yi, da kyar na amsa mishi sallama. "Kunshi kuke yi ne? " Ban amsa ba. Hakan ya sa ya kalli Ramla "Babyna ana miki kunshi ne." Kai ta daga ba tare da ta ce komai ba, Sam magana ba ta dameta ba. Ita ma kamar Affan take, indai ka ji surutunta to da ni ce, ni din ma watarana shiru take min. "Yan matana, ya na ga yau kamar an taba min ke?" Ban ce komai ba, sai ma leda da na dakko ina saka hannun Ramla a ciki. Shi ma bai kara magana ba, guri ya nema ya zauna, har na karasa mata na dayan hannun, sannan na ce mu je ki kwanta. Rigima ta sanya ita dole sai an yi a kafa, iya lallashin ta ki yin shiru rikici take ji da alama yau, shi ma ya yi bakin kokarinsa amma ta ki, dole ita sai an yi mata lallen a kafa. Dole na dauketa na dora a baya, ina neman zane ne, na ji an dauketa a bayana "kina hauka ne, da wannan katon cikin za ki goyata?" "To ba shiru za ta yi ba idan ba goya tan na yi ba" cikin dakusasshiyar murya nake maganar don sosai nake jin haushinsa. "Kin riga kin shagwaba yarinyar nan ya yi yawa, haka nan ma sai ki kama goyata, yanzu kuma ba da ba ne, ba ni zanen." Ram ya goyata a bayanshi, duk yadda raina yake bace, na kasa danne dariyata, musamman dana kallesa yana ta zagaye falo da ita, kawai sai na tuntsire da dariya mai sauti. " Hmmm! Ai ke kam Sa ce, ba ki dariya sai ta baci. " Na kuma tuntsirewa da dariya, hade da dakko wayata ina mishi hoto. Buga kofa ne ya dakatar da ni, shi ne ya bude kofar. Rike da haba ta shigo tana fadin "Ashe haka kuke shagali a dakin shi ne ba ku kirana in gani" Na tuntsire da dariya, kafin in ce "Ai hanawa yake a kira ki" Ina sane na fadi haka shi yaki ai dan zamba ne, kamar yadda ta fada. yau ne karon farko da ya goya Ramla amma gara in fada mata dama yana yi, duk da yarta ce na tabbata sai ta ji wani abu. "Wai kunshi aka yi da daren nan?" ta canja salon hirar "Eh, ta damu wai sai an yi, don ba a yi na kafa ba ne fa ta sanya rigima" Ta kuma rike Haba tana kallon Ramla da ke goye a bayan tsohonta. "Ai yarinyar nan tana yadda ta ga dama, Allah kin shagwabata, da can ina ma ta san wani abu lalle." Dariya kawai na yi, ba tare da na ce komai ba. "kin yi ragowar baking powder ne ki ba ni" "Eh." na fada lokaci daya kuma na mike zuwa kitchen don dakko mata. Ina mika mata ta fice, duk da bai yi magana ba, amma na san tabbas shigar Maman Khalil ta tafi da shi. Wando ne baki mai kama jiki ta sanya, tsawonsa bai wuce gwiwa ba, jar riga wacce hannunta ya tsaya rabin cinyar hannu, ba ta kamata ba sosai amma kuma ta fito mata da dirinta, bakar hular da ta dora a kanta ma ta kawata mata kwalliyarta. Sam bana son ganin giccinta idan ina tare da mijina, don muddin za ta gitta muna tare da shi ta kan janye hankalinsa zuwa wajenta gabadaya. Shiru ya ratsa wajen bayan tafiyarta. "Kin ki fada min laifina ko?" ya katse shirun namu A yanzu dai ba zan iya fada ba, Maman Khalil ta kuma dagula min komai. Ganin ban yi magana ba, ya sa ya kwantar da Ramla da ta yi bacci, sannan ya ce "To mu kwana lafiya." "Allah ya sa" na fada a lokacin da yake fita Kamar ransa a bace, amma ban damu ba, matar Sonshi za ta wanke mishi shi tas. Matar J✍🏻 [12/22, 14:42] 08080966571: *HASASHENA* *Page 16* Karfe hudun asuba, na tashi Ramla na yi mata wanka, lallen hannun ya yi kyau sosai, fulawar ta fita radau ba ta dame ba, saboda na yi ta kula da hannun. Tea na ba ta bayan na shiryata, cikin riga da wando masu kyau a irin tsarabar Rahma ne. Wandon na jeans fari mai taushi, sai pink din riga ita ma mai laushi, sosai ta yi kyau musamman dana dora mata pink din takalmi a kafarta. Duk da akwai alamun bacci bai saketa ba, hakan bai hana na yi mata hotuna ba. Sannan na goyata a bayana don ta koma bacci. Ina cikin jijjigata na ji alamun an shigo, a kofar shigowa bedroom din muka hadu. Ta dan ja baya tana dariya "Wallahi na dauka ba ku tashi ba." Ni ma dariyar na yi "Haba tun 4am mu ka tashi." Miko min bowl din hannunta ta yi mai dauke da cin-cin "Ga na ki nan, na tsaraba ne da na yi." Na karba hade da godiya mai yawa "Wai yanzu da wannan katon cikin kike goya yarinyar nan? Don Allah ki sauketa kar ta nane mana hancin yaro." Murmushi na yi kafin in ce "To sai me idan ta nane, ni dai ga amanarta nan a hannunki." "Ni!! Allah ban karba ba, ba zan iya wannan kicimillen ba, wai daka da miji goye." "To Allah zan hanata zuwa." "Dama ni na ce zan je da ita, ke ma kin san idan ni ce da yarana zan tafi, wa zai dauki wannan rigimar. Kuma ga amanar yarana nan a hannunki, idan kika ci Allah sai ya tambayeki" "Guda kika bari guda za ki taras, ni ma kuma da gaske ki kula min da yarinyata." "Ni gaskiya ba zan iya ba" "amma kuma ni na karbi ta ki amanar?" "Yarana ai ba kamar yarinyarki ba ne, yauwa Baban Khalil..." ta yi saurin kiran sunansa dalilin shigowarsa "Ka shaida na bawa Khadija amanar yarana, kar in ji kar in gani, amma kuma ni ban karbi tata amanar yarinyar ba." Dariya duk mu ka yi, ni kuma na nufi kitchen hade da dakko mata flask din da na zuba tsarabata, na mika mata "Ki kai wa Inna, sannan ki ce ina mata sannu." na kuma mika mata ƙaramin food flask na ce "Wannan kuma ku ci a hanya" "Kai madalla, An gode kuma sha Allah za ta ji." Bayan ta fita ne ya zuba min ido "Ba na ce ki daina goya yarinyar nan ba wai?" Ban yi magana ba "Je ki sauketa." Babu alamun wasa akan fuskarsa. Ban yi magana ba, na dai zumbura bakina hade kawar da kaina gefe alamun bana son yin abin da ya fada. "Ba ki ji ba ne?" Na kuma turo baki ina kallonsa, yanayin da na gani a fuskarsa ne ya sa na shige bedroom na kwantar da ita ba don naso ba. A in da yake tsaye nan na same shi. Key ya je ya sanyawa kofar falon, sannan yan janyoni jikinsa, ya rungume hade da shafa bayana. "Na san fushin da kike yi, a kan maganar Inna ne ko? I'm sorry, ni ma a shekaranjiyan na ji maganar, kuma sai na shafa'a ban fada miki ba, sai can dare abun ya fado min, kuma a lokacin kina bacci. Da safe kuma hankalina ya tafi office sai da Maman Khalil ta yi maganar na tuna. Please sorry Kar in tafi kina fushi. " Har yanzu kwance nake a kirjinsa, ban yi magana ba. Dago fuskata ya yi" say something please . " " Ba komai na fahimta." "Thanks" ya fada hade da kissing din goshina. "Zan yi kewarki sosai, Inna ce ta ce kar aje da ke cikinki ya yi nauyi." Na danyi murmushi mai alamar kunya "I love you" cikin wata irin murya ya yi maganar. Jikina ya mutu likis. Ya kuma dago fuskata da na boye a kirjinsa. "Do you love me?" Hannayena biyu na sanya a kan fuskata ina murmushi. "Sarkin kunya" ya fada a daidai lokacin da yake fita "Ki kawo Ramlan tafiya za mu yi." ya yi maganar ne a kofar daki. Sabota na yi a kafadata daya hannun kuma rike da flask, don kayanta tun jiya na ba wa mamanta. A kan cinyar Maman Khalil na dorata. Har yanzu bacci take yi, na mika mata ƙaramin flask din ina fadin" Ku kula min da yarinyata don Allah." Zuwa lokacin zuciyata ta gama karyewa, hawayen da nake kokarin boyewa suka gangaro a kan kumatuna. " Ikon Allah!" Abun da Maman Khalil kawai ta iya cewa kenan tana kallona. Baban Khalil ne ya mayar da ni daki yana rarrashi, har zuwa lokacin da yake ganin zuciyata ta yi taushi. Ina jin fitarsu daga gidan, sai na ji jikina ya kuma mutuwa, zuciyata ta yi kunci, komai nawa ya tsaya Haka nan na yunkura zuwa bangaren Maman Khalil in duba su Affan ko sun tashi, har lokacin bacci suke yi. Tashinsu na yi muka dawo sashena, su ka yi alwalla da brush, ni kuma na shige kitchen don nema mana abun kari. Lallai sabo ake wa kuka ba mutuwa ba, mutum rahama ne, ji nake kamar ni kawai ce na rage a duniya ba kowa, gidan duk ya min fadi. Duk da Ramla ba mai yawan surutu ba ce, amma zirga-zirgarta da rigimarta ta kan debe min kewa. Idan kuwa na gaji da zaman shiru wajen Maman Khalil nake tafiya sai ta debe min kewa. Ga mai gayya mai aiki wato mijina, idan har yana kusa da ni to tabbas sai na yi dariya, ya kan mantar da ni da yawan damuwata. Duk da ba na ganin yan gida, idan yana kusa ba na kewar rashin ganinsu. Wani lokaci yana bata min rai sosai in ji kamar in yi ta bugunsa, amma kuma dai sonshi da kaunarsa na nan daram a zuciyata. Kiran da ya shigo ne a wayata ya katse min tunani, Maman Khalil ce, cikin sauri na dauka. "Kin kirani, wayar na a cikin jaka kuma a silent?" "Dama so nake in tambayeki yarinyata ta tashi?" Ina jin sautin dariyarta kafin ta ce "Ta tashi yanzu?" "Tana kuka na yi saurin tambaya?" "To wa za ta yi ma wa? Dama ai don ganinki ne ya sa take wannan tabarar." Tausayin Ramla ya kama ni , ji nake kamar in yi tsuntsuwa in bi su, don na san duk a takure take, kuma na san tana son ganina. "Don Allah ki kula min da ita" wannan karon cikin sanyin murya na yi maganar "Yanzu kam kin ba ni tausayi, zan kula miki da ita sosai kamar kina wurin " Na dan yi murmushi mai sauti "Allah ya kiyaye hanya" na fada hade da yanke kiran. Sosai na ja su Affan jikina suka saki jiki mu ka yi break fast, sannan na yi masu wanka, suka shirya cikin kaya marasa nauyi. Cartoons suke kallo a tashar St kids ni ma ina taya su, duk da dai hankalina yana kan masu tafiya. Misalin sha daya na safe sai ga Rahma wai ta zo daukarsu Affan. Mamaki ya kama ni, don ni ba mu yi haka da uwarsu ba. Ganin hakan ne ya sa ta ce "Su Farhan ne za su yi birthday shi ne za su je taya su murna, amma bayan haka ba komai wlh" Duk da ban ji dadi ba, haka nan na hakura saboda Oga ya sa baki. Ina gani Rahma ta kwashesu zuwa gidanta. Sai gidan ya kuma yi min fadi na zama kamar wata mayya. Shirun duk ya min yawa,, har ji na yi ban lafiya, waya kuwa minti-minti nake kira, ga Ramla za ka shekara dari kana mata magana a waya ba ta amsawa, sai dai ta yi kasake kamar wacce ake yi wa susar kunne. Haka nai ta yawo kamar macen da aka saki da sauran so, ba ni ɗaka ba ni waje. Da yamma kuwa kifa hajabina na yi, na mike layin unguwa na yi ta tafiya, har sai da na ji na gaji sannan na dawo. Dalilin da ya sa kenan na kwanta da wuri bacci mai nauyi ya dauke ni. A firgice na farka sakamakon wani mafarki da na yi, jikina sharkaf da gumi duk kuwa da saitin fanka nake. Kirjina harbawa yake yi da karfi kamar yadda yake harbawa a mafarkin. Waya na janyo, na fara laluben lambar Rahma sai na tuna ashe ma ban da lambar. Wata shida baya na taba wani mafarki, wai an yankewa Affan hukuncin kisa ta hanyar rajamu (jefewa) amma wai an ce a jira sai ya kara girma, don haka aka debi wasu shekaru da ake ganin zuwa lokacin ya kara girman. A cikin mafarkin ni ban damu ba, dariya ma abun ya rika ba ni , saboda gani nake ba za su jefeshi ba, kawai ana tsoratashi ne, koma kafin lokacin da aka diba din mutanen sun manta. Amma fa wasu har da kuka suke ta yi, ni kam ko a jikina. Yau kuma sai na yi mafarkin wa'adin da aka dibarwa Affan din ya cika, muna zaune ba zato ba tsammani sai ga wasu fararen larabawa su biyu, da shiga irin ta larabawan, wai sun zo sun kama Affan yana zaune yana wasa suka ce wa'adin da aka debar mishi ya cika. Duk mutanen wurin babu wanda ya yi kokarin karbar Affan sai ni. Muka fara kokawa da mutanen ina kuka, amma suka karbeshi da karfi yana kuka ni ma ina kuka, irin kukan nan mai nuna tsananin damuwa. Ganin sun fi karfina sai na ce masu to su yi hakuri su ba ni shi mu yi bankwana. Sakinshi ke da wuya sai ya fado jikina yana kuka, ni ma ina kuka wata sabuwar kaunarsa na ratsa jikina, cikin kuka na ce "Affan ina sonka wallahi, kar ka ga kamar ban damu da kai ba amma ina sonka sosai, don Allah ka yafe min rashin kulaka da nake yi." Yaron bai yi magana ba sai dai kuka, da karfi suka banbareshi yana turjewa suna jansa, har muka daina hangensa da jin kukansa. Ina zuwa nan na farka. Sosai mafarkin ya ban tsoro, na rasa ta ya zan ba shi fassara. Jiki a mace na yi sallahr asuba, hade da rokon Allah ya sada ni da alkairin mafarkin sharrin kuma ya tsare ni da shi. Ina idarwa na kira Maman Khalil "Turo min lambar Maman Farhan" Abin da na fara fada kenan bayan ta daga "Lafiya?" cike da mamaki ta tambaya "Lafiya kalau." Ni ma na ba ta amsa, har yanzu muryata a sanyaye take. "Kodai alamun haihuwa kike ji" Dariya na yi kafin in ce "Ni ina na san wani abu alamun haihuwa. Kawai ina son yin magana da Affan ne" Ita ma can dariyar ta yi "Ai alamun haihuwa idan ya zo ko ba a fada miki ba za ki gane. Yau kuma da Affan kika tashi ba yar gold dinki ba, Affan din da kike koro min idan ya zo inda kuke." Na kuma yin dariya "Ni dai turo min, yau soyayyarmu ce ta tashi." "OK." ta fada "Yarinyata ba ta tashi ba?" "Ba a nan ta kwana ba ai, tana wurin Inna" "Ni na fi natsuwa ma da zamanta a wurin Innar?" Dariya ta yi sannan ta ce "Kin ci bashi, sai mun dawo an jima kadan sha Allah za mu ta so." "Ai gara, kwana dayan nan kamar shekara nake ji, Allah ya kawoku lafiya" "Amin" ta fada hade da yanke kiran. Sai da na ji muryar Affan sannan hankalina ya dan kwanta. Misalin karfe goma kuma sai ga kiran Oga "Ni ɗin ma da ba kya so ina lafiya." abin da ya fara fada kenan bayan na daga Siririyar dariya na yi "Ma sha Allah da kake lafiya" "Ga mu nan zamu taso yanzu sha Allah" "Allah ya kawo min ku lafiya" "Amin ya Rabbbb! Sannan ki shirya idan na dawo za ki yi biyan bashi, na gaji da kullum ki ce min ciki." "Amma dai Maman Khalil ba ta kusa da kai ko?" "To idan tana nan fa, ba ta san muna yi ba ne? Cikin jikinki na waye?" Dariya na yi sosai daga bisani na yanke kiran ba tare da na ba shi amsa ba. Matar J ✍🏻 [12/22, 15:01] 08080966571: *HASASHENA* *Page 17* A yadda muke waya dasu na san sha Allah 7:30pm zuwa 8:pm sun shigo gida. Dalilin da ya sa kenan karfe biyar na fara shirin abincin tarbarsu, kowa abin da yake so na yi niyyar yi mishi, Oga tuwo, Maman Khalil dambu, yarinyata kuma danwake. Tun da nake kira ba ta cewa komai amma haka nan zan sanya a kanga mata wayar a kunne in yi ta surutu tana ji, amma dazu da na ce "Me kike so in dafa miki" Sai cewa ta yi "An wake" Ina jin su Maman Khalil na mata dariya, ni ma na yi dariya sosai. Shi ya sa zan yi mata daidai cikinta. Zuwa 7:pm kuwa na kammala komaina har da watsa ruwa, na haye sallaya don gabatar da sallahr magriba, saboda tun 6:47 aka yi sallah. Ina kan sallaya na ji sallamar Rahma don haka na fito, ina tunanin ko yara ta maido. Amma kuma sai ban ga yaran ba. Gaisawa mu ka yi sannan ta ce "Kun yi waya dasu Sakeena ne?" "Eh tun dai wajen shida da mu ka yi bamu kara ba, dama jira nake in idar da sallah in kirasu in ji suna ina." na ba ta amsa ina kallonta. "Ok. Sun iso tun dazu amma sun buga ma wani mota yanzu haka suna asibiti" Na yi saurin sakin casbahar da ke hannuna tare da fadin "Subhanallah! Amma su ya suke?" "Su kam suna lafiya, motar dai wancan ce ta samu matsala." Na sauke ajiyar zuciya mai karfi "To yanzu ya aka yi?" "Zuwa na yi mu je tare." Ban yi wani dogon tunani ba na ce "To mu je kawai" Ita din ma ba ta ce komai ba, ta yi gaba na ja kofata na bi ta a baya ko wayata ban dauka ba. Tun da muka fara tafiya ba mai cewa komai tukinta kawai take yi, ni kuma na kosa in je in gansu, ji nake ma kamar ba ta sauri. Tun da mu ka shiga asibitin nake karo da abokan Baban Khalil da makotanmu wadanda na sani. Yadda nake ganin fuskokinsu kamar abun babba ne. Kofar A&E din cike yake da mutane, da yawansu kuwa makusanta ne ga Baban Khalil Matan da ke wurin basu da yawa maza sun ninkasu yawa. Sai kallona suke yi suna kus-kus, ga Rahma ta shige ciki ta bar ni a tsaye. Can kuma sai ga ta, jan hannuna ta yi, tana kokarin boye hawayenta. Ni dai tuni jikina ya gama mutuwa, na rasa duk wani wayau nawa. Gefe ta kai ni, hade da zaunar da ni a daben barandar wurin . "Khadija!" ta kira sunana Daga kai kawai na yi ina kallonta, saboda bakina ya yi nauyi ba zan iya amsawa ba "Sakeena, Ramla da Basheer suna cikin wani hali, ki sanyasu a addu'arki, sun ji ciwo amma dai sha Allah ana ganin akwai sauki." Ta karasa maganar hade da share hawayen da ke bin fuskarta. Daga bisani kuma sai ta rushe da kuka mai sauti. Ni dai ina jin mutuwar zaune na yi, don kuwa ko zuciyata ma a lokacin ba ta aiki, saboda ni dai ban ji na tuna komai ba. Kwakwalwata ma a cunkushe take, ta yi jingim. Sosai Rahma ke kuka, har sai da wasu mata da ina jin kawayenta ne ita da Maman Khalil su ka iso asibitin suka karaso gurinmu suna ba ta hakuri, kuma su din ma kukan suke yi. Ni dai nawa ido kawai, bayan shi ba na jin akwai wani abu a jikina da yake aiki. "Ku kai ni in gansu." Da kyar na iya kalato maganar a bakina. Ina jin su suna ta gardama wasu su ce a kai ni wasu su ce kar a kai ni. "Ku kai ni in gansu don Allah." na kuma fada da kyar. Rahma ce ta mike tare da fadin "Ina zuwa" Ban san ina ta je ba, can kuma sai ga ta, kama ni ta yi ta mikar, sannan ta ce "mu je." Kamar rakumi da akala haka nake bin ta, har zuwa wani daki, gaban wani gado muka tsaya, ta yaye zanen da aka lullube mara lafiyar. Cikin kaduwa na ja baya ina kallon Rahma, ita ma ni take kallo. Hannu ta sanya hade da share hawayenta. "Khadija kin ga aminiyata, kawata ta amana, masoyiyata, abokiyar sirrina, mai share min hawayena. Yau ta tafi ta bar ni ni kadai." kuka ta kuma fashewa da shi mai sauti. Sauri na yi na juya gadon da ke bayana, saboda wani tunani da na yi, bayan zuciyata ta dawo aiki cikin sauri. Da sauri na kai hannu na yaye zanen da aka rufe koma waye a kwance Ramlata ce kwance cikin jini hannunta guda daya fit ya fita, idan ka dauke wannan ciwon babu ko kwarzanen wani ciwo a jikinta. Idanuwanta a lumshe kamar tana bacci. Sabanin Maman Khalil da ta fita a kamaninta, hatta hakoran bakinta ba na jin akwai saura. Saurin sakin zanen na yi, na nufi kofar fita, har ga Allah ban san ma ina nake zuwa ba, ban san ma wacece ni ba, Kwakwalwata ta daina aiki, tafiya kawai nake yi ko waige ba na yi. Daga nan kuma ban san ya aka yi ba Kawai dai na farka, na ga kanwar Ummata da ke Zaria a gefena, da yayar Baban Khalil, Bin su kawai nake da kallo, su kuma suna ta min sannu. Ina jin ma fadawa mutane a akai na farka, shi ya sa wannan ya shiga wannan ya fita. Da na fahimci su dan rage shigowa, yunkurawa na yi da zummar tashi, amma kafin hakan cikin sauri Yaya Habi (yayar Baban Khalil) ta mayar da ni tare da tambayata ina zan je. Bakina ya yi nauyi, da hannu na nuna mata kofar toilet. Ita ce ta kai ni, na yi fitsari hade da yin brush na fito, sai kuma kanwar Mamata (Inna Saude) ta miko min kofin tea mai kauri. Gefe na kawar da kaina, ko ganinsa ba na son yi. "Sha Khadija ko don abun da ke cikinki" cewar Aunty Habi tana lallashina. Yadda suka rufu a kaina ne ya sa dakyar na dan kurba kadan na ba ta, sannan na mayar da kaina a kan filo na yi shiru. Fuskar Maman Khalil ta fado min, wasu hawaye masu zafi suka gangaro daga ramin idona. Cikin hanzari na tashi, kamar ba ni ce dazu na kasa tashi ba. Wannan karon ma yaya Habi ce ta yi saurin dakatar da ni, na zuba mata idon cikin dabara na fizgo maganar da nake son yi "Ina Maman Khalil, Ramla da kuma Baban Khalil? Me ya faru da Maman Khalil na ga kamar fuskarta a kumbure, yarinyata kuma fa?" na karashe maganar cikin muryar kuka ina kallonta. "Natsu Khadija! Ki natsu don Allah, rika ambaton Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un. Dukkanmu bamu isa mu ja da hukunci ubangiji ba. Allah ya bukaci abunsa, kuma sun karɓa kiransa,ki yi hakuri don Allah, mun san akwai damuwa da tashin hankali amma ki yi hakuri."kallonta nake yi ina tsiyayar da hawaye, ba zan ce ban fahimci abin da take fada ba. Amma na kasa gasgatawa. Shigowar Ummata ne ya sanya ni rushewa da kuka mai sauti hade da kwacewa daga hannun yaya Habi zuwa wajen mahaifiyata, ita ma sai ta rungumeni tana kuka da alama zuwanta kenan ma, sai daki da falon ya kuma cika da koke-koke. "Umma wai da gaske su Baban Khalil duk sun rasu? Don Allah ki ce min ba gaskiya ba ne, duka yaushe muka gama waya dasu, har yana fada min me zai sawo min sun kusa shigowa Abuja, amma to yaushe ya rasu?" Umma ba ta ba ni amsa ba, wani kukan ta kuma fashewa da shi, wata Auntyn su Baban Khalil ce ta janyeni hade da yin waje da ni, can baya ta kai ni, mara yalwar jama'a. Bayan mun tsaya ne har a lokacin kuka nake yi sosai. " Ce Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un Khadija" Na dade ban furta ba saboda kukan da ya ci karfina, da kyar na fada "Innalillahi.... Wa'inna.... Ilaihir.... Raji'unnn" "Ci gaba da fada." Ba musu kuwa na ci gaba da fada, tun muryata na yayyankewa har na fara fada daidai. Har sai da ta gamsu natsuwata ta dan daidaita sannan ta dafa kafaduna ta ce "Khadija ki yi hakuri, mutuwa a kan kowa take, idan ta zo ba tsumi ba dabara sai an tafi, akwai zafi da ciwo mun sani, amma ki yi hakuri don Allah, addu'a za ki rika yi masu." Kallonta nake yi, hawaye masu dumi na bin kuncina. "Yanzu suna ina?" "Khadija an kai su gidansu na gaskiya tun jiya." Ido na zuba mata kafin in ce "Cikin daren aka kai su? To ni ina na je, da ba za a kirani in gansu ba?" "Ki yi hakuri yau kwana biyu da rasuwarsu ai, ke kuma kin riga kin shiga wani hali bai kamata a yi ta ajiyarsu ba." Kenan idan na fahimceta kwana na biyu ban san inda kaina yake ba "Kenan har da Bashir, shi ma ganin karshe na yi mishi. Wayyo Allahna ni Khadija." cikin sabon kuka na furta mata maganar Jikinta ta janyo ni, muryarta ta yi rauni ta ce "Yi hak'uri Basheer kam yana nan da ransa har yanzu yana dai bukatar addu'arki" "Zo ki kai ni wurin shi " na yi maganar ne daidai ina tafiya ban damu da rashin takalmi da ke kafata ba. Kafin ta ankara har na fara ratsawa cikin mazan da suka taru a harabar gidanmu tsallakasu kawai nake wasu kuma ina takasu, da katon cikina da na manta yana jikona Rahma ce ta farkon wacce ta fara isowa wajena tana fadin "Subhanallah! Ya akai aka bar ta ta fito?" Ni kuwa kokarin kwacewa kawai nake daga rikon da ta yi min "Ni ki sake ni wajen mijina zan je, ki sake ni na ce." Wajen mata biyar ne suka kama ni zuwa dakina. Idona a bushe na kasa yin kukan ma, cewa nake kawai a kai ni in ga mijina. Yadda na nace ne ya sa Rahma dole ta samo wanda zai kai ni babban asibitin Abuja inda Baban Khalil ke kwance, ni da yaya Habi da kuma kanwar Babana ne a motar. Tun da muka shiga Kalamai masu laushi da kwantar da hankali suke fada min har zuwa lokacin da muka isa asibitin. Kai tsaye dakin da yake kwance muka nufa, su Abdul ne kannensa a kofar dakin zaune. Suna hangomu cikin sauri suka mike hade da tararmu. "Ya mai jikin?" Aunty Habi ta fara tambaya "Akwai sauki" Abdul ya fada cikin sanyin murya. "Ya farka ne?" ta kuma tambaya, don ni kam yanzu idan akwai abun da ke mun wahala to magana ce. " Eh ya farka." "Ya yi magana?" "Eh ya yi" wannan karon Hassan ne ya ba ta amsa. A kuma daidai lokacin ne muka isa kofar dakin. Kwance yake yayin da aka sanya mishi irin robar nan da take taimakawa wajen yin numfashi, kanshi nade da bandage, kafarsa ma akwai alamun gyaran karaya na asibiti. Ido na zuba masa ina kallon yadda halittarsa ta canja lokaci daya, kamar ba shi ne mijina dan gayu mai son kwalliya ba, lallai dan Adam ba a bakin komai yake ba. Fitowa na yi waje na zauna, har ga Allah na rasa kalar tunanin da zan yi. Ni dai gani nan zaune kamar gunki, bayan mintuna talatin da fitowata sai ga sauran ma sun fito wai in tashi mu tafi. Na kafe kam babu inda zan je ina nan, iya lallashinsu kin tafiya na yi, dole su ma suka hakura muka zauna tare. Zaman makokin sai ya koma asibiti, saboda na ki tafiya gida. Idan ka dauke ido babu wani abu a jikina da yake aikinsa yadda ya kamata, bana iya magana, idon ma ya bushe babu hawaye, zuciyata ba ta iya wani tunani mai zurfi. Abinci ma sai surukata ta sani a gaba da Mamata sannan nake iya ci. Yayin da Baban Khalil ke kwance kamar gawa. Saboda komai sai an yi mishi. Lokaci daya kuwa na zube, na yi baƙi, har da wasu kurajen tashin hankali suka fito min. idan ka dauke cikin jikina babu wani abu mai kauri. Tsawon sati amma babu wani cigaba, kullum jiya iyau, har an fara tunanin fita da shi waje, da taimakon Rahma da kuma mijinta. Yanzu kam idan ka dauke ni, Inna (mahaifiyar Abban su Khalil,) Aunty Habi, Abdullahi, Hassan, Ni da kuma Maryam kanwata, to ba kowa. Sai Rahma da ba ta taba gajiyawa wajen kawo mana abinci ba. Su Affan ma duk suna wajen ta. Daga can ake kai su school a kuma dakko su. Yau ma zaune muke a dakin, masu hira na yi, ni dai dama zan iya wuni ban yi magana ba, ni ban san ma me zan rika cewa ba. Abin da yake damuna kadai ya ishe ni. Wuni nake kuka, ga na kewar Maman Khalil, ga na rashin lafiyar mijina. Ina lura da yadda Inna ta kafe ɗanta da ido tun bayan da suka shigo dakin. Dalilin da ya sa kenan ni ma na mayar da hankalina a kanta, duk kuwa da kukan da nake yi. Abdullah ta ja zuwa waje, jimawa kadan sai gasu da likita. Maganar da likitan ya fada ba ƙaramin daga min hankali ta yi ba, sannan ta yi sanadiyyar yankewar duk wani network da yake jikina. Saboda cewa ya yi, wai numfashi ya yi nisa da gangar jikin Basheer. Kwance bisa gadon marasa lafiya na ganni bayan na farka. A hankali kuma komai ya rika dawo min har zuwa furucin likitan, a hanzarce na yunkura da niyyar tashi. Amma na ji an mayar da ni, Aunty Habi ta ce "Kwanta, jikinki akwai ciwo." "Aunty Basheer fa." na yi saurin tambayarta ba tare da na koma na kwanta din ba. "Aunty da gaske shi ma ya rasu?" na kuma tambayarta a karo na biyu. "Kwanta na ce miki, Basheer yana nan bai rasu ba, doguwar suma ya yi." Na dan lumshe ido cike da jin dadin abin da ta fada min. Koda ba gaskiya ba ne, tabbas na ji sanyi. Sai a lokacin na ji zafi a kasan cikina. "Me ye wannan?" na yi tambayar hade da shafa wajen. "an yi miki aiki ne an cire abin da ke cikinki" A lokacin ne na kuma na shafa cikina don gasgata abun da ta fada lokaci daya kuma ina tuno wata maganarmu da Maman Khalil. Bacci nake yi sosai bayan na idar sallahr magriba, ban san ma ya daukeni ba, a cikin baccin na ji tana tashina. Firgigit! Na bude ido hade da dorasu a kanta. "Me ya faru?" na yi maganar cikin yanayin bacci hade da mikewa zaune "Haihuwa kika yi." ta yi maganar cikin murmushin da baya bacewa a kan fuskarta. Ni ma a lokacin murmushin na yi tare da fadin "Ace ko haka ake yi, ai da kila kullum mutum sai ya haihu." Tare mu ka yi dariya kafin ta ce "Ke kam haka haihuwarki za ta kasance ba za ki san kin haihu ba. Sai dai a ba ki labarin haihuwa kika yi" Har zuwa lokacin dariya nake yi, bayan da na karbi plate din da ke hannunta mai dauke da wainar Fulawa da yajin da ya sha garlic. "na gode" na fada a daidai lokacin da da take ficewa. Na share hawayen da suka gangaro kan fuskata, ban san ranar da zan daina kukan rabuwa da Maman Khalil ba, na yarda mutum ko namanka yake yanka, idan ka rasashi sai ka ji babu dadi. Barrantana ita da ko bakar magana ba ta taba shiga tsakaninmu ba. "Sannu! Akwai ciwo ne?" Aunty Habi ta tambaya hade da zuba min ido Kai na girgiza alamar a'a sannan na ce "Ina son ganin Bashir Aunty ." "To jira in je wurin Doctor tukun." Fitarta ke da wuya sauran 'yan' uwa da ke waje suka rika shigowa suna min sannu, wasu kai kawai nake iya daga masu. Nurse din da suka shigo da Aunty ne ta taimakeni na ta shi zaune, sannan ta dora min Babyn a kan cinyata hade da bude mata fuska, cikin murmushi take fadin "Ya kika ga Babynki, lafiyayya kuma kyakkyawa ga gashi tamkar ba'Indiya." Na zubawa yarinyar ido ina kallonta, abin da duk nurse din ta fada gaskiya ne, amma zuciyata babu dadi sam da zan ji dadin kalamanta. Hasalima hawaye ne suka gangaro kan kumatuna bayan na jingina kaina jikin bango. Ramla nake tunawa, watarana tana danna cikina, na ce "Ke bari Baby ne a ciki" Ta zuba min ido, kafin ta ce "Baby?" "Eh." na amsa cikin murmushi. Ba tare da ta dauke idanunta akan cikin ba, ta shiga murmusawa na san akwai maganganu sosai a bakinta amma ba hausar da za ta yi su, hakan ne ya sa na kara mata haske. "Baby ne me kyau a ciki zan haifo miki, ki samu abokiyar wasa yadda su Affan ba zasu kara korarki ba idan kin je wurin wasansu." Wangale baki ta yi sosai alamun ta ji dadi, a lokaci daya kuma ta kai hannu tana shafa cikin. Ni ma fadada fara'ata na yi, hade da janyota zuwa jikina. Tun daga wannan ranar ko me ta samo sai ta kawo min wai a ba Baby, ku kuma ta bude cikina ta dora abun wai Baby ta dauka. Na so ace Ramla na raye na haihu, in ga wace irin murna za ta yi? Za Ta bari a dauki Babyn ko ba za ta bari ba?. Tun ina kukan a hankali, har na bude murya sosai na shiga rera shi. Kowa a dakin hakuri yake ba ni da fada min magana mai dadi. Da sauri na mayar da hankali kan Abbansu Khalil da aka turo cikin keken marasa lafiya. Matar J ✍🏻 [12/22, 15:04] 08080966571: *HASASHENA* *Page 18* Kasa janye idanuna na yi a kanshi, har zuwa lokacin da Abdullahi ya tsayar da kujerar a gaban gadona, yayin da mutanen cikin dakin suka shiga jero mishi sannu. Bayan mutanen sun watse ne, ya zaro littafi ya yi rubutu hade da miko min. Hawayen kan fuskata na dauke, hade da karbar littafin na shiga karanta abin da ya rubuta. _"Bana iya magana Deejah sakamakon aikin da aka yi min a muka-muki, amma kuma na damu da sanin halin da kike ciki tun da aka ce kin haihu."_ Abun da ya rubuta kenan, ni ma sai na mayar mishi da amsa. _"Ina lafiya Alhamdulillahi, amma na fi damuwa da halin da kake ciki Abban Khalil, yanzu me ye ya fi damuna? "_ _"Kafata ce ta fi damuna da alama yanketa za a yi, ban san ya rayuwa za ta juya min ba kuma."_ Ba tare da na share hawayen da ke diga a kan littafin ba na shiga ba shi amsa _"a ko wane irin yanayi ina sonka Bashir, zan kuma ci gaba da sonka har karshen numfashina, bare ma sha Allah za ka warware, ni bukatata kawai shi ne ka rayu, koda babu kafa zan yi ma komai, zan kula da kai"_ Silent murmushi ya yi, a lokacin da ya karasa karatun, kafin ya yi rubutu ya miko min _"Ya kika ga Babynki, kyakkyawa kamar Affan ko? "_ Bayan na karanta na dan yi gajeren murmushin da na manta ranar da na yi irinsa, na san ya canja salon hirar ne, dalilin da ya sa kenan na zuba ma yarinyar ido. Gaske yake yi, tamkar Affan ne ya koma jariri yake kwance. _"Basu yi kama ba, fuskar Ramla ce."_ Murmushi ya yi, lokaci daya kuma ya shiga ba ni amsa _"Don ba ki san Affan yana yaro ba shi ya sa, amma da Maman Khalil na kusa abin da na fada na san ita ma shi za ta fada._ Shiru na dan yi bayan na karanta sakon, shirun da na rasa me ma na tuna. _" Yanzu me suka ce game da kafar taka?"_ Ni ma na canja salon tawa hirar, ba na son abin da zai tayar mishi da hankali _"Basu ce komai ba, kawai dai da an gyara ne, sai gyaran ya baci"_ _"Ko zamu gwada na gargajiya"_ Wannan karon dago fuskarsa kumburarra ya yi yana kallona. Yayin da ni ma na zuba mishi ido cike da tausayawa, ya yi baki, ya rame, fuskarsa ba sajen nan da yake shan gyara duk an askeshi, haka ma gashin kansa. Kuma a yanzu ne na fahimci karfin hali kawai yake yi, amma yana jin jiki. "Bashir!" na kira sunanshi cikin sanyin murya, bayan na matso daf da shi, hade da kama hannunsa. "Ina sonka a ko wane irin yanayi, fatana ka samu lafiya, don Allah ka rage damuwa, idan har kana son mu bar asibitin nan da wuri. Ba ni kawai ce ke bukatarka ba, hatta Sakeena da Ramla suna bukatarka a raye , saboda kullum za ka nuna kulawarka garesu ta hanyar yi masu addu'a." Na dan tsagaita hade da kallonsa, shi ma ni yake kallo. "Sannan ga su Khalil da Affan, su ma suna bukatarka, idan ka tafi maraici sai ya fi masu yawa." Wannan karon hawayen da nake boyewa sai da suka samu damar gangarowa. Hannu ya sanya yana share min hawayen, yayin da shi ma na shi hawayen ke sauka kamar ruwa. Ban san ko tsawon mintuna nawa muka kwashe a haka ba, kuma a haka Aunty Habi ta shigo ta same mu, ita ce ke shaida min zuwan Yusrah kanwata. Kuma ita ce ta kira Abdullahi ya tura Abbansu Khalil zuwa dakinshi. Zuwan Yusrah ba karamin kewa ya kara debe min ba, Idan tana yi min hirar ƴan'uwa da gida sai in rinka jin dadi sosai. Haka rayuwarmu ta kasance a asibiti, kodai ni in tafi wajen Baban Khalil, ko shi a kawosa wajena. Matsala daya shi ne baya iya magana, cikin sati littafai uku muka cika dam da magana, mun bude na hudu ne aka ba ni sallama. Shi ma zuwa lokacin sosai akwai sauki, idan ka dauke rashin maganar da kuma kafarsa. Amma ciwukan da ke jikinsa da yawansu sun warke. Ranar da zan tafi gida, da kuka muka rabu, na so su bar ni har zuwa lokacin da za a cirewa Baban Khalil karfen da ke bakinsa, su bamu sallama tare, saboda za a koma Ruma da shi don yi mishi aikin gargajiya. Amma suka ki, wai suna bukatar gadon. Ban hak'ura ba, kullum sai na zo asibitin, saboda na fahimci yana jin dadin hakan. Sannan Abdallah ya sawo waya ya ba shi, ni ma kuma wayata tana nan, Sai mu rika yin chat koda ban je asibitin ba. Kullum cikin lallabashi nake yi. Ba bukatar bayyana ya damu da rashin matarshi da kuma yarshi, ko bai bude baki ya fada ba ni na san yana jin zafi. A tare da ni a gida akwai kanwar Abbansu Khalil budurwa mai suna Jamila, ni ma kuma akwai kanwata Maryam, saboda Yusrah kwananta uku ta koma gida. Sakamakon rashin lafiyar yarinyarta. Sai kuma Aunty Habi, wacce ke kula da ni sosai a bangaren jego. Rahma kullum sai ta zo, kuma har zuwa lokacin ba ta maido yaran ba. Ni ma kuma ban yi maganarsu ba. makotana ma, suna dan yawan shigowa, ba kamar baya ba, don ban ma sansu sosai ba. Gidan dai kullum sai an yi baki. Amma kuma hakan bai debe min kewar Ramla da Sakeena ba, kullum cikin tunaninsu nake da tuna rayuwar da mu ka yi. Sai in ji kamar zan ji tashin motarta ta fita ko ta dawo. Idan na kalli motar lullube ba na sanin lokacin da hawaye ke zubo min. Kamar mafarki Sakeena ta zo, ta kuma ta fi. Ashe dama rayuwar zamanmu da ita ba mai tsawo ba ce. To yanzu da ta zauna da ni da mugun hali, ta cutar da ni kamar yadda wasu ke yi wa abokan zamansu da shi kenan yanzu ta tafi ta girbi abun da ta shuka, tun da ko gafarata ba ta samu damar nema ba. Ni ma ga shi ban nemi tata gafarar ba, kuma ba san na yi mata abubuwa marasa dadi. Abu ma fi a'ala shi ne ka zama mutumin kirki sannan ka jira mutuwa, saboda a ko wane lokaci tana iya riskarka, ba ruwanta da kana aikata mai kyau ko akasinshi. Shigowar Affan ce ta katse min tunanina Na rika bin shi da kallo ina tuna mafarkin da na yi a kanshi. Abun ka da yara babu ruwansu, komai bai canja nasu ba "Kai da wa kuka zo?" Don na san idan ba ya canja ba, ko zamu shekara a haka, daga sallamar da ya yi da kuma gaishe ni ba zai kara komai a kai ba. Kafin ma ya ban amsa Rahma ta shigo rike da manyan ledoji guda uku, Khalil na bin ta a baya. Shi kam kan jikina ya fada cike da murnar ganina, rungume shi na yi tsam, lokaci daya kuma Ina ta kokawa da hawayen da ke son zubo min. Kan stool din mirror Rahma tan zauna, lokacin daya kuma muna gaisawa. "Affan ya dauki Babyn?" Ta yi tambayar hade da kallona. "Bai dauka ba, kin san halinsa ai ba ya magana." "Kuma a can ya dame ni, in kai shi wurin Abbanshi da kuma Babynsu yana son ya dauketa." Na dan yi murmushi, lokaci daya kuma ina kallon irin ramar da Rahma ta yi, lokaci daya ta zube, sai ta kara haske fayau, har ba kyau. Samun kawa kamar Rahma a wannan lokacin abu ne mai wahala, tana da rikon amana. Karbar yarinyar na yi a hannun Khalil ina fadin "to zo ka dauke ta " Ba musu ya zauna aka dora masa ita, Rahma ta rika mishi hotuna, ni ma sai na rika daukarsa. "Wadannan kayan Sakeena ce ta saya da hannayenta, ta bar su a wajena ta ce idan kin haihu sai in kawo mata ta ba ki. Dama jira nake abubuwa su yi sauki in kawo miki." Ta karashe maganar hade da turo min ledojin. Jiki a mace na rika budasu, latest kayan baby ne masu kyau da tsada, overrall, da unique sex masu kyau, sannan akwai na mata yankanti masu kyau sosai da takalma, zanen daukar baby da na goyo, socks, feeding bottles, pampers, maya-mayai na Baby, turare, kai tarkace ne cike leda biyu. Dayar ledar kuma, less, atamfa, da kuma shadda ne masu kyau, sai ta kalmi gyale, turaren Wuta, na kaya da kuma na jiki. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, maimakon Rahma ta lallasheni ita ma sai ta fashe da kukan. "Aunty kayan da Momy ta saya miki ne ba kya so?" cewar Khalil bayan ya dafa kafadata. Girgiza kai na yi alamar a'a. "Aunty wai Mamana da Ramla sun mutu?" cewar Affan yana kallona Nan ma girgiza kan na kuma yi. "To suna ina, Abbanmu ba shi da lafiya, amma su ban gansu ba?" ya kuma tambayata "Suna Ruma" Na ba shi amsa hade da share hawayena "Amma Aunty mutane sai cewa suke sun rasu, yanzu shi kenan ba mu da Mama." cewar Khalil yana kallona. Take zuciyata ta kuma karyewa na kira Affan na rumgumesu gabadaya ina fadin "Kuna da Mama Khalil, ga ni ga kuma Aunty Rahma mu duka iyayenku ne, na yi alkawari zan yi maku riko tamkar Sakeena na raye, zan rike amanar da ta ce ta bar ma ni, muddin ina raye ba za ku yi kukan rashin uwa ba sha Allah." Kuka mu ka yi sosai, har sai da mu ka gaji don kanmu. Sannan Rahma ta tafi, bayan ta bar su Affan a kan za ta zo da yamma ta daukesu. Duk wata hidimar zuwa school nasu ita ce ke yi, haka asibiti kullum sai ta je ba ta gajiya, kullum cikin hidimarmu take. Sosai su Khalil suka debe min kewa fiye da su Zainab, duk da suna yawan tuna min da Ramla. Saboda muddin suka shigo bangarena da ita za su yi ta kiriniyarsu, abu kadan ta sanya kuka, wani lokaci sai na koresu bakina yake yin shiru. Amma yanzu sai su biyu kawai suke yi, sai ni da nake taya su kadan. Yamma kam sai ga Rahma ta zo daukarsu. Time din ma daga ni har ita, kowa sai da ya yi kuka sannan suka tafi. ******* Safiyar talata misalin karfe tara na safe na fito cikin doguwar riga mai kalar ja, babu wata kwalliya a kan fuskata, dan ƙaramin hijab fari na yi amfani da shi wanda ya tsaya daidai saitin cikina. Baby sanye cikin riga yar kanti, irin Sayayyar Sakeena, ta yi kyau sosai Jamila ta shiryata. Aunty Habi da ke zaune tana kallon tashar Arewa24 ta dago kai hade da kallona sannan ta ce "To ko ke fa, duk da ba ki yi kwalliya ba, amma ai kin yi kyau, kina abu kamar wacce ba ta yarda da kaddara ba, don Allah ki samawa kanki salama, su Sakeena yanzu addu'a suka fi bukata fiye da yawan koke-koken nan" Murmushi kawai na yi, hade da zama ina ba Baby Nono. Sai da na tabbatar ta koshi sannan na mikawa Zainab ita, muka fice zuwa asibiti Don jiya ko baccin kirki ban yi ba, tun da aka ce an cire karafan da aka sanya a bakin Abbansu Khalil na kosa gari ya waye in gan shi. Muna shiga dakin na hango fuskar Hassan cike da walwala, hakan ya sa na ji gwiwata ta kara karfi. Shi ma tun da ya hangomu sai ya tashi zaune, hade da zuba mana ido har muka karaso. Irin wannan kallon tsoro yake ba ni sosai, kashe min jiki yake yi. In ji kamar yana min kallon bankwana ne. Har yanzu fuskarsa da sauran kumburi, kafarsa ma a kumbure take. "Ya jikin naka." abin da na fara fada kenan bayan na je daf da shi. "Akwai sauki." ya fada a hankali hade mika hannu yana son daukar Baby Ya zuba mata ido "Wane suna kuka ba ta ne?" "Babu" na ba shi amsa Da sauri ya dago kai yana kallona "Yarinyar fiye da sati biyu amma ba ku yi mata huduba ba, wane irin abu ne haka?" Wannan karon ranshi a bace ya yi maganar, idonsa ma ya nuna hakan Dalilin da ya sa kenan na yi shiru. "Wane suna kike so a sanya mata?" "Ramla da Sakeena nake so" "Suna biyu wa ita kadai?" Shiru nan ma na yi ban ce komai ba. Shi din ma bai kara magana ba. Har zuwa lokacin da Abdallah ya shigo. "yi ma yarinyar nan huduba Abdallah, ka ba ta duk sunan da kake ganin ya dace." Baban Khalil ya fada Ba musu Abdallah ya karbeta, mintuna kadan ya maidota hade da cewa "Na sanya mata Sakeena." "Allah ya rayata, ya albarkaci rayuwarta, ya sa ta yi koyi da halayen ta kwararta masu kyau" fadin Baban Khalil "Amin duk mutanen gurin suka fada." "Kin ji sunanta ko?" Kai na daga alamar eh, idona na cika da kwalla. "Bana son a boye sunan, a kirata da Sakeenanta" Komai ban ce ba. Shi ne ya kara cewa "Ko ba kya ji?" "Akwai nauyi a baki, a yi mana afuwa zamu kirata da Maama yallaboi, saboda ita din mamarmu ce, ta yi mana abun da uwa ke wa yaranta. Ba zan daina kukan rashinta ba." Bai ce komai ba, da alama zuciyarsa a karye take. Yau kam sai na dan ji farin ciki, saboda Bashir yana magana, duk da ba da kowa yake yi ba. Misalin karfe hudu kuma, sai ga Rahma da dukkan yaran har da maigidanta. Na fahimci Abbansu ya yi farin cikin ganinsu sosai. Sai magriba mu ka taho Rahma ta ajiye mu har kofar gida, ita kuma ta wuce. Tun daga wannan lokacin duk bayan kwana daya sai na je asibiti, saboda Aunty Habi ta ce fita kullum ga danyen jego ba zai yiwu ba. Babu wani abu da muka nema muka rasa, daidai gwargwado bamu rasa komai ba, duk da ana ta kashe kudi, amma Abdallah da Hassan suna kokari sosai da abokan Baban Khalil. Babu abin da zamu ce masu sai godiya, shi ya sa ake cewa ka nema ka aje ko don ciwo ma. Sannan ka iya mu'amala kuma kada ka raina mutane watarana sai su zama gatanka. Matar J ✍🏻 [12/22, 15:07] 08080966571: *HASASHENA* *Page 19* Bayan sati biyu da cirewa Abbansu Khalil karafa a baki, muka nemi sallama da kanmu, saboda gyaran da ake mishi a asibiti babu ya ƙi kyau. Tun da ya iso kuwa gidanmu bai yanke da mutane ba. Rahma ta kawo yara sun wuni wurin Babansu, Sai magriba mijinta ya zo ya daukarsu. Sun dade da Abbansu Khalil suna tattaunawa a kan kodai fita waje za a yi da shi, amma ya ce za a fara gwada na gidan tukun. Sun jima tare, don sai wajen 9pm ya ta fi. A lokacin ne kuma na samu damar shiga dakinsa na bangarena. Zaune yake, yana danna wayarsa, shigowata ya sa shi mayar da hankalinsa a kaina. "Ba ki yi bacci ba?" "Eh" na fada hade da zama a gefen katifar da yake. Na gaishe shi, hade da kara yi mishi sannu, sannan na ce "kana bukatar wani abu ne?" "Tea kawai idan akwai." Mikewa na yi, tare da hado mishi tea din mai kauri na kawo mishi. Bayan ya sha ne ya bukaci wanka, a kan kekensa na turasa har zuwa toilet,, ni ce na taimaka masa ya yi wankan, har da shaving, bayan ya fito na shafa mishi mai, hade da sanya mishi boxer da vest sannan na yi mishi sai da safe, don su Abdallah ne zasu kwana da shi, ganina ne ya hanasu shigowa. Haka muka kasance kwana biyu muna, ana tattauna mafita, Rahma, maigidanta da kuma wasu daga cikin abokan Bashir sun fi karkata a kan a tafi da shi Indiya, yayin da ni da danginshi mu ka fi bukatar komawa gida. Ni dai kawai ban gamsu da maganar Indiya din nan ba, aje a kara jagwalgwala kafar, karshe ace dole a yanke ta. Bangaren Bashir kam, mune muke damuwa da ciwon shi, shi hankalinshi Sam ba a, wurin yake ba. Ya tafi a kan rasa matarshi, na tabbata da za ace ya zaɓi tsakanin Ramla da Sakeena wa yake son a maido mishi, da gudu zai ce Sakeena. Amma yana cikin damuwa sosai a kwanakin fiye da lokacin da yake zaune a asibiti. Ina yi kamar bana lura da halin da yake ciki ne kawai. Saboda tsayawa tattaunawa ko ba shi hak'uri a kan batun kamar fami ne, shi ya sa nake share shi. Ranar Asabar da misalin karfe tara na safe muka bar garin Abuja zuwa Ruma, don yi wa Baban Khalil magani. Tafiyar da mutane da yawa basu so ta ba. Kar ma mijin Rahma. Bamu tafi da su Khalil ba, suna gurin Rahma saboda school, amma ta ce ana yin hutu za ta kawo su. A gidansu Baban Khalil muka sauka, abu da babban gida, ai nan da nan mutane suka cika kofar Inna, kai har da makota, kun san kauye da kara. A ranar wasu suka yi kukan mutuwar Maman Khalil, abin da ya kara tayar da hankalin Bashir, mutuwar ta dawo sabuwa dal. Safiya ma haka mutane suka dasa shigowa, musamman ƴan'uwansu na nesa, da ƴan'uwan Maman Khalil, duk wanda ya zo jimamin mutuwar Maman Khalil yake yi da yaba halayenta. Wasu kuma su rika tambayar su Affan. Ni dai bukata a tafi wurin gyara, ji nake kamar ana zuwa zai warke. Amma ba a kira mai gyaran ba sai da mu ka yi kwana uku da zuwa, ana ta shawarwari na wanda ya dace ma a dakko. Ni dai koda na ji an ce an tafi dakko mai gyara raina fes, har addu'a nake Allah Ya sa su same shi. Can wajen shabiyu na rana kuwa suka dawo, nan ma aka dora wata shawarar, na rasa abin da ake tattaunawa. Sai wajen uku aka fita da Abbansu Khalil cikin zauren gidan. Kuryar dakin Inna na shige cike da tashin hankali, yayin da nake fatan a yi wannan gyara cikin nasara. Ban taɓa tunanin haka gyaran zai kasance ba, kila shi ya sa ake ta tsugune tashi ina jin haushi. A sume aka shigo da Bashir bayan an gama gyaran, zuwa lokacin duk mun ci kuka mun koshi. Sai la'asar ya farfado, dama yana zagaye ds ƴan'uwa, kowa ji yake kamar ya cire mishi ciwon. Haka aka ci gaba da kula da shi, ni ba komai nake yi mishi ba, duk ƴan'uwanshi ke yi. Jego kam ga shi nan dai, a watse na yi arba'in. Kwana uku da canjawa Abbansu Khalil gyara dangina suka yo mota guda suka zo duba shi. Sosai na yi farin ciki, kuma na fahimci hakan ya kara kimata a idanun danginshi. Saboda dama dangin Sakeena kullum suna hanya. Ranar da aka cika sati mai gyaran ya zo, cikin ikon Allah gyara ya yi, farin ciki guna ba a magana. Ba ni kadai ba duk wani masoyinshi ma. Kafar dai ba ta takuwa, Sai dai a kan keken nan, amma yana iya dagata da kanshi, har mikewa ma ya hau keken duk yana iyawa. Ban san me ya faru ba, na ji dai an ce aje a share mana gidanmu, wai can zamu koma. Cikin kwana biyu kam aka gama gyare shi tsab muka koma. Sai na ji na fi sakewa, musamman wajen kulawa da shi. Saboda a can akwai idanun mutane, ba komai nake iya yi mishi ba. Sosai na tattara hankalina a kanshi, duk wani abu da na san zai sanya shi farin ciki kokarin yi mishi nake yi. Auran mijin mamaciya akwai kalubale sosai, saboda kullum bakinshi a kan radadin yadda yake ji ne game da rashin matarshi, tun abun baya damuna har na rika jin babu dadi, daurewa kawai nake ba na nuna damuwata. Ni kaina ina kewarta, ballantana kuma shi. Wani lokaci zan dage in yi masa abu, amma sai ya ce "Ina ma Sakeena na da rai na tsinci kaina a wannan halin, na san zan samu kulawa ta musamman" Idan na ce ni bana kula da shi, sai ya ce wai shi ba haka yake nufi ba. Kuma iyakar bakin kokarina ina yi, bana barinsa da datti. Yi mishi wanka, kai shi toilet, fitowa da shi, abincinsa, kasancewar ba komai yake ci ba. Amma a hakan dai korafi yake. Ga ni dai yake da matarsa na da rai za ta fi kulawa da shi a kaina. Ga kafar tana yin wasu baroro kamar ya kone, wai sai aka ce daji ne, haka aka shiga karbo magunguna, amma ni ba na ganin wani ci gaba, kullum ciwon da sabon salo yake zuwa. Yau Rahma da maigidanta za su kawo su Affan duba jikin Babansu. Shi ya sa tun safe nake ta lilo a tsakar gida, ba ni kitchen ba ni daki, ba na wajensa, ga Maama da rikici, idan ta fara kuka, kamar ana kwakule mata idanu. Ga kiwar tsiya, ba ta yarda da kowa, daga ni sai Jamila da Babanta, su din ma idan tana borinta basu isa su dagata ba. Jamila na zuwa ta taya ni raino, don Zainab kanwata tuni ta koma gida. Ina kitchen ina fama da aiki, ga Maama na ta kuka, ashe shi kuma yana kirana, zan kai shi toilet ban ji ba saboda kukan Maama. Ban fita ba, har sai da na gama hada miya, dakinsa na nufa ba wai don na san yana kirana ba. Sai don kawai in leka shi. Ina shiga kuwa sanda tsakar ka. Tun da na shiga yake bala'i kamar dama Jirana yake, ya hanani ma in yi magana. Har sai da na jira ya kai aya sannan na ce "Ka yi hakuri, ban ji kiranka ba, Maama na kuka, kuma ina kitchen ba na son su Affan su iso ban kammala abinci ba." "Ki yi min shiru, tun da Sakeena ta rasu na tabbata na yi rashin da ba zan iya cike gurbinsa ba, yarinya daya kawai amma kin kasa kula da ita, ki bar ta ta yi ta kuka, aiki ki kasa gamawa da wuri." Daurewa kawai na yi kafin na ce mar "Ka yi hakuri don Allah, mu je in kai ka toilet din." Da kyar na samu ya yarda na taimaka masa, sai da na tabbatar na yi mishi duk abin da ya dace sannan na koma kitchen, a lokacin kuwa miyata ta fara konewa. Bayan na motsa miyar hade da rage gas, cigaba da zagaye kitchen din na yi da goyon Maama so nake ta yi bacci. Yayin da a zuciyata nake jin wani irin zafi, ku san kullum Baban Khalil sai ya nuna gazawata a kan abu, kamar haushina yake ji, abu kadan sai fada, ya dauki alhakin mutuwar matarsa ya dora a kaina. Kamar ni ce na kashe ta. Bai san ni ma ina jin babu dadi a kan mutuwar tata ba Komai na yi, bana burgesa, sai ya ga abun kushewa. Ban da ina jin tsoron bakin mutane da na yi tafiyata na ba shi guri. Kar ya kai ni makura in fara tankawa. Misalin karfe biyu na rana su Rahma suka iso, wannan ya tabbatar min da tun asuba suka dakko hanya. Sosai na ji dadin zuwansu, bayan gaishe-gaishe, suka yi sallah, ni kuma na kai wa su Bashir abinci shi da mijin Rahma. Su Khalil kam tuni suna gidan kakanninsu. Rahma zaune tana cin abinci ta ce "Aunty Ramla haka ƙafar Abbansu ta kara yi?" Cikin jimami na ce "Wlh fa, an ce wai daji ne, ana ta magani, amma babu karayar yanzu" "Yanzu wannan ciwon ana magani kenan? kalli fa yadda kafar ta zama" Kai na jinjina alamar eh, saboda ni kaina ba na ganin wani ci gaba, kawai dai ana magani ne, amma kullum kafar kara caɓewa take yi, duk da wani farfashe. Ga shi ta kumbura sumtum, nan kashi nan fitsari. "Ya kamata a fitar da Abbansu waje Auntyn Ramla, wannan ciwon akwai daga hankali. Managarcin mutum ingarma kamar Abbansu, amma kalli yadda ya koma, komai sai yana zaune za a yi mishi. Gaskiya hankalina ya tashi. Idan kawata na da rai ba za ta amince ce ba. " Komai ban ce ba, Sai hawaye da nake sharcewa. Ban san me ya sa mutane suke cewa idan Sakeena na da rai ba za ta yarda ba. To idan ba ta yarda ya za ta yi, ko za ta cire mishi ciwon ne? Ni ban san me zan yi ba kuma? " Kalli ke ma duk kin rame kin yi baƙi?" cewar Rahma A zuciyata na ce "Ba dole ba," ( wai arne ya tambayi pastor Idan ya mutu zai shiga aljanna? Pastor Ya ce ba dole ba, mutum da gidan uban shi) ai dole in yi rama, abubuwa da yawa ne a kirjina. Jimamin mutuwar Sakeena da Ramla, ga ciwon Bashir, ga jinya, ga tsotso, ga rigimar Maama. Ga ta Bashir da kullum nake zama mai laifi. Haka muka rika hira da Rahma wata ta kwantar min da hankali, wata kuma ta tayar min da shi. Da yamma na raka Rahma gidansu Sakeena, daga can muka wuce gidansu Bashir. A can na samu su Affan lan ci wasa da rashin ji an gaji. Sai magriba muka baro gidan. Inda duk zamanmu tattaunawar dai a kan ciwon Bashir ne. Da safe ma haka aka dora, mijin Rahma ya dage lallai a fita da Bashir zuwa kasar waje Wannan karon kam basu ki ba, amma sun ce wai a jira nan da sati biyu, akwai sabon mai maganin da aka samu, idan abun bai yi ba, Sai a fita wajen. Haka su Rahma suka koma duk jiki a mace ******* Bayan tafiyarsu Rahma kam ciwo sai dai godiyar Allah. Amma naman ƙafar Bashir zafkewa yake da kanshi yana faduwa. Fadin tashin hankali da muke ciki ba sai an fada ba. A haka aka kwashe shi zuwa babban asibitin Katsina. Kwanansu daya mu ka bi bayansu. Tun bayan da na isa asibitin mu ka gaisa komai ba kara cewa ba. Damuwa ta ishe ni, a shekaruna 23 abubuwa sun haye min. Na rasa da wanne zan ji. Yanzu kam da nake kallon Bashir kwance cikin jinya, ji nake kamar in ce ya ba ni in karbar mai ya dan huta. Ga Maama ta ishe ni da fitina sai mu fita waje, haka na mike zuwa wajen, ina rarrashinta, bayan ta yi bacci ne na kuma dawowa ɗakin. Zuwa lokacin ne kuma su Aunty Habi suka rika fita yin alwalar la'asar. Ni kam dama ba sallahr nake yi ba. Shi ya sa na koma kan tabarma na zauna, hade da yin shiru, jin muryar Bashir yana kiran sunana ne ya sanya ni saurin dagowa. Saboda na dauka bacci yake yi. Da sauri na isa wurinshi ina fadin "Kana son wani abu ne? Sannu Allah Ya ba ka lafiya" Maimakon ya amsa min, Sai ya zuba min ido yana kallo na, ganin ba zan iya jure kallon ba ne ya sanya ni janye idanuna. Hannuna ya guda daya ya saka cikin na shi, a hankali ya ce "Allah Ya yi miki albarka Khadija, na gode da dawainiyarki a kaina" Komai ban ce ba, hakan ya sa ya dora da "Ki daina tayar da hankalinki, kalli yadda kika koma Khadija" Hawayen da nake ta kokarin dannewa suka gangaro min, cikin muryar kuka na ce "Hankalina ba zai kwanta ba Bashir muddin kana cikin wannan halin, idan na ce ma zai kwanta karya nake yi. Babban burina in ga ka samu lafiya koda kuwa haka yana nufin za a cire kafar nan. A hakan ma ina sonka" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Kirjina yana zafi Khadija, ji nake ina ma ace ni ma na bi Sakeena, ga shi yanzu ina rayuwa cikin ba tare da ita ba. Na rasa wanne abu ya fi min zafi tsakanin jinyar nan da rashin Sakeena. Wani lokaci in ji kamar wasa, wani lokaci kuma in gasgata ba ta a duniya. Da ace ni ma na rasu da duk ba ki shiga wannan tashin hankalin ba. " Hannunshi da ke cikin nawa na matsa a hankali kafin na ce" Ina bukatarka a raye, ba ni kadai ba, muna da yawa ka daina fadin haka. Mu yi addu'ar ka warke " " Yaushe? Khadija yaushe zan warke kullum ciwon gaba yake kara yi" "Bawa ba ya fitar da rai daga rahamar Allah Bashir, Sha Allah za ka warke, za ka samu lafiya" Duk mu ka yi shiru, shi ne ya katse shirun namu da fadin "Na ce su yanke kafar nan, amma sun ce a'a, wai kashin bai mutu ba" Sabbin hawayen da ke zubo min na dauke, kafin na ce "Allah Ya zaɓa abin da ya fi alkairi. Bamu da wata dabara" "Miko min Sakeena" ya yi jin Maama na kananan kuka Bayan na sauke ta kan cinyarshi ya dorata yana kallon ta. Ita ma shi din take kallo. Murmushi ya yi kadan kafin ya ce "Kin faye rigima Sakeena, takwararki ba haka take ba" Kallon shi kawai take yi, kallon shi ya mayar kaina kafin ya ce "Khadija kodai akwai abin da ke damun yarinyar nan ne ba mu sani ba. Ko a, gargajiyance haka? Rigimarta ta yi yawa." "To ni dai ban sani ba. Amma Maama kam ai tun aka haife ta haka take" Kai ya jinjina hade da fadin "An ce yara idan suna ganin mutuwar waninsu. Kodai ta fahimci mutuwa zan yi ne?" "Haba Abban Khalil! Me ya sa kullum kake son kashe min jiki, maimakon karfafa min gwiwa?ka san me mutuwarka kake nufi a wajena? To ni kaina ban sani ba. Amma na san shi ne karshen tashin hankalina" Kafin ya ba ni amsa aka turo kofar, su Abdallah suka shigo, wannan ya sa ya mayar da hankalinshi kansu. Matar J✍🏻 [12/22, 15:41] 08080966571: *HASASHENA* *Page 20* Duk yadda su Aunty Habi suka so in koma gida tare da su ki na yi. Ji nake ina juya baya abu mara dadi zai faru da Bashir. Hankalina ma ba zai taba kwanciya ina gida shi yana asibiti ba. Ba don sun so ba, suka bar ni, amma sai aka ce zan zauna gidan wata matar abokinshi Mustapha, gidanta yana kusa da asibitin ne. Ni dai ba haka na so ba, na so ace a nan nake kwana kuma nake tashi. Amma hakan ma ya yi min, ko ba komai dai zan rika kallon shi kullum. Yanzu zaune nake a kan kujerar da ke fuskantarshi, Maama na shan nono, lokaci daya kuma ina yi mishi fifita a kafar, duk da lokacin karfe shidda da rabi na yamma. "Su Affan sun kusa yin hutu Khadija, ina jin ya kamata su dawo gida, a nema musu makaranta, mun bar wa su Rahma dawainiya" Kai na jinjina a hankali cike da rashin jin dadi, saboda school din su Khalil tana da kyau sosai, ba na jin za a samu kamarta ko a Katsina ba ma a Ruma ba. "Gaskiya ne, amma kam ba na son a cire su a makarantar can, ka ga a Ruma babu makaranta mai kyan wacce suke yi" "To ya za a yi, su ma wannan din kaddararsu ce, zan yi waya da Dr Nura, ya karbo min transfer latter yaran da school clearance na makarantar" Ban kai ga ba shi amsa ba, wata mata doguwa, mai matsakaicin jiki ta shigo, sanye take da abaya blue, ta rolling ɗankwalin abayar. Kallo daya za ka yi mata ka fahimci akwai wayewa ta ilmi a tare da ita. Cikin fara'a suka gaisa da Bashir ta yi mishi ya jiki, shi kuma ya amsata hade da yi mata godiya a kan dawainiyar da suke yi da shi. Kaina ta juyo cikin sakin fuska ta ce "Madam barka da yamma ya mai jiki?" Murmusawa na yi kadan kafin na ce "Jiki Alhamdulillah, mun gode da dawainiya Allah Ya saka da alkairi" "Babu komai. Ita ce za mu je tare" ta yi maganar hankalinta a kanshi "Eh. Ta ki yarda ta bi su" Yanzu kam ni ta kalla hade da murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tana fadin "Tana da gaskiya ai. Ko ta koma hankalinta ba zai kwanta ba, gara tana kusa da kai. Allah dai ya kara afuwa" "Amin" muka hada baki a tare, kafin ya ce, "Ta shi ku je" Ba musu na mike hade da saɓa Maama a kafaɗata na ce "Sai da safe, Allah Ya ba ka lafiya" "Amin, na gode" Na juya kan matar da take amsa waya, a haka ta yi wa Abbansu Khalil sallama muka fita tare. Wata farar mota mai kyau na ga ta tunkara, har zuwa lokacin kuma waya take yi. Da kanta ta bude min front seat na zauna, ita kuma ta zagaya driver seat ta zauna daidai tana gama amsa kiran. "Baby ya sunanki?" ta yi tambayar hade da yi wa Maama wasa "Sakeena, amma muna kiranta Maama" "Ma Sha Allah! Bari mu je ta hadu da wata Maaman mai rikici" "Ita ma wannan ai tana taɓawa" na yi maganar cikin murmushi. Daidai lokacin ne kuma take fita daga asibitin "To ko duk haka Maama suke?" "Ba mamaki" na amsata, lokaci daya kuma mu ka yi dariya. Haka ta rika ja na da hira har zuwa lokacin da ta yi horn a kofar wani kyakkyawan gida, ba jimawa, wani yaro ya bude kofar gate. Muka silala. Dandanan yaran suka zagaye motar, suna mana sannu da zuwa cike da nutsuwa. Sosai na ji sun burge ni, na ji Ina ma ace ni ce, zagaye da yarana cikin kwanciyar hankali. Ko yaushe zan ga wannan ranar ni ma oho. Da wannan tunanin mu ka shiga cool parlor nata, komai unique cikin tsari, babu wasu tarkace, take na ji wata nutsuwa na shiga ta. Wani daki ta nuna min, ta ce in shiga in huta. Dakin madaidaici ne, akwai katuwar katifa, net, ac. Wardrobe Mai biyu, Sai karamin TV. Toilet din ma madaidaici ne, amma sosai yake a tsabtace. Maama na kwantar hade da dauro alwala, ina sallah yara suka kawo min abinci. Kamshinshi da miyar ke yi, ya sanya ni cin tuwon duk da rashin son cin abincina. Ina cin abincin ne ta kuma lekowa tana fadin "Zan ɗan kaiwa Abban Khalil abinci asibiti, mai kai mishi abincin ba ya kusa" "Ba damuwa" na amsa ta. Sai da na yi sallahr isha'i sannan na yi wanka, na canjawa Maama kaya zuwa marasa nauyi. Duk surutan da ke tashi a falo ban leka ba. Haka na yi zamana a cikin dakina. Muna chat da Bashir A chat din ne yake fada min matar da na zo gidanta sunanta Fatima, amma Maman Hana ake kiranta, matar Mustapha Sandamu ce. Na san Mustapha Sandamun, Sai dai iya wannan kawai na sani, ban san wani abu da ya shafe shi ba bayan wannan. Sosai muka sha hira da dare da Bashir, hirar da ta sanya ni yin bacci mai dadi. Dakyar na tashi na yi sallahr asuba ina kan sallayata, na rika jin ɓuruntun matar gidan a kitchen, wata zuciyar na fada min in je wurinta, wata kuma na hanani. Daga karshe dai na mike zuwa waje, sound din na rika bi har na gano inda take. Gani na ya sanya fadada fuskarta da murmushi ta ce "Amarya har kin tashi" Kai na jinjina a hankali kafin na ce "Ina kwana?" "Lafiya kalau, ya bakunta ya kuma Maama, sarkin rikici?" Wani murmushin na yi kafin na ce "Tana bacci ba ta tashi ba. Akwai abin da zan taya ki" "Babu komai wlh, ki koma ki huta" Nan fa muka shiga jayayya, ta dage lallai sai in tafi in huta, ni ma na dage lallai sai na taya ta. Haka ta hak'ura ta bar min soya doya. Ina muna hira, abin da na fahimta tana da faran-faran sosai. A shekaru kuma za ta yi tsarar Maman Khalil. Misalin bakwai muka kammala komai har da gyara kitchen din, zuwa lokacin kuma tuna yaranta suna ta shirin tafiya makaranta. Kominsu cikin tsari gwanin sha'awa, saboda ita ma ce min ta yi za ta je ta yi shirin tafiya aiki. A falon na zauna ina kallon yaran su bakwai, dukkansu kama suke da juna, duk da na fahimci akwai tagwaye a cikinsu. Ina zaune a wurin na ji kukan Maama, wannan ya sanya ni mikewa zuwa dakin, Sai da na, gyara mata jiki sannan muka fito, a lokacin kuma yaran break fast suke yi, wacce ake kira da Ihsan ce ta mike hade da nufo mu tana fadin "See Beautiful baby Ya Zeeyad" wanda aka kira da Ziyad din ya waigo yana kallon Ihsan da ke ta kokarin daukar Maama amma ta ƙi yarda Kamar za ta yi kuka ta ce "Tana ƙin mutane ne?" Kai na jinjina mata alamar eh ina murmushi "Oh my God! I like her" Kan dinning din muka karasa, da kanta ta haɗawa Maama tea ta shiga ba ta, wannan kam tana amsa, amma a kan jikina. Sai da ta koshi sannan ta kyale ta. Daidai nan Mamansu ta fito cikin shirinta, doguwar rigar atamfa irin dinkin Hajiyoyin nan ya sha stone, dauri mai kyau, fuskarta farar powder ce kawai da lipstick, Sai kamshi Mai dadi. Kafardarta sagale da blue mayafi wanda ya dace da atamfar "Kina nan dama?" ta yi saurin tambayata "Eh" na amsa hade da murmushi Hannu ta mikawa Maama tana fadin "Beauty zo mana" Yadda ta makale hannun ne ya sanya dukkanmu yin dariya, ita kuma ta dora da "Daga yau ga Beauty nan, daga yau Beauty ba sunan ki Beauty ba" Duk suka kalli wacce ake maganar a kanta suna dariya "idan za ki je asibitin yanzu, ki shirya kafin in kai yaran nan school in dawo" "To" na amsa. Haka suka fice gwanin sha'awa, ni kuma na shiga ciki don yin wanka, duk da ba ni da kayan canjawa. Ina yin break kuwa ta dawo, Sai da ta jira na gama, sannan muka fita zuwa asibitin, a can ma ba ta jima ba ta baro asibitin. Ni kam ina zuwa na iske su Abdullahi na kokarin kar Bashir toilet, bayan sun kai shin, na ce su bari kawai zan yi mishi duk abin da yake so. A kan toilet din ya zauna hade da dora kafarshi mara lafiyar a kan wani dan stool, a haka na yi mishi wanka, ya yi brush, na sawo shaving stick na yi mishi shaving,kafin na karbo wasu kayan na canja mishi. Su kuma suka dauke shi zuwa gadonshi. Abincin da Maman Hana ta kawo na hada mishi ya ci kam babu laifi, sannan ya shiga tambayata ya wurin Fatiman akwai dadin zama kodai a canja min. Zuwa lokacin dai ban ga wata matsala ba, don haka na ce a yanzu dai babu. Haka na ci gaba da debe mishi kewa, yayin da ƴan dubiyarshi basu yankewa a asibitin. Duk wani abu da ya shafe shi, idan har zan iya ni ce ke yi. Haka na ci gaba da zaman jinyanshi, kullum safe Maman Hana za ta kawo ni, yamma ta zo ta dauke ni, ba mu da matsalar abinci, har ragewa muke yi. Sosai nake hidima da Bashir, bana barin shi da kazanta, ina kokarin kwantar mishi da hankali. Saboda ciwon dai ga shi nan, kullum dai sai an wanke an sanya sabon bandage. Gami da zamana gidan Maman Hana kam shi ne abu mafi dadi gami da soyuwa a zuciyata gami da jinyar Bashir. Maman Hana mace ce mai saukin kai da dadin zama, irin mutanen ne da ba taba zama dasu sai sun ba ka dariya. Duk irin damuwar da nake ciki, muddin tana wurin tana kokarin mantar da ni. Ina jin dadin zama da ita sosai babu hantara ko kyara. Yau ma misalin karfe shida na yamma ta zo daukata, kamar ko wane lokaci cike da rashin jin dadi na bar Bashir saboda na fahimci yau din yana jin jiki, kawai yana karfin hali ne don kwantar min da hankali. A hanya ma haka muka rika tafiya shiru, saboda ban cika responding maganar Maaman Hana ba. Bayan shigarmu dukkanmu a falo muka yada zango, Maman Hana tana warware dankwalin kanta wata mace ta yi sallama, ni ce na amsa sallamar, ita kuma ta ce "To ga yar jarabar matar nan, magriba ma ta yi ba ta iya zama gida" lokacin da ta kai karshen maganar tuni matar ta shigo cikin falon, sosai na yi mamakin yadda ba ta yi shiru da maganar ba. "An je an zo, ai gidan ba naki ba ne, yar rainin wayau, yaushe rabon da ki ganni?" matar ta ba ta amsa "To da ban ganki ba, Umaima me ya same ni?" "Na tabbata kin ji ba dadi" cewar wacce aka kira da Umaiman kafin ta juyo kaina tana fadin "Baiwar Allah ina wuni, ya mai jiki" na amsa da murmushi da "Jiki Alhamdulillah, yana samun sauki sosai" "To Allah Ya kara sauki" ta yi maganar hade da bin bayan Maman Hana da ta shige dakin tana fadin "Mutum da gidanshi ba za ku bar shi ya huta ba" "An ƙi a bari" Umaiman ta fada lokaci daya kuma suka shige bedroom din Dalilin da ya sanya ni mikewa zuwa nawa dakin, cike da sha'awarsu, su basu da matsala har lokacin tsokanar juna suke da shi. Maama na fara yi ma wanka hade da canja mata kaya, saboda an kawo mana kaya daga can Ruma. Ni ma na yi wankan hade da yin sallah. Yayin da nake ta jin hayaniyar yaran a falo gwanin sha'awa. Ko yaushe ni ma zan kai wannan lokacin, in ga yarana cikin walwala ni ma cikin walwala muna farin ciki? Allah dai ni ma Ya nuna min wannan ranar. Ina zaune a wurin su Ihsan, Beauty da Maama da kuma Khadija suka shigo dauke da abinci, a gabana Ihsan ta aje min nawa, kafin ita ma ta nemi wurin zama, suna ci ana hira. Na fahimci sosai suke sona, ban san me ke musu dadi gami da ni ba. Amma duk inda nake suna wurin, bacci ne kawai ke raba mu. Maama babba ma da suka dawo garin shekaranjiya sosai ta fara sabawa da ni. Maama duk ƙiwarta, cikin kwanakin da mu ka yi a gidan ta hak'ura yadda take yi su dauke ta. A nan suka yi sallahr isha'i, sai 9pm na na sallame su. Na kira Bashir, saboda duk abin da nake yi hankalina yana wurin shi. Matar J✍🏻 [12/22, 15:44] 08080966571: *HASASHENA* *Page 21* Satinmu daya a garin Katsina, yan gidanmu suka kuma zuwa duba jikin Bashir har da Ummata. Sosai na ji dadin hakan, ko ba komai zuwansu na kara daga kima ta a idanun Bashir da ƴan'uwanshi. Ummata nasiha ta yi min sosai a kan in kara hakuri, in kula da mijina, kar in bari wani abu ya sa in watsar da shi. Zaman jinya ɗan hak'uri ne. Ni kaina na fahimci jinya sai da hak'uri, shi wanda kake jinya yana jin kamar ba haka ya kamata ka yi mishi ba. Kai kuma mai jinya kana jin kamar an danne ka. Kar ma jinyar Bashir ta ji labari, shi kam sosai nake kai hankalina nesa, in gama hidima da shi ya kwaɗa sallallami ya ce ina ma ace Sakeena na kusa da ni. Ta dalilin wannan furucin na shi har zuciya na yi, na ce zan koma Ruma, Maman Hanan ce ta lallashe ni na hak'ura, amma sai da na yi kwana biyu ba na sake mishi, kuma ko a jikinshi, ya lura bai lura ba, oho, tun da bai yi min maganar ba. Haka na hakura na warware. Sai la'asar suka dau hanyar komawa. A satin kuma kawata Samira Badiyya su ma suka zo min, sosai su ma na ji dadin ziyarar tasu, mun tattauna a kan abubuwa da yawa, suka kuma ba ni shawara a kan abubuwa da yawa. Satinmu biyu a asibiti babu laifi kam, amma har zuwa lokacin ana wanke kafar hade da yi mishi dressing, Sai dai ba kamar can baya ba. Ni kam tuni na zama yar gidan Maman Hana. mu kan yi hira sosai, kasancewar ita din mai sakin fuska ce da saurin sabo. Abin da na fahimta Sam ba ta san Sakeena ba, saboda a bakina take jin labarinta. Ranar Asabar muka tashi da jiran zuwan Rahma da su Khalil sakamakon hutun da aka yi. Shi kanshi yau Abbansu na fahimci yana cikin nishadi, saboda yadda yake ta fara'a. Misalin karfe uku kuwa suka iso, har da yaran Rahma guda uku duk maza, da wani irin zumudi su Affan suka dira asibitin, zumudin da na san bai wuce na son ganin Babansu ba. Sai dai kuma yanayin da suka ganshi da alama ya sanyaya musu jiki, domin lakwas suka yi, duk murnar nan da dokin nan babu, Sai shi ne ke ta kokarin ganin ya dawo musu da farin cikin da suka shigo da shi, amma abun ya ci tura, saboda karshe ma Affan kanshi ya kwantar jikin gadon ya shiga kuka. Kukan da ya kara sanyaya duk jikin wanda yake wurin har da shi kanshi Bashir din. Rahma kam har da kuka, dama wannan ta saba, duk zuwan duniya sai ta zubar da hawaye. Duk wanda ya san Bashir a baya, ya kuma gan shi a yanzu dole ya shiga firgici da damuwa. Allah Ya yi ikonshi kam a kan Bashir cikin kankanen lokaci. "Sannu Abbansu!" cewar Rahma cikin muryar kuka Da karfin hali ya ce "Na gode Maman Farhan, sannunku da kokari, Allah Ya bar zumunci, na gode sosai." Hawayenta ta dauke ba tare da ta ce komai ba, shi, kuma ya juya kan Dr Nura da hankalinshi kaf yake a kan kafar Bashir ya ce "Na gode Dr, ubangiji Allah Ya kara rufa maku asiri ya raya zuriyarku. Na gode sosai" "Amin, Sannu Bashir Allah Ya sa ciwo ya zama kaffara" "Amin" muka amsa gabadaya Rahma ce ta ce "Wai yanzu babu abin da za a yi Abban Farhan?" File din da yake budewa ya rufe kafin ya ce "Duk abin da ya dace suna yi, sai dai mu yi addu'ar samun lafiya. Kin san ita cuta ta kan shiga a gabadaya ne, warkewa kuma sai a hankali. Komai ba mu ce ba,, Bashir ne ya ce" To ga mu nan dai, ko zamu warke din, ko kuma muna jiran lokaci ne Allah kadai ya sani" Yanzu din ma ba mu ce komai ba, Sai Rahma da ta fara harhada kan yaran zuwa waje, ni ma bayansu na bi, a kan barandar kofar dakin muka zauna. Har zuwa lokacin jikin yaran a mace, hatta Maama shiru abun ta kamar ba ta wurin, ta dai lafe a jikin Khalil. Rahma ce ta fara cewa wato "Auntyn Ramla mutum ba a bakin komai yake ba, Allah Ya sa mu cika da imani" "Amin" na amsa a sanyaye "Ina ta son mu yi magana a kan maido da su Khalil gida. Auntyn Ramla me ya sa? Ko muna yi musu wani abu da bai gamsheku ba ne?" Idanuna na dora a kan yaran, jikinsu ya fallasa irin kulawar da suke samu, dukkansu jikinsu a murje lub-lub gwanin sha'awa. Idanun na dauke daga kansu zuwa wani bangare daban kafin na ce" Ai, tsakaninmu da ku Maman Farhan sai godiya kawai, babu wani abu da za mu yi muku mu saka muku. Sai dai addu'a. Amma babu wani abu na rashin dacewa da ya sa aka nemi su Khalil su dawo gida. Ni dai nan idan akwai wani abu ma to ban sani ba wlh." Zamanta ta gyara kafin ta ce" makarantar da suke they dealing okay, burin Sakeena Shi ne yaranta su samu ilmi mai inganci, za ta iya sadaukar da rayuwarta a kan hakan. Ba na jin Idan tana da rai za ta amince a cire su Khalil daga makarantar can a dawo dasu kauye. " Sosai raina ya sosu, abubuwa da yawa idan suka faru sai ka ji an ce da Sakeena na nan, ba za ta yarda ba, ba za ta bari, ko ace ba zai faru ba. Bawai iya Rahma ce ke fadin wannan ba, dangin Abban Khalil suna yawan fada, bare kuma Bashir da ya zame mishi kamar karatun sallah. Jin na yi shiru ne ya sa ta ce "Auntyn Ramla, ba tare da sanya hannun mijina ba, ina nufin misali ya janye hannunshi a kan Affan da Khalil, kuma sannan babu ran Bashir, to zan iya rike su hade da basu ilmi mai tarin yawa bangaren addini da na zamani. Kila na san Bashir da ƴan'uwanshi suna ganin kamar sun dora mana wahala ne, za mu iya yin abin da ya fi haka ga ahlin Sakeena, don Allah na kawo kokon barata gare ki Khadija, ki sanya baki, idan hutu ya kare su Khalil su koma makarantarsu" Shiru na yi ina nazarin maganarta, kamar tana ganin da sa hannuna a cikin lamarin, kamar kuma da gaske tana neman alfarmar tawa ne. Da wannan tunanin na ce "To zan yi kokari." haka mu ka shiga tattaunawa har la'asar. Sai da na je na yi wa Bashir alwala sannan na dawo ni ma na yi, a lokacin kuwa tuni Dr Nura ya kwashe yaran zuwa masallaci. Bayan na idar da sallahr na kara yi wa Rahma ta yin abinci a karo na ba adadi, saboda akwai flasks din abinci, wasu ma ko taba su ba mu yi ba. A karo na ba adadin ta kuma cewa "Ba na jin yunwa, Sai dai ko yaran za su ci idan sun dawo" Su din ma kadan suka taba, wai sun koshi. Dr Nura kam zarya ya rika yi tsakanin manya likitocin da ke asibitin, saboda Bashir ya matsa lallai sai a nemar mishi sallama, don wanke kafar da sayen magani za a rika yi ko yana gida ne. Muna zaune a barandar ni da Rahma, Maman Hana ta iso, cikin sakin fuska suka gaisa da Rahma, kafin ta wuce ɗakin da Bashir yake, nan ma ba ta ji ma ba ta fito zuwa wurin mu "Ashe ƴan Abuja suka iso?" ta yi maganar daidai tana zama gefenmu "Ai kuwa, tun dazu" na amsa ta cikin murmushi, Rahma ma murmushin take yi, wata sabuwar gaisuwar suka shiga yi, kafin Maman Hana ta ce "Tubarakhallah yan maza zira gasu nan. Ya kuke fama da rashin ji?" "Akwai kam. Dambe dai kamar filin boxing" cewar Rahma cikin dariya "Na sani ai, ni ma mai guda uku fama nake bare biyar" Daga haka suka shiga hirar rashin jin yara maza. Ni kam ma mikewa na yi zuwa wajen Abban Khalil, tun da ya ga shigowa ta ya mayar da hankalinshi a kaina har na karaso "Khadija!" ya kira sunana cike da kulawa Duk lokacin da ya yi hakan sai in ji jikina gabadaya ya mutu, tausayin kaina ya kama ni, in rinka jin kamar na zama wata abar tausayi, mai kuma neman taimako, Sai na yi da gaske nake iya matse hawayena, kamar yanzu ma da na rike hawayen da karfin tsiya "Me ya sa kake son a sallame ka wai?" "Saboda ke Khadija, sosai tausayi kike ba ni, kalli yadda kika koma kamar ke ce ba ki da lafiyar, kin je gidan wata kin zauna a raɓe, na tabbata dole ce ta sanya ki zaman gidan nan" "Tabbas dole ce, amma ina jin dadin zama da Maman Hana, idan don ni ce, don Allah ka tsaya a kula da lafiyarka" "A'a, ya kamata ki koma gida ke ma ki huta, ni kaina na gaji da zama a nan. Ya fi in koma gida, idan ma fita wajen za a yi sai mu fara shiri" Shigowar Dr Nura da wasu likitoci ne ya sanya ni yin shiru, Sai ma kunnuwana da na raba a tsakaninsu, discussion din nasu kaf a kan file din Bashir ne. Kowannensu da abin da yake fada, wani lokaci kuma maganar tasu ta zo daidai. Kiran sallahr magriba ce ta fitar dasu. Ni ma alwala na yi wa Bashir, ni ma na yi na kabbara sallah. Bayan na idar ina kan sallaya Affan ya shigo kusa da ni ya zauna idanunshi a kan Babanshi, har zuwa lokacin bai saki jiki ba. Da kulawa na ce "Ko kana jin yunwa ne Affan?" kai ya girgiza alamar a'a, ban yi tsammanin zai yi magana ba, su kuma na ji ya ce "Yaushe za mu tafi gida?" a hankali ya yi maganar, saboda ni kadai ce na ji "Ruma ko Abuja? " Kauye"ya kuma amsawa a hankali. "Kila zuwa gobe sha Allah" "To shi fa Abbanmu" "Muna jiran ya ji sauki Affan" na amsa shi a sanyaye Hawaye ya shiga daukewa, a cikin kukan ya ce "Yaushe to zai ji Auntynmu?" Ka cinyata na kwantar da shi a hankali na ce "Affan yi hak'uri ka daina kuka, kana dagawa Abbanku hankali. Sha Allah zai ci sauki soon. Ku dai ku rika yi mishi addu'a" "Ai muna yi kullum, har ma da Mommynmu da Ramla, Mommynsu Farhan ta ce mu rika yi musu addu'a" Idanuna na lumshe a hankali, wani abu mara dadi yana min yawo a kirji. "Me same shi?" sautin Bashir ya katse min tunanin da nake son fara yi. "Babu komai, ya gaji ne" na ba shi amsa, hankalina na a kan Khalil da yake shigowa dauke da Maamah. Abun mamaki sai ta ki yarda in dauke ta, wannan drama ita ce abin da ya sanya mu dariya yau, cikin dariya Abban Khalil ya ce "Kawo ta nan mu gani ko za ta yarda, Sai ka huta" Ya nufe shi da ita, cikin sa a sai ta yarda, muka kuma yin dariya, Abban Khalil ya ce "Wato yaro ma ya san na shi, kalli kiwa irin ta Maamah fa, amma wai ba ta ƙin ƴan 'uwanta" "Abba kafar na yi ma zafi?" Khalil ya katse mana dariyar da muke da ta tambayarshi idanunshi a kan ƙafar "Ba sosai ba Khalil, ku dai rika yi min addu'a kun ji" ya ba shi amsa shi ma yana kallon kafar. Su Rahma ne suka shigo da Maman Hana, a nan Bashir ke fadawa Rahma Maman Hana matar Bashir Sandamu ce. Cike da mamaki Rahma ta ce "Wacce ke ta bamu wahala kenan, kin ki zaman Abuja, kuma kin hana mijinmu ya zauna" Cikin dariya Fatima ta ce "Mijinku dai bai yi niyyar zama ba, amma ni ina ruwana" duk mu ka yi dariya. "Rahma ya kamata ku tafi masauki, yaran nan sun gaji" cewar Bashir yana kallon yaran daya bayan daya "Gaskiya kam, tun ba Haidar ba, kamar kaza yake, ga shi an sha tafiya." Daga haka mu ka shiga shirin tafiya, Rahma dai mu ta bi. Dr kuma ya tafi hotel. Matar J ✍🏻 [12/22, 15:44] 08080966571: *HASASHENA* *Page 22* Lokacin da muka isa Umaima ta shirya abinci, shi ya sa sallah kawai mu ka yi, aka shiga cin abincin da kuma hira, wani irin shauƙi da farin ciki nake ji, wanda na rabu da jin shi, saboda yadda mutane suka hadu ana ta hira gami da nishadi. Sai after 10pm muka kwanta, kuma 5am mun tashi, bayan sallahr asuba muka shiga kitchen taya Maman Hana abincin breakfast. Misalin 9am muka bar gidan zuwa asibiti, a can muka samu Dr Nura, sun dora daga inda suka tsaya. Ni dai breakfast na haɗawa Abbansu Khalil, ya dan taba ya ce ya koshi. Tabarma muka baza a kofar dakin muka zauna, muna taba hira gami da ganin yadda ma'aikata ke ta shige da fice. Karfe daya Dr Nura ke sanar damu an bamu sallama, amma za mu rika zuwa ganin likita duk Monday. Maman Hana na kira hade da shaida mata, ba jimawa kuwa ta zo ta dauke ni zuwa gidanta na tattaro kayana, na asibitin kuma na bar Rahma da tattarewa. Ba dai mu bar garin Katsina ba sai wajen karfe uku, A hanya ma dai hirar ciwon Bashir aka fi yi, da irin matakin da ya kamata a dauka, kai tsaye gidanmu muka nufa, a maimakon gidansu, hakan kuma ya yi min dadi, ko babu komai na fi sakewa a nan. Tun muka isa mutane ke zarya, lallai na yarda Katsinawa akwai kara, tun ba kauye ba. Wajen satinmu uku a Katsina amma kullum sai sama da mutane ashirin sun shigo asibitin nan wajen Bashir, wasu ƴan'uwa wasu kuma abokan arziki. Gidan bai yanke da mutane ba sai wajen goma, zuwa lokacin kuwa ba kowa a gidan daga ni sai shi, saboda Rahma gidansu Sakeena ta tafi ita da yaranta. Dr Nura kuma yana part din baƙi. Dakin na shiga da sallama, cikin alamun bacci ya amsa min "Wai har ka fara bacci?" na yi tambayar ganin Abdullahi bai jima da fita ba. "Wlh kam, sosai na gaji ne" Gefen shi na zauna ina kallon kafar sannan na ce "Sannu, Allah Ya kara sauki" "Amin Ya Rabbb." ya amsa hade da janyo ni gefen jikinshi. Saman kirjinshi ya kwantar da ni, lokaci daya kuma yana shafa gashina da yake a tsefe. "Kin watsar da komai, kalli yadda gashinki ya cunkushe hade da yin karfi" Sosai na kara kwantar da kaina a kirjinshi, ina jin yadda kasusuwan kirjin suke a jere, sabanin da can baya da tsoka ta lullubesu. "Ba ki ji ba?" ya yi maganar da wata irin muryar da na rabu da ji. Dalilin da ya sanya ni lumshe ido, kafin na ce "Ba ta gyaran kai nake yi ba, kai zan gyaramawa kuma ga ka kwance" "Ki, gyara min gobe idan Allah Ya kai mu ina so" Kai na jinjina alamar to, saboda ba zan iya ba shi amsa ba, abin da ban yi tsammani ba shi ne ya faru, ni kaina ba na ce ga ta yadda komai ya faru ba, sai dai bayan faruwar komai din ni ce na taimaka mishi wajen gyara kanshi, yayin da muka sha jinya cikin dare, saboda mun tsokano kafar. Safe su Rahma suka fara shirin komawa, babu laifi sun sha tsarabar kauye kam, yayin da Abbansu Khalil ya sha shawarwari wajen Dr Nura na yadda zai kula da kafarshi. Yanzu kam gida ya koma daga mu sai mu, Sai ƴan dubiya dasu Abdullahi ƴan jinya, yara kuma rabi suna wurina, rabi gidan kakanninsu na bangaren uwa ko na bangaren Baba. Ba ni da case da su. Bashir kam kullum dare za mu sha soyayyarmu, mu dawo muna jinya da safe, wani lokaci har sabon ciwo muke jiwa kafar. Inda Allah Ya taimakemu ma kafar na sauki ba laifi, saboda magunguna da yawa aka hada, a yi na gargajiya, a yi na asibiti har da na Islamic. Lokacin da hutu ya kare Saminu kanen Abbansu Khalil shi ne ya yi hidimar samarwa su Khalil makaranta a Batsari mai hade da boko da Islamiya , tun safe idan suka tafi sai yamma ake dakko su. Yayin da ake kai Bashir ganin likita ko wace ranar Litinin. Kuma Alhamdulillah a cikin wata biyu sosai kafar ta yi sauki, taka ta ne kawai ba ya yi, amma yana iya mikewa tsaye da kanshi, zai iya canjawa kafar position daga wani wuri zuwa wani. Kuma ta daina ɗiwa, wani wuri ne kawai bai gama warkewa ba. Kasancewar an fara zafi zaune nake saman tabarma da misalin karfe 5pm ina yankewa Maama farce, Bashir ya shigo gidan saman kekenshi, babu wanda zai ganshi a haka ya ce ba shi da lafiya, saboda ya yi fes abun shi, har wata ƴar ƙiba yake yi. "Ba na ce ki daina yankewa yarinyar nan farce da reza ba, kar watarana ki yanke ta" ya yi maganar daidai yana jan burki a gabanmu Shiru na yi kamar ba zan amsa ba, Sai kuma na ce "To" shi a kan yara to komai ba ka iya ba, zai ga kuma dai ba ka kula da su yadda ya dace. Ko a kan su Khalil dannewa kawai nake yi, amma kam da tuni mun yi babu daɗi. Zai iya shigowa ya iske su suna wasansu ya ce "Khadija kin ba yaran nan abinci?" sosai wannan tambayar ke ɓata min rai, ta ya zan dafa abinci in cinye kaf ba tare da na basu ba. Har ya tuka keken zuwa gaba, Sai kuma ya dawo baya yana fadin "Khadija kin san kina da ciki kuwa?" Wata irin faduwa gabana ya yi, yayin da na bude baki da idanu ina kallon shi, murmushi ya yi kafin ya ce "Cikin nan naki zai kai wata uku ko hudu" Ni dai poster Kawai na ajiye yayin da shi kuma ya ja keken nashi zuwa gaba. Idanuna na dauke daga kanshi na mayar kan Maama, wacce ba ta wuce watanni goma ba, Sai kuma na shafa cikina, kafin daga bisani na bi hannayena da kallo wadanda suka yi Fresh gwanin sha'awa Bayan wannan fresh din da na yi ban ji wani canji mai kama da alamar ciki ba, musamman da ya kasance ba na period, kuma an ce idan mace na shayarwa wai ba ta period ba ta samun ciki. "Tabbb!" na yi maganar hade da mikewa na bi bayanshi, idan har ya kasance da gaske ina da ciki aiko da Sai dai mu koma Abuja, ina zan iya da wannan abun kunyar ni Khadija. Mijin na fama a ganni da ciki kuma. Zaune yake gaban wata loka yana duba wasu takardu, shigowata ce ta sanya shi dagowa yana kallo na "Wai da gaske ina ciki?" Sai da ya yi murmushi kafin ya ce "Idan ba ki yarda ba, gobe ki je asibiti" Kama zan yi kuka na ce "aiko idan da gaske ina da ciki to gaskiya ka shirya mana komawa Abuja, ta ya zan fara kallon mutanen garin nan, kana fama da jinya ni kuma a ganni da ciki" "Ciki kam ba nawa ba ne, me ye abun damuwa" Fuska na kara narkewa kafin na ce "Kai nan ba ka komai ba, kana zaune kullum ace kuma Ina da ciki. Apart from that ma, duka fa Maama watanta goma" Komai bai ce ba, Sai takardunshi da yake ta dubawa. Na shiga bubbuga kafa ina fadin "Kana ji na ka yi banza ko" Takardun ya ajiye hade da janyo ni zuwa jikinshi kafin ya ce "Yanzu ina jin ki, me kike so?" "Mu koma Abuja" "Abuja kam Khadija sai dai ki kai ziyara, amma mun baro ta kenan, yanzu haka an sanya gidan a kasuwa" Da matsanancin mamaki na tashi daga jikinshi ina kallon shi, kamar in ce wani abu sai kuma na fasa, saboda abin da zan fada din zai iya kawo sabani a tsakaninmu. Amma na tabbata da Maman Khalil na raye ba zai yanke wannan shawarar ba tare da sanin ta ba, amma ni idan ban da yanzu magana ta kama ba zai fada min ba. Tashi na yi daga jikinshi tsam, saboda hayaniyarsu Khalil da na ji a tsakar gida. A babban falo mu ka yi kicibus, dukkansu na raba su da jikina ina jin dadin dawowarsu, yayin da suka shiga kiciniyar dakkowa Maama tsaraba. Hakan yana tuna min da Ramla, saboda duk lokacin da suka dawo daga makaranta burki a dakina, wai za a ba Ramla tsaraba. Na dauka sun manta, ashe abun na ransu har yanzu, ga shi ana yi wa Maama. Ruwan wanka na hada masu, kasancewar dukkansu sun girma, bana duk za su fita primary, na kwashe uniform din zuwa laundry basket, ina kitchen Affan ya shigo "Har an yi wankan?" Kai ya jinjina alamar eh. "To abinci fa?" na kuma tambayarshi "Sai an jima zan ci." Na juya kan Khalil da ya shigo ina tambayar "Kai ma abincin sai an jima?" "Eh" ya amsa ni, kafin mu ka shiga labarin makaranta, yadda suke nuna suna jin dadin makarantar sosai yana sanya ni farin ciki. Kuma ni kaina ina ganin ci gaba sosai musamman bangaren addini. Bashir ne ya tsaya kofar kitchen din, lokaci daya kuma yana dire Maama da ke kan cinyarshi tare da fadin "Yaran nan kin ba su abinci?" Kamar in ce ban basu ba, Sai kuma na yi shiru, saboda Khalil ya riga ni amsa tambayar da fadin "Sai an jima za mu ci" shi ma bai kara cewa komai ba ya tuka kekenshi zuwa waje. Wani abu na ɓacin rai ya tsaya min a wuya, dama da haushinshi na fito a kan zai sayar da gida ban sani ba. Ya kuma zuwa ya bata min rai da maganar ba yara abinci. Ban san me yake kallo na ba, ta ya zan yi abinci in hana yaran. A zuciyata Ina jin kaunar yaran tamkar ni ce na haife su, Sakeena ta fada min ga yaranta nan amana. A lokacin da take fada min wannan maganar, ba ta san za ta rasu ba, da wasa ta yi min ita, Sai ga ta ta zama gaskiya. Don haka na yi wa kaina alkawarin zan rike mata yara tamkar ita ce take raye kuma take rikon su. Tare muka gama aikin kitchen din, su Affan suka yi alwala zuwa masallacin magriba, ni ma na shiga dakin don yin tawa alwalar, lokaci daya kuma Ina lallashin Maama da ke kukan dole sai ta bi su masallaci. Bayan na idar da sallahr magribar, ina zaune kan sallaya ina ba Maama nono da take son yin bacci, maganar ciki ta fado min, take na yi sake da ni, jikina ya mutu likis, Yarinya wata goma ciki wata hudu, kenan tana da 6month na samu cikin "Wayyyo Allahna!" na fada cike da jin kunyar yadda zan rika hada ido da mutane, Bashir na zaune cikin keke ni ina kayan ciki turtsi-turtsi. "Allah Ya sanya ma ba cikin ba ne" na fada a sanyaye, lokaci daya kuma Ina jin lallai gobe in je asibiti domin tabbatarwa. Jin Maama ta yi bacci, na zare daga jikina a hankali, na kwantar da ita saman katifa, kafin na dawo na kabbara sallahr isha'i. Ina idarwa su Khalil suka shigo, Sai muka runguda zuwa falo, na sanya mana abinci mu ka ci, mu ka yi home work, sannan na karbi haddarsu hade da yi musu gyararraki, Affan kam ana gama karbar haddar ya yi bacci. Shi ma Khalil ina tattare falo ya yi bacci. Sai da na kintsa ko ina, kafin na shiga tashinsu zuwa dakinsu. Ina tsaka da tashin Affan Bashir ya shigo, ya zuba mana ido yana kallon yadda nake fama da Affan, saboda akwai lafiyar magagin bacci, dakyar na samu ya tashi. So hannayensu na rike zuwa dakinsu, daidai zan shiga dakin ya ce "Yaran nan sun ci abinci kuwa za su kwanta?" "Sai dai yanzu da ka zo ka ba su" na amsa shi ba tare da na tauna maganar ba. Ko ta dace ko ba ta dace ba, ni dai na sako ta. Babu halin kuma mayar da ita. Matar J ✍🏻 [12/22, 21:12] 08080966571: *HASASHENA* *Page 23* A falon na dawo na same shi, kamar in yi banza da shi a kan maganar na shi abincin, Sai kuma na shige kitchen na hado mishi komai da komai na kawo mishi. Na wuce dakina, yau gabadaya duk bata min rai yake yi, sosai raina yana baci a kan yadda baya sakani cikin ko wacce sabga ta shi, Sai dai kawai in ga ana yi, ko in ji an yi, sabanin Sakeena, da komai da shawararta yake yi. Aiki gonarshi na bana ban san ko me ya samu ba, zakka da ya fitar ma ban san yadda ya fitar da ita ba, amma lokacin Maman Khalil na raye duk wadannan abubuwan da yake yin su. Ni kuma ina ta wahala a kanshi da yaranshi baya gani. Jin alamun shigowarshi ne ya sanya ni juya baya kamar ina bacci. Yadda na ji kamshin turarurrukan kwanciyarshi ya cika dakin, na tabbatar har ya yi wanka. Ina jin lokacin da ya sauka saman keken, ya hau gadona amma ban motsa ba. Without anything ya shiga shafa ni, na ji kamar in buge hannun, takaicinshi ya kara kama ni. Wannan dabi'ar tashi na masifar bata min rai, ta yadda bai dauki fushina a bakin komai ba, zai fahimci ina fushi, amma sai ya share kawai ya shiga harkokinshi, ga ni ni ba Sakeena ba, da ta iya danne abu, idan ban magantu ba; ban jin dadi. Shi ya yi kidanshi, na kuma ya yi rawarshi, hakan kuma bai sanya ya damu ba, Sai ma kawai ya shiga baccinshi, kamar a duniya babu abin da ke damunshi. Toilet na shiga hade da gyara jikina, na yi raka'a biyu hade da shafa'i da wutri, kafin na kwanta amma sai da na sanya Maama a tsakiyarmu, asubar fari kuma na shiga kitchen don yi wa su Khalil abinci breakfast da wanda za su tafi da shi school. Shi kuma ya je ya hada kansu suka tafi masallaci, bayan ya dawo daga masallacin baccinshi ya koma, ni kuma na shiga taya su Affan shiryawa, ga Maama ta tashi ita ma, duk na zama busy. Koda suka tafi ma ban huta ba, gyara kitchen Wanke-wanke, da gyaran gidan. Sai wajen 8:30am na kammala, sannan na zauna don yin break, bayan na gama kuma na shiga shirin zuwa asibiti. Gefen gadon na zauna bayan na shirya, ina jin wani zafi a zuciyata, da ace ina da kudi kawai zan yi tafiyata ne ba ma sai na tambaye shi, amma ko don kudin asibitin dole ya sani. Zaman nan na ba kwandalar da take shigo maka sosai yana damuna. A hankali ya bude idanunshi hade da zube su a kaina, fuska na kara hadewa, shi kuma ya lumshe idon a hankali kafin ya yi doguwar mika, cikin muryar bacci ya ce "Me ya faru?" "Asibiti nake son zuwa" na amsa murya a cunkushe. "Yin me?" "Ni dai ina son zuwa ne kawai" "To Allah Ya kiyaye hanya" ya yi maganar hade da gyara kwanciyarshi ya juya min baya. Tsawon 5mns bai juyo ba, kuma komai bai ce ba, yayin da zuciyata ke ta wani irin zafi, yana jiran in ce ya ba ni kudin zuwa asibiti. Ni kuma ba zan fadi hakan ba, tun da ya san ba ni da su ai. Mikewa na yi hade da saba Maama na nufi kofar fita "Yaran nan sun tafi school kuwa?" Ban amsa shi ba, na yi ficewata, zan zauna da yaran ne har tara basu tafi makaranta ba. Raina bace nake jefa kafata, har na isa family house dinsu, haka nan na ji Ina son barin gidan. Tun da na shiga gidan ake tambayata lafiya, ban cika zuwa da safe haka ba, ba ma sosai nake zuwa ba, to ko wane lokaci cikin aiki nake, babu hutu in gama wannan in fada wancan. Da lafiya ƙalau na rika amsa musu, har na shiga bangaren Inna, wanda aka zagaye da doguwar katanga, aka kuma buge shi da rufi mai kyau na zamani, ga interlock shimfide a farfajiyar wajen. Lokacin da na shiga wangalelen falon nata mai dauke da kujeru masu kyau ya sha tiles, sagale ta yi da kofin kokon hade da tambaya ta "Lafiya?" Maama na kwanto hade da dora ta saman kujera, ni kuma na dire kafafuna kasa ina gaishe ta, ta amsa cike da kulawa kafin ta ce "In ji dai lafiya?" Cikin murmushi na ce "Lafiya ƙalau fa Inna, kowa sai tambayata yake yi wai lafiya" "To ai dole, tun da ba a saba ganinki haka da sassafe ba, sannan ciwon nan na Abbansu Khalil kamar da iska, yau sauki gobe kuma sai godiyar Allah" Kadan na murmusa kafin na ce "Alhamdulillah, jiki ya bi da haka ai sai dai mu godewa Allah." "Haka ne kam" ta yi maganar hade turo min kular kosai tana fadin "Ga mutuminki nan, ya su Affan din har an tafi makarantar" "Sun tafi tun dazu" na amsa ina cin kosan, sosai ina son kosai "Wannan makaranta ai ta hana su rashin ji kullum aka tafi tun safe sai yamma, kuma babu Asabar ba Lahadi" "Wallahi fa, hutun kawai ranar Juma'a ne" "Ai kuma kin huta da bari-bari" Na yi murmushi ba tare da na ce komai ba. Ta kai kallon ta kan Maama da take bacci ta ce "ita wannan lafiya ko take?" "Lafiya kalau, muna kan hanyar zuwa nan ta yi bacci" "To madalla. Kin tabbatar dai ƙalau ko?" Cikin murmushi na ce lafiya ƙalau Inna, kawai na ga na gama aikina da wuri ne, shi ne na ce bari in zo nan in gaishe ku" "To madalla aiko kin kyauta." Haka muka shiga hira sosai, a hankali kuma falon ya rika cika da matan gidan, Sai na ji zuciyata ta yi sanyi, sun mantar da ni takaicin Bashir. Ban baro gidan ba sai da na yi sallahr magriba, na san dai na taro match Kuma ba ni da ƴan wasa. Lokacin da na isa gidan duk suna masallaci, kitchen na yi wa tsinke, saboda na san kaf rigimar tana a cikin kitchen din Wani kamshi mai dadi ya bugi hancina, da sauri n isa wurin tukunyar na bude, jalof din taliya ce ta sha kayan miya ga kifi ice fish manya-manya a ciki. Duk da na ci tuwo sai da yawuna ya tsinke, Bashir kam gwanin iya girki, amma ko ya aka yi ya yi yana zaune oho, duk da yana iya mikewa tsaye, tafiya ce dai bai iya wa. Kuma da alama suna kashe gas din suka tafi masallaci. Da kaina na tayar da injin, kafin na shiga wanka, ina fitowa na ji kiran sallahr isha'i, Sai kawai na yi sallahr, bayan na idar na saka wando baki wanda da kadan ya wuce gwiwata, na dora riga armless pink wacce ta tsaya daidai kwankwasona. Komai ban shafa ba, Sai humra. Falon na dawo inda Maama ta nutsu tana kallo cartoon kamar ta san abin da ake yi, ban zauna ba sai da na je kitchen din na zubo abinci na zuba kifi wajen yanka bakwai manya, sannan na dawo falon na zauna, ina ci ina ba Maama, ban fi spoon biyar ba suka shigo gidan, na yi fuska abuna, su Khalil dai murnar na dawo suke yi, ita kuma Maama murnar ganinsu take yi. Bashir kuma poster ya ajiye a kofar falon yana kallo na, ni kuma na ki yarda in kalle shi. Loma ta kawai nake yi hankali kwance. Keken ya murzo ya shigo tsakiyar falon sosai kafin ya ce "Lallai yarinyar nan ba ki da kunya, dole ki ƙi kallo na" Dariyar da nake ta dannewa ta kwace min, don haka na kai hannuna saman bakina ina yin ta a hankali "Lafiya zamu rabu Khadija" ya fada yana kokarin sauka daga Keken, Khalil da Affan suka taimaka mishi, kuma sune suka zubo abinci, ina jin Khalil na korafin duk babu kifin, na yi banza abuna kamar ba na falon. Bayan sun gama mu ka yi homework, na karbi hadda, kafin suka wuce dakinsu, zuwa lokacin tuni Maama ta yi bacci. Na dauka Bashir zai tambaye ni ina na je, amma bai yi hakan ba, abun da ya fi so kawai ya yi, ya baccinshi. Tun ina fushi da sanya ran zai tambaye ni ba'asi har na gaji na warware, na ci gaba da hidindumu na. A satin kuma Dr Nura ya zo, yadda suke ta kus-kus na san akan maganar siyar da gidan Abuja ne, yadda basu sanya ni ba, ni ma sai na yi gum abuna. Kwananshi daya ya juya, still a satin sai ga Mustapha (mijin Maman Hana) shi da wani Dr Jamil, su ma dai kus-kus dinsu suka gama, suka tafi, bayan na nemi tsarabar kauye na bayar a kaiwa Maman Hana. Sosai jikin Bashir ke sauki, saboda yanzu tafiya yake koya da crochet, Sai dai baya taka kafar dage ta sama yake yi, duk lokacin da yake koyan tafiyar sai in yi ta mamakin ikon Allah, dakyar yake yunkurawa minti 2-3 zai ce ya gaji. Har haki yake yi. Alamun da gaske ya gajin. A kullum dai ya kan yi hakan sau biyu, safe da kuma yamma. Wani lokacin kuma idan ya fita majalisar kofar gidanshi, abokan zaman majalisar kan kara sanya shi ya gwada yin tafiyar, koda ba ya so. Ni kam zuwa yanzu na fahimci da gaske ina da ciki, saboda har ya fara motsi, dadina daya bai sanya ni laulayi ba, haka bai taba Maama, kila Allah Ya tausaya min ne, yadda Maama ke da rigimar nan, ace kuma ciki ya taba ta ai na shige su, ban san da me zan ji ba. Ranar Asabar misalin karfe biyu na rana kwatsam sai ga Ummana da kanwata Yusrah, zuwansu ba karamin dadi ya yi min ba. Tun da suka zo nake hidima dasu, sosai mu ka sha hira, Sai biyar na yamma suka tafi, Bashir ya yi musu kyauta sosai, haka ma yan'uwanshi, ina jin dadin yadda yake girmama yan'uwana. Ni ce dai idan rashin kirkinshi ya motsa zai yi min shi sala-sala. Matar J✍🏻 [12/22, 21:14] 08080966571: *HASASHENA* *Page 24* Kasancewar yau juma'a su Khalil babu makaranta, hakan kuma bai sanya sun zauna a gida ba, suna gidan kakanninsu, ni kadai ce a gidan hatta Maama wata diyar Kawunta ta zo ta fita da ita. Zaune nake cikin falo na tasa turtsersen cikina a gaba, abubuwa da yawa ne suka bata min rai a wannan satin. Kuma na san kila haka zan gama fushina Bashir ci kanki ba zai ce min ba, iyaka ci dare ya yi ya zo ya biya bukatarshi ya juya min baya. Ki tausayina ma ba ya ji Abin da na fahimta kamar idan ina fushi to ya fi matsa min, kuma baya damuwa da ina performing Ko ba na yi. Abu na farko da ya bata min rai shi ne, jin labarin Bashir ya sayi fili a Katsina har yana gini amma ba. Sai dai na ji a gidansu da na je, da na kasa dannewa na yi mishi maganar, Sai ya yi min kallon shekeke, kafin ya ce "komai zan yi sai kin sani, abin da ya kamata ki sani din ba ina sanar da ke ba. Waye zai zauna a gidan ba ke ba. Ni fa ba na son tsokano tashin hankali" Haushin da ya ba ni ne, ya sa ban kara ce mishi komai ba. Abu na biyu kuma a kan yayen Maama ne, mutane sun damu in yaye ta, saboda sosai cikina ya yi girma, shi ne na sanar mishi, na ce idan babu damuwa zan kaiwa Ummata ita, ni kuma in ji da cikin da hidimar gida sai cewa ya yi wai yaronshi baya zuwa wani gida. Sosai maganar ta bata min rai da ba ni mamaki, wai yaronshi baya zuwa wani gida. Gidanmu ne wani gida "Mtswww!" na ja bayyanan ne tsoki, lokaci daya kuma Ina amsa sallamar da aka yi daga can gate. Ido na zubawa kofar falon, har zuwa lokacin da wasu mata biyu suka shigo, ɗayar dai gajeruwa ce, sanye cikin riga da zane na atamfa, ta yafa bakin mayafi, dayar kuma doguwa ce siriruwa, ita ma riga da zanen ne a jikinta amma hijab ta sanya. Dukkansu fuskokinsu dauke da irin zanen fuskar Bashir, Sai dai su na su a saman kumatu suke a kwakkwance guda uku, Sai kuma a, gefe kunne guda biyu. Kamshin turaren Safiyya ya cika falon, lokacin da suke kara doka min wata sallamar. Na kuma amsawa ina fadin "Ku shigo, sannunku da zuwa" "Yauwa" suka amsa a tare, hade da neman wuri a falon suka zauna. Muka gaisa cike da girmamawa kafin doguwar ta ce "Bashir din ma baya nan ko?" "Eh wlh, suna Batsari" "Allah sarki, idan ya zo kin fada mishi, su Saratu sun zo duba shi da jiki" "In Sha Allah zan fada mishi" Mu ka danyi shiru kafin gajeruwar ta ce "Ai kafar da sauki ko?" "Ah! Alhamdulillah Gaskiya, tun da yanzu yana taka da kanshi" Na ba ta amsa "To Ma Sha Allah, Allah Ya kara lafiya" cewar doguwar "Amin Ya Rabbb" na amsa "Yaran ma duk basu ko?" cewar gajeruwar "Eh. Duk sun fita" na kuma amsawa. Doguwar ta mike tana fadin "Bari mu je, a yi mishi sannu idan ya dawo" "In Sha Allah" Ni ma na mike da zummar taka musu. Bayan na dawo sai kawai na shiga tattare dakinsu Khalil na gyara, saboda idan ba ni ce na gyara ba, su kam ba za su gyara ba, na yi fadan har na gaji. Idan ina yi ma sai Babansu ya ce wai ba aikinsu ba ne, a kan me zan rika sanya su aikin mata. Daga Bashir har su Khalil sai da aka yi sallar isha'i suka shigo gidan, na yi mishi sannu da zuwa hade da kawo mishi abinci, ina son yi mishi maganar Maama wata kuma zuciyar na hana ni, saboda har zuwa lokacin ba a maido ta ba. Yana cin abinci ne na ce "Wata wai Saratu ta zo duba ka da kafa" Dakatawa ya yi da cin abinci alamun nazari kafin ya ce "Saratu kuma, ya take?" Zamana na gyara kafin na ce "Ai a cikin su biyun ban san wacece Saratun ba, akwai dai wata doguwa siriruwa, Sai kuma wata gajera, tana da ɗan haske haka" "Ta kai ki haske?" Hannayena na kalla, ai ba ita ba ko Maman Khalil na fi ta haske, amma sai na ce "To ban dai sani ba kam" "Suna da zane a kan kumatunsu?" ya kuma tambaya "Eh" "OK, na gane ta, Sarai ce." Har 9pm babu Maama, kuma Bashir ko ya tambaya, da ace su Khalil ne bai gani ba, da yanzu ya tambaye ni, fiye da ashirin. An jima kadan "Ina yaran nan ne?" zuwa can ya kuma cewa "Wai ina yaran nan suka tafi?" Haka zai dosa ya ga sun dawo. Na kasa daurewa na ce "Wai Abban Khalil, ba ka ga babu Maama ba?" "Eh na gani" "Kuma shi ne ba za ka tambayi ina take ba?" Komai bai ce min ba, abun da ya kara sanya raina ya kuma baci, na ce "Da ace ba ita ce ba ka gani ba, da tuni ka cika min kunne da tambaya" "Dukkansu dai yarana ne" "Amma akwai na so ai" "Wannan kuma ke ce kika fada" "Saboda hakan ne" na kuma fada zuciyata na kuna. Komai bai ce min ba, cikin bacin rai na ce "Bashir don Allah kar ka sanya kiyayya a tsakanina da yaran can, komai da zuciya daya nake yi musu, ina son su tamkar ni haife su ka amma kai kullum sai ka ta yin abin da za ka sanya kiyayya a tsakaninmu" "Me na yi?" cikin halin ko in kula ya yi tambayar Haushinshi ya kara kama ni, na ce "Ba ka san me ka yi ba ma? Kiri-kiri fa kake nuna kamar ina cutar yaran nan, komai na yi sai ka tuhume ni. Sannan fifitasu kake yi a kan Maama, na ga kuma dai duk yaranka ne, ko don ita mace ce?" Tun da na fara maganar yake min wani irin kallo, kallon da bai sanya ni yin shiru ba, na dade ina rike wannan abun a zuciyata, kullum yana damuna " Khadija! Za ki fara ko? Kar ki sake ki kawo min wannan abun a cikin gida, Maama da su Affan duk yarana ne, kuma Ina son abu na, babu wani wanda ba na so. Kar ki kara kawo min irin wannan zancen" "Eh tabbas yaranka ne, amma yadda ka fi son mahaifiyar sauran haka ka fi ƴaƴanta, ni dama tun can zaman hak'uri nake yi ai." Kallona yake yi kamar ya samu tv, Sai kuma ya mike hade da daukar kafafun karfenshi ya wuce dakina. Takaicinshi ya kara cika min zuciya. Saman kujera na zauna ina ta kokarin hana idanuna kuka, lokaci daya kuma Ina jin kamar maganganun da na yi basu dace ba. Haka nake wasu lokutan sai na yi abu, in ji kamar ban kyauta ba. Waya da ke yashe a kasa na dauka, na kira layin Inna. Muka gaisa sannan na ce "Kubra ta zo ta dauki Maama, kuma na ji su shiru har yanzu" Daga can Inna ta ce "Yo shi mijin naki bai fada miki za a yaye Maama din ba? Ai tana nan wurina, dazu ma ya kawo mata kayan yaye" Bakina a bude nake sauraron maganar Inna, bayan ta dire maganar ne na ce "Eh mun yi maganar kam, ban yi tunanin yau ba ne" "Aiko dazu gab magriba ya shigo ya ganta a nan, Sai ya ce kawai a bar ta a nan din" Na shiga jinjina kai kamar Inna na gani na, kafin na ce "To shi kenan ai, Allah Ya tashe mu lafiya" "Amin" ta amsa hade da yanke kiran. Wayar na sauke hade da matse ta a hannuna, zuciyata na kara baci ta yadda Bashir ke aiwatar da abu kai tsaye ni ban isa in sani ba, wanda na san ba haka yake yi da matarshi. Da yawan lokuta ma ita ce take yanke hukunci ya bi. Na juya a hankali zuwa dakin, yana kwance saman gado daga shi sai boxer wayarshi a hannunshi Gefen gadon na zauna ina kallon shi, cike da bacin rai na ce "Bashir abun kan nan ya ishe ni gaskiya. Wlh Sam ba ka yi min adalci. Ta ya ina matarka komin ka sai dai in ji a fulanin talla, ka siyar da gida, ka sayi fili ka fara gini, duk ban san ko daya ba, bayan ba haka kake yi wa matarka ba, komai tare kuke da shawarar juna, amma ni ka ajiye ni a gefe, kawai in yi ma rainon yara ka biya bukatarka, ko shawarar na kawo ba ka amsa"na karasa maganar cikin kuka, saboda raina ya kai kololuwa wurin baci Wayar ya ajiye kasan filo hade da janyo ni jikinshi yana fadin "Yanzu ma bari in biya bukatar tawa"na shiga kiciniyar kwace kaina amma na kasa, to ina ma zan iya ga tsohon ciki. Sai bayan da ya yi abin da ya yi niyya ne sannan ya ce" Da kin san yadda kike tayar min da hankali idan kina fushi da kin daina yi. Ko ban yi niyyar kusantarki ba, idan kina fushi sai in ji Ina son hakan" Komai ban ce ba, na mike zuwa toilet, raina a bace Haka na fito ina ta tura baki, na kwanta gefen shi, a cikin kunne ya ce min "Wani fushin kike yi?" Banza na yi mishi, birkitoni ya yi, yana fadin "Fushin kike yi kenan, bari in sauke shi" Dole na ce "Ni ba fushi nake yi ba" Sautin dariyarshi ya fita, a hankali ya ce "Da kin ce ba kya ji" Kamar kullum asubar fari na tashi, don yi wa su Khalil abincin tafiya makaranta, misalin 7am direbansu ya zo. Bayan sun tafi kuma na shiga gyaran gida Sai misalin 9am na goma, komai na gidan ya yi fes, kamshi mai dadi na fita kasancewar sanyi na shigowa hakan sai ya karawa yanayin dadi. Zaune nake ina karyawa ya fito sanye cikin kananan kaya, wannan ya tabbatar min har ya yi wanka. Crochet din ya ajiye bayan ya zauna sannan ya ce "Ina abincina, ko har yanzu fushin kike yi?" Harara na aika mishi hade da mikewa zuwa kitchen na hado mishi komai a kan babban tire na kawo mishi. "Ina kwana" ya fada daidai lokacin da nake hada mishi tea Maimakon in amsa sai na tura mishi baki Murmushi ya yi kafin ya ce "Khadija tawa, rigima iya rigima, idan ba ni ba, Khadija waye zai iya da ke" Komai ban ce ba, shi kuma ya shiga shan tea din a nutse kafin ya ce "Kar su Rahma su iso, ki ce ban fada miki ba, suna hanya, a yi abinci da su" Kamar in ce ban yi, sai kuma na yi shiru ban ce komai ba. Abincinshi ya ci gaba da ci kafin ya ce "Idan ban da rigima irin ta ki, me ye abun haushi don maigida ya yanke hukunci a gidanshi" Yanzu din ma ban ce komai ba, shi ne ya kuma cewa "Na siyar da gidan Abuja ne, saboda ba zan iya ci gaba da zama a can ba, Abujar ma gabadaya ta fita kaina. Abin da ya sa ban fada miki ina gini a Katsina ba, just I want surprise you. Ga shi an bata min surprise din" Yanzu kam na kalle shi cikin ido, girarshi ya tattare a goshinshi kafin ya ce "Shi kenan ko matar ɗan gurgu" Na murmusa kadan, saboda duk lokacin da zai ce min matar gurgu, yana ba ni dariya. Hannuna daya ya saka cikin nashi kafin ya ce "Ina sonki Khadija, ki, yarda da wannan, ban taba yin abin da zai bata ranki ba. Ki bi a hankali za ki je inda Sakeena ta je kila ma ki wuce. Za ki zama wuya da za ki rika juya kan duk inda kike so. Just be patient" Shirun nan dai ita na yi, ya kuma cewa "Idan za ki ci gaba da fushin ne kuma, in rage kayan jikina" Silent murmushi na yi, hade da matsawa gefe kadan, don na san zai iya tsikari na. Ganin haka ya yunkuro kamar zai tsikare nin, da sauri na zabura ina dariya sosai. "Ki duba abin da kike bukata wajen girki sai ki yi magana a kawo miki" "Tam" na amsa a hankali kafin mu ka ci gaba da hira, kamar ba ni ce nake ta kumburi ba. Matar J ✍🏻 [12/22, 21:17] 08080966571: *HASASHENA* *Page 25* Tun bayan fitar Bashir na shiga aikin abinci, idan da sabo dama na saba, idan na kwanta to dare ne, da rana hutun daga 1pm ne zuwa 4,shi ma wani lokacin Maama ba ta bari na in huta din, ko ina kwanciya Bashir zai fara kirkiro min aiki, kamar yana gaba da ganina a kwance. Alalar gwangwani na yi wa Rahma, tana sonta sosai, misalin karfe daya na gama, Sai na bar tukunyar a kan murhu don kar ta huce, kasancewar da itace na yi amfani. Su Affan rice and stew na yi musu, dukkansu sun tsani alale har Baban nasu ma. Karfe biyu da rabi na samu na kammala komai har da gyaran gidan, da kuma wanka, a lokacin ne kuma na samu na yi azhur, zuwa lokacin kam na gaji likis, kamar wacce aka yi wa duka, abincin ma ji nake kamar in ci daga kwance. Haka nan dai na daure na mike zuwa falon bayan na zira doguwar riga mara nauyi, kicibus muka yi da Bashir yana shigowa "Ɗangurguna!" na yi maganar cikin tsokana Shi ma cikin tsokanar ya ce "Matar Ɗangurgu, kina fushi ne in zo in sauke miki shi" Cikin dariya na ce" a'a ba na yi" "Amma kin yi kyau ai, bari in zo in biya kudin kwalliya" "Ai ban yi kwalliyar ba ma, bare ka biya kudinta" "Guduna fa kike yi Khadija" cikin alamun mamaki ya yi maganar "Ba dole ba" Duk muka yi dariya, lokaci daya kuma Ina ajiye mishi abincin da na zuba a gaban shi. Sai da ya fara ci sannan ya ce "Rahma fa za ta kawo miki kayanki ne, saboda wadanda suka sayi gidan suna son shiga" Shiru na yi, yayin da fuskata ta canja alamun rashin jin dadi. Kila ya lura da hakan ne shi ya sa ya ce "Ki yi addu'a, Sha Allah za a samu sama da shi" "Allah Ya amince" "Amin" ya amsa, ni kuma na ce "Kana nan dai ba za ka canja ba, yanzu ace kayan nawa za a kwaso daga Abuja zuwa nan shi ne ba za ka fada min ba. Sai bayan da suka shigo hanya, Allah Ya kyauta" "Amin" ya kuma amsawa, kafin ya ce "Ke ma kina nan, ba za ki yi canja komai sai kin yi korafi" Murmushi na yi ina ci gaba da cin alaleta, Rahma ba ta iso ba sai 5pm,ba sai an tambayi gajiya ba kam, ta gaji kam, ta yi likis kamar fulawar bredi, ni kaina naga kokarinta Isowarta ba da jimawa ba, su Khalil suka dawo, take gidan ya rude da ihun da ganinta, suna tambayarta su Farhan. Bayan sun natsa ne ta ce "Yaran nan sun yi girma sosai wlh, ko don ba na ganinsu" "Ba mamaki, ni dai nan yadda na sansu haka nake ganinsu" "Gaskiya sun yi girma, tun ba Khalil ba" "Sai dai rashin ji ai" na fada ina dariya "To ai shi ne ke sanya su girman." Duk mu ka yi dariya. Sai da suka dawo sallahr isha'i sannan suka ci abinci, bayan nan na karbi haddarsu, daga nan kuma na ce aje a kwanta saboda gobe. Bayan tafiyarsu ne Rahma ta ce "Ma Sha Allah! Da alama makarantarsu Khalil ana karatu, kin ga Affan yadda ya dage, da kuwa ba ya son Islamiya" "Gaskiya babu laifi, ana karatu, kin ga da shigarsu makarantar dai ina jin sun hada hizif biyar" "Gaskiya kam akwai karatu, duka yaushe aka fara karatun" "Ba jimawa kam, tun da har sun fara 2nd C.A" Zamanta ta gyara sosai kafin ta ce "Allah Ya saka miki da mafificin alkairi Khadija, kin rike amanar yaran nan, Allah Ya biya ki da gidan aljanna, ya kuma jikan kawata" "Amin" na amsa kafin na ce "Ni Sakeena ba ta yi min komai ba sai alkairi wlh, idan ma ta yi min ban sani ba na yafe mata. Kishiya irin Sakeena abun so ce ga ko wace mace. Har gobe ina jin kewarta, bayan mahaifina ita ce ta biyu da zan iya cewa a dawo min da ita duniya da ana yin hakan. Mutuniyar kirki ce. Koda ba na tare da Bashir, to tabbas zan yi wa su Khalil abun da uwa ke yi wa ƴaƴanta. Ina sonsu, ba son ganin ido ba" Numfashi ta sauke a hankali kafin ta ce "Tabbas Sakeena mutum ce har da rabi, kawata ce but she's like sister to me, tana yi min abin yan'uwana ba su yi min. Har in mutu ba zan sake kawa kamar Sakeena ba." "Gulma ta kuke yi ko?" Duk muka juya kan kofar shigowa falo muna murmushi, shi ma ya karasa shigowa yana fadin "Ai halinku ne mata, da kun ci kun koshi, Sai ku fara gulma mazajenku" A tare mu ka yi dariya da Rahma, kafin suka shiga gaisawa yana yi mata sannu da hanya, saboda lokacin da ta iso yana Batsari. Bayan na ba shi abinci na basu wuri, saboda yanzu a wajen shawara Rahma ita ta haye kujerar Maman Khalil, idan ba ita ba mijinta, Sai ko Inna. Abin da na fahimta bayanin kayan Sakeena take yi mishi, ashe gidansu Sakeenar aka kai kayan, shi ya ce ba ya son ganin komai hankalinshi tashi zai yi Sai wajen 10pm sannan Ja'afar kanen Sakeena ya zo ya dauke ta zuwa gidansu Sakeenar. Washegari sai wajen goma ta leko, muka gaisa sama-sama sannan ta wuce family house nasu Bashir. Ni kuma ta turo min yan matan gidan, suka muka shiga gyaran gida, saboda kayan dakina nake son mayarwa na gaji da zama daki babu kujeru, Sai kwanciya a kan katifa Ranar kam ba karamin aiki muka sha ba, komai bai koma normal ba sai wajen karfe biyar na yamma, amma fa sosai part din nawa ya yi kyau, shi kanshi Bashir da ya shigo sai cewa ya yi "Lallai gyara shi ne gida." Kowa ya zo kam sai ya yi sha'awa ya yaba, amma fa ranar hadda da homework din su Khalil Sai dai Babansu ya yi musu. Ni kam ina idar da sallahr isha'i sai bacci. Ko Rahma ta dawo gidan ma ban sani ba. Misalin karfe biyu na dare wani matsanancin ciwon mara ya tashe ni, tun ina jin abun da wasa, har na kasa jurewa na tashi Bashir, daga ni har shi ba mu kawo haihuwa ba, ni na fi ganinta a irin juyin nan da ake cewa. Zuwa karfe hudu kam na jigata, ga wani ruwa da yake zubo min. Yau ne na tantance haihuwa, saboda haihuwar fari ban san ya aka yi na yi ta ba, Sai dai na farka na ganni da Baby. Amma yau kam na gane Allah da girma yake. Ban san ya aka yi ba, ni dai na ji murya Aunty Habi da Yaya Murja suna yi min sannu. Lokaci daya kuma suka kama ni zuwa waje. Ban san waye yake tukin ba. Ba na iya tantance komai sai azabar ciwa. Ana dora ni saman gado yaro na fadowa, Sai a lokacin ne na ji lummm, jikina ya mutu lubus, sama-sama nake jin su Aunty Habi da nurse din suna cewa yaron bakwaini ne. Oho ni dai idan ma shidaini ne tun da ya fito sai a yi min barka. Ban san haka haihuwa take ba sai yau, azaba, iya azaba wayyo Allahna. Kai Allah Ya jikan iyaye mata. Amma haihuwa kam ba ta da mahadi a duk ciwurwukan duniya. Ita kadai ce. Idan ka dauke rashin karfin jiki ba na jin komai, zuwa 5:30am an, gyare min jikina fes, taro kuma yana wani dakin daban a cikin wata kwalba. 6am asibiti ya fara cika da mutane, kun san kauye da kara, duk da babu tafiyar kirki tsakanin Batsari da Ruman amma yadda suke zuwa tawaga-tawaga yana ba ni mamaki. Rahma ma da ta zo mamaki ta yi sosai na jin wai na haihu, a kai ta cewa aikin da na yi jiya ne. Daga asibitin Rahma ta wuce. Mu kam zaman asibiti ai sai ya kama mu, saboda yaron, ni dai lafiyata ƙalau. Yaron ne dai kam dan firit, don ma yana samun kulawar likitoci, amma wani lokacin idan na zo na ba shi nono, Sai in ga kamar ba zan sake dawowa in same shi da rai ba. Ba ni kadai ba, duk wanda ya samu damar ganinshi sai ya yi jimamin anya kuwa zai rayu. A haka dai aka yi mishi huduba da Abubakar Siddiq, muna kiranshi da Assidiq. Samira da Badiyya duk sun zo duba ni, haka ƴan'uwana mota biyu suka yi, da kayan gararsu, bayan an sauke kayan garar kuma suka nufo asibiti. To ai babu maganar taron suna. Iyayen Sakeenar ba a bar su a baya ba, saboda duk abin uwa ke wa Ƴa shi Mahaifiyar Sakeena ke yi min, haka ma mahaifinta, ni ma ina kyautata musu da abin da nake da. Wasa-wasa sai da mu ka yi sati biyar a asibiti sannan aka sallame mu, zuwa lokacin babu laifi ya yi girma, kuma siffarshi ta koma ta cikakke jariri, abin da duk ba mu yi zato ba. A karo na uku Saratu ta zo duba ni a gida, saboda zuwanta biyu muna asibiti, yanzu kuma da muka dawo gida sai ga ta har da kayan jarirai masu kyau babu laifi. Bayan ta tafi ne na kalli Shafa'atu tare da fadin "Wai wacece wannan? Ya kuke da ita?" Wata irin dariya Shafa'atu ta yi kafin ta ce "Ni ba za a ji mutuwar sarki a bakina ba" Jamila da Lawisa suka yi dariya irin shakiyancin nan, yayin da ni kuma na ci gaba da magiya a kan su fada min wacece ita. Fir suka ƙi faɗa min, amma the way yadda seke manna min hauka, jikina bai ba ni ba, shi ya sa na aje mata bayar tambaya, na kuma kudiri niyyar canja mata, hade da taka mata burki a kan zuwa gidana. Duk da na yi hutun makaranta, to su fa su Khalil suna zuwa, Sai dai yanzu suna tafiya karfe biyu ne a tashi shidda, sabanin baya da suke tafiya tun safe. Kuma yanzu haka suna hutun 2nd term ne, kenan term daya ya rage musu su tafi js1. Bangaren karatun Kur'ani kam, suna da wajen hizif arba'in. Fatan da nike yi su sauke kafin su gama makarantar, ko basu yi hadda ba, hakan ma ya wadatar. Misalin karfe takwas na dare Abban Khalil ya shigo, kamar kullum "Ina yaran nan?" shi ne abin da ya fara tambaya "Suna cikin gida" na ba shi amsa, saboda yanzu tun da suka ga Maama na can kuma an yi hutu, su ma sai suka tare a can din. Sai da na bari ya gama cin abinci, muna ta hira, sannan na sako abin ds ke damuna "Wai Abbansu Khalil wacece Saratu?" "Me ya faru?" ya tambaye ni, cikin rashin ba wa zancen nawa muhimmanci. "Nothing, kawai ina son sanin yadda kuke ne, dazu ta kawo ma Assidiq kaya" Ido ya waro alamun mamaki kafin ya ce "Da gaske, mu gan su" Assidiq na ajiye saman kujera, hade da shiga dakin na dakko mishi kayan na kawo mishi. Ya shiga budasu yana yabawa, har yabon ya fi kayan yawa. Wannan ya sa na tabbatar da abin da nake zargi. Don haka na ce "Yarinyar nan sonka take yi ko?" na tambaya kai tsaye Maimakon ya amsa min sai ya yi dariya mai da sauti, hade da ajiye kayan a kan kujera. Ku san halina da kishi, don haka take ya taso min na ce "ka mayar mata da kayanta ni ba na so. Sannan ka fada mata, wlh kar kafarta ta kara takowa gidan nan" "Sannu maigida" ya yi maganar hankalinshi a kan kiran da yake shigowa wayarshi. Yadda ya yi receiving called din ya fahimtar min da masu aikin gidanshi a Katsina yake magana, kuma da alama aiki ya yi nisa, na ji ana zancen fenti. Bayan ya dire wayar ne ya ce "Ko kina da zabin kalar fentin da kike so?" "Ba ni da shi" na amsa, duk da kuwa ina da zabin "To shi kenan" ya mike hade da jan kafarshi zuwa bedroom, saboda yanzu yana iya tafiya ko ba crochet, amma fa da alama kafar ta tsaya a haka. Ba za ta taku ba, irin da. Na gama cika da batsewa ta, na bi shi zuwa bedroom din, na kwanta hade da sanya Assidiq a tsakiyarmu, ina addu'ar Allah Ya sa kar ya ce zai taba ni, cikin ikon Allah kuma bai yi hakan ba. Matar J ✍🏻 [12/22, 21:19] 08080966571: *HASASHENA* *Page 26* Safiyar Monday 8am Bashir ya tashi daga bacci, abun da ya ba ni mamaki sosai musamman lokacin da na zo na same shirye tsab cikin manyan kaya. Cike da mamaki na kalle shi, kamar zan yi magana sai kuma na fasa na ce "Dama zan kai Assidiq rigakafi ne?" Hankalinshi a kan laptop din gabanshi ya ce "Break dina fa?" "a kawo ma nan ne ko, a bar shi a dinning din?" "Bar shi a can" "Ok" na fada hade da juya da zummar fita "Khadija!" ya kira sunana Wannan ya sa na juyo duk da ban amsa ba "Zan fara zuwa aiki yau" "Ma Sha Allah! Wannan ai labari ne mai dadin ji. Allah Ya sa aje lafiya a kuma dawo lafiya, Ya kara ba ka lafiya" "Amin Ya Rabbb, na gode sosai" Komai ban ce ba, na kuma juyawa da zummar fita ya ce "Zo nan mana" Ba musu na dawo baya, hade da tsayawa ina kallon shi. Hannuna ya janyo har ya zaunar da ni kusa da shi kafin ya ce "Sarkin fushi. Menene kuma yanzu" Na danne yadda nake ji na ce "babu komai, ba fushi nake yi ba" "Na ji" ya fada lokaci daya kuma yana plying wani video. Na ranar sunan Ramla ne, Maman Khalil sanye cikin lace purple, ta yi mugun kyau, sosai sai murmushi take yi, hannunta rungume da Ramla, ya jima yana kallon videon kafin ya danna pause hade da sauke ajiyar zuciya ya ce "idan na tafi ina sai ranar Alhamis ko Friday" Duk da na ji ba dadi amma ban nuna ba, na ce "Allah Ya kai mu" "Amin."ya amsa Jin bai kara cewa komai ya sanya ni mikewa" Ki duba kitchen din, idan akwai abin da kuke bukata let me know " " Ok"na amsa shi. Kai tsaye kuma na fita zuwa kitchen din, zuciyata na min babu dadi, saboda na san ba yau ne aka shirya komawarshi aikin ba, yau dai din ne ni na sani. Na dawo mishi da abubuwan da muke bukata a rubuce, bayan ya gama dubawa ya ce "Shi kenan Sagir zai kawo miki" "To mun gode" Daki na koma hade da karasa shirina na zuwa asibiti, na saba Assidiq sama kafadata, ina rufe kofar bedroom na ji fitowarshi. Wannan ya sa muka hadu a falo, hannunshi rike da karamar jaka. Yadda yake shagida kafar sai na ga kamar jakar ta yi mishi nauyi, shi ya sa na mika hannu na karba ina fadin "Har ka yi break din" "Kunun kawai na sha. Ya isa haka" Tare muka jera har zuwa wurin da aka wanke mishi motarshi tas, ta fito kamar sabuwa,. "Shiga sai in ajiye ki a asibitin" A, hanya muke taba hira, a nan ne ma yake shaida min ya nemi transfer zuwa Katsina. Na yi mishi fatan alkairi. A kofar asibitin ya ajiye ni, ya juya ya wuce, ban wani jima sosai ba, aka yi wa Assidiq allurar na taho gida Kai tsaye kuma na wuce family house din su Bashir. Sashen Murja na fara shiga, saboda muna ɗasawa da ita. Da Maama na fara cin karo, ta rugo da gudu hade da makale ni tana fadin "Oyoyo Auntynmu" haka take kirana ita ma. Na ɗan daga ta sama, kasancewar akwai Assidiq a bayana sai na dire ta, lokaci daya kuma muka shiga dakin Murja. Kwance take saman kujera 3sitter da waya a hannunta Cikin tabe baki na ce "ana sana'ar ne" Murmushi ta yi hade da mikewa zaune tana fadin "Ki bari kawai, wani novel na samu mai shege zaƙi" "Haka dai, daga Monday har sati" na ba ta amsa ina zama kusa da ita "Daga ina kike?" "Asibiti, Assidiq na kai allura" "Ki ce yau akwai kuka" "Ki bari fa, ga shi Babansu ba ya nan, bare ya taya ni rarrashi." "Har ya fara zuwa aikin ne?" Kai na daga a hankali, kafin na ce "gulma na zo mu yi" Cikin dariya ta ce "Ina jin ki" "Don Allah wai wacece Saratun nan ne? Na ga ranar can kuna ta raina min hankali. Amma yanzu na fahimci akwai wani abu tsakaninta da Abban yaran nan" "To ba dai ruwanki, na ki ido" ta yi min maganar da alamun kashedi "Dama ni ina ruwana, ni fa so nake kawai ki fada min wacece ita" "Auho! Bazawara ce, mijinta ya rasu bai dai yi shekara da mutuwa ba" Cike da mamaki nake kallon Murja, mijin nata bai yi shekara da mutuwa ba, amma har ta fara barbarar wani. Kodayake Ai duk ɗaya ita Abbansu Khalil din. Mun jima muna hira, kafin na shiga part din Inna. "Tun dazu Maama ta fada min kin shigo, kuma sai na ji ki shiru" cewar Inna bayan ta amsa sallamata Assidiq na sauke, a lokacin da nake kokarin zama saman kujera sannan na ce "Na shiga Sashen Maman Abida ne" "Shi ya sa" Cike da girmamawa na gaishe ta, sannan mu ka shiga labarin duniya. Da kaina na shiga kitchen na girka mana abinci, har da wanda zan diba zuwa gida Assidiq kam sai karfe daya allura ta fara tabashi, inda Allah Ya taimake ni na gama abinci, kuma gida da yawa wannan ya dauka wannan ya dauka, Sai 4pm aka samu ya yi bacci. Ni ma na samu damar yin sallahr la'asar. Muryar da na ji tana rangaɗa sallama ba karamin kayar min da gaba ta yi ba. Na yi tsum ina tambayar kaina, me ya kawo ta gidan kuma, tun yaushe take zuwa? Juyowa na yi sosai, wannan ya ba kwayoyin idanmu damar haduwa, yau kuma sanye take da riga da zane na atamfa, ta saka madaidaicin hijab. Kasa ta tsugunna, suka shiga gaisawa da Inna wacce take goye da Assidiq. Kafin daga bisani ni ma ta miƙo min gaisuwar na amsa ba yabo ba fallasa. Sannan ta shiga kiran Maama wacce ke zaune saman kujera ta na cin abinci, amma mirsisi ta ƙi zuwa ko ta amsa ta. Kamar ma ba da ita take ba. Omo da subalai ta ajiye Inna, sannan ta mike tana fadin "Dama zuwa na yi in gaishe ku" "To an gode Allah Ya saka da alkairi, ki gaishe da Innar taku" Ta amsa da to hade da ficewa daga dakin zuwa tsakar gida. Idanuna na janye daga kanta hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya. A raina na ce "Iska na wahalar da mai kayan kara" Saboda a jikina nake jin Bashir ya wuce da ajin Sarai, irin yaran nan ne girman talla, da alama ba ta yi karatu mai tsawo ba. "Ki tashi kar yaran nan su dawo kina nan" Inna ta katse min tunanina Na mike daga zaunen da nake, kafin in yi magana ta kuma cewa "Ki bar Assidiq din a nan, idan ya tashi a kawo miki shi, tun da an samu ya yi bacci" Sosai na ji dadin maganar, saboda dama Ina ta jimamin yadda za mu kaya idan an tashe shi Maama kuma ta kafe sai ta bi ni, na fito hannunta cikin nawa, daya hannun kuma rike da foodflask. A tsakar gidan na hadu da Murja, ta ce "Wai har za ki tafi, na dauka na za a kawo su Affan din" "Ai ban fadawa mai mashin din su ya kawo su nan ba." "Sai ki ga mutuniyar ki" Wani abu ya daki kirjina kafin na ce "Dama tana zuwa ne?" "Wannan shi ne zuwanta na uku ina jin dai" Gabana ya kuma faduwa tsoro ya kama ni, amma ban nuna a fuska ba na ce "Hu'umm" "Sosai son yayanmu take yi, idan da alkairi Allah Ya tabbatar" Sai na kasa cewa amin, Sai yake da na yi hade da nufar kofa ina fadin "Idan kin samu lokaci ki zo ki sanya min salataf zan yi kunshi" "To" ta amsa min, kafin in yi magana kuma kiran Abbansu Khalil ya shigo wannan ya sa na daga Bayan ya amsa sallama ta ya ce "Har yanzu kina fushin ne, na ji ba ki kira ni ba, ko irin ya hanyar nan" "Kai din ma ai ba ka kira ba" "Ni aiki ne ya min yawa, kin san sabon wuri" "Ni kuma Assidiq ne ya rufa ni da kuka" "Amma ya yi shiru ai" "to ga shi nan dai bacci yake yi. Yanzu na hadu da bazawararka" duk yadda na so in rike abun na kasa "Wacece?" ya tambaye ni "Kenan suna da yawa?" ni ma na tambaye shi cike da kishi Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce "Khadija tawa" Kiran na yanke cike da jin zafi, wai haka mutum yake ji idan ya ga mijinshi na neman wata. Kqi akwai zafi gaskiya. Ji nake komai babu dadi. A haka na karasa gida. Maama na fara yi ma wanka, na canja mata kaya zuwa doguwar rigar atamfa dinkin yara mai kyau. Sosai ta yi kyau, musamman kitson kanta ya kara fito da ita, yadda take ta tsalle-tsallenta sai ta koma min Ramla. Na yi ta kallonta zuciyata na kara min babu dadi Misalin karfe shidda su Khalil suka dawo, su ma wankan na sanya suka yi, hade da canja kaya sannan suka wuce masallaci, daidai lokacin kuma aka shigo min da Assidiq ya sha kukanshi ya yi gwaɓe-gwaɓe. Dole na yi zaman ba shi nono, sannan na lallabashi na kwantar na yi sallahr magriba. Sallahr isha'i kam sai da su Khalil suka dawo masallaci, suka rike min shi sannan na samu na yi ta. Haka muka rika karba-karba har 10pm Sannan ya yi bacci, su ma suka kwanta. Ramla kam dama tuni ta yi bacci. Sai da na gama shirin kwanciyata tsab, sannan na kira Bashir "Ba ki yi bacci ba?" abin da ya fara tambaya ta kenan "Kewarka ta hana ni" na ba shi amsa "Kuma da ina nan kin iya saka Assidiq a tsakiyarmu ai" Dariya mai dan sauti na yi kafin na ce tsoro nake ji. "Shi ya sa na yi nesa da ke ai, saboda ba zan iya hak'uri ba, kuma na ce ki yi planning kin ƙi yi" "Zan yi" "Ya kamata, don ba zan iya ba, in fada miki gaskiya." Na kuma yin murmushi kafin na ce "na ga bazawararka yau" haka kawai na ji na kasa rike maganar "Wacce?" ya tambaya "Kenan suna da yawa?" ni ma na jefa mishi tambaya. Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce "Khadija tawa" Na haɗiye wani abu mai daci sannan na ce "Don Allah ina son zuwa gida, a wannan karon dai ka duba min don Allah." na karashe maganar kamar zan yi kuka. Saboda rabona da in je gidan tun kafin su yi accident, sama da shekara daya kenan, saboda ko yanzu Khalil watanshi hudu. "Zan duba, kin san ba na son a bar yaran nan" Shiru na yi komai ban ce ba, saboda kullum abin da yake fada kenan, bai so a bar yara. Yaran da gasu nan a tsakiyar dangi. Kila ni na daina zuwa unguwa saboda su. "Na gode" na amsa hade da sauke ajiyar zuciya "Take care!" "Thank you!" na fada hade da lumshe idanuna, saboda yadda ya yi maganar Ajiye wayar na yi batun Sarai na dawo min cikin kai, ban san haka mata ke ji ba, idan alamu suka nuna mijinsu na shinshinar wata mace, ko ita macen na shinshinarshi. Abu kamar wasa sai na kasa bacci, har 12am,idanuna biyu, comparing kaina da Sarai kawai nake yi, ta ko wane fanni na yi mata fintinkau, amma lamarinta ya dame ni, kodayake an ce kishiya ba ta da kadan. Bacci ba shirin daukata Assidiq ya farka, don haka muka dosa har 2am,sannan na samu ya yi bacci, ni ma na samu baccin ya dauke ni. Safe kuma na dora hidimar gida, daga wannan sai wannan babu wani hutu. Wannan abu sosai yake damuna. Ranar Alhamis da yamma sai ga Bashir kwatsam, saboda bai fada min zai zo ba. Inda Allah Ya taimake ni, komai nawa tsab, amma yana zuwa da batun Maama ya fara ko zama bai yi ba "Har yanzu ba ki mayar da Maama ba?" ya yi tambayar da alamun bacin rai. Na danne nawa bacin ran na ce "Ita da kanta ta zo" Wani kallo ya yi min kafin ya ce "Tun daga can gidan take zuwa nan ita kadai" "To zan yi karya ne, ka gwada tasa ta gaba ka sha mamaki" "Na san halin ki ai, za ki iya zuwa ki dakko ta" Baki kawai na rabe,idan na ce zan mayar mara dadi ce, wai ya san hali na, irin na saba dakkotan nan. Assidiq ya amsa da yake ta kallon shi ya ce "My boy, ka girma fa" Shi ko ya wangale mishi baki "Ina sauran yaran?" na dauka ma tambayar da zai fara kin kenan, Sai ya fara da batun Maama. "Suna cikin gida" na ba shi amsa lokaci daya ina zare mishi takalman kafarshi da socks din. "Ya gidan?" "Yana nan lafiya sai kewarka" Murmushi ya yi kafin ya ce "Kamar gaske" Ni ma murmushin na yi ina fadin" gaske ne mana" Ruwan wanka na hada mishi, bayan ya fito ya yi shirin masallaci saboda ana ta kiran sallah. Ni kuma na shiga gyara tsarabar da ya zo da ita, na kuma ware wacce za a kai cikin gida Misalin 8:30pm ya shigo tare da yaran a zuciyata na ce "Sai da ka lalubo su kenan" Abinci na hada musu, suna ci suna hira, ban samu kanshi ba, Sai da suka yi bacci sannan. Muna kwance bayan ya gama sauke nauyin da yake ta cewa ya zo da shi ya ce "An gama komai na gida fa sai tarewa" "Kai Ma Sha Allah, yaushe kenan tarewar?" "Shi ne har yanzu nake ta tunani, ba na son a kara cire yaran nan daga makarantar nan zuwa wata, abun sai ya yi yawa. Tun da saura term daya su gama na ce ko mu jira su kawai, kin ga muna komawa js1 za su tafi." Kai na jinjina alamar gamsuwa kafin na ce "Tunani mai kyau, hakan ya fi, Allah Ya nuna mana lokacin" "Amin" ya amsa hade da janyo ni jikinshi sosai ya ce "Sosai fa na yi kewarki, ina jin kamar a koma second round" Da sauri na janye jikina, ina fadin" matsa don Allah " Dariya ya yi mai sauti hade da maido ni jikinsa ya ce" Khadija idan zan yi aure ya za ki yi? " Matar J ✍🏻 [12/22, 21:21] 08080966571: *HASASHENA* *Page 27* Na tabbata ya ji yadda zuciyata ta buga, ba iya zuciyata ba, har numfashina sai da ya yi season for some seconds Kafin ya dawo daidai. Na yi ta kokarin daidaita nutsuwata kafin na ce "yaushe za ka yi auran? "Ni ma na jefa mishi tambayata " Ban san ya rana ba, amma ina ji a jikina zan yi, kin san an ce duk namijin da ya saba da mata biyu ba zai iya zama da guda daya ba" Idanuna na lumshe a hankali, kafin na ce "Sarai za ka aura?" "I don't know" "Ka aure ta, tana sonka" na fada har cikin zuciyata, saboda ina ji a jikina za ta fi min saukin kishi, bazawara ce wacce miji ya mutu ya bari, secondly ba ta yi boko ba, ba ta da wayewa, na fita cika mace a zahiri dai, duk wanda ya kalle ta, ya kalle ni, tabbas zai fahimci ni ba sa'arta ba ce, kuma a haka kamar ba ta da matsala Ya kuma janyo ni sosai jikinsa kafin ya ce "Me ya sa ita?" "Saboda tana sonka" "kodai don kin fita wayau?" Karon farko da na yi murmushi jin ya harbo jirgina ba tare da na ce komai ba. Shi ne ya kuma cewa "Allah Ya iya mana" A hankali na ce "Amin" Daga haka ya kuma shigewa jikina ba jimawa na ji saukar numfashinshi alamun ya yi barci. Ni kuwa na nemi baccin sama da kasa na rasa, maganganun da muka tattauna suna ta min yawo, in juya can in juya can. Amma tabbas Ina ganin cinta a kan Sarai. Safiyar juma'a kasancewar yara ba makaranta sai aikin safen ya dan yi min sauki, saboda suna taya ni, Babansu ma ba a bar shi a baya ba. Cikin kankanen lokaci muka hada break fast muka karya, a tare muka kara gyaran gida, ni kuma na shiga hidimar abincin rana, kasancewar ana fita da abincin kofar gida duk ranar Friday. Su Khalil ke taya ni, zuwa 1pm ya rage saura karashe, yayin da su Affan suka yi shirin masallaci. Shadda gambari fara dinkin babbar riga suka yi anko, sosai suka yi kyau, girman Khalil yana ban mamaki, girman jikinshi ya fi shekarunshi. Bayan sun dawo masallaci suka ci abinci, suka dauki abincin Inna da kuma na Hajiya mahaifiyar Maman Khalil, saboda duk lokacin da na dan yi abinci na canji ina kai mata, kuma duk ranar Friday ma ina kai mata. Misalin karfe biyar na yamma ina zaune a falo cikin kwalliyar Lace riga da siket wadanda suka karbe ni sosai, hannuna rike da wayata ina chat da su Samira da Yusrah aka yi sallama kofar falon, na amsa Sarai da Baban Khalil suka shigo, gabana ya yi wata irin faduwa, har suka karaso cikin falon ban janye idona a kansu ba. Musamman Sarai wacce take sanye cikin Lace ita ma mai saukin kudi riga da zane hade da farin hijab. "Za ta wuce na ce ya kamata ta shigo ku gaisa" cewar Baban Khalil a lokacin da yake zama kan kujera "Ai kam na gode. Sarai ya gida?" "Lafiya kalau" ta amsa min a hankali Daga nan duk mu ka yi shiru, Sai shi ne yake ta jan mu da surutu, like 30mns ta mike tana fadin "Na gode, a gaishe da yaran, na ga ban ga ko daya ba" Mikewa na yi ni ma tare da fadin "Wlh duk sun fice har Assidiq din ma" Iyakacina bakin kofar falo, na yi tsaye Ina kallon yadda suka jera, Bashir ana ta jefa kafa, ita kuma tana tafiya a nutse daurin zanen nan Das kamar an yi mata da injin. A zuciyata na ce, wai kodai daurin zanen nan ne ke daukar Bashir ne, na son shi da son ganin mace a cikin riga da zane. Shigowar Murja ce ta katse min tunanina, cike da girmamawa ta matar kane ta gaishe da Bashir, kafin ta nufo cikin gidan. Tare muka juya zuwa falo tana fadin "Wai abun nan kodai da gaske yin shi za a yi?" "Sai Allah kam. Amma ku a nan babu damuwa ne mace ta rika sintiri a gidansu saurayin ta?" "To ya danganta, amma mu nan kin ga kauye ne, babu wata matsala idan matar saurayi ko bazawari ta haihu ka je barka da ɗan ihsani, duk gyaran hanya ne. Haka zuwa gaishe da suruka ka yi mata ihsani duk gyaran hanya ne." Baki na rike cike da mamaki kafin na ce" To ni dai gaskiya ba na bukata, idan za ta je can cikin gida ban damu ba, amma ni ban da wurina" "Kin ga, ki rufawa kanki asiri ki zuba musu ido, idan kika bari aka fara kasa ki a wannan familyn to za ki ji jiki. Tun da suna yin ki, to kar ki yi abin da zai ɓata ki kuma" Rike da haɓa alamun mamaki na ce "Menene abin da zai bata ni din, kawai don ba na son bazawarar mijina na zuwa gidana?" "Ba Za ki gane ba Maman Maama. Amma ki gwada sai dai tsakaninki da mijinki kar ki bari maganar ta je kunnen Saro din. Kuma wlh ki yi hankali da ita, ba ki san wacece Saro ba" "Wacece ita?" na yi saurin tambaya "Babu ruwana, idan zama ya hada kin san wacece" Tsoki na ja, kafin na ce "Ina za ki je?" "Gidan suna, wata kawata ce ta haihu. Ko za ki je?" "Da yake ni ce gayyatar ni mijina bai fada" Dariya ta yi hade da mikewa ta nufi kofar fita, tana fadin "Assidiq na can na ta yi wa Inna rigima, yau aikinshi take yi" Dariya na yi kafin na ce "Ai rigimarshi da sauki, idan kika hada da rigimar Maama tana kamar shi. Kai Maama ta ba ni wahala, har wata rama na yi" Duk muka yi dariya a tare, har gate na yi mata rakiya sannan na dawo, a zuciyata ina tunanin wane irin hali Sarai ke da shi da Murja ta ce in bi ta a hankali. "Da gudun bala'i zan bi ta" na fada a bayyane ina cusgune fuska. Miji ya tafi for some days ya dawo to an fi marmarin juna, kwanaki ukun da Abban Khalil ya yi kamar kar su wuce, wata irin soyayya muke yi mai tsayawa a zuciya. Ranar Monday da safe ya tafi tare da su Khalil ya sauke su, shi kuma ya wuce. A hankali nake shirye-shiryen tafiya ta, duk wasu ƴan kudi da nake adanawa na rika fito dasu ina sayen tsaraba. Ba karamin dadi na ji ba, lokacin da su Khalil suka fara jarabawa, ji nake kamar in janyo kwanakin su yi su gama. Ranar Asabar suka yi prize and giving day, lokacin da Rahma ke fada min za ta zo, na dauka da wasa take, amma sai ga ta ranar Juma'a har da gifts nata. Taron ya yi kyau hade da kayatarwa, ina jin su Khalil sun fi kowa tara dangi a wajen taron nan, dangin mamanshi sun je, ga kuma dangin Babanshi, mu da su da kuma yaranmu mun tasar ma ashirin. Shi ya sa gamu nan zuga guda. Bamu dawo gida ba sai yamma, Rahma gidansu Maman Khalil ta wuce, mu kuma mu ka yo gida, yau kam hirar kaf a kan graduation ne. Ni kuma a zuciyata jiran umarni tafiya nake yi, saboda na kosa sosai in tafi. Safiyar Lahadi Rahma ta wuce Abuja. Kullum jira nake yi, in ji Bashir ya yi min maganar tafiya amma shiru, har sati da yin hutunsu Khalil. Wannan ya sa na ji akwai bukatar in tunasar da shi, tun da ya zo, weekend kafin ya koma. Safiyar Asabar muna zaune muna hira na ce "Alhajina, ka yi min shiru!" Cikin rashin fahimta ya ce "Da me?" Marairaicewa na yi kafin na ce "Ka ce idan aka yi hutu zan je Kano" Kanshi ya dauke gefe kafin ya ce "To da yaran za ki tafi ko? Amma ya za a yi ki tafi ko bar su suna ta gararanba a gari" "Da yara kuma?" na tambaya cike da mamaki "Eh mana, ni ba ni nan, ke ba ki nan, a ina za su zauna" Baki bude nake kallon shi kafin na ce "Yanzu don Allah Abban Khalil a cikin yaran nan wanne za a yi wa wanka, kamar wasu masu shan nono, to ko Maama ce na ce ba zan je da ita ba, ai ba abun damuwa ba ne, bare Affan da Khalil" "Ni fa ba na son in ga yarana suna bin gidaje" ya yi maganar with his serious Baki na bude ina kallon shi, saboda ban san me zan ce ba kuma, ina ne gidajen, gidansu Sakeena ko gidansu "Idan da yaran za ki tafi, shi kenan gobe ma kishirya, amma idan ba da su ba kam to ban amince ba" "Kenan yanzu ni idan zan yi tafiya dole sai da su?" "Kwarai, idan ke kika haife su za ki bar su ne?" Na yi saurin tarbar numfashinshi da "Sosai ma kuwa, kamar dai Affan da Khalil ba zan rika zuwa unguwa da su ba" "Ashe kam ba za ki je ba" ya yi maganar hade da mikewa ya bar min falon. Shiru na yi cike da takaici, ina son yaran nan sosai, amma Bashir nema yake ya tura min kiyayyarsu da karfin tsiya, ta ya zan kwashi yara rabe-rabe har hudu tun daga Ruma zuwa Kano, fisabilillahi an kyauta min kenan. Zuciyata ta rika wani tukukin bakin ciki da bacin rai, Affan ne ya kawo min wayata da take hannunsu suna game ya ce "Auntynmu, Aunty Yusra na kiran ki" Na lumshe idon bacin rai kafin na daga kiran. Gaisawa muka fara yi kafin ta ce "Auntynmu ya maganar tafiyar ne, ke fa nake jira" Cike da jin bacin rai na ce "Yusra ki tafi kawai, ni ba zan je ba" "Me ya sa?" ta yi saurin tambayata Kamar zan yi kuka na ce "Wai Abban Khalil sai dai in tafi da duk yaran nan, yanzu fisabilillahi Yusrah yaushe zan kwashi yaran nan daga nan har Kano, su Khalil basu yi girma da zuwa unguwa ba?" "Don wannan ya sa kika ce kin fasa?" kamar tana kallo na, kai jinjina mata, ita kuma ta dora da "Gaskiya kam babu dadi, tafiya da yaro ma ko daya ne babu dadi bare da yawa. Amma tun da ya ce haka shi kenan, kudin fa tafiyar daga aljihunshi za su fito, mu gaskiya muna son ganin ki, kawai ki taho" "Da yaran Yusrah?" "Eh mana, me ye a ciki, ba fa fitsari ko kashi za ki wanke musu ba" Ajiyar zuciya na sauke, kafin na ce, "shi kenan idan ya shigo zan ce mishi na amince, duk yadda mu ka yi kuma zan sanar miki" Cike da murna ta ce "Haba ko ke fa" Da haka mu ka yi sallama, na shiga kokarin warwarewa, na yi ta tausar zuciyata har zuwa lokacin da ya shigo cin abincin rana. Fuska a sake na gabatar mishi da komai na abincin, yana ci muna taba yar hira. A cikin hirar ne na ce "To yaushe zan tafi?" "Ina?" Sosai tambayar ta ba ni haushi amma sai na share na ce "Kanon" "Da yaran ko?" "Yadda kake so ai haka za a yi yallaboi, su ma ka ga sun ji dadi sun dan yi balaguro" Murmushi ya yi kafin ya ce "Ki shirya ranar Monday sai Salisu ya kai ku" Lumshe idanun dadi na yi, ganin kai mu za a yi, komai ya zo da sauki ma ai, cike da ɗoki na ce "Na gode Yallaboi, Allah Ya kara lafiya da nisan kwana" "Amin" ya amsa, kafin ya ce "Me kike so a matsayin tsaraba?" Na ɗan yi ahiru kafin na ce "To me zan saya, ya wuce lemo da yar ayaba, wannan kuma ko a hanya ai mun saya." Kai ya jinjina alamar ya fahimta. A zuciyata na ce "Lallai ma wannan mutumin, yanzu don Allah ni ce zan fada mishi abin da zan yi tsaraba, shi bai san abin da ya dace ba." Ai cikin kwana biyun nan ba zama, shirin tafiya kawai, kitso, lalle, wanki, guga, zuwa Lahadi da yamma na yi package na duk abin da na san zan tafi da shi, kayan su Khalil akwati guda, haka Maama da Assidiq, ni kuma nawa daban. Irin yadda su Khalil suke murna, Sai na ji gara ma da ya ce a tafi dasu din, yadda suke farin ciki, kamar za mu kaiwa mahaifiyarsu ziyara. Lokacin da suka dawo masallacin isha'i ne Bashir ya shigo hannayenshi du biyun rike da manyan ledoji, da sauri na tarbe shi, na ajiye a tsakiyar falon, sannan na shirya mishi abinci shi da yaranshi, yana cin abincin ne ya ce "Ki bude wadannan ledojin, ki ga ko akwai abin da babu." Na shiga bude ledojin, ledar farko dai tarkacen Assidiq ne, pampers, cerelac, custard, da ɗai Sauran tarkacen shi " Daya ledar kuma kayan tea ne, manyan gongoni "Wadannan na yaranki ne, kar ki je ku dora musu hidima" Murmushi na yi kafin na ce "Mun gode" Daya ledar ma kayan tea ne, sabulai, omo, Manshafawa kala-kala cike fal. "Wannan na Umma ne" ya kuma fada yana kallo na Wani murmushin na kuma yi kafin na ce "Umma ta gode sosai, Allah Ya kara budi" "Amin" ya amsa yana ci gaba da cin abincinshi. Daya ledar kuma zannuwa ne da yadin shadda, nan ma kafin in ce wani Abu ya ce "Turmi biyu na Umma ne, turmi daya Maryam, daya Yusra, shaddar kuma ta su Usman ce" "Yallaboi, wannan ai, hidima muka dora maka, da na san haka zai faru ai da ban yi tafiyar nan ba" "Ina hidimar?" "Ga ta ka yi, da gaske abun ya yi yawa" "Bai yi ba Khadija, Umma ta cancanci komai, suruka ce mai kawaici hade da dattako, Allah dai Ya ara mana rai da lafiya" "Amin, to mun gode Allah Ya kara budi. Ni kam ko mai ɗangyashin kudin nan da ake ma kirari da gaske ne?" cikin zolaya na yi mishi maganar Ba shi kadai ba, har yaran sai da suka yi dariya, shi ma cikin dariyar ya ce "Da ba ki sani ba, lallai yarinyar nan na ki wasa ne" Wata dariyar muka kuma yi, kafin ya ce "kafin ku dawo Sha Allah za a gama saka komai na sabon gidan can, kuna dawowa sai tarewa" Tuni yara suka fara tsalle wai za su tare a sabon gida, ni kam kayan na shiga tattarewa ina fadin "Allah Ya kai mu" Matar J ✍🏻 [12/23, 11:20] 08080966571: *HASASHENA* *Page 28* Ana fitowa sallahr asuba muka dau hanya, farin ciki wurin su Khalil ba a magana. Tun muna wuce wurin da suka sani, har suka fara tambayarshi "Auntynmu ina ne nan?" In da na sani in yi musu bayani in da kuma ban sani ba Salisu ya yi musu bayani. Gab za mu isa gidan mutum daya suka yi bacci, sannan motar ta yi shiru, Bashir kam kira minti-minti ya yaran nan, fatan babu wata matsala, idan akwai abin da suke so ki siya musu. Aikinshi kenan. Ni fa tafiya da yaran nan riba ta zame min, saboda ni kaina na san wani abun don su aka yi min shi. Har da buhun shinkafa, carton na taliya, manja da Mangyada wai kar a dorawa Umma wahala. Misalin karfe biyu muka saba sa Kano, abun mamaki har mun riga Yusrah isa, aikam gida ya kacame da murnar ganinmu, ni kaina wani farin ciki nake ji mara misultuwa, karo na biyu da na zo gida tun bayan aurena. Abinci da sallah kawai Salisu ya yi ya juya, muna ta rabon tsaraba Yusrah ta iso, aka dora murna daga inda aka tsaya. Yara kam sai tsalle, Khalil ya samu abokai, Usman da Haidar. Maama kuma ga Ammatullah din Yusrah da Ahmad. Assidiq ne ba shi da aboki, Sai ƴan dauka, Maryam kam ko ina da shi take zuwa. Misalin karfe bakwai muna cin tuwon dare a daki, yaran kuma suna waje suna cin nasu Bashir ya kira. "Ya kuke?" ya fara tambaya bayan na daga "Alhamdulillah!" na ba shi amsa "Babu wata matsala ko?" "Babu komai" "To Ma Sha Allah! Ina yaran?" Affan na kwaɗawa kira, ya kara so a guje, na mika mishi wayar. "Kai Bashir akwai son ƴaƴa" cewar Yusrah tana murmushi "Tun ba biyun nan ba, son da yake musu babu yadda za a kwatanta shi" "Ba za ki gane yadda yake ji ba ne, kin san babu ran mahaifiyarsu, ji yake kamar duk abin da ya yi musu sai sun yi kukan maraici" cewar Umma "Haba Umma, me yaran nan suka rasa, da za su yi maraicin uwa, wlh daga mutuwar mahaifiyarsu kawo yanzu ba su yi kukan rashin uwa ba, yan gata ne gaba da baya. Ni idan har na san bayan na mutu yarana za su samu gatan wadannan yaran, to yanzu ma in mutu" Yusrah dai dariya ta yi, Umma kuma ta rike Haba tana fadin "Baki da hankali, ke uwa fa, uwa ce, babu wacce za ta taba me ye musu gurbin uwar su" "Wlh Umma ina jin yaran nan kamar yadda nake jin Maama da Assidiq, amma kullum mutumin nan nunawa yake yi dai ina yi musu ba daidai ba, kullum ban iya ba a kan yaran nan, _yaran nan sun ci abinci suka tafi makaranta kuwa, yaran nan sun tafi da abinci makaranta, abin da na sawo jiya na ce ki basu kin basu._ kullum aikinshi kenan cikin tuhuma ta, sosai abun ke ɓata min rai" "Na ce miki ki yi hak'uri, tun da haka yake, Sai ki rinka bin shi a zauna lafiya ba shi kenan ba" Yusrah ta yi caraf ta ce "Idan ma ban da Auntynmu, idan wata macen ce ai ta samu weak points na Shi, da wannan damar za ta yi amfani ta shiga jikinshi sosai. Yanzu ba ga shi ba, da kika amince za ki taho dasu, ba ki ci riba ba" Umma ta ce "Idan ban da shirme ma, yaran da ba goyasu za ki yi ba, me na bacin rai" "Kin san Allah Umma, da ace mahaifiyarsu na nan ba za ta rika yawo dasu ba, amma ni Bashir ko gidan suna zan je a cikin gari sai ya ce to wa zan bar wa yaran?" na yi maganar cike da jin haushi. Kafin su ce wani abu na kuma cewa "Ko fa gidansu na ce zan je, Sai ya ce to yaran fa, irin basu san hanyar nan ba. Kai ina ganin ikon Allah" Dariya Yusrah ta yi tare da fadin "Gaskiya kam abun ya yi yawa" "Ke da Allah can, to kara tunzura ta" cewar Umma tana tashi daga wurinmu Yusrah ta kuma yin dariya, ban da ni da nake jin zafin abun kamar yanzu yake faruwa. Daidai lokacin Khalil ya kawo min wayar ya ce "Auntynmu ga shi, Abbanmu ya ce zai turo kudi ki kai mu wurin shakatawa gobe" "Allah Ya kai mu" na yi maganar hade da amsar wayar Yusrah kuma ta ce "Hankali a jikin yaran nan kamar ya yi magana" "Ai ni ba ni da case da su, da ubunsu ne, amma yadda yake min a kansu da ace suna min rashin kunya da tuni na nemi mafitata." Komai Yusrah ba ta ce ba, ta mike zuwa tsakar gida, ni ma sai na mike na bi bayan ta Da safe kam sai ga kudi Bashir ya turo har 100k,wai in kaisu shoprite su sayi duk abin da suke so, idan kudin sun yi kadan in yi magana ya karo. Na ce to. Cike da mamaki na nunawa Yusrah alert din na ce "Kin ga mutumina ko." Murmushi ta yi hade da karbar wayar ta ce "Da ba ki zo da su ba, ba zai turo wadannan kudin ba, bayan kwana biyu kuma ki ce mishi za ki kai su Minjibir park" Mu ka yi dariya hade da tafawa. Karfe biyu kuwa muka fita zuwa shoprite, yadda yaran suke farin ciki da walwala, ni kaina sai abun ya yi min dadi, su hau lilo, su hau wancan abun wasa duk su kadai. Kayan ciye-ciye kam kaca-kaca. Haka muka juyo gida yamma lis, gajiya kam ba a magana , shi ya sa ana yin sallahr isha'i kowa ya ci abinci sai bacci. Ba ni kadai ce nake jin dadin ziyarar Kano ba, har da su Khalil, musamman yawon da su Usman ke fita da su, Yusrah dai satinta daya ta juya, ni kuma Bashir ya ce in dawo ranar Alhamis, ranar da ya kama kwana goma cif da zuwana. Tun bayan tafiyar Yusrah Umma ta shiga hidimar tsaraba ta, ina taya ta da yan kudin hannuna, su dai su Khalil tsarabar yar gullisuwa, kwakumeti, tuwon madara loga sune nasu. Ni kuma rabin buhun fulawa aka saya, aka yi min fura sa, Sai kuma mu ka sayi gyada kwano uku aka yi min kuli da mai. Barkono daddawa da kuka. Muna zaune da Umma da dare muna hirar bankwana saboda washegari zan tafi ta ce min "Kin ce kuna komawa za ku koma sabon gida, to babu abin da kike bukata?" "Ba komai gaskiya, kayana duk sabbi ne basu sha jiki ba, dama-dama kujeru, idan da ina da hali su zan canja" "Ai da kin sani ba ki wahalar da kanki wajen yin wannan tsarabar ba, Sai ki tattala kudin, a siyar da kujerun a yi ciko a siya miki sabbin" Zamana na gyara kafin na ce "Ai na yi siyayyar tsarabata tun da dadewa fa, ban san zai yi mun wannan hidimar ba, yanzu haka ma dai ta dalilin tafiyar nan ina da wajen dubu hamsin, ina jin zan yi amfani da su, a canja min yadin kujerun" "To hakan ma ya yi, Allah Ya taimaka, Sai a yi ta hak'uri, ki rika kawar da idanunki a kan yaranshi don Allah. Ko me zai yi musu babu ruwan ki" Kai na jinjina alamar fahimta, nasiha ta ci gaba da yi min sosai a kan kawar da kaina da hidimar yaranshi. Salisu ne ya kuma dawowa daukarmu, yanzu din ma sai da muka cika boot da tarkace, ga buhun gurasa, ga tarkacen su Khalil na tsaraba. Haka muka dau hanya, ku san a tare muka isa da Bashir, yana isa muma muka isa, yara suka makalkale shi, suka cika mishi kunne da labarin Kano, Affan har yana cewa shi dai a can zai yi makaranta. Ni kam aikin kakkabe gida na shiga yi, don ma an kawo mana abinci daga cikin gida. Sai 10pm na ɗan kammala abin da zan iya, zuwa lokacin yara duk sun yi bacci. Sai ni da Babansu, ranar kam na yarda da gaske Bashir yake yi, ya yi kewata, saboda ya kara tara min gajiya, ban yi bacci ba sai wajen 2am,shi ya sa sai wajen 6:30am na yi sallahr asuba. Na shiga kitchen kuma, bayan mun karya mu ka shiga rabon tsaraba, aka kaiwa Hajiyar Maman Khalil, cikin gida, da kuma makotana da abokan arziki. Yanzu kuma hankalinmu ya fi karkata ne a shirin tarewa sabon gida, da na yi wa Bashir shawarar yadda zan yi da kujeruna, Sai ya ce in bari, wai ba sai na tafi da komai ba. Hakan ya sa na kara adana kudina, sana'ar nake son farawa, ba zan iya zama sai abin da miji ya miko min ba. Kamar ko yaushe ranar Monday Bashir ya koma aiki, inda ya ce next week idan ya dawo Sha Allah tare za mu juya. Don haka in yi package na kananun abubuwan da nake so na amfani. Na ce to. Na kira Umma na fada mata yadda ake ciki, ta ce to in jira mu tare tukun in ga ya abun yake. Ni ban san me ya sa ba, ba na jin murna da karsashi a kan maganar tarewa sabon gidan nan, yaran ne kawai suke murnarsu, ni kam sai dai in yi ta yake, na rasa dalilin hakan. Matar J ✍🏻 [12/23, 11:46] 08080966571: *HASASHENA* *Page 29* Satin nan duk kare shi mu ka yi a shirye-shirye, Alhamis ne kamar ko wane lokaci Bashir ya dawo, mu ka ci gaba da kintse-kintse, juma'a da safe aka fara dibar wasu kayan namu musamman na sanyawa zuwa Katsina, safiyar Asabar kuma mu ka bi su a baya, akwai kanwar Maman Khalil Momy, Sai Aunty Habi da kuma Murja. Duk yadda nake imagination din gidan sai ya wuce da tunanina, gida ne tangameme, mai dauke da katon farin gate, fentishi daga gaba white and ash ne, sosai ya haska hade da bayar da kala. Kana shiga akwai dakin maigadi, wanda daga saman dakin ne, aka dora water tank Manya guɗa biyu, daga nan sai katuwar farfajiyar gida mai dauke da doguwar katanga wadanda madaidaitan fulawa suka zagaye saboda yanzu suka fara girma. Daga can bangaren yamma wajen dakin maigadi akwai bishiyoyin mangoro, guava, cashew, umbrella, gwanda da kuma ayaba. Wadanda su ma basu gama girma ba. Sai ka dan yi tafiya kadan sannan za ka iske part din farko, wanda yake bangaren gabas kofarshi tana kallon yamma, daga bangaren yamman kuma akwai wani part din, kofarshi na kallon gabas, wannan ya sa suke facing din juna. Idan ka dan kara gaba, to a kawai wani part din daga bangaren kudu, kofar shi na kallon arewa, kenan part din can biyu su dan ba shi baya. Kuma duk ya fi su girma, saboda shi upstairs ne ma. Shi ma kuma a gaban entrance din akwai doguwar farfajiyar ko in ce tsakar gida, wacce za a iya parker motoci uku a tsaye ba a kwance ba. Kuma nan Bashir ya ce mu shiga shi ne part dina. Ban gama tsinkewa da lamarin ba, sai bayan da na shiga, an zuba komai na gyaran falo, very unique babu hayaniya, Irin cool falon nan dai na ƴan gayu. Kujeru leda ash colour mai haske, Sai stool da katuwar plasma. Idan ka dauke wannan babu komai a cikin a falon. Sai bangare daya da aka yi dinning area. Ta Kuma cikin dinning din ne kofar kitchen take. Still a cikin falon daga kasan stairs din haurawa sama akwai corridor, wanda a nan ne dakin yara yake, dakuna ne guda biyu da aka zuba komai da yara ke bukata, na san daya na mata daya kuma na maza. Upstairs kuma akwai wani room and falon guda biyu, daya nawa daya na Bashir, su ma an zuba komai na gyara. Ban san lokacin da na fadi ina yi wa Allah sujuda ba, na fashe da kukan dadi, Murja ta dago ni tana fadin "Ikon Allah, abun murna sai kuka" Su Yaya Habi suka shiga dariya suna "fadin kukan murna ne" tabbas kam kukan murna nake yi, a rayuwata ban taba koda mafarkin ina a irin wannan gidan ba. Bashir ya shigo ya same ni zaune ina ta kuka su Aunty Habi sun zagaye ni, yara ma sun yi cirko-cirko suna kallo na. "Me ya faru?" ya yi tambayar fuskarshi na nuna damuwa Cikin dariya Aunty Habi ta ce "Kukan murna take yi." Siririn tsoki ya ja komai bai ce ba, Sai Assidiq da ya dauka, Aunty Habin ta dora da"Dole ta yi kukan murna. Bashir Allah Ya kara arziki, Ya sa ka fi haka, Allah Ya saka aminci a wannan gida, ya kare ku da dukkan sharrin abun ki, ya tsone idon makiya" "Amin" duk suka amsa. Yara kam bin bayanshi su ka yi suna murnar, wai nan gidan ya fi na Abuja kyau. Ba jimawa aka shigo mana da katuwar kula, katon na ruwan gora da minerals. Har da plate da spoon, Wai daga makotana. Nan fa aka hau cin abinci aka yi sallahr azhur, kafin nan muka sauka kasa muka shiga zagaye gida. Kowa na kara yabawa. Sai da muka yi sallahr la'asar sannan muka shiga makotana, na kusa sosai na yi musu introducing kaina. Sannan na yi godiya ga matar da ta kawo min abinci, ita ce muka hada katanga da ita a bangaren dama, ta ce min sunan ta Amina. Amma ana kiranta Maman Aiman Ita kuma ta bangaren hagun ba ta nan, wai tana Amerika ita da mijinta. Naso su Yaya Habi su kwana, amma suka ce ina tafiya za su yi. Misalin biyar na yamma kam suka bi motar da ta kawo mu. Ni kam jina nake kamar sabuwar amarya, ashe dama haka sabon gida yake. Gidan na kara kalkalewa na kunna turaren wuta, yaran kam suna can rashin ji a tsakar gida. Sai da aka yi sallahr isha'i Bashir ya dawo, hannunshi dauke da ledar take away, yaran ne suka tarbe shi, kusa da ni ya zauna yana fadin "Washhh Allahna!" a hankali "Sorry!" na fada cikin nuna kulawa "Thank you" ya amsa hade da kwantar da kanshi jikin kujera. Yayin da ni kuma nake zaro robobin take away, na ba kowa daya-daya. "Yallaboi kai fa?" na yi maganar lokacin da nake aje mishi robar ta shi take away din a kusa da shi. Mikewa ya yi daga kishingiden da yake yana fadin "Sosai na gaji ne." "Sannu" na kuma fada lokaci daya kuma Ina bude robar take away din Bayan na mika mishi ya fara ci ne ya ce "Khadija kin ga gida, ya yi kyau?" "Sosai ma, ai ni ko bai yi wa kowa kyau ba ni ya yi min. Duk wani abu daga gare ka ai mai kyau ne, bare na wannan kowa ya yaba. Sai dai a yi fatan alkairi kawai" Murmushin jin dadin maganar da na yi yake yi, yana tauna abincin a hankali ya ce "A cikin gidan menene bai yi miki ba?" "Komai ya yi min Yallaboi, tsakanina da kai sai addu'a kawai, Allah Ya saka maka da mafificin alkairi. Ummanmu na ta ma godiya kafin ta zo" "Me kika ce mata?" "Ka yi min gata mana." Na ba shi amsa. Ya kuma murmusawa kafin ya ce "You deserve it. Na san fa kina da hak'uri. Ki kara hakuri da halina. Ko na yi niyyar kawar da kai a lamarin su Affan sai in ji na kasa. Ba wai don kina cutar dasu nake tambayarsu ko tambayarki wani abun game dasu ba. Kawai idan ban yi hakan ba ne ba na samun nutsuwa " " Ba komai, na fahimta " Na yi maganar a sanyaye, lokaci daya kuma na juya ina kallon Assidiq da yake kuka. Kafin ma in yi magana har Affan ya kwaɗe Maama, kamar kiftawar ido shi ma Khalil ya kwaɗe shi, Sai fada ya kacame. Komai Bashir bai ce ba, ni ce na mike da sauri na shiga tsakaninsu kowa na ta huci "Me ya faru?" na yi tambayar ina kallon su. Maimakon amsar Affan ne ya fashe da kuka, saboda shi idan abu ya ba shi haushi, ko idan yana da gaskiya ba ya magana sai kuka. Wannan ya sa na juya kan Khalil na ce "Me ya sa za ka duke shi?" Sai da ya gama kumbura sannan ya ce "Shi ne fa ya duki Maama" "Haba Khalil, kai babba ne, ka dinga hak'uri don Allah" na yi maganar ina shafa kanshi, Affan kam tuni ya fada kan kujera yana gursheƙin kuka, alamun dai ya hau jakar kuturu. Hannunshi na kamo hade da dago shi daƙyar, saboda yadda yake dagewa na ce "Haba ɗanɗana, ka san yanzu da kai nake yi, tuni na yaye Khalil, ka yi shiru kar a ganmu a rana. Kuma ka sha kurumin ka, zan koma Ruma in dakko ma Maryam in kawo ta gidan nan ka rika kallon ta kullum kana farin ciki" Ina zuwa wannan gaɓar, Sai ya fada kan jikina yana kunshe dariyarshi "Ashe dai da gaske Affan son Maryam kake yi, lallai ya kamata in kai toshi," ina kai wa nan ya kwace daga jikina hade da rugawa a guje ya hau stairs yana dariya, Khalil din ma bin bayan shi ya yi yana dariya. Duk budurin da muke komai Bashir bai ce mana ba, Sai abincin shi da yake ci a nutse. Sai bayan da suka haura ne ya ce" Wacece Maryam kuma? " Cikin dariya na ce" Yarinyar Kawunshi Shamsu. Ya ce min kin ga Auntynmu idan na tashi aure Maryam zan aura, tana da kyau, ga gashi" Baki bude Bashir ke kallo na, yana murmushi, kafin ya ce "Wai shi Affan din, dama yana magana haka, har ya san wani kyau?" Dariya na saki kafin na ce "Har ga shi ma ya fada" "Tabdijam! Allah Ya kawo mu zamani. Affan just 11-12years fa. Aiko zai ci uban shi" Wata dariyar na kara yi, ina fadin "Kuma sai ka ga abin da ba mu yi tsammani ba ya faru. Yanzu fa duk yarinyar shekerarta biyu, ka ga ko lokacin da za ta isa aure ai Affan ya mika" Kai ya jinjina kafin ya ce "Babu mamaki a lamarin ubangiji kam. Allah Ya rufa mana asiri" "Amin" na amsa, ina kallon Assidiq da yake ta rashin jin shi, shi kadai, saboda Maama ma ta bi su. "Affan idan yana fushi yana min kama da Mamanshi, idan ta yi fushi." ya yi maganar yana dan murmushi mai ma'anoni da yawa Ni dai Allah Ya jikanta kawai na ce, hade da kawo batun da zai tafiyar da waccan hirar, saboda na tabbata hakan zai iya shafar abin da na yi mishi tanadi a daren yau. Cikin ikon Allah kuwa na kawar da hirar, shi ya sa daren ya zame mana rayayye, kuma abun tunawa a gare mu ba ki daya. Da safe babu wani wahala komai na kammala gyaran gida, da kuma hada break fast. Bayan mun karya ne Abban Khalil ya ce zai je wata makaranta ya siyowa su Affan form da Maama. Bayan fitarshi da kaina, na zagaye gidan, ina ganin yadda aka kashe kudi ba na wasa ba, wurin gininshi. Su Khalil kuma ball suke yi a farfajiyar gidan. Bayan na gama zagayen ne na koma kan entrance na zauna Ina kallon yadda suke buga ball din cike da Nishadi. Idanuna na dora a kan plat din nan guda biyu, wannan yana nufin akwai sauran mace guda biyu a kan hanya kenan. Gabana ya bayar da wani irin rass, ina ta imagining yadda zan yi ranar da za a yi mini kishiya, dama-dama ma idan Sarai ce, amma jikina yana ba ni Bashir ba zai dakko Sarai ya aje ta a wannan kayataccen gidan ba. Kila wata mai degreen zai dakko ya zo ya hadamu in yi ta fama, idan haka ne kam, Sai in kwashe tarkacena in nufi Ruma, babu dalilin zama hankalina yana tashi. Ina zaune a wurin Bashir ya yi horn, yaran suka nufi gate a guje suka bude mishi, tun da ya fito daga motar idanunshi suke a kaina, har sai da na harare shi, sannan ya yi murmushi hade da dauke idanun na shi a kaina. Bayan ya iso inda nake ne, ya yi amfani da hannunshi wajen jan hancina kafin ya ce "Anya daren jiya ban je fa kwallo a raga ba?" Wata irin faduwa gabana ya yi kafin na ce "Don Allah ka daina irin wannan maganar, duka Assidiq din watanshi nawa" "bakwai" ya ba ni amsa hade da zama kusa da ni "Shi ne kuma kake min fatan ciki, don Allah ka bari, ni to asibiti ma zan je a yi min allura" "Irin soyayyar da na samu jiya Khadija idan ban yi ajiya ba, ai na zama ragon maza, kuma na fada miki ba na son allurar nan ko, ke ce za ki haife min yaran da Sakeena ta tafi ba ta haifa ba, dama ita guda shidda take so, uku mata uku maza, to ga biyu kawai Allah Ya ba ta iko haifa, kin ga Sai ki cika mata burinta, yanzu dai kin gama da maza, saura mata biyu, daga nan sai ki haifi na ki" Wata irin dariya na yi mai cike da Nishadin maganar ta shi, ba tare da na ce komai ba. Shi ne ya mika min envelope din hannunshi. Da hannu biyu na karba, hade da zaro takardun ciki, form din wata makaranta ne, wai MERIT ACADEMY. Bayan na gama karanta instructions din nasu na mika shi ina fadin "Allah Ya sanya alkairi" "Amin. Na hadu da Fatima (Maman Hana) ta ce an jima za ta bullo ta ga gida." Cikin jin dadin maganar na ce "Kai amma kam na gode, Allah Ya kawo ta. Ummanmu ma ta ce kila satin sama ta shigo" "Allah Ya kawo ta lafiya" ya yi maganar hade da mikewa tsaye ya dago ni gabadaya. Na shiga kiciniyar kwacewa, Sai bayan da na dire ne na ce "Ka manta akwai yara a gidan ne?" "To menene, ba ke ce jiya kike fada min Affan ya ce yana son Maryam ba" "Don ya ce yana son Maryam kuma shi ne za ka daga ni a gabansu" Yadda na karasa maganar ne ya sanya shi yin dariya, kafin ya ce "Kina ba ni mamaki, ke fa ko zama kusa da ke ba kya son in yi idan yaran nan suna gida. Kai jama'a" ya yi maganar hade da rike haɓa alamun mamaki. Ni kuma yadda ya yi din ne ya ban dariya, shi ya sa na shige cikin dakin ina dariya, yayin da shi kuma ya biyo bayana. Matar J ✍🏻 [12/23, 12:16] 08080966571: *HASASHENA* *Page 30* Tare mu ka yi aikin abincin rana da Bashir, don a, harkar kitchen kam Bashir Oga ne, ko mace sai haka, karfe hudu ya fita da yaran, wai zai kai su gidan ƴan'uwansu ta, bangaren shi, da kuma bangaren mamarsu. Gidan ya yi shiru har hudu da rabi, lokacin da na ji ana buga min kofa na dauka Maman Hana ce, saboda ita kawai nake jira, sosai nake son matar, Sai dai kicibis na yi da Maman Aiman a lokacin da na bude kofar, murmushi ta yi tana fadin "Ina fatan ban katse miki jin dadi ba" Ni ma murmushin na mayar mata kafin na ce "Ko daya, dama Ina kaɗaici ne" Duk mu ka yi siririyar dariya, kafin mu ka shiga, kan kujera ta zauna na kawo mata ruwa da fruit sai mineral gora ɗaya na ajiye mata. Muka shiga hira, da alama tana da sakin fuska sosai kuma ba ta da bakunta. Muna cikin hira na ga kiran Maman Hana, wani dadi na ji, saboda na tabbatar tana kan hanyar zuwa, ilai kuwa ta ce min ga ta a gate. Excusing din Maman Aiman na yi, na je na tafi bude mata kofa Tun da ta shigo take yaba gidan da tsarin shi, abin da ya yi mini dadi, tarba ta musamman na yi mata har da abinci, kuma na ji dadi sosai yadda ta ci abincin har sama na yi mata jagora, saboda Maman Aiman ta tafi. Sai gab mangariba ta tafi, inda na yi mata alkawarin da zarar na samu chance ni ma zan zo. Sai da aka yi sallahr isha'i su Bashir suka dawo, na sha labarai kam wajen Khalil da Maama shi Affan miskilanci hana shi magana yake sai idan ya so. Washegari ma haka na yi ta samun baki, makotana na kusa, da kuma ƴan'uwan Bashir da Sakeena wadanda suke cikin Katsina. Haka muka cinye wannan satin, satin sama kuma a kan hidimar makaranta ya tafi, Asabar din karshen satin Ummana ta zo ganin gida, ita da wata Goggona, da kuma Auntyna, sosai su ma suka yaba, musamman yadda Bashir ya gyara min daki, ya zuba min kaya masu tsada haka suka yi ta yi mishi godiya. Karfe hudu suka tafi. Tun da suka tafi nake tattauna maganar da mu ka yi da Ummata a kan sana'a, ni dai zaman haka ba na son shi. Umma ce min ta yi, in yi sana'ar kayan kamshi, misali humra, kwalakca, freshners, morning fresh, Sai Kuma supliment tun da yanzu su ake ya yi, da kuma atamfofi. Amma kudin sun yi kadan, Sai dai zan fara gwada kadan mu ga abin da Allah zai yi. Da dare bayan mun kintsa komai, muna kwance na ce "Alhajina ina da magana" sai da ya kara jana jikinshi sannan ya ce "Ina jin ki Hajiyata, za a yi min wayau ne?" Cikin siririyar dariya na ce "A'a" "To menene?" Jikinshi na kara shigewa kafin na ce "Ina son gwada yin sana'a ne kafin aikin ya samu" "Tunani mai kyau, saboda ni dai aikin nan ma ba lallai ki yi shi ba, ina son kawai ki zauna, ki kular min da yarana, har da na nan" ya kai karshen maganar hade da mayar da hannunshi kan marata Hannun na dauke ina fadin "Don Allah ka daina min fatar ciki yanzu, ni ba ni da komai" "To zamu gani ai, me kike son sayarwa?" "kayan kamshi, da kayan yara, Sai kuma atamfofi" "Lallai ke Hajiya ce, da na san kina da wadannan kudin ai da na daina fita kasuwa da wurin aiki na yi zamana" Siririyar dariya kawai na yi ba tare da na ce komai ba, shi ne ya ce "ya abun zai kasance to?" "Da turaren zan fara kafin mu ga abin da Allah zai yi" "To Allah Ya taimaka" "Amin" na amsa kafin mu ka rika taba hira a hankali har bacci ya dauke mu. Sai Monday su Khalil suka fara zuwa makaranta, kasancewar hutu ya kare, Sai bayan sun tafi na shiga kasuwa sawo kayan hadin turare, kasancewar ranar farko ce, ba karamar wahala na ci ba. Shi ya sa na dawo gida a wahale, har da su amai na sha. Abu kamar wasa sai ga shi na kasa dora girkin rana, saboda aman da nake yi duk ya kashe min jiki, zuwa azhur dakyar na yi sallahr. Dole na kira Bashir na ce ya zo ban lafiya, after 30mns na ji bude gate din Shi. "Me ya faru?" ita ce tambayar da ya fara jeho min, lokacin da ya shigo falon ya iske ni kwance saman center cafet. Dakyar na mike zaune na ce "Ban lafiya, Sai amai nake yi, daga zuwa kasuwa" "Subhnallah! Sannu, bari mu je asibiti" Ban yi musu ba, saboda ina jin jiki, shi ne ya dauki Assidiq, ni kuma na lallaba dakyar zuwa wurin motar. Wani private hospital mu ka je ma fi kusa, bayan gwaje-gwaje suka daura min ruwa, inda Allah Ya taimake ni ma, su Affan sai 6pm za su dawo. So wajen 5:30 aka sallame mu, shi ya sa ku san tare mu ka dawo da su Khali, Maama kam ƴan first day at school, an ci kuka an koshi, sosai ma ni ta ban dariya, musamman yadda ta fada jikin Abbanta tana kuka, wai ita ba za ta kara zuwa ba. Kamar ba ita ce ke bacci da Lunch box da school bag bag. Bread da miya suka ci, yayin da Bashir ya shiga kitchen yaran na taya shi da wasu abubuwan, ni kam ina kwance. Yau kam dole a gida ya yi sallahr magana, yana idarwa kuma ya zubo mana jallof din taliyar ya yi, wacce ta ji busasshen kifi. Muna cin abincin ne ya ce "Yar kasuwa, a haka za a yi kasuwanci, farawa da iyawa da shan ledar ruwa" sai da na kusa shakewa saboda dariya Cikin dariyar na ce, "Wlh kamshin turarurukan nan ne, suka hau kaina" "To a canja sana'ar, Babyna baya son kamshin turaren nan" Sai da na kalli su Khalil, na ga hankalinsu ba a kanmu yake ba, sannan na ce "Wai waye ya fada ma akwai Babyn ne, don Allah kai daina yi min maganar nan" "Likita ya fada min yau, don haka ki kula da kanki, kar ki jefar min da yaro a wajen kasuwancinki" Abincin da nake ji na ji babu test ko kadan, kamar zan yi kuka na ce "Don Allah da gaske?" "Ba na fada miki ba tun ranar can, ni da zarar na jefa kwallo a cikin raga nake ganewa" Spoon din na ajiye, idanuna suka ciko da kwalla, da, gaske ba na son ciki a yanzu, ban shirya mishi ba, ina bukatar in huta, ni ma in ji yadda mata suke ji, yayin da suke zaman ba ciki ba goyo Hawayen na dauke hade da mikewa na haura sama, saman gadona na fada na ci gaba da kukana. Bashir kam bai shigo ba, Sai da ya sallami yara da duk wani homework, sannan ya hauro saman sabe da Assidiq da ya yi bacci. Ni kaina baccin ne ke dauka ta, shi ya sa sama-sama na ji shigowar shi. Gefena ya kwantar da shi ya shiga toilet, sama-sama nake jin buruntunshi, har zuwa lokacin da ya kammala shirin shi ya kwanta a Gefena, ba tare da ya ce min komai ba, abin da ban tsammani ba. Da safe tare da shi mu ka shiga kitchen, yayin da su Affan ke ta shirin makaranta, su suka shirya Maama wacce ke ta rigima wai ta ba za ta je ba. Around 7:30am mai kekensu ya zo, bayan sun tafi ya rage gidan daga ni sai shi. kuma a lokacin ne na zauna ina cakular abincin, saboda Sam ba na jin dadin komai, ina zaune a wurin ya sakko cikin shirin fita office, kai tsaye dining din ya tunkara, dalilin da ya sanya ni hada mishi komai, da Bismillah ya fara kurbar tea din kafin ya ce "jikin ne?" Kai na girgiza a hankali kafin na ce "Kawai bakina ne babu dadi and it seems like kana fushi" na yi maganar cikin langabar da kai gefe "Ta ya ba zan yi fushi ba, a gabana fa kike kukan hada zuriya da ni Khadija, ba kya son jinina kenan" Tea cup din na ajiye hade da kallon shi kafin na ce "Haba yallaboi, ya za ka juya min magana, wlh ba haka nake nufi ba, kawai dai na ga cikin ne ya yi wuri, ya kamata in dan huta, shekara hudu da aure yara uku" "Me suka rasa?" ya yi tambayar idanunshi a kaina "Ba komai" na ba shi amsa "To babu ruwan ki, kawai ki yi ta haifa min, Allah ba zai hana ni abin daukar dawainiyarsu" "To ka yi hakuri don Allah, Allah Ya bamu masu albarka" "Amin, haka ya kamata ki ce. And cikin wata uku ne, an ce babu yawan zirga-zirga ko aiki mai nauyi, saboda har yanzu bai zauna daidai ba." Kai na jinjina alamar fahimta, kila wannan dalilin shi ya sa jiya da dare bai kusance ni ba kenan, don shiga kitchen ba bakon abu ba ne a wurin shi. A nutse ya yi break din shi muna taɓa yar hira, Sai bayan da ya gama ne zai tafi ya ce" Khadija please take good care of my baby, ba na son komai ya samu cikin nan I'm telling you. Abinci ki yi mai sauki" "In Sha Allah" da haka na rako shi wurin mota, hade da bude mishi gate ya fita. Bayan fitarshi aikin hada turarena na shiga yi, ina tsaka da aikin ne Maman Aiman ta shigo, don haka mu ka ci gaba da yi tare da ita muna hirar duniya. Akwai humra, da kuma su roll on kananu masu taushin kamshi da kuma masu karfi irin na maza. Sosai Maman Aiman ta rika yabawa da turarurukan, ita ce ma ta dauki hotunansu ta daddora a status tana min talla. Tun kafin ta fita na ga mutane na ta tambayarta nawa, kuma a ina za su samu. Abun ya yi min dadi, na rika addu'ar Allah dai ya sanya min albarka a abun. Ragowar abincin break fast din mu na ci, na yi sallahr azhur na kwanta bacci, Sai la'asar na farka, shi ma Assidiq ne ya tashe ni, ruwan zafi na fara dorawa, sannan na yi wanka hade da yin alwala na yi sallahr la'asar, bayan na idar na yi azkhar dina, na yi wa Assidiq wanka, na shirya mu gabadaya, zuwa lokacin kam har farar taliyar da na dora ta dahu, na yi mana souce din cabbage. Na shirya a dining, saboda na san nan da 30mns, da maigidan da yaran gidan duk sun dawo. Bashir dai 5:30pm ya dawo, su Affan ne sai 6pm,saboda makarantar hade take da Islamiya. Haka dai rayuwa ta ci gaba da juyawa cike da farin ciki, saboda zamana a sabon gidan nan, farin cikin da nake samu da kulawar da nake samu, ban same ta lokacin da nake amarci ba. Shi ya sa lokaci kankane na yi haske hade da yin ƴar ƙiba, musamman da ya kasance akwai yaron cikin. Bangaren sana'a kam, a hankali Maman Aiman ke kawo min customer na cikin unguwa da wajen unguwa, ni ma kuma Ina samun nawa, haka na matsa sai da Maman Hana ta rika yi min talla a wurin aikinsu, nandanan idan na hada turare ya kare, tun ina sawo kayan hadi kadan, har na fara sawo da yawa. Bashir ma yana dibar na maza ya tafi dasu wurin aikinshi, kuma sosai saye ake yi, wani lokaci har nema ake yi. Kila dalilin hakan ne ya sanya shi ba ni jarin miliyan daya, wai in gwada saro atamfofi da rigunan yaran mu gani, idan komai normal sai ya kara min. Ranar farin ciki hana ni bacci ya yi, da safe kam na kira Ummata na fada mata, ta ce za ta hada ni da wani mai irin sana'ar a kwari. Aiko a waya muka gama komai, ya turo min kaya latest, ni kuma na tura mishi kudi, yanzu din ma dai Maman Aiman, Maman Hana, Bashir sune ƴan tallata, atamfofi da rigunan yaran basu tafi kamar turare ba, don sai da suka yi sati jibge babu wanda ya saya, har na fara karaya, na fadawa Ummata da Bashir. Sune suka rika karfafa min gwiwa a kan kar in damu za a saya. Sai da kayan nan suka yi sati biyu, sannan na fara ciniki, shi din ma bashi, wai karshen wata, abu kamar wasa, kasuwancin atamfofin ya koma za a dauka amma sai karshen wata kudin . Cikin sati biyu komai babu, har ana nema, haka Bashir ya kara min 500k na karo, cikin sati su ma suka kare, inda Allah Ya taimake ni satin karshen wata ne. Na zauna zaman jiran tsammani. Sai dai karshen wata na yi na fara jin alert, wadanda suka dauka kadan take suke biyana, wadanda suka yi siyayyar 150k,sune ke ba ni rabi, ko 100k,wasu kuma duk suke biyana, cikin sati da salary kudin dakko wasu kayan suka hadu. Wani irin farin ciki nake ji babu misultuwa. Daga lokacin kasuwancin atamfofi ya koma na ƴan albashi. Za a dauka, wata a hada min kudi, turaren ma ana daga kafar sati. Na yadda, idan mutum na taba kudi, ba komai ne ke ɓata mishi rai ba. Kamar ni yanzu ba komai ke ɓata min rai ba. Duk tunanina a kan yadda zan inganta kasuwancina ne. Kuma Alhamdulillah kullum gaba nake ci ba baya ba. Assidiq dole na yaye shi da shekara daya, saboda ciki ya fito sosai, yana neman wata takwas. Na sha rigima sosai, ko in ce ina kan sha, don ma su Affan na hutu, suna janye min shi. Matar J ✍🏻 [12/23, 12:55] 08080966571: *HASASHENA* *Page 31* Yau kam Murja na turawa kaya zuwa Ruma ta hanyar Bashir da ya shirya zuwa shi da yara wai weekend hatta Assidiq ba a bar min ba. Gidan shiru ba kowa, bayan duk na gama ayyukana, na shiga gidan Maman Aiman, a can na samu Maman Hisham, daya makociyar tawa, aiko mu ka zauna hira, Sai 6pm na baro gidan ganin magriba ta yi. Ina isowa gida na yi alwala don yin sallahr magriba. Ina raka'ar karshe na ji cikina ya yi wani irin juyi, kamar an sanya hannu a juya shi da karfin tsiya. Kafin daga bisani na ji marata ta daure gam, dakyar na dago, ba zan iya cewa ga abin da na karanta atahiyar nan ba. Ni dai kawai na farka, na ganni kwance saman sallaya, kafin kuma in kara yin wani yunkuri wani ciwon ya kuma tashi. Wani zufa ya rika lullubeni, yayin da wani ruwa ke bin kafafuna, cikin 5mns na ji kukan jariri, ganin abun nake kamar mafarki, wai na haihu cikin 30mns. Daga kwancen da nake na janyo wayata da ke saman gado, na kira Maman Aiman na ce ta zo na haihu. Yadda take dariya na san ba ta yarda ba, ga shi na rufe gate, babu yadda za ta iya shigowa ni kuma ban iya fita, saboda uwa ba ta biyo, ba ta kara gasgata na haihun ba, Sai da ta nemo namiji ya duro gidan ya bude mata kofa. Mamakin haihuwar take yi ba kadan ba, Maman Hisham ta kira, suka gyara yaro da ni, da tsakar ɗakin, bayan an rage kazantar jikinta. Sai da komai ya zama normal sannan na kira Bashir na fada mishi cewa na haihu, na samu Baby boy. Shi din ma bai yarda ba, Sai da na tura mishi hoton Baby, haka na rika kiran mutane ina shaida musu na haihu. Ummata murna ba a magana, haka Yusrah da su Badiyya kawayena. Karfe biyu kam na safiyar Asabar Bashir na a gate din, tare ya taho da Jamila kanwarshi, yara tsalle, da murna sun yi kane, Maama kam fushi take yi, wai mace take so. Ni kaina macen na so, ina son in samu Ramla. Yarinyar na raina. Haka na rika amsar yan barka, musamman customers dina, Ana gobe suna yan Kano suka iso da yan Ruma, gida ya cika taf, musamman ranar suna, ban taba haihuwar da na tara mutane gami da samun abun arziki ba kamar haihuwar Aliyu Haidar. Tabbas ya zo min da goshi, Sai godiya kawai. Raguna biyu Bashir ya yanka min, washegari aka suya hade da rabawa makota, da duk wanda yake da rabo, ranar lahadin gidan ya koma namu, saboda a ranar Jamila da Yusra kanwata suka tafi, yayin da Bashir ya dakko min wata yarinyar mace, za ta 45 years, sunanta Uwani, wai mijinta ne ya rasu, ya bar ta da yara hudu, ita ce ke taimaka min da aikin gida, za ta zo safe, ta tafi bayan magariba. Duk wata muke biyan ta. Ina jin dadin zama da Uwani sosai, mace mai kawaici, mara kiwa ga tsabta da taka-tsan-tsan. Ga hak'uri da yara, ba ta da saurin hasala. Har kayan siyarwa ta take dauka zuwa unguwarsu, idan ta siyar in sammata wani abu, aikin hada turare duk tare muke yi. Yau ma da ya kasance Asabar Bashir tun safe ya tafi Ruma, wai za a yi mishi sharar gona. Gab magriba muna zaune a falo Uwani na zuzzuba turaruka a mazubi ni kuma ina ba Haidar nono mu ka ji horn din Shi. Kasancewar akwai yara a waje, shi ya sa ban damu da ta shi in bude mishi gate ba. Tare suka shigo da yaran, suna ta murna, Uwani ta fara tattare kayanta bayan ta yi mishi sannu da zuwa, shi kam sama ya hau da yaran shi, ni kuma sai da Uwani ta taya ni kintsa wurin, sannan na bi bayan shi. Haidar ya fara dauka yana fadin "Zakina, yau ba kuka?" kamar ya ji abin da ya ce, ya wangale mishi baki Bayan yaran sun fita ne na ce "Sannu da dawowa, ya hanya, ya ka baro su Inna" "Duk suna lafiya Hajiyar kamshi (haka yake kirana idan yana jin Nishadi) duk suna gaishe ku" "Muna amsawa mun gode" Wanka ya shiga shaf-shaf ya fita zuwa masallaci shi da yara. Sai da aka yi sallahr isha'i sannan suka dawo, aka hau dining, dukkanmu cikin Nishadi. Zuwa 10pm yaran sun yi bacci, daga ni sai shi da kuma Haidar wanda yake shirin na shi baccin. Shi kuma Bashir lissafin abin da gona za ta ci yake yi. Bayan ya kammala rubuce-rubucen ne ya ce "Khadija an kai min kudi gidansu Saratu" Jin maganar na yi wata kala, na rasa menene ma kai kudi yake nufi, shi ya sa na ce "Wane irin kudi?" "kudin aure" ya ba ni amsa kai tsaye Ilahirin jikina babu inda bai amshi wannan sakon ba, na rika kokarin danne shock din da na ji, dakyar na daidaita na ce "To Allah Ya tabbatar da alkairi" "Amin" ya amsa hade da shiga wata sabgar ta shi. Ni kuma na yi shiru, zuciyata na harbawa da sauri, na rasa a wane yanayi nake, a haka na kwantar da Haidar, ni ma na lallaba na kwanta, duk yadda na so in ba Bashir hadin kai wajen biyan bukatarshi sai na kasa, jikina sama baya responding stimuli din, hakan kuma bai dame shi ba, bukatarshi na biya ya hau bacci, ni kuma baccin ya kauracewa idanuna. Na ɗauka tun da Sarai ce ba zan damu ba, yarinyar da na fi ta komai, kamata ya yi ace na godewa Allah za kawo min yar kauye mara wayewa, amma duk sai na ji na kasa aminta da ita din ta yi karama. Har 2am idona biyu, gab asuba bacci ya dauke ni, shi ya sa har Baban Khalil ya dawo masallaci ban tashi ba, shi ne ya shiga kitchen ya fara dora abin break kafin ya dawo ya tashe ni. Dakyar na iya yin sallah, bayan na idar na nufi kitchen kafin Haidar ya tashi. Koda ya tashin ma Bashir ya ci gaba da kula da shi, har na kammala break fast, na dauke shi na yi mishi wanka hade da ba shi nono. Haka nan nake cin abincin ba don ina jin dadinshi ba, amma Sam babu test, ina tsaka da juya doyar da na gutsura a bakina kiran Saratu ya shigo wayarshi. Saboda da sunanta ya yi saving, ni kaina a baya can da Khadija ya yi saving lambata, Sai daga baya ne ya sanya Auntyn yara. Sosai sunan ke ban dariya, wai Auntyn yara, kamar wata yar aiki. Bayan ya daga wayar ne ya ce "Lafiya kalau, Alhamdulillah" Ban san me aka ce a wancan bangaren ba na ji ya ce "Ok, wata biyun ya yi daidai, Allah Ya nuna mana lokacin." Ya kara yin shiru kafin ya ce "Hakan ya yi miki, ba na son kananun maganganu" Wani shirun ya kara yi kafin ya ce "To shi kenan, zan kara miki 50k a kai, kin ga ya zama 150k kenan" Ya yi shirun kafin ya ce "Ok, Sai an jima" Daga haka ya yanke wayar hade da kallo na yana fadin "Saratu ce, dama ana bayar da kudin lefe ne, maimakon a yi lefen?" Wani abu ya tokare min kirji, dakyar na kawar da shi da fadin "Eh, idan haka amaryar ke ra'ayi" "To ai ba na son kananun maganganu ne, ta ce a ba ta 100k,na kara mata 50k na hidimar biki hakan ai ya yi ko?" Wani yawu na haɗiye dakyar kafin na ce "Eh ya yi sosai ma. Allah Ya kara budi" "Amin." ya amsa kafin ya dora da "An sanya bikin wata biyu, kin ga lokacin yara na cikin hutu ma" Yanzu kam ban yi magana ba, ban san dalilinshi na yin hirar bikin shi da ni ba, da ya san yadda nake ji, da ya kyale ni. "Yaran kin nan, ko wannensu zan ba shi 100k ki yi mishi siyayyar cin biki" ya dora daga inda ya tsaya "Sun gode sosai, Allah Ya kai mu lokacin" "Amin" ya amsa kafin ya ce ke kuma "500k za su ishe ki ko?" Mamakin yadda yake ta lissafin nake yi, ko a jikinshi sai raba kudi yake yi, wai shi zai yi aure. A, sanyaye na ce "Za su ishe ni. Allah Ya saka da alkairi" kai karshen maganar tawa ya yi daidai da shigowar alert din 1million. Ya kuma cewa "Idan ba su isa ba, Sai ki sanar min" "To" na kuma cewa, shi kuma ya mike yana fadin "Bari in shirya zuwa kasuwa, akwai wasu kaya da za a kawo min daga wani kauye" Komai ban ce ba, shi kuma ya haura sama, na dade zaune a wurin ba tare da na san abun yi ba. Har sai da na ji takunshi alamun yana sakkowa, sannan na fara tattara kayan kan dining, da shi ke yara sun tafi Islamiya. Yau kam ko rakiya gate din bai samu ba, yana fita kuma Uwani ta zo, ragowar break fast din na ba ta. Ta ci wanda za ta ci ta ajiye wanda za ta ajiye. Tare muka gyara gidan tsaf, sannan muka dora a kan aikin jiya na zuzzuba turarurruka. Muna aikin ne ta ce "Auntynmu yau kam ba kya jin dadi ko?" Kai na cira a hankali ina kallon ta kafin na ce "Me kika gani?" "Na ga kin yi shiru ne" Yaƙe na yi kafin na ce "Kaina ne ke dan ciwo" "Haba koda na ji, ai shirun naki ya yi yawa. To ki je ki huta ki bar min aikin na karasa" "Zan iya kar ki damu" na yi maganar a kokarina na danne damuwata. Haka mu ka yi ta hidimar gidan har yara suka dawo. Bashir kam sai 8:pm ya dawo. Abu kamar wasa, ba na iya bacci, idan na samu na yi baccin da wuri, can dare sai in farka, kuma ban kara komawa, wani lokacin kuma sai can gab asuba baccin ke dauka ta, abinci ba na jin dadin shi, cikin sati na fara zubewa, yar ƙibar da na yi ta fara bin iska. Ga shi na kasa fadawa kowa a ƴan'uwana wai Bashir zai yi aure, hatta Ummata ban fadamawa ba. Ni kawai nake dakon abun a zuciyata. Shi ya sa kila nake ta karewa kamar kudin guzuri. Wani lokaci har jiri nake ji. Yadda zan bude bakin in fadi cewa Bashir zai yi aure ne damuwata, Sam ba ni da courage din Yau kam da yamma Uwani na tura kasuwa siyayyar kayan hadin turare, yayin da ni kuma nake zaune a gida ina lissafin kudin kayan da za a kawo min, kasancewar an yi salary duk an biya kudina. A haka Maman Aiman ta shigo ta same ni. Bayan mun gaisa ne na ce "Waye ya bude miki kofa?" "Lawal ne, da yake ban ruwan fulawa. Na ga gwaibarku har ta fara haihuwa" Ban dago daga rubutun da nake yi ba na ce "Ai tana samun kulawa, kullum Lawal sai ya ba ta ruwa safe da yamma" "Ai kam tana ta kyau, matar gidan kuma na ta lalacewa" Da sauri na dago kai ina kallon ta alamun mamakin maganarta kafin na ce "Ban gane ba" "Ai ba za ki gane ba, amma wannan ramar ta ki, ta fi karfin karayar tsotso Maman Maama." Idanuna na lumshe, yayin da nake jin wani zafi a kirjina, komai ban ce ba, na duka hade da ci gaba da rubutuna. "Barin kashi a ciki baya maganin yunwa, ba ki sani ba, ko ina da maganin matsalarki" Daga duken da nake na ce "Ba ki da ita" "Me ya sa?" "Saboda haka ne Maman Aiman, ni kaina ban son damuwar da nake yi, saboda bai kamata ace na damu har haka ba, amma na kasa." Komai ba ta ce min ba, ni ce na ce mata "Abbansu Khalil ne zai yi aure, ina jin idan Asabar din ta zo saura sati biyar" Cikin kwalo ido ta ce "Aure!" "Yadda kika ji" "Tabbb!" ta ce hade riƙe baki, ba tare da ta ce komai ba. Ni ce na kuma cewa "Tun ina Ruma suke tare da yarinyar, bazawara ce, mijinta ya rasu, Sai kin ganta, ina jin ko sunanta ba ta iya rubutawa ba." "Ki ce min masu wahalar kishi?" Cike da faduwar gaba na ce "Me ya sa kika ce haka?" Ta ce "Raba kanki da kishi da jahilar mace, na yi ban ji da dadi ba wlh. Su da asiri suke takama, kishi da asiri kuma Sam bai yi ba" Gabana ya ci gaba da faduwa ras! Ras!! Ras!!! Kafin in ce wani abu ta dora da "Tun ba ƴan kauyen nan ba, sun san kusfa-kusfa inda Malamai suke, wlh ki yi ta addu'a" Cike da sanyin jiki na ce "Haba Maman Aiman, kin tsorata ni fa" "Gaskiya na fada miki ba zuga ba, kin san an ce ruwan da ya dakeka shi ne ruwa, ki tambayi mutanen unguwar, wlh da muka kwaso kokawa daga cikin gida har wajen gate. Duk shuruna, Sai da matar nan ta koya min bala'i" Yanzu kam dariyar karfin hali na yi ina fadin "Kai Maman Aiman. Kokawa kuma" "Yasin kuwa haushi ta ba ni. Amma ki kwantar da hankalinki wlh ki daina saka damuwa, kishiya ba ta da wuta ba ta da aljanna. Iyakaci idan ta ce zaman lafiya kuyi, idan ta ce tashin hankali ku fara daga nan har birnin Sin" Wata dariyar na kuma yi, ko ba komai sai na ji wani kaso na damuwata ya ragu, duk da ba maganin abun Maman Aiman ta yi min ba. Har Uwani ta dawo hirar kishiya muke yi, irin zaman da ta yi da tata, ni ma ina fada mata irin zaman da na yi da Maman Khalil, zama mai dadi da tsafta. Matar J✍🏻 [12/23, 14:12] 08080966571: *HASASHENA* *Page 32* Maman Aiman ce ta ba ni kwarin gwiwar faɗawa ƴan'uwana, Abban Khalil zai yi aure, kowa dai hak'uri yake ba ni, da kuma fada min in kawar da kai, hatta kawayena Samira da Badiyya abin da suka fada min kenan, Sai kuma alkawarin da suka yi min na za su zo biki. Ummata ma da Yusrah kwantar min da hankali suka yi, hade jaddada min in yi ta hak'uri. Wannan ya sa wani kaso na damuwata ya kara raguwa. Saboda na fahimci dole sai na yi hak'urin,wani lokaci Sarai ba ta tashi kiran Bashir sai yana gida, kila kuma coincidence ne oho. Shi kuma baya jin nauyin dagawa, Sai dai ni idan abun ya ishe ni in tashi in bar wurin. Tursasa kaina kawai nake yi, a kan danne kishina, amma abun ya ci tura, kullum jikina nunawa yake yi. Is not easy handling din wannan situation din. Akwai matukar wahala wajen jiran shigowar kishiya. A lokacin na san lallai Maman Khalil ba karamin hak'uri ta yi ba. Ai koda wannan fargabar a ka bar mutum na jiran shigowar kishiya ya ishi mutum. Abin da na fahimta kawai kishiya, kishiya ce, ba ta da gaba bare baya. Ba ta a farko kuma ba ta a karshe. Idan ke ce farkon za a karo miki wata sai kin ji babu dadi, idan taraswa za ki yi nan ma dai hakan ne. Babu abu mai sauki. Ana saura sati hudu biki Bashir ya fada min wai a cikin satin Saratu za ta zo ganin gida. To kawai na ce. Maman Aiman kawai na fadamawa, ta ce eh ana yin haka, Sai na dan rage damuwa. Ranar Asabar ta zaba a matsayin ranar da za ta zo, tun juma'a Abban Khalil ke maganar, safiyar Asabar din ma, bai bar ni na huta ba, haka ya dame ni fa zuwan Saratu har su Khalil ya fadamawa, wai sabuwar Auntynsu za ta zo. Son barka ba su yi maraba da abun ba, tun ba Affan ba, gara ma Khalil ya na ce da tambayar wacece. Bare Maama da ba ta ma fahimci ina zancen ya dosa ba. Abban Khalil bai tsaya iya nan ba, har Uwani ya fadamawa da ta zo aiki da safe, wai a yi abinci special akwai baki. Wannan abu ba karamin kona min rai ya yi ba. Saran kamar wata queen Elizabeth. Bayan ya fita ne Uwani ta ce "Auntynmu me za a girka, na ji yallaboi ya ce akwai baki" "Tuwo" kai tsaye na amsa mata "Wane iri?" ta kuma tambaya, na dan yi shiru kafin na ce "Ayi na shinkafa miyar ganye" "Dole sai an je kasuwa ai, lokaci bai kure?" Na kuma yin shiru kafin na ce "To a yi miyar wake, tun da akwai ganyen ugu a gida." Da to ta amsa. Komai ban taya Uwanin ba, na haye sama da Haidar na kyale ta. Sabanin baya da muke girki a tare. Misalin 1pm Bashir ya kira ni, wai a bude musu gate gasu nan. Ban amsa ba kawai na yanke kiran, Sai da na ji horn din motarshi, sannan na sakko kasa na cewa Uwani ta bude musu kofa. Cikin falo na zauna, saitin windown da ke hango min farfajiyar gidan. Ina daga zaune na ga fitowar Sarai, cikin wani lace coffee color, dinkin riga da zane, ta yafa gyale golden jaka da takalmin ma duk golden ne, ba dressing dinta kawai ne ya ban mamaki ba, har da yadda ta yi wani haske hade da yin kina mai kyau, kasancewarta gajera ba ta faye tsawo ba, hips din nan ya fito sosai. A zuciyata na ce "Dole Bashir ya rude, yana kallon wannan cikar, lallai ba zai zauna lafiya ba, amma yaushe yarinyar nan ta yi wannan kibar, da wannan uban hips din, ga wani haske. Tabbb! Ikon Allah kenan" na karashe maganar zucin hade da rike habata alamun mamaki Ban san me suke cewa ba, amma dai na ga Bashir ya koma cikin mota ya dakko key hade da bude mata gudan part din nan mai kallon yamma. Bayan shigarsu ciki ne, na sake labulen hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya ina fadin "Wayyyo Allahna ni Khadija. Ashe haka Maman Khalil ta ji da za a kawo mata ni, har nake cewa da ma ni ce ta taras. Baiwar Allah ashe ba karamin hadiya ta yi ba. Don Allah Sakeena ki yafe min?" na yi maganar hawaye na son taruwa a idanuna. Da sauri na mayar da su ina fadin" No! No!! No!!! Khadija kada ki yi kuka, waccan yarinyar ba ta kai matsayin da za ki yi mata kuka ba." Ina zaune a wurin Bashir ya shigo, kallo daya na yi mishi na kawar da kai, shi ne ya ce min" Khadija baƙi sun iso" "Eh na ji su, sannunsu da zuwa" Baki ya washe kafin ya ce "Ba za ki je ku gaisa ba" Da sauri na mayar da kallo na kanshi, kafin na ce, ban gane in je mu gaisa ba? Kamar ya in je mu gaisa, ba sune suka same ni a nan ba, ai kamata ya yi su fara zuwa nan kafin su shiga ko ina" Dan shiru ya yi kafin ya ce "Kuma fa haka ne, to ina zuwa." Ni dai komai ban ce ba, ya ja shagidaddar kafarshi ya fita. Ina jin shi yana cewa Uwani ta kai musu abinci. Kamar mintuna biyar Uwani ta shigo, kallon ta na yi, ina fadin "Kin kai musu abincin?" Cike da girmamawa ta ce "Eh" Har za ta fita kuma, sai ta dawo ta ce "Auntynmu kar ki ce zan yi gulma fa" Kallon ta na yi ba tare da na yi magana ba, hakan ya sa ta ce "Wai ita waccan din wacece, na ji Alhaji na ta fama da ita, ta zo ku gaisa, amma wai ta ce ke ya kamata ki je ku gaisa, tun da su baƙinki ne" "Kan bala'i! Haka ta ce?" na yi saurin katse Uwani Kai Uwani ta gyaɗa alamar eh. Wani murmushin takaici na yi kafin na ce "Aiko koda ubanta take yawo a zariyar wando, wlh ba zan je in gaishe ta ba. Yau za ta ga sarautar uwargida. Ai idan dai amarya ba ta hau doki ba, to kuwa bai kamata a dora mata kaya ba" Kallo na kawai Uwani ke yi, jin tahowar Bashir ya sa ta nufi kofar fita. Ni kuma na hade fuska ina tattaba wayata, yadda ya yi tsaye cikin rashin sanin abun yi ne ya sa na ce "An kai musu abincin?" "Eh" ya amsa min, kafin ya zauna kujerar da ke fuskantata ya ce "Saratu ta zabi wancan part din" "Shagalinta" na fada cikin ko in kula, kuma har zuwa lokacin ban kalle shi ba. Ya kuma cewa "Khadija bakonka Annabinka, ki je ku gaisa da yaran nan, wai su kunyarki suke ji" Wani kallo na yi mishi kafin na ce "Kunya! Wace irin kunya kuma? Sai yau ne suke jin kunyata, a Ruma sau nawa suna zuwa wajena, ni ba na son gulma da munafurci." "Haba me ye kuma ya kawo wannan furucin?" ya yi saurin tara ta "Ga abin da ya kawo shi nan, dama fa ba wurina suka zo ba, idan sun yi abin da ya kawo su kawai su tafi, ni ba ni da case da su. Basu ji kunyar zuwa gidan ba, Sai kunyar zuwa gaishe ni." na karasa maganar da jan siririn tsoki "To tsokin na waye?" ya tambaye ni yana dan hade fuska. Maimakon in amsa mishi, mikewa na yi, kawai na nufi stairs, don Ina jin kila ma Haidar ya tashi. Ban san lokacin da ya bar falon ba, kuma tun da na hau saman ba sakko ba, Sai da Uwani ta sanar min sun tafi kafin na dawo falon. A zuciyata nake fadin "Ka ji min kilbabbar yarinya, yau wata gulma ce ta tashi, da ni ce zan je in, gaishe ta, ai uban kuturu ma ya yi kadan bare na makaho. In ji yara" haka nan sai raina yay ta baci, abincin ma kasa ci na yi. Sai da yara suka dawo sannan na dan warware. Shi kam bai dawo ba sai bayan sallahr isha'i. Na hade fuska kam, don ma Kar ya ce zai min wani sharhi. Saboda a sama nake ya hancin gauta, yana taba ni, zan fado kanshi. Ana saura sati biyu biki na zabar mana shadda mai kyau, mu dukkanmu iri daya, sannan na zabi lace, atamfa kala biyu lace ma kala biyu, wa mu matan bayan shaddar. Mazan ma na kara mu shadda kala daya, da yadi masu kyau kala biyu. Sannan na sawo musu yan kanti, da takalma kafa hurhudu da huluna. Sosai na kashe mana kudi, kuma babu wanda na nunawa Bashir, shi din ma bai tambaya ba, harkar bikinshi kawai yake yi, abun da yake bata min rai kenan. saura sati daya aka, zo aka kara fente gidan tas, har da part dina, abun mamaki sai Bashir ya ce a kwashe kujeruna, wai canja min za a yi. Saura kwana uku daurin aure sai ga kujeru, masu kyau da tsada yan waje, aka kara canja min tv wacce ta fi waccan girma, da kuma labulaye. Ni kaina dakin ya yi min kyau sosai, duk da zuciyata babu dadi. Ana saura kwana biyu daurin aure muka fara karbar baki, part din nan daya aka bude yan Ruma da dangina, kasancewar akwai dakuna da yawa a ciki, kuma akwai toilet a ciki. Makotana ma suna da lekowa don ganin ko akwai ayyukan yi. Bangarena kam, ba zan iya misilta yadda zuciyata take ciki ba, komai baya min dadi, musamman idan na kalli Bashir yana ta rawar kafa, in ji kamar in rufe shi da duka Har wani gayyar abokanshi na Abuja yake yana washe baki kamar bai taba aure ba. Sosai nake jin tausayin Sakeena idan har haka ta ji a lokacin da Bashir zai aure ni, lallai ta yi ta ji babu dadi sosai , kuma ta isa gwarzuwa, Sai dai in ce Allah Ya kai haske kabarinta, ni kam ba zan iya irin hakuri da kawar da kan da ta yi ba. Saboda dole ce kawai ke hadani magana da Bashir, dolen ma idan na jefa daya biyu, sai kawai in yi shiru. Shi din ma bai kula ba, hidimarshi kawai yake yi. Abin da ya fi kular da ni. Ana gobe daurin aure ya tafi Ruma, wai za su yi party a ranar da yamma washegari kuma za su taho da amarya bayan an daura aure. Jin abun nake yi kamar mafarki, wai za a yi min kishiya, ranar kam ban warware ba, Sai da su Yusrah, Samira da Badiyya suka zo, ga makotana sun cika gida, ga su Maman Hana da Umaima, ai fa sai na sake aka yi ta sha'ani, magriba gidan ya koma shiru. Uwani ma ana yin isha'i ta tafi. Ranar kam an sha hira, labarai da suka shafi kishiya nai ta ji mai dadi da mara dadi, a nan na kara fahimtar lallai kishiya kala-kala ce, kowa da irin ta. A wannan karon ko da wace kala zan hadu oho. Safiyar daurin aure dama ba zama, abincin da za a kai aikatau aka kai, wanda kuma za mu yi a gida aka fara. Zuwa 12pm mun kammala duk wani abincin da za a ci, wanda aka kai aikatau ma an kawo. Daya part din duk muka kintsa kayan abincin, sannan aka shiga gyaran gida, ko ina ya yi fes, kamar ba biki ake ba, part dina su Maman Aiman suka rufe bayan an gama gyarawa muka koma dayan part din. Dama tun 12pm abokan Bashir suka tafi da Affan, Khalil da Assidiq Ruma, wai daurin aure. Wajen 3pm na fito fes cikin irin shaddar da su Assidiq suka sanya da za su tafi, haka Maama ma, hatta Haidar irin ta ce, light make up aka yi min, sosai na yi kyau, musamman kunshi da kitson da aka watsa min ya kara fito da fatata mai haske. Su Maman Hana ne, suka matsa lallai sai a dakko Dj, zuwa karfe hudu kuwa, Dj din ya gama decoration din gidan, an kafa runfuna, ga manyan speakers masu duka. Gida a cika makil da mata yan gayu masu aji da ji da kansu, kuma wai don duk ni suka taru. Sai na ji zuciyata wasai, duk babu wannan tarin damuwar. Tun ba da sauti kida ya fara tashi a tsakar gidan ba, nan da nan mata suka cika fili ana rawa, kun san ƴan Katsina da rawa dai 5&6 ne. Ai tun ina yin bayan fage na shige tsakiyar fili aka rika takawa da ni. 5pm amare da angwaye suka iso. Tare da wasu dangin Bashir da na Maman Khalil. Yadda dangin amarya ke nuna ni sai na ji ni a sama uwa hula, saboda zame masu na yi kamar wata a tsakiyar taurari, wannan ya tuna min lokacin da aka kai ni Abuja. Dangina suka ci karo da Maman Khalil mace mai matukar kwarjini da iya ado, ga wani sassanya kyau, tana cikin kawayenta wayayyu ƴan gayu. Haka dangina suka rika bin ta da kallo cike da tsoro gami da fargabar yadda zan zauna da ita. Saboda dai babu wani abu da zan nuna mata, to irin wannan kallon dangin Saratu ke yi min. Ita kam wucewa aka yi da ita lullube zuwa dakinta. Ni kuma na shiga hidima da bakina da suka iso yanzu. Ga Affan yana ta bi na uwa jela ran nan a bace, na rasa abin da ke damunshi, na ce zai ci abinci ya ce kuma a'a Kaya ma su Khalil duk sun kara canjawa, amma shi bai canja ba. "Wai wannan me yake so ne, yake ta bin ki kamar bindi?" cewar Hadiza kanwar sannu Sakeena Na juya kan Affan ina kallon shi kafin na ce "Wlh ban sani ba, na ce ko abinci ya ce a'a." "To ai wannan baƙin ran tun da suka isa yake yin shi, a can din ma ko ruwa bai sha ba. Kuma ya ƙi yi wa kowa magana" cewar Murja da take cin abinci. Aunty Habi ma da take shigowa ta ce " Ni ma tun da ta shigo na tambaye shi ko ba shi da lafiya amma ya yi shiru" Duk maganganun da ake yi yana ji komai bai ce ba. Kuma har lokacin gefen doguwar rigata yana rike a hannunshi, kamar na ce zan gudu Bayan na sallami duk wadanda suka iso da abinci, ba wai iya bakina ba, har dangin Saratu, Sai da na tabbatar an kai musu komai, kafin na ja Affan zuwa sama. Gefen gado na zaunar da shi, ina fuskantarshi kafin na ce "Babban masoyina ya aka yi? Me kake so? Wa ya taba ka? Fada min" Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Na kuma cewa "Ko dinkin ne bai yi ma ba?" Kai ya girgiza alamar a'a Murmushi na yi kadan kafin na ce "Mutane sun cika gidan ko?" Kai ya daga alamar eh. Bayyanan nen murmushi na yi, saboda tun da naga yana ta kumburi na san mutanan ne suka yi mishi yawa. Shi bai son hayaniya, baya son ya ga ana taro a gidansu. Gefenshi na zauna cikin sigar lallashi na ce" Ka yi hakuri Affan, daga gobe kowa zai watse ka ji ko" Kai ya jinjina, kamar ba zai yi magana ba, Sai kuma ya ce "Auntynmu wai Abbanmu aure ya yi?" Wani abu mara dadi ya taso daga a kirjina, a hankali na daga mishi kai alamar eh. Saboda ba zan iya magana ba Rai ya kuma ɓatawa kafin ya ce "Amma ba a nan gidan za ta zauna ba ko?" "A nan za ta zauna mana Affan, ba ka ga an kai ta dakinta ba" Fuska ya kuma hadewa ya ce "To ni dai ba zan zauna da ita ba, Sai dai in koma wurin Inna ko wurin Momyn su Affan idan sun dawo daga tafiyar da suka yi" "Za ka ci abincin ko?" na kawar da waccan maganar, saboda kara tayar min da hankali yake yi Kai ya jinjina alamar eh. Waya na dauka hade da kiran Yusrah na ce ta kawo min abinci Affan zai ci. In less than 5mns Sai ga ta dauke da abincin, hannunta daya kuma rike da Haidar. Abincin ta ajiyewa Affan, ni kuma na dauki, Haidar da zummar ba shi nono, saboda daga bacci ya tashi. Bayan na ba shi nono, aka kira min mai kwalliya, ta dan kara gyara min kwalliya, na dora wani farin lace mai golden a jiki, haka ta yi min dauri mai kyau. Ni kaina na san na yi kyau. Haidar kuma na canja mishi kaya zuwa yan kanti masu kyau irin wanda Assidiq da Khalil suka sanya. Shi ma Affan irin su ya sanya bayan ya gama cin abincin. Na dauki lace din Maama na sauka zuwa kasa, don in canja mata. Lokacin da na sauka filin tsakar gidan ya kara cika, dangin amarya ma sun bi layin yan kallo. Tun da Mc din nan ya hango ni, aka canja waka zuwa "Uwargida ran gida..." Ai ni da kaina sai na ji takuna ya canja, kamar wata sarauniya ta gaske, tun daga wurin kuma kawaye da abokan arziki suke zuba min kudi har cikin fili, ana ta rafka guda. Takun rawa nake na kasaita ana dauka ta video ga kudade ana ta zuba min. Dangin amarya sai kallo da rike haba, ana gulma.... Matar J ✍🏻 [12/23, 14:57] 08080966571: *HASASHENA* *Page 33* Daga lokacin da Bashir ya fada min ya kai kudin aure, ban taba jin wata rana da na yi nishadi da farin ciki kamar wannan ranar ba. Jin zuciyata nake wasai kamar an yi min sharar bakin ciki. Shi ya sa da dare na sha bacci sosai, dama ga gajiya, dakyar na tashi da asuba, na yi sallah muka shiga hidimar abun kari, su Affan na fara sallama, saboda Babansu ya ce su tafi Islamiya, ai an gama biki. Sauran mutane kuma zuwa karfe tara mun sallami kowa da abun kari. Zuwa shadaya kuma baƙi duk sun fara watsewa, musamman dangin Bashir da ƴan'uwan Sakeena wadanda suka yi mana kara. Wadanda suka rage daga Samira, Badiyya, Yusrah, Goggo Saude, Aunty Na'ima da Maryam. Su kuma duk a bangarena suke. Sai Murja da ba ta bi 6an Ruma ba, saboda za ta shiga cikin gari. Ina zaune a falo bayan na yi kintsa kaina cikin atamfa doguwar riga da ta sha stone work Ina ba Haidar cerelac Murja ta shigo. Bayan ta zauna ne ta ce "Uwargida ana can an fama da amaryarki, ta zo ku gaisa ta ki" Baki na tabe ba tare da na ce komai ba, saboda ni ban san irin wannan sabuwar tsirfar da take yi ba. Matar da take zuwa har dakina, amma yanzu ta zo da sabuwar gulma. Ni dai ta kan maganar ma ban sake bi ba, su Yusrah ne ke ta tattauna maganar. Misalin sha daya su Samira suna shirin tafiya dangin amaryar suka shigo, amma babu amaryar. Tun da suka shigo idanunsu a ko wace kusurwa ta dakina, tun jiya suke zuwa min kallon kurillar daki suna kus-kus. Yanzu din ma muna gaisawa suna karewa dakin kallo, a haka mu ka yi sallama, suka tafi, ni ma na saka hijab di ta don yi wa su Yusrah rakiya zuwa tasha. Ban baro tashar ba sai da naga motarsu ta tashi, shi ya sa ban dawo gidan ba sai sha biyu saura. Da yake na bar Uwani ban damu ba, na san za ta yi komai kafin in dawo. Lokacin da na dawo har ta sauke farar shinkafa, saura miya. Shi ya sa ina sauke Haidar, ban huta ba, na shiga kitchen. Don taya ta sauran ayyukan. Har muka gama komai Uwani ta kai mata abinci ban ji motsin ta ba, kuma ban lekata ba, saboda tun da aka kawo ta, kafata ba ta taka ko entrance dinta ba. Ni da ita zan ga wanda ya taras da wani. Around 2 mun gama komai ni da Uwani, dalilin da ya sanya ni kwanciya in gwada sa a ta ko bacci zai dauke ni. Cikin ikon Allah kam baccin ya yi awon gaba da ni. Sai hudu da mintuna karar wayata ta tashe ni, Yusrah ce ke fada min sun sauka Kano lafiya, bayan mun gaisa da Umma tana kara jaddada min in yi hak'uri da kawar da kai, Sai kuma na kira su Samira, su kuma suka tabbatar min suna Zaria. Daga nan toilet na shiga, wanka na yi hade da alwala, na yi sallahr la'asar, kafin na shirya cikin atamfa dinkin riga da siket, sosai dinkin ya zauna jikina. Haidar ma da ya tashi a bacci na kintsa cikin kaya mara nauyi, sannan na sakko kasa. Uwani zaune tana kallo, gani na ya sanya ta rissinawa ta ce "Sannu da sakkowa Auntynmu" Na amsa fuska a sake, bayan na zauna ne, ta zube min cinikin turaren da aka yi, da kuma wadanda suka kawo biyan bashi. Bayan ta gama min bayanin ne na ce "Abban yaran nan bai shigo ba?" "Ya shigo, na ce kina bacci, Sai ya wuce sashen amarya." Kai na jinjina alamar fahimta, kafin na ce "Sai an yi abincin dare ne?" Cikin kwantar da kai ta ce "Haka ya kamata Auntynmu, kin san ba mu kadai ba ne" Kan na kuma jinjinawa kafin na ce "To a wanke shinkafa, Sai a yi tuwo miyar shuwaka, akwai sauran wacce kika sawo ranar can a kasuwa." Kai karshen maganar tawa ya yi daidai da mikewarta. Bayan fitarta, na bi bayanta, kasancewar muna da kitchen a waje, kuma shi ne general kitchen na kowa da kowa. Tare muke aikin har yara suka dawo school, daga nan ne na sakar mata, na koma kan yarana. Har zuwa lokacin ban ga keyar Bashir ba, abun gwanin mamaki, koda yaran ma suka dawo bai zo wajensu ba. Ni ma kuma na hana su zuwa wajen shi, musamman da basu tambaye ni shi ba. Sai da suka tafi masallaci ne Uwani ta dauki abincin daren Sarai don kai mata, haka ta kawo foodflask din abincin rana, cokali ba a wanke ba. Bayan sallahr magriba Uwani ta tafi, ina kan sallaya bayan na idar da sallahr isha'i su Khalil suka dawo, wannan ya sa na sakko kasa, don zuba musu abinci, suna cin abincin ne Bashir ya shigo, sanye da jallabiya coffee color, kamshi na bin shi. Yaran suka gaishe shi, ni ma na gaishe shi ba yabo ba fallasa. Don wani irin haushinshi nake ji. "Dazu na shigo kina barci" kai na daga alamar eh Ya ce "Ya hidima da baƙi?" "An gode Allah." na ba shi amsa "To sannu da kokari, na gode sosai, Allah Ya saka miki da alkairi" "Amin" na amsa. Ya dan yi shiru kafin ya ce "An kai wa Nana Saratu abinci ko?" A zuciyata nake mamakin sabon sunan "Wai Nana Saratu" "Eh an kai mata, ban san ko kuna bukatar wani abu ba." "A'a ba komai. Amma ki yi hak'uri za ki ci gaba da dafa abincin har kwanakinta na amarci su fita" Kai kawai na daga alamar fahimta, saboda abin da nake ji a zuciyata mara dadi ba zai bar ni in yi magana ba. Ba na son yin kuka, gani nake Saratu ba ta kai matsayin da hawayena za su zubo saboda ita ba. Shiru ya ratsa falon kafin ya katse shirun da "Kuna bukatar wani abu ne?" Kai na girgiza alamar a'a Muka kuma yin shiru, so yake ya tashi, kila ya rasa yadda zai yi, wannan ya sa ni na mike sabe da Haidar na yi hanyar upstairs ba tare da na ce komai ba. Wannan ya ba shi damar barin falon. A bedroom su Khalil suka taras da ni, Affan ne ya bata fuska sosai kafin ya ce "Auntynmu wai Abbanmu ba a nan zai kwana ba?" Laluben amsar da zan ba shi nake yi, amma na kasa, shi din yana aji daya a secondary, ya ɗan san wani abu gami da zamantakewar aure, wani abun kuma bai sani ba. Ajiyar zuciya na sauke kafin na ce "A'a zai dawo zuwa an jima" reaction din shi ya nuna min bai gasgata ni ba, ni ma sai na kori maganar ta hanyar tambayar ba a basu Assignment ba. Khalil dai ya ce tun a makaranta ya yi, shi ko gogan komai bai ce ba. Dalilin da ya sa na ce su je su kwanta. Bayan fitarsu na yi shirin bacci, Sai dai tun da na kwanta idona ya ce bai san zancen ba, na dauka ko don na yi bacci da rana ne, amma abu har karfe biyun dare babu bacci. negative imagination nake yi a kan Bashir. Jin zuciyata na neman fashewa ya sanya ni shiga toilet na dauro alwala. Raka'a biyu na yi, kafin na daga hannu sama ina rokon ubangijin sammai da kassai ya yaye min abin da nake ji. Lallai kishi ciwo ne mai girma. Sakeena ta yi kokari, ba abu ne mai sauki ga macen da aka fara aure ba, ace an karo mata wata. Gara ma amarya ita dama bakuwa ce. Yau kam Hasashen da nake yi a kan ina ma ni ce aka fara aure, kafin aka auro Sakeena, shi ma na janye shi, farkon da ta biyun duk na dandana babu dadi. Na dire hannayena kasa ina furta "Wayyyo Allahna!" a hankali. Hawayen da nake dannewa na shiga lalubowa ko za su zubo in ji dadi amma fir na neme su na rasa. Haka na Duke kan sallayar tsawon lokaci zuciyata na kuna. Na rasa da me zan ji, da sabuwar gulmar Sarai, koda yadda Bashir ke rawar kafa a kanta. Yadda yake shigewa ɗakinta ya yi shiru kamar an aiki loma zagayar wuya, ba karamin daci yake min ba. Numfashi na sauke mai nauyi, kafin na mike dakyar, jiki ba ƙwari na goya Haidar, sannan na saba Maama a kafadata, dama Assidiq yana dakin su Affan. A hankali nake sauka kan stairs din kamar Ina tsoron aji karar takuna, ban yi tsammanin samun kofar a bude ba, Sai dai ina murza handle din na ga ta bude, wanda ya yi daidai da tashin Affan zaune. Kasancewar akwai fitila amma mara haske, hakan ya sa ya gane ni. A hankali ya ce "Auntynmu, lafiya?" Maama na fara kwantarwa saman gadon, kafin na kwanto Haidar shi ma na kwantar. A hankali na ce "Koma can wurin Khalil ka kwanta ka bar mana wannan gadon" Komai bai ce ba ya koma wurin Khalil din ya kwanta. Ni ma kwanciyar na yi bakina dauke da addu'ar Allah Ya sa bacci ya dauke ni. Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauke ni, wanda ya sanya ko kiran sallah ma ban ji ba, sama-sama dai na ji su Khalil na shirin zuwa masallaci, daga nan kuma ban kara sanin komai ba, Sai jin muryar Bashir na yi yana fadin "Khadija, a nan kika kwana?" Idanuna na bude masu cike da bacci na dora kanshi, Sai kuma na mayar da su na rufe a hankali. Ban bude ba sai da na ji ya zauna kusa da ni, kafin na kuma bude su a hankali na dora a kan su Affan da suka yi tsaye suna kallon mu, dalilin da ya sanya ni mikewa dakyar na shige toilet din su. Lokacin da na fito duk basu nan, har su Assidiq da Maama, Sai Haidar da yake bacci da kuma Bashir da ke zaune a inda na bar shi. Bayan na idar da sallah, azkhar da na karatun kur'anin da nake yi kullum na ce mishi "Ina kwana?" "Lafiya kalau, fatan kin tashi lafiya?" "Alhamdulillah" na amsa shi, hade da mikewa zuwa kitchen. Ganin ruwan zafi a akan electric da kuma a kettle ya tabbatar min ya shigo kitchen din. Doya na dakko na shiga ferewa, ita ce ma fi sauki da zan dafa saboda yan makaranta, ga shi kuma na makara. Ban jima da fara fere doyar ba ya shigo, ya sanyawa kofar key, sannan ya kwanto bayana, wuyanshi a kan kafadata, yayin da ya zagayo da hannayenshi kan cikina, a takaice dai ya rungume ni ta baya. Kamshin turarenshi ya rika ratsa kofofin hancina. Dole na dakata da yanka doyar da nake yi. Wukar ya zare daga hannuna hade aje ta gefe guda. Cikin kunnena ya ce "I'm sorry Khadija, I'm sorry please, I don't mean to hot you. Na san halin ki da kishi. Don Allah ki yi hak'uri, dan lokaci kadan ne, zai wuce ki ji kamar ba a yi ba" Hawayen da na so fitar su jiya ba su fito ba sai yanzu suka zubo shar zuwa kan hannayenshi da suke saman cikina. Kanshi ya kara kwantarwa sosai saman kafadata ya ce "Ina sonki, so ba na wasa ba. Khadija a yanzu ba na jin akwai macen da za ta kai ki kima a wajena. Rikon marayun yarana kadai ya isa ki yi ma ko wace mace fintinkau, amma Saratu kaddarata ce, don Allah ki karba hannu bibbiyu ki yi hak'uri. Na san ba ki mori komai a zaman aure ba, tun farko na hada ki da kishiya, tun ba ki so dole kika so ta da yaranta. Bayan nan kika koma zaman jinya da raino, lokacin da ya kamata ace kin dan mori rayuwar auran kuma na kara hada ki da wata. Don Allah ki dauka ibada kike yi. Please Khadija ki zama kamar Sakeena don Allah, ki samar min da kwanciyar hankali a gidana. Kin fi Saratu komai, shekaru, ilmi, wayewa da kuma hankali, don Allah kar ki bari a samu bara ka ta wajen ki. Please Khadija na roke ki"ya kai karshen maganar hade da birkito ni ina fuskantar shi. Sosai ya rungume ni hade da bubbuga bayana, kafin daga bisani ya hau kissing dina ta Ko ina yama fadin "I love you" har na fara ganin kamar ya zare. Dalilin da ya sanya ni ture shi da karfi, na juya ina neman inda ya jefar min da wukar da ya amshe a hannuna. Har zuwa lokacin hawaye ne ke wanke min fuska. Sosai zubar hawayen ke min dadi, ina jin kamar ina zubar da dukkan damuwata ne. Kara kwantowa ya yi jikina a hankali ya ce "Kin san idan kina fushi na fi bukatar ki, ko ki sauke fushin nan, ko kuma komai ya faru a kitchen din" Ni dai komai ban ce ba, har zuwa lokacin kuma hawaye na saukar min. Ganin ya amshe wukar hannuna ya sa na duke a wurin na ci gaba da kuka mai sauti, shi din ma dukawa ya yi hade da rungumoni, ganin da gaske nema yake ya yi abin da yake so din, ya sanya ni yin amfani da karfina, na kwace jikina, kafin kuma ya yunkura har na bude kofar kitchen din na fita da gudu. Daidai Khalil na fitowa dakinsu sanye cikin uniform, yadda na fito din ne ya sanya shi fadin "Auntynmu lafiya, ko kin kone ne?" a rude yake tambayar Komai ban ce mishi ba, na haura saman da sauri, shi kuma ya nufi kitchen din. Matar J ✍🏻 [12/23, 15:02] 08080966571: *HASASHENA* *Page 34* A dakin na tarar da Affan yana shirya Maama, wannan ya sa na wuce toilet. Saman toilet din na zauna ina sharce hawayena, duk yadda na so in tsayar dasu abun ya gagara. Ban san ko minti nawa na kwashe a cikin toilet din ba, kafin na fito. Gefen gado na zauna shiru, ba na ce ga abin da nake tunani ba, amma zuciyata babu dadi. Ina zaune a wurin Khalil ya shigo ya ce min za su tafi makaranta. Bayanshi na bi zuwa kasa, duk sun yi break, amma bread da kwai. Sai da naga tafiyarsu sannan na dawo ciki, inda Bashir ya shirya abincin break din Saratu ya kai mata. Tea kawai na iya sha, zuciyata Sam babu dadi, Sai da Uwani ta zo ne na dan ji sauki, musamman yadda Bashir bai fita aiki ba, ba karamin kara min damuwa ya yi ba. Na yi ta sake-sake marasa kyau. Haka muka gama abincin rana Uwani ta kai mata, ta kwaso kaya break ko spoon ba a wanke ba, da aka kai na dare ma, haka aka kwaso na ranar ba a wanke ba. Ban taba gajiya ba, ko ina so, ko ba na so, haka nake abinci sau uku in ba ta a rana, sannan kafarta ba ta taba ta kawo sashena ba, ni ma kuma ban taba lekawa nata sashen ba. Haka ma yara. Ranar da muka cika kwana uku, ne na zuba ido in ga Ikon Allah, in ga abin da zai faru. Misalin karfe takwas na dare, muke zaune da yarana cikin falo, ni dai sanye nake da doguwar rigar robber material, blue Mai yankakken hannu. Affan sanye da boxer da ya ɗan wuce gwiwa, Sai vest yayin da ya goya Haidar a baya, saboda ya hana Khalil ya yi wa Maama homework. Khalil ma sanye yake da irin kayan jikin Affan, hannunshi rike da hannun Maama da ke tracing a littafin writing din ta. Assidiq kam kwance yake yana kallon cartoon, ni kuma hankalina a kan wayata yake. Kwankwasa kofar da aka yi ne, ya sanya Affan budewa, Bashir da Saratu suka bayyana. Lokacin da kwayar idanuna suka shiga cikin tata, Sai da gabana ya yi wata mummunar faduwa, na lumshe idanuna tare da furta "Innalillahi Wa'inna IlaihirRaji'un, La'ila Ha Illah Anta Subhanaka Inni Kuntu minazzalumin" idanun na bude hade da amsa sallamarsu. Shi da ita a kan 2 sitter suka zauna. Ina kallon yadda take bin ko wacce kusurwa ta dakina da kallo. Affan da ya hade fuska kamar bai taba dariya ba ya kalli Bashir, da kyar ya ce "Good Afternoon Dad?" Ba na jin ya jira amsawarshi ya yi hanyar upstairs. Khalil MA Sai ya bi bayan shi, bayan ya gaishe shi. Falon dai ya koma daga ni sai su. A hankali na kalli Bashir na ce "Ina wuni?" Ya amsa min, lokaci daya kuma yana zungurin Saratu alamun ta gaishe ni. Ni dai na ɗaukarwa kaina, idan har ba ta gaishe ni ba, ni kuma ba zan gaishe ta ba. Bayan ta gama shan kamshinta ta ce min "Ina wuni?" Ni ma sai da na sha nawa kamshin kafin na ce "Lafiya" Daga nan komai ban kara cewa ba. Na Ci gaba da danna wayata. Shi ne ya ce "Mun zo yi miki godiya ne bisa dawainiya damu na kwanaki uku, Allah Ya saka miki da alkairi" Sai da na dan murmusa kafin na ce "Amin" "Sai abu na gaba, yau Saratu ta fita daga kwanakinta na aiki, kenan zama zai koma normal yadda kuka tsara. Shi ya sa nake son in ji ya kuke son abun ya kasance?" Duk mu ka yi shiru, jin shirun ta yi yawa ne ya sa na ce "Ni ba ni da matsala, duk yadda aka tsara hakan ya yi" Ya juya kan Saratu ya ce "To ke kin ji, ya kike ganin abun zai kasance?" Sai da ta tura baki kafin ta ce "Ni dai kowa ya yi girkinshi, ba zan iya girkin mutane har bakwai ba" Ban san lokacin da na dago kai ina kallon ta cike da mamaki ba, a zuciyata na ce "Farawa da iyawa" Da alama maganar ta zo wa Bashir a bazata, don shiru ya yi, kamar ba zai kara magana ba, Sai kuma ya ce "To ya za a yi kenan, za ki rika girkin a kitchen din part dinki ne?" "Ga kitchen a waje na kowa da kowa. Duk mai girki ita ke da iko da kitchen, Sai ta gama abin da take yi, wacce ba ta da girki ta shigo" Ni dai baki bude nake sauraron wannan Ikon Allah, wannan yarinyar ya aka yi duk ta san wannan, anya kuwa ba wani ne yake ɗorata a hanya ba. Tun kafin Bashir ya ce wani abu na yi saurin fadin "Ma Sha Allah, hakan ma ya yi" Ni nan bangaren ba ni da matsala, ko cewa ta yi wanda ba shi da girki ba zai shiga kitchen ba. Kitchen dina na ciki babu kayan aikin da babu, komai ina da shi. To me ye damuwata. Shiru ya ratsa falon, ganin kamar babu mai abun fada, kawai na mike zuwa sama ina fadin "Mu kwan lafiya" Bayan na zauna saman gado ne na ce "Affan me ya sa ba kwa gaishe da Auntynku?" Baki bude alamun mamaki Khalil ya ce "Wacece Auntyn tamu? Don Allah Auntynmu ki bari, ni ba ruwana da ita." Affan ma ya yi caraf ya ce "Ni ma babu ruwana da ita. Ko za ta shekara dubu a gidan nan ba zan yi mata magana ba" A hankali na sauke numfashi kafin na ce "Babu ruwana, don Allah kar ku daura min jakar tsaba ku hada ni da kaji. Babanku zai yi fada. Kuma mutane za su ga kamar ni na sanya kuke mata rashin kunya" "Rashin kunya kuma! Mu da ba mu yi mata magana wace rashin kunya kuma" cewar Khalil idanunshi a kaina. Shigowar Abbansu ya sanya ban ba Khalil amsa ba. Bayan duk sun fita dakin ne ya ce "Khadija yaran nan kamar suna fushi da ni, musamman Affan, idan ya ganni sai ya hade fuska, ko ba ki lura ba" Kai na girgiza alamar a'a kafin na dora da "Kana man ce Affan ne, amma ai shi haka yake, wani lokaci ka gan shi kamar mai jinnu" "To Khalil fa?" ya kuma tambaya "Khalil kuma yallaboi, na ga ko dazu kun gaisa ai, kuma ranar can da safe ma tare kuka hada break fast" Shiru ya yi kafin ya ce "Just you're barking them Khadija, don Allah kada ki yi involving yaran nan a cikin zamantakewarmu" Kamar ba zan tanka ba, Sai kuma na ce "In Sha Allah" Aje duk wani kishi na yi a gefe, na karbi mijina sosai, shi kanshi na san ya yi mamakin yadda ba tarbe shi. Da safe tare muka shiga kitchen kuka hada breakfast. Ita kam Amarya ba ta leko ba, kuma na daukar wa raina, na gama kai mata abinci, ba dai ta ce ba za ta iya dafa mana abinci ba, muma ba za mu iya dafa mata ba. Idon Bashir na faka, na turawa mai adaidaitan da ke kai su Khalil makaranta sakon ba sai ya zo da safe ba, Babansu zai kai su. Yaran na break na ce "Abbanmu yau fa kai za ka kai su Affan school, mai kekensu ba zai samu zuwa ba, mashin din ya lalace" "Subhnallah! Sai su matsa kar su makara" Jin haka ya sa na haye sama, na canja kaya zuwa doguwar riga mara nauyi sosai, na nade kaina da veil din, Haidar ma na canja mishi kaya haka Assidiq. Time da na sakko har sun gama break din, shi ne ya kalle ni kafin ya ce "Ina za ki je" kai na langabe kafin na ce "Ni ma zan raka su ne" Kallona kawai yake yi, wannan ya sa na mayar da kallo na kan yaran na ce "Ko ba ku so in raka ku" "Muna so wlh" suka hada baki a tare. Baki Bashir ya tabe kafin ya ce "in ya so ma ki zauna a can har sai an tashi kin dawo" ya yi maganar hade da daukar key din motarshi da ke kan center table Muka rufa mishi baya muna dariya. Burina kawai shi ne Sarai ta son ina da kusanci da mijina, kuma zuwan ta bai hana mu farin ciki ba. Na dauri ɗamarar zama kamar Sakeena, wajen danne damuwata da boye bacin raina a gaban makiyaya. Time da muka dawo daga kai yara makaranta Uwani ta zo. Har ta share tsakar gida ta ba fulawoyi ruwa. Cikin girmamawa ta gaishe mu, kafin ta juya wurin aikinta, ni kuma sai da na salami Bashir zuwa wurin aiki kafin na zauna break. Kuma sai a lokacin ne ya leka dakin Saratu. Sai na ji ni kamar wata Sakeena yau, ni ma na rike miji da hidimomina, ashe haka abun yake ban sani ba. Sai kawai na ji ni ina murmushi. Bayan Uwani ta yi breakfast, kan entrance muka dawo, domin hada turaren wuta, na kamshi, humra da kuma roofreshener, aikin da ya dauke mu har 12pm. Kuma har zuwa lokacin Saratu ba ta fito ba, sosai abun ya ba ni mamaki, ni dai ban kai mata abinci ba, kuma ban ga Bashir ya sawo mata ba. Na fita batunta muka shiga hidimar girkin rana. Sai dai misalin karfe 1pm sai ga Bashir da take away, kai tsaye kuma ya wuce bangarenta, after like 20mins ya fito, a kitchen ya same mu ya ce an gama abincin rana, na ce yana hanya dai, daga haka ya wuce abin sa, wai ya koma wurin aiki. Sosai takeaway din Nan ya taɓa min zuciya, kun san kishi dai, bare ni mai nawa a kusa. Sai dai haka na danne ban tanka ba. Abu kamar wasa, har na fita girki Sarai ba ta taba ko shiga kitchen din ba, bare ta dora abinci, take away ake yi mata. Na zuba ido in ga Ikon Allah tun da girki ya dawo kanta. Da dare Bashir ya koma ɗakinta, haka na rarrashi kaina dakyar na yi bacci. Karfe hudun asuba alert dina ya tashe ni, alwala na yi, hade da yin sallah raka'a biyu, bayan na idar na yi lazumi hade da karatun alkur'ani, ban tashi ba dai sai da na yi sallahr asuba na nufi kitchen. Abun mamaki a rufe gam, tun ina tunanin datsewa ya yi har na fahimci an rufe kitchen din ta waje ne. Ga shi ba ni da extra key, haka na koma kitchen dina na ciki na yi tsaye, babu wani abu da zan sarrafa a ci, komai yana kitchen din waje. Fadin takaici da bacin ran da na ji bata lokaci ne, musamman da na ga rana ta fito, ga yara har sun gama shirin makaranta. Khalil ne ya ce "Auntynmu ko mu je mu yi wa Abbanmu magana ya bamu wani key din?" "Kyale shi kawai Khalil, dakko min jakar da nake ajiye kudi, ku sawo bread da kwai, da mai, Sai kuma Maggi." Na yi maganar zuciyata babu dadi. Affan ne ya dakko jakar, ya ciri kudi, suka tafi tare da Khalil. Basu jima ba suka dawo, don haka na soya musu kwan, suka hada da bread suka karya, ni dai ɓacin rai hanani cin komai ya yi. Juice kawai da biscuits suka tafi da shi school, Sai na hada musu da kudi, koda ba a kawo musu abincin rana ba. Haka na zauna zuciyata na ta min daci, gyaran dakin ma na kasa, Sai da Uwani ta zo, ta gyara ko ina. Sai 10am Bashir ya fito cikin shirin fita aiki, lokacin ina sama, ina ta aikin lallashin zuciyata. Sanye yake cikin royal blue din yadi da aka yi wa ɗinkin zamani. Sosai ya yi kyau, jikin lukui bai boye jin dadin da yake samu ba. Daga kwancen da nake na ce "Ina kwana?" Ya amsa min, lokaci daya yana zama kusa da ni, hannuna ya saka cikin na shi kafin ya ce "I'm sorry, na so leko ki da Asuba, Sai Nana ta tashi da ciwon ciki" Ba tare da na kalle shi ba, na ce "ba komai" "Me kika dafa da safen?" Kamar in fada mishi abin da ke min zafi sai kuma na fasa na ce "Ban yi da yawa ba, ni ma da ciwon kai na tashi" Hannunshi ya kai saman goshina kafin ya ce "Kodai ba ki yi bacci ba?" Karon farko da na kalle shi muka hada ido na ce "Me zai hana ni bacci?" Maganar ya kawar da fadin "Zan tafi aiki, akwai abin da kuke bukata ne?" Kai na girgiza alamar a'a Ya mike daga zaunen da yake lokaci daya yana daukar Haidar da yake wasa, ya ce "My lion, za a yi min rakiya?" Ni dai yi na yi kamar ba na jin su. Ya gama surutanshi ya aje min Haidar din ya fita. Misalin 11am na sakko kasa, Uwani zaune tana kallo a falo. Ganina ya sa ta gyara zamanta hade da kara gaishe ni. Kafin ta ce "Dama Ina ta addu'ar Allah Ya sa ku tashi da wuri, na ji kitchen a rufe" Sai da na zauna saman kujera, sannan na ce "Je ki wurin Amarya ki amso mana key din" Komai ba ta ce ba, ta mike, yayin da ni kuma na zauna zaman jiran dawowarta. Ko minti biyu lafiyayyu ba ta hada ba, ta dawo min da amsar wai ta ce ita ce da kitchen yau. Wani kullutu, da wani mulmulallan baƙin ciki, suka taso min zuwa zuciyata suka dunkule wuri daya, wannan ya sa na shiga kokawa da su,. Tsabar ɓacin rai bishi-bishi ma nake ganin Uwani. Matar J ✍🏻