1- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* _"Ƙungiyar Marubuta masu tasawa, Rubutunmu shi ne tafiyar da ke wuce lokaci, mu ne masu ɗaukar harshen gobe a yau. Marubuci ba ya zana kalma kawai, sai dai ya zana mafarki a zuciya, ya maida shi haske ga al'umma. Wannan shi ne alwashinmu a matsayin mu na matasan marubuta. Taken mu shine ɗaga darajar Marubuta masu tasawa."_ 🌻🌻🌻 *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* Hasashen soyayya free book ne,amma ga masu bukatar complete #500 ne, zaku iya magana ta wanan lambar 08129553971. _Page 01_ Labarin rayuwar Bhatool Senate,Soyayya mai ɗauke da salon burgewa, rayuwar aure mai cike da hargitsi da ruɗani. Matashiyar buduruwa ce wacce aƙalla zata kai shekara 22 zaune a backseat na motar ƙirar GLK, tana sanye cikin atamfa Super holland mai adon ja da touch din green, fara ce kyakkyawa tagani tafaɗa, tana da tsayi amma ba doguwa can ba, dara-daran idanunta masu matukar kyau, haka ƙananan pink lips dinta masu ɗaukar hankali, green veil ta yafa sai kuma ƙaramar handbag da takalmi golden cloud, wuyanta yasha manya sarƙoƙin gold haka yatsunta. Yau ne fitar ta farko tun bikinta da aka yi, sati uku da ya wuce, bikin wata coursemate ɗinta akeyi wacce sukayi amarci a lokacin bikinsu, hakan ya sa ta fito. Tunda driver yayi parking motar tasu wacce a wajen rubuta lamba aka rubuta *Senate* gaba ɗaya hankalin yan matan yayo kan motar, driver ne ya fito daga wajen da yake tare da buɗe mota ƙofar inda take zaune, hill sheo ɗinta ne ya fara fitowa kafin kuma ita ta fito, ai tuni wajen ya ruɗe da faɗin. “Fatima senate! Fatima senate!!.” ~ Asalin labari ~ Fatima Ahmad Ishaq shine asalin sunanta, haifaffiyar garin Yobe state cikin unguwar Nyan’ya, Mahaifinta Malam Ahmad dan kasuwane mai rufin asiri yayi aure tare da matarsa Habiba da yara guda uku. Karima itace babba, sai kuma Fatima da ƙaninta Abdulwahab wanda tsiran shekara ɗaya ne tsakaninsu,hakan yasa suka zama abokan tsama na gaske. Cikin yaran Malam Ahmad Allah ya jarabceshi da son Fatima, tun baya iya bayyanawa har ya fara, Habiba tayi duk ƙoƙarinta wajen kar ya bayyana hakan domin zai’iya kawo saɓani cikin yaran nasu. Sunanta Fatima amma ana kiranta da Bhatool, Bhatool ta taso yarinya mai rawar kai, gayu da kuma iyayi, ko magana Bhatool take abun tsayawa a kallane, bare kuma tafiya da yanayin rayuwarta. Wanan rawar kai ta Bhatool taja mata rashin so daga ɓangaren mahaifinta, waƴanda dama basa wani ƙaunar mahaifiyarta tun farko, saɓanin Karima wacce take shiru-shiru bata da wata damuwa, tana da haƙuri. Haka shima Abdulwahab, bashi da wata damuwa, idan kaga damuwarshi ko hayaniyarshi to da Bhatool ne, domin shi a yanayin rayuwarshi ma bashi da hayaniya, shiru yafi yawan maganarshi, Bhatool ce kaɗai kansashi magana harda faɗa da hayaniya. Karima nada shekara sha takwas, Bhatool sha shida, Abdulwahab kuma nada sha biyar. Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa sakamakon hawan jini daya dameshi. Lokacin da rashin lafiya taci ƙarfinshi, yahaɗa amininshi Alhaji Aminu da Abdulwahab man yanuna masa harkokin kasuwanci, domin yasan yana mutuwa ƴaƴansa da matarsa sun rasa gata, yasan halin ƴan-uwanshi ciki da bai, haka bayan ya haɗa Abdulwahab da Alhaji Aminu yanemi Alhaji Aminu daya raba dukiyarsa gida uku, ya ajiye gida biyu zuwa sanda ƴan uwansa zasuyi rabon gadonsu na son zuciya, sai yaɗora Abdulwahab akai yasan zaikula da kanshi da ƴan-uwanshi. Haka kuma acikin gida bashida magana sai dai. “Habiba ki kulamun da yarana, ki tsaya kai da ƙafa su samu ilimi da rayuwa mai kyau.” A cikin ƴaƴansa kuma bashi da magana sai. “Ku haɗe kanku, kuzama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya, kuso junanku, ga kuma amanar ƴar-uwarku nan Bhatool ku kula da ita, takasance mai rauni, Abdul Allah ne gatanku, kaine gatansu, kazama gatanta,kar kabari ko sau ɗaya tayi kukan rashin mahaifi.” Sai yajuyo ga Karima itama ya fara. “Karima kizama babba, komai ki ɗauka Bhatool ƙanwarki ce mai kuma rauni, ki zama yayata ƙwarai a gareta, karki bari ko sau daya tayi kukan rashi na.” Da irin waƴanan kalaman yake kwana yake tashi, kowa yasa ba dasu a cikin gidannan, ranar da zaiyi magana ta ƙarshe dasu ya tarasu baki ɗaya, ya fara magana. “Karima, Kamar yadda nasha faɗamiki ke ce babba,Allah ne gatanku kece na ƙannenki, Allah zai buɗamiki, domin ki kula da ƙannenki, ga Bhatool nan ako yaushe ina faɗamiki, dan Allah dan Annabi karki bari koda sau ɗaya tayi kukan rashin mahaifi.” “Fatima! Karima yayarki ce, Abdulwahab ƙaninki ne, inaso ki haɗa kiyimusu biyayya kai ɗaya shida yayarki, ki maidashi yayanki, Bhatool koda sau ɗaya karki bijire musu, nasan bazasu taɓa barinki kiyi kukan rashi na ba.” “Abdulwahab! Kaine ƙarami amma Allah ya baka girman, kazama uba a garesu, kazama bango a garesu, kubi umarnin mahaifiyarku sau da ƙafa, Abdul ko sau ɗaya karka bar ko ɗaya tayi kukan rashi na.” “Karima banida abinda zance miki, kiyi tarbiya a wajen yaranmu, amma ako yaushe ina faɗamiki amanar Bhatool.” Shuru sukayi baki ɗaya, sun saba jin irin wannan maganar awajenshi, amma na yau sai yayi musu daban, harta Bhatool dake jindaɗi idan yayi irin wanan maganar amma yau sai abun yazo mata wani kala. A daren ranar Alhamis wayewar garin juma’a Allah yayi mai rasuwa, wacce ta kiɗima iyalanshi haka kuma ƴan-uwanshi sukazo sukayi ta ihu, bayan kwana uku sukace sunaso araba gado. Malaminsu na bogi suka ɗakko yazo yayi rabon ha’inci da son zuciya, ya kwashe rabi da kwata na dukiyar yabasu, ƙarshe dai gidan da suke ciki suka tsira dashi. Bayan ƴan-watanni da rasuwarshi Alhaji Aminu, ya buɗewa Abdulwahab babban shago a kasuwa, bayan yayi mai tsallake-tsallake a makaranta ya tsira da takardar gama secondary. Abdulwahab ya fara kasuwanci, kuma Allah ya dafa mai aciki, Karima da fatima sun cigaba da makaranta, suna rayuwa cike da nutsuwa abubbuwa daya ba sufi ƙarfinsu ba. Ana wannan matakin ne kuma ƴan-uwan mahaifinsu waƴanda basu sake bibiyarsu ba, tun mutuwar mahaifinsu suka zo da buƙatar sunason aurar da Karima da Bhatool, a lokacin Karima nada shekara sha-tara zuwa Ashirin ita kuma Bhatool tana da sha bakwai. A lokacin akwai wani mutumi da suka haɗu da Karima lokacin tana aji na farko a makarantar kwaleji ta, Shehu Sule collage of Health science shiyasa da sukazo da maganar, Maman tace musu Karima nada wanda takeso amma Bhatool ba yanzu zatayi mata sure ba, domin ko secondary school bata gama ba, sanan shekarunta basu kaina wacce zata yi zaman aure ba, ga kuma halinta na rawar kai ba kowanni namiji bane zai zauna da ita. Wanan kalami na Mama ya tayar da tashin hankali babba ba ƙarami ba, a cikin ahalinsu domin su akwai wanda ma sukesu subawa yaran a cikin ƴaƴansu dasuka lalace, sanan kuma sunsami labarin yanda kasuwancin Abdulwahab ke haɓaka a kasuwa, amma Mama ta d’age ta tsaya sosai domin tasan aure shine cikon rayuwar ƴa mace, to baza taso akai su inda aure zai wahalal dasu ba, bata taɓa magana akan hukuncin da suka yanke akan yarantaba sai yanzu. Badan ransu yaso ba, Bashir ya gabatar da kansa a matsayin wanda yake son Karima, aka saka lokacin aurensu wata shida. Su da suka zaƙe akan sai an aurar da yaran baka ƙarajin bakinsu ba, sun koma gefe sai Mama suka bari da ƴan-uwanta, daman kuma Maman mai tanadace. A haka bikin Karima yazo da mijinta Bashir wanda yake ma’aikacin NNPC, a lokacin wannan bikin ne Bhatool taja magana mai tsayi cikin ƴan-uwanta domin abunda tayi, tayi ɗinkuna irin waƴanda ake gani a jikin ƴan film da kuma mutanen da akewa kallon ƴan-iska su *Zuge darling*, *Show me your back* da sauran ɗinkuna, hakama eyelashes (gashin ido) a wanan lokacin a iya idanun ƴan film ake ganinshi sai kuma waƴanda ba musulmai ba, ga kuma karin gashi na brazil mai-jar kala. Wannan abu ya jawa Bhatool magana sosai da sosai, wasu nacewa tazama ƴar iska, wasu na cewa zata zama,haka akayi biki aka tashi kowa da magana a bakinsa. Haka rayuwarsu Bhatool taita tafiya, tana samun duk wata kulawa a wajen ƴan-uwanta baki ɗaya, barima yanzu da Karima ta yi aure kuma mijinta irin mazajen nan da’ake kira *mijin marainiya ne*, domin duk wata buƙatar data ƴan gidansu ya ɗauke mata, ya tsaya mata akan karatunta harta kammala, yanzu haka yana ciku cikun buɗemata clinic ne. Haka shima Abdulwahab yazama babban ɗan-kasuwa mai nasibi, gashi yaro amma da manyan ƴan-kasuwa yake mu’amala, ya koma karatu part-time a yanzu haka akwai shagona guda biyu bayan na farko da akabuɗe musu. A ɓangaren Bhatool ma, yanzu ta girma kyawunta ya ƙara fitowa, gayu da iyayi sunƙaro amma yanzu sun haɗu da ilimi da wayewa, komai nata classy ne. A yanzu tana first year a jami’ar Yobe State University (YSU), tana karanta Entrepreneurship. A yanzu haka suna first semester ne sababbun ɗalibai, ƙawayenta guda uku ne waƴanda suma gani sukayi halinsu yazo ɗaya kuma tana burgesu yasa suka nemi ƙwance da ita, domin Bhatool akwai farin jini. ~~~~~Unguwar Red Bricks Makeken gida ne iya ganinka, ya gaji da haɗuwa tundaga girman shi, yanayin tsaruwar shi da kuma adon shi. Gida ne irin flat house amma mai girma sosai da sosai, part ɗaya ne mai girma da kuma tsaruwa. A cikin gidan wani ƙaramin part wanda a ƙalla shima yayi girman wani gidan, kyawawan samari ne guda biyu, ɗaya fari ɗayan kuma baƙi. Farin baya kama da mutanen Nigeria gaba ɗaya, yafi kama da mutanen ƙasashen larabawa,amma yanayin sumar shi yana akwance kuma ya zubo har zuwa wajen giransa kamar na ƴan Korea. Lips dinsa pink ne sosai da sosai kamar baitaɓa kai wani abu bakinsa ba, girarsa a cike take da gashi kuma baƙi ne huluk, ɗayan kuma baƙine, kuma mai kyau amma kuma baikai ko rabin kyan farin ba, baƙin ne yake ta magana amma farin ya yi shiru. “Senate magana nake fa.” Shiru yaƙarayi amma idanunsa nakanshi, ko ƙiftawa bayayi. “Idan bazakayi magana ba I will leave..” Girgiza masa kai yayi alamun “A’ah” “To talk.” A hankali yafara magana yana buɗe karamin bakin kamar mai koyan magana. “Bud-die.” Wata iriyar murya mai mugun sanyi da sanyaya zuciya. “Basan ta’ina zanfara ba.” “Fara ta ko’ina, Senate.” “Idan naganta zuciyata canja bugu take, tanayi da ƙarfi kaman zata fito, and I'm scared.” Yaƙara faɗa cikin sassanyar muryarsa, kallon shi ya yi sannan ya ce: “Wace?.” “Idan bangantaba bana jindaɗi, zanjini empty, Idan nayi nesa da ita zanji kamar I'm leaving what I love the most.” “Senate who is she?.” Girgiza kai Senate ɗin ya yi sannan ya ce: “Actually I don't even know her name.” “A ina kake ganinta?.” “School.” “Which school?.” “ ( YSU).” “What take you to Yobe state university, Senate?.” Girgiza kai yafarayi kamar ƙaramin yaron dayayi laifi aka kamashi, sannan ya ce. “ Naje wajen wani secondary school mate ɗinane da mamansu ta mutu, time ɗin ina Cyprus, shine naje yimai gaisuwa ya ce muhaɗu school ɗinsu.” “Kafaɗawa Momy?.” “Nope naso faɗamata amma nakasa Anas, shiyasa nakiraka inajin tsoro.” Murmushi Anas yayi domin yasan tabbas dagaske Senate ɗin najin tsoro, domin haka allah yayi sanyi kamar ƙaramin yaro, magana ahankali sanan babu abinda take tsoro kamar mata, amma fa yanada zafi sosai idan yatashi ɗaukan zafin, he is cool but difficult to handle. “You know you have to tell her ko?, dan bazan yi advising naka ba daga baya kaje kace nina hanaka faɗamata.” “I will okay, but please Anas what do you thinks is this?.” Dariya Anas ɗin yayi sanan ya ce. “Might be you fall in love.” “Love.” Senate ya faɗa aɗan tsorace. “Yes.” Anas ya faɗa tare da ficewa, kwantawa yayi kan gadonsa tare da rufen idonsa, amma itaɗin yagani ɗazu cikin ƙawayenta suna hira tana ta dariya amma cike da yanga da kuma gayu, bude idon yayi sannan kuma ya sake rufeshi. ~~~~~~ Yobe State University (YSU) Bhatool da team ɗin ƙawayenta zaune wajen da suka saba zama suna hira, ɗaya cikin ƙawayen nasu mai suna Jannah ce ta ce: “So yanzu ankon yakama 78thousand kenan, Kuma payment ɗin cikin satinan za’ay.” Daga kai sukayi sannan ɗaya maisuna Amrah ta ce. “Nan da 2weeks bikin, amma gaskiyya Suhaima baki kyauta mana ba, aiko engagement ɗin kyafaɗamana muzama cikin shiri, yanzu ina zamuje mu samu dubu ɗari da motsi.” Dariya wacce aka kira da Suhaima tayi sanan ta ce. “Time ɗin da muka shigo school ɗinan ai anyi engagement ɗin, kuma nasan ku big girls ne sannan kuna da rich-boyfriend's they can afford anything for you.” Sai a lokacin Bhatool ta bud’e baki ta yi magan. “Amma Suhaima kinci kai, kina tunanin samarinmu kemana wannan sutturar, to ni wallahi Yaya Karima da Abdulwahab ne, kuma nakaisu bango banji zasuyimun naki.” “Nima dai nakai Anty bango, banjin zatayi mun.”Amrah ta faɗa tanakai hannunta kan cinyar Bhatool tana taɓota da alamun gulma. “What?.”Bhatool ta faɗa tana dukan hannun Amrah. “Have you girls notice this guy.” Amrah ta faɗa tana nuna musu Senate da baki wanda ke zaune ɗan nesa dasu yana danna wayarsa, amma hankalinsa nakansu kuma zuciyarshi na bugawa da saurin data saba. “Yes.” Jannah ta faɗa sannan taƙara cewa. “Kusan 3weeks kenan.” “Nikam bantaɓa kula dashi ba.” Cewar Bhatool cikin ranta, domin da gaske bata taɓa kula dashi ba. “Gaskiyya yadaɗe yana bibiyarmu, namayi tunanin ɗaya cikinmu yakeso.” Suhaima ta faɗa, tana kallonsu shiru Bhatool tayi na ƴan-mintina saikuma ta ce. “Ku barshi Allah yasa gobe yazo.” Daganam suka tashi sukabar wajen, shi kuma yayi shiru na cankuma ya ce. “ I have to tell my Mother.” Daga haka ya tashi ya nufi motarsa ya wuce gida, su Bhatool kam wata lectures ɗinsuka shiga, sannan su a tsarinsu koda sungama lectures basa tafiya gida sai shida, kullum fitar takwas komawar shida. ~~~~~Red bricks A makeken main falo ɗinta ya sameta, wanda yasha ado da tsadaddun royal chairs, datijuwar mata wacce kuɗi da ilimi suka ɓoye shekarantu, domin a kallon farko zaka iya cewa batafi shekara 30 ba wanda a zahiri takai shekara 45, farace itama mai kamanni da larabawa, tana sanye cikin wani ɗan ubansu lace maroon clour. Shigowa yayi ba tare da yace da ita ko ƙala ba, zama ya yi nan kujera tare da haɗe hannayensa biyu ya zuba tagumi. Matsowa ta yi kusa dashi tare da sa hannu ta cire mai tagumin da ya yi. “My prince, what is going on?.” Kallonta yayi idanunshi cike da ƙwalla, a hankali ya buɗe baki ya ce. “Mom! I'm scared.” “What happen, and what are you scarring for?.” “Mom the girl.” “Which girl?.” “Mom Idan na zauna kusa da ita, zuciyata na bugawa da ƙarfi kamar zata fito, idanta tashi zata fice zanji kamar ina nesa da abinda nakeso, idan banje naganta ba banajin daɗi, I don't know what to do Mom.” “Nutsu kaji! Faamun komai from the beginning.” Legends pen 08129553971 2- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 02_ “Mom Idan na zauna kusa da ita, zuciyata na bugawa da ƙarfi kamar zata fito, idan ta tashi zata fice zanji kamar ina nesa da abinda nake so, idan banje naganta ba banajin daɗi, I don't know what to do Mom.” “Nutsu kaji! Fa’amun komai from the beginning.” Shiru yasa ke yi sai kuma bakinsa dake karkarwa, jawo shi tayi tare da ɗaura kanshi akan cinyarta ta fara shafa masa gashi. A hankali ya fara sauke ajiyar zuciya, sai da yaɗau kusan minti goma sannan ta fara magana. ~~~~~Usman Yunusa Ahmad Shine asalin sunansa, haifaffen garin Yobe state Damaturu kamar yadda mahaifinsa yake. Saɓanin mahaifiyarsa dake yar asalin garin kano. Alhaji Yunusa babban mai kuɗi ne wanda akaf garin Yobe asandashi da kuɗinsa. Babban ɗan kasuwa ne wanda yake kasuwanci har kasashen ƙetare. A lokacin da yaje Kano gudanar da wani harkar kasuwanci ya haɗu da Zainab wacce yaji ta kwanta masa arai kuma ya yi magana da iyayensa da ƴan-uwansa sukayiwa nata magana akasaka lokacin aurensu. Bayan anyi auren suka fara gudanar da rayuwar aure mai kyau da tsafta, Yunusa na bata lokacinta a matsayinta na iyalinsa, haka itama tanayi masa biyayya iyakacin yinta, sukan ware lokaci sufita ƙasashen ƙetare. A wani lokaci da sukaje ƙasar Dubai suka daɗe wajen wata shida, a lokacin ne Zainab tasamu ciki. Yunusa yayi murna sosai da sosai hakama ƴan-uwansa da kowa da kowa. Sai da cikin yakai wata bakwai sannan sukabar Dubai, suka tafi Korea inda ananne kuma ta haihu, yaron yaɗakko kammanin mahaifinsa amma yana yanayi da larabawa kodan a ƙasarsu akasami cikinsa, haka kuma gashin kasan ya yi kama dana ƴan korea. Bayan yaron yayi wata ɗaya suka huce Saudi Arabia alokacin aikin hajji suka gudanar da Hajjinsu, sannan suka dawo gida. Usman ya taso cikin gata- gata na gaske domin Usman ko zaman sati biyu cikakke bayayi a Nigeria, Nursery School kawai yayi anan amma ko primary school ɗinshi acan south korea yayi, lokacin dasuka tafi tare da Mahaifiyarsa. Wacce bata dawo ba sai da yashiga Junior secondary school. Sai da Usman ya gama Secondary school kuma yatafi Madina ya had’e haddarshi daganan kuma yakoma Cyprus ya cigaba da karatunshi. Usman ya dauko sanyin hali dana mu’amala irin naƴan South Korea, idan yana magana kamar mai koya, tafiyarshi dai yanayinta cike da ƙasaita, bashida fushi ko kaɗan amma idan yayi fushi tashin hankaline domin bai iyaba. Usman yanas on wasa, ya iya wasa da yara sosai sannan kuma yanason yara, ko dan shikaɗai ne wajen iyayensa, sannan yaransa yasa ko da yaushe gidansu yake cike da ƴaƴan-ƴan uwa. Tun a south korea Usman yasamu sunnan “Senate” sunnan da ya karɓa yakuma ɗorawa kansa, duk da wani wanda yasanshi to da wannan sunan ya sanshi. “Senate” Anas cousin Brother ɗin shi ne, ɗan wajen ƙanwar Momy wanda Usman take matuƙar ƙauna, yayarda dashi sama da kowa, Usman baya iya doguwar magana da mutane, Daga Momy saikuma Abba domin idan yana tare da Mahaifinsa yakan zama serious cikakken mutum, kowanan sanyin maganar bayayi,saikuma Anas yana magana da Anas sosai da sosai domin gani yake bashida wani ɗan-uwa kamar Anas. Tsiran shekara biyu ne tsakaninsu, shiyasa Usman yake gani kamar Anas ɗin ƙaninshi ne. Senate yana da abokai guda biyu, Salman da Juraij, sukam sun iya rayuwa dashi a yanda yake, sun haɗu da Juraij a south Korea ne a primary school, shi kuma Salman abokin Juraij ne na gaske, hakan yasa suka zama abokai. Senate bai taba jin rashin daɗin zama dasu ba, domin suna fahimtarshi akan komai, abokaine na ƙwarai, yana Cyprus mamansu Salman ta rasu, hakan yasa ranar da ya dawo yaje gidansu, anan yafaɗa masa yana school. Kai tsaye Senate yatafi School ɗin. Shigar shi makarantar ya kira Salman waya, Salman dake lectures yayi text. “Wait me at the Garden” Okay kawai ya ce, Sanan ya nufi Garden ɗin. Tun shigowarshi makarantar yaji bugun zuciyarshi ya canja, yaƙaro amma ya alaƙanta hakan da yawan mutanen dake ciki, wani saurayi yagani yana tafiya, da sauri yace masa. “Assalamu alaikum, Garden please?.” Hannu gayen ya ɗaga masa tare da nuna masa Garden ɗin, godiya yayi masa sannan ya wuce. Shigarshi Garden ɗin ƙarin bugun zuciyarshi. “ Yasalam.” Yafurta dai-dai lokacin da yashiga Garden ɗin, sakamakon wani irin bugun da zuciyarsa tayi da mugun ƙarfi. Guri yasamu ya zauna bugun zuciyarna daɗa tsananta, runtse idonsa yayi tare da fara sauke ajiyar zuciya, sautin da ya fara jine yafara rage bugun zuciyar, a hankali sassanyar muryarta ta shiga cikin kunnensa, ƙwaƙwalwarsa ta yi masa record and save ɗinta a lokaci ɗaya. “Wani yaron zai cewa bazaiban ba, aikuwa na kwanta a ƙasa na ƙwalla ihu ina faɗin, Abba yau nayi kukan rashinka, kafin naƙarasa yayi sauri yatoshemun baki yana faɗin yi haƙuri Yaya nawa zan baki.” Dariya ƙawayenta suka saki sannan Suhaima ta ce. “ Gaskiyya baki da kirki, duk ƙoƙarin da mutanen nan suke akanki gun mutuwar mahaifinku amma sai kince kinyi kukan rashinshi.” “Aikin ga ko Abdulwahab ko Yaya Karima, ke har Umma ma idan inason anko sai na kwanta a ƙasa nace nayi kukan rashin uba, last time Umma cewa tayi naita kukan rashin uban, amma nace mata nayi mafarki Abba yace bazaiyafe musu ba, ai Wallahi bayan anko Abdulwahab harda kaini Shopping.” Dariyar suka ƙarayi sanan Amrah ta ce. “Nikam wallahi Yaya Sulaiman yafi ɗanyen kashi ɗoyi, ai ban isaba.” “Ke waya faɗamiki Abdulwahab ɗin Yayanane, ƙaninane fa shiyake bini amma shine mai kuɗin.” Dariya suka sake wanda ko da yaushe idan suka zauna a wannan seat ɗin basu da aiki sai hira kala kala, daganan kuma ajuye gulma. Kalmar rashin Mahaifi ta Bhatool tashiga cikin zuciyar Senate tasamu waje ta zauna gamgam, wanna hirar tasu itace ta dinga saukarmai da yawan bugum zuciyar harta yi dai-dai, hankalinshi nakan Bhatool da ƙawayenta, hankalin yan mata Yobe State Universtity nakan Senate. Wayarsa ce tahau ƙara da sauri ya ɗaga yana faɗin: “Man how far.” “Kana ta ina acikin Garden ɗin?.” “Ina daga wani gefe.” “okay naganka.” Yana Zaune Salman yazo yana faɗin. “Man how far.” Murmushi yayi sanan yace: “Nml Man ya ƙarin haƙurin Momi kuma?.” “Haƙuri sai ma’aiki broo.” “Yasu Haliman kuma.” Murmushi Salman yayi tabbas Senate yanada matuƙar damuwa da kula akan ƴan-uwan abokansa. “Suna lafiya, kasan ayu engagement ɗinsu dukansu to yanzu kawai ansakko da bikin nasu nan da 3weeks.” “Masha Allah hakan yayi sosai da sosai, Abban yadawo ne?.” Girgizakai Salman yayi batareda yace wani abu. “Ayyah to yanzu aina ka tsaya.” “Akwai wani gida na Mama shi akayanke za’asiyar harma antayashi 10million, za’ayi hidiman biki ragowar kuma a gyara shi wannan gidan damuke ciki zuwa ko hayane sai asa, nikuma zankoma gidansu juraij.” “Wannam shawarar tayi amma banajin yakanata asiyar da gidan man, sabida gaba zanbada tawa gudumawar insha Allah koda basu isa duka ba za’ayi wani abu.” Senate ya faɗa yana danna wayarshi, Transfer ɗin kuɗi yayiwa Salman ₦10’000’000 kuɗin daka taya gidan sanan yace: “Wanam gidan abarshi Salman gaba zaiyi muku amfani and insha Allah zanyi magana da Uncle za’anema wane acikin company dinsu kafin ka ƙarasa degree ɗin, sai mubuɗe namun.” Hawaye ne sukafara fitowa daga idanun Salman, gun tasowarsu Senate da Juraij ke ƙoƙari akansu, yanzu haka Juraij ɗin shima yabashi 5million. “Bani da bakin da zanyi muku godiya kunyimun komai a rayuwa.” “Shut off bro, mene haka dan Allah. Menene amfanin abotar da ba’a taimaki juna ba?.” Shiru Senate yayi domin jiyayi zuciyarshi na tsinkewa kamar yanarasa abinda yafi ƙauna, rufe idonshi yayi yasoma faɗin. “Inna’illahi wa’inna illahir raji’un.” Da sauri Salman yariƙeshi da faɗin. “Senate lafiya, meyafaru?.” Shiru Senate ɗin yayi kusan minti biyar kuma bugun zuciyarshi yafara dai-daituwa, a hankali yabuɗe idonshi ya kalli Salman sai kuma ya kalli inda ƴan-matannan suke amma babusu. “Meyafaru?.” Salman yaƙara tambayarshi. “ I don't know wallahi, kawai naji bugun zuciyata yasauya.” “Yasalam yakamata kaga likita.” kai kawai yaɗaga sanan yace: “Yanzu zakatafi ko kana school ɗin.” “No ina school.” “Okay Sai anjima.” Senate yafaɗa tare da tafiya, bin bayanshi Salman yayi yana faɗin. “Ka tsaya naraka kamana.” Buɗe baki yayi daniyar yin magana amma yaji zuciyarshi tabuga da wani irin ƙarfi. “Wallahi bazan shiga class ɗinnan ba, jifa yanda ajin yacika ko attendance bayi zaiba.” Ya jiyo sansanyar muryata na magana, da sauri ya juyar dakai idanunsa suka sauka akan kyakyawar fuskarta, da ɗankaramin bakinta dake magana. Dum yaji Zuciyarshi tabuga da wani mugun ƙarfi sakuma bugin yadaidaita. Ƙuramata idanu yayi yana kallonta, yanayin yanda take magana ya haifar masa da wata kasala ta mussaman,bai taɓa kallon mace yaji wani yanayi bayan na tsoro sai wanan, wani irin abu yake gani a ciki Idanunta masu kamada taurari. “Man mekake kallo?.” Da sauri yajuyo ya kalleshi yana faɗin. “Na’am, muje” Tafiya sukayi amma baidaina waigen taba, haka yadawo gida yanajinshi empty kamar yabar rabin rayuwarshi kowani babban ɓangare na rayuwarshi a wani waje. Gaba ɗaya yakasa mantawa da fuskarta ko yanayin maganarta, haka yayini yana faman tunani, babban abinda ya tsoratashi shine yanda yakasa bacci daya rufe idonshi ita yake gani. Haka washe gari yatashi da tunaninta, yakasayin komai. Haka kawai yaji zuciyarshi na azalzalallashi akan yatafi school ɗinsu, a dai-dai lokacin dayaje jiya kuma wajen da yasamesu jiya, wanan ganin dayayi mata shi yarage masa duk wani yanayi dayakeji a zuciyarsa. Abu kamar wasa yazama kullum idan yatashi da wannan yanayi yake tashi, jinshi yake empty kamar bai cikaba har sai yaje yaganta, har zuwa yau daya fuskanci ƙawayenta sunfara noticing nasa. ~~~~~ Kallonshi take har yagama bata labari tundaga zuwanshi wajenshi wajen Salman har zuwan dayayi yau dakuma abinda ƙawayenta suka faɗa. “Tsoranta kake itama?.” Girgiza kai yayi daga kwancen dayake akan cinyarta. “Is different acikin zuciyata nakejin maganarta, idan nayi nesa da ita inajina empty kamar fankon ashana baby ƴaƴan ashanar aciki.” “Do you believe you're in love?.” “No mom, ta ina zansota bansantaba sai ranar kuma haka akeyinso daga ranar dakaga mutum?.” “Tashi nabaka labari.” Tashi yayi ya zauna yana kallonta, itakuma tafara magana. “Kasan Dad ɗinka ɗan Yobe state ne ko?.” “Yes Mom.” Yafaɗa tare da daga kai. “Good! kuma kasani yar kano state ce ko?.” “Yes Mom.” “Bakayi mamaki ta inda muka haɗu ba?, zuwan Dad ɗinka kano nafarko yahaɗu dani,kuma a lokacin yafara sona, kuma yabbayanamun and nayi accepting ɗinshi, to kaima haka ne.” “Mom bangane ba?.” “Senate kafaɗa soyayyar yarinyanan a lokacin farko dakaganta wanan shi ake kira “Love at first sight”.” Shiru yayi alamun yatafi tunani, itakam tana tunani take ɗanta yafaɗa soyayya mai zafi da kuma nauyi, gashi ɗanta tasan yanda take itadai fatanta Allah yasa yarinyar ƴar mutunci ce, wacce zata kula da rayuwar ɗanta. “Mom mene solution?.” Ta tsinkayi muryarshi, kallonshi tayi sannan tace: “Kaje kasameta.” “Mom I can't.” “Kaifa namiji ne zaka iya.” Girgiza kai yayi idanunsa suka ciko da ƙwalla kamar zaiyi kuka. “A haka zakace kanason yarinya, zakaje mata kana hawaye salan ta raina ka… Legends pen 08129553971. 3- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 03_ ~~~~~ Unguwar Nyan’ya “Kaga Abdulwahab ka tsaya muyi magana a nutse ta fahimta.” Bhatool dake zaune cikin ɗakinsh bayan tagama yi mai shara da mopping, hardasu turaren huta ta saka masa. Kallonta yayi yasan dole akwai abinda take buƙata kuma babbane tunda ta kai ga yi masa shara harda mopping sannan kayansa da’aka kawo daga wanki ta jera mai a cikin sif. Mama na kallonta tana yi ta ce mata. “Fati mai kuma ake buƙata!.” “Haba Mama shikenan ni bazanyi abu dan Allah ba.” “To ai Fati ansan halinki ne?.” “Ni ba abinda nake buƙata kuma idan akwai abinda nake buƙata ai munfi kusa wajen ɗan-uwanah.” Shiru Mama ta yi, dan tasan dai dole akwai abinda take ɓukata hakan yasa yanzu dataji tanayiwa Abdul daɗin baki yasa tayi murmushi. “Yaya kaci abincin kona daƙƙo maka ruwa ne?.” “A.a barshi kawai ki faɗi abinda zaki faɗa.” “Yaya kaga wallahi ina wannan ƙawartawa Suhaima?.” “Suhaima!.” Ya maimaita sannan kuma ya ce: “Ni ban santa ba gaskiyya.” “Baka gane ta ba, wacce muke makaranta tare to bikinta za’ayi nan da sati biyu, wani mai kuɗine yazo zaiyi wuff da ita, shi ne ankon nata da kuɗin kwalliya da komai da komai zai kai dubu ɗari.” “Dubu ɗari Bhatool?.” “Eyh Yaya!, wai nace yama sunan buduruwarnan taka, ai ranan mun hadu da ita har ƙasa na tsugunna na gaisheta, tana da mutunci sosai gaskiya kayi dance.” Dariya ce ta kwace masa amma ya riƙeta. “Bhatool yaushe kika bani atamfofi na siyomiki, kikace bikin ƙawayenki za’ayi.” Marairaice fuska tayi sannan ta ce: “Yaya kasanni da farin jini.” Haɗe rai yayi sannan ya ce: “Farin jinin nake ne yasa har yanzu baki da tsayayyen saurayin dazai aureki.” “Haba wannan ai gori ne, kuma Allah bai manta dani ba, wallahi natashi kawo mijina duk sai kunyi mamaki, ni yanzu kabani kuɗinnan na wuce.” Ta ƙarashe maganar cikin asalin yanayinta da take mai magana dashi na isa da izzah. “Bazasu samu ba.” Miƙewa tsaye tayi sannan ta ce: “Wallahi sai kabiyani sharar da mopping ɗin danayi maka.” “Aibani nasaki ba.” Tsaki taja sannan ta fice zuwa dakinta, mayafi ta ɗauka da jaka ta fice. Mama tana faɗin: “Ina za ki?.” “Police station.” “Bhatool wallahi karki fita.” Dawowa tayi ta ajiye jakar da mayafin nata takwanta akan gado. ~~~~~Washe gari Tun 7:30 tagama shirinta, fitowa tayi Mama da Abdulwahab na falon tahucesu tana shirin ficewa. “Ina za ki?.” “Makaranta.” Ta faɗa a dakile. “Bazaki karya ba.” Mama ta tambayeta, shikuma Abdulwahab ya ce: “Kuɗin makarantar fa.” “Naƙoshi. Zanje a ƙafa.” Duka tabasu amsa a haɗa tare da ficewa, bakin titi ta nufa tasami napep tahau, bama makarantar ta nufa ba Gidan Yaya Karima ta nufa dake unguwar. Red bricks. Itama gidan nata babbane amma bai kai ko rabin nasu Senate ba, amma suna thesame line ne, su Yaya karima sune gida na biyu, a ɓarin hannun hago, sukuma su Senate suna gida na biyar a ɓarin hannun dama. Yana zaune man kujera a parking space yaji zuciyarshi tafara bugu da sauri da sauri, bugun yana ƙaruwa akai-akai, runtse idonsa yayi saikuma yaji kamar Abinda yakeso na tunkaro dashi. Da sauri ya sauka daga kan kujerar ya nufi gate, hannu yasa ya buɗe ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin ya fito. Dai-dai lokacin da ita kuma ta tsaya ƙofar gate ɗin gidan Yaya Karima. Kallonta yake kamar wata sabuwar hallita yanajin bugun zuciyarshi yana daidaita sannan shi kanshi yanajin shi very full, kamar yagama cika cikakken mutum. Ƙofar gate ɗin aka buɗe mata tashige ba tare da tasan da tsayuwarshi a wajen ba. Kasa komawa ciki yayi yasamu waje ya tsaya yanabin ƙofar data shiga da kallo, itakam tana shiga cikin gidan main falo ɗinta tafara faɗin. “Anty! Anty!!.” Yaya karima dake cikin ɗaki ta fito tana faɗin. “Inna’illahi lafiya?.” Tsayawa tayi turus ganin Bhatool, ita kam Bhatool naganinta ta kwanta a ƙasa tare da fara birgema tana faɗin. “Anty Abba yace karku barni nayi kukan maraici, karku barni nayi kukan rashinshi. Amma kun rantse sai nayi.” Barrister Bashir ne yafito yana faɗin. “Autar Abba, me ya faru kuma me akayi miki?.” Kukan ta cigaba tana faɗin. “Sunkasa riƙe amanar da akabasu, sunkasa cika alƙawarin da suka ɗauka.” Kallon Karima yayi yana tambayarta me sukayi mata, girgiza mai kai tai alamun bata sani ba. “Kiyi haƙuri kidaina kukan-nan haka, kar yaranki sufito suganki haka.” Tashi tayi tare da fara goge hawayen nata. “Yawwa, yanzu faɗamana abinda ya faru?.” Goge hawayen tafarayi sannan tace: “Kafin Abba yarasu saida yabasu amanata ita da yaron can, sannan yace nayimusu biyayya sabida haka nayarda nabarmasa girman, amma su sunkasa riƙe amanar sunbarni sai garari da shan wahala nake: Kallonta sukayi baki ɗaya, Yaya Karima kuwa ta ƙufula hae wuya jitake kamar takamata tafara dukanta har sai taga banta numfashi. “Me kuma sukayi miki?.” “Yaron canne nace yabani kuɗi nayi ankon bikin Suhaima amma yaƙi.” “Ubanki ke da Suhaiman.” Yaya Karima ta faɗa a fusace sannan taɗora da ce wa: “Ke rayuwarki baki da aiki sai anko da biki, a haka rayuwarki zata ƙare, Bhatool kinayiwa kanki faɗa?.” “Kiyi shiru Karima, ai lokaci ne idan tayi aure bayi zata yi ba.” “To yanzu waye zai aureta a haka, tasawa ranta masifar girman kai, bata kulakowa sai yawon biki biki, duk kayanta anko ne baki ɗaya.” “Kiyi shiru dai na faɗa miki.” Barrister Bashir ya faɗa, yana maida hankalinsa kan Bhatool. “Ki daina kuka Bhatool ai hardani Abba yabawa amanarki, dan haka idansu sunƙi riƙe amanar ni kizo zanriƙe, nawane kuɗin ankon?.” Goge hawayenta tayi sannan ta ce: “Shi ankon 65 thousand saikuma kuɗin ɗinki da make-up.” “Bhatool wallahi sainaci ubanki, kuma karki ƙara zuwarmun gida.” Yaya Karima ta faɗa a fusace tare da tashi tabarmusu wajen, tasan kome zata faɗa Bashir sai yabata kuɗin nan. “Shikenan bari nakawo miki zaikijeki siye ankon, Allah yasanya Alheri.” ~~~~~ “Meyasa zaka bawa yarinyarnan kuɗin-nan, kullum ita bazatayi hankali ba? Yar waye ita da zata dinga yin irin waƴanan anko ɗin?.” “ita ɗin ƙanwar matar barrister Bashir ce, ko laifine idan tayi?.” “Bazaka gane ba, tunda Abdulwahab ya hanta kuɗinan yakamata kaima ka hanata, last zuwan danayi gida atamfofi guda biyar yakawo mata, waita bashi ƙyallen kuma duka na ankon bikin ƙawayenta ne, sannan yanzu tazo tana maganar bikin wata Suhaima, yarinyar da anan Makarantar da suke suka haɗo.” “Inaso kigane komai lokaci ne, yanzu nanda wani ɗan lokaci bazatayi ba.” Shiru Yaya Karima tayi amma itadai tagaji da wanan halin na Bhatool, zama yayi kusa da ita tare da dafamata kafaɗa. “Kiyi haƙuri kuma ku cigaba dayimata addu’a.” “Shikenan Allah ubangiji ya shiryata.” “Amin ya Allah, sannan dan Allah banaso kinuna mata ɓancin rai kinji.”, Ya ƙarashe maganar kamar mai naiman alfarma. Tashi ta yi tadawo falon tasame Bhatool data zauna ɗai-ɗai tana faman danna waya. “Bazaki makarantar bane?.”, ɗagowa tayi ta kalleta sannan ta ce. “Hutawa zanyi yau nagaji da wahalal makarantar nan.” “Bhatool muyi magana dake mana, idan kinada time?.” “To Yaya inajinki.” Ta faɗa tana kashe wayar alamun tabata hankalinta baki ɗaya. “Bhatool kinsanfa kin girma, sannan ƴan-uwan Baba sunsa ido akanki, meneyasa bazaki nutsu kifitar da miji ba kiyi aure.” Kallonta Bhatool tayi sosai cikin yanayin nutsuwa sannan tace: “Yaya wai idan mijinan baizo ba, ni zanjanyo shi ne?.” Kallonta Yaya Karima tayi ido cikin ido sannan ta ce: “Kinaso kicemun duk cikin samarinki babu wanda kikeso?.” “Gaskiya ni bakowann irin namiji zan aura ba.” “Wane iri kikeso?.” Gyara zama Bhatool ta yi kamar wacce zatayi karatu ko dogon jawabi sannan ta ce: “Yaya inason namiji wanda zai bani ƴancina, wanda zaibani soyayya, yabani damar da zanyi duk wani abu da name buƙata.” Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce: “Bhatool kina *Hasashen soyayya* a rayuwarki, kina tunanin akwai sakaran mijin da zai ɗauki duk wani shirmenki ne?.” “Kamar ya ina *Hasashen soyayya*, *Yaya nasan Mace bata canja Namiji, yana canjawa ne sabida yana sonta* to nima zannemi maisona wanda zai canja.” “To Allah yabaki sa’a akan wanan *Hasashen soyayyar*” Legends pen 08129553971. 4- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 04_ “Kamar ya ina *Hasashen soyayya*, *Yaya nasan Mace bata canja Namiji, yana canjawa ne sabida yana sonta* to nima zannemi maisona wanda zai canja.” “To Allah yabaki sa’a akan wannan *Hasashen soyayyar*” ~~~~~ Yana tsaye jikin bango tun shigarta gidan, ya rufe idonsa yana sauraron bugun zuciyarsa. “Bud-die what are you doing outside?.” Buɗe idonsa yayi ya sauke su akan Anas,sannan ya sake rufesu. “Senate magana fa nake?.” “The Girl!.” Kallon shi Anas yayi sannan yace: Which Girl?.” Sai kuma ya ce. ”Unnamed?.” Ɗaga kai Senate yayi sannan yace:” I just saw her right now?.” Dariya Anas yayi sannan ya ce: Harta fara maka gizo ne?.” “Ba wasa nake ba Anas, wancan gidan naga tashiga.” ya faɗa yana nuna masa gidan da hannu, kallom gidan Anas yayi sanan yace: “Gidan Barrister?.” “Bansan gidan ba nima.” “Kuma ka tabbatar ita ce?.” “Wai maika ɗaukeni ne, idanba itace ba zance itace?.” “To yanzu mene zakayi?.” “I will wait naga tafiyarta.” Senate yafaɗa babu alamun ko damuwa da tsayuwar da zaiyi. “You know this isn't the solution?.” “Ka ƙyaleni.” Wucewa ciki Anas yayi ya barshi a wajen tsaye. A falo ya haɗu da Momi wacce fitowarta kenan daga ɓangaren Senate, Kallon Anas tayi sannan tace: “Where have you been?.” “Morning joking, ina kwana Momi?.” Anas yafaɗa tareda durƙusawa. Amsawa tayi sanan tace: “Ina Senate ɗin?.”, Amsa yabata dacewa “Yana waje Momi?.” Kallonshi tayi sosai sannan tace: “Waje kuma meyakeyi?.” Zama Anas yayi sannan yace: “Yayi miki maganar wata yarinya da yakeso, duk da shima baison yana sonta ba?.” “Yes yayimun daman neman danayi maka jiya, inaso nace kaje YSU ɗin kaganta.” “To wai yanzu ita yaga tashiga gidan Barrister.” “Inanema Gidan Barrister?.” Taƙarashe maganar da alamun son tunawa. “Matar da tazo ranar nan kika ce tanada tarbiya.” “Oh oh Gidan Karima zakace, toshi nan yaga tashiga?.” “Haka dai yace Momi, ninafi tunaninma gizo tayi mishi, it seems yafaɗa soyayya mai ƙarfi.” “Yes I understand too, Allah yasa yarinyar tazama ƙanwar Karima ɗinma. Yanzo go and call him.” Kallonta yayi sanan yace: “Momi sa masu aiki dan yanzu zai sauke mun kwandon masifa.” Tashi tayi da kanta tana dariya tasan tabbas yanzu zaizo yana bubbuɗe baki, waishinan masifa yake Maigadi tasa yakiramata shi, wanda shima sai dayace masa Momi ɗin tana compound. Shigowa yayi yana turu baki gaba yana haɗe gira kamar ƙaramin yaro yana shirin fara rigima. Momi kam naganin yashigo tashige ciki, bin bayanta yasakeyi har zuwa falo, wato uwar harara yamakawa Anas wacce tasa Anas tuntsirewa da dariya. “Momi kinganshi ko?.”, “Meyayi maka?.”, “Dariya.”, “To sannu.” Dariya Anas ɗin yasakeyi ganin yanayin dasukayi maganar kamar masu gasar maida martani sannan kuma a ƙarshe ta gwaleshi. Senate kam zama yayi kan kujera ba tare da yace ko uffan ba. “Katabbatar ita kagani tashiga gidan Barrister ɗin?.” kallonta yayi da mamaki sannan yace: “Allah ita ce.” “Okay have your breakfast, ina zuwa.” Daga haka ta tashi tashige ɗaki, shikuma yanufi dining Anas ta tsokanarshi amma yayi masa banza. Sunanan zaune Momi tafito, kallonta sukayi gaba ɗaya itakam tasa kai ta wuce. Yau ce rana ta farko da Momi tataka ƙafa tashiga gidan wata mata a unguwar, bayan wani gida data taɓa shiga sabida mutuwar maigidan. Maigadin gidan naganinta yabuɗe mata yana faɗin. “Barka da safiya Hajiya.” “Barka masu gidan na nan.” “Sunanan mai gidan ne kawai yafita.” “Okay.” kawai ta faɗa tare da shigewa, A fall tasami Yaya Karima wacce ke zaune tana danna waya. Baƙaramin mamaki Yaya Karima tayi ba ganin Momi acikin gidan nata, baki buɗe ta tashi tana faɗin. “Momi ina kwana?”. Murmushi Momi tayi tana amsaww da faɗin. “Lafiya kalau ƴar-momi ya maigidan.” “Alhamdulillah Momi, ga waje zauna dan Allah.” Zama Momi tayi tana yaba karamci irin na, Karima tana kuma addu’ar Allah yasa yarinyar da tilon ɗanta yafaɗa soyayya da ita takasance ƙanwarta. Fitowar Bhatool kenan daga kitchen hannunta rike sa plate wanda ta Soya plaintain tana faɗin. “Yaya gashinan nasan zakiji daɗinshi.” Tsayarda maganar tayi ganin baƙuwa mai cike da kwarjini. Ajiye plate ɗin Bhatool tayi tareda durkusawa sannan tace: “Ina kwana.” Murmushi Momi tayi sannan ta amsa da faɗin. “Lafiya Ƙlau ɗiyata.” “Momi ga Plaitain.” Yaya Karima ta faɗa tana ɗakko plate ɗin tare da miƙamata, Murmushi Momi tayi sannan tace: “A,ah ɗiyata, wanan ƙanwarkice?.” “Eyh Wallahi Momi, itace ke bina.” “Allah sarki, Allah itakuma yaushe ne bikinnata?.” Murmushi Yaya Karima tayi itakuma Bhatool takoma kitchen. “Munafata dai.” “To Allah yakawo nagari, daman yau kawai nace zanzo gidan Ƴar Momi mugaisa.” “Naji daɗi sosai Momi, Allah yaƙara lafiya.” “Amin-amin , bari na wuce.” “To Momi nagode sosai da sosai.” “Yasunan ƙanwartaki, tabiyoni ta ƙarbi turare.” “Sunan Fatima Bhatool.” Yaya Karima tabawa Momi amsa sanan ta ƙara cewa:”Angode sosai Allah yaƙara arziki.” “Amin.”Momi ta faɗa itakuma Yaya Karima tashiga Kitchen ɗin. “Ke zoki bita gidanta ki amsa saqo, sanan kuzuba plantain ɗin a bowl mai kyau kibita dashi.” “To.” kawai tace sanan, tazuba plantain ɗin a bowl mai murfi tarufe tafito, Momi na tsaye taɗauki mayafinta tayafa tareda bin Momin suka fice. Kallon Bhatool Momi tayi sanan tace: “Ɗiyata ya makaranta.” murmushi tayi sanan tace: “Makaranta Alhamdulillah Momi.” “Masha Allah, shekarunki nawa kuwa?.” Bhatool bataji komaiba dangan da tambayoyin Momi tace: “20 amma zanshiga 21 nanda 5months.” “Ah masha Allah angirma Saura kuma aure.” Shiru Bhatool tayi batare da tace komai ba suka tunkari gidan. ~~~~~Suna zaune kan dining ɗin. Anas namasa hira shikuma hankalinshi nakan wayaa. “Dum Dum” yaji bugun zuciyarshi naƙaruwa da sauri-sauri, hannu yasa yadafe ƙirjin tareda rufe ido. Da sauri Anas ya ce: “Senate are you okay?.” Bai kaiga bashi amsa ba Muryar Momi tayi sallama. Legends pen. 08129553971 Masu bukatar complete kofa abude ta ke. ‎5- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 05_ “Dum Dum” yaji bugun zuciyarshi na ƙaruwa da sauri-sauri, hannu yasa ya dafe ƙirji tare da rufe ido. Da sauri Anas ya ce: “Senate are you okay?.” Bai kai ga bashi amsa ba Muryar Momi tayi sallama suka shigo cikin falon Batool na biye da ita. Da sauri ya mike yana kallon ta yayin da yaji bugun zuciyarsa ya samu nutsu, wani sanyayyen murmushi ne ya kufce masa. Momi ta dubi Bhatool da take tsaye ta ce. “ Daughter ki zauna mana.” Murmushi ta mata tana zama a k’asa. “ Ah haba ki zauna a sama mana k’asan akwai sanyi ai.” Tashi tayi tana zama a kan kujera mai zaman mutum uku dan shine kusa da ita. Anas ya dube inda yake yaga ita yake kallo, taba shi yayi ya buge masa hannu, murya k’asa k’asa kamar wanda ya buya baya son a gan shi ya furta. “ Anas leave me Abeg!.” Momi na fadin. “ Ina zuwa.” Gurin su ta iso tana kallon shi cike da so da kauna, kafin ta ce. “ Son kaje ku gaisa.” Girgiza kai yayi. “ Ina tsoro gaskiya.” “ Har yaushe tsoron zai tsaya? Anas ka raka shi.” “ Ok Momi.” Ya kama hannu Senate yaja zuwa tsakiyar falon. Tana zaune ta aro nutsuwar dole ta sawa kanta, jin kamar tsayuwar mutane yasa ta dago kanta a hankali ta zuba masa sexy eyes dinta, ji tayi kamar ta taba ganin fuskar nan a wani guri. Da sauri ya janye idanunsa daga gareta yana matse hannu da karfi, Anas na sakar mata murmushi. “ Sannu fa.” “ Yawwa ina wunin ku.” “ lafiya, ya gida?.” “ Alhamdulillah.” Zama suka yi a kujera mai facing nata, duk motsin da zata yi akan idanunsa, sai ta jita duk a takure, can Anas ya katsai shurun da fadin. “ Ya sunanki Sis?.” “ Bhatool.” “Wow” ya fada a ransa yana lumshe ido kafin ya bude ya zuba mata, karaf suka had’a ido, wani kwarjini ta gani a tattare dashi hakan yasa ta sunkuyar da kai. “ Wani school kike ne?.” “ YSU.” Ta fad’a a dakile dan ta fara gajiya da tambayar. “ Ya ban sanki ba a school din? Wani department?.” “ ENT.” “ Ok bana daukar ku shiyasa, iya yan Anatomy nake dauka.” “ Ayya.” “ Ni baki sanni bane?.” Daga kai tayi ta gan shi ta girgiza kai alamu bata gane shi ba. Hararansa Senate yayi jin yana zakewa dayawa, dariya kawai yayi bai sake cewa komai ba. Momi ta fito hannunta rike da leda fari. “ Daughter kinyi shuru, ga yayunki bakwa hira dasu.” Sunkuyar da kai kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta tana murmushi da iyakacinsa fuska. Mika mata ledan Momi tayi ta karba tana mikewa ta ajiye bowl din hannunta ta ce. “ Mun gode sai anjima.” Ta juya zata fita. Da sauri Senate ya dubi Momi kamar zai yi kuka yana girgiza mata kai, ya mike da wuri yana kallonta har ta fita a falon, zuciyarsa ce ta harba da karfi yasa hannun yana dafewa, Momi tayi saurin isa gurin shi. “ Ka ajiye tsoron nan ka fuskanci soyayyarka, if not you’ll loose her.” “ A.a Momi, ki ce ta dawo.” ~~~~~Bayan ta fito daga gidan ne ta shiga gidan Yaya Karima tana mita. “ Yaya Karima ni fa bana son takura, haba.” Fitowa Yaya Karima tayi daga d’aki. “ Yanzu kuma me aka miki?.” “ Tun dazu kawai jiran sak’o, ta kawo da wuri shine ta ajiye ni ta tafi ciki, tabarni da yaronta mai surutu, amma Yaya naga wani kyakkyawa fa.” Zama Yaya Karima tayi tana ganin yanda take wani lumshe ido tana juyawa. “ Ke!! Kina lafiya kuwa?.” “ Hmm Yaya kenan bazaki gane ba, guy din ya hadu over, sai dai har na tafi ko magana bai yi ba, sai na gefensa da yake over sabi ya dame ni da surutu.” Zuba mata ido kawai Yaya Karima tayi tana ganinta. “ Yaya ina miki magana ma kin mantar dani! Uhm to nikam nama tafi zanje na siya anko, dan yanzu ko bazaku min ba Uncle zai min.” Ta dauki jakarta ta fice daga gidan. A waje takira wayar Suhaima tasa taturamata ankon dan so take taje kasuwa da kanta. Ta dade tsaye a bakin titin amma ba machine, dan dama unguwar ba machine ake samu ba saboda yayi nisa da gari. Tana tsaye wata baƙar mota ta tsaya a gabanta, sauke glass ɗin motar akayi, Anas ne da kuma Senate, ɗan haɗe rai tayi kafin Anas ɗin yayi magana. “ Ah Bhatool ina zuwa haka?.” “ Bayan tasha zanje.” “ Ok shiga mu kai ki ko?.” “ Dama kun bari ai zan samu machine.” Bata rai Senate yayi yana mintsinin Anas. “ Ah ah baza ‘ ayi haka ba, shiga muje.” Madadin ta shiga ta gurin Anas sai ta zagaya ta shiga ta bayan Senate, wani sanyi yaji ya mamaye shi lokacin da ta shiga, sanan yaji bugun zuciyarshi yadaidaita tsaf. jan mota yayi suka nufi hanyar bayan tasha. “ Yau ba makaranta ne?.” “ Bazan je bane, yau zan huta.” Ta fada a dakile dan haushin Anas ta fara ji. Bakin Senate na rawa ya furta. “ Kahh-rage music ɗinn.. nan.” ‘ Dama yana magana kenan? Na dauka ai kurma ne.’ tafaɗa aranta afili kuma murmushi kawai tayi domin muryarshi kaɗai abunso ce. Daganan babu wanda yaƙara cewa komai harsuka isa bayan tasha. Anas ne yace: “ A ina za ki sauk’a?.” “ A shagon Alhaji Mala.” “ Ok.” Yayi parking kusa da shagon, ta bud’e ƙofa tayi tafice Senate ne yabi bayanta ya fita, da mamaki Ansa ya fito yana kallon Senate. “ Senate where?.” Ɗame fuska yayi yana kallon Anas ɗin, nufan shagon tayi yana biye da ita Anas ma ya mara musu baya. Ankon Suhaima tanuna hoton,Nan aka ciro mata su guda uku. “ Nawa ne?.” “ Ya kama 76k.” Bud’e jakarta tayi da niyar bada kudin Senate ya miƙa ATM dinsa da sauri, bin hannunsa da ido tayi. Cire kudinsu suka yi suka mata package nashi a leda, ya dauka mata, murmushi ta sakar masa tare da fadin. “ Thanks.” “ You’re welcome.” ‘ Dai-dai ne, ai kuwa shagon takalma zamu wuce da gyelle idan yaso har da jaka ni ai gaba takaini gobarar titi.’ Ta fada a ranta a fili kuwa sai murmushi take masa. Bud’e baya yayi ya saka mata, Anas da ya zama dan kallo ya ce. “ Saura ina?.” “ Ina ta baku wahala fa da kun barshi ma kun tafi sabida daganan inaso naje wani shago ne.” Ta karashe tana dan sosa kai. “ Don’t take it some bother.” Anas ɗin yasake faɗa, shidai Senate sai binta abaya amma baya cewa ko ƙala. “ Thanks.” Tafaɗa. Kafin ta nufi shagon Alhaji Nuhu Tata suna biye da ita, duk da yana tsoro amma hakan bai hana binta ba sai dai baya bari su hada ido. “ Veils nakeso da shoes and handbag.” “ Wani colours?.” Juyawa tayi ta kalle shi. “ Please key din motar zan dauko kayan.” Mikawa Anas yayi bai yi magana ba kuma kansa a sunkuye, fita Anas yayi dan dauko kayan, yayin da shi kuma ya isa kusa da ita dan ganin wani yana mata magana hakan kuma ba karamin taba zuciyarsa yayi ba. Ganin ya tsaya kusa da ita ne yasa ta kalle shi. Y’an matan shagon sai ganinsa suke dan duk inda Senate ya shiga abun kallo ne, namiji iya namiji ga kyau ga hali ga k’asaita uwa uba farin jini. Dawowa Anas yayi yana bata kayan, cirowa tayi tana kallon colour kafin ta kalli pink din jaka da takalmi ta ce a kawo, haka ma taga maroon da brown, gyalle kuma ta dauki shentili baki da brown. Lissafa kudin kayan suka yi aka ce. “ 64k.” Nan ma kafin ta ciro kudi Senate ya bada ATM an cire. Tsaya kallon shi tayi a ranta tana fadin. ‘ Akwai Capacity ba laifi, shima kila Abba ya basa amanar nawa ne, amma shi sai yanzu ya bayyana.’ Hada kayan suka yi daya daga cikin yaran shagon ya dauko musu, fita suka yi suna jerawa tana ta danne-dannen waya, aka saka kayan a baya. “ Nagode sosai fa Allah ya biya.” Kallam da ya fara shiga zuciyarsa kenan ya zauna. “ Bansan ina zaku yi ba na katsai muku tafiya.” “ Don’t worry, yanzu ke ina za kiyi?.” “ Gida zan tafi.” “ Ok shiga mu kai ki.” Shiga tayi kafin suma suka shiga. “ Wani unguwa?.” “ Nyan’ya.” Hanyar suka nufa tana musu kwatance har suka isa. Fitowa tayi tana bud’e bayan ta fito da kayanta, Senate ya fito yana jin zuciyarsa na harbawa tamkar abun da yake buk’ata yana nisa da shi. Jin an zuba mata ido yasa ta ce. “ Nagode sosai sai anjima.” “ Uhmm yaushe za ki dawo gidan Barrister?.” “ Bani da lokaci kawai duk sanda naji inason zuwa nake.” “ Ok sai anjima.” “ Nagode.” Da haka ta shige ciki. “ Senate shiga muje.” “ A nan zan zauna.” “ Lover boy, muje gobe ma zaka ganta ai.” Numfashi ya sauke kafin ya shigo motar. ~~~~~~ Tana shiga Main falon ta tarar da Abdulwahab da Mama suna zaune. “ Rayuwa dadi, dadi! Rayuwa dadi! Wayyo dadi! Wayyo dadi! I’m so happy! I’m so happy, dama haka rayuwa take idan wani yakika wani zai sonka, y’an uwana sun kasa rike amanar da Abbana ya basu yayin da wasu bare suke rike amanar hannun biyu.” “ Ke! Waya baki kudi kika siya kayakin nan.” “ Mama kenan! Kyautata wacce ba’a tsammani tana zuwa daga masoyi ne wanda yassan soyayya kuma ya damu da mai son shi.” “ Tambayar ki fa ake?.” “ Abdulwahab ka min shuru a nan, wait tukun ni sa’arka ce ma.” “ Lallai yau Bhatool ta samu duniya.” “ Ai da kaki bani kudin Allah ya turo wanda ya bani.” Ta fada a asalin yanayinta na isa da izza. “ To waye ya baki?.” Cewar Mama tana zuba mata ido. “ Mijin Yaya Karima da kuma wani Kyakkyawan saurayi.” “ Waye ne shi din?.” “ Bazaku gane ba.” Daga haka ta tattare kayakinta ta nufi daki. “ Ni yanzu ba mutumiyar banza bace da kudina a aljuhu….. Legends pen 08129553971. Masu bukatar complete kofa a bude ta ke. 6- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 06_ “ Bazaku gane ba.” Daga haka ta tattare kayakinta ta nufi daki. “ Ni yanzu ba mutumiyar banza bace da kudina a aljuhu.” “ Abdul yarinyar nan fa sai an dakatar da ita, rawan kanta ya fara yawa.” “ Hmmm Mama yanzu kana magana zata kwanta ta fara burgima tana fadin ita sam ba’a kyauta mata, daga karshe ma ta ce amanar da abbana ya baku baku rike ba.” “ Haka za’a zuba mata ido?.” “ Mama zata daina fa, komai lokaci ne.” Ya daura da fadin. “ Sai dai wani abun da yake burgeni da ita bata kula maza bare har ta bari a bata mata suna, iya iskanci ta dai a gida ne da kuma gurin kawayenta, sai Yaya Karima kuma.” “ To! Allah ya shiryar da ita.” “ Ameen.” Akan gado ta zuba kayan tana video din su, WhatsApp group nasu na iya yen Team nasu ta shiga tayi posting tana caption da *bayan ni sai wacce? Saura dinki kawai ya rage min guys* Nan da nan Amrah ta gani. “ Kina wuta ina binki da fetur, yarinyar nan akwai capacity ba laifi.” Jannah da itama yanzu ta hau online tagani, voice ta danna da wuri. “ This gurl Wallahi kina bamu a jikinmu, da nayi calculation over a 150k fa.” “ Dey play yara, remain dinki shi ma zai kai 50 ko?.” Ta tura tana danna musu emojin dariya. Suhaima ta danna Video call, nan kowa ta shiga aka fara hira, sai hura mata kai suke chan da hiran nasu yayi nisa ne ta furta. “ Ina zamu kai dinki ne? Coz inaso a cire ni sosai a samu a fitar da shape kamar zasu fito a kayan.” “ Ke!!! Ki bari kawai gobe a school muyi maganar.” Cewar Suhaima tana kashe kiran. “Dama naje wajen ɗinki, sunbiya kudin. Kokuma karson zuciyata yayi yawa.” Tafada a ranta bayan sun kashe wayar.Cilli tayi da wayar ta nufi toilet. ~~~~~~~~~~ Red Bricks Yana kwance a kan gadonsa ya rungumi filo idanunsa a rufe, yayin da Anas ke zaune kusa da shi yana fama magana. “ Senate yanzu ko maganar kirki ka gagara yiwa yarinyar nan, haka za’a yi soyayyar.” Mantar dashi yayi ya sake rungume filon a kirjinsa yana lumshe ido. “ Senate are you okay kuwa?.” “ Anas barni, ka hanani kallonta me kyau sai damuna kake.” “ Wait a ina kake kallonta?, don’t tell me that you’re imagining her?.” Bar masa kan gadon yayi ya dawo kan kujera dake tsakin ya dunkulu a ciki yana rufe ido, dariya Anas ya saka yana kallon shi tare da ficewa daga dakin. Momi da fitowarta daga kitchen ta kalle shi ta ce. “ Are you okay? Laughing for?.” “ Momi Senate mana! He’s gone crazy, wai fa imagination nata yake tun da muka dawo.” “ To why not yaje ya same ta.” “ Momi yanzu zai fara I’m scared.” Ya karashe yana kwaikwayon yanda Senate yake. Dariya kawai Momi tayi ta nufi dakin nasa, Anas kuma ya tafi gida dan dare yayi. ~~~~~~~Washe gari Tun 7:35 ta gama shirinta dan zuwa makaranta, fitowa tayi hannunta rike da wayanta ta rataya handbag dinta. Wajen daining ta nufa tana kallon su kafin taja kujera ta zauna. “ Mama ina kwana?.” “ Lafiya! har kin shirya?.” Gyada mata kai tayi. “ Kai baka iya gaisuwa bane? Ko baka san akwai manya a nan ba?.” “ Bhatool da alamu daga jiya zuwa yau akwai kwayar da kike hambuda ko?.” “ Bana son raini irin naku na yaran zamani, yanzu kai Abdulwahab zaka dubi cikin idona ka fadamin zancen banzan nan tsabar raini da fitsara.” “ Yau din kuma Fati? Da alamu bakya buk’atar komai a gurin shi ko?.” Mama tafaɗa ganin yanda ta zaƙe sai rufe ido take wai ita babba. Tashi ma tayi ta dauko wayarta da jakarta ta fice bata kula su ba, murmushi kawai Abdulwahab yayi Mama ta bita da addu’a. Tana fita ta samu machine ta hau, boss stop ya kaita ta bashi kudinta kafin ta hau wani machine zuwa Makaranta. Direct gurin garden ta isa ta zauna akan resting bench, wayanta ya fara ruri ta dauka. “ Rich kid ban ganki ba.” “ Ina resting bench.” Tafaɗa tare da kashe wayar. Isowa gurin ta su Amrah sukayi suna fadin. “ Sai da ke yar kuna bakin wake, tamu ba irin tasu bane.” Dariya suka kwashe da shi kafin ko wacce ta samu guri ta zauna sannan Suhaima na fadin. “ I can’t believe wai har kin gama siyan komai na auren, remain dinki fa.” Gyara zama tayi tana kallon su daya bayan daya. “ Ba abun surprise bane fa, kudi ne zai yi magana.” Shigowa haraban Makarantar yayi tare da yin parking ya nufi gurin garden, bugun zuciyarsa ne ta fara sauyawa ta soma bugu da sauri sauri a hankali ya furta. “Bata shiga ajin ba kenan.” Inda ya saba zama ya zauna yana ciro wayansa ya soma dannawa. “ Ni fa yanzu bani da damuwar komai, yau kuma sai 2-4 muke da shi, so ina gamawa zan ware gida kawai, dan wannan yaron sai ya bani kudin dinki ban isa ba bazan kashe kudina ba kuma.” Dariya suka yi Jannah na cewa.“ Kina son kudinsa kuma kina ce masa yaro Bhatool ke fa sai shiriyar Allah.” “ To ai Yaron ne tun da kam na girme shi, a kudi ne kawai ya girme ni, kuma idan bai bani kudin nan ba yau sai Hizba.” Taba ta Amrah ta soma, buge hannunta tayi. “ What dalla kina mintsini na.” “ Dalla ke baki iya gulma ba, ga can Guy din nan fa yau ma ya sake zuwa.” Idan ta nuna musu suka kallo Jannah na dariya k’asa-k’asa. “ I think guy din nan yana son daya daga cikin mu ne.” “ Idan ma daya daga cikin ku yake so ai is not forbidden ko?.” Shiru ita dai Bhatool ta yi tana zuba masa ido ko giftawa bata yi Jannah na dariya da fadin. “ Wata fa ta fola.” “ No ba falawa nayi ba fadawa nayi gaba daya.” Murmushi ya yi yana gyara zaman shi tare da kiran Salman. “ How far?.” “ I’m waiting for you fa.” Sanyayyar muryansa ya daki dodan kunnen ta. Tashi tayi tsaye ta kalle su. “ Guy din nan ya kamata yau na tambaye shi me yake zuwa yi.” “ Bhatool dawo ki zauna ko kin manta school ne? Kowa kan iya zuwa yayi harkan gaban shi, mu da kullum muke zama a nan an taba yi mana magana ne, let him.” “ Maybe ta fada love ne.” Jannah tafaɗa tana dariya ƙasa ƙasa. “Jannah daily talk naki kenan Love.” Cigaba da hiran su suka yi amma hankalinta ya dawo kansa, duk ta gagara nutsuwa kawai so take taje taji dalilin bibiyar ta din da yake, dan ta fara ganewa bibiyarta yakeh. “Ke ban iya barin bala’i yayi sleep ba, ko barni naje.” Bata jira amsarsu ba tatashi. Jiyayi zuciyar ta buga da wani mugun ƙarfi, da sauri ya juyo idanunsa suka faɗa cikin nata. “Hey.” Tafaɗa tana zama, jikinshi ne yafara rawa ƙafafunshi na ƙakaɗawa, amma ya ƙureta da idanu. “Senate!!.” tafaɗa sakamakon jiya taji ankira shi da haka, wani sanyi yaji acikin zuciyarshi gaba ɗaya a rayuwarshi baitaɓa jin wani yakira sunanshi dai-dai ba kamar haka ba. “Yeyes.” Yafaɗa tare da sauke ajiyar zuciya kamar yau yafara magana a rayuwarshi. “Kaine kenan, anan school ɗin make?.” Girgiza kai yayi alamun “A’ah”, sai a lokacin ta tuna cewar baya magana. “Ko Anas kake jira?.” “A’ah, Eh.” Yafaɗa duka da sauri, murmushi tayi sanan tace. “Okay nagode faa.” “Dame?.” yafaɗa yana kallonta ciki da mamakin yanda yakejin shi complete kaman yasamu duk abinda yakeso a rayuwa. “Jiya mana ko kamanta?.” “A’ah wanan baby komai.” “Tom zantafi.” Tafaɗa tare da tashi ta koma cikin ƙawayenta. Dai dai lokacin da Salman yazauna yana faɗin. “So my man is now fall in love.” Girgiza kai Senate yayi sanan yace “No.” Karfe goma cif ya tashi ya bar Makarantar. Juyawa tayi dan ganin ko yana nan taga wayam, numfashi ta sauke kafin ta ce. “ Muje capteria.” Legends pen 08129553971,masu bukatar complete kofa a bude take. 7- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 07_ A Hanyar Cafeteria ne Amrah tace “Wancan gayen mai kyau ne.” “Wane gaye kuma?.” Suhaima ta tambaya its dai Bhatool ba face ko ƙala ba amma tabbas ta yarda Senate mai kyau ne. Sai ƙarfe 06:00 na yamma suka bar YSU daman su kullum shigar 08:00 fitar 06;00 ne ko sun gama classes ɗin su haka zasu zauna suyi ta surutu. Alla Alla take ta koma gida domin ta karɓi kuɗi wajen Abdul, wani ɓari na zuciyarta ma cewa take taje can kasuwar suyi ta ta watse, a haka ta samu ta ƙaraso gida. Da sallama a bakin ta kamar abun arziƙi ta ajiye jakarta ta ɗauki tsintsiya tana faman shara. “A’ah Bhatool sharan me like?.” Murmushi tayi ta cigaba da sharar tana faɗin. “Yanzu idan ban gyara gidan nan ba wa zai gyara, idan ban taya uwata aiki ba wa zai taya ta.” Kallonta sosai Mama tayi sanan face “ Banbu ƙaci aikin ba Bhatool balle nan da ƴan mintina kizo kina cemun ban riƙe amana ba nasaki aiki, idan wani abun kikeso kawai faɗi.” A jiye abun sharar tayi tana faɗin “Wallahi Mama so nake kisa yaron can Abdul yaban kuɗin ɗinki.” “Ke yanzu fisabillahi Bhatool baki da wata magana sai abaki abaki, ke ko tanadi baki iya ba?.” “Ta nadin mene, naga dai haƙƙin kune ki ciyar da ni, ku tufatantar dani sanan ku ilmantar dani haka zalika ko kaini ɗakin Miji, sanan kuma gashi Allah yabani ƙani mai mai kuɗi, Sister na tana auren mai kuɗi sabida nice Nan banza zan zauna na yi tanadi.” Baki Mama ta riƙe sanan tace “Uhm ke ba bamza bace.” daga haka ta koma ɗaki, itama Bhatool ta ɗau jakarta ta shige ɗaki. ~~~~~~~Red bricks “Mom please introduce me to her.” Kallon Senate Mom tayi, wani kululin takaici kamar ta kwaɗe shi, wanan sanyi halin nashi yayi yawa. “Senate wane introducing yarinyar da na kawo maka har gida, akwai wani introducing da make ɓukata?.” “Mom yau tayi mun magana, amma ba a soyayya ba, I want you to introduce me to her as lover.” “Senate idan nayi introducing dinka as her love, sai na dinga raka ka zance ina yi maka hira ko?,bayan kunyi aure sai na koma gidan ko?.” Girgiza kai yayi sanan yace ”Ba haka ba Mom, ina so ne tace mun tana so na” “Sabida ita ta rako mata duniya ko, kaine yaka mata kayi proposing da kanka, and please ka nemi Anas ya taya ka ka barni na huta.” Shiru yayi kamar zaiyi kuka, idon sa ya ciko da ƙwalla, bakin shi ya fara rawa. “Ya Allahu.” Momi ta faɗa tare da tashi ta matso inda take, hannu tasa akan ka faɗar shi sanan tace “Senate what?.”. “Mom I so much loved her, I'm always going far.” “I know kana sonta but yaka mata ka nemo soyyarta da kanka, shine zata so ka ta ga girman ka as her Husband.” “Mom taya zanyi hakan?.” “Kabani two days kaji.” Gyaɗa mata kai yayi daga man ya tashi ya nufi ɗakinshi, Anas yaje gidan su kasancewar Maman shi ta dawo daga Kano. ~~~~~Nyanya Zaune take kan ƙaramar kujera a tsakar gida, Mama kuma na daga gefe kan abun sallah, hankali Bhatool na kan waya tana chatting tare da zaman jiran Abdul ya dawo ta karɓi haƙƙinta, ita ko acikin gadonta ne. Sallama yayi ya shigo hannunsa riƙe da ledar da ya siyo fruit wanda wanan abu ne wanda kullum sai ya siyo, Tashi tayi tana faɗin “Yaya Abdul sannu da dawo wa.” Kallon ta yayi sanan yace “Yawwa sannu Yaya Bhatool ya makaranta ya gida.” “Ai kune manya , ya kasuwa kawo na riƙe ma.” ta faɗa tana karɓar ledar, kamar abun arziƙi ta shiga kitchen ta ɗakko plate ta zuba, suna zaune ta kawo musu ta ajiye tana faɗin. “Yaya ya kasuwa?.” “Kasuwa mungode Allah, ya makaranta.” Murmushi tayi sanan tace “WallaHi Alhamdulilah, Yaya.” Shiru ne ya biyo baya Kafin Abdul yace “Yawwa Mama ɗazu ake faɗamun Goggo Larai ba ta ji daɗi ba, ina ga yanzu zanje na duba ta ko?.” Dariya Bhatool tayi sanan face “Abdul kanada shishigi a rayuwar ka, mene haɗin ka da wanan matar?.” “Ubanki Bhatool yayar mahaifin naku, uwa ɗaya uba ɗaya zaki ce mene haɗin ku da ita, to kisani har ke za’aje dubiyar nima gobe zanje.” “Ai shikenan, da shi wanda ya bada amanar, da amanar da ya bayar aka hada aka zage, Abbana ka mutu ka barni inda ba’aso na, ina da ba ƙauna ta ko ƙaunad farin ciki na, Abbana ka mutu ka barni wajem waƴanda basa sauke hakkinka akaina, Abba ba samun sutura abinci kawai suke banI.” Kuka take sosai kamar gaske, gaba ɗaya jikin Abdul yayi sanyi, tashi yayi yadawo kusa da ita. “Bhatool kiyi haƙuri yanzu me aka yi miki.” Kuka take yi sanan tace “Yanzu nazo da anko aka kasayimun aka barni, yanzu kuɗin dinki ma an hanani so ake naje titi nayi bara.” “Waye ya hanaki, kin tambaye ni ne?”. Girgiza kai tayi sanan tacee “Nasani Yaya Baza ka bani ba.” “Yanzu tashi ki shirya muje gidan Goggo Lami ɗin sai mu biya wajen mai ɗinkin na bashi kudin. Miƙewa tsaye tayi tare da kar ka ɗe jikinta ta shige ɗaki, Girgiza kai kawai Mama tayi sanan tace “Allah ya kyauta.” Bayan mintina kaɗan ta fito cikin wata doguwar ta wani lace, irin ɗinkin nab da amare keyi sai zuba uban kyalli take, ankon bikin wata ƙawarta ne shima da tashin hankali akayi mata shi wajen dubu saba’in amma tun da akayi bikin ta watsar ba ta ƙara ɗaukan shi ba sai yau. “Bhatool ina zaki da wanan kayan?.” Takalmin ta mai tsini ta ajiye ƙasa tana faɗin “Zani gidan maƙiyana ai gwanda nasa ka ka ya masu kyau, yanda baƙin ciki zai ƙarasa Goggo Lami ta mutu har lahira.” “Innullahi wa inna illahir rajiun, ni Habiba wanan yarnya Allah yakawo mata sauƙi da nutsuwa da kuma hankali, walallahi ko da wasa wani yazo neman auren ki sai na bashi kuje can ku ƙara ta.” Dariya Abdul yayi yana faɗin “Mama da ƴar ta.” “Faɗi ka ƙara Mama da Ƴar ta, ƴan bakin ciki.” Ficewa yayi itama tabi bayanshi tana faɗin “wallahi kafin mu ƙarasa sai na siya sabon cover ɗin waya mai kyalli dan wallahi so name bakin ciki ya ƙarasa munafu kar matar naman ~~~~~~ Red bricks Senate ne zaune cikin ɗakinshi tare da wani kyakyawan saurayi wanda take sanye cikin ƙanan kaya, saurayin ne ke magana yana cewa. “Senate you're so annoying wallahi, na dawo daga Cyprus ba ka barni na samu isashen hutu ba kace kana da magana kuma nazo kasani a gaba.” “Am sorry Juraij, Na faɗa soyayya.” kallon shi Juraij, sabida Juraij ya nada baiwar Fahimatar Senate ssosai da sosai. “Who is the lucky girl.” Murmushi Senate yayi sanan yace “Sunan ta Bhatool I mate her last three months but ba mu taɓa magana da ita ba sai yau, I mean yau da kanta tayimun magana.” “Hahaha.” Juraij ya faɗa sanan yace “Muga hotonta kuma yanzu me make tunanin yi.” “I don't know.” Ya faɗa yana nuna mai hoton ta dake kan screen ɗin wayarsa wanda ya dauke ta a makaranta ba ta ma sani ba. “This Girl?.” Juraij ya faɗa cike da mamaki. Legend's pen 08129553971 8- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ _Page 08_ “This Girl?.” Juraij ya faɗa cike da mamaki, ”Kasanta.” ɗaga kai Juraij yayi yana dariya “Uwar ƴan rigima kenan yayanta abokina nane, ina siyan shadda wajensa daga nan muka fara mutanci dashi, wanan yarinyar ƙanwar sa ce the stubborn girl I ever meet in my entire life.” “Juraij she is my future wife stop addressing her like that.” Senate yafaɗa Kamar zaiyi kuka. “Okay nadaina but kana ganin haɗin ku zaiyi?.” “Why not?.” Senate ya faɗa tare da ta shi ya shiga toilet, shima Juraij ɗin tashi yayi ya fice. ~~~~~Suna cikin mota tana baza ido inda zata hango masu fruit ko provision store, dan tayi alƙawarin sai ta ƙunsa musu takaici sanan kuma tana son canja case ɗin waya, cikin ikon Allah ta hango wani kusa da shi kuma masu fruit ne sai kuma provision store. “Abduk wai haka zamuje gidan nan hannu mu na dukan cinya?.” Tsayar da tuƙin yayi ya kalleta sanan yace “Bangane ba?.” Girgiza kai tayi sai kuma tace “ Ai daman ba zaka ganw ba, zaka je gidan maƙiyan ka shine zaka tafi a tsiyace ƙarshen asara babu ko leda.” Kallon ta kawai Yake shi tsoron sa ma kar taje tace musu maƙiyan ta. “Kinga nutsu yanzu me kikeso ayi?.” “Kaga mu sauka muje wancan provison ɗin kasiya mata ƙwai, madara, suger sanan muje wajen mai fruit shima kasiya ma ta dayawa ma, yanda baƙin ciki da takaici zai ƙarasa ta.” Da mamaki yace ”Ke Bhatool!.” Rufe ido tayi tana faɗin “Abdul umarni na baka ba shawara ba.” Shi dai mamaki ya kusa kashe shi yanda ta rufe ido tana faɗa wai ita umarni ta bayar. “Abdul wallahi idan naƙara maimaita kaina baza kaji daɗi ba.” Parking yayi zuwa gefen titi suka fito, wajen mai fruit su ka fara zuwa “Mai fruit inaso kabani lemo na dubu biyu, kankana ta dubu biyu? Abar ba ta dubu biyu, ko kuma kabani kowanne na dubu uku uku, sai ƙabani ayaba ta dubu daya kaga yakama dubu goma.” Mamaki kam zai iya kashe Abdul a wanan lokacin, dan yanda take abu kamar itace Mama. “Bashi dubu goma.” Abdul yaji ta faɗa, hannu yasa a aljihu ya ciro kudin gaba ɗaya ya bata. Lissafa wa tayi tabawa mai fruit ɗin 10k sanan ta shiga provison store ɗin, man madara tasa aka ɗakko mata babban gwangwani da kuma milo shima babban gwangwani sai ƙwai kiras biyu, akayi mata lissafi taba su kuɗin aka biyo ta dasu. A wajen mai fruit ɗin ta ga Abdul Yana tsaye,”Amso fruit ɗin ka haɗa da kayan Nan kasa a bayan mota, sanan mai fruit ka ware mun banana ɗin daban, dan bazan ba taba tunda ba kuɗin ubanta ne, wanan ɗin ma Allah ya isa.” Daga haka tashiga shagon masu cover ta siya wata mai ƙyalli sosai sanan ta dawo mota suka nufi hanya. Babu wanda yayi magana a cikin motar sai Bhatool da take cin ayaban ta hankali kwance, har suka ƙarasa ƙofar gidan Abdul yayi parking. Saida ta gama gyara jikinta sanan tafito daga cikin motar, hannun ta riƙe da Wayarta wacce cover ɗin ke ƙyalli da sheƙi, a yangance take tafiya Abdul riƙe da ledoji kamar wani ɗan aikinta a haka suka shiga cikin gidan. Kasancewar gidan family house ne, duk ƴan uwan Abbansu na cikin gidan, ɗai-ɗai ku ne basa gidan, cike yake da hayaniyar yara kamar ba farkon magariba, duk inda sukayi binsu ake da kallo. Abdul ne ke tsugunnawa yana gaidasu, itakam daga tsaye take cewa “Ina wunin ku.” su bama ta gaisuwar ta suke ba, kayan jikinta dake ƙyalli suke kallo. A haka har suka ƙarasa ɓangaren Goggo larai wanda shima cike yake da mutane, Sallama sukayi aka fara gyara musu wahe da faɗin. “Bisimillah ku shigo.” Shiga sukayi Abdul na ta washewa ƴan uwa baki, Bhatool kam ta haɗe rai a zuci kam cewa take “Kai Abdul anyi asararre waƴanan kake washe baki haka wallahi sai kaci gidanku.” “Goggo ina wuni, ya ƙarfin jikin.” Abdul ya faɗa bayan sun zauna, “Lafiya ƙlau Abdul bawan Allah.” Goggo larai ta faɗa murya ƙasa ƙasa. “Ai kings leda munafuka done kice bawan Allah.” Bhatool ta faɗa a ranta, a fili kuma cewa tayi “Ina wuni ya jiki naki, Allah yasa kaffara ne.” “Batula jiki Alhamdulillahi, ya maman taku.” wata uwar harara Bhatool ta maka mata “Wai Batula.” Abdul ne yace tana lafiya, itama gobe zata shigo.” “To Allah ya kawo ta lafiya.” Goggo Larai ta faɗa zuciyarta cike da mamakin yanda ‘ya’yan Ahmad suka samu cigaba a rayuwa, yaran da suke kira ‘ya’yan mace, gashi sun sami cigaba sama da ‘ya’yansu. “To Goggo ga wanan ba yawa.” Bhatool ta faɗa ta miƙo ledojin sanan ta buɗe jakarta ta ciro canjin kuɗin ta miƙawa Goggo tana faɗin “Ga wanan ma Goggo.” Hannu na rawa Goggo larai ta amshi damin kuɗin tana faɗin. “Allah ya yi muku albarka yaran nan, Allah ya yi wa mahaifinku rahama.” Miƙewa Bhatool tayi tana faɗin “Ameen.” Haka Abdul ma yatashi ya fito yana mamakin wanan Abu na Bhaool, su kam su Goggo larai mamaki ya kusan kashe su yanda yaran suka canja baki ɗaya, kana ganin su kasan suna cikin huti da jindaɗi, Furai ce tace “Ni kam kunga kayan jikin yarinyar nan kuwa?.” Habi ce tace “Furai nagani wallahi, ke mijin karima ke mata suttura dan ubanta basu da kuɗin da za suyi wanan suttura.”. “Ba kiga wayar hannunta ba, har wani sheƙi take.” Furai ta sake faɗa. “Uhm kwaji da shi nidai na samu abun duniya cansu ƙarata, idan na gama ci na tufa abinda ke bakina.” Goggo Larai ta faɗa tana buɗe ledojin. “Ni Balaraba wacce aka haifa tabawa ranar sa’a, wanan kayan duka?.”Goggo larai ta faɗa tana duba kayan duka. “Aike Goggo waɗan nan yara sun gwangwaje ki.” Habi ta faɗa tana kallon kayan “Ni wallahi waƴanan kayan a banza bazan daina tsanar yaran nan ba, da uwarsu gashi yanzu sunyi arziƙi sun bar namu yaran.” Furai ce face “A’a Goggo likita yace karki saka damuwa a ranki.” Tsaki Goggo larai taja tana shan lemo tana faɗin “Banso rayuwar ‘ya’yan Ahamadu tayi kyau haka ba.”. “Wai kinga wani banza kallo da wanan mara kunyar yarinyar take mana.” Jumala dake gefe tun ɗazu ta faɗa, “Nagani wai its yar iska,Wallahi Goggo ki ta da bori sai anhaɗa ta aure ko da kamisu ɗan wajen Baffa ne.” Jumala ta faɗa sabida ita tana mugun bakin ciki Karima ma shekara ɗaya ta bata amma gashi ita tayi sure gidan hutu amma ita auren ta biyu duk sun rabu sai yara guda uku, amma gashi wanan yarinyar ma tana cikin kuɗi. “Nikam maganarki da gaskiyya Jumala.” Furai ta faɗa tana kwance sauran kaya, ita dai Goggo ba tace komai ba. ~~~~~~Parking ya yi dai dai ƙofar gidansu bayan sun biya ta wajen mai ɗinki an bashi kuɗin, kallon Abduk Bhatool ta yi sanan face “Allah ya isa kuɗin mu, nasan suna can suna ta zagin mu amma ko ba komai mun barsu da kayan bakin ciki.” “Ke dai kika sani, fitar mun daga mota.” Abdul ya faɗa yana koƙarin buewa ya fita “Mara kunya.” ta faɗa tana fita, a haka suka shiga cikin gidan tana gaba yana baya. Kai tsaye ɗakin ta huge tana faɗin “Wanan kayan kamar huta haka nake jinsu.” “Ke dai kika sani da wani yace ki saka su.” Mama dake cikin ɗaki ta faɗa, Abdul dai ɗakin Mama ya shiga yana faɗin wanan ‘yar taki halinta sai ita, yau idan ki kaga abinda tayi sai kinsha mamaki.” “Ai wallahi Bhatool bazata taɓa hankali ba, ina tausayin Wanda zai aure ta.” Bhatool daga cikin ɗaki face “In Allah yayarda miji nane zai fara kaiki aikin hajji tunda wanan yaron kaiki Umara.”. Washe gari ~~~~~~Red bricks Ganin hae ƙarfe 08:00 babu Senate babu alamun shi yasa Mom tafiya ɗakinsho domin ganin mai ya hana shi tashi, kwance yake yana bacci fuskarshi ɗauke da murmushi da alama mafarki take mai daɗi, juyawa Mom tayi zata fita taji yana cewa “Bhatool I so much love you,please karki taɓa barina.” Kallonshi Mom tayi sosai its tana mamakin yadda Senatr yafa ɗa soyayya mai zurfi da Yarinyar da ba ta masan yana sonta ba. Komawa ɗakinta tayi ta ɗau mayafin ta ta fice zuwa gidan Karima, Yaya Karima na Zaune ta ji sallamar Momi, tashi tayi tana faɗin “Ina kwana Momi.” murmushi Momi tayi tana faɗin. “Lafiya ƙlau daughter ya mai gidan naki?.” “Alhamdulillah Momi.” Yaya Karima ta faɗa tana ta mamakin zuwa Momi ɗin, Zama Momi ta gyara sanan tace “Karima na tambaye ki wani abu mana?.” “To Momi Allah yasa na sani.” Kana jin yanda tayi maganar kasan tana cike da ruɗu da mamaki. “Wanan yarinyar da kika ce ƙanwarki ce mene alaƙarku da ita?.” Legendspen 08129553971. 9- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 09_ *Not editing* “Wanan yarinyar da kika ce ƙanwarki ce mene alaƙarku da ita?.” Kallon Momi tayi da mamaki sosai sanan tace ”Bhatool!?.” Ɗaga kai Momi tayi alamar “Eyh” Zama Yaya Karima ta gyara sanan tace “Ƙanwata ce, itace ke bina amma kuma sakamakon amanarta da mahaifin mu yabamu kafin rasuwar shi,yasa muka mayar da ita kamar itace last born ɗin, shi Abdul ne ƙarami amma kasnacewar shi namiji ne kuma duk kasuwnaci Abban mu a wajen shi yake yasa muka bashi girman, ni kaina ganin shi nake kamar shine sama dani sai ita muka bata kankantar.” “Kunyi mata miji ne?.” Momi ta tambaya, Girgiza kai Yaya Karima tayi sanan tace “Banjin ta fara kula samari yanzu fa tana 18 duk da nima bankai 20 nayi aure ba.” A jiyar Zuciya Momi ta sauke sananface “I can't hide anything for you, impact ma abun ya shafe ki, Senate ne yafa ɗa soyayya da ita tun wata rana da yaje school ɗinsu, kuma soyayyar da ya faɗa wata kalal soyayya ce ni tsoro ma take ban, yanzu haka tun dazu yakasa tashi kawai murmushi yake yana kiran sunanta, gashi kuma da tsoron mata kamar masifa bana jin zai iya tunkararta ma” Itama ajiyar zuciya yaya Karima ta sake sanan tace ”Momi Bhatool wata iriyar yarnya ce mai muguwar rigima, ta kwanta a kasa taita burgima bawani abu bane a wajenta, haka zatazo nan tai tamun ihu, last time ma da tazo kukan tayi mun kuma ga Sebate very silent anya tafiyarsu xatayi dai-dai kuwa?.” “Daughter shi yaji yagani yace yanaso, to zai iya yanzu wata alfarma nake nema wajenki.” “wace alfarma ce momi?.” Dafa kafaɗar Yaya Karima Momi tayi sanan tace “Kinsan ba’a taɓayin aure sai duka ɓangare biyu sunso juna, inaso ki taimaka ki zamo tsani wanda Senate zai taka ya samu soyayyar Ummi dukda nasan abu ne mai wahala.” “Momi me kenan zanyi?.” Yaya Karima ta tambaya “Daughter ki kawo Bhatool gidanki ta zama kusa da Senate.” Shiru yayi Karima tayi Rigimar Bhatool ba’abunda zata iya ɗauka bane, amma kuma tabbas a karamci irin na Momi ta cancanci Karima tayi mata sama da haka, sanan Mama da Abdul zasu ɗan samu bakim su ya huta na kwana biyu, kuma tabbas Bhatool za tayi dacen sirika. “Daughter!.” Momi ta faɗa ganin tayi nisa cikim tunani “Ki yarda dani ba zan taɓa cutar da ƙanwarki ba, ko wani ma sanan bawai ina nuna son nawa ɗan bane, nasan matsalal shi sanan ko ke a ɗan shiga gidana da kikayi kinsan yana da matsala tsoron mata kuma indai har baiyi nasarar saka soyayyar a zuciyarta ba, dole ya haƙura.” “Shikenan Momi insha Allah zanyi.” Murmushi Momi tayi sanan tace “ Tabba gidan ku yasamu kyakyawar shaida, mahaifiyarku tayi ƙoƙari akanku bayan rasuwar mahaifin ku, a ɗan karamin binciken da nasa akayi mun, Allah yajikanshi da rahama.” “Ameen yah Allah.” Yaya karima ta faɗa, ba tayi mamakin binciken da Momi tasa akayi mata ba domin dama ya dace duk wanda zai nemi aure yayi. ~~~~~ YSU Tun wajen 10 Bhatool ke baza ido a cikin garden ko za ta hango Senate, amma babu shi babu alamun shi gaba ɗaya hirar da suke hankalin ta baya kai, Jannah ce tace “Yanzu ke Amarya ina zaki Make-up?.” “Teemarhs glow zanje, ina ga ma ta 150k za’ayi mun.” Dariya sukayi sanan Amrah tace “Sai dake Suhaima Amarya, Bhatool ke fa.” Sai a lolacin hankalin ta ya dawo kansu, Murmushi tayi sanan tace “Me?.” kallon ta su kayi baki ɗaya “Do you mean you're not with us?.” Girgiza kai tayi sanan tace “Ban dai ji mai kuka ce last ba.”.“Muna magana ne akan wajen kwalliya.” . “Uhm ina zamu.” Bhatool ta tambaya alamun dai ba taji mai suka ce ɗazu ba. Jannah ce tace “Ita dai amarya wajen Teemahs glow zata, ayi mata ta 150k.” Kallon Suhaima Bhatool tayi sanan tace “Sai dake capaciteted ko ina zaku.” ta ma yarda hankalin ta gasu Jannah da Amrah “Ni wallahi sister na ta iya kwalliya wajenta zani.” Amrah ta faɗa alamun dai tayi broke. “Uhm nima da kaina zanzi zara abata jiya haka kawai naje nasa yaron nan yayi asarar kuɗi sanan kuma ya biya mun kuɗin ɗinki, ko bani da imani bazan ƙara amsar kwabo ba a wajen sa.” Dukkanin su sunsan idan tace yaro to Abdul take nufi, haka sukayi ta hira kowa yana faɗin abinda yake bakinsa, kamar ko yaushe dai sai shida suka bar makaranta kowacce ta nufi gidan su. A cikin gidan ta tarar da Yaya Karima, wani tsalle tayi taje ta rungume ta tana faɗin “Yaya Karimancy.”. Neman faɗuwa su ka fara daga ita har Yaya Kariman da ƙyar Yaya Karima ta dafa bango tana faɗin “Ke wai mai yasa baki da kwakwalwa ne?.” Cuno baki tayi gaba tana faɗin “Ke kuma mai yasa ba’a yi miki abun arziki ne?.” Kallonta Yaya karima tayi sanan tace “Bhatool indai wanan ne abun arziƙi to riƙe abunki bana buƙata.” Kallonta ta mayar ga Mama sanan tace “Mama nadawo.”. “Naganki.” Mama ta faɗa tana mayar da kallonta ga Karima, sai bayan Bhatool ta shiga Mama tace “Anya Karima yarinyar nan tabiki kuwa, ke da kike da ƙaramin ciki.” Ajiyar zuciya Karima ta sauke sanan tace “To Mama ya za’ayi su likitocin ne suka ce ina buƙatar mai ta yani aiki, kuma idan ba ita ba wa nake da ita, haka dai zanyi hakuri da ita.” “Shikenan bari nayi mata magana.” Mama ta faɗa tana shiga ɗakin da Bhatool ke ciki,Zaune ta sameta tana danna waya. Zama Mama tayi kusa da ita tare da kiran sunanta “Bhatool!.” Ɗagowa tayi ta kalleta “Na’am Mama.”. “Inaso ki buɗe kunanki kijini, Yayarki Karima bata da Lafiya a asibiti ance ta naimi mai ta yata aiki hakan yasa zaki bita gidanta na kwana biyu kafin ta samu ƙwarin jiki.” Kallon Mama tayi sanan tace “Gidan Yaya Karima zanje na kwana biyu?.” tayi maganar kamar mai tambaya. “Eyh can zaki.” Mama ta bata amsa, shiru tayi sai can tace “To yaushe zandawo.” “Bayan ta samu sauƙi.” Shiru Bhatool tayi tana son tace bazata ba, sai kuma ta tuna dole zata ga Senate Mutumin da kyansa da sautin muryarsa ya tsaya mata arai. “Shikenan bari na haɗa kayana.” ta faɗa tare da tashi. Cikin ƙanƙani lokaci ta haɗa kayanta da kuma jakar makarantar ta, fitowa tayi tsakar gidan ta tarar da Mama da Yaya karima, Mamace ta kalleta sanan tace “Bhatool kinga bata da lafiya ki nutsu dan Allah.” Cikin sanyi murya tace “Insha Allah Mama, ki gaishe mun da Abdul ɗina.” Daman haka Bhatool take tana da rigima amma tabbas bata son nisa da Mama ko Abdul, Kasancewar Yaya Karima na da mota kuma a ita tazo ba mijinta bane zaizo ya ɗauke ta kuma ga Yamma yara sun kusa dawowa daga school, daman tun safw tazo sunje duba Goggo Larai ita da Mama. Ko a mota ma Bhatool ba tace uffan ba, har suka ƙarasa Gida tayi nisa a cikin tunani taji Yaya karima tace “Dan Allah je gidan Momi kice mata nadawo ta aiko da saqon.” Tabbas Bhatool taji dadi sosai domin tunanin da takeyi kenan tinda suka tawo har tazo, “Tom Yaya.” ta faɗa tare da nufar hanyar gidan. ~~~~~Yana zaune cikin gidan Yau bai samu ko yaje makarantarsu Bhatool ba sabida gaba ɗaya ita yake gani da ya rufe idonshi, bama yaso yayi tafiyar da zaiyi nisa har yakasa rufen idon, kuma abunda ke sa mai jindadi shine idan ya ganta murmushi take masa, kuma Salman ne da juraij sunzo a gidan suka yini, sun tattauna kan bikin ƙannen Salman da kuma company da zasu buɗe, Rabin kuɗin da za’a bude company ɗin Abban Senate ne ya bashi sanan shima ya haɗa da nashi, shi ke da kaso 75 cikin ɗari na campanin sai Kuma juraij da yasa kaso 25 wanda yasawa Salman ne domin Juraij Dad ɗinshi ya bashi company shi dake Cyprus shiya ba cika zama nigeria ba. Sunyi ja’inja sosai wajen saka sunan kamfanin inda Senate yadage sai dai asa Bhatool, Shi Salman bai cika hayaniya ba Juraij ne dai yayi ta ja dashi,shima kuma wasa yake mai sabida yana so yaga Senate na doguwar hira kuma a rayuwar Senate dasu kaɗai yake iya hirar sakamakon sanin halinsa da Juraij yayi hakan yasa yake janshi da doguwar hirar, ƙarshe dai suka amince a haka. Bayan tafiyarsu ne yadawo falo, su na zaune tare da Mom suna hira sama-sama,sai kuma Anas da bai daɗe da daowa ba, Anas ɗin ne ke tsokanar Senate yana cewa”Ango mijin Amarya.” Wani kallo senate ya watsa mai ba tare da yace komai ba. “Angon Batula.” kallonshi ya ƙarayi sanan yace “Stop.” cikin sasanyar muryarshi. “Na batula.” Anas ya sake faɗa yana dariya, kallon Mom senate yayi wacce take zaune kamad ba ta jinsu. “Mom! kiyi masa magana.” Harara ta makawa Senate ɗin sanan tace “Komai ni zan maka ko?.” Hannu yasa ya fara sosa ƙeya shi kuma Anas ya ƙara cewa “Senate Bhatool.”. “Mene yasa ba zaka kira ta da Anty ba.”Daga Mom har Anas juyowa sukayi suka kalleshi, jin yanayin da yayi magana kamar bashi ba,Murya cike da ƙarfi da ƙwarin gwiwa da kuma kwar jini,son ƙara tabbatarwa ne yasa Anas ƙara cewa “Bhatool senate.”. “Anas ba kai naiwa magana ba?.” Tabbas shi yayi maganar wallahi,Mom ce tace “Senate, daman ka iya magana haka?.” cikin fushi yace “Mom mai yasa bazai kirata Anty ba,ai na girmeshi dan haka mata ta ta girmeshi.” kallon ikon Allah Mom ta tsaya yi, kenan idan yana cikin ɓacin rai shine yake magana haka lallai ne. “I'm sorry.” Anas ya faɗa”Sorry for your self.” Senate ya faɗa tare da tashi. Rufe idonshi yayi da ƙarfi tare da riƙe ƙirjinshi.. Legend's pen 08129553971. 10- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 10_ Rufe idonshi yayi da ƙarfi tare da riƙe ƙirjinsa, dai-dai lokacin da tayi sallama ta shigo falon, da sauri ya bud’e manyan idanunsa yana sauke su akanta. Momi ta mike tsaye tana murmushi ta amsa sallaman tare da cewa. “ Daughter k’araso mana.” Murmushi tayi tana shigowa cikin falon, har yanzu idanunsa na kanta ya gagara daukewa. Har k’asa ta durkusa tana fadin. “ Momi ina kwana?.” “ Lafiya Daughter ya gida? Kin zo lafiya? Tashi ki zauna a sama.” Momi ta fad’a tana murmushi. Da lafiya ta amsa tana zama a kan kujeran kafin ta kalli Anas ta furta. “ Ina kwana?.” Washe mata baki yayi yana cewa. “ Lafiya kalau Bhatool ya Makaranta? Yasu Mama da kowa da kowa an same ku lafiya? Ya…” Hararan da Senate ya masa ne yasa yayi dif bai ce komai ba sai dariyar da yake yi ƙasa-ƙasa, kallon Senate din tayi ta ce. “ Yaya ina kwana?.” Sanyayyen murmushin nan nasa ya yi ya ce. “ Lafiya.” Yana komawa ya zauna yana facing nata. Momi ce ta nufi fridge ta dauko mata ruwa da juice ta ajiye a gabanta tana fadin. “ Daughter ki sha ruwa ko.” Murmushi tayi bata ce komai ba, Senate sai murmushi yake yi kamar wanda ya zauce, kafin ya ce. “ Bhatool ruwan gidanmu ne bazaki sha ba?.” Da sauri ta kalle shi dan batayi tunanin zai sake yin magana ba har taji zazzakar muryansa mai kwantar mata da hankali, wani sanyi taji a zuciyarta kafin ta ce. “ A koshe fa nake.” “ Haba daughter dan ban dibo miki abinci bama ko?.” Cewan Momi tana bata fuska. “ Momi Wallahi na koshi yanzu nasha ruwa, dama Yaya Karima ce tace nazo za ki ban sako.” Ta karashe suna hada ido da Senate. “ Ok to ina zuwa bari na dauko miki.” Cewan Momi ta nufi dakinta. Tashi Senate yayi ya dawo gujeran da take kai yana fadin. “ Za ki dade a nan ko?.” “ Eh nazo taya Yaya karima zama ne bata da lafiya.” Hannunsa ya saka a cikin sumarsa yana shafawa kafin ya kalli Anas ta gefen ido yana sakar masa murmushi, girgiza kai kawai Anas yayi bai ce komai ba. Momi ce ta dawo hannunta dauke da bakin leda, mikawa Bhatool tayi tare da fadin. “ Gashi nan Daughter.” Karba tayi tana mai tashi tare da cewa. “ Momi sai anjima.” “ To Daughter ki gaishe da Karima.” Da sauri Senate ya mike yana mara mata baya da fadin. “ Momi bari na taka mata zuwa gidan.” Ya fita da sauri dan ya isa gurinta. Momi ta dubi Anas tana fadin. “ Naga Senate ya canja ne lokaci kadan, daga yanayin maganar zaka gane yana magana tamkar zaki, ina nufin muryansa da kausashi.” Momi ta karashe da dan mamaki, dan Senate idan zai yi magana duk a cikin sanyi yake sai dai daga dazu ya canja ya zama cikekken na miji, amon muryansa ma ya isa ya sa jikin mutum ya dau rawa. Anas ya ce. “ Momi kila dan ya fara soyayya ne ya chanzu.” “ Maybe.” Kafin ta nufi kitchen. Bayan ya iso inda take suka jera suna tafiya, fuskarta dauke da murmushi haka ma nasa, kamar ba zaiyi magana ba kuma sai ya ce. “ Bhatool.” Ya kira sunan a wani irin voice. Ji tayi babu wanda ya kai shi iya kiran sunan ta, a wani irin yanayi ta kalle shi ta furta. “ Na’am Senate.” Tsayawa cak suka yi babu wanda ya motsa, kafin ya ce. “ Kina da wanda kike so ne?.” Girgiza kai tayi, wani naunauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya saki murmushi ya ce. “ Muje ko.” Suka cigaba da tafiya babu wanda ya cewa wani kala. A bakin get ya tsaya ta shiga, ganin ya tsaya yasa ta ce. “ Ka shigo ku gaisa da Yaya mana.” Girgiza mata kai yayi ya ce. “ A’a yanzu kunyar ta nakeji, akwai lokacin da zan shigo har mu gaisa muyi hira da ita.” “ Ok nagode ka gaishe min da Momi.” Ta fada tana masa bye bye ta shiga falon. Har sai da ta bace kafin ya sauke numfashi yana furzar da iska ya ce. “ Yau na mata magana, yesss God kasa kar tayi wani saurayi har ta gane inason ta.” Ya fada yana tsalle da murmushi kafin ya koma gida. Tana shiga falon ta fara ihu wanda ya tsorata Yaya Karima ta fito da gudu daga kitchen. “ Wallahi sona yake, yess na kamu da soyayyar Kyakkyawan saurayi fari ajin farko irin na fita cikin kawaye da shi, na kece raini.” Cike da haushi Yaya Karima ta ce. “ Shi ne zaki shigo da ihu?.” “ What the fuck, Yaya Karima ki barni kawai.” Ta fada tana fadawa akan three seater ta lumshe ido. Filo Yaya Karima ta dauka tana buga mata, da sauri ta tashi tana dariya ta nufi dakin da ta sauka ta ce. “ Sai hakuri idan zaki iya, kisan wanda ya fada soyayya baya jin shawara.” Yana komawa gida ya shigo falon da gudu yazo ya rungume Momi. “ Babana Lafiya? What’s wrong?.” “ Momi babu wanda ya kai ki sona a duniya, ina kaunar ki Momi.” Dariya Anas yayi yana ciro waya ya fara musu video yana fadin. “ Cigaba mana da maganar, irin yau kaga bugun zuciyarka, ai har yaran ku sai sun ga video nan In Sha Allah.” Turo baki gaba Senate yayi yana hade fuska ya nuna Anas yana kallon Momi ya ce. “ Momi ki ce ya daina bana so.” “ Anas ka daina baya so.” Cewan Momi tana dariya. “ Ke ma dariya kike min Momi?.” “ A’a kuka nake.” Juyawa yayi ya tafi dakinsa yana guna-guni kamar yaro karami. *Bhatool* Tun bayan da ta shiga dakinta bacci ya dauke ta, sai kusan mangarib ta fito tana bata fuska. Yaya Karima ce da Barrister a falon yaran sun tafi wasa, kallon ta Barrister yayi yana cewa. “ Yar dakina nazo kina bacci.” Sakin fuska ta yi tana cewa. “ Uncle ina wuni?.” “ Lafiya ya gajiya.” “ Alhamdulillah.” Tashi yayi yana cewa. “ Ni kam na wuce masallaci kar na makara.” “ A dawo lafiya.” Yaya Karima ta fada tana masa murmushi, da haka ya fice. Duban Yaya Karima tayi tana yamutse fuska ta ce. “ Yaya abinci.” “ Ni zan kawo miki kenan?.” “ Ni bance haka ba, naga bakon ka Annabin ka.” Da mamaki Yaya Karima ta ce. “ Ke ce bakuwar kenan?.” “ Eh mana.” Jinjina kai tayi tana danna wayanta, zama Bhatool tayi a kasan tana fadin. “ Nikam gurin Abbana zan tafi, duk babu wanda yake so na sai shi, abinci ma ana ma mutum yanga, abun duniya da za’a mutu a barshi ana hana ni.” Ta fashe da kuka. Jikin Yaya Karima ce yayi sanyi ta tashi tazo gurin ta tana durkusawa ta jawo ta jikinta, tana bubbuga bayanta ta ce. “ Bhatool kiyi hakuri mana, ba fa hanaki abincin nayi ba, amma ai kema ba bakuwa bace.” “ Babu wani nan, kawai bakya sona ne, amanan da Abba ya baku kukeson ku ci.” Ta kuka take maganar. “ Wallahi Bhatool ba haka bane, bari na dibo miki abincin kiyi hakuri.” Ta mike ta nufi kitchen din. Bata dade ba ta dawo hannunta rike da tray da abinci a ciki. Mikewa Bhatool tayi tana karba ta nufi daining table, zama tayi ta fara cin tuwo miyan egusin tana mita wai yaji yayi yawa, Yaya Karima bata kula ta ba ta nufi dakinta tana cewan Momi ta kawo mata masifa. Tana gama ci ta tashi ta dauki ruwa a fridge ta koma dakinta, salla tayi kafin ta dauki waya ta fara charting da friend’s nata kuma duk hiran akan auren da suke dashi ne, tana zaune aka kira Isha ta tashi tayi, sai kusan goma kafin tayi bacci. *Yaya Karima* Kallon mijin nata tayi tana cewa. “ Barrister sai ina ganin kamar Senate zai sha wahala a hannun yarinyar nan, dan ko mu da muke yayunta muna shan wahala bare kuma mijinta da zasuyi zama na har abada.” “ Karima bana jin zaman Bhatool dashi akwai matsala, Bhatool tana da hakuri sannan kuma tana da tsoro, kuma miji ai ba wasa ba, ni a ganina a musu fatan alkhairi idan har auren nasu alkhairi ne.” “ Hmmm! Barrister Bhatool fa….” Dakatar da ita yayi yana cewa. “ Karima kar baki yayi yawa a ciki, Allah ya tabbatar.” Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa. “ Amen.” Kasan zuciyarta kuma yana raya mata cewa akwai matsala. ✍�Legends pen 08129553971. 11- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 11_ Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa. “ Amen.” Ƙasan zuciyarta kuma yana raya mata cewa akwai matsala. Murmushi yayi ganin ta tafi duniyar tunani ya ce. “ Mar’atussaliha!.” Juyowa tayi tana kallon shi ta ce. “ Na’am Hayati.” “ Kar ku saka damuwa a ranki kinsan ciki ne dake, yanzu ba lokacin tunani bane, yanzun lokacina ne.” Ya daga mata gira. Dariya tayi tana fadawa kirjinsa. *Senate* Yana zaune a tsakiyar gadonsa shi da Anas suna video call da Juraij da Salman. Salman ya ce. “ Senate soyayyar yarinyar nan ya saka baka gane komai.” Anas ya ce. “ Hmm!! Ku da bakwa tare dashi kenan amma har kun gane, idan zaku bawa yaron nan shawara tun wuri ku bashi, bayi da magana sai na Bhatool.” Rai a bace ya kalli Anas yana cewa. “ Na fada maka ka daina kiran sunanta tsirara kana cewa Anuty Bhatool.” Dariyar rainin hankali Salman yayi yana cewa. “ To kaji dai ko Anas, saboda haka take note.” “ Ni fa bazan ce mata Anuty ba, after all na girme ta.” “ Wallahi da Anuty zakana kiranta.” Senate yayi maganar yana hararan shi. Dariya kawai yayi yana kallon Juraij ya ce. “ Ya kayi shuru fa?.” “ Hmm!! Ba shuru nayi ba, lamarin Senate ke ban tsoro, nifa nasan yarinyar kuma akwai rawan kai, ga rigima, kaga Senate kuma bai iya ba, shine nake tunanin soyayyar nasu.” A tsawace ya yi maganar wanda yasa dukan su yin shuru. “ Ina ruwanku idan tana da rigima, ko ku zaku zauna da ita ne? For the last time idan daya daga cikin ku ya sake embarrassing din matata ban yafe ba, kuma sai mun rabu dashi.” “ Gaskiya ne baka so kuma dole sai mun fada maka.” Cewan Juraij a fusace yana disconnecting din nasa, Salma ya ce. “ Mun ji ayi hakuri.” Shima ya kashe. Anas ya tashi ya nufi kofa yana fadin. “ A dakin k’asa zan kwana sai da safe.” “ Ku kuka sani kuma.” Ya fada yana jan bargo ya rufe fuskarsa. ~~~~~~~Washe gari Tana tashi da safe ta shirya dan yau suna da lecture na karfe takwas kuma tana so tayi attendance, shiryawa tayi cikin abaya blue mai ratsin fari, sai sheki da daukar ido yake, tayi roiling din veil dinsa. Handbag dinta ta dauka ta saka perfume nata da lips glow ta jefa biro a ciki, kafin ta dauki wayanta tana bud’e wardrobe ta dauki kudi ta zuba. Sauri sauri ta fito, a daining ta hangi Yaya Karima da mijinta suna breakfast, isa gurin su tayi ta gaishe su tana cewa. “ Na tafi muna da class eight.” Barrister ya bata kudin machine, ta karba tana godiya ta fito waje. Tana tsaye machine yazo ta hau, a bus stop ya ajiye ta ta bashi kudinsa ta hau wani machine zuwa Makarantar. Tana shiga Makarantar ta kira number Amrah, bugu daya ta dauka tana cewa. “ Billahil lazi kiyi sauri wai test zai yi.” Kashe wayan tayi tana sauri ta isa department nasu. “ Excuse.” Ta fada cikin sanyin murya. Kusan duka ajin sai da suka juyo da hankalin su zuwa gare ta, a hankali Lecturer ya sauke glass din idanunsa ya zuba mata ido. Magana class din ya dauka wasu na fadin bazai barta ta shiga ba wasu na cewa ya fada soyayya da ita. Muryansa taji yana cewa. “ Ki shiga test zanyi.” Da mamaki team nasu suka kalli juna, Jannah ta ce. “ Kun ga kallon da ya mata kuwa?.” Amrah ta rage murya tana murmushi ta ce. “ Ni kuwa na gani.” Suhaima na fadin. “ Ku bari sai mun fita kafin muyi magana, yanzu any slice of mistake zai fitar damu.” Shuru suka yi suna zubawa Bhatool ido. Duk taji wani iri, a sanyaye ta soma tafiya zuwa gurin su ta zauna, paper ta ciro ta rubuta reg no ta, kafin ta fara rubuta question din, question biyar ya rubuta ya ce a amsa duka kuma 30 minute, sannan ko wanne da a and b. A hankali ya soma zagaye class din yana kallon su daya bayan daya, dai-dai bayanta ya tsaya yana zubawa yatsunta kallo ganin yanda take rubutu a natse. Ji tayi kamar an tsaya a kanta hakan yasa ta juya ba shiri, karaf suka had’a ido, da sauri ta janye idanunta tana kallon Amrah ta gefen ido, murmushi kawai suka yi wanda iya sune suka gane abun su. Sai da ya tabbata ta gama kafin ya ce. “ Submit, before I count 1 to 5.” Kafin ka ce me har kowa yayi submitting. Suna fitowa daga ajin Amrah ta ce. “ Guys I don’t get rite, me hakan ke nufi?.” Tafiya suka cigaba da yi zuwa wajen garden Jannah na cewa. “ Maybe kawai ya taimake ta ne.” “ Wannan ba taimako bane, ko kin manta waye Dr Hashim? Ranar fa bani da lafiya nazo amma ya hanani shiga lecture dinsa, yau kuma Bhatool tazo kuma tayi letting amma ya bar ta ta shiga.” Suhaima ta fada tana zama a kujera bayan sun iso garden din. Kallon su kawai Bhatool tayi kafin ta gyara murya ta ce. “ I don’t think that so, maybe kawai ya taimake ni ne kamar yanda Jannah ta ce.” Tabe baki suka yi suna chanja hira, a cikin hiran ne Amrah ke cewa. “ Yau ban ga wannan kyakkyawan saurayin yazo ba.” Lokaci daya Bhatool ta hade rai tana cewa. “ Ina ruwan ki dashi?.” “ No kawai tambaya nayi fa, naga ya saba zuwa ne, kin ga dole na tambaya ko lafiya.” Ba ta bata amsa ba suka wani yazo gurin su yana cewa. “ Bhatool tazo inji Dr Hashim nan da minti biyar.” Ya karashe yana juyawa ya tafi. A tare suka hada baki gurin furta. “ Whatttt!!!!.” Amrah ta ce. “ Wallahi na fada muku dama kallon da ya mata ba’a banza ba akwai dalili, ya fola.” Ta karashe suna tafawa ita da Suhaima. “ Kai dalla shut up, ku fa kun zare I swear, kun san me nayi ne?.” Tayi maganar tana duba gefe da gefe kafin ta cigaba da cewa. “ Amma idan ya nuna alamun soyayya, to idan mun kara yin karatun shi make i bend, ai na banza ya samu.” Ta mike da wuri tana cewa. “ Bari naje kar na makara.” “ Bhatool idan kin ga ruwan sanyi ki kawo mana.” Cewan Jannah suna dariya. *Senate* Ko da suka hadu da Anas a daining babu wanda ya yi wa wani magana, har sai da Momi ta lura da haka ta ce. “ Naga yau baku yiwa junan ku magana ba, is that any problem?.” Girgiza kai Anas yayi yana cigaba da cin abinci, mikewa Senate yayi ya koma perlo ya zauna yana kallo amma rabi da kwatan hankalin shi yana gurin Bhatool. Sallaman abokanan shi yaji, da sauri ya juyo dan tabbatar da su din ne. Salman ne da Juraij kowa rai a hade, suna kallon shi suka dauke ido, gurin Momi da Anas suka nufa suna murmushi. Da mamaki Senate ya mike yana kallon su, kamar zai yi kuka ya ce. “ Ni kuke sharewa? Then sai me idan kun ki yimin magana, Mtsw.” Ya dauki key din motansa ya fice daga falon Momi na cewa ya tsaya bai saurare ta ba. Salman yayi murmushi yana cewa. “ Momi zafin soyayya ke rudar shi, yanzu ba’a isa a fada masa gaskiya ba inde akan Bhatool ce.” Fuskar Momi da damuwa ta ce. “ Me ya faru ne?.” Juraij ya ce. “ Hmm! Momi dan kawai mun ce yarinyar tana da rigima shine yayi fushi damu, shi ne muma muka yi fushi da shi.” Bata ce komai ba ta nufi dakinta dan dauko wayanta ta kira shi. *Bhatool* Da sallama a bakinta ta shiga office din nasa, yana zaune akan gujera mai juyi yana facing din kofar shigowa. Bayan ya amsa sallaman ne ya nuna mata kujera yana cewa. “ Have a seat.” Zama tayi tana sunkuyar da kai, bata ankara ba taji maganar da ya kusa toshe mata kunne da ganin ta…. ✍🏼 Legend's pen 08129553971. 12- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 12_ Bayan ya amsa sallaman ne ya nuna mata kujera yana cewa. “ Have a seat.” Zama tayi tana sunkuyar da kai, bata ankara ba taji maganar da ya kusa toshe mata kunne da ganin ta. “ Za ki aure ni?.” Da sauri ta dago da manyan idanunta ta zuba masa, kamar wacce aka ce an aikowa da sak’on mutuwa, muryanta har rawa yake gurin cewan. “ Sir Ina da wanda nake so.” “ I don’t care 🤷‍♂️, ba shawaran ki nake nema ba umarni na baki.” Ya fada yana nuna ta da yatsa, kafin ya cigaba da cewa. “ If not duk abunda kika gani ke kika jawowa kan ki, na baki nan da gobe kadai.” Wani yawu mai kauri ta hadiye, tun da take ba’a taba yi mata barazana ba sai yau, hakan kuma ba karamin tasiri yayi ba a kanta. “ You can go.” Ya fada yana juyawa akan kujera. Da sauri ta tashi ta fita daga office din har tana k’ok’arin fadi. Gudu yake tsulawa akan titin, horn kawai yake yi sai motoci su matsa, da gudu ya shigo YSU yana parking a tsakiyar Makarantar. Ya dade a ciki kafin ya fito yana bata fuska saboda zafin ranar yau din daban ce, gurin garden ya fara nufa amma sai yaji zuciyarsa bata canja bugu ba, da mamaki ya furta. “ Bata nan kenan..” Bai karasa ba ya hango ta tana nufo garden din duk a burkice. Duk da ya ganta a burkice amma sai da murmushi ta kufce masa, cike da k’asaita ya fara nufo inda take yana murmushi, wanda ita ko lura dashi bata yi ba. Tana shirin shiga garden ne tayi tuntube za ta fadi, cikin zafin nama ya taro ta ta fada kirjinsa, yana furta. “ Subhanallah tunanin me kike yi haka.” Sai da ta runtse ido kafin ta bude tana zuba masa, duk a tunanin ta zata fadi, janye jikinta tayi tana dan yin baya kafin ta ce. “ Thanks.” “ Tunanin me kike yi?.” Senate ya fada yana duban fuskarta. Girgiza kai tayi tana cewa. “ Babu.” Bai ce mata komai ba har ta isa gurin su kawayen ta ta zauna. Dukan su ita suke kallo, kafin Suhaima tayi magana a sanyaye. “ Me ya faru Bhatool?.” Shuru ta musu bata ce komai ba, ganin kamar bata tare dasu ne yasa Amrah taba ta tana fadin. “ Bhatool!!!.” A furgice ta juyo tana kallon su. Jannah na fadin. “ Me ya fada miki?.” Girgiza kai ta shiga yi tana kallon inda Senate yake tsaye ya zuba mata ido, duk kuma maganar da suke yi yana jin su. Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta ce. “ Babu abunda ya faru, just kawai gaisawa muka yi.” Dariyar rainin hankali Jannah tayi tana cewan. “ Wallahi karya kike Bhatool, tun yaushe muke tare da ke, mun sanki ciki da bai fa.” Hararan ta Amrah tayi tana cewan. “ Barta ta raina mana hankali ne, idan bata yarda damu bane ai shikenan damuwar ki.” Amrah ta mike a fusace zata tafi. Tashi tayi kamar zata yi kuka ta rike ta tana fadin. “ Ba wai ban yarda da ku bane, after all kun fi kawaye a gurina kun koma jinina ne.” Suhaima ta girgiza kai ta ce. “ Idan har kin dauke mu jininki ai zaki fada mana ba wai kice ba komai ba.” Wani yawu ta hadiye mai kauri, kafin ta juya ta dubi Senate da ya hade hannun a kirji ya zuba mata ido yana jiran yaji me zata ce, kafin ta sunkuyar da kai ta ce. “ Wai sona yake yi, dana ce masa ina da wanda nakeso shi ne ya ce ya bani daga yau zuwa gobe wai na yarda, ko kuma duk abunda ya faru ni na jawo.” Maganar da ya kusa hargitsa zuciyar Senate kenan, bai san sanda ya bar gurin a furgice ba. Kusan a tare suka furta. “ Whatt!!!.” Jinjina musu kai tayi tana cewa. “ Bansan me yake nufi ba, and….” Ta juya taga baya gurin hakan yasa tayi shuru tana tunanin ina yayi. Amrah ta ce. “ Dama kwarto ne, ai na dade da fada muku kune baku yarda ba.” “ Yanzu ya zamu yi Bhatool?.” Cewan Suhaima a dan tsorace. Numfashi ta sauke ta ce. “ Duk abun da zai yi yayi, karshe dai ya ce bazan yi passing din course na shi ba ko.” “ Ni fa ba wannan ba ne tsoro na.” Cewan Jannah tana cigaba da cewa. “ Kin san duk yarinyar da ya ce yana so sai ya same ta, idan kuma bai same ta ba to ya saka ayi raping na ta.” Dukan su shuru suka yi kowa da abun da yake tunanin a zuciyarsa, kafin ta kalli agogon hannunta tana fadin. “ Ni zan koma gida.” Suhaima tayi magana a sanyaye cike da damuwa. “ Ki bari mu gama lecture mana.” “ A’a akwai abun da zanyi ne.” Ta karashe tana daukar handbag din ta. Har bakin get suka raka ta ta hau machine kafin suka dawo cikin Makarantar ita kuma ta nufi gida. *Senate* Bai san sanda ya isa gurin motarsa ba ya shiga ya mata key ya fice a 360, idanunsa yayi ja ga wani ruwan da ya kwanta a ciki, fuskarsa tayi ja abunka da fari, jijiyoyin kansa sun fito rad’a-rad’a. Gudu kawai yake zubawa akan titin kalamanta yana masa yawo a kwakwalwa. < Wai sona yake, ni kuma na ce masa ina da wanda nake so.> Bai lura ba da machine din da yake gabansa har ya kusa bugawa, wani burki ya danna da karfi ji kake chusssss, buga kansa ya soma da stirring yana fadin. “ Why? Why!!!! Waye wanda take son? Dama tana da wanda take so ban sani ba? Ba zai yu ba, ni zan aure ta ba kowa ba! Ni neeeee!!!.” Ya karashe da karfi. Wayansa ce ta soma ruri ya duba, Momi ce hakan yasa ya ki dauka dan yana kusa da gida, tada motan yayi ya karasa gida yana horn da karfi wanda ya saka mai gadi lekowa dan yasa waye ne. Yana kallon motan yasan Senate ne hakan yasa ya bude da sauri, cilla hancin motar yayi ba tare da yayi parking dai dai ba ya fito ya nufi ciki. Duk suna tsaye a parlon Momi na fadin. “ Yaki picking fa, me ya…..” Bata k’arasa ba ya shigo falon. “ Subhanallah.” Kusan a tare suka fad’a, kafin Momi ta nufi gun sa da gudu tana kama shi ta soma furta. “ Me ya faru da kai? Hatsari kayi ne? Kai da waye?.” Ido kawai ya zuba musu, kafin ya janye jikinsa zai haura sama ya ce. “ Duk wanda zata aura ni ne ajalin shi, idan kuma ban aure ta ba to ni zan kashe kaina.” Ya karashe yana shiga dakinsa ya rufe da key. Duk sakin baki suka yi Juraij na cewa. “ Ta haukata shi, saboda yarinyar nan Senate ya zare, idan ba’a aura masa ita ba Wallahi zamu rasa shi kamar yanda ya fada din.” Ya karashe yana kallon su. A hankali Momi ta tako ta zauna tana had’a tagumi, ta rasa ta ina zata fara duk kanta ya dau zafi. Anas ya zauna kusa da ita yana dafata ya ce. “ Momi the best solution shine a kai kudin auren yarinyar nan.” Salman ya ce. “ Ita ta ce muku tana son shi ne?.” Ajiyar zuciya Momi ta sauke kafin ta ce. “ Ita fa bata ma san yana wannan shirmen ba….” Bata k’arasa fad’a ba suka ji karar fashe-fashe a dakinsa. A guje suka haura upstairs har Juraij na buge Momi dan sauri, buga k’ofan suka shiga yi Momi na kuka tana fadin. “ Senate kar ka kashe kan ka dan Allah.” Legend's pen 08129553971 13- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 13_ A guje suka haura upstairs har Juraij na buge Momi dan sauri, buga k’ofan suka shiga yi Momi na kuka tana fadin. “ Senate kar ka kashe kan ka dan Allah.” Magana ya soma musu yana kuka. “ Kun ce HASASHEN SOYAYYA na ke, gashi ina ji ina gani za’a kwace min ita, dukan ku babu wanda zai iya kwato min ita.” “ Senate ka bud’e kofan nan, ka daina fashe-fashen nan, ka kasa zuwa ka tunkare yarinya ka fada mata kana sonta, wai kai tsoro.” Cewan Anas kamar yayi kuka dan haushi. Bai kula su ba ya cigaba da buge-bugen da yake yi. Salman ya dube su ya ce suyi baya, suka matsa da karfi ya buga kofar sai gashi ya fadi, inda yake tsaye suka nufa duk dakin kwalba ga hannunsa din da yake digar jini alamun ya tsage. Cikume rigarsa Juraij ya yi yana cewa. “ Mad kawai, akan mace kana k’ok’arin halak’a kanka da rayuwarka.” Kafin ya sake shi yana shafa gashin kansa ya ce. “ Ka je ka same ta kace kana sonta mana.” Bai bari yaji me zai ce ba ya kama hannunsa suka fito daga dakin, suma suna mara musu baya. Idanunsa yayi ja har da hawaye a ciki ga hannunsa dake zubar da jini, ganin zasu fita daga falon ne yasa ya ce. “ Where?.” “ Gurinta.” Cewan Juraij yana jan shi. Turjewa yayi yaki tafiya ya ce. “ Me zan ce mata?.” “ Kana son ta.” “ Tana Makaranta ai.” “ Muje gidan idan bata nan sai muje school din.” Juyawa yayi yaga Momi da su Anas yana cewa. “ Bazan iya ba, I can’t Momi.” Momi ta gyada masa kai ta ce. “ Zaka iya, kuje zaka iya.” Jan hannunsa Juraij yayi suka nufi get masu aiki na kallon su, ta karamin kofa suka fita, tafiya kadan suka yi suna tsayawa a bakin get din gidan, kwankwasawa Juraij yayi mai gadi ya bude musu, ganin Senate ne ya saka shi cewa. “ Alhaji da kansa.” Murmushi ya kwakulo ya masa Juraij na tambayan shi. “ Bhatool tana nan?.” “ Eh Yallabai yanzu ta shigo tana masifa.” Basu kula shi ba suka nufi cikin falon. *Bhatool* Mai machine yana ajiye ta ta bashi kudinsa ta nufi get, bugawa ta shiga yi tana fadin. “ Zaka bude ko sai na balla get din.” Da gudu mai gadi ya bud’e yana cewa. “ Ina band’aki ne ayi hakuri Hajiya.” Hararan shi tayi tana cewa. “ Yanzu zaka matsamin ne ko sai na buge ka?.” Da sauri ya matsa mata ta shige tana masifa, a falo ta wurgar da handbag dinta tana kwalawa Yaya Karima kira. “ Yaya Karima!!.” Yaya Karima tana daki ta kwanta kenan taji kiran, da sauri ta fito tana cewa. “ Bhatool lafiya?.” Fashewa tayi da kuka tana zama a k’asa, da mamaki Yaya Karima ta iso gurin ta tana dafata ta zauna ta ce. “ Me ya faru?.” Kasa tsayar da kukan nata tayi tana fadin. “ Yaya ni na hakura da Makarantan nan.” Cike da mamaki ta ce. “ Me kuma ya faru? Me aka miki?.” Nan ta bata labarin komai bata boye mata ko daya ba, ta karashe tana kuka. Shuru Yaya Karima tayi, gefe guda na zuciyarta na tuna mata da Senate, kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce. “ Dago fuskarki ki kalle ni Bhatool.” Da idanunta da suka danyi ja ta dago tana kallon ta. Yaya Karima ta ce. “ To ke waye kike so?.” “ Yaya burgeni kawai yake yi.” “ Waye ne shi din?.” Shuru tayi kafin tayi magana suka ji sallaman Juraij da Senate, lokaci daya zuciyarta ya tsinke ta kalli Yaya Karima wacce ke sakin murmushi tana fadin. “ Yau Senate ne a gidan.” Murmushi ya mata suna k’arasowa cikin falon, gaishe da ita suka yi ta amsa tana tambayar su Momi suka ce tana lafiya. Idanunsa na kan Bhatool da taki juyowa dan kukan da tayi ya saka idanunta ja. Yaya Karima ta ce. “ Bari na dauko muku ruwa ko.” Ta fada tana nufan fridge. Juraij yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa. “ Anuty da kin bari daga gida muke fa, dama gurin Bhatool muka zo.” ‘Dum-dum’ haka taji zuciyarta na bugu, yayin da Senate yayi saurin dafe saitin zuciyarsa yana karanto addu’a duba da yanda lokaci daya ya harba masa. Yaya Karima ta ce. “ Laifi ta muku ko?.” Ta fada tana dariya. “ A’a mun isa ta mana laifi.” Dubanta Yaya Karima tayi tare da cewa. “ Bhatool baki ji ance anzo gurin ki ba.” Jinjina kai tayi tana cewa. “ Naji Yaya.” Kafin ta mike ta ce. “ Ina zuwa bari na shiga daki na fito.” Tayi sauri ta yanda kar a ce ta tsaya. Yaya Karima ta zauna tana duban su ta ce. “ Me ya faru?.” Kallon Senate Juraij yayi kafin ya ce. “ Anuty wannan na rako fa.” Ya nuna Senate kafin ya cigaba da cewa. “ Wai Bhatool…..” Saurin katsai shi yayi ta hanyar buge k’afarsa yana marairaya ido. Tsaki Juraij yayi yana cigaba da cewa. “ Wallahi Anuty hauka ya fara yi akan Bhatool.” Runtse ido Senate yayi saboda kunyan da yaji lokaci daya ya kama shi, Yaya Karima ta ce. “ Ikon Allah, wai Senate har yanzu tsoron ne da kai? Tsoron ma na Bhatool?.” Juraij ya ce. “ Hmmm!!! Shi ne yau na jawo shi nace yazo ya fada mata ko zamu samu sauki.” Yaya Karima ta dubi Senate da kyau ta ce. “ To idan kana tsoron ta taya zakuyi zaman aure kenan? Ko ka taba ganin inda miji ke tsoron mata?.” Girgiza mata kai yayi, ta cigaba da cewa. “ Ka cire tsoro ka ajiye shi a gefe ka tunkare ta da zancen.” Gyada mata kai yayi kafin ta mike ta ce. “ Bari na kira ta.” Ta nufi dakin da Bhatool ke ciki. Da sauri ya dubi Juraij zai yi magana ya ga ya ciro waya yana tashi da alama kiransa aka yi. ‘ Inna’illahi!! ‘ Ya furta a zuciyarsa kafin yaji wani bangare na zuciyarsa na ce masa. ‘ Zaka iya, idan baka fada mata ba wani ya rigaka fa kamar yanda wancan ya rigaka’ Ji yayi wani kishi ya tokare masa makoshi lokacin da yaji ta ce. < Ce masa nayi ina da wanda nakeso>. Ko da Yaya Karima ta shiga dakin ta same ta zaune da waya a hannu tana dannawa, kusa da ita taje ta zauna tana cewa. “ Bhatool!!!.” Ta kira sunanta. Mayar da hankalinta tayi zuwa gareta baki daya tana amsawa. “ Bhatool baki fadamin wanda kikeso ba?.” “ Yaya burgeni kawai yake yi.” “ Waye ne shi din?.” “ Dan Momi ne.” Ta fada tana turo baki gaba ta dauke kai. “ Ke bana son shirmen kin nan fa, dan Momin bashi da suna ne.” “ Yaya Karima Senate ne fa.” Sakin baki tayi tana kallon ta. ‘ Shi sonta yake, ita kuma burge ta yake, me hakan ke nufi?.’ Sanin babu mai bata amsa ne ya saka ta dubi Bhatool me kyau ta ce. “ Ke ko dai son shi kike?.” Da sauri ta juyo tana girgiza kai. Yaya Karima ta yi murmushi tana rike hannunta ta ce. “ Bhatool kin san Senate baya surutu, kuma baya kula mata ko?.” “ Yoo to ni Yaya taya zan sani.” “ Ungo naki🖐 ai fada miki nake yanzun ba wai kin sani ba.” “ To ina ji.” Ta ajiye wayanta ta zuba mata ido. Tsaki Yaya Karima tayi tana tashi ta ce. “ Ki je falo yana neman ki.” Dariya tayi tana cewa. “ Allah yasa outing zamu fita ya kashe min zuciya da kudi.” Kallon ta Yaya Karima tayi tana tsaki ta fita. Mayafin Abayan jikinta ta yafa ta fito falon. Yana zaune yayi shuru kamar maraya, kamar mutuniyar kwarai ta iso da sallama a bakinta. Amsawa yayi ba tare da ya dago ya ganta ba, a kujeran dake kusa da nashi ta zauna bayan ta gaishe shi ya amsa. Shuru ne ya biyo baya babu wanda yayi magana tsawon mintuna, kafin da kyar ya dago da kai ya kalle ta yana fadin. Legend's pen 08129553971 14- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 14_ Da sauri ta d’aga kai ta kalle shi, jinjina mata kai yayi yana cigaba da cewa. “ Za ki iya aure na?“ “ Uhm…. Uhm…. Ni wai?.” Ta nuna kanta tana kallon shi. Gyada mata kai yayi yana mikewa tsaye ya zuba hannunsa a aljuhun wandonsa ya ce. “ Kiyi shawara kafin ki yanke amsa, na baki daga yau har zuwa lokacin da kika ji kin amince.” Ya ajiye mata kudi da bai san nawa ba ya tafi. Da ido tabi bayansa har ya fita kafin ta kalli kudin, dariya kawai tayi dai-dai lokacin da Yaya Karima ta fito. “ Yaya wai fa tambaya na yake zan iya auren shi, can’t believe it wai wannan handsome guy din ke cewa zan iya auren shi, to ai ko baya gani ne sai na aure shi balle kuma yana kallo.” Ta karashe da wani murna a tattare da ita. Dariya ita ma Yaya Karima tayi tana fadin. “ To ke me kika ce masa?.” “ Yaya me zance masa kuwa, barshi na dan wainasa a tunkunyar masa tukun, na ja masa aji sosai kafin nayi accepting.” Murmushi kawai Yaya Karima tayi ta ce. “ Kar ajin dai ya tsinke.” Tashi tayi ta nufi dakinta bayan ta bawa Yaya Karima kudin ta ce ta ajiye mata. *Senate* Yana fitowa a falon ya sauke wani lafiyayyar ajiyar zuciya yana dafe saitin zuciyarsa, lumshe ido yayi yana jin wani karfin guiwa. Dafa sa da akayi ne ya saka shi bude ido ba shiri yana sauke su akan Juraij, dariya Juraij ya fara masa yana cewa. “ Wani irin tsoro ne haka Senate.” Hararan shi yayi yana nufan hanyar fita, shi ma ya mara masa baya yana tsokanan sa amma ya mantar dashi har suka shiga gidan su. A falo suka tarar da Momi, Anas da Salman sun zuba tagumi suna jiran me zai je ya dawo. Momi na ganinsa ta mike ta iso gurin shi tana zuba masa ido alamun tanaso taji karin bayani. Dariyan da Juraij ke yi ne ya saka Anas cewa. “ Ya kwafsa ko?.” “ No bai kwafsa ba.” Ya fada yana dariya kafin ya ce. “ At last ya fada mata yana sonta.” Lokaci daya suka saki murmushi, Momi bata san sanda ta rungume shi ba tana cewa. “ Babana ya zama jarumi.” Murmushi kawai yayi yana fadin. “ Momi dama jarumin ne tun a baya, kuma In Sha Allah ta sanadiyarta na canza, na zama jarumi.” Sakin shi Momi tayi tana jan kumatunsa ta ce. “ Better.” Salman yayi murmushi ya ce. “ Shikenan ai yanzu sai kar ka kashe kanka ko.” Rarumo filon kujera yayi yana wurga masa, da sauri ya matsa yana dariya da fadin. “ Senate na Bhatool.” Dariyan da ya dade bai yi ba yayi yana shafa sumarsa ya ce. “ Fadi da k’ara Senate na Bhatool kuma Bhatool na Senate.” Dariya falon suka saka kafin aka zauna ana hira ana zolayan shi, har su Salman da Juraij suka tafi *Washe gari* Rawar kai, ya mantar da Bhatool tashin hankalin dake makaranta. Hakan yasa ta shirya tun wajen ƙarfe bakwai, so take taje ta kaiwa ƙawayenta gist ɗinan. Ƙarfe 7:45 a bakin gate ɗin YSU tayiwa Bhatool, tana tafe tana danna wayarta. So take takira wata cikin ƙawayenta taji ko sun ƙaraso cikin school. Horn din taji anayi mata a baya, hakan yasata waigawa a fusace, wa zata gani?. Dr Hashim. “Ya Allahu.” ta furta kaman tayi kuka, a hankali ya kawo motar kusa da ita. “Bhatool. Ya maganar mu.” Murmushin dole ta jawo tayi sanan tace. “Nayi shawara, zanzo office ɗinka anjima.” “Okay.” kawai yace yaja motarsa, da harara tabi motar tasa. Wayarta ce tayi ƙara alamun kira. “Wai Suhaima ina kikasa wayarki ne.” “Ina kan mashin. sai yanzu na sauka, Kinzo school din ne?.” “Da banzo ba, zan kiraku?.” “Okay gani nn shigowa.” Kashe wayar tayi ta nufi wajen da suke zama kafin su shiga hall. A wajen ta tarar da su Janah suna zaune, dan su tsarin su sai sun hadu baki daya zasu shiga class tare, yanzu ma takirasu sabida tayi tunanin ko sun shiga. Sabuda bata ce dasu zata zo ba. Ƙarasawa tayi ta zauna, tare da fadin. “Amarya wace zatayi miki make-up?.” Da kallo suka bita, su sunanan cikin tashin hankali da fargaba, ita tana nan tana musu zancen make-up. “Kikace bazakiyi make-up?.” Wata uwar dariya Bhatool tayi, sanan tace. “Ai yanzu banza ta faɗi, arziƙi yazo, gayu sai yaci uban na daa.” Legends pen 08129553971 15- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 15_ Da ido suke kallonta, ita kuwa sai zuba take. “Yanzu ba wannan Bhatool da kuka sani bace, ƙanwar Abdul, yanzu yayar Abdul ce. Ko yaya karima ma sama nake da ita.” “Bhatool. Bamu labari me ya faru?.” Suhaima da bata dade da ƙarasowa ba ta faɗa, gyara zama Bhatool tayi sannan ta ce. “Ashe Abba, ba iya Yaran can yabawa amana ta ba?, can you girls remember that cold, giant, handsome and classy guy dake zama inda muke a garden?.” Ɗaga kai suka yi duka, tare da faɗin.”Yes!.” cike da mamaki. “To shima Abba ya bashi amanata, jiya nan ya ajiyemun kudi. Ban dubasu ba sai yau naga 150k.” “150k!.” suka fada gaba dayan su cike da mamaki. “Yes, 150K.” Bhatool ta maimaita. “Bhatool, kina cikin Alheri dumu-dumu.” “Wallahi faa, and guest what?”. “What?!.” Suka sake fada. “Wai yana sona.” “Ayirrrrr, Bhatool tayi goshi.” Jannah ta fada kamar tayi rawa. “Amma kema kince kina sonsa ko?.” Suhaima ta tambayeta. “Haba mana gurls, atleast ai ya kamata naja Class ko yane.” “Eyh.. Amma kija a hankali.” Jannah ta fada, sai kuma tace. “Dr Haisam fa?.” Dariya Bhatool tayi sannan tace. “Wasa zanyi dashi, zance mai na aminci, amma ya jira mugama 100lvl mushiga 200. Sai ayi engagement da munje 300 sai ayi auren. Nasan shi wanan bazai fi six months ba, za’ayi komai a gama.” “Har bikin!?.” Cewar Suhaima cike da mamaki. “To mai zanjira Allah yakawo mun miji.” Dariya sukayi baki daya, daga nan suka shiga class. *Senate* 07:45 yaƙaraso ƙofar gidan Yaya Karima, sai dai mai gadi yace mai tun 07 Ta fita. Komawa gida yayi rai babu dadi kwata-kwata. Har yanzu bai samu amsa daga wajenta ba, sannan yanaso yaji jiya akan wa take magana. Domin kasa bacci yayi gaba ɗaya, da tunanin maganar ya kwana. Bai san yana da kishi har haka ba. “Good morning Momy nah.” ya faɗa bayan ya shigo falon. “Morning, angon Bhatool.” Murmushi yayi sannan yace. “Momi har da ke.” “Ni dai yanzu zo ka zauna anan.” zuwa yayi ya zauna, Momi ta kalleshi. “Yanzu zuwa yaushe kakeso, a saka bikin nan. Sabida nima na matsu, duk ƙawayena sun fara aurar da yaransu. Har da masu jikoki.” Dariya Senate yayi, sannan yace.”Momi nima bansani ba.” “Zan fara zuwa nayi magana da yayarta, sai asamu iyayenta.” *Bhatool* “Haba Abdul, tunda nace kazo ina son ganinka ai kasan ganinka nakesonyi. Nifa yayarka ce.” bhatool dake waya ta faɗa, shiru tayi Sannan ta ƙara cewa. “Idan kuɗi ne zance sai kazo, ai fada maka zanyi, ni yanzu turumun account number dinka na sama ko 10k ce dan kasan ni yanzu kuɗi basu bane matsala ta.” “Shikenan sai kazo.” daga haka ta kashe wayar ta juyo ta kalli su Suhima tace. “Shi kadai ne Hope dina, sanan bani da wani wanda zai tsayamun daya wuce shi.” “Hakane Bhatool, sanan zai baki mafita sosai. Domin tabbas Dr Haisam ba karamin makirin mutum bane.” “Nasani wallahi Suhaima, kinaji yadda mukaji ‘yan accounting dazu suna magana, kamar damu suke.” “Wallahi kiga dai yace zaki aureshi, to itama ƙawarsu yace zata aureshi. Mai hakan ke nufi.” Jannah kuma ta faɗa. “Alllah ya tsare mu baki daya, ni Abdul din ma idan yazo tare zamu tafi.” “Gwanda ki bishi Bhatool, wallahi banason ganinki a makarantar nan.” “Ke kuma da tsoro kike Jannah.” Ba’afi minti goma ba Abdul yazo makatantar, kiranta yayi a waya ya sanar da ita yazo. “jirani bakin gate.” ta fada tare da kashe wayar. “Ladies yazo, sai munyi waya.” .”Wait baki amshi cards dinki ba, banjin zan sake shigowa school.” Suhaima ta fada tana bude jakarta. “Ɗibi.” ta fada tana miƙamata jakar. “Kala nawa ne.” ta tambayeta. “Dinner, kamu, mothers eve. Su kadaine masu card, bridal babu, henna ma babu card.” “Okay, kowanne ban biyar, zanbawa senate da abokinsa, nabawa Yaya karima da mijinta sai abdul.” “Okay.” Suhaima ta fada tana lissafa mata.”Ga six nan ma ko zaki kara wani, ku nawa-nawa zan baku.” ta tambayesu Jannah. Bhatool dai amsa taita huce, sauri-sauri ta karasa bakim gate. Motar Abdul ta gani da sauri ta nufi motar tare da budewa ta shige a kan idon Senate da zuwansa kenan zai shiga Makarantar. Ji yayi zuciyarsa ta harba da karfi, da sauri ya fara karanto addu’a yana Astagfirullah a zuciyarsa, yana gani ta shiga motar tana murmushi, gashi baya ganin ko waye ne dan tinted glass ne. Numfashi ya sauke ganin motar ya bar gurin kafin a fili ya furta. “ Bhatool!!.” Yana dafe saitin zuciyarsa dake masa zafi. Ta da motan yayi ya bar gurin a 360 ransa a bace, yana isowa get din unguwarsu yaga motar tana fita alamun ya ajiye ta ta shiga gidan Yaya Karima. Har zai tare shi sai kuma ya fasa ya wuce ya nufi get din su, horn ya danna mai gadi ya bud’e masa, ya cinna hancin motar ciki yana parking, ya dade a ciki kafin ya furzar da iska yana fitowa ya nufi dakinsa direct. ~~~~~~~~ Ko da Abdul ya ajiye ta a kofar gidan Yaya Karima sai ta ce. “ Abdul ga card na event din Suhaima, na Dinner, Kamu, nasan baza kazo Mothers eve ba.” “ Abun naku har da mu ne?.” Ya tambaya yana amsa tare da ajiyewa. Hararansa tayi tana cewa. “ Kai ka sani kuma, sannan idan zaka zo Hilis ka shigo da kudi na kari.” “ Uhm naji fita zan koma kasuwa.” Ya fada yana yiwa motar key. Tabe baki tayi ta fita daga motan ta shiga gidan Yaya Karima shi kuma yaja motarsa ya wuce. Da sallama ta shiga falon, Yaya Karima na amsawa dan tun dazu zaman jiranta take ta dawo taji ya suka kare da Lecturer din. “ Yaya Karima ya gida?.” Bhatool ta fada zata wuce d’aki. “ Ke, tun dazu fa ke nake jira amma kinzo zaki wuce.” Cewan Yaya Karima tana jin kamar ta kai mata duka. Reverse tayi tana cewa. “ Sorry Yayata ta kaina, me ya faru? Me kike jira?.” Hararanta tayi tare da fadin. “ Ya kuka kare da Lecturer din naku?.” Dariya tayi tana fadin. “ Ohh wai Dr Hashim? Ai wasan buya muka tayi dashi har na fito, nace zan same shi a office anjima shine na kira Abdul nace yazo ya dawo dani.” Ajiyar zuciya Yaya Karima ta sauke ta ce. “ Alhamdulillah!!! Yanzu ina Abdul din?.” “ Ya koma kasuwa abin shi.” “ Baku da kirki dukan ku, tunda yazo har get ina laifin ya shigo mu gaisa yaci abinci.” Ta fada ranta a bace. Tabe baki Bhatool tayi ta nufi daki tana cewa. “ To ki kirasa ki masa fada mana, amma kin wani sakani a gaba kinamin fada da rungumeman cikin naki… Legends pen 08129553971✍🏼 16- *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 16_ Taɓe baki Bhatool tayi ta nufi ɗaki tana cewa. “ To ki kirasa ki masa faɗa mana, amma kin wani sakani a gaba kinamin faɗa da rungumeman cikin naki.” Yaya Karima ta ce. “ Allah ya shirye ki idan mai shiriyar ce, amma ke kam Bhatool halinki sai ke, mijinki ya shiga uku.” Dariya Bhatool ta mata tana bud’e kofar ta lek’o ta ce. “ Cewa za kiyi Senate ya shiga uku dan shine Nurul Hayat dina, kuma Zauj dina.” Ta rufe kofar tana cigaba da dariya. Girgiza kai kawai Yaya Karima tayi sannan ta wuce d’akinta. *SENATE POV* Tun da ya shiga d’akinsa bai fito ba sai guraren sallan Mangrib, dan sallan Azahar ma a d’aki yayi, haka kuma bai kula kowa ba ciki kuma har da Mom, dan yau jinsa yake wani iri duk a burkice. Sauk’owa ya fara yi daga upstairs yana jin hayaniya, sake tamke fuska yayi lokacin da ya lura da su Juraij ne da Salman da Anas, sun tusa Mom a gaba suna hira kuma duk akan yanda za’ayi bikin Senate din ne. Kallo daya ya musu yana tura baki a ransa ya ce. ‘ Gaibu kenan, ko accepting dina fa bata yi ba amma sun zage sai shirye-shirye suke.’ Mom ce tayi murmushi tana tasowa tazo gurin shi tana kama shi ta ce. “ Son kazo mu zab’a wani event da wani event zamu yi.” “ Mom kuje ku zaɓa.” Ya faɗa yana wucewa ya fita daga parlon. Baki a sake suka bisa da ido kafin Juraij ya ce. “ Idan kun ga haka to shi da Bhatool ne.” “ Kai da kasani kuma, kila ko bata masa magana bane yasa yau ransa duk a bace, kamar wanda aka masa bushara da wutan jahannama.” Cewan Anas. Salman yayi murmushi ya ce. “ Ku dai gulma ne naku, ai gwara shi ya nemo wacce yakeso duk da tana bashi headache, amma ku fa? Ko ince mu fa? Kamar wanda basu da farin jini ko haske a rayuwar su.” Dariya Anas yayi yana cewa. “ Cewa zakayi kamar wanda bakin iyaye ya bisu, ni fa tunda nake babu macen da ta taɓa cewa tana sona, anya ma ba aljana bace ta aure ni?.” Juraij ya daura da cewa. “ Ko dai ta aure mu dai, dan nima haka ne lakamtu summa lakamtu.” Mom ta zauna tana fadin. “ Ku tashi ku tafi masallaci, ku fake da cewa aljana ta aure ku, ku dai kuka auri aljanun tunda kune kuka ki auren.” Da haka suka tashi suka tafi masallaci. Ana idar da salla ya fito ya nufi hanyar gidan Yaya Karima, Juraij na cewa ya jira shi amma yayi banza dashi. Ƙwanƙwasawa yayi mai gadi ya buɗe, ya tambaye shi. “ Bhatool na nan?.” Ya ce. “ Tana nan, dazu ta dawo daga Makaranta.” “ Ban tambaye ka ba Malam.” Senate ya fad’a yana nufan hanyar falon, dan shi fa jinsa yake dai-dai da kowa yanzu, duk haushin biyu ya taru masa ya masa yawa, ya rasa waye ne na Makarantar ga wanda ya kawo ta dazu. A bakin kofar ya tsaya yana sallama. Fitowan ta kenan taji sallaman shi, da mamaki ta ce. “ Kamar Senate nake ji.” Yaya Karima da itama fitowarta daga kitchen ta ce. “ Shi ne ma ba kama ba.” Tabe baki tayi tana komawa d’aki dan dauko mayafi. Yaya Karima ta amsa masa tana cewa. “ Haba Senate gidan ne sai kace bak’on ka, ka wani tsaya daga waje.” Dan sosa keya yayi kafin ya shigo kansa a k’asa, ya durkusa yana cewa. “ Ina wuni?.” “ Lafiya ka tashi ka zauna.” Tashi yayi ya zauna yana ta kwakulo murmushin dole, Yaya Karima ta danyi murmushi kafin ta ce. “ Bari na kira maka mutuniyar taka, yanzu ta shiga ciki.” “ To Nagode.” Ya fad’a dan dama ya rasa ta ya zai fara tambayar ta ina Bhatool. Yaya Karima na k’ok’arin shiga dakin, Bhatool ta fito sanye da Hijab har k’asa Maroon color dinkin jalbab, matsawa gefe Yaya Karima tayi tana binta da ido, dan rabon da taga Bhatool da hijab har ta manta idan ba Sallah zatayi ba. Kamshin turarenta ne ya fara masa sallama kafin tayi sallama tana zama nesa dashi. Amsawa yayi yana d’aga kai ya kalle ta, murmushi ta sakar masa wanda ya ratsa zuciyarsa da gangar jikinsa gabaki daya, lokaci daya ya nemi fushi da bacin ran da yake yi ya rasa, yaji zuciyarsa tayi haske furannin cikin sun samu ruwa. Lokaci daya ya tsinci kansa da furta mata. “ Kinyi kyau sosai.” Murmushi ta masa tana sunkuyar da kai kamar munafuka kafin ta ce. “ Nagode.” “ Ba godiya a tsakaninmu ai.” Jinjina kai tayi tana tashi ta mika masa card guda hudu, dan ta kaiwa Yaya Karima guda biyun tace baza su je ba, karba yayi yana kallo kafin ya ce. “ Na mene ne?.” “ Na auren Suhaima ce, da Dinner da Kamu, ko zaka bawa friends naka coz you’re also invited.” Ta karashe tana komawa gurin da ta tashi ta zauna. Murmushi yayi yana cewa. “ In Sha Allah I will be there.” Shuru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai, can ya dago kai ya kalle ta yana cewa. “ Kina da matsala da wani ne a school naji kuna hira? Sannan waye ya kawo ki dazu?.” Da sauri ta dago manyan idanunta ta sauke masa tana cewa. “ Kenan ranar kaji komai?.” Shuru yayi dan shi kawai yaji ta ce akwai wanda takeso ne, amma ga dukkan alamu da ya tambaye ta yaga tsoro kenan akwai bayani, hakan yasa ya ce. “ Eh naji komai.” Marairaice fuska tayi ta fara cewa. “ Wai fa Dr Hashim ne yake sona.” Kalman da ya caki zuciyarsa kenan *SO NA!!!*, ta cigaba da cewa. “ Shi ne nace masa ina da wanda nakeso, wai yace bai damu ba ya bani nan da kwana daya nayi tunani ko kuma duk abunda na gani ni na jawowa kaina.” Ta karashe tana kallon yanda yanayin fuskarsa ya canja lokaci daya, daga fara’a ya dawo bacin rai zalla, amma sai ya dake ya ce. “ Shi ne kawai?.” Gyada kai tayi tana turo baki gaba ta ce. “ Eh.” Murmushi ya mata ya ce. “ Solve, idan dai wannan ne angama da shafin shi.” “ Thanks.” “ Dm.” Sannan ya daura da cewa. “ Wanda ya kawo ki fa?.” “ Abdul ne fa, kanina ne uwa daya uba daya.” “ Ohh 😲.” Ya fada yana sosa keya a ransa ya ce.’ Ina kishi da kaninta kenan.’ Kafin a fili ya ce. “ Akwai wani abu ne?.” Girgiza kai tayi ta ce. “ Bakomai kuma, kawai so nake kuzo events din duka biyu.” “ Idan shi ne baki da matsala an gama.” Kafin ya mike tsaye yana cewa.” Nikam bari na tafi.” Tashi tayi tana rakasa, a bakin get ta tsaya tana ciki shi kuma yana waje. “ Ba ki bani amsa ba.” Sunkuyar da kai tayi ta ce. “ Accepted.” Ta koma ciki da sauri tana dariya. “ Yessss!!!.” Yana sakin dariya, juyawa yayi sukayi ido hudu da su Anas sun zuba masa ido. Saurin tamke fuska yayi dan yanzu zasu mayar dashi karamin mahaukaci, ai kuwa bai gama ba suka fashe da ihu Anas na cewa. “ Senate na Bhatool.” “ Bhatool na Senate.” Cewan Juraij suna sake sakin ihu. Kamar yayi kuka ya ce. “ Ku dena kiranta da sunanta ai wannan raini ne.” Dariya suka sake yi Salman na cewa. “ To Zahra na Senate.” Bai kulasu ba ya shiga gida yana kwalawa Mom kira, da sauri Mom ta fito daga daki tana cewa. “ Lafiya wannan kiran Senate.” Nuna mata su Anas yayi wad’an da har yanzu suna dariya ya ce. “ Mom ki ce su daina kiran sunanta haka raini ne.” Da mamaki Mom ta ce. “ Ban gane ba, sunan waye za’a daina kira haka?.” “ Sunan Bhatool suke kira fa babu cewa Anuty.” “ Ikon Allah.” Kafin Mom ta dube su tana cewa. “ To dai kunji Anuty Bhatool zamuna kiranta dashi.” “ Mom ban da ke, su kadai.” Bata kula shi ba ta koma dakinta dan dama gyara kayanta take. Ya juya ya kalle su ya ce. “ Kuka kara ce mata Bhatool duk sai na kaiku kara police station.” Ya karashe yana nufan d’akinsa. Juraij ya ce. “ Prison za’a kaimu kawai yafi ai.” Nan ma dariya suka masa, yayi kwafa ya shiga daki ya danna sakata. Bhatool kam, tun fitar Senate ta koma ɗaki tana famam xancen zuci. “Tabbas Senate mai kyau ne, ɗan gayu, mijin nuna wa sa’a, mijin shiga taro, idan har nayi sa’a na aure Senate mai zai dame ni a duniyar nan?.”  Ta yi wa kan ta wanan tambayar. “Babu fa.” Ta sake bawa kan ta amsa, tana cikin wanan tunanin wayarta ta hau ƙara alamun kira na shigowa, hannu ta kai ta ɗauka tare da ɗagawa bayan ta ga Sunan Amrah a kai. “Hello Amrah.” Ta faɗa bayan ɗaga wayar. “Bhatool ya garin?.”  “Normal Amrah is everything okay, na jiki wani kala?.” “Not Okay, wallahi Bhatool kuɗi nake nema urgently dan Allah ki aramun ko 30thousand ne.” “Haba Amrah, ai kinfi ƙarfin haka ki bani account ɗin zansa miki.”  “Na gode sosai Bhatool, bari na samiki.” “Okay.” Bhatool ta faɗa tare da kashe wayar, yanzu hankalinta ya koma kan na ta bikin dan ta san dai Senate son ta yake, Abinda ya rage kawai ya yi proposing asha biki, .”Kai zan ta shi kan munafukan ‘yan uwan Abbanah, har na hango Goggo larai ta ga Mijinah, su Fure da hari sun suma, ƙila ma baƙin ciki ya kashe su, wallahi ba za a fasa bikina ba ko sun mutu.” Bhatool ta faɗa tana miƙewa zuwa Toilet.  Wayarta ta ɗauka ta yi wa Senate Sallama ta whatsapp, yana kwance kan gado tun da ta shigo tunanin ta yanda zai yi proposing, sanan shi bai son Auren ya wani daɗe ayi a huce wajen kawai, ga kuma matsalal wanan malamin na su da ta ce. “Ƙila fa neil Abuja zan mai da ta kawai.” Ya faɗa dai-dai lokacin da ya kai hannu zai ɗauke wayarsa, sakamakon ƙarar shigowar saƙƙoni da ta ishe shi. Idonsa ne ya sauka a kan message ɗinta da ta ce. “Salam Yaya Senate.” Da sauri ya shiga yi ma ta Reply da faɗin. “Wa’alaikussalam Bhatool.”  “Na’am Yaya senate, barka da dare.” “Barka Bhatool ya su Yayan?.” “Suna lafiya ƙalau, ya su Mom?.” “Alhamdulillah Bhatool.” “Daman Yaya Senate dan Allah Account ɗin Amrah ƙawata xan baka ka tura ma ta 30k, da safe sai na baka Cash, banda kuɗi a account kuma Yaya ta hanani fita Pos🥹🙏.” “🤩Okay badamuwa turu.” “Na gode🙏❤️22xxxxxxx42.”  *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 17_ Tun a farkon littafina na sanar daku cewa Hasashen soyayya Free book ne, ku bar ni na rubuta shi a nutse amma hakan ya garara, a kullum kuna cemum kuna son complt, ayi agama da huri. Tom Allah ya amsa addu’arku, Hasashen soyayya ya zama paidbook amma Vip Paidbook page uku kullum, sabida mu gama shi da huri kafin January. Payment via. 8129553971 Opay Sani Muhammad lawan. Shaidar biya 08129553971 Daga page 22 zamu gama posting Free pages  Ngde. *Bayan kwana biyu* ~~~~Red bricks “Tom yanzu Hajiya daga ganin yarinya sai ku yankw hukuncin gidan da ta fito?.” Dad dake zaune kan kujera ya faɗa yana kallon Mom dake yan ka masa fruit. “Yarinyar fa ƙanwar matar barrister ce, kuma kasan matar barrister ai.”  “Duk da haka fa Hajiya, kawai dan dai kina son yarinyar ne shi yasa haka.” “Tabbas kam, yarinyar ta na da shiga rai kuma ɗan lalena ne ya kawo ta.” Dariya Dad ya yi sanan ya ce. “Shikenan zan sa a yi binciken da ya ka ma ta.” “Amma fa ni cikin ƙan-ƙanin lokaci nake so ayi komai a gama.” Mom ta faɗa sabida ta fuskanci kamar bai shirya aurar da Senate ba, wata dariyar ya sake yi saman ya ce. “Komai saurin ki dai, sai kin jira lokaci ko?.” “Eeyh!.” Ta faɗa kawai tare da ci gaba da haɗa masa fruit ɗin. Senate ne ya fito cikin shiri, ya sha ado cikin milk clour na shadda wacca ta yi matuƙar amsar jikinsa, fuskarsa mai kama da ta larabawa ta fio fes cikin browm clour ɗin hulal da ya saka, tsintsiyar hannunsa ɗaure da golden clour Rolex watch, turaren jikinshi ya ƙarade gidan baki ɗaya, a hankali ya tako zuwa falon. Da kallon soyayya Mom ta bi shi, a ranta tana yi masa addu’ar kariya da neman sa’a an kan komai. “Dad barka da hutawa.” “Barka dai Amgo, sai ina?.” Murmushi ya yi, tare da yin ƙasa da kan sa. “Zanje dinner ne.”  “Tom Allah ya tsare.” “Amin Dad.” Ya faɗa tare da miƙewa xuwa inda Mom take, bai ƙarasa ba Dad ya ce. “Akwai kuɗi a wajen ka ko?.”  “Eyh Dad akwai.” Gyaɗa kai Dad ya yi, ya ci gaba da shan fruit ɗin sa, shi kuma ya ƙarasa inda Mom take. “Mom zan huce.” shafa kan shi ta yi sanan ta ce. “Allah yatsare, a kula mun da Bhatool.”  “In sha Allah Mom.” Daga haka ya fice, motarshi ya hau ya nufi address ɗin da ta ba shi na wajen kwalliya. ~~~~~~Bhatool. “Amrah, banga gold ɗina ba.” Bhatool ta faɗa tana bincike jakarta. “Innullahi wa’inna illahir raji’un, Bhatool sake dubawa dai.” Amrah ra faɗa ana ci gaba da mata kwalliayar. “Wallahi Amrah banganshi ba; Allah yasa gida na bar shi.”  “Amin dai kam.” Amrah ta faɗa dai-dai lokacin sa Jannah ta shigo,wacce daman angama yi mata ta kwalliyar ita da Bhatool. “Suhaima ke ce mun wai sun kusa ƙarasawa.” jannah da ta shigo ta faɗa. “Chaii, Amrah ayi a gama miki ɗaurin nan.”  “Bhatool ya baki sa ɗan kunne ba?.” Jannah ra tambaye Bhatool. “Na bar shi gida wallahi.”  “Ya salam!, yansu ya za’ayi?.” “Ɗaurin na wa za a sakko mun da shi har kunne.” “Eyh kam hakan zai yi ma.” Mai kwalliayar ta faɗa bayan ta gama yiwa Amrah ɗauri, dai-dai lokacin da kiran Senate ya shigo wayar Bhatool. “Laa kunga yazo.”  “Waye?.” Amrah ta tambayeta. “Senate.” Ta bata amsa. “To mu yi sauri kar mu ɓata mai lokaci, kun san manyan mutane ba sa son jira.” Amrah ta faɗa tana haɗe kayanta. “To ko mu fara fita ne.” Amrah dan ta ƙara faɗa. “Ke matsalata da ke hutar ciki.” Jannah ta bawa Amrah amsa. “Duk hutar cikin ta dai nima angama mun.” Bhatool ta faɗa tana sauka daga kujerar kwalliyan, daga nan suka ka ɗai su ka fice.  Haka kwai Senate ya ji kwalliyar Bhatool ta yi yawa, gaba ɗaya ya ji shi wani kala duk ya damu, “Dama ba ta yi ba.” Ya faɗa a zuciyarsa, a fili kuma ya sakar ma ta murmushi. “Ina yini.” Amrah ta faɗa tare da Jannah. “Lafiya kalau, ya taro?.”  “Taro gashi ana ta sha, ya gajiyar jiya?.”Amrah ta ba shi amsa, ita dai Jannah tana ƙoƙarin shiga mota. “Alhmdlh.” Ya faɗa a daƙile tare da shigewa mota, su ka huce hall ɗin. Ko a hall ɗin Senate ya hana Bhatool sakewa, ko ina suna tare yana binta a baya, yan maza na ta kallonta haka shima yan mata na ta kallonsa, zallan kishi kawau ke ɗawainiya da shi, ya yu kicin-kicin ya haɗe rai, Bhatool kam da ta fuskancin haka sai ta yi banza da shi, ko ina ya yi ta bin na ta.  ~~~~~~Hausari “Toh Isiyaku bari ka ji mun isa har mun yi yawa mu aurar da ‘ya’yan Ahmad, ko da ran Ahmad ko babu ran sa; domin ni ce babba cikin ku.” Goggo larai da ke zaune kan kujera yar tsugunno ta faɗa, kawu Isiyaku ne ya ce. “To ai Larai wanan zancen banza ne zancen wofi, idan ba mu aurar da ita ga na gida ba wa zamu bawa? duk lalacewa Saddiku ɗan mu ne, kuma shi da kan sa ya ce idan an aurar mai Bhatool yar gidan Yaya Ahmad zai nutsu, zai daina shaye-shaye, da wanan yawon tafiya legas ɗin.”  “To ko ba zai daina ba tun da ya ce yana son aurenta ai sai an ba shi;dan haka na gama magana, kawai ku haɗa kayan nagani ina so ku kaiwa uwarta.” Goggo larai ta faɗa tare da mikewa tana dafa bango. Furai ce ta kalli Habi su ka kwashe da wata shegiyar dariya, sanan Habi ta ce. “Ina baƙin cikin ganin su Bhatool sun ci gaba.”  “Wallahi Habi nima haka, ke da ina da dama Karimar ma sai na kaso na ta auren.”  “Bari muje fa Bhatool gidan Yaya Sadik, ita ma sai ta fito.”  “Ai wallahi nasan da zarar an aurar da Bhatool ga Yaya Sadik, ta ta taƙare, sai ta hulaƙanta ta sha wahala, ta gane Allah ɗaya ne.” Dariyar su ka ƙara fashwewa da ita. ~~~~~Senate & Bhatool. “Wai bazaka zauna ka ci Abinci ba?.”  Bhatool ta faɗa, dan ta fara gajiya da wanan bin bayanta da Senate ke yi. “Naƙoshi.” Ya faɗa murya kamar zai yi kuka, kujera ta samu ta zauna shima ya zauna kusa da ita, sanan ta ce. “Senate mene matsalal wai?.” Turo baki ya yi gaba sanan ya ce. “Duk kin yi wani kyau, yan mazan sai kallonki su ke.”  “To ai kai ma ka yi kyau ko?; kuma ‘yan mata sai kallonka suke.” “Mu ta fi gida.”  Legendspen 08129553971 Page 18 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 18_ “Mu ta fi gida kuma?.” Bhatool faɗa tana kallonsa, shi kuma ya gyaɗa ma ta kai. “Ni dai A’ah, yaushe mu ka zo haba.”  “Ni zan tafi to.” Tsaki ta ja ta dau jakarta ta fice, shikuma ya bi ta baya gwanda ta yi ta fushin amma bazai jure ganin yadda samarin wajen ke ta kallonta ba, a ƙafa ta fara tafiya. Motar ya shiga ya biyo bayanra, ta na ji yana mata hon amma ta yi banza kamar ba ta ji ba, sauka ya yi daga motar ya nufu ta yana faɗin. “Bhatool, ki tsaya mana.”  “Me zan ma?.” “Ki tsaya mu tafi gida.” Ci gaba ta yi da tafiyarta hankalinta kwance ba ta ko kula shi ba, sai da ta yi tafiya mai nisa sanan ta juyo, ga mamakinta sai ganin Senate ta yi zaune a kan wani tudu yana kallonta, fuskarshi kamar zai yi kuka. “Oh ni Bhatool, mai na kwasowa kai na haka?, shi da zai lallaɓani amma shike fushi.” Ta faɗa a cikin ranta, a fili kam cewa tayi. “Idan bazaka tawo ba zan koma wajen bikina.” “To a ƙafa zamu tafi?.” Harara ta maka mai sanan ta ce. “A me muka zo?.”  “To ai kin ƙi shiga motar.” “Ɗakko mu tafi.” Juyawa ya yi ya nufi motar ita kuma ta bishi da kallo. “Ga mutum har mutum amma sai shashanci kamar wani ƙaramin yaro.” Motar yakawo inda take sanan ya buɗe ma ta ta shiga, haɗe rai ta yi ba ta ce ko ƙala ba dan haushin senete ne fal a ranta, dan wallahi gobe ma ba zata bashi katin dinner ba. “Oh wa ma ya aike ni.” Ta faɗa a ranta. “Bazaki kulani ba?.”  “Wai wane irin abu kakemun haka, kamar ƙaramin yaron, ni banajin yin magana.”  “Ki yi hakuri.” Ya faɗa yana cuno baki gaba. “Me ka yi mun?.” “Na baro ki daga wajen biki, Bhatool wallahi ina son ki, so mai tsananim gaske mai kuma nauyi, Bhatool bazan iya jure ganin maza na kallonki ba, Bhatool a kowanne dare kafin na kwwnta sai na yi kukan rashinki kusa da ni. Bhatool ban san so ba sai lokacin da na sanki, ban san zan iya tunkarar mace ba sai a kan ki, Bhatool ban san zan zama sakarai a kan mace ba sai a kan ki. Bhatool ban san zan iya kuka a kan mace ba sai a kan ki, Bhatool son ki ya shige ni a lokacin farko, ya mamaye rayuwata ta yadda banajin zan iya rayuwa ba tare da sautin bugun zuciyarki ba.”  Shiru Bhatool ta yi, duk kalaman Senate suna shiga sassan jikinta, suna ratsa ƙashi da ɓargonta, wani irin san yi yana mamayw rayuwarta. Tabbas Senate abun a so ne, Senate mai son ta ne, ita kan ta ba ta tuna lokacin da son Senate ya shige ta, sai da tasan ya yi wa zuciyarta kamun da cire shi zai zama babbar wahala.  “Bhatool bana jin akwai abinda zai gagari sadaukarwa sabida ga soyayyarki.” Kalaman da suka dawo da ita daga tunanin da take. “Bhatool nu dake haɗin Allah ne, ki yarda da ni, zan baki gata, zan baki kula, zan baki soyayya, zan zame miki bango da zaki jingina da shi a rayuwa, zan zame miki tsananin da zaki taka ki samu nasara a rayuwa, zan zame miki matattakalal da zaki taka ki samu al-jannah, Bhatool zan zame miki abokin rayuwa na har abada,  Bhatool” ya kira sunata a ƙarshen maganar. Ɗagowa ta yi amma ta kasa kallonsa. “Ɗago ki kalli idona dan Allah.” A hankali ta ɗaga idanunta ta sauke su a kan na sa. “Bhatool..”  “Na’aam.”  “Bhatool ki so ni dan Allah, Bhatool na miki alƙwarin soyayya mai tsafa fa iganci, na miki alƙwarin sadaukar da komai nawa domin siya miki farin ciki Bhatool.” Ƙasa ta yi da kan ta, ta fara wasa da yatsunta. “Ina sonka Senate.” Ta faɗa a cikik ranta, a fili kam shiru ta yi, amma kalaman senate suna amsa kuwa a cikin kunnuwanta, tabbas ta cika mai sa’a da samun senate.  “Kin yi shiru Bhatool.”  “Na’am.” Ta faɗa a ɗan tsorace. “Ba ki ce komai ba.”  “Na ce mana.”  “Banji ba sake faɗa.” “Allah ka ji.” Dariya ya yi sanan ya ce. “Banji ba fa.”  “Na ce Eyh.” “Eyh, me?.” Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kai. “Ba zaki ce komai ba?.”  “Ina son ka nima.” Wani sanyi Senate ya ji a cikin zucoyarsa, daman kuma amsar da yake sa ran ji kenan, godia ya yi wa Allah a fili sanan ya ce. “Bhatool na yi miki alƙwarin ba zan taɓa bari ki yi kuka ba, bazan ta ɓa bari ki ji babu daɗi ba, zan fara ta miki da komai nawa, in Allah ya yarda Bhatool.” (Uhm, ni kam na ce Team senate and Bhatool ku yi screemshot ɗin wanan alkwari na senate ku ajiye shi, dan wata rana ku dinga tuna mai😂😂) ~~~Red bricks. Mom ce ta kalli Dad dake zaune yana danna waya, sanan ta ce. “Nifa bangane inda wanan zancen nala ya dosa ba, me kake nufi?.” “Wai mene baki gane ba, tun ɗazu muna ta maimaita zance ɗaya.”  “Shi Justice audun mai ya ce, har da zaka ce baka amince da auren Senate ba, wane abu ya binciko a game da yarinyar?.” Miƙewa Dad ya yi sanan ya ce. “Nima ban san me ya gano ba, amma tun da ya ce mun akwai matsala to kin san dole akwai, dan haka ba zan taɓa yarda ɗana ɗaya tak ya yi aure waje mai matsala ba.”  Yana faɗin haka ya shige ciki, ta shi ta yi ta bi bayan sa ta na faɗin. “To mene yasa bazai faɗi matsalal ba sai dai ya ce akwai matsala, sanan justice Audu ai ba shi yake da ikon yin bincike a kan matar da Senate zai aura ba ko?.”  “Ban san lokacin da kika fara mayar mun da magana irin haka ba, kin sani, na sani justice Audu abokin kwarai ne, tun kafin na sanki na san Audu kuma yakasance abokin shwara a kowanne lokaci, kuma kema a haka kika ta so.” Daga page 20 zamu gama free pages, ranar littinin in sha Allahu zamu shiga paids page, kuma 3 pages za a dinga posting kullum. 8129553971 Opay sani Muhammad lawan Shaidar biya tanan  08129553971 Legendspen. *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 19_ “To amma ko da yake abokin kwarai kawai sai ya ce yaro ba zai auri yarinya ba, kuma babu wani ƙwaƙwarran dalili.” Mom ta faɗa bayan ta shigo ɗakin da Dad yake. “Kina so mu ci gaba da maganar kenan, to nima ban san dalilinsa ba, kuma shi nake jira nan yanzu zai zo.”  Ta shi ta yi ta fice ba tare da ta ce ko ƙala ba, sai dai Senate da ta gani tsaye ya yi matuƙar ba ta tsoro.  “Har ka dawo?.” Ta tambaye shi. “Eyh Mom, wace yarinya ce ba za a aura ba?.” “Wai Bhatool.” Da sauri ya matso kusa da ita sanan ya ce. “Me yasa Mom, Bhatool fa ta ce mun tana sona.”  “Nima Senate ban sani ba, wai Justice ne ya ce masa da matsala.” “Ba dai tare da Bhatool ba ko?, Bhatool ba ta da matsala Mom.” “Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, sanan ka yi addu’a ka ji.”  “Thom Mom.” Ya faɗa tare da shigewa ɓangarensa, zama ya yi gefen gado yana faman tunani. “Yanzu idan aka ce bazan aure Bhatool ba, na yi ya da rayuwata, na yi farin ciki a kan me?.” Hawaye ne su ka fara gangarowa ta kuncin sa, sanan ya fara addu’a.  “Allah Ka sani ina son Bhatool, kai ne ka samun soyayyarta, Allah ka malakamun ita, Allah ka ba ni Bhatool a matsayin mata, ka ba ta ikon yi mun biyayya ka ba ni ikon kyautata ma ta, Allah ina son Bhatool, Allah ka so ta, Allah ka kula da Bhatool, ka mallakamun ita har ƙarshen numfashi na ya Allah.”  ~~~~~~Bhatool. Tun da Senate ya ajiye ta a gida ta shigo kai tsaye ɗakinta ta nufa, ba ta ko bi takan Yaya Karima da mijinta ba, kalamansa sai yawo suke mata a kwanyar kanta, wani farin ciki na ratsa zuciyarta, ta na ji kamar tafi kowa sa’a a duniya domin samun Senate abu ne mai girma, wayarta ta ɗauka ta shiga groups ɗinsu. Ta tara da saƙƙonin da yawa sa tarin hotona, Jannah sai tsiya take ma ta wai Baby Senate ya sa ta a gaba sun tafi, Suhaima ce ma ta tanka, amma Amrah bata ce komai ba, sallama ta yi musu sanan ta ce. “Yan uwama ku ta ya ni murna, Senate ya furta mun kalmar so tare da aure.” Cikin yan mintuna suka bibiyeta da congratulation, Amrah ce ta fara kiranta a waya cike da farin ciki take magana. “Congratulation ƙawata kece akwai wani shagalin nan gaba.” Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. “Bai fi wata ɗaya ba fa.”  “Ke dan Allah, muna cikin Alheri.”  “Tsamo-tsamo ma.” Bhatool ta faɗa tana dariya, daga nan sula shiga hira da sauran ƙawayen na su har zuwa 12 na dare sanan su ka yi sallama.”  A Ɓanagaren Dad kam ya kasa zaune ya kasa tsaye kalmar “Akwai Matsala.” Da justice ya faɗa masa kaɗai ta ka ɗa masa hanjin cikin sa. Waya ya ɗauka ya ƙara kiran justice Audu amma bai ɗaga ba, sai dai ƙarar warn da ya ji  ya sa shi tabbatar da cewa Audun ya ƙaraso, ta shi ya yi ya yare shi acan su ka yi wancan part ɗin. Bayan sun zauna Dad ya ce. “Audu mene matsalal?.” Kallon Dad Justice Audu ya yi sanan ya ce. “Yunusa kasan me?.”  “Faɗi mana.” “Yarinyar nan yar gidan Habiba ce.” “Wacece Habiba kuma?.” “Habiba dai da ka sani, Habiba ta ka.” Justice Audu ya faɗa yana kallon yanayin Dad. “Ni fa bangane ba Habiba wacce.” Ta shi ya yi ya matso kusa da Dad sanan ya ce. “Habiba wacce kasani guda ɗaya, matar da ka so kamar ranka, matar da ka so kamar ka yi hauka.”  “Innullahi wa’inna illahir raji’un! Justice kama nufin Habiba ce ta haifi yarinyar da Usman ke neman aurenta?.”  “Tabbas ita ce, ita ta haife ta har da wasu ma guda biyu.” Mikewa Dad ya yi ya fara tuna lokutan baya da suka huce, irin soyayyar da suka shimfiɗa da Habiba, irin ƙaunar da ya nuna ma ta, yana tunanin ko Senate a yanzu bai yiwa Bhatool irin son da ya yi wa Habiba mahaifiyar Bhatool ba. ~~~~~~Years Back. A lokacin kallo ɗaya zaka yi wa Dad ka ga kammanin Senate Sak a tare da shi, sai dai Senate ya fi shi jikim hutu da gayu, A lokacin Dad yana tsaka da neman kuɗi a kasuwa, kasuwanci shi bai yi wani nisa ba amma a hakan ma yana samu dai-dai gwargwado. Ranar wata juma’a, bayan sun dawo daga Sallar juma’a shi da Abokinsa Audu su ka yanke shawarar shiga cikin unguwa neman abinda zasu ci, sakamakon gajiya da abincin cikin kasuwa.  Wani gidan da ake siyar da abinci su ka tsaya, ganin samari ƙofar gidan suna tsai-tsaye, a lokacin ne Habiba ta zo shiga gidan tare da ƙawarta, tun a kallon Farko ya ji wani Abu ya ratsa shi, wani baƙon yanayi ya ziyarce shi. Audu ne ya yi magana da su domin shi kam Yunusa ya yi nisa cikin Habiba. “Yan mata dan Allah me da me ake siyarwa gidannan?.” Habiba ce ta  tsaya ita kuma ƙawarta ta shige ciki, domin irin matan nan ne masu jin kai. “Taliya da wake, sai kuma gurasa da miya.” “Yawwa dan Allah, za ki iya amso mun taliya da waken?.” Audun ya ƙara tambaya. “Kawo.” Kuɗin ya miƙa ma ta sanan ya ce. “Mai za’a siya maka?.” “Koma mene ta siyo.” Ido ta ɗago ta kalleshi, ita ma take a lokacin ta ji wani abu ya ratsa zuciyarta, irin kallon da yake ma ta ya shige ta. “A’a ka faɗa me za’a siyo ma ka.”  Ta ba shi amsa. “Si yo gurasa to.” Ba ta ce komai ba ta shige gidan. Bayan ta shige gidan ne, ya kalli Audu ya ce. “Abokina wallahi na sami matar aure.” Dariya Audu ya yi sanan ya ce. “Ai tun kallon da kake ma ta na fahimci haka, Abokina kar ka yi wasa ita dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa.”  “To ta ina xan fara?.”  “Ya kake Abu kamar ba ka san yadda xaka fara ba?.”  “Audu kasan ban ta ɓa kula mace ba ko?.” “Amma ai kana da ‘yan matan.” Tsaki ya ja sanan ya ce. “Kamar ba ka san sune ke kawo kan su ba.” “Yanzu dai ka fara tambayar sunanta, da gidansu, daga nan zaka san yadda zaka bi da ita.” “Angama abokina.” Suna tsaye ta fito riƙe da ledar, ta miƙa mu su. “Mun gode.” Audu ta faɗa, shikuma Yunusa ya ce. “Yan mata anan gidan kike?.” Girgixa kai ta yi sanan ta ce. “ A’a, nan baya na ke.”  “Ina ne nan baya kuma?.” Murmushi ta yi mai sanyi sanan ta ce. “Layin dake bayan wanan.” “Ohky, nagane toh amma ai baki fadan sunanki ba,  kuma ni na faɗa miki nawa.”  “Bala fadamun ba Allah.” Ta ba shi amsa cike da shagwaɓar da ta ƙara burgesa. “Anya kuwa bam fadamiki ba.” Ya faɗa cike da wasa. “Allah dagaske.”  “Toh, sunan Yunusa.”  “Ni kuma Habiba.” Daga nan suka fara yar hirar, wacca ta jawo shakuwa sosai a tsakaninsu, tun daga wanan lokaci Yunusa ya dawo siyen Abinci a wana unguwar, hakan nan zasu tsaya su yi ta hira shida Habiba, a hankali shaƙuwa ta na ginuwa tsakaninsu, soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin su, wacce shi Yunusa ya sa ni amma ita Habiba ba ta san ta yi nisa cikin kogin ƙaunarsa ba.  A haka shekaru su ka fara tafiya, har ta kai ga Yunusa yana zuwa takanas wajen Habiba, duk da ba ta ba shi damar tsayawa ƙofar gidansu ba, domin tasan a tsarin mahaifinsu da zarar yarinya ta tsaya da saurayi a ƙofar gida to daga wanan lokacin zata fara ƙirgan raguwar kwanakin da zasu rage ma fa a cikin wanan gidan, kuma dukkanin yayyunta mata da suka yi aure mahaifinsu ne ke xaɓa musu miji, wasu ma ba sa sanim waye mijin sai bayan an kai su gidan mazajen su, Amma habiba ta kasance mai fatan cewa mahaifinsu ya canja tsari akan ta.  A haka aka ɗauke shekaru biyu suna tare, har ta kai ga Yunusa ya yi wa Habiba maganar cewa yana son ya tura iyayensa, sai dai ba ta ba shi dama ba sai cewa ta yi ya ɗan ba ta lokaci kaɗan, ko da ta zo gida ta yi magana da yayarta sai cewa ta yi. “Ki gwada sa’ar ki, ki ba shi dama yazo tun da sauran dai ba su ta ɓa tura maneman na su ba.” Haka Habiba ta ɗauki shwarar Yayarta ta sanar da Yunusa cewa ya gwada tura iyayensa.  Ranar da Yunusa ya tura iyayensa, ranar mahaifin Habiba ya sanar da su cewa ya daɗe da fitarwa da Habiba miji, da wanan su ka dawo gida suka sanar da Yunusa, ta shin farko Yunusa ya faɗi ƙasa sumamme. Hakan ma ɓangaren Habiba a ranar mahaifinta ya sanar da ita cewa ya fitar ma ta da miji kuma nan da makwanni biyu za’a ɗaura ma ta aure, ta fara lissafa kwanakin da suka rage, Habiba ta kaɗo matuƙa da jin wanan lamarin, ta yi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita, ganin ta na neman har gitsa musu gidan ya sa mahaifinta haramta ma ta fita har zuwa ranar da za’a ɗaura aurenta, tun daga wana lokacin Habiba ta shiga damuwa, kullum kuka babu ci babu sha, cikin yan kwanaki ta rame ta fige ta fita hayyacinta. Haka ɓanagaren Yunusa ma, kullum sai yazo unguwarsu Habiba, kullum nan yake yini ko zai samu ganin ko giftarwa Habiba ba ya gani, daga baya ya yanke shawarar tun karar ƙawarta, sai dai ta tabbatar mai da halin da Habiba ke ciki, tun daga hukuncin sa mahaifin ta ya yanke na ɗaura ma ta aure cikin yan kwanaki ƙalilan, da kuma hukuncin hana ta fita gaba ɗaya, sanan ta gaya masa halin da take ciki na ƙunci da damuwa.  Daga page 20 za mu gama Free pages, in sha Allahu ranar monday xamu fara paids page, a kan kuɗi Naira 500 ta wanan asusun. 8129553971 Opay sani Muhammad lawan. Gobe da safe zan sako muku last free page, shafi na Ashirin.  *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 20_ Last of Free pages….. A cikin kwanaki ƙalilan Habiba ta fita a hayyacinta, ta rame ta canja gaba ɗaya, kuma hakan bai dakatar da mahafinta kan ƙudirinsa na aurar da ita ga mutumin da ba ta san shi ba. Ranar da makwannu biyu suka cika, ranar aka ɗaura auren Habiba da Ahmad mutumin da ba ta san shi ba, ba ta san ko sunan sa ba sai ranar, Habiba ta gigice bayan ɗaurin auren, amma ganin an ɗaura auren ya sa ta haƙura ta fawwalawa Allah komai, tasan hakan ya zaɓa ma ta, ta koma tausayin Yunusa da halin da yake ciki, ta dai na tausayin kan ta gaba ɗaya.  Yunusa kam yana lisaafe da kwanakin auren Habiba, domin ranar ɗaurin auren har ƙofar gidansu yazo domin tabbatarwa da kan sa, ya matuƙar kaɗuwa shima, ya koma tausayin Habiba da halin da zata shiga, ya bar tausayin kansa. Bayan dawowarsa gida ne ya ga babu amfanin zaman shi cikin garin Yobe, hakan yasa ya tarkata ya bar garin Yobe zuwa Kano, ya sha matukar wahala a kano kafin ya mance da tunanin Habiba, ya fuskanci sabuwar rayuwa da sabon sauyi. Habiba kam sai da ta ƙara sati guda a gidansu kafin a kai ta na ta gidan, sakamakon doguwar jinya sa ta yi, Ahmad mijinta mutum ne mai zurfin tunani da hakuri, yasan Habiba ba ta son shi shima kuma hakan, domin umarnin mahaifinsa ya bi, hakan ya sa ya yi amfani da iliminsa da tunaninsa ya dinga bin Habiba sannu a hankali yana hakuri da halayenta, har zuwa wasu shekaru da ta yarda ta karɓe shi a matsayin mijinta, ta man ta da Yunusa.  Haka shima ya ɗauke shekaru da son ta a ran sa, domin har san da ya haɗu da matarsa ya aura bayan ya samu abin hannu ya dawo Yobe state, ko da ya dawo tunanin Habiba ya sake dawo wa sabo cikin rayuwarsa, da ƙyar ya dinga yaƙi da zuciyarsa a kan ta. Wanan shine labarin Mahaifin Senate da Mahaifiyar Bhatool.  Ci gaba. “To Amma Justice aina kasamu wanan tabbacin?.” “A binciken da na yi a kan lamarin auren mana.” “Amma Justice idan haka ne ai bai kamata na hana auren Senate da ‘yar wajen ta ba, ina ganin kamar Allah ne ya tsara kasancewar su tare.”  “Yanzu zaka iya zuba ido ɗan ka ya auri ‘yar Habiba.” “Justice kenan, mai Habiba ta yi mun a rayuwa ban da alheri, sanan shi kan shi mijin Habiban ai ba shi da laifi.” “To ai mijin ma ya rasu, shekaru da dama.”  “Allah ya yi masa rahama, amma akan wanan dalilin bazan hana auren su ba.” Daga haka Dad ya shige ciki ya bar justice. Ɗakin Mom ya shiga, tana zaune gefen gado tana faman tunanin halin da ɗan ta zai shiga idan ya rasa auren Bhatool. Da sallama Dad ya shigo, amsawa ta yi ba tare da ta ɗaga ido takalleshi ba, zama ya yi gefenta sanan ya ce. “Fushi kike da ni?.” Girgiza kai ta yi kawai. “Justice ya zo mun yi magana da shi, kuma ya faɗamun dalilansa.”  “Tom yanzu me ka yanke?.” “Na yanke shawarar nema masa aurenta, domin dalilin da ya ba ni ba wanda zai hana aure ba ne.” Da murmushi a fuskar mom ta juyo sanan ta ce. “To ko kai fa, amma da ka ɗaga hankalina ka ɗaga na ɗana.”  “To yanzu sai ku sauke shi ko, domin gobe sa safe ma zan tura aje gidansu yarinyar, kuma har da ni za a je.” “Alhamdulillah ya rabbi.”  ~~~~~Bhatool…. Ƙarar da wayarta ke yi ne ya tashi daga baccin da ta koma bayan ta yi sallar asuba, hannu ta kai ta ɗauke tana jan tsaki, ba tare da ta kula da mai kiran ba. “Hello.” Ta faɗa murya cike da magagin bacci. “Bhatool.” A zabure ta miƙe jin muryar Dr Hisham. “Na’am.” Ta faɗa a tsorace. “Bhatool aure zaki yi?.”  “Innullahi wa’ina illahir raji’un.” Ta furta a zuciyarta, a fili kuma sai ƙara cewa ta yi. “Waye?.”  “Dr Haisam ne.” “Ina kwana?.”  “Bhatool tambayar ki nake fa.” “Ni ba auren da zan yi, bikin Suhaima fa a ke yi.”  “Nasan ai bikin Suhaiman ake yi, amma ke ma ai aure zaki yi ko?.”  Shiru ta yi ba ta iya cewa komai ba, sai zallan mamakin yadda a ka yi yasan da maganar. “Toh Bhatool, ki je ki yi auren kin ji, zaki ga ni a idonki.” Daga haka ya kashe wayar, shiru Bhatool ta yi “wanan wace irin masifa ce, waye yasan ma zan yi aure?.” Ta tambaye kan ta, amma sanin babu mai ba ta amsa ya sa ta yi shiru, ƙofar ɗakin aka buga sanan a ka ce. “Wai yau ba zaki fito ba?.”  “Gani nan Yaya.” Ta faɗa tana mikewa, a falo ta sami Yaya Karima da mijinta suna zaune, ƙarasawa ta yi inda suke sanan ta ce. “Ina kwana?.”  “Lafiya kalau Bhatool, kin ta shi lafiya?.” “A’a Yaya da matsala Babba.”  “Wace irin matsala kuma, ke fa mahaukaciya ce.” yaya Karima ta faɗa. “Ba irin wanan matsalal ba ce, kuma ni bake nake wa magana ba, Yaya Ka na ji?.”  “Ina jinki Bhatool.” “Akwai wani malami a makarantar mu Dr Haisam, ya ce yana sona, kuma ɗan iska ne kowa ya san shi a makaranta, ranan ya yi mun baraxana na zo na faɗawa Yaya Karima, yau kuma ya ƙara kirana yanzu wai aure zan yi ko?.”  “Ai ina ya samu labarin zaki yi aure to?.” “Nima Yaya bansani ba wallahi.”  “Yanzu da safe nan mahaifin senate ya kira ni, bayan na je ya sanar da ni yana so zai ce ya samu su kawu yau shi da yan uwan sa, a sanya lokacin aurenku na yi tunanin ke ma bakisan maganar ba?.” “Yanzu dai nasan magnar da kafaɗamun.” Bhatool ta faɗa sabida ita gaba ɗaya ta tsorata da lamarin Dr. “To amma shi ina ya sa ni?.” Yaya Karima ta sake tambayarta. “Wallahi bansani ba Yaya.”  “Ba ni lambarsa kawai.” Miƙa masa wayar ta yi yaɗauki lambar. “Ki ta shi ki je ki yi breakfast.” Yaya Karima ta faɗa ma ta. “Tom.” Ta faɗa tana miƙewa zuwa dinning, gaba ɗaya jikin ta ya mutu.  ~~~~~~Hausari….. Gaba ɗaya yan uwan Mahafinsu Bhatool ne zaune a ɗakin Goggo Larai, cike har da Furai da Habi wayanda suka kawo gulmar, wacce suma ƙarya suka shirgo abun su.  “Ku maimaita abinds ku ka faɗa.” Isiyaku ya faɗa, wanda shine mahaifin Habi kuma yayan wanda suke son bawa Bhatool Saddiƙu, Furai ce ta fara magana. “Daman mun sami labarin cewa Bhatool tana shirin barim gari ne, ita da Yayarta da mijin yayarta, sanan Abdul za su tafi ƙasar waje shi da mahaifiyarsa da yarinyar da yake son aura har da iyayenta.”  “Kutumar b***a u**a.” Ɗan ladi ya mako wata ƙatuwar ashariya, sanan ya ɗora da cewa. “Lallai yaranan ‘yan iska ne, mun sun mayar da mu banzaye kenan ko me, Shi Abdul ɗin har ya yi kuɗin da zai tafi ƙasar waje da iyayen yarinyar da zai aura, mu gamu anan shashashai.”  “Ai yaron da manyan yan kasuwa yake mu’amala dole ya yi kuɗi, amma sabida baƙat zuciya irin ta uwarsa ba zata ba shi umarnin xuwa nan cikin dangin ubansa ya nemi aure ba shine ta tura shi duniya.” Isiyaku ya faɗa rai a ɓace.  “To ni yanzu so  nake mu yi musu dirar wuri, a yau ɗinan a ɗaura auren Bhatool da Saddiƙu, sanan shima Abdul a ɗaura masa aure da Sajida yar wajen ka Ɗan ladi, shikenan a raba komai.”  “Tabbas Larai kin yi basira kin yi tunani, kuma kin cika babba.” Auwala ya faɗa wanda shine ɗan autan su. “Yanzu yaushe zamu samesu?.” Isiyaku ya faɗa. “Ai yanzunan zamu je, ayi komai da a kan lokaci. Zasu san girman dangin uba.”  GIRMAN DANGIN UBA😂😂 1 Dangin mahaifin su Bhatool zasu ɗaura ma ta aure yau? 2 Idan mahaifiyar senate ta san asali alaƙar dake tsakanin mahaifin senate da mahaifiyar Bhatool zata bari ayi auren? 3 Mahafin senate zai je nema masa auren Bhatool,amma dangin mahaifinta sun neman riga shi, shin wane zai auri Bhatool? 4 Aina Dr Haisam yake samun bayanai, zai iya haƙura da rashin Bhatool? 5 Idan Senate ya samu auren Bhatool zai iya cika alƙwarin da ya ɗauka, ita ma Bhatool za ta yi biyayya ga Senate? Mu haɗu a cikin paids page na Hasashen soyayya, wanda zai fara zuwa ranar littinin idan Allah yakaimu, ba jira sunan jirgin namu.  Naira ɗari biyar kuɗim tikiti. 8129553971 Opay Sani Muhammad lawan Shaidar biya 08129553971 Legendspen *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 21_  ~~~~~~Nyan’ya Umma ce zaune kan kujera yar tsugunno ta figar zogale, daga gefen ta kuma Abdul ne tsaye jikin rijiya yana ɗebo ma ta ruwa cikin rijiyar. Kwankwasa ƙofar gidan na su aka fara yi da ƙarfi babu nutsuwa. “Waye anan?.” Abdul ya faɗa, bai ƙarasa magana ba Goggo Larai ta shigo cikin gidan babu ko sallama, tsayawa ta yi sanan ta ce. “Ku shigo mana.” Ba ta rufe baki ba Su Isiyaku da Ɗan-ladi suka shigo, har da saddiƙu da wasu yan cikin gidan. Da mamaki dai Umma da Abdul suke kallonsu, domin basa iya tuna lokaci na ƙarshe da su ka zo gidan gaba ɗayansu haka, zai iya kasancewa tun lokacin mutuwar mahafinsu. Ta shi Umma ta yi ta shiga ɗakko musu tabarma tana faɗin. “Sannunku da zuwa.”  “Yawwa.” Goggo Larai ta faɗa, sauran kam shiru su ka yi na su ce ko ƙala ba. “Ga waje ku zauna.”  “Bazama ya kawo mu ba, ina sauran yaran?.” isiyaku ya faɗa. “Wane yara?.” Abdul ya yi tambayar ganin zasu nemi rainawa mahaifiyarsu hankali. “Sauran yayun na ka.”  “Au ba sa nan.” Ya faɗa yana ci gaba da jan ruwan sa, domin yasan ba alheri ba ne ya kawo su. “To anemo su.”  “Yaya Isiyaku Lafiya dai?.” Umma ta tambaya. “Wai ba mu isa mu nemi ganin su ba ne?.” Goggo larai ta faɗa tana wani hare-hare. “Basa nan ne, Bhatool suna biki ta je gidan biki, ita kuma Karima ta na gidan mijinta.” “To duka ayi musu waya su zo muna son ganin su.”  “Abdul kira mun Karima.” Waya ya shiga dannawa, bayan ya kira Yaya karima ne ya bawa Umma wayar, Bhatool ce ta ɗaga wayar tana faɗin. “Ƙanina ya ake ciki ne?.”  “Bhatool.”Ummah ta faɗa. “Na’am Ummana ina kwana?.” “Lafiy ƙalau Bhatool, ina Kariman?.”  “Suna ciki ita da Yayan.” “Kai ma ta wayar.” “Lafiya dai Ummah?.” “Kai ma ta Bhatool.” Ummah ta faɗa a dakile. “Yaya zo ki karɓi waya.” Bhatool ta faɗa, tana zuwa ƙofar ɗakin na ta, fitowa ta yi tana faɗin. “Me yasa baki da hankali ne dan Allah?.” Cuno baki ta yi gaba sanan ta ce. “Ni dai amshi.”  “Hello, au wai Ummah ce?.” Yaya karima ta faɗa a lokaci guda. “Ni ce Karima mijinki na nan?.”  “Eyh yana nan Ummah.” “To ina so dake da shi da Bhatool duk kuzo gida yanzu.” “Iyayen Senate ɗin sun zo ne?.” “Waye Senate? , ni dai na ce ku zo yanzu.” “Mu bamu gayyaci mijinta bah.” Yaya Karima ta jiyo muryar Goggo Larai ta faɗa, kashe wayar Umma ta yi ba ta so su Yaya Karima su ji mutanen dake gidan. “Goggo Larai?.” Yaya Karima ta faɗa a ran ta. “Su wane Goggon?.” Bhatool ta tambayeta. “Haka Umma ta ce mu zo gida dukan mu yanzu, kuma na ji Goggo Larai ta na magana wai ba su gayyaci mijina ba.”  “Mene ya kawo su gidanmu haka?.” “Wallahi Bhatool nima bansaniba, je ki shirya dai.” Yaya Karima ta faɗa tare da shigewa ciki. “Wai wane mutumi ne take kira haka?.” Ɗan-ladi ya tambayi Isyaku. “Nima bangane wanda take nufi ba.”  “Lauya mijin yarta ta fari.” Goggo Larai ta faɗa. “A’a mene na gayyato mana shi kuma, to kar ya kuskura yazo.”  “Dole yazo mana, domin a yanzu shine wakili a kan ta da sauran ‘yan-uwata, domin wayanda ya kamata su zama wakilan na su sun watsar da su.”  “A’ah, kar ki kuskura ki gaya mana magana fa.” Goggo Larai ta faɗa. “Muma kar ku kuskura ku faɗawa Mahafiyar mu magana.” Abduk ya faɗa, domin wani mugun haushin su ne ya dirgar masa a zuciya. “Kai ka kiyaye fa.” Saddiƙu ya faɗa cikin muryarshi ta marasa jin magana. “Rufe bakin ka Abdul.”  “Wallahi Umma babu wanda ya isa ya zo cikin gidanan ya ce zai gaya miki magana, idan da sun yi sum ci banza yanzu basu isa ba, yanzu ‘ya’yanki sun ta sa, sun yi girman da zasu tsaya miki a ko ina, wallahil azim duk wanda ya ce zai ɗaga miki hankali sai na haɗa shi da shari’ah.”  “Eyh, Lallai yaro ka fara riƙe kuɗi.” Ɗan-ladi ya faɗa yana kallon yadda Abdul yake magana. “Kabarshi kawai.” Goggo Larai ta faɗa.  Ba’afi mintinu ashirin ba su Bhatool suka shigo gidan, Bhatool na sanye cikin doguwar rigar atamfa, ta yafa ƙaramin mayafi fuskarta a haɗe kamar wacce aka aikuwa da saƙon mutuwa haka ta shigo gidan, tsayawa ta yi ƙiƙam tana ƙare musu kallo. “Lafiya?.” Ta faɗa cike da mamaki. “Bhatool masoyiyah.” Saddiƙu ya faɗa, yana washe ma ta baki. Da wani mugun kallo tabi shi, sanan ta ce. “Waye wanan kuma?.” Dan ota harga Allah ba ta gane shi ba. “Mijinki, wanda zai aure ki.”  Goggo Larai ta faɗa, tsaki ta ja sanan ra shige ciki kusa da Ummah dai-dai lokacin da Yaya Karima suka shigo, gaishe su su ka yi sanan su ka ƙarasa wajen Ummah, ba su kai ga zama ba Goggo Larai ta ce. “Ba ma son bare ya zauna a nan.”  “Duk maganar da zakuyi anan, to a gabansa za ayi domin shine yake kamar jagora a garesu, shi ke tsaya musu a kan komai da komai, Allah ne gatan ‘ya’yana, shine gatan su.”  “Mu mu yi maganar da zamuyi da abunda zamu yi mu huce.” Isiyaku ya faɗa. “To daman mun zo ne mu gaya muku cewa zamu ɗaura auren Bhatool da Saddiƙu, Abdul da Sajida, kuma mun zo ne mu daura auren a yau.” “Dake a garin mahaukata ake ko?.” Abdul ya faɗa yana wani hararasu, Bhatool kam miƙewa tsaye ta yi sanan ta ce. “Ni kam wanan rashin hankalin ba a gaba na ba.” daga haka ta yi cikin ɗaki. “Bari na fara kiran jami’an tsaro daman Umma nema nake kawai su shigi hannu, wallahi sai sun yi aman kuɗin da suka ci na gadon mahaifinmu.” Abdul ya faɗa yana zaro wayarsa, wani ƙululu cikin su Goggo Larai ya ba da. “Ah kaga kai me yasa baka da hankali ne?.” Ɗan-ladi ya faɗa. “Bar shi dai ya kira su, tun da jahili ne.” In ji Isiyaku. “Abdul kar ka kuskura ka kira wani.” Umma ta faɗa daga inda take, wayar ya mayar cikin aljihunsa sanan ya ce. “Ku ta shi ku fice mana daga gida, kar ku kuskura na sake ganin ƙafar wani cikin gidanan, dan wallahi sai na ɗauki mummanan mataki a kan sa.”  “Ai ba mu yi lalacewar da zaka yi mana haka ba, to ba zamu fita ba.” Isiyaku ya faɗa. “Abdul ka rufe baki kar na sake jikin bakin ka anan.” Ɗakin da Bhatool ta shiga nan shima ya shiga. “Ni Umma a ganina wanan abu ne mai sauƙi, a matsayina na babban lauya kuma mai kare su Bhatool, ki bar su su yi duk abinda su ka ce zasu yi, ai shari’a na nan.”  “Kai ɗan ɗorin ɗo sa no, rufemun baki mara kunya.” Goggo Larai ta faɗa tana maka mai harara. “Yoo ban da rashin ta ido har mu ne zai faɗawa shari’a, muna matsayim sirikan sa.” Ɗan-Ladi ya faɗa, dama su uku ne suke ta magana sauran duk sun yi shiru. “Ai da an nuna masa darajar mu dai bazai mana haka ba, har yau ina baƙin cikin Ahamdu da ya aura wanam figaggiyar mitsiyaciyar.” Goggo Larai ta faɗa. “To Shima ba Umarnin Baba ya bi ba, amma nasan har ya mutu baya farin ciki da aurenta.”  “Kum ga bayin Allah ya isheku haka, tun da bakwason harkar arziƙi bari ayi ta tsiya.” Yaya Karima ta faɗa tana miƙewa. “Abdul fito ka kira mutanen kawai, gwanda mu dan gana ga kotu.” Sallama su ka ji a ƙofar gidan duk kan su su kalli ƙofa. Abdul da ya fito yanzu ne ya nufi ƙofar, ya bar su Goggo Larai ciki na ƙululu.  Manyan mutanen da ya gani ne ya sa shi tsugunnawa ya gaida su, ciki har da Alhaji Habu Naira wanda suke kasuwanci sosai da sosai. Alhaji Habun ne ya ce. “Abdul nan ne gidan ku kenan?.” “Eyh yallaɓai nan ne.” “Toh Ma sha Allah, Abdul muna son masauki domin magana mai muhimmanci ce ta kawo mu.”  “Tom yallaɓai.” Abdul ya faɗa tare da komawa ciki, daga farkom gidan ya tsaya ya kira Barrister, tasowa Bartister ya yi zuwa inda Abdul ɗin ya ke sanan ya ce.” Su waye?.”  “Wasu manyan mutane ne, ciki har da Alhaji Habu naira ɗan kasuwarmu, sun ci magana ce mai muhimmaci suna son waje kuma ga shi wayanan tijararrun suna ciki.”  “Wallahi kam Abdul, yanzu za su iya musu hauka.” *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 22_ “Ka na ji Abdul.” Barrister ya faɗa. “Ina jinka.”  “Mu zaunar da su nan ɗakin ka na zaure kawai, su wayanan ɗin zan yi magana da Karima ta san yadda zata riƙe su da surutu ko abinci ne ta da fa musu, kar dai ta bari su fito kuma kar ayi hayaniya.”  “Hakan ya yi bari na buɗe musu.” Abdul ya faɗa yana nufar ɗakin, shi kuma ya yi cikin gidan. Yaya Karima ya kira ya sanar da ita cewa ta san yadda zata kula da su, kafin su gama da yan uwan su Senate. “Shikenan yanzu zaku tafi ne ko kuwa zaku jira a gama abincin ne kawu?.” Yaya Karima ta faɗa bayan mijinta ya matsa. “Ita kuma maganar da mu ka zo da ita fa?.” Goggo Larai ta faɗa. “Yanzu Abdul ya hau dokin zuciya ya fice, mijin ya bi shi kuma kun san ba zai ta ɓa fahimtar ku a haka ba.”  “Shikenan dafa mana abincin mu ci mu tafi, gaba ma dawo.” Ita dai Umma da mamaki take kallon abinda Karima ke yi. “Umma me kike da shi?.” “Shiga Kitchen ɗin ki duba.” Shigewa ta yi ɗaki ta sami Bhatool zaune. “Wai Yaya girkin me zaki yi mu su?.” Bhatool ta tambayi Yaya Karima. “Ke dalla malama yan uwan Senate ne su ka zo, kin san idan aka bar su hauka zasuyi musu.”  “Hakane kuma wallahi.” Ta shi Yaya Karima ta yi ta fice zuwa kitchen ta shiga haɗa musu abincin. A ɓangaren su Abdul kam bayan ya buɗe ɗakin ya yi musu iso su ka shigo, yan mintuna kaɗan Barrister ma ya shigo, bayan gaisuwa ne Alhaji khamisu ƙanin Dad ya fara magana. “Da farko dai mun zo nemawa ɗan mu Usman Yunusa aure ne na ƙanwarka Bhatool, sai dai zuwan namu ya kasance ba tare da sanarwa ba, hakan yasa bamu buƙaci ganin wasu cikin dangin mahafinku ba tun da mun sami labarin shi mahaifin naku Allah ya yi masa rasuwa, mun yu bincike sosai kafin zuwan mu nan.” Murmushu Abdul ya yi tare da yin godiya ga Allah sanan ya ce. “Gaskiyya na yi farin ciki kuma na ji matuƙar daɗi da hakan, sai dai a yanzu ma muna cikin wata matsala da dangin mahaifin namu, rabun mu da su tun lokacin da su ka amshi gadon mahaifinmu, sai yau ɗinan su ka zo wai zasu ɗaura mun aure da wata yarinya sanan zasuyi Bhatool ɗin ma aure da wani yaronsu kangararre,  ko zasu samu ya dawo kan hanya.” Cike da mamakin wanan rashin hankali na yan-uwan mahaifinsu Bhatool Alhaji Habu Naira ya ce. “Ikon Allah, kuma suna cikin gidan yanzu babu kunya?.” “Wallahi suna ciki yallaɓai.”  “Kira mana su.” Justice Audu ya faɗa, miƙewa Abdul ya yi ya shiga ciki yana mamakin dalilin da yasa suka nemi ganinsu, bayan ya ta shi ne Justice ya ce. “Ai tufkar za’ayiwa hanci kawai, rabon a ɗaura auren Senate da Bhatool yau ne ya kawo mu.” Dad dai yana zaune bai ce komai ba, kamar ba shi ne mahafin Senete ba. Tun da ya shigo gidan zuciyarsa ke ma sa wani irin bugu, kallon Abdul kawai yake yana ganin kammanin Habiba a tare da shi, Abdul na shiga cikin ya ce da su Iliyasu. “Ku zo kuna da baƙi.”  “Su waye?.” Goggo Larai ta tambaya. “Ban sa dake ba, su mazan.”  “Kar da ka ce zaka zageni dai.” Banza ya yi da ita shi dai. “Kai su waye su ke kiran mu?.”  “Baƙi ne a waje, harkar samun kuɗi ce kar ku rasa.” Daga haka ya fice, har rige-rigen ta shi suke su bi bayanshi.  Baki sake suke kallon manyan mutanen dake cikin ɗakin,kallo ɗaya zaka yi musu kaga arziƙi a tare da su. “Ku zauna?.” Justice ya faɗa, zama su ka yi babu wani musu. “Barkan ku.” Ɗan-ladi ya faɗa. “Barka dai, nasan baku gane mu ba ko?.” “Eyh sai kun yi mana bayani.” “Mune masu nemawa ɗan mu auren ‘yar wajenku Bhatool.”  “Wanan zancen banza ne, mun riga da mun yi wa Bhatool miji.”  “Muna so a janye wanan mijin akan naira dubu ɗari biyar.” Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Ɗan-ladi da su Iliya, can kuma Iliya ya ce. “Ba sadakin ta ba ne wanan?.” “Ba sadaki ba ne, naku ne kawai.”  “To Mun bayar.” Hannu Alhaji Habu Naira ya sa cikin aljihu ya fito da dollors ya miƙa musu sanan ya ce. “Muna so za ayi komai yau har da ɗaurin Auren.”  Daga nan aka shigo  hada hadan ɗaurin aure, har da gayyato mutanen unguwa suka shaida ɗaurin auren, Usman Yunusa Ahamd (Senate) da Kuma Fatima Ahmad ishak (Bhatool) ‘yan cikin gida na zaune sai ji suka yi ana shafa fatiha, tare da yin Allah yasanya alheri.  Bayan ɗaura auren Abdul ya ce da su. “Ya kamata ku shigo cikin gidan ko?.”  “A’a ma shigo wata rana.” justice ya faɗa, dan ya fuskanci Dad fa ya fara rasa ƙwarin gwiwarsa na haƙura da Habiba. “Shikenan mun gode sosai.” Abdul ya faɗa sanan suk rakasa zuwa motococinsu shi da Barrister, Bayan sun tafi ne Abdul ya kalli Barrister sanan ya ce. “Ka ga bayin Allanan ko?.”  “Hakuri za ka yi Abdul, ƙannen mahafinka ne kuma iyayenka ne, sanan rabon ɗaura auren Bhatool da senete yau ne ya kawo wu su gidan.”  “Hakane kam.” Abdul ya faɗa suka shige cikin gidan,  lokacin su Ilaysu sun koma ciki suna cin Abincin abun su, bakuma su ce da kowa ga abinda ya faru ba. “Wai baxaki faɗi abinda ya faru ba ne?.” “Larai bari su shigo dai su yi muku bayanin kawai.”  Ɗan-ladi ya bawa larai amsa, tsaki ta ja kawai ta ci gaba da kai lomar abinci bakinta. Bayan su Abdul sun shigo ne Barrister ya ce. “Toh Alhamdulillah, babu abinda zamu ce da Allah sai godiya, a yau dai an ɗaura auren Bhatool.” A zabure Bhatool ta fito daga ɗaki ta na faɗin. “Wace Bhatool ɗin?.” Goggo Larai ce tasaki guɗa tare da faɗin. “Kai mun ji daɗi Saddiƙu an angwance.”  “Ba fa da Saddiƙu aka ɗaura ba.” Ɗan-ladi ya faɗa. “Bamgane ba fa, kar ku raina mun hankali.”  “Mu ba da Saddiƙu muka ɗaura auren Bhatool ba, mun ɗaura shine da dan gidan Alhaji Yunusa.” “Ai wallahi ba isa ba, anyi kaɗan wallahi.” Goggo Larai ta miƙe tsaya tana faɗi. “Kinga ki zauna idan zaki zauna, idan ba zaki zauna ba ke kika sani, ni ma fasa cin Abincin ma baki ɗaya.” Iliyasu ya faɗa tare da ficewa. “Nima haka.” Ɗan-ladi ya faɗa, ai duk sai mazan su ka miƙe suka fice, aka bar Goggo larai da saddiƙu, sai Habi da Fure. “Kutamma dumadu, Goggo kinga avinda akamun?.”  “Yi shiru Saddiƙu, ai babu asararre sai ubanka.” Goggo Larai ta faɗa tana ficewa, ba shiri Furee da Habi suka bita, shima Saddiƙun ya fice. “Wai mene ya faru a wajen, ku yi mun bayani.” Umma ta tambaya, zama su ka yi sanan Barrister ya ce. “Umma daman akwai wanda suke soyayya da Bhatool anan unguwarmu.” “Eyh nasan da shi, mun yi maganar da Karima.” “To yanzu fitar da Abdul ya yi sune su ka yi sallama da shi sun zo neman auren, bayan ba su labarin abinda ke faruwa cikim gidan shine ɗaya cikin abokan mahaifn  yaron wanda yake abokim kasuwancin Abdul ya buƙaci kawai a ɗaura auren, gudun wata matsala.”  “To amma ta ya akai suka amince?.” Yaya Karima ta yi wanan tambyar. “Da farko sun fara rashim arzƙin na su, shine akayi musu tayin hamsin-hamsin suka amince.” Abdul ya faɗa. “Kai Allah ya sawaƙawa mutanen, ni naga sunkasa zama, ashe tsoron kar Larai taga kuɗin ne?.” “Wallahi fa Umma.” Yaya Karima ta bawa Umma da ta yi maganar amsa. Ihu suka jiyo daga cikin ɗaki na Bhatool, tare da faɗin. “Wallahi bana so.”  Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 23_ “Mene bakya so?.” Yaya Karima ta tambayeta, bayan ta shigo ɗakin. “Aure, ni ba yanzu ba.”  “Dalla mahaukacya, ba taimakokin su ka yi ba, da wayanan ɗin sun ɗaura miki da Saddiƙun ai kyayi kukan na gaske.”  “Ni dai Allah ba yanzu ba.” “Kyaji da shi.” Yaya Karima ta faɗa tana jan tsaki, tare da ficewa. Ta shi Bhatool ta yi zaune, tare da faɗin. “Wai yanzu na zama matar aure, matar Senate?.” Wayarta ta ɗauka ta duba lokaci, ganin sha biyu ma rana ga kuma tarin Missed call ɗin su Jannah ya sa ta tuna da ɗaurin Auren Suhaima, da sauri ta ta shi ta fita tsakar gida. Suna nan zaune ta huce su ta ɗibi ruwa ta yi toilet, a gaggauce ta yi wanka ta fito suna zaune suna kallonta, yan mintuna kaɗan da shigarta ta fito  sanye da riga da skert na lace, ta yafa mayafinta mai ɗan girma ba ta yi wani makeup ba. “Ina zaki kuma?.” Yaya Karima ta faɗa. “Ni wallahi duk na sha’afa da daurin auren nan?. “Ɗaurin auren wa?.” “Suhaima mana.” Ta faɗa hankalinta na waje. “Wai Bhatool baki da hankali ne?.” Ummah ta faɗa. “Me na yi Umma?.”  “A ɗaura miki aure yanzunan ki ce zaki wwni tafi biki, baki da hankali ne ko bakisan me ya faru ba?.”  “Me ya faru Umma?.” Ta faɗa tana dawowa kusa da Umma ta zauna. “ Bhatool ke fa yanzu matar aure ce, fita ai ba naki ba ne?.”  “Ko na tambayesa?.” “Wai me yasa baki da hankali, ɗaurin aure fa kawai aka yi ba ayi wani abu ba.” Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ita ba ta gane kan wanan al’marin ba, wayarta ce ta fara ringing kira na shigowa. “Hello Suhaima.” Ta faɗa tana mikewa tsaye bayan ta ɗaga kiran. “Suhaima ba zan samu zuwa ba wallahi.” Ta ƙara faɗa. “An ɗaura mun aure fa yanzun nan.” Sai a lokacin Muryar Suhaima ta fito. “Ki bana son iskanci.”  “Wallahi Suhaima daga zuwa tambaya.”  “Ka Alhamdulillah, amma Bhatool naji daɗi sosai wallahi.” Daga cikin wyar Amrah ta tambaya. “Ba zata zo ba, me yasa.”  “An ɗaura aurenta ita ma da Senate.” Jannah ce ta ƙwace wayar tare da faɗin. “Bhatool da gaske! ?.”  “Walahi dagaske Jannah, daga zuwa tambaya.”  “Kai! Allah Alhamdulillah Bhatool, Allh yasanya alheri yanzu zamu tawo nan.”  “Dan Allah ku zo ina gida, nasan ma bazan koma gidan Yaya Karima ba.”  “Yanzunan in sha Allah.” Jannah ta faɗa tare da katse wayar. ~~~~~~~Red bricks. Tun fitar su Dad, Mom tasanarwa da Senate an tafi nema masa aure, sai faman washe baki yake zai auri Bhatool. Suna nan zaune su Dad suka shigo gidan shi da Justice, bayan sun zauna ne Justice ya ce da. “Ango.” Murmushi ya yi tare da yin ƙasa da kai. “Allah yasanya alheri, yasa abokiyar rayuwa ce ta har abada.”  “Amin Uncle.” Ya faɗa kansa na ƙasa. “Alhmdulillah, an gama komai kenan?.” Mom ta faɗa ta na washe baki, dariya Dad ya yi sanan ya ce. “Ai har sai kin ba ni tukwici.” Dariyar ita ma ta yi sanan ta ce. “Na baka.”  “To dai Senate Allah ya yi, ba iya nema masa aure a ka yi ba har da ɗauro auren duk anyi.”  “Bangane ba.” Mom ta faɗa. “Daga zuwa neman aure mu ka ɗauro auren baki ɗaya, a taƙaice dai an ɗaura auren ɗan lelenki da Bhatool.” Justice ya yi wa Mom wanan bayanin. “Kai Alhamdulillah, Alhamdulilah.” Mom ta faɗa tana hawaye. “Wai Dad kana nufin yanzu an ɗaura mana aure da Bhatool?.”  “Eyh tabbas haka ne, yanzu ka zama mijin Bhatool.”  “To Daddy tana ina?.” “Tana gidansu mana, yanzu za a zo a shirya duk wasu abubuwa da ake yi a kai wa iyayenta, sana a tsyar da lokutan shalin biki kamar one month haka.” “One month kuma daddy, ina laifin one week haka?.”  “Kaci gidanku, jimun ja’irin yaro.” Dariya suka yi baki ɗaya, sanan Mom ta ce. “Ai kam dai ba za a huce two weeks ba har tarewar amaryar, yanzu kam sai a sanar da ɗaurin auren.” “Ai wanan aikin ki ne.” Dad ya faɗa. “Ai kam dai nawa ne, yanzu zan yi shela.” Dariya suka yi baki ɗaya, daganan kowa ya ta shi zuwa ɗakin shi. Senate na shiga ɗaki ya fara kiran abokansa ya sanar da su, cikin ƙanƙanin lokaci su ka cika gidan nasu, haka ma ɓangaren Mom ta hau snaar da mutane. Cikin ‘yan awanni zancen auren ya fara zaga gari baki ɗaya. Bayan abokansa sun tafi ne ta dau waya ya kira Bhatool, wacce itama su Jannah da Amrah ba su daɗe da tafiya ba sabida zasu je kai Suhaima, har da kukan Bhatool tasan ita da fita yanzu sai Baba ta gani, ɗaga wayar ta yi ba ta ce komai ba. “Bhatool.” Ya kira sunanta a hankali, kuka ta fashe da shi wanda dama yana ranta. “Bhatool mai ya faru?.” Kukan ta ci gaba da yi a hankali wanda ke ratsa zuciyarsa. “Me ya faru wai, Bhatool?.” Ya tambayeta. “Bakomai, kawai ina yi ne.”  “Bhatool godiya ya kama ta mu yi wa Allah ko?.”  “Hakane.” Ta ba shi amsa, gaba ɗaya jikinta ya mutu, sai ka ce ba Bhatool ba. “Ki ta shi ki yi alwala ki yi sallah, nima yanzu zan yi.”  “Tom.” Ta faɗa tana mikewa bayan ta kashe wayar, su Umma na zaune tsakar gida, sai dai babu barrister ƙila ya tafi aiki. Huce su ta yi zuwa banɗaki ta ɗaura alwala ta dawo, bayan ta idar da sallah ne ta yi godiya ga Allah, sanan ta roƙa musu zaman lafiya da soyayya mai ɗaurewa.  Bhatool tana ji tana gani Yaya Karima ta tafi ta barta wajen Ummah, ta sha kuka sosai mussaman da Yaya Karima ta ce mata.”Ke Bhatool yanzu ai kinga ma kwana gidana in sha Allahu.” Kukan ta ci gaba da yi har Yaya Kariman ta tafi, daddare ma sun sha waya da Senate ɗinta sosai da sosai, har zuwa sanda ta yi bacci.  Ƙarar kiran wayarta ne ya tashe ta daga baccin da take, hannu ta kai ta ɗaga wayarta tare ba tare da ta kula da lambar da ke kiranta ba. “Hello.” Ta faɗa bayan ta ɗaga wayar. “Bhatool.” A furgece ta miƙe zaune tana faɗin. “Na’am.”  “Kin yi aure ko?.”  “Eyh na yi.” Dan ita ta fara gajiya da lamrin Dr ɗinan, mutum kamar mai aljanu. “Ni kike cewa kin yi?.”  “To me zance maka malam, na yi aure sai ƙaƙa?.” Cike da mamaki yake saurarun ta, sai ji ya yi taƙara cewa. “Shirun da nake maka bafa tsoro ba ne, ni Bhatool wallahi ba kanwar lasa ba ce, kainuwa nake dashen Allah, sai gani sai hange.” Ta na gama faɗi ta kashe wayarta, dan koma mene yanzu ta riga ta yi aure ta huce duk wani sharrinsa, saukowa ta yi sa gadon ta fito tsakar gida tare da nufar banɗaki. ~~~~Red bricks.  “Yanzu wayanan laces ɗin duka ta bayar akawo mun?.” Mom ta faɗa tana tambayar wata mata dake zaune kan kujera. “Eyh Hajiya, cewa ta yi wai aƙara a cikin lefe.”  “Kai Ma sha Allah, matar minster ta cika ‘yar halak wallahi, mgde sosai.” Mom ta faɗa tana ƙara duba tsaddadun laces ɗin da suke baje a gabanta, wayanda sun fi kala 30 kuma dukkanin su masu tsada ne, dan babu na ƙasa da dubu ɗari biyu. “To Hajiya zamu tafi, driver na jiranmu.” Matar da ta kawo kayan ta faɗa. “Ah, Ina zuwa.” Mom ta faɗa tana ta shi ta nufi cikin ɗakinta, a hanya ta ci karo da senate yana shirin sakkowa. “Yawwa Senete je falo kaga kayan da Hajiya Na’ima matar minsta ta aiko da shi, wai asa a lefe.”  “Okay Momi, daman nasan ke ai bazaki rasa irin wanan ba, domin duk lokacin da ‘ya’yan ƙawayenki suka ta shi aure haka kike musu.”  “Hakane Senete, amma wayanan fa suna da yawa sosai, ka je ka gani banma san me zan bawa wanan mai aikin na ta ba, da ta kawomun.”  “Bara na gani.” Ya faɗa yana sauka ita kuma ta haye samanta, shi kan shi senate ya yi mamakin yawan laceses ɗin da kuma tsadarsu, domin kana ganinsu kasan masu tsada ne. Yana nan zaune mom ta sakko da wata ƙatuwar leda a hannunta cike da kaya, ta miƙawa matar tare da faɗin. “Ga shi wanan naki ne.” Karɓa ta yi tana faɗin. “Na gode Hajiya, Allah yaƙara buɗi.”  “Amin-amin.” senate ya faɗa yana ciro daloli daga aljihunsa shima ya ba ta, bayan ta fita ne shima ya ce da Mom. “Amma kayan da yawa gsky.”  “Nima haka na ce, gashi jiya sai da na yi order wasu laceses ɗin wajen 50pcs.” “Kai Mom, nima fa na yi nawa order ɗin kar kayan su yi yawa.”  “Senate wane kayane zasuyi yawa, kasan kuwa wa za a aurar, Senete The whole Alhaji Yunusa’s Son.” Murmushi ya yi a ran shi yana tunanin anya Mom ba ta fi shi Murna da wanan auren ba kuwa? “Me ake ta tattaunawa ne?.” Dad dake sakkowa ya faɗa. “Barka da safiya.” Senate ya faɗa yana duƙawa. “Barka Lil Son, an ta shi lafiya?.”  “Alhamdulillah Dad.”  “Ya kwnana Amarya?.” Ƙasa ya yi da kai, ya hau sosa ƙeya yana murmushi. “Kaga abinda matar minster ta aiko da shi, wai asa a lefe.” Mom ta faɗa tana nunawa Dad. “kai Ma sha Allah, an gode sosai.” Ya faɗa yana kallon kayan. “Wai yaushe ne xa a kai musu kayan?.” Mom ta tambayi Dad. “Ai wanan kuma naku ne, mu mun yi namu mun gama, sai dai ko shi Angon?.” Ta shi Senate ya yi ya fice, dan shi kunyar Dad ɗin ma yake ji.  Yana fit ya nufu gidan Yaya Karima, sai dai bai ƙara sa ba ya tuna da cewa jiya Bhatool ta ce mai an hanata komawa gidan, ga shi yana son ganinta amma yana jin kunyar Ummah.  Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 24_ Waya ya ɗauka ya kira lambar Bhatool, dai-dai lokacin da ta gama shiryawa bayan ta fito daga wankan da ta shiga, ɗaga wa ta yi tare da faɗin. “Hello, salamu alaikum.” Wani sanyi Senate ya ji cikin ransa, sai da ya rufe ido  sanan ya amsa da. “Amin wa’alaiki salam, Fulani Barka da safiya.” “Barka dai ina kwana?.”  “Lafiya kalau Alhmdlh, ya su Mama?.”  “Kowa lafiya, ya su Mom?.”  “Alhmdulillah, gani ƙofar gidan Yaya Karima zan shigon sai kuma na tuna kina gida.” Dariya ta yi sanan ta ce. “Ko zaka zo nan ɗin?.” “Ina son zuwa, amma ina jin kunyar Ummah.” “Hahaha ita Umma ɗin, bara naje na faɗa mata.”  “A’ah Fulani, ban saki ba fa.” Dawowa ta yi ta zauna sanan ta ce. “To kawai ka zo.”  “Tom Fulani, zan ɗakko Anas sai muzo kawai.”  “Ni da kai kaɗai zaka zo Allah.” Ta faɗa kaman za ta yi kuka. “Shike nan Fulanina zan zo kin ji.” Daga haka suka fanjama duniyar soyayyarsu. ~~~~~~~~Hausari Fure da Habi ne xaune sun rafka uban ta gumi, abin duniya duk ya ishe su. “Wai yanzu haka zamu zauna mu zubawa su Bhatool idanu, sun abinda suka ga dama suna ta samun duniya.” Habi ta faɗa. “Ni kinga Habi duk jikina ya mutu gaba ɗaya, jikina ya na bani kawai na je gidansu mucu arziƙi tare.”  “Eyh lallai ne asararriya, amma kin ji kunya wallahi.”  “Ba zancen jin kunya Habi, tun da sun fi mu nasara a rayuwa sai mu haƙura, faɗan da yafi ƙarfinka sai ka masshe shi wasa.”   “Kin san yaranan ‘yan iska ne wulaƙantamu za su yi, amma wallahi da sai muje kawai.” Itama Habin ta faɗa. “Ai a hankali zamu shiga jikinsu, muci arziƙi mu yi ɓulɓul ko zamu samu masu kuɗin nan kamar su.”  “Hakane kuma, yanzu kawai mu shirya muje gidan yau.”  “Ke Habi matsalal ki rawar ƙafa, mu bi a hankali mana.” Furee ta faɗa tana tunani, sai kuma can ta ce. “Mu sami kuɗi muje kasuwa mu siyo su bulugari da turmi da kujeru na katako mu kai gudumawa, sai muje da yamma kinga sai muce dare ya yi mu kwana ɗaya.”  “Gaskiyya Furee kina da lissafi, ayi hakan kawai.” “Wai Uban me kuke tattaunawa ne, kun ƙunshe a ɗaki?.” Goggo larai ta faɗa. “Bakomai Goggo muna fira ne kawai.” “Har kuna da nutsuwar yin fira yanzu, iyayen ku suna can asararru sun biyewa abun duniya, sun ba da auren Bhatool, shine ku xaku zo nan kuna wani fira.”  “To mu Gaggo mene ruwanmu a ciki?.” Habi ta faɗa. “Yoo kema ai irin uban naki ce marar hankali sha-sha-sha.”  “Bawani Goggo, mu yanzu ya za ayi ace mun zauna muna baƙin hali kamarku mu tsani mutane kuma ga shi sai samun ci gaba suke.”  Furee ma ta faɗa tana hararar Goggo laran. “Sai ku yi asararru.”  “Kema sai ki yi.” Suma suka faɗa.  ~~~~~~~Nyan’ya.  Kwalliya Bhatool ta ɗauka cikin wani arnen lace da ya matuƙar amsar jikinta, fuskanta ta sha ta ɗau light make-up. “Wai Bhatool wanan kwalliyan na mene haka?.” Ummah da ta shigo ɗakin ta tambayeta. “Baƙo zan yi.” Kallonta kawai Ummah ta yi sanan ta fice, a ranta ta na nemawa Bhatool shiriya. Sai bayan salkan Magariba Senate ya zo gidansu Bhatool, lokacin Bhatool ta cika ta yi fam, jira kawai take yazo ta sauke mai kwamdon rashin mutunchi, a ɗakIn Abdul na zaure aka sauke shi, da kayan ciye-ciye da na sha.  Yana zaune ya kafe ƙofa da idanu yana jiran shigowarta, a hankaili ta tako cikin ɗakin bakinta dauke da Sallama. Ba tare da ya jira ta gama shigowa ba ya ta shi da sauri yana faɗin. “My Amarya.” Ƙasa ta yi da kanta a karo na farko da ta ji tana kunyar haɗa ido da Senate, xama ta yi kan abun zama daga ɗan nesa da shi sanan ta ce. “Ina yini.”  “Lafiya kalau Fulani Amarya.” Murmushi ta yi kafin ta ce. “Yasu Momy.”  “Kowa lafiya kalau, Momy anyi bixi shirye-shiryen biki.” Shiru ta yi bata iya cewa komai ba, sai shi Senate ɗin ke ta zuba, ya kamo wancan xancen ya kamo wancan. Ya daɗe sosai kafin sukayi sallama ya tafi bayan ta gaisa da Ummah.  A cikin yan kwanaki aka ci gaba da shirye-shiryen biki, ƙawayen Mom sun yi matukar kokari da kara, sun haɗa akwati 36 sanan abokan Senate sun haɗu nasu 12 wayanda suma suke maƙil da kayayyaki masu tsada, ganin haka yasa Dad ya ƙara cika wasu biyan da manyan laces masu tsada daya kuma da manyan shaddoji, baya ga mukullin mota ƙirar GLK da ya sa a cikin kayan, kallo ɗaya zaka yi wa kayan kasan ankashe masu gidan rana, komai very Expensive su kansu akwatunan masu tsada ne sosai baya ga kayan da suke ciki.  An sanar da su Bhatool ranar da za a kawo kayan, hakan yasa Abdul da Yaya karima suka saki kuɗaɗe wajen yin abinda suma zasu fita kunya, duk da basu san adadin kayan da za a kawo ba amma dai sun san manyan mutane zasu kawo kayan. Haka bangaren Bhatool da ƙawayenta sun shiga hada hada na hidima, duk da Bhatool ta daina zuwa makarata, amma su kanzo gidansu ayi shirye-shirye, sun he gidan Suhaima sau ɗaya ita ka ɗai ce fitar da ta yi, kuma Senate ya kai ta da ddare yazo ya dauke ta, Jannah da Amrah dai kullum sai sun zo, Amrah ce a matsayin babbar ƙawa, ita ke fitar da kowwnne bayanai a social media, gaba ɗaya Yobe State ta ɗauka Maganar auren Senate da Bhatool.  Yau ta kama ranar da xa a kawo kayan lefen, tun safe ake gyaran gida da sauran abubuwa, duk wwni Abu da za a ci ko a bawa masu kawo Kaya Abdul da Yaya Karima ne suka ɗauki nauyi, kuma order su kayi, Ummah na zaune tsakar gida bayan ta gama turaren huta ta ji anyi Sallama, ba ta gama tantance mai Sallanar ba ta ga Hari da Furee sun shigo.   Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 25_ Hannusu rike da ƙaramin bakko, da mamaki sosai take kallonsu har suka karasa shigowa,har ƙasa suka tsugguna tare da faɗin. “Ummah ina kwana?.” “Lafiya lau, ya mutan gidan?.” “Alhamdulilah Ummah, mun zo ne a amshi kayan Bhatool da mu a matsayinta na yar uwarmu” murmushi Umma ta yi sanan ta ce. “Sannunku da zuwa, ko shigo ciki.” Bhatool dake ɗaki ce ta ce. “Ubam wa ya gayyace su, wallahi sai sun koma mumafukai.”  “Kar ki fara Bhatool wallahi.” Yaya Karima ta tare ta. “Yaya idan ba munafunci ba mai ya kawo su?.”  “Ko ma munafuncin ne mene a ciki, ai sai ka kai za ayi maka munafunci, ke kina musu ne?.”  “Me zai sai na yi musu munafunci, sai ka ce mara aikim yi?.” “To kinga ke kenan kin kai su yi miki, dan Allah idan sun shigo karki yi musu rashin kirki.”  “In sha Allah.” Bhatool ta faɗa, sai kuma can ta ce. “Yaya yanxu nan zan zauna har su su zo.”  “A’a, zai dai ki shirya ku je gidansu Na’ima idan sun buƙaci ganinki sai a kiraku.”  “Okay, daman Amrah ta ce mun tana hanya ma.”  “Yawww to, Allah ya kawo ta.” Yaya Karima ta faɗa dai dai lokacin da su Furee da Hari suka shigo, da mutunchi Yaya Karima ta karbesu haka ma Bhatool ɗin, faran-faran a kawo musu abinci da na sha, suma kuma suka miƙe aka shiga aiki da su har zuwa lokacin da Amrah ta zo, Jannah ba ta sami zuwa ba. Ko da a ka ce su tafi gidansu Na’ima sai Amrah ta ce ita zata tsaya ta yi bidiyon shigowa da kayan ne.  Shigarsu gidansu Na’ima kenan Senate ya kira wayarta. “Hello Fulani.”  “Na’am.” Ta faɗa a hankali. “Sun isu?.”  “Bansaniba, yanzu na fito daga gidan.”  “Ina zaki kuma?.” Murmushi ta yi sanan ta ce. “Kasuwa.”  “Wane kasuwa kuma, me zaki yi.”  “Abu zan siyo.” Ta faɗa tana kunshe dariyarta. “Wai dagaske kike.”  “Dagaske mana ranka ya daɗe.”  “Gaskiyya ban yarda ba ki dawo.” Dariya ta yi sanan ta ce. “Gidansu Na’ima fa na shiga, kasan dai ba a zuwa a sami mata a gidansu indai ba babban gida suke ba.”  “Auh, har na ji daɗi amma sun yi delay fa.”  “Na ji hayaniya kaman sune suka iso.”  Ƙarar guɗa ce ta cika ko ina, kamar anan gidansu Na’ima akeyi domin mutanen unguwa gaba ɗaya su ka fito domin yi wa Mama kara kasancewarta mutuniyar kirki a unguwan, Furee ce ta ce. “Kunga bara dai na leƙa.” Ba ta jira cewar su ba ta fita, motoci ne sunfi guda goma, sanan kuma ga wata katuwar mota irin a kuri kurar nan, guda biyu cike maƙil da akwatuna baki sake mutane ke kallon motocin, har aka fara suke kayan, manyan mata suka fara fitowa cike har da matar minista, masu bidiyo sai dauka suke suna ɗorawa live cikin ƙanƙanin lokaci Live ya zaga ko ina, dakin da Mama ta ajiye na tarbar baki da kayan lefe ya cika maƙil da kaya hakan yasa Anty Asabe kawar Mama ta ce. “Ku fito da kayan waje kawai, su shiga ciki.” Hakam a ka yi suka shiga fito da kayan, manyan matan sun saki jiki babu ƙyama ko wani abu, haka su ka zauna falo suna ta gaisawa da maƙwaftan Mama, haka aka kawo musu kayyyakin da a aka yi order ɓasu yawa, hakanan suka buɗe suka fara cin abinda za su ci, daya cikinsu ta ce. “Akawo mana Amaryar mana.”  Yaya Karima ce ta kalli Amrah da ke tsaye tana ta faman daukan hotona ta ce. “Amrah kuje ku shigo da ƙawarki.” “Tom Yaya.” Ta faɗa tare da ajiye wayar ta fita zuwa gidansu Na’ima. “Ke ƙawatah kin gama yin goshi, akwati hamsin fa.” Amrah ta faɗa bayan ta shigo. “Yoo aini na aza arba’in ne ma.” Furee ta faɗa. “Hamsim ne cif, ki taso suna nemanki zasu tafi.” Tsuke fuska ta yi sanam ta ce. “Yamzu dole sai naje.”  “Idan bazakije ba, ni sai na rufe fuskana na je.” Amrah ta faɗa. Mikeww Bhatool ta yi suka rufa mata baya zuwa gidan, lokacin kowa ya fito daga dakin anbarsu su ka dai, makwaftan nata santin yawan kayan da aka kawo wa Bhatool. “Ki shiga ku gaisa.” Yaya Karima ta faɗa bayan su Bhatool sun shigo. “Tom.” Ta faɗa tare da shigewa ciki, Amrah ta bi bayanta. A hankali ta taka ciki, bakimta dauke da sallama, wanda suka amsa kowacce baki washe da fara’a. “ ina yininku?.”  “Lafiya kalau Amarya.” Suka amsa baki daya. “Buɗe mana fuskar mana.” Daya cikimsu ta faɗa, ido Bhatool ta kai kanta kana ganinta kaga Mom. “Da alama ita ce ƙanwar Mom, Maman Anas.” Bhatool ta faɗa a ranta, sanan ta kai hannu ta buɗe fuskar, dukkansu sun yaba da kyan Bhatool a ransu, haka kuma da irin tarbar da Mama ta yi musu, sai da suka dan jima sanan suka ce. “To zamu huce, kamar yadda lissafi yake saura kwama goma sha biyu tariyar, amma evennts ɗinmu saura kwana biyar In sha Allah mu fara.” wanan mai kama da Mom ta faɗa. Yaya Karima ce ta ce. “To Allah ya nuna mana.”  “Amin ya Allah.” Suka faɗa tare da ta shi suna ficewa. “Ya sunanki.” Wacce ta yi mgana ɗazu ta faɗa tana kallon Amrah. “Sunana Amrah.”  “Amarah Allah ya yi albarka, Bhatool nice Maman Anas.” Murmushi Bhatool ta yi sanan ta ce. “Aina gane ki kam.” Myrmushi matar ta yi sanan suka fice da tawagarsu, bayan sun fita ne aka hau duna kaya ta ko ina, tun ana lissafa yawan atamfofi amma tun da aka zo kala ɗari biyu da hamsin kowa ya gaji, ƙarshe dai ansami atamfofo kala dari uku da goma, laces kala ɗari da hamsin, manyan shaddoji kala saba’in materials masu kyau da tsada kala talatin, dogayen riguna kala dari da goma sai kuma sauran kayyaki, ga Gold da kuna mukkullin mota.  Cikin yan awanni zamce ya karaɗe media, kowa kiran Bhatool yake yana ta ya ta murna, haka shima Senate ko ina taya murna ne, wasu ma na cewa zasu daukar masa nauyin events kasancwwar shi na Mutane, yana da yawan taimako ko mai kuɗinka cikim abokansa, in dai yaji zakayi aure sai ya daukar maka nauyin wani abu mai girma, haka Mom wasu ƙawayen nata sai waya suka mata wai bata kyauta musu ba, Aminyarta Hajiya Shuwa ma cewa ta yi, Ajira na ta lefen yana zuwa gobe, gaba daya gida ya kacame ya rikice.  “Bhatool, ya zamu yi da zancen ashobe ne wai events nawa za ayi?.” Kallon Jannah da Amarh dake zaune ta yi sanan ta ce. “Wallahi nima bansaniba.”  “To ai ba a haka daya zaki haɗa da shj Senate ɗin ya haɗa ta da abokinsa a tsara komai, kina ji events ɗin fa saura gaba daya kwana 12 yanzu.”  Amrah ta faɗa. “Hakane kam, amma Amrah sai dai ta haɗaki da abokin nasa gaskiyya, domin kinfi deserving komai you’re a good friend.” Jannah ta faɗa, domin ita kanta tana sarawa Amrah bisa yanda ta jajjirce a lamarin bikin Bhatool. “Eyh hakane, bara na kira shi ko.” Bhatool ta faɗa dai-dai lokacin da Habi ta shigo, hannun ta rike da plast. “Gashi Bhatool.” Amsa ta yi sanan ta ce. “Ni wanan masifa ta fara isata wallahi.” Dariya suka yi baki daya sanan Habi ta ce. “Bara naje naƙarasa aikina, yanzu sai kiji baƙi tun da yanzu mu bama rasa baƙi.”  “Ai Bhatool ta jawo jama’a.” Jannah ta faɗa tana dariya, sai da Habi ta fice sanan Amrah ta ce. “Wai wayanan zaman me suke yi basu tafi ba, basu ne marasa mutuncin nan ba?.” Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce.” Ai sun canja wallahi, kuma Mama ce ta ce kawai su zauna har biki, jiya ta ce da Yaya Karima idan abun arzikin ta dore ai sai ta riƙesu kafin suma su yi aure, kinsan Furee bazawara ce to naji ma ta ce ita karatu take son komawa.”  “Ai kam dai Mama ta kyauta wallahi.” In ji Jannah ita dai Amrah ba ta ce komai ba kiran Senate ya shigo,bayan sun gaisa ne ta ce. “Annur wai su Amrah ne ke tambayar Events ɗin sabida muna son fito da Ashobe.”  “Hakane Fulani, dazu mun yi magana da Mom ta ce ita dai nata events ɗin na kanta guda uku ne, sanan ƙawayenki gaba daya mutum sha biyar ake so, akwai Ashobe din da aka tanadar musu na dukka events ɗin, za aka wo su gida ko zuwa gobe, sauran kuma bansan yadda za ayi ba, mu guda nawa zamuyi?.” Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 26_ “Ni gaskiyya bansan nawa za ayi ba, kai nawa kake so?.” “Ina da abinda nake so ne bayan wanda kike si Fulani.” “Zan iya shawara ko?.” Dariya ya yi sanan ya ce. “Ki yu shawarar ki, zuwa Anjima zamu zo ni da su Anas gaba dayanmu, sai ki kara su Amrah.”  “Tom Annur, Allah ya kawo ku lafiya.”  “Amin Fulaninah.” “Shegiya soyayya, Allah ka aurar damu.” Jannah ta faɗa, dariya suka yi baki daya  sanan Amrah ta ce. “Fulanin Annur, ya aka yi?.”  “Ya ce Events din Mom guda uku ne, kuma ƙawayena sha biyar ake so, duk ashobe da kayan da zansa za a akwo su yau zuwa gobe.” Wata uwar guɗa Jannah ta saki sanan ta ce. “Kaji masu yi dan Allah.”  “Ke banza ki bari muƙarasa ji.” Amarah ra faɗa, sanan ta ce. “Naki fa.”  “Ya ce wai guda nawa muke so, muyi shawara.”  “To yanzu dai Bhatool ai inaga baki da ƙawaye sama da sha biyar ko?.” Jannah ta faɗa. “To ai ko sunfi sha biyar ɗin cire su za ayi.” Amrah ta faɗa. “Kunga dangin Abba za a dauki Furee da Habi, dangin Mama akwai guda uku, sai kuma Na’ima da wata Rukayya yan nan unguwar.”  “Bakwai.” In ji Jannah. “Wai shikenan?.” Amrah ta faɗa. “Gaskiyya su nake tunanin xan iya sawa a harkar bikina, sai dai ko wata fauziya dake kusa da gidan Yaya Karima.”  “A’a ƙyale ta, ni su Furee din ma da an ciresu.”  “Ke Amrah gaskiyya abarsu, ni wallahi Bhatool kin burgeni da kika sunansu, yanzu ragowar takwas din sai a haɗa, idan ansami extra sai asa Fauziya ɗin ko?.”  “Ta ina za a sami extra?.” Amrah ta sake faɗa. “Ke jarabar duniya, yanzu ya zamu yi da bakwai.”  “Nima ai kallonta kawai nake.” Bhatool ta faɗa. “Dalla malamai, ko a makaranta biyar sun fita, sabida ina so mu bayar a cikin team din su Hafsa alƙali, kinsan idan muka bayar muka ce Free Ashobe wallahi zasu je kuma kinga su biyar ne, muka bawa biyu ai sai mun haɗasu faɗa.”  “Mene ribar mu dan mun haɗa su faɗa, mu bar su suje da muguwar aniyarsu ko banza yanzu cikinmu biyu sun yi aure, kuma sauran biyun ma in Allah yayarda muna hanya.” Jannah ta faɗa. “Idan ma za a bayar a cikinsu Fadila za a bawa ita kaɗai muke mutuncin da ita, har a waya ta kirani jiya, amma wallahi sauran babu shegiyar da zan bawa dan ubansu.” Bhatool ta faɗa. “To yanzu dai kinga Amrah ke, Sai ni, sai kuma Suhaima, sai Fadila, to asa Fauziya ɗin, biyar kenan.”  “Kun manta da su Lawisa?.” Amrah fa faɗa, dariya sukayi sanam Jannah ta ce. “Aikuwa da muncika butulu, bikin Labiba mukaje har aka ce munfi kyau a akan su namu kuma mu manta da su.” Dariya suka sake yi sanan suka yanke shawara. “Yanzu bara naje na ji yadda zamuyi da Mama akan nata event ɗin sai mu tsayar da namu ko?.” Bhatool ta faɗa tana mikewa.  “Ke Bhatool fita idona, babu wani event da zan yi.”  “Haba Mama,gaskiyya a’a ko daya ne ki yi.”  “Zaki mun dole ne?.” Waya Bhatool ta dauka ta kira Abdul. “Kai na ina?.” “Ina inda kika aike ni Uwata.”  “Dalla maganar serious nake maka.”  “Munfita ni da Yaya Karima, muna nan muna bauta miki kina mana iskancin, kayan gado Set uku muka siya miki wajen 7million duk jarin shago na ya ƙare.” Dariya ta yi sanan ta ce. “Ai daman danni kake fita neman dan albarka, yanzu wai Mama ce ba zata yi event ba.” “A’a wasa take miki zata yi.”  “Zaka mun dole ne.” Mama ta faɗa daga inda take. “Ni na isa Hajiya Mama, amma dai zakiyi inji babbar Yaya.”   “Zai zo ne anjima zamuyi magana yadda za a tsara komai, su za su yi guda uku shine ya tambayeni Mama fa.”  “Kece za ta yi guda ɗaya, yanzu ma zamu biya mune mi Hall.”  “Shikenan dan albarka.” Daga haka ta kashe wayarta ta ta shi zuwa ɗaki. Bayan ta yi zauna ne ta ce. “Mama daya, yanzu shi zamu fitarwa da Ashobe, sai ladies night namu ko?.”  “Eyh Bhatool, amma ba za ayi cocktail ba harda abokan Ango.” Amrah ta faɗa. “Eyh gaskiyya dai zai yi kyau, amma bara muji dame suka zo.”  ~~~~~Red bricks.  Senate ne da team din abokansa baki daya, wansa ya haɗa da Anas, Juraij, Salman, sai kuma Faruq. Senate ne ya ce. “Duk wasu events na Mama already ta gama da komai, sanan yanzu Anas ya ce zai haɗa night party da ƙawayenta, i think komai ya isa haka kar bidi’a ya yi yawa.”  Faruq ne ya ce. “Yanzu ka ta shi muje wajen nasu, a tsayar da komai ba mu da enough time fa.” Mikewa suka yi zuwa inda Mom take, itama duk ta yi busy baƙi ta ko ina, bayan sun gaisa ne ya ce. “Mom zanje gidansu Bhatool, zamu tattauna yadda events ɗin zasu kasance.”  “Okay, ita kayan da zata sa an kawo su ɗazu gaba daya, na ƙawayen na ta ne ba a kawo ba har yanzu.” Amma ga cards nam kowanne events ga 50cards nan, banda ƙawayenta masu Ashobe.”  “Okay Mom, kawo cards ɗin kayan nata idan an kawo wancan a haɗa gaba daya.”  “Okay.” Ta faɗa tare da ta shi, kallon jama’ar dake gidan ya yi, yau saura kwana goma cif Bhatool ta tare a gidansa. “Gaskiyya ina cikin alheri.” Ya faɗa yana murmushi. “Ungo sanan ka ce mata, kar su wahalal da kansu akan cards din mu na na su event ɗin, idan bai da yawa.”  “Tom Mom.” Ya faɗa tare da amsa ya fice, a waje ya sami abokan nasa kowa cikin motarsa. “Ina zamu da motoci haka kuma?.”  “Zamu raka ango ne.”  “Dan Allah kar su yi yawa, daya ma ta ishemu duka?.”  “Allah Senate A’a, kai ka shiga ta Anas amma mu duka daga nan gidajen mu zamu huce.” Juraij ya faɗa, sauran kam duk suka shige nasu motocin, ba dan ya so ba ya shiga suka tafi. A hanya ya yi mata text gasu nan sun tawo. “Kun ji gasunan sun tawo, sai mu ta shi mu gyara.” Ba musu suka ta shi suka hau shiri.  Ba daɗewa suka kara so, gaba dayansu suka zauna a barandar gidan kan kafet, bayan an cika gabansu da kayan ciye-ciye ciki har da Furee da Habi, su Amrah dai sai ƙara kame jiki ake. “Amare namu.” Anas ya faɗa yana murmushi. “Angwaye namu.” Amrah ma ta faɗa, nan suka kwashe da dariya gaba dayansu, daga nan suka shiga tattauna yadda komai zai kaya musu, har da sanye cocktail din da zasu yi da abokan ango da ƙawayen amarya, sanan suma suka ware Backlorate party da za suyi abokan Angon ranar da zasu yi ladies night, sanan Faruq ya dauki nauyin duka rogowar Ashoben ƙawayen Amarya, suka yanke matsayar gobe zasu shiga kasuwa da Jannah da Amrah su zaɓo komai, bayan sun gama ne aka bar Senate da Bhatool ya bata cards da kuma mukkin gidan sabida masu zuwa Kafi (jere), sanan ya ce zai a aiko da kayan da zata sa da na ƙawayenta zuwa gobe har da Mint (kuɗaɗen liƙi).  Sai yamma su Abdul suka dawo, lokacin duk ƙawayen Bhatool sun tafi sai su Furee da hari, komai da aka siyo ya yi kyau sosai sanan aka yanke shwarar gobe zasu a afara zuwa ayi jerin jibi kuma a ci gaba, cikin daren aka aiko da kayan nata da Ashoben ƙawayen, kuwa ya ji daɗin lissafi da ta yi mussaman da tasa Furee da Habi.  ~~~~~~Washe gari Masu kafi sun sha matukar mamakin ganin girman gidan, domin kuwa a iya part daya Bedroom uku ne, falo ya kai biyar ga maka-makan kitcehn guda biyu, hala ma daya part ɗin, Yaya karima ce ta ce. “Chaɓ, ai wallahi mu zuba abinda muke da shi.”  “Daman ai abinda za ayi kenan, kar ma asanar da wancan fitinanniyar yarinya, bare ta tayar mana da hankaki.” Anty Sailuba ƙanwar Mama sa ta zo daga Jigawa ta faɗa, suna cikin jerin ne wata motar kayan ta shigo, itama dauke da kayan gado seat biyu, kujeru seat uku, waya Yaya Karima ta dauka ta kira Abdul ta tambaye shi ko shi ya kawo, amma ya ce A’a, nan ta kira Umma ita ma ta ce A’a, Bhatool ta kira itama ta ce A’ah. “To kira mijinki ko shine?.”  “Banajin shine Yaya, ko ɗazu mun yi waya kuma bai faɗan ba.” “Kirashi dai.”  “Tom.” Ta faɗa tare da kiransa, bayan ya ɗaga ne ta ce. “Wai kai ne ka tura da kaya gida?.”  “Eyh nine Bhatool, kinsan gidan yana da girma so wanam kawai na yi sune ba tare da kowa ya sani ba, kuma banaso kowa ya sani, sanan ki faɗa musu daya part ɗin banda shi, Anty Shuwa ta dauki nauyin cika komai na shi.”  “Tom bara na faɗa musu, kayi magana da masu zuwa kasuwa?.”  “Eyh, sun ce suma hanya.”  “Okay.” Ta faɗa tare da kashe wayar ta mai da kiran na ta ga Yaya Karima. “Ai daman na yi tunanin shine.” Yaya Karima ta faɗa bayan Bhatool fa faɗa mata shine, daga haka suka ci gaba da jerensu.  Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 27_ Sai yamma su Jannah suka shigo niƙi-niƙe da kaya, wai Amrah ta huce gida ana kiranta, bayan sun yi sallah suka shiga ware na kowa da niyar washe gari za abawa mai delivery ya kai wa kowa, sai bayan takwas Faruq ya zo ya ɗauke Jannah, ita dai Bhatool har wani murmushi take dan ta fahimci kamar Faruq ya faɗa son Jannah ne, haka kawai sai kuma tausayin Amrah ya faɗo mata, kawar da tunanim ta yi baki ɗaya ta shigi hidimar dake gabanta.  Washe gari.  Da ci gaban bidirin da hada-hada kowa ya tashi, Gida gaba daya ya kacame, daga gidansu Bhatool har gidansu Senate, Yaya karima ma ta kwaso kayanta ta tawo biki, ganin rana ta yi Amrah ba ta zo ba yasa Bhatool ta kirata, sai ta sanar da ita sunje Kaduna amma suma hanye ne, baban Anty ne ya mutu kishiyar mamanta, hakan yasa Faruq da Jannah suka wakilci komai harda zuwa kai Ashobe, anan wata shaƙuwar ta ƙara shiga tsakaninsu, wani abin arziƙi da Faruq ya dinga yi duk wacce aka kaiwa Ashobe sai anɗora mata da 20k na ɗinki akai.  Amarh bata sami zuwa ba sai washe gari, wanda ana gobe za a fara gudanar da Kamun Mom, mai ƙunshi guda aka ɗakko zuwa gidan ta ke yiwa mutane, banda Bhatool da ƙawayenta da aka dakko musu wata ƙwararriya daban tana musu. Abunka da kuɗi a ranar da za afara events kowacce ta amso dinkunanta, an saki kuɗi anyi musu ɗinki masu kyau sosai da sosai.  A babban Hall na Dehall Event Centre za a gudanar da kamun yau, babban waje biki da ya amsa sunansa kaf garin Yobe, da misalin karfe 04:30 kowa da kowa ga hallara manyan mata ƙawayen Mama sun ci Ado, gwala-gwala nai ke wai ke kyalli da walwali, am warewa Mama da na tawagar nasu wajen cikin mutunchi, duk wacce ka kalla cikin kawayen Mom sai ka sake kalla, dan yadda suke walwali da adon gwala-gwala, events na ta tafiya MC na ƙara kambaba waje da zazzaƙar muryarta, da misalin karfe 06:30 sautin wajen ya canja, sakamakon shigowar Amarya Bhatool da Amgonta Senate, Bhatool na sanye cikin wani tsaddaden yadi, wanda kuɗinshi ya bawa 1million baya, sai kyalli take da gwala-gwalan dake wuyanta, fuskarta ta dau make-up da ya matukar kara fito da ita da kyanta, Senate na sanyi cikim arniyar babar rigar Getzner shadda fara, suna tafiya a hankali, bayansu kuma ƙawayen Bhatool ne, akwai tazara tsakaninsu, Murya Mc ce ta fito.  “Tauraruwar ziniyar da dukkan gari ya haɗu dominta❤️ Kowacce zuciya cikin farin ciki😻🎉, cikin soyayyah🥰, cikin ƙaunah❤️ Babu abinda ake marari, babu abinda ake so, sai ganin shigowar wanan amraya💃🎉 Cikin wani irin haske😻hasken da ya gama sararin samaniya❤️ A hasken da ya kai kamar na wata daren goma sha huɗu❤️ daren da inda turawa ke zaune suke cewa she look beautiful, sparkling like full moon. Ma sha Allah fa tabarakallah🎉ahasanil kaliƙin. Dukkan inda ka ƙure mata kallo, tun daga kan babban ɗan yatsan tafin kafarta har zuwa kanta🤭idan kana kallonan shauƙi kake ka kara kallonta🎉💃 Domin babu wani abu da zai sanya ka ji da kallon tauraruwar da asararin samaniya idam guda miliyan ne, ita kaɗai ce take hasken da kowanne haske tafi shi haske🎉🌚 Cikin irin hasken da idan allura ta faɗi a ƙasa zaka gani ba sai ka nemi abinda zaka kara haskawa da shi ba, Wanan ita ce Amarya Bhatool, matar Senate! Aka ce matar Senate ɗa ɗaya tilo wajen manyan masu kuɗin Yobe state, Senate dan gata mai iyaye, Senate dangata mai iyayi, shine angonki Bhatool💃❤️🫶💍.” Wanan shine kirarin da Mc ta bi Bhatool da shi tun daga shigowarta har zuwa mazauninta, daga nan kuma events ya fara. Komai cikin tsari ake gudanar da shi, Mc na bawa dangin amarya dama su fito, haka ma dangin Ango, ƙawayen Mom sai barin kuɗi suke mata naira da daloli, anci ansha cikin tsari sosai da sosai, ana haka ne aka zo matakin buɗar kai, lokacin da dangin Ango zasu yi wankan amarya wajen ƙawayenta, Mama dai da tawagatar suna zaune suna kallon bidi’a kala-kala.  Ba tare da wani kwana-kwana ba, ƙawayen Mom suka siya wankan Amarya naira miliyan biyu kash, daga nan aka ci gaba da biki, ango na zubawa amarya liƙi abokansa na zuba mai liƙi, haka amarya ma na zuba ƙawayenta na zuba mai, kasancewar kamu ne ba dinner ba karfe 09:00 aka ta shi daga event ɗin baki daya, kowa ya kama hanya, abokan ango suka dakko yan uwan amarya, aka huce  gida.  A gidansu Na’ima Bhatool da ƙawayenta suka sauka, ɗaki guda aka ware masu suka zauna, haka suka raba dare kowacce na waya da saurayinta, Amrah ma ta yi saurayi cikin abokan ango, wanda da alama duk abokan angon yafi su kuɗi, rafa guda na dollars ya ba ta ta yi liƙi.  Haka gidansu Senate abun sai sun barka, duk kuɗin kawayen Mom sun yaba sa tarbiya da nutsuwa irin na Mama da yan-uwata, babu hayaniya babu rawar kai, duk girma irin na gidan amma ya cika ya batse. Daga gari gari ake zuwar wa Mom, wasu ma daga wata ƙasa suka zo mata.  Shima senate part ɗin shi akwai hayaniyar mutanen, duk da dai abokansa babu wani mai kwana, Aziz da yazo daga America wanda ya bawa Amrah kuɗi.  ~~~~~Washe gari  Tun safe kowanne ɓangare suka shiga nasu hada-hadar, yau Dinner ce za ayi sai karfe takwas za a fara, hakan ya rage musu yawan abubuwa. Ragowar jeren da ba a ƙarasa jiya ba aka tafi ƙarasawa, da misalin karfe daya dai-dain aka zo daukan Bhatool da kawayenta zuwa gidan kwalliyya.  A can gidan kam, masu jeren bangaren Senate ma sunzo, haka akayi jeren ciki da mutuntawa, duk wata karramawa dangin senate sun yi, basu nuna kuɗi ko ƙyama ko wani abu ba,  har suka gama suka fito.  Yau ma karfe takwas dai dai dakin taro na Coral Garden event centre ya fara ɗiban jama’a, kowa cikin kaya na ke ce raini, kowa cikin ado na daukar ido, a haka kawayen Mom suka karaso tare da ita, Mc tana zuba musu na su kirarin, ana musu ɓarin kuɗi har suka isa mazauninsu.  A can ɓangaen Amarya suna gidan kwalliya ana ta kashe su da make-up, Jannah da Amrah ma duk a nan ake musu, Suhaima ce ma take yin abarta daga gida, Yaya karima ma wajen wata ƙwararriyar mai kwalliya ita ma taje, ta yi ɗinkuna na gaske na gani kasheni, masu kyau da tsada. Mussaman da ya zamana yau ita da Abdul ne zasu riƙo hannun Amarya su shigo da ita, duk da ba wasu gayya suke yi ba, sai bayan kwana ɗaya  za’ayi nasu event ɗin, gobe Ladies night ne, jibi kuma nasu event ɗin daga nan sai cocktail, sai kuma Event ɗin Mom na karshe wanda tun rana za a fara shi, zuwa yamma za a ta shi daga nan Amarya zata nufi gida ta shirya akaita ɗakin mijinta.  “Yanzu mukayi waya da Azez ya ce sun kama hanya fa, amma sn turu mana motoci nan.” Amrah ta faɗa. “Ni yanzu Abdul nake kira ya je ɗakko Yaya ne.” Bhatool ta faɗa tana ƙara danna wayarta. “To ki kira su Furee mana naga tare suka tafi.” Jannah ta faɗa, nan take Amrah ta kwashe da dariya sanan ta ce. “Kun san wani abu?.”  “A’a, sai kin faɗa.” “wai Jiya Furee ta yi wani saurayi da alama ma cikin yan uwansu Senate ne, yana tambyarta sunan ta sai cewa ta yi Farha.” Ai kuwa suna suka kwashe da dariya, sanan Jannah ta ce. “Allah Sarki ai ba ta ce Furee ba kam.” Dai-dai lokacin Abdul ya ɗaga wayar. “Kuna ina?.” Bhatool ta tambaye shi. “Na ɗakko su, yanzu zamu huce Hall ɗin.”  “Mama fa?.” Ta tambaya. “Mama ba zata sami zuwa ba, tun ɗazu su Ɗan-ladi da Gaggo larai suka zo suna ta faman tijara, amma su Anty zata wakilce ta kuma duk ƙawayenta zasu zo.” “Kai wayanan mutanen ba su yi ba wallahi, sai na saita musu zama.” Daga haka ta kashe wayarta. “Amrah wai masu daukan namu ba su zo ba?.”  “Kinga yanzu yake kirana.”  “To ku ku huce dan gaskiyya sai na fara zuwa gida, wai Mama ba zata zo ba, sai na ci mutuncin su Larai wallahi.”  “Bhatool ba lokaci.” Amrah ta faɗa. “Allah sai naje.” Daga haka ta fice zuwa mota, su ma su ka shiga zuwa gidansu na su, cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa gidan lokacib su na tsaka da wata sabuwar tijarar wai an basu abinci kaɗan, babu ko sallama Bhatool ta shiga cikim gidan. “Ke lafiya mai ya kawo ki?.”  “Ummah na zo ne ki shirya mu tafi.”  “Bhatool maza tafi ba lokaci.” Umma ta faɗa, kallonsu Bhatool ta yi sanan ta ce. “Me yasa Ummah.”  “Bhatool kafin ranki ya ɓaci ki shige ki tafi.”  “Tom Umma, amma dan Allah ban ruwa na sha.” Ɗaki Umma ta shiga ɗakko mata ruwan, Bhatool na ganin haka ta juya wajensu, ta kai hannu ta fisge plate din abincin sanan ta ɗauke kulan. “Ku ta shi kubar gidanan, tunda babu sisin ko ciki, mugaye azzalumai, wallahi sai nayi shari’a daku a kotun abuja.”  “Kizo ki kawo abincin nan kafin na sumar dake, mara tarbiya.” Ɗan-ladi da Iliyasu suka haɗa baki suka faɗa. “Idan da kuɗin ku a ciki sai ku ci.” Ta faɗa dai-dai lokacin da ta fice, bata ƙarasa fita ba taga almajirai waje ta juye musu, kuma gaba daya gidan babu komai sai tuwo, an basu shinkafa sun cinye sunci basu ƙoshi ba kuma ba za su ci tuwo ba, shine aka dafa musu taliya leda biyar, taji kayan haɗi ko gama zuba ta cikin faranti basuyi ba. Umma ce ta fito daga ɗaki tana cewa. “Ungo sha na maganinki.” Dai-dai lokacin Bhatool ta shigo da kula babu komai ciki. “Bhatool mene haka?.” Ummah ta faɗa. “Amma anyi tsinanniyar yarinya a duniya, yanzu kin zubar da abincin?.” Goggo larai ta faɗa. “Ai sai kunga jami’an tsaro zaku tabbatar da tsinanniya nake.”  “Wai Bhatool mene haka, me kike aikata?.” Umma ta yi mata wanan tambayar. “Umma su ta shi subar gidannan, tun da su harkar arziƙi bata kawo su waje.” “Gidanku Bhatool, ina kika kai abincin?.”  “Na bawa almajirai.”  Salati suka saki baki ɗaya, Goggo larai ta fashe da ihu tare da faɗin. “har abada bazan manta da wanan cutar da kika mun ba, wanan taliya ta ji jar miyar, taji nama, ta me star amma kika bayar, Allah wadaranki.” Su sauran ma ba su iya magana ba sabida mamki da alhini. “Bhatool fita ki bar gidannan.” Umma ta faɗa dai-dai lokacin kuma wayarta ta fara ringi, sunan Senate ne hakan yasa ta fice zuwa mota.  Ba wata doguwar tafiya suka yi na zuwa wajen bikin, lokacin kowa ya iso wajen ya shiga shida abokansa, cikin wami irin salo wanda yadauka hankali, ya karaɗe mediya domin abokansa sun yi watsin dala, sun yi watsin nera.  Ƙawayen Amarya ne a gaba, bayan yan taku sai kuma Amarya tare Yaya Karima da Abdul sun riƙe mata hannu, Mc ta yi gyaran murya ta fara maganaa.  Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 28_ “Zinariyar tana tafe a baya cikin ƙasaita, cikin isahhhhh a tare da ‘yan uwanta.  Ga aji….. ga ilimi. Ga isa da kwalliya kaman wata ɗawisu. Ga nasaba……. Duk a gurin Senate ɗinan ke kaɗai gayya. Kin kira taro an amsa, kin tara gari, garin ya haɗu gaba ɗaya.  Amasu kyawu ita ɗin mai kyawu ce ajin farko. Irin kyan da zaka ji masana na bada labarin guda ɗaya akeyi a nahiya.  Kyawunta ya kai kyawun da mutum zai bada labari, ya doki ƙirji ya ce ga mai kyawu ta iso.  Murmushinta kaɗai abun ka kalla ka ƙara kallo ne.  Murmushin da yake sanyaya zuciyar dukkan wani masoyi.  Murmushi da ko a hanya idan ka kalli murmushin nan sai ka ce wayyo Allah kalon Senate bai isheni haka ba.  A kyawu keɗin za a bada labarin kina sa kyawu.  A aminci, amintaciyace a cikin bayi.  Muna ƙarai muku lale, muna ƙarai muku marhabun, muna ƙarai muku sallama Assalamu alaikum, warahmatullahi ta ala wabarakatuhum. Yau kuma da wanan kirarin Bhatool ta ƙarasa mazauninta, Masu hoto da bidiyo sun cika wajen kamar za ayi daukan film, banda manyan wayoyi da suke ta shi wajen, daga ɓari daya adon da ƙawayen Mom su ka yi yau, ya ninka na jiya dau dari dan kamar anyi musi gorin gwala-gwalai, kowacce fantamawa take da Gwala-gwala da leshi mai tsada.  Abincin yau har ya fi na jiya, liƙin da aka yi yau ma ya fi na jiya, komai ci gaba aka samu. Sai wajen ƙarfe 12:30 na dare aka tashi, kowa ya nufi makwancinsa.  Washe gari kasancewar bawani babban events ba ne, Amarya ce zata yi da ƙawayenta shima Ango zai yi na shi daban da abokansa. Anam gida kuma Mama ta haɗa saukar alƙur’ani mai girma, haka ma ɓangaren Mom ta ɗakko manyan malamai suna sauka wasu anam gidansu, wasu kuma can gidan da amarya da ango zasu zauna.  Duk masifar su Goggo larai ds su Ilyasu sai da suka kwana gidan, abun kunya har da su mazan, sai shago aka nema musu a waje wai sun zauna a ci arzikin dan-uwansu da su, Goggo Larai tun safe take faman zuga Furee da habi, amma sunƙi sauraronta sai ma ce mata da sukeyi. “Yanzu babu ƙyashi babu hassada a tare da mu, kalli yadda mukayi ƙiba muka murmure, dan haka mu zama nan yanzu muka fara har karatun boko zamu koma, mu samu gina gobe mai kyau.”  “Eyh lallai ne asararru, to ku sani wyaanan iyayen baƙar zuciyar ba zasu taɓa son ku ba.” Goggo larai ta faɗa musu. “Ni kinga tafiyata.” Furee ta faɗa, habi ma ta ce. “Kuna cin arzikinsu kuna musu hassada.”  Haka Goggo larai taita sababi tai ta masifa, kowa kuma ya yi mata banza, har ƙanwar Mama autarsu ta ce zata ci mata mutuncin amam sauran suka hanata, wacce ita Bhatool ta gado sak a wajen rashin mutunci, basa shakkar kowa ba sa shayin kowa.  Yau a S Twinkles zasuyi Ladies night ɗin nasu, kawayen sun yi ankon baƙi ita kuma ta yi na fari sun bada style mai kyau da daukan hankali, sun yi abu a gayyacin, cike da ilimi da wayewa. Ƙarfe tara dai-dai suka ta shi abunsu.  Washe gari kuma Kamun Ummah, shima Hall ɗin da suka kama yana cikin manyan hall a garin Yobe, sun yi ƙoƙari sosai wajen abinci da tsarin wajen, sanan ƙawayen Mom da ita sun samu hallarta, an mutunta sosai sama da yanda suka yi suma, duk da suma sun yi matukar kokari, abokan amgo sun xo amma sai daga baya, Abdul da abokansa ne suka cika wajen kuma suma sun zuba liƙi, sai ga ƙawayen Bhatool da wata sabuwar al’ada wai suma sun siya wankam ango naira miliyan ɗaya, wajem da ya yi trending sosai a social media, bidiyon ya zaga ko ina tare da burge mutane, wamsa karshe ma abokan angon sai da suka bada sama da kuɗin da suka amsa.  Washe garin kuma suka yi Cockail, anan ne aka zuba biki, ango da abokansa amarya da ƙawayenta babu mafaɗi, Ashe senate taƙadirin kansa ne, sai yanzu ya sami dama har mamaki yake bawa Bhatool na irin rawar da yake yi a wajen shi da abokansa, itama Bhatool da ƙawayenta suka sha rawa abunsu.  Washe gari yakama ranar ƙarshe, Mom za ta yi nata event ɗin amma na rana uku za a ta shi a huce da amarya gidansu, su yi nasu yini kafin daukan amarya, yau ƙawayen amarya basu da anko, kowacce dress ɗin ta za ta yi, kuma iya ƙawayen amrayar ne zasu su ƙawaye da yan uwan mama suna gida suna yininsu, wasu ƙawayen ma na Bhatool gida zasu.  Tun takwas suka fita gidan kwalliya, amma ba su suka isa wajen ba sai ƙarfe ɗaya na rana. Yau komai na wajen kamar na sarauta, ga basu da algaita kayan da suka saka, ango har da rawani amaryar da alyabba, kirarin Mc ya da ce da komai na wajen.  “Wanan busar idan ba Saraki ba, ko an busa ta ba za ta hau ba.  Algaita iya algaita, busar ɗan gidan Saraki ango senate, da busar ƙasaitaciyar basarakiya zinariya abar adon yan mata.  Zinariya abun alfaharin kowa ya riƙe.  Lu’u-lu’u abun alfahari ba gidan kowa ba. Takowar da ake a gurinan, da ango ne Senate da Amarya Bhatool, da Anti Fauza matar ministan kuɗi, da Anti Shuwa ƙawar da ta zama yar uwa, da Momin Amarya momin Ango, Yau Bhatool ta zama zinariyar mata.  Lu’u-lu’u abun adon da ba kowa yake taɓa gani ba Lu’u-lu’u abun adon da kowa sai dai ya gani a addu’a.  Haka kike ko acikin al’umma.  Kainuwa ce dashen Allah.  Itace kalmar da ake kira kyawu. Idan aka kalli wasu za ace masu kyawu ne. Itako idan akace kyau, dukkan wata fassara da ake nema a duniya itace fassarar kyau.  Bata taɓa zama mai kama da model ba. Domin ita da kanta model ce. Kuma role model ce.  Idan katara mace ɗari. Guda hamsin sai tace maka Bhatool nake kwaikwayo. Dukkan ɗabi’unta cassain da takwas a cikin ɗari. Dabi’une da kowane mahaluki yake cewa yana son irinsu. A cikin mu’amala, ba kowa kake samu mai halinta ba. Idan ka kallesu a tare ka kwana kana kallo, Bhatool ne da senate.  Bazaka gaji da kallonsu ba. A cikin alfarma ta uwa. Acikim albarka uwa. A soyayya ta ‘yan uwa. A karamci irin na uba mahaifi. A haka suka rayu.  A haka aka haife su. Saboda haka dukkan rayuwarsu aminci ne cikin aminci.  Aminci da muke kara nema a yarda da amincin Allah.  Daren su Bhatool, masu algaita, sarkin busa, da sauran yan-uwa muce Allah ya kyautata makwancin mahaifin Bhatool.  Kukam da Bhatool ke riƙewa ne ya fito, da sauri Senate ya rungumeta, tun lokacin da aka fara ambatar kalamar mahaifi Bhatool ta fara zubar da hawaye, ita shikenan nata ya mutu, da yana raye haka za a dinga faɗin sunanshi tana jin daɗi, amɓa yanzu babu shi, ba ta taɓa kuka daga cikin zuciyarta ba tun rashin Abbanta ba sai yau, daga cikin zuciyarta take yin shi, tana matuƙar kaunar abbanta, amma tun tana ƙarama ya mutu.  A hankali senate ke shafa mata bayanta, har tasamu sauki daga kukan da take. Gaba ɗaya Bhatool ba ta ji daɗim event ɗin ba, mussaman da ta ƙara tunawa yau fa zata bar gidansu, zata bar Umma za ta tafi wani wajen tayi ta rayuwa a can, zama bana kwana daya ba bana biyu ba, ba irin zaman da take yi gidan Yaya Karima ba, ji tai kamar ta kwanta a ƙasa ta fashe da kuka taita burgemi a ƙasa.  A haka aka lallaɓa aka ƙarasa Senate ya dawo da ita, a lokacin gidansu ya cika maƙil, Yaya Karima ce ta tsaya a kanta ta shirya sabida Senate ya sanar da ita kukan da ta yi wajen, daga nan ta kawo mata abinci ta dole ta cusa shi, daga nan ta fito aka dinga gaisawa da yan uwa da iyaye.  Daga nan aka sake sa Bhatool a ɗaki ta hau wani shirin, bayan ta shirya aka naɗe ta cikin lafaya aka barta zaune a ɗakin ita ka dai babu kowa, su Amrah suna can tare da sauran ƙawayensu. Kuka ta fara a hankali a hankali hae ya fara nisa, sai da ta yi kusan awa guda aka shigo da Mama da Anty Abu Babar yayarsu Mama sai kuma Yaya Karima.  Anty Abu ce ta fara magana. “Bhatool! Aure wata rayuwa ce sabuwa, rayuwa mai cike da abu kala-kala, rayuwar da dole hakuri ne mahaɗin tafiyar, ba wai faɗa ko nuna zallan soyayya ba, Bhatool rayuwa ce da ake fatan dauma tare har mutuwa, kamar yadda kila ga mahiafiyarki na zaune gidan mijinta duk da baya raye, kamar yadda kika ga yayarki na xaune gidan mijinta ba tare da samun wani saɓani ba, to Bhatool duk wanda ya ce mili gidan aure gidan ba gidan hakuri ba ne ya yi miki ƙarya, duk irin daɗi da kika mace na sha a gidan mijinta akwai matsalal da take fuskanta, a rayuwa a naso a ko da yaushe ka dinga ganin alkhairin mutum fiye da sharrinsa.Bhatool ki yi hakuri, ki yi biyayya ga mijinki zaki yi nasara a rayuwa, ki ba shi sau da ƙafa.”  Gaba daya jikin Bhatool ya yi sanyi, hawaye na sauka a fuskarta ɗis-ɗis. Yaya karima ta fara magana. “Bhatool duk wacca kika ga ta ji daɗi gidan mijinta ita ta siya da kuɗinta, haka duk wacca ta sha wahala ma ita ta siya da kuɗinta.”  Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 29_ Ɗagowa Bhatool ta yi ta kalli Yaya karima, Yaya karima ta ɗaga ma ta kai sanan ta ce. “Bhatool ita ta siya, namiji da kike ganinsa Sha-sha-sha ne, duk wani fushinsa da fiffigarshi ba abakim komai ba ne, duk ta yadda kika raini shi ta haka zai ta shi, a yanzu Senate kamar ƙaramin yaro jariri ne a wajenki, yadda kika raini shi haka zai ta shi, idan kin sa ba masa da mutuntawa da girmamawa da soyayyaa da fahimtar juna to haka zai ta shi, idan akasin haka to haka zai ta shi, mussaman ke mijinki dake shiru-shiru ki riƙe shi da mutunci da karramawa, ki nuna hallarci ga mahaifiyarsa da ta zage ta tsaya tsayin daka a kanki.” Kuka Bhatool ta ci gaba da yi, Anty Abu ta ce. “Ya kamata kema kiyi mata nasiha, domin duk abinda zaki faɗa mata babu shida muhimmancin da ya kai wanan lokaci.” Kallon Bhatool Umma ta yi sanan ta ce. “Duk wanda ya ci riba a rayuwar duniya, to ya haɗa da hakuri, Bhatool ki je Allah yabada sa’a, Allah ya albarkaci rayuwar aurenki da zuri’a ta gari.” Ummah ta faɗa tana mikewa zuwa sif ɗinta. “Ga  wanan alkur’ani ne da azkhar, a kowannw yanayi kidinga tunawa da Allah, a yanayin farin ciki ko na akasin sa, ki tuna shime ya jarabce ki da wanan, kuma zai iya canja shi a ko yaushe.” Kuka mai ƙarfi ne ya ƙwacewa Bhatool, ta shiga yinsa babu ƙaƙƙautawa, babu mai rarrashin ta ko hanata, domin Yaya karima ma nata kukan take, haka Umma ma ta shiga matse na ta hawayen, ta shiga Anty abu ta yi ta basu wajen.  Sai da suka dau kusan mintu goma a haka sanan Umma ta ce. “Ya isa haka, Allah ya yi muku albarka.” Tasowa Bhatool ta yi ta rungume Ummah, Yaya karima ma ta taso suka haɗe abunsu suna kuka, can sai ga Abdul nan da ta shi ƙwalal, sai da suka dau mintuna suna kukan sanan aka fara shirin tafiya da Bhatool.  Tun Bhatool na kuka ƙasa-ƙasa, har ta fara da ƙarfi. “Wayyo Umma, wayyo Allah na, Ummah ni bazan tafi ba.” Irin ihu da take yi kenan, kowa sai da ya tausayawa Bhatool amma a haka aka fice da ita xuwa gidan Mom, sai da suka kusa isa sanan ta samu ta yi shiru, sai dai tana ta sauke ajiya zuciya da shasheƙar kuka.  A haka suka ƙarasa gidan bakin ta shiru, babu abinda take sai faman tunanin Ummanta.  Wata sabuwar hidimar suka tarar gidan Mom, tarba ta mutunci a ka yi musu, sanan daga baya ƙawayen Mom suka zo suna ta yi Bhatool kyauta, kowace da abinda take bayarwa. Sai wajen ƙarfe takwas da rabi aka huce da Bhatool gidan mijinta da ke G.R.A. Gida iya ganinka ya tsaru matuƙa, duk da bai cika wani girma ba, amma kana ganin kasan namasu hannu da shuni ne. Bhatool bata ta shi kuka ba sai lokacin da ta ga kowa zai tafo yabarta har da Yaya Karima, kuka sosai take kamar wacce ke tsoron azo a sace ta ko yankata, daƙyar da sinɗin goshi aka tafi aka barta.  Tana zaune tana fama shasheƙar kuka Senate ya shigo, shi kaɗai babu abokansa dan duk sun koma daga gate, wani irin bugu yaji zuciyarsa na yi kamar ranar farko da ya fara ganin Bhatool, sai ya ji ya zama asalin Senate ɗin sa mai rauni da tausayi akan al’amuran Bhatool, wata sabuwar soyayyarsa tana shigarsa a haka ya shigo cikin ɗakin, Bhatool tsoro ya gama cika ta, mussaman da ta ji ana shigowa a hankali kuma tasan ango dai ba zai taɓa shigowa shi kaɗai ba sai da gayya. Da gudu ta saklo daga kan gadon ta rungumeshi tana kuka, a hankali ya kai hannu shima ya rungumota. Sai dai ya bari ra ɗauki lokaci tana kukan sanan ya fara rarrashinta, da ƙyar ya samu ta yi shiru……………………………………………………………………………………….. toopa, Allah ya kyauta.  ~~~~~Washe gari.  Ƙarar ƙararrawar bakin ƙofar bangaren da suke ce ta tashi Senate, a hankali ya buɗe idonsa ya sauke su kan Bhatool da ta cukwikwiyeshi, ya kusa minti biyar yana kallon kyakyawar fuskarta, kafin ya xare jikinsa a hankali ya miƙe. “Ina zaka?.” Ta faɗa cikin muryar bacci, juyowa ya yi ya kalleta idanunta a rufe. “Naji ana knocking.” Ba ta ce komai ba shima ya fice, mai gadinsu ne riƙe da ƙatoton kwandon abinci. “Ranka ya daɗe gashi.”  “Musa ya zaga dinga mana bugu da sassafe haka?.” “Ranka ya daɗe, bana so abinci ya yi sanyi ne, naga an kusa awa biyar da kawo shi ne.”  “Ƙarfe nawa yanzu.” Senate ya tambayeshi, wayarsa ya danna sanan ya ce. “Sha biyu da kwata.”  “You’re not serious.” Senate ya faɗa tare da shigewa ciki, a ran shi ya na cewa. “Garin da ko tara ba ta yi ba zaka ce wani 12:15.” dawowa ya yi ya kalli sama yaga yadda rana ta fito tas, ba shiri ya koma ciki bayan ya ajiye kwandon ya shiga cikin ɗaki. “Wifey, ta shi rana ya yi.” Buɗe idonta ta yi sanan ta ce. “Ƙarfe nawa ne?.”  “12:30.”  Ya amsa mata.  ~~~~~~~Nyan’ya.  Tun daren jiya da yan kai amarya suka dawo ake ta kuzaza gidan Amarya, kowa yana faɗin albarkacin bakinsa yana yaba gidan. Haka har gari ya waye ana ta maimaita zancen, ita dai Umma addu’a take kowa ya gama shiri a rabu lafiya ba tare da wani sabon tashin hnakalin ba, Su Amrah da Jannah sake kwana sukayi gidansu Na’ima, sai yau da safe suka shigo su ka yi wa Umma Sallama bayan sun yi breakfast, sosai Umma ta yi mus godiya tare da fatan sauka lafiya. A hankali baki kowa ya gama shiri suka fara tafiya gidajensu, kafin karfe biyu na rana gida ya zama daga Umma sai Yaya karima, sai Abdul dake shigowa yana fita.  Umma da Yaya karima na zaune suna hira, bayan sun kammala duk wani aikace-aikacensu an mayarwa sa makwafta yan kwanuka da su ka shigo cikin hidimar biki. “Ummah shikenan yanzu sai ke ka ɗai, ni dai aganina Abdul kawai ya ƙara gyara gidannan, ya yi part ɗin shi daban ya zauna.” Yaya karima ta faɗa. “Wallahi kam Karima, ni kaina duk naji wani iri da zarar kin tai shikenan.” Umma bata ƙarashe maganar ba kira ya shigo wayarta, ganin lamba babu suna ya sa ta ɗaga tana faɗin. “Kowa na samu?.” “Hello Ummah.” Muryar Bhatool ta ƙaraɗe kunnenta. “Na’am wake magana?.” Umma ta faɗa a sigar zolaya. “Haba Umma, daga kaini jiya har kin manta dani, to ‘yar da kika fi so ce.” Dariya Umma ta yi sanan ta ce. “Ƴar da nafi so ai gata a kusa dani.” Kuka Bhatool ta fara tana cewa. “Ai daman na san Umma mantawa zakiyi dani.”  “Ke ni bana son shirme, ina mai gidan naki.”  “Gashinan Umma, nabaki shi?.”  “Na shiga uku, ke wai bazakiyi hankali ba ne?.” Umma ta faɗa tana mamakin hali irin na Bhatool. “Umma to me na yi?.” “Bakomai ya aka yi ne?.” Umma ta tambayeta. “Na kirane na gaishe ki, sanan naje yaushe zaki zo?.”  “Ina hanya yanzu xan zo.” Umma ta faɗa tana jan tsaki. “Dan Allah fa, me zan dafa miki?.”  “Kai ni nagamu sa sha-sha-sha.” Umma ta faɗa tana miƙawa Yaya Karima wayar, amsa ta yi sanan ta ce. “Amarya Amarya.”  “Na’am Hajiya Yaya ya gida, ta cikin naki?.”  “Wai ni auren nan shirme ya samiki ko me?.” Shiru Bhatool ta yi, ita ba ta ga abuj faɗa ba amma sai faɗa suke, a yadda ta kwana da kewarnan tasu amma su kamar ma ba su fuskanci ba ta gidan ba. “Yaya ke yaushe zaki zo?.” Ta faɗa a hankali. “Yau dai zan koma gida, bari mu gani zuwa satin sama.”  “Kai! Yaya sai satin sama?, za fa muje Dubai a satin sama.”  “Kafin ku tafi zan zo in sha Allah.”  “To Allah yayarda, ina Abdul fa?.”  “Yanzu ya fita raka su Anty Hanya.”  “Allah sarki bara na kira shi.” Bhatool ta faɗa, daga haka suka ɗan ƙara gaiswa ta kashe wayarta, Umma ce ta ce da Yaya Karima. “Haka fa, kowacce macw rayuwarta gajeriya ce a cikin gidansu, yanzu daga haka har za’asaba.”  “Wallahi fa Umma, muma duk a haka mu ka saba.” yaya Karima ta bawa Umma amsa. “Allah dai ya dauwamarmuku da zaman lafiya a cikin gidajenku.” “Amin ya Allah Umma.” ~~~~ Bhatool kam suna kashe kiran Umma, Mom suka kira itama lokacin duk bakinta sun fara ta fiya, saura su Anty shuwa sa wayansu ƙawayenta na jiki. Bayan sun gaisa da ita suka fara kiran ƙawaye. Amrah kam tun cikin biki Maman Anas ta amshi lambarta, har wani daɗi Amrah ke ji dan tasan ƙila aure zata haɗa ta da Ɗanta ko ba Anas ba, domin ta fahimci Faruq ba saurayin aure bane, saurayin kashe kuɗi ne kuma ya ce da ita gobe zai koma ƙasar da ya fito, duk ta matso maman Anas ɗin ta kirata dan itace ta amshi lamvarta, amma da ita ma ta amshi tata tuni ta kirata ko bangajiya ne ta yi ma ta. Tana faman tunanin ne kiran Bhatool ya shigo, da fara’a ta ɗauka tana faɗin. “Amarya! amarya.”  “Amrah, ya gida ya gajiyarku?.” Bhatool ta faɗa. “Uhm, aike za a tambaya gajiya dan mu mun warware.” Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. “Kuma ai akwai taku gajiyan, yaushe xaku shigo?.”  “Ahaba dai Amarya, ai akwana biyu ko?.” Amrah ta faɗa. “A’a gaskiyya kuzo dan Allah, zamuyi tafiya ne fa.” “Ina zaku?.” Amrah ta tambaya. “Dubai.” Bhatool ta ba ta amsa. “Aha lallai ne Amara, zamu zo kowa.”  “Yawwa to sai kun zo, bara na kira Jannah, da Suhaima.”  “Okay to shi ke nan.” Daga haka Bhatool ta kashe wayar, ta kira Jannah daga nan ta kira Suhaima, ranta a ɓace da Jannah, wai dan ta ce mata zasu tafI Dubai shine zata ce wai ta dinga riƙw sirrinta, to me takw nufi da ita?. Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 30_ “Okay to shi ke nan.” Daga haka Bhatool ta kashe wayar, ta kira Jannah daga nan ta kira Suhaima, ranta a ɓace da Jannah, wai dan ta ce mata zasu tafI Dubai shine zata ce wai ta dinga riƙw sirrinta, to me take nufi da ita Mahaukaciya ko me?, Haka Bhatool tayi ta mita yinin ranar. Sai can yamma ta sake kiran Amrah, bayan sun gaisa ne ta ce. Wai Amrah kin san me?.” “Sai ki! faɗa Bhatool.” “Hhm, wai ni Janna zata ce na dinga riƙe sirrina.”  “Banganeba, wane sirri?.” Amrah ta tambaya. “Daga na ce mata zamu tafi Dubai, na ce mata na faɗamiki zan faɗawa Suhaima shine wai na riƙe sirrina.”  “To me take nufi dan ubanta, mu munafukai ne ko me?.” Amrah ta faɗa a fusace. “Oho ita ta sani.”  “Ke Nifa daman tun a biki naga kamar tana baƙin ciki, mussaman da ta yi saurayi cikin abokan Senate, sa ta wani kame gefe.” Amrah ta faɗa. “Ita ta sani, ni dai ta yi da ‘yar halak wallahi.” Bhatool ta faɗa, daha nan ta yi alƙwarin ba zata sake faɗawa Jannah abinda ya shafe ta ba tun da haka take, Amrah kuma ta yi ta famfata.  Haka Rayuwa ta fara tafiyarwa Bhatool da Senate, kullum cikin sabuwar soyayya, kullum cikin sabuwar shaƙuwa. Da ka taɓa Senate zai ce Bhatool, daka ta ɓa Bhatool za ta ce Senate ko da yaushe suna tare cikin gida, yau su yi hirar can gobe su yi ta can. Girki da aikin gida komai tare suke, yana taya ta yana mata hira, a kowacce ranar da sabuwar soyayya suke ƙara ta shi, kowa yana nisa cikin zuciyar ɗan uwansa.  “Yau tun safe Senate take ta faman yi wa Bhatool tambayoyi game da rayuwarta, ya tambayeta can, ya tambayeta can.  “To amma ranar da kika fara gani na me kika ji?.” Miƙewa ta yi sanan ta ce. “Bara na fara duba abinci na dawo?.”  “To ɗagoni mu ta shi.” Ya faɗa yana miƙo mata hannu, kama hannu ta yi ta ja amma kamar ba ta ja ba. “Kaga kawai ka tashi, ba zaka ƙarar mun da ƙarfina ba.” Dariya ya yi sanan ya ce. “Ki ɗagani dan Allah.”  “Hannu ta kai ta ƙara ja, amma me makon ya tashi sai ita ta faɗo kansa, dariya ya yi sanan ya ce. “Zauna ni zan duba.” “Ai baka isa ba, ka je ka ƙara zamɓaɗa mana maggi kaman jiya.”  “Allah ni zan duba.” Ya faɗa yana ta shi ya fice, miƙewa ta yi ta bi bayanshi tana faɗin. “Allah ka tsaya na duba, bazaka lalatamun abinci ba.” A cikin kitchen ɗin ta tarar da shi yana buɗe tukunyar, tsayawa ta yi ya buɗe ya jujuya sanan ya ce. “Ta dawo.”  “Mugani.” Ta faɗa tana ƙarasawa kusa da girkin. “Wanan ne ya dawo?.”  Ta faɗa tana karewa abincin kallon. “Ni to yunwa nake ji.” Ya faɗa fuskarshi a shagwaɓe. “Duk yunwanka ai bazaka ci ɗanye ba.”  Ficewa ya yi ya koma falo ita kuma ta rage gas ɗin sanan ta dawo falon, lokacin yana zaune yana danna waya, zama ta yi sanan ta ce. “Mun fara noticing kana bibiyamun a garden, amma Amrah ta ce muja steez ɗin mu kar muje bamu kake bibiya ba.” Dariya ya yi sanan ya ce. “To kinji so a kallo ɗaya da ake faɗa?.”  “Ni banji ba, kawai dai kyanka ya ɗauki hankalina.”  “Ni kuma kin san me?.” Girgixa kai ta yi, shi kuma ya ɗora da cewa. “Tun da na shiga gate ɗin makarantarku na ji, heart beat ɗina ya sauya, yana yi da wani ƙarfi abun har tsoro yabani fa.”  “Tsoro kuma?.” Ta tambayeshi. “Eyh tsoro.” Ya faɗa yana gyaɗa kai sanan ya ɗora da cewa. “Na dawo gida na faɗawa Mom, na ce i’m scared, su Anas su ka ce Aljanna na gani, and kinsan me ya ƙara ban tsoro?.” Girgiza kai ta yi, shi kuma ya ce. “The Next day, na fito daga gym kawai na ji heart beat ɗina ya ƙara sauyawa, direct na fito sai kawai na ganki kin shiga gidan Yaya Karima, i was like ko dai aljanna ɗin ce?.” Dariya Bhatool ta yi mussaman yanayin da ya yi magana kamar yanzu yake jin tsoron. “Dagaske fa Bhatool, son ki ya wahalal da zuciyana wallahi, fatana kawai ki yi ta sona har abada kamar yadda nake fata nima.”  “Zan soka Senate, zan so ka so na har abada, zan rayu da sonka ina fatan na mutu da sonka.” Rungumo ta ya yi jikinsa sanan ya ce. “Ina alfahari da saninki, ina alfahari dake a matsayin matata, ina godiya sosai da soyayyarki gareni Bhatool.” Sun ɗauki lokaci tare suma bayyana soyayya ga junansu kafin ƙaurin da ya fito daga kitchen ya katse musu daddaɗan yanayin dasuke ciki, ita ta tashi ta shiga kitchen ɗin bayan ‘yan mintuna ƙalilan ta fito da abinci ta kai kan dinning suka fara ci.  ~~~~~~~~Nyan’ya.  Hayaniyarsu Ɗan-ladi da ta Gaggo Larai ce ta karaɗe gidansu Bhatool. “Wallahi tun da yaran nan sunce nan zasu zauna, Larai sai an bar su.” Iliyasu ya faɗa, dan shi yana ganin ‘yarsa ta hau matakin da zata sami miji mai kuɗi, haka ma Ɗan-ladi, amma Goggo Larai ra fitike akan sai sun dawo, su kansu yaran sun ce babu inda zasu. “Ni fa ki gama abinki babu inda zani, a yanzu nakai matakin samun Addmission a kwalleji, zan zama ‘ya kamar kowa shine zaki ce na baki?.”  “To Fure ki sani dai ubanki ba zai iya biya miki kuɗin karatu ba, tun da dai kinsan karatun akwai kashe kuɗi mahaifinki kuma faƙirin talaka ne.” Goggo Larai ta faɗa, shi kan shi Iliyasu jikinsa ya yi sanyi da yaji ancw karatu. “ai mijin Karima ya ce zai dauki nauyin karatunmu shi da Abdul.” Habi ta faɗa. “Kunyi baƙar asara, kwalamammu.” Goggo larai ta faɗa, tana bakim ciki da wanan abun ita a kullum burinta ta ga ‘ya’yan Ahamd a hulakance sai ga shi yau za a ce albarkacinsu ‘ya’yan ‘yan uwanta zasu ci.   Umma dai na zaune ba ta tanka ba, ita dai Furee da Hari ba ta da matsala da zamansu kuma idan za’abar mata su tana so, amma fa bazata buɗe baki ta ce abarsu ba, duk yadda suka yanke tsakaninsu sun fi kusa. “Ɗan-ladi, kuzo mu shawarta.” Goggo Larai ta faɗa, ba musu suka bita suka yi waje. “Kunga yaranan sun fara samun abun arziƙi, a yanzu haka suna da sanari a hannu idan muka barsu nan wallahi komai aka kawo ita zasu bawa, mu muna can ɓasho, ko mazajen nasu ma sai sun fi ganin mutuncinta a kan mu, idan ko muka karɓesu komai mu za a kawo wa.” “Da ɗan gaskiyya fa a maganarki Larai.” Iliyasu ya faɗa. “Nima na fara ganin haske fa.” Ɗan-ladi shima ya faɗa. “To kumga mu ɗauke su, bakwa ganin ita munafukar ta yi shiru ƙus ta barmu muci kanmu.” Goggo larai ta sake faɗa. “Nima duk shine haushina.” Daga haka suka yanke shawarar ɗaukan ‘ya’yansu su tafi.  “Gaskiyya yanzu mun yanke shwarar tafiyar da yaran mu.” Ɗan-ladi ya faɗa. “Haba Baba Ɗan-ladi, dan Allah ku barmu mu zauna mu yi karatun nan.” Furee ta faɗa, kamar zatayi kuka. “Harira, Furaira.” Umma ta kira sunansu. “Na’am.” Suka amsa a tare. “Tun da sum takura sai kun koma to kawai ku koma ɗin, idan da rabon karatun naku sai ku yi, zan yi magana da shi Mijin Karima sai ɗauki nauyin karatun naku.” Kuka su ka fara, amma Umma ta fara ba su haƙuri har suka haɗa kayansu suka bi iyayensu.   ~~~~~~~~New bra bra.  Zaune suke kan dinning suna ci abinci, cike da soyayya senate ya bata a baki, itama ta ba shi a baki. Suna taɓa hirar sama-sama. “Bhatool.” Ya kira sunanta. “Na’am.” ta faɗa. “Kinsan ina son sunan fiye da komai?.” Murmushi ta yi sanan ta ce. “Sunan yafi daɗi a bakinka fiye da bakin kowa.”  “Daman ai bazaiyi daɗi ko ina ba, sai bakin mallakinshi.”  “Bhatool, wallahi ina sonki.”  “Wallahi nima ina sonka mijina.” Ƙarar kiran waya ne ya katse musu hirar ta su, ɗauka tai ta duba taga sunan Amrah. “Hello Amrah.” Ta faɗa bayan ta ɗaga wayar. “Na’am Bhatool, ya gida?.”  “Alhamdulillah Amrah, ya makaranta.”  “Lafiya kalau, yau zan shigo daga schll.”  “Okay, ke da Jannah?.”  “A’a ai Jannah bata shigo ba ma.”  “Okay Allah ya kawo ki.” “Amin na gode.”  Bayan ta sauke wayar ne ta ce. “Amrah ce zata zo.”  “Yau?.” Ya tambaya. “Eyh, daga makaranta.”  “Okay, Allah ya kawo ta lafiya.”  “Amin ya Allah.” Ta faɗa tare da ci gaba da cin abincin. “Kin san wanan ƙawar taki Jannah, tana da saurayi ne?.”  “A’a, wani dai cikin abokan ya ce yana sonta ko?.” Bhatool ta ba shi amsa. “Eyh, ya dage fa dagaske a yanzu so yake ya tura iyayensa aje ayi magana fa.”  “Kai Ma sha Allah! Am so happy, Allah ya tabbatar mana da alheri.” Bhatool ta faɗa a fili, a ranta kam tana mamakin yadda Jannah ta ɓoye mata komai.  Bayan sun kammala cin abincin ne ya fara shiri zai fita. “Wai ina zaka?.” “Zanje wajen Mom, sanan zanje wajen abokaina.” Haɗe fuska ta yi sanan ta ce. “Ka fara zuwa wajen abokan naka, daga nan sai kaje wajen Mom nasan ita ba zata barka ka yi dare ba, su kam babu ruwansu.” Dariya ya yi sanan ya ce. “Ko ina naje ba zanyi dare ba, in sha Allah.” “Allah yayarda.” Ta faɗa tare da tashi ta rakashi zuwa waje, ɗaya cikin tsadaddun motocin dake harabar gidan ya shiga ya fice, ita kuma ta dawo cikin gida.  Tana zaune falo tana kallon TV, gaba ɗaya gidan ya yi mata faɗi sabida babu senate a cikin gidan, so take ma ta zaga cikin gidan amma ta kasa. Wayarta ce ta fara ƙara alamun kira na shigowa, ɗagawa ta yi tare da faɗin. “Amrah kin ƙaraso ne?.”  “Eyh, na ƙaraso Bhatool.”  “Okay ina zuwa.” Bhatool ta faɗa tare da tashi, wani abu ta danna ya yi ƙara; ƙarar da ta sanar da mai gadin cewar tasan da zuwan mutumin dake waje. Ƴan mintuna kaɗan Amrah ta sake knocking ƙofar falon. “A buɗe take shigo.” Bhatooɗ ta faɗa. “Kai ni wanan gida naku tsare-tsarensa ya yi yawa.” Amrah ta faɗa bayan ta shigo ciki, dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. “Dan fa mai gadin bai ganeki ba ne, amma da ya ganeki bazai miki haka ba.”  “Bawani nan.” Amrah ta faɗa, tana zama. “Bhatool Amarya.” Amrah ta sake faɗa. “Uhm wai kin san me?.” Bhatool ta faɗa. “Faɗi ina jinki.” Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 31_ “Bawani nan.” Amrah ta faɗa, tana zama. “Bhatool Amarya.” Amrah ta sake faɗa. “Uhm wai kin san me?.” Bhatool ta faɗa. “Faɗi ina jinki.” “Wai kinsan an fara zancen neman auren Jannah, amma matarnan ko ta faɗa mana.”  “Aurenta kuna da wa?.” Amrah ta faɗa cike da mamaki, dan ita ko yau sun haɗu da Jannah a makarantar, kawai bata sam zuwa tare da ita ne. “Saurayin da ta yi a bikina, abokin Senate mana.” Bhatool ta faɗa. “Kai, amma yarinyar nan ta cika muguwar munafuka, kinga yadda take mun yanzu a makaranta?.”  “Me take yi miki?.”  “Wani iskanci-iskanci, kin san yanzu ma Suhaima bata zuwa ta fara laulayi.”  “Eyh ta faɗamun ɗazu, amma Jannah ta cika butulu.” Bhatool ta faɗa. “Ki bar shigiya in dai mune damu take zancen.”  “Wallahi Allah kam.” Bhatool ta faɗa. “Me kike da shi?.” Amrah ta tambaya. “Komai ma, muje babban kitchen.” Bhatool ta faɗa, ta shi suka yi suka nufi kitchen ɗin Amarah na ta santin gidan, kaza kawai ta gasa da dankali ta ci sun ta hira daga haka suka shiga zaga gidan, ko ina sai da suka shiga kuma ko ina sai Amrah ta ƙare musu kallo, har sai Bhatool ta gaji da ganin wajen ta yi gaba ta bar ta tana faman santi.  Haka suka gama zagaye gidan, sai yamma Amrah ta tafi ta bar Bhatool da kaɗaici.  Sai bayan magariba Senate ya dawo cikin gidan, lokacin Bhatool na zaune da waya a kunneta. “Ai ni kallonki kawa nake, ace anzo maganar aurenki bazaki faɗamana ba sai dai muji a bakin mutane.” Bhatool ta faɗa cikin wyaar. “Bawani nan, yanzu wane kinibibin ne yasaki faɗamun kuma?.” Ta faɗa bayan an bata amsa a cikin wayar, kallon ta ya yi ya shige ɗaki ita kuma ta ci gaba da wayarta abunta. “Bawani fa, bawani wallahi.” Ta sake faɗa, sai kuma can ta ce. “To Allah yasanya alheri, yaushe zaki shigo?.”   “Tom sai kinzo, sai anjima.” Ta faɗa tare da kashe wayar ta bi bayan senate, kwance ta same shi kan gado ya yi rub da ciki, idanunshi a rufe. “Sannu da zuwa.” Ta faɗa, amma shiru babu amsa, ƙarasawa ta yi sanan ta ce. “Kagaji ne, xaka yi wanka?.” Buɗe idonsa ya yi ya kalleta sanan ya ce.”kaina ke ciwo.” “Ya salam!, sannu bara na kawo ma magani.” Ta faɗa tana ta shi ta nufi Frist aid box dake falon gidan. Maganin ta dakko mai ta haɗa masa da ruwa ya sha, bayan ya sha ta ba shi waje ta dawo falo, sai dai takasa yin komai sabida ba ta saba zama ita kaɗao gidan ba, kullum ko da yaushe tana tare da shi. Yau sai take jin ta kamar marainiya, har wajen tara da rabi bai fito ba haka yasa ta tsakuri abinci iya yanda zata iya ta shigo ɗakin, yana kwamce idonsa a rufe haka ta raɓa ta kwanta. Ta daɗe a kwance kafin bacci ya dauketa.  Washe gari.  A hankali ta buɗe idonta tare da kai su ga inda Senate ke kwamce sai dai babu shi a wajen baki ɗaya, a hnakali ta ta shi tana mamakin ina ya je, toilet ta shiga ta ɗaura alwala ta fito ta yi sallah, tana idarwa ta nufi kitchen ɗaura breakfast sabida takwas ta kawo kai. Ta yi mamaki sosai ganin senate a falo yana danna wayarsa, amma sai ta kauda mamaki ta hanyar cewa. “Ina kwana?.”  “Kintashi lfy?.” Ya faɗa hankalinsa a kan wayarsa, kasa tanka masa ta yi sai hucewa da ta yi zuwa kitchen, sai dai ta kasa tsinana komai cikin kitchen ɗin sai faman tunani kala-kala. “Me kuma na yi wa senate, me ya faru da shi kuma haka?.” Ta ce wancan ta ce wancan, daƙyar dai  ta kammal tea ta soya ƙwai ta fito. Sai da taga jera kayan akan dinning sanan ta ce. “Ga Breakfast.”  “Yanzu zanje gidan Mom, zan yi acan.” Ya faɗa yana miƙewa, wata ƙwalla ce ta gangaro da fuskar Bhatool ba ta sami damar yin magana ba ya fice. “Na shiga uku ni Bhatool.” Ta faɗa tana shigewa ɗaki, wayarta ta ɗauka ta dannawa Yaya karima kira, ringi biyu ta yi ta ɗaga tare da faɗin. “Lafiya Bhatool zaki kirani da farar safiya haka?.” Cikin muryar Kuka Bhatool ta ce. “Yaya ba lafiya wallahi, Senate ya daina sona?.”  “Bangane ya daina sonki ba?.” “Yau tun da ya ta shi bai kulani ba.”  “To Bhatool ko dai kin masa laifi ne?.”  “A’a Yaya Babu abinda na masa wallahi, yanzu ma yaƙi breakfast anan wai gidan Mom za shi.”  “Ki nutsu Bhatool kin ji, idan ya dawo ki zauna ki yi magana da shi cikin ladabi da biyayya, bawai da harigido ba kin ji.”  “Tom Yaya, Allah yasa ya kulani.”  “Zai kulaki ma kin ji. Sanan ki dinga yi masa uzuri ba ko yaushe yake da son hayaniya ba.”  “Shikenan Yaya na gode.” Daga haka su ka ƙare wayr, Bhatool ta zauna ta rafka uban tagumi.  ~~~~~Red bricks  Mom da Dad na zaune kan dinning suna breakfast, Dad dai ya rasa nutsuwarsa tun ganin Umma da ya yi a cikin hidimar biki wanda yasan ita ba ta gan shi ba, a kullum Justice ne yake ƙara lallaɓashi da basho haƙuri a kan kar yaje ya same ta. Da mamaki sosai suke kallon Senate bayan sun amsa sallmar da ya yi, ba gausuwa kawai ya huce part ɗinsa ya kulle kansa, Mom ce ta kalli Dad ta ce. “Lafiyan yaronnan kuwa?.”  “Gashinan dai kamar ba lafiya.” Dad ya bata amsa, ta shi ta yi zata bi bayanshi ya riƙe ta sanan ya ce. “A’a, bar shi zuwa Anjima.” Ba dan ranta ya so ba ta dawo ta zauna. Tana cin abincin amma hankalinta gaba ɗaya yana kan Senate. “Ina faɗamiki magana fa.” Dad ya faɗa dan ya jawo hankalinta. “Sorry mema kake cewa?.” Dad ya ɗan ji ba daɗi, amma sai ya ce. “Ina faɗamiki cewa na haɗo da tsohuwar buduruwata.”  “Wace tsohuwar buduruwar kuma kake da ita ba labari?.”  “Habiba mana.” Ya bata amsa, yana faɗan sunan Habiba komai ya dawo kan Mom iri yadda ya dinga fama da soyayyar Habiba har bayan aurensu, yasu Allah ya bashi ‘ya mace ya sanya mata sunan Habiba. “Amma da idan na tambayeka cewa kake ta mutu, shi yasa kake son sanyawa ‘yar ka sunanta?.”  “Ƙwarai ada ta mutu a duniya ta amma yanzu ta sake rayuwa.”  Wani abu ne ya tokare ma Mom maƙoshi, hakan yasa ta ce. “Zaifi kyau mu ajiye wanan maganar anan, mu mayar da hankali akan ɗan mu muji mene damuwarsa.”  “Okay ni tawa damuwar ba damuwa ba ce?.”  “Bance ba, amma ina ganin kamar kai kaɗai ta dama.” Murmushi mai cike da takaici Dad ya yi, sanan ya miƙe zuwa sashensa, ita kuma Mom miƙe zuwa sashen Senate. Yana kwance yana kallon sillin ta shigo ta zauna gefen gadon. “Senate are you okay?.”  “Yes Mom, just a little headche.”  “So why don’t you even stay at your own house?, duk ka tsorata ni.” Juyowa ya yi ya kalleta sanan ya ce. “Gidan gaba daya babu daɗi, yanayin iskarshi wani kala.”  “Kai dan ka saba da nan ne amma can ai yafi nan, ya Bhatool ɗin?.” Mikeww ya yi zaune sanan ya ce. “Na barta ma tana haɗa breakfast, kawai ni banason zaman cikim gidan ne.”  “To ka kuma ofis mana, ya zancen tafiyanku?.”  “Zamuje Mom, but not recently.”  “Okay na kawo ma breakfast ne?.” “Yes Mom.” Miƙewa ta yi ta fita zuwa falon.  Dad, tun da ya shiga cikin ɗaki yake mamakin yadda Mom ta nuna rashin damuwa da al’amuransa ba, duk da cewa magana ya yi mata akan wata but atleast ya kamata ta saurareshi ko yane,yanzu kuma da zarar ya ce zai ƙara aure ta ce bai kyauta mata ba, amma ta tsaya ya bata labari su tattauna taƙi. Wayarsa ya ɗauka ya shiga nemawa kansa flight, dole zai bar ƙasar ko na wata guda ne ya samu nutsuwar zuci.  ~~~~~~New bra bra.  Tun gama wayarta da Yaya Karima ta sami waje ta zauna ta rafka uban tagumi, me ke shirin faruwa da ita kuma? Duk tsoronta kar ace Senate ba wai son ta yake ba. “Me ya kawo wanan maganar?.” Zuciyarta ta tambayeta, a fili ta ce. “Yau kwananmu nawa da aure, amma har ya canja komai.”  Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 32_ Tun gama wayarta da Yaya Karima ta sami waje ta zauna ta rafka uban tagumi, me ke shirin faruwa da ita kuma? Duk tsoronta kar ace Senate ba wai son ta yake ba. “Me ya kawo wanan maganar?.” Zuciyarta ta tambayeta, a fili ta ce. “Yau kwananmu nawa da aure, amma har ya canja komai.” Sai kuma wani ɓari na zuciyarta ya ce. “Bhatool ki yi masa uziri ko wani abu ke damunsa.” Haka ta yini fama tunani. Sai wajen ƙarfe biyar ya shigo gidan, lokacin Bhatool ta ci Kuka ta ƙoshi, ko wanka ba ta iya yi ba tun tana kiran Yaya Karima ta faɗa mata bai shigo ba, har ta gaji ta fawwalawa Allah komai.  Da sallama ya shigo cikin falon,amma Bhatool ba ta iya ɗaga kai ta kalleshi ba. “Na dawo.” Ya faɗa tare da shigewa ciki bai jira amsarta ba. “Wai ni zaman me nake a gidannan ne?, wanda ya ajiye ni ba ya ta ni; me zan zauna na yi.” Ta yi wa kanta wanan tambayar a fili, tambayar da ta doki kunnen Senate, bai fargaba ya ji ta kun ta ta shige ɗaki. Yana tsaye ya ga ta fito sanye da mayafi hankalinta ya yi waje gaba ɗaya. “Bhatool.” Ya kira sunanta, ba ta waigo ba bare ta ba shi amsa. “Ki tsaya karki fita.”  “Wallahi sai na tafi, tun da banda amfani a wajenka.” Daga haka ta buɗe ƙofa ta fita, kasan bin bayanta ya yi sai tsayawa da ya yi yana kallon hanyar da tabi ta huce. Kusan mintuna goma sanan ya fara tunanin kiran Mom, ringi ɗaya ta ɗauka tare da faɗin. “Senate lafiya dai?.”  “Mom ta tafi.” Ya faɗa kamar zai yi kuka. “Wace ta tafi?.”  “Bhatool.”  “Ta tafi ina?.”  “Gidansu wai tun da wanda ya ajiye ta baya ta ita.”  “Bangane ba ka ta ita ba, wai me ya faru a gidan naka ne?.” “Mom nima ban sani ba, kawai dai…..” sai kuma ya yi shiru. “Kawai me?.” Ta tambayeshi. “Kawai dai….” Ya sake yin shiru. “Okay yanzu ta ina?.”  “Ta fita, ta tafi gida wai.”  “Innullahi wa’inna illahir raji’un, Senate ashe baka gama hankali ba na ɗakko maka auren ‘yar mutane, mun shiga uku.” Ta faɗa tana kashe wayar, tare da faman tunanin “yanzu idan Bhatool taje gida ta ce me?, tabar wa kan ta abun magana, to amma me Senate ɗin ya yi, tabbas nima ina da laifi yazo tun safe ko karyawa bai yi ba kuma na barshi anan har yamma.” Wayarta ta ɗauka ta fara kiran Bhatool amma wayarta ba ta tafiya, daga nan ta mayar da kiran ga Yaya Karima, bayan sun gaisa ne take faɗa mata abinda Senate ɗin ya ce da ita, sai da Yaya Karima ta sauke ajiyar zuciya sanan ta ce. “Kai Bhatool ba ta ji wallahi, tun ɗazu nake faɗamata wani aikin ne ta riƙeshi amma ta kasa haƙura, bata zo nan ba amma bara na kira Umma na ji.”  “A’a turumun lambar Umman naku kawai.” Mom ta faɗa. “Okay bara na turu.” Yaya karima ta faɗa tare da kashe wayar, ta hau mita da faɗin. “Na rasa yaushe ne yarinyar nan za ta yi hankali, gaba ɗaya ko sati baki rufa ba cikin gidanki amma kin fara ficewa kice zaki tafi gida, matsalal yi wa yarinya aure a ƙanana shekaru kenan.” Tana faɗan ta turawa Mom lambar Umman, sanam ta ci gaba da kiran lambar Bhatool amma ba ta tafiya.  Umma na zaune ɗaki, wayartav ta samo ringi alamun kira na shigowa, kallo lambar ta yi ta ga babu saving a jiki a fili ta furta. “Allah yasa alheri ne.” Domin tun ɗazu take jin jikinta babu daɗi. “Hello, salamu alaikum.” Ta faɗa bayan ta ɗaga wayar. “Amin wa’alaiku salam, Maman Bhatool ina wuni?.”  “Mun yi ni lafiya?.”  “Lafiya kalau Alhmdlh, Maman Usman ce.” “Aouho, ya gida ya gajiyarmu?.”  “Gajiya ta biki jiki, yanaku?.”  “Alhamdulillah wallahi.”  “Ma sha Allah, na ce su Bhatool ba su zo ba?.” Mom ta tambaya. “A’a gaskiyya basu zo ba, lafiya dai ko?.”  “Ina fa lafiya, kin san yaran duk kansu sai addu’a, wai ya fita baisanar da ita ba, kuma bai dawo ba sai dare shine ta yi zuciya ta tawo gida.” “Na shiga uku na lalace, wai har yanzu Bhatool ba za ta yi hankali ba ne, du-du-du kwanan ta nawa da auren shine zata kwaso jiki ta tawo gida?.”  “Ki baro kawai, abune na rashin hankali, da rashin hankali.”  “Iskanci ne kawai wallahi, ba ta zo nan ba sai dai ko gidan Yayarta ta je.”  “Ai ita na fara kira ta ce ba ta zo ba.”  “To ina ga tana hanya, zan kuwa ci ubanta.”  “Ayi hakuri dai, Allah yakawo ta lafiya.”  “Amin-amin.” Umma ta faɗa. “Idan ta ƙaraso ki taɓani dan Allah.”  “Babu damuwa ngde.”  Bhatool kam na fita waje ta sami waje ta tsugunna ta fara kuka, kuka sosai da sosai take yi ɗaɗinta ma anguwar nasu babu mutane sosai, ta kusa awa guda a wajem sanan ta fara tunanin inda xata nufa. “Yanzu idan naje gida xai xama abin magana a unguwa, idan naje gidan Yaya Karima faɗa xata mun, gashi ni ba maƙwafta ba bare naje gidansu.”  Ta kusa awa biyu tana zaune ta kasa tsayar da matsayar inda zata amma kam ba zata koma gidan Senate ba tun da abun na shi hakane. “Bhatool.”  ta ji ankira sunanta, ta gane muryarsa hakan yasa ta miƙe ta fara tafiya, shi kuma ganin ta fara tafiya ya sa ya biyo ta da gudu yana faɗin. “Ki tsaya Bhatool.” Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 33_ “Bhatool ki tsaya.” Amma ta yi banza ta ci gaba da tafiya, tafiya take bata kallon gabanta shi kuma yana bin ta a baya da sauri da sauri, cikin rashin sa’a mota ta fito daga wani gida a guje kafin ka ce wani abu Bhatool ta yi sama ta dawo ƙasa, a ruɗe mai tuƙa motar ya fito yana faɗin. “Innullahi wa’ina illahir raji’un.” Dai-dai lokacin Senate ya ƙaraso yana faɗin. “Bhatool! Bhatool.” Wancan ne ya fara ƙoƙarin ɗaukan ta zai sa ta a mota, Senate ya kai masa wata mahaukaciyar cakuma sanan ya ce. “How dare you’re, karka kuskura ka ce zaka kai hannu jikin matata.”  “And so f**cking What dan tana matarka, ni na buge ta ni nake da right na kai ta asibiti.” Gayen da ya buge Bhatool ɗin ya faɗa. “You’re very stupid, bakasan abinda ake cewa mata ba?, she is my wife.”  “Bayin Allah, ba cece-kuce zaku tsaya yi ba, ku kaita asibitin baku ga halin da take ciki ba.” Wani mutumi da ya jiyo hayaniyarsu ya fito daga gidan da yake gadi ya yi musu magana, Senate ya sunkuya ya ɗauke ta shi kuma gayen ya buɗe masa motarsa, ba dan Senate ya so ba ya shiga motar suka tafi zuwa Asibiti. Kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ce babu nisa da wani makeken asibitin kuɗi, kai tsaye aka amshi Bhatool a a ɗakin gaggawa, tsyawa ya yi a bakin ɗakin yana ƙoƙarin daukan wayarsa, sai a lokacin ya tuna da cewa yabar wayar a gida. “Ya Allahu.” Ya faɗa a fili, sanan ya kai kallonsa ga gayen da ya buge Bhatool. “Me wanan Bitch ɗin yake a wajen?.” Ya tambayi kan shi, ƙarasawa ya yi inda yake sanan ya ce. “You can go.” Kallonsa ya yi sanan ya ce. “Wai kasan me na yi kuwa?, mutum na buge, rai guda ana halim rai ko rayuwa amma sabida wani banzan kishinka zaka ce i can go, to bazan tafi ba ina nan.” Tsaki Senate ya ja kawai, sana ya koma wajen da ya baro ya zauna.  Kusan mintuna ashirin suna zaman Doya da Manja, duk wanda ya kalli ɗan uwansa sai ya zabga mai harara. Likitan ne ya fito daga cikin ɗakin, a tare su ka taso su ka tare shi har suna haɗa baki wajen faɗin. “Doctor how is she?.”  “Calm down! Yanzu za’ayi payment na dubu ɗari uku, sanan jikinta yana good condition, kawai sai zazzaɓi da ciwon kai da take fama da shi, wanda yana da alaƙa da damuwar da take ciki.”  “Okay ina za’ayi payment?.” Gayen da ya buge ta ya faɗa. “No you don’t have too, matata ce zan yi da kai na.” Senate ya tare shi. “Amma ai nina bugeta, haƙƙinane.”  “Na ce karkayi.” Senate ya faɗa a tsawace. “Sir ayi haƙuri bamasom hayaniya anan, muna da marasa lafiya.” Likitan ya faɗawa Senate, sanan ya juyo ga gayen. “Tun da mijinta ya ce zai yi kabarshi, kai ka taimaka ta wani wajen.” Banza ya yi da su daga shi har Senate ɗin ta huce. “Doctor please help me with your phone.”  ~~~~~Red bricks Tun Mom na jiran kiran Senate har tagaji ta kirashi, ta yi matuƙar mamakin ganin taki kirashi bai ɗauka na, hakan yasa ta yi masa na biyu shima bai ɗaga ba, wasa-wasa sai gashi ta masa kira goma bai ɗaga ba nan-da-nan hankalinta shi ya ta shi, ta mayar da kiranta ga Anas. “Anas kuna tare da Senate?.” Ta faɗa bayan ya ɗaga wayar. “No Mom.” Ya bata amsa. “Kana ina yanzu?, je gidansa ka dubamun shi.”  “Okay Mom.” Ya faɗa tare da saita motarsa zuwa hanyar gidan Senate, dai-dai lokacin kuma Yaya Karima ta kira ta. “Karima ta zo?.”  “A’a Momi ba ta zo ba wallahi, yanzu Umma ma ta ce ba ta zo ba.”  “Innullahi me yake faruwa da yaran nan, shima kinga senate ɗin wayarshi baya ɗagawa tun ɗazu.”  “Ya salam, To ko dai naje gidan nasu nagani?.”  “Na tura Anas ya tafi.”  “Innullahi, bara natura Abdul.” Yaya karima ta faɗa sanan ta kashe wayar, ta shiga lalubar ta Abdul. Bugu ɗaya ya ɗauka da faɗin. “Yaya Karima yanzu Umma ke cemun wai Bhatool ba ta gidanta.”  “Eyh wallahi Abdul, mijinma kaga ana kiran wayarsa baya ɗagawa ko zakaje gidan nasu ne?.” “Yanzu abinda Umma ta faɗamun kenan.”  “To katashi kaje, duk yadda akayi kafaɗamun kafin ka fara faɗa mata.”  “Toh shikenan.”  Ya faɗa tare da kashe wayar, motarsa ya ɗauka ya nufi gidan Bhatool ɗin sai dai a bakin gate yaco karo da Anas, fitowa ya yi daga motarsa suka yi musabaha sanan ya ce. “Suna ciki?.”  “Basa ciki fa, yanzu ma naga wayarshi a ciki da tarin Missed calls ni ina tsorom ma faɗawa Mom.”  “Itama Bhatool ɗin wayarta tana ciki, tun da idan an kira bata ɗauka mu shiga aduba.” Abdul ya faɗa. “Okay mu shiga.”  Wayar Abdul ya fara kira tun da suka shiga gidan, can suka juyo ƙarar ta a cikin bedroom, ita ma da tarin missed calls sosai, Anas ne ya kalli Abdul sanan ya ce. “Me kake tunani?.”  “Ni wallahi duk kaina ya kulle, amma an ce Bhatool ɗin ce ta fara fita, ina tunanin shi bai yi nisa ba ya shiga Anguwa dubawa ko zai ganta.”  “To mu ta shi mu shiga Anguwan muma.” Anas ya faɗa, Abdul ya ta shi suka shiga zaga Anguwan. “Kana ganin ba zamu fara tambaya ba?.” Abdul ya faɗa ganin sun zaga Anguwan sosai. “Mu fara, amma wanan abun na Bhatool ne.” Ya faɗa yana tsugunnawa ƙasa, braclet ya ɗakko wanda yasan yaƙin da sukayi da Bhatool a kan shi. “Mu tsaya anan muyi tambaya to.” Anas ya faɗa. “Wa zamu tambaya ko ina babu mutane.”  “Bayin Allah lafiya.” Mai gadin da ya yi wa su Senate magana ɗazu ya faɗa. “Dan Allah Baba muna cigiyar ‘yan uwan mune mata da miji, yanzu anan mukaga abun hannun matar.”  “Ayyah, ɗazu macen ta tawo tana kuka shi kuma mijin na binta a baya, cikin rashin sa’a yaro ya fito daga gidan da kuke tsaye a mota ya buge matar, amma sun tafi kai ta asibiti.”  “Innullahi, Baba wani asibiti?.” Abdul ya faɗa kamar zai yi kuka. “Nima bana ce ba, amma nasan asibiti mafi kusa zasu je.”  Wanne ne mafi kusan?.” Anas ya faɗa. “Akwai wani a farkon Anguwan nan. “Abdul calm down, everything will be okay.” Anas ya faɗa ya taɓa Abdul ganin ya shiga damuwa sosai. “Bhatool fa amanace a hannuna.” Abdul ya faɗa ƙwalla na zubowa daga idonsa. “Ka yi haƙuri kazo muje mu duba.” A hankali ya fara tafiya yana bin Anas a baya har suka isa inda motar Abdul ɗin take, kasancewar ta Anas na cikin gidan. “Ina key ɗin ka?.” Anas ya tambayeshi, hannu yasa a aljihu ya fito da shi ya miƙa mai.  A hankali Anas ke jan motar, zuciyarsa cike da tunanin me ya faru da Bhatool da Senate har ya kai ga ta fito waje yana binta, a haka suka ƙarasa asibitin. “Mu fara duba emergency.” Anas ya faɗa, bayan sun fito daga motar. “Tom.” kawai Abdul ya faɗa suka nufi emergency ɗin, dai-dai lokacin da Likitan ya miƙama Senate wayar da ya tambayeshi.  “Senate!.” Anas ya kira sunanshi, juyowa Senate ya yi kalleshi a take ya miƙa ma Likitan wayar tare da cewa. “Thanks you.”  “You’re welcome.” Likitan ya faɗa tare da hucewa. “How is she?.” Abdul ya faɗawa likitan. “Tana cikin ƙoshin lafiya.” Likitan ya faɗa. “Me yasa me ta?.”  “Kai kuma mene alaƙanka da ita?.” Likitan ya tambaya, dam shi abun ya fara ɗaure masa kai, wan can ya ce mijinta ne, wan can ya ce shi ya bugeta. “Ɗan-uwanta ne na jini, yayanta ne.”  “Okay bata da wani rauni sosai, hasali ma bugewar bai wani taɓa ta ba daman dai tun farko tana cikin damuwa ne.”  “Damuwa kuma wane kala?.”  “Wanan mijinta zaka tambaya kuma.” Likitan ya ba shi amsa tare da hucewa. Waje Abdul ya samu ya zauna, dai-dai lokacin da wayarsa ta fara ringi. Sai da ya fara sai ta nutsuwarsa, sanan ya ɗaga wayar da faɗin. “Umma anganta suna tare da mijin.” Ajiyar zuciya Umma ta sauke sanan ta ce. “Kai Alhamdulillah, ba ni ita.” Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 34_ *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 34_ "Umma na fito waje zan kira ku kenan kika kira, bara na fara kiran Yaya na faɗa mata duk ta damu, sai in shiga gidan."  "Hakane kuma Abdul kira ta, Allah Ya yi muku albarka."  "Amin ya Allah Umma." Ya faɗa tare da kashe wayar, sao da ya goge ƙwallan da ta sakko daga idonsa sanan ya tafi kiran Yaya Karima, kamar jira take kiran ya shigo dan bai gama ringi va ta ɗauka. "Hello Abdul ya ake ciki?."  "Yaya angansu duka."  "Kai Alhamdulilalh, amma sai na ci uban Bhatool wallahi, duk ta wahalal damu."  "Yaya tana asibiti." Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Bangane asibiti ba, me take yi?."  "Yaya wai motane ya bige ta."  "Innullahi wa'ina illahir raji'un garin Yaya kuma, ya salam." Ta faɗa tana kuka. "Nima bans sani ba Yaya amma alamun sun nuna matsala suka samu."  "Eyh matsala suka samu tun safe ta faɗamun, yanzu wani asibiti kuke?."  "Zan tura miki live location ki duba, danni ma ban sani ba."  "Turumun yanzu, bara nasa ya kawo ni."   "Sannu bawan Allah." Abdul yaji an faɗa, ɗagowa ya yi yaga wane. "Nine na buge ƙanwarka, nazo hucewa yanzu naga kana waya."  Miƙewa Abdul ya yi sanan ya ce. "Garin ya haka ta faru ɗan-uwa?."  "Wallahi bisa tsautsayi, ta tawo da gudu ne shi kuma wan can yana binta a baya, na yi duk ƙoƙarina amma haka Allah ya ƙadddara."  "Waye yake binta kuma?."  "Wan can mana da ya ce Mijinta ne." Ya faɗa yana nuna Senate. "Eyh Mijinta ne." Abdul ya faɗa. "Gashi wanan na yi payment na duk kuɗin da suka caza, sanan na ƙara musu dubu ɗari biyu ko zasu buƙaci wani ƙarin, zaka samun lambarka anan, zan dinga taɓa akai-akai in sha Allahu, yanzu zanje ɗakko mahaifina a filin jirgi ne."  "Ayyah ka bar shi kawai, hakan ma da ka yi mun gode sosai da sosai."  "A'a baza a yi haka ba ɗan uwa, kasamun dai lambar taka sanan Sunana Ahmad." Ya faɗa yana miƙama Abdul waya, amsa ya yi ya rubuta mai lambar sanan ya ce. "Sunana Abdul."  "Na gode, Allah yabata lafiya."  "Amin ya Allah." Abdul ya faɗa.  "Kagani ko Anas, wanan gayen akwai wani abu a ransa." Senate ya faɗa yana kallonsu. "Wane abu ne a ransa wai, mutumin da ya yi muku wanan abun kake cewa haka."  "To shi Abdul ɗin mene zai kulashi, har ya ba shi lambarsa."  "Kaga Senate bazan iya da wanan abun naka ba, gaka ga Abdul ɗinan kaje ka tambayeshi mana." Anas ya faɗa yana kiran lambar Mom. "Ban ce ka yi mun rashin kunya ba." Banza dai Anas ya yi masa ya mayar da hankali ga kiran Mom, sai da ya kira sau uku sanan ta ɗauka. "Anas na yi salla ne, kun gan su."  "Eyh Mom, gamu a asibiti wai mota ta buge Bhatool ɗin."  "Ya salam! Garin ya kuma."  "Wallahi banda masaniya."  "Turamun location ɗin inda kuke, gani nan." "Tom." Ya faɗa tare da tura mata, zama suka yi jingun-jigun kusa mintuna goma sha biyar sanan Senate ya ce. "Ban card ɗinka, zan ayi payment." Miƙa mai ya yi ba tare da ya ce ko ƙala ba, shi kuma ya amsa ya huce wajen biyan kuɗin. "I'm sorry sir, your payment is already done." Abinda ma'aikaciyar wajen ta faɗa kenan. "Banagne ba, who paid it?."  "Someones named Ahamd." Ta faɗa, tsaki ya yi sanan yabar wajen ya koma ciki, lokacin Abdul ya tashi zai shigo da Yaya Karima da mijinta. "Abdul, me wan can gayen ya ce da kai?." Senate ya tambayeshi. "Nothing, kawai ya ce shi ya bugeta ya bada hakuri, sanan ya ce ya yi payment har ma da extra kuɗi ya bari."  "Mun ce mushi muna buƙata ne?."Ya faɗa a fusace. "Ƙila yaga kun yi kala da masu buƙatar ne." Abdul ɗin ya bashi amsa ya huce, tun da dai yaga ba ubansa ba ne shi dai zai zo yana mai tsawa, Senate kamar ya haɗiye zuciya haka ya ji. "Me wanna yake nufi?." Ya tambayi kan shi. "Yana jin haushinka ne, a kan abinda ya sami ƙanwarsa." Wani ɓari daga zuciyarsa ya faɗa masa. "To kuma nina ja?."Ya sake tambayar kan shi. "Ai kai ka biyo ta gudu, da kazo a nutse duk haka ba lallai ba ne ya faru." Tsaki yaja sanan ya ce. "Rubbish." Abdul kam a waje ya tarar da su Yaya Karima, kana ganin idonta zaka san ta ci Kuka ta gaji. "Ya salam Yaya mene yasaki Kuka haka?, jikin na ta fa da sauƙi.”  “Yanzu Abdul idan Umma ta ji ya za ta yi?.” yaya Karima ta faɗa. “Ai baza ta ji ba in sha Allah.”  “Kana nufin za’aɓoye mata ne?.”  “Yaya likitan fa ya ce jikinta da sauƙi, bigewan bai mata komai ba kawai ciwon kai ne kuma wai dashi ta yini, ni haushin sakaran mijin nan na ta nake ji, duk shine ya ja komai.”  “A’a Abdul, wai dan ya fita daɗe shine fa ta yi zuciya ta bar gidan.” Yaya Karima ta faɗamai. “Mitchew Sakarar yarinya.”  “Yanzu dai muje muga jikin na ta.” Barrister ya faɗa. “Ai bacci take fa, kuma tana ta shi za’a tafi da ita gida.” Abdul ya faɗa. “Gidan mijinta amma.” Yaya karima ta faɗa. “Daman Yaya gidan  mijinta, ina za’a kai ta da ya huce nan?.” Abdul ya faɗa. “Yanzu ya za ayi da Umma?.”  Yaya karima ta tambayeshi. “Ta kirani na ce mata anganta, amma yanzu zan kira ta na ce na huce anguwa.”  “Yawwa bara na fara kiranta.” Yaya Karima ta faɗa sanan suka shiga ciki, Wajen Senate ta ƙarasa shima yana ganinta ya ta so. “Senate ya jikin nata?.”  “Da sauki Alhamdulillah Yaya.” “Allah ya ba ta lafiya, ina likitan yake?.”  Nuna mata ofis ɗin ya yi, sanan ta ce. “Bara naje.” Dai dai lokacin kuma Umma ta ɗaga wayar. “Hello Ummah.”  “Na’am Karima.”  “Umma mun yi waya da Bhatool ɗin, wai bazata kiraki ba sai da safe bata so ki yi mata faɗa.”  “Aikuwa ko jibi zata kirani faɗane sai na mata, idan takama ma har gidan zan zo na ci ubanta.” “Ayi hakuri Mama, gata nan kamar ma ba ta da lfy.”  “To ta ci kuka tum safe daman ya za ayi ta yi lafiya.” “Sai da safe Umma.” “Allah ya tashe mu lafiya.” Yaya karima na sane ta katse wayar ganin ta ƙaraso ofis ɗin likitan.  Shigar Yaya karima babu daɗewa Mom ta ƙaraso asibitin, Senate na ganinta ya fara matse ƙwalla. “Kar ka yi mun kuka yanzu na tsinka maka mari a wajennan.” Mom ta katse shi. “Haba Mom, yau na sha wahala sosai.”  “Wahala ta huce wacce kajefa ‘yar mutane a ciki, sabida baka da hankali ko?.” Shiru ya yi ya shiga shafa kan shi. “Ta ina?.” “Har yanzu ba ta ta shi ba.”  “Kariman fa?.”  “Taje wajen Likita.”  “Ina ne ofis ɗin?.” Ta tambayashi, hannu ya nuna mata kamar yadda ya nunawa Yaya Karima.  “Babu wani abu da yasame ta, sanan a gwajin da muka yi ma tana ɗauke da jaririn ciki, wanda ko sati biyu bai yi ba.”  “Ciki kuka likita, yau kwanansu goma sha ɗaya da aure fa?.”  “To na ce miki cikin ko sati biyu bai yi ba.”  “Aouho hakane kuma.” Sallamar Mom ce ta katse musu maganar da suke yi da likitan, Yaya karima ce ta miƙe da faɗin. “Sannu da zuwa.”  “Yawwa Karima ya jikin na ta?.” “Da sauƙi, yanzu ma ina tambayarsa idan da yadda za ayi su tafi ba sai sun kwana anan ba, sabida wallahi Ummanmu ƙarya mukayi mata batasan suna asibiti ba.”  “To amma naji kamar ana maganar shigar ciki?.” Mom ta tambaya. “Eyh, wai tana ɗauke da cikin da bai kai sati biyu ba.”  “To Alhamdulillah, amma likita daman ana haka?.”  “Anayi ranki yadaɗe, kawai dai ba’a gwada wane a wanan lokacin shi yasa ba a gani, amma da yawa zaki ga wasu suna cika wata tara cif da aure suke haihuwa.”  “Eyh hakane kam akwai su da yawa ma.” Mom ta faɗa, Yaya Karima kuma ta ce. “Likita za ayi ɓoye musu, sabida wallahi Bhatool sai ta gayawa ƙawayenta su kuma sai sun zagaya duniya da wanan batun, cikin da ko wata bai kai ba.”  “Da gaskiyyarki kam Karima.” Mom ta faɗa. “Eyh, zaku iya amma kun san akwai abubuwa da yawa da ya kamata mai ciki ta dinga kula da su.”  “Zai a aika mata da mai aiki, sanan zan sa shi ya dinga kula da ita.”  Mom ta faɗa. “Shi ke nan hakan badamuwa.”  Legendspen  08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 35_ Sai da Bhatool ta kwashe sama da awanni uku sanan ta tashi, Yaya Karima ta gani a ɗakin ita kaɗai a hankali ta kira sunanta. "Yaya." Da sauri Yaya Karima ta ta so zuwa bakin gadon, sanan ta ce. "Bhatool, kin farka?." "Yaya ina Senate?." Ta tambaya. "Ya fita yanzu." "Waye ya bugeni?." Bhatool ta sake tambaya. "Wani ne kuma ya tafi, ya jikin naki?." "Kai ne kawai ke ciwo, zan shiga banɗaki." Kama ta Yaya Karima ta yi ta shiga da ita banɗakin, suma cikin banɗakin Senate ya shigo. "Ta tashi ne?." Ya tambaya. "Eyh ta ta shi." Yaya Karima ta ba shi amsa bayan sun fito. "Bhatool ya jikin naki?." Kau da kai ta yi ba ta bashi amsa ba, kamar ba shine abinda ta fara tambaya bayan ta tashi ba. "Ki yi hakuri kin ji." Ya faɗa kamar zai yi kuka. "Bazan ƙara ba." Ya sake faɗa, sai a lokacin ta ce. "Da sauƙi, mu tafi gida." "Tom Bhatool, amma yanxu Mom ta ce wai mu huce gidanta mu kwana biyu." Ya faɗa. "Eyh, kam hakan zaifi." In ji Yaya Karima, dai-dai lokacin Abdul ya shigo, bayansa kuma gayen da ya buge ta ne; Ahamd ya shigo. Lokaci ɗaya Senate ya haɗe rai, kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. "Bhatool kin farka?." Abdul ya tambaya. "Eyh Abdul na farka, waye wannan?." Ta faɗa tana kallon Ahamd dake bayansa. "Ina ruwanki?." Senate ya katse ta, turu baki ta yi gaba kamar za ta yi kuka. "Shine wanda ta bugeki." Abdul ya faɗa, dai-dai lokacin shi kuma ya ce. "sannu ya jikin?." "Idan zaka dinga fita da mota kana kula Malam, kawai ka bugeni." Abinda Bhatool ta faɗa kenan, murmushi ya yi sanan ya ce. "Tom in sha Allah na gode, ya jikin naki?." "Malam baka da damuwa da jikinta, as you see gashinan ta warke so leave us please." Senate ya faɗa. "A'ah Senate, mene haka kuma?." Yaya Karima ta faɗa tana mamakin Senate, mene na fushi har haka. "Komai fa da ya faru ba ni da laifi, ubangiji ne ya tsara hakan tun kafin yanzu, dan haka babu amfanin ka dinga jin haushi na."  Ahamd ya faɗa. Ta shi Senate ya yi ya fice gaba ɗaya, Anas yabi bayanshi yana mamakin wanan baƙin kishi irin na Senate. "Senate wai mene haka kake yi?." Anas ya faɗa mai bayan sun fito waje. "Anas baza ka gane ba, bana son ganinsa kwata kwata a kusa da ita." "To ai ba kusa da ita ya ke ba." Anas ya ba shi amsa. "Ya zo inda muke ma bana so wallahi, nifa Abdul ɗin ma yanzu bana son yadda yake shige mata wallahi." "To mahaukaci, ƙaninta ne dai uwa ɗaya uba ɗaya, kuma a yadda kake gani Bhatool tafi son Abdul akan kowa cikin gidansu." "Amma wanan faɗan da suke fa?." Senate ya tambaya. "To ai faɗan shine nuna soyayyar, akan Abdul; Bhatool za ta iya haƙura da rayuwa da kai." "Bakada hankali kai fa Anas." Senate ya faɗa. "Ka ga koma mene yanzu kawai mu shiga." Kama hannun sa Anas ya yi suka shiga ciki, lokacin kuma Ahmad ya juyo zai fita. "Allah Ya bata lafiya." Ahamd ɗin ya faɗawa Senate. "Amin." Ya amasa ba tare da ya kalleshi ba, Senate ya shiga Ahmad ya fita. "Mene wanan kuma kike ci?." Senate ya tambayi Bhatool. "Apple ne." "Wane ya baki?." "Ahamd ne ya kawo." "Waye kuma Ahamd?." "Wai wanan tambayar kuma na lafiya ne." Bhatool ta faɗa, Yaya Karima dai miƙewa ta yi ta basu waje, sai da ya jira ta fita sanan ya ce. "Waye Ahamd?." Kuka ta fashe da shi, tana faɗin. "Ni gaba ɗaya na yi hasashen soyayya mai kyau a gidanka, amma ban samu ba sai faɗa."  Ta shi ya yi ya dawo kusa da ita sanan ya ce. "Bhatool wane faɗa na yi miki?." "Gashinan, ka ce wannan ka ce wannan." "Bhatool ni fa mijinki ne, ina da haƙƙin tambayar ki komai." "To shi wannan ɗin da ka tambaya, wanda fa ya buge ni ne." "To Bhatool daga buge ki kuma sai ya hau kawo miki Apple kina ci." "Sha'awa ya bani fa." Ta faɗa. "Ba sai kice ni na siyo ba." "Tun da ga shi a kusa kuma mene na sai an wahalal da kai, kawai yanzu kaje wajen likitan assalamemu mu tafi gida, banason warin asibitin." "Tom." Ya faɗa tare da tashi. Sai wajen ƙarfe 12:30 na dare suka isa gidan Mom, kai tsaye sashen Senate suka nufa dan acan zasu zauna. Sai washe gari suka fito ɓangarensu Mom, kallo ɗaya Dad ya yi wa Bhatool ya gano sahibarsa a cikin ƙawayar idonta, da mamaki ya kalli Mom sanan ya ce. "Yaushe suka zo kuma?." "Nan suka kwana, Bhatool ɗin ce ba lafiya." "Ya salam! Me ke damunta." Ba ta sami zarafin bashi amsa ba su ka ƙaraso wajen. "Ina kwana Dad." Bhatooɗ ta faɗa. "Ina kwana Mom." Ta faɗa duka a tare. "Lafiya ƙalau Bhatool, ya jikin?." Mom ta faɗa, Dad kuma ya ce. "Daughter me ke damunki?." "Zazzaɓi." Senate ya faɗa. "Kunga likita ko?." Ya tamabaya. "Eyh, daga asibitin mu ka yo nan." "Okay Allah ya ƙara lafiya." "Amin Dad." "Zauna mana Bhatool." Mom ta faɗa tana nuna mata kujerar kusa da ita, zama Bhatool ta yi shi kuma ya tsaya a tsaye. "Kai kuma ba zaka zauna ba ne?." Mom ta tambaya. "Na ga ita kawai kike so." "Kai dalla ka zauna, yanzu ka girma." Mom ta faɗa, shi dai Dad bai ce komai ba, sai can ya ce. "Bhatool ya mutanen gidan naku?." "Lafiya ƙalau Dad." Ta faɗa kan ta a ƙasa. "Ma sha Allah." Daga haka suka fara cin abincin, sai bayan sun gama ne Bhatool ta miƙe za ta tashi Dad ya ce. "Ki zauna mana mu yi hira." Dawowa ta yi ta zauna. "Ba fa a hira sa surikai." Mom ta faɗa tana dariya. "To aini bana surukunta ka da ita, 'ya nake da ita." Ya faɗa yana dariya, sai kuma ya ce da Bhatool. "Mahaifinku ya yi shekara nawa da rasuwa?." Daman abinda yake so ya tambaya tun-tuni kenan yake wanan kwana-kwanar. "Tun ban kai shekara biyar ba, yanzu kuma shekarata ashirin da ɗaya." "Ya kai shekaru sha-shida kenan?. Ya faɗa yana mamakin yadda akayi wanan tsohon lokacin Habiba ba ta nemeshi ba. "Eyh, Dad." Ta faɗa. "Allah ya jiƙansa da rahama." "Amin Ya Allah." Suka amsa baki ɗayansu, daga haka ya dinga jan ta da hira sama-sama wanda duk neman bayanai ne a kan Umma. Haka zaman Bhatool da Senate ya fara tafiya gidan Mom, komai yadda ya kamata. Kulawa da Soyayya tana samu a wajen Senate kamar yadda ya fara mata a farko, babu wata matsala ko wata damuwa har ta fara mantawa da wani abu ya taɓa faruwa tsakaninsu na saɓani, Amrah ta kirata a waya ta faɗa mata ba ta da lafiya tana gidansu Senate. *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 36_ Bayan sati uku. Zaman Bhatool da Senate a gidan Mom ya daure, Bhatool ta canja ta yi kyau ta yi ƙiba, haka shima Senate ya yi ƙiba abunsa. Kasancewar a part daban suke gidan kamar gidansu su kaɗai, Jannah sun zo bayan an yi mata baiko an kuma saka lokacin aurensu, amma Amrah ba ta samu zuwa gidan Mom ba. Sai da su Bhatool su ka yi wata biyu cif a gidan Mom sanan suka fara shirin komawa gidansu, daga Bhatool ɗin har Senate babu wani dake ɗaukin komawa gidan nasu, tun da nan babu wani da su ka rasa, rayuwa suke kamar gidansu. Da yamma Senate ya dauke ta, sai da su ka fara zuwa gidan Yaya Karima su ka yi ma ta sallama sanan suka huce gida wajen Umma, Bhatool na ganin Umma ta ce sai ta kwana gidan. Sai da Umma ta yi mata jan ido sanan ta bi Mijinta suka tafi, lokacin dare ya yi sosai suna shiga gida kwanciya kawai su ka yi. Washe gari. Ko da Bhatool ta buɗe idonta ba ta sami Senate a ɗakin ba, a fili taja tsaki sannan ta ta shi ta nufi bayi ta ɗaura alwala ta yi sallah, ran ta duk a ɓace na yadda Senate ya tashi ya ƙyaleta. A daddafe ta yi sallah ta koma sabida yadda ta ji cikin ta na ma ta ƙugi alaman yunwa, ta rasa wanan cin abincin da ta ke kwana biyu na mene?, ganin har tara na kusa wucewa ya sa ta lallaɓa ta ta shi ta fito falo, ta yi matuƙar mamakim ganin senate zaune kan dinning yana breakfast, amma sai ta kawar da mamakin ta hanyar cewa. "Shine ko ka ce ma fito ko?." Banza ya yi da ita ya ci gaba da cin abincinsa, takowa ta yi zuwa wajen dinning ɗin ta fara kokarim ta ɓa plast ɗin shayin amma sai ta ji shafal kamar babu komai a ciki. "Ina nawa tea ɗin?." "Ni zan dafa miki?." Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "Wai mene haka, me na yi kuma daga safiyar?." "Kawau kin je kina wani baccin asara, baki san ki yi wa mijin girki ba, haka kika ga Mom na yi?, idan ku haka ake a gidanku mu namu gidan ba haka ba ne?." Wani irin abu Bhatool ta ji ya soketa a ƙirji. "Wai idan haka ta ga ana yi a gidansu, shi ba haka ake yi a nasu gidanba, zagin ta yake ko me, so yake ya ce ita ba ta ta so tarar da mahaifinta a raye ba ko me?." Cike da ɓacin rai ta ce. "Usman, zan juri komai, amma ba zan juri hulaƙamci da cin mutunci ba." "Did you just called me Usman?." Ya faɗa a tsawace. "Yes! Kai baka ji kunyar yi wa uwata rashin mutunci ba, sai ni zan ji kunyar kiran sunanka?." "Lallai Bhatool, ashe haka kike? Allah a fili, fir'auna a zuci, kin yi asara kuwa wallahi." "Ai idan akwai mai fuska biyu Senate bai huce kai ba, ka manta da duk irin abu da ka ce kafin ka aureni; amma duk ka watsar. A can gidan Mom ne kawai kake nuna mun kulawa ko soyayya, amma idan muna namu gidan babu komai sai hulaƙanci da cin mutunci." "Matsa ki ba ni waje kafin na tsinka miki mari anan wajen." Ya faɗa yana kauda kai. "Mari fa, da ba ƙara ba wallahi." Ta faɗa tana barin wajen, ta koma cikim ɗaki. "Wai wanan wane irim aure ne, daman haka ake zaman auren, yau fari gobe baƙi? To ni bazan iya ba." Ta faɗa tana ɗaukar wayarta. "Kawai ya sake ni na koma gidan ubana na yi zamana." Ta ƙara faɗa tana danna lambar Yaya Karima, Yaya Karima dake zaune ɗaki tana ganin kiran Bhatool sai da gabanta ya faɗi, jiki a sanyaye ta amsa wayar. "Hello Bhatool." "Na'am Yaya ina kwana?." "Lafiya kalau, ya gida, ya mai gidan." "Yaya wai daman haka ake zaman aure?." Bhatool ta tambaya ba tare da ta amsa ma ta wayancan tambayoyin ba. "Me ya faru kuma?." "Kinga na ta shi da safe na ga baya ɗakin, kuka na ji cikina yana kukan yunwa, daƙyar na iya komawa na kwanta yanzu kuma na ƙara ta shi zanje kitchen na yi girki na gan shi yana breakfast." "Ya ga kina bacci ne shi yasa bai tashe ki ba." Yaya Karima ta katse ta. "Ki bari na kai ki mana Yaya." "To na bari." Nan ta hau zayyana mata duk abinda ya faru, har da marin da ya ce zai ma ta. "Kai Bhatool mari fa, anya ba ƙarya kike ba?." "A kan mene zan masa ƙarya, wallahi Yaya dagaske na ke miki, Senate ba ya sona, idan muma gidan Mom ne yake nuna mun kulawa." "Kin san me Bhatool, abu na farko sai kin yi hakuri, sanan ki dai na mayar masa da magana, ko me ya ce ki yi hakuri ko da zaki mayar mai da amsa sao ki faɗa mai ta cikin sigar soyayya da sanyi, ba wai yana  magana da ƙarfi ba kina yi ke ma." "Ni da Yaya kawai ya sakeni." "Bhatool wai saki abun so ne?." "Ni ban sani ba, kawai dai senate bai san darajar mace ba." "Yanzu kina ji Bhatool, zamu gwada shi sau uku, idan bai tsallake ba sai na sa ya sake ki." "Amma Yaya fa ina son shi." "To yanzu Bhatool, ki bi wayanna abubuwan guda uku da zan lissafa miki, nasan shima zai dawo son ki." "Tom Yaya." "Yanzu kina ji, da farko dai ki yi mai banza kar ki kulashi, ki je kitchen ki yi breakfast ɗin ki ki ci sosai da sosai, sanan da rana ki tabbatar kin yi girki da wuri kin kai masa idan kuma bayanan ki tabbatar kin masa na dare, idan kuka zo kwanciya sai ki ba shi hakuri ki ce masa In sh Allahu hak bazai sake faruwa ba, amfanin yi mai shiru yanzu shine, zuciyarshi tana cikin fushi yanzu, amma zuwa anjima ta sakko." "Tom Yaya na gode." "Ba komai Bhatool, saura na biyu." "Tom ina jinki." "Ki tabbatar baki ƙara samun irin wanan matsalal da shi ba, duk abinda ya ce miki ki yi, to ki yi." "Shi ke nan Yaya, sai me?." "Rashin kunya, kar ki ƙara masa rashin kunya ko kiran sunansa kai tsaye." "Tom Yaya in sha Allah." "Allah yabaku zaman lafiya." "Amin mun gode." Bhatool ta faɗa tare da ta shi, ba ta same shi a falon ba da alama ma baya gidan, kitchen ta nufa ta ɗora abinda zata yi karin kummalo da shi, bayan ta gama ne ta dawo ta yi ɗan gyare-gyaren ta kafin mai aikin ta ta zo. Bayan ta gama abinda za ta yi ne ta hau online, su ka fara chatting da Amrah take tambayarta ta dawo, ta ce Eyh, nan ta ce ma ta za ta shigo daga makaranta, amma kusa fara jarrabawa. Tana zaune wajen ƙarfe uku da rabi ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta, kaman ba zata duba ba dai ta jawo wayar. Saƙone daga Senate. Ɓuɗe saƙon ta yi ta fara karantawa. "Barka da rana masoyiyah ta Bhatool, ina fatan kin wuni cikin ƙoshin lafiya, ina mai matuƙar baki haƙuri a kan abinda ya faru ɗazu, ina so na sanar miki cewa, ina sonki, ina ƙaunarki, ban san wani abu da zan yi a duniya ba inda babu ke a cikinta." Murmushi Bhatool ta yi bayan ta gama karanta saƙon, sanan ta fara mayar masa da amsa. "Nima ina sonka mijinah, ina kuma baka haƙuri akan rashin fahimtar ka da na yi, kai nake so ka kaɗai, kai ne rayuwata, kai ne farin cikinah." Take ta mayar masa da amsa, zuciyarta fari tas har ta ma manta da wani abu da ya faru, take wani ƙarin ƙarfi ya zo ma ta, ta ta shi ta shiga haɗa ma sa abincin dare. Ta kusa minti goma a kitchen ɗin tana faman tunanin me zata da fa masa, daƙyar ta iya tuno lokacin da ya ce ma ta. "Ina son dambun kus-kus, ayi shi da miyar ƙwai." Ai kuwa ba shiri ta shiga haɗa dambun kus-kus da miyar ƙwai, daga nan ta shiga haɗa masa lemon kankana, sai wajen biyar da rabi ta kamalla komai lokacin kuma Amrah ta ce da ita ta ƙaraso, sai sa ta gama kwashe komai nasa a plast sanan ta kai cikin wata warm high, ita kuma bata taɓa barin abin ciki ya yi san yi. Sanan ta bar ragowar a cikin kula, har sai da Amrah ta ƙara kiranta a kan ta gaji da jira. Bayan ta danna ƙararrawar ne masu gadin suka bar Amrah ta shigo, ita kuma Bhatool ta shiga ɗaki ta hau gyara jikinta, duk da ba ta yi wanka ba, ta bari sai darw kafin ya dawo. A kan kujera tasami Amrah zaune ta haɗe rai. "Lafiya kamar wacca aka aikoma da saƙon mutuwa?."  Bhatool ta tambayeta. "Haba wannan mistiyatan masu gadin naku mana, sun fiya iskanci wallahi." Amrah ta faɗa. "Yi hakuri Amrah." Bhatool ta faɗa tana zama. "Kema kin wani shanya mutane." "Wallahi ina ɗakine, yanzu na sauke girki ina son gyara jikina ne, da wanka ma zan shiga ma." "Eyh sai dake Amarya, kin san wai Jannah ta faɗamun an kusa kawo kuɗin ta jiya." "Sai jiya ta faɗa miki Amrah, ni fa tun ina gidan nan." "Wai me ya kai ki gidansu ne?." *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 37_ "Wai me ya kai ki gidansu ne?." Amrah ta tambyaeta. "Ke ban da lafiya fa, rashin lafiya har da kwana asibiti." Bhatool ta faɗa ma ta. "Shegiya ko dai ciki ne?." Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. "Ke dallah lokacin ko sati biyu ban yi ba." "Hakane kuma." Amrah ta faɗa. "Dalla zubamun abincin." Amrah ta sake faɗa. "Ta shi ki zuba." "A'a zubamun." Ta shi Bhatool ta yi ta shiga kitchen ɗin, 'yan mintuna kaɗan ta fito da abincin ta nufi kan dinning. "A'a kawo mun nan malama." Amrah ta tare ta, dawowa Bhatool ta yi ta ajiye kan centre table. "Ke wallahi jarabarki ta yi yawa wallahi, ya makaranta." "Alhamdulillah, mun kusa fara exam fa Bhatool." "To yanzu ni Amrah ina ruwana da exam." Bhatool ta faɗa. "Ni kam Bhatool da zaki bi shawarta ki yi exam ɗinki, wanan Neil ɗin fa kina zaune baki fara ba har ma gama waccan, yanzu da ciki zaki ce a jira ki haihu, daga haihuwa zaki ce sai kin yaye shi, a ƙalla shekara uku lokacin kam mun gama YSU." "Hakane kam, nima ina wanan tunanin amma kuma naga Senate bai son YSU." "Bai son ta kuma Bhatool?, sai dai idan ke ce kika nuna mai bakyaso har shima ya ce baya so, anam fa ya ganki kuma da kin masa magana ta fahimta wallahi zai barki, ai yana sonki ke ma kin sani, ko da a farko ya cize dakin nuna mai ke fa kina so wallahi shi ke nan zai barki." "Zan gwada ma sa magana kam, tun da fa yanzu muna yin wanan jarrabawar aji uku zamu shiga, kuma kin ga shi a frist semester duk siwess ne abun da zai zo da sauƙi." "Shine dai 'yar gari." Amrah ta faɗa ta na kai abincin bakinta. "Ke ni fa kin san me?." "Sai kin faɗa." "Bikinsu Juju za a yi fa?." "Ƴa'yan yayar Abbanku?." "Su fa shegu, Kuma kin san wani iskanci Bhatool?." "A'a sai kin faɗa." "Wai babu anko." "Dalla ai sun hutar da ku ma." "Ke Bhatool ba zaki gane ba, yanzu ai salan aga ƙure adakar mutum ne, ga shi duk kayan bikinki nagama status da su." "Au sai yanzu fa nagane, kai wayanan shegu ne Amrah." "Lamba ɗaya ma Bhatool, nifa ina ga wallahi sai dai na zo nan na ari kayanki."  Dariya Bhatool ta yi sanam ta ce. "Wallahi ki zo ki amsa, har da gwala gwala mai." "Shegiya ba zan amshi gwala-gwala bai, sun san ba nawa ba ne, ku koma su sa abini hanya a ƙwace asareni." Dariya Bhatool ta yi sanan su ka ci gaba da hirar su. Sai bayan magariba Amrah ta fara shirin tafiya, Bhatool ce ta ce. "Yau dai sai na raka ki har bakin titi, ko na samu naga anguwan?." "Wai baki taɓa fita ba?." Amrah ta tambayeta. "Sau ɗaya na ta ɓa fita, shima da daddare ne." "Gaskiyya ne agaisheki." "Yanzu yaushe zaki zo ki amshi kayan?." "Sai satin bikin." "Allah ya kaimu." Daga haka suka fice. Fitowar Bhatool bakin gate idanunta suka saukan akan Ahmad wanda ya bugeta, fuskarta cike da murmushi ta ce. "Ina yini?." "Lafiya ƙalau Bhatool, nan e gidanku kenan?." "Eyh Wallahi anan muke." "Ya jikin naki?." "Jiki da sauƙi wallahi." "To Allah ya ƙara sauƙi." "Amin Na gode." Daga haka suka huce suka barshi, sai da suka yi nisa ne Amrah ta ce. "Ke wanan fine boy ɗin fa?." Dariya Bhatool ta yi sanan ta ce. "Ke ni naga kishi wajen Senate akan wanan gayen." "Anan unguwar yake kenan?." Amrah ta tambaya. "Eyh nan yake, kwanaki ne fa na zo fita ya bugeni, shine muka je asibiti anan naga kishin senate." "Ah ba dole ya yi kishi ba." "Ke Amrah zan juya, ki gaida gida." "Toh shi ke nan Bhatool Na gode." "Aha." Bhatool ta faɗa tare da juyawa, har lokacin  Ahamd ɗin na tsaye da alama wani yake jira wajen ita dai bata ce da shi komai ba ta shige gida. Wanka ta yi ta ɗau shiri cikin doguwar rigar ta ta wani material da ta yi matuƙar yi ma ta kyau, tasan dai Senate zai ƙara awa guda kafin ya dawo, amma ta gwammaci ta yi shirintata jira shi. Tana cikin shirin ne ta je Senate na ƙwala ma ta kira. "Bhatool! Bhatool!! Bhatool!!!." A firgeci ta miƙe tana faɗin. "Lafiya?." "Ban sani ba, me wanan yake yi a ƙofar gidan nan?." "Waye?." Ta faɗa. "Bana son raini hankali, wancan Ahamd ɗin." "To ni yanzu ya za ayi nasan me ya ke yi dan Allah." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Kinsan na tsani rainin hankali fa, ki faɗamun me ya ke yi ko na ci mutunci ki." "Wallahi Senate bansaniba, ni fa ban ma san yana wajen ba." "Aouh, bakisan yana wajen ba." Ya faɗa yana ɗakko wayarsa. "Wannan bake ce ba?." Ya faɗa yana nuna mata wayar, karɓa ta yi tana kallon hoton tabbas ita ce da shi, amma bata san lokacin da aka ɗauki hoton ba da kuma dalilin da yasa aka ɗauki hoton ba. "Bake ba ce?." "Ni ce." Ta faɗa zuciyarta cike da tunani da ruɗani. "Me ya fitar dake?." Cikin inda inda ta fara magana. "Am...rah ce." "Amrah ce me, Amrah ce a hoton?." "A'a, ita ce ta zo shine na rakata." "Haka ake fita babu umarni miji, Bhatool karki raina mun hankali." Kuka ta fashe da shi ta kasa cewa komai. "Wallahi Bhatool ki kiyayeni, ku fita sabgar wancan ɗan iskan na faɗa miki, ke bakisan muhimmancin aure ba ne ko me?, sai yanzu na gama ganewa baki da wani cikakken hankali a tare da take, to wallahi zan sai ta miki zama na gaya miki." Kukanta ta ƙarawa ƙarfe, zuciyarta na mata wani irim zugi wanan abun da me ya yi kama, ita dai ita ce amma ba ta san menene amfani wannan hoton ba, sharri ne ake so ayi mata ko me. Ƙarar takunsa ta ji ya shige cikin ɗaki, ta ɗago da kai ta kalli kan dinning abincin da ta dafa. "Wanan wace irin rayuwar aure ce ni Bhatool?." Ta yi wa kanta wanan tambayar. "Komai sai cakuɗemun yake, babu farin ciki kwata-kwata." Haka tai ta faman tunane-tunane har dare ya fara yi sosai Senate bai fito ba. Ta shi ta yi ta nufi ɗaki ta ɗaura alwala ta yi sallah, sanan ta ɗaga hannu sama ya fara addu'a. "Ya ubangijin sammai da ƙassai, na kawo kuka na a gareka, ka shiga cikin al'amarin gidan Aurena, ka duba ni ka kawo mun sauƙi da mafita, Ya Allah idan da alheri a zaman aurena da Senate ka tabbatar, idan babu ka kawo karshen zaman ta hanyar da yafi sauƙi, ya Allah wannan abun da ya faru yanzu, kasan komai ban da masaniya, Ya Allah Ka kawo mun sauƙi." Haka tai ta addu'a ta ce wannan ta ce wannan. Bayan ta idar ne ta koma gefen gado ta zauna tare da rafka tagumi kamar wata marainiya marar ga ta. Can kuma shawarwarin Yaya Karima suka faɗo ma ta mussaman na bada haƙuri, ba shiri ta miƙe ta fito zuwa ɓangarensa, ta yi mamakin ganinshi kan dinning yana cin abinci, sai dai ta ji daɗi ko bakomai ba ta yi asarar lokacinta ba. Daga nan ta koma ɗaki ta zauna, zaman jiranshi ko zai shigo amma bai shigo ba har ta yi bacci. Washe gari Bhatool ta yi ƙoƙarin ta shi da huri ta haɗa ma sa breakfast, sai dai ba ta kai ga kammalawa ba ta ji ficewarsa daga gidan, kuka ne kawai ya rage Bhatool ba ta yi ba amma ta je wuya iya wuya, ta fara gajiya da Senate da abinda ya ke ma ta, idan ba ya son ta ne kawai ya hakura su rabu. (Ayi mun afuwa dan Allah, wannan week ɗin ba za ku sami Post sosai ba, amma in sha Allahu by next week komai zai dawo ready Na gode." Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_     _Stroy and written_              By    Sayyid (Legend's pen)✍️    *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚*     *The Fearless Writers Team*   _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 38_ Haka Bhatool ta yi ni ranar zuciyarta babu daɗi, ta rasa gane kan Senate da al'amuransa. Ta wani fannin sai ta ji kamar daman tun can Senate ba wai son ta ya ke ba, wani abu daban yake nufi da ita, amma kuma tana iya hango soyayyarta a idonun Senate, wanan lamarin kawai abarwa Allah. Can yamma dab da lokacin dawowarsa ta shiga kicin ɗora masa abincin dare, wani ɓari na zuciyarta na kwaɓarta a kan kar ta dafa ta jawa kanta ɓacin rai, wani ɓarin kuma na ba ta shawara kan ta dafa, haka dai ta dinga yaƙi da zuciyarta har ta kai ga dafa masa abincin. Bai sami shigowa gidan ba sai bayan ƙarfe tara na dare, in ran Bhatool ya yi dubu ya gama ɓaci a wannan lokacin. "Sannu da zuwa." Ta faɗa muryarta a ƙasa. "Bakiyi bacci ba?." Ya faɗa ba tare da ya amsa ba. "Banyi ba, ina jiranka ne." "Da matsala ne?." Girgiza kai ta yi sannan ta ce. "Babu, amma dan Allah ina son na yi maka wata tambaya." "Faɗi ina sauraronki." "Me yasa ka aure ni, bayan baka sona?." A wani fusace ya ɗago ya kalle ta, ita kan ta sai da ta tsorata ganin yadda idanunsa sukayi wani jaa, amma sai ta sake maimaita tambayar. "Mene amfanin aure na baka sona, dan ka dinga baƙanta min rai?." "Bhatool, idan baki da tambayar da zakiyi ki tashi ki bani waje." "Yanzu wannan ba tambaya ba ce, wane irin zama ne mukeyi haka?." "Mai zaman ya yi miki?." Wani ƙululun takaici ne ya matse Bhatool ba shiri ta tashi ta shige ɗaki, ta kwanta ta fara rusa kuka. Bayan tashin Bhatool, Senate ya ji jikinsa kamar an watsa ma sa ruwan sanyi, yana so ya tashi ya bita ɗakin amma kamar an riƙe shi. Ya na juyo sautin kukanta wanda yake jin kamar an watsa masa ruwan zafi a cikin zuciyarsa, amma yakaaa ta shi yaje ya rarrasheta. Bhatool haka tai ta kuka har bacci ya ɗauke ta, sai da ya ji ta daina kukan sannan ya fara jin sauƙi a zuciyarsa, kafin ya iya tashi ya tafi ɗakin shi ya kwanta. Washe gari da Safe Bhatool ba ta yi gigin ta shi da wuri ba, dan tasan Senate ba tsayawa zai yi ba. Haka kuwa aka yi dan da ta fito ma Senate ya daɗe da fita ofis. "Ikon Allah." Ta faɗa tana kama ƙugunta. "Wannan zaman fa ba zai yu haka ba, idan na kira Yaya na faɗa ma ta ta ce na yi haƙuri, Mama ma ta ce na yi hakuri, Mom ma ta ce na yi hakuri, wai ni Bhatool wane irin hakuri zan yi?." wayarta ta ɗauka ta kira Amrah, ta san a yanzu wajen ta ne kawai zata iya samun shawarar arziƙi, bugu ɗaya Amrah ta ɗauka da faɗin. "Amarya ba da kan ki asare." "Uhm Amrah kenan, ya gida ya makaranta." "Makaranta ana ta fama, kin ƙi dawowa dai?." "Zan dawo Amrah, dan Allah zaki iya zuwa gidana?." "Lafiya Bhatool?." "Amrah ki zo kawai, Wallahi ba lafiya ba." "Ya salam Bhatool, gani nan zuwa yanzu ma." Amrah ta faɗa tare da kashe wayar, zama Bhatool ta yi akan kujera, ta haɗa kai da gwiwa ta shiga tunanin irin alƙawaran da Senate ya dinga ma ta, amma duk ya kasa cika ko ɗaya. Ji ta yi zuciyarta na ta shi, da sauri ta nufi banɗaki ta hau kwara amai, sai dai babu aman kawai kakari take sabida ba ta iya cin komai ba, bare ya fito. Sai da ta gama ta wanke bakin ta sannan ta nufi kicin ta fara ƙoƙarin samawa cikinta abin da za ta ci, kamar wasa ta ji warin gas ɗin ya yi ma ta daɗi a hanci, ba musu ta tsaya a cikin kicin ɗin har ta gama dafa shayin ta soya ƙwai ta fito. Ba ta yi nisa da fara ci ba Amrah ta shigo gidan, a yanzu mai gadin ya gane ta ba ya hana tun da Bhatool ta yi masa magana. "Ah lallai sai dake, ina nan kin ɗagan hankali amma ke kina nan zaune kina cin ƙwai." Amrah ta faɗa tana shigowa cikin ɗakin. "To zan zauna yunwa ya kashe ni?." "Ba wannan ba, mene matsalal Bhatool kin ɗagan hankali wallahi."  Amrah ta faɗa tana zaman kan kujerar da Bhatool ke kai. "Nutsu ki ci abinci Amrah, ba na son abinda zan faɗa miki ya dame ki, nima ina yi cin abinci." "Ke dalla ni na ƙoshi, in zaki faɗamun ki faɗa." "Bara na ƙara sa nawa." "Wai Bhatool mene haka." Amrah ta faɗa cike da ƙosawa. "Amrah zaki iya yarda idan na faɗa miki bama zaman daɗi da Senate?." "Bangane ba kwa zaman daɗi ba?." Amrah ta faɗa, mamaki ƙarara a fuskarta. "Ina nufin tun farkon aurenmu muke samun saɓani da Senate." "Gaskiyya Bhatool ba lallai na yarda ba, sai dai kuma ance mai ɗaki shi yasan inda yake masa yoyo." "Gwanda da ba ki mus ba Amrah, wallahi ko cikakken sati biyu ba mu yi ba mu ka fara samun matsala." "Amma dai Bhatool na san koma mene ke ce mai laifi, domin a yanayin Shiru shiru irin na Senate bana jin zai iya yi miki wani abu har haka?." "Hhm Amrah kenan, kin san mutumin nan da muka ganshi a ƙofar gidan nan?." "Yaushe kenan?." Amrah ta faɗa. "Last zuwan da kika yi." "Okay okay na tuna." Amrah ta faɗa tana ɗaga kai. Nan Bhatool ta hau bawa Amrah labarin komai tin da ga matsalal su ta farko, har abinda ya fara haɗa su da Ahmad, har abinda ya faru jiya ma. Wata nannauyar ajiya zuciya Amrah ta sauke sannan ta ce. "Wallahi Bhatool na yi tunanin Senate mutumin kirki ne." "Ni ban masan me zan ce ba, amma tabbas Amrah na kasa gane asalin Senate, kullum a bauɗe yake." "To kuma kina ba shi hakuri?." "Wane irin hakuri Amrah, mutumin nan fa a yanzu ya mai da ni wata sauna, ba ni da amfanin komai wajenshi, ba ya cin girkina, ba ya damuwa da yadda nake da yadda na kwana ko na ta shi." "Ni a ganina ki ci gaba da lallaɓashi, amma ki dage ya barki ki koma makaranta ko yaƙi ko ya so, idan ma ta kama ki sa mom a maganar, wannan fitar ki makaranta zai rage miki wanu raɗaɗi sosai da sosai, dan idan ba haka ba wallahi ciwon zuciya na iya kamaki." "Ciwon zuciya kuma Amrah?." "Eyh wallahi Bhatool, tun da kina son mijinki, kin damu da shi, dole zai ki dinga damuwa da shirun da yake miki amma idan kina fita wasu abubuwan zasu ragu." "To amma babu wata mafita da zamu dawo dai dai, Amrah?." "Bhatool a yanda kika faɗa baki yi masa laifin komai ba, shi ka ɗai ya canja to ki ƙyaleshi zai dawo dai dai, ina tunanin irin sune mutanen da ake kira da introvert." "Introvert?, wane irin mutane ne haka?."  Bhatool ta faɗa cike da mamaki. "Wasu nau'in mutane ne da na ji ana maganarsu a tiktook, wai haka kawai suie fita daga sabgar mutum, ba sa son hayaniya, basu da yawan surutu, ba a fiya gane alƙibilal su ba." "I, to ba laifi in dai hakane Senate na cikinsu." "To dan haka Bhatool kar ki ɗorawa kan ki wannan damuwar, kamar ki wami faɗawa Umma ko su Yaya Karima ma ki daina faɗawa, gwanda ma Mom tum ita uwarsa ce ta san halinsa, ita ma bakomai ba." "Shi ke nan Amrah na gode da wannan shawarar." "Badamuwa Bhatool, in shaa Allah komai zai yi dai dai, amma ki tabbatar kin dawo makaranta." Amrah ta faɗa bayan ta kama hannun Bhatool. Zaune yake cikim ofis ɗin sa ya haɗa uban tagumi, yana so ya yi tunanin ta amma kamar an janye zuciyarshi daga yin tunaninta, yana so ko muryarta ya dinga tunowa amma ba iya wa, da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya furta. "Ina son ki Bhatool, ki yi hakuri da wasu abunuwan amma tabbas ina sonki." "Kana son wa?." Anas da ya shigo tun ɗazu yake kwaɗa sallama amma babu amsa ya faɗa, da sauri Senate ya ɗago ya kalleshi. "Anas mene haka, yaushe ka shigo?." "Haba Senate, na fi mintuna goma tsaye nan ina magana amma ka tafi tunani, idan ganin matar ta ka ne bai ishe ka ba sai ka koma gida ba sai kazo nan kana mana zancen ta ba." Tsaki Senate ya ja sanan ya ce. "Ya aka yi ne?." "Zancen wannan project ɗin ne fa, ina tunani dole sai ka je Abuja ka yi one week ɗin nan." "My god, bana son barin garin nan wallahi." Senate ya faɗa yana karɓar takarda hannunsa ya fara dubawa. "Yaushe suke so a zauna ɗin." "Jibi idan Allah yakaimu za ayi zama na farko,  sai kuma bayan kwana biyu a sake zama na biyu, bayan wasu kwanaki biyun sai ayi zama na karshe." "Kasan tafiyar aiki ce, bana son zuwa da Bhatool." "To ka kawo ta gida mana, ko kabarta a gidanta ai kana da guards." "Bari dai muga yadda za ayi." Senate ya faɗa, shi kuma Anas ya fita, waya ya ɗauka yana son ya kira Bhatool amma kamar wanda ake kwaɓar hannunsa, haka ya ajiye wayar ya shiga aikinsa. Amrah ba ta tafi ba sai yamma, bayan ta gama bawa Bhatool shawarwarin da take ganin za ta iya ba ta, bayan ta tafi Bhatool ta tashi ta yi wanka, ta yi shirinta cikin jar abaya mai kyau. Tana zaune a falo tana danna wayarta ta ji ya yi sallama, ba ta ma yi tunanin dawowarsa yanzu ba tun ta ga yana kaiwa dare. "Sannu da zuwa." Ta faɗa tana miƙewa. "Yawwa Sannu, ya gida." "Lafiya." Ta faɗa tana zama shi kuma ya shige ɗaki abunsa, tana nan zaune ya fito ya kalli dinning babi abinci ajiye, kamar daga sama ta ji ya ce. "Da abinci ne ko babu?." "Akwai yana kicin." Ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba, ba musu ya nufi kicin ɗin ya zubo abincin ya dawo kan kujera ya zauna ya fara ci, sai da ta ga ya yi nisa cikin cin abincin ta ce. "Ya maganar komawa makaranta na?." "Bazaki koma ba." Ya faɗa yana ci gaba da abinda yake. "Saboda me?." "Ban yi niya ba." Legendspen 08129553971 *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 39_ Whatsapp group https://chat.whatsapp.com/DPr8Zlw33HeAkt3hhxIPYv "Banyi niyya ba." Bhatool ta yi mamakin wannan maganar ta shi, "Wai Senate mai yake nufi, zaman rashin mutunci yake so mu yi kamar ba masu aure ba ko me?." Ta tambayi kan ta. "Dan Allah." Ta faɗa kamar za ta yi kuka. "Na ce bazaki koma ba, idan kuma zaki koma ga hanya nan." Ya faɗa a fusace kamar zai dake ta, tashi ta yi ta shige ɗaki ta fara kuka. Har cikin zuciyarsa yake jin zafin kukan na ta, amma kamar an ɗaureshi da igiyoyi. Bhatool na shiga ɗaki ta dau waya ta kira Mom, tana kuka Mom ta ɗaga wayar. "Subahanallahi Bhatool me ya faru?." "Mom, wai bazan koma makaranta ba." "Bangane ba?." "Wai ya ce bazan koma makaranta ba kuma gashi jarabawa zamu fara." "Ki yi shiru Bhatool, zan kira shi gobe ku zo gaba ɗaya." "Tom Mom." Ta faɗa tana kuka. "Ki daina kukan kin ji zaki koma karatunki kin ji?." "Na daina Mom." Ta faɗa, Mom takashe wayar ita kuma Bhatool ta kwanta. Washe gari da safe ta tashi ta fara aikinta na gida, tana cikin kicin ya shigo ya ce. "Kishirya zamuje gidan Momi." "Tom." Tafaɗa tana kashe gas ɗin. A mota ta same shi yana jiranta, sai dai suka yi nisa da tafoya sannan ya ce. "Bhatool mene matsalalki?." Da mamaki Bhatool ta kalleshi, a ranta ta na maimaita kalmar Matsalalta. "Shin ni ce mai matsalal?." Ta tambayi a kan ta. "Eyh Bhatooɗ?." "Babu." Ta faɗa ba tare da ta ƙara kallonshi ba, shiru shima ya yi bai ƙara ce ma ta komai ba har suka isa gidan, tun da suka shig gidan Senate ya ji wani irin sanyi a ran shi, a fili ya furta. "Sweet Home Sweet." Ita dai Bhatool ba ta kula shi ba ta shige ciki, Mom na zaune a falo Bhatool ta yi sallama ta shigo, fuskar momi fal da fara'a ta amsa ma ta. "Momi ina kwana?." "Lafiya kalau daughter." Mom ta amsa dai dai lokacin da Senate ya shigo. "Momina." Ya faɗa yana shigowa ciki. "Uhm da bamu da uwar da munyi kuka." Bhatool ta faɗa a cikin ranta tana taɓe baki. "Ina kwana Mom." Ya faɗa yana zama kusa da ita. "Lafiya Kalau." "Mom yana ga bakya murna da zuwana." Hararshi ta yi sanan ta ce. "Kawai ka hana yarinya komawa makaranta, sabida me?." "Au shine ta faɗa miki?." "Bazata faɗa mun ba?." "A'a." "To me yasa ka hana ta?."  Kallon Bhatool ya yi sanan ya ce. "Mom ta faɗa miki abinda take mun a gidan, komai tana mun a gutsire, magana a gajrace. "Gashi, zaka ci, sannu da zuwa, zan koma makaranta, Momi Babu girmamawa babu kulawa, babu soyayya." Kallon Bhatool Mom ta yi sanan ta ce. "Me yasa Bhatool?." "Mom, ko abinci bai fiya ci ba, da ya shigo xai fara haɗe rai yana cin magani, idan na ce mai ya yi hakuri sai ya ce wai me na yi?." "Mom har ni yarinyar nan za ta ce wai daman ba son ta nake ba na aureta." "Oh Allah, ashe ba zaman daɗi kuke yi a gidan ba kenan, to kusani kuna dauke da Ɗa, Bhatool na da cikinka, ke ma kina ɗauke da ciki a jikin idan kuka ci gaba da hauka ku kuka sani." Har cikin zuciyar Bhatool ta ji wani abu, wai tana ɗauke da ciki. "Mom did you mean she is pregent." "Yes, tana ɗauke da ciki." "Kai Alhmadulillah." Senate ya faɗa yana kallon Bhatool, fukarsa fes da farin ciki. "Mom ki yi hakuri ta ci gaba da zuwa makarantar." "Allah Ya yi muku Albarka, ya baku zaman lafiya mai ɗorewa." Mom ta faɗa suka amsa da baki. "Mom zanje gidan Yaya Karima." Bhatool ta faɗa. "Okay Bhatool." Tashi ta yi ta fice, Senate ya miƙe zai bi ta Mom ta kama hannunsa ya tsaya, sai da Bhatool ta yi nisa da fita sannan Mom ta ce da Senate. "Kasan wani abu?." "A'a sai kin faɗa." Ya bata amsa yana zama. "Wai Abbanka aure yake son ƙarawa." "Aure Kuma?." Ya tambaya. "Eyh, wai aure." Mom ta ba shi Amsa tana taɓe baki. "To shi yanzu wace zata aureshi?." "Wai wata frist love ɗin shi ce, daman already ya taɓa bani labarinta.  Amma haka ya ce ta mutu, to yanzu ya gano mijinta ya mutu shine yake so ya aureta, yayata uku ma." "Chaɓ, Dad ya fiya matsala." "Kabarshi kawai Allah Ya ba shi sa'a, amma wallahi ya jamun surutun da bazai ƙare ba cikin ƙawayena, tun da yarinta ba ayi mun kishiya ba, sai yanzu da girmana har na kusa fara ajiye jikoki." "Gaskiyya Mom bai kyauta ba, amma zan yi magana da shi." "A'a kar ka fara, kar ma ka nuna mai kasan maganar ka barshi kawai." "Okay." Yaya Karima na zaune a ɗaki ta ji an faɗo a kan ta, ba ta kai ga tantance wand aya faɗo ba ta ji anfashe da kuka, a firgrcr ta ɗago Bhatool tana faɗin. "Ke lafiya?." Kuka Bhatool ta ci gaba da yi. "Bhatool bana son iskanci, kawai zaki shigomun babu sallama ki fara kuka." "Shine baki ƙara zuwa gidana ba, da nice da tuni nazo kamar mara mafaɗi har kwana nake yi a gidanki." Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "To bikiga banda lafiya ba, haihuwa ta fa ta kusa." "Amma ai bai hana ki zuwa unguwa ba." "To wai ma ke Bhatool me ya fito dake da wannan safiyar?." "Gidan Momi ya kawo ni." "Shine kika bar gidan kika tawo nan?." "To me zan musu, ashe haka auren yake duk wahala, gashi har na sami ciki. Ni bana wani farin ciki wallahi." "To ai daman a ko da yaushe ana faɗa miki aure gaba ɗayanshi ɗan haƙuri ne, ke ce daman kile wami Hasashen soyayya zalla a gidan mijin, bawai ba a samu ba ne amma tana ɗauke da ƙalubale kala kala." "Uhm, to Allah Ya kyauta." Bhatool ta faɗa tare da kwantawa a kan kujera. "Yaya soyamun ƙwai." "Ba ki ga banda lafiya ba ne?." "Nima ai ba lafiyar ce dani ba, ciki gareki ciki gareni." Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "Allah Ya shirye ki Bhatool, bara na sa mai aikin nan ta yi miki." "Ni kinga Momi ta aikon mu da masu aiki, amma iya share share na ce suna yi sai su tafi, idan ɗaya ta yi na safe, ɗayar ta yi na yamma." "Eyh hakan ma ya yi, ni dake cikin nawa ya tsufa ai." "Aini Yaya cikina ya na fitowa zan tafi gida, ko ya yarda ko bai yarda ba." "Wai ke waya faɗa miki a aure ana cewa ko ya yarda ko bai yarda ba." "Ni dai tashi kika soyamun, ɗan cikina yunwa yake ji." Bhatool ta faɗa tana danna wayarta, ta shi Yaya karima ta yi fa shiga kicin, ta lallaɓa ta soya mata ƙwan, tana addu'ar Allah Ya kawo Senate yazo ya kwashe ta su tafi. Bhatool kam na gama cin ƙwan ta miƙe ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai azhar, lokacin zuwa Senate biyu, amma ganin tana bacci sai ya ce abarta. "Yaya Shinkafa." Bhatool ta faɗa tana miƙe ido. "Ki tashi ki bi mijinki." Sai a lokacin Bhatool ta kula da Senate dake zaune yana kallonta. "Ni anan zan kwana." Wata uwar harara ya watsa ma ta sannan ya ce. "Sannu cin kai." Ba ta ba shi amsa ba ta sake mai da kan ta ga Yaya Karima. "Ni yunwa nake ji." "Bhatool tun ɗazu fa yake jiranki, idan kun je gida kwanci. Kinga ni nan ban ɗora shinkafa ba, kunnun gyaɗa na yi." "To zan sha." Ta shi Yaya Karima ta yi ta shige kicin. "Ke ta shi mutafi." "Nifa na dawo gidan yar uwata, idan ba za a dinga hulaƙanta ni ba." "Na daina fa, ki ta shi dan Allah."  Ya faɗa yana karyar da kai. "Sau nawa kana cewa ka daina?." "Bhatool ke zuma ce sai da huta." "A'a sauro ce, ka ta shi ka tafi gidanka ni ba inda zani, daga nan ma gidanmu zan tafi, bari na kira Abdul ya zo ya ɗauke ni." Ta faɗa tana ɗaukar wayarta, ganin tana shirin ɓa ta masa rai ya sa ya miƙe tsaye to na tafi. "Kafi ruwa gudu." Ai ba ta yi aune ba ta ji ya kinkice ma ta, ya ɗaga ta cas kamar wata yar baby ya yi waje da ita. Yaya Karima na fitowa taga sun fice. "Kai ma shaaa Allah, Bhatool ko rigima." Ko ɓangaren Mom bai kai ta ba ya tura ta a mota suka bar gidannan,  tun da suka fara tafiya ran ta a haɗe yake ko kallon inda yake ba ta yi, ƙasa ma ta mayar da kan ta. "Ki yi haƙuri Habibty." Ba ta ɗago ta kalleshi ba ta ce. "Yanzu muna komawa gida zaka daina duk wannan murmushin, duk wannan dariyar, ka wani haɗe rai." Dariya ya yi sannan ya ce. "Na ce fa na daina gaba ɗaya in shaaa Allah." "Tom Allah Ya yarda." "Kalli inda muka zo." Ɗagowa ta yi, ina zata gani idan ba gidansu ba, yau za ta ga Umma. Koƙarin buɗe motar ta fara, ya riƙe ma ta hannu. "Ki jira ni mana." "Thom." Ta faɗa, sannan ya cika ta ya buɗe suka fito, hannunshi cikin na ta suka shiga cikin gidan, sai dai shi kaɗai ya yi sallama ita ba ta yi ba sakamakon jirin da ta ji yana ɗibarta. "Ash." Ta faɗa. "Bhatool are you okay?." Ya tamabaye ta, girgiza kai ta fara yi sannan ta ce. "Kai na." "Me ya samu kan?." Ba ta iya buɗe baki ba ta ji jikinta ya sake, shuuu ta faɗa. Da sauri ya riƙo ta ta faɗo jikinsa. "Bhatool! Bhatool." Ya shiga kiran sunnanta, amma ba ta ko numfashi bare motsi. "Bhatool!." Ya sake faɗa, Umma dake xaune ɗaki ba ta san me yake faruwa a tsakar gidanta ba sai murya ta ji daga sama kamar ana kuka. "Umma! Umma!! Umma!!!, Bhatool." Miƙewa tsaye Umma ta yi tare da faɗin. "Subhanallahi." Amma ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ji ansake kiran sunnan na ta. "Umma! Bhatool." Da sauri ta fito, tsaye ta yi turus ganin Senate da Bhatool a kwance. *HASASHEN SOYAYYA*❤️‍🔥🥹 _Imagination of love_ _Stroy and written_ By Sayyid (Legend's pen)✍️ *FUTURE WRITERS ASSOCIATION* *(FUWA)🖋️📚* *The Fearless Writers Team* _Marubuta masu tsage gaskiyya_ *BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫* _Page 40_ "Subahanallahi, mai yafaru daku?." Umma ta faɗa tana ƙarasowa inda suke, cikin kuka Senate ya ke magana. "Umma yanzu mun shigo, mun shigo kawai ta faɗi ƙasa." "Ya salam, ɗakko ta ku shigo."  Kamar wanu dutse haka Senate ya ji nauyinta, kamar ba ita ya ɗakko daga gidan Yaya Karima har zuwa gidan Momi ba a hannusa. Daƙyar ya kai ta ɗakin, Umma ta ce dubu waccan akwatin ta saman sif, akwai zamzam a ciki ka miƙo mun. "Tom." Ya faɗa tare da miƙewa, ya kusa minti biyar yana dubawa kafin ya ganshi ya miƙo ma ta. Bayan ta yi addu'o'i ta shafa ma ta, a hankali ta fara sauke ajiyar zuciyar sannan ta buɗe idonta. "Sannu Bhatool!." Senate ya faɗa, gyaɗa ma sa kai ta yi sannan Umma ta ce. "Ya jikin na ki?." "Da sauƙi Umma." "Ku tashi ku tafi gida, ta na buƙatar hutu." Umɓa ta faɗa. "Dan Allah Umma na huta anan." Bhatool ta faɗa kamar za ta yi kuka, dai dai lokacin wayar Senate ta fara ringing. "Ina zuwa Umma." Ya faɗa yana miƙew ya fita. "Hello Anas." Daga can Anas ya amsa da faɗin. "Na siya maka ticket ɗin, na yi maka booking hotel da komai." "Okay badamuwa, gobe ne ko?." "Eyh gobe ne, amma me yake damunka na ji ka haka?." "Ashe Bhatool na da ciki, kuma ka ga yanzu munzo gidan su kawai ta yanke jiki ta faɗi." "Ya salam! Kuna asibiti?." "A'a ta farfaɗo, ina tunanin ko zan barta gidansu zuwa na dawo." "Eyh hakan ya yi sosai da sosai, amma ka faɗa ma Mom." "Okay." Ya faɗa tare da kashe wayar ya kira Mom, tana zaune abin duniya duk ya isheta ta ɗaga wayar. "Son ya aka yi?." "Mom munxo gida Bhatool za ta gaida Umma ta yanke jiki ta faɗi." "Ya salam! Kuna ina yanzu?." "Muna gidansu, komai ya yi sauƙi." "Allah Ya ƙara sauƙi." "Amin-amin, daman zancen tafiyar nan ne." "Gobe ne ko?." "Eyh, na ce ko barin ta zan yi a gidansu?." "Eyh, hakan ya yi, sai ka je gida ka ɗakko mata kayanta, sannan idan ta ji sauƙi ta fara zuwa makaranta." "Tom shikenan Mom." Ya faɗa tare da kashe wayar, bai koma gidan na su ba ya hau mota ya nifi gida, ɗakin ta ya shiga ya hau haɗo ma ta kaya, wayanda ya gani a cikin akwati, wayanda duk rabi na lefen ta ne ba ta ma da niyar sa su yanzu ya ɗebo ma ta, mayafai kam bai tsaya ya ga sun yi kala da kayan ba ko ba su yi ba ya ɗebo ma ta haka takalma, wani lace ɗin ta ya gani, yana son wannan lace ɗin tun da Mom ta nuna mai lokacin da ake haɗa kayan lefenta, ɗaga shi ya yi yaga ɗinkin da aka yi ma ta. "So Ma shaa Allah." Ya faɗa yana hango yadda Bhatool za ta yi kyau da shi. Haka ya haɗa kayan ya fitowa ya sa su a mota ya tawo. Mom na gama waya sa Senate ta kira Yayarta, Maman Anas. "Hello Yaya." "Lafiyanki wai n ji muryar ki a haka?." "Bakomai Yaya." Mom ta faɗa. "Wane abu ya faru ne?." Mom ta sake faɗa. "A'a naji muryarki kamar da damuwa." "Oh! Wai matar Senate ce fa faɗi a gidansu, ni Allah Yasa ma cikin bai sami matsala ba, yanzu dai na ce ya barta gidan nasu tunda shi zashi Abuja ya yi sati ɗaya." "Eyh hakan ya yi kam, Allah Ya sawaƙe." "Amin, Amin." Daga nan suka shiga hirarsu. Bhatool kam Kam Senate na fita ta kalli Umma ta ce da ita. "Umma dan Allah ko kwana ɗaya ne." "Bhatool kin san dai ba zance da mijinki ya barki anan ba ko?, idan ya ga dama ya barki shikenan, idan kuma ya ce ku tafi shikenan." Taɓe fuska ta yi tare da kawar da kai gefe ta kwanta. Kusan mintuna 20 babu senate babu alamunsa. "Umma kinga bai dawo ba." "Ko ya barki anan ne?." "Idan yabar ni ai zai faɗamun." "Ko yabarki zuwa ya je aiki ya dawo." "Shima ya sani." Bhatool ta faɗa tare da komawa ta kwanta, ba ta daɗe da kwanciya ba ya shigo gidan, hannushi riƙe da akwati. Wani daɗi Bhatool ta ji, sai dai kuma taji wani irin tsoro kar fa ya ce sakinta ya yi. Da ido ta bi shi har ya zauna. "Umma daman zanje Abuja, to na yi niyar nabarta ta zauna a can gidan namu, amma wannan abun da ya faru ya naga ya fi dacewa ta xauna anan, zuwa na dawo." "Tom Allah Ya kai ka lafiya, ya dawo da kai lafiya." "Amin Umma." Ya amsa dai dai lokacin da Umma ta ta shi ta fice. "Bhatool." Ya kira sunanta. "Na'am." Ta amsa kamar za ta yi kuka. "Babu matsala ko?." "Me yasa baka faɗamun zaka yi tafiya ba?." "Ki yi hakuri, nima tafiyar ban so ma ta ba, amma ai kina tare da Umma babu abinda zai dame ki, ko missing ɗina ba za ki yi ba." "Ga shi tun yanzu na fara missing ɗinka, yaushe zaka dawo." "Sati ɗaya ne cif, sannnan idan kin ji daɗin jikin ki, zaki iya zuwa makaranta." "Har sati ɗaya." Ta faɗa tana goge idonta. "kina fa tare da Umma." "Ni dai kawai ka tafi da ni." "Ai baki da lafiya." Shiru ta yi ba ta ce komai ba, ya taso inda take ya riƙe hannunta. "Take care please, kin san kina da Baby." "Take care too." Haka suka yi ta musayr kalaman soyayya, wayanda tun da suka yi aure ba su yi irinsa ba. Anan gidan ya yi magariba sannan ya tafi gidan Momi zai kwana can gobe da sassafe ya tafi, sun yi da Bhatool xai zo kafin ya tafi. Kusa raba dare suka yi suna waya,  Bhatool har mamakin sauyin Senate ta yi, sai kuma ta yi tunanin ko ƙila sabida cikin dake jikinta ne, haka dai ta yi bacci da tunani kala kala.  Washe gari ƙarfe bakwai da rabi ya zo, a tsaitsaye suka ga gaisa sabida jirgin takwas zai bi. Wajen ƙarfe goma da rabi, Bhatool na zaune Amrah ta kira ta a waya. "Allah sarki Amrah, duk lokacin da bana jindaɗi sai ta kira ni." Bhatool ta faɗa a fili sannan ta ɗaga wayat, tana faɗin. "Amrah yakike." "Lafiya Ƙalau Bhatool, ya jikin?." "Ah! Aina kika san banda lafiya?."' "Ke ki jiki ki, kin manta ranan nan kin ce mun bakya jindaɗi." "Laa! ai nasami sauƙi, yanzu ma dai gani a gida ya tafi Abuja zai yi sati ɗaya, kuma ya ce nakoma makaranta." "Ya salam! Da fa kayan nan zan zo na amsa." "Ai ya tawo mun da masu kyau kuwa, kizo ki xaɓa kawai." Bhatool ta faɗa. "Okay badamuwa." "Ina Jannah kuwa?." Bhatool ta tambayeta. "Ni fa rabona da na kwana biyu, ta canja ƙawaye fa ko a makaranta." "Ai shi ke nan, nima dai gobe xan zo." "Ah! Allah Ya kaimu." "Amin, amin." "Sai nazo." Amrah ta faɗa, Bhatool kuma ta kashe wayar, tana nan zaune Abdul ta shigo hannunshi riƙe da baƙar leda, washe baki Bhatool ta fara yi tare da faɗin. "Ɗan Albarkan Umma, me aka samu mana?." "Idon ma tambayi." Ya faɗa yana zama. "Bamu mu ci." Miƙa ma ta ledar ya yi sannam ya ce. "Bhatool ya zaman gidan naku yake?." "Komai yana tafiya yadda yakamata, tun da dai ance aure ɗan haƙuri ne, to muna ta haƙurin dai." "Allah Ya ƙara muki haƙuri, amma ni yanayin ki sai naga kamar ba wani daɗin zaman kike ji ba, Bhatool ba fa zama a babban gida mai cike da kayan alato ba ne jindaɗi, zama cikin soyayya da kulawa." "Eyh, nasani Abdul." "Tom Allah Ya dauwamar muku da zaman lafiya." "Amin amin." Ta faɗa tana kwance ledar, shi kuma ya ta shi ya fice. Sai yamma lis Amrah tazo gidan, suka shige ɗaki ita da Bhatool suka hau hira, nan Bhatool ta nuna ma ta kayan ita kuma ta zaɓa, da faɗin gobe kawai za ta yi amfani da shi, jibi za ta ba ta a makaranta. Washe gari. Bhatool da murnar zuwa makaranta ta tashi, bayan sunyi waya da Senate ya yi ma ta addu'a tare da jan kunne akan ta kula da kan ta, yanzu ita matar aure ce. Haka ta shirya cikin atamfa Super holland mai adon ja da touch din green, driver da Senate ya turu ma ta yazo ɗaukan ta. Tunda driver yayi parking motar tasu wacce a wajen rubuta lamba aka rubuta *Senate* gaba ɗaya hankalin yan matan ya yo kan motar, driver ne ya fito daga wajen da yake tare da buɗe mota ƙofar inda take zaune, hill sheo ɗinta ne ya fara fitowa kafin kuma ita ta fito, ai tuni wajen ya ruɗe da faɗin. "Fatima senate! Fatima senate!!." *Cigaban labari* Wani murmushi Bhatool ta saki, Allah Ya sani she miss alot from her school. Amrah ce ta tawo da gudu ta rungume ta, tana faɗin. "Welcome back Bhatool." Nan da nan sauran yan ajin suka yo inda suke kowacce na cewa. "Welcome Bhatool." Cikinsu har da Jannah, da Amrah ta ce ba ta zuwa makaranta. Harara Bhatool ta makawa jannah, bayan sun ke ɓe su uku sannam ta ce. "Sannu Jannah, mara mutunci." "Kai Bhatool rashin mutuncin me na yi kuma?." "Baki zo inda nake ba kwata kwata, sai na nemi ki ke ba zaki nemi ni ba." "Tun yaushe nake bin Amrah yaushe zamu zo sai daga baya ta ce wai ita ta zo." "Ah to ba dole na naje ba, kullum ba a gane kan ki a school." Amrah ta faɗa. "Bawani nan." Ita ma Jannah ta faɗa, ita Bhatool mamakin yadda Amrah ta nuna ma ta basa tare da Jannah take, ita dai tun zuwan ta tare ta gansu, gashi yanzu ma suna hira tare. "Ai shi ke nan, yanzu me na yi missing a class." "Oh! You missed alot, dan ma ina miki attendence, tun da Amrah ta ce mun zaki dawo na fara miki."' "Kai amma na gode sosai da sosai." Nan suka shiga hira, hankalisu kwance kamar yadda suke yi da, banda suhaima da aure ya kai ta kano. Kowa a class ɗin kallon Bhatool yake sa suturar da take jikinta, har aka ta shi baki ɗaya. "Bhatool yau kin baza kafasity, dan Allah gobe ma ki baza." Amrah ta faɗa, dariya Bhatool ta yi sannan ta ce. "Bawani kafasity." "Wallahi kin baza." Janna ta faɗa tana ta shi, "bara na siyo mana ruwa." "Okay." Amrah ta faɗa, jannah na huce Amrah ta ce. "Kin san an ɗaga wancan abun da zani, ko kayan ma ban sa ba gasunan, ashe haka ɗinkin ya yi kyau." "Kai ya yi kyau sosai baki ga yadda Senate yake son kayan ba, ina ga ma gobe su zan sa." "Aikuwa dai ki sa su." Amrah ta faɗa suka cigaba da hira, driver Bhatool ne ya kai ƙawayen na ta duka gida. Washe gari Bhatool ta sanya lace ɗin ta yi kyau sosai da sosai, haka tai ta baza kafasity a cikin Ajinsu har aka ta shi, ita dai ta fahimci babu wani saɓani da ya shiga tsakanin Amrah da Jannah, kawai dai Amrah ce ta faɗa, ko kuma sun sasanta kansu ne daga baya. Wajen ƙarfe tara na dare Bhatool na kwance ta ji wayarta na ƙara, kasancewar ringing ɗin shi daban ne ya sa ta ɗaga wayar da faɗin. "Salamu akaikum." "Riƙe sallamarki, munafuka muguwa, Bhatool me kika aikata haka?, daman shine dalilin da yasa kika dage sai kin koma makaranta, sabida ki dinga bin maza a waje, me yasa haka." Senate ya faɗi maganar gaba ɗaya lokaci guda babu ko sakin numfashi. Cike da tashin hankali Bhatool ta ce. "Me na yi kuma, me na yi haka?." "Tambaya ta kike me kika yi, Bhatool ki je nasake ki Saki ɗaya, kuma haƙƙina dake kanki banyafe ba." "Innullahi wa'inna illahir raji'un, na shiga uku." "Idan kina tunanin kin yi komai a sirrance to asirinki ya tuno, ki duba kiga hotonan da na tura miki." Cike da ruɗewa Bhatool ta shiga whatsapp ta duba saƙon na shi, hotonane ya turu guda uku. Na ɗaya ita ce zaune a cafetria amma ba tasan waya ya ɗauki hoton ba, sai dai tasan ita da Jannah da Amrah ne ɗazu, hoto na biyu kuma babu fuskar ta kalli gefe amma ita ce tabbas dan ga kayan nan, sai kuma na uku irin na biyu ne amma wani namiji ya rungumota ya kuma riƙe hannunta. "Innullahi wa'inna illahir raji'un." Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa. End of Book one🥹🥺 Anan zamu dakata a cikin littafin Hasashen soyayya, Book one in shaa Allahu zamu shiga Book kafin azumi, idan kuma ya kaimu lokacin azumi kuma sai bayan Sallah ngde Hasashen Soyayya Book2            By Sayyid Legendspen _Amanar-Janafty_ _Sadaukarwa_ Fatima isa Manu (Sahiba) Shafi na Arba'in da ɗaya.    (41) A hankali Bhatool ta bude idonta da ta ji ya yi ma ta wani irin nauyi, da sauri ta sake runtse shi da faɗin. "Hasbunallahu wani'imal wakil." Sakamakon wani azababben jiri da taji. "Kamar magana ta yi." Sautin Muryar Umma ya fito, a hankali Bhatool ta gyaɗa sannan ta ce. "Uhm!." Abdul ne ya yi saurin zuwa kanta yana faɗin. "Bhatool! Bhatool me ya faru?."  "Kar ka yi ma ta ihu dan Allah." Umma ta faɗa, daidai lokacin aka turu ƙofar ɗakin aka shigo, Mom ce tare da Dad suka shigo a tare, Umma iya Mom ta kalla ba ta bari sun haɗa ido da mai shigowa bayan Mom ba ta kauda kai, amma haka kawai ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa, mussaman lokacin da ya yi sallama. "Bhatool ya jikin naki?." Mom ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita. "Yanzu ta fara magana." Umma ta faɗa a hankali. "Ina yini?." Abdul ya faɗa yana gaida Dad. "Lafiya ƙalau my son, ya jikin na ta?."  "Alhamdulillah." Abdul ya faɗa yana kallon yadda Dad yake bin Umma da wani irin kallo, ba tare da Umma ta kalleshi ba ta ce. "Ina yini?." Dan ita gaba daya ya cika ɗakin, tana mamaki ko sirikinta mahaifin mijin Karima ba ta jin kunyarsa haka. "Lafiya ƙalau ya mai jikin?."  "Da sauƙi." Ta faɗa muryar na dawo mata a kunne, ita fa tasan wannan muryar. "Umma, ina Senate?." Bhatool ta faɗa murya cike da wahala. "Zaki sha ruwa?." Mom ta tambayeta. Gyaɗa kai ta yi alamar 'Eyh.'  "Miƙo ma ta ruwan." Mom ta faɗawa Umma, Umma ta sa hannu ta miƙo ruwan daidai lokacin idanunta suka faɗa cikin na Dad dake zaune kan kujera ya kafe ta da ido, kamar walƙiya haka Umma ta gani, da sauri ta sake kallonsa. "Innullahi wainna illahir raji'un."  "Lafiya?." Mom ta tambaya, da sauri Abdul ya ƙaraso inda take yana faɗin. "Umma me ya faru?." Hannu tasa tana nuna masa Dad dake zaune. "Umma mahaifin Senate ne fa." Mom ce ta juyo ta kalli Umma ta kalli Dad. "Lafiya wai?."  Miƙewa Dad ya yi ya matso kusa da Bhatool. "Daughter Allah Ya baki lafiya." Ya faɗa tare da ficewa, a take Mom ta miƙe ta yi bayanshi tana fadin. "What's wrong?." Mom na fita Abdul ya masto kusa da Umma. "Umma waye wannan din, kinsan shine?." Hawaye ne suka fara zarya a fuskar Umma wanda ya matuƙar daga hankali Abdul da Bhatool. "Umma ya sake ni." Bhatool ta faɗa. "What!." Abdul ya tambya. "Senate ya sake ni." Ƙofar ɗakin ce ta bude Mom ta shigo, a bayanta kuma Ahmad ne wanda ya kaɗe Bhatool kwanaki, a yanzu ya zama abokin Abdul sosai da sosai, sun yi waya ne ma dazu yake ce masa yana asibiti Bhatool ba lafiya shine ya zo. " Bhatool me kike cewa haka?." Mom ta faɗa cike da tashin hankali, ga abinda ta ga ya faru yanzu mijinta da surikarta, ga kuma yanzu ta ji ance wai Senate dake mugun son Bhatool ya sake ta.  "Ina waya ta?." Bhatool ta faɗa. "Tana gida." Abdul ya bata amsa. "Wallahi ya sakeni, wai ina cin amanarsa." Bhatool ta faɗa tana rushewa da kuka, Mom ce ta ɗakko wayarta ta fara neman lambar Senate, sai dai har ta ƙara ci bugunta bai ɗauka ba.  "Innullahi wa'inna illahir raji'un." Abinda kowa ke maimaitawa. "Wannan auren tun farkon shi yaran nan basu sami zaman lafiya fa, ga dai soyayyar suna nunawa junansu amma abubuwan kamar an riƙe su." Umna ta faɗa jikinta duk ya yi laushi. "Wallahi Maman Bhatool, kwanaki haka na ce kamar lamarin asiri ne fa." Mom ta faɗa. "Yanzu gashinan har ta kai ga saki ya shiga."  "Ai wannan sakin yanzu zai warwarshi." Mom ta bawa Umma amsa. "A'a mene dalilin yin sakin, Senate fa kowa shaidane yadda yake matuƙar ƙaunar Bhatool." Abdul ya faɗa. Ƙara gwada lambar Senate Mom ta yi amma ba ta tafiya, ita yanzu duk tsoronta kar wani abu ya sami Senate ɗin. "Umma ina kwana?." Sai a lokacin ma idon su ya kai kan Ahmad da ke tsaye. "Lafiya ƙalau Ahamd."  "Ya mai jikin?."  "Jiki Alhamdulillah wallahi." "Allah Ya ƙara lafiya."  "Amin Amin."  "Bhatool sannu." Ya faɗa yana kallon Bhatool. "Yawwa."  "Ya jikin naki?."  "Da sauƙi."  "Allah Ya ƙara sauƙi."  "Amin na gode." Daidai kuma lokacin likita ya shigo, kallon Bhatool ya yi sannan ya ce. "Ma sha Allah, ta bude idon kenan?." "Eyh wallahi Dakta." Umma ta faɗa. "Daman na faɗa miki, ba wata matsala ba ce kuma Alhamdu Lillah cikin jikinta bai sami matsala ba, sai dai tana buƙatar dogon hutu sosai da sosai."  "Tom in sha Allah za ta huta." Umma ta faɗa. "Yanzu zuwa yaushe za a iya sallamarta?." Mom ta tambayi likitan. "Ko yanzu ma, magunguna kawai za a amsa."  "Okay tom ba matsala, Maman Bhatool me zai hana Bhatool ta tawo gidana?." "Amma da ta ce gidan Yaya Karima zata zauna, kuma ina ganin kamar hakan zaifi sabida 'yar uwarta ce kuma zata fi sakewa ta yi magana da ita akan abinda ke damunta." Abdul ya faɗa, sabida ba ya so ta je gidan Mom.  "Eyh hakan ma ya yi tom." Mom ɗin ta faɗa. "Ai Abdul da taje can ɗin, ko ina ɗaya ne ai." Umma ta faɗa. "A'a ai ba matsala gidan Kariman da gidana ai duk abu daya ne, kuma kinga kusa ne, sannan kinga ni bamfiya zama ba."  "Tom babu matsala hakan ma, Allah yasa hakane yafi alheri."  "Amin Amin."  Tashi Abdul ya yi ya riƙe hannun Ahmad suka fice, daman Abdul haka yake buƙata bai bari sun gama fita ba ya ce. "Wai sakin Bhatool yaron can ya yi?." "Wallahi haka ta ce."  "Amma fa yaron nan baida hankali, gaba daya an sangarta shi da kudi a gida, ya dauka aure hauka ne?."  "Zafin kishi ne kawai ya yi masa yawa, kwanaki da muka yi magana da ita ta ce wai zarginta yake tana kula ka."  "Ni kuma?." Ahamd ya tambaya. "Eyh kuma ya ga yanzu muna mutuncu shine yake tunanin ni nake so na kashe mata aure na baka ita."  "To yanzu ai ya kashe auren, ba a jindaɗi da mutuwar aure, amma kuma ance wani hanin ga Allah, baiwa ce."  "Allah Ya kyauta." Abdul ya faɗa. "Yanzu ina zaka?." "Zan kira Yaya Karima na faɗa mata ne, sabida ba tasan komai ba akai."  "Okay yakamta kam."  ***** A motar Mom aka dauƙi Bhatool, Umma dai ta ce gida zata tafi tazo daga baya, Senate kuma da Ahmad suka bi su a baya.  Yaya Karima ba ƙaramin Mamaki ta yi ba da aka ce wai Senate ya saki Bhatool, abun ma kai bazai dauka ba. "Yaya nifa ba duk wannan ba ne ya dameni, akwai wani abu da Umma ke ɓoye mana tsakaninta da Abban Senate."  "Waye Abban Senate?." Yaya Karima ta tambaya. "Baban Senate dai, ɗazu ni da Bhatool mun ga abinda muka gani a asibiti."  "Me kuka gani?." "Ni nasan komai." Bhatool ta faɗa. "Me kika sani?." Inji Yaya karima. "Abba Senate shine Yunusa wanda Umma ta so shi kafin aka aura mata abbanmu."  "Tabbas Abba ya sha faɗan mana cewa, Umma mutuniyar kirki ce ta aureshi ba tare da tana son shi ba, amma ta yi masa biyayyar da ba ta taɓa saɓa masa ba."  Yaya Karima ta faɗa. "Ke waye ya ce miki shine?."  "Tun ranar da na fara ganinsa a gidansa naji a jikkna kamar nasan shi, kwanaki da muka zuana a gidan ni da Senate, na shiga babban falonsa kai masa fruit da Mom tasa Senate shi kuma yasani, log book ɗinsa dake kan table na bude hoton Umma ne a farko amma tun ba ta kai shekaruna ba, sao dgaa baya ma na yu tunanin yana sane yasa naga hoton sabida na fahimci komai." "Ikon Allah." Yaya karima ta faɗa, Abdul kam cewa ya yi. "To sai mene, a yanzu dai yasan baza ta taɓa auren sa ba."  "Abduk kai yaro ne bakasan soyayya ba, kai nufinka hawayen da ka ga Umma na yi na mene idan ba na soyayya ba." Bhatool ta faɗa. "Nine yaron dan ubanki abinda nasani baki sani ba." "Dan Allah ku bar wannan maganar haka, ni hankalina yana kan mutuwar auren Bhatool."  "Wallahi ni Yaya mamaki abun yake bani fa." Abdul ya faɗa. "Ni kaina haka me yake damun Senate."  "Yaya ba abin mamaki ba ne idan kika duba hotonan da ya turumun."  "Wanne hotona?." "Shi yasa na tambaya ina wayata, hoto ne a zaune cafteria kuma asalin hoton ni da Jannah da Amrah ne, amma aka yanke su, sanan wani kuma  ina rungume da namiji."  "Rungume kuma, innullahi wainna illahir raji'un." Yaya karima tafaɗa, Abdul kama ta shi ya yi ya fice. "Ina zaka?." "Zanje na ɗakko wayarta ta ne."  "Eyh yakamata kam." Kuka Bhatool ta fashe da shi, gaba ɗaya abun ya dawo ma ta sabo, wane irim abu ne haka me aka shirya ma ta haka.  "Ki yi hakuri Bhatool, komai zai zo da sauƙi."  "Yaya me na yi haka, waye yake son kashen aure haka?."  "Koma wane komai zai bayyana in sha Allah." ***** Amrah ce zaune kan gadon ɗakinta wayarta na riƙe a hannu ta kara ta a kunne. "Salamu alaikum." Ta faɗa bayan an ɗaga wayar, bayan amsa ne ta ce. "Anty aiki ya cika, Senate ya saki Bhatool."  Mun dawo bayan sallah, littafi ya kusa kammala, ina fatan kunyi sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana ya kuma sa munyi ibada karɓaɓɓiya.  Legendspen 08129553971. HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da biyu (42) Amrah ce zaune kan gadon ɗakinta wayarta na riƙe a hannu ta kara ta a kunne. "Salamu alaikum." Ta faɗa bayan an ɗaga wayar, bayan amsa ne ta ce. "Anty aiki ya cika, Senate ya saki Bhatool."  Shiru ta yi na 'yan mintuna sannan ta ce. "Anty ya nawa saƙon."  "Zakiji ni." Matar ta faɗa, Amrah ta yi wani murmushin jindaɗi, Bayan kusan mintuna talatin da amsa kiran "Anty", Amrah ta zauna a gefen gado tana duba wayarta, zuciyarta fara ƙal , idanunta kawai zaka kalla ga wani irin farin cikin da ba za a iya misalta shi ba. Ta dade tana jiran wannan ranar, ranar da za ta ga rugujewar auren Bhatool. A ganinta, Bhatool ba ta dace da Senate ba, kuma ba ta dace da dukiyar da take ciki ba.  "Ke wacece da zaki mallaki zuciyar Senate, mutumin da tun ranar da na fara ganinshi a makaranta ya mallake zuciyata?" Ta fada kasa-kasa tana huci. Wayarta ce ta sake yin ruri alamun saƙo ya shigo, ta ɗauka ta duba ta ga sunnan Jannah. "Amrah, ina kike? Na ji labari wai Bhatool ba ta da lafiya tana asibiti, kuma na kira wayarta ba ta shiga, kina ina kizo muje ki kirani, idan na kiraki ba ta tafiya." Tsaki Amrah ta ja, ta watsar da wayar gefe. "Ke dai nan kika sani Jannah, baki san sauran ba. Ai yanzu an wuce wurin jinya, gidan miji ne aka raba ta dashi daman ba na ta ba ne." Ta sake murmushin mugunta, ta tashi ta nufi banɗaki tana jin kanta kamar wata da ta ci nasara a babban yaƙi. A can gidan Yaya Karima kuwa, dakin ya yi tsit, Bhatool ce kawai ke kuka sama sama, wanda yake fitowa a hankali. Yaya Karima tana zaune gefenta tana shafa mata baya, amma ita kanta Yaya Kariman zuciyarta ba daɗi. "Bhatool, dakata da kukan nan haka. Kin san fa kina da juna biyu, kuma likita ya ce kina buƙatar hutu." Yaya Karima ta faɗa cikin muryar lallashi. "Yaya, ta yaya zan yi shiru, wani irin hutu kuma? Ta yaya zuciyata za ta samu natsuwa bayan anyi mini ƙazafi a wajen mijina. An zubar mun da mutuncina? Senate ya kira ni 'munafuka', 'muguwa', sannan ya ce bai yafe mini hakkinsa ba. Me na yi masa Karima? Me na yi wa Senate?" "Kiyi hakuri, kishi ne ya rufe masa idanu. Amma babban abin dubawa a nan shi ne. Waye ya dauki hotunan nan? Kuma waye ya tura masa? Kinsan Senate yana Abuja, wani ne yake leɓe dake a yake kai masa rahoto." "Yaya baki ga hoton ba fa, har da wanda nake rungume da namiji da zallunci."  Bhatool ta share hawayenta, ta tashi zaune da kyar. "Yaya, kin san abin da nake tunawa? Ranar da muka je cafeteria da Amrah da Jannah. A ranar ne kawai na sanya wannan lace ɗin da aka nuna a hoton, sai dai kuma Amrah da na arawa lace din ta je biki dashi, kuma ma ta ce bata saba sabida ta yi ankon."  Yaya Karima ta zuba wa Bhatool ido. "Amrah? Bhatool, kina nufin Amrah ta ari kayanki?" "Kwarai kuwa Yaya, kuma ranar tare muka je cafteria ita da Jannah ne kawayen da nake tare da su." Shiru dakin ya sake yin, kowacce cikinsu tana juya tunani a ranta. Yaya Karima tana son halin Amrah tun a lokacin bikin Bhatool, ta ga yanayinta kamar mace ce mai son kai, amma ba ta taɓa tunanin za ta iya kaiwa ga ruguza auren kawarta ba. A Abuja kuwa, Senate yana zaune a cikin dakin hotel dinsa, dakin ya yi kaca-kaca da takardu da rabobin ruwa da ya watsar. Gaba daya aikin da ya kai shi ya fice masa a kai. Duk lokacin da ya rufe idonsa, hoton Bhatool yake gani tana murmushi, amma sai hoton da aka turo masa ya dishasha wannan murmushin. Anas ne ya shigo dakin, ya dade yana bugawa ba a bude ba, sai da ya sanya ma'aikatan hotel din suka bude masa. "Senate! Me kake yi haka? Ka duba kanka kuwa?" Senate bai dago ba, muryarsa ta fito a shake. "Anas, na sake ta. Na raba kaina da ita." "Kayi hauka ne? Saki? Akan hoton da baka tabbatar da gaskiyarsa ba? senate, kasan fa makiya suna da yawa. Kasan yadda kake da kudi da daukaka, mutane da dama ba sa son ganin ka rasa afarin cikinka." "Anas, hoton fa na gani da idona. Tana sanye da lace din da na saya mata, lace din da na kwaso mata da kaina daga gida. Ta yaya zan karyata abin da idona ya gani?" "To amma baka ga fuskar namijin ba, kuma baka ga babu fuskar macen a jikin namijin ba. Me zai hana ka jira ka dawo? Me yasa ka yi gaggawa?" Senate ya tashi tsaye, idanunsa sun yi jawur. "Saboda ina son ta Anas! Ina son ta fiye da yadda kake tunani. Zafin soyayyar ne ya sa nake jin kamar ana huda zuciyata da mashi. Ba zan iya jure ganin wani namiji ya taba ta ba." "To idan ta kasance ba ita ba ce fa? Idan sharri aka yi mata fa? Usman, ka tuna tana da juna biyu. Ka taba tunanin halin da za ta shiga?" Anas ya girgiza kai, ya san halin abokinsa idan kishi ya taba shi, baya gani baya ji. Ya juya zai fita, sai ya tsaya ya ce, "Mom ta dade tana kiran wayarka ka ki dagawa. Tana can asibiti wurin Bhatool. Idan kana son kanka da alheri, ka kira mahaifiyarka." Can gidan Dad kuwa, Mom ta samu Dad a daki zaune yana kallon wani tsohon hoto. Tunda suka bar asibiti Dad ya shige daki ya ki fitowa, har abincin dare ma cewa ya yi ba ya bukatar sa. Mom ta karasa kusa da shi, muryarta a sanyaye.  "Alhaji, mene ne tsakaninka da Maman Bhatool? Na ga yadda kuka rude lokacin da kuka hada ido." Dad ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ya mika mata hoton dake hannunsa. Hoton Umma ne tun tana budurwa, tana murmushi dauke da littattafai a hannunta. "A'isha, wannan ita ce 'First Love' dina da nake fada miki. Wannan ita ce Habiba da na shafe shekaru ina nema, wadda nake tunanin ta rasu." Mom ta ja numfashi, ta zauna a gefen gado. "Kace min mahaifiyar sirikarka ita ce macen da kake so ka aura?" "Ban sani ba Zainab. Ban taba sanin cewa diyar Habiba ce Usman ya aura ba. Sai yau da na ganta a asibiti, na ga kamaninta da Habiba suka kasance daya. Tabbas, Habiba ita ce rayuwata ta baya, kuma har yanzu ina jin muryarta a cikin zuciyata." "Amma Alhaji, kasan fa yanzu 'ya'yanku sun yi aure? Kasan irin sarƙaƙiyar da wannan zai haifar?" "Na sani. Amma ai yanzu Usman ya sake ta, ko ba haka ba?" Dad ya tambaya yana kallon Mom. Mom ta gyada kai cikin damuwa. "Eh, ya sake ta. Amma ina kyautata zaton akwai makirci a ciki. Alhaji, idan har kana son Habiba, kuma Usman yana son Bhatool, ta yaya zamu daidaita wannan lamarin ba tare da kowa ya ji ciwo ba?" Dad ya yi shiru, tunaninsa ya tafi can shekaru ashirin da suka wuce, lokacin da aka raba shi da Habiba. Yanzu kuma ashe ɗansa ne ke fuskantar kaddara irin tasa? Abdul ne ya shigo ɗakin fuskarsa babu fara'a. Su Bhatool na ganin shi suka miƙe. "Lafiyanka Abdul?." Yaya karima ta tambaya. "Bhatool, na je na ɗakko miki wayar taki, amma kuma naga Screen ɗin wayar ya fashe gaba ɗaya, alamar ya bugu ne lokacin da kika yanke jiki kika faɗi." Bhatool ta kalli wayar, ta ji wani sabon takaici. "Abdul, dan Allah ka kai mini gidan gyara, ina son ganin hotunan da ya tura mini, ina son sanin yadda aka kulla mini wannan makircin." "Karki damu, yanzu zan kai ta kasuwa a gyara screen ɗin, kafin nan ki kwanta ki huta," Abdul ya faɗa tare da ficewa da wayar a hannunsa. "Bhatool na tambaye ki mana." Yaya karima ta faɗa. "Ina jinki Yaya?."  "Yaushe ne ranar da kuka fara samun matsa da Senate a aurenku?." Shiru Bhatool ta yi, tana son tun ranar da suka fara samun matsala da Senate. "Yaya kamar ranar ta biyu ko ta uku?."  "Wani abu ya faru ranar, kin masa laifi ne ko ya saki wani abu kin ƙi yi?."  "A'a Yaya, ya fita lafiyar Allah har Amrah ma da tazo munyi waya a gabanta, bayan ya dawo ne ya ce kansa yana masa ciwo, to daga nan muka fara samun matsala."  "Amrah ta zo gidanki a ranar, me ta yi daga kaiki?."  "Tazo ganin gida ne fa, mun shiga mun duba ma ko ina da ita."  "Bhatool yaushe zaki yi hankali ne dan uwarki?." "Me na yi kuma?." "Bayanan sai yaushe kuka sake samun saɓani?." "Ai Yaya daga ranar muka fara har zuwa ranar da muka rabu." "Wanne irin abubuwa ne suke faruwa ranar da Amrah ta zo gidanki?." Shiru Bhatool ta yi sannan ta ce. "Da yawa bazan iya tunawa ba, amma akwai lokaci da ta zo ta ce sai na rakata waje wallahi a ranar lafiya kalau muke da shi ya fita, amma da ya dawo sai dai ya ce angaya masa na kula Ahmad."  "Jannah fa?." Yaya Jarima ta tambayeta.  "Ita ba sosai ba, ba ta zuwa gidana Amrah ta ce sunyi faɗa amma ranar da naje makaranta sai naga ba haka ba ne, wai sai take ce mini wai  tana cewa Amrah yaushe zasu sai Amrah ta ce ba yanzu ba, kuma fa Amrah idan tazo sai ta ce Jannah ba ta zuwa makaranta kuma Jannah ta ce duk attendence tana mini, ni nakasa gane kan Amran ma wallahi Allah."  Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da Uku (43) Shiru ya ratsa ɗakin na wasu mintuna, baka jin komai sai ƙarar fanka dake juyawa a hankali tana raba iska. Bhatool tana zaune ta jingina bayanta da jikin gado, idanunta sun yi jawur saboda kuka, yayin da Yaya Karima take zaune a gefenta, tana kallon yadda ƙanwar tata take abun tausayi.  Yaya Karima ta gyara zama, ta kalli Bhatool cikin nutsuwa sannan ta ce, "Bhatool, kinsan rayuwa tana da ban mamaki. Wani lokacin mutumin da muke gani a matsayin garkuwanmu, shi ne yake zama silar rugujewarmu. Ba na son in yanke miki hukunci akan kawayenki, amma ina so ki duba abubuwan da suka faru a baya da idon basira. Shin babu wani abu da kike gani ya yi hannun riga da gaskiya?" Bhatool ta numfasa, sanna ta ce. "Yaya ƙawaye na guda biyu ne, daga Amrah sai Jannah sai kuma Suhaima, tun da ta yi aure suka bar ƙasar, ada ina ganin Jannah kamar ba mutuniyar arziƙi ba, tana mini baƙin ciki ne janye jikinta daga gare mu sabida bakin ciki."  "Me yasa kika yi wannan tunanin?." Yaya karima ta tambayi Bhatool, shiru Bhatool ta yi tana son ta tuna da abinda ya faru, sai kuma can ta ce. "Ranar da na faɗa musu zamuje honeymoon sai ta ce wai na dinga riƙe sirri na, da na fa ɗawa Amrah sai ta ce wai baƙin ciki take mini, na auri Senate."  "Yanzu kuma ya kike gani?."  "Yaya Amrah ce kawai ke mini yawo a raina, kuma bana so ace ita ce ta yaudareni, bana so ace ita ce ta ci amanata wallahi." "Ki nitsu Bhatool, ki yi tunani duk wasu matsaloli da kika samu a rayuwarki tun kafin aure da lokacin aure, sai kiga akwai mai alaƙa da Jannah ko Amrah?."  Shiru Bhatool ta yi ta fara lissafa abubuwan da suka faru a baya a cikin ranta. Can kuma sai ta tuna wani abu, ta kalli Yaya Karima da sauri. "Yaya, kin tuna ranar da Dr. Haisam ya kira ni ya ce mini zan yi aure, har ya ce zanga abinda zai faru ko?." Gyaɗa kai Yaya Karima ta yi sannan ta ce. "Ranar babu wanda na faɗa wa maganar daga Jannah sai ita Amrah, kuma ita Jannah a lokacin muna tsaka da waya ya kirani sabida ita Amrah mamansu ta kira muna voice call ɗin ta sauka, to ni dai su biyu na faɗawa wannan labarin, na aure na da Senate kafin maganar ta fita. Sannan akwai wata rana da Amrah ta kirani ta ce mini wai Dr. Haisam yana yi mata barazana akan sai ta ba shi address ɗina. Ta ce mini tana tsoron abin da zai faru idan ba ta ba shi ba, shi ya sa ta ba shi gidanmu. Ranar da yazo gidan nan ɗinnan har naƙi fita, yaya wai me ke faruwa ne tsakanina da Amrah daman ba soyayya ba ce, ba ƙawance ba ne, to mene?."  Yaya Karima ta girgiza kai cikin tsananin takaici. "Bhatool, a ko da yaushe ina faɗa miki cewa kiyi hattara, amma kika ce ƙawaye ƙawaye, yanzu wa za ki tin kara ki ce. Ƙawar ki ce ta kashe miki aure, wannan abun ya yi kama da na hankali Bhatool, Amrah tana amfani da rauninki ne wajen cin miki dunduniya. Ta yaya Dr. Haisam zai yi mata barazana akan address ɗinki alhali tana da ikon ƙin ba shi, ko kuma ta ba shu na gaibu, Wannan duk dabarun raba miki hankali ne." Bhatool ta runtse idonta, tana jin wani irin daci a ranta. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Yaya, ashe Amrah ba ƙawa ba ce, ashe ita ce take kitsa mini dukkan wannan masifar?"  "Idan Amrah da kitsa miki ai kina da babban laifi, har da daukan suttura ki ara mata, me ya shiga kanki ne?." ~~~~Hausari.  Gidansu Goggo Larai ya cakuɗe, su Hari da Furee yan maza sun daina zuwa sabida yadda su kawu Ilyasu suke roƙarsu kuɗi kai tsaye, Goggo Larai ta matso taga yaran sunyi aure amma iyayensu maza basa bari samarin su zauna, yau tun safe aka tashi da tashin hankali akan jiya kawu Mufi ya roƙi saurayin Furee shi kuma ya ce ya daina zuwa. Furee da Habi duk sun rasa inda za su sa kansu, ita kanta Goggo Larai ta yi danasanin karɓo su "Wannan wane irin hauka ne haka? Yanzu abin da ake gudu ya faru kenan? Saurayi ɗaya da ya rage ya ce shima ya daina zuwa, mene amfanin haka, bakwason yaran naku su auro ne ko ya?." Goggo Larai ta faɗa tana kuka tana. Furee ta kalli Habi, sannan ta ce, "Mu tafi gidan Umma kawai. Ba za mu iya zama a nan ba muna ji muna gani. Kowa zai gudu mu aure muke so." "Ku tafi na amince wallahi, ku tafi ni ƙiyayyar Habiba da 'ya'yanta ba ta yi minu rana ba, wallahi na yi danasani, na tuba ku tafi dani na nemi yafiyarsu haba." **** Amrah tana zaune a ɗakinta, ta kira wayar Anty kusan sau biyar amma ba ta ɗaga ba. Gaba daya abun ya tsaya ma ta, ita ta raba auren Bhatool da zuciya biyu ne, ita duk ƙiyayyarta ba ta kai ta ga raba auren su ba, amma wannan matar tai ta ɗora ta akan hanya ba ta yi mata alkwarin aura mata ɗan ta bayan ta raba auren, to amma yanzu gashi kwata kwata ta daina daukar wayarta, ƙara buga wayar ta yi amma still ba a ɗaga ba, ba shiri ta miƙe ta ɗau mayafinta. "Banga ta zama ba wallahi." Ta faɗa tana ficewa.  Kai tsaye gidan Anty ta nufa, duk da ba mazauniyar garin ba ce amma tana garin babu wamda yasan ta na nan sai Amrah, ita ma sabida tana bata abinda za ta sawa Bhatool a gida ko Senate a ɗaki. Tana cikin napep tana faman tuna-tuna ne kala kala. "Yanzu idan matar nan ta yaudare ni ina na kama?."   "Ai walalhi ita ma sai na yi mata tijara, kan uba." Ta faɗa daidai lokacin da ta ƙaraso ƙofar gidan. Tana shiga gidaan ta tarar da Anty zaune a babban falonta tana kallon talabijin cike da natsuwa. Amrah ta shiga da sallama ta durƙusa tana gaisheta, wani mugun kallo Anty ta watsa ma ta. Wadda ba kowa ba ce fa ce  Maman Anas, ƙanwar Mom uwa daya uba daya.  "Ina kiran wayarki bakya gani." Amrah fa faɗa ganin baza ta amsa ma ta ba. "Ina gani Amrah me zan yi miki?." Da mamaki Amrah ta kalleta sannam ta ce. "Kinsani ayyuka kuma na yi miki su, kin yi mini alƙwari kala kala ciki har da na zaki auran ɗanki Amas bayan na raba Bhatool da Senate, sabida acewar ki 'yar ki Namrah ce ta da ce da Senate, kinsanni duk wani aiki, ki bani magani na zuzuba a gidan, kin sa naje na jawo ta waje, kin haɗa tuggu da hoton Ahmad wanda kika sa aka kira shi da muryar namiji akan yazo su haɗu da abokinsa, wanda ba komai ba ne fa ce son haɗa Bhatool da Senate faɗa, bayan ta fito kika ɗauƙi hotonsu suna gaisawa aka turawa Senate, kinsa na ari kayanta na kawo miki, kinsan na jata cafetria da kayan kinsa anyi mata huto, an turawa mijin kuma auren ya mutu, na cika miki alƙwarin da na yi miki a lokacim bikin, dan haka nima a yanzu ina buƙatar nawa cikon alƙwarin."  "Amma Amrah baki da hankali, kina tunanim yadda kika sam amfanin bin malamai a yanzu zan bari na haɗaki da ɗana ki yi aure shi, tabbas Amrah, kinyi mini aiki mai kyau. Dan haka kingama amfanin ki."  "Wallahi kin cuceni wallahi Allah." Dariya Anty ta yi sannan ta ce. "Ban cuce ki ba, kika cuci kanki, ni kawai na yi amfani da kishinki, mugun halinki, baƙin ciki irim naki, na haɗa su da hikimata na yi amfani dake wajen ganin na raba su." Anty ta faɗa sannam ta ce. "Yanzu ki tashi ki bani waje sannan karki sake zuwa inda nake."  "Wallahi baki isa ba, sai kin biya farashin abinda kika yi kuma sai na tona miki asiri, sai kin hulaƙanta, wallahi." Amrah ta faɗa tana tashi. ***** Su Bhatool suna zaune Abdul ne ya shigo gidan, hannunsa ɗauke da wayar Bhatool. " Sannu da zuwa." Bhatool ta faɗa. "Yawwa Bhatool, ga wayar nan an gyara."  "Ka fara cin abinci." Bhatool ta faɗa, zama ya yi sannan ya ce. "Na ci a waje." Karɓar wayar ta yi ta buɗe wayar ta shiga cikin gallery, idanunta suka sauka akan hotunan da Senate ya turu. Hoton farko ita ce zaune a cafeteria, an yanke hoton su Amrah an bar ta ita kaɗai. Amma babban tashin hankalin shi ne hoton gaba wanda take rungume da wani.  Wani irin kuka ne ya ƙwace wa Bhatool lokacin da ta ga yadda aka shirya hoton. "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Yaya kalli hoton! Wannan fa ba ni ba ce, kina gani, yaushe na kai haka ƙiba, wallahi wata macen ce aka saka da kalal kayan nawa."  "To ko Amrah ɗin ce?." Yaya karima ta tambaya tana amsar wayar. "Ita ma ba ta kai haka ƙiba." Abdul ne ya karɓa bayan Yaya karima ta gama gani. "Wannan hoton wata ne aka sanya fuskarki a jiki ta hanyar amfani da computer (AI). Yaya kalli yadda wuyan macen yake daban da na Bhatool." "Amrah... Amrah kin cuce ni!" Bhatool ta faɗa tana kuka mai ban tausayi. A Abuja kuwa, Mom tana ta ƙoƙarin kiran Senate. Daga ƙarshe ya ɗaga wayar, amma muryarsa ta fito a shake, irin ta mutumin da ya sha kuka ko kuma ya rasa natsuwa. "senate me kake yi haka? Ka dawo gida yanzu! Ina son mu tattauna wannan maganar fuska da-fuska," Mom ta faɗa cikin murya mai zafi. Senate ya yi shiru na wasu daƙiƙoƙi, sannan ya ce, "Mom, don Allah ki yi haƙuri. Ba zan iya dawowa yanzu ba. Zuciyata tana mini zafi, kuma ba na son in ga kowa a halin yanzu. Na san abin da kike son faɗa, amma hotunan da na gani sun riga sun yanke mini hukunci." "senate karka zama mai saurin fushi! Shin baka san cewa makiya na iya shirya komai ba?" "Mom, please... zan dawo idan na samu natsuwa. Amma yanzu, bar ni in kaɗai Bhatool kuma na haƙura da ita har Abada."  Ya faɗa  tare da kashe wayar cikin halinsa na rashin son yawan magana idan ransa ya ɓaci. Ya kashe wayar ya bar Mom cikin damuwa. "Na haƙura dake Bhatool... na haƙura dake har abada Bhatool, ki je ki yi duk abinda kike so, duk abinda kika ga dama." Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da huɗu (44)) "senate karka zama mai saurin fushi! Shin baka san cewa makiya na iya shirya komai ba?" "Mom, please... zan dawo idan na samu natsuwa. Amma yanzu, bar ni in kaɗai Bhatool kuma na haƙura da ita har Abada."  Ya faɗa  tare da kashe wayar cikin halinsa na rashin son yawan magana idan ransa ya ɓaci. Ya kashe wayar ya bar Mom cikin damuwa. "Na haƙura dake Bhatool... na haƙura dake har abada Bhatool, ki je ki yi duk abinda kike so, duk abinda kika ga dama." Amrah ta fito daga gidan Anty (Maman Anas) tana wani irin kuka mai cin zuciya, wanda ya sa har mutanen dake wucewa a kan titi suke kallonta. Zuciyarta tana mata wani irin zafi, kalaman Anty dake nuna cewa an yi amfani da ita ne kawai don biyan bukatar wata daban suna ta kai-kawo a kanta. "Ashe ni ma yaudarata aka yi? Ashe ba don ni aka yi wannan shirin ba?" Ta faɗa a cikin ranta tana goge hawayen dake bin kuncinta. Ba ta tsaya ko'ina ba sai gidansu Jannah. Tana shiga ta iske Jannah a tsakar gida tana gyara wasu littattafai. Jannah ta tashi da sauri ganin halin da Amrah take ciki. "Lafiya Amrah? Me ya faru kike kuka haka?" Jannah ta tambaya cikin firgici. Durƙusawa Amrah ta yi a ƙasa, ta rufe fuskarta da hannu biyu tana sheshsheƙar kuka. "Jannah na cuci kaina, na cuci Bhatool, na ruguza auren da ba ni da tabbacin zan iya maye gurbinsa. Jannah ashe Anty amfani da ni ta yi, ashe kishina ne aka yi amfani da shi aka raba auren Senate da Bhatool ba don ni ba." Jannah ta zaro ido, ta jawo Amrah ta zaunar da ita a kan kujera. "Amrah me kike cewa haka? Kina nufin duk abubuwan da suke faruwa ke kika kitsa su?" Cikin kuka da nadama, Amrah ta kwashe dukkan abin da ya faru ta faɗawa Jannah. Ta faɗa mata yadda suka shirya hotunan da aka liƙa fuskokin Bhatool ta hanyar amfani da fasahar zamani (AI), da yadda ta ari lace ɗin Bhatool aka yi amfani da shi aka ɗauki hoton wata daban. "Jannah ina son in wanke Bhatool, ina son in gyara kuskurena ko da hakan zai sa kowa ya tsane ni. Zuciyata ba ta ba ni damar yin bacci ba tun bayan da na ji an sake ta." Amrah ta faɗa muryarta tana rawa. Jannah ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalli Amrah cikin tausayawa da kuma fushi. "Amrah, gaskiya kin tafi wurin da ya wuce tunaninki. Amma tunda Allah ya sa kin yi nadama, to tashi mu tafi gidan Yaya Karima yanzu. Dole ne kowa ya san gaskiyar abin da ya faru kafin lokaci ya ƙure." Jannah ta faɗa tana miƙewa don ɗauko mayafinta. A can gidan Yaya Karima kuwa, falon ya cika makil. Mom ce zaune a kan kujera, fuskarta ɗauke da damuwa tana ta kallon Bhatool dake kwance a jikin Yaya Karima. Abdul yana zaune a ƙasa riƙe da wayar Bhatool dake gyare, yayin da Mijin Yaya Karima, Barrister Al-Amin, yake zaune yana duba wasu takardu, amma hankalinsa duka yana kan maganar da ake yi. "Mom, gaskiya wannan lamari akwai duhu a cikinsa. Usman ya yi gaggawa wajen yanke hukunci ba tare da ya bincika ba," Barrister Al-Amin ya faɗa yana kallon Mom. "Haka ne Al-Amin. Ni kaina kiran da na yi masa ɗazu na ga cewa ya rufe kunnensa daga jin gaskiya. Amma ina tabbatar muku, muddin muka sami shaidar cewa wannan sharrin wani ne, to ni kaina zan sa ya dawo ya ba ta haƙuri," Mom ta ba shi amsa cikin murya mai natsuwa. Bhatool dai tana can tana saurarensu, hawaye kawai yake zarya a idonta. Tana tunanin yadda Amrah ta iya aikata mata haka, kawai sai ta ji an turo ƙofar falon. Amrah ce ta shigo, idanunta sun yi luhu-luhu saboda kuka, Jannah tana biye da ita a baya. Ganin Amrah ya sa Bhatool jin wani irin zafi ya taso mata daga ƙasan zuciya. Wani irin ƙarfi ne ya zo mata, ta miƙe tsaye da kyar tana nuna Amrah da yatsa, muryarta tana rawa saboda tsananin fushi. "Amrah! Me kika zo yi a nan? Kina son ki zo ki ƙarasa abin da kika fara ne? Kin cuce ni Amrah! Kin raba ni da mijina, kin zubar mini da mutuncina a idon duniya! Don Allah ki fita mana daga gida, muguwa kawai! Ba na son sake ganin fuskarki a rayuwata!" Bhatool ta faɗa tana rushewa da kuka mai ban tausayi, yayin da jikinta yake wani irin rawa. Mom da Yaya Karima duka suka miƙe tsaye cikin mamakin ganin Amrah a wannan lokacin. Abdul ya daka wa Amrah wani irin kallo na tsana, yayin da Barrister Al-Amin ya gyara zamansa yana jiran jin abin da zai biyo baya. Amrah ta kasa cewa uffan, sai kuka da take yi tana ƙoƙarin durƙusawa a ƙasan ƙafafun Bhatool. Jannah ce ta matso kusa da Bhatool, ta riƙe hannunta cikin lallashi. "Bhatool, don Allah ki yi haƙuri. Na san abin da Amrah ta yi miki ya wuce misali, amma don Allah ki saurare ta. Ta zo ne don ta gyara, ta zo ne don ta faɗi gaskiyar da za ta wanke ki a idon kowa." Jannah ta faɗa cikin muryar roƙo. Anan duka falon ya yi tsit, kowa yana jiran jin wane irin asiri ne Amrah za ta tona wanda zai iya canja akalar wannan babban al'amari. Falon ya yi tsit, har ana iya jin numfashin kowa dake wurin. Amrah ta durƙusa a ƙasa, kanta a duƙe, yayin da take sheshsheƙar kuka mai ban tausayi. Ta ɗago idanunta da suka yi jawur ta kalli Bhatool, sannan ta kalli Mom da Yaya Karima. "Bhatool, na san ba za ki taɓa yafe mini ba, amma don Allah ki saurari abin da zan faɗa. Ni ce na kulla miki dukkan abubuwan da suka faru, tun daga ranar farko da kika tare a gidan miji," Amrah ta faɗa muryarta tana rawa. Bhatool ta rufe fuskarta tana kuka, yayin da Barrister Al-Amin ya gyara zama ya ce, "Ci gaba Amrah, muna jinki. Faɗi komai filla-filla." Amrah ta ja numfashi, ta fara bayani cikin muryar nadama. "Ranar farko da na zo ganin gidanki Bhatool, ba ta yaki murna na zo ba. Na zo ne don in dasa miki abin da zai raba ki da Senate. Lokacin da kika kai ni zagaya gida, na yi amfani da damar da kika ba ni na shiga ɗakin baccinku, na ɗauki wani magani na fesa a ƙarƙashin gadonku, wanda nake tsammanin zai sa ku dinga jin ƙyamar juna. Kuma ranar da kika ga Senate ya dawo yana ciwon kai, ni ce na sanya hakan  turaren da fesa ne ya sanya mai ɓacin rai lokacin da yake waje." Mom ta zaro ido, ta dafe ƙirji tana faɗin, "Subhanallahi! Amrah ashe dukkan wannan abin ke kika yi?" Amrah ba ta tsaya ba, ta ci gaba. "Sannan ranar  dazo gidanki  na ja ki kika rakani waje duk shiri ne. Shi ma Ahamd mune muka shirya masa zuwa amma bai san da zuwan ki ba, mun yaudareshi ne kuma mine mu ka yi miki hoto, haka hoton nan na ari lace dinki nasa akayi hoton, shi ya sa na matsa miki lallai sai kin sanya wannan lace ɗin naki mai kyau. Na ce mikk na ari lace ɗin a wajenki da sunan zan tafi biki, amma ba inda naje nasanya ne, aka ɗauke ta hoto tana rungume da wani namiji a wani gida, sannan aka yi amfani da hoton fuskarki aka liƙa a jikinta." Yaya Karima ta girgiza kai cikin takaici. "Lallai Amrah kin yi nisa. Amma wacece ta ba ki wannan shawarar? Domin na san ba za ki iya yin wannan duka ke kaɗai ba." Amrah ta kalli Mom cikin tsoro, sannan ta ɗauko wayarta ta kunna wani sauti (recording). Muryar Anty (Maman Anas) ce ta fito sarai tana faɗin: "Amrah kinyi mini aiki mai kyau. Kin san fa Senate ɗana ne, kuma ba na son ganinsa da wannan yarinyar tun farko. Ke kin yi amfani da kishinki, ni kuma na yi amfani da hikimata wajen ganin na raba su..." Wani irin jiri ne ya kwashi Mom, ta koma ta zauna da sauri. "Anty? Maman Anas? Ƙanwata ce take son ruguza farin cikin ɗana?" Mom ta faɗa cikin wani irin murya mai ban tausayi, hawaye ya wanke mata fuska. Abdul ya daka wa Amrah tsawa. "Muguwa! Kalli irin abin da kika aikata. Kin ruguza aure saboda kishin banza." Bhatool ta miƙe tsaye, tana kallon Amrah cikin wani irin yanayi na tsana da tausayi lokaci guda. "Amrah, na gode da kika faɗi gaskiya. Amma ki sani, kin riga kin illata zuciyata. Kin raba ni da mutumin da na fi ƙauna a duniya." Barrister Al-Amin ya miƙe ya karɓi wayar Amrah dake ɗauke da recording ɗin. "Wannan ita ce shaidar da muke buƙata. Yanzu saura abu ɗaya, dole ne Senate ya ji wannan muryar, kuma dole ne ya ga wannan gaskiyar." Amrah ta rushe da kuka tana neman gafarar kowa dake wurin, amma kowa ya juya mata baya, domin abin da ta aikata ya wuce duk yadda ake tunani. "A'a tunda har Senate bai sami yarda dani ba, ya yarda da wani abu daban, har ya iya sakina nima na hakura da Senate har Abada." Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da Biyar  (45) Bayan kowa ya saurari muryar Anty (Maman Anas) a cikin rikodin ɗin da Amrah ta kawo, falon ya sake yin tsit na wasu daƙiƙo, Kowa yana sarrafa abin da ya ji a cikin ransa. Bhatool kam ta daina kukan da take yi dazu, fuskarta ta koma wani iri, babu sauran alamar karaya ko wani yanayin damuwa, dan ba ta ma san abinda zai dame ta ba, shin ƙawarta da ta ci amanrta ko kuma mijin da ya kasa yarda da ita?.  "Yanzu ke Amrah mene ribarki a wannan abun da kika aikata, gwanda ma ita Maman Anas din ta yi ne da burin ta raba auren dan 'yar uwarta dan tana ganin kamar bai dace da ita ba, da ta ta 'yar ya dace, ke fa?." Yaya Karima ta tambayi Amrah. "Nasani na kasance azzaluma, maci amana, mai fuska biyu na cuci kaina na cuci ƙawar da ta Aminta dani."  "Tabbas kincuci kanki, kincuci yarda da aminci amma baki cuci Bhatool ba, sabida ubangiji ya riga da ya tsara mata hakan, sannam Bhatool tun a farkon auren ku na nuna miki cewaer ki dinga riƙe sirrinki amma sai kika watsar dani, karshe ma kika daina nemana, har ita Amrah ta fira sabgata a makaranta sai dai ni na me ta, yanzu wa gari ya waya, na fada miki cewa ba kowanne murmushi ba ne soyayya." Jannah ta faɗa. "Ki yi haƙuri ki yafe mini Bhatool dan Allah dan Annabi."  "Amrah ni bazan riƙe ki ba, sabida na zauna dake da zuciya ɗaya na yarda dake, amma kika ci amana, na barki da ubangiji ya yi miki duk sakkayar da ya ga dama, muddin kina doran duniya bana jin zan yafe miki, amma daga ranar da na riga ki mutuwa tabbas kam na yafe miki." Kuka Amrah ta fashe da shi, Mom kam ta ce. "Ni Amrah banda bakin da zance na yafe miki ko a'a, abun kunyar da 'yar uwata tabar mini ka ɗai ya isheni."  Jannah ce ta miƙi tsaye sannan ta ce. "Amrah idan kina da tunani yanzu lokaci ne da zaki gyara rayuwarki, ki tuba kafin ki koma ga mahallinci ki, ni baki yi mini komai ba a zaman mu dake, idan ma kin yi to bansani ba kuma na yafe miki, amma  kanwance kamar da na gama in sha Allah."  Taba fadin haka ta fice, Bhatool ta kalli Abdul. "Ka mayar dani gida wajen Umma zan koma, duk kayana da suke gidansa a dawo dasu kawai."  "Me yasa Bhatool?." Mom ta tambayeta. "Mom duk abun nan da ya faru ba zai canja abin da Senate ya yi mini ba. Ya yarda da kowa, ya ƙaryata ni. Ya yarda da hotuna, ya yi watsi da amanar da ya ce yana da ita a kaina." Mom ta matso kusa da ita, muryarta a sanyaye. "Bhatool, kiyi haƙuri. Kina gani yanzu asiri ya tonu. Kowa ya san gaskiya yanzu. Senate ya yi kuskure ne saboda tsananin kishi, amma idan ya ji wannan gaskiyar, na tabbata zai dawo ya roƙi gafararki." Murmushin takaici Bhatool ta yi, ta girgiza kai. "Mom, don Allah kiyi haƙuri. Ni kam na haƙura da Senate tun da har shi ma ya iya haƙura da ni cikin sauƙi haka. Ba zan koma gidan da aka wulakanta ni ba. Zan raini cikina a duk inda nake har Allah Ya sa na haife shi lafiya, amma batun Senate na riga na cire shi a raina. Yanzu abin da nake so, Abdul ka ɗauko mini kayana, gidan Umma zan koma yanzu." "A'a Bhatool! Kar kiyi haka. Kina cikin idda fa, kuma kinsan idan kika koma gida kowa zai ta yamaɗiɗi ne da zancen," Yaya Karima ta faɗa cikin tashin hankali tana son ba ta baki, dan duk sunyi mamakin hukuncin da ta yanke. Amrah dai simi simi ta faki ido ta tashi ta fice, Bhatool kam ta ce "Yaya Karima, na riga na yanke shawara. Ba na son zama a inda zan dinga tunawa da wannan cin amana. Abdul, don Allah ka shirya mu tafi," Bhatool ta faɗa cikin murya mai nuna cewa ba za ta canja ra'ayi ba. "Tashi to mu tafi." Abdul ya faɗa. "A'a fa Abdul anan zata zauna." Yaya karima ta faɗa. "To muje wjen Umma duk hukunci da ta yanke shikenan." Ba musu kowa ya tashi, Mom ma ta tashi ta yi na ta gidan, a falo ta tarar da Dad yana zaune, tana shiga ta zauna akan kujera ta hada hannu da kai. "Lafiya dai?."  "Ina lafiya." Mom ta fada tare da fara zubar da hawaye. "Me yafaru ne?." Dad ya faɗa hankali a tashe yana matsowa kusa da ita, kuka ta fara kamar ƙaramar yarinya domin tabbas abun yana cinta a rai. "Wai yanzu ace kamar 'yar uwata ce za ta yi wa Senate asiri, za ta sam duk yadda zata yi ta raba aurensa, duk akam tana son ya auri Ikilima."  "Ki yi hakuri, karki sa damuwa ki jawa kanki ciwo don abin da wata ta aikata," Dad ya faɗa yana tausar kafaɗunta. "Alhaji, yaya zan yi haƙuri? Ƙanwata ce fa! Matar da nake gani a matsayin jini na, ita ce ta sa aka raba auren ɗana. Kuma ga shi yanzu Bhatool ta ce ta haƙura da shi gaba ɗaya. Alhaji, idan Senate ya dawo ya iske ya rasa Bhatool, yaya kake jin zai kasance?" Mom ta faɗa cikin kuka. Dad ya numfasa, ya ce, "ki kyale ta da Allah. Ita kuma Bhatool, karki damu da fushin da take yi yanzu. Ai mace ce, kuma tana cikin raɗadi ne. Ga shi kuma tana da juna biyu. Kina ji ai yadda likitoci suke cewa, mai ciki tana saurin fushi. Amma kiyi tunani, akwai idda mai tsayi a gabanta tunda tana da juna biyu. Har sai ta haihu kafin lokacin auren ya ƙare gaba ɗaya. Kafin wannan lokacin, Senate zai dawo ya san gaskiya, ita kuma za ta sauko daga fushin da take yi. Mu ba ta lokaci kawai." Nasiha mai ratsa jiki Dad ya dinga yi wa Mom, yana nuna mata cewa komai lokaci ne, kuma Allah zai daidaita komai tunda asiri ya riga ya tonu. Bhatool ta takura lallai sai an kai ta gidan Umma. Abdul ya kasa musa mata ganin yadda take cikin matsanancin fushi. Yaya Karima ta ga ba za ta iya barin su su tafi su kaɗai ba, ta kalli mijinta. "Barrister, mu tashi mu tafi gaba ɗaya kawai. Ba zan iya barin Bhatool ta tafi a wannan halin ba." Haka kowa ya shirya, suka sanya Bhatool a mota suka nufi gidan Umma.   A cikin gidan Umma kam, tana zaune tana gyaran kayan miya ta ji sallama, murya har xa ta Goggo Larai, a ranta ta ce. "Kana tsaka da tashin hankali zasu zo su ƙara ma wani." Shigowa suka yi Umma ta miƙe da faɗin. "Goggo sannunku da zuwa." Cike da hawaye Goggo ta ce. "Yawwa, Yawwa Habiba, Habiba dan girman Allah, dan girman maaiki, dan daraja, dan ƙudura, dan zatin...."  "Goggo lafiya wai?." Umma ta katse ta cike da tashin hankali da fargabar abinda zata faɗa. "Habiba ki yafe mini, kisa 'ya'yanki su yafe mini, na cutar dake dasu cutarwa da banga amfanin ta ba, cutarwa da ba ta yi mini rana ba dan Allah ki yafe ni." Shiru Umma ta yi na 'yan mintuna sannan ta ce. "Tabbas kun cutar damu, amma bakomai ta ni na yafe muku suma 'ya'yana nasan zasu yafe muku." Goggo Larai ba ta kai ga yin magana ba Su Bhatool suka shigo.  Baki sake suka kallon Goggo Larai durƙushe gaban Umma a gefe kuma ga Fure da Habi nan, Yaya Karima ce ta ce. "Umma Lafiya? Goggo mai ya faru?." Rarrafowa Goggo Larai ta yi zuwa inda suke, sannam ta ce. "Ku yi wa Allah ku yiwa Girman ma'aiki ko yafe mini dukkan cutarwa sda na dinga yi muku, da irin tsanar da na yi muku."  Legendspen 08129553971 Jama'a ba ƙarya na gaji da Littafin nan HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da Biyar  (46) Baki sake suka kallon Goggo Larai durƙushe gaban Umma a gefe kuma ga Fure da Habi nan, Yaya Karima ce ta ce. "Umma Lafiya? Goggo mai ya faru?." Rarrafowa Goggo Larai ta yi zuwa inda suke, sannam ta ce. "Ku yi wa Allah ku yiwa Girman ma'aiki ko yafe mini dukkan cutarwa sda na dinga yi muku, da irin tsanar da na yi muku." "Haba Goggo mene kuma na tsugunnawa mun yafe muku komai tun ba yanzu ba." Yaya karima ta faɗa tana kamo Goggo Larai. "Na gode 'yar nan! Na gode." Ta faɗa tana komawa wajen Abdul. "A'a nima na yafe miki komai da komai."  "Na gode kaima, Bhatool kema dan Allah."  "Bakomai Goggo, Allah Ya yafe mana baki ɗaya." Bhatool ta faɗa muryarta sanyi kalau, kamar ba Bhatool me hayaniya ba. Daga nan suka zauna aka dan taɓa hira, amma su Yaya karima basu buɗe baki sunyi magana a gabansu Goggo Larai ba, Al'amin Mijin Yaya Karima kam tun da ya ga su Goggo Larai daman ya juya, bayan laɓe yaji abinda yake tafe dasu.  Sai Yamma Goggo Larai suka tafi, har Furee da Habi suma sunce tafiya zasuyi, tun da a yanzu Goggo Larai ta nemi afuwa ƙila samarin nasu su dawo. Sai bayan sun tafi su Yaya karima suka zayyanewa Umma komai, ciki har da hukunci da Bhatool ta yanke, anan ne Umma ta ce dasu. "Nima zan faɗa muku wani Sirri mai girma, ina su ku riƙeshi a zuciyarku." Dukkansu suka nutsu suna sauraren Umma, ta buɗe baki ta fara magana. Mahaifin Senate Yunusa, shine mutumin da mahaifinku yake baku labari a matsayin saurayi na na farko, shine mutumin da na fara so idan ka cire iyayena, amma ƙaddara ta raba mu sai dai ashe akwai wata ƙaddara ta auren Bhatool da Senate, sai dai bansan ko ƙaddara auren nasu ta zo ne domin ta sake nuna mana fuskokin juna ko wani abu daban. Shuru suka yi baki ɗaya, daman sun tattauna wannan magar ɗazu da safe.  "Umma duk komai munsani, mun tattauna aka hakan dazu, kuma muna yi miki duk wani fatan alheri idan har Allah Ya ƙaddara aure a tsakaninku." Yaya Karima ta faɗa amadadin dukkan 'yan uwanta.  **** "Zainab ki yi wa girman Allah ki daina sa wannan damuwar aranki dan Allah." Dad ya faɗawa Mom dake zaune ta na zubar da ƙwalla. "Tom Alhaji Tom!."  Ta faɗa kamar zata yi kuka, domin ita kaɗai tasan nau'in azabar da take ji a ranta game da abin da ya faru, wai 'yar uwarta, 'yar uwarta da ta riƙa a matsayin komai ita ce ta yi wa ɗanta guda ɗaya tilo asiri.  "Ko albarkacin Anas ta ci ya saki manta da wannan abun." Dad ya  faɗa. "Alhaji ai Anas ɗana ne, rainona ne, tarbiya ta ce, dan haka bashi da wani aibu a wajena." "Ba aibu na ce ba, ita mahaifiyrsa ta ci albarkacinsa ki manta da wannan abun, kar ya taɓa miki lafiya fa. A ɗayan ɓangaren kuwa, Jannah ta nufi gidan Amrah. Ta iske Amrah a ɗaki ta duƙufa tana kuka, idanunta sun yi jawur kamar garwashi. Jannah ta zauna a gefenta, ta fara mata nasiha mai sanyaya jiki. "Amrah, kukan nan ba shi ne mafita ba. Kin riga kin yi kuskure, kuma kin riga kin tona asiri don neman gyara. Yanzu abin da ya rage miki shi ne kiyi ta roƙon gafarar Allah, kuma ki ci gaba da neman gafarar Bhatool. Shaiɗan ne ya yi amfani da kishinki, amma tunda har kin iya faɗar gaskiya, to akwai alamun alheri a tare da ke. Kiyi haƙuri Amrah, komai zai wuce," Jannah ta faɗa tana shafa bayan Amrah. Amrah ta ɗago kai tana sheshsheƙar kuka. "Jannah, yaya zan yi? Bhatool ta ce ba ta yafe mini ba. Ta ce ta tsane ni. Ta yaya zan iya rayuwa da wannan nauyin a wuyana?" Jannah dai taci gaba da lallashinta har sai da Amrah ta ɗan samu natsuwa. A can kuwa, Anty ta fara shiga cikin tashin hankali. Jin cewa Amrah kwana biyu shiru, baya neme ta ba ta zo gidanta ba, tana tsoron kar fa ace yarinyar nan ta tona mata asiri ne, gashi idan ta kira lambarta ba ta tafiya, gaba daya hankalinta a tashe yake kwana biyunan, waya ta dauka ta kira Anas dake Abuja tare da Senate, bayan ya dauka ne ya gaida ta, ba ta amsa ba ta ce. "Kai Anas me ke faruwa a gidanku?." "Anty wane gida?."  "Gidanku mana." Ta faɗa a fusace. "Anty ni banji komai ya faru ba, tun da Senate sa yaskai matarsa, kuma har yanzu yaƙi dawowa gida, yanzu haka sai fama nake dashi amma wallahi yaƙi." Tsaki taja sannan ta ce. "Bakaji ana cewa komai ba game da mutuwar auren?."  "Anty ba acewa komai." Ya faɗa kanshi tsaye sabida bai ji ana maganar ba. "To wane bincike ake yi akan hakan?." "Babu fa, sabida Senate ɗin yaƙi maida hankali ma akan maganar." "Ka dai tabbatar ko?." "Eyh Anty." Ta kaste wayarta ta saukw ajiyar zuciya. "Aiki yana kyau, shi kuwa Senate ai bazai koma yanzu ba, har sai bayan wata uku ta fita daga takaba, tun da Malam ya ce indai ya ganta ido da ido tofa sai ya koma wa aurenta, amma idan ta fita daga takaba shikenan." Ta faɗa a ranta tana zama. Anas kam suna gama waya da Anty yaji hankalinsa bai kwnata ba, ya ɗau waya ya kira Mom dake zaune a ɗaki, Dad yana mata nasiha bayan likita yazo ya duba ta ya bata magungun. Ɗagawa ta yi tare da faɗin. "Anas! Yakuke?."  "Muna lafiya Mom."  "Ya shi Senate ɗin?."  "Lafiya kalau, amma har yanzu yaƙi bari mu yi wata magana ta gida ko ta Bhatool." Shiru Mom ta yi, shikuma ya ƙara cewa. "Wani abu ya faru anan gidan ne?."  "A'a." Mom ta faɗa. "Yanzu Anty ta kirani tana tambayata wai wani abu ya faru ana gidanmu na ce a'a ta ce wai ko maganar aurensu Senate na ce ma ta a'a." Ajiyar zuciya mai cike da ɓacin rai Mom ta sauke, sannan ta ce. "Nima ta kirani." Ta faɗa ne gudun kar ta zargi wani abu. "Okay badamuwa." Daga haka yakashe wayarsa.  A gidan su Bhatool kuwa, Bhatool ba ga da wani aiki sai faman tunane tunane kala kala, damuwa tana neman shigarta, ga ƙananan zancen ya fara tashi a unguwar kan cewar  Bhatool ta yi auren kuɗi kuma anyi mata hulaƙancin ansake ta. A yanzu babu wani zance dake tirandin a unguwa sai shi. Gaba daya abubuwa sun ƙara cakumewa Bhatool, kullum sai ta yi kuka ta gode Allah, kuma duk tafi ɗora alhakin hakan akan Senate da ya kasa gasgata ta ya yarda da waya akanta.  Ahmad ne da Abdul zaune a falon ma, Ahmad ya kalli Abdul, nifa yau banga Bhatool ba. "Hhm Ahmad Bhatool abinta kullum gaba yake, damuwarta yawa take ƙarawa, abubuwan ta ba sauki."  "To me ya sa baka yi amfani da shawarar da na baka ba, ka dinga fita da ita tana zaga gari ko da sham ice cream ne." Ahamd ya faɗa. "Bazaka gane ba ne, Bhatool tana da taurin kai."  "Duk da haka fa, baki tabi ta yadda zata yarda ba ne."  Umma da tazo shiga ɗaki ce ta ce da Ahamd. "To kai ka gwada taka sa'ar mana ko Allah zai sa adace, kaganmu nan duka mun damu da wannam halin da take ciki wlalahi."  "Shikenan Umma," Ahmad ya faɗa yana tashi, Bhatool na zaune a ɗaki bayan sun gama waya da Jannah ta ɗan tausashe ta, har ta ke faɗa mata cewar ta dinga fita tana shan iska, ko ita ce idan ta sami lokaci zata dimga zuwa suna zaga gari. Da sallama a bakinsa ya shiga, Bhatool ta amsa ba tare da ta kallesa ba. "Yakike?." Ya faɗa idanuwansa akanta. "Ina lafiya." Ya yi murmushi sannan ya ce. "Wace lafiya?." Ɗagowa ta yi ta kalleshi ta ga idonsa akanta. "Na ce lafiya, ya aka yi?."  "Yanzu da mutum ɗaya ya barki shine zaki ƙudundune kanki, ki matse rayuwarki, ki kori farin cikinki, ki sa kanki a damuwa kisa muma na jikinki a damuwa Bhatool?."  "Ni waca damuwa nake ciki?."  "Gashinan kin sauya, kinsan halin da Umma take ciki?, kinsan Yaya Karima, ko kinsan Abdul duk sun daina walwala,  hankalinsu yana kan Bhatool ga cikin dake jikinta, dan Allah Bhatool ki nuna musu komai ya huce."  "Ta ya zan nuna musu komai ya huce, har yanzu zuciyata zafi take mini, a duk lokacin da natuna Senate ya yarda da ƙarya sama dani, ya sake ni akan abinda baiyi tunani ba."  "To ya zaayi, haka ƙaddara ta tsara muku, kuma kinga da sa hannun wasu mutanen Bhatool, ina so yanzu ki nunawa kowa kin warke daga abinda ke damunki, kin janyo farin ciki a rayuwarki." Shiru Bhatool ta yi, tabbas tasab kowa yana cikin damuwa da halin da ta shiga, kuma dole ta samar musu da farin ciki, domin wannan aikinta ne, kuma haƙƙi akanta, mutanen ta tun haihuwarta  suke kokari akanta, kullum burinsu ta yi farin ciki, ba ta taɓa neman abu ta rasa daga wajensu ba. "Ta ya zan nuna musu hakan?." Murmushin jindaɗi Ahamaf ya yi sannan ya ce. "Ki fara fitowa gida, kina surutu kina rigima kamar yadda kike yu da, ki dinga fita kina shan iskar rayuwa, ni nan indai zaki bini na miki alƙwarin duk weekend zan dinga zuwa ina fita dake.  Shru Bhatool ta yi na wasu 'yan mintuna sai kuma can ta ce. "Na amince."  Legendspen  08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da Biyar  (47) "Na amince." Bhatool ta faɗa, murmushi ya ƙara sakar mata sannan ya ce. "To yanzu ki tashi ki shirya kinji, ina jiranki." Ya karashe faɗa yana tashi. "Tom." Ta faɗa tare d tashi bayan ya fice, a falo ya sami Umma da Abdul duk suna zaune zungwi zungwi. "Me ta ce?." Abdul ya tare shi. " in sha Allahu za a sami sauyi." Ahmad ya faɗa yana zama. "Allah Ya sa." Umma ta faɗa.  ***** Abu kamar wasa Ciwo ya tasarwa Mom,Yawan haki ga kuma tari, ciwon ya fara tsananta hakan ya sa Dad ya ce zasu huce ƙasar india domin ganin babban likita, Mom ta hana a sanar da kowa cikin 'yan uwanta sbaida ma kar Senate ya sami labari, ga kuma Anty a gefe, shi kam Senate gaba daya ya watsar da lamarin gida da wata Bhatool, rayuwa yake baya tunawa da anyi wata mace wai ita Bhatoool, daman kuma Bokan Anty ya faɗa mata indai Bhatool ta fita daga takaba Senate ko yasa ta a ido bazai taɓa jin Sonta ya dawo ma sa ba, dan haka Amty tasa aka cire masa son gida da sha'awar gida har sai bayan wattanni uku, dan ita ba ta yi tunanin akwai cikim a tare da Bhatool ba.  ***** Su Umma na zaune a falo Bhatool ta fito sanye cikin doguwar rigar atamafa, duk da ba ta yi wani hayaniya ba amma ta yi kyau, ɗan ƙaramin cikinta ya fara tasawa. "A'a Maman boy irin wannan kwalliya haka?." Abdul ya faɗa yana washe baki ranshi fari ƙal. "Kana nan zaune zan haifi kamarka." Bhatool ta faɗa tare da wucewa, Umma ce ta ce. "Uwaki da baki da kunya." Dariya ta yi Ahmad kuma ya tashi. "To Umma zamuje mu dawo."  "Ubamgiji Allah Ya tsare hanya."  "Amin, Amin." Ahamad ya faɗa, Abdul kuma ya ce." Na taso ne?." "Duk yadda kagani."  Daga wannan ranar fa wani sabo ya fara shiga tsakanin Bhatool da Ahamd, kamae yadda ya alƙwaranta duk weekend sai ya zo ya ɗauki Bhatool sun fita, a yanzu damuwar dake zuciyar Bhatool ta ragu fiye da kaso saba'in cikin ɗari, a hankali cikin jikinta yake ta sawa har ya shiga wata na haɗu, ta ƙara kyau abinta, sannan ita kanta a yanzu ta san ta faɗa cikin wata sabuwar rayuwar, ta kamo da kaunar abinda ke cikinta da kuma wata sabuwar kaunar ta Ahamd, tabbas ta a yanzu ta fara son Ahmad, ba wai kuma ta daina som Senate ba ne, amma ta yi koƙari sosai wajen yaƙi da soyyayyarsa a zahiri, dan a yanzu ko tunaninsa ma ba ta bari ta yi.  Ahmad kam kulawarsa ga Bhatool kullum sai ƙara gaba take, Yanzu ba wai kulawar jinya yake ba mata ba, kowane mataki nasa yana nuna tsantsar ƙauna ce dake tafasa a cikin zuciyarsa. Ya zama tamkar inuwar da ba ta rabuwa da ita. Duk lokacin da ya zo, sai ya sanya Bhatool ta yi farin ciki, taji daɗi koda kuwa murmushin yaƙe ne. Har kuma a kazo ita ma ta fara kamuwa da ƙaunarsa.  Wata rana da yamma, suna zaune a cikin motarsa bayan sun dawo daga zaga garinsu ɗan kullum, da yanzu ba wai sai Weekend ba duk lokacin da yake free kawai zai zo ne su fita, wani lokacin ma harda Abdul suke fita, duk dan ganin a sanya mata farinciki. Ahmad ya kalli Bhatool wadda take wasa da yatsun hannunta. Ya nisa, sannan ya kira sunanta cikin muryar dake nuna tsantsar gaskiya. "Bhatool, na san abubuwan da kika fuskanta sun yi miki nauyi. Na san kuma har yanzu zuciyarki tana jinin raɗadin abin da ya faru. Amma ina so ki sani, tun ranar da na fara ganinki, ban taɓa jin wata mace ta shiga raina kamar yadda kika yi ba. Bhatool, ina sonki. Ina son in zama silar farin cikinki na har abada, in zama mahaifi ga abin da kike ɗauke da shi, in kuma share miki dukkan hawayenki idan kin ba ni dama." Bhatool ta ɗago kai tana kallonsa, idanunta suka cika da ƙwalla. Ba ta yi tsammanin furucin zai zo a wannan lokacin ba. Ta kasa cewa uffan, sai dai wani irin sanyi da ta ji yana ratsa ta. Furucin Ahmad ya zo mata a matsayin maganin radadin da take ji, ko da kuwa ba ta riga ta amince da soyayya baki ɗaya ba. "Kuka kuma Bhatool ki yi hakuri bazan taɓa miki dole ba, kowani abu da zai saki kuka."  Ta goge hawayen dake fuskarta sannan ta ce. "Bawai furucinka ya sani kuka ba, ina tuna ɗinbin alherinka gareni ne, Na gide sosai da dukkan abinda ka yi mini, kuma nima a shirye nake na yi rayuwa ta farin ciki da kai har Abada." **** A ɓangaren Amrah kuwa, tana cikin wani hali na nadama da kaɗaici. Duk da cewa ta tona asirin komai, amma har yanzu tana jin nauyin abin da ta aikata. Tana yawan kiran wayar Bhatool don su gaisa, duk da cewa Bhatool tana amsawa ne a taƙaice, babu sauran waccan muryar ta abota da hira. Jannah ce kawai take yawan zama da Bhatool, tana ƙarfafa mata gwiwa tare da raba mata damuwar da take ciki. A yanzu Amrah dai ta canja dan hatta karatun ma ta watsar kamar yadda Bhatool ta watsar da na ta Jannah ce kawai ke zuwa makarantar, Amrah kullum cikin neman yafiya take wajen Ubangiji da Bhatool, cikin kwanaki kaɗan wani bawan Allah mai rufin asiri ya fitowa Amrah, amma taki ba shi dama. Da ya matsa mata ne ma ta bashi labarin abinda ta aikata sannan ta tambayeshi cewar. "Kana ganin ya dace a aure mace mai muguwar zuciya irina?." Ya gyaɗa mata kai, sannan ya ce. "Ai kin tuba, ko ubangiji muna masa laifi kuma mu tuba."  "kana ganin kenan ya dace ni na yi aure bayan wacca na kashe mata na ta auren tana nan zaune?."  "Shi ai aure nufine na ubangiji, kuma komai muƙaddarine daga Allah." Amrah ta yi sannan ta ce. "Tom zan yi shawara." Daga haka ta shige gida, bayan ta shiga gidane ta kira Jannah a waya ta sanar da ita komai. Jannah ta ce. "To ai Amrah komai nufine na ubangiji, sannan rashin yin auren ki ba zai canja abinda ƙaddara ta tsara ba, ki yi addu'a idan har shi mafi alheri ne a wajenki to Allah zai tabbatar."  "Shikenan Jannah Na gode."  Amrah ta faɗa zata kashe wayarta. Jannah ta ce. "Ɗazu Sudais ya kirani ya dawo kuma suna so asa lokacin biki sati biyu, daman wancan lokacin sunyi da mahaifana da ya dwo daga tafiyarsa za a sa sati biyu." Murmushi Amrah ta yi sannan ta ce. "Kai Alhamdulillah, Allah Ubangiji Ya sanya alheri Ya kaɗe fitina da sharri."  "Amin Ya Allah." Daga haka suka kashe wayar, Amrah tana jin daɗi a ranta ko ba komai Senate zai zo bikin, kuma zata san duk yadda zata yi ta gana dashi ta faɗa masa komai, kuma tasan in sha Allah zai mayarwa da Bhatool auenta.  Acan ɓangaren Mom kam jiki ta Alhmdlh tum bayam zuwansu india, ta fara samu sauƙi duk da dai damuwa ta kasa barinta, a kullum zancen ta ɗaya. "'Yar uwata da nake ganin ko babu raina xata kula da nawa, ashe ita ce zata kashe nawa."  Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da Biyar  (48) Acan ɓangaren Mom kam jiki ta Alhmdlh tum bayam zuwansu india, ta fara samu sauƙi duk da dai damuwa ta kasa barinta, a kullum zancen ta ɗaya. "'Yar uwata da nake ganin ko babu raina xata kula da nawa, ashe ita ce zata kashe nawa." Haka Dad zai ta tausarta yana bata hakuri, shi kam Senate bai ma san bata da lafiya, kawai dai yana kira suna Gaisawa ta ce masa ta je india.  Yau tin safe Senate ya tashi da son dawowa gida, gaba ɗaya ji yake idan bai je gida ba bazai iya duk wani aiki ba, haka ya sa Anas ya shirya musu flight. Anas farin ciki kamar ya kashe shi ya kira Mom ya sanar mata, wamda ita ma gobe zata dawo Nigeria, Dad kuma zai ce Rasha amma ta ce lallai ita ma Flight din yau take son bi.  **** Bhatool kam kwana biyu wata irin soyayya ce mai dadi take faruwa tsakaninta da Ahamd, ko da yaushe suna tare a waya, ko aiki yake sai ya kirata ko abinci zai ci sai ya kirata, kullum suna cikim waya sannan basa ɓoyewa junamsu komai, duk abinda daya yake to daya ya sani, a yanzu Bhatool ji take ina ma ta haihu yau, a daura musu aure a washe gari. Zaune take a falo kan kujera suna faman waya da Ahmad da ya kwana biyu bai zo ba. "To yanzu yaushe zaka zo?." Bhatool ta tambaya kamar zata yi kuka. "Ko yanzu kike so ranki ya dade, zan iya ajiye komai na tawo." Murmushi ta yi sannam ta ce. "A'a kabari ka gama ayyukanka goben sai ka zo, me zan dafa maka?." Dariya ya yi sannan ya ce. "Kamar iyawa za ta yi." Itama dariyar ta yi sannan ta ce. "Zan iya mana, ai yanzu ya yi kwari yana barina na yi girki."  "Au, aiki ne bai barinki ki yi sai girki?."  "Ina fa aiki, jiya nina gyara ɗakin gado gaba ɗaya fa, sannan na dafa Tea."  "To waannan ne aiki?." Ya faɗa yana dariya. "Kasan fa ni bana son aiki."  "Nasani ranki ya daɗe, 'yan aiki nawa kike so?."  "Goma." Aikuwa ya yi dariya sannan ya ce. "Tom shikenan."  "Shikenan kuma?." Ta faɗa kamar zata yi kuka. "Eyh mana shikenan." Ya maimaita. "Ni wasa nake ma, bana son ko ɗaya." Daidai lokacin kuma akayi sallama aka shigo. "Waye ya shigo?." Ya tambaya. "Jannah ce." Ta bashi amsa. "Okay sannunta zuwa, mu yi waya anjima."  "Okay." ta faɗa tare da sauke wayar a kunnenta. "Ke da wa kike shan wannam soyayyar?." Jannah ta tambya tana zama, dariya Bhatool ta yi sannan ta ce. "Ahmad ne." Murmushin yaƙe Jannah ta yi sannan ta ce . "Dagaske dai kin haƙura da Senate ."  "Har duniya ta naɗe." Bhatool ta faɗa. "Ai shikenan, Allah Ya sa haka yafi alheri."  "Amin Amim Jannah, ya garin?."  "Ke gari ya ci huta. An kawo kayana fa jiya, kuma kwana takwas suka sa." Jannah ta faɗa. "Suka sa me?." Bhatool ta tambaya. "Auren." "Ah Lallai baki da hankali, idan kin shirya to mu bamu shirya ba." Bhatool ta faɗa, dariya Jannah ta yi sannan ta ce. "To ya zaayi, hutu ya samu ya dawo kuma yana so mu dan zuana ko kwana biyar ne anan kafin mu huce can Legos ɗin."  "To Allah Ya sanya alheri, yanzu ina muka kama?."  "Hajiya me ciki, Ladies kawai zamuyi sai Walima kuma."  "Kin dau darasi a auren Bhatool da Senate kenan da aka cika bidi'a." Bhatool ta faɗa tana dariya. "Bana son wulakanci, da fasaara, kawai lokaci ne yazo a kure, shi ya sa."  "Tom Allah Ya sanya mana alheri, bari mu fara shiri." Daga nan suka shiga wata hirar daban da shirye shiryen biki, sai yamma Jannah ta bar gidan ta nufi gidansu Amrah, nan ma Amrah ta yi nata mamakim da fatan alheri.  Ƙarfe biyar na Yamma Jirgin su Senate ya sauka, haka Mom ma duk a tare suka shigo gari, Mom ta rungume Senate bayan sum haɗu, daga nan suka hau mota zuwa gidansu, a mota Senate ya ce. "Ina Bhatool?." "Tana gidansu." Mom ta faɗa a daƙile. "Ya cikin na ta."  "Senate karka isheni, kaje ka duba ta da kanka mana."  "Mom ai na sake ta."  Ya faɗa kamar zaiyi kuka. "Ka kyauta to." Mom ta bashi amsa. "Baki tambayeni me ya sa ba."  "Akan me zan tambayeka? Mata ta ce? Ni nake aurenta, ko zamana take?."  "A'a Mom,  wasu mazan fa take kulawa a waje."  Ku yi hakuri da short page Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Arba'in da Biyar  (49) "Kana da tabbacin akan mazan da take kulawa."  "Ina da shi Mom."  "Tun da kana da shi ai shikenan, amma ka tabbatar kana da sahihinaci akan shaidar."  "Mom, mene sahihanci?." Kallonshi ta yi sannan ta ce. "Tabbatciyar shaida." Shiru ya yi gaba daya abun ya canja masa, ji yake kamar ba Senate dake Abuja ba, wanda ya manta da Bhatool da rayuwarta ba, dan tun da ya dawo nan ba shi da wani aiki sai faman tunanin Bhatool, tun da ya sa ƙaffarsa a garin.  "Mom ni dai kawai gani nai an turu min hotonta." Daidai lokacin motarsu ta shiga gidan. "Ka bincika wa ya turu, ka tabbatar ita ce, ba hadin Ai ba, kasan yanzu muna cikin wani zamanu na fasaha, a yanzu fasaha ta yawaita kuma zata iya abinda hankali ba zai tunani ba." Shiru ya yi gaba daya jikinsa ya mutu, yana fitowa daga mota ya yi dakinsa ya kwanta, sai dai tunanin Bhatool da tausayinta ya cika masa rai, ya hana shi sakat gaba daya.  **** Washe gari Bhatool da aiki ta tashi, ta yi alƙwarin bawa Ahamad mamaki, dan girki za ta yi masa yaga ƙoƙarinta da yake cewa bata iya komai. Umma ce ta shigo cikin kicin din. "Bhatool lafiyanki dai?." Murmushi ta yi sannan ta ce.  "Lafiya Umma, daman Yaya Ahamd ne zai zo."  "Wai Bhatool wani abu dai na soyayya bai ta ɓa shiga tsakaninku ba ko, kinsan dai yanzu kin haramta ga kowanne namiji har sai kin fita daga iddarki ko?." Shiru Bhatool ta yi, a ranta ta ce. "Nasani Umma, amma dai tabbas wani abu na soyayya ya shiga tsakaninmu, dan a yanzu ina jin Ahmad a zuciyata fiye da Senate."  "Ki yi hakuri, lokaci ƙalilan ya rage miki."  Umna ta faɗa, tana fucewa daga Kicin din. Ci gaba da aikinta ta yi a ranta ta dauki aniyar yau idan Ahmad yazo za ta sanar dashi cewar su yi nisa da juna, su kuma janye al amarin soyayya zuwa lokacin da Allah zai sauketa, ko ranar ne ma sai a ɗaura musu aure.  Wajen karfe uku da rabi Ahmad ya shigo gidan, lokacin Umma ta zagaya maƙwaftansu Barka anyi haihuwa. Bayan ya zauna a falo Bhatool ta shiga fito masa da filasai na abinci, da mamaki sosai yake kallonta. "Kar dai ki ce ke kika yi girkin nan?." Ya tambya.  "Ba daman kaine kake cewa wai bana iya girki ba, gashinan kuwa yamzu ka gani."  "Gaskiyya dai kam nagani, naga girki iya girki." Ya faɗa yana tashi ya fara zuba abincin. "Aikuwa kasan dai ba iya zubawa zanyi ba, dan nagaji."  Dariya ya yi sannan ya ce. "Ai na hutarshe ki." Bayan ya zuba abincin yana ci ne ta ce. "Cikina ya shiga wata bakwai." Kallon ta ya yi sannan ya ce. "Ina lissafe fa."  "Har yanzu akwai iddar tsohon mijina akaina." Ta faɗa kanta a ƙasa. "Nasani Bhatool, lafiya dai ko?."  "Lafiya kalau, wata alfarma kawai nake nema a wajenka."  "Faɗi Bhatool ina saurarenki."  "Ina so Ranar da na fita daga idda, ma'ana na haihu indai na haihu lafiya ina son a ɗaura mana aure a ranar."   ****** Senate haka ya raba dare yana faman tunanin Bhatool, gaba daya kalaman Mom sun cika masa kai, sun tsaya masa a cikin zuciya sun ƙi gaba sunƙi baya. Sai tsakar dare ya samu bacci ɓarawo ya yi gaba dashi, amma kuma da safe yana tashi da wani tunanin Bhatool ɗin, gaba ɗaya mamakin kansa yake lokacin da yake Abuja fa mantawa ya yi an hallic wata Bhatool, har ma ya yi rayuwa da ita, amma tun da ya sa ƙafarsa anam ta dawo.  Sai wajen 1 ya fito ya yi breakfast, Mom tana kwance kan doguwar kujera tana kallonsa, har ya gama sanan ta kirashi ya zo. "Me ya hanaka fitowa da wuri?."  "Mom bana jindadin jikina."  "Meke damunka?."  "Headche." "Zaka iya tuna ranar da ka fara samun saɓani da Bhatool?." Mom ta tambayeshi, ya yi shiru na 'yan mintuna sannan ya ce. "A'a gsky."  "A cikin saɓanin da kuka samu, kafin azo na saki wanni yafi tsaya maka a rai?." "Wanda ta fito waje ta tsaya ita da wancan ɗan iskan."  "Wa ya sanar da kai?." "Hoto aka tura min."  "Waya tura ma hoton? Kasa wani ya dinga bibiyar ma ita ne?."  "A'a bansa kowa ba."  "To wanda ya tura ma kasan shi?."  "A'a." "Kasan lambar?." "A'a." "To me ya sa ya tura ma?."  "Mom! Nima bansani ba." "Ita lambar ita ta sake tura ma hoton da kake magana na ƙarshe?."  "Eyh ita ce."  "Sannu Shashasha, an tura ma hoton matarka da wani, sai baka bibiyi wanda ya tura ma ba, amma kazo ka saki matarka, kai ko hakan bazai sa ka yi tunanin cewar akwao wata maƙarƙashiya a ƙasa ba?." "Mom, wallahi sai yanzu na yi tunanin nan, waye yake son raba ni da matata haka?."  "Wa ya rabaka da matarka dai Senate, ai ka riga da ka saketa, saki mafi hulaƙanci shine ta waya. Shin ta waya ka karɓi aurenta? Da zaka sake ta ta waya?."  "Innullahi wainna illahir raji'un! Astagfirullah Lallai dole na yi bincike akan hakan."  "Babu wani bincike da zaka yi domin gasky ta gama bayyana kanta, kai kuma ka zama miji mara adalaci, mara tausayi."  "Mom waye da wannan aikin, ko waye wallahi sai na dau mataki akansa."  "Hhm, kawai kabar maganar wayanda suka yi sun bayyana kansu. Wata ce ta yi amfani da ƙawarta, sai daga baya ƙawarta ta  ta faɗa."  "Amrah ko?." Ya tambaya a fusace. "A'a." Mom tabashi amsa. "Jannah take ko jannat."  "Ita ma ba ita ba, wata ƙawa can daga gefe."  "To wace ta yi amfani da ita?."  "Senate ba za ta fadu ba, amma tabbas ba kai ta cutar ba ni ta cutar, dan har kwanciya na yi asibiti kuma har yanzu jikina babu daɗi."  "Mom wace dan Allah?." "Har abada ba zakaji wace ba Senate." ***** Suna zaune a falo Ahamd Yana cin girkin Bhatool yana ta murmushi abunsa, ya kai lomar abincin karshe bakinsa, sannan ya ajiye cokalin yana hamdala. Ya kalli Bhatool wadda take zaune a kasa gefen kujerar da yake kai.  "Bhatool, gaskiya na gamsu da wannan girkin. Amma maganar da kika fada din nan, ita ce ta fi kowane dadi dadi," Ahmad ya fada yana murmushi, idanunsa suna kallonta cikin so da kauna. Bhatool ta sunkuyar da kanta kasa, tana wasa da yatsun hannunta. "Yaya Ahmad, na yi wannan maganar ne saboda ina son in biya ka dukkan kulawar da kake nuna mini. Kuma ina son in nuna maka cewa na yarda da kai fiye da kowa." Ahmad ya sauko daga kan kujerar ya dawo kasa kusa da ita, ya rage muryarsa yadda ita kadai za ta ji shi. "Bhatool, alkawarin da kika ba ni, ya zama tamkar igiyar da za ta jawo ni zuwa ga rayuwar farin ciki. Zan jira ranar da za a sauke ki, zan kuma jira ranar da za a kulla igiyar aure a tsakaninmu. Ina son na zama uba ga danka, kuma zan zama miji gare ki wanda ba zai taba yarda da jita-jita ko sharrin makiya ba." Hira ta balle a tsakaninsu, hira mai cike da natsuwa da bayyana sirrikan zuciya. Ahmad ya dinga gaya mata yadda zai gyara mata daki a gidansa, da kuma yadda yake son su gina rayuwa mai sauki amma cike da aminci. Bhatool ta saki ranta sosai, tana jin wani irin dadi yana ratsa ta, har ta manta da cewa tana cikin idda. A can gidan Mom kuwa, Senate ya gaza zama. Kalaman Mom na cewa an yi amfani da fasahar AI wajen yaudararsa sun riga sun rikita masa kwakwalwa. Ya tashi ya dauki mukullin motarsa, ba tare da ya sanar da kowa ba, ya nufi hanyar gidan Umma. Wani irin nauyi yake ji a kirjinsa, yana son ya tabbatar da abin da zuciyarsa take gaya masa. Yana isa kofar gidan, ya yi fakin a gefe. Ya dade a cikin motar yana saƙawa da warwarewa. Daga karshe ya fito, ya taka zuwa cikin gidan. Bai sami kowa a tsakar gidan ba, bayan ya yi sallama babu amsa kai tsaye ya turo kofar falon, idanunsa suka sauka a kan abin da bai taba zato ba. Ahmad ne zaune kusa da Bhatool, suna hira cikin wani irin yanayi na shauki. Bhatool tana dariya irin wadda Senate ya dade bai gani ba a fuskarta. Fuskarta cike da so da ƙauna, duk da ramar da take da ita, tana kallon Ahmad cikin wata irin kulawa. Senate ya tsaya cak a bakin kofa, numfashinsa ya fara fita sama-sama. Wani irin kishi ne ya turnuke shi, kishin da ya fi na farkon zafi. Ya kasa magana, sai dai kallon da yake jifa da shi zuwa gare su. Ahmad ne ya fara lura da mutum a bakin kofa. Ya  kai idonsa ga bakim ƙofar, fuskarsa cike da zallam mamaki yake kallom Senate a tsaye.  Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin  (50) Bhatool ta juyo da sauri. Ganin Senate tsaye a bakin kofa, sanye da riga mai launin toka, fuskarsa ta canja kala, ya sanya ta jin wani irin shock. Ta mike tsaye da kyar saboda nauyin jikinta, ta rike gefen kujera. Senate bai sake kallon Ahmad ba, idanunsa duka suna kan Bhatool, musamman ma yadda ya ga cikinta ya girma sosai. Wani irin tausayi da bakin ciki suka hadar masa. "Bhatool... me kike yi haka?" Senate ya fada cikin muryar dake nuna tsananin rauni da bacin rai. "Dama ashe tun kafin iddarki ta kare kin riga kin maye gurbina da wanda kike so?" Ahmad ya matso kusa da shi ya fara magana. "Haba Senate."  Senate ya daka masa tsawa. "Karka kuskura ka sanya baki a tsakanina da matata! Ko ka manta har yanzu akwai igiyar aure a kanta?" Bhatool ta ja numfashi, ta share hawayen da ya fara zubo mata. Ta kalli Senate, sannan ta ce  "Senate, ka kira ni 'munafuka', ka kira ni 'muguwa', sannan ka sake ni ta waya. Me kake nema a nan yanzu? Mutumin da kake gani, shi ne ya share mini hawaye lokacin da kake Abuja kana jin dadinka. Don haka, don Allah ka fita mana daga gida!" Senate ya yi turus, kalaman Bhatool sun dake shi kamar saukar aradu. Falon ya rikice da wani irin yanayi mai nauyi. Senate ya dubi Ahmad, idanunsa sun yi jajur, jijiyoyin kansa sun fito radau saboda tsananin kishi da raɗadi. Bai sake cewa uffan ba, ya damƙi wuyan rigar Ahmad da ƙarfi, yana huci tamkar zaki. "Dama ashe jira kake saɓani ya shiga tsakani ka bayyana kanka? Kai na laɓe kana kunno masifa daga gefe domin rugujewar gidana?" Muryar Senate ta fito a shake.  Ahmad bai yi yunkurin ramawa ba, sai dai ya riƙe hannun Senate yana ƙoƙarin kwatar kansa.  "Senate, ka yi bincike kafin ka yi hukunci. Karka ƙara kuskure a kan wanda ka riga ka yi..." Kafin Ahmad ya ƙarasa, Bhatool ta ƙwala wani uban ihu wanda ya sanya Senate sakin rigar Ahmad ba tare da ya sani ba. Ta matso tsakiya, duk da nauyin cikin dake jikinta, ta tsaya tana kallon Senate ido cikin ido babu sauran ƙauna a cikinsu, sai dai tsantsar tsana da jin haushi. "Ya isa haka Usman!" Ta kira sunansa na yanka, wanda hakan ya fi kowane mari zafi a wurinsa.  "Karka kuskura ka taɓa shi. Shi ba irinka ba ne. Shi mutum ne mai daraja, mutumin da ya tsaya mini a lokacin da mijina ya gudu ya bar ni. Mutumin da ya yarda da ni a lokacin da kai kake kirana da karuwa kuma kake watsar da ni!" Senate ya ja baya, ya dafe ƙirjinsa, ya ji kamar an soka masa wuƙa a zuciya. "Bhatool... kina nufin yanzu Ahmad kike so? Bayan dukkan soyayyar da muka yi? Bayan kwanakin da muka shafe na so da ƙaunar juna eyee Bhatool?" Bhatool ta saki wani murmushi na takaici, hawaye ya wanke mata fuska. "Soyayya? Soyayyar da ba ta da amana ai ba soyayya ba ce, guba ce. Tabbas, ina son Ahmad. Ina son shi fiye da yadda na taɓa tunanin zan iya son wani namiji. Domin shi ya gani, ya sani, kuma ya tabbata ni mace ce ta gari. Kai kuma Usman, ka riga ka mutu a zuciyata. Ka tafi Abuja ka ci gaba da rayuwarka, ka bar ni in haifi ɗana a cikin natsuwa tare da mutumin da zai zama uba na gari a gare shi." Wani irin sanyi ne ya ratsa ko'ina a jikin Senate. Ya kalli Bhatool, ya kalli cikin dake jikinta, ya tuna ranar da suka ji labarin samun cikin nan ranar da suka rungume juna suna murna. Yanzu kuma ga shi, ita ce take gaya masa cewa wani namijin ne zai zama uba ga ɗansa. Senate ya durƙusa a ƙasa a tsakiyar falon, ya rufe fuskarsa da hannu biyu, ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, kukan irin na mijin da ya gane kuskurensa a ƙurarren lokaci. Sautin kukan nasa yana fita a shake, yana nuna tsananin nadama. "Bhatool... don Allah karki yi mini haka. Na yarda na yi kuskure, na yarda makirci aka yi mini... amma don Allah karki ce kin daina sona." Ya faɗa cikin muryar kuka, yana sheshsheƙa kamar ƙaramin yaro. Bhatool ta kauda kanta, ta nuna masa hanyar waje da hannunta dake rawa. "Ka tafi Usman. Karka sake dawowa gidan nan. Ba na son ganinka, ba na son jin muryarka. Ka rabu dani, nima kuma na rabu da kai." Ahmad ya matso ya taɓa kafaɗar Senate cikin tausayawa, amma Senate ya harzuƙa ya ture hannunsa, ya miƙe da ƙyar. Ya kalli Bhatool a karo na ƙarshe, fuskarsa ta jike da hawaye, sannan ya juya ya fice daga falon yana layi kamar mashayi. Yana fita waje, bai tsaya ko'ina ba sai cikin motarsa. Ya kife kansa a kan sitiyarin motar, ya ci gaba da kukan da ya kusa raba shi da numfashinsa. "Na rasa Bhatool na har abada saboda wautata." Kukan da yake yi ya toshe masa maƙogwaro, ganinsa ma ya fara dishi dishi saboda hawaye da kuma wani irin jiri dake ɗibansa, ya kifa kansa a kan sitiyari, numfashinsa yana fita da ƙyar. Bai san tsawon lokacin da ya ɗauka a haka ba, kafin ya tada motar ya nufi gida. A can falon kuwa, Bhatool ta koma kan kujera ta zauna, ta ci gaba da kukan da ya fi na ɗazu ciwo. Ahmad yana tsaye a kusa da ita, ya rasa abin da zai ce mata, sai dai tausayinta da yake ji yana sake ratsa shi. Daidai wannan lokacin ne Umma ta shigo gidan, ta iske falon a hargitse, ga kukan Bhatool yana tashi. Umma ta tsaya cak, tana kallon Bhatool sannan ta kalli Ahmad. "Lafiya? Me yake faru a gidan nan?" Umma ta tambaya cikin muryar firgici da damuwa. Ahmad ya sauke numfashi, ya gyara tsaiwarsa. "Umma, tsohon mijin Bhatool ne yazo. Ya iske mu muna hira, shine ya tada hankalinsa har aka samu saɓani." Umma ta zaro ido, ta kalli Bhatool dake faman kuka. "Senate? Me ya dawo da shi kuma?" Ahmad bai iya ƙara cewa uffan ba, ya ga yanayin ya canja. Ya kalli Bhatool cikin tausayi, sannan ya kalli Umma. "Umma, bari na tafi. Zan dawo an jima mu gaisa." Bayan ficewar Ahmad, Umma ta ƙarasa kusa da Bhatool ta zauna a gefenta, ta fara shafa bayanta cikin lallashi. "Kiyi shiru Bhatool. Ya isa haka nan." ***** A can gidan Mom kuwa, Senate yana shiga gidan, bai ko bi ta kan kowa ba ya nufi falon sama. Mom tana ganinsa ta miƙe tsaye saboda yanayin da ta gani a tare da shi. "Senate? Lafiyarka?" Senate bai iya ba ta amsa ba, sai wani irin nishi mai nauyi da yake yi. Ya dafe ƙirjinsa, ya kalli Mom da idanuwan da suka canja launi zuwa jawur, sannan kafin ya ce komai, idanunsa suka rine, ya tafi luuu ya faɗi a ƙasa tim! Wani irin uban ihu Mom ta saki dake nuna tsantsar firgici. "Usman! Senate!" A guje ma'aikatan gidan suka shigo. Ganin Senate a ƙasa shame-shame ya sa kowa ya rasa natsuwa. Cikin gaggawa aka ɗauke shi aka sanya shi a mota, aka nufi asibiti da shi, Mom tana kuka tana kiran sunansa. **** A gidan Umma, falon ya yi tsit bayan Bhatool ta ɗan lafa daga kukan da take yi. Umma ta kalli ɗiyarta, sannan ta gyara zama, fuskarta ɗauke da wani irin yanayi na nazari. "Bhatool, tashi ki wanke fuskarki ki zo mu zauna. Akwai maganar da nake son mu yi, magana mai muhimmanci," Umma ta faɗa cikin muryar dake nuna cewa ba wasa take ba. Bhatool ta tashi ta je ta wanke fuskarta, ta dawo ta zauna a ƙasa gaban Umma. Umma ta nisa, sannan ta ce, "Bhatool, na ga abin da yake faruwa tsakaninki da Ahmad.  Ina so ki sani, ni mahaifiyarki ce, kuma ba zan taɓa so miki abin da zai cutar da ke ba. Amma akwai abubuwan da ya kamata mu fuskance su da hankali, ba da fushi ba." Bhatool ta ɗago kai tana kallon mahaifiyarta, tana jiran jin abin da Umma za ta ce. Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da ɗaya   (51) Umma ta ja numfashi mai nauyi, ta kura wa Bhatool idanu cikin tausayawa. Ta mika hannu ta kamo hannun ɗiyarta, ta ji shi a sanyaye.  "Bhatool, na san raɗadin da kike ji a zuciyarki. Na san yadda kike jin tamkar an ci amanarki, amma ina so ki buɗe kunnenki ki ji maganar nan da zan gaya miki a matsayina na mahaifiyarki, kuma uwar da take tsoron miki fushin Allah." Bhatool ta sunkuyar da kanta ƙasa, muryarta a shake ta ce, "Ina jinki Umma." "Bhatool," Umma ta kira sunanta cikin muryar lallashi. "Allah (S.W.T) Ya tsara mana rayuwa da dokoki a cikin Alkur'ani. Kina sanye da iddar Senate ne a yanzu tunda kina da juna biyu. Addini ya haramta miki sauraren wani namiji ko yin soyayya da shi a wannan lokacin. Allah Ya ce a cikin Suratul Baqarah: 'Kuma kada ku ƙulla ƙudurin ƙulla auren a cikin zuciyarku har sai idda ta ƙare.' Wannan yana nufin koda a zuciya ne, bai kamata ki sanya soyayyar wani ba har sai kin sauke abin da yake cikinki." Umma ta ci gaba da bayani, "Annabi (S.A.W) ya yi hani akan mace ta dinga tattaunawa ta soyayya da wani namiji alhali tana cikin iddar wani.  Ahmad mutumin kirki ne, ya tsaya miki, amma duk abin da kuke yi yanzu kuskure ne a addini. Idan kika bari soyayya ta shiga tsakaninku a yanzu, kuna sanya wa rayuwar ku sharri ne kuma kun cire k albarka." Jikin Bhatool ya yi wani irin sanyi ƙalau. Ta ji kalaman Umma suna ratsa kowace jijiyar jikinta. Tabbas, fushin da take yi da Senate ya rufe mata idanu har ta manta da wasu iyakoki na Ubangiji. "Umma," Bhatool ta kira sunanta da ƙyar. "Na gode da kika tunatar da ni. Na yi kuskure, kuma zan janye daga dukkan wata hira ko soyayya da Ahmad har sai na haihu. Amma Umma, ina neman alfarma guda ɗaya; ranar da na haihu, ina son a ɗaura mini aure da Ahmad. Ba na son sake komawa rayuwar baya." Umma ta sauke ajiyar zuciya, ta rungume ɗiyarta. "In dai wannan ne, Allah Ya nuna mana ranar lafiya. Amma yanzu, kiyi haƙuri ki fuskanci Ubangijinki." ***** A can babban asibitin kuma, yanayin ya sauya.  Gaba ɗaya maaikatan gidansu Senate kowa ka ganshi fuska babu fara’a, Mom tana zaune sai kuka take, shi kuma Senate yana ciki, manyan likitoci kusan su biyar suna kansa, kowanne yana ƙoƙarin ganin numfashinsa bai tsaya ba. Daga ƙarshe, babban likitan ya fito yana goge gumin dake goshinsa. Mom ta ruga wajensa tana kuka. "Doctor, yaya jikin nasa? Don Allah ka gaya mini." Likitan ya kalli Mom cikin damuwa. "Gaskiya numfashinsa yana neman agajin gaggawa. Zuciyarsa ta kusa bugawa ne sakamakon wani babban abu da ya danne shi lokaci guda. Dole ne mu mayar da shi sashin kulawa na musamman (ICU) a yanzu haka. Kuma muna buƙatar addu'arku, domin sa'o'i ashirin da huɗu na gaba sune za su tabbatar da rayuwarsa." Mom ta saki wani kuka mai ban tausayi, ta zube a ƙasa tana kiran "Usman! Usman!". Dad da suke waya da Mom tana fada masa komai liktan ya fito ya ce kar ta kashe, ya runtse idonsa, yana ambaton sunan Allah. An tura gadon Senate zuwa dakin ICU, fuskar nan tasa dake cike da kwarjini ta yi fari fat, injina ne kawai suke taimaka masa wajen jawo numfashi. Masu aikin gidansu Senate dake waje duk sun zubar da hawaye ganin yadda mai gidansu gashi kwance matacce ko rayayye ba a sani ba. A gidan Umma kuwa, Bhatool ce ga dauki waya ta kira bayan ta ɗaga Yaya karima ta ce. “Yana ji kin yi wani jugum.” Ita kuwa Bhatool tunanin maganganun Umma da kuma yanayin da Senate ya fita daga gidan suna ta yawo a ranta. Zama  ta gyara sannan ta ce . “Senate yazo.”  "Mene ne ya faru? Da Senate ya zo ɗin?" Bhatool ta sauke numfashi, ta kwashe dukkan abin da ya faru ta gaya wa Yaya Karima. Ta gaya mata yadda suka yi faɗa da Senate, kalamai masu zafi da ta gaya masa, da kuma yadda ta fito fili ta nuna tana son Ahmad a gabansa. Ta ƙara da gaya mata nasihar da Umma ta yi mata na janye soyayyar Ahmad har sai ta haihu. Yaya Karima ta yi shiru na wasu mintuna, sannan ta ce, "Bhatool, gaskiya Umma ta faɗi gaskiya. Dokar Allah ta fi ƙarfin komai .Amma ina so ki sani, kalaman da kika gaya wa Senate a halin da yake ciki na nadama, suna da nauyi sosai. Na san yana da kuskure, amma zuciyar namiji idan ta karye tana da wuyar gyara. Kiyi haƙuri ki fuskanci addu'a yanzu, ki bar maganar Ahmad tukunna har lokacin da Allah zai sauke ki." Bayan sun jima suna tattaunawa, Yaya Karima ta yi mata sallama ta kashe wayarta, zuciyarta ba daɗi. Tun da suka yi waya, Yaya Karima ta kasa samun natsuwa. Ta sanya mayafinta ta nufi gidan Mom don gaishe ta da kuma jin halin da ake ciki. Tana shiga, ta iske gidan shiru, ma'aikatan gidan suka shaida mata cewa gaba ɗaya su Mom suna asibiti tun ɗazu domin Senate ya yanke jiki ya faɗi. Wani irin uban razana Yaya Karima ta yi. "Asibiti kuma? Me ya faru?" Ba ta tsaya jiran amsa ba, ta kira mijinta Barrister Al-Amin ta gaya masa halin da ake ciki. Shi ma hankalinsa ya tashi, ya zo ya kwashe ta a mota suka nufi asibitin. Suna isa, suka iske Mom a waje tana kuka, Yaya Karima ta ƙarasa wajen Mom tana tambaya. Mom ta nuna mata dakin ICU da hannu, muryarta a shake ta ce, "Usman yana neman mutuwa Karima... zuciyarsa ce take kumbura." Yaya Karima ta leƙa ta gilashin dakin ICU. Ganin Senate kwance, an yi masa rubdugu da wayoyin na'urori, fuskarsa ta yi fari  tamkar gawa, ya sanya ta jin wani irin tsoro da firgici. Ta tuna yadda Bhatool ta gaya mata kalaman zafin da ta gaya masa ɗazu, sai ta ji jikinta ya yi sanyi. "Wannan sharrin na Maman Anas ya kai Usman ga rami," Yaya Karima ta faɗa a cikin ranta, hawaye yana zubo mata. Ta san cewa idan wani abu ya sami Senate, rayuwar Bhatool ma ba za ta taɓa natsuwa ba saboda nauyin nadama. Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da biyu   (52) Bayan dawowar Yaya Karima gida daga asibiti, ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana shiga ɗaki ta iske mijinta Barrister Al-Amin zaune a gefen gado, shi ma fuskar nan tasa cike da damuwa. Ta zube a kan kujerar dake ɗakin, ta rufe fuskarta da hannu biyu. "Barrister, gaskiya halin da na ga Senate ya kr ciki ya tsoratar da ni. Mutumin da kake gani jiya yana takawa da ƙafafunsa, yau gashi kwance numfashinsa ma na inji ne," Yaya Karima ta faɗa cikin murya mai rauni. Barrister Al-Amin ya nisa, ya gyara zamansa. "Karima, lamarin nan akwai nauyi. Kin ga dai kalaman da Bhatool ta gaya masa su ne suka zama sanadiyyar rugujewar lafiyarsa. Gobe ina so ki koma gidan Umma, ki zauna da Bhatool ki sake yi mata nasiha. Ki bayyana mata halin da yake ciki na mutuwa-ko-rayuwa. Ba don lallai ta koma gare shi ba, amma don ta san cewa tana da nauyi a kanta idan wani abu ya same shi." Haka kuwa aka yi, washe gari tun safe Yaya Karima ta nufi gidan Umma. Ta iske Bhatool zaune tana gyara wasu kayan sanyi na jariri, fuskarta babu alamun damuwar abin da ya faru jiya. "Bhatool," Yaya Karima ta kira sunanta cikin sanyin murya. "Ina so ki buɗe kunnenki ki ji ni. Jiya na je asibiti, na ga Usman. Yana can kwance a ICU, zuciyarsa ta fara kumbura saboda kalaman da kika gaya masa. Likitoci sun ce sa'o'i ashirin da huɗu ne kawai aka ba shi na rayuwa idan bai farfaɗo ba." Bhatool ta dakata da abin da take yi, ta ɗan yi shiru na wasu daƙiƙoƙi, sannan ta ɗago kai ta kalli Yaya Karima sannan ta ce "Yaya Karima, na ji dukkan abin da kika faɗa. Kuma ina mishi addu’ar Alllah ya bashi lafiya idan zai tashi. Amma ina so ki sani, ni na riga na gama da shafin Senate a rayuwata. Mutuwar sa ko rayuwarsa ba ta gabana dan bazan sake komawa dgareshi ba. Shi ya zaɓi ya yarda da ƙarya, ni kuma na zaɓi in yarda da gaskiyar da Ahmad ya kawo mini." Yaya Karima ta ji jikinta ya yi sanyi, ta kasa sake cewa uffan ganin yadda Bhatool ta rufe idonta baki ɗaya. Bayan ficewar Yaya Karima, Bhatool ta ɗauki wayarta ta kira Ahmad. Muryar Ahmad ta fito a sanyaye lokacin da ya ɗaga. "Bhatool, kina lafiya? Na damu tun jiya ina kiranki ba ta shiga." Bhatool ta nisa, sannan ta gaya masa nasihar da Umma ta yi mata na su janye maganar soyayya har sai ta haihu don gudun fushin Allah. "Yaya Ahmad, don Allah karka ga laifina. Ina son mu bi dokar Allah ne don aurenmu ya sami albarka." Ahmad ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin muryar roƙo, "Bhatool, na yarda da duk abin da kika faɗa, kuma zan bi umarnin Umma. Amma ina roƙonki don Allah, karki guje ni. Kar kice tunda tsohon mijinki ya dawo kuma yana asibiti, hakan zai sa ki fasa aurena. Ba zan iya jure rashinki ba." Wani irin karsashi Bhatool ta ji ya dawo mata. Ta danne dukkan wani rauni, ta ce, "Yaya Ahmad, karka damu. Na riga na ba ka zuciyata. Ina sake ba ka alƙawari, komai rintsi, komai wuya, kuma ko ma mene ne zai faru da kowa, ina tare da kai. Ranar da na haihu, ina jiran ganinka a matsayin mijina." Ahmad ya sauke numfashi na jin daɗi. "Na gode Bhatool. Na gode da kika zaɓe ni." Haka suka kashe wayar, kowanne yana jin daɗin amana da alƙawarin dake tsakaninsu. A can dakin ICU na asibitin kwararru, na'urorin dake jikin Senate suka fara bada wani sauti na daban. Likitoci suka taru a kansa cikin hanzari. Senate ya fara motsa yatsunsa, sannan a hankali ya buɗe idanunsa dake dishi-dishi. Abin da ya fara fitowa daga busasshen bakinsa shi ne sunan da ya zame masa abincin zuciya. "Bha... Bhatool... Bha... tool..." Ya faɗa muryarsa tana rawa, kafin ya sake lumshe idanunsa ya koma wani dogon bacci sakamakon magungunan da aka ba shi ta hanyar allura da ruwa. Babban likitan ya fito ya kalli Mom. "Hajiya, muna buƙatar wadda yake kira a kusa da shi. Wacece Bhatool? Domin a yanzu, jin muryarta ko ganin fuskarta shi ne kaɗai zai iya sanyaya kumburin zuciyarsa." Mom ta fashe da kuka, ta rufe fuskarta. "Matarsa ce da ya sake ta a cikin fushi Doctor." Dad ne ya shigo asibitin a daidai wannan lokacin. Mom ta tare shi cikin kuka ta gaya masa duk abin da likita ya faɗa. "Alhaji, don Allah ka taimaka ka je gidansu. Ka yi amfani da damarka tun da Mahaifiyartatana ganin mutuncinka. Idan kai ka je, ba za ta ƙi ba. Rayuwar Senate tana cikin haɗari, xuwam Bhatool a yanzu a yanzu zai taimaka." Dad ya yi shiru, ransa bai so zuwa ba saboda kuskuren da ɗansa ya yi, amma ganin halin da Senate yake ciki, ya gyada kai ya nufi gidan Umma. Dad ya isa kofar gidan Umma, zuciyarsa tana wani irin bugun da ya daɗe bai ji irinsa ba. Haka ma Umma dake zaune a falo, tana jin fakin ɗin motarsa, ta ji wani irin faduwar gaba.  Kusan mintuna biyar sannan almajiri ya shigo yana faɗin. “Wai Akwai baƙo a waje.” Daƙyar Umma ta iya cewa. “Ka ce yab shigo.”  Tana fitowa ta iske shi tsaye. Idanunsu suka sarke a cikin na juna na wasu daƙiƙo, wani tsohon so ya ratsa tsakaninsu. "kiyi haƙuri na zo miki a wannan lokacin," Dad ya faɗa muryarsa na rawa. "Usman yana cikin wani hali a asibiti. Likitoci sun ce sai Bhatool ta je. Don Allah ku taimaka mini." Umma ta ji jikinta ya yi sanyi. "Alhaji, shigo ciki. Bari in kira ta." Umma ta shiga ɗaki ta gaya wa Bhatool halin da ake ciki. Bhatool ta miƙe tsaye, amma maimakon ta fito, sai ta ɗauki wayarta. "Umma, bari in kira Yaya Ahmad in tambaye shi. Ba zan iya fita ba tare da izinin sa ba." Ran Umma ya ɓaci matuƙa, ta daka wa Bhatool tsawa. "Bhatool! Akan wannan yaron ne kike son nuna wa mahaifin Senate rashin kunya? Mutumin da ya riga ya zo har gida? Tashi ki sanya mayafinki mu tafi yanzu!" Bhatool ta ga ran Umma ya ɓaci, kuma tana jin nauyin Dad dake jiran su. Ta sanya mayafinta jikinta a sanyaye, amma a ranta tana jin tamkar tana ci wa Ahmad amana ne. Suka fito tare, Dad yana gaba, Umma da Bhatool suna biye da shi a baya. Suka shiga motar Dad, gaba ɗaya motar ta cika da wani irin shiru mai nauyi. Umma tana kallon titi, Dad yana tuƙi cikin tunani, yayin da Bhatool take tattaunawa da zuciyarta akan yadda za ta kalli mutumin da ya riga ya zama gawa a rayuwarta. Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da uku   (53) Tafiyar da suke yi a cikin motar ta kasance cike da wani irin yanayi mai wuyar fassara. Dad yana riƙe da sitiyari, amma hankalinsa ba ya kan titi gaba ɗaya. Duk lokacin da ya kalli madubin motar ya ga fuskar Umma, sai ya ji wani irin bugun zuciya wanda ya yi tsammanin ya binne shi shekaru ashirin da wani abun da suka wuce. Dad ya riga ya tabbatar da ceqa har yanzu, akwai wani sashi na zuciyar sa dake son Umma fiye da kowace mace, kuma hakan ne ya sa yake jin nauyin dukkan kuskuren da ɗansa ya yi wa ɗiyarta. Ita ma Umma, ƙamshin turaren Dad dake cikin motar ya tuna mata da zamanin ƙuruciya. Ta runtse idonta tana jin yadda zuciyarta take bugawa, tana mamakin yadda rayuwa take juyawa; yau ga ɗiyarta tana fuskantar kusan irin jarrabawar da ita ma ta fuskanta na rabuwa sa masoyi, ita ga mahaifin Senate, ɗiyarta ga Senate.  Suna isa asibitin, suka iske Mom da Yaya Karima a ƙofar ICU. Mom ta taso da sauri ta riƙe hannun Bhatool, tana kuka ƙasa-ƙasa. "Bhatool, na gode da kuka zo. Don Allah Bhatool, ki taimaka ki shiga wajensa. Rayuwarsa tana rai fakwai mutu fakwai." Bhatool ta tsaya cak, ta murtuke fuska ta kame a wani gefe ta zauna a kan doguwar kujerar dake corridor ɗin asibitin. Ta duƙar da kanta ƙasa, tana wasa da yatsunta, fuskarta babu alamar tausayi. "Bhatool, tashi ki shiga," Umma ta faɗa cikin muryarta mai natsuwa da ratsa jiki. Bhatool ta girgiza kai. "Umma, ba zan iya shiga ba. Na riga na gaya muku shafin Senate ya rufu a wajena. Kuma na yi wa Ahmad alƙawarin ba zan ƙara kusantar wani namiji ba." Yaya Karima ta ƙaraso kusa da ita. "Bhatool, wannan fa maganar rai da mutuwa ce. Ba wani abu za ki yi ba, kawai kiran sunanki yake yi." Bhatool ta ƙara tamke fuska. "Sai me idan ya kira sunana? Lokacin da nake kiran sunansa yana Abuja me ya faru dani? Don Allah ku bar ni in zauna a nan." Dad ya kalli Umma cikin wani irin yanayi na roƙo, idanunsa suka bayyana mata raunin da yake ciki. Umma ta ji wani irin zafi ya taso mata. Ta ƙarasa gaban Bhatool, ta daka mata wani uban tsawa wanda ya sanya kowa a corridor ɗin waigowa. "Bhatool! Na ce ki tashi ki shiga ɗakin nan yanzu! Shin rashin kunya kika koya ne ko kuwa taurin kai? Mahaifinsa yana tsaye a nan yana roƙonki amma kina nuna isa? Tashi ki shiga kafin raina ya ɓaci fiye da haka!" Bhatool ta san idan Umma ta yi magana da  irin muryar kuma cike da faɗa. to da gaske take komai za ta iya yi. Ba shiri tamiƙe jiki a sanyaye, jikinta yana rawa saboda ɓacin ran mahaifiyarta. Ta kalli Dad, ta ga yadda idanunsa suka cika da ƙwalla, sai ta ji wani irin nauyi a ranta. Ta taka zuwa ƙofar dakin ICU. Ma'aikaciyar jinya ta buɗe mata ƙofar. Bhatool ta ja numfashi, sannan ta sanya ƙafarta a cikin ɗakin dake warin magunguna da ƙarar injina. Tana shiga, idanunta suka sauka akan Senate. Ya rame sosai, fuskarsa ta yi haske amma hasken dake nuna rashin lafiya. An sanya masa na'urori a ƙirji da hanci. Ganinsa a wannan halin ya sa Bhatool jin wani irin abu ya soke mata zuciya, wanda ta kasa tantance ko tausayi ne ko kuma sauran soyayyar da take ƙoƙarin kashewa ce take son tashi. Ta ƙarasa kusa da gadon, ta tsaya tana kallon fuskarsa. Muryarta a shake, ta kira sunansa can ƙasan maƙogwaro. "Usman..." Yana jin muryar Bhatool, koda yake a shake take, sai ga shi na'urorin dake jikin Senate sun fara bayar da sauti mai sauri, alamar zuciyarsa ta buga da ƙarfi. A hankali ya fara buɗe idanunsa, waɗanda suka yi dishi-dishi. Ganin fuskar Bhatool a kusa da shi ya sanya shi ƙoƙarin miƙa hannunsa dake maƙale da ƙarin ruwa, amma ya kasa. "Bha... Bhatool..." Ya faɗa muryarsa tana rawa, numfashinsa yana sarƙewa. "Bhatool ina sonki... Don Allah karki rabu da ni. Bhatool don Allah, don Annabi, karki tafi ki bar ni a cikin wannan halin." Bhatool ta tsaya tana kallonsa, amma maimakon tausayi, sai ta ji wani irin zafi yana taso mata. Ta dinga jifan sa da wata irin harara mai cike da tsana da raɗadin abin da ya yi mata a baya.  Hararar tata ta kasance tamkar kibiya ce dake huda masa ragowar zuciyarsa. Daidai wannan lokacin ne su Umma, Dad, da Mom suka kasa jurewa, suka turo ƙofar ɗakin suka shigo don ganin halin da ake ciki. Senate ya ga mahaifinsa da mahaifiyar Bhatool, sai ya ji wani irin ƙarfi ya zo masa kawai ya yanke shawarar amfani da damar a matsayin damar ƙarshe. Ya kalli cikin idanuwan Bhattol da suka cika da ƙwalla. ya nisa cikin wani irin yanayi na ban tausayi. "Bhatool... Na janye sakin da na yi miki... Na mayar da ke ɗakinki a matsayin matata ta sunnah. Ina neman yafiyarki... Ina neman afuwarki a gaban iyayenmu. Don Allah karki ƙi ni..." Kalaman Senate su ka sauka a kunnen Bhatool tamkar saukar aradu. Mayar da auren? A daidai lokacin da ta riga ta yi wa Ahmad alƙawarin rayuwa? A daidai lokacin da zuciyarta ta riga ta kyamaci kowane numfashi na Senate? Wani irin jiri ne ya kwashe ta. Ta ji duniyar tana juya mata, numfashinta ya fara sarƙewa. Zuciyarta ta buga da ƙarfi sakamakon ruɗanin da ta shiga; tsakanin nauyin iddar dake kanta, alƙawarin Ahmad, da kuma kalaman mayar da auren da Senate ya yi a mazauninsa na miji. "A'aaaaaaa!" Bhatool ta sake wata irin razananniyar ƙara wadda ta karaɗe cikin asibitin, ta fara tafiya  kamar wacca ta sha wani abu aikuwa ta tafi luuuuu ta zube a ƙasa shame-shame, sumammiya! "Bhatool!" Umma ta faɗa tare da nufar ɗiyarta da ta faɗi a ƙasa.  Senate kuma ganin abin da ya faru, sai numfashinsa ya fara daukewa, na'urar ICU ta fara yin sautin dake nuna cewa zuciyarsa tana neman tsayawa baki ɗaya. Falon asibitin ya rude, likitoci da ma'aikatan jinya suka shigo a guje suna tura kowa waje, yayin da rayuwar Bhatool da ta Senate suka zama tamkar fitila a cikin hadari. Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da huɗu   (54) Bayan kusan sa'o'i biyu da sumewar Bhatool, a hankali ta fara buɗe idanunta waɗanda suka yi jawur saboda tashin hankali. Tana ganin kanta a kan gadon asibiti, sai dukkan abubuwan da suka faru a dakin ICU suka dawo mata daki-daki. Tunawa da kalaman Senate na cewa ya mayar da ita matarsa ya sanya ta yi wani irin kukan kura ta miƙe. "Wallahi ba zan zauna da shi ba! Na tsane ka Usman! Na tsane ka!" Bhatool ta fara ihu tana ƙoƙarin fizge ƙarin ruwan dake hannunta. Ta haukata asibitin gaba ɗaya, nurses sun kasa riƙe ta, sai kuka take yi tana surutai tamkar wadda ta zauce. "Saki na zai yi! Gara in mutu da in sake zama matar Senate! Umma don Allah ki ce ya sake ni!" Umma dake tsaye a gefe, hawaye ya wanke mata fuska, ganin yadda ɗiyarta take neman fita daga hayyacinta. "Alhaji, don Allah a sanya ta a mota a kai ta gida kawai. Wannan tashin hankalin zai iya shafar abin da yake jikinta," Umma ta faɗa cikin muryar roƙo ga Dad. Daidai lokacin da aka fito da Bhatool daga ɗakin, tana kuka tana fizge-fizge, sai ga Abdul da Ahmad sun shigo asibitin a guje, sakamakon kiran da aka yi musu. Abdul ya nufi ƙanwarsa da sauri.  “Lafiya me yake faruwa, ihun me take?.” Yaya Karima ce ta kwashe dukkan abin da ya faru aka gaya masa. Bhatool tana ganin Abdul, ta faɗa jikinsa ta rungume shi, tana kuka mai ban tausayi wanda ya sanya kowa a wurin zubar da hawaye. " Abdul, ka ji abin da ya yi mini ko? Ya ce ya mayar da ni bayan ya wulakanta ni. Don Allah ka ce ya sake ni, ba na son sa!" Abdul ya ƙanƙame ƙanwarsa, idanunsa suka cika da ƙwalla. "Yi haƙuri Bhatool. Komai zai wuce, kiyi haƙuri ko don abin da yake jikinki." A gefe ɗaya kuma, Ahmad yana tsaye tamkar wanda aka shuka. Kalaman Senate na cewa ya mayar da Bhatool matarsa sun dake shi fiye da saukar aradu. Ya kalli Bhatool yadda take kuka a jikin Abdul, ya kalli yadda dangi suka taru suna jajanta wa juna. Wani irin raɗadi Ahmad ya ji a zuciyarsa, amma sai ya tuna da kaddara. Ya tuna cewa duk yadda ya so Bhatool, idan Allah bai nufa ba, ba za ta taɓa zama tasa ba. Ya juya a hankali, hawaye guda ɗaya mai zafi ya zubo masa a kumatu. Ya fice daga asibitin gaba ɗaya, bai jira kowa ba. Yana shiga motarsa, ya dafe sitiyari. "Bhatool ba rabona ba ce," ya faɗa a cikin ransa cikin murya mai cike da sadaukarwa. "Idan har mayar da aurenta shi ne zai ba ta natsuwa kuma ya ceci rayuwar Senate, to na haƙura. Allah Ya ba su zaman lafiya, Allah Ya sanya hakan shi ne mafi alheri a gare ta." Ahmad ya tada motarsa ya bar asibitin, ya bar zuciyarsa a can, ya tafi da wani babban nauyi aransa, shin nadama ce ko kishine shi dai yakasa  cewa komai, yasan dai ya yi jarumta ta ƙarshe. A cikin motar Dad kuwa, Bhatool tana kuka a jikin Umma har suka isa gida. tana isa gida, ta fada kan gado tana wani irin kuka mai cin zuciya. Kowane sassa na jikinta rawa yake yi saboda fushi da radadin kalaman Senate. Abdul ya shigo dakin, ya zauna a gefen gadon yana kallon kanwarsa cikin tsananin tausayi. Ya sa hannu ya dafa kafadar ta, muryarsa a sanyaye ya ce. "Bhatool, kiyi shiru haka nan. Na san abin da kike ji, kuma na san yadda zuciyarki take tafasa. Amma ina so ki kwantar da hankalinki, na miki alkawari, muddin wannan auren zai zama silar damuwarki, zan tsaya miki da kaina wajen neman saki a wurin Senate. Ba zan bar ki a inda ba kya so ba, kiyi hakuri ko don abin da yake jikinki." Jin kalaman Abdul ya sanya Bhatool jin wani dan sanyi, ta dan rage kukan amma har yanzu hawaye ba su daina zuba ba. A can asibiti kuwa, bayan ficewar su Bhatool, Senate ya fara farkawa a hankali. Na'urorin dake jikinsa sun nuna cewa bugun zuciyarsa ya fara daidaita. Ya bude idanunsa, wannan karon babu dishi-dishi. Ya kalli Mom dake gefensa, ya yi wani dan gajeren murmushi na rauni. "Mom... ina Bhatool?" Ya tambaya murya can kasa. Likitoci sun tabbatar da cewa kumburin zuciyarsa ya fara raguwa sakamakon ganin Bhatool da ya yi, wanda hakan ya ba shi karsashin rayuwa. Jikinsa ya fara sauki sosai, har aka fara cire masa wasu daga cikin na'urorin dake maƙale da shi. Bhatool tana kwance a gida, hannunta rike da waya. Ta kira Ahmad kusan sau goma amma bai daga ba. Zuciyarta tana wani irin bugawa, tana tsoron kar Ahmad ya fahimcita ba dai dai ba. Ta sake tura masa sako fuskarta ɗauke da ƙwalla.  "Yaya Ahmad, don Allah karka guje ni. Karka yarda da kalaman Senate, kai nake so..." Ahmad, wanda yake zaune a cikin motarsa a gefen titi, yana kallon wayar tana haske. Hawaye ne ke zuba a idanunsa, amma ya daure ya kudurce wa kansa cewa sadaukarwa ita ce kololuwar soyayya. Ya dauki wayar, ya rubuta mata sako mai ratsa zuciya kamar haka. "Zuciyata, Bhatool. Na karbi sakonki, kuma na ji dukkan kukan dake cikin muryarki. Bhatool, soyayya ba wai mallakar masoyi ba ne kawai, soyayya ita ce ganin farin cikin masoyi a inda ya fi dacewa da shi. Senate ya mayar da ke dakinki a daidai lokacin da yake tsakanin mutuwa da rayuwa, hakan ya nuna cewa ke ce numfashinsa.  Ni kuma, zan zama silar da zan janye domin ki sami natsuwa da danginki da kuma mahaifin abin da yake cikinki. Ba zan iya gina farin cikina a kan rugujewar rayuwar wani ba, musamman mutumin da yake neman yafiyarki a mawuyacin hali. Na yafe miki dukkan alkawarin dake tsakaninmu. Kiyi biyayya ga mijinki, ki raini danki a cikin soyayya. Zan kasance mai taya ki murna daga nesa. Allah Ya bar ku tare, Allah Ya sanya alheri a rayuwarki ta gaba. Salam." Bhatool tana karanta wannan sako, ta saki wani uban kuka mai taɓa zuciya. Ta kankame wayar a kirjinta, tana jin yadda Ahmad ya nuna mata tsantsar karamci da sadaukarwa. Sakon Ahmad ya sauka a zuciyar Bhatool tamkar ruwan kankara, duk da radadin dake tattare da shi, amma ya sanyaya mata jiki sosai. Ta fahimci cewa Ahmad mutum ne mai daraja wanda ba zai taba zama silar rugujewar gidanta ba. Cikin kuka ta kira Jannah, ta kwashe dukkan abin da ya faru da kuma sakon Ahmad ta fada mata. Ba a jima ba sai ga Jannah ta bayyana a gidan Umma. Ta zauna kusa da Bhatool, ta fara mata nasiha mai ratsa jiki. "Bhatool, kaddara ta riga ta gifta har wani abu ya faru tskanin ku da  Senate, amma Ahmad ya nuna miki girmansa, mutunci da karamci, kuma ya sauke miki nauyin dake kanki. Yanzu abin da ya rage miki shine kiyi hakuri ki koma ga mijinki, musamman yadda ya nuna nadama a lokacin da yake tsakanin rai da mutuwa." Bhatool ta ja numfashi, ta goge hawayenta. "Jannah, na hakura. Zan zauna da Senate tunda haka kaddarar take. Amma ina so in nuna masa cewa na yafe masa ne don Allah." Jannah ta yi murmushi, "To idan har hakan ne, tashi ki shiga kicin ki yi masa girki na musamman, ki kai masa asibiti. Wannan zai nuna masa cewa baki rike shi a zuciya ba, kuma zai kara masa karsashin tashi daga rashin lafiyar." Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da biyar.   (55) “Ahamd jiya ka kona mini rai, na so maka ka aure Bhatool, ka zauna da ita ka rabata da wancan Senate din, amma ka nuna kai ba haka ba, canka yanka.” Bhatool ta amince, ta shiga kicin ta hada wani daddadan girki wanda kowa ya gani yasan ta yi bajinta akansa. Lokacin da ta kai asibiti, kowa ya yi mamaki da murnar ganin Bhatool da abinci a hannunta. Wannan karimcin ya burge Mom, Dad, da dukkan dangin Senate. Washe gari, garin Yobe ya dauki dumi da shagalin bikin Jannah. Dangi da abokan arziki duk sun hallara.  A daren Ladies Night da ake yi a gidan Yayar Jannah, falon biki ya cika da mutane yan uwa da kawaye. Bhatool tana zaune a cikin wasu kawayenta, sai ga Amrah ta shigo. Tana ganin Bhatool, Amrah ta kasa karasawa cikin taron. Ta tsaya daga nesa, idanunta suka cika da kwalla. Bhatool ta lura da ita, ta mike ta karasa wajenta. Amrah ta fashe da kuka, ta kama hannun Bhatool tana neman gafara. "Bhatool, kiyi hakuri. Na san abin da na yi miki ya wuce misali, amma don Allah ki yafe mini. Zuciyata ba ta ƙara samun natsuwa ba tun ranar da kika bar gidan mijinki." Bhatool ta tausaya mata, ta kamo hannun Amrah ta ce, "Amrah, komai ya wuce. Na yafe miki duniya da lahira. Allah Ya yafe mana baki daya." Amrah ta ji wani irin dadi, ta gaya wa Bhatool cewa itama bikin ta ya rage saura sati biyu kacal. Suka gaisa cikin mutunci, abin da ya ba kowa mamaki ganin yadda suka yafe wa juna. A can gidan Mom kuwa, Senate ya wartsake sosai. Kumburin zuciyarsa ya ragu, kuma likitoci sun ba shi damar komawa gida domin ya ci gaba da hutawa. Yana shiga gidan, ya iske ko'ina an gyara masa. Zama ya yi a falon kasa, yana kallon hoton Bhatool dake manne a bango. Ya ji wani irin dadi a ransa jin cewa Bhatool ta duba shi har ta yi masa girki, kuma ya ji labarin yadda ta hakura da zama da shi. "Zan nuna miki soyayya fiye da wadda na nuna miki a baya, Bhatool," Senate ya fada wa kansa, yayin da yake jin karsashin lafiyarsa na dawowa gaba daya. Bikin Jannah ya ci gaba da ƙawata gari Bayan taron Ladies Night da aka yi wanda ya zama silar sasanci tsakanin Bhatool da Amrah, washe gari aka gudanar da gagarumar Walima. Malaman addini mata sun gabatar da wa'azi mai ratsa jiki, inda suka yi bayani a kan haƙuri da zaman takewar aure. Bhatool tana zaune cikin sauran ƙawaye, tana sauraren kowane kalma, tana jin tamkar kanta ake yi wa wa'azin. An tashi taro lafiya, kowa ya fito fuska cike da annuri. Rana ba ta ƙarya. Ranar Juma'a aka ɗaura auren Jannah da abokin Senate a babban masallacin Juma'a. Taron ya cika da manyan mutane, kuma an yi komai cikin tsari da albarka. Senate, duk da cewa bai daɗe da fitowa daga asibiti ba, ya halarci ɗaurin auren, koda yake bai zauna ya sha wahala ba. An gama biki lafiya, amarya ta tare a gidanta na Abuja cikin so da ƙauna. Bayan kwanaki biyu da kammala bikin Jannah, Senate ya fara fitowa waje don ƙara samun natsuwa. Yanzu hankalinsa gaba ɗaya ya karkata ga neman gafarar Bhatool ta hanyar nuna mata tsantsar soyayya. A karon farko, Senate ya nufi gidan Umma da yamma. Ya tsaya a ƙofar gida, ya kira wayar Bhatool. Muryarsa a sanyaye ya ce, "Bhatool, ina kofar gida. Don Allah ki ba ni dama ko da na mintuna biyar ne in ganki." Bhatool ta ɗan yi shiru, sannan ta sanya mayafinta ta fito. Ta iske shi jingine da motarsa, ya ɗan rame amma kwarjininsa na nan. Ganin Bhatool ya sanya Senate sakin wani murmushi mai sanyi. Bai yi mata maganar baya ba, sai dai ya miƙa mata wata leda mai ƙamshi. "Na kawo miki abubuwan da kike so ne. Na gode da kika amince kika fito," ya faɗa cikin girmamawa. Haka Senate ya dinga zuwa kusan kowace rana. Wani lokacin yakan zauna da Abdul su yi hira, wani lokacin kuma ya samu damar zama da Bhatool na ɗan lokaci. Yanzu ya daina nuna isa ko izza, ya koma tamkar wani sabon saurayi dake neman soyayyar budurwa. Wannan sauyin hali na Senate ya fara sanyaya zuciyar Bhatool, duk da cewa har yanzu akwai tabon abin da ya faru a baya. A haka aka kwashe sati biyu, inda zumunci ya fara dawo wa tsakaninsu. Ahmad ma ya janye gaba ɗaya kamar yadda ya yi alƙawari, wanda hakan ya ba Bhatool damar fuskantar rayuwarta ba tare da rudani ba. Gari ya sake ɗaukar wani sabon dumin na bikin Amrah. Tunda amincinsu ya dawo, Bhatool ta tsaya tsayin daka wajen taya Amrah shirye-shiryen bikinta. An yi shagalin biki na gani ta fada, kowa yana mamakin yadda Bhatool ta ci gaba da mutinci da Amrah har ta taya ta abubuwan bikim ta , wanda ya nuna a tsakaninsu akwai wani aminci da zumunci mai ƙarfi. Ranar ɗaurin auren Amrah, gidan ya cika da murna. Amrah tana kuka tana sake neman gafarar Bhatool yayin da take shirin tafiya gidan mijinta. "Bhatool, kaddara ce ta sa na yi miki kishin hauka, amma yau gashi zan tafi nawa gidan. Don Allah karki daina sanya ni a addu'a." Bhatool ta rungume ta, "Allah Ya sanya alheri a aurenki Amrah. Komai ya wuce." Bayan an tafi da Amrah, Senate ya zo ya ɗauki Bhatool don mayar da ita gida. Suna cikin mota, ya kalle ta cikin sanyi. "Bhatool, yanzu kowa ya fara samun natsuwa. Saura mu kadai. Ina so ki sani, ina jiran ranar da zaki ce mini kin yafe mini baki ɗaya." Bhatool ta yi murmushi ta kalli titi. "Zuciyata tana kan hanyar hakan, Senate." Soyayya tsakanin Senate da Bhatool ta koma sabuwa ful, tamkar yanzu aka fara zancen. Duk da cewa tana gidan Umma, amma Senate ya mayar da gidan tamkar nasa. Kullum yana nan, idan ya zo ba ya tafiya sai dare ya yi, hira suke yi ta natsuwa inda Senate yake ta ba ta haƙuri tare da nuna mata tsantsar nadama. Sai dai, duk da wannan shauƙi, Mom ta tsaya a kan matsayarta na cewa: "Babu maganar Bhatool ta koma gidan Senate har sai ta haihu lafiya, ta yi jegon ta ta gama." Wannan hukunci ne Mom ta yanke wa Senate a matsayin horo na rashin bincike da gaggawar da ya yi wajen sakin mata ta wayar tarho. Senate ba shi da yadda zai yi, ya amshi wannan hukunci cikin sanyin jiki, yana mai cewa, "Mom, zan jira koda shekara nawa ne, muddin zan sake samun Bhatool a matsayin matata." Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da shida   (56) A ɓangaren Abdul kuwa, labari ya sauya. Ganin yadda Ahmad ya nuna halin girma da sadaukarwa, sai shaƙuwa ta ƙaru tsakanin iyalansu. Cikin ikon Allah, Abdul ya ga ƙanwar Ahmad, mace mai natsuwa da tarbiyya. Ba tare da ɓata lokaci ba, aka shiga maganar magabata. Cikin ƙanƙanin lokaci, aka ƙulla auren Abdul da ƙanwar Ahmad. Ganin yadda kowa yake son ƙulla wannan zumunci, aka sanya lokacin auren a gurguje wata guda kacal! Wannan lamari ya sanya farin ciki a zukatan kowa, musamman Bhatool dake jin daɗin cewa zumuncin da ta so ƙullawa da Ahmad ta hanyar aure, yanzu zai tabbata ta hanyar ɗan'uwanta. Kwanaki sun fara gudu tamkar walkiya. Shagalin bikin Abdul ya kankama, yayin da cikin Bhatool shi ma ya ƙara girma, ya shiga watan ƙarshe wanda daga shi sai watan haihuwa. Senate ya dage wajen ganin bikin Abdul ya ƙayatar, domin yana jin nauyin yadda Ahmad ya janye masa fage. Wata rana, suna zaune a tsakar gidan Umma, Senate ya kalli Bhatool wadda take fama da  jikinta saboda nauyin ciki. Ya kamo hannunta, ya dube ta cikin ƙauna. "Bhatool, saura kwanaki kaɗan biki, kuma saura kwanaki kaɗan mu ga jaririnmu. Ina addu'ar Allah Ya kawo ranar lafiya, domin ranar ita ce zan fara rayuwa ta gaskiya da ke." Bhatool ta yi murmushi, wanda ya bayyana kyakkyawar fuskarta dake cike da annuri. "Insha Allah Senate. Komai zai wuce lafiya. Amma karka manta, ka yi mini alƙawarin ba zaka sake saurarar maganar kowa a kaina ba." Senate ya rungume hannunta a ƙirjinsa. "Na miki alƙawarin dake tsakanin rai da numfashi, Bhatool. Ke ce tawa har abada." Mom tana zaune a falo tana nazarin wasu takardu, sai ga Anas ya faɗo gidan yana kuka mai ban tausayi, muryarsa tana rawa. Mom ta miƙe cikin firgici tana tambayarsa abin da ya faru. "Mom! Anty ce... ba ta da lafiya! Daga Abuja aka kira ni ake gaya mini wai tun safe take surutai, ta haukace gaba ɗaya!" Mom ba ta ɓata lokaci ba ta kira Senate, nan take suka garzaya Abuja tare da sauran yan uwa. Suna isa gidan, abin da suka gani ya tsoratar da su. Maman Anas ce zaune a tsakar ɗaki, gashin kanta ya hargitse, ta yayyage kayan jikinta tana ta surutai marasa kan-gado. Tana ganin Senate, sai ta miƙe tana nuna shi da yatsa, tana wata irin dariya mai ban tsoro. "Usman! Ka zo ganin aikina ne? Ni ce na sa Amrah ta yi dukkan abin da ta yi! Ni ce na raba ka da Bhatool! Na tsani ganin farin cikinku!" Ta fara ihu tana kiran sunan Bhatool da Amrah, tana bayyana dukkan makircin da ta ƙulla na raba aurensu. Senate ya tsaya cak, jikinsa yana rawa saboda jin tsantsar muguntar da ‘yar uwar mahaifiyarsa ta aikata. Kafin kowa ya yi yunƙurin kamata, Maman Anas ta daka wani uban tsalle ta fice daga ɗakin da gudu. Su Mom da Senate suka biyo bayanta suna kiranta, amma ta riga ta fita har kan titi tana gudu ba tare da kallon hagu ko dama ba. A daidai lokacin, wata mota mai gudu ta taho, direban ya yi ƙoƙarin taks birki amma abin ya faskara. Motar ta bige ta, ta yi sama ta faɗo. Kafin su ƙarasa kanta, rai ya yi halinsa. Maman Anas ta mutu a take, tana girbar abin da ta shuka na sharri da maƙarƙashiya. A can kuwa, rayuwa ta ci gaba da gudana cikin farin ciki da annuri. Bikin Abdul ya kankama, inda aka yi shagali na gani ta faɗa. Abin farin cikin shi ne, ashe shi ma Ahmad, bayan janyewar da ya yi, Allah ya haɗa jininsa da wata kyakkyawar Cousin ɗinsa, inda aka haɗa aurensu lokaci guda da na Abdul. Bhatool, duk da nauyin cikin dake jikinta, ita ce ta zama "Uwar Biki" a wajen Abdul. Ta dage wajen ganin kowa ya ci ya sha, fuskarta ɗauke da murmushin jin daɗin yadda dangantakarsu da Ahmad ta koma zumunci mai ƙarfi. Tana tsaye a tsakiyar mata, tana raba abinci, sai ta ji wata fāɗuwar gaba. Ta dafe ƙirjinta, ta tuna da Maman Anas ba tare da ta san abin da ya faru ba. Amma ganin yadda Abdul da Ahmad suke cikin murna a matsayin ango da ango, sai ta share damuwar ta ci gaba da taya ɗan'uwanta murna. Bata sani ba cewa a can Abuja, Senate yana tsaye a kan gawar wadda ta zama silar rugujewar farin cikinsa na wani lokaci Senate ya dawo Kano cikin wani irin yanayi na nauyin zuciya. Ko da ya isa gidan Umma, ya iske Bhatool tana cikin hidima da shagalin bikin Abdul. Tana ganinsa, ta fahimci akwai damuwa tattare da shi. Senate ya zauna a gefen gado, ya kasa boye abin dake damunsa, nan take hawaye ya fara zuba a idanunsa. Cikin muryar kuka da rawar jiki, ya kwashe dukkan abin da ya faru a Abuja ya gaya mata. Ya bayyana mata yadda Maman Anas ta haukace, da kuma yadda ta fadi asirin cewa ita ce ta rura wutar kiyayya tsakaninta da Amrah har ta raba aurensu, sannan kuma ga mutuwarta mai ban tsoro a kan titi. Bhatool ta dade tana kallonsa, zuciyarta tana wani irin bugawa. Maimakon ta nuna farin ciki akan mutuwar, sai ta sauke numfashi, ta share wa Senate hawayensa. "Allah Ya jikanta. Ya riga ya kai ta inda babu sauran maƙarkashiya. Gaskiya ta bayyana, kuma wannan shi ne babban abin farin ciki na," Bhatool ta faɗa cikin nutsuwa. "Yanzu don Allah ka bar kukan nan, mu ci gaba da shagalin bikin Abdul cikin farin ciki, tunda Allah Ya wanke mu." Duk da mutuwar ta girgiza ta, Bhatool ta ji wani irin natsuwa a ranta. Sanin cewa ba kuskurensu ba ne ya ruguza aurensu a baya, sai dai tuggun wani, ya sa ta ƙara jin son Senate yana ƙaruwa a ranta. Amrah ma acan gidanta ta sami labarin mutuwar Maman Anas. Ta girgiza matuƙa, ta dinga kuka tana tuna yadda Anty ta dinga zuga ta tana ba ta shawarwarin banza. Ta yi nadamar yadda ta bar kanta a matsayin kayan aiki a hannun wata, har ta kusan ruguza rayuwar Bhatool. Ta kira Bhatool a waya cikin kuka sukayi ta jajantawa juna, inda Amrah ta sake roƙon gafararta a kan dukkan abubuwan da suka faru a baya. Bikin Abdul da Ahmad ya ci gaba da ƙayatarwa. Kasancewar Bhatool ce uwar biki, ta dage sosai duk da nauyin jikinta, Ko'ina aka ga Bhatool, za a ga Senate a bayanta tamkar inuwarta, yana ƙoƙarin kare ta daga kowace irin wahala. A daren ranar walimar su Abdul, an yi taro mai cike da albarka. Ahmad ya zo har kusa da Senate da Bhatool, ya gaisa da su cikin mutunci da ƙauna. Ganin yadda Ahmad ya rungumi ƙaddara har ya auri Cousin ɗinsa, ya sanya Senate jin wata irin kunya da kuma girmama Ahmad a ransa. "Alhaji Usman, Allah Ya bar zumunci," Ahmad ya faɗa yana murmushi. Senate ya dafa kafaɗarsa, "Ahmad, kai jarumi ne. Na gode da komai." Bhatool tana kallon su, tana jin daɗin yadda rayuwarta ta fara fuskantar haske. Gaskiya ta bayyana, maƙiyi ya tafi, sannan masoya duk sun sami natsuwa. Sai dai kuma, a duk lokacin da ta juya, tana jin wani irin nauyi a cikinta, alamar cewa lokacin da kowa yake jira na saukar numfashi ya riga ya ƙarato. Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da bakwai   (57) An kammala bikin Abdul da Ahmad lafiya cikin nasara da albarka. Amaryar Abdul, wato ƙanwar Ahmad, ta tare a gidanta dake kusa da su Umma, yayin da Ahmad shi ma ya tare da tasa amaryar cikin kwanciyar hankali. Wannan aure ya ƙara danƙon zumunci tsakanin gidajen guda biyu, inda kiyayya ta koma soyayya, zargi kuma ya koma yarda. Bayan bikin, hankali gaba ɗaya ya koma kan Bhatool. Senate ya ware kusan dukkan lokacinsa a kanta. Babu inda yake zuwa idan ba asibiti ko wajen aiki ba, to yana gidan Umma. Soyayyar da suke nuna wa juna a wannan lokacin ta zarce kowace irin soyayya da suka yi a baya. Senate yakan zauna ya yi ta yi mata tausa a ƙafarta, yana mata hirar yadda gidan nasu zai kasance idan ta dawo. Wata rana da yamma, suna zaune a tsakar gidan Umma, iska mai daɗi tana kaɗawa. Bhatool ta jingina kanta a kafaɗar Senate, tana kallon cikinta dake ta motsi. "Senate," ta kira sunansa cikin muryar dake cike da natsuwa. "Na'am rayuwata," ya amsa yana ƙara gyara mata zaman mayafinta. "Gaskiya na gaji da wannan zaman gidan Umman. Na matsu in haihu lafiya, in ga jaririnmu, sannan mu koma gidanmu mu ci gaba da rayuwarmu. Ina son in riƙa tashi a kusa da kai, in riƙa kula da kai kamar yadda ya kamata." Senate ya yi murmushi, ya sunbaci goshinta. "Bhatool, nima abin da nake jira kenan kullum a raina. Amma kin san dokar Mom; tace sai kin gama jegonki sannan zaki dawo. Ko kina son mu karya dokar Mom ne?" Bhatool ta ɗan yi fushi na wasa, "A'a, ba karya doka ba, amma gaskiya kewarka tana sanya ni kuka wani lokacin idan dare ya yi." Senate ya ji daɗin wannan kalaman nata. Ya rungume ta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa don ƙaunarta. "Kiyi haƙuri ragowar kwanaki ne suka rage. Insha Allah duk yadda kike so, haka za a yi. Zan sake gyara miki gidan nan ya fi yadda kika sani, domin ke ta musamman ce a gare ni." Haka suka ci gaba da nuna wa juna soyayya mai tsayawa a rai. Kowa ya gansu yakan yi musu fatan alheri, domin sun zama ababen koyi wajen haƙuri da yafiya. Amma a tsakanin wannan annurin, Bhatool tana yawan jin wani irin bacci da kasala dake ziyartar ta, wanda take gani tamkar nauyin ciki ne kawai. Washegari da safe, Senate ya dira a gidan Umma da wani irin hanzari. Fuskarsa dake cike da annuri ta bayyana cewa akwai wani abun farin ciki dake tafe. Bhatool tana zaune a falo tana shan kwanon tatacciyar madara, ta kalle shi tana murmushi. "Wannan annuri haka? Ko an kara maka girma ne a wajen aiki?" Senate ya yi dariya, ya kamo hannunta ya mike da ita. "Tashi mu fita waje, ina son nuna miki wani abu." Bhatool ta mike tana dambarwa saboda nauyin jiki har suka isa kofar gida. Tana fita, idanunta suka sauka akan wata hadaddiyar mota kirar Lexus 2024, fara sol, wadda aka yi mata ado da furanni da kuma rubutun "For My Queen" a jiki. Bhatool ta zaro ido, ta rufe bakinta da hannu biyu saboda mamaki. "Senate Wannan motar fa?" "Kyautar ki ce Bhatool. Kyautar hakurin da kika yi da ni, da kuma farin cikin da kika shigo mini da shi. Ina so ko da yaushe kije asibiti ko wani waje, kije cikin girma da mutunci," Senate ya fada yana mika mata makullin motar. Tana cikin murnar nan, ashe Umma tana tsaye a bakin kofa tana kallonsu tana dariya. Ganin yadda Senate yake ta faman sosa keya da nuna damuwa akan Bhatool, sai Umma ta katsa musu hira cikin barkwanci. "Wai kai Usman, yaushe ne zaka daina wannan rashin kunyar taka? Ka dame mu, kullum kana gidan nan tamkar a nan aka haife ka. Na gaji da ganin fuskarka kullum!" Umma ta fada tana boye murmushin dake fuskarta. Senate ya yi dariya, "Umma, ai kece kika ce na jira sai ta haihu." Umma ta tabe baki a wasa, "To na janye maganar nan. Na gaji da takura, zo ka dauke matarka ku tafi gidanku kawai, tunda gani nake yi kusan tare kuke kwana." Bhatool ta fashe da dariya, ta rufe fuskarta da mayafi saboda kunya. Senate kuwa ya saki wani uban murmushi na jin dadi. "Umma gaskiya kika fada? To yanzu ma zan dauke ta mu tafi!" Haka suka yi ta barkwanci, inda Umma ta kara nuna musu cewa ta yafe wa Senate kuma tana kaunarsa matsayin danta. Wannan ranar ta kasance ranar farin ciki mara misaltuwa. Senate ya dauki Bhatool a sabuwar motar suka zagaya gari, suna jin dadin haduwar kawunansu. Amma a cikin wannan murnar, Bhatool ta kalli Senate ta ce, "Usman, na gode sosai. Amma ina so ka sani, babban burina ba mota ba ne, babban burina shine mu rayu tare cikin aminci har karshen rayuwarmu." Suna tsaka da wannan murnar ta sabuwar mota da kuma barkwancin Umma, farat ɗaya sai yanayin Bhatool ya sauya. Ta saki wani ɗan gajeren nishi, ta dafe ƙugunta yayin da zufa ta fara keto mata a goshi. Senate ya kalle ta cikin firgici, "Bhatool, lafiya? Ko nakuda ce?" "Usman... marata... marata tana murɗawa," ta faɗa cikin murya mai rauni. Ba tare da ɓata lokaci ba, Senate ya sungume ta ya sanya ta a sabuwar motar nan, Umma ma ta rigo ta ɗauki jakar kayan haihuwa suka nufi asibiti a guje. Senate yana tuƙi yana addu'o'i, hankalinsa gaba ɗaya ya tashi, yana kallon yadda Bhatool take ta faman nishi da ambaton sunan Allah. Suna isa asibiti, ma'aikatan jinya suka karɓe ta suka kai ta ɗakin bincike. Bayan kusan mintuna talatin, likita ya fito yana murmushi. Ya kalli Senate da Umma dake jiran jin bayani. "Alhaji, ku kwantar da hankalinku. Wannan  alamun nakuda ne ba naƙudar ba. Duban da muka yi mata ya nuna cewa lokacin haihuwarta (EDD) bai cika ba, akwai sauran mako guda cur. Yanzu za a iya mayar da ita gida ta ci gaba da hutawa." Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da takwas   (58) Wani irin ajiyar zuciya Senate ya sauke, ya kalli Umma suka yi murmushi. Haka suka sake loda kayansu suka dawo gidan Umma. Dawowar nan ya sanya aka ƙara shiga wani sabon shafin na soyayya da kulawa. Senate ya ƙi tafiya gida, ya ce shi a falon Umma zai kwana har sai Bhatool ta haihu. Kullum yakan zauna a ƙasa kusa da ƙafafun Bhatool, yana shafa cikinta yana yi wa jaririn magana. "Ka ga yadda kake wahalar da mahaifiyarka ko? Muna jiran ka ka fito mu nuna maka duniya," Senate yakan faɗa yana dariya, yayin da Bhatool take shafa kansa cikin tsantsar ƙauna. Wannan satin ya zama tamkar karni a wajen Senate. Kowanne motsi na Bhatool yana sanya shi tashi tsaye. Sun ƙara shakuwa fiye da kowane lokaci, suna musayar kalaman soyayya dake ratsa jini da ɓargo. Bhatool tana jin wani irin daɗi a ranta, tana jin tamkar dukkan matsalolin rayuwarta sun ƙare. Mako guda ya wuce cif cikin kwanciyar hankali da annuri, makon da Senate da Bhatool za su dade suna tunawa da shi a matsayin makon da suka fi kowane lokaci shakuwa a rayuwarsu. A duk tsawon kwanakin nan bakwai, Senate bai bar gidan Umma ba. Ya zama tamkar inuwar Bhatool; idan tana daki, yana kofar dakin, idan tana falo, yana zaune a gefenta. Soyayyar da suke nuna wa juna ta kai matsayin da ko Umma idan ta gansu, sai ta sauke ajiyar zuciya tana musu addu'ar Allah Ya bar su tare. Senate ya riga ya gama shirin komawarsu gida, har ya sa an sake yanayin gidan, komai ancanja kujeru da komai da komai, fenti ma kalar da Bhatool take so, sannan ya cika dakin jariri da kayan wasan yara na zamani. Wata rana da yamma, sa'o'i kadan kafin cikar makon, suna zaune a falon Umma a kan sallaya daya. Bhatool ta jingina bayanta a kirjin Senate, tana jin yadda bugun zuciyarsa yake bugawa cikin natsuwa. "Senate," ta kira sunansa cikin murya mai dadi. "Na'am masoyiyata," ya amsa yana wasa da yatsun hannunta. "Ina so ka sani cewa, duk abin da ya faru a baya na yafe maka duniya da lahira. Kuma ina so ka sani cewa kaine babban burina. Idan Allah Ya sauke ni lafiya, ina so ka san cewa ba zan taba manta da irin soyayyar da ka nuna mini a satin nan ba. Ka sanya na ji ni tamkar mace mafi daraja a duniya." Senate ya kara kankame ta, ya sunbaci gefen kanta. "Bhatool, ni ne ya kamata in gode miki. Kin ba ni damar gyara kuskurena, kuma kin karbe ni da dukkan raunina. Allah kadai Ya san yadda nake sonki. Yanzu dai addu'armu daya; Allah Ya kawo ranar nan lafiya mu ga danka a hannunki." Bhatool ta gyada kai, "Amin. Insha Allah komai zai zo da sauki." Haka suka yini cikin farin ciki da nuna wa juna kauna. Dare ya yi, kowa ya kwanta, amma Bhatool ta kasa bacci. Ta dinga kai-komo a daki, tana jin wani irin canji a tattare da ita. Tana kallon agogo, karfe biyu na dare ya buga, daidai cikar mako guda da suka dawo daga asibiti. Farat daya, Bhatool ta ji wani irin nauyi ya sauka mata, wanda wannan karon ta san cewa lallai bako ya iso.  Ƙarfe biyu na dare, shiru ya mamaye ko'ina sai ƙarar injinan sanyaya ɗaki da kukan tsuntsayen dare. Bhatool ta miƙe zaune tana jan numfashi da ƙarfi. Wannan karon, marar ta ba murɗawa take yi ba; ji take yi tamkar ana raba ƙasusuwan ƙugunta gida biyu. "Us...man... Usman!" Ta kira sunansa cikin muryar dake nuna tsananin wahala. Senate dake kwance a kan doguwar kujera a falon Umma, ya farka tamkar wanda aka watsa wa ruwan zafi. Ya faɗo ɗakin Bhatool a guje, ya iske ta tana zufa duk da sanyin AC. "Bhatool! Me ya faru? Nakudar ce?" Ya tambaya yana riƙo kanta, hannunsa yana rawa. "Usman... ta zo... yanzu take... daban take da ta wancan karon," ta faɗa tana kankame hannunsa, har yatsunta suna nutsewa a cikin fatarsa. Senate bai tsaya wata-wata ba. Ya kwala wa Umma kira, ita ma ta fito cikin gaggawa. Nan take aka nufi asibiti. Senate yana tuƙi, amma wannan karon idanunsa sun cika da ƙwalla yana jin kowane nishi na Bhatool a cikin ransa. Suna isa asibiti, likitocin dake kan aiki suka karɓe ta cikin gaggawa. "Alhaji, yanzu lokaci ya yi. Ruwan jikinta ya fashe," in ji wata nurse yayin da suke tura gadon Bhatool zuwa Labour Room. Bhatool ta riƙe hannun Senate gam kafin su shiga. "Usman... don Allah ka yafe mini. Ka kula da kanka... ka kula da jaririnmu idan wani abu ya faru." Senate ya girgiza kansa, hawaye ya zubo masa. "Bhatool, ba abin da zai faru! Zaki fito lafiya, mu koma gidanmu. Don Allah karki faɗi haka." Haka aka raba hannunsu, aka tura Bhatool cikin ɗakin da yake zaman rayuwa ko mutuwa. Senate ya dube ƙofar ɗakin, ya ji wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa. Ya zube a kan kujerun corridor ɗin asibitin, ya rufe fuskarsa da hannayensa yana kuka mai cin rai. Umma tana gefe tana faman jawo carbi, tana addu'o'i. Senate ya kalli hannunsa dake har yanzu akwai alamar kankamen da Bhatool ta yi masa, ya ji tamkar ransa yana son fita. Awanni sun fara shura. Ƙarfe uku... huɗu... har aka fara kiran sallar asuba, amma har yanzu shiru daga ɗakin haihuwa. Duk lokacin da Senate ya ji nishin wata mace a ciki, sai ya miƙe tsaye yana zaton Bhatool ce, amma sai ya ji shirun ya ƙara yawa. Lokaci ya tsaya cak a agogon asibitin, ko kwanakin da Senate ya yi a gadon rashin lafiya ba su yi masa nauyin waɗannan awannin ba. An kusa kwashe sa'o'i biyar ana faman nakuda, amma har yanzu shiru kake ji. Likitoci da ma'aikatan jinya suna kai-komo, fuskokinsu cike da damuwa, domin jaririn ya ƙi fitowa, yayin da ƙarfin Bhatool ya fara raguwa sosai. A cikin ɗakin, Bhatool tana cikin wani hali na ban tausayi. Jikinta ya jike sharkaf da zufa, muryarta ta dashe saboda nishi da kiran sunan Allah. Tana jin tamkar ranta ne yake neman fita duk lokacin da marar ta ta murɗa. "Bhatool, ki ƙara ƙoƙari! Kaɗan ya rage!" In ji babban likitan dake kanta. Bhatool ta rufe idonta, tana jin yadda duniyar take juya mata. A ranta, addu'a ɗaya take yi “Ya Allah, ko da raina zai fita, Allah Ka tashi jaririna lafiya." A wajen corridor, Senate ya kasa zama, ya kasa tsayuwa. Ya dinga kai-komo, rigarsa ta jike da zufa duk da sanyin asibitin. Umma kuwa ta karkata a wani gefe, tana ta zubar da hawaye tana jan carbi. Duk lokacin da suka ji ihun wata mace a wani ɗakin, sai hantar Senate ta kaɗa, yana zaton ko Bhatool ce take cikin wannan halin. Ƙarfe bakwai na safe ya buga. Daidai lokacin da hasken rana ya fara gauraye gari, sai aka ji wani irin nishi mai ƙarfi daga cikin ɗakin Bhatool, biyo baya kuma sai ga kukan jariri ya kara su! Wani irin ajiyar zuciya Senate ya sauke, ya durƙushe a wurin yana kuka, amma wannan karon kukan daɗi ne. "Umma! Ta haifu! Alhamdulillah!" Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Hamsin da tara   (59) Ba a jima ba, sai ga wata nurse ta fito tana murmushi, ɗauke da wata kyakkyawar jaririya da aka naɗe a cikin farin kyalle. "Masha Allah, an sami mace kyakkyawa. Jaririya tana cikin ƙoshin lafiya." Senate ya miƙe ya karɓi 'yarsa. Tana kuka, amma ganinsa ya sanya ta yin shiru kamar ta san kowaye shi. Ya sunbaci goshinta, hawaye yana zuba a fuskarsa. "Masha Allah... kyakkyawa ce kamar mahaifiyarta." Amma murnar tasa ba ta dore ba lokacin da ya ga nurse ɗin ta koma ciki da gudu ba tare da ta ce masa komai game da halin da Bhatool take ciki ba. Ya kalli Umma, sai ya ga ita ma fuskarta ta sauya. "Nurse! Bhatool fa? Inna mahaifiyarta?" Senate ya kwala kira, amma ba wanda ya saurare sa. Daga cikin ɗakin, sai aka fara jin sautin injina da gaggawar likitoci. Senate ya ji wani irin sanyi ya ziyarci ƙafafunsa, ya kalli 'yarsa dake hannunsa, ya ji wani irin tsoro ya ziyarci zuciyarsa, tsoron cewa wannan jaririyar ita ce kyautar da Bhatool ta bar masa kafin ta tafi. Bayan kusan mintuna ashirin da haihuwa, likitan ya fito yana goge gumi, ya kalli Senate cikin wani yanayi na tausayawa. "Alhaji, tana son ganinka. Amma don Allah ka daure, karka nuna mata damuwarka." Senate ya mika wa Umma jaririyar, ya shiga dakin jikinsa a sandarare. Ya iske Bhatool kwance, fuskarta ta yi fari sol, numfashinta yana fita da kyar, amma idanunta suna nemansa. Ya karasa kusa da ita, ya kama hannunta wanda ya riga ya fara yin sanyi. "Bhatool... gashi nan kin tashi lafiya, kin kawo mana kyauta," ya fada yana kokarin hadiye kukan dake taso masa. Bhatool ta yi wani raunannen murmushi, ta kalli Senate cikin ido. "Usman... lokaci na ya kusa... ina jin sa a jikina. Ina son ka sani cewa ina sonka sosai, na yafe maka komai..." "A'a Bhatool, karki ce haka, zaki tashi, zaki warke mu raini 'yarmu tare," Senate ya fada yana kuka, hawayensa suna digawa a kan hannun Bhatool. Bhatool ta girgiza kanta a hankali. "A'a Usman... ka saurare ni. Ina son ka kula mini da 'yata... Ka bawa Umma ko Abdul su rike mini ita, nasan za su so ta yadda nake so. Ka gaya wa Yaya Karima ina son ta, na gode da kula da ni da kuka yi... na gode da gatan da kuka nuna mini." Ta danyi shiru tana neman numfashi, sannan ta ci gaba. "Ka gaya wa Abdul ina son shi sosai, ina masa fatan alheri a rayuwarsa da sabon aurenshi. Kowa ya yafe mini..." "Bhatool kiyi hakuri don Allah, zaki warke, muna bukatar ki," Senate ya fada yana kukan dake cin rai, ya kankame hannunta tamkar hakan zai hana ranta fita. Bhatool ta kara matse hannunsa da sauran karfin dake jikinta. "Usman... karka damu. Na tafi ina mai farin cikin cewa na bar maka gurbin da zai dinga tunatar da kai ni. Ka kira sunan Allah a kunne na..." A lokacin ne Umma da Abdul suka shigo dakin. Abdul ya iske kanwarsa a wannan halin, ya durkushe a gefen gadon yana kuka. Bhatool ta kalli Abdul, ta yi masa wani kallo na karshe dake nuna tsantsar soyayya da fatan alheri. Dakin ya cika da kuka, yayin da Senate ya fara karanto mata kalmar Shahada a kunne, muryarsa tana daukewa saboda zafin rai. Bhatool ta bi shi, tana motsa bakinta a hankali, idanunta suka fara lumshewa yayin da wani irin sanyi ya ziyarci dakin. "La'ilaha illallahu..." Wannan ita ce kalmar ƙarshe da ta fita daga bakin Bhatool, tare da wani sanyayyan numfashi wanda ya fita bai sake dawowa ba. Hannunta dake maƙale da na Senate ya saki, idanunta suka lumshe tamkar mai bacci, fuskarta kuma ta bayyana wani irin haske. "Bhatool?" Senate ya kira sunanta, muryarsa tana rawa. "Bhatool don Allah ki buɗe idonki. Gashi 'yarki tana kuka tana nemanki!" Shiru! Babu amsa. Abdul wanda yake duƙe a gefen gadon, ya ɗaga hannun ƙanwarsa ya ji shi tamkar auduga, babu sauran dumi. Wani irin ihu mai ban tausayi Abdul ya fasa, ya ɗora hannunsa a ka. "Bhatool! Don Allah karki tafi ki bar mu! Wayyo ƙanwata!" Daidai nan, Yaya Karima ta faɗo ɗakin a guje, tana iske wannan yanayin, ta saki wani uban kuka ta zube a ƙasa tana kiran sunan Allah. "Bhatool! Yanzu duk gatan da muka yi miki ashe na bankwana ne? Ashe dukan wahalar da kika sha a baya kika jure, ashe domin ki tafi ne yanzu?" Asibitin ya ruɗe da kuke kuke. Masu jinya ma kansu sun kasa daurewa, domin kowa ya shaida yadda Bhatool ta yi gwagwarmaya da rayuwa. Senate kuwa, ya kasa kuka, ya kasa magana. Ya kafe gawar Bhatool da ido, yana tunawa da hirar da suka yi a falon Umma mako guda da ya wuce. Ya tuno alƙawarin da ya yi mata na cewa za su raini 'yarsu tare. "Kin tafi kin bar ni da wannan nauyin, Bhatool," ya faɗa a cikin ransa, yayin da wani irin daci ya ziyarci maƙogwaronsa. Umma kuwa, tana can a kusurwa, ta ƙanƙame jaririyar a ƙirjinta, hawayenta yana zuba a kan fuskar jaririyar. Jaririyar kuma ta fara kuka mai ƙarfi, tamkar tana kiran mahaifiyarta dake kwance shame-shame, wadda ba za ta sake amsa kiran kowa ba har abada. Wannan rana ta kasance baƙar rana ga masoyan Senate da Bhatool. Mutuwar Bhatool ta zama wani babban darasi dake nuna cewa rayuwa ba ta da tabbas, kuma nadama takan zo ne a lokacin da gyara ba shi da amfani. An fito da gawar Bhatool daga ɗakin haihuwa, aka naɗe ta a farin kyalle. Senate ya bi bayanta da kallo, yana jin tamkar ƙashin bayan rayuwarsa ne aka fitar da shi. Ya kalli Abdul dake kuka tamkar ransa zai fita, ya fahimci cewa wannan raunin ba na mutum ɗaya ba ne; rauni ne da zai dade yana raɗadi a zukatan kowa. Labarin mutuwar Bhatool ya karaɗe garin Yobe tamkar wutar daji, musamman yadda kowa ya san wahalhalun da ta sha da kuma yadda yanzu take dab da samun natsuwa. Gidan Umma ya cika ya batse, mutane sun kasa gaskata abin da suke ji. A gefe guda na falon, kawayen Bhatool na kusa da na nesa sun hallara, kowacce ka kalla fuskarta ta kumbura saboda kuka. Jannah dake kwance a kasa, kuka take yi tana kiran sunan Bhatool, tana tunawa da yadda suka yi biki kwanan nan.  Amrah kuwa, wadda take jin nauyin abin da ta yi wa Bhatool a baya, kukan nadama da tausayi ne ya cika ta tana jin kamar ba ta sami isasshen lokacin da za ta nuna wa Bhatool soyayya ba kafin wannan ranar. Haka Suhaima ma, kuka kawai take yi. Gaggo Larai, Furee, da Habi, duk sun shiga wani irin tashin hankali. Kowa yana tuna wata hira ko wata hidima da Bhatool ta yi musu. "Bhatool ba mace bace mai rikon mutum, mace ce mai hakuri," in ji Habi cikin shesshekar kuka. Shuru ya mamaye falon duk lokacin da aka kalli jaririyar dake hannun Umma, wadda kukan ta ya ki tsayawa tamkar tana kiran mahaifiyarta. Karfe biyu na rana aka shirya janizar Bhatool. Kowa ya hallara a babban masallacin dake layinsu Bhatool. Abdul yana tsaye, kansa a kasa, hawaye yana zuba a fuskarsa ba kakkautawa. Ahmad ma yana can a gefe, zuciyarsa tana tafasa da tausayin wannan baiwar Allah da kuma kaddarar dake tattare da ita. Senate kuwa, tun asuba rabon sa da magana. Yana tsaye kusa da gawar Bhatool lokacin da aka sauke ta don yin salla. Ya dube ta a cikin makara, an nada ta a cikin farin kyalle, fuskar nan ta ta mai kyau yanzu babu sauran numfashi. A nan ne Senate ya ji cewa lallai rayuwarsa ta sauya har abada. "Allahu Akbar!" Muryar liman ta karaɗe ko ina.  Bayan an gama salla, aka dauki gawar zuwa makabarta.  Nan fa kuka ya dawo sabo Jannah da Amrah suna can daga ƙofar gidansu Bhatool, kukan su yana tashi yana ratsa zukatan mutane. Babu wanda bai yi kuka ba a wannan ranar, har wadanda basu san Bhatool ba sun ji radadin mutuwar tata. Haka aka wuce da ita maƙabarta Kowane taku da ake yi, Senate yana jin tamkar ana kara nisa da shi ne daga duniyar farin ciki. Aka tafi da ita cikin kuka da addu'o'i, aka sanya ta a cikin kabarinta. Lokacin da aka fara zuba kasa, Senate ya kalli Abdul suka yi ido hudu, kowannensu ya juya kansa gefe yana kuka. An gama jana'iza, mutane suka fara rarrabuwa, amma Senate ya ki tafiya. Ya tsaya a kan kabarin, yana kallon sabuwar kasar da aka zuba. "Bhatool, na yafe miki duniya da lahira. Kuma na karbi amanar 'yarki da kika bar mini. Insha Allah zan rayu ina tuna kowace hira tamu," ya fada cikin murya can kasa. Wannan rana ta kasance babban bankwana. Kowa ya koma gida da tunani daya "Ina ma ace Senate ya sani tun farko, ina ma ace Anty ba ta shiga tsakaninsu ba." Amma kaddara ta riga fata. Legendspen 08129553971 HASASHEN SOYAYYA (BOOK 2) By Sayyid Legendspen Amanar-Janafty Shafi na Sittin (60) Assalamu alaikum warrahmatullah! Yan uwa masoya ya kuke, ya hakurin rashin Bhatool? Ina mai baku hakuri akan hakan, nima ba wai nayi da Niya ba ne tsarin labarin ne a haka, kuma dama babu wamda yake dauwamme kowa ɗan haka ne ya zo ya koma, ya zo ya koma, Allah Maɗaukakin Sarki Yana cewa a cikin Littafinsa mai girma "Kullu nafsin daikatul maut" (Kowannr mai rai ɗanɗanar mutuwa ne). Haka nan, Manzon Allah (S.A.W) ya koya mana cewa mu kasance a duniya kamar baƙi…. Rasuwar Bhatool a cikin wannan labari, ba wai ƙeta ba ce ga masoyanta, face ishara ce gare mu duka cewa rayuwa baki ɗaya mai ƙarewa ce, kuma duk abin da yake da mafari, tabbas yana da ƙarshe. Ina godiya da yadda kuka nuna damuwarku, hakan yana nuna yadda Bhatool ta shiga rayuwarku. Amma ina so ku sani, wani lokacin mutuwa ita ce take ba wa labari ma’ana ta har abada. Ku ci gaba da kasancewa da ni don jin yadda zamu ƙarashe labarin.    Naku, Sayyid Legendspen (Amanar Janafty) Bayan rasuwar Bhatool, rayuwa ta ci gaba cikin wani irin yanayi na jimami. Jaririyar da aka bari, wadda kowa ya shaida kyakkyawar kamanninta da mahaifiyarta, aka sanya mata suna Bhatool. Yaya Karima ce ta ɗauki nauyin shayar da ita da kulawa da ita tamkar ita ta haife ta. Bayan an yaye Little Bhatool, sai ta koma gidan Ahmad da amaryarsa, inda suka riƙe ta cikin tsantsar gata da ƙauna. A gefe guda, ganin yadda zama ya kasance ga Umma mahaifiyar Bhatool da kuma yadda zumunci ya ƙara ƙarfi, Mom ta dage wa Dad a kan lallai ya aure Umma. Bayan dogon nazari da tattaunawa, aka ɗaura auren Dad da Umma, wanda hakan ya sa dukkan iyalan suka koma gida ɗaya. Little Bhatool ta zama ƴar kowa; tana hutu a gidan su Mom, tana zama wajen Ahmad, amma zuciyarta gaba ɗaya tana wajen mutum ɗaya ne Mahaifinta. Senate ya canza gaba ɗaya. Tun ranar da aka rufe Bhatool, Senate ya daina dariya, ya daina yawan magana, ya kuma janye jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta duniya. Furfura ta fara fito masa a suma da gemu, amma bai taɓa tunanin ƙara aure ba; ya ce Bhatool ɗaya ce a rayuwarsa, kuma ya riga ya kai ta makwancinta. Idan ka ga Senate yana hira, ko yana murmushi, to tabbas yana tare da Little Bhatool ne, wadda yake kira da "Little." Soyayyar dake tsakaninsu ta zarce tunanin mai tunani; tana son mahaifinta fiye da komai, shi ma kuma ita ce rayuwarsa. SHEKARU GOMA SHA BIYU BAYAN HAKAN "My mother died to give me life, and my father lived to give me love," Kyakyawar yarinya ‘yar shekara goma sha hudu dake zaune a kan babban stage a babban ɗakin taro na alfarma dake ƙasar Amurka (USA), hasken lantarki ya mamaye ko'ina. Taron na musamman ne inda aka gayyato yara daga sassa daban-daban na duniya don su ba da labarai masu taɓa zuciya (Inspirational Stories) yarinyar sanye take da doguwar riga ta alfarma, kamarta ɗaya da marigayiya Bhatool, idanunsu, hancinsu, har zuwa murmushinsu, babu abin da ya bambanta. Cikin natsuwa da harshen Turanci mai sauƙi da daɗin saurare take magana.Hannunta riƙe da babban littafi mai suna “The Journey of Bhatool Senate.” Wanda mahaifinta ya ɗauki tsahon shekaru yana rubutawa. A cikin taron, a sahun gaba, ga Mom da Dad suna kuka. Umma da Yaya Karima suna share hawaye. Abdul yana zaune da matarsa da yaransu biyu (namiji ɗaya da mace ɗaya mai suna Bhatool). Ahmad ma yana nan da matarsa da ƴarsa mai suna Bhatool. Hatta Jannah da mijinta sun kasa riƙe hawayen su. A tsakiyar su, ga Senate zaune. Ya tsufa kaɗan, furfura ta bayyana sosai a fuskar sa, amma kwarjininsa na nan. Yana kallon ƴarsa a kan stage, hawaye na zuba a fuskarsa. Yana jin tamkar Bhatool ɗinsa ce take tsaye a wurin take yi masa magana. Lokacin da Little Bhatool ta kammala labarin ta hanyar cewa, "My mother died to give me life, and my father lived to give me love," dukkan mutanen dakin taron suka miƙe tsaye suna tafi, yayin da kuka ya sarƙe kowa. Senate ya miƙe ya nufi kan stage ɗin. Yarinyar ta rugo ta faɗa jikinsa, ya rungume ta tsam yana kuka. A daidai wannan lokacin, ya ɗaga kansa sama ya kalli silin ɗin ɗakin, yana jin tamkar yana hango murmushin Bhatool. "Mun gode Allah, Bhatool. Ga amanarki nan ta zama tauraruwa," ya faɗa a cikin ransa. “Ni wallahi Allah sai an siya mini.” Ta faɗa tana burgima a ƙasa. Tare da fara kuka. “Mama kin mutu kin barni, kin bawa ɗan uwanki amana ta amma yakasa cikawa.” Little Bhatool ta faɗa tana kuka, shi kam Abdul da ido yake kallonta, yana tuna yadda Bhatool take kuka tana kiran Mahaifinsu da ya rasu. “Oh Allah! Bhatool ga abinda kika barmin nan.” Ya faɗa yana murmushi.  ALHAMDULILLAH! Tsokaci.  Daidai da lokaci ɗaya Little ba ta bar komai na halin mahaifiyarta ba, duk ta kwashe su tana kuma yinsu, haka Abdul da Yaya Karima zasu sa ta a gaba su yi ta kallonta suna jjn dadin abinda take yi.  Senate ya rasa Bhatool, amma tabbas ba ta tafi duka ba, domin ta bar masa little da take masa dukkam soyayyar da Bhatool take masa, girki, ruwan wanka, taje masa kai, fesa masa turare, har da zaɓar masa kayan da zai sa, indai Little na nan ita ce zata yi masa. Yana jin kamar bai rasa Bhatool ba.  Mom da Umma zama suke cikin so da mutunta juna, Dad yana ƙoƙari wajen yin adalci a zamansu, amma soyayyar da yake yi wa Umma ta ninka wacca ya yi mata a baya.  Amrah da Jannah da Suhaima suna rayuwa da rashin Bhatool, amma suna jin Little a ransu kamar su ne suka haife ta, ita ma tana ganinsu kamar sune suka haifeta.  Haka gidan Ahmad Little ta dauke shi kamae gidansu, idan tana jin rigimarta har nan take zuwa tai ta bori. Yaya Karima ce Uwar little, nan ta taso ta girma ta yi yawo, baka gane banbanci tsakaninta da ‘ya’yan Yaya Karima sai ma babban ɗan Yaya Karima da ya ke son ta, ita ma take son sa, amma Senate yaƙeƙashe ƙasa ya ce, Little Bhatool ɗinshi yarinya ce ba yanzu za ta yi aure ba. Daidai da rana ɗaya Senate bai taɓa jin sake son wata mace ba, haka babu wanda ya takura masa akan hakan.  ALHAMDULILLAH! Wanan shine ƙarshen a labarin Bhatool da Senate, kuskuren da cike ubangiji ya yafe mana, alherin dake ciki ubangiji ya bamu lada baki ɗaya.  Na gode da bibiyar ku tun daga farko. Mu haɗu a labrin mu na gaba Sartse.  Legendspen 08129553971