*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *BAN YARDA A JUYA MUN LABARI TA KOWACCE SIGA BA TAREDA YARDATA BA* *WANNAN LITTAFI ZARIA TV KADAI KEDA LASISIN WALLAFASHI A YOUTUBE, DUK WANDA YA AIKATA HAKAN BA TAREDA SANINA BA TABBAS HUKUMA CE ZATA RABA MU* *IDAN HAR KIN SAN ZAKI SIYA NE SABODA KI YADA KI TURA A GROUPS NA HADA KI DA ALLAH KARKI SIYA, BAZAN YIWA KOWA ALLAH YA ISA BA DAN SOYAYYA CE HAR TAKE SAKA WA A FITAR DA LITTAFINKA A KARANTA AMMA MU SANI DUK WANDA YA DARAJA KASUWANCIN WANI SHIMA ALLAH BAZE BARI A KASSARA NASA BA* *RUBUTUN LITTAFI SHINE KASUWANCIN MU DAN HAKA DAN ALLAH MASOYA KU TAYA MU GINA SHI BA RUSAWA TA HANYAR FITAR MANA DA LITTATTAFAI BA* *GA MASU SO A TALLATA MUSU HAJAR SU QOFA A BUDE TAKE* *KUNA IYA TUNTUBATA TA KAN LAYIN* *07061838488* *A QARSHE INA MIQA TARIN GODIYA GA MASOYA NA INA KUMA YI MANA FATAN ALKHAIRI GABA DAYA, ALLAH YA BAMU IKON AMFANA DA SAQON DA YAKE CIKIN LABARIN NAN YA KUMA YAFE MANA KURAKUREN DA ZAMUYI A CIKI* 🤲🏼🤲🏼🤲🏼 *SHIMFIDA* Ita Uwa tana da wani matsayi na daban da Allah SWT da kansa ya bata, kaifin harshen uwa ya zarce duk yanda muke tsammani. Cikin sani ko akasin haka furucin uwa nada tasiri akan Da wanda ba kowane ya gane hakan ba. Idan rai ya baci musan abinda baki yake furtawa akan yaran mu, domin yanke hukunci cikin fushi yana haddasa Nadama da dana sani mara amfani a rayuwa. Free Page 1 "Mama qarfe uku zamu tafi gidan Kamun fa, kinga unguwar su da nisa kuma Abba yace mu dena yin dare a waje" Umaimah dake tsaye daga bakin qofar daki ta fada tana kallon Babbar Macen dake tsinke danyan zogale tana jefawa a cikin babar robar dake gaban ta. Banza tayi mata taci gaba da aikinta, se kuwa ta takwarkwashe fuska kana ganinta kasan tana fama da tsiwa da shagwaba tace "Mama kina jina fa kikayi shiru, se kuma an jima na gama shiryawa kice ban gaya miki ba" "Idan baki matsamun daga nan ba UMAIMAH sena bata miki rai a gidan nan, na gaya miki babu inda zaki je wallahi idan bakiyi wankin nan ba, ke ko kunya bakyaji a shiga dakinku wai sunan dakin Yanmata kin hargitsa muku ko ina da shirgin dattinki qazamar banza qazamar wofi" Maman ta dago a fusace tana fada tana kallonta. Wata Fara doguwar mace ta fito daga Kitchen tana cewa "Maman yara kenan, ki barta mana bana ji dazu tana cewa Nazifi gobe yazo ya mata wanki ba naga fa kayan da yawa idan kika ce seta wanke ai seta makara zuwa gidan bikin ko" "Ai Antyn su Ko shekara zatayi wallahi seta wanke su kuwa na gaji da iskancin ta, shekara goma sha tara ai ba wata sha tara bace da kullum ita tana girma tana cin qasa, in ba haka ba ko dakin su Saddiqa ka shiga ai baka tarar da bolar da UMAIMAH take tarawa, ni wallahi ma baiken Nuratu nake gani da har ta iya hada daki da qazamar banza bayan ita komai nata tsaf tsaf yake" Maman ta sake fada tana Harara Umaimah dake ta faman tura baki. "Haba, ai bazaki hada ba, da zama da mutum yana saka ka koyi halinsa ai da Umaimah batayi qazanta ba dan duk gidan nan babu wanda yakai Nuratu tsafta, su Umaimah kuwa ba'a magana" Antyn ta Fada tana zama a kusada Mama dan tayata qarasa gyaran zogalen. "Munafuka kawai, kece qazama bani ba dai" Umaimah ta fada qasa qasa tana juyawa cikin dakinsu, Mama dake kallon Bakinta tsaf ta fahimci abinda ta fada dan daman tasan za'a rina, Umaimah se gyara da shiriyar Allah kawai. Daga cikin dakin ta ringa watso kayan wankin tsakar gida babu wanda ya tanka mata daga maman har Anty har ta gama iskancinta ta fito ta tattara su zuwa gaban fanfo ta tara ruwa a bokitai ta hau wanki. Cikin qanqanin lokaci kuwa se gashi ta gama yanda kasan wacce ake tayawa, ta zagaya bayan gidan inda igiya take ta shanya kayanta tas ta dawo ta dauraye gurin da tayi wankin lokacin har Anty ta sauke dambun da suka girka a matsayin abincin rana. Tana dacin rai dan tunda ta fara wankin tafi ku mutu bata ce musu ba har ta gama ta shige dakinsu, can ma bata zauna ba, gadonta dake nan a hargitse ta gyara bayan data saka sabon zanin gado dan ta wanke na kai yanzu nan da nan ta share dakin ta hado ruwa ta goge ko ina kafin ta fada wanka ganin har qarfe biyu ta gota dan tun kusan goma take aikin. Tana bandakin ta jiyo sallamar Anty Laure, qanwar Mamansu ce da suke uwa daya uba daya ta tabe baki dan tasan yanzu zasu qara haduwa su sakata a gaba da magana dan ma Allah yaso bata tarar da ita tana wankin ba amma tasan se munafukar Antyn can ta gaya mata ma, haka tayo wankan ta tareda alwala ta fito tana ta sauri, dukda qarfe biyar aka saka a katin kamun amma so take ta tafi da wuri dan seta biya ta inda Amarya taje kwalliya dan itace babbar qawarta. Daren da sukayi jiya a gurin Bridal shower ya saka Abba hanata tafiya tun sassafe dan da gaba daya ma hanata yayi seda Anty ta saka baki kafin ya kafa mata sharadin kar ta wuce qarfe shida yau amma dukda haka bata mata gwani ta ba. Tana cikin yin sallah qawarta Rumasa'u Murtala tayi sallama, kamar ta sallame ta dakatar da ita karta shiga falon inda take jiyo muryoyin su Maman dan tabbas seta rusa mata shirin da tayi amma ba hali haka ta shiga karatun sallar sauri sauri tana jiyo ta suna gaisawa tana kuwa sallame wa ta fice falon da sauri har Hijab na neman tadeta ta kwalawa Ruman kira. "Ke kuma fa kamar wadda aka biyo?" Anty Laure ta fada tana kallonta, seta saki murmushin da yake qara mata kyau tace "Babu komai Momy ina wuni? Yasu Bintu? Ruma shigo mana kin ganni na kusa qarasawa ma" ta fada tana kama hannun Rumasa'un. "Uhm kyaji dashi, ai wallahi da ace Ruma bata zo gidan nan ba da yau babu inda zakije daman se kuma Allah ya ceceki" Mama ta fada tana binta da harara. "Ke kuma dana ce miki idan na fito zan kiraki me yasa kika zo?" Umaimah ta fada tana kallon Ruma bayan data zauna akan gado. "Toh naji ki shiru, na kira Nadiya Isah wai tana gidan kwalliya ma ita shiyasa kawai nayo gaba, ni kuma Kinsan bana son kaiwa dare wallahi shi yasa nake so muje da wuri ko ba'a fara ba indai mun gaisa da Amarya Shikenan dawowata zanyi" "Lallai ma to me kikayi kenan bari ma kiji se bayan magriba za'a fara biki qarfe biyar din da kika ga an saka dinma kawai rubutawa akayi dan ko ita Haliman yanzu ta tafi kwalliya" Umaimah ta fada tana qoqarin zura doguwar rigar fitted gown din da akayi mata a ankon bikin, se kuma me ta tuna ta cire ta ta janyo wata baqar doguwar rigar Abaya ta saka ta zauna ta hau daurin dankwali dan daman ita bata kwalliya, powder kawai ta saka se kwalli da man lebe ta gyara gashin girarta me cika da baqi hakan kuwa ba qaramin fito da sanyayyan kyanta da kalar fatar me wani irin kyau da sheqi ya sake qawata ta. Ita dai Ruma na daga bakin gado tana kallon ikon Allah, koda yake ta saba gani baze wuce tayi irin dinkin da Mama ta hanata bane shiyasa ba zata saka ba qarshe tayi qarya tace wani guri ya yage zata shiga gidan Maman Nana me dinki ta take mata daga can su wuce, haka kuwa akayi suna fitowa Falon aka hau tuhumarta meya faru bata saka kayan ba ta nuna musu gefen Hammata inda Ruma bata san sanda ta farke shi ba wai be dinku ba. Sukayi musu sallama suka fice har sun kai qofa ta jiyo muryar Anty Habi tana cewa "Yata Allah dai ya nuna mana ranar naki auran tunda ita waccen Allazi bokon ta auri littafi bazamu jirata ba, kina kammalawa zamu sha biki abin mu" Anty Habi ta fada tana bin ta da kallo ganin yanda tayi kyau dukda ba wata kwalliya me yawa tayi a fuskar tata ba. "Lallai kuwa, ita Allazi bokon ai tafi wannan alqibla tunda ita naga alamar har yau bata san Annabi ya faku ba, duk wani saurayin kirki da zatayi seta kore shi da mugun halinta. yanzu da rana irin ta yau kika zo gidan nan da kinga irin diban Albarkar da tayiwa Qasim akan kawai ya gaisa da wata yarinya sanda yaje dakkota daga makaranta. Yarinyar nan saboda ta isa ta zama yar kanta a qofar gidannan ta tsaya mutane na kallonta tana zuba masa tijara ai ni nayi mamaki ma da har yau basu aiko a basu kudib su ba, Umaimah kibi a sannu dai tunda kin kori samarin qarshe idan kinci sa'a ki qare da me mata biyu ko uku ai" Mama ta fada, se ta juya bakin qofa i da Umaimah ta coge tunda Maman ta fara magana tace "Kika tsaya ko da magana ne", cikin muryar kuka kuka tace "Saboda kawai an miki kishiya Mama se ki ringa yimun fata nima na auri me Mata, in sha Allahu mijina ni kadai ze aura daga ni babu qari har abada" taja fuuu tayi waje. "Hmmm" kawai Mama tace dan lamarin Umaimah kam se Addu'a. "Oh ni Anya Yaya Malika lamarin Umaimah babu iskokai a ciki kuwa? Kiga dai farin jini irin na yaran gidan nan, tun fa kafin su gama sakandire suke tsaida mazaje amma ace Umaimah har tana shirin gama HND babu wani tsayayye abu kullum watangaririya ake, se an shirya magan rigidi rigidi se wani tsautsayin ya gifta. ita ba mummunar sufa ba bare ace finta sauran sukayi, waccen miskilar ma ta samu tsayayye balle ita me wayayyen kai ace abu ya gagara? Nifa wannan fadan nata ma gani nake bana lafiya bane gaskiya ya kamata mu tashi tsaye" Anty Laure ta fada tana kallon yayar tata. "Babu wasu iska sedai iskanci Laure kamar baki san wacece Umaimah ba. kuma da like batun tsayayye ai ba samarin me bata dasu ba, kullum zuwa suke amma mugun halinta da baqin kishi na ba gaira babu data dorawa kanta shi yake korar su. Ni damab na deba lissafa kawo mata kudin aure a wani abu, idan ba ji nayi an daurawa Umaimah aure ba shine kadai zan tabbatar da Miji ya tsaya dan a cikin sakanni tana iya tafka wautar da zata sa ace anfasa auranta. Toh wane gantalalle ne tun be aureta ba zata fara dora masa ciwon kai ya tsaya? nake gaya miki fa nan tayiwa Qasim cin mutunci ko kare baze ci ba wai kawai dan ya gaisa da abokiyar karatun ta shi kuma junior sace yarinyar tare sukayi secondary wallahi bakiji ba ina sallah a tsakar gidannan ina jiyota Allah Allah nake na idar na fita naci ubanta akayi sa'a yayansu yazo ya faffalla mata mari tayo ciki, ni nayi mamaki ma da har yau basu aiko sun karbi kudin auransu ba" Mama ta fada cikin matuqar takaici. "Ashsha abu beyi kyau ba amma me yasa take haka ne, ya ilahi ke ace saurayinki baze kula wata mace ba toh inaga anyi aure kuma" Anty Laure ta fada cikin jimami tana juya hannu. "Kema kya fada dai, shi yasa na dena raba takaici ta da kowa duk abinda tayi wanda ya gani ya gani shikenan fatana dai kullum shine ubangiji ya shiryeta dan dai wannan halin nata ba hali me kyau bane" "Addu'ar dai kam ita ce amma dai Yaya karki qi ta tawa Allaha binciketa dai qila da sharrin iskar kin san fa daman baa ganewa se abu yayi tsamari baa fata sannan suke bayyana" "Allah ya rufa asiri" kawai Mama tace mata ta janyo wata hirar dan ita duk wata sabga da zaace ta hada da malamai ba sonta take ba. Balle kuma Umaimah da sarai ta san babu abinda yake damunta, suma mantaqa sukayi amma ai tun tana qanqanuwarta haka take da bala'in kishi wani baze fita ba, idan kuwa abu ne idan bata dashi tofa sedai kowa ya rasa. Tayi iya qoqarinta gurin canza mata wannan muguwar Dabi'a abin kuma yayi sauqi se a yanzu da shekarun hankali suka zo mata kuma abu ya ke sake ta'azzara, kuma a duk sanda Shedan ya buga mata gangar ta hau bata ji bata gani sedai fatan Allah ya shirya kawai. UMAIMAH Suna fita fuskar nan tata a cukule saboda maganar da Maman tayi suka shiga gidan Maman Nana, basu bata lokaci ba ta take mata rigar ta saka. Dinkine akayi mata na dibar Albarka ya fito mata da duk wata sura da take da ita domin kuwa Allah ya mata qira me kyau, tana da wani irin shape da ko mace ta kalleta seta qara kallo ta. "Yanzu Umaimah da wannan Kayan zaki fita? Wai me yasa kike haka ne, baki san wannan abin da kike cin amanar iyayenki kike ba? Ya za'ayi ki fito daga gidanku da shigar Mutunchi amma a waje a ganki da wata shiga ta daban? Wallahi ina jiye miki ranar da wani a gidan ku ze san abinda kikeyi nasan se kin gane kurenki wallahi kiyi ta biyewa su Nabila Sani su dai kin san a gida suka samu lasisin yin duk abinda sukeyi sedai su jira Kamun Allah" Rumah ta fada tana qarewa Umaimah dake daukar selfie Kallo. Kayan sun kamata matuqa ga kalar Atamfar data karbi fatarta dole ma ta fuzgi hankalinka ka kalleta. "Sedai idan ke zakije ki fada, ni wuce muje ga me Napep din nan an samo" Umaimah ta fada ko a jikin ta tana zura wayarta a jaka daidai sanda Nana data aika ta taro musu dan sahu ta dawo, haka Rumah ta bita a baya cike da Takaicin halin qawar tata, badan gudun abinda kaje ka dawo ba wallahi seta fadawa Mama wannan muguwar dabi'ar data koya a gurin su Nabila. Da sam ba haka take ba, da wuya kaga Umaimah ta saka kayan daya bayyana surar ta dan ba tarbiyyar gidan su bace amma shigar su Poly tunda ta hadu da sababbin qawaye irinsu Halima Mailafiya, Fannah Babagana, Nabila Sani se Fauziyya Kura, Izawaqa Mansur da ita Rumasa'u da daman tun Secondary suke tare . acikin su Ruma ce me sanyin Hali ba kuma tayin irin abinda sukeyi. Nabila da Fauziyya sun fi kowa budadden ido a cikin su bayan Ruma sune mafiya kusanci da Umaimah kumasu suke qara dorata akan duk wani bigire mara kyau kasancewarta me saurin yarda da sakewa da mutane, gashi ita a rayuwarta tana jin maganar qawa kusan sama data kowa. Tun tana dardar idan zaayi bikin qawar su aka fitar da Anko su suke kawo Style dinda zaayi na zamani na rashi mutunchi tace baza abarta ta saka a gida ba su suka kawo mata dabarar kin sakawar ta bari seta fito waje, dan a Auran Fannah ma dinki biyu aka mata. Wanda ta saka ta fito daga gida daban haka bayan sunje gurin bikin ta cire ta canza wani. Rumasa'u na matuqar baqin ciki da wannan dabi'a tasu kuma duk ta yanda zata fahimtar da Umaimah cewar tsakanin ta dasu akwai Banbanci na tarbiyya da mutunchi taqi ta ji, sabo da shaquwar da take tsakaninsu tun yarinta ita tasaka ta kasa fita daga cikin group din nasu amma duk da haka kullum cikin yi musu Nasiha take bata damuwa da kyara da hantara da kiranta bagidajiya da sukeyi ita dai fatanta su dawo kan Hanya. Haka suka kama hanya, suna cikin tafiya Kiran Fauziyya ya shigo wayar Ruma. "Bawa Umaimah wayar" ta fada bayan data amsa, seta miqa mata tana tabe baki dan yana yin da tayi mata magana ya sa ta tuna da fadan da sukayi shekaran jiya a makaranta akan zasuje sabon gari a saka musu farce da kitson qari duk na shirin bikin, tayi musu nasihar data saba Shine Fauziyyan ta zageta har tana kiranta bagidajiya batayi sanya ba itama ta rama danta fara gajiya da yanda suke maida ita kamar wata bolar su dan kawai tana da haquri shine ashe ita bata wuce ba. "Umaimah muna Beejay fa, yanzu zaa fara yiwa Lims kwalliya" Fauziyyan ta fada bayan da Umaimah ta karbi wayar, "Kai haba dai har yanzu shida saura fa" "Dalla se waccen yar yawar taji kawai ku wuto nan akwai motocin da zasu dauke mu an kusa gama mata ma fa" Fauziyya tayi saurin kwabarta sukayi sallama. Me Adaidaitan ta gayawa inda ze juya dasu, Ruma ta kalleta tace "Ban gane ba ina kuma zamuje?" "Kin fiya matsala wallahi toh saqo zan karba na manta ne se yanzu" ta fada tana tsuke fuska. Agogon wayar Rumah ta kalla kamar tayi magana kuma tayi shiru, haka suka qarasa tafiyar babu me cewa wani qala har me Adaidaita ya sauke su a bakin gurin kwalliyar. "Me kuma zamuyi anan kedai nasan ba kwalliya kike ba bare nace" Rumah ta sake fada bayan sun sauka "Wallahi Rumah kin fiya matsala, bana gaya miki saqo zan karba ba.." Se tayi shiru ganin Nabila ta nufo su fuskar nan tasha kwalliya kamar Aljana se karairaya take dinki ta irin na jikin Umaimah amma sam be mata kyau ba saboda jikin ba iri daya ba, siririya ce ta gaske ga tsaho tana dashi se ta zama kamar wata bulala. "Mu shiga ciki an kusa gama mata" ta fada tana kama hannun Rumah dan itace zatayi qorafi, haka suka shiga Reception din, abin takaici Amarya Halima na zaune ashe layi ma bezo kanta ba. Wai wata akeyiwa da an gama se ita. Hira suka shigayi da daukar Hotuna, Umaimah na daga gefe kadan kadan take saka baki tana danna wayarta da tun suna hanya take ta qoqarin kiran Qasim amma ta kasa samun sa. Tsaki taja ta kalli Rumah tace "Bani aron wayarki nayi kira please" dan duk cikin clique din nasu ita kadai ta yarda da ita take kuma iya sakata a sabgar samarinta hakan kuma ba shi yake hana idan abin ya motsa mata itama tayi mata horon da ta saba yi ba. Bugu biyu Qasim ya daga kiran da tayi masa da wayar Rumasa'u, sallama yayi tsabar mamakin abinda yasa ita wayar ta ake ta ce mata not reachable amma gashi kira daya nan ta same shi ya hanata magana. Seda ya maimaita sallama sau uku kafin ta bude baki cikin fushin da yake taso mata tace "Blocking layina kayi kenan Qasim tunda gashi na same ka da wata wayar" Qasim kuwa yana jin muryarta daga daya bangaren 'Qit' ya kashe kiran, ta zare wayar daga kunnenta tana dubawa, kashewa yayi da gaske kai lallai yau akwai babban tashin hankali ashe. Kusan sati kenan tun waccen ranar ya dena kiranta, idan ta kira shi farko farko ze amsa amma yanayin da ya koma yi mata magana a dake ba kamar yanda suka saba bane daga baya ma seta kira ta qaraci ringing di ta baze daga ba toh abin ya qaru jiya zuwa yau ma kwatakwata bata shiga shine yanzu ze qara mata da wannan wulaqancin ai kuwa ze san da ita yake zance. Wayar ta mayarwa da Rumah ta qara harde qafa akan Kujera tana kadasu, a ranta ayyana irin tijarar da zata masa duk randa ya huce ya kawo kansa take. Ita badan ma tana son yazo ya mayar da ita gida ba ai ba zata kirashi ba amma shi kenan. Basu bar gurin kwalliya ba dai qarshe seda akayi sallar Magriba ko kafin su Isa Gurin Kamun ma takwas saura dan da tafiya daga gurin kwalliyar zuwa can. Ruma kamar zatayi kuka, ita ba kanta ma takeji ba dan a gida ta fada daman zasu iya kaiwa Zuwa Takwas haka kuma an barta amma Umaimah take jiwa dan yanda Mama ta ringa jaddada mata kar tayi Magriba awaje idan ba haka ba zata hadu da Abban su tasan akwai abinda ta aikata da ya saka ake horata. Sun tarar da Anties din Amarya da daman tun suna gurin kwalliya ake doka mata waya, wata daga ciki ta tare su da wani mulmulallan Ashar tana cewa "Banda tsabar iskanci Kamu ba dinner ba ki tafi ki share guri kiyi zamanki har takwas uban waye ze zauna yana jiranki? Kwalliyar da kika bata kudi kikayi ta tashi a banza dan rabin mutane sun kama gabansu su kansu dangin mijin naki gasu can har sun fito zasu tafi dakyar aka lallabasu suka zauna shegiya kuma baki kyau bama" Amarya Halima ta tura baki dan daman tasan se Anty Mara tayi masifa dan tafi kowa fada a cikin Anties din nata, haka suka rankaya suka shiga Yammata na take mata baya. Amarya na zama a kujerarta Rumah ta zagaya aka musu hoto kafin ta rada mata a kunne ta tafi se gobe zata zo gidansu daurin aure da yini. Da sauri ta qarasa inda Su Umaimah suka zauna tana ce mata "Kije kuyi sallama da Halima mu tafi Umaimah takwas fa keda aka ce kar kiyi magriba a waje". "Kuje ina haba malama kema ba inda zakije nemi guri ki zauna yanzu fa zaa fara biki ki wani ce ku tafi baza ku tafin ba" Fannah ta fada tana qoqarin zaunar da ita seta turje tana cewa "Barni Fannah tafiya zamuyi Umaimah muje dan Allah dare na dada yi". "In zaki tafi ga hanya nan ban riqe ki ba amma ni kam se naga kwal uwar daka, daga zuwan mu kice mu tafi ba wannan maganar"  tana rufe baki kiran Mama ya shigo wayarta data ajiye akan Table "Kin gani ko gashi nan Mama tana kiranki kar ki jawa kanki wani Fadan ki tashi kawai mu tafi" Rumah ta fada a rikice kamar ita ce tayi laifin "Ai se kiyi, kona koma yanzu ko ban koma ba duk daya fada ne sena sha shi toh in zaki zauna ki zauna idan kuma tafiya ce a sauka lafiya"  ta bata amsa tana kashe wayarta gaba daya dan tasan Mama yanzu idanta dosa mata kira ba haqura zatayi ba, kuma dai laifi ne dai ta rigada tayi tunda kafin Magriba akace ta dawo gashi har isha ta wuce bata komaba. ©️2️⃣0️⃣2️⃣3️⃣ *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR*👹🥰 *And now* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE* *KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA* *07061838488* *A BIYA A KARANTA* Free page 2 Biki yayi biki, an raqashe anci an sha yammata sunyi rawa, Umaimah bata an kare da lokaci ba seda aka tashi ta kunna waya lokacin qarfe goma harda rabi tayi, daga gurin zuwa gidansu kuwa taci kusan Minti talatin a qiyasi dai sha daya ce zata kaita gida lallai kam yau ta taro Match me zafi dan tasan ma kafin taje tuni an kulle gida. A motar Mijin Fannah suka tafi da yake hanyar su daya, ita bayin daren ne yafi daga mata hankali ba, Aa Abayar data saka da zata fito ta barota a gidan Maman Nana saboda bazata shiga jakarta ba kuma batayi zaton zasuyi dare har haka ba. Cikin taraddadin abinda zata tarar suka sauketa a qofar gidan su, jiki a sabule ta sauka tana gyara yafen dan babban mayafin data samu sukayi musanye da Fannah ko ta dan qara rufe jikinta. A darare ta qarasa jikin qaramar qofar Get din da niyyar bugawa dan tasan dai an kulle se taji takun takalma a bayan ta. A mugun zabure ta matsa, Abbane, da torchlight a hannunsa saboda an dauke wuta yayi mata kallo daya kafin ya saka muqulli ya bude gidan ya shiga ba tareda ya ce mata komai ba haka ta bishi zugui zugui a baya, ganin yayi kamar ma besan da wanzuwarta ba yasa ta kwasa da saurin gaske tayi ciki tana qara godewa Allah da ya saka babu hasken Nepa kuma be haska jikinta da fitilar hannunsa ba balle yaga irin shigar da tayi. Dan dama daman da ta sake ji dayaga dawowarta ba ita kadai ba dan seda Fannah ta fito ta bude mata murfin motar da ya samu matsala, yanzu da ace saurayi ne ya ajiyeta a daren nan tana ga kawai tsirenta za suyi su huta. Dakinsu ta fada tana sauke numfashi, bata tsaya ba seda ta tube kayan ta jefa can cikin wardrobe kafin tayi maza ta fada bandaki ta watsa ruwa tareda Alwala. Tayi mamakin ganin harta idar da sallah babu wanda ya biyo sahunta, amma tasan tarko ne. Tana jin yunwa haka nan ta haye gado ta kwanta, tunda dai ta shigo gidan zance ya qare duk wacce zaayi ayi da safe ai. Washe gari ta kama Asabar, yanda taga babu wanda ko a fuska ya nuna mata tayi laifi jiyan ya fara daga mata hankali, tana so ta tafi gidan su Halima Daurin aure tana tsoron abinda tambayar hakan ze janyo mata. Wuraren 11 tana zaune a dakinsu, tsoro take ta fita tsakar gidan su hadu da wani daga cikin Mama ko Abban ga Yunwar data kwana da ita ta hadu da ta safiya tana ta sakudarta. Nuratu Yayarta da take bima ta shiga dakin da farantin qosai da kofin da ta zubo kunun gyada ta nemi gefen gadonta ta zauna tana aikawa da Umaiman harara dan daman tun Asuba data farka ta ganta bata ce mata komai ba sedai idan sun hada ido ta maka mata harara kawai. Ganin qosan da kunu ya qara wutar rura yunwar da take ji amma yanayin fuskar Yaya Nuratun yasa ta kasa ce mata zata ci, gashi babu motsin kowa a tsakar gidan qannensu duk sun tafi Tahfiz bare ta yafito wani ta saka ya debo mata. Ganinfa tana neman illata kanta dan damanita bame jumurin yubwa bace yasa ta yunqura da niyyar ta roqi yayar tata sega sallamar Qaninta. Daga bakin qofar yace " Yaya Umaimah kije inji Abba yana kiranki" ya juya abinsa. Seda cikinta ya bada wani qulululu, ashe ba kyaketa akayi ba jira suke gari ya gama wayewa tas ayi mata taron dangi dan taji shigowar Baba Abdullahi da Yaya Aminu babban Yayansu gidan. "Yaya Nuratu dan Allah ki bani ko kunun ne nasha wallahi banajin zan iya tafiya ma yunwa nake ji" ta fada a marairaice dan gara ta karya bille ta roqeta, bata sani ba ko baa girka da ita ba kar taje garin diba ta qarayin wani laifin. Banza Nuratun ta mata seda ta sake roqonta kafin ta turo mata kwanon qosan da kunun da ko rabi bata ci ba dan tana yi tana duba wani texbook nasu na yan medicine tace mata "Gashinan Mayya se kici ai" "Idan ni mayyace ke ma ai mayyar ce" Umaimah ta fada cikin qunquni ta ja kayan ta fara ci hannu baka hannu kwarya cikin dan lokaci ta cinye tas ta zura dogon Hijab har qasa ta fita tana nanata La'ilaha illah anta subhanaka innikuntu minazzalimin a zuciyarta harta isa qofar Sitting room din Abbansu. Ta shiga da sallama kai a qasa kamar ta Allah ta rabe a bakin qofa tana gaishe su ba tare data bari sun hada ido da kowa a cikin su ba.  Yaya Aminu ne ya daka mata tsawa yace "Zaki matso ciki ne kose na zo nan na tattaka ki mara jin magana kawai" "Barta Aminullahi fada da hargagi baya gyara, nasihar dai ita zaa ci gaba har sanda Allah ze sa ta dena abinda takeyi" Taji Muryar Baba Liman Aminin Abbansu ta katse hargagin da Yaya Aminu ya fara yi mata. Wata nutsuwa taji ta dan saukar mata dan ko ba komai akwai me kareta dan baze bari su mata komai ba amma da ta gama saddaqarwa yau kashinta ya bushe dan daga Yaya Aminun har Baba Abdullahi babu me sauqi, Abba kuwa zuba ido zeyi su caskalata babu abinda ya masa zafi. "Ina wayarki take?" Baba Abdullahi ya fada cikin zafin nan nasa, seta daga kai ta kalleshi aranta tana cewa "Toh takunkumi zaa sakamun kenan a hanani fita a karbe mun waya tab aikuwa da sake" "Ba magana ake miki ba?" Aminu ya sake zaburowa, qasa qasa ta harare shi kafin tace "Tana cikin gida" "Kije ki dakkota da duk wani abu da kika san Qasim ya mallaka miki ki kawo nan" Baba Liman ya fada. "Duk abinda tasan nasa ne ko tsinke ne ta hado" wani mutum da sam bata lura da shi a palour bama ya fada se faman girgiza qafa yake kamar ana yaqi, Se ta dago tana kallon shi dason jin qarin bayani, amma yanayin da tagani akan fuskar Abbanta da irin hararar daya watsa mata tasa ta miqe babu shiri. Sabuwar Iphone din da Qasim ya siya mata bayan kawo kudin auran su da kwana biyu ta dakko tana jujjuyawa, to me ya faru me zasuyi da wayar? Kuma ai ce mata aka yi ta dakko duk abinda ya mallaka mata kenan ba wai kwace wayar zaayi ba wani abun ne daban. Tunanin me dame ma Qasim din ya taba siya mata ta shiga yi, shi ba gwanin siyan kaya bane gara dai kayan maqulashe duk zuwa da abinda ze kawo mata. Wardrobe ta bude ta zaro lesina guda biyu daya dinkakke ne dayan baa dinka ba se Atamfa guda daya itama dinkakkiya kayan toshin wannan qaramar sallar da yayi matane, ta saka Atamfar Leshin kuma daman yau tayi niyyar saka shi. Ragowar tarkacen Jaka da takalmi da mayafai ta debo ta hada cikin babbar Leda, ta kalli turarukan dake kan Mudubin su wanda suma a cikin kayan take ta tabe baki a fili tace "Bazan hada dasu ba tunda bansan me zaayi ba" Nuratu dai se kallonta take ta zare cajar wayar daga soket ta hada ta sake fita. A tsakiyar ta dire musu ledar, mutumin dazu ya jata gabansa ya hau duddubawa yana cewa "su kenan dai ko? Ko da yake idan ma da saura zan tambaye shi muji" ya miqe yana sabar ledar Yaya Aminu yayi saurin dakatar dashi da cewa "Dan jira dan Allah" ya saka hannu ta dauki wayar dake saman ledar ya miqa mata yana cewa "Budeta ki goge komai na ciki" Umaimah da tayi mutuwar zaune saboda mamaki ta karbi wayar tana juyawa, tsawa Abba ya daka mata yace "Zakiyi abinda akace ne ko kin tsaya kina kallon mutane". Jiki na rawa ta cire password din wayar ta shiga setting nan take tayi resetting nata komai ya goge. Bayan wayar ta bude ta zaro allura ta zare Sim dinta da rigar wayar dan zuwa yanzu ta gama fahintar abinda yake faruwa tana gamawa ta miqa musu wayar. "Ita rigar wayar fa" Mutumin ya fada da ganinsa irin mara mutunchin nan ne daman, dake gidan tsiwar ya tarar kai tsaye tace masa "Ai ba shi ya siya mun ba" Shidai ya kinkimi leda yayi waje suka rakashi da kallon takaici. "Gara da Allah yasa akayi haka ashe dan qananan mutane ne bamu sani ba gara da Allah ya kiyaye mu hada zuri'a dasu" Baba Abdullahi ya fada. "Karo na Uku kenan Umaimah karo na Uku, na rantse da girman Allah ku zama sheda,saura wata biyu ta kammala karatun ta, idan har aka kai wannan lokacin bata fitar da tsayayyen miji ba a masallaci zanyi shela duk kuma wanda ya nuna yana son ta zan bashi ita sadaka. Badai juninki rashin mutunchi da rashin jin magana ba toh kici gaba, nidai bazan bari baqin cikin ki ke kadai ya dameni ba tunda haka kika zaba wa rayuwarki shikenan" Abba ya fada cikin kaushin murya "Aa Alhaji kausasa kalami ba naka bane, Addu'a dai da nasihar ita za'a ci gaba dayi mata amma irin wadannan kalaman su suke sake ta'azzara al'amuran a maimakon a samu sassauci se kaga abu na qara lalace wa. Ke kuma Umaimah ki nutsu, ki sani fa kullum girma kike qarawa ba wai baya kike komawa ba. Me yasa zaace kullum aka tashi kwatancen rashin kirki kece a gaba yanzu jin dadin kine ace an fasa auranki har sau uku cikin abinda be wuci shekara daya da rabi ba? Toh kar kiga kina samun maneman duniya ta ringa miki kida kina taka rawa. Duk namijin kirkin da ze zo neman auranki aka gaya masa an taba fasawa da wasu har sau uku se ya nemi jin ba'asi kuma bakisan abinda zaa gaya masa ba, ki yiwa Allah ki kama kanki ki san me kikeyi ki qyale zukatan iyayenki su huta" Baba Liman ya saka baki. Nasiha yaci gaba dayiwa Umaimah dake faman rusa kuka. Bata taba jin baqin cikin fasa auranta da akeyi ba irin na Alqasim dan da gaske take son sa kuma yayi daidai da irin mijin da take mafarkin samu a rayuwarta amma daga faruwar dan wancan abin shine zece ya fasa auranta har ya turo a karbar masa komai nasa da yake gidan su bayan koma menene shine sila ai, akan me ze kula wata mace suna tare bayan yasan Irin HALIN KISHIN ta, sam ba jin Baba Liman din ma take ba harya gama nasihar sa yace ta tashi taje wanda ba haka Yaya Aminu yaso ba, yaso ya mammaketa dan tun jiya Mama ta gaya masa fitar da tayi da sanda ta dawo yaso amma ze bita cikin gidan seya ci ubanta wallahi. Kuka wiwi ta fita tanayi, sam ta manta da tasu da Mama kai tsaye dakin ta ta wuce ta zube tana ci gana da rusa kuka kai kace mutuwa aka mata. Mama dake sallar walaha ta sallame tace "Idanna idar na tarar dake a dakinnan Umaimah sena lahira ya fiki jin dadi ki tashi ki fita karki qara mun baqin ciki akan wanda nake ciki" "Ai wallahi ko kashe ni zakiyi babu inda zanje, gurin wa zanje nayi kuka idan ba dakin uwata ba" Umaimah da har sannan bakinta be mutu ba ta fada tana ci gaba da rusa kukan ,kwafa Maman tayi ta tayar da sallarta, harta idar kuwa tana zaune bata tashin ba tayi kuka kana ganinta kasan daga qasan ranta take kukan nan. "Mama ya zanyi, kullum ina roqon Allah daya ragemun zafin kishi, wallahi Mama ji nakeyi kamar zuciyata ta kama da wuta idan na ganshi da wata macen, me yasa shi ya kasa kiyaye wa ko ze kula mata me yasa zeyi akan ido na?" Ta fada cikin tsananin kuka. "Dan ubanki keba musulma bace? Duk girman abinda kike ji idan kika nemi taimakon Allah zakiji sauqin sa, amma seki biyewa zuciya ki zama kamar mahaukaciya kiyi abinda ranko ya raya miki se saga baya kizo kina Nadama toh kici gaba Nadama kuwa yanzu kika daura dambar yinta. Ina jiye miki tsoron gaba Umaimah idan baki canza Hali ba wata rana sekin tsinewa wannan mummunan HALIN KISHIN naki" Mama ta fada tana ficewa daga dakin, ga tausayin Umaimah ga takaicinta. Ranar haka ta wuni zur tana aikin kuka, idan ta tuna wai fa Qasim ya fasa auranta se tayji duniyar ta mata zafi ita yanzu ina zata kuma samun kamar sa Dan gayu daya iya daukar wanka ga kalamai masu sanyaya zuciya, duk idanta hau zafin ta yasan yanda yake bi ya lallabata, gashi ya mata alqawarin idan ya aureta har mutuwa ita kadai ce matarsa har rabtsuwa ya mata da Alqur'ani amma shine daga dan wannan abin zece ya fasa auranta. Tunawa tayi da Ibrahim saurayinta na farko da aka yi musu baiko tun tana Aji biyar na secondary, shima fa akan kawai ta mari wata yar iskar Cousin dinsa da take sonsa, suka tareta a islamiyya ita da qawayenta kowa ta mata mari biyu tana dawowa gida da daddare se ji tayi wai Babansa yace baze aureta ba. Bayan shi se Lagin, koda yake shi daman tafiyar su bazata zo daya ba dan namamajone, daya rabu da tarin tarkacen yan matansa ya gwammace ya fasa auranta bayan har an saka musu rana wata shida yace ya fasa yanzu ga Qasim, a qarshen watannan fa suke zancen saka rana tunda watanni biyu suka rage mata ta kammala HND dinta. Sun gama tsara komai daidai da gidan da zata zauna ya kaita ta gani wanda aka tsara shi iya tsaruwa kadan ya rage a kammala, kullum cikin tura masa irin kayan da take so ya saka mata a lefe take shi kuwa yana lafta kudi yana siya yanzu shikenan wata banza zeje ya kaiwa? Abinda ya faru yasa ta manta da batun zuwa yinin Halima gashi babu waya bare su kirata, washe gari da take Lahadi ma a gida ta wuni cur ba um babi um um fuska duk ta kode saboda kuka. Mutanen gidan kuwa babu wanda ya shiga sabgarta gara ma Anty ita ce me leqata har ta kai mata abinci wanda a gurin Umaimah ba gwaninta take mata ba dan data fita zata rakata da harara. Ranar Monday tana da Test dan haka dole ta shirya fita makaranta dukda babu abinda ta karanta saboda wancan satin duk sun qarar dashi a yawon shirin biki, Lahadi da tayi niyyar zama a gida tayi karatun kuma ga yanda abubuwa suka kasance. A tsakar gida ta tarar da Abbansu yana sallamar Anty dake da girki ranar, kallo daya ya mata ya ci gaba da magana da Antyn ko gaisuwar da tayi masa be amsa ba dan tun wacceb ranar ya dena Amsa gaisuwarta haka babu sakin fuska ko yaushe suka hadu harara ce take rabasu. Gaba tayi da niyyar fita ya daka mata tsawa yana tambayarta ina zataje, se ta lumshe Idanunta da suka kawo hawaye ta juyo murya na rawa tace "Makaranta zanje ina da Test yau". Be tanka mata ba haka itama bata motsa daga inda take ba harya yi sallama da Anty kafin kamar baya so yace mata " muje" yayi gaba ta bishi a baya. A motarsa ya kaita har cikin makarantar, tafiyar kurame sukayi dan babu me cewa wani qala se sheshsheqar Kukanta dake tashia hankali duk a sonta na tausayinta yayi tasiri azuciyar Abban saboda sam baya so yagansu a damuwa amma kamar dutse ko ajikinsa. "Qarfe nawa zaku tashi" ya tambayeta yana miqa mata naira dubu, ta karba tace "Qarfe sha biyu ne test din, se kuma ina da practical 2-4pm" "Karki kuskura na rigaki komawa gida, idan kuma ba haka ba zamu gauraya" ya fada a kausashe kafin yaja motar ya fita. Kujera ta samu a gurin ta zauna kawai ta fasa kuka, ita ya zatayi? Ko tausayin abinda ya sameta bazasuji ba kuma se abi a ringa tsangwamarta ana daure mata fuska. A gurin Su Fauziyya da Nabila suka sameta dan daman nan suka saba zama su jira junansu "Umaimah lafiya zaki zauna kina rusa kuka kamar wadda akawa mutuwa jifa har kin fara tarawa kanki mutane ana kallonki" Nabila ta fada tana kama hannunta "Toh ina ruwan wani dani kowa yaji da damuwar sa mana an san abinda yake damuna ne da zaa zo ana kallo na" ta fada cikin kukan. "Kinga tashi mu bar nan, ga Malam Tsalha guntsi fesa can ta taho tun kafin ta debi wani sharrin taje tana yayaki a gari" Fauziyya ta fada ganin wata course mate dinsu Jamila ta nufo gurin, irin masu dan banzan gulma da sa idon nan ce, zance kuwa na kowa a makarantar nan kaji shi a bakinta shi yasa suke ce mata Malam Tsalha. A hanya suka hadu da Rumasa'u da shigowarta kenan suka rankaya cafteria suka samu guri can baya suka zauna anan take basu labarin fasa auranta da Qasim yayi. "Amma gayen nan dan yarfi ne,yanzu akan dan abin nan shine zece ya fasa auranki? koda yake kansa yayiwa dan dai nasan baze taba samun hadaddiyar baby kamar ki ba wallahi dan wahala shi yayi Asara. Seki share hawayenki da kyanki da quruciyarki bazaki rasa mijin aure ba. Kuma duk mutumin ma daya kasa haquri da halinka tun kafin ya aure ka ta yaya zaku zauna dashi bayan aure ki manta dashi kawai" Nabila ta fada. "Amma fa Umaimah kema da laifinki ko nace laifinki ma yafi yawa, kishi ai ba hauka bane amma ke idan naki ya tashi rufe miki ido yake kiyi tayin abu kamar wata me tabin hankali. Jifa yarfin da kika masa ranar a gaban mutane dan Allah, be yi fushi ba ya dauke ki har mukaje gida kina zaginsa shi da iyayensa kika sauka kika kuma qara masa, ina ke kika ce idan ya haifu cikin uwar sa ya je ya auri Siyaman ke ya qyale ki? Gashi kuwa ya nuna miki ya haifu saura ki jira ganin IV auran sa da ita nan gaba kadan" Ruma ta fada iya bakin gaskiyar ta. "Ai ke daman kina baqin ciki da duk wani farin cikin Umaimah a rayuwa ni na dade da sanin kina baqin cikin tarayyarta da Qasim waya sani ma ko da sa hannunki a ciki? Toh Umaimah dai nan gani nan bari duk mugun abin mutum sedai ya koma kansa saboda ke kin rasa mashinshini shiyasa kike farin ciki dan ta rasa nata" Fauziyya ta hayayyaqo mata, seta miqe tsaye itama tana kallo ta tace "Dani dake babu meyiwa wani gorin ya rasa mashinshini dan gara ni ana gani ana yabawa ke fa? Cusa kai kike amma mazan yi suke kamar basu san da wanzuwarki ba. Ita gaskiya daya ce daga qinta kuma se fada, the earlier da kika gane laifinki kika gyara the better. Amma idan kinga zaki ci gaba da zama da maqaryata suna dora ki a keken bera shikenan, nidai har a gurin Allah na fita dan na fada miki gaskiya ruwanki ki gyara ruwanki kiqi amma Umaimah babu Namijin da ze aure ki da wannan mugun HALIN KISHIN naki" Rumasa'u ta qara fada idon ta akan Umaimah da tayi shiru. "Kut baki kike mata na karta auru? Toh wallahi tun wuri Umaimah kisan abinyi dan bamu san irin bakin ta ba, Mune shaida" Nabila ta fada cikin son qara kambama abun. "Ke kika hadu da ita rana tsaka dab haka ke zamu bincika muji ko kina da mugun baki amma ni ki tambayeta ta sanni ta san asalina, kuma duk wanda ze so Umaimah a cikin ku baya nane dan ni son tsakani da Allah nake mata ina kuma so ta gyaru ta rabauta ba irin naku na son zuciya da sake ingizata zuwa ga Halaka ba" Ruman ta fada a fusace kafin ta juya ta bar gurin, a ranta ta qudurce ko Su ne kadai suka rage da zatayi qawance dasu a rayuwa ta haqura, ita Nabila zata kira Mayya? Umaimah kuwa zama sukayi a gurin Fauziyya da Nabila na sake yi mata famfo da gaya mata kalam da suke fasa mata kai take ganin takai inda bata kai ba. Basu bar gurin ba seda lokacin shigar su test yayi suka tabbatar da sunyi brain washing nata ta hanyar nuna mata daidai abinda take aikatawa da kuma cewar duk wanda ya rabu da ita shi yayi Asara ba ita ba. Haka suka shiga test din babu wadda ta karanta komai a cikinsu, daman ita ce me qoqarin da take goyasu to yau itama batayi karatun ba gashi anyi fada da Ruma bare ta basu Amsa. Da suka fito daga practical ma sun so su jata wai suje gidan Halima dan tun safen ta ke musu waya suje ita bata zo yin test din ba se taqi saboda tuna gargadin Abba na dazu, haka suka rabu a get ta kama hanyar gida ita kadai dan Ruma da gaske ta dauki fushi ko sashin da suke bata sake kallo ba. *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 3 Sosai take jin ta a takure saboda rashin waya, idan taje makaranta ta dawo sedai ta zauna shiru in ta gaji ta dauki littattafanta ta duba dan har yanzu babu me shiga sabgarta a gidan se Anty ita kuma ba kulata take ba. Ita bata ga abin da zesa gaba daya su wani dauke mata ba bayan ita abun jaje ya sama kamata yayi ataru a tayata amma duk an tsangwameta hatta da Yayyanta da suke gidan Aure kowa tazo harara da zagi ne yake raba su a cikin wannan yana yi taci sati biyu, sauqin ta ma bata zaman gidan sosai saboda gabatowar jarabawa da zasu fara ta qarshe kusan idan ta fita makaranta takwas se biyar take dawowa. Tana da buqatar waya saboda harkar karatu wani abun softcopy ne zaa bayar dole seda wayar ko system hakan yasa ta niyyaci tunkarar Abban su da zancen siya mata waya. Bayan sallar Isha ta same shi a palour sa, sam ta manta da Mama ce da girki seda tayi sallama ta shiga ta tarar da ita tana hadawa Abban shayi, kamar ta juya amma ba hali tunda sun tigada sun ganta haka  ta nemi guri ta zauna ta shiga gaishe su kai a qasa. "Ya akayi Hajia Umai" Abba ya fada cikin sakin fuska ba kamar yanda yake mata tsahon kwanakin ba hakan ya bata kwarin guiwa ta gyara zama tana cewa "Daman Abba saura sati uku mu fara jarabawa ne, kuma handouts da yawa softcopy ake bamu, bayan nan wani lokacin ina so na danyi browsing babu dama tunda bani da waya" "Yanzu me kike buqata" Abban ya tambayeta, seda ta kalli Mama da tayi kamar babu ita a gurin kafin tace "Waya nake so dan Allah Abba ko taka ce ka ringa bani aro in zan duba abu" "Tawa kuma Aa salon kiyimun jagwalgwalo, bari dai zanyiwa Yayan ku magana se a samo miki ko qarama ce" Abban ya sake fada. Da alama yau yana cikin yanayi me dadi, kamar tace Aa karya saka Yaya Aminu dan tasan da wuya idanze bari a bata sedaita kanne tayi masa godiya kafin ta miqe ta fita. Daga bakin qofa ta labe tareda kasa kunne ilai kuwa ta jiyo Mama tana cewa "Haba Alhaji, yanzu kai har ka yarda da wannan lambon da tayi kamar ka manta wacece Umaimah shine zaka dauki waya ka bata" Murmushi Abban yayi yana kallo ta yace "Malika kenan, takura da tsanani fa baya gyara sedai su qara kangarar da yaro, iya lokacin da aka dauka ai taji a jikinta idan muka ce zamu ci gaba da takureta kuma tun tana biyuwa har zaa iya kaiwa matakin da zata fito da wata sabuqar hanyar da bamu sani ba. Zan gayawa Babangida ya kawo mata  wayar, daman ko batayi magana ba ina da niyyar sawa ya kawo dan jiya ina jinta tana yiwa Nuratu magiyar ta bata aro ta hana ta, amma hakanbaze chanza komai ba, sannan ina me sake tabbatar miki ki kuma jaddada mata idan wata biyun nan ta cika bata tsaida miji ba sadakarta zan bayar" "Sadaka kuma Alhaji se kace wata wadda ba'a so" Mamanta fada tana zare ido, se ya miqe tsaye yana cewa "Kun dauka wasa ne kenan? Daman Lawan megadin gidan Alhaji Manniru ya taba nuna sha'awar auranta toh inaga shi zanyiwa magana kawai, Allah ya nuna mana lokaci zaku gani" ya shige dakin sa ya bar Mama tana cewa "In sha Allahu Allah ze fito mata da miji amma wane irin sadaka da ita abu babu dadin ji haka". Qirji Umaimah dake labe a bakin qofa ta dafe, a fili ta furta "na shiga uku daman Abba da gaske yake ni ze bayar sadaka?" Saurin barin gurin tayi gudun kar su ganta a ranta tana ayyana irin diban Albarkar da zatayiwa Lawan duk randa suka hadu, saboda ya raina mata hankali ita ze kalla yace yana so harma ya samu Abban su? Ai kuwa seya gane kurensa, ze san ita ba sa'ar wasan sa bace. Tana barin gurin Abbaya fito daga daki yana murmushi yace "Ja'ira, Allah dai ya shirya Umaimah yasa ta dena abinda takeyi" Mama dake jimami ta amsa da "Amin dai, amma Alhaji zancen nanda watan nan daka qara daga qafa. Aurefa ba abin gaggawa bane, dole seta samu wanda suka daidaita ya ga ze iya da ita tukunna dan kasan bazaayi abu a gurguje ba ba tareda an fahimci juna ba ba fata ba daga baya ta falle halinta mutum yazo yana cewa an rufe shi". Seda ya zauna yaja shayin data saisaita masa kafin yace " Nasani nima na fada ne kawai saboda na qara tsoratar da ita dan tana tsaye ta labe ba tafiya tayi ba, dukda haka da gaske nake ta mayar da hankali ta tsayar da Miji dan naga sako sakonda taga ana mata ya saka take duk iyashegen da takeyi, dan haka karma ki kuskura ta gane ba haka bane". Umaimah kuwa Haka ta kwana tana juya maganar fito da miji a wata daya, toh ta ina zata fara ma bayan tunda Qasim ya fasa kamar wanda ya tafi da duk farin jininta ko a hanya wani be sake tare ta da sunan soyayya ba. Idan ta tuna wai Lawan yace yana sonta kuwa wani takaici ne yake taso mata, ta quduri niyyar qare masa tanadi tsaf duk randa sukayi ido hudu kuwa. Washe gari guraren 10 sega Yaya Aminu da sabuwar waya Infinix me kyau ya kawo mata. Ta karba tayi godiya kafin ta kunnata ta jona a chaji ta wuce makaranta dan daman shiri take. Fix lecture ce ta wani malami da be samu ya gama musu darasin sa ba ga lokacin Exam yayi. Tana shiga Ajin ta hango Rumasa'u da yanzu ko kallon arziqi ba tayiwa inda suke se ta zarce gurin nata dukda su Halima dake mata magana suna nuna mata gurin da suka tanadar mata amma bata kula ba. Sallama tayi musu ka gaisa da wadanda ke kusa da Ruman kafin ta zauna akan desk din gabanta tace "Hajiya Ruma fushin ne har yanzu baa sakko ba" dauke kai gefe Ruma tayi tace "Fushi? Aini ba fushi nake ba Umaimah, buqatata ne bakyayi a cikin rayuwar ki shi yasa na fita na barki da masu hali da ra'ayi irin naki tunda bakya son gaskiya". "Uhm to yanzu dai ai komai ya wuce, bayan haka fa keda Nabila kukayi cacar baki ba dani ba amma da kika tashi kikayi mana kudin goro gaba daya" "Ai sanda take zagina ta kirani mayya kurmancewa kikayi da kika kasa magana ko kuwa? Kinga dan Allah matsamun a nan ga malam nan ya shigo" ta qarasa tana janyo littafi daga cikin jakarta. A kusa da ita Umaimah ta zauna har aka qare lecture din dukda Ruman ba kulata take ba, malamin na fita ta sake kafa mata surutu har seda Rumah ta sakko daga fushin tace mata "Na haqura amma dai bazan sake jerawa dake ba in dai kina tare da wadancan da basu san ciwon kansu ba" ta fada tana hararar Nabila da tun zaman Umaimah a gun hankalin na kansu. "Baki haqura ba kenan, itama Nabilan zan mata magana zata baki haquri akan abinda tayi shikenan?" "Ba shikenan ba, kinsan ni a rayuwa bana jurar wulaqanci bazan tsaya wata banza ta gaya mun magana ko da da nake musu shiru kin sani ba tsoron su nake ba kawaici ne amma yanzu daidai nake da kowacce yarinya a cikin su" "Ohni Rumah kin zama masifaffiya toh dai dan Allah kiyi haquri" Umaimah ta sake fada "Shikenan, na haqura" Da haka suka miqe gaba daya suka nufi qofa. A kusa da su Fauziyya Umaimah ta tsaya tana cewa "Ku tashi muje mu karbo exam card" "Yar wulaqanci se yanzu kika san damu bayan kina shigowa muka baki seat amma kika share kikayi tafiyarki abin ki" Fauziyyan ta fada, Nabila kuwa tabe baki tayi suna yar harara da Rumasa'u dake gaisawa da Halima Amarya. A waje suka zauna saboda Me bayar da Exam card dinbe riga ya qaraso ba, "Waini meya farune Ruma da Nabila naga se wani fizge fizge kukeyi lafiyar ku kuwa?" Halima ta fada tana kallo su. Fauziyya ce ta labarta mata abinda ya faru tsaf se ta kalle su gaba daya tace "Ai gaskiya ta fada muku, wallahi Umaimah idan baki canza wannan halin ba babu namijin da ze iya zama dake. Kai gidan aure fa ya wuce duk yanda kuke hasashensa, kunga dai zazzafar soyyar nan da mukayi da Hayati to wallahi ko sati bamu rufa ba muka fara bala'i kawai dan ya bar wayarsa na dauka ina bincike. Da na zata shwarwarin banzar da muke a nan zasu kawo mun mafita na hau na zauna akai ashe qara tabarbara abubuwa kawai zanyi badan Allah yaso ni Anty Zully tamun orientation ta gayamun gaskiyar abinda yake akwai ba ai inaga da yanzu wani zancen ake ba wannan ba. Toh wallahi tun wuri in zakuyi hankali kuyi in ba haka ba, jikin yarinya ne ze fada mata" "Gashi can an bude office din, ku tashi muje" Umaimah ta fada da rashin bama maganar Halima Muhimmanci, suka miqe gaba daya Halima nacewa "Ina nan da daya da daya zaku same ni, dadina da gobe ai saurin zuwa" suka rankaya office din. Kwankwasawa sukayi aka basu izinin shiga suka tura kai gaba dayan su ciki, mutumin na zaune akan kujerar sa se wani akan kujerun da suke a gefe suna Hira suka shiga Umaimah ce akan gaba tayi sallama karaf idanunsu suka hadu da wanda yake zaune akan Kujerar gefen, kallo daya ta masa ta dauke kai dan vata taba ganin fuskarsa a office dinba is dai idan sabon ma'aikaci ne aka dauka suka qarasa gaban teburin suka gaishe shi ragowan suka waiwaya suka gaida baqon banda Umaimah data kafa kai tana binciko musu Exam cards dinsu a jikinta tana jin ido na yawo akan ta abinda yasa ta ringa sakin gajerun tsaki kenan tana mita a ranta. Ita ta ringa miqa wa kowa nata suna signing a takaddar dake gefe har suka gama, dake ita ce qarshen fita seda takai bakin qofa kafin ta kalli baqon dake binta da kallo tunda suka shiga ya kasa dauke idonsa akan ta ta maka masa harara qasa qasa tace "Ayita kallon mutum kamar an bashi ajiya saboda sa ido" tayi waje abinta. Tsaf ya ji abinda ta fada se kawai yayi murmushi ya kalli abokinsa dake cewa "Umaimah kenan, sarqa uwar rikici. In kana neman danger wutar baya ka samu yarinyar nan ka gama kawai abokina" "Allah ko? Ni kuma ta burgeni. Da ace na shirya aure dana gwada sa'a ta dan a kallo daya ta shiga raina kuma tayi dai dai da matar da nake so na aura". Hannu ya bashi suka tafa yana cewa " Bayero Bayero namu, to ka afka mana, amma fa karka ce ban gaya maka ba zaka sha rikici da ciwon kai a gurin nan kai kuma gaka ba gwanin daukar hayaniya ba" Murmushi Khalil yayi yace "toh ai hadin shine daidai, idanna dakko mara hayaniya irina ai gidan mu will be boring, gara dai a samu wadda zata ringa mayar dashi lively" "Hakane, toh Allah ya tabbatar mana da Alkhairi abokina, kace wannan ziyarar bazata da ka kawomun ashe rabone ya kiraka" "Amin amma da saura, ni yanzu babu ma shirin aure a gabana kasan dai yanda ake lallaba rayuwar ga aiki yaqi samuwa yar buga buga kawai akeyi, qoqari nake na gama hada Masters din nan nayi settling. Akwai abubuwa da yawa danake da buqatar kammalawa kafin na dakkowa kaina maganar aure tunda bazaka dakko yarinyar mutane kazo kana bata wahala ba dole tana da buqatar abubuwan more rayuwa ko yayane a gidan ka" Khalil ya fada. "Hakane, amma kuma ko a yanzu Bayero ai Alhamdulillah rayuwarka na tafiya daidai zaka iya ajiye iyali, mutum nawa kafin cikin abokan mu da suke aikin abin fa duk intihani ne kawai amma idan kace seka samu yanda kake so zakayi aure zaa dade gaskiya" Nasir ya fada. Se Khalil ya gyara zaman sa yace "Hakane nima ba wai ina nufin sena tara kudi zanyi aure ba komai rabo ne a rayuwa, ta yuwu ma naka arziqin seka yi auran zaka same shi amma yanzu Nasir kadai san nauyin gidan mu a kaina yake. Nine ci, sha da suturar mahaifiyata da qannena guda biyu da suke gabanta, kai har masu auran idan suna da wata buqata nifa suke kira ka sani. Yanzu haka ni ina Masters, ga Jalila nk nake dauke da nauyin karatunta, Halifa bana ze gama secondary ya shiga Jami'a shima ga dai abubuwa nan kala kala babu yanda zaayi yanzu na tattago maganar aure da wadannan nauyin a kaina bayan ba wani kwakwkwaran aiki ne dani ba, bani da muhallin da zan ajiye mace a yanzu, samun nawa na lokacine, se mun samu yar kwangila anyi sannan muke samu, muna dai ta fatan Allah ya buda ya bamu yanda zamuyi tunda dai Allah yaga zuciyar mu". Numfashi Nasir ya sauke yana kallon abokin nasa da tausayawa, rayuwa kenan. A shekarun baya idan akace akwai wata rana da Khalil Bayero zasu shiga halin da suke ciki a yanzu babu me yarda. Irin gatan da suka tashi a ciki, mahaifinsu tsayayyan mutum me wadata iyalansa su kansu sun shaida tarin Alkahiran sa a rayuwa dan da yawan abokan Khalil da sukayi primary tare ta gomnati lokacin da budi yazowa babansu ya chanza musu makaranta zuwa ta kudi haka ya hada dasu duka ya kaisu ya ringa biya musu kudin makaranta. Banda Scholarship daya samar musu na fita qasashen waje sukayi karatun degree dinsu gashi yanzu ganiyar sa suke ci, duk kuma abinda suka zama a rayuwa sanadin sa ne. Bayan rasuwarsa ne abubuwa suka damewa iyalansa, wani amininsa da suke harkar kasuwanci yazo da takaddun da duk me hankalin daya gani yasan na bogi ne akan yana binsa bashin wasu maqudan miliyoyin kudade, ya samu goyon bayan qaninsa da suke uwa daya uba daya wanda ya bada shedar zur a kotu kan Marigayin da bakinsa ya gaya masa cewar akwai bashi tsakaninsa da Alhajin amma kuma babu wanda yasan da hakan ciki harda matarsa da Kuma Khalil din kansa wanda a sannan kusan komai na Mahaifinsu shine akai. Ansha badaqala musamman da Iyalansa suka kafe akan basu yarda ba, da ace akwai irin wannan magana me muhimmanci da Alhajin ya fada tun yana jinya tunda ba mutuwar fuji'a yayi ba yasha jinya sosai da har seda ya fitar da rai da rayuwa kuma a sannan seda ya fadi duk wani da yake bi bashi ko shi ake binsa amma da yake duniya babu gaskiya, aka je kotun ma suka siye Alqali suna ji suna gani haka suka tattara kudaden daya ce suka bashi wanda seda suka hada da siyar da kadarorinsu kafin suka tada kudin, qarshe gidan da suke ciki kadai suka tsira dashi se wani qarami da suka saka yan haya a ciki. Duniya kenan wata shari'ar se a lahira. Hira suka taba sosai kafin Khalil yayi masa sallama suka fito ganin dalibai nata zuwa karban exam card zaman shi kuma kamar yana raba masa hankali. "Ka gaida Hajiya dan Allah, insha Allahu qarshen satin nan zamu shigo da madam tunda sunyi arba'in" Nasir ya fada daidai sanda suka isa inda Khalil ya ajiye Lifan dinsa. "Aa abokina ina motar ne naganka da Mashin kuma?" Nasir din ya sakw fada. "Kai rabu da motar nan, kasan 306 da matsalar belt, haka kawai ina tafiya se ya cire kai na gaji dai kawai na siyar da ita na siyi wannan yafi mun na shiga ko ina hankalina a kwance". "Tab, gaye iya gaye ashe gurgune" Nabila Sani ta fada tana kallon Khalil dake buga machine, tunda suka fito ta saka su zama a kujerun da suke kusa da Office din saboda harga Allah Khalil din ya tafi da imaninta, jira take ya fito tasan ta yanda zata yi masa magana se ga wannan big turn off din, ashe ma wankan ne kawai aljihu babu ko sisi. "Arziqi nufin Allah ne, kuma dan kin ganshi da lifan shine aka ce miki matsiyaci ne wallahi Nabila ki dena abinda kike shiyasa har yau kika rasa ko wanda ze kiraki a waya ki rage dare" Umaimah data kalli Khalil din itama ta juya tana gayawa Nabila. "Allahu akbar, Allah ka nuna mana Annabi, yau Umaimah ce takewa wani fadan yayi ba daidai ba lallai inda ranka kasha kallo" Halima ta fada cikin sigar tsokana dan daman ita gwanace. "Se ku tashi mu tafi ai" Nabilan ta fada a fusace fuu tayi gaba suka rufa mata baya suna sake caccakarta. Murmushi Khalil da duk abinda suka fada yaji yayi dan da dan qarfi suke maganar bayan haka yana da kunne sosai, Kallon Nasir yayi dake danna waya yace "Nas kodai na shiga gurin nan ne, dagaske fa yarinyar nan tamun over taking" "Abokina ka shiga kawai mana tsoron me kake ji, babu komai in sha Allahu tsamu tsaya maka kawai dai ka shirya ina qara gaya maka akwai daru" Nasir ya fada yana bashi hannu, "Shikenan zanyi tunani akai" daga nan sukayi sallama ya buga mashin dinsa yayi gaba. A bakin get ya sake haduwa dasu suna jiran abin hawa, sukayi ido hudu da Umaimah ta kuwa murguda masa baki da harara yayi mata murmushi ya wuce abinsa. Cikin taimakon Allah suka qare jarabawarsu tsaf saura jiran sakamako, ranar ansha hotuna anyi celebration, akwai Dinner da suka shirya yi an dade ana hada kudi daman dan harda anko suka fita Umaimah ta biya kudin komai amma bata jin zataje, tasan ma baza'a barta ba yanzu kuwa da take gudun laifi bazata fita babu izini ba. tunda suka fara jarabawa daman a faduwar gaban abinda yake gaba take, furucin Abba na idan bata fitar da Miji ba ze bada ita sadaka na bala'in damunta ta kuma rasa yanda zatayi. Ta nemi shawarar Rumasa'u akan maganar tace mata tayita Addu'a kawao Allah ya yi mata zabi na gari, ta kuma ce mata ta gwada neman wanda taga hankalinta yafi kwantawa dashi cikin samarinta na baya ko Allah zesa a dace amma babu nasara. Duk wanda tayi qoqarin bugun cikinsa akan batun aure zillewa suke, qiriqiri suke nuna mata suna sonta da gaske amma bazasu iya da halinta ba wannan abin na bala'in qona mata rai, ita wane hali ne da ita? Shin laifi ne dan kayi kishin abinda kake so su ba abin alfaharin su bane ma ace ana kishin su? Kusan sati da gama makarantar su babu wanda yace mata qala akan batun aure, ba kamar baya ba yanzu komai ya dawo daidai a gidan itace ma take dararewa wani lokacin saboda gudun kar a diro mata da maganar fito da Miji katsahan. Fita ce dai aka hanata, dan ko Islamiyyar da take zuwa Asabar da Lahadi ma Abban ya soke yace yawo ne kawai, daidai gwargwado ta samu ilimi ta zauba agida tayita tilaqar abinda ta sani amma fita indai bada dalili me qarfi ba be yarda ba. Ana haka Yayarsu Anty Hajiyayye ta haihu, dayake CS akayi mata da farko akace a dawo da ita gida ta zauna idan jikinta ya warware seta koma tunda a can babu mataimaki ga yara kuma amma Abban su yaqi, daga qarshe dai dakyar Mama ta lallabashi akan tunda Umaimah bata komai taje ta zauna mata tareda wata mata da aka samu har zuwa sanda zata warware. Seda ya kafa mata warning sosai ya kuma jawa Hajiyayyae kunne akan duk in yaji ba daidai ba se ranta yafi na kowa baci haka ta tattara ta tafi gidan Yaya Hajiyayyen. Washe garin suna da yake ba taro sukayi ba bayan an gama suyar nama an kasa Yaya Hajiyayye ta bata tace ta shiga gidan da yake kallon nasu takai. Dogon Hijabi har qasa ta dora akan Doguwar rigar material din jikinta fuskar nan kamar ko yaushe babu ko digon kwalli akan ta amma da yake kyanta daga Allah ne se gata ta fito shar abin ta. Tun daga wajen gidan ta tabbatar da gidan masu arziqi ne, idan ma a yanzu babu to tabbas da an samu ta tura qofar get din da take a bude ta shiga qaton compound din gidan da sallama. Babu kowa a tsakar gidan, taja ta tsaya ganin qofofi biyu ne manya bata san wanne ne ta shiga ba, gashi ma ta manta ta tambayeta wa zaa kaiwa dan qila mata biyu ne a gidan. Daga bayanta taji ance "Ya kika tsaya? Bismillah ki shiga suna ciki" seta juya a firgice dan bataji takun takalma ba se magana kawai, ido hudu sukayi da Khalil dake tsaye a bayanta yasha wanka da wata danyar Shadda Fara gurin gaba daya ya karade da Qamshin turarensa. *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 4 Ya ganeta, amma da alama it bata gane shi ba tace,qasa qasa ta harareshi tace "Ka tsorata ni wallahi, kuma bansan qofar shigan ba. Daga gidan Maman Asad nake ta bada naman suna a kawowa Hajiya" ta qarasa tana miqa masa ledar Naman. Se yayi gaba yana cewa "Muje na nuna miki" Tsabar neman magana irin nata bibsa take a baya tana kwaikwayon tafiyar sa da yake yi cikin nutsuwa kamar me qirga takunsa. Gulmarsa take a zuciya tana cewa "Ji yanda yake wani yanga dan Allah kamar mace ya ware qafa yayi sauri Aa se batamun lokaci yake" a haka ya tura babbar qofar dake part din farko ya shiga da sallama ta rufa masa baya. "Zauna, bari nayi mata magana inaga tana sama" ya fada yana wucewa matakalar bene, seta nemi daya daga kujerun palour ta zauna tana bin ko ina da kallon. Kayan cikin palour sun dan tsufa amma da yake masu kyau ne da asalin tsada ga kuma ingantacciyar tsafta da suke samu seya boye tsufan nasu. Ko ina qalqal se daukar ido yake ga qamshin turaren wuta daya hadu da sanyin Ac suka qarawa gurin nutsuwa ta musamman. Babban Enlargement photo dake kafe a bangon palor ta ringa kallo, Wanda take kyautata zaton shine megidan tareda matar gidan se yaransu guda bakwai maza biyu mata biyar. Kallon su take tanaso ta tuna inda tasan fuskar dan kusan duk kamar su daya sedai wasu sunfi wasu haske a ciki amma ta kasa tunawa. Bataji sakkowarsu ba se maganar babbar mace da take cewa "Sannu da zuwa yammata" Zamowa tayi daga kujerar tayi ta shiga gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska. Kanta a qasa saboda kwarjinin da matar tayi mata ta miqa mata ledar tana cewa "gashi inji Maman Asad tace a kawo" "Toh naman suna ne aka biyo mu dashi dukda bamu shiga ba? An gode Allah ya raya Ummu-salma, kice mata tayi haquri wallahi qafata ce ta motsa abinda ya hanani fitowa kenan amma in sha Allahu zanzo naga baby" Hajiyan ta fada kafin ta cigaba da cewa "Qanwarta ce ko qanwar Habibu?" "Qanwar tace ni" Umaimah ta bata amsa cikin qaguwa, to tambayar kuma ta mecece haka. Ita kuwa Hajiya cikin son janta da hira ta ci gaba da cewa "Allah sarki ban taba ganinki ba, na dan san qannen nata kuma musamman Nuratu indai tazo takan shigo mu gaisa" "Gwana uwar an cusai kenan, wato taga qaton gida har wani shiga take su gaisa Allah ya sawwaqawa Yaya Nuratu dai" Umaimah ta fada a ranta a fili kuwa tace "Allah sarki ai Nuratun nake bi, nice autar su a Mata" se ta miqe tsaye "Aa badai tafiya ba kuma muna cikin yar hirar mu, gashi ma ko ruwa baa kawo miki ba 'Habiba kina ina ne? Ki kawo mata ruwa" Hajiyan ta fada. Se ta fara tafiya tana cewa "Aa wallahi babu komai Hajiya bari naje aiki mukeyi ne se an jima" "Toh shikenan ki gaida gida na gode, se kin sake shigo mana ko, yaya sunan yar tawa?" "Umaimah" ta bata amsa tana dan murmushi "Toh Umaimah ki gaishe da Hajiyayyen nagode kinji" daga nan sukayi sallama ta fice kamar wadda take akan qaya. Tana fita Khalil ya fito daga wata qaramar qofa ya canza kayan jikinsa zuwa dogon wadon jeans da T-shirt yanata zuba qamshi. "Sannu Babana mutanen zazzau kunsha hanya amma kunyi sauri kamar wanda kuka taho a iska" Seda yasha ruwan da aka kawowa Umaimah bata sha ba kafin yace "aikinsan yanzu hanya ta gyaru sunci qarfin aikin titin sosai shiyasa tafiyar take sauri kuma bamu zauna ba ana daura auran muka taho harda Amaryar dan a shirye suke suma" "Masha Allahu Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana na yan baya lafiya, kana kallo dai daga sa'anninka gashi nan layi ya fara zuwa kan qannenka sun fara aje iyali kai ko kunya baka ji sedai kasa shadda ka tafi daurin aure ka kasa yunquri kai azo naka" Hajiya ta fara qorafin nata na kullum indai aka yi zancen aure. Murmushi yayi ba tareda ya bata amsar maganar tata ba ya waiwaya yana duban palour yace "ta tafi kenan" "Wacece?" Hajiyan ta tambaye shi, seda ya sake kurbar ruwa kafin yace "Umaimah" shikansa se da yaji wani iri, yama akayi ya riqe sunanta?/yanda ya kira sunan seka rantse shiya rada mata shi. Kallonsa Hajiya tayi da mamaki jin ya kama sunanta, "ka santa ne daman?" Ta tambaye shi tana tsare shi da ido. Seya duburburce, ya manta shaf da halin Hajiyar tasa, yanzu abinda be faru bama tunda akayi haka seta qullo shi wai wa ma ya aike shi nuna ya santa ne? Koda yake yarinyarce, ta shige masa yanda beyi zato ba. "Magana nake maka ka tsareni da ido kayi shiru, ko baka ji me nace bane?" Ta fada ganin gaba dayama hankalinsa baya gurin, se yayi firgigit yana shafa kai yace "Aa fa Hajiya ni ban san ta ba, sau daya na taba ganinta dalibar Nasir ce ranar dana je makaranta gurinsa na ganta a office din shine fa naji ya fadi sunanta se kuma dazun na ganta a compound wai an aikota amma ba wani abu daban bane da kike tunani" "Toh ni me kaji nace Babana, yarinyar ma ai ta gidace qanwar Hajiyayye ce kuma dai kai shaidane akan nagartar Hajiyayyen tunda Mijinta kusan abokinka ne kaima kana yabonta, babu komai Allah ya tabbatar mana da Alkairi" Hajiyan ta fada tana murmushi me kama da dariya saboda murnar wannan al'amari, ita daman tunda taga yarinyar tayi mata, harta fara saqa yuwur hadi ta da Khalil din nata se gashi ma ashe tuni Allah ya hada abinsa, to Allah yasa abokiyar arziqi ce. Khalil da gaba daya ya rikice jin Hajiya na neman kwanto masa ruwa ya miqe yana cewa "Nifa Hajiya ba wani abu tsakanina da ita idan baki yarda bama ki aika a kirawota kiji idan ko sunana ta sani karma ki kawo wannan maganar" ya fice da sauri kafin ta kwanto masa wata kurar. "Ja'iri, ai har na fara tunanin kodai baka da lafiya ne ace mutum shekara Talatin da dori amma babu wanda zece ya taba ganinka a qofar wani gidan da sunan kaje zance, to yanzu hankalina ya kwanta, bari na kirawo yan uwanka na shaida musu abin arziqi sannan na kirawo kawunka ma na fada masa dan da zafi zafi ake duka qarfe" Hajiya ta fada, nan ta shiga kiran Habiba akan ta kawo mata wayarta, Habiban na cewa "Oh Hajiya kina jin fa abinda yace shine zaki fara yayatawa se yazo ya baki kunya daga baya" "Ke dallah tafi can kece baki gane borin kunya yake ba, amma daman ina kallonsa dazu nasan da wata a qasa itama baki ga duk a takure take ta kasa sakewa ba? Ga yarinyar kuwa tabarakallah kyakykyawa da ita ga nutsuwa Allah yasa ta dore da haka" Ita dai Habiba dariya ta ringayi tana kallon ikon Allah dan dagaske Hajiya take, waya ta ringa kiran yayanta kaitsaye gaya musu take Khalil ya samu mata su fara shirin biki kowacce aka fadawa kuwa nan zata hau murna a fara lissafin abinda zaayi da auran nasa. Tana komawa gidan wanka ta fada dan saurin da take tayi daman su Fauziyya ne zasu zo wa Yaya Hajiyayyen barka, ta gama shirin ta tsaf ta shirya cikin wasu riga da skirt na Atamfa da suka matuqar yi mata kyau. Bata daura dankwali ba se hula ta zura akanta ta fesa turare ta fito palor inda Yaya Hajiyayye da Anty Larai dake taya ta da wasu aikace aikacen suke zaune suna hira. "Dan Allah Umaimah goya yarinyar nan bacci zatayi take ta rigima" Hajiyayyen ta fada tana miqa mata Ummu-Salma seta ja da baya tana cewa "Tabdi haka kawai daga fitowata kice wani in goyata in bacci zatayi a kwantar da ita mana tayi kawai tun jiya nake goyata da daddare kusan kwana tayi a bayana gashi yanzu tasa mun ciwon baya". " yanzu Umaimah wannan abar da bata fi nauyin pure water ba ce ta saka miki ciwon baya kedai kiji tsoron Allah, koda yake kamar yaune kema kin kusa ki haifi naki se naga uban da ze goya miki ba ciwon baya ba wannan ko ciwon qunquru duk ya hada ya saka miki" Anty Larai ta fada tana miqewa ta karbi yarinyar tace "Kema neman magana yasa kika ce ta goyata ai, tun dazu da kin bani ita da yanzu ta dade da yin baccin ai" ta saba yar a baya ta daure da zani. "Gani nayi kin sha aiki da yawa ai Anty ita kuwa babu abi da tayi, ina jinta dan iskanci cewa tayi inta taba danyan nama kanta ciwo yake amma kin iyaci idan an soya ko?" Hajiyayye ta fada tana Hararar Umaimah, ko a jikinta ta zauna kusa da ita tana latsa waya, ba jimawa suka jiyo sallamar su Fauziyya Umaimah ta fita da dan gudunta ta taro su. Seda suka gaisa da Maman Asad kafin suka qule a dakin da Umaiman take, se yaba haduwar gidan suke dan sabon gini ne suka yi ko shekara basuyi a cikinsa ba. Basu tashi tafiya ba se dab da magriba suka fito bayan da suka sake kwalliya kowa ta baza turare aka kashe daurin dankwali. "Bazaku bari ayi sallah ba zaku tari goshin magriba ku fita" Maman Asad ta fada tana qare musu kallo, "Bari kawai muje Anty, Allah ya raya a gaida su Asad da Mimi" suka hada baki gurin fada "Zasuji suna gidan qanwar Babansu hutu, ki duba kitchen ki daukar musu kullin nama" ta fada kafin ta shige daki ta barsu tsaye suna jiran Umaimah data tafi kitchen. "Ke ai irin unguwar nan dab da magriba ne kake ganin mutanen ciki ta, kinsan yan gayun nan basa yawo a rana yanzu ne daidai masu fita sallah sun fito masu dawowa daga aiki suna shigowa da qafa zamu taka har titi ko Allah ze sa mu dace da rabo" Nabila ta fada tana rarraba ido tana qarewa qerarrun gidajen unguwar kallo, unguwa ce ta yan gayu me kyau da tsari, "Kedai Allah ya shiga lamarin ki Nabila naga alama kina neman zaucewa akan neman Miji, koda yake tsarin da kika dakko ne bame bullewa ba kin tsaya ke se hamshaqin me kudi bayan su kuma ba irin ki suke so ba" Fauziyya ta fada tana qunshe dariyar dake son kufce mata saboda yanda Nabilan ke faman rangwada da karairaya se jefa dogayen qafafunta take ala dole tana yanga. "Wallahi Fauza zan miki rashin mutunchi, idan Allah ya kawo munme kudin dan Allah ki hana shi aure na banza yar baqin ciki" ta fada a fusace tana kallonta, har Fauziyyan ta bude baki zata bata amsa Umaimah ta dakatar dasu tana cewa "Malamai ya ishe ku zaku fara halin naku kamar kaji, ke kuma sauka daga titi kafin ya rage miki farashi" ta qarasa tana kamo Nabila gefe saboda hango Khalil daya fafaro mashin dinsa kamar ze tashi sama. "Wannan kamar guy din nan na office din Sir Nasir" Nabila ta fada tana binsa da kallo se Umaimah ta gyada kai tace "Tabbas shine, daman ina ta tunanin ina na san fuskar sa ashe saurayin Nabila ne" ta fada da sigar wasa. Baki Nabilan ta tabe tace "Wallahi ya hadu kawai dai matsakar sa rashin chanji, kome yazoyi nan oho qila gidan su wani abokin nasa yazo" tayi tambaya ta bawa kanta amsa duk ita kadai se Umaimah ta nuna mata gidan su tana cewa "Kinga gidan su can, ko zaki shiga ki gaida surukarki" "Aa kakan surukata banason wulaqanci" daga haka suka ci gaba da tafiya har ta raka su bakin get din layin kuwa babu wanda yace musu tafi ku mutu dukda ga Maza nan samari da magidanta suna ta qoqarin Shiga masallaci dan an kira sallah kota kansu basu bi ba. A bakin Get din tayi musu sallama ta juya. A qofar masallacin taga Khalil yana alwala ya bita da kallo ta galla masa harara se ya sakar mata murmushi ba shiri ta dafe qirji jin zuciyarta ta buga da qarfi kamar wadda ta tsorata. A haka ta shiga gidan faran faran kamar wadda aka biyo saboda yanda taji gaba daya zuciyarta na tsere kanta har wani sarawa yakeyi. "Ke lafiyar kuwa kika fadowa mutane babu ko sallama" Maman Asad ta fada tana qare mata kallo, se Umaimah ta kalleta tace "Inaga Gamo nayi, wani mutum na gani, kai ba mutum bane Aljanine" ta fada kamar me tantamar abin "Idan ma rauhanine zaki gani ai, saboda baku da hankali da magribar nan haka kuka kwashi qafa kuka fita, ni sam bana son wadannan qawayen naki gaba daya basu da nutsuwa har gara gara Halima a cikin su daman amma wadannan biyun bansan wadda tafi wata rashin hankali a cikin su ba" "daga abin arziqi kuma shine zaki zagesu yan gidan mu nawa suka haihu basuje musu barka ba seke, daman mantawa nayi baa miki abun kirki dama basu zo ba" Umaimah ta fada tana zumbura baki, "Da suka zo din uwar me na qaru da zuwan nasu fitsararriya? Ki shiga hankalinki idan ba haka ba kuma sena hadaki da Abba ina daman an raba ki dasu kinqi ji ko? Shikenan" Hajiyayye ta fada tana wuceta, Umaimah ta rakata da harara, wallahi badan tafi samun yanci anan ba da gidan su zata tafi haka kawai mata ta sakata a gaba ta ringa mata masifa daga an mata abin kirki anzo mata barka? Ai shikenan maganin ta itama gobe ta qara. Haka rayuwa taci gaba da mirginawa da dadi babu dadi Umaimah na zaune gidan Hajiyayye har Sukayi arba'in ranar kuwa bata qara kwana a gidan ba ta tattara ta wuce dan daman tuni taso tafiya Mama ce ta hana saboda Anty Larai ta tafi qauyensu yarinyarta bata da lafiya gashi su Asad sun dawo daga hutu dan haka hidimomin sunwa Hajiyayyen yawa. A dan zaman da sukayi ko fada anyi shi yafi sau cikin kwando, Umaimah rashin jiz Hajiyayye rashin haquri, haka zata biye mata suyita hayaniya musamman da Mijinta ba mazauni bane shiyasa Umaiman ke samun yanda take so. Sam ta manta da wani Khalil da shirginsa dan tun waccen ranar bata sake haduqmwa dashi ba daman ba fita ta fiya yi ba, idan ma ta fita ko kallon gidan su batayi, abu daya ta kasa gane kansa Khalil din na yawan fado mata a rai, duk kuma sanda ta tuna shi se taji irin faduwar gaban ranar na har ta ringa ayyana a ranta kodai maye ne? Idan ma mayene to sedai yaci kansa amma ita kam kurwarta daci ne da ita. ko ranar da Hajiyarsu ta shiga gidan yiwa Maman Asad barka qin fitowa tayi su gaisa tana ji tana ta tambayar ta ina take ta bige da baccin qarya, tana jinta tana wasu soki burutsun data kasa gane kansu. Ita kanta Yaya Hajiyayyen bata fuskanci abinda Hajiyar take magana akai ba kawai dai ta ringa binta da toh, koda ta sake tambayar Umaiman itama babu wata magana daga gareta da haka zancen ya shiririce. Komawarta gida da kwana biyu result dinsu ya fito masha Allah ta fita da sakamako mekyau, nan da nan aka shiga hidimar registration na NYSC bayan dan lokaci kadan suka shiga Camp, badan taso ba aka barta a Kano saboda gaba daya qawayen nata basa Kano, Fannah sun koma Miduguri da Mijinta dan shima dan can ne, Rumasa'u ma Jigawa ta tafi zata zauna a gidan Yayarta, Fauziyya, Nabila da Nadiya daman Kudu suka ce zasuje wanda itama tayi niyyar bin ayarin dukda bata da tabbacin a gida za'a barta amma dai da ko iya camping taje tayi in yaso daga baya a nema mata Relocation se gashi ana fara Registration din Yaya Aminu ya shiga ya fita ta hanyar abokinsa aka barta a Kanon tayi Camp dinta a Qaraye bayan sun fito akayi posting nata nan cikin Sakatariyar Audu Baqo. Lafia lau take fita aikinta da take jin dadi a yanzu ko ba komai yana debe mata kewa, zancen manena dai abu shiru kamar anyi ruwa an dauke, ita a yanzu bazata iya tuna yaushe rabon da ace ana sallama da ita ba. Duk samarin sun zama sedai a kira waya ko ayi chatting, data fuskanci gaba daya ma bata mata lokaci sukeyi tunda babu wanda ya yarda da maganar a fito ayi aure wasu ma sedai su sako wata maganar banzar nan take kuwa zata qarewa mutum tanadi kafin ta dannawa lambarsa block, gaba daya ma ita ta fita sabgar samari yanzu, inda take dan samun nutsuwa ganin Abba be tada maganar ba, amma a tsorace take dan tasan yana iya mata dirar mikiya a koda yaushe gashi har yanzu bata samu tsayayye ba, a cikin haka Me neman auran Nuratu ya turo da saka rana shekara daya yayi daidai da kammala karatun Likitancinta haka itama Umaimah lokacin ta kammala Bautar qasa. A daren ranar da Abba ya tara su ya shaida musu tare ze hada ya aurar dasu ita da Nuratu ba qaramin dadi taji ba, ta tabbatar da yardar Allah shekarar nan bazat cika ba seta samu wanda zasu daidaita su kuma daddale da maganar aure. Akace wai ana zatom kura tayi lafiya ashe da sauran zawo, ranar wata Asabar babu aiki, tana kwance a dakinsu suna Voice call dasu Nabila mutanen Lagos acan suke bautar qasar su. Sun samu guri suna tsula tsiyarsu babu me ce musu su gyara sedai fatan shiriyar Allah kawai. "Ke qawata ina ta so na miki magana se na manta ina guy din nan kuna haduwa kuwa idan kinje gidan Anty Hajiyayye" Nabila ta fada daga can bangaren, Kwanciya Umaimah ta gyara bayan data zura Earpiece a wayar tace mata "Wane mutumi kuma, kefa a rayuwarki baki da zance sena samari kodan baki dasu ne se Allah" "Karki nemi ki gaya mun magana malama daman kinsan ance wani jinkiri Alkhairi ne toh da alama nima nawa jinkirin ze zama Alkhairin" Nabila ta fada tana fari da ido, se Umaimah tace "Toh ina jinki meya faru yanzu?" "Last week bana fada miki munje Birthday partyn wani corper da muke service guri daya ba a wani Restaurant akayi, kawai in gaya miki se gashi mun hadu da Guy din nan na office din Sir Nasir. Oh my God Umaimah kinganshi kuwa yanda ya hade cikin wasu J and T wallahi da farko ban ma gane shine ba kawai naji ya qara tafiya da imanina seda muka matsa kusa na ga fuskarsa na gane shine ashe. Akayi Sa'a cikin wadanda muke tare kawai naji wani Ya kira Sunansa *Architect Khalil Umar Bayero* bansan sanda na saki ihun murna ba, Maims daga yanayin kayan jikinsa da abincin da sukayi order kadai kinsan akwai chanji a hannuna, se daya bude baki yayi magana gaba daya ya qarasa kwance mun kai kinji Husky Voice dinsa Umaimah? Kinga wata arniyar mota daya tuqa suka bar gurin? Na rantse i can die for that guy yayi mun to the core shine daidai mijin da nake ta jira na samu, ga kyau ga aji a yayan banki ashe basaja kawai yake yi a Kano yana yawo akan Lifan". Tunda Nabila ta fara magana ta fuskanci akan wa takeyi taji wani irin duhu ya fara mamaye mata idanu, gaba daya ma dena fuskantar ta tayi tana jinta ne amma sam bata gane me take cewa idanunta kawai hasko mata Khalil suke yanayiwa Nabilan wannan tsadaddan murmushin nasa daya saka ta fara tunanin mutum ne ko Aljani? "Umaimah kina jina kuwa kin barni se magana nake kinyi shiru" Nabilan ta fada jin shirun yayi yawa. Bata san ya akayi ba se jin bakinta kawai tayi yana furta "Daga yau Nabila babu ni babu ke, idan kuma kika sake kika qara yi mun magana na rantse da Allah se naci kutumar ubanki, yar iska kwartuwa mebin mazan mutane" tana gama fadar haka qit ta kashe wayar tayi wurgi da ita ta hadu da bango nan take ta tarwatse. Hannu biyu ta dora akai ta fasa ihun daya saka nuratu wuntsulowa daga kan gado dan tuni tayi suman zaune tun sanda Umaiman ta fara korawa Nabila warning. "Meya faru? Akan waye? Sune tambayoyin da Nuratu takewa kanta da bata da me bata amsarsu se Umaimah dake birgima tana zunduma ihu a qasa kamar wadda ta hau iskokai. *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 5 Da gudu Nuratu ta fita kiran Mama ganin yanda Umaiman take ihu tana birgima kawai wadda ta hau iska. "Nuratu leqa ki kira Malam Sadi ko Auwalu suyi mata ruqiyya, mun shiga uku a ina kuma Umaimah ta kwaso iskoki" Mama data shiga dakin zani a hannu Anty na take mata baya ta fada suka shiga qoqarin riqeta amma ina se zillewa take tana ihu da kururuwa haka Malam Sadi ya same su ya shigo da dogon carbin sa ya samu guri ya zauna daga gefe ya su riqeta, qarfi suka hada su ukun suka mata muguwar dannan shi ko ya shiga karanto Ayoyin ruqiyya yana tofeta daga i da yake zaune. Banda Kukan baqin ciki babu abinda Umaimah takeyi, wannan shine duka biyu, ga abinda yake damunta sannan anzo an wani danne ta ana mata ruqiyya se kace tace musu iskokai takeyi. Ganin da Malam Sadi yayi ta dena bige bigen se kuka ya saka shi cewa su saketa kowa taja gefe tana numfashi kamar wanda sukayi gudun famfalaqi, se ya cewa Nuratu ta samo garwashin wuta, fita ta debo masa ya ciro wani qullin magani daga Aljihunsa yana kallonsu yace "A samo abu a rufa mata se ku fita daga waje, idan kuma zaku iya shaqar hayaqin maganin ku tsaya tunda sunqi magana gara a sakasu ta dole" ya qarasa yana barbada magani a kaskon nan take suka fara jera Atishaqa saboda wani yajida maqaqi da suka taso lokaci daya suka nemi su shaqe su, shi kansa tarin yake ba shiri aka fara rige rigen fita daga dakin harda Umaimah da damanita ba shiri take da hayaqi ba. "Ku riqota karku bari ta fita" Malam Sadi ya fada ganin ta nufi qofa Nuratu ta matsa da niyyar riqeta ta hankadevta tana cewa "Dallah kyaleni ni lafiyata qalau babu wasu Aljanu da nakeyi, abu ne ya same ni ku barni nayi kukana ko zanji sanyi kun wani dakko shi bayan ma ko Ruqiyyar be iya ba" tana gama fada ta zaka kai tayi waje ta barsu da baki bude. "Hajiya baku san sharrin Jinnu ba qarya ce irin tasu kawai sunji magani ne shine zasu fake suce itace da kun kamota ta shaqi hayaqin nan da kansu zasu bar jikinta yanzun nan" Malam Sadi ya sake fada. Se Mama ta daga masa hannu tana cewa "Kaje kawai mungode, Nuratu fita da hayaqin ki kashe a bude winduna iska ta shigo" tayi waje itama. Umaimah ko can kan Dandamalin qofar dakin Mama ta samu ta zauna taci gaba da rusa kukan da bata san ko na menene ba, idan ta tuna wai Nabila taga Khalil kuma tana sonsa ji take kamar tayita buga kanta a bango har se ya fashe ta dena tuna abin. "Zo Umaimah" Mama ta fada a tausashe kafin ta shige uwar dakinta ta zauna bakin gado tana jiran Umaimah, ita fa wannan lamari ya fara bata tsori, a yanda take abubuwa tabbas duk wanda ya gani zece shafar Aljanu ne amma kamar yanda tace lafiyarta qalau itama ta yarda da hakan bari tazo taji menene dan gaskiya idan ba Aljanu ba qila toh yarinyar nan nada tabin kwakwalwa basu gane ba. "Meya sameki kike ihu haka gaba daya kin rikitamu?" Maman ta sake fada a tausashe tana kallon Umaimah dake jera Ajiyar zuciya kamar zata shide, wannan tambaya da Mama tayi mata ta sake fama mata ciwon aiko ta fashe da gunjin kuka tana riqe kai Mama dai se ido dan abin ya fara tsoratata. Seda tayi me isarta ta tsagaita tace "Nabila ce, wai..wai tana son Khalil" "Waye Khalil?" Maman ta sake tambayarta, seda taja numfashi ta dan ja baya daga gaban maman kafin tace "Wani ne, a makaranta ta taba ganinsa, shine yanzu suka hadu a Lagos kuma wai tana son sa auransa zatayi" ta qarasa tana fashewa da sabon kuka kalmar auran data fada tana mata ciwo. Mama da taji bacin rai ya mata dirar mikiya saboda ko kusa kalaman ta babu na hankali a ciki bata ma fahimci me take nufi ba, daga Nabila taga wani tana so zata aure shi se ya zama dalilin da zata ri ga wa mutane irin wannan Haukan a gida, cikin kaushin murya tace mata "Kinsan ni ba sa'ar wasan ki bace da zaki zauna kina gaya mun shirme, zaki fada mun dalilin kukan ko sena saba miki yanzun nan" "Wallahi Mama gaskiya na fada miki, wai son sa take yi ni Kuma bana so, akan me duk mazan duniya zata ce shi take so? Wallahi baze aure ta ba sedai ta tafi can ta samu wani" "Saboda uwarsa ce ke ko ubansa? Meye ma hadinki dashi da shiga sharafin rayuwarsa?" Mamanta sake fada cikin bacin rai kamar zata kai mata duka, se Umaimah ta miqe tana ci gaba da kukan tace "Bani da hadi dashi amma wallahi baze aureta ba sedai ya tafi can ya nemi wata matar badai ita ba, haka kawai ya aure ta na ringa ganin shine mijinta ai bazey...." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta yasa tayi shiru, tsawa ta daka mata tana nuna mata hanya tace "fita daga nan fitinanniyar yarinya da bata qaunar a zauna lafiya. Tsabar neman masifa ina ruwanki da sabgar ta? Kiji da kanki mana ko kuwa baqin ciki kike mata ta samu miji ke kina zaune kin rasa? To kici gaba karki fasa daga mana hankali a gidan nan dan ubanki idan kika kaini bango ni kaina bansan abinda zan miki ba Umaimah". Fada sosai Mama ta ringayi dan abin ba qaramin qona mata rai yayi ba, tama kasa gane kan dalilin wannan rashin hankali amma shikenna zatayi maganinta ne. Umaimah kuwa har dare tana ta ciwon rai, idan abin ya ciwo ta ta zura kanta cikin pillow ta fasa ihu dan Mama ta ce wallahi ta sake jin muryarta seta mata dukan mutuwa a gidan, tasan kuma zata aikata dan haka ta qule a daki tasha kukanta ita kadai, tambayar da takeyiwa kanta data rasa amsa shine wai duk wannan abin da takeyi a wanne dalili me? Meye hadinta da Khalil din da har taje jin wannan zazzafan Kishin akansa? Ko kuwa kishin nata ya burunqasa ne ya zama akan kowa da komai ma yinsa take? Toh ita dai koma yaya ne tana kishin *Khalil*, kishi me tsanani da bata zaton ta taba yiwa wata halitta shi. Washe garin ranar data fita aiki ta nemi qaramar waya ta dora layinta akai tunda waccen ta tashi daga aiki. Messages din Nabila ne suka ringa shigowa na martani akan abinda Umaiman ta fada mata, ta kuma sake jaddada mata se tayi soyayya da Khalil, "Idan ma sonsa kike sedai kuwa Son nan ya kashe ki dan wannan karon yafi qarfin ki, kina ji kina gani zamuyi aure sedai ki hadiyi zuciya ta mutu shashasha mara hankali" Message din qarshe kenan na Nabila daya shigo wayar Yanda kasan zatayi aman wuta saboda bacin rai haka ta shiga neman Layin Nabilan amma yaqi shiga alamar tayi blocking di ta kenan, kiran ta mayar kan Fauziyya ita din ma yaqi shiga, "bakin su daya kenan?" Ta ayyana a zuciyarta. Kwafa tayi idanunta suka kada sukayi jajir ta shiga turawa da Nabilan saqo kamar haka "Ko a mafarki kika ganki tare da Khalil ki tabbatar da kin fara irga kwanakin da suka rage miki a duniya dan ni Umaimah se nayi Ajalinki, idan kuma kina ganin wasa ne kuma kin cika mara kunya ki bari mu hadu" ta tura mata. Ajiye wayar tayi ta hade hannu biyu tareda dora qafa daya kan daya tana girgizawa, jiran Amsar Nabila take amma har aka kwashe kusan awa biyu bata yo reply ba, excuse ta dauka akan bata da lafiya ta tattara kayan ta ta tafi gida lokacin tashin su beyi ba dan ba zata iya ci gaba da zama a gurin. Seda ta kwashe sati tana jinyar zuciyarta akan kishin wanda bema san tana yi ba, Alwashi kala kala taci akan haduwarsu da Nabilan duk randa Allah yasa sukayi ido hudu zasu kwashi yan Kallo kuwa. QARSHEN QAWANCEN UMAIMAH DA NABILA. Watan kusan biyu kenan da faruwar wancan Al'amarin, zuciyarta tayi sanyi hankalin ta ya dawo jikinta har tana jin haushin kanta akan abinda ta aikata. Ita da kanta ta yarda da shirmen da tayi be kamata ba kuma akan wanda be ma san tana yi ba ita a yanzu bata tsammanin ma idan ta ganshi zata gane fuskarsa sabon tsahon lokacin data dauka bata ganshi ba. Tana so ta nemi Nabila ta bata haquri amma wata zuciyar da take saka ta aikata mugun abun ta hanata, gaya mata take ai ba laifi tayi ba kuma ita Nabilan ita ya kamata ta fara neman ta ta bata haquri sannan su shirya da wannan ta shashantar da maganar ta fita akanta. Tayi sabon saurayi a gurin aikinsu, Balarabe Isha, yana aiki a ma'aikatar da take bautar qasa bangaren Finance. Ba yaro bane a qalla zeyi shekara Arba'in sun kuma samu kyakykyawar Fahimta dashi dan har yana zuwa gida hira gurinta sun ma fara shirye shiryen saka manya a maganar. A yanda ya gaya mata Matarsa ce ta rasu yana kuma da yara hudu, dukda yace matar ta rasu amma hakan be hana baqin kishinta motsawa akan Matar da bata ma duniyar gaba daya ba, Sumayya sunanta wannan dalili yasa ta debi karan tsana ta dora akan duk wata me suna Sumayyan. Ko a hanya aka kira sunan in sha Allahu seta bankawa me sunan Harara tayi tsaki. Sauqin da aka samu Balarabe Isah na matuqar qoqari gurin kiyaye duk abinda ze motsa mata da Kishin nata dan yana matuqar sonta da gaske. Ranar wata Juma'a bayan sun taso daga aiki ya dakkota ze kawo ta gida, suna tafe suna hirar su gwanin dadi dan sosai Balarabe yake ririta Umaimah duk wani abu da ze sosa ranta baya yinsa. Suna tafe sun shiga layinsu kenan aka kirashi a waya da yake wayar na ajiye a tsakiyarsu ne karaf Umaimah taga sunan me kiran 'Wife'. Wani qululu daya taso mata ta hadiye ta kalli Balarabe da yayi tsilli tsilli da ido kamar wanda aka qure tace "ka daga mana ba kiranka ake ba" ta fada a dake, sosai take kokawa da abinda yake taso mata, so take ta koyi haquri da dauke kan da kullum ake ce mata bata dashi. Shiru yayi yana aikin rarraba ido ga wayar se qara take dan kiran na katsea wani ya sake shigowa, Tsawa da daka masa akan ya dauki wayar kamar wani danta dan ta kasa riqe bacin ranta, kai Dole ma taci kutumar uban mutumin nan dan ya goge mata hadda iya hadda. Ya yaudareta yace mata matarsa ta mutu  nufinsa se ta aureshi sannan zataje ta tarar da wata kome? Ai kuwa da a ranar daga shi har matar sedai suyi kwanan barzahu sedai duk yanda zaayi da ita ayi. Daga inda take tana iya jiyo muryar matar se shagwaba take masa akan tana jiransa fa yazo ya kaita gidan biki ana rana bazata iya fita ta hau Napep ba, Allah sarki Balarabe zufa yake sharewa kota ina yanda kasan wanda ya zauna akan kunama, magana yake so yayi amma ya kasa se kawai ya kashe wayar ya ajiye yana kallon Umaimah data tsura masa ido kamar me nazarin ta inda zata shaqeshi ta aika shi lahira. "Kace mun ta mutu, yanzu daga lahirar ta kiraka kenan?" Ta tambaye shi ido ta akan sa, Balarabe ya hadiye miyau qut saboda yanda tayi bala'in yi masa kwarjini nan ya shiga laluban kalaman da ze kare kansa dasu, dakyar ya iya cewa "Dagaske nake Matata Sumayya ta rasu shekaru uku kenan yanzu, bayan rasuwarta da shekara daya akayi mun madadi da qanwarta da suke uba daya Surayya dukda bana sonta amma haka na karba ko dan saboda Yarana da banida me riqemun su saboda Mahaifiyata ta tsufa bazata iya kula dasu ba, amma ki yarda dani badan ina sonta na aure ba, nayi ne kawai saboda samun mafita, kuma yanzu a shirye nake dana rabu da ita saboda ke" "Sedai ka saketa ka auri uwarka Balarabe, kuma yanda ka cuceni ka bata mun lokaci ka yaudareni kaima Allah yasa ayiwa yarka, wallahi ko kallon sani ka sakeyi mun se na maka rashin mutunchin da bazaka manta dani ba" ta fada cikin Fushi kafin ta bude motar ta fice, badan tana tsoron karta tijara shi a wajen a jiyota daga cikin gida ranta ya baci ba da wallahi seta masa rashin mutunchin da har ya mutu baze manta da ita ba. Haka ta shige gida sukuku babu wanda yasan abi da ya faru tasha kukanta a daki washe gari tayi qaryar bata da lafiya dan haka bataje aiki ba. Kiran gaggawa ta samu daga makaranta akan wasu takaddu basu cika ba na credentials dinta, dole ranar litinin ta debi original din duk wata takadda data san zaa buqata a makaranta ta tafi. Seda ta gama duk abinda zatayi a Academic Office har zata fice daga makarantar tace bari ta leqa Office din Sir Nasir su gaisa saboda anyi zaman mutunchi dashi. Tun daga bakin qofa tutarensa yayi mata sallama, daga ciki take jiyo muryarsa yanayiwa Nasir din bayani akan abinda bata san ko meye ba. "Kinji Husky voice dinsa Umaimah" Kalaman Nabila suka dawo mata, lokaci daya taji ranta ya baci kamar ta juya se kuma ta tura qofar office din nan rai a hade kamar wadda ta kawo saqon mutuwa. Nasir da Khalil suka juyo a tare suka zuba mata ido, Nasir ya saki murmushi yace "wata sabon gani, Hajiya Umaimah ce yau a office din mu bismillah shigo mana". Qarasa shiga ciki tayi ba tareda ta kalle su ba tayi musu kudin goro ta gaishe su, haka kawai take jin haushin Khalil din da bema san abinda take ba se faman doka mata murmushi yakeyi. "Yar unguwarmu kwana da yawa?" Khalil ya fada yana kallonta, kamar kuwa tana jira ta doka masa uwar Harara harda murguda baki, gani take kamar ma suna tare da Nabilan, qila ma soyya tayi nisa har suna shirin aure. Jan ta Nasir ya ringayi da hira amma ina hankalinta na kan Khalil daya duqar dakai yana dannan waya yana murmushi, Albishir ne akayi masa, ya samu aiki da wani babban construction company a Lagos interview din yaje kwanaki har Nabila ta ganshi tareda wani abokinsa Taufeeq Babatunde wanda shi yayi masa hanyar aikin da yake Babansa babban mutum ne a Lagos din. Yanzu yana gaya masa ne cewar comapany sun bude branch a nan Kano dan haka anan ze zauna. Ita kuwa Umaimah gani takeyi ai da Yammata yake chatting zuciya tayo sama fuu ta fizgi jakarta murya a cunkushe tayiwa Sir Nasir sallama ta fice yana tsayar da ita amma taqi tsayawa. Dagowa Khalil yayi jin an buga qofa da qarfi yace "lafiya? Me aka mata?" "Kai zan tambaya dan tunda ta shigo kai naga tana harara da alama ka mata wani abun ne" Nasir ya fada yana dariya. "Ni a ina zan ganta na wanta wani abu?" Ya fada yana daga hannu sama, Nasir daya miqe ya fara tattara takaddu yace "Na sanin muku ba naji kace yar unguwarku ba waya sani ko tuni kun jone babu labari" "Can da dadewa ne naganta a gidan mu an aiketa kai naman suna, ashe sister matar Habib Neighbor din mu ce, shine muka gaisa daga nan sau daya na sake ganinta tare da wadannan qawayen nata masu kalar rashin ji kusan six months kenan fa se yau na sake ganin ta ma ni" Khalil din ya fada cikin son kare kanshi. "Nifa bance wani abu ba kake koro mun bayani kamar wani Lawyer, muje dan Allah ka sauke ni gareji na dauki motata nasan yanzu an gama gyaran, qarfe hudu zan kai Amir dressing Asibiti" Nasir ya fada bayan daya dauki abubuwan da ze buqata ya nufi qofa. Miqewa Khalil yayi shima yabi bayan sa yana cewa "Dressing name? Meya samu Amir din?" "Wallahi qonewa yayi da ruwan tea a qafa amma da sauqi inagadaga yau ma mun gama zuwa" Nasir ya bashi amsa daidai sanda suka isa gaban Motar Khalil din daya siya kwanannan Toyota Yaris Fara me kyau da ita. Suna tafe yana masa qorafin rashin gaya masa qonewar Amir din suka isa get, rana ta take dan haka ana wahalar abin hawa. Daga can gefe suka hango Umaimah a rabe fuskar nan kamar hadiri kai kace zata fasa kuka da alama tasha tsayuwa har ta gaji dan a jingine take da bango. "Ga mutuniyarka can fa inaga ta rasa ride ne" Khalil ya fada yana kallo ta, se Nasir ya waiwaya shima ya kalleta yace "Kai dai duk inda yarinyar nan take se idon ka ya hasko maka ita, toh ka mata lift ka kaita gida mana tunda hanyar ku daya" "Bafa hanyar mu daya ba na gaya maka gidan sister tane a layin mu kai ka fiya matsala wallahi" "Toh kaga daga nan seka gano Asalin gidan su mana ko ni me nace ne" Nasir ya fada yana qunshe dariya. Qarasawa kusa da inda take ya danna mata horn. Hararar da tayiwa motar idan da ace mutum tayiwa se ya kusa faduwa qila, ta qara tunzura baki gaba, ita ba akan titi take ba bare ace ta tare hanya amma koma waye ya kuskura ya qara mata horn seya gane kurensa. Nasir ne ya sauje glass din bangarensa ya kalleta da murmushi yace "kina tsaye a rana abin hawa yayi wahala koh? Bismillah muje mu rage miki hanya". Badan gajiya da ranar da ake kwallawa ba da babu abinda ze sa ta hau motar mutumin nan, tana qunquni haka ta bude baya ta shiga, sanyin Ac da qamshin turarensa suka sakata sakin ajiyar zuciyar dole seta qara bajewa tana jan iska a hankali, ta centre mirrow yake kallo ta ta sani amma tayi kamar bata san yanayi ba a ranta cewa take " shi kuma ciwon kallon mata ne dashi qilan. A hanya Nasir ya sauka suka rabu akan da daddare Khalil zeje gida ya duba Amir din, Nasir ne ya bude mata qofa yace ta koma gaba, ba tayi niyya ba da taso ta mayar dashi Driver ne ya jata ya kaita gida amma ta daure ta sakko ta koma gaban. Seda ya tsaya a wani guri ya siyo Youghort na L and Z manya guda uku masu Azabar sanyi da ruwan gora kafin suka ci gaba da tafiya. Youghort din ya miqa mata guda daya da ruwa ya ajiye ragowar "Ban iya cin abinci a waje ba indai ba girkin Hajiyata ba sedai kona matata idan nayi aure shiyasa kullum wuni nake ina shan youghort idan bana gida" Khalil ya fada da son kawar da shirun da sukayi. Seta tabe baki, haka kawai ta samu kanta da cewa "Amma ka iya zuwa Restaurant a Lagos kaci abinci har ka yi zance da yammata". Kallon ta yayi cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa yace "Waya gaya miki naje Lagos?" "Aljanuna ne suka gaya mun" ta bashi amsa kai tsaye, se ya saki murmushu, tana da tsiwa, kamar a jininta abin yaje hakan kuma kyau yake qara mata daidai sanda suka zo kwanar gidansu bisa kwatancen data bashi tace ya tsaya a nan. "Har munzo ne?" Ya tambayeta yana gyara parking. Kayanta ta shiga tattarawa tana cewa "Aa ka sauke ni a nan na qarasa cikin layi, bana so aga ka sauke ni a mota" "Saboda me?" "Saboda zaayi mun fada ace waye kai?" Ta bashi amsa a qage, dan bata so wani ya ganta, jiya jiya Mama ta gama yi mata fada akan shige shigen motocin samari kullum da wanda ze sauketa a gida da sunan abokanan aikinta hakanba mutunchi bane yanzu se mutane su chanza mata manufa dukda ita ba wani abu ta aikata ba. "Mu qarasa, idan kina gudun fada ne zan shiga har cikin gidan na gayawa Mamanku ni na kawo ki bazata ce komai ba" Khalil ya fada yana taka motar ya shiga cikin layin, "Se kace tasan ka, nidai ka koma baya ka sauke ni kawai dan Allah hakanma nagode" ta fada kamar zatayi kuka, be kulata ba yaci gaba da tafiya bata da zabi ganin yana neman wuce gidan ta tsayar dashi, a gurguje tayi masa sallama ta fice a motar, Layin kamar anyi shara babu kowa saboda uwar ranar data kwalle ta samu ta shige gida, ita kanta tana jin yanda gaba daya jikinta ya game da qamshin turarensa wanda ya kama motar. Tsakar gidan ma babu kowa se Anty dake girki a kitchen ta rabe daga qofar gurin saboda rana. "Allah shi qara, baku iyayi masu tausayin miji ba kuka jajibowa kanku girkin ice ai gashinan kuna ji a jikinku" Umaimah ta fada a zuciya, a fili kuwa murmushin qeta tayiwa Antyn harda gaisheta da yi mata sannu da gida ta wuce dakinsu saboda ta hango qofar Mama a rufe qila bata nan. "Kai Yaya Umaimah turarenki dadi, zanzo dan Allah ki sammun, Salman qaninta ya fada daidai sanda tazo giftashi, tana qoqarin bashi amsa Mama ta shigo gidan da sallama idonta akan Umaimah data duburburce, Addu'arta Allah yasa Maman bata ga shigowarta ba. *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 6 Kallo daya Mama ta mata ta girgiza kai kawai ta shige ciki dan akan idonta Umaiman ta fito daga motar Khalil tana tsaye a soron gidan Maman Nana dan ta aiki Nanan tun tuni taji shiru ga babu yaron da zata tura shine tabi sahu da kanta. Ita dai fatanta kullum Allah ya shiryi Umaimah yasa ta ringa jin magana, bata zarginta da aikata wani abu amma wannan shegen rawar kan nata da kwashe kwashen ya isa ya janyo mata magana abinda batayi bama ace tayi. Umaimah ko dakin su ta shige tunda dai batace komai ba idan ma ta gantan ai shikenan, ruwa ta fara watsawa saboda mugun zafin da ake ta saka doguwar riga me siririn hannu da hula ta nufi kitchen inda Anty take girki, yau Alhamis tasan dole a samu dan farfesun wani abun saboda kusan kowa na gidan yana azumi, litinin da Alhamis din kuwa se Abba ya siyo abinda zaayi romo aci da buda baki duk satin Allah. Tundaga tsakar gidan kuwa ta fara jiyo qamshin dahuwar nama, ta hadiyi yawu tayi murmushi kafin ta qarasa daga qofar kitchen din ta kalli Anty da ido yayi ficifici saboda hayaqi ga zafin wuta gana gari tace "Sannu Anty, an abinci ya sauka ne a sammin yunwa nake ji" Murmushi Antyn ta mayar mata, harga Allah har cikin zuciyarta tana qaunar Umaimah amma a duk yaran gidan babu wanda ya rainata yake mata rashin kunya da diban Albarka irinta duk cikin taya mahaifiyarta kishi wadda ita sam ko a jikinta, tunda aka aurota bazata iya cewa yau ga ranar da Mama Malika tayi mata wani abu da sunan Kishi ba sedai sabani irin wanda kowanne yan Adam suke samu in dai an zauna amma kam maceceme tsananin kirki data kama girmanta haka tsayyaya ce aka yaranta kaf dinsu girmama Antyn suke hatta da Aminu da zasuyi Sa'anni idanya zo gidan yanda ze durqusa ya gaida Mahaifiyarsa haka ze durqusa mata wannan me ido atsakiyar kan ce se Addu'a kuma ita sam halin Umaiman ma ba damu ta yake ba. Taf ta cika mata bowl da farfesun Naman rago daya ji kayan qamshi yawun Umaimah har tsinkewa yake, "Ki duba fridge a dakina ki debi Zobo, akwai biredi akan Dining se ki hada tunda shinkafar bata sauka ba" Antyn ta sake fada tana kallonta. "Nagode" ta fada a fili ta juyaa ranta kuwa cewa tayi "Dole in sha ai tunda da kudin ubanmu kike hada sana'ar dama base kin gaya munba" Ta wuce dakinnata ta bid Frizer da take zuba zobon siyarwa a jarkoki suke sunyi sanyi sosai dan wasu har sunfara qanqara, yaron daya ke daukar mata ne ma be qaraso ba da tuni yanzu qila an gama wawason sa saboda yanda takeyin sa da kyau ga dadi sosai ake rububinsa. Daki Umaimah ta baje, tana zama aka kawo wuta tayi Hamdala ta kunna Fankar sama data qasa ta shiga dangwalar Romon tana ci da biredi gefe ga L and Z dinta ta cika kofi tana kurba duniya sabuwa ga iskar fanka ta ko ina, bata ji shigowar Mama ba se maganar ta taji a kanta tana cewa "Kwarai da gaske, baki dafa ba amma kece farkon ci koh? Toh idan kin gama kije ki gyaramun daki" Maman ta fada tana qare mata kallo. Ajiyar zuciya tasaki dan a zatonta fada maman zata mata tace toh, seda ta qoshi ta kora da zobonta me sanyi ta huta kafin ta tafi dakin maman. A palour ta tarar da ita da wata baquwa sun baje kuloli masu kyau suna dubawa da alama talla ta kawo mata dan se koda mata su take, gaishe da baquwar tayi ta shige ciki ta fara gyarowa, tana jiyo baquwar tana cewa Maman "Hajiya na zata saiti bibbiyu zaki dauka tunda yan matan naki biyu ne ko" "Aa yanzu dai dayan zan dauka ita wannan da saura idan lokaci yayi a siya" Maman ta bata amsa "Ai kuwa da kin siya kin huta dan kinsan kullum qara kudi kayan suke abinda ka siya dubu daya yau gobe idan kika koma se kiji daya da dari biyar koma dubu biyu, wannan hauhawar fara shi dai Allah ya mana maganin sa" matar ta sake fada. Murmushi Mama tayi tace "Yanzu dai bari na dauki na dayar da nayi niyya ita ce me garanti, wannan kinsan sau nawa ina mata tarin kayan kitchen? Da takaici ya isheni fitar dasu nayi na rabawa yan uwanta wasu na biki dasu duk randa Allah yasa ta tsayar da hankalinta ta fitar da Miji a kaita da abinda ya sawwaqa" "Allah dai ya rufa asiri, in sha Allahu ma tareda yar uwarta zaki saka su a Lalle". Baki Umaimah ta tunzura gaba, wayasani ma ko irin wadannan maganganun da maman take a kanta ne suka hana mijin tsayuwa ita kullum me laifi ce a idon Maman, Allah dai ya yanke mata ta tafi itama kowa ya huta a sannan zaa gane amfaninta ai. Haka ta gyaro dakin ta wanke Bandaki tsaf lokacin matar sun gama ta wuce se Maman ita kadai tana waya da wanda yake kawo mata Manja daga Kudu da yake tana siyar da Manja da Mangyada, hannun kujera ta nema ta zauna tana jiranta harta gama. "Ya akayi?" maman ta tambayeta, "Na gama gyara ciki saura nan" "Toh bismillah mana ko na hana kine" Maman ta sake fada, seta miqe ta shiga tattare kwalayen tace "Ina zaa ajiye wadannan kayan toh" "Saka su can dakin" Maman ta nuna mata dayan dakinta data mayar dashi na aje shirgi Wanda da Su Umaimah suke ciki kafin Yayyensu suyi aure su koma dakin da suka bari na tsakar gidan. Bude dakin tayi ta shigar dasu, "Mama duk kayan can Yaya Nuratu zaa jibgawa su? Toh Allah yasa dai ta samu gidan da ze dauka koda yake ma gidan quaters ne ai kin ma san yanda suke sedai idan an a tafi dasu a dawo da wasu a san dai kin mata kaya da yawa kawai" Umaiman ta fada tana kade kujeru, da kallo kawai Maman take binta, a ranta tana nema mata shiriya daga gurin Allah dan lamarin nata kullum qara gaba yake. Bata damu da shirun da Maman tayi ba taci gaba da cewa "Qilama ni da bakya ta tawa na fita samun babban gida, kinga lokacin ai a tasheki a tsaye ki rasa yanda zakiyi" "Allah baze hanani yanda zanyi ba dan ubanki keda bakinki sam besan abinda ze fada ba, fita ki bani guri na fasa gyaran daman idan baki yi niyyar abu ba se kin san yanda kika jangwalo aka ce ki barshi" Maman ta fada kamar zata kai mata duka, Dariya ta sheqe da ita ta shiga cewa "Haba Hajiyar mu easy mana, nifa wasa nake miki. Yo ko yanzu aka ce a fito Hajiya ai a shirye kike Allah dai ya bar manake Hajjaju". Ganin da Mama tayi tana neman mayar da ita wata abin tsokana yasa ita ta bar mata dakin ta koma tsakar gida inda inuwa ta dan fara sauka suka shiga hira da Anty Saratu. Umaimah ko tas ta gyara dakin ta goge ta saka qamshi, tada zafin nama idan ta saka kanta ta iya aiki sosai dan wannan horon Mama ne duk yaranta seda ta tabbatar da ta horasu yanda duk inda sukaje bazata ji kunya ba, daman Umaimace me son jiki a ciki, amma idan ta tashi yin aikin kuma zatayi shi dakyau. Dakinsu ta koma ta kwanta kafin rana tayi tana so taje kitso, tana hawa kan gadon wayarta dake jikin chaji ta fara qara, kamar bazata daga ba se kuma ta janyo ta ta amsa kiran ba tareda tayi magana ba. "Amincin Allah ya tabbata a gareki" Aka fada da muryar da tanaji ta gane waye, murmushi ne ya kufce mata, "Tareda kai, ina fatan kaje gida lafiya?" Ta bashi amsa. "Ban sani ba, da kin so kiji aike zaki kirani ba se yanzu dana kira zaki tambayeni ba" Khalil ya fada daga dayan bangaren, "Thats remind me, a ina ka samu number na?" Umaimah ta fada tana gyara kwanciyarta da kyau akan Gadon, "Baqauya kawai, wayace miki har yanzu ana tambayar ina aka samu number budurwa ne" "Ni ba baqauyiya bace" ta fada a sakalce tana tura baki, akan me zece mata baqauya, ita da take yar tsakiyar birni bama shi dan bayan badala ba. "Toh yi haquri yar birni" ya fada yana dariyar yanda tayi maganar kafin yaci gaba da cewa, "Dadin tuqina ya saka kin manta da folder credentials dinki, kinga da a commercial car ne da yanzu se ki tafi gidan redio cigiyan wanda ya tsinta". Dafa baki Umaimah tayi tana tashi zaune tace "Subhanallahi, wallahi na manta shaf kuma ban lura ba. Dase nazo daukar wani abun sannan ne zan ga babu su" "Daman kinji tuqin babban Driver ina zaki tuna" ya sake fada cikin sigar tsokana, seta mayar masa da cewar "Babu wani nan, bayan nama fika iya tuqin kanayi a hankali kamar me tsoron hanya" "Oh haka kike ce? Toh next time idan mun hadu za'a gwada se muga wanda yafi wani iyawa" "Allah ya kaimu zan kuwa baka mamaki" ta fada cikin tabbatarwa bayan a zahiri inda ake takawa ma mota tayi tafiya bata sani ba, ba kuma dan babu inda zata koya ba Aa koda basu da Mota a gida banda ta Abbansu amma Yayyenta mata masu aure kowacce nada motar hawa, ita dan karambanin nan ma yasa ta hau bata taba ba tafi gane ta kame a kujera a jata. Hira suka danyi kafin ya mata sallama da cewar idan ya samu dama zuwa dare ze kawo mata, idan kuma bezo yau ba se dai zuwa Litinin dan washe garin juma'a zeyi tafiya zuwa Dutse akwai aikin da sujeyi acan kuma se ranar Lahadi ze dawo. Wannan waya da sukayi ba qaramin nishadi ta saka Umaimah ba, ta ringa walwala, su kansu mutanen gidan seda suka ringa tambayarta Albishir din me ta samu da take farin ciki haka sedai tayi murmushi tace babu komai. Be kawo mata a daren ba, ai kuwa baqin ciki ya mata dirar mikiya ya shafe walwalar data wuni a ciki dan tun magriba ta fesa wanka dukda batayi kwalliya ba amma ta saka kaya da suka qara haska tah tayi fes, shiru har akayi isha babu shi babu kiran wayarsa tun tana zuba ido qarshe se jiyo radion da Abba ya kunna tayi a tsakar gida ana wani shirin siyasa da yake ji qarfe Goman dare. Ita kadai ta ringa zuga tsaki tana juyi a gado, kamar ta kirashi amma in ta tuna daman ya gaya mata ba lallai yazo a yau din ba se ta Kanne, yanzu har se ranar litinin zata sake ganinsa kenan? Wannan abu ya mata ciwo da yawa. Haka ta cinye weekend gashi ko a waya be kirata ba, sundai yi magana ta whatsapp ta saka status ya duba suka gaisa daga nan be sake ce mata komai ba. Ranar Litinin bayan magriba suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shiga "Wai ana sallama da Umaimah a qofar gida" yaron ya fada, se tayi tsam daga abinda takeyi ta kalle shi. Wane dan rainin hankalin ne ze aiko sallama da ita? Tasan dai duk masu zuwa gunta se sun kirata a waya shi wane isashshen ne haka da ze aiko ba tareda tasan da zuwan sa ba. "Kaje kace ba ta nan" ta fada se Mama tayi saurin dakatar dashi tana hararta tace "Je ka tambayo wane ne kace tana zuwa" "Mama fa ni bamuyi da kowa ze zo gurina ba kawai se a aiko kice ace ina zuwa indai mutumin kirki ne ai seya fara sanar dani kafin yazo" ta fada kamar zatayi kuka dan tasan tabbas baze wuce irin yan yawar samarin nan masu bi gida gida suna sallama da yammata ba. Banza Mama ta mata taci gaba da lazumin da takeyi, sega sallamar yaron ya sake dawo yace "wai Khalil ne, kuma yace sauri yake yi kizo ki karba saqon". "Khalil?" Ta fada a fili tana kallon yaron kamar shi ze bata amsa kafin ta shiga qarewa kanta kallon, Zani ne da T shirt a jikinta tunda tayi wanka da La'asar ta sakasu se qaurin manja takeyi saboda suyar wainar fulawa take a lokacin. Miqewa tayi ta nufi daki, Mama da tunda akace Khalil ta zuba mata ido tana so ta tuno ina ta taba jin Umaimah ta ambaci sunan tana tunanin Umaiman ta fito ta chanza kayan jikinta zuwa baqar doguqar riga ta yafa mayafinta, "Mama bari na karbo, credentials dina na manta ranar a makaranta shine ya kawo min" ta fice da sauri. Su biyu ta gani tsaye jikin mota sunsha kwalliya kamar masu zuwa gurin daurin aure, "Allah yaso ki kin fito, yanzu na ke shirin neman wani yaron na bashi ya kai miki se fa dana ce wancan ya gaya miki sauri nakeyi" Ya fada bayan data gaishe su, harar wasa tayi masa kafin tace "Sauri zuwa ina? Kun wani sha shadda kamar masu zuwa tambayar aure" "Kin canka daidai tambayar aurana zamu je, saurin da nakeyi kenan saboda baban yari yar qarfe 8 yace muzo kinga be kamata tun yanzu na fara sabawa sirikina lokaci ba" Khalil ya fada yana miqa mata Folder da kuma wata farar leda me dan girma. Idan tace tayi suman wucin gadi batayi qarya ba dan daga can sama ta ringa jin muryarsa yana ce mata "Ki karba mana, kin tsaya kina kallona karki sa na rage kyau kafin naje gurin Amaryata". 'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' tayi nasarar furtawa a fili kafin ta tafi tamkar zata kifa yayi saurin tarota, a rikice ya shiga jijjigata yana cewa " Umaimah Umaimah ke Umaimah lafiyar ki kuwa? Mansur shiga gidan na kayi sallama dan Allah muji ko daman bata da lafiya" ya fada ganin tana lumshe ido kamar me shirin tafiya dogon suma. Abokinsa Mansur daya yi mutuwar tsaye ya zura da gudu zuwa cikin gidab su Umaimah se ganin mutum kawai sukayi, a taqaice ya kalli Nuratu da Salima babbar Yar Anty Saratu yace "kuzo dan Allah" kafin ya juya ya fice,ai gaba daya suka rufa masa baya harda Anty da Maman tunda basu san me ya faru ba. Hango Umaimah dake riqe a hannun Khalil ya qara daga musu hankali suka isa gurin da sauri, Anty ce ta karbeta Nuratu ta taimaka gurin qara kamota suka riqeta dakyau suna tambayar sa meya faru "Wallahi Hajiya bamu sani ba, lafiya lau ta fito na miqo mata kayan nan(ya nuna kayan da suka watse a qasa tun daya taro ta kafin yaci gaba da cewa) kawai naga kamar hankalinta baya kaina na sake mata magana se ji kawai mukayi tayi salati ta tafi zata fadi na tareta amma wallahi babu abinda mukayi mata, zaki iya tambayar samarin can dan tunda muka zo suna zaune a gurin" ya qarasa yana nuna mata majalisar su Malam Sadi, kamar kuwa yana jira Malam Sadin ya taso yana cewa "Ashsha Ashsha mutanenne suka motsa mata ko, daga jin yanda taja dogon salatin nan ina ga gamo tayi ku kamata muje cikin gida" yayi gaba ze shiga gidan Mama data kasa magana ta tareshi da cewa "Jeka abinka, idan muna da buqatar ka zaa kira ka, Samari mun gode ko ku gaida gida" ta qarasa tana kallonsu Khalil da gaba daya kana kallonsa kasan hankalinsa a tashe yake kafin tabi bayan su Anty da suka shige gida da Umaimah. Akan babbar tabarmar dake tsakat gidan suka kwantar da ita Nuratu ta shiga daki ta dakko abin auna jini da bugub zuciya ta shiga dubata, ita kuwa Umaimah Abinda take ji yau ya wuce ta dora hannu aka tayi ihu, kukan take amma na zuciya hawaye kadai ke kwaranya a idonta. "Mama kodai a kirawo Malam Sadin ne ni banga komai daya same ta ba qila abin bana Asibiti bane" Nuratu ta fada tana kallon Mama data zabga tagumi, se ta girgiza mata kai alamar Aa, kafin ta juya ga Umaimah dake Hawaye idonta a rufe ta kira sunan ta tace "Zo Umaimah, taso ki gaya mun meya same ki" Kamar jira takeyi kuwa ta tashi daga kwanciyar ta fada jikin Maman tareda fashewa da kukan da kana jinsa kasan tundaga qasan zuciyarta yake fitowa. "Qila gidan su Nabila zeje, dan daman jiya Rumah take cewa ta gansu a hanya sun shigo Kano ashe amma basu kulata ba, qila maganar auran nasu ta kankama da gaske kenan" ta sake rushewa da Kuka kamar Numfashinta ze dauke Bayanta Mama ta ringa bubbugawa kawai da sigar lallashi gaba daya ranta a jagule yake, dagaske akwai akwai Alamomin Aljanu tattare da Umaimah masu yawa haka wani sa'in tana nuna alamar me motsi a kwakwalwa ya kamata su dauki mataki dan da alama abin kullum gaba yake ba baya ba. A haka Abba ya shigo ya same su, Nuratu ce ta gaya masa iya abida suka sani da farko yayi kamar ya shareta dan yasan be wuce iskanci ta ne ya motsa ba amma kuma ganin irin kukanda take dole ta baka tausayi, anyi anyi tayi magana taqi, data bude baqi baqin cikin abun yake shaqeta ta kasa magana se sabon kuka ya kufce mata, sun yarda da zancen Malam Sadi na cewar Gamo tayi dan haka suka kwanta da qudurin da sassafe zasu kaita gidan wani babban Malami da Abban suke daukar karatu Asabar da Lahadi. A bangaren Khalil kuwa kai a kulle suka bar qofar gidan nasu, tsabar yanda ya rikice kasa tuqa motar yayi se Mansur ne ya karba. "Khalil, dama yarinyar nan nada matsalar Jinnu ne?" Mansur ya katse shirun da sukayi kowa na jimami a zuciyarsa, se Khalil yaja ajiyar zuciya kafin yace "Wallahi bansani ba. Gaba daya wannan itace haduwa ta da ita ta biyu da mukayi doguwar Magana ban san komai a kanta ba amma naji wannan mutum yana fada qilan ko tana dasu ne" "Tab ai kuwa da sake dan bazan baka shawarar ka kwasowa kanka shirgin Iska ba, mata masu lafiyar ma yaya aka qare da rigimar su bare kuma gyaran Malam. Tunda dai abu beyi nisa ba gaskiya Dude back out" Mansur ya sake fada daidai sanda yasha kwanar gidan su Budurwar sa, kwalliyar da sukayi zasuje duba Maman Budurwar ne da bata da lafiya. "Daman matsalar Aljanu tana hana a aure ne maimakon ma kace na nema mata magani, beside mun tabbatar da Aljanu takeyi ko kuma wani health issue ne na daban, kawai ka tayani Addu'ar Allah ya bata lafiya amma maganar na janye ma babu ita dan yanzu na fara Son Umaimah" "Allah dai ya biya mijin gyaran Malam, se ka koyi ruqiyya saboda tashin dare, dan wallahi Matar Iro Black har kan kwano take hawa, kota kwasa a guje tayi titi, seka shirya yar tsere a layi mutumina" Mansur ya sake fada. Banza Khalil ya masa har suka qarasa gidan, da farko ma cewa yayi baze shiga ba, seda Mansur din ya nuna bacin rai kafin suka shiga. Yana mata yaya jiki ya fito waje ya baro shi kiwa yana ta sake gwada kiran wayar Umaimah da tun dazu ya jita a kashe abinda ma ya saka yayi aike kenan amma har sannan a kashe. Yana so yaji lafiyarta amma babu hali, haka ya koma gida bacci kansa rabi da rabi yayi, duk juyin da zeyi seta fado masa a rai Addu'arsa Allah ya bata lafiya zuwa safiya kafin ya wuce aiki zw biya ya ga yaya jikinnata. *KHALIL DA UMAIMAH SOYAYYA GAMON JINI* *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 7 Washe gari kuwa kamar yanda Abba ya fada qarfe 8 suka isa gidan Babban Malami Sheik Ali Musa. Sun tarar da Malam yana bada karatun safe, dan haka Abban ya zauna a gurin bayan anyiwa Su Umaimah da Mama iso cikin gidan Malam. Idan kaga yanda ta zabge a dare daya seka yi zaton ta dade tana jinya, akan fuskarta zaka karanci tarin damuwar da take ciki shiyasa koda Mama tace ta shirya zasu fitan batayi musu ba, bazasu fahimceta ba dan haka idan anje gurin suka fada musu bata da wasu Aljanu sa qyaleta ta sarara. Se gurin qarfe tara Malam ya samu shigowa, a sitting room dinsa suka zauna bayan sun sake gaisawa yana kallon Umaimah data jingina da bango ta tafi duniyar tunani yacewa Abba "Lafiya dai Alhaji Sabo naganku da sassafe haka?" "Eh to lafiya ba lafiya ba Akaramakallahu" Abban ya fada kafin ya gyara zaman sa a taqaice ya zayyanowa Malam Ali duk abinda yake faruwa da Umaiman, ya rufe da cewa "Jiya haka nan ta yanke jiki ta fadi shine har yanzu ta ke aikin koke koke babu magana kuma. Shiyasa nace gara muzo tun kafin abu yayi tsamarin da magance shi zeyi wahala". Malam Ali da tun fara maganar Abba yake nazarin Umaimah, shidai a iya sanin da ilimin da yake dashi ta bangaren abinda ya shafi aljanu bega wata alama a tattare da ita ba saboda koda ace Aljanun sun barta kafin su shigo gidan ne indai tana da shafar su seya gane amma dai bari ya sake bincikawa tunda shaqiyancin jinnu kullum qaruwa yake, wani lokacin idan sukayi wani alayen badan qarfin Ayar Allah ba bazasu gane ba. Wani turaren mai ya dauko ya miqawa Mama yace ta shafa mata a goshinta,kunne da kuma qofofin hanci yasan duk inda Aljani ya buya a jikinta idan turaren ya shiga jikinta seya fito, Umaimah kuwa haka ta tsaya Mama ta shafa mata turaren dukda rashin dadinsa amma yata iya, gara a wuce wannan maganar adena qaqabamata iskokai babu gaira babu dalili a barta taji da damuwarta. Karatu Malam din ya yafa yi mata, ya dauki tsahon lokaci yana yi amma ko gezau batayi ba harya gaji dan kansa ya dakata. Wayarsa ya dauka yayi kira, babu dadewa sega wata babbara Mace da zasuyi Sa'a da Maman ta shigo da kaskon wuta da garwashi, karba yayi zata tafi yace ta tsaya. Wani turaren hayaqi ya debo ya zuba ya bata ta ajiye a gaban Umaiman data zura musu ido tana kallon ikon Allah jin hayaqin yasa ta kauda kai, matar ta janyo fuskarta ta dawo da ita saitin Hayaqin, Umaimah ta fara zuga Atishawa saboda sam bata shiri da hayaqi, Mama dake gefe ji tayi kanta ya fara mata wani Yuummm dan daman tunda ta shafa mata maganin nan warinsa yake damunta, miqewa tayi tace "Alhaji bari naje daga waje hayaqin nan ya dameni" ta fice baranda inda iska take kadawa ai kuwa Umaimah bata san sanda ta fashe da dariya ba har seda Abba yai saurin matsawa dan abin yazo masa a bazata. A ranta tace "Allah shi qara, idanni baa tayar mun da Aljanu ba ai gashi nan zaa tsokalo miki naki" "Allah gafarta Malam sunzo ko?" abba ya fada yana raba ido dan fa shi yana da tsoron Aljanu daman, murmushi Malam yayi yace "Aa, shaqiyanci ne irin na dan yau baka gani ba da mahaifiyarta take saboda hayaqin ya koreta kar nata na gado su motsa" "Allah ya rufa asiri" Abba ya fada ya sake rabewa gefe. Har hayaqi yaci ya cinye dai babu Aljanun Umaimah babu dalilinsu, Matar ya umarta da ta sakeyi mata karatun, ta zauna a gabanta ta kama babban dan yatsan hannunta kafin ta fara mata karatu a kunne nan ma dai shiru ba labari. "Gaskiya Alhaji sabo duk wani ilimi da dabara da nake dashi akan al'amarin nan na gwada ka gani kuma, yarinyar nan bata da shafi ko rabar jinnu a tare da ita. Sedai idan wata matsala ta daban ce take damunta da tayi kamanceceniya da matsalar Iska" Malam ya fada yana duban Abba, shima ya gamsu da hakan dan haka ya gyara zama yana cewa "Toh Allah gafarta malam, a yanda mahaifiyarta take fada abin nata yawanci yana tashi ne dalilin Kishi, tana da tsananin Kishi kaga karo uku kenan ana fasa auranta kuma duk ita take jawowa da baqin HALIN KISHIN ta, shin ko akwai wasu Aljanu da suke saka mutum ya zama me tsananin Kishi haka??" "Murmushi Malam yayi kafin yace " Shi Kishi halittace Alhaji Sabo kuma ko wanne dan Adam yana dashi sedai na wani yafi na wani zafi, ko kuma wani yafi wani sanin yanda ze sarrafa kishin nasa. A yanayinta tana da zafin zuciya da saurin fushi, kuma kaga su wadannan siffofine da basu da kyau, sam fushi bashi da kyau. A duk sanda mutum yayi fushi, idan ba anyi dace ba yana iya aikata abinda daga baya zezo yana dana saninsa shi yasa da wani mutum ya taba zuwa gurin Manzon Allah SAW yace yayi masa Nasiha se Annabi yace masa 'kada kayi fushi' ya maimaita masa hakan har sau uku. Bayan haka akwai hanyoyi da dama da mutum zebi gurin ganin ya kare kansa daga fadawa dana sani dalilin fushin zuciya shine ta hanyar lazimtar ambaton Allah, a duk sanda kaji zuciya ta yunquro maka tana raya maka aikata abinda yake ba daidai ba kayi qoqari gurin kama Ambaton Allah, kayi hailala kayi Istigfari kayi tayi har se kaji wannan Fushin ya sauka. Bayan haka abu na biyu shine yin shiru a duk sanda kake cikin Fushin, idan kasan bude bakinka a lokacin fushi baze sa ka furta a khairi ba to kayi shiru ka kama salati Na uku shine nisantar duk abinda ze jawo motsuwar Fushinka, idan gurine kake zuwa ake bata maka rai to ka nisance shi, idan wani mutum ne ko wasu mutane suke tunzura ka zuwa ga fushin toh ka rabu dasu hakan shi yafi zama Alkhairi a gare ka, idan ma wani abu ne kake yi duk ka dena se kaga mutum ya zauna lafiya a rayuwar sa. Ke kuma yata maganar kishi kiyi qoqari ki sassautawa kanki, mace ce ke wata rana gidan wani zakije ba kuma ki da tabbacin ke kadai zaki zauna dashi a rayuwarki. Baya ga haka a koda yaushe ki tuna cewar Allah ne ya halastawa maza damar ajiye mace sama da daya dan haka ba wani abu bane ba kuma abin da zesa ki daga hankalinki bane kama ta yayi ki ringa Addu'ar koda Allah ze kawo miki abokiyar zama ya baki wadda zaku zauna lafiya, amma wannan mugun kishin baze haife miki Da me ido ba dan bama ko wanne Namiji ne zeyi sha'awar auranki ba saboda gudun abinda ka iya faruwa a gaba". "Saboda kalamsa basuyi mata bama sam hana kanta fahimtarsu tayi ta hanyar tafiya dogon tunanin, seda Abba ya kira sunanta da qarfi kafin tayi firgigit ta farka, malam ya hada mata yan magunguna na tsari da baki ya bata itama Mama aka bata wasu kafin sukayiwa Malam sallama suka kama hanya. "Yanzu Alhaji meyw abinyi, tubda matsalar nan bata Iska bace inaga fa toh sedai asibiti ko abin a kwakwalwarta yake" Mama ta fada cikin Jimami, Umaimah dake bayan mota ta tunzura baki, daga iskoki kuma yanzu Tabin hankali ake yayibo mata? To ai shikenan aje duk inda za'aje kudinsu ne zeyi ciwo tunda dai ita tasan lafiyarta qalau. "Gaskiya Hajiya Babu inda zan sake zuwa kuma, kindai ji abinda Malam ya fada ita zatawa kanta fada ruwanta ta sakawa zuciyarta salama ruwanta taci gaba da abi da takeyi mudai Allah ya gani iyayi munyi namu zagi kuma da take jawo mana ita ta sani" Abban ya fada a fusace maganar Malam ta babu me auranta tana dawo masa, kwarai gaskiya ya fada dan duk wanda yayi aure yayi ne dan ya samu cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali, waye ze siyi tashin hankali da kudinsa ya kai gida? Duk ma wanda yazo yaga halinta doke ya gudu ai su kansu dan babu ya da suka iya da ita ne sun kuma karbi hakan a matsayin tasu Jarabawar. "Haba Alhaji ka dena fadar haka, gatan da zamu mata kenan a yanzu mu tabbatar da lafiyarta saboda nidai wadannan abubuwan da takeyi ban dauke su a mutum me cikakken hankali ba, kaga yanzu idan Asibiti suka tabbatar da lafiyar kwakwalwarta daga nan zamu san matakin da zamu dauka akan ta tu da munsan zallar iskanci ne abinda takeyi" Mama ta sake fada cikin kwantar da murya. Yi yai kamar bazeje ba sedai meya tuna ya zaro wayarsa ya kira wata lamba, bayan sun gaisa a taqaice ya tambayi mutumin yana gida ne ko Asibiti kamin ya kashe ya mayar da ita Aljihu. A lokacin har sun kusa isa gida ya karkata kan mota suka qara gaba, a zaton Mama zasuje Asibitin Malam ne ko Murtala se gani tayi Abban ya dauki hanyar Dawanau. "Alhaji Dawanau zamu je ne?" Ta fada tana kallonsa, se ya juyo a fusace yace "Can zamuje Malika, ko akwai inda suke da kwararrun likitocin manya da qananan mahaukata ne banda can din? Ki fa rabu dani idan ba haka ba tam" ya buga sitiyari, shiru Mama tayi dan da alama ran maza ya baci, shi kansa zafin ran na Umaimah ai daga gurinsa ta gado kawai dai nata ya zarce nasa ne amma shima ai ba baya bane a yanzu ne da shekaru suka ja ya rage wa kansa hayanjya da fada saboda hawan jini ammada akan qanqanin abu be qi ya wuni yana fada da mita ba. Tsuru Umaimah tayi a bayan mota, Dawanau fa yanzu haka zaa kaita a daura mata injinan da ake saka mahaukata karfa a garin neman gira a lalubo mata haukan da bata dashi. Kamar tace kar aje amma tasan yanda Abban ya hasala beqi ya tsaida mota ya lallasa ta suji gaba da tafiya ba, tana ji tana gani suka isa Asibitin da tundaha haraba ha kalinta ya fara tashi ganin masu lalurar rangwamen Hankali kala kala an fito dasu suna ta hidimominsu. Harta hango kanta ance zaa ajiyeta anan, ai bata san sanda ta ruqunqumo mama ta baya ba ta zabura tace "Subhanallahi jikin ne Alhaji kaga ni ko daga zuwa abu ze kuma rikicewa". Tsabatmr takaici ko kallonsu Abban beba har ya qarasa yayi parking motarsa a bakin Clinic din. A dardar suka fito suka bi bayanshi da alama yasan gurin suka ringa ratsa mutane suna wucewa abinda ya dan kwantarwa da Umaimah hankali kenan ganin mutane fes fes masu lafiya babu alamar wata lalurar hauka a taredasu, dagaske dai da akace ba Asibitin mahaukata bane, duk wani me lalura data shafi Kai ko kwakwalwa yana zuwa tana wannan tunanin har suka isa qofar wani office Abban ya kwankwasa. Kamar ana jiransu daman aka bude, Babban Mutum dan kadan ne bazasuyi Sa'anni da Abbaba ya miqe ya tare shi ya bashi hannu da gani akwai kyakykyawar Alaqa a tsanin su. "Mukhtar Mukhtar ashe ana ganin ku daman" Likitan ya sake fada fuska dauke da Murmushi bayan da suka gaisa da Mama, Mukhtar da taji ya kira ya tabbatar mata da Abokinsa na quruciya ne da sukayi makaranta tare ne. "Wallahi fa Dr Kabiru haduwa tayi wuya, rabona da kai fa tun Daurin auran yar gidan Faruk Saleh daga nanaka ce ka bar qasar, se kwananan muka sake jiyo ka" Abban ya fada shima. "Toh ya zaayi, rayuwar se a hankali, zumunchi yayi qaranci, amma lafiya kuwa na ganka tareda Madam da yarinyata, daka kirani fa na zata kawai tsohuwar Aminta ce ta motsa yau zaka kawo mun ziyara" Umaimah Abban ya nuna masa lokaci daya bacin rai na taso masa yace"Ga tanan Dr, duk wani gwaji da akeyi a gane lafiyar kwakwalwar mutum ayi mata. Acaje ta tsaf ta yanda zan san abinyi a gaba". "Subhanallahi ta samu Accident ne ko me" Dr ya fada yana miqewa tsaye, kan Umaimah ya dafa ya shiga duba kwayar idonta yana sake cewa "Ina referral letter da file dinta muga menene matsalar?" "Ba accident tayi ba, abubuwa take yi irin na masu tabin hankali kuma mun kaita Ruqiyya ance na Aljanu bane shiyasa nace bari na kawo ta nan". Dariya Dr Kabiru yayi kafin ya koma kujerar sa yana cewa "Haba Mukhtar wani irin abu takeyi haka da har kake zaton tana da matsala a kwakwalwa?" A taqaice Abban yayi masa bayani, Dr yayi shiru yana saurarensa yana kallonta, yes she looks depressed kana ganinta kasan akwai abinda yake damunta. Seda Abbanya gama tsaf kafin ya kalle shi yace "Ko zaku bamu some minutes nayi magana da daughter may be ni zata gaya mun abinda yake damunta daku ta kasa gaya muku" Miqewa sukayi suka koma wajen office din inda akwai kujeru se a sannan Mama take qorafin Yunwa takeji dan basu karya ba suka fito dan Haka Abbanya fita dubawa ko ze samo musu wani abinda zasu ci. A ciki kuwa cikin lallami da dabara Dr Kabir ya samu Umaimah da yana fara mata tambayoyi ta saka kuka ta fara bashi amsa. Tambayarta yake akanme yake damunta? Wane yanayi take ji a jikinta da sauran abubuwa daya kamata likitan kwakwalwa kamar sa ya tambayi mara lafiyarsa. Sosai mamaki ya qulle masa kai yanda take masa bayanin abinda takeji dangane da kishi akan wanda take so. "Idanna ganshi da wata ko naji yayi maganar mace ji nake kamar zuciyata tana ci da wuta, kawai rayawa nake a raina zan iya kashe ko wacece ta shiga rayuwarsa kuma kome za'ayi mun bazan damu ba indai akan sa ne" Umaimah ta fada hankali kwance ba tareda shakku ko dar a zuciyarta. "Uhm lallai kam akwai matsala" Dr kabir ya fada kafin yayi rubutu a wata takadda ya miqe tsaye yace mata yana zuwa. Waje ya fita inda su Abba suke, a taqaice ya masa bayanin akwai gwajin da zasu mata guda uku, biyu zasuyi mata yanzu dayan kuma sedau suje Aminu Kano dan Injinsu na nan ya samu matsala. Abban yace ya bashi yaje ya biya kudin amma yaqi yace dai su bata abinci taci bari yaje ya gani idan gurin suna aiki. Wasa wasa sega Umaimah a dakin gwajin kwakwalwa, gajin farko general check up ne na kwakwalwa dan a ga ko akwai wani ciwo data samu dalilin buguwa ko faduwa ko kuma an haifeta dashi ba'a sani ba se yanzu yake bayyana. Daga nan kuma akayi mata gwajin tunani. Basu suka bar Dawanau ba se kusan la'asar, har suka isa gida jin kanta take wani gingirin kai yaji inji, dan dayan gwajin se wani satin ma sannan zasu samu saboda se da appointment. Wani lallaba ta Mama harma da sauran yan gidan suka shigayi kafin fitowar sakamakon gwaji tasan matsayinta. Bayan sallar Magriba tana zaune ta jona wayarta da se lokacin ta tuna ashe tun jiyan a kashe take chaji, ta manta shaf data kashe ta jiyan qila shiyasa Khalil be kirata ba ya aiko yaro. Tuno sunansa da tayi nan da nan abinda take ji ya nemi dawo mata sabo, qoqarin kiran sunayen Allah ta shigayi kamar yanda Malam ya gaya mata amma shedan da ya rigada ya samu gurin zama me kyau a zuciyarya ya shiga bijiro mata da wasu tunanikan na banza raya mata yake yanzu fa jiya yaje neman aure gidan su wata qila ma an bashi ita, kai an bashi ma inane Khalil zeje neman aure ace za'a hana shi kawai seta shiga rera kuka mara sauti. Qarar da wayar ta tayi ce ta sakata dagowa, sunan Khalil ta gani yana yawo akai, meya kira kuma ya gaya mata yanzu idan baso yake ya qarasa ta ba? Da so samu ne bazata amsa wayar ba amma ina zuciyarta bazata iya ba, ta rigada ta yarda zuciyarta ta kamu da mummunan Son Khalil, So me tsanani irin wanda ka iya saka me yinsa ya zauce. Tana can tana tunani bata san wayar ta katse ba sega wani kiran ya sake shigowa, ta miqa hannu ta dakkota ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba. "Hankalina ya tashi Umaimah, tun jiya nake kiran wayarki a kashe, dazu da safe nazo akace kun tafi Asibiti meya same ki daman baki da Lafiya ne?" Khalil ya jero mata tambayoyin ba tareda tsayawa ba. A maimakon ta bashi amsa sw kawai ta sakar masa sabon kuka me tafe da sheshsheqa, "Yah salam Umaimah ki dena Kuka dan Allah kiyi mun magana ko jikin ne?" Ya fada yanda kasan shima ze fashe da kukan. Lallashinta ya ringayi amma kamar wanda yake qarawa wuta fetur haka ta ringa rusa masa kuka, bata san tsahon lokacin data dauka tana qona masa credit ba dan ta zata ma ya gaji ne ya ajiye wayar ba tareda ya kashe ba se ji tayi yace "Zaki iya fitowa gani a qofar gida". Da mamaki ta cire wayar ta duba, minti Arba'in da hudu ta kwashe tana masa kukan banza ashe tahowa yayi, seta miqe da zumbulelen Hijabin jikinta ta fito ta gani da gaske yake ko wasa ai kuwa ta hango shi a durqushe a qofar gidan suna gaisawa da Abba. Rabewa tayi ta qi qarasawa har seda Abban yazo ze shiga gidan yace mata "Ki bude masa sitting room ku zauna acan" zeta gyada kai ta juya ta dakko muqullin gurin ta bude kafinta leqa tayi masa iso. Kallonta kawai yake kamar wanda ya samu Tv ita ko ta samu guri ta kame fuskar nan a hade kai kace wani mugun saqo ya kawo mata, sallamar Imran dan Anty Saratu ta katse musu shirun da sukayi, ya ajiye Try me daukeda ruwan roba da zobo se gireba a cikin wani dan bowl me kyau. "Sannu nagode yaya sunanka?" Ya fada yana kama hannun yaron, Imran ya bashi amsa kafin ya zura hannu a aljihu ya zaro Yan dari biyar guda hudu ya bashi yace "Maza jeka kasha sweet kaji" yaronya fita da gudunsa yana murna Umaimah ta raka shi da harara. "Umaimah!!!" Ya kira sunanta da wani sauti da ya saka tsigar jiki ta zuba saboda yanda kiran ya shigeta, bata iya amsawa ba illah kyawawan idanunta data dagota zuba masa tana qare masa kallo. Khalil Kyakykyawa ne, irin kyan da kana kallonsa zaka ce wannan yanada kyau. Dukda baqi ne amma hakanbe boye kyansa ba, yana da hanci, ga bakinsa leben qasan yayi ja na saman baqi abinda yake qara matar da yammata akan sa kenan ga kuma wasu irin idanu da Allah yayi masa, koda yaushe ka kalli idonsa kamar mejin bacci, idan kuwa akayi sa'a ya budesu gaba daya akan ka mace ko namiji duk dakiyar ka se kaji wani abu me kama da tsoro ko kwarjininsa ya tsirga maka. "Karki saka na komawa Hajiyata a rabi irin wannan kallo haka" ya fada yana waving hannayensa a gaban fuskarta ganin kamar ma bata gurin tsabar nisan da tayi a tunani. "Oya tell me, meya sameki jiya gaba daya kin daga mun hankali gashi na kasa samunki a waya bare naji ya kike" Kunya ce ta kamata amma ta kanne ta jefeshi da hararar wasa tace "Wayace maka kallonka nakeyi? Me zan kalla mani itama wadda kaje gurin nata rufa ido kawai kayi mata tace tana sonka bawai dan ka hadu ba" ta fada cikin matuqar qarfin danne abinda take ji, so take ta bugi cikinsa taji ya ake ciki sannan taji view dinsa akanta dan bazata zauna a banza da wofi son sa ya kashe ta ba. "Na hadu ko? Thank you for the complement, itama danaje jiya haka ta fada" Yanda tayi da fuska dole ya fashe da dariyar dabe shirya ba, ya fuskanci yarinyar ta folla masa kamar yanda ya fada sonta ba tareda ya sani ba, yana kuma iya karantar tsananin kishinsa a kwayar idanunsa. Dariyar da yayi ta qara qonawa Umaimah rai se kawai ta bude baki ta saka kuka, "Allah ya baki haquri, waike baki san wasa ba komai kuka kamar wata Doll baby" ya fada yana zamowa gabanta. Hijab tasa ta rufe fuska taci gaba da shaqar kukanta, ta tabbata dagaske yana da wata ashe ba Nabila ce zata fara qirga kwanakin ta ba itace lokacin ta yayi. Ganin da yayi dagaske fa take Kukan yasa ya sassauta murya ya shiga bata haquri, "Wasa nake miki, kuma ko jiyan nan da kika ganmu ba dagaske nake miki ba Abokina Mansur na raka duba Maman budurwarsa bata da lafiya shine kwalliyar da kika ga munyi". Dagowa tayi ta kalle shi irin kallon " ka tabbata?" Da ido ya mayar mata da amsar "kiyarda dani" dole tayi qasa da kanta dan bazata iya jurewa kallon cikin idonsa ba, a haka ma tana ji kamar ta mutu saboda shi inaga yana mata wannan kallon me narkar da zuciya. "Nifa bani da budurwa, gashi Hajiya ta takuramun aure take so nayi. Ranar fa da kika je gidan mu shikenan Hajiya ta saka ni a gaba akan ki ita a dole ke budurwa tace. Harfa ta gama gayawa sisters dina nayi mata. Harfa gurin Sister ki taje akan taso tazo nan gidan tayi magana kafin a turo maza dakyar fa na fahimtar da ita ni babu komai tsakanin mu, ta yarda amma ta kafa mun sharadin kafin qarshen shekarar nan dole nayi aure gashi ni ko budurwa bani da ita yanzu bansan yanda zanyi ba, ko kina da qawa ko qanwa data shirya aure ki hada ni da ita? Ni kinga tsoron yammata nake ban taba zuwa nace wa wata ina sonta ba". PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 8 Yanayin kallon data watsa masa ya sakashi daga hannaye sama yace "Allah ya baki haquri, ki barshi base kin samo mun ba", gani yayi kamar Almutsutsan nata zasu motsa dan sak kallon data masa jiya kafin ta fadi. Buda baki tayi zatayi magana ya sake tareta yana miqa mata kofin daya zuba ze sha yace " karbi kisha zuciyarki tayi sanyi kinji Umaimah, maida wuqar mantawa nayi daman ance mata kishi ne daku bakazu iyayiwa abokin ku budurwa ba" Khalil da neman magana yake, se yayi kamar yana rarrashin ta se kuma ya sake soko wata maganar Ita kuwa se aikin asarar hawaye takeyi. Ganin dai abin nata bana qaro bane ya saka shi daidaita nutsuwarsa yace "Umaimah ya isa, me yasa kike asarar hawayenki bayan kin san masu tsada ne, wai kukan me kikeyi ne ma? Indai magana tace ta saka ki kuka toh kiyi haquri kinji ni wasa nakeyi" "Dagaske baka da budurwa?" Umaimah ta fada bayan data dan tsagaita da kukanta, se ya dago ya kalli cikin idanunta, irin abinda yake gani a ciki ya wuce ya misaltashi. Tsakanin shi da ita besan wanda yafi wani mutuwa a soyayyar wani ba, yana fatan wannan hadin nasu ya zama Alkhairi. "Dagaske nakeyi sedai idan yanzu zaki zama budurwar tawa" ya sake fada yana kallonta. Qasa tayi da kanta tana sakin wani murmushi ji takeyi kamar ta taka rawa Alhamdulillahi Allah ya cika mata burinta. "Kinyi shiru ko bakya sona ne?" Ya fada yana leqen fuskarta, seta dago tareda gintse fuska tace "Bayan kace kayi soyayya da Nabila kuma kace kana Sona" "Wacece Nabila?" Ya tambaya, yanayin da yayi magana ya tabbatar mata da cewa besan Nabilan ba. Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta shi kuma yana qare mata kallo harta gaji ta kalle shi da hararar wasa tace "Kallon fa ya isa haka" "Bazan iya dena kallonki ba, tun a ranar farko danafara ganinki kika sace mun zuciyata ban kuma samu sukuni ba se a yanzu dana furta miki muradin zuciyata, dan Allah Umaimah ki soni har qarshen rayuwata kinji, ban taba soyayya ba na tabbata kuma abinda nake ji akanki ya zarce So Qauna ce" ya fada cikin wani sanyi daya ratsa duk ilahirin jikinta. "Ina da tsananin kishi akan abinda nake so da har ake mun kallon me matsala a kwakwalwa, idan har ka tayani kare duk abinda ze jawo motsuwar kishina zaka same ni yanda bakayi tunani ba" ta samu kanta da furtawa ba tareda tayi niyya ba. Haka kawai take jin bazata boye masa komai a kanta ba, gara ta gaya masa ko ita wacece saboda gudun wata rana yaga wani abu daban da beyi zato ba wani abu ya faru. "Kice ni dan gata ne tunda dan gata shi yake samu ma har a damu dashi ayi kishin sa. In dai nine baki da matsala, bazan taba baki wata dama da har zuciyarki zata baci akai na ba" A nan gurin soyaya me qarfin gaske ta samu matsuguni a zukatan Umaimah da Khalil, Musayar kalamai suka ci gaba dayi har basu san lokaci ya tafi ba, seda Salman Qanin ta ya leqa akan Abba yace ya tafi dare yayi kafin yayi mata sallama ya wuce kamar karya tafi. Folder takaddunta da ledar jiyan ya bawa Salmanun ya shigar mata dasu harda qarin wata ledar me dauke da Turare da tundaga jikin ledar kake jin qamshinsa. Basu haqura ba, kusan raba dare sukayi bayan tafiyar sa suna waya, ya bayyana mata komai akan sa duk wani abu daya shafe shi daya kamata ta sani ya gaya mata. Ya kuma sanar mata da cewar shi ba da wasa yake ba aurenta yake so yayi, kuma a yanda yake hasashe baya so abin ya wuce qarshen shekara dan haka tayi tunani akan sa ta gani, idan har ta amince dashi a shirye yake ze turo magabatansa a tsayar da magana dan burin Hajiyarsa kenan a koda yaushe. Itama a nata bangaren tayi amanna dari bisa dari dashi, kamar yanda yayi mata bayanin kansa haka ita ma ta zayyana masa komai bata boye masa ba hatta da auranta da aka fasa karo uku seda ta fada masa. "Amma menene dalilin daya saka aka fasa?" Ya tambayeta, "Sunce kishina yayi yawa" ta bashi amsa. Mamaki ne yake kama Khalil idan tayi maganar Kishi dan abu kadan seta sake jaddada masa batun ita fa tana da kishi, "Wai Umaimah wane irin kishi ne dake haka da har ze saka mutum uku su fasa auranki?" Khalil ya fada a ransa yana juya maganar wane kakar Kishi ne da har zesa a fasa auran Mace. "Ba zasu iya tsayawa akan mace guda daya ba se sunyi biye biye ni kuma bazan jure hakan ace Mijin da zan aura yana kula wata mace a waje bayan ni ba shine idan nayi magana suke zabar dasu fasa amma ni na dauka hakan lokaci na ne beyi ba, duk ranar da Mijin aurena yazo zanyi". "Basu dace dake bane shiyasa Allah yake kawo dalilai na rabuwarku saboda ke rabo na ce" Khalil ya bata amsa cikin tabbatarwa, kamar tana gabansa ta sunkuyar da kai cikin qaramin sauti tace "Allah yasa". Haka suka ringa aikawa da junansu dadadan kalamai masu sanyaya zuciya har suka gaji sukayi bacci zuciyar Umainah fes tana jin kamar an saka Hypo an wanke mata ita. Baccinta na ranar kuwa cike yake Mafarkai masu dadi na gata sunyi aure da Khalil har sun haifi kyawawan yara suna rayuwa cikin jin dadi da kwanciyar hankali. *MAFARIN SOYAYYAR UMAIMAH DA KHALIL (QADDARARSU)* Yanda ta farka washe garin ranar cikin walwala da farin ciki ya bawa kowa Mamaki banda Mama da tasan za'a rina saboda tun a daren da Abban ya shaida mata sunan wanda yazo gurin Umaiman ta tuna da dramer su ta kwanaki ta kuma gane shine dai yaron da yazo jiya da Magriba. Fatan Alkhairi tayi musu da fata Allah yasa qarshen damuwarta kenan danta yaba danutsuwa da hankalin yaron,tana kumada kyakykyawan yaqini na cewar Umaiman zata samu kulawa da jin dadi a gurinsa. A cikin sati daya daya biyo baya abubuwa sun chanza sosai wanda suka hada da dawowar walwalar kowa na gidan saboda Farin ciki ko akasin haka na gidan ya ta'allaqa da Umaimah ne, a yanzu kuwa babu wanda ya kaita walwala da farin ciki, saboda yanda a kullum take samun sabuwar kulawa da tattali daga Sabon Habibin nata Khalil. Wannan dalilin yasa ko da satiya zagayo suka manta da batun zuwan su Aminu Kano yin cika makon Gwajin kwakwalwar da za'ayi mata har seda Dr Kabiru ya kira yayi wa Abba tuni ya kuna sanar masa da sakamakon gurinsu sun fito, yana jira a kawo wancan dinne yayi Nazarin su gaba daya hakan yasa dole suka je Asibitin akayi dukda Umaimah bata so ba, toh daman ita tasan matsalarta kuma ga magani ta samu ina dalilin da zaa ringa kaita ana soka mata qarafuna a kai. Sakamako ukun duk da suka fito sun nuna cikakkiyar lafiya da kwakwalwarta take dashi, bata taredada wani ciwo ko damuwa illah irin saqon gaggawa na tashin hankali da take aikawa da kwakwalwar tata nema yake neman ya jawo mata ciwon damuwa wanda a gwajin qarshe ma babu alamar hakan dan haka Dr Kabiru yayi mata gargadi sosai tareda bata shawarwari akan ta kula da lafiyar ta dan itace gaba da komai. BAYAN WATA UKU A cikin wannan lokacin abubuwa da dama sun faru na jin dadi ciki kuwa harda tsayar da ranar auran Umajmah da Khalil da akayi. Watan su daya da fara soyayya Mahaifiyarsa tazo da kanta suka gana da Mama ta jadda mata irin so da qaunar da sukeyiwa Umaiman, sosai Maman taji dadi ta kuma godewa Allah daya azurya Umaimah da samun suruka ta gari me kuma qaunarta, ba'a rufa sati ba iyayensa maza sukaje da kudin aure da saka ranar su watanni biyar masu zuwa kamar yanda Khalil dinda Umaimah suka tsara wanda yayi daidai da saka ra ar Nuratu da Angonta Dr Sabi'u. Rikici da hauragiyar Umaimah ya zama tarihi dan tun daga declarationna soyayyartada Khalil wani abu na rashin jin dadi be sake faruwa ba, Khalil na matuqar taka tsantsan da duk wani abu daze bata mata rai har ya kai ga motsawar Matsalarta dan a lokacin da yaje gaishe da Abban ta be rufe shi ba, yayi masa kyakykyawan bayani game da Umaimah da HALIN KISHIN ta. Hatta da Gurin Malami da Asibi da aka kaita seda ya gaya masa ya kuma Nuna masa takaddun Asibiti da suka nuna shaidar lafiyarta. "Umaimah yarinyace da duk wanda ya zauna da ita ze sota, banda halinta na rashin sanin yanda zata sarrafa kanta acikin Fushi bata da wata matsala. Nasan zakaji matuqar dadin zama da ita idan har ka kiyaye duk wani abu da ze janyo motsawar rikicinta saboda idan tana son abu, tana kula dashi ne da dukka rayuwarta" Kalaman Abba da ya riqe kenan yake kuma amfani dasu. Shi da kansa ya shaida Umaimah tana sonsa har wani lokacin ya kanyi mamakin tsakanin shi da ita waya fi wani son wani atsakanin su. Yanda take riritashi da tattalinsa yana saka shi yaji kamar yafi kowanne Namiji sa'a a rayuwarsa, yana yawan hasaso yanda rayuwar auransu zata kasance.  Irin soyayyar da zasu shimfida me tsafta, yayan da zasu haifa a kullum ya zauna shiru lissafinsa kenan. A farko farko ne ma suka fara samun sabani wanda tunda yayi wa tufkar hanci komai ya koma musu daidai. Abinda ya faru wata rana ya dakkota daga gidan Yayarta Nasiba, suna tafe a hanya Abokiyar tagwaitakarsa  Jalila da yayi sabin Numberta da 'Rabin jiki' ta kirashi'. Tunda Umaimah ta kyalla ido taga kiran wayar yanayinta ya chanza daga murmushin da takeyi zuwa fuskar bacin ran da yayi mata dirar mikiya lokaci daya. Har ya kammala wayar sa ya ajiye be lura da yanayinta ba seda ya kashe wayar yake ce mata "Kinji Jalila ko, wai mata wayonku yayi muku yawa wallahi. Tana gidan Mijinta amma duk idan tana da buqatar kudi se taci tudu biyu, mijinta yayi mata nima nayi mata dan Allah ba wayo bane wannan? Koda yake nima dai na kusa ajiye tawa matar dole a ringa daga mun qafa tunda yanzu inda uzurin da zanyi da Kudi" ya qarasa yana kallon fuskar jin harya gama maganar bata ce komai ba. Umaimah kuwa wani irin daci ne ya taso mata kamar zatayi amai saboda tsabar dacin da maganganunsa sukayi mata. Ya iya duban tsabar idanunta yake gaya mata tsohuwar budurwarsa ta kirashi tana neman kudi a hannunsa babu kunya babu tsoron Allah, "Kinyi shiru, lafiya dai naga fuskarki ta chanza" ya fada yana qare mata kallo ganin yanda ta hade fuskar tam har wani ja ja yaga fuskar tayi. A fusace ta bude baki tace "Toh ni ina ruwana can ta shafe ku kaida ita, amma dai ka sani yanda kake magana da matar wani kaima se Allah ya sakawa mijinta anyi da taka. Ita kuma ballagaza mara kamun kai tana gidan wani tana waya da tsohon saurayi zataje ta tarar da Allah, wai Rabin jiki idan ma gangar jikince kai ka sani ai baka burge ba tunda har ka bari wani ya aureta idan kuma da auranta kuka hadu kake neman ta ma duk matsalar kuce ba tawa ba" ta qarasa a mugun fusace kamar zata kai masa mari. Gefen hanya ya gangara ya faka motar ya tsaya kawai yana kallonta dan gaba daya ya rasa mamakin kalamanta zeyi ko kuwa tsoron yanda ta birkice gaba daya tana jifansa da maganganu zeyi? "Wato ga mahaukaciya tana magana ka sakani gaba kana kallona ba? Ai wallahi bansan haka kake ba Khalil kuma ka bani mamaki, ka rasa wa zakayi tarayya da ita se matar aure to wallahi kaida Allah za kuma kaga sakayy....." "Shut up Umaimah ya isheki" ya daka mata tsawar da ta sakat yin shiru ba tareda ta shirya ba. Cigaba yayi da cewa "Kina hankalin ki kuwa kin san me kike fada? Wai ma dakata duk akan me kike wadannan maganganun har kina nema ki jefeni da abinda bana fatan Allah ya jarabceni da aikatawa ba. Bari kiji, ni mace idanba yar gidanmu ba babu abinda yake hada ni da ita balle har muyi magana a waya kece mace ta farko a tsahon rayuwata da wata doguwar magana me muhimmanci ta shiga tsakanin mu. Idan kuma duk saboda Jalila kike wannan babatun" ya dauki wayar ya shiga whatsapp ya kirata video call tana dagawa yace "Ina gayawa yayarki banason mace ta fiya qiba shine na kira mata ke video call taga yanda kika saki jiki kika zama shirgegiya waye za'a cewa ke qanwata ce ya yarda" ya fada cikin tsokana. Daga cikin wayar ta amsa da cewar "Wallahi Khalil ka raina ni, minti daya fa ba kadan bane amma ka ringa cewa ni qanwarkace karma ka saka ta yarda wallahi nice Hassana ni nake gaba da kai kulkum se Hajiya ta raba mana Musun nan amma kaki ka dena cemun qanwarka". "Gata ki fada mata toh amma dai bazan taba yarda ba nine Hassan ke kuma Usaina kawai muje a haka" ya fada yana juya wayar saitin Umaimah da tayi sak tun sanda ya ambaci sunan Jalilan, a sanyaye suka gaisa ko ba'a fada ba kamannin sa dake fuskar Jalilan sun isa su gasgata alaqar jini da take a tsakaninsu. Tsokanar ta ta ri gayi Umaimah na dan murmushi tana satar Kallon Khalil daya zuba mata ido kawai a ransa yana tunani. "Nice Hassanarsa nasan ya ce miki shine Hassan ko, son girma irin na Khalil qila ya gaya miki ya girmi Jamila ma to Yayar muce ita amma ni na karbi qanqantar na bar muku girman kinji Matar Yaya, ki kula mana dashi da kyau" Jalilan ta fada bayan da suka gama gaisawa. Janta take da hira amma ta kasa sakewa, qarshe sukayi sallama ta miqawa Khalil wayar,karba yayi ya kashe still yana kallonta yace "Ko dan gaba karki sake jifana da irin zargin da kika darsa a zuciyarki kuma banyi tsammanin haka daga gare ki ba amma nayi miki uzuri a yanzu ya wuce" kafin ya tada motar suka cigaba da tafiya. "Amma ai kaine ka saka abinda zesa nayi zargi akai,  bakaga da sunan da kayi saving number ba ai da sunanta ka saka ko Sister zan gane ammaka saka wani rabin jiki" ta fada tana tura baki dan ba wai hakan ya saka ta naba'a bane, dukda jikinta yayi sanyi da abinda ta aikata din ta kuma ji kunya dan sam ta manta da sunan Hassanar sa kenan Jalila dan tun a wayarsu ta farko ya gaya mata duk sunayen yan uwansa ciki daya da kuma Jamila wadda ita kadai ce suka Uba daya Mamanta ta rasu itama a hannun Hajiyar su ta tashi. Shiru ya mata har ya kaita gida basu sake cewa komai ba dan sosai ransa ya sosu da abinda tayin, yanzu ace ma da wata can yake waya ba Jalilan bace beyi zaton zata iya masa magana da irin lafazin da tayi amfani dasu ba sam basu dace ba, amma yayi mata uzuri tunda karo na farko ne. Umaimah na faman bata rai ta sauka daga motar, a cukulece tayi masa sallama har tayi gaba kuma se ta dawo shidai yana tsaye yana mamakin sabon halin nata na yau tace "Kuma dai gaskiya ka canza sunan da kayi saving number in dai ba kana so zuciya ta ta buga ba idan ina ganin sunan a wayar ka" tana gama fada ta shige gida ta barshi zaune cikin mota yana tunani. Shikam yau abubuwan nata daure masa kai sukeyi, wannan shine Kishin da take fada daman? Idan kuwa haka ne wannan ai shirme takeyi, duk kishin da zesa ka kasa banbance daidai da rashin daidai ai ya zama shirme. Seda suka kwana biyu tana fizge fizgr, sam shi ya manta ma me akayi kawai dayaga take taken ta ya dauki hakan a matsayin yanayi da kowanne dan Adam yana iya riskar kansa a ciki na damuwa ko rashin jin dadin wani abu, ya tambayeta ko da wata matsala ne ta nuna babu komai se kawai ya shareta. Daman lokacin shima ayyuka sun fara masa yawa. Branch office dinsu ya fara aiki kuma shi aka bawa matsayin manager na bangarensu dan haka ayyukansu da yawa. Ga aikin gyaran gidan da ze zauna a ciki wanda yake da yan haya da a ciki suka tashi yana ta aikin gyara da yiwa gidan kwaskwarima saboda tsohon gida ne. Dukda Hajiyan su taso ya zauna a dayan bangaren da basa amfani dashina gidansu wanda yake mallakin Mahaifinsu amma yaqi yace gara dai ya zauna acan din. Dan kanta da taga ya fita a sabgarta ta nemi shiri suka koma daidai, bata haqura ba da naci da mitar tsiya seda tasa ya chanza sunan Jalila daga Rabin Jiko zuwa twinny. Ranar ana yar dadi da kansa ya bata wayar yace ta chanza, bayan ta chanza ta shiga contacts, mesaagesa, hatta da whatsapp dinsa seda ta duba amma babu wani abun azo a gani da zesaka ta tada masifar tata. Abinda ya mugun mata dadi ganin yanda yake qin amsa saqon ni daga number da be sani ba, taga chats daga yammata amma data hau kububuwar fushin fuuu idan ta shiga chat din ta karanta kuma seta sakko ganin babu wani abu a ciki. Saqonnin yammatan ne suke turowa, wasuma sunfi wata da watanni be bude ba se ita data bude su sannan. Bi ta ringayi tana tura musu da "shegiya mayya karki sake yiwa mijina magana" sannan ta bisu da block. Ko a Jikinsa ta qaraci duk abinda zatayi ta gama ta bashi wayar shikenan zaman lafiya ya qara wanzuwa a tsakani tunda ta sake yarda da Khalil din nata ne ita kadai baya cin Amanrta da kowacce mace. Qauna kuwa se abinda yayi gaba aka ci gaba da tsinkar furen soyayya. Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah se gashi Umaimah ta gama service ga kuma shirin aure dan ana maganar saura sati shida biki ne dan har an kawo lefen Nuratu sune suka zo da saka rana sati shidan dan haka na Umaiman ma aka ce idan sunzo da tasu hakan za'a saka. A cikin satin da suka ce zasu kaqo legeTsautsayi ya samu Hajiyar su Khalil ta fadi a bandaki ta samu karaya a hannunta na dama. Anyi mata dori a Asibiti sedai tsorata da tayi lokacin da ta fadin ya saka jininta ya hau dole aka bata gado suna ci gaba da kula da yanayin jikin nata. Kwananta biyu a Asibitin Umaimah suka shirya zuwa dubota, lokacin itama bata jin dadi tana fama da Malaria amma taji sauqi. Da yamma Khalil yazo ya dauke su ita da Nuratu suka tafi Dubiyar. Sun tarar da Dakin cike da yan uwan Khalil bangaren Hajiyarsa da suka zo dubiya suka gaishe su tareda yi mata fatan samun afuwa, Nuratu ta dire ledojin Fruits da suka taho mata dasu Hajiya se saka musu Albarka take tana nuna wa yan uwanta Amaryar Khalil. Sun zauna can Khalil daya fita bayan daya raka su dakin ya dawo, yana zama wata fara kyakykyawa mai matsakaicin tsaho da jiki ta shigo dakin, tana ganin Khalil fuskarta ta fadadada Fara'a tace "Jinin jiki idon ka kenan" "Cikin farin cikin ganinta ya miqe tsaye ya nufeta yana cewa " Dazu da zan fita daga gida naga shigar mota Layin kamar taku amma saboda banji anyi maganar zuwan ki ba shi yasa ban kawo ko ke bace". Wata Ashar Umaimah ta lailayo a zuciyarta ta dire kafin ta dora da cewa "Ranar nan yace Rabin jiki yar uwarsa ce yau kuma Jinin jiki?" Hannu da suka gaisa akan idon ta ya qara ingiza wutar abinda take ji, lokaci daya idonta ya kada yayi jajir taji kamar jiri na neman dibanta daga zaune lokacin da taji wata mata na cewa "Oh wannan qauna da shaquwa ta Khalil da Jamila an girma amma suna nan kamar lokacin yarinta". Miqewa tayi, dakyar take daga qafarta Nuratu tayi qoqarin kama mata hijab amma ina tuni ta fincike tayi waje gaba daya yan dakin suka rakata da ido. "Ko jikin nata ne ya motsa?" Khalil ya fada yana kallon Nuratu, ta gyada kai dakyar tana hadiyar yawu dan ita tasan ba jiki bane sedai idan Baqin HALIN KISHIN nata ne ya motsa, Khalil ya fita da sauri yana cewa "Bari na dubata, idan jikin ne se mu ga likita a nan ya sake dubata" yayi waje da sauri ya bi bayanta. PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 9 Hangota Khalil yayi ta doshi hanyar waje yabi bayanta da sauri kamarta sani ta qarawa tafiyarta sauri, cikin sassarfa ya bita ganin har ta kusa isa gate din Asibitin ya daga murya yana kiran sunanta amma bata juya ba jefa qafunta kawai take tana tafiya, ji take ina ma data rufe ido ta bude zata ganta a gida tsabar yanda ta tsani Asibitin da Duk wadanda suke ciki sa. "Umaimah meye haka ne kina ji ina kiranki ina zakije ko jikin ne ya tashin miki?" Khalil ya fada bayandaya tararda ita yasha gabanta. Wani shegen kallo ta watsa masa, yanda ya ke washe baki yana riqe da hannun wannnan matar ya dawo mata seta kauce shi taci gaba da tafiyarta ya qara tare ta cikin fada fada yace "Wai ke meyasa kike haka, ina miki magana shine zaki wuce kici gaba da tafiya ina zakije? Idan wani abun ne ya faru ki gaya mun mana se muje na kaiki" "Allah ya kiyeye na sake shiga motar ka kaje dai kaci gaba da diban wadancan jakan marasa kamun kai da kake kulawa, tsabar rashin kunya a gaban uwar data haife ka da sauran mutane kake kama hannun wata qatuwa kuna dariya" "Jamilar ce baki sani ba? Meyasa idan wulaqancinki ya tashi se kin nemi abinda zaki cimun mutunchi ko yan uwana?" Ya fada yana kallonta cikin ido saboda yanda kalmar Jaka data alaqanta da yar uwarsa. Seda ta harare shi kafin tace "Toh dan Jamila ce se aka ce ku tsaya kuna iskanci a gaban mutane" "Iskanci Umaimah, nine nake iskancin?" Ya sake katseta yana nuna kansa da yatsa. Dauke kanta gefe tayi tana qunquni qasa qasa wanda tsaf ya jita "toh idab ba iskanci ba menene zaka wani kama mata hannu a tsakiyar mutane ita kuma se wani murmushi take tana yaqe haqora" ta fada. Seda Khalil ya hadiye malolon baqin cikin daya taso masa zuciyarsa tana ayyana masa rashin dacewarsa da wannan mara kunyar yarinyar qarara. Dakyar ya iya bude baki yace "ki jira na yiwa Nuratu magana ta fito na mayar daku gida" dan ko babu komai shi ya dakko su daga qofar gidansu kuma seda Abba ya jaddada akan su dawo da wuri dan haka dole ya mayar dasu daga baya ze zauna ya yankewa kansa hukunnci akan ta, dan ya fara hango dalilan da suka saka har mutum uku fasa auranta, sannan yaga tasa wautar qarara da yake qoqarin daukar ta ya kaita nasa gidan. "Ni? Ai wallahi bazan shiga motar ka ba ita dai da bata da zuciya taje ta zauna seka maida ita amma ni kaga tafiyata, kuma ka qaddara daga nan gurin babu ni babu kai kaje can cikin yan uwan naka ka auri daya idan zaka iya" Umaimah ta fada cikin tsananin rashin kunya kafin ta murguda masa baki tareda baza Hijabinta da yake har qasa ta tafi ta barshi a gurin kamar wanda aka dasa. Dakyar ya iya jan qafafunsa da sukayi sanyi ya koma dakin, yana shiga suka hau tambayarsa ina take lafiya dai? Ya rasa me zece musu ga tunanin maganar data fada masa da ke neman ruguzashi haka ya daure ya tattaro yawun bakin sa yace "Amai ne ya taso mata, gata can A mota Nuratu muje na mayar daku gida tace akwai sauran magungunanta da bata gama shanyewa ba". Nuratu da duk ta tsargu dan tun fitar sa wata daga cikin matan ta fara qananun maganganu akan taga wani kallon wulaqanci da Umaiman ta watsa musu kafin ta fita, aka samu wata ta goyi ganin zasu tada hayaniya Hajiya ta tsawatar musu, ita dai tayi tsuru, Jamilan ta zauna kusa da ita tana janta da magana amma ta kasa amsawa se murmushin yaqe kawai take tasan Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a wajen nan, Allah yasa kar tayi rashin hankalin nata data saba ta tarawa kanta mutane har magana ta dawo dakin su samu nayi shigowar da Khalil yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya dukda a kallo daya da tayi masa ta gane akwai matsala Umaimah tayi tsiyar, yana cewa ta tashi kuwa ta miqe tana qara yiwa Hajiya Addu'ar samun sauqi ta fice. Dama bata saka ran ganin Umaimah a waje ba tasan kuma shima ya fada ne kawai dan haka suna shiga motar tun  kafin yayi magana ta kalle shi tace "Dan girman Allah Khalil kayi haquri, Al'amarin Umaimah se Addu'a se tayi abu kuma daga baya tazo tana nadama" "Gaskiya I'm sorry to say amma Nuratu sam yar uwarki bata da tunani, could you believe ni ta kalla ta kira da dan iska a matsayina na mijin da zata aura? Ba tun yau ba take fada mun maganganu marasa dadi amma ina mata uzuri sedai naga a kullum a maimakon abin ya rage gaba ya ke qarayi. Beside me nayi mata? Saboda kawai na gaisa da yar uwata shine ya bata damar da zata gayamun maganganu haka har tana fadin babu ni babu ita naje cikin yan uwana na nemi wata na aura me yake damun Kwakwalwar Umaimah? Ko kuma daman wannan rashin hankalin shine zafin kishin da take cewa tana dashi?. Indai haka ne na godewa Allah daya nuna mun ainihinta tun kamin na aureta na aurar wa kaina damuwa, kuma banga laifin duk wadanda suka fasa auranta a baya ba saboda sam Umaimah ba macen aure ba. Macen da zata iya tsayawa a gabanka ta gaya maka duk maganar datazo baki ta ba tareda tayi shayi ko taga qimarka ba ai ba matar aure bace, dukda ma dai ta fada da bakinta babu ita babu ni Allah yasa hakan shi yafi Alkhairi, ki shiga ciki idan Abba yana nan kiyi mun sallama dashi dan Allah tunda wuri gara mu sama ma kanmu sauqi Allah ya hada kowa da rabonsa" Khalil da yau zuciyar yan maza ta motsa masa ya fada daidai sanda ya tsaya kofar gidan su Umaiman. Ido kawai Nuratu ta saka masa tasan gaskiyar sa ya fada amma bata fatan yar uwarta ta rasa nagartaccen Namiji irinsa, shi kadai ne take tunanin ze iya chanza Umaiman gashi tun ba'aje ko ina ba shima ya sare da halinta yana zancen fasa aure. Bude baki tayi dakyar tace "Kayi haquri Khalil nasan halin Umaimah sam idan ranta ya baci bata sanin me take fada..." "Ranta ya baci da akayi mata me? Saboda na gaisa da yar uwata? Yayata ce fa uban mu daya. Haka kwanaki tayi mun saboda Jalila ta kirani twin sister na, ta ringa zagina har tana kirana da Mazina ci. A lokacin nayi mata uzuri a lokacin amma banda  Yayi da babu wani abu da bata sani a kaina ba. Yan uwana mata babu wadda ban gaya mata sunanta na nuna mata hotunansu ta yanda ko a hanya suka hadu zata gane su ba. Saboda gudun bacin ran Umaimah na chanza layin da nake harkokin kasuwancina dasu. Ba dan ina tsoro ta ba, kamar uwar data haifeni duk sanda ta raya mata zata ce nabata wayata tayi bincike ban taba nuna mata rashin jin dadi akan hakan ba ko babu komai waya sirfi ce nima ina da sirrikana da ya kamata ni kadai nasan dasu amma ko mai da ko ina na bata damar shiga ta duba a wayata, hakan ne ya bata damar da zata tsaya ta zageni duk a sunan kishi? Kishi ko hauka? To nidai na haqura taje kawai Allah ya bata wanda ze iya da halinta" Khalil yayi saurin katse Nuratun a fusace dan ransa qara baci yake yi duk idan ya tuna maganganun data yaba masa. Bude baki tayi da niyyar sake magana ya bude motar yana cewa "kije dan Allah, ki bar Abban ma duk randa na sake biyowa nan haka nazo. Ki bawa Mama haquri nasan babu dadin amma hakan shi kadai ne abinda ze sama mun maslaha dukda ina son Umaimah amma bazan iya auranta ba, a waje tayi mun haka inaga na aureta na kai cikin gidana kinga wannan kome tayi ni na siya da kudina". Jiki a mace Nuratu ta fita daga motar daidai sanda Adaidaita ya tsaya a qofar gidan Umaimah ta fito daga ciki, kallo daya tayi musu daga Nuratun har Khalil din kafin ta maida ido ta kan Nuratu tace "kuma da kika shiga motarsa ke kadai Allah ya isa bazan yafe ba, idan ma Amana aka ci mutum yaje shida Allah" ta sake fada tana kallon Khalil kafin fuuu ta shige gida. Murmushin zallar takaici Khalil ya saki, ya fara hasashen yarinyar nan bata da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ko kuma dai saitin kanta na gocewa ne lokaci lokaci. koma dai yaya shidai he is done with anything concerning Umaimah, yana sonta amma dole ya haqura da ita dan beyi zaton Rigima da Hayaniyarta da Nasir ya ke fada ba ya kai haka. Koda yake ya so ya rufe shi ne amma banda haka ai kaitsaye kawai kamata yayi yace masa tana da matsalar saiti. Gata dai mace har mace amma babu cikakken hankali Allah kenan me yanda yaso. Haka ya juya Asibiti bangarorin zuciyarsa na mahawara da juna, tabbas yana son ta so me tsanani amma menene amfanin soyyar da babu kwanciyar hankali da girmamawa a cikinta. Idan ya tuna yanda take riritashi tana lelen sa idan suna yar dadi se yaji kamar baze iya rabuwa da ita ba, amma abinda tayi masa dazun ya saka shakku a zuciyarsa game da auranta. Tayi kishi da yan uwansa na jini inaga kuma duk randa tsautsayi yasa ta ganshi da wata, bama wannan ba ita rayuwa bata da tabbas. Har zuciyarsa bashida burin ajiye mace sama da daya musamman ace Allah ya cika masa burinsa ya bashi mace irinta amma babu wanda yasan gobe, idan qaddarar sa ta auran mace sama da dayan ce fa yaya zasu kaya? Yanda yanzu kullum ya kunna radio labarai ne marasa dadi akan mata sun kashe mijin ko sun kashe kishiyar toh maganin kar ayi kar a fara, indai soyayyace ze roqi Allahn daya saka masa ita a zuciyarsa ya cire masa ita kuma ze ci gaba dayi mata fatan Alkhairi ubangiji ya rage mata abinda yake damunta a zuciya amma tabbas baze siyawa kansa tashin hankali da kudinsa ba amma ta yaya ze tunkari Hajiya da wannan magana yanda take son Umaimah kamar ta goyata? Bama wannan ba, gaba daya fa auransu befi sati hudu masu zuwa ba anya idan yace ze fasa yaya iyayenta zasuji dan shi su yafi tausayawa, mutanen kirki, Mamanta ta dauke shi kamar dan cikinta basu boye masa komai akan Umaimah ba tun fara zuwansa gurinta dan hatta da takaddun Asibitin gwajin kwakwalwa da aka mata seda Abba ya nuna masa amma sam shi be fahimci Al'amarin ba, be taba zata haka abin nata yake ba se yanzu da tafiya take qara nisa daman hausawa sunce Hali zanen dutse ashe lokaci take jira ta fara zayyano masa su, toh koma dai menene ze jira a sallami Hajiya ta koma gida kafin yaje mata da wannan maganar. A can gidan su Umaimah kuwa rigima ce sosai ta sarqe tsakaninta da Nuratu dan tsayawa tayi daga cikin Gareji Nuratu na shiga ta hau kanta da kokawa itama batayi wata wata ba kuwa ta zage suka fara kwasar dambe dan a zuciye take da lamarin Umaiman, tayaya zatayiwa kanta asarar miji kamar Khalil wanda tasan muddin ta rasa shi bazata maida kamar sa ba sannan rantsuwar Abba ta bada ita sadaka ta tabbata kenan. Dambe sukeyi haiqan har cikin gida sosai kuma Nuratun ta zage tana jibgar Umaimah dan ko a qirar jiki zubinsu ba daya bane. Nuratu doguwa ce me garin jiki dan ta ninka Umaiman da tsabar tsaurin ido ne ma ya sakata cukumarta da dambe. Sosai ta lallasata, dan takaicin shekara da shekaru ta samu dama tana sauke mata shi yau akayi sa'a babu kowa a gidan dan suna fita ba dadewa akayi rasuwa a bayan layi dab haka su Mama da Antyn sun tafi Jana'iza se Salis ne kadai a gidan Dan Anty na biyu da suke sa'anni da Umaiman, shi kuwa yana leqowa daga dakinsu yaga abinda yake faruwa ya koma ciki harda turo qofa. Yaya Aminu ne yaje gidan, tundaga waje yake jiyo ihu da kururuwar Umaiman tana zagin Nuratu a ransa yace "abin ya motsa kenan, ai kuwa yau zaki ci ubanki daman ina da cikin ki ai" se ya juya ya koma motarsa. Dorinar da yake ajiyewa saboda horon yaran sa idan ta kama ya dakko har wani murmushi yake yana hasaso irin dukan da ze mata kafin su Mama su dawo dan sunyi waya ta gaya masa sunje jana'iza amma gasu nan zuwa. Yana shiga kuwa beyi wata wata ya shiga sakar musu duka kan me uwa da wabi saboda yanayin daya tarar dasu gaba daya kowacce jikinta na buqatar ya gaya mata. A zabure kuwa suka rabu kowacce ta hau sosa jiki dan dukan ya shige su musamman da daman rabi kaya rabi tsirara suke dan tun a Get aka tuge Hijabai da dambe yayi dambe kuwa aka ringa farke farken kaya. "Ashe baku da mutunchi a cikin gidan kuke mana kokawa se kace wasu yan tasha?" Ya fada a fusace yana kallon yanda kan ko wacce yayi buzubuzu kamar sababbin kamu se sosa inda ya tsula musu bulala suke, jikin bango suka maqale kowa tana sosa jiki, ya sake kallon Nuratu yace "Harda ke ina miki kallon me hankali ashe zama da ita yasa kema kin koyi hauka ko? Uban me ya hada ku fada?" Ya daka mata tsawa, se Umaimah ta fashe da kuka tace "Wallahi Yaya babu abinda nayi mata kawai ta hau ni da duka..." Bulalar ya kai mata duka da ita tayi azamar gocewa ta fada dakinsu da gudu tana masa Allah ya isa a zuciya. Kan Nuratu ya juya ya shiga surfa mata masifa uffan batace ba har yayi shiru dan kansa kafin ta miqe ta shige dakin Mama dan tasan idan ta shiga nasu Umaimah na ciki tabbas fada be qare ba shi kuwa Yaya Aminu samun su zeyi kamar jakai ya lafta. Baafi minti sha biyar ba kuwa su Maman suka dawo, Aminu ne ya fada musu abinda yazo ya tarar se a sannan Salil ya fito daga daki yace "Umaimah ce da laifi dan ta riga Yaya Nuratu shigowa ta labe a bakin qofa se ji nayi sun kaure da dambe". "Ai ko baka fada ba daman nasan itace da tsokana amma itama Nuratu da laifinta akan me zata biye mata har suyi dambe se kace wasu qananan yara" Maman ta fada. "Ki qyale su Allah ya taimaki wata yarinya ta sake mana dambe a gida wallahi se jikinta ya gaya mata dan se nayiwa mutum mugun duka a gidannan" Aminu ya fada, daki Mama ta wuce yabi bayanta bayan sun gaisa da Anty. Nuratu na ganin Maman ta saka kuka, babu bata lokaci ta zayyane mata duk yanda akayi a Asibiti da abinda Khalil ya gaya mata a hanya harda dalilin yin damben nasu. "Ai shikenan" Mama data gama saurarenta ta fada tana miqewa tsaye, Allah kadai yasan abinda taji a zuciyarta se kuma wanda Ubangiji ya jarabta da fitinanniyar yarinya irin tata. "Ai kuwa sena ci ubanta yau a gidan nan, kuma bata isa ba a wannan karon ta sake lalata magana tunda naga abinnata ya zamana tsantsar iskanci tana da buqatar a dawo da ita kan hanya" Aminu ya fada afusace yana miqewa shima se Mama tayi saurin dakatar dashi da cewa "Karka kuskura ka taba ta, baka ji abinda akace bane shima yaron yace ya fasa toh ka barta zaman gidan nan ne ko gata gashinan. Kuma kar naji zancen a bakin wani koda mahaifin ku ne kuwa, idan sunzo da kansu sun janye a lokacin ya sani. Amma Umaimah koh idan har ta bata wannan auran bazata maida kamarsa ba" ta qarasa maganar cikin rawar murya tareda daga kanta sama a qoqarin ta na dakatar da hawayenta daga zubowa dan daman daga yanayin muryarta suka gane kuka ne yake neman zuwar mata abinda ya qara sanyayawa Aminu da Nuratu jiki. "Dan Allah Mama karkiyi kuka, kin sani hawayen ki masifa ne a tattare da ita addu'ar dai ita zaki ci gaba dayi mata in sha Allahu wata rana se labari" Aminu ya fada sedai kamar me jira kuwa kukan ya kwace mata tace "Na gaji, nagaji Aminu da halin qanwarku. Kullun ta Allah da zullumin ta nake kwana nake tashi a raina, yanzu idan aka fasa auran nan karo na hudu fa kenan me kake zato mutane zace a kanta? Ni kadai nasan irin qunci da baqin cikin nake fama dashi akan lamarin auranta yanzu ina murna yan satittika suka rage ta tafi shine ta ja gwalo abinda ze saka a fasa ko ai shikenan" tana gama fada ta shige daki tana ci gaba da matsar hawaye. Nuratu dake nata hawayen a zuciyarta tana dana sanin sanarwa da Maman, amma tasan dole zata ji, kuma ita a nata dabarar ta fada mata da wuri ne saboda idan da yanda zaayiwa tufkar hanci ayi se gashi ta sake lalata al'amarin. "Indai junin mutum munafunci dason ya hadani da uwata sedai abinsa ya qare masa in sha Allahu badai aga bayana ba sedai mutum yaga nasa, kuma aure na babu fashi duk baqin cikin mutum" Umaimah da basu san da tsayuwarta ba ta fada tana jijjiga jiki irin na tsabar fitsara da rashin kunya, Aminu ne ya yunqura kafin ya tarar da ita ta kwas ada gudu ta koma dakinsu harda sakawa qofa sakata dan tasan a yanda ya zaburo tabbas ya riqeta toh ko be kasheta ba se tayi dogon Suma. Zama tayi akan gadonta gaba daya kuma seta rasa sukuni, hawayen da ta gani a fuskar Mama sun daga mata hankali dan ita ba jahila bace ba kuma mahaukaciya bace tasan illar da hakan ze yi mata wai me yasa a kullum itace sanadin Kukan Mama? Bama ita kadai ba duk wanda ya tashi qorafi a gidan akanta ta fita zakka a cikin su goma sha uku da aka haifa a gidan. Iya qoqari kuma tanayi gurin kaucewa duk abinda zaace tayi ba daidai ba amma sau tari ma tsokanarya akeyi idan ta maida martani kuma ace tayi laifi, ko kuma su dauki damuwar data shafeta su dorawa kansu kamar yanzu da wannan munafukar Yaya Nuratu taje ta fadi qarya da gaskiya ita sam bataga abin tayar da hankali a ciki ba. Aure ita ce me auren nan ko maza ashirin suka fasa auranta mijin tane bezo ba hakan kuma baze hana shi zuwa ba sannan maganar Khalil da tace ta fasa wasa takeyi bacin raine kawai yasa shima kuma tasan haka ne idan an barsu daga nan zuwa dare ma zasu shirya kansu amma shine Mama zata dauki damuwa har tana zubda hawayenta. Tsaki taja tareda gyara kwanciya, tana so ta koma dakin ta bata haquri amma tasan muddin wancan zalimun na gidan ta kai kanta mahallaka ne gara ta bari se ya tafi, haka ta ringa juyi a gado hankalin ta sam yaqi kwanciya, yanzu fa idan Maman tana can tana ci gaba da kuka ai se tashin hankulan su mata yawa, ga abindatake ciki ga Hawayen uwa ita ina zata saka ranta? Miqewa tayi ta bude qofar,gara taje idan ma kashe ta Aminu zeyi sedai yayi din amma seta je gurin Maman, tana zare sakatar kuwa ta jishi yana yiwa Anty sallama, dakatawa tayi har tajiyo qarar bude qofar fita kafin tayi wuf ta shige dakin Maman Nuratu na durqushe gabanta tana ci gaba da bata baki bayan Aminu ya gama nasa ya tafi ta shiga, kallon banza suka aikawa juna kafin ta tattare fuska tana kallon Mama tace "Yanzu Mama kawai dan anzo an gaya miki qarya da gaskiya shine zaki ringa zubda hawayenki a kaina bayan kinsan abinda hakan ze iya janyo mun? Duk fa qaryace kawai baqin ciki ake mun dan an ga na samu wanda nake so yake sona anga kwana biyu muna zamab lafiya dake babu wani abu shine ake so a hada mu"ta qarasa tana Harara Nuratu da ta dauke kai dan yanzu tayiwa Maman Alqawarin bazata sake biye mata suyi fada ba amma badan haka ba seta sake gurje bakin yarinyar nan ta nuna mata banbancin dake tsakaninsu. "Idan daidai kikeyi Umaimah kin sani in ma akasin haka ne duka keta shafa, babu abinda yayi mun zafi da sabgarki duk yanda kika ga dama kiyi ba kuma zan sake bata raina akan abinda ya shafe ki ba in Allah ya yarda. Na kuma godewa Allah da ya saka bake kadai na haifa ba kinga idan kin sakani baqin ciki ina da wasunki da zasu sakani farin ciki dan haka kije kiyi duk yanda kimaga yayi miki rayuwarki ce ba tawa ba" tana gama fada ta miqe ta shige bandaki ta barta a tsaye dan daman tuni Nuratu ta fice itama daga dakin. Jiki a sanyaye ta koma dakinsu, kan gadonta ta kwanta tana tunani. ita da kanta ta san tana jawo mutane da yawa ciwon kai amma ya zatayi haka Allah ya halicce ta bata da ikon canza kanta (kodai kika mayar da kanki ba). Wayarta ta janyo ta shiga neman layin Khalil, badai duk akan auransa ne Mama take wadannan maganganun ba bari ta kirashi, da dai tayi alqawarin se tayi sati bata amsa wayar sa ba idan ma yazo gida bazata fita ba amma yanzu saboda farin cikin Mama da kanta zata kira shi ta bashi haquri, ita azo kawai ma ayi abinda za'yi idan ta kama wannan Juma'ar ma a daura musu aure kawai idan yaso duk randa aka a Shirya ayi bikin shikenan dai ta wuce gorin Mama da tsoron ko wanne lokaci ana iya fasa auran ta. Tana can tunani wayar dake ta faman ringin ta katse, sake kira tayi nan ma baa dauka ba seda ta jera masa kira goma amma ko daya be daga ba na qarshe ma rejecting yayi kafin aka kashe wayar ma gaba dayanta kamar yanda Computer ta sanar mata sanda ta sake kira Tayi sororo da waya a hannu tana kallo, tunda take dashi bata zaton ta taba masa kira biyu, duk sanda ta kirashi kome yake ze dakata ya kirata dan baya dagawa sedai ya kashe ya kira, ba qaramin abu yakeyi ba da ze saka ya kasa daga wayarta. Idan ma yana da wani uzuri me muhimmanci tun kafin lokacin yana sanar mata dan kar ta kira bata same shi ba amma shine yau tayi masa missedcalls 10 be daga ba bayan tasab babu abinda yakeyi yana Asibiti gurin Hajiya ko ya tafi gida ya huta. 'Qila ma yana can tare da wannan Jamilar har yana jinhaushi dan an tabata wai yar uba amma sun wani daukaketa kamar ciki daya suka fito' ta raya a zuciyarta, a fili taja tsaki dan ita abinda yasa ta qara tsanarta kenan kasancewar ta ba ciki daya suka fito dasu Khalil din ba. Haka kawai ta bata musu lissafi su kuma sun wani jata a jiki kamar uwarsu daya gaba daya ita kam bata ga dan uban da zata hada kai dashi ba, dan Kishiya ne fa. 'Idan kuma da gaske Nuratu take da tace Khalil din yace ya fasa auranta fa dalilin daya saka yaqi daukar wayarta har yayi rejecting tareda kashe waya gaba daya?' Zuciyarta ta sake raya mata, seta miqe zaune babu shiri ta dafe qirji, Khalil ya fasa auranta tabi ina taga haske Jama'a??? PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 10 Last free page Tun Umaimah na daukar abin wasa har ta fara shiga rudanin rashin sanin abinda Khalil yake nufi da qin daga kiranta. Raba dare tayi tana kiran wayarsa, ya kunna amma haka zata qaraci qara ta tsinke ba tareda an daga ba, ta tura masa da SMS sunfi nawa shima babu amsa, WhatsApp kuwa idan ta tura saqon ma baya tafiya tsabar rudanin da ta shiga bata san ashe Datar ce bata kunna ba. Kafin safiya idanunta sunyi zuru zuru kamar wadda ta kwana tana zawo saboda rashin bacci da damuwar data kwana a ciki. Tana idar da sallar Asuba ta sake gwada kiran layin, call waiting aka gaya mata. Qirjinta ya buga Dam har seda ta saka hannu biyu ta dafe wayar ta subuce daga hannunta. Tun haduwar sa dashi a irin wannna lokacin tasan da ita kadai yake waya, ze kirata idan ya tashi sannan idan ya dawo daga masallaci ze sake kiranta zuwa gari yayi haske kafin suyi sallama toh dawa yake magana yanzu? Ta tambayi kanta. Wayar ta dakko ta sake danna kiran layinsa, still yana waya cikin sa'a ringing biyu taji ya daga da sallama, seda ta saki wata ajiyiyar zuciya kafin cikin karyewar zuciya ta kira sunansa tace "Khalil, me nayi maka? meyasa kaqi daga wayata tun jiya daga baya ma ka kashe wayar gaba daya?" "Am kinga Umaimah ina wani important call ne yanzu kiran da kike tayi yana diverting attention nawa shiyasa na daga ki bari idan na gama zan kiraki" Khalil ya fada daga daya bangaren kafin ta sake cewa wani abu ya datse kiran se kawai ta cire wayar daga kunnenta ta bita da ido kamar zata ganshi a ciki, ita yau Khalil ya kashewa waya. Tagumi tayi hannu bibbiyu gaba daya kwakwalwarta ta cunkushe ta kasa samun damar yin wani tunani, me tayi masa da ze dauki zafi haka? Ita dai a saninta indai akan abinda ya faru jiya ne beci ace yayi fushi me yawa har haka ba indai ba kuma daman yana neman hanyar da ze wulaqantata bane tuntuni amma meye abin daukar zafi anan. Bata san tsahon lokacin data dauka tana tufka da warwara ba seda ta jiyo muryar Mama daga tsakar gida tana kwala mata kira tayi firgigit ta miqe ta fita. Kallo daya Maman tayi mata bayan data amsa gaisuwarta ta nuna mata inda kwanukan wanke wanke suke tace "Ga wanke wanke da shara nan, ki dama kunu kafin a kawo markaden qosai, da wuri Abban ku ze fita sannan za'a kai gidan rasuwar can" tana gama fada ta juya abinta ta bar Umaimah a tsaye kamar wadda aka dasa. Wanke wanke, shara, suyar qosai duk ita kadai? A cire shara da suyar qosan ma dai a duniya abun data tsana yabi bayan wanke wanke kuma kowa yasan da wannan musamman irin na gidansu da yake da mugun yawa kamar kwanukan gidan biki. Ta waiwaya ta kalli kamfacecen tsakar gidan nasu dayayi kaca kaca da ganyayyakin bishiya da qasa saboda iskar da akayi cikin dare jiya wannan kafin ma ta gama ai bayanta ya karye wai ma ina su Nazifi da Arma da suke aikace aikacen tsakar gidan shine za'a ce ita zatayi yau? Yaushe rabon ma da a raba aikin gidan da ita tunda ta shiga Higher institution dan idan ma an sakata ba zatayi a dadin rai ba daga qarshe ma aka dena cewa tayin sedai idan yan hankalin suna kanta taga Maman na aiki ta karba ta qarasa shine yau za'a dawo da abinda ya wuce. "Au kina tsaye tun dazu ko babu abinda kikayi? Ai shikenan ki bari Alhajin ya fito baki hada abin karyawa ba zakiyi bayani" Mama data sake fitowa cikin shirin fita ta fada tana kallonta. Tsintsiya ta dauko ta fara sharar kamar mara laka a jiki ba tareda ta tankawa Maman ba daidai lokacin Anty Saratu ta fito daga dakinta suka gaisa da Maman ta juya tana kallon Umaimah tace "Aa, Umaimah ce da shara yau kuma ina su Arman tun dazu fa naji motsin shigowarsu, nima yau baccine yafi qarfina wallahi se yanzu na samu na miqe" "Na basu markaden qosai sukai, bari naje Yusuf na jirana a waje Rabi'a aka kai Asibiti haihuwa yanzu Yaya ta kira take gayamun babu kowa a wajenta" (Rabi'a yar yayarta ce da suke uba daya). "Toh se kin dawo Allah ya raba, idanan gama abin karyawa a biyo ku dashi" Anty ta fada tayi hanyar kitchen tana ci gaba da cewa "Bari toh na dora ruwan kunun kafin su kawo markaden, Allah ma ya taimaka ruwa be sauka ba jiya yanda aka baje itacen nan a waje da yau mun gayawa aya zaqinta". Har Maman taje qaramar qofar fita daga gidan ta juyo tace " Saratu karki kama mata aikin nan, ita zatayi komai zuwa anjima idan ban dawo da wuri ba ki bata abinda za'a dafa na rana tayi" ta juya ta fice daga gidan. Hawayen takaici ne suka zubowa Umaimah wato da wannan uban aikin za'a horata kenan? Ai wallahi gara kullum a yi mata bulala goma akan wannan uban shara da wanke wanken gidanga qarin girki da itace, ina zata tsoma ranta wai? Ba'a bar mutum yaji da abinda ya dame shi ba za'a rikito masa da wani bala'in. "Halan wani laifin kika mata ko Umaimah?" Antyta fada taba kallo ta amma yanda kasan da dutse tayi magana haka tayi,bata damu ba ta shiga hada murhu ta dora ruwan zafi kafin ta dakko qullin kunun ta shiga damawa daidai sanda Almajiran suka kawo markadan qosan, Wanke wanken tace suyi, sega Abba ya fito daga dakinsa da waya a kunnensa. "Kai kuje abinku idan an gama abinci ku dawo ku dauka, daga yau kun bar aikin nan har zuwa sanda za'a ce ku ci gaba" Ya fada yana kallon su Nazifin, suka tsame hannu daga kumfar da suka kada tareda daurayewa kafin suka fice daga gidan. "Wai Alhaji ya haka ne? Ya zaka hana su yin wanke wanken bayan kasan aikinsu ne yanzu waye zeyi?" Anty ta fada bayan data dakata daga buga qullin qosan da takeyi. Ba kiji Abinda Malika tace bane da zata fita? Ga wadda zatayi nan. Kema ki tashi daga wannan aikin kije ki hadamun ruwan wanka da wuri zan fita" yana gama fada ya juya cikin daki abinsa. Umaimah ta kalla da tayi mutuwar tsaye da tsintsiya a hann, ta fara murnar Allah ya kawo mata dauki dan sharar da takeyi kadai jin bayan ta take kamar ze cire inaga ta kama sauran ayyukan se ga Abba yazo da wannan zancen kuma. Rau rau tayi da ido tana shirin fashewa da kuka Antyn tayi saurin dakatar da ita da cewa "Karma kiyi asarar hawayenki bari naje na same shi wannan wane irin abu ne? Itama Maman banda abi ta ina ita ina saka Amarya aikin wahala ku da ya kamata yanzu ku qara hutawa kafin a fara gyaran jiki idan wani abin kikayi ai hanyoyin horo da yawa ba lallai seta wannan hanyar ba. Ina baze ma sabu na ace za'a sakar miki wannan uban aikin ke kadai dole da sake" ta goge hannu ta ta wuce dakin Abban tana ci gaba da mita. Karon farko da Umaimah taji yau Antyn ta mata abin arziqi dan ko babu komai ta nuna tausayawa akan ta abinda uwa da uban da suka haifeta basu mata ba. Sharar taci gaba dayi tana share hawaye, a kan window ta ajiye wayarta yabda da Khalil ya kira zataji qara amma har sannan bataji ko qarar shigowar saqo ba ga wannan sabon bala'in da taje ciki kuma haka ta qarasa sharar ta kwashe, Ruwan kunun ya tafasa har sannan kuma Antyn bata dawo ba, tasan halin Abban sarai dan haka sahunta a likafa gara tayi abinda zata iya kafin ya fito ya nemi abin kari, ruwan ta sauke a garin juyewa ya dan zubo mata a qafa saboda gaba daya hankalinta baya kan abinda take yi ta kuwa saki qara ta wancakalar da tukunyar a qasa tana yarfe hannu tareda sosa inda ruwanya zuba. Daga cikin daki inda Anty da Abban suke dauki ba dadi suka leqo a tare, da sauri ta qaraso gurin tana cewa "meya faru? Badai qonewa kikayi ba?" Umaimah babu bakin magana se kuka take tana yarfe hannu, Anty ta dubi Abba daya ja ya kwafe a a tsaye tace "Ka gani ko gashi nan haka kawai kun jawo ta qona qafarta, fisabilillahi Alhaji me yasa kake haka? Duk fa abinda Nasiha da Addu'a basuyi maganin sa ba duka ko aikin wahala bazeyi ba. Yanzu gashi nan tun baa je ko ina ba ta qona qafa ta yaya kake zaton zata iya da aikin gidan nan ita kadai? Ko mu din da muke yi ai muna da mataimaka ballantana" ta ci gaba da mita dan itama gwanace a fannin kafin ta debo qulli ta zuba mata akan qafar bayan data tofa mata Addu'a tace "Tafi ki zauna haka kawai da safiyar nan an jawo miki" "Ruwan bada yawa ya zuba ba ba? Ko zamuje a duba mata qafar?" Abba ya fada yana kallo ta, se Umaimah ta girgiza kai har sannan tana hawayen tace "Aa Abba baze tashi ba tunda Anty tayi mun tofi, anjima se naje gurin Ya'u me Chemist ya bani magani" "Allah ya sawwaqe" ya fada tare da juyawa dakinsa. Umaimah ta dingisa ta dauki wayarta ta shige daki, seda ta wanko qafar a Bandaki kafin ta zauna kan gadonta tana sauke ajiyar zuciya fa ruwan kadan ne ya dan zubar mata, yanda abin yazo mata a bazata ne ya sakata sakin tukunyar ta fake da hakan ne kawai saboda ta samu mafita gashi kuma Allah ya fiddata. Number Khalil ta danna zata kira sega kiran sa ya shigo cikin azama ta daga tareda fashe wa da kuka kamar wadda aka cewa Mamanta ta mutu. Be ce mata qala ba ya barta tayi iya yinta, abinda ya ringa qarawa kukan nata qaimi shirun da yayi mata, ta saba idan tana so ta daga masa hankalo kawai zata kirashi ta fasa kuka shi kuma ya ringa lallashi da banbaki kenan har se tayi shiru amma yau yana jinta yai buris da ita dan kanta tayi shiru kafin tace "Wai me nayi maka Khalil kake Azabtar dani haka? Kasan yanda nake ji kuwa? Ko so kake se zuciyata ta buga na mutu sannan zaka yarda da sonka ya gama yi mun illah?" Daga bangaren Khalil dake zaune a office dinsa ya rufe ido ya dafe kansa da hannu daya, shi kadai yasan wahalar daya sha daga jiya zuwa yau saboda rashin magana da ita, gaza jure ganin tana kira baya dagawa yayi abinda ya saka ya kashe wayar gaba daya kenan daga baya kuma ya kunna ya sakata a cikin drawer kawai dan juriyarsa ta kusa qarewa. Yanzun da take wannan kukan jinsa yake kamar ana masa yayyafin ruwan zafi, ita take kukan shi yake jin zafin abin a ransa amma yaya zeyi? Umaimah bata dace dashi ba. Dole ta qarfin tuwo ya yakiceta daga ransa in har yana neman zaman lafiya a rayuwarsa amma yaga abin da kamar wuya dan ji yakeyi wutar son ta tana qara ruruwa a zuciyar sa a maimakon tayi qasa. "Khalil Khalil kana jina kayi shiru" Umaimah ta fada abinda ya dawo dashi daga tunanin daya tafi kenan, gyaran murya yayi yana jin wani na taso masa akan abinda yake shirin aikatawa amma yasan shine kadai gatan da zeyi musu daga shi har ita, "Umaimah duk wannan drama da kike yi ta mecece wai? Kin manta irin zagin da kikayi mun jiya da irin kalaman da kika gaya mun? Kefa kika fada da bakinki babu ke babu ni na fita daga sabgarki to me kuma kike so nayi miki yanzu?" "Duk abinda na fada maka bacin rai ne ya saka, kasan yanda nake sonka nake kishinka wallahi Khalil idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na kashe kaina tsabar baqin ciki kuma duk abinda na fada maka ba daga zuciyata bane kawai raina ne ya baci amma ba da gaske nake ba" Umaimah tayi saurin katse shi. Se yayi wani dan murmushi kafin yace "Bacin rai se ya saka hankali ya gushe kuma? Sannan Kishi ya rufe miki ido kin kasa banbance yan uwana da sauran Mata, idan kinyi haka akan yar uwata ta jini da babu aure a tsakanina da ita Umaimah me ze faru kuma duk randa kika ganni da wata daban, kinga komai yana iya faruwa kenan. Bazan iya saka rayuwata a cikin matsala ba, zan aureki ne saboda ki yi daidai da tsarina ina sonki ina kuma samun farin ciki a gurinki bansan wannan rashin hankali shi kike kira da kishin da kika ce kina dashi ba, a ban aureki ba kin zage ni saboda wata kinga kuwa idan mu kayi aure tsaf zaki iya neman rayuwata dalilin wannan baqin HALIN KISHIn, Se yanzu na gano ainihin abinda ya saka sauran samarinki fasawa nima Allah ne ya soni da rahama ya kawo faruwar hakan da qila watarana ina bacvi sedai kawai na farka na ganni a lahira dalilin abinda bansan mafarinsa". "Allah ya tsareni da kashe ka, ina sonla Khalil dana rasa ka gara na rasa raina, dagaske zanyi fito na fito da duk wadda tace zata shiga tsakanina da kai amma bazan taba bari wani abu ya shafi lafiyarka ba, zan kareka da iya kar kulawata, zan baka farin ciki har qarshen rayuwata saboda kai din kaine Rayuwata" Umaimah ta fada tana fashewa da wani sabon kukan daya ke jinsa har cikin ransa, so yake yace tayi haquri ta dena amma ya rigada yayi making mind di sa akan tarayyarsu ba kuma ya son wani abu da ze karya masa lago, ko wannan doguwar maganar da suke yi ji yake kamar ze rasa qarfin guiwarsa. "Wallahi Khalil ina sonka, idan kace zaka barni rayuwata zata shiga cikin garari, zan iya rasa raina idanka rabu dani saboda na rigada na saddaqar maka da ruhina. Nayi maka alqawari zan zama me maka biyayya bazan taba tsallake umarninka ba, bazan sake tayar maka da hankali akan wani abu ba zan shanye komai saboda farin cikinka koda hakan yana nufin yankewar numfashi na saboda na sani wata rana kishinka ze iya zama ajalina" Umaimata sake fada cikin wani irin kuka me tsuma zuciya da ya saka jikin Khalil daukar rawa, a maimakon ya samu nutsuwa da  kalamanta sema qara shiga rudu da tashin hankali yakeyi, tabbas yana son Umaimah ko yace yana Qaunarta, amma ita a nata bangaren wannan ya zarce Love sedai a kirashi da Obsession. "Umaimah ki dena kuka haka, kiyi haquri amma bana tunanin zamu rayu tare, wannan tsananin kishinda kike dashi a kaina ze iya zamar mana tangarda a cikin rayuwar auranmu saboda a kullum zuciyarki zata ringa raya miki abubuwan da ba haka suke ba, kinga kuma ke yanda kike handling bacin rai, bana so muyi abinda wata rana za muzo muna dana sani. Ina sonki amma bazan iya auranki ba, Kiyi haquri muyi Addu'a Allah ya hada kowannen mu da Alkhairinsa" Khalil ya sake fada abinda ya janyo tsayawar ji da tunanin Umaimah na wani lokaci, sedata kwashi kusan minti biyar shi kansa A nasa bangaren seda Numfashinsa ya rage sauri na wasu sakanni kafin yaci gaba, jiran amsa yake daga bangarenta amma yaji shiru, har ya yi tunanin ko Network ne ya dauke yaji yo ta tana magana cikin wani irin sauti me kama da wadda kw komawa da numfashinta tace "Khalil daman ka shiga rayuwa ta ne saboda kaga bayana? Waya turo ka? Me nayi wa wani daya zabi hukuntani da irin wannan hukuncin me tsanani, kasan yanda Sonka ya yi wa zuciyata illah? Ka qaddara a ranka Khalil tunda na rasa ka babu wata mace data isa ta rabeka, yanda zanqare rayuwata babu aure kaima haka idan kuwa har kayi gigin kula wata to tamkar ka siya mata tikitin tafiya lahira ne dan kuwa sena kasheta, muddin ina numfashi sena kashe duk wata Mace data shiga cikin rayuwarka. Saboda ni aka halicce ka babu macen data isa ta ratsa zuciyarka bayan ni, idan kuma kana ganin wasa ne ka gwada Khalil, ka gwada kula wata mace wallahi sena ga bayanta" ta qarasa tana sakinwani siririn kuka daya saka Khalil zabura ya miqe dan tunda ta fara magana hankalinsa yayi qololuwar tashi, kafin yace wani abu ta kashe wayar. "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" yake maimaitawa yana zagaye office din, dukda kasancewar Ac a kunne take amma zufa ce take keto masa ta ko ina kamar wanda yake naquda, wannan shi ake kira da anyi gudun gara an tadda zago. Shi daya ke neman rabuwa da ita saboda gudun tashin hankali gashi ya gayyatowa kansa babban tashin hankalin daya shallake na da. Kisa fa take iqirarin yi akansa kenan shi kansa tasa rayuwar a cikin hadari take, idan har zata kashe wata saboda shi toh shine ze zama target dinta na farko kenan yanzu yaya zeyi? Meye mafita? Zabi biyu gare shi a yanzu, kodai yayi jahadi ya auri Umaimah ya siyi tashin hankali da kudinsa ko kuma ya barta ta zama barazana ga rayuwar duk wata mace da ze kula, duk cikin wadannan zabin kuma babu wanda yake jin ze dauka dole akwai wata hanya bayan wannan, dole ya nemawa kansa mafita daga Tarkon Umaimah. End of free page Domin jin yanda zata kaya tsakanin Umaimah da Khalil Ku hanzarta biyan 500 dinku zuwa Asusun 8142548705 Opay Maryam Farouk Seku tura shedar biyan zuwa ga 07061838488 Yanzu ma aka fara wasan, Littafin Halin kishi yazo muku da sabon salo tareda tabo jigon da yake jijjiga mata a halin yanzu, ina me baku tabbacin bazakuyi nadamar bibiyar labarin Umaimah ba, kudai ku hanzarta biyan kudin karatun ku se naji ku 💃🏾💃🏾💃🏾 PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *(NADAMAR UMAIMAH)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 11 Umaimah Kuke take tamkar ranta ze fita ta kasa yarda wai Khalil yace ya fasa auranta, wai me yasa? Me takeyi wanda har suke kasa jurewa suke iqirarin bazasu iya ajiyeta a gidan su ba? Laifine dan tayi kishin abinda take so? Ita a ganinta ai abin Alfaharin namiji ne ma ayi kishinsa amma a maimakon ta burge se gashi hakan ya zamar mata kamar wani tabo da kowanne namiji ya tashi yake fakewa da shi ya gujeta. "Wayyo Allah na na shiga uku zuciyata zata fashe" ta fada cikin kuka tana dafe qirjinta da take jin kamar ana hura mata wuta. Anty na tsakar gida tana suyar qosai har sannan tana mitar abinda ya faru ta kwallo mata kira akan tazo ta debi Abin karyawa kafin yayi sanyi, ta kirata yafi sau uku dan haka data tsame na kaskon seta miqe ta dauko plate da cup ta zuba mata komai ta wuce dakin tana cewa "Qila qafarce, a zafin nan ka qone ai dole mutun yaji jiki. Gaskiya dole ma a kaota Asibiti a duba ko bata tashi ba sa bata abinda zata shafa ya rage zugi" dai dai nan ta isa qofar dakin wanda tun daga wajen take jiyo nishi da kuka kukan da Umaimah takeyi tamkar me Naquda. Cikin tashin hankali ta ajiye kayan kan mudubi ta hau jijjiga Umaimah dake kwance a qasa tana juyi fuskarta tayi kaca kaca da Jini da alama Habo tayi in banda wayyo wayyo babu abinda take fadi. Na shiga Uku nu Saratu, Umaimah meya same ki? Alhaji" Anty ta kwala kiran Abba se gashi a firgice dan da qarfi tayi kiran kuma kanaji kasan bana lafiya bane Yanda yaga Umaiman shi kansa hankalinsa ya tashi, bugun lugude zuciyarsa ta shigayi a ransa yana tunanin jinin daya gani a jikinta na meye? Kardai yarinyar nan nema tayi ta lahanta kanta akan rashin hankali? "Alhaji ka kamata mu kaita Asibiti ka tsaya kana kallon mu" Anty ta fada cikin kuka, seya sunkuya ya dauki Umaiman cak ya juya ya fita, bin bayan sa tayi saboda rudewa ko mayafi bata saka ba seda ta kai qofa ta tuna da mai data bari a kan wuta gashi babu kowa a gidan kar kuma wani abun ya sake faruwa dan haka ta koma jikinta na rawa da kyar ta iya tattara hankalinta ta sauke Man gefe ta kashe wutar kafin ta rurrufe sauran kayayyakin ta figi Zanin data samu akan Igiya tayi waje jin An fita da mota. Emergency aka karbi Umaimah, Abba, Anty da Salman da suka kawo ta se zarya suke a qofar dakin da take likitoci nata shige da fice amma babu wanda yace musu komai. Seda aka kwashi kusan Awa daya kafin wani likita ya fito fuskar sa dauke da damuwa ya kalli Abba yace "Bismiah Alhaji muje office ina son magana dakai" "Dr a wane hali take? Zamu iya shiga mu ganta? Anty tasha gabansa tana tambaya, seya girgiza mata kai Alamar Aa yace " Babu matsala hajiya munyi qoqarin ganin ta fita daga dukkan hadari yanzu munyi mata Allurar bacci ne wanda dakyar ta dauke ta shi yasa baza muso ayi wani motsi me qarfi a kusa da ita ba, idan ta tashi se ku shiga ku ganta". Guri ta samu ta zauna tareda Salman Abban ya wuce shida likita, yanda ta shiga tashin hankali tamkar ita ta haifi Umaiman a cikinta, koda yake basu banbanta yaran, yanda Mama ta ja nata ta riqe kamar ita ta haife su dole itama ta cusawa zuciyarta irin wannan aqida duk kuwa da zuga ta yan uwa da qawaye harma da wadanda abin be shafa ba amma da ta toshe kunnenta gashi nan sama da shekaru Ashirin suna zaune lafiya idan ka cire qananan sabani da ake samu tsakanin ko wandanne yan Adam. Suna da kyakykyawar fahimta da alaqa me kyau wanda kuma Maman ce ta assasa. Daman ita Uwargida itace bango, duk yanda ta tsara ta tafiyar da rayuwar gida haka ake dorewa koda kuwa ace an samu fitinanniyar Amarya indai Uwargida ta tsaya akan gaskiya da Adalci ana samun daidaito. A office din likita bayan sun zauna ya dubi Abba yace "Damuwa ce tayiwa yarinyarka yawa data haddasa wa jininta hawa, kuma idan abin yaci gaba bama fata amma ze iya shafar zuciyarta ko ta kamu da ciwon damuwa (Depression). Amma Alhaji a shekarun ta wane abu ne ya dameta haka da har yake barazana da rayuwarta?" Abba da tashin hankalin sa ya nunku, Umaimah keda hawan jini a yan shekarun ta da basu wuce Ashirin da daya? ba yanzu bazata samawa kanta salama a rayuwa ba kullum daga wannan matsalar ta kau wata zata kunno kai shi yama rasa abinda zeyi akan lamarin Umaimah. Yanzu dai Alhaji zamuyi iya qoqarin gurin bata kulawar data kamata sauran aiki kuma yana gurinku, dole kuyi qoqarin sanin damuwarta domin a maganceta amma fa cikin rarrashi bada fada, Allah ya bata lafiya" Likitan ya sake fada kafin ya turawa Abban takadda dayayi rubuce rubuce akai yace yaje gurin biyan kudi da kuma pharmacy a karbi magani. Godiya yayi masa jiki a sanyaye ya tashi ya fita. Salman ya bawa takardar da katin bankinsa yaje ya biya kudin sannan ya kira Mama ya shaida mata abinda ake ciki, "Allah ya bata lafiya tace" sukayi sallama, Abban na shirin tafiya saboda ana jiransa zasuje Gumel wata Gaisuwa ta Abokinsu sega Anty Laure qanwar Mama nan tazo, nan suka barta suka wuce shida Anty Saratu da take son zuwa ta debo abubuwan da zasu buqata. Sanda ta koma gidan yaran sun dawo daga makarantar Asuba, da yake weekend har Sharifa da Abida yammatan ta sun qarasa abin karin sunci tunda Su Nazifi sun gaya musu sunje Asibiti ne, su ta barwa girkin rana ta gaya musu idan sun gama su kai Asibitin kafin ta debarwa Umaimah duk abinda tasan zata buqata ta sake komawa Asibin har sannan Umaiman bata farka ba, Anty Laure dai tace mata ta farka tana surutai aka qarayi mata wata allurar baccin. Khalil A bangaren Khalil kuwa kasa zama yayi a office din, yana tsaye daya daga cikin ma'aikatan sashin su ta shiga office din Balaraba tasha gayu se yauqi takeyi, tuntuni ya gane abinda take nufi dashi amma ko a fuska be taba nuna mata ya fahimceta ba, za dai su gaisa idan aiki ya hada su suyi amma ya qi bata qofar da zata gabatar masa da qudirinsa. Yanzun ma yana cikin wannan hali na tashin hankali da rudu ta shigo tana karairaya ta zauna a kurar dake gaban office din, "Architect ashe ka shigo banga wuce warka ba kuma yau na shigo da wuri" ta fada tana fari da ido, "Uhm" kawai ya iya ce mata dan bashi da nutsuwar jan wata magana a yanzu, seta sake gyara zama tana narke fuska tace "Ni na rasa yanda akayi so ya zama laifi Khalil, tunda ka fahimci ina sonka shi kenan ko kallo me daraja na dena samu a gurinka bare a je ga batun murmushi ko magana me dadi, wai me yasa? Ban kai ace ina sonka bane ko yaya?" A firgice ya dago kai daga dannan wayar da yake ya kalleta, Mansur yake so ya kira dan yana da buqatar wanda zasu tattauna wannan al'amati na Umaimah dashi sega wata sabuwar maganardaga bakin Balaraba kuma. "Sena kashe duk macen data rabe ka" kalaman Umaimah sukayi masa shawagi a kwakwalwa, se ya kalli Balaraba cikin rarrabewar murya yace "Ki fita indai kina son rayuwar ki" "Ban gane ba? Saboda nace ina sonka kake nufin zaka kashe ni ko yaya?" Balaraba ta fada a kidime tana miqewa tsaye, seda ya kalli cikin office din dan ya gama tsorata da Umaimah, ji yake kamar maganar nan da suke yi ma tana ganinsa. Qoqarin daidaita kansa yayi ganin yanda ta rikice take daga murya tun bata tara masa mutane ba yace "Ina da wacce nake so kuma tana da tsananin kishi, idan ta samu labarin kina zuwa gurina zata iya aikata miki komai". Se Balaraba taja tsaki ta koma ta zauna tana cewa " wallahi ka bani tsoro ni na zata ma cewa zakayi Aljana ce ta aure ka, amma mutum fa mace yar uwata zanji tsoro wadda baka ma aureta ba aikin banza kenan nida itan duk daya idan na fita Sa'a ma na same ka" "Balaraba please go out i need privacy" ya fada yana nuna mata hanyar waje, ta yatsina fuska tana kallonsa tace "Wai lafiyarka ma kuwa kaga yanda ka jiqe da zufa duk wannan uban sanyin AC" "Zazzabi nake ki fita ki bani guri dan Allah" ya sake katseta, seta juya tana cewa "Toh ai da clinic kaje aka duba ka amma kazo ka zauna haka duk wanda ya kalle ka yasan ba lafiya ba, Allah ya qara sauqi if you need help ina Reception" taja masa qofar office din ta fice. Bin bayanta yayi ya sakawa qofar key kafin ya kuma kan couch dake gefe ya zauna, Mansur ya sake kira yaci sa'a kuwa ya daga "Malam inada patient idan na gama zan kiraka" Mansur din ya fada bayan daya amsa wayar kafin ya kashe Khalil yayi saurin tare shi da cewa "Kana Asibiti? Gani nan zuwa dan Allah ka sallami duk wasu patient zanzo ka dubani" qit ya kashe wayar ya shiga tattara abinda ze fita dashi, yana zuwa reception tun kafin ya bada excuse suka hau yi masa sannu dan fuskar sa ta nuna yanayin dayake ciki, dakyar ya tuqa kansa zuwa Asibitin su Mansur sanda yaje ya tarar da patient a office din haka ya azazzala Mansur daya sallame su ragowar na waje dake jira se gurin wani likitan Mansur ya kaisu. "Wai Khalil me yak faruwa ne, ka ganka kuwa yanda ka hargitse kamar wanda kura ta biyo me yake faruwa?" Mansur ya fada sanda Khalil din ya zauna akan kujera. "Mansur Umaimah ce, na rasa yaya zanyi da yarinyar nan gaba daya nema take ta zauta ni" Khalil ya fada. Tsaki Mansur yayi yana kallonsa yace "Yanzu daman akan wannan gyaran malam din ne duk ka tashi hankalinka ka tashi na mutane? Ina kao kace kaji ka gani yanzu kuma meya faru, ko Jama'ar tata ne suke firgitaka?" "Gaskiya nima na fara yarda da maganar ka da alama yarinyar nan kanta da motsi" Khalil ya fada kafin ya fara zayyanowa Mansur duk abinda ya faru tun daga case din Jalila har zuwa na Jamila da matsayar da ake akai yanzu. Dariya Mansur ya bushe da ita da har seda Ran Khalil ya baci ya miqe yana cewa "Wato ga Mahaukaci na kawo maka damuwata a maimakon ka bani mafita shine zaka saka ni a gaba kana dariya, ba laifinka bane laifi nane dana gaya maka" ya yi hanyar fita Mansur ya tareshi yana cewa "Matsalata da kai saurin fushi a inda be dace ba mutumina, ga qaramar yarinya can ta gwara maka kai ka hargitse ka rasa abin yi shine ni marainin wayonka daga nayi dariya zaka yi fushi" "Get out of my way" ya fada yana janye hannunsa daga riqon da Mansur ya masa,se Mansur din ya shanye dariyar sa yace "Na dena toh, zauna bari na hada maka coffee ya danyi calming naka" ya zaunar dashi akan kujera kafin ya wuce inda Coffee maker take ya shiga hada musu coffee din yana kallon Khalil dake ta zare ido. "Toh yanzu kai me ka zaba a ciki, fa fasa auran nata ta sheqe duk wacce ka kula ko kuma zaka aure din a yanda take?" Mansur ya fada yana miqa masa cup dake cike da Coffee.  Seda ya kusan shan rabi kafin ya ajiye yana kallon Mansur din yace "I don't know Mansur, nima ban san me zanyi ba. All i know is i do love Umaimah alot, kuma ko maganar fasa auranta da nayi barazana kawai nake mata amma wannan maganar da tayi itace ta qara tsoratani ta saka mun shakku akan ta. Kisa fa Mansur she is saying it with full confidence zata kashe ko wacce mace akaina sedai itama a kasheta, what do you think she will do randa aka ce na aureta ina so na qaro wata kaga ni zata kashe kenan" "Wannan ma ai a rubuce take Abokina kai dare zata bi ta yanka ka sedai da safe kawai ace mana Bayero ya sheqa matar sa ta masa yankan rago" Mansur ya sake fada, wata harara Khalil ya maka masa yace "Kaidai wallahi mutumin banza ne, ana neman mafita zaka sake tayar mun da hankali, please Mansur give me solution, kaina baya aiki kwata kwata i can't think" ya qarasa maganar yana dafe kansa daya ji ya dauki ciwo. "Nifa ko a duk abin nan banga wani abin damuwa ko tashin hankali ba,  daman yarinyar nan kasan bata da saiti ka kwasota babu yanda banyi da kai akan ka kyaleta ka nemi wata ba kace No, se yanzu da ake maganar lessthan a Month biki zakace ka fasa? Yarinyar nan fa har certificate na brain check dinta kace Dad dinta ya nuna maka to tell you that ita dinKwankwararriyar mara jin magana ce har ana zaton tana da mental illness amma kace kaji ka gani a haka kake so se dan yanzu tayi maka wannan dan qaramin shirmen ai ni banzata za'a ja lokaci bama har haka halinta be fito ba kuma ai you should expect morethan this ma duk wani shirme da zatayi maka dole ka shanye tunda kai ka kai kanka. Yanzu dai abinda za'i kawai dai kayi qoqari ka dora mata saiti, ka zare mata ido sosai ka kuma kora mata warning, tunda tana sonka nasan she will comply with all your conditions". Tagumi kawai Khalil ya zabga yana kallon Mansur dake koro bayani kamar besan girman kalmar kisan da Umaimah take ambata ba ko dan bashi tace zata kashe ba oho, jin yayi shiru alamar ya gama ya saka ya numfasa yace "No Mansur I'm scared, like I'm fucking scared wallahi. Dane fa mata suke kurari akan abu su kasa yi amma yanzu kana kallo kullum a social media se kaga sabon case na mace ta kashe Mijinta akanabinda be kai ya kawo bama and you are saying duk kurari kawai takeyi wadanda basu akita ba ma yara qanana zakaga sun aikata, yarinyar nan fa Kishi ne da ita na Bala'i". "Toh Khalil yanzu ya kake so ayi? Kuma maganar wani kishi kowacce mace tana da irin nata, yawanci kum loud ones din nan nasu Kishin iya baki ne suyi hayaniya shikenan, amma masu shirun sunfi hadari, sune suke kashe mutum din lokaci daya a ringa mamakin bazasu iya ba. Umaimah ka barta da shirmenta harda yarinta duk suna damunta amma maganar Kishi ko zata kashe wani saboda kai duk shirme ne tana fada ne kawai saboda ka tsorata and she succeeded ga kanan ka birkice kamar wanda ya bigi motar sojoji amma bazata iya ba, beside wanda zeyi abu ai baya fada sedai a gani a aikace" Mansur ya sake fada, se Khalil ya girgiza kai yace "Aa Mansur, i wish you were there kaji yanda take jaddadamun da zata kashe kowa sannan zan saka kaina a ciki? Aa gaskiya, ina son Umaimah amma barinta shi yafi mun Alkhairi Mansur". "Ok assume ka fasa auranta how about the life of innocent girls da zakayi puting at risk? Kace cewa fa tayi tunda ta rasa kowa ma baze samu ba zata kashe duk Macen data shiga rayuwarka, to is it not better to Marry her and save lives ko kuma ka zabi ka jazawa yaran mutane ko kuma zaka zauna ne babu aure? Think about it Khalil ba fata ba ace qanwarka akayiwa haka in a month time to her wedding mijin yace ya fasa kai baka san zafin abin ba ni na sani because it happend to my sister kana kallo sanadin haka Lubabatu har depression ta shiga, tun farko ai Iyayenta basu rufe ka ba sun gaya maka komai amma zaqin soyayya ya kwasheka ka kasa ganin aibunta se yanzu? Kishi kuma kaine zakayi abinda ze motsa mata shi indai ka kiyaye zaku zauna lafiya, idan kasan halin mutum kaci maganin zama dashi shikenan. In  dai shawara ta kake nema Khalil just go on with Umaimah, kayi Addu'a Allah yasa hakan ya zamar muku Alkhairi". "Shikenan Mansur nagode zanje na cigaba da Addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkhairi" Khalil ya fada yana miqewa tsaye, sukayi musabaha ya kama hanyar fita a ransa sam beji wata magana da Mansur din ta fada ta kama shi ba. Ta ina ma ze fara wannan gangancin? Shima Mansur din qin Allah ne yasa yake gaya masa haka yanzu bayan tun farko ma shine ya fara nuna baya son Alaqarsu a sannan ma zato kawai yake na tana da Aljanu, se yanzu daya samu babban dalilin rabuwa da ita yace masa wai Aa karyayi saboda bashi aka ce za'a kashe ba ina ba wannan maganar. Daga Asibitin su Mansur Asibitin da Hajiyar sa take kwance ya wuce dan su biyun nan sune manyan abokan shawararsa, duk kuma abinda suka yanke masa dashi yake amfani toh yau Mansur yayi Failing yanzu saura Hajiya dukda be so ya tado mata da maganar tana Asibiti yaso ace se ansallame ta amma lokaci yana tafiya. Ko jiya da daddare seda tayi mitar me yasa ba'a kai lefe ba aka tsaya saboda jinyar da takeyi ta kuma ce a cikin satinda za'a shiga ko ba'a sallameta ba a saka rana akai. Daga yanayin sallamar sa Hajiyan ta gane babu lafiya, yaja kujera ya zauna suka gaisa da Mama Talatu matar qanin Hajiyar ce da suke matuqar shiri tun qaninnata yana raye har yanzu kuma daya rasu suna zumunchi sosai yanzun ma ita take zaman jinyarta. "Ango kasha qamshi, yanzu fa zancenka muke Hajiya tace na miqa mata waya ma ta kiraka ashe kana tafe" Mama Talatun ta tsokane shi, se yayi murmushin da be kai zuciya ba ya shiga gaishe su, mace ce me wayayya daga yanayin da Khalil dinya shigo ta fuskanci da magana a bakinsa dan haka ta miqe bayan ta tura masa kayan karin da su Habiba suka kawo tayi waje ta basu guri dan bata san maganar da yake so yayi kota sirri bace. Hajiya dake qare masa Kallo tunda ya shiga dakin tace "Babana lafiya kuwa? Kaga fuskarka yanda tayi meya same ka bayan ka bar nan jiya, koda yake tun a daren na fahimci baka da walwala ko jikin Umaiman ne yaqi dadi?" Sunan Umaimah data ambata ya qara saka zuciyarsa tsinkewa, toh Mansur ma yaqi bashi goyon baya inaga Hajiya datafi kowa son hadinsa da Umaimah bama ya zaton zata saurari duk abinda ze zo dashi amma koma yaya ne dole ya gaya mata tunda dai bashi da wadda ta fita. Kansa ya shiga sosawa ba tareda sunhada ido ba yace "Hajiya daman akan maganar tane, inaga Kawai a dakata da maganar kai kayan nan yanzu" "Kamar yaya a dakatar da kai kaya Babana? Ina saura sati hudu daurin aure ya kama yau? Idanba'a kai lefe yanzu ba har se yaushe za'a kai musu bayan da tun satin daya wuce za'aje wannan tsautsayin ya faru, idan ma dan maganar kudi da akace ka bada ne baka dasu ka barshi zan gayawa Sa'adah ta ranta a qarasa komai in yaso ni daga baya se na bata" Hajiyan ta fada cikin kulawa tana kallonsa. Tasan harkar biki da cin kudi kuma Khalil din yayi Namijin qoqari sosai tundaga kan gyaran gidansa daya dawo kamar sabo kai bakace an taba rayuwa a ciki ba har zuwa kan lefen sosai ya saki kudi akayi masa siyayya dukda Yan uwansa Mata sun saka hannu amma shi yayi rabi da kwatan kayansa. "Hajiya ba maganar Kudi bace ta saka ita Umaiman ce kawai nake ganin kamar zamn mu baze yuwu ba saboda HALIN KISHInta" Ya sake fada kansa a qasa. Se Hajiya ta saki murmushi taredagyara zamnta dakyau tana kallonsa tace "Se yanzu kenan yan tsurku da munafuncin suka tarar dakai, Baban yaushe ka fara saurarar qananun maganganu na mutane? Tun sanda ka fara neman auran yarinyar nan babu kalar gulma da tsugudidin da ba'a kawo mun akan ta ba ance baqin kishi ne da ita, bata da nutsuwa, aa mutuniyar banza ce kai har akwai wadda tace ta zubar da ciki shi yasa sau uku ana saka mata ranar aure ana fasawa". PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK(UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 PAGE 12 Da sauri Khalil ya daga kai ya kalli Hajiyan jin wannan qundumemen batu, ta daga masa kai da sigar tabbatarwa kafintaci gaba da cewa "Tabbas, magana ba irin wadda ba'a gaya mun ba amma duk naji na toshe kunnena saboda nasan da cewar qarya ce. Tun kafin naje gidan yarinyar seda yar uwarta ta zayyana mun komai akanta tun kama daga kan Kishin da mutane suke ganin tanayi yayi yawa har halin tsiwarta da komai yar uwarta bata boye mun ba. Haka zalika da naje gidan su Mahaifiyarta ta sake tisa mun tamkar yanda yar uwarta ta fada abinda ya qara musu qima kenan a idona dukda take tasu ce basu boye aibunta ba sun bayyana wanda shine gaskiya dan aure ba'ayi masa rufa rufa, idanma an rufe shi hali baya buya dole wata rana ze bayyana kansa kuma kaima nasan ka san komai kuma kaga kaji ka gani kana sonta a hakan, se yanzu da dan lokaci ya rage sannan zaka bari hudu bar shedan da gulmar mutane tayi tasiri a zuciyarka? Meye matsalar ta, kishi koh? Toh kaje ka tambayi Hajiyar Gaya (Mahaifiyarta) zata baka tarihin quruciyata, kuma yau da Mahaifinka yana raye da ka tambayeshi shima ya baka labarin Kishina dukda haka kana iya zuwa gurin Babanku Jibril (Babban Aminin Mahaifinsu ne) dan dashi aka sha gwagwarmayar komai. Dan haka idanma abinda ya gigitaka kenan kazo kamar wanda aka biyo toh kama dena wani tunani akan batun kishi kowacce mace zaka aura tana da kishi sedai kawai na wata yafi na wata zafi, kuma wata tafi wata iya danne nata, in dai kuma kace zaka ringa daukar zugar mutane akan iyalinka toh kana tareda matsala kuwa. Dan wani qyashi da hassada ce zata saka ya ringa kawo maka gulmar da zata haifar da rashin zaman lafiya a gidan ka". Shiru Khalil yayi, daga yanda hajiya take jero masa bayanin nan ya tabbatar da babu wata kalma da zeyi amfani da ita da zata saka ta ga baqin Umaimah, amma dukda haka baze sare ba dan shi harga Allah ya tsorata da auranta saboda duk wadanda zasu ce yayi basune zasu zauna da ita. Ba fata ba kuma ranar da abin qi ya faru ace shi ya jawo wa kansa dan haka tun kafin azo wannan qadamin dole ya nemar wa kansa mafita, idan Kuma Allah ya qaddara faruwar auransu shi kenan, amma dai Allah ya gani yayi iyawarsa dan ya tseratar da kansa daga wahala. Zaman sa ya gyara yace "Hajiya wannan ba zancen zugar Mutane bane, jiya fa Hajiya saboda mun riqe hannu da Jamila shine tayi fushi ta tafi ko mota ta qin hawa tayi se Nuratu kawai na mayar gida ita ta hau Adaidaita, sannan bakiji abinda ta ringa fadamun ba har cewa tayi ta fasa auran ma gaba daya ita. Toh Hajiya tayi haka akan Jamila da tasan babu aure a tsakanin mu inaga kuma idan ta ganni tareda wata macen? Ni dai tsoro nakeji Hajiya, kina kallo dai yarinyar nan matar Hafizu na can qasan layi da ta cakawa masa wuqa saboda zeyi aure, yanzu da yazo da qarar kwana da tuni fa an manta da babinsa". Seda Hajiya ta gama jin sa tsaf ta kalle shi da hararar wasa tace "Nidai Babana takwaranka kafin ya mutu se da yayi mata takwas kuma hurhudu suka zauna idan wata ta rasu ya maye da wata kana kallo da dai wayon ka ya bar hudu rayayyu gashi nan kuma har yanzu suna zaune a cikin gida guda dukda baya nan, se kai kake tsoron guda daya jal Khalil? Kuma banda abinka Mijin da ake so ai shi ake kishi. Da bata sonka idan matan duniya zaka kula ko a qasan takalminta sannan maganar Jamila ai dole tayi kishi yanda kuke abu kamar wasu qananan yara su Allah ne be taba kai idon Mazajensu sunga kuna wannan rungumar da riqe hannun ba da tuni sun taka muku burki, nasan kuma kai yanzu da ace zatayi haka da nata dan uwan se anji kanku dan kaima ai zani ce ta taradda muje zuwa kishin ne da kai.   Haba idan mutum ya girma yasan ya girma mana ai koda suke muharramanka kunyi girman da kun wuce irin wadannan abubuwan indai ba lalura ba yanzu ina kai ina hada jiki dasu yanzu ai ko dan gudun bacin ran matarka ka kiyaye ai" "Yanzu dai Hajiya duk baki fahimci abinda nake nufi ba" Khalil ya fada kamar ze fasa kuka, hujjar da yake ganin ze fake da ita ya fada amma bata da niyyar fahimtar sa sema qara goyon bayan Umaiman takeyi, shi kuma baya so ya fada mata furucin ta na na kisa saboda gudun abinda zeje ya dawo toh yanzu yaya zeyi? Haka ze zuba ido yana ji yana gani a qulla masa ita. "Idan ma wani ne ko wata ya zugoka zaka zo ka mayar da mutane qananan mutane tun wuri ka koma ka gaya musu basuyi nasara ba, koda wani ya zabo maka ita ba kai kace kana sonta zaka aureta ba? Daga Ilun har Zahra'un ai na gaya musu babu wannan maganar dan dukda Badawiyya take tawa amma nasan Umaimah ta fita Nagarta nesa ba kusa ba" Hajiya ta fada cikin tsare gida, seya daga kai ya kalleta da mamaki yace "Hajiya Kawu Ilu kuma? Me yace miki ni bamuyi wata magana dashi ba wallahi rabona ma da gidan sa tun sanda na kaiki kika duba Fauzan da bashi da lafiya, kuma magana tsakanina da Badawiyya da take tsohon zance, ita fa taqini kuma ni ban sake koma mata ba shine yanzu zasu dawo da maganar" Oho dai duk ma yanda kukayi nidai na qara jaddada musu da babu wannan magana kuma koda ace babu saka ranar wata akanka bazaka aureta ba. Nan yazo yana zancen wani a qarfafa zumunchi tunda daman ka taba nemanta ayi haquri da abinda ya wuce yanzu ta gama karatu kamata yayi ka dawo ayi aure ita wannan tunda yarinyar mutane a basu haquri ace ka fasa gida be qoshi ba ba'a kaiwa dawa ba, nayi masa fata fata be daddara ba ya sake turo uwarta itama na silleta tas Wato ada tunda baka da abin duniya shi yasa suka qi hadin yanzu ka samu Allah ya buda maka shine zasu lallabo yarsu taqi auruwa su liqa maka ba yanzu ko nan gaba babu wannan maganar dan hakan idan ma sune suka hure maka kunne, kai ko Asiri suka maka sena warwareshi auren ka da Umaimah babu fashi sedai idan iyayenta ne sukace sun fasa baka". Sababi Hajiyan ta hauyi tana tariyo masa abinda ya faru a baya lokacin daya taba neman yar qanwar Babansu Badawiyya, ganin abinbana qare bane yayi musu sallama a hanya yana tafe yana mamakin wai Kawu Ilu da Goggo Zara'u ne suka iya duban idon Hajiya suce ya komawa Badawiyya. Kusan ze iya cewa a rayuwar sa kaf itace mace ta farko daya taba sha'awar yin zaman aure da ita duk da asannan daga shi har ita suna da qananun shekaru basu kai ga isa aure ba. Sunyi soyayya a lokacin Mahaifinsa yana da rai duk abinda ya samu Badawiyya lokacin yana karatu a UK idan z dawo haka ze shaqo mata uban akwati da tsaraba su karbe baki har kunne a sannan babu ya ita a Yayan dangi bare aje ga yan unguwa. Bayan rasuwar Mahaifinsu lokacin da al'amura suka chanza suka rasa duk abinda suka mallaka se kuma aka bude sabon shafi, da farko bashi da matsala da yarinyar amma idan yaje gidansu ba kamar yanda ya saba ba Goggo Zara'u ta ringa haba haba dashi kenan kamar sabon jariri, abinci kuwa idan aka fara jera masa kwanuka se yace a barshi haka amma da rayuwa ta canza ya zama ko ruwan sha seya roqa, tafi tafi ma zancan aka koma yi a soro dan se Goggonn taji zuwan sa zata baje kolinta a palour da suka saba zama suyi hirar, gaisuwa kuwa tana shan qamshi da yatsina zata amsa masa daga baya ta hurewa yarinyar kunne itama ta fara lale masa nata katin rashin mutunchin tunba da samari suka yo mata caa ba saboda a sannan ta sake zama cikakkiyar budurwa gata da kyakykyawar sufa. Wulaqanci na qarshe da akayi masa da ya saka ya janye jikinsa gaba daya shine bayan ta qare secondary school, a yanda aka tsara acan baya data gama za'a daura musu aure dan da ita da iyayenta basu da sha'awar taci gaba da karatu dukda Khalil din yaso haka sukaqi, se gashi wata rana yaje gidan Babanta da kansa ya tareshi akan wai ya dakata da zuwa saboda Badawiyya zata fara zuwa makaranta kuma zuwansa ze ringa dauke mata hankali. Sosai yaji dadi, ya tattara dan abinda yake hannunsa duk da a lokacin suna cikin matsi sosai yace tayi littattafai se gashi ashe makarantar tara samari ta shiga, qofar gidansu ta zama majalissar Samari da Alhazan birni wannan yazo wannan ya tafi Goggo Zara'u ko murna yarta me farin jini kowa yazo ya ajiye masu abin arziqi. Tun tana boye wa karya sani har ta fito fili take abu ta ko a gaban idon sa ne zata tsaya da saurayu, Tsabar cin fuska wani lokacin idan zatayi zancen ya zama Baqon na musamman ne ma nan gidan su take kawo shi, da yaso yayi magana Hajiya tace ya barsu, duniya ce ta ishi kowa se gashi tun ba'aje da nisa ba kasuwar samarin ta watse ba tareda an samu na aure ba, shine kuma saboda tsabar rashin kunya suka dawo suna rara gefe harda cewar ya fasa auran wata ya komawa yarsu tunda daman Asali ita ya fara nema dan Adam kenan. Gaba daya haka ya qarar da ranar daga tunanin mafitar lamarin Umaimah se jinjina qarfin hali irin na iyayen Badawiyya, toshi yanzu ko ya rasa macen aure me zeyi da ita? Yarinyar da ba daya ba biyu ba yasha ganinta a mabanbantan Hotels a lokacin da take ganiyar rashin mutunchinta ta kuma maze tamkar babu wata alaqa ta jini bare soyayya a tsakanin su ita za'a ce ya koma ya aura ai gara ya qarata da Umaimarsa sau dubu dan yana son abarsa, halinta ne kawai yake bashi tsoro. Harya kwanta bacci be sake ganin kiranta ko saqon waya ba, kenan da gaske ta haqura da auran itama ta daura sabuwar Aniyar addabar rayuwarsa. a ransa ya qudurce baze nemeta ba, idan ta sake kiransa ze haqura ya dauka zabin da Allah ya masa kenan daga nan ya gindaya mata duk sharudan da suka kamata idan taji ta yarda shikenan amma idan bata kirashi ba tabbas sedai Hajiya tayi haquri amma wannan magana ta watse babu ita hakan yana nuni da rabuwar ce mafi Alkairi. Umaimah A can Asibiti kuwa se Yamma Lis Umaimah ta farka daga dogon baccin dolen da likita ya sakata, jikinta yayi tibis dan banda idonta babu abinda take iya motsawa se kallon yan uwanta dake ta kaikawo a dakin suna mata sannu takeyi. Anty Saratu da Anty Hafsa babbar yayarsu ne suka kamata suka kaita Bandaki saboda Fitsari datace tana so tayi daga nan Antyn Hafsan ta hada ruwa ta taimaka mata tayi wanka ko zata ji qarfin jikinta hakan kuwa ya taimaka tana gamawa ta dauro Alwala suka fito. Cikin kayan da Anty ta debo mata dazu ta bata duguwar riga mara nauyi ta saka, shayin data hada mata kafin tayi wanka ta miqa mata ta shiga yatsina fuska alamar bazata sha ba, da rarrashi da komai suka sakata tasha shayin, se gashi ta bige da cin faten dankali da Yaya Hajiyayye ta kawo taci sosai ta dora da wani kofin shayin nan da nan kuzarin jikinta ya fara dawowa dan harda Yunwa a mutuwar jikin nata saboda ko karyawa batayi ba. Seda tayi sallar Azahar da la'asar kafin ta idar aka kira Magriba dan haka ta hada tayi, ta mimmiqe qafafu akan sallayar ya gawar sababi anata yi mata sannu tana gyada kai tana qare musu Kallo, kowa ya hallara a dakin banda Mama, can kawai se ji sukayi ta fashe da kuka na irin wanda ya tuni wani gagarumin abu da yake ci masa rai. Gaba dayansu suka gigice saboda yanda dazun wata Nurse me shegen kanbama abu ta rikitasu akan jikin Umaiman, fadi take Zuciyarta ta kumbura qiris ya rage ta fashe dan haka dole a lallabata kar a kuskura wani abu ya sake bata mata rai, zancenta ya gigita Yaya Aminu har seda ya tafi gurin likita babu shiri dan ya tabbatar nan fa likitan ya rufe Nurse din da fada yana tuhumarta akan me zata fadi qarya abinda ba haka ba, ya gaya musu gaskiyar abinda yake damunta, babu abinda ya samu zuciyarta kawai dai idan taci gaba da shiga halin damuwar ne suke ganin zata iya samun matsala. "A haf duk daya abinda ta fada kenan itama ai kawai dai saboda hankalin mu ya kwanta ne ya saka ya wani sassauta abin, koma menene mudai fatan mu Allah ya bata lafiya" Yaya Hafsa ta fada. "Umaimah menene? Meya same ki ko jikinne?" Suka hada baki waje fada kowa na qoqarin zuwa inda take, mutuniyar an samu yanda ake so ai nan ta kware baki ta ringa zunduma ihu baji ba gani, idan ta tuna wai fa Khalil yace ya fasa auranta se taja wani Kukan me hade da shashsheqa ta dafe qirji duk tabi ta ruda bayin Allah sunyi cirko cirko akanta, Anty Momy matar Yaya Aminu ce tayi hanzarin tafiya kiran Likita, yazo ya ringa balbaka musu masifa kuwa akan me zasu tada mata da hankali, me suka fada mata daya saka ta kuka haka kowa dai tayi gum da baki tana kallon ikon Allah to su me suka ce kuma? Qarshe da daya da daya suka silale aka barta ita da Anty bayan da likitan ya mayar mata da ruwan da aka cire mata, se lallashin ta yake tana ajiyar zuciya kamar wata yar baby, bw bar dakin ba seda ya jawa Anty kunne akan a guji abinda ze bata mata rai ko ya sakata kuka, magana idan ba dole ba ayi shiru saboda basu sani ba ko zasu fadi wani abun da ze sosa mata rai. Haka suka kwana Anty dole tayi gum daga sannu se idan zata tambayeta ko akwai abinda take da buqata ne, nan Umaimah ta samu yanda take so, kwana tayi tana tsara yanda cikin ruwan sanyi zata saka su nemo mata Khalil su sasanta ba tareda hankalinta ya sake tashi ba dan ta rantse ita da Khalil mutu ka raba, badai yace ya fasa auranta ba wallahi. A haka ta shafe kwana uku a Asibitin kafin aka sallameta, sau daya Mama taje dubata dan ita dai tace kallonsu kawai takeyi amma bata yarda da wannan rashin lafiya ta Umaimah ba, Anty data sha zaman jinya har qaramin ciwo tayi itama bayan an sallamosu saboda fi'ilin datasha gurin Umaimah. A gidan ma bata haqura ba sabon salo ta fito dashi na zaman daki bata leqowa ko qofar dakin tana ciki duk kuma sanda za'a leqata kuka takeyi seda ta kwashe kwana hudu tana wannan halin abinda ya fara damun Mama kenan dake daukar abin nata da a matsayin wasa gashi har sannan basuji wata magana daga bangaren Khalil ba, a lissafi kuma biki yana ta qaratowa dan saura sati uku ne da kwana biyu. A kwana na hudun ne Maman ta kasa shiru da safe ta samu Abba yana shirin fita tace masa "Alhaji yanzu kana gani haka zamu zubawa Umaimah ido tana nema ta illata kanta? Bafa ta fitowa ko tsakar gida tana cikin daki, abinci kansa se Saratu tayi da gaske sannan take ci babu abinda takeyi se aikin kuka gaba daya ta lalace a yan kwanakin nan ta fita hayyacinta". "To yanzu Malika me kike so ayi? Na kaita Asibiti an bata magunguna likita ya kafa mata dokoki da sharuda ai ita ba qaramar yarinya bace da za'ace se anyi mata tuni akan muhimmancin lafiyarta, tunda abinda ta zabawa kanta kenan taga ya fiye mata se tayi duk wanda zeji mata babu dadi ai ba kamar ita da ciwo yake a jikinta ba" Abban ya bata amsa cikin halin ko in kula. "Haba Alhaji be kamata kace haka ba mafita dai za'a nema tunda dai ko yaya Umaimah fayar muce muna kuma son farincikinta. Damuwarta dai gaba daya akan yaron nan Khalil take, kaga tun waccen ranar bana tunanin ya sake zuwa kuma basu turo wani babba akan maganar tana nan ko sun fasa din da gaske ba.." Katseta Abba yayi da cewa "Toh se ku jira duk daren dadewa ai zasuzo, idan suna ciki za'a sani idan ma fasawar sukayi duk za'aji. Kawai a ci gaba da shirye shiryen ita Nuratu tunda shine magana dahir a yanzu ita kuma zuwa lokacin se muga abinda Hali yayi". "Baza'ayi haka ba Alhaji kenan haka zamu zuba mata ido a cikin wannan yanayin? Dan fa baka leqawa ka ganta ne Alhaji kai da kanka nasan se tabaka tausayi wallahi" Maman ta fada cikin muryar karaya, se Abba ya kalleta yace "Ai saboda karma naji tausayin nata ta sakani yin abinda banyi niyya ba ya saka bana leqawar, sannan duk ki dena wani zagaye zagaye nidai bazan kira yaron nan ko iyayensa ba akan maganar auransu a yanzu tunda damab ba tallanta na kai masa ba shi ya gani yace yana so. Akwai iya lokacin dana diba idan basu magantu ba a sannan ni da kaina zan tattara komai da suka kawo a mayar musu shikenan magana ta qare. Kije kiyiwa yarki fada ki nuna mata muhimmancin tawakkali ba komai da kake so a rayuwa kake samu ba, kuma sau tari abinda kake so be fiya zamar maka Alkhairi ba dan haka ta bawa zuciyarta haquri, ta kuma qudurce koda Khalil ko babu shi zata rayu. Sannan shi aure lokaci ne duk sanda ubangiji ya tsayar mata zatayi" yana gama fada ya dauki jakarsa da waya dake ajiye yayi mata sallama ya fice. Jiki babu kwari Maman ta biyo bayan sa tana yi masa Adawo lafiya, dakinta ta shige gaskiya a wannan gabar bazata zuba ido yarta ta shiga depression akan Namiji ba. Gara susan abinda ake ciki, idan ya fasa da gaske ya fada da Addu'a da roqon Allah zasu san yanda zasu cire mata sonsa daga zuciyata amma wannan zaman rashin sanin madafar baze kaita ko ina ba. Gaba daya hankalinta a rabe yake bata ma da nutsuwar da zatayiwa Nuratu nata shirin auran, tana murna Allah ya kusa yanke mata zata aurar da yammatanta gaba daya ashe da wata a gaba toh Allah ya zaba abinda yafi Alkhairi. Da yammacin ranar Jikin Umaimah yaqi dadi, kuka ta dasa tun rana tun tana na qarya sega abu na neman ya zama na gaske se kokawa take da numfashi kamar me cutar Asthma. Suna tsaye a tsakar gidan suna jiran Nura dan maqotansu ne Salman ya nemo shi dan akai Umaiman Asibiti a motarsa sega Yaya Hajiyayye. "Alhamdulillahi gara da Allah ya kawo ki Hajiyayye, Sharifa kamata muje tunda ga mota" Anty dake tsaye kan jiki kan qarfi akan lafiyar Umaimab ta fada. Se Hajiyaye ta bisu da kallo ta shiga tambayar meya faru, ganin halin da take ciki yasa ta bawa Salman key tace ya kaisu kawai su zasu biyo bayansu a Adaidaita aka ciccibi Umaimah aka yi Asibiti da ita. Tareda Mama da Hajiyayen suka hau Adaidaitan, a hanya take gaya mata dalilin zuwanta Hajiya Maryam Babbar Yayarsu Khalil ce ta kirata akan gobe zasu kawo lefe, tana ta bada haquri na rashin sanar dasu da wuri saboda sun so su bari se cikin weekend Hajiya ta dage akan se an kawo goben, "Na gayawa Yaya hafsa da Naziyya suna hanyar zuwa gidan yanzu suma nasan saboda mu shirya yanda za'a tarbi baqin ga kuma wata sabuwa ta tashi" Hajiyayyen ta fada. "Alhamdulillahi, ai da tun a gida kika bada wannan daddadan labarin da ba se munzo Asibiti bama" Mama ta fada cikin tsananin murna, se Hajiyayye ta kalleta da rashin fahimta, a taqaice Maman ta fayyace mata yanda akayi tun zuwansu dubiyar Hajiyar Khalil da dalilin kwanciya ciwon nata. "Amma Umaimah anyi mara hankalin yarinya, setayi abu kuma tazo ya dameta, tace ta fasa toh duk wannan ciwon na magani da menene takeyi in banda tsabar iskanci. Wallahi Mama har tunani nake kar azo ayi abin nan taje ta zubdawa da mutane mutunci da mugun halinta, dan ma Allah ya rufa asiri ta rabu da wadannan yan iskan qawayen nata da suke qara ingizata tana rashin hankali" Hajiyayyr ta fada cikin jin haushin abinda ya faru, "Kedai addu'a zamu cigaba da yi mata ina tayi ba dare ba rana Allah ya shiryeta, yasa kuma Auran nan ya zama Alkhairin da kowa se yayi farin ciki dashi, kuma ina ji a jikina in Allah ya yarda auranta da Khalil shi ze kawo qarshen duk wasu fitintunu nata, se kowa yayi mamakin yanda Umaimah zata dawo" Mama ta fada daidai sanda suka sallami me Adaidaita Hajiyayye ta amsa da "Amin". Sun tarar dasu a Emergency suna zaune babu gado, kusada Umaimah dake ta kuka tana Jan numfashi Yaya Hajiyayye ta tsaya tana kallon Anty tace "Nifa nazo muku da good news gobe za'a kawo lefen Umai, se gashi ashe ita tana qoqarin sheqawa lahira ma. To bari na kirasu na gaya musu ashe tace ta fasa bani da labari dan in suka rigada suka  kawo fa kaya ya shiga sahun gado mu zamu rabe abinmu". Kafin wani ya bata Amsa Umaimah ta yunqura ta dire a gabanta tana zare ido tace "lefen wa Maman Asad? Kardai kice mun nawa da gaske Khalil be fasa aure na ba?" Hararar wasa Hajiyayyen tayi mata tana danne dariyar data taso mata saboda irin alkafurar da Umaimah tayo tace "Toh in ba naki ba wace za'a kawo lefe, kinsan dai an kawo na Nuratu koda yake yanzu  nake samun labari kin fasa gara tun wuri na sanar musu su san abin yi..." "Wallahi qarya nake ban fasa ba" Umaimah ta katseta kafin ta miqe tsaye kamar wata iska Feee tayi waje bakin ta a washe yanda kasan an mata bushara da Aljanna mutanen dake zaune a gurin suka bita da kallo, ranga ranga aka shigoda ita gashi ta miqe akan qafarta har tana gudu wannan abin Al'ajabi da yawa yake. PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 PAGE 13 Dole suka tattaro suka koma gida dan ita mara lafiyar ma Adaidaita ta tare zata hau seda Yaya Hajiyayye ta zageta tas kafin ta kama kanta ta rage zumudin murnar da takeyi. A hanya kuwa bakinta yaqi rufuwa, tambayarsu take dagaske ne gobe za'a kawo lefen? Kenan Khalil be fasa ba amma me yasa ya dena kiranta harta kwanta Asibiti beje babu wanda ya tankata se Anty ce me biye mata dan gaba daya haushi take bawa sauran. A gidan ma haka suka hadu suka cashe mata, sakarya, mara aji sunkirata dashi yafi sau a qirga amma ko a jikinta ita kam hankalinta naga kiran wayar Khalil da tun dawowarsu take gwadawa amma ana gaya mata a kashe take amma taqi haqura. "Wallahi tun wuri idan zakiyi hankali kiyi dan Maza ba'a yi musu wannan rawar jikin, kinja ajin ma ya Allah ya cika ballantana kin nuna masa duk duniya babu ya shi muna nan wata rana se kinji yace ze dakko wata idan kin nemi ba'asi yace saboda biyayyarki tayi yawa" Naziyya ta fada. "In banda sharri Naziyya a ina aka taba cewa biyayyar mace tayi yawa? Yaya Hafsa ta fada tana dariya, Naziyya ta Harari Umaimah dake jifanta da wani kallo saboda ambaton auro mata wata da tayi tace " Wallahi fa Yaya baki taba ji bane? Nan ga maqociyata nan da aka mata kishiya matar nan babu ta inda ta ragi bawan Allahn nan amma da yake Namiji Namiji ne se gashi wai zeyi aure saboda ita komai yace mata bata musawa zatayi wani lokacin ma bece tayi abuba zatayi shi kuma baya son haka, yafi so wani lokacin dai itama ta dan nuna nata ra'ayin bawai komai ya fada tace daidai bane, ai kuwa yanzu ya samo me ido a tsakiyar kai, tace tana jinsu wani lokacin zata cancareshi amma mutumin nan ko a jikinsa tunda shi abinda yasa ya aurota kenan toh balle Umaimah me suma akan Saurayi idan akayi auran kuma ai se mutuwa". Qunquni ta shigayi qasa qasa tana cewa "idan gaba da mutuwa ce zanyi ina ruwan mutum, haka kawai baza'a fadi alkhairi akan abu ba ai se ayi shiru nidai babu ruwana baqin bakin mutum ya qare akansa" ta harare su kafin ta fice ta bar musu falon. Tattauna abinda ya kamata ayi goben sukayi, abin yazo da sauqin musamman da akace mazane zasu kawo dan haka nan take Yaya hafsa ta kira mutuniyarta *Zuhree snacks bar* suka saka orders Meatpie, samosa da springrolls ta kuma tabbatar musu babu matsala zasu karbi order su goben akan lokaci. Sosai Yaya Hafsa take jin dadin hulda da ita saboda cika alqawari, bayan dan karan dadi da snacks dinta suke dashi ga sauqin farashi duk wanda yaci se ya qara musamman tunda taje taga yanda takeyin aikinta komai a tsaftace shi yasa duk wata hidima data tashi da ake buqatar snacks bata sanya gurin nemo Zuhrii Snacks. (Domin order snacks dinku na kowanne irin taro, koma haka kawai ki siya ki ajiye a fridge ki ringa soya abinki kina ci ku tuntubeta takan lambar waya 08146426724) Se dab da magriba suka gama komai dan hatta da kajin da zasuyi pepper chicken an siya an gyara sukayi marinating nasu kafin aka saka a fridge akan Nuratu zata soyasu da safe kafin suzo a qarasa hadawa. Sun kira Aminu sun gaya masa shi kuma ya sanar da kawun nan su daya kamata su halarci karbar lefen yaceze kawo ruwa da lemo iya adadin da sukace za'a bayar Baba Abdullahi kuma yace ze bada tukuici danshima sun yanke abinda zasu bayar idan an kawo kayan. Har Kowacce ta dauki jakarta zata wuce kenan Naziyya tace "Af an gama lissafin snacks banji an saka da cake ba, ko iya su Samosan za'a basu?" "Ai kuwa dai nima shaf na manta, Hafsa ki sake kiranta ki gaya mata dashi kar lokaci ya qure" Hajiyayye ta fada, se Hafsan ta zaro wayarta tana cewa "Ina sane dashi, kunsan ko wanne abu yana da gwani, to wata sabuwar gwana na samo a fannin cake. Sunanta *Mcubes bakery, ranar da Baban Mimi ya shigo da wani loaf cake yace a gurinta akayo musu order tsabar dadi har takaddar na hada na cinye, yanzu kuwa cupcakes din yara na makaranta gurinta muke siyowa kar kuso kuji dadin sa koda yake zaku dandana kuji gobe idan an kawo, kai wannan mata ta iya cake, dadinsa baya faduwa se kawai idan kaci bakinka ya gaya maka" "Gaskiya Yaya Hafsa ki fara sana'ar tallah irin wannan koda cake haka ni har kinsa na qagu naci naji yanda yake, bani numberta ma na ajiye a wayata saboda tsaro" Naziyyan ta sake fada tana zaro wayarta, se Hafsa ta shiga karanto mata tana cewa (08134606093 Mcubes bakery, cake dinda ba'a bawa yaro me qyuya) "Bazaki gane bane Naziyya sekinci kinji tukunna keda bakya raina abin dadi ai inaga se sunusi ya saka miki waigi" suka kwasheda dariya gaba daya kafin sukayiwa Mama sallama kowa ta hau motarta tayi hanyar gida. Hajiya Umaimah  kuwa can quryar daki ta shige ta haye gado, kamarbata jin abinda computer take fada nacewar wayar A Kashe take haka taci gaba da kira har seda aka kira sallar Magriba kafin nan ta haqura ta dauro Alwala tayi sallar,bayan ta idad addu'arta gaba daya akan Allah ya mallaka mata Khalil ce ya kuma saka ta ita kadai a zuciyarsa karya taba kallon wata mace da sunan so ko sha'awa bayan ita, bata tashi a gurin ba sedatayi sallar Isha'i hade da shafa'i da wutri kuma har sannan wayar Khalil dintana kashe abinda yasa jiki ta yayi mugun sanyi kenan. Ta tuno da sanda za'a kawo lefen Nuratu Ango taDr Sagir dakansa ya kirata ya gaya mata cewar za'a kawo tun kafin ma ayo waya daga gidan su a fada za'a kawo din a lokacin har tana mata iskanci saboda gaba daya wayar da sukayi batafi ta minti daya ba yana gama fada mata saqonya kashe Umaiman ta samu nayi wai kamar Wanda za'ayiwa auran dole babu wani zumudi babu komai kawai wani 'Gobe za'a kawo kaya' ya kashe waya" ta fada tana kwaikwayon yanda Sagir din yayi magana, se gashi ita yau bata samu arziqin ma nata Mijin ya kira ya gaya mata ba. Koma dai yaya ne a yanzu babban abinda yake a gabanta shine tabbatuwar auranta da Khalil, dukda wani abu da ze faru ya faru daga baya kuma kawo lefen nan shine babban mataki na gaba da yake tabbatar da cewar maganar auransu tana nan daram. KHALIL Tun bayan da suka rabu da Hajiyarsa da kuma matsayar da ya barta akai ya koma gida gaba daya ya kasa sukuni, duk wata hanya da yake tunani zebi dan ya karkato da hankalin Hajiyar ta fahimci abinda yake nufi ya auna yaga bazata bulle ba musamman da ya zamana da zancen Badawiyya a ranta duk wani qoqari da zeyi na fasa auran Umaimah a gurinta zataga yayi hakane danya komawa Badawiyyan wadda sam shi idan badan Hajiyar ma ta tayar da zancen ba ya manta da ita. Ganin tunani baze fishshe shi ba ga qarin faduwar gaba a duk sanda ya tuna kalaman Umaimah se ya zubar da komai ya kama Allah, Addu' aya dukufa yi babu dare babu rana akan neman zabin Allah. Kwanaki hudu a tsakani bayan waccen maganar da sukayi sega kiran Hajiyar da rana yana office take sanar masa da cewar ya kawo kayan da suke gurinsa dan gobe za'a kai lefe. kasa ce mata komai yayi in banda "Toh" ya saka hannu biyu ya dafe kansa bayan daya kashe wayar, a duk kwanakin nan da ya tsananta addu'a tamkar ana sake saka masa Umaimah ne a cikin zuciyarsa. Wani irin sonta da kewarta ce ta addabe shi, ba qaranar dauriya yayi ba da har ya kwashe kwanaki biyar din nan ba tareda ya nemeta ba amma idan ya tuna itama bata sake  kiranshi ba se jikinsa yayi sanyi dan besan ma'anar wannan shirun da tayi masa ba, ta haquran ne ko kuwa wani abun take shiryowa. Koma dai menene yanzu dai magana ta qare tunda yanzu lissafin sati uku akeyi ta zama matarsa. A daren bayan ya tashi aiki ya hada dukka kayan da suke a gurinsa ya kai gidan babbar Yayarsu Maryam da suke kira da Ummi, yawanci dogayen rigunane da takalma se su agogo da sauran kayan kyalekyalen mata wanda yawancin  abuwan da idan ya gani yayi sha'awane yake siya ko ita Umaiman ta turo masa tace tana so,besan sun taru da yawa ba seda ya ringa zaqulosu shi kansa ya ri ga mamaki kayan. Sanin Halin Ummi da surutu ya saka ya rage wasu daga ciki musamman qananan kaya ya ajiye idan tazo gidan sa se ya bata kawai. Washe garin da za'a kai lefen da sassafe ya tafi dutse duba wani site da suke aiki, tun yana hanya wayar sa take kukan rashi chaji dan haka yana isa ya kasheta gaba daya ya jona a chajin kafin shiga aiki dukda yaso ya kira Umaimah suyi magana tunda ita taqi kiransa amma ya bari zuwa dare idan nutsu sayi magana kafinya koma Kano. Ya rigada ya yanke amfani da shawarar Mansur ta cewar  ya sameta suyi magana ta nutsuwa da ze shigar mata da hankali jikinta dan babu yanda za'ayi suyi aure ta tafi gidan sa da wannan tunanin nata na yin fito na fito da duk macen data shiga rayuwarsa, shi be shiryawa tashin hankali ba dan haka idan har taga zata zubar da makaman yaqin su yi qoqarin gina goben su fine, idan kuma hanyar data zaba ita take ganin me billewa a gareta toh tabbas sedai Hajiya tayi haquri, dan yana da inda ze kai maganar da ita kanta Hajiyan bazata tsalkake umarnin sa ba dole ta haqura ta barshi ya nemo wata da zasuyi aure su zauna cikin lumana ba tareda kullum ya fita yana dardar da faduwar gaba ba. ********* An kawo lefe da yake sabgar maza ce bata mata ba qarfe sha daya har sun gama komai sun juya da tarin kayan tukuicin da akayi musu. Kaya kam se sambarka duk wanda ya gani se ya yaba abu ne sukayi shi cikin tsari. Basuyi qarya ba haka babu qaranta daidai rufin asirin yanda babu inda za'akai kayan a raina su dan gaba daya kayanta manyan suturune kuma kaloli masu kyau da tsari se tsokanarta sukeyi wai tayi goshi amma ita sam ba wannan ne damuwarta ba, rashin ji daga Khalil har zuwa wannan lokaci yafi komai daga mata hankali. Da safen har ta quduri niyyar zuwa office dinsa taji ba'asin kashe wayar da yayi sedai wayar da sukayi da Rumasa'u ta hana ta zuwan, dukda haka bata haqura ba, idan har wunin yau ya qare Khalil be kirata duk inda yake seta nemo shi taji matsayar ta a gurinsa, shiyasa ma ta hada kayanta idan Yaya Hajiyayye ta tashi tafiya binta zatayi taje ta kasa ta tsare qofar gidan su ayi wacce za'ayi kawai. Tana kwance a daki saboda gajiya da tsokanar da masu shigowa kallon lefe suke mata wayarta dake gefe ta dauki qara, tasan wanene saboda shi kadai ta sakawa wannan kidan, cike da doki da shauqi tareda kewar sa da duk suka taso mata lokaci daya ta daga wayar da sallama kamar wata ta Allah. Daga dayan bangaren Khalil ya saki ajiyar zuciya saboda yanda muryarta ta ratsashi amma saboda karya bada kansa se yayi gyaran murya a dake ya amsa mata sallamar tareda dorawa da tambayarta ya take "Ba lafiya ba Khalil, na kusa mutuwa da yanzu sedai kaji wani ya dauki wayar nan ba ni ba" ta qarasa tareda fashewa da kukan da tasan yana karya masa zuciya ai kuwa tayi nasara dan nan da nan ya rikice ya shiga lallashinta, batayi shiru ba seda tayi me isarta taji sanyi a ranta sannan ta fara magana cikin sheshsheqa "Nifa ba dagaske nake ba duk abinda na fada maka wallahi bacin raine ya saka amma kayi fushi ka dena kirana idan na kiraka ma baka dauka ko naji wayar a kashe har kwanciya nayi a asibiti kwana uku ban mayi zaton zan rayu ba" "To yanzu dai ai baki mutu ba koh gaki da sauranki" ya bata amsa, seta bata fuska kamar tana gabansa dan sam yanda yake magana ba irin yanda suka saba a baya bane da alama har yanzu da wani abun a ransa, be haqura gaba daya ba kenan. "Haka ma zakace, da na mutun ai se kafi kowa shiga damuwa tunda kaine kayi silar mutuwata" ta fada tana tura baki, murmushin da beyi niyya ba yayi yace "Ko a mafarki kikaga me kama dani ya cutar dake ki tabbata shedan ne yake so ya shiga tsakanin mu dan in har ina numfashi bazan taba bari wani abu mara kyau ya same ki ba". Wani sanyi taji har ranta dan Khalil dinta ya fara dawowa, seta gyara kwanciya tace "Nayi kewarka sosai, you have no idea yanda kwanakin nan suka kasance mun ba tareda kai ba, dagaske Khalil idan na rasa ka zan iya rasa raina...." "Umaimah, rayuwa da mutuwa duk na Allah ne dan haka kik dena cewa idan babu ni bazaki rayu ba, kafin nan Umaimah ina son magana dake, ina so mu zauna akwai maganganun da nake so mu tattauna masu muhimmanci" Khalil ya katseta, daga yanda yayi maganar ta fahimci da gaske yake dan haka itama ta tattara nutsuwarta tace "Daman yau zan biyo Maman Asad idan zata taho gida, da baka kirani da sedai kawai Hajiya taga baquwar da babu sanarwa kaga shikenan idan nazo se mu hadu a gidanta hakan yayi?" "Yayi, yanzu zan taso daga Dutse, zuwa bayan sallar Isha idan Allah ya kaimu zan ganki" ya fada daga daya bangaren, jin yana qoqarin kashe wayar yasa Umaimah saurin tare shi da cewa "Kashewa zakayi, bazaka bari muyi magana ba?" "Umaimah na gaya miki zan hau hanya ne i see you in the evening alright?" Ya fada sounding pissed off "Shikenan, Allah ya tsare hanya ya kawo ka lafiya" ta fada a sanyaye saboda yanayin da yayi maganar qarshen yasa taji babu dadi. Haka ta ajiye wayar amma ko babu komai kiran da yayi mata ta ji sanyi a ranta ta kuma tabbatar da sanin sa ake ci gaba da shirin auransu. Tashi tayi ta bude wardrobe dinta ta shiga neman kayan da zata saka anjiman dan gaba daya dogayen rigunan material ta diba da hijabai tunda tayi shirin zuwa wasan kwaikwayo ne, yanzu kuwa da aka samu change of plan dole ta dibi kayan kwalliya. Kala biyu masu kyau ta diba da mahadin su tana murmushi ta zuba a cikin jaka, koma wace magana ce tasan dai bazata wuce ta shirin biki da abinda zasuyi ba, ita kuwa bata da ra'ayin yin komai daze halarta ballantana yammata su gane mata shi. Ganin Yaya Hajiyayye ta shantake ta azalzaleta akan ta tashi su tafi, qarshe da taga zata bata mata lokaci ma gaba tayi ta hau adaidaita dan tana so taje ta dan samar masa wani abin tabawa  ta kuma shirya a nutse kafin lokacin da zasu hadu. Ana idar da sallar Magriba ta hau shiri dan tana zuwa me delivery ya kawo saqon cup cakes da Yaya Hajiyayyen tayo order daga *MCubes bakery* (08134606093) bayan data ci na dazu da safe ta gigice da dadi nan da nan ta saka order wa Baban Asad da yayi tafiya ze dawo washe gari da safe. Umaimah na karba ta bude ta samu bowl me kyau ta zubawa Khalil, ga Pepper chicken da ta bata tayo musu gaba dashi ta dumama a microwave shima ta ajiye samman ta hada da ruwa da lemo masu sanyi komai yayi mata daidai ta shiga shirya kanta. Doguwar rigar Atamfa ta saka A line data yi matuqar yi mata kyau ta kafa dauri a gaban goshi ita da kanta tayiwa kanta kyau, turarukan Yaya Hajiyayye sun ci qaniyarsu dan feshin banza ta fadi tayi musu bayanta gama ta shiga daukar hotuna tana canhar bata san an idar da sallah ba saboda tana fashin ta ne ita. Sallamar me gadi ce ta katse mata daukar hoton, ta leqa suka gaisa yace tana da baqo a waje, seta dafe qirji shaf ta manta ta zare Sim din daga babbar waya ta saka a qarama dazu kafin ta fito daga gida ta maye shi da data Sim, fuskarta ta sake gyarawa ta fito, tana hangoshi ta narke fuska ta sake ragewa tafiyarta sauri kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta qarasa inda ya tsaya ya harde hannu biyu a qirji yana qare mata kallo. Khalil Tun fitowarta ya zuba mata ido yana jin yanda sonta yake qara huda zuciyarsa yana shiga, tayi masa kyau, yanda take qara narke fuska kamar wata qaramar yarinya ba qaramin tafiya yayi da shu ba har besan sandata qaraso ba seda ta tafa hannayenta a fuskarsa, a shagwabe tace "Wannan kallon fa? Qiris ya rage ka saka na fadi". Murmushinsa me kyau ya sakar mata kafin yace "Kinyi kyau", fari tayi da ido itama tace "Kaima kayi kyau" ta bashi amsa suka saki murmushi gaba daya kafin tayi gaba ya take mata baya zuwa inda kujeru suje ajiye a tsakar gidan. "Bari na kawo maka ruwa" ta fada tana juyawa ya rakata da ido harta bacewa ganinsa a ransa yana hasaso irin asarar da zeyi idanya rasata, amma idanya tuno wannan dayan side dinnata gaba daya se yaji komai yana juya masa. Yana can tunani yaji qarar ajiye try akan table dake gabansu, ta bude ruwan ta tsiyaya a glass cup ta miqa masa ya karba da murmushu yace "Thank you". Seda ya shanye ruwan ya miqa mata ta qara masa ya shanye ya ajiye cup din yana kallonta yace "Umaimah, kin shirya aure na dagaske?" PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 PAGE 14 Kallon rashin fahimta ta bishi dashi kafin tace "Kamar yaya na shirya auranka da gaske, daman ana auran wasa ne?" Gajeran murmushi Khalil yayi tareda gyara zamansa ya tattara hankalinsa gaba daya a kanta ya zuba mata ido, dole tayi qasa da nata idanun saboda yanda yayi mata kwarjini ta shiga juya zoben Azurfar dake hannunta a ranta tana so ta gano ma'anar tambayar da yayi mata wai ta shirya auransa, to me Khalil yake shiryawa ne? "Tambayarki nayi kuma amsa nake da buqata taqaitacciya Eh ko Aa, Umaimah kin shirya aure na?" ya fada still idonsa akanta, seta dago tayi masa kallo daya kafin ta juyar da fuskarta dayan gefen tace "Eh" "Good, kinsan me Aure yake nufi?" Ya sake jefa mata wata tambayar har sannan yana kallonta, seta juyo itama ta kalleshi, harara taso maka masa amma yanda ya tsare gida dole yasa ta saita idonta ta bige da qiftasu kamar an jijjiga bera a jarka kafin ta bude baki tace "Wai me yasa kake mun irin wannan tambayoyin ni ban...." "Umaimah! Ba wasa ya kawo ni ba, magana nake so muyi kuma dole ki amsa mun duk tambayoyin da nayi miki kai tsaye ba na son wata magana ko nuqu nuqu" yayi saurin katseta, seda ta watsa masa harar qasan ido kafin tace "Aure ibadah ce da Mace da Namiji suke zama a qarqashin inuwa daya matsayin mata da miji dan su bautawa Allah kuma su zama ababen debe kewa ga junansu". "Menene matsayin Namiji a cikin aure?" Ya sake jefa mata wata tambayar, "Guy din nan fa ya raina mun hankali ji wasu tambaya kamar dan jarida" Umaimah ta fada a ranta, a fili kuwa tace "Namiji shine shugaba wanda haqqin ci, sha, sutura, muhalli, neman lafiya da biyan buqatar matarsa ya rataya a wuyansa" "Ita kuma mace fa" Khalil ya sake fada yana bin bakinta da kallo, yanda take bayanin tana murguda bakin ba qaramin birgeshi yake ba. A'uziyya yake taja lodi lodi a zuciyarsa saboda yanda shedan yake sake qawata masa bakin nata. "Ita mace Allah ya wajabta mata yiwa mijinta biyayya akan duk wani abu da be sabawa Mahalicci ba saboda Aljannarta ta koma qasan qafarsa daga sanda tabar gaban iyayenta. Sannan dole ta girmamashi, babu musu ko jayayya a tsakaninsu, ta kuma mutunta Iyayensa da yan uwansa sannan zata kula dashi tayi tattalin dukiyarsa data qunshi Arziqi na Yaya da kudi" Muryar Umaimah ta dawo dashi daga tunanin daya tafi. Kai ya jinjina ya dan tabe baki kafin yace "se kuma me?" "Se kuma dukkan su suji tsoron Allah su zauna da junansu Amana kar wani ya cutar da dan uwansa" ta fada murya a cunkushe dan ta gaji da wadannan tambayoyin na titsiye. "Idan har kinsan duk wadannan abubuwan da kika fada me yasa ke bakya girmamani" Khalil ya fada yana kallonta, se ta dago kanta data duqar qasa ta kalle shi itama, yar banzar zuciyar ta tana ce mata "kice saboda shi ba mijinki bane" ta kirkin kuma tana kwabarta, "Magana nakeyi kinyi shiru, Umaimah me yasa bakya ganin qimata, kin raina ni bakinki yana iya furta mun duk kalmar data zo miki a duk sanda kika ga dama, a gabanido na kike zagina ki zagi yan uwana hakan yayi miki kama da suffar mace ta gari wadda take neman Aljannar ta a gurin Mijinta? Ko kuwa kina ganin tunda bamu rigada munyi aure ba dan haka kina da damar da zaki yi mun duk abinda kika ga dama? Toh bari kiji, halin da kika nuna a waje shine ze bani haske akan halinki acikin gidana bayan munyi aure, tun daga waje bakya shayin ki kalli idonaki zageni Umaimah ki jefeni da kalmomi marasa dadi a haka kike tunanin zan aure ki? Ban samu kwanciyar hankali dake a waje ba sanda baki zama doke na ba taya ya zanyi tunanin samun sa bayan na kawo ki gidana? Gaskiya Umaimah ina tsoron abinda ze faru idan har haka kike, ba kuma zan daukarwa kaina damuwa na kai cikin gidana ina sane ba, macen da bata girmamani ba a waje bana tunanin zata girmamani acikin gida bayan data gama sanin koni wanene" Khalil yayi maganar cikin daga murya da dakiya gaba daya ya chanza daga Khalil din nan me sanyi ya dawo wani daban dan. Kallon sa ta kumayi saboda yanda taji muryarsa har tsakiyar kanta kafin ta kalli can gefe tana qoqarin hadiye maganganun dake son fitowa daga bakinta dan a yanayinfuskar sa ta tabbatar yau baze dauki raini ko kadan daga gurinta ba, abinda yafi mata sauqi ta kama kanta ta kuma gyara bakinta dan haka ta maye gurbin kalamn tsiwar tata da cewa "Kayi haquri nasan nayi kuskure, raina ne ya baci amma in sha Allahu bazan sake ba. Zan koyi yanda zan ringa sarrafa zuciyata akan kishinka" ta qarasa maganar cikin rawar murya tana janhanci kamar me son fashewa da kuka. "Kar kiyi mun kuka" ya fada, kamar me jira kuwa sega hawaye shaaa sun fara zubowa, ta rigada tasan weak point dinsa, baya son kukanta ko kadan shiyasa take amfani dashi gurin karya lagonsa. "Kinga ni ba kuka nace kiyi ba magana kawai mukeyi kuma dole na nuna miki kuskurenki saboda aure zaman aure zamuyi, babu yanda za'ayi mu tafiyar da rayuwa a haka babu girmamawa a tsakaninmu, bacin rai ai ba gushewar hankali bane da zesa ki manta matsayina a gurin ki ki gaya mun duk maganar da kika ga dama" Khalilya fada cikin kwantar da murya, se ta sake fashewa da wani kukan harda sheshsheqa tace "Toh ya kake so nayi? Duk abinda nayi kishinka ne ya saka ni ba dan bana ganin girmanka ko na raina ka ba. Ina sonka da yawa Khalil ni kaina ban san irin son da nake maka ba, idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na shaqe kaina shi yasa bana sanin sanda nake fada maka magana mara dadi amma ka yarda dani na fika jin daci da haushin duk wata kalma mara dadi dana gaya maka, kuma nayi maka alqawarin bazan sake ba, tun waccen ranar nayi nadamar abinda ya faru na kuma chanza. Alqawari ne nayi maka Khalil bazaka taba nadamar aure na ba, Zaka sameni me matuqar biyayya tareda gujewa bacin ranka, zanzamar maka baiwa banida wani aiki se aiwatar da unarninka muddin be sabawa Allah ba kuma inada yaqinin bazaka taba sakani nayi abinda ya kaucewa shari'a ba, amma nima ina roqonka daka tausaya mun, kar kayi amfani da raunina akan Soyayar ka ka cutar dani. Ina matuqar kishinka ka tayani rufe duk wata qofa da zata kawo matsala a tsakanin mu dalilin kishi ni kuma nayi maka alqawarin zame maka duk irin matar da kake so. Bazan bawa idon ka damar ganin wani abu a waje kayi sha'awa ba ni kadai na isheka Khalil zan kuma tabbatar maka da haka dan seka bigi qirji wata rana ka gayawa duniya kafi kowa yin sa'ar mata saboda ina sonka Khalil, kuma farincikin ka shine nawa" ta qarasa maganar tana saka kwayar idonta dake jiqe da hawaye cikin tasa suka yiwa juna kallon tsakiyar ido n dan lokaci kafin ta janye nata tana ci gaba da jan shashsheqar kuka. Wani irin yarrr yaji tundaga kansa har tafinqafarsa, yanda kasan wanda aka tsoma a baho dake cike da ruwan qanqara a lokacin sanyi haka haka jikinsa ya dauki rawa seda ya hada hannayensa biyu ya rungume kansa tare da rufe idonsa yana furta "Hasbunallahu wani'imal wakeel" a zuciyarsa a hankali sanyin da yake ji ya ragu nutsuwarsa ta fara dawowa, be dena ambaton Allah ba seda yaji komai ya daidaitar masa ya bude idanunsa da suka kada sukayi jaa lokaci daya kamar wanda aka watsawa yaji ya kalli Umaimah da kanta ke sunkuye har sannan tana kuka qasa qasa. "Umaimah!" Ya kira sunanta cikin wani irin sauti, bata amsa ba illah sagowa da tayi ta kalle shi ta sake mayar da kanta qasan. "Look at me Umaimah, look directly in to my eyes" ya sake fada cikin shaqaqqiyar murya yanda kasan shine yayi kukan ba ita ba. Jiki a sanyaye ta dago ta kalle shi idanunsu suka sarqe. Ji takeyi tamkar yana cake mata ido da wani abu amma ta kasa janye idonta kamar yanda shima ya saka mata ido yana kallonta, sun kwashe kusan minti biyar a haka kafin Khalil ya bude baki yace "Ina sonki, and i will prove it to you ranar da kika zama mallakina, zan riritaki zan baki gatan daya dace dake a matsayin ki na mace da Allah yayi muku daraja ta daban, and I am giving you this assurance, ni KHALIL ke kadai kin isheni a rayuwata Umaimah. Idan har kika ga wata mace bayan ke a duniyata to ki tabbata qaddara ce wadda babu wanda ya isa ya kauce mata kuma idan haka ta faru ina fatan dani dake zamu rungumeta da hannu biyu, amma ki sani baki da ta biyu a zuciyata duk kuma wani abu da ze zo toh bayan UMAIMATAH NE". Yanda kasan ta taka rawar murna haka taji sanda yace ita kadaice a duniyarsa amma qarashen kalaman nasa suka datse murnar tata, wato yana fata kenanwata rana wata ta shigo rayuwarsu? Ita kuwa zata dawwa ma tana roqon Allah da karya nuna mata wannnan rana da ranta, dan kuwa bata san yaya zatayi ba. Tabbas idan bata kashe ko wacece ta shiga rayuwar Khalil dinta ba toh ita zata kashe kanta ta huta da baqin ciki. Hannunsa daya kai fuskarta ya dawo da ita daga tunanin data tafi, "Tunanin me kikeyi Amaryata?" Ya fada yana mata murmushi, seta mayar masa da martanin murmushin, a ranta tana jin dadin halin Khalil na rashin ruqo, yanzu sun gama wannan maganar kenan har abada sedai idan ita ta sake tayar da ita. "Ke kikayi wannan cake din, yayi dadi sosai" ya fada bayan daya gutsiri cupcake din, seta girgiza kai tace "Aa, amma zan tambayi Maman Asad inda ta siyo naje a koyamun tunda kana so" "Thats my babe" ya fada yana kashe mata ido, kafin yaci gaba da cewa "An kawo kaya dazu ko? I'm sorry i was supposed to tell you ban samu dama ba, koda yake laifin kine da kika shareni kwana da yawa bayand kika gama yimun barazana. Ni ai ban san yar sara suka bace ke se ranar" ya qarasa yana mata dariya, seta shagwabe fuska tace "In dai akan ka ne ka kirani yar Daba ma, kuma ni ba qin kiranka nayi ba tun ranar bani da lafiya seda na kwanta a Asibiti kwana hudu". Ayya sorry my princess shiyasa she nayita jina se a hankali, kinsan sati dayan nan was the longest week in my whole life saboda rashin ganinki da banayi, kawai na ringa rayuwa ne amma ni kaina nasan nayi loosing focus, God i can't imagine life without this my little troublesome lover" ya fada yana jan kumatunta irin yanda akeyiwa yara wasa. Dariya suka saka gaba daya, daidai nan Yaya Hajiyayye ta shigo gidan. Seda ta gama daidaita parking ta fito daga motar dan yaran tuni sukayi gurin Khalil da gudu me aikinta kuma ta shige da Baby Ummu-salma. A mutunce suka gaisa tana tsokanarsa Ango Ango se sunkuyar da kai yakeyi, ta faki idonsa ta gallawa Umaimah data qunshe fuska Harara dan taga aika aikar da tayi mata, daman tasan za'a runa ai kuwa seta biya kudinsa dan Mijinta ta siyowa shine zata kwashe ta bawa nata Mijin. Yaya Hajiyayyen na wuce wa basu dade ba sukayi sallama bayan daya ce tayi lissafin abinda take da buqata na hidimar biki ta tura masa, shidai a bangarensa reception kawai zeyi bayan an daura aure tace masa ita ba abinda zatayi tasan dai Mama zatayi Kamu da Mothers eve, yace dai taje tayi tunani daga nan suka rabu akan idan sun shawarta abinda zasuyin zata gaya masa, ta raka shi har bakin Gate ya wuce gida. A cikin gidan tana shiga kuwa Maman Asad ta tsareta seda tayi mata transfer kudin cake dinta cif sannan ta kyaketa bayan ta kwashe ragowar wai zasuci ita da yaranta gobe a kawowa Dadyn wani, ko a jikin Umaimah dan ita zuwan Khalil da daidaitawar su yau ya wanke mata komai. Haka tayi baccin farin ciki bayan da suka sha waya suka kuma kashe junansu da kalaman qauna masu tsuma zuciya. Washe gari Asubanci tayi ta bar gidan tunda ta gama abinda ya kawota tao zaman me zatayi dan haka bata bari ma Maman Asad din ta tashi daga bacci ba ta fece dan karta tsayar da ita tace ta tayata girkin tarbar Mijinta. Bayan ta isa gida ta kwanta ramuwar baccin safen kenan seda Imran autan Anty ya tadata wai taje Antyn tana kiranta. Kamar ta kwada masa mari amma ta kanne dan ko babu komai Antyn nan duk wulaqancin da take mata ta shanye kuma a yanzu kaf gidannan babu me yin ta tata kamarta, haka ta tashi tana hada hanya ta tafi dakinnata. Can uwar daki ta same ta ta baje wasu jarkoki da robobi da aka zuba garin magunguna ta kalleta tace "Zauna Umaimah bamu da lokaci, ta miqa mata jarka tsumi tace "Maza shanye ki bani robar, gasu nan zan saka miki a fridge, safe da yamma kullum kizo ki dauki daya ki sha kinga Nuratu inaga yanzu ta gama shanye wadanda na bata". Kallon ta Umaimah tayi ta kalli jarkar, kullum se taga Nuratu na shan abun amma da yake tun wancan incidence din ba magana suke ba shi yasa bata tambayeta menene ba, tana kallo kullum zata hada yan abubuwanta tasha, ga Fruits da tun Asali daman cimarsu ne amma na kwanannan yafi yawa dan wani hadi na musamman taga Nuratun na shiga daki dashi na Kankana, kwakwa, dabino da madarar gari suna da yar qaramar blander a dakin a ciki zata hade su ta markade abinta Umaimah na kallo ta shanye ta barta da hadiyar yawu, sedai idan ta faki idonta idan ta ajiye ta kurba ita dai bazata ce mata komai ba. Bayanin sauran abubuwan Antyn tayi mata, ingantattun magungunane da Antyn da kanta take hada saiwoyi da itatuwan ta daka wanda kuna yammata kamar su zasu iya sha, tun bayan tsayar da ranar auran daman suka fara shan maganin sanyi wanda yake mataki na farko na gyaran mace dan duk maganin matan da zaki sha indai da sanyi a jikinki kamar kina shuka dusa ne. Bayan kawo lefen Nuratun Anty ta fara bata tsumi da magungunan wanda daman duk yarinyar da za'a aurar a yaran Maman ita take daukar Alhakin yi musu gyaran na ciki da waje, Umaimah dai saboda rashin sanin inda aka dosa da maganar auran yasa se yanzu da aka samu tabbaci sannan za'a fara nata. Sosai taja mata kunne akan kullum tazo tasha magungunan dan tasan idab ta bata a hannunta qarshe zuwa zatayi ta ajiye su ayi a sara. Wani hadin sabulu ta dakko cikin bokiti da bata, daga yanayin qamshin da yakeyi Umaimah ta tabbatar da zeyi kyau, koda yake ita shaidace dan ga Antyn nan tas da ita dan kullum cikin gyara take da kwalliya , ba ita kadai ba hatta Mama dake neman tsufar da kanta Antyn bata bar haka ta faru ba, ita take hada muau duk wani abu da ze taimake su ayi gyaransu tare shiyasa gasu nan tas dasu abinsu. Godiya tayi mata ta wuce da bokitin a ranta tana yaba kirkinta, tasan Anty na sonsu tana kuma zaune da Mamanau lafiya amma ita laifin Anty daya a gurinta data hada Miji da Mamanta. Data sani a matar wa ko qanin Abba tazo da tabbas setafi shiri da ita sama da kowa saboda halin son gayun su yazo daya amma yanzun ma dole zata danne zuciyarta kodan saboda Khalil dinta tunda duk abinda Anty zatayi mata na gyara yanU shi akayiwa. Kwana biyu a tsakani Su Yaya Hafsa, Naziyya, Maman Asad da Anty Mamy matar Yaya Aminu, Anty Ruqayya Autarsu Mamansu se Zee Mama cousin dinsuce da itama ta tashi a gidan tareda su Naziyya, taruwa sukayi saboda su tattauna yanda za'a gabatar da shagulgulan biki, Dr Sagir ya rigada ya sallami Nuratu ya bata dubu dari biyu kudin hidimar biki da duk abinda zata buqata, sannan a bangarensa yace zasuyi Dinner abokansa sun shirya masa amma se bayan an kai amarya. Suna zaune a falon Anty, Dinkunan Nuratun da Tailor ya kawo sannan ya karbi Na Umaimah suka baje suna dubawa Maman Asad ta daga wata peplum blouse da dinkin ya zaunu breastcup din ya fita kamar an saka shi ma a jiki tace "Wai ni a ina kuka samo wannan multitalented Matar ne Naziyya? *BIISHAQ LINKS*, sanda naga kayan furnitures din Nuratu seda na rantse na waje ne muka ringa musu da Yaya Aminu yace shi yaje kamfanin suka debo kayan bana waje bane a nan akayi sannan ga dinkuna kuma wai duk na mace ce kamfanin ashe, gaskiya sun iya dinki dan Allah kiga rigar nan a tsaye kamar an saka ta a jiki ni nayi mamakin kudin danaji kin fada duk kyan dinkin nan amma farashin yayi sauqi". Naziyya da ita ta hadasu da Shagon dinkin na *lBIISHAQ LINKS Dake Tudun-Yola gate 2 Kano* tace "ai ki jira sema an kawo dinkunan da zasu saka na Kamu da Yini zaki sake shan mamakin yanda suka iya occasional dinki a farashi me sauqi, ni ai tuni na dawo daga rakiyar yan qaryar designer dinnan a qare da bata maka kaya ga gangariyar kamfanin dinki na samu kina kallon yanda suke gwangwajeni da dinkuna duk inda na shiga se an tambayeni wayake mun dinki" "Ga shaida na gani muma ai zamu warwasa da bikin nan dan har na hango yanda dinkunana zasu bada Ma'ana, bani number CEO din ma kiga na sake kiranta ina so naje su dauki measurement dina dakyau, sannan ga maganar Console da Dining Table da nake so na sake danna Nuratu sun tafi da Imani na" Maman Asad ta sake fada, se Naziyyan tace "Zakiyi mamaki idan nace miki ban taba zuwa an gwada ni ba, Tailor ta daya kawai ta aiko da za'a karbi dinkin da aka kawo su na gwada cif yanda kika san an gwada ni kuwa ai tun daga nan suka sake tashin kaina, shiyasa dinki ko babu awo zan basu nasan bazan ji kunya ba gashi sun san darajar kaya, ko wanne abu sunsan irin dinkin da zasuyi miki a jiki da ze qara fito da kyansa da qimarsa, Dining kuwa ki jira kiga na Yar gaban goshi, ai ni har cewa nayi ma Hajia Bilkisu tayi Son kai dan kayan Umaimah na neman sufi na Nuratu kyau tace ba haka bane, su haka aikinsu yake duk sanda aka maka sabo se kaga yafi na baya haduwa kuma na yarda dan duk sanda aka mun dinki qara sonsu nake saboda kullum sabuwar fasaha suke fito da ita" *(Ku tuntubi Hajia Bilkisu CEO BIISHAQ LINKS home of funitures and fashion design akan lambar waya 08033950747, suna nan a Tudun-yola get 2 dake birnin kanon dabo)* Hira suka ci gaba dayi suna daga kayan, Zee Mama ta sakw daga wata fitted gown data shawu shape din nan ya fita ta ko ina tace "Har na hango rigar nan a jikin Nuratu yanda zata fito amma se tayi ciko sosai a saman nan dan cup din yayi mata yawa" "Kamar kin shiga raina, tun dazu abinda nake tunani kenan cup din kamar zasuyi mata yawa koda yake daman haka take saka kaya a saka Bra me soso ko ina ya ciko cif ba'a san coge bane, da dai su iya rasa kunya ne ko ina ya cika da kaya sun fito da kyau" Yaya Hafsa ta fada. Umaimah dake kwance daga can gefe duk a zatonsu bacci take dan tunda suka fara bata saka musu baki ba ta tuntsure da dariya tace "Ba ciko bane Allah ne ya bamu, wasu ko sedai a hada da soso" "Shegiya ashe idonki biyu dake an tabo sabgar tsokana zaki fara rashin mutunci ba toh Allah yasa ta jiki yanU ta nada miki na jaki" Zee Mama ta fada, Umaimah ta harareta ta mayar da kai taci gaba da chatting dinda sukeyi da Khalil. "Wai dagaske kuke ko wasa? Daman duk abin nan cukone Nuratu takeyi ba nata bane" Anty Mamy ta fada tana kallonsu, se Maman Asad tayi caraf tace "Ki bari kedai ai duk abin tsiyar a kanta ya qare a gidannan, kowa an raba an bashi ita se aka bata iya qasan babu saman ni har tunanin yabda zasu kwashe da Angon nake idan ya gano gaskiya wallahi, bari ma in kirata dai" ta shiga kwalawa Nuratu kira se gata daga ita se Daurin qirji da alama daga wanka ta fito babu cikon qirjin nan a shafe, Umaimah dake jiran qiris ta kwashe da dariya kuwa harda hantsilawa qasa Nuratun tayi kanta a fusace dan tasan dariyar me takeyi tunda ba yau ta saba yi mata ba, wani lokacin ma setaga ta fito daga wanka zata tashi itama ta tube ta daura zani tayi ta yawo a dakin tana waqe waqen neman tsokana. "Rabu da ita karki kulata Nuratu daman neman nayi takeyi, Wannan ba matsala bane dukda dama ace na sani da wuri da tuni na baki magani kan biki duk se masuyi miki dariyar sunsha mamakin yanda abubuwa zasu cicciko har sufi nasu" Anty Mamin ta fada tana zaro wayarta daga jaka ta dannawa *MAMAN ILHAM ME TULA-TULA* kira. *Fadila UJ kid's dresses* indai ɗinkin yara ne, we got you covered 💯.Ana kawo mana mu ɗinka sannan muna siyar da ready made muna kuma aikawa ko ina in sha Allahu.Kina fama da ƙyallaye ƙanana da bazasu isa ayi ma princess riga ba?No worries *Fadila UJ kid's dresses* zasu saffara maki su izuwa mini skirts,ba zakuyi dana sani da ɗinkin *Fadila UJ kid's dresses in sha Allahu* 07037977211 Location:Katsina state muna aikawa ko ina cikin Aminci 🙌🏼🙌🏼 *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 15 A speaker ta saka wayar tana dagawa suka gaisa tace "Maman Ilham qanwata ce zatayi aure ashe dai saman in gaya miki se a slow babu komai duk ciko ne, shine fa hankalinmu ya tashi biki saura sati uku ban sani ba ko akwai abinda za'a iyayi mata" Daga dayan bangaren Maman Ilham ta amsa da cewa "Hajiya Mami ai ba abun tashin hankali bane irin hadin nan dai naki za'a bata in sha Allahu kafin satin biki se kinyi mamaki yanda abubuwa zasuyi TULA-TULA" Anty Mami ta kwashe da dariya tace "kai sunan abun nan na bani dariya Maman Ilham, to ya za'ayi, naga yanzu yamma tayi za'a samu motar da zata taho Kano daga Kadunan kuwa?" "Kiji ki fa kamar waddaza'a kai saqo Niger ai da yardar Allah kafin Isha ma saqo yazo hannunki yanzun nan zanyi packaging na baya a saka miki a tasha, ki gayawa Amarya ta kwantar da hankalinta wannan matsakar an maganceta, idan da TULA-TULA, babu jin kunya" suka kwashe da dariya daga nan sukayi sallama. "Allah ya kamaki matar nan, yanzu gashi a bagas munji sirrin yanda akayi abubuqa suke tsaye qyam kamar baki shayar ba" Yaya Hafsa ta fada, se da Anty Mamin tayi fari da ido kafin tace "Toh ya ranki, yaya hudu na shayar yanzu waze kalleni yace sati na uku da yin Yaye?" "Au wai kin Yaya Ni'ima amma kalli Nonon a cike koda yake tunda kike yaye ma ai ban taba ganin Nononki ya zube ba, tunda dai yau Allah ya matsi bakinki kin tona sirrin se ki gaya mana da kin gantalar damu da shan wata sabaya, sedai jiki yayi kyau amma abinda ake so ya tsaya din se a hankali, taimakamun kinji Surukata, nima na saka ranar Yaye wallahi har fargaba nake gaba daya nono ya zube ya koma kamar wanda qullin zobo ya fashe" Anty Ruqayya ta fada yanda tayi maganar dole ta baka dariya. Seda suka dara kafin Anty Mamin tace "wani maganine na samo shi gurin Maman Ilham Sunansa *TULA TULA* Magani ne sadidan na gyaran nono kuma kowa yana iya sha Yan Mata da zawarawa masu Shirin yin aure, me shayarwa dukka kowa nasha Daga mambila Ake kawoshi kunsandai yanda Matan fulanin nan nasu suke qirji a tsaye kamar na babyn roba to TULA-TULA ne sirrin kuma yanayi sosai Bada wasaba koda yake ku zaku bada shedar haka. Kinga kamar ke yanzu da zakiyi Yaye zaki fara Sha sati daya kafin yayen to In sha Allahu bazakiyi ciwon nono ba ko zubar ruwan nono lafiya lau zekiyi  yayenki Kuma nono baze kakkabeba". "Amma matar nan anyi me baqin abun, yanzu da shine kika barmu muna ta bulayi kullum kyaji muna jimamnin neman maganin gyaran nan amma kinyi bulumbuqui idan anyi magana kice ku Natural ne toh kin wa kanki" Maman Asad ta fada tana kama baki, Se Anty Mamin tayi dariya tace "Toh ai ku dangin miji ne ba'a iya muku haka kawai in bankada muku sirrina, Aa gara dai na adana abuna" "Allah ya yafe miki matar nan, kinga sake kiranta yanzu a hado dashi ina son qulli goma nawane?" Anty Ruqayya ta fada, "Sannu duk me zakiyi da har guda goma?" Mamin ta fada tana zare ido, Anty Ruqayya ta murguda baki cikin wasa tace "Ina ruwanki, kedai kirata kawai" sauran ma suka dauka gaba daya kowa tace a hado mata dashi tana so nan da nan kuwa ta Kira Maman Ilham ta gaya mata adadin da suke so, basu bar gidan ba se bayan Isha'i lokacin har saqon ya iso daga Kaduna sun aika an karbo musu a tasha kowa ta adana nata a jaka (Indai matsalar ki Zubewar ko kwanciyar Nono ce tazo qarshe, ki nemi Maman Ilham akan 08135613021 ki siyi naki akan farashi me sauqi, tana Kaduna tana aikawa ko ina a fadin qasar nan da yardar Allah). Kwanci tashi aka ce asarar me rai se gashi ana lissafin biki ya rage kwanaki biyar a fara, tuni Amare suka dauki harami jiki yayi mulmul fata tayi subul saboda ingantaccen gyara da suke samu daga gurin Anty, sal take sillesu da kurkum da dilka su shige cikin Hayaqin Dukan (wanda ba qaramin gyara mace yake ba, idan so samu ne kowannce mace ya zama tana da itacena gidan ta lokaci lokaci ki ringa turara jikinki yana maganin sanyi da sauran matsalolin mata ga matsi ciki da waje) idan suka gama wannan sukayi wanka kuma su sake mulke jiki da hadaddiyar kolakca sannan a shiga sabon turaren jiki shi yasa qamshi ya kama su duk inda suka gifta se sun bar mutane da bude hanci. Idan kaga yanda Nuratu ta cicciko abin kamar almara dan Tula Tula ya karbeta, Umaimah me mata iskanci se gashi itama tana bin dare tana diba dan itafa duk ta inda za'a ce wani ya fita se tabi ta toshe qofar, Khalil yayi Namijin qoqari dan dubu dari biyar cis ya bata kudin hidimar biki, sanda ta gayawa Mama abinda ya turo din fada ta ringa yi mata akan me yasa zata takurashi ta karbi kudi masu yawa haka bayan babu abinda ba'a yi musu ba, har Khalil din ta kira, ya tabbatar mata da ba ita ta roqeshi ba. Kawai dai ya samu kudade ne shima dan sosai yake samun gudummawa tunda katin daurin auran ya fita Manyan mutane da ya tabayiwa aikin zanen gida kawai sedai yaga Alert ko yaji an kirashi a waya ance yaje ya karbi cash. Allah kenan, a lokutan baya idan yana tunanin aure se ya ringa ganin kamar ba ze iya ba dan bashida abinda zeyi hidimomin se gashi yanzu ya yarda da abinda Hajiya take fada masa na cewar shi aure ba'a shirya masa shi yake shirya kansa, duk sanda mutum ya niyyata yinsa se kaga Allah ya buda masa gashi kuwa ya gani dan rufin asiri samun sa yake ta ko ina babu abinda ze ce sedai ya qara godewa Allah ya kuma tabbata Umaimah Alkhairi ce a rayuwarsa dan tunda ya hadu da ita yake samun budi ta hanyoyi daban daban, shi yasa bazeji qyashin kashe mata ko nawa bane a cikin dukiyarsa. Ranar Alhamis ana gobe Kamu sukaje qunshi da gyaran gashi. Wani Hadadden Salon sukaje na mataasu Aji dan tundaga harabarsa zaka gane hakan saboda irin manyan motocin dake zube na matan da sukazo qunshi, gyaran gashi ko gyaran jiki. Da yake sun rigada anyi musu booking basu bata lokaci ba nan da nan aka farayiwa Umaimah Jan Lalle wata kuma ta shiga wanke mata kai akayi steaming dan kitso zatayi Nuratu kuma aka saka mata Relaxer. Cikin abinda be wuce awa uku ba se gata ta fito a Amaryarta fes, tayi kyau na gaske lallen da aka mata Jan yayi maroon sosai ya kwanta a fatarta da bata da haske sosai amma gyaran data samu ya taimaka gurin sake fito da ainihin kyan lallen ga qananan kitso an yarfa mata dole ka kalleta seta burgeka. Tana zaune daga kan kujera ana zanawa Nuratu Baqin lalle bayan an gama mata jan dan ita Umaimah cewa tayi bata so duk yanda masu lallaen suka kada suka raya kuwa taqi dole suka haqura. Khalil ne ya kirata Video call, santin kitson da jan lallen ya ringayi dan ba qaramin kyau suka masa ba. "Babe har an gama ne na taho na dauke ku? Dan bazan iya bari wani ya fara gane mun wannan gayun naki ba" ya fada bayan daya gama kodata, Murmushu tayi masa tace "Aa Yaya Nuratu ake qarasa baqin lalle amma ana qarasawa zan kiraka kafin kazo yasha iska se mu tafi ta wanke a gida". "Yauwa ke ba'ayi  miki wannan flower black ba da naga anayi yanayi mun kyau sosai, kice su rubuta miki sunana a nan" ya fada yana nuna mata gefen wuyanta, fuska ta dan bata tace "Ni bana sonsa amma tunda kana so bari ayi mun" "No ki barshi in bakya so wannan ma ya isa amma yanayin kyau sosai idan na ganshi a hannun mutane yana burgeni kuma musamman ma nasan idan akayi miki se yafi na kowa yin kyau" Khalil din ya fada, jin haka kuwa ba shiri ta bata fuska tace "Wato kallon yammata kake yi har lallensu yana burge ka koh?" "Ba haka nake nufi ba, idan su Habiba sunyi nefa nake gani. Ni ina naga lokacin kallon wasu yammata kullum ina site ina fama da sumunti da yashi" ya bata Amsa yana qunshe dariyarsa, ta maka masa harara kafin tace "Se anjima idan mun gama i will call you" "Ok ayi miki ke kyau kinji Babe, love you" ya fada tareda huro mata kiss, baki ta tura masa yayi dariya ya kashe wayar, seta kalli wadda ke zanawa Nuratun lallen sun gama saura qarashen hannu daya, murya a cukule tace "Idan kin gama mata zakiyi mun, kuma yafi nata kyau" "An gama Amarya" matar ta fada tana dan murmushi dan tun tana wayar suke kallonta daman kuma Nuratun ta fada tace su jira su gani zayi gashi kuwa. Lalle me kyau matar ta zana mata na Amare dukda Umaimah nata noqewa a barshi yayi yawa amma ta shareta seda tayi mata yanda ya kamata ita da kanta kuma ta dawo tana Admiring lallen ganin yanda ya qawata hannunta sosai. "Hajia Ango fa yace a rubuta miki sunansa a wuya" Me lallen ta fada bayan sun gama dataga Umaiman na shirin kishingida a kujerar da take, wani kallo ta watsa kafinta fara magana cikin fushin da bata gama saukowa ba na zancen lallen da Khalil yayi tace "Daman samun ido kikayi har kina jin abinda mijina yake fada? Irin kune daman masuyiwa mutane labe kuna sauraran conversation dinsu ko? Toh bari kiji Mijina yafi qarfinki sedai ki qare a nan kina zana baqin lalle da baqar fuskar ki a gurin" sosai ta ringa spark tana bala'i ma'aikatan gurin na bata haquri dan a policy dinsu customers are always right, koda kuwa sune da rashin gaskiya. Nuratu da ta shiga toilet wanko lallenta ta jiyo hayaniyar babu shiri ta fito "Umaimah meye haka? Me yasa ke baki da mutunci daga abin arziqi shine zaki fara zaginta" Nuratu ta tareta se kuwa ta juya kanta tace "Babu ruwanki saboda ba naki mijin tayiwa labe ba shi yasa zaki tare mata, akan me zata saka kunne harta ji muryar sa?" "Da kika san bakya so aji muryar me yasa zakiyi waya a gaban mutane ko kin manta da video call kikayi kuma a speaker baki saka earpiece ba? Wallahi Umaimah ki shiga hankalin ki tun wuri kafin ki jawowa kanki baki" Nuratunta fada a fusace itama, Umaimah ta bude baki zata bata amsa wayarta tayi qara, Khalil ne. A fusace ta miqe bata damu da lallen ta da be gama shan iska ba ta yayibi mayafi da jakarta tayi waje Nuratu taja tsaki ta koma ta ci gaba da wanke lallenta a ranta tana takaicin halin qanwar tata da duk inda akaje seta siyar da Hali, tana guje mata taje cikin dangin miji tayi musu wannan haukan tabbas babu inda auranta zeje dan babu Namijin da ze yarda ta ringa wulaqanta masa yan uwa haka. A waje kuwa a fusace Umaimah ta qarasa inda ta Hango motar Khalil, bawan Allah daya sha gayunsa ya fito da murmushi amma ganin fuskarta a dinke kamar Hadirin August yasa ya tsaya daga inda yake harta qaraso "Mu tafi" ta fada tana qoqarin kama murfin motar yayi saurin bude mata yana cewa "Easy Babe, wa kuma ya bata miki rai haka" "Duk ba kai kaja ba, akan me zaka kirani bayan kasan ina cikin mutane su kuma mayu daga jin muryarka har wata ta riqe abinda ka fada" tayi maganar cikin fada kamar meyi da dan cikinta. Sakato Khalil yayi yana binta da ido, ikon Allah yanzu kuma kiran da yayi mata ne ya zama laifi gaskiya yarinyar nan ya yarda saitin kanta na gocewa. Ganin ta dage tana surfa masa masifa dan har masu wucewa sun fara kallo su yasa ya dakatar da ita, cikin tsawa ya kira sunanta Yace "Kirawo Nuratu mu wuce" Yanda ya hada fuska babu wasa sam yasa dole ta juya ba taredata musa ba amma da taso suyi tafiyarsu ne su barta idan yaso ta hau Napep ko ta kira nata Mijin yazo ya daukota tunda tafison me lalle akanta. Kafin ta qarasa shiga gurin Nuratun ta fito da wata ma'aikaciya a bayanta ta ruqo mata Paper Bags masu tambarin salon din guda biyu seta juyo tana ci gaba da kumbure kumbure ta tsaya a kusada Khalil daya harde hannu biyu a qirji kawai yana binta da kallo, ran Nuratu babu dadi ta bude baya ta shiga yarinyar ta miqa mata Jakunkunan ta karba tareda godiya kafin ta juya har tayi gaba ta waiwayo ta kalli Umaimah da Khalil, ita Umaimah daman idonta akan yarinyar yake shi kuma Khalil yana nazarin Umaiman yarinyar na juyawa kuwa tayi missing step ta tafi taga taga zata fadi Allah ya taimaketa dafe bango "Mayya dama kin fadi kin karya haqori gobe kya sake kallon Mijin wata" Umaimah ta fada, cikin jin haushi yarinyar ta mayar mata tace "Ni ba mayya bace kuma na kalle shi din tunda ai Namiji ne badan ke kadai akayi ba" "Kan babbar bala'i, me kika ce?" Umaimah ta zabura tayi kan yarinyar, Tsawa Khalil ya buga mata, ba ita ba hatta da Nuratu dake cikin mota tana kallon ikon Allah seda ta razana, "Get in side" ya fada yana nuna mata qofar motar, dole ta shige dan a yanda taga bacin rai a idonsa tabbas yana iya kai mata mangari. Seda ya kulle mata qofar kafin ya zagaya bangaren sa ya tada motar, da gudu ya figeta suka fice daga gurin zuciyarsa na tafasa wannan wane irin zubar da qima ne? Yanzu daya barta se tace zata kama yarinyar da kokawa kome? Anya ma Umaimah nada hankali kuwa? Haka ya ringa tunani a zuciyarsa yana sharara gudu dasu a titi kamar masu tafiya Lagos Nuratu na baya tana zare ido da addu'ar Allah ya sauke su lafiya ita kuma hamshaqiyar ta hada kai da guiwa tana kukan baqin ciki biyu, maganar da yarinyar ta fada mata ga wanda akayi saboda shi ya banzatar da ita ko a kwalar rigarsa be nuna yasan tana kukan ba. Yana tsaida Mota a qofar gidan su Nuratu ta kwashi komatsan ta tana hamdala tayi waje, Umaimah ta dago zata fara masa qorafi ya dakatar da ita da cewa "Fita malama" "Khalil ni kake kora daga motar ka?" Ta fada cikin mamaki tana nuna kanta, se ya kalle ta da idonsa da suka chanza kala saboda bacin rai yace "Haka nace, Umaimah ba fita daga mota ta ba idan har bazaki dena wannan halin jahilcin ba zan fitar dake daga rayuwata ne gaba daya ba iya mota ba. Yanzu ke abinda kike yi yayi kama da na me hankali wadda tasan me takeyi? Kishi hauka ne? Ko kuwa a zamanin Jahiliyya muke da zaki doshi wata a cikin mutane zakiyi dambe saboda bakida nutsuwa, waye ze kalli actions dinki yace kin taba zama a ajin koyar da karatu. Toh wallahi bari kiji, ba jibi za'a daura mana aure ba ko a safiyar ranar ne kika kuskura kika maimaita something stupid as this maganar aurena dake ta tashi, kar kuma kiyi tunanin idan an daura mana aure kinci banza kenan, Umaimah idan baki shiga hankalinki ba you better get ready to deal with the othersidenof me da bazaki taba son na bayyana miki shi ba danba ke kadai ce saitin ki yake gocewa ba, idan kuma kika bari nawa saitin ya goce kece zaki sha wahala fitar mun daga mota". Tunda ya fara magana ta daskare a gurin, Jahilci, rashin hankali, rashin nutsuwa duk ita kadai Khalil ya jefa da wadannan kalmomin saboda tayi kishi akan sa, saboda ta nunawa duniya muhimmancinsa a gurinta? Dakyar ta iya bude baki saboda yanda kukan gaske ya taso mata dan ashe dazu na samun guri kawai tayi tana kallonsa tace "Saboda ina kishinka kake kirana da Jahila Khalil?" "To hell with the kishi fitar mun a mota Umaimah kafin kisa na aimata abinda ni dake zamu zo muna regretting, get out of my fucking car" ya fada cikin daga murya jikinsa na rawa jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu ai bata jira komai ba ta fice a sittin dan ta tabbata ya kai matakin qarshe a fushi, yanda ya figi motarsa ya bar layin ya qara dugunzuma mata hankali idan wani abu ya same shi fa itace sila. Wayarta ta fara lalubawa a jikinta taji babu se sannan ta tuna ta bar jakar a motar a garin sauri, jiki a sanyaye ta shige gida majalisar munafukan unguwarsu suka rakata da ido tana shiga suka fara tattara analysis na tunanin abinda ya faru dan basuji komai ba. Can dakunan dake bayan gidan su ta nufa falle daddaya ne wanda sune dakunan gidan daga baya da Abban ya samu hali ya qaro wani fili shine yayi musu wani gini suka koma ciki wannan aka barshi a BQ saboda amfanin taro kamar yanzun, dakin da suka koma ciki ta bude ta shiga, babu kowa a ciki tasan Nuratu nacan tana bada kanun labarai seta maida qofar ta saka sakata ta haye kan katifa kawai ta saki Kuka, seda tayi iya yinta taji sanyi a zuciyarta kafin ta tashi ta shiga wanka ta wanke lallen da Allah ya sota garin ana iska sosai be jaguke ba. Tunanin halin da Khalil yake ciki takeyi, ina ya tafi? Me yake yi yanzu gashi babu waya bare ta kirashi ta bashi haquri kuna bata so ta shiga cikin gidan yanzu tasan se sun cinyeta a danya. Bubbuga qofa taji anayi da kiran sunanta, seda ta kasa kunne kafin ta gane muryar Rumasa'u ce da Halima se wasu da bata tantance su waye ba. Bude qofar tayi suka shigo kusan su biyar kaya kaya suka fara mata cari "Amma Umaimah baki da kirki, yanzu ace sedai muji labarin auranki a gari? Toh gani tunda bani da zuciya na taso gari ya gari tundaga Maiduguri nazo" Fannah da sam Umaimah batayi tsammanin ganinta ba ta fada, qarin mamakin ta qaton cikin da ta gani a jikin Fannah haihuwa ko yaushe amma ta iya yiwo wannan takakkiyar. Halima tace ta sauke goyon yarinyarta Umaiman ta karbe ta tace "Ki rabu da ita ni ban taba ganin inda laifin wani ya shafi wani ba a rayuwa, saboda kin samu matsala Nabila da Fauziyya shikenan se ki dauki gaba damu, mu menene namu a ciki? Mutanen nan fa ke kika kwaso mana su kika kawo su group dinmu amma da taku ta hado ku se kika mana kudin goro duk kina toshe lambarmu. Ni wallahi naji dadin abinda ya faru sosai ko babu komai mun rabu da alaqaqai dan duk wani abu mara kyau su suke qara saka mu a ciki musamman ke da kike daukar shawararsu kamar me gashi da Allah yaso ki da rahma kun rabu kin samu miji zakiyi aure na tabbatar da ace har yanzu kuna tare wallahi bazasu barki ba, se sun san yanda sukayi suka lalata maganar kamar yanda suka saba tunzuraki kina lalata auranki". Yanzu dai komai ya wuce ayi haquri, sannan ke kuma Katinan da kika bani sunyi kadan akwai wadanda sukace zasu zo dan haka seki qaro wasu na gaya musu mu hadu a gurin kawai goben" Ruma ta katse musu cece kucen. Umaimah da duk jiki yayi la'asar, tunaninta yana can kan sanin halin da Khalil yake ciki tayi murmushin yaqe kawai, se kuma ta miqe ta ajiye Baby Ayra tana kallon Ruman tace "Dan aramun wayarki nayi kira" "Gaskiya bazaki cinye mun kati ba dan ke kina da me saka miki ki kirashi yanzu ya turo na samu nima kimun transfer" Ruman ta fada tana miqa mata wayar. Fita tayi tacan gefe inda babu hayaniyar mutane ta shiga kiran layin Khalil, seda tayi kira uku ba'a daga ba, harta haqura se dabara ta fado mata. Text ta rubuta masa ta tura "Rumasa'u ce Aminiyar Umaimah, daman ta bani number kane tace muyi magana akan motocin da zaka turo mana gobe na tafiya gurin Kamu" tana turawa ta dakata, ba'afi minti biyu ba kuqa se gashi ya biyo bayan kiran tana dagawa ta fashe masa kuka ba tareda tayi magana ba. PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 16 Khalil Bayan daya bar qofar gidan rasa inda ze nufa yayi haka yayita yawo a titi dan baya so ya koma gida a yanayin da yake ciki, tambaya ce ze shata a gurin Hajiya ga gidan kuma ya fara cika da yan uwa da sukazo se kace wani bikin mace a fadar sa zasu taho tun ana sauran kwana uku bayan babu abinda za'ayi. Mansur ne ya fado masa a rai, da safe sunyi waya ya gaya masa yana off se da dare ze shiga Asibiti dan haka ya karkata kan motar ya nufi gidan su Mansur. A tsakar gida ya tarar da Mamansu tana aikace aikave suka gaisa a mutunce dan tamkar Hajiyar sa haka ya dauketa saboda Amincinsu da Mansur tun Primary gashi yanzu sun wuce Aminai ma sedai a kirasu yan uwa. "Ango Ango, ya shirye shirye? Bamu dade dayin waya da Hajiyan ba ai nake tambayarta ko akwai abinda za'ayi tace Aa se gobe ne za'a rage girkin daurin aure, gashi dai abin Allah nan Dan uwanka kullum yake tasaka gaba a gidan nan ashe ma seka rigashi yin auran Allah dai ya sanya Alkhairi yasa mutuwa ce zata raba" Hajiyar su Mansur ta fada, Khalil dake ta faman sunkuyar da kai dan karta ga idon sa da yayi ja ya amsa qasaqasa kafin ya wuce can inda dakin Mansur yake. Buga qofar ya shigayi Mansur dake bacci ya farka yana tambayar waye "Malam zoka bude mun qofa" Ya fada muryarsa a cunkushe, Mansur din na jin shine ya taso ya bude yana cewa "Me kuma ya kawo ka? Dan Allah ku barni na huta. Kana kallo kwana biyu na jera straight ina call morning to Evening saboda na samu off muyi hidimar biki shine yanzu zaka biyo ni ka hanani bacci me zan maka" Mansur ya shiga Mita shidai Khalil be kula shi ba kai tsaye toilet ya nufa ya kunna famfo ya ringa zuba ruwa akansa seda yaji ya samu nutsuwa kafin ya dauro Alwala ya fito lokacin Mansur harya koma baccinsa. Kan kujerar dake dakin ya samu ya zauna yai shiru lokaci lokaci ya buga tsaki, ji yake yi zuciyar sa na zugashi akan ya fasa auran nan. Wannan yarinyar babu alamar samun zaman lafiya da nutsuwa a tattare da ita gara tun yana da sauaran dama ya raba kansa da alaqaqai ya huta saboda idab ya rigada ya aureta Saki is the last thing da ze iya aikatawa. Bashi da burin ya auri mace ya saki kai duk girman laifin da zata masa sedai ya nemi wata hanyar ya hukuntata amma banda saki saboda shi ya saka a ransa idan yayi aure to se dai idan shi ya mutu ko matar ta mutu amma babu rabuwa shi yasa ya dade yana laluben wadda halinsu ze zo daya su zauna suyi haquri da junansu amma qarshe ga inda ya qare. Tsaki me qarfi ya qaraja Mansur ya miqe zaune tareda jifansa da Pillown daya tashi saga kai yace "Dallah Malam tashi ka fita, kaje palour Mama ka zauna kazo se uban tsaki kake wa mutane ka duk ka cika mun kunne na kasa bacci". Shiru Khalil yayi masa ya gyara zaman sa akan kujerar ya harde qafa yana girgizasu, se Mansur ya dawo gefen gadon yana kallonsa yace "Talk to me Man me yake damunka why are you upset?" "Mansur waccen yarinyar ce gaba daya so nake nima nayi going crazy kamarta. Shikenan abinta ya zama kamar wani season film ko da yaushe i should be anticipating new episode kullum da kalar sabon haukan da zatayimun display" Khalil ya fada cikin bacin rai. Dafa kafadar sa Mansur yayi yana bubbugawa ba tareda yayi magana ba se Khalil din yaci gaba da cewa "Daga na kirata tana Salon lafiya lau muka gama magana the next thing naje daukan su kawai ta hau kaina da bala'i sannan saboda bata da hankali zata cakumi wata yarinya da dambe a gaban mutane kawai dan yarinyar ta kalle ni" "Dambe?" Mansur ya fada yana bude ido dariya nason kufce masa ya danne se Khalil ya maka masa harara yace "Na zama laughing stuff kenan, ina gaya maka matsala kana neman kayi mun dariya ko bayan duk kai ka qara jefani a halin da nake ciki, sanda na nemi shawarar ka daka qarfafamun guiwa ai da yanzu ba wannan maganar akeyi ba". "Yanzun ma Khalil lokaci be qure ba you can call the wedding off na tabbata kuma babu me ganin laifinka tunda kowa yasan halinta. Bari na saka rigata ma ba se nayi wanka ba kawai ka tashi kawai muje mu gaya musu ka fasa, su riqe komai mun bar musu ma Allah ze bamu kudin da zamu hada wasu dan gaskiya nima na fara tsorata da halinta, dambe fa? Ni rabonda naga Mata na dambe tun zamanin muna zuwa Ma'ahad Islamiyya" Mansur ya qarasa yana yar dariya ganin yanda Khalil ya zaro masa idanu se kace bashi ne ya tayar da maganar ya fasa din ba. "You must be mad Mansur, jibi fa ne daurin auranmukake cewa na fasa so kake na bata mata suna ko yaya? Sannan duk wadannan mutanen daka je kayo gayyar daurin aure me zaka koma ka gaya musu?" "To Khalil me kake so ayi, kasan ni me sonka da Alkhairi ne. Bazan so ka auri matar da zata ringa saka ka a damuwa ba kullum shiyasa kuma da tun wancan lokacin kayi mun bayani sosai qila dana fahimceka nayi supporting abinda kazo dashi amma yanzun ma lokaci be qure ba, zamu iya fasawa kawai kowa ya huta" Mansur dinya sake fada kamar gaske, se Khalil ya juya kai yayi shiru kamar baze ce komai ba can kuma ya juya ya kalle shi yace "I love her Mansur, i just hate thia bad side of her. Da zata zauna a yanda na fara ganinta har na fada sonta we would be the happiest couples because we are madw for each other" "Toh Romeo ai shikenan kana sonta tana sonka the soyayya will hold the bond karka damu she will change for better data shiga gidanka" Mansur ya fada kafin ya komawarsa kan gadon ya kwanta daidai nan aka buga qofar dakin Mansur din ya bada damar shigowa wata yar farar yarinya ta shiga da sallama ta gaishe su kafin ta ajiye Try din da aka doro kayan abinci akai tana cewa "Gashi Mama tace a kawowa Yaya Khalil" "Lallai Mama wato Khalil ta aikowa abinci bayan ni ina zaune nan ko abincin safe baa kawo mun ba" Mansur ya fada yana jan kwanukan gabansa, se yarinyar tayi yar dariya tace "Lah Yaya ai bamu san kana nan bane ni ta tambaya ma nace baka dawo ba shi yasa amma bari na koma na qaro muku toh idan wannan baze isa ba" ta juya zata fita Khalil ya dakatar da ita dacewa "Barshi duk cinsa wannanya ishe mu danni bada yawa zanci ba" "Toh Yaya" ta fada kafin ta juya ta fita. "A ina Mama ta samo yarinya" Khalil ya fada yana gutsirar Funkason da aka kawo musu. "Yar gidan Kawu Sani ce na Jama'are, kasan Mamansu ta sake aure yayarta Muhsina ma anyi mata aure se ita kadai tana hannun Inna Sadiya to ruqon Tsofaffin nan babu wani da ze ringa sakawa yaro ido ba dadi shiyasa Mama ta dakkota tunda nan din ita kadai ce yanzu ta samu yar tayin zama" Mansur ya fada yana cin abincinsa. Se Khalil ya gyada kai yace "Oh rayuwar fa kenan duk ka gama haqilonka ma akan macen ka mutu watanni kadan ta auri wani su cinye abinda ka tara tare, jifa gaba daya Kawu banjin ya shekara biyu da rasuwa duk Kururuwar nan data ringayi ranar jana'iza wai har ta sake wani auran". "Hmmm ka bari kawai Abokina abin takaicin ma a cikin gidan fa take zaune anyi magana wai ai rabonta ana yayanta ne kuma ze ringa biyan haya shine saboda dan Akuya ne wai baze riqe mata Yarinyar nan guda daya ba ita kuma inaga Asirce ta yayi ko yaya ta tattarata ta mayarwa da Inna Sadiyan, toh muna dai zuba ido kowa dai yasan abinda yasa ya aureta kudin kuma na qarewa gayyar zata watse, yanzu ma shirin shiga Kotu suje da Kawu Labaran akan ta dawo da komai na yaran tunda tayi aure" "Allah ya rufa Asiri" Khalil ya fada yana rufe baki wayarsa ta fara qara ganin besan number ba yasa ya shareta suka ci gaba da cin abincin suna yan hirarrakinsu. Ganin ana ta kira anqi haqura ya saka Mansur cewa "Ka daga mana ka sani ko cikin mutanen mu ne wani yake kira" "Kyale su kawai ko waye ya yi text in na gane na kira ko kai ka daga kaji waye". Jan wayar Mansur yayi yana dannawa kuwa sega Text ya shigo ya bude ya karanta yace wa Khalil "Ka gani ba Aminiyar Amaryace, se taje ta gaya mata ka mata wulaqanci ka qara wani laifin tukunna" Tsaki Khalil yayi yace "Seka kira kaji me suke so, in kudi ne wallahi sisi bazan bayar ba dan na bata komai dama muna yar dadi ne sena qara mata amma yanzu kuwa tayiwa kanta" "Allah ya taimaki Angon Umaimah" Mansur ya fada cikin shaqiyanci kafin ya danna kiran layin. Kukan da Umaimah ta fasa tana daga wayar ya saka shi kallon Khalil kafin ya janye wayar daga kunnensa ua sakata a speaker ya ajiye a gaban Khalil. Kuka take bilhaqqi harda sheshsheqa, Khalil ya daya tsame hannu daga cikin abincin ya dafe kansa saboda yanda yake jin sautin kukan nata, tabashi Mansur yayi yana masa alamar ya daga, ya cije baki kamar baya so ya dauki wayar ya cire ta daga speaker ya saka a kunne "Wai bakya gajiya da kuka ne" ya fada murya a cukule, Umaimah taja doguwar sheshsheqa kamarme shirin shidewa tace "Ba kaine kayi fushi dani ba, dan Allah kayi haquri bazan sake ba. Wallahi kasa controlling kaina nayi shiyasa amma na gane nayi kuskure bazan kuma maimaitawa ba" ta fada tana shirin cigaba da kukan. "Kullum haka kike cewa ai amma idan kika tashi se kinyi abinda yafi na baya. Dambe fa kikayi niyyar yi a cikin mutane, kina zaton da kunyi da yanzu video ki be gama zagaye Social media ba yanda qiris mutane yanzu suke jira su fara recording abu wane irin kallo kike so mutane suyi mun ace matar da zan aura aka gani a titi tana dambe? Saboda kinga ina kyaleki ne yasa kike abinda kika ga dama ko? Shi kenan zan dauki mataki" Khalil ya fada a hankali amma a muryarsa zaka karanci bacin rai. Marairaicewa tayi sosai tace "Ai bamuyi ba ma zan tabayi ba in sha Allah kayi haquri, na yarda in dai na sake yin wani abu irin wannan ka dauki kowanne mataki na yarda" "Haka kikace ko? Kinsan irin matakin da zan dauka ne?" "Koma wanne irine na tabbata ma bazan sake ba balle kayi wani abun" ta tareshi a shagwabe kafin ta sake cewa "Ka haqura toh?" "Da ban haqura ba bazan amsa wayar ba ai, wayar waye wannan? ina taki wayar ma da kika kirani data mutane?" "Ba ka tafi da jakar a motar ka ba wayar Rumasa'u na ara nasan ma koda ace wayata na nan idan na kira bazaka dauka ba. "Oh ashe akwai wadanda kika yarda dasu haka da har zaki iya kirana da wayar su?" "Ruma ce fa Aminiyata, nasan ko kowa zeci Amana ta a duniya banda ita amma ai ba barin number zanyi muna gama magana zan goge, yaushe toh zaka kawo mun tawa wayar? Nasan mutane suna ta kirana" Umaimah ta fada, se Khalil yace "Nayi seizing dinta se kinzo gidana sannan zan baki nima zan duba ciki na gani yanda kike mun bincike a waya" "Babu abinda zaka samu a wayata, amma ka taimaka ko Sim din ne ka kawomun na saka a qarama saboda qawayena da zasuje Kamu gobe zasu kirani" "Zan duba na gani" ya bata amsa daga nan sukayi sallama. "Gaskiya zan Hada Umaiman nan da Nusyta ta rakata inda takai sunanka nima a shawo mata kaina, jifa yanda ka gama masifa kana fadar maganganu kai zaka fasa, ka shigo fuska kamar wanda ya fada cikin kashin shanu amma daga jin muryarta ta kalallame ka duk kububuwar daka hau ka sakko kana wani kashe murya dole da abinda yarinyar nan ta taka shi yasa take iskanci son ranta" Mansur da tunda suka fara wayar ya saki baki yana kallon ikon Allah ya fada. Se Khalil ya saki murmushi yace "Inason yarinyar da yawa Mansur ko nayi fushi da ita baya dorewa tana da shiga rai yanda baka tunani" "Naga alama" Mansur ya fada kafin yaja kwanon funkasonsa yaci gaba daci. Umaimah kuwa ajiyar zuciya ta saki a fili tace "An rufe wannan case din saura na cikin gida". Dakin ta koma ta tarar da Halima na shirin wucewa itada Fannah. "Aa ina kuma zakuje" Umaiman ta fada bayan data miqawa Ruma wayarta se Haliman ta amsa ta da cewa "Gidana zamu wuce ta huta se gobe idan mun hadu a gurin Kamu" "Kedai ki wuce amma ita ai biki tazo dan haka babu inda zata je, yi haquri Fannah bari na kawo miki ruwa da abinci wallahi wata wuta na kashe ne se yanzu na samu nutsuwa" Umaimah ta fada tana mayar da Fannan ta zauna. Haka Halima ta tafi ita kadai bayan da suka daukowa Fannan akwatinta daga mota. Cikin gida Umaimah da Ruma suka shiga karbo abincin, Anty ta samu da wasu qannen Mama biyu a kitchen suna hidima suka dibi wanda ze ishe su ga ruwa da Zobo masu sanyi, sabulun wankanta ta tuna yana dakinsu dan haka ta cewa Ruma tayi gaba gata nan zuwa. A dakin ta tarar da Mama tana zaune akan gado Nuratu na durqushe a gabanta tana kuka. "Zonan, ina kika tsaya tunda kuka dawo baki shigo gida ba?" Maman ta fada tana kallonta idonta da alamar itama kukan tayi ko take so tayi se Umaimah ta qarasa kusada Nuratun ta zauna a ranta tana cewa "Bata bada labarin abinda ya faru ba kenan". "Kamar yanda na fara gayawa yar uwarki daga yau ba zamu sake samun lokaci irin haka nida ku mu zauna ba, duk abinda ya kamata ku sani kun rigada kun gani a aikace tsahon shekarun da mukayi tare daku. Kuna shirin shiga wata sabuwar rayuwa ce me cike da qalubale kala kala wadda idan kukayi haquri kuka jure sakamakonta me girma ne wato Aljanna. Aure ya wuce duk yanda kuke zato, duk abinda kuke hange a cikin rayuwar gidajen wasu zahiri ne amma badinin aure bazaka sanshi ba se randa ka tsinci kanka a cikin sa. Abinda nake so ku saka a ranku shine Aure ibadar Allah ce, kamar yanda zakuyi sallah dan lada to ku tabbata duk wani abu da zaku aikata a cikin gidan aure kuyi shi domin samun lada. Banida matsala da Nuratu amma dukda haka zanja kunnenku gaba daya shi Miji shugabane ubangiji ne ya bashi wannan girma da darajar dan haka a matsayin mace da take qarqashinsa dole ta girmama shi in har tana so ta gama lafiya. Umaimah duk wata rashin kunya da fitsara da kikeji dasu ki tattara su ki ajiye a cikin gidan nan domin idan har kika tsallaka da daya zuwa gidan aurenki ki tabbata da cewar kin qulla guzurin kai kanki wuta da qafarki Allah ya kiyaye. Girmamawa tsakanin ku da Mazajen ku dolece haka iyayensa da duk wani da yake gaba daau dole ku girmamashi tamkar yanda kuke girmama na gaba daku sannan kuso qannensu kamar yanda kuke son naku. Karku zama masu yawan qorafi da kai qara, Banda fitar da sirrin gidan auranku, matsala idan ta faru ku zauna ku warwareta a tsakanin ku indai ba tafi qarfin ku ba shine zaku sako na gaba daku a ciki. Ku zama masu tattali da kula akan duk abinda Mijinku ya kawo kuma ku zama masu godiya da nuna jindadi idan sunyi muku abu komai qanqantar kyauta ku gode koda kuwa abun beyi muku ba ko bakqmwa so hakan yana qara musu qarfin guiwar suyi muku. Umaimah banda jajibe jajiben qawaye, Kullum addu'ata Allah ya rabaki da qawayen banza Allah ya karbi Addu'ata ina fatan zaki dore kici gaba da rayuwarki a haka tunda babu abinda ya ragu a jikinki saboda kin dena tara qawaye sema qarin samun nutsuwa da kika samu a rayuwarki to kiyi qoqari ki dore a haka. A qarshe ina so ku dauki rayuwar gidannan data sauran yayyenku dan ta zame muku madubin dubawa. shekarata Talatin da Tara a cikin gidan nan tareda Mahaifinku amma daidai da rana daya ban taba fita da sunan yaji ba, da dadi babu dadi nayi haquri mun zauna gashi har na haife ku kun girma ina shirin aurar daku da kuka rage a gabana kunga bani da abin cewa sedai na godewa Allah na kuma qara gode masa kuma ba komai bane jigon zamana se haquri da Addu'a sune manyan makaman da in har bawa ya riqe su baze taba tabewa ba a rayuwarsa. Allah yayi muku albarka, Allah ya albarkaci gidajen auren ku yasa mutuwa ce zata fito daku, Allah yasa ku zama sanyin idaniyar abokanan zamanku ku ya basu ikon riqe ku da Amana". Kuka Nuratu takeyi Hajiya Umaimah kuwa jiki dai yayi sanyi se qifta idanu takeyi. Muryar Mama taji tana cewa Nuratun taje taci gaba da sabgoginta se itama ta miqe Maman ta dakatar da ita tace "Zauna ban gama dake ba" seta nemi guri ta zauna a ranta tana cewa "Ashe da saura na zata bata fada ba wallahi kuwa in har aka mun fada itama se ranta ya baci sedai muci bikin kowa da bacin rai". "Umaimah" Maman ta kira sunanta sam babu wasa a muryarta kafin taci gaba da cewa "Bana buqatar jan wani dogon bayani, Allah ya gani a cikin yaya bakwai daya bani ban banbanta wani da wani gurin bayar da tarbiyya ba, na raine ku akan turba daya na koyar daku abu daya amma kin fita daman da sauran ta kowacce siga. Ina so ki sani daga yanzu zaki koma cin gashin kanki ne kuma zuwa nan da wani lokaci kema zaki zama uwa me bada tarbiyya dan haka kisan abinda kikeyi. Ki nemi guri ki zube duk wani shirme da rashin hankali da kika mayar dabi'a ki gane ainihin rayuwa da inda ta saka gaba. Aiki da ake sakaki kiqi yi ko kiyi abinda kika ga dama, girkin da kike cika mana gishiri ko yaji a ciki da duk wasu sauran Iyashege da kikeyi a cikin gidan nan tamkar karatune yanzu ne zaki fara zana jarabawar abinda kika koya, idan kinyi da kyau ki wuce lafiya idan kin fadi kece a ruwa dan ni babu ruwana Allah shine shaidata duk abinda ya kamata Uwa ta koyawa yarta na koya miki. Ina sake jaddada miki batun qawaye babu ke babu su, ki tattara kowa da komai a gefe ki fuskanci gobenki Umaimah, wannan Azabar kishin da kika sakawa ranki ki cire idan kinqi ke zaki sha wahala dan karki taba zaton yanda yake biye miki a waje kici mutuncinsa ki bashi haquri daga baya ya haqura ki zata haka zata ci gaba a cikin gidan, bana miki fatan ya zama daga cikin mazan da suke shanye wulaqancin Mace a waje idan ta shiga hannunsu su rama amma koma me ya biyo baya ke kika siya da kudinki dan abinda kika shuka ne zaki girbe". Da sauri Umaimah ta daga kai ta kalli Maman tace "Mama karkiyi mun baki dan Allah ki yafe mun duk abinda na tabayi miki na ba daidai ba wallahi sharrin shaidan ne kuma in sha Allahu Mama se kinyi Alfahari da aurena se na bawa kowa mamaki duk wanda yake jiran yaji wani abu mara kyau a kaina sedai ya gaji amma babu abinda ze faru" ta qarasa maganar tana sakin kuka saboda wasu tunani da suka yi mata dirar mikiya a zuciya. Irin labarin izayar da mata suke sha a hannun maza datake ji kota karanta a Novels yanzu idan ta fada cikin irin wannan rayuwar ina zata saka kanta. "Ba baki na miki ba Umaimah a kullum ina roqon Allah da karya kamaki da laifin bata mana da kikeyi cikin sani ko rashin sani kullum Addu'ata itace Allah ya shirye ki yasa ki gane gaskiya ki dena abinda kikeyi kuma in Allah ya yarda Addu'ata bazata tabe ba, zaku samu kyakykyawar rayuwa a gidan auranku tamkar sauran yan uwan ku amma dukda haka se kin dage kin chanza halinki, na yafe miki duniya da lahira Umaimah, Allah yayi miki Albarka Allah ya zama gatanki" Maman ta qarasa tana miqewa saboda kukan daya taho mata. Babu shakka dagaske Da mara ji yafi shiga zuciyar iyaye dan a cikin yaranta son da takewa Umaiman na daban ne haka ma Abbansu ta sani amma Halinta ne yasa suke dannewa suke nuna tamkar basu damu da ita ba. Kuka Umaimah tasha sadidan ga tunanuka kala kala na gifta mata a kwakwalwa, yaya gidan auranta ze kasance? Zata samu farinciki da soyayyar da take hasashe a gurin Khalil? Shin Khalil din ma ze dore da halayensa na yanzu har cikin gidan auransu ko kuwa shima yana cikin irin mazan da suke kwantar da kai a waje dan su samu abinda suke so?. Tsoro da fargaba ne suka rufeta har tana jin kamar zazzabi ze kamata dan ita bata taba zama tayi tunani akan yaya makomarta a gidan aure zata kasan ce ba, shin idan Khalil ya canza mata ina zata tsoma ranta?.. Washe gari akayi Kamun Amare tareda Mother's Eve a hade, Amare sunsha kyau cikin shigar Lace da sukayi iri daya kai tsaye bazaka iya cewa ga wadda tafi wata kyau ba saboda yanda kayan sukayi matuqar karbarsu, Dangin Khalil sun nuna mata qauna kowa fadi yakeyi tayi sa'ar dangin Miji se fatan Allah yasa su dore a haka, seda aka kusa tashi Angwaye suka je gurin wanda Anty Laure ce qanwar Mama ta takura se sunje ko yaya ne saboda mutane su gansu musammab Khalil tunda ita Nuratu washe gari idan an kaita zasuyi dinner. Umaimah nacan tsakiyar Qawayen ta suna kwasar shoki akayi sanarwar shigowar angwayen, a zaton ta Dr Sagir ne kadai tunda daman shi dan bidi'a ne tasan ze aikata Khalil kuwa ko kafin su taho bayan an gama mata kwalliya sunyi video call yana kwance a dakin Mansur dan can ya kwana tasan baze zo ba. Wani qum taji kamar an buga mata guduma akai lokacin da angwayen suka shigo, Dr Sagit da Architect Khalil suka jero a tare sun sha Milk din shadda dinkin babbar riga iri daya kamar yanda amaren nasu suka saka Lace kalar cream saboda dukkan su fatarsu bame haske bace dan haka kalar ta haskaka su sosai. Kallon daga sama har qasa tayi masa a qasa da second talatin, yanda ya kafa hula yana sakin wannan murmushin nasa saboda Jalila dake binsa ta gefe tana rada masa abinda Umaiman bata san ko menene ba, kallon mutanen da suka ciro wayoyinsu suna daukar angwayen hoto tayi, idan ba qarya idonta ya mata ba fiye da rabinsu Khalil suke dauka. Daga gefenta ta ji daya daga cikin qawayen ta tana cewa "Lah Amina ina wayarki ki daukar mana Angon Umaimah Sabo mu samu na dorawa a status ai a sittin ta juya sedai cikin rashin sa'a tsinin takalminta ya karkace ta tafi luuu ta gama saddaqarwa Amarya zata sha qasa taji ta ta fada jikin mutun ya saka hannu biyu ya riqeta da kyau yana ce mata "Yi a hankali Babe karki ji ciwo". Fuskarsa ta shiga qarewa kallo, ashe kyan data hango yayi mata daga nesa wasa ne se da yazo kusa sannan taga asalin kyau, askin da yayi da gyaran fuska an gyara masa gemun daya fara tarawa ga kuma Kyan Angonci suka qara bawa fuskarsa wani kwarjini na daban, yanzu haka duk matan da suke gurin zasu kalle shi harma sun dauki hotunansa a wayarsu amma wallahi an cuceta kawai se gani Khalil yayi ta fashe da kuka yanda kasan wadda ya fallawa Mari. PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 PAGE 17 "Menene?" Khalil ya fada yana qoqarin miqar da ita tsaye daidai lokacin da Yaya Hafsa ta qaraso gurin tana tambayarsa lafiya ko taji ciwo ne. "Me yasa kazo bayan kasan bana so kowacce mace ta ganka? Yanzu gashi nan har hutunanka suke dauka da wadda ta isa da wanda bata isa ba suna yaba kyan da kayi, wallahi ka fita idan ba haka ba sena watsa taron nan kowa tashi" ta fada tana ci gaba da ziraro da hawaye. Tsabar takaici sakinta kawai yayi ya miqe tsaye daidai sanda Anty Hafsa ta qaraso tana tambayarsa lafiya ko ciwo taji, a taqaice yace mata "Wai saboda nazo ne take kuka yammata zasu kalleni su dauke hotona" "Amma Umaimah ban taba sanin yar kutumar uba bace ke se yau, a gurin taron bikin ma sekin siyar da hali? Toh karki fasa na rantse da girman Allah yanda bakiyi hankalin ajiye haukarki a gida kafin ki fito ba haka nima bazan ji shayin nada miki dan iskan duka a gurin nan ba,karki miqe ki koma mazaunin ku wallahi se kinci ubanki" Anty Hafsan ta fada a fusace dole Umaimah ta miqe bayan data share hawaye dan tasan idan iya shege take ji dashi Hafsan ta fita, kamar yanda ta fada ta daketa a gurin ita ba wani babban abu bane a gurinta. Haka aka qarasa taron biki Amarya Umaimah da Angonta dai babu armashi daga bangarensu, Daga ita har Khalil din fuskarsu babu fara'a, shi tsabar takaicinta ne ya hadu ya qume shi. Da murnar sa ya shigo, irin kyan da ta masa baze misaltu ba yana jira yazo ya rada mata a kunne irin yanda ta burgeshi yayi mata liqi da sabbin dollars din da aka bashi kyautarsu dazun da safe saboda ya sake nuna wa mutane ita din yar gatansa ce se gashi kalar tarbar daya samu a gurinta kenan ita kuwa takaici da baqin ciki qiris ya rage su qarasata, yanda ake ta daukar su a hoto sam mutane basu damu da hade fuskar ma da sukayi ba kai kace su kadai ne Amaren a gurin ita kuwa Nuratu da Dr ta shagalinsu sukeyi sun more ranar tarihinsu dan ba sake dawowa zatayi ba. Da aka tashi a mota daya suka tafi, tana zama tun bata kai ga rufe qofa ba dan ya rigata shiga ya tare ta da cewa "Na rantse da Allah Umaimah wallahi kika kuskura kika qure haqurina bazata mana da kyau ba, ke bakya gudun abin kunya a rayuwarki? A gurin taron biki ma se kin nuna musu rashin nutsuwarki? Akan me? Kanki aka fara aure ko yaya ko a kaina ango ya fara zuwa gurin biki da zaki nemi ki jawowa mutane magana? Ai wallahi da kinci gaba da abinda kika fara da kinga qarshen hauka yau ai na gaya miki bake kadaice saitin kanki yake gocewa ba" Khalil ya fada cikin masifa kamar ze rufeta da duka Mansur dake gaba kuwa yace me zeyi idan ba dariyacenDariya yake harda dungurawa dantun farkon Dramarda akayi a Hall din har video yayi a ransa yana sake jajantawa abokinsa dan dagaske yanzu ya yarda ya dakko cin kai. Allah sarki Umaimah ko sakato tayi tana kallon Khalil dake zabga bala'i, seda yayi shiru dan kans kafin ta sunkuyar da kai qasa se sababbin hawaye shar suka fara zubo mata. "Kinsan Allah akan ina miki fada kina mun kuka se kin gane kurenki, kawai saboda kin mayar dani wani sauna se kinmun laifi ina miki fada ki fara kuka ki mayar da abun kamar ma nine nake cin zalinki ko kici gaba" Khalil ya sake hayayyaqo mata ita dai kanta na qasa tana hawaye, idan ta tuna yanzu fa hotunan Khalil nacan suna yawo se taji kamar ta kurma ihu haka suka dauki hanyar gida tana hawaye Khalil na buga tsaki. A Murtala Suya Mansur ya tsaya ya juya ya kalle su da murmushi yace "Afuwan Amarya bari na karbo miki kaza nasan hidima bata barin ku kuci abinci" be gama rufe baki ba ta dago a fusace tace "Naqoshi" "Kinwa kanki, Malam karbo mana mu zamu ci" Khalil ya fada yana galla mata harara se  Mansur ya juya yana ci gaba da dariya yace "Easy Ango kasan Amarya fa s ana lallabata", be wani jima ba ya dawo da ledoji ya bude sit din gaba da babu kowa ya zuba suka qara gaba, seda ya sake tsayawa a Rufaida ya siyo Yoghurt da Lemo kafin suka qarasa gidan su Umaimah yana tsaida motar tun be ida parking ba ta balle murfin ta fice har tana yarda Asoken hannunta da cloche. Mansur da kansa ya dauki ledojin Kazarta da yoghurt ya nemi daya daga cikin yammatanda ya gani suna fira a qofar gidan ya bata da kayan ta data zubar kafin ya koma mota lokacin har Khalil ya dawo gaban ya cire hular sa yana shafa kansa. "Khalil be kamata ka ringa mata ihu haka ba, kasab matsalar yarinyar nan nasiha da lallami ne ze tafiyar da ita bawai hargagi ko fada ba" Mansur din ya fada bayan daya tayar da motar suka fara tafiya, Khalil yayi shiru kamar baze yi magana ba can ya sauke ajiyar zuciya yace "Mansur ina son Umaimah amma bazan boye maka ba ina tsoron irin zaman da zamuyi da wannan halin nata. Ace ita bata san ya kamata ba? Ka kalla fa Mansur idan badan Anty Hafsa tayi mata horo ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba na tabbata yarinyar se tayi abinda har a freedom radio se anji labarin mu sannan kana kallo ina mata magana a maimakon ta bani haquri ma se wasu hawaye takeyi saboda tasan bana son kukanta to ta dena yaudarata da su wallahi". Shidai Mansur yayi bakan yana jinsa har suka qarasa gidansu, suna shiga Mukhtar daya daga cikin Abokansu ya kira wayar Mansur yana musu masifar gasu a Hotel tun dazu su ina suka tsaya dan sun hada Barbeque zasuyi, haquri ya bashi kafin ya shiga lallaba Khalil din da gaba daya Umaimah ta gama bata masa mood ya tashi ya shirya suka fita bayan daya bawa qannensa Kajin da suka siyo dan shaf ya manta da batun barbeque din. Umaimah kuwa tana shiga cikin gida a sittin tayi kwana saboda hango Anty Hafsa data kasa ta tsare bakin hanya tana jiran shigowar Umaiman daman sedai ta makara dan tara tara suka mata Anty Laure na daga bayanta dan haka tana juyawa ta riqeta. Yanda kasan sun samu Damin gero haka suka hau jibgarta ihun ta ya fito da yan biki ana tambayar lafiya Anty ta kwaceta da kyar daga hannunsu tana masifa tace "Wannan wane irin wulaqanci ne Hafsa? Kema Laure zaki biye mata ku kama yarinyar da duka salon ku ja mata tsautsayi ta tafi gidan miji da jinya" "Idan bata tafi da jinya ba ai mu data zubar mana da mutunchi ta barwa kanta abin magana har yaya da jikoki, banda tsabar iskanci dan ubanta ta rasa ranar da haukarta zata tashi se yau a cikin taron jama'ata bata mun tari? Ai ba a nan ya kamata ku dake ta ba, so nayi seta tube ta shiga wanka zan kama yar banza ga Darbejiya can na saka Salmanu ya tsinko mun na farfasa wa yar banza jiki idan yaso tayi jinyar da kyau" Mama data qaraso gurin ta fada. Ita dai Umaimah tunda ta samu Anty ta ceceta sukayi ciki shikenan, can uwar dakinta ta wuce da ita ta hada mata ruwan wanka tana yi tana mata fadan abinda tayin "Yanzu Umaimah idan bakiyi hankali ba se yaushe zakiyi? Kina kallo Allah ya taimakeki ya hada ki da dangin miji masu sonki ki kalli yanda suke rawar jiki dake a gurin nan shine kikaje zaki bada kanki. Dan Allah ko koyi haquri ki kuma ringa sakawa zuciyarki salama dan wallahi yanda Khalil yake binki yana lallabaki a waje ina tabbatar miki daga gobe labari se chanza, halinki na gari ne ze zaunar dake a gidan miji, duk wannan buyagin da hayagaga babu abinda zasu ja miji se wahala" Antyn ta fada tana shafa mata dilka a jikinta. Umaimah dake jin kamar ta sauke fushinta akanta ta dai daure ta ringa cewa toh dukda qasab ranta tasan gaskiya suke fada mata dan gashi nan tun ba'aje ko ina ba ta fara ganin chanji a gurin Khalil din, gashi jiya dakyar suka sasa ta yanzu ma ta sake kunno wata rigimar kai ita dai Allah ya shiga lamarinta. A dakin Antyn ta kwana dan da Abba ya aiko kiransu shida yan uwansa zasuyi musu Nasihar bankwana ma Antyn ce ta rakata ta kuma kasa ta tsare har aka gama suka dawo ta bata Kazar data dafa musu da tafasashshiyar madarar shanu taci tayi nak kafin tayi bacci. A safiyar washe gari dakyar ta yarda akayi mata light Make up ta shirya cikin fari da Golden din Lace iri daya dana Nuratu dake walwalarta kamar kowacce Amarya, ita kuwa ta samu guri ta zauna zugudi duk yanda qawayenta suke tsokanarta da amma ta kasa tanka musu dan rashin ji daga Khalil da batayi ba tun daren jiya ya bala'in daga mata hankali. Furucinsa take tunawa da yace mata idan ta sake yin wani shirme ba ana gobe daurin auransu ba ko a ranar ne seya fasa yanzu ita ta rasa ma a wanne matsayi take dashi dan tun jiyan be kirata ba ita kuma tsoron abinda zeje ya dawo ya hanata kiransa a waya haka ta zauna ana ta hidimar daurin aure kowa ka gani cikin farinciki banda yana walwala banda ita. Alqawarin Allahya cika, qarfe 11 na safiyar Asabar din Aka daura Auran Dr Nuratu Sabo da Angonta Dr Sagir Nafi'u Tareda na Umaimah Sabo da Angonta Architect Khalil Umar Bayero akan sadaki naira Dubu 100 kowaccensu. Dafe qirji tayi lokacin data ji sanarwar daurin auran ta cikin lasifiqar masallacin layin nasu inda ake daurin auran, Khalil be fasa ba kenan?. A zahiri babu wata murna ko farincikin data nuna amma badininta ko fadar yanayin da take ciki ma bata bakine, wai dagaske yau ta zama matar Khalil ta halal daga yau sun zama daya ita dashi ina zata saka kanta dan murna amma sam halin da take ciki ita da angon nata ya danne murnar se ya zamana kawai gatanan ne tana zaune. Lokacin da Angon Nuratu da Abokan sa suka shiga gidan Dakin Anty ta shige ta zauna dukkiran ta da ake akan ta fito suyi hoto taqi to ta fita tayi musu me? Baqin ciki ya kasheta tunda ita nata angon ba zuwa zeyi ba? Tana nan zaune ta jiyo wata maroqiya ta ware murya tana zabga kirari, idanba kunnenta ne ya jiyo mata qarya ba sunan Khalil tajiyo tana ambata sannanga wata sabuwar hayaniyar maza na shigowa seta miqe da sauri ta daga labulen window ta leqa idonta ya sauka kan Khalil daya sha Light blue din shadda yayi kyau har bata san yanda zata misalta ba, kumallon ya motso mata saboda yanda ake ta daukar Angwayen hotuna da wayoyi amma taringa qoqarin dannewa se numfarfashi take kamar wadda kunama ta harba daidai nan Maman Asad ta turo qofar dakin tana cewa "Allah ya yaye miki baqin hali Umaimah, nan kika zo kika boye ga angonki can yana nemanki dalla wuce muje mutuniyar banza kawai da bata san Annabi ya faku ba" Maman Asad din ta qarasa tana kamo hannunta suka fice daga dakin. Kasa riqe hawayenta tayi lokacin da Maman Asad ta qarasa da ita gaban Khalil dake tsaye fuskarsa babu yabo babu fallasa, girgiza mata kai yayi alamar kartayi kukan amma ina kamar yace tayi sega hawaye sha se kawai ya bude mata hannu ta fada jikinsa ta qarasa sake masa kukan harda sheshsheqa. Ihu aka dauka masu daukar su hoto da Video kuwa daman sun samu nayi qawayenta se ihu suke suna daukar su a hoto "Awwn love in Tokyo, Umaimah bazaku kashe muda salonku ba wanda bashi da masoyi ai se takaici ya qume shi" Yaya Naziyya ta fada cikin salon wasa aka sake fasa dariya Umaimah dai tunda tayi luf A jikin Khalil, a kunnenta ya rada mata "I get you wife" . Haka aka ringa daukar su hotuna, ran Umaimah kamar an saka Hypo an wanke matashi tas dukda fuskar Khalil din babu fara'ar nan data sanshi da ita amma kukawar daya bata a gaban mutane ta gama mata komai, ta kuma tabbatar da zuwa dare zasu sasanta dan bazata bari ta shiga gidan sa suna takun saqa ba. Haka aka gama photo session Angwaye suka wuce gurin reception Amare kuma aka shiga hidimar yinin biki da shirin miqasu gidajensu saboda da wuri za'a kaisu dan Dangin Mijin Nuratu zasuyi Dinner. Qarfe hudu aka dauki Amare, Nuratu aka fara kaiwa Umaimah tayi mata rakiya har cikin dakinta, shaquwa ba qarya ba, duk irij tarangahumar tashin hankalin da suke sha a gida kamar masu ganin hanjin juna se ga Umaimah ta fashe da kuka da batayi ba a gida har aka taho dasu ta fada jikin Nuratu suka rungume juna. Yanda suke kukan dole suka karyawa sauran yayyensu zuciya suka hade gaba daya suka ruguntsune, jarumtar da sukayi a gida se gashi Umaimah ta karya musu dakyar aka yakiceta suka wuce nata gidan aka bar Nuratu da wasu daga cikin Masu halartar Dinner kafin sukaita itaka su koma gida su shirya. A dan madaidaicin gidan na Khalil aka sauke Amarya Umaimah. Gidan two bedrooms ne a cikin madaidaicin palour asalin ginin daki daya da bandake ne daya babu daya tashi gyara ya tashi wani daki falle daya dake tsakar gida ya shigar da bandaki a dayan dakin ragowar ya qara mata a kitchen da yake atsakar gidan shima aka fitar fa store se qaramin bandaki na tsakar gida. Gaba gidan bashi da girma dan filin tsakar gidan mota daya ze dauka amma yanda Khalil din ya saka kudi ya gyara gidan abinka da Architecture dole duk wanda ya shiga seda ya tafi da santin gidan ga hadaddun Furniture da suka qara qawata gidan sun saka komai yanda ya kamata. A dakin da yake matsayin nata suka ajiyeta, Nasiha sosai Anties dinta sukayi mata irin me ratsa jiki da tasa Umaiman tayi tubus kamar wadda ruwan sama yayi wa duka kafin sukayi mata sallama aka barta da qawayenta uku, Rumasa'u, Farida Cousin dinta se Fatima. Su suka gyara mata gidan tsaf suka wanke bandakuna. Seda sukayi sallar Magriba kafin Umaiman ta sake wanka, kafin ta fito sun bi gidan lungu da saqo sun saka hadaddun Turaren wutar da Akayi musu a gurin *Meerah_Perfumes_More* wanda Gudummawa ce takanas Aminiyar Mamansu Hajiya Findiga ta aiko musu shiga daga Adamawa inda take. Seda sukayi sallat Isha kafin su Ruman suka fara haramar tafiya dan shiru babu Angwaye, tana cikin yi musu magiyar kar su tafi su barta ita kadai su qara jira yanzu zasu zo Farida na masifar me yasa ita bazata kira Khalil din ta gaya masa zasu tafi ba se wani su zauna take cewa suka jiyo qarar bude Get. A dakin suka barta suka koma palour Khalil suna zama su Khalil din suka shigo su hudu, Mansur, Mukhtar se Cousin dinsa Awwab. Rumasa'u ce ta fito musu da Umaiman data sha uban lullubi da laffayar data nade jikinta har fuska ko gani batayi se Ruman ce take mata jagora ta zaunar da ita akan two sittet inda Khalil ke zaune. Basu wani bata lokaci ba bayan barkwanci da aka san kowanne abokan Ango da qawayen Amarya nayi daga nan Mansur ya bude musu taro da addu'a, sosai sukayi musu Nasiha da shaqarwari ta daidai matsayi irin nasu na Abokai Awwab ya rufe musu bayan da suka ajiyewa Amarya kedojin kayan siyan baki suka bawa qawayenta kudin kati kafin sukayiwa Amarya da Ango sallama kowa ya miqe aka fara haramar tafiya. Umaimah bata taba zaton zataji irin abinda taji lokacin da suka fara barin palor suna mata sallama da fatan Alkhairi ba, shi kenan yanzu fa ita tazo ita da gidansu ko wani guri sedai yawo duk inda zataje ta dawo nan din dai nan zatazo ta shigo sabuwar rayuwa da bata da tabbacin a yanda zata zo mata. Tana zaune tana tunanin taji motsin rufe qofar Khalil da yayi musu rakiyaz kamar munafuka ta dago ido ta saci kallonsa karaf suka hada ido gabanta ya yanke ya fadi, fuskar sa a dinke ga wanu kallon da taga yana jifanta dashi data kasa fassara kona menene gashi kamar wadda ya sakawa glue ta kasa janye idonta daga nashi. "Zo" ya fada yana kallonta, seta miqe jiki babu laka ta nufeshi, hannu ya bude mata bata bata lokaci ba ta fada jikinsa ya mayar da hannun ya rufe. Wata irin runguma yayi mata da seda taji kamar ze hade mata qasusuwan jikinta tayi yar qara saboda taji zafi dagaske, rabata yayi da jikinsa fuskarsa dauke da murmushin da yau ta kira dana mugunta yace "Na dena bata yawun bakina yanzu ian da hanyoyi da yawa da zan hukuntaki yarinya karki fasa rashin ji" kafin ta samu damar cewa wani abu ya sake sakata a jikinsa tareda hade bakinsu ya shiga mata wani kalar kiss daya sa taji kamar hankalinta ze bar jikinta. Abu biyu ne suka dirar mata lokaci daya, na farko tsoron sabon Al'amarin daya risketa san a rayuwarta babu wani Da Namiji daya taba rungumarta kamar haka balle har ya kai ga kissinga nata. Duk rashin kunyarta da fitsara ta wannan bangaren babu ita a lissafi, bata yarda da Namiji ya tabata ba koda cikin kuskure ne se tayi maka tas balle ka aikata mata hakan a cikin sani ranar me rabasu se Allah. A cikin samarin da tayi daman Alqasim ne me halin son taba jikin mace shima tunda tayi masa kadan daga haukanta ya kiyayeta se gashi yau Khalil ya fara dora mata karatun da ba'a kowacce makaranta ake koyashi ba. Bata ankare daya warware mata laffayar dake jikinta ba seda taji su warwas a qasa, zip din rigarta da taji yana lalube ya sakata dawowa hayyacinta ta tureshi zuciyarta na tsalle kamar zata fito tsabar yanda ta tsorata ga Labbanta da lokaci daya suka dauki zugi na rashin sabo da abinda suka gamu dashi yau ji take kamar harshenta ma ciwon yake, dakyar ta ja jikinta ta takure a jikin kujera inda Gogan ya kwanta shiru kamar wanda ruwa ya cinye kusan minti biyar kafin ya yunqura ya tashi zaune, yanda Umaimah taga fuskarsa ta qara tsorata, wani irin jaa da idonsa sukayi suka qanqance gaba daya ta tafi tunanin maganar da Halima ta gaya mata da tace masu shiru shirun nanirin Khalil idansuka kama mace seta gane kurenta. "Kuka kuma me akayi miki?" Ya fada cikin dasashshiyar murya kamar wanda yasha kayan maye se Umaimah ta kai hannu idonta ta shafa taji danshi kuwa ashe kuka take ita bata ma sani ba, hannu yakai ze taba ta ta zabura yanda tayin dole ta saka Khalil dariyar da be shirya ba yace "Rekax, ba abinda zanyi miki yunwa nakeji sosai ki bani abinci naci". A dari ta miqe ta tafi luu zata fadi saboda skirt dinta daya harde ta, "yah subhanallahi" ta fada a fili ta shiga tattaro skirt samata zuge kafainta mayar da zip dinrigar daya fara zugewa shima, toh wai duk a yaushe hakan ta faru ne? Laffayarta ta sake tattarowa tana so ta daura amma rawar da jikinta yakeyi yasa ta kasa Khalildaya jingina da kujera kawai yana kallonta kamar ya samu TV ya miqe dakyar ya qarasa bayanta, Laffayar ya karbe ya dora kansa a wuyanta, cikin kunnenta ya rada mata "It is just me and you, lullubin me kike nema? Ki barni na kalli baiwar da Allah yayi mun Babe" Ai gaba daya ya idasa wargaza mata yar nutsuwar da tayi mata saura a jiki, yanda take wani abu kamar wadda Shocking ya kama ya sakashi dariya sosai, jan ta yayi ya zaunar da ita akan kujera kafin ya shiga kwashe ledojin da suka shigo dasu ya fita dasu kitchen. Seda ya fitar da komai ya sakashi a inda ya kamata kafin ya daurayo plates da cups da duk abinda zasu buqata ya sake komawa palour har sannan Amarya Umaimah na nan zaune ta dai nemo dankwalinta ta lullube kanta zuwa qirji dashi. "Oya come lets eat" ya fada bayan daya gama juye gasashshiyar kaza a plate dayan kuma ya zuba tsire, ga qatuwar robar yoghurt ya ajiye musu a gefe da lemon exotic be tsaya bata lokaci ba ya fara aikawa cikinsa dan rabonsa da abinci tun safe. Ganin yayi loma biyu bata sakko ba ya waiwaya ya kalleta yace "Umaimah sakko mana" "Ni na qoshi bana jin yunwa" ta fada a hankali, se ya saki murmushi yace "Gara ki sakko kici ko bakya jin yunwa saboda ki qara samun qarfin daukata" ya qarasa yana kashe mata ido seta saki baki galala kamar lefen sakara kawai tana kallonsa, kai itafa Khalil ya fara bata mamaki yanzu duk kunyar nan tasa da shiru shiru ina suka tafi da ze ringa mata abubuwa haka yana zaro zance? Naman daya kawo bakinta ya dawo da ita tunanin data tafi, ba yanda ta iya dole ya sakata ta sakko suka ci naman, dadin daya mata se gashi bata san lokacin da suka cinye kazar tas ba dan itaka kura ce ta gaske. "Da kina noqewa gashi nan kin tashi da kazar ni ko ci ma banyi ba" ya fada cikin sigar tsokana seta sunkuyar da kai dan taji kunyar yanda ta zage taci naman. Plate din tsiren ya tura mata tace ta qoshi, ya cika cup taf da madara ya bata ba yanda ta iya swda ta shanye ta ajiye masa kafin yana murmushi yace "Good girl, yanzu se muje muyi wanka muyi sallah ko? Kinsan Ibadah bata yuwuwa se ciki ya dauka" ya fada yana shafa cikinsa. Kwanukan ta fara hadawa ya dakatar da ita, dakansa ya sake kwashe komai ya fita dasu abinda basu cinye ba ya saka a fridge ya dauko qaramin akwati daga motarsa kafin ya sake tofe ko ina da addu'a kafin ya shiga ya kulle qofar palour gaba daya. Be tarar da Umaimah a palour ba ta tattara yanata ya nata ta shige daki. Dakin da yake tunanin nata ya tura ya shiga tana tsaye tana cire kaya jin shigowarsa ta durqushe qasa da sauri tareda sakin ihul tana janyo Towel din data ajiye akan gado dan ta rigada ta cire skirt da rigar, Bra jikinta take ballewa. "Duk ki gama boye boyen yarinya zakizo hannuna" ya fada yana ajiye mata ledar daya dakko kafin ya fita yaja mata qofar dakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta tashi da sauri ta murzawa qofar key. Wanka tayo hade da Alwala ta shirya a nutse kamar yanda Anty Hafsa ta karanta musu. Ledar daya ajiye ta jawo ta bude, wata hadaddiyar rigar bacci ce kalar ja me jikin silk, yanda ta dagata tasan da kadan zata wuce mata mazaunai, hannun vest ne da ita ga qirjin ta da akayi da Lace tasan babu abinda zata kare seta ajiye tana cewa "Tabdi ni zan saka wannan abun ma kenan? Yanzu kuma idan ban saka ba se yaji haushi, bari na saka sena dora Hijabi akai" ita kadai tayi kidanta tayi rawarta. Sanda ta saka rigar ita kanta juyawa ta ringayi tana kallon kanta, tayi mata kyau ta kuma karbi jikinta, bugun qofar da taji yanayi ya sakat saurin rarumar Hijab ta saka kamar mara gaskiya ta bude qofar. "Muje" ya fada bayan daya shaqi daddadan qamshin da dakin yakeyi, ya nuna mata qofa tayi gaba yana binta a baya zuciyarta kamar zata fito waje saboda tsorio. Dakin da yake mazaunin nasa suka shiga, se taga gadon ciki har yafi na dakinta ma kyau ta tura baki tana qarewa dakin kallo "Lafiya" ya fada yana kama hannunta, seda ta kuna shagwabe fuska kafin tace "Gani nayi gadonka yafi nawa kyau" "Gadon mu dai, nan shine dakin mu ni da Umaimatah" ya fada yana yi mata peck a baki ta sunkyar da kai dan ita fa kunya abun yake bata. Sallah yaja su raka'a biyu bayan sun idar ya dafa kanta ya yi musu addu'a, duk tambayoyin daya kamata yayi mata akan addini ya mata kuma Alhamdulillah ta bashi amsa daidai saninta bayan sun shafa addu'ar yace ta hau gado ta kwanta shi kuma ya fice daga dakin, kusan minti biyar da fitarsa har idonta ya fara rufewa saboda dagaske ta gaji tana buqatar hutu taji an turo qofar. Jallabiyyar dake jikinsa ya cire ya ajiye kafin Kai tsaye ya nufi kan gadon Umaimah na ganin ya taho ta buga tsalle ta koma gefe, ita fa da yace ta kwanta harga Allah ta zata ita kadai zata kwana bata ankare ba se ji tayi fit ya zare mata hijabin da take ta faman nuqu nuqu dashi da fasa qara saboda yanda ya sake kunna ragowar fitilun dakin masu haske yana qarewa rigar jikinta kallo, zillo tayi zata sauka daga gadon ya kamota da hannu daya ya saka dayan ya kashe fitilu, ganin bata san dare ba ita ta ware baki tana masa ihu yayiwuf ya hade bakinsu guri daya daga nan labari ya chanza salo. Asuba ta gari Mr and Mrs Bayero PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 PAGE 18 A hankali ta zame jikinta daga nashi ta tashi zaune tareda jingina bayanta da Allon fuskar gadon tana qarewa Khalil kallo yana sharar baccinsa harda munshari. Badan kartayi qarya ba se tace har wani kyau da kyalli fuskarsa ta qara, kamata yayi ace taji haushinsa akan al'amarin daya farun a daren jiyan tsakaninsu wanda ya girmi tunanin kwakwalwarta ballantana harshen ta ya iya furtawa. Yanda Khalil din ya gigice mata ya ringa sarrafata kamar ya samu pencil da takadda yana zane abinda yafi kwarewa akai sannan bakinsa ya kasa rufuwa daga surutan da idan ta tunosu ma seta rufe ido tsabar kunya abinda yafi tsaya mata a rai yanda ya ringa maimaita kalmar yana sonta yana qaunar ta da irin ruwan Albarkatun daya ringa zuba mata su suka taru suka wanke gingimemen laifin lallasa mata jiki da yayi. Sauke qafafunta tayi qasa a nutse ta miqe cikin takatsantsan gudun kartayi wani motsi me qarfi ta jigata jikinta da a daren jiya ta ringaji kamar tayi hatsari sedai lafiya lau ta ringa takawa har tabar dakin bayan ta kulle masa qofar a hankali. Dakinta ta koma, irin ruwan daya hada mata cikin dare ya wanketa dakansa ta sake hadawa ta shiga ciki ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Khalil qarshene gurin tattalin mace ta shaida hakan a qasa da awa ashirin da hudu da zuwanta gidansa. Yanda ya ringa lallabata yana tarairayarta a daren jiya bayan da komai ya kammala a tsakaninsu take tunawa, ya tara ruwa duk noqewa da rakin da take haka ya sakata ciki yana diba yana gasa mata jikinta seda ya canza ruwa uku kafin ya barta tayi wankan tsarki ta dawo dakin da har ya canza bedsheet ta sake kwanci. Be barta haka ba ya sake tada ta, madara me sanyi ya cika cup da ita ya bata ta shanye sannan ya ballo mata pain killers tasha ya ringa bubbuga bayanta yana fada mata kalamai masu dadi har ta koma bacci kafin shima ya kwanta. Da asuba me seda ya saka ta sake gasa jikinta kafin ya tafi masallaci ya barta bayan ya kulleta ta waje dan kamar ya sani niyya tayi yana fita ta gudu dakinta saboda cewar da yayi idanya dawo za'a qara tunda yaga ta warke shiyasa tana idar da sallah ta haye gadon ta qudundune kamar me bacci bawan Allah kuwa be tada ita ba se kwanciya yayi shima a bayanta ya rungumeta a jikinsa, tun tana jin motsinsa har baccin gaske ya dauketa se gurin qarfe tara ta farka. Jin ruwan da take ciki ya salamce ya sakata fita daga bahon ta bude rariya ruwan ya tsiyaya, har ta tara wani ruwan zatayi wanka ta tuna da wani Kwandon turaruka da Rumasa'u ta bata jiya a matsayin gudummawarta tace turarukan wanka ne, seta dauki towel ta daura ta fita. Kwance ledar da aka lullube su tayi ta juye Manya da qananan robobin akan gado wani irin cakudadden qamshin su me shegen dadi ya daki hancinta seta dauki guda daya ta duba sunan dake rubuce jikin sticker *MEERAH_PERFUMES_MORE* kamar ta san sunan, tabbas wanna sunan Matar da Akayi musu turaren wutar da aka jera musu a Show glass a gurinta ne lallai dole ma suyi kyau. Dubawa ta shigayi ta kwashe wadanda aka rubuta *Bath Mist* ajiki ta wuce dasu bandakin, ita kadai ta ringa sakin murmushi sanda ta zuzzubasu a ruwan wankan wani irin Exotic qamshi me sanyi da kwantar da hankali sukeyi haka tayi wankanta ta fito kamar kar ruwan ya qare amma babu komai kuma ta samu nayi. A gaban mirror ta zauna tana shanshana fatarta dake kyalli da walwalin ingantaccen gyaran da Anty tayi mata ga wani kata'in qamshi da takeyi na Birth mist din *MEERAH_PERFUMES_MORE*. Seda ta dauko Manzaitun me kyau da Anty Hafsa ta ajiye mata jiya ta zuba a hannunta ta shafe qasanta dashi kafin ta janyo lotion ta shiga shafawa a jikinta, ragowar qananan kwalaben *MEERAH_PERFUMES_MORE* ta duba ilai kuwa ta samu body oil ta budeshi ta kai hancinta seda ta rufe ido ta bude saboda qamshinsa. Da dan tsinke dake ciki ta ringa dangwala ta shafa a bayan kunnenta, wuya, saman cibiyarta, matsi matsin cinyarta baya ta goge ragowar akan cinyarta tana murmushi saboda yanda qamshin yake ratsata ta tabbatar idan Khalil yaji dole ya yaba. Wardrobe ta bude, kai sufa yan gata ne dan hatta da kayan sawarsu an jera musu, riga da skirt ta ciro na wata farar Atamfa me adon ja. Tunda aka dinka take cin burin sakata saboda yanda dinkin ya fita, seda ta saka undies kafin ta zura skirt din dakyar ya zugu saboda yanda mazaunanta suka cikashi taf ta juya ta sake juyawa a fili tace "Fatabarakallah ina ma yan ciki baqi na kusa sedai suyi bunga" ta saki dariyar iya shege ita kadai kafin ta dauki rigar ta saka. Daurin ture kaga tsiya tayi bayan ta barbada farar powder ta saka kwalli da lipglose me kyalli dan ita daman ba gwanar kwalliya a fuska bace. Turaren ta na dindindin Kalta Maryam ta sake fesawa ta ringa juyi a gaban mudubi ita kadai tana ihu kamar mara abin yi can kuma meta tuna ta zabura ta shiga tattare kayayyakin data yi amfani dasu kafin ta nufi palour jin cikinta ya fara kukan Yunwa. Seda ta kai tsakiyar palour ta tuna da ashe fa ba ita kadai ba, gaskiya zataji kunya Khalil ya ganta da wadannan damammun kayan seta juya dakin, jan mayafi ta dakko ta sake fita, palour qal babu dattin komai se ta wuce inda aka jera turarukan wuta ta dauki kasko ta bude qofar palour ta wuce kitchen. Seda ta kunno Magic coal ta koma dakin, a kasko biyu ta saka ta harhada kalolin turarukan wuta ta zuba a kowanne kasko ta shige da daya dakinta ta bar dayan a nan palour bayab ta kunna Ac kafin ta koma kitchen. Ganin akwai kusan komai na amfani dan daidai da kayan miya ta tarar a freezer ga nama nan da kifi haka cikin store akwai dankali da doya harda plantain ga kuma garar Abinci nan da aka hado su da ita se kawai ta debi dankalin ta shiga ferewa. A nuts take aikinta tana yan waqoqinta, tana tsaye gaban Gas tana jiran Dankalin data zuba a mai ya qarasa soyuwa ta kwashe sam bataji shigowar mutum ba se hucin numfashi taji agefen kunnenta babu bata lokaci ta fasa qara tayi gefe saura qiris ta tunkude kaskon man dake kan wuta Khalil ya riqota yana cewa "Kiyi a hankali karki jima kanki ciwo fa" "Ba kaine ka bani tsoro ba banji tafiya ba kawai naji numfashi a kunnena" ta fada a shagwabe tana kai masa dukan wasa, seya riqe hannayenta yana murmushi yace "Kice dai kina ta waqa amma ni har sallama nayi kece dai baki jini ba". Janye hannun tayi saboda hango dankalin ta ya fara ja alamar ya kusa qonewa tayi saurin saka ludayi tanakwashe wa tace "Ka gani ko gashi nan kasa dankalina ya qone Allah idan yayi ba dadi bazan yadda ba" "My strong woman, wayace miki Amarya tana shiga kitchen irin yau? koda yake alama kike mun ta kin warke, bari mu koma daga ciki toh muci gaba dan kinsan ban qoshi ba kawai na dan tausaya miki ne yanda kika ringa kuka kina kiran Mama jiya" Khalil daya sakata a tsakiya rungumeta ta baya ya fada cikin kunnenta, kunya kamar qasa ta tsage Umaimah ta shige se qoqarin kwacewa take amma ya hanata sema qara cusa kansa yake a wuyanta yana cewa "Wow Babe wane turare kika saka haka i love the scent, its really amazing and erotic". "Khalil bazaka kasheni da raina ba" ta fada a zuciyarta tana qoqarin yakice shi daga jikinta jin ya fara lasar mata kunne kamar wani tsohon maye, qara janyota yayi ta fasa kukan qarya tace "Wallahi yunwa nakeji ka barni na qarasa hada abinci" se ya saketa yaja da baya ya jingina da cabinet yace "Ok na barki, kije ki zauna bari na qarasa miki ma" "Aa" ta fada tana noqe kafada, Tumatir da Attaruhu da Albasar data wanke zata soya kwai ta shiga yankawa gaba daya jikinta rawa yakeyi, ta fasa kwai a qaramin bowl ta ajiye kafin ta dora wani kaskon ta zuba Mai se taja ta tsaya saboda yanda take jin idanunsa a jikinta ta tabbatar in ta ci gaba da aikin za'a samu matsa, in ma ta qona kanta ko kuma ta qona abinda take dafawa. Gas din ta kashe ta juya ta kalleshi tace "Ni gaskiya ka fita duk ka sakamun ido na kasa yin komai...." Be barta ta qarasa saboda cafkar da yayiwa bakinta ya shiga kissing dinta babu ji babu gani, seda ya gaji dan kansa kafin ya saketa ya juya yana cewa "Ki qarasa bari nayi wanka" ya fice daga kitchen din Hajiya Umaimah ido yayi fici fici kamar an jijjiga bera a jarka taja numfashin daya maqale mata tareda tattaro yawu ta hadiye, wannan karatun na Khalil ya girmi kanta taga alamar zata sha wuya kafin ta haddace, amma dole ta bada himma tun kafin ta zama daqiqiyar daliba. Jiki a mace ta soya kwan, ta zuba komai a kwanuka masu kyau ta ringa dauka tana shiga dasu cikin palour, seda ta ajiye duk abinda tasan zasu buqata kafin ta qarasa inda ta ajiye kaskon turaren wutarta ta dauka tana shirin qarawa dan na ciki ya cinye, yanda qamshinsa yake tashi babu qauri ko kadan irin yanda wasu turaren sukeyi a farko ko idan sun qare ya sake burgeta da Turarukan na *MEERAH_PERFUMES_MORE* tana shirin zubawa Khalil daya fito daga daki ya dakatar da ita yace "Karki zuba", seta kalle shi da rashin fahimta tace "Lafiya? Ko qamshin babu dadi ne?" "No i love the scent qamshin da dadi sosai zaki ma zubamun na kai office na ringa sakawa amma hayaqin ne bana so, idan zaki kunna turare ki ringa sakawa hayaqin ya fita kafin na shiga guri saboda yana damuna a maqogaro sosai wannan sedai ki kaishi cikin daki tunda a nan zamu zauna" "Noted Sir" ta fada kafin ta dauki kwalbar turaren da kaskon ta shige dakinsa ya rakata da murmushi. Ko ina tsaf dan har gadon ya gyara ta bude toilet nan ma qal dashi da alama ya sake daurayewa bayan da yayi wanka, taji dadin wannan sauqin halin nasa tasan idan ya dore a haka zasu ji dadin zama dan ta dade tana addu'ar samun  irin mijin da yake taya matarsa aiki. Turaren ta zuba ta kullo qofar ta dawo palour, nan suka zauna suka karya abinsu a nutse yana tsokanarta wai meye sirrin yaga ta miqe garau ko daman duk abinda ta ringayi dazu lambo ne saboda ya qyaleta dan haka seta biya bashi ita dai se murmushi take tana sunkuyar da kai dan kunya yake bata idan yana irin maganganun. Haka suka wuni cikin gidan abinsu gwanin dadi, tun tana zazzamewa idan ya jata jikinsa har ta haqura ta fara sakewa dashi dan ta fahimci irin mazan nan ne masu nanewa Mace duk inda take suna nan dan ko tashi tayi yin wani abun qafarta qafarsa seya bita har bandaki data shiga yin fitsari bin bayanta yayi seda ta nemi saka masa kuka kafin ya haqura ya barta. Guraren bayan La'asar su Yaya Naziyya sukaje gidan tilas Khalil ya fita ya basu guri badan yaso ba nan suka tasa Umaimah da tsiya kala kala wai har sun chanza daga ita har shi a dare daya abin Allah sega Umaimah wai tana sunkuyar dakai baki ya mutu babu tsiwa bare rashin mutunchi, suka qarasa mata yan gyare gyaren daya kamata suka gyara gidan qal Yaya Naziyya data hada ruwan Mopping Umaimah ta dakko Mata Mopping Mist din *MEERAH_PERFUMES_MORE* ta zuba ta kalleta tace "Wai ni Umaimah ina kika samo wadannan sirrin qamshin haka, dazu dana shiga bandakinki kamar karna fito wallahi nasan dai ba'a gida aka hado miki kayan nan ba". Fari da ido tayi tace sirrin *MEERAH_PERFUMES_MORE* wadda Anty findiga ta hado mana turarukan wuta a gurinta ta Yolan nan ce to a gunta qawata Ruma tayo mun wadannan hade haden, kingansu ga *Turaren wanka, body oil, gana kaya, ga air freshner, turaren Mopping, ga Spray na mota ma na boyewa Khalil se randa ze koma aiki zan saka masa a motarsa sannan ga wadannan turarukan hayaqi na daki dana jiki su kin san ingancinsu ma ba se na fada miki ba tunda kun satar mana*" Duka Naziyya takai mata ta goce tace "Ke fa baki da mutunci daman wato satar mukayi ai daman ba ku kadai aka ce gidan ku yayi qamshi me dadi ba, dakko mun Roba daya na dauki lambar me turaren nima a hado mun dan sisi zan fara kwanannan nima". (Domin samun ingantattun turaruka masu sirrin qamshi na musamman ku tuntubi *MEERAH_PERFUMES_MORE 0706 9239573*, tana Adamawa Yola, suna aika kaya ko ina a fadin qasar nan cikin Aminci). Se bayan magriba suka tafi bayan da suka sakata ta sake falle wanka da sababbin turarukan wankanta data samu kamar ta goyasu ta ringa yawo dasu saboda qauna ta saka dogurar riga yar kanti silk Peach color me dogon hannu ta lafe a jikinta ta fitar mata da shape ta nade a palour tana kallon Tv tana shan lemon kwakwa da dabinon da suka zo mata dashi aka saka a fridge yayi sanyi. Horn din motar data jiyo a waje ya sakata ajiye cup din ta miqe, seda ta qara gyara fuskarta a daki ta fito lokacin har ya bude Get ya shigo da mota ta fita palour daidai sanda Khalil din ke shigowa da yammata biyu a bayansa dauke da kulolin abinci dan daman ya kirata ya gaya mata kartayi girki tana ganinsu nan da nana fara'ar data fito da ita akan fuskarta dan ta tarbeshi ta gushe. Kallon yammatan ta shigayi kamar wadda taga kashi, ta gane Habiba Autarsu amma ita dayar me ruwan sadaka yalla fa? Khalil daya cake yana jira tazo ta tareshi yaji shiru se yayi saurin qarasawa kusa da ita saboda hango irin kallon da take jifan qannen nasa dashi tun kafin a kwata wani abun ya rungumeta yana cewa "Bazakizo kiyi welcoming din ba" "Wacece waccen?" Ta fada tana kallon cikin idonsa, nan da nan ya hade fuska shima ya juya ya kalli Habiba da daya yarinyar me suna Iman, yar qanwar Hajiyarsu ce, haka kawai suka nace se sun biyo shi wai tun safe suka so zuwa Hajiya ta hana su su dai suna so su gaida Amarya dan washe gari ita Iman din za'a mayar da Ita Minjibir inda take makaranta dan saboda bikin aka dakkota. "Ku ajiye kwanukan mana kun tsaya kamar wasu sojoji" ya fada yana kallonsu, se suka wuce kan Dining suka ajiye flasan hannunsu, har suna rige rigen gaida Umaimah dake jifansu da irin kallon da suka kasa tantancewa dan dai a ganin da suka mata sau biyu duk irinsa takeyiwa mutane, to kodai idonta ne a haka su dai basu sani ba. A shaqe ta amsa musu kafin tabi bayan Khalil daya shige daki suka bar su Habiba da baki a bude. "Habiba me yake damun Amaryar Yaya Khalil ne? Kingafa ko yar murna ta ganmu batayi ba se bata rai takeyi, haka fa ranar kamun nan ta ringa kuka kodai bata son sa auran dole akayi mata?" Iman din ta fada dan irin masu shegen surutun nan ce bata gani tayi shiru, ita kuwa Habiba da yake miskika ce guri ta samu ta zauna tana qarewa palour kallo gurin ya mata kyau ga qamshi me dadi da sanyin Ac yana tashi. A cikin daki kuwa Umaimah na shiga tun kafin tayi magana Khalil ya tareta da cewa "Karki kuskura ki tayar mun da hankali a daren nan, babu sannu da zuwa babu komai se ki tsareni da wasu tambayoyinki marasa kan gado akan me danki ne ni ko yaya da zaki tsareni kina tuhuma a gaban yara Habiban ce baki sani ba ko kuma salon se kin jawo abinda rai ze zo yana baci ne? Ko kuwa bani da ikon shigo da wanda naga dama naga dai cikin gida nane bana wani ba" Umaimah datayi shiru tana jinsa se ga hawaye shaa sun fara zubo mata ta fara magana cikin kuka tace "Yanzu kawai saboda na tambayeka suwaye ka shigo dasu shine zaka fara yi mun gorin gidanka ne banawa ba amma dai nice matar gidan kuma ina da haqqi akan duk wanda ze shigo mun seda yardata. Kuma ni ai bance bansan Habiba ba, ita dayar me kama da Sadaka Yallan da kuka taho da ita nake tambayarka wacece, amma shikenan in sha Allahu bazan sake magana ba ko kasuwa zaka dakko ka kawo cikin gidan nan tunda abin ya zama harda gori" wiii ta saki kuka. Kallonta kawai Khalil yake takaici kamar yayi me dan yarinyar ta gama raina masa hankali, jifa yanzu idan wani yaji ai se a zata wani mugun laifi ko wata baqar magana ya gaya mata shi beyi kuka ba se itace me bakin kuka? Volume data qarawa kukannata kamar wadda yake duka yasakashi janyota jikinsa cikin takaici yace "Wallahi Umaimah idan baki saurara ba sena hukuntaki da irin hukuncin da jikinki seya gaya miki, badai yau har kin samu damar tayar da tsiyatakunki ba? ki bari na riqeki gobe idan ance ki bude baki ki gayamun magana bazakiyi ba" kafin ma ya dire maganar ta hadiye kukan ta hau share fuskarta dan ba mantawa tayi da baqar wahalar data sha a hannunsa jiya ba, kawai gatan daya mata ya gasa mata jiki da maganin daya bata ne suka taimaka mata amma wunin yau duk idan ta tuno dare zeyi ji take gaban ta na faduwa. Yanda take goge fuskar tana ajiyar zuciya se ta bashi dariya da tausayi, "Maza ki wanko fuskarki muje ku gaisa na aiki Khalifa yana hanyar dawowa ze wuce dasu gida" ya fada yana riqe kafadunsa, seta daga masa kai ta wuce bandakin ta wanko fuskar ta tsane da towel ta fito har sannan yana tsaye a tsakiyar dakin. "Muje" ya fada yana nuna mata hanya, seta marairaice fuska dan bafa ta haqura ba se ya gaya mata wacece wannan yarinyar "Khalil dan Allah wacece ita?" Ta fada a marairaice, se ya juyo ya kalleta fuskarsa da murmushi yace "Wato koma me zanyi bazaki fasa halinki ba ko? Toh Iman ce Autar Anty Uwa qanwar Hajiya ai kinsanta ko? Habiba ma ta girme ta ko nine shugaban masu son mata babu abinda zan tsinta a jikin waccen yarinyar kin dai san tayi mun kadan". Gaba tayi ta barshi ya bita a baya yana murmushin takaici, tayi qoqarin gaske ta dora fara'a a fuskarta suka gaisa da yaran basu jima ba zega Khalifan ya kirashi akan yana qofar gida, fita yayi ya bude masa suka shigo tare ya karbi kayan daya kawo masa ya shige dasu shi kuma ya zauna suka gaisa da Umaimah a mutunche ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo harda dambun nama tana ta jan Habiba da hira idan Iman ta saka baki seta dan harareta kafin zata amsa, haka suka dan zauna kafin sukayi musu sallama suka tafi. Ganin da tayi Khalil nata wani shan qamshi da farko itama seta share shi, har suka ci abinci ta gyara gurin se ya dakko system dinsa ya kunna ya shiga danne danne tana yi masa magana ze amsa ta ba tareda ya dago ya kalleta ba se kuma duk taji babu dadi tayi shiru kawai tana kallon Tv gashi ita ba waya ba dan ta bayar da kyautar wayarta tunda ta saka ran ze siya mata wata. Har gurin goma saura suna zaune ita tana kallon da ba fahimta takeyi ba shi kuma yana ta aikinsa lokaci lokaci yana satar kallonta a ransa yana sake jinjina halinta. Wato bazata iya bashi haquri ba kenan ai kuwa zega qarshen gudun ruwanta. Qarfe goma na bugawa ya rufe system din ya shiga tattara kayayyakinsa yana kallonta yace "Seda safe, karki manta ki kashe komai kafin ki kwanta" ya wuce ya barta a gurin ta rakashi da kallo baki a bude, ita ze wulaqanta akan dan wancan abin daya faru ze tashi ya barta wai idan ta gama ta kashe komai ta kwanta? Yana dab da shiga dakin ya jiyo shashsheqar kukanta, be tsaya ba ya shige ciki abinsa ya ajiye kayan hannunsa kafin ya wuce bandaki yayi wanka. Seda ya bata lokaci yayi shirin baccin sa tsaf kafin ya fito palour lokacin Hajjajun tayi kuka ta qoshi baccin wahala ya dauke ta a qasan carpet data sauka tana birgima kamar wata qaramar yarinya, seda ya kashe kayan kallon data bari kunne da Ac kafin ya dawo daidai kanta ya tsaya yana qarewa fuskarta kallo a fili yace "Drama Queen kenan" kafin ya sunkuya ya dagata gaba dayanta ya fara tafiya da ita ta bude ido, baki da kware zata fasa masa wani ya hanata damar yin hakan ta hanyar rufe mata bakin da nasa, be direta ko ina ba se kan gadonsa. Yanda ya gaya mata seya hukuntata kam ta karbi hukunci me tsanani dan irin tausayi da lallabawar da ya ringa yi mata jiya sam yau din babu su, gashi daman kamar fami ne gurin har yafi jiya yi mata zafi. dirzarta yayi son ransa duk kuka da magiyar da ta ringayi masa be saurara ba seda ya gaji dan kansa kafin yaja gefe yana mata dariyar mugunta, ya kuma hada mata ruwa me shegen zafi ita dai ta jera masa Allah ya isa tafi cikin kwando a zuciyarta ta kuma quduri niyyar tunda shi mugune bazata sake yin abinda ze hado su dashi ba ballantana ya ci zalinta. Haka suka ci gaba da cin kwanakin Amarcinsu cikin wata irin soyayya da tattalin junansu, sosai take qoqari gurin kiyaye duk abinda baya so haka tana nazartar abinda yafi so da wanda yafi yabawa idan tayi. A cikin wata daya da auransu Sabgar Aza room ce dai ta kasa sabawa da ita dan Khalil din jarumi ne na gaske, ta kuma fahimci baya gajiya da abin dan baya tsallaken rana idan ma ba tayi masa wuta wuta ba beqi ayi sau biyu ko uku ba wannan abun ne yake damunta da har ya saka ta fara rama dukda kyau da gogewa da fatarta ta qarayi amma ta rame. Seda suka cika wata da aure kafin ta fara fita duk irin nacin da take masa idan ze fita tace zata bishi baya yarda, da daddare ranar ya kaita gidansu ta gaida Hajiyarsa. Kaya sosai ta diba daga akwatun lefenta ta dora da kudi irin wanda yake bata saboda sallamar baqin da suke dan zuwar mata sanna ta sake hada kayan kwalliya a wata ledar daban na Habiba. Khalil be san dasu ba seda sukaje gidan, sosai Hajiya taji dadin zuwanta ta cika ta da kayayyaki tana ta sa musu albarka kafin ta dora da fadan tsabara data kai musun tayi yawa dan Atamfa ce super ta dakko da wani dandatsetsen Lace harda Mayafi ta kaiwa Hajiyar, kudin kawai ta karba tace ta gode amma ta juya da kayan dan tayi amfani dasu aka zuba mata ba na rabarwa ne, Umaimah bata ji dadi ba haka ta dakko suka dawo Habiba ko se tsalle take da murnar kayan kwalliyar dan Hajiyar na fara fada ma ta kwashe nata tayi sama karma ace itama a juya dasu. Kwana biyu a tsakani ya kaita gidansu, wannan tun da safiyar ranar da zasuje yace mata karta dauki komai zasu tsaya a hanya suyi tsaraba haka kuwa akayi tsaraba sosai sukayiqa yan gidan bayan isha suka isa abin dadi suka tarar da Nuratu da Mijinta a gidan suma sunje zo kaga murna aka ruguntsume kowa tana tsokanar yar uwarta wai ta chanza Mama ko har kwallar farin ciki ta share na ganin Umaiman tata tayi hankali ta zama cikakkiyar mace. Da zasu tafi Anty ta kirata dakinta ta bata wata leda tace zasuyi waya, har zata fita ta tsayar da ita tace "Umaimah kinyi kyau amma kin fada ko mu fara shirin taron megida ne ko kishiya". Fuska ta yatsina dan dagaske itama taga ramar da tayi dan kayanta da suke cikata dam yanzu sun dan sassauta mata, babu kunya bare tsoron Allah tace "Wallahi Anty wancan mutumin ne mugu duk shi yake ramar dani, wai idan mutum yayi masa abu bazeyi magana ba sedai ya qullaceka se munje bacci sannan ze sameni kamar sakwara ya daka ni ni wallahi har na fara tunanin ma na gudo gida ku kirashi kuyi masa magana dan gaskiya na fara gajiya tun ban rame na zama kwarangwal ba a ringa zaton wani ciwon ne dani ba'asan shi yake zuqeni da jarabarsa ba". Zukudi Anty tayi ta rafka tagumi tana jinta seda ta dasa aya kafin tace "Uhm Allah ya rufa asiri kowa da haka ta saba ai Umaimah, kije zangayawa Mama in yaso se a harhado miki abubuwan da zasu taimaka miki ki dena ramar" "Ni kawai Anty kiransa zakuyi ku masa magana dan wallahi baki san irin abinda yake mun bane..." "Ai bana ma so na sani Umaimah kije Allah ya bada haquri ki ringa shan fruits sosai zasu taimaka miki ki kuma cire tsoro a ranki ramar zata dena" Antyn tayi saurin katseta jin tana neman baro mata aiki, daga haka sukayi sallama suka kama hanyar gida ranar ba'a tsaya doguwar hira ba saboda washe gari Khalil ze koma aiki dan haka suna komawa wanka sukayi suka kwanta dan sunci abinci a gida. WASA FARIN GIRKI Assalamu Alaikum mutanen Kwarai👍 Shin kina son kwarewa fannin girke girken zamani,snacks da sauransu Hajiya ta💃 ga dama ta samu Mun bude online class wanda zamu koyar da girkin zamani yanda ake sarrafasu ta hanyoyi da dama…Akan kudi qalilan 200 ga mutane 10…daga bisano ze koma 300 kacal kedai kawai tura kudin ki ta wann acct din….. 1509536481 Rabiatu Nuhu Aliyu Access bank https://chat.whatsapp.com/IL3QnKmFxojAATF6WkzGxK 8142548705 *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 20 "Amarya ina kwana? Yau na taki sa'a kin hau online kenan, toh ki taho ganin baby na haihu jiya da daddare yanzu muka dawo gida ma" ta fada bayan da Umaimah ta daga kiran, Umaimah data hade rai da farko tana jiran jin dalilin kiran seta saki fuska dan a duniya tana sonyara tana kuma son taji waniya haihu. "Masha Allah me aka samu?" Ta fada muryarta a washe, se Rufaidan ta amsa mata da cewa "Macece Zulaiha, sunan babarsa ya saka" "Allah raya zan shigo in Allah ya yarda" "Toh shikenan se kinzo, kinji voice din dana miki ko? Zanyi adding naki zakiji dadin groups din akwai qaruwa sosai kuma duk yawanci matan unguwarnan suna ciki kinga zaki qara sanin mutane" Rufaidan ta sake fada daganan sukayi sallama bayan da Umaimah tace ta sakatan ko group din meye haka se Allah da ta nace seta sakata a ciki suna kashe wayar kuwa tayi adding nata. Groups uku ta sakata, Qasaitacciyar mace, Mutaimaki kanmu se wani Matsalolin ma'aurata wanda yake a kulle Admin ne kadai suke magana. Daga yanayin sunayen taji groups din sun mata daman yanzu Halima qawarta suke magana tace zata bada number ta a sakata a groups saboda abubuwa da yawa zaka koya ka kuma samu waye war kai akan wasu matsalolin dakanka zaka iya warware su. Tana nan zaune tana aikin danna waya se ji tayi ana kwada kiran sallar Azahar tayi firgigit ta miqe tana salati "Kai ashe haka lokaci ya tafi ina zaune babu abinda nayi" ta fada a fili kafin ta wuce jikin socket ta jona wayar a chaji ta shiga daki. Seda tayi sallah ta wuce kitchen, doyar data narke dazu ta dumama ta daketa a turmi, tana da ragowar stew ta diba bayan ta hada shayi ta koma cikin palour tana ci tana duba saqonnin da suka shigo a sababbin groups din da aka sakata. Group din Matsalolin Ma'aurata ta fara budewa ganin shine me saqonni kadan, ta dafe qirji tareda gwalalo ido tana karanta bayanin da Admin din ta turo ganin abin ya girmi qaramin kanta ya sakata ta tsallake ta wuce kan videos da hotunan aka turo tareda saqon wanda sun rigada sun bude kansu "Innalillahi na shiga uku ni Umaimah group din yan iska matar nan ta sakani" ta fada tana cilli da wayar saboda mugun gamon da tayi a video data bude jikinta in banda rawa babu abinda yakeyi kwakwalwarta na qara hasko mata masha'ar da akeyi a cikin video to meye amfanin wannan? Kuma group ance saboda Matan aure daman abinda ake koyawa a ciki kenan Batsa? Ta yiwa kanta tambayar. Wayar ta dakko Allah ya taimaketa bata fashe ba bata bata lokaci ba ta goge chats din tsaf bayan ta shiga gallery ta goge hotuna da videos din data bude kafin ta koma ta fice daga group din yanzu ace Khalil ya dauki wayar yaga wannan aika aikar wane kallo zeyi mata ita ko da wane baki zata fara masa bayani? "Allah kayi mana maganin masifa da bala'i su kuma masu yin wadannan rubuce rubucen da tura video ka shirye su" ta fada a fili tana rafka tagumi. Abin ya daure mata kai da yawa daman tun suna makaranta Nabila tana cikin ire iren wadannan groups din na matan aure wani lokacin haka za'a turo rubututtuka akan sirrin kwanciyar aure ko makamantansu harda ma video a lokacin suyi ta mata fada sai tace wai gara ta koya ta san komai kafin lokacinta wanda ita dai a iya saninta ta san wannan ilimine da bashi da malami ko baka sani ba da zarar lokacinka yayi ka shiga Ajinsa zaka sani amma shine wasu marasa tsoron Allah suke fakewa da fadakarwa suna yada badala a cikin Al'umma suna lalata yaran mutane dan da yawan matan da suke taruwa a groups din da sunan Matan aure qananan yara wanda basu kai matakin ace sun san wannan abin da wata babbar banzar take zama tana koya musu ba Allah dai ya rufa asiri ya ganar da masu ganewa. Wannan abun ya sakata ajiye wayar ta shiga aikin gida jiki a sabule har aka kira La'asar bata gama goge goge ba. Se gurin qarfe biyar ta samu ta kintsa gidan, ta shiga wanka kenan ta jiyo horn din motar Khalil gabanta ya bada ras shaf ta manta da ya gaya mata da wuri ze dawo tayi abincin rana dashi nan da nan ta shiga tunanin qaryar da zata shirga masa, haka tayi wankan tayi ta fito tana lankwashewa ido zuru zuru kamar mara lafiya ta jingina da bango tana jan numfashi daidai danda Khalil din ya shiga dakin da sallama. "Lafiya Babe meya sameki?" Ya fada yana qarasawa kusa da ita ya ruqota jikinsa. "Subhanallahi ya naji jikinki da dumi zazzabi kikeyi?" Ya sake fada yana taba fatar jikinta data kwararawa ruwan zafi dukda zafin da akeyi a garin, daman tayi ne saboda ya dauka zazzabin takeyi. "Tunda ka tafi kaina yake ciwo dakyar na iya tashi nayi aikin gida ma na sake kwanciya se yanzu na yi wanka kuma naji zazzabi yana neman rufeni" ta fada tana matso kwallar qarya. Gaba daya yabi ya rikice ya zaunar da ita a gefen gado se faman sannu yake mata tana ita kuwa tana qara lankwashe wa. "Bari na dakko miki kaya muje asibiti ko ga jikin nan da zafi" ya fada yana bude wardrobe dinta, seta sake marairaice masa, kar aje Asibiti suce babu abinda yake damunta dan haka tace "Aa kabarshi nasan zuwa anjima ze dena daman kwana biyun nan haka nake yi idan ka fita zan tajin babu dadi yamma nayi kuma zan warke" "Yanzu baki da lafiya shine zakiyi shiru baki fada mun ba har kwana nawa? Bana so karki sake yimun wasa da lafiyarki, duk idan kikaji ba daidai ba ki gaya mun muje Asibiti karki sake zama da ciwo a jikinki" Khalil ya fada cikin bacin rai, shiru tayi daga neman hanyar kare kai ta sake kunno wata matsalar. Ba yanda ta iya ya tasata a gaba suka wuce asibiti yana ta mata mitar qin gaya masa bata da lafiya da batayi ba ya kuma jaddada mata idan sunje duk abinda yake damunta ta gayawa likita, kamar ta gaya masa gaskiya itafa lafiyarta qalau shiririta ta zauna bata yi aikin gida da wuri ba shi yasa ta masa qarya amma dai tayi shiru dan a yanda ya hasalan nan bata san yanda zasu kwashe ba kuma. Kai tsaye wani private Asibiti me kyau ya kaita, babu bata lokaci aka bude mata file kafin suka zauna jiran ganin likitan dan sun tarar da mutum biyu a gabansu. Da suka shiga gurin likitan ya tambayeta me yake damunta shiru tayi seda Khalil din ya zazzare mata ido kafin ta yanko qarya tace kanta da cikinta ne suke ciwo se jiri wannan kuma da gaske kusan sati daya kenan ko a zaune setaji kamar jiri na dibanta, data gayawa Mama se tace mata ta ringa yawan shan ruwa kuma ta ringa hutawa da tayin kuma ta samu sauqi amma yanzu tunda an qureta duk ta harhada qarya da gaskiya tace suna damunta. Tambayarta yayi yaushe tayi Al'ada na qarshe ta gaya mata se a sannan ta tuna ya kamata ace tun satin daya wuce ma jinin ze dawo mata amma bezo ba, da yake wani lokacin yana mata delay shiyasa ma bata damu ba amma dai be taba qara har sati daya ba. Test din jini dana fitsari likitan ya basu bayan daya auna jininta ya dudduba idonta suka wuce gurin biyan kudi daga nan ya rakata qofar lab din ta shiga shi kuma ya tsaya daga waje aka dauki jininta suka bata robar da zatayo fitsari a ciki tayi ta mayar musu kafin suka koma can inda ake zama ayi jira. Suna zama aka kira Sallar Magriba Khalil ya wuce masallacin Asibitin ya barta yana tashi ta zaro wayarta dake cikin Aljihub doguwar rigarta ta shiga WhatsApp. Da saqon Rufaida ta fara cin karo "Wannan mata ko mayya ce se haka ta haihun ma bazata zauna ta huta ba seta addabi rayuwata da takura haba" Umaimah ta fada a fili kafin ta bude saqon tambayarta take me yasa ta fita daga group tace mata babu komai groups din ne sun mata yawa. Daga nan take gaya mata qarfe goma na dare zata gabatar da ita a Qasaitacciyar Mace group din dan haka sukeyi, idan sabon Member ya shigo ze gabatar da kansa saboda kowa ya sanshi daga nan ya zama dan gida dan haka ta zauna online kafin lokacin. Cigaba da duba saqonnin mutane tayi seda ta hango Khalil tayi sauri ta kashe Data ta jefa wayar a Aljihu, yana qarasowa aka miqo musu Test result din kai tsaye suka koma office din likita ya karba ya duba fuskar sa dauke da murmushi ya miqawa Khalil hannu yana cewa "Ina tayaka murna madam nada shigar ciki". Daga ita har shi bude baki sukayi suna kallonsa da mamaki, cikin tabbatarwa yace "Kuna mamaki ne? Gashi nan abinda sakamako ya nuna kenan, yanzu zaku dawo nan da Two weeks zaku dawo ayi scanning musan cikin sati nawane" ya hau rubutu a takadda ya basu yace su karbi maganin a pharmacy kafin ya qara musu da shawarwarin yanda zata kula da kanta da abinda yake cikinta. Khalil da Umaimah dai se yar kallo kallo ake bakin nan kamar ya tsage dan tsakanin su bazakace ga wanda yafi wani farin ciki ba, 'ikon Allah daga qaryar cuta ashe silar jin abin arziqine' Umaimah ta raya a ranta haka suka dauki hanyar gida bayandaya tsaya yayi musu take awayn abinci da kayan kwalama, duk abinda ya gani a hanya seya tambayeta zata ci abin nasa ma tun yana bata dariya har ta fara jin haushi. Da suka isa gidan ma hanata fita yayi daga motar, kamar wata yar baby haka ya dauketa ya kaita kan kujera ya ajiye yana cewa "Kina ji dai likita yace a kula dake dakyau banda aikin wahala, dan haka duk wani aiki me yawa a gidan nan na sauke miki shi, kiyi wanda zaki iya ki bar sauran idan na dawo zan ringayi. A daren nan taga tarairaya da ririta ta kuma shaida yanda Khalil yake son haihuwa dan harya fara lissafin abubuwan da zasu siya da sunan da za'a sakawa Babyn idan Macece ko Namiji. "Nidai nafison Namiji" Umaimah ta fada tayi daidai akan cinyarsa yana bata Ayaba a baki bayan da suka gama cin abinci. "Ni kuwa koma menene indai Mutum ne kika haifa ina so" Khalil ya bata amsa yana jan hancinta kafin ya qara cewa "Wai, yanzu fa hancin nan nan da kwana kadan ze bude ya zama qato naga haka hancin su Jalila yakeyi idan suna da ciki duk su fita a kamanninsu, bari ma na kirata na gaya mata su shirya samun sabon baby a family" ya qarasa yana janyo wayarsa dake gefensu, hade rai tayi tace "Kawai kuma seka wani fara kiran mutane kana gaya musu ai ka bari dai muji ma kwanakin cikin kafin a fara yayatawa". Daga yanda tayi maganar yasan halin tsiyar ne ze motsa dan haka ya bata rai shima yace "Eh na yayata din yan uwana zan gayawa kema ban hana ki kira naki ki gaya musu ba" ya fada yana danna kiran layin Jalila babu dadewa ta daga tana cewa "Dan qanina kamar kasan yanzu nake so na kiraka kwana biyu dai Amarya ta kwace mana kai baka neman mu muma bama samun ka" "Ba haka bane wallahi kin san na koma aiki idan na fita bana samun zama dana dawo kuma kashe wayar nakeyi saboda masu damuna, amma zan ware layi daban dai inaga" ya fada cikin jin kunya dan dagaske ya yada su, kai hatta Hajiyarsa seda tayi qorafin rashin zuwansa gidan kamar farkon auransa da kullum idanbeje da safe ba zeje da yamma yanzu kuwa seya jera kwana biyu uku be leqa su ba sedai ya kirata a waya shima tace Umaimah tafi kiransa akanta dan kullum ta Allah ne seta kirata sun gaisa da safe. "Toh ai shikenan daman lafiya ce ai take buya, yanzu ya akayi ta samu ne naga kira da tsohon daren nan" Jalilan ta sakw fada, "Albishir na kira nayi miki kin kusa yin sabon baby, Amarya nada ciki" ya fada yana shafa kai dan wata yar kunya kunya yaji na neman kamashi. Cikin muryar farin ciki Jalilan tace "Ah kace dan qanina ya girma no wonder ka buya ashe kai kasan aikin da kakeyi irin wannan sharp sharp haka? Ta bari na shiga group yanzu na shelanta musu a saka sabon adashi matar Usaini tayi ciki, ka gayawa Hajiya ko na gaya mata?" ta qarasa cikin dariyar shaqiyanci. "Kefa baki da kirki wallahi daga gaya miki abin arziqi zaki farayiwa mutum tsiya kuma karki sake cemun Usaini wallahi" Khalil din ya fada yana dariya. "Aa zancen gaskiya mana toh bari zan gayawa Hajiyar tunda naga kunya kake ji, ina qanwar tawa mu gaisa?" Kallon Umaimah data tunzura baki gaba yayi dan a speaker ya saka wayar tana jin duk abinda suke fada se yace "Ta kwanta Kinsan likita yace ta ringa hutawa" "To shikenan zuwa da safe zan kirata in Allah ya yarda amma fa ba wai kuma ance ta huta ka saka ta tayita kwanciya kamar ruwa bata motsa jikinta ba, Aa ana so a ringa motsawa aikin da ze jigata ta ne dai ba'a so kaima seka rage zalama ka bar yar mutane ta nutsu tunda kayi abinda kake so, Allah ya inganta ya bada lafiya" Jalilan ta fada daga nan sukayi sallama tana sake jaddada masa daya kula da Umaiman. Umaimah kuwa hankalinta na kan Agogo, qarfe goma na bugawa ta tashi ta dakko wayarta dake jikin chaji ta koma kan kujera ta harde, shima bebi ta kanta ba ya chanza tasha zuwa Channels ya fara kallon labaran qarfe goma. Tana hawa ta bude group din kuwa ita ake jira dan har an rufe group anyi mata Admin, shugabar gidan me suna Anty Haris kamar yanda ta gani a rubuce ce ta fara gabatar da ita a matsayin sabuwar member daga nan ta bata dama akan ta gabatar da kanta. "Sunana Umaimah Sabo Mukhtar, ni yar Kano ce, ina da aure. Shekaruna 22" ta tura musu a taqaice. "Masha Allah Malama Umaimah muna mik barka da zuwa wannan gida, amma baki fadi Unguwar da kike ba saboda idan da wanda kuke kusa kinga se ku qulla zumunchi haka mukeyi a nan" daya daga cikin Admins din ta bata amsa, "Ina unguwar Tudun-yola Gate 4" ta sake turawa tana yatsina fuska, sun fiya iyayin tsiya Allah sa dai ana abin arziqi a group din. "Aa kice yar unguwarsu uwar daba ce, Ke Rufy kina ina fito ga yar Area kin samu" Admin Anty Haris ta turo da Emojin rawa kafin ta sake ce da Umaiman "Saura ki turo da Hotonki ki kuma yi voice note saboda mu tabbatar da Macece yar uwar mu ba masu shigewa cikin mata ba" "Kan bala'i lallai ma mutanen nan da rainin wayo suke" Umaimah ta fada a fili tana gyara zama, Khalil ya juya ya kalleta beyi magana ba ya maida kai yaci gaba da kallon News dinsa se yaga ta miqe ta shige cikin daki kuma. Tana shiga kan gado ta haye, hotunanta ta shiga dubawa ta samo wani da sukayi weekend din daya wuce sunje Zazu cin Abinci da yamma Khalil ya dauketa tayi kyau sosai dukda Hijabi ta saka tana turawa ta sake aika Voice note tace "Inayiwa kowa fatan Alkhairi" daga nan aka bude group aka shiga yi mata barka da zuwa yan group dai masu kirki anata faran faran da ita nan da nan itama ta sake aka fara hira sam bata ankare da lokaci ba seda taji an turo qofar dakin tayi saurin tura wayar qasan pillow tayi lamo kamar me bacci dan daman ta kashe fitila. "Umaimah" Khalil ya kira sunanta daga bakin qofa tayi shiru bata amsa ba, seya qarasa ya tsaya daidai kanta murya a cukule yace "Tashi muje mu kwanta" nan ma tayi masa shiru bata motsa ba. "Nasan kina jina dan haka ki tashi karki bata mun rai" ya sake fada, yabda yayi maganar sam babu wasa a ciki ya sakata yin miqa tana tura baki ta kalle shi tace "Nifa bacci nakeyi ka tasheni" "Wuce muje" ya fada yana matsa mata hanya, se data harareshi ta qasan ido kafin tace "Kaje zan taho bari na shirya". Kwafa yayi ya fita dan tunda dazu da ta tashin ya rage volume din Tv yana jiyo ta tana playing voice notes din mutane har kuma yazo jikin qofar yaji dariyarta seda ya taba qofar tayi qara kafin yasan ta ajiye wayar shine zatace masa bacci takeyi to dole ya taka mata burki dan baze dauki wannan salon chatting din daren ba, yana zaune ta mayar dashi hoto tana hira da wasu can a waje da mazansu basu damu dasu ba da har suke barinsu su raba dare suna chatting Kusan minti goma da shigarsa dakinsa yaji ta shiru a fusace ya sake komawa dakin nata, bata ciki, jikin socket din da take saka chaji ya duba bega wayarta ba dan haka kai tsaye ya wuce bandaki. Umaimah kuwa Khalil na fita ta dauki wayarta ta shige Bandaki, akan Masai ta zauna taci gaba da duba Messages din group dan wata ce take neman shawara akan mijinta nada kule kulen yammata shine ake ta bata shawarwarin abinda ya kamata tayi ta sakankance se jin bude qofa tayi, a sittin ta jefa wayar cikin kwandon kayan wanki ta durqushe a qasa ta fara kakarin Amai daidai sanda Khalil ya tura qofar ya shiga. "Subhanallahi Amai kuma?" Ya fada yana qarasawa inda take duk fushin daya shiga dashi lokaci daya ya washe ya ruqota jikinsa yana shafa bayanta ganin yanda take kakarin Aman kuma babu abinda yake fita. Sunfi minti biyar tana ta yunqurin iska kafin ta miqe tana riqe ciki a qaryarta wai juya mata yake Allah sarki haka ya ringa mata sannu yana lallabata ya tara mata ruwa me dumi ya wanketa tas ya dauketa suka wuce dakinsa, madara tace masa zata sha kuma se an tafasa, ba yanda ya iya haka ya kwantar da ita ya wuce kitchen din dukda sha biyu ta gota a sannan Umaimah ko tanajin ya sakaya qofa ta fito daga dakin sadaf sadaf taje ta dakko wayarta daga bandaki, bata tsaya bata lokaci ba ta kashe ta gaba daya kafin ta jona a chaji ta koma dakinsa ta kwanta. Daya kai madarar ma kurba biyu tayi tace ta qoshi ya karba ya ajiye yana ta mata sannu ita kuwa tayi kwanciyarta dan har yanzun fa ba wai ta yarda dagaske tana da wani ciki bane ma tunda babu abinda take ji ko wata alama da ake fada ta masu ciki. Ita haushin ta katse mata hirar da yayi tana shirin bada tata shawarar, amma babu komai sa hadu da safe. Washe gari da ta kama juma'a tunda Asuba yace ta shirya idan ze fita seya sauketa a gida ta wuni, sosai ta ringa murna, tare suka hada abin karyawa dan cewa yayi tabar shara kwanukanda suka bata kuwa suna gamawa yace ta shiga wanka shi kuma ya daurayesu kafin shima ya shirya. Qarfe tara suka fita seda zasu gota gidan Rufaida tace masa "Au na manta wallahi matar gidan nan ta haihu idanna dawo yau ko gobe zan shiga nayi mata barka" "Allah ya kaimu, idanda abinda zaki kawo mata se ki gaya mun" ya bata amsa kafin suka ci gaba da hirar su har suka qarasa, a gurguje ya gaisa da Anty dan basu tarar da Mama ba tun sassafe sun fita tareda Abban taje asibiti ganin likita idonta ya matsa mata da ciwo dan haka be zauna ba ya wuce Office dan ya makara, Umaimah kuwa guri ta samu ta fara zuba iskancinta yanda ranta yake so. Da farko Doya da kwai Anty ta kai mata da kunun gyada, saboda tsabar shahara a iskanci irin nata da son ta nuna musu tayi ciki Antyn na ajiye flask din doyar ta toshe hanci da hannu biyu tana ja baya, kallonta Antyn tayi da mamaki tace "Lafiya Umaimah?" "Bana son qamshin doyar ki fita da ita" ta fada kamar zatayi kuka se Anty ta saki murmushi tace "Toh ai da tun kafin kuzo ya kamata ki kira ki fadi abinda kike so a dafa miki, yanzu me zaki ci toh?" Yatsina fuska Umaiman tayi tace "ba komai" "To ko a baki kunun zallah shi zaki iya sha ai dan yanzu ma aka tafi kaiwa Nuratu tace tana so" Antyn ta sake fada. Kamar wadda aka wa dole haka ta ringa wata yatsina tana shan kunun, can cikin ranta ko hadiyar yawu take dan doyar ta shiga ranta gashi ta rigada tace bata ci. Tana kallo Yaya Aminu yazo ya zubo doyar da kunun ya zauna kusa da ita yana ci Anty na ce masa daya koma gefe Umaiman bata son qamshin. Yace "Ikon Allah su kuma daga ita har Nuratun daga zuwa ko wata biyu baku rufa ba se ciki tab Allah ya raba lafiya toh" "Kaji mun mutun se kace shi ba wata tara tasa matar ta haihu ba ze sakawa Mutane ido" Umaimah ta fada a zuciyarta tana hararar sa qasa qasa dan duk rashin mutunchinta bata shiga sabgarsa dan ubanta yake ci, Anty ce ta tare musu ya gama cin doyarsa ya tashi daidai sanda Anty take tambayar Umaiman me zata ci "Wai yau Juma'a ba wake da shinkafa akeyi a gidan nan gaba daya dana sadaka ba shine zaki tsaya kina tambayar me zataci se ta dafo abinda take so daga gidanta ai ta taho dashi ko" ya fada yana ficewa daga dakin Haka ta wunitana nade a daki tana aikin dannan waya, sanda Mama ta dawo taga iskancin nata bana qare bane bata bi takanta ba, abincin ranar ma da aka saka mata man gyada har tayi loma biyu ta ture wai da Manja take so aka sake janzawa ana ajiyewa tace a fita dashi bata so Anty ce take ta jigila akan ta me take so me za'a mata se wana baiwar Allah take can qasan ranta tana tuntsura dariya tana kuma hasaso yanda zata saka Khalil a gaba da laulayin qarya ba ita ta samu salama ba se da Khalil ya dawo ya dauketa suka tafi bayan da Mama ta ja mata kunne sosai akan shegen Chat din da take tayi tunda taje gidan. Daga nan gidan Hajiyarsa suka biya, beyi zaton Jalila zata gaya mata zancen cikin ba seda sukaje kunya tsakanin shida Umaimah aka rasa wanda ze boye wani ita kuwa Hajiya ko a jikinta jan Umaiman take tana gwada mata hanyoyin da zata kula da kanta da abubuwan da zata ringayi. A gidan sukayi sallar Magriba da Isha sukaci Tuwon da Hajiyar tayi da kanta kafin ta zuba musu wani suka tafi dashi ko zasuyi dumame tana sake jaddadawa Umaiman ta kula da kanta ta kuma ringa Addu'a, karta yi wasa da Azkar din safe da yamma dana kwanciya bacci idan an kwana biyu zatazo gidan zata taho mata da saqo da haka sukayi sallama bayan data hada ta da tarin kayan kwalamar da akasan masu ciki dasu, zuciyar Umaimah fal da soyayyar Dattijuwar, yanda take ji da ita take nuna mata qauna ko Mamanta data haifeta bata nuna haka a fili ita kam me zatacewa Allah banda godiya. Suna tafe a hanya tana duba waya, abin da ta lura da sababbin yan group din nasu basu fiya hira da rana ba seda daddare, koda yake daga jiyan zuwa yau ta fahimci da yawan su manyan mata ne ma'aikata da kuma yan kasuwa shiyasa basu da lokaci da rana se dare lokacin kowa ya gama uzurinsa. "Nifa wayar nan taki ta fara shiga haqqina gaskiya, shikenan yanzu bazakiyi hira dani ba sedai kiyi ta danna waya kina dariya ke kadai" Khalil ya fada yana tabata ganin yana ta magana shikadai bata ma san yanayi ba. Dagowa tayi ta kalle shi tayi murmushi tace "Kasan na dade bani da waya yanzu ina dokinta ne" "Nidai ban yarda ba daga yanzu indai muna tare karbe ta zan ringayi na yarda idan bana nan kiyita chatting dinki amma indai ina nan dukka lokacinki nawa ne" Ya sake fada daidai sanda suke karya kwanar gidansu, seta kashe data ta zura wayar a jaka tace "An gama yallabai ka gani ma na kashe ta bazan sake kunna Data ba se Allah ya kaimu gobe" "Yawwa na tuna gobe Saturday ko may be zamuje Kaduna akwai aikin da zan duba ban dai gama tabbatar da tafiyar ba tukunna amma dai ki kwanta cikin shiru saboda tsaro" "Allah ya kaimu, yanzu se na hada kaya kwana nawa zamuyi?" Ta tambaye shi dukda qasan ranta bata so dan ita haka Allah yayita bata son tafiye tafiye ba kuma tayi zaton idan sunyi aure da ita ze ringa yawon gari garin da yakeyi duba aiki ba. "Karki damu kawai kiyi parking abubuwa masu muhimmanci, kayan sawa idan munje zamu siya dan nima ban san kwana nawa zanyi ba kinga daman bamu je honeymoon ba daga can kawai se muyi can muyita zaga gari har se an ganmu kawai" ya fada yana kashe mata ido daidai sanda ya paka mota a qofar gida, seta jefa masa hararar wasa ya fita ya bude Get ya dawo yana cewa "Kinga da kin iya mota kawai shigo da ita zakiyi amma yanzu se naje na kuma dawowa" "Uhm" Umaimah tace, ta gaji sosai dan haka suna shiga wanka ta farayi da ruwa me zafi sosai ta gasa jikinta, cikin kayan da Hajiya ta bata ta lalubo tsami gaye ta zauna tana sha saboda jin bakinta da tayi babu dadi, wai yanzu cikine da ita itama zata haifi Da tab lallai akwai bidiri ranar. Da wuri suka kwanta saboda tafiyar da aka tabbatar masa zeyi a goben, Umaimah dake kwance lamo kamar me bacci ta miqe a hankali bayan data tabbatar da baccin Khalil din yayi nisa. Palour ta koma ta kwanta ta hau WhatsApp lokacin qarfe goma da yan mintina a sannan kasuwar gidan Qasaitacciyar Mace ta faraci. Hira tayi dadi ita da ta fito da niyyar tadan duba abinda aka tattauna ta koma se gashi ta shantake se jin muryar Khalil tayi a kanta yana tambayar me takeyi a nan cikin daren nan? Assalamu Alaikum mutanen Kwarai👍 Shin kina son kwarewa fannin girke girken zamani,snacks da sauransu Hajiya ta💃 ga dama ta samu Mun bude online class wanda zamu koyar da girkin zamani yanda ake sarrafasu ta hanyoyi da dama…Akan kudi qalilan 200 ga mutane 10…daga bisano ze koma 300 kacal kedai kawai tura kudin ki ta wann acct din….. 1509536481 Rabiatu Nuhu Aliyu Access bank https://chat.whatsapp.com/IL3QnKmFxojAATF6WkzGxK *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 21 "Na kasa bacci, shine na fito nan saboda bana so na tashe ka kaga zakayi Driving da safe" ta fada tana tura wayarta qasan pillow. Se daya karanci yanayinta na wasu seconds kafin ya qarasa kusa da ita yana cewa "Shine zaki fito cikin dare ki zauna ke kadai kina dariya? Me yasa baki tashe ni ba ko ki zauna a cikin dakin?" "Bana so na katse maka baccinka kuma kwanciyar ce naji bazan iya ba shiyasa na fito nan kar motsina yayita damunka" ta sake marairaicewa, "Hmm" Khalil yace dan beyarda sam da maganar ta ba amma ya share ya ruqo hannunta yana cewa "Tashi muje ki kwanta kuma ko ba yau ba karki sake tashi cikin dare ki fito ki zauna ko dan saboda lafiyarki da abinda yake cikinki". Seda tayi Addu'a ta kwanta kafin ya kashe musu fitila shima ya kwanta a gefenta, ji yayi baccin da yaje idonsa ya tafi dan daman ruwa ya farka ze sha ya duba be ganta ba abinda yasa ya fita nemanta kenan. Wannan sabuwar Dabi'ar tata ta chatting din dare ta fara damunsa dan shi a rayuwarsa duk inda qarfe goma take ya sauka Online, ko kafin ya aureta haka suke goma nayi sukeyin sallama kenan idan ya kashe Data ita ci gaba takeyi da chatting dinta har tsakar dare kenan? "Wai ma dawa take chatting din?" Zuciyarsa ta jefo masa tambayar, baya so ta dasa mata zargin wani abu a ransa amma qaryar da takeyi masa da yanda take boye waya duk sanda ya kamata yasa yaji yana son ganin menene a cikin wayar tata. Kallon Umaimah da bacci yayi awon gaba da ita daga kwanciyarta tana sauke numfashi hankali kwance yayi, a nutse ya miqe dan ma karta ji qarar qofa daya bude se ya tokareta ya barta a bid ya wuce kan kujerar data bar wayar ya dauka. Da contacts dinta ya fara daga farko har qarshe numbobin tarkaceb qawayentane babu adadi sena yan uwa dan ze iya irgi number dayaga sunan namiji akai. Bangaren kira ya koma nan ma yawanci kiransa ne sena yan gidansu da kuma Hajiyarsa, haka yayi ta shige da fice yana bincike a wayar har WhatsApp da Facebook dinta seda ya duba babu wani abu na rashin gaskiya a ciki, lokacin qarfe biyu harta gota da yake a kunne tabar Datar yana kallon messages nata shigowa daga wasu groups daya tabbatar da abinda yake sakata raba dare tana chat din kenan, to kuwa tabbas ze taka mata burki be hanata hira da kowa ba da rana amma duk inda ya dawo gida lokacinta nasa ne dole ta ajiye kowa da komai ta fuskance shi idan ba haka ba kuma ya kwace wayar kowa ya huta tunda ita batajin magana. Kashe mata Datar yayi ya jona a chaji kafin ya koma ya kwanta, da Asuba dukkansu suka makara tashi saboda rashin komawa bacci da wurin da basuyi ba, shiya ja su jam'i, suna idarwa Umaimah ta kwanta a gurin dan wani bacci takeji sosai. "Ki tashi kin san muna da tafiya a gabanmu" Khalil ya fada murya a daure, seta miqe zaune tana tura baki, be kulata ba ya shige bandaki tana jin alamar zubar ruwa tasan wanka yake seta fice daga dakin tana qunquni "Se kace ni nace ina so naje ni da zakayi tafiyarka ka barni ma da nafi son haka" ta wuce kitchen ta dora ruwan shayi ta soya kwai tunda akwai bread. Qarfe takwas suka kama hanyar Kaduna, shi yake tuqi tana zaune a gefensa tasha kwalliya da wata farar Abaya fuskarta se walwali takeyi suna tafe suna yar hira jefi jefi har Khalil ya gaji da yanda idan yayi magana daya seta dauki lokaci kafin ta bashi amsa saboda hankalinta gaba daya yana kan wayar ta se yayi mata shiru ya kunna radio kawai a ransa yana ayyana yanda zero magance wannan danne dannen wayar tata. Qarfe sha biyu saura suka shiga Kaduna, kai tsaye hotel din daya rigada yayi musu booking daki ya nufa da ita, a gurguje ya karbi mukulli ya rakata dakin ya nuna mata wayar tafi da gidanka da zata kira idan tana da buqatar wani abun a kawo mata kafin ya wuce Site din da zeyi aiki dan tun suna hanya suke kiransa a waya. Khalil na fita ta zare doguwar rigar jikinta ya rage skin tight da vest da ta saka a qasa ta haye kan gadon daya sha shimfida bayan data ware Ac ta duqufa kan wayarta tana sana'ar Chatting. Rufaida ce tayi mata magana tana mata qorafin bata shiga barka ba kwana biyu bata online ma bata nemeta ba se Umaimahn ta bata haquri da uzurin bata gari amma da sun dawo zata shigo. "Ai naga kin zama yar gida a Group har cigiyarki ake idan anjiki shiru" Rufaidan ta turo mata, se Umaimah tayi murmushi kafin ta mayar mata da cewa "Ai group din naku akwai qaruwa kullum ana kawo topics masu ma'ana da dole kaima se ka bayarda taka gudummawar" "Wai me yasa ma kika fita daga wancan group din bayan abubuwan qaruwa ake turowa? Kinsan fa zamanin nan dole seka tashi tsaye ka zama karuwa a cikin gidanka idan kina so ki kama mijinki a hannu dab dai kinsan yanda yanzu maza suka baci da yawon biye biye, to duk irin abubuwan da matan wajen suke musu kenan mu na gida kace kunya ka kasa sakewa ka bawa miji farinciki. Wani ma ko baya biye biye zakiga yana kallo a waya se ya zama kome zakiyi masa da yar qaramar wayewarki ba zaki burge shi ba" Rufaidah ta turo mata da voice. Ta voice din ta bata amsa tace "Hakane amma ni gani nakeyi wannan abin ai ba se an koyawa mutum ba ko kuma se kaje ka kalli haram zaka koya saboda wannan kallon daidai yake da mutum ya aikata zina bayan zunubi ga illar da kallon tsiraici yakeyiwa ido gaskiya bazan iya zama a group din ba ni, iya ilimin da nake kwasa a group Malamina ya isheni kuma da qaramar wayewar tawa haka yake gigicewa idan na masa abu" ta qarasa tana murguda baki kamar tana gaban rufaidan dan gaba daya haushinta taji ya rufeta kuma ta farayi mata kallon yar iska dan ita ko irin sakin bakin nan da mata sukeyi idan ana hira raina mace takeyi ta kuma ringayi mata kallon yar iska, to idan ba dan iska ba waye ze ringa zancen batsa ko ya kunna a waya ya kalla? "Allah ya baki haquri ni bada wani abu nake nufi ba" Rufaida ta fada saboda jin martanin Umaiman, se itama tace "Nima ba wani abu nake nufi ba ai ra'ayina kawai na gaya miki iya wannan ma da nake ciki ya isheni, bari nayi sallah an kira" daga haka ta kashe Datar gaba daya ta tashi jin cikinta na qugi dan yanzu tana yawan jin yunwa qila nata kalar laulayin kenan dan dai har yau ita bata ji wani abu da ze saka ta yarda dagaske tana da ciki ba. Waya ta kira ta fadi abinda za'a kawo mata kafin ta shiga bandaki, "uhm ko nawa ya kama dakin nan se Allah" ta fada tana qarewa bandakin kallo tayi fitsari ta dauro alwala daidai nan aka buga qofar dakin, seda ta zura dogon hijabi a jikinta kafin ta leqa ta yar hudar dake Jukin qofar taga ma'aikaciyar hotel dince da Tryn abinci dan sosai Khalil yaja mata kunne akan idan an buga ta fara duba waye kafib ta bude qofa, bude mata tayi ta shigo ta gaishe ta kafin ta ajiye abincin ta fita. Seda ta qulle qofar da muqulli kafin ta tayar da sallah dan har biyu ta gota tana can tana surutu bayan ta idar ta dauko wayar data saka a chaji ta zauna tana cin abinci tana danne dannenta, data gama goge hannunta kawai tayi da tissue ta mayar da qafafunta kan dogowar kujerar da takr kwance ta miqe da kyau yanda zata ji dadin kwanciyar ta ci gaba da gashi. Kiran Maman Asad ne ya katse mata fafatawar da sukeyi a wani group da Halima qawarta ta sakata ana zancen kishiya. "Ke gani qofar gidanki muna ta bugu shiru halan baccin nan naki na asara kike yi" Maman Asad din ta fada bayan data amsa kiran, se Umaimah ta harari wayar kamar tana gabanta tace "Toh ni bana nan ai da se ki kirani kafin kizo ko idan baccin ma nake sena tashi". "Karki ga kinyi aure kice zaki mun rashin kunya ubanki zanci wallahi, zaki bude ne ko kuwa na kama gabana dan ina da gurin zuwa ni" Maman Asad din ta fada a hasale, se Umaimah ta kwashe da dariyar shaqiyanci tace "Nifa dagaske bana nan muna Kaduna dazu da safe muka tafi" "Yanzu zakuyi tafiya bazaki fadawa kowa ba ko dan abubuwan gyara a baki ki dan sabunta shine kika tafi ziqau dake ko bayan ko jiya ance a gida kika wuni? ai shikenan zanga randa zakiyi hankali kedai. Me kuka jeyi kuma wadanne irin kaya kika diba?" Cewar Maman Asad. "Woh Yah Hajiyayye sarakan gyara yanzu tafiyar ma se anyi mata wani gyara gaba daya watana nawa a gidan mijin ma bare a faramun wani garanbawul? Kawa kuma yace karna dauki komai zamu siya a nan ni nigh gowns da undies kadai na debo kuma fa aiki yazo yi ba wai hutu muka zo ba" Umaimah ta fada "Ai shikenan ki zauna kar kiyi gyara kinji idan baki fara tun yanzu ba ya zamar miki jiki sanda jikin naki yake da buqatar gyaran bayi zakiyi ba dan baki saba ba a shegen halin son jikinki da qazanta ma ai ke kam dole a ringa miki garambawul din akai akai, saura kije ki zauna masa shabar kamar buhun masara kina sana'ar danna waya dan jiya naga last seen dinki har kusan dayan dare toh ki shiga hankalinki, idan zaki ware ki ringa masa salo da kisisi na kala-kala yaji kamar karku dawo gida, inda ba hutun yake so kuyi ba in iya aikine ai shi kadai zeyi tafiyarsa. Idan yaji dadin tafiya dake kinga shikenan kin samu lasisi duk inda zashi kina gefensa idan ba haka ba kuwa kina kallo zeyita yawace yawacensa kina gida kina masa gadi" Maman Asad ta sake fada kafin sukayi sallama ta kashe wayar tana sake jaddadawa Umaimah da tayi kwalliya ta daukar magana kafin ya dawo, idan ma bata da kaya ta zauna da Towel shima duk cikin salon gayun ne. Hamshaqiyar kuwa kofi ta cika da lemo tana sha ta koma WhatsApp suka ci gaba da cece kuce tana kumfar bakin babu macen data isa ta kula mata miji, "Ai ni mijina dan ni kadai aka yi shi babu kuma macen data isa ta rabeshi a duniya idan ta wuce uwar data haifeshi se yan uwansa da suke ciki daya, duk wata mace bayan wannan tace zata tsallaka hurumin Mijina toh kuwa ta taro yaqin da ze qarar da danginta kaf bama ita kadai ba, shima ya sani ba kuma zeyi gangancin saka yar mutane a masifa ba dan na rantse da Allah zan iya halaka yarinya sedai duk abinda ze faru ya faru shi da kansa ya fada ni kadai na ishe shi" Umaimah ta tura da voice note. Sabon cece kuce ne ya tashi, masu goyon bayanta suna yi masu nuna mata kuskurenta da cewa ta rage zafin kishi sunayi, wata me suna Rabi'atu dake da rabon karbar nata kason rashin mutunchin tabi Umaimah Pc tace mata "Haba baiwar Allah kamar ba musulma ba ki ringa iqirarin halaka wata akan kishi ko dauki dakon rai, ba a aure ke ya aureki? Kinga ai bazaki fitar da ran wata rana ze sake gano wata yayi sha'awar auranta ba kawai dai kiyi addu'a idan Mijinki nada rabon qara aure Allah ya hada kanku ya bashi ikon yin Adalci amma irin wannan kalaman ai idan kika zamu wata yar tijarar irin ki tsaf zata iya cewa ita kuma zata nemi mijin naki taga yanda zakiyi". Zabura Umaimah tayi daga kwancen da take ta miqe tsaye tana qara karanta saqon daga baquwar lamba kafin ta shiga mayar mata martani da cewa "Nice yar tijara? To uwar data haifi Uban Kakarki itace Tijararriya kuma da zaki ce wata ta nemi Mijina kai tsaye ki fito kice ke zaki auri Mijina,  idan baki fasa neman Mijina kin aure shi ba ke tsinanniyace kuma uwarki shegen ki tayi ta kaiwa ubanki, ni kuma ko sunan Mijina naji kin kama a bakinki ballantana ta kaiki ga neman inda yake sena nuna miki ni Umaimah na haifu kuma ina fada da cikawa idan kuma keep na ganin wasa nakeyi ki gwada". "Allah ya shiryeki idan kina da rabo kuma in sha Allahu se an miki kishiya ko dan kiga iyakarki" Matarta sake tura mata kafinta danna mata block dan bazata iya da dingimemen tashin hankalin Umaimah ba. Hohoho ina wuta Umaimah ta jefata? Wasu mulmulallun Ashariya masu maiqo ta shiga antaya mata amma ganin da tayi messages din basa tafiya alamar tayi blocking dinta kenan yasa ta koma group tayi tagging sunanta taci gaba da zaginta tana sake nana ta mata idan ta cika mara kunya ta fada mata inda take ita kuma zata zo ta sameta ita dai baiwar Allah yayi tsit dan taga abin yafi qarfinta yan group nata bawa Umaimah haquri masu fushi da fushin wani da basu san kan zance ba suka shiga tayata tagging matar suna zagi, a cewarsu baze wuce ta bita Pc bane zatayi mata wa'azinta na munafunci data saba ai gara haka yau ta jangwalo wadda tafita baki ita dai mata da taga babu sarki se Allah babu bata lokaci ba tayi left daga group bayan data sake cewa Umaiman "Ko iya wannan jahilin kishin naki ya isa ya saka ayo miki kishiya kuma kina ji kina gani ze samo kamilar mace me aji ba ballagaza me zage zage a social media ba" tana turawa ta arce daga group. Kiran layin matar Umaimah ta shigayi tana jin zuciyarta kamar zata fito saboda tsabar baqin ciki, ita zatayiwa wannan cin mutunchin? Ai kuwa duk inda matar nan take seta nemota taga ubanda ya tsaya mata se kuma ta nuna mata ita ba kanwar lasa bace. Wayar taqi shiga ta gwada da dukka layukanta guda uku bayan wanda take chatting dashi dan daman tasan dole zatayi blocking nata amma duk a banza basu shiga ba, kwafa tayi ta jefar da wayar ta zauna tana jijjiqa qafa a zuciyarta tana ayyana ta inda zata binciko matar nan. Da ace Yaya Aminu mutumin kirki ne shi zata bawa Lambar ya nemo mata ita tunda shi jami'in tsarone amma tasan seya tsareta da tambayoyin jin ba'asin abinda yasa take nemanta qarshe idan magana ta fashe itace a ruwa dan tasan babu me goyon bayanta dan haka dole tasan ta ina zata zaqulo matar nan dan wallahi bata zagi bulus ba. Tana kallon Halima na kiranta a waya tayi banza da ita dan tasan baze wuce labari ya isar mata na abinda ya faru a group din ba tunda bata Online ita, tana zaune nan zaman saqa da warwara har bata san lokaci ya tafi ba sejin motsin bude qofa tayi ta zabura ta miqe tsaye tana kallon kanta da gurin da take zaune kwanukan abincin data ci na nan a bude ko murafen bata iya mayarwa kai ba bare aje ga kawar dasu gefe ga lemon da take sha ma ashe ta ture shi ya zube a garin masifa bata sani ba ya bata farin centre carpet din dake dakin seta juya ta kalli Khalil dake takowa zuwa inda take, ganinsa tayi tas sam beyi kama da wanda ya fito daga Site ba inda ake aikin Yashi da sumunti se ji kawai tayi hawaye na ziraro mata "Umaimah lafiyarki kuwa" Khalil ya fada yana jijjigata ganin yanda ta zura masa ido tana hawaye tunda ya bude qofar ya shiga har ya isa gabanta bata motsa ba yanayinta kuma ya tabbatar masa da bata cikin hayyacinta. Ajiyar zuciya me qarfi ta saki kafin ta fada jikinsa ta fashe da kuka kamar wadda aka kwadawa Mari, yanda take kukan har jikinta na rawa ya dagawa Khalil hankali babu shiri ya shiga karanto addu'oi yana tofa mata dan abinda zuciyarsa ta bashi gamo tayi dan haka ya dage yana karanto Addu'oin tsari yana tofa mata Umaimah kuwa banda kuka babu abinda takeyi, idan ta kalli fuskar Khalil ta tuna abinda matar can ta gaya mata seta sake rushewa da kukan. Ganin da yayi bazatayi shiru ba ya kuma tabbatar in har shaidanu ne dagaske irin addu'ar daya tofa mata zasu lafa sedai idan nata shedancin ne ya motsa dan haka ya jata gefen gado ya zaunar da ita yana cewa "Ya isa kiyi shiru menene?" Seda ta kwashi kusan wasu mintuna biyar kafin ta fara tsagaita kukan tana jan shashsheqa da Ajiyar zuciya. "Babe, kiyi magana meya same ki dan Allah wani abu ya faru a nan ko a gida?" Ya sakw fada cikin sanyin murna dan ya fara tsorata da kukan nata kar fa wani mugun abun ne ya faru da ita ko bayan fitarsa. Dakyar Umaimah ta iya bawa kanta haquri ta fara magana cikin muryar kuka tace "Ba wata mata ce ba haka kawai tace wai in sha Allahu se kayi mun kishiya kuma..kuma ta kwace mun kai sedai na zama yar kallo, na rantse da Allah duk inda take a Nigeria sena nemota naci ubanta, sena nuna mata ni ba sa'ar ta bace idan ma itace take shirin shiga rayuwarka zan dakatar da ita sena mata abinda ko ance ta sake kallon mijin wa...." "Ke da Allah ya isheki haka" Khalil ya fada a fusace yana janyeta daga jikinsa,idan da ace yasan sakarcin da yake damunta kenanda ko dakin baze shigo ba ze juya abinsa. Ya kwaso gajiya tunda ya fita tsaye yake akan qafafunsa shine zata qara masa wani zafin da wauta da rashin nutsuwarta, tsaki ya sake ja me qarfi ya shige bandaki ya bar Umaimah da tunda yayi mata tsawar ta saki baki tana kallonsa. Wankansa yayo da alwala ya fito daure da towel a qugunsa har sannan tana tsaye fuska shabe shabe da hawaye kamar wata qaramar yarinya ya wuceta ya bude qaramar Akwatinsa daya sako abubuwan buqata tana ajiye yanda suka shigo da kayan bata motsa su ba sema tata Akwatin data bari a bude data dauki Hijabi. Vest da Boxers ya dauka da jallabiyya se mai da turare ya koma gefen gado ya shiga shiryawa, tamkar babu wata halitta a dakin haka ya shareta ya gama shirinsa tsaf ya dauki wayarsa ya nufi qofa daidai lokacin da aka kwada kiran Sallar Magriba Umaimah da ta sandare a tsaye babu La'asar ga Magriba tayi ta bi bayansa da sauri tana cewa "Ina zaka tafi kumaka barni?" "Masallaci zanje" ya fada yana bude qofar ya fice gaba daya ransa babu dadi. Duk irin burin daya gama ci akan zuwan su Kd baya tunanin ko daya daga ciki ze tabbata, yanzu dawowa yayi da niyyar idan sukayi sallah su fita yayiwo mata shopping kayan sakaqa tunda ya ce karta dakko amma bayajin ze iya dan in sun fitana bacin raine kowannen su ze sha dan bazata fasa abinda ta faro ba shi kuma ya dena daukar shirmenta dan ya kamata ace yanzu tayi hankali ta gane daidai da rashinsa. Daya idar da sallar a Restaurant din Hotel din ya zauna yaci abinci ransa a jagule musamman yanda yaga mutane kowa da yar matarsa ko budurwa suna cin abincinsu suna nishadi, daya gama ma waje ya fita can inda suka zuba kujeru ya zauna se kusan qarfe tara ya koma dakin nasu. Umaimah kuwa bin bayan Khalil daya rufe qofa tayi da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma jiki ba kwari ta zauna ta rafka tagumi, yanzu kuma meye abinda ya bata masa rai shi kuma? Amma koma menene waccen matar ce ta jawo kuma tayi alqawarin setaci uwarta wallahi bari su koma Kano zata biya kudi duk inda take a lalubo mata ita toh shi kuma da yayi wanka ya fesa turare ina zashi daga masallacin? Kuka wiwi ta dasa, seda tayi dagaske ta iya tashi tayo Alwala tana sallar tana goge hawaye tana idarwa ta haye kan gado taci gaba da kukan dukda yunwar data ji tana taso mata har sannan kayan data zo dasu tun safe ne a jikinta, dakin data tarar tsaf ko ina a kintse ta hargitsashi da shirgi. Tafi qarfin awa daya tana aikin kuka har akayi sallar Isha'i bata motsa daga inda take ba tana ji ana buga qofar daga waje tayi banza dasu dan tasan idan shine yana da katin qofar a hannunsa sedai ko Ma'aikatan Hotel din, idan ta tuna gurin wata ya tafi ya kulleta a daki seta sake rushewa da kuka zuciyarta nayi mata suya, Wani tunani ya zarga mata ta miqe da sauri ta isa jikin window da yake kallon Harabar hotel din inda swimming pool yake tuni gurin ya fara cika da mutane saboda duhun dare yayi ga motoci nata shigowa Mata nata yawo da shiga kala kala yanzu a haka ya ratsa su ya fita a ina ma masallacin daya ce zashi yake? Anya ba bakin da waccen yar iskar tayi mata bane ze fara kamata wata budurwar Khalil yayi shine ze ce mata ya tafi Masallaci dan ita dai bata ga alamar masallaci a cikin hotel din nan ba ko kiran sallar da take jiyowa tana ganin daga waje ne amma ba a nan ba ai kuw fita zatayi ta nemo duk inda masallacin yake ta tsaya ta jirashi, juyawa tayi zata bar gurin seta koma da sauri saboda hango wani da tayi kamar shi a zaune. Ido ta gwalo tana kallon sa, Khalil din ne a zaune ga wata yarinya a tsaye gabansa ta saka wata shegiyar rigar Atamfa bata ga fuskarta ba amma ta ga bayanta da dikin ya matse tsam kamar idan ta sunkuya rigar zata yage suna fuskantar juna shida ita idan ba gizo idonta ya mata bama hannayensu take gani kamar a sarqe. Wani jiri taji ya kwasheta ta kama qarfen window ta riqe da kyau tana jera numfashi kamar wadda tayi tsere kamar kuma wadda aka tsikarawa Allura seta juya da sauri ta zari Hijabinta dake kan sallaya har tayi gaba ta hango wuqar data yabka Apple da ita akan Plate ta dauka dukda bata san me zatayi da ita ba haka ta nufi qofa batareda ta saka hijabinba ta dai riqe a hannu. Daqarfi ta finciko qofar zata bude ta jita a bame, ta jijjiga ta gama murde murdenta qofa taqi buduwa take ta fahimci ya kulleta ne ta waje saboda yasan abinda ze fita aikatawa. Dukan qofar ta shigayi kamar mahaukaciya tana kuka amma ko gezau qofa batayi ba dan kanta ta gaji haka ta fada kan gadon tana ci gaba da kuka tamkar ranta ze fita nan da nan ciwon kai da zazzabi suka rufeta cikinta ya murda kafin kace me ta shiga kelaya Amai akan gadon har tana neman shidewa saboda yanda ya taho mata har ta hanci daidai sanda Khalil ya bude dakin ya shigo hannunsa da ledojin abincin daya taho mata dashi. Da sauri ya dire ledar yayi kanta yana salati ganin yanda take yunqurin kamar zata amayar da kayan cikinta, ya ruqota ta fincike dukda yanayin galabaitar da take ciki be hanata harararsa ba ta ce "Karka tabani da qazamin hannunka da kaje ka taba karuwa dashi" Be damu da kalanta ba ya sake matsawa yana qoqarin riqota yace "Umaimah ki tsaya na taimaka miki jikinki yayi zafi, ki bari muje Asibiti kinsan dai bake kadai bace ko" amma ina ta fitittike ta shiga kai masa duka tana kuka da zaginsa akan yaci Amanarta a kan idonta taga ya riqe karuwa kuma tsahon lokacin nan daya dauka qila daki suka kama wallahi seta kashe kowacece ai ta ganeta shidai be kulata ba kamota yake tana zillewa dayaga tana neman bashi wahala ya saka mata qarfi gaba dayanta ya dauketa ya shige toilet da ita, jikinta ya rigada ya saki saboda Zazzabi da kuma Aman da tayi se bakinta ne be mutu ba, babu yanda ta iya yayi mata wanka tas tana kuka da koma ya saka mata qaramar Riga da Hijabi ya sake daukanta a kafada ya fita da ita suka wuce Asibiti "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wannan wace irinmasifa ce" Khalil ya fada yana dafe kai saboda yanda Umaiman ta ware Murya tana masa ihu a mota tana zaginsa kamar wanda ya satota, a fusace ya juya ya kalleta ya daga hannu kamar ze kwada mata mari yace "Na rantse da Allah idan baki rufe mun baki ba sena tattaka ki a nan karki dauka tsoronki nake da yasa nake rabuwa dake kina mun duk iskancin da kika ga dama,mata kuma yanzu na fara kulawa tunda baki da amfani baki iya komai ba se tashin hankali da masifa kala kala, mtsw" yaja tsaki. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 22 Tsit tayi saboda ta tsorata dan yanda yayi mata magana seta maida kanta ta kalli window taci gaba da share hawayen da suka qi tsaya mata, idan ta tuna ganin da tayi masa da karuwar dazu se taji kamar ta shaqeshi idan yaso motar ta kwace masa su mutu gaba daya kowa ya huta amma yanda ya hade girar sama data qasa ta saka ko motsi me kyau ta gagarayi, alwashi taci a zuciyarta wallahi se ya gane kurensa. Saboda zafin da jikinta yayi dole likita yayi mata akluran saukar da zazzabi kafin ya hado mata da magungunan da zata sha tareda dogon gargadi akan sakawa ranta damuwa kodan qaramin cikin da take dauke dashi, shi ya gaya musu satikan cikin bayan da yayi mata scanning a yanzu cikin nata na sati na takwas su kuma suna sati na goma da aure haka suka kama hanya babu me cewa dan uwansa qala har suka dawo Hotel din, bata jirashi ba dukda yanda take jinta kamar zata fadi saboda rashin kwarin jiki amma haka ta shige sedai tun a reception ta rikice dan ta manta inace hanyar bangaren da suka saukan, seta samu kujera ta zauna tana mayar da numfashi, ta daga kai kenan ta hango yarinyar dazu data gani da Khalil. Fara kyakykyawa kana ganinta kaga fulanin usul koma ace ta hada jini da Larabawa suna tsaye da wani babban mutum suna magana, mantawa Umaimah tayi da duk wani ciwo datake ji a jikinta ta miqe a zabure ta nufeta sedai bata kai ga isa kusada ita ba Khalil da shigowarsa gurin kenan ya riqeta kamar dan sanda ya kama barawo. "Ka sakeni na koyawa waccen kilakin hankali ta yanda bazata sake gigin kula Mazan wasu ba" ta fada muryarta bata fita sosai sabo kukan data sha, be kulata ba se qara daure fuska da yayi ya shiga janta tana turjewa "Bayero" sukaji an kirashi se ya tsaya tsak tareda Juyowa Umaimah ta sake zabura amma riqon da yayi mata bana wasa bane,gaba daya ya mannata da jikinsa sannan ya kama tsintiyar hannunta seda tayi qarar Azaba ta shiga kiciniyar qwacewa har budurwar ta qaraso inda suke. "Lafiya dai naga kana riqeta?" Ta fada tana kallon Umaimah da Khalil ya matse kamar burodi bugun qato ta kasa kwakwkwaran motsi, tafiya ya farayi yana cewa "Bata jn dadi ne daga Asibiti muke, baki tafi ba kenan ko kun fasa Dinner?" "Ai yanzu goman tayi nayi meeting da wani client dina ne akan wata kwangila idan abunuwa sun zama ready zanyi maka magana ma kayi taking care of the Arcitectural part" Burdurwar ta fada har sannan tana kallon Umaimah data haqura ta fawwalawa Allah, haka ya jata qiii suna isa dakin kafinma tace wani abu ya saketa ta tafi taga taga zata fadi Allah ya taimaketa ta dafe kujera. Nunata yayi yace "Wallahi Umaimah karki kuskura ki kaini bango dan bazaki ji dadina ba ki kuma shiga hankalinki karki kuskura ki sake maimaitamun irin shirmen da kikayi yau idan ba haka ba Allah zaki gane shayi ruwane" yana gama fada ya shige bandaki ya barta zaune tana binsa da kallo. Kukan baqin ciki ta sake rushewa dashi, har yayi wankan ya fito tana zaune, seda ya gama shirin baccinsa tsaf kafin ya dakko ledar Abinci data magunguna ya dawo gabanta ya zauna, hannunsa ya dora a goshinta ta janye, jikin nata har sannan da zafi rau. Tausayinta ne ya kamashi dan haka ya sassauta fuskarsa dake dinke babu fara'a cikin lallashi yace mata "Zo kici abinci kinga jikinki da zafi har yanzu ki dena wannan koke koken ya isa haka" "Ni bana ci, kaje ka kaiwa waccen me kama da bulalar tunda itace..." "Umaimah" ya kira sunanta cikin dakewa amma murya a tausashe kafin ya saka kwayar idonsa cikin nata dake zubar da hawaye dolenta ta sauke idonta qasa dan bazata jure irin kallon da yake mata ba. "Me yasa ke baki son zaman lafiya koda yaushe kin fi so ayita tashin hankali? Abinci nace kici ba wata doguwar magana ba idan kuma kinqi zan danneki na dura miki dan bazan lamunci ki ringa barmun baby da yunwa ba" "Seka durawa babyn yaci dan indai ta bakina abinci ze wuce ya samu ba kuwa zeci ba tunda shi ka damu yaci bani ba" ta fada tana murguda masa baki tareda juya masa qeya, murmushi yayi a ransa yana jinjina irin qaunar da Umaimah takeyiwa tashin hankali, seya saka hannu biyu ya juyo da ita yace "Allah ya baki haquri Maman baby dukkanku na damu kuci, kinga zafin jikinki qaruwa yake ki ci ko yaya ne kisha magani ki kwanta dare yana qarayi". Shiru tayi masa tana ci gaba da jan hanci a ranta kuwa Allah kadai yasan me take ayyanawa. "Bazaki matso kici ba?" Ya sake fada yana kallonta amma ko gezau sema miqe qafafunta da tayi ta jingina da kujerar bayanta tana shirin bacci, Abincin ya bude, Soyayyen dankali ne da Kaza dan ya se shawarma, sun rigada sunyi sanyi. Tashi yayi ya saka a Microwave ya dumama mata sannan ya hado shayi me kauri yana ankare da yanda take satar kallonsa ya gama ya dawo gabanta ya ajiye, muqut ta hadiye yawu saboda yanda qamshin abincin ya daketa amma ta dauke kai sema ta shigayin kamar zatayi Amai, be ko bi ta kanta ba gaba dayanta ya dorata a jikinsa ya daga kofin shayin daya rigada ya saisaita ya kai mata baki, ta kauce ya saka hannu ya danne kanta dole uwar naqi ta bude baki ta shiga kwankwadar shayin dan dama a yunwace take ita kanta tasan yaudarar kanta take amma bazata iya bacci bata ci komai ba. Tas ta kurbe shayin kafin ya sake ta yana kallon yanda zufa take keto mata kamar wadda ta watsa ruwa, kumbura baki tayi ta sauke kai qasa ta janyo kwanon dankalin ta shiga ci Khalil yaja gefe yana kallonta cikin dan lokaci ta cinye abincin tas ta shiga sauke numfashi dan ji tayi abincinya tafi da duk wani abinda yake damunta. "Good girl, saura wanka" ya fada yana kwashe kwanukan ya hada da tun na rana data bari ya killace su gefe, ya zata zatayi musu se yaga ta tashi zugui zugui ta wuce bandakin, wanka tayi tsaf tareda Alwala ta fito zazzabinya sauka jikinta ne dai take jinsa babu kwari se quncin zuciya wanda ta dorawa kanta. Rigar baccindaya rigada ya ciro mata ta dauka ta saka ta dora dogon hijabibta ta tada sallah Khalil na daga kan gado yana kallonta ta idar ta gama Addu'ointa ta shafa seta zame ta kwanta a gurin. "Ya haka zaki kwanta a qasa? Ki tashi kisha maganin se ki kwanta gaba daya" Ya fada yana qarasa wa inda take, tashi zaune tayi ya balla mata maganin ya bata ruwa ta kora tana gamawa ta sake kwanciya ta duqunqune da hijabinta. "Wai meye haka Umaimah ya zaki kwanta a qasa cikin sanyi bayan kinsan ba lafiya ce dake ba?" Ya fada yana tsaye a kanta, seta miqe zaune tana kallonsa tace "Dan Allah bacci nakeji ka qyaleni, idan gadon ya maka girma ka kirawo karuwarka ku kwanta tare ni nan ya isheni" "Kee Umaimah" Khalil ya daka mata tsawar da seda taji wani abu ya tsirga mata kamar zata saki fitsari a inda take, "Ni kike hadawa da Karuwa? Ni kike kira mazinaci Umaimah kije cewa na kira karuwa mu kwanta saboda baki da mutunci?" Ya fada yana matsota jikinsa har rawa yake saboda tsabar bacin rai, seta shiga jada baya tana girgiza masa kai dan ta tsorata da yanayinsa amma dukda haka shedaniyar zuciyarta bata rusuna ba dakyar ta bude baki muryarta na rawa tace "Wannan ta dazun wacece? Kuma ai na ganku ta window ka riqe mata hannu sannan kuka shigo ciki kuma da zaka fita ka kulleni a daki, idan ba gurin karuwa ba ina kaje?" Hannu ya daga da niyyar kai mata mari ya sauke hannun tareda kaiwa iska naushi, yasan idan yace ze dora hannunsa a jikinta tabbas seya mata dukan mutuwa, safa da marwa ya shigayi a dakin, baya so ya bude baki yayi magana dan yasan baze furta Alkhairi ba, a yanda zuciyarsa take tafasa yana iya furta mata duk abinda yazo ransa amma baze yanke hukunci cikin fushi ba, se ya juya ya kalleta ta maqure jikin gado tana raba ido, Kallonta yayi na wasu sakwanni a ransa tuhumar kansa yakeyi waya aikeshi ya auri wannan yarinyar? Qasa da wata uku ace ya fara fuskantar wadannan tashin hankulan, Amma qaddar ta riga fata. Dakyar ya hadiye yawu ba tareda ya kalleta ba yace "Tashi ki hau gado ki kwanta" "Ni a qasa zan kwant...." "Na rantse da girman Allah kika bari na tako inda kike Umaimah sena illataki" ya zaburo mata babu shiri ta haye kan gadon zuciyarta ta shiga lugude kamar zata fasa qirjinta ta fito ganin yana cire jallabiyar dake jikinsa, kafin ta samu damar yin wani yunquri ya kashe fitilar dakin ya zama dundum ko tafin hannunta bata iya gani ta shiga laluben inda zata sauka daga gadon damqar da yayi mata ta sakata yin ihu babu shiri, babu tausayi ko lallashin daya sabayi mata ballantana wannan soyayyar me bin jini da jijiya ya shiga sukuwa akanta kamar ya Samu dokin sallah. Duk ihu da roqon da ta ringa masa beji taba seda yayi mata lilis ya gaji dan kansa kaso hamsin na bacin ransa ya sauka kafin ya tsallaketa ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwan sanyi lokacin ko dan yatsanta bata iya dagawa jikinta ya saki gaba daya banda tana numfashi ma se ace suma tayi. Wanka yayi ya fito har sannan tana kwance tana jan numfashi dakyar, so take taja abu ta rufe jikinta saboda zazzabin daya mata rigib ga sanyin Ac ya cika dakin amma ta kasa, kukan zuciya take hawaye na zuba ta gefen idonta tana kallonsa ya fito ya saka jallabiyarsa ya kunna fitulu masu sauqin haske ya tayar da sallah beko nuna yasan da zaman ta a dakin ba. Yanzu ita Khalil yayiwa wannan cin mutunchin se kace ya samu Dabba sannan ya tsallaketa ya barta a haka? Jan jiki ta ringayi dakyar ta samu ta sauka daga gadon ta rarrafa ta shiga bandaki, a gefen bahon wanka ta durqusa bayan ta kunna ruwa ta shiga rera kukan baqin ciki, seda ruwan ya taru ta cicciba dakyar ta shiga ciki, ta kwashe sama da awa daya tana gasa jikinta tana kuka gaba daya jin qasanta take kamar ba'a jiki ta ba kai gani take kamar ya qarata ma ai kuwa bazata yarda ba dole ta dauki mataki akai tunda akan gaskiyarta take da idonta ta ganshi da karuwar kuma tayi magana ya hakke mata kamar wata Baiwarsa Allah yana kallo kuma seya saka mata. Sanda ta fito Khalil ya dade dayin bacci abinsa tana tafiya kamar yar kaciya ta bude ledar magungunan da aka bata ta dauki Paracetamol tasha, seda ta qara hada shayi me kauri tasha kafin ta koma kan doguwar kujerar dake dakin ta kwanta tana jin jikinta kamar ana kwankwatsata tsabar yanda ko ina ya dauki ciwo. Da Asuba daya tashe ta dakyar ta miqe shi kuwa har yayi shirin masallaci ya fice abinsa ya barta da matsar kwalla saboda yanda jikinta ya sakeyin tsami ga azabar zafi da takeji a qasanta se kawai ta zauna a gun ta shiga rusa kuka. Seda gari yayi haske ya koma dakin har sannan zuciyarsa babu dadi, idan ya tuna kalmar karuwa da take jinginashi dashi se yaji sam Umaimah bata dace da zama matarsa ba, bata ganin mutunchinsa bata qimanta shi duk menene ya jawo hakan. Sanda ya shiga dakin beyi niyyar kukata ba amma ganin yanda fuskarta ta canza ta kumbura ya bashi tsoro dole ya qarasa kanta yana kallonta da alama ko sallar batayi ba tana nan yanda ya barta, murya a daure yace mata "Baki tashi kinyi sallah ba ko?" "Bazan iya tashi ba dan Allah ka kaini Asibiti jikina, marata ko ina ciwo yake mun inaga ma mutuwa zanyi" ta fada cikin kuka, seya kama hannayenta da niyyar miqar da ita ta fasa qara saboda azabar zafin da taji, da sauri ya durqusa a gabanta yana kallon yace "Kwanta mu gani" ya fada yana qoqarin daga dogon Hijabin jikinta, bata da qarfin hana shi ba yanda ta iya ya bude jikinta ya kunna fitilar wayarsa ya haska, saurin kawar da kai yayi wani irin tausayinta ya tsirga masa. Sosai yaji mata ciwo dukda ba likita bane shi amma yasan wannan raunin ko ba'a dinke taba dole se an mata yan dabaru zata dawo dai dai, kallonta yayi yanda ta rufe ido tana tsiyayar da hawaye bayan duk ita ta jawo komai, bata jin magana ya rasa wace irin zuciya Allah yayi mata da sam bata san daidai ba se rashinsa. A akwatinta ya dauko doguwar riga mara nauyi ya zura mata tana kuka dukda yanda ya ringa lallaba mata jiki kamar me taba kwai ya dauketa a hannu ya fita da ita, kafin su isa Asibitin seda yaji kamar shima ya fasa kuka saboda yanda ta gigita masa kwakwalwa da kokekokenta da ya tabbatar bayah na ciwo harda na jidalinta. Sunyi sa'ar tarar da likita macece on duty a Asibitin daya kaita jiya ta ringa surfa masa bala'i kamar zata dake shi sanda ta duba Umaiman dan ita a zatonta ma Amarya ce daren farko, Alluran rage zugi da ciwo tayi mata ta bata wani magani na shafawa tace ba se tayi mata dinki ba ta dage da shiga ruwan dumi ta kuma ringa cin Nama me romo da fruits gurin ze warke kar kuma ta kuskura ta koma masa se taji jikinta ya dawo daidai so samu ta dauki kamar wata biyu tayi jinya shidai Khalil jinsu kawai yake tana wa Umaimah huduba a ransa yace "Ba'a koya mata abin tsiya bama tayi inaga an bata lasisi". Ranar haqura yayi da fita site ya kira ya bada uzurin Madam bata da lafiya, dukda be sakar mata fuska ba amma ya tsaya ya bata kulawa sosai dan motsi idan tayi seya tambayi me take so idan zata shiga bandaki kuwa daukarta yakeyi ya kaita ya kuma tsaya seya tabbatar da ta gasa jikinta kamar yanda Likita ta fada sannan ze rabu da ita. Duk yanda Umaimah taso da ta samu kansa abin yaci tura dan ta fahimci fushin nasa me girma ne dan ba ita kadai ba ko kiransa akayi a waya daga yanda yake magana zaka fahimci yana cikin damuwa. Tayi nadamar abinda tayi ko babu komai da yanzu bata karbi sakamon wannan Azabar da take ciki ba abinda ko daren farkonta baya fuskanta ba gashi babu wannan sakin fuskar da tarairayar data saba dasu duk abinda yake mata kamar wanda akayiwa dole. Da sukazo kwanciyar bacci ma kan kujera ya kwanta ya bar mata gadon, tayi masa magana ya mata banza seta saki kukan da dama yana maqale a wuyanta ya kuwa shareta data ishe shima ya saka Airpod ya toshe kunnensa dan kanta tayi ta gaji bacci ya kwasheta. Khalil kuwa wani irin kallon takaici yabita dashi, a cikin halayenta yana daga abinda yake qona masa rai bata san idan tayi kuskure ta bashi haquri ba. Duk sanda abu ya hadosu sedai idan ya gaji da fushinsa ya sakko ko tayi ta rara gefe sa shagwabarta ta banza har ya sakko amma dai ace ta bude baki ta bashi haquri bata iya ba. Shi gaba daya ya rasa ma inda ze sakata ne, bata da ladabi sam be kuma san yanda ta dauki rayuwar aure ba amma ze koya mata hankali, daga yanzu baze sake bari wata yaudararta tayi tasiri akansa ba, dole ta koyi ladabin idan ma bata dashi dan baze yarda su dora rayuwa a haka ba. Washe gari jikin nata yayi sauqi dan haka ya fita gurin abinda ya kawo shi, honeymoon dai ya koma zamandoya da manja dan haka suka cinye kwanakin da zasuyi idan ya fice tun safe se dare ze dawo, kuma haka zaau zauna magana idan ba wadda ta zama dole ba ko tayi masa baze amsa ba. Tun Umaimah na daukar abin wasa har yazo ya fara damunta. Koda suka dawo Kanon ma bata chanza zani ba sema qara tabarbarewa da zaman nasu yayi dan gaba daya ya fita a sabgarta takai ta kawo ko gaishe shi tayi sedai ya daga mata hannu wanda daman ba kullum ba ne take gaisuwar yanzu nema da aka shiga wannan yanayin take neman abinda ze sa suyi magana ta dage da gaisuwar. Daman tunda suka dawo ya raba musu daki, acewarsa likita tace ta samu hutu sosai shi kuma baze iya jurewa suna kwana gado daya ba dan haka ta koma dakinta tayi jinyar, girki ma ya sauwaqe mata abin kari da kansa yake shiga kitchen ya dafa idan yaje aiki yaci na rana acan wata rana yayiwo take away idan ze dawo ko ya biya gidan Hajiyarsa yaci wadda ita a zatonta laulayinciki ne ya saka Umaiman bata iya girji dan haka idan yaje seta zubo musu ko haka kawai ma ta dafa abun kwadayi ta bawa Habiba ta kai mata. Wasa wasa sun kwashe sati kusan uku a cikin wannan halin, tun Khalil najin wani iri akan matakin daya dauka musamman idan yaga ta zauna tayi shiru har ya zamana abin ya zamar masa jiki ya fara sabawa da rayuwarsa shi kadai. Umaimah kuwa gaba daya ta fita hayyacinta musamman da laulayi yayi mata dirar mikiya ga rashin kulawar datake fuskanta daga bangaren Khalil gaba daya se abin ya hadu yayi mata yawa. Wauta da rashin wayo irin nata sun kasa barinta ta hango kuskurenta ballantana ta gyara sannan ta gaza gayawa kowa a nata shirmen zata iya fuskantar matsalarta ita kadai sedai abin ya zama ana bata goma biyar bata gyaru ba. Wata safiyar Laraba ta tashi bata jin dadin jikinta, a kwanakin daman gaba daya qarfin hali kawai takeyi ita ba zazzabi ba ba wani takamaiman ciwo ba amma jikinta sam baya mata dadi se taji kamar tayita ihu ko zata ji sauqin abinda yake damunta gashi babu abokin hira ballantana ta fada masa damuwarta ya tayata koda kalamai masu dadi ne taji sanyi. Tun asuba data idar da sallah bata koma ba saboda tana son magana da Khalil din gida take so taje dan tunda suka dawo bata fita ko ina ba. kusan kullum bata sanin fitarsa, data dan koma baccin safe sedai ta farka taga ya fita ko ta tarar da saqon kudin cefane ya ajiye mata a palour dukda itama ba girkin take ba yayime yayime kawai take taci. Tana zaune ya fito daga dakinsa cikin shirin fita tsaf dashi kai bazakace yana da wata damuwa ba. Ta bishi da kallo dakyar ta iya tausar zuciyarta ta gaishe shi ya amsa mata a taqaice yana nufar qofa seta bi bayansa tana cewa "Magana nake so muyi" "Toh yanzu kuma? Gashi sauri nakeyi na kusa makara ko zaki bari sena dawo idan ba na sauri bane" ya fada yana qare mata kallo dan qarara ya hango ramar da tayi se dai ta qara haske da kyau. Yamutsa fuska tayi tana kallon gefe tace "Ni gidan mu nake so na tafi bani da lafiya ni kadai na san me yake damuna kar nazo na mutu a gidan nan babu wanda ya sani tunda ba'a damu dani ba" "Me hali baze chanza ba" Khalil ya fada a zuciyarsa yana maimaita kalamanta a ransa da sam babu ladabi ko tausasawa a cikinsu a fili kuwa ya gyara tsayuwa yace mata "Wa kika gayawa baki da lafiya kuma waye be damu dake ba?" "Kai mana, daga fadar gaskiya gaba daya ka dena kulani ka fita harkata a gidannan sena shafe kwanaki magana bata hadamu dakai ba, nidai na gaji wallahi gida zan tafi gara naje inda ake sona ba zan zauna a inda ake zaman gaba dani ba" ta fada cikin karyewar murya tana shirin sakar masa kuka. Tafiya yaci gaba dayi yana cewa "Idan izinina kike tambaya banyarda ba idan kuma kinga zaki yi gaban kanki ne to ki tabbata idan kika tafi bazan biyo bayanki ba" ya kunna motarsa kafin ya qarasa ya bude get ya fita da motar ya dawo ya rufe har sannan tana tsaye tana hawaye. Yana fita ta juya dakinta da gudu tana kuka, kaya ta shiga hadawa dan ita tafiya zatayi da gaske bazata zauna ba gara can a kirashi ya fadi abinda yake nufi da ita daya jingineta ita da babu a gidan matsayinsu daya. Khalil kuwa yana fita gefen hanya ya samu ya faka motarsa ya dora kansa akan sitiyari, Allah ya sani yana son Umaimah son da shi kansa besan iyakarsa ko a yanzu daya nesanta kansa da ita shi kadai yasan irin azabar kewarta da yakeyi. Dakyar yake iya bacci, ya tabbata ya fita shan wahalar wannan yanayin da suke ciki amma so yakeyi su dawo kan saiti suyi rayuwar aure kamar sauran ma'aurata cikin girmamawa da mutunta juna. Baze dauki salon data zo dashi ba na zama kamar wasu haduwar bariki ya zaman bata shayin ta zageshi kota gaya masa duk maganar data zo mata amma yaga alamar sam bata da niyyar gyarawa sema qara batawa da take so tayi, ba kuma yaso ace har ta kaisu gaban magabatansu yanaso su koyi sasanta duk wani sabani daya gifta a tsakanin mu to yaya zeyi? Ya tabbatar yanzu tunda ta quduri niyyar tafiya koda yace be yarda ba sedau wani ikon Allahn amma mawuyaci ne ya koma gidan ya tarar da ita Ji yakeyi kamar ya koma ya sauke nasa fushin ya lallabata amma yana tsoron abinda hakan ze haifar masa a gaba idan ta miqe akan sedai shi yabi ta ze sha wahala dan ba ita kadai ba hatta da yayan da zasu haifa a gaba se hakan ya shafi tarbiyyarsu, dole ya danne duk wani tasirin da take dashi a zuciyarsa ya kunna mota yaci gaba da tafiya amma ya qudurce idan ya dawo ya tarar da ita zero zaunarda ita ya nuna mata kuskurenta tunda ta kasa fahimta da kanta. Umaimah kuwa kaya ta shiga hadawa da gaske tana kuka, kiran wayarta da akayi ya dakatar da ita ta daga ganin Anty Hafsa ce take kira ta shaida mata zata zo gidan tana hanya. Jefa wayar tayi taci gaba da hada kaya gara ma tazo su tafi kawai ta huta da nemo Adaidaita. Tsaf ta cika akwatuna biyu da duk abinda tasan zata buqata ta kaisu palour ta ajiye, a gurguje ta watsa ruwa ta saka doguwar riga bata nemi abin kari bama taci a gida ta zauna a palour zaman jiran Anty Hafsa tana jin an buga Get kuwa ta fita da saurinta ta bude. "Wadannan akwatunan fa Umaimah ko balaguro zakuyi tunda daman ke ba'a sanin tafiyarku balle dawowa" Anty Hafsan ta fada tana kallon akwatunan data jera, kamar tana jira kuwa ta rushe mata da kuka tana cewa "Na gaji Anty gida zan tafi Khalil ya deba sona ya rigada ya samu abinda yake so ya hadani da kaya shine ze fara nuna mun halinsu na maza". "Subhanallahi me ya faru? Dama kina da wata matsala ne da kikayi shiru tuntuni baki fada ba har ta kai ga kice zaki koma gida" Anty Hafsa ta fada cikin tashin hankalin irin kukan da taga Umaiman tanayi. Dakyar ta tsagaita nan ta shiga labartawa Anty Hafsan abinda ya faru zuwansu Kaduna har zuwa yanda sukayi dashi yau da safen, ta rufe da cewa "Daga na nuna masa nasan abinda yakeyi naganshi da karuwa shikenan ya dauki gaba dani ya fita sabgata, ina tunanin ma idan ya fita can yawon biye biyensa yake tafiya babu abinda ya shafeshi dani bare yasan damuwata". "Ba shakka Umaimah duk inda ake neman yar bura uba mahaukaciya kin kai har kin wuce, aini wallahi be burgeni ba dabe dawo mana dake a kakkarye ba. Kamata yayi ace ya sauke miki kafada ya karya miki qafa daya sanda kika ce ya dakko karuwar su kwana tare. Banda ke bakida hankali baki san abinda yake miki ciwo ba ki kalli tsabar idon mijinki ki kirashi mazinaci koda ace da gaske ne ballantana tsabar hauka da baqin kishinki da kika dorawa kanki ne, anya kina tsoron gamuwarki da Allah Umaimah? Toh bari kiji tun kinada sauran lokaci ko tuba kibi Allah ki kuma nemi yafiyar sa. Islamiyyar da kikayi bata amfane ki da komai ba tunda baki koyo ilimin sanin darajar miji da yanda ake zaman aure ba, idan kuma baki tuba kinbi Allah ba zaki tashi a tutar babu, ki qare rayuwa bakiji dadin zaman aure ba dan babu dan iskan da ze zauna dake kina zaginsa yanda kika ga dama idan be ringa cin ubanki ba to kuwa zakiyi rayuwar qunci da baqin ciki kamar yanda kikeyi yanzu sannan kije lahira walakiri yaci ubanki ki tafi wuta ba fata nake miki ba. Allah ya taimakeki ya baki miji me sonki da yake ke ba yar arziqi bace ashe abin tsiyar da kike shuka masa kenan yana shanyewa ina ma ace banzo ba ki debi kayan nan kije gidan na tabbata dayau se anyi miki dakan hatsin matan qauye yanzun ma kuma daga nan gidan zani na zayyanewa Mama duk abinda ake ciki gara ta sani a san ta inda za'a taroki danna fuskanci baki da hankali ko kadan". Tas ta silleta tayi fada tayi masifa kafin ta dora da nasiha da lallashida bata dabarun yanda zata riqe mijinta bata hanyar hauka ko rashin hankalin data daukarwa kanta ba. Da kanta ta tayata suka gyara gidan tsaf dan shara tunda aka shiga wannan hali idan bata gaji da zaman tunani ba bi ba batayi, cikin kayayyakin gyaranta ta harhada mata wasu tasha tana cewa "Dan uban likitan da tace ki kwashi wata biyun idan ta kashe miki aure mijinta zata baki ki aura ko ke kuma ga sauna da yace ki koma dakinki kika kwashi kaya ziqau ziqau kika tafi Allah ya ganar dake dai Umaimah. Seda tayi mata lafiyayyen girki bayan data sakata tayi wanka ta sheqa kwalliya suka shirya komai tsaf sannan tace mata "Ki dauki waya ki kirashi yanzu kisan yanda zakiyi duk abinda yakeyi ya baro ya taho gidan nan, idan yazo saura ki sauka daga layin dana doraki, ki sauke kanki ki bashi haquri ki nuna masa kin gane kuskurenki ba zaki sake maimaitawa ba ba kuma wai ya zama iya fatar baki ba Aa har zuciyarki nake so ki yarda kinyi kuskure kuma kodan gaba ki kiyaye, ki sani duk abinda kika aikata masa na rashin kirki kanki kikayiwa saboda shi Allah babu ruwansa ze kamaki da laifin qin yiwa miji biyayya. Gara ace shi ya cuceki se Allah ya saka miki da ace ke ce kika cuce shi kikai kanki wuta a banza, kuma idan na koma zanyo miki aiken ingantattun magunguna dana samo a gurin *SUMAYYA'S HERBAL APHRODISIACS AND COLLECTION*, idan kika gwada magungunanta babu ke babu sake siyan duk wasu jigari jigarin magungunan mata da baki san dame aka hada su ba. Jikin Umaimah yayi laqwas, Anty Hafsa bata tafi ba seda ta kirashi a wayar tana numfashi kamar wadda ake yankawa wai cikinta, Khalil dake Tsakiyar aiki a wani Site babu shiri ya kamo hanya dan daman gaba dayan ranar tana maqale a ransa yana ta tunanin ta tafin ko tana nan. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 23 Cikin yan mintuna ya isa gidan a ransa yana ta taraddadin abinda zeje ya tarar, meya sameta? Shine tambayar da yake tayiwa kansa har ya qarasa qofar gidan ya kashe motar ya barta a waje tunda sake fita zasuyi ya kaita Asibiti. Turus yayi yana qarewa yar madaidaiciyar harabar gidan kallo, ko ina yayi qal hatta da interlocks din dake shimfid sunsha wanki da kallo daya zaka musu ka hango tas din da sukayi. Qara bude hanci yayi yana shaqar daddadan turaren wuta dana Airfreshner ga kuma sanyayyar iskar yamma se suka hadu suka bada wata Atmosphere me sanyi da sanyaya zuciya. Be qarasa suman tsaye ba seda ya shiga palour, tana zaune akan kujerar dake fuskantar qofar shigowa. Riga da skirt ne na wani Yellow Lace irin yellow nan me kamar butter da yayi bala'in karbar fatarta da bata da haske sosai ta kashe daurin gaban goshi irin yanda yake sonsa wani kallo ta watsa masa tana raurau da ido kamar me shirin yin kuka be san sanda ya dage zuciyarsa da hannu biyu ba ya lumshe ido saboda yanda kallon nata ya tasirance shi. Cikin wata irin tafiya taso babu inda baya motsawa a jikinta tana zuwa ta fada jikin Khalil daya zama mara amfani na wani lokaci ta sakar masa kukan zallar shagwaba da kissa. Fitinannan Qamshin ta ya kai masa ziyara, qafafunsa sunyi sanyin da bazasu iya daukarsu ba se yayi saurin dafe bango da hannu daya ya riqeta gam a jikinsa da daya hannun ya gagara ce mata komai se ajiyar zuciya yake saki kamar Jaririn daya kwana besha Nono ba. Qasa ta tafi zata tsugunna ya yi yunqurin tarota ta zame seda ta ajiye guiwoyinta a qasa ta dafa nasa da hannu biyu hawaye na bin fuskarta tace "Bazan iya cigaba da jure fushinka ba Khalil na tuba ka yafe min, nayi nadamar duk abinda na aikata maka a kuma shirye nake da karbar duk wani hukunci daga gareka amma banda na qaurace mun, Allah kadai yasan irin quncin dana shiga na rashinka. Muna rayuwa guri daya amma ka nesanta kanka dani baka san yanda nakeji ba Kuma Wallahi duk abinda ya faru sharrin shaidan ne yayi amfani da tarin sonka da kishinka da nakeyi ya makantar dani amma yanzu na fita daga cikin duhu na dawo haske, in sha Allahu bazan sake kwatanta makamancin abinda ya faru ba bazan sake ba, ka yafe mun kaji Ibbahna, mu koma rayuwar mu irin tada me cike da qauna da Aminci". Shiru yayi kawai yana kallonta, yanda take maganar har akan fuskarta yana iya karantar gaskiyar zuciyarta da kuma nadamar da tayi amma fa Umaimah ce, yanzu shi ai sedai ya bawa wani labarin halinta badai a bashi ba dukda haka yana fatan Allah yasa da gaske take ta gane gaskiya dan ya tabbatar da yafita Azabtuwa da wannan zaman da sukayi, kawai ya jure ne saboda ya nuna mata kuskurenta kuma Alhamdulillahi gashi nan yaci nasara amma dukda haka bazeyi saurin bada kai bori ya hau ba, dole ya sake shata mata wasu sharuddan in har Nadamar ta gaske ce kuma ta shirya suyi zaman lafiya zata bi. Hannu biyu ya saka ya dagota daga durqushen har sannan bata dena tsiyayar hawaye ba, cikin palour ya qarasa shiga ya zaunar dasu akan kujera daya ya kama hannayenta duka biyu yana fuskantarta, kallon cikin ido yayi mata Umaimah dake kallonsa itama tayi saurin sadda kanta qasa, cikin kasalalliyar murya wadda halin da yake ciki da kuma Dramar Umaimah suka haddasa masa yace mata "Look at me Umaimah, i want you to look in to my eyes while I'm talking. Bana so kice baki ji ba ko ki manta wani abu da zan fada". Hannunta ta saka ta share hawayenta kafin ta dago idanunta da suka canza kala saboda kuka ta kalle shi itama, a tare suka sauke ajiyar zuciya, ya matsa hannunta dake cikin nasa yace "Ina sonki Umaimah irin son da bazan iya misalta miki shiba amma a kullum halayyarki tana goge wani kaso daga cikin son da nake miki, Umaimah yazo Mana a cikin Hadisi Manzon Allah SAW yace 'Jublatul qulubi ala hubbi man ahsana ilaiha, wa bugudu man aasaha ialihi'. Ita zuciya da kike gani an halicceta akan son me kyautata mata haka kuma tana qin duk wanda yake munana mata ko dabba ki ka kalla yafi zuwa gurin wanda yake bashi abinci yake kyautata masa ballantana mutum. Ina tsoron kar wata rana a waye gari tarin soyayyar da nake yi miki ta shafe gaba daya saboda a kulle halayenki marasa kyau suna rinjayar na kirkin akan sikelina. Soyayya ita ce gadar da take kaiwa ga aure amma kyawawan dabi'u su suke zaunar dashi kuma girmamawa da mutunta juna dolene a cikin aure bawai zabi bane. Idan ma wasu kike kwaikwayo ko suke doraki akan hanyar da bazata bulle ba qarshe zakiyi batan baqatantan babu nan babu can dan haka tun wuri ki farka dan nasan wannan ba tarbiyyar gidan ku bace, ba itace tarbiyyar da nayi sha'awa har ta kaini ga auranki ba ce wata ce daban kika aro a gurin wadanda suke zama irin zaman bariki, mace ta zagi mijinta idan ta kama ya daketa kuma gobe suci gaba da zama har suyi dariya toh ni bazanyi irin wannan zaman dake ba, idan kuma shi kika zaba kamar yanda kika gani a yanzu na fara zan fita daga sabgarki in barmi kiyi rayuwarki ke kadai nima nayi tawa saboda hakan ze fi samar mun da zaman lafiya da kwanciyar hankali". Cikin nutsuwa da kwantar da murya yake maganarsa ta yanda duk taurin kan wanda akeyiwa seya saurara kafin ya gama kuwa jikin ta qaura yayi la'asar liqis ta sunkuyar da kai qasa kamar gaske tana matsar kwalla. Qara kama hannunta yayi yaci gaba da cewa "Dan Allah Umaimah ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya kamar kowanne ma'aurata. Wallahi banida burin sake sako wata mace a cikin rayuwata bayanke, inasonki, ina son komai naki yayi mun irin macen da nake so na qare rayuwata da ita idan kika cire Jidalinki shikadai ne fargabata a kullum na aure ki saboda ina sonki ina son zama dake amma sam kin gaza bani kwanciyar hankalin da nake kwadayi a tare dake. Idan naji dadinki na kwana daya se nayi fama da tashin hankalinki na sati a haka kike so na zauna dake ke kadai? Idan aka ci gaba a haka baki tunanin wata rana zan nemi inda zan ringa samun nutsuwa da kwanciyar hankalin dana rasa a tattare dake? Umaimah kwalliya, girki, gyaran gida ko gamsuwa a gado ba su kadai ne jindadin aure ba da akwai Nutsuwar zuciya wadda duk irin jin dadin da kake ciki idan baka da ita bazaka taba samun yanda kake so ba daga ni har ke abinda muka rasa kenan kuma kece sila. Kullum zuciyarki da tunaninki yana kan kar wata ta kulani karna kalli wata, idan akasi ya gifta wani abu ya faru kin ringa tashin hankali kenan kina bori duk akan me azatonki hakan ne ze hanani kula mata ko qara aure duk sanda naga dama? Toh ki sani wannan halin naki tamkar kina ingizani ne zuwa ga wasun kuma duk ranar da kika kaini qarshe sedai kiji ana cewa ki matsa za'a shigo da Amarya idan yaso ki kashe mu duka kamar yanda kika sha fada kinga munyi shahada ke kuma kinyi dakon zunubi dan babu wanda ze hanani qara aure idan na tashiyi hujjar tayar mun da hankali kadai da kikeyi kullum ta isheni in qara aure kuma kowa ze goyi bayana da babu wanda besan Halinki ba idan kika cire Hajiyata amma kowa yasan Umaimah danja ce duk abinda akace kinyi za'a yarda da wanda yafishi ma duk saboda me" Kuka ta fashe dashi me sauti tana kallonsa, idan yasan irin wutar da take ruruwa a zuciyarta da be fara kawo zancen qarin aure ko makamancinsa a hirar su ba, amma ya zatayi ko wutar zata cinyeta yau dole ta hadiye kodan ta samu su sasanta dan ita da kanta bangaren kwakwalwarta me hankali ya mata karatun ta nutsu kuma ta yarda da duk abinda yake fada za kuma ta zage dantse in Allah ya yarda kwanciyar hankali ya samu gurin zama a gidansu tunda dai yace tijararta bazata hana ya mata kishiya ba toh kuwa zaman lafiya ze hana. Cikin kuka tace masa "Duk naji na kuma karbi laifina ina roqonka daka yafe mun bana so Allah ya kamani da laifin bata maka rai" "Ni ban taba riqeki a zuciyata ba, a kullum ina miki addu'ar Allah ya shiryaki yasa ki gane abinda kikeyi ba daidai bane kuma duk abinda kikayi mun na yafe har wanda ma bakiyi ba kafin yazo na rigada nayi clearing nasu" ya fada yana dan murmushi da sake janyota jikinsa. "Nagode, kuma ka gaya mun duk abinda kake so na dena zan bari indai hakan ze saka ka huce kuma kayi farinciki" ta sake fada tana shigewa jikinta, seya dora bakinsa akan kunnenta ya sakar mata kiss me qara da seda ta zabura ta kalleshi tana bata fuska, shima bata fuskar yayi yace "Wannan Chatting din dayake dauke miki hankali bana sonsa, bance ki dena kwata kwata ba amma kisan yanda zaki raba lokacinki ya zamana kinada lokacina dana sauran ayyukan da suke a gabanki ba danna waya ba" "Se kuma me?" Ta fada tana kallonsa, ya daga kai kamar me tunani sannan yace "Shikenan". Wayarta ta janyo ta bude, Khalil ya tsaya yana kallonta ta shiga cikin WhatsApp kai tsaye tayi deleting account din kafin tayi uninstalling nasa gaba daya daga kan wayar ta miqa masa tana cewa "Gashinan na goge gaba daya ma saboda kar na barshi ya ringa dauke mun hankali" "Nifa bance ki goge ba, idan kuma ina so muyi video call in bana nan fa ko zaki turamun da pictures.." "Nidai bana so tunda dai baka sonsa, shikenan mun shirya ko?" ta fada cikin shawagwaba bata ida maganar ba Ya saka hannu biyu ya kama qugunta ya qara matsota jikinsa sosai kafin ya shiga aika mata da kiss cikin kwarewa, ya kwashe kusan minti goma yana kissing nata kafin ya saketa jikinta yayi mugun sanyi saboda wata fitinanniyar kewarsa data taso mata. "Yunwa nakeji, tunda na shigo nake jin qamshin abinci me kika dafa" Khalil ya fada yana janyewa daga jikinta kamar beyi komai ba dukda shikansa qarfin haline kawai ba amma ba qaramin ruwa ya kunnowa kansa ba, kuma yana gudun ciwon daya ji mata kwanaki ya warke koda saura. Kukan sangarta ta saka masa ta fada jikinsa tana qoqarin sake hade bakinsu ya riqeta yana cewa "No Umaimah bakida lafiya kuma Dr tace se kinyi two months kina hutuwa" ya fada harga zuciyarsa dagaske ya dauka se tayi wata biyun kamar yanda likita tace dan ya tsorata da hukuncin nasa ya kuma yi nadama da alqawarin baze sake hakke mata yana cikin fushi ba. Kamar zata shige masa ciki ta qanqameshi tana cewa "Ni na warke ka duba ma ka gani, please Ibbah i miss you badly" ta qarsa tana hade bakinsu ta shiga bashi haddar karatun daya dade yana dora mata "Innalillahi yarinyar nan zata kasheni" Khalil ya fada a zuciyarsa jin Umaiman tasa tana masa wasu abubuwa da ko a hasashe be taba zaton ta iya su ballantana tayi masa, ashedai ba Jidali kadai ta iya ba ita din ta kowanne fanni gwanace. Dakyar suka rabu shima seda sukaji an kwada kiran sallar Magriba a masallatai. Kallonta kawai yake yana sakin murmushi kamar wani wawa dan kuwa yau din ta shayar dashi mamaki ba kadan ba. Ita ya sakarwa filin tayi sukuwa son ranta soyayya iri iri babu wacce be gani ba seda komai ya lafa kuma ta juya ta hade da kujera yanda kasan wadda Siriki ya rutsa. "Wai dan Allah Babe course kika je kikayo ne ko yaya ni bangane wannan al'amari ba ya daliba take neman tafi Malamin hazaqa ne?" ya fada yana kama qugunta tareda leqa fuskarta data kife a kan kujera, seta zabura saboda yanda taji ruqon nasa har tsakiyar kanta ya kwanto ta jikinsa gaba daya yana shafata yace "Kidena zabura haka fa kina mantawa bake kadai bace yanzu ko?" Kwacewa tayi ta yayimi Rigar shaddar daya cire ta rufe jikinta, ta dai fi babu ta miqe tsaye Khalil kuwa qara kwanciya yayi yana qare mata kallo yanda Albarkatun jikinta suka qara cika taf gaba da bayan nan masha Allah a fuska ne kadai zaka ga ramar da tayi, tafiya tayi kamar zata kife yayi saurin ruqota ta sakar masa harara tana cewa "An sakawa mutane ido se sunje sun fadi" "Ya akayi kika san ana kallonki, daman baya tana da ido ne?" Ya fada yana mintsinin mazaunanta ta fada qara ta kai masa duka sallamar daya jiyo daga masallaci alamar an idar da sallah ta saka shi miqewa da sauri yana salati. "Kingani kin saka na rasa jam'i ko" Baki ta tura ta sake nada rigar a jikinta tana janta qasa dan tadan qara rufe mata jiki ta shige daki tabar Khalil na mata waqar sittin saba'in, idan yana wani shaqiyancin kawai mamaki yake bata dan kafin suyi aure tsaf in aka ce zeyi zata rantse baze iya ba saboda yanda yake shiru babu ruwansa. A dakinta tayi wanka ta gasa jikinta sosai da ruwan dumi, seda tayi sallar Ishah kafin ta shirya cikin wata Armless top da Three quater dan tun tana sallahr magriba taji fitar Khalil. Palour ta fito ya tattare komai ya gyara kayansu da pillows din da suka watsar, kan Dining ta wuce saboda yunwar data taso mata kamar zata fadi, ita nata kalar laulayin kenan ci kamar gara se kuma wani lokacin ta rasa me yake mata dadi bayan wannan babu wani abu da yake damunta. Abincin ta zuba soyayar shinkafa data ji niqaqqen nama ta janyo kwanon da ta zuba Salad ta tsiyaya dressing din akai ta juya kafin ta dibi wanda ze isheta ta rufe sauran dan tasan duk inda yake shima yana hanyar gida, tana kai lomar farko taji an bude Get, seta miqe ta dauki Qaramin mayafin data ajiye akan kujera ta yane kanta ta fita har ya shigo da mota ta qarasa ta kulle Get din tana masa sannu da zuwa. "Yawwa Malama Umaimah sannunki" ya fada yana mata dariyar data rasa ta mecece, "Yau kuma Malama na zama" ta mayar masa sanda suka shiga cikin palour, Jakar Laptop dinsa daya dakko ya miqa mata yana cewa "Yau ai ko makaranta na kiraki kin wuce nan hajjaju, bari nayi sauri naci abinci muje a doramun sabon darasi dan ina buqatar qarin ilimi sosai nima" ya qarasa yana kashe mata ido daya, se sannan ta fuskanci inda ya dosa seta juya kawai ta wuce dakinsa a ranta tana mamakin Khalil, ahidai bashi da damuwa sabgar gabansa kawai yake ji fa ko kunyarta baya ji yake wannan magana toh Allah ya shirya. Tare suka ci abincinsu cikin nutsuwa suna yan hiraraki, babu abinda yakai zaman lafiya dadi a rayuwa, basu ba hatta da gidan kansa yasan an samu daidaito a cikinsa saboda yanda suka koma sabgoginsu yanda suka saba. Bayan sun gama cin abincin suka buga Tv game seda Abin ya kusa zama rigima dan har ta fara kukan wai wayo yake mata yana mata Game over kafin ya kashe suka kwanta bayan an qara dora karatu sadara biyu. Kwanakin da suka biyo baya kam se sambarka dan zaman lafiya dai ya samu guri yayi daram a gidan Khalil da Umaimah. Tattalin junansu sukeyi, idan ya fita har ya dawo suna maqale a waya. Wanka da kwalliya kuwa se wanda ta manta dan sosai take tashin kan Khalil da gayu na safe kafin ya fita daban na dare idan ya dawo daban ga karatun makarantar dare da take dora masa babu sassauci gaba daya ta rigada ta shagwaba Khalil din nata ji yake nan duniya kamar babu Namijin da ya kaishi sa'ar Mata itama kuma hakan take a bangarenta dan kuwa Khalil ya isa Namijin kere Sa'a. Idan yayi kwalliya ze fita aiki ji takeyi kamar ta saka masa Niqab saboda kishinsa da takeyi na nan babu inda yaje a zuciyarta tana dai qoqari matuqa gurin ganin ta kawar da idonta akan duk abinda ze kawo tashin hankali a tsakaninsu. Tsakaninta da maqotanta kuwa sedai idan sa'a ta gifta ta fita unguwa ko tayi baqi ta rakasu su hadu su gaisa dan ko barkar Rufaida bata samu ta shiga ba kuma tana da yaqinin yanzu tayi Arba'in koma fiye da haka dukda taji a bakin Khalil cewar bata nan, Mijin ze tafi wani aiki Kudu yace ta koma gida kafin ya dawo wai a Masallaci suka hadu yake gaya masa shiyasa ta bari se taji ta dawo zata shiga. Wata safiyar Talata bayan Khalil ya gama shirinsa ze fita take ce masa tana so taje kitso. "Wayon kije gida ne kina dai ji wancan zuwan da mukayi Mama tace kar ta sake ganin qafarki a gida se an nemeki shine ko sati ba'ayi ba zakice zaki kitso" Khalil dake daura agogo ya fada yana kallon fuskarta data fara canzawa saboda cikin daya bi jikinta. A lissafi wata na biyar yake yanzu amma sam babu alamar sa sedai qibar datayi ta ko ina har fuskar Allah ya taimaketa dai dogon hancin be kai ga bajewa ba. "Dadin Iyaye da yawa kenan ai kaga iata Mama korata takeyi idan naje ita kuwa Hajiyata nasan bataqi kullum naje na wuni a gidan ba kai kuma saboda jelousy baka so ka kaini" ta bashi amsa tana masa fari da ido. "Ke dince ai na rasa me kikewa Hajiya haka kullum bata da zance se naki komai ta samu tace a kawo miki shiyasa idan banyi dagaske ba kwacemun ita zakiyi" "Toh ai kaima ka kwacemun Mamata ka shiga tsakaninmu,  ina murna Nuratu ta matsa zan kwato fada ta se ga sabon snatcher yanzu magana indai bakai ka fada ba komai na gaya mata bata yarda, kaga shikenan munyi 1-1, na kwace Hajiya ka kwace Mama" ta bashi amsa tana dariya, "Yawwa na tuna yau irin Cream cheese maccaroni nan ta ranar zakiyi mun" Khalil ya fada, seta dan yamutsa fuska, shidai yana son shegun continental dishes din nan da ba dadi ne dasu ba, be kuma fahimci duk randa yaga ireirensu toh Maman Asad ta kawo mata ziyara ita ce gwanar girki ita takeyi mata amma dai tana ga dole ta ajiye quiya ta koya saboda ranar yar qure tunda gashi an fara da kansa yace tayi masa. "Idan bazaki iya ba ki barshi naga kina ta bata fuska a sharrinki yanzu se kice ze saka ki Amai" ya fada yana daga hannu sama fuskarsa da murmushi dan sabon salon iyashegen data samo kenan, Allah ya yaye mata be dora mata ciki me laulayi ba amma se kalato shi takeyi. Idan batayi niyya ba shara se tace idan tayi Amai zata sakat sedai shi ya share balle girki yanzu kullum suna kan hanyar zuwa gidan Hajiya cin abincin dare dan tunda akaje Restaurant ranar nan wata classy babe ta biyo Khalil akan ya bata number sa aka kusa kwasar yan kallo Allah dai ya taqaita shikenan ya yaye wa kansa fita da ita. Yaje shikadai din ma tace bata yarda ba dan bata san me zeje yayi ba yanzu suda abincin waje sedai suyo order a musu delivery toh ya za'ayi zaman lafiya ai yafi zama dan sarki tubda outing din ba dole bane. "Anjima zan fito na duba, akwai yaran da sukeyin ball a qofar gidan nan su Aliyu zan tambaye su koda gidan kitso kusa se naje kan ya dameni da yawa" ta sake fada sanda ta rakoshi bakin mota "Yanda kasan wata me gashi bayan qwaiqwaido ce zaki damu mutane da wani kitso ki bari idan na dawo sena yi miki da kaina" Khalil ya tsokaneta, seta zumbura baki ya zuro kansa ta glass yayi pecking bakin nata kafin yaja mota tana daga masa hannu ya fice daga gidan. Tana qoqarin maida Get din ta hango Aliyu daya daga cikin yaran dake wasa a qofar gidan ita bata ma san dan wane gida bane tana dai aikensu wani lokacin ko idan tayi ragowar abinci ko abinda ta kasaci na kayan dadi ta fita ta raba musu. Kiransa tayi ya tawo da saurinsa yana murna dan yasan bata kiran banza ko aikene idan ka dawo seta baka na alawa. "Anty ina kwana" ya fada yana dan rusunawa, seta amsa masa tace "Lafiya lau Aliyu, baka je makaranta ba ne yau na ganka da safe?" "Ai babu makaranta yau public holiday akeyi" ya bata amsa seta daga kai tace "Oh, yawwa ni a unguwar nan a ina ake kitso ne Ali?" "Anayi a gidan mu Mamanmuce takeyi" ya bata amsa yana nuno mata qofar gidansu da yake kallon nata ta dayan bangaren. "Yawwa jeka ka tambayomin naji yaushe zanje ayimun kaji" ta fada se ya juya da saurinsa ita kuma ta koma cikin gida, kayan wanke wanke ta fito dasu tsakar gidan bakin famfo ta shiga wanke wa, bata dade da farawa ba ta jiyo bugun qofa da surutunsu seta dauraye hannunta taje ta bude shida Hibban ne yaron Gidan dake jikin nata shi ta gane fuskarsa dan kamar sa daya da Mamansa da suka shigo mata tareda Rufaida. "Wai tace ko yanzu ma kizo idan bakya komai" Aliyun ya fada mata saqon Mamansa. "Toh shikenan, bari na qarasa wanke wanke sena zo" "Kawo nayi miki Anty" Hibban din ya fada yana murmushi dan irin masu yawan Fara"ar nan ne, Murmushin ta mayar masa tace "Aa nagode, gadai tsintsiya nan ku share mun tsakar gidan kafin na gama" suka Amsa da toh taci gaba da wanke wanken suna mata sharar suna yar hira har suka gama. Ciki ta shiga ta kira Khalil a waya ta shaida masa zata shiga gidan su Aliyun ayi mata kitson yace ta duba rigar daya cire jiya da akwai kudi ta dauki dubu biyu tayi masa godiya kafin ta gyara fuskarta ta zura dogon Hijabinta ta hada kayan kitson a qaramar jaka ta fita. Seda ta daukar musu Apple daddaya da chocolate ta basu sunata godiya kafin suka rakata gidansu Aliyu. Da sallama ta shiga wata mata baga mara jiki na zaune a tsakar gidan tana hura gawayi a Dutsen gugar charcoal ta amsa mata fuskarta da fara'a tana mata sannu da zuwa. A mutunce suka gaisa Umaimah na satar kallon gidan da a kallo daya zaka fahimci cewa mazauna cikinsa na fuskantar matsin rayuwa dan dukda cewa ginin zamani ne amma ya tsufa alamar rashin gyara a haka ma da alama dan mutanen gidan nada tsafta saboda a sannan ma tsakar gidan dukda qasace amma qal yake babu ko tsinken datti an share ko ina. "Kitso nazo, Aliyu ya gaya miki ko" Umaimah ta sakw fada ganin matar tayi shiru bayan da suka gama gaisawa, se matar ta nuna mata dakin dake fuskantar su tace "Tana ciki Maman Aliyun ki qarasa" daidai nan matar dakin tayi fit ta fito tana gyara daurin zaninta dake neman faduwa. Wata harara ta makawa Abokiyar zaman nata se kuma ta saki murmushi ganin idon Umaimah akanta ta fara cewa "Au Amarya ashe kece bismillah qaraso ai dangidan naki yace zakizo da fita zanyi ma na fasa" Murmushin yaqe Umaiman ta sakar mata itama dan sam matar bata mata ba, ta tuna fuskarta itace Maman Hauwa wadda suka shiga tareda budurwar yarta da tana Amarya. Cikin palour suka shiga Maman Hauwa nata faman jera mata sannu da zuwa Umaimah ta tsaya tana kallon kujerun palour tunanin inda zata zauna takeyi dan sunci uwarsu da datti ga wani zarni zarni na tashi kamar anyi fitsari a palour a haka har turaren tsinke taga an kunna. "Zauna mana Amarya, kin tsaya" Maman Hauwa ta sake fada baki a washe, Umaimah ta dosana mazaunanta akan kujerar data ga nada dan dama dama a ranta tunanin yanda zasuyi kitso a wannan dakin takeyi dan tuni cikinta ma ya fara hautsina mata. "Ina kwana?" Maman Hauwa ta fada, seta dawo daga kalle kallen da take ta amsa mata suka gaisa. "Ai muna ta ganin abin arziqi komai Aliyu ya shigo dashi yace Anty ce ta bashi ko mijin Anty, nace ita Antyn taka ce bame son mutane ba aida mun shiga munyi godiya" Maman Hauwan ta sake sako magana, se Umaimah ta saki murmushi bata ce komai ba Maman Hauwa taci gaba da cewa "Eh mana, tunda muka shigo muna ta zuba ido ko zaki shishshigar mana shiru. Lokacin haihuwar Rufaida ma matan layi duk an hadu ana ta tambayar ina Amarya a sannan yara sukace kamar bakya nan kai har ma aka gaji da tambaya kowa yace baki shigar masa ba dake mun saba nan idan aka kawo sabon zuwa zakiga duk za'a ringa haduwa ana gaggaisawa" "Allah sarki" kadai Umaimah tace seta dakko wayarta ta shiga dannanwa dolen Maman Hauwa tayi shiru. Kusan minti uku a tsakani tana qarewa Umaimah data hade fuska tana danna waya kallo se tace "Bismillah toh kinzo da kibiya ko na dakko?" "Aa nazo da ita" Umaimah ta fada ta bude jakar ta dakko Comb, kibiya da Mai. Tana shirin zame Hijabinta aka dauke wuta, Maman Hauwa tace "Oh sunyi halin nasu sedai mu koma tsakar gida dan yanzu zakiji dakin ya gume da zafi ga shi daman yara sunyi fitsari a gun" Hamdala Umaimah tayi a zuciyarta ta tattara kayan tayi waje, ita badaban bama gudu zatayi amma yata iya tubda tazo zata daure amma dan ba qara. A tsakar gidan suka zauna kitson sunayi dayar matar nata gugar kaya ta gama ta shiga hidimar girki Maman Hauwa nayiwa Umaimah hira ita dai sedai ta amsa da Eh ko Aa dan sam ba dadin hirar takeji ba gashi ta debar mata kitson qanana dan ma tana da sauri nan da nan zuwa sha biyu se gashi sun gama zuwa sannan gidan ya fara cika da Mata wasu yan kitso wasu kuma kawai hirarsu ce ta shigar dasu harda masu kai zubin Adashi dan taga duk wadda ta shiga zata bawa Maman Hauwa dubu daya ko dari biyar ita kuma tasa yara su rubuta a littafi duk wadda ta shigo kuna se an mata bayanin Amaryar can gidan ce. Dubu daya ta bata kudin kitson dan yayi kyau sosai ta kuwa ringa godiya kamar zata durqusa mata. Tana shirin fita daya matar ta fito daga kitchen tana murmushi tace "Har kun gama kenan sannunku" Umaimah ta amsa mata da murmushi itama dan jininta yafi haduwa da ita sama dana me kitson, bata damu da hararar da Maman Hauwa da sauran dake zaune ba ta sake cewa Umaiman "Ga Abinci ya kusa sauka bazaki tsaya kici ba Alalen gwangwani ne abin marmari" "Toh uwar kinibibi gurinki tazo ko yaya da zaki tsareta da surutun banza ko tace miki mayunwaciyace ita duj inda taje se taci Abinci" Maman Hauwa ta hayayyaqowa matar sauran matan dake zaune suka hau qunqunin wai ta fiya cusa kai daga ganin mace zata fara mata shishshigi, baze wuce wanki da guga zata ce ta ringa kawo mata ba kuma ba samu zatayi ba dan duk dan dakin Maman Hauwa bazeyi hulda da Ramatu ba. "Idan kin gama a bawa Aliyu ya kawo mun toh" Umaimah ta fada kafin tayi musu sallama tayi ficewarta a ranta tana mamakin wadannan mata da suka taru, a haka dai gasu kamar wayayyu ashe duk taron marasa sanin ciwon kai ne. To in banda rashin sanin ciwon kai qarfe sha biyun rana ki kullo gidan ki lokacin da kowacce Mace take qoqarin dora abincin rana ki tafi yawon daukar magana wani gidan toh Allah ya kyauta. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 24 Umaimah na zuwa qofar gida wayarta dake cikin jaka ta hau qara, seda ta zarota sannan ta bude qofar ta shiga, Khalil ne ya ke kira ta daga da sallama tana narke masa muryar shagwaba. "Me kuma ya faru?" Ya tambayeta cikin rarrashi, seta narke fuska kamar tana gabansa tace "Na gaji da zama kitson me yawa tayi mun duk yanzu bayana ciwo yakeyi". "Ayya sorry Babe idan na dawo zan miki Massaging bayan kinji, na kiraki da zu Hajiya ma tace ta kira baki amsa ba" "Lah wayar tana jaka se yanzu na dawo banma duba taba kiranka ya sake shigowa bari toh na kira Hajiyan sena sake kiranka" ta fada tana shirin kashe kiran ya dakatar da ita da cewa "Base kin kirata ba daman su Habiba ne zasu zo da yaran Kawu Najib shine zata sanar miki" "Ohk to shikenan se sunzo"  ta bashi Amsa daga nan suka yi sallama ta kashe wayar. Azahar tayi dan haka ta daura Alwala tayi sallah a ranta tana tunanin me zata dafawa baqin nata dukda bata san manya ne ko yara ba dab Kawu Najib din kansa sunansa kadai ta sani, tunanin ta dora musu dafa dukan shinkafa da pepper chicken tayi, seta miqe ta shiga kitchen ta dakko kaza a Freezer ta gyarata tsaf ta hada kayan qamshi dasu maggi tayi marinating nata ta mayar cikin fridge dan ta tsumu dan ba tafasata zatayi ba. Bazata dora abincin ba se sunzo dan kwanaki kusan sau biyu ta shiryi yin baqi se ta gama girki tsaf suqi zuwa sedai ta bayar kota aika dashi gidansu kona Hajiya shiyasa ta yanke shawarar dena yin girki idan zatayi baqi se sunzo, sedai ta tanadar musu qananan abubuwa da zasu dan taba kafin ta gama. Daki ta koma ta miqe akan doguwar kujera kafin kace me bacci yayi awan gaba da ita can cikin baccin qarar wayarta data ajiye saman kanta ta fara qara, a firgice ta farka tana zare ido, ta daga wayar daga dayan bangaren Khalil yace "Babe ina kika shiga ko wanka kikeyi? Gasu can a waje sunata bugu baki jiba". Cikin muryarta da tayi qasa saboda baccin da yazo mata me nauyi tace "Waifa dan kwanciya nayi na huta shine bacci ya kwasheni" "Ai ke dai yanzu kin zama kasa is a sace ki ma kina bacci baki sani ba" Khalil ya tsokaneta seta mayar masa sa cewa "Naji din, idan zaka dawo ka taho mun da rake" "An gama, jeki bude musu kinga ana rana suna tsaye a ciki" sukayi sallama ta miqe. Seda ta wanke fuskarta ta gyara daurin dankwalinta dan bata san su waye ba karsu rainata kafin ta yafa mayafinta ta fita, tana budewa Habiba qanwar Khalil na tsaye da dutse a hannunta se wasu guda biyu da bata san fuskarsu ba Habiban ta saki murmushu tace "Yawwa Anty Umaimahtundazu muke bugu seda muka kira Yaya yace qila bakya nan ba bari ya kiraki" Habiban ta fada da murmushi se Umaimah ta mayar mata da martanin murmushin ta qarasa ta bude musu qofar tana cewa "Kitso na shiga can gidan ai ba nisa nayi bama dana dawo kuma bacci ya daukeni shiyasa banji bugun naku ba bismillah ku shigo" tayi ciki suka rufa mata baya. A mutunce suka gaisa tana binsu sauran biyun da kallo qasa qasa musamman farar ciki da se wani yatsina take tana qarewa Palour kallo seta tashi ta kawo musu ruwa da lemo, tana da sauran Samosa danya a Freezer ta soya ta hado musu da ita ta zauna tana cewa Solar taje ta kunno saboda an dauke wuta ta kunna Musu Tv ta miqawa Habiba remote tana cewa "Bari na dora abinci Habiba ku fara da wannan, sedai baki gaya mun su waye baqin nawa ba" "Lah na manta ban miki bayanin su ba, wannan Yaya Shafa'atu ce yar gidan Yayan Hajiya da akayi bikinta kwanaki kin tunata? Wannan kuma Yaya Lubna qanwarta ce" Habiba ta fada bayan data Ajiye kofin da tasha ruwa. "Ayya Amarya sannu ai munso zuwa Allah beyi ba" Umaimah ta fada tana fadada fara'arta, Shafa'atu tayi mata murmushi tace "Babu komai ai gashi yanzu mu munzo" se Umaiman ta miqe tana cewa "Kusha ruwa bari na dora abincin rana tana qarayi"  se Habiba tabi bayanta tana cewa "Muje na tayaki Anty". Tare suka shiga kitchen din ta bawa Habiba gyaran Attaruhu da Albasa ita kuma ta fito da Kazar data saka fridge ta shiga ta dora mai. "Ita dayar bata da aure ne?" Umaimah ta jefawa Habiba dake yanka Albasa tambayar se tayi shiru dan bata tsammaci da ita take ba, seda Umaiman ta sake maimaita mata kafin tace "Wa? Wai Yaya Lubna? Bata da aure ta tsaya ruwan ido dan da tare zaayi bikinsu da Yaya Shafa'atu aka fasa. Itafa nan a dole da Yaya take so, idan kinga kukan data sha lokacin bikinku se kinci dariya bafa ta zo ba ko yanzu dakyar Hajiya ta sakata ta biyo mu" Habiba ta jerowa mata bayani. Sakare tayi tana jnta, zafin da taji ya ratsa mata hannu har zuwa cikin kwakwalwarta ya sakata watsar da robar data zuba naman kazar da zata soya. Sam ta manta da ta dora mai tana shirin zubawa ne take tambayar Habiban ta tsoma hannunta bata sani ba. Da sauri Habiba ta taso ta shiga yi mata sannu da qoqarin riqe hannun da Umaimah keta faman yarfewa saboda Azabar radadi. "Sannu Anty, kawo a zuba ruwan sanyi Allah yasa karta tashi" Habiba datayi saurin dakko ruwan qanqara ta sakr fada. Se Umaimah ta miqa mata hannun tana sakin kuka kamar wata yar yarinya  kukan baqin ciki biyu. Na farko ga radadin zahiri na qonewar da tayi ga radadin zuciya najin budurwar Mijinta ce tazo mata gida, ai kuwa setaci ubanta seta gaya mata dalilin daya kawota da har ta jawo mata guzurin qonewa, sannan shima ze dawo ya sameta, wato saboda budurwarsa nae har yake cewa taje ta bude suna tsaye a rana ko Habiba na gama zuba mata ruwan ta fice daga kitchen din dan bata ga ubanda zata girkawa abinci ba kuma, dakinta ta shige Habiba na biye da ita fuskarta dauke da damuwa tace "Anty kona kira yaya na gaya masa?" Kallon hannun Umaimah tayi, dukda tana jin radadi a saman yan yatsunta da sukayi jaa amma bata zaton qunar tayi munin da se anje Asibiti musamman da an zuba ruwan sanyi ta tabbatar ze taimaka gurin hana ta tashi seta girgizawa Habiban kai tace "Aa karki kirashi, kije ki fara girkin ina zuwa" se Habiba ta juya tana qarayi mata sannu ta fita. Shafa'atu ke tambayarta lafiya ta gaya mata Umaiman ce ta qone seta miqe tana cewa "subhanallahi muje na gani amma bada yawa bane ko?" "Eh en yatsuntane suka shiga cikin Mai Allah yasa beyi dai zafi sosai ba" tayi gaba ta kwakwasa qofar dakin Umaimah data kwanta shiru zuciyarta na suya, a fusace ta miqe ta bude qofar, suka shiga Shafa'atun ta shigayi mata sannu tana tambayarta ko zasuje Chemist tunda taga wani a kan layin nasu. "Babu komai fa ai Man beyi zafi sosai ba kuma an zuba ruwan sanyi na kuma tofa Addu'a daman yanzu zan fito na qarasa girkin" Umaimah ta fada tana qaqalo fara'ar dole se Shafa'atu ta tareta da cewa "Wane irin girki kuma ga Habiba da Lubna nan s su qara sa idan da wani abinda za'a miki ma duk se muyi kafin mu tafi ki zauna ki huta". Kamar tace wace shegiyar Lubnan ce zata shigar mata kitchen sedai ta danne ta qaqalo murmushi tace "Aa wallahi zan iya ai ya dena radadi hannun ya za'ayi na saka baqina aiki"  ta shiga qoqarin fita daga dakin suka bita a baya Shafa'atun na cewa "Haba Anty Umainah ai wallahi indai mu zaki dafawa bazakiyi ba gara mu zauna da yunwa idan bazaki barsu suyi ba in kuma na Yaya ne ki gaya masa kawai yayiwo take away ko ya karbo a gidan Hajiya tunda nasan bazeci girkin su ba" "Kamar ya baze ci girkin mu ba, me kike nufi? Idan da Allah yayi naga girkin wa ze ringaci?" Lubna da bata saka musu baki ba tuntuni ta fada a tsiwace tana kallon Yayarta. Se Umaimah ta zuba mata ido kawai, badan tana tsoron hukuncin da Khalil ze sake dauka akanta ba da babu abinda ze hanata nadawa wannan yar iskar duka a cikin gidan. Ita mamakin kanta ma take yau da har ta iya tsayawa inuwa daya da yarinyar da ake iqirarin budurwar Mijinta ce koda yake gashi ma ta tabbatar mata ta fada da bakinta. Tanajin Shafa'atun ta rufeta da fadan bata da kunya ne waye sa'anta a cikinsu Lubna data dauke kai ta harde a kujerar Umaimah ko a jikinta tana danna waya har yayar ta gaji tayi shiru se Umaimah ta saki murmushin takaici tace "Ki barta ba laifinta bane kinsan quruciya akace dangin hauka gaskiyarki kuma Habibi bazeci jagwalgwalon yara ba sedai su dafa abinsu suci, Habiba kuje Jellop din shinkafa za'ayi se a soya Kazar da akwai ruwan zobo a cikin Fridge se ku hada" ta qarasa tana zama akan Threesitter irin zaman gadarar nan na me abu da abunsa idonta na kan Lubna aika mata da wani mugun kallo daya sakata shan jinin jikinta kuma Umaiman tayi mata kwarjini seta miqe tana zumbura baki tabi bayan Habiba data fice daga palour. "Kiyi haquri sam Lubna bata da kunya wallahi" Shafa'atu ta fada tana zama itama se Umaimah ta tareta da cewa "Haba wani haquri kuma quruciyace take damunta muma duk muyi a lokacinmu ai wata rana ai bazatayi ba, naga alamar kishi takeyi dani nayi mata kwacen saurayi ko" ta qarasa tana yar dariyar da duk me fahimta ze gane bata dadi bace, yaqe ne kawai Gyara zama Shafa'atu tayi tana dariya itama tace "Tab jifa wata magana kema Anty Umaimah yanzu idan aka ce miki Yaya Khalil ze kula wannan yarinyar seki yarda ai ni inaga magana ma me tsaho bata taba shiga tsakaninsu ba saboda rawar kanta shi kuma kinsan baya shiri da marasa ji, itace dai take haukanta wai sonsa takeyi amma ai bata taba gigin fada a gabansa ba se mu data raina ta ringa wa hauka da Drama lokacin bikinku, ai abun ma ba gaske bane ba kuma me yuwuwa bane shirmenta ne kawai takeyi" "Uhm Allah sarki" Umaimah ta fada tana shafa yatsunta da har sannan suna mata zafi, hira suka shigayi kadan kadan dan rabin hankalinta naga tausar zuciyarta karta botsare ta sakata yin abin kunya dan dagaske ji tajeyi kamar take kitchen din ta watsawa yar banza man da ta jiyo suna soya kaza idan yaso taga da bakinda zata sake yi mata rashin kunya har tace da Mijinta ne ze aureta. Acan kitchen kuwa Habiba data gama kwashe Kaza daga Mai ta kashe Gas din ta bude Tukunyar shinkafar ta juya ta qara tabbatar da komai yayi kafun ta rufe ta juya kalli Lubna da tunda suka shiga kitchen din ta samu kujera ta zauna tana danna waya bata tayata da ko tsinke ba, cikin bacin rai tace "Wai Yaya Lubna me yasa kike haka yanzu saboda Allah kizo har gidan mata ki mata rashin kunya dan kinga tana da haquri wallahi idan wata ce nasan seta kwakwkwada miki mari sedai duk abinda za'ayi ayi kuma yanzun ma idan muka koma sena gayawa Hajiya wallahi" "Karki kuskura kiyi mun rashin kunya idan bata mare ni ba ni sena mareki a nan banza da tafi son bare akan yar uwarta ta jini. Ni wallahi ma sena raina ta na raina ajin yaya Khalil, ace akan wannan dusar ne duk ya tsallake yammata irin mu ai kuwa ya fado qasa" "Tab wayaga daskindaridi, wai ke nan kina wa kanki kallon wata hadaddiya ne ko kyakykyawa?" Habiba ta fada tana qunshe dariya kafin taci gaba da cewa "Ai wallahi idan da Anty Umaimah a guri ko a me goge goge bazakiyi daraja ba, fari ne fa kike taqama dashi shima Allah ne ya taimake ki na rantse da a baqa kika zo se an hada da roqon Allah zaki samu shiga koda yake da farin da komai ma gashi nan har yanzu se a slow, ni wallahi banma ci dariya ba Yaya Lubna se jiya da kika cire wadannan sosunan da kike sakawa Ruler sunan wata aba nace na godewa Allah da Hajiya kullum take jajanta sirantata ashe akwai wanda nafi qiba" Habiba da takai baqin qofa ta qarasa fada Kukan kura Lubna tayi ta kai mata cafka ta goce suka fita tsakar gidan kafin kace me sun kaure da dambe fuskarta tayi jaa saboda bacin ran wannan cin mutunchi da Habiba tayi mata. "Kaikai meye haka, baku da hankali ne?" Shafa'atu ta fada tana qoqarin raba su dan daga ciki suka jiyo hargagin Lubnan tana zagin Habiba, qin rabuwa sukayi suka ci gaba da casuwa dan dukda Lubna ta bawa Habiba kusan shekara uku a qirar jiki kusan daya suke koma Habiban ta fita kwari dan haka qarfi yazo daya kowa ta kasa kada yar uwarta. Umaimah na tsaye akan barander ta harde hannu tana kallonsu kawai, Addu'a take Allah yasa Habiba ta damfarata da qasa dan da alama tana dab da samun nasara akanta dan ta fi Lubna dabarun damben tana kallon shafa'atu nata qoqarin rabasu suka maujeta taja gefe tana sosa inda aka daketa tana zaginsu, Allah ne ya bawa Lubna Sa'a ta tade Habiba ta fadi a qasa ta haye ruwan cikinta tana sakar mata blows a fuska bata ankara ba se ji taji an kwasheta da marin daya gigita mata kwakwalwa kafin taji an watsar da ita gefe ta qume qum da Abin flower. Daga Habiba Umaimah data zazzabgawa Lubna mari da biyu tayi tana kallon Lubnan tace "Saboda kin zama babbar banza zaki haye kanta kina duka se kin mata lahani?" "Wallahi bazan yarda ba tunda kika mareni" Lubna ta fada cikin kuka tana miqewa Shafa'atu ta tareta tana kai mata wani marin ta goce tana cewa "Wallahi bazan yarda ba haka kawai me nayi mata da zata mareni sena rama duk abinda za'ayi ayi" ta nufo Umaimah data tsaya tana jiran isowarta, dama ta samu seta nadawa yarinyar nan dukan mutuwa yau da dalili Lubna na zuwa kuwa ta cakumi wuyan Umaimah duk yanda Shafa'atu take janta tana zaginta akan ta bari ina se zare ido take tana kallon Umaimah da itama take kallonta. "Sake ni" Umaiman ta fada cikin sigar umarni se kuwa Lubna tayi caraf tace "Bazan sake ki ba se mun kece raini yau ko ni koke a gidan nan, kin kwacemun saurayi sannan ki Mareni duk kici banza wallahi bazan yarda ba" Lubna ta fada yana kiciniyar ture Umaiman dako gezau batayi ba, kalmar saurayinta data kira Khalil da ita ta sake zabura ta cikin shammata ta kwashi Lubnan ta watsar. Dukan ya da Uwa tayi mata daga Shafa'atu har Habiba babu wanda yakai mata ceto dan ita Habiba kan girkinta da har ya fara kamawa ta koma ta shiga hada Salad ranta fes yau an samu maganin rashin mutunchin Lubna daman ta addabi kowa. Ihu da kururuwa ta ringayi tun tana zagin Umaimah harta dawo bata haquru da roqon ta kyaleta bazata kuma ba dan ba dukan wasa Umaimah take mata ba, duka ne irin na wanda yake amayar da fushi seda tayi mata lilis suna jin maqota da suka jiyo ihun Lubnan suna buga qofa da roqon azo a bud dan su a zaton su ma matar gidan ce wani abun yake samunta amma basu bude ba, seda ta gaji dan kanta sannan ta qyaleta ta wuce ciki abinta ranta fes tunda yau ta samu damar lallasa daya daga cikin masu kula mata miji. "Allah nagode maka daman ai idan junin mutum rashin mutunchi da tijara wata rana ze hadu da daidai shi yayi maganinsa kingani yau duk tijarar taki da rashin kunyar da kike taqama dasu kin samu me saita miki zama kai amma Anty Umaimah nagode miki daga yanzu ma duk idan ta Sam yi mana iskanci wallahi nan zamu kawota ki saita mata zama" Shafa'atu ta fada tana kallon qanwar tata dake juye juyen ciwon jikin da Umaimah ta tara mata. Shiru Umaimah tayi tana sauraren maganar Shafa'atun, se taji tamkar tilawar abinda kullum yan gidansu suke fada akanta na Allah ya hadata da daidai ita ne amma ita kam bata hasaso wannan ranar da za'ace ta gamu da wadda ta fita jidali, idan har aka ganta a qasa to ita taso yin badda bani amma badan an kada ita ba. Daga wannan duka dai Lubna ta sulale ta bar gidan ba tareda ta yiwa kowa sallama ba. Alwashi kam tasha shi kala kala se dai muce Allah bada sa'a. Shafa'atu da Habiba kuwa a gidan suka wuni har qurin qarfe hudu da kusan rabi sannan Khalil ya dawo. Shafa'atu da Habiba suka gaishe shi ya amsa babu yabo babu fallasa yana kallon Umaimah dake masa murmushi, dakinsa ya wuce tabi bayansa harya fara balle boturan rigarsa ta shiga taya shi tana cewa "Yau ka dawo da wuri ko duk missing dina ne ya saka" "Uhm, Uhm ina wayarki?" "Tana palour, meya faru?" Umaimah ta tambayeshi tana karantar yanayinsa, be amsa taba seda ya daura towel a qugubsa ya sake kallon ta yana cewa "Ya nagansu su biyu ina Lubna ko ba tare suka zo ba?" Yatsina fuska tayi a zuciyarta tace "Sedai uwar Lubna ba Lubna ba a fili kuma tace masa "Ta tafi gida wai" "Kamar ya ta tafi meyasa ba ta jira sun tafi da sauran ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar, seta hade rai tana kallonsa tace "Se ka kirata ka tambayeta ai kaji dalili, wato shiyasa ka dawo gida da wuri kafin lokacin dawowarka saboda kana sauri kazo kaga budurwarka ko toh na koreta". "Ta tabbat kenan" ya raya a ransa amma be tanka mata ba ya janye gefe ya wuce bandaki ya barta tana qananun maganganu. Seda yayi wanka ya fito, ransa gaba daya a dagule, besan ya Hajiya zataji ba idan taji da gaske ne Umaimah taci mutunchin Lubnan ta kuma korota daga gidan dan abinda Lubna taje gida tana kuka kamar ranta ze fita ta gayawa Hajiyar kenan wai suna zuwa bata san waya gayawa Umaimah akwai alaqar soyayya a tsakaninsu da Khalil ba ta rufeta da masifa da zagi har tana ce mata Karuwa kwartuwa ta biyo mata miji gida ita kuma Shafa'atu tana qara zuga Umaiman tana gaya mata maganganun qarya dagaskiya daga ta rama suka hadu suka rufeta da duka dakyar ta kwato ta gudo daga gidan. Hajiyar tayi kiran layin Umaimah a lokacin dan taji gaskiyar meya faru dukda hankalinta ya tashi sosai da ganin Lubnan tayi budu budu ga fuskarta tayi jajir gefen bakinta ya fashe leben ya kumbura dukda bata yarda da cewar Umaiman ta aikata abinda ta fada ba amma idan ma tayin dole da dalili kuma shi take so taji. Tayi kiran layinta kusan sau uku bata daga ba ta mayar da akalar kiran kan Shafa'atu itan ma samma kal. "Ai Hajiya bazasu daga ba, dan fa bakiji irin mugun abun da Shafa taje tana fada mata bane a kanmu ta na kwance mu gara kawai ki kira Yaya Khalil din shi yaje ya same su a gidan" Lubna ta fada tana matsar kwalla, Hajiya ta kalleta kawai ta dauke kanta gefe tace "Ai mu bamu da wani mugun abu ko abin kwance kai da Shafa'atu zata gayawa Umaimah, kuma idan Shafa ta muzantamu ai kanta ta muzanta ko tunda ubanda ya haife ki shiya haifeta karki manta, ba dangin uwa kadai kika hada dani ba, dani da Najib Uwa daya Uba daya suka kawo mu duniya dan haka keda Shafa abu daya ne a gurina" tana gama fadar haka ta mayar da kiran zuwa layin Khalil. A taqaice tayi masa bayanin zuwa da dawowar da Lubna tayi gidan da abinda ta fada mata ta qarasa maganar da cewa "Na kira wayarta bata amsa ba idan ka koma kayi bincike ka gane gaskiyar abinda ya faru dan bana son abinda ze kawo wata baraka tsakanin matarka da yan uwana saboda yanzu idan wannan yarinyar ta tafi tana yada abinda ta gaya mun ko gaskiya ne ko qaryane Allah kadai yasan abinda hakan ze haifar a cikin dangi dan haka kaji ta bakin Umaiman idan Habiba da Shafan sun dawo nima zan tambaye su yanda akayi" da haka sukayi sallama abinda ya saka shi ya tattaro ya dawo gidan kenan kafin lokacin tashin sa. Sanda ya fito daga wanka bata dakin, yana shafa mai ta shigo da Try ta dora kayan abinci akai ta ajiye akan Table din dake gaban gadon fuskarta a hade kamar wadda ya zaga shi se ta bashi ma dariya yace "Toh kuma me akayi miki kike faman bata rai bayan kin korar mun budurwa ina ta sauri nazo muyi hira" Dagowa tayi daga zuba masa abincin da takeyi ta aika masa da wata mugur harara seta dire farantin ta miqe tana cewa "Wallahi duk yar iskar yarinyar data sake tako qafarta gidan nan da sunan budurwarka tayi mun iskanci se dai ta koma gida a gurgunce, saboda tsabar raini da ba'a ganin mutunchina duk abinda zakayi kayi a waje mana amma shine za'a biyoni har cikin gidana yarinya ta zauna akan kujerun da ubana yayi mun tana zagina tana gaya mun da yanzu itace a gidannan bani ba, toh wallahi ka gaya mata dukan dana mata yau kadan ne nan gaba idan muka hadu ko kallon banza tamun sena saba mata kamanni Mtsw" taja tsaki tana wullar da serving spoon din da yake hannunta. Kallon ta kawai Khalil ya tsayayi har ta gama, ya fuskanci Tijara a jininta take idan kuma tanayi manta dawa take ko a gaban waye takeyi idan ya tsaya kulata zata zubar masa da mutunchine a gaban masu ganin girmansa tunda dai yaji abinda yake so cewar ta daki Lubnan toh bin ba'asi ma be taso ba dan yasan dalilin dai Kishi ne sila Allah ya rufa asiri shi kuma ze san ta yanda ze fahimtar da Hajiya abinda ya faru kafin ta bata rawarta da tsalle a idonta. Abincin yaja ya faraci bayan ta fice daga palour, a lomar farko ya gane ba girkinta bane girkin Habiba ne dan Allah yayi wa bakinsa baiwar shaida dandano indai ya saba jinsa. Umaimah kuwa palour ta fita tana mita Shafa'atu da Habiba suka bita da kallo ta shige dakinta se suka miqe suka fara shirin tafiya, Habiba ce ta buga mata qofa ta fito ganinsu da jaka a hannu tace "Aa ina kuma zakuje naga kun dauki jaka?" "Tafiya zamuyi kinga yamma tayi ga Yaya ya dawo mun hanashi sakewa gara mu tafi mu baku guri" Shafa ta fada se Umaiman ta bata fuska tace "Haba ku bari seda Magriba mana se mu mayar daku gidan tunda dai ba wani guri zakuje ba" "Aa Anty gara muje dan nasan yanzu Yaya Lubna nacan Allah kadai yasan qaryar data hada ta gayawa Hajiya gara tun bata qulla sharri ba mu koma gida" Habiba ta sake fada, se Umaimah ta yamutsa baki tace "Allah ya kyauta, ku jirani toh ina zuwa" ta juya dakinta. Cikin kayanta da suka matseta ta zabarwa Habiban kala uku masu kyau laces ciki babu wanda ya shiga ruwa sau biyu wani ba ba'a taba wanke shi ba qibar da tayi ce ta saka duk kayan suka matseta seta waresu zata bayar. Kayan kwalliya ta qara mata dasu da turaruka ta sake ware wata ledar daban cikin kayan baccin ta ta dauki guda biyu masu Azabar kyau na daukar magana ta sakawa Shafa'atun ta qara mata da wata humrar sirri da Halima Qawarta ta kawo mata taji dadinta dan haka ta dibarwa Shafan sannan ta debar mata kayayyakin gyaran da Anty bata gajiya da aika musu dasu. Fitowa tayi ta bawa kowa ledarta suka karba suna godiya tace su jira tayiwa Khalil magana ta qarasa dakin yana zaune ya jingina da fuskar gado yana waya dan haka taja gefe ta tsaya tana harararsa, kashe wayar yayi ya kalleta ba tareda yayi magana ba tace "Zasu tafi" Wallet dinsa ya bude ya zaro dubu biyar ya miqa mata ta karba ta koma ta basu, seda ta raka su har qofar gida sukayi Sa'a Adaidaita ya sauke wata mata seda ta kalleta dakyau ta gane Rufaida maqociyarta ce da wata da take zaton qanwarta ce goye da baby tayi qiba tayi kyau su Habiba suka shiga ya wuce dasu ita kuma ta tsaya suna gaisawa. "Ai baki da kirki dai Amarya" Rufaidan ta fada tana qarasowa qofar gidan Umaiman, ta saki murmushi tace "Na yarda amma kiyi mun afuwa tunda kin dawo yanzu zan shigo ko yaushe in Allah ya yarda" "Toh shikenan dukda dai ban dawo ba se jibi share share zamuyi yanzun" Rufaidan ta bata amsa daga haka sukayi sallama ta juya cikin gida. Su Habiba sun rigada sun gyara mata gidan dan haka ta samu guri a palour ta zauna tana duba hannunta da yatsun suka tashi da alama dai se taje koda Chemist ne an duba dan har sannan tana jin zafi akan fatar ga kuma tashin da gurin yayi. Bude qofa Khalil yayi ya fito yana kallonta ta dauke kai, haushin sa takeji shi har yana da bakin tambayarta wata yar iska ma ko saboda kawai yaga tayi sanyi kwana biyu shine ze nemi ya taka ta to su zuba su gani. Zama yayi a kujerar dake kallon wadda take kai yana kallonta yace "Akan wane dalili zaki zagi Lubna kiyi mata gori kuma saboda ta rama ki rufeta da duka har kika ji mata ciwo" "Kan babbar bala'i au abinda ta gaya masa kenan?" Umaimah ta ayyana a zuciyarta a fili kuwa gyara zama tayi irin na me shirin tarar duk abinda ze zo tace "Saboda na isa shiyasa na daketa kuma ba Lubna ba ko uwar Lubna da ubanta ne suka zo cikin gidan nan suka gaya mun makamanciyar maganar data fada akanka tayi mun gadara sena ci ubansu ballantana ita qaramar Alhaki". *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 25 Kallonta kawai Khalil yakeyi ya kasa cewa komai saboda tsabar mamakin rashin mutunchi da tsaurin idonta dakyar ya iya bude baki yace mata "Umaimah, uwa da uban Lubna kika zaga kin san matsayinsu a gurina?" Zumbura baki tayi gaba tareda matsawa gefen kujerar da take kai ya zamana sun qara samun tazara a tsakaninsu kafin tace "Oho nidan koma suwaye uban yarinya zanci idan ta sake shiga sabgata gara ma ka gaya mata wallahi" "Lallai zaki iya zagin Hajiya koda yake ma kin zageta dan da ita da Kawu Najib da Anty Dubu abu daya ne a gurina, toh bari kiji kinyi na farko kinyi na qarshe duk ranar da da wasa kika sake kuskuren gayawa wani nawa maganar banza ma ballantana ta kai ga zagi se na baki mamaki Umaimah dan nasan darajar iyayena bakuma ayi macen da zata wulaqantasu ko ta zage a gabana ba" Khalil ya fada cikin matuqar bacin rai yana miqewa tsaye, dakinsa ya nufa se kuma ya fasa shiga ya juya da niyyar fita yana jin qunquninta tana cewa "Oho dai kuma na daki banza, ai baka burgeni ba da baka rama mata dukan ko zagin ba" "Ni nasan mutunchi da qimar iyaye bazan zagi naki ba, duka kuma kibi a sannu duk ranar da kika tiqeni zaki gane ba tsoronki nakeyi ba da ya saka nake raga miki" ya sake fada yana aika mata da wani irin kallo daya saka qirjinta bugawa. Fita yayi saga gidan ya samu kan wani dakali daga can gefe ya zauna yayi shiru, shi kuma tasa qaddarar akan aure, wayar sa datayi qara ce ta katse masa tunani ya cirota daga Aljihunsa ya daga ganin Hajiya ce take kira. Tiryan tiryan ta fada masa abinda su Habiba suka gaya mata ya faru a gidan, "Ni daman nasan qarya takeyi Umaimah bazata aikata abinda tace tayi mata ba tareda dalili ba kuma ni tayi mun daidai data zaneta tunda bata da kunya idan ba haka ba taje har cikin gidan ta tace zata mata rashin kunya ai idan bata dubi darajar matarka ce ba ta dubi na tazarar shekarun da ta bata, Allah ya rufa asiri ka bawa Umaiman haquri dukda nima zan kirata" Hajiya ta fada se Khalil ya saki murmushin takaici a ransa yace "Almura, duk mugun halin ta babu me yarda se wanda ya gani da idonsa" a fili kuwa yace "Koma menene abinda Lubna tayi be kamata ace Umaimah ta daketa ba, me yasa bazata kirani ni ta gaya mun na dauki mataki ba kawai seta kama yarinya da duka" ya fada cikin bacin rai se Hajiya ta tare shi da cewa "Akul Khalil karka kuskura ka zama cikin irin mazan da suke goyon bayan qannensu sama da matansu koda kuwa sune da gaskiya, yanda kake da damar hukunta na qasa da kai idan sunyi laifi haka matarka matsayin ku daya kaida ita a gurinsu kar kuma ka kuskura ka basu qofar da zasu rainata dan kai kanka bazaka ji dadi ba, saura kuma naji wani abu daban" daga haka ta kashe wayar tana jin haushin son kan da Khalil din yake neman nunawa, a zatonta da yaji kan labarin zece ze qarawa Lubnan wani dukan ne se taji akasin haka, maza dai Allah ya shirya su da son kai. Khalil kuwa cikeda qarin takaici ya maida wayarsa Aljihu yanzu idanya gayawa Hajiya zagin da tayiwa yan uwanta cewa zatayi qarya ne saboda makauniyar soyayyar da takeyiwa Umaimah shidai yana fatan Allah karya kawo ranar da notin kan Umaimah ze goce a gaban Hajiya ko inda zata samu labari dan besanyanda zata kaya ba. A gurin yaci gaba da zama har aka kira sallar magriba kafin ya wuce masallacin cikin layin nasu yayi sallah, har ya zauna dan baya son kowama gidan ta qara bata masa rai se kuma ya tuna da ya taho da wani aiki da zeyi dan haka ya miqe ya tafi gidan. Tana zaune tayi daidai akan daddumar da tayi sallah ga faranti a gabanta ta yankakken mangwaro da gani me qanqarane, kallo daya yayi mata bayan da yayi sallama ciki ciki ya dauke kai, ya ja mata kunne akan shan sanyi amma taqi ji, be kukata ba ya wuce cikin dakinsa ya kunna Laptop ganin chajinta yayi qasa ya saka shi neman chaja amma be ganta ba, daga cikin dakin ya kwalawa Umaimah kira, tana jinsa sarai amma tayi banza har seda ya gaji ya fita ya tsaya a qofar dakin yana kallonta, yasan taji shi sarai wulaqanci ne ya hanata amsawa amma bashi da lokacinta a yanzu. A dake ya ce mata "Ina kika saka mun Chager Laptop dina?" Wani kallo ta watsa masa me kama da harara kafin ta tura baki gaba tace "Ni ka bani ajiya ne ka duba a inda ka saba ajiyewa mana". Seda ya hadiye abinda ya tsaya masa a maqoshi kafin ya sake ce mata "Idan tana gurin da nake ajiyewar ai da banzo na tambayeki ba, ki taso malama ki dakko mun ina da abunyi" Yanda yayi maganar babu wasa ya sakata miqewa dole ta wuce shi tana qunquni, magana takeyi sarai kuma ya jita tace "Haka kawai ayi mun laifi dan na dauki mataki kuma ya zama abin fushi toh ko kububuwa mutum ya zama ba abinda ya shafeni wallahi yarinya ta sake zuwa tayi mun hauka naci ubanta na kuma daketa na daki banza babu abinda za'a iya" ta shige ta dakko Chager data saka a cikin drawer sabanin saman drawer daya saba ajiyewa. Akan gado ta dora masa ta fice tana juya jiki Khalil ya bita da kallo ya saki murmushin zallar takaici kafin ya jona chager ya shiga aikin da zeyi Qunquninta ne ya ringa dawo masa haka kawai yaji ransa yana qara baci wato babu abinda ya isa yayi mata koh wai wane irin raini Umaimah take dashi haka ace mace har mace amma babu ladabi harshenta babu linzami? Yaga alamar dauke kai da yakeyi yana kyaleta a maimakon tayi hankali iskancinnata qara gaba yakeyi, dole ya dauki mataki tunda shi ta rainashi ai akwai na gaba da ita da take shakka. Wayarsa ya janyo ya shiga kiran Yaya Aminu dan yasan shine maganinta ba kuma yaso kai tsaye ace ya kai qararta gida ko ya kira daya daga cikin yayyenta mata gara Aminun ze iya musu maganin matsalar ba tareda Mama ko Abba sunji ba. A mutunce suka gaisa ya tambayeshi yana gida ne zasu shiga yace Eh har yana masa tsiyar tunda sukaje musu bangajiya ai basu sake leqawa ba har ita Umaiman daman dai ba gwanarzuwa gidansa bace dan ba wani shiri sukeyi da Mamy matarsa ba. Bayan ya kashe wayar yaci gaba da aikin da yakeyi har aka kira Isha kafin ya fita masallaci, tana zaune tana aikin danna waya ya wuceta, seda ya kai qofa ya juyo yace mata "Ki shirya idan na dawo zamu fita" "Ai kuwa babu inda zani zakazo kana wani ciccin magani saboda na daki budurwarka, ai dana sani ma na balla qafar shegiya se inga ta tsiya, mtsw" taja tsaki duk a cikin kunnen Khalil daya dakata dan yasan se tayi magana ita kuwa daman ba tsoron yajin takeyi ba shiyasa ko qunqunin zatayi a fili take abinta duk abinda ze faru ya faru ai kuwa har yaje sallah ya dawo tana zaune inda ya barta dan ko sallar ita bata tashi tayi ba. Wuceta yayi ya shiga daki ya chanza kaya ya dakko muqullin mota ya fito, a maimakon zaunen da take da ta kwanta ne akan carpet tana waya ya fito ya tsaya akanta amma bata nuna ko kusa tasan da tsayuwarsa bama. Ya kao bango da rashin mutunchinta dan haka ya fizge wayar yayi jifa da ita take ta rotse a gurin Umaimah ta tashi zaune tana cewa "Lalala, ka fasa mun waya? koda yake ina ruwana ma kudinka ai ba nawa ba" ta juya zata sake kwanciya ya saka hannu ya fizgota a mugun tsorace ta miqe hatta da dan cikinta seda ya hantsila ta shiga raba ido tana kallonsa yace "Wuce ki dakko Hijabinki" ya saketa tayi taga taga zata fadi ta samu ta dafe kujera, yanda taga fuskarsa ta tsorata dole ta kama hanya ta shige daki sum sum ta dakko Hijabin a ranta tan tunanin toh ina zasuje koda yake tasan baze wuce gidan Hajiyarsa ba. Qarar rufe Get da taji ya tabbatar mata da har ya fita seta zura takalmanta taja qofar palour ta fita itama. Yanda yake fizgar motar ya tabbatar mata da zuciyarsa a wuya take seta kama kanta, ganin sun hau kan State road ta sake tabbatar da gidan Hajiya zasuje, ai kuwa a shirye take da ta sake gurzar bakin yarinya a gaban Hajiyar idan tayi mata sharri ehe sedai ayi wacce za'ayi, ganin ya dauke hanya yayi Hotoro ya sakata shan jinin jikinta, a saninta bashida wani dan uwa a hotoron da zasuje gidansa a daren, Jalila ce kuma basa Kano suna Warri inda mijinta yake aiki se anyi hutu suke zuwa kanon. Bata qarasa shiga tasku ba seda taga yayi parking a qofar gidan Yaya Aminu. Cikin ta ya bada qululu ta waiwaya ta kalleshi daidai sanda ya kashe motar yana qoqarin fita irin yanda ya hade rai bata da ma qwarin guiwar yi masa magana amma Khalil ya isa mugu, yanzu daga wannan dan qaramin abun shine ze kawo qarar ta gurin Yaya Aminu? Lissafin yanda zatayi take har ya shige gidan ya barta a mota dan tuni Ummi babbar Yar Yayan ta bude masa qofa, seta balle murfin ta fita cikin mutuwar jiki, abinda yake dan kwantar mata da hankali tasan a yanzu dai bazata doku a gurin Yaya Aminun ba, ai koshi Khalil din baze bari ba ko badan aure ba ai a qyaleta dan abinda ke cikinta haka ta shiga gidan kamar munafuka tayi sallama Ummin tazo ta rungumeta tana mata oyoyo Anty Mami ta fito daga palourta tana cewa "Wata sabon gani yau Umaimah a gidanmu lallai za'ayi ruwa da qanqara". Yaqi tayi ta shiga gaisheta ta tareta tana cewa "Haba kamar za'a gudu, mu shiga ciki mana ma gaisa a nutse" tayi gaba Umaimah da Ummi suka bita a baya a ran Umaimah ko zaginta take tana cewa "Algunguma me makon da kikaji ya kawo qarar tawa ki kirani ki gaya mun karna bishi ko ina yau shine yanzu zaki wani ringa yaqe mun baki toh Allah ya isa". A palour Yaya Aminu ta tarar da shida Khalil suna hira kamar bashi ne suka taho yanzu fuska a daure kamar yaci kashi ba, gefw ta samu ta rabe ta gaida Yayan nata ya amsa yana karantarta Anty Mami na janta amma taqi sakewa se satar kallon Khalil takeyi tana marairaice masa fuska fatanta ya fahimci roqon da takeyi masa na karya fadawa Yayan komai dan tasan da ace ya rigada ya gaya masa bazata samu fara'ar da yayi mata yanzu ba amma sam Khalil yaqi bari ma su hada ido seya duba agogon hannunsa ya kalli Yaya Aminu yace "Gurinka muka zo Yaya" "Toh Allah yasa lafiya, koda yake daga yanda naga idon wannna shaqiyyar tana sunne kai nasan da abin tsiyar data shuka" se Mamy ta miqe tana cewa "Haba dai ai ta girma yanzu ko Umaimah, bari na baku guri toh taso muje can" ta fada tana kallon Umaimah data miqe kamar me jira se Yayan ya dakatar da ita yace "Jeki zatazo idan tayi free" Mamy ta saka dariya ta fice. A taqaice Khalil ya zayyanowa Yaya Aminu kokensa akan Umaiman, abu biyune zuwa uku qorafinsa yanda sam babu ladabi a tsakaninsu ba kuma ta tauna magana duk dacinta haka zata yaba masa ita se kuma rigimar da sukayi da Lubna yau a gidan dukda be gaya masa zagin da tayiwa Kawun nasa da Goggonsa ba ya dai qare da cewa "Kullum abun qara gaba yakeyi shiyasa naga gara ka shiga ciki qila kai idan kayi mata magana taji, yanzu dan Allah Ya dace ace daga zuwan baquwa gidanta koma me tayi mata ta kamata da duka ita kwata kwata bata da aji bata san abinda ya kamata ba a ko ina tace zatayi dambe da mutane haba dan Allah" Caraf Umaimah da ta kasa kunne duk tana jin qararrakin nata daya kawo ta karbe zancen tace "Ai idan gaskiya ce seka gaya masa matsayin wacce na daka din a gurinka, budurwarsa cefa Yaya tazo har cikin gidana zatamun rashin kunya saboda bata da tarbiyya harda cewa fa zata dakeni shine ni kuma na saita mata zama yanda gobe ko layin gidan saurayinta ba...." Bata qarasa ba saboda marin da Yaya Aminun ya dauketa dashi da ya saka kunnenta toshewa na wani lokaci bata dawo saiti ba ya qara mata wani ta kuwa dage ta fasa ihu tareda zabura tayi kan Khalil be haqura ya sake duma mata dundu a baya ta gantsare ta sake fasa wani ihun tana "Wayyo cikina bayana" A rikice Khalil ya riqota yana cewa "Innalillahi Yaya abin be kai da duka ba ka manta ba ita kadai bace" ya rungumota jikinsa ta fizge Yaya Aminu ya daka mata tsawa yace "Zauna a nan ki kuma rufe mun baki kafin na dakko bulala na hada miki jikinki a nan mutuniyar banza kawai, ke har kike kiran wata da mara tarbiyya ga rashin tarbiyya nan qarara kina nunawa? Ai gara ki tabbatar masa da babu wanda ya isa dake idan ma ya kawo qararki ne dan a miki fada toh kinfi qarfin kowa". Kuka Umaimah take mara qara tana sosa bayanta Khalil na tayata kamar shima ze fasa kukan, cike da takaici Yaya Aminu yaci gaba da cewa "Ni daman nasan shirun da akaji Allah kadai yasan iskancin da kike shukawa ilai kuwa gashi da shukar ta isa girbi an gani toh karki fasa duk abinda kikeyi kinji ina daidai da duk wani iskanci da lalatar ki, kai kuma" ya juya kan Khalil yaci gaba da cewa "Kaine babban me laifi da har ka bari wannan abar da batafi ka hadiyeta ba take gaya maka maganar banza baka saba mata kamanni ba, daga yau ko kallon banza ta sakeyi maka dakata ni na sakaka saboda ita tun asali idan har ba an taba lafiyarta ba ba'a daidaitawa da ita. Bata jin Nasiha ko fada se taji a jikinta sannan take nutsuwa". Kamar Khalik zeyi kuka ya sake rungumo Umaimah jikinsa yace "Amma Yaya Umaimah yanzu ai ta wuce duka a gurin ku ma ballantana ni a matsayin mijinta na daketa, nasihar dai ita ya kamata ayi mata musamman yanzu a yanayin da take ciki tana buqatar kulawa ne ba damuqa ba". Harara Yaya Aminu ya maka masa yace "An dame tan dan ubanta da kasan bakaso ayi mata fada meya kawoku? Ai dole ma ta rainaka ka zauna kamar sakarai kana wani rarrashinta bayan ita ce tayi maka laifi toh tunda wuri ka tashi kasan abinda kakeyi idan ba haka ba wannan seta maida kai abinda bakayi tsammani na, dan zuma ce ita da wuta ake cinta, a haka dai gaka nan kamar namijin gaske amma ka zauna wannan abar tana gigitaka, zaki miqe ne ko kuwa sena qara miki wani dundun makira zaki narke saboda kiyimun sharri" Yaya Aminun ya sake fada yana zaburo mata se gata kuwa ta zaune dungurgur akan kujera dan da se malele kuwa take a jikin Khalil din tana riqe baya. Fada sosai Yaya Aminun ya hada daga ita har Khalil din yayi musu dan daga baya ma laifin kansa ya koma yace shi ya bata fuskar da take masa kowanne iskanci dan gashi yanzu ma a gabansa ya gani to kuwa tunda ya bari tasan lagonsa haka zata ringa wana shi gaba gaba kuma tafi qarfinsa bazata lankwasu ba zasu zama sedai shi ya bita ba ita ta bishi ba. Yayi musu tatas kafin ya dora da nasiha basu bar gidan ba se Goma saura Umaimah ko kallon qofar Mamy batayi ba ta fice daga gidan dan Khalil da Yaya Aminun sun tsaya yana sake jaddada masa ya tashi tsaye akanta idanba haka ba kar yayi kuka da kowa ya kuka da kansa a gaba. Suna shiga mota ta barke da kukan da bata samu damar yi a gidan ba, kuka me hade da ihu ta ringa kurma masa duk yanda yaso ya daure kamar yanda Yaya Aminun ya jaddada masa kasawa yayi ya faka motar ya shiga lallashinta nan ta botsarewa kuwa ta baje kolin sabon rashin mutunchi tana cewa ai yana sane ya kaita aka ci zalinta, ya ringa bata baki yana lallashinta amma a banza qara watse wa takeyi seda ya gaji ya dauki wayarsa yana cewa "Bari na kirashi na gaya masa tunda daman yace duk abinda kikayi na gaya masa ze zo har gida ya mun maganinki" ya shiga dannan kiran Yaya Aminu ta wafce wayar tana cewa "Saboda bakai ya daka ba ai wallahi se Allah ya sakamun da kai dashi duka ba yafewa zanyi ba". Abinda yafi qarfinka aka ce seka mayar dashi wasa haka ce ta kasance da Khalil tunda dai ya fuskanci bakin ne babu linzami unguwar zoma bata gasa mata shi ba gara ya lallabata su rabu lafiya, haka suka qarasa gida ranar dai baccinsa ragagge ne saboda kuka da tashin hankalin data ringayi na zallar Jidali dan yayi zaton zatayi kukan ciwon baya amma kamar ma ta manta da an daketa a gurin, fuskarta ce dai ta tashi taji hannun Maza a haka suka lallaba suka kai safiya, da wurwuri ya bar mata gidan saboda sabuwar tijarar data dira da safiyar Allah ta'ala shikam dai tasa Jarabawar akan mace akai masa. Umaimah kuwa Khalil na fita ta shiga ta fesa wanka ta hada shayinta me kauri tasha. Duk Dramar tana sane tayi abarta ta kuma yi alqawarin seta tayar masa da hankali gwargwadon zafin mari da dundun daya kaita aka mata. Tana gamawa ta kwanta ramuwar baccin da bata samu tayi cikin dare ba, wunin ranar haka tayi shi har Yamma tana nade a gado sedai idan an kira sallah ta sauka tayi ta kuma komawa ranar se bayan magriba Khalil ya dawo saboda baqi da sukayi a company Umaimah kuwa ta saka a ranta saboda gudun jidalinta ya saka shi qin komawa gidan da wuri. Tana zaune a palour ya shiga da sallama ta amsa ciki ciki tareda yi masa sannu da zuwa ya amsa yana qarawa inda take bayan ya ajiye ledojin daya shiga dasu yana tambayarta ya jikinta, fuska ta yamutsa batace komai ba, ya wuce dakinsa yayi wanka dan ya rigada yayi Magriba kafin ya shigo ya dawo palour ya zauna yana janta da hira gimbiyar se cika take tana batsewa Ledojin daya ajiye ma suna nan babu wanda ta taba se shine ya janyo su ya fitar dana abinci ya ajiye a gabanta ya dauki nasa ya bude ya fara ci. "Ki duba waccen Ledar wasu dogayen riguna ne aka kawo talla Office dinmu na daukar miki naga yanzu kinfi jin dadinsu" ya fada yana nuna mata wata leda me dan girma, a ciki tace masa ta gode bata tashi ta dauki kayan ba se yaji ba dadi dan ya saba idan ya siyo mata abu komai qanqantarsa zata karba tayi murna tareda godiya, be sake magana ba yaci gana da cin abincinsa yana gamawa aka kira Isha ya tashi ya fita. Janyo ledar tayi ta bude, irin Egyptian silk gowns din nan ne masu aiki a jiki guda hudu kowacce kalarta daban ta tabe baki ta mayar cikin ledar dan sam ita basu burgeta ba, asalima da irin rigunan baccin yan saudiyyan nan sukayi mata kama na gumama ta miqe da ledar ta shige daki ta watsa ta cikin wardrobe dan bata jin zata saka su ma seta wuce ta dauro alwala itama ta tayar da sallah. Be gaji ba bayan ya dawo haka ya ringa janta da hira yana lallaba abarsa dan shiya kaita aka daketa yasan yayi laifi dole ya nemi shiri tana ta basarwa hardai ta fara sakkowa tana amsa masa hirar kadan kadan, wani abokinsa ya kirashi a waya bayan sun gaisa yake gaya masa Gwal ya sauka dan tun farkon auransu yayi masa maganar yana so ya siyawa Umaiman Sarqa yace ya bari Dala ta dan sakko tunda ana saka ran saukarta, farashin ya tambaye shi ya gaya masa yace ya hau whatsapp suyi magana. Designs yace ya turo masa na sarqa da dan kunne da zobe da suka kai nauyin Gram Ashirin zuwa da biyar haka, ya turo masa su masu kyau seya miqawa Umaimah wayar yace "Duba mun wacce tafi kyau a nan" ta karba ta shiga dubawa, wata ta zaba ta miqa masa tana cewa "Idan ni zaka siyawa ma karka wahalar da kanka dan wadanda nake dasu ma ba sakawa nake ba bana son sarqa qara dan kunne da zobe da awarwaro sarqa damuna takeyi kuma ni wannan Indian design din ma ba wani burgeni suke ba". Wani iri yaji toh wai duk cikin fushin da takeyi ne ya saka take gwasale duk abinda yayi mata ko kuwa daman haka halinta yake? Amma da ai ba haka take ba kai shifa lamarin Umaimah yana cakar masa da kai wani lokacin. Badan ya rigada yayi niyya ba da fasawa zeyi dan bega alamar idan ya siya din ma zata yaba ba amma badan halinta zeyi ba dan idan yace ze biyewa halin Umaimah abinci baze bata a gidannan ba dan ko tayi masa abin arziqi yaji dadi ya bata tukuici seta zobe ladanta dana tsiya harda qari. Wayar ya karba ya cewa Abokin nasa ya fasa sarqa ya samo masa dan kunne me kyau kawai babba da awarwaro da zobe, sukayi lissafi aka hada masa seda ya kai Gram Talatin akan dubu talatin da uku take yayi transfer kudinsa 1M yace ya siyawa yara alawa da dubu goman da safw zeje ya karba, daya tambayeshi sunan da ze rubuta a Receipt yace ya saka Umaimah Sabo dan kyautace ya siya mata halak malaj nata ne tayi duk yanda taso dashi. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 26 Zama yayi dadi tsakanin Mutuniyar ta sakko shi kuwa yana ta faman hidima da ita, kwana biyu  tsakani ya karbo mata dan kunnen daya siya. "Wato abokina kana ji da Amaryar nan taka gaskiya a zamanin nan ka zare Miliyan a tashi daya ka se mata Dan kunne, koda yake qila kaja kaya da yawa ka samu wata kwangila me zafi ne ko" Abokin nasa ya fada yana miqa masa Dan Akwatin da suke ciki. Murmushi Khalil yayi ya karba ya na dubawa yace "Toh Bashir meye amfanin arziqi idan bazaka wadata iyakinka ba? Nifa ka ganni bazan sha wahala na nemi kudi dan na tarasu ba ba gara mu kashe su muji dadi dan idan ka tara ka mutu be zama lallai iyalan naka ma su mora ba. Kana kallo dai mu da aka mutu aka bar mana tarin dukiyar wasu suka danne suka cinye komai amma kaga ko a jikin mu dan tun yana raye babu abinda muka nema muka rasa yayi mana duk abinda ya kamata yanzu kuma da baya nan mun tashi muna neman Rabon mu shine shari'ar gaskiya ka mori arziqinka kaji dadi" "Gaskiya ne mutumina toh Allah ya qara rufa mana Asiri duniya da lahira" Bashir ya fada Khalil ya amsa da Amin kafin ya nuna masa wasu zobuna yace ya miqa masa. Guda biyu ya cira yace "Zasuyi kyau a hannun Hajiyata nawa suke ko bashi ne na karba" "Kai Alajin Allah" Bashir ya fada yana dora su a abin awo, ya auna ya buga lissafin ya nuna masa, bashida isassun kudin da zasu kai ya karbi biyun seya ajiye qaramin ciki yana cewa "Kudi bazasu isa ba bari na dauki wannan idan an kwana biyu na samu sarari sena qara mata" "Ka dauka kawai babu damuwa duk sanda Allah ya hore seka bani ai ana tare" Bashir ya fada yana saka masa su a mazubi se Khalil yace "Aa bana son bashi ka sani idan ina dashi zanyi abu idan babu a haqura kuma na san sana'ar ku babu bashi kaga bazan saka kayi abinda baka yi ba" "Haba Bayero yanzu ko kyauta na baka ai ban fadi ba dan Alkhairin da kayi mun a rayuwa bazan taba biyanka ba, kaje dasu duk sanda ka samu ka bani" da haka ya saka shi dole ya karbi zobunan ya hada dana Umaimah ya wuce gidan Hajiyarsa. Bayan sun gaisa ya ajiye mata kayan a gabanta ta bude tana cewa "Wai wai zankadi Babana wadannan fa?" "Kudin aikin da nayi a Kaduna kwanaki ne aka biyani, kin tuna daman nace miki idan na samu sarari zan siyawa Umaimah sarqa shine naga wadannan zobunan zasuyi miki kyau na taho miki dasu" ya qarasa yana ware mata natan. Seta dauka ta zura a hannunta tana cewa "Kai amma mungode kwarai Allah ya qara budi na Alkhairi amma biyu sunyi yawa Babana ina laifin daya ni yanzu ma da tsufa ya kamani kwalliyar ma bayi nakeyi ba kana kallo nawa duk su Jalila sun are amma wannan dai zan barshi a hannuna wannan kuma ka qarawa Umaiman tayi ta cancada maka kwalliya" "Aa Hajiya ke na siyawa itama ai ga nata nan" "Hajiya idan bakya so ni ki bani dan Allah" Habiba da ta fito daga kitchen tayi caraf ta fada, Khalil ya maka mata harara yace "Seki kwata ai" "Kai Yaya Khalil dan Allah" Habiban ta marairaice fuska, seya dauke kai bece mata komai ba Hajiya tace "Kyaleshi kinji auta zan ringa baki aro" seta taho da sauri tana cewa "Yawwa bari na gwada yanzu ma Hajiya" ta karba ta saka a hannunta tana juyawa Hajiyan na mata dariya, sama tayi da gudu wai zata dakko wayarta ta dauki Hoto se Hajiya ta mayar da hankalinta kan Khalil dake dannan waya tace "Amma Babana dawainiyar nan batayi yawa ba kuwa? Kaga yanzu akwai nauyin iyali a kanka dole seka daidaita abubuwa fa da yanda kake kashe Kudi, jiya Jamila take gaya mun ka tura mata da kudi tayi jari, ba'ayi sati ba ka biya kudin makarantar Khalifa ba yanda Kawunku beyi ba akan ka bari kaqi yanzu kuma yau ga zobuna har biyu ya kamata a rage kashe kashen kudin nan a fara tanadi, yanzu nan da yan watanni za'a samu qaruwa ya kamata ace ka fara himmar ginin filinka saboda can din dan lokaci kadan zeyi muku kadan ya kamata ku samu inda ya fishi wadata" "In sha Allahu hajiya hidimomi kuma ai haqqinane dukka gaba daya babu wanda be zama dole ba tunda Allah ya hore za'ayi kedai kici gaba dayi mana addu'a kawai amma akwai haske sosai abubuwan Alkhairi suna ta samuwa dan yanzu haka akwai kwangilar da muke nema A Abuja, idan ta tabbata abubuwa zasu qara chanzawa in sha Allah" Khalil ya fada, se Hajiya tace "Toh Allah ya qara rufa asiri ya tsareka daga sharrin mahassada, na saka Malam Babba ma yayo maka rubutun tsari da baki dan dole kana buqatar dafa'i" "Ga babban dafa'i nan addu'ar da kike mun ba dare babu rana ai kici gaba dayi kawai Hajiyata itace fitila duk tsananin duhu tana haska mun na samu hanya" ya fada a fili a zuciyarsa yace "Ga kuma dayan hasken tawa yar rigima, tunda na hadu da ita nake ganin nasara a rayuwata, Allah ya bar min ita ya chanza mun halinta". Hira suka ci gaba dayi ta tambayi shi watan haihuwar Umaiman ya gaya mata zuwa wani lokaci yayi mata sallama ya tafi gida. Be bawa Umaimah nata a ranar ba se bayan kwana biyu da daddare suna zaune ya gaya mata inda ya ajiye yace ta dakko masa, seda ta bude akwatin taga meye a cikin kafin ta kai masan, receipt din da ta gani ta duba ta fasa ihu ganin kudin jiki ga kuma sunanta se a sannan ta fahimci gold ne na gaske ba Indian design yanda tayi tunani ba sanda yace ta zabi wadancan, data sani me sarqar ta dauka amma wannan dinma sunyi kyau sosai tayi murna dan ta dade tana son a siya mata zinare ko iya zobe ne amma Mama taqi kuma duk yayyenta babu wanda Maman bata siyawa masa ba lokacin auransa dan har harda Nuratu akace wai ba'a zata tare za'a hada auransu ba shiyasa kuma dai tasan kawai da ke ita ba'a sonta ne shiyasa ba'a sai mata ba. Washe garin daya bata kuwa da sassafe ze fita aiki ta bishi ya sauketa a gida dan ta nuna musu. "Nima dai nayi Zinare irin na mata, me sona na gaske ya siyamun kuma dukda bansan kudinsa ba nasan duk yafi na sauran" ta fada tana juya ido, Mama ta kalleta ta girgiza kai kawai tana murmushi tace "Toh ai shikenan kinga kudina ya huta dan daman inata Adashe inaso kafin Allah ya saukeki lafiya Abban ku ya cika a siya miki sarqar toh Khalil ya fanshenu se na qara jari da kudina kawai" Maman ta bata amsa tana moqawa Anty da tayi dariya tace "A haba dai ai haqqin tane idan ma baza'a siya ba se a bata kudinta gara ma dai a siya miki ki qara kadara ce bata yawa, Ina kwadon sarqar, ko kon baro shi gida a garin zumudi?" "Abinda nake shirin fada kenan ko kuma ta yar ba da shegen rawar kanta, ni ai tuntuni tsoron Asara yake daqileni da siyawa Umaimah Zinare, tana iya zuwa ta yardashi ko ta kyautar tunda ba hankali ta cika ba" Mama ta fada se Umaimah ta yatsina fuska tace "Ni ba yarwa nayi ba ni nace bana son sarqa cimun wuya takeyi" "Allah ya yaye miki wauta dai Umaimah, kuma a gidan ubanwa sarqa take ci miki wuya" Mama ta fada se Anty tayi dariya tace "Umaimah rikici ai kuwa kwalliya bata cika idan babu sarqa musamman irin wuyanki Masha Allah baki ga yanda take miki kyau ba amma ace irin wannan saiti har saiti babu sarqa ai kinyi wauta". Zumbura baki tayi tana hararar Antyn a fakaice jin tana cewa "Badan ba ai seki koma ki lashe Amanki kice masa kinason sarqar" "Tab saboda zubar da kai wannan din ma ai ba roqarsa nayi ba" ta bata amsa tana juya ido Mama ta kai mata duka da mafici tana cewa "Laure (qanwar Maman ce) kika juyawa ido ba ita ba mara kunyar banza kawai" Umaimah ta goce tana cewa "Haba Mama nifa yanzu na wuce duka bakuga abinda yake jikina bane? Haka fa Yaya Aminu daga zuwa gidansa ya rufeni da duka kamar..." Seta rufe baki jin tayi subul kalam, Mama ta kalleta tace "Uhm kamar me, Me ma kikayi da Aminu ze dakeki halan wata ta'asar kikayiwa Khalil din ya kai masa qararki ko?" "Aa fa Mama mantawa nayi ba haka zan ce ba" Umaimah ta marairaice dukda ta rigada ta kwafsa yanzu se Mama tabi diddigin abinda ya faru idan ya gaya mata kuwa ai ta shiga uku da fada da mita ita wane shegen surutu nema ya kaita taso da maganar? "Kyaci ubanki kuwa Aminun ze zo zanji koma menene ya faru" Mama ta sake fada daga nan suka ci gaba da hirarsu, se yamma lis Khalil ya dauketa bayan da yaci abinci Anty ta juye mata tuwon Masara da miyar busashshiyar kubewar da tace tana so ta tafi dashi gida sun rabu da Mama tace mata ta tambaye shi idan ya yarda zata cika a canzo mata saiti me sarqa gaba daya. A hanya yake gaya zeje Dutse gobe amma tare zasu tafi. "Yanzu kwana biyun kawai kaje ka dawo shine se mun tafi tare, nifa kasan bana son tafiya a mota wallahi" Umaimah ta fada cikin shagwaba, hancinta yaja yace "Ba kwana biyu zanyi qila mu iya kaiwa sati daya ma saboda ayyukan da zanyi da yawa kuma kinsan dai bazan iya yin sati ba tareda ke ba gashi babu Jirgi Kano to Jigawa da se mu hau tunda bakya son tafiyar mota Ajebo" ya qarasa maganar cikin sigar tsokana seta harareshi tace "Nifa ba mota ba gaba daya tafiya ce bana so, nifa a rayuwata ko garin su Abba zan iya irga sau nawa na taba zuwa saboda bana son tafiya, nifa Makkah kadai nake qulafucin zuwa a rayuwata bayan nan ni ko wata Dubai da Paris da akw zuwa ba burgeni sukeyi ba" "Toh kuwa gara ki mayar da Travelling one of your hobbies dan kin auri matafiyi kuma duk inda zanje ina maqale dake kamar handbag kinsan dai dakyar nake iya kwana biyu banji duminki ba ko" yayi maganar yana shafar qirjinta ta doke masa hannu a zuciyarta tace "Jarababbe kawai" a fili kuma tace "Toh idan yanzu bana komai zan ringa binka ko ina idan muka fara tara yara fa suka shiga school?" "Kina tunanin yara zasu hanani jin dadin rayuwata ne ni babu ruwana suyi sabgarsu nayi tawa, nan da shekara saba'in idan muna raye babu abinda ze chanza na soyaya da tarairayar da nake yi miki sedai idan kuma kinyi sadaka dani kin barwa qanwarki da zata zo" kallon data watsa masa ya sakashi tuntsurewa da dariya ai kuwa ta hade rai har sukaje gida bata sake ce masa komai ba. Kamar yanda ya fada kuwa washe gari da yamma suka wuce Dutse, dukda taso tayi masa gardama akan bazataje ba yayi mata jan ido dole ta bishi tana fushi tana komai shidai be kulata ba dan tasan lalurar sa, babu kuma yanda za'ayi ace zeyi tafiyar sati yana da mata ya tafi shi kadai bayan babu wani uzuri da ze hanata zuwa. Sun cinye sati a Dutse lami lafiya babu tashin hankali dan se ya zaman Umaimah tafishi jin dadin tafiyar dan se bayan sunje tayi waya da Rumasa'u take ce mata itama tana Dutsen, akayi sa'a unguwar da take tana kan hanyar Site din da yake zuwa dan haka kusan kullum ze fita seya ajiyeta a gidan su Ruman idan ya tashi ya dauketa ita kuma tayi amfani da damar gurin koyon abubuwa a gurin yayar ruma data kasance hadaddiyar mace yar gayu ta gaske. Kwararriya ce ta fannin girke girke da ado da kwalliya, a sati dayan da Umaimah tayi ta mayar da hankali ta koyi ire iren girke girken da Khalil din yake so dan ta taki sa'a a lokacin Anty Farida tana practical class na girki se Umaimah ta shige ciki aka ringa yi da ita. Da suka tashi tafiya ta hada mata tsaraba ta gaske da Umaimah ta gode mata saubabu Adadi bayan tayi amfani da kayan tsarabar. Ingantattun kayan gyara ne gangariya da Anty Faridan take siya a gurin *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS  07031876677* Ruma ce tayi mata zancen qorafin da Umaimah tayi mata akan damunta da Khalil yakeyi, washe gari ana gobe zasu koma Kank da taje gidan ta kirata dakinta ta tambayeta, Umaimah ta sunkuyar da kai qasa a ranta tana ayyana yanda zata ci uban Ruma tunda dai ita ba terere tace taje tayi mata ba kawai ta nemi shawararta ne a matsinya na aminiyarta banda abin Umaimah ina Ruma taga abin cewa ita da ba aure ba shiyasa ta kai maganar ga Anty Farida se gashi ta gwangwajeta da magungunan matsalarta harma da wadanda bata nema ba. Shawarwari ta bata akan yanda zata kula da kanta data tashi tafiya ta bata Hadin qasaitacciyar mace tace ta shanye ta bata robar, ingantacciyar zuma da akayita daga itatuwa masu amfani ga jiki da qara kuzari wanda basuda illah ko kadan sannan bazasu cutar da ita ko abinda yake jikinta ba take ta shanye ta bata wata jaka dake dauke da wasu sirrikan bata buqatar bayani dan kowanne akwai yanda zatayi amfani dashi a jiki, ranar tun a hanya Khalil ya fuskanci mutuniyar tasa akwai magana, seda ta kusan Kashewa Hajiya danta da soyayya dan duk kuzari da qoqarinsa ranar seda sukayi kankankan ta kusan qureshi. Ya sakata gaba da tambayar yau ina raki Umaimah kuwa sedai ta sadda kai qasa tayi murmushi, tunda suka dawo kuwa sosai ta dage da amfani da sauran sirrikan da Anty Farida ta bata na *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS07031876677* da kanta taji chanji, koda yaushe cikin kuzari take ga Ni'ima da sam bata yanke mata ta saki jiki sosai suna tsinkar furan soyayya yanda ya kamata ta kuma sake samun kan Khalil din nata dan ji da ita yake yana lallabata kamar ya goyata, idan ya fita aiki kuwa suna manne a waya voice call da video call dole ta sake bude WhatsApp saboda shi. A haka aka ci gaba da lallaba rayuwa tun sannan wani abu be qara tashi ba, yanzu baya buqatar yace ze tafi da ita wani guri duk inda zeje tana maqale dashi dukda cikinta ya fara nauyu dan yana wata na bakwai a sannan hakan babu abinda yake hanata, ta nutsu tsaf ta zama cikakkiyar matar aure data san kanta, tsakaninta da kowa yanzu lafiya lau koda yake ba'yi saurin yanke hukunci ba tunda babu wanda ya sake takalota. Yanzu jefi jefi tana hulda da maqotan nata musamman Rufaida da Maman Hibban se wata Aisha da take bayan layinsu sun hadu a gidan Maman Hauwa gurin kitso daga nan suka qulla qawance da Umaiman, Maman Hauwa dai duk yanda taso ta shiga jikinta ta gagara bata fuska, sam matar batayi mata ba ita kuma kishiyar ta da jininsu yafi haduwa Maman Hauwan tayi kane kane ta hana huldarsu, dukda hakan Umaimah na kai mata wanke bayan da Zuwairan ta gaya mata tana wanki da guda, akan naira Hamsin takeyi amma ita Umaimah dari take bata duk saiti dan tana tausayin matar ta karanci irin zaman haquri da cin kashin da Maman Hauwa da yayanta sukeyi mata a gidan dukda kasancewar itace uwargida a dalilin bata haihuwa ya saka mijin qaro aure ya auro Sadiya da tazo ta gallabeta. Tayiwa Khalil zancen chanzo dan kunnen da Mama tace zata cika a bata saiti gaba daya yace babu damuwa ai nata ne tayi duk yanda taso, da yana da kudi ma da kansa ze mayar ya chanzo matan dan haka ta gayawa Mama yanda sukayi da kanta taje Khalil ya basu Lambar Bashir sukaje shagon aka chanza mata wata seda Mama tayi mata cikon dubu dari hudu da sittin. A satin akayi bikin wata yar wan Babansu Khalil ranar yinin bikin ta Luncha sarqarta, tasha kwalliya da wani uban Lace ga zinare wuya da hannu duk inda ta gifta kallonta ake ana surutu qasa qasa masu fadin Khalil ya tare a qasanta yana bauta mata nayi masu ji mata dadi na dace da Miji me hidimtawa iyalinsa sunayi ita dai ko a jikinta aka gama Yinin biki suka wuce tare da Hajiya dan daman da ita suka tafi. Da yamma bayan ta gama abinda takeyi ta kira Khalil da suka tafi gaya wata gaisuwa shida Hajiya tace zata shiga gidan Rufaida, harda ita ya kamata ayi tafiyar Hajiya ta hana a cewarta hanya bata da kyau zata jijjiga jikinta iya gaisuwar da tayi musu ta waya ma ta wadatar. A gidan ta tarar da maman Hibban suka hadu suna hira Rufaida take cewa "Wai ni kin dena WhatsApp ne bana ganinki online" "Number chatting din na sake, ni yanzu Whatsapp idan bada Khalil ba se yan gidan mu kadai nake magana" Umaimah ta bata amsa se Maman Hibban tace "Aiko kin huta dan nima inaga barin WhatsApp din nan zanyi na gaji haka ko na tafi hutu se an kwana biyu, keni ya a ka qare da rigimar su Aisha da Moon ne?" Tayi tambayar tana kallon Rufaidah, Rufaidan ta rushe da dariya tace "Kai ai Anty Fati naga tashin hankali da ruwan bala'i kai kishi masifa ne, kinsan fa har gidan Eshan seda mukaje dan mu ganewa idonmu dagaske dai in gaya miki mijinta Moon ta aura nace Aminta tayi rana amma dani akayiwa wannan akuyancin wallahi dana koyawa yar iska hankali. Kiga fa irin qawancen da suke a group rimi rimi ashe binta take dan ta gama sanin sirrinta tayi wuf da mijinta Allah dai ya rufa asiri". Baki Umaimah ta bude tana kallonta, a dan zaman da tayi a wancan group din kafin ta goge WhatsApp ta gane Esha da Moon din da suke magana akai qawaye ne na qut da qut dan Lovey ma suke kiran junansu dan ita yanda taga suna magana abin har haushi yake bata tace kamar wasu yan iska shine daya ta zagaye ta aure mijin daya tab ai Aminta tayi daidai. "Toh yanzu me tayi ita wadda aka aurarwa Mijin" Umaimah ta fada se Rufaida ta gyara zama tace "Me kuwa tayi, se fa da aka daura sannan tasan mijinta ne angon dan duk amintar nan ashe bata san wa zata aura ba kuma da ita akayi shirin biki tas in gaya miki. Yanzu dai ta gama tashin hankali da haukan shi kuma miji yace fa yayi mata babu abinda zesa ya rabu da Amaryarsa da gida daya ma ze hada su yanzu kuma ya fasa ya kamawa Moon din gida a wani gurin ita kuma ta tattara ta koma gidansu wai ta gama auransa nace kuji shirme, ta aurar miki miji ki bar mata gidan riba biyu kenan" "Kan babban bala'i kenan, ai na rantse da Allah duk qawar da tayi mun wannan cin Amar ba ita kadai ba sena qarar da Ahalinta gaba daya kai Allah dai ya kauda abinqi amma tab" Umaimah ta fada tana girgiza qafa tsabar yanda abin yaci mata rai, ji take inama zataga Ita Amaryar da Mijin data taya Esha daukar fansar wannan qundumemiyar cin Amana. Dariya Maman Hibban da ke kallon ta tayi tace "Ke ko Amarya maida wuqar irin wannan huci haka kamar ke akayiwa kishiyar, aini banji haushin Mijin ba wallahi ita data jata a jikinta ta kaita gidanta bayan tasan ta fita komai da Namiji ze kalla yayi sha'awa itace me laifi. Babu dangin iya babu na Baba qawa har kwana takeyi a gidanki ta fito Mijinki ya fito su ringa cin karo qila da shigar da be dace ya ganta bama ai da sauqi tunda auren Sunna sukayi ba watsewar su sukaje sunayi a waje ba" "Yo yanzun waya sani, ai daman maganar da akeyi kenan kamar sun dade tare dalilin auran ne yasa ta sani, ai bazaki san Esha daqiqiya bace se kinga yanda Moon din ta samu guri a gidan ta ta baje, Haihuwar da tayi ta qarshe kinsan naje suna lokacin ma farko farkon shigarmu group din ni na dauka ma yar uwarta ce saboda yanda ta zaqalqale tafi kowa yan uwanta ma gefe suka koma suna kallon ikon Allah se fa tayi sati a gidanta har fita Unguwa take ta barta jiran yara keko ta ina bazata san yanda ta shige wa Miji ba daman tana neman inda zata lafe ga Miji da abin hannunsa gida kamar Aljannar Duniya ni banga laifinta ba wallahi" Rufaida ta sake fada tana tabe hannu. Ita dai Umaimah ta rafka tagumi, hasaso kanta kawai take ace ita akayiqa qila da yanzu a Police station za'a maida Statement din nan ba'a gida ba, Ajiyar numfashi tayi tace da Rufaida "Ki maidani group din dan Allah",seRufaida tace "Wane group ai tuni kowa yayi takansa aka rufe group, ke bakisan gurmin da aka sha bako ai tuni Admins suka sallami kowa ina zasu iya wannan tashin hankali, sedai in kaiki wani sabo da na samu shima yana kawo haske dan har yafi wancan hada yan gwarama" "Kedai Allah ya shiryeki ya kiyaye randa rigimar zata hado dake tunda bakida aiki se shige shigen groups din yan rigima" Maman Hibban ta fada Rufaida ta tura dankwali gaba tace "Ai mu duk inda gwarama take muna nan muna daga gefe muna iza wuta muna watsa mata fetur" "Allah ya shirye ki toh" Maman Hibban ta fada suka ci gaba da hira, se dab da magriba suka fita daga gidan bayan data bawa Rufaida sabuwar lambarta da za'a  sakata a group, a qofar gidan Umaiman suka tsaya Maman Hibban ta kalleta tace "Amarya karki biyewa Maman Anam dan wannan turbar da ta ke kai bame bullewa bace wallahi kullum kuma ina nuna mata amma taqi ji, bance karki shiga group ba dan ana samun qaruwa da ilimin rayuwa sosai a ciki amma kisan irin wanda zata saka ki a ciki ki kuma lura da irin mutanen da zakiyi mu'amala dasu danni kin ganni tsakanina da yan group din WhatsApp mu hadu a can mu rabu a can, kadan daga ciki ne muka samu fahimtar da har muna chatting ta pc wasu ma mun zama qawaye mun hadu a zahiri muna zumunchi dan haka ki kula, mutane yanzu babu Allah a ransu, baki san mutum ba be sanki ba babu dalili ya jefaka a bala'i" "Hakane Maman Hibban in sha Allah zan kiyaye" Umaimah ta fada sukayi sallama kowata shiga gidanta. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 27 Bayan tayi sallar Magriba ta miqe a gurin ta bude WhatsApp din dan taga ko an sakata dan daman duk a takure take tsahon lokacin nan na rashin groups din dan taji dadin su wancan karon. Halima dai tayi rantsuwar bazata qara sakata a WhatsApp group ba tunda bata da mutunchi dan kona class dinsu ma na secondary s zuwan da tayi Dutse Ruma ta saka aka maida ita dana Poly. Cikin sa'a tana shiga WhatsApp din ta ga an sakata a groups hudu harda na girki, tsaki tayi ganin na girkin da sauran biyun a rufe suke iya Admin ne suke magana ta tsani irin groups din nan da ba'a sharing idea to ko meye amfanin hakan oho sedai ayi ta turo muku abu ku bazakuyi magana ba gara gara ma na girkin tunda shi Recipes ne ake turowa amma in kana da tambaya sedai ka bi Admin pc kenan ta tabe baki shiga wanda yake a bude daga sakata zuwa lokacin ta tararda messages sama da dari. Info din group din ta fara dubawa taga mata sun kusa dubu a ciki a fili tace "Tab kace a kwai gwarama dan nasan nan ba mutane kadai ba harda Aljanu se an samu" ta rubuta sallama ta tura ba a dauki lokaci ba aka shiga amsa mata wata azakwai tace "Ban taba ganin wannan sunan ba a gidan nan da gani sabuwar zuwa ce se ki gabatar da kanki ki turo hoto da voice note". "wani sabuwar dokar groups ce haka da za'ace dole seka tura hoto da voice" ta fada a ranta, a taqaice tayi bayanin kanta da voice message ta tura kafin ta shiga laluben hoton da zata tura, daga cikin hotunan datayi ranar da sukaje Yinin cousin din Khalil ta zabi wani da tayi a gaban Mudubi yayi kyau sosai ta tura aka ringa mata sannu da zuwa anata yaba hoton ta da zuzu tawa suna cikin haka Adminta rufe group akan za'a fara gudanar da Program na ranar,a tsarinsu kullum suna da abinda suke gabatarwa na qaruwa na dan wasu mintina idan an gama se abude group aci gaba da sharholiya. Fita tayi ta ci gaba da bude status da duba massages din mutane kafin a gama program din da akace za'ayi ranar zasuyi ne akan Ado da kwalliya. Wata number taga tayi mata magana kamar ta share se kuma ta bude "Assalamu alaikum Asiya dama rai kanga rai" aka rubuta, seta bude info din number, Zee Ladan sunan me lambar ga hotonta nan akan Dp tayi zooming ita dai ko a irin fuskokin da bata gama tantancewa babu wannan sannan sunan data kirata Asiya ba sunanta bane kuma gashi suna cikin group daya sabon da aka sakata dazu dan haka ta rubuta mata "Wrong number" kawai ta tura. "Lallai Asy, daman ance kin zama big girl yanzu kin yada duka yan GGC amma ban zata nima zaki ce kin manta dani ba duk irin zaman mutu chin da mukayi daga yin Candy kikayi batan dabo akace kun koma garinku Zamfara se yau Allah yasa naganki a group ina ganin hotonki na gane ki" matar ta sake turo mata da dogon rubutu, se Umainah taja tsaki a fili tace "Baiwar Allah inaga kinyi kuskuren lamba dan ni ba Asiya sunana ba Umaimah nake kuma ni ba yar Zamfara bace a Kano nake" Se matar ta turo mata sticker irin ta mamakin nan tareda voice note tace "Kai amma wannan kama da yawa take, dan Allah bakuda yan uwa a Zamfara? Kamar ku daya da wata qawata da mukayi Secondary Asiya Sani ina ganin hotonki bakiji yanda nayi murna ba dan nafi shekara goma ina nemanta" Umaimah na shirin bata amsa tajiyo horn din Khalil dan haka ta kashe datar ta ajiye wayar ta miqe dakyar dan cikinta yayi nauyi, daga bakin qofa ta jirashi ya shigo da mota ya kulke gidan, hannunsa dauke da manyan ledoji ya ajiye su aqofar kitchen seta qarasa tana masa sannu da zuwa ya amsa yana cewa "Zabi ne Kawu Labaran ya saka aka yanka mana an gyara su se ki saka a Frizeer" ta amsa ta toh ta shiga kitchen din dasu shi kuma ya shige daki. Seda ta kai masa ruwan sanyi da Lemon Tamarin da tayi tun da rana ta barshi ya shiga wanka ta koma kitchen din ta kunna Gas ta shiga dumama miyar zogale da yake tuwo tayi ta cire zabin ta sake wanke su dakyau ta saka a Freezer sannan ta shiga hada kayan abincin tana kaiwa kan Dining tana gamawa Khalil ya fito da shirin fita masallaci. Sannu yayi mata yace bari yaje yayi salla tunda an kira se itama ta wuce ciki ta sake Alwala ta dawo palour tayi sallar ta, tana idarwa ta sake zarar waya, Khalil ya shigo ta tashi ta koma kan Dining din ta zuba masa abinci ya fara ci yana kallonta ganin ta maida hankali tana kallon waya tana zuba murmushi, "Me kike kallo a wayar haka da kike murmushi" ya fada yana kallonta, seta dago tace "Babu komai nida Maman Asad ne wai jiya ashe Nuratu tayi naqudar qarya har Asibiti aka kaita sun zata haihuwa ce akace da saura bakaga yanda ta gigice ba wai tana ta sambatu" "Uhm daman ana naqudar qarya ne qila dai ita tasan abinda take ji a jikinta" ya bata amsa yana ci gaba da aikawa cikinsa tuwo Umaimah ko ta maida kai taci gaba da danna wayarta. "Ke bazaki ci ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar ta daga masa kai kawai alamar eh se ya saka hannu ba tareda ta ankare ba ya zare wayar daga hannunta ta dago tana marairaice fuska yace "Uhm kice kin koma sana'ar taki ta chatting ko" ya fada yana bin chats din group din dan tana ciki lokacin. "Wato abinda kukeyi kaiwa daren kenan ku zauna kuna qare mana zagi da sharri kala kala ko?" Ya fada yana yamutsa fuska saboda ganin wata mata data ke cewa 'ai duk maza tsinannune, idan ba ana cin kutumar ubansu ba ba'a daidaitawa dasu' ya miqa mata wayar yana cewa "Ita wannan harda uban ta a ciki kenan ko? Allahya rufa asiri" "Bafa kasan me akayi mata da take fadar haka ba" Umaimah tayi saurin katse shi seya tareta shima yace "Duk ma me akayi mata ya kamata tayi jam'u ta tsinewa mazan duniya duka? Daga jin kalamanta kinsan ba matar arziqi bace bana so ki fita daga wannan group din idan ba haka ba ranki ze baci Umaimah, na fuskanci a nan kike kwasu duk baqin halayen da kike zuwa dasu toh ki fita idan ba haka ba zan karbe wayar gaba daya ki rasa" ya qarasa yana miqewa tsaye dan gaba daya abincin ya fita a ransa. Cikin palour ya koma ya kunna labarai Umaimah ta bishi da kallo kafinta miqe itama ta koma kusa dashi tana cewa "Honey bafa wani abu bane ba kuma ni banma san wacece ba kawai magana akeyi ta sako baki kagani ma Admin seda tayi mata magana tace be kamata ba abinda ta fada" "Nidai na gaya miki ki fita, ba kijw kin shiga cikin marasa hankali bama ya aka qare" ya fada ba tareda ya kalleta ba, seta zumbura baki tace "Me kake nufi" "Duk abinda kike tunani shi nake nufi" ya bata amsa kamar me jiranta seta tabe baki tace "Toh Allah ya naka haquri da alama dai a waje aka bato maka rai to kayi haquri". Be tanka ta ba, maganar matar ce take ta sukarsa a rai wato shi yasa kenan Umaimah kullum cikin tayar masa da hankali take saboda tanajin karatun irin wadannan matan da suka kwashe kayansu daga gaban ma'aiki suna tunzura mata su kai su wuta ko? Umaimah ko gefe ta koma ta zauna akan carpet ta ci gaba da danna wayarta, matar dazu ta sakeyi mata magana se sannanta tuna dazu batayi mata reply ba ta bude "Naji kince a Kano kike dan Allah toh ina so mu qulla qawance ki zamar mun makwafin qawata da nake ta nema ban samu ba dan wallahi har yanzu ban gama yarda baku hada jini da ita ba, a ina kike kuma yaya sunanki?" Mayar mata amsa tayi da cewa "Ni sunana Umaimah, ina Kano Unguwar Tudun-yola get 4 kefa?" "Nice name Umaimah ni kuma sunana Zainab Ladan zaki iya kirana da Maman Nihal bamu da Nisa ina Janbulo Third Gate, ina da aure yarana Uku" ta tura mata tareda hotonta da wasu kyawawan yara mata guda a wani tamfatsetsen palour. Hira ce ta sarqe a tsakanin su tun Umaiman na shareta har ta fara sakewa dan Zainab din nada faranfaran da ban dariya a dan lokaci bawa Umaimah labarinta ta dana Mijinta, mijinta hamsahqin me kudi ne kuma ba ita kadai bace matarsa yana da wata matar a Kaduna, ta ringa abin nema ya samu Umaimah taji aibun kishiya nan suka hadu suka ringa kwashewa Kishiyar Zainab da bata ji ba bata gani ba Albarka Umaimah na jaddada ai ita bazata taba iya zama da kishiya ba a rayuwarta idan taga masu itama mamaki suke bata. Khalil na kallon news dinsa sedai ya waiwaya ya kalleta kawai yayi kwafa se gurin goma ya tashi itama ta yiwa Zainab sallama ta kashe Data ta bishi cikin dakin. Ya shareta haka tayita rara gefe dakyar ya kula ta bayan daya sake jaddada mata kan ta fita daga group din nan idan tana son zaman lafiya dashi tace toh zata fita badan zata fitan ba sedan a zauna lafiya. A Achieve chats ta saka groups din tayi saiti yanda ko saqo ya shigo baze fito a jerin chats dintaba se ta shiga can ta duba, tana qoqri idan yana gida ma ba kasafai ta fiya daukar wayar ba daya saka qafa kuwa ya fita wuni take a kwance tana sana'ar Chatting a group ko da sabuwar qawarta da yanzu babu abinda Umaimah bata sani akanta ba, kusan ko yaushe suna chatting dan har mamaki Umaimah takeyi yanda Maman Nihal din is always online kamar bata da aikin yi. Koda yake Mijinta tace ba mazauni bane kuma wannan uban gida nata dole tana da masu aiki kala kala tasan shiyasa zata samun lokacin wuni a online. Duk wani abu daya shafeta ko takeyi seta gayawa Umaiman har Mamakin rashin sirri irin na Maman Nihal din takeyi dan ko Maggi Mijinta ya siyo seta gaya mata an siyo mata kaza anyi mata kaza wayarta kuqa harta kusancika da hotunan tarkacen Maman Nihal, kayan sawa ne, wani abin amfani komai ta siya swta nuna mata ita a ganin ta sun zama daya ta dauki Umaiman kamar yar uwarta. Sati daya tsakani Nuratu ta haihu akayi mata Cs ta samu Ya Mace dalilin haka ba'ayi taron suna ba se ranar da sukayi sati biyu, guri aka kama aka sha budirin suna Umaimah nata iyashegen wai dangin Dr Sagir anya ba Yarabawa bane sun fiya son bidi'a in ba haka ba suna ma ace se an kama guri anyi kamar wani biki haka aka watse taro yarinya taci sunan Maman Dr Sagir Ummulkhairi suke kiranta da Khairi. Da daddare tayi posting hotunan da sukayi a gurin suna a status dukda ba wani kyau tayi ba dan ta rigada ta zama se an hankali. Zainab ce ta fara dubawa tana gani kuwa se gashi ta kirata a waya Umaima na zaune kusa da Khalil dake aiki a Laptop wayar tayi qara ya kalleta yace "Waye kuma a daren nan" ta daga tana cewa "Maman Nihal ce", shi kamya rasa wacece haka ta samo da yanzu motsi kadan zatace maman Nihal, abu kaza irin Maman Nihal Maman Nihal tayi kaza. Last week daya nuna mata hotom wata mota da yake so ya sake tana gani tace irin ta Maman Nihal ta dakko wayarta ta nuna masa shidai yana tunanin Umaimah tana da irin ciwon nan da mutumyake zama too attached to somethings, wani ko gurin zama ne baya iya chanzawa saboda baze manta ba lokacin suna secondary da akwai wani senior dinsu da yake da ciwon seda ya maimaita SS1 sau uku duk sanda aka K promotional exam seya fadi ayi masa repeating se daga baya aka gane ba qoqarine bashi dashi ba yanasane yake faduwa saboda wai baya so a chanza masa aji to itama dai yaga alamar tana da wannan ciwon akan qawaye kwafa yayi ganinta tashi daga kusa dashi ya maida kai yaci gaba da aikin da yakeyi. Umaimah kuwa can kan Dining ta koma bayan sun gaisa Zainab take cewa "Ashe suna kuka sha haka babu gayyata gaskiya Umaimah baki da kirki baki daukeni yanda na dauke ki ba. Nidai ina sonqawance dake tsakani da Allah kuma inason zumunchin mu ya dore amma ke naga ba haka bane a gurinki har na gaji da tambayar  yaushe zakizo gidana tunda ke bakya so nazo, haka nayi ta kiran wayar ki ranar nan ina unguwarku kika qi dagawa dan kar nazo na sha Ac a Mansion dinki" Dariya Umaimah tayi tace "Ba haka bane Maman Nihal kin san nayi nauyi bana fita yanzu se wadda ta zama dole ko zuwa Asibiti amma in sha Allahu na haihu ai inaga se kin gaji kin ce na sena zuwa, gida na kuma fa sau daya ne kika ce zaki zo ranar bana nan naje gidan Hajiya wayar na cikin jaka amma kiyi haquri qofa a bude take duk sanda kika shirya kizo muna maraba da ke" "Haba na sake zuwa kiqi daga waya in kin ganni a gidan ki to se randa kika zo nawa gidan tukunna kika tabbatar mutum ce ni ba aljana ba sannan zan saka rana nazo miki dan nasan qila har yanzu baki gama yarda dani bane" Zainab sin ta sakw fada se Umaimah tayi dariya tace "In sha Allahu zan wuce gorin nan ki bani Address gobe zanje Antinatal zan fita da wuri idanna gama zan shigo" "Wane Asibiti kike zuwa?" Zainab ta tambayeta se Umaimah tace "Nan UMC nake zuwa" "Amma kin cika kwankwararriyar mara kirki kice ma kusan duk sati kike zuwa layin mu amma baki taba leqo ni ba anya Umaimah" Zainab din ta sake fada kafin taci gaba da cewa "Kamar qarfe nawa zaki zo toh dan in sani kar muyi sabani", se Umaimah tace "Idan zaki fita mu bari kawai se wani lokacin dan se bayan la'asar likitan yake zama, zan yi qoqarine daman na fito da wuri yanda zan zama ta farko dana gama se na biyo" "Aa ba nisa zanyi ba ai kinsan munata shirye shiryen bikin Hamida qanwata saura sati biyu to goben zamuje ganin gida amma inaga da safe ne ma, koma da yamman ne zan iya fasa zuwa tunda zakizo" Zainab ta bata amsa daga nan suka yi sallama bayan sun rabu akan Umaiman zata kira idan tazo Asibitin taji idan tana nan ta qarasa. Bayan ta gama wayar ta koma kusada Khalil ta zauna tareda dora qafafunta da suka tasa akan cinyarta, ture qafar yayi ta bata fuska tace "Haba mana Honey ka matsamun ciwo sukeyi" "Ba kinje kinyi rawa ba ai dole qafa tayi ciwo kuma da kikaje kika zauna acan duk baki san zata qara ciwon ba kina ta shegen surutu se yanzu" Ya fada yana harararta seta yi qaramar dariya tace "Maman Nihal ce fa qawata inaso ma dan Allah gobe daga Asibiti na leqa gidanta kaga kullum se tayi mita" "Wai a ina kuka hadu ne haka?" Ya tambayeta yana kallonta seda tayi masa fari da ido kafin tace "A WhatsApp group din da baka so gashi nan muna ta zumunchi da ita" "Kinga ki raba kanki da kwashe kwashen matan online din nan ba dukkansu ne na kirki ba" ya fada yana nunata seta bata fuska dan tasan yanzu ze fara fadan nasa na ba gaira babu dalili akan WhatsApp tace "Toh kaima fa naga ka hadu da mutane da yawa a online din nan baga Kabir Bala ba ina kace a Facebook kuka hadu kuma yanzu kuna ta harkokin qaruwa da juna" "Ai ban fada miki a group din shashanci muka hadu ba daman a group din qaruwar muka hadu harkokin mu iri dayane shiyasa muka qulla alaqar kasuwancin mukeyi" ya fada jin tana neman ta raina masa wayo, seta juya kai tana cewa "Mune bamu da group na qaruwa kenan se na shashanci kawai mutum shi bazeyi qawance na a rayuwarsa da Mama ce take takuramun yanzu kuma ka karba shi kenan ni banida yanci a rayuwata se abinda kuka tsaramun" "Saboda baki san irin mutanen daya kamata kiyi mu'amala dasu ba dan haka dole se mun saka miki ido, kuma ni wannan matar batayi mun ba bana son mu'amalarku da ita dan bata da kamun kai bata da sirri ki fita a sabgarta" Khalil din ya fada ba tareda ya kalleta ba ta kuwa qara zumbura bakin rashin kunyarta tace "Ai duk qawayena basuyi muku ba nima din ai bayi muku nayi ba daga kai har Maman dan dai Allah yayi babu yanda zakuyi dani ne kawai" Banza ya mata dan yaga alamar so take ta fara tijarar tata. Washe gari kuwa kafin ya fita seda ya jaddada mata akan daga Asibiti be yarda taje ko ina ba ta wuto gida, bata ji ba Qarfe uku ta shirya tsaf cikin wata doguwar riga yar Dubai me kyan gaske, wani Abokin Khalil ne ya kawo mata ita da yaje musu kwanaki bata taba sakawa ba se ranar. Harda simple makeup tayi wai kar Zainab ta rainata ta fesa turarukanta Designer ta kawo zobunanta guda biyu na zinare ta saka a hannu ga Agogonta Versace ta daura da cogen takalmi ta ciro Vinci data tuna Asibiti zata tasan yanzu sa rufeta da bala'i seta mayar ta dauko flat baqi na C&K da yar qaramar jakar sa mw baqi da ja me kyau ta saka. Tuni ta kira me Adaidaitan da yake kaita unguwa duk sanda zata fita ita kadai ba tareda Khalil ba yana qofar gida yana jiranta dan haka ta kulle gidan ta hau suka tafi. Ita aka farayiwa Awon tana gamawa ta kira Maman Nihal ta shaida mata tace ta tsaya a qofar Asibitin yanzu zata turo a taho da ita, ta nemi guri ta tsaya dan ta sallami me Adaidaitan daya kaita tace idan ta gama zata kira shi haka kuwa akayi mintina kadan sega wani saurayi a wata hadaddiyar mota sunzo shida Nihal babbar yarta data gama haddace kamanninta saboda yawan hotunanta da akw tura mata. Babu nisa daga Asibitin nan da nan suka isa, Umaimah ta saki baki kawai tana kallon Aljannar duniya dan gidan na Maman Nihal ya zarce duk yanda take Hasashensa. Seda suka wuce kantama kantaman palour guda biyu kafin suka isa qaramin palour Maman Nihal da haduwarsa bazata fadu ba, tana zaune akan akan kujera ta taso da fara'a ta tari Umaimah ta zaunar da ita tana tayi mata faman sannu da zuwa. Cikin dan lokaci aka cika mata table din gabanta da kayan maqulashe iri iri tadan taba kadan Maman Nihal dai ta rasa ina zata saka Umaimah saboda murna tana ta janta da hira sauran yaranta sukazo suka gaisheta yar tsakiyar data zo ta kalli kwalbar Red wine da aka kawowa Umaimah ta tabe baki tace "Kai harda wannan, na Dady ne fa ko Mommy bata tabawa shine kika bata" cikin tsiwa tayi maganar tana kallon Maman nata abin ya bawa Umaimah mamaki, hannu Zainab takai zata janyo ta ta kwasa da gudu tana cewa "Se naje na gayawa Momy" Zainab din ta shiga kiranta amma bata waigo ba seta kalli Umaimah tana murmushi tace "kinga Sumy tafi duk yan uwanta rigima yarinyar nan" "Ayya daman hakane a cikin yara se ka samu wanda yafi wani qiriniya. Hira suka ci gaba Umaimah na ankare da agogo jira take biyar tayi ta ware kafin Khalil yasan tayi wani wajen. Qarar takun takalmi sukaji daya sa gaba daya suka juya, wata hadaddiyar Macece ta fito fara kyakykyawar gaske da kana ganinta kasan hutu ya ratsa fatarta fuskarta babu yabo babu fallasa tayi musu kallo daya tace "Baquwar taki ce sannu, zan dan fita zaki jirani ne ko zaki wuce". Yanayin maganar tata kamar da Umaimah take amma kuma Zainab take kallo, "Ina nan se kin dawo" Zainab din ta bata amsa se ta dan tabe baki ta saka kai ta fice Zainab din na mata a dawo lafiya. Kan Umaimah ya daure ita kuma wannan wacece da zata zo cikin gidan mutum tana cika tana batsewa kamar nata, kamar kuwa Zainab tasan tunanin da Umaiman takeyi tana yar dariya tace "Anty Maryam kenan Yayata da nake gaya miki tana aure a America, jiya tazo ta sauka a nan ni kaina bason saukar tata nakeyi ba dan gaba daya ta kura mutum takeyi" "Allah sarki" Umaimah tace kafin ta gyara zaman mayafin kanta ta miqe, "Aa badai tafiya ba? Zainab din ta fada itama tana miqewa se Umaimah tace "Tafiya zanyi yamma tayi ai" "Haba dai ki bari idan kikayi magriba kika ci Dinner se Walid ya mayar dake gida amma muna hirar mu zaki wani ce tafiya" "Kai so kike yau Honey ya kulle mun qofa kenan, daman ai biyowa kawai nayi na wanke laifina a denayi mun gori" Umaimah ta fada tana dariya, dariyar Zainab din itama tayi tace "Aiko da sauran laifi kin dai goge kadan se ranar da kika zo kika wunar mun sannan ze goge gaba daya amma banji dadi da zaki tafi baku gaisa da Baban Nihal ba yana gari, kinsan har na gaya masa Mijinki Architecture ne akwai filinsa a Nasarawa GRA da nake ta nacin ya gina mana mu koma toh naga alamar ze yarda idan an tashi shi za'a bawa contract din" "Toh Allah ya tabbatar babu damuwa wata rana idan na sakw zuwa se mu gaisa". Sama ta haye ta dawo da wata leda qarama ta bawa Umaiman sannan ta shiga kitchen ta saka akayi mata packaging ragowar snacks da Dambun naman da akayi mata ta saka Wanda ya dakko ta ya mayar da ita se Umaimah tace Aa driver yana Asibiti yana jiranta irin itaka ta kankarowa kanta mutunchi dan haka suka je ya maida ita Asibitin ta kira me Adaidaitanta da daman beyi nisa ba yazo suka tafi a ranta tana ta yaba kirkin Maman Nihal. Ledar data bata ta bude, turaren wuta ne Al-Haramain  tun bata kunna shi ba tasan zeyi qamshi dan budeshi kawai tayi taji qamshi. Allah sa a wanye lafiya Hajiya Umaimah da sabuwar qawarta *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 28 Umaimah na isa gida ta adana Snacks din nan da dambun nama ta canza kaya ta shiga kitchen dan samarwa da Khalil abinda zeci tasan yana hanya. Soyayyar Taliya tayi an hado mata da peppered turkey seta saka shi a Microwave kafin ya dawo ta dumama dan karya kuma yin sanyi tana aikin tana santin gidan Maman Nihal gida kamar baza'a mutu ba amma kuma se taga a fili tayi mata daban, wannan fresh din da kalar hutun nata na hoto ba sosai ba gara yaran su suna nan yanda take ganinsu harma sunfi kyau a filin. Tana tsaye tana gyara kan Dining bayan tayi sallar Magriba Matar da Maman Nihal takira da yayarta ta fado mata a rai se ta tabe baki a fili tace "Wannan irinsu ne masu shegiyar dagawa da raina mutan dadin ta ma bata ganni a qulaqance ba ahto nima da rufin Asirina qila ma a American a qasan Gada suke (kuji fa sharrin Umai ). "Ke kuma dawa kike faman sambatu" taji an fada daga bayanta ta zabura dan sosai taji tsoro Khalil yayi saurin tareta yana cewa "Kee yi a hankali mana" "Ba kaine ka tsorata ni ba, kuma banji qarar mota ko bude Get ba se jin muryar mutum kawai nayi" ta fada kamar zatayi kuka, seya kama hannunta ya sakko da ita daga steps din Dining yana cewa "Ai bazakijini ba kina faman magana ke kadai inata sallama hankalinki yayi gaba, kedawa kike fada?" "Hmm wata matace fa dazu a Asibiti ta ringayi wa mutane wani kallon raini se kace tafi kowa ita na tuna ta bani haushi nake mita" ta shato qarya ta fada masa, dakinsa ya wuce yana cewa "Kedai Allah ya shirya ki Umaimah rigimarki tayi yawa" tabi bayansa tana qara nana ta masa irin kallon rainin da matar tayi mata dan dagaske abin yaci mata zuciya dan bata son wukaqanci a rayuwarta. Qarar wayarta ce ta dakatar da ita daga taya Khalil cire kayan jikinsa, yace "Yawwa gashi can ana kiranki a waya" dan ta dame shi da shegiyar mita shi kuma ya gaji kansa ma ciwo yake dan wunin Site sukayi. Fita tayi tana cewa "Ni ka kora ko, zaka sake cewa na tayaka wani abune nima sena rama" ta fice kafin ta qarasa wayar ta katse ta dauka Maman Nihal ce tana shirin kiranwa wayar ta sake daukan qara seta daga tareda Zama akan kujera suka gaisa tana tambayarta ya taje gida tace lafiya lau, godiya tayi mata akan zuwan da tayi Umaimah nata bagararwa dan gudun kar Khalil na jiyota yazo ya tusata da tambaya se Maman Nihal din tace "Kinga ban kiraki da wuri ba, order kayan gadon Hamida ne ya iso har an kawo kayan ma nan Kano shi muka tafi dubawa daman dazu can Anty Hadiya zataje ta fara yin gaba se na bita daga baya, duk ma raina ya baci wallahi dan akwai kayayyakina da nayi order babu su a ciki kuma na amfanin bikin ne yanzu ban ma san yaya zanyi ba" "Se haquri shiyasa ni daman ban yarda da harkar order nan ba nafi gane naje shago na dauki kaya na biya kudi" Umaimah ta bata amsa, qorafi Zainab taci gaba dayi mata akan kayan nata da ba'a sako mata ba Umaimah dai ca take se haquri to me zata ce mata fitowar Khalil daga daki ta sakata yi mata sallama ta ajiye wayar suka qarasa kan Dining ta shiga zuba masa abincin, "Ina aka samo Turkey?" Ya fada lokacin daya kai naman bakinsa, taste din da qamshin spices din basuyi kama da na gidansa ba dan bakinsa da hancinsa akwai iya tantance qanshi da dandano. "Anty Hafsa ce ta aiko mun dasu dazu harda Dambun nama da Samosa da spring rolls da wani ko meat bag sunansa oho tasan kana sonsu shine ta bawa Salman dazu da yaje gidan ya kawo mun" Umaimah ta sake yanko wata qaryar a karo na biyu dan bata da wata Mafita seta jingina abin da Anty Hafsa, tasan dai ko haduwa sukayi baze tambayeta ba dan akwai yar kunya tsakaninsu. Gyada kai yayi yaci gaba da cin abincinsa suka gama suka koma cikin palour harta zauna yace ta dakko masa snacks din, sosai dadinsu ya ratsa shi ya kalleta yace "Amma yayi dadi ita takeyi?" "Anya kuwa inaga siyowa tayi sedai na tambayeta naji" ta bashi amsa tana janyo wayarta ta dannawa Maman Nihal kira tana dagawa tace "Honey ne yaci snacks din nan yake santi shine nace bari na tambayeki a gida akayi ko siyowa kukayi" "Ba ita bace, bari na kai mata wayar" taji muryar wani yaro ya fada, daga nesa ta jiyo Maman Nihal din cikin fada tana cewa "Uban waye ya daukar mun waya,muttaqa dan ubanka ba nace ka dena daga mun waya idan an kira ba bani a bata" ta wafce wayar Umaimah na jira taji anyi magana se taji dif an kashe, 'Waye kuma Muttaqa? Yau Maman Nihal ce take hayaniya haka ita da kullum take murya a qasa kamar sarauniya kodai duk bacin ran kayanta da suka bata ne, qila tunda Allah kadai yasan Asarar nawa tayi' Umaimah tayi kidanta tayi rawarta a zuciyarta, Khalil dake faman cin snacks yace "Me tace yayi mun dadi sosai fa damab akwai conference meeting da zamuyi ranar Juma'a ni aka bawa kwangilar abinci a menu din akwai snacks se tayi mana" "Bata jina sosai bari na sakw kiranta yanzu" Umaimah data zama maqaryaciyar qarfi da yaji ta fada tana sake kiran wayar Maman Nihal ta daga da sallama murya qasa qasa irin ta wanda yake cikin damuwa tace "Yi haquri qawata dazu kin kira yarom me aikina wani me shegiyar qiriniya ya shigo ya dauki wayar, a garin na karba ma kinga ya fadar mun da ita screen ya tsage ni ban san ya zamu kwashe da Abban Nihal ba idan ya dawo dan kinga ba ko sati biyu wayar bata rufa ba" "Wai subhanallahi Allah ya mayar da Alkhairi, daman Honey ne yace snacka yayi masa dadi yana so zeyi order zasuyi amfani dashi a kamfaninsu ban sani ba a gida aka yi miki ko siyowa kukayi" Umaimah ta fada bayan data jimanta mata wayarta. Se Maman Nihal tace "Oh dan Allah ai da kince shi zaki kaiwa da an qara miki da Frozen muna dasu da yawa a freezer a gurin wata Baker *MUNATCAKES* nake yin order gaskiya gwanace a harkar yin snacks duk irin wanda kika sani kuma duk wanda yaci seya tambayi a ina akeyi, kin tuna birthday cake din Amal da kika gani kika ce yayi kyau shima ita tayi dan ma bakici kinji dadinsa a baki ba wallahi so soft and moist, yanzu kayan garar Hamida ma ita muka bawa aikin" "Dan Allah kice har kayan gara tanayi, ta iya Alkaki? Dan kinsan a sabgar gara ba abinda nake so kamar shi" Umaimah ta fada se Maman Nihak tayi dariya tace "Duk abinda kikasan anayi da fulawa to *MUNATCAKES* Ogar sa ce, snacks irinsu Samosa, Meatpie, Whole cake, cupcakes, springrolls, meatbag, Cinamonrolls, Doughnut su gireba da duk sauran abubuwan da ban lissafo ba tana yi kuma akan farashi me sauqi" se Umaimah tace "Toh shikenan ki turo mun da lambarta dan Allah yanzu se nayi order nima, zan tambayeta naji ma idan tana koyarwa nima na koya" "Ai kuwa tana yun class na koyar da abubuwan idan kina so din se ki shiga bari na tura miki number Abban Nihal ya dawo mayi magana kota Online ne" Maman Nihal ta fada kafin Umaimah tayi magana ta katse wayar ba'a bata lokaci ba ta tura mata da lamabar *(07046462003 MUNATCAKES)* "Kaji order ne ga number matar ta turo bari na kirata yanzu" Umaimah ta fada tana kallon Khalil daya kusa tada tulin snacks din gabansa, ta cicciba ta miqe tana cewa "Me da me za'ayi order? Kuma pieces nawa?" "Ta tura miki da menu se mu gani" ya bata amsa ta shige dakinta mintina kadan ta fito bayan sunyi waya da me snacks ta tura mata Menu din a whatsapp, kusa dashi ta zauna ta karanto masa kudin ko wanne ya gama lissafi ya fada mata a dadin daya ke buqata da rana da lokaci da inda za'a kai musu suka gama deal take ya tura mata da kudinta. Gulma na cin Umaimah so take ta bawa Khalil labarin irin haduwar gidan Maman Nihal amma bata so ya gane ta biya gidan, haka ta hadiye gulmarta duk da ta qudure a ranta wata rana seta jashi yaga gidan idan zeyi musu gini wata rana yayi irinsa da tsarin gidan ya burgeta matuqa. Haka aka ci gaba da gungurawa zumunchinsu da Maman Nihal nata qara danqo dan a rana idan basuyi waya ba suyi sau uku wato safe rana dare chatting kuwa yanda kasan marasa aikin yi, Khalil yayi fadan yayi Nasihar amma kamar yana qara tura ta ne dan duk uzurin da Umaiman takeyi Maman Nihal ta kira ko tace ta hau WhatsApp zata ajiye ta tafi nata dayaga lamarin nata ya zarce na masu hankali se kawai ya zura mata ido yasan dai duk daren dadewa wannan qawancen ze watse. Bikin Hamida qanwar Maman Nihal saura kwana uku ta dira gidan Umaimah kai mata kati, dukda Umaiman ta shaida mata babu lallai Khalil ya barta musamman idan yaji bikin na waye dan ya tsani Maman Nihal din nan kamar me amma tace ita dai babu ruwanta zata kai mata Kati kuma duk yanda zata qoqarta tazo mata biki tazo tunda dai Edd dinta da saura ai kuma ta rigada tabi yan uwanta kaf ta gama gaya musu sabuwar Aminiyarta zata zo. Ranar da ta kai mata katin aka taki Sa'a Khalil baya gari sun tafi Danbatta tasan kuma dawowarsa se dare dan basu tafi da wuri ba. Tarba tayi mata ta mutunchi dukfa bata kai irin wadda Maman Nihal din tayi mata toh ai zaren ba kalar yadin bane. Suna zaune a palour Umaimah Maman Nihal nata yaba gidan wai ya bata sha'awa dan qarami amma an qawatashi sosai duk wanda ya shigo dole yayi sha'awarsa wayar ta ta dauko qara ta daga da sallama daga nan tayi shiru alamar tana sauraron me magana ne kusan minti biyu ta ajiye wayar tana cewa "Shikenan nagode ai hakan ma kin mun qoqari amma dai mutanen nan sun cuceni wallahi sedai Allah ya saka mun, dole yanzu na nemi wata mafitar da zan fitar da kaina kunya". Bayan ta ajiye wayar duk yanayinta ya canza daga raha da walwala zuwa damuwa dan har tagumi ta rafka hannu biyu, Umaimah dai ta kama bakinta tana kallonta bata ce komai ba, can Maman Nihal din taja numfashi cikin muryar damuwa tace "Nidai wannan Order babu abinda ta janyo mun se asara da bacin rai, na tattara duk kudadena na narka da niyyar idan kaya sun zo da masu su sun karba sun biya in maida wasu yanzu gaba daya kinga abinda aka kawo mun sun zama asara. Ni bama ta tawa nake ji ba yanzu Abban Nihal ya bani kudi na siyi sarqar da zanyi fitar biki da ita dan baya so na saka daga cikin tsofaffin nawa na hada da kudin duka nayo sari, gashi da bin kwakwkwafi tun satin daya wuce daman yake tambayata ina sarqar dana siya nace ban karbo ba wallahi ba qaramin aikinsa bane ya tijarani a taron bikin nan idan be ga na saka tsohuwar sarqa". "Ikon Allah, yanzu toh ganewa zeyi idan kika saka tsohuwar?" Umaimah data zuba mata ido ta fada, se Maman Nihal ta sake marairaicewa tace "Uhm baki san mutumin nan ba kamar wanda Aljanu suke fadawa abu, tunani nayi da naje nayi musanye a kasuwa na karbi wata amma nasan dole se ya sani dan shi yake bada Design din a Dubai ayi mana idan ma na kai aka chanza ze gane tunda duk yan Gwal din Kasuwar Rimi mutanensa ne" Maman Nihal ta sake fada, Umaimah ta tabe baki a ranta tace "Saboda shi yafi kowa ko kuma na'ura ya saka a jiki da idan an siyar ko an chanza zeji a jikinsa, yanzu ina laifin wannan ta wuyanta idan taci bikin da ita?" A fili kuma tace mata "Toh se ki kai wata kasuwar daban ba wadda kika san yasan mutanen ba, idan ma kina so akwai abokin Honey shi a Sabon gari yake nima a gurinsa aka siya mun tawa se na hadaki dashi ki kai masa taki ya baki aron wata da an gama biki ki karbo ta ko" "Eh to wannan ma dabarace, ina takin na gani se ki bani number sa yanzu dana je gida na bayar a akai masa" Maman Nihal ta fada,se Umaimah ta miqe ta shiga dakin Khalil, akwatin sarqar ta dakko gaba daya hatta da Receipt din yana ciki ta bata, Zainab ta bude sarqar tace "Wai wai cancadi gaskiya matar nan kina shanawa Honey yana ji dake irin wannan sarqa haka" ta fada tana kara sarqar a wuyanta, Umaimah ta kalli dambasheshiyar sarqar dake wuyanta da ta tabbatar idan aka auna tayi darin tata a nauyi amma take wani santi akanta tace "Zagina dai kawai kikeyi Maman Nihal kin ganta bata fi wuyan Amal ba ko" "Wallahi dagske ta burgeni, design din very unique kuma tayi kalar nauyi kinsan irin ta manyan Hajiyoyin nan da idan aka auna se sikelinda kansa ya girgiza" Zainab din ta sake fada, kafin Umaimah tayi magana ta sake cewa "Allah yasa Abokin Megidan naki yana da irinta" "Ai kuwa babu dan lokacin ita kadai ta rage itama matarsa ya daukarwa Allah yayi rabona ce, bakiga yanda wasu suka ringa nacin ta ba har wata tace ma zata qaramun kudi na bar mata naqi" Umaimah ta bata amsa, seta maida sarqar ta zaro awarwaron tana gwadasu tace "Ai kuwa gashi zanyi miki fashinta har gida yanzu dan musanye zamuyi, ni kota wuya na ce ki karba kawai ki bar min ita na yafe na se kinyi mun ciko ba idan kuma ba haka ba ki bani aro" ta qarasa tana duba receipt din, se Umaimah tayi dariya tace "Haba ni na isa in saka wannan sarqar so kike a tareni a hanya a kwace,gata nan dai kiyi amfanin bikin idan kin gama se ki dawo mun da ita" Umaimah ta fada dukda yanda takejin zuciyarta sam bata Aminta da bada aron ba, kashedin Mama take tunawa da tace seta ci uban ta idan taji labarin ko gwaji ta bawa wata balle aro dan tasan zata aikata amma kuma mutum kamar Maman Nihal data fi qarfin yar sarqarta ta nuna tana so meye dan ta bata aro dai na kwana daya. "Aa kibar kayarki wasa nake miki zanje gurin nasa in karbi wata dukda dai naso wannan din wallahi" Zainab ta fada tana miqa mata sarqar se Umaimah tace "Kice dai kin rainata bazaki iya saka qaramin abu kamar wannan ba" "Karki mun sharri ni bance haka ba, tunda kin dage zan karba amma sedai na bar miki ta wuyana a gurinki, In sha Allahu da an tashi daga Kamun ba dan dare bama zan biyo na kawo miki da sassafe kuwa zan bawa Walid tunda yaga gidanki" ta fada tana qoqarin cire dan kunnenta Umaimah ta tareta da cewa "Haba dan Allah meye haka kamar wata da zata gudu, ki bar abinki wallahi babu komai kije da ita duk sanda kika gama amfanin seki dawo mun da ita dan ni ba sakawa zanyi ba se ranar Suna idan Allah ya sauke ni lafiya". Dagewa Maman Nihal tayi akan sefa ta barwa Umaimah tata sarqar akan dole ta qyaleta ta cire sarqa da dankunne harda Qwandalelen zobenta ta aje mata akan Centre table kafin ta maye gurin su dana Umaiman ta zura Akwatin a jakarta daidai nan wayarta tayi qara ta dauka tana cewa gata nan zuwa "Masu daura gado ne sun gama zanje na sallamu suna jirana" Ta fada tana miqewa Umaimah ta miqe tareda daukar mayafinta suka fita zata rakata Maman Nihal dinna cewa ta barshi saboda yanayinta tace ai seta rakata har bakin mota, suna kaiwa Get Yaya Naziyya ta turo qofar da ta rigada ta bude, sukayiwa juna kallon cikin ido da Zainab, idonta akan sarqar ta juya ta kalli Umaimah dake cewa "Lah Yah Naziyya daga ina haka zuwa ba notice?" "Kona koma ne?" Ta fada tana harararta se ta saka dariya tace "Ni na isa bismillah shigo sannu da zuwa, Maman Nihal ga Yayata Naziyya ki daina mun gorin baki san kowa nawa ba". Washa baki Maman Nihal tayi ta miqawa Naziyya hannu sukayi musabaha sam ita Naziyyar fara'arta batayi mata ba, kai matar ma gaba daya batayi mata ba ko a ina Umaimah ta kwasota se Allah. Sallama sukayi ba tareda Umaimah ta rakata motar ba ta wuce su kuma suka juya ciki, Kitchen Yaya Naziyya ta fara shiga tana cewa "Ke daga kasuwa nake na kwaso qishirwa bari na sha ruwa nayi alwala" se Umaimah ta shige palour idonta ya sauka akan sarqar da suka bari tayi saurin qarasawa gurinta kwashe su ta wuce dakin Khalil dan tasan Yaya Naziyya da saka ido,yanzu zata tasata gaba da tambayar ya akayi ya za'ayi. Cikin safe dinsa da yake ajiyar muhimman abubuwa ta bude ta saka, kallon sarqar tayi se taga tayi yellow sosai ba kamar tata ba ta tabe baki data tuna ance ai Gwal hawa uku ne qila wannan nw babban ko ta mayar ta rufe jin Yaya Naziyya na qwala mata kira. "A ina kuma kika samo wannan tsohuwar guzuma?" Yaya Naziyyan dake nade abin sallah ta fada tana kallonta se Umaimah ta bata rai tace "Daga ganin mace kawai kice mata tsohuwar guzuma tsabar daukan Alhaki toh qawata ce" "Haka dai tun kina qawancen da sa'anninki har kin fara debo wanda suka kusa haifarki toh ki dai yi a hankali dan yanzu duniya babu gaskiya mata sun baci, ke kuwa ba wayo ne dake bare hankali sedai Allah ya kyauta kawai, duk wannan uban abubuwan ita kika kawowa kenanan?" Harararta Umaimah tayi ba tareda ta bata amsa ba ta nemi guri ta zauna tana cewa "Cikin mutum daya shine kika hado mata wannan kayayyakin saboda Khalil din tsinko kudi yake a bishiya ko?" "To nima dan bakiga tarbar da tayi mun da naje gidanta ba, har shi seda yaci ragowar abinda aka hado mun na taho dasu" Umaimah data zauna a qasa ta fada tana tunzura baki, shi yasa basa shan inuwa daya da Yaya Naziyya dan ita ta fiya saka ido da fadan tsiya. Shareta Naziyya tayi ta janyo kwanon Dambun nama ta shiga ci Umaimah ta kalleta tace "Gashi nan kema ai kinci albarkacinta zaki zo kina cewa wani anyi almubazzaranci" "Kafin nazo gidanki naci abinci kinje nawa kinci sau ba adadi kinga idan ma biyana nace kiyi be isa ba" Naziyyan ta fada a zafafe tana ture kwanon gabanta Umaimah data qunshe dariya ganin yanda ranta ya baci ta mayar mata tana cewa "Allah ya baki haquri bari na kawo miki abinci shinkafa da wake nayi kina ci" bata kulata ba ta wuce kitchen ta zubo mata ta ringa damunta da magana har seda ta sauka daga fushin taci abincin suna yar hira. "Wai ke bakiyi scanning bane an gaya miki me zaki haifaz kuma tanadin me kika fara kinja kinyi shiru shiyasa nace ni bari nazo naji ya ake ciki" Naziyyan ta fada tana kallonta, Umaimah ta shafa cikinta tana yatsina fuska tace "Bansani ba wallahi nace su bari idan na haihu kawai na ga koma menene itama Hajiyar sa da yayyensa haka suka ringa tamabaya kwanaki, tanadi kuma kamar na me bangane b?" "Uhm ke dai ai se addu'a kawai to Allah ya raba lafiya se mu ga abinda aka samu tanadi kuma na kayan haihuwa da abubuwan da ake buqata na tafiya Asibiti ko suma se kin hauhu sannan za'a nemo?" "Lah ni wallahi nama manta tun kwanako fa aka bani wata takadda a Asibitin ta abubuwan da ake tafiya dasu ni ko nuna masa ma banyi ba, kayan baby ma duk nace ya bari se an haihu se a siya ko? Ni duk ba wannan ba na gama wani siye siye ma naje na mutu a gun haihuwa na bar jariri " Umaimah ta fada tana kallonta, Naziyya ta girgiza kai cikeda takaici tace "Eh idan kin haihu se a nade miki babyn a fatar jikinki ai tunda ke sakarya ce baki san abinda ya kamata ba kuma ko mutuwar kikayi ai baza'abar Dan tsirara bako dole yana buqatar kayan da za'ayi masa amfani dasu" "Toh idan kuma dan ne yazo babu rai fa" Umaimah ta sake fada se Naziyya ta shiga tafa hannu tana cewa "Ko wacce me cikin duniya tanawa kanta fatan sauka lafiya banda ke Umaimah? Nan maganin Zaqi ance da aka kawo miki kinqi sha wai Honey yace ba'aso me ciki na shaye shayen magunguna barkatai ko zakiga Honey a labour room, Allah ya saukeki lafiya idan kuma silar tafiyar ce Allah ya karbi shahadarki kinji" Naziyya ta fada tana miqewase kawai Umaimah ta fasa mata kuka ta saki baki tana kallon ikon Allah to kukanna menene kuma? Cikin Kuka Umaiman tace "Wato daman fata kike mun na mutu ko toh in sha Allahu lafiya lau zan haihu in reni Dana ko Yata" "Fatan mu a kullum kenan Allah ya raba ku lafiya, kinga bari naje daman Mama ce jiya mukayi maganar nace zan shigo naji ya ake ciki tunda naji bari na wuce" Naziyya ta fada tana sabar jakarta dan bazata iya da jidalin Umaimah ba kafin ta qulla mata wani sharrin kuma tace tayi mata. Naziyyan na fita ta share hawayenta ta shiga tattare kayan da suke gurin, ta gyara ko ina tsaf ta kunna turare daidai aka fara kiran sallar magriba ta wuce tayi Alwala ta tayarda Sallah, tana cikin lazumi taji ana buga Get taje ta bude bayan data tambayi waye, Rufaida ce sabe da yarta Anam da gani daga unguwa take tace "Amarya kin ganni da magriba ko wallahi in gaya miki ashe na manta muqullina a cikin gida shi kuma ya fita ya kulle se yanzu dana dawo ina sauri na duba banganshi ba" "Wai irin haka akwai ciwo musamman ka dawo kana da wani uzuri ki shigo ciki toh kafin ya dawo". Ciki suka shiga Rufaida ta yi Alwala Umaimah ta na yiwa Anam wasa harta idan kafin ta tashi ta kawo mata ruwa da abinci ta karba tana cewa "Kamar kin san Yunwa nakeji wani biki naje in gaya miki abu dai tsiya tsiya ko yar shinkafar dai aka saba babu" "Allah ya rufa asiri toh" Umaimah ta bata amsa tana danna Remote ta kunna musu Zee world. Kamar an matsi bakinta ta waiwaya ta kalli Rufaida take cin abinci hankali kwance Shinkafa da wake da mai da yaji taji danbun nama tace mata "Dazu kuwa Zainab Ladan tazo gidan nan" "Wacece Zainab Ladan kuma?" Rufaidan ta tambayeta se tace "Wannan ta sabon group din da kika sakani mana baki ganeta ba Zainab Ladan wadda naji suna cewa Zeezy QQ" "Zeezy Qarya Qarya zaki ce mun, me tazoyi gidan nan shegiya wato ta ganki kalar lasa shine zata maqale miki yaushe ma kuka fara mutunchi har da zata zo gidanki?" Rufaida data ture abinci gefe ta fada tana kallon Umaimah. *Assalamu alaikum barkanku da wannan lokaci,to damuna tazo fa gida saida kamshi, Turaren 2SISTER HEAVENLY SCENT ba yabon kai ba idan aka kona a daki kamshi har Maqota .2sisters sunada nau'in turaruka kamar haka:* *Turaren wuta kala kala*, *Humra baka da fara,* *Kwalacca,* *Air freshener da sauransu* *Masu biki bayan sallah 2sisters suna yin na rabo,za ku iya siya ku bada gudummawa akan parashi me sauki daidai aljihunku.* *Location kano*. *07068387382, 09161661999* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 29 "Bangane Qarya Qarya ba, yar qarya ce ko kuwa dai irin iskancin da yan group din suka sabane su sakawa mutum sunan banza" Umaimah ta fada itama tana kallonta can qasa zuciyarta na tsinkewa, Rufaida ta watsa shinkafa a baki ta taune tace "Tab ke tambaya ma kikeyi yar qaryace ko yaya? Baki taba jin tana sheqa qaryar tata a group ba ko kiga ta turo abubuwa irin a zuwan ba nan zata turo ba ko tace yara ne sannan duk abinda yaka fada se tace ta sanshi ko tana dashi koda yake qawarki ce ke ya kamata ma ki bani labarin qaryar tata ai". Tsaki Umaimah tayi tace "Ni wallahi na dauka ma wani abun ne saboda duk tsomaye aka tara a group din shiyasa suke ganin duk abinda tayi ko ta fada qaryane, nifa shiyasa kikaga na dena magana sosai tunda wata tace wai ina maqe murya idan ina magana suka nemi sumin taron dangi nayi musu tas shiyasa na rage kula yan group din nan dan naga duk masu kalan wayewa ne suke claiming su wayayyu ne, Maman Nihal kuwa ni  dana ganewa ido na zahiri akanta ai bazan musa mata ba, ai da nasan kallon da kike mata kenan na yar qarya da dake zamuje gidanta wallahi ki ganewa idonki, amma ki shirya Wani satin bakin qanwarta dukda da bazanje ba amma yanzu ko dan ke da sauran munafukan yan group zamuje, ga katin nan ta kawo mun dauka ki gani" Umaimah ta qarasa tana miqa mata hadadden katin gayyatar Kamun da aka Rubuta sunanta wato Zainab Ladan a matsayin me gayyata. Rufaida ta karba tana bude baki cike da mamaki tace "Dan Allah dagaske yanzu duk wannan Aljannar duniyar da take daukar hoto a ciki ki cemun gidanta ne, kinga wasu danqara danqaran daham da take sakawa kuwa kai ni Umaimah ina tantama gani nakeyi kamar dakko hoton irin hamshaqan matan nan takeyi a IG" "Se kiyi ai, nan nan Third Get gidanta yake cikin sabuwar Abuja, qarshen tika tika dai ki shirya muje bikin qanwarta ki ganewa idonki" Umaimah ta sake fada, "Aikuwa Allah ya kaimu dole ma naje na kashe qwarqwatar ido na dan indai da gaske itace wannan hamshaqiyar dole bikin na manya ne za'a gwangwaje. Umaimah dai shiru tayi, tana jin kamar ta gayawa Rufaida zancen aron sarqarta da tayi amma tayi shiru haka suka ci gaba da hira har kusan takwas da rabi kafin mijinta ya kirata akan ya dawo suka fita ta rakata daidai sanda Khalil shima yayi fakin a qofar gidan. Haka aka qarasa cinye sati daga Umaimah har Rufaida babu wanda ya samu zuwa bikin Hamida qanwar Maman Nihal, a ranar Umaiman ta tashi da ciwon Mara dan har seda sukaje Asibiti aka ce ba haihuwa bace da saura itama Rufaidan ashe Anam ce tayi fama da zazzabi seda aka kwana biyu ta shiga take gayawa Umaimah daga nan suka yanke idan Umaimah zataje asibiti zata rakata se su je gidan. An yi bikin Hamida da kwana uku Maman Nihal ta aiko mata da uban hilin kayan fulawa na gara harda su soyayyun kaji da dambunsu ko wanne cikin Farin bokiti qarami, me delivery ta bawa ya kawo mata tana zaune kawai aka kirata wai ga saqo inji Maman Nihal Janbulo lokacin Habiba Qanwar Khalil da Sharifa qanwarta yar dakin Anty suna gidan saboda anyi hutun makaranta sukaje tayata zama saboda Khalil din be cika zama sosai ba saboda aiki. Bayan sun karbo saqon ta bincike tas bata ga abinda take tsammani ba koda yake ya za'ayi ta bawa me delivery sarqa ya kawo mata itama ta bada tata ya kai mata ai ganganci ne seta shiga kiranta a waya, sau biyu ta kira wayar ta qaraci ihunta ba'a daga ba, tunanin yi mata magana a WhatsApp tayi dan daman tunda suka fara bikin basu yi waya ya kai sau uku ba sedai a WhatsApp shima atsaitsaye saboda Zainab din itace kamar uwar Amarya ita ce akan komai. Dadi taji ganin tana online tayi mata sallama tareda godiyar kayan da aka kawo har tana cewa sunyi yawa kafin tace mata "Da zan bada sarqar ki ya kawo miki se naji tsoro ban san ko na gida bane kin saba harka dashi kuma nayi kiran wayarki baki amsa ba" "Kedai kice kina mun tunin sarqar ki Amma ni tawa ko shekara zatayi babu damuwa ki ci gaba da ajiye mun, taki kuma abinda yasa ban bayar ya taho da ita ba gaskiya ban sanshi ba wata ce ta hadani dashi Walid nake so na bawa ya kawo miki dan ma bazan samu shigowa da kaina ba dan yanzu haka ma kin ganni muna Aiport zamu tafi America kai Amarya, kinsan da na gaya miki babu yan rakiya se fa jiya uban mijin yace wai bazeyuwu ace babu wanda yaje yaga dakinta ba" Maman Nihal ta turo mata da dogon voice note, Mamaki ya kama Umaimah dan gaskiya bata tuna sunyi zancen Amwrica za'a kai Hamida ba ta dai gaya mata a Tarauni gidanta yake amma Mijin a Abuja yake aiki bayan biki zasu tafi can to qila kuma chanjin shawara suka samu abun na masu dashi, Vn din tayi mata tace "Toh Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, babu damuwa ki bawa Walid din idan yazo kinga ma sena bashi takin" "Kawo miki in sha Allahu bari naje an fara kiran mu idan mun sauka zamuyi magana" Maman Nihal ta bata amsa kafin ta sauka offline. Warkaja min su sukaji gaba dayi da kayan gara, koda Khalil ya tambayi daga ina tace masa Mama ce tasa akayi mata tace tana so ya ringa mata fadan cin zaqi dukda be yarda Maman bace ta bayar sedai idanda kudinta ta saka akayi mata zata fake da cewa Mama qarshe da Habiba da Sharifa zasu wuce ya kwashe ya raba musu suka tafi dashi. Seda aka kwashe sati biyu babu Maman Hanif babu labarin zuwan Walid, da farko Umaimah ta shiga damuwa amma data tuna akwai tata sarqar a hannunta se taga babu amfanin damuwar dan ko riqe waccen tayi tasan taci riba akanta dan wannan tafi tata daraja ko daga gani a ido ma. Sati biyu a tsakani ta tashi da naquda, cikin ikon Allah zuwan su Asibiti a qasa da awa biyu se gashi ta haifo qaton danta me kama da Khalil kamar yayi kaki ya ajiye, haka suka tafi ziqau babu ko kyallen da za'a lullube jariri dashi dan dama shi Khalil be san ana tafiya da wasu kaya ba, a tasa wautar ma a Asibiti akw bayarwa duk se ayi maka bill ka biya shiyasa be taba ma tambayarta wani ko da akwai abinda za'a tanada ba, kayan barka da Hajiyar sa tayi masa magana kadai ya sani kuma ya gama dasu dab tuni ya bada kudin komai yace kar su siyi riguna dan basusan abinda za'a haifa ba. Metron din tayi musu uzurin qila basu san haihuwa bace tunda a EDD dinta na farko ma tana da sauran kusan sati daya dan haka ta ari zani a gurin wata da take labor itama aka nannade yaron bayan an gogeshi tacewa Khalil yaje ya kawo abubuwan buqata. Kaitsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, kamar daga sama taji labarin haihuwar ga kuma zancen ai basu je da komai ba dan shi bema san me za'a dauka ba koda yake daman me suka ajiye a cikin gidan. Fada ta ringayi masa ta hada duk abinda ya kamata daga wanda suka siya sannan suka wuce can gidan tace ya dibo mata kaya kala uku masu zani, dakyar aka samu daya qarshe se dogayen riguna ya diba suka wuce Asibitin acan suka tarar da Mama da Anty harda Maman Asad dan ita ya fara kira ya gayawa ita kuma ta gayawa su Maman. Sun tarar da Mama akan Umaimah tana surfa mata fada ga Jaririn da ya sha nadi a zanin Atamfa saboda sanyi a hannun Anty, Hajiya ce ta shiga tayi sasanci Mama tace "Banda wauta da shirme Hajiya ka taho haihuwa babu ko rigar da za'a sakawa Jariri, daidai da Pad da zatayi amfani da ita fa se ara akayi ni na rasa me yake damun wannan yarinyar sam ace bazata ringa abu irin na masu hankali ba" "Haquri za'ayi abin barkar dai an samu kai qalau duk komai daga bayane gashi nan an kawo se a mayarwa da wadanda akayi aron a gurin su" Hajiya ta fada tana nuna mata qatuwat Akwatin data shaqo da duk abinda tasan za'a buqata, hatta Tissue paper sedata dakko. Mama bata haqura ba seda ta kuma yi musu tas daga ita har Khalil din kafin ta kama hanya Salman da ya kaisu ya maida ita gida ta bar Anty dan daman abinda ya kaita kenan taje ta karantawa Umaiman. A Asibitin suka kwana se washe gari aka sallame su aka wuce da ita gidanta tareda Anty da zata zauna mata kwana bakwai zuwa ayi suna kafin su koma can gidansu taci gaba da wanka dan haka sukeyin Al'adarsu. Khalil be saka a ransa ze bari ta tafin ba dan baya jij ze iya rabuwa da Dan babyn nasa da yake ji kamar ya hadiye shi tsabar qauna, ance dashi yake kama amma shi yafi hango kamannin Umaimah a fuskar yaron dan idonsa, bakinsa duk nata ne hancin ne da yanayin fuskar irin nasa kawai shidai Addu'arsa Allah yasa karya kwaso masa halin Tijararta. Jego me kyau Anty ta dage tanayi mata suna samun kulawa daga ita har yaronta da Khalil yayiwa huduba da sunan Mahaifinsa Umar Bayero zasu ringa kiransa da Mu'ayyad, ranar kwana biyar aka kawo kayan barka daga gidansu Khalil, kaya wane kaya dan bayan wanda ya bada kudi aka siya yan uwa da abokanan arziqi sun ringa kai nasu Aka hado komai rigijib lefen dangata aka kaiwa Umaimah washe gari kuma aka kawo na gidansu shima sunyi qoqari sosai da sosai sukayi Babyn da ita kanta kaya. A ranar Maman Asad ta karbo mata dinkunan kayan da zatayi fitar suna dasu Wanda daban Khalil ya bada kudin aka siye su, kayane kala biyar Atamfa biyu, Lace biyu se Shadda guda daya da sukayi anko dashi zasu saka da safe. Duk wani abin amfanin suna an tanada kama daga abinci da sha da kayan rabo sunyi komai cikin tsari ranar suna aka yankawa Yaro manyan ragunansa guda biyu ga su Biscuit alawa da dabino duk wanda ya shigo barka yan unguwa se an bashi. Da safiyar tasha kwalliya da danyar  shaddar da sukayi anko da Khalil, Habiba ce tayi mata dauri me kyau dan ita din gwana ce gurin kwalliya dan ma Umaiman tace ba sannan za'ayi mata make up seda yamna dan haka hoda da man lebe kadai ta saka aka ringa kashe musu hotuna da babynsu daya sha kaya na alfarma yana ta bacci abinsa. Kafin Azahar gida ya dinke da jama'a daga bangarenta har zuwa Na Khalil ta ko ina se bubbulowa sukeyi dole se wangale Get din gidan akayi suka saka kujeru tu daga waje har ciki dan daman an tanade su kafin yamma su koma cikin Wani Kango dake gefensu na Mijin Maman Hibban ne su Anty Hafsa suka roqi alfarma aka ara musu tunda taqi bari a fita a kama guri kamar yanda sukayi Na Nuratu sunce duk da haka se sun dakko Dj sunci uwar sabada yau Umaimah Qiriniya tayi Da. Tunda tayi kwalliyar shaddar Anty Hafsa take baza ido taga ta saka sarqarta taga wayam se wata fashion me kyau ta saka se tayi tunanin ko ta bari ne da yamma idan tayi kwalliya sannan zata saka haka kuwa akayi bayan la'asar me kwalliyar da suka kira ta gama tsatsowa Umaimah kyanta dukda ba wata me yawa akayi mata ba, ta daura mata gwagwgwaronta fuskar nan ta fito tas kamar ranar ne auransu da Khalil tasha kwalliya da wani Dan ubansun Lace da akayi mata dinkin fitted Bubu ta cikata saboda qibar da tayi se hakan ya qara fitar da kyan dinkin da kwalliyarta. A dakin Khalil ta qarasa shiryawa tana tsaka da saka dankunne Anty Hafsa ta shiga dakin cikin kwalliya tana kallonta tace "Kai Umai kinyi kyau masha Allah daman ga Khalil can a waje bari a kirashi yazo kuyi hoto kar kwalliyar ta tafi a banza" harta juya idonta ya kai kan sarqar data saka seta dawo tana cewa "Aa ya haka? Wai ina sarqar ki ne da kike ta fama da wasu fashion malama dakko ta ki saka ko kuwa daman dan ki ajiye aka siya miki" "Kin rigani jira nakeyi in idar da Sallah nima nayi mata magana tun safe nake saka ido naga ta saka ban gani ba" Anty Laure data idar da sallah ta fada. Se Umaimah ta shiga zare ido, gaban Safe box din Khalil ta isa ta bude gurin security swta kalli Anty Hafsan tace "Ya kulle kuma bansan password din ba" "Se ki kirashi a waya ya gaya miki ai meye amfanin siyan ta idan bazaki saka a gani ba" Anty Laure ta sakw fada tana miqa mata wayarta,bata da mafita ta karba ta hau danne danne a ranta tana shirya yanda zata kufcewa wannan tuhunar tasu, to me zata ce musu? Kusan kwana goma kenan rabon da suyi magana da Maman Nihal, daman tunda tace mata ta tafi America suka dena waya a WhatsApp suke chatting tace mata Walid din ya koma makaranta daga baya kuma tace wai ta manta ta tafi da key din dakin nata sedai idan ta dawo kuma zasu biya Saudiyya suyi Umara a taqaice dai se nan da kusan wata daya take shirin dawowa daga baya ma ya zama idan tayi mata magana baya tafiya duk da har sannan Umaiman bata kawo komai a ranta ba, se jiya data kira layin Maman Hanif din taji ya shiga har ta daga se kuma ta kashe daga nan kuma take ta kira baya shiga abinda yasa hankalinta ya tashi kenan da rashin sanin abinda take nufi da ita kuma ta rasa dawa zatayi maganar tunda babu wanda yasan sanda akayi sedai idan ta tuna da tata a hannunta hankalinta yana kwanciya yanzun ma gudun tambayoyi ne ze hana ta saka ta Maman Hanif din. "Anty yace baze iya ratso cikin mata ya shigo ba kuma fingerprint ne security din" Umaimah data gama qayar qarya ta fada, Anty Hafsa da Anty Laure suka kalli juna kafin suka fita suka barta ta qarasa shirinta a ranta ta qudure zuwa gobe idan bata samu Maman Hanifa gaskiya zata bada akai sarqar nan kasuwa a siyar, ta cire kudin tata ta siyi wata ragowar ta tura mata tunda tana da account number ta data karba ta tura mata da 20k a matsayin gudummawar bikin Hamida wanda dakyar ta turo matan. Ansha taron suna an raqashe kkwa ya koma gida cikin farin ciki, daga gurin suna Anty Hafsa kaitsaye gida ta wuce gurin Mama dan ita bataje gidan sunan ba wai me zataje tayi duk ga sunan Hajiyar Khalil dai taje abinta da sauran yan uwanta. A taqaice Anty Hafsa tayiwa Maman Bayanin ita fa bata yarda da zancen Umaimah ba dan idan dagaske ne da tun safe zata saka ya bude mata ta dauki duk abinda zatayi amfani dashi ai Mama tace mata ta rabu da ita kar kuma tayiwa kowa magana ai gobe zata zo gidan ta sameta. Haka kuwa akayi washe gari da wuri sukayi suyar nama suka raba kowanne bangare suka dauki nasu, daman sun gama shirin su tsaf Anty ta kira Khalil daya fita tun safe akan zasu tafi yace besan zance ba, kashe wayar tayi ta kira Hajiyarsa dan tuni sun gama magana da ita tace ba matsala su jira kusan minti Ashirin se gashi yana cika yana batsewa haka yaje ya kaisu gida. A tsohon dakinsu da yake a gyare dan anan Nuratu ta zauna, ana gobe Umaimah zata haihu tayi arba'in ta koma gidanta dan haka qara shareshi kawai akayi aka zuba musu nasu kayan. Se dare Mama ta sameta a daki tana zaune tana shayar da Mu'ayyad suna magana da Khalil dake ta faman zuba qorafi a waya, jiranta tayi harta gama sannan ta kalleta tace "Ranki ya dade banga kinsaka sarqarki a hotunan suna ba, bata tayi ko kinyi kyauta da ita" "Mama nafa gayawa Anty Hafsa tana cikin safe box din Abban Mu'ayyad kuma lokacin akwai mutane yace baze iya shigowa ba amma tana nan babu inda taje hauka nake zan bada aro? Mantawa nayi ma dazu da mun taho da ita amma zance ya kawo mun" Umaiman ta fada tana zumbura baki, Mama tayi qwafa tace "Zaki ci ubanki keda Safe box din, Allah ya kaimu goben ki kira Khalil din kice ya kawo mun da safe kafin ya wuce aiki" "Haba Mama kamar wani abin tashin hankali, a bari dai da daddare idan ze zo ganin mu seya kawo" ta fada tan dan murmushi, Mama tayi qwafa ba tareda tace mata komai ba ta fita. Seda aka kwashe sati biyu tsakani Mama bata sake yi mata magana ba itama kuma da ba gaskiya ce da ita ba daman bata tada zancen ba, kullum cikin gwada layin Maman Nihal takeyi amma amsar daya ce a kashe yake a group ma tayi cigiyarta aka ce tace ta tafi America har Rufaida na mata tsiyar ita da Aminiyarta ai ita za'ayi cigiyar Maman Nihal a gurinta. Da safe ranar Mama ta sake tirketa da zancen, Umaimah tayi fiqi fiqi da ido dan qaryarta ta qare Mama waya ta dakko tace zata kira Khalil din, cikim muryar damuwa tace "Mama dan Allah karki kirashi, abinda yasa kika ga ina tayi miki kwana kwana wallahi sarqar Khalil din ne ya karba. Wata kwangila yakeyi kudi suka yanke masa, shine ya karba yace idan an biyashi se ya mayar mun da wata". Kallonta kawai Mama takeyi har ta kai qarshen maganar, kwata kwata zancen be shiga kanta ba amma kuma bazata ce bata yarda ba saboda yana iya zama gaskiya Khalil din ya karba se kawai ta miqe tana cewa "Toh Allah ya rufa asiri tuntuni me yasa baki fada ba kika tsaya kina nuqu nuqu" "Shi yace mun baya so kowa ya sani kawai idan ya samu kudi ze siyamun wani" Umaimah ta fada tana dauke kanta gefe, Mama ta kalleta, bata yarda da zancen nan ba amma koma yayanw zata bincika taji dan lamarin Umaimah babu Allah a ciki. Hafsa ta kira take shaidawa yanda sukayi da Umaiman, "Zata iya yuwuwa Mama tunda kinga yayi hidima sosai da sunan nan ze mayar matan kamar yanda yace" Anty Hafsa ta fada. Mama bata haqura ba ta kira Naziyya, tana shaida mata ta bushe da dariya tace "Kuma kin yarda Mama, Khalil din ne ze karbar mata sarqa ya siyar idan zeyi haka me yasa tun farko ya siya mata, ai seya bar kudinsa ya gama kwangilar sannan duk abinda zeyi yayi ko? Qarya takeyi ki matsata zata fadi duk inda ta kaita sedai idan kuma itan ce ta siyar wannan se muji inda takai kudin. Nidai akwai ranar da naje gidanta ta rako wata baquwa idan dai ba idona bane to sak sarqar na gani a wuyan baquwar". "Ai kuwa dole ma ta fadamun yanda tayi da ita dan sam hankalina be dauki cewar Khalil ne ya karba ba, amma zanyi maganinta, Khalil din zan tambaya da kaina duk ma yanda akayi zanji" Mama ta fada daga nan sukayi sallama. Barinta tayi seda aka kwana uku tsakani ranar Khalil yazo da daddare, yana zaune a dakin da Umaiman take yana cin tuwo, Mu'ayyad na hannunsa yaron yayi bulbul dashi tabarakallah bazakace dan kwana Talatin da wani abu bane. Mama tayi sallama a bakin qofa suka amsa ta daga labule ta shiga, seda suka sakw gaisawa a zuciyar Umainah tana ayyana maganar qarin kwanaki akan Arba'in din sune dan yan gidansu duka zasuyi tafiya zuwa Qaraye bikin diyar wani Abokin wasan Abbansu kwana biyu bayan Arba'in dinta, shine tace Anty ta sa baki Mama ta yarda A tambayi Khalil ta qara sati daya suje tare. Rigigib qirjinta ya buga sanda taji Mama na tambayar Khalil zancen sarqa, ko kusa bata taba zaton Maman zatayi haka ba shi yasa data tashi ta jona qaryar dashi, Khalil ya saki baki tsabar mamaki yana kallonta Mama dake kallonsu gaba daya tayi murmushin takaici dan yanayin fuskarsa ya fahimtar da ita besan zancen ba. "Wallahi Mama ko naira hamsin ban taba ranta a hannun Umaimah ba ballantana na karbar mata sarqa na siyar, nifa kyauta na bata bayan haka ba kudi na ne kadai a ciki ba harda naki idan ma zan karba ai se nace tayi shawara dake sannan" Khalil ya fada yana kallon Umaimah data duqe kai qasa kamar ta fasa kuka. Mama ta kalleta tace "Zaki fadi inda kika kaita ko kuwa har yanzu kina da sauran qaryar da zaki fada?" "Wallahi Mama qawata ce ta ara kuma sun tafi America da Mijinta se qarshen watan nan zasu dawo nasan idan na gaya miki fada zakiyi amma akwai tata a gurina kuma tafi tawa tsada na sani" Umaimah ta fada tana janyo qaramin Kit din kayansu ta bude, Sarqar Maman Nihal ta dakko ta miqawa Mama ta karba tana cewa "Wace qawar taki, Rumasa'u ko Halima?" Seda ta kalli Khalil da mamakinta ya hanashi magana kafin cikin rashin gaskiya tace "Maman Nihal, baki santa ba" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wace shegiyar barauniyar kika bawa sarqarki ta baki ajiyar wannan?" Mama ta fada cikin jimami tana daga barawon gwal din da Maman Nihal ta bawa Umaimah a matsayin zinaren gaske. "Barauniya kuma Mama, baki ga girmansa ba yafi nawa ko? Tace nawan yana nan gidanta a Janbulo ta barwa Driversu ya kawo mun, idan ma baki yarda ba kawai ko siyar dashi ma za'a iyayi in dauki kudin nawa in tura mata sauran idan yaso ta riqe wancan dan inata nemanta a waya bana samunta har a WhatsApp kamar ma ta canza lamba ne ban sani ba" Umaimah ta fada, se Mama ta wullo mata qwandalelen kwadon sarqar ya same ta kuwa a goshi ta dafe tana cewa "Kai Mama daya sameni a ido fa?" "Ai gara ya sameki a idon yar banza mara hankali, banda kwakwalwar kifi ce dake wannan yayi miki kama da zinare? In banda hauka da rashin sanin ciwon kai a ina kika hadu da matar dan ni ban taba jin sunanta ma a gidan nan ba shine zaki dauki sarqar kusan miliyan biyu ki bata tunda bada guminki aka siyo ba, to zaku ci ubanku daga ke har ita ba America ba ko bangon duniya ta tafi seta fito dashi, ina kinsan gidanta tashi maza maza yanzu zamuje duk wadda za'ayi ayita a daren nan tashi muje" Mama ta fada tana miqewa se a sannan Khalil ya iya bude baki yace "Mama ayi haquri yanzu dare yayi zuwa da safe idan Allah ya kaimu se aje tunda tace ta san gidan matar, ni daman tun asali mu'amalar su batayi mun ba saboda yanda matar sam bata da sirri komai ya seta fada" Umaimah ta harareshi Mama tace "Khalil gara muje tun yanzu dan jikina ma baya bani za'a samu sarqar nan amma dukda haka muje mu kama barauniyar zaune dan kwandala bazatayi ciwo ba idan babu sarqa seta bada kudinta" "Wai dan Allah waya ce guduwa tayi matar da tafi qarfin dan wannan abin shine duk za'a ringa wani tashin hankali kuma wannan Mama idan baki yadda me kyau bane a kaiwa Bashir mana ya auna a gani" Umaimah ta fada tana zumbura baki Mama ta kai mata mari tana gocewa tace "Wallahi sena bata miki rai idan baki rufemun baki ba sakarya da bata da tunani, idan rashin mutunci ne da tsiya kala kala babu wadda baki iya ba amma kwakwalwarki sam bata aiki balle tayi tsinkaye, yanzu zamuje idan kuma qarya kikeyi mata dan ubanki duk idan munje maji yanda akayi". Mama ta dage akan adaren nan qarfe kusan goma za'a tafi idan Maman Nihal dakyar Anty da ta shiga itama suka hadu da Khalil suka lallabata ta bari seda safe, washe gari kuwa qarfe takwas bata cika ba Mama ta tasa Umaimah a gaba suka tafi gidan Maman Nihal Salman ya kaisu dan Mu'ayyad ma a gurin Anty suka barshi yana bacci. A bakin babban Get din gidan salman ya faka mota, Megadin dake sanye da Uniform ya fito suka gaisa yana tambayarsa gurin wa suka zo haka Umaimah tace gurin Maman Nihal, "Amma bakusan dokar gidan nan se Hajiya ta bada umarni daga ciki baqo yake shiga musamma ma ku da kuka dako wannan sammakon, ku kirata a waya, zata bamu unarni idan tace a barku ku shiga toh" Me gadi ya fada musu kafin ya koma can bakin qofa inda sauran yan uwansa masu gadi suke. "Se ki kirata, gadai gida nan har gida amma matar ciki yar damfara" Mama ta fada tana hararar Get din kamar shine Maman Nihal, Umaimah ta kira layin kamar kullum dai a kashe ta kalli Mama kamar zatayi kuka tace "A kashe take Mama, dan Allah kiyi haquri mu koma gida nasan ba guduwa tayi ba gadai gidanta kin gani idan lokacin da tace zasu dawo yayi bata dawo mun dashi ba sannan se a dauki kowanne mataki" "Karki fita kisan yanda zakiyi su bude miki get din" Mama ta fada ba tareda ta kalleta ba, haka Umaimah ta fita daga motar kamar zata rusa kuka daidai sanda aka bude Get din mota ta fito, ta gane driver wanda Walid shine ya dakkota wancan karon da tazo ga su Nihal a baya da uniform ze kaisu makarantaya tsaya dan ya gane ta shima, Niihal ta leqo tana dagawa Umaimah hannu itama ta daga mata ta qarasa jikin motar Nihal din ta gaisheta "Mamanku tana ciki?" Umaimah ta tambayeta ta daga mata kai, seta maida kallonta kan Driver tace "Inata kiran wayar Mamansu bata shiga Me gadi kuma yace se na kira ta bada umarni ze barmu mu shiga". Shi yayiwa masu gadin magana suka bude musu shi kuma ya wuce kai yaran makaranta. A palour na farko akayi iso, Mama tabi palour da kallo tana tabe baki kusan minti goma sha biyar sannan Maman Nihal ta shigo palour da sallama ciki ciki kamar wadda akayiwa dole jikinta sanye da kayan bacci alamar tashinta kenan. Kallon Umaimah tayi da mamaki kamar yanda itama take kallo ta, cikin muryar isa tace "Baiwar Allah lafiya, ko kinyi mantuwa ne a gidan nan?" Maman Nihal ta fada tana kallon Umaimh, "Saqon na da Maman Nihal ta bari nazo karba" Umaimah ta bata amsa kai tsaye, seta kalleta irin kallon bangane abinda kike nufi ba Mama da gaba daya haushin matar ya cikata bama itace Maman Nihal din ba kenan ta harareta tace "Sarqa da Maman Nihal ta ara a gurinta tace ta barta a nan ita muka zo karba" "Ban gane me kuke magana ba akai Hajiya nice Maman Nihal ko wata daban kuke magana a kai, kedai na ganeki kece qawar Abu da kika zo kwanaki lokacin kamar kinada tsohon ciki koh" Matar ta fada tana kallon Umaimah, se Mama da Umaimah suka kalli juna jin wata sabuwa kuma, Itace Maman Nihal, wace ce kuma Abu da take fada??? *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 30 Wayarta ta danna alamar kira bayan an daga tace "Walid idan ka dawo ga baqi nan a palour ka kaisu gidan Abu" tana gama magana ta miqe ta kalle su tace "Za'a raka ku gidanta yanzu" "Ban gane za'a raka mu gidanta na ita wa kuma ke din wacece?" Mama ta fada tana miqewa tsaye itama ganin Maman Nihal din ta juya, seta kalli Mama tace "Ita wadda kuke nema din nan ba gidanta bane, kuma ba wannan ne karo na farko da tayi qarya da sunana ko gidana ba amma wannan ne na qarshe, kuje can ku warware matsalarku ni ban san komai a kai ba" tana gama fadan haka ta juya ta barsu a palour. Mama ta tafa hannaye tana salati Umaimah dai tagumi ta buga to idan Maman Nihal qarya take yi wanne irin kusanci ne da ita da wannan matar to da har ta bata damar shiga gidanta tayi abinda take so kamar matar gidan. Zuwan Walid ya sakasu tashi suka fita, a motar da suka zo suka dunguma gaba daya Walid na gaba yanayiwa Salman kwatance tiryen tiryen har suka isa Unguwar Hausawa ya nuna musu wani gida ginin bulo ne amma babu fulasta ta wajen yace musu nan ne daga nan yayi musu sallama ze juya Mama ta dakatar dashi tace "Ina zakaje, ai se mun shiga mun tabbatar ita dince ka kawo mu gurinta kafin ka bar nan dan bangama yarda daku ba" "Walid yayi murmushi ya qarasa soron gidan suna biye dashi daidai sannan wata yarinya da bazata haura shekaru goma ba ta fito daga gidan, cikin fara'a ta gaida Walid ya tambayeta Mamansu tana ciki tace eh ta juya tana cewa "Bari na gaya mata kazo" ya dakatar da ita da cewa "Aa wuce aikenki Amina baqi na rako zasu shiga ciki" seta wuce abinta. Umaimah ya kalla yace "Yanzu kin yarda ko kuwa" ta daga masa kai alamar Eh saboda tun ganin yarinyar kamanninta da Maman Nihal din suka tabbatar mata dan haka yayi musu sallama ya tafi. Mama ce kan gaba suka shiga gidan, Abu na zaune gaban murhu daya turnuqr da uban hayaqi tana fifitawa saboda jiqewar da itacen yayi sakamakon ruwan saman da akayi a safiyar ga wani rafkeken madambaci akai da alama dambu takeyi se yara biyu maza da Mace daya suna wasa da ruwan da aka tara a babban baho daga gefenta. Daya daga cikinsu ya jefa dan uwansa a ciki ruwan yayi fallatsi har inda Abun take "Wane dan abu ta kazan uban ne ya watso mun ruwa, wai ku wadanne irin shaidanun yara mara sa jin magane ma dan ubanku ba tun dazu nace ku bar wasan ruwan nan ba shegu masu kunne qashi wallahi duk wanda sanyi ya kama sedai ya mutu amma kwandalata bazan kashe gurin siyan magani ba" Abu ta fada cikin masifa yaran duk sukayi tsuru suna kallonta. Labulen daki aka daga wani dogo baqin mutum ya leqo yana cewa "Wai Zainab sau nawa zan miki magana akan tsinewa yaran nan ke ace baki da aiki s zaginsu dayi musu mugun baki se kace bake kika haife su ba" "To ina ruwanka kasan me sukayi mun ne kana cikin daki saboda mutuwar zuciya ni ina nan ina fafutukar yanda zanyi na rufawa kaina asiri s an zage su ne zaka fito kace zakayi magana aikin banza zaku wuce daga nan ku bani guri ko se na tarar daku" ta qarasa atsawace tana zare musu ido. Gaba dayan su suka zabura, cikin tsautsayi daya daga ciki ta ture robar da Abu ta zuba zogale ya zube cikin jar qasar data sha ruwa a tsakar gidan. "Na shiga uku yanzu dan ubanki kika zubarmun shegiya me kama da yayan Allah bani toh wallahi kiyi maza kije duk inda zaki ki samo mun wani idan ba haka ba yau na riqeki se na miki dukan mutuwa" Abu ta fada tana miqewa ko kafin ta qarasa yarinyar ta arta da gudu tayi waje, bata haqura ba ta bita nan idonta ya sauka kan Mama da Umaimah da sukayi mutuwar tsaye tun shigowarsu ganin wannan balahira ta Abu. Dafe qirji tayi se kuma me ta tuna cikin iya bariki ta shiga washe baki tana cewa "Hajiya sannunku da zuwa, kuyi haquri banji shigowarku ba" Wani kallon banza Mama tayi mata, Umaimah kuwa kallonta kawai takeyi a ranta tana tuna irin qarairayinda Maman Nihal ta ringayi mata. "Hajiya ku qaraso mana" muryar Abu ta dawo da ita daga tunanin data tafi se Mama tayi saurin tareta da cewa "Me qaraso ina malama karki bata mana lokaci ki shiga ki dakko mana abinda ya kawo mu ba surutu muka zo yi ba" "Yi haquri Hajiya kinga yau ruwa ya saka dambun be sauka da wuri ba" Abu ta fada Mama tayi saurin tareta da cewa "Ke ki fita a ido na, idan baki sanni ba ita ma wannan zaki ce zakice baki santa ba ko kuwa wani wasan kwaikwayon zaki sake yi mana a nan? To tun wuri ki shiga hankalinki idan ba do kike na tara miki gajiya ba a nan barauniyar banza kawai". "Haba Hajiya ya daga magana zaki nemi kici mun mutunci har cikin gidana meye hadina dake a ina na san ku da zaki zo kina kirana da barauniya yanzu idan na kai zancen nan gurin hukuma ai s an bimun haqqina" Abu ta fada taba bata fuska tana rufe baki kuwa Mama ta kwashe ta da mari tana cewa "Idan baki kai mu gurin hukuma ba baki qaunar Allah, ke kuma da kika tsaya a nan zaki matso ne ko kuwa sena ci ubanki kema, a shegen kwashe kwashenki ai yau ga abinda kika dauko barauniya har cikin gida" "Wallahi bazan yarda ba se an bi mun kadin marina da kirana da barauniya da kikeyi haka kawai ban san ku ba kuzo daga sama daga abin Arziqi ki hau dukana, Salisu bazaka fito ba kana kallo anzo har gida ana cimun mutunchi" Abu ta fada tana kururuwa se Umaimah ta kalleta tace "Amma Maman Nihal kinji kunya wallahi ban taba zatonki da qarya ba ashe daman kin shiga jikinane saboda ki damfareni da a zatonki kinci banza kenan kin gudar mun da sarqa sedai kinyi batan basira da kika kaini inda aka sanki, yanzun ma can mukaje kuma Matar da kike qarya da sunanta ta saka aka rako mu har nan". Tsilli tsilli tayi da ido jin magnganun Umaimah amma saboda iya bariki seta kwasa tayi dakinta tana kwalawa Mijinta me suna Salisu kira tace "Salisu ka fito kana ina kana ji matan nan sunzo zasu daura mun sharrin sata wallahi bazan yarda ba ka fito ka kirawo mun yan sanda a bimun kadin sharrin da suka mun" "Idan ke baki kira yan sanda ba ni yanzu zan kira su tunda bazaki fito da ita ta laluma ba" Mama ta fada tana danna wayarta, Aminu ta kira a taqaice tace ya turo mata yan sanda ya kira Salman ze bashi Address din gidan da take, yana tambayarta meya faru ta kashe tana jaddada masa ya turo su ba'a wuci minti sha biyar ba kuwa sega jiniyar yan sanda ta karade unguwar Abu ta dafe qirji amma qi fadi ya hanata cewa komai se Mijinta ne ya fito yana tambayar Maman ya akayi tace idan sunje can yaji komai. Matan yan sanda biyu ne suka shiga gidan da sallam Mama ta nuna musu Abu dake shirin fadawa daki data gansu tace gata nan suka cafketa kuwa suka tasata a gaba haka suka sakata a mota su Mama suka bisu a baya tareda mijin Abun. A station Sanda Yaya Aminu ya isa station din aka shigar dasu office din DPO fafur taqi yarda da tuhumar da ake mata ta kafe akan ita bata sansu ba sharri suke mata. Umaimah ta bada wayarta duk wani hirar su da Maman Nihal din tana ciki ga hotunanta nan da voice messages muryarta ce amma dukda haka ta musanta ita ba ita bace, ran DPO ya baci ya saka mata nan su jefata a Cell, su tuhumeta seta fadi gaskiya haka kuwa suka sameta suka ringa jibgarta musamman suna jin haushin zaginsu data ringayi a hanyar tahowa, seda taga suna neman hallakata da duka kafin tace zata fadi gaskiya aka fito da ita fuskarta tasha maruka ta kumbura suka koma Office din DPO, Mama ta maka mata harara Umaimah dai na gefe kanta a qasa dan itama ba tsira tayi a gurin Maman ba masifa take mata tana zaginta. Khalil daya je gida da safen aka ce sun fita ne ya qaraso dan ya kirata ta gaya masa inda suke bayan ya zo Yaya Aminu ya fita ya shigo dashi office din. Abu na sheshsheqar kuka ta zayyana musu yanda suka hadu da Umaimah da duk abinda ya faru tsakaninsu, ta qarasa da cewa "Kiyi haquri wallahi sharrin shaidan ne, kuma ni banyi niyyar guduwar miki da abu ba tsautsayine ya fada akai na rasa ta yanda zan gaya miki shiyasa amma wallahi ba gudu nayi ba" Tsaki Mama tayi tace "Can ke kika san tsautsayi ni sarqa kawai na sani ki fadi inda take salin alin kowa ya kama gabansa". Rantse rantse ta ringayi akan ita ba satar sarqar tayi ba, takamaimai kuma taqi fadan inda take da DPO ya gaji yace ze cike mata FIR a tura su kotu can Alqali ya san yanda zeyi dasu nan idonta ya sake raina fata jin zancen kotu, ta riqe qafar Umaimah tana roqonta Mama ta hadasu su dukata qunduma musu zagi tace "Babu kotun da zamuje anan zata fito da ita dan ko munjr qarshe gidan yari za'a turata sarqa kuwa seta Allah yanzun ma bata daku bane idan kuka lallasata zata fadi inda ta kaita ko ni ku bani kulkin na daka yar banza". Murmushi DPO yayi yace "Ayi haquri Hajiya, Officer kuje ku cike mata takaddar kawai ku turasu kotun zefi sauqi" kuka Abu ta fasa ganin dagaske fa kotu za'a kaita tasan kuma daga nan se gidan yari, Salisu Mijinta ne ya kalleta yace "Yanzu Abu bazaki fadi inda kika kai musu abinsu ba kinfi so a kaiki kotun da kudin su zakiji koda na tara ga zaman gidan yari? Ina jiya naji kina zancen da kudinki a hannun Alhaji Auwalu yana juya miki ga daukar Adashin da aka kawo miki dazu da safe idan kin hada ko basu isa ba ai zaki rage wani abun". Wata uwar harara ta galla masa kamar idonta ze fado tace "Salisu kaji tsoron Allah daman ashe labe kake mun a gidan uwar wa kaji nace inada kudi ana juyamun saboda kawai ka sakani a wata masifar ko bayan wadda nake ciki" "Shikenan kiyi yanda kike so amma nidai babu ruwana daga nan gida zanyi su kaiki ko ina ne sedai ki rube a can amma babu wanda zan gayawa ballantana a fito dake tunda haka kika zaba" ya fada yana miqewa tsaye, se kuma tayi qasa da kai, muryarta na rawar kuka tace "Ranka ya dade a bani wayata toh na danyi kiraye kiraye ko zan samu na hado kudin" "Ranka ya dade wannan matar bata da mutunchi wallahi kana ji mijinta ya fada tana da kudi tunda babu sarqa seta bada kudinta dan wallahi seta biya kudin nan" Mama ta fada se DPO ya kalli Matan yan sanda yace su maida ita, suyi ta dukanta har seta magantu kar su saurara mata Abu na ganin sunyo kanta ta fasa kuka tana roqon su tsaya, daya daga ciki ta kai mata mangari, ta dafe haqarqarinta jij Azabar zafi na ratsata suka fara janta tace a tsaya zata fadi inda kudin suke. A wayarta Salisu ya kira Alhaji Auwalu kamar yanda ta bashi umarni tana kuka ya shaida masa Abun tana cikin wani hali aba buqatar kudi da za'ayi belinta, Alhajin ya jajanta musu yace kudinta dubu dari bakwai da Hamsin ne a hannunsa amma yanzu bazasu samu duka ba dan yayi sari, sedai akwai kudin da aka kawo masa yanzu na wasu dubu dari biyar, ze bayar idan yaso saga baya idan dari biyu da hamsin din ta hadu seya ciko musu ya gaya masa inda zeje ya same shi ya karba Salisu ya tafi bayan data gaya masa inda kudin Adashin data dauka suke. Be dade ba ya dawo da kudaden harda Receipt din Sarqar Umaimah yana nan a inda kudin suke gaba daya abinda aka samu dubu dari shida da sha biyar. Mama ce ta kalli Khalil tace "Kirawo mun Abokin naka kaji nawa gram din gwal yake yanzu" zeyi magana ta harareshi dole ya kira Bashir ya gaya masa ta bude wayarta ta buga lissafi ta nunawa DPO tana cewa "Kaga kudin da zata biya nan, ga receipt nan a hannunka ka kuma ji farashin sa a kasuwa ka lissafa ka gani". DPO ya karbi kudin ya saka akayi rubutu a takadda aka rubuta kudin sarqa da kuma abinda aka samu a hannunta da ragowar cikon da zatayi, Salisu ya nemi Alfarmar dasu barta ta koma gida, shi ze tsaya duk sanda ta samu kudin da kansa ze ringa kaiwa Police station din har a warware amma yana neman alfarmar su bata lokaci dan ta samu ta hada kudin, haka aka rabu DPO ya damqa kudi a hannun Mama nan take ta irge dubu sha biyar din sama ta miqawa Khalil tace "Na cire kudina dan ni bazan dauki asara na yanda naga kana wani fuskar tausayinta tsaf zaka iya cewa ka yafe to kuje ku qarata in ta biya ku kukuka sani idan ma ta cinye matarka taja maka asara" tana gamawa tayi gaba abinta ta barsu suka qarasa. Har sukaje gida tana mita da zagin Umaimah da tayi muqus, ita mamaki Maman Nihal ne ya cikata lallai mutum se a barshi. Har aka kusa cinye sati Mama na mita kafin ta haqura tayi shiru da zancen, Mijin Abu kuwa ya cika alqawari dan da ya ganta da kudi seya san yanda yayi da kanta ba bayar aka kai Police station din, shi kadai yasan ta yanda yake tsoratar da ita kuka kuwa da tsinuwa da Allah ya isa tayi su babu Adadi. A haka Umaimah taci gaba da jego cikin kulawa ita da yaronta sunyi kyau sunyi bulbul dasu abin sha'awa har suka cinye kwana Arba'in dinsu, ana gobe suyi Arba'in aka aiko da rasuwar Babban Yayansu Abba da suke kira Baban Qaraye dan shi acan yake zaune wannan dalilin yasa ta roqi Khalil akan ya barta suje gaisuwar idan sun dawo seta koma dukda beso ba haka ya haqura dan harga Allah a matse yake, shikadai yasan irin halin da yake ciki na rashinta a kusa dashi kullum cikin Azumi yake. Shi be taba sanin mabuqaci bane bama shi se bayan da yayi aure dukda tun kafin auransa daman yana da buqatar amma saboda ya tsare kansa yana yawan Azumi sannan baya kai idonsa ga kallon abinda ze tayar masa da hankali. Sunje Qaraye seda akayi sadakar uku suka dawo ta tararda Khalil shi kuma ya tafi Sokoto wani aiki zeyi sati daya dan haka yace tayi amfani da wannan damar taje duk wani gaishe gaishen Arba'in da akeyi kafin ya dawo. Da bangarenta ta fara a kwanaki biyu ta gama zagaya duk inda zataje suka huta kwana biyu kafin Khalifa da kuma Habiba Hajiya ta saka suka ringa yawo da ita nasu dangin suna gaisawa, sun yawata sosai dan har Gaya sda sukaje suka kwana daya suka dawo kuma ranar ne zagayen su na qarshe a sannan saura kwana biyu Khalil ya dawo dan har su Maman Asad sunje sunyi mata shara da gyaran gida ita kuma washe gari zatayi lalle da kitso gyaran jiki ciki da waje kuwa daman sun dade suna yi. Washe gari da safe Hajiya ta kirata akan idan babu damuwa ta shirya yanzu Khalifa zezo ya kaita gidan Goggo Zahra'u qanwar Mahaifinsu Khalil da shaf ta manta basuje can ba se jiya ta kirata tana qorafin an kaita ko ina a dangi ta gaishe su bada gidanta saboda ita bare ce. Wadda zatayi mata kitso da lalle ta rigada tazo amma haka ta saka doguwar riga ta dauki Mu'ayyad suka tafi tana ta Mita Mama ta kwabeta. Goggo Zahra'u ta karbe ta faran faran ta rasa ina zata sakata haka yaranta suka ringa zuwa suna gaisheta ita dai hankalinta yayi ta tafi gida tayi uzurin gabanta, sun kwashe sama da awa daya a gidan sam Umaimah ta kasa taba komai na abinda aka kawo musu ita kuwa Goggon ta qanqame Mu'ayyad tana ta janta da surutu, suna haka tayi baquwa suka gaisa ta zauna take tambayar Goggon wacece Umaimahn tace mata matar Khalil din Yaya Bayero ce seta riqe baki tace "Oh kinga rabo wani baya haifar dan wani, da yanzu yaron Bariyyah ne" "Kin rigani a fili ne Hajara ni kaina tun shigowarsu Nake juya yaron nan a raina ina cewa da yanzu na Bariyyah ne, idanda rabo ai seta haifi qannensa" Goggo Zahara'u ta fada tana yar dariya. Kallonsu Umaimah ta ringayi har suka dire zancensu ji tayi kanta yana juya mata kamar wadda tayi hajijiya, bata manta sunan nan ba Bariyyah, tsohuwar budurwar Khalil cousin dinsa daman nan ne gidan su shine saboda rashin mutunchi za'a ce tazo ta gaishe su lallai ai kuwa yau zasuga qarshen rashin mutunchi kuwa se sun gane ita din ba kanwar lasa bace. Maganar da baquwar ta sakeyi tace "Ai dai wallahi duk munso hadin Allah ne beyi ba da kuma rabo amma yanzu kinga se azo a sasanta kuma zamanku zakuyi lafiya lau dan naganki kema shiru babu ruwanki kamar Bariyyan" Baquwar ta fada tana kallon Umaimah "Sedai mu zauna da kutumar uban Bariyyah, ni za'ayi wa rashin mutunchi ace nazo na gaishe ku sannan ku sakani a gaba kuna kawo mun zancen wata kucaka karuwa da taqi auruwa wai na hada miji da ita to wanda be fasa ba, ba ita ba harke uwarta se kin saka kanki a masifa da bala'in da baki zata ba wallahi aikin banza kawai" Umaimah ta fada kafin ta miqe ta fizge Mu'ayyad dake hannunta tayi waje, a bakin qofar suka ci karo da wadda take da tabbacin ita ce Badariyyan dan ance tana Islamiyya ganin mace ta shigo da Uniform ba tayi wata wata ba ta kwasheta da mari tace "Wallahi ko inuwar mijina kika kalla se nayi Ajalinki ballantana ki saka tunanin hada miji dani a ranki banza garwa kawai" taja tsaki ta fice. Khalifa na qofar gidan dan tuni ya gaji da soki burutsun Goggon tasu ya fita ya barsu se ganinta yayi kamar an jefota ta bude motar ta shiga tana huci dan haka yabi bayanta shima ya shiga ya tayar da motar, sau daya ya tambayeta meya faru tayi shiru bata amsa masa ba daga nan shima ya kama kansa be kuma ce mata komai ba har suka isa gida ya ajiyeta ta fice daga motar ba tareda ta rufe ba jakar goyon Mu'ayyad ma se shi ya bita ciki dasu. Tana shiga kai tsaye dakin da take ta shiga ta ajiye Mu'ayyad akan gado, safa da marwa ta shigayi a dakin ji takeyi tamkar zuciyarta zata fashe saboda zafin da takeyi mata idan ta tuna maganganunsu se taji kamar ta koma ta shaqe su duk su biyun har se sun dena numfashi wai me ma ya saka ta taho ba tareda ta lallasa su ba amma ba laifinsu bane, laifin Hajiyar da tace taje ta gaishe su ne daman sun san rashin mutunchin da suka shirya shine za'ace taje ita gaishe su? Wayarta ta janyo ta shiga kiran Khalil, tana so taji dalilin turata a wulaqantata da sukayi sedai tayi Rashin sa'a wayar a kashe. Mama data gaji da kiran Umaiman tun shigowarta ta bita dakin tana cewa "Lafiyarki kin shigo ana magana kinyi banza da mutane kin wuce, sannan tun dazu ake kiranki a waya kun tafi kunyi zamanku ko kin manta da kin bar mata tana zaman jiranki" "Ni Mama ta tafi na fasa bazanyi lallenba" ta fada ba tareda ta kalli Maman ba, se Mama ta qarasa shiga dakin tana kallonta tace "Uhm, fadan kukayi ko? To ki wuce tun muna shaida juna kije ayi miki abinda za'ayi miki kafin ranki ya baci yanzun nan" Kuka ta fasa mata tana cewa "Ni wallahi bazanyi ba, gidan ma bazan koma ba se yaje ya auro yar uwar tasa ya sakata a gidan ai amma ni na gama zama dashi" Baki Mama ta bude tana kallonta har ta gama kafin tace "Allah ya rufa asiri" ta juya abinta. A can gidan Goggo Zahara'u kuwa daga ita har baquwarta kasa motsi sukayi har Umaimah ta gama tijararta ta fice ta barsu, qarar mari da Kukan Bariyya ne ya dawo dasu daga gajeran suman da sukayi suka zabura gaba daya sedai kafin su kai qofa Umaimah ta fice daga gidan. "Zara'u wannan wace irin tijararriyar yarinya ce kinga tashin hankali daga magana se cibi ya zama qari har ta bi yarinya da tukuicin Mari gaskiya karki bar maganar nan gara ki kira Yaya Aishan ki gaya mata abinda surukarta tayi" Baquwarta ta fada tana kama baki, "Wa ai fada ma bata baki yanzu kuwa zan kirata da take zagin Bariyyah tana kiranta mara tarbiyya ai ga qarshen rashin tarbiyya nan matar danta tazo ta mana, kuma wallahi bata daki banza ba auren Khalil da Bariyyah kuwa idan taga ba'ayi ba toh kice bana numfashi" Goggo Zahara'u ta fada tana numfarfashi nan take ta kira Hajiyar su Khalil a waya ta shiga tsara mata qarya da gaskiya wai Umaiman tazo tayi musu cin mutunchi ta daki Badariyyah dakyar aka kwaceta, tsaf Hajiya ta gama jinta bata kama zancenta ba saboda sanin matsayar da suke da ita dan har a sannan bata haqura ba tana mata nacin in da hali Khalil ya qara da Badariyyan shiyasa yanzu ma ta dauka duk cikin sharrin tane daman tunda ta damu da suje din tayi tunanib wani abu. Suna gama wayar Khalifa ta kira lokacin ya ajiye Umaimah kenan take tambayarsa meya faru a gidan Goggon tasu tax be sani ba danshi daya gaji waje ya koma ya zauna amma yaga ta fito ranta a bace ya tambayeta bata kulashi ba ya ajiyeta gashi nan a hanyar gida yanzu yana hanyar dawowa. Maida akalar kiran tayi kan Umaimah, seda wayar ta qaraci qararta tana daf da katsewa sannan ta daga cikin muryar kuka. UMAIMAH Tana zaune tana saqa da warwara taga kiran Hajiyar, zuciyarta ta ayyana mata karta daga, wani bangaren kuma yace mata ta daga ta daddana mata Ashar ai duk bakinsu daya ai. Rasa wanne zatayi a ciki tayi har seda taji wayar na neman katsewa kafin ta daga cikin muryar kuka ta amsa sallamar Hajiyan. "Umaimah lafiya meya faru a gidan Zara'u? Ta kirana tana gaya mun wadansu maganganu da ban ganewa kansu ba sannan na tambayi Khalifa yace be san komai ba" Hajiyan ta fada cikij muryar damuwa musamman yanayin kukan da taji kamar Umaiman nayi. Kuka Umaimah ta fashe dashi kamar yanda zuciyarta ta kitsa mata ta fara cewa "Hajiya wacece wadda kika tura mu gidanta, haka kawai da farko baki ga yanda ta karbe mu ba faran faran muka gaisa amma tana ganin Khalifa ya fita ta canzamun fuska ta shiga zagina tana zagin iyayena, bata gaji ba Hajiya ta gayyato wata mata itama tazo suka hadu har tana cemun mayya wai na cinye muku zuciya keda Khalil ya zabeni ya bar yar uwarsa to wallahi ban isa ba se taga bayana, in saka ido in gani seta rabani da Khalil" ta qarasa tana fashewa da kuka. Salati Hajiya ta ringayi kamar zatayi kukan itama ta ringa bawa Umaimah haquri amma kamar wadda take tunzurawa se qara rusa kuka take tana cewa "Babban abinda ya fi mun ciwo hajiya har fa cewa takeyi Khalil ya gurbata muku zuri'a ya auro mayya gashi nan na haifi maye wai mu'ayyad ya zura mata ido yana kallonta duk abinda ya sameta bazata yarda ba" seta sake rushewa da kuka. Ran Hajiya ya baci tace "Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi, maita kuma data dora miki seba bi miki kadinki ki barni da ita" haka ta ringa lallashinta ita kuwa se sake rura wutar take ta hanyar fadar maganganun qarya akan Goggon ta jefeta dasu da haka sukayi sallama. Wasa wasa qaranar magana ta zama babba dan korar ne lalle Umaimah tayi tace bazatayi ba ta kuma rantse akan bazata koma gidan Khalil ba an tanbayeta meya faru tayi shiru se kuka takeyi da suka gaji suka qyaleta. Washe gari Khalil ya dawo, kansa a qulle saboda maganganun da Hajiya ta gaya masa da wanda Badariyya da Mahaifiyarta suka kira suka gaya masa ya rasa wanene me gaskiya a ciki? Haka kawai zuciyarsa tafi gasgata zancen Badariyyah musamman da tun a daren yake neman layin Umaimah yana shiga amma bata dagawa. Kai tsaye gidansa ya wuce dan duk tunaninsa ya bashi ta koma sedai yana zuwa ya tarar da qofa a rufe, da muqullin hannunsa yayi amfani ya bude qofar ya shiga, gidan tsaf an gyara ko ina dakinsa ya wuce ya ajiye kayan daya shigo dasu ya fada wanka dan ya kwaso gajiya a mota sukayi tafiyar kuma shi yayi tuqin. Seda ya shirya sannan ya wuce gidan Hajiyarsa, a can yaci abinci tana sake maida masa zancen abinda ya faru cikin bacin rai bece mata komai ba se haquri daya bata ya ci abinci ya wuce gidan su Umaimah. Tana kwance akan gado Saufullahi ya shiga yace tazo inji Mama, doguwar rigar Atamfa ce a jikinta ta mayar da hular data zame daga kanta tabi bayansa, tun daga qofar palour take jiyo qamshin turarensa seta sake tamke fuskarta ta shiga sa sallama ciki ciki. Yana zaune akan kujera da Mu'ayyad a hannunsa ta samu kujerar bakin qofar ta dofana tana masa sannu da zuwa, fuska babu yabo babu fallasa ya amsa mata hankalinsa na kan yaronsa, abin ya bata mata rai ta sake tunzura baki gaba, bece mata komai ba yana ci gaba da yiwa Mu'ayyad wasa Mama ta shigo tana kallonta tace Kije ki nunawa su Nazifi kayan da zasu fitar miki dasu ku wuce dare yanayi" "Nifa Mama na gaya miki babu inda zanje, yaje can ya auro yar uwar tasa su zauna tare" Umaimah ta fada tana tunzura baki se suka kalleta gaba daya, a zuciyaraa yana sake samun tabbacin abinda aka ce ta aikata dagaske tayi shine ta zagaye ta karantawa Hajiya qarya da gaskiya ta sakata ciwa Goggo Zara'u mutunchi har abin ya nemi ya zama rigima seda Baffansu ya tsawatar shine yanzu nan zata nemi ta caja masa kai ko. "Banason iskanci Umaimah, ki wuce ki hada kayanki nace miki idan ba so kike ranki ya baci ba" Mamanta fada murya babu wasa se Umaimah ta miqe tana cewa "Wallahi Mama dagaske nakeyi bazan koma gidansa ba, seyaje ya auro duk wadda yaga dama" tana gama fadan haka ta miqe ta bar dakin. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 PAGE 31 Juyawa Mama tayi da niyyar binta Khalil ya dakatar da ita da cewa "Ki barta Mama yanzu tana cikin bacin rai idan ta sakko dan kanta seta dawo" ya miqe tareda kwantar da Mu'ayyad akan kujerar yayi mata sallama ya fita, dakin da Umaimah take ciki ya shiga tana tsaye a jikin window tana dakon ganin wucewarsa daman ta waiwayo da sauri tana cewa "Na gaya maka bazan koma ba, harni za'a tura gidan su budurwarka su wukaqantani, daman kuna tare har yanzu qarya kayi mun da kace kun rabu toh Allah ya tona maka asiri na sani kuma zama dakai na gama sedai kaje ka aurota ragowar wasu can ka qarata da ita". Cikin bacin rai ya kalleta yace "Karki sake aibata ta dan jinina ce bazan iya canzata ba sabanin ke da zan iya rabuwa dake, sannan ita wadda kikaje kika yiwa rashin kunyar qanwar mahaifina ce uwa daya uba daya har kika iya tsayawa a gabanta kika zageta idan da kinsan darajar babba kome zatayi miki ai bazaki tanka ba taci albarkaci na amma shikenan kici gaba da duk abinda kikeyi akwai ranar da zaki kwashe kashinki a hannu. Zama kuma kiyi ta zama gaki ga gidan nan har sanda kika gaji" Yana gama fadar haka ya fice daga dakin cikin bacin rai ya bar gidan a ransa ya qudurce shekara dari daga yanzu baze sake waiwayarta ba, duk abinda ta yanke a wannan gabar akansa ze tafi. Saboda bacin rai be iya komawa gida ba gari ya shiga ya ringa yawo abinda be iya ba ga wutar sha'awarta dake damunsa sabida ya gama saka ran a ranar zata dawo, har wasu hadi Abokinsa ya bashi acan sokoton yasha danma bacin ran da yake ciki ya danne kaso hamsin na buqatar da yake ciki amma duk da haka yana cikin wani yanayi. Gajiya yayi da yawo ya samu wani gurin shaqatawa ya zauna, daga gefe can yana hango yammata da yawa sunsha anko kamar dai wani shagalin biki suke gabatarwa a gurin dan yaga wata da tafi yin kwalliya kamar Amarya. Yana zaune a gurin har suka gama suka fara watsewa hankalinsa yayi nisa a tunani yaji sallama a kusa dashi. Firgigit yayi ya kalli masu sallamar, yammatane guda biyu suna sanye da kalar Ankon daya gani suka gaishe shi ya amsa yana kallonsu da rashin sani. Wadda tafi kalar rawar kai a ciki tace "Sannu Malam kayi haquri mun dameka ko dan Allah taimako muke nema" "Toh, taimako kamar na me kenan?" Ya fada yana kallonsu a ransa yana tunanin me ze taimaka musu dashi. "Biki mukazo kaga ni bamu sani ba har dare yayi ashe mun rasa motar tafiya gida duk wanda muka tsayar se yace mana ba hanyar zeyi ba ga lokaci yana ta sake tafiya dan Allah idan babu damuwa ka taimaka ka kaimu gida mana" Budurwar ta sake fada dayar tana zungurinta akan tayi shiru amma taqi. Kallonsu yayi sama da qasa, a haka dai basuyi kalar watsatstsun yammata ba kuma ya ga dagaske bikin sukazo amma me yasa sun san unguwarsu ana wahalar samun mota zasu kai dare a gurin har qarfe sha daya na dare shi ya rasa ma wannan abu da zaace biki ba zaayi shi a cikin gida ba se an tafi yawon guraren shaqatawa kuma ita Amaryar ya za'ayi ta tafi bata tabbatar da duk jama'ar data tara kowa ya isa gidansu lafiya ba? "Dan Allah ka taimaka mana idan kuma ba zaka iya ba mu nemi wani dare yanayi" yarinyar ta sake fada taba marairaicewa, se Khalil ya kalleta kamar yace bazashi ba se kuma tausayinsu ya kamashi, Mata ne idan be taimaka musu ba besan gurin wa zasuje ba shin zasu samu na gari ko kuma mugu a yanda rayuwar nan ta lalace haka, muqullinsa da wayarsa ya dauka yayi gaba ba tareda ya musu magana ba suka bi bayansa, har sun isa jikin motar suka waiwaya, "Hadiza bazakizo mu tafi ba" suka hada baki gurin fada se ya waiwaya ya kalli wadda suka kira da Hadizan, tana sanye da irin kayansu sedai ita ta dora hijabi daya kai mata guiwa akai. Su ukun suka shiga ya dauki hanyar Na'ibawa kamar yanda suka gaya masa sunan unguwarsu, seda ya kaisu har qofar gida, a lungu suke cikin ransa kamar ya dake su ganin yanayin unguwar tasu sannan hat su iya kaiwa dare haka dole su rasa motar dawowa ai. "Bazaki bari ya qarasa dake gida ba Hadiza?" Mw rawar kan cikinsu ta sake fada ganin itama Hadizan ta sauka bayan su biyun sun fita seta girgiza kai tace "Aa nan ma yayi, na kira Musa nace ya jirani a nan mu qarasa gida kin ganshi can ma" ta fada tana nuna dan matashin saurayi da suke tsaye su biyu daga gefe, Khalil yabi shi da kallo kamar su daya da ita hakan ya nuna qaninta ne ya tabe baki ya tada motarsa sunayi masa godiya be ko bi ta kansu ba ya juya mota yana jin dayar na cewa "Kunga be karbi lambar ko daya daga cikinmu ba babu wadda tayi masa ai shikenan". Kafin ya kai gida sha biyu tayi, haka ya lallaba yasha ruwan lemon tsami ya kwanta, kafin bacci kuwa ya dauke shi yayi wanka yafi sau goma haka yayi bacci a wahale. A can gida kuwa fada Mama ta rufe Umaimah dashi kamar zata daketa seda Anty ta shiga tsakani, "idan kika kashe auranki Umaimah ki nemi gurin zama badai a gidan nan ba tunda ke shaidaniyar yarinya ce mara jin magana. Yanzu daman abinda kika je kikayi kenan sannan kika hada musu rigima a cikin family saboda bakya tsoron Allah kici gaba Umaimah idan daidai kikeyi zaki gani" Mamq ta fada muryarta na rawa kamar zatayi kuka Anty ta shiga bata haquri ta fice ta barsu. Fada Antyn ta ringayi mata se kuma jikinta yayi sanyi, tun a daren ta fara neman Khalil amma bata samun wayarsa ita kanta bata iya bacci me dadi ba a ranar har washe gari kuwa yaqi amsa mata waya seda aka kwana biyu sannan ta same shi shima amsa daya ya bata bayan data gama surutunta yace ta zauna ta qara hutawa sosai karta dawo yanzu. Kuka wiwi ta dasa musu akan se su nemo shi su bashi haquri daman Abbansu baya gari lokacin da ta qulla tsiyarta, koda ya dawo aka mayar masa da yanda akayi be ce mata komai yace a rabu da ita ai Bari ba shegiya bace idan taji jiki da kanta zata maida kanta gidanta shiyasa koda tana tanbotsan haukanta babu wanda ya kulata, data ishesu da iface iface Mama tayi mata biji biji dole ta shiga hankalinta. Binbini da kiran waya kuwa babu irin wanda bata yiwa Khalil amma kullum amsar daya ce ta zauna ta qara hutawa dukda dauriya ce kawai yakeyi dan ya fuskanci idan ba ya zama namiji akan Umaimah ba iskancinta kullum qara ta'azzara yakeyi. Seda aka shafe sati uku a haka, ganin fa dagaske Khalil ya fita a sabgarta dan daga baya dena daga wayarta yayi ko idan ya daga yace mata yana aiki ze kira kiran da bazeyi ba kenan seta komawa fakewa da Mu'ayyad. Haka kawai zata kirashi tace suna son abu, ranar farko yazo har qofar gidan ya kaqo mata siyayya tuli abinda ta nema da wanda bataa nema ba be shiga ba ya bawa yara ya hada mata da kudi cikin envelop yace akai mata. Ranar akan yan aiken ta huce ta ringa rashin mutunchi da tijara a cikin gidan kwana biyu a tsakani ta dorawa Mu'ayyad ciwon qarya nan ma bezo ba ya turo mata Khalifa dan bama ya gari a sannan yayi tafiya. Kuka wiwi ta kirashi a ranar tanayi masa ta bashi haquri yace mata yanzu dagaske ze haqura amma da sharadi, sharadin kuwa shine se taje ta gayawa Hajiya da bakinta duk abinda ta fada mata qaryane saboda yanzu haka akan wannan dalili gaba me qarfi ta qullu tsakanin Hajiyar da Goggo Zara'u haka cikin dangi sun kasu biyu kowa da wanda yake goyon baya. Hankalin Umaimah ya tashi da jin wannan sharadi nasa toh ta ina zata fara zuwa ta cewa Hajiya qarya takeyi yanzu? Amma da yake neman shiri takeyi tace masa ta yarda washe gari kuwa babu wanda ta gayawa inda zata da sassafe ta wanke qafa tayi gidan Hajiya, Mamakin da Hajiya ta nuna na ganinta da kuma tambayarta da takeyi na yaushe suka dawo ya sakata chanza plan ashe Hajiya batasan da cewar har sannan tana gidansu ba daga baya ne ma da taji shiru kwana biyu ta tambayi Khalil yace mata ta tafi Minna gurin Yaya Naziyya da suka koma can da Mijinta dan ko haihuwar Umaiman bata samu zuwa ba shine taje gaisheta. A maimakon ta gyara abinda ya kaita seta zauna ta sake zuba sabon lalen gurmi, kuka ta fasa wa Hajiya akan Khalil yayi fushi da ita tun akan waccen maganar dan har yanzu tana gida yace ba zata koma ba seta je ta bawa su Badariyyah haquri, ran Hajiua ya baci ta dauki waya zata kirashi Umaimah ta hana "Idan kika kirashi Hajiyavze qarayin wani fushin yace na hadaki dashi, nidai dan Allah karki gaya masa na fada miki wani abu, kawai ki nuna masa kinsan ina gida har yanzu ya barni na koma dakina dan yanzu wallahi Hajiya gidanmu kowa fushi yake dani babu meyi mun magana" Umaimah ta fada tana matsar hawaye, Se Hajiya taja kwafa tace "Da kin barni na kirashi ai naci masa mutunci mutumin banza kawai yanzu shi har idan yana da zuciya ze saka daga ido ya kalli Zara'u da duk wani natane mutanen da suka qishi saboda abin duniya shine yanzu zasu dawo masoyansa, ze dawo ya sameni ita kuma Hajiya Malika da zata ringa biye masa itama zanje har gidan na sameta ai haba shikenan se abi a tsangwameki kuma akan gaskiyarki" haka ta ringa fada daga qarshe tace ta koma ta hada kayanta ta koma dakinta shi kuma Khalil din zata hadu dashi idan ya dawo suka rabu Umaimah na sake roqon karta gayawa Khalil komai, a daren ranar kuwa se gashi da kansa ya kirata yace ta shirya washe gari ta koma shi se jibi ze dawo, Roqonsa tayi akan ya bari ta koma jibin da safe dan gobe zatayi kitso da sauran shirye shirye haka kuwa akayi washe gari ita kadai ta ringa hidimarta daman Anty ce me tayata ita kuma bata nan Ankwantar da yayarta a Asibiti ita take jinyarta. Bayan komawarsu tayi zaton zeyi mata fada ko ya tado da maganar sedai taji shru, tun tana dari dari harta sake suka ci gaba da rayuwarsu tamkar babu abinda ya faru. Sabon  babi suka bude na rayuwa me cike da qauna da tattalin junansu, Tsakanin Khalil da Umaimah kullum cikin rige rigen kyautatawa junansu suke tareda tattalin tilon dansu da suke ji dashi kamar tsoka daya a miya. Qarin hidimar Mu'ayyad da rashin sabo ya saka aiki ya kan kacamewa Umaiman musamman da Mu'ayyad din ya koyi rigima ya koda yaushe yafi son yaji shi jikin mutum dan haka idan dai ba yana hannun Khalil ba to sedai ta goyashi idan tanaso tayi ayyukan gida, saboda rashin sanin yanda zata tsara ayyukanta se ya zamana wani lokacin har Khalil ya dawo daga aiki bata samu ta kammala abinci seya jirata haka wankin yaron duk takarar da Mama tayi mata a gida akan karta ringa tara wanki tayi qoqari da tayi masa wankan safe ta wanke kayan daya bata amma bata iyawa gajiya takeyi dan lokacin hutun nata idan yayi bacci sannan take samu ta leqa social media dukda yanzu ta kiyayi duk wata da take shishshige mata dason yin qawance da ita qarqarinta hira a group shikenan. Qarin abinda Yafi damunta a yanzu shine yawan tafiye tafiyen da Khalil yakeyi kuma yace dole da ita ze tafi dan idan har tafiya ta wuce ta kwana biyu tofa qafarsa qafarta wanda sam ita abin beyi mata ba bata so kullum cikin qorafi take da wuya kuma suyi tafiyar aje a dawo lafiya basu bata ba, ta ringa mita kenan da fadar maganganu da azatonta zasu saka yayi zuciya gaba ya qi tafiya da ita kamar yanda Rufaida ta bata shawara amma ko a jikinsa, yi yake kamar besab tanayi ba. Wata shida da haihuwar Mu'ayyad idanka ganta seka dauka Yara biyar take raino yanda gaba daya ta hargitse shikansa gidan ya fita a kamanninsa duk inda ka duba kayane zube na sakawa da kayan wasan Mu'ayyad. Misalin qarfe tara bayan Khalil ya fita aiki tana kishingide akan kujera da waya a hannunta Mu'ayyad data samu ta lallaba dakyar yayi bacci na kwance akan dan gadonsa me lilo yana shillashi, wani series take kallo a YouTube taji ana qwanqwasa Get, tasan baze wuce Aliyun Maman Hauwa ba ko yayi mantuwar wani abun, wake ta aikawa da Ramatu kishiyar Maman Hauwan tayi mata Alalan gwangwani zatayi baqi qannen Hajiyar Khalil ne sukazo daga Gaya zasu zo ganin Mu'ayyad din. Hijabi ta saka taje ta bude, Rufaida ce da qaton cikinta ta sako wani uban Hijabi se haki take saboda tafiyar da tayi ta bud mata ta shigo tana cewa "Uwar biyu daga ina haka?" "Wallahi gajiya nayi da zama ni kadai shine nace bari na shigo na dan rage lokaci kafin rana tayi" Rufaidan ta bata amsa suka wuce ciki Umaimah na cewa "Kin ganni nima fa wai baqi zanyi amma babu abinda nayi na samu dai na bada Ramatu tayi mun Alala ina da zobo in hada musu dashi gyaran gidan ne na gagara yi wallahi duk na gaji" "Ai kina ma qoqari ni idan kinga nayi shara yanzu ai Abban Anam yana gari ne, ina zan iya dazu ma na kira Maman Salaha inji yaushe zata dawo idan ba haka ba na nemi wata kawai na gaji da wanne zakaji da aikin gida ko da wahalar kanka, kema da me aikin kika nema kawai kika huta ta rage miki aiki" Rufaida ta fada, Umaimah ta yatsina fuska tace "Me aiki ni Allah ya rufamun Asiri zanyi abinda zan iya na bar sauran kawai" "Iyayen kishi" Rufaida ta fada cikin sigar tsokana kafin taci gaba da cewa "to ko ba me kwana ba ai seki nemi me zuwa ta tafi, da safe idan megidan ya fita tazo kafin yamma ya dawo ta gama miki ayyukanki ta tafi ba shikenan ba" "Ke nifa me aikince gaba daya bana so ki barni zanyi aikina" Umaiman ta fada cikin qosawa da zancen me aikin da kullum Rufaida se tayi mata kamar ita take mata ayyukan gidan balle tace ta gaji, a maimakon ta tashi tayi abinda zatayi kafin zuwan baqin nata nan suka shantake suna hira bata ankare ba se jin bugun qofa tayi ta kalli Agogo qarfe sha daya na safe ta miqe tana salati ta je ta bude, Ramatu ce da kanta da kular data bada a zubo mata Alalen, daga bakin Get ta tsaya ta bata tana cewa "Yaran duk suna makaranta kuma naga lokaci yayi shiyasa nace bari na miqo miki da kaina" Umaimah ta karba tana cewa "Wallahi nima ban ankare da lokaci ba se yanzu, nagode sosai Allah saka da Alkhairi" daga haka ta juya ciki da kular Alalen ta ajiye a kitchen tana jiyo kukan Mu'ayyad daya farka daga bacci ta shiga tana yamutsa fuska ta kalli palour tana tunanin ta ina zata fara gyaransa, Mu'ayyad din ta karba ta bashi Nono, Allah ya sota da wuri tayi masa wanka yayi kashi ya bata jikinsa ta hada gaba daya tayi masa wanka kawai, yana gama sha ta ajiyewa Rufaida shi, kayan wankin dake kan kujera ta shiga kwashe tana watsa su a kan gadon dakinta, ta tattare Gadon da sauran tarkacen Mu'ayyad ta kai Store. Sama sama ta share palour ta kunna turaren wuta ganin sha biyu saura kwata yasa ta kwaso kaya da diaper ta ajiyewa Rufaida tace ta canza masa ita kuma ta shige bandakin dake palour ta daurayeshi ta dauraye jikinta dan tasan zasu buqaci shiga yin Alwala dakinta kuwa baze shigu a yanzu ba dan gyaransa ze dauki lokaci. Tana gama saka rigarta taji bugun qofa tasan baqin ne suka iso dan qarfe sha biyu daman aka ce zasu zo, ta goge fuskarta da soson powder ta fesa turare ta yafa mayafi, ita da kanta data kalli kanta seda taji wani iri yanda kasan wadda ta tashi daga bacci duk a firgice haka ta fita ta bude musu tana yiwa Rufaida datayi rashe rashe magana kan ta gyara. Su biyu ne manya da tana ganinsu taga kamanninsu da Hajiya se wata da zasuyi Sa'anni da Khalifa daya kawo su. Ta tarbe su da fara'a tayi musu iso cikin palour suka zauna, seda ta gabatar musu da Ruwa da Lemo da Cake suka gaisa tana kallon yanda yarinyar ciki ke qarewa palour kallo duk seta tsargu taji wani iri, basu taba zuwa ba be kamata ace sunzo sun  tarar da wani abu ba daidai ba. Sun jima sosai a gidan har seda Khalil ya dawo sunci Alalen suna ta santinsa da zasu tafi ta juye musu ragowar da tarin tsarabar data hado musu cikin kayayyakin data samu na barkar Mu'ayyad ta hada musu da turaren wuta, Khalil ne ya tafi kaisu suna fita ta goye Mu'ayyad ta shiga gyaran gidan dan ta tabbata mita ce zata sha ta kamar ba gobe idan ya shiga dakin ya tarar dashi yanda ya barshi da safe. Allah ya taimaketa har ta gama ta sake wanka tayiwa Mu'ayyad sannan ya dawo gidan lokacin har anyi sallar Isha. Wanka ya farayi shima ta kawo masa Taliyar data dafa ta dumama masa stew yace ya qoshi yaci abinci a gidan Hajiya. "Anty Umma tace ya kamata a samo miki me aiki wai taga kamar aiki yayi miki yawa sannan ga raino" Khalil ya fada yana kallon Umaimah dake shayar da Mu'ayyad, ta yamutsa fuska a ranta tace "Tsabar munafunci ko ina ruwanta oho" a fili kuwa tace "Ni na gaya mata ina da buqatar me aiki ko nace na gaji, kaima sonbata bakinka ne kawai amma sau nawa zna gaya maka bana son wata yar aiki indai ba kuma so suke su kawo mun wadda zata kwacemun miji ba" "Kin yarda wata zata iya kwace miki mijin kenan?" Ya tambayeta yana dage gira ta harareshi tareda tura baki tace "Sedai uwar yarinya ta haifi wata kuwa" "Toh nidai na gaya miki ne dan kar kiga me aiki daga sama dan ta rigada tayiwa Hajiya magana ma kuma an kira wata da take kawo su tace a bata kwana biyu, karki damu na wassafa musu irin wadda za'a kawo baqa mummuna da bazan iya kallon fuskarta" Khalil ya fada cikin sigar tsokana, bata kulashi ba se qananan mitocinta ta dura a ranta ko ta ayyana ko uwar wa tazo mata gida seta koreta dan ita bata ce musu tana da buqatar mataimaki ba balle a mata iyayi. Ashe abinda ya faru tun a hanyar mayar dasu gidan Anty Umma da sam bata gani tayi shiru tayiwa Khalil maganar hargitsewar gidan nasu da rashin kintsin ita kanta Umaimar. "Ita wannan matar taka daga haihuwa daya ji yanda ta fita hayyacinta se kace me yaya goma gida duk ya qazance kodai daman kazamace se yanzu ne abin ya fito fili? To koma dai yaya ne ka nema mata me aiki ta ringa kama mata wasu ayyukan dan idan ba haka na wannan ta qara tara yara bamu san yanda zata zama ba kuma" Anty Umma ta fada, Khalil yayi shiru a ransa yana juya maganarta, shikansa halin qazantar da Umaimah ta koya yaja damunsa danshi Allah yayi shi sam baya son datti ko kadan ita kuwa yanzu ta daura abota da qazantar da take fakewa da sunan jego. Gida se yayi kamar anyi yaqi a ciki sannan zata gyara, kwalliyar safe kuwa ya manta yaushe rabon daya fita ya barta tsaf se an auna arziqi ne ze dawo ya tarar tayi wankan tayi kwalliya kayan wanki kuwa na Mu'ayyad se yayi kamar me sannan zata wanke abubuwan dai gasu nan kala kala se shegen chatting din da baze amfana mata komai ba ta tasa a gaba shi yasa koda suka isa gidan Hajiya Anty Umma tayi mata zancen a nemawa Umainah me aikin be musa ba dukda yana hango takurar da zasuyi saboda yanayin gidan amma in har zata ringa kintsa gidan yanda yake so zasuyi manaji na dan lokaci kafin ya samu yanda yake so ya canza musu muhalli wanda shine plan dinsa na gaba. Kwana biyu a tsakani kuwa sega Habiba tareda wata yarinya da bazata wuci shekaru sha uku zuwa sha hudu ba da qullin kayanta Habiba take gaya mata Hajiya ce tace a kawo mata me aiki aikuwa ko ruwa bata basu sun sha ba tace su juya bata buqata ranta kamar ana hura mata wuta saboda ganin yarinyar fara kyakykyawar bafulatana dukda yarinya ce amma tana da kyau me daukar hankali. Ta ringa surfa masifa ita kadai a gida koda Hajiya ta kirata akan me yasa tace a maida yarinya kai tsaye tace "Nifa Hajiya ban buqaci wata me aiki babu abinda ya gagareni yi a gidan nan" ta bawa Hajiyar Amsa kanta tsaye, Hajiyar bata ja ba tace shikenan tunda tace haka sukayi sallama ta kashe. Koda Khalil ya dawo shima seda ta tasa masa wata mitar akan kawo me aikin ya mata banza har ta gaji tayi shiru dan kanta kafin ya kalleta yace "Tunda kin kori me aiki ki tabbata karna sake ganin wani abu da ba daidai ba a gidannan, daka kan tsaftar jikinki zuwa ta cikin gida har abincina bana son a sake samun wani akasi idan ba haka ba dole ki nemi me aiki dan bazan iya rayuwa cikin qazabta ba" "Amma dai ina iya qoqarina, kana kallon dai yaron nan idan ya tasa rigimarsa komai hanani yi yakeyi sedai na goyashi ni kuwa ina zan iya sunkuyon aiki dashi a baya, zanyi abinda zan iya kawai wanda be samu ba a ringa haquri kwana nawa ne ze girma komai ya dawo daidai" ta bashi amsa tana daddanna wayarta se ya ja tsaki dan kulata ma qara masa ciwonkai zatayi tunda ita duk maganar da aka fada tana da amsarta. Hakan da sukayi yasa kwana biyu ta dage ta dena komawa bacci bayan Asuba, da tayi sallah zatayi qoqari tayi shara da mopping ta wanke Bandakuna tsaf ta gyara gida kafin ta hada musu abin kari har tayi wanka Mu'ayyad na tashi tayi masa shima idan Khalil ya fita seta samu ta lallabashi su koma baccin se ya zamana bata da lokacin hawa social media yanzu sosai da rana seda daddare a lokacin kuma suyi ta fada da Khalil da yake cewa tana shiga haqqinsa. Bangaren tara wanki ne dai ta kasa denawa dan seta hada na kwana uku hudu taga kayan sa na tsakar gidan sun kusa qarewa sannan zata wanke su sedai ba'a kwashe cikakken wata ana haka ba ta sake komawa ruwa a cewarta ayyukan sunyi mata yawa wani lokacin ta zama se a hankali gidan ya fita a hayyacinsa musamman da Mu'ayyad ya fara rarrafe haka ze ta watsar da kaya wani lokacin ta ajiye ruwa ko lemo ya zubar akan carpet din haka gurin duk ze hadu ya ringa warin ruma ko kuma ta barshi babu Diaper duk ya fitsare palour abin na Umaimah dai se Addu'a kawai babu abinda ya dameta idan ta sake shi ya shiga sabgoginsa ita kuma zata harde a kujera ta hau chatting. Tafiya ta tasowa Khalil zuwa Abuja wani aiki kuma ze dauke shi a qalla sati biyu zuwa sama ya san sarai zasu sha daga da ita akan tafiyar dan haka be sanar da ita ba seda ya rage sauran kwanaki biyu da daddare ya gaya mata, yanda ya daure fuska tamau yayi maganar ya saka ta kasa yi masa musun baza taje ba, a zuciyarta ta ringa juya yanda zata kaucewa tafiyar nan dan ita dagaske ta tsani binsa ko ina, sedai tasan idan tace kaitsaye bazataje ba rigima zasuyi dan haka tayi shiru har washe gari bata shirya komai ba, sanda ya gaji yayi mata maganar bega tana hada kaya ba bata ce masa komai ba ta shiga daki ta hada masa jakarsa tsaf tana cikin hada kayan ya shiga ya sameta, ya kalli akwatin tasa yace "Ku ina naku kayan naga nawa kadai kike hadawa" "Zan hada mana so nakeyi na gama da nakan" ta bashi amsa badan zatayin ba, Allah ya sani bata son binsa tafi so ya tafi ya barta a gida ta samu yancin yin yanda take so bayanan bare ya ringa damunta. Be sake kulata ba yayi shirin kwanciya yana sake jaddada mata da qarfe goma zasu tafi kuma karta kwashi kaya da yawa dan jirgi zasu bi yayi kwanciyarsa ya barta tana ganin yayi bacci kuwa ta gyara Mu'ayyad da shima yayi baccin ta kwantar dashi ta bar musu dakin. Palour ta koma ta dauki wayarta ta hau WhatsApp taci sa'ar samun Rufaida Online nan take gaya mata har yanzu ta kasa samun mafita fa akan tafiyarsu gashi har gobe ne "Kema dai son wahalar da kai kawai seda nace miki ki fito kawai kice masa ke bazakije ba dan ni haka mukayi da Abban Anam shikenan wai yayi zuciya be Sam cewa ze tafi wani guri dani ba niko ko a Jukina indai z ajiye mun komai ya tafi Allah ya dawo dashi lafiya" Rufaida ta fada, Umaimah taja numfashi kamar tana gabanta tace "Baki san halinsa bane shi yasa nidai gara ki bani ko wata qaryarce da zanyi masa ya barni amma ba kai tsaye bace bazani ba" "To ai kuwa se ki tashi ki hada kaya ku tafi tunda bazaki iya ce masa ba zaki ba, nikam bari naje na kwanta dan nima gobe zani Asibiti idan kun tafin to idan kuma kina nan ma hadu in Allah ya kaimu" daga nan sukayi sallama. A palour taci gaba da zama tana chatting da duba Ticktok da IG har bacci ya kwasheta seda Mu'ayyadya farka yana kuka Khalil ya fito ya tasheta yana mitar wannan dabi'ar data samu ta zaman kallo har tayo bacci a tuninsa, ta wuce ta koma dakin daman ko kayan jikinta bata samu canzawa ba taci gaba da bacci. Da Asuba suka tashi da Alhinin rasuwar Mijin Anty Hafsa sanadiyyar ciwon ciki da yayi a cikin dare kafin Asuba rai yayi halinsa. Sosai suka kidima da jin wannan labari dole suka tafi gidan Jana'izar daga can bayan an gama Khalil yayi mata sallama ya wuce Abuja shi kadai ya barta nan wannan dalili ya rushe tafiyarsu tare sedai sati daya bayan rasuwar ya kirata akan ta shirya ze saka Khalifa ya siya musu Ticket din jirgi zata same shi a Lagos dan daga Abuja can suka wuce anyi canjin Manager bangarensu na kamfani dan haka an bashi ruqon kwarya kafin a gama tantance wanda za'a bawa be san tsahon lokacin da abin zero dauka ba kuma Allah ya sani baze iya ci gaba da zama shi kadai ba ba tareda ita a kusa dashi ba. Duk da sanin yanayin Khalil din da irin halittarsa ta san baya iya jure dogon lokaci ba tareda ita ba amma tayi biris da maganarsa, daman tana gidan Anty Hafsa tun bayan rasuwar har akayi bakwai da aka watse Mama tace ta koma gidanta tace dan Allah ta barta ta zauna da Anty Hafsan kodan Halin da take ciki dakyar Maman ta barta shima saboda Khalil din baya gari dan haka koda yayi mata maganar bin nasa babu wanda ta gayawa har ana ya gobe ranar da yace zasu tafin tazo a ranar Taje gida dauko musu kaya ita da Mu'ayyad Khalilfa ya kirata akan zeyi booking musu ticket na qarfe nawa take so kai tsaye tace masa sunyi magana da Yayansa yace a barshi. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 32 Hankali kwance taci gaba da sabgoginta musamman da daman ya aiko mata da kudade masu nauyi da sunan ko zatayi wani shiri na tafiyar ta tasa su gaba siyi banza siyi wofi rantawa qawaye da zubin Adashin Maman Hauwa da Rufaida ta sakata shiga dole duk a haka ta rabar da kudin Khalil nacan tun yana zuba idon ganinsu har hankalinsa ya fara tashi musamman daya kira wayarta a kashe se ya maida akalar kiran ga Khalifa wanda nan take ya shaida masa yanda sukayi da Umaiman. Sosai ran Khalil yayi baci lokacin daya kira Khalifa yake tambayarsa zancen tahowar tasu ya gaya masa ai tace sunyi magana an fasa. Bece masa komai ba ya kashe wayar, ya gwada wayar Umaimah yafi sau a qirga amma a kashe daya gaji ya sake kiran Khalifan yace yaje gidan ya gaya mata ta kunna wayar ko ya bata tasa suyi magana dukda a lokacin dare ya farayi haka ya tafi ya tararda gidan kulle da kwado abinda ya sake harzuqa Khalil din kenan ya qudurce aransa baze sake kiranta ba, duk ranar da ta kirashi da kanta a sannan zeji ba'asin abinda tayi masa. Kamar wasa kuwa seda ya kwashi kwana uku a Lagos ba tareda sunyi magana da Umaimah ba, duk yanda yaso akan ya shareta karya kira wayarta ya kasa jin kuma har kwana ukun wayar a kashe se ya fara tunanin kodai ba lafiya ba amma idan da wani abu ya faru da za'a kirashi a sanar dashi dan haka ya yanke shawarar kiran Mama tunda dai bata gida ya tabbatar da idan ba gidansu ba babu inda zataje dukda be bata izinin hakan ba. Cikin mutuntaka suka gaisa da Mama bayan daya kirata ya sake yi mata gaisuwar Mijin Anty Hafsa ta amsa tana tambayarsa aiki tareda godiyar Kayan Sadakar da aka ringa kaiwa daga gidan Hajiyarsa. Shiru sukayi gaba daya a ransa yana tunanin idan Umaimah bata gidan fa tsahon wannan lokacin ya za'ayi, Kukan Mu'ayyad da yajiyo ta cikin wayar da Ashar din da Umaimah take korawa wata da be san ko wacece ba ya warware masa damuwarsa dan haka kawai ya cewa Maman daman ya kira su gaisa ne yayi mata sallama ya kashe ransa na masa suya, kenan tana sane ta kashe wayar tunda tasan batayi daidai ba tunda Koda ace wayarta ce ta lalace ai yaci ta ari ta wani ta kirashi sannan da izinin wa ta bar gidan kuma meye dalilin qin binsa da tayi. A bangaren Mama kuwa yana kashe wayar ta dakawa Umaimah dake zagin Munawwara yarinyar maqotansu dake shiga tana daukar mata Mu'ayyad din, ta tasata a gaba tana zagi saboda ta riqeshi ya zille ya kifa da baki, "Wai ke baki san tsautsayi ba tana sane zata bar shi ya fadi ne ko yaya da zaki tasa yar mutane a gaba kina zagi, ki kiyaye ni kuma wannan zaman naki ma ya ishe ni haka yanzu Mijinki ya kirani daga yanayinsa na karanci akwai magana a bakinsa amma ya kasa fada, daman ina an kare dake tunda kika zo gidan nan banji ko sau daya kunyi waya dashi ba idan ma wata tsiyar kika tafka ya koroki gida tun wuri ki sanar damu a san yanda za'a magance ta" Zumbura baki gaba tayi ta kalli Maman tace "Ni me zanyi masa ya koroni tafiya yayi baya gaya miki bama shine yace mu dawo gida, wayata kuma ta lalace na fi so se ya dawo ya kaita gyara da kansa dan kar a batamun" ta fadi haka ne kawai amma gaskiyar magana kashe wayar tayi kamar yanda Rufaida ta bata shawara bayan ta qufuri aniyar bazata bishi ba. Mama ta wuceta ba tareda ta kulata ba amma jikinta yana bata qarya Umaiman takeyi dan a saninta tafiya kota kwana biyu ce tare sukeyi dukda wani lokacin se an yi sulhu kafin tafiyar ta yuwu shine yanzu kusan sati biyu ace baya gari ta taho gida gaskiya akwai lauje cikin nadi. Khalil kuwa bayan ya ajiye wayar sa shiru yayi yana tunanin ta inda ze hukunta Umaiman, rainin dake tsakaninsu ya fara yawa har ya zamana kenan be isa ya bata umarni tabi ba se abinda ranta ya ayyana mata koh dole kuwa zeyi maganinta. Tun da ya bar Kano haquri kawai yakeyi musamman da yanda Umaiman ta sake chanza masa tun bayan data haihu saboda ingantaccen jego da kuma gyaran data samu ko tunaninta yayi se hankalinsa ya tashi, a lokacin ma abinda ya faru dashi kenan lokaci daya jikinsa ya farayi masa babu dadi shikadai yasan yanda yake bacci yake tashi ya gama saka ran zuwan nata shine tayi masa wannan cin kan yanzu besan ya zeyi ba, yanzu dole yayi qoqari yaje Kano a weekend din nan dan bashi da inda ze kai lalurar sa idan ba canba. Wunin ranar gaba daya haka yayi shi sukuku harya tashi daga aiki ya koma gida, flat ne me daki biyu da duk wani abun buqata a ciki aka bashi yake zaune sanda aka kaishi masaukin a ransa har yana cewa anyi maganin mitar Umaimah da take cewa ita ba tafiya dashi ne bata so ba Aa haushinta zaman Hotel kullum tana kulle a daki kamar kaza yanzu ga gida nan ta samu kuma taqi zuwa. Ruwa ya fara watsawa kafin yayi sallar Magriba data riskeshi a hanya, fridge ya bude ya tarar da babu wani abin kirki naci da ze qosar dashi yaja tsaki ya rufe, a yanda yake jin yunwa baze iya tsayawa dafa komai ba dan ya siyo kayan abinci duk a shirin zuwan Madam din tasa se kawai ya zari key din motarsa ya fita, a bakin Get din compound din sukaci karo da Sa'id Abokin aikinsa ya fito shima a shirye da alamar fita zeyi, gaisawa sukayi ya shiga qoqarin tada motarsa Sa'id din ya tsayar dashi, be fiya son doguwar magana tana shiga tsakaninsu ba saboda sam halinsa dana Sa'id din basu zo daya ba. Sa'id nada rawar kai ga shegen kule kulen Yammata kullum da macen da zaka ga tazo gidan gurinsa shi yasa sam Khalil baya bashi fuskar da wata magana me tsayi zata hada su data wuce gaisuwa. "Mr Bayero fita zakayi ne, ur face shows that you are tired and Famished, nima fita zanyi naci abinci idan babu damuwa muje tare motana na barta gurin gyara" Badan ran Khalil yaso ba suka fita tare, a hanya se surutu yakeyi masa shi dai amsar sa Eh ko Aa ce dan gaba daya ransa a dagule yake, a gurin cin abincinma seda yaji kamar ya tashi ya bar gurin saboda shegen surutun Sa'id da yanda yammata suke ta zuwa yana gaisawa dasu. Magana yaji daga gefensu, haka nan yaji kamar ya taba Jin muryar kuma jin suna hausa kuma kamar gulmar wani sukeyi haka kawai ya samu kansa da juyawa ya kalle su karaf idanunsu suka hadu, ya kalleta na tsahon seconds uku kafin ya dauke kai kwakwalwarsa na qoqarin tuna inda ya san fuskarta. "Na gaya miki wallahi shine, ai bazan taba manta fuskar Guy din nan ba dan yayi bala'in burgeni" ya sake jin muryar data sakashi waigawar tana fada nan take ya tuno da inda ya sansu, yammatan daya taba taimakawa ya kaisu gida ne wata rana da daddare amma me sukeyi a nan? Ko daman yan duniya ne kawai raina masa hankali sukayi ranar da sukace biki suka zo. Sallamar daya ji a saman kansa ta dawo dashi tunanin, me shegen rawar kance tana tsaye tana masa murmushi tace "Sannu Malam, ka gane ni kuwa" Kallon banza ya mata ita kuwa ko a jikinta se uban murmushi takeyi masa Sa'id ne ya mayar mata da martani yana cewa "Zauna mana yammata kin tsaya kuma" seta ja kujera ta zauna har sannan tana kallon Khalil kamar zata lashe shi. "Tunda kuka shigo na gane fuskarka, na cewa Hadiza kai ne tayi mun musu gashi ashe daman zamu sake haduwa tun waccen ranar nake Addu'ar Allah ya sa na sake ganinka dan ko godiya bamu samu damar yi maka ba waccen ranar" yarinyar ta fada tana yauqi kafin ya samu damar yin magana ta ci gaba da cewa "Ni sunana Khausar, kai dai na san sunanka Khalil dan na gani a motar ka tun waccen ranar" Tissue yaja ya goge bakinsa dan gaba daya abincin ya fita a ransa saboda surutun da tazo tana yi masa akai, shi daya sani ma Cornflacks yasha ya kwanta kawai da wannan fitowar da yayi haka kawai zata qara masa ciwon kai, tsaki yayi ya dauki muqullin motarsa tareda ajiye ATM card dinsa yana kallon Sa'id yace "Gashi nan idan ka gama ka biya ni na wuce seka taho" yana gama fadar haka ya juya abinsa yana jin dayar yarinyar tana cewa "Seki tashi mu tafi ai tunda kin gama zubarwa da kanki mutunchi aikin banza kina ta rawar jiki kamar kinga wani autan Maza". Waiwayowa yayi ya kalli me maganar, waccen dayar ce wadda ta saka Hijabi ranar ya gane fuskarta ne saboda duk ta fisu haske fara ce sosai se yayi murmushi kawai wai Autan Maza. Washe gari yana zaune a office aka kirashi da baquwar number, be dauka ba dan ba kasafai ya fiya amsa number da be sani ba musamman idan ya duba true caller yaga be san sunan me kiran ba. Yana kallon wayar seda tayi masa kira biyar kafin message ya biyo ba ya dauka ya duba "Khausar ce, ina fatan ka tashi lafiya" iya abinda ta rubuta kenan yaja tsaki bayan ya gama karantawa ya goge ya tabbatar Sa'id ne ya bata number sa nan take ya dannan ta a blacklist, to shi ko bufurwar zeyi me zeyi da ita babu abinda ta ajiye se shegen rawar kai. Umaimah ce ta fado masa a rai kawai ya hasaso ace sun hadu ita da Khausar din wayaga yaqin duniya na uku ya tabbatar da haukarsu zata zo daya. Wasa wasa Khausar ta mayar da kiran sa a waya dayi masa text kamar ibadah, data fuskanci yayi blocking layinta seta canza lamba, zata kira sau daya sannan ta tura masa da saqo safe da yamma, a cewarta idan da rai da rabo wata rana ze kulata abinda ta gayawa Hadiza lokacin da takeyi mata gorin rashin zuciya. Aiki ne ya kaisu Lagos din qarqashin qunyar su me rajin kare haqqin mata da qananan yara, a qa'ida sati daya zasuyi amma tunda Khausar ta hadu da Khalil seda ta san yanda tayi aka qara musu lokaci saboda tace bazata tafi ba har seta samu soyayyarsa. Sa'id ne yake qara mata kwarin guiwa akan hakan yana kuma bata tabbacin zata samu Khalil din indai tayi haquru, kuma shi ya gaya mata yana da Mata daya da Yaro hatta da irin sin da yakeyiwa matarsa da baqin kishinta daya samu labari ya gaya mata tace taji ta yarda kuma a shirye take data tunkari kowacce ya mace akan Khalil. A bangaren Khalil kuwa be san ma tanayi ba dan ko messages din nata datake faman aikawa ba dubasu yake ba, shi yanzu hankalinsa gaba daya yana kan aikinsa ne saboda ayyukan da yake kula dasu suna da yawa tuni kuma ya yakicewa kansa Umaimah da tunaninta dan ya fuskanci idan ya daka ta tata baze moruba,lalacewa zeyi da ciwon bacin ranta kawai dan har yanzu da ake kusan kwana goma da zuwansa bata kunna wayarta ba kuma nemi wata wayar ta kirashi ba. Da yammaci yana kan hanyar dawowa daga duba ginin wani company da sukeyi, a hankali yake tuqi saboda yanda gaba daya jikinsa bayayi masa dadi. Damuwa da buwatuwar mace a kusa dashi sun hadu suna neman saka masa ciwo a yankwanakin qarfin hali kawai yakeyi ya kuma yi rantsuwar seya koyawa Umaimah hankali abinda ya dakatr dashi daga tafiya Kano kenan dan a jiya harya hada kayansa ze tafi ya fasa. Tuqi yakeyi sam hankalinsa yayi gaba Allah ya taqaita ya tsayar da motar yayi gefe cikin wani ruwa daya kwanta saura qiris ya bige budurwar dake qoqarin tsallaka titi. Dafe kansa yayi yana mamakin zurfin da yayi a tunani da har beganta ba, seya kashe motar ya fita ganin ta tsaya tana duba jikinta da alama ya watsa mata ruwan daya fada. A fusace ta kalle shi daidai sanda yake bata haquri tace "Dama se anyiwa mutum ba daidai ba ake bashi haquri ai, tun daga nesa dana hango motar nasan koma waye a ciki ba a daidai yake ba, duk yanda nayi qoqarin kauce maka amma ji sda ka batani da ruwan kwata haka kawai". Tunda ta fara maganar yake kallonta, qawar wannan mayyar yarinyar ce, to wai su a nan garin suke ko kuwa yawon rashin jin nasu ne ya kawo su? Kallonta yayi sama da qasa yanzuma tana sanye da doguwar rigar Atamfa ta saka Hijabi Light blue daya zarce guiwarta, sosai Hijabin ya baci da ruwan kwatar daya watsa mata, cikin gajiya da masifar da takeyi masa yace "Kiyi haquri, banganki bane" "Dama ai bazaka ganni ba" "Nace kiyi haquri" yayi saurin tareta ganin tana neman tara masa mutane, shiru tayi shima ya tsaya, kamar baya so yace mata "Ina zakije ga magriba tayi?" Sedata harareshi sannan ta gaya masa, kallonta yayi fuskarsa na nuna mamakin jin sunan Hotel din data fada amma kuma meye nasa a ciki ma, juyawa yayi ya bude motar yana cewa "Muje na saukeki" seta juya tabi bayansa. Tafiya sukeyi babu me magana da wani, wayar dake hannunta ta dauki qara ta daga da sallama yanda take maganar ya fuskanci da Mahaifiyarta suke wayar, sannan a maganganunta ya gane cewar aiki ne ya kawota Lagos din to amma aikin me takeyi? Bayan ta gama wayar ta kashe haka kawai ya tsinci kansa da tambayarta aikin me tazoyi nan, seda ta harareshi kafin ta gaya masa suna aiki da NGO ne kuma an turo su yin wani assignment ne. Har qofar Hotel din ya sauketa, ta kalle shi fuska babu yabo babu fallasa tace ta gode, kallonta yayi yace "Nawane kudin wankin Hijabin naki da kike tayi mun tsaki a mota saboda ya baci" seta harareshi bata ce komai ba, murmushi yayi dan se ya ganta kamar Umaimansa dukda a yanzu daya qare mata kallo ya fuskanci ba yarinya bace, a qalla zatayi shekara Talatin ko fin haka. Wayarsa dake ajiye ya miqa mata yace "Ki saka mun number ki idan kin tsayar da farashin se ki gaya mun". Kallonsa tayi kamar bazata karba ba kuma seta miqa hannu ta karbi wayar ta shigar masa da number ta bashi yayi Dialing wayarta tayi qara ya kalleta yace "I'm Khalil, and you" "Hadiza" "Nice to meet you Khadija" ya fada yanayiwa motar key ta dan ya mutsa fuska tace "Hadiza sunana" "Khadija ne sunanki na Asali ni dashi zan kiraki, ki shiga ciki se wani lokacin" yana gama fadar haka ya taka motar ya bar gurin. Yana tafe yana tuhumar kansa dalilin daukota har zuwa karbar number ta da yayi, zuciyarsa ta bashi amsa da yana da buqatar Abokin hira ne daze debe masa kewa shine dalili, sannu sannu Abota ta qullu tsakaninsu a hankali shaquwa me qarfi ta shiga ya zamana cewa a kullum se sunyi waya dukda Hadizan ta koma Kano amma a koda yaushe suna maqale da juna a waya musamman da dare bayan ya koma gida bashida abinyi sedai ya kiraya su sha hirarsu. Yasan kusan komai a kanta, Ita din Lauya ce me zamankanta kuma tana aiki da qungiyoyin kare haqqin mata da qananan yara. Yanzu idan ya tuna da Umaimah to kewar Mu'ayyad ce ta dame shi akan dole kuma ya sakawa kansa haquri tunda bashida hanyar da zeji lafiyarsa ko ya ganshi, abinda ya sani dai ko bajima ko ba dade dole ta nemi shi, idan bata neme shi ta arziqi ba zata neme shi ta tsiya. UMAIMAH Tun tana daukar abun a wasa harta fara shiga taitayinta ganin ana neman wata daya da doriya babu Khalil babu dalilinsa, a tunaninta data kashe waya ze nemeta kota wayar Mama ne ko ya aiko Khalifa se gashi babu daya daga ciki hasalima ita kanta Maman bata ce mata komai ba akan zaman nata, kowa ya zuba mata ido ne kawai suga iya qarshen Al'amarin. Kudaden hannunta da suke rudarta sun qare tas ko na siyan Data bata dashi dan daman wayarta a kunne take, layinta da aka santa dashi ta cire ta ajiye ta dora wani duk a shawarar Rufaida taci gaba da sabgoginta, sanda tayi mata maganar ita zata Kira Khalil dan da alama yayi fushi da yawa ce mata tayi idan tayi haka ai ta zubda kanta, ta daure kawai harya gama fushinsa ya sakko duk tsiya dai ai ze dawo baze koma can da zama gaba daya ba. Yau ta tashi gaba daya babu yanda take, Allah ya sani tana son mijinta kuma tana kewarsa daurewa kawai takeyi kamar yanda Rufaida take gaya mata wai ta kama Ajinta karta kuskura ta bari ya gane ta karaya dan daman yanayi ne dan ya qureta. Salma ce ta shiga dakin da sallama ta ajiye mata Ruwan zafi a babban Mug se burodi a leda, kallon kayan tayi daman tun tuni ake wulaqantata a gidan nan abinci se a bata kamar wata mabaraciya wani lokacinma idan an dafa seta roqa za'a bata cewa suke sun manta da ita. Kayan taja gabanta ta kalli baqin ruwan shayin ta ja tsaki, gwangwanan kayan Tea din da Khalifa ya kawo mata tun wancen watan da tulin siyayyar Mu'ayyad su Diaper, wipes, madararsa da cereals sabulun wanki da duk wani abun buqata seda ya hado musu da yawa kuma yanda zata dade kafin ta buqata. Kallon Madarar tayi bata wuci kwata a ciki dukda qaton gwangwani ne amma ta kusa shanye shi cikinta ita kadai saboda yanda take barnarsu haka kawai ma kwabawa take tana sha gashi yanzu sun kusa qarewa bataji daga me siya mata dinba kai ita wannan zaman ma ya isheta haka ita ba sakakkiya ba ita bame aure ba bari kawai ta karya billenta ta kira shi ai durqusawa wada ba gajiyawa bane. Layinta data ajiye ta dakko ta saka a wayar, Allah ya taimaketa tana duba balance taga akwai kudi a ciki, layin Khalil ta shiga kira tana kallon Agogo ta san dai yanzu duk inda yake yaja Gym kamar yanda yakeyi duk Asabar da Lahadi se yaje. Seda tayi masa kira uku be amsa baana hudun yana shiga akayi rejecting se ta riqe wayar sororo a hannunta jikinta yana qarayin sanyi, tasan fushin Khalil yana daukar lokaci kafin yayi amma fa idan ta taboshi seta sha wahala kafin ya sauka amma dukda haka ita a yanzu buqatarta ya haqura da gayyatarta idan zeyi tafiye tafiyensa idan dai haka ta samu zata san yanda zata lallabashi su shirya. Maida wayar tayi ta ajiye ta shiga karyawa a ranta tana ayyana qaryar da zatayi dan ta samu hankalinsa cikin ruwan sanyi batareda wata matsala ba. A dakin taci gaba da zaman tsammanin ko ze biyo bayan  kiran da tayi masa, Mu'ayyad na can gurin Anty dan kusan kwanciyar baccin dare kadai ke kaishi gurinta se shan Nono wanda bema damu dashi sosai ba tunda ya kama abinci. Tana nan jiran gawon shanu har aka kira sallar Azahar, seda tayi sallah ta quduri sake kiransa. Tana zaune akan sallayar ta janyo wayarta ta shiga kiran layin Khalil din ringing uku taji an daga taja wani numfashi ta dire ta narke murya kamar Kitse yaji wuta tace "Habibi" "Umaimah, ina aiki ne. Idan babu damuwa ki bari zuwa dare idan na koma gida zan kiraki ok" Khalil ya fada cikin dakakkiyar murya daga daya bangaren, kafin ta samu cewa wani abu dif ya kashe wayar seta cireta da kunnenta ta zura mata ido kamar zata ganshi ta cikin wayar, ita ze cewa yana aiki ta bari ze kirata daga baya? Khalil din data sani Sallah ce kadai zata kirashi yana yi da baze katse ya amsa kiranta ba shine yanzu ze gaya mata yana aiki ne. Tagumi ta rafka hannu biyu karfa kwabarta tayi ruwa daga neman gira a rasa ido, to waima tsahon wannan lokacin da suka dauka Khalil din be nemeta ba ya ya yake rayuwa, wacece take debe masa kewarta da duk sauran buqatunsa ina yake kaisu? Kai wai ita wace toshewar basira ce ma ta sameta haka data sake shi a bariki shi kadai, sam ta manta da yanda Lagos din nan take. Mata ne suke neman maza ba maza ke neman mata ba ballantana irin Khalil daya hada duk wasu qualities da zasu saka mata su soshi, to yanzu shirun nan da yayi mata idan ya zama na wata ya samu take debe masa kewarta fa? Zabura tayi ta miqe tana salati saboda wannan tunani daya fado mata dagaske idan ya zamana Khalil wata ya samu fa shiyasa ya manta da ita dan Khalil din data sani baze yi fushin wata daya da ita ba ballanta har ya iya zama a wani gari daban ba tareda ita ba na tsahon wannan lokaci bama ze yuwuba sedai idan kuma wani abin ne ya faru dashi bata sani ba kuma ba'a gaya mata ba. Hannu ta dora aka tana juyi a dakin, tunani biyu ne suke mata zarya kodai Khalil ya samu wata ko kuma wani mummunan abu ya faru dashi an boye ba'a gaya mata ba. Wayarta ta dauka ta shiga sake kiransa, missed calls ta ringa tara masa ita kanta bata san Adadin kiran datayi ba kafin ya daga cikin fada fada yace "Wai Umaimah bana gaya miki ina aiki bane ki bari zan kiraki idan na gama" "Khalil ka amsa mun kawai lafiyarka qalau ko Aa? Idan kuma qalau kake wace yar iskar Karuwar ce ta dauke maka hankali da har ka manta damu tsahon wata daya baka waiwaye mu ba" ta fada cikin tashin hankalin daya rufeta ga mamakinta se ji tayi yaja wani shegen tsaki kafin tace wani abu ya kashe waya seta fasa ihu iya qarfinta tareda yin wulli da wayar ta fadi a qasa, Mama dake tsaye bayanta ba tareda ta sani ba ta watsa mata Marin daya sakata dauke wuta na wani lokaci, nuna ta tayi da yatsa tace "Ki shiga hankalinki Umaimah, ki shiga hankalinki" kafin ta juya cikin matuqar bacin rai tabar dakin. Ta rasa wacce irin yarinya ce Umaimah, ita dai bazata taba yarda da lafiyar kwakwalwarta qalau ba dan abubuwan da Umaimah takeyi sam basuyi kama dana me cikakken hankali ba. Uwar dakinta ta wuce Anty na tambayarta meya faru dan gaba daya sunji Ihun Umaimahn bata amsa ba ta wuce ta. Wayarta ta dauka ta shiga kiran layin Khalik, ta gaji da wannan zaman na Umaimah, gara ta sani idan kaso auran tayi ko ma menene dukda Abba yace ta bari ta saka mata ido kawai, koma menene idan ta gaji da boyewa zata fada. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS* *Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so* *Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa* *Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah* *A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu* *Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki* *A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu* *Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah* *Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan* *07031876677* Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 33 KHALIL Tun kiran farko da Umaimah tayi masa yana tsaye a Site yana duba aiki,ginin wani company sukeyi da sun kammala shi finishing ne ya rage kuma suna buqatar gamashi cikin kwanaki biyu abinda ya fitar dashi da safiyar kenan saboda akwai sauran ayyuka kuma dole seya zaman na yana gurin. Yana tafe a hanya suna waya da Hadiza da yanzu baya iya shanye wasu awanni ba tareda yayi magana da ita ba. A rayuwar sa be taba zaton ze sake son wata mace bayan Umaimah ba se gashi Hadizan tayi masa shigar farat daya, yana jinta a zuciyarsa dukda babu hadi tsakanin soyayyarta data Umaimansa amma ya yarda itama yana sonta, tana da sanyin hali da dabi'u masu kyau da suka taimaka gurin jan zuciyarsa zuwa gareta. Har ga Allah yanzu mantawa yake yi da ita idan ba ya kunna screen din wayarsa yaga hotonsu da yake kai ba shiyasa koda ta kirashin beji komai a ransa ba, ya qudurce indai dan yana nuna damuwa da ita ne take wahalar dashi to ze yaqi zuciyarsa ko zatayi yaya ze jingineta a gefe na wani lokaci har zuwa tasan mutunchinsa shima koda ace abubuwa zasu daidaita tsakaninsu. Data sake kiransa yana cikin yin sallar da be samu yayi akan lokaci ba, yana tayarwa ta fara kira bata haqura ba kuwa har seda ya idar sannan ya daga tarin missed calls din daya gani ya sakashi tunanin ko wani abun ne ya faru sedai maganganun data tareshi dasu suka tunzurashi, lokaci daya ransa ya baci musamman kalmar Karuwa data hadashi da ita. Ya rasa abinda yake damun Umaimah da sam harshenta bashida linzami, bata tauna magana kafin ta fadeta musamman shi datafi rainawa sama da kowa duk abinda yazo mata a zuciya fada masa tayi amma zeyi maganinta. Kiran Hadiza ne ya shiga wayarsa, cikin girmamawa da mutuntawa ta gaishe shi tareda tambayarsa aiki. Yanda take yi masa ba qaramin dadi yake masa ba dan shi a rayuwarsa mutum ne da yake son a girmama shi kuma babban abinda ya rasa daga Umaimah kenan shiyasa Hadiza ta samu wani matsayi babba a zuciyarsa. A taqaice sukayi magana da ita, daga muryarsa ta fahimci kamar yana cikin damuwa dan haka bata barshi ba seda ta fada masa kalaman da suka rage masa kaifin fushin da ya ke ciki sukayi sallama akan idan ya koma gida ze kirata. Can bangaren Umaimah kuwa kuka ta dasa kamar wadda akacewa Mama ta mutu, Anty ta leqa tana tambayarta abinda ya faru tunda Mama taqi magana tayi mata banza se qara rusa kuka takeyi haka ta gaji tabarta sedatayi me isarta kafin ta tashi ta shiga hada kaya. Tas ta hada akwatunanta danma Allah yaso jiya anyi mata wankin da seda Mama taci ubanta kafin ta hada kayan su Nazifi suka wanke mata dan a gidan ma babu abinda ta ajiye idan ba chatting da waya da qawaye ba se bacci wanka kansa se da daddare in tazo kwanciya zatayi taimakon My'ayyad daya Anty gurinta yake wuni ita take gyarashi tsaf har kayansa duk suna gurinta da shi kansa Allah kadai yasan qazantar da ze ringa sha. Sanda ta gama hada kayan tsaf ta zura Hijabinta ta fita,Mama na daki Anty kuma sun kwanta baccin qailula ita da Mu'ayyad Umaimah ta ringa jidar kayanta tana lodawa a Taxi din data kira seda ta gama tsaf ta shiga dakin Anty ta dauke yaron tayi tafiyarta ba tareda kowa ya sani ba. Gidan Rufaidah ta shiga bayan da me mota ya gama sauke mata kayanta, gidan yayi budu budu bazata iya gyarab sa ita kadai ba dan haka ta shiga roqon Alfarmar qanwarta dake zaune da ita tun bayan data haihu akan tazo ta tayata nan Rufaidan tace mata ta kirawo Hauwan Maman Hauwa su hadu dan sufi sauri haka kuwa akayi yaran suka zage sosai suka gyara mata gidan tas har dakin Khalil suka wanke tsakar gidan ta tattara musu ragoye ragoyen Turaruka da sauran kayan kwalama irinsu chocolate da biscuit suka tafi. Seda dare yayi ta fara jin tsoro kuma dan bata taba kwana a gidan ita kadai ba, goma harta gota ta goya Mu'ayyad ta shiga gidan Maman Hauwa ta roqeta ko Hauwa zata tayata kwana jiki na rawa Maman hauwan ta tasota dan harta fara bacci suka tafi, a dakinta tace ta kwanta ita kuma suka kwana dakin Khalil da Mu'ayyad. Da safe seda ta sake gyara mata gidan tsaf suka karya tayi wanke wanke kafin ta wuce gidan su ta gaya mata yau ma tazo, Khalil baya nan zata ringa tayata kwana har zuwa sanda ze dawo. A can gidansu kuwa duk abinda tayi akan idon Mama dake tsaye jikin window tana kallonta ne, girgiza kai tayi a fili tace "Allah ya shirya ki Umaimah" ta koma ta zauna ranta sam babu dadi. Anty kuwa data farka a bacci ta fito tana tambayar waya dauki yaron, lokacin Mama tana sallah gaba daya yaran dake tsakar gida suka ce basu ganshi ba, Mama data idar ta leqo tace mata uwarsace ta dauke shi sun koma gidan su seta kama baki cikeda mamaki tace "Se a gaida Umaimah wace irin tafiya ce haka babu shiri ko Khalil din ne ya dawo ai da tayi magana se aje a gyara musu gidan tukunna, ga kayan megidan nawa ma ta barsu a bita dasu daga baya" ita dai Mama batayi magana ba dan ranta a matuqar bace yake da Umaiman kawai bata son furta wani abu ne balle ta fadi mara dadi. Umaimah kuwa seda ta shafe kwana biyu tana dakon kiran Khalil amma taji shiru, abin ya dameta sosai, tana so ta kirashi amma ta kasa saboda gaba daya zuciyarta qarya take gaya mata akan Ita Khalil yayiwa laifi daya yi tafiyarsa uwa duniya yaqi ya waiwayesu sam ta tak nata laifin na qin bin umarninsa da tayi ga wani bangare dake mata hudubar tabbas Khalil wata ya samu a can shiyasa har ya iya daukar wannan lokacin be waiwayi gida ba, idan kuwa haka ne ta rantse da Allah daga shi har koma wacece sun tarowa kansu abinda bazasu iya dashi ba, tana nan ze dawo ya iske ta ze kuma gane kurensa. Sabgoginta taci gaba dayi bata aikin fari balle na baqi se chatting da bacci su kadai ta saka a gaba dan yanzu Hauwa keyi mata komai a gidan, da sun tashi zata yi mata shara da duk wani aiki daya kamata tayiwa Mu'ayyad wanka ta bashi abinci ta goyashi su tafi gidansu, a can yake wuni zir idan ta maidashi to sedai idan ya saka rigima sunyi sunyi yaqi shiru shine zata kaishi yasha Nono daya gama ta kuma sabarsa ko su zauna anan gidan kota koma can gidansu dashi ita kuma hamshaqiyar ta samu guri tayi yanda take so ta qudurce bazata sake kiran Khalil ba, Maman Hibban ce ta tallata mata wasu kayan mata datace ta siya a gurin *Sumayyas herbal aphrodisiacs*  tana jin sunan bata bata lokaci ba lale kudaden data gaya mata ta bata dan ta san mutunchinsu sune ingantattun kayan da Yayar Rumasa'u ta Dutse ta taba bata ta, taji dadinsu kwarai a lokacin ita kanta ta samu lafiya a jikinta ga Khalil seda ya zame mata tamkar raqumi da akala saboda yanda take gigita masa tunani da taimakon kayan *SUMAYYAS HERBAL APHRODISIACS (07031876677)*. Murmushin mugunta tayi lokacin da Maman Hibban din ta kawo mata saqon, bata bata lokaci ba a ranar ta fara amfani dasu ga hadaddiyar dilkarta da take goge jikinta tas da ita saboda so takeyi duk randa Khalil din ya dawo mata idan suka gamu seya manta sunansa ta rigada tasan lagonsa ta wannan fannin zata kamshi ram babu boka babu malam shiyasa zatayi wasa da komai banda gyaran jikinta ta wannan fanni. Ranar Juma'a misalin qarfe sha daya tana zaune a palour taci kwalliya da wani Lace fari ta kashe dauri yanda kasan me zuwa wani taron biki, wayarta na hannunta ta jona sabon ringlight din da ta siyo jiya saboda daukar videon Tiktok. Tsabar zaman banza da rashin abinyi da takeyi ya saka ta fara sha'awar Matan dake video suna dorawa a Tiktok din, daman Rufaida ta dade tanayi ta na kuma tayi mata maganar itama ta fara dan ita a yanzu ta kai yawan followers da har Tiktok sun fara biyanta saboda irin badalar da takeyi da sunan comedy marasa tunanin irinta suna kalla sunayi mata like wasu su zageta, bata mutunta kanta matsayinta na musulma mace ba kuma matar aure take banzatar da kanta a Social media. Waqa ta kunna bayan data gama saita wayar ta ajiye nan ta shiga bin waqar daga zaunen da take tana dan juya jiki wayar na dauka. Waqoqi ta ringa sakawa abinta tana yin videos wasu a zaune wasu a tsaye wani ma jikin mudubi ta tafi ta dauka seda ta gaji ta koma ta zauna bayan ta kashe Ringling din ta shiga duba videos din tana editing. Hankalinta yayi nisa a abinda takeyi sam bataji sanda aka bude Get ba se sallamar sa da taji a tsakiyar kanta. KHALIL Ranar Alhamis aka fitar da sunan sabon manajan bangaren da aka dorashi ruqon kwarya dan haka a ranar ya tattara ya damqa masa duk wasu abu na office din da suke hannunsa musamman daya kasance ya kammala duk wata kwangila da aka fara se sababbi wanda suka fara proposing shiyasa be sha wahala ba gurin damqa masa komai a daren kuma ya hada kayansa yayi booking jirgi zuwa kano dan ya gaji da zaman garin matuqa sati kusan bakwai ba wasa ba yayi kewar Kano kullum Hajiya cikin mitar sun tafi sunyi zamansu takeyi dan duk a lissafinta da Umaimah suka tafi, kuma da yake itama yar gaske ce tunda ta fahimci tunanin Hajiyar ko kiran ta tayi a waya suka gaisa bata taba nuna mata basa taren ba. Tara da yan mintuna ya sauka a Kano, ya taho da wasu takaddu dole ya wuce office kai tsaye danya bayar dasu kafin ya wuce gida tunda ranar aiki ce, be bata lokaci ba yana kai takaddun inda ya dace ya kama hanyar gidan. Sanda ya isa ya rigada yasan babu kowa a gidan shiyasa be kashe motar ba ya fita ya bude Get sedai mamaki ya kamashi jin daddadan qamshin turaren wuta yana tashi a tsakar gidan, ya kalli gurin dakyau yaga ko ina fes da alama ba'a jima da wankewa bama dan gurin be qarasa bushewa ba kuma ba lokacin damuna bane ballantana yace ruwa akayi seya tabe baki ya juya ya koma mota ya shigo da ita ciki. Jakar computer sa kadai ya dauka dan ya gaji bacci kawai yake so yayi yanzu kafin lokacin sallar juma'a yayi yana so kuma yaje gidansu Hadiza, so yake ya shammaceta dan be sanar da ita dawowarsa ba. Muqulli ya zura a qofar yaqi shiga seya zare dan alama sun nuna akwai wani ta ciki kenan ya murda handle din ya tura qofar hancinsa na sake shaqar qamshin turaren wutar da Hauwa ta cika gidan dashi. Da mamaki yake kallonta, tana zaune gaba daya hankalinta yana kan wayar da take dannawa fuskarta a washe tayi wani sanyayyan kyau seya ga ta qara masa haske da qiba irinta wanda yake cikin kwanciyar hankali. Dauke idonsa yayi daga kanta ganin yana neman shagala da kallonta ya ci gaba da takawa cikin palour bakinsa dauke da sallama daidai nan ta dago a dan firgice ta kalle shi, wannan murmushin nata na yaudara ta sakar kafin ta ajiye wayar hannunta ta miqe tsaye ta nufeshi cikin takun jan hankali tana qarasawa kusa dashi kafin yayi wani abu se jinta yayi a jikinsa ta ta zagaye wuyansa da hannu biyu ta sajar masa peck akan lips dinsa kafin tayi far da idonta tace "Sannu da zuwa honey". Sakin baki yayi kawai yana kallonta tsabar mamakin abinda tayi, babu ko digon damuwa ko tashin hankalin daya zata zatayi masa idan sun hadu dukda be saka ran ganinta a gidan kuna a yanzu ba ko dab saboda haukan data so ta farayi masa waya ranar nan hakanan babu ko digon damuwa ko nadama akan laifin da tayi masa se zallar rainin hankali da iya bariki take nuna masa lallai Umaimah ta wuce duk inda yake tsammaninta. Hannu ya saka ya janye ta daga jikinsa saboda yanda turarukan datayi amfani dasu da yanda take goga masa jikinta suke neman yin tasiri akansa ya shige daki ba tayi fushiba ta bishi tana masa sannu da zuwa. Sake kama rigar da yake qoqarin cirewa tayi seya dago ya kalleta ido cikin ido yace "No thank you i can help my self" fuska a daure haka muryarsa babu wasa a cikinta, a maimakon yaga tayi fushi sema wani munafukin murmushi ta saki tana cewa "Toh bari na hada maka ruwan wanka sena sama maka abinda zakaji dukda dawowan naka babu sanarwa aida na hada maka special" ta wuce bandakin tana kada jiki. Binta yayi da kallo kamar wani soko, yanda take abubuwanta yanda kasan sunyi rabuwar mutunci ya dawo daga office ko wata gajeriyar tafiya, kai shi baya jin ma ya taba samun tarba irin haka a gurinta fuska a sake, gida qalqal ita kanta tsaf se an samu wani abun be cika ba. Yana tsaye ya gagara ci gaba da cire kayan ta fito daga Toilet din, ido daya ta kashe masa tare da hura masa kiss kafin ta saka kai ta fice daga dakin seda ya saki ajiyar zuciyar dabe san sanda tazo masa ba yaci gaba da cire kayansa a ransa yana jimamin hali irin na Umaimah. Ya fuskanci ta rigada ta san lagonsa akanta shi yasa take masa iskanci yanda ranta ya bata idab kuwa hakane wannan karon shima ze zama namiji baze sake bari ta mayar dashi Soko ta qibin umarninsa sannan tazo tana masa kissa da kisisina tayi zaton ze sakko ba saboda ga Jarababbe. Wankan ya shiga yayi, a kan bedside drawer ya tarar da Butar shayi da cup se madarar ruwa wadda yake amfani da ita se qaramin Bowl data zubo wani abu kamar cookies kamar cake. Seda ya sakawa qofar dakin key kafin ya shafa mai a jikinsa sama sama ya koma gefen gadon ya tsiyaya ruwan shayin a kofi se tashin qamshi yakeyi irin yanda yake so amma idan ba ita tayi ra'ayi ba farin ruwan fanfo zata tafasa ta zuba masa a flask ta bakinta da fada can ya gane. Tas ya cinye cookies din ya sha shayin ya ture kayan gefe ya haye gado, se a sannan ya kunna wayarsa da tunda ze hau jirgi ya kasheta. Saqon Hadiza ne ya fara shiga na barka da Safiya sena Juma'a ya biyo bayansa, yayi murmushi yana mayar mata da amsa kafin ya danna mata kira dan yana so yaji muryarta. Seda gabansa ya fadi sanda yaji motsin Umaimah tana taba qofar, Hadiza ta daga wayar kamar wani munafuki yayi qasa da murya yace mata "Sorry Dija zan kiraki" kafin tace wani abu ya kashe wayar. Daga kan gadon cikin daure murya yace "Ya akayi ne" qirjinsa na dukan saba'in saba'in saboda tsoron ko Umaimah taji maganar da yayi a waya, Umaimah dake tsaye a waje ta harari qofar cikin kissa tace "Ban gane ya akayi ba mace zata shiga dakin Mijinta ka ringa tambayarta ya akayi wai meye ma dalilin rufe qofar da key?" "Bacci zanyi bana son damuwa please, idan qarfe daya tayi ban tashi ba ki tasheni" ya bata amsa kafin yaja bargo ya rufe jikinsa ya juya baya kamar tana cikin dakin. Baqinciki ya shaqe wuyan Umaimah ita Khalil ze wukaqanta dan ma yaga tana ta tasa ko, wallahi badan da abinda take nema ba ko kallo be isheta ba tunda ai ita ya kamata tayi fushi ya tafi yawonsa ya barta kusan wata biyu kamar wata gantalalliya. Kwafa tayi ta koma cikin palour ta zauna, tayi niyyar har girki tayi masa amma yayiwa qaton kansa badai yaci na rana ba sedai da dare idan taga dama tayi. Khalil kuwa yanajin ta matsa daga qofar ya sake kiran Hadiza suka shiga hira dukda a hankali yake maganar kuma cikin takatsantsan ita kanta Hadiza seda ta tambayeshi lafiya tajishi haka yace mata babu komai, sunyi kusan minti goma kafin sukayi sallama saboda tace masa ta tashi aiki zata wuce gida ya ajiye wayar babu dadewa bacci ya dauke shi bayan ya saita alerm dan ya san indai Umaimah ce sedai ya kwana yana baccin nan ba tashinsa zatayi ba musamman da ya rufe mata qofa. Tana nan zaune tana danne danne a waya har Azahar tayi, bataji motsin fitowar se tambayar ta da yayi ina Mu'ayyad, a firgice ta dago kamar mara gaskiya, yana tsaye akanta yayi wanka ya saka manyan kaya Light blue din shadda data karbeshi sosai ya kafa hula daman Khalil ba daga baya ba gurin iya saka hula, haka nan taji wani abu ya soketa, ba yanzu ya fara saka manyan kaya ba musamman da yake yau juma'a amma haka kawai taji kwalliyar tasa ta yau tayi yawa ga uban turare daya fesa seta tura baki tana kallonsa tace "Gaskiya kaje ka canza kaya kayi kyau da yawa ba zaka fita a haka ba" "Se kizo ki cire mun ai, ina tambayarko kina yi mun wani shirme" ya bata amsa yana kallonta. Gefe ta kalla ta tunzura baki tace "Ai shikenan, amma wallahi duk wadda ta kalleka Allah ya isa". Yana shirin tambayarta shi take yiwa Allah ya isan ko kuma wadda zata kalleshin suka jiyo bugun qofa da qarfi. Tsaki yaja ya fita, seda ya tambayi waye kafin ya bude qofar jin muryar mace yasan baze wuce jama'arta ba tunda tun a kwanaki ya lura yanzu tana hulda da maqota suna shige da fice a gidan. Hauwa dake goye da Mu'ayyad ta gaishe shi ya amsa yaron ya juyo da sauri ya kalleshi seya hau zillo yana bangala dariya alamar ya ganeshi, sakko masa shi tayi ya karbeshi ya rungumeshi a qirjinsa yanajin qaunar yaron tana sake ratsashi. Ya qara girma da wayo sosai akan lokacin daya tafi, tsawar da Umaimah ta katsawa Hauwa data saki baki tana kallon su Khalil dince ta dawo dashi daga shauqin kewar Dansa. Masifa take mata akan kallon meye ta kafe su dashi kamar wata mayya "Wayace ki zo ma yanzun kuma da kika shigo meya hana ki wuto ciki kaitsaye zaki tsaya kina kallonsa kamar wani sa'anki" Umaimah ta fada cikin daga murya, Hauwa tayi rau rau tace "Yaqi zamane Anty se kuka yakeyi sannan ya bata kayan jikinsa shine Mama tace na dawo dashi idan ya huta se mu koma". Kallon kayan jikin nasa Khalil yayi se a sannan yaga bacin da sukayi da kamar gasarar koko komenene har sun bushe, fuska a hade ya miqawa Umaimah shi jin ana kiran sallah yace "Kiyi masa wanka ki canza masa kaya, kar a sake fitar mun da yaro wani guri kinji na gaya miki" ta karbeshi ya bude Get din, tana tsaye ya fita da Mota ya dawo ya sake rufewa kafinta raka bayansa da harara tareda jan dogon tsaki seta juya kan Hauwa data sunkuyar dakai tun masifar data farayi mata tace "Daga yau se yau karki sake shigowa gidan nan idan Mijina yananan, kuma ko a hanya kika ganshi karki kuskura ki nuna kin sanshi ballantana ki gaidashi idan kuwa na sani zaki gane kurenki". Kallonta Hauwan tayi a ranta tace ikon Allah a fili kuwa se tace "Toh Anty tayaya zan san idan yana gida kuma ko yanzun ai bugawa nayi bansani ba shiya zo ya bude kinga bazanqi gaishe shi ba" Ciki ta juya ta bita tana cewa "Daga yau ki bar zuwa sedai idan ni na kiraki" Hauwa ta amsa da "Toh Anty". Wanka ta saka tayiwa Mu'ayyad din ya ringa tsala kuka kuwa tana falo tana mata masifar me take masa yake kukan tace babu komai ashe da ruwan sanyi take masa wankan kuma garin daman da sanyi. Haka ya ringa Atishawa bayan gama wankan amma sam hankalinta be kai ba, ta dauko mata kaya ta shirya shi ta dama masa abincinsa shima dakyar suka dura masa ana gamawa ya dawo dashi ta ringa surfawa Hauwa masifa se kace ba ita tace tayi masa durar ba, ita dai data samu ta gyara masa jikinsa yayi bacci ta sulale tabar mata gidan. Khalil daga Masallaci gidan Hajiyarsa ya wuce, a can yaci abincin rana tana tambayarsa su Umaimah tareda qorafin meyasa be fada mata yau zasu dawo ba ai da anyi musu girki yace mata babu komai tafiyarce tazo musu babu shiri dukda haka tace se anyi na dare an kai musu ya gayawa Umaiman kar ta dora komai. Yadan jima suna hira har gurin uku kafin yayi mata salkama ya kama hanyar Na'ibawa gidansu Hadiza, tiryan tiryan se gashi a qofar gidan daya saukesu waccen ranar har mamakin kansa yakeyi yanda ya iya ganewa, guri ya samu yayi parking yana tunanin ta inda ze gano gidan su dan baya so ya kirata surprising nata kawai zeyi. Glass din gefensa aka kwankwasaz qawar Hadiza ce me shegen rawar kan nan da baze ma iya tuna sunanta ba, sauke glass din yayi ta washe masa baki dole shima ya qirqiro murmushin da be kai zuci ba ya amsa sannun da take yi masa. "Yau gaka a unguwarmu" ta fada tana qara fadada fara'arta, "Eh wallahi gara da Allah ya kawo ki ma, daman neman wanda zan tambaya nakeyi tunda gaki ma shikenan" ya fada yana kallonta. Murmushin dai ta kumayi tace "Gurin wani kazo kenan da har ina tunanin..." "Gurin wata dai, gurin qawarki Khadija nazo kinsan wancan ranar anan na tsaya ban san ina ne gidansu ba kuma bana so na kirata so nakeyi na shammaceta kawai se naje qofar gidan zan kirata" Khalil ya katseta kafin ta fara masa shirme. Idan da ace hankalinsa akan Khausar yake da yaga sanda numfashinta ya tsaya na wani lokaci sakamakon jin abinda yake fada, abinda ta dade tana addu'a, tun ranar data fara ganinsa rana bata fito ta koma ba ba tareda ta roqi ubangiji daya mallaka mata shi ba shine yanzu zezo har qofar gidansu yana tambayarta gidansu wata, abinda take muradin samu daga gareshi ya mallakawa watanta kenan "Khausar kinyi shiru kina kallona lafiya dai" ya fada yana kada yatsunsa akan fuskarta ganin ta tsura masa ido babu alamar kuma hankalinta yana kansa ne. Firgigit tayi kamar wadda ta tashi daga bacci kafin tayi qoqarin danne duk wani abu da takeji a ranta tace "Yi haquri kaina ne yake ciwo magani na fito na karbo daman a Can Chemist din, bari na kwatanta maka babu nisa da ka kai qarshen layin nan kace a nuna maka gidan su Salim nan ne" "Maimakon ki shigo ki rakani?" Ya tambayeta, seda ta dauke kukan dake shirin zubo mata kafin ta girgiza masa kai tace "Aa, kaje kawai idan kan ya sauka qila kafin ka tafi zan shigo". Motarsa ya kunna ya qara gaba, yana bacewa ganinta ta fasa ihu tareda zubewa a gurin kamar wadda ta hau iska seda Mahaifiyarta dake tsakar gida ta fito da gudu tana tambayar menene. Kuka Khausar takeyi tamkar ranta ze fita, tunda ta dora ido akan Khalil soyayyarsa tayi mata kamun kazar kuku, ta saka rai da samunsa a shirye kuma take da tayi duk me yuwuwa akan ta same shi shine yanzu ma Hadiza zata sake yi mata kwacen saurayi? To wallahi sedai kowa ya rasa a wannan karon ma ta gwammaci suci gaba da zama gaba dayansu har qarshen rayuwarsu ba tareda aure ba idan har bata samu abinda take so ba toh kuwa ba zata barwa Hadiza ba Khalil kuwa kamar yanda ta bashi kwatance haka yabi, a can qasan layin ya samu yara ya tambayesu suka nuna masa gidan. Gidane qaramin na masu rufin Asiri ya samu guri yayi parking kafin ya aika daya daga cikin yaran akan yayi masa sallama da Hadizan. Dawowa yayi yace tace ace bata nan abin ya bashi dariya daman ta gaya masa bata fita zance in har bata san da zuwan saurayi ba dan haka ya ciro wayarsa ya kirata. Sosai tayi mamaki dan bata yarda dagaske bane seda ta ganshi. Har cikin gidan ta shiga dashi suka gaisa da Mahaifiyarta tana ta saka musu Albarka duk se kan Khalil ya qulle ya rasa gane me Hadizan ta gaya mata yake tsakaninsu da take irin wadannaj maganganun. A qofar gida suka qarasa zancen shida yaje da niyyar yin minti talatin ko qasa da haka se gashi ya kwashe kusan awa biyu ya rasa dalilin dayasa yake jin dadin hira da Hadizan kodan tana da hankali ne sannan gogaggiya ce a kan harkokin rayuwa saboda yanayin aikinta da mutanen da take mu'amula dasu shiyasa duk wata magana tata take zama ta hankali da nutsuwa. Wayarsa da ake ta kira ce sakasu katse hirar da sukeyi, gabansa ya bada Rass ganin me kiran, kafin ya daga wayar ta katse se a sannan ya ga tarin missed calls din da tayi masa har goma haka nan yaji jikinsa ya dauki rawa, a iya saninsa babu abinda ze saka Umaimah jera masa wadannan kira sedai rashin lafiya ko kuma ta ganshi ko ta samu labarin yaje gurin wata a zuciyarsa ya raya Allah yasa rashin lafiya ce dan ta fi masa sauqin tashin hankali akan ace Umaimah ce ta ganshi ko taji labarin yaje hira gurin wata mace. Sallama yayiwa Hadiza ya shiga mota tana tambayarsa lafiya ganin yanda ya rikice lokaci daya yace mata babu komai ta shiga gida zasuyi magana. Seda ya bar Titin Na'ibawa gaba daya kafin ya samu gefen hanya ya gangara ya tsaya. Kamar wanda zeje gaban Alqali ya bada shaida haka ya ringa gyaran muraya yana gwada yanda zeyi magana dan harga Allah hankalinsa a tashi yake. Daurewa yayi ya danna kiran wayarta. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS🧕🧕* *💞Barkan mu da warhaka en uwa mata, bugu da qari ba kadai a bangaren kayan gyaran aure ingantattu ta tsaya ba, ta na bada magunguna na musulunci akan cututtuka na yau da kullum wanda suke damun al'umma.* *Cututtuka irin su matsanaicin ciwon mara a lukuta mabanbanta ko kuma lokacin al'ada, daukewan al'adan lokacin daukewan bai zo ba, al'ada ya rinqa wasa, rashin sha'awa ko ciwon kai, ciwon qirji wanda aka rasa gane kanshi ana tunanin ulcer ne, kuma anyi maganin amma har yanzu ba a dace ba, matsalar Ashiq wato aljanin soyayya(wannan sai bayan tambayoyi sannna za a tabbatar). Ciwon ciki, hawan jini, ciwon sugar, ciwon hanta, typoid/malaria, basir, ciwon baya da qafa, ciwon qashi da kuma matsalar infertility, duk da haihuwa Allah ne ke badawa amma kuma a wasu lokutan akwai cututtuka da kan kama mahaifa ko kuma reproductive system din mace wanda su kan iya hanata daukan ciki. Cututtuka irin su Endeomatriosis, cervicitis, fibroids, etc.* *Ku karzayo domin lafiya uwar jiki💪💪, sannan ta bangaren gyaran aure, sumayyas herbal ta lashi takobin qara zage damtse wajen inganta kayayyakin ta domin samun maslahan ku a* *rayuwar ku da auratayyan ku. Aure dai ibada ne a don haka gyaran aure wajibi ne, musamman idan kin samu in da zaki gyara kan ki da kayayyaki na kwarai wanda basu da illa ga lafiya kuma ba irin kayan da zasu Kai ki ga halaka ba,su saki rasa imanin ki duk wai da sunan gyaran aure. Ah ah er uwa ayi hattara kar garin neman gira a rasa ido.🧏🏻‍♀️ Allah ya tsare mana imanin mu🙏🙏* *Garzaya ki dannan link din kuma kiyi saving number ta domin kuwa akwai alfano mai yawa.* *Wa.me/+2347031876677* *Ko kuma akan Instagram* *https://www.instagram.com/p/CqQJVrVIdjq/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==* *Allah ya biya mana buqatun mu na alkhairi amin.* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 34 Har wayar ta qaraci ihunta bata daga ba, ya sake kira nan ma haka, ajiyar zuciya me qarfi ya saki ya zari tissue ya goge zufar sata tsatstsafo masa a goshi dukda Ac motar a kunne take. Key yayiwa motarsa ya koma kan titi yaci gaba da tafiya. Tunawa da yayi beyi sallar La'asar ba dan yana qofar gidansu Hadiza aka kira yasaka shi neman Masallaci akan hanya yayi sallar sa. Tunanin inda zeje yakeyi, kamar ya koma gidan Hajiya sa seya tuna tace masa zataje barka matar dan qawarta ta haihu haka nan ya yanke shawarar zuwa ya gaida Mama babu bata lokaci ya kama hanya. Seda ya tsaya yayi musu tsaraba kamar yanda ya saba baya tana zuwa gaida surukan nasa haka nan ko babu yawa seya riqe wani abun. A qofar gida ya hadu da Yaya Aminu wanda shima zuwansa kenan suka gaisa kafin suka shiga cikin gidan tare. Mama bata nan taje gidan Anty Hafsa dan tun Rasuwar Mijinta bata cika lafiya ba, shiyasa kusan duk sati Maman ko Anty wani zeje ya gansu dukda akwai yar Uwan Abban su Goggo Halima dake zaune tareda ita kafin ta gama takaba. Be jima a gidan ba ya ajiye musu tsarabar daya je da ita ya tafi bayaj Anty ta hada masa kayan Mu'ayyad tana masa tsiyar ashe shi yayi kira Umaimah ta gudu babu sallama. Haka ya ringa yawo a gari bashi ya koma gida ba se da yayi sallar Isha. Da fargabar abinda ze tarar ya bude Get ya shiga da motarsa. Seda ya kwashe kusan minti biyar a bakin qofa yana gwada budeta yana fasawa, qin amsa wayarsa da kuma rashin fitowarta ta tareshi suka qara sakashi a rudanin abinda ze tarar haka dai yayi shahada ya tura qofar da sallama ya shiga. Tana kishingide akan kujera ta miqr qafafunta akan centre table. Skin tight ne fari a jikinta ya matse ta tsam  iyakarsa qaurin ta ga sarqar qafa silver data saka. Fuskarta ya kalla zuwa qirjinta se yayi sauri dauke kansa saboda yanda Armless rigar data saka bata boye komai na jikinta na, daman iya karta saman cibi kuma ta net ce ganin kamar bata ji shigowarsa ba ya saka shi hade fuska ya kama hanyar dakinsa se a sannan ta kalle shi, fuska a sake sabanin yanda yayi tunani tace "Sannu da zuwa Honey" "Yawwa ya amsa mata yana qarasawa inda Mu'ayyad yake akan tabarmar sa ta zuba masa kayan wasa. Dagashi yayi ya kalli Umaimah da itama su take kallo yace "Ya naji kansa da zafi sannan hancinsa kamar a toshe yake" "Haqori ne inaga" ta bashi amsa daidai nan yaron yayi Atishawa me qarfi se khalil ya sake kallonta yana cewa "Baki dena kunna masa Ac kuna kwana da ita bako, gashinan mura ta kamashi" seta zumburi baki ba tareda ta bashi amsa ba ya wuce dakinsa da yaron a hannunsa yanayi masa gwaranci ta rakashi da harara kafin itama tabi bayansa. Ajiye yaron yayi akan gado yana sauke numfashi daidai nan ta turo qofar ta shigo ya zabura kamar mara gaskiya amma ganinta da Try da ruwa akai ya sakashi dai daita nutsuwarsa ya sake kame fuska. Ruwan ta miqa masa ya karba a ransa yana ayyana abubuwa da yawa. Wannan ladabin nata na gaske ne ko kuwa tarko take dana masa kafin ta fara buyagin nata. "Dazu kin kirani wayar tana silent ban cire ba tunda naje masallaci na kira kuma baki daga ba" ya tambayeta yana cire rigarsa, seta ce "Eh, daman so nake na gaya maka Unit ya qare lokacin kuma ina kallon wani series ne se kawai na ahiga gidan Maman Anam na qarasa bayan na dawo kuma Khalifa yazo ya kawo Abinci shine ya saka mana". "Akan Unit ne kika mun ten missed calls na zata ma wani abun ne ya faru kuma da ya qare ba zaki kunna Solar ba" ya fada jin dalilin kiran da gaba daya ya saka jininsa ya kusan hawa saboda farga ba ashe shirmenta ne kawai, "Toh idan da solar tana yi zan kiraka nema ai saboda taqiyi ne ya saka nake amfani da Nepa har Unit dinma yayi saurin qarewa" ta bashi amsa tana harararsa qasa qasa, se yaja qaramin tsaki yace "Meya sameta? Kin qara dora mata abinda yafi qarfinta ko?" "Nifa karka daga mun hankali a daren nan bansan meya sameta ba idan na kunna da safe rana na dagawa zata ringa mutuwa tana kawowa sedai da sanyin safiya ko da daddare ne kadai take tsayawa" ta fada tana miqewa tsaye. Be sake kulata ba ya shige bandaki bayan ya sauke Mu'ayyad qasa. Itama fita tayi tana mita, badan wallahi da abinda take so ba da ko kallo be isheta ba shima ya sani. Kallonta taci gaba dayi, Khalil kuwa seda yayi wanka ya shirya kafin ya fito da yaron a hannunsa. Ajiye mata shi yayi ya fita Chemist din bakin layinsu ya karbo Masa Bonababe syrup da akace yana taimakawa yara gurin sauqin laulayin haqori. Kuka ya tarar dashi yanayi ita kuma tana dannan waya abinta kamar batajinsa ma, cikin bacin rai ya fizge wayar yana cewa "Meye haka yaro yana kuka kina ji kin zauna kina danne dannen banza a waya" "To me zanyi masa? Na bashi abinci ya qoshi rigimar sa ce kawai kuma bacci zeyi ba wani abu ba" ta fada tana nuna masa kwanon abincin Mu'ayyad din dake gefe. Base ki goyashi ba tunda bacci zeyi amma se ki barshi yaringa kuka bayan kince baya jin dadi" ya sake fada yana jijjiga yaron. Zama yayi ya bude maganin, da kansa ya bashi sannan ya bashi ruwa yasha ya ringa zagayawa dashi a palour yana jijjige har yayi bacci hamshaqiyar kuwa tana nan zaune qafa daya kan daya tana dannan waya, ai yasan bata goyo ita shima rigimar banza ce saboda ya saba da suna gida Anty zata goyashi idan zeyi bacci da suka dawo ma haka Hauwa take masa. Dakinsa ya wuce dashi ya kwantar, seda ya duba Diaper jikinsa yaga bata dade da saka masa ba beyi komai a cikinta baka kafin yayi masa addu'a ya kashe fitilar dakin ya fito bayan ya tokare qofar ya barta a bude. Kan dining ya wuce ya zuba abinci yana kai lomar farko bakinsa wayarsa ta dauki qara gabansa ya bada Ras ganin me kiran Hadiza ce, kamar me ciwon wuya ya juya ya kalli Umaimah karaf suka hada ido dan tunda ya fito dakin take binsa da kallo kamar yaci mata bashi. Abincin ya hadiye dakyar kafin ya danne wayar gaba daya ya kasheta dan dai baze iya wannan gangancinba, amsa wayar Mace a gaban Umaimah. Har ya gama cin abincin tana nan zaune tana kallo a Tv tareda danna waya. Daga kan Dining din ya tambayeta akwai Maltina a Fridge tace masa babu, yasan Babun dan daman shi  yake amfani da ita ita bata sha kuma tun kafin yayi tafiya ta qare be siyo ba seya miqe ya shiga dakinsa ya dakko kudi yana cewa "Bari naje na siyo" "A daren nan sekace shan ya zama dole ka bari da safe ka siyo mana" ta fada tana kallonsa, be kulata ba ya fice daga palour. Cana gaban gidan ya samu guri ya tsaya ya kunna wayarsa ya kira Hadiza, qarya yayi mata akan tana kira wayar ta mutu seda ya saka chaji yanzu ya kunnata tayi murmushi tace "Nima seda na kira sannan na duba lokaci naga dare yayi karna shiga haqqin Yayata, ina taso tun dazu na kira naji yanda kaje gida ban samu kaina ba nima se yanzu". Hira ce ta kunce tsakaninsu sam Khalil ya manta da me ya fito yi seda yaji alamar wani kiran yana shigowa kafin ya zare wayar a kunnensa ya duba, Umaimah ce take kira, ya kalli Agogo qarfe sha daya da kwata ba shiri yayiwa Hadiza sallama ya miqe yaci gaba da tafiya yana zuwa kantin ya tarar sun tashi dan daman basa wuce goma da rabi. Auna abinda ze gaya mata ya samu bacci a daren nan kawai yakeyi haka ya qarasa gidan, a bakin Get ya tarar da ita da dogon Hijabi ga Mu'aayad ta sabo a kafada. "Ina ka tafi daga siyo Maltina kafi awa daya na kira wayarka kuma baka daga ba" Umaimah da duk ta rikice ta fada seya kama hannunta suka shiga ciki dan da qarfi take maganar karta taso musu maqota a daren nan. "Khalil tambayarka nakeyi fa ina ka tafi" ta sake fada yayi saurin tareta da cewa "Ba gani na dawo ba, naje kantin Dan Baffa babu sena qarasa can titi ko zan samu, ina hanya kuma Muktar ya kirani kinsan bikinsa ya taho kuma be qarasa ginin sa ba shine muke lissafin abinda ze isa a qarasa gidan ban ankara dare yayi ba seda naga masu shagunan sun fara rufewa, kingama ko Malt din ban tsaya karba na taho" Khalil ya sheqo mata qaryar da shi kansa be san sanda ya qirqireta ba. Kallonsa takeyi kamar meson gano gaskiyar abinda yake fada, amma idan bata yadda bama wace hujja take da ita ko kuma zargin me zata masa? Hijabin jikinta ta cire bayan ta kwantar da yaron tace "Naji ka shiru na kira wayarka baka amsa ba shiyasa nace bari na leqa dan yanzu unguwar nan se a hankali mantawa nayi ma ban gaya maka ba an ce a rage kaiwa dare a waje bata gari suna shigowa" "Toh kuma shine zaki dauki yaro ku fita bayan kinsan unguwar babu lafiya, duk inda na tafi ai zan dawo idan ma ba lafiya ba za'a sanar miki" Khalil ya fada yana miqewa tsaye se itama ta miqe tana cewa "Tunda ka dawo ai shikenan Allah kiyaye na gaba" ya amsa mata da Amin ya shige daki yana sauke ajiyar zuciya. Message ne ya shigo wayarsa a garin ya danne wayar ta subuce ta fadi daidai nan Umaimah ta shigo da butar shayi, kallon tuhuma ta bishi dashi ganin yanda duk ya rikice amma se qoqarin hade fuska dan karta kawo masa wargi yakeyi. Butar ta ajiye da dan cup a gefen gado ta wuce bandakinsa. Beko bi takan shayin nata ba ya haye gado bayan ya kashe wayarsa ya jonata a chaji. Yana jinta tana ta buruntu a dakin, harta gama shirinta ta fita babu dadewa ta dawo da Mu'ayyad ta kwantar dashi a cikin gadonsa kafin ta kashe musu fitila ta hau gadon itama. Duk yanda zuciyarsa da gangar jikinsa sukayi kewarta haka ya danne yayi mata shiru kamar me baccin gaske. Babu yanda bata shafashi ta shiga jikinsa ba amma yaqi motsawa haka ta gaji saboda haushi qarshe dakin ta bar masa gaba daya ta koma palour, kukan baqin ciki ya kufce mata ita Khalil yau ya wulaqanta abinda yake binta yana naci yau ta kai masa a arha amma ya wulaqantata yaqi tankawa ze kuwa san da ita yake zancan. Duk su biyun kwanan wahala sukayi babu Wanda ya samu wadataccen bacci. Umaimah kwana tayi murqususun ciwon mara saboda ta rigada ta shirya masa, harda maganin qarin kuzari tasha gashi duk ya tashi a banza haka shima Khalil din kusan rabin daren a bandaki yayi shi yana faman kwararawa kansa ruwan sanyi ko zeji sauqin abinda ke damunsa amma a banza daya dawo ya kwanta ze sake komawa ji yakeyi kamar yaje ya dawo da ita ga mayataccen turaren data shafa ya kama Gadon da jikinsa duk ya rasa inda ze tsoma ransa yaji dadi amma yaci Alwashin baze saki da wuri ba, dole ya horata yanda gobe bazata sake masa irin abinda tayi ba. Da safe haihai suka gaisa dukkansu babu me cikakkiyar walwala. Data so neman magana yawo ta ringayi rabi tsirara a cikin palour yana zaune yana kallon labarai ita kuma tana hada musu abin kari qarshe dayaga babu arziqi ya koma daki ko breakfast dinma a ciki ta kai masa yana gamawa kuwa yayi wanka ya bar gidan dan yaga abin nata qara lalacewa yakeyi. Yana fita Umaimah ta kira Maman Hauwa a waya kan ta turo mata Hauwan, ita ta gyara mata gidan tsaf tayiwa Mu'ayyad wanka bayan ta gama mata komai ta goyashi suka fita ita kuma ta kulle gidan ta shiga ramuwar baccin jiya. Khalil kuwa se bayan daya bar gidan sannan ya kunna wayarsa. Saqonni Hadiza guda biyu suka shigo, daya tun dare ne tana gaya masa yanda yayi kyau a jiyan da yaje gurinta se kuma na barka da safiya da fatan ze wuni lafiya. Shikam ya shiga rudani da yawa, harga Allah yana son Hadiza kuma yana son auranta dan yana neman matar da zata tsamoshi daga wannan uqubar da Umaimah ke qoqarin jefa shi kuma daga haduwarsu da Hadiza zuwa yanzu yana ganin zata share masa hawayensa amma ta ina ze fara tunkarar Umaimah da zancen zeyi mata kishiya? A ture maganar Umaimah ma shi a karan kansa yana ganin beyi mata adalci ba ace shekaru biyu da auransu kacal yayi mata kishiya koda yake halinta ne ya jawo ai. Wani lokacin yakanyi mata uzurin cewar har yanzu bata gama sanin inda ta dosa a cikin zaman auran ba amma tsoronsa idan be dakatar da ita ya dorata a saitin da yake so ba haka zata miqe kuma a gaba se yafi shan wahalarta sama da yanzu. Sannan yana ganin kamar qarin aure ba shine mafita a matsalar sa da Umaimah ba, yana sonta baya qaunar abinda ze bata mata ko ya janyo matsala a tsakaninsu yanzu kuwa ya tabbatar tashin hankali ne babba yake shirin siya da kudinsa sedai kamar yanda wani abokinsa Sadiq ya taba gaya masa a lokacin yana neman aure yace saboda ya firgita matarsa tashiga hankalinta ta dena yi masa abinda baya so kuma yayi nasara dan tunda yace mata zeyi auran ta nutsu, har zuwa yanzu kusan shekaru biyar kenan be sake jin kansu ba amma da kullum cikin rigima suke kamar dai shida Umaiman sa toh amma shi yanzu idan yayiwa Hadiza haka ai beyi mata Adalci ba dan dagaske take sonsa idan yayi amfani da ita dan gyara zaman auransa ya kuma barta yasan haqqinta baze barshi ba dan haka dole ya zabi daya kodai yayi shahada ya aurota ko kuma ya rabu da ita yaci gaba da zama da qaddarar da Allah ya zaba masa. Ranar ma wuni yayi a waje, yaje gidan Hajiyarsa ya dade sosai yana taso yayi mata zancen Hadiza amma taraddadin yanda zata karbi maganar ya saka harya tafi be gaya mata ba se maganar siyan gidansun da take ciki yayi mata. Daman ya dade da gaya mata yana so ya siyi gidan gaba daya ya fitarwa da sauran yan uwansa haqqin su ya zama nashi sunyi magana kuma gaba daya sun yarda dan haka yanzu ya taso da maganar saboda kudaden da yake hadawa sun kusa kammala, sunyi maganar da Hajiyan tace yaje ya samu Kawunsu Murtala duk yanda suka yanke shikenan. Seda ya tashi tafiya harya kai qofa zuciyarsa tace ya gwada Sa'a mana, seya koma ciki Hajiya dake duba wayarta ta kalle shi tace "Aa Babana ya ka dawo ko da sauran magana ne?". Shafa kansa yayi ya zauna yana cewa." Wallahi Hajiya wanj abu ne yake damuna nace dai bari na gaya miki" "Toh Allah yasa lafiya, ni daman tunda jiya da na ganka nasan akwai wani abu dukka fige kamar wanda yayi jinya amma na zata ko aikin ne tunda kace hidimar da kayi a can da yawa" Hajiya ta fada tana gyara zamanta se yayi shiru yana jinjina ta yanda ze fada mata maganar kafin yayi qundumbala yace "Daman Hajiya wata yarinya na hadu da ita, toh kuma na yaba da hankalinta sosai mun fahimci juna shine da nake tunanin idan na samu yanda nake so kuma in Allah ya nufa zan qara da ita". Kallonsa Hajiya tayi harya kai qarshe yayi shiru cikin muryar dake nuna babu wasa tace "Akul dinka Khalil, wato saboda kaga ka fara samun dama shine zaka tattagowa kanka aure ko? Gaba daya shekarar ka nawa da auran fari ma da har ka fara hangen wata nawa ma kake da kake neman dorawa kanka Jidalin mata? Toh karna sakeji na kashe maganar daga nan babu ita ko zaka qara aure ba yanzu ba kai sedai idan ma yana cikin qaddarar ka ne amma ban lamunce ba, Allah ya baka mata ta kwarai me hankali da nutsuwa tana sonka tana riritaka banga ta inda ta rageka ba ko kuwa jin dadi ne yasa kake neman qari? Toh babu wannan zance haka kawai yarinya na zaman zamanta ba zaka debo mata damuwa ka hanata walwala ba toh ban yarda ba koma wacece ka bata haquri ka gaya mata kana Son Matarka ita kadai ta isheka dan nasan qarshe tallan kanta ta kawo maka dan me mata irin taka dai a shekara biyu baza'a ace ka fara hange hange ba musamman kai da na farin ma da yaya kayi shi". Kansa na qasa harta diga aya kafin cikin sanyin jiki yace mata 'Toh' kawai ya miqe tareda qarayi mata sallama ya fita. Daman yasan ko auran zeyi a yanzu kam se sun fafata da Hajiya dan ya rasa kalar Rufa idon da Umaimah tayi mata da sama bata ganin laifinta koda yake bata tabayin halin nata a gabanta bane shiyasa har take mata kallonta kirki tana haqilon ba za'ayi mata kishiya ba  amma duk wannan me sauqi ne, idan har maganar auran dagaske tazo yasan yanda zeyi ya lallabata ta yarda kai duk ma wani da ze kawo tasa maganar duk ze iya dasu ita babbar Madam dince abin tsoronsa dan baze taba manta kalmar kisa data ambata zatayi ba akan duk wadda ta shiga rayuwarsa. Yauma seda yayi Isha ya koma gidan dan daga gidan Hajiya gurin Mansur ya tafi can yakai dare dan har abinci acan yaci kafin ya kamo hanyar gida. Ya zaci ze tarar da ita tana fushin kamar yanda ya barta da safe amma seyaga akasin haka. Yauma tasha kwalliya kamar me tafiya club harda lalle tayi baqi hannu da qafa ga Qananun kalba da akayi mata akanta dan in ya tuna jiya kamar kanta babu kitso. Ta gyara gidan ko ina se qamshi yakeyi tana bawa Mu'ayyad Abincinsa ya shiga. Fuska a sake ta amsa masa sallama tareda sannu da zuwa, Ya dauki yaron yana mata sannu da gida itama a ransa yana jin dadin chanjin daya gani daga jiya zuwa yau musamman jiyan dukda bata san da dawowarsa ba amma yazo ya tarar da gida ko ina fes haka ita kanta a kintse, toshi indai zata gyara ta ringa abinda yake so ai babu maganar wata tunda daman rashin kulawarta ta sakashi bawa wata dama. Qarar wayarsa ta maidoshi daga tunanin daya tafi, seda ya saci kallonta yaga tana tattare kayan abincin Mu'ayyad din kafin ya daga da sallama yana cewa "Ina abu ne idan na gama zan kira" ya shige daki Umaimah da tun daga wayar tasa tayi sak dan sarai ta ga yanda fuskarsa ta canza ta bishi da kallo. Bata so ta bar zuciyarta ta ayyana mata abinda ba shikenan ba amma yanda Khalil din yake abubuwa sun fara bata tsoro. Jiya kiran da aka masa yana cin abinci yanda ya rikice ya bata mamaki, sannan fitar da yayi ta kirashi taji call waiting tasan Khalil ko wayar aiki ce qarqarinsa qafe goma baya attending mutane bayan nan amma jiya sha daya ta gota sanda ymta kirashi call waiting dukda yace da Mukhtar yayi waya sannan A iya saninta dashi komai dare baya kashe waya se gashi jiya ta danna wayar da niyyar ganin lokaci ta ganta a kashe, tayi masa uzurin ko chaji ne ya qare gaba daya ta mutu kuma daya saka be kunna ba amma taga da safe harya futa tana lura bataji an kirashi ba kuma shima bata ga yayi amfani da wayar ba ga kuma na yanzu, dukma abinda yake boyewa ko yakeyi zata bincika idan kuwa taga abinda ba haka ba tashin hankali ne ze siyowa kansa dan ya santa bawai chanzawa tayi ba. Khalil kuwa daya shiga daki Text yayiwa Hadiza akan tayi haquri ze kirata da safe yanzu ya rigada ya shiga gida tayi masa reply kan babu komai yana karantawa ya goge duka messages dinta, call log din ya shiga nan ma ya goge kiran da tayi masa har ya aje wayar wata zuciyar raya masa ya goge lambarta gaba daya bayan ya kalleta da kyau ya haddace haka yabi ya goge chat dinsu na WhatsApp ma sannan yaji hankalinsa ya kwanta. A qasa ya ajiye Mu'ayyad ya kunna masa carton a Tv dakin ya shiga wanka, yana shiga ta tura qofar dakin ta shiga kai tsaye idonta ya sauka akan wayarsa dake ajiye akan gado, seda taje jikin qofar ta kasa kunne taji alamar saukar ruwa kafin ta dawo da sauri ta dauki wayar, call log ta shiga, lambar farko dataga an kirashi ta kwafe a wayarta cikin sauri ta shiga gurin messages tana yi tana kallon qofar bandakin ganin idan ta bata lokaci ze iya fitowa ya tarar da ita yasa ta ajiye masa wayar bayan ta goge shaidar da ze gani na ta bude wayar. Dakinta ta wuce tana shiga ta dannan kiran number data kwafo wayar ta shiga ringing seda ta kusa katsewa aka daga Muryar Namiji ce daga ji ma ba bahaushe bane. Tambayarsa tayi ina me wayar yace mata shine, bata yarda ba ta sake ce masa Amina take nema yace shi besan wata Amina ba wannan layinsa ne sedai idan tayi missing number. Har zata kashe ta sake tambayarsa dan Allah waye shi toh dan dukda tabbacin daya bata na layinsa ne bata gama yarda ba, a fusace yace mata sunansa Bala kuma shi Electrician ne ya kashe wayarsa seta sauke ajiyar zuciya tanajin hankalinta ya qara kwanciya. Qila cikin jama'ar da suke kwangila ne masu aikin wuta kenan wani ya kirashi. Palout ta fito jin yana kwala mata kira ya bata Mu'ayyad da yayi pupu ashe babu Diaper a jikinsa ya wanke masa ya sake masa wanka yace tayi masa shirin bacci. Ranar ma dai haka suka sake kwanciya kowa na juyi da murqususu a gado. Khalil ya qudure in har Umaimah bata bashi haquri akan abinda tayi masa ba ze zuba mata ido daga gaisuwa babu abinda ze sake shiga tsakaninsu haka itama ta ja nata layin dan ta san duk abinsa dole ya haqura ya sakko baze iya dogon fushi da ita ba, tana lura da yanda yake kwana wanka da shan Lipton da lemon tsami idan safiya tayi ta sake gigita masa kwakwalwa da zafafan shigar da takeyi sedai ya fita ya bar mata gidan wannan kuma tasan na dan lokaci ne dolensa ya bada kai bori ya hau a haka ya cinye hutun sati daya da aka bashi kafin yaci gaba da zuwa aiki office dinsa na nan Kano. Tunda Sukayi maganar Hadiza da Hajiya ya fara jada baya da ita yawan wayar da sukeyi duk ya rage dan yana tsoron ta zargeshi da laifin yaudararta a gaba idan ya kasa shawo kan Hajiyarsa akan lamarin. Tun tana yarda da uzururrukan aiki da yake bata ko kuma wani lokacin yace yana gidan idan ta kira harta fara gane kawai yana qoqarin yakiceta ne daman tun wancan zuwanda yayi gidansu ranar daya dawo be sake komawa ba ya dai je office dinsu sau biyu har suka je cin abinci a zuwansa na biyun tareda ita da Khausar a ranar ne yake nuna musu hoton Umaimah da Mu'ayyad Khausar din take tambayarsa ina Madam Hadiza tace har yanzu be hada su sun gaisa ba shine ya nuna musu hotonsu da suka dauka tare. A hannun Khausar ya bar wayar tanaci gaba da kallon Hotunansu se zuzuta kyan da sukayi takeyi shi kuma suna yar hirar su da Hadiza seda lokacin break ya qare sannanya mayar dasu gurin aiki shi kuma ya wuce Site dan ranar be zauna a office ba. A ranar chan gida kuma Umaimah ta karbi baquncin yayyenta Maman Asad, Yaya Naziyya data shigo Kano se Yaya Nuratu. A daki suka sakata suka fara dayi mata wankin babban bargo dan duk cikinsu babu wadda tasan zaman da Umaiman tayi a gida se daga baya. Yaya Naziyya na Minna, Maman Asad taje Umarah daman ta Somotto suka tafi garinsu Mijinta da suka dawo ma can suka yada zango Nuratu kuwa aiki ya hanata Sakat Mijinta ya tafi wani aiki ita take riqe masa Call tayi nata tayi nasa shi yasa bata samun lokacin kanta balle taje ko ina shiyasa basu sani ba seda Yaya Naziyya tazo Maman take gaya mata babu shiri ta kirawosu mitin din gaggawa. "Amma Mama idan da laifin Umaimah kema da naki, na rasa wai fin qarfinku yarinyar nan tayi ko tsoronta kukeji da kuke zuba mata ido tana duk iskancin data ga dama. Me yasa sanda tazo baki saka ta a gaba ta kira Mijin kiji da kunnenki dagaske shi yace ta taho gida ba idan taqi kuma se ki kirashi ko ki gayawa Yaya Aminu? Gaskiya Mama sekun sake lale akan lamarin Umaimah idan ba haka ba kuma wallahi gaba se tayi abinda kowa zezo yana ya za'ayi tunda bata da tunani, ganin kuma idan tayi tana cin banza ya saka kullum iskancinta gaba yakeyi ba baya ba" Yaya Naziyya ta fada sanda Maman ta gama gaya mata yanda akayi washe gari da safe shine suka rankaya suka tafi gidan. *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS🧕🧕* *💞Barkan mu da warhaka en uwa mata, bugu da qari ba kadai a bangaren kayan gyaran aure ingantattu ta tsaya ba, ta na bada magunguna na musulunci akan cututtuka na yau da kullum wanda suke damun al'umma.* *Cututtuka irin su matsanaicin ciwon mara a lukuta mabanbanta ko kuma lokacin al'ada, daukewan al'adan lokacin daukewan bai zo ba, al'ada ya rinqa wasa, rashin sha'awa ko ciwon kai, ciwon qirji wanda aka rasa gane kanshi ana tunanin ulcer ne, kuma anyi maganin amma har yanzu ba a dace ba, matsalar Ashiq wato aljanin soyayya(wannan sai bayan tambayoyi sannna za a tabbatar). Ciwon ciki, hawan jini, ciwon sugar, ciwon hanta, typoid/malaria, basir, ciwon baya da qafa, ciwon qashi da kuma matsalar infertility, duk da haihuwa Allah ne ke badawa amma kuma a wasu lokutan akwai cututtuka da kan kama mahaifa ko kuma reproductive system din mace wanda su kan iya hanata daukan ciki. Cututtuka irin su Endeomatriosis, cervicitis, fibroids, etc.* *Ku karzayo domin lafiya uwar jiki💪💪, sannan ta bangaren gyaran aure, sumayyas herbal ta lashi takobin qara zage damtse wajen inganta kayayyakin ta domin samun maslahan ku a* *rayuwar ku da auratayyan ku. Aure dai ibada ne a don haka gyaran aure wajibi ne, musamman idan kin samu in da zaki gyara kan ki da kayayyaki na kwarai wanda basu da illa ga lafiya kuma ba irin kayan da zasu Kai ki ga halaka ba,su saki rasa imanin ki duk wai da sunan gyaran aure. Ah ah er uwa ayi hattara kar garin neman gira a rasa ido.🧏🏻‍♀️ Allah ya tsare mana imanin mu🙏🙏* *Garzaya ki dannan link din kuma kiyi saving number ta domin kuwa akwai alfano mai yawa.* *Wa.me/+2347031876677* *Ko kuma akan Instagram* *https://www.instagram.com/p/CqQJVrVIdjq/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==* *Allah ya biya mana buqatun mu na alkhairi amin.* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 35 An ci babbar Sa'a sun tarar da ita tana zaune a palour tana danna waya Hauwa na goye da Mu'ayyad tana mopping da yake Get din a bude yake ta aiki Aliyu bata so ya dawo yayi ta bugawa shiyasa sun zuwa suka shige se ganinsu tayi tsulum akanta. Ashariya me maiqo Naziyya ta fara aika mata da ita sanda taga Hauwa ta fito daga dakin Khalil da bokitin mopping kafin taci gaba da cewa "Babu shakka Umaimah kin shahara, kina zaune babu aikin fari balle na baqi wata zangamemiyar budurwa ce zata shiga ta gyara miki inda Mijinki yake kwanciya taga sirrin sa ko? To zakici ubanki, notikan kanki da suka kwance yau munzo da spanun da zamu daure miki su tamau" Seta juya kan Hauwa da tayi tsamo tsamo tace "Ke kuma a gidan nan kike ko kuwa?" Da sauri Hauwa tace "Aa zuwa nakeyi" "Kwanto shi ki fita ki bamu guri" Naziyyan ta sake fada fuska babu wasa jiki ba rawa ta kwance yaron Maman Asad data fi kusa da ita ta karbeshi daman da Hijabin ta a wuya ta fice da sauri Umaimah dai tunda ta sunkuyar da kai bata dago ba tasan yau kan kashinta ya bushe a gurin Naziyya cinyeta ne kadai ba zata yi ba. Seda suka fara da zageta tatas wannan ta aiko mata ta nan waccen ta aiko tata, fadan qazanta da sakaci suke mata Nuratu tace "Ashe kishin naki na banza ne da har zaki bar qatuwar budurwa kamar wannan ta shiga dakin Mijinki ta gyara saboda sakarci da rashin sanin ciwon kai" murya na rawa dan ta zagu a gunsu tace "Bafa ta zuwa se baya nan kuma kafin ya dawo ta gama yimun komai ta tafi" "Dalla rufewa mutane baki a nan gyaran wannan gidan ne har wani abinda se kin nemo matayi saboda lalaci ina aikin yake? Kuma idan ma zaki nemi me aikin kiyi abinda hankali mana idan seta miki gyaran ta gyara palour zuwa tsakar gida da kitchen ke aikin uwar me kikiye banda Chatting din banza da bazakiyi komai ba? Ai wallahi Umaimah kin bani kunya mudai ba'ayi mata tarbiyyar qazantaba amma gashi nan ke kinzo kinayi kuma duk in kika sa aka zagi Mama Allah seya saka mata dan tarbiyya daya tayi mana gaba daya zubar da taki kikai a hanya" Maman Asad ta fada a hasale. Haka suka kasa suka tsare seda ta tashi ta qarasa aikin da Hauwa ta fara dan daman mopping din palour kadai ya rage se wankin Mu'ayyad data fita dasu tsakar gida zatayi. Se bayan da suka nutsa Naziyya ta tada maganar zuwanta gida da tayi ta share sama da wata babu wanda yasan Dalili, hade rai tayi tana kallon gefe tace "Tafiya yayi kuma lokacin Babansu Shahida ya rasu shiyasa bamu tafi tareba da aka gama zaman makoki yace na zauna a gida kawai har ya dawo". Kallon junansu sukayi Nuratu ta numfasa tace "Amma Mama tace ko waya bakuyi ba har kika gama zamanki se qaninsa ne yake kai miki kayan amfani kuma da zaki dawo basu sani ba kika gudo, bayan nan ma seda aka ci kusan sati kafin ya dawo Kano" "Toh wai dan Allah ina ruwanki kuma lauya kika zama da zaki tasani da tambaya ko yaya? Gajiya nayi da zaman na dawo gidana waya kuma lalacewa wayata tayi seda ya dawo ya kai mun gyara ai Maman ta sani" Umaimah ta fada tana hararar Nuratu tunda itace marainiyar wayonta ta baya Naziyya ta taske mata qeya ta dafe gurin dan zafin hannu ne da ita tace "Haba Yaya Naziyya da zafi fa" "Ai daman saboda kiji Zafin na dakeki dama ban daukeki da mari ba, duk cikin mu babu yaro kuma babu sakarai irinki ballan tana kiyi mana wasa da hankali. Uban me kikaje yi gida har kusan wata biyu bayan kowa yasan duk Tafiya kota kwanaki ce tare kukeyinta da Khalil wallahi ki fada tun a mutunce idan kinqi zan kirashi na tambayeshi yanzu" Naziyya ta fada se Umaimah ta hau zare ido, ganin babu sarki se Allah da Naziyya ta kirashi ya fadi gaskiyar yanda akayi gara tayiwa kanta qiyamullaili tayiwa zancen kwaskwarima yanda baza'a ga laifinta ba dan haka tace "Nifa ba wani abu nayi masa ba tafiya ce ta taso masa ranar da zamu tafi Mijin Anty Hafsa ya rasu ya barni ya tafi shi kadai ni kuma daman bani da lafiya, da aka gama zaman makokin yace na bishi na gaya masa bani da lafiya shikenan fa yayi fushi yace na zauna ko naje babu amfanin da zanyi masa" "Baki da lafiya wace irin cutace take damunki data hanaki binsa kuma duk bamu sani ba sannan akan me zeyi fushi in har dagaske rashin lafiya ce ta hanaki binsa" Maman Asad ta katseta, Umaimah ta matso hawayen qarya tace "Toh ai kansa kawai ya sani daman shi dai biyan buqatarsa ne matsalarsa shiyasa da nace bani da lafiyar yayi fushi ai" "Dan ubanki wace rashin lafiya kika samu abinda muke so muji kenan" Naziyya ta sake zaburo mata se Nuratu tayi murmushi tace "Bata bakinku kuke babu kowacce rashin lafiya baze wuce tace bazata bishi bane yanda ta saba shine zeyi fushi kuma daman ai dole za'a zo nan, duk sanda zeyi tafiya bazata bishi ta dadin rai ba daman wata rana zeyi zuciya yace ta zauna a gida mana". "Ai wallahi nidai na dade banga Macen da bata san kanta ba irin Umaimah. Duk ni'imar da mace zata roqa a gidan aure Allah yayi mata amma bata godewa to kici gaba idan baki godewa Ni'imar Ubangiji ba zaki godewa azabarsa. A zamanin nan Ki samu Miji ya ringa yawo dake ai abin ki gode Allah ne kina ma da matsayin da baya so yayi nesa dake Allah na tuba matan gasu nan birjik a titi idan ya fita ze samu dari da zasuyi masa rakiya duk inda zeje amma Allah ya tsare miki mijinki ya tsare mutunchinsa shine kike so ki turashi duniya ko kici gaba" Maman Asad ta fada se Naziyya taci gaba da cewa "In banda daqiqiyace ma Umaimah Mijinki mabuqaci kin sani amma har a ringa tababa dake akan binsa wani guri idan be tafi dake ba gurin uwar wa kike so yaje ya sauke lalurar sa ko kuwa matan banza kike so yaje ya nema? Ai idan kinada hankali wallahi dama kika samu da zaki qara kafa kanki a zuciyarsa duk inda ya shiga kina gefensa kina bashi farinciki ta yanda babu wadda ta isa ta sako miki kai amma ki saki Miji a bariki Yanzu wata biyun da kika barshi shikadai a can kina nan kina ballan sorinki kinsan abinda yaje yayi ko kuwa se an zo maganar kin ganshi da Mace ne zaki fara yiwa mutane hauka kina rashin hankali babu kintsi babu gyara se Tijara da rashin mutunchi kika kware dayi ko to ki kuka da kanki wallahi duk abinda yaje ya dawo da kudinki kika siya kuma ko Matan banza ya nema ki tabbata zunubinki yafi nasa ga tsinuwar mala'iku ta saba masa da kikayi ga kason zunubin duk tsiyar daya aikata naki ma seya fi nasa yawa". Kamar Kazar da ruwan sama yayiwa duka haka jikinta yayi sanyi qirjinta ya shiga dukan dari dari yanzu fa tsahon kusan sati uku da dawoqar Khalil banda kwanakin da yayi a can ace be nemi wani abu a gurinta ba ga rashin gaskiyar da take gani idan an kirashi waya yanzu ko tashi daga aiki ya qara lokaci seya kai Bayan Magriba be shigo gida ba wata ran har Isha kao abubuwan da yawo se yanzu ma take tunano su haka ranar nan taji qamshin wani turare a kayansa abinda yasa batayi magana ba taga turaren a Jakar Office dinsa amma ai ba cikakke bane qila ma ragowar na budurwar tasa ne ya karbo, Su Naziyya nata magana se gani sukayi ta dora hannuwa biyu aka tana kiran "Na shiga uku shikenan Khalil ya fara neman Mata" "Uhm kunga kalar haukan nata ko duk cikin maganar da mukayi ita abinda zuciyarta ta ayyana mata kenan anya Umaimah kitse be lullube miki kwakwalwa ba inaga shi yake hanaki tunani dakyau" Yaya Naziyya ta fada, Umaimah kuwa kukan gaske ta fashe dashi tana cewa "Wallahi Yaya Naziyya sedai idan Khalil mata ya fara nema shine kadai ze saka yaqi kulani kusan wata uku" "Wata uku?" Suka hada baki gurin fada, ta gyada musu kai cikin tabbatarwa tace "Tsakani da Allah bayan ya tafi har kudi ya turo akan na bishi nace bazanje ba. Ni wallahi bana son tafiye tafiye tun Asali kuma kun sani kuma idan mukaje wani guri qara damuna yakeyi kusan ko yaushe muna tare koya fita baya dadewa yake dawowa duk gajiya nakeyi a maimakon na huta shiyasa wannan karon nace masa ba zanje ba shine fa yayi fushi har ya gama zamansa be kirani ba se sau daya kuma daya dawo ma baya shiga harkata daga gaisuwa shikenan tsakaninmu, nayi duk abinda zanyi har kaina na kai masa amma yayi mun wukaqanci" ta qarass cikin kuka sosai se aka rasa me magana a cikinsu dakyar Nuratu ta iya cewa "Amma Umaimah kinyi wauta waya ce miki kana nunawa Miji ka gaji da buqatarsa? Tsanarki zeyi tunda bazaki iya biya masa buqata ba baki da wani amfani a gurinsa. Ke bama zaki godewa Allah bakya aikin komai se zaman gida ba, ni yanzu nace me? Wallahi har mantawa nakeyi da wani abu Sex kwata kwata hankalina ma baya kaiwa kanshi kina kallo kullun sena fita aiki banida lokacin kaina ballantana na hutu amma dukda hKa ban taba qin Amsa kiran Mijina ba. A na gaji wani lokacin rabi bacci rabi ido biyu a hakan zan biya masa buqatarsa, wani lokacin a Asibitin ze nemeni haka zanje amma ke kici kisha ki kwanta kuma a hakan kike cewa kin gaji gaskiya kiyiwa kanki fada" "Duk bazaku gane ba" ta fada kafin taci gaba Maman Asad ta katseta da cewa "Daman ai bazamu gane ba, kuma da kike cewa tunda ya dawo yaqi kulaki ta ina ze kulaki kuwa baki san kin masa laifi bane, koda ya dawo kin bashi haquri? "Haquri kuma? Ni me nayi masa da zan bashi haquri naga nima ya shiga haqqi na ya tafi ya barni tsahon lokaci a gida baya ko kira yaji ya muke" Umaimah ta fada tana zumbura baki Maman Asad tace "Ahaf ai na sani to shi ce miki akayi maye ne da ze kulaki bayan ke baki san kin masa ba daidai ballema ki bashi haquri? Ko kuwa tunda ga Namamajo daga kinyi masa karairaya shikenan ya manta duk laifin da kaika masa se ya sakko yaci gaba da binki gara ya nuna miki ai koda abin ko babu shi ze rayu kinga se ki jiqa abinki kisha tunda rowarsa kike masa. Ke baki san idan miji ya qauracewa matarsa shine qololuwar horon da zeyi mata ba ko Aa se shirme da hauka kika saka a gaba a wautar ki idan jarabarsa ta tashi dole ze kawo kansa to kici gaba tsinuwar Mala'iku kadai ta isheki ai. Yadai kamatu zuwa yanzu ace kinyi hankali kuma kema kin isa ki gayawa wani yanda yavkamata yayi ba ace kullum ke ake yiwa fada ba. Zaman auran nan fa ibadah ne Umaimah yana kuma da dokoki da sharudda ba kara zube ake yinsa ba, idan baki nutsu kinbi Allah ba wuta zaki kai kanki a banza babu ruwan Khalil dan yana shiru baya ce miki komai akan abinda kikeyi Shi Allah babu ruwansa zeyi miki hukunci daidai da abubuwan da kika aikata" Haka suka ringa yi mata fada da Nasiha tare da bata shawarwari tayi laqwas kamar ta dauka harda yar kwallarta ta kuma Alqawarin zata gyara idan Khalil ya dawo zata bashi haquri in sha Allahu ba za bashi haquri basu bar gidan ba seda sukayi sallar Azahar ta dafa musu Indomie sukaci sannan sukayi Haramar tafiya zasu biya gidan Anty Hafsa. Bayan tafiyarsu ta tashi yin tuwon shinkafa da Miyar Yakuwa saboda Khalil yana sonsa. Hauwa ta kira ta daukar mata Mu'ayyad dukda jan kunnen da suka gama shi mata akan hakan amma bataji ba. Ta tuqa tuwanta ta malmale ta hada miyar gaba daya gidan ya dauki qamshin girki dan Umaimah gwana ce gurin iya sarrafa abinci musamman na gargajiya qyuyace take hanatayi. Seda ta sake gyara gidan ta turare ko ina kafin qarfe shida ta gama komai har Mu'ayyad an dawo mata dashi ta masa wanka ta shirya shi tsaf suka zauna jiran Khalil Tunda ya shaqi qamshin turare daya cakude dana girkin da yayi ya saki murmushi, har ga Allah yayi missing komai nata, dole ta saka yake nesanta kansa da ita dan yana so ta fahimci girman laifinta tayi nadama amma abin ya gagara. Da sallama ya shiga, fuska babu yabo babu fallasa daidai nan ta shafa Addu'ar da takeyi ta miqe tana cire Hijabin da tayi sallah tayi masa sannu da zuwa. A sama ya amsa yana nufar dakinsa yana kallon yanda take kallonsa se yaga kamar jikinta a sanyaye yake ba kamar yanda ya saba ganinta ba, tabe baki yayi ya shige daki yasan wani wasan kwaikwayon ta shirya kuma. Wanka ya farayi, yana bandakin wayarsa daya ajiye akan gado ta dauki qara, a jikinsa yaji cewar Hadiza ce dan ta kirashi yana tuqi yace idan ya tsaya ze kirata yasan taji shiru ne ta sake kiransa dan ita kuma haka take da nacin tsiya bata da Jan Aji irin na Umaimansa. Tunawa da yayi Umaimah zata iya shigowa dakin a ko wanne lokaci ya sakashi watsa ruwa babu shiri ya fito, wayar ta katse dan haka ya sakata a Silent, hakan be masa ba ya jefata a Aljihun rigar daya cire kafin ya koma yaci gaba da wankansa. Tana zaune a kan kujera ya fito tana ganinsa ta miqe tana ce masa "Ga abinci nan tuwo nayi naga kwana biyu baka cin abinci sosai" "Sannunki" ya bata amsa yana nufar Dining din ta bishi a baya, ita ta zuba masa ta tura masa komai gabansa kafin ta nemi kujera ta zauna kamar me gadinsa yau ko danne dannen wayar da takeyi babu shidai cin abincinsa yakeyi lokaci lokaci yana kallonta tareda karantar yanayinta harya qarasa ya dauki bowl din data zuba fruit salad ya koma cikin palour ya chanza channel zuwa tashar labarai. Sake binsa tayi ta zauna a kujerar kusada wadda yake kai ya zuba masa ido ba tare datace komai ba. Yanda kasan an daure mata harshe, so take ta bashi haqurin amma shedanna nan yana zugata akan kartayi zata bada kanta daga qarshe dai ta yakice shi ganin ya mayar da Hankali kan Tv tamkar ma besan da zamanta ba ta bude baki dakyar tace "Khalil kayi haquri ka yafe mun laifin da nayi maka wallahi sharrin shaidan ne". Shiru yayi kamar beji taba, ta sake maimaitawa kafin ya dago fuskarsa da dan murmushi yace "Wane laifi kikayi mun kuma?" "Qin binka da nayi Lagos, kayi haquri wallahi...." "Wannan ai ba laifi kikayi ba, ra'ayinki ne bakya son zuwa ni ya kamata na baki haquri da nake neman tilasta miki ki ringa bina wani waje alhalin bakya son zuwa, kiyi haquri kinji in sha Allahu bazan sake cewa kiyi mun rakiya wani guri ba duk inda zanje zan tafi ni kadai" Khalil ya tareta, yanda yayi maganar babu damuwa sam a fuskarsa amma tasan magana ce kawai ya gaya mata ta yaya ma zece beji haushi ba seta sake marairaicewa tace "Toh idan bakayi fushi ba me yasa tunda ka dawo kaqi kulani?" "Ni kuma naqi kulaki yanzu ma ba gashi magana mukeyi dake ba?" Ya fada yana kallonta seta tura baki wato so yake ma ya raina mata wayo be gane me take magana akai ba kenan dan haka tace "Ba irin wannan ba, nasan baka iya daukan lokaci ba taredani ba amma ka iya zama kusan wata biyu a can kai kadan sannan yanzu ma daka dawo kai kadai kake kwana ko nazo korata kakeyi". Dariya yayi a ransa yana jinjinawa Umaimah da wautarta wato Maye ta dauke shi ko,ta aza ze jure duk wukaqancinta saboda jikinta to shima ya koyi yanda ze hadiye zalamar tasa seta qarata can da abinta kafin ya samo wata. Kallonta yayi yace "Toh yazanyi? Daman saboda ina ganinki ne na saka rai da zan samu shiyasa nake damuwa amma tunda babu kinga dole nayi haquri kuma koda na dawo daman ai akansa ne kike mun wukaqanci shine na barki ki huta ko, ban nema bama ballantana raina ya baci idan kin hanani". Shiru sukayi gaba daya, shi ya maida hankalinsa kan TV ita kuma tana ta jan yatsun hannunta tana auna abinda zata gaya masa, ganin tayi shiru taqi magana ya sakashi miqewa yana cewa "Karfa ki sakawa ranki damuwar ko ina fushi dake ne Aa, kawai ina baki space ne kamar yanda kika zaba" "Dan Allah kayi haquri" ta fada kamar zatayi kuka har idonta sun kawo kwalla, qoqarin wuceta ya shigayi yana cewa "Bakiyi mun komai ba" seta riqr qafarsa ta sakar masa kukan shagwaba hade da kissa tana cewa "Kayi haquri ka yafe mun wallahi na horu bazan sake yi maka gardama ba ko China kace na bika zanje amma dan Allah ka yafe mun bazan iya ci gaba da jure rashin ka ba" "Ikon Allah" ya fada a zuciyarsa a fili kuma ya saka hannu biyu ya dagota ganin tana neman kayar dashi tana miqewa kuwa ta fada jikinsa gaba daya ta kanainayeshi tana sake sakar masa wani kukan tana nanata yayi haquri" "Ya isa Umaimah kinga karki tashi Mu'ayyad na haqura shikenan?" Ya fada yana qoqarin janyeta daga jikinsa, noqe wuya tayi tace "Ba shikenan ba, baka haqura ba" "To me kike so nayi da zaki yarda na haqura" ya sake fada yana jan numfashi saboda kusancinsu yayi yawa tana qoqarin tayar masa da abinda yake dannewa. Kanta ta kwantar a wuyansa tana cewa "Nima ban sani ba amma baka haqura ba na sani" "Toh sakeni se naji me kike so nayi" ya fada yana dago kanta daga wuyansa saboda yanda dumin numfashinta yake shigarsa, kamar wata kaska haka ta maqale masa yayi yayi ta sake shi amma taqi qoqari takeyi ta hade bakinsu yaqi bata dama dan yasan inhar ta samu dama zancen fushi kuma dole ya qare dan baze iya tsalkakewa tarkonta ba shi kuma be yarda da nadamarta ba yanzu, ko ze sakko se ta sake horuwa tukunna wannan tuban nata beyi kama dana gaskiya ba. Wayarta da aka kira ce ta cece shi, babu bata lokaci ya shige dakinsa ya barta tsaye tana hawayen baqin ciki a ransa yace "Kema kiji irin yanda nakeji idan da dadi" dan ya karanci a buqace take sosai. Da safe yayi zaton tayi fushi se yaga akasin haka dan kafin ya fito harta hada musu breakfast, jikinta a sanyaye sosai fuskarta ta kode kamar wadda take jinya se yaji tausayinta ya tsirga masa amma daya tuna tasa jinyar daya sha se ya danne tausayin nata yaci abincin ya kama hanyar office. Seda suka sake cin sati a wannan yanayin zuwa sannan ya tabbatar da ko badan Allah ba Umaimah ta biyu, ranar daya shammaceta ya amsa gayyatar ta har kuka seda tayi masa se ya rasa tsakanin shida ita wayafi kewar dan uwansa daga nan komai ya daidaita sukaci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi ko sanda ya fahimci Hauwa keyi mata ayyukan gida bece komai ba tunda daman ya dade yana mata maganar ta nemi me aiki dan baya son qazanta tunda bazata ringayi na ta nemo wadda zata tayata, kawai yaja mata kunne akan karta kuskura ta bata gyaran dakinsa haka girki tayi da kanta se rainon Mu'ayyad da take tafiya dashi ya hana, yace duk abinda zata tayata dashi tayi a nan a gabanta karta qara bayar masa da Yaro a tafi dashi wani gida tadai kiyaye wasu daga sharuddan amma wasu kam ta take kamar maganar Raino kam daya fita idan Hauwan tazo tayi mata aikin da zatayi zata bata shi su tafi, se yamma lis kafin lokacin dawowarsa zata kawo mata shi girkin ma wata rana bata takeyi sedai ta tsaya tana dubawa ko gurin saka maggi da sauran kayan hadi ta saka da kanta ta barta ta qarasa toh ina zata iya ita tunda tasan dadin me aiki ai kuma shikenan. A bangaren Khalil da Hadiza kuwa tun daidaiton sa da Umaimah ta kasa gane kansa, gaba daya yanzu shareta yakeyi dan harga Allah yana mantawa da ita wani lokacin tunda me guri ta dawo dole yar haya ta kama gabanta. Lokutan da yake samu ya kira daman irin lokacin da suke waya da Umaimah ne idan yana office dan haka yanzu ma sun dinke abinsu sau da yawa idan Hadizan ta kira sedai taji call waiting in taci sa'a ya daga yace mata yana aiki ze kira shi kenan sedai idan ita ta sake kiransa kuma. Ranar wata Laraba ta kirashi akan tanason magana dashi, magiyar datayi masa ta sakashi yarda su hadu a wani gurin cin abinci. Ya rigata zuwa dan ita tareda Khausar suka fita sun tsaya wani guri qarshe ma tafiya tayi ta bar Khausar din saboda yana jiranta. "Khalil bansan me yasa kake guduna ba, baka son magana dani a waya ballantana kazo inda nake, idan nayi maka wani abun ne ka sanar dani na baka haquri dan Allah?" Hadiza ta fada kamar zatayi masa kuka. Shiru yayi dan besan ta inda ze farayi mata bayani ba, dukda cewar be taba yi mata alqawarin aure ba a zuciyarsa kadai yake qudurta hakan sedai yasan itama lissafinta kenan tunda soyayyarsu ba soyayyace ta banzaba, suna mu'amala ne irinta wanda suke shirin gina wata rayuwa a gaba tare. "Khalil kayi shiru kayi magana" ta sake fada, se ya qaqalo murmushi yace "Bakiyi mun komai ba Hadiza kawai ayyuka ne suka sha kaina, sannan kinga nan akwai banbanci da snada ina Lagos, a nan idan na tashi aiki gida nake komawa gurin iyalina kinga babu dadi ace na koma gida kuma na ringa waya da wata a waje Matata ba zataji dadi ba". Shiru tayi kafin tace "Na sani amma a qalla ko sau daya ne ka ware lokacin da zamuyi magana duk sanda na kiraka fa uzuri kake bani, daga na aiki se kana kan hanya tuqi kakeyi kuma idan ka gama ba zaka kirani ba me yasa?" "Hadiza, qorafi kike so ki koya kema? Na gaya miki uzurina baki yarda dani bane ko yaya" ya fada yana tsareta da ido, itama kallonsa tayi tace "Hadiza?" "Oh sorry Dijahna, shikenan?" Ya fada yana dage mata gira daya seta sun kuyar da kanta qasa, wato tana son Khalil da yawa, she can't wait ace ta zama matarsa". "Yanzu ya akayi, kin ce kina son muyi magana me muhimmanci" ya katse mata tunaninta seta daga kai ta kalle shi tace "Daman Yaya ne yayi mun magana akan ya kamata idan da gaske kakeyi ka turo da manya su shiga maganar" ta qarasa a sanyaye, Khalil dake shan ruwa be san sanda ya kware shi ba ya shiga tari duk ta rikice tana masa sannu, seda ya lafa masa kafin ya kalleta da idonsa da sukayi ja yace "Dijah, amma bakiyiwa su Mama bayani akaina bane ba?" "Kamar Yaya Khalil wane bayani kake so nayi musu kuma? Na fada musu wanene kai da Komai naka dana sani shine dalilin ma da Yayan yace na gaya maka ka turo dan yayi bincike a kanka kai mutumin kirki ne" Hadiza ta fada tana kallonsa. Seda ya hadiye yawun daya tarar masa a baki a ransa yana cewa "Abinda nake gudu kenan" a fili kuma yace "Amma baki fada masa shekarata biyu da aure ba ko?" "Meye hadin shekarun auranka da maganar namu auran kuma?" Ta mayar masa da tambayar seya tareta da cewa "Yana da Hadi sosai ma Hadiza, yanzu misali ace kece Matata, haka kawai babu wata matsala tsakaninmu shekara Biyu nace zan qara aure zaki yarda? Bama Matata kadai ba hatta da iyayena nasan idan naje musu da maganar a yanzu se sun tuhumi dalilin da ya saka nake son qara auren". "Kenan yaudarata kake yi daman ba aurene ya kawo ka gurina na?" Hadiza ta fada muryarta na rawa se Khalil yayi saurin cewa "Wallahi Aa, Allah shine shaidata banzo gurinki da niyyar yaudara ba amma nima ki fahimceni dole ina da buqatar saita abubuwa da yawa kafin nace zan taso da maganar aure yanzu, dole ne na fara samun goyon baya daga gurin Magabatana sannan ita kanta Matata sena samu hadin kanta kafin nace zan turo da magana gidanku" "Kenan ni kuma ina zaune ina zaman jiranka idan baka samu hadin kan nasu ba na tashi a tutar babu koh? Wallahi Khalil ka cuceni ka bata mun lokaci. Da kasan baka shirya auran ba me yasa ka shigo rayuwata har ka saka na kori kowa duk a tunanina na samu Mijin aure? Lokacin da kake cewa idan ka samu yanda kake so kafin qashen shekarar nan zakayi aure daman duk yaudara ce ko kuma akwai wadda kake nema bayan ni ni bata mun lokaci kawai kakeyi? Hadiza ta fada cikin Kuka tana miqewa tsaye se shima ya miqe ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu. "Kiyi haquri Ki zauna kinga mutane suna kallonmu karsu dauka wani abin nayi miki" ya fada cikin lallashi seta zabura tace "Su kalle mu mana kuma ai wani abun kayi mun yaudarata kayi ka ha'ince ni" ta fada cikin daga sauti kafin ta figi jakarta tana cewa "Bazan yafe maka ciwon son daka jefani a ciki ba, in sha Allahu kaima se Allah ya jarabceka da son wata kuma ta wahalar dakai" miqewa yayi ganin ta fara tafiya ya sha gabanta yana cewa "Haba Hadiza ya zaki yimun Allah ya isa ki tsaya muyi magana nifa ba cewa nayi bazan aureki ba lokaci nace ki bani na samu na daidaita abubuwa" "Ka matsa mun na wuce Khalil" Hadizan ta fada yanda tayi maganar se yaga kamar ba'a hayyacinta take ba, dafe qirjinta da yaga tayi ya sakashi tunawa da tana da Ciwon qirji kuma damuwa ce take tayar mata dashi ta gaya masa, qoqarin yi mata magana yakeyi amma taqi tsayawa so kawai take ya bata guri ta wuce, ganin da yayi tana layi kamar zata fadi ya sakashi riqota yana cewa "Ki nutsu kinga zaki fadi muje mota dan Allah ki nutsu badai maganar na turo bane zan turo ina sonki zan aureki Hadiza". Tallafeta yayi a jikinsa har suka qarasa jikin motar sa ya bude gaba ya sakata seda ta zauna dakyau ya kulle qofar ya zagaya mazauninsa. Da qarfi qirjinsa ya buga ganin wani Saurayi fuskarsa sanye da Facemask dab dasu ya daga wayasa kamar meyin video, sakin murfin motar yayi ya nufeshi sedai saurayin na ganinsa ya juya da sauri ya bar gurin nan take ya bace masa. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 36 Motar ya koma yana tunanin wanene wannan din kuma me yake dauka? Ganin bashi da me bashi amsa ya saka ya mayar da hankalinsa kan tuqin da yakeyi yana yi yana lallashin Hadiza dake kuka, har qofar gidansu ya kaita, be barta ta fita ba seda ya tabbatar ta sakko kuma ta dena kukan da takeyi ya lallabeta ya kuma tabbatar mata da In sha Allahu ze aureta amma tayi haquri ta bashi lokaci kuma ta ringa musu Addu'a. "Ina son Matata sosai bansan ta yanda zan kalleta nace mata zan qara aure ba" ya fada yana kallon Hadizan ta buga masa wata harara tareda jan tsaki kafin ta kama murfin motar ta fice batareda ta tanka masa ba ya rakata da Murmushi, haega Allah yana son Hadiza kodan sanyin Halinta da kulawar da take bashi kuma tafi sonsa akan wanda yake mata yasan zata riritashi ta kiyaye bacin ransa to amma damuwar ta inda ze tunkari ita Uwargidan da wannan magana dan ta Hajiya da duk wani da ze iya kawo cikas me sauqi ne. Gaba ya danyi ya bar qofar gidan nasu ya samu guri ya tsaya. Jalila ya kira ringing biyu ta daga tana cewa "Aa Hussaina yau ka tuna dani kenan" "Dama na taba cewa na manta dake ne?" Ya bata amsa se tayi yar dariya tace "Toh ai muj sallamawa Maman Mu'ayyad kai, ta tsare gaba ta tsare baya Hajiya kadai ake bawa damar ganinka da magana dakai sanda taso mu kuwa idan mun gaji da neman ka sedai mu kirata mu bada saqo" "Kina da Matsala Jalila yanzu duk meya kawo wannan qorafin" ya katseta, seta sake cewa "Gaskiya ce kawai ba qorafi ba gaba daya ka maqalewa Mace baka da lokacin kowa yanzu se nata duk sunkasa fasa maka ne ni kasan bazanyi shiru ba" Qaramin tsaki yaja yace "Mutum na cikin wata damuwar zaki zo ki qara masa, kiranki nayi ki bani shawara amma zaki cikamun kunne da mita haba" yanda yayi maganar cikin alamun abu na damunsa ya sakata sassauta murya tace "Yi haquri toh dan qanina meya faru, wace damuwa kake ciki kuma shawarar me zamuyi?" "Aure nake so na qara Jalila" ya bata amsa kaitsaye dan bayaso aja maganar se tayi shiru kusan minti daya kafin ta numfasa tace "Aure Khalil, ka gayawa Hajiya kuma ta yarda?" "Ban gayawa kowa ba shawararki nake nema me kike gani akai nayi ko Aa?" Ya mayar mata da wata tambayar se Jalila ta ajiye numfashi tace "Wannan ai ba maganar da kai tsaye zance maka yi ko karkayi bace. Qarin aure yana zuwa ne akan abu biyu, buqatuwar yin hakan ko kuma yazo maka baqatatan daga Allah dukda dukka biyun nufin Allah ne amma kashin farko da niyya kuma mutum yaso yin hakan kai wannene naka a ciki?" "Nima ban sani ba" bata amsa kamar me shirin fasa kuka, baya so Hadiza ta zarge shi da laifin yaudara dukda wani mummunan abu be taba shiga tsakaninsu ba ze iya cewa ko hannunta be taba ba sedai bisa kuskure amma dukda haka bazeso haqqin Soyayyar da takeyi mishi ya kamashi ba kuma tsoron sa Allah tsoronsa yanda ze tunkari Umaimah musamman da yanzu suke zaune lafiya babu wata matsala a tsakaninsu. Dariyar Jalila ce ta dawo dashi hayyacinsa yaji tana cewa "Dan qanina maganar nan bata waya bace, ka samu lokaci kazo mu tattauna in fahimceka kafin nasan abin da zan baka shawara akai" Yayi Na'am da shawararta dan haka yace mata "Shikenan zanzo, amma dan Allah kar wanda yasan wannan maganar ko da Hajiya ce na gaya miki ban sanar da kowa ba seke, ba kuma naso suji se na gama yanke shawarar yi ko akasin haka" "Haba kaima kasan babu meji, ko mun taba kashewa mun rufe kaji wani ya tada maganar?" "Naga kin koyi tsogumi ne yanzu shiyasa musamman tunda kun sakawa Matata ido qila ku kuke ta mata Addu'a har naji abin ya darsu a zuciyata" se Jalila ta saka dariya tana cewa "Ai ko ace muna da wata matsala da Matarka bazamu goyi bayan haka kawai kayi mata kishiya ba indai ba da wani babban dalili ba ballantana ma babu, ka samu lokacin ka shigo se mutattauna kaji" daga haka sukayi sallama ya tada motar yaci gaba da tafiya. Office ya koma amma gaba daya ranar be iya gane abinda yakeyi ba dan hankalinsa ya rabu da yawa. Kwana biyu a tsakani cikin damuwa yayi su, tunanin yanda ze magance Matsalar Hadiza yakeyi gashi tayi fushi koya kirata a waya se taga dama zata dauka har tana cewa ashe yana da lokaci daman niyyar kiranta ne kawai bashi dashi se yanzu se ya ringaji toh kawai ya rabu da ita mana salin alin su rabu ga mafita ya samu amma yana tsoron haqqinta, yasan zafin soyayya tunda yanzu haka cikin karbar gashinta yake idan har haka Hadiza takeji a kansa idan ya barta beyi mata Adalci ba. Umaimah kanta ta lura da rashin walwalarsa data tambaye shi yace mata bayajin dadi ne ga kuma ayyuka da suka yi masa yawa ta ringa mitar ai shi yake dorawa kansa me yasa duk Architects din da suke a kamfaninsu ace duk wani babban aiki shi ze ringa kula dashi ai se a bawa wasu dama. Sanda take maganar kallonta kawai yayi, shi kam Umaimah ta dena bashi mamaki yanzu dan duk abinda tayi yana tsammanin zatayi wanda ya fishi, yanzu ita ba Jin dadinta bane ace Allah ya daukaka shi cikin daruruwa shi aka zaba Aa mita takeyi akan me yasa akayi hakan toh Allah ya rufa Asiri, shidai Tsuntsun soyayyar sa beyi masa Adalci ba daya rasa inda ze sauka se akan wannan butsuwar yarinyar. Be samu zama da Jalila ba se bayan sati daya ranar Weekend yacewa Umaimah ta shirya suje gidan dukda yasan ba zuwa zatayi ba latsine, ya rasa me yasa yanzu take ja baya da yan uwan nasa wanda sam farkon auransu ba haka bane sosai suke shiri take daukarsu tamkar su Yaya Naziyya amma tunda ta haihu abubuwa suka chanza, shi kansa gidan Hajiyar da take yawan zuwa ta rage sedai ta kirata a waya su gaisa wannan dai babu fashi kullum ta Allah seta kirata. Umaimah ko daya gaya mata zasuje din kaitsaye tace bazata ba saboda akwai sunan Mariya maqociyarsu da za'ayi a ranar Amaryace matar qanin Mijin Maman Hibban da sun fara zama a wata unguwa barayi suka damesu shine ya gina filin jikin gidan Maman Hibban din inda sukayi Suna suka tare a anan. Ya gama shirinsa tsaf ze fita tana zaune a palour kanta ne yake sara mata haka a kwanakin take yawan fama da ciwon kai wani lokacin harda jiri ta gayawa Khalil yace yawan kallon waya da takeyi gashi bata samun isashshen bacci ta raba dare Online su suka saka shiko ya dena mata magana duk yanda tayi daidai ne tunda tana masa abinda yake so idan ta gama can taje ita ta sani. "Baka bani kudin barka ba toh zaka fita" Umaimah ta fada jin yana mata sallama, se ya kalleta yace "Kudin barka kuma? Ina kudin da kike kaiwa can gidan duk sati da kikace kuna tarawa ne saboda irin haka idan hidima ta tasowa wani se a bashi a madadin matan unguwa?" Baki ta tura tace "Toh ai wancan na gidauniya ne wannan kuma personal ne da zan bata" "Ai Namiji kika ce ta haifa ki duba cikin rigunanku ki kai mata ko ki dauka a kudin dana baki jiya ni banda kudi yanzu" yana gama fada ya saka kai ya fita yana mamakinta. Jiyan nan dubu talatin ya bata wai zata siyi kayan gyara, sannan duk satin duniya se ya bata dubu biyu ta zubin gidauniya data ce banda idan ya samu kudi haka kawai ma bata yakeyi ko idan zata fita unguwa duk suna ina da seya bata kudin wata barka ai bashi ya aiketa ba. Da dai Umaimah bazatace ya bata kudi ba duk abinda yaga dama ya bata zata karba tayi godiya wani lokacin har tace ya rage saboda tana tausayinsa amma yanzu ta zama yar fashi daga zaune. Bill ne take masa harda na banza, ana zaune lafiya zata qirqiro abu tace tana so idan yaqiyi kuma ta ringa fushi da baqin rai kenan da mita har se ya mata abinda take so yanzu a ritsin nan Iphone 13 ta saka seda ya siya mata shi yana fama da X tun kafin auransu be chanza ba ita kuwa 12 take riqewa rana daya tace duk qawayenta 13 ce dasu dole ya karbi ta hannunta ya cika aka bata wata. Umaimah kuwa harara ta rakashi da ita babu arziqin a dawo lafiya tunda ya hanata kudin barka. Shifa yace dan ita yake nema a da tausaya masa takeyi ganin yana da dawainiya dayawa akan sa amma tunda Rufaida ta wayar mata dakai ta dena. Ita ta koya mata dabarun karbar kudi a hannunsa dukda kota karba ba wata tsiyar take dasu ba sedai rantawa qawaye da zubin Adashi se siyi banza siyi wofi abin kirki kadai da zata ce tana siya shine kayan gyaran jiki wannan ko bata wasa dasu dan da jikin take yaqarsa tayi iskancinta son rai kuma taci riba. Kiran wayarta ne ya dakatar da ita ta janyota, Rufaida ce tana dagawa tace "Madam kin shirya mu shiga gidan sunan kuwa?" "Na dauka seda yamma ai" Umaimah ta bata amsa se tace mata "Aa zamu shiga yanzu mana muga koda abinda zamu kama musu" "Gaskiya sedai kije ni se zuwa yamma bana jin dadi kaina yana ciwo" Umaiman ta sake fada cikin jimami Rufaidan ta mata sannu tareda cewa bari ta shigo toh. Basufi minti goma da waya ba taji bugun qofa taje ta bude mata ta shigo ta zumbulo Hijabi da gani ko wanka ba tayi ba, seda suka zauna take tambayarta "megidan baya nan naga babu motarsa". Baki Umaimah ta tabe tace "Ya tafi gidan Anty Jalila" "Kice yau seta Allah ko ba ita ce tazo kwanaki da qanwar Mijinta ba?" Rufaida ta fada tana gyara zama Umaimah ta girgiza kai alamar Aa kafin tace "Ba ita ba wannan Yan biyunsa ce ba Anty Amina ba ita ce babbarsu" "Au wai yan biyune, toh Allah ya fishsheki dan kinsan idan ka hadu da yayyen Miji mata se a hankali musamman keda ake ganin kina ciki daula yanzu se kiji zantuka kala kala". "Uhm" kawai Umaimah tace tayi shiru, hudubar Rufaida ta rigada ta gama tasiri a zuciyarta ita ta nuna mata tunda yayyen Khalil matane bazasu sota tsakani da Allah ba zasu ringa kishi da ita suna ganin Dan uwansu na bauta mata yana mata abinda su basa samu a gidan auransu dalilin da ya saka taja baya dasu dukda ko kallon banza babu wadda ta tabayi mata a cikinsu, yanzu hatta da Habiba da take yar gidanta ta rage kiranta tazo gidan acewar Rufaida zata ringa kwashe sirrinta tana kaiwa gida ita kuma taga hakan ze yuwu. Nan suka zauna basu shiga gidan sunan ba se bayan la'asar Rufaida ta koma tayo wanka itama ta shirya bayan Hauwa ta dauki Mu'ayyad ta tafi dashi gidansu seda aka yi Isha'i suka baro gidan sunan ta shiga gida har sannan kuma Khalil be dawo ba. Khalil Seda ya fara biyawa gidan Abokinsa Mukhtar da yake shirin angwancewa nan da sati uku, fenti akeyi, ya duba masa aikin suka dan taba hira kafin ya wuce gidan Jalila. Cikin murna ta tareshi dan ya dade rabonsa da gidan nata, ita kadai ya tarar se Almajirinta yana mata wanki a tsakar gida suka shiga ciki ta kawo masa ruwan Lipton da Dumamen tuwo miyar Kuka yaji man shanu. "Kai amma Allah ya tsundumaki a Aljanna kamar kinsan na kwana biyu banci tuwo ba" ya fada sanda ya bude kwanon. "Ai tun da kace mun yau da safe zakazo, banyi niyyar tuwo ba jiya saboda kai nayi nace dan qanina nasan ba lallai Maman Mu'ayyad nayin tuwo ba balle ka samu dumame". Hannunsa ya wanko a Kitchen ya saka tuwon a bowl hade yake da miyar ta dumama irin yanda yake so yayi bismillah ya fara ci ita kuma ta tsiyaya masa baqin shayin daya sha kayan qamshi a kofi. Seda ya cinye tas yasha shayin yayi hamdala, shi ya kai mata kwanukan kitchen ta rigada tayi wanke wanke dan haka ya dauraye wanda ya bata ya kife mata su a kwandon daya gani cikin sink ya futo da gorar ruwa a hannunsa. "Ashe dai har yanzu kana aikin gida" ta fada cikin tsokana ya zauna yana murmushi yace "Nasan mitarki idan na ajiye ban wanke ba har na tafi kina mun surutu" "Kasan haka muke da Abbansu tun be iya wanke wanke har seda ya saba yanzu da sun bata kwanuka zece a wanke se kaji Zee tana ayi wanke wanke kafin Mama ta fara mita" suka saka dariya gaba daya. "Ina yaran nema naji gidan shiru" ya tambayeta bayan daya zauna tace "Kamal da Asiya sun tafi Tahfiz, Nuradden kuma yana Jalingo kasan Hajiya da Didi kuma qanwarsa ta kai su gidan kitso jiya wai sunyi dare suka kwana a gidanta inaga se anjima zata dawo dasu" "Wai har yanzu Nuraddeen be dawo ku haqura da yaron nan kawai ku bar musu shi mana" Khalil ya fada tayi murmushi tace "nima haka nace jiya da yake zancen ze kira Hajiyar ya gaya mata an dade da komawa makaranta nace ai sun sani ka barshi kawai yayi zamansa nan da can ai duk daya ne toh kasan shi da qulafucin Yaya bedai ce komai ba kuma be kirata ba yana dai mitar wai Nura nada wasa baya sonkaratu idan ba an takura masa ba acan in ya samu sake sangarcewa zeyi" "Haka dai ze haqura ya barshi da ya samu kakannin ma masu so su riqe jikan, nan Hajiya data dauko Inteen kina ganin yanda suka qare" Khalil ya fada suka fashe da dariya gaba daya. Seda suka lafa Jalila ta kalle shi tace "Toh ya ake ciki ranar mun fara magana a waya?" Tattara hankalinsa yayi akanta yace "Wato wata yarinya ce muka hadu da ita kin gane, harga Allah tana burgeni kuma ina sonta amma kuma ni banyi tunanin nan kusa zata kawo maganar muyi aure ko wani abu ba kuma ita bala'in sona takeyi, nidai in taqaice miki magana yanzu kinsan dai matsayin da nake ciki a yanzu bazance zanyi aure ba saboda kowa seya tambayeni dalili idan kika duba aurena shekara biyu kwata kwata ni kuma bani da wani dalili me qarfi dazance gashi ya saka zanyi aure". Shiru Jalila tayi tana kallonsa har ya kai aya kafin taja numfashi tace "Ita yarinyar yaushe kuka hadu, kuma tsahon wane lokaci kuke tare?" "Bamu wani dade ba wata uku zuwa hudu kenan da haduwarmu lokacin da naje aiki Lagos din nan, dukda dai mun taba haduwa a nan Kano amma dai Officially mu fara magana da ita yanzu za'ayi 3 months" Khalil ya bata amsa tayi shiru tana kallonsa, so takeyi tace masa lokacin da Umaimah taqi binsa Lagos kenan kuma ta tambayeshi wace irin alaqa ce tsakaninsu dukda bata zargin qanin nata amma tasan abinda Umaiman tayi masa yana iya sakawa shedan ya zugashi ya fada abinda ba halinsa ba. Itama ta samu labarin ne a bakin Khalifa kuma ya roqeta akan dan Allah karta gayawa Kowa dan Yaya Khalil yaja masa kunne kawai ya kasa hadiye maganar ne yasa ya gaya mata dan ita ana sirri da ita ba irin su Yaya Jamila faransai bace. "Kinyi shiru kina kallona kamar wanda nayi miki qarya" Khalil ya fada se tayi murmushi tace "So nake na auna soyayyar da kakeyi mata da irin wadda na gani a idonka sanda kake gaya mun ka hadu da Umaimah" "Babu hadi Jalila babu macen da zata kamo qafar Umaimah a zuciyata" Khalil yayi saurin tareta a zuciyarta tace "Ta gano lagon ka shiyasa take garaka kamar kwallo a fili kuwa seta gyara zamanta tace "Toh tanada wannan matsayin ya akayi har idonka ya iya hange hange ka samo wata ka fara so, kuma a yanda kake jaddada soyayyar nan tata ace a ayan shekarun nan zaka mata kishiya Khalil? Idan har da gaske ka daukeni yar uwar da zamu kashe mu rufe ka gaya mun gaskiyar meye damuwarka, meye dalilinka na son qara aure? Ni kuma zanyi maka hukunci bisa adalci in sha Allah dan bazan so ka tauye kanka ba haka itama Umaimah bazan bi bayanka kayi mata rashin Adalci idan har ya zamana son ranka ne kawai". Shiru Khalil yayi yana nanawa maganarta a zuciyarsa, yanada yaqinin Jalila zata riqe masa sirri idan ya gaya mata amma yana tsoron ta farayiwa Umaimah wani kallo na daban a matsayin me musgunawa dan uwanta, yasan zata qullaceta dan Jalilan nason duk abinda yake so tana kuma qin abinda yake bata masa. "Kayi shiru dan qanina ko da akwai matsala ne" ta fada cikin tsokana ya dago ya harareta tayi dariya tace "Sarkin son girma duk tsiyarka dai minti biyar ba wasa bace" dole yayi murmushin shima ta sake cewa "Yawwa ina jinka kayi magana mu samu mu san ta inda zamu kamo bakin zaren maganar nan" "Kina ji Jalila ina son Umaimah kuma bani da wata matsala da ita, damuwata guda daya ce kawai yanayin aikina da bana zama guri daya a koda yaushe ana turani garuruwa nayi ayyuka kuma ina yin kwanaki wani lokacin ma satittika ni kuma ina da sha'awar duk ina zani na tafi da Matata, matsalar anan ita kuma Umaimah bata son tafiya. Duk sanda wata tafiya ta taso se rayukan mu sun baci kafin ta bini, kinga last tafiyar da nayi Lagos har na gama zamana na dawo bataje ba acan nema na hadu da Hadiza dan a lokacin fushin da nake ciki na yanke shawarar aure kawai zan qara na auro wadda ko bangon duniya nace zanje zata bini" Yaci gaba da bata labarin yanda ya hadu da Hadiza da irin soyayyar fa sukayi har zuwa matsayin da suke yanzu akai na zancen turowa da tayi masa. Ya rufe da cewa "Banaso haqqinta ya kamani dan dagaske yarinyar tana so na ni kuma bansan ya zanyi ba yanzu. Tun bayan dawowata na tuntubi Hajiya da maganar dan naji ta bakinta tayi futufutu tace babu wannan maganar ba yanzu ba har gaba babu ita. Toh ni maganar Hajiya ma da sauqi nasan idan na lallabata tana iya yarda, Umaimah nada bala'in kishi irin wanda bakiyi tunani ba, idan zancen auran nan ya fito na tabbata babu sauran zaman lafiya tsakanin mu". "Hmmmm" Jalila taja dogon numfashi tareda sauke taguminda tayi tana kallon Khalil tace "Ni har na rasa ta ina zanfara ma, idan na fahimceka abinda yasa ka fara kula Sabuwarka saboda rashin Umaimah a kusa ne bari na fara da wannan bangaren in har kana ganin cewar Umaimah bazata haqura ta ringa binka duk inda zakaje ba kana da hujjar da zaka qara aure kuma duk wanda ka gayawa dalilinka baze hanaka ba kodan gudun fadawa halaka. Amma idan shawara kake nema se nace maka qarin aure ba shine mafita ba ka zauna da ita kuyi magana ta fahimta ka nuna mata buqatarka da abinda bijirewa hakan ze iya janyowa idan har bata gyara ba daga nan kana iya daukar mataki na gaba sannan ita wannan Hadiza kace kowa sunanta ba son ta kakeyi ba, Umaimah ta riga ta siye filin a ganina ka saurareta ne kawai a lokacin saboda fushin Umaimah inda dagaske ka gantan kake sonta zuciyarka bazata kawo maka wani tunani ba balle har kaji shayin tunkarar kowa da maganar auranta. Kuma koda ace ka aureta be zama lallai ka iyayin adalci a tsakaninsu ba, idan auran kake so dagaske ka bari ka samu wadda soyayyarta tayi takara data Umaimah a zuciyarka idan ba haka ba yanda kake Son matar nan kake tsoronta duk wadda ta shigo gidanka bayan ita wahala kawai zata sha". "Kema bakya goyon bayan maganar kenan?" Khalil ya tambayeta fuska babu walwa kafin tayi magana yaci gaba da cewa "Ni wallahi tsoron hakkinta ya kamani nakeyi na san soyayya nasan zafinta, bakiga irin Kukan da takeyimun ba jiya tana nanata tana sona naji tausayinta sosai" "Tausayinta kakeyi ba Son ta ba Khalil, idan kuwa hakane ka barta kayi mata Addu'a Allah ya bata wanda ya fika dan bata da gurbi a zuciyarka Umaimah ta gine duka filayen sedai idan rusau za'ayi" Jalila ta fada cikin tsokana a zuciyarta tana sake auna maganar Khalil din, ita dai a iya tata Basirar abinda ta gani kenan, ba son hadiza yakeyi ba tausayinta yake kuma fushin Umaimah ne ya saka shi harya fara kulata, ko a yanzun bata raba daya biyu bata masa rai tayi shiyasa har yake tunanin yayi auran. Tattaunawa suka cigaba dayi akan Abubuwan da suka shafesu har suka gangara batun gidansu daze siya da yanda yake so yayi dashi, be bar gidan ba se gurin qarfe uku na rana shima saboda Mansur ya kirashi yana so su hadu ya tafi bayan ya cikata da Alkhairin dayaje mata dashi tanata godiya, suna son dan uwan nasu saboda yanda yake sonsu. Maganar da sukayi da Jalila ta saka ya qara ja baya da Hadiza kuma ya yarda dagasken ba son ta yakeyi ba tausayine da kuma huce takaici da yaso yayi da ita amma dukda haka yana tausaya mata, kullum cikin rarrashinta yake da gaya mata cewar ta fawwalawa Allah idan hat ya qaddara zasuyi aure zasuyi a sanda yaso. Data matsa masa akan Yayanta yace yana son ganinsa ranar ya haqura yaje, be boye masa komai ba ya gaya masa uzurinshi ya kuma fahimce shi yayi musu fatan Alkhairi idan Hadiza matarsa ce Allah ya tabbatar, bayan ya gama da Yayan ya turo masa ita sukayi magana, kamar ze zubda Hawayen tausayinta saboda yanda duk ta rame dalilin damuwar da ta saka kanta a ciki. Haquri ya bata tateda lallashi, yace mata baze ce ta jirashi ba, amma idan da rabon aure a tsakaninsu yana fatan Allah ya matso musu dashi kusa sannan ya roqeta da suci gaba da gaisawa idan tana ganin babu matsala tace zatayi tunani haka suka rabu rabuwar da yake ganin sunyi ta kenan shida ita. Ciwon kai da jirin da suka matsawa Umaimah ya saka dole sukaje Asibiti wata ranar Litinin, bayan likitan yayi mata yan tambayoyi ya auna jininta ya rubuta mata magunguna akan taje tasha idan bata samu afuwa ba su sake komawa. A hanya Khalil ya ringa mata fadan rashin bacci da wuni da takeyi akan waya dan hatta idonta jini ya kwanta shiyasa likitan be kawo tunanin kowanne ciwo ba yace rashin bacci ne ta ringa samun isashshenhutu suna tafe ta tunzura baki gaba saboda fadan da yake mata kai tsaye gidan su ya kaita, idan da Umaimah tasan can ze ajiye ta yasan bazata yarda ba dan tunda ta gudo kamar yanda Anty ta fada bata sake komawa ba. A tsaitsaye suka gaisa yayiwa Mama bayanin bata da lafiya daga Asibiti suke, ya qarasa da cewa "Dan Allah Mama ki saka mata ido ta samu tayi bacci karta zauna danne dannen waya" "Uhm abin nata har ya kai ya saka mata ciwo kenan ko, jiyan nan naji Salman yana maganar tsakar dare tayi masa magana akan yaje zata aike shi seda Safe yaga saqon ya duba lokaci yake cewa Ashe Umaimah bata dena kaiwa dare tana chatting ba toh Allah ya shirya" tayi masa fatan Alkhairi ya wuce Umaimah dai tunda ta shige daki tayi luf, da mama ta tashi yi mata tsiya wayar gaba daya ta kwace, Mu'ayyad daman suna shiga yara suka dauke shi dan haka tana cin abinci tasha magungunan tana nan zaune shiru Mama nata shige da ficenta kota kanta bata bi ba baccin dole ya dauketa saboda magungunan data sha. Da suka koma gida kuwa yasha mita yayi mata banza dan kanta tayi shiru, doka ya kafa mata ta bacci qarfe goma kuma ta kashe wayarta ta bashi. Yanda ya hade fuska yana gaya mata dokar dole ta amsa a lokacin dan yanzu lallabashi takeyi bata so nan kusa ace an sake samun wata matsalar musamman da take da buqata a gurinsa so take a kwana biyu komai yayi daidai ta nemi abinda take so. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 37 Motar ya koma yana tunanin wanene wannan din kuma me yake dauka? Ganin bashi da me bashi amsa ya saka ya mayar da hankalinsa kan tuqin da yakeyi yana yi yana lallashin Hadiza dake kuka, har qofar gidansu ya kaita, be barta ta fita ba seda ya tabbatar ta sakko kuma ta dena kukan da takeyi ya lallabeta ya kuma tabbatar mata da In sha Allahu ze aureta amma tayi haquri ta bashi lokaci kuma ta ringa musu Addu'a. "Ina son Matata sosai bansan ta yanda zan kalleta nace mata zan qara aure ba" ya fada yana kallon Hadizan ta buga masa wata harara tareda jan tsaki kafin ta kama murfin motar ta fice batareda ta tanka masa ba ya rakata da Murmushi, haega Allah yana son Hadiza kodan sanyin Halinta da kulawar da take bashi kuma tafi sonsa akan wanda yake mata yasan zata riritashi ta kiyaye bacin ransa to amma damuwar ta inda ze tunkari ita Uwargidan da wannan magana dan ta Hajiya da duk wani da ze iya kawo cikas me sauqi ne. Gaba ya danyi ya bar qofar gidan nasu ya samu guri ya tsaya. Jalila ya kira ringing biyu ta daga tana cewa "Aa Hussaina yau ka tuna dani kenan" "Dama na taba cewa na manta dake ne?" Ya bata amsa se tayi yar dariya tace "Toh ai muj sallamawa Maman Mu'ayyad kai, ta tsare gaba ta tsare baya Hajiya kadai ake bawa damar ganinka da magana dakai sanda taso mu kuwa idan mun gaji da neman ka sedai mu kirata mu bada saqo" "Kina da Matsala Jalila yanzu duk meya kawo wannan qorafin" ya katseta, seta sake cewa "Gaskiya ce kawai ba qorafi ba gaba daya ka maqalewa Mace baka da lokacin kowa yanzu se nata duk sunkasa fasa maka ne ni kasan bazanyi shiru ba" Qaramin tsaki yaja yace "Mutum na cikin wata damuwar zaki zo ki qara masa, kiranki nayi ki bani shawara amma zaki cikamun kunne da mita haba" yanda yayi maganar cikin alamun abu na damunsa ya sakata sassauta murya tace "Yi haquri toh dan qanina meya faru, wace damuwa kake ciki kuma shawarar me zamuyi?" "Aure nake so na qara Jalila" ya bata amsa kaitsaye dan bayaso aja maganar se tayi shiru kusan minti daya kafin ta numfasa tace "Aure Khalil, ka gayawa Hajiya kuma ta yarda?" "Ban gayawa kowa ba shawararki nake nema me kike gani akai nayi ko Aa?" Ya mayar mata da wata tambayar se Jalila ta ajiye numfashi tace "Wannan ai ba maganar da kai tsaye zance maka yi ko karkayi bace. Qarin aure yana zuwa ne akan abu biyu, buqatuwar yin hakan ko kuma yazo maka baqatatan daga Allah dukda dukka biyun nufin Allah ne amma kashin farko da niyya kuma mutum yaso yin hakan kai wannene naka a ciki?" "Nima ban sani ba" bata amsa kamar me shirin fasa kuka, baya so Hadiza ta zarge shi da laifin yaudara dukda wani mummunan abu be taba shiga tsakaninsu ba ze iya cewa ko hannunta be taba ba sedai bisa kuskure amma dukda haka bazeso haqqin Soyayyar da takeyi mishi ya kamashi ba kuma tsoron sa Allah tsoronsa yanda ze tunkari Umaimah musamman da yanzu suke zaune lafiya babu wata matsala a tsakaninsu. Dariyar Jalila ce ta dawo dashi hayyacinsa yaji tana cewa "Dan qanina maganar nan bata waya bace, ka samu lokaci kazo mu tattauna in fahimceka kafin nasan abin da zan baka shawara akai" Yayi Na'am da shawararta dan haka yace mata "Shikenan zanzo, amma dan Allah kar wanda yasan wannan maganar ko da Hajiya ce na gaya miki ban sanar da kowa ba seke, ba kuma naso suji se na gama yanke shawarar yi ko akasin haka" "Haba kaima kasan babu meji, ko mun taba kashewa mun rufe kaji wani ya tada maganar?" "Naga kin koyi tsogumi ne yanzu shiyasa musamman tunda kun sakawa Matata ido qila ku kuke ta mata Addu'a har naji abin ya darsu a zuciyata" se Jalila ta saka dariya tana cewa "Ai ko ace muna da wata matsala da Matarka bazamu goyi bayan haka kawai kayi mata kishiya ba indai ba da wani babban dalili ba ballantana ma babu, ka samu lokacin ka shigo se mutattauna kaji" daga haka sukayi sallama ya tada motar yaci gaba da tafiya. Office ya koma amma gaba daya ranar be iya gane abinda yakeyi ba dan hankalinsa ya rabu da yawa. Kwana biyu a tsakani cikin damuwa yayi su, tunanin yanda ze magance Matsalar Hadiza yakeyi gashi tayi fushi koya kirata a waya se taga dama zata dauka har tana cewa ashe yana da lokaci daman niyyar kiranta ne kawai bashi dashi se yanzu se ya ringaji toh kawai ya rabu da ita mana salin alin su rabu ga mafita ya samu amma yana tsoron haqqinta, yasan zafin soyayya tunda yanzu haka cikin karbar gashinta yake idan har haka Hadiza takeji a kansa idan ya barta beyi mata Adalci ba. Umaimah kanta ta lura da rashin walwalarsa data tambaye shi yace mata bayajin dadi ne ga kuma ayyuka da suka yi masa yawa ta ringa mitar ai shi yake dorawa kansa me yasa duk Architects din da suke a kamfaninsu ace duk wani babban aiki shi ze ringa kula dashi ai se a bawa wasu dama. Sanda take maganar kallonta kawai yayi, shi kam Umaimah ta dena bashi mamaki yanzu dan duk abinda tayi yana tsammanin zatayi wanda ya fishi, yanzu ita ba Jin dadinta bane ace Allah ya daukaka shi cikin daruruwa shi aka zaba Aa mita takeyi akan me yasa akayi hakan toh Allah ya rufa Asiri, shidai Tsuntsun soyayyar sa beyi masa Adalci ba daya rasa inda ze sauka se akan wannan butsuwar yarinyar. Be samu zama da Jalila ba se bayan sati daya ranar Weekend yacewa Umaimah ta shirya suje gidan dukda yasan ba zuwa zatayi ba latsine, ya rasa me yasa yanzu take ja baya da yan uwan nasa wanda sam farkon auransu ba haka bane sosai suke shiri take daukarsu tamkar su Yaya Naziyya amma tunda ta haihu abubuwa suka chanza, shi kansa gidan Hajiyar da take yawan zuwa ta rage sedai ta kirata a waya su gaisa wannan dai babu fashi kullum ta Allah seta kirata. Umaimah ko daya gaya mata zasuje din kaitsaye tace bazata ba saboda akwai sunan Mariya maqociyarsu da za'ayi a ranar Amaryace matar qanin Mijin Maman Hibban da sun fara zama a wata unguwa barayi suka damesu shine ya gina filin jikin gidan Maman Hibban din inda sukayi Suna suka tare a anan. Ya gama shirinsa tsaf ze fita tana zaune a palour kanta ne yake sara mata haka a kwanakin take yawan fama da ciwon kai wani lokacin harda jiri ta gayawa Khalil yace yawan kallon waya da takeyi gashi bata samun isashshen bacci ta raba dare Online su suka saka shiko ya dena mata magana duk yanda tayi daidai ne tunda tana masa abinda yake so idan ta gama can taje ita ta sani. "Baka bani kudin barka ba toh zaka fita" Umaimah ta fada jin yana mata sallama, se ya kalleta yace "Kudin barka kuma? Ina kudin da kike kaiwa can gidan duk sati da kikace kuna tarawa ne saboda irin haka idan hidima ta tasowa wani se a bashi a madadin matan unguwa?" Baki ta tura tace "Toh ai wancan na gidauniya ne wannan kuma personal ne da zan bata" "Ai Namiji kika ce ta haifa ki duba cikin rigunanku ki kai mata ko ki dauka a kudin dana baki jiya ni banda kudi yanzu" yana gama fada ya saka kai ya fita yana mamakinta. Jiyan nan dubu talatin ya bata wai zata siyi kayan gyara, sannan duk satin duniya se ya bata dubu biyu ta zubin gidauniya data ce banda idan ya samu kudi haka kawai ma bata yakeyi ko idan zata fita unguwa duk suna ina da seya bata kudin wata barka ai bashi ya aiketa ba. Da dai Umaimah bazatace ya bata kudi ba duk abinda yaga dama ya bata zata karba tayi godiya wani lokacin har tace ya rage saboda tana tausayinsa amma yanzu ta zama yar fashi daga zaune. Bill ne take masa harda na banza, ana zaune lafiya zata qirqiro abu tace tana so idan yaqiyi kuma ta ringa fushi da baqin rai kenan da mita har se ya mata abinda take so yanzu a ritsin nan Iphone 13 ta saka seda ya siya mata shi yana fama da X tun kafin auransu be chanza ba ita kuwa 12 take riqewa rana daya tace duk qawayenta 13 ce dasu dole ya karbi ta hannunta ya cika aka bata wata. Umaimah kuwa harara ta rakashi da ita babu arziqin a dawo lafiya tunda ya hanata kudin barka. Shifa yace dan ita yake nema a da tausaya masa takeyi ganin yana da dawainiya dayawa akan sa amma tunda Rufaida ta wayar mata dakai ta dena. Ita ta koya mata dabarun karbar kudi a hannunsa dukda kota karba ba wata tsiyar take dasu ba sedai rantawa qawaye da zubin Adashi se siyi banza siyi wofi abin kirki kadai da zata ce tana siya shine kayan gyaran jiki wannan ko bata wasa dasu dan da jikin take yaqarsa tayi iskancinta son rai kuma taci riba. Kiran wayarta ne ya dakatar da ita ta janyota, Rufaida ce tana dagawa tace "Madam kin shirya mu shiga gidan sunan kuwa?" "Na dauka seda yamma ai" Umaimah ta bata amsa se tace mata "Aa zamu shiga yanzu mana muga koda abinda zamu kama musu" "Gaskiya sedai kije ni se zuwa yamma bana jin dadi kaina yana ciwo" Umaiman ta sake fada cikin jimami Rufaidan ta mata sannu tareda cewa bari ta shigo toh. Basufi minti goma da waya ba taji bugun qofa taje ta bude mata ta shigo ta zumbulo Hijabi da gani ko wanka ba tayi ba, seda suka zauna take tambayarta "megidan baya nan naga babu motarsa". Baki Umaimah ta tabe tace "Ya tafi gidan Anty Jalila" "Kice yau seta Allah ko ba ita ce tazo kwanaki da qanwar Mijinta ba?" Rufaida ta fada tana gyara zama Umaimah ta girgiza kai alamar Aa kafin tace "Ba ita ba wannan Yan biyunsa ce ba Anty Amina ba ita ce babbarsu" "Au wai yan biyune, toh Allah ya fishsheki dan kinsan idan ka hadu da yayyen Miji mata se a hankali musamman keda ake ganin kina ciki daula yanzu se kiji zantuka kala kala". "Uhm" kawai Umaimah tace tayi shiru, hudubar Rufaida ta rigada ta gama tasiri a zuciyarta ita ta nuna mata tunda yayyen Khalil matane bazasu sota tsakani da Allah ba zasu ringa kishi da ita suna ganin Dan uwansu na bauta mata yana mata abinda su basa samu a gidan auransu dalilin da ya saka taja baya dasu dukda ko kallon banza babu wadda ta tabayi mata a cikinsu, yanzu hatta da Habiba da take yar gidanta ta rage kiranta tazo gidan acewar Rufaida zata ringa kwashe sirrinta tana kaiwa gida ita kuma taga hakan ze yuwu. Nan suka zauna basu shiga gidan sunan ba se bayan la'asar Rufaida ta koma tayo wanka itama ta shirya bayan Hauwa ta dauki Mu'ayyad ta tafi dashi gidansu seda aka yi Isha'i suka baro gidan sunan ta shiga gida har sannan kuma Khalil be dawo ba. Khalil Seda ya fara biyawa gidan Abokinsa Mukhtar da yake shirin angwancewa nan da sati uku, fenti akeyi, ya duba masa aikin suka dan taba hira kafin ya wuce gidan Jalila. Cikin murna ta tareshi dan ya dade rabonsa da gidan nata, ita kadai ya tarar se Almajirinta yana mata wanki a tsakar gida suka shiga ciki ta kawo masa ruwan Lipton da Dumamen tuwo miyar Kuka yaji man shanu. "Kai amma Allah ya tsundumaki a Aljanna kamar kinsan na kwana biyu banci tuwo ba" ya fada sanda ya bude kwanon. "Ai tun da kace mun yau da safe zakazo, banyi niyyar tuwo ba jiya saboda kai nayi nace dan qanina nasan ba lallai Maman Mu'ayyad nayin tuwo ba balle ka samu dumame". Hannunsa ya wanko a Kitchen ya saka tuwon a bowl hade yake da miyar ta dumama irin yanda yake so yayi bismillah ya fara ci ita kuma ta tsiyaya masa baqin shayin daya sha kayan qamshi a kofi. Seda ya cinye tas yasha shayin yayi hamdala, shi ya kai mata kwanukan kitchen ta rigada tayi wanke wanke dan haka ya dauraye wanda ya bata ya kife mata su a kwandon daya gani cikin sink ya futo da gorar ruwa a hannunsa. "Ashe dai har yanzu kana aikin gida" ta fada cikin tsokana ya zauna yana murmushi yace "Nasan mitarki idan na ajiye ban wanke ba har na tafi kina mun surutu" "Kasan haka muke da Abbansu tun be iya wanke wanke har seda ya saba yanzu da sun bata kwanuka zece a wanke se kaji Zee tana ayi wanke wanke kafin Mama ta fara mita" suka saka dariya gaba daya. "Ina yaran nema naji gidan shiru" ya tambayeta bayan daya zauna tace "Kamal da Asiya sun tafi Tahfiz, Nuradden kuma yana Jalingo kasan Hajiya da Didi kuma qanwarsa ta kai su gidan kitso jiya wai sunyi dare suka kwana a gidanta inaga se anjima zata dawo dasu" "Wai har yanzu Nuraddeen be dawo ku haqura da yaron nan kawai ku bar musu shi mana" Khalil ya fada tayi murmushi tace "nima haka nace jiya da yake zancen ze kira Hajiyar ya gaya mata an dade da komawa makaranta nace ai sun sani ka barshi kawai yayi zamansa nan da can ai duk daya ne toh kasan shi da qulafucin Yaya bedai ce komai ba kuma be kirata ba yana dai mitar wai Nura nada wasa baya sonkaratu idan ba an takura masa ba acan in ya samu sake sangarcewa zeyi" "Haka dai ze haqura ya barshi da ya samu kakannin ma masu so su riqe jikan, nan Hajiya data dauko Inteen kina ganin yanda suka qare" Khalil ya fada suka fashe da dariya gaba daya. Seda suka lafa Jalila ta kalle shi tace "Toh ya ake ciki ranar mun fara magana a waya?" Tattara hankalinsa yayi akanta yace "Wato wata yarinya ce muka hadu da ita kin gane, harga Allah tana burgeni kuma ina sonta amma kuma ni banyi tunanin nan kusa zata kawo maganar muyi aure ko wani abu ba kuma ita bala'in sona takeyi, nidai in taqaice miki magana yanzu kinsan dai matsayin da nake ciki a yanzu bazance zanyi aure ba saboda kowa seya tambayeni dalili idan kika duba aurena shekara biyu kwata kwata ni kuma bani da wani dalili me qarfi dazance gashi ya saka zanyi aure". Shiru Jalila tayi tana kallonsa har ya kai aya kafin taja numfashi tace "Ita yarinyar yaushe kuka hadu, kuma tsahon wane lokaci kuke tare?" "Bamu wani dade ba wata uku zuwa hudu kenan da haduwarmu lokacin da naje aiki Lagos din nan, dukda dai mun taba haduwa a nan Kano amma dai Officially mu fara magana da ita yanzu za'ayi 3 months" Khalil ya bata amsa tayi shiru tana kallonsa, so takeyi tace masa lokacin da Umaimah taqi binsa Lagos kenan kuma ta tambayeshi wace irin alaqa ce tsakaninsu dukda bata zargin qanin nata amma tasan abinda Umaiman tayi masa yana iya sakawa shedan ya zugashi ya fada abinda ba halinsa ba. Itama ta samu labarin ne a bakin Khalifa kuma ya roqeta akan dan Allah karta gayawa Kowa dan Yaya Khalil yaja masa kunne kawai ya kasa hadiye maganar ne yasa ya gaya mata dan ita ana sirri da ita ba irin su Yaya Jamila faransai bace. "Kinyi shiru kina kallona kamar wanda nayi miki qarya" Khalil ya fada se tayi murmushi tace "So nake na auna soyayyar da kakeyi mata da irin wadda na gani a idonka sanda kake gaya mun ka hadu da Umaimah" "Babu hadi Jalila babu macen da zata kamo qafar Umaimah a zuciyata" Khalil yayi saurin tareta a zuciyarta tace "Ta gano lagon ka shiyasa take garaka kamar kwallo a fili kuwa seta gyara zamanta tace "Toh tanada wannan matsayin ya akayi har idonka ya iya hange hange ka samo wata ka fara so, kuma a yanda kake jaddada soyayyar nan tata ace a ayan shekarun nan zaka mata kishiya Khalil? Idan har da gaske ka daukeni yar uwar da zamu kashe mu rufe ka gaya mun gaskiyar meye damuwarka, meye dalilinka na son qara aure? Ni kuma zanyi maka hukunci bisa adalci in sha Allah dan bazan so ka tauye kanka ba haka itama Umaimah bazan bi bayanka kayi mata rashin Adalci idan har ya zamana son ranka ne kawai". Shiru Khalil yayi yana nanawa maganarta a zuciyarsa, yanada yaqinin Jalila zata riqe masa sirri idan ya gaya mata amma yana tsoron ta farayiwa Umaimah wani kallo na daban a matsayin me musgunawa dan uwanta, yasan zata qullaceta dan Jalilan nason duk abinda yake so tana kuma qin abinda yake bata masa. "Kayi shiru dan qanina ko da akwai matsala ne" ta fada cikin tsokana ya dago ya harareta tayi dariya tace "Sarkin son girma duk tsiyarka dai minti biyar ba wasa bace" dole yayi murmushin shima ta sake cewa "Yawwa ina jinka kayi magana mu samu mu san ta inda zamu kamo bakin zaren maganar nan" "Kina ji Jalila ina son Umaimah kuma bani da wata matsala da ita, damuwata guda daya ce kawai yanayin aikina da bana zama guri daya a koda yaushe ana turani garuruwa nayi ayyuka kuma ina yin kwanaki wani lokacin ma satittika ni kuma ina da sha'awar duk ina zani na tafi da Matata, matsalar anan ita kuma Umaimah bata son tafiya. Duk sanda wata tafiya ta taso se rayukan mu sun baci kafin ta bini, kinga last tafiyar da nayi Lagos har na gama zamana na dawo bataje ba acan nema na hadu da Hadiza dan a lokacin fushin da nake ciki na yanke shawarar aure kawai zan qara na auro wadda ko bangon duniya nace zanje zata bini" Yaci gaba da bata labarin yanda ya hadu da Hadiza da irin soyayyar fa sukayi har zuwa matsayin da suke yanzu akai na zancen turowa da tayi masa. Ya rufe da cewa "Banaso haqqinta ya kamani dan dagaske yarinyar tana so na ni kuma bansan ya zanyi ba yanzu. Tun bayan dawowata na tuntubi Hajiya da maganar dan naji ta bakinta tayi futufutu tace babu wannan maganar ba yanzu ba har gaba babu ita. Toh ni maganar Hajiya ma da sauqi nasan idan na lallabata tana iya yarda, Umaimah nada bala'in kishi irin wanda bakiyi tunani ba, idan zancen auran nan ya fito na tabbata babu sauran zaman lafiya tsakanin mu". "Hmmmm" Jalila taja dogon numfashi tareda sauke taguminda tayi tana kallon Khalil tace "Ni har na rasa ta ina zanfara ma, idan na fahimceka abinda yasa ka fara kula Sabuwarka saboda rashin Umaimah a kusa ne bari na fara da wannan bangaren in har kana ganin cewar Umaimah bazata haqura ta ringa binka duk inda zakaje ba kana da hujjar da zaka qara aure kuma duk wanda ka gayawa dalilinka baze hanaka ba kodan gudun fadawa halaka. Amma idan shawara kake nema se nace maka qarin aure ba shine mafita ba ka zauna da ita kuyi magana ta fahimta ka nuna mata buqatarka da abinda bijirewa hakan ze iya janyowa idan har bata gyara ba daga nan kana iya daukar mataki na gaba sannan ita wannan Hadiza kace kowa sunanta ba son ta kakeyi ba, Umaimah ta riga ta siye filin a ganina ka saurareta ne kawai a lokacin saboda fushin Umaimah inda dagaske ka gantan kake sonta zuciyarka bazata kawo maka wani tunani ba balle har kaji shayin tunkarar kowa da maganar auranta. Kuma koda ace ka aureta be zama lallai ka iyayin adalci a tsakaninsu ba, idan auran kake so dagaske ka bari ka samu wadda soyayyarta tayi takara data Umaimah a zuciyarka idan ba haka ba yanda kake Son matar nan kake tsoronta duk wadda ta shigo gidanka bayan ita wahala kawai zata sha". "Kema bakya goyon bayan maganar kenan?" Khalil ya tambayeta fuska babu walwa kafin tayi magana yaci gaba da cewa "Ni wallahi tsoron hakkinta ya kamani nakeyi na san soyayya nasan zafinta, bakiga irin Kukan da takeyimun ba jiya tana nanata tana sona naji tausayinta sosai" "Tausayinta kakeyi ba Son ta ba Khalil, idan kuwa hakane ka barta kayi mata Addu'a Allah ya bata wanda ya fika dan bata da gurbi a zuciyarka Umaimah ta gine duka filayen sedai idan rusau za'ayi" Jalila ta fada cikin tsokana a zuciyarta tana sake auna maganar Khalil din, ita dai a iya tata Basirar abinda ta gani kenan, ba son hadiza yakeyi ba tausayinta yake kuma fushin Umaimah ne ya saka shi harya fara kulata, ko a yanzun bata raba daya biyu bata masa rai tayi shiyasa har yake tunanin yayi auran. Tattaunawa suka cigaba dayi akan Abubuwan da suka shafesu har suka gangara batun gidansu daze siya da yanda yake so yayi dashi, be bar gidan ba se gurin qarfe uku na rana shima saboda Mansur ya kirashi yana so su hadu ya tafi bayan ya cikata da Alkhairin dayaje mata dashi tanata godiya, suna son dan uwan nasu saboda yanda yake sonsu. Maganar da sukayi da Jalila ta saka ya qara ja baya da Hadiza kuma ya yarda dagasken ba son ta yakeyi ba tausayine da kuma huce takaici da yaso yayi da ita amma dukda haka yana tausaya mata, kullum cikin rarrashinta yake da gaya mata cewar ta fawwalawa Allah idan hat ya qaddara zasuyi aure zasuyi a sanda yaso. Data matsa masa akan Yayanta yace yana son ganinsa ranar ya haqura yaje, be boye masa komai ba ya gaya masa uzurinshi ya kuma fahimce shi yayi musu fatan Alkhairi idan Hadiza matarsa ce Allah ya tabbatar, bayan ya gama da Yayan ya turo masa ita sukayi magana, kamar ze zubda Hawayen tausayinta saboda yanda duk ta rame dalilin damuwar da ta saka kanta a ciki. Haquri ya bata tateda lallashi, yace mata baze ce ta jirashi ba, amma idan da rabon aure a tsakaninsu yana fatan Allah ya matso musu dashi kusa sannan ya roqeta da suci gaba da gaisawa idan tana ganin babu matsala tace zatayi tunani haka suka rabu rabuwar da yake ganin sunyi ta kenan shida ita. Ciwon kai da jirin da suka matsawa Umaimah ya saka dole sukaje Asibiti wata ranar Litinin, bayan likitan yayi mata yan tambayoyi ya auna jininta ya rubuta mata magunguna akan taje tasha idan bata samu afuwa ba su sake komawa. A hanya Khalil ya ringa mata fadan rashin bacci da wuni da takeyi akan waya dan hatta idonta jini ya kwanta shiyasa likitan be kawo tunanin kowanne ciwo ba yace rashin bacci ne ta ringa samun isashshenhutu suna tafe ta tunzura baki gaba saboda fadan da yake mata kai tsaye gidan su ya kaita, idan da Umaimah tasan can ze ajiye ta yasan bazata yarda ba dan tunda ta gudo kamar yanda Anty ta fada bata sake komawa ba. A tsaitsaye suka gaisa yayiwa Mama bayanin bata da lafiya daga Asibiti suke, ya qarasa da cewa "Dan Allah Mama ki saka mata ido ta samu tayi bacci karta zauna danne dannen waya" "Uhm abin nata har ya kai ya saka mata ciwo kenan ko, jiyan nan naji Salman yana maganar tsakar dare tayi masa magana akan yaje zata aike shi seda Safe yaga saqon ya duba lokaci yake cewa Ashe Umaimah bata dena kaiwa dare tana chatting ba toh Allah ya shirya" tayi masa fatan Alkhairi ya wuce Umaimah dai tunda ta shige daki tayi luf, da mama ta tashi yi mata tsiya wayar gaba daya ta kwace, Mu'ayyad daman suna shiga yara suka dauke shi dan haka tana cin abinci tasha magungunan tana nan zaune shiru Mama nata shige da ficenta kota kanta bata bi ba baccin dole ya dauketa saboda magungunan data sha. Da suka koma gida kuwa yasha mita yayi mata banza dan kanta tayi shiru, doka ya kafa mata ta bacci qarfe goma kuma ta kashe wayarta ta bashi. Yanda ya hade fuska yana gaya mata dokar dole ta amsa a lokacin dan yanzu lallabashi takeyi bata so nan kusa ace an sake samun wata matsalar musamman da take da buqata a gurinsa so take a kwana biyu komai yayi daidai ta nemi abinda take so. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 38 Hotunane su fi guda Ashirin nashi da Hadiza a gurare daban daban da suke haduwa. Ba hotunan ne suka tayar masa da hankali ba, aa yanayin daukarsu ne da ko kusa ko alama besan a lokacin da akayi hakan ba dan yawancin hotunan sun nunashi ne rungume da Hadizan ko kuma tana kwance a jikinsa. Video dayayi zargin an dauke su a ranar nan shine na qarshe, wata irin faduwar gaba ta ziyarceshi lokacin da ya kunna vice yana kallo, tabbas ya riqe Hadiza a jikinsa saboda gudun karta fadi ya sakata a mota sannan ya ranqwafa kanta yana mata magana amma a yaushe har ya sumbaceta dan shine abinda yake gani a video qarara gashinan yana Kissing Hadizan baki da baki. "Innalillahi wa'innq ilaihi raji'un" ya fada a fili yana miqewa tsaye, wacece ko wanene wannan? Me suke nema a gurinsa da suke neman wargaza masa rayuwa tayi masa sharri ta zubar masa da mutunchi a idon masu ganin girmansa dan wannan ya zarce yaji tsoron Umaimah ta gani, idan duniya taga wadannan hotunan me zatayi tunani akansa saboda dukkansu an daukesu ne a cikin mutane kuma yake aikata hakan me za'ayi zargin yana yi idan ya kebe inda babu me ganinsa se Allah?. Qarar wayarsa ce alamar shigowar saqo ta katseshi ya zabura ya duba, "Nasan zuwa yanzu kaga saqona, shin ka shirya magana dani ko kuwa na turasu inda dolenka ka magantu idan sun isa?" Abinda aka rubuta a saqon kenan yana gama karantawa be jira komai ba ya dannan kiran layin. Qofar Office dinsa yaje ya rufe dan a halin da yake ciki yana da buqatar kadaici ko ze samu ya warware abinda yake ciki. "Nasan dole zaka kira ai dan bazaka so Matarka tayi katari da wadannan Hotunan ba, Uhm Hajiya Umaimah iyayen kishi, ko yaya zata kaya idan tasan mijinta yana neman mata a waje?"  Aka fada bayan da aka daga wayar kafin yayi magana taci gaba da cewa "Malam Khalil, buqatata ba wata me wahala bace amincewarka kawai nake nema amma fa idan ka sauqaqawa kanka" "Khausar" ya fada cikin wani sauti me nuna bacin rai da kuma tashin hankalin da yake ciki seta kwashe da dariya tace "Ya akayi kayi saurin gane nice? Koda yake wannan bashi da amfani, yanzu ka shirya muyi magana ko na qara maka lokaci ka sake kallon hotunan da kyau kayi tunanin abinda zan iya aikatawa dasu?" "Khausar mekike tunanin kinyi? Meye wannan me kike nema a gurina da har zakiyi mun irin haka?" Khalil ya fada cikin tsawa kamar yana gabanta se tace "Aa fa ka denayi mun tsawa Malam me nayi maka?" "Me kikayi mun kike tambaya na ma? Wadannan hotunan a ina kika same su yaushe aka dauke su?" Khalil ya sake jefa mata wata tambayar, Khausar taja qaramin tsaki tace "Lokacin da kuke fita yawon shaqatawarku da Hadiza ni kuma na saka wanda yake bibiyar mun dukka sahunku yana daukar mun hotunana" se yayi saurin katseta da cewa "Qarya kikeyi wadannan hotunan ba gaskiya bane, babu ko guda daya da yake ainihin yanda aka dauke shi dan ban taba riqe Hadiza kona taba jikinta cikin sanayya ta ba" "Wannan kuma matarka da sauran mutane zakayiwa bayani idan na watsasu bani ba, ni daman abinda yasa na kiraka na zata zamu samu fahimta ne cikin sauqi amma naga alamar cikamun kunne da ihu kawai zakayi dan haka na barka lafiya ka kuma kuka da kanka duk abinda ya biyo baya" Khausar ta fada tana qoqarin kashe wayar ya dakatar da ita cikin wata murya yace "Me kike da buqata?" "Yawwa now you are talking like a smart Man amma da se wani surutu kawai kakeyi" Khausar ta fada kafin taci gaba da cewa "Da farko inabuqatar ka turamin da 1M a account dina kudin bata lokacina da kudin aikin yaron da na saka yake daukan mun hotunanku, sannan idan kayi wannan se muyi magana kuma akan buqata ta ta gaba" tana gama fadin haka ta kashe wayar ba tareda ta jira amsarsa ba, qarar shigowar Message ya sakashi rufe bakinsa daya bude tsabar mamakin Khausar, account number ta turo masa kuwa tana sake jaddada masa ya tura sannan ya kirata su qarasa magana. Tissue yaja ya goge zufar data tsatstsafo masa a goshi gaba daya ma ya rasa tunanin me zeyi yanzu kenan Khausar Blackmailing nasa take so tayi ta ringa tatsar sa kudi akan laifin da ne aikata ba amma me yasa zatayi masa haka? A zatonsa Aminiyar Hadiza ce me yasa zatayi musu haka dan wannan abin bashi kadai ta shafa ba harda Hadizan wannan tunanin da yayi ya sakashi saurin daukar wayar ya shiga kiran Hadiza sedai tun daga yanayin muryarta jikinsa ya qarasa yin sanyi. "Ta turamun nima ta kuma fada mun wasu banzayen sharudanta idan ba haka ba zata turawa Mama da Yaya hotunan" Hadiza ta fada lokacin da ya gaya mata saqon Khausar daya samu. "Amma me yasa zatayi haka Hadiza daman Khausar ba Aminiyarki bace me yasa zata ci amanarki ta nemi saka mu a tashin hankali?" Khalil ya fada murya a sanyaye se Hadiza ta saki kukan da take riqewa tana cewa "Daman Mama tace tana zargin ka gama dani shiyasa ka gudu kaqi aurena. Bansan waya dasawa Mama zargina a zuciyarta ba ada duk inda zanje Mama bata damuwa ta yarda dani ita da kanta tana fada amma haka kawai komai ya chanza. Ta kai ta kawo har tana fada mun da bakinta cewar tasan duk Barikin da nakeyi nake fakewa da sunan aiki, tun abin yana damuna nayi kuka har ya zaman mun jiki sedai kullum ina addu'a Allah ya wanke ni ya kuma kawo min Miji nayi aure sannan ina Addu'ar Allah ya tonawa duk wanda ya shiga tsakanina da mahaifiyata Asiri se yanzu na gane Ashe Khausar ce, me nayi mata? Yanzu idan ta fitar da hotunan nan da sauran da tace tana dasu da wane baki zan kare kaina a gurin Mama?" Hadiza ta qarasa tana fashewa da wani kuka me tsuma rai. Gaba daya kansa ya qara zafi ga damuwar da yake ciki ga kukan Hadizan, cikin muryar rarrashi yake mata magana "Kiyi shiru Allah shine shaidar mu bamuyi duk abinda yake a cikin hoton ba, kuma qarya takeyi da tace miki tana da wasu kawai so takeyi ta firgitaki. Ki kwantar da hankalinki yanzu zan kai report gurin yan sanda akan tana so ta bata mana suna idan anje can ta fadi gaskiyar yanda ta hada hotunan qarya". "Aa Khalil ni nasan wacece Khausar hatsabibiyace ta gaske duk abinda tace zatayi zatayin, kuma ba ita kadai ta shirya wannan abin ba, ko da ace ka saka an kama ta ragowar Abokananta zasu iya aikata abinda bamuyi tsammani ba. Ta taba bani labarin wani abokinta da yake aikin computer, a lokacin wata yarinya aka saka yayiwa sharri ya dora fuskarta akan wani nude video suka turawa Mijin da zata aura qarshe haka suka lalata auran ita kuma suka kassara mata rayuwa" Hadiza ta sake fada cikin kuka kafin taci gaba da cewa "Dan Allah Khalil ka bita a hankali, duk abinda tace kayi idan da hali kayi mata mu samu mu tsira da Mutunchinmu daga ni har kai" "Miliyan daya fa tace na tura mata yanzu" Khalil ya katseta se tayi saurin cewa "Miliyan daya, Anya Khausar tana da hankali?" "Koma menene idan na tura mata yanzu kinsan gaba abinda zata nema a gurina? Zata ci gaba da blackmailing nawane kuma hakan bashine yake bada tabbacin bazata fitar da hotunan ba kamar yanda tace. Nidai bazanyi falling ma tricks finta ba, inada Aboki DSS ne zan kirashi na gaya masa su zasu san abinda zasuyi akan maganar" "Aa Khalil dan Allah kabi a hankali bana son abinda ze janyo daga ni har kai mu shiga matsala" Hadiza ta sake fada cikin kuka da tsoron abinda ze iya biyo baya. Tayi kuka tayi nadamar sanin Khausar a rayuwarta. Tsakaninta da ita Alkhairi ne bata san me ya saka ta aikata mata ahakan ba. "Ki dena kuka kuma ki kwanatar da hankalinki in sha Allahu babu abinda ze faru kinji" Khalil ya fada cikin rarrashi, dakyar ya samu ta yi shiru da kukan, ya kuma tabbatar mata duk abinda ake ciki ze kirata ya gaya mata daga nan sukayi sallama. Message ne ya shigo wayar ya dauka ya duba. "Ba DSS ba Allah yasa FBI zaka kaini ka tabbata in har ka kai maganar nan gurin hukuma wallahi sena saki abinda ze sakaka nadama har Qarshen rayuwarka kuma ka turamun da Kudin ina jiranka" abinda ta turo masa kenan ya share zufar data keto masa yana salati a zuciyarsa. Wato tayi Hijacking wayar sa kota Hadiza ne da har take iya sauraron abinda suke fada tabbas Khausar Hatsabibiya ce kamar yanda Hadiza ta fada. Rasa mafita yayi a lokacin ya kuma rasa shawarar wa ze nema. Gaba daya haka ya qarasa wunin ranar cikin tashin hankali da neman mafita, sanda ya koma gida kasa shiga yayi ya ajiye motar a qofar gidan. Gani yakeyi kamar Umaimah ta rigada taga hotunan nan be san kuma wane kalar tashin hankalin ze fuskanta a gurinta ba. Yana nan zaune a motar har aka kira sallar Magrib seya kulleta ya wuce masallaci a can din ma ya bata fin minti talatin kafin yayi qarfin halin miqewa ya tafi gidan. A waje ya bar motar dan ya yankr shawarar zuwa gurin Mansur ne bashida Aminin daya fishi ya tabbatar kuma ze bashi shawarar abinda ya kamata yayi. Da sallama ciki ciki ya shiga palour, Umaimah na kwance a qasa Mu'ayyad na gefe can ta zube masa kayan wasansa yana ta surutai irin na yara. Yunqurawa tayi dakyar ta tashi zaune tana kallonsa. Idan ba idonsa bane se yaga ta zabge idanunta duk sun shige ciki kamar wadda ta wuni tana kuka nan da nan gabansa ya yanke ya fadi kodai Khausar ta tura mata da hotunan amma kuman idan haka ne yasan abinda zatayi baze iya hasasoshi ba. Dakyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da tayi masa yana qara kallon fuskarta yace "Lafiya meya sameki naga fuskarki ta fada?" "Banajin dadi wuni nayi da ciwon kai da zazzabi" ta bashi amsa tana yatsina fuska dan dagaske bata da lafiyar, yana fita kamar an aiko zazzabi da ciwon kan suka rufeta ba dan Hauwa ba da bata san ya zatayi ba. "Sannu, bari na chanza kaya se muje Asibiti tunda likitan yace idan bakiji sauqi ba mu koma" ya fada kafin ya daga Mu'ayyad da se sannan ya lura dashi ya taho da gudu suka shige dakinsa. Wayarsa ya kunna masa ya shiga wanka, yana shiga yaji an kira sallah se yayi danasanin ya tsaya yayi isha gaba daya kafin ya shigo. A dakin yayi sallar sa yana jin yanda cikinsa ke qara alamar neman abinci amma bashida nutsuwar da ze iya saka wani abu a cikinsa. Sanda ya fito har sannan tana kwance a inda ya barta, shi ya taimaka mata ta saka hijabi yanajin yanda jikinta yayi zafi alamar zazzabin ya kulle gidan suka tafi Asibiti. Har sukaje babu Wanda yayi magana a cikinsu, Khalil tunanin mafita yakeyi a zuciyarsa dan ko kafin su fito yaga Text din Khausar akan tana jiransa, idan ya kai gobe be tura mata ba ya kuka da kansa, ita kuwa Umaimah abinda takeji a jikinta shiya isheta. Sun isa Asibitin bayan yan tambayoyi likita ya rubuta mata teat yace suje Lab. Jininta suka dauka bayan yan mintina Aka basu Result, tundaga qofar Lab din ta fasa masa kuka dan ita aka bawa ta bude ganin abinda yake ciki yasakata Kukan Khalil kuwa yi yayi tamkar baya gurin dan damuwar da yake ciki tafi wannan shirmen banzan da take nema tazo masa dashi. Sanda suka koma gurin likita kwanciya yace tayi a gado ya janyo computer scanning ya shiga dubata sega ciki ya tabbata kamar yanda Test ya nuna har na sati 13 ai nan Umaimah ta sake fasa wani kukan ciki wata uku ita tana me har haka ta faru bata sani ba. Ta gama sakan kancewa tunda bata Period bazata dauki ciki ba, shiyasa tace ma bazata Yaye Mu'ayyad ba seya shekara biyu, yanzu shekara daya da wata biyu ace tana da ciki har na wata uku ina zata saka kanta. Kuka takeyi dagaske gaba daya ma ta hanashi fahimtar abinda likita yake gaya masa qarshe yace suje kawai idan sun nutsu sa dawo suji koma menene dan ya fahimci shima Khalil din hankalinsa a rabe yake. A hanya kuwa seda yayi mata ihu kafin ya samu tayi shiru, suna isa gida a waje ya tsayar da motar yace ta shiga zeje ya dawo tana fita ya juya da Mu'ayyad dan karya bar matashi yasan ba kulawa dashi zatayi ba. Gidan Mansur ya wuce kai tsaye, seda yaje qofar gidan sannan ya kira shi akan gashi a waje ya fito yana cewa "Kai haka ake zuwa gidan mutane da ina Asibiti kuma fa" sedai ganin fuskar Khalil din ya saka yayi shiru suka shiga gidan yana riqe da Mu'ayyad, matarsa Umma tazo suka gaisa ta karbe shi tana tambayar Ina mamansa ta bari ya fito dashi da darennan yace mata bata jin dadi seta wuce dashi ciki ganin kamar yana jin yunwa ga bacci kuma. "Bayero ya ake ciki ne, ka ganka kuwa kamar wanda Ya samu saqon Kidnappers duk ka hargitse fuskarka tayi zuru zuru ko Madam din ce abin nata ya motsa?" Mansur ya fada yana kallonsa. Hannu biyu ya saka ya dafe kansa da yake ji kamar ze tsage saboda ciwo kafin ya dago idonsa da sukayi Jaa ya kalli Mansur yace "Mansur wannan matsalar tafi qarfinta Umaimah, wata yarinya ce take nema ta sakani a damuwa na rasa abinda take nema a gurina" "Yarinya kuma, yaushe ka fara neman Mata bansani ba" Mansur ya fada yana gyara zama se Khalil ya jefa masa wata harara kafin ya dauki wayarsa ya bude hotunan ya miqa masa. Karba yayi yana dubawa ya gama ya dago fuskarsa da alamar tambaya se ya karbi wayar ya sake bude Messages din da ta tura masa ya bashi. Dariya Mansur yayi yace "She must be Mad,1M akan wadannan yan hotunan me akayi a ciki da har zata nemi 1M akan su" yayi tsaki ya miqa masa wayar yana cewa "Muje daga waje kasan ita kuma wannan labe take yiwa mutane yanzu karkayi mamaki ta kasa kunne taje me za'a fada" suka miqe suka koma harabar gidan. "Yanzu wannan abin ne ya saka hankalinka ya tashi har haka ko kuma akwai wani abu tsakaninku da ita bayan wannan da baka so ta bayyana" Mansur ya fada yana kallonsa, se yaja qaramin tsaki yace "Ta hoton daban, wadda ta turomun da Threat din daban" "Ban gane ba?" Mansur ya fada yana gyara zama A taqaice Khalil yayi masa bayanin Hadiza da kuma Khausar din, ya qarasa yana cewa "Aswear Man none of this is true, hadawa tayi kuma ita Hadizan ta gaya mun Khausar nada connection da all those computer literates daman sun saba yin irin wadannan abubuwan shiyasa take jin tsoro kar tayi wani abin". Numfashi Mansur yaja kafin yace "Ni ina ganin abin nan me sauqi ne, kamar yanda ka fada ita ce ta fara showing interest akan ka kai kuma you went to her friend baka tunanin haushin wannan abin nr yasa tayi muku haka?" "Toh ai yanzu itama qawar tata bama tare, kuma ko a lokacin da muke tare muna haduwa harda ita bata taba nuna wani abu akan haka ba" Khalil yayi saurin Katse shi se Mansur yace "Hakan bashi yake nufi babu komai a ranta ba lokaci ta jira gashi yanzu kun gani,kana ji ko ka kwantar da hankalinka kayi tunani zaka iya warware komai. Tayi ne saboda haushin bata same ka ba kaje kana Neman qawarta you can turn the table ka koma mata ka nuna yanzu ita kake so ko daman can itan kake so ka damu ku daidai ta shikenan fa". Kallon baka san me kakeyi ba Khalil yayi masa kafin yace "Saboda a shirin film muke ko yaya, kasan yanzu duk abinda zan gaya mata bazata yarda ba dan tasan kawai saboda na yaudareta ne. Ni yanzu shawarar dana yanke zan yi magana da Hafiz Sale zuwa da safe, su zasu iya nemota su saka ta goge kuma suyi mana iyaka da ita" "Wane Hafiz Sale?" "Hafiz speaking" "Oh, wai da securities kake so ka hada ta, think about it Khalil it will just worsen the situation ko ka manta abinda qawarta ta gaya maka ne kasan bazata yi abin nan ita kadai ba dole tana da backup, nidai a shawara kabi a hankali ka shawo kanta kuyi magana sannan idan taqi cooperating se ka dauki mataki akai" Mansur ya sake fada. Iska Khalil yaja kafin yace "Zan gwada amma idan kuma na tsaya lallabata tayi mun shirme fa, think about what will happen idan Umaimah taga hotunan nan" "Oh kai Umaimah ce kadai matsalar ka ma toh Allah ya rufa asiri, nidai shawarar da zan baka kenan kabi komai a hankali ka kirata kuyi magana ko ka nemeta ku hadu, and about the ransom she requested ka tura mata da wani abu ka gaya mata baka da kudi tayi haquri zuwa end of the month then you settle her" Mansur ya sake fada, akan haka suka rabu ya shiga ciki ya dakko masa Mu'ayyad da har yayi bacci abinsa se a sannan suka lura da lokaci sha daya da rabi ta wuce. Kafin ya isa gida Sha biyu tayi ya samu ya shiga da mota ya kasheta sannan ya dauki yaron suka shiga. Da kukanta ya fara cin karo tana kwance kusada bakin qofar tana kuka qasa qasa alamar tayi ta gaji ne, kansa ya sara masa ya tsallaketa ya wuce seda yaje ya kwantar da Mu'ayyad kafin ya dawo dukda zuciyarsa na ayyana masa ya rabu da ita idan ta gajo dan kanta ta tashi amma ya kasa. Dakinta ya shiga ya hada ruwa me zafi kafin ya dawo inda take ya dagata ba tareda yayi mata magana ba, zazzabin jikinta ya sauka ya wuceda ita bandakin tana kuka da komai yayi mata wanka tas ya nadota a towel ya kwantar da ita akan gado. Kitchen ya wuce ya hado shayi me kauri a kofuna biyu ya debo Cake dan shima yunwar yakeji sosai, a gaba ya sakata seda ta shanye ya hade fuska yana shan nasa ya kuma qi bata damar ta kawo masa wata maganar banza har suka gama ya dakko mata riga ta saka suka wuce dakinsa ta kwanta bayan tasha maganin ciwon kai cikin sa'a tana kwanciya bacci yayi gabada ita. Juyi ya ringayi a gadon kawai ya rasa me yake masa dadi, gurin qarfe uku Mu'ayyad ya farka yana kukan neman nono dole ya tashi ya hada masa madara a feeder ya bashi dan lokacin sosai jikinta ya sake daukan zafi har rawar dari takeyi ya samu ya lallabashi ya koma bacci kafin ya drbo ruwa ya goge mata jikinta itama zafin yadan ragu. Ganin baze iya bacci ha ya saka shi tashi yayiwo alwala ya shiga jera salloli yana roqon Allah daya bashi mafita akan abinda ya tunkaro shi, bayi aune ba seji yayi ana kiran Sallar Asuba. Wanka ya sakeyi ya canza jallabiyar jikinsa ya fita masallaci se a sannan ya fara jin baccin na neman daukarsa dakyar ya dawo gida ya tarar Umaimahta farka har tayi sallah kuma da alama jikin nata da sauqi dan har ta hadawa Mu'ayyad da shima ya farka Shayi a feeder yana sha, a taqaice suka gaisa ya tambayeta jikinta tace da sauqi, kafin ta kawo wata maganar ya shige daki ya kullo qofar harda saka muqulli dan jin kansa yakeyi tamkar ze fashr tsabar damuwa da rashin bacci. Yana kwanciya ko minti biyar beyi ba baccin ya kwashe shi gaba daya ma ya manta da cewar ranar aiki ce be tashi farkawa ba se qarfe Sha daya harda rabi shima qarar wayarsa da ya manta ya ajiyeta a saman kansa ce ta tashe shi. "Wato ka dauka da wasa nakeyi ko shiyasa kayi banza da maganar da mumayi, daman na gaya maka idan ka tsallake jiya ka kuka da kanka da duk abinda ze biyo baya dan haka ka saurara ka gani" Khausar ta fada bayaj ya daga wayar babu shiri ya miqe tsaune yana goge ido dan baccin da yayi ya taimaka masa ya manta da duk wata damuwar da yake ciki" Cikin taraddadin abinda ka iya faruwa yace "I'm sorry Khausar tun jiyan bana jin dadi ne ko office ban fita ba yanzu ma haka bacci nakeyi kiranki ne ya tayar dani, kiyi haquri ki bani dama muyi magana a waya ko ki fada mun inda kike so mu hadu nayi miki alqawari zanyi duk abinda kike so kinji". Cikin wani irin lallashi yayi mata maganar dashi kansa seda ya gama yake mamaki, shiru tayi kamar ba zatayi magana ba har ya cire rai se ji yayi tace "Shikenan babu damuwa ka samu kasha magani idan kaji sauqi a yau ka kirani se na gaya maka inda zamu hadu idan babu dama ka bari se gobe Allah ya qara afuwa" Qara narkewa yayi yace mata "Amin nagode kwarai, se na kirakin" daga nan ya kashe wayar yana tuna maganar Mansur da yace ya lallabata zero iya shawo kanta gashi kuwa ya gani ashe duk iskancin nata ma na qarya ne. Wanka ya farayi yana jin cikinsa kamar anyi yasa babu komai a ciki, qananan kaya marasa nauyi ya saka ya zauna a gefen gado ya shiga kiran layin Sakatariyarsa Hajjo ta daga suka gaisa tana tambayarsa lafiya be shigo ba kp Site ya tafi yace mata baya jin dadi ta rubuta report duk abinda aka turo office din wanda zata iya tayi attending wanda bazata iya ba idan softcopy ne ta tura masa ta Email sukayi sallama. Umaimah na kwance akan Tiles ya fito, rigar baccin data kwana da ita ce jikinta fuskarta tayi qozai qozai alamar kuka ga kuma rashin jin dadin jikintada batayi, kallonta yayi yace "Me yasa kika kwanta a qasa cikin sanyi ki tashi ki koma kan Carpet mana idan kwanciyar qasan kike so" "Nafi jin dadin nan" ta bashi amsa tana goge hawaye se yayi kamar be gani ba ya wuce kitchen dan yasan bata girka komai ba. Ruwan zafi ya dafa, ya soya musu kwai ya hado komai har sannan tana kwance a qasan ya ajiye. "Ki tashi kici abinci" ya fada yana kallo ta ta toshe hancinta ta tashi zaune tana cewa "Banason qarnin kwan" tana rufe bako ta fara yunqurin Amai yayi saurin qarasawa ya dagata suka wuce bandaki tayi Aman, kuka ta fasa masa tana cewa "Bana son cikin Khalil dan Allah ka rabani dashi wallahi ban shirya sake haihuwa yanzu ba". Be kulata ba ya saketa ta sake kwanciya a qasan ya wuce gurin abincinsa ya shiga karyawa, kukanta ya dameshi amma yaqi kallon sashin da take, kalmar bata son ciki na qonamasa rai amma yayi shiru dan abinda yake gabansa yanzu yafi qarfin maganar ciki shiyasa ya qyaketa tayi kukan harta gaji dan kanta ta kwanta se kuma tausayinta ya kamashi. Kanta ya tsugunna yana tambayarta me zata ci tace babu komai daya matsa ta sake fasa kuka akan ita ya kaita gida yace toh ta tashi ta shirya se a sannan ya lura da Beji Motsin Mu'ayyad ba zuciyarsa ta bashi yana gidan da take kaishi kenan, Shiya taimaka mata tayi wankan tana sake nanata masa bata son cikin har sannan be tanka mata ba. Seda ta shirya sannan yace ta kira a dawo da yaron babu dadewa Hauwa ta kawo shi da kwanon Alala da tace ta siyo mata a bakin titi, shi taci shi kuma yayi masa wanka ya shirya shi ya hada mata jakar kayansa da duk abinda yasan tana sakawa kafin suka fita ya kaita gidansu. Bayan ya ajiyeta kai tsaye ya shiga kiran layin Khausar, sunyi da ita zasu hadu a Zazu nan da awa daya yana kashewa ya nemo number Hadiza har ze kira ya tuna da jiya be san ta yanda akayi Khausar tasan abinda suka tattauna ba seya fasa. Zuciyarsa ce ta ringa bashi qarfin guiwar Ya kira Hafiz dole shima baze rasa abinda ze iyayi akai ba koda ace ya yaudareta bashida tabbacin ze iya sakawa ta goge kuma idan ma yayi nasara shidai ba ci gaba da Mu'amala zeyi da ita ba kenan idan ya barta zata iya sake hada wasu kenan. Wayar Hafiz din ya kira, seda sukayi wa juna tsiyar rashin zumunchi kafin yace masa yanaso su hadu dan Allah idan babu damuwa kai tsaye Hafiz ya amsa yace ya same shi a Office yanzu babu abinda yakeyi. Da awa dayar data bashi kafin su hadu ya je gurin Hafiz suka tattauna, be boye masa komai ba ya bashi hotunan harda number wayarta duk ya karba yace kwantar da hankalinsa zeyi bincike akanta ya tabbatar da abinda ta fada idan gaskiya ne sannan su san ta inda zasu bullo mata kuma yaje su hadun hakan ma ze saka su sake samun wasu Informations akanta. Ya rufe da cewa "Yanzu sabuwar hanyar da mata suka samu kenan ta blackmailing, ranaku kadan ne zakaga baa kawo case gurin nan na kaga babban mutum da mutunchinsa amma yazo da qarar wata yarinta tana masa barazana da hotuna ko wani abu nasa da be kamata duniya ta sani ba, Allah dai ya rufa asiri amma karka damu wannan ba wata matsala bace. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 39 Ya samu Khausar a inda tace su hadu, ya rigata isa dan haka ya samu Table ya zauna sannan yayi order abin sha gaba daya hankalinsa a rabe yake yana ta raba ido da dube duben ko wani na daukarsa a hoto irin na wancan ranar. Seda yayi kusan minti Talatin kafin ta iso taci uwar kwalliya kamar me zuwa biki se yauqi da karairaya takeyi tana zuwa kusa dashi ta tafi kamar zata rungume shi ya kauce yana yaqen dole qasan ransa kuwa ji yakeyi kamar ya shaqeta a gurin kowa ya huta. "Sannu kaga har fuskarka ta fada kuwa daman baka da lafiya ne?" Ta fada bayan data zauna. Murmushin dole yayi yace "Nafi sati banajin dadi daman, jiya da yau nema na dan samu sauqi" ya yanko qaryar dan karta dauka barazanarta ce ta firgitashi harya rame dare daya seta katse shi da cewa "Ayya sannu Allah ya qara afuwa, kace kana so muyi magana gani nazo amma karka batamun lokaci dan daga gurin aiki nake na dauki excuse". "Bari a kawo miki abinci" ya fada yana yafito masu karban Order Abinci dayazo wucewa ta kusa dasu, Yar takadda ya bata, ta zabi abinda take so ya tafi kawo mata se Ya kalleta yanaMarairaicewa kamar wani qaramin yaro yana kallonta cikin ido yace "Na kasa gane kan saqunan da kika aiko mun dasu jiya ne, yanzu tsakanina dake idan kina da buqatar wani abu har se kinyi mun barazana bazaki iya zuwa kaitsaye ki gaya mun buqatarki ba?" Ya fada yana qara tsareta da idonsa, dadi yaji ganin tayi qasa da nata idon alamar kallon nasa yana tasiri a kanta, daman ya sani ko Umaimah data fita jidali bata iya hada ido dashi idan tsiyatakunta suka motsa sedai ta kalli wani gurin tayi masa badai ido cikin ido ba. Shirun da Khausar tayi ya bashi damar ci gaba da magana yace "Kuma abin naki harda Sharri Khausar kinje kin hada wasu hotuna kamar wasan yara, waya gaya miki Hadiza har takai ajin da zan iya hada jiki da ita? Ni daman qaddara ce ma tasaka na fara kulata, kuma daga baya dana fuskanci ba Aji na bace na rabu da ita, ko ranar qarshe da kika saka aka dauke mu wannan Video ita ta damu se mun hadu saboda na dena daga wayarta ta dameni shine naje na sameta, ai kin sani tunda kuna tare a lokacin kuma na jaddada mata babu ni babu ita ta nemi wani shine har ta nemi ta tayar mun da Aljanu dalilin daya saka na kamata na sakata a mota kenan har aka dauki wannan video kuma tun ranar bamu sake magana da ita ba se jiya". Dadi Khausar taji na maganganun daya fada, dukda tayi zargin basa tareda Hadizan a yanzu amma bata tabbatar ba saboda ta dena gaya mata tsakaninta da Khalil din bata san me ya saka ba shiyasa ta yanke shawarar rabasu ta wannan hanyar Ashema basa tare data sani ai kawai zura kanta zatayi base ta tsaya wani yi masa barazana ba ga asarar kudi da tayi dan hada mata wadannan hotunan da akayi kusan dubu dari biyar ta biya banda kashedin da suka mata akan idan ta kwabe karta kuskura ta sako su a ciki in ba haka ba se sun hada mata Wanda ya fishi muni sun baza a duniya. Duk fadar tana da wasu da suka fi wannan ko kuma ta ajiye wani copy barazana kawai tayiwa Khalil din da Hadiza ta kuma samu yanda take so dan Hadizan ta tsorata dagaske ko a jiya seda ta tura mata dubu dari biyu data sake tura mata saqo "Ni fa daman tun Asali ke na fara so banma san ya akayi na koma kanta ba abin kamar tayi mun Asiri kuma daya karye na rabu da ita kawai naji tsoron idan na dawo miki bazaki karbeni ba saboda Aminiyarki ce shi yasa na haqura daku gaba daya" Khalil ya sake sakin wani dialogue din ganin ta sakawa guri daya ido tana faman doka murmushi ai kuwa tayi saurin kallonsa ya kashe mata ido daya ya sake cewa "Eh mana kema ai kina sona ko tunda gashi kin kasa haqura kina so ki kwatoni daga gurin Hadiza ta qarfin tuwo" yayi maganar cikin sigar tsokana yana kallonta ya rausayar dakai irin taji kunyar nan har sannan batayi magana ba sedai murmushi dan haka ya sake cewa "Kinyi shiru baki ce komai ba ko baki son nawa ne? Kinyi shiru kiyi magana" ya sake fada yana leqa fuskarta data sunkuyar qasa, seta dago tana hade fuskarta daga murmushin da takeyi tace "Ina sonka mana kaima ka sani kuma ni daman saboda na sameka ya saka nayi abinda nayi. Amma dukda haka bazan yarda da dadin bakin ka ba dan jiyan nan na gama jin kana gaya mata zaka kaini gurin DSS waya sani ko yanzun ma kayi report? To dai koma yayane na gaya maka kuma zan maimaita idan ka saka an kamani kamar ka qarawa wuta fetur ne dan na raba copys na hotunan nan dama wasu da baku san dasu ga ga Qawayena da abokanaina. Ko yanzu da zan taho seda na gaya musu inda zanje kuma dakai zan hadu idan wani abu ya sameni karsu jira komai su sake su a Internet". 'Dum' qirjinsa ya buga a zuciyarsa yace "An yanka ta tashi" amma afili qoqari yayi ya daidaita nutsuwarsa yace "Haba dai kina wata magana kuma ko jiyan da kikaji na fada mata haka nayi ne dan na kwantar mata da hankali bawai dagaske nakeyi ba dan haka ki kwantar da hankalinki infact ni koda ace kin fitar da hotunan da kike fada babu abinda ze shafeni saboda ni namiji ne kin sani me hausawa suke cewa ai duk abinda mukayi Ado ne kawai dai ita nake jin tausayi a matsayinta na Mace" "Oh haka ma kace baka tsoron Abokanan huldarka su gani ko yan uwanka? Bama wannan ba matarka da take da bala'in kishi idan ta gani me kake tunanin ze faru?" Khausar ta fada fuskarta ta kasa boye mamakin jin yace wai babu abinda ze dame shi ita duk kanta ya kulle ma. Jiya fa ya rikice a waya amma yanzu ya ringa nuna abin be dame shi ba kuma har kan fuskarsa bata ga alamar qarya a abinda yake fada ba, maganar sace ta katse mata tunani yace "A ina kika san Matata da har kika san tana da Kishi?" Seta harareshi qasa qasa kafin ta danna wayarta ta nemo number Umaimah data kwafa ranar daya nuna musu hotunanta a waya ta juya masa wayar tana cewa "Ko ba wannan ce Number taba? Na tabbata idan taga hotunan nan seka gwammace kida da karatu dan kaida kwanciyar hankali har abada". Dariyar da shikansa ya rasa ta mecece yayi kafin cikin tsananin dauriya daga rudun ganin number Umaimah a wayarta yace "Toh ko zaki gwada aika mata yanzu ko gani? Kinga naga alamar bazamu daidaita ni abinda nake miki magana akai daban ke kuma kina wani shirme daban, kina zaton zakiyi blackmailing dina ne kiringa mun barazana da wata Matata ko wani abu to bari kiji ki koma ki sake shiri dan wannan bazeyi aiki ba, maganar soyayyar ma kuma na fasa tunda naga ba ita bace a gabanki na barki kije kici gaba da shirmen da kike ganin dabara ce a gurinki" ya fada yana miqewa tsaye zuciyarsa na wani tsalle akan fargabar abinda ze biyo bayan hargagin nasa amma ga mamakinsa se yaga itama ta miqe tsaye tana kallonsa tace "Ta yaya zan yarda gaskiya kake fada mun ba yaudarata kakeyi ba?" Ajiyar zuciya ya sauke a boye kafin shima ya kalleta yace "Kibi abinda zuciyarki tafi yarda akai". Seta koma ta zauna ganin haka shima yaja kujerarsa ya zauna yana Addu'a a zuciyarsa, shiru sukayi na wani lokaci kafin ta bude baki tace "Ni ba soyayya ko bata lokaci nake so muyi ba Sonka nakeyi da aure dan haka idan ka shirya belin kanka a shirye nake ko a gobe ka tura a nema maka aurena ni kuma nayi maka Alqawarin zan goge duk wani hoto da video na gurina da gurin wadanda na bawa Ajiya" "Well, ni idan zan aureki zan aureki ne a ra'ayin qashin kaina badan wata barazanarki ba, sannan idan dan wannan nema ai kin rigada kin lalata abin tunda har kin turawa wasu a matsayin Ajiya ko? Ta yaya zan yarda suma basu nunawa wasu ba kinga kenan idan ina gudun fitarsu ne magana ta qare kin rigada kin fitar dasu tunda bake kadai kika mallake su ba" Khalil ya fada yana tsareta da ido, shikansa yayi mamakin yanda ya iya dakewa yake magana ba tareda ta gano shi ba. Duburburcewa tayi cikin in ina tace "Toh ai toh nasan wadanda na bawan zasu boye ba zasu nunawa kowa ba, kuma ma ni da kaina na boye su kansu basu san menene a ciki ba" "Amma dazu fa kikace kin gaya musu zaki hadu dani idan wani abu ya sameki nine kinga kenan sun san abinda yake faruwa ko?" Ya sake jefa mata wata tambayar yana kallonta kamar wani Jami'in tsaro seta hade rai ta miqe tana cewa "Saboda kaga na tsaya muna magana shine har kake nema ka titsiyeni ka raina mun hankali ko? Toh shikenan kaje zakaga abinda ze biyo baya, zakazo kana dana sani da bashida amfani tunda har ka kasa amfani da damar dana baka. Kuma wallahi kaci sa'a ina sonka ne amma a yanda na quduri daidaita rayuwar Hadiza dan saboda kaine na rangwanta mata abin ya tsaya iya haka amma tunda bakaga abinda nayi maka ba, zaka gwammaci kida da karatu" ta dauki jakarta da wayarta dake ajiye zata juya shima ya miqe yana cewa "Na gaya miki ni bana tsoron ki yada koma menene amma ki sani kin dabawa kanki wuqa kuma ita ramuwar gayya akace tafi ta gayya zafi. Idan kin sabayiwa mutane haka kina cin banza ki tabbatar wannan karon kin tabo tsuliyar Dodo dan Khausar idan bakiyi wasa ba seba batar dake" yana gama gaya mata haka ya juya ya wuceta fuuu kamar iska ya barta tsaye tana binsa da kallo daidai sannan. Khausar Sosai tsoron yanayin da Khalil din yayi magana ya kamata daman kuma ta fuskanci kamar ya gano duk wani shirinta amma yanzu yaya zatayi? Batar da ita fa yace zeyi ta tabbatar da kuma ze iya tunda komai kudi ne yake aiki a yanzu. Komawa tayi ta zauna ta dauki wayarta dake ajiye ta shiga kiran qawarta Shema wadda da ita suka qulla duk wani shiri ita ce ma ta hada ta da wanda yayi mata hotunan da Video "Ke kamarfa gayen nan ya gama gane shiri na gaba daya fa ya nuna baya jin tsoron ma na saki hotunan ba kamar jiya da nake gaya miki ba" Khausar ta fada bayan da Shema ta daga wayar, tsaki Sheman tayi tace "Kefa banzace daman ai dole ze nuna miki be damu ba saboda ki karaya ki fasa abinda zakiyi Allah sa dai bake ce ma kikaje kikayi abinda ya gano ki ba" "Ko daya wallahi nuna mun yayi shi be damu ba ko jiyan ma saboda Hadiza ne kuma ma ashe basa tare yanzu harfa yana maganar daman yana sona kuma ze aureni to fa daga na tambayeshi ya zaayi na gane ba yaudarata yake so yayi ba shine kuma yayi fushi har yana cewa Ze iya batar dani" Khausar ta sake fada se Shema ta buga tsaki me qarfi tace "Ai daman ke banza ce wai wa ma yace ki hadu dashi daga fara abu jiya har zaki bari ku hadu yau dole ma ya gane bada gaske kike ba, yanzu ya turo miki da kudin da kika nema jiya ne? Seda nace miki idan be turo ba kaitsaye ki aikawa da Matarsa shine ze tabbatar bada wasa kike na amma jiki na rawa daga yace kizo kuyi magana kinje seki shirya tarar abinda ze biyo baya tunda daman idan baka iya kama barawo ba ai shi se ya kamaka" "Toh yanzu ya zanyi Shema, ni fa batarwar nan daya ce ta daga mun hankali ke kika bani labarin qawarki da haka ta fau da ita fa" Khausar ta sake fada kamar zatayi kuka daga can bangaren Shema tace "Minal ba shekara biyu kenan babu labarinta se tashin zancen, iyayenta ma da suka gaji da nema Addu'a kawai aka mata sun saddaqar ta mutu amma ita ai babban mutum tayiwa, daman a lokacin seda muka hanata wata qawarta tace mata babu komai itama ta tabayi ta samu kudi sasai dan daman su badan a aure su bane kawai Kudi suke karba a gurin mutanen, aiko randa ta tura masa da Video washe gari ta fita aka dauketa a hanya shikenan qila se a lahira". Cikin Khausar ne ya bada qarara quuu jin wai a hanya aka dauketa tace "Karfa nima yanzu kiji babu ni ko kuma yasa a tareni a kwace mun waya kin san komai yana ciki kawai bari in jira kizo mu tafi tare ne kinji dan Allah" "Ai seda nace ki tura a wayata saboda tsaro ke ga me wayo kika ce Aa, Ai se ki zauna barazana yayi miki kuma kin rufta Allah yasa ma ba labewa yayi yaga yanda zakiyi ba kinga kuwa idan haka ne kina ruwa wallahi ya gano lagonki, ina yaga kudinda ze biya a batar dake banda ma ke sauna ce da har zaki wani tashi hankalinki? Dallah ki kamo hanya ki taho musan yanda zamu gyara shirmen da kikayi" tana gama fada ta kashe wayar. Waigawa Khausar tayi iya hangenta bata ga Khalil ba babu kuma ma wanda hankalinsa yake kanta, Muryar wanda ya kawo musu abinci taji daga sama yana cewa "Hajiya kin gama ne zamu gyara gurin wasu zasu zauna" bata iya magana ba ta daga masa kai kawai, ka garindaukar kwanukan ya ture mata wayarta data ajiye kan Table din cikin sauri ya dauko ya miqa mata yana bata haquri ta harareshi kafin ta karba ta jefa a jaka, jiki babu kwari ta fice daga gurin, Adaidaita ta tare ta hau, bata samu nutsuwar baza'a tareta a sace ta ko a kwace mata waya ba seda ta ganta a Office dinsu. Tana zuwa ta tararda Mata biyu da suka zo shigar da qara, Ogarsu tace taji dasu dan haka suka shiga ciki ta ajiye jakarta ta dauko wayar da suke recording ta kuna ta fara tambayar matar. Mijinta ne yake dukanta shine data gaji yau da yazo dukan nata ta kwada masa Tabarya ta gudo, dayar da sukazo tare qawarta ce kuma daman ita ta bata shawarar ta nemi madoki a kusa dik randa ya sake yunqurin dukanta ta rama toh kuma an samu kuskure tana rafka masa tada ya fadi a gun bata da tabbacin yana da rai ko ya mutu shine ta gudu qawar tace suje Human right ta shigar da qarar yanda koma menene ya faru abin ze zo da sauqi. Seda ta gama nadar komai taje ta kaiwa Ogar tayi mata bayani se tace ta tura mata Matan. Kujerar Hadiza da  babu kowa a kai ta kalla tayi murmushi a fili tace "Tukunnama, se kin rasa komai da kike taqama dashi a duniya ai duk wanda yaci tuwo dani miya yasha". Tunawa da barnar da tayi kuma ya sakata miqewa da sauri ta suri jakarta da sauran tarkacenta ta fice ba tareda tayiwa kowa sallama ba kaitsaye gidan su Shema ta wuce dan tana so su tattauna. Khalil Seda ya tabbatar da Khausar tabar gurin dan akan idonsa ta hau Napep kafin ya fito daga gurin daya boye ya koma ciki, kiran Hafiz ne ya shigo masa ya daga daga can bangaren Hafiz yace "Yaya, an dace kuwa?" "Yanzu nake komawa bata dade da barin gurin ba" Khalil ya bashi Amsa. Gurin yaron daya kai musu Abinci ya qarasa yana zuwa ya dauko masa waya ya miqa masa ya karba yana murmushi tareda yi masa godiya. Kudin da shi kansa be san nawa bane ya zaro daga Aljihunsa ya bashi kafin ya juya ya hau motarsa ya bar gurin a zuciyarsa yana fatan Allah yasa qarshen matsalar kenan. Jin kansa yakeyi kamar an dora masa dutse saboda Nauyi da ciwon da yakeyi masa, haka kawai yarinya na neman ta dora Masa Hawan jini babu gaira babu dalili. Daga gurin kai tsaye office dinsu Hafiz ya koma, ya miqa masa wayar yana cewa "Gata, amma Ya akayi kayi wannan tunanin?" Hafiz ya karbi wayar yana murmushi yace "Na gaya maka wannan ai qaramin aiki ne, da nayi niyar na tura ne a karba a hannunta se kuma kawai naga ma ga hanya me sauqi kuma gashi an dace, kaga qarin Sa'a wayar tata ma babu Security akai amma dai wannan wawiyar yarinya ce ma ita haka ake Blackmailing din babu wani shiru babu matakan tsaro" Bincike ya shigayi a wayar bayan ya saka Sim din a flight mood yanda kira baze shigo ba. Messages ya shiga, chat din dake sama ya bude ganin message din da aka turo mata 'Bani dasu kuma karki kuskura ki sake nemana idan ba so kike ranki ya baci ba' lokacin da aka turo ya duba yaga suna tareda Khalil ma se ya bude Saqon ya fara bin sauran saqonnin da sukayi musaya da me Number shine wanda yayi mata aikin hada hoton kuma a nan ciki ya samu tabbacin ita kadai ya turawa kamar yanda ya fada shima ya goge saboda haka ne qa'idar aikinsa baya ajiye hoto ko video bayanya hada maka saboda tsaro. Seda suka bincike wayar tas daga suka samu tabbacin mutum biyu ta turawa da Hoton daga Khalil se Hadiza se kuma mutum daya da tayi saving da 'Best' ita kuma da ita suka shirya komai dan ita ta bata shawarar aikata hakan ma ita a son ta Akan Nude Video za'a dora fuskokinsu Khausar din tace Aa. Bayan sun gama binciken nan take Hafiz yayi formating memoryn wayar gaba daya ya kuma bi duk inda yasan za'a iyayin back up ya goge shima. Miqawa Khalil wayar yayi yana cewa "Case close hankalinka ya kwanta ka maida qibarka kaga yanda fuskarka ta zabge kuwa kamar wanda ya shekara yana jinya ni gaba daya ma ka bani kunya se kace na Namiji ba haba mana" "Kai bazaka gane ba, yanzu dai tunda Allahya taqaita shikenan amma idanda ace Umaimah ta kai ga ganin hotunan nan, inaga sedai na dawo nan office din ku bani mafaka" dariya sukayi gabadaya Hafiz yace "Mata mata wato na ko ina dai haka suke da kishinnan, ni fa ina ganin babu Wanda yakai tawa yar darun" Khalil yayi saurin tare shi da cewa "Na tabbata ko yatsanta gidanabata kama ba kawai Allah yaci gaba da rufa mana Asiri" "Amin, yanzu ya za'ayi da wannan wayar" Hafiz ya fada, Khalil ya daga kafada yace "May be idanna samu wandaze kai mata a mayar mata da abarta ko" "Haba dai taci banza ma kenan ai an musanya maya wayarta, wannan 12 pro ce ma aka bata pro max ai kaje da ita kawai ka rage kudinka" Hafiz ya fada, Khalil ya girgiza kai yace "Ko nawa na kashe bazanji komai ba tunda na samu biyan buqata" cewar Khalil se Hafiz ya maida wayar kan Table dinsa yana cewa "Kaga Allah yaci dani daga sama na samu waya" "Shikenan kuwa ka samu ka riqe kawai" Khalil ya fada yana miqewa, kiran La'asar da akayi ya saka dole ya jira yayi sallah a gurin kafin ya tafi. Seda ya hau hanya ya tuna da Umaimah daya kai gida tun  safiya kuma ko shiga ciki beyi ba yace seya dawo lallai wani tashin hankalin ya girmi wani yanzu kuma se yazo yaji da nata tunda ya gama da wannan. Hadiza ya kira ya shaida mata halin da ake ciki, Hamdala ta ringayi tana qarawa tace "Nagodewa Allah nagode maka Khalil shiyasa bazan taba dena kukan rasa jajirtaccen Namiji irinka ba, ina kuma Addu'a idan da rabo a tsakanin mu Allah ya gaggauto dashi kusa" Da 'Amin' ya amsa mata kafin sukayi sallama ya kashe wayar tausayinta yana tsarga masa. Gidan hajiya ya tafi ta sa shi gaba da tambayar meya same shi taga ya rame haka yace mata babu komai aiki ne, a can yaci Abincin rana dabe iya ci a waje ba. Seda yayi sallar Isha sannanya tafi dauko su Umaimah yana tunanin yanda zasu qare da ita kuma. Khausar Tana isa gidan su Shema a tsaitsaye ta gaida Mamansu ta shige dakin Sheman tana cewa "Qawata Na shiga uku, yanzu ya za'ayi?" "Kiyi dagaske har Mama tajiyo ta san me kika qulla zaki wani shigo tun daga waje kina wa mutane terere" Shema dake kan gado ta fada, se Khausar ta rufe baki da hannunta tace "Au wlh kaina ne ya dauki zafi na manta" ta zauna kusada ita tana sake cewa "Ki bani mafita me ya kamata nayi yanzu kafin abubuwa su cakude mun?" "Mafita daya ce da zata saka ya shiga taitayinsa kawai ki turawa Matarsa" Shema tta fada ba tareda ta kalleta ba Khausar tace "Matarsa? Kina ganin hakan dabara ce nafa gaya miki yanda yake son matar nan tasa da kuma irin haukan kishinta da na samu labari idan na tura mata baza'a samu matsala ba?" A hasale Shema ta kalleta tace "Toh ke ina ruwanki kece a cikin hoton ko kuma ke zatayiwa haukan da kike jin tsoro? Kinga ni idan ba zaki ringayin abinda na gaya miki ba kije can ki qarata da yawarki karki kuma nemana" "Haba Qawata abin be kai haka ba ai kawai dai ina jin tsoron kar wani abu ya faru nice sila yaqi aurena a qarshe kuma dai kinga abinda nake yiwa fafutuka kenan" Khausar din ta fada jiki a sanyaye se Shema ta sake galla mata harara tace "Toh ai seki zauna kinga kinyi asarar kudinki da lokacinki a banza da wofi, kuma ki tashi ki fita karki sake kirana wallahi duk abinda ya faru" "Aa baza'ayi haka ba yanzu nan zan tura mata bari kiga" ta fada tana zaro wayarta daga jaka. Budewa tayi sabanin hotonta dake kan wallpaper se taga babu daman tun sanda Waiter dazu ya miqo mata ta lura amma saurin da takeyi ya saka bata mayar da hankali ba. WhatsApp ta shiga nema bata gani ba, se a sannan hankalinta ya dawo jikinta ta lura da wannan wayar kamar babu komai ma a cikinta. Miqawa Shema wayar tayi tana cewa "Ke tayani dubawa, daidai nake gani ko duk rudewar ce" Shema ta karba ta duba seta kalleta tana cewa "Ya haka wayar babu komai akai? Allah yada ba a garin rawar jiki kika yi Restoring nata ba, ke kamar ma fa babu Sim akai" ta sake fada ganinbabu alamar Network. Wurin kira ta shiga ta loda number ta ta danna yaqi tafiya seta miqa mata tana dariya tace "Tab lallai mutumin nan a shirye yake, ni daman nayi mamakin da ace wai zaku hadu keda bakya aiki da kwakwalwarki kika kwashi jiki kikaje, gashi nan ya nuna miki ya fiki iya wasa chanza miki wayar yayi". Hannu biyu Khausar ta dora akai tana zare ido, se kuma ta tuna da Khalil ya rigata tafiya, "Anya, bashi bane saboda ya rigani tafiya kuma se bayan ya tafin na kiraki" "Toh a ina aka canza miki? Daga gurin se ina kika tsaya?" Shema ta sake tambayarta. Khausar da hankalinta idan yayi miliyan ya tashi tace "Ban tsaya ko ina ba se office kuma ko a can ban fito da wayar ba sannan idan Khalil ne dole zan sani dan tunda muka zauna har ya tafi wayar tana gabana ko tabata beyi ba sedai idan..." "Sesai idan me?" Shema ta fada tana kallonta, "Shine ma wallahi, wani Waiter yazo daukar kwano wayar ta fadi ya miqomun sedai idan shiya musanya mun da tasa" Khausar ta fada kamar zatayi kuka. Dariya Shema tayi tace "Na yarda dai Khausar baki da wayo, haka nan ze chanza miki wayane sedai idan saka shi aka yi gaba daya abin Set up ne kinga ke baki samu biyan buqata ba ya kwace wayar gaba daya, da ace kin ajiye a wani gurin nema da sauqi se ki godewa Allah da ya baki wata kuma kamar ma babbar taki ce kinga Asarar tazo miki da sauqi sorry babe" Ta qarasa tana fashewa da dariya se ganin hawaye tayi sha suna bin fuskar Khausar ta kuwa samu ta ringa tuntsira mata dariya kamar mahaukaciya. "Yanzu duk abinda nayi ya tashi a banza kenan babu biyan buqata se wahakar banza dana sha" Khausar ta fada cikin kuka se Shema ta tsagaita dariyarta tace "Maganin mara jin shawara kenan, ba yanda banyi dake baki samu wani gurin ki ajiye copy kikace Aa, idanma ni baki yarda dani ba nace ki siyi Flash ki saka a ciki duk kikaqa gashi yanzu baki ga tsuntsu baki ga tarko" "Wlh banzan yarda ba zuwa zanyi na gaya masa nasan me yayi ya bani wayata ko na kai qararsa" Khausar din ta fada tana miqewa tsaye se Shema ta dakatar da ita da cewa "Ki tabbata kin shirya tafiya kurkuku dan yanzu na tabbata idan ma qararki zeyi yana da duk wasu hujjoji a hannunsa karki manta wayarki sukutum ce a hannunsa, duk wani sirri ba naki ba har shi wanda ya hada abin yanzu yasan ko waye, bari ma na kira Dini na gaya masa yayi ta kansa a garin wawancinki kin tona muku Asiri" ta fada tana janyo wayarta Khausar ta riqe tana cewa "Karki kirashi dan girman Allah, baki san irin warning dindaya mun akan idan aka samu matsala karna kuskura na sako sunansa ba idan ba haka seya mun ninkin abinda nasa akayi musu. Ki bari zansan yanda zan shawo kan abin dan wlh bazan haqura ba be isa yaci bulus ba". Ajiye wayar tayi tana kallon ta tace "Me kuma zakiyi yanzu bayan duk abinda kike taqama dashi ya goge?" Goge hawayen fuskarta tayi ta janyo jakarta ta zazzage komai a qasa sega Memory ya fado, a wayar Sheman ta sakashi ta bude duka hotunan data aikawa da Dini yayi Editing ne a ciki Shema ta kalleta tace "Amma wace toshewar basira ce ta saka kika iya ajiye wadannan amma baki ajiye masu amfanin ba? Wlh Khausar Dusa ce akan ki yanzu me zakiyi da wadannan hotunan?" "Zasuyi amfani saboda a yanda na samu labarin matarsa tana da bala'in kishi yanda baki tsammani. Tare sukayi Poly da Bilkisu Auwal a gurinta na samu cikakken bayani akanta kuma zan sakw karbo lambarta a gurinta dan nasan bazata rasa ba idan ma bata da ita zata nemo mun kinga kuwa hotunan zasuyi amfani, wlh Khalil seya san ni ya yaudara dan wannan karon bazan bi takansa ba kaitsaye ita zan tun kara" Khausar ta fada tana wani murmushin mugunta. "Kinyi dabara, amma ki bari ba yanzu zaki tura mata ba. Ki bari a dauki lokaci seya gama sakankancewa a qalla nan da wata biyu ko uku a sannan ya manta da abinda ya faru kuma baki neme shi ba, lokaci daya ki kunna masa wuta ki koma gefe kisha kallo" Shema ta fada tanabata hannu suka tafa. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 40 Umaimah Tana shiga dakin Mama ta samu kan kujera ta zube kaman jiqaqqun kayan wanki daman Mu'ayyad tun daga qofar gida Salman ya karbe shi. Mama na daga gefe tana sallar walaha seji tayi Umaiman ta fashe da kuka, gabanta ya yanke ya fadi, surar da take karantawa ta kwace mata se kawai tayi kabbara ta tafi ruku'u. A sujjadarta ta dade tana roqon Allah da koma menene Umaiman tazo dashi ya zama me sauqi ya kuma bata ikon iya dauka dan zuciyarta ta gama ayyana mata an sako Umaiman ne. Koda ta idar tafi minti biyar kafin ta iya tashi ta isa kanta ta tsaya har sannan kuma Umaiman Kuka takeyi tana juyi akan kujerar kamar qaramar yarinya, kallon tsaf tayi mata, a haka dai batayi kalar tashin hankalin da za'ace sako ta akayi ba, ramar da taga tayi a fuska yasa tayi tunanin ko bata da lafiya se ta saki ajiyar zuciya taji sanyi a ranta seta nemi guri ta zauna tana cewa "Lafiyarki Umaimah zaki kwanta kina kuka kamar wata qaramar yarinya meya sameki?" Tashi zaune Umaiman tayi jin muryar Maman ta fada jikinta tana sake fashewa da kukan dayafi na farko, cikin kukan take cewa "Na shiga uku Mama dan Allah ki kirashi kiyi masa magana da kanki qila yaji wallahi bazan iya na bana so". Gaba daya ta jefa Maman a rudani, data furta shiga ukun nan seda taji wani rugugi a kanta amma maganganun da suka biyo kuma suka daure mata kai, zarginta na saki ya wanku sedai idan kuma wata tsiyar ta qullo. Ganin bazata nutsu tayi mata bayani ba se uban kuka takeyi ya sakata rabata da jikinta tana cewa "Ya isa ki dena kukan Naji zan kirashi amma se kin yi mun bayani sosai dan ni ban fahimci abinda kike nufi ba, menene bakya so meye kuma bazaki iya ba? Wani abun Khalil din ya sakaki da bazaki iyayi ba kome?" Hadiyar zuciya ta ringayi tana qoqarin tsayar da kukan dakyar Mama ta bata ruwa me sanyi tasha ta ringa jera ajiyar zuciya ita dai Maman ta zuba mata ido kawai tana kallonta, seda ta gama daidaita kanta kafin dakyar ta bude baki tace "Ciki ne dani fa Mama, kuma na gaya masa bana so ban shirya ba amma ko magana yaqi yayi mun, yi yakeyi kamar ma baya jin me nake fada nidai ki kirashi ki gaya masa da kanki bana son cikin nan bazan iya haifarsa ba" tana gama maganar ta sake fashewa da wani kukan. Hannu biyu Mama ta daga tana kallon gabas tace "Allah kai ka bani ita saboda kasan zan iya, Allah karka barni ni kadai ka kama mun a cikin lamuran Umaimah" tana gama fadar haka ta miqe dan bata san me zata ce mata ba, kai idan ta ci gaba da zama a gurin tsaf zata rufeta da dukan da ze iya sanin cikin jikin nata da take iqirarin bata so, Allah ya shiryi Umaimah kawai yasa ta gane gaskiya kafin lokaci ya qure mata. Dakin ta ta shige ta barta nan palour tana ganshe qar kuka, kiran sunanta da Anty take kwalawa ya saka ta fito, Antyn na tsaye kan Umaimah dake Amai tsabar yanda ta galabaitar da kanta da kuka tana ganin Maman tace "Bakijiyo kakarinta ba? Nifa tun daga tsakar gida na jiyota banma san da zuwanta ba dan na dauka ma Nuratu ce tazo itace me lalura". "Uhm banji ba nika baccine ya fara kwasata, kuma tsabar iskanci duk gidan nan ki rasa a ina zakiyi wa mutane Amai se a cikin palour na, to ki tashi ki gyara gurin wallahi kafin raina ya baci nayi miki abinda ba zakiji dadi ba" Mama ta fada tana kallon Umaimah dake mayar da numfashi se Anty tayi saurin cewa "Haba Mama bakiga halin da take ciki bane kiyi haquri kin fa san yanayin Amai idan ya taho ba'a iya tare shi" "Nata ai na iskanci ne masifarta ce ta janyo shi, wallahi Umamaih kibi duniya a hankali idan ba haka tam" Maman ta sake fada tana juyawa ciki Anty ta bita da kallo gaba daya kanta ya daure da maganar Maman seta juya kan Umaimah dake sabon kuka qasa qasa, 'uhm' ta fada kafin ta kamata ta miqe daga cikin Aman tana cewa "Ki shiga ki gyara jikinki bari na gyara nan" ta shigar da ita dayan spare dakin Mama ita kuma ta fita dakko paker da tsintsiya. A cikin daki Mama kasa zama tayi ta juyo ta dawo palour ganin Anty na kwashe amai yasa ta tambayeta tana ina ta nuna mata dakin da take seta ta wuce ciki kaitsaye daidai sanda Umaiman ta fito bayan ta wanke fuskarta. "Zonan Umaimah" ta fada tana juyawa waje. Dakinta ta koma ta zauna akan gado tana jiranta se gata ta shigo kamar munafuka ta samu can gefe ta rabe kai kace mabaraciya ce. "Ki dawo nan ki zauna magana zamuyi dake" Maman ta fada tana nuna mata gefenta, seda ta daka mata tsawa sannan ta taso bata zauna kan gadon ba ta zauna a qasa, Mama ta hadiye abinda kw taso mata cikin muryar limana tace "Ki fadamun meye matsalarki Umaimah" Cikin rashin fahimta ta kalli Maman, Mama ta sake maimaita mata ta qara da cewa "Ki fada mun idan akwai wata cutarwa da Khalil yakeyi miki a zaman auranku" "Babu komai Mama, ni babu wani abu da yakeyi mun" ta bata amsa tana kallon qasa. "Kin tabbatar babu wani abu a idan da akwai ki gaya mun kinsan dai babu abinda zaki boye mun ko?" "Wallahi Mama babu abinda yakeyi mun, wani ya ce miki anayi mun wani abun ne?" Ta fada cikin sigar tambaya se Maman ta girgiza kai alamar Aa kafin tace "Idan babu cutarwa a zaman ku me yasa kike gudun haihuwa dashi, ko yana da wani mugun hali da bamu sani ba da yasa baki so ki hada zuri'a dashi?" Kamar tace tayi kuka sega hawaye sha sun fara zuba, seta daga mata hannu tace "Ba kuka nace kiyi mun ki bude baki kiyi mun magana kinji koh" "Ni Mama babu abinda yake dashi kawai haihuwar ce yanzu bana so. Gaba daya fa shekarar Mu'ayyad daya da wata biyu kuma ance inda ciki har wata uku fa Mama Kwanika fa kenan ni gaskiya bana so se kace wata Matar qauye kawai ina goyo se a ganni da ciki ai se mutane suyi mun dariya ma..." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta ya sakata yin shirun dole hawayenta kuma suka qara qarfi kamar an kunna Famfo. Nunata Mama tayi da yatsa cikin bacin rai tace "Ai daman idan bakiyi haka ba baki cika tantiriya mara mutunchi ba, yanzu abin naki har ya zarce kan mu mu ababen halitta kin koma kina fito da mahaliccinki ko, ubanki ne yake raba cikin balle kice saboda sanayya ce tasa ya baki? Mata nawane suke neman Allah ya azurtasu da haihuwar, zasu iya sadaukar da komai nasu dan su samu abinda suma zasu kira Ya ko dan su amma ke ubangiji ya zabeki cikin Miliyoyi yayi miki baiwa shine kike kiran bakyaso bazaki iya haifarsa ba ko? Toh karki fasa, kiyi duk yanda kika ga dama da cikin idan Ajalinki ne kinga seki janyo shi kusa, a garin salwantar dashi seki salwantar da taki rayuwar ki bishi ku tafi tare. Kuma idan Ubangiji ya qadarta zuwansa doron qasa ke kinyi kadan ki hana faruwar hakan, kina ji kina gani se ki mutu shi ya rayu shasha sha da baki san ciwon kanki ba. Ba'a haihuwa aka haifeki gashi nan tunda kikazo baki bar mutane sun huta ba kullum da kalar sabon jidalin da zaki tattarowa mutane. Ina jiye miki tsoron duniya Umaimah ki taka a sannu karki ga Allah ya ara miki dama kina yanda kika ga dama lokaci daya idan yaso ze iya canza komai ki dawo abin tausayi dan haka kibi a sannu ki kuma yiwa kanki guzurin Arziqi" Tunda Maman ta fara magana take kuka kamar ranta ze fita, ita sam bata ga aibun abinda tayi ba amma shine har Mama zata ce tana fito na fito da ubangiji ita a wa? Amma a duba mata mana, yanzu da yaro daya ma yaya takeyi kullum cikin yi mata carin tana qazanta bata kula da yaron ake yi ballantana ace ta sake haihuwa nan kusa sun zamar mata jarirai biyu kenan. Kuma da zata ce zata mutu idan Allah yayi Haihuwa ce Ajalinta ai dole ta mutu kuma ko babu komai tayo shahada, duk baqaqen maganganu da bakin da suke mata a wanke mata su ta tafi lahira salin alin abinta. Tsawar da Maman ta katsa mata akan ta fita ta bata guri ce ta dawo da ita hayyacinta ta miqe jiki na rawa ta bar dakin gaba daya ta tafi dakin Anty. A can ta dasa mata rashin mutunchin da bata samu damar yiwa Maman ba tana birgima tana kuka kamar yarinyar goye tana cewa ita dai a rabata da wannan cikin bazata iya ba. Anty dai ganin abin tayi kamar ba'a hayyacinta take ba seta miqe ta tafi dakin Mama ta gaya mata, Umaimah na jiyo muryarsu a tsakar gida Antyn na ce mata tazo ta ga abinda takeyi anya lafiya tana jin motsinsu ta miqe da gudu ta afka dakin Anty ta banko qofa. "Da ki tsaya mana da yau sena sauke miki duk wani iskanci da yake miki yawo akai yar banza me qeqashashshiyar zuciya kamar ta mutanen farko" ta fita ta bar Anty na jimami. Yanzu Nuratu kuma tace me ita da nata cikin ya kai kusan wata shida yanzu idan ma befi ba gashi tana aiki ga hidimar gidan Amma daga ita har Mijinta farinciki suke da qaruwar da suka samu har ta yaye yarta Maman Mijin ta dauke mata ita kafin ta haihu se ita me zaman banza babu cas babu As ita ce zata ce bata son haihuwa kuma ta tabbatar da shi Khalil din baze ce baya so ba. "Kai wannan Umaimah dai jidalinta se Allah" ta fada a fili kafin ta koma tsakar gida taci gaba da ayyukanta. Qarshe wunin daki tayi ranar dan abinci ma kamar wata yar birsin ta window ta saka Salma ta miqa mata shima seda taji Yunwa na neman ta halakata Anty ko duk uzurinta na cikin daki se haqura tayi dasu. Bayan an idar da sallar Magriba Ummu-salma tayi kiranta inji Abbansu. Badan tana jin tsoronsa ba da bazatajeba danta tabbayar da Mama ta gama karanta masa komai. Haka ta zura Hijabin Anty ta fito kanta a qasa ta wuce bangaren Abban. A zaune ta tarar dasu, Abban, Mama, Khalil se Yaya Aminu. Ta samu can gefe daga bakin qofa ta zauna kafin tayi musu kudin goro gaba daya ta gaishe su. "Yaya jikin naki?" Abba ya tambayeta cikin kulawa yana kallonka kafin ma ta amsa Mama tayi hanzarin cewa "Alhaji tambayarta ma kakeyi yaya jikinta kamar ban sanar dakai abinda ta gama yi dazu ba? Nida na zata tana zuwa zaka kwashe mun yar banza da Mari ka tumurmusata idan ka gama Yayanau ya dora nasa" Seya yi murmushi yace "Haba Mamansu ayi mata haquri badan ita ba ko dan abinda yake jikin nata" ya sake juyawa kan Umaimah yace "Umaimah kiyi haquri kinji ko, ita haihuwa ce baiwace da kudi ko wata isa basa bawa mutum Allah ke bayarwa ga wanda yaso a sanda yaso. Karki sake furta bakyason kyautar da Allah yayi miki kije ki raine cikin ki ki haifa kiyi fatan Allah ya baki me Albarka wanda zeji qanki kinji ko?" Seta daga masa kai hawaye nabin fuskarta. Nasiha ya sakeyi musu gaba daya Mama dai ta cika fam qiris take jira ta fashe, haka ya gama ya saka musu Albarka kafin yace su tashi su tafi dare yayi, Umaimah ce ta fara yin gada da sauri ta shige dakin Mama ta kwaso tarkacenta tana fitowa suka ci karo a bakin qofa. Aminu da Khalil na daga gefe suna magana Maman ta kalleta sama da qasa kafin ta juya kansu tace "Ku zama shaida, idan har wani abu ya damu cikin jikin yarinyar nan bisa gangancinta ban yafe mata ba". "Haba Mama haba Mama kalmar tayi tsauri da yawa kiyi haquri ko sauqaqa mata akwai fa qaddara zata iya fadawa akai" Aminu yayi saurin fada yana matsowa gaban Maman, seda ta harari Umaimah da ta daskare a gurin kafin ta sake kallonsa tace "Na fika saninqaddara kuma nasan kuma san halin Umaimah sarai da kafaffiyar zuciyarta tunda ta furta bata so na san tabbas seta salwantar dashi toh taje na kuma fada idan har tayi sanadin cikin nan da kanta ban yafe mata ba" tana gama fada ta shige daki ta barsu a nan Umaimah ta fashe da kuka tana sakin kayan hannunta tace "Tsine mun fa tayi Yaya" Aminu ya make bakinta yace "A ina ta tsine mikin ke da bakinki babu abinda ya sani se janyo masifa, sharadi ta baki idan kuma kika saba kinji abinda ta fada. Ku wuce kuje zan lallabata idan ta huce ke kuma ki kula da abinda ta fada" Tana Kuka Khalil ya kama hannunta suka fita shi gaba daya kansa ma ya rufe ya rasa bakin Magana, wannan tsakanin da Mama tayi mata ya masa dadi dan yasan tashin hankalin da ze sha akan cikin nan se Allah idan da ba'ayi haka ba amma kuma Maganar tata tayi tsauri da yawa. Seda suka shiga mota aka fito da Mu'ayyad da yayi bacci Anty da kanta ta kawo shi, tana dakinta duk budurin da akayi dazu taqi fita ta gaji da lamarin Umaimah kullum babu sauqi se qarin ciwon kai. A cikin gida kuwa bayan Aminu ya bi Mama cikin daki yake ce mata "Haba Mama ya zaki fadi haka bayan kinsan halin Umaimah sarai duk abinda aka hanata shi tafi bada muhimmaci akai tayi, dan Allah ki janye maganarki, kin saka mata Albarka ma ya Allah ya cika ballantana kin fadi akasin haka akanta?" "Aminu duk iskancin da Umaimah takeyi saboda tasan babu abinda za'a mata ne illah fada wanda baji takeyi ba, ai ba mahaukaciya bace ita taje tayi duk yanda taga shine daidai a gurinta nidai na gama magana ta" tana gama fada masa haka ta shige daki ta barshi. Abba ma dai da Aminu yaje ya gaya masa yayi mata magana abi daya ta maimaita masa akan ba zata janye ba, kuma ta qara da in har ta cire cikin babu ita babu ita ta nemi wata uwar daban tunda bata isa ta gaya mata taji ba. A bangaren Umaimah da Khalil dai ranar kwana tayi tana masa kuka shi kuma yana aikin bata haquri dan abin yazo da sauqin da beyi tsammani ba amma fafur taqi bawa Mu'ayyad Nono a daren seda safe daya dameta da kanta kuma ta jashi ta bashi bayan ta gama kuma ta fasa Kukan yanzu idan wani abu ya same shi fa ance idan yaro yasha ciki lalacewa yakeyi, dole ya kwasheta suka koma Asibiti, Likita ya tabbatar mata da babu komai taci gaba da shayar da shi har zuwa sanda taga zata Yaye shi, sannan ya rubuta mata magunguna da zata sha su qara taimaka mata, haka suka dawo gida a zuciyarta idan taji kamar tayi masa maganar cikin se ta tuna da kalaman Mama ta fasa sedai taci kuka ta godewa Allah yanzu kwanika zatayi? Tana zagin masu ciki da goyo ta ringa cewa sun fiya haihuwa kamar Awaki gashi yanzu itama ta zama Akuyar. Dole ya dakko mata Habiba ta dawo gidan da zama dan wannan karon cikin nata me zafin laulayine, kusan kullum cikin jinya take ga quncindata sakawa zuciyarta dan har sannan ba wai ta gama aminta da tana son cikin bane shi yasa duk tabi ta lalace ta fita hayyacinta. Khalil ya samu saqon Khausar da take zarginsa da yi mata zagon qasa ya kwace mata waya, ta sanar masa da cewar yaci nasara akanta wannan lokacin amma ya jirayi abinda ze biyo baya dan bazata saki ba kuma ya aika mata da layukanta. Murmushi kawai yayi sanda yaga saqon ya saka lambar data turo a blacklist, ba ita ba Hadizar kanta yayi blocking number ta dan bayan faruwar wancan abin ta sake neman dawowa rayuwarsa tana kiransa da magiyar ya duba ya sama mata gurbi a rayuwarsa shi kuwa yanzu baya buqatar wata damuwa, shirye shiryen tafiyar da zasuyi ce a gabansa ga yanayin jikin Umaimah da yau lafiya gobe Asibiti duk hankalinsa akanta yake ga aikin ginin daya tattago dan tuni an Baje gidansu gaba daya Hajiya ta koma dakunan da yake ciki shida Khalifa a da an faro aikin ginin daga bangarenta dan so yakeyi idan Allah ya nufa a cikin shekara daya ya kammala ginin harda nasu bangaren su koma can. A cikin wata biyu da suka biyo baya shirin tafiyarsu SouthAfrica ya tashi dan da maganar ta kwanta lokaci daya Babban Manager su ya kirashi akan ya fara shiri nan da sati daya zasu tafi, Kwangila ce suka samu daman kuma se ta nemi ta lalace saboda Manyan companies da suka fi nasu sun nemi su karbe da Allah kuma ya nufa ta tabbata tasu. Kwangila ce babba da suke saka ran jan manyan kudade idan ta kammala. Tafiyarsu da Umaimah bazata yuwu ba saboda yanayin jikinta da yaqi dadi dole ya yanke shawarar ta koma gida kawai dan hakan zefi samun nutsuwa idan yaso zeyi qoqarin yaga yana samun damar zuwa duba su dan a qalla aikin da zasu je ze dauke su kusan wata shida ko sama da haka, duk idan ya gama da bangarensa na zane zane ze iya dawowa, amma dole yana da buqatar tsayawa dan tabbatar da duk abinda ya zana haka aka aiwatar dashi. Yana ta shirin tafiya gaba daya yana cikin damuwar yanda ze tafi yayi watanni ba tareda iyalinsa ba sedai sam bega wata damuwa a tattare da Unaimah ba dan ita murnar komawa gida ma takeyi dan tuntuni taso Mama ta hana, shiyasa ma ta yaye Mu'ayyad, idan ya tafi Habiba zata wuce dashi gidan Hajiya ita kuma ta koma gidansu. "Nikam naga murna kikeyi zan tafi na barku me yasa Umaimah" Khalil ya fada yana kallonta, Umaimah ta muskuta daga kwancen da take, cikin ta ya fito dan yana cikin wata na shida ne ta kalle shi tace "Haba dai wani irin murna kuma" "Eh mana, jifa ko a jikinki sabgogonki kawai kikeyi ni kuwa duk na damu i can't imaging me living for 3 months without you" ya sake fada yana janyo ta jikinsa seta narke masa tana cewa "Daurewa kawai nakeyi nima amma nasan zanyi missing naka sosai" "Toh mu tafi tare kawai, kinga kin Yayae Mu'ayyad zasu tafi gurin Hajiya muyi tafiyarmu kawai hankalina zefi kwanciya" ya fada yana kissing wuyanta ta noqe tana cewa "Nidai Aa, kana kallon dai kullum bani da lafiya tunda na samu cikin nan" "Kiyi addu'a Allah ya raba ki dashi lafiya bana son irin maganganun da kikeyi bana jin dadi idan kina cewa bakya son cikina kamar bakya so nane". Baki ta tunzura gaba tace "Kaima dan baka san wahalar da ake sha bane shiyasa" "Shikenan tunda bakya so daga wannan kin gama ni kuma se na nemo wadda zatayi ta haifamun wasu yaran ba tareda tayi qorafi ba dan ni ina so na tara yara da yawa" Khalil ya fada yana saka kansa a wuyanta da qarfi ta ture shi ta tashi zaune tana harararsa, dariya abin ya bashi har ya kasa riqeta ai kuwa ta fasa masa kuka ta hau dukansa ganin abin nata da gaske ne ya saka ya riqeta yana rada mata magana a kunne daga nan labari ya canza. Da yamma suka fita sukayi shopping sosai na kayayyakin buqatarta da wanda Mu'ayyad ze tafi dasu gidan hajiya, bayan sun gama suka biya gidan Maman Asad, Dambun Nama, kilishi, soyayyar Miya, yaji ja dana daddawa ga cake da cincin haka ta hada mata anyi packaging nasu tsaf yanda bazeyi masa wahalar dauka ba. Ita tayiwa Umaiman maganar ya kamata tayi masa dan a lissafinta ko gishiri batayi tunanin ya kamata ya tafi dashi ba suka karbo kayan a daren ya kai Habiba da Mu'ayyad gidan Hajiya kuma yayi mata sallama dan washe gari zasu tafi qarfe biyu na rana. A daren ta tayashi ya hada kayansa tsaf itama ta hada nata. sunyi kwanan farinciki da soyayya me tsayawa a rai washe gari qarfe goma suka kulle gidan. Khalifa ne yazo ya dauke su, seda ya fara sauketa a gida yayiwa su Mama sallama kafin suka fito ta rako shi seda taga tabbacin tafiyar ze yi sannan zuciyarta ta karaya ta saka masa Kuka, Khalil da daman dauriya kawai yakeyi amma shi yasan ze azabtu ba kadan ba a wannan tafiyar ya rungumeta a jikinsa yana rarrashi ji yake kamar shima yayi kukan ko zeji sanyi a ransa. Seda yayi dagaske tareda yi mata qaryar bayan wata daya ze dawo sannan ya samu ta haqura ya lallabata ya tafi dan Abokanan tafiyarsa suna ta yi masa waya. "Kamar gaske, wanda be san halinki ba Umaimah kin sha dashi" Yaya Nuratu da suka tarar a gidan ta fada, Umaimah ta balla mata harara bata kulata bata shige cikin daki ta kwanta kewar Mijinta na damunta. Bayan wata daya Umaimah na kwance a qasan Dakin Anty duk maganar da taketa faman yi mata akan kwanciyar qasan taqi tashi, tace mata sanyi ze kamata tace ai sanyin take bi daman har ta gaji da magana ta qyaleta. Wayarta ce a hannunta tana dannanwa, basu dade da gama magana da Khalil ba dukda daman kusan kullum cikin waya suke, daya samu sarari z kirata Audio call ko Video call wani yammatanci sukeji haka zasuyi musayar kalaman soyayya masu tsuma zuciya a cewarsa ji yake yi kamar yayi tsuntsuwa ya dawo gida amma babu dama. Saqo a turo mata ta WhatsApp da wata sabuwar number, bata fiya amsa baqin lamba ba tun abinda ya faru tsakaninta da Maman Nihal wanda se daga baya ta samu cikakken bayani ashe ita din Asalinta yar me aikin gidansu Maman Nihal ta gaskiya ce. Sun tashi sa'anni dan haka suke shiri kuma itama tana matsayin me aikin Maman Nihal din ce a haka tayi aure ta tafi tareda Abun saboda sun shaqu, takai ta kawo ko fita qasar waje zatayi har bayan Abu tayi aure idan tana buqatar me kular mata da yara zata kirata haka kuma batayi mata iyaka da komai nata shine har ya bata damar yin basaja da sunanta a gari tana janyo rigima. Fita tayi daga WhatsApp din ba tareda ta bude saqon ba ta tashi dakyar saboda fitsarin da taji ya dameta. Bayan tayi ta dawo ta dauki wayarta data tarar da Missed call biyu akai still number babu suna amma ta kira data tuna akwai wanda Rufaida tace zata hada ta dashi me siyar da kayan Jarirai ko shine ya tura mata da hotuna ta gani. Sallama tayi daga daya bangaren wata mace ta amsa sukayi shiru gaba dayansu kafin cikin jin haushi Umaimah tace "Naga Missed calls na kira kuma anyi shiru wacece?" "Yi haquri baiwar Allah, na tura miki da saqo ne ta WhatsApp naga baki bude ba shi yasa na kiraki, amma kije ki bude idan kinga abinda yake ciki seki kirani muyi magana" matar ta bata amsa daga dayan bagaren kafin ta samu damar magana ta kashe wayar. Shiru tayi tana nazari, sam muryarta batayi mata kama data wanda ta sani ba amma haka nan zuciyarta ta kwadaitu dason ganin saqon menene da har zata kirata suyi magana bayan ta gani. Zeta koma kan Kujera ta zauna dakyau ta shiga WhatsApp din babu bata lokaci ta bude chat din nata hotunan sun rigada sun bude saboda wayar a auto download daman take. Wata irin zabura tayi ta miqe tsaye kai bazakace ciki ne a jikinta daya tasanma wata bakwai ba hannunta har rawa yakeyi tana bin hotunan gaba daya ma ta gagara gane abinda take gani kamar idanunta suna mata gizo haka tabi su daidai tana kallo har zuwa kan Video da shine na qarshe ta kunna take numfashinta ya tsaya na wani lokaci kunnenta yayi mata duuummmm, a dukka sauran hotunan bata gama yarda ba amma a video ta tabbatar da Khalil ne dan bayan fuskarsa ga muryarsa nan yana gayawa wata cewar ze aureta. Bata san wayar ta subuce a hannunta ba seda taji Ummu-salma tana cewa "Yah Umaimah zaki fasa wayarki fa kuma babu screen guard akai" Bata kulata ba tabi wayar ta dauka ta riqe kawai dan ta rasa ta ina zata fara a lokacin, Khalil zata kira ko kuwa seta fara binciko wace wadda ta gaji da zaman duniyarce ta shigo duniyar Mijinta. Kira ne ya shigo ta daga da sauri kafin tayi magana aka ce "Nasan zuwa yanzu kinga saqon dana tura miki ko? Zan tura miki da Address, number waya da duk wani abu da zaki buqata gurin binciko wadda take qoqarin shigowa gidanki. Amma karkiyi gaggawar nunawa Mijinki kinsan abinda yake shiryawa ki bari harse bayan kin gama tattara duk wasu hujjoji da kike da buqata dan kinsan maza yana iya qaryatawa sedai kiji ya shammaceki, na barki lafiya" ta kashe wayar. Kamar wata sokuwa haka Umaimah ta tsaya ta kasa aiwatar da komai seda taji qarar shigowar Message kafin ta bude. Kamar yanda tace kuwa Number wayar ce da Address da duk wani bayani da zata nemi sani akan Hadizan harda Address din gurin aikita. Hijabin da tayi sallah dashi ta figa ta saka, bata damu da lokaci ba dan a lokaci qarfe biyar ta gota tayi waje, seda taje qofar gida suka ci karo da Salman daya shigo yana kallonta yace "Aa ina zakije haka da Hijabi a baibai?" Seta kalli jikinta sannan nema ta tuna da babu ko sisi a hannunta da zatayi kudin mota, kallonsa tayi tace "Key din Motar Abba yana hannunka?" "Eh gashi nan yace naje na shawo masa mai gobe ze dawo ai" Salman ya bata amsa yana daga muqullin seta juya zuwa inda motar take tana cewa "Yawwa muje dan Allah ka kaini in mun dawo zan baka kudi ka qara wani Man" "Ina, wai Asibiti?" Ya tambayeta yana bin bayanta dan abinda zuciyarsa ta ayyana masa kenan bata da lafiya idan ba haka ba me ze sakata fitowa haka a rikice kamar wadda aka koro amma ina mutanen gidan kuma? Tsawar data buga masa ta saka shi bude motar ya suka shiga yana kallo ta, seda ya fita daga layinsu suka dauki hanya kafin tace masa "Na'ibawa zaka kaini" "Na'ibawa kuma Yah Umaimah, ba Jambulo Asibitin da kike zuwa yake ba?" "Zaka kaini ko kuma na sauka na hau Adaidaita" ta katsa masa wata tsawar seya juya kan motar ya tafi inda tace a ransa yana tunanin ina zataje. Address din ta bashi ya ringa dubawa inda basu gane ba suyi tambaya tiryan tiryan se gasu a qofar gidan su Hadiza. "Ka jirani a nan ina zuwa" ta fada kafin ta balle murfin motar ta fita Salman ya rakata da ido harta qarasa inda wasu Samari suke zaune, tambayarsu tayi suka nuna mata gidan bata jira komai ba ta fada babu sallama Maman Hadiza na zaune tsakar gida tana Alwalar sallar Magribar da ake dab da kira se ganin mace tayi a kanta fuska babu alamar Rahama. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 41 "A'uzubillahi" Maman Hadiza ta fada a firgice dan sam bataji shigowarta ba se dagowa tayi taga mace da uban Hijabi a tsaye akanta "Kece shaidaniyar daya kamata a nemi tsari dake" Umaimah ta fada tana jifanta da wani mugun kallo kafin taci gaba da cewa "Koda yake ba gurinki nazo ba, ina ita karuwar yar taki me bin Mazan mutane ita nake nema?" "Baiwar Allah wacece ke, ya zaki shigo mun gida babu neman izini kizo kina zagina?" Maman Hadiza ta fada tana miqewa tsaye, Umaimah ta yatsina fuska tace "Ita sallama anayinta a inda ya kamata ne ba irin gidan nan ba, kinga tsohuwa na gaya miki ba gurinki nazo ba, ki kama kanki ki kiramun wadda nazo gurinta idan ba haka ba na zazzage duk wani buhun rashin mutunchi dana zo dashi akanki". "Amma dai duk daga inda kika fito ke ba yar arziqi bace ba, haka dai gaki nan harda ciki za'a saka miki ran cewar matar aure ce ke ta kirki amma shine zakizo har muhallina ki tarar dani ki zage ni akan me?" Maman Hadiza ta fada, se Umaimah ta gyara tsayuwarta tace "Kece tsohuwar banza da kika haifi karuwa da take yawo kwararo kwararo tana kwartanci da bin mazan mutane, to wallahi a wannan karon ta janyo abinda yafi qarfinta tunda ta bi Khalil, sena wulaqantata yanda ko sunan Namiji idan taji seta gudu daga gurin balle ta sake kallon Mijin wata". Shiru Maman Hadiza tayi idanunta suka ciko da kwallar, cikin raunin murya tace "Ba laifinki bane, Hadiza taja mun da bata fita tana zubar mana da mutunchi da qima ba da baki samu damar zuwa har gida ki ci mun mutunchi ba. Zan roqe ki kiyi haquri ki tafi, nayi miki alqawari babu Hadiza babu Mijinki daga yau..." "Lallai ma, ai wallahi idan kinga na dara qafata daga nan gurin toh mun kece raini nida ita ta banbance Aya da tsakuwa, har zaki yi mun wata fuskar tausayi bayan nasan bakinku daya waya sani ko dake da itan duk sana'ar ku daya kema yawon bin...." Jinta ne ya dauke na wani lokaci kafin ta ankare da abinda ya faru se jin ruwa tayi yana bin hancinta ta saka hannu ta sha fo se ganin jini tayi lokaci daya kuma radadin Marin bazatan da aka falla mata ya ziyarceta ta fasa ihu tayi baya Allah ya taimaka bango ya tareta, Hannu Isma'il ya sake dagawa ze zabga mata wani Marin Maman ta riqe shi tana cewa "A kul Isma'il karka qara tabata, waya aikeka ka daki mace da ciki idan wani abu ya same ta fa?" "Wallahi Mama ba'a haifi wani Da a duniya daya isa ya ratso har cikin gidan mu ya zagi Mahaifiyata ba ko labari naji ba akan ido na ba sena sauke masa haqora ballantana wannan tazo har gabanki tana kiranko da" seya kasa qarasawa idanunsa sun kada sunyi jajir jikinsa har rawa yakeyi saboda tsabar baqin cikin da yakeji. Tundaga qofar gida yake jiyo tashin muryar Umaiman yana shigowa kunnuwansa suka jiyo masa tana kiran Yar uwarsa da Mahaifiyarsa karuwa. "Ki tafi nayi miki Alqawarin Hadiza zata rabu da Mijinki" Maman ta sake fada tana matsawa inda Umaimah ke zunduma ihu tana riqe da hancinta da jini yake zuba. "Wallahi bazan yarda ba, na rantse da Allah seka san ka dakeni se an bimun haqqina a kurkuku zaka qare rayuwarka shegu jinin masifa jinin bala'i yayan Karuwa" Umaimah ta fada cikin Kuka se ya sake zabura zeyi kanta Maman ta shiga tsakani tana cewa "Na haneka Isma'il duk abinda tayi mana Hadiza taja, da bata fita tayi abinda takeyi ba babu wanda ya isa ya zo ya zage mu amma shikenan ita ta ja mana" Maman ta qarasa tana fashewa da kuka "Wallahi idan bata fita daga gidan ba sena Halakata sedai duk abinda za'ayi mun ayi" Isma'il din ya sake zabura Maman ta tare shi tana kuka ta juya kan Umaimah data gama tsorata tace "Ki tafi baiwar Allah ki fita dan Allah kodan cikin jikinki karki sake jaza manata wata Masifar" bata ma qarasa ba Umaimah ta kwashi qafafunta daman tun sanda ya mareta ta cire takalma haka ta fita daga gidan kamar wadda aka harbo Salman na hangota ya taso daga majalisar daya zauna cikin tashin hankali ya shiga tambayarta meya faru. Bata amsa shi ba ta shige mota, seda suka fita daga layin ta sake fashewa da wani kuka cikin ihu tace "Wallahi tallahi bazan yarda ba, qanwarsa tabi mun Miji sannan yazo ya dake ni na rantse da Allah se nayi qararsa se an bi mun haqqina" Kuka takeyi kamar zata qarar da Hawayenta shidai Salman yama rasa abinyi. Fuskarta ta kumbura suntum ga jini faca faca akai, so yake ya tambayeta gida zasu ko Asibiti amma yana tsoron karta huce a kansa dan haka ya kama hanyar gida kawai. Motar su Umaimah na fita daga layin Adaidaita ya dire Hadiza, tun daga soro ta fara jiyo Kukan Mahaifiyarta ga Muryar Yaya Isma'il yana maimaita "kiyi haquri Mama kar kiyi mata baki" Gabanta ya yanke ya fadi, yau kuma wane sabon tashin hankalin Khausar ta hada mata? Take ta tuna da abinda ta gaya mata dazu da safe "Kin dauka na qyaleki ne ko to ba haka bane na barku ne se kun sakan kance kafin na sake kunno muku da wani sabon tashin hankalin. Keda kwanciyar hankali a rayuwarki Hadiza se ranar da na samu cikar burina da kika dade kina wargaza mun, na dade ina dakon wannan lokacin, kuma yanzu na samu wadda zata aiwatar mun da komai ta daidaita rayuwarki hankali kwance". Gabanta ya yanke ya fadi ta shiga karanto duk addu'ar data zo bakinta, kasa shiga gidan tayi ta tsaya a Soron, tsoron abinda zata tarar ya cika mata zuciya amma idan bata shiga ba ina zataje? Zata qara wa kanta wani laifi da zargi a zuciyar Maman ne dan ko a yanzun tunda ta taho cikin taraddadi take dan ta zarta lokacin tasowarta daga aiki saboda wani case da sukaje kashewa a wani gida. Shahada kawai tayi ta shiga gidan da Sallama, Mama da Isma'il suka dago a tare suka kalleta ba tareda sun amsa mata ba. Jiki a sanyaye ta qarasa gabansu ta durqusa kan guiwoyinta bakinta na rawa ta bude da niyyar magana Isma'il ya daka mata wata tsawa yana cewa "Wacece waccen kika janyo tazo taci mutunchin mahaifiyar, Matar waye a cikin Yan iskan da kike bi" ya qarasa a tsawace se tayi saurin ja da baya tana girgiza kanta ya taso daga gaban Maman ya biyota yana cewa "Ba magana nake miki ba Matar waye waccen" "Wallahi ban santa ba Yaya, shigowata kenan banga kowa a qofar gida ba" ta fada a gigice ganin yana nufota fuskarsa babu rahama "Matar Khalil, haka naji ta ambaci sunansa" Mama ta fada daga inda take se Hadiza tayi sak a fili ta maimaita "Khalil kuma, me matarsa zatazo yi a godan nan?" "Ubanki tazoyi, wato da nace ki rabu dashi ba auranki zeyi ba ashe baki barshi ba kuna ci gaba da yawon shashancinku ko? To a kanki zan huce zagin da tazo tayiwa Mahaifiyarmu har cikin gida" Isma'il ya fada kafin ta yi yunqurin tashi ya kai mata qafa ta koma ta zauna tareda fashewa da kuka "Ka barta Isma'il duniya ce idan bataji maganar mu ba zataji tata" Mama ta fada cikin kuka itama seya juya ya fice daga gidan yana huci kamar sabon zaki, da ace zoo sake ganin yarinyar nan seya mata dukan mutuwa sedai duk uban da ze faru ya faru. Hadiza kuwa yana fita ta rarrafa gaban Mama tana cewa "Wallahi Allah shine shaidata Mama ban taba aikata duk abinda kike zargina dashi ba Khausar bata ni takeyi a gurinki ko yanzu ita ta turo wannan matar saboda kafin yanzu ma taso ta hada mana wata qullin Allah yafi qarfinta shine ta sake qulla wani, amma wallahi Mama bana tareda Khalil, na rabu dashi tun sanda kuka umarce ni wallahi sharrin Khausar ne ita take hada komai" "Ki tashi ki bani guri Hadiza tun kafin kisa zuciya ta debeni na furta miki abinda bazaki so ba" Maman ta fada seta miqe tsam ta wuce daki tana ci gaba da kukan da yake nuna quncin da zuciyarta take ciki. Me tayiwa Khausar a rayuwa da take saka mata da haka? A iya saninta tsakaninsu babu komai se Alkhairi, qawarta ce tare duk sukayi fadi tashin rayuwa tundaga secondary har Jami'a zuwa yanzu da suke aiki guri daya a duk tunaninta bata hango wani abu data tabayiwa Khausar da har zata nemi ramuwarsa yanzu ba. Wayarta ta ciro a jaka ta shiga neman layin Khalil amma kamar koda yaushe bata shiga, dabarar yi masa magana a WhatsApp tazo mata se tayi saurin kunna Data, da lambarta da take WhatsApp kan abinda ya shafi aiki tayi masa magana cikin Sa'a yana Online. "Matarka tazo gidan mu yau, me ya kawota?" Ta tura masa ta zauna zaman jira shiru shiru har kusan minti Ashirin be duba ba dukda har sannan yana Online din se kawai ta ajiye wayar jiki a sanyaya ta fita tayo Alwala. Ta dade tana kaiwa Allah kukanta akan ya wanketa a gurin Mama ya kuma tonawa duk me nufinta da sharri Asiri. Umaimah. Hijabin kanta taja ta rufe fuskarta ta shiga gidan, Mama da Anty harda sauran yaran na tsaye cirko cirko a tsakar gida tana shiga Mama tace "Ahaf me na gaya miki yawonta ta tafi gashi nan ta dawo duk kun tada hankulanku a banza" ita dai bata saurara na ta shige daki, kai tsaye bandaki ta shiga ta cire Hijabin jikinta ta tsaya gaban mudubi tana qarewa fuskarta data canza kamanni tashi daya kallo. Kuka ta sake fashewa dashi idonta kansa radadi yakeyi mata musamman bangaren da ya mareta bangaren ya kumbura suntum idon yayi ciki. Seda tasha kukan ta sannan ta kunna ruwa ta fara wanke fuskar, ganin bazata fishsheta ba ya sakata fita ta window ta kwalawa Salma kira tace ta dora mata ruwan wanka ta koma kan Gado ta zauna tana ci gaba da share Hawaye zuciyarta ta ayyana matakai sunfi dubu da zata dauka akan Hadiza da Ahalinta amma duk wanda ta hasaso se taga ai yayi kadan akan abinda suka mata. Ta bibiyar mata Miji kuma taje jin ba'asi wanta ya daketa wallahi basu isa ba. Ummu-salma ta kawo mata Ruwan ta tsaya tana kallonta ta falla mata harara tareda daka mata tsawa ta fita daga dakin da sauri "Munafuka" ta fada tana sakin tsaki kafin ta tashi dakyar ta shige bandakin tayi wanka. Sosai ta gasa jikinta da fuskarta da ruwan ta kuma samu sauqin kumburin amma fa ba duka ba ta fito ta saka doguwar Riga ta tada sallar Magriba da Isha. Ummu-Salma na fita jiki na rawa ta tafi dakin Mama, a can ta tarar da Salman da shima shigowarsa kenan dan ya koma ya shawo Man da dazu be samu zuwa ba ganin Maman suna magana yasa ta juya seta dakatar da ita tace "Salma ya akayi?" "Am bari naje Mama ku gama se na dawo" ta fada tana juyawa saboda hararar da Salman din yake aika mata. Yasan sarai munafunci ta kawo dan ita haka take duk wani tsegumi na gidan zakajishi a bakinta. "Zonan" Mama ta sake fada seta shiga tana rarraba ido Mama ta sake cewa ya akayi?" "Daman, daman na kaiwa Yaya Umaimah ruwan wanka ne shine naga fuskarta ta kumbura sosai kamar ko faduwa tayi inaga ko Kuka tayi" ta fada tana satar kallon Salman se Mama ta daga mata hannu alamar taje ta kuwa fita da sauri kafin ta juya kan Salman tace "Zaka fadamun inda kukaje ko se na hada dakai duka naci ubanku" "Nidai Mama wallahi a waje muka hadu tace nazo na kaita Asibiti, seda muka dauki hanya tace Na'ibawa zamuje kuma koda mukaje a waje na tsaya ta shiga wani gida ban kuma san abinda tayi ba ta fito a yanda kuka ganta muka taho bata ce mun komai ba har muka zo gida" Salman ya fadi iya gaskiyar abinda ya sani. Mama dake kallonsa ta sauke ajiyar zuciya tace "Shikenan tashi kaje Allah ya rufa asiri" ya miqe yana cewa "Amma dan Allah Mama kar kice mata na gaya miki komai, kinsan Halin Yah Umaimah seta huce a kaina" "Kaje abunka" Maman ta sake fada daga nan tayi shiru ta zubawa Tv ido dukda ba kallon abinda ake yi a ciki takeyi ba illah kogin tunani data tafi. Umaimah ko ranar ko abincin dare bata fito taci ba kuma babu wanda yayi mata tayi haka ta kwanta seda cikin dare taji Yunwa na neman ranta kafin ta sanqami Burodi da ta kada madara da Milo a ruwan sanyi tasha, washe gari kuwa da wurwuri tun farar ta fita da kanta ta dora ruwan Wanka ta zuba wani a falask da zata sha shayi ta qule a daki. Batason a tuhumeta, kuma yanzu duk wanda yaga fuskarta seya tambayi meya faru. Har goman safe tana daki, bata zata ba se ji tayi ana murnar dawowar Abbansu da ya tafi Umarar Mauludi, dafe kanta tayi dan yanzu kam bata da dama dole ta fita tayi masa sannu da zuwa amma ba zataje yanzu ba seda daddare. Wayarta ta dauka ta sake gwada kiran number Khausar amma har sannan a kashe ake gaya mata dan tun jiya bayan ta dawo daga gidan su Hadiza take kiran layin amma a kashe. Kiran Rufaida ne ya shigo mata taja tsaki kafin ta latsa wayar ta shiga silent dan a yanzu haushin kowa takeji, idan ba ta rama abinda Yayan Hadiza ya mata ba kuma ta ci uban Hadizan bazata samu sauqin abinda takeji a zuciyarta ba kuma ba zata tunkari Khalil yanzu ba se bayan ta gama da qaramar yar iskar tukunna zata koma kansa shima taci masa uwa, qilan karuwar tasa ta gaya masa abinda ya faru shiyasa tun tsahon jiya zuwa yau be nemeta ba amma zasu hadu ne, seya gane ita ya ciwa Amana. WhatsApp ta shiga tana budewa kuwa sega saqon Khausar harda sauke ajiyar zuciyavta bude ta tarar da Voice note data turo mata bata bata lokaci ba ta kunna ta fara ji "Jiya naji labarin abinda ya faru, yanzu kika yarda ace ga mari ga tsinka jaka? Ta bi miki miji kuma kinje bin ba'asi yayanta ya dokeki wallahi karki yarda idan ba haka ba kina nan zaune ganin idonki zata aure miki miji kuma daga nan sunanki sorry, dan haka idan kin shirya inada qarin hujjoji da idan kika same su ko a qafa aka daurawa Mijinki na tabbatar da seya kwance ta ya gudu. Kafin nan dai kiyi qoqari ki kwaci yancinki ki rama abinda akayi miki idan kuma kinyarda kin karbi faduwa shikenan". Cikin sauri ta fara typing bayan da ta gama Jin voice din se kuma ta goge ta mayar mata itama da Voice tace "Idan na gama da ita ina nan kan juyowa kanki tsohuwar Annamimiya dan na tabbata bakinku daya dake da ita tare kuka hada duk wata qulla qullar datake bin mijina Allah kadai yasan dalilin da ya saka yanzu kika zame kika dawo kina bani bayanai a kanta, toh ni ba mahaukaciya bace da kike zaton zan yarda dake, idan ma kin angizani ne saboda a cutar dani toh ta Allah ba taki ba gani nan garas babu abinda ya sameni kuma zan dawo da shirin cin kutumar ubanku gaba daya keda su, kin gama mun aiki tunda har kika kaini gidansu, ki jirayeni idan na gama da ita kanki zan juyo" tana turawa ta dannawa lambar block dan zuciyarta ta gama bata bakinsu daya da Hadizan, qila ma wani shiri ne sukeyi na su fitar da ita daga gidanta dan su samu damar samun Khalil ita kadai toh kuwa uban da ya haifi uwarsu ma yayi kadan kuma daidai take da qugun kowaccen su. Wuraren uku na rana saqo ya shigo wayarta. "Naji saqonki kuma naga kinyi blocking numberta, toh ki duba na tura miki saqo da wata sabuwar number. Ni me qaunarki kuma bana nufin cutar dake sema kareki daga cuta da ha'incin da ake miki a bayan idonki amam zaki gane ba yanzu ba". Tsaki ta buga duk yanda bata so amma zuciyarta seda ta tilastata ta bude saqon da tace ta tura mata a waya ta kirata, kai tsaye tace idan zata samu dama zata tura mata, Hoton Hadiza da Khalil ne idan batayi kuskurena Ranar da ya tafi SA ne, babban abinda ya daga mata hankali hoton a cikin jirgi akayi shi, a zuciyarta ta ayyana 'kenan tare suka tafi' kamar kuwa Khausar tasan tunanin da takeyi kenan ta turo mata da cewar "Tare suka tafi, a cikin satin daya wuce ta dawo kuma tace zata sake komawa dan daqyar ya barta ta taho". Wani abu taji ya danne zuciyarta yana neman katse mata numfashi se kawai ta sulale a qasa wasu hawaye masu zafin gask suka shiga kwararo mata. Kwakwalwarta tamkar an liqeta ta kasa kawo mata kowanne tunani illah na Khalil da Hadiza ya tafi, kenan shi yasa sam baya wani nuna kewarta lallai Khalil. Anty da shirun Umaiman ya dameta ce ta ga Abba ya dawo har su Maman Asad sunzo tace bari dai ta leqa ko lafiya Mama dai ko a jikinta sabgarta takeyi. Yanda Antyn ta tarar da ita ya bata tsoro, ta dagota tana tambayarta lafiya meya samu fuskarta ta kasa cewa komai se kuka kawai. Qirjinta zafi yake zuciyarta kamar zata fashe wai Khalil ya raba musu kansa ita da wata Karuwa a waje wallahi ko duniya zata tashi bazata yarda ba, seta daidaita yarinyar nan idan ma bata halakata ba. Kuka kashirban ta dasa sanda Anty ta yayibo mutanen gidan akan suzo su ga yanda take, Mama dai bata zo ba tunda taji kan zancen jiya ta barwa ranta duk ma inda taje da abinda tayi z fito ne a bakin su taji wai tace musu zamewa tayi a bandaki Hankulansu suka sake daguwa Maman Asad na ta tashi su tafi Asibiti tace babu komai lafiya lau take jinta dukda haka bata haqura ba seda ta kira wata qawarta ta hadata da Umaiman tayi mata tambayoyi kafin tace mata babu komai in taji wani abu ba daidai ba taje Asibiti sannan suka haqura. Mama dai dariya tayi daman tana dakin Abba daya kwanta baccin gajiya Anty take mata bayanin tace Allah ya rufa asiri daga haka bata tanka ba. Umaimah bata samu fita zuwa inda Khausar ta kirata ba, kwana tayi idonta biyu tana saqa da warwarar matakin da zata dauka akan Hadiza da Khalil. Qarfe daya da rabi na dare ta gaji da juyi a gado ga shi ta rasa mafita akan abinda ya kamatu tayi bata daddara ba ta sake dannan kiran layin Khausar cikin Sa'a ya shiga ringing biyu ta daga muryarta da alamar bacci take tambayar wanene "Umaimah ce, dan Allah kiyi haquri da maganar dana gaya miki dazu raina ne ya baci baki san irin halin dana tsinci kaina a ciki ba tunda kika bayyanamun abinda yake faruwa tsakanin Mijina da Qawarki, yanzu abinda yasa na kiraki akan taimakon da kika ce zaki yimun ne shi nake so naji wane shiri kike dashi akan ta da kika ce zai taimaka mun? Sannan ke din wacece, meye alaqarki da ita sannan me tayi miki da har kika zabi ki bayyanamun alaqarta da Mijina akan ki rufa mata Asiri a matsayinta na qawarki?" Umaimah ta fada murya a dashe saboda kukan da ta sha. Shiru Khausar tayi dan har Umaimah ta cire tsammanin tana tareda ita sannan taji tace "Tabbas qawatace Hadiza koma nace miki Aminiyatace amma tayi mun abinda har duniya ta nade bazan manta ba kuma na kasa yafe mata, kamar yanda take qoqarin shiga tsakaninki da Mijinki haka ta ringayi mun, duk saurayin dana hadu dashi a rayuwa baya zuwa biyu gurina in gar sun hadu ze koma yace ita yake so, ta rabani da duk wasu namemana kuma itama ba auransu takeyi ba, zata cucesu ne ta karbi abinda zata karba agurinsu kafin ta barsu kinga daga ni har ita munyi Asara kenan. Sannan bayan wannan da akwai babban sirrinta wanda qalilan mutane ne suka sanshi, Hadiza mata take nema yan uwanta abinda har yasa nake sakewa ina nunawa Samarina ita kenan dukda tafini kyau da haduwa a zatona babu abinda zatayi dasu tunda ba layinta bane amma kuma sedaga baya na fuskanci ba haka bane, qazamar rayuwa takeyi tana hada mata da Maza duka tana mu'amala dasu abin mamaki kuma Mijinki ya sani a hakan kuma yake tareda ita dukda ina zargin abin nata harda Asiri a ciki, a cewarsa idan ya aureta yayi jihadi zata dena duk abinda takeyi Wani dum Umaimah taji akanta, yanzu a ce duk matan duniya Khalil ya rasa wadda ze nema se yar Lesbian kuma har yana fadin wai Jihadi zaiyi, sam kwakwalwarta bata nemi hango gaskiya ko qaryar abinda Khausar ta gaya mata ba ta hau kai daram ta zauna, "Kika ce Khalil ya sani?" Ta tambayeta cikin wani irin sauti, Khausar ta juya ta kalli Shema data rubuta mata duk abinda zata gayawa Umaiman ta bata hannu suka tafa kafinta jinjina kai kamar tana gabanta tace "Na tabbata, na sanar Miki da cewar Aminiyata ce idan kinada tantama ki tambayi Mijinki wacece Khausar qawar Hadiza" duka Shema ta kai mata a baki ita kanta bata san sanda ta bige bakin nata ba ta zaro idanu, kallon bakida hankali Sheman tayi mata se tayi saurin gyaran murya tace "Karima qawar Hadiza zaki ce masa idan kika fadi haka duk wata maganada ze ji a bakinki baze taba qaryata wa ba danyasan nasan komai akansa da ita Hadizan kuma yanzu zan tura miki da evidence din da nace dan ki sake tabbatarwa da kanki". Umaimah bata iya magana ba, a maganganun kaf iya abinda ta gane yar Lesbian Khalil yake shirin dauko mata a matsayin kishiya se kuma sunan Khausar da ya samu guri a kwakwalwarta dan ita bata ma ji wani rudewa da tayi akan subul da bakan na balle canza sunan da tayi, Khausar din kawai ta riqe kuma tana katse kiran tayi saving number da sunan sannan ta koma WhatsApp tayi unblocking nata sega hotuna kuwa sun fara shigowa harda videos. Dubasu ta farayi, a zahiri hotunane irin wadanda Yammatan yanzu harma da wasu matan auran suka daukesu a matsayin wayewa. Da yawansu ta fito daga Wanka tana daure da towel qarami daya bayyanar da irin kyan dirin da Allah yayi mata, wadansu rabin qirjinta a waje anyi wasu irin dauka dai da sam basu dace ba, wasu ita kadai wasu tareda mutane sun rungume juna ko suna kwance tare typucal hotuna dai irin na wadanda suka aro dabi'ar yahudawa suka dorawa kansu sam babu ganin rashin dacewa ko wani aibu kan abinda suke yi din sannan mafi yawancinsu a Hotel aka dauke su Wanda yake alamanta da yawa a lokutan tafiye tafiyensu na aiki take daukar su wannan a tunani irin na me hangen nesa da kyautata zato akan duk abinda ya gani kenan, banda Umaimah data rigada ta hau tayi daram akan zantukan Khausar din dan haka batareda ta bata lokaci ba ta ware wadanda take ganin sunfi muni da bayyanar da abinda take son isarwa ta aikawa da kafatanin yan gidan su Khalil din tun daga kan Hajiyarsa har zuwa kan Habiba autarsu, babu kodar a zuciyarta ta qara da saqon "Ita ce matar da Khalil yake qoqarin aurowa a ta biyu, na kuma samu tabbacin cewar yar Lesbian ce ina kuam da shaida akan hakan". Bayan ta gama turawa ta ajiye wayar, Agogo ta kalla qarfe biyu da minti sha biyar shi acan yanzu uku fa sha biyar kenan qila yana bacci, koda yake dole yayi bacci ya dauki farka ragowar Maza da Mata ya tafi da ita shiyasa har ya kwashi kwana biyu be kira ta ba balle yaji lafiyarta data cikindaya qaqaba mata. Wayar ta sake dauka ta shiga WhatsApp, zuciyarta ta rigada ta bushe ba kuma ta tsoron ta mutu ko tayi rai balle abinda ze iya zuwa yazo babu tunanin komai Umaimah ta ringa aikawa da hotunan data turawa su Hajiyar Khalil zuwa duk wani WhatsApp group da take ciki tare da bayanin cewar gagarumar yar Lesbian ce sannan ta sake wucewa Tiktok ta dora hotunan da irin bayanin data tura a WhatsApp. Se bayan data gama aiwatarwa sannantaji hankalinta ya kwanta zuciyarta tayi sanyi, ko iya haka aka tsaya tasan ta gaka da rayuwarta ta tona mata Asiri a idon duniya babu me sake kallonta da idon rahama sannan ba Asiri ba ko tsafi tayiwa Khalil dan ya so ta tasan wannan magana ta rushe in dai yan uwansa suka gani. Bacci ne ya kwasheta irin na wanda ya samu nutsuwar zuciya, ranta fes kamar an wanke shi da Hypo dan ta san ta gama da wannan maganar kuma sedai wata a gaba. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 42 Bata sake duba whatsapp din bama se wash gari da kusan qarfe tara bayan tayi wanka ta karya kuma se a sannan taje ta gaida Abba yayi mata yaya jiki da tambayarta Aboki kamar yanda yake kiran duka Jikokinsa Maza tace yana gidan Hajiya. Zam zama da dabinon Ajuwa ya bata yana cewa "Gashinan musamman nayi dawafi dashi saboda ke, kisha ki shafe jikinki da niyyar Allah ya shirya ki ya shirya tunaninki ya kuma baki lafiya keda abinda yake cikinki ku rabu lafiya". Seta tura baki gaba wai ita me takeyi da kullum ake faman cewa Allah ya shiryata koda yak shariyar Allah ai bata yawa Allah ya shiryeta din. Seda suka taba yar hira kafin ta fita Mama dai daga amsa gaisuwar da tayi mata bata ce komai ba ta bita da kallo a ranta tana mamakin walwala da annashuwar data gani a fuskar Umaiman, sannan har yanzu da dan sauran kumburi a fuskar tata ga jini daya kwanta cikin idonta bangaren da ta sha mari. Seda taci dumamen Tuwo ta qoshi kafin ta ciro wayar daga chaji ta bude, Missed calls ta gani sunfi Ashirin, Anty Amina, Jamila duk sun kirata ga na Jalila da yafi na kowa yawa a ciki dan haka ita ta fara kira "Umaimah saqon da kika turamun duk su Jamila sunce suma kin aika musu harda Hajiya me yasa, badan Allah yasa wayar ta na Hannun Khalifa ba shi ya gani ya goge me kike tunanin ze faru idan ta gani? Ai da kin bari mun fara magana dake kafin kowa ya sani musamman Hajiya kin san bata son damuwa musamman kuma akan abinda ya shafi Khalil" Jalilan bayan data amsa sallamar Umaimah. Wayar ta harara a ranta tace 'aikin banza' a fili kuwa kukan qarya ta fashe dashi tana cewa "Toh ya kike so nayi Anty Jalila so kike na zauna ina ji ina gani ya dakko mun masifa ya kawo gida? Na san baze taba fada muku gaskiya ba dan nima besan na sani ba shiyasa ban bi takansa ba kai tsaye na sanar daku dan nasan idan na fara masa magana qaryatawa zeyi sannan ya toshe duk wata hanya da gaskiya zata fito. Nidai wallahi tun wuri kuyi masa magana idan ba haka ba ni bazan zauna ba ya aurota haka kawai wani Gingimemen baka'i ya sauka a gidan mu ba iya kanta ze tsaya ba harda mu ze shafa" ta cigaba da rusa kuka kamar gaske ita dai Jalila ta kasa magana dakyar ta iya cewa "Shikenan kiyi shiru hakan ma bazata faru ba da iznin Allah kuma na tabbaatr da shi kansa Khalil din be san haka take ba da babu abinda ze kaishi gurinta. Kuma ma ana ta neman layinsa kusan kwana biyu kenan daman bana samunsa ko a Whatsapp bana ganin sa Online in sha Allahu komai ze daidaita kinji ki dena kuka" daga haka sukayi sallama akan zata sake kiranta. Tana kashe wayar ta sheqe da dariyar shaqiyanci dan ko a jikinta wai an mintsini kakkausa. Whatsapp ta shiga, Messages ta tarar rututu a duka  groups din nata kaitsaye kawai ta bude Group din daya fi mata dadi, kusan kaf maganar ita akayi tagging abinda ta tura jiyan, qarshe ta tafi inda taga wata tace "Kai wannan ai Hadiza Musa ce, Lawyer ce kuma tana aiki a hukumar kare haqqin mata da qananan yara ta garin nan ko amma kuwa dai ta bata wayonta wallahi, kunsan yanda ake yabon kirkinta da kamun kanta kuwa ko kwatance za'ayi a gurin na mata masu kamun kai da ita akeyi amma ashe ashe tab abinda take aikatawa a boye kenan amma anji butur wallahi" "Daman ai laifi bashi da kama yanzu da Allah ya tashi tona mata Asiri ai gashinan, kuma ta jira taga sakamakonta" Umaimah ta rubuta nan sukayo mata caaa kowa da tambayar a ina ta jiyo wannan magana dan daman tun cikin daren wadansa suka fara gani suke tambayarta, har PC gwanayen gulma suka bita tuni kuma da yawa suma sunyi forwarding saqon zuwa sauran group sedai Allah ya taqaita tsayuwarsa kawai. Rufaida ce ta kirata a waya ta daga tana cewa "Ke tun Asuba nake kiranki baki dauka ba" "Bangani ba se yanzu na dauki wayar kuma banma lura da kiran ki a ciki ba" ta bata amsa, se Rufaidan tayi saurin cewa "Umaimah ina kika samo waccen jaridar, naji fa ana ta fadar Lawyer ce matar kuma da Human right take aiki bakya tsoron labari ya koma mata ki shiga uku? Koma ba wannan ba kinsanfa irinsu wallahi daurin gindi ne dasu a qasa ance duk matan manyan nan harkar suce yanzu idan tana da Connection da wata babba kar ki jawa kanki fa kina zaman zamanki azo a kamaki". Tsaki Umaimah ta buga kafin tace "Wanda be kamani ba baya qaunar uwarsa da ubansa, ke an gaya miki ni ina tsoron ta mutu ne balle tayi rai? To bari kiji ba Lawyer ba ko ita ce An tourney matsalarta ce ita ya shafa bani ba. Bana kwaina seda zakara dan haka daga nan gar majalisar dinkin duniya muje inada shaidar da zan tabbatar da abinda na fada akanta, saboda bakisan wacece ita ba shiyasa har kike magana" "Au wai kinsanta a gaske ne, ni na zata fa a social media kema kika samo kike yadawa?" Rufaida ta fada cikin salon son jin labari, nan Umaimah ta karkace ta fara zayyano mata hadinta da Hadizan, Rufaida ta qunduma Ashar kamar diyar Maguzawa tace "Amma Allah ya isa tsakanina dake Umaimah yanzu haka ta faru baki gaya mun ba, me yasa tunda zakije gidan su matsiyaciya baki gaya mun mun hadu a hanya ba? Ai wallahi da se munci Abu ta kaza kazan uwarta kai lallaima. Banga laifinki bari ma ki gani yanzu zan dora a Facebook qarshen terere shegiya La'ananniya ta qara shan tsinuwa ta tagayyare yansa ko tuba tayi bazata samu me kallonta ba" Rufaida ta fada kamar zata fito ta cikin wayar sbaoda hayagaga. Magana suka ci gaba dayi, ita a sonta ma su sake komawa gidansu Hadizan tunda Umaimah tace bata sameta na dukda ta boye mata dukan data sha ba seta ce mata su bari kawai iya wannan ma ya isheta sukayi sallama ta koma WhatsApp aka ci gaba da fafatawa masu tsinewa Hadiza da aibatata sunayi masu tausaya mata da nema mata shiriyar Allah sunayi ita dai Umaimah ta shiga wannan group ta fita wannan tana kallon yanda abubuwa suke gudana zuciyarta qal kamar an mata Albishir da wani muqami ko a yanzu Kasuwa ta tashi ita ce da riba. Chat ta yiwa Khausar take gaya mata ta fallasa sirrin Hadizan a duniya yanzu kowa yasan wacece ita, ganin bata online yasa ta koma ta kirata amma layin a kashz ta tabe baki irin ko oho daman dan ta gaya matane kawai tunda itama tana da fushin Hadizan tunda bata dauka ba shikenan se kawai ta shiga sabgoginta. HADIZA Seda ta kwana biyu bata fita aiki ba saboda yanayin rashin jin dadi da take ciki, gaba daya Mama ta fita a sabgarta ballantana Yaya Isma'il da tasan Mama ce ta hana shi tabata amma in har suka hadu kallon dayake aika mata dashi bata iya ko gaishe shi take wucewa. Ranar ta tashi da dan qarfin jiki saboda amsa gaisuwarta da Maman tayi har take tambayar ta dalilin rashin fita aikinta kwana biyu dan haka ta hau shiri a ranta tana Addu'ar Allah yasa Maman ta fahimceta ne kamar yanda kullum bata gajiya da addu'ar Allah ya wanketa a idon Maman daga mugun qazafin da Khausar take mata. A qofar gida ta hadu da Isma'il daya zo gaida Maman kamar kowacce safiya, ya banka mata harara kamar koda yaushe tayi saurin kauce masa, ta tabbatar da Mamace ta hana shi taba lafiyarta da babu shakka se ya huce fushinsa akanta. Titi ta fita dan ta nemi abin hawa, ta tuna in lafiya lafiya ne zece ta jirashi shi ze sauketa a gun aiki suna tafe suna hirar su gwanin sha'awa amma banda yanzu da sam Khausar ta shiga ta fita ta hana faruwar hakan. Kallon qofar gidansu tayi, idan suka taho da Yayan se sun tsaya sun dauketa zasu wuce idan ma badashi bane seta biya mata tun yarinta har zuwa yanzu amma ashe ita tana da wani mugun nufi a ranta da take ajiye dashi tsahon lokaci "Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu" ta fada a fili tana share kwallar data ziraro mata. Sanda ta isa gurin aikin nasu kamar yanda ta saba tun daga gate ta fara gaisarda Ma'aikatansu manya sa qanana sedai yanayin da suke amsa mata ya bata mamaki ga wani kallo da suke rakata dashi da sam ta kasa fahimtar na menene ne haka ta wuce ciki jiki a sanyaye can dinma dai kamar na wajen dan ko sallamarta babu wanda ya amsa illah idanu da suka zubo mata kamar sunga Mujiya. Jikinta ta kalla ita dai bataga wani abu da ze saka a kalleta ba dan doguwar rigar Lace ce a jikinta ta dora dogon Hijabi ya wuce guiwarta, haka fuskarta tasan farar powder da kwalli kadai ta saka ballantana ace ko wani abun ne yayi yawa ta zama abar kallo, wucewa tayi Table dinta dake can loko ta ajiye jakarta ta fara karkade qurar da gurin yayi da alama babu wanda ya taba a kwanakin da tayi bata zuwan idonta ya sauka a mazaunin Khausar da babu kowa a ranta ta ayyana qila bata qaraso bane ko sun fita yin wani aikin. Tana zama ko cikakken minti biyu ba tayi ba Zuhra Secretary Shugabar su ta zo kanta, bata ji zuwanta ba se dogon tsakin da taja tana kallonta kamar kashi tace "Kije Hajiya tana kiranki kuma kiyi sauri karki bata mata lokaci" ta sake jan wani tsakin harda tsartar da miyau abinda yayi bala'in qonawa Hadiza rai amma ta hadiye bata kulata ba. A iya saninta suna shiri da Zuhra kai ita kaf gurinma bata da Abokin fada kowa gaisuwar mutunchi da wasa da dariya ne yake hadata dashi to duk me ya kawo wannan sauyin kuma yau? Bata da me bata amsa dan haka ta miqe da wayarta a hannu Zuhran tayi saurin dakatar da ita da cewa "Tsaya ki dauki jakarki dan nasan daga can gaba zaki qara kinga ba sekinyi tafiya biyu ba" se kuwa ta tsaya ta tattara abubuwan data fito dasu ta mayar harga Allah a ranta ta ayyana wani aikin zata fita shine dalilin kiran da Hajiyar tayi mata dan haka ta sa kai ta fita tana jin wata na cewa "Uhm a haka dai kamar ta Allah ashe Akuya ce da fatar kura, kai Allah yayi mana tsari da masifa ya shiryesu idan suna da rabo". "Toh fa wai me yake faruwa ne?" Ta tambayi kanta abinda bata da me bata amsa. Tunani takeyi kala kala a zuciyarta harta isa office din Hajiya. Dukda daman ba Mace ce me yawan fara'a ba amma yanayin data ganta a ciki yasa tasha jinin jikint. Kujerar gaban Table din ta nuna mata ta zauna a darare tana gaisheta, bata amsa ba ta turo mata wata farar takadda da biro akai kafin ta dago fuskarta sam babu fara'a tace "Ki saka hannu a nan, takaddar suspension ce saboda bazamu iya ci gaba da aiki dake ba a wannan yanayin da ake ciki, idan da ta tawa ne zamuyi Firing naki ne take amma na samu directives daga sama akan karnayi hakan saboda suna ganin kinada Influence sosai a wannan ma'aikatar, to koma menene ni bazan taba tolerating misconduct irin naki ba, ba zan ci gaba da aiki dake ki jawo mana bacin suna a wannan Qungiya ba dan haka kije ki kuma dauka cewar mun koreki kawai dan ko zaki dawo kamar yanda suke tunanin badai ina nan ba, ba kuma idan nasan wanda yake heading Ma'aikatar nan ba". Gaba daya kanta ne ya qarasa qullewa, taja takaddar gabanta tana dubawa badan tana gane komai ba saboda ya da tunani suka cushe mata harta rasa wanne abu zata tuna a ciki. 'Meta aikata da har yayi zafi haka?' Shine tambayar da takeyiwa kanta, tsawar da Hajiyar ta daka mata ce ta sakata dagowa da sauri ta kalleta, "Kiyi sauri ki saka hanni Malama ki fita ki bani guri, bana son ganin wannan disgusting face din taki" ta fada cikin tsawa jikin Hadiza ya dauki rawa, dakyar ta iya riqe biron ta saka hannu kamar yanda ta umarceta ta fincike takaddar tana harararta tareda nuna mata qofa. Kaitsaye Get ta nufa tana jin yanda duk inda ta wuce suke jifanta da maganganu marasa dadida har sannan ta kasa gane inda suka dosa a haka har ta fice daga gurinta tsaya bakin titi tana tarar abin hawa. Seda ta zauna a cikin Adaidaita tayi shiru tana saqa da warwara domin gano bakin zaren.e tayi da za'a dakatar da ita daga aiki, yanzu idanta je gida ma me zata gayawa Mama? Ji tayi kanta ya sara mata saboda tunanin da tayi, yanzu ace hotunan da Khausar tayi musu barazana dasu ne ta watsa kamar yanda tayi iqirari fa? Babu shiru ja ciro wayarta dake cikin jaka saboda sauri har tana subucewa ta fadi qasa ta duqata daukota cikinrawar jiki ta kunna Dat ta shiga WhatsApp dana kwanakin bata samu nutsuwar yin chatting bama. Saqonni ne babu adadi suka ringa shigowa amma bata su takeyi ba, Searching sunan Khausar tayi ko zata ga ta aiko mata da wani saqo amma babu komai, qarshen maganarsu tunda ta tura mata da receipt na dubu dari biyun data sa ta aika mata basu sake magana ba. Fita tayi daga chat din, saqonnin wasu mutane da ta manta rabon ma da su magana ya dauki hankalinta, abin Mamaki da yawansu Tsofaffin samarinta ne se qawayen da sukayi karatu tare irin wadanda inbada babban dalili ba ko a chatting dinba l akeyi ba. Yanda taga saqunan nasu a jejjere wani na bin wani ga kuma tarin numbobi da babu suna ya qara sakata a rudu seta bude chat din farko na Umar Tsohon saurayinta ne wanda daga shi ne ta hadu da Khalil, taso shi amma halayyarsu bata zo daya ba dan tantirin manemin matane tunda ya fito mata da muradinsa ta nuna masa ba haka take ba ya dauke qafa ya dena nemanta. "Hadiza kenan, nayi matuqar mamaki na kuma tabbatar da baki da kunya, ke a yanda kike har kike iya mun wa'azi da gaya mun Allah yace Annabi yace ko? Koda yake daman na zargin hakan..." Kiran waya ne ya shigo ya katse mata karatun da takeyi seta daga ganin Anty Bilkisu ce matar Yaya Isma'il. "Duk inda kike Hadiza ki maza kizo gidan nan yanzu karki koma gidan Mama" Abinda ta fada mata kenanta kashe waya daga muryarta ta karanci zallar tashin hankalin da take ciki seta kalli me Adaidaita dake ta yan waqe waqensa tace "Malam bi nan Darmanawa zamu koma" "Toh Hajiya" ya bata amsa yana shiga kwanar yan Katako suka ci gabada tafiya. A qofar gidan ya ajiyeta ta bashi kudinsa ta shiga, Anty Bilkisu na tsaye bakin qofar palour ta cikin shirin fita tana hangota tace "Allah sa baki sallami me Adaidaitan ba fita zamuyi" seta juya da sauri har ya fara tafiya ta tsaidashi ta fito suka shiga yaja. Aisami tace ya kaisu unguwar su Anty Bilkin seta raya a ranta ko ba lafiya ba. "Bani wayarki Hadiza" ta fada seta zarota a jaka ta miqa mata daidai sannan kiran Yaya Isma'il ya shigo zata daga Bilkisunta fizge ta kashe wayar gaba daya ta saka a jakarta. Tata wayarce ta shiga ruri, ta ciro ta duba shidin ne seta riqeta a hannu har kiran ya katse wani ya dake shigowa sanann ta daga. Seda ta daidaita muryarta kafin tayi sallama muryarsa ta katseta yana cewa "Duk inda kuka tafi ku dawo yanzu Bilkisu keda Hadiza, wallahi in har kuka dara Minti talatin baki kawota gidan Mama ba a bakin auranki kuma saki uku" yana fadar haka ya kashe Bilkisu ta kalli Hadiza data tabbatar da taji abinda Yayan nata ya fada saboda kidima bata iya magana ba se Hadizan ce ta tsaida Me Adaidaita tace su Koma Na'ibawa ya karkata Mashin yana cewa "Ba matsala hajiya aikin kudi nakeyi ai". "Anty Bilki ki gaya mun abinda yake faruwa dan Allah dan na fara rasa tunanina. Daga zuwana gurin aiki aka bani takaddar sallama, kin kirani babu shiri kince nazo sannan ga maganganun da Yaya ya fada menene dalilin da z kafa sharadi a bakin auranki? Meyake faruwa dani dan girman Allah ki gaya mun saboda nasan abinda zan tunkara" Hadiza ta fada tana jijjiga Bilkisu da tayi shiru kamar wadda ruwa ya cinye, kallon tausayi tabi Hadizan dashi ba tateda tace komai ba ta maida kanta tana kallon waje ganin haka ya saka itama Hadizan taja Hijabinta ta rufe har fuskarta a zuciyarta tana maimaita duk addu'ar datazo bakinya. Bata san menene ya tunkaro rayuwarta ba amma tana fatan koma menene Ubangijin daya jarabceta dashi ya bata ikon dauka. Tundaga qofar gidan tasan ba lafiya ba, Kukan Mama da kururuwarta dake jiyowa da wasu muryoyi da bata tabbatar da masu su ba suna bata haquri nan take jikinta ya dauki rawa ta coge a qofar soron saboda wani matsanancin tsoron abinda zata tarar daya dirar mata a zuciya. Anty Bilki ce ta kama hannunta tana cewa "Muje Hadiza Allah yana tare da me gaskiya muma kuma muna tare dake karkiji tsoron komai in sha Allahu ubangiji ze wanke ki" "Me akace na aikata?" Ta fada cikin wata irin karyayyar murya tana kallon Anty Bilki da kwalla ke zubo mata, seta jata suka shiga gidan ba tareda ta amsa mata ba, a tsaitsaye suka tarar da Mata uku, Malama Lawisa maqociyarsu ce kuma Aminiyar Mama se Hajiya Zuwaira itama qawarta ce ta kusa da sukayi aiki tare se kuma Alhaji Sunusi Mahaifin Khausar wanda suka riqe tamkar uba. "Yawwa gatanan, na gaya miki daman babu inda Hadiza zataje, kiyi haquri ki sauqaqawa zuciyarki Karima idan baki shaidi yarki ba waye ze bata kariya a duniyar nan" Hajiya Zuwaira ta fada tana kamo hannun Hadizan zuwa gaban Mama data yi saurin ja da baya tana cewa "Ta fita bana son ganinta, ta fita na barwa duniya ita. Yanda kika ci mutunchinmu hadiza kika tozarta mu kema Allah yayi miki haka. Kin cucemu kin cuci Ahalinmu kije kici gaba da abinda kika zabawa kanki amma daga yau ki saka a ranki baki da uwa, ki fauka tamkar daga sama kika fadi baki da kowa ki riqe rayuwar da kika zabawa kanki ta zamar miki uwa da uba da dangi kije gaki ga duniya Hadiza". Sulalewa tayi daga hannun Hajiya Zuwaira ta zube ta shiga jan guiwoyinta har zuwa gaban Maman dake kuka kamar ranta ze fita, cikin rawar jiki ta kai hannu zata tabata kafin ta kai ga hakan Maman ta dauketa da wani gigitaccen Mari da seda jinta ya dauke na wani lokaci kafin ta kalleta tana cewa "Idan kika kuskura kika tabani da qazamin hannunki ban yafe ba ki kuma tashi ki fice daga gidan in har ba qarasani kike so kiyi da baqin cikin ki ba, wallahi Hadiza nayi nadamar haihuwarki. Da nasan abinda zaki jawo mun kenan dana danneki tun dana haifeki kin mutu kowa ya huta" "Subhanallahi wai Karimatu bazaki dena jifan yarinyar nan da mugayen kalamai ba. Koma menene hannunka baya taba rubewa kayar, addu'a da neman shiriyar ubangiji ita take da buqata a yanzu ba mugayen kalaman da zasu qara tagayyara rayuwarta ba. Ke Hadiza tashi kije, kuje can gidan ki zauna karkije ko ina daga nan ina zuwa" Alhaji Sunusi ya fada cikin bacin ran abinda Maman takeyi. Tunda mugun labarin ya riske shi yana kasuwa yaji yaran shagonsa suna surutu da la'antar yarinyar har yaji daya yana fadin yar unguwarsu ce ya santa abinda yaja hankalinsa kenan har ya nemi jin ba'asin meya faru suka nuna masa. Hankalinsa yayi masifar tashi babu shiri ya baro kasuwar ya taho gida yana zuwa Matarsa take sake jadda masa ita ma ta gani a wayar ta an tura a group Khausar bata kwana gida ba tana gidan Yayarta shiyasa bata ji gargar din maganar ba dan a cikin tashin hankali ya sameta na tsoron ko itama Khausar din irin rayuwar da takeyi kenan tunda a koda yaushe suna tare shine babu shiri ya tafi gidan su Hadizan yaje ya tarar da Isma'il ya rigada ya kwazawa Maman labarin tana ta tashin hankali abin dai babu dadi. Anty Bilkisu ce ta kama Hadiza da sam ta gagara kuka se zare ido takeyi kwakwalwarta tamkar an wanke ta babu tunanin komai a ciki. Ta rasa gane me yake faruwa, gaba daya duk wani motsi ko magana sake jefata cikin rudani yakeyi. A bakin qofa suka ci karo da Isma'il daya bi sahun Hadiza gurin aiki aka tabbatar masa tazo ta tafi daga can ya wuce gidansa yana zuwa yaran sukace Mamansu ta fita da Anty Hadiza dalilin kiran da yayi mata kenan akan ta dawo daga can kuma ya wuce gurin wani abokinsa ya kai masa hotunan dan ya duba masa sahihancinsu saboda zuciyarsa ta kasa yarda cewar yar uwarsa Hadiza zata aikata hakan sedai ya tabbatar masa da hotunan gaskiya ne ba hadasu akayi ba wani irin rugugin tashin hankali yake ji a cikin kansa dakyar ya iya tuqo mota ya dawo gida. Yana sako kai Soron suna saka nasu zasu fita, daga Hadiza har Bilkisu babu wadda zatace taga sanda ya iso gabansu illah mahangurbar daya kaiwa Hadizan a fuska jini yayi tsartuwa daga hancinta da bakinta da suka fashe lokaci guda, kafin tagama sanin abinda yake faruwa ya rufeta da wani irin mugun duka kamar yanda kasan ya kama Barawo, da gudu jama'ar cikin gidan suka fito amma an gagara samun wanda ze iya kwatarta a hannunsa dan duka yake kai mata ta ko ina babu ji babu gani qafa da hannu tuni qofar gidan ta cika maqil da jama'a yan kallo harda masu daukar video dan daman hotunan sun gama karada unguwa anata yamadidi masu gaskgatawa nayi harda kafa hujja ta bata kula samari wasu kuma suna ganin ba gaskiya bane ba. Duk irin roqo da magiya dasu Alhaji Sunusi suka ringa yi masa Isma'il be dene dukan Hadiza ba seda yaga bata motsi idanunta sun qaqqafe sannan ya tsallaketa ya shiga cikin gidan Hajiya Zuwaira da Malama Lawisa suka dagota a tare suka fasa kuka suna cewa "Ya kasheta, Isma'il kayi kisan kai" Daga cikin gidan Mama dako gezau batayi ba kan dukan da yakeyi mata tace "Ai gara daya kasheta dan daman hukuncinta kenan kuma ko shi be kasheta ba ni da hannuna zan miqa ta ga Kotun musulunci a yanke mata hukunci, mun huta an rage mugun iri a doron qasa" ta qarasa tana fashewa da wani irin kuka da duk wanda yaji se ta bashi tausayi. Gabanta ya durqusa shima yana kukan tamkar mace yace "Naje Mama suntabbatar mun hotunan gaskiya ne ba hadasu akayi ba, da gaske ne Mama Hadiza Mata take nema yan uwanta shi yasa taqi tsayar da Miji tayi aure. Kuka suke babu me rarrashin wani, acan soro kuwa haka suka kamata aka sakata a motar Alhaji Sunusi wanda dakyar aka kori mutane da suka taru suna kallo. Asibiti suka kaita, seda likitoci sukayi dagaske kafin numfashinta ya daidaita kafin sukayi mata allurar bacci saboda jininta daya hau ya samu daidaito. Sanadiyyar dukan ta samu tsagewar qashi a hannun dama da qa targade babu adadi banda fuskarta data kumbura suntum saboda duka taimakon da Allah yayi mata be sameta a ido ba. Malama Lawisa ce ta zauna da ita Hajiya zuwaira da Anty Bilkisu suka koma gida tana taraddadin hukuncin da zata fuskanta daga mijin nata itama shiyasa bata koma gidan Maman ba kaitsaye ta wuce gidanta a ranta tana tausayawa Hadiza har kuma sannan bataji daidai da kwayar zarra ta yarda da abinda ake zarginta dashi ba. Ita shaida ce akan Hadiza a ko ina kuma zata bugi qirji ta qarya ta cewar Hadizan bata aikata abinda ake tuhumarta ba. Hadiza Seda ta kwana biyu kafin ta farfado daga baccin dolen da likito ci suka ringa sakata, har sannan Malama Lawisa ce tareda ita tayi mata sannu sannanta taimaka mata tayi wanka da ruwa me zafi sosai ta gasa jikinta. Seda ta rama sallolin da ake binta a kowacce sujjadarta seta yiwa Allah kirari ta roqeshi daya kawo mata dauki cikin halin data tsinci kanta wanda har sannan bata tantance shi ba. Shayi ta hada mata tasha ta zuba mata abincin da Anty Bilkisu take kai musu a boye dan daga Mama har Yaya Isma'il babu wanda yabi sahunsu balle susan halin datake ciki. Bata cibatace ta qoshi, ta jingina kanta jikin pillow data saka mata ta rufe idanunta da suka qanqance saboda kumburinda fuskarta tayi tayi shiru bazatace ga abinda take tunani ba. Gajiya Malama Lawisa tayi da shirun Hadizan ta numfasa tace "Hadiza ki zalimci istigfari da hailala kinji, shiru ko tunani bazasu amfana miki komai ba kiyi ta neman taimakon Ubangiji Allahya bayyanar da gaskiyar wannan Al'amari". Bude ido tayi dakyar ta kalli Malama Lawisan kafin cikin muryarta da bata fita tace " Umma ki fitar dani daga duhun da nake ciki, bansan meya faru ba. Mun rabu da Mama lafiya yau dan kwanakin da suka wuce mun samu sabani har tayi fushi dani amma yau mun tashi lafiya dan ita tace mun na fita aiki ma. Umma tunda na fita mutanr suke kallona suna fadar maganganu dana kasa gane kansu sannan an bani takaddar sallama daga aiki akan dalilin da bansani ba nima. Anty Bilki ta kirani tace nazo muka fita tareda ita daga nan Yaya yace muzo gida bansan komai daya faru ba se yanzu na ganni a Gadon Asibiti dan Allah Umma ki fahimtar dani ko gaya mun me na aikata da har Mama takeyin irin kalaman nan akaina tace ta barwa Duniya ni, menayi da yayi zafi harda na zama abar kallo da zunde a gurin mutane" ta qarasa fada muryarta na rawa alamar kuka. Shiru Malama Lawisa tayi kamar ba zata ce komai ba kafin kuma ta miqe ta dakko wayarta dake jikin chaji ta dawo kusada Hadizan, hotunan ta bude mata tareda rubutun dayake tareda su ta miqa mata wayar Hadiza ta karba tana kallonsu daddaya har zuwa kan rubutun ta karanta idonta ya tsaya kyam akan rubutun tana sake maimaitawa a zuciyarta. Wayar ta miqa mata ta maida idonta ta kulle bayan data zame ta kwanta a zuciyarta tana maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel, Allahumma ajirnifimusibati wa'aklifni khairan minha" yinsu takeyi babu iyaka har seda taji wani hayaki daya lullube mata kwakwalwa ya washe,jirin daya fara dibarta daga kwance ya tsagaita mata kafinta bude idanunta da suka kada sukayi jajir lokaci daya ta kalli Malama Lawisa da itama ita take kallo tace "Umma, yanzu Mama ta yarda da cewar ni yar Lesbian ce" "Abin akwai rudarwa Hadiza, da ace fada mata akayi qila ta qaryata amma wadannan hotunan sune suka bada tabbacin abinda aka fada" Malama Lawisa ta fada Hadiza tayi saurin tareta da cewa "Kema kin yarda kenan? Idan hakane me yasa zaki zauna dani, me yasa baku bari ya kasheni ba kowa ya huta da masifar da na jawo muku?" Ta fada tana kallo taze Malama ta girgiza kai tace "Ni bazance naAmince ba saboda ina kyautata miki zaton bazaki aikata hakan ba amma a yanzu ba kowa ne ze iya tsayawa yayi dogon tunani ba, komai ana buqatar shaida ne kuma gata an samu kinga kuwa zeyi wahala kafin ka fahimtar da mutane gaskiya ko akasin haka akan wannan al'amari. Koma menene yanzu ba lokacin mayar da magana bane ki yi haquri ko samu lafiyarki ta daidaita idan yaso daga baya se a san abinda za'ayi. Koda ace dagske kina aikatawa idan kika tuba tuba na gaske kika nemi yafiyar ubangiji kika gyara rayuwarki se kiga komai ya wuce tamkar be taba faruwa ba". Wani irin kuka ne ya kwace mata da seda zuciyar Malama Lawisa ta karye hawaye suka fara zubo mata itama. "Wallahi Allah shine shaidata Umma ban aikata ba ba halina bane, bansan mena tsarewa mutane a duniya da a kullum suke bibiyata da sharri ba. Yanzu wane ne ze yarda dani? Waye ze wankeni daga wannan mugun zargin da aka jefani a ciki" Hadiza ta fada cikin tsananin kuka tamkar ranta ze fita, babu zato se ji sukayi daga bakin qofa ance "Ni na yarda dake Hadiza kuma Ubangiji ze wanke ya kunyata maqaryata da masu munafunci". Da sauri ta daga kai ta kalli inda take jiyo maganar, Khalil ne a tsaye, ba zata iya fassara yanayin dake kan fuskarsa ba ya qaraso cikin dakin wata Mace me tsananin kama dashi tana biye dashi a baya. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 43 KHALIL Cikin injin markada sumunti wayarsa ta subuce ta fada dalilin da ya saka ya kwana biyu kenan be kira gida ba haka idan an kirashi ba'a samunsa. A kwana na uku ya samu wata wayar ya siyi sabon layi ya dora dan baze iya swapping layukansa ba dole se ya dawi Nigeria se kawai ya siyi wani ya saka akan wayar yayi backup na numbobinsa ta Gmail. Hajiya ya fara kira ita take gaya masa Jalila nata neman sa bata same shi ba ya kirata yaji dan zuwanta gidan kusan nawa tana tambayar Hajiyan koya kirata kamar dai akwai wata matsala yace toh ze kirata. Bayan sun gama magana da Hajiya ya kira Umaimah. Lafiya lau sukayi magana ko a murya be tsinci wani abu daze nuna akwai wata matsala ko wani abu ba, suka sha hirarsu yace tayi saving number da ita zeyi amfani kafin ya dawo ya maida wancan layin. Yaso ya gaya mata a kowanne lokaci daga gobe zata iya ganinsa dan ya gaji da zaman yayi kewarta sosai ammakuma so yakeyi ya shammaceta sedai kawai ya kira waya yace azo adauke shi daga Aiport shi yasa yayi shiru suka rabu suna nanatawa juna yanda kowanne yayi missing dan uwansa. Ya manta shaf da kiran Jalila da Hajiya tace yayi yaci gaba da sabgoginsa se bayan Magriba yana masallaci ta kirashi, bata bari ko gaisuwa sunyi ba tace "Khalil meyake faruwa, menene gaskiyar abinda matarka take yayatawa a gari?" "Kinga ki nutsu kiyimun magana a hankali yanda zan fahimta, Bangane me kike magana akai ba, meya faru a ina kuma me take yadawa?" Shima ya jefa mata tambaya dan be fahimci inda kalamanta suka saka gaba ba. Se Jalilah taja numfashi kafin tace "Kana ji ko, shekaran jiya matarka ta aika mana da wasu hotuna dukkanmu harda Hajiya, amma na saka Khalifa ya goge na wayar Hajiyan bata gani ba. Na kuma ce kar wanda ya gaya mata ballantana hankalinta ya tashi, yanzu ni abinda kawai nake so naji dagaske ne abinda ta fada ko kuwa qarya ne?" "Jalilah" Khalil ya kira sunanta cikin qosawa da maganar da sam be gane inda ta dosa ba kafin yace "Dan Allah kiyi magana irin wadda zan gane, ban san wane hoto kike magana akai ba ballantana na fada miki gaskiya ko qarya akansa". "Toh, kana WhatsApp da wannan number ne? Gara na tura maka ka gani da idonka zefi sannan muyi magana, ak na zata kaima ta aika maka ne shiyasa kaji ina maka magana kaitsaye" Jalilan ta sake fada ko kafin ya amsa mata da yana WhatsApp din ko bayayi ta kashe wayar se shima ya shiga WhatsApp din yana jiran saqonta. Wayarce ta subuce daga hannunsa tsabar kidima ya bita ya dauka ilahirin jikinsa babu inda baya rawa. Khausar ce ta fado masa arai, wato abinda ta fada kan wanda zatayi musu a gaba se yafi na baya kenan innalillahi amma Khausar ta cika la'ananniya da bata tsoron Allah, me Hadiza ta tsare mata a duniya data zabi ta cutar da ita cuta mafi muni tayi mata qazafin Lesbian, Lesbian fa? Tasan girman Zunubinsa Neman Jinsi kuwa laifi ne babba wanda akansa aka halakar da Al'ummar Annabi Lud. Dabi'ace da ko cikin dabbobi basa aikata ta se a cikin mutane gafalallu da suka rigada suka juyar da zukatansu daga neman Rahamar Ubangiji. Number Jalilah ya shiga kira a ransa yana tunanin toh a ina har Khausar ta samu numbobin yan gidansu dukka dan idan yaji daidai har Hajiya Jalilan tace an turawa, tana dagawa yace "Jalilah yaushe ta turo muku da wannan saqon, bama wannan ba a ina ta samu numbobinku kinsan yarinyar data aiko ne?" "Bangane a ina ta samu numbobinmu ba kuma Umaiman zaka ce na sani kana cikin hankalinka kuwa Khalil?" Jalilah ta fada cikin mamakin kalamansa da basuyi kama da yasan me yake fada ba. Se ya tsaya cak yana maimaita Sunan Umaimah a zuciyarsa, Umaimah fa yaji tace Umaimah dai wadda ya sani ko kuma wata shaidaniyar aka samu me irin sunanta? Sabida ya tabbatar yace mata "Wace Umaimah haka ta gaya miki sunanta?" "Karka rainamun wayo Khalil, Umaimah nawa muke da ita banda matarka? Daman ta fada tace idan ka sani qaryatawa zakayi ashe kuwa dagaske ne gashi kana neman ka rainamun wayo ka nuna itama baka gane wa nake nufi ba. To wallahi ba'a zuri'ar mu ba, idan aure kake so kaje ka nemo yar mutunchi amma ba zaka kwaso mana kara da kiyashi ka kawo mana ba" Jalila ta fada cikin qunar ran jin ze raina mata wayau. Cikin tsawa Khalil ya mayar mata da cewa "Ya isheki malama, yanzu saboda kema bakida hankali har Umaimah ce zata gaya miki abu ki hau ki zauna saboda baki san halinta ba ko? Ita Umaiman a ina ta jiyo wannan maganar kuma yanzu bayan ku se waye ya sani?" "Tabbas abinda take fada ya tabbata tunda gashi har mara hankali kake kirana saboda asirin lalatacciyar da kake neman kwaso mana ya tonu, daman ginin daka digirgiri hankali ka tada ita zaka kawo kusada mahaifiyar mu ka goga mata bala'i ana neman Mata a cikin gidan da take ko? to ka kirani da komai ma kai kajiyo amma wallahi baka isa ba. Ko asiri tayi maka se mun karyashi kuma da ni nace kar a gayawa Hajiya amma yanzu da kaina zan tafi na gaya mata yau base anjima ba tunda naga akamar baka san me kake yi ba" Jalilah ta hayayyaqo masa se yaja tsaki,hannu ya sa ya dafe kansa daya dauki ciwo lokaci daya kafin yace "Qarya takeyi wallahi sharri sukayi mata kuma itama Umaiman bayin kanta bane na sani sakata akayi amma duk ma wanda yake da hannu a cikin wannan al'amarin wallahi bazan barshi ba, sena bi mata haqqin bata mata suna da sukayi kuma karki kuskura ki gayawa Hajiya komai kinji na gaya miki idan kuma kika fada kika tayar mata da hankali shikenan" "Ba shakka Khalil to Allah ya taroka dan naga alamar ka zauce" Jalilah ta fada kafin yace wani abu ta kashe wayarta a ranta tana gasgata zancen Umaimah datace yasan komai akan maganar. Badan tana tsoron ta zama silar motsawar Hawan jinin Hajiya ba da a daren nan zata je ta gaya mata amma dukda haka se ta sani dan ita kadaice zata iya hanashi auran nan ya hanu. Khalil kuwa tana kashe wayar layin Umaimah ya kira, bata daga ba harta katse ya sake kira sannan ta daga ta bashi Uzurin Alwala takeyi Ankira sallah. Seda yayi namijin qoqari gurin danne bacin ransa ya saisaita muryarsa yace mata "Kunyi maganar Hadiza da Khausar ne?" UMAIMAH Ranar da take jira ce tazo gashi ya kawo kansa da kansa dan haka yanzu za'ayi maganar, shigewa daki tayi ta zauna gefen gado wutar kishin daya qyastawa ashana ta shiga ruruwa a zuciyarta tace "Daman ina jiran Allah ya kawo ranarda kai da kanka zakayi mun zancen yar iskar karuwar da kake nema a matsayin mata. Ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan ido na toh Asirinka ya tonu munafikin Allah dakai da yar iska ragowar Maza da Matan da kake nema. Wallahi kaji kunya Khalil, in ma mace zaka nema ka nemi me aji mana amma se yar Lesbian dabba me neman jinsinta" "Ya isheki Umaimah" Khalil din ya daka mata razananniyar tsawar da seda taji dan cikinta ya juya kafin yaci gaba da cewa "Tambayarki nayi kunyi magana da Khausar kuma naji amsata, sannan ina so ki sani ita Wadda kike kira Dabba karuwar tafi ki sau dubu a gurina, ban taba sanin wawiya ceke mara tunani ba se a wannan karon Umaimah, kinsan girman laifin da kuka aikata kuwa? Kinsan girman qazafi kuwa qazafi ma mafi muni saboda ke Mahaukaciya ce a hada kai dake a ruguza rayuwar yar uwarku mace, To ki shirya kin tayata kun lalata rayuwar wata a dalilina yanzu kece next target dinta, sannan ki shirya karbar sakamakon abinda kika aikata nan bada dadewa ba" yana kaiwa nan ya datse kiran wayarsa wata irin tsanar Umaimah nayi masa dirar mikiya. Zare wayar tayi daga kunnenta tana so ta tabbatar da Khalil tayi magana ko kuwa wani ne yayi mata basaja. Ita Khalil yake kiran karuwarsa ragowar Mata ta fita daraja a gurinsa? Anya ma kuwa yana cikin hayyacinsa? Neman guri tayi ta zauna saboda yanda taji kanta yana juya mata, ita Umaimah dai har tayi lalacewar da Khalil ya zabi karuwa akanta kuma yake iqirarin zeyi shari'a da ita saboda wata banza, ai kuwa seta tabbatar masa da be gama sanin wacece Umaimah ba, fili zata siya a gidan Radio da Jarida ta buga labarin idan yaso ya kaita Majalisar dinkin duniya ma qarewar Shari'a. Qwafa tayi tasaka Hijabi ta tayarda sallar da sam babu nutsuwa a cikinta saboda hankalinta gaba daya yana ga daukar fansa. Tana idar da sallarta kira Rufaida, a taqaice tayi mata bayani Rufaida ta janyo Jimlar Ashar ta dire kafin tace "An dira ki da ka Umaimah, kinfa san daman masu neman matan nan babu wanda ya kaisu bin Malamai da haka suke Asirce Yaran mutane suna lalata su toh Wallahi Khalil ma ta gama dashi dan dai kinsan da hankalinsa da mutunchinsa baze taba bari ko gaisuwa ta hadashi da irin matan nan ba. Se kin tashi tsaye kin rabasu in kuma ba haka ba kinaji kina gani za'a kwaso miki jangwangwama" "Ai wallahi ko zan tafi tsirara Khalil be isa ya aureta ba, bama ita ba duk wata mace me daura zani da dankwali ita da Khalil sedai hange daga nesa dan nawa ne ni kadai ba Asiri ba ko tsafi Mace takeyi sedai ta gaji amma Khalil yafi qarfinta, ni kinga gobe inda ranka zan tafi na kai musu rahoto har address din unguwarsu dana inda take aiki duk zan hada na basu, badai Mahaukaciya ya cemun ba? Zega qarshen hauka kuwa" Umaimah ta fada se Rufaida tayi saurin tareta da cewa "Aa karkiyi haka, wannan ma da mukayi ya isa. Ki ga ki bari gobe zanzo mu zauna se musan abinyi na gaba. Amma Su Mama basu san labarin nan ba ko naji baki ce komai ba?" "Oho in ma sun sani banji kowa yayi zancen ba, jiya nema da Maman Asad tazo take maganar wai ta gani a Facebook suka taru sunata surutansu wai wadda ta yada bata kyauta ba wanda ya rufawa wani Asiri shima Allah ze rufa masa a raina nace kanku akeji na shige daki, duk tsiya dai zasu sani idan ta fashe kowa zeji ai" Umaiman ta sake fada daga nan suka qarasa shiryawa akan Gobe Rufaida zata zo dan haka ta dakata karta dauki wani mataki har se sun tattauna sannan. Khalil Be taba zaton rashin tunaninta yakai haka ba, koda ace Khausar ce ta shirya komai Umaimah tafi kowa laifi tunda ai ba mahaukaciya bace ita ko qaramar yarinya da bata san me takeyi ba, tayi amfani da wauta da rashin tunaninta ta sakata a matsala dan yanzu duk inda akaje aka dawo Umaimah ce a ciki ita za'a kama da laifi ba Khausar ba. Tunanin kiran Khausar din yazo masa har yayi dialing number ya katse saboda yanzu idab har tasan yasan da hannunta a ciki zata nemi hanyar kare kanta ne, gara ya rabu da ita ta yanda z samu dama ya kanata a hannu cikin sauqi. A daren ya hada dan abinda zeyi amfani dashi, yasan akwai jirgin Nigeria gobe dan a cikin wadanda suke aiki akwai wanda zasu taho goben take shima ya yanki ticketz ya rubuta uzurin cewar buqatar gaggawa ta same shi ta zuwa gida washe gari kuwa qarfe sha biyu na rana tayi masa a Kano bayan ya sake hawowa jirgi daga Lagos inda suka sauka. Already Jalilah daya gayawa dawowar tasa tana jiransa a Aipirt, ita ta dauke shi kai tsaye yace mata Na'ibawa zasuje yana mata kwatance har suka isa qofar gidan su Hadiza. Kasancewar rana ta kwalle babu yaro ko daya a layin dan haka ya rasa wanda ze aika yayiwo masa sallama da ita seya koma yacewa Jalilan ta shiga ita ciki haka kuwa akayi ta shiga gidan da sallama aka amsa mata daga cikin daki ta qarasa qofar inda taga takalma a zube ta shiga. Maman Hadiza na kwance akan Qaramar Katifa da aka shimfida mata a tsakiyar palour, idan ka santa a da ka ganta a tsakanin kwanaki biyu da faruwar abin bazaka gane ta ba. Ta zabge lokaci daya tayi wata irin rama idanunta sun koma ciki zagayensu yayi baqi saboda tsabar Kuka da damuwar data saka kanta a ciki. A lokacin da Jalilah ta shiga ta tarar da Manyan Mata guda biyu tareda ita se Matashiya da zasuyi Sa'anni a gefe tana ballo magunguna. Maganar daya daga cikinsu ta tsinta tana cewa "Se kace ba Musulma ba Karimatu ace kin kasayin tawakkalli ki karbi qaddarar da ubangiji ya dora miki, wannan wane irin abu ne, bafa kanki aka fara ba. Jarabawar ubangiji babu ta inda bata riskar bawa se ke ce zaki kasa karbar taki kiyi haquri yanzu ance ba'asan inda yarinya take ba kin kadata duniya me kikayi kenan ina kikeso taje kinga yanzu duk abinda ta aikata idan ma da gaske ne kinada kamasho a ciki" se dayar tayi saurin cafewa da cewa "Ballantana ma wallahi Innani ko Qur'ani aka bani zan iya rantsewa da qaryane ba halin Hadiza bane. A wannan zamanin irin wannan sharrin ai ya zama ruwan dare. Babu damar aga mace ta kama kanta bata kula kulen maza Allah ya rufa mata asiri se magauta sun sakata a gaba sun bibiyi rayuwarta da sharri. Nan kullum idan ta gayamun abinda qawarta take zuwa tana fada akan ta me nake cewa? Ce mata nakeyi idan har Gaskiya ne abinda take fada akan Hadizan to itama halinta ne tunda tare suke komai duk inda zasuje tare suke zuwa, sannan har ta zagayo ta kawo mata gulma da munafunci kuma ta hau kai ta kasa yarda da yar data haifa ta raina ta yarda da maganar wata maqaryaciya me suffar munafukai. Bana raba daya biyu ma ko wannan abun da saka hannunta ciki dan ai babu dadewa Akayiwa Hadizan qarin matsayi kuma ance wannan din ita taso ta samu. Sannan an dade ana yamadidi a unguwar nan akan tana zargin Hadizan na mata kwacen samari duk wanda suka hadu daya ganta se ya koma kanta toh ba dole ba tana yawo da fuska kamar duwawu ga fara kyakykyawa ko wannan qyashi da hassadar ma yasa ta iya aikata mata komai wallahi" "Kuma fa Barira kinyi tunani me kyau, to wai duk wannan abin ma an tsaya anyi bincike an tabbatar da sahihancin maganar an ji daga inda labarin ya bulla kuwa se neman kashe kanki kika zauna kinayi?" Wadda aka kira da Innani ta sake fada, ganin da Jalilah tayi kamar sun manta da shigarta itama kuma ta samu labari tayi shiru se tayi gyaran murya suka kalketa gaba daya Barira tace "Sannu baiwar Allah, ke kuma wacece daga ina? Jajen gaskiya kikazo ko kuwa kuwa kema gulmar ce ta kawoki ku taru ku sake turata daman ga alama nan kin shigo kinyi muqus kina kwasar zance to ta Allah bata ku ba, kuma duk me yunqurin ganin bayan Hadiza sedai yaga bayan kansa wallahi" "Haba Barira me yayi zafi haka" Innani ta fada kafin ta juya kan Jalilah data sadda kai qasa tace "Yi haquri baiwar Allah waceceke kuma meya kawoki?" Kallon Maman Hadiza Jalilah tayi cike da tausayi tace "Sunana Jalilah, munzo gurin Hadiza ne tareda dan uwana Khalil yana waje ko zamu iya ganinta dan Allah?" Daga kwancen da Maman Hadiza take ta daga kai dakyar tana kallonta tace "Bata nan, kuma ki gaya masa karya sake zuwa nemanta gidan nan ko kuwa beji abinda take aikatawa bane?" "Wallahi Karima kika sake wata magana mara dadi a nan sena saba miki" Innani ta fada cikin bacin rai, seta juya tana kallon Jalilah tace "Wanene Khalil?" "Shine saurayin daya gama bata mata lokaci har nake gaya muku ta samu Miji se daga baya yace baze aureta ba. Waya sani ko tun a sannan shi ya gano mugun halinta mune bamu sani ba" Maman Hadizan ta sake fada nan kuwa daga Innani har Barira sukayi kanta kamar zasu daketa ta fasa musu kuka tana kiranta su qyaleta taji da baqin cikin da take ciki a qyaleta duk saboda ba yar suce ta jawo musu wannan tashin hankalin a shi yasa suke cewa tayi shiru Jalilah ganin abin nasu yana neman ya zama rigima ya saka ta sulale ta fice daga dakin zuciyarta na tsinkewa, a yanda Khalil yayi mata bayani Umaimah da wata wadda bata sani ba sune silar komai yanzu ina zasu kai haqqin wannan yarinyar? Ko iya munanan kalaman da Mahaifiyarta tayi akanta sun isheta banda tarin ala tsine datake sha a bakunan mutanen gari dukda da yawan wadanda suka santa suke mu'amala da ita sun qaryata amma kamar yanda aka fada ne laifi bashida kama dan haka duk wanda yaji labari seya gasgata alhalil qaryace. Hassada ce ta qawa da baqin Kishi na matar Saurayinta suka jefa rayuwarta cikin gararin da Allah kadai ze iya fiddata. Yau koda ace gaskiya ta bayyana ba kowane ze yarda cewar sharri aka mata ba, tabbas wata shari'ar se a lahira. Hannunta da Khalil ya kama ne yasa ta gane ta fito daga gidan, "Naga kin dade, ina Hadizan?" Ya fada cikin qaguwa seta bude baki zatayi magana daidai nan Anty Bilkisu da tunda ta shiga bataji tace komai ba ta qaraso gurin, takadda ta miqa mata tana cewa "Gashi tana wannan Asibitin kuje zaku sameta" ta juta dasauri saboda bata so wani ya ganta. Kwatancen Asibitin sukabi Khalil ne yake tuqi kamar ze tashi sama saboda sauri. Harda room number a jiki shiyasa basu sha wahalar gane dakin ba, tundaga waje yake jiyo kukan Hadiza da maganganunta da yake jinsu tamkar zubar ruwan zafi a zuciyarsa. Umaimah ta cuceta bata kyauta mata ba, idan Hadiza bata yafe mata be san yanda zata qare da haqqinta ba. Tura qifardakin yayi daidai sanda take cewa "Waye ze wankeni? Na tabbata rayuwata tazo qarshe Umma saboda banida sauran wanda ya yarda dani. Uwar data haifeni ta kasa shaidata, mutanen da nake tare dasu sun kasa shaidata me yayi mun saura? Wallahi dana san abinda duniya take kallona dashi kenan da tunda na fita bazan dawo gida ba, gara na hau Titi na tsaya mota ta taka ni na mutu dana ci gaba da rayuwa mutane suna kallona a matsayin me aikata mugun fasadi. Lesbian fa Umma Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ta qarasa tana girgiza kanta da take jinsa kamar ze rabe biyu saboda ciwon da yake mata. Malama Lawisa ta riqota tana zubda hawayen tausayin Hadizan hatta da Khalil da Jalila dasuka shiga kasa riqe hawayensu sukayi. Dakyar ya iya qarasawa jikin gadon cikin dakiyar daya aro dakyar ya sakawa ransa yace "Ki dena fadar haka Hadiza kin sani ko duniya zata taru akanki ni zan tsaya miki. Idan kowa ya yarda kin aikata ni nace qaryane qazafi akayi miki kuma bazan bar duk Wanda yake da saka hannu a ciki ba sena bi miki haqqinki. Ki dena kuka kina Asarar hawayenki na rantse da Allah sunanki baze baci a banza ba nine sila kuma zan share miki hawayenki". Kasa dagowa tayi ta kalleshi ta kife kanta jikin Malama Lawisa tana kuka me karyar da zuciya, Jalilah ta qarasa ta dafa bayanta cikin muryar kuka tace "Kiyi haquri kinji Allah yana tareda me gaskiya". Seda sukayi dagaske kafin ta tsagaita da Kukanta, kallonta Khalil yakeyi wani tausayinta yana narka zuciyarsa shidai soyayyarsa bata qareta da komai ba se wahala da tashin hankali. Shi bata samu biyan buqata daga gareshi ba sannan ana bibiyar rayuwarta da sharri duk a sanadiyyarsa. Kallon Malama Lawisa yayi se a sannan suka gaisa yake tambayarta game da jikin nata tace masa da sauqi, tsagewar qashin data samu ce kadai yanzu ta jininta da bugun zuciyarta sun daidaita sedai Likitan yana ta jaddada mata akan a kula da duk abinda ze bata mata rai. Kai ya daga alamar ya gane ya sakawa Hadiza ido ta sauke kanta qasa har dannan hawaye basu bar digar mata ba. Se Malama Lawisa ta miqe tana cewa "Bari nayi alwala naji ana kiran Sallah Jalilah ma ta bita suka fita daga dakin ya rage daga ita se shi. "Kiyi haquri Hadiza nasan nine silar komai daya sameki" ya sake fada yana zama a inda Malama ta tashi, Hadiza ta kalle shi da idanunta da basa buduwa dakyau ba tareda tace komai ba "Ki kwantar da hankalinki nayi miki alqawarin bazan zauna ba sena gurfanar da duk wanda yayi miki sharri sun wanke ki da bakinsu sun fadi cewar sharri sukayi miki" Khalil ya sake fada, seta bude baki dakyar tace "Khausar ce ko?" "Ba ita bace, amma ita ce sila, Ita ta shiryawa Umaimah komai ita kuma ta aiwatar" Khalil ya fada ba tareda ya bari sun hada ido ba, besanya zata dauki abun ba idan taji cewar matarsa ce silar shiga damuwarta. Ga mamakinsa se ji yayi tayi murmushin daya tabbatar na baqin ciki ne tace "Tazo gidan mu amma bamu hadu ba" "Ita ce ta watsa hotunan a social media, zan bi miki haqqinki gaba dayansu se sun fuskanci shari'a dole a kwatar miki haqqinki" Khalil ya sake fada, seta zame ta kwanta tana cewa "Na yafe musu, kai su gaban shari'a ko akasin haka babu abinda ze chanza, shi mutunchi tamkar madara ne sun rigada sun bararmun da nawa ba kuma zan qullace su ba dan dukkanninsu suna da dalilinsu na aikata hakan". Kallonta kawai Khalil yakeyi saboda Mamaki ya kasa ce mata komai, ta yaya zata yafewa wanda yayi mata wannan mummunan qazafin? "Amma Hadiza..." "Ni sukayiwa kuma nace na yafe, Allah ya yafe mana gaba daya" ta sake katse shi sannan ta juya masa baya saboda wani Kuka daya taho mata ba kuma tason ya gani. Sam bata ji haushin Umaimah da yace ba, bata santa ba tasan haka kawai bazata qirqiri abu ta liqa mata ba Khausar ce silar komai daya faru. Tunda take da ita koda wasa bata taba sanar da wani irin rayuwar da takeyi ba saboda roqonta da tayi akan ta rufa mata asiri kuma ta tayata da Addu'a saboda ta dena, ta riqe mata amana haka zalika bata taba yin sallah ta tashi ba tareda ta roqar mata yafiyar ubangiji tareda shiriya ba amma shine ta rasa abinda zata saka mata dashi seta bibiyeta da sharrin abinda ita take aikatawa? Amma ba laifinta bane, laifin kanta ne data ci gaba da Mu'amula da ita har bayan tasan zahirin wacece ita, gashi yanzu ta shafa mata baqin fentin da har abada baze taba gogewa gaba daya ba amma yaqinin daya take dashi Allah yana madakata yana jiran kowa da komai. Gajiya Khalil yayi dayi mata magana tayi shiru kamar me bacci, yana kallonta yace Zanje gida na huta dan dawowata kenan daga SA ko gida banje ba na wuto nan, zan tafi amma ki sani koda kince kin yafe ni bazan haqura ba dole na dauki mataki akai" "Kaje amma karkace zakayi rigima da matarka saboda ni, Sonka da kishinka ne suka saka ta aikata komai da taimakon wasu kaga laifi bana ta bane ita kadai" Hadizan ta sake fada ba tareda ta kalleshi ba dole ya juya ya fita daga dakin, a waje ya tarar da Malama Lawisa da Jalilah suna magana yayi mata sallama yayi gaba Jalilah ta bishi. "Wai ta yafe musu tace" ya fada yana kallon Jalilah dake tambayarsa yanda sukayi da Hadizan, bude ido tayi tana kallonsa kafin cikin wani yanayi tace "Allah sarki anyi mata mummuna ta saka fa Kyakykyawa ubangiji ya saka mata da mafiyin haka. Anyi amfani da kyakykyawar zuciyarta an cutar da ita. Na tabbata irin wannan halayyar tata ce har ta bawa qawar tata damar cutar da ita ba tareda ta sani ba ita Kuma Umaimah bata kyautawa kanta ba, ban taba zaton koda wasa zata iya aikata kwatankwacin sakarci irin wannan ba ita yanzu koda ace dagaske ne ya kamata ka yayata irin wannan abin a duniya? Idan baka rufawa dan uwanka Musulmi Asiri ba ai baka kuma bankadashi kowa ya sani ba" "Hmmm kawai Khalil yace dan idan ita tace ta haqura shi be haqura ba, Umaimah ta dade tana abubuwa yana shanyewa, idan har zata iya yiwa Mace sharri irin wannan ba tareda tana da hujjaba gaba besan me zata aikata ba. Dole ya taka wa abin burki ya kuma dauki mataki daidai wanda ya dace da laifinta, A hanya suka rabu da Jalilah tasauka ta bar masa motar ya wuce yana sake jaddada mata akan karta bari kowa yasan da zuwansa ko halinda ake ciki. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 44 Gidansu Umaimah ya nufa kai tsaye, yana so ya fara tattara hujjojin da suke hannuntaa kafin ya hada Khausar da Umaimah da hukuma su girbi abinda suka shuka. A qofar gida ya tarar da Ummu-Salma da Yasir kowanne fuska face face da hawaye, ya kashe motar ya fito yana tambayarsu lafiya Yasir ya tafi da gudu ya fada jikinsa yana cewa "Yan sanda ne suka zo suka tafi da Antyn Boy boy" ya sake rushewa da Kuka. Kallon Ummu-Salma yayi cikin rashin fahimtar maganar Yasir yace "Meya faru Ummu? Ina mutanen gidan kuke kuka haka?" Ita tayi masa bayanin yan sanda ne sukazo suka tafi da Anty Umaimah, se sannan ya tuna Mu'ayyad suke cewa Boy boy, da sauri ya tambayeta me tayi ta watsa hannu alamar bata sani ba kafin taci gaba da gaya masa su Mama da Anty sun bisu, Yaya Aminu ne ya tafi kaisu dan Abba bayanan ya tafi daurin aure Qiru. Dafe kansa yayi da hannu daya dayan yana riqe da Yasit dake rusa kuka kamar wanda aka ce Umaimah bazata dawo ba. Seya zaro wayarsa cikin rashin Sa'a ta mutu daman babu wadataccen chaji a ciki ya taho. "Kina da waya ki kirasu muji inda suka tafi?" Ya tambayi Salma tace "Aa, amma wayar Anty Umaimah na daki bata tafi da ita ba ko na dakko maka?" Kafin ma ta kai qarshe yace eh. Ta ruga gida da gudu ta dakko wayar ta kawo masa ya karba ya bude dan yasan password dinta. Number Yaya Aminu ya kira cikin Sa'a ya daga suka gaisa yake sanar masa gashi a gida su Yasir sun gaya masa abinda ya faru suna ina ne? "Daga dawowarka se kaji tashin hankali kuma, muna state CID wallahi yarinyar nan ce ta jangwalowa mutane bala'i ana zaune lafiya" Yaya Aminu ya fada kana jin muryarsa kasan yana cikin matuqar bacin rai, cikin Jimami Khalil yace masa gashi nan zuwa. Ya kalli Ummu-Salma da Yasir da suke jiran su bishi yace "Ku shiga gida yanzu zanje na same su acan" "Dan Allah zamu bika Yaya" Yasir din ya fada se ya kama hannunsa yace "Aa ba'a zuwa da yara shiyasa ma kaga ba'a tafi daku ba. Kuma idan mun tafi gidan a bude babu kowa kaga za'a shiga ayi barna. Ku koma ciki ku zauna yanzu zamu dawo ba dadewa zamuyi ba kinji?" Suka amsa da "Toh". Seda suka shiga gidan kafin ya tada motar ya bar gurin. Tunani yakeyi a ransa me kuma ta sakeyi da aka kaita CID? Shikan Bala'in Umaimah ya fara shallake tunaninsa ace mace kamar Shaidan, daga wannan fitina se wannan gaskiya da sake, baze iya ba. Ya isa CID ya tarar dasu Mama a waje duk wanda ka kalli fuskarsa kasan cikin tashin hankali yake. Abinda ya qara daure masa kai ganin Dr Ma'aruf Mijin Rufaida a gurin kenan tare suka jangwalo Koma menene shi daman ya tsani wannan qawancen nasu, ya rasa abinda yasa Umaimah bata sa'ar qawaye a rayuwarta duk kuma na kirkin daya santa dasu irin Su Rumasa'u ta dena hulda ta kusa dasu se abinda ya zama dole ko idan su suka kawo kansu sannan zeji tayi zancen su ko makamancin haka. Se taron marasa tunani irinta da babu meyiwa wani fada idan yayi ba daidai ba a cikinsu. Yaya Aminu ne yayi masa bayanin suna ciki yanzu qoqari sukeyi a basu damar su gansu a kuma yi musu bayanin laifin da suka aikata amma dai kamar yanda sukaji wai Qungiyar masu kare haqqin Mata da yara ne suka shigar dasu qara dalilin me dai basu kai ga sani ba. ABINDA YA FARU Tun bayan da aka fita da Hadiza zuwa Asibiti dakyar Isma'il ya iya tausar Mama wadda itama jininta ya haye saboda damuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ranar a gidan ya kwana bayan ya kaita Asibiti sun dawo seda akayi mata Allurar bacci saboda ta kasa dena kuka. Adaren kwana yayi yana sallah da Addu'oi akan Allah ya bayyanar da gaskiyar wannan al'amari, washe gari ne iya zuwa aiki ba a nan gidan ya sake wuni saboda mutane magulmata da suke shigowa gidan da sunan Jaje suna qarawa Maman damuwa dan haka ya kasa ya tsare ya hana kowacce Mace shiga har sannan kuma basu bi ba'asin jin inda aka akai Hadizan ba. Wurin qarfe biyar na Yamma ya kunna wayarsa da tun bulluwar labarin ya kasheta ya ajiye saboda yanda mutane suke kiransa suna sake tura masa da hotunan abin har mamaki yake bashi tamkar masu turo masa abin Alkhairi. Kirane ya shigo da baquwar number, a True caller yaga sunan me Kiran Musa Sale (SAN) aka rubuta, har beyi niyyar dagawa ba haka nan wata zuciyar tace ya amsa se ya daga wayar ya saka a kunne da sallama daga dayab bangaren me kiran ya amsa masa suka gaisa yana qoqarin tuna inda yasan muryar amma ya kasa. "Sunana Barr Musa Kallah, kuma nine shugaban Lauyoyi masu aiki qarqashin hukumar kare haqqin Mata da Yara ma'ana hukumar da yar uwarka Hadiza take aiki" Mutumin ya fada cikin kamilalliyar muryarsa data ke bayyana ba yaro bane shi. Isma'il ya gyara zamansa a ransa yana ayyana dalilin kiran nada nasaba da abinda ta aikata kuma yasan korar ta sukayi daga aiki se yaji yana cewa "Idan ba zaka damu ba inaso mu hadu da kai muyi magana akan abinda yake faruwa da Yar uwarka ne" Ajiyar numfashi Isma'il yayi yace "Toh ranka ya dade nasan baze wuce takaddar sallamarta daga aiki bace zaku bada indai babu damuwa a dan bani lokaci na samu nutsuwa se nazo na karba saboda a halin yanzu Mahaifiyar mu bata da wadatacciyar lafiya kuma ni nake kula da ita" Se Barr Musa yayi yar dariya yace "Har ka yanke hukuncin dalilin kiran kenan to ba wannan bane ba, wannan na kiraka ne a qashin kaina dan akwai abubuwan da nake so na tattauna da kai domin samun damar warware matsalar da ake ciki, maganar mu bazata dauki lokaci ba, zama mu iya yinta a waya amma na zabi mu hadu fuska da fuska dan mufi fahimtar juna dan haka idanbabu damuwa ka samu wani ya zauna da Maman na dan wani lokaci kuma in sha Allahu abinda zamu tattauna ze saka ta samu rangwame cikin gaggawa. Zantura maka da Address din gidana kazo ka same ni idan kuma ni zanzo inda kake babu damuwa ka sanr dani inda zan same ka" daganan sukayi sallama akan Isma'il din zeje dan dukda be sanshi a fuska ba yasan ba Qaramin mutum bane ko iya matsayin SAN daya gani a sunansa ya wuce yace shi yazo ya same shi. Seda yayi Magriba ya cewa Maman zeje wani guri ya dawo ya barta da Bilkisu tareda Hajiya Zuwaira, a bakinta yaji zuwan Goggonninsu guda biyu Hajiya Barira qanwar Maman ce se Mama Innani ita kuma yayarta ce data ke bi, tuni suma labarin tashin hankalin ya riske su yasan rashin kyan hanya ne ya hanasu zuwa tun a jiyan dan ita Hajiya Barira a Zamfara take aure Mama Innani kuma tana Birnin Gwari ta Jihar Kaduna. Can Sharada NNDC yaje inda gidan Bart Musa yake, gida ne na alfarma dukda bashi da wani girman gaske amma ya tsaru iya tsaruwa kana gani palour gidan kasan me shi ya juqu a boko saboda yanda aka qawata gidan ya fito tamkar gidan turawa kuma babu wasu tarkace se tulin uban littattafi a kowacce kusurwa kan Shelfs masu kyau da aka kakkafa a bangwayen. Yara biyu Maza da sukayi masa iso ciki su suka kawo masa ruwa da lemo suka sanar dashi babansu yace yana zuwa, qaramin ciki ne ya qara da cewa "Waaya sukeyi da Momy amma sun kusa gamawa" babban ya harare shi yana cewa "Aku, waya tambayeka" daidai nan Barr Musa ya sakko daga matakalar benen dake can gefe a cikin palour sanye yake da Jallabiyya ruwan madara a qiyasin shekaru ze kai Hamsin da biyar zuwa sama ya qaraso ciki yana miqawa Isma'il hannu daya tashi tsaye shima yana kallonsa. Tabbas yasan fuskarsa yana yawan ganinsa a TV ko shafin jaridu shiyasa ashe yaji kamar yasan sunansa amma ya kasa tuna a ina. "Yi haquri fa na barka kana jira muna waya da Madam ne bata gari sunyi tafiya toh kasan su ba'a raba su da qorafi wai tunda ta tafi bamuyi wata doguwar magana ba shine fa yau na wanke laifina" Barr ya fada bayan daya zauna, Isma'il yayi dan murmushi ba tareda yace komai ba, shi ba wannan labarin yake so yaji ba dalilin kiransa kawai yake son ji. Kallon yaran Barr yayi yana cewa "Aa kai Baba ya zaku kawo masa ruwa da Lemo kadai baku da wani dan abin tabawa a gidan ne? Ina Amal bata gama abincin ba har yanzu kenan?" "Wannan din ma yayi ranka ya dade a qoshe nake ma banjima da cin abinci ba" Isma'il yayi saurin tare shi se Barr ya miqe yana cewa "Haba ai ko a qoshe kake dai ka dan taba wani abin" ya shiga kitchen se gashi sun fito tareda wata yar budurwa da gani ita ce yar tsakiyar Samarin sun jero ya dago kanta tana cewa "Dady soyawa fa na tsaya yi, seda nace su bari a hado duka suka qi kuma Baba ne" ta ajiye a gaban Isma'il kafin ta durqusa har qasa ta gaishe shi ya amsa yana kallonta dukka yaran da Baban suke kama sedai su Farare ne sabanin shi da yake baqi. Zama Barr yayi yana cewa "Bismillah Malam Isma'il ka sha ruwa se mu fara abinda ya ajiye mu ko?" Isma'il ya cika kofi da Ruwa ya kwankwade dan shi kadai ne abinda yake iya shiga cikinsa tunda suka shiga wannan tashin hankalin gaba daya ya fita hayyacinsa, yayi wata rama ta farat daya kana ganinsa kasan bashida nutsuwa. Gyaran murya Barr yayi kafin ya dora da cewa "Gaba dayan mu munsan abinda ya faru so maimaitawa bashida wani amfani. Bayan na shiga Office a jiya na samu saqon cewar an dakatar da Hadiza daga aiki dukda na rigada na samu saqon abinda yake faruwa amma abinya bani mamaki saboda idan kayi la'akari da zamaninda muke ciki a yanzu wannan abin ba wani sabon abu bane da har ze janyo cecekuce irin wanda naga anatayi kuma har ace an dakatar da ita daga aiki, kar kayi mun mummunar fahimta" Barr ya fada ganin yanda Isma'il yake binsa da wani kallo se ya ci gana da cewa A nan cikin Ma'aikatar tamu da akwai Mata harda Maza masu irin wannan dabi'ar, wasu mun sansu wasu bamu sani ba kuma ana ci gaba da aiki tareda su ba tareda nuna musu wani abu ba shine tambaya ta farko dana farayi me yasa aka dauki matakin Korar Hadiza bayan ba ita kadai bace me irin wannan dabi'ar idan ma har da gaske ne abinda ake fada akanta? Amsar da suka bani duk wanda yakeyin nasa yana yi a boye ne, kuma ba'a taba kamasu da wani abu daya shafi aiki ba amma ita nata ya fallasu a gari kuma abin har ya fara shafar Qungiyarmu da yawa har suna cewa dalilin daya saka suke kashewa Mata aure kenan suna bude musu ido su koya musu karuwanci, ada ana rade radi ne amma yanzu gashi an sami tabbaci akan daya daga cikin ma'aikatan mu. Amma dai yanzu duk wannan ta rigada ta wuce, kuma mun shirya committee domin binciko mana gaskiyar wannan al'amari kuma Alhamdulillah a yanzu har munyi babban kamu da ze kaimu ga samun duk wasu bayanai da muke da buqata, ina nufin mun samu cikakkun bayanai akan wadda ta fara wallafa labarin a shafin Facebook, dukda ance daga WhatsApp aka fara samo shi kaga zeyi wahala mu iya binciko number data fara watsa labarin amma shi Facebook cikin sauqi mun gano wanda keda alhakin yadawar". Cikin qaguwa da surutan da Barr yakeyi Isma'il yace "Ina ganin idan har akan wannan ne ranka ya dade bakuda buqatar bata lokaci gurin binciken komai. Ni kaina da farko bayan da saqon ya riskeni seda na nemi kwararru da suke iya tantance hoton gaskiya da kuma wanda aka hada kuma na samu tabbaci daga gurinsu cewar hotunan gaskiya ne kaga duk wani bincike ma be taso ba tunda ga babbar hujja an samu. Baya ga haka daman tuntuni munsan Hadiza tanataba rashin jinta, kawai dai abinya riskemu ne a wani yanayi da bamuyi tsammani ba sannan kuma yanda labarinya watsu a duniya kaga ba ita kadai ya shafa ba illar abinda ta aikata kuma ze ci gaba da bibiyar mu ne da Ahalinmu gaba daya". "A haka dai gaka nan a haka kamar wayayye amma kalamanka sun nuna akasin haka" Barr ya fada kafin Isma'il yace wani abu yaci gaba da cewa "Yanzu kai ka yarda da qazafin da akayiwa yar uwarka kenan har kana kafa hujja da daman tana rashin ji, kana da shaida akan hakan? Yanzu zaka iya tsayawa a gaban Alqali ka bada shaidar cewa gaskiya ne abinda aka fada akanta ta aikata? Gaskiya ka bani kunya da har ka kasa shaidar yar uwarka da kuka fito ciki daya, uwa daya ta raineku tayi muku tarbiyya sedai idan kuma irin tarbiyyar da kuka tashi da ita kenan shi yasa baka zaka musanta duk abinda aka ce ta aikata ba". Da sauri Isma'il dake kallon qasa ya dago kai ya dube shi, Barr ya daga masa kai cikin tabbatarwa yace "Kwarai hakan ne kadai zesaka farat daya ka yarda da duk abinda aka ce ta aikata idan daman kasan akan haka ta ginu amma babu yanda za'ayi rana daya azo ace mutum yayi abu dukda ba'a shaidar mutum amma Akwai abinda idan an gaya maka akan wani seka tirza ka ciza ko kuma kaga kwakwkwarar shedar da babu wanda ze qaryata sannan kuwa amma kai ka kafa hujja da hotunan da nida kai munsan basu isa su tabbatar da zargin da akeyi ba. Kasan girman laifin da ake zargin qanwar ka dashi kuwa? Dani dakai duk musulmaine mun kuma san menene Madigo da hukunci da makomar me aimatashi a duniya da lahira. Yanzu idan kotun musulinci akaje se an samu Shaidun gani da iso guda uku wanda suka ganta tana aikatawa sannan ne katu zata karbi shaidarsu ta yanke mata hukunci ko kana zaton akwai alqalin da ze saurari wadannan shirman hotunan da ake yawo dasu ana mata qazafi akan su. Na tabbatar a cikin wayarka yanzu idanan duba se an samu wadanda suka fisu muni idan ba'ayi wasa ba. Nidakai mun sani ba wani abu bane a gurin yammatan yanzu daukar hotuna su bayyanar da sassan jikinsu su turawa samari kaima na tabbatar ba zaka rasa wadda take tura maka ba Nida kai munsan komai babu abinda zaka boye mun idan kuma qarya nakeyi ka kawo wayarka na kawo tawa a gani idan baza'a samu ba". Yanda kasan qasa ta bude Isma'il ya shiga haka yaji, se yake ganin kamar Barr yasan abinda yake cikin wayar tasa ne dan gaskiya ya fada Yammatan da suke tura masa da hotunan da videos dinsu na tsiraici bazasu irgu ba wasu ma bashi yake tambayarsu ba. Wata ma daga sama baka san wacece ba zata kawo maka tallan kanta kuma da yawa idan ka gansu seka rantse bazasu aikata hakan ba shi yasa yake kasa musawa idan Aka ce Hadizan ta aikata abu tunda yaga wadanda suka fita fuskar Salahai ma suna aikatawa. "Kayi shiru ko ba haka bane?" Barr ya katse masa tunani seya daga kai alamar haka ne ba tareda yayi magana ba. "Toh ka gani ba, dukda bani da wata doguwar Mu'amala da ita banyi mata sani na sosai ba amma kai tsaye ina ganin abin nace qarya ne. Akwai wanda idan an fadi abu akansa koda ba gaskiya bane kai tsaye za'a gasgata shi amma akwai kuma wanda se kayi dagaske zaka yarda yayi abu koda kuwa a gabanka ya aikata se kaji shakkun anya kuwa shidinne. Kuma irin wannan abin ba wai yanzu aka fara shi ba haka kawai mutane zasu samu hoto suyi ta yadawa da sharri kala kala qarshe idan zaka kamasu basu san ma mutumin dake jikin hoton ba ba kuma a san daga inda labarin ya faro ba dalilin da ya saka muke so mu daqile irin abubuwan nan kenan kuma zamu zurfafa bincike, duk wani wanda yake da saka hannu a ciki zamu gano shi sannan mu miqasu gaban shari'a tayi musu hukuncin daya dace dasu dan haka nanemeka, ina so kayi tunani ko akwai wani da kuke zargi da ze iya aikata mata hakan dukda na fada maka mun samu bayanan wadda ta wallafa abin a Facebook, amma bazamu dogara da ita kadai ba dan zata yuwu itama ta samo ne tayi karambanin dorawa a nan din". "Toh nidai a iya hasashena bazan iya cewa ga wani abokin fada da Hadiza take dashi ba da har ze iya yi mata wannan abin, hasalima ita ko qawaye bata dasu qawarta kwaya daya ce Khausar kuma itace wadda take fada mana daman duk irin rashin jin da takeyi a boye tunda ita koda yaushe suna tare a gida ko a gurin aiki kuma ko yanzun kafin na yarda da maganar seda na titsiyeta ta gaya mun gaskiya kuma ta tabbatar mun da haka din ne abinda Hadizan take aikatawa kenan" Isma'il ya fada a sanyaye dan gaba daya maganganun Barr sun sake dulmiya masa tunani sun kuma fara maido dashi kan hanyar daya kaucewa. Allah ya sani ba wai ya yarda da cewar tanayin bane sedan bashida hujjar qaryata hakan. Maganar Barr tace ta sakashi dagowa da sauri ya kalleshi jin yana cewa "Wannan ce Khausar din da kake magana ko" ya fada yana miqa masa screen din wayarsa daya kunna Video seya karba bakinsa yaqi rufuwa saboda tsabar mamakin abinda yake gani Khausar ce zaune a tsakiyar qartin maza sun kai biyar ta kwanta jikin daya daga ciki hannunta riqe da dogon pipe na shisha tana zuqa. Shigar dake jikinta tayi muninda kai tsaye ze iya cewa ba ita bace amma hasken gurin daya haska fuskarta tarwai ga sunanta da wanda yakeyin video ya ambata akan ta dago fuskarta yayi mata video ta kuwa dago tana wani shegen fari da ido besan lokacin daya fara maimaita Innalillahi a fili ba. Barr ya zare wayar daga hannunsa yana cewa "Se kayiwa kanka Alqalanci ka kuma dora maganganun da take gaya muku akan sikeli, abu na qarshe da zan gaya maka kaje ka taushi yar uwarka Ubangiji kadai yasan halin da take ciki kuma yanzu ne take da buqatar kulawarku da qarfafa guiwa, koda ace abinda akw yawo dashi akanta gaskiya ne a halin yanzu tana cike da nadamar abinda ta aikata kuma tana buqatar wanda ze tallafa mata yajata a jiki ya taimaketa ta bar abinda takeyi ballantana ita da akayiwa Sharri". Isma'il yayi shiru ya kasa cewa komai gaba daya kunyar kansa ce ta dabaibayeshu, ya akayi ya kasayiwa Tilon yar uwarsa uzuri koda na minti daya yaji ta bakinta? Tunda ake kawo musu magana akanta daga shi har Mama babu wanda ya taba bata damar da zata kare kanta sun kasa yarda da ita duk da daga shi har Maman idanza'a tsire su basu da shaidar da zata tabbatar da gaskiyar abinda suke zarginta dashi ko ake fada akanta suna yarda kawai zallar Son zuciyarsu ne yasa suke gasgata maganar wasu can daban sun kasa yarda da tarbiyyar dasuka bata, Allah sarki Alhajinsu ya tabbatar yau da yana raye baze taba juyawa Hadiza baya ba komai girman abinda ta aikata kuwa dan kamar yanda yake gaya musu a koda yaushe ba'a gyara laifi da laifi. Idan mutum ya aikata kuskure ana gyara masa ne ta hanyar janyo shi jiki a kyautata masa har shi dakansa ya fahimci kuskurensa kuma ya gyara amma sam su basu taba kwatanta hakan ba. "Karka ji haushin kanka saboda ko wanne dan Adam a rayuwa da yanda yake iya tunkarar damuwa. Wani yakan saka nutsuwa da tunani gurin warware damuwarsa wani kuma yanayi mata gaggawa, dan haka yanzu ka tashi kaje gida ka huta zuwa gobe in Allah ya kaimu, duk wani ci gaba da muka samu akan binciken zan sanar maka. Sannan ka lallabi yar uwarka ina sake jaddada maka ka bata qwarin guiwa akan duk abinda ze fuskantota a gaba, ta qaddara cewar wannan abin da ya faru jarabawa ce daga ubangiki idan tayi haquri ta cinyeta se ta zame mata sikar takawani matakine na Nasara da batayi tsammani ba" Barr ya sake fada kafin suka miqe gaba daya. Har bakin Get ya rakashi yana sake jaddada masa daya je ya taushi hadiza ya kuma bata haquri da kwarin guiwa. A hanya tunani Isma'il ya ringayi har seda kwallar tausayin Hadizan ta shiga zubo masa. Sam wani abu me kama da tausayinta be zo masa ba se a yanzu, a sanda abin ya faru wani mugun baqin ciki da tsanarta yaji sunyi masa dirar mikiya saboda yasan ta rusa masa shirin daya kwashe tsahon shekaru yanayinsa seda Mafarkinsa yazo dabda cika ya samu Tikitin tsayawa takarar Dan Majalisar Jaha wanda dakyar da roqon Allah damar ta samu se gashi wannan abun ya bullo wanda take Yan Adawa suka samu nayi suka fara sukar sa tun kafin bayyanuwar takarar tasa kowa yasanda ita. Zafin wannan ne ya sake ingiza shi yayi mata dukan da beqi ace ta mutu ba ko ya ji sauqin wani kaso na baqin cikin data qunsa musu. Gidan Mama ya wuce, ya tarar da Bilkisu ta tafi saboda dare ta baro yara su kadai se Hajiya Zuwaira da Wata Asabe itama maqociyarsu ce Hajiya Zuwairan ta kirata akan tazo ta taya Maman kwana kafin gobe su Mama Innani su iso tuni ma har tasha magungunanta ma bacci ya dauketa se su biyun suna zaune suna ta mayar da yanda akayi. Be zauna ba yayi musu sallama dan yana buqatar yaje gida ya harhada tunanin da suka tarar masa akai ko ze samu amsar abinda yake gabansa. Harya fita ya dawo, daga bakin qofa ya tsaya kamar baya son magana yana kallon Hajiya Zuwaira yace "Momy wane Asibiti aka kwantar da Hadizan ne?" Karkata kai Hajiya Zuwaira tayi tana kallonsa tace "Se yanzu zaka tambayi halin da yar uwarka take ciki Sama'ila? Ai wallahi banyi tsammanin haka daga gareka ba ko kusa ko alama kuwa. Idan hankali ya gushe ai nutsuwa ce take nemoshi fisabilillahi idan baka zama bango majinginarta ba wa kake so ta dafa tayi kuka a rayuwarta? Ka dagawa Mahaifiyarku hankali a maimakon ka kwantar mata sannan ka kama baiwar Allah da duka idan da abin yazo da Ajali ai yanzu ai wani zancen ake ba wannan ba shikenan saboda kaji abu da Allah kadai yasan Al'amari seka nemi Ran baiwar Allah nan duk da mukaje ceto babu wanda be fita da tabon ka ba akan meye eye? To wallahi kayiwa kanka fada kuma ka nemi yafiyarta, mugun bakin da ka saka uwarku ta ringayi mata idan baka saka ta gogesu qaiqayine ze koma kan masheqiya danbata da haqqinku daga kai Har Karimatun". Shiru yayi mata har ta kai qarshe kansa na qasa kafin ya sake maimaita mata tambayar da yayi ta harareshi tace "Se kaje ka tambayi matarka yarinyar arziqi ace har tafi ka qaunar Jininka ai wallahi wannan yarinya ta isa yar halak babu kuma abinda zamuce maya sedai muyi mata fatan Alkhairi kaje ka tambayeta zata gaya maka inda take" yana gama jinta ya saka kai yayi waje yana jinta tana cewa "Dan banza me shegiyar baqar zuciya". Washe gari gurin qarfe tara Barr ya kirashi yace yazo office dinsa, a can ya gaya masa an gano me Facebook account din Sunanta Rufaida Usman Hamza an kumayi tracing nata har gidan da take zaune sun gano yanzu haka qungiya ta rigada ta shigar da qara magana tana State CID dan basu yarda ma aje wani qaramin Division ba sunfi so ayi me gaba daya dan haka yanzu antura da Jami'ai zasuje su taho da matar. Yanzu zasu tafi can CID dinne dashi su jirayi zuwansu. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 45 Guraren goma da rabi Jami'an da aka tura suka dira a qofar gidan Rufaida suka kwankwasa qofa. Da yake Asabar ce Baban Anam yana gida yana zaune a palour yana kallon labarai A shirye yake dan fita zeyi Rufaidan ta tsayar dashi tana so ya sauketa gidansu Umaimah kamar yanda tayi mata alqawarin zata zo. Jin ana buga qofa ya saka shi fita ya bude yaga mutane biyu maza se Mace guda daya dukkansu sanye da baqaqen Suit. Daya daga ciki ne ya zaro ID card dinsa ya nuna masa kafin yace "Sunana Detective Ahalan Rano, kuma muna da takaddar izini ta tafiya da matarka me suna Rufaida Usman. Zamuje da ita can Office dinmu dan ta amsa wasu tambayoyi". Jikin Baban Anam ne ya dauki rawa dan shi irin mutanen nan ne masu tsananin tsoron hukuma shiyasa yake matuqar takatsantsan da duk abinda ze hada shi dasu. Jin cewar Rufaida suka zo tafiya da ita se ya danji dama dama dukda haka tunani ya shigayi na laifin me ta aikata har haka da akw nemanta a CID koda yake shige shigen Rufaida ai se Allah kullum fadan da yake mata kenan yanzu ga irinta nan Allah kadai yasan abinda ta jefa kanta a ciki. Kallon Detective yayi yace "Ranka ya dade ko zan iya sanin abinda ta aikata kuwa" "Gaskiya ba'a bamu wannan damar ba, amma kana iya biyo mu muje can dan kaji cikakken bayanin abinda ake zarginta dashi, please muna sauri ne ka shiga idan tana ciki kayi mata magana ko kuma mu tura da Jami'ar mu ta fito da ita" Detective ya fada fuskarsa babu alamar wasa. Jikin Ma'aruf ya sake daukar rawa ya shiga cewa "Toh toh bari na shiga yanzu zata fito" ya juya ciki Detective yayiwa Macen da suke tare alamar ta bishi suk shiga a kusan tare daidai nan Rufaida ta fito tana kullo qofar palour ta cakare da wani Dandasheshen Leshi ta kawo dauri gaban goshi daman yaran suna gidan su Ma'aruf din ta kalleshi tana cewa "Ina ka tafi ne na fito ban ganka ba bayan ka azalzaleni da nayi sauri" matar data gani a bayansa yasa ta gimtse maganarta se ya waiwaya shima dan bema lura da ta biyo shi ba ya hadiye yawu yana kallon Rufaidan yace "Gurinki sukazo, daga State CID suke zasu tafi dake ki amsa wasu tambayoyi" "Ban gane ba wa aka ce na kashe ko fashi da makami nayi da za'a kaini CID" Rufaida data saki jakar hannunta ta fada tana dafe qirji, matar ta nuna mata hanya tana cewa "Muje ba wani abun damuwa bane yan tambayoyi ne zaki amsa su da kin gama zamu sallameki" "Toh ki tambayeni anan mana baiwar Allah idan da gaske ne base munje can ba, na shiga ukuna dan Allah me aka ce nayi wallahi a rayuwata ko Office din yan Vigilante ban taba zuwa ba bare CID ki gaya mun waye ya kai qarata" Rufaida ta fada hannu aka tana tsalle kamar wata biri saboda tashin hankali, ganin tana neman bata musu lokaci ya saka matar kama hannunta ta fizge zata fada daki matar ta kalli Ma'aruf tace "Idan tayi gardama zan gaya musu su shigo su saka mata ankwa, kuma zamuyi waya a zo da Hilox da Yan sanda masu uniform su tasata a gaba kaga yan unguwa gaba daya se su san abinda yake faruwa. Na gaya mata ba wani babban abu bane bincike ne ya fado ta kanta idan har mukaje ta fada mana gaskiya zamu sallameta tayi tafiyarta. Jin da tayi za'a saka mata ankwa a sakata a bayan mota ya sakata tafiya tana matse hannaye idonta har ya fara hawaye ta kalli Ma'aruf tace "Amma tare zamuje ko?" "Ina? Kuje kawai ai sunce ba dadew zakiyi ba in kun gama se kimun waya nazo na daukeki" yayi saurin bata amsa. Dariya ya bawa matar dan gani tayi har yafi Rufaidan rikicewa tace masa "Dagaske ba wani abu ne me zafi ba, ka bimu zata fi samun nutsuwa tayi abinda ake so". Dakyar da sidin goshi Ma'aruf ya bisu a baya da motarsa. Sun isa aka shigar da Rufaida wani daki, wani Jami'i da fuskarsa sam babu Rahama ya ajiye mata hoton Facebook profile dinta da sukayi printing da kuma na posting din hotunan Hadiza data saka yana kallonta da jajayen idonsa ya tura mata profile din yace "Wacece wannan?" "Nice, Facebook dina ne" ta bashi amsa a tsorace tana matse fitsarin dake neman zubo mata tunda tayi arba da fuskarsa. Na post dinya tura mata kafin ma yayi magana tace "Maqociyata ce Umaimah, tace wannan din budurwar Mijinta ce kuma wata ce ta tura mata hotunan tace mata yar Lesbian ce. Ita kuma saboda ya fasa auranta yasa ta watsa su a social media, na rantse da Allah iya gaskiyar abinda na sani kenan idan kuma baku yarda ba ga wayata nan ku duba zaku ga sanda ma ta turamun harda groups dinmu na WhatsApp data tura a ciki zaku gani". Isma'il da suke zaune a wani daki tareda su Barr da sauran wakilan qungiya suna ji da kallon duk abinda Rufaidan take fada ya miqe yana cewa "Tabbas zata aikata mayar Saurayinta ce Khalil". Barr ya kalleshi yace "Ka santa ne daman?" "Kwanaki taje har gida taciwa Mamanmu mutunci ta kuma jaddada mata akan Hadiza ta rabu da mijinta kuma zatayi komai dan ganin ta rabasu. A lokacin na tarar da ita har seda ma fasa mata baki ta tafi da Alwashin seta lalata rayuwar Hadizan shine tayi mata wannan abin kenan" ya fada yana hade hannayensa biyu idonsa suka kada sukayi jajir. Barr Unaizatu daya daga cikin wakilan qungiyar tasu tace "Naji tace wata ceta turawa da ita matar saurayin hotuna ta kuma gaya mata hakan to wacece ita?" "Idan aka kama ta zata fadi duk ma wanda yake da saka hannu a ciki dan haka yanzu mu saurara mu gani komai yazo qarshw tunda har an samu inda Asalin labarin ya fito" Barr Musa Kallah ya fada se suka mayar da hankali kan Rufaida dake tambayar mutumin zata iya tafiya tunda ta amsa tambayar tasu ya galla mata harara se gashi ta kife kai a Table tana kuka kamar qaramar yarinya abin haushi abin dariya. Bayan gama tattara bayanai kai tsaye Jami'ai suka kama hanyar gidan su Umaimah. Suna zaune a tsakar gida sun baza babbar Tabarma a qasan Bishiya suna cin gujjiyar da Anty sukaje qauye shekaran jiya ta taho da ita se yanzu da safe Umaimah ta saka jarabar se an dafa. Hira sukeyi abinsu a ranta tana lissafin zuwan Rufaida dan jiya dakyar tayi bacci saboda baqaqen maganganun da Khalil ya yaba mata kawai jira takeyi taji shawarar da zata bata akan yanda zata rama abinda yayi matan. Salman suka samu a gofar gidan dawowarsa kenan daga Makaranta yaje rubuta jarabawar safe. A darare ya gaisa dasu dan ko hannu da suka bashi ne karba se kallonsu yakeyi yana jiran yaji abinda ya kawo su. "Kayi mana sallama da me gidan nan mana" daya daga cikin su ya fada, Salman ya kalle shi daga sama har qasa kafin ya shiga cikin gidan, har yayi nisa ya tuna da ai Abban ma baya nan yaje daurin aure Qiru kuma yanzu dai beci ace sun dawo ba se ya juyo da baya daga jikin qofa ya daga murya yanda zasuji shi yace "Wai baya nan yayi tafiya" "Toh kayi mana magana da wani babbaa ciki naga alamar kamar kai ka tsorata da ganinmu" Mutumin ya sake fada se ya juya ba tareda yace musu komai ba ya shige gidan. Yanayin da yayi sallama ya saka suka bishi da kallo gaba daya, ya kalli Mama data fi kusa da qofar tsakiyar yace "Mama wasu mutane sun zo neman Abba na gaya musu baya nan sunce wani babba yaje" "Kamar Yaya wani babba? Kai din baka isa ka wakilce shi ba zaka taho wani zoqai zoqai dakai" Maman ta fada se yayi ciki yana cewa "Jami'an tsaro ne, gara dai a cikinku wata ta leqa taji me yake faruwa" "Ba shakka wato idan ma tafiya za suyi damu shikenan ba, baci gidanku kuwa kai zaka koma kaji abinda ya kawo su" Maman ta fada seya marairaice yana cewa "Jiya fa na baku labarin case din wayar Hassan idan kuma sune suka biyo nifa dan Allah tunda dai su sukace na turo wani Mama ko Anty kuje, ga Yah Umaimah nan ma ai itama babbace" Umaimah data bubbude qafafu ta aje ciki tsakiya ta galla masa harara harda murguda bakinta dayayi labcece dan wannan karon sosai ciki ya canza mata kamanni tana kallonsa tace "Inda ace harkar samu ce ai da bazak shigo kace wani yaje ba ko" Sallamar da aka buga daga gareji ta saka su yin shiru. Mama ta maida Hijabin da tayi sallar Walha ta miqe tana cewa "Bari na leqa karsu ce an barsu a tsaye". Bayan sun gaisa ya zaro ID card ya nuna mata yana cewa " Daga State CID muke, an bamu umarnin mu tafi da Umaimah Sabo". Mama ta dafe qirji tana kiran sunayen Allah kafin tace "Umaimah kuma? Ni Malika rigimar wa ta janyo mana" "Idan munje can Zakuji koma menen Hajiya, ayi mata magana ta fito saboda ana jiran mune bamason bata lokaci" ya sake fada a qagare yana zazzare ido, badan doka ba da cikin gidan ze shiga dakansa ya fito da ita. Jiki a sabule Mama ta koma ta tarar dasu cirko cirko dan tun Salatin da ta rafka suka jiyota, abinda yazo musu a rai su Abbane sukayi Hatsari amma yanayin data shigo beyi kama da na wadda aka fadawa zancen Mutuwa ba idonta akan Umaimah da ita kadai ce a zaune tace "Tashi ki sako Hijabinki ana jiranki a waje" "Ni kuma waye yake nemana?" Ta fada tana kallon Maman, tsawa ta buga mata da seda ta zabura ta miqe babu shiri kafin tace "Ki wuce kiyi abinda nace, dukma wanda yake nemanki zaki gani tunda kinsan rigimar da kika siyowa kanki". Sum sum Umaimah ta shige daki ta sako Hijabi, silifas ta zura bata iya tsayawa daukan wayarta ba saboda Tsawar da Mama ta sake buga mata ta fice tana waiwayensu, a garejin taga Mutane sunsha baqar Suit su hudu suna jiranta girjinta ya bada qara Dumm, badai Khalil ne ya turo a tafi da ita ba? Anty data biyo bayanta ganin qatti har hudu ta kwalawa Mama kira tana cewa "Na shiga uku ina zasu tafi da ita? Haka kawai kince yarinya ta fita Kallarau fa mutane babu alamar Rahama a fuskarsu su waye wadannan?" Shiru Mama dake tsaye a bakin qofa tayi mata seta koma ciki da gudu ta sako Hijabi tabi bayansu tuni sun tasa qeyar Umaimah a mota Anty ta sako kwasowa da gudu ta shigo gidan tana cewa "Sunfa tafi da ita, a zamanin nan Idan wani abu ya samu yarinyar nan me zamu cewa Mijinta" "Sunce daga CID suke kuma laifi tayi aka turo su tafi da ita" Maman ta fada tamkar ta rusa ihu saboda abinda takeji, Salman ya dora hannu biyu a kai yace "Mama kika bari suka tafi da ita? Kin tabbatar daga can suke innalillahi, se ya zabura yayi waje yana cewa "Ku kira Yaya Aminu ku gaya masa bari nabi bayansu naga inda zasuje" ya burga Mashin dinsa ya bisu da gudun tsiya dan har sun fice daga layin. Seda Salman din yayi magana kuma taji wani tsoro ya dirar mata, meyasa ba tayi tunanin kiran Aminun ba kafin su tafi da ita kai ita kam ta shiga boni. Maganar Anty ta jiyo tana waya da alama da Aminun ne dan taji tace Yayansu seta nemi guri ta zauna kawai a zuciyarta tana Addu'ar Allah ya tsare mata Umaiman yasa tana hannu na gari. Kusan minti goma sha biyar sega Aminun ya shigo daga bakin qofa yace su fito, Anty da Maman suka runtuma har suna ture juna Salma da Yasir zasu bisu ya daka musu tsawa dole suka koma suna hawaye. Har suka isa tambayar junansu suke akan me yake faruwa? A can suka hadu da Mijin Rufaida da Mamanta wadda Mama ta ganeta saboda sunzo sunan Nuratu da akayi Sati biyu da suka wuce tareda Rufaidan nan suka shiga tambayar juna ba'asi babu me amsar bawa dan uwansa se suka samu guri suka zauna jiran Aminu da aka barshi ya shiga Albarkacin kasancewarsa Jami'in tsaro. Sanda Khalil ya iso a sannan Aminu yakeyi musu bayanin tuhumar da akeyiwa su Umaiman, Mama dake zaune akan Benci tace "Yanzu meya hada yaran nan da wata hukumar kare haqqin Mata da har suka kawo su qara kai lamarin Umaimah baze kashe taba. Umaimah Tana fitowa daga mota idonta ya sauka akan Isma'il da suka fito daga sallar Azahar. Wani mugun kallon tsana ta bishi dashi ta tuna Marin da yayi mata amma in ta tuno da abinda ta aikata musu se taji ranta yayi sanyi, haka aka tasa qeyarta shi be ma ganta ba suna magana da Barr Kallah tana shiga ta ga Rufaidah a rabe a wani guri tana aikin Kuka fuskarta tayi qozai qozai duk kwalliyar nan ta kama gabanta dan dankwalin dashi take faman goge hawaye tana ganin Umaimah ta miqe tana cewa "Gata nan wallahi, dan Girman Allah ku sallameni na tafi tunda tazo. Wallahi bani da hannu a ciki ita ta shirya abinta kawai gani nayi ta tura mana". Turus Umaimah tayi tana kallonta wata mata ta bugawa Rufaidan tsawa tana cewa idan bata rufe mata baki ba zata jefata a Cell saboda ma taga an barta a waje ne take musu surutu criminal din banza kawai seta koma ta zauna jiki na bari tana ci gaba da share hawaye. Gurinta Umaimah ta nufa wanda ya shigo da ita ya dakatar da ita ya nuna mata wata qofa, batayi musu ba ta tura ta shiga. Dakine babu komai ciki se Table da kujeru guda biyu daya na kallon daya ta nemi guri ta zauna tana kalle kalle. Mutumin da ya tambayi Rufaida ne ya dawo ya qara tamke fuskar nan ta kalleshi take itama ta sake hade tata fuskar ta na muzurai se kawai ya tsaya yana kallonta tsabar mamaki. Ba Mace ba ko Maza manyan Criminals sukayi Arba da fuskarsa shiga taitayinsu suke ballantana wannan da tsaf ze iya hadiyeta tazo tana masa muzurai seya buga takaddun da ya shigo dasu akan Table din Umaimah ta daga kai ta harareshi a fakaice ta kalli qasa. Hotuna ya watsa mata yana kallonta da jajayen idonsa yace "Wacece wannan?" Ta debesu tana dubawa, baki ta tabe irin ko a jikin nan nata kafinta maidasu ta ajiye tana cewa "Wai sunanta Hadiza kowa" "Ki shiga taitayinki nan ba gurin wasa bane" Mutum ya fada cikin tsawa yanabuga bencin gabansa. Umaimah ta gyara zama har ranta taji tsoron tsawar daya mata amma ta dake. Kallonsa tayi tace "To wai ma nan din ina ne kuma menayi da zaka zo ka sani a gaba kana mun Ihu? Nidai karka firgitamun Da a ciki, idan tambayata zakayi salin alin base kayimun hargagi ba". Dukda dokar da aka bashi ta karya taba lafiyarta besan sanda ya kwasa mata mari da lafcecen hannunsa ba ta fasa ihu tayi baya qiris ya rage ita da kujerar su fadi yayi saurin tareta yana sake buga mata tsawa yace "Naga alamar bakida kunya kuma baki san a inda kike ba, to ki tattara hankalinki guri guda ki amsamun tambayoyina mu rabu lafiya idan haka ba sena saba miki kamanni kafin ki fita daga nan". Magana akayi masa ta cikin abinda ya maqala a kunnensa cikin girmamawa yace "Sorry Sir, yarinyarce bakinta bashi da saiti amma za'a kiyaye" seya juya kan Umaimah shatato hawaye kamar lalataccen famfo ta toshe bakinta da hannu daya tana shafa inda ya mareta da dayan. Murmushin mugunta yayi ya sake tura mata hotunan yana cewa "Wacece wannan, kuma menene alaqarki da ita?" Cikin kuka tace masa "Sunanta Hadiza kuma budurwar Mijina ce" "Budurwar Mijinki?" Ya maimaita ta daga masa kai ba tareda tayi magana ba se ya sake bude wani envelope dinya zaro hotunan da take yadawa ya ajiye mata yana cewa "Me kika sani akan wadannan hotunan?" Kallonsu tayi ta kalleshi kafin ta juyar da kai gefe tace "Wata ce ta turamun dasu, tace ita Aminiyar Hadiza ce sannan itace ta gaya mun abinda yake tsakaninta da Mijina da duk irin Badalar da suke aikatawa a bayan idona ta turamun da shaidar hotuna da videos ta kuma hado mun da wannan tace mun daman Hadizan yar Leabian ce, kuma Mijina ya sani yace a hakan ze aureta, shine ni kuma na turawa da yan uwansa dan su gani su san irin matar da yake so ya auro kuma na watsa a media saboda na tona mata Asiri kowa yasan abinda take aikatawa". Kallonta ya ringayi yana nadar abinda take fada har ta kai aya, a ransa ya jinjina mata wannan ita Gaba gadin ai babu Tsoro ko shakkar komai a ranta kuma da alama iyakar gaskiyar abinda ya faru ta fada. Jin tayi shiru ya sakashi ya sake tamke fuska ya kalleta yace "Kecw kika yada hotunanta a Media kenan kikayi mata qazafi saboda kawai Mijinki yana nemanta koh?" "Ni ba qazafi nayi mata ba, na ma santa ne ballantana nayi mata qazafi? Na gaya maka Aminiyarta ce ina zaman zamana ta kirani a waya ni badan ta gaya mun ba babu ta yanda za'ayi nasan tana tare da Mijina kuma ita ta gaya mun Halinta ni kuma na tonata a duniya saboda wanda basu sani ba su sani ni meye nawa a ciki?" Umaimah tayi saurin katse shi seya miqe tsaye yana zaro mata ido yace "Bazaji gyara bakinki ba ko? Naga alamar se jikinki ya gaya miki sannan zaki fahimci a inda kike, wato ke ga Fitsararriya kin aikata laifi sannan har kinada bakin kare kanki. To ki adana duk wasu surutanki zasuyi miki amfani a gaban Alqali, idan kinje can se kiyi muau bayanin dalilin daya saka kika Lalata Rayuwar Baiwar Allah ta hanyar yi mata mugun qazafi" ya shiga tattara takaddun daya barbaza a gurin. Kotun da taji ya ambata ta saka ta qarasa shigewa cikin nutsuwarta murya na rawar Kuka tace "Yanzu kuma me nayi dan girman Allah, kai fa kace na fadi gaskiyar abinda na sani kuma na fada. Wallahi banida laifi nima fada mun akayi ba Sharri nayi mata ba. Idan ma kuma baka yarda ba aje a duba wayata lambar qawartata tana nan da duk maganar da mukayi da ita zaku gani wallahi bani na qirqiri maganar ba". Banza yayi mata ya juya ya fice daga dakin, hankalin Umaimah ya dugunzuma, ita bata ma san ina suka kawota ba tadai san office din Jami'an tsaro ne amma bata san wadanne iri ba shikenan daga zuwa se yace ze kaita Kotu? In ma kullewar Za'ayi ai qawar Hadiza zasu nemo su kulle tunda ita ta fada mata ai. Sake bude qofar akayi mutumin ya dawo yana kallonta yace "Wacece wadda kika ce ta tura miki kuma ina wayar taki take?" "Nima bansanta ba kawai a waya muke magana, amma ka bani aron wayarka na kira gida se su kawo wayar tawa daga nan ma seka fada musu inda nake dan nasan yanzu suna can hankalinsu a tashe yake basu san inda nake ba" Umaimah tayi caraf ta fada se ya tsaya yana kallonta wannan yarinya lamarinta da ban mamaki yake, da alama ta dauka shirin film sukeyi ko amma zata gane kurenta. Fita ya sakeyi daga dakin babu jimawa wata mace ta shigo itama fuskar dai kamar Hadiri tace mata ta taso. A gaba ta tasata a zatonta gida zasu maida ita se gani tayi sun sake shigewa can cikin gurin, birki taci ta shiga zare idanu ganin inda ta kawota, Cell ne Matan dake ciki suka zuro musu ido kamat Kura taga Nama Umaimah ta hadiye yawu dakyar ta kalli mayar tace "Dan girman kuyi haquri ku maidani gida wallahi iyakar gaskiyata na gaya muku, in baku yarda ba muje tare na baku wayata se ku nemota nidai ku qyaleni" bata kulata ba ta iza qeyarta har zuwa gaban wani Cell da babu kowa Se Rufaida tana can qurya ta hade kai da Guiwa itama Umaiman saboda kayan jikinta ta gane ta. "Shiga ciki Malama idan ba so kike jikinki ya yagaya miki ba" Matar ta fada tana turata, Umaimah ta maqale a bakin qofar tana cewa "Fitsari nake ji toh" banza ta mata taja qofa ta mayar ta kulle ta juya kan sauran Matan dakw cikin dakunan tace "Saura naji wani surutu" ta fice daga gurin tana fita kuwa wata me suffar Yan daba ta matsi jikin qofar su Umaiman harda zura hannu ta jikin qarfe zata tabata tayi saurin yin baya suka kwashe da dariya kamar wasu mahaukata matar tace "Daga yanayinki dai nasan qaramar kwaruwa ce baze wuce ashe Kishiya kima yiwa wani abun ba aka kawoki nan ko?" Murguda mata baki Umaimah tayi tana hararta tace "Aa Uwar kishiya ba kishiya ba, dallah malama kiyi takanki ina ruwanki da ni da abinda ya kawo ni? Naji ni kalar qananan qwari ke ai ana ganinki anga anga Tsohuwar yar ta'addah". "Gyara kintsi yarinya idan ba haka yanzun nan nayi miki balli balli, naga alamar kanki yana hayaqi to kibi a sannu baki san inda kika shigo ba. Ni in fardeki in miki tiyata a nan gurin qaramin abu ne a gurina nan da kike ganinmu mun ci dubu se ceto" Daya daga cikin Matan ta zaburowa Umaimah ganin tana neman ta zagi shugabarsu. Umaimah tayi ciki can kusada Rufaida a tsorace jin za'ayi mata Tiyata da alama wadannan manyan yan tasha ne. "Rufaidah ya akayi kika zo nan kema?" Umaimah ta fada tana dafata kamar tana jira kuwa ta dago cikin bacin tace "Tambayata ma kikeyi ya akayi nazo bayan kece sila haka nan ina zaman zaman kin jefani a masifa daga taimako to wallahi idan Allah yasa muka fita daga nan kowa yayi takansa babu ni babu ke ballantana ki ringa janyo magana kina sako ni a ciki a ringa kulleni a Cell" "Lallaima to daman gayyatar ki nayi ko kuwa ni bace kije ki dora a Facebook ni bance kin jawo mun ba tunda nasan ai ta silarki har aka bincikoni se kece zaki ce wani waye waye aikin banza kawai duk kinbi kin wani rikice kamar wadda akace tayi kisan kai" Umaiman ta hayayyaqo mata itama se kuwa Rufaida ta miqe tana cewa "Ai da banyi kisan kai ba gashi nan an sakani cikin Yan ta'addah, wallahi Allah ya isa tsakanina dake Umaimah idan har naje Prison ta dalilinki bazan taba yafe miki ba" ta qarasa tana sake fashewa da kuka wiwi kamar yarinya. Hasko kanta kawai takeyi a prison yanda take jin labarin irin gwale gwalen da ake sha ina zata iya, da ace tasan yarinyar nada daurin gindi da bata saka kanta a sabgar Umaimah ba, yanzu gashinan daga solidarityn qawance se ta zurme da gidan yari gaskiya Umaimah ta cuceta. A can waje kuwa bayan dogon cuku cuku da Yaya Aminu yayi dakyar ya samu jin bayanin tuhumar da akeyiwa su Umaiman, kansa ya dafe yana kallon Detective Adnan dake kora masa jawabi ya qarasa yana cewa "Yanzu abinda ya rage mu samu ita wadda tace ta tura mata hotunan a farko daga nan zamu tattara dukka shaidun da muke dasu mu turasu koto ta yanke musu hukuncin daya kamata dan haka muna buqatar wayarta tace komai yana ciki". Jiki a sabule ya koma ya shaidawa su Mama abinda aka gaya masa daidai lokacin Khalil ya dawo daga Sallar Azahar din da beyi ba, ya kalli Mama dake hawaye tana cewa "Yanzu daman Umaimah ce? Itace ta tozarta yarinyar nan haka duniya gaba daya take mata tofin ala tsine amma shine a gabanta muke maida zancan yarinyar nan tayi funfurus bata ce komai ba yanzu ina zata kai haqqin wannan baiwar Allah? Me yake damun Umaimah anya Umaimah naso ta gama da duniya lafiya kuwa?" "Aa Mama ki dena fadar haka, addu'a dai zaki ci gaba dayi mata kina nema mata shiriya a gurin Allah shine kadai mafita" Anty da gaba daya itama jikinta yayi sanyi ta fada. Mama ta goge hawaye da gefen Hijabinta tace "Tunda na haifi Umaimah ban huta ba Saratu ke shaida ce babu ta inda na banbanta tarbiyyarta data sauran yan uwanta amma ta fita zakka a cikinsu. A kullum abinda yake faranta mata rai shine ta dakko mana magana, duk wani abin tsiya Umaimah ce daga yari tarta har girmanta bata barmu mun huta ba se yaushe zamu rabu da Jidalin Umaimah? Wallahi da nasan fitinar da zata zamar mun kenan dana zubar da cikinta na huta tun tuni qila da Rayukan kowa ya zauna qalaubarshi ya shiga" ta qarasa tana rushewa da sabon Kuka wani Dattijo dake tsaye gefensu shima tasa ta kawo shi yace "Ashsha Ashsha kiyi gaggawar yin istigfari ki nemi yafiyar ubangiji. Duk abinda kikaga Allah ya jarabci bawansa dashi yasan ze iya ne kuma Duk mumini baya rayuwa haka ba tareda jarabawa a rayuwarsa ba, idan rai ya baci ya kamata asan abinda baki ya furtawa dan a lokaci da yawa Dan Adam yana warware Ayyukansa da kansa ba tareda ya sani ba. Yanzu da kanki kin fadi kina yi mata Addu'a kina nema mata shiriya a gurin Allah sannan idan ranki ya baci kina jifanta da Kalamai masu muni wanda sune suke dada tasirantar rayuwarta. Kinsan kaifin bakin uwa kuwa? Ko fushi kikayi da ita a zuciyarki abin seya shafeta ballantana kin bude baki kin jefeta da mummunar kalma ya za'ayi ki ambaci Yar da kika haifa a cikinki da Fitina kuma kiyi tunanin Ubangiji baze jarabceki da ita ba? Kin zubar mata da hawaye, kin aibatata kin butulcewa Allah bisa kyautar da yayi miki ta samunta kinga kuwa bazaki taba ganin daidai akanta ba. Dukda bansan me yarki ta aikata ba da har kike wadannan kalaman amma nasan be kama qafar abinda Dana ya aikata ba. Yanzu haka an kamashi ya haura gida ya kashe Mata da Miji da Yayansu guda biyu kuma ya amsa laifinsa akwai abinda yakai wannan tashin hankali? Kenan da kece Uwarsa take yanke zaki tsine masa yabi duniya ko? To bari kiji sanda labarin ya riski Uwarsa Tasbihi tayiwa Ubangiji ta gode masa ta shiya bata Dan ya kuma tsara cewar qaddarar sa ce a haka tun kafin ayi mu Ubangiji ya shirya yanda kowanne bawa ze gudanar da rayuwarsa ta kuma roqi ubangiji yasa hakan ya zamo amsa kaffara. Tana can kwance, kowa yasan gigitar abinda ya aikata ce ta kwantar da ita amma bakinta be mutu daga ambaton Allah da nema masa sauqi a gurinsa ba dan haka na horeki da kiyi koyi da Matata, ki yarda da qaddara a duk yanda ta riske ki daman su Yaya da Dukiya Jarabawa ce". Yanda kasan anyi ruwa an dauke haka gurin yayi tsit babu wanda ya iya motsi me qarfi gaba daya suka raka Dattijon da ido sanda wani da suke zaton Lawyer ne yayi kiransa. Aminu ne yayi qarfin Halin bude baki dakyar yace "Kiyi haquri Mama na kira Abdulbasit yana hanya yanzu dan sunce da Lawyer kadai zasu bari tayi magana sun hanani ganinta, yanzu ku tafi gida mu zamu tsaya muga yanda abun ze kasance in Allah ya yarda ma baze dauki lokaci ba za'a sasanta komai su dawo gida shi yasa ma ban sanarma Abba bana so hankalinsa ya tashi yana kan hanya". Haka suka taru suka lallabasu dakyar Ma'aruf ya kwashe su a motarsa harda Mahaifiyar Rufaida suka tafi Ya rage Aminun da Khalil se Barr Abdulbasit wanda Dan Yayan Maman ne da ya qaraso yanzu. Se a sannan Khalil ya iya bude baki yace "Ga wayar tata a hannuna, nasanita wadda ta tura mata da hotunan dukda na duba babu wani abu da za'a samu a ciki dan ta rigada ta goge duk wani Chat da sukayi exchanging kuma tayi blocking layin kaga babu wata shaida da zata tabbatar da ita dince saboda bada layin da aka santa tayi amfani ba. Yanzu idan da hali ina so na gana da wadanda suka shigar da qarar, ina fatan idan nayi musu bayani zasu gamsu mu samu fahimtar juna ta yanda za'a warware komai cikin sauqi". Barr Abdulbasit ne ya karbi wayar tata ya duba kamar yanda Khalil din ya fada an yi deleting message din da aka turo seya kalli Khalil yana cewa "wannan ba wata matsala bace tunda ga amsoshin da ta bata nan suna nan kaga ko daga mam za'a samu Idea na abinda suka tattauna. Yanzu bari na fara shiga cikin na gani idan da hali se kuyi magana dasu kamar yanda ka nema tunda kaima abin ya shafeka kai tsaye" ya wuce ciki ya barsu. A ciki kuwa bayan ya gabatar musu da kansa yayi cike ciken takaddu kafin aka sake fito masa da Umaimah, kamar yanda dai suka tambayeta shima tishi yayi akai ya dauki bayanan da yake ganin zasuyi masa amfani kafin ya koma inda Musa Kallah da Isma'il tareda sauran wakilan qungiya suke zaune. Bayan sun gaisa ya gabatar musu da kansa da kuma buqatar Khalil nason yin magana dasu kai tsaye Ismai'il ya ce Aa, seda Musa Kallah ya saka baki yace ya shigo sannan ya haqura badan yaso ba. Tiryan tiryan Khalil ya labarta musu yanda sukayi da Khausar a wancan karon da kuma abinda ya samu a wayar Umaiman, Musa Kallah ya karbi wayar yana dubawa tareda nazarin maganganun Khalil din ya gama ya miqawa Detective din dake akan case din shima ya karba ya duba. Number suka dauka suka saka ta a computer su ta bincike, wani rashin Azanci da Khausar din tayi shine na amfani da Layi Wanda tayi register shi da sunanta dan ana shigar da number nan take duk wasu bayanai nata dake kan layin suka bayyana. Khalil ya sauke ajiyar zuciya, daga Umaimah har Hadiza a yanzu suna buqatar daukinsa kuma kamo Khausar a hannu ne kadai ze rangwantawa Umaimah laifinta ya kuma wanke Hadiza daga Qazafin da sukayi mata. An tura da Jami'ai dasu nemo Khausar din duk inda take kasancewar yamma tayi Barr Abdulbasit ya nemi da abasu Belin Umaimah da Rufaidan zuwa gobe se su dawo a ci gaba da bincike amma qememe suka hana, a cewarsu har yanzu itace prime suspect, dan haka babu halin bada belinta har se zuwa yanda hali yayi domin koda an kawo Khausar da sun gama tattara bayanai zasu miqasu kotune gaba daya su girbi abinda suka shuka matuqar ba wadanda suka shigar da qara bane suka janye wanda kuma ba abune me yuwu ba. Wannan ya tayar musu da hankali dan dukda abinda ta aikata dole su tausaya mata kodan halin da take ciki ga Tsohon ciki, ko iya sauron da ze cijeta tsakanin dare zuwa safiya aka barya dashi ya isheta jin jiki amma ya suka iya haka suka tafi bayan an barsu sun gansu dakyar Khalil ya fita ya siyo musu abinci da abin sha harda guzurin barguna da maganin sauro suka tafi da niyyar gobe da safe zasu dawo a dora daga inda aka tsaya. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 46 A gurin Ismai'il da Musa Kallah sukayi sallama akan se goben zasu dawo, kaitsaye gidan Mama ya wuce dan be sanar da ita abinda yake faruwa ba ya bari se komai ya kammala tukunna. A can ya tarar da an sallamo Hadizan, tundaga soro yake jiyo irin Tijarar da Mama take zubawa Malama Lawisa da Hadizan akan su fitar mata daga gida ita kuma Malama Lawisa ta kafe akan babu inda Hadiza zataje dan bata da inda yafi nan din, idan ma da Wanda ze fita toh Mamance dan ita Hadizan Gadon Ubanta ne gidan. Mama Innai da Hajiya Barira basa nan ake wannan dambaruwar sun tafi Asibitin dubota sukayi sabani, yana shiga soron yaci karo da Hadiza dake durqushe tana rusa kuka kamar ranta ze fita, gabanta ya durqusa da niyyar kamata tayi saurin sunkuyarda kanta tsakanin cinyoyinta jikinta har rawa yake saboda Azabar tsoro bata manta dukan da yayi mata ba dan ga shaidarsa nan hannunta daya tsage a nade da bandeji ba'a kwance ba. "Dan girman Allah karka dakeni wallahi Umma Lawisa ce seda nace mata bazan dawo ba kun koreni tace se nadawo" Hadizan ta fada tana kuka kamar zata shide tsabar tausayinta besan sanda Hawaye suka fara zubo masa ba shima ya saka hannu biyu ya dagota gaba daya ya runguneta yana cewa "Ki yafe mun yar uwata nayi nadama ki yafe mun Hadiza". Mama da tsabar qarfin Hali ta miqe tana watso kwanukan abincin da Anty Bilkisu take kai musu suka taho dasu ta tsaya tana kallonsu, dakyar ta iya bude baki tace "Isma'il ka rabuda yarinyar nan idan ba so kakeyi fushinta ya shafeka ba" "Mama ki tsaya ki saurareni Hadiza bata da laifi sharri akayi mata munyi kuskure da muka kasa yi mata uzuri har bincike ya tabbatar da gaskiya ko akasin haka akan abinda ake zarginta dashi. Wallani sharri akayi mata kuma yanzu haka wadanda suka aikata suna hannun Hukuma. Kabbara Malama Lawisa ta dauka tana kallom Mama data sandare a tsaye tana kallon Isma'il din sw tace "Allah nagode maka daka wanke yarinyar nan tun ba'aje ko ina ba. Kin gani ko Karimatu kinga abinda ake fada miki akan kibi komai a hankali? Yanzu wa gari ya waya, da wanne ido zaki sake kallon yarki bayan duk mugayen kalaman da kika gamayi akanta kin gagara daukar qaddara gashinan tun ba'aje ko ina ba Ubangiji ya wanketa sol ya bar munafukai da jin kunya". Jiki babu kwari Maman ta juya ta zauna a inda ta tashi, Isma'il ya kamo Hadiza da itama take cikin mamakin kalamansa, ya akayi ya gano wanda suka qulla mata wannan sharrin 'Khalil ne' Zuciyarta ta bata amsa. A gaban Maman suka zauna shida ita yana kallonta yace "Kamar yanda na fada miki Mama an gano cewar sharri akayiwa Hadiza kuma yanzu haka ana kan bincike. An kama biyu daga cikinsu dayar ce bata rigada tazo hannu ba kuma wallahi Mama bazaki yarda ba idan kikaji su waye keda saka hannu a cikin wannan abun". "Zan yarda mana Isma'il tunda har ka iya gamsar dani cewar Hadiza ta aikata abinda ake fada akanta babu kuma sauran wani abu da zaka fada ya bani mamaki kona kasa yarda" Maman ta fada tana kallon gefe. Yanda kasan qasa ta bude ya shige ciki haka yaji kunyar furucin Maman, shi ya kawo mata labarin ta qaryata ya kuma tabbayar mata da yayi bincike gaskiya ne se a yanzu yake nadama tabbas be kasance dan uwa na gari ba ya tabbatar idan Hadiza ce a matsayinsa zata kare shi da iyakar iya warta. Kansa na qasa ya bude baki yace "Ki yafe mun Hadiza na cutar dake ba akan haqqinki ba, nayi gaggawar yanke hukunci ba tareda na samu qwaqwqwarar hujjaba ki yafe mun dan Allah, kuma nayi miki alqawari bazan zauna ba har se na tabbatar da anyi miki aldalci s an bi miki kadin bata miki suna da sukayi". "Ka dena bani haquri Yaya ba kai ba koma wanene irin wannan al'amari ya riske shi ze iya aikata abinda yafi wnada kayi. Baqin cikina guda daya ne dana rasa samun yardar ko mutum daya daga cikinku, daga kai har Mama kuka kasa shaidata amma nayi muku uzuri zamanin da muke ciki ne yayi lalacewar da bazaka iya shaidar halin Dan Adam ba saboda munfi Hawainiya saurin rikida a yanzu. Kuma ni na rigada na gayawa Khalil na yafe musu dan haka karka wahalar da kanka gurin yin shari'a da kowa, ni suka sabawa kuma na yafe musu Allah yasa hakan ya zama izina ga sauran mutane baki daya" Hadiza ta fada hawaye na sakko mata idanunta akan Mama data juyar da fuskarta gefe ta gagara ce musu komai. Harga Allah nauyi da kunyar Hadizan ne ya kamata, ta haifeta a cikinta ta raineta, halayyarta babu wadda bata sani amma lokaci daya wani al'amari ya bijiro ta kasa bata mafaka a lokacin da duk duniya take mata kallon fasiqa. Tana jin Malama Lawisa nata jefa mata magana, Isma'il yayi musu sallama akan gobe da safe ze zo su tafi can tare gaba daya yana kuma jaddadawa Hadizan da tayi haquri ta yafe masa ita dai tayi shiru har sannan tana durqushe gaban Mama, jira take yi tayi magan, so take taji ta yarda da ita ko kuwa har yanzu tana kan bakanta kuma bazata barta ta zauna a gidan ba. "Ki tashi kije dakinki ki kwanta saboda jikinki" Maman ta fada kamar bata son magana ba tareda ta kalleta ba, se Hadizan ta miqe dan daman abinda take jirane ta wuce cikin dakin tana jin wani nauyi daya danne mata zuciya yana raguwa. A gaba daya abinda ya faru yardar Mahaifiyarta da Dan uwanta data rasa su suka fi komai yi mata ciwo kuma ko a yanzu idan har suna tareda ita zata iya fuskantar duk wani qalubale da ze tunkarota a gaba. Mama kuwa Hadiza na shigewa daki ta fashe da kukan da take dannewa daidai nan kuma Mama Innani da Hajiya Barira suka shigo, masifa Hajiya Barira ta farayi akan kukan me Maman takeyi, Malama Lawisa tace "Ku tambayeta dai, qila baqin ciki takeyi Allah ya bayyana gaskiya ya wanke yarinyar nan dukda muggan kalaman data gamayi akanta. Ni kunga tafiyata, Hadizan na ciki ga ledar Magungunanta nan kuma se an taimaka mata saboda Daurin da yake hannunta. Ke kuma Karimatu wannan ya zamar miki ishara, Jarabawa ce ubangiji ya saukar miki kuma kika gaza dauka se kije kiyita istigfari kuma ki nemi gafarar yarki dan idanbata yafe miki ba la shakka se kun tsaya a gaban Allah cikin wadanda suka yi mata qazafi" a fusace take maganar tana gamawa ta figi jakarta tayi waje bata ko tsaya amsa tambayar da suke mata ba. Kan Maman suka juya, tana kuka ta gaya musu yanda sukayi da Isma'il, "Nayi kuskuren daukar fushi ba tareda anyi bincike ba, yanzu da wanne baki zan bawa Hadiza haquri? Kuna kallo wasu a bakina suka qara gasgata maganar a maimakon na zama me kareta ni na sake zama silar tona mata Asiri kaicona" ta qarashe tana kuma rushewada kuka Hadiza dake maqale jikin qofa ta sulale a qasa tanaci gaba da nata kukan mara sauti. Tabbad Qazafi yanada radadi kuma wanda aka tabayiwa ne kadai ze fahimci halinda dan uwansa yake ciki amma dukda haka ta yafe musu Allah ya yafe mata nata kura kuren itama. KHALIL Daga CID rasa inda ze tafi ya zauna yayi, baze iya zuwa gidan Hajiya ba dan besan me ze gaya mata ba, gidansa kuma ya manto muqullin hannunsa acan SA ba kuma ze iya komawa gidansu Umaimah ya karbi nata ba dan haka kawai ya karya akalar motarsa ya kama hanyar Chilla hotel ze fi masa sauqi ya kama daki acan ya kwanta ko ze samu nutsuwa a jikinsa da zuciyarsa gaba daya. Wayarsa ya fara sakawa a chaji dan ta mutu tuntuni, Seda yayi wanka ya rama sallolin da ake binsa kafin ya zura Slippers din bandaki ya dauki wayarsa da wallet ya fita dan ya samu abinda ze saka a cikinsa da kuma Paracetamol saboda ciwon da kansa yakeyi. Abubuwan da suka faru sun dagula masa lissafi kwarai, har yanzu daya rufe idonsa Hadiza yake gani yana kuma jin sautin Kukanta me ciwo wanda matarsa ce sila. Ita kanta Umaimah a dayan hannun yanzun abar a tausaya mata ce. Idan da ace Hadiza ce ko yan uwanta suka shigar da qarar da abinze iya zuwa da sauqi qila a sasanta a gida ba tareda anje gaban Alqali ba amma fa Hukumar Human Right ce gabadaya yanzu ta karbi case din ahannunta, baya tunanin ko ta furta a gabansu cewar ta yafe musu kamar yanda ta gaya masa zasu yarda su janye qarar nan. Dan sauqin da yake da yaqinin zata samu shine idan an samu nasarar kama Khausar kuma ta amsa laifinta wanda ba lallai tayi hakan ba amma koma menene Umaimah ita ta jawa kanta. Rashin tunanita da Baqar zuciyarta su zasu kaita su barota a inda ba zata iya fiddo da kanta ba. Idan ba Mahaukaci ba wa ake cewa yayi barna kuma yayi ba tateda tunanin me hakan ze janyo masa daga baya ba. Tsaki yaja yana qoqarin kulle qofar ya tuna da ba lallai a ya smau magananin a ciki ba dole seya fita dan haka ya koma dakko muqullin mota. Har ya shiga ya juyo da baya saboda gilmawar wata daya gani kamar Khausar. Saurin mayar da qofar yayi ya kulle ganin sunfara sauka daga benen sunyi qasa a hankali yabi bayansu, tana gaba wani Dogon saurayi fari na binta a baya waya ce kare a kunnenta daga yanayin fuskarta ya karanci cikin tashin hankali take da alama ta samu saqon anje nemanta ne. Bin bayansu yayi har suka fita yana ganin sun nufi wata mota yayi saurin yin inda ya ajiye tasa motar ya dauka, seda ya bari sunfita kafin yabi bayansu, a sannu yake binsu cikin kwarewar da shi kansa besan yana da ita ba ta yanda babu yanda za'ayi su fahimci ana binsu a baya. Dukda Gajiya da mugun ciwon da kansa yakeyi masa haka ya daure yaci gaba da binsu, Hadeja road yaga sun dauka, to ina zasuje? lissafinsa dai yasan ba zasu bar Kano a daren nan ba, Amma koma inane baze taba bari su tsere masa ba. Wani gidan mai daya ga babu kowa ya tsaya ya qara saboda gudun karya qare masa a hanya man motar yayi qasa. Gudu ya ringa shararawa a Titi ko tsoron dare ba yayi da yanayin hanyar da take Titi daya ya ringa tafiya amma ko qyallin motarsu be hango ba, be sare ba yaci gaba da tafiya, yasan dai babu wata hanya da zasu dauke subi indai ba kuma cikin qauyuka suka shiga ba Titin dai yaci gaba da bi harya kai Munjibur basu gamu ba ya gama saddaqarwa sunyi masa nisan da baze iya taddasu ba danhar idan tafiya sukeyi kuma Titin nan suka bi a irin gudun da yayi da ya tarar dasu a hanyar. Baze yuwu ya juyo Kano a sannan ba dan Goma har ta gota ga muguwar yunwa da ciwon kan da suke damunsa se kawai ya dauki hanyar Munjibur park, canze kwana zuwa da safe ya koma cikin gari. Yana tafe yana cizon yatsa da dana sanin tsayawar da yayi gashi yanzu Allah kadai yasan inda suka tsere, wata nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke daidai sanda ya shigar da motarsa gurin parking yayi arangama da Motar da yake bi. Gaggauce ya shiga ciki, ya ringa baza ido a reception ko ze gansu amma shiru seda ya biya kudi aka bashi muqullin daki ya shiga kafin tunanin kiran Yaya Aminu yazo masa. A taqaice yayi masa bayanin komai da kuma inda yake a yanzu Yaya Aminu ya bashi tabbacin zasu dauki mataki dan yanzu haka ma yana office be tafi gida ba saboda wani pending case da basu qarasa na. Dakyar ya iya shan coffee a cafeteria dukda baqar yunwar da yakeji ya koma can bakin qofar gurin ya kafa ya tsare duk wani me shiga da fita akan idonsa har zuwa sanda Yaya Aminu ya sake kiransa akan gasu sun shigo Munjibur, yayi mamakin yanda suka fito operation din da daren nan, yanda kasan wanda sukazo kama wata qasurgumar yar fashi haka suka zagaye gurin, a cikin daren akayi Nasarar damqe Khausar dake can cikin daki ita da saurayinta Nasman suna shirya yanda za'ayi ta fece daga Kano har zuwa sanda abubuwa zasu lafa. Shiya takura akan su tsaya a nan su kwana kafin da safe su wuce dan daman sun hadu kenan zasu tafi yawon sheqe ayarsu ta samu kira daga gidansu cewar Jami'an DSS sunje nemanta kuma an baza nemanta a duk inda aka san tana zuwa suna fakonta shiyasa babu shiri tace su tafi, shi kuwa ya rigada yayi caji dalilin da yasaka yace su kwana anan kenan ya samu ya rage zafi kafin da safe ya gudu ya barta dan baze saka kansa a rigimar da be san mafarinta ba haka kawai. Kwanan da Khalil beyi a can ba kenan ya biyo su suka dawo Kano, tunda ya kife akan gadon dakin Hotel din daya koma be farka na se qarfe goma da Rabi na safe shima saboda bugun qofar da ake tayi daga waje. Dakyar ya tashi ya zauna yana dafe kansa, labulen window a dage suke hasken rana ya cika dakin abinda ya ankarar dashi cewar gari ya waye kenan ya miqe a hankali yana jin kamar iska zata kwashe shi saboda rashin kwarin jiki ya bude qofar. Room service neda kayan shara, ya sanar dashi ya dade yana bugu dan har ya fara zaton ko ba lafiya ba tunda an tabbatar da mutum a ciki Khalil ya daga masa hannu yace yaje, idan ya gama abinda yakeyi ya fita se yazo yayi aikinsa Mutumin ya juya yana waigensa yanayinsa yayi masa kama da wanda yasha tafi qarfinsa dan dakyar yake iya bude idonsa haka tsayuwa seda ya jingina da qofa. Wanka ya farayi tareda Alwala yayi sallar Asubar da ta kufce masa. Ta Landline yayi order abinda za'a kawo masa abinci tuli a hakan ma gani yake kamar bazasu qosar dashi ba dan rabonsa da Abinci tun wanda yaci a Jirgi se Coffee daya sha da daddare tas kuwa ya tada abincin nan sunfi kala uku yasha ruwa yayi qyatsa sannan ya fara fahimtar abubuwa dakyau. Kan Gado ya koma ya miqe bayan ya cire jallabiyyar jikinsa, wayarsa ya lalubo tana cikin Aljihun rigar daya fita da ita da daren Tarin Missed calls din daya gani akai sunfi Hamsin duk ya share ya tafi kan na qarshe wanda Yaya Aminu ne ya kirashi. Sanar masa yayi da tun dazu suna CID shikadai ne bezo ba har yan gidansu Hadiza gasu nan harda ita ya bashi haquri akan baccine yaci qarfinsa amma gashi nan zuwa ya kashe daga nan ya kira Jalilah da itama ta kirashi sau ba Adadi. Muryar Hajiya yaji ita ta dauki wayar, cikin tsananin bacin rai tace "Ibrahim kana ina? Duk abinda kakeyi ka bari kazo nan inason ganinka kaji ko?" Da "Toh" kadai ya iya amsa mata danyasan tunda ta kirashi da Ibrahim yau ranta a Asalin bace yake. A gurguje ya shirya ya fita, gidan Hajiyar ya fara zuwa ko zama bata barshi yayi ba tace su tafi ya daga kai ya kalleta ya Kalli Jalilah da Anty Amina da suke zaune duk sun sunkuyar da kawuna cikin son qarin bayani amma babu wadda tayi magana. "Ka tashi mu tafi Office din yan sandan, saboda rashin Imani a hada baki dakai a dauki yarinya da tsohon ciki a kukketa a Cell baka ko tsoron wani abun ya sameta sannan a rasa cikinku Wanda ze sanar dani badan wannan yaron Munzali Abokin Khalifa ya ganku acan ba ya gaya masa da sedai mugun labari kake so naji ko me? Kun hada kai da uwarka Jalilah abu na faruwa kun boye mun har ka dawo qasar nan ban sani ba ai shikenan" Hajiya ta ringa sababi a mota gaba dayansu dai suka mata shiru babu wanda yace komai har suka isa. Sun tarar da Abban su Umaimah tareda qaninsa Baba Abdullahi fuskar Abban kadai zaka kalla kasan yana cikin tsananin damuwa. Tun a daren Jiya da Mama ta sanar dashi bayan ya dawo seda hawan jininsa ya tashi jiri ya debe shi badan Allah ya taqaita ba ya zauna a kujera da ba'asan abinda ze faru ba, ya ringa sauke ajiyar zuciya yana nanata hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarsa kafin yaji dama dama har ya iya miqewa ya tafi dakinsa. A daren kwana yayi da ciwon rai, Asuba nayi ya kira dan uwansa ya shaida masa se gashi kuwa tun gari be gama haske ba ya ringa fadan me yasa tun a jiyan su Maman basu kirashi ba ya za'ayi su barta ta kwana a can haka suka dungumo gaba daya suka tafi amma ko kallon arziqi basu samu ba dan a sannan bangaren Hadizan basu rigada sun qaraso ba. Daidai isowarsu Khalil a sannan kowa ya hallara bangare hudu harda yan gidansu Rufaida Babban yayansu da Mijin Yayarta da shima Jami'in tsarone aka hadu ana ta jajantawa juna ga Babansu Khausar daya iso a rikice shima dan katsahan a safiyar mugun labari ya riskeshi. A daya daga cikin ofisoshin gurin suka hallara, sega Umaimah, Rufaida da Khausar an taso qeyarsu cikin dare daya sun zama abin tausayi karma Khausar taji labari. Ita Umaimah da Rufaida tsabar Azabar cizon sauro da zafi ga warin da gurin yakeyi ne ya gigitasu. Maganin sauron da Khalil ya kai musu masu gadinsu ne suka kwace harda bargon Rufaidah Umaiman cema suka dan tausaya mata suka bar mata nata haka sukayi kwanan zaune suna make maken sauri jikinsu kuwa yayi rudu rudu kamar wanda Sukayi birgima a gidan tururuwa Umaimah tayi Amai yafi sau goma daga daren zuwa safiya shiyasa ta sake jigata tafiya ma seda wata ta ruqota sannan take iya daga qafarta. Khausar kuwa abin nata yafi muni, daman sanda suka kamata sun tarar dasu a daki bayan sun gama sheqe ayarsu suna kora kwayoyi saboda su samu nutsuwar bacci a cewarsu, tun a hanya ta ringayi musu shirme da masifar me tayi da zasu kamata rabi cikin hankalinta rabi a maye dan haka suna zuwa a maimakon waddata taho da ita ta sakata Cell din su Umaimah seta jefata cikin Matan nan da dama cike suke da haushin su Umaimah da suke ganin suna da gata. Tana shiga ta taka daya daga ciki bata yi wata wata ba ta hankadata Khausar na daidaita tsayuwarta dan ta kusa ta fadi ta kwashe mata da mari nan fa sauran sukace dawa Allah ya hadasu suka rufu akanta sukayi mata dukan kawo wuqa masu ganin na kallonsu babu wadda ta kai mata dauki. Kaca kaca sukayi mata fuska ta kumbure baki kamar ta boye fanke saboda yanda ta tashi kamar ma sun cire mata haqori ne oho sannan tun farar safiya aka jefata a dakin tuhuna. Kamar masu jin haushinta seda suka fara lallasata abinda ba'ayiwa su Umaimah ba kafin suka fara mata tambayoyi. Da farko tayi gardama, dukda wayarta dakw hannunsu sun binciko duk wata shaida da suke buqata harda ma abinda be shafi case din ba sun qara tara wani chages din akanta amma dukda haka tayi qememe taqi amsa laifinta. Dukan mutuwa suka mata har daya daga ciki na cewa a bashi belt ya shaqw mata wuya kawai ta mutu su huta dan sun fahimci yanzu tura nasu laifi Kotu bata lokaci ne kawai dan idan sunada hanya se kaga shari'ar bata wani kasancewa yanda ya kamata ake sallamarsu amma idan suka kasheta anan sun kashe banza qarshenta suce sun wayi gari sun tarar da gawarta shikenan ai kafin ma ya kai aya jiki na rawa Khausar tace zatayi magana. A gaba suka sakata suna mata video ta amsa duk abinda ake tuhumarta dashi harda dalilan ta da ya sakata aikata komai daga nan suka mayarda ita se yanzu aka sake dakko su. Kowacce na ganin idon iyayenta ta fashe da sabon Kuka, Hajiyar Khalil ta shiga tafa hannu kwalla ta kawo mata tana cewa "Na shiga uku ni Aisha kalli yanda kuka mayar da yarinya a dare daya fisabiliklahi bakuda tausayine baku ganin halin da take ciki me tayi muku?" "Idan baki rufe mana baki ba Hajiya zaki fita daga nan, ita ce bata tausayin kanta da har ta jefa kanta a wannan halin kinga kuwa babu abinda ya shafe mu" daya daga cikin Jami'an ya fadawa Hajiyar a dake dole ta kama bakinta tana share kwallar tausayin Umaimah. Bayani Detective Adnan ya farayi akan bincike ya kammala ga kuma sakamakon da suka samu dan haka yanzu sun gama cike duk wasu takaddau da suka kamaya zasu turasu kotu kowanne yaje ya nemi lauya dannan zasu ci gaba da tsare su ne a hannunsu ba wai zasu barsu su tafi gida ba. A tare Su Umaimah suka fashe da mugun kuka kowacce ita kadai tasan azabar data dandana adare dayan nan inaga ace zasu ci gaba da zama anan kawai mutuwa zasuyi. "Dan girman Allah Khalil ka saka baki ka bata haquri wallahi ni ba laifina bane gata nan wannan ce ta sakani ni banma taba ganinta ba se yau itace ta shirya komai tunda an ganta su kyale mu, wallahi na qara kwana a nan mutuwa zanyi, daman nasan dan cikina ya mutu dan tun jiya na dena jin motsinsa" Umainah ta da cikin matsanancin Kuka tana kallon Khalil da shi kuma Hadiza yake kallo wadda itama kukan takeyi tana jingine jikin Hajiya Barira. "Ballantana kuma ni da bansan komai ba ai tsakanina dake Umaimah se Allah ya mana hisabi kuma bazan taba yafe miki ba, dan Allah Yaya Abubakar kasa baki a barni na tafi tunda dai ni babu ruwana tsautsayine kawai ya shigar dani" Rufaida ta fada itama cikin kuka, Khausar dai babu baki kanta yana qasa ta kasa hada ido da kowa a gurin. Tsawa Detective ya daga musu sukayi shiru gaba daya ya kalli Musa Kallah yace "Yanzu magana tana hannunku, kamar yanda na fada mun gama cike takaddu gobe zamu turaku koto. Kuma duk wata shaida da ake da buqata muna da ita a hannu ya rage nasu su nemi masu kare su ko akasin haka dan haka ina ganin mun gama wannan zaman kowa ze iya tafiya" Kafin Musa Kallah yace wani abu sukaji muryar Hadiza cikin kuka tana cewa "Indai har saboda ni ne da abinda sukayi mun na yafe musu har gaban Abada ku barsu su tafi gida" "Akan me zakice kin yafe musu, beside ai bama ke kika shigar da qara ba ballantana kice zaki janye" Yaya Isma'il ya fada a fusace kamar ze kai mata duka. Tun a hanya ya ringa kafa mata kashedin karta kuskura tayi wata magana indai bata neman haqqinta ba daman Mama bata biyosu ba tareda Hajiya Barira suka zo shine yanzu zatace ta yafe ai kuwa baze sabu ba. "Amma duk abinda mukeyi saboda ita ne kuma tana da damar da zata janye ko jaddada qarar nan dan haka idan tace ta yafe musun magana ta zauna za'a janye qara, sedai idan akwai wani bangare da abinda suka aikata ya taba ko ya janyo masa wani damage to wannan suna iya shigar da qara tareda hujjoji na gaske" Musa Kallah ya fada yana kallon Hadizan seta sake daga kai tace "Na yafe musu nidai" "To wallahi bazasu tafi haka kawai ba, bacin sunan da suka jawo mana se sun koma duk inda suka bata ta sun wanke abinda sukayi su fada da bakinsu cewar Qazafi sukayi mata" Yaya Isma'il ya sake fada cikin hasala yana hararasu su ukun, gaba dayan mutanen gurin da suka cika da tausayin da Mamakin Hadiza bisa wannan abu da tayi sukayi na'am da maganarsa. Kafewa yayi akan sedai a kira taron yan jarida su dauki komai Musa Kallah yace Aa, kamar yanda suka yada wancan a waya ya zaga ko ina yanzun ma haka zasu maimaita da bakunansu ta hanyar video bama rubutu irin wancanba nan take aka kawo Camera da professional me hoto ya fara daukar video. Babu bakin musawa dan a iya adalci sun san anyi musu su ukun suka jeru kowacce aka dauketa tana bayanin duk abinda ya faru da role din da tayi playing a cikin lamarin. Kasa rufe bako Hajiyar Khalil tayi sanda take jin kan zancen na gaskiya dan ita Abokin Khalifa gaya mata yayi wai fada sukayi da maqociyarta shine aka kamasu ta girgiza kwarai da jin lamarin, badan da kunnenta take ji Umaiman tana maimaitawa abinda ya faru ba da wallahi ba zata taba yarda zatayi haka ba. Haka aka gama daukarsu Video akayi rubutu kowanne bangare suka saka hannu na anyi musu tsakani babu au babu Hadizan. A take aka sallami Umaimah da Rufaidah babu wadda ta kalli Yar uwarta kowa tayi ta kanta Khausar kuwa ciki suka maidata saboda sun bude mata sabon case ita da saurayinta da yake can a garqame Wanda ashe qundumemen case ne akansa ana suspecting informa ne na yan Kidnapping kuma an dade ana bibiyarsa se yau Allah ya basu sa'a akansa a ka kamoshi ba tareda yayi zato ba. Mahaifinta yanke jiki yayi ya fadi dajin wannan sabon tashin hankali, ragowar kowa ya kama gabansa banda Isma'il da be bar gurin ba seda aka tura masa copy na video confession dinsu Umaimah be kuwa bata lokaci ba gurin uploading nasa a Media kan kace kwabo labari ya yadu a ko ina. Daga CID Asibiti aka zarce da Umaimah, Hajiyarsu Khalil dai kasa magana tayi haka shima ya zama kurman dole ya rasa abinda yake ji a ransa. Yaji dadin wanke Hadiza daga zarginda ake mata da akayi amma yayi baqin ciki da takaicin wai matarsa ce aka dauki video ta tana fadar abinda ta aikata idan ya tuno abinji yakeyi kamar yayi bindiga ya fashe shi yasa koda suka tashi tafiya ya dauki su Hajiya kamar yanda sukazo ita kuma yan gidansu suka tafi da ita. Be taba nadamar auran Umaimah ba irinna yau, yayi nadamar zuwansa gurin Nasir da har ya janyo haduwarsa da ita amma qaddara ta riga fata. Yanzu babu abinda yake ganin zeyi ya goge baqin cikin data qunsa masa ya kuma biya Hadiza bacin sunan data ja mata kamar ya auro ta su zauna tareda Umaimah kuma babu yanda ta iya da ita. Yana ajiye su Hajiya be tsaya na ya juya dan be samu damar magana da Hadiza ba a can gurin qudurinsa kuma baya so ha dauki lokaci idanso samune kafinya koma SA yake so a daura musu aure su tafi tare idan yaso kafin ya dawo Umaimah tayi bunga ta mutu tsabar baqinciki. Hanyar gidansu Hadizanya dauka a ransa yana addu'ar Allah yasa ta aminta da maganar sa ba taredabata lokaci ba. "Zama ta amince saboda Hadiza tana tsananin Sona" ya bawa kansa tabbaci da kwarin guiwa. Acan Asibiti kuwa Emergency aka karbi Umaimah, Ruwa suka fara daura mata kafin suka bata duk wani taimako da takeda buqata sun kuma tabbatar da lafiyar abinda yake cikinta wanda a shegiyar qaryarta tace ya dena motsi, anan suka barta da Anty Abba da Baba Abdullahi se Maman Asad da itama ta bisu suka koma gida daman Mama bata jeba ragowar Drama se in ta koma gida za'a qarqareta. A gidan Hajiyar su Khalil kuwa zaman kurame aka shigayi bayan ya ajiye su ya tafi, dakyar Hajiya ta iya bude baki tace "Amma ban tana tsammamin ko a mafarki Umaimah zata aikata irin wannan abunba, ina mata kallon me hankali da tunani, wallahi idan ne ya gayamun wannan abun take yanke zan qaryata dukda a yanzun ma na tabbatar da bayin kanta bane, zugar wannan shaidaniyar yarinyar ce kuma Allah kadai yasan abubuwan data gaya mata harta yarda tayi hakan". "Yanzu fisabilillahi hajiya koma me ta gaya mata ita Umaiman bata da hankali da A'ace tayi abu tayi? Me ya hana ita waccen din tayi da kanta ai saboda tasan illar abun se ita data fi kowa wauta babu tunani babu komai ta aikata. Kafin ta watsa a social media din ai mu ta fara aikowa har a wayarki ta turo mu muka saka Khalifa ya goge dan karki gani hankalinki ya tashi, a wauta da rashin tunaninta wannan abin ne ze saka Khalil ya fasa auranta kinga ai yanzu ko bashi da niyya ta saka shi dole ya aureta dan babu yanda za'ayi a tozartata saboda kuma ya qita dan wallahi dukda wannan abun da aka saka sukayi wasu se sun kalleta da abun, wasu ma cewa zasuyi qaryane anyi kawai dan a wanke ta" Anty Amina babbar yayarsu Khalil din ta fada a fusace se Jalilah tace "Ai wlh Anty bakiga abin tausayi ba seda mukaje Asibiti dubata, sun dauki haqqin yarinyar nan kuma Allah ne kadai ze rama mata wallahi" "Allah ya rufa asiri" Hajiya ta fada kafin ta tashi ta shige dakinta, har a sannan mamaki takeyi amma ita tayiwa Umaimah uzuri ta kuma dora laifi kacokan akan Khausar dan ita ta shirya komai. HALIN KISHI 47 *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 47 KHALIL Tun daga Nesa ya hango Hadizan tsaye da wani da be tabbatar da waye ba dan ya bashi baya. Ya samu guri ya ajiye motarsa daga dan nesa dasu kafin ya tako a qafa seda ya isa kusa dasu ya gane Musa Kallah ne. A mutunce suka sake gaisawa yana kallonsa yace "Wato Khalil ka godewa Hadiza, badan tace ta yafe ba ina me tabbatar maka se mun daure matarka daurin da ze saka tayi hankali" se Khalil ya gimtse fuska yace "Ban fahimta ba, da aka ce muku bata da hankaline ko yaya?" "Idan ma tana dashi toh be kai yawan wanda ya kamata matured mutum irinta ya mallaka ba, any way Allah ya taimaketa dan da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba" Musa Kallah ya sake fada kafin ya juya kan Hadiza yace "Kin daiji abinda na gaya miki, ki samu ki huta sosai ki kuma cire duk wata damuwa daga zuciyarki, if you need someone to talk to I'm always available for you and karki manta think about what we discussed ki kuma bani amsa da wurwuri dan bana son jira". Kanta na qasa ta amsa masa da cewa "In sha Allah Sir, na kuma gode kwarai Allah ya saka da alkhairi akan qoqarin da kayi mun na gode banida abinda zan saka maka dashi sedai naci gaba dayi maka addu'a Allah ya tsare gabanka da bayanka" "Amin, amma kece kike da abida zaki biyani dashi kuwa Hadiza sedai idan kuma kai tsaye kina so kice nayi miki tsufa ne se na tattara na koma gurin tsohuwar Matata mu qarasa, bari naje, i have somethings to attended in the office se munyi magana kinji" Musa Kallah ya sake fada yana yar dariya kafin ya juya ya kalli Khalil daya cika yayi tam ya masa wani dan murmushi ya juya inda Driver sa yake jiransa. Shiru yayi yana kallonta bayan da Musa Kallah ya bar gurin, har wani sama da qasa yaji numfashinsa yana yi masa saboda bacin rai kamar yabi shi ya shaqo wuyansa ya lallasa shi nan shi gani yakeyi ya zama wani Hero a gurinta ko? Kawai saboda yayi shishshigi daya barshi ai shi zeyi handling komai amma ya kwaso wasu qafafunsa kowa ya gayyatoshi ma oho. "Na gaji da yawa Khalil, ko zaka bari idan ka shirya seka dawo dan naga yanzu kamar baka zo don muyi maganaba" Hadiza ta fada ba tareda ta kalleshi ba se ya sassauta fuskarsa yana qoqarin danne bacin ransa yace "Amm nasan ba yanzu ne lokacin da ya kamata nazo ba amma na kasa samun nutsuwa ne Hadiza har yanzu ina kallon kaina a matsayin me laifi a gurinki. Nine silar duk abinda ya faru dake nina jawo miki dan Alllah...." "Na gaya maka ka dena zargin kanka, kuma ko ba wannan ba su kansu wanda suka aikata mun laifin na yafe musu nace me yasa zaka ci gaba da damun kanka idan kuma wannan ne ya kawoka shima babh wata damuwa, zan iya shiga ciki?" Ta fada tana kallon cikin idonsa. Seya kasa ce mata komai, dukda bada fushi ko hayaniya tayi maganarta ba amma shi ya fahimci jin zafinsa a kalamanta. Ganin bashi da niyyar sake cewa komai yasa ta fara tafiya yayi saurin dakatar da ita da cewa. "Hadiza, ina roqon da ki bani dama ta biyu. Kuma a wannan karon da gaske nake yi idan kin Amince daganna zuwa qarshen satin nan a daura mana aure mu koma SA tare nasan a yanzu kina da buqatar kiyi nesa na dan wani lokaci kodan saboda nutsuwarki ta dawo". Tsayawa tayi cak na kusan minti biyu kafin ta waiwayo fuskarta dauke da wani murmushi tace " Thank you Khalil, idan da rabo wata rana ko a hanya zamu hadu mu gaisa amma daga yanzu bana buqatar ka sake takowa inda nake, ka dauka qaddara ce haduwarmu wadda ta rigada ta afku, ina kuma so kayi qoqarin manta wanzuwata a duniyarka gaba daya kamar yanda na dade da gogeka a tawa duniyar, ina yi maka fatan Alkhairi ina kuma yi maka fatan idan kana da Rabo Allah ya baka macen da zata kula da kai saboda kai mutumin kirki ne. Tsakanin da akayi mana a Station bada matarka ne kadai ba harda kai, idan kuma kaci gaba da bibiyata" ta saki wani murmushi ta juya tana cewa "Na barka lafiya". Yanda kasan hoto haka ta barshi a gurin seda ya dena hangota gaba daya kafin ya iya jan qafafunsa yabar qofar gidan daman yasan da wahala, ba ita ba baya tunanin akwai macen da zata yarda ta rabe shi idan har tasan labarin ta'asar matar sa. Kwana uku ya qara ya koma SA a lokacin an sallamo Umaimah daga Asibiti kuma har sannan magana bata shiga tsakaninsu ba. Sau daya yaje ya dubata a Asibitin se randa ze tafi daya koma shima bisa takurawar Hajiyarsa. Haushinta yakeji matuqa, dukda yanda ta koma kalar tausayi seka rantse daga sannan Ta shiryu amma shi ya tabbatar da na dan lokaci ne, idan har Umaiman daya sani ce ana nan saboda hali aka ce zanen dutse. Haka ya tattara ya koma yaci gaba da abinda yake a gabansa gaba daya ya watsar da wata Umaimah koda yake ai ita ya kamata ace ta nemeshi ta bashi haquri akan abinda ya faru kafin ya duba ya gani idan da yuwuwar katbar tuban nata. Yanzu kammaluwar ginin gidansa daya dauko ne a gabansa, an kammala bangaren Hajiya har suna shirye shirye komawa ciki sannan a rushe daya bangaren dayake nasa danhar an shigo da qarin filin daya siya ciki. Da yaso ya dakatar da aikin zuwa wani lokaci amma a yanzu yana jin kawai ze ci gaba, idan har ya samu yanda yake so baze rufe shekarar nan ba tareda ya qara aure ba danya gaji da bala'in Umaimah, nema takeyi ta dora masa ciwon da bashi dasu. UMAIMAH Takunkumi Mama da Abba suka saka mata dan daman wayarta tunda Yaya Aminu ya karba ba'a maida mata ba a cewar Abba ma ta gama riqe waya tunda da ita take jaye jayen bala'i fada kuwa ta shashi da nasiha har seda taji ta tsani kanta ta tsani halinta. Babban abinda ya qara damunta yanda ta kasa samun fuska a gurin Khalil. Sau saya ya dubata a Asibiti se ranar da ze koma SA da safe Ya sake komawa shima bisa tursaswar Hajiya, da zuwansa kuma da tafiyarsa beyi minti goma ba. Magana daya ta shiga tsakaninsu ya sake maimaita mata duk abinda take da buqata ta nemi Khalifa Already daman ya biya kudin Antinatal dana haihuwa lokaci kawai ake jira sannan ya saka mata wasu kudi matsayin na siyayyar haihuwa. Cikin kukan daya zo mata ta tsaya gabansa tana cewa "Dangirman Allah Khalil kayi haquri, wallahi....." Gani tayi ya juya ya fice daga dakin abinda ya hanata qarasa magiyar data debo kenan. Tana jiyo yanda su Anty suke masa fatan sauka lafiya da nasara akan abinda ya tafiyi yayi musu sallama ya fice daga gidan nan ta zube taci gaba da rusa kuka baji ba gani. A zatonta ai komai ya wuce tunda me afkuwa ta afku akan me ze dauki fushi da ita bayan duk ma abinda ta aikata sanadiyyar son da take masa ne da kishinsa ya janyo. Haka taci gaba da zama a gidan cikin takura da qunci, ga rashin waya ballantana ta samu ta kira Khalil din ta rarrashe shi, sau saya ta saci ta Anty ta kirashitunda yaji muryarta daga ranar kota kira baya dagawa, qarshema dena shiga tayi qilan ya tosheta ne. A cikin haka wata rana Maman Asad tazo gidan, Umaimah na daki ta shiga ta sameta. Cikin tausayawa ta kalleta dan cikinta da ya ke wata tara yanzu harta haura EDD na daya dana biyu gaba daya ta fita hayyacinta baqiqqirin ga uwar rama saboda damuwar data saka a ra ta ta rashin magana da Khalil. Zama tayi a gefe ta kalleta tace "Sannu Umaimah, se kizo daki ke kadai ko zauna kina faman tunani bakya ko tsoron wani ciwon ya kamaki ga tsohon ciki? Yanzu daman Anty take gaya mun abinci ma ba ci kikeyi ba, wani sa ilin yanda aka ajiye haka ake zuwa a dauka baki taba shi ba anya hakan da kika daukarwa kanki mafita ce?" Kamar daman tana jira ta fashe mata da kuka tana cewa "Toh daman waya damu ko jiyo ya kamani na mutu nayi rai duk damuqata ce ba taku ba ina ku kuna rayuwarku cikin walwala da farin ciki? Daga Abban har Mama babu wanda yake hade muku fuska koya hantare ku se nice ba'a tausayi ko duba halin da nake ciki ba'ayi ake mun abinda aka ga dama" "Ai Umaimah duk abinda ya sameki ke kika jawa kanki, kuma ke ya kamata ki fara tausaya kanki. Ai baki duba halin da kice cikin ba ki ka dauko magana da yanzu badan Allah ya taqaita ba ai qila kina can kurkuku a kulle wayasan ranar fitowarki? Kuma har yanzun babu alamar kinyi nadama dan babu wanda kika nuna wa hakan ballan tana ki nemi afuwarsu su denadaure miki fuskar, ko kuwa zaman da kike a daki da qin cin abincin ne kike zaton ze saka su dakko su shiga harkarki? To idan ma dan haka ne gara tun wuri ki chanza tunani dan a banza zaki kashe kanki qarqari mu miki Addu'a idan mun tunaki" Maman Asad ta sake fada se kuwa Umaimah ta qara ware baki tana cewa "Daman na sani duk ba qaunata kukeyi ba, fata ma kukeyi na mutu sabida na tsare muku wani abun sannan me qaunar tawa ma an shiga an fita an raba tsakanina dashi wallahi duk abinda mutum yayi shida Allah" Dariya wauta da rashin hankalin Umaimah ya bawa Hajiyayye tana kallonta tace "Halinki ne ba'a qauna bake ba, kuma shi me son naki da kike magana ke kika raba tsakaninku ai. Ke yanzu bakiji ko dar ba bakiyi tunanin mutunchinsa ba yanzu ace matarsa ce tayi abinda kikayi? Yanzu haka video ku yana nan yana zaga gari kowa yasan ta'asar da kika aikata dayawa kallon Mahaukaciya ma suke miki saboda kishi kin zubarwa kanki da Mijinki mutunchi ta ina kike tsammanin ze sake bi ta kanki? Ai wallahi kin wa kanki wauta Umaimag kuma kin barar da kanki a gurin Khalil na tabbatar yanzu a kaso dari babu ko Ashirin na So da girman da yake baki dan kin nuna masa baki san darajar kanki ba. Nidai shawarar da zan baki ki maida hankalinki jikinki ki, ki ringa fita kina motsa jiki ki samu ku rabu da cikin jikinki lafiya kafin ki fara yaqin maido da kanki a gurin Khalil dan dai a yanzu nida ke munsan bakya gabansa" tana kaiwa nan ta fice ta bar Umaimah cikin tunani da neman mafita. Kwana hudu da zuwan Maman Asad gidan ta tashi da naquda, guraren qarfe goma sukaje Asibiti cikin ikon Allah kafin sha biyun rana ta haifo kyakykyawar yarta itama me kama da Khalil. Seda ta uku a Asibiti saboda jini daya balle mata bayan haihuwar basu dukda komai ya daidaita suka qi sallamarta a cewarsu se sun tabbatar da lafiyarta saboda gudun kar wani abu ya sake tasowa bayan sun koma gida haka yan barka da dubiya suka ringa zarya a Asibitin daga bagaren ta zuwa na Khalil da har yanzu suke cike da jin zafin Umaiman Hajiya ce kadai take rawar jiki da ita dan kullum setaje Asibitin har aka sallame ta da ita suka koma gida ga tarin kayan barka data kawo dukda Khalil dinya gaya mata wannan karon ya bawa Umaiman Kudi ta siyi abubuwan da take buqata amma seda ta hado nata. Fitowarta kenan daga wanka ta daura Zani sannan ta lullubo jikinta qaton towel, ta zaune a bakin Gado tana jin yanda jikinta daya daddaure yake saki, tunda ta haihu bata samu wanka me kyau ba se yau da safen saboda zaman Asibiti, jiya kuma da suka dawo dare yayi dan haka suka bari se yanzu da safe Anty Laure tayi mata wanka gangariya ta zane mata jiki da darbejiya kuma taji dadinhakan. Nuratu ta shiga dakin sabe da jaririyarta Aidah me kimanin watanni biyu ta miqawa Umaiman wayar hannunta tana cewa "Gashi za'ayi magana dake" seta karba tana kallon wayar ganin ba akan kira take ba ta ajiye a gefe ta shiga shiryawa. Tana qoqarin zuge zip din doguwar rigar data saka wayar ta shiga qara, se sannan ma ta ankare da cewar wayar tace aka bata, ta zumburi baki ganin me kiran wallahi badaban muguwar kewarsa da tayi ba da bazata dauka ba. Ai ko babu komai taci darajar haifar masa ya da tayi ya kirata yaji lafiyarta amma ace har se yau kwana hudu sannan ze kirata taja kwafa tana hararar wayar daidai nan kiran ya katse wani ya sake shigowa. A daqile tayi masa sallama ya amsa murya ba yabo ba fallasa ta shiga gaishe shi ya amsa tareda tambayarta qarfin jiki, seda taja tsaki qasa qasa kafin tace da sauqi sukayi shiru gaba dayansu na kusan minti daya. Jira takeyi taji ya bata uzuri na rashin kiranta sannan ya rarrasheta ya gaya mata kalamai masu dadi irin yanda ya ringa mata sanda ta haifi Mu'ayyad dan har ta fara tattare fuska tana kwabeta zata fasa masa kuka taji yace "Abba yayi mata huduba da Aisha ya gaya miki ko?" "Be gaya mun ba, amma ba kace idan mace na haifa ba sunan Mama za'a saka mata?" Ta mayar masa da amsa tana maimaita Aisha daya fada sunan Hajiya kenan ai ba haka sukayi dashi ba "Munyi magana Abban yace baza'ayi taron suna ba, Khalifa ze kawo raguna da duk abinda za'a buqata sannan zan saka miki kudi yanzu ina fatan babu wata matsala" ya bata amsa a dake ba tareda ya mayar da hankali kan abinda ta fada ba. Kuka ta fasa masa tanacewa "Yanzu Khalil kayi mun adalci kenan, ka tsallake kayi tafiyarka ka barni baka damu da halin danake ciki ba, sama da wata biyu baka kirani ba ina raye ko na mutu duk ba matsalarka bace sannan na haihu na kwanta a Asibiti tsayin kwana uku baka kira kaji ya nake ba se yanzu ne kawai zaka ce kira saboda ka gaya mun ka sakawa yata sunan da bashi mukayi dakai zaka saka mata ba wannan ai rashin Adalci ne". "Zan koma bakin aiki, idan da wata damuwar kina iya kirana tunda kin kunna wayarki" ya sake fada kafin ta bashi amsa ya katse kiran. Sororo tabi wayar da kallo wasu hawaye masu dumi suna bin kuncinta, ta daga kai ta kalli Anty Hafsa da bata san ta shigo ba se ji tayi tana cewa "Bakiga komai ba Umaimah idan har dai bazaki nutsu ki kuma gyara bakinki ki kuma san abinda kikeyi yanzu kika fara ganin haka" ta juya ta fice abinta bayanta kwantar mata da Babyn data shigo kawo mata. KHALIL Tun bayan komawarsa kacokan ya mayar da hankali kan abinda yakeyi ya cirw duk wata damuwa da zata iya distracting nasa. Daman be tsammaci zata kirashi ba shi yasa ma be saka ko a kai ba, randa ta kirashi da wayar Anty yana ganin kiran jikinsa ya bashi itace dan suna magana da Yaya Aminu a bakin sa ma yaji cewar an kwace wayarta dan haka yasa jefi jefi yakan kira Mama su gaisa ya kuma tambayeta lafiyarsu, yanda bata taba cewa zata bashi Umaiman suyi magana ba shima be tambaya ba se ranardata kirashi yana kwance a Hotel room dinda yake, farkawarsa daga bacci kenan wanda cike yake da mafarkin Umaiman suna gudanar da irin soyayyar da yayi tsammanin samu idan ya aureta ya farka kenan yaji qarar wayarsa ya janyota ya duba kamar baze dauka ba kuma wata zuciyar ta saka shiya daga ba tareda yayi magama ba yana jin muryarta kawai ya kashe shi kansa besan dalilinsa nayin hakan ba amma kawai yana so ko yaya ne ya koyawa Umaimah hankali dukda dai yasan Umaimah dai Umaimah ce. Haka yaci gaba da lallaba rayuwa, a duk sanda tunaninta da kewarta suka bijiro masa har yaji zuciyarsa na neman karaya ta sakashi ya kirata se yayi saurin tuno abinda tayiwa Hadiza da irin tozarcin da ta saka Hadizan a ciki dan har kawo yanzu hotunanta basu dena yawo ba,wasu ma se yanzu suke sake yada shi a matsayin sabon abu, qarin baqin cikinsa na rasa Hadizan da besan yana sonta har haka ba se lokacin da yayi tozali da katin daurin auranta da Musa Kallah nan da sati biyu masu zuwa. Baqin ciki kamar yayi me, yanzu ta qishi ta zabi wannan tsohon da duk boko ta gama tsotse shi ya tabbatar babu abinda ze iya mata, bazata wani samu wata kukawa a gurinsa ba kamar ace idan shi ta aura haka ya wuni ya kwana ranar da takaici, haushin Umaimah ya sake cikashi, duk ita ta janyo masa tasa Hadizan taqi amincewa da auransa wannan tasa ya qara tsahon zaman da zeyi a SA, ya kamata ace ya dawo Nigeria yanzu amma ya zabi yaci gaba da zama acan zuwa sanda yake ganin zuciyarsa tayi sanyi ze kuma iya sauraran Umaiman. Sanda ya samu saqon an kaita Asibiti sosai hankalinsa ya tashi, ya tuno naqudar Mu'ayyad wadda tayita akan idonsa ya tuna irin wahalar data sha se yaji zuciyarsa ta fara tsinkewa. Ya tabbatar da tana buqatarsa a kusa da ita ya riqe hannunta yana mata sannu kamar yanda sukayi wancan tare ta yanda bazataji cewar ita kadai bace yana tare da ita a kowanne yanayi. Yana nan yana kaiwa da komowa yana mata addu'ar sauka lafiya be samu nutsuwa ba seda yaji kiran cewar ta sauka ya ringa Hamdala a fili da zuciya, ransa qal dayaga kyakykyawar yarinyar data haifa masa kuma a kallo daya ya hango kamar da takeyi da Hajiyarsa babu bata lokaci ya ayyana sunanta kenan takwarar Hajiya ce. Tun a ranar yaso magana da ita se daga bayane ma aka sanar dashi Ballewar jinin data samu lokacin har komai ya daidaita babu wata matsala dukda haka hankalinsa be kwanta na seda ya ganta a Video call tana bacci hankali kwance aka kuma hadashi da likitan da ta dubata ta tabbatar masa da babu wata matsala sannan ya samu nutsuwa. Babu dadewa matar wani abokinsa Mannir ta haihu lafiya har suna shirin tafiya gida jini ya balle mata kafin kace me Ajali ya risketa shiyasa ya godewa Allah da basu gaya masan bama har seda komai ya daidaita dan qila da fargaba ce zata kashe shi kafin ita. Kullum seya kira yaji jikin nata, yanda bece su bata wayar ba haka babu wanda yace masa gata se yau da safe bayan an sallamo su daya kira shine Nuratu tace zata kai mata wayarta seya kira tacan. Sam beyi mamakin maganganunta ba indai Umaiman daya sani ce zata aikata sama da haka ma amma a halin da suke ciki beyi tsammanin har zata iya ce masa wani abu ba dan ya saka wa yarsa sunan da bashi yayi mata akqawari ba kuma fa sunan uwarsa ya saka ba wata ba ballantana tace kai Umaimah dai bazata canza hali ba. Da har yayi niyyar komawa amma wannan abun da tayi masa yasa ya fasa, ze ci gaba da zama har se randa tayi hankali tasan abinda takeyi idan ta nemi su shirya sannan zasu shirya. A bangaren Umaimah kuwa sabon fushi ta dauka da baqin rai, sam tunani ta be kawo mata cewar bata yi daidai ba, a yanzu ma gani takeyi ai ita yayiwa laifi, ya tsallaketa ya tafi uwa duniya sannan yanzu ya sake zuwa ya saka wa yarta sunan uwarsa bayan tata uwar yayiwa alqawarin takwara ai kuwa bazata sabu ba, badai Abba yace yayi mata huduba ba? To dakanta zata gayawa Abban yanda sukayi ai dai shima se yafi so a saka sunan matarsa akan wata. Kukan da Babyn ta fara ya saka ta dauketa ta shiga shayar da ita. Fuskar Khalil take gani sak dan kamar ma tafi Mu'ayyad kama dashi, ta sake qanqame yarinyar wata irin qaunarta da kewar Mahaifinta na shigar ta kome ta tuna kuma ta zumburi baki tareda kwantar da ita a gefe dukda da alama bata qoshi ba dan tana cire ta ta fara kuka a fili tace "Bazaki sha din ba ubanki yazo ya baki nasa" ta dungure mata kai kamar wata meyi da sa'arta yarinta kuwa ta canyara kuka. Anty Laure data debo garwashi ta shigo da sauri dan a zatonta ita kadai ce seta tarar da Umaiman na dannan waya "Wallahi idan baki aje wayar nan kin dauketa ba se kin ci ubanki Umaimah" ta fada tana aje garwashin hannunta. Umaimah ta zumburi bakinta da be gama sacewa ba kafin ta harari yarinyar tace "Nafa bata shegen cine da ita kamar gara, kumani zafi yake mun sedai a hada mata madara". Banza Anty laure tayi mata ta shiga tattare kayan wanki kafin ta watsa mata harara ganin har sannan bata dauke ta ba tace "Ki bari na dawo wallahi sena zaune ki a gurin nan shashasha kawai" ta fice abinta. Umaimah tabita da kallo kafin ta dauki yar tana ayyana yanda tsaf zata zaunetan kuwa da wadannan qattan mazaunan nata. Anty Laure irin masu qaton Duwawun nan ce har idan tana tafiya seka tsaya ka kalleta saboda girman su kuma da alama sam basa damunta ita dan abinda siriri zeyi tsaf zakaga tayi itama. Nonon ta cigaba da bata tana dannan wayarta. Layin Rufaida ta kira wayar tayita qara harta katse bata dauka ba ta sake kira nan ma dai seta haqura qila tana wani abun idan ta gani daga baya ta kirata. Tunda suka rabu a CID basu sake haduwa ba daman ba waya balle ta kirata se yanzun, daga nan Data ta kunna ta shiga whatsapp, messages suka ringa shigowa amma duk sunqi budewa saboda dadewar da tayi bata hau ba. Status ta wuce ta dora cewar ta Haihu, ta samu baby girl kafin ta aje wayar lokacin babyn tayi bacci ta kwantar da ita a gefe itama ta kwanta tana jiran kiran Rufaida har bacci ya kwasheta bata kira ba. Surutan Mu'ayyad suka farkar da ita yana tsaye akanta tana bude ido ya daneta cikin murna yana mata gwaranci. Rungumeshi tayi itama cikin farin ciki, rabon data ganshi tun kafin case dinsu da Hadiza se yau din. Ta daga shi ta dora akan gado tana tambayarsa shidawa sukazo, ya gane me tace amma babu bakin mayarwa dan haka kawai yace mata "Papa, Bibi". Bata gane abinda yake nufi ba tayi dariya kawai ta miqe ta shiga bandaki, fitsari tayi ta canza pad kafin ta fito bata tarar dashi a dakin ba dan haka ta saka safa a qafarta ta zura Hijabi ta fita jin muryar Khalifa a tsakar gidan da Alama tare suka zo. Gaisawa sukayi tana cewa "Aa badai tafiya ba ka shiga ciki mana" "Ai daga cikin nake mun dade da zuwa akace bacci kikeyi zanje seda yamma zan dawo na tafi dasu daman saqo na kawo shine Hajiya tace a taho da Mu'ayyad yaga Baby suna ciki shida Habiba" daga nan yayi mata sallama ya tafi. Parlour Maman ta shiga inda take jiyo Hayaniya, gurin cike da yan barka, ta samu guri kusada Habiba ta zauna ta gaidasu kafin Habiban dake riqe da baby ta shiga gaisheta fuska washe da fara'a. "Mama, Bibi" Mu'ayyad ya sake fada yana leqa Babyn, se sannan ta gane wato Babyn ce Bibi tayi murmushi kawai ba tareda tace komai ba, Habiba ta katseta da cewa "Anty me za'a ringa ce mata, Yaya yace sunan Hajiya taci" "Ku zabar mata duk sunan da kukaga ya dace nidai Aisha zance" ta fada tana dan murmushi, Habiba ta kalleta ta kalli yarinyar fuskarta ta nuna alamun rashin jin dadin abinda ta fada din amma seta qirqiri murmushi tace "Itama Hajiyan haka tace kar a boye amma Yaya yace Aa baza'a fada ba" Umaimah kuwa qin yarda tayi ta kalli Mama wadda ta tabbatar da taji abinda ta fada dan tunda ta shigo ta saka mata ido, daga qarshe ma tashi tayi tana cewa Habiban tazo suje can dakin. Haka suka qarasa wuni yan barka nata shigowa Umaimah nata faman duba waya ko zata ga kiran Rufaida amma shiru, kuma taga ta bude status dinta amma batace mata komai ba. Se yamma lis su Habiba suka tafi dakyar da kuka shabe shabe aka dauki Mu'ayyad daya dage se su tafi da Bibi, Umaimah daya fito daga wankan yamma tana shiryawa Mama wayarta dake kan mudubi tayi qara ta dakkota ta duba, Naziyya ce ta kirata akan zancen dinkin suna dukda ba taro za'ayi ba dai ya kamata tayi kwalliya a cewarta. Ta tabe baki tana cewa "Ni babu abinda na siya ma wallahi, idan kinada latest kaya ki turamun na zaba toh" "Bani da kaya amma bari na baki lambar *Ummu-Maheer Collection* kiyi mata magana, duk abinda kike so daga kan Atamfa, Laces, Voile, Mayafai, takalma da Bags duk tana siyarwa kuma latest and unique design da se ki gama yayinsu ko a hoto baki ga me irunsu ba akan farashi me sauqi daidai da aljihun kowa" Naziyyan ta fada se Umaimah tace "Toh ki turo yanzu amma kinga lokaci ya qure saura kwana uku, wai har zan samu dinki ma kuwa?" Dariya Naziyya tayi tace "Bakida matsala da wannan dan tana da kwararrun Tailoli da zasuyi miki dinki daidai da zamani idan kin siya kaya sedai kawai ki aika da measurement ko kije da kanki a gwadaki" "Turamun da number tata yanzu kuwa nayi mata magana tunda ga sauqi daga Allah" Umaimah ta fada kafin suka kashe wayar sega number Naziyyan ta tura mata (Zaku iya tuntubar mu kai tsaye akan 08142548705 Ko kuma ku dannan wannan link din ku shiga group dinmu kai tsaye domin samun sababbin kayayyaki akan farashi me sauqi https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP) Bata bata lokaci ba ta dannan mata kira, suka gaisa ta gaya mata ita qnawar Naziyya ce nan suka sake gaisawa cikin fara'a dan Naziyya customer tace sosai. Magana sukayi akan tana son kaya Ummu-Maheer din tace tayi mata magana ta WhatsApp nan ta tura mata da Latest Laces da take dasu ga hadaddun Atamfofi na yan gayu Umaimah saboda yanda ta rude kasa zaba tayi gani takeyi idan aka ce ta kwashi gaba daya ma tana so. Dariya dariya Ummu-maheer ta ringayi mata qarshe ita ta tayata zabe bayan ta nemi ta tura mata da hotonta dan ta ga kalar da zata dace da fatarta ta kuwa yi mata zabe me kyau, Laces ta diba yan ubansu guda uku se Atamfa biyu ba Brocade shima biyu tace ahada mata da mayafin kowanne sukayi total take ta saka mata kudinta suka rabu akan da safe zata shiga gidan Maman Nana ta aunata seta aika da measurement a dinka mata wanda zatayi amfanin suna dasu. Se gurin qarfe goma Abba ya dawo gida kuma har sannan tana zaune batayi bacci ba saboda tana son magana dashi duk haushin ragunan da Khalifa ya kawo dazu an daure su ta bayan dakin da take se kuka suke sun cika mata kunne. Kamar mara gaskiya ta zumbula Hijabi ta fita daga dakin, Mama data hado kayan abincinsa zata kai masa sukaci karo a hanyaz gabanta ya fadi dan bataji motsin tafiya ba se ganin Umaiman tayi da uban baqin Hijabi ko a ina ta samo shi oho taja tsaki bayan dataga fuskarta tace "Ke kuma ina zakije a daren nan haka?" Umaimah da sam ganin Maman be mata dadi ba taji kamar ta juya amma ta dake tace "Gurin Abba zanje ina so muyi magana dashi" "Wace magana ce da bazaki iya bare seda safe kuyita ba zaki fito yanzu da danyan jego ga gari da sanyi" Maman ta sake fada tana harararta, Ummaimah tayi qasa da kai, Abba daya jiyo su yace ta shigo mana, yana kallon Mama yace "Ya zaki hanata shigowa kika san abinda take so ta gaya mun" Mama ta wuce inda yake cin abinci ta dire kwanuka tana kallon Umaimah data nade a qasa kamar ta Allah tana gaida Abban, tun dazu taso su kebe tayi mata fadan abinda tayi a gaban Habiba amma baqin da suketa zuwa suka hana gara ma da suka hadu yanzu a nan din ta samu ta kwabeta. "Kinyi shiru Yar Umai ya akayi, ina kika bari Indon taki" Abban ya fada cikin tsokana ganin tayi shiru se sunkuyar da kai takeyi, Umaimah ta dago ta sace kallon Inda Mama take tsaye itama itan take kallo tayi saurin mayar da kai qasa, Abba yayi murmushi ya kalli Mama yace "Dan bamu guri Malikah, kinsan fa ki din nan idan kika bata rai kamar Boss kike koni wani sa'ilin tsoron magana nake a gabanki" ya fada cikin sigar zolaya Mama ta murmusa itama tace "Kunsan zaku fadi ba daidai ba shi yasa kuke shakkar fada a gabana dan an san bazanyi shiru ba nima, kiyi maza dai ki tashi ki koma kinbar jaririya ita kadai" tana gama fada ta fice daga dakin dan daman bata kawo masa butar shayinsa ba tasan kuma seya nema. "Uhm ina jinki ya akayi" ya sake fada yana kalllonta. Umaimah ta shiga wasa da yatsun hannunta tana cewa "Daman Abba dazu munyi magana da Khalil ne yace ya fada maka sunan da zakayi wa Babyn huduba ko?" "Eh ai tun washe garin da kika haihu ma nayi mata ashe Mamanku bata fada miki ba" "Bata fadamun ba Abba, kuma shima ba haka mukayi dashi ba tun kafin na haihu yace sunan Mama za'a saka idan macece ae kawai yau yace wai Hajiyarsa ya saka" Umaiman tayi saurin katse Abba se ya tsaya yana kallonta cikin rashin fahimta yace "To yanzu yaya akayi dai a taqaice bangane inda maganarki ta dosa ba?" "Ni Abba gaskiya sunan za'a chanza tunda dai shi yayi alqawari in yana son saka sunan Hajiyarsa ba seya bari idan na kuma haihuwa ba amma sabida rashin Adalci Mu'ayyad ya saka Babansa sannan yanzu ma yace Hajiya ze saka se kace ni banida Iyaye haba gaskiya ka kirashi kawai ka ce masa ka canza sunan Mama aka saka mata" Umaimahta fada cikin iyakar gaskiyarta. Tsabar mamaki Abba baki kawai ya bude yana kallonta, kai shifa wautar Umaimah ta fara bashi tsoro ace yarinya ita abinda ranta ya raya mata kadai shine daidai babu ruwanta kuma ko a gaban waye zata fadi ra'ayinta ko yayi maka daidai ko kar yayi ita dai in ya mata shikenan. "Dan Allah Abba ka kirashi kaji, kaga ni haushina yakeji har yanzu akan budurwarsa, tunfa lokacin se yau mukayi magana a waya nasan kona masa maganar ma baze kula ba amma idan kaine ka bashi umarni bazece komai ba ze yarda" Umaimah ta shiga magiya jin Abban bece komai ba seyaja numfashi ya ajiye kafin ya soma magana cikin lallami dan ya fuskanci fada baze tafi da Umaimah ba, nasihar dai ita ta dace da ita dan da alama kwakwalwarta tunanin yara takeyi. "Naji be kyauta ba gaskiya daya karya miki alqawari amma kinga shi suna duk wanda kika ga an sakawa mutum toh Allah ne ya zaba masa, yanzu ya rigada ya saka sunan mahaifiyarsa har an fadawa kowa kinga baze yuwu ace an chanza da wani ba, daman dai ace sunan wata daban ne can ya saka to idanan mayar dana mahaifiyarki babu wani abu amma yanzu Umaimah ai baxe yuwu ba. Kamar fa kece ace ya fara saka na Maman naki se kuma ya canza ya mayar dana Hajiyarsa zaki yarda?" "Tab baze yuwu bama wallahi" tayi saurin katse shi se ya saki murmushi yana sake jinjinawa wauta irin tata yace "To kin bawa kanki amsa baze ma yuwu ba se kiyi haquri kije kiyi Addu'a Allah ya sake baki wata ki saka sunan taki uwar bashi kenan ba?" "Amma Abba..." "Amma me Umaimah? Son zuciya qiriqiri? Kince idan taki uwar ya fara sakawa ya canza bazaki yarda ba sannan shi saboda besan dadin uwa ba se mu saka ya canza sunanta? Ban son shirmen banza tashi ki bani guri na zata maganar kirki ce ya kawoki ashe shirmenki da bashi da qarshe kikazo kiyi mun, tashi ki koma gurin yarki bana son wata magana a nan" Abban ya katseta cikin hade fuska dole ta miqe cikin qunquni tayi masa seda safe ya raka ta da ido a ransa yana mata Addu'ar Allah ya shiryeta, yarinya kamar wadda ke tunani a juye. Da Mama ta shigo yake gaya mata yanda sukayi da Umaiman kai kawai ta girgiza tace Allah ya rufa Asiri, labarin baranbaramar da tayi gana qanwar Khalil ta bashi taci gaba da cewa "Ni a cikin marasa hankali ma samun kamarki Umaimah se an tona, in ba haka ba mutum ya saka sunan uwarsa kice be miki ba se an canza ina aka tabayin haka fisabilillahi? Matar nan yanda take sonta koni uwarta ai se haka kaga fa irin hidimar da ta ringayi kullum wuni take a Asibiti har aka sallamo su bata gajiyawa ga waya akai kaia taji yaya suke duk wannan soyayyar bata sa ta raga mata ba se waye ze tsere daga Halin Umaimah?" "Addu'a zamu cigaba da yi mata wata rana se kiga ya zama labari" Abban ya fada ganin ranta ya fara baci, ta miqe tana zuba masa abinci ba tareda tace komai ba amma a ranta tana ayyana yanda zataci Uban Umaimah tunda taga alamar duk Horon da akayi mata a baya be shiga kanta ba tana sane ta hana duk wata hanya da zata samu magana da Khalil din a zatonta zatayi laushi ta bada haquri ta kuna nemeshi amma taga alamar Umaimah bata tunani irin na mutane. Anyi suna lafiya dukda ba'ayi wani taro ba Umaimah da Babynta sun sha gayu da hadaddun dinkunan da Ummu-Maheer tayi mata duk wanda yaga hotonta seya tambayi inda ta siyi kaya ta ringa yanga tana iyayi wai itama ta zama yar Unique collection, har kuma sannan bawai ta saki ranta akan sunan da aka sakawa Babyn da dasuka gaji da tambayarta me za'a ringa kiranta taqi fada ba suka fara kiranta da Bibi kamar yanda Mu'ayyad yake fada. A WhatsApp taga Hotunan da suka dauka ita da yaran Khalil ya dora, ta qulu iya quluwa, wato yana ganin status dinta ma ashe toshewa yayi yanda ba zata gani ba dan ko saqo ta tura masa baya nuna blue tick duk ita tayi zaton ma ko baya WhatsApp din dan tun da sukayi wayar nan be sake kiranta ba ita ce ma tayi masa magana a WhatsApp kuma be amsa ba to ashe yana gani wulaqanci ne ya hana ya amsa ta ze sani kuwa. HALIN KISHI 48 *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 48 Kamar wasa sukayi Arba'in, zuwa sannan Umaimah tayi laushi iya laushi ta kuma naba'a neman shiri take da Khalil ta kowacce shiga amma yaqi ya bata dama. Zaman ya ishe ta, wata kusan biyar ba wasa ba tana zaune ita ba me aure ita ba sakakiya ba kuma a gidan babu wanda ko a fuska ya nuna ya damu da zamanta sabgoginsu sukeyi kamar ma sun manta da wanzuwarta dan idan bata fito tsakar gida ba sedai taji suna hidimomi har wani lokacin ace mata ai an manta ma da tana gidan. Randa zuka cika kwana Arba'in Hajiya ta aiko Habiba akan tana gayyatar su Maman gobe zasu tare a sabon gidansu. Mamaki fal ya cika Umaimah dan sam bata da labarin ginin daya fara lokacin ana dambaruwar zancen ciki an gama wannan kuma aka shiga ta Hadiza basu damu wani lokaci ba balle har ya gaya mata zancan. Su Mama sunje sundawo sunata santin gida. A bakinsu taji cewar itama yana mata ginin gida dayane tareda Hajiyar amma kowa Get dinsa daban dan har ciki aka kaisu suka gani Sunata saka albarka da fatan gamawa lafiya. Abin ya sake qule ta, wai me Khalil ya mayar da itane yazo ya jingineta ya kamata ayi wacce za'ayi tasan matsayi ta dan ta gaji da wannan wulaqancin nasa. Seta kirashi sau nawa baze amsa ba idanma ya saga basa doguwar magana, data kawo qorafi ze ce mata yana abu ya kashe wayarsa WhatsApp kuwa tayi zuciya ta dena kulashi dan koya duba baya bata amsa dukda irin abunuwan da take aika masa dasu da atunaninta dole su saka hankalinsa ya tashi ya dawo gareta amma kamar me shuka dusa. "Koda yake yanzu ai yasan nasan barikin da yakeyi shi yasa bazeji shayin yin komai ba, qila yana can ya sake samun wata yarinyar shiyasa yayi zamansa ya manta da ita idan ba haka badai Khalil din data sani bane ze kwashe tsahon wata biyar na tareda mace ba" abinda take rayawa a ranta kenan duk ranar da tayi wannan tunani kuwa kwanan kuka da baqin ciki takeyi, ta kuma qudure a ranta duk randa sukayi arangama da wadda ta janye mata hankalin Miji sedai uwarta ta haifi wata dan seta kasheta idan yaso ayi mata duk abinda za'ayi. Kwanan su hamsin da biyar ta shirya da safe tace Salman yazo ya kaita gidan Hajiyar, Babu Wanda ya hanata suka kama hanya tinqis tinqis se gasu a gidan, mamaki ya kasheta ganin yanda gaba daya aka canza gidan, dan da sukaje seda sukayi gaba suka dawo, ta sake irga gidaje daga tsohon gidan Maman Asad da suka tashi tasan dai gida biyu ne tsakaninsu amma nasu Khalil din na daya bangaren. Ma'aikatan dake ta faman kwasar sumunti suna shiga dashi ciki suka tambaya ko Hajiya tana nan suka ce mata Eh, wani dan saurayi baqi da zeyi Sa'an Salman din ya taso ya bude musu qofa, qaton compound suka tarar ga qananun Get biyu dama da hagu, ya nuna musu na hagun yace nan ne gurin Hajiya Umaimah dai ta kasa dena kallon Hadadden ginin dake gabanta dukda bata shiga ciki ba gani takeyi yafi yanda su Anty suka ringa bada labarinsa haduwa. A sabon qerarren palour Hajiya suka yada zango, Habiba ta fito daga kitchen da gudu ta rungume Umaiman da ta tafi duniyar kalle kalle da mamakin a yaushe duk Aka yi wannan aikin bata sani ba? "Mamaki kikeyi ko Anty, ai se ma kin shiga naku kinga Aljannar duniyar da yaya yake qera miki zakiyi tsallen murna, nima dai Anty ki taimaka kiyiwa Yaya magana cikin Abokanan sa ya samo mun wani Architect yayi wuf dani, ko nima na samu a qera mun gida na haduwa irin naki" Habibata fada tana kallon Umaimah data kasa zama kamar wata yar qauye tana kalle kalle a parlour koda yake dole tayi kallo yanda a ka qalqalewa Hajiyar gida kamar na wata sabuwar Amarya, Khalil yayi nasa bangaren ya mata gini sauran yan uwansa suka qarasa qawata mata gida da kayan daki na alfarma, kujerun palour kansu saiti ne na Royal hade da gado da Dining Miliyan biyar cis suka siye shi a hakan ma Mijin Anty Amina ne yake kawo su yayi musu sauqi Hajiya ta ringa fada akan me zasu siya mata wadannan kaya suka cwme sun sanda Mahifinsu na raye na sama da haka ma ze siya ya zuba mata kuma yanzun suna dashi ne shiyasa sukayi. Ranar har kuka seda tayi, ta ringa saka musu albarka da addu'ar suma Allah ya kawo randa yayansu zasuyi musu haka. Dukan wasa ta kaiwa Habiban tana cewa "Lallai ma yarinyar nan kin riqa, a fakaice dai gayamun kike aure kikeso ko? To bari Hajiya ta fito in gaya mata musamu mu tattaraki mu miqawa me rabo" suka saka dariya gaba daya daidai nan Hajya ta sakko daga sama cikinshigar Alfarma harda Mayafi a jikinta da alama fita zasuyi Mu'ayyad na binta a baya yana mata surutu, hango Mamansa da yayi ya sakashi kwasowa da gudu ya sakko yana kiran Mama ya dane ta, dagashi sama tayi suna dariya Hajiya ta qaraso itama cikin dariyar take cewa "Ikon Allah, sakkowar nan tamu gurinku zamuje ashe kuna tafe? Idonki kenan yau a gidan nan Umaimah" Ta qarasa tana karbar Bibi daga hannun Habiba. Umaimah ta zube a qasa tareda Mu'ayyad dake ta tsallen murna a jikinta ta shiga gaishe da Hajiyar ta amsa tana tambayarta mutanen gida da yanda suka koma tace duk suna lafiya kafin suka gaisa da Salman shima "Kasa gane gidan mukayi Hajiya har seda mukayi tambaya" Umaimah ta fada Hajiya tayi dariya tace "Ai daman ba zaku gane ba, yaushe rabonki da gidan nan? Inaga tunda aka fara aikin ma baki zo ba?" "Munzo lokacin da kuke shirin komawa daya part din lokacin nema yayi mun zancan za'a fara aikin daga nan be sake cemun komai ba" Umaiman ta fada tana shan lemon da Habiba ta kawo musu. Hajiya ta kama baki tace "Tab kice kusan shekara guda kenan, gashi nan har an gama an tare, nakun ma qarashe yarage, da da aka gama nan yace ze dakata kuma bansan ya akayi ba mukaga an ci gaba da aiki, a yanda yake so ma kafin ya dawo an gama yanda kawai tarewa zakuyi" "Uhm" kawai Umainah tace ta ci gaba da cin abinda aka ajiye musu Hajiya kuma nata yiwa Bibi wasa ga Mu'ayyad daya hanata sakat wai se ta bashi ita. Hira suka ringayi Hajiyan nata mata labarin ginin, tace ta tashi ta zaga ko ina ta gani Habiba ta rakata suka shiga kurya da saqon gidan se santi takeyi a ranta ko tattara irin rashin M din da zatayiwa Khalil take, yanzu ace bata da darajar daze gaya mata yana gini kenan, qila da se rana daya zece zasu tashi ko kuwa da a nan din yayi niyyar ajiye Hadizan tasa. "Guri yayi kyau Hajiya Allah yasa raida lafiya akayiwa, su kuma Allah ya saka musu da Alkhairi ya cigaba da buda musu" Umaimah ta fada bayan sun dawo palour se Hajiya ta amsa da Amin cikin jin dadin Addu'oin Umaiman, abinda yasa take matuqar sonta kenan saboda hankalinta da sanin ya kamata ga kyauta da fara'a babu wanda zeje gidan nan ya dawo be yaba kirkinta ba in banda bangaren su Gwaggo Zara'u da tasan da biyu suka tsani Umaiman, saboda yaqi auran yarsu ya aureta ne. (Aa dai Hajiya ke da masu sa'a ne zasu bada wannan sheda akan Umai) Murmushi tayi tace "Ai ni banma so ya barnatar da kudi yayi wannan gini haka ba, ina laifin a mun dan daki biyu na da palour Flat nida ba yara ba nan da kwanaki idan Habiba ta daga gidan ai ya mun girma daga ni se Khaleefa, koda yake kinga an huta yayiwa dan uwansa tanadi se kuyi zamanku tare idan ya tashi aure ni se na koma inda zaku baro ko ya kika ce?" "Haba dai, Allah ze hore ayi masa nasa Wanda yafi wannan, kullum qara samun sababbin qere qere ake hajiya musammansu Yaya Khalil da harkar su kenan kar kiyi mamaki shekara iyanzu yace za'a rushe gidannan a sake wani" Habiba ta fada Hajiya ta kwalo ido kamar anzo rushe gidan tace "Saboda yace miki shima kwarkwarne irinki ba, Allah na tuba wannan gida ko a Aljanna ka samu kamarsa ai ka more wallahi menene babu a ciki? Har gurin wankan nan da Garden naji yana za'ayi idan masu filin bayan mu sun yarda sun siyar masa, nidai nace yajashi can cikin gidanku ku qarata wane gurin wanka ne ana zaune lafiya yan ruwa suzo su tare mana a gida". Dariya sosai suka ringayiwa Hajiyan, wai yan ruwa kamar wanda ze gina wani Teku. Umaimah da taje da niyyar qulla Sharrin da ze saka Hajiya ta kirawo Khalil ko be shirya ba ya dawo se gashi ta buge da hira, a gidan suka wuni sur se bayan la'asar suka fita tareda Hajiyan suka shiga wani gida da ake suna yarinyar gidan ta haihu. Basu fito ba se ana kiran Magriba dan haka suna idar da Sallah Umaimah ta hau shiri Hajiya na kallonta tace "Nadai gayawa Babana wannan zaman ya isa haka tunda dai Allah yasa kin haihu lafiya se ya zaba ko ya dawo ki koma dakinki ko ya shirya miki ki bishi can, ai su Malikan ko basuyi magana ba abin ze damesu a ajiye maka Ya sama da wata biyar ai babu dadi, gara ki tattara ki koma dakinki in yaso ki nemi me tayaki zama kafin ya gama walagigin nasa ya yanke shawara dan ya fara cewa wai gurin zama waye waye dinsa dai". Wani sanyi taji ya ratsa ranta, tun dazu shirya abinda zata fadawa Hajiyan takeyi ta rasa se gashi ta rage nata aiki dan haka ta marairaice fuska tace "Wallahi ko Hajiya, kinsan mutane da surutu, wasu ma cewa sukeyi akan abinda ya faru kwanaki ai sakina yayi muke boyewa" "Subhanallahi innalillahi wa'inna ilahi rajiun inji wane me mugun bakin? Kai mutane mutane Allah ya shiryi mutum. Baka da gadon mutum amma yana da na maganar ka ta kuwa zanyiwa tufkar hanci tun kafin abu yayi yawa ya kai inda ba'a zato. Nan ma fa seda nasha fama da munafukai wasu kigansu da shegen tsugudidi sun kawo mun video se in sage musu guiwa nace a gaba akayi, daman ina so naja kunnenki kema kiyi ta kanki ki fita sabgar duk wasu masu jefa mutum a masifa. Yanzu fa duniya ta baci, wani ma dariya kuke dashi amma neman damar da ze cuceka yake dan haka ki kiyaye duk wata harkar qawaye balle azo ana gaya miki abinda ze daga miki hankali har ki aikata abinda be kamata ba. Duk wadda ta kawo miki wata gulma da baki da tabbaci kiyi watsi da ita kin daiga izina haka kawai yarinya taso ta sakaki a bala'i badan Allah ya tsare ba yanda yayan yarinyar nan yake zare zaren ido ai beqi a tafi gaban Alqali ba. Kedai babu ruwanki ki ci gaba da kula da kanki kina kula da Mijinki shikenan zaman aure daman dan haquri ne, duk namiji bakya raba shi da kule kulen yammata dan haka Allah ya halicci zukatansu dan haka ki saki ranki koda ace Allah ya qaddara wata rana ze kawo miki abokiyar zama idan ya zamana kin kama kanki duk wadda zatazo sedai ta biki, ballantana nasan Idan Babana gadon Marigayi yayi ke din dai kece babu qari, So dayan nan ne tak sukeyi ba kuma sa iya rabashi biyu. Ko Mahaifiyar Jamila daya auro gaba dayan mu munsan rabonta ne ya saka tunda kinga wata tara da auran ta haifeta kuma Allah ya karbi ranta sanadin haka to wani abun baka kaucewa qaddararsa dan haka dai ina nanata miki ki qara haquri". Yanda kasan me daukar karatu a gaban Malam haka ta nutsu ta duqar dakai har Hajiya ta kai aya kafin ta dago tace "In sha Allahu Hajiya wani abu makamancin haka baze sake faruwa ba, wancan dinma sharrin shaidan ne ni kaona daga baya na ringa tunanin meya shiga kaina harna aikata hakan amma qaddara ta riga fata kuma na miki alqawarin haka bazata sake faruwa ba kuma ko a yanzu Abban Mu'ayyad yaga damar qara aure a shirye nake dana bashi goyon baya dari bisa dari idan har ya samo macen da tayi daidai dashi. Kuma dan Allah Hajiya ki tayani bashi haquri dan tunda abin nan ya faru yaqi bani damar da zamuyi magana ballanatana har na nemi yafiyarsa. Fushi yake dani me tsanani baya ko kirana a waya se idan na kirashi nan ma ba wata magana muke ba daga gaisuwa yake kashewa" ta qarasa tana fashewa da wani munafukin kuka. Hajiya ta dauki salati tana cewa "Amma Babana anyi shakiyyin yaro wato baqar zuciyar tasa ce ta motsa koh? Waye baya kuskure a rayuwa, Allah ma muke masa laifi ya yafe mana yacigaba da wadata mu da dukkan ni'ima da mun roqa da bamu roqa na se shi? Daman ni jikina ya bani wannan tafiyar da yayi ya share guri ya zauna da walakin to kuwa zeci gidansu" haka ta ringa rarrashinta tareda bata assurance na seta ci qaniyar Khalil, da kansa ze dawo ya lallabata su koma. Ran Umaimah qal ta bar gidan Hajiya. Suna tafiya ta cewa Salman su biya ta Alpen zata siyi Mai da turare, a mota tabarwa Salman Bibi ta shiga dantafi sauri, tana cikin duba wasu Turaruka taga wata ta wuce kamar Rufaida, saurin bin bayanta tayi tana kiran sunanta amma bata waigo ba seta dauka kawai kamace ta juya da niyyar tafiya daidai sannan Ma'aruf ya qaraso gurin tana jinsa yana cewa "Naji kamar ana kiran sunanki ko ke baki ji ba?" Tabe baki Rufaida tayi tace "Banji ba, ko kuna bani din ake kira ba" "Yanzu saboda wulaqanci kna jina kenan daman kikaqi juyowa" Umaimah ta fada a fusace tana qarasawa gaban Rufaidan, qugu Rufaida ta riqe tace "Toh se akayi Yaya najiki din banyi niyyar amsawa ba ko kuwa cewa akayi dole sena kulaki? Wai ni bana ja miki kashedin babu ni babu ke ba, akan me iya bala'in da kika jamun na kwana a Cell be isheki ba me kuma kike nema a gurina? Daga yau ko a hanya kika ganni karma ki nuna kin sanni wallahi idan ba haka ba se na baki mamaki Mtsw" taja tsaki tareda aikawa Umaiman wata muguwar Harara tayi gaba bata ko saurari Ma'aruf dake faman ce mata "Meye haka Rufaida, ya zaki ringa yiwa mutane hayaniya gashinan har kin tara muku Jama'a". Kallon Umaimah da tayi suman tsaye yayi yace "Kiyi haquri kinji" ya juya yabi bayanta. Jiki babu kwari Umaimah ta juya ga mutane da suke ta kallonsu kamar sun damu Tv, tana jin wata tana cewa "Baki gane su ba? Sune fa sukayi wata sharrin Lesbian aka kamasu har aka sa sukayi video ban haquri" seta yi saurin ajiye kayan data diba, shopping din da batayi ba kenan ta fice daga gurin saboda zamanin nan yanzu kana tafe salin alin ma video ake maka ayita yawo da kai a Social media inaga ita da tayi qaurin suna har an samu wanda suka gane fuskarta dukda a Video sun chanza saboda wuyar da suka sha. Rufaida kuwa a mota har fada seda sukayi da Ma'aruf akan yana mata magana abinda tayi bata kyauta ba. "Ina ruwanka, Kai ka hadamu ko kuwa da yanzu rabuwar mu zata dameka? Malam kayi ta kanka kawai saboda bakai tajazawa kwanan cell ba shiyasa ai har kake so na kulata" ta fada a fusace kafin ta juya masa qeya. Mugun haushin Umaiman takeji, bayan kwanan Cell data ja mata ga Asarar dubban followers dinta na Tiktok data sha wahalar tarasu, dab take da Tiktok su fara biyanta wannan abun da sukayi ya jawo mata kuma shine zata sake kukata? Allah ya sawwaqe. Umaimah ko gida suka wuce Mama ta ringa musu fada ace tun safe su fita se yanzu kusan Tara zasu dawo ina suka tsaya Salman ya rantse mata gidan Hajiya suka wuni se yanzu suka taho ita kuwa oganniyar daki ta shige ba tareda ta bada amsa ba. Da ta saka damuwar abinda Rufaidan tayi mata se kuma ta yakice, a fili ta furta "Ita ta rasa, daman ita take amfana dani ai ballantana na damu dan ta dena kulani nima hutu nane". Washe gari da safe sega Kiran Khalil a wayarta, kamar yanda ya kona mata magana a dake tun sabaninsu da Hadiza yau dinma haka suka gaisa yake gaya mata ta shirya a cikin satin nan ze dawo bata ja maganar ba tace masa Allah ya nuna mana suka kashe wayar. Ko a jkinta ta fara shirye shiryenta dan daman tasan tunda Hajiya tace zata kirashi to zata kirashin qarshe dai fada ne zeyi yace ta kuma kai qarar sa to anci Sa'a be mayi fadan ba. Anty ta sanarwa da zancen dawowar tasa nan kuwa ta shiga yi mata gyara na musamman dukda bayan ta haihu ta danyi kadan tace ta bari se goshin dawowar Khalil din sannan suci gaba dan haka kuwa suka tashi da haiqanba dare ba rana qalqaleta take ciki da waje. Idanda dan halin Umaimah ne ba zata mata ba amma a kaf yaran Maman haka kawai Allah ya dora mata sonta dukda tasan duk cikinsun babu wadda ta tsaneta kamarta ta shanye gashi yanzu komai ya wuce tunda tana mata rana, abu da yawa nata kafin Mama ta sani ta gaya mata. Ranar Lahadi yace ze dawo bayan sun sake yin waya dan haka ranar Alhamis sukaje gidan tareda Maman Asad da Ummu-Salma sukayi gyare gyare, bayan sun dawo Maman Asad take cewa Mama "Mama da da hali da an chanzawa Umaimah ko iya kujeru ne wadannan din sun fara jin jiki" "Kema kinsan da kudina bazan canzawa Umaimah komai ba dan ba sanin darajar su tayi ba idan banda shegiyar qazanta ya za'ayi ace kayanta duk kyansu da kwarinsu basu cika shekara uku cif bafa ace sun lalace? Ga dakin Nuratu nan kulllum ka shiga fes kamar yau aka jera su, se ta chanza da kudinta idan tana so amma ni bazan yi asarar kudina bata sake kashe su a banza kuma nan kusa ai chanza gida zasuyi, idan Mijin yaga dama ya mata wasu mudai munyi namu na farillah" Mamanta bata amsa ita se a sannan ma ta san da zancen canjin gidannasu dan haka tace "Ai banma sani ba tunda haka ne seta fara tanadi kafin lokacin dan dai ba zata tare sabon gida da wadannan kayan ba, bafa ki ga yadin ba duk ya dafe daga Fari ya koma Ash" "Daman ai kuna sane kuka saka akayi mata kala me Haske, ni baqi nace ai mata ai taje ta qaraci qazantarta" Mama ta sake fada Maman Asad ta fashe da darita tana cewa "Kai Mama ina kika taba ganin baqaqen kujeru idan ba Lether sit ba? Ai baqi sema yafi nuna datti a leda ne kawai yake kyau tunda su basa nuna qura" "Ku kuka sani" Mamanta bata amsa kafin taci gaba da abinda takeyi se ta miqe ita kuma ta wuce palour Anty inda akeyiwa Umaimah kitso. Zama tayi suna dan taba hira kafin a gama mata dan itama kitson take so ayi matan, u guwar da suka koma babu me kitso idanba tazo gida kamar haka ba bata samu tayi daman. Ana gamawa Umaimah ta shige daki ta hau mulke jikinta da hadin Dilkar da Anty tayi mata, seda ta bushe tayi wanka ta saka Salma ta debo mata garwashi ta turara hayaqi na tsugunno dana jiki tanayi tana murmushi ita kanta dadin jikinta takeji yanda tayi kyau tayi mulmul abinta Jegon ya bala'in karbarta har yafi na fari tasan idan sukayi arba da Khalil manta komai zeyi su sha soyayyar su, tayi missing dinsa over wallahi. "Ke kuma lafiya kike ta zuba murmushi kamar wata sauna" Maman Asad data shiga ta fada tana kallonta, dariya ta saki ta zauna akan gado tana cewa "Tunanin irin love din da zamu kashe da Habibi idan ya dawo nakeyi mana" "Sefa Habibi, to dai kafin kiyi tunanin kashe love ya kamata ki fara tunanin yanda zaki wanke laifinki a gurinsa, ki samu ku fahimci juna kafin Live dinta tafi yanda ake so" Maman Asad ta fada. Se Umaimah ta gyara zama tace "Baki san Khalil ba, duk fushinsa fa shi dana kawo dauri gaban goshi na fesa turare an gama magana manta komai yakeyi in gaya miki" se Hajiyayye ta zauna dan abin yafi qarfin tsayuwa tace "Na yarda Umaimah bakida hankali ashe, wato daukar sakarai kike masa saboda kawai yana biye miki ya yafe duk haukar da kike masa ko? To wallahi ki kiyayi kanki da fushin me haquri, ranar daya tashi fashe miki sekin raina kanki. Ke yanzu har kina zaton Daura dankwali da turare zasu saka ya manta tozarcin da kika ja masa ko? Ke bashi ba ko mu yan uwanko dan bamu da yanda zamuyi dake ne yasa muka ci gaba da kulaki amma wallahi abinda kikayi har yau idan ta juyo zagin mu akeyi dan gani ake duk da sa hannunmu kikayi ai kin auna arziqi wallahi dabe baki tukuicin Saki ba ya barki kikayi zaman gida kawai danna tabbatar idan Bashir ne da yanzu na gama Iddah na fara zawarci dan bazan ma kuskura na kama hanyar gidansa ba daga Station din nan. To tunda har Allah ya dubeki ya baki me iya daukar halinki seki taimaki kanki kiwa kanki gata ki nutsu Umaimah, karki dauka kinyi wannan kinci banza dukda har yanzu ba ace haka amma nasan tsaf zaki iya gaba kice zaki maimaita ina jiye miki abinda ze biyo, kuma kibi Mijinki a hankali ki kwantar dakai ki nuna masa kinyi nadama ta gaskr ba tuban muzurun da kika sabayi ba. Daman base n miki magana akan Maqociyarki ba, idan kinga dama ki koma kuci gaba da jaye jayen bala'i tare jiki magayi, kuma ki nemi Islamiyya ta matan aure Umaimah ki shiga dan Allah kije ki qara sanin menene aure dan karatun da kikayi a baya banida tabbacin kin san me aka koya miki ki koma ki sake tilawa dan da kina amfani da Duk Litattafan da muka karanta da nutsuwarki tafi haka, ita kanta bokon idan da hali ki koma Degree, ko bazakiyi karatun ba ki shiga cikin mutane ki qara samun wayewa ta zaman takewa dan ita Jami'a amfanin ba iya kayi karatun boko bane harda koyon karatun zaman duniya dan zaka shiga ka zauna da mutane kala kala". Kumbure fuska Umaiman tayi, da farko tana sauraron nasihar tata amma tunda aka zo gabar ta koma makaranta ta hade rai wato kallon baqidajiya mara Ilimi ma suke mata kenan, se kuwa tace "Lallai ma Yah Hajiyayyen nan wato ma daukata kike a mara Ilimi wadda akayi a sarar kudin tara ko? Naga dai a gidannan idan za'a dakko takaddu a duba har ita Nuratun da take wani ji ita ga likita na fita qoqari kawai dan banyi niyyar inyi irin abinda tayi bane ya saka kuma ko a Islamiyya wallahi nafi qarfinace mun jaka danhar yau da hotona kafe a office din Headmaster kowa yasan ni me qoqari ce" "Dallah rufe mun baki shashasha ai ga gidadancin nan kina aikatawa, ce miki akayi sakamakon jarabawa shine tabbacin mutum yasan abinda yake koyo? Mutum nawane irinki masu karatu dan kuci jarabawa amma idan za'a tsare ki da wuqa ba zaki kawo abinda kika rubuta na. Qarara Ayyukanki sunfi kama dana wadda bata taba shiga Aji ba Umaimah dan wallahi Mace yar secondary data san kanta ba zatayi haukan da kikeyi ba, kiji ko kar kiji ke kika sani gaskiya ce bakya so kuma se mun fada miki in kinga dama ki gyara in kinga dama kici gaba da yanda kike dukkanin mu a gidajen aure muke kuma Alhamdulillah cikin rufin asuri da kwanciyar hankali da dadi babu dadi babu Wanda yasan ya muke rayuwa sabaninke da kaf matsalar gidan auranki a titi, ruwanki ki gyara ruwanki karki gyara ni nan ba abinda ya shalleni haqqine na sauke na yan uwanta ka kuma bawai dole bane dan haka kinga tafiyata" ta fice ta barta a zaune tana cizon yatsa, gaskiya ta gama cinta wasa amma zasu gamu ai tasan bata isa tayi mata wannan cin mutunchinta barta haka kawia ba bari dai ta samu daidaito da Habibinta sannan zatayi lokacin kowa ma. Ranar Asabar ta tattara yanata yanata ta koma gidan Khalil bayan dogon fada, Nasiha da gargadin data sha. Daren ranar gani tayi yayi mata tsayi da yawa saboda zumudi, tuni ta fara rage aikin abubuwan da zata masa ta tarba gwada tafiya da magana kuwa ita da kanta seda ta ringa yiwa kanta dariya dan kamar ta zare, gaskiya kewar Khalil na dab da zarar da ita. HALIN KISHI 49 *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 49 KHALIL Kiransa Hajiya tayi ta rufeshi da fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba taqi bashi ko damar ya gaisheta har seda ta kao aya kafin ta kashe wayarta, yasan baze wuce Umaimah taje ta gaya mata qarya da gaskiyar data saba bane shine zata hau kansa ba tareda shi taji ta bakinsa ba haka ya tashi shirin tahowa dan ce masa tayi ko ya dawo ko Umaiman ta bishi shi kuwa daman ba zaman wani abu yake ba aikin ma da suke gaba daya an kusa kammalashi kuma ya gama bangarensa tuntuni kawai wasu harkokin kasuwanci ya sake samu a can da taimakon wani Co-Architect da sukayi aiki tare shi ya nuna masa hanya ta irin abubuwan da suke tafiya a can wanda basu dashi se an shigar musu daga wasu qasashenda kuma namu na nan da suke da sauqi acan nan da nanya fantsama harkar shigowa da fitar da kayayyaki kuma da Allah ya saka albarka a abin yana ganin haske, ga harkar Gold da yake da sauqi sosai a can, sunq ulla Bashir, danye yake siya su kai Dubai a canza shi zuwa abubuwa da dama wannan hidimomin ne suka dauke masa hankali gaba daya har mamakin kansa yake ta yanda ya iya share tsahon lokacin ba tareda Mace ba kuma baya jin wata damuwa kodanbaya kawo abin a ransa ne yana fushi dame abun sabanin da da ko muryarta yaji yanzu jikinsa ze amsa? Shidakansa yasan zazzafar soyayar da yakewa Umaimah ta dishashe ba kuma ya zaton zata sake samun matsayi irin wanda take dashi a da cikin zuciyarsa ta rigada ta barar da damarta. Ranar Lahadi kamar yanda ya fada qarfe sha biyun Rana tayi masa a gidan Hajiya. Dakyar ta barshi yayi sallar Azahar banda ruwa ba abinda yasha ta korashi wanda be so haka ba, so yayi ko ze koma gidan se cikin dare amma haka ya tafi yana ta doka tsaki Mu'ayyad nata kukan ze bishi aka lallabashi da kyar akan se an kwana biyu za'a maida musu shi. A Mota Khalifa dai sedai ya juya ya kalle shi ya dauke kai, tunawa yakeyi lokuta baya idan yayi tafiya ya dawo yanda yake doki da zumudin komawa gidan ya ringa Azalzalarsa da yayi sauri kenan amma yau har fada yake masa wai yana gudu da motar. Har cikin gidan ya shigar masa da mota ya fita yayi masa sallama ba tareda ya tsaya sun gaisa da Umaimah ba. Numfashi yaja ya fitar kansa na kallon qofar palour da aka liqa wata sticker me qyalqyali an rubuta 'WELCOME HOME HABIBI" A jiki. Waiwayawa yayi ya kalli qaramin compound din da yayi qal Interlocks se daukar ido suke alamar sunsha shara da wanki ga wani daddadan qamshi turaren wuta da yake tashi kamar anyi barinsa a gurin. Da sallama ya tura qofar palour ya shiga, wani qamshi, sanyi, nutsuwa da ya rasa ta mecece suka bige shi lokaci daya, cikin seconds goma ya qarewa palour da babu kowa a ciki kallo. Gyaranda akayi masa is morethan perfect, yanda kasan babu wanda yake rayuwa a ciki saboda yanda komai ya zauna daidai a muhallindaya dace dashi haka ya fara jefa qafafunsa yana tafiya duk taku daya yana jin wata kewar gidanna kama shi, gaskiya masu magana sunyi gaskiya da suka ce no place like home. Qofar dakinsa ya tura kai tsaye ya shiga da sallama a bakinsa, wani sabon qamshi na daban yayi masa maraba tareda fuskar kyakykyawar Diyarsa dake kwance akan gadon daya sha shimfida ta alfarma itama cikin irin shigar da yake so ya gani jikin yara kamar ta sanshi suna hada ido ta bangale masa bakinta da babu haqori ta qara qarfin gwalantoyin da takeyi daga kwancen. Be san sanda ya dire jakar hannunsa ya isa kan gadon ya dagata ba ya hadeta da qirjinsa yana kissing fuskarta ita kuwa se dariya take abinta. Umaimah ta bude qofar bandakin da ta shiga tana hada masa ruwan wanka saboda Habiba ta kira ta gaya masa gashi nan a hanya ya baro gidan Hajiya. Daskarewa tayi daga bakin qofar, So, shauqi tareda kewarsa suka shiga shawagi da ita a sararin samaniyar qauna bata san yanda akayi ba se ganin kanta tayi a bayansa ba kuwa ta tsaya tunanin komai ba ta saka hannuwa biyu ta zagaye cikinsa dasu kafin ta dora kanta a bayansa se ji tayi hawaye suna bin kuncinta da ita kanta bata san na menene ba. A bazata abun yazo masa dan sam beji fitowarta daga bandakin ba gaba daya hankalinsa nakan Yar Babyn tasa da yake jin qaunarta har qololuwa, da yanzu Umaimah ta salwantar masa da ita tab da kuwa ta cuce shi. Saukar hannun mutum kawai yaji a cikinsa se saukar abi me dumi da yatabbatar hawayene ya shiga ratsa jini da jijiyarsa har zuwa cikin bargonsa, sosai yayi ta maza ya dake ya kuma hana kansa juyowa dan yasan tarko ne, idan har ya bari tayi tasiri akansa shikenan duk wani shiri daya dawo dashi ya wargatse. Hannu daya ya saka dayan na rungume da Bibi ya janye hannayen Umaimah data zagaye shi dasu ya fara takawa zuwa gana kujerar dake cikin dakin ya ajiye yarinyar ya shiga zame rigar coat din daya dora, hannunta ya sake ji a kafadarsa tana taya shi, kafin muryarta da tayi wani irin laushi da sanyi ta ratsa dodon kunnensa tana cewa "Barka da zuwa Habibin Umaimah, banji shigowarka ba ina ciki ina hada maka ruwan wanka, u are highly welcome" ta qarasa cikin wani sauti daya sakashi saurin sakar mata rigar ta qarasa cireta kafin ta juyo ta shiga balle masa maballin farar yar cikin jikinsa suka shiga kallon juna ido cikin ido kowanne yana karantar tsantsar kewar sa cikin idon Dan uwansa, tana gama balle masa rigar be zata ba yajita cikin jikinsa gaba daya suka yi baya ya samu ya dafe kujerar gabansu tareda qanqameta yana qarewa fuskarta kallo data sha simple kwalliyar nan tata wato pawder da man lebe ta gyara kyawawan idanunta da kwalli da Mascara gashin idon sun qara tsaho da baqi. Lumshe idonta tayi ta sake bude su akan sa kafin ta raba labbanta data pente da jan lipstick ta sake shafe su Lipbalm me maiqo se daukar ido sukeyi tayi kamar zatayi magana amma ba tace komai ba, Idan yace yace beji wani abu na yayi qary, wani sanyi yaji ya taso masa tun daga tafin qafa ya dire a kwakwalwarsa, wani irin kallo take masa na cikin ido dashi kadai yasan ma'anarsa kuma ji yakeyi tamkar ta saka muqulli tana bude duk wasu qofofin jikinsa da suka jima a rufe, numfashinta da yaji cikin nasa kafin ta kai ga aikata abinda ta niyyata zumbur ya tashi tareda ita a jikinsa, sauketa yayi a qasa kan qafafunta kafin ya juya ya shige bandaki yanajin yanda jikinsa yake harbawa ba tareda ya qarasa cire kayan jikinsa ba ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana gangarowa daga gashin kansa har zuwa qafafunsa. Bazece ga iya adadadin mintinan daya kwashe a qasan ruwan ba, gajiya yayi dan a maimakon ya samu sauqin abinda yake ji se ya zamana tamkar ma yana qara iza wutar ne. Cikin ruwan data hada masa a bahon wankaya shiga bayan da ya cire jiqaqqun kayan jikinsa ya kwanta a ciki tareda rufe idonsa so yake ya tunano duk tarin laifukan da tayi masa ko zasu dishashe abinda yake bijiro masa akanta amma abin takaici ko daya yaqi zuwa, idan ma sunzo sam sun gagara bata masa rai ballantana har su gushe kaifin abinda yake ji qarshe dai yayi wanka ya dauro towel din data rataye masa ya fito. UMAIMAH Da kallo ta rakashi harya shiga ya kullo qofar kafin ta sauke ajiyar zuciya ta zauna kusada Bibi dake ta wulga idanu tana kallon fitilar dakin. Gaba daya jiki ta yayi mugun sanyin da batajin zata ko iya tafiya, abinda ta hango cikin idonsa ya sake sare mata guiwoyi, dagaske ne Khalil ya tsaneta ya zatayi da ranta? Tana nan zaune cikin duniyar Lissafi har ya kwashe mintocinsa ya fito daure da towel a qugunsa, Kallo ta bishi dashi kamar wata tsohuwar mayya, ya wuceta ya dauki wayarsa dake kan gado kafin ya koma gaban mudubi yaja kura ya zauna bayan dayayi yan danne danne a wayar ya saka a speaker "Kaje Ten to Ten ka karbo mun usually meal dina yanzu" ya fada kafin ya latse wayar ya janyo Mansa ya fara shafawa. Hadiye abinda ya tsaya mata a wuya tayi ta tashi dakyar ta isa kusa dashi, ta cikin mudubin yake qare mata kallo, doguwar fitted gown din data saka ta Dark Orange din Lace tayi bala'in yi mata kyau ta fito da duk wani tudu da komadar jikinta daya qara cika dam kamar zata fashe, saurin dauke kansa yayi sanda ta iso ta karbi Man daya diba ta shiga shafa masa a banyansa, daga shi har itan ba zasu misalta yanda sukeji ba, Ta gaka shafa masa a bayan ya juyo tana fuskantarsa, hannu biyu ta saka taja shafa masa man A fuskarsa da tasa gyara saboda jiya yayi Aski cikin muryarta da tayi rauni kamar zatayi Kuka tace "Nayi maka abinci, kuma naji kana cewa a kawo maka" "Oh, thanks" ya fada yana miqewa saboda ya tabbata idan ta sake bude baki tayi magana cutarsa kawia zatayi. Wardrobe ya bude ya dauko Jallabiyya da boxer ya saka ya sake dawoa inda take tsaye ya dauki turare ya fesa kafin ya juya ya dauki Bibi data bingire da bacci ya fice daga dakin. A kan Dan gadonta da ya gani a gefen kijera ya kwantar da ita tareda pecking goshinta. Kai tsaye kan Dining din ya wuce ya kalli wasu Luxury warmer data zuzuzuba abincin a ciki su kadai kyan su ya isa ya saka ka cin abinda yake ciki ko bakayi niyya ba. Zama yayi ya bude babbar ciki, Tuwon shinkafa ne fari so a ciki, ya waiwaya ya kalli Umaimah data biyo bayansa kamar mara gaskiya, da yar mutunchi suke tashi zeyi ya dagata yayi juyi da ita dan kamar ta shiga zuciyarsa, abinda yake muradi kenan yaci har mafarki yake ya samu tuwo dan tunda ya tafi ko a ido be ganshi ba, zuwan da yayi kwanaki ma zaman hotel ya qare harya tafi be ci ba. Qaramin murmushi ya sakar mata, Umaimah ta sauke ajiyar zuciya har yana ganin yanda maqogaronta yayi sama da qasa kafin ta taho kamar wahainiya ta shiga bude masa sauran warmers din. Miya kala biyu tayi masa, Miyar Egusi dataji duk wani kalar Wasali da ake sakawa miya ga hadaddiyar Kuka wadda tayi digiri a London tasha zabi da suka dagargaje saboda yanda ta bata lokaci ta dafu. Dayan kwanon Jellop din shinkafa ce itama dai se wanda ya gani ga wani Musulmin peppe meat tsabar qyallin da yake kamar zaka ga fuskarka a jiki. Se casserole data zuba hadin potatoe Salad dayan kuma ganyan lattece yasha garnishing se wani bowl me kyau data zuba Samosa da spring roll ga kuma Jug din Coconut drink dana Zobo se Jarkokin ruwa me sanyi har diga yakeyi Duk yanda yaso ya daure seda ya kama hannunta na dama ya sumbata, qarshen abincin sa kenan ta hada masa su, ga Tuwo ga shinkafa ga nama.ga kayan fulawa. Kadan ta zuba masa kowanne a plate yayi bismilla ya shiga ci yana kallon fuskarta data marairaice kamar marainiyar Mage, tuwo ya gutsira ya nufi bakinta dashi, Allah sarki yanda take abu se yaji kamar zata bashi tausayi amma ya kanne haka suka shiga cin abincin yana ci yana bata har suka gama ba tareda wani yace qala ba. Ita ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo ta goge gurin harda fesa freshner, a ransa yace "Ikon Allah, su Umaimah course din tsafta aka yo kenan yana kallo ta ta shige daki babu dadewa ta fito ta zauna akan kujerar gefensa. "Na same ku lafiya?" Ya fada yana chanza channel, da sauri ta amsa masa ya daga kai ya kalleta, yanda take muimui da baki alamar tana son yin magana se juya yatsunta take kamar me jin tsoron yayi bala'in sake kunna shi. "Kaak...kayi haquri dan Allah" ta fada dakyar hawaye na kawowa idonta, banza ya mata yaci gaba da chanza channel din da yakeyi "Dan Allah Khalil ka yafe mun, wallahi sharrin shaidan ne bazan sake ba" ta sake fada cikin muryar kuka" juyowa yayi ya kalleta, a cikin idonta ya karanci laushin da tayi na gaske ne ya kuma tabbatar da wannan ladabin bana qarya bane da gaske takeyi amma dukda haka baze saki da sauri ba, haka nan baze fasa qudurinsa akanta ba. Hannu ya miqa mata fuskarsa dauke da wani murmushi da kai tsaye bazata iya fassara ma'anarsa ba yace mata "Zo nan, haka ake bawa Miji haquri a garinku" ya qarasa yana dorata a cinyarsa ya zura kansa cikin wuyanta yana shaqar qamshin turarenta da tun gamuwarsu ta dazu ya hautsina masa kwakwalwa. Baki ta buse da niyyar sake magana yayi saurin rufe mata da nashi, daga nan labari ya canza, da farko cikin nutsuwa da soyayya ya ringa tafiyar da ita, seda tafiya tayi nisa ya birkice mata. Cikin wani irin fushi da sauri yake saraffata, tayi kuka tayi magiya Bibi kanta dake bacci seda ta farka ta shiga taya Mamanta kukan neman ceto amma be saurare su ba, seda dan kanshi yaji ya samu nutsuwar da yake da buqata kafin ta qyaleta, be ko bi takanta ba ya tsallake ta ya shiga dakinsa ya yiwo wanka ya dawo ya dauki yarinyar dake faman tsala kuka. Ki tashi kiyi wanka ki karbeta" ya fada yana kallonta cikin sigar bada Umarni dole ta tattara jikinta da take ji kamar Buldozer tabi ta kanta, dakyar take iya daga qafarta ta kuma tabbatar da yaji mata ciwo ba kadan ba. Haka ta ringa gas jikinta tana kuka taredajera masa Allah ya isa a zuciya. Da tasan muguntar daya shirya mata kenan da bata shige masa ba. Ta gaya masa da wannan salon muguntar tasa gara ya saka bulala ya zane ta idan tayi masa laifi amma Allah yana kallo kuma seya saka mata. Tsawar daya bugo mata akan tayi sauri ta fito ta karbeta ce ta sakata qarasa wankanba shiri ta fito, an kira sallar La'asar dan haka tana karbarta ya fice daga gidan yana sakin wani mugun murmushi na jin dadi, riba biyu, ya kwashi dadin da yaji kamar ze manta sannan ya horata yanda zataji a jikinta, Allah ya kaimu dare zata sake gane kurenta, tunda ita bata ji ta haka ze ladabtar da ita har se kunnenta ya ringa jin abinda yake gaya mata. Da daddare daya kirata dakinsa kuka kawai ta saka masa dan ta tabbata ranta kuma yake nema, tun dazu da yammar zazzabi ya saukar mata, wani irin azaba takeji a qasanta dukda yanda ta shiga ruwan zafi ta gasa kanta dakyau amma kamar batayi ba ta tabbata hakan nada alaqa da uban maganin matsin da tayi amfani dashi bayan dinki da akayi mata na haihuwa. Daman seda Nuratu taja mata kunne sanda tace ta bata dan ita Allah ya taimake ta duk haihuwar da tayi bata samu qari ba shiyasa take yan gyare gyarenta amma Umaimah ga dinki ciki da waje ta nace seta bata, "Jiki magayi" abinda ta fada kenan gashi kuwa tana gani. A daren nan haka Khalil ya sake moreta seda yayi bidirinsa tsaf ya gama kafin kuma ya fara jin tausayinta, haqoranta har haduwa suke saboda zafin zazzabi ya taimaka mata ya gasata sosai kukan ma ta denayi se ajiyar zuciya kafin ya hada mata tea me kauri tasha da maganin rage zugi daya siyo bayan daya fita sallar Magriba dan yasan zata buqace shi dole sannanta samu bacci ya dauke ta. Da safe seda ya tsokaneta tana kwance yazo kamar ze shiga jikinta yanda ta zabura idonta ya fito seda ta bashi tausayi da dariya. Yanayin zafin jikin dayaqi sauka yasa dole sukaje Asibiti, dinki dai ya farke tas oho shi bema ji ba haka aka saka Umaimah a Theatre aka sake sabon dinki, bala'i dai ta ganshi muraran dan suna hanyar dawowa daga Asibitin kuka ta ringayi tana roqonsa ya maida ita gidansu. Da wannan Azabar data sha daga jiya zuwa yau ai gara zaman Cell din da tayi Aradun Allah shidai Khalil dariya kawai yakeyi a zuciyarsa dan ba wai iya hukuncinta kenan ba, ta gama wannan jinyar yana nan ze jijjigo mata gagarumar jinya ta gaske. Seda Umaimah ta kwashe kusan sati hudu tana jinyar jikinta, Ummu-Salma ce ta dawo gidan tana taya ta da ayyuka saboda suna hutu sannan, a bangaren Khalil kuwa wani mugun tsoronsa ne ya darsu a ranta, duk abinda takeyi idan taji muryarsa se gabanta ya fadi ta fara tsuma musamman da ya samu sarar daure mata fuska a yanzu tun bayan daya gama dagargazarta ya dinke fuskarsa tsaf baya mata dariya, idan kaji muryarsa yana wasa to da Salma yake magana ko kuma ya dauki Bibi yana mata wasa ita kuwa tsakaninta dashi gaisuwa ce daman itama bata so din wata doguwar magana ta hadasu ballantana har a sake maimaita abinda ya faru. Se a yanzu tayi nadama ta gaske ta kuma tsinewa shegiyar Khausar data ja mata, da bata shigo rayuwarta na da duk wadannan abubuwan basu faru ba. A haka aka ci gaba da gungura rayuwa, Umaimah ta canza lokaci daya tayi wani irin sanyi qalau. Gidansu me cike da soyayya da kwanciyar hankali ya dawo kamar wani gidan Makoko, babu wani karsashi a cikinsa idan kaji magana me qarfi Tv aka kunna ko Bibi ce take rigimarta, a bangaren Khalil kuwa be ma cika zaman gidan ba yanzu se dare. Daga office idan ya tashi ze wuce sabgoginsa dan yanzu Yana taba abubuaa da yawa ga kuma sabgar ginin gidansa da bayan dawowarsa seda yasa aka canza abubuwa da yawa saboda ba'ayi su yanda ya tsara ba, idanya koma gidan ma tsakanin su gaisuwa ce idan tayi abinci in yayi niyya yaci idanbega dama ba ya ciyo a gidan Hajiya haka suka kwashi kusan wata biyu a wannan yanayi. Babu inda take zuwa gashi maqotan da suke gaisawar ma gaba daya Rufaida ta rabata dasu yanzu babu me shigowa gidanta se Kishiyar Maman Hauwa da ita kadai suka ci gaba da zumunchi se wata Amarya da aka kawo ita kuma ba mazauna bane Mijin a kudu yake aiki kuma tare suke tafiya haka zata wuni a gida sedai tayi ayyukanta dan yanzu tsafta kam babu kama qafar yaro, Khalil har gulmarta yake a zuciya daman ita tun Asali idan suna fada ko suka samu sabani tafi nutsuwa ta ringa abinda ya kamata yanzun ma haka ta kasance gidan nan ko yaushe qal ta saka turare wannan karon jego take na masu hankali daga ita har Bibi bazaka gansu da qazanta ba musamman da tayi sa'a yarinyar bata da rigima sam idanta qoshi zatayi wasanta daga nan tayi bacci gashi har sannan ba'a dawo da Mu'ayyad ba, tsabar tunani da zaman Kadaici ya saka depression ya nemi kamata. Wani mugun ciwon kai tayi ranar Allah ya saka yana gida Weekend ne, tana cikin daki daman tun dare take fama da ciwon kan zuwa safiya ko motsin kirki bata iyayi saboda yanda takeji tamkar ana kwada mata guduma idan akan. Kukan Bibi daya keta jiyowa ya saka shi shiga dakin nata dan a zatonsa ko ta shiga bamdaki ta barta ne sedai yanayindaya tarar da ita dole ya kwasheta suka tafi Asibi babu shiri hankali a matuqar tashe, seda tayi jinyar sati kafin aka sallameta yan gidansu dasu Hajiya gaba daya sun dauka ciki ne da ita musamman saboda muguwar ramar da tayi ta dashe kowanne bangare da suna mitar tunda Mijinta ya dawo ta yada kowa ba inda take zuwa se suka bata uzurin qila bata so a san daga komawa tayi ciki shiyasa ta guji kowa. Randa aka sallameta suna komawa ta dasa masa kukan gida zata tafi, ba zata zauna ta mutu a banza ba tunda ya dena sonta ya sallameta kawai ai haquri babu irin wanda bata bashi ba idan baze yafe mata ba gara ya sauwaqe mata kawai ta kama gabanta akan baqin cikinsa ya kasheta. Isaraa tayi da surutan banza, dukda jikinta har sannan da saura haka ya jata sula shilla sama lulaye amma wannan karon ya banbanta da wancan, tafiya ce akayita ta nutsuwa suka goge duk wani Virus daya shiga memoryn su ya dawo sabo fil daga nan aka bude sabon babin soyayya da zaman lafiya tsakanin Sabuwar Umaimah da Khalil din nata. BAYAN WANI LOKACI Zama yayi dadi tsakanin Habibi Khalil da Habibtynsa Umaimah. Zama ne sukeyi irin wanda Khalil ya dade yana mafarki cikin zallar soyayya, zaman lagiya da tattalin Juna dan Umaiman tasa ta kintsu irin kintsin daya bawa kowa Mamaki ta kowanne banni yanzu ta dauki gyara. Tuni ta koma Islamiyya kamar yanda Maman Asad ta gaya mata, bayan dogon nazari da karatun ta nutsu da tayiwa kanta ta fuskanci gaskiya ta gaya mata dan haka ta sanarma da Khalil son komawa Islamiyya da bokon ya kumayi na'am da Islamiyyar, bokon ne yace tayi haquri. Da akwai shirin da yake dashi idan Allah ya tabbatar zatayi dan haka ta rungumi Islamiyyarta, sau uku sukeyi a sati litinin zuwa Laraba Goma na safe zuwa qarfe daya dan haka da ta gama ayyukan ta na safe zata fita makaranta idan ta dawo ta huta kafinta shiga aikin girki da tarbar Khalil bata da matsalar yara dan Bibi sam bata da rigima Mu'ayhad ko ya zama dan gidan Hajiya sedai yazo musu ya tafi. Sosai ta qaru da komawar tata Islamiyya ta farfado da karatunta ga kuma sabon karatun darasin rayuwa da take samu a gurin sababbin gogaggun qawayen da tayi matan da suka san me sukeyi ba tarikican qawayen banza data sabayi ba wadannan matane da duk maganar da zasu fada ta qaruwa ce me amfani haka ta sake shiga whatsapp group a karo na biyu bayan Rufaida tasa an cireta daga duk wanda suke ciki a baya sedai wannan karon groups ne na qaruwa da har seda ta gayyato su Nuratu dasu Mamab Asad duk suka shiga harda Anty ba'a barta a baya ba ta shige suna kwasar darasussukan rayuwa daga Matan da sukaga jiya suka ga yau. A dai taqin shekara da wani abu Abubuwa da dama sun faru na dadi dana akasin haka. Babban abin dadi daya faru shine budin da Khalil ya samu da har ta kai ga ya bude construction company nasa na kansa wanda ya kafu bisa jajircewarsa da kuma aiki me nagarta da yakeyi wanda shine ya janyo masa samun manya manyan kwangiloli da beyi tsammani ba qarqashin Jaririn Companyn sa dake tasowa a yanzu. Bayan nan se tafiyar Sa Umaimah da Hajiyarsa aikin Hajji wanda suka sauke faralli cikin wannan shekarar. Base na baku labarin Hajiya Umaimah a saudiyya ba, anyi ibadah dai matuqa addu'a kam Khalil ya shata ta Allah ya hana idonsa ganin wata mace bayan ita, Rikici kuwa babu abinda ta fada dan sedai idan basu fita siyayya tare ba. Haka kawai idan abinta ya motsa zatace wata na kallonsa, idan anyi sa'a yar uwarta ce Bahaushiya ta zageta su kwashi fada kowa ya kama gabansa, idan kuwa ba yarenta bane zagi take musu na tsamar nama sedai su kalleta su dauke kai toh basu ma san abinda rake fada ba kuma duk abin nan bata tabayi a gaban idon Hajiya ba, dan yawanci yawon Kasuwar su Hajiya bata binsu se tayi zamanta a masauki shidai Khalil Sallar sa da dawafi kaf babu a wanda baya roqarwa Umaimah shiriya da kuma zabin Allah akan komai na rayuwarsa, haka dai aka sauke Hajji lafiya aka dawo gida nan kuma Umaimah ta tarar da sabon abu, ginin gidansu da akeyi an canza masa fasali daga yanda aka qirqire shi zuwa zaman Mace biyu a tata fahimtar. Asalin ginin komai anyi shine a cakude, bangarenta dana Khalil din a hade suke amma suna dawowa yace taje ta duba gida a fara shirin zuba kaya dan damansun siyo wasu abubuwan irinsu Labulaye da Carpet tana zuwa taga wannan tashin hankali, part guda Khalil din ya warewa kansa saboda rainin hankali a cewarta fa harda Kitchen da store, guri dai tsaf kamar mace za'a ajiye. Babu kalar rantsuwa da bayanin da beyi mata ba ta toshe kunnenta, ta ringa tijara tana rashin mutunchi a gaban ma'aikata, bokitan penti da aka ajiye dan ana pentin gidanne haka ta ringa bi tana zubar masa dasu penti masu tsadar gaske. Ran Khalil ya baci matuqa, babban abin kuma daya qara bata masa rai da sukaje gaban Hajiya ta goyi bayanta. "Akan me zaka canza tsarin gidan kuma ba tareda kayi shawara da ita ba?" Hajiya ta fada cikin fushi tana kallonsa. Khalil ya kalli Hajiya ya kalli Umaimah dake faman share hawaye bayan tazo ta gama zayyanawa Hajiyar qarya da gaskiya ya hadiye wani abu me daci daya tsaya masa. Badan be taba kama Umaimah da wani abu dayayi kama da Bin Malamai ba da tabbas zece Asirce Hajiya tayi, wannan makauniyar soyayar da Hajiua take mata ba kuma ta ganin laifinta abin yayi yawa. Gyara zamansa yayi yana cewa "Hajiya ni sam ba abinda take tunani bane yasa nayi hakan. Kinga dai tsarin ginin a farko komai a cakud akayi shi, babu wani kebantaccen guri ko ina kowa yana iya shiga akoda yaushe babu sirri ni kaina se daga baya naga rashin dacewar hakan a matsayi na na me gida ya kamata ace ina da turakata data qunshi komai da komai a ciki bana buqatar fita idan ina buqatar wani abun. Sannan iyali muke tarawa dole yaranmu wata rana zasu girma, be kamata ace muna cakude dasu a koda yaushe ba dole akwai buqatar sirri tsakaninmu ni wannan ne kawai dalili na ba wani shirmenta mara tushe ba" "Kuma ahine harda Kitchen da store duk a bangaren naka? Three bedrooms ga qaton palour da dining duk me zakayi dasu?" Umaimah tayi tsugul ta fada kafin ma Hajiyar tayi magana, Harara ya galla mata kamar idonsa ze fado ba tareda yayi magana ba jin Hajiya nacewa "To ai kamata yayi tun kafin ayi seka gaya mata, base kawai tazo taga abu ba ai koma wacece tunanin daze zo mata kenan a zuciya" "Idan qara auren tana da hujjar Hanani ne ko kuma akwai Haramci a cikin Hakan?" Yayi wa Hajiya tambayar amma idonsa akan Umaimah data gwalo nata idanun saboda jin wannan gingimemen tashin hankali, "Bana son neman rigima Khalil, bana so. Ke kuma kinji abinda ya fada dan haka karna sake jin wata magana bayan wadda akayi a nan" Hajiya ta fada musu gaba daya Khalil be jira yaji koda sauran maganar tata ba ya tashi ya fice daga gidan cikin bacin rai. Iya Asarar pentindata masa da yawa kuma wallahi zata sani a cikin kudin da yayi niyyar bata na gyaran gidan idan yaso in basu isa ba ta tare da tsofaffin kayanta. Ya gaji da iskancin Umaimah ba kuma ze sake biye mata ta mayar dashi kamar wani takalmin sawarta ba. Ya dauka nutsuwar da tayi tun bayan wancan Al'amarin ta gaske ce tunda gashi kusan shekara daya da wani abun bata sake masa shirme ba suna zaune lafiya se yanzun kuma baze dauka ba. Da daddare be koma gida ba se gurin sha daya sabodaya zauna meeting da wasu campany da zasuyi hadin guiwar wani aiki. A palour ya tarar da ita daman kuma ya tsammaci hakan maganar ba zata mutu ba kamar yanda hajiyar ta yanke hukuncin son rai dan haka yana ganinta ya qara hade fuska ya wuce ze shiga dakinsa tasha gabansa tana cewa "Kai nake jira tun dazu dan gara ma ka sani bazan koma gidan nan ba idan baka rushe wannan gurin ka maida shi yanda yake ba" ta fada tana karkada qugu kamar Mazari, kallon sama da qasa yayi mata takaici ya rasa abinda ze fada mata seya zagaye ta ya wuce cikin dakin ta bishi cikin daga murya bata ko tunanin yara na bacci karta tasahe su tace "Khalil dakai fa nake ka wuce ni wato ga mahaukaciya tana magana ko?" "Ai sunan daya dace dake kenan Umaimah, na yarda baki da hankali kuma idan baki fita kin bani guri ba se ranki ya baci wallahi. Gida kuma karki koma, ke kika rasa gobe idan naga dama zan samo ukun ki na zuba a gidan kin kuma san yana da girman da ze dauke su dan haka ki fita ki bani guri ki koma ko karki koma keta shafa bani ba" Khalil ya fada yana kallon tsakiyar idonta kamar yanda itama ta zuba masa ido kafin ta juya da gudu tabar dakin nasa. "Mtsw" yaja wani matsiyacin tsaki ya zauna a gefen gado yana dafe kansa da yake masa ciwo ciwo,Umaimah bazata canza hali ba, shekara dubu tana abin kirki idan tsiyarta ta juyo cikin minti daya zata wargaza komai. To wannan karon kam sedai abinta ya qare mata dan bashi da lokacin da ze tsaya yana batawa akanta abubuwan gabansa ma su Ishe shi.HALIN KISHI 49 *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 49 KHALIL Kiransa Hajiya tayi ta rufeshi da fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba taqi bashi ko damar ya gaisheta har seda ta kao aya kafin ta kashe wayarta, yasan baze wuce Umaimah taje ta gaya mata qarya da gaskiyar data saba bane shine zata hau kansa ba tareda shi taji ta bakinsa ba haka ya tashi shirin tahowa dan ce masa tayi ko ya dawo ko Umaiman ta bishi shi kuwa daman ba zaman wani abu yake ba aikin ma da suke gaba daya an kusa kammalashi kuma ya gama bangarensa tuntuni kawai wasu harkokin kasuwanci ya sake samu a can da taimakon wani Co-Architect da sukayi aiki tare shi ya nuna masa hanya ta irin abubuwan da suke tafiya a can wanda basu dashi se an shigar musu daga wasu qasashenda kuma namu na nan da suke da sauqi acan nan da nanya fantsama harkar shigowa da fitar da kayayyaki kuma da Allah ya saka albarka a abin yana ganin haske, ga harkar Gold da yake da sauqi sosai a can, sunq ulla Bashir, danye yake siya su kai Dubai a canza shi zuwa abubuwa da dama wannan hidimomin ne suka dauke masa hankali gaba daya har mamakin kansa yake ta yanda ya iya share tsahon lokacin ba tareda Mace ba kuma baya jin wata damuwa kodanbaya kawo abin a ransa ne yana fushi dame abun sabanin da da ko muryarta yaji yanzu jikinsa ze amsa? Shidakansa yasan zazzafar soyayar da yakewa Umaimah ta dishashe ba kuma ya zaton zata sake samun matsayi irin wanda take dashi a da cikin zuciyarsa ta rigada ta barar da damarta. Ranar Lahadi kamar yanda ya fada qarfe sha biyun Rana tayi masa a gidan Hajiya. Dakyar ta barshi yayi sallar Azahar banda ruwa ba abinda yasha ta korashi wanda be so haka ba, so yayi ko ze koma gidan se cikin dare amma haka ya tafi yana ta doka tsaki Mu'ayyad nata kukan ze bishi aka lallabashi da kyar akan se an kwana biyu za'a maida musu shi. A Mota Khalifa dai sedai ya juya ya kalle shi ya dauke kai, tunawa yakeyi lokuta baya idan yayi tafiya ya dawo yanda yake doki da zumudin komawa gidan ya ringa Azalzalarsa da yayi sauri kenan amma yau har fada yake masa wai yana gudu da motar. Har cikin gidan ya shigar masa da mota ya fita yayi masa sallama ba tareda ya tsaya sun gaisa da Umaimah ba. Numfashi yaja ya fitar kansa na kallon qofar palour da aka liqa wata sticker me qyalqyali an rubuta 'WELCOME HOME HABIBI" A jiki. Waiwayawa yayi ya kalli qaramin compound din da yayi qal Interlocks se daukar ido suke alamar sunsha shara da wanki ga wani daddadan qamshi turaren wuta da yake tashi kamar anyi barinsa a gurin. Da sallama ya tura qofar palour ya shiga, wani qamshi, sanyi, nutsuwa da ya rasa ta mecece suka bige shi lokaci daya, cikin seconds goma ya qarewa palour da babu kowa a ciki kallo. Gyaranda akayi masa is morethan perfect, yanda kasan babu wanda yake rayuwa a ciki saboda yanda komai ya zauna daidai a muhallindaya dace dashi haka ya fara jefa qafafunsa yana tafiya duk taku daya yana jin wata kewar gidanna kama shi, gaskiya masu magana sunyi gaskiya da suka ce no place like home. Qofar dakinsa ya tura kai tsaye ya shiga da sallama a bakinsa, wani sabon qamshi na daban yayi masa maraba tareda fuskar kyakykyawar Diyarsa dake kwance akan gadon daya sha shimfida ta alfarma itama cikin irin shigar da yake so ya gani jikin yara kamar ta sanshi suna hada ido ta bangale masa bakinta da babu haqori ta qara qarfin gwalantoyin da takeyi daga kwancen. Be san sanda ya dire jakar hannunsa ya isa kan gadon ya dagata ba ya hadeta da qirjinsa yana kissing fuskarta ita kuwa se dariya take abinta. Umaimah ta bude qofar bandakin da ta shiga tana hada masa ruwan wanka saboda Habiba ta kira ta gaya masa gashi nan a hanya ya baro gidan Hajiya. Daskarewa tayi daga bakin qofar, So, shauqi tareda kewarsa suka shiga shawagi da ita a sararin samaniyar qauna bata san yanda akayi ba se ganin kanta tayi a bayansa ba kuwa ta tsaya tunanin komai ba ta saka hannuwa biyu ta zagaye cikinsa dasu kafin ta dora kanta a bayansa se ji tayi hawaye suna bin kuncinta da ita kanta bata san na menene ba. A bazata abun yazo masa dan sam beji fitowarta daga bandakin ba gaba daya hankalinsa nakan Yar Babyn tasa da yake jin qaunarta har qololuwa, da yanzu Umaimah ta salwantar masa da ita tab da kuwa ta cuce shi. Saukar hannun mutum kawai yaji a cikinsa se saukar abi me dumi da yatabbatar hawayene ya shiga ratsa jini da jijiyarsa har zuwa cikin bargonsa, sosai yayi ta maza ya dake ya kuma hana kansa juyowa dan yasan tarko ne, idan har ya bari tayi tasiri akansa shikenan duk wani shiri daya dawo dashi ya wargatse. Hannu daya ya saka dayan na rungume da Bibi ya janye hannayen Umaimah data zagaye shi dasu ya fara takawa zuwa gana kujerar dake cikin dakin ya ajiye yarinyar ya shiga zame rigar coat din daya dora, hannunta ya sake ji a kafadarsa tana taya shi, kafin muryarta da tayi wani irin laushi da sanyi ta ratsa dodon kunnensa tana cewa "Barka da zuwa Habibin Umaimah, banji shigowarka ba ina ciki ina hada maka ruwan wanka, u are highly welcome" ta qarasa cikin wani sauti daya sakashi saurin sakar mata rigar ta qarasa cireta kafin ta juyo ta shiga balle masa maballin farar yar cikin jikinsa suka shiga kallon juna ido cikin ido kowanne yana karantar tsantsar kewar sa cikin idon Dan uwansa, tana gama balle masa rigar be zata ba yajita cikin jikinsa gaba daya suka yi baya ya samu ya dafe kujerar gabansu tareda qanqameta yana qarewa fuskarta kallo data sha simple kwalliyar nan tata wato pawder da man lebe ta gyara kyawawan idanunta da kwalli da Mascara gashin idon sun qara tsaho da baqi. Lumshe idonta tayi ta sake bude su akan sa kafin ta raba labbanta data pente da jan lipstick ta sake shafe su Lipbalm me maiqo se daukar ido sukeyi tayi kamar zatayi magana amma ba tace komai ba, Idan yace yace beji wani abu na yayi qary, wani sanyi yaji ya taso masa tun daga tafin qafa ya dire a kwakwalwarsa, wani irin kallo take masa na cikin ido dashi kadai yasan ma'anarsa kuma ji yakeyi tamkar ta saka muqulli tana bude duk wasu qofofin jikinsa da suka jima a rufe, numfashinta da yaji cikin nasa kafin ta kai ga aikata abinda ta niyyata zumbur ya tashi tareda ita a jikinsa, sauketa yayi a qasa kan qafafunta kafin ya juya ya shige bandaki yanajin yanda jikinsa yake harbawa ba tareda ya qarasa cire kayan jikinsa ba ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana gangarowa daga gashin kansa har zuwa qafafunsa. Bazece ga iya adadadin mintinan daya kwashe a qasan ruwan ba, gajiya yayi dan a maimakon ya samu sauqin abinda yake ji se ya zamana tamkar ma yana qara iza wutar ne. Cikin ruwan data hada masa a bahon wankaya shiga bayan da ya cire jiqaqqun kayan jikinsa ya kwanta a ciki tareda rufe idonsa so yake ya tunano duk tarin laifukan da tayi masa ko zasu dishashe abinda yake bijiro masa akanta amma abin takaici ko daya yaqi zuwa, idan ma sunzo sam sun gagara bata masa rai ballantana har su gushe kaifin abinda yake ji qarshe dai yayi wanka ya dauro towel din data rataye masa ya fito. UMAIMAH Da kallo ta rakashi harya shiga ya kullo qofar kafin ta sauke ajiyar zuciya ta zauna kusada Bibi dake ta wulga idanu tana kallon fitilar dakin. Gaba daya jiki ta yayi mugun sanyin da batajin zata ko iya tafiya, abinda ta hango cikin idonsa ya sake sare mata guiwoyi, dagaske ne Khalil ya tsaneta ya zatayi da ranta? Tana nan zaune cikin duniyar Lissafi har ya kwashe mintocinsa ya fito daure da towel a qugunsa, Kallo ta bishi dashi kamar wata tsohuwar mayya, ya wuceta ya dauki wayarsa dake kan gado kafin ya koma gaban mudubi yaja kura ya zauna bayan dayayi yan danne danne a wayar ya saka a speaker "Kaje Ten to Ten ka karbo mun usually meal dina yanzu" ya fada kafin ya latse wayar ya janyo Mansa ya fara shafawa. Hadiye abinda ya tsaya mata a wuya tayi ta tashi dakyar ta isa kusa dashi, ta cikin mudubin yake qare mata kallo, doguwar fitted gown din data saka ta Dark Orange din Lace tayi bala'in yi mata kyau ta fito da duk wani tudu da komadar jikinta daya qara cika dam kamar zata fashe, saurin dauke kansa yayi sanda ta iso ta karbi Man daya diba ta shiga shafa masa a banyansa, daga shi har itan ba zasu misalta yanda sukeji ba, Ta gaka shafa masa a bayan ya juyo tana fuskantarsa, hannu biyu ta saka taja shafa masa man A fuskarsa da tasa gyara saboda jiya yayi Aski cikin muryarta da tayi rauni kamar zatayi Kuka tace "Nayi maka abinci, kuma naji kana cewa a kawo maka" "Oh, thanks" ya fada yana miqewa saboda ya tabbata idan ta sake bude baki tayi magana cutarsa kawia zatayi. Wardrobe ya bude ya dauko Jallabiyya da boxer ya saka ya sake dawoa inda take tsaye ya dauki turare ya fesa kafin ya juya ya dauki Bibi data bingire da bacci ya fice daga dakin. A kan Dan gadonta da ya gani a gefen kijera ya kwantar da ita tareda pecking goshinta. Kai tsaye kan Dining din ya wuce ya kalli wasu Luxury warmer data zuzuzuba abincin a ciki su kadai kyan su ya isa ya saka ka cin abinda yake ciki ko bakayi niyya ba. Zama yayi ya bude babbar ciki, Tuwon shinkafa ne fari so a ciki, ya waiwaya ya kalli Umaimah data biyo bayansa kamar mara gaskiya, da yar mutunchi suke tashi zeyi ya dagata yayi juyi da ita dan kamar ta shiga zuciyarsa, abinda yake muradi kenan yaci har mafarki yake ya samu tuwo dan tunda ya tafi ko a ido be ganshi ba, zuwan da yayi kwanaki ma zaman hotel ya qare harya tafi be ci ba. Qaramin murmushi ya sakar mata, Umaimah ta sauke ajiyar zuciya har yana ganin yanda maqogaronta yayi sama da qasa kafin ta taho kamar wahainiya ta shiga bude masa sauran warmers din. Miya kala biyu tayi masa, Miyar Egusi dataji duk wani kalar Wasali da ake sakawa miya ga hadaddiyar Kuka wadda tayi digiri a London tasha zabi da suka dagargaje saboda yanda ta bata lokaci ta dafu. Dayan kwanon Jellop din shinkafa ce itama dai se wanda ya gani ga wani Musulmin peppe meat tsabar qyallin da yake kamar zaka ga fuskarka a jiki. Se casserole data zuba hadin potatoe Salad dayan kuma ganyan lattece yasha garnishing se wani bowl me kyau data zuba Samosa da spring roll ga kuma Jug din Coconut drink dana Zobo se Jarkokin ruwa me sanyi har diga yakeyi Duk yanda yaso ya daure seda ya kama hannunta na dama ya sumbata, qarshen abincin sa kenan ta hada masa su, ga Tuwo ga shinkafa ga nama.ga kayan fulawa. Kadan ta zuba masa kowanne a plate yayi bismilla ya shiga ci yana kallon fuskarta data marairaice kamar marainiyar Mage, tuwo ya gutsira ya nufi bakinta dashi, Allah sarki yanda take abu se yaji kamar zata bashi tausayi amma ya kanne haka suka shiga cin abincin yana ci yana bata har suka gama ba tareda wani yace qala ba. Ita ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo ta goge gurin harda fesa freshner, a ransa yace "Ikon Allah, su Umaimah course din tsafta aka yo kenan yana kallo ta ta shige daki babu dadewa ta fito ta zauna akan kujerar gefensa. "Na same ku lafiya?" Ya fada yana chanza channel, da sauri ta amsa masa ya daga kai ya kalleta, yanda take muimui da baki alamar tana son yin magana se juya yatsunta take kamar me jin tsoron yayi bala'in sake kunna shi. "Kaak...kayi haquri dan Allah" ta fada dakyar hawaye na kawowa idonta, banza ya mata yaci gaba da chanza channel din da yakeyi "Dan Allah Khalil ka yafe mun, wallahi sharrin shaidan ne bazan sake ba" ta sake fada cikin muryar kuka" juyowa yayi ya kalleta, a cikin idonta ya karanci laushin da tayi na gaske ne ya kuma tabbatar da wannan ladabin bana qarya bane da gaske takeyi amma dukda haka baze saki da sauri ba, haka nan baze fasa qudurinsa akanta ba. Hannu ya miqa mata fuskarsa dauke da wani murmushi da kai tsaye bazata iya fassara ma'anarsa ba yace mata "Zo nan, haka ake bawa Miji haquri a garinku" ya qarasa yana dorata a cinyarsa ya zura kansa cikin wuyanta yana shaqar qamshin turarenta da tun gamuwarsu ta dazu ya hautsina masa kwakwalwa. Baki ta buse da niyyar sake magana yayi saurin rufe mata da nashi, daga nan labari ya canza, da farko cikin nutsuwa da soyayya ya ringa tafiyar da ita, seda tafiya tayi nisa ya birkice mata. Cikin wani irin fushi da sauri yake saraffata, tayi kuka tayi magiya Bibi kanta dake bacci seda ta farka ta shiga taya Mamanta kukan neman ceto amma be saurare su ba, seda dan kanshi yaji ya samu nutsuwar da yake da buqata kafin ta qyaleta, be ko bi takanta ba ya tsallake ta ya shiga dakinsa ya yiwo wanka ya dawo ya dauki yarinyar dake faman tsala kuka. Ki tashi kiyi wanka ki karbeta" ya fada yana kallonta cikin sigar bada Umarni dole ta tattara jikinta da take ji kamar Buldozer tabi ta kanta, dakyar take iya daga qafarta ta kuma tabbatar da yaji mata ciwo ba kadan ba. Haka ta ringa gas jikinta tana kuka taredajera masa Allah ya isa a zuciya. Da tasan muguntar daya shirya mata kenan da bata shige masa ba. Ta gaya masa da wannan salon muguntar tasa gara ya saka bulala ya zane ta idan tayi masa laifi amma Allah yana kallo kuma seya saka mata. Tsawar daya bugo mata akan tayi sauri ta fito ta karbeta ce ta sakata qarasa wankanba shiri ta fito, an kira sallar La'asar dan haka tana karbarta ya fice daga gidan yana sakin wani mugun murmushi na jin dadi, riba biyu, ya kwashi dadin da yaji kamar ze manta sannan ya horata yanda zataji a jikinta, Allah ya kaimu dare zata sake gane kurenta, tunda ita bata ji ta haka ze ladabtar da ita har se kunnenta ya ringa jin abinda yake gaya mata. Da daddare daya kirata dakinsa kuka kawai ta saka masa dan ta tabbata ranta kuma yake nema, tun dazu da yammar zazzabi ya saukar mata, wani irin azaba takeji a qasanta dukda yanda ta shiga ruwan zafi ta gasa kanta dakyau amma kamar batayi ba ta tabbata hakan nada alaqa da uban maganin matsin da tayi amfani dashi bayan dinki da akayi mata na haihuwa. Daman seda Nuratu taja mata kunne sanda tace ta bata dan ita Allah ya taimake ta duk haihuwar da tayi bata samu qari ba shiyasa take yan gyare gyarenta amma Umaimah ga dinki ciki da waje ta nace seta bata, "Jiki magayi" abinda ta fada kenan gashi kuwa tana gani. A daren nan haka Khalil ya sake moreta seda yayi bidirinsa tsaf ya gama kafin kuma ya fara jin tausayinta, haqoranta har haduwa suke saboda zafin zazzabi ya taimaka mata ya gasata sosai kukan ma ta denayi se ajiyar zuciya kafin ya hada mata tea me kauri tasha da maganin rage zugi daya siyo bayan daya fita sallar Magriba dan yasan zata buqace shi dole sannanta samu bacci ya dauke ta. Da safe seda ya tsokaneta tana kwance yazo kamar ze shiga jikinta yanda ta zabura idonta ya fito seda ta bashi tausayi da dariya. Yanayin zafin jikin dayaqi sauka yasa dole sukaje Asibiti, dinki dai ya farke tas oho shi bema ji ba haka aka saka Umaimah a Theatre aka sake sabon dinki, bala'i dai ta ganshi muraran dan suna hanyar dawowa daga Asibitin kuka ta ringayi tana roqonsa ya maida ita gidansu. Da wannan Azabar data sha daga jiya zuwa yau ai gara zaman Cell din da tayi Aradun Allah shidai Khalil dariya kawai yakeyi a zuciyarsa dan ba wai iya hukuncinta kenan ba, ta gama wannan jinyar yana nan ze jijjigo mata gagarumar jinya ta gaske. Seda Umaimah ta kwashe kusan sati hudu tana jinyar jikinta, Ummu-Salma ce ta dawo gidan tana taya ta da ayyuka saboda suna hutu sannan, a bangaren Khalil kuwa wani mugun tsoronsa ne ya darsu a ranta, duk abinda takeyi idan taji muryarsa se gabanta ya fadi ta fara tsuma musamman da ya samu sarar daure mata fuska a yanzu tun bayan daya gama dagargazarta ya dinke fuskarsa tsaf baya mata dariya, idan kaji muryarsa yana wasa to da Salma yake magana ko kuma ya dauki Bibi yana mata wasa ita kuwa tsakaninta dashi gaisuwa ce daman itama bata so din wata doguwar magana ta hadasu ballantana har a sake maimaita abinda ya faru. Se a yanzu tayi nadama ta gaske ta kuma tsinewa shegiyar Khausar data ja mata, da bata shigo rayuwarta na da duk wadannan abubuwan basu faru ba. A haka aka ci gaba da gungura rayuwa, Umaimah ta canza lokaci daya tayi wani irin sanyi qalau. Gidansu me cike da soyayya da kwanciyar hankali ya dawo kamar wani gidan Makoko, babu wani karsashi a cikinsa idan kaji magana me qarfi Tv aka kunna ko Bibi ce take rigimarta, a bangaren Khalil kuwa be ma cika zaman gidan ba yanzu se dare. Daga office idan ya tashi ze wuce sabgoginsa dan yanzu Yana taba abubuaa da yawa ga kuma sabgar ginin gidansa da bayan dawowarsa seda yasa aka canza abubuwa da yawa saboda ba'ayi su yanda ya tsara ba, idanya koma gidan ma tsakanin su gaisuwa ce idan tayi abinci in yayi niyya yaci idanbega dama ba ya ciyo a gidan Hajiya haka suka kwashi kusan wata biyu a wannan yanayi. Babu inda take zuwa gashi maqotan da suke gaisawar ma gaba daya Rufaida ta rabata dasu yanzu babu me shigowa gidanta se Kishiyar Maman Hauwa da ita kadai suka ci gaba da zumunchi se wata Amarya da aka kawo ita kuma ba mazauna bane Mijin a kudu yake aiki kuma tare suke tafiya haka zata wuni a gida sedai tayi ayyukanta dan yanzu tsafta kam babu kama qafar yaro, Khalil har gulmarta yake a zuciya daman ita tun Asali idan suna fada ko suka samu sabani tafi nutsuwa ta ringa abinda ya kamata yanzun ma haka ta kasance gidan nan ko yaushe qal ta saka turare wannan karon jego take na masu hankali daga ita har Bibi bazaka gansu da qazanta ba musamman da tayi sa'a yarinyar bata da rigima sam idanta qoshi zatayi wasanta daga nan tayi bacci gashi har sannan ba'a dawo da Mu'ayyad ba, tsabar tunani da zaman Kadaici ya saka depression ya nemi kamata. Wani mugun ciwon kai tayi ranar Allah ya saka yana gida Weekend ne, tana cikin daki daman tun dare take fama da ciwon kan zuwa safiya ko motsin kirki bata iyayi saboda yanda takeji tamkar ana kwada mata guduma idan akan. Kukan Bibi daya keta jiyowa ya saka shi shiga dakin nata dan a zatonsa ko ta shiga bamdaki ta barta ne sedai yanayindaya tarar da ita dole ya kwasheta suka tafi Asibi babu shiri hankali a matuqar tashe, seda tayi jinyar sati kafin aka sallameta yan gidansu dasu Hajiya gaba daya sun dauka ciki ne da ita musamman saboda muguwar ramar da tayi ta dashe kowanne bangare da suna mitar tunda Mijinta ya dawo ta yada kowa ba inda take zuwa se suka bata uzurin qila bata so a san daga komawa tayi ciki shiyasa ta guji kowa. Randa aka sallameta suna komawa ta dasa masa kukan gida zata tafi, ba zata zauna ta mutu a banza ba tunda ya dena sonta ya sallameta kawai ai haquri babu irin wanda bata bashi ba idan baze yafe mata ba gara ya sauwaqe mata kawai ta kama gabanta akan baqin cikinsa ya kasheta. Isaraa tayi da surutan banza, dukda jikinta har sannan da saura haka ya jata sula shilla sama lulaye amma wannan karon ya banbanta da wancan, tafiya ce akayita ta nutsuwa suka goge duk wani Virus daya shiga memoryn su ya dawo sabo fil daga nan aka bude sabon babin soyayya da zaman lafiya tsakanin Sabuwar Umaimah da Khalil din nata. BAYAN WANI LOKACI Zama yayi dadi tsakanin Habibi Khalil da Habibtynsa Umaimah. Zama ne sukeyi irin wanda Khalil ya dade yana mafarki cikin zallar soyayya, zaman lagiya da tattalin Juna dan Umaiman tasa ta kintsu irin kintsin daya bawa kowa Mamaki ta kowanne banni yanzu ta dauki gyara. Tuni ta koma Islamiyya kamar yanda Maman Asad ta gaya mata, bayan dogon nazari da karatun ta nutsu da tayiwa kanta ta fuskanci gaskiya ta gaya mata dan haka ta sanarma da Khalil son komawa Islamiyya da bokon ya kumayi na'am da Islamiyyar, bokon ne yace tayi haquri. Da akwai shirin da yake dashi idan Allah ya tabbatar zatayi dan haka ta rungumi Islamiyyarta, sau uku sukeyi a sati litinin zuwa Laraba Goma na safe zuwa qarfe daya dan haka da ta gama ayyukan ta na safe zata fita makaranta idan ta dawo ta huta kafinta shiga aikin girki da tarbar Khalil bata da matsalar yara dan Bibi sam bata da rigima Mu'ayhad ko ya zama dan gidan Hajiya sedai yazo musu ya tafi. Sosai ta qaru da komawar tata Islamiyya ta farfado da karatunta ga kuma sabon karatun darasin rayuwa da take samu a gurin sababbin gogaggun qawayen da tayi matan da suka san me sukeyi ba tarikican qawayen banza data sabayi ba wadannan matane da duk maganar da zasu fada ta qaruwa ce me amfani haka ta sake shiga whatsapp group a karo na biyu bayan Rufaida tasa an cireta daga duk wanda suke ciki a baya sedai wannan karon groups ne na qaruwa da har seda ta gayyato su Nuratu dasu Mamab Asad duk suka shiga harda Anty ba'a barta a baya ba ta shige suna kwasar darasussukan rayuwa daga Matan da sukaga jiya suka ga yau. A dai taqin shekara da wani abu Abubuwa da dama sun faru na dadi dana akasin haka. Babban abin dadi daya faru shine budin da Khalil ya samu da har ta kai ga ya bude construction company nasa na kansa wanda ya kafu bisa jajircewarsa da kuma aiki me nagarta da yakeyi wanda shine ya janyo masa samun manya manyan kwangiloli da beyi tsammani ba qarqashin Jaririn Companyn sa dake tasowa a yanzu. Bayan nan se tafiyar Sa Umaimah da Hajiyarsa aikin Hajji wanda suka sauke faralli cikin wannan shekarar. Base na baku labarin Hajiya Umaimah a saudiyya ba, anyi ibadah dai matuqa addu'a kam Khalil ya shata ta Allah ya hana idonsa ganin wata mace bayan ita, Rikici kuwa babu abinda ta fada dan sedai idan basu fita siyayya tare ba. Haka kawai idan abinta ya motsa zatace wata na kallonsa, idan anyi sa'a yar uwarta ce Bahaushiya ta zageta su kwashi fada kowa ya kama gabansa, idan kuwa ba yarenta bane zagi take musu na tsamar nama sedai su kalleta su dauke kai toh basu ma san abinda rake fada ba kuma duk abin nan bata tabayi a gaban idon Hajiya ba, dan yawanci yawon Kasuwar su Hajiya bata binsu se tayi zamanta a masauki shidai Khalil Sallar sa da dawafi kaf babu a wanda baya roqarwa Umaimah shiriya da kuma zabin Allah akan komai na rayuwarsa, haka dai aka sauke Hajji lafiya aka dawo gida nan kuma Umaimah ta tarar da sabon abu, ginin gidansu da akeyi an canza masa fasali daga yanda aka qirqire shi zuwa zaman Mace biyu a tata fahimtar. Asalin ginin komai anyi shine a cakude, bangarenta dana Khalil din a hade suke amma suna dawowa yace taje ta duba gida a fara shirin zuba kaya dan damansun siyo wasu abubuwan irinsu Labulaye da Carpet tana zuwa taga wannan tashin hankali, part guda Khalil din ya warewa kansa saboda rainin hankali a cewarta fa harda Kitchen da store, guri dai tsaf kamar mace za'a ajiye. Babu kalar rantsuwa da bayanin da beyi mata ba ta toshe kunnenta, ta ringa tijara tana rashin mutunchi a gaban ma'aikata, bokitan penti da aka ajiye dan ana pentin gidanne haka ta ringa bi tana zubar masa dasu penti masu tsadar gaske. Ran Khalil ya baci matuqa, babban abin kuma daya qara bata masa rai da sukaje gaban Hajiya ta goyi bayanta. "Akan me zaka canza tsarin gidan kuma ba tareda kayi shawara da ita ba?" Hajiya ta fada cikin fushi tana kallonsa. Khalil ya kalli Hajiya ya kalli Umaimah dake faman share hawaye bayan tazo ta gama zayyanawa Hajiyar qarya da gaskiya ya hadiye wani abu me daci daya tsaya masa. Badan be taba kama Umaimah da wani abu dayayi kama da Bin Malamai ba da tabbas zece Asirce Hajiya tayi, wannan makauniyar soyayar da Hajiua take mata ba kuma ta ganin laifinta abin yayi yawa. Gyara zamansa yayi yana cewa "Hajiya ni sam ba abinda take tunani bane yasa nayi hakan. Kinga dai tsarin ginin a farko komai a cakud akayi shi, babu wani kebantaccen guri ko ina kowa yana iya shiga akoda yaushe babu sirri ni kaina se daga baya naga rashin dacewar hakan a matsayi na na me gida ya kamata ace ina da turakata data qunshi komai da komai a ciki bana buqatar fita idan ina buqatar wani abun. Sannan iyali muke tarawa dole yaranmu wata rana zasu girma, be kamata ace muna cakude dasu a koda yaushe ba dole akwai buqatar sirri tsakaninmu ni wannan ne kawai dalili na ba wani shirmenta mara tushe ba" "Kuma ahine harda Kitchen da store duk a bangaren naka? Three bedrooms ga qaton palour da dining duk me zakayi dasu?" Umaimah tayi tsugul ta fada kafin ma Hajiyar tayi magana, Harara ya galla mata kamar idonsa ze fado ba tareda yayi magana ba jin Hajiya nacewa "To ai kamata yayi tun kafin ayi seka gaya mata, base kawai tazo taga abu ba ai koma wacece tunanin daze zo mata kenan a zuciya" "Idan qara auren tana da hujjar Hanani ne ko kuma akwai Haramci a cikin Hakan?" Yayi wa Hajiya tambayar amma idonsa akan Umaimah data gwalo nata idanun saboda jin wannan gingimemen tashin hankali, "Bana son neman rigima Khalil, bana so. Ke kuma kinji abinda ya fada dan haka karna sake jin wata magana bayan wadda akayi a nan" Hajiya ta fada musu gaba daya Khalil be jira yaji koda sauran maganar tata ba ya tashi ya fice daga gidan cikin bacin rai. Iya Asarar pentindata masa da yawa kuma wallahi zata sani a cikin kudin da yayi niyyar bata na gyaran gidan idan yaso in basu isa ba ta tare da tsofaffin kayanta. Ya gaji da iskancin Umaimah ba kuma ze sake biye mata ta mayar dashi kamar wani takalmin sawarta ba. Ya dauka nutsuwar da tayi tun bayan wancan Al'amarin ta gaske ce tunda gashi kusan shekara daya da wani abun bata sake masa shirme ba suna zaune lafiya se yanzun kuma baze dauka ba. Da daddare be koma gida ba se gurin sha daya sabodaya zauna meeting da wasu campany da zasuyi hadin guiwar wani aiki. A palour ya tarar da ita daman kuma ya tsammaci hakan maganar ba zata mutu ba kamar yanda hajiyar ta yanke hukuncin son rai dan haka yana ganinta ya qara hade fuska ya wuce ze shiga dakinsa tasha gabansa tana cewa "Kai nake jira tun dazu dan gara ma ka sani bazan koma gidan nan ba idan baka rushe wannan gurin ka maida shi yanda yake ba" ta fada tana karkada qugu kamar Mazari, kallon sama da qasa yayi mata takaici ya rasa abinda ze fada mata seya zagaye ta ya wuce cikin dakin ta bishi cikin daga murya bata ko tunanin yara na bacci karta tasahe su tace "Khalil dakai fa nake ka wuce ni wato ga mahaukaciya tana magana ko?" "Ai sunan daya dace dake kenan Umaimah, na yarda baki da hankali kuma idan baki fita kin bani guri ba se ranki ya baci wallahi. Gida kuma karki koma, ke kika rasa gobe idan naga dama zan samo ukun ki na zuba a gidan kin kuma san yana da girman da ze dauke su dan haka ki fita ki bani guri ki koma ko karki koma keta shafa bani ba" Khalil ya fada yana kallon tsakiyar idonta kamar yanda itama ta zuba masa ido kafin ta juya da gudu tabar dakin nasa. "Mtsw" yaja wani matsiyacin tsaki ya zauna a gefen gado yana dafe kansa da yake masa ciwo ciwo,Umaimah bazata canza hali ba, shekara dubu tana abin kirki idan tsiyarta ta juyo cikin minti daya zata wargaza komai. To wannan karon kam sedai abinta ya qare mata dan bashi da lokacin da ze tsaya yana batawa akanta abubuwan gabansa ma su Ishe shi. ...*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 50 Washe garin ranar dukda Asabar ce ya fita saboda qarasa wani paper work da yakeyi na wani aiki. Dukda kwararrunma'aikata daya dauka sau da yawa duk wani shi yake tsayawa yanayi dakansa dan baya so a samu akasi, mutane sun yarda dashi sun bashi amanar ayyukan da beci ace qaramin company irin nasa yanayi ba dan haka yake gudun duk wani akasi. Yana office Hajiya ta kirashi cikin fadan da ko bata fayyace masa ba yasan Umaimah ce taje ta hada wani gurmin. Hajiyar na kashe wayarta ya kira Yaya Aminu, ya gaji da yanda take zuwa tana hadashi da mahaifiyarsa amma shi baze kai qararta gurin nata iyayen ba dan haka ze hadata da Yayanta yaja mata kunne duk abinda zasuyi ya tsaya tsakaninsu karta sake kai qararsa gurin Hajiya. Tsaf ya labartawa Aminun komai ya ringa fada ya kuma dora kacokan laifin akan Khalil kamar koda yaushe sabodaa ganinsa shi ya sakar mata take duk iskancin dataga dama. "Kuzo da ita dan ubanta tunda bata ji nima na dena handling case dinta ni kadai gara mune gaban Abban ko kuma Baba Abdullahi ai tasanshi kamar yunwar cikinta ubanta zeci tunda ita batajin magana" Aminu ya fada suka rabu akan yau da daddare zasuje gidan sa da Umaiman. Sanda ya koma gida bata nan kenan gidan Hajiyar ta koma dan da yayi zaton ko a waya ta kirata. Yana Alwalar sallar Magriba ta shigo gidan ita kadai dan daman tun tafiyarsu Aikin Hajji ta yaye Bibi tana can gidansu ba'a dawo da ita ba kallon ta yayi ganin yanda take tafiya kamar wadda akawa dukan tsiya jikinta a mugun sanyaye daman kuma ya lura a kwanakin kafin ta bullo da wannan fitinar jikinta ya canza kullum cikin snayi take. Hada ido sukayi ta dauke kai gefe tana qunquni be kulata ba ya fice ransa na masa zafi haka yayiwo sallarsa har Isha kafin ya dawo gidan ya tarar da ita a palour tayi wanka ta zaka wata Red Rubber gown me spaghetti hand tabi jikinta ta lafe surarta babu abinda ya buya ta dora qafa daya kan daya tana taunar chewing gum. Kallo daya yayi mata ya wuce dakinsa, dab da ze shiga ya tuna da batun zuwa gidan Yaya Aminun seya juyo ya kalleta fuska a daure yace "Ki shirya yanzu zamuje gidan Yaya Aminu". UMAIMAH Wata muguwar faduwar gaba ce ta sameta sanda ya kira sunan Yaya Aminun take mafarkin da tayi dashi a daren jiya ya fado mata. Qirji ta dafe da hannu biyu tana cewa "Me ya same shi?" "Babu abinda ya same shi, qararki na kai gurinsa kuma yace kije yana nemanki koda magana ne?" Ya fada yana tsareta da ido, seta zumbura baki gaba tana wani banqaro Qirji a ranta tana cewa "Ai wallahi ko gurin Abba zamuje ba tsoro zanji ba, tunda dai Hajiya na bayana duk kaje inda zakaje ai dai ita ta isa dai" daga haka ta moqe ta shiga dakinta har sannan kuma can qasan zuciyarta tana jin wani tsoro data rasa na menene. Ta kwana biyu tana jin wannan rashin jin dadin dan har tunani take ko Abba ne ze mutu saboda yayi ciwo sosai lokacin suna Saudiyya kamar baxe tashi ba kafin Allah kawo masa sauqi kuma. Tana cikin shiryawa Mama ta kirata, ta dauki wayar cikin Mamaki dan da wuya Maman ta kirata idan bada wani abu ba sedai ita ta kirata toh ko har an kai qarar tata gidan ne? Wayar ta daga yanda taji muryar Mama se taji hankalinta ya tashi cikin murya me cike da Rauni ta amsa gaisuwar da Umaiman take mata kafin tace "Lafiya kike Umaimah ko akwai abinda yake damunki?" "Lafiya ta qalau Mama wani abu aka ce miki ya sameni?" Umaimah ta bata amsa cikin mamakin abinda yasa Maman yi mata wannan tambayar, se Maman tace "Toh Alhamdulillah tunda kina lafiya daman abinda na kira naji kenan Ya Mijin naki ina fatan dai babu wata damuwa ko?" "Duk lafiya muke Mama, kodai kema kina jin yanda nake ji ne? gaba daya bana jij dadi ji nakeyi kamar zan rasa wani abu?" Umaimah ta fada muryarta na karyewa kamar zata fasa kuka se Mama tayi saurin tareta da cewa "Aa babu abinda ze faru in sha Allahu kawai na kwana biyu ban kiraku bane shiyasa duk na kira yan uwanki Yayanku ne kadai ban samu ba na kirashi be daga ba amma nasan idanya gani ze biyo ni" "Yanzu ma kuwa gidan sa zamu je da Abban Mu'ayyad" Umaimah ta fada "Toh shikenan ku gaida shi idan kunje, Allah yayi muku Albarka gaba daya aci gaba da haquri dai" Maman ta fada daga nan suka yi sallama jinin Umaimah na qara tsinkewa. Kodai Mama ce zata mutu ta kira su suyi sallama? Se kawai taji Hawaye sun bin kumatunta. Khalil dake tsaye tun dazu yana kallonta yace "Tashi muje dare yanayi" ya juya ya fita. A mota suna shiga ta kalle shi har sannanda hawaye akan fuskarta tace "Dan Allah mu fara zuwa gida naga Mama" "Idan mun dawo se mu biya" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba. Tafiyar kurame sukayi har zuwa gidan Yaya Aminun, sun tarar dashi cikin shirin fita an kirashi operation emergency, wani target ne da suka dade suna bibiya suka samu information akan ya shigo gari hat anyi masa talala ana jira suje su kamashi abinda ya tashi fitar tasa babu shiri kenan. Yana. Gyara Bulletproof jacket din daya saka ya kalli Umaimah dake kallonsa itama ta rasa abinda yake damunta dan ko gaishe shi kasayi tayi yace "Wati Umaimah ba zaki dena halinki ba idan kinyi sanyi an dauka kin shiryu se ki dawo da sabon salon fitina ko? Yanzu idan baki taimaka masa ya rabu da mahaifiyarsa lafiya ba me yasa zaki zama silar samun sabani a tsakaninsu? Toh karki bar abinda kikeyi kinji duniya ke rudarki kuma gaki gata nan kina kallo dai mutuwa akeyi, idan yau an kawo qararki gobe be zama lallai kina da wanda za'a kaiwa qararki ba ke zakiyiwa kanki fada ga yara nan kin fara tarawa a haka zasu tashi suga kin wannan shashancin su me za suyi kenan? Kiji tsoron Allah ki bar mijinki ya huta yaji da damuwar waje idan ya dawo cikin gidansa ya samu nutsuwa". Dukda ba wani fadan azo a gani yayi mata ba haka kawai takejin maganganunsa har cikin zuciyarta nan take ta ringa shatato hawaye kamar an kunna famfo. Kallon Khalil yayi yace "Kai kuma a karo na qarshe da zan gaya maka ka tashi ka zama namiji a gidanka, kai ka bata kuma kai zaka tashi ka gyara daga yau karka sake kawo mun matsalar gidanka tunda dai ka zama solobiyo se ka zauna yarinya qarama ta ringa caza maka kai". Qarar horn da suka jiyo ya saka shi shiga dakinsa da sauri ya fito da pistol guda biyu yana soke su a jikinsa. "Abban Nu'aima wai aikin me zaku fita ne kace mun yanzu zaka dawo ammana ganka harda bindiga" Anty Mami ta fada cikin tashin hankali dan a duniya babu abinda ke tsorata ta irin taga ze fita operation da bindiga tasan gurin da ze shiga me hatsarine hankalin kuma baya kwanciya se taga ya dawo gida. "Yanzu zan dawo in sha Allah Mamy ki kula da yara ki gaya musu Dady na sonsu" ya fada yana rungumeta lokacin da aka sake danna horn din da qarfi ya saketa yana cewa su Khalil "Dare yayi ku tafi gida kunsan fa yanzu garin se a hankali ba'a son kaiwa dare a waje". Tare suka fito har ya shiga mota Umaimah ta tuna da saqon mama ta zura dagudu tana tsayar dasu, wayar ya zaro ya duba yana ce mata zan kirata ina shiryawa sanda ta kira shiyasa banji ba" Driver yaja mota suka bar gurin da sauri dan sun kusa missing target din an sanar musu yana shirin barin gurin. Umaimah shiru tayi batacewa Khalil komai ba ganin ba hanyar gida ya dauka ba. A laundry din da yake kai wanki suka tsayaya shiga, be jima sosai ba ya fito yaran gurin na binsa da ledojin da aka sako masa kayan wankinsa ya bude musu back sit suka zuba kafin ya zaro dubu biyu ya basu su biyun suka karba suna masa godiya ya shiga motar. Sesa suka kusa shiga gida shi ya tuna basu da bread dan haka ya nemi wani gurin da ake siyarwa ya tsaya. Wayar Khalil din daya bari a mota ce ta dauki qara, kamar ita aka kira tayi zuruf ta daga tana fatan wata me tsautsayin ce ta kirashi sedai ganin sunan 'Dr Sagir' data tabbata Mijij Nuratu ne ya bata mamaki kiran me zeyiwa Khalil a daren nan? Wayar ta katse ya sake kira ganin Khalil din ya tsaya dan da akwai me siyar da Nama a gefe da alama shi ya tsaya karba yasa ta daga "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Khalil kun koma gida kaji abinda ya faru ko? Ance kune baqinsa na qarshe Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Dr Sagir ya fada a rikice "Meya faru, meya samu Yaya Aminu?" Umaimah ta fada cikin wani yanayi dan dai a kalaman Sagir tasan shi yake nufi, gidansa kadai sukaje se Lundary da suka tsaya karban wanki kuma sune na qarshe da ya gani a gabansu ya fita ta tabbata akansa yake magana. Qit Sagir ya kashe wayar jin muryar Umaimah, qoqarin kira ta shiyayi rawar da hannunta yake ya sa ta kasa bude wayar daidai nan Khalil ya bude motar da sauri saboda hango wayarsa a hannun Umaimah da yayi, baya son wani sabon tashin hankalin shiyasa ko kayan be karba ba ya taho seta miqa masa wayar tana cewa "Ka kira Sagir ya gaya maka waye ya Mutu, wayyo Allah na shiga uku" ta qarasa tana dora hannu biyu a kai da fasa ihu. "Ke meye haka? Wazan kira?" Ya fada yana duba wayar ganin Sagir ne kiran qarshe yasa yabi bayansa. Salati ya ringa ja yana maimaitawa jikinsa yayi wani mugun sanyi haka yazare wayar daga kunnensa ya kasa juyawa ya kalli Umaimah da yanayinsa ya tabbatar mata dagske Yaya Aminun ya mutu. Ihu ta shiga rusa masa ya yi shiru dan besan yanda ze rarrashe taba, shi kansa mutuwar ta dake shi yanzu fa, yanzun nan ko minti Ashirin cikakku basuyi da rabuwa ba ashe fitar Ajalice, saurinda yakeyi na ya taradda Ajalinsa ne. Komawa yayi gurin masu bread da nama yace suyi sadaka dashi kafin yaja motar suka wuce gidan su Umaiman. Fadar kalar tashin hankalin da suka tarar bata baki ne, yanda gidan ya cika da Mata ba zakace dare bane har mamakine ya kama Khalil na yanda akayi labarin mutuwar tasa ya bazu cikin dan lokaci idan ya duba taqin rabuwarsu to yaushe har ya rasun? A bakin Baba Abdullahi da suke shirin tafiya Asibiti karbo gawar yake jin wai ashe wanda sukaje kamawa sun samu labarin zuwansu, a cikinsu aka samu wani ya ha'incesu ya sanar masa dan haka sukayi musu qofar rago suna shiga gurin sukayi surrender suna qoqarin saka musu Handcuffs akayi attacking nasu se jin harbi kawai sukayi ta ko ina, su takwas uku sun rasu a take harda Yaya Aminun Biyar suna Asibiti. Allah sarki rayuwa mai rai na tafe Ajalinsa na binsa a baya be sani ba haka a daren nan aka kawo gawar Yaya Aminu daya fita daga gida cike da burika kala kala ba tareda yasan yayi fitar da baze dawo bane. Fadar irin tashin hankalin da Iyalan gidan suka shiga bata bakine, Daga dare zuwa safiya Suman Mama biyu, Mamy matarsa ko tunda ta zube ba'a sake jij bakinta ba har seda safe da aka zo fita da gawarsa sannan ta sake fasa wani ihu ta zube sumammiya a gurin dole aka hada ita da Mama da Jininta ya haye akayi Asibiti dasu Abba kansa daga maqabarta Asibitin aka wuce dashi saboda yanda Numfashinsa keta hawa da sauka har ana ganin dagawar qirjinsa gashi ya kasa magana toh ya za'ayi? Allahn daya fisu son Aminu ya karbi abinsa ba tareda yayi shawara da kowa ba sedai a bishi da fatan samun dacewa kamar yansa ya samu kykykyawar shaida daga bakin jama'ar unguwa da Abokan aikinsa. Sun bada shaidar mutum ne me Amana ba kuma ya karbar cin hanci haka mai laigi duk daurin gindinsa idan aka sakashi akan case seya tsaya iya yinsa yayi ansha kaiwa rayuwar sa Hari Ubangiji na tseratar dashi se yanzu da tafiyar tazo babu wanda kuma ya isa ya dakatar da ita. Rasuwar Yaya Aminu ta sake maida kowa na gidan cikin hayyacinsa musamman Umaimah da wasiyyar da yayi mata ta qarshe ta samu guri radam ta zauna a kwakwalwarta, damanya fada wata rana baya nan bare akai masa qararta gashi kuwa ashe abinbada nisa bane yanzu sedai su tunashi su sakashi a Addu'a Allah sarki Anty Mamy ta shiga sahun su Anty Hafsa Allah ya daga musu. Wannan rasuwa ta sakata watsar da makaman yaqi sabon gidanma gaba daya ji tayi ya fita a ranta qila ma duk haqilon da takeyi ta mutu kafin a tare ko idan an shiga ba zata dade ba zata mutu. Ranar da tayi tunanin idan ta mutu Khalil wata ze auro kwana tayi tana kuka har abin ya bashi tsoro ya rinfa tofa mata Addu'a da farko duk a zatonsa Yaya Aminu ta tuno amma se yaga ta kalle shi seta rushe da kuka se kuma ya fara tunanin ko shima mutuwar zeyi ne ta fara Alhini? Alwala ya dauro ya fara jera salloli, idan ma mutuwar zeyi ya mutu yana sallah haka suka kwana ita kuka shi sallah. Bayan wasu watanni Yaya Khalil, bari naje na kaiwa Hajiya abin nan" Umaimah dake tsaye akansa ta sako wani uban zumbulelen Hijabi ta fada. Khalil ya zare Glass din dake idonsa kafin ya ture takarddun gabansa ya nuna mata kan cinyarsa yana cewa "Bazaki dena cemun Yaya Khalil bako? Gashi nan kin koyawa su Bibi sun deba Dady se wani Yaya zan saba miki fa" ya qarasa yana jan hancinta daya fara budewa. Yar qara ta saki kafin tace "Toh za'a dena, suma zan hanasu fada" "Yawwa ko kefa, me zaki kaiwa Hajiyar?" Ya fada yana qoqarin bude kwanan hannunta ta qanqame tana cewa "Bazaka gani ba" "Wai dagaske kike matar nan rowa zaki mun ko kadan bazaki sammun ba?" Ya fada sanda yayi nasarar bude kwanon ya debi dambun naman dake ciki ya zuba a baki yana taunawa yana lumshe ido. Bubbuga qafa ta shigayi da kuka qarya wai seya biyata, kwanon ya karbe ya sake dibar wani ya watsa kafin ya ajiye gefe yana cewa "Zo na biyaki toh, ai abun bana rigima bane". Bakinsu ya hade ya shiga kissing nata passionately, seda suka kwashi kusan minti goma kafin Umaimah tayi saurin janye jikinta jin Alamun ana hawowa saman da gudu. Tana zama kusadashi kuwa Mu'ayyad ya fado da gudu yana sallama Bibi a bayansa tana kuka da yar tsanarta a hannu babu kai" Jikin Umaimah ya fada ita kuma ta wuce gurin Khalil ya riqeta yana cewa "Meye haka, me kayiwa Mamana take kuka?" se ta sake fashewa da kuka cikin magarta da bata gama nuna ba ta nunawa Khalil din kan yar babynta tana cewa "Yaya ya kace ta, ya ciye mata kai". "Lalala baka kyauta ba Yaya, ya zaka kashe mata Babynta ka cire mata kai? Kyaleshi kinji Mamana an jima zamuje mu siyo wata babba maza share hawayenki" saurin goge fuskarta ta shigayi jin za'a siya mata wata ta dane cinyar Khalil din tana qoqarin taba takaddun zanen dake gabansa ya janye su yana cewa Umaimah "Kije dasu dan Allah na samu na qarasa aikin nan yau" "Uhm kafi sati kullum haka kake cewa yau zaka gama, ni na fara gajiya da wannan aikin me cinyewa mutane lokacinsu" ta fada tana zumbura baki, seya daga wata takadda ya nuna mata yana cikin tsokana yake cewa "1 Billion contract ake gaya miki yarinya, kedai kiyita salati kina mana addu'a idan harkar nan ta fada ai ke kanki zaki sha mai Hajiyata" "Toh Allah yasa" ta fada tana miqewa ta bawa Mu'ayyad kwanon ita kuma ta kama hannun Bibi suka fita ya bita da kallo yana wa tafiyarta data fara canzawa kallo. Watanninsu Shida da tarewa a Sabon gida kuma watannin cikinta tsarabar Sabon gida. An tare lafiya kuma tun sannan zaman lafiya ya sake jaddaduwa a gidan idan ka cire qananan sabani da kowanne gidan aure ake samun su musamman ma da akayi katari da Khalil din me dauke kaine abinda yake qarawa zaman nasu Armashi kenan dan ko tsiyatakunta sonso motsawa baya kulata yanzu. A bangaren Alaqarta da Hajiya kuwa se abinda ya qaru saboda qaruwar kusancinsu yasa ta sake siye zuciyar Hajiyan da mugun ladabi da biyayya. Kusan koda yaushe tana bangaren Hajiyar, da safiya tayi Khalil ya fita ta gama abinda zatayi zata wuce can. Habiba ta shiga jami'a dan haka yanzu itake duk wani abu daya shafi Hajiya harda Abinci dan sauda yawa can take girki seta debar musu dan dama yaran kusan ko yaushe suna can, Mu'ayyad ya fara zuwa makaranta se Bibi ce kawai a gida. Da sallama ta shiga palour Hajiyar Jalilah da zuwanta kenan ta dago suka kalli juna kowacce ta watsar da yar uwarta. Tun case dinsu da Hadiza Jalilan ta fita a sabgarta. Haduwa seta zama dole gaisuwa ko se akan idon Hajiya in ba haka ba babu meyiwa wata kallon arziqi. Ita Umaimah gani takeyi Jalilah ke zuga Khalil, ita kuwa abinda Umaiman tayi ne ya saka ta fitar mata akai ga kuma wannan rainin da tayi mata tunda ai ko banza ta girmeta tayi qanwa ta kusan nawa da ita bataga dalilin da ze saka ta fara kulata ba. "Aa, Umaimah kin shigo yanzu yau Weekend dinma bazaki zauna ki huta ba ai Habiba tana gida" Hajiya data fito daga kitchen ta fada cikin fara'a, Umaimah ta zame qasa ta shiga gaisheta ta amsa tana tambayarta jiki jiki ta amsa harda satar kallon Jalilah data sakawa waya Ido kamar ma bata parlour. Kwanon hannunta ta ajiye Hajiyan tana cewa "Dambun kaza na miki tun jiya Hajiya shi nace bari na kawo miki yanzu" "Toh Madallah na gode kwarai Allah yayi miki albarka kamar kuwa kinsan bakin yana kwadayi, bana so na sakaki aiki ne ga nauyin jiki shi yasa na saka Habiba kin ganshi can na kasa ci duk ta qonashi ka shegeb qarni daga ji bata saka kayan qamshi a kazar ba" "Kai Hajiya kawai dan kin saba cin na Anty Umaimah ne amma wallahi abuna yayi dadi, dan Allah Anty ci kiji" Habiba data taho da kwanon dambunta ta miqawa Jalilah. Ta dibi kadan ta saka a baki tace "Aiko yayi dadi kuma ni banji wani qarni ba Hajiya se qamshin spices ma yakeyi" "Oho duk ta zuba wasu abu masu warin kyankyaso ba ni nafi son abu na haka daga citta se Tafarnuwa ci kiji banbancinsa da wannan" Hajiyan ta fada tana miqa mata kwanon Umaimah seta miqe tana cewa "Kedai kici abinki tunda ya fi miki dadi" Umaimah ta harareta qasa qasa yanda baza'a lura ba amma tsaf Jalilan ta gani a ranta tace "Da haka kika shanye mana uwa kenan ai kuwa zamuyi maganinki". Miqewa Umaimah tayi tana cewa "Bari naje Hajiya, Anty Jalilah amma yai dai zaki shigo mana dan ina lissafe tun ranar tariyar mu baki sake leqa bangaren ba". Yanda take murmushi seka rantse har zuciya tayi maganar, Jalilah ta mayar mata da martanin murmushinta tace "Zan shigo, ki gayawa dan qanina ina nan zuwa" da haka ta juya ta bar sashen. Ta tarar da Khalil ya tashi daga aikin da yakeyi, wayarsa dake ajiye akan centre Table ta dauka,seda ta leqa dakinsa, qarar zubar ruwa dataji yasa ta gane wanka yakeyi dan haka ta dawao palour ta bude wayar ta shiga yi masa binciken data mayar dabi'arta. A sabuwar Islamiyyar data chanza a nan cikin unguwar saboda tasu tada tayi mata nisa daga nan dukda yanzu tana jan mota babu inda bata shiga amma akwai tazara sosai to a Islamiyyar tayi wata sabuwar qawa wai ita Safina ana kiranta da Maman Halima. Qawance suka qulla tamkar sanda suke da Rufaida, Rufaidanda saboda qin Allah yanzu take so ta dawo mata suci gaba da qawance saboda ganin cewa Allah ya sake dagata Mijinta ya samu budi sosai ga tangamemen gida na kerewa Sa'a tana ciki se gata ta debi zugar yan unguwa su Maman Hauwa wai sunje yi mata Allah sanya Alkhairi dukda bata fada musu zata tashi ba se a bakin Maman Hibban sukaji dan suna hulda da ita har yanzu ita kadaice bata ji hudubar Rufaida ta dena kulata ba se Ramatu kishiyar Maman Hauwa. Ita Safina ita ta qara mata sabon course na binciken wayar Miji. Dukda daman sa'i da lokaci takanyi amma yanzun da Safina ta karanto mata wasu gurbatattun tunani ta dasa mata zargi a ranta ya sa ta maidashi sana'a a cewar Safina Maza yanzu gaba daya yan iska ne kawai wasu ne suka fi wasu iya taku shiyasa ba'a gane su amma in kika zurfafa bincike da wayo se kin gano duk abinda Mijinki yake aikatawa a boye. Ba iya binciken waya ta koya mata ba harda Mota. Haka kawai zata ce ya bata Aron mota ta fita ta samu guri ta bincike masa mota tsaf tun Khalil baya lura har ya fara gane idan ya ajiye takaddu ana canza musu tsari ya fara zargin ko a office ne wani yake masa haka se daga baya wata rana ya kamata,ta ari motar ta fita can qasan ta tsaya tayi parking shi kuma fitar gaggawa ta same shi dan haka ya dauki motarta ya fita. Ya dade yana mamakin me take nema, be nuna ya ganta ba ya tafi sabgarsa bayan ya dawo ya duba motar tsaf dan a ranar akwai tsabar kudi naira miliyan biyar daya karbo daga banki ze kai wani guri ya barsu a motar zuciyarsa ta darsa masa ko kudin zata dauka amma ya qaryata hakan dan a zamansu naira biyar dinsa be taba nema ya rasa ba idan ze aje abu ya shekara ze dawo ya tarar dashi batta idan tana da buqata zata uzzura masa ya bata amma bazata taba taba masa kudi idan bashi ya dauka ya bata ba Bayan ta ajiye motar ya koma ya duba kamar yanda ya tsammata komai yana nan inda yake ko tsinke bata dauka a ciki ba dan yana da lura haka idanya ajiye abu be fiya mantuwa ba kuma ko ya aka taba seya gane shiyasa yasan komai dake cikin motar da kuma yanda suke tanbayar da yake yawan yiwa kansa itace me take nema? Se daga baya ya samu amsarsa randa ya taba jinta tana waya take gayawa wadda besan ko wacece ba ita Mijinta Dabanne da sauran Maza kuma baya cin Amanarta dan babu inda bata bincika ba har dirar mikiya data tsiri yi masa a Office se yana tsaka da Aiki zataje kuma bata taba kamashi da wata alama ta rashin gaskiya ba. A nan ya gane ashe duk wannan binciken na neman hujjar yana cin Amanarta ne kai Mata se a barsu. Tsaye Khalil yayi a bayanta yana kallon yanda take bincika masa waya kamar wani danta, messages ta gama dubawa ta bude WhatsApp kenan ya fuzge wayar dan akwai abinda baze so ta gani ba, badan yana tsoron komai ha sedan kawai yanzu yana da buqatar nutsuwa wata kwangila yake nema yana kan Tsara papee work din ne kafin yayi presenting idan yayi ayi awarding nasu yanzu idan ta shigar Masa WhatsApp sabuwar chapter bala'i zasu bude a gidan kuma be shirya asarar wannan kwangilar ba. "Wai sau nawa zan miki magana akan ki dena yi mun bincike a waya ne?" Ya fada cikin fushi, Umaimah data zabura dan sam bata san yana wajen ba ta dauka wanka yakeyi ashe ruwa ya tara be shiga wankan ba, hade rai itama tayi tace "Idan mutum yana da gaskiy ai baze damu ba in an duba masa wayar ammaji yanda ka wani zabura ka kwace da alama wani abun kake boyewa a ciki" "Ni dan ki ne da zaki ringa mun bincike dukma abinda nake boyewa ina ruwanki? Ki shiga hankalinki wallahi bana son shirme kinsan sarai yanzu da da ba daya bane bazan dauki ko wanne rashin hankalinki ba" Khalil din ya fada a hasale se kuwa ta riqe qugu tana cewa "Lallai Khalil, ni kake kira mara hankali ko saboda na kusa na bankado Asirin abinda kake aikatawa a waje ko? To mu zuba mu gani, ni din dai nice Umaimah ba janzawa nayi ba kuma zan tabbatar maka da hakan duk wadda ta shirya siyan tashin hankali da kudinta taci gaba da kulaka" tana gama fadar haka ta haye sama fuuuu ta barshi a tsaye. Bayanta yabi da kallo, shikenan Aljannun da aka saka a batta tun mutuwar Yaya Aminu sun balle bala'i ya dawo kai wannan yarinya shaidan yana jinjinawa Umaimah. Zama yayi akan kujera ya shiga WhatsApp din nasa ya bude, kamar yanda yayi tunani kuwa message dinta ne a farko ga saqon data turo na qarshe ya fito ras I love you da manyan baqi harda Jajayen heart emoji. Beko bude ba yayi deleting chat din gaba daya yana zauke numfashi, Zahra nema take seta saka shi a bala'i, shidai Addu'arsa Allah ya taimake shi kwangilar nan ta samu daga nan ba kare bin damo kowa ya kama hanyar sa amma kafin nan dole ya lallaba wannan yar Tijarar ya samu ta barshi ya kammala abinda yake gabansa. Umaimah ko kasa zama tayi sanda ta shiga dakinta, tabbas akwai abinda Khalil yake boyewa kuma ko menene seta bankadoshi idan ba haka ba me yasa ze fuzge wayar bayan a baya kota dauka ya kamata sedai ya mata fada kawai amma baya wannan rikicewar,to wallahi ya tarowa kansa abinda baze iya ba kuwa in har ta kamashi da laifin cin Amana ba zata saurara masa ba. Kayanta ta cire ta shiga wanka, fita zatayi tanaso taje gida ta duba Anty ance tayi targade a hannu ta manta ma se yanzu abin ya fado mata daga nan ta biya gidan Safina ta bata wannan labari lallai ta yarda da tace Khalil ya iya taku ne kawai amma babu yanda za'ayi ace Matashi da kudi kamarsa ya rasa Yammata ko be nema ba dole su bishi ai. Sanda ta gama shirinta bata tarar da Khalil ba ya rigata fita, tayi kwafa wato baze mata sallama bama waya sani ko gurin Matan ya tafi. Motarta ta hau ta fice, a babban Get suka hadu da Jalilah da Habiba da alama fita zasuyi suma amma ba nisa zasuyi ba dan slippers ne a qafar Habiban ko kallonsu batayiba ta bawa mota wuta ta fice a sittin. Bata jima a gidansu ba ta tafi musamman da Mama ta fara mata fadan Yawo dan a Satin sau uku yan ganin sabon gida da basu samu zuwa ba se yanzu dangin Abba na Qarayeda sukazo biki gidan Baba Abdullahi da akayi wancan satin zuwan su uku bata nan, jiya juma'a ne kawai ta zauna gashi yau ma ta sake fita. A parlour Safina ta yada mayafin Abayar data saka bayantasha ruwan sanyin data kawo mata ta zauna a qasa dantafi jin dadi Safina na kallonta tace "Na ganki ke kadai, ina yaran?" "Ki rabani da wasu yara dallah akwai matsala wallahi" Umaimah ta faa se Safina ta gyara zama tana cewa "Matsala a ina meya faru?" Labarin yanda sukayi ta bata, Safina ta shiga tafa hannu tana cewa "Tab Umaimah kinyi sake wallahi an gama dake kina me har haka ta faru? Kawai ma kice abu yayi nisa sedai fatan Allah ya kiyaye" "Ni ba surutu nazo kimun ba mafita nake nema" ta katse Safina, seta gyara zama tace "Kinga yanzu dai ki fara gano wace tsinanniya ce ko tsinannu ma tukunna ne zamu san ta inda zamu bullo. Ba kwanaki nake gaya miki naje gidan su budurwar Baban Halima na zage shegiya tas ba? Wai ko wancan satin naje gidan Hajiyarsa se ji nayi suna yada zance wai ai satin nan Kabir zekai kudin aure, nayi dariya, daga gidan in gaya miki na wuce Sharp Sharp. Jiya ina nan kwance ya shigo wurgai wurgai dashi sedaga baya Rabi take gaya mun ashe yarinya da mamanta harda Wanta wai sunje gidan Hajiyar sun kai kashedi akan ya fita a sabgar yarsu ba zata aure shi ba. To ina zan iya wahala ga inda zan kai kudina a share mun hawaye". "Nifa na gaya miki babu wani shege da zan kaiwa kudi yana zaune yaci, yawwa bala'ina ma yafi duk wani Asiri da baya dorewa idan kuma kika hadu da wadda tafiki iya bin malaman fa ta shigo da qarfin tsiya ya za'ayi?" Umaimah ta fada cikin qosawa da zancen Malamai da kullum aikin Safina kenan, taje ta kai kudi ayi mata aiki kullum a tafe shiyasa ga ta nan sedai qaton gidan amma babu abinda ta ajiye suturar Arziqi se tayi da gaske take dinkawa badan Mijin baya mata ba sedan ta qulla zubin Adashin da babu kwasa. "Yanzu dai kiyi qoqari wayar tazo hannunki ki dauko lambar shegiya daga nan zamu san abinyi" Safina ta jaddada mata. Nan ta kusan wuni seda tazo tafiya ta dakko wata jigida ta bata tana cewa "Gata an kawo amma fa ta qara kudi dubu goma sha biyar dakyar ta bari a sha uku saboda ma nace ta hado miki sauran kayan ne suma wani satin zatayiwo aike seki tanadi kudi" "Jarabar duniya Safina kin dai nace sena daura abin nan" Umaiman ta fada tana karbar jigidar, duwatsun da akayita dasu masu kyau ga wani qamshin turare da takeyi Safina tace "Nasaka naji dadi ne Hajiyata Mallaka ce sadidan se kin gwada zaki tantance idan tana jikinki Khalil be isa ya musa miki ba se yanda kikayi dashi wallahi" "Kice ta tsafi ce" Umaimah ta fada, se Safina ta hada rai ta miqa hannu tana cewa "Kinga bani kafin ki fara iskancin naki ta uwar tsafi ce daman ai ke baki san abin arziqi ba bani na aimawa da Hadiya daman tace tana so" "Ke baki san wasa ba ne,bari naje yamma nayi se munyi magana" ta saka a jakarta Safina ta rakata har bakin mota ta shiga ta bar gidan. Ta riga Khalil din komawa, yau saboda a sama take ko bangaren Hajiya bata sake komawa ba ta shiga tsara yanda wayar Khalil zata zo hannunta. Be shigo gidan ba se bayan Isha kafin sannan tayi qoqari ta saki fuskarta, wanka ta dauka ta saka wata farar crop top iyakarta saman cikinta da yayi girma ta kawo wani Skirt dan qarami shima fari ta saka, barin turarukan datasan yana so tayiwa jikinta ta taje gashinta da bata dade da gyaransa ba Albarkacin cikin gashin ya qara cika da tsaho haka ta daure shi a tsakiya ta saki jelar ta juya a gaban mudubi ita dakanta tayiwa kanta kyau. Badan da abinda take son aiwatarwa ba da yau ko kallon Arziqi Khalil be isheta ba. Jakar data fita da ita ta bude zata dauki chewing gum taga Jigidar dazu danharta manta ta ita seta ciro ta shiga nadawa wanda dakyar ta saka ta danbata tana daurawa ba nadi uku tayi mata kuma kamar an gwadata Jajayen duwatsun suka fito shar akan fatarta da ciki ya sake haskawa nan ta qarsa qalqale qalqalenta ta koka palour ta zauna jiransa dan tuni su Bibi suka mata sallama a gurin Hajiya zasu kwana [8/12, 10:19 PM] Maman Aslam: *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 51 Se gurin tara da Rabi ya shigo gidan fuska a hade yayi sallama ciki ciki Umaimah dake nan zaune ta daga kai ta kalle shi, seda tayi dagaske gurin danne abinda yake ranta kafin ta qaqalo murmushin yaqe ta miqe tanayi masa sannu da zuwa. A ciki ya amsa mata ya wuce kai tsaye ze hau sama tabi bayansa tana cewa "Yau ka dade a waje, tun dazu ina zaune ni kadai shiru har nagaji da kallon Tv ma". Be kulata ba yaci gaba da tafiyarsa dukda yayi mamakin ganin tana fara'a sabanin tunanin taradda tashin hankali da yayi. Har dakinsa da yake a nan bangarenta ta bishi. Wanka ya shiga tana nan zaune idonta akan wayarsa daya ajiye amma bata so ta bata shirinta shiyasa ta kasa dauka, tana kallo wayar ta kawo haske alamar shigowar saqo, ta sace kallon qofar bandakin kafin ta miqe a hankali ta isa inda wayar take 'Zahra SB' taga sunan wadda ta turo da saqon, layi biyun daya fito ta karanta ta fahimci saqon bangajiya ne tare da fatan ya isa gida lafiya take taji wata juya na neman kada ita tayi qarfin halin komawa kan gadon dakyar ta zauna tana sauke numfashi kamar wadda tayi tsere. Kallonta Khalil daya fito daga bandaki yayi ganin yanda take zufa dukda Dakin da akwai sanyin Ac, yanda ta zubo masa ido itama ya saka ya qara tamke fuskarsa tam ya wuce gaban mudubi yana jin yanda take binsa da kallo. Umaimah ko tamkar wani baqin kumurci haka fuskar Khalil din tayi mata muni yau, wato daya fita gurin sabuwar Budurwar ya tafi lallai ashe yaqin duniya duniya na uku na dab da aukuwa. Haquri ta ringa bawa kanta tana tausar zuciyarta harta samu ta iya danne Kishin daya taso mata ma miqe ta isa inda ya ke. Man da yake shafawa ta diba ta shiga shafa masa a bayansa zuwa wuya a lokacin ji take kamar ta shaqe shi kawai ta huta amma ta dake suka gama shafa man ya shige Walk In closet dinsa ya sako Pyjamas farare qal masu taushi ya sake dawowa gaban mudubin ya fesa turare har sannan tana tsaye. Wayarsa dake ajiye ya dauka ya duba se ya dago ya kalli Umaimah data maida hankali kan gyara kayan dayayi amfani dasu kamar bata san me yake ba alhalin akan idonta ya dauki wayar. Kan Sifa dake dakin ya zauna yana maidawa da Zahran martani, Umaimah tayi ta maza ta qaqalo murmushi tace "Abinci fa?" "Naqoshi, naci a gurin Hajiya" ya bata amsa ba tareda ya dago daga kallon wayar tasa ba. "Toh Tea fa?" Ta sake tambayarsa swya daga mata alamar ta kawo. Hadiye yawu tayi ta qarasa inda yake zaune ta zauna itama ta saka hannu biyu ta riqe hannunsa da baya amfani dashi, cikin shagwaba tace "Wai saboda abinda ya faru dazu kake fushi Hubby? To kayi haquri ka yafe mun kaji bazan sake ba". Ajiye wayar hannunsa yayi ya juyo ya kalleta yace "Sau nawa zan gaya miki bana son abinda kikeyi mun amma bakyaji se ana zaune lafiya se kin san yanda kika jangwalo wani abun. Ni na taba daukar wayarki nayi miki bincike keda kike qasa dani amma se kece zaki ringa daukar mun waya haka kawai, idan inada abinda zan boye I'm not a fool da zan ajiye a wayar ai bayan nasan har dare bi kikeyi ki daukar mun waya sannan abin naki qara gaba yakeyi har mota ta bincikawa kikeyi me kike nema a ciki?" Mismis ta shigayi da ido tana motsa baki yaci gaba da cewa "Bana so karki sake idan ba haka ba kuma zamu samu gagarumar matsala dake kinji ko?" "Bazan sake ba In sha Allah, kayi haquri" ta fada kanta a qasa, seya dago fuskarta yayi pecking lips dinta Kafinya saki hannunta yana cewa "Better, ki kawo mun tea din, Lipton kawai karki saka komai". Miqewa tayi ta fita daga dakin zuwa kitchen. Tokare hannayenta tayi da Cabinet din kitchen din tana sauke numfashi mamakin kanta ya cikata yanda har ta iya daurewa bata kwancewa Khalil buhun Rashin mutunchi ba. Wani irin zafi da daci take ji a ranta dukda bata gani ba tasanyar iskar yake rubutawa amsa shiyasa har ya gagara daga kai ya kalleta yana mata magana amma babu komai ya bari ta gano wacece ta fara cin uwar ubanta kafin ta juyo kansa ai ya santa sarai ba canzawa kuma tayi ba. A Kettle me kyau ta glass ta zuba shayin ta kalli powder green leaf data sakawa yammatan kaduna dazu ta manta bata maidata store ba, wata shaidaniyar zuciya tace mata "Ki zuba a ciki" kafin tunanin ya samu karbuwa dayar zuciyar ta kwabeta, Khalil fa, Khalil zata kashe? Idan ta kashe shi me tayi kenan? Dakin ta koma har sannan yana zaune sema kishingida da yayi yana waya tana kuma shiga taji yana sallama tareda kashe wayar. "Zakuci kutumar ubanku ne daga kai har ita" ta fada a qasan ranta kafin ta aje masa shayin ta shige bandaki dan ranta ya sosu da yawa idan ta tsaya tsaf zata rusa shirinta. Khalil kuwa mamakin kansa yake yanda sam ya dena shayin Umaiman yanzu ya rasa ta inda ya samu qarfin guiwar da har ya iya waya da mace a cikin gida bayan yasan kowanne lokaci zata iya shigowa dakin. Yasan taga message din Zahra dan ko bata furta magana da baki ba yana iya gane fushi a idanunta kuma yasan a cike take dashi sedai be san dalilinta na shanyewa ba koma menene yana fatan ya zama alkhairi, Ya zamana cewa Umaiman ta zama mace tana kuma kishi irin na mata masu hankali ba kishin hauka da jahilci ba. Harya gama shan shayin bata fito ba se ya miqe da niyyar zuwa yaga abinda take yi kusan minti nawa kar fa taje tayiwa kanta lahani yana nan zaune yana zuwa bakin qofar ta fito itama jikinta daure da Towel qarami da alama wanka tayi fuskarta wasai ta masa kallo daya ta dauke kai, seya ruqota yana cewa "Ya kika cire kwalliyar bayan ban gama gani ba" "Naga kamar baka cikin mood na dadi ne shiyasa nace bari nayi wanka na kwanta kawai karna dame ka" ta fada ba tareda ta kalli fuskarsa ba dan Allah kadai yasan wutar dake ci a zuciyarta. Hannu biyu ya zuwa cikin towel din ya kama qugunta yana shafa Duwatsun jigidar jikinta, wani abu yakeji yana fizgarsa kamar mayen qarfe tunda yaga jigidar ta tafi da hankalinsa daman. Qasa yayi da idonsa yana mata wani kallo yace "Ni nace miki bana jin dadi? To ki maidamun kwalliyata yanzu idan ba haka ba" ya qarasa yana matsa qugunta har seda tayi qara ya saketa ta zauna akan kujerar gaban mirror tana tura baki. Murmushi yayi ya dawo ta gabanta ya tsaya yana kallon bakin nata, hannun sa ya shanshana yanajin qamshin jigidar na shigar masa har kwakwalwa seya sake kamota yana cewa "Wane turare ne wannan, yayi mun dadi sosai a ina kika samo shi?" Ya qarasa yana saka kansa a wuyanta. Umaimah ta saka hannu biyu ta ture shi, qarya nema yake ze nemeta wallahi bayan yaje ya dawo daga gurin wata yar iska karya dauka shirun data masa na sakarci ne ya jirayi come back dinta ze gane kurensa. Tsayawa yayi yana kallonta ganin yanda ta hade rai tana ture shi daga jikinta, hannu ya saka ya dago habarta ya sarqe idanunsu dan taqi yarda ta kalle shi tun dazu, a cikin idon ya hango zallar, fushi, kishi da damuwa daman yasan dannewa takeyi se ya dagata gaba dayanta ya aje akan gado ba tareda ya bata damar yin wani abuba ya shiga sarrafata son ransa tun tana qi harta sake masa ta bada kai bori ya hau "Ke din kece limamiyar zuciyar Khalil, duk wadda zata zo daga baya Mamu ce" ya fada cikin wani mayen shauqi daya debe shi, jinta yakeyi ta canza masa koda yake a kullum sabuwa yake jin Umaimah shiyasa baya taba gajiya da ita yake kuma iya dauke kai akan duk abinda take masa dan nutsuwar da take bashi ya tabbatar da ba duk mace ba, idan da ace duk mata kamarta suke da babu namijin da ze yarda yayi asarar tasa. Umaimah ko kalamansa a maimakon su mata dadi jinsu tayi kamar ya faska mata mari, wato yana dai so ya gaya mata wata na nan tafe kenan ko? To su zuba su gani shida ita da duk wadda yake shirin dakkowar shege ka fasa. Washe garin ranar gaba daya a gida ya wuni naniqe da ita kamar wani chewing gum, bangaren Hajiya ma tare suka shiga suka gaidata, a can ta sake tarar da Jalilah ashe wai gyaran gida ake musu pipe ne ya fashe ta cikin gini ruwa yayi musu barna shine ta taho gidan kafin a gyara. Sama sama suka gaisa albarkacin idon Hajiya da Khalil din, ta dan zauna kamar yanda ta saba dan ma karta tafi Hajiyan ta zargi wani abu ne, bata jima ba Bibi ta shigo da gudu wai Dady na kiranta, ta miqe tana satar kallon Jalilah karaf kuwa itama kallo ta take se kuwa ta wani gyara tsayuwa ta shiga tafiya ta taqama tana cewa "Bari naje kinsan idan yana gida baya iya minti daya ba taredani a kusa dashi ba" tayi wata dariyar iskanci kafin ta fita Jalilah ta bita da ido kawai ba tareda tace komai ba. A can kuwa tana shiga ta tarar dashi tsaye bakin qofa yana jiranta, be ko barya ta ida shiga ba ya dagata cak ya wuce dakinsa da ita, son ransa ya moreta tun ana abin dadi har abin ya fara bata tsoro ganin kusan sama da awa biyu amma babu alamar ze barta ba kuma dan be samu nutsuwa ba Aa shi kansa tana kallonsa ta fahimci kamara dole yakeyi, data tashi ze janyota su koma dafa taga abu bana qare bane ta fasa masa kuka dolen dole ya qyaleta ta shige bandaki dakyar saboda yanda jikinta gaba daya yayi tsami abinda ke cikinta ya cure guri daya dan shi kansa ya galabaita. Wanka tayi ta fito ta tarar da Khalil din a zaune har sannan ya dafe kansa, ganin ta fito ya sakashi tashi dakyar yake tafiya ya shiga bandakin shima yayi wanka. Shi kansa besan meya same shi yau din ba, abinda ya sani kawai Sha'awarta yakeji kamar ze mutu ga wani mugun dadi data qara masa shiyasa ko yayi kamar ze bari yake kasawa, yanzun ma da yake wankan ji yakeyi sha'awar na dawo masa amma ya tabbatar ruwan jikinsa na gab da qarewa in be nutsu ba tsaf ze kashe kansa a banza. Umaimah qasa ta sauka dakyar saboda wata azababbiyar yunwa da takeji, shayi ta hada me kauri tasha kafin ta dumama ragowar wata shinkafa ta dibi wadda zata ci ta barwa Khalil sauran dan tasan shima zeci ta dauki robar yoghurt daya ta wuce dakinta. Tana gama cinye abincin ta sake tara ruwa me zafi ta zuba gishiri a ciki ta shiga dan har sannan bata ji daidai ba, seda ta kwashe mintuna a ciki ta samu sa'idar abinda take ji kafin ta fito tana tunanin abinda ya saka Khalil wannan qarin jaraba. Ita dai a ritsin nan babu abinda take sha duk wani gyara ma ta ajiye saboda cikinta ya tsufa qarqarinta tasha zuma se fruits balle ace, mintsini taji a gefen cikinta ta kai hannu ta shafa nan taji Jigidar data daura da sam ta manta ma da ita take hirar Safina da wata Maman Amal yar ajinsu ta fado mata a rai dan a ranar ne ma tace itama a kawo mata saboda yanda suketa zuzutata idan mace ta daura haka miji ze ringa binta a qugu wato abinda suke nufi kenan ai kuwa data sani da bata karbowa kanta wahala ba, to ita lafiya lau ma Mijinta Jarumi ne base ta hada da sihiri ba. Kunce ta tayi taja drawer ta saka a ranta tana mitar Safina ai seda tace sihiri ne tace mata ba haka ba to kuwa sauran abubuwan ma data ce zaa kawo mata bata so dan bata san wace jarabar suke qullawa a ciki ba. Dukda ta cire din dai seda suka kwashi kusan kwana uku a haka dukda dai ya rage amma fa be koma kamar daba ga ciki ga takurar sa gaba daya ta rasa nutsuwarta haka dai suka ci gaba da lallabawa ta kira Safina ta qare mata tanadi tas ta ce kuma bazata biya kudinba, Safina ta ringa dariya tana cewa "Au daga gwaninta ai bansan ke shar kike ba bakida matsala da wancan fannin shiyasa ashe wannan ba harkar ki bace, to wlh haka kuwa zakiyi ta haquri se randa Mayen turaren jiki ya bar jikinki sannan zaki samu sa'ida dan ni kaina idan ta kwana biyu daman cirewa nake na ajiye in yayi sanyi na mayar" "Shegen turare kamar na yan bori aikuwa Dilka zanje a mun tas a goge shi" Umaimah ta fada Safina ta ringa mata dariya wannan dalilin yasa zancen Zahra ya bar zuciyarta na dan lokaci kafin abubuwa su qara rikicewa. Da safiyar Talata cikin sauri sauri suke shiri dan tare zasu fita gaba daya a sauke Mu'ayyad a makaranta kafin itama ya sauketa gidan Maman Asad data haihu jiya da daddare se ya wuce gurin aiki. Ba yanda beyi da ita ba akan ta bari gari ya qara waye wa sannan ta tafi amma qarfe bakwai tajewa mutane gida kaman tashin hankali amma tayi biris, baya son jan magana ya sa ya rabu da ita, Bibi ko wanka batayi mata ba ta tasata a gaba bayan ta dibar mata kaya suka fice daga gidan, seda aka fara aje Mu'ayyad kafin ya dauki hanyar gidan Maman Asad din da su yanata Mita ita dai bata tanka shi ba kuma tunda ta niyyata se taje. A waje ya tsaya, Bibi ta sauka da Jakar goyonta da aka zubo mata kaya Umaimah na mayar da takalmanta data cire saboda qafarta da ta dan tasa wayar Khalil dake tsakiyarsu ta shiga qara. 'Zahra S' ta gani, ta dago ta kalle shi yanda ya zabura ya dauke wayar ya qara qona mata rai me ze boye to bayan ta gani? A fusace ta bude murfin motar ta fice ko jakarta bata tsaya dauka ba ya bita a bayabda jakar wani yaro ya bawa yace ya kai mata kafin ya koma mota yana jin wayarsa daya saka a Aljihu nata faman qara. Seda yaci rabin tafiya office kafin ya tsaya ya dauki wayar da kamar mayya har sannan bata gaji ta dena kira ba. A fusace yace "Wai Zahra wace irin yarinya ce ke me nacin bala'i, da kika kira sau daya ban dauka ba base ki haqura ba ai kinsan idan na gani zan biyo ki ko? Wai ma akan me zaki kirana da safiyar nan bayan kinsan ta yuwu matata tana kusa dani?" Daga can bangaren Zahra cikin ko in kula da banbamin da yakeyi tace "Tun jiya kace zaka kirani har nayi bacci baka kiraba, da Asuba na kiraka wayarka a kashe ni kuma na kasa samun nutsuwa banji muryarka ba shi yasa nake ta kira" "To ai seki zuba ruwa a qasa kisha hankalinki ya kwanta kin hadamun rigima a gida, ke bari kiji daga yau ma karki Sake kirana idan ni naga dama zan kiraki haba duk kibi ki addabi mutum ba dare babu rana ke ko dan jan ajin nan na mata ma baki dashi haba, nin yanzu na fita aiki, karki sake kirana ki bari idan na samu free time zan kiraki dan Allah" Khalil ya katseta yana gama fadar haka ya kashe wayar yana sauke numfashi, wannan kwarzaba ta Zahra ta ishe shi Allah ya kawo masa lokaci Contract din nan ta tabbata kowa ya kama gabansa dan wallahi babu yanda ze iya da wannan yarinya me shegen nacin jaraba sedai Dr Sabitu yayi haquri. Motarsa ya tayar yaci gaba da tafiya, ba'a ko ci minti biyar tsakanin wayarsu da Zahra ba wani kiran ya shigo masa, gabansa ya fadi ganin Me kiran, Dr Sabitu Bashir seya gangara gefe ya kashe motar jikinsa har rawa yake ya daga wayar cikin ladabi yana cewa "Barka da Asuba Dady" "Riqe gaisuwarka Injiniya, wato har kayi kaurin wuyan da zaka saka mun yarinya kuka da safiyar nan ko? To bari kaji wallahi ko ka kira Zahra ka bata haquri ka lallabata ko yanzun nan kira saya zanyi a kwace kwangilar nan daga hannunka a bawa wasu. Kasan dai akwai wadanda suka fika cancanta na shiga na fita aka baka saboda to karka manta da yarjejeniyar da take tsakanin mu kuma duk wani shirme da zakayi ka tabbatar kana rage chances na tabbatuwar kwangikar ka ne, foolish boy kawai" Dr Sabitu ya fada cikin saurin bakin sa wanda a maganganun gaba daya kwangila da Zahra kaai Khalil ya iya tattarawa ya fahimci abinda yake nufi. Wallahi bada ban wuyar daya sha gurin tsara paper work da sauran abubuwan da yayi akan aikin nan ba da saki zeyi ya haqura, ina dalili? Shin tun farko ma waya kaishi shiga wannan bala'in da yayi haquri idan rabonsa ce kwangikar nan yana kwance zata same shi. Gaba daya Anwar Saleh ne yaja masa, Abokinsa ne tare sukayi karatu kuma yanzu yana aiki a Companynsa shi ya fara kwadaita masa Zancen kwangilar wanda tunda ya gaya masa a lokacin yace baze iya shiga ba dan Kwangila ce ta dubunnan miliyoyin kudi yasan babu yanda za'ayi ma ayi considering qaramin company irin nasu. Anwar ne ya ringa pushing akan suje su nema ai abin na Allah ne baya ga haka ai shima yayi ayyuka da yawa manya a Company daya bari kuma mutane da yawa sun sanshi dan haka kar yaji komai suje suyi Addu'a qila sa'ar tasu ce haka ko akayi suka shirya takaddun tsare tsare da budget da komai Anwar yaje yayi submitting se gashi cikin ikon Allah an kirasu cikin Kamfani goma na sama da a ciki za'a zabi wanda zaayi awarding aikin. Anwar be haqura ba seda ya binciko masu fada aji a Ministry da za'ayi aikin a ciki ya gano Dr Sabitu Bashir daya daga cikin Directors din gurin yace ya sanshi abokin Uncle dinsa ne ze roqi Uncle din ya hadasu dashi haka kuwa akayi cikin Sa'a se gashi sun samu appointment da Dr Sabitu ya basu lokaci yace suje gida su same shi. Sun samu Dr Sabitu a gida ya tarbe su da fara'a saboda akwai kyakykywar alaqa tsakaninsa da Uncle din Anwar. Sun gabatar masa da abinda ya kaisu ya karbi Blueprint din da sukaje dashi ya duba kai tsaye babu kwana kwana ya gaya musu suyi haquri bazasu samu wannan kwangila ba dan akwai manya manyan kamfanunuwa da suka shafe su yamayi mamakin yanda akayi suka fito a Top Ten dan kamfanin nasu dako cikakkiyar shekara beyi da kafuwa ba amma hakan na nuni da idan an samu kwangila daidai dasu za'a neme su kenan haka suka tattara suka tafi gida jiki a sanyaye. Sati daya tsakani Anwar ya same akan Dr Sabitu ya kira shi yace yana son ganinsu haka suka dunguma suka tafu bayan sunje suka same shi yasa aka kira masa yarsa suna zaune wata zuqeqiyar yarinya me kyan sura dukda ba fara bace tas ta shigo palour, jikin Dr ta tafi ta lafe kamar mage ba tareda ta ko kalli bangaren da suke zaune ba. "Kalle su ki gani Daughter wanne ne a cikinsu?" Dr ya fada yana shafa kanta seta dago da sauri ta kalli inda baban nata yake nuna mata dan sam bata ma lura da mutane a gurin ba karaf idonta ya sauka cikin na Khalil, baki ta washe kamar wata wawuya ta nuna shi tana cewa "Wannan ne Daddy". Khalil da Anwar suka kalli juna cikin rashin fahimtar abinda yake faruwa. Dr dake dariya shima kamar yar tasa ya shafa kanta yana cewa "Oh My daughter Allah ya shiryaki, to tashi ki koma ciki kinji" seta noqe kafada kamar wata yarinya Dr ko ya sake washe baki yana cewa "Idan mun gama zan saka a kiraki kinji maza kije kiyi wanka kiyi kwalliya kafin nan" se a sannan ta miqe ta fice fuskarta kamar gonar Auduga tana aikawa da Khalil wani kallo da ya kasa tantance na menene. "Zahra baby kenan, tun ranar da kuka zo gidannan yarinyar nan ta shiga wani hali bata da aiki se kuka da damuwa qarshe ko abinci se munyi dagaske take iya ci kuma taqi fada mana damuwarta sam se jiya dana matsa mata sannan take sanar mun da a cikin baqin da suka zo gidannan ne ta kamu da son wani, bayan ta fada mun ranar ne nayi tunanin wadanda na gana dasu ya zama ku biyu nan ne ze Aminina Alhaji Zakari dalilin daya saka na kirawo ku kenan dan ta tantance wannan ne ne a cikinku kuma kunji, kai Khalil kaine kayi mun fashin zuciyar yarinya daga zuwa neman kwangila" ya qarasa cikin barkwanci. Kallon Anwar Khalil yayi lokaci daya yaji ransa ya baci, daya ce Dr Sabitu na neman su ya dauka wata kwangilar ce ta samu a she wani zancen shashanci ne kawai ya saka ya kirasu, to shi yayi me da wannan sangartacciyar yarinyar da kana ganinta kasan bata qoshi da tarbiyya ba? Taba shi Anwar yayi ganin yayi nisa a tunani dan sam be ma san Dr na magana ba "Yanzu dai kunji dalilin kiran, zaku iya tafiya idan yaso ka jirata a waje tazo ku gaisa daga nan se ku musayar lamba ko amma kafin nan zan ja maka kunne, kaga Zahra ita kadaice yata mace. Ina bala'in sonta yanda baka tsammani kuma zan iyayin komai akanta dan haka ka lallabamun ita dan badan ita tace tana sonka bama kai baka kai ajin da zan baka auran Zahra ba". Wani kallo Khalil ya ringa bin Dr dashi har ya disa wa maganar sa aya, ransa ya kai qololuwar baci, ya hasaso yar tasa da yake magana a idonsa bata kai macen da ze kalla ba balle har azo ana gaya masa maganganu irin haka akanta, seya miqe tsaye yana kallon Dr yace "Ai ranka ya dade ina ganin a cigaba da duba mata daidai da ita Wanda zasu dace danni already I'm happily married with the love of my life, qila ko sedai Anwar shine single idan sun daidaita shikenan" yana gama fadar haka ya juya ya fice dan rainin wayon mutumin ya ishe shi. A Compound din gidan suka ci karo ta fito daga wani part taci uban gayu da wani shegen Lace dinkin fitted gown ganinsa yasa ta nufe shi tana karairaya haushi ya qara kamashi wai wannan abun ake cewa bekai matsayin da ze aureta 'Mtsw' yaja tsaki ya fice daga gidan yana ji tana tsayar dashi. Besan yanda suka qare da Anwar ba dan be jirashi ba ya tafi, kwana biyu a tsakani ya sake samunsa akan Dr na neman sa urgently ya rantse ba zashi ba Anwar da baqin naci seda ya shawo kansa sukaje can suka tarar da Dr Sabitu da Zahra tsakanin su kasa gane Wanda yafi wani fita hayyacinsa sukayi abinma ya basu dariya ya basu takaici. Wai ashe bayan ya fita binsa tayi da gudu tana ganin ya wuce da mota ta zauna nan bakin get ta ringa birgima tana ihu dakyar aka shiga da ita gida tsabar kuka tana a kira mata Khalil seda aka nemo likita yayi mata allurar bacci. Mamanta daman bata shiga sabgar iskancinta shiyasa koda taga ta fara tayi hayewarta sama ta barta da Uban, hankalin Dr ya tashi abu dai ba kan gado haka ta ringayinsa har tana zata kashe kanta idan be aura mata Khalil ba dalilin daya saka ya sake kiran Anwar kenan dukda haushin abinda Khalil din yayi masa ya fita suna magana amma farin cikin yarsa yafiye masa komai. Babu wani kwana kwana Khalil ya sake jaddada masa shi yana da matarsa ba kuma ya buqatar wani qarin aure a yanzu, Zahra ta fasa ihun da kusa toshe musu dodon kunne Dr ya qara gigicewa kamar zeyi kukan shima ya shiga roqon Khalil akan ya amshi tayin Zahran amma ya sunkuyar da kai yaqi ce masa komai "Ka auri yata, ni kuma nayi maka alqawarin zan shige maka gaba ku samu wannan kwangilar" Dr Sabitu ya fada ganin bashi da wata sauran mafita dan roqo ba kalar wanda beyiwa Khalil ba amma yayi biris. Kallon kallo Khalil da Anwar sukayi, A zuciyar Khalil ya raya wasa kawai zeyi da hankalinsa bayan shi da kansa yace bazasu samu ba dan akwai sharadan da basu cika ba sannan yanzu saboda yana so ya yaudare shi zece zasu samu. "Ranka ya dade kamar yanda na gaya maka ne ina da mata kuma ina sonta dan haka koda kwangila ko babu bazan yi mata kishiya ba, kayi qoqari ka fahimtar da yarka tayi haquri kawai" Khalil ya fada. Dr Sabitu yace "I'm serious Khalil, nasan dai duk son da kake yiwa matarka ba zaka qi damar mallakar wannan kwangilar ba saboda ita, dan haka na baka kwana biyu kaje kayi tunani dan muna kan tattara alqaluma ne domin fitar da wanda za'a bawa, idan har ka amince da buqata ta to ni kuma zan cika alqawarin da nayi maka" akan haka suka rabu tun a hanyar su ta komawa Anwar yake ce masa "Khalil tunanin me zakayi? This is what you have been dreaming for ka kuma samu dama a sama ka na neman kayi wasa da ita? Please mu koma just tell him ka amince, gafa kwangila ga bonus na mata me kuma kake nema?" "Anwar bazaka gane ba. Yes maganar gaskiya zanso ace mu samu abun nan amma sharudan ciki kuma fa akan me zece sedai na auri yarsa kai baka ga yarinyar ba tayi maka kalar matar da ni zamu zauna lafiya da ita? Beside i love my wife ka sani, and bringing any issue like adding another wife is like sending an invitation for word war 3, baka san Umaimah bako? To kai kanka idan ta samu labarin da kai aka hada wallahi ba zaka zauna lafiya ba. I know my wife's capabilities, yar bala'i ce ta kaiwa BBC dan haka na haqura Allah ya bani rabo na a gaba". Anwar be haqura ba, mutum ne me dan banzan naci tsiya ga iya tsara mutum, haka ya ringayi har seda ya samu ya rinjayi ra'ayin Khalil din. "Ni bance ka aureta dole ba, amma zamu iya using opportunity din muma muyi wasa da hankalinsa, da zarar buqata ta biya se musan ta yanda zamu zame ai dai baze iya kwacewa ba bayan an rigada an bamu mun fara aikin ko?" Anwar ya fada cikin rarrashi, da haka ya samu ya shawo kan Khalil din dan gaskiya baze bari suyi asarar aikin nan ba dan ba qaramin kaya zasu ja, shi me yasa ma batace shi take so ba, duda shidin ma.tarbiyyarta batayi masa ba amma da ze iya maneji da ita, shiyasa yake ganin baiken Khalil din ba seya aureta ba taje ta qaraci shirmenta tunda shi yanada wata matar a gefe. Dukda tsoron abinda ze iya biyo baya Haka Khalil ya koma ya sanarwa Dr cewar ya amince da sharadinsa, sedai shima da nasa. Dole yana buqatar lokaci su fahimci juna da Zahran har zuwa bayan tabbatauwar kwangilar danshi a halin yanzu ma bashi da kudin da zeyi aure dan haka a qalla yana buqatar shekara Daya ya gama duk shirinsa ya kuma lallaba matarsa ta gida kafin sannan kuma sun samu fahimtar juna da Zahran itama ya gayawa Dr. Dukda maganar ta zowa Dr Sabitu kamar wani rainin wayo ma amma se yayi murmushi yace masa babu komai, idan shi yaro ne me wayo shi kuma ze nuna masa tun kafin a haifeshi yasan takan duniya dan haka babu yanda za'ayi ya yaudareshi, kuma kamar yanda yayi alqawari ya cika, ya shiga ya fita ya samo musu kwangilar dukda tarin qalubale daya fuskanta amma akan farin cikin Zahra ze iyayin komai. A bangaren Khalil kuwa ba qaramin qoqari yakeyi gurin tolerating Zahran ba, sangartacciyar yarinya ce ta ajin qarshe da sam bata san daidai ba haka take rayuwa sakaka babu kwaba babu gyara gata da nacin tsiya, son sa take kamar tayi me sam bata da aji idanta ganshi jikinta har rawa yakeyi waya kuwa idan ta dosa kiransa se duk abibda yakeyi seya bari ya daga sannan yake samun lafiya a cikin haka yake matuqar taka tsan tsan dan kar Umaimah ta fahimci halin da ake ciki shiyasa a kullum daya fito daga office zeyi blocking number Zahran ya kuma goge duk ubannin messages din sa take cika masa waya dasu kamar zararriya. Ranar data dauki wayarsa ya tabbatar bataga komai ba dan da babu yanda za'ayi tayi saurin sakkowa har ta bashi haquri yanzun kuwa ya tabbatar wannan kiran ya gayyato masa yaqi. Tsoronsa Allah yanzu tsoron Umaimah tayi wani sakarci da ze janyo masa matsala dan ya rigada ya gama paper work dinsa tsaf a satin nan ze kammala yayi submitting daga saka hannun Dr Sabitu kawai yake buqata a sakar masa kudin aikin, dukda yayi mamakin yanda akayi ya zama Signatory din amma yasan duk cikin shirin daurin talalar da yake masa ne na ya auri yarsa, shi kuwa ya qudurce dayaji Dirim kudin aiki sun sauka magana ta qare zeyi ta kansa ne dan be gama da ta gidan ba ballantana ya dakko wadda tafita cin kai ya hadasu. [8/13, 7:46 AM] Maman Aslam: *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 52 Tunawa yayi da furucin Dr na ya kirata ya bata haquri ko kuma ya manta da zancen kwangilar, wayarsa ya dauko takaici fal ransa, shi ta hada masa bala'i sannan kuma ya kirata ya bata haquri amma shikenan na dan lokaci ne. Kamar tana jira ringing daya ta daga wayar cikin shagwababbiyar muryarta da sam bata burgeshi tace "Yanzu kawai dan na kiraka shine zaka rufeni da fada kana zagina akan matarka ko?" "Oh daman cewa Dady kikayi na zageki kenan, yaushe na zageki? Ke baki ga abinda kika mun ba? Sau nawa zan gaya miki ki dena kirana qasa da qarfe goma na safe in dai bani ne na kiraki ba? Kuma sannan duk abinda ya faru tsakanin mu se kin gayawa Dady a haka zamuyi aure duk abinda ya faru ki kwasa ki gaya masa ya kira waya ya ringa fada to wallahi ko ki canza ko kuma mu samu sabani dake haba da wanne mutum zeji" Khalil ya fada cikin bacin rai be idasha shaqar numfashi ba Zahran ta fasa masa kuka kamar wata qaramar yarinya. Takaici yazo masa wuya amma ya daure ya sassauta muryarsa yace "To yanzu kuma me akayi da zaki yiwa mutane kuka uhm? Shikenan bazakiyi ba daidai ba a miki magana se kuka se tashin hankali?" "To meyasa zaka ringayi mun ihu bayan ko Dady lallabani yake yi? Wallahi sena gaya masa ba yace zaka kira ka bani haquri ba shine kake mun ihu da fada se na gaya masa?" Ta fada cikin zallar sakarci, Khalil ya bawa kansa haquri kafin ya ce "Toh kiyi haquri shikenan base kin sake gaya masa ba". Banza tayi masa taci gaba da gunsheqar kuka, yana jiyo muryar mahaifiyarta na cewa ta tashi ta bar kusa da ita kafin ta maketa tunda ita bata da hankali da yaga dai bazata bar kukan ba dole ya sassauto ya shiga rarrashinta yana gaya mata kalamai masu dadi har ya samu ta haqura. Besan lokaci yaja ba seda suka kashe wayar ya duba Agogo tara harda rabi tayi yana tsaye a gefen hanya. Gabansa ya fadi sanda yaga Missed calk din Umaimah dan wallahi beji ma sanda ta kirashi ba yana fama da waccen psycho din yarinyar. Kiranta yayi back wayar ta qaraci ringing bata daga ba haka ya haqura ya cigaba da tafiya ya tabbatar dai yau kam Allah kadai ze fidda shi. A office dinma be iya yin wani abin kirki ba. Ga Zahra ta ishe shi da waya yaqi dagawa cibi ya zama qari haka dole yake biye mata qarshe tace ya biya idan ya tashi tana son ganinsa ba yadda ya iya haka yaje gashi sunyi da Umaimah idan ya taso ze biya ya dakkota su wuce gida dukda bashi da tabbacin bayan abinda ya faru zata jirashin amma haka ya wuce bayan ya gama da Zahran. Yasha mamaki daya kirata ta dauka ya sanar da ita yana waje se gata ta fito fuskarta a washe suna sallama da Nuratu da itama zata wuce gida suka gaisa ta shige motarta kafin Umaiman ta bude bayan mota ta shiga fuskarta a dinke kai baka ce ita ta fito yanzu tana dariya ba. Bibi ce ta shiga gaba ya tada mota suka dauki hanya ta Rear mirror yake kallonta hankalinta naka wayarta da take dannawa har suka isa gida ya kasa ce mata komai dan gaba daya ya tsorata da yanayin fuskarta. Har suka kwanta batace masa qala ba abinda ya qara dugunzuma hankalinsa kenan dan shirun Umaimah ba Alkhairi bane, be manta yanda suka qare da Hadiza ba, bata yi masa magana ba seda komai ya lalace kafin ya tsinci zancen yanzun ma yana tsoron ta sake kwata wani da ze jefa su a bala'i gaba dayansu. UMAIMAH Yanda ta shiga gidan ya saka Maman Asad da Baba Talatu dake zuwar mata duk haihuwa suka juya suna kallonta. Mamakin zuwanta da sassafen ya kamasu ga yanayin data shigo da ko ba'a fada ba sun san ba lafiya ba. Dakin Maman Asad ta wuce kao tsaye Bibi ko daman kujera ta haye ta kwanta abinta dan bacci be isheta ba Baba Talatu ta kalli Maman Asad tace "Hajiyayye leqata mana kiji lafiya irin wannan Asubanci bayan fitar safe ba halin uwar dakina bace". A dakin ta sameta zaune a gefen gado ta zubawa qofar shigowa ido da gani tayi zurfi a tunani har Maman Asad din ta qarasa ta zauna gefenta tareda dafata sanann ta farga. "Lafiya Umaimah, me ya faru?" Ta fada tana kallonta kamar tana jira kuwa ta fada jikin Hajiyayyen tareda fashe da kuka seda tayi me isarta gaba daya ta dagawa Hajiyayyen hankali kafin ta fara magana tana cewa "Wallahi ko ni ko Khalil, se ya gayamun da shegiyar da yake cin amanata". Numfashi Maman Asad ta sauke a zuciyarta tana yiwa Allah godiya da abin tsaya iya haka, yanda ta ganta da sassafen nan ga kuka ta dauka auren ne ya samu matsala ashe iskokan kishin ne suka motsa dan haka ta gyara zama tace "Me kuma Khalil yayi keda bakya rabo da abin magana?" "Wata yar iska ya samu take dauke masa hankali, daman na dade ina lura da ya canza taku se ya ringa wasu abubuwa irin na munafukai. Kwanaki na dauki wayarsa haka ya fitittike ya ringa mun fada akan me zan masa bincike saboda yasan akwai abinda yake aikatawa a boye da baya so na sani shiyasa se gashi yau Allah ya tona masa Asiri yanzun nan a qofar gidan nan mun tsaya Karuwar tasa ta kirashi" Umaimah ta fada cikin zafin rai. Harara Maman Asad ta balla mata kafin tace "Umaimah ki iya bakinki, wai ke baki da hankali da zaki ringa danganta mijinki da karuwa ko kuwa an ce miki babu wata alaqa tsakanin mace da namiji seta iskanci? Wallahi samun Khalil din kikayi a bagas har yake takatsantsan da fushinki idan wani ne tunda ya fuskanci ke mahaukaciya ce bakisan abinda yake damunki ba ai sabgogin gabansa ze ci gaba dayi qarqari idan kin sani kiyi haukanki ki gama hakan bashi ze hana ya cigaba da yawon kula yammatan shi ba. Kuma bari kiji, tun wuri idan zaki hada hankalinki guri daya ki kama kanki kiyi tun kafin ya kawo miki wata tazo taga ballagazancin da kikeyi da sunan kishi ta rainaki dan kinsan qarya kike kice ke kadai zaki zauna a gidan nan ko beyi niyya ba na tabbata se yan uwansa sun saka shi ya qara aure dan in kika cire Hajiyarsa a yanzu dai kaf cikinsu babu wadda takr ganinki da gashi kin zubar da qimarki a gabansu kuma ko mune matar dan uwanmu tayi abinda kikayi a baya wallahi baza'a rufe case din nan ba se mun masa aure muga qarshen tsiya, dan haka in zaki ajiye kishi ki fuskanci gaskiya kiyi dan na tabbatar da lokacin zuwan wata ne yayi ba kuma ki isa ki hana ba dan baki da hujjar hakan". Kallonta kawai Umaimah take har ta kai aya yanda kasan ta kwashe ta da mari, yanzu ta kawo mata matsalarta a maimakon ta tayata jin haushi seta goyi bayansa harda qarin wani jafa'in take janyo mata to kuwa ya qare akanta, kishiya ba sedai ta ganta a gidanta ganin idonta wallahi. Tsaki kawai tayi ta miqe ta bar MamanAsad da baki a bude tana kallonta, bandaki ta shiga ta wanko fuskarta haushin kanta ma data tsaya yiwa Hajiyayye bayani ya kamata bayan tasan tafi qaunar Khalil akan ta. Palour ta wuce dan neman abinda zata sakawa cikinta ta gaida Baba Talatu sama sama bata ko kula tsokanar da take mata ba ta shige musu kitchen a ranta tana ayyana wannan Yaqin tane ita zata kwatarwa kanta yanci, yanda ta rabashi da Hadiza ba tareda shawarar kowa ba wannan karon ma haka zatayi amma kafin ta san abinyi dole ta fara gano ita yarinyar a ina take da duk abinda ya kamata ace ta sani akanta. Haka ta qarasa wuni a gidan bayan ta taushi zuciyarta ta saki ranta sukayi ta hidima bayan zuwan Nuratu, Anty Hafsa da Anty Zee. Taga missed calls dinsa har biyu ta share saboda idan ta daga wayar danniyar datayi wa zuciyarta zata wargatse ta kokora masa Ashar shiyasa ta barshi dan bata san kiran me yake mata bama. Da yazo daukar su ma seda tayi da gaske ta iya shiga motar shiyasa ta zauna a baya har sukaje gida kuma bata ce masa komai ba. Seda suka kwashe kwana uku tafi ka mutu bata ce masa ba, zatayi duk abinda ta saba a gidan girki da sauran ayyuka ammafa bazata shiga sabgarsa ba abin ya damu Khalil matuqa gashi baya so yayi mata wata doguwar magana ya kunnota Addu'a yakeyi abinda ya saka gaba ya kammalu kafin ta fashe, zuwa sannan yana da bakin yi mata bayanin komai game da Zahran amma yanzu kam akan tsini yake. Ita kanta Zahra da Mahaifinta sun taso shi a gaba akan ya turo magabatansa su shiga magana kullum cikin basu uzuri Yakeyi yana kuma Addu'ar Allah ya tabbatar da aikin nan su rabu kowa ya kama gabansa. Gaba daya shima ya shiga rashin walwala, haka idan ya fita aiki ze kirata yanda ya saba dukda bazata dauka ba har lokacin dawowa ya rage ya zamana yana dawowa gidan da wuri kuma idan ya dawo sallah kadai take qara fitar dashi sedai ya zauna zuru a palour ko yayi ta yan tabe tabe a Laptop dan wayar kanta baya so ya dauka balle tayi zargin Chatting yake da wata. A hankali da kanta kuma se gashi ta fara sakkowa tana kulashi, tun yana dari dari har ya fahimci dagske ta sauka daga fushin nata ya saki jiki suka koma sabgoginsu kamar da, yanda bata daga maganar Zahra ba shima beyi mata ba ya kuma qara toshe duk wata kafa da zata bata damar fahimtar wani abu dan wani sa'in ma daya dawo yake kashe layinsa da Zahran ta sank dan tunda ta fahimci bata samunsa idan ya koma gida ta chanza lamba, randa ta kira ya shiga kuwa yasha mitar Bala'i akan me yake blocking dinta yace saboda baya so ta kira a gaban matarsa, ta kuwa samu nayi har Dadynta seda ya shiga maganar yayi masa tatas yana kuma sake jaddada masa yabi a sannu dole ya chanza taku a haka dai ake ta lallabawa. UMAIMAH Kallonsa kawai takeyi da yanda yake raina mata hankali yana daukar bata san abinda yakeyi ba amma ta zabi tayi shiru kamar yanda suka sake shawartawa da Safina tace ya nuna masa komai ba komai na ta shammace shi hakan kuwa akayi, dukda ya chanza password abinda ya qara baqanta mata rai zarginta ya tabbata akansa kenan amma seda tasan ta yanda ta gano sabon daya saka. Ranakun Lahadi yana gida throughout be fiya fita ba seda kwakwkwaran dalili. Da rana suna yin lunch ita dashi, Bibi sun tafi gidan Jamila da Habiba kusan satinsu daya tunda Habiban ta samu Hutu Mu'ayyad yana islamiyya. Abinci sukeci suna yar hira jefi jefi wayarsa dake ajiye tayi qara yanda ya zabura seda ta zura masa ido kawai tana kallonsa ganin haka ya sakashi daidaita nutsuwarsa ya dauki wayar cikin borin kunya yake cewa "Namanta shaf na qaro qarar wayar dazu yayi yawa har na firgita" "Uhm" ta iya ce masa kafin ta mayar da kai taci gaba da tura abincin da gaba daya ya fita a ranta. Be amsa kiran ba seda wani ya sake shigowa shima gudun zargi ya sakashi amsawa a gaggauce yace "Abinci nake ci idan na gama zan kiraku please" bata san me aka ce masa ba daga can bangaren ya sake cewa "Toh, naji" kafin ya kashe yana jan tsaki yace "Anwar ne, haka kawai wai sun shirya mana walima akan kwangilar dana baki labari bayan ko gama kammaluwa batayi ba. Bayanda banyi dashi ba akan ya bari ba yanzu ba amma wai ya rigada ya sanarda duka Employees dinmu yau za'ayi qarfe hudu nidan bazanje ba se suyi abinsu su kadai" "Aiko dai da kaje" ta fada tana kallonsa, yanda yayi maganar da bata san abinda yake shiryawa ba tsaf zata yarda amma ina ta gama rafko shi babu ta yanda ze layance mata. "Gaskiya bazanje ba tunda yaqi jin maganata ya bari ba yanzu ba se suyi su kadai, ni yanzu ma so nakeyi mu shiga daga ciki na gaya miki wani abu" ya fada yana zagayowa ta bayanta yayi kissing wuyanta. Janye jikinta tayi ta miqe tana cewa "Gara dai kai tafi dan ni nan me kitso nake jira kaina ya dameni gara tazo ta lallabe mun shi" ta qarasa tana tattare kwanukan da suka bata. Shiya tayata suka kwashe komai suka kai kitchen kafin suka fito ta wuce dakinta shima ya tafi nasa dan shiryawa ransa qal da ya samu damar fita ba tareda ta zargi wani abu ba. Zahra ce ta addabeshi, tun farkon satin nan take gaya masa qawayenta zasu zo yau daga kuma tana so ya hadu dasu su gaisa dan duk ta basu labarinsa. Baya son su samu wata matsala a ritsin shiyasa ya amince yana ta lalubo abinda ze fitar dashi daga gidan ita kuma gata da shegen gajen haquri se kiransa take tana tambayar yaushe ze zo. Wanka ya shiga, Umaimah data biyo bayansa ta labe seda ta tabbatar ya shiga wankan kafin ta dauki wayarsa a gaggauce ta kwafi number Zahran daya chanzawa suna zuwa Engineer Z tsabar sa idonta yasa ta gano shi, har ta mayar da wayar saqo ya shigo daga Zahra. Budewa tayi ta karanta "Dear kazo da wuri saboda su ganka a cikin hasken rana suga irin zaben mijin da nayi, Love you" abinda ta rubuta kenan. Goge saqon Umaimah tayi zuciya tazo mata wuya, a hasale ta qarasa jikin qofar bandakin cikin rashin Sa'a muqullin qofar ta ciki aka sakashi dan da so tayi ta kulle shi a ciki taga ta inda ze fita se kuma meta tuna ta fice daga dakin da sauri zuwa nata. Khalil daya jiyo qarar rufe qofa cikin Sauri ya dauraye jikinsa ya fito ko gama daura towel din dakyau beyi ba ya tsaya yana dube dube bega kowa ba, ya qarasa inda wayarsa take ya duba tana nan yanda ya ajie dan haka yayi tunanin kunnensa ne yajiyo masa badaidai ba saboda ba a nutse yake ba. Wankan yakoma ya qarasa. A gurguje ya shirya cikin Wani baqin Wandon Jeans da Farar Long sleeve shirt da aka rubuta 'I'm all yours' a jiki saboda garin akwai sanyi sanyi anyi ruwa da safe. Tsaf ya feshe jikinsa da turarukansa masu qamshin gaske, ya gyara gashin kansa da Gemu shida kansa yasan yayi kyau ya fito kamar wani qaramin saurayi ba zaka ganshi kace yana da shekaru Talatin da takwas a duniya ba. Yana cikin daura Agogo Umaimah ta shigo dakin da sallama ya kalleta ganinta cikin shirin fita Ta saka Baqar Abaya tayi rolling da mayafinta ga qaramar Jaka da waya a hannunta. Kallonta yake harta qaraso gabansa yace "Kinyi kyau, se ina haka kuma?" Umaimah da wani hadarin kishi ke haduwa a zuciyarta tayi qarfin halin cewa "Kaima kayi kyau, amma dai babu mata a gurin da zakaje ko?" "No haba dai kema kinsani ai, iya mune babu mata kuma badan kin matsa bama ba zanje ba ni" ya fada yana janyota jikinsa ya rungumeta ta bata saboda cikin jikinta. "Zakaci abu ta kazan ubanka ne" Umaimah ta raya a ranta tana kallo ya daga wayarsa yayi musu hoto yana ta doka uban murmushi ita dai fuska babu yabo babu fallasa ta kalle shi tace "Na kira me kitson wai ba zata samu zuwa ba ko zaka saukeni a Salon idan yaso in kun gama se ka biyo ka daukeni" "Ok, babu damuwa muje yama fi sauqi dan ni daman banaso ayi kitso a gida duk gashi ya bata ko ina kayi ta tsintarshi a abinci" ya bata amsa yana yin gaba ta bishi a baya. Dakinta ta koma ta dakko Jakar data zuba kayan kitson, a palour qasa ta tarar dashi yana waya yana hangota ya kashe ya qarasa inda take ya riqe mata hannu Umaimah dai murmushi kawai tayi masa ita kadai tasan me take shiryawa a ranta. Seda suka shiga bangaren Hajiya suka gaidata, basu jima ba suka kama hanya suna tafe yana mata hira ita dai amsa biyu take bashi Eh ko Aa dan gaba daya hankalinta yayi gaba. A wani guri da bata san me akeyi ba ya tsaya yace mata minti biyu yana zuwa, wayarta tayi saurin dauka bayan ya fita ta shiga kiran Harun, wani yaro ne dan unguwarsu yana jan Adaidaita Sahu yawanci idan zata fita bada mota ba shi take kira ya kaita ko ya dakkota daga inda zataje. A taqaice tace zata turo masa da Address yanzun, idan yana kusa da gurin kuma ze iya qarasawa a wasa da minti goma yayi mata Reply kawai karya kirata. Address din Salon din da zataje ta tura masa, yana gani yace mata ai yana ma kusa da gurin yanzu ya ajiye customer ya tafi se tayi saurin kiransa tace ya koma ya jirata gata nan zuwa daidai sannan Khalil ya dawo motar ya bude Sit din baya ya ajiye babbar Ledar daya taho da ita ya shiga mazaunin sa ya dora mata wata qarama a jiki yana cewa "Anwar matsala ne, wai Icecream zasu sha kamar wasu mata dan Allah, ni banma san gurin nan abinda suke siyarwa ba kenan se yau, bari zamu samu lokaci muzo da su Bibi bakiga ciki ba yayi kyau sosai" "Allah ya kaimu" kawai ta iya cewa ta sauke ledar daya dora mata a qasa, har suka isa Salon din bata sake magana ba shima ya kama kansa ganin kamar ta fusata kome aka mata oho. Dubu goma ya zaro a Aljihunsa ya bata, ta karba ba tareda tace komai ba dan in ta bude baki tsaf zata rusa shirinta ta bude murfin motar ta fice ba tareda ta dauki ledar Icecream din ba ta shige gurin. Khalil na tsaye har seda yaga ta shiga an rufe qofar, seda ya qara minti biyar a tsaye haka nan yakeji gabansa na faduwa ya dai daure ya tayar da mota dan yana jin wayarsa dake aljihu se vibrating takeyi yasan kuma Zahra ce take kira. Yana Juya kan motar Umaimah dake tsaye tuntuni ta fito sanye da dogon Hijabi har qasa ta dora Niqab akai,tsayuwar da yayi ya bata lokaci tayi mata amfani dan ta samu ta shirya duda daman tana shiga ta kira Harun tace ya saka mata ido akan motar Khalil din, idan ma ya tafi ya bishi zasuyi waya duk inda suka nufa zata biyo su. Da sauri ta shige Napep din tace yabi bayansa. A sannu a sannu Harun ke binsa ta yanda baze taba gane cewar wani na biye dashi ba har suka isa unguwar YanKaba ya karya kwanar wani layi data ga an rubuta 'Dr Sabitu Bashir Street' a jikin wani dan Allo take cikakken sunan Zahran data gani a truecaller ya dawo mata. A farkon Layin tace ya tsaya, ta sauka ta taka da qafa ta shiga a qofar wani katafaren gida ta hango motar Khalil din a ajiye taci gaba da tafiya harta wuce gidan Get din yana kulle dan haka bata ga komi ba ta wuce qarshen layin inda ta hango Hasumiya da alama Masallacine a gurin. A qofar masallacin ta zauna, mutum biyu ta hango a ciki suna karatu ta zauna shiru gaba daya kwakwalwarta ma ta tsaya cak ta dena aiki. Tunani takeyi ta shiga gidan ne suyi aran gama taji abinda ze gaya mata ko kuwa ta jira ya gama abinda yakeyi ya tafi kafin ta shiga taci uwar yarinyar? Tayi zurfi a tunani Samarin dake karatu a masallaci suka fito, daya ya kalleta yace "Malama lafiya kuwa tun dazu kike zaune anan?" Niqab din fuskarta ta daga dan kar suyi mata zargin rashin gaskiya, wani gida data gota taga kwado a Get din ta nuna musu tace "Can gidan nazo kuma nayi rashin sa'a basa nan shine na zauna nake hutawa anan" "Ayya halan bakuyi waya ba, ai bana jin sunyi cikakkiyar awa da tafiya garinsu ma sannu kuma da alama daga nesa kike?" Wanda ya fara mata maganar ya sake fada da ganinsa yana da surutu, se Umaimah ta yamutsa fuska kamar gaske tace "Kash wallahi ban kiraba dake babu waya a hannuna kuma daga Kura nake" "Tab sannu gashi kin daki gurbi, seki daure ki tashi ga magriba ta kawo kai yanzu za'a fara shigowa masallaci" dayan da beyi magana ba ya fada me surutun na shirin cewa wani abu yajashi suka tafi. Umaimah ta rakasu da ido daidai nan taga an bude Get din gidan su Zahra ai bata san sanda ta miqe tsaye ba ta nufi gurin. Khalil ne ya fito wata zuqeqiyar yarinya da a halitta bazata gwada mata komai ba ta biyo bayansa fuskarsu washe suna dariya daga inda take tana jin yarinyar na cewa "Amma Dear naji dadin zuwanka, harfa su Sury sunyi fushi zasu tafi na ringa lallabasu kaga yanzu ai haka yafi kunga juna kun gaisa ba se lokacin biki yazo ba". Khalil dake kallonta yana murmushi like an idiot yace "Ai kuwa dai nima naji dadin haduwa dasu sosai shikenan dai yanzu qorafi ya qare ko?" Ya fada yana aika mata da wani kallo da Umaimah ta zata ita kadai yake yiwa irinsa. "Baiwar Allah yi a hankali fa karki fadi" taji muryar saurayin dazu ya fada se a sannan ta lura da a guri daya take a tsaye tana kallonsu Khalil din jiri ke neman kadata ta dafe bangon kusada ita shine yake mata magana. Kai ta daga masa ta shiga jan qafarta dakyar numfashinta na mata wuyar shaqa. Khalil da Zahra suka bita da kallo, qirjinsa ya buga da qarfin gaske sanda suka hada ido da matar kafin ta dauke kai taci gaba da tafiya tana cira qafarta dakyar. Kamar idon Umaimah haka ya gani haka tafiyarta da yanayin jikin sunyi masa kama da nata amma me ze kawota nan? Kuma ya tabbata idan itace tabbas Allah kadai yasan abinda ze faru a gurin. Muryar Zahra yaji tana cewa samarin "Kai Aliyu wacece wannan din da kuka bari ta shigowa mutane layi da magriban nan da wannan shigar, kunsan dai yanda criminals sukayi yawa ko?" Se wanda ta kira da Aliyu ya bata amsa da cewa "Gidan Barrister tazo kuma basa nan shine ta zauna gurin masallaci ta huta" "Dear kaima baka yarda da ita ba ko?" Zahra dataga ya zubawa inda Umaiman tabi ido ta fada se yayi firgigit ya kalleta yana cewa "An Bari naje na bar Madam a Salon tana jirana zan dauketa". Fuska ta bata bata ce masa komai ba yayi mata murmushi ya shiga motarsa yana daga mata hannu, hannun itama ta daga masa daga nan yaja ya tafi har sannan zuciyarsa na masa wasi wasi akan wacce ya gani din. Kiran daya shigo wayarsa ya sakashi dubawa, Umaimah ce, muryarta babu yabo babu fallasa tace "Base ka biyo daukana ba na wuce gida ban samu kitson ba" Ajiyar zuciya ya sauke jin cewar ta tafi gida kenab dagaske ba itan bace, lallai tsoron da yakewa Umaimah har ta kai ta fara masa gizo. UMAIMAH Dakyar ta iya maida kanta imda Harun yake jiranta, ta zauna a Napep din tana jan numfashi jikinta na wata irin rawa. Harun ya kalleta yace "Anty lafiya kuwa?" "Maidani gida" ta fada dakyar kafin ta dora kanta akan qarfen adaidaitan tayi shiru dan ta kasa tunanin komai. Khalil ya iya yi mata qarya ya taho gurin wata ko? Wani tunani ne ya fado mata nan ta shiga jan numfashi tana fesarwa har seda taji ta samu nutsuwa kadan kafin ta dauki wayarta ta kirashi ta gaya masa ta wuce gida, gara taje tashirya yanda zataci ubansa a ruwan sanyi. Se yayi danasanin munafuntarta yayi mata qarya wallahi kafin ta juya kan ita qaramar Shegiyar. Wato saboda tsabar ya shirya ci mata mutunchi seda ya samo daidai da ita dan ita da kanta ta yarda ba zata gwadawa Zahran komai ba a halitta sema dai ita ta fita dan ba zaka hada jikin budurwa da Wadda ta haihu har biyu ba. Bata san ko nawa ta zaro ta bawa Harun ba ta shige gida kai tsaye kan gadon dakinta ta fada wasu hawaye masu dumi suka shiga tsere akan fuskarta idan ta tuna yanda Khalil yake kallon yarinyar yana mata murmushi se taji kamar ta shaqe kanta saboda baqin ciki. Wai meya shiga kanta daya hana ta tsaya tayi musu tijara a gurin? Yanzu meye amfanin dawowar da tayi tazo tana kuka anan? Wani ihu ta kwara kafin ta miqe ta watso da duk tarin kwalabe da robobin dake kan Mirror dinta, tamkar farin shigan hauka haka ta shiga dukan duk abinda hannu ta ya kai kafin wani lokaci tayi wa dakin rotse hannayenta bada zubar jini babu abinda sukeyi. A haka Khalil ya dawo gidan, tunda yayi arangama da Hijab da Niqab a kan kujerar palour yaji lakar jikinsa na tsiyayewa, kasa gaba yayi balle baya qirjinsa ya ringa bugawa a sittin wato dai ta tabbata Umaimah ce, kenan bin bayansa tayi, tayi badda kama dan taga inda zeje me yasa sam tunanin zata iya aikata hakan be zo masa ba tun Sanda tace zata bishi ya kamata ace ya zargi wani abu kai tun farko ma shirun da tayi masa yasan ai ba haka kawai ba dole akwai abinda take shiryawa, bashida mafita a yanzu illah yayi mata bayanin komai ko Allah ze sa ta fahimce shi dukda yasan abune me wahala amma ze gwada. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 53 Kamar wani mara gaskiya haka ya tura qofar dakinta da sallama, Umaimah dake zaune a qasa ta dago ta kalleshi da jajayen idanunta dan ba qaramin kuka tasha ba. Yawu ya hade ya shiga qarewa dakin data sauyawa kamanni kallo, besan da me tayi aikin ba amma duk wani abi da yake na glass a dakin ta fasashi kuma tana zaune a cikin gilasan kanta yayi buzu buzu kamar wata hauka sabon kamu. A hankali ya shiga takawa zuwa inda take yana kuma qara baza idonsa dan ya tabbatar da babu wani makami a kusa sa da ita da zata iya yi masa lahani dashi a haka har ya isa gabanta ya durqusa dan tunda tayi masa kallo daya ta maida kanta qasa tana jan Ajiyar zuciya. "Umaimah" ya kira sunanta a tausashe bata amsaba kuma bata dago ta kalle shi ba dan haka ya qara matsarta yana qoqarin kama hannunta daya ga jini ya bata yana cewa "Umaimah please..." "Karka kuskura ka tabani Khalil idan ba haka ba wallahi sena baka mamaki" ta fada tana fizge hannunta tareda tashi tsaye sam ko nauyin cikin jikinta bataji, miqewa yayi shima da saurin ganin tana qoqarin taka kwalaben dake zube a qasa dan ko shi da yake sanye da takalmi da taka tsantsan ya tsalleke su, ruqota yayi ta fizge ta tafi baya saura qiris ta fadi ya sake tareta be bi takan dukan datake kai masa ba ya dagata cak suka fice daga dakin "Ka ajiye ni Khalil ka ajiyeni dan kutumar ubanka" ta fada cikin wani irin sauti ai kafin ta kai qarshe ma ya direta a qasa yana bin bakinta data qunduma masa Ashar dashi da kallo. "Ni kike zagi Umaimah?" Ya fada cikin mamaki yana nuna kansa, idon ta cikin nasa tace "Na zageka maqaryaci maci Amana, taron da zakuyi da su Anwar din kenan ka tafi gidan su Budurwa a Yankaba, saboda ka mayar dani bansan abinda nakeyi ka dauka akwai wata qarya da zakayi mun ban gane ba? Wallahi kar nake kallonka Khalil, kuma tun ranar dana fahimci kana cin Amanata na dana maka tarko, duk wani motsinka akan ido na kakeyinsa ban kuma tabbatar daka cika qasurgumin maqaryaci ba se yau da har ka iya tsara zance ba tareda ka koji tsoron Allah ba ka yaudareni". Kallonta kawai yakeyi har ta kai aya, jikinsa ya qarasa mutuwa, yanzu shi Umaimah ta zaga haka kai tsaye ba tareda shayin komai ba? Lallai abinta ci gaba yakeyi ba kuwa ze dauka ba, baze taba zama sakarai a gabansa mace ta zage shi ba dan haka nan take shima ya hade fuska yana kallonta yace "Eh naje gurin budurwa se akayi yaya? Ajiyarki aka bani da zaki ringa bibiyar rayuwata ki daka mun ido ko kuwa? Sannan da izinin wa kika je, ba Salon na ajiyeki ba amma saboda baki dauki aure a bakin komai ba kina ganin zaki iya duk abinda kika ga dama shiyasa kika bini ai, kuma gashi nan a garin bin diddiginki ki tono abinda ze hana ki zaman lafiya dan da banyi niyyar sanar dake ba se komai ya kammala saboda kar hankalinki ya tashi amma yanzu tunda kin sani shikenan, auranta zanyi ita yarinyar da kika ganmu tare kuma baze dauki lokaci ba dan dakyar za'a ci wata daya nan gaba" ya fada da wani kalar expression akan fuskarsa. Umaimah da tayi kasaqe tana kallon sa lokaci daya tayi kansa tana cewa "Qarya kakeyi wallahi Khalil, baka isa kayi aure ba kai nawa ne ni kadai babu macen data isa ta shigo rayuwar mu. Idan kuma ka shirya ja mata bala'i shikenan karka manta da abinda ya samu Hadiza wallahi se nayi mata ninkinsa se ta zama mujiya a cikin mutane ba ita ba har iyayenta se sun zama abin tausayi". Tsaki yayi ya wuce dakinsa ransa yana bala'in zafi, Ya rasa Umaimah wace irin mutum ce da idan ranta ya baci hankalinta yake gushewa. Ganin ta sauka qasa da sauri ya saka shi juyawa yabi bayanta amma kafin ya tarar da ita har ta fice daga palour seya qara sauri yana kiran sunanta ganin a yanayin da take kuma ta fita a hakan Umaimah kuwa ganin ya biyo ta ma se ta saka gudu, a parlour Hajiya ta zubr tana wani irin kuka ga numfashinta na qoqarin daukewa. Hajiya data idar da sallar Isha tana zaune a saqon kujera ta miqe a gigice tayi kanta tana tambayar lafiya? Koda yake babu alamarta a tattareda ita. Yanda take a hargitse ga jikinta duk jini ya bada amsar abinda yake faruwa. "Khalil ne" ta fada cikin jan numfashi, Hajiya ta dafe qirji tace "Dukanki yayi? Shaye shaye ya fara kome?" Daidai nan ya shigo shima kamar an jefo shi Hajiya ta miqe da sauri tana cewa "Me kayiwa yar mutane Khalil, me tayi da zaka aikata mata wannan mugun abun?" "Wallahi Hajiya babu abinda nayi mata nima dawowa nayi na tarar ta fasa komai na dakinta ni ban mata komai ba" ya fada da sauri ganin Hajiya na neman laqaba masa abinda beyi ba. Umaimah dake kwance lakadan saboda wani azababben ciwo da mararta ta dauka ta bude baki dakyar tace "Qarya yakeyi Hajiya ya san me yayi mun, ki gaya masa ko ya fasa abinda yayi niyya ko na kashe kaina wallahi". "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Umaimah wace irin magana kike haka kamar ba musulma ba? Ki kashe kanki a saboda me saboda damuwar duniya? Kar na sake ji, kai kuma kamata mu tafi Asibiti kalli, innalillahi wainna ilaihi raji'un" Hajiyan ta sake fada tana zare ido ganin jinin na bin qafafun Umaiman. A rikice yayi kanta ya dagota, hankalinta ya fara nisa daga jikinta shiyasa ta gagara hanashi bata san yanda akayi ba se farkawa tayi ta ganta a Gadon Asibiti gefenta Khalil na zaune ya dora kansa akan gadon da take kwance. Abinda ya faru ne suka fara dawo mata, murmushin da yakeyiwa Zahra ta hango bata san sanda ta saka hannunta da ba'a daura mata ruwa ba ta kwada masa mari a qeya. A gigice Khalil ya farka yana zare ido, tun daren jiya da aka kawo ta be runtsa ba se yanzu da safe bayan su Hajiya sun tafi gida aka barshi shi kadai koda yake yace ze zauna da ita. Kama hannunta yayi ganin tana qoqarin fizge qarin ruwan da aka saka mata ta juyo a fusace tace masa "Ka sake ni karka sake tabani Khalil" "Ki nutsu Umaimah ba'aso kiyi wani dogon motsi dan Allah saboda jijjiga jikinki da kikayi jiya seda akayi miki daurin bakin Mahaifa saboda babyn tana nema ta fito lokacinta baiyi ba ki koma ki kwanta" Khalil ya fada cikin muryarsa da bata fita dakyau saboda bacci da gajiya ga ciwon kai. Bata ko saurara na ta zare allurar, jini ya fara zuba daga hannun ko a jikinta ta dire qafarta qasa tana yunqurawa zafi da jiri suka ziyarci kwakwalwarta lokaci daya ta koma ta kwanta tana kwala ihu dan ji tayi kamar ganinya ya dauke saboda jiri ga wani ciwon Mara daya sake taso mata. Nurse ce ta shigo dakin, take ta rufe Khalil da fada ta fita da gudu ta kira likita haka suka rufu kanta aka sake maida mata qarin ruwan tareda yi mata allurar bacci data rage radadi saboda yanda take ta faman juye juyen ciwo tana wayyo. Fada likita ya shiga yiwa Khalil, abin ya bashi haushi ya fice daga dakin ya barsu idan dai Umaimah ce gasu gata nan ai su da kansi zasu bada labarin halinta. Gida ya wuce yana zuwa ya tarar da Hajiya cikin shirin sake komawa Asibiti, jiyan bata baro ba seda komai ya daidaita aka bawa Umaiman gado gurin daya na dare kafin Khalifa ya kaita gida ta bar Khalil ya kwana dan yace baza'a kira yan gidansu a cikin daren a tayar musu da hankali ba a musamman Mama bata da lafiya malaria ta kwantar da ita dan haka yace a bari seda safe tukunna a kirasu. "Khalil, ya jikin nata ta farka kuwa?" Hajiya ta tsare shi da tambayoyi. A taqaice ya bata amsa ya wuce ciki dan gaba daya ji yake kamar kansa ze fashe tsabar bacci da ciwon da yake masa. Jin ana binsa a baya ya sakashi dakatawa ya juya, Hajiya ce se ya qarasa shiga parlour ta biyo ciki suka zauna akan kujera tana kallonsa tace "Khalil meya hadaka da Yarinyar nan a wannan yanayin da take ciki zaka bigeta? Yaushe ma ka fara dukan Mace ban sani ba karfa giyar kudi tasa ka sauka daga layin da nasan ka aki Khalil?" Dafe kansa yayi daya sara masa, shikam ya rasa wace irin makauniyar soyayya Hajiya takewa Umaimah da duk abinda ya hado da ita kawai bayanta take bi. Dakyar ya iya bude baki yace "Haba Hajiya ko banida hankali dai ai kinsan bazan daki Umaimah ba, abune ya hadamu kuma taqi ta tsaya nayi mata bayani ta shiga haukanta da ta saba" "Au mahaukaciya ma kake kiranta? Idan ma haukan ne ai a gidanka ta same shi kuma akanka takeyinsa" Hajiya ta fada tana harararsa seya bude baki kawai yana kallonta ya kasa cewa komai, gaskiya kuma son zuciyar Hajiya ya wuce misali, to ko Umaimah ta haifa bashi ba ai iyakarta kenan. Ganin idanma ya mata bayani ba fuskantar sa zatayi ba yasa ya miqe yana cewa "Kishinta ne na banza ya tashi, kuma yarinyar da take haukan akanta ma data kwantar da hankalinta ba auranta zanyi ba" ya haye sama ya bar Hajiyar a zaune tana kallonsa. Ajiyar zuciya ta sauke tareda miqewa, tunda take da Khalil baya iya ko kallon cikin idonta ya gaya mata magana sedai ya sadda kai amma yau shine ya tashi ya barta a zaune lallai dole akwai wani abu sata kasa fahimta anan. Miqewa tayi a sanyaye ta wuce inda Khalifa yake jiranta. Sun tarar da Anty, Nuratu se Anty Laure tareda ita wanda Khalil ya kira ya sanar dasu. Umaiman na barci har sannan tambayar Hajiya suke abinda ya sameta a taqaice tace musu itama bata sani ba, ta shigo gurinta a gigice shikenan kuma jini ya balle mata kuma shima Mijin yace haka yazo ya tarar da ita a qoqarin yayi calming nata ne ta fita da gudu zuwa gurin Hajiyar. "Ko gamo tayi? Amma haka kawai ace yarinya ta fito da gudu ai abin dubawa ne" Anty Laure ta fada tana hararar Hajiya qasa qasa dan tunda sukazo ta tarar da Umaiman ita kadai ranta ya baci. Ya za'ayi su kawo yarinya Asibiti subarta ita kadai tun jiyan ai se suyi waya gidansu a zo idan su bazasu iya zama da ita ba. "Uhm" kawai Nuratu tace dan Maman Asad ta gaya mata yanda sukayi da Umaiman ta kuma tabbatar baze wuce akan zancen bane take tashin hankali, ai shikenan, idan ta kashe kanta a banza kowa ya huta. Se bayan Azahar ta sake farkawa, kuka ta ringayi saboda radadin da hannayenta data yanke da kwalabe suke mata saboda Allurar da akayi mata ta saketa ta kuma ida dawowa hayyacinta gaba daya. Seda ta kwana biyu a Asibiti Anty Laure ce tareda ita take jinyarta kafin aka sallameta ta koma gida da gargadin karta kuskura ta ringa abinda ze jigata jikinta. Da farko ma gida Anty Laurentace ko zasu wuce da ita Mama tace Aa ta barta ta koma dakinta idan yaso ta bita ta qara mata kwana biyu kafin a samo mata me aiki tunda iya hidimar aikin gida ce yara dabdalarsu duk a gurin Hajiya sukeyi bata da matsala dasu. haka kuwa akayi suka wuce gidan da Anty Laure washe gari se ga me aiki Nuratu ta kai mata yar uwar me aikintace tana jin dadin zama da ita sosai shiyasa tayi mata magana idan da wata tace akwai yar uwarta babbace a qalla zatayi shekara Arba'in Mininta ne ya rasu amma bata taba haihuwa ba daman tun tana Asibiti sukayi maganar ba'a yi shawara da ita ba dan sun san ma ba zata yarda ba se ganinta kawai tayi. A cikin Bedrooms din qasa Umaiman ta koma daya ita da Anty Lauren saboda hawa da saukan baze yuwu ba saboda yanayin jikinta ga dakinta data rigada ta sauyawa Kamanni Khalil yasa an fitar da Furnitures din dukka dan ta lalata su, rabi Glass ne kuma ta rusa shi dole sedai a chanza wasu. Sanda Anty laure ta shiga dakin debo mata kayayyakinta riqe baki kawai tayi cikin mamaki ganin se Gado kawai ba komai a dakin kayan sawarwa ma an juye su akan gadon haka ta tsinto abinda zata iya ta sauka qasa tana wassafa abinda ya faru a gidan. Daman tun tana Asibiti ta lura sam da wata a qasa tsakaninta da Mijin nata. Idan yazo baya wani dadewa yake tafiya kuma ko magana bata hadasu sedai su ya musu yame jiki ya qara gaba haka tunda suka dawo yau kwana hudu safe da yamma ze shiga ya gaidata ya duba Umaiman amma ko kallon arziqi taga baya hadasu. Ta qyaleta ne batayi mata magana ba taga iya gudun ruwansu amma har sukayi sati babu abinda ya canza Khalil dinma baya nan ya tafi Zamfara daze tafi ma ita yayiwa sallama ya bata kudi ya kuma gaya mata idan buqatar komawa Asibiti ta tashi Khalifa yana nan. Hajiya ma kullum safe da yamma aeta shiga ta dubata su dan taba hira da Anty Lauren. Kwana uku tafiyar da yayi ta dauke shi ya dawo cike da farin ciki saboda samun kiran da yayi daga Dr Sabitu akan gobe yaje da sauran takaddun kwangila ya saka masa hannu za'a tura masa da kudi ya fara aiki. Dawowar safe yayi, cikinfara'a ya shiga gidan, suka gaisa da sabuwar me aikin me suna Ruqayya ya tambayeta Anty Laure tace taje gida wai surukarta ce bata lafiya Maman Mijinta marigayi kuma jikin yayi tsanani shine taje dubata a Asibiti amma bazata jima ba. Dakin da Umaimah ta koma ya tura a hankali ya shiga da sallama. Tana zaune ta jingina bayanta da Gado da waya a kunnenta tana magana ta dago tayi masa kallo daya ta mayar dakai taci gana da maganarta. Fuskarsa har sannan dauke da murmushi ya zauna a gefenta saboda tsokana harda kai hannu ya shafi gefen fuskarta. Yayi missing dinta sosai amma nisantar ta da yayi shine maslaha hat zuwa sanda ze kammala abinda yake gabansa gashi kiwa komai yazo qarshe. Yafi minti goma a zaune yana jiranta amma taqi kashe wayar, yi tayi tamkar ma bata san da wanzuwarsa a dakin ba seda ya gaji ya saka hannu ya zare wayar daga kunnenta ta juyo a fusace tace "Malam meye haka? Kana da matsala dani ne da zaka shiga rayuwata ko yaya?" "Yi haquri maida wuqar naga kamar baki san da zamana bane shiyasa ki bari mu gaisa se kici gaba da wayar taki ko" ya fada yana murmushi se kuwa ta galla masa harara ta miqe tana jan qwafa, miqewar yayi shima yana kama kafadunta ta baya ya rungumeta yana cewa "Wai fushin ne har yanzu baki dena ba?" "Wallahi Khalil ka fita a sabgata kafin nayi maka rashin mutunchi, badai aure kace zakayi ba? To mu zuba nidakai a gidan nan shege ka fasa" Umaimah ta fada a fusace tana fuzge jikinta se yayi saurin sakinta yana cewa "Easy Ma, duk da kin kwantar da hankalinki zancen auran nan fa wasa ne. Da kin haqura dakaina zanyi miki bayanin komai amma kima shiga tashin hankali yanzu kalli abinda kika jawa kanki" Kallonsa tayi da son jin qarin bayanin wasan da yace maganar auran. Khalil ya daga mata gira kafin yace "Yes, wasa ne, idan kina so kiji komai kizo muje dakina nayi wanka na huta zan warware miki yanda abun yake". Numfashi ta sauke har sannan tana kallonsa, idan kuma wasa yake so ya qarayi da hankalinta fa? Zuciyarta ta raya mata. "Muje" ya katse mata tunanin, se kuwa ta bishi kamar wata sokuwa seda sukaje gaban matakalar ta tsaya tana kallonsa tace "Likita yace karna hau bene" "Ohk" ya sakw fada kafin ya shiga nade hannun rigar jikinsa. Cak ya dagata cikin takatsantsan ya fara hawa saman da ita be direta ko ina ba se kan gadon dakinsa ya ajiyeta tareda saka mata pillow a bayanta yana mata murmushi ya wuce bandaki. Tana jiyo qarar saukar ruwa alamar wanka yake ta dannawa Safina kira. "Ki tsaya kiji abinda zw fada amma dukda haka bazamu fasa wannan plan dinba dan kin ganni ma na kusa layin nasu amma bari na shiga gidan Hadiza Sani na jira muji abinda zece miki" Safinan ta fada bayan data gaya mata yanda sukayi da Khalil. Sun gama tsarawa daman Safina zataje gidansu Zahran tayi tijara ta yanda da kansu zasu fasa bashi auran yar tasu tunda ita jikinta baze bari ta fita ba amma zata dakata taji rainin wayom da ze mata yanzu kafin su aiwatar da nufinsu. Da kansa ya sauka qasa ya soyo kwai ya hada shayi kafin ya dawo dakin Umaimah data qagu da jira se tsaki takeyi. Dole ta sakata zama inuwa daya dashi dan bala'in haushinsa take ji. Da yayi mata tayin shayin ma harara ta maka masa yayi dariya ya shanye abinsa seda ya gama tas kafin ya dauko Laptop dinsa ya hawo kan gadon da take yana murmushi ya bude. Wasu hotuna ya shiga bude mata, Taswirar gini ce kamar Kasuwa kamar kuma gidaje ita dai bata wani gane ba saboda yanayin ginin anyi shi rututu gasu nan in ma gidajene sunfi dari seta dago tana cewa "Nifa ba wannan tasa na zauna jiranka ba tam" ta qarasa tana zumbura baki. Dariya yayi ya koma ta bayanta ya raba qafarsa ya zamana tana tsakiyarsa. Kwantar da fuskarsa yayi a gadon bayanta yace "My troublesome lover" kafin ya kama hannunta biyu cikin nashi ya shiga labarta mata yanda ya hadu da Zahra har zuwa yarjejeniyar da sukayi da Mahaifinta zuwa kiran da yayi masa na yau ya qarashe da cewa "Kinga daya saka mun hannu kudi sun shigo shikenan babu ni babu yarsa, daman na yarda ne saboda na samu Kwangilar tunda bayayin abu dan Allah kinga ai idanna yaudare shi nima banyi laifi ba dan Yarsa ba type dina bace kuma ko aure zanyi babu abinda zanyi da sangartacviyar yarinya irinta. Sam bata da Class taya ya ma Mace daga ganin Namiji kawai kice kina sonsa sanna kinga irin rawar jiki da nacin da take mun kuwa? Nooo na raina ajinta bazan iya auranta ba". Gaba daya surutun da yakewa Umaimah tamkar suna shiga ta kunnen dama ne suna bullewa ta hagu, banda ma ya raina mata wayo wato saboda yana neman abu a gurin Mahaifinta yasa ya yarda ze aureta yanzu so yake ta yarda cewar daya samu biyan buqata ze gujeta kenan shi Mahaifin nata sakaran inane da ze yarda haka ta faru? Ko kuwa ita yake so ya mayar sakarya ta yarda da qaryarsa sedai kawai taji ana matsa zata shigo da Amarya ko? To zatayi maganinsu daga shi har Uban Zahran, Kwangila ce ta hada kuna zata raba kowa ya kama gabansa yaje can ya nemawa yarsa data qi auruwa yake neman kai da ita wani Mijin badai Khalil ba. Janye jikinta tayi daga ruqon da yayi mata Khalil ya kallonta yace "Are you now happy? Kin yarda ba cin Amanarki nayi ba ko?" Murmushin da ita kadai tasan ma'anarsa tayi kafin tace "Hajiya tace zatayi mun Danwake yu wa nakeji ko zaka duba idan an gama" "Sure, kinsan kuwa ban shiga gurinta ba gaba daya hankalina yana kan nazo na wanke kaina a gurin Babbar Hajiyata, bari nayi maza na karbo miki kici nima kizo ki bani nawa danwaken kar ma kice mun Dr ya hana" ya qarasa yana miqewa tareda kashe mata ido daya ya fice daga dakin. Ta balcony dake saman taga fitarsa daga part dinsu kafin ta koma dakinsa tana tafiya a hankali dan idan tayi motsi da yawa har sannan Marar ta na mata ciwo. Wayarsa daya manta akan Mirror ta dauka. Bata bata lokaci ba gurin nemo number Dr Sabitu ba tareda tunanin komai ba ta danna masa kira ta wayar Khalil din. "Aa, My son badai har ka iso ba? Kasan itama mutuniyar ina gaya mata zaka zo gata can se fushi take ashe baka sanar mata yau zaka dawo ba" Dr Sabitu ya fada cikin maganarsa me sauri, Umaimah taja iska ta jiqa hunhunta kafintace "Saboda uwarsa ce ita ko yaya da ze gaya mata ze dawo? Kai kuma tsohon banza me neman kai da yarsa wato ta gama yawon ta zubar dinta ta kasa auruwa shine kake so ka laqabawa Mijina ko to baka isa ba wallahi Mijina nawane kuma yafi qarfin wannan kucakar yar taka. Ka duba a gaba ka nemo mata me rangwamen hankali irin ta ka hadasu badai Khalil ba, kwangilar da kayi masa talala da ita ka riqe abarka ka cinye ka nemo mata Miji cikin abokanan ka masu budurwar zuciya sune zasuyi daidai da ita su rufa mata asiri kuma wallahi kaja mata kunne idan ta sake kiran Mijina a waya sena ci uwar ubanta, har cikin gidanka zanzo na zaneta wallahi" Taja dogon tsaki kafin ta kashe wayar ta juya zata fita kenan idonta ya sauka akan Laptop dinsa dake ajiye. Komawa tayi ta dauka, computer ta karanta dan haka bata da matsala da ita shiga tayi ta goge hotunan daya nunamata dazuna aikin da duk wasu Documents da suka shafeshi folder gaba dayanta ta goge, takaddun dake cikin jakar laptop din ta ciro ta duba, paper work nr na aikin ba bata lokaci ta rabasu biyu dukda ta fahimci sune ainihin Original takaddun, yagawar bata mata ba ta shige toilet ta watsasu a Sink ta saki ruwa seda ta tabbatar da sun jiqe jagab kafin ta ja qofar ta rufe tayi ficewarta. A hankali ta ringa sauka daga saman harta isa qasa kai tsaye ta shige daki bayan ta kwalawa Rukayya kira tace mata zatayi bacci kar a dameta yan zuwa dubiya ta shige dakin ta murza muqulli seda ta kwanta akan gadon kafin gabanta ya fadi, dana sanin taba masa Laptop yazo mata data tuna wannan din data goge itace kamar backup dinsa na komai. Yanada wata da yake fita office da ita banda Desktop da yake aiki da ita acan wanann yana aje duk wasu muhimman abubuwa da yake gudun rasawa shi yasa da wuya yayi amfani da ita se buqatar haka ta taso kuma daya gama ze maida ita ma'ajiya yana bala'in kaffa kaffa da ita yanzu ya zatayi "Aikin gama ya gama se ki jira hukunci kawai" zuciyarta ta ayyana mata dan haka taja bargo ta yi luf duk jikinta yayi sanyi dan ita da kanta ta tabbatar da yau ta tsallake limit. KHALIL A kitchen ya tarar da Hajiya tana jefawa Umaimah dan waken suka gaisa tana tambayarsa hanya seda suka dantaba hira kafin ya gaya mata abinda ya zo karba. "Daman wanda ya shiga fadanka da Umaimah shine da jin kunya, gashinan na kusa qarasawa kaje idan an gama za'a kawo mata" Hajiya ta fada tana kama baki seya sosa kai yana murmushi yace "Bari dai na jira Hajiya kinsan lallabata nake karna koma babu shi sabon balli ya tashi" sukayi dariya gaba daya. Seda Hajiya ta tsame dan wake ta zuba mata a kwano tareda sauran kayan hadin da aka yayyanka. A try ta dora masa da dan kwanon mai dana yaji ya dauka ya fita. A palour ya ajiye ya shiga dakin nasa yana kiran sunanta. Ganin bata ciki ya sakashi tunanin ko bandaki ta shiga dan haka ya qarasa jin qofa yana cewa "Ga danwaken an kawo Babe" ya juya gurin wayarsa dake qara alamar kira ya shigo. Anwar ne ya daga yana cewa "Kana shiga rayuwata Anwar kiran me kuma kake mun yanzu bayan na gaya masa bazan zo office ba?" "Khalil what have you done? Kana right senses dinka kuwa yanzu ka janyo mana Asara haba Khalil" Anwar ya fada cikin tashin hankali. Cikin rashin fahimtarsa Khalil yace "Heye hey yi a hankali mana, me kake magana akai sam bangane ba me nayi wace Asara na janyo mana?" "Dr Sabitu be kiraka ba? For Goodness sake taya ma zaka bari wayarka ta shiga hannunta? Yanzu ba iya wannan contract din mukayi loosing ba i don't think we are going to be able to get any government contract again dan wallahi Dr Sabitu ya wuce yanda kake tunani ko da yake you can tell, we are doomed Khalil Matarka ta gama damu" Anwar ya sake fada tamkar ze fashe masa da kuka. Qirjin Khalil ya buga dum jin ya ambaci matarsa me Umaimah kuma tayi? Saurin zare wayar yayi daga kunnensa jin Anwar ya kashe se sannan yaga tarin missed calls daga Zahra sena Baban nata guda daya. Qofar bandakin ya shiga bugawa yana kiran sunan Umaimah jin shiru bata amsa ba ya saka ya bude, wayam babu kowa a ciki, takaddu ya hango cikin sink cikin sauri ya debosu tuni sun narke yana dagawa suna qarasa ratattakewa kamar wanda ya warke daga makanta haka ya shiga gwala ido yana kallonsu dan ya tabbatar da abinda idonsa yake gani, "kan bala'i" ya fada a fili kafin ya watsar da takaddun ya juya da sauri ya shiga hada matakala biyu biyu saboda sauri. Kamar iska haka ya nufi dakin da take, Ruqayya data ga yanda ya sakko ta miqe kanta a qasa tana cewa "Yallabai Uwar dakina tace zatayi bacci kar a tashe ta" "Get lost my friend" ya fada cikin tsawa jijiyoyin kansa har tashi sukayi saboda bacin rai nan ya shiga dukan qofar dakin da take cikin saboda ya murda yajita a kulle, Umaimah dake kwance akan gado lamo dan ba bacci takeyi ba tunanin yanda zasu kwasheta da Khalil take. Ba tayi nadamar kiran Dr Sabitu ba illah na goge masa Laptop shi ya dameta. Data sani bata taba ba danta tabbatar ita zagin datayiwa Baban Zahra ya isa ya hana shi auranya kuma kwace kwangilar. Yanda yake dukan qofar kamar ze ballata ya bata tsoro, wayar Hajiya ta shiga kira tana dagawa ta saka mata kuka tana cewa "Hajiya kizo Khalil ne" bata jira amsarta ba ta kashe wayar ta wullata kan gado ta shiga yarfe hannu cike da tsoro. Khalil kuwa wayarsa da ake kira ya sakashi dakatawa da bugun qofar,bema san waye ya kira ba ya daga muryar Dr Sabitu ta daki kunnensa cikin tsananin bacin rai yace "Ka tabbata kafin qarfe sha biyun rana ka kawomun da duk wasu takaddu da suka shafi kwangilar nan idan ba haka seka fuskanci wulaqancin Khalil, badai ni ka bawa Matarka waya ta zageni ba zaka san cewar ba'a wasa da Dr Sabitu Bashir" yana gama fadar haka ya kashe kiran. "Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un" ya fada yana dafe kansa, Umaimah ta saka shi a Bala'i ta janyo masa masofa yana zaman zaman wai shi wace irin mata ya aura se kace dangin shaidan. Saman ya koma da sauri ya zazzage jakar ko Allah zero saka ya samu takaddar Da Dr yake da buqata amma babu komai ciki se flash drive daya fado, gefen gadon ya samu ya zauna yana dafe da kansa, yanzu ya zeyi da rayuwarsa? Takaddun kwangilar ta yaga ta jiqasu me ze koma ya gayawa Dr Sabitu bayan bashida masaniyar irin dibar Albarkar da tayi masa a waya? Laptop din ya janyo gabansa ya fadi ganinta a bude bayan yasan ya rufe daze tafi karbo mata danwaken, kai tsaye folder ya nufi budewa ganin babu ita babu alamarta yasa ya shiga Recycle Bin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin yanda zuciya take yunquro masa kamar zeyi amanta. Wallahi yau me raba shi da Umaimah se Allah daya hadasu, duk iskancin da take yi masa yake shanyewa yau ta kaishi bango tunda ta taba masa bangaren aiki seta gane bata da wayo. Kamar wani mahaukacin zaki haka ya sakko daga Saman, Anty Laure ta rafko sallama ta shigo palour suka hada ido da Khalil take tayi baya tana dafe qirji dan harga Allah yanda idonsa ya canza kala badan kamannin fuskarsa ba cewa zatayi Gamo tayi. Qarar faduwar qofa dataji ce ta dawo da ita daga hayyacinta ta dora hannu biyu aka tana kiran "Na shiga uku ni Laure me yake faruwa a gidan nan a cikin Daki kuwa Hajiya da shigowarta kenan Umaimah ta bude mata bayan ta tabbatar Khalil baya qasan yana balla qofar a tare suka fasa ihu saboda razana da ganin yanayinsa. *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.* Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu. *Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari. *Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari. *Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.* *Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda. *Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku. *Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu. *Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500. *Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍* *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 54 Gadan gadan ya nufi Umaimah dake take jin tamkar numfashi ta ze dauke saboda Azabar tsoron yanayin data ga Khalil din a ciki, Hajiya da ita kanta jikinta rawa yake ta shiga tsakiyarsu, cikin muryar da bata taba jinsa da ita ba yace "Hajiya ki matsa, ki matsa karkisa nayi Abinda Allah zeyi fushi dani" "Khalil saurara tsaya Khalil ka tsaya nace maka" Hajiya ta fada a rude tana tokare qirjinsa da hannayenta ganin yana neman zagayeta ya isa ga Umaimah data durqushe a jikin bango tana jiran jin sauakar Aradu "Wallahi Hajiya sena illata yarinyar nan yau sena illata Umaimah" ya fada cikin qaraji kafin Hajiya ta ce wani abu ya isa gaban Umaimah cikin qasa da second biyu ya dagota tsaye da hannu daya kafin ya sharara mata mari da daya hannun ya shaqe mata wuya duk a lokaci daya. Kuka Hajiya ta fashe dashi ta shiga qoqarin kwatarta amma ina Ran Maza ya baci jikinsa rawa yake kamar Mazari ya zurawa Umaiman idanunsa da suka koma Ja yana kallon yanda nata idon suka firfito tana kokawa da Numfashi. "Laure ze kashe ta kira su Sammani" Hajiya ta fada cikin kuka sanda Anty laure ta shigo dakin ta kuwa kwasa da gudu tayi waje tana kururuwar azo a taimakawa Umaiman. Khalil kuwa seda yaji jijiyar wuyan Umaimah daya matse ta dena bugawa kafin ya saketa kamar kayan wanki a qasa ya juya a zuciye ya bar dakin. A palour ya tsaya daidai sanda yan agajin da Anty Laure ta kwaso suka shigo ya watsa musu wani kallo daya sa babu shiri suka juya kamar muna fukai suka bar gurin se ya juya yabi bayansu dan be gamsu da abinda yayi mata ba idan yaci gaba da zama a gidan tabbas ze koma ya qarasata. Tsakanin Hajiya da Anty Laure rasa me rarrashin wani akayi sanda suka kai Umaimah data Suma Asibiti. Hankalinsu be dan kwanta ba seda Likita ya tabbatar musu da tana lafiya sunyi mata Allura dan ta danyi bacci ta samu sauqin firgicin da ta shiga. Se a sannan Anty Laure ta iya kiran Mama tana kuka tace "Malika ashe mahaukaci kuka aurawa Umaimah? To ki taho idan kinada rabo ku gana da yarki dan ya dandana mata qamshin mutuwa gamu a Asibiti babu tabbacin ta mutu ko tana raye". MAMA Salati ta saka tana kallon Abba dake shan shayi jin salatinta ya sakashi kallonta shima. "Laure ce, ban fahimci abinda take fada ba tadai ce muzo Asibiti Umaimah bata da lafiya" Maman tayi qarfin halin gaya masa se Abban ya miqe yana cewa "Subhanallahi jikin ne ya tashi? Muje to daman na gama se mu ganota". Seda suka shiga mota sannan ta lura da dan mayafin Abaya ne ta yafa akanta daman doguwar riga ta saka budaddiya, bata da nutsuwar da zata koma sako Hijabi haka suka tafi Abban na cewa "Ikon Allah wannan cikin dai ya zowa Umaimah da sammatsi Allah ya rabasu lafiya" Mama dai bata iya cewa komai ba dan tunaninta gaba daya yana can, Allah Allah takeyi su isa taga Umaiman da Laure tace tazo idan suna da rabon ganawa wane mugun abu Khalil yayi mata har haka? Sun isa Asibitin a Reception suka tarar da Hajiya da Anty Laure kowa da inda take kallo dan bala'in haushin Hajiyar Laure takeji shiyasa tunda ta gama wayarta ta juya mata qeya tana sharar hawayen tausayin Umaiman. Tana ganin su Mama ta miqe da sauri tana sake rushewa da kuka gaban Mama ya fadi data kalli fuskokinsu, shi kansa Abban hankalin sa tashi yayi nan take suka qarasa cikin kuka Anty Laure take cewa "Shaqeta yayi, haka muka kawota bata numfashi. Daman tunda muka koma nake lura dashi sam basa jituwa da alama wancan ciwon ma dukanta yayi shine yanzu kuma yake neman daukar ranta" "Subhanallahi wace irin magana ce haka kikeyi Laure? Yanzu dai ina likitan naji abinda ake ciki Hajiya kiyi haquri ki dena kuka haka" Abba ya fada yana kallon Hajiya dake sharbar Hawaye har sannan jikin baiwar Allah be dena bari ba saboda yanda ta tsorata da yanayin Khalil. Gurin likitan Abba ya wuce, kamar yanda ya gayawa su Hajiya haka ya sake maimaita masa cewar babu wata matsala bacci kawai takeyi data farka komai ze daidaita. A Asibitin ya bar Mama ya wuce kasuwa haka suka zauna su ukun babu me cewa wani qala se Anty Laure ce take ta maimaita Khalil mahaukaci ne kuma idan wani abu ya samu Umaimah se sunyi qararsa. Guraren La'asar Umaimah ta farka a firgice, Nurse ta shiga cire mata ruwan daya qare ta farka yanda taga tana zare ido ya sakata kama hannunta tana cewa "Is ok you are in a safe hand". Umaimah ta qarewa inda take kallo ta sake maida kallonta kan Nurse din kafin a hankali cikin muryarta data dashe saboda Azabat shaqa tace "Khalil, is he here?" Nurse din ta girgiza mata kai alamar Aa kafin tace "But your Mum and Aunties are outside, let me call them for you" ta dafa kafadarta cikin son kwantar mata da hankali kafin ta juya ta fita. A tare su ukun suka shiga, Umaimah na ganin Mama ta fashe da kuka Maman kanta zaro ido tayi ganin yanda gefen fuskarta ya kumbure idon ya shige ciki ga wuyanta nan inda ya shaqeta shima yayi baqi. "Na shiga uku Hajiya me Khalil yayiwa yarinyar nan?" maman ta fada tana qarasawa kusada Umaiman, tana zuwa kuwa ta riqeta tareda qarawa kukanta qarfi tace "Mama ki tafi dani wallahi kasheni Khalil zeyi idan na koma" ta sake fashewa da wani kuka tana tuna qanshin mutuwar dataji. Shaqar daya mata tasa sam bata ji zafin marin ba har yanzu maqogaronta a cushe yake wani mugun tsoronsa ya darsu a ranta dan ko a mafarki bata taba zaton Khalil ze aikata mata haka ba. Rarrashinta Mama ta shigayi Hajiya da gaba daya jikinta yayi sanyi tace zataje gida ta dawo. Tana fita Anty Laure ta kalli mama tace "Kingani ko Malika, duk lokacin da aka debo rigima se a dorawa yarinyar nan laifi gashi yanzu a gaban ido na na gani ashe cutar ta yakeyi yanzu wannan shaqar da yayi mata yau da da qarar kwana ai mu ze bari da Jimami shi bashi da asara ga mata nan birjik yana kulawa kullum da wacce zakiji shi suna waya yana qyalqyala dariya se ya shigo gurinmu ya ringa daure fuska ai wallahi ya bani mamaki". Daga Maman Har Umaimah ido suka zuba mata, qirjij Umaimah ya shiga lugude wato ba Zahra kadai yake kulawa ba she sunada yawa? Ta tambayi kanta Mama kuwa duk ta rasa inda zata ajiye maganganu su. Ita dai tasan sedai idan Khalil shaye shaye ya fara shine kawai zeyiwa Umaimah irin wannan abun in kuwa ba haka ba toh wani mugun abun tayi masa da har ta kaishi bango wanda kadan ne daga aikinta, ita ta haifi abarta ta kusan me zatayi. Numfashi taja ta kalli Umaiman tace "Ke me kikayi masa da har ya shaqe ki?" "Me kuwa zatayi masa? Bafa ya nan ya tafi Zamfara yau kwana uku, ni na fita da safen naj dubo Inna ai na gaya miki shigowar da zanyi na ganshi ya sakko daga sama kamar wanda Aljanu suka koro. Ze jin kururuwar uwar sa nayi tana a kawo musu dauki da alama daman ya zaba ita take zuwa ceto ko shiyasa yau din tun kafin ya fara ta shigo" Anty Laure ta ceci Umaimah dake zare ido dan bata san me zata cewa Maman ba Kallonta Maman tayi take ta karanto zallar rashin gaskiya ko daga yanda take sunkuyar dakai kasan da wata a qasa dan haka bata qara magana ba taja bakinta tayi shiru. Sallamar Anty ce ta katse mata shirun suka shigo tareda Salman daya ruqo kwandon Abinci, cikin jimami ta qarasa gadon tana kallon Umaiamah. Suka gaisa da Anty Laure shigowarta baby dadewa sega Nurse tace su fito likita ze dubata suka fita gaba daya Anty Laure na mayar mata da yanda akayi. Bayan Dr ya gama dubata ya rubuta magunguna tareda Sallama ya basu. Salman ne yaje Pharmacy ya karbo ya tambayesu kudin sukace yaje kawai an saka a bill ya karbo ya dawo suka tattara suka wuce gidansu suna Hanya Hajiya ta kira Mama akan ta dawo Asibiti ance an basu sallama tace mata eh sun wuce gida. Jiki a sanyaye Hajiya tayi mata fatan samun sauqi suka kashe wayar, Anty Laure ta mere baki tace "Da so take a mayar musu da ita su qarasa kashe mana ita ko to baze yuwu ba auren babu dole se a haqura, daman an fada ai yawancin matan da suke a qaton gidan nan in ka tona zaman da suke se kasha Mamaki amma dai yaron nan ya shammaceni yanda nake masa kallon mutumin arziqi ban zaymta haka yake ba". Babu Wanda ya tankata har suka isa. A dakin Mama Umaimah ta kwanta bayan tayi wanka tasha kunu dan ta kasa hadiyar Abinci, maganin ma dakyar ta iya sha daga nan bacci yayi awon gaba da ita. KHALIL Rasa inda ze nufa yayi bayan daya bar gidan ga Dr Sabitu dake ta faman antayo masa kira a waya shi har mamakin yanda yake abu kamar wani qaramin yaro yakeyi. Daman yayi blocking number Zahra, yana ga Mahaifinta ya sanar mata da halin da ake ciki ne data fara kiransa babu qaqqautawa take ya jefa lambar a blacklist. Shi tun farko ma meya aike shi ya yarda da wannan abunne gashi nan yanzu babu biyan buqata se damuwa da ya jefa kansa duk Anwar ne yaja masa da baqin nacinsa babu yanda beyi akan su haqura ba ya kafe yace su gwada ai gashi nan yanzu basu samu ba kuma sun janyo matsalar da zata iya shafar company su gaba daya. "Umaimah, Umaimah, ya fada a fili zuciyarsa na tafasa. Ya yarda Umaimah bata da hankali, tsantsar raina shi da tayi ne kuma tana taking nasa for granted shi yasa har tayi masa hakan tunda ta saba sha idan tayi masa abu ya qyaleta to an gama, baze sake daukar iskancinta ko misqala zarratin ba tunda bata san Annabi ya faku ba toh dole ya saita mata tunani. Kiran Hajiyarsa ne ya sakashi komawa gida saboda yanda ta bashi umarni duk inda yake yazo tana neman sa. Dafe kuncinsa yayi yana kallon Hajiya data sharara masa mari abinda ko zamanin yarinta da wayonsa baze tuna sanda ta mare shin ba se yau a shekarunsa kusan Arba'in Hajiyar ta mareshi a tsakar gida gaban ma'aikatan gidansa duk saboda Umaimah. Hadiye wani qululu daya taso masa yayi dakyar Hajiya dake huci kamar ta hadiyi wuta ta ce "Kana kallona ko nima zaka shaqe nin ne kamar yanda ka kusa hallaka yar mutane iye? Anya Khalil kanka daya kuwa baka fara kora abinda yake gusar maka da hankali ba?" Ta sake fada cikin tsananin fushi. Kallon su Sammani da sukayi cirko cirko suna nadar gulma yayi kafin kace me sun fashe daga gurin ya juya dakyar ya iya bude baki yace "Hajiya mu shiga ciki kiga abinda tayi mun" "Me tayi maka? Har akwai abinda yafi ranta da lafiyarta ne a gurinka" Hajiyan ta fada se ya miqe daga tsugunnan da yayi a gabanta ya shige bangarensu dan a compound ya tarar da ita ta sharara masa Welcome Marin. Bin bayansa Hajiya tayi tana cewa "Tabbas wuyanka yayi Kauri Khalil wato harni zan maka magana ka tafi ka barni a tsaye saboda ka isa ko? Shidai be tanka ba kai tsaye ya haye sam, roba ya samu ya zubo takaddun a ciki dan daya taba suke narkewa ya dawo palour inda Hajiya take bambami kamar ta ari baki ya ajiye mata yana kallonta yace "Takaddun kwangilar da kullum nake ce miki kiyi mana Addu'a ta jiqa, ta kuma goge na cikin laptop dita sannan ta kira wanda ya bamu aikin tayi masa zagi na rashin mutunchi" ya fada dakyar saboda zafin da zuciyarsa take masa. Tsam Hajiya tayi tana kallon takaddun, kwangilar da iya abincin sadaka da ruwa da akayi akanta bazata iya qayyade nawa suka lashe ba ita ta kora a ruwa haka kuma tabi wanda ya samo musu ta qare masa tanadi akan me? Ji tayi kamar an kwada mata guduma akai saboda wani tunani daya fado mata, jiyan nan Hajiya Saude maqociyarsu take mata zancen yanzu lalacewar da duniya tayi ba iya mata ake neman lalata dasu ba kafin ayi musu abu harda maza, wani dan Qawarta yaje neman aiki aka ce seya yarda anyi Homo dashi yace ya haqura shine abin basu mamaki suke ta jajantawa karfa ace abinda Khalil dinta yayi kenan shima ya samu kwangilar Umaiman ta gane shine ta lalata? "Hajiya wanda ya samo mun munyi yarjejeniya dashi akan zan auri yarsa, ranar nan da wancan abin ya faru bina tayi a baya naje gidansu yarinyar shine ta dawo tayi wannan haukan ta fasa kayan dakinta tsaf har ta jiwa kanta ciwo. Shine yau saboda na fada mata gaskiyar abinda yake faruwa na kuma bata tabbacin ba auran yarinyar zanyi ba na karba ne kawai dan na samu kwangilar nan kuma da zarar komai ya kammala shikenan zan rabu da ita shine yarinyar nan tace nazo na karbo mata danwake bayan na fita ta dauki wayata ta kira Dr tayi masa cin mutunchi sannan ta lalata mun takaddun ta goge softcopy din, ko inda zanyi backup bata barmun ba ta goge komai, Hajiya kinsan wahalar dana sha akan aikin nan kuwa? Kinsan tsahon lokaci da kudin dana kashe akan kwangilar nan amma wannan yarinyar ta lalata komai saboda haukan baqin kishinta?" Khalil ya fada idanunsa suka sake rikidewa sukayi jaaa bakinsa da hannunsa suna rawa. Kasa cewa komai Hajiya tayi dan ita da kanta tasan irin qoqarin da yake akan kwangilar, kullum ne seya nanata mata akan tayi musu Addu'a, haka abincin sadaka tunda aka fara maganar sau biyu akeyi a sati sabanin da da sukeyi Juma'a Juma'a sadakar ruwa da alawa kuwa basa yankewa akwai masallaci a layin gabansu hade da Islamiyya can ake kaiwa kullum asha ayi alwala yara kuma a raba musu alawa (Sadakar ruwa nada matuqar tasiri yan uwa mu daure koda sau daya a sati ki siya akai masallacin mutane suyi alwala haka alawa a ringa rabawa yan yara Sadaka maganin Musiba ce). Gwauron numfashi ta sauke kafin a sanyaye tace "Dukda haka wannan be kai ace ka shaqeta ba Khalil idan wani abu ya sameta fa me zaka cewa iyayenta? Akan ka rasa kwangila ka illata musu yari ya kome, ina rabaka da wannan zuciyar idan rai ya baci ai hankali ne yake nemo shi kuma abinda be faru ba shi ake gudu wannandaya rigada ya faru sedai ayi adfu'a Allah ya taqaita na gaba bata kyauta ba kaima kuma beci kayi hakan ba tunda kasan idanta sani ranta ze baci" "Ranta ze baci Hajiya? Yanzu bacin ran Umaimah kike gudu akan Asarar dani ta janyo mun?" Khalil ya fada cikin zallar mamakin Hajiyar tasa seta gyara zama tace "Ba haka nake nufi ba, gani nayi kuna zaune lafiya da matarka wata matsala bata taba giftawase irin haka ta faru tunda kasan zafin kishin matarka se kayi haquri da duk wani kule kulen mata tunda babu abinda ta rageka dashi koba haka ba?" "Babu abinda kika sani akan zamana da Umaimah Hajiya ban kuma san dalilinki na bin bayan duk abinda take aikatawa ba amma inajin tsoron ranar da haukarta zata gifta ta kanki" Khalil ya fada ba tareda ya kalle ta ba, se ta miqe jiki a sanyaye tana cewa "Asibiti zan koma na gano yanda take ka tashi muje tare dan iyayenta sunzo nasan dole zasu buqaci jin abinda yasa kayiwa yarsu haka" "Kiyi haquri Hajiya amma bazan iya zuwa ba, kuma daga can ta wuce gidansu bana buqatar ta sake dawomun cikin gidan nan" Ya fada se Hajiya data fara tafiya taci burki baki na rawa ta kalleshi tace "Karka ce mun sakinta zakayi Khalil akan abin duniya me faruwa ya qare zaka saki matarka da tun baka dashi take tareda kai?" "Ni ban yanke hukunci ba amma idan kika matsamun naje inda take a yanzu zan iya furta abinda duk baze mana dadi ba, ta tafi gidansu kawai" ya sake fadawa Hajiyan daga haka ya miqe yana tafiya dakyar ya haye sama kansa ne yake masa ciwo kamar me, ga Dr Sabitu shima kamar m kwantaccen kai se kiran sa yake a waya yana iko masa da Text kala kala, Threatening nasa yake akan seya saka an kwace masa Licence din company, seya lalata masa career ta yanda sharar fili baze samu a bashi ba ballantana gini kai shirme dai kala kala gashi nan. BAYAN SATI DAYA Uncle din Anwar daya yi musu hanyar ganin Dr Sabiyu shiya shiga ya fita dakyar ya kashe wutar dake tsakanin su Khalil da Dr Sabitu bayan ya kai masa burbushin takaddun daya ajiye suka bushe, Khalil ya roqi daya maido masa da copy din proposal da paper work din da yayi submitting tunda bashi zeyi aiki ba se a maido masa da basirar sa da wahalarsa Dr Sabitu ya banka masa harara ba tareda yace komai ba haka suka baro gidan zuciyar Khalil na masa zafi, idan ya tuna wanine ze mori wahalar sa se yaji kamar yayita kurma ihu irin basirar daya zuba a gurin tsara yanda ginin ze kasance ba kadan bace amma yanzu a bagas wani ze mori abinda yayi wallahi Umaimah ta cuce shi. Wayarsa ce ta shiga qara ya zarota a Aljihu ganin me kiran ya sakashi daidata muryarsa kafin ya daga. "Barka da Rana Alhaji" ya gaida Aminin Mahaifin nasa daya kirashi Alhaji Garba daga daya bangaren yace "Barka dai Ibrahima ya gida ya mahaifiyar taku?" "Lafiya lau Alhaji" ya sake fada kafin yayi shiru se Alhajin yace "Waliyyin matarka ne ya kirani a matsayina na waliyyinka, yace kusan sati daya kenan ashe matarka tana can gidansu shine suka kira suji ma'anar zaman nata saboda tunda ta koma kamar yanda sukace daga Asibiti aka sallameta ko basuji komai daga gareka ba". Numfashi yaja kafin yace "Eh hakane Alhaji, sabani muka samu na barta ta zauna ne a can zuwa wani lokaci kafin muga yanda hali zeyi" "Wace irin magana ce haka Ibrahimu kamar yaya yanda hali zeyi jingine musu yarinya zakayi ba tareda tasan matsayinta ba kenan se sanda kayi ra'ayi tukunna?" Alhaji Garba ya fada se Khalil yayi shiru dan be san me zece masa ba, shidai wallahi baze dawo da Umaimah yanzu ba se ya gama jinyar asarar data janyo masa sannan "Me ya hadaku?" Alhaji Garba ya jefo masa tambayar, ya sakeyin shiru kafin ya nisa yace "Laifi tayi mun kuma daman ta dade tana mun abu ina tarata shiyasa yanzu na bata hutu ko zatayi hankali ta dena abubuwan da takeyi" Khalil din ya fada kamar baya so se Alhaji Garba yayi murmushi yace "Zuwa yau da Magriba idan kana da lokaci kazo nayi magana da Kawunku Alhaji Abubakar se muje can gurin iyayen nata tareda kai a sasanta, zaman aure ko ina haquri akeyi Ibrahimu su mata duk daya suke wani lokacin in sukayi maka abu seka rasa hukuncin da zaka dauka akansu amma haka ake shanyewa aci gaba da zama. Kayi haquri ta dawo dakinta kodan halin da take ciki an rigada an fara tara zuri'a be kamata ace shekarun da aka kwashe ana zaune qalau ba se yanzu ne da girma ya fara hawanku matsaloli zasu fara bullowa, mutane da magana yanzu se kaji wani abu na daban ace ka fara wulaqanta matarka saboda ka samu budin rayuwa baza'a binciki kai me takeyi maka ba". Kamar ze rusa kuka haka ya amsawa Alhaji Garban badan yana so ba sedanbaze iya musu dashi ba. Haka sukayi sallama yana ayyana ko sunje Umaimah ba zata dawo masa gida a yanzu ba, a gaban iyayennata ze fadi abinda tayi masa ai sun san ya dade yana shanye takaicinta idan kuma za'a masa Adalci yanzu daya ce ta tafi baza'a takura masa ya dawo da ita ba. Gida ya wuce ya tarar da Hajiya na fama da Rigimar Bibi data dawo daga gidan Jamila jiya tana ta kukan ina Mummynta, Mu'ayyad dai daman tunda ya tambayi tana ina akace tana gidan Mama yaci gaba da sabgarsa Bibin ce me rigima Hajiya nata lallabata taqi Khalil na shigowa tace "Yawwa, gatan tunda taje ta buga qofarku ba'a bude ba ta tasa kukan Mummy bayanda ba'ayi da ita tayi shiru ba taqi haqura ko za'akai mata ita can gidan ne?" "Babu inda zataje" ya fada yana kamo hannun Bibin ta fada jikinsa tana Dady zanje Mummy akaini gurin Mummy" "Zakisha Ice cream?" Ya fada yana goge mata hawaye, dake sarkin son zaqi ce nan ta daga kai da sauri tana cewa "Harda Chocolate da Pizza, Mummy J is not letting me eat some chocolate" "Oh Mummy J bata kyauta ba, maza kije Raziqa tayi miki wanka muje mu siyo yanzu" Khalil ya fada yana jan kumatunta ta kusa yi murmushinta me kyau kafin ta falla da gudu Hajiya na cewa tayi a hankali. Kallonta ta mayar kan Khalil da gaba daya ya rame a yan kwanakin nan tace "Khalil baka cin abinci ne ko kaga yanda ka zabge kuwa" Murmushi kawai yayi yaqi ce mata komai, seta sake cewa "Yanzu dai ai ranka yayi sanyi ya kamata kaje ka dawo da matarka haka babu dadi ka barta a gida ga ciwo nasan iyayen sun zuba ido ne suga gudun ruwanmu kafin su biyo ba'asin abinda ya samu yarsu dan kwana biyu idan na kira mahaifiyarta ma naji jikin yanda take amsa mun nasan suna cike damu". "Baban Qoqi ya kirani, yace sunyi magana da Baba Habu wai yau zamuje can gidan amma ni gaskiya Hajiya ki kirashi kice yayi haquri ya qaramun lokaci" Khalil ya fada se Hajiya ta kama baki tace "Au magana na fika iyawa kome dakai ka kasa gaya masa hakan seni kake so na fada? Ok so kake ka janyo mun bakin duniya ace ni na saka ka kori matarka ko? To ahir dinka ka kuma fita a ido na. Har wani abin duniya daka rasa yafi ta a gurinka da zaka dauki fushi ka hana ranka sakat saboda shi, rabo ne bana ka ba kuma koda ba'ayi hakan ba bazaka samu na se Allah ya kawo wani sanadin da ze saka ka rasa ballantana ka zauna kanayiwa mutane baqin rai in ka haqura ka dangana se kaga Allahn ya maida maka da wanda yafi haka" "Da se ta bari wani silar ya gifta ai base ta zubar mun da mutunchi taja mun bala'i ba, Hajiya na fuskanci baki san girman Asarar da Umaimah ta jawo mun ba ko? Kinsan qarfin Dr Sabitu a cikin gwamnati kuwa? Kinsan abinda ze iya yi? Hajiya yau idan yaga dama yace a rufe company na take za'ayi haka babu me tambayarsa dalili ko yanzu dukda Uncle Mus'ab da wasu abokanansu sun shiga ciki an sasanta kina zaton har zuciyarsa ya haqura ne musamman da ita yar tasa da yake komai saboda ita yanzu haka fa tana Asibiti bata da lafiya saboda ance na fasa auranta. Ni kadai nasan damuwar da nake ciki Hajiya amma idan na rasa komai dani da itan daku duk tare zamu zauna musha wahalar" ya fada yana miqewa cikin sabon bacin ran daya taso masa. A rutsin nan banda wannan babbar kwangilar seda ya rasa wasu guda biyu daya har sun fara ginin ma mutumin ya kirashi yace ya dakata ashe wai Surukin Dr Sabitun ne yana auren yar yayanshi, to idan aka ci gaba da haka ai yana cikin cakwakiya banda qungurmar Asarar record din Ayyukansa na baya wasu tun kafin ya shiga Jami'a yake zanensu yana ajiyewa seda ya nutsu yaga ashe ba iya waccen folder ta taba ba wannan Ifrituwar matar ta goge komai ai wallahi idan ya maidota nan da shekara daya ma ya mata Adalci adai abinda tayi masa. "In sha Allahu bazamu shiga wahala ba babu kuma abinda ze iyayi maka ai Allah ne yakeyi bashi ba kuma dashi muka dogara. Kayi haquri kawai ita jarabawar ubangiji babu ta inda bata fa bawa idan kuma kayi haquri se kaga ka tsallake ta, yanzu dai kuje din kuma duk yabda iyayenka sukace kayi karka musa musu kaji ko" Hajiya ta fada Khalil kuwa tafiya yaci gaba dayi yana jinta kawai, Indai Umaimah ce ai gata gatanan, sedai Allah ya kiyaye randa zata hado su kawai. UMAIMAH Seda ta kwana biyu a gidan kafin ta iya fara hadiyar abinci da kyau saboda yanda wuyanta ya daure dan ba qaramar shaqa Khalil din yayi mata ba. Sau daya Mama tayi mata tambayar meya hadasu ta saka mata kuka dan bata san me zatace ba. Idan tayi qarya kuma gaskiya ta fito daga baya ita ce a ciki haka in ta fadi gaskiyar ma ba fita zatayi ba dan qila qarasa shaqeta Maman zatayi kawai dan bata manta kashedin datayi mata lokacin case din Hadiza ba, taja mata kunne ta gargadeta tace mata yau ko cikin gidanta Khalil ya dakko mace ya kawo koda wasa karta kuskura ta ce zata dauki wani hukunci a hannunta, ta gaya mata kota kira yan uwanta karta yarda tayi amfani da tunanin da kwakwalwarta take bata to yanzu idan taji akan Macen ta sake wannan aika aikar ai qarasata zatayi kowa ya huta. Anty Laure ce take kareta duk sanda aka tada maganar jin meya hadasu ita zata shiga zayyano qarya da gaskiyar abinda take hasashe, tace Kule kulen mata yakeyi dan kullum seta ganshi yana waya yana dariya ko yayi wanka ya fice da daddare tsabar sharri cewa tayi sau biyu tana tsintar dan kunnen Mace akan Dan Table din da yake ajiye muqullin mota da yake a bakin qofar palour qasan wai yana ajiyesu tare be sani ba, ita ta gama concluding neman mata yakeyi shine ta gane sukayi rigima ya shaqeta Umaimah dai in tana bada labarinta sedai ta sunkuyar dakai, jira take ta sake jin dama dama ta neme shi ta bashi haquri salin Alin ba se wani yaji abinda ta aikata ba. Kwananta biyar Baba Abdullahi yazo gidan da safe Abba ya kirawo shi, tana zaune gaban Murhun gawayi Anty na soya musu qosai dan ranar Kunun gyada da qosai tace tana sha'awa Baba Abdullahin ya shigo ta gaishe shi yace "Ke me kike a gidan nan da sassafe haka, badai nan kika kwana ba?" Qasa kawai tayi dakai suka gaisa da Anty ya wuce bayan tace masa Abban yana ciki shi yake jira. Anty ta hada abin kari ta tafi kai musu tana cewa Umaimah "Kince se me zafi gashi nan a gabanki kuma kin bari yana hucewa". Umaimah ko gaba daya Kosan ne ya fita a ranta, bata so Abba ya kira Baba Abdullahi ba tasan yanzu Asirinta ze tonu bayan yau take shirin ta kira Khalil ta lallaba abunta yazo su tafi salin Alin babu wanda yaji amma yanzu Abba ya rusa komai, Baba Abdullahi da taratsinsa zuwa zeyi yace zeyi masifa in jayi an dake tan daga nan kuma liqi ya balle. A cikin palour Abba kuwa fada Baba Abdullahi yakeyi kamar ze hadiye harshensa yake cewa "Wallahi Yaya bana jin dadin abinda kake mun musamman akan Umaimah, yanzu haka kwanaki yasa aka kulle yarinya a Cell kamar mara galihu ba'a gayamun ba, aka gama wannan ya jingineta a gida sama da wata biyar harta haihu yarinya tayi wayo sannan ta koma kawai dan kun nuna masa bata da gata in ba haka ba a ina ka taba ganin ana wannan abun da yakeyi? Shikenan daga ta masa abu seya korota gida se sanda ya mula yace ta koma who does that? Dan ubansa haka ake aure? Ko kuwa saboda an tsani yarinya ba'a bin ba'asi duk sanda suka samu matsala sedai a dora mata laifi ai qarfe daya baya Amo shi kadai amma kun rigada kun nuna masa bata da wani gata yayi yanda yaga dama da ita ai dole yanzu gashi nan anzo gabar da ya fara dukanta yana shaqeta, tunda yasan ko kasheta yayi qarshe ita za'a dorawa laifi ace ita ta nemi halakashi in the process of self defence ya kasheta ko to wallahi bazata sabu ba, ni ina son abata in ku duk bakwaso zan kuma kwato mata haqqinta daga nan police station zanje in aka bi mata kadin Shaqeta da yayi sannan yazo muji matsayar auran na gaji ya sallameta kawai ai ba rasa masu auranta zatayi ba yarinya da kyanta da komai bazata zauna baqin cikin Miji ya kasheta ba bayan ta gama shan naku. [8/18, 9:52 PM] KYAUTA: *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGE WA DA WANNAN SAIWOWIN ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN*. *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* . *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 55 Kallonsa Baba Absullahi kawai Abba yakeyi baki bude saboda mamaki koda yake be kamata ma yayi mamakin ba sanin waye Baba Abdullahin ai daman shi Umaimah ta gado kuma da ace Mace ne shi daman Hassana da Hussaina zasu zama gurinjaye jayen bala'i kpda yake yanzun ma ya aka qare rigima ai se wadda ya manta ce baya janyowa kuma saboda halinsa sedai a haqura a barshi dan ko bashida gaskiya se ya san yanda ya ci galaba akanka. Miqewar daya ga yana qoqarin yi ce tasa ya dakatar dashi dan har yana qoqarin hambarr da abincin da Anty ta kawo Abban yace "Zauna Abdullahi, magana na kiraka muyi ba yawon tafiya gurin yan sanda ba". Baba Abdullahi ya zauna Abba yaci gaba da cewa "Nima a wannan gabar abinda ya faru beyimun dadi ba dan kaga ba'afi wata bafa nan ma suka yi wata rigimar har Asibiti ta kwanta dalilin daya sa Laure qanwar Malika take zama da ita yanzun kenan saboda anyi mata daurin Mahaifa kuma sukaqi fadar abinda ya hadasu daga shi har itan shiyasa ma ban tsaurara ba saboda nasan da tana da gaskiya zata fadi abinda ya hadasu..." Baba Abdullahi yayi saurin katse shi da cewa "Au bama wannanne na farko ba ashe kaga ya daketa na farko yaci banza dole ya yanzu ya qara kuma da zakace bata da gaskiya ta ya akayi ka sani?" "Koma menene yanzu dai anzo gabar da dole muyi interfering, duk abinda ze faru ya faru amma bazan dauki duba ba. Ban taba daga hannu na daki yar wasu ba dan haka nima baza'a dakar mun tawa yar ba yanzu abinda nake so dakai ai kana da Number Iyayensa ka kirasu ka sanar musu da halin da ake ciki, yanda aka qulla dasu haka za'a warwareta dasu dan daman a baya idan sunyi rigimarsu gurin Marigayi yake zuwa yanzu babu shi shine ze ringa daukar mataki a hannunsa to bazan lamunta ba" Abba ya fada, Baba Abdullahi ya ciji yatsa tareda yin qwafa kafin ya zaro wayarsa ya shiga kiran Alhaji Garba. Tiryan tiryan ya kora masa jawabi kamar a gabansa akayi Alhaji Garba ya ringa salati ya shiga bashi haquri akan sam be sanda labarin nan ba amma yanzu ze kira Alhaji Abubakar zasu zo tsakanin yau ko gobe dan Allah suyi haquri. Ya kashe wayar yana cewa "Ahto gara dai suzo, kuma sena rama mata marinta dan ma yaji da jinsa da gatanta" Abba dai murmushi yayi suka shiga karyawa Baba Abdullahi nata Mita har seda Abba ya gaji yace fita zeyi sannan ya tashi suka fita tare bayan sun gaisa da Mama itama ya dira mata Mitar ta shige daki ta barshi. "Ke daga yau karki sake zuwa gidan nan duk abinda ya hadaku kije can gidana ki gaya mun, kina kallom wannan uwar taki kamar ma tafi sonsa akanki, ji ina mata magana yanda ta hade rai wato an tabo Zuciyarta haka kawai ba dole ma ya ringa jibgarji yanda yaso ba uwar data haifeki ma ta nuna masa bata qaunarki" Baba Abdullahi ya fada yana kallon Umaimah dake zaune har sannan a gaban Murhu Anty Laure kuwa ta cafe tace "Kai ma ka fada Baban Nabila yo dan ma bakaji abinda take fada bane gaba daya fa ta toshe kunne fadi take haka kawai baze daki Umaimah ba dole da abinda ta masa ni na taba ganin inda ake haka ace ka zabi bare akan naka? Ai ko naka keda laifi kamata yayi ka mora masa baya in yaso a gefe ka nuna masa kuskurensa". Jin ya samu yar tayi se ya fasa tafiya yaja kujerar zama ya kafa suka dora Abba dai yayiwa matansa sallama ya fice a ransa yana cewa "Ga inda Umaimah ta gado halinta su biyun nan basa son gaskiya qiri qiri suna kallo zasu take abu indai bayazo daidai da ra'ayinsu ba". KHALIL Bayanda ya iya haka yaje suka rankaya zuwa gidansu Umaimah. Yana tuqin ji yake kamar ya tsayar da motar yace su sauka saboda yanda suka rufeshi da fada wannan nayi wancan nayi a haka har suka qarasa qofar gidan. Salman daya hango su ya taho da sauri cikin ladabi ya gaida dattijan kafin Khalil ya miqa masa hannu suka gaisa yana tambayarsa Abba yana nan "Suna ciki, Baba Abdullahi ya hada chamber guda ka shirya yau zakasha Rapping" Salman ya Fada Khalil yayi yar dariya yace "Tare dakai zamu shiga ka tayani ji" "Wani, bari dai na gaya masa kunzo" Salman ya fada yana gwalo ido kafin ya juya ya shiga gidan. A palour Abba ko kamar yanda Salman ya fada yanda kasan wani taron daurin auran Bazawara Haka Baba Abdullahi ya tattago yan uwansu da Aminan Abba samada mutum bakwai, suna zaune yana qara zayyana musu qarya da gaskiyar da Anty Laure ta kora masa, Abba dai takaici ya hanasa magana kallonsa kawai yakeyi Baba Liman Aminin Abba ya kalli Baba Abdullahi yace "Kai amma kuwa ban zaci yaron nan haka yake ba, ina masa kallon mutumin kirki shiyasa fa tsananta bincike nada kyau amma kaga duk sanda rigima ta taso se mu taru mu goya masa baya ba'a ma neman jin ta bakinta ashe dai shima da nasa halin". Bude baki Abba yayi zeyi magana Salman ya doko sallama, sanar musu yayi da zuwan su Khalil Abba yace su shigo Baba Abdullahi aka gyara zama harda qara tamke fuska shi ala dole zeyi rashin M dan ya rantse ko an sasanta kafin Umaimah ta koma seya rama mata marin da aka mata ai ba jaka suka aura masa ba. A qasa Khalil ya samu guri ya zauna ya shiga gaishe su, wasu suka amsa faran faran irinsu Baba Abdullahi da Baba Munzali kuwa iyayen daukar dumi da harara suka bishi shima be damu ba ya sake duqar dakai yana jira su gama gaishe gaishen ayi wadda za'ayi ya tafi amma fa duk bala'i badai Umaiamah ta koma masa gida yau ba. Baba Abdullahi ya zabura ze fara magama Baba Liman ya dafe hannunsa ya girgiza masa kai dole ya koma yayi shiru Alhaji Abubakar yayi sallama tateda bude taro da Addu'a kafin ya fara koro bayanin ban haquri ya ringayi kafin Alhaji Garba ya karba shima ya dora nasa jawabin ban haqurin tareda roqon Alfarmar komai ya wuce yanzu Umaimah ta shirya ta koma dakinta. Yanda suka sadda kai suna bada haqurin ya saka jikin kowa yayi sanyi yan korar Baba Abdullahi da sukayi shirin yin tijara jiki yayi sanyi. Alhaji Abubakar ya kalli Khalil yace "Kayi shiru, ga surukanka nan ka basu haquri ka dauki matarka ku koma shikenan magana ta wuce" kafin ma yace wani abu Baba Abdullahi yayi caraf yace "Ai bazeyi magana ba, tunda ya daketa ya daki banza anzo ana bada haquri su koma kaga ya samu lasisi gobe ma ya qara. To wallahi bari kaji, ka sake ko dungurar mun Ya Three quater zan saka nazo na casaka har cikin gidan naka dan ka sani tambaye su kaji tsohon dan Dambe ne ni ban kuma manta komai ba balle ka dauka na fara tsufa zan kasa lallasaka". Dariya palour ya dauka banda Khalil daya daga kai ya kalle shi yana hasaso wai shi Baba Abdullahi ze daka, ai ko yanzu yake da ganiyar quruciya yasan qirar ba daya ba, lallasashi zeyi ya watsar balle yanzu da shegiyar rigimarsa ta tsufar dashi lokacinsa beyi ba dan idan ka ganshi seka dauka ya girmi Abban. "Kayi shiru kuwa ana magana" Alhaji Garba ya fada a fusace jin Khalil din bece komai ba, seya dago da kansa a hankali ya kalli Abba da shima shi yake kallo ya sake maida idonsa qasa yace "Abba kuyi haquri, amma kafin a yanke kowanne hukunci ina so a kira Umaimah tazo a gaban kowa ta fadi gaskiyar abinda ya faru, idan ina da laifi zan nemi yafiyarta da taku mu tafi kamar yanda kuka ce..." "Idan kuma ba haka ba fa?" Sarkin katsalandan Baba Abdu ya tareshi harda miqewa tsaye kamar ze rufeshida duka se Alhaji Badaru wanda yake bin Abba yayi saurin tareshi shima yana cewa "Aa Abdullahi maganarsa gaskiya ce ai ba'a shari'a da shaidar bangare daya, a kirata tazo din kamar yanda ya buqata itace shari'a ta gaskiya". Ajiyar zuciya Khalil ya sauke dan baze sake daukar wani dakon laifin da beyi ba gara tazo in ma wata qaryar ta shirga ta warwareta da kanta kuma in har ta domin Allah za'ayi babu Wanda zece ta kyauta da abinda tayi masa. A fusace Baba Abdullahi ya fice saga parlour ya tafi dakin Mama, a bakin qofa yaci karo da Umaimah da tunda taji qamshin turaren Khalil ta kasa tsaye ta kasa zaune. Tana can bacci bata san taron da Baba Audu ya hado ba shigowarsu Khalil ce ta farkar da ita saboda taji suna gaisawa da Anty ta kuwa fito da sauri amma sunrigada sun shige bangaren Abban se qamshin turarensa daya bari a iska tun sannan ta kasa zama Baba Abdullahi ya gama da ita wallahi. Muryarsa taji a tsakiyar kanta yana ta sako Hijabinta ta biyo shi. Ta zabura tana raba ido tace "Uhm Ina zanje Baba?" "Kizo muje wancan mara kunyar Mijin naki me yace wai se kizo ki fadi abinda ya hadaku, daman karki ji nauyin kowa ki fadi komai da kika sani idan shi be iya kama barawo ba ai shi ze kamashi. Ina Laure itama ta zauna cikin shiri dan itace shaidar gani da ido". Jiki Babu Laka ta shige dakin Mama ta samo Hajibi, Maman dake zaune kan kujera ta kalleta tace "Kinga da kika qi fada mun komai yanzu zakije gabansu ki fada in ma kece mara gaskiya kin jawowa kanki fadandaya fi wanda zanyi miki ai sannan a tafi dake a bakin duniya ana yamadidi kinga se kiji dadi" ta mayar dakai taci gaba da danna wayarta. Baba Abdullahi ya sake fafaro mata kira dan yana tsaye yana jiranta. Suna tafe yana qara qissima mata abinda zata fada harda qarin gishiri da Maggi har suka isa ta nemi gu daga bakin qofa kamar sabuwar munafuka ta shiga gaishe su suka amsa mata a kusan tare. Alhaji Garba da Alhaji Abubakar sukayi mata ya jiki ta amsa da sauqi kafin gurin yayi shiru. "Mijinki ya nemi kizo aji ta bakinki akan abinda ya hadaku har kika dawo gida" Alhaji Badaru ya fada cikin kulawa yana kallonta. Umaimah ta dago kai ta kalli sashen da Khalil yake kafin ta hadiye miyau dakyar ta kalli Abba seta sunkuyar da kai tace "Ni Dady komai ya wuce a gurina, daman dan sabani muka samu amma ya wuce" "Ban gane komai ya wuce ba, zaki bude baki kiyi magana ne ko kuwa na kira Laure ita ta fada tunda naga alamar tsoronsu kikeji?" Baba Abdullahi ya fada se sannan Abba yayi magana yace "Umaimah" ta dago ta kalle shi yaci gaba da cewa "Me kika yiwa Mijinki da har ya saka shi ya dakeki ya shaqe miki wuya?" "Ji wata irin tambaya dan Allah Yaya, kai anya ba Asirce mata iyaye kayi ba ace basa ganin laifinta se naka?" Baba Munzali ya fada nan cece kuce ya barke, wasu na fadin koma me ya mata tunda dai tace ya wuce to abarshi ya wuce din ta tattara ta koma dakinta ai damanko wacce Mace zaman haquri takeyi idan yaso shi kuma ya kiyaye kar haka ta sake faruwa Alhaji Badaru kuwa da yake nazarin Khalil da tunda ake maganar be dago ya kalli kowa ba ya kuma dubi Umaimah dake ta faman raba idanu alamun rashin gaskiya sun gama bayyanar mata ya dakatar da kowa, cikin muryar babu wasa dan daman shi bame wasan bane yace "Kinsan Allah ko ki fada da kanki ta lallami ku kuma mu tashi mu tafi, duk ranar da kika bude baki kika fadi abinda ya faru se a sake zama danba zamu maidake cikin taraddadin irin zaman da kikeyi ba" "Nidai wallahi Dady na yafe kuma yayi haquri kawai zan koma" ta fada tana fashewa da kuka se a sannan Khalil ya dago kai ya kalleta kafin ya kalli Alhaji Badarun shima yace "Kuyi haquri Alhaji amma idan har Umaimah bata fadi abinda tayi mun da bakinta ba bazata koma gidana ba". Shiru palour yayi kamar an dauke wuta Umaimah ko idanu ta zaro tana kallonsa bakinta na rawa amma ta kasa cewa komai, Baba Abdullahi ne ya ceceta ya furta abinda take so ta tambayi Khalil din yace "Sakin ta zakayi?" "Ko ban saketa ba bazan iya ci gaba da zama da ita ba har ze ranar data san daidai ta kuma koyi karban laifin da tayi ta bada haquri, daga nanzan duba idan da yuwar cigaba da zamana da ita dan wallahi ta kaini bango, Halin Umaimah ya isheni" Khalil ya sake fada cikin wani sauti dake nuna zallar takaicin dake cin zuciyarsa. Suka sakeyin shiru kafin cikin tsawa Alhaji Badaru yace mata "Zakiyi magana ko mu tashi mu kama gabanmu dan duk muna da abinyi ba irinki ba" Se sannan ta sake fashewa da Kuka, ta kalli Abbadaya tsura mata ido kafinta fara zayyano duk yanda akayi tundaga sanda ta fahinci Khalil yana kula Zahra, binsa gidansu da tayi, yanda ta lalata kayan dakinta har zuwa kwanciyarta a Asibiti da kuma sanadin Mari da shaqar da yayi mata. Palour ya dauki shiru na kusan minti goma banda shashsheqar kukanta babu abinda kakeji tana cewa "Dan Allah kayi haquri wallahi sharrin Shaidan ne, nikaina seda na aikata na fara nadama kuma da baka zo da fushi ba wallahi tun a sannan zan baka haquri "Ki bashi haquri bayan kin cuce shi?" Alhaji Badaru ya fada cikin wani irin fushi da muryarsa ta kasa boyewa kafin yaci gaba da cewa yana kallon Baba Liman "Zancen da nake maka zaman mu anan na wata kwangila da aka bayar a Office dinmu DG ya shiga ya fita ya bawa wasu qananan constructors se daga baya wai ya gano ashe yan Damfara ne ban masan Comapany Mijinta bane ashe yar iskar yarinyar nan ce take nema ta bata masa suna har yaushe zakiyi hankali Umaimah ki dena jefa mutane a masifa? Yaushe akayi wancan Case din datayiwa yar mutane sharri aka gama saboda kin ga kinci bulus shiyasa kika sake kwanto masa wata kurar ko? Daman tun wancan incidence din nake cike daku gaba daya yanda ace babu Wanda ya sanar dani se daga baya naji labari da kukayi yanda kuka ga dama. Dan ubanta da an dauki kwakwkwaran mataki akanta a sannan zata sake tunanin repeating any nonce like this ne? Ita ga shafaffiya da mai, tayi tarnishing image din yarinya amma the only punishment she served was tayi video ta bada haquri shikenan taci banza saboda tsabar son kai da qin Allah irin naku. Idan itace aka yiwa qazafin iya abinda zamuyi kenan? Da yanzu wata magana ake ta daban because se nayi making sure that the culprit rot in jail, ai da aka tafi da ita ma be kamata ku bita ba se tayi sati ta fita hayyacinta sannan ta qara zaman prison kona shekara daya ne daga nan bazata sake dakkowa kowa magana ba amma yanzu gashi, ga abinda ta sakeyi saboda tasan qarqari kuyi mata fada shikenan ya wuce kai kuma lusari ka koma kaci gaba da zama da ita ba tareda ka nuna mata kuskurenta ba who does that? Kinsan waye Dr Sabitu kuwa kin san irin tuggu da manaqisar daya iya hadawa? Ubanwa ma ya saka ki shiga sabgar Business din Mijinki ina ruwanki dawa yake sabga dan ubanki idan ma uwar Zahra yace ze auro kina da matsala da hakan ko akan ki zata zauna eye? To ai shikenan, yanzu kinyi yadda kike so ba daular da kike ciki kike baqin ciki wata tazo taci ba itama se ki shirya Allah ya kiyaye amma Jarabar da kika janyo masa sekin fi uban kowa dana sani wallahi dan ba'a shiga komar Dr Sabitu a fita lafiya musamman ta hado da wannan yar da yakeji kamar ransa". Maganganun Alhaji Badaru ba qaramin tension suka qara a palour Khalil da yayi wuri wuri da ido yana kallon Alhaji Badarun, kalaman Uncle Anwar na sake dawo masa da yace "Se kuyi taka tsantsan da duk wata contract da zaku dan Dr Sabitu mugune tsaf ze iya framing naku ya saka ku a matsa". "Am nace kwangilar harta nawa ce ne haka?" Baba Abdullahi ya katse musu shirun a zafafe Alhaji Badaru ya sake cewa "It worth billions of naira, inda yayi aikin nan Alkhairin daze samu Allah kadai ya sani amma yar baqin ciki ta hana" "Biliyan kace, amma Umaimah anyi yar kutumar uba wallahi" Baba Abdullahi ya fada yana miqewa tsaye, kafin su ankara ya isa gabanta ya faska mata mari ya sake kifa mata wani Alhaji Garba dayafi kusa dasu ya riqe shi yana cewa "Haba haba Alhaji ya haka kuma" "Barni naci uban yarinyar nan ko bakaji abinda tayi bane? Ai wallahi baka burgeni ba Khalil daka sani a Injin da kuke niqa sumunti ka jefa yar banza ka markadeta in yaso kazo kace mana ta bata kawai daga baya ka lallabo ka.gayamun abinda tayi maka mu taru mu rufe maganar wannan abin takaici har ina" Baba Abdullahi ya fada yana ciza yatsa, duk yanda suke cikin jimami seda maganarsa ta bawa kowa dariya suka murmusa banda Alhaji Badaru da Abba da yayi quri kawai yana kallon Umaimah. He can't believe it ace rashin tunanin Umaimah har ya kai haka. Maganar Alhaji Badaru ta katse shi da yake cewa "Dallah rufe mana baki ba nan ka gama fuffuka da ihun zaka rama mata ba shine yanzu zaka zo da wata Dramar ka ta qarya. Ni dana san ma akan wannan yarinyar ne da babu abinda ze hanani komawa Abuja na zauna jin takaici, daman ki tashi yanzu ki shiga ki hada kayanki, tare zamu tafi gobe in sha Allahu zan wuce Abuja da ita tunda babu me iya wanke mata kwakwalwa a cikin ku to ni zanyi idan ta saitu ta dawo hayyacinta se a sake zaman". Bala'i Alhaji Badaru ya ringayi kamar ze tashi gurin duk sukayi tsit aka rasa me dakatar dashi dan daman yan gidan su Abban ba laifi akwai bala'i dan zamanin suna yara idanka takali daya da fada tofa danginka kaf sun shiga uku haka zasu taso ku a gaba se randa Allah ya huci zuciyarsu. Dakyar Alhaji Badarun ya iya yin shiru kafin Baba Liman ya dora da Nasiha shi kuma yana nunawa Umaiman rashin dacewar abinda tayi. Umaimah hankalinta idan yayi cikin tirela ya tashi da jin wai zatabi Baba Badaru, ita kuwa wane tsautsayi nr ze ritsa da ita haka? Ai wallahi gara ta koma Khalil idan gunduwa gunduwa zeyi da ita yafi mata sauqi. Tun suna yara bata taba sha'awar ko zuwa hutu gidansa ba duk kuwa yanda su Nuratu ke doki da rizgillin son zuwq Abuja sedai su dawo suyi ta bata labari amma koda wasa bata taba zuwa ba. Bata jin magana Baba Badaru kuma baya daukar nonsense dan ko gidansu yazo daga gaisuwa gudu takeyi karma ta tsaya tayi shirme a gabansa yaci ubanta shiyasa ko yaransa babu wata shaquwa tsakaninta dasu bama zata iya cewa ga Adadinsu ba dan ba shiga abinda ya shafesu take ba tana gudun masifar Babansu shine yanzu zece ta bishi salon ya kasheta acan sedai ya aikowa yan uwanta jana'iza tab. "Yanzu dai ayi haquri gaba daya dan laifi Umaimah bata kyauta ba amma shima Khalil yayi laifi. Me yasa ze saka yaidara a cikin lamarin ai ba ga Umaimah ba ko a gurin ubangiji beyi daidai ba hakan ma da yayi yasa Allan ya nuna masa wayonsa baze bashi kwangilar ba sannan dan ta zama sila hakan bashi ze bashi damar ya taba lafiyarta ba, ko dan gaba karka sake, idan tayi maka abu da bazaka iya jurewa ba ka kawota gaban magabatanta su tsawatar mata amma koda wasa karka sake cewa zaka taba lafiyar jikinta" Alhaji Abubakar kawun Khalil ya fada kafin ya dora da cewa "Yanzu dai magana ta wuce Alhaji muna sakw baku haquri komai ya wuce ke ki bawa mijinki haquri sannan ki shiga ki hado kayanki mu tafi dare yanayi" "Ai Yaya Badaru ya gama magana Alhaji, kuyi haquri kuje kawai, idan aka kwana biyu zuciyoyi suka qarayin sanyi seta dawo amma yanzu idan akayi haka tamkar an shiga haqqin yaron ne, kowa yasan abinda akayi masa babu dadi kuma yana da buqatar a bashi lokaci ya samu nutsuwa" Baba Liman ya fada nan su Alhaji Garban suka dage akan lallai fa se an basu bikon Umaimah sun tafi da ita. "Kayi haquri Khalil dan girman Allah wallahi sharrin zuciya ne amma nayi alqawari bazan sake ba" Umaimah dataga Lamari yana qara rikicewa ta fada cikin matsanancin kuka, fata take yace ya yarda ta bisun dan abinda Baba Liman ya fada kenan se anji ta bakinsa amma yayi mirsisi ya zubawa qasa ido yaqi ce musu komai, "Babu shakka, Khalil ma kike kiransa kai tsaye saboda kin rainashi ko" Baba Munzali ya katseta se tayi saurin cewa "Abban Mu'ayyad na tuba bazan sake ba, na yarda daga yanzu in na kuma duk hukuncin daka ga dama ka yanke akaina amma yanzu ka yafe mun dan Allah". Cikin tashin hankali take dan idan yace baze tafi da ita ba bata san inda zata tsoma ranta ba. Zancen tabi Baba Badaru ma baze yuwu ba dan ko duniya zata taru bazata gidansa ba wallahi kuma idan ta zauna a cikin gidan nasu ma tamkar ta fito daga rana ne ta fada wuta dan Shirun da Abba yayi yana kallonta kawia ta tabbata idan be hada mata jikinta da duka ba to qila wuqa ze saka ya yankata balle labari ya isa kunnen Mama kai ita bata shirya fuk wani tashin hankali ba gara ta bishi suje can zata jure duk abinda zeyi mata har ya haqura ya sakko daga fushin. "Ya isa haka, ina ganin magana tana hannun Khalil yanzu, idan ya yarda ya dauketa su tafi idam kuwa ba haka ba babu me tilasta masa akan ta koma. Zata cigaba da zama anan har zuwa sanda shi dakansa ya gamsu ya nemi ta koma din" Abbada tunda aka zauna bece komai ba yayi maganar ganin takaddamar taqi qarewa. Khalil ya daga kansa ya kalli Abban wanda shima shidin yake kallo. Iyayen Umaimah na daga abinda yasa yake daga mata qafa a lokuta da yawa dan mutanen kirki ne, a yanzun ma ta sake cin darajarsa dukda hakan ba yana nufin ya yafe mata bane Aa ze haqura ta koma ne saboda ya ragewa Abban radadin da abinda take aikatawar yake haifar masa wanda kwayar idonsa take gaza boyewa. Ya tabbatar idan aka auna jininsa a yanzu ya hau. Rintse idonsa yayi cikin wata murya yace "Na yarda ta koma amma..." "Karma ka bata bakinka Yi shiru Halilu kaidai Allah yayi maka albarka ya qara maka hasken zuciyar musulunci, yanda ka iya shanye wannan baqin ciki Allah ya saka maka a mizani dan abinda kadai zan iya cewa kenan, Amma Alhaji sefa kunyi haquri dan ba zata biku yanzu ba saboda dole zamu sake yi mata fada a matsayin mu na iyayenta, idan Allah ya kaimu gobe da kaina zan rakota har gidan mun gode Allah qara Arziqi, ke tashi muje" Baba Abdullah daya miqe yana nade babbar riga ya fada. Umaimah tayi wuri wuri da ido take murna ta koma mata ciki, jin Khalil ya yarda ta koma ga kuma wani sabon zance a gun baba Audun seta bare baki zata kuma rusa wani kukan ya daka mata tsawa yana cewa "Na rantse da Allah ko ki tashi ko yanzu nayi ball dake a gurin nan, qarqari akai mi gidan yari na shekara na fito dan ba dauruwa zanyi ba" yanda yayi maganar kuma taga a gun babu wanda ya ce komai ya saka ta miqe jiki na rawa tana waiwayen Khalil da taqi kallon sashin da take. Gabaya tasata, tun daga qofar falon yake antaya mata maruka a fuska da qeya har suka isa falon Mama, Mama da Anty na zaune kowa ta rafka tagumi dan Umaiman ta fado tana ihu. Cikin rashin Jin dadi kawunan Khalil sukayi sallama da kowa suka tafi, Alhaji Abubakar ya ringa sababi wai ya wulaqanta su ya nuna basu isa ba, sun bashi umarni yaqiyi shidai Khalil ransa fes ya biya ya sauke kowanne a gidansa kafinya wuce gida yana zuwa ya tarar da Hajiya na jiransa, a taqaice yace mata kawai gobe Umaiman zata dawo, taja doguwar Hamdala ya tsaya yana kallonta kawai kafinya girgiza kai ya yi mata seda safe ya fita. Kwana yayi yana ayyana ta yanda ze iya manta abinda ya faru yaci gabada rayuwa da Umaiman. Har ga Allah ba rasa kwangilarda yayi ne yafi damunsa ba, tunanin irin rainin da Umaiman tayi masa da harbata shayin tayi masa duk abinda taga dama. Idan har zata iya aikata haka bayan tasan cewa ze taba rayuwarsa ya taba aikinsa gababe san me zatayiba, dole ya dauki mataki kafin ranar nadama mara amfanita riskeshi. Tunanin hukuncin da zeyi mata ya huce kawai yakeyi amma har bacci ya kwashe shi be samu ba. UMAIMAH Seda Baba Abdullahi ya kumbura mata fuska da marukan daya ringa zabga mata tamkar Allah ya aiko shi kafin ya kalli su Mama da sukayi cirko cirko suna kallonsu aka rasa wadda zata kai mata taimako yace "Ki gayawa wannan mahaukaciyar yar taki ta yanda kika hadu da ubanta". Kallon rashin fahimta Mama tabi shi dashi, Baba Abdullahi da seka rantse shine ma Khalil din saboda yanda ya ara ya yafa a masifance yace "Eh Malika, ki sanar mata da yanda akai kika auri Ubanta, koda yake bazata fahimta ba idan ke kika gaya mata, bari ni nayi mata gwari gwari ta yanda zefi shiga kwakwalwarta" ya juya kan Umaimah data dafe kunnuwanta da takeji kamar sun toshe yace "To bari kiji, Hajiya Lawisa ta qaraye ai kinsanta Uwar Mijin Naziyya yayan maza muke da ita kuma itace Asali wadda suke soyayya da ubanki Sabo, sanda ya baro qaraye ya shigo birni Alhaji Madaki Mahaifin Malika gatanan data haifeki shine ya zamar masa ubangida, ya koya masa neman kudi har ya dorashi akan harkokin dukiyarsa da sharadin ze auri yarsa, bazawara ce ma a sannan baya sonta amma ya yarda kuma haka akayin ya koma gida ya fadawa iyayenmu ya fasa auran Lawisa duk da dadewar da sukayi suna soyayya haka kowa ya dauki qaddara aka barshi ya auri yar ubangidan nasa itama Lawisan kuma a cikin Abokanansa da sukaje daurin aure daga Birni Allah ya fitar mata da Miji tayi auran. Sanadin auran uwarki duk muka baro qauye muka dawo nan masu boko suka kama masu kasuwanci suka kama da ba'a aure dan wata biyan buqata da yanzu ba a haifeki ba shegiya me kalar ibilisai kinzo kin gallabi kowa se kece zaki hana saboda baqin ciki da kyashi ya cika miki zuciya to ai kin kyauta, kuma yanda kika rusa kwangilar nan kikayi masa baqin cikin samun wasu a gaba in sha Allahu seya janye miki tallafi" Baba Abdullahi ya fada yana kai mata wani marin ta goce kafin ya gallawa Anty da Mama da suka zama hoto harara yaja tsaki ya fice daga gidan. Muryoyin ragowar sukaji da suka fito suna musanyar sallama, suna tsaye kamar mutum mutumi Abba daya raka yan uwansa ya dawo jiki a sabule ya leqa falon Maman. "Ki sameni a daki ina son magana dake" ya fada mata kafin ya juya Anty taja numfashi ta fesar kafin tace "Bari naje na kwanta Allah ya tashe mu lafiya" ta fice daga dakin tana tariyo maganganun Baba Abdullahi da bata tabajinsu ba. Iya saninta Abban ya sanar mata da auran soyaya sukayi da Malika daman dai tasan yar ubangidansa yanzu kuma taji wata cakwakiya ashe shine dalilin da ya saka Sam Hajiya Lawisan basa wani shiri da Mama dukda bata nunawa Naziyya komai amma fa idan suka hadu ko a taro ne tafi yi da Anty akan Maman da suke matsayin surukai. Mama ko tamkar wadda aka watsawa ruwan sanyi haka taja qafafunta da sukayi sanyi tabi Abban ba tareda ta bi takan Umaimah dake nan tsugunne tana kuka ba. Wannan cin mutunchi na Abdullahi har ina? A gaban kishiya yayi mata tijara, wai ma me Umaiman tayi daya juye kanta ake mata wannan tonon sililin? Sanda Abba ke labarta mata abinda Umaiman ta sake aikatawa kuwa kasa motsi tayi a gurin banda binsa da kallo ba abinda takeyi dan ko tunani ta kasayi a kwakwalwarta. "Wallahi Malika saboda kunya kasa cewa komai nayi se su Badaru ne sukayita fadace fadacensu. Yanzu ace Umaimah bazata bar rayukan mu su huta ba kullum ta Allah da sabuwar rigimar da zata janyo mana? Nidai na yanke shawara zan kira yaron nan daga baya, ya fadi gaskiya karya ji kunyar mu idan har yana ganin da cutarwa a cikin zamansu ya sawwaqe mata kawai kowa ya huta tunda dai ita bata san inda yake mata ciwo a rayuwarta ba, gara ta dawo ta zauna kawai kafin wata rana ta dakko abinda zata saka a hada harda mu a kulle". Hannu Mama ta saka ta share hawayen dake mata tsere akan fuska amma suka qi tsayawa, cikin sheshsheqa tace "Alhaji na gaji da Halin Umaimah na gaji ban san wace irin yarinya bace ba, Allah ya gani iyakar iyawa babu ta inda na banbantata da yan uwanta a gurin tarbiyya, raino daya nayi musu harma nafi lura da saka ido akan al'amuranta. A kullum na daga hannu kafin na roqawa kaina komai sena roqawa Umaimah amma na sani Allah ba mantawa yayi dani ba yana sane kuma in sha Allahu jarabawar da yayi mana akanta zata zamo mana kaffara" ta qarasa tana sakin wani kukan me nuna zallar zafin da zuciyarta takeyi. Cigaba tayi da magana tana cewa "Yanzu Abdullahi seda ya qare min tanadi tas akanta kafin ya fita, a gaban Saratu yake fadar cusa maka ni akayi saboda na rasa ma'auri baka sona ka aureni a bazawara ya gama fadar maganganunsa ya fita duk saboda Umaimah, shikenan saboda na haifeta bazan samu nutsuwar zuciya ba? Kullum tazo gidan nan cikin fargaba nake se naga ta tafi salin alin sannan hankalina yake kwancita har se yaushe? Se yaushe zamu huta da matsalolin Umaimah?". Kuka take sosai Abba ko ya rafka tagumi ya kasa rarrashinta, seda tayi me isarta kafin ta miqe tayi masa saida safe, kai kawai ya iya daga mata danshi kansa zuciyarsa a dagule take da zeyi kukan ma daya ji dadi. Koda ta koma dakin inda ta bar Umaimah nan ta tarar da ita. Kallo daya tayi mata ta wuce cikin dakinta kai tsaye Alwala ta daura ta shinfida Sallaya ta fara jera nafiloli. Kwana tayi tana sallah ko kadan bacci be ziyarci idonta ba, toh ta ina zatayi bacci bayan Allah ya hada ta da yarinya irin Umaimah? Da Asuba Umaimah da tayi kwanan zaune ita ba sallah ba ba salati ba tana ta faman sharar hawayen da bazasu magance mata komai ba, dakyar ta iya miqewa saboda yanda qafafunta suka haye saboda zaman da tayi ta ringa dafa bango harta shiga dakin Maman. Alwala ta dauro, Mama data idar da Raka'atanul fajr tabita da kallo harta fito daga bandaki ta nemi gefe kusada Maman ta zauna dan ba zata iya sallar a tsaye ba. Seda suka idar da Asuba kafin ta kalli Maman cikin muryarta da bata fita saboda kukan data sha ta gaisheta. Da "Lafiya" ta amsata batareda ta kalleta ba taci gaba da lazumin da takeyi, Umaimah ta sunkuyar da kai hawaye suka kawo a idonta cikin muryar kuka tace "Dan Allah Mama kiyi haquri wallahi...." "Dan Allah karki dameni bakiga abinda nakeyi bane? Tunda ke daman sallar kadai kikeyi bakya addu'a se ki tashi ki bani guri nikam inada buqatu da yawa gurin Allah karki dameni" Maman ta katseta ba tareda ta bari ta fadi abinda take so tace ba. Se kuwa ta saki kukan da take qoqarin hana fitowarsa, a fusace Maman ta juya tace mata "Tashi ki bar nan kafin na saba miki" "Dan Allah Mama ki tsaya kiji, wallahi Allah bayin kaina bane, Safina ca ta bani shawara kuma tace mun ta tabayin hakan itama shi yasa nayi amma ban zata abin zeyi zafi da yawa haka ba" Umaimah ta fada cikin kuka tana matsawa gaban Maman. Carbin da take ja ta kai mata duka dashi ta goce dukda haka ta sameta a hannayenta data saka ta rufe fuska dukan ya shigeta kuwa sosai "Badai ke kince bakya jin magana ba? Bazaki bar zukatan mutane su huta daga tashin hankalinki ba ko? Ai shikenan kici gaba da daukar hudubar mutane suna ingizaki kina rashin hankali, Qawaye ko? gaki gasu Umaimah wata rana se sun kaiki kurkuku sun ja miki daurin rai da rai sannan zaki dawo shikin hayyacin ki shashasha kawai" cikeda takaici Maman tayi maganar tana miqewa dan barin mata dakin tunda ita taqi fita. Palour ta koma, tana jiyo Umaiman na kuka daga ciki. [8/18, 9:52 PM] KYAUTA: *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGE WA DA WANNAN SAIWOWIN ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN*. *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* . *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 56 Abba yayi sallama ya shiga falon ta amsa ya nemi guri ya zauna kusada ita. Bayan sun gaisa yake ce mata "Malika kinga idonki kuwa a dare daya har kin zabge dan Allah ki cire damuwa daga zuciyarki, ita rayuwar mumini bata cika dole se ana jarabtarsa dan gwada imaninsa dan haka mu mayar da komai ga Allah kuma mu ci gaba da neman taimakonsa shi kadaine ze iya mana". Hawaye ne suka fara sakko mata cikin tsananin tausayinta ya kama hannyenta biyu yana cewa "Ki dena kuka, wadannan hawayen suna daga abinda yake qara dagula rayuwarta kiyi shiru kici gaba dayi mata addu'ar da kikeyi kullum in sha Allahu wata rana se labari kiyi haquri". Haka ya ringa lallashinta yana gaya mata kalamai masu dade harta samu ta tsayar da hawayen wanda sosai nauyin da qirjinta yayi mata ya ragu, a kullum Addu'arta Ubangiji yaci gaba da bata juriya akan al'amuran Umaimah karta kaita bango tayi mata baki. Seda Abban yaga ta samu nutsuwa kafin ya miqe yace zeje ya duba Saratu, Mama ta rakashi da ido, shikansa tasan qarfin hali kawai yakeyi. Yana fita ta mayar dakai taci gaba da jan carbinta. A tsaye ya tarar da Anty Saratu tana cire Hijabi alamar lokacin ta idar da sallah. Ya nemi gefen gadonta ya zauna, seda ta ninke hijabin kafin itama ta zauna tana gaishe shi. "Jiya har nayi bacci shiru baki shigo ba" ya fada kasancewar ita ce da girki, seta yi murmushi kadan tace "Ina nan jiran baqinka su tafi bansani ba bacci ya kwashe ni". Kallonta yayi shima yayi murmushin, Saratu kenan bata san Mama ta gaya masa a gabanta Abdullahi yayi mata tijara ba. Yasan zancen ne bata so a tayar dashi shiyasa tayi masa alaye da cewar bacci tayi se ya miqe yana cewa "Idan da akwai dumame ki kawo mun yanzu zan sha magani, jiya ban samu naci abinci da daddaren ba" ya juya ya fice daga dakin. Kallon tausayi ta rakashi dashi, tun jiya Salman ya labarta mata abinda ya faru ta dade tana ta''jibin taqadaranci irin na Umaimah tana kuma tausayawa Mama dan itace babbar abar tausayi ma sama da Abban. Dan ma shidin ya kasance me shiga lamuran iyalansa shinr sauqin da take samu, da ace tayi katari da irin iyaye Mazan nan da sanda yaro yayi abin kirki yake nasu, duk wata rigima ko damuwa ta yaro uwarsa ta shafa qila da yanzu qasa ta dade da rufe idon Maman dan ba zata iya da baqin cikin Umaimah ita kadai ba. A iya zamansu sama da shekaru Ashirin idan ka cire sabani na yau da kullum da dole a same shi tsakanin mutane idan aka zauna bazata ce yau ga wani mugun abu da Maman ta tabayi mata a matsayinta na kishiyarta ko wani ba a zahiri, haka har badininta zata iya shaidarta da babu komai a zuciyarta se Alkhairi ba kuma ta nufin kowa da sharri ballantana ace ko wani mugun abu da take aikatawa ne take ganin sakayya akan Umaiman, kawai ta qaddara kalar tata jarabawar rayuwar kenan tunda kowa da akwai ta inda Allah ya rage shi ko yake jarabtarsa sedai suyi fatan Allah ya shirya Umaimah in tana da rabon shiriyar su kuma ya qara musu juriya. Bayan La'asar bisa Umarnin Abba badan Maman taso ba ta shirya suka tafi mayar da Umaiman kamar yanda sukayiwa Waliyyan Khalil din alqawari. Daya kira Baba Abdullahi shi daya ce ta zauna goben ze mayar da ita cewa yayi in yaje Allah tsine masa, daman dan ya samu ya sauke fushinsa yasa ya hana tafiya da ita yanzu kuwa ko banza zata koma da tabon marinsa gidan Khalil. Dariya abin nasa ma ya bawa Abba, haka suka kama hanyar gidan qarfe biyar suka isa, a qofar gidan suka tarar da Khalil tareda abokinsa Nasir Tsohon Malamin su Umaiman ya kawo masa ziyara ze tafi ya fito rakashi. Cikin ladabi yayi musu sannu da zuwa, suka gaisa da Nasir kafin yaja motarsa ya tafi yana jimanta abinda Khalil din ya gaya masa Umaimah tayi. Yanzun ma yana kallon yanda taja hijabi ta rufe fuskarta ruf kallonta yake mamakinta na kashe shi gaba daya ji yake kamar shine silar janyowa Khalil din wannan tashin hankali, da beje gurinsa ba ranar da beganta ba. Qila da yanzu ya auri wata matar yana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. A falon Hajiya rasa inda zata ajiye su tayi murnar dawowar Umaiman da kunyar Iyayenta duk suka dabaibayeta. Anty Amina, Jamila da Jalila da suka tarar a zaune suka gaishe su kafin gaba daya suka miqe dan su basu guri. Dakin Habiba suka shiga, Jalilah ta tabe baki tace "Ai dole su maidota dan na tabbatar su kansu zaman ta addabarsu zeyi haba yarinya kamar jikar shaidan" "Kedai Jalila kin fiya daukar dumi, tunda Mijinta yace ta dawo ai dole ta dawo nasan baze wuce sunzo su qara bada haquri bane kawai amma duk mugun halin da ai iyayensa bazasu gujeshi ba" cewar Jamila se Jalilan ta sake cewa "Banda dai me irin halin matar Khalil, kana zaune ta jefaka a masifar da za'a kulleka a kurkuku haba ai wallahi Khalil dai beyi sa'ar aure ba kwata kwata kuma wallahi bari a nutsa, ko bokan kan dutse ne yake mata tsafi qarewar bin malamai se mun karya alqadarinta Khalil yayi aure dan bazan zuba ido ina kallo ta kashe mun dan uwa a tsaye ba haba". "Rigimar gidan Khalil dai in kika shiga ke zakiji kunya, kuma ma keda yar dakin taki ina ta kinfi kowa shigar mata idan anje gidan tawa mutane iskanci kice tsokanarta sukayi? Qiri qiri ta daki Lubnan Kaduna amma keda Hajiya kuka daure mata qugu wai rashin kunya tayi mata ni wallahi tun sannan nasan bata da mutunchi in ba haba daga zuwan baquwa dangin Mijinki ki kamata da duka ai kome ta miki kya jira Mijin yazo ya dauki mataki amma gata isashshiya to ai yanzu da abin yazo kan kowa kwa kiyayeta" Anty Amina ta fada. A can Falon Hajiya kuwa bayan sun gaisa Abba ya shiga bawa Khalil harda Hajiyar haquri akan abinda ya faru, Hajiya ta tare shi da cewa "Haba Alhaji, ai mune ya kamata mu bada haquri dan mu mukayi laifi. Ai dukiya bata fi lafiya ba kuma shima na nasa fada sosai akan abinda yayi be kyauta ba duk neman da yakeyi dan su wa yakeyi? Badan dai itan da Yayanta bane kuma dan an rasa wani abu shikeban se yace zeyi fushi da hukuncin Allah bayan ba laifinta bane? Abu in rabonka ne kana kwance ze same ka in kuwa ba nakan bane ko ka saka a baki se kayi amansa balle kuma abinda tun farko a ka qullo shi ta sigar yaudara Allah nema ya kama shi yaga nufinsa nason cutar da yarinyar mutane ya hana qulluwar abun". "Maganar gaskiya Hajiya abinda tayi ko kusa da daidai beje ba kuma mutum me cikakken hankali baze ringa tunani irin na Umaimah ba. Sannan Hajiya irin wannan goyon bayan da take samu a gurinki shiyake sakawa take raina Mijinta take masa duk iskancin data ga dama dan tasan zaki tsaya mata wanda ba daidai bane. Ni na haifi Umaimah nafi kowa sanin halinta zuma ce ita seda wuta ake cinta dan haka na roqeki Hajiya da ki dubi Allah ki ringa tsawatar mata idan tayi ba daidai ba. Idan ba zaki iya ba ki bar Khalil ya dauki matakin daya dace akanta ki dena dakatar dashi. Hajiya Alkhairin Umaimah kawai kika sani na yarda kuma kina Qaunarta dalilin daya sa kike kasa hango duk tarin laifin da aka ce ta aikata amma a Yanzu Khalil Shi yake zaune da ita, koni bazan gaya masa Umaimah ba a yanzu tunda ta fita daga hannunmu shi yake tareda ita. Duk wasu mugayen dabi'u da take koya a gurin qawayen banzan da take mu'amala dasu ya sani dan haka idan yace ta masa abu ki yarda ki kuma kirata ki tsawatar mata saboda kin fimu kusa da ita a yanzu" Mama ta fada se Hajiya tayi shiru gaba daya jikinta yayi sanyi. Gani takeyi kamar Maman tana nuna cewar cutar Umaimah take ta hanyar qin nuna mata gaskiya tabi bayanta a koda yaushe wanda ita tsakaninta da Allah har a yanzu rashin kyautawar ta data gani bata kai irin yanda suke zuzuta abin ba. Tana yi mata uzuri saboda ta kasance itama a lokacin da take ganiyar quruciya kamar ta Macece me tsananin kishi sedai ko kwatan abinda Umaiman takeyi bata aikata ba dan ita nata kishin baya ko barinta ta kula Mijin ballantana wadda yake tareda ita. Lokacin Babansu Khalil din ya auri Mahaifiyar Jamila wanda auran gaba daya sun yarda qaddara ce da rabon samun Jamilar harta rayu shekara daya tareda Mijinta ta rasu a yayin haihuwar Jamilan magana bata taba hadata da ita ba, haka shima Babansu Khalil din, daga randa Fatiman ta tare ta raba shimfida dashi seda suka kwashe tsayin shekara biyu har bayan rasuwarta kafin ta iya danne zuciyarta ta karbeshi a matsayin Miji shiyasa ko kadan bata ganin laifin Umaimah dan tasan menene kishi, ta san zafinsa da abinda ze iya ingizaka ka aikata idan har bakayi takatsantsan ba. Har suka tafi jikin Hajiya a sanyaye yake, seda ta rakasu ta dawo kafin ta kalli Umaimah da tunda suka shigo ta rabe a jikin kujera bata motsa ba. Maganganun da Abba da Maman sukayi mata a hanya ne suketa nuqurqusarta, nasiha ce me ratsa jini da jijiya sukayi mata a hanya har suka iso gidan. Idan da ace kunnenta najin magana ne daga lokacin ko kallon banza ba zata sake iya daga ido tayiwa wani ba albarkacin roqon da iyayenta sukayi mata na ta tausaya musu ta zauna lafiya a gidan auranta. Kusada ita Hajiya ta zauna tareda dafata Umaimah ta dago fuskarta data canza kamannin saboda marin Baba Abdullahi idonta ya kawo kwalla Hajiya tace "Subhanallahi, wa yayi miki wannan aiki haka?" Seta saki hawayen suka fara zuba, cikin tausayi Hajiya tace "Ki dena kuka kinji komai ya wuce yanzu tunda dai gashi kin dawo. Dan Allah ki koyi haquri Umaimah duk abinda ya faru tsakaninku kizo nan ki gaya mun kar ki dauki hukunci a hannunki dan kinga dai har iyayenki sun fara ganin ni nake goya miki baya kina abinda kika ga dama ina ga sauran mutanen gari? Yanzu ki tashi maza kije dakinki kiyi wanka ki huta babu komai in Allah ya yarda". "Toh Hajiya Amma Khalil be haqura ba, kinga fa ko kallona beyi ba tsoro nakeji kar na koma ya sake yi mun wani abun ni dai zan zauna anan har zuwa sanda ze sakko daga fushin Hajiya" Umaiman ta fada tana kuka. Hajiya tayi murmushi kafin ta kalli bangaren da Khalil ke zaune bayan ya dawo daga rakiyar su Abban tace "Ki rabu dashi babu abinda zeyi miki ko kallon banza ya sake yi miki a cikin gidan nan sena saba masa balle yace ze taba lafiyarki. Maza share hawayenki ki kuma cire damuwar komai daga ranki kodan saboda halin da kike ciki, ni se naga cikin ma ya rage girma gaba daya ma kin rame da alama bakya cin abinci, bari na kawo miki Tuwo maza kici kiyi wanka cikinsu Jamila wata ta raka ki Asibiti su sake dubaki dan bazan ma hadaki dashi balle kuje ya ringa miki muzurai". Yanda kasan gunki haka yayi musu bema nuna alamar yaji abinda Hajiyar take fada ba balle ya tanka. Laptop din dake kan cinyarsa kawai yake dannanwa amma tunaninsa yana kan abinda Abban Umaimah ya gaya masa yanzu. "Idan ka gaji da halinta babu me takura maka Khalil ka sawwaqe mata ni na haifi Umaimah idan kuma da ace kaine a matsayin Dana tabbas bazan goyi bayan kaci gaba da zama da kafaffiyar mace mara jin magana irinta ba. Ka bawa zuciyarka damar yin tunani in har kaga da cutuwa a zamanku ka sawwaqe mata kawai kowa ya huta" nazarin maganar yakeyi tausayin dattijon yana sake shigarsa. Sukam dai tasu jarabawar kenan kuma ze cigaba da haquri da ita saboda su zataci albarkacin su da kuma na Yaran dake tsakaninsa da ita amma wallahi da ace be haihu da Umaimah ba a wannan gabar da tuni ya sallameta dan be tabajin ta fitar masa a rai duk wani abu nata yayi masa baqi ba se a wannan karon, ya kuma tabbatar babu wani abu da zata sakeyi da ze wanke ta a idonsa ya dena tuna abinda tayi masa. Jin Hajiya zata dame shi ma dan se magana take tana sako sunansa a ciki ya saka ya tattara ya bar gidan gaba daya, su Jalila ma dai datayi musu zancen daya daga ciki ta raka Umaimah Asibitin gaba daya zamewa sukayi kowacce tace tana da uzuri suka yi tafiyarsu gaba daya. Qarshe se ita da kanta ta rakata bayan tayi wanka sabon Driver da Khalil ya daukarwa Hajiyan saboda Khalifa ya koma makaranta ya kaisu. Likita ya dubata ya tabbatar musu da komai lafiya cikin kuma daman tun wancan karon ya sanar musu da yuwuwar ya qara lokaci akan lokacin daya kamata ta haihun a farko saboda jinin data zubar ze iya sakawa ya koma baya ga rashin nutsuwar da take ciki zata iya affecting cigaban girman jaririn dan haka dole seta haqura da duk ma abinda yake sakata damuwar kodan lafiyarta data abin cikinta. Ya rubuta mata yan magubgunan da zasu taimaka mata yace taje taci gaba dasha daga nan suka kama hanya tsabar daurewa qarya Ass Hajiyan harda saka Driver ya kaisu gurin da ake siyar da kayan maqulashe ta siyowa Umaiman da sam bakinta babu appetite. Tunanin yanda zata kwashe da Khalil kadai ya saka jininta yana neman hawa, idan ya kuma maimaita mata irin waccen shaqar ta tabbatar kafin azo ceto ta margaya ta yuwu ma ajaline yasa su Maman suka dawo da ita gidan ganin qarshe ta musu toh Allah ya jiqanta kawai. Tas ta tarar da bangaren nata dan hatta da dakinta an zuba sababbin furnituresda suka fi wanda ta fasa kyau da tsada dukda ba'a gaya mata ba. Ruqayya ta kwalawa kira ta hau saman cikin rawar jiki ta sake gaisheta, Umaimah ta tambayeta yaushe aka saka kayan nan tace dazu da safe. Sosa kai ta shigayi cikin son amayar da gulmae dake cikinta tace "Ai tun jiya da Alhaji ya sanarwa Hajiya yau zaki dawo muna daga dakin Furera na jiya tana ce masa se ya saka a kawo miki sabon gado a saka. Yace baze siya ba, kinga rigimar da suka kwasa kuwa? Kai gaskiya Hajiya kinyi sa'ar uwar Mini matar nan tafi sonki ma inaga akan dan nata har cewa fa tayi zata saka azo a kwance nata gadon a saka miki tunda baze siya ba shine fa Alhaji hankalinsa ya tashi ganin tana neman tayi kuka yace ze siya. Wallahi Gadon ma ita ta zaba dan da safen tare mukaje wani kanti aka siyo kusan Miliyan nawa in gaya miki qarshe ma ita ta cika kudin dan abinda ya bayar be isa ba tasa aka zuba miki su". Hannu kawai ta dagawa Ruqayyan akan taje ta zauna bakin gadon tana shafa katifar kamar wadda bata taba ganin ta ba se yau zuciyarta fal tunanin irin wannan Qauna da Hajiya takeyi mata. Turo qofa akayi da qarfi ta zabura dan a zatonta Khalil ne sega Mu'ayyad ya shigo da gudu Bibi na binsa a baya suka fada jikinta gaba daya suna ihun murnar ganinta. "We missed you Mummy kullum muka cewa Daddy ya kaimu gurinki se yace gobe zaki dawo har na gaji da irga gobe" Mu'ayyad ya fada yana nuna matan goben daya irga da hannunsa. Qara jansu jikinta tayi tana murmushi dan itama tayi kewar yaran nata sosai tace "To gani na dawo ai shikenan?" "Yes Momy, meya samu face dinki it looks scary?" Ya sakw fada yana shafa fuskar tata da duk ta fita a kamanni ta swta riqe hannunsa kawai tayi murmushi dan bata san me zata ce masa ba, "Where you involved in an accident?" Ya sake jefa mata wata tambayar, se kawai ta daga masa kai dan Mu'ayyad wayo ne dashi idan bata amsa ba ya ringa tambayarta kenan, saurin dagowa tayi jin muryar Khalil a dake yanayiwa yaran magana akan suje su kwashe kayan da suka zubda a falo. A firgice ta kalle shi dan bata ji shigowarsa dakinba kodan qofar a bude take shi yasa. Seda yaran suka fita kafin ya taka a hankali har ya isa gabanta, zuciyar Umaimah dake bugu kamar zata daka tsalle ta fito saboda tsoron yanayin fuskarsa. Tunda take dashi bata taba sanin ya iya hada fuska irin haka ba gaba daya se taga ya sauya mata ma tamkar ba Khalil dinta da koda yaushe idanunsa suke cike da bege da shauqin soyayyarta ba. KHALIL Kallon yanda ta firgita da ganinsa yakeyi daga inda yake tsaye yana jiyo yanda take fizgar numfashi tana dawo dashi da sauri da sauri kamar wadda Miciji ya ritsa. Kallon salihar fuskarta yake wadda take yaudarar mutane da ita ciki harda Hajiyarsa da ya rasa me Umaimah take mata da ta kasa ganin laifinta. A cikin fa wannan marrar data ja masa muguwar Asara Hajiyar ta tursasashi siya mata Gadon Miliyan daya, akan yace baze siya ba Hajiyar ta nemi zubarda hawayenta. Batayi masa kuka bama yana ganin ta kansa a hannun mace inaga tayi dolensa ya zare kudin ya bayar baqin ciki kamar ze qumeshi ya mutu. Wato tukuicin Asarar data janyo masa ya bayar yanda gobe idan ta tashi zata jijjigo wanda yafi wannan toh wallahi bataci banza ba, Hajiyar na fita ya dauki motar da Umaiman take hawa ya fita da ita ya siyar ya mayar da kudinsa garda riba. Da batayi masa baqin ciki ba ba Gado ba ko gida take so seya gina ya mallaka mata acikin abinda ze samu daga aikin da zeyi amma yanzu kuwa gadai gidan nan ta dawo ta zauna zata gane shayi ruwane za kuma tasan ba Lusaranci bane yasa yake dauke kai akan duk abubuwan da take masa a baya, tunda haka ta zaba yanzu zaman ze chanza zata san cewar shi Khalil ba kanwar lasa bene ba. Juyawa yayi ya fice daga dakin Umaimah ta saki ajiyar zuciya ganin ya kullo mata qofa kafin ta miqe dakyar ta shiga bandaki saboda fitsarin daya matsota na tsoro, jan qafarta kawai take danhar sannan basu gama sauka daga kumburin da sukayi ba. Shirin bacci tayi gaba daya, seda ta leqa ta kira Ruqayya ta tambayeta ina yaran tace sun tafi gurin Hajiya da Yallabai kafin ta koma dakinta ta kwanta bayan ta jaddada mata ta tabbatar ta kashe komai kafin ta kwanta. Bata zaton zataji dadin me aiki ba se yanzu, haka ta raba dare tana sake saken sanda ya dace ta bawa Khalil din haquri har bacci ya kwasheta a sabon gadonta. Washe gari kafin ta yi wanka ta shirya ma Khalil ya fice daga gidan, dan haka data fito kai tsaye dakinsa ta wuce da niyyar zuwa ta gaida shi tunda tasan a yanzu dai baze shiga dakinta ba kamar yanda suka saba. A kulle taji qofar dan haka ta shiga kwankwasawa ko daga ciki ya rufe, Ruqayya data hawo saman da kayan share ta gaisheta kafin tace "Aiko ya fita Hajiya" "Ya fita?" Ta maimaita a zuciyarta tareda tsurawa Ruqayyan idon tana mamakin ya akayi tasan Khalil din ya fita, kamar tasan me take tunani tayi saurin cewa "Ina kitchen naji an bude qofa dana leqo se naga shine na koma, ga abin kari canna gama hadawa nan za'a hawo miki dashi ko na bari a qasan?" "Ki kawo mun nan" ta bata amsa kafin ta juya dakinta. A nan falon saman ta karya kafin Ruqayyan ta gama gyaro mata dakinta ta dawo falon ita kuma ta koma ciki. Tun zuwanta daman Anty Laure ta zayyana mata ayyukan da zata ringayi, gyaran gidan gaba daya banda dakunan Khalil, Anty Lauren ke musu girki yau kuma da bata nan yasa tayi karambanin yi tunda kusan tasan me suke karyawa dasu da rana ko dare ne taga tana tambayar Umaiman abinda za'ayi. Umaimah ko kan gado ta koma ta miqe gaba daya bata jin dadin komai, so takeyi ta kira Mama ta bata haquri amma bata san inda wayarta take ba dan haka ta tashi ta fito daidai Ruqayyan ta fesa Airfreshner ta dakata tana tambayarta ko akwai abinda take da buqata ne? "Dakin da na zauna a qasa zaki duba mun ko wayata tana nan" ta fada mata se Ruqayyan tayi saurin cewa "Tana nan kuwa, jiya da mukayi gyaran gidan na ganta se nasaka miki cikin drawer bari a dakko" da rawar jiki ta sauka qasa, Umaimah ta bita da harara, bata zaton zasu shirya gaskiya dan da ganinta zatayi tsugudidi ga shegen rawar jiki. Abinda yasa ma ta yarda da zamanta dan ta iya aikine kuma tasan ko mi maitar Khalil babu abinda zeyi da wannan kallo ma bata ishe shi ba sannan a yanzu tanada buqatar mataimaki kafin ta haihu ta komo hayyacinta sannan ne zata tantance tana da buqatarta ko Aa. Wayar ta kawo mata harda chaja ta koma cikin dakin ta jonata a chaji dan a kashe take, bayan ta kunnata ta fara dubawa, ta tarar da tarin missed calls na Jama'arta, Safinah ta kirata yafi sau a qirga ga Text messages tana tambayar lafiya idan ta kira bata dauka da alama duka kafin wayar ta mutu ne akayi ta kiran da messages din. Maman ta fara kira, yanda ta amsa mata ya qara sanyaya mata jiki bata ma bata damar yin wata magana ba daga gaisuwa ta dakatar da ita tace se anjima. Seta maida kiran kan Abba, shikam ya amsa mata a dan sake har yana tambayarta Khalil tace ya fita. Nasiha ya qara dora mata kafin sukayi sallama yana saka mata Albarka wannan yadan sanyaya mata rai ta qudurce zatayi ta kiran Maman kulkum har se itama ta haqura ta sakko. Maman Asad ta kira, missed calls hudu tayi mata amma taqi dagawa na qarshe ma rejecting tayi hakamya tabbatar mata da tana kallo dagawar ne batayi niyya ba seta aje wayar kawai dan ta tabbata tunda Hajiyayye bata dauki wayarta ba to gaba daya sauran ma bazasu dauka ba alamar labari yaje musu kenan daman kuma har ta gama jinyarta babu wadda tazo gidan a cikinsu ai shikenan babu dai yanda suka iya da ita duk fushinsu dole suyi su gama su sakko. Khalil dai dagaske yake shareta a gidan dan daya dawo da yamma ma tana zaune a falon saman tayi masa sannu da zuwa bata zaton ya amsa dan bataji ba ya wuce dakinsa ya bude ya shiga, data bishi ta kwankwasa kamar su da wani suke zaune a gidan yake tambayarta wai waye, abin ya qona mata rai amma ta daure tace Umaimah ce. Seda ta kwashi minti biyar a tsaye tana jira ya bude amma shiru, bata haqura ba ta sake kai hannu da niyyar bugawa se gashi ya bude yayi bake bake a bakin qofar tareda tsareta da ido. Duk seta duburburce ta kasa ce masa komai ganin tana bata masa lokaci yasa ya juya ciki ya sake rufe qofar tana ji ya murza muqulli wani abu ya tokare mata wuya, ta tsani wulaqanci a rayuwarta koda ace laifi ta masa ai be kamata yayi mata haka ba se ya bari ta shiga yaji abinda ya kawota ko yana nufin a bakin qofar zasuyi magana. Komawa tayi ta zauna tana cika da batsewa, kusan minyi Ashirin ya fito ya sake wanka daidai nan kuma aka fara kiraye kirayen sallar Magriba. A zatonta sallar zeje ya dawo, dakanta ta shirya masa abincin data saka Ruqayyan ta dafa anan falon sama ta koma dakinta bayan tayi sallah ta sake gyara fuskarta da tana nan har sannan da yatsun Baba Abdullahi duk sanda ta kalla seta masa Allah ya isa kuwa. Haka ta kasa ta tsare a falon tana jiran shigowarsa. A gurin tayi sallar Isha ta kunna Tv suna kallo da yaran da suka shigo shiru shiru har Tara tayi me aikin Hajiya Basira tazo kiran yaran suje su kwanta Khalil be shigo ba. A qasan carpet din da take zaune taja pillow ta kwanta saboda ta gaji da zaman, ga yunwa tana ji amma taqi cin abinci tana jiran Khalil, Fitsarin daya matseta nw ya farkar da ita daga baccin da bata san sanda ya dauketa ba. Falon duhu dundum an kashe dukkan fitilu harda Tv data bari a kunne. Wayarta data san ta ajiye a kusa ta shiga lalube, Allah ya taimaketa ta samota ta kunna agogo ta fara kallo qarge biyu da minti Ashirin na dare setayi saurin kunna flash light ta miqe dakyar ta kunna fitulun falon. Kayan abincin data aje ta kalla suna nan inda suke babu alamar an taba kenan ya shigo gidan kuma shi ya kashe Tv da fitila amma saboda wulaqanci ya kasa tashinta dan tasan da Ruqayya ce dole zata tasheta kuma ta kwashe kwanukan bama zata hawo ba dan ta mata iyaka da hakan indai ba ita ta kirata ba, ai kuwa zega rashin mutunchi indai abinda haka yace zasu tafi to su zuba su gani. Fitsarin ta fara zuwa tayi dole ta zuba abincin taci dan wata yunwa taji tana neman kada ita. A gurin ta bar kwanukan ta miqe tana shiga dakinta taji qarar bude qofa tasan kuma baze wuce shi ba, kamar ta fita taga meya fito dashi se kuma ta haye gado saboda baccindaya cika mata ido. Tun daga ranar haka suka ci gaba da tafiya da safe kafin ta tashi ya fice daga gidan duk sammakon da zatayi kuwa ba zata ganshi ba haka da yamma idan ya shigo tana zaune wata rana ya amsa in ta gaishe shi wata ranaya shareta sannan idan ya fita sallar magriba baya dawowa se tayi bacci daman tuni ta sawwaqewa kanta jiransa dan sau uku tana kwanan falo kuma zezo ya kashe fitila da Tv amma baze tasheta ba sedai da Asuba ta tashi jikinta na ciwo saboda kwanciyar qasa haka kuma ko ta taki sa'a sun hadu idan zata kwana tana masa magana baze kulataba haka abinci bata san inda yake ci ba, dan gurin Hajiyar kanta idan ya shiga baya dadewa gaisheta kawai yake yayi ficewarsa. Duk sanda ta shiga Hajiyar ta ringa tambayarta komai dai lafiya ko sedai tayi murmushi tace mata Eh, "Ki qara haquri, Khalil nada sanyin hali amma idan wannan zuciyar tasa ta motsa kafin ya sakko daga fushi ana shan wahala amma kuma daya huce shikenan komai ya wuce a gurinsa dan yana da yafiya shi" Abinda Hajiyan take gaya mata kenan sedai tayi murmushi kawai. BAYAN WATA DAYA Daga yanda yake tuqin zaka san cewar a gajiye yake, seda ya tsaya a hanya ya siyo panadol night dan kansa ciwo yake masa ga gajiya, so yakeyi yayi bacci sosai musammanda yake gobe Juma'a bazasuyi aiki ba, Site zeje kuma se bayan an sakko sallah. Wayarsa dake qara ya kalla yaga Umaimah ce take kira, a fili yayi tsaki kafin ya daga ya sakata a speaker beyi magana ba ita ta fara cewa "Ance se nayi scanning, kuma ga kudin test da akayi mun duka ba'a biya ba" ta fada a qufule, da irin muryar da tayi masa maganar ya mayar mata da tambayar nawane? Tace dubu goma, "Ok" kawai yace mata ya katse kiran, yana tuqin yana mata transfer, dubu biyar ya tura mata, ai ya sani scanning dubu uku ne test din kuma da take magana yasan qarya takeyi idanma anyi ga 2k nan ai baze wuce haka ba shikansa scanning din ai a cikin Antinatal bill dinta duka ya biya dan dai zuwan nata na yau ba ranar awo bace haka kawai da safe ta tsareshi da cewar bata da lafiya wai Ruwane yake zubo mata, bashi da lokacin tsayawa ya bata shiyasa ya bata dubu goma yace taje Asibitin shine tun safen bataga dama taje ba se yanzu kusan Magriba zata sake ce masa ya tura mata wani kudin. Tun bayan dawowar tata dai sauyi kadan aka samu a zaman nasu, yanzu yakan zauna a gidansa koda tana zaune a falon ze fito shima yayi sabgar sa dan yayi tunani babu dalilin da ze saka shida gidansa ta hana shi zama sedai ya fita yayi ta yawo a titi har lokacin kwanciya yayi kafin ya dawo dan haka ya canza, magana cedai har yanzu ba wata meyawa take shiga tsakaninsu ba se abinda ya zama dole ko kuma idan yaran suna tare dasu shine sukeyin magana kamar babu komai a tsakaninsu dan gudun karsu fahimci wani abu musamman Mu'ayyad da yake da shegen wayo ga tambaya. Tun daga bakin layin yake hango kamar Mu'ayyad da wasu yara suna buga Ball a tsakiyar layin, ransa ya qara baci akan yanda yake, tunda Hajiya ta tafi Gaya yaja mata kunne akan barin yaran suna fita waje, ya gaya mata ko wasa zasuyi karsu wuce cikin compound din gidan amma bataji shine yanzu ta kama hanyar tayi tafiyarta ta bar masa yaro yana garari a cikin layi, kwafa yayi tareda yiwa yaron horn, yana ganin motar Dadyn sa ya saki kwallon dayake bugawa ya tafi da gudu ya bude masa ya shiga. A mugun fusace ya taka burki daidai Qofar gidan, kallon Bibi dakw zaunw dare dare a cinyar Sammani yayi tana shan raken da shi da sauranmasu gadin gidajen da suka mayar masa da qofar gida Majalisarsu ta zama. Qarar taka birkinsa ce ta ankarar dasu dan sam basu ga zuwan motar ba suna kyalkyala dariyar labarin da Muttaqa yake basu. Ajiye yarinyar Sammani yayi jiki na rawa ya fara bude Get din Khalil ya fito daga cikin motar a fusace ya dauke Bibi da itama ta nufoshi ya koma motar yana ballawa Sammani da Abokanansa hararar da suka rasa ta mecece. "Karka kuskura na fito na tarar da kowa a qofar gidan nan, kaima idan ba zakayi aikin ba ka kama gabanka" Khalil ya gaya masa sanda yake qoqarin shigar da motar ciki. Yarsa a tsakiyar maza akan cinyar me Gadi, lallai Umaimah kuwa zata gane kurenta, besan ma for how long take sakar masa yarinya tana shiga cikin qarti ba, ita rashin sanin daidanta a komai ma gwada shi takeyi. Beko amsa sannu da zuwan da Ruqayya take masa ba ya rufeta da masifar akan me tabar yaran suka fita, kasa magana tayi har ya gama bambaminsa ya haye sama da yaran, tare suka sake sakkowa, tana rabe a gefe dan fadandaya shigo dashi yau dinya bata tsoro. Kallonta yayi yana sakin hannun Bibi yace "Gata nan, saura ki barta ta sake fita dake da Ita yau duk se kun gane kurenku a gidan nan useess kawai" ya finciki Mu'ayyad suka fita masallaci. Ita dai Ruqayya da ido ta rakashi tana tunanin ita dawa zasu gane kuren nasu, Bibin ko Uwar Bibin?? A compound suka ci karo da Umaimah tana fitowa daga mota, wani banzan kallo ya aika mata kafin ya miqa mata hannu yana cewa "Da izinin wa kika daukar mun mota, kinga Umaimah ki shiga hankalinki wallahi. Karki dauka sako sakon dana farayi miki na manta abinda kika mun ne a cike nakw dake kuma har yanzu ina kan duba abinda zanyi miki na rama karki dauka na manta" ya fada yana fincike muqullin hannunta. Kallonsa tayi ta riqe baki tace "Ikon Allah" kafin ta shige ciki ranta a dagule. Zuwan data shiryi yi Asibiti saboda ta samu kudi a hannunsa ne dan tunda ta dawo komai ya canza. Yar dubu dayar da yake bata ta cefane a kullum ta Allah dukda babu abinda take siya dan komai na amfani siyowa yake ya ajiye wanda ze ajiyu a Fidge ko Freezer ta saka wanda baya buqatar haka ta barshi a waje amma dukda hakan seya bata wai koda zata nemi wani abun girki da babu a gidan. Lokacin da suka tsohuwar unguwarsu Zubin Adashi take dasu, Adashin da bata tsinana komai dashi ba dana rance yake qarewa saboda sun rainata sun kuma maidata saniyar tatsa haka ta qaraci zubin sau daya ta taba dauka itama seda suka ringa bi me rantar dubu biyu dubu uku suka kashe. Bayan dawowarsu nan ne tayi hankalin adana kudin idan zataje gida ta siyi wani abu ta kai musu na neman Albarka ko ta basu kudin dan ada duk lissafinta be taba gaya mata tayi hakan ba a ganinta basu da buqatar komai, zata iya cewa wannan ce kadai dabi'a me kyau data koya gurin Safinah dan ita taga tana siyan abubuwa takai gidansu duk kuwa da cewar masu wadata ne sosai dan sunfi iyayen Umaiman ma to yanzu ko tunda ta dawo se a hankali kayan cefanen ma duk abinda be zama dole ba da ya qare be siyo ba. Shekaran jiya data ce masa Madara ta qare ce mata yayi su sha baqin Tea bashi da kudi, se dazu da safe ne da Bibi tasa rigimar zata sha madara ya bawa Sammani ya siyo mata Peak ta Sachet, abinda ba'a taba siya a gidan ba dan madara kafin Gwangwani yayi rabi ya kawo wata. Tana shiga Ruqayya ta shiga wassafa mata a yanda Khalil din ya shigo da abibda ya gaya mata, se a sannanta gane fushin da yake na an bar yara sun fita ne toh canya gane goya su yake so a ringayi ko yaya ita yanzu ya barta da tunanin yanda zata hado kudinda Safinah tace ta kawo. *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGE WA DA WANNAN SAIWOWIN ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN*. *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* . *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 57 Khalil kuwa be shigo gidan ba se bayan da suka idar da Sallar Isha. Bamgaren Hajiya ya wuce, Suna shiga palour kiran Mansur ya shigo wayarsa seda ya zauna kan kujera kafin ya daga wayar. Bayan sun gaisa Mansur yake ce masa "Abokina dan Allah idan babu takura akwai saqon da zan aiko dashi ta gurin wani abokin aikina da ze taho Nigeria zuwa wani satin, Magungunan Mama ne, kullum tasha na nan din cewa take ciwo babu sauqi shiyasa na aiko mata dasu ta gwada ta gani ko za'a dace da irin na nan din toh Habibu kuma yana Dutsin Ma sun kona makaranta ko zaka taimaka ka karba mata idanya iso danshi ba dan Kano bane besan gurare ba" "Babu damuwa, ka turamun da number sa idanya zo se na karba mata. Gaskiyar Mama ai dan nidai paracetamol kadai nasha na saudi na fahimci da banbancin ingancin magunguna tsakanin mu dasu, Allah dai ya kawo mana sauqi Nigeria amma komai namu se anyi ha'inci a cikinsa kana shan magani dan neman lafiya qarshe ya janyo maka wata lalurar". Hira suka dantaba kafin sukayi sallama yana kashewa kuwa lambar mutumin daya turo masa ta shigo. Da Yake ya sanar dashi be rigada ya iso Nigeria ba dan haka yayi saving zuwa randa ze iso din se ya kirashi kafin na ze masa magana a WhatsApp yaji ina ne masaukin sa idan ya iso Kanon. Yana ajiye wayar Hajiya ta sakko daga sama, fuska babu cikakkiyar walwala kamar yanda ya koma a gidan ya shiga gaisheta Dan Sosai Hajiyan ke takura masa da maganar Umaimah wanda shi kumabaya soshiyasa yanzu baya wani jimawa a bangaren nata yake fita ya gwammace yayi zamansa a palour Sama yayi kallo dan tuni ya saba da zaman kadaici ya dena Hira da Umaiman. Tuwo Hajiyar ta saka aka kawo masa, sanin babu lallai ya samu abinci a nasa gidan yasa sukaci shida Mu'ayyad yana ci Hajiyar na masa hira shidai Eh da Aa ne amsar sa harya gama yayi mata sallama ya fita dan Mu'ayyad ya wuce Habiba zatayi masa wanka ya kwanta. Da mamaki ya ringa kallon falon daya sha gyara se tashin qamshi yake, dukda dai Ruqayya na qoqari gurin gyaran gidan amma na yanzun daya gani na daban ne dan dazu daya fita sallah babu wannan qamshin ko kuma be lura bane oho. Tabe baki yayi ya haura saman, Mamaki ya sake kashe shi dan gyaran da akayiwa falon saman har yafi na qasa ga kalar turare me sanyi da qamshin da aka saka yana shaqarsa yaji gabbansa sun fara sanyi gajiyar daya kwaso ta hauro masa so kawai yake ya kwanta a kan kujera yayita shaqar daddadan qamshin. Qarasa shiga ciki yayi, yabi Kwanukan abincin da aka jera akan Table mat a qasa da kallo harda Jug din Zobo me shegen sanyi dan se diga yakeyi ya gani ga fruit salad a bowl an rufe da Clingfilm ya hadiye yawu qut saboda yanda ransa ya biya Sanyin zobon amma ya hadiye kwalamarsa ya wuce dakinsa yana mamakin yau kuma meya hau kanta ya sakata wannan aiki ita da tace bata da lafiya? Shi kansa gadon a lailaye ya tarar dashi an chanza masa Bedsheet se kawai ya wuce bandaki yana mamakin wannan sabon salo kuma na Umaimah. Matar da tunda tayi ta shige masa yana shareta na dan lokaci ta yakice shi itama ta watsar hidimar gabanta kawai takeyi ita ce yau harda gyara masa daki abinda rabon da tayi tun kafin tasan alaqarsa da Zahra. Da ruwandaya tarar ta tara masa ya sheqa wankansa me kyauya fito. Tsaf ya shirya cikin kayan bacci Farare Cotton marasa nauyi ya dauki wayarsa ya dawo falon dan yana so ya kalli labarai. Umaimah na zaune tasha kwalliya da doguwar rigar Material Light Pink me santsi dan haka rigar tabi jikinta ta lafe cikinta ya fito sosai a gaba ya mata kyau dan shi bema taba lura da yanda ciki ke mata kyau ba se yau din ko kuma wannan din ne dai oho. Fuskarta ya kalla data sha joda da Lip balm pink bakinta se qyalli yakeyi, wani abu yaji ya tsarga masa wanda rabon da yaji makamancinsa tun kafin ta janyo masa Asara se yayi saurin dauke kai daga kallonta ya wuce can kujerar gefenta ya samu guri ya zauna. "Sannu da dawowa, ashe ka shigo ina ciki banji shigowarka ba" Umaiman ta fada tana masa murmushi. Seya bita da kallo. Mamakinta ya sake kamashi amma seya kanne shima ya maida mata da murmushin yace "Yauwa, ai yanzu na shigo wanka kawai nayi". "Bari na zuba maka abinci toh" ta fada tana qoqarin kaiwa qasa se yayi saurin dakatar da ita da cewa "Aa, I'm full naci gurin Hajiya kafin na shigo". Yanda tayi da fuska ya nuna rashin jin dadinta amma ta daure ta tsiyaya Zobon a cup ta miqa masa tana cewa "Ga zobo toh nasan dai shi ba zaka ce ba zaka sha ba". Karba yayi ba tareda yasha dinba, haka kawai yau yakejin shakkar cin abinda ya fito daga hannun Umaiman, badan yana zarginta da yi masa wani abun ba sedai kawai chanjin fuskar tata a abinda be wuci awa biyu ba ya bashi mamaki, dole tana da wani shiri daya sakata aikata hakan. Ganin ya riqe kofin be sha ba ya saka ta tsiyayawa a wani kofin itama ta sha, Khalil dake kallonta yayi murmushi a ransa yace "Ta wanke kanta" kafin ya kafa cup din shima ya kwalkwale dan sosai zobon yayi masa dadi harda qara wani ya sake sha. Umaimah ta saki murmushin jin dadi ganin haqanta yana dab da cimma ruwa seta dauki Bowl din fruit Salad din ta bude ta saka masa cokali ciki ta miqa masa babu musu kuwa ya karba ya hau sha ita kuma tana masa hira babu laifi kuma ya biyeta yana amsawa dukda rabin hankalinsa nakan labaran da yake kallo. Agogon falon na buga qarfe goma ta miqe, Khalil ya daga kai ya kalleta, wani yumm yakeji a jikinsa daya rasa kona menene gaba daya neman rasa nutsuwarsa yakeyi. Da kanta ta ringa kwashe kwanukan tana kai su bakin qofar shigowa falon kafin ta kwalawa Ruqayya kira akan tazo ta kwashe su, tana tsaye a gurin har ta gama kwashewa tas tayi mata seda safe kafin ta waiwaya ta kalli Khalil da shima ita yake ta bida kallo tayi masa murmushi sannan ta shige dakinta. Ajiyar zuciya Khalil ya sauke yana gyara kwanciyarsa dan zaman ya gagareshi. Zuwa sannan ya gama fahimtar abinda yake faruwa dashi, wato Umaimah magani ta saka masa a Zobon nan kenan? Juye juye ya shigayi shi kadai kamar me naquda saboda wani azababben feelings da yaji ya taso masa. Daman can haquri yake yana dauke kai shine saboda mugunta yanzu zata janyo masa wahala. Yafi minti talatin yana malelekuwa tsakanin kan kujerar da qasan a zuciyarsa ya qudurce ze daure bazeje gareta ba dan har yanzu be tabbatar da ta ladabtu akan abinda ta aimata masa ba sannan ga wani ta qara, akan me zata cutar dashi ta saka masa magani a abinci? Ganin abin yana neman ya zamar masa babba yasa ya miqe dakyar ya nufi dakinta, dakyar yake iya daga qafarsa saboda wani mugun qullewa da ciwo da mararsa take masa daga ji maganin ba kadan ta saka masa ba ko kuma ba a iya zobon bane ta yuwu har fruit salad din ta zuba a ciki. A hankali ya tura qofar dakinta dake a bude, cak ya tsaya saboda jiyo muryarta da yayi da alamar waya takeyi tana cewa wadda suke maganar "Kin tabbata kuwa maganin nan zeyi aiki? Kusan awa daya fa har yanzu shiru ni banga yayi wani abu ba". Be san me waccen tace mata ba yaji ta sake yin tsaki tana cewa "Wallahi nima nasha gani nayi kamarbe yadda da zobon ba yanata juyashi a hannu shine nasha kadan gashi ni duk ya dameni ma wallahi", shiru ta sakeyi kafin tace "Bana son iskanci kedai ki tayani Addu'a na samu kansa dan nikam da gaji da wannan zama hala ta ko ina komai ya qulle mun ina zan saka raina naji dadi" daga nan sukayi sallama taci gaba da shafa man da takeyi da alama daga wanka ta fito. Fita yayi daga dakin ya dafe bango yana maida numfashi dan bayajin zeiya zuwa gareta kuma, Wato saboda biyan wata buqata tata yasa ta saka masa magani kenan bawai dan tana da buqatarsa ba to wacce buqatace haka? Ya tambayi kansa. Dakinsa ya koma dakyar ya kwanta kwanciyar taqi masa dadi, dole ya miqe ya dakko ruwa me sanyin gaske yasha ko zeji sauqin abinda ke damunsa ammaa banza ji yayi ma kamar qara masa akeyi. Miqewa yayi da niyyaryaje ya watsa ruwa ko ze samu Sa'ida Umaimah ta turo qofar dakin da sallama. Cura mata ido yayi zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri qamshin turarukan data saka suna sake rikita masa hankali a sannu ta tako zuwa inda yake duk yanda yaso ya yaqi zuciyarsa ta shareta amma ya kasa kafin ma ta qaraso ya janyota jikinsa ya shiga shinshinata kamar wani mayen kare be jira wani abu ba ya sunkuceta ko nauyin ta dana cikin jikinta beji ba ya direta akan gado kafin ya bita suka kwanta. Sosai suka gurji Junansu cikin tsantsar soyayya da kewar da kowanne yayiwa dan uwan nasa ga tasirin maganin data zuba masan yasa suka dade cikin shauqi har seda ta gaji ta fara masa kukan shagwaba kafin ya iya kyaleta. Tsam ya rungumeta a Jikinsa yana sauke numfashi. Yana son Umaimah tana kuma da matsayi na musamman a zuciyarsa saboda yanda take bashi nutsuwar daya tabbatar baze samu kamarta a gurin kowa ba se itan amma halin ta na kishi da rashin jin magana yake hada shi da ita. Tare suka kwana a gadonsa bayan lokaci me tsawo da suka dauka basu hada shimfidar ba, a daren kuma ma'auratan suka sasanta. Sosai Umaiman ta kwantar da kai ta ringa sake nanata ban haquri tareda tarin alqawarurrukan ta shiga hankalinta ba zata sake ba. Za kuma ta dage da Addu'a Allah ya maida masa da mafiyin Alkhairin abinda tayi masa sanadiyyar rasawa. Toh Khalil da Umaimansa dai se Allah haka ya karbi tuban mutuniyar ya kuma rungumi abarsa suka shiga shimfida sabuwar rayuwa me ciki da qauna da zaman lafiya. Sati daya a tsakanin ranar wata Juma'a da safe Mansur ya sake kiransa akan Abokin nasa ya iso yana Kano kuma a yau din ze wuce zuwa Kebbi garinsu dan haka yayi qoqari su hadu ya karbi saqon. Yana Office lokacin daya kirashin yana shirin fita duba wani Site, dan haka ya kira AbdulMajid babban yaronsa da yake aike ya bashi muqullin motarsa tareda number mutumin ya tafi ya karbo saqon shi kuma suka fita a motar company tareda sauran Engineers dinda zasuje Site din. Ranar cur a Site dinya wuni dan can AbdulMajid ya bishi da motar saboda baze koma Office ba. Guraren qarfe Shida ya kama hanyar gida yana tafe yana sakin qananan tsaki saboda muguwar Gajiyar da yayi ga Umaimah bata nan sun tafi gidansu wuni tace kuma se dare ma zasu dawo bashi da tabbacin tayi girki kafinta fita abinda ya qara bata masa rai kenan dan Yunwa yakeji. Yana tsaye a Traffic ta cikin center Mirror ya hango Baqar leda wadda yake zaton itace saqon Maman su Mansur. Tsaki yayi dan shaf ya manta da batun saqon ma kuma ko a dazunda sukayi waya seda ya sake jaddada masa akan dan Allah ya kai mata gaba daya wanda take sha sun qare,Hawan Jini ne da Sugar suke damun Maman dan haka ya juya akalar motarsa ya dauki hanyar gidan Maman. idonsa. Seda ya tsaya a hanya ya siyi gasashshiyar Kaza da Yoghurt manyan roba masu sanyi ya qara da Gwangwanin Madara da Milo, Sugar se buredi kafin ya kama hanyar gidan su Mansur. Sanda ya isa be tarar da kowa a qofar gidan ba majalisar da Habibu qanin Mansur yake hadawa da Abokansa duk basa nan jin ana kwada kiran sallar Magriba ya saka ya dauki ledojin ya kira wani Almajiri daya zo wucewa ya taya shi dauka suka shiga gidan dan qofar a bude take. A bakin qaramar qofar da za'a shiga tsakar gidan ya tsaya tareda yin Sallama. Gidan tsit kamar babu kowa a ciki ga duhun Magriba daya fara kawo kai dan babu wutar lantarki, daga bakin famfo ya hango kamar mutum tsugunne yana alwala dan haka ya sake daga murya yayi sallama suna shiga cikin gidan. Saurin jan Hijabi Humaira dake Alwala tayi ta rufe kanta kafin ta juyo tana wanke qafarta ta amsa sallamar tasa. Cikin hasken daya ragena rana Khalil din ya ga fuskarta, dukda be gane wacece ba haka suka qarasa shiga cikin gidan, ta qarasa Alwalar ta nufosu daidai nan aka kawo wutar Nefa haskenta ya gauraye tsakar gidan gaba daya. Daga dan nesa Humairan ta tsaya ttanayi masa sannu da zuwa. Khalil daya bita da kallo yana so ya tantance wacece ita dan dai qannen Mansur Mata biyu ne kuma duk sunyi aure, babu ma me qananun shekaru kamarta. Dauke idonsa yayi daga kanta yace "Mama tana ciki?" kafin ta bashi amsa Maman ta daga labulen palour ta tana cewa "Aa, Khalilullahi ne yau a gidan bismillah shigo ciki mana ka tsaya kamar baqo, ina ciki Alwala nakeyi nima". Sake kallon Humaira yayi wadda itama shidin take kallo kafin ya shiga falon Maman Yaron na biye dashi a baya da Ledoji, karba yayi ya sgiga dasu kafinya zaro dari biyu a Aljihunsa ya bashi ya karba yana godiya ya fita. Seya koma bakin famfon data baro ya shiga daura Alwala jin an shiga Masallaci yana gamawa ya fice daga gidan da sauri ya tafi masallacin. Se bayan da aka idar ya dawo gidan, a falo ya tarar da Maman inda ta idar da sallah tana lazumi yana zama aka dauke wuta. "Oh kaga mutanen nan se da duhu ya kawo kai da sun kawo wutar kamar gaske kuma sun dauke abarsu" Maman ta fada tana kunna fitilar data ajiye daga gefe sanin daman wutar babu tabbas. Khalil ya kunna Flash ligh din wayarsa shima kafin ya shiga gaisheta ta amsa tana tambayarsa Hajiya dasu Umaimah yace duk suna lafiya. "Bari a tada Gen din toh Mama, ya kamata ma dai a hada miki solar ki huta kawai" Khalil ya fada yana miqewa tsaye Mama ta ce "Aiko Allah sa fetur din ma be qare ba, daman Habibu ne duk yake wannan hidimar tunda ya koma makaranta kuma shikenan sedai in sun kawo wutar muga haske idan basu kawo ba zauna a duhun dan waccen salo salon ba iya tada injin tayi ba niko bazan iya yawon kiran yaran maqota ba kullum". Fita yayi ya wuce gurin injin, Seda ya bude ciki yaga babu mai ko kadan ya qare. Jarkan da Ake zuba man ya duba na cikin ma bashi da wani yawa ko an zuba baze wuce daren yau ba ze qare dan haka ya juye ya kunna Injin kafin ya fito da Jarkar a hannunsa. Humairah na tsaye a bakin qofar dakin Injin, cikin muryarta me sanyi tace "Daman Mama ce tace nakawo maka fitila ka haska kuma naga kama gama" be amsa taba ya wuceta ya ajiye jarkar a baqin qofa kafin ya leqa yana cewa Maman zeje ya dawo. Gidan Mai yaje aka ciko masa jarkar taf kafin ya sake komawa gidan. Seda yayi musu magana akan ze kashe injin ya qara Mai kafin ya kashe, full tank yayi musu ya ajiye ragowar kafin ya fito ya tsaya bakin famfo yana duba inda zega omo. Humaira ta fito daga kitchen dauke da Try data shiryo kayan abinci, fahimtar abinda yake nema yasa ta ajiye akan barander ta dawo bakin famfon ta dakko ledar klin ta miqa masa. Hannu ta miqo mata alamar ta zuba masa, cikin sanyin da kana gani kasan dabi'arta ce ta shiga zazzaga masa klin din. Khalil dayaji tamkar ya fizge ledar saboda yanda take laqai laqai ya dago da niyyar ce mata tayi sauri ta zuba daidai nan itama ta dago suka hada ido. Wata faduwar gaba ce ta ziyarce shi, abinda ya gaza fahimtar ko menene ya soki zuciyarsa se kawai yaja tsaki ya fizge ledar Klin din daga hannunta tana ganin haka itama cikin sanyi ta wuceta barshi a gurin. A falon Mama ta aje masa Abincin data saka ta hado masa ta wuce can kan dining taja kujera ta zauna tana jin qirjinta yana bugawa da sauri da sauri. Khalil ya gama wanke hannunsa ya koma falon, Mama ta gabatar masa da abincin be musa ba yaja Try din gabansa ya bude. Lafiyayyen Tuwon shinkafa ne fari qal yanda aka lailayeshi a leda kadai ya isa ya sa kayi sha'awar ci. Leda biyu ya ware ya saka a plate dan malmalar bata da girma kafin ya janyo flask din Miyar ya bude qamshin Miyar hade dana man shanun da aka bita dashi ya bugi hancinsa har seda ya lumshe ido ya bude. Shidai yana son abinci, both Local and continental dishes girki kuma yana daya daga cikin makaman da Umaimah take yaqarsa dasu dan bata barinsa da yunwa koda yaushe cikin yi masa girkuna masu dade da kashe kwadayi take. Sosai ya kwashi tuwon dan bayan wanda ya saka seda ya qara Malmala daya. Dukda yana fara ci ya fuskanci ba girkin Maman bane, yanda yake son abinci haka yake iya gane banbancin dandano musamman na abincin wadanda yake so yake kuma ci dan Maman ta iya abinci, zamanin quruciyarsu haka suka rabawa yau idan anci na Hajiya to gobe abincin Mama za'aci, be damu da son jin wa yayi abincin ba tunda ya masa dadi daga yanayinsa kuma ya tabbatar da tsafta da ingancinsa dan haka ya ware ciki ya kwashi abinci dan yasan ba samu zeyi ba idan ya koma gida ba dan Umaimah bata nan Hajiya kuwa yanzu idan ya shiga cin abinci ta ringa fada kenan tana ganin kamar har yanzu basa zaman lafiya da Umaiman ne shiyasa yake zuwa can neman abinci. A nan yayi sallar Isha, be bar gidan Maman Mansur ba se gurin Tara saboda hira da suka zauna tana ta tuna masa da lokacin quruciyarsu, ya kira Mansur ya hadasu ya sake yi mata bayanin magungunan seda Umaimah ta kirashi akan sun dawo taga baya gida kafin yayiwa Mama sallama ya tashi tafiya tana ta saka masa Albarka da godiyar siyayyar daya yiwo musu. A waje daya fita ya lura da an dawo da wuta, har ya bude motarsa ya kashe ya koma. Mama na tsakar gida ta fito shanya Hijabinta da ruwa ya zuba akai tace "Aa, Khalil ashe baka tafi ba mantuwa kayi halan" "Aa Mama naga an dawo da wuta ne shine nace bari na dawo na kashe muku injin, ina yarinyar take na nuna mata yanda ake kunnawa koda ace sun qara daukewa" Khalil din ya bata amsa. Seta daga murya ta kwalawa Humaira kira ta fito da sauri tana amsawa, Khalil ya bita da kallo ganin yanda ta fito itama ganin sa tsaye yasa ta juya da saurin gaske har tana shirin faduwa Mama nace mata tabi a sannu ta shige dakin. Hijabi ta zumbulo kan Doguwar riga me hannun vest dake jikinta dan ko dan kwali bata dauko ba ta fito amsa kiran Maman san sam batayi zaton wani ya shigo gidan ba. Kanta a qasa kamar tana gaban suruki ta qarasa tana cewa Maman gata. "Yayanki ne yace yace kizo ya nuna miki yanda ake kunna Inji da kashewa saboda wata rana, banda ma sakarcinki abinda sukace muqulli ake murdawa ina wahala a ciki" Maman ta fada tana nuna mata Khalil daya shige inda Injin yake se tabi bayansa tana tafiya a hankali. Itafa tsoron taba Injin take, tunda wani dan Unguwar yaje kunna inji yayi bindiga wuta ta kama har jikinsa ya qone sosai har yanzu be gama warkewa ba kusan fin shekara shiyasa take baya baya da sabgar Injin ko Yaya Habib yace taje ta haska masa daga baya take tsayawa. "Ki dago qafa Malama sauri nakeyi fa" taji muryar Khalil akanta se ta daga qafar ta qarasa. Daga bakin gurin ta maqale tana leqensa, Khalil kalleta ganin yanda ta tsaya kamar wadda take tsoron wani abu ya kamata be san lokacin da ya ja tsaki ba yace "Da Allah ki matso ko wani abun ne ze kamaki a nan din?" Cikin sanyin murya kamar me shirin kuka har tana jan qafafunta baya tace "Ni tsoro nakeji bana son zuwa kusa sa Gen" se kawai ya saki baki galala yana kallonta tsabar mamaki wai tsoro takeji Kura ne ko Zaki da zataji tsoronsa? Hadiye bacin ransa yayi yace mata "Ki matso babu abinda zeyi miki" ya fada yana kallonta. Seda ta zuba masa idanunta da suke masa wani iri idantana kallonsa kafin ta matsa kusa dashi din kadan a haka ya nuna mata inda ake Kunnawa da kashewa da inda zata danna wuta ta kawo kafin ya matsa yace tazo ta kashe Injin. Yana kallon hannunta har rawa yake ta murda muqullin ta kashe, Change over bashi da tsaho dan haka yace ta daga ta mayar dashi Nepa bata musa ba jikinta na rawa tayi abinda yace dan ya tsare fuska ganin hasken Nepa ya gauraye gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya Khalil ya kalleta yace "Ba gashi nan ba yanzun meya cijeki da zakice kina jin tsoro?" Bata amsa shi ba se kanta data sunkuyar tana wasa da zoben hannunta ya wuce ya barta a gurin bata ma lura ba seda ta jiyo shi yanayi Mama sallama kafin taja qafafunta ta wuce itama. "Seda safe" ta fada daidai ze gota ta ya fita, ya waiga ya kalleta kawai ba tareda ya amsa na ya fice daga gidan se tabi bayansa ta kulle qofar ta dawo tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi wani abun ta cire Hijabinta ta aje kan kujera tana kallon Mama tace "Mama shine baban Mu'ayyad ko?" "Oh ni Humaira gani daya kin riqe sunan yaron nan ni wallahi mantawa nakw shiyasa kawai nake ce masa ina su Alhaji amma ke caraf kin riqe, me yasa to baki tambaye shi yana ina ba?" "Tab ni tsoronsa ma nakeji wallahi Mama ina kallonsa se naji gabana ya fadi tun lokacin da yake zuwa gidan nan gun Yah Mansur" Humairan ta fada se Mama ta girgiza kai tace "Ai kowama tsoronsa kikeyi ke daman ki wuce ki debo abinci kici toh". Miqewa tayi ta zubo tuwon ta dawo taba ci tana yiwa Maman zancen Mu'ayyad wai tana so taga yaron yanzu tasan ya girma sosai. Tun lokacin da Umaimah tajewa Mama yawon arba'in Yaron ya shiga ranta sosai, tayita nacin suje gidansu da Mama amma taqi sedai suje gidan Hajiya. Kwanan nan ma da sukaje yiwa Hajiyar murnat sabon gida seda ta tambayi Habiba Mu'ayyad din tace yana gidansu Umaimah a sannan basu rigada sun tare ba ita yanzun ma seda tayi noyyar tambayar Khalil din kawai yanda ya hade rai ne yasa ta kasa masa magana se wani muzurai yakeyi kamat wanda akayiwa laifi. Khalil kuwa be qarasa gida ba kusan goma da rabi dan ya tsaya ya siyawa su Umaimah Gasashshen nama data ce ya taho musu dashi da fura. Hajiya ya fara kaiwa nasu har sun kwanta Habiba ta karba ta saka a Fridge yaran ma sunyi bacci kafin ya wuce part dinsu. A falon qasa ya tarar da Umaiman tana kallon wani hausa film a Arewa 24. Tayi masa sannu da zuwa bayan ta karbi ledojin daya shigo dasu ta wuce kitchen shi kuma ya hau sama dan yayi wanka. Sanda ya sako harta sake dumama Naman a Micro wave ta zuba a plate tana zaune tana shan fura ya zauna kusada ita ta miqa masa furar yace Aa a qoshe yake shi yaci tuwo a gidan Mama. Hira sukeyi dukda rabin hankalinta nakan kallon da takeyi seya tashi ya shiga kitchen ya dora qaramar tukunya akan Gas bayan ya zuba Spices din Shayi ya kunna. Yana tsaye yana jiran ruwan ya tafasa, haka kawai ta fado masa a rai, a cikin kansa yake jin muryarta me sanyi tana masa yawo yaja tsaki to akan me ze wani ringa tuna yarinyar kuma. A Mug ya juye ruwan bayan ya tasafa ya zuba sugar cubes ya koma falon, Umaimah data gama cin Namanta da fura ta hada sauran zata kai kitchen din ya fito se ya karbi farantin naman ta wuce ciki ta ajiye sauran kowanne a muhallinsa. Kadan yaci Naman ya shanye shayin gaba daya ji yake kansa yana neman yayi masa ciwo saboda wani tunanin shirme da kwakwalwarsa take kawo masa na yarinyar, meye hadin sa da ita da zata ringa fado masa a rai haka kawai saboda son ta hana shi sukuni. Har sukaje kwanciya ya rasa abinda yake masa dadi lokaci lokaci yakan saki tsaki Umaimah dake saka rigar bacci ta kalle shi tace "Wai nikam lafiya kake ta tsaki kai kadai"? Tsakin ya kumayi kafin ya nufi bandaki yana ce mata babu komai. Bata tsawwala ba dan yanzu kaffa kaffa take da duk abinda ze saka ya sake birkice mata. Tana kwanciya ko minti biyar batayi ba bacci ya dauke dan yanzu haka take data aje haqarqarinta a qasa bacci ze kwasheta har mamakin irin wannan bacci haka takeyi. Khalil kuwa bayan yayi wanka ya kwanta sam barci ya gagara zuwar masa. Abin daga haushi se ya koma bashi Mamaki irin yanda haka kawai yarinya ke neman shiga rayuwarsa ta hanashi zaman lafiya. Tsaki ya sake ja a karo na babu Adadi ya juya kwanciyarsa yana rufe ido, hotonta ya gani sanda ta fito babu Hijabi a jikinta. Doguwar qirar jikinta da babu wani abu da zece ya rudeshi da har ze saka ya ringa tunaninta tanayi masa gizo se ya miqe ya wuce bandaki ya dauro Alwala ganin ya kasa bacci. Nafila yayi tayi har seda bacci yaci qarfinsa kafin ya kwanta. Da Asuba dakyar ya iya farkawa daga baccin da yake cike da mafarkin Humairah. Zuwa yanzu lamarinya ya fara bashi tsoro tunani yakeyi anya ba Mayya bace yarinyar take neman lashe masa kurwa? Idanba haka ba meye darin gaminsu da zata zo masa a mafarki, to koma dai yaya ne yafi qarfinta ba zata ci galaba akansa ba ze kuma sake dagewa sa Addu'a da kuma neman magani yana zaman zamansa Mansur ya ja masa ko a ina ma suka samota oho dan ya ya tabbatar duk yanda akayi suma basu san Mayyar bace shiyasa suke zaune da ita. Haka yaje ya dawo daga masallaci yana ta ta'ajibin lamarin Humaira a ransa. Bacci ya sake komawa dan rashin kwanciya da wurin da beyi ba ya saka baccin be ishe shi ba. Da yake Asabarce ne tashi da wuri ba har gurin goma na safe. Umaimah bata dakin sanda ya farka ya dai ji qamshin turarukanta alamar anan tayi wanka ta shirya dan haka shima yayi wankan yana Jin cikinsa na qugin neman abinci. Falo ya fito, nan ya tarar da Mu'ayyad da Bibi suna cin Doya da Ketchup suka tashi da gudu suka fada jikinsa ya dagata sama ya riqe hannun Mu'ayyad din suka koma inda suka tashi. A tare suka gaida shi ya amsa yana tambayarsu Umaimah Mu'ayyad yace masa tana gurin Hajiya. Da kansa ya sauka qasa ya debo abin karyawa ya dawo suka qarasa da yaran. "Dady yau kacewa Anty Habiba ta kaini gidansu Humairah" Bibi data kwanta a jikinsa ta fada. Wani duka qirjinsa yayi jin sunan data ambata. Idan be manta ba haka yaji Hajiya ta kirata jiya nan take tunanin yarinyar da yayi yaqi dashi dakyar ya sake bijiro masa. Maganar da Mu'ayyad yakeyi ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi yana cewa "Dady itafa Humairan bata zuwa nan gidan sw Bibi ce kullum zata ce akaita shine Anty Habiba tace itama ta dena zuwa gidansu". Rigima Bibin ta saka akan se an kaita gidansu Humairan, sunan kadai da take ta maimaitawa faduwar gaba yake haifar masa. Umaimah ta shigo ta tarar dasu ita ta lallabata akan ta bari seda yamma akaita gidansu qawar tata yanzu basa nan da haka suka tattara suka wuce bangaren Hajiya. Kallon Khalil tayi da sam beyi kama da wanda yake tareda su ba, seda ta taba hannunsa kafin yayi firgigit kamar wanda ya farka daga bacci yana zare iso dan gaba daya wani tunani yakeyi da idan an rutsashi bazece ga abinda yake tunanowa ba. "Lafiya dai Abban Mu'ayyad, ko wani abu yana damunka?" Umaiman ta fada tana tsare shi da ido. Gefe ya kalla ya ce mata "Lafiya lau. Me kika gani?" Se ta sake zura masa ido tana qoqarin gano dagaske lafiyar yake ko akasin haka. Tun da Asuba ta lura kamar baya cikin nutsuwa haka daya koma bacci yanda ya ringa juyi har yana wasu surutai da bata gane abinda yake fada ya sake gasgata mata cewar bashi da lafiyar dan haka takai hannunta jikinsa tana cewa "Yanayinka ya nuna baka jin dadi, ko zazzabi kakeyi? Ya kamata kaje Asibiti kasan dai ciwonka yanda yakeyi maka babu dadi gara ka tareshi tunda wuri". Hannun da take taba wuyansa ya janye yana miqewa tsaye yace "Keni lafiyata qalau fa wane irin zazzabi ana zaune qalau" seda yayi gaba se kuma ya waigo yana kallonta yace "Yaushe ne naga kuna hayaqi keda yara kika ce na miyagune? Idan yana kusa dan kawo mun nima na turara". Dariyar da bata shiryawa bace ta kwace mata ta shiga qyaqyatata babu ji babu gani har tana zamowa daga kan kurar da take. Khalil ya shaqa yayi fam yana kallonta, to meye abin dariya kuma daga cewa ta bashi hayaqin Miyagu se kace wanda yace wani abu daban. Cikin bacin rai ya kalleta yace "Meye haka daga tambaya zaki tasani gaba kina mun dariya kamar wani mara hankali". Seda ta hadiye dariyar dukda haka bakinta a washe tace "To ai kaine da abin dariya, yau kuma da bakinka kake neman maganin Miyagu a ina kukayi arangama Allah sa ba a yawon zuwa Jeji Site suka qwamusheka ba. Ashe shiyasa jiya ka ringa surutai a bacci ai dana sani tun a sannan zan banka maka hayaqin suyi ta kansu" ta qarasa tana fashewa da wata dariyar. Tsaki yaja saboda takaici ba tareda ya sake ce mata komai ba ya shige daki abinsa. Tunani yakeyi da tace yayi surutai gaskiya ne ko wasa take masa? Amma dai koma yayin da gaske yasan ba abinda yake gani a mafarkin ne ya fada a zahiri ba dan idan haka, da yanzu ba dariya takeyi ba qila tashin hankali suke kwasa. Ranar haka suka wuni tana zolayarsa daya gaji ya fice ya bar mata gidan. Ta isheshi da magana ga uban hayaqi data bulbulo ta kawo masa harda dakko bargo wai ya rufa abin yafi ratsa shi. Haka ko ya biye mata yayi hayaqin dan harga Allah ya gama yarda da cewar Humairan mayya ce dan wallahi har gizo take masa yana ganin suffarta na giftawa a gidan. Sau kusan uku yana daukar waya da niyyar kiran Mansur akan yaji salsalar wacece ita ya kuma tambayeshi ko yasan suna da alaqa da Maita se ya kasa. Tsoro yake kar magana ta koma mata ta qarashi cinyeshi a dare daya qila ta hada harda Mansur din dan dai shi ya tabbatar da ba yar uwarsu bace wannan be kuma san inda suka kwasota ba. Yasan kusan dangin Mansur kaf na uwa da Uba, Bare barine baqaqe ita kuma wannan gata nan kamar Zabiya daman tunda yaga kyanta yayi yawa yasan da walakin wai goro a Miya. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 58 Wasa wasa tunanin Humairah ya samu gurin zama a zuciyar Khalil. Haka kawai take fado masa, dan shi hayaqin da Umaimah ta samu nayi tana faman banka masa a maimakon ta sakar masa kurwa ma qara damqe ta tayi. Cikin qasa da sati biyu tsabar tunaninta har rama yayi abinda yasa hankalin Umaimah ya fara tashi kenan harta kasa daurewa ta sanarwa da Hajiya halin da ake ciki dan da gaske ta yarda da cewar Mayun ne suka kama mata Miji. Hankalin Hajiya ya tashi itama, babu shiri ta bazama karbo masa rubutu dasu hayaqi a cewarta babu wasu Mayu sedai Mahassada da masu kambun baka ne suke neman sakashi a gaba saboda daukakar da Allah ya kawo masa. Khalil kuwa jinsu kawai yakeyi dan zuwa sannan lamarin tsoro yake bashi da gaske. Babu ranar Allah da ze kwanta ba tareda yayi mafarkin Yarinyar ba, kuma mafarki me nutsuwa dan wata rayuwa yake ganin suna shimfidawa irin wadda ko a sanda yake zirgillin Son Umaimah be hasaso musu irinta ba wannan dalili yasa ya qara mata Matsayi daga Mayya zuwa Aljana. Ya yarda kawai waddaya gani a Gidan su Mansur ba itace ainihin mutum dinba. Aljana ce ta bishi gidan ta samu damar dabaibaye tunaninsa ta jikin Humairan. Da wuri ranar ya tashi aiki dan baya jin dadin jikinsa da baze fita bama to da akwai wasu takaddu daya taho dasu gida jiya kuma a ranar zasu aika dasu wani waje shiyasa ya fita. Yana tafe akan Titi kamar bayason tuqin da yakeyi, gaba daya tunaninsa ya rabu gida biyu. Da niyyar tafiya gida ya kwanta ya baro office amma kuma se gani yayi ya dauki hanyar gidansu Mansur. Wani mugun Azalzalarsa zuciyarsa takeyi tun kusan kwana biyu yakejin yana son sake ganin yarinyar. Magana yake so suyi dan ya fuskanci wace kalar mutumce ita kafin ya dauki Matakin gaggawa saboda nema take ta zauta shi. Sau biyu yana kuskuren kiran Sunan wasu da nata gara yayiwa tufkar hanci ya roqeta ta fita daga rayuwarsa tun abu be tabarbare ba. Seda ya kai qofar gidan kafin ya tsaya kuma yana tunanin idan ya shiga me zecewa Maman? Bama wannan ba yana iya cewa gaidata yazo to ita kuma yarinyar ta yaya har ze samu damar magana da ita dan bayaso Maman tasan abinda ya kawo shi. Rasa mafita yayi wata zuciyar na gaya masa ya juya kawai yaci gaba da binta da Li'ilafi inda zuciyar dake mararin ganinta ta hana faruwar hakan dole ya saduda ya balle murfin motar ya fita Habibu dake zaune da Abokanan sa a Majalisa yana hangoshi ya taso dan daman tun tsayuwar motar yake kallonta kamar ta Khalil din amma beyi gaggawar tashi ba. Cikin girmamawa ya gaida shi ya amsa yana tambayarsa makaranta yace masa yazo kawo SIWES letter nr gobr zero koma Dutsin Ma din. Tare suka shiga gidan. A falon Mama ya zauna Habibu ya wuce dakinta da niyyar ya kirata sukaci karo da Humairah dake shirin fitowa itama taci kwalliya kamar me shirin zuwa Biki. "Ke ina Mama?" Habibun ya fada yana kallonta, cikin nutsuwarta tace "Ta shiga gidan Hajiya Asabe, Anty Ummi ce ta haihu an dawo da ita gida nima can zanje tace idan na gama abinda nakeyi bata dawo ba na bita". Kallonta yayi sama da qasa kafin yace "Shine kika ci uban kwalliya haka ke zaki gidan surukai ko?" Mayafin jikinta taja ta rufe fuskarta tana murmushi irin taji kunya kafin tace "Kai Yaya wanka fa kawai nayi ko so kake na fita busu busu dani?" "Yarinya in ma zaki dawo daga rakiyar wannan Cima zaunen tun wuri kiyi ga mutanen kirki nan suna Sonki kin zauna kina batawa kanki lokaci akan wanda bashi da Future" Habibu ya fada yana juyowa ya dawo gurin da Khalil ke zaune. Humaira ko yanda kasan wadda Habibun ya durawa Iyayenta Ashar haka ta bishi da kallo kafin kace me hawaye sun fara zarya akan fuskarta. Khalil da tun fitiwarta yake kallonta yana kuma sauraran duk abinda suke cewa wata irin faduwar gaba yaji sanda Habibun yake zancen tana bata lojacinta akan wani bayan ga masu sonta da gaske, ji yayi kamar an kwada masa guduma maganar ta dake shi sosai kafin ya farfado kuma hawayen da ya gani suna sunturi a fuskarta suka sake jefa Zuciyarsa cikin wani yanayi. "Yah Ilahi me yake shirin faruwa dani ne akan wannan yarinyar?" Ya jefawa kansa tambayar da babu me bashi amsa. Maganar Habibu daya ajiye masa ruwa da Lemo ta dawo dashi daga kallon daya raka Humaira dashi se sharar hawaye take kamar wadda Habibu ya mara. "Mamakin shagawabarta kake ko Yaya? Haka take fa yarinyar nan kallonta kayi idan taso sharri seta saka maka kuka dan ma Mama bata nan da yanzu ta hau sababi an taba mata Marainiya se kace akanta aka fara rasa Iyaye". Maida kallonsa yayi kan Habibun yace "Wacece ita?" Se Habibu ya zauna akan kujera yace "Yar gidan Baba Sani ce Qanin Mama na Jalingo, kasan ya dade da rasuwa da Mamanta tayi aure ta maida ta gurin Hajiya ita kuma kasan ba Lafiya ta cika ba shine Mama ta dakkota bata fi shekara biyu a nan din bama itama Maman tata ta rasu, shikenan fa Mama ta dauki Son duniya ta dora mata ni da nake Autan ma ta kwace mun Matsayi se yanda tace a gidan nan Mama takeyi idan kuwa kana so kaga bacin ran Mama ka taba Humairah shiyasa ta daure mata gindi take son ranta a gidan nan". A duk surutan Habibun babu abinda ya tsinta se Kalmar Marainiya data rasa uwa da Uba. Wani Tausayinta yaji ya masa rubdugu ya kanainayeshi. Tun Asalinsa shi daman me tausayin Marayune, ya taso cikin gata ya rasa Mahaifi sannan ya dandana dacin wannan rashin Mahaifin shiyasa idan yaga Maraya yake tausaya masa to sedai ita tausayin nata a na daban ya fado masa. Surutu Habibu yaci gaba dayi shidai jinsa yake amma babu tabbacin yana fahimta dan zuciyarsa tana ga son sanin Halin da Humairan take ciki, ta dena kukan ko tana ci gaba dayi? Sallamar Mama ce ta cece shi daga dan banzan surutun Habibu, har qasa ya durqusa ya gaidata Mama ta amsa tana tambayarsa daga ina haka da yamman nan, qeyarsa ya sosa dan besan me zece mata ya kawo shi ba. Saboda yanayin aiki be fiya samun damar leqa Maman ba sedai kamar in Mansur ya yi saqon da dole shi ze je da kansa in ba haka ba kuwa ko Alkhairi yayi niyyar yi mata kai tsaye Habibu yake kira ya bashi gashi yanzu ko sati biyu ba'ayi da zuwansa ba ya sake komawa dole Maman tayi mamaki ai. Sallama Humairah tayi ta shiga falon, ya daga kai ya kalleta ta dena kukan amma fuskarta a daure ta wuce can kusa da Maman ta zauna "Yawwa Habibu ka kyauta. Yanzu saboda Allah daman da nace maka da an fara Rijistar Jamb ka gaya mun ko baka gari zansa akai Humaira tayi shibe kaqi fada? Se yanzu a gidan Hajiya Asabe nake ji wai gobe za'a rufe. Ai kuwa yanzu zaka tashi ka kaita tayi" Mama ta fada se Habibu yayi saurin cewa "Nifa Mama ban san anfara bane kuma ma wannan yarinyar nagaya miki tayi qanqanta da zuwa Jami'a wannan shekarar gata da shegen sanyi a haka zatayi karatun" "Firinji ce qarewar sanyi. Na gama ganoka dai baqin ciki kakeyi baka shiga Jami'a da wuri ba tazo ita zata shiga da quruciyarta to koma menenr yanzu ka tashi ka kaita kar dare yayi ai ance ana samun Cafe yanzu" Mamanta sake fada tana hararar sa, Habibu ya kumbura baki yana hararar Humaira dake masa dariya daga nesa Mama ko se sababi take tana gayawa Khalil yanda Habibun baya so Humaira ta tafi Jami'a. Kamar wanda aka fizgi maganar daga bakinsa yace "Ta shirya ni se na kaita yanzu tayi". Da sauri ta daga kai ta kalleshi, Mama ko ta washe baki tana cewa "Aa daga zuwa ziyara se na hadaka da aiki shidin dai shi ze rakata ko baya so" "Aa Mama babu komai ai daga nan gida zanje ba wani guri ba se na kaitan tunda kinga baya son zuwa kar su tafi yayi ta yi mata fada a hanya ko ya sakata cike abinda bashi take so ba tunda beyi niyya ba" Khalil ya fada se Mama tace "Ai kuwa kamar kasan qudurinsa kenan, ina jinsu tace ita harkar zane zane take so wai bazatayi ba kamar shi zeyi mata karatun. Ni na rasa wannan hali na Habibu a inda ya dakko shi wallahi" "To haka kawai yarinya duk kin wani fi sonta akan kowa" Habibun ya fada cikin qunquni yana miqewa jin Khalil yace ze kaita. Tashi yayi shima yana cewa "Ta sameni a waje idan ta shirya" yabi bayan Habibun suka fita. A jikin motarsa ya jingina a zahiri kallon Habibu dake masa hira yake amma a badini ya lula cikin tunanin abinda yayin. Wai meya shiga kansa ne da yasa yake wasu abubuwa daya kasa gane kansu? Hangota yayi ta fito daga gidan sanye da Dogon Jilbab kalar dark blue daya qara fito mata da hasken Fatarta haka tsahonta ya fito sosai gabansa ya fadi, saurin bude motar yayi ya shiga yana cewa Habibu "Shigo muje" "Aa Yaya kuje kawai, ni kallon kwallo ma zamu tafi yanzu" Habibun ya bashi amsa yana shirin juyawa. Hannu ya saka a Aljihu ya zaro kudin da besan adadinsu ba ya miqawa habibu daidai nan ta iso gurin taja ta tsaya kanta a qasa kamar me qirga duwatsun gurin. "Se an ce ki shiga motar ko? To ki kwana a tsaye. A haka zakije kinawa mutane wanan salo salon wallahi Yah Khalil inta bara maka lokaci ka barota a can kawai kayi tafiyarka" Habibu ya fada yana harararta ita dai bata tanka masa ba ta kama murfin gidanbaya zata bude ya sake katseta da cewa "Wato ga Driver kin samu, kefa yarinyar nan kin samu guri da yawa wallahi" "Nifa na dauka da kai za'aje" ta fada kamar zatayi kuka, Khalil dake zaune ya kalli Habibu yace "Ka rabu da ita haka mana, shiga mu tafi". Gaban motar Habibu ya bude mata saboda cin zali harda ranqwashinta. Tafiyar kurame sukayi, ita dai ta riqe Takaddunta a hannu ta sunkuyar da kai ga uban Ac daya qure da qamshin turarensa sun dameta. A bangaren Khalil kuwa yanda kasan an bame masa baki da kwado haka yaji duk tarin tambayoyin da warning din daya shirya kora mata akan ta qyale kurwarsa ta huta ji yayi sun shafe se ma wata nutsuwa da yaji ta daukar masa sanadiyyar zamanta a kusa dashi. Lokaci lokaci yake waiwayawa ya kalleta har suka Isa wani babban Cafe yayi parking motar kafin ya fita Humaira ta bishi a baya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki dan ita wannan hade fuskar tasa tsoro yake bata. Basu bata lokaci a gurin ba akayi mata duk abinda ya dace dan suna shiga ya hadata da ma'aikatan gurin ya koma gefe ya tsaya har aka gama kafin suka gaya masa kudin ya biya. Wanda yayi mata aikin ya kawo masa takaddar da aka fitar mata ya karba yana gaya masa ranar da zata dawo dan ta san rana da lokacin da zata rubuta Jarabawar. Seda suka ci rabin hanyar komawa gida kafin ya kalleta yace "Wane course kika cike?" Daga kai tayi ta kalle shi ganin shima itan yake kallo yasa tayi saurin sada kanta qasa tana juya zoben hannunta muryar ta na dan rawa tace "Fine art" "Fine art" ya maimaita be qara ce mata komai ba yaci gaba da tuqinsa har suka kusa shiga layinsu kafin sake kallonta yace "Ina wayarki?" "Banida waya" ta bashi amsa. Se ya kalli hannunta itama hannun ta kalla kafin yayi magana tace "Wayar Mama ce ni Yah Mansur yace ba yanzu za'a siya mun waya ba". "Da layinta kikayi rijistar kenan" ya fada ba tareda ya kalleta ba seta daga masa kai kafin da sauri ganin baya kallonta tace "Eh, shiyasa ta bani wayar ai". Gani tayi ya dauke hanya daga komawa gida yayi wani gurin daban, ko motsi batayi ba har suka isa qofar wani shago ya kashe motar yaceata yana zuwa. Be dade a ciki ba ya fito da Leda fara qarama ya shiga motar suka juya zuwa gida. Suna isa ana kiran Sallar Magriba dan haka be shiga ba ya miqa mata Ledar daya fito da ita daga shagon dazu tareda kudi dubu goma yace ta kaiwa Mama. Ko saurar godiyar data tsaya yi masa beyi ba ya juya kan motarsa. A kan hanya ya samu masallaci yayi sallah, se a sannan ya duba wayarsa da tunda ya fito daga Office be sake dubata ba. Tarin Missed calls ya gani s sannan ya tuna da ya sakata A Silent da zeyi sallar Azahar kuma ya manta be cire ba. Kiran Umaimah ya fara bi, tambayarsa tayi yaushe ze dawo gida dan ta fita amma tana hanyar dawowa. Sabon salon data tsiro dashi kenan se ta fita inda zata sannan zata sanar masa kuma yasan baze wuce gidan wannan qawar tata da sam yaqi Jini ba shi ya rasa ma tsakanin ita da Rufaida wacce yafi tsana a cikinsu. Gaba daya matar kalar munafukai ne da ita ga Ladabi da kana gani kasan bana Allah da Annabi bane, ya rigata komawa gidan, ta shigo da tarkacen kayan Jarirai ta baje masa su wai a gidan Safina ta siyo maqociyarta ce ta kawo shine ta diba. Har ya kwanta saqo ya shigo wayarsa dake hannunsa. Baquwar number ce. Bude saqon yayi ya karanta abinda yake ciki "Nagode kwarai Yaya Khalil, Allah ya saka da Alkhairi ya qara arziqi. Mama tace ayi maka godiya Allah ya raya su Mu'ayyad". Ya maimaita karanta saqon yafi sau Goma kafin ya gane daga inda yake. Inda ta samu number sa yake mamaki koda yake baze wuce a wayar Maman ba. Maida wayar yayi ya ajiye kamar wanda aka tsikara kuma ya janyota ya sake bude saqon. Number da ta turo yayi saving da 'Fine Art' kafinya goge text din dai dai nan Umaimah ta shigo cikin shirin kwanciya. Yana jinta tana mitar qafarta na ciwo kafin ta koma kan maganar kudin kayan data dauko. Be ko tanka taba yaja bargo ya rufe jikinsa alamar bacci zeyi. Tun bayan da sauka dawo shiri take neman yanda zata samu kudi a hannunsa shi kama ya tsuke bakin Aljihunsa tsaf ya qudurce a ransa kudi indai ba akan abinda ya zama dole ba ya dena bata. A da da yake bata dinma bega abinda ta tsinana dasu ba balle yanzu da shida kunnensa yaji tana shirya yanda zata samun kudin da besab abinda zatayi dasu ba. Da safe yana zaune kan Dining yana jiran Umaimah da take soya masa kwai ta gama dan Ruqayya bata nan, anyi mata rasuwa ta tafi garinsu kwana uku kenan. WhatsApp ya shiga, abinda be fiya dubawa ba Status haka nan yau yaji sha'awar dubawar yana shiga kuwa da status din 'Fine Art' ya fara cin karo. Waqoqin hausa ne na soyayya ta dora a jere guda uku, se hoton wani da aka rufe fuskarsa da Emojin Zuciya ta rubuta 'Haskena' a qasan hoton. Haka kawai yaji ya qware da ruwan Tea daya kurba ya shiga tari har seda Umaimah dake kitchen ta fito ta bashi ruwa tana masa sannu. Seda tarin ya lafa masa kafin ya miqr tsaye idonsa yayi jajir saboda kwarewar da yayi ya sabi jakarsa dake kan kujerar kusa dashi Umaimah ta kalleshi da mamaki tana cewa "Naga ka miqe, ina kuma zakaje baka karya ba?" "Ki barshi kawai na qoshi, da akwai kudi na ajiye miki akan Dressing Mirror na zuwa Asibitin" ya bata amsa kafin ma ta sake magana ya kusa kaiwa qofa se kawai ta bishi da Adawo lafiya a ranta tana mamakin abinda ya harzuqashi haka dan fuskarsa da Muryar sa sun nuna fushin da zuciyarsa take ciki. Khalil kuwa seda ya fita daga layinsu kafin ya samu guri ya tsayar da mota. Wayarsa ya dakko ya sake komawa WhatsApp din ya bude status dinta. Hoton ya tsurawa ido kamar wanda yake son goge Emoji din ya samu damar ganin fuskar wanda aka boye din har wani huci yakeyi saboda yanda zuciyarsa take tafasa kai kace Umaimah ce ta dora hoton wani Namiji bashi ba ta kirashi da haskenta. Kiran wayar Anwar ne ya katse masa kallon status din, suna gama magana ya tada motar yaci gaba da tafiya ita kanta motar tasan yau ran me ita a bace yake saboda yanda yake fizgarta kamar ze tashi sama. Sama sama ya ringa amsawa masu gaishe shi, a office dinsa ya tarar da Anwar dake jiransa zasu fita ya jefar da jakarsa kan kujera Anwar ya bishi da kallo ganin yanda yake abubuwa kamar wanda yake fada da kayan office din. "Khalil lafiya kuwa?" Anwar ya tambayeshi ganin yayi wurgi da Chajar wayarsa da yake qoqarin jonawa amma taqi hawa alhalin ba laifinta bane shine be kunna socket din ba yake ta danna chaji. Tsaki yayi ya zauna akan kujera ba tareda ya amsa shi ba. Anwar yaja daya daga cikin kujerun gaban Table din shima ya zauna yana fuskantar sa, yasan matsalar sa daya ce bazata wuce Umaimah ba amma ya zata sunyi magana tun kwanaki kuma Khalil din da bakinsa yace baze sake bari lamarinta ya dameshi ba ballantana har ya shafi aikinsa yanzu kuma me tayi masa haka da ya zuciya yake qoqarin yiwa abubuwa rotse. Gyaran murya Anwar yayi yana kallon Khalil da shi kuma yake kallon wayarsa, status din yake sake kallo dan ta qara wasu hotunan guda biyu, daya dai Hasken nata ne se na qarshe ita da Mama da Nusaiba matar Mansur a Harami da alama Umarar da Mama take da Mauludi tare suka tafi kenan. "Khalil" ya kira sunansa, se ya dago daga kallon wayar ya dubi Anwar, "Meya faru?" Tsaki Khalil yayi kamar bazece komai ba se kuma cikin qufula yace "Wata yarinya na siyawa waya saboda ta raina mun hankali yanzu kawai naga ta saka hoton wani gaja da caption wai Haskenta" ya fada muryarsa na nuna zallar takaicin da status din Humairan ya qunsa masa shi dai Anwar kasa riqe kansa yayi seda ya fashe da dariya harda kyakyatawa yana kwanciya akan Table dan maganar ba qaramin shiharsa tayi ba. Yanzu wannan fushin duk akan mace yakeyinsa lallai Khalil yayi nisa sedai fatan Allah ya taro shi. Kallonsa Khalil ya ringayi har yayi dariyarsa ya gaji takaici kamar ya shaqoshi ganin irin kallon da yake binsa dashi ya saka Anwar dakatawa da dariyar yana cewa "Allah ya baka haquri, maganar taka ce ai dole ta sakani dariya. Wai ka siyawa yarinya waya ta dora hoton wani a Status, kai dole ma na kai labarin nan NH yau gayu suji su dauki darasi" ya sake sheqewa da wata dariyar da tafi ta da abin haushi. Tashi Khalil yayi ya shiga hada abubuwan da zasu fita dasu din ransa a bala'in bace kamar ya rufe Anwar da duka. "To amma tsaya, Ina Umaimah da har aka siyawa wata waya kuma kake fushi dan ta saka wani a status? Kai bama wannan ba da alama mayyar data kama ka ta sakar maka kurwa kenan har ka iya yin budurwa ka siya mata waya lallai Khalil ka shahara wuyanka ya riqa ko ince Alqadarin Umaimah ya karye tunda gashi ka dena tsoronta kai tsaye kake abinka yanzu" Anwar daya tsaida dariyarsa dakyar ya sake fada. Shidai Khalil be kulashi ba ya gama tattara abinda yake da buqata ya fita Anwar dinya rufa masa baya. A mota ma haka ya tasashi da magana shidai yayi masa shiru dan abinda ke cin ransa ya ishe shi haka suka gama zagayen duba ayyukan da zasuyi ransa a dagule babu dadi. A wani restaurant suka tsaya cin Abinci bayan sunyi Sallar Azahar. Anwar ya sake kallonsa ganin gaba daya ranar bashida walwala gashi bini bini ya dauki waya ya duba ya riga Khalil din cinye abincinsa dan haka ya jirashi ya gama, ganin sauran da suke tare basu qarasa ba ya saka shi amfani da damar ya kalli Khalil yace "Mutumina kasan abu na farko da zan fara ce maka shine duk abinda zaka yi a rayuwa kayishi tsaka tsaki. Idan zaka so abu ka so shi daidai Misali haka idan zaka qi abu ka qishi saisa saisa saboda wata rana duka abu biyun nan suna iya rikida su koma akasin Asalinsu. Kaga kai babbar Matsalar ka a rayuwa ita ce zurfafa Soyayya. A duk sanda kaso abu kana daukarsa ka bashi muhimmanci sama da kowa da komai a rayuwarka bana buqatar tunatar da kai Matarka kadai ta isheka isha idan haka ne zamantakewarku kadai ta isheka karatu akan duk wata mace da zaka sake mu'amalanta anan gaba. Duk abinda ya faru dakai Soyayyar ka tayi amfani da ita ta yaqe ka, nayi zaton ka koyi darasi se gashi yanzun ma kana qoqarin sake afkawa a ramin da yafi wanda ka baro Zurfi da duhu. Ni nasan Wannan Mayyar da ka ringa iqirarin ta kamaka babu wata mayya se Maitar Soyayya, ka sake fadawa tarkon Love at first site din daka saba ne shine kazo kana mana wata Drama wai Wata Mayya ta kamaka ashe ban sani bama har abu yayi nisa kun daidaita harta kai ga ka siya mata waya. To nidai abunda zan iya gaya maka daya ne zuqa biyu, yanzu dai gashi da Idonka ka gani cewar ba kai kadai take kulawa ba kamar ma shi wancan yafika fawa a gurinta tunda da wayar daka siya akeyin status dashi ana kiransa da Haske kai ko Arziqin duhu baka samu ba. Ita Mace daka ganta a sanda kake nacinta kana nuna mata So da kulawa ba takai take ba,se kaga zuciyarta tana ga wanda be kaika ba, sedai ka qare a wahalta mata ita kuma tana Wahalta masa tunda shi take so". Yanda kasan me daukar karatu haka yasa kunnuwa yana sauraron Anwar, fashin baqin da yayi masa yasa ya shiga tunanin kenan da gaske Son yarinyar yakeyi? Saurin qaryata hakan zuciyarsa tayi se kuma daya bangaren ya jefo masa tambayar "Idan ba sonta kakeyi ba ina ruwanka da sabgarta har kake kishin ta saka hoton wani a status?" "Tab da kuwa an fadi babu nauyi ace ina son wannan yar yarinyar da bata wuce na haifi Sa'arta ba" ya fada. Be ankara da cewar a fili yayi maganar ba seda yaji Anwar yace "Ai babu wani aibu idan kaso qaramar yarinya abu daya ne dai A yanzu idan aure zakayi Khalil kamata yayi ka nemo matar da take sonka ba wacce kai kafi so ba, bani da buqatar gaya maka dalilin haka dan ka fini sani. Bance karka so koma wacece ka samo ba amma ka zauna kayiwa kanka Hisabi shin ta dace dakai? Zata share maka hawayen da kake fata ko kuwa? Idan ta gaza cin wadannan Test din ka haqura da ita ka nemi wata cikin manyan yammata da suka gogu da rayuwa kuma su suke sonka ba wai kai kake sonsu ba na tabbata se sunfi binka sun baka nutsuwar da kake nema sannan ka sani duk macen da zaka aura a yanzu dole ya zaman cewar tayiwa matarka zarra ta kowanne fanni shi kadai ne ze samar maka da zaman lafiya a cikin gidanka dan ka fini sanin da wadda kake zaune, amma idan da ita wannan din zuciyarka ta aminta, ka nemi zabin Allah ka bar masa komai a hannunsa duk kuma hukuncin daya yanke maka kar kayi Jayayya da hakan ka karbeshi da kyakykyawan Yaqini". "Bafa tasan ina sonta ba, ni dakaina ban yarda cewa Sonta nakeyi ba. Haka kawai tun daga randa na fara ganinta na rasa nutsuwata. Yarinya cefa Qarama Anwar, she is just 18 me zan tsinta a jikinta kawai Shaidan ne yake nema yayi mun wasa da hankali amma ni ba wani abu game da ita a raina" Khalil ya fadawa Anwar din iyakar gaskiyarsa. Murmushi Anwar yayi yace "Lokacin daka fara Son Badar haka kace soyayyar yan uwantaka ce, se gaka harda kwanciya a gadon Asibiti da tace ba zata aureka ba. Umaimah kuma Friendship ita kuma wannan Tausayinta kake ji halan tunda kace yarinya ce?" "Exactly, tausayinta naji. I learnt that she is an orphan babu uwa babu uba, shine ma har yasa na siya mata wayan saboda tace bata dashi. Cousin din Mansur ce, a gidansu take. amma ni ba wani sonta nakeyi ba kawai haushin da naji akan me daga na siya mata waya zata ringa saka hoton wani saurayi bayan ni purposely saboda tayi karatu na siya mata" Khalil ya sake fada, se Anwar ya miqe yana murmushi yace "Abokina ka nemi zabin Allah kawai kaji idan kaji ta kwanta maka daga nan ka nemi yardarta ka dage kuma da Addu'a Allah yasa qarshen wahalarka ne yazo". Har ya koma gida maganganun Anwar nayi masa yawo a kai, sam baya so ya yarda da cewar wai Son Humaira yakeyi to ta Yaya ma? Amma kuma duk wasu Shika shikan soyayya sun gama bayyana a tare dashi. Wannan faduwar gaban da yawan tunaninta da yakeyi harya dora mata Maita ashe duk na kamuwa da Soyayya ne be sani ba amma kuwa idan haka ne So be kyauta masa ba daya rasa inda ze sauka se akan wannan yar tatsitsiyar yarinyar da Yasan kwakwkwarar tsawa idan Umaimah tayi mata zata iya suma. Kai bama wannan ba ya tabbatar babu yanda za'ayi Mansur ya yarda ya barshi ya aureta dan yace matarsa bata da hankali dukda shine babban zagin da kullum yake Addu'ar Allah yasa ayi mata kishiya to dai dara taci gida Addu'a ta karbu kuma akan Qanwarsa sedai fatan Allah ya taqiata dan idan har ze qara aure dagaske to babu wata Mace da ze aura idan ba Humairan ba, ita kadaice tayi masa irin shigar da Umaimah tayiwa zuciyarsa. Raba dare yayi yana kallon Umaimah dake baccinta hankali kwance saboda duniyar tana gara mata yanda take so, ta samu kan Mijinta bata da wata damuwa. Tunanin irin yanda zasu kwasota kawai yakeyi idan har maganar nan ta tabbata amma a wannan karon baya jin zeji bari, ko shi ko Umaimah. HUMAIRAH *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 59 HUMAIRAH Bayan da Khalil ya sauketa tana shiga gida ta ajiye ledar daya bata da saqon Mama ta faa bandaki saboda fitsarin daya matseta tunda suka fita take jinsa. Habibu ta tarar ya bude ledar data ajiye ya zaro kwalin Waya Iphone bata dai san ko wacce ce ba dan ita ba sanin waya tayi ba. "Ke waya siya miki IPhone?" Ya fada ganin ta fito daga bandakin, Mama dake juya kwalin ta kalle ta tace "Humaira wadannan fa daga ina haka?" "Yaya Khalil ne ya bani, mun taho a hanya ya tambayeni inada waya nace masa Aa ta hannuna takice shine ya tsaya a wani shago ya siyo wannan ga kudi nan kuma yace na kawo miki ya wuce yana sauri" ta bawa Maman Amsa cikin nutsuwa, kafin ma Mama tayi magana Habibu ya amshe yana cewa "Kan bala'i kuma shine ze siya miki IPhone? Lallai Yah Khalil qaiqayi kudi suke masa besan ko Keypad baki gama sanin yanda ake dannata ba ballantana wata IPhone ai kawai ni ya siya wallahi, alfarma daya zan miki na jefeki da Infinix dita ki qarasata" ya fada yana zaro wayarsa data sha jiki daga Aljihu. Bata fuska tayi kamar zatayi kuka Mama tace "Sha kuruminki, kai kuma me son abin duniya baka isa ba. In kai na roqa ka rakata kaqi gara da baka je ba gashi nan rabo ne ya kirata. Maza karbi wayarki an gode masa Allah ya saka da Alkhairi daman yaushe muke zancen da Yayanku yace ze turo miki da wayar to ga dan uwansa ya hutashshe sa ya siya miki" "Mama kinsan kudin wayar nan kuwa, Humairan za'a barwa ita lallai ma" Habibu ya sake fada Mama ta fizge kwalin wayar daga hannunsa tana cewa "Ko Miliyan dubu ake saida ita haka zaka barta da abarta shi wanda ya siya beyi kyashi ba se kai dan hana ruwa gudu ko to ka canza hali. Maza ki kaita daki ki boye, Sumayya tace zata zo anjima naga hoton kamar irin tata da tazo seta saita miki ita kema ki samu ta daddannawa kinji Uwata Allah dai ya sakawa Khalil da Alkhairi" ta tattara mata wayar da ledar ta bata ta shige cikin daki Abinta. Tsalle ta ringa bugawa na murna tana kallon kwalin wayar. Wai yau ita ma tayi wayar kanta kuma IPhone babba duk cikin yan qaryar Ajinsu masu zuwa da waya babu me irinta dole ranar Graduation kuwa ta wanke su sedai su ganta da waya tana daukar hotuna itama. Saboda zumudi bata iya jira Sumayyan tazo ba ta bude wayar ta jona chaji, Kati ta gani na dubu daya a ciki MTN, ta duba bataga Layi a ciki ba dan haka tana idar da Sallar Magriba tacewa Maman zata shagon Lawi ta siyo layi yayi mata Register Mama ta bata Dari biyar ta tafi, bata jima ba kuwa ta siyo ta dawo dan babu nisa daga gidansu tana dawowa ta tarar da Sumayyan tazo har Mama ta dakko mata wayar ta kunna Hotspot tana saita mata ita. Dakyar ta iya haqura ta bar Layin ya kai awannin da aka ce mata kafinta dora ta shiga WhatsApp da an rigada an mata downloading, number Noor data haddace tsaf ta loda tayi masa magana. Be yarda ita bace seda tayi masa voice yaji muryarta babu bata lokaci ya tura mata da hotunansa da tacs tana so, ya tafi Training din aikin Soja wanda shine karo na uku da yake zuwa biyun baya duk be samu ba amma haka ya sake nema ya tafi a karo na ukun dan ya dage shi idan ba Soja ba baya tunanin akwai aikin da ze iya yi. A wayar Mama ta kwafi number Khalil layin na hawa kuwa ta rangada masa text na godiya kafin taci gaba da sabgoginta ta loda numbers din qawayenta da daman a wayar Mama take saving dinsu kafin ta shiga dora status din Haskenta kamar yanda take fata a kullum itama tayi waya ta ringa saka hotonsa a status kamar yanda yake saka nata. KHALIL Tun bayan maganar da sukayi da Anwar yake ta qoqarin ganin ya yakice Humaira da tunaninta daga zuciyarsa amma abun ya gagara. Tamkar yana jiran ayi masa fashin baqi akan abinda yake ji din akanta, maimakon ya cireta daga ransa kamar yanda yake niyya se abun ya faskara kullum qara samun guri takeyi tana narkewa a zuciyarsa idan kuwa ya ga tayi status na soyayya ji yakeyi kamar yayi bindiga amma a hakan kullum qaryata zuciyarsa yakeyi akan baya sonta. A gari yaji za'a fara rubuta Jamb kwana biyu masu zuwa dan haka ranar ya shirya da Yamma tareda Mu'ayyad haka kawai suka tafi gidan Mama. Kewar Humairan yakeyi amma ya rasa ta inda ze jr gidan dan baya son Maman ta zargi wani abu yanzu daya samu zancen Jamb din seya fake dashi, kwalliya yasha da wata Danyar Shadda Cream color ya kafa hula. Yana cikin fesa turare Umaimah ta shiga dakin. Kallo daya ta masa ta dauke kai ba tace masa qala ba tabi lafiyar gado ta kwanta dan kwana biyun wani Mood swings take ji dashi kowa na gidan ma haushinsa take ji ko bangaren Hajiyan se a kwana a wuni bata leqa ba. Turare ya dauka yana qara fesawa a jikinsa dukda ya saka amma ji yayi be ishe shi ba. Ya gama fesa turare ya sake daukar comb yana taje Gemu daga nan ya koma gyaran hula. Umaimah dake kwance abin ya isheta, yanda yake ta wani faman qalqale qalqale kamar sabon Ango yasa ta miqe zaune murya a cukule tace "Wai ina zakaje kake ta wani faman kwalliya kana gyara fuska?" Waigawa yayi ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Inda kika aikeni" dan shima yanzu gasa mata magana yake a tsaye yanda take masa. Aiko ta harareshi ta koma tayi kwanciyarta yana jinta cikin qunquni tana cewa "Duk abinda mutum yakeyi dan kansa ni dai idan anci Amanata ba yafewa zanyi ba". Murmushi kawai yayi be tankata ba ya fice daga dakin, a bangaren Hajiya ya dauki Mu'ayyad bayan ya gaya mata zasu fita tayi masa a dawo lafiya kafin suka kama hanya. Seda ya tsaya a hanya yauma yayi wa Maman cefanen kayan miya masu kyau daya gani ya biya gurin da ake siyar da Kaji ya siya Frozen kafin suka kama hanya. Seda sukaje qofar gidan zuciyarsa ta raya masa cewar ya kamata ace ya zowa da Humaira da tsaraba, wa yaga azarbabi. A cikin Get din gidan yayi mugun gani, Humaira na tsaye ta saka dogon Hijabi kamar kullum har qasa tajawoshi ta refe fuska ta kamar mejin kunya. Ya maida kallonsa kan Dogo siririn Saurayin dake tsaye kusa da ita yana mata magana dukda be jiyo abinda yake fada ba da alama shi ya bata kunyar. Wani abu me daci yaji ya taso masa, kamar ya juya amma Mu'ayyad daya dakko ledar Tumatir ya rigada ya shige ciki dan shi ya tsaya hado kan ragowar Ledojin, haka ya ratsa su ya wuce. Yana jin tana masa sannu da zuwa harda shima saurayin nata amma yayi kamar beji su ba ya shige ciki. Mama nata yiwa Mu'ayyad sannu da zuwa ya shiga, ta juyo kansa tana cewa "Gaskiya ka kyauta, yau zuwan naka yafi na kullum tunda ka taho mun da Megida harda Cefanensa" Seda yayi da gaske kafin ya iya danne abinda ke taso masa ya shiga gaisheta, ta amsa tana tambayarsa gida tareda godiyar Wayar daya bawa Humairan. Shiru yayi kawai ya zubawa qofa ido yana jiran yaga sanda zata shigo Mama data tafi kawo musu ruwa ta dawo da babban Try data doro ruwan da Lemo. Ta ajiye wani kwano gaban Mu'ayyad tana cewa "Wannan na megida ne". Alkaki ne a ciki nan take kuwa ya hau ci ta shiga tsokanarsa da cewa Shazumamu shidai Khalil ya gaza shan koda muqurwar ruwa daya dan ya tabbatar bazasu iya wucewa ta maqoshinsa ba. Hira Mama take masa ganin ya maida hankali yana ta danna waya yasa tayi shiru ta mayarda hirar tata kan Mu'ayyad. Seda suka ahafe kusan minti Ashirin a zaune kafin ta shigo da sallama cikin siririyar muryarta. "Oh ni Hauwa'u, wallahi na manta shaf da batun bakya gidan nan Humaira se kace wadda ta tafi rubuta jarabawar gaba daya kusan awa nawa keda kika ce ba zaki dade ba" Mama ta fada tana riqe baki dan da gaske ta manta da Humairan ta fita. Baki ta tura cikin shagwaba tace "Kai Mama ko fa awqa biyu banyi da fita ba kuma ni na dade da dawowa muna tsaye da Noor a Get, sanda su Yah Khalil ma suka zo muna nan fa" kallonta yayi, yanda ta ambaci Khalil din ka rantse ita ta saka masa sunan yanda ta fada yayi mugun masa dadi amma haushin maimaita cewar tana tsaye da koma waye yazo yasa ya galla mata wata harara. "Ai fa Allah ya dawo da Nura se kuma abinda aka gani. Yanzu dai makaranta zaki fara dole ki tsayar da hankalinki idan ba haka ba kuma ya fito kawai a hada a kaiki ku qarata can, wannan soyayya taku se kace kanku a ka fara. Yanzu ina takaddar ranar yaushe zakiyi?" Mama ta tambayeta,, seta miqa mata takaddun dake hannunta tana cewa "Jibin zanyi, mune farkon yi ma" Mama ta karba ta duba tana cewa "Toh Allah ya bada sa'a. Se ki maida hankali kiyi karatu dan ka ganta nan tunda ta samu wayar nan babu sakat, aikin gida ma se anyi da gaske take tashi tayi bini bini suna hira da wannan yaron Nura daman abinda yasa Mansur yaqi bari a bata waya kenan toh kuwa inaga kwace ta zanyi har se sun gama jarabawar". Shidai Khalil shiru kawai yayi yana hadiyar zuciya, Humairah ta wuce dakinta tareda Mu'ayyad shi kuwa Mama na tayi masa hira amma sam hankalinsa baya kanta tunanin waye wannan Nuran yakeyi ya dai gane shine yaron daya gansu tsaye to kuwa dole yayi maganinsa. "Bari muje Mama, Magriba ta kawo kai zan tsaya kuma wani guri bayan nan" Khalil ya fada yana miqewa, se Mama ta kwalawa Humairah kira suka fito tana riqe da hannun Mu'ayyad kamar Yaya da qaninta, Mama tace "Megida kazo ku tafi, ko zaka kwana anan" Mu'ayyad dake shan chocolate ya maqe kafada alamar baze kwana ba Humaira tace "Kai ba yanzu kace mun zaka zauna ka kwana ba tunda babu School?" "Aa ni bazan kwana ba, sedai kizo mu tafi gidan mu". Dariya Mama tayi tana cewa "Ja'iri, wato sedai ta bika naku gidan ko ai shikenan, laifinka ne da baka kawo mana shi daya saba damu ai" ta maida maganar kan Khalil, yaqe kawai yayi dan tsayuwarsu a kusa ma damunsa take dan haka yayi gaba daya yiwa Maman Sallama. Humaira ta koma daki da sauri ta hado Alawoyi da biscuit wanda Noor ya kawo mata ta biyo su dashi. A bakin mota ta same su, ta miqawa Mu'ayyad tana murmushi tace "Yah Khalil me yasa baku zo da qanwarsa ba? Yace su biyu ne ni ban santa ba". Yanda take maganar fuskarta dauke da murmushi yasa ya zuba mata ido kawai yana kallonta wani abu na sake fizgarsa akanta, ganin yana nema ya shagala yasa ya bude motar ya shiga yana kallonta yace "Qarfe nawa ne Exam din naki?" "7am suka rubuta" ta bashi amsa seya gyada kao yace "Zanzo na kaiki". Baki ta bude kamar zatayi magana kuma se ta fasa tace "Toh Allah ya kaimu ku gaida gida, Mu'ayyad bye" ta daga masa hannu kafinta juya ya bita da kallo saboda yanayin da tayi maganar ya nuna kamar bataji dadin cewar da yayi ze kaita ba. Tana shiga gida ta zube akan kujera Mama ta kalleta ganin fuskarta ba kamar yanda ta fita ba tace "Ke kuma lafiya kike hada fuska?" "Mama wai Yah Khalil ne yace ze zo ya kaini rubuta Jamb, kuma ni munyi magama da Noor tare zamuje" ta yi maganar cikin shagwaba. Mama ta kama haba a ranta tana mamakin jin Khalil ze kaita a fili kuma tace "To menene abin bacin rai dan yace z kaiki? A dadinki ai" "Mama da Noor fa zamuje na gaya miki" ta sake fada se Maman tace "Se ki gaya masa Yayanki ne ze kaiki ai". Bubbuga qafa ta shigayi zatayiwa Maman shagawaba tace ta tashi ta bata guri. Tana shiga daki ta kira Noor ta sanar masa da abinda aka ce "I'm sorry My Humy nima ina shigowa gida yanzun Hajiya take gaya mun zan kaita Gabasawa Ranar kuma da wuri zamu tafi, daman anjima nake shirin idan nazo na gaya miki" Noor din ya fada seta sake bata fuska amma bata ce komai ba. Lallashinta ya shigayi har seda ta sauko suka shiga hira kiran Dallar Magriba ne ya katse su daga nan ya gaya mata yana idar da sallar Isha ze zo sukayi sallama. Humairan Noor kenan, kusan yan unguwar kaf da haka suke kiranta saboda irin so da shaquwar dake tsakaninsu babu wanda be sani ba. Noor Matashi ne dan kimanin shrkaru Ashirin da hudu, gidajr uku ne tsakanin gidan su dana su Noor din haka zalika tun suna Makarantar Primary suke tare dukda ba ajinsu saya ba soyayya ce tunta quruciya akeyinta har zuwa yanzu da suka kawo hankalin kansu dukda mutane da yawa suna ganin soyayyar tasu bata da matsaya da yawa suna ganin Humairan tayi masa girma a irin matakin da yake a yanzu da ko Makarantar gaba da Secondary be kai ga shiga ba dan ya dage akan aikin soja yake so yayi. Baya ga haka baya wata sana'a da za'ayi tunanin zata iya riqeshi har yayi aure kuma be fito daga wani babban gida ba da zasuyi masa auran gata iyayensa masu rufin Asiri ne kawai amma dashi da Humairan tasa sun yarda cewar suna son junansu a hakan kuma zasu jira har zuwa lokacin da burikansu zasu cika suyi aure akan hakan suke yanzu musamman da suka samu goyon baya daga Iyayensu Mata, Mama da Hajiya Asabe mahaifiyar Noor din sunyi Na'am da hadin dan qawayene sudin wasu daga cikin yayyensa da nata ne dai suke ganin batawa kansu lokaci kawai sukeyim dan yayyensa sun sha nuna masa akan ya rage irin zafin son da yake mata dan sun tabbata wata rana zata shammaceshi ta tafi ta auri wani, Macece ita babu yanda za'ayi ace ta jira Namiji amma yaceshi ba haka ba yasan ko nan da shekara dubu Humaira tasa ce kuma bazata iya barinsa ta auri wani ba abinda take fada mas akenan lullum. Kamar yanda yayi alqawari ranar da zata rubuta Jamb qarfe shida da yan mintina a qofar gidansu Mansur tayi masa, be shiga ba a waya ya kirata kawai yace ta fito. Tana zaune gaban Mama tana shan shayin data takurata seta sha kafin ta tafin tana ganin kirankuwa ta miqe, Hijabinta ta zura dogo ta dauki qaramar Jakar data zuba abubuwan da za'a buqata tayiwa Mama sallama dake mata fatan nasara ta fita. Seda ta zauna cikin motar kafinta gaida shi ya amsa mata suka fara tafiya. Har suka isa inda zatayi jarabawar babu wanda yayi magana a cikinsu se sautin karatun daya kunna ne kadai ya karade motar. Seda ya tabbatar ayi mata screening ta hau layi kafin ya koma inda ya ajiye motarsa. Ciki ya shiga ya kwantar da kujerar saboda yaji dadin hutawa kafin ta gama. Jakarta data bari a motar ya janyo ya ciro wayarta dake ciki. Hotonta dake kan screen dinya kalla tayi kyau tana sanye da Uniform din Islamiyya fuskarta dauke da murmushi. Bude wayar yayi yaga da key akai, zuciyarsa ta raya masa ya gwada sunan Saurayin nan nata da take sakawa a status yana rubuta Haskena kuwa wayar ta bude, yaja kwafa kai tsaye WhatsApp ya shiga amma ta rufe da Fingerprint seya ja tsaki rufe. Messages ya koma wannan Hasken ne kadai yaga suna musayar kalamai dashi daman babu wasu numbobi da yawa akan wayar duk na yan gidansu ne se qawayenta. Qarar wayarsa ce ta tsayar dashi daga binciken da yake mata, ya janyo wayar daga Aljihunsa Umaimah ce. Bayan ya daga take tambayarsa ina ya tafi da sassafe ta farka baya nan, "Wata Jana'iza na tafi, Baban wani Ma'aikacinmu ne ya rasu yanzu ana shirye shiryen kaishi ne da an gama zan dawo" Khalil ya shiryo mata qaryar dashi kansa besan sanda Idea tazo masa ba. Jajantawa tayi da Addu'ar Allah ya jiqan wanda ya mutu kafin sukayi sallama seya kashe wayar gaba daya ya ajiyeta. Kwanciyarsa ya gyara ya rufe idanunsa yana tunanin abinda zuciyarsa take ayyana masa yayi ko kar yayi yana cikin haka bacci ya daukeshi. Besan iya Adadin lokacin daya kwashe yana baccin ba kwankwasa Glass din da akeyi ya farkar dashi. Humaira ce, ya cire lock din motar kafin ya gyara kujerar da yake kai ya tashi zaune. Bakinta a washe ta shigo motar ya kalleta yace "Har kun gama kenan" "Mun gama kuma tayi sauqi sosai wlh" ta bashi amsa tana duba jakarta. "Allah ya bada sa'a" ya fada kafin ya tada motar seta kalle shi ganin bata ga wayarta a jakar ba, shima kallonta yayi yace "Yaya dai?" "Waya ta ce bangani ba kuma na taho da ita" ta bashi amsa. Da ido ya nuna mata Aljihun motar taja ta bude sega wayar ta dakko, satar kallonsa tayi dan tana budewa a kan Gallery ta tarar. Hotunanta na shirme ta shiga dubawa a ranta tana addu'ar Allah yasa be bude ba da kuwa tasha kunya Khalil dake ankare da ita yayi murmushi a zuciyarsa kawai. Wani gurin cin abinci taga ya tsaya, ya kalleta bayan ya kashe motar yace "Muje kiyi breakfast" "Na qoshi, seda na sha Tea kafin na fito daga gida" ta bashi amsa. Fita yayi ya barta be jima ba ya dawo da Ledoji masu tambarin gurin a jiki ya saka a bayan motar kafin ya shiga suka ci gana da tafiya. "Wanene Noor?" Ya jefa mata tambayar dake ta cin zuciyarsa. Humaira dake danna waya ta dago da sauri ta kalleshi ganin shima itan yake kallo yasa ta sadda kai kamar munafuka qirjinta na bugawa saboda wani abu da taji ya tsarga mata saboda irin kallon fa yayi mata. "Uhm na tambayeki kinyi shiru" ya sake mata magana seta qara sunkuyar da kai tace "Abokinane" dan haka kawai taji ba zata iya ce masa saurayinta bane, karya mammaketa irin na Yaya Mansur da yace tayi qanqanta da fara kula samari shekara sha bakwai. "Aboki, shine naga kina saka hotunansa kullum kina rubuta haskenki?" Ya sake jefa mata wata tambayar seta kalleshi kamar zatayi kuka tace "Toh ai fassarar sunansa ce haka, Noor ba Haskenan ba?" Ta qarasa da sigar Tambaya. Yanda tayi maganar cikin sangarta da quruciya ya sakashi sakin murmushi. Rage gudun da yakeyi yayi, so yake yayi amfani da wannan damar yasan wasu abubuwa akanta dan haka ya sassauta muryarsa cikin lallami yace "Toh amma naga harda waqoqin soyayya kike sakawa duk saboda shi sannan kuma kince Abokinki ne. Ki fada mun gaskiya daman wani ne ya ganki yave mun yana Sonki ni kuma naga kinada saurayi shiyasa bana so na hada ku kice bakya sonsa bazanji dadi ba dan dan uwanane". Kallonsa ta ringayi harya yi shiru, ta tuna qawarta Mimi da tace mata ita banza ce da takr kula saurayi guda daya saurayin ma yaro duk ga mutane masu sonta nan da yawa amma tana musu wulaqanci gara ta qara samun ko mutum biyu ne da zata ringa hira dasu ta qara gogewa ta san Halayyar Maza da yawa. Wannan maganar ce ta sakata ce masa "Eh to zan gaya maka gaskiya dai Saurayina ne kuma shi nake so na aura, amma daman ina so na qarayin wasu Samarin nima dan qawayena duk ba saurayi daya ne dasu ba" Yanda take ke maganar zaka gane zallar yarinta a tattare da ita, kafin yayi magana taci gaba da cewa "Kuma dan uwan naka indai dan gayune irinka toh ina sonsa amma fa a Aboki ba saurayi ba dan ni inada wanda zan aura". "Ikon Allah" ya fada a ransa a fili kuwa ya kalleta yace "Toh ai shi gaskiya da aure yake sonki kinga babu dama kuma kice sedai kuyi abota, sannan wa ya ce miki ma Mace da Namiji suna Abota ne?" "Sunayi mana a school ina da Abokanai yan class dinmu sannan Friends dina ma bayan yan class dinmu suna da wasu Abokanan a waje kuma manya ne ma ba kamar mu ba" ta sake bashi amsa Innocently se yayi murmushi yace "Yan class dinku wadannan class mates ne karatu ne ya hadaku bayan haka babu wata alaqa ta Abota da za'ace tsakanin Mace da Namiji se ta soyayya, idan kinyarda zaki bashi dama ya gwada miki tashi soyayyar toh sena hada ku". Shiru tayi tana tunanin maganarsa se taji yace "Zan bashi number wayarki, sati daya kacal ze gwada Sa'a idan har kika fara sonsa shikenan idan kuma sati ya cika baki fada sonsa ba ze haqura kin yarda?" Haka kawai ta kasa musa masa, na farko cewar da yayi Abokinsa ne tasan Dan gayune irinsa ita kuma tana son Namiji me gayu shiyasa take qara son Noor dinta abu na biyu kuma itama tana so ta gwada Double dating kamar yanda qawayenta suke ta kwadaita mata dan haka ta amince ba tareda bata lokaci ba. "Bari na baki number sa kiyi saving dan karya kira baki san waye ba kiqi dagawa" ya sake fada yana ciro wayarsa. Number ya karanta mata tayo saving kamar yanda yace, Abokin Yah Khalil ta saka saboda tafi ganewa. Yanzun ma daya maida ta be shiga ba yace ta gaida Maman ya bata ledojin Abincin daya siyo kafin ya kama hanyar gida. Yana zuwa ya tarar da Umaimah na murqususun ciwon Mara, ko zama beyi ba suka sake juyawa Asibiti. A can ya barta ya dawo gida dan yayi wanka saboda sunce zata dan kwanta ta huta zuwa yamma kafin a sallameta. Already ya sanarwa da Anwar baze je office ba ranar shiyasa yanayin wankan ya samu abinci yaci ya haye gado dan yayi baccin da be samu yayi da Safe ba kafin ya koma Asibiti. Qaramar wayarsa ya dakko ya kunna, ba kasafai ya fiya amfani da ita ba number Layin da yake kanta ya bawa Humairan a matsayin number Abokinsa, seya dakko dayar wayarsa ya kwafi number ta ya saka akai kafin ya dannan mata kira. HUMAIRAH Tana shiga bayan ta gama bawa Mama labarin Jarabawa ta dora mata dana Abokin Khalil daya bata number sa. Mama tace "Ikon Allah, nifa nace zaryar nan ta Khalil da walakin, harna fara tunanin ko Dan uwansa Khalifa yakeyiwa kamu kinji ashe wani Abokinsa ne. Nayiwa Mansur zancen nasan baze gaza sanin waye ba, me yace miki sunan Abokin?" "Tab ya manta be fadamun ba nima kuma ban tambayeshi ba kawai da Abokinsa nayi saving number" Humairan ta bata amsa se Maman ta sake cewa "Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi, se ki nutsu idan ya kiraki kar kiyi masa maganar yarintar da kuka saba da Nura, kinga dai shi da hankalinsa dukda ban ganshi ba nasan Khalil baze hada ki da mutumin banza ba". Tura baki tayi gaba tace "Nifa cewa yayi sati daya kawai idan ban fara son Mutumin ba shikenan kuma kema kinsan inada wanda nake so kawai dan kar Yah Khalil din yaga na masa rashin kunya ne shi yasa na yarda". Se Maman ta kama baki tace "Eh ai ni gashi kina mun rashin kunyar, ke ni na dawo daga rakiyar wannan alaqar taku da bata da Alqibla, Addu'ata kawai Allah ya zaba miki Miji na gari da ze rungumeki ya kula da ke ko bayan raina na samu nutsuwa nasan bazakiyi kukan maraici ba. Dan haka kema kiyi ta addu'a kawai lokaci da yawa abinda kake nacin So bashine Alkhairi a gareka ba". Ita dai jin Maman kawai take amma ta tabbata babu wani Alkhairi a rayuwarta daya wuce Noor, shiyasanta yake kuma Sonta tun bata san kanta ba ta tabbatar kuma ze tarairayeta ya riqeta Amana kamar yanda Maman take mata fata. Bacci ta kwanta, a cikin baccin taji qarar wayarta tana farkawa taga Abokin Khalil ne yake kira. Kafin ta daga wayar ta katse se ga wani kiran ya sake shigowa dan haka ta miqe zaune tana goge ido kafin ta amsa wayar da Sallama tana tattaro dukkan Nutsuwarta kamar yanda Mama tace ta nutsu. KHALIL Yanajin ta amsa wayar tayi sallama gaba daya seya duburburce ya rasa abinda zece mata, meyasa kai tsaye be gaya mata shine ba yanzu idan ta gane muryarsa ai girmansa ya fadi zataga yayi mata qarya ne daya sani kai tsaye kawai ya fada mata shine ba wani Abokinsa ba. Sallamarta data sake ratsa kunnensa ya sakashi tattaro nutsuwarsa gaba daya ya amsa mata da dakakkiyar murya se sukayi shiru gana dayansu kafin ta shiga gaishe shi. Maganar Minti goma sukayi, ya sanar mata da sunansa Ibrahim kuma shi dan Kano ne yana da Mata daya da yara biyu, Jim tayi kafin ta amsa masa dukda daman tasan da wuya ace Abokin nasa ya zama saurayi amma daya fada mata cewar yana da matar taji wani iri to wai ma meya shafeta ko mata dari ne dashi? Itama a taqaice ta gaya masa Sunanta Aisha shikenan tayi shiru, ya tambayeta mutanen gida da kuma yaushe ya kamat yazo suga juna kafin magana tayi nisa a tsakaninsu se tayi shiru bata ce masa komai ba. "Naji kinyi shiru Aish, koda akwai matsala ne?" Ya fada jin bata amsashi ba. Gabanta ya fadi, tunda suka fara magana daman muryarsa take mata wani iri, kodan ta sakawa ranta ne taji kamar Muryar Khalil din oho amma maganar da yayi yanzu ta sake jin muryar tankar ta Khalil din seta bude baki a hankali tace "Ai munyi magana da Yah Khalil be gaya maka ba?" "Be gaya mun komai ba, kawai ya turomun da number yace nakiraki shikenan" ya bata amsa. "Toh ka tambayeshi kaji ze gaya mata yanda mukayi" ta sake fada masa se yayi murmushi yace "Aa, ai Khalil ya fita daga cikin Maganar mu yanzu ni dakene, ki fada mun komai kanki tsaye karkiji nauyin komai kinji". Dan Jim tayi kafin tace "Daman na gayawa Yah Khalil ina da saurayi, sedai kawai in kana so mu zama Abokai se yace Aa, wai na baka 1 week ka gwada Sa'arka, idan kafin satin daya ban fara sonka ba shikenan" tayi shiru "Idan kuma kika fara so nafa?" Ya tambayeta cikin sigar wasa se ta yi murmushi ba tareda tace komai ba ya sake ce mata "Hakan ma nagode ni kuma na tabbatar miki kafin cikar wannan wa'adin sena kafa gwamnati na a zuciyarki tunda ina sonki zan kuma yi duk yanda zanyi kema ki soni. Ki saka a ranki kawai kin zama tawa dan satin nan yana cika tofa babu wata sauran magana se kawai na turo iyayena ayi maganar auranmu ba kuma nason ya wuce wata daya kin zama matata". Shiru kawai tayi tana jin ikon Allah ji wani azarbabi to taji ta gani ai ita dai tasan ba zata taba son wani bayan Noor ba kawai dai zata bata masa lokaci nr sati yacika ya kama gabansa da haka sukayi sallama akan ze sake kiranta. Wasa wasa a hankali cikin kwana biyu wata irin shaquwa ta shiga tsakaninsu. Rashin lafiyar da Umaimah takeyi ta sake bashi damar samun lokaci da Humairan dan ta koma dakinta na qasa gaba daya bata hawa saman sedai shi ya sauka ya sameta shiyasa ya samu guri yake baje kolin soyayyarsa da yar yarinyar da a hankali ya fuskanci bata san komai ba. Soyayyar da take iqirarin tana yiwa Noor din soyayya ce ta yarinta kawai dan haka yayi amfani da wannan damar ya cusa mata sonsa a ranta ba tareda ta sani ba. Kullum sukanyi waya sau uku sau hudu ko be kirata na zata kirashi ita, Chat kuwa duk sanda ya bude ze tarar da saqonta dukda maganar tasu rabi duk shirmen yarintarta ne wanda yake masa dadi sosai. Ranar da suka cika kwana shida da yarjejeniya da daddare yana kwance a Falonsa suna waya yake ce mata "Kinga Gobe wa'adin da kika dibar mun ze cika, dan haka ya kamata ki fada mun sakamakona idan har naci nasara a goben zan bayyana miki kaina, idan kuma banyi nasara ba se in ce miki Allah ya hadamu da Alkhairi, idan mun hadu a Aljanna na gaya miki nine Ibrahim". Humaira da shaf ta shagala ta manta da wani zancen Yarjejeniya a tsakaninsu, tana zaune a kusada Mama suke wayar seta tashi dan bata so taji abinda zata fada masa. Daman tunda ta fahimci yawan maganar da sukeyi da Ibrahim din take mata tsiya. Noor kansa yanzu ba wani bashi lokaci take kamar da ba da yawanci ita take nacin kiransa ko tace yazo yanzu da ta samu wani yasa idan ya kirata mara ba idan be kira ba shikenan ita da kanta ta gane banbancin soyayyar yarintar da ake ta fahimtar dacita data babban mutum. Ita da Noor ko yaya tayi masa abu ya ringa fada da Masifa kenan se tayi ta bashi haquri amma Ibrahim ko lallabata yake kamar kwai baya son bacin ranta ko kadan. Ko waya suke yaji muryarta wani iri ya ringa tambayar meya sameta ko me take so kenan ita kuma daman tana son ayita lelenta seta shagwabe tayi ta masa sangarta yana biye mata abinda bata samu a gurin Noor. Seda ta kwanta akan Gadonta kafin ta bashi amsa da cewa "Toh ai da sauran lokaci har zuwa gobe, sannan nima bazan fadi maka sakamakon ba se na ganka ido da ido wannan ne qarashen cin jarabawar dan bazanyi cinikin biri a sama ba. Kai ka sanni kasan komai a kaina amma ni sunanka kawai na sani ko Yaya Khalil dana tambaya hotonka cewa yayi kace karya nuna mun. Toh gobe kazo na ganka sannan se na yanke hukunci". Murmushi yayi a ransa yana cewa " Ashe tana da wayo" a fili kuwa yace mata "Shikenan, amma ina so kiyi mun wani alqawari, koda ace kin ganni in har a zuciyarki da farko kin yarda da soyayyata karki canza" "Ban gane ba?" "Ina nufin idan kika ganni karkice saboda matsayina a gurinki zaki qini, in har dagaske kin kamu da sona karki bari wani abu ya canza miki ra'ayi..." Maganar ce ta maqale saboda ganin Umaimah da yayi tsaye akansa. Yayi nisa cikin shauqin soyayya da sam beji zuwanta ba. Kashe wayar yayi ya miqe zaune yana kallonta. Duk wata dakiya da Mazantaka dayasan yana dasu seda ya tattaro ya yafa dukda yanda zuciyarsa take bugawa da irin kallon da take jifansa dashi amma haka ya dake, dakyar ya iya bude baki yace mata "Wani abun kike buqata, me yasa baki kirani a waya nazo dakaina ba kika hawo bene bayan likita ya hanaki?" "Kira nawa zanyi maka Munafuki? Gara da baka daga ba ai saboda Allah naso na yana so nazo na tarar da cin Amanar da kakeyi mun yasa shiyasa baka dauki wayar ba. To wallahi ka dauka yanda kake iqirarin ta fada soyayyarka ka dauka cewa ta fada a ramin masifa da bala'i ne dan koma wacece kake magana da ita senaga bayanta wallahi" Umaimah ta fada tana huce kamar wadda ta hadiyi Maciji. Wani kallo ya watsa mata kafin ya miqe tsaye yana kallonta shima yace..... "Kin san yanda kika huda zuciyata ba tareda sallama ba kika shiga? Toh haka tayi mun. Ki saka a ranki keda ita matsayinku daya a zuciyata kuma ki saka ran shigowarta cikin gidan nan bada dadewa ba" yana gama fadar haka ya wuce ya bar Umaimah da mamaki ya sa ta kasa rufe bakinta. Seda ya shige daki kafin ta dawo hayyacinta babu bata lokaci tabi bayansa tana cewa "Wallahi baka isa ba Khalil qarya kakeyi babu wata mace da zaka iya so bayan ni ballantana har ka kawota cikin gidanka, duk kuwa wadda tayi kuskuren shiga rayuwarka ta fara qirga kwanakin da suka rage mata a duniya" 'Bam' ya bugo qofar dakinsa ya rufe daidai ta tura kai zata shiga har seda ya bugeta. Ihu ta fasa ta shiga buga qofar da qarfin gaske tana zage zage amma ko Gezau Khalil dake cire kayan jikinsa beyi ba. Wanka ya shige dan fita ma yake so yayi daga gidan, gara yaje gurin Humairanshi ya ganta ko zeji sanyi a ransa Umaimah ko idan taga dama ta qona gidan saboda Masifa amma a wannan karon babu gudu babu ja da baya yaga matar aure. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 60 "Wallahi baka isa ka fita daga gidan nan ba yau" Umaimah da tayi caraf ta riqe rigar Khalil ta fada. Kallonta yayi yanda ta birkice gaba daya kamar wadda ta shiga hauka shida yaji shiru ta dena bugun qofar ma ya zata sauka tayi ashe tana tsaye. Qoqarin zame rigarsa ya shigayi a hankali dan baya son abinda ze saka ya jajjigata saboda jikinta amma ina ita bata duba hakan ba sake cukuikuye shi takeyi tana zabga Masifa wanda shi bama gane abinda take fada yake ba. Ganin tana neman bata masa lokaci yasa ya daka mata tsaawar da ta saka ta sakinsa babu shiri taja baya, da hannu ya nunata yace "Ki kiyaye ni Umaimah" se ya ja tsaki ya barta a tsaye, wayarsa da muqullin mota ya dauka ya fice, kafin ta sakko qasan se jin tashin motarsa tayi alamar ya bar gidan gaba daya ma. Bata damu da yana yin da take ciki ba ta fice zuwa bangaren Hajiya tana rusa kuka kamar wadda aka aikowa da saqon mutuwar Mama. Hajiya dake kishingide kan kujera bata jima da dawowa daga Asibiti ba jikine ya motsa mata daren jiya kwana tayi da ciwon kai seda taje aka ce hawan jininta ne ya tashi gama shan maganinta kenan tana hutawa Umaiman ta fado seda qirjin Hajiya ya buga ganin yana yinta ta tabbatar da ba lafiya ba. A qasa ta zube tana kuka kamar ranta ze fita, Hajiya ta rude tambayarta take meya faru amma ta kasa bude baki tayi magana sema qara qaimi take gurin Kukan tana dafe kai da ciki ita dai Hajiya ganin ba zatayi magana ba ya sa ta wawuro wayarta ta shiga kiran Khalil. Yana tafe tuqi yake cike da nishadi saboda zejr yaga rabin ransa. Kiran Hajiya ya shigo wayarsa ko ba'a fada ba yasan Umaimah ce dan haka ya amsa wayar ya saka a Speaker yaci gaba da tuqinsa. Muryar Hajiya yaji tana cewa "Khalil lafiya? Me ya faru? Meya samu Umaimah take irin wannan kukan ko mutuwa aka mata?" A tausashe ya kira sunan Hajiyar jin yanda take magana yasan hankalinta a tashe yake dan haka yace "Hajiya, kinga dazun nan muka dawo daga Asibiti kuma sunce ki samu hutu karki bari wani abu ya dameki. Dan Allah ki tafi sama ki kwanta ki qyale Umaimah, babu abinda akayi mata, damuwarta ce ta motsa take so se ta dagawa kowa hankali ki rabu da ita kawai gani nan dawowa gidan nima na fita abu zanyi yanzu zan dawo ba dadewa zanyi ba. Dan Allah Hajiya karki biye mata ki shiga daki ki kwanta saboda jikinki". "Amma Babana meya faru har haka kaga kaga irin kukan da takeyi kuwa...?" Hajiya ta sake fada se yayi saurin katseta ga kuka me hade da ihun da Umaiman takeyi ya dame shi yace "Na sani Hajiya nidai ina roqonki karki damu kanki ki barta yanzu zan dawo koma menene zanji dashi" "Shikenan, seka dawo din amma kayi sauri" ta fada kafin ya kashe wayar. Tagumi ta rafka tana kallon Umaiman dake rusa kuka duk ta hada zufa saboda masifa, Ajiyar zuciya tayi ta miqe sakyar tana kallonta tace "Kiyi haquri kiyi shiru Khalil din yana hanya bari na shiga ciki idan yazo se naji abinda ya hadaku" tana gama fada ta wuce sama dakyar take takawa saboda kanta dam sara mata ga jiri haka ta ringa kama qarfen Benen harta haye. Umaimah data tsayar da kukanta kamar anyi ruwan sama an dauke tabi Hajiyar da kallo baki sake saboda tsabar mamamkin abinda tayi mata. "Bantan uban nan" ta fada a fili kafin ta yunqura ta miqe. Fita tayi ta koma part dinsu, a falon ta ringa safa da marwa tana lissafin abinda zatayi, wato hade mata kao zasuyi shida uwarsa, ke nan ma tasan da zancen auren da yake iqirarin zeyi? to wallahi ko sama da qasa zasu hade ba'a isa ayi mata abinda ake shirin yi ba, daga shi har Hajiyan daidai take dasu. Zabura tayi ta shige daki, Ruqayya dake goge goge tana satar kallonta a fili tace "Allah ya kyauta' dan tunda aka fara rigimar tana jinsu har sanda Khalil din ya fita Umaiman ta bishi, da ace uwar dakin nata me fahimtace da tayi mata magana akan abubuwa da yawa da takeyi da basu dace ba. Ta girmi Umaimah nesa ba kusa ba da ta fita ilimin zaman duniya shiyasa take ganin baiken Umaimah akan irin abubuwan da takeyi. Khalil Yana fita daga gidan ya kira Humairah a zuwan Ibrahim akan gashi nan a hanya. Ce mata yayi tafiya ta kamashi yau da daddare dan haka baze iya jira har gobe ba kafin yaji amsarta ta tanadeshi kawai yana tafe. Suna gama wayar sega kiranta a dayan Layinsa, seda yayi dariya son ransa har kiran ya katse kafin ya bita. Haka take, duk sanda Ibrahim ya rikita qaramar kwakwalwarta seta kirashi neman mafaka yanzun ma tana dagawa tace "Yah Khalil abokinka ne, wai kaji yanzu ze zo bayan kuma se gobe ne kwana bakwai din zata cika" "Eh munyi magana dashi wani aikine ya taso masa ze tafi Lagos yau shiyasa yace ze zo dan idan ya tafi ze dade be dawo na shiyasa. Nima naso muzo tare amma ban samu dama ba ina wani abu duk yanda kukayi dashi zanji dukda ma dai nasan mun rigada mun cinye jarabawar ai" ya bata amsa se tayi shiru kafin a sanyaye tace "Toh Allah ya kawo shi lafiya, amma dai ni da ya bari ma kawai seya dawo din" "Aa yanzu kuma? Yaushe ne kike cewa kedai kin matsu ki ganshi seda zezo kuma kice wani ba haka ba saboda gulma" Khalil din ya sake fada seta rufe fuska kamar tana gabansa a ranta tace "Shi komai mukayi magana s ya gayawa Yah Khalil" a fili kuwa tace masa "Ni dai Aa, indai be fito ba kace ya bari ba yau ba wannan ma ai kwange ne dan kwanakin basu cika ba ai". "Toh sedai idan kin fita ki gaya masa dan gashi nan yamun Text cewar ya iso yana qofar gidan, kiyi masa iso". Ba shiri ta kashr wayar qirjinta ya shiga bugawa jin cewar ya iso, ta rasa me yasa take ta faduwar gaba akan haduwar tasu, ita dai ba zata ce bata damu dashi ba dan tasan ba wai Sonsa ta fara ba kawai tana jin dadin hira dashi kuma bata so su dena magana shiyasa ma tace ya bari se ya dawo daga tafiyar duk ma lokacin da ze dauka acan. Qarar wayarta ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi, Noor ne, gabanta ya sake faduwa data tuna sunyi dashi zezo tasan kuma ya iso din ne shiyasa ya kirata dan Habibu yana gida yazo hutu shi kuma baya shigowa cikin gidan idan Habibu na nan dan basa ga maciji da dai baya nan daman a falon Mama ake hirar kosu saka kujera a tsakar gida. A salube ta zura Hijabin da tayi sallar La'asar ta fita, babu batun tsayawa gyara fuska duk irin burin da ta ci na shan kwalliya randa zasu hadu da Ibrahim har kayan da zata saka ta ware su ta ajiye amma shirinya rushe. Mama na zaune tana Lazumi ta fito, da kallo ta bita ganin yanda take jan qafa fuska kamar me zazzabi tace "Ke se ina haka kike jan qafa kamar me ciwo?" Dakatawa tayi tana kallom Maman tace "Abokin Yah Khalil ne yazo" "Abokin Khalil? Ina gobe kika ce ze zo har na bawa Maryam tayi masa kayan kwalama kuma in shi din ne haka zaki fita da farar fuska qozai qozai kamar wadda ta tashi daga jinya?" Mama ta fada tana tashi tsaye daga inda take seta sake narke murya kamar zata fasa mata kuka tace "Nima bansan ze zo yau ba kawai kirana yayi wai gashi nan zuwa goben zeyi tafiya, kuma ni munyi magana da Nuru zezo yana waje ma shima ya kirani". Se Mama ta tafa hannu tace "Ni Asiya naga ikon Allah. Yanzu saboda Allah kinsan mutum ze zo gurinki tun dazu ba zaki tashi ki gyara ba haduwar farko zaki fitar masa a haka kamar wata tsintacciya? Shi kuma Noor din da kika gayyato na magani da menene? Da yace miki ze zo ba zaki ce masa Aa ba?" "Nifa Mama bansan yau zezo ba, seda muka gama magana da Nuru kafin shiya kirani nama kira Yah Khalil ko zece masa ya dakata yace wai ai ya kusa qarasowa ma da tare zasu zo" Humairan ta sake fada se Mama ta aika mata daquwa tana cewa "Ba Nuru ba Fitila ma taci gidansu. Wuce ki cire wannan Hijabin kamar me takaba ki nemi kayan Arziqi ki saka kuma ki gyara fuskarki, shi Nuran zan saka Habibu yanzu ya korashi in Baqon ya tafi ya dawo kuci gaba da shashanci da batawa juna lokacin" tana gama fadar haka ta shiga kwalawa Habibu dake cikin daki kira. Juyawa Humaira tayi dakinta dan tasan Mama ba zata bari ta fita a hakan ba tunda tace, ta bude Wardrobe din kayanta tana kallonsu, bata ma bi takan kayan da tayi niyyar sakawa ba ta zaro wata Abaya baqa Mansur ne ua aiko mata dasu kwanaki. Hijabin Jikinta ta zare ta mayar da Abayar. Ribbon din data daure gashinta me tsaho da santsi irin na Asalin fulani ta zare ta sake matse gashin ta mayar dan bata da lokacin tajewa, bama tason taba kan se dole zafi yake mata. Farar hoda ta goga da Vaseline a bakinta kafin ta qara turare kadan dan bata jima da wanka ba ta shafa turare kuma, mayafin rigar ta rufe kanta dashi, qirjinta ya buga sanda taga kiran Noor, hannu na rawa ta daga wayar tasan za'ayi haka muryarsa a hade cikin fushi yace "Da kinsan kina aiki me yasa zaki ce nazo kinsan daga inda na taho yanzu kuma ba zaki gaya mun da kanki ba se ki aikomun wancan Ajawo din yazo yanawa mutane hayaniya wallahi ki ja masa kunne ya kiyayi randa zamu hade dashi kuma karki kuskura ki kirani" be bata damar cewa komai ba ya gama bambaminsa ya kashe waya. Ta maida wayar kan mudubi jikinta na daukar rawa yanzu tasan yayi fushi kafin kuma ya sakko se Allah saurin da take tayi akan ta fita ita ta lallabashi ya tafi kafin Yah Habib yaje dan tasan daman seya ja mata gashi yanzu yace karma ta sake kiransa. Goge kwallar data ziraro mata tayi jin Muryar Mama tana shirin shiga dakin, Maman ta shigo ta kalleta yanda taga fuskar Maman kamar wadda aka biyawa aikin Hajji ya bata mamaki amma tayi shiru "Kina nan tsaye kina solobiyancin naki ga mutum zaune yana jiranki, yi maza da Allah ki fita in banda ma Allah me kyauta da qari har ina ke ina shi koda yake Addu'a tace ta karbu kai Allah na gode maka". Ita dai bin Mama tayi da kallo danbata fahimci inda zancenta ya dosa ba, wannan murna da takeyi kuwa itama bata san ta mecece ba sedai jin da tayi tace baqon yana jiranta ta gane ciki suka shigo dashi kenan, to ko Mama tasan shi ne? Zama ta sanshi tunda shima Abokin Yaya Mansur ne. Tsaki taja a fili ta fito ranta babu dadi duk wani zumudin ganin Ibrahim ya disashe mata saboda batawa Nurun ta rai da akayi. Ji tayi bugun zuciyarta ya qara sauqi ta tsaya daidai corridor da ze fitar da ita daga inda dakunan su yake zuwa cikin falon tsabar yanda gabanta ke tsinkewa seda ta dafe qirjin da hannu biyu. Muryar Khalil take jiyowa qasa qasa yana magana da alama waya yakeyi, wannan ne ya bata kwarin guiwar daga qafarta taci gaba da tafiya kenan ba shi kadai yazo ba amma da Yah Khalil yace baze rakoshi ba. Kanta a qasa kamar farin shigan munafunchi ta shiga falon da sallama. Daga bakin qofar ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, ganin Khalil din shi kadai a zaune yana waya yasa ta qarasa shiga ta samu kujerar gefensa ta zauna qirjinta naci gaba da bugawa a gefe kuma tana satar kallonsa yanda yayi kwalliya yasha shadda kamar wani sabon Ango se zuba qamshi yake ga Turanci yanayi yanda kasan Rainon Ingila. Seda ya qara kusan minti biyar bayan ta zauna kafin ya kashe wayar yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi. Murmushin itama tayi ta shiga gaisashi ya amsa yana kallonta sukayi shiru na dan lokaci Humaira ta waiwaya ta kalli qofa, so take ta tambayeshi ina Ibrahim amma tanajin kunya dan haka ta mayar da kai qasa tana wasa da zoben hannunta. Khalil kuwa ido ya zuba mata yana sake qare mata kallo a yanzu ne yake sake ganin quruciyarta yarinya ce sosai kodan da da Jilbab yake ganinta shiyasa take dan cika masa ido? Lallai se abar zuciya idan ba haka ba shi da yake da cikakkiyar Mace ta ko ina me zeyi da wannan yar yarinyar. "Yaya, naganka kai kadai" Humaira tayi maganar a hankali ganin kusan minti goma ya zura mata ido bece komai ba, komawa yayi ya jingina da kujerar da yake kai sosai ya sake zuba mata idanunsa da suka saka taji zuciyarta na tsinkewa ga wata sabuwar faduwar gaba da takeji seta miqe tsaye danbazata iya cigaba da jure kallon da yake mata ba Khalil na ganin ta miqe shima ya miqe da sauri ya tareta ganin tana neman barin falon yace. "Ina kuma zakije?" "Uhm ruwa zan sha" ta bashi amsa tana ja da baya tareda rarraba ido saboda yanda ya matsota. Da ido ya mata nuni da ruwa da Lemon da aka kawo masa seta hadiye yawu dakyar tace "Daman na manta wayata ne a ciki zan koma na dakko" "Koma ki zauna" ya fada yana sake tsareta da ido, kamar kuwa zata fasa masa kuka haka ta tabe fuska ta koma inda ta tashi ta zauna. Allah ya sani wannan kallon da yake mata ita tsoratata yakeyi kuma shi Ibrahim din ina ya tsaya da har yanzu be qaraso ba bayan yace ma ba tare zasu zo ba. "Aisha" ya kira sunanta da wani sauti da seda tsigar jikinta suka zuba, sautin muryar da Ibrahim yake mata magana taji dan haka ta daga kai a hankali ta kalli bakin qofa dan taga shigiwarsa amma bata ga kowa ba. "Aishatu" ya sake kiranta da ainihin yabda Ibrahim din yake kiranta gaba daya ta shiga rudani, me kenan hakan yake nufi? Wannan Yah Khalil ne amma ya akayi yayi muryar Ibrahim har ya kirata da sunan da shi yake kiranta. "Aishatu, na kasa zurewa na jira har zuwa gobe, son ki yayi mun yawa idan na wuce yau banji matsayina a gurinki za'a iya wayar gari a ga na sheqa Soyayyarki tayi Ajalina" ya sake fada kansa tsaye yana kallonta, yanda take mutsu mutsu ya tabbatar masa da ta shiga rudani. Humairah kuwa wannan karon a mugun firgice ta daga kai ta kalle shi jin abinda yake fada, kasa fassara maganar sa tayi dan haka tace kawai tace masa "Ina Ibrahim?" Shi kadai ne amsar da take da buqatar ji a yanzu "Gani" ya bata amsa kai tsaye seta ware ido akansa tana kallonsa jin abinda yace "Nine Ibrahim Khalil, ko akwai wanda kike tsammanin gani daman bayan ni?" Ya sakw tambayarta yana dage mata gira. Yanda tayi da fuskarta seda ya bashi dariya harya kasa hadiyeta. Yanda kasan wanda ya gayawa wani mugun Abu haka ta miqr da sauri tayi cikin gida be tsayar da ita ba shima ya bita da dariya kawai, komai aka hada da yaro dai se an ga quruciya. Wayarsa ya dauka ya shiga kiran Layin Mansur. "Yaya Mansur ina wuni ko nace barka da dare dan nasan ku daren ku ya shiga" Khalil ya fada bayan daya amsa sallamar da Mansur yayi masa. Daga daya bangaren Mansur yace "Da alama shaye shaye ka fara ko idan ba haka ba ni zakace wa Yaya saboda Dan iska ne kai? Ni ba surukinka ba ba komai ba kace mun wani Yaya bayan ko a shekaru aka qirga ka girme balle kace hankali ka qaro yau zaka bani girma". Dariya Khalil ya fashe da ita shima Mansur din na tayashi kafin yace "Ka sani ko zaka zama surukin nawa ai abun na Allah ne" "Wa Allah ya tsareni da zama surukinka dadai wannan matar a gidan ka ko yan uwan maqotan mu da na sani bazan bari su baka mata ba" Mansur ya sake fada se Khalil yayi murmushi yace "Toh Yaya Mansur ya zanyi dakai tunda haka kace" "Ka gama iskancinka ka fada mun abinda yasa ka kirani Malam" cewar Mansur, se Khalil yayi saurin cewa "Zan sake kiranka zansu ina tsakiyar wani Important deal ne, kaidai da yayi clicking ka fara saka ranar zuwa Naija nan kusa" be jira amsar Mansur ba ya kashe wayar ganin ta qaraso cikin falon tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Humaira Wani fitsari taji ya matsota saboda maganganun Khalil din ba shiri ta miqe dan karya zubo tayi abin kunya, dakin Mama daya fi kusa a cikin corridor ta fada, Mama na waya dukda bata san dawa suke magana ba amma tasan maganar ta akeyi dan taji Maman na cewa "Wallahi in gaya miki, gashi can a falo" ita dai ta wuce ta tsula fitsarinta. Sink ta dafe bayan data wanke fuskarta ta tsaya tana kallon kanta a mudubi. Tunani takeyi ta yaya akayi Yah Khalil ya zama Ibrahim kodai wasa suke so suyi mata da hankali? Kiran da Mama take mata ya sakata fita ta tsaya a bakin qofar. "Ke kuma lafiya kika shigo kamar an koroki?" Maman ta fada tana kallonta seta narke fuska tace "Mama Yah Khalil ne, wai shine Ibrahim yace" "Aa, ke da baki san Khalil Ibrahim bane ko Yaya?" Maman ta sake fada kamar bata fahimci abinda take nufi ba. Kan gadon Maman ta zauna tana cewa "Mama bafa suna ba, wai shine Ibrahim din da muke waya dashi wai fa Mama Yah Khalil ne yake sona" ymta qarasa maganar kamar zata fashe da kuka dan tunanin wai Khalil ke sonta ma qara firgitata yakeyi, ita fa Humaira Khalil yake so ai abin ya mata nauyi. "Ke fa shirmenki yawa ne dashi, to se akayi Yaya dan Khalil nasonki ina nan kike raba rana da dare kina zancen Ibrahim kuma yazo shine zaki bi duk ki kidima kanki kamar wadda tayiwa sarki qarya. Ni da Allah wuce kin baro mutum shi kadai a zaune" "Mama wai baki gane abinda nake fada ba" ta sake fada ganin babu wata alamar damuwa a zantukan Maman, se kuwa Maman ta miqe tana cewa "Wuce, idan ya tafi kya ganar dani koma menene". Babu yanda ta iya haka ta fito, tana qarasawa tajishi yana waya a hankali take tafiya harta zauna akan kujera kanta a qasa. "Kin gama gudun da babu gurin zuwa" ya fada yana zura wayarsa a Aljihu, ita dai bata amsa masa ba kanta na qasa tana sake nanata wai Khalil ne Ibrahim dinta, dashi duk suka ringa wannan waya da hira. Tunanin yanda suka musayar maganganu ta ringayi taji kamar qasa ta bude ta shige, yanda ya ringa mata wayo yana tambayarta abubuwa ita ko ta ware tana bashi amsoshi daidai da saninta ashe duk Yah Khalil ne kai wannan abin kunya ina zata kaishi. "Haba Mana Aisha, har cewa fa kikayi badan Haramun bane da idan muka hadu har Rungumeni zakiyi saboda yanda kike Jina a ranki ko kin manta" Khalil ya jefo mata maganar, ta daga kai ta kalleshi kafin taha pillow ta rufe fuska se jin shashsheqar kukan ta yayi ba shiri ya isa inda ta ke ya durqusa qasab kujerar yana cewa. "Subhanallahi me kuma akayi na kuka daga wasa? Allah ya baki haquri baki ce haka ba. Ni ne nace da ze yuwu har rungumeki zanyi dan kiji yanda zuciyata taje bugawa akanki koba haka". Rarrashinta ya ringayi har seda ta dena kukan ta dago fuskarta da tayi Ja. "Me yasa ka boye mun baka gaya mun kaine Ibrahim ba?" Ta fada cikin muryar Kuka, Khalil dake tsiyaya ruwan sanyi a cuo ya miqa mata ta karba amma bata sha ba. Murmushi yayi mata yace "Ki sha zan gaya miki komai". Seda tasha ruwan ta aje cup din se ajiyar zuciya take shiko a zuciyarsa mamaki yake na abinda ya sakata Kuka, yanzu meye abin zafi a nan da har Mutu zeyi kuka banda dai Humaira da son maida qaramin Abu babba. "Kinsan me yasa naqi na bayyana miki kaina? Saboda wannan abun da kikayi. Nasan idan na fito kaitsaye nace ina sonki zakiyita koke koke ne na rashin dalili kuma nasan be zama lallai ki yarda ba sannan daga qarshe nayi loosing respect din da kike bani na Yaya saboda ku Mata haka kuke, masu qananun shekaru precisely. Da babba wanda ya zarce shekarunku ya nuna yana sonku se ku maida abun wani daban ku dauka kamar wani babbanlaifi ya aikata dan ya ce yana sonku. Shiyasa na zabi na fara shigar miki da soyayya ta idan na samu karbuwa na yarda da kona bayyana miki kaina ba zakice Aa ba kamar dai yanzu na san na rigada na samu fili a zuciyar Aisha ko kawai nayita baza shanyata". Kanta ma qaa harya qare magana bata iya dagowa ta kalleshi ba, da gaskeyarsa kamar yanda ya fada din gani takeyi kamar sabo ace kamar sa yana sonta shi kansa Ibrahim din kawai bata san yabda akayi ya shiga ranta ba. Amma ita ko a hanya taga Babba ya kula yar yarinya ma kallon Dan iska take yi masa a ganin ta kowa ya ji da daidai dashi babu dalilin da ze saka babban mutum irinsu Yah Khalil din yazo yana son yan yara irinsu sedai a barsu dasu Noor sune daidai shekarun su. "Kinga bamuyi haka dake ba, kinyi mun Alqawari duk randa muka hadu zaki gayamun gaskiyar abinda kikeji game dani a zuciyarki babu kwange bare coge amma shine yanzu ina magana kinyi Shiru. Ki dago ki kalleni kiyimun magana. Ni na rigada na fada miki duk abinda ya kamata ki sani game dani, dagaske nake sonki da aure ba wasa ne ya kawoni gurinki ba, kuma saboda bana so na takuraki ko na zama silar da za'ayi miki dole ya saka na zabi neman soyayyarki da kaina kinsan idan naso kai tsaye zan tunkari magabatanki da magana sedai kawai ki ganki a gidana amma banyi haka ba saboda ina son aurenki aka yardarki shine ze bamu damar shimfida rayuwa irin wadda nake fata dake". Ita dai kamar wadda aka daurewa baki haka tayi shiru tana jinsa harya gaji da magana shima yayi mata shirun kawai yana kallonta. "Matsalar qananan yara kenan" ya ayyana a zuciyarsa, yanzu da babbar budurwa ce data san kanta ba ruwansa da wannan bata lokacin kai tsaye zeje ga buqatarsa amma yanzu kalleshi yanda ya lalace a gaban Kusan yar cikinsa yana lallabata ta masa shiru kamar gunki. Tsaki yaja saboda ransa daya sosu ya miqe yana daukar muqullin motarsa ya kalli Humaira da itama ta dago jin tsakin nasa suka hada ido. "Bakya buqatar ki gaya mun baki karbeni ba dan naga hakan a aikace. Nagode da lokacin da kika bani inaso kuma ki dauka Ibrahim be taba wanzuwa a rayuwarki ba. Kici gaba da daukata a Khalil kamar yanda baki karbi alaqata ba bana so ki ringa tunota ballantana har ki kalleni da abinda ya wuce, ki gaida Mama idan kin Shiga ki gaya mata na wuce" ya fada yana kallonta kafin ya juya ya nufi qofa. A sanyaye ta miqr tabi bayansa, maganar bata son Ibrahim bata ma taso ba amma fa Yaya Khalil a matsayin Ibrahim shine abinda ta kasa yarda dashi. Ta yaya ma zata iya zama dashi a matsayin Miji abin da wuya wai gurguwa da auran Nesa. Binsa ta ringayi a baya har zuwa gurin motarsa. Khalil da besan tana biye dashi ba saboda yanda take tafiyar kamar mara Laka ya juyo ze bude motar ya ganta se ya tsaya yana kallonta. "Kayi haquri" ta iya fada dakyar idonta yana kawo ruwa "Haquri kuma name? Ai ni ya kamata na baki haquri bake ba, sannan ki goge wannan hawayen kar mutane su dauka wani abun nayi miki" ya fada ganin Samarin dake zaune a Majalisar Habibu suna kallonsu. Hannu biyu ta saka tana goge hawayen kafin cike da quruciya tace "Nidai dan Allah idan wasa kuke yimun ku dena, ka gayawa Ibrahim kawai inason sa daman ai cewa yayi sena fada masa sannan ze zo qila ma shiyasa ya turoka kayi mun wayo". Murmushi yayi yace "Me yasa ni bakya sona se Ibrahim?" "Kai ai Yayanane" ta bashi amsa da sauri se ya sakeyin qaramar dariya yace "Shikenan yanzu dai tunda bakya sona bari na tafi, zan roqi Allah ya bani wadda zata soni tunda nayi baqin jini a gurinki". Shiru tayi ya bude motar ya zauna kafinya janyo wata Leda me kyau daya ajiye a dayan sit ya miqa mata yana cewa "Ga Alqawarinki". Kasa karba tayi ya janyo hannunta ya saka mata ledar kafin ya tada motar. Bata motsa daga gurin ba har yaja motarsa ya tafi bayan ya daga mata hannu, fizgar da akayi mata ce tare da radadin da taji a fuskarta daya tabbatar mata da marinta akayi suka dawo da ita daga tunanin data lula lokacin har Motar Khalil ta bace daga gurin. "Wato wannan ne dalilin daya saka kikamun qarya akan aiki kikeyi har wannan Wawan yazo yana gayamun? Wani Dan iska ne yazo gurinki har kika rakoshi qofar gida dan ki nunawa yan unguwa ke kin riqa ko kin fara tara Samari?" Noor dake numfarfashi kamar wnada ya hadiyi kunama ya fada. Farar fuskarsa ta rikide tayi ja kanar wanda ya shafa Barkono. Kallonsa take har ya ida maganar cikin bacin rai ta fizge daga riqon da yayi mata, bata iya ce masa komai ba saboda yanda ranta ya shiga tafasa lokaci daya ta juya ta shige gida tana jinsa yana kwala mata kira amma bata ko juya ba. Haka ta wuce Mama dake zaman jira ta dawo ta gaya mata yanda sukayi da Khalil, tunda yazo suka gaisa be tsa qumbiya qumbiya ba ya fayyace mata cewar shine Ibrahim da yake waya da Humaira haka itama bataji kunya ba a gabansa ta ringa jera Hamdala ta kuma jaddada masa goyon bayanta akan hadin nasa da Humairah. Shigarta daki kuwa kaf seda ta kira yaranta ta shaida musu Mansur ne kadai bata samu ba kuma kowa yayi murna da hadin hatta da dangin Maman Humaira seda ta kira qanwar Mahaifiyarta ta gaya mata saboda tsabar zumudi. Kasaqe tayi tana kallon yanda ta shigo ta cillar da ledar hannunta ta wuce daki, tana shiga ta fada kan gado ta rasa abinyi se kawai ta fashe da kuka. Abinda Noor din ya mata ya bala'in qona mata rai,a gaban yan unguwa ze mareta kamar wani ubanta? Tunda take dashi kullum yanamata abun da bata jin dadi amma bata taba jin haushin sa irin na yauba kuma ta tabbatar da baya darajata dan idan yana ganin darajarta ko kallon banza wani yayi mata se inda qarfinsa ya qare ballantana ace shi da kansa ze daga hannu ya mareta a bainar jama'a. Kuka me ciwo ta ringa rerawa, Mama data biyo bayanta a tsorace ta dagota tana tambayarta lafiya seta fada jikin Maman tana sake rushewa da kuka har seda tayi me isarta kafinta haqura bacci ya kwasheta. Mama kuwa cike da damuwa ta koma falo ta zauna tana tunanin meya sakata kuka? Shigowar Habibu yana masifa nan ya gaya mata abinda ya faru a wajen baya nan abokansa suka kirashi yazo "Wallahi Mama Yan sanda zanje na dakko masa, akan me ze Mareta ce masa akayi jaka ce ko bata da gata da ze mareta? Idan bashida hankali ya shawo kwayarsa ta gaya masa qarya to zan hada shi da wadanda zasu ladabtar dashi" Habibun ya fada. Mama dake jimami ta tareshi da cewa "Aa Habibu abin be kai ga hukuma ba, ka bari ni dakaina zan rufa gyale na shiga gidansu na samu Asaben na gaya mata ta jawa danta kunne, ni tayi masa iyaka ma da Humaira tunda abun ya zama da haka toh kowa yayi takansa babu shi babu ita dan na gaji da wannan sa magana na Nura, kuma Alhamdulillahi ubangiji ya kawo mata Miji se yaje yaji da quruciyarsa daman abinda yasa tuntuni ban rabasu ba ganin bata da wani tsayaye ne". Dakatawa tayi a bakin qofa saboda jin abinda Maman take fada, yanzu rabata da Noor zasuyi kenan? Hawaye taji suna zubo mata, dukda haushinsa da taji akan abinda yayi mata bataji cewar zata iya rabuwa dashi ba dan tana sonsa, shi ta fara so kuma bata zaton akwai abinda ze rabata dashi. Wayarta dake hannunta ce ta shiga qara, sunan Ibrahim ta gani akai, duk yanda taso taqi daga wayar amma ta kasa, haka ta amsa ta saka a kunne amma ta kasa cewa komai. KHALIL Yanayin Humairan ya nuna mass koda ace be gama samun karbuwa ba yo yanada yaqinin hakan dan haka zuciyarsa a washe ya koma gida. Be tarar da Umaimah ba, shi sam ma ya manta da batunta seda ya shiga Hajiya ke tambayasa abinda ya hadasu sannan ya tuna. A taqaice ya cewa Hajiyan "Kishinta na rashin dalili ne ya tashi kawai dan taji ina waya kuma na shirya zan fita shikenan ta tayar da hankalinta" "Khalil kenan, nasan Umaimah nada rikici amma batayi haka kawai, dole sedai idan kai ka tsokanota ko kayi wani abu da ze tonota tukunna, kuma ko ba Umaimah ba, ni kaina daka shigo a haka daga yanayin shigarka zuwa fuskarka na zargi cewar akwai wani abu a qasa, duk kuma inda ka fito daga gurin Mace kake" Hajiyan ta fada tana karantarsa. Murmushi yayi yana cire hular kansa ya kalli Hajiyar yace "Kin canka daidai daga gurin sabuwar autarki nake. Ita kuma waya taji munayi da yarinyar shikenan ta tada hankalinta". Baki Hajiya ta saka tana kallonsa jin yanda kai tsaye yake sanar mata gurin Macen yaje, lallai ta tabbata koma wacece wannan dagaske take dan Khalil nada kunya kai tsaye baya iya sanar da ita irin wadannan maganganun sedai taji a bakin Yayyensa amma yau kai tsaye ya kalli idonta yake gaya mata gurin autarta yaje, wato auta ma ya sake yo mata. Gyara zama tayi tana kallonsa tace "Nikam Khalil meye ribarka idan ka dagawa matarka hankali ne? Sanin kanka ne idan ta tashi ba kai kadai ba duk Wanda ya shafe ta seta raba bacin ranka dashi me yasa bazaka haqura da duk wannan kule kulen Matan ba ku zauna lafiya tunda nidai banga ta inda ta rageka ba iyakar kyautatawa da kulawa koni Mahaifiyarka babu ta inda ta rageni ballantana kai da kake zaune da ita to me kuma kake nema da bazaka iya haquri da ita kadai ba? To idan har da gaske kake maganar auran nidai bada yawuna ba, bana son abinda ze kawo mana wani tashin hankali cikin gida muna zaune lafiya " A hankali ya zame daga kan kujerar da yake zaune ya durqusa kan guiwarsa a gaban Hajiyar yace "Hajiya, kiyi haquri da abinda zan fada kinga a lokacin da na hadu da Umaimah har na fara sonta baki sani ba. Na sani Soyayyar da kike munce ta shafeta da kuma kyautatawar da take miki yasa kike zaton kowa ma haka takeyi masa har ya zamana tasa kika fi sonta da kiyaye bacin ranta ma a yanzu sama dani da kika haifa. To muje a hakan Hajiya a gurinki Umaimah mutuniyar kirkice saboda ban taba kawo miki aibunta ba to mu cigaba da tafiya akan haka, amma ina roqon kiyimun adalci a wannan gabar ki ajiye tasirin Umaimah a zuciyarki ki kalleni a matsayin dan da kika haifa nazo miki da buqata ina so zan qara aure, badan Umaimah ta gaza ba sedan ina son wadda nake so na auro kamar yanda itama nake sonta. Dan Allah karkice Aa Hajiya, kar kuma ki kafamun wani sharadi kiyimun izini ko a gobe naso na daura aure karki hanani a duk sanda buwatar hakan ta taso mu ". *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 61 Sosai jikin Hajiyar yayi sanyi dan ya gama daureta da jijiyoyin jikinta, ya roqeta da karta hanashi kar kuma ta gindaya masa sharadi, daga yanayin muryarsa da yanda yake magana ita ta haifi abinta ta karanci wani daci a ciki ta tabbatar akwai abinda yake damunsa Wanda yake hadiyewa shikadai baya amayar mata. Kuma tabbas yayi gaskiya, dukda cewar tun a sanda ta fara ganin Umaimah haka nan yarinyar ta shiga ranta kuna ta qudurce zata nema masa auranta a sannan ma bata san da wata alaqa a tsakaninsu ba amma Soyayar da takeyi mata ta qara tasirabtuwa ne akan Son da takeyiwa Khalil din. Shidin na daban ne a cikin Yaranta ta fi sonsa saboda yafi kyautata mata. Sannan kamar yanda ya fada a kullum yana sake nanata mata Alkhairan Umaiman a gareshi kuma itama tana gani. Daidai da rana daya be taba zuwa ya kawo mata qararta ba idanka dauke abubuwan da suka faru wanda suma da idonta ta gani ba wai shi ya sanar mata ba kuma har kawo yanzu duk abinda ya faru ya wuce shikenan be taba dawo da maganar akan su sake tattaunata ba shi yasa take jin cewar Dan nata bashida wata matsala ita ma kuma take qoqarin ganin ba'a tauye yarinyar ba ta kowanne bangare kamar yanda itama bata tauye kowa ba. Ba yanda ta iya dan ya kashe mata bakin Magana ko qorafi a sanyaye tace "Shikenan Babana, Ina roqon ubangiji idan ya tashi baka ikon qarin ya hadaka da mace ta gari wadda zaku hada kanku ba tazo ta wargaza maka gida ba. Sannan ka kula dan Allah, bana so ka zama cikin irin mazan da suke wukaqanta matansu idan suna shirin kawo wata. Ka kula da matarka ka rarrasheta ka kuma nuna mata badan baka sonta ko ka gaza zaka kawo wata ba, Allah yayi muku Albarka yayi muku zabi na gari" "Amin Hajiya naji dadin maganar da kikayi kuma in sha Allah bazakiyi dana sani da zabin da nayi ba dan seda na duba yarinyar data dace dani tukunna saboda ba zanyi aurene haka kawai saboda ganin dama ba Aa ina da dalili kuma dole seda na nutsu na samo wadda zata cike mun gurbin da nake da gibi kafin na saka maganar a zuciyata" "Ikon Allah Babana wannan wace me sa'ar ce take neman ture gwamnatin Umaimah har kaniya aje kunyar nan take a gefe kake nuna mun muhimmancinta a gurinka" Hajiya data riqe haba saboda Mamakin Khalil ta fada. Seya shafa kansa alamar yaji kunya yace "Wallahi Hajiya wata yar yarinya ce, takwarar kice inaga ma Habiba ta girmeta" "Tofa, a ina ka samota kuma" ta sake tambayarsa, se ya miqe yana komawa kan kujera yace "A gidansu Mansur take yarinyar Qanin Mama ce" "Toh naji kardai wannan yarinyar Fara doguwa ko? sunzo lokacin tarewae mu tare da Hauwan. Ai kuwa tana da nutsuwa ga Hankali. Ni a sannan ma Khalifa nayiwa sha'awarta Allah nema be nufa nayi maganar ba saboda naga yarinya ce qarama sosai zasuyi daidai dashi to ashe yaya babba yayi masa shigar sauri, Allah ya tabbatar da Alkhairi amma batayi maka qanqantaba kuwa Babana?" Sauke kansa qasa yayi yana murmushi yace "Shekararta Sha bakwai fa Hajiya, in zan tuna su Jalila sanda aka musu aure ai duk basu wuce haka ba muna gama secondary kika ce aure za'a musu kowa taci gaba a dakinta to itama hakan ne bana ta qare makaranta zata ci gaba a nan idan tazo". "Toh Allah ya tabbatar mana da Alkairi yasa zamuga lokaci, amma ka zauna da Matarka ka sanarwa mata ta lumana dan Allah bana son wannan tashin hankalin kodan Halin da take ciki" Hajiya ta fada ganin Khalil na nemanya baro mata aiki. Miqewa yayi ya dauki hularsa yayi mata sallama ya fita ransa fes, ita ce zata iya kawo masa cikar a cikin tafiyar tunda kuma ya gyarota duk wani wanda ze zo da matsalarsa me sauqi ce. Dakinsa ya koma seda ya cire shaddar jikinsa kafin ya shiga kiran Humairan dukda bashida tabbacin zata dauka. Yana jin alamar ta daga yayi murmushi, kusan minti biyu yaji batace komai ba amma yanajin fitar numfashinta kamar irin na wanda take a tsorace ko wani abu "Yammatana babu ko kira kiji ya naje gida ko?" Ya fada yana zama a bakin gado. Shiru tayi bata ce komai ba, ya ringa janta ta da magana har seda ta fara amsa masa da Eh ko Aa, wato tunda ya kallafawa kansa soyayya da ita ya koyi yanda ake tafida masu qananun shekaru kamarta shiyasa be sha wahala ba gurin shawo kanta harta bude baki suka shiga hira kamar babu abinda ya faru, cikin dabara yake sake jaddada kansa a gurinta tareda yi mata alqawarurruka na yanda ze kula da ita ya riritata idan har ta bashi dama ta zama tasa. "Amma Yah Khalil Anty Umaimah fa? Na tabaji Anty Nusaiba tana fadar kishine da ita sosai, ni daman tun Asali ina tsoron Kishiya...." "Aisha" ya kira sunanta da dole tasa tayi shiru da maganar da takeyi, jin tayi shirun ya sakashi ci gaba da cewa "Ki fadamun tsakani da Allah kina so na kuma zaki aureni?" Shiru tayi saboda yanda tambayar tayi mata girma, dukda har zuciyarta amsar tambayarsa 'Eh' ce amma bata jin harshenta ze iya furtawa saboda kunya "Kinyi shiru ki bani amsa" ya sake katse mata tunani, kamar tana gabansa ta shiga mutsu mutsu tana so tayi maganar amma ta kasa se ji tayi yace "Idan ba zaki fadamun a waya ba zan dawo yanzu se ki fada mun face to face" "Aa karka dawo, ni wlh kunyarka nakeji" ta fada kamar zatayi kuka. Se ya saki murmushi ya ce "Toh ina jinki ki gaya mun, kina sona? Kuma zaki aureni?" Seda taja numfashi ta ajiye, ta kasa hana kanta cikin sanyi kamar me rada tace "Ina son Ibrahim, kuma zan aure shi". Kamar wanda ta kwararawa ruwan qanqara haka yaji wani sanyi ya ratsashi, qasa yayi shima da muryarsa sosai yace "Dagaske kike? Kin yarda na turo neman auranki ko wanne lokaci?" "Eh, amma ba yanzu ba ai sena gama makaranta na qara girma nan da shekara hudu" ta bashi amsa cike da sakalci se ya saki dariyar da be shirya ba yace "An gama yarinya tunda har kika fada da bakinki kin Yarda ai kin gama mun komai insha Allahu kuma ba zakiyi dana sanin zabata a matsayin abokin rayuwarki ba" daga haka sukayi sallama ya kashe wayar. Cike da doki da murna ya fita daga gidan, seda yayi sallar Magriba kafin ya sake kiran Mansur yana dagawa kuwa ya shiga yi masa masifa akan ya dameshi. "Kai qyaleni Mama tana kira idan mun gama waya zan kira ka?" Mansur din ya fada jin Kiran Mama na shiga wayarsa. MANSUR A rude yake cewa "Mama Khalil? Khalil dai Abokina kike nufi ko wani daban?" "Khalil nawa kake dasu Mansur da zaka wani kidime se kace wanda aka gayawq Sharri. Zancen aure fa nayi maka abin Alkhairi Amininka nason yar uwarka ai abin ka runtuma da gudu ka shiga Harami kayi sujuddushshukur ne amma ka tsaya kana wata barbarar baki. To shidin dai Ibrahim na gidan Alhaji Bayero, daman na gaya maka zaryar daya tsira a gidan nan duk zatona ma Qaninsa yakewa kamu ashe shi ta kansa yakeyi to yau dai yazo har gidan nan ya gaya mun da bakinsa yana sonta kuma sun dade suna soyayyarsu itama na tambayeta tace mun tana sonsa to me yayi saura kuma in ba muji daga gareshi yaushe yake son Auran ba kawai ayi a gama kowa ya huta. Daman na gaji da wannan yaron dake mana zarya, yau fa har Marinta yayi a qofar gida saboda ya ganta da Khalil din idan aka daura mata auranta ta tafi ba shikenan kowa ya huta ba yaje canya qarata da Rashin hankalinsa da zafin rai" Maman ta tare Mansur, "Gaskiya Mama in dai Amincewata ake da buqata toh ban yarda ba. Mama Khalil fa? I mean ba shine me matsalar ba Mama kinsan Mahaukaciyar da yake zaune da ita a matsayin Mata kuwa kinsan wacece Umaimah da ita kike so a hada Humairah kishi? Toh wlh ko Unaizatu bata isa tayi zaman kishi da Umaimah ba balle Humairah da a haihuwar Qauye ta kusa haifarta sedai idan kun shirya saka yarinya a masifa da bala'i to wannan kuwa idan ba haka ba tun wuri ki gaya mata ta kama kanta babu ita babu shi yaje can ya nemi mata amma ba'a gidan mu ba". "Toh naji abinda kace amma ni sam banga wata hujja da za'a ce za'a hana Khalil auran wannan yarinyar ba. Kai da kanka kace mutumin kirki ne tun yarinta har girma tare kuke halinsa babu Wanda baka sani ba sedai ka gayawa wani to me kuma ake da buqata bayan haka tunda an samu kyakykyawar shaida akan Ma'auri ina ruwanmu da wata matarsa ita zata aureta ko akanta zata zauna?" Mama ta fada cikin Halin ko in kula. Mansur ya dafe kansa, yasan Mama da bala'in kafiya akan abinda tayi niyya sannan ba tun yau ba tun kafin qannensa su gama aure take nuna sha'awar Khalil dinya nemi wata daga ciki tasha yi masa magana akan shi ya samu Khalil din da maganar ya bashi daya daga cikinsu amma yaqi, yakance mata "Ai Mama duk ya sansu idanda akwai wadda takr burgeshi a ciki da kansa ze magantu base na kai masa tallansu ba" Gashi yanzu ta samu cikar burinta kuma akanyar da take da ita kamar tsoka yasan kafin a shawo kanta ta gane illar da hadin yake tattare dashi za'a sha wahala. Haba Umaimah fa, babu ta yanda za'ayi ya bari a cuci rayuwar Marainiyar Allah a hadata da wannanmara tunanin da tsaf zata salwantar da ita a banza kuma shikansa Khalil din babu uwar abinda ze iya yi akai. Magana Maman take masa amma yana canya lula duniyar tunani seda ta sake cewa "Duk abinda Zakayi sedai kayi shi amma dan kaji aure ne babu fashi da yardar Allah gara ma ka saki ranka kayi fatan Alkhairi" "Shikenan Mama, Allahya zaba mata mafi Alkhairi" ya fada saboda ya datse maganar se kuwa tayi saurin cewa "Ai yama zaba mata sedai kace Allah ya tabbatar musu da Alkhairi" "To Allah ya tabbatar musu da Alkhairi" ya sake fada daga nan sukayi sallama. Layin Khalil ya shiga kira harta qaraci Ringing be daga ba ta katse ya sake kira nan ma haka dole ya haqura yasan idan ya gani ze kirashi zasuyi magana kuma dole ya janye qudurinsa dan inya kasa fahintar da Mama ta hana aurannan tota qarfin gaske ze saka Khalil dinya janye shi ai dole ta haqura. UMAIMAH Ganin da tayi zagayen dakin baze bata Mafita ba ya saka ta zura dogon Hijabi a jikinta ta zari muqullin mota ta fita. A karon farko tunda tayi aure ta nufi gidan Maman Asad da niyyar kai mata damuwarta ta kuma nemi shawararta. Kusan suma tayi a bakin qofa sanda ta shiga gidan, kunnuwanta suka jiyo mata Maganar Baban Asad din yana gabatarwa da Hajiyayyen wata yarinya dake ta faman sunne kai a matsayin qanwarta wai tazo duba Asad daya samu Tsautsayin karaya. Kasa qarasawa ciki tayi ta kafe a bakin qofar tana binsu da kallo daddaya, mamaki ya kasheta ganin ita Maman Asad din ko a jikinta tanata jan yarinyar akan tasha ruwa da lemon da aka kawo mata, tana qoqarin zuba mata ne ta lura da Umaimah dake tsaye, seta dakata tana cewa "Aa ke kuma daga ina haka kika cakare a bakin qofa? Ki qara so ciki ki zauna mana". Qarasawar tayi cikin kamar yanda tace ta nemi kujerar data fi kusa da qofa tanzauna har sannan tana kallon baquwar. Baban Asad cikin barkwanci ya kalleta yace "Aa me ciki ce da yamma sakaliya haka?" Banza ta masa idonta qur akan yarinyar data dago tana gaisheta, itan ma dai bata tanka mata ba Maman Asad ta hade rai tana kallonta tace "Bakiji tana gaisheki bane Umaimah?" "A matsayina na qanwar uwarta kota ubanta da zata gaidani? Nace ina buqatar gaisuwarta ne ko yaya ko kinji na kulata dana shigo gidan?" Ta hayayyaqowa Hajiyayyen se Baban Asad ya miqe baquwarsa ma ta mara masa baya yana kallon Maman Asad yace "Sweetheart bari na mayar da honey gida, akwai abinda kike da buqata ne na taho muku dashi?" "Babu komai Habibi Allah ya dawo da kai lafiya, qanwata nagode kwarai ko gaida mutanen gida Allah ya bada ladan ziyara ku jirani ina zuwa" Maman Asad ta fada tana shiga dakinta. Ita dai Umaimah baki kawai ta bude tana kallo ikon Allah da wannan yammaci. Hajiyayye ta fito da wata leda fara me tambarin wani company a hannunta ta miqawa yarinyar taqi karba tana ta barshi Baban Asad ya karbar mata harda cewa wai kunya take ji "Se Anjima, Anty ki gaida gida" yarinyar ta sake fadawa Umaimah kafin ta juya ta nufi qofa "Idan kika sake shiga sabgata se naci kaza kazan ubanki" ta dannawa yari yar ashariya ita dai bata waigo ba haka Baban Asad daya tasata gaba suka fice daga gidan. Masifa Hajiyayyen ta shiga surfa mata tana cewa ta wulaqantata a gaban baquwa yanzu zata tafi da ita tana cewa yar uwarta bata da mutunchi "Ina budurwarsa ce ya kawo miki ita har cikin gida kike washe mata baki baki dauki tabarya kin raba kan yar bura uba biyu ba?" Umaimah ta jefa mata tambaya seda ta harareta kafin tace "Budurwarsa ce se akayi Yaya? Dan kiji da kunnenki ma an saka musu rana wata shida masu zuwa zata zo gidan nan mu zauna tare". Tsaki taja na tsabar takaicin Hajiyayen ta miqe tana cewa "Idan har wannab rashin zuciyar Mama take cewa na koya a gurinku to wallahi bazan iya ba, in zauna Namiji ya takani, saboda tsabar rashin mutunchi ya dakko mun mace har cikin gida da sunan tazo gaisheni ko? Na rantse da Allah da nice sedai uwarta ta haifi wata, fetur zan zazzagawa yar iska na qoneta tas yanda zata zama izina ga sauran mata masu kula mazan mutane" "Ai kuwa da kema a tsakiyar kasuwa za'a ratayeki bayan an feraye miki naman jiki saboda ki zama izina ga sauran mahaukata irinki" Maman Asad ta fada tana jifanta da wani mugun kallo juyawa tayi ta fice tana cewa "Wallahi dana san abinda zan tarar kenan da banzo ba, ina neman maganin matsalata haka kawai nazo na sake haduwa da wani ciwon zuciyar ai dai Yah Hajiyayye kinyi asara wallahi kuma mata kika rako duniya". Ita dai Hajiyayye da kallo ta rakata harta fice daga falon kafin ta koma ta zauna akan kujera tayi shiru, idan tace ranta be sosu da zuwan budurwar Baban Asad ba tayi qarya. Kamar wasa ta fahimci ya qulla alaqa da wata a waje, da ta kwantar da hankali tayi amfani da wayo da fikira se gashi da kansa ya fito ya gaya mata yana neman aure har ya sanar mata da wacece yarinyar ya na hadasu a waya suna gaisawa kuma koda wasa bata taba nuna masa damuwa akan hakan ba. A kullum addu'arta Allah yasa su zauna lafiya da koma wacece ze kawo cikin gidan, abinda yake shirin yi ba haramun bane haka tashin hankalinta baze hana ba dan haka ta zabi da dayi haquri ta kuma maida komai nata ga Allah shiya qaddara qarin auran tana fatan ya sanya zaman lafiya da lumana a zaman su. Hajjaju Umaimah kuwa tana fita gidan Safinah ta nufa, wato Mama so takeyi ta zama lusara ta zauna namiji ya takata son ransa shiyasa tace duk damuwarta ta ringa sanarwa da yan uwanta su zasu nema mata mafita irin wannan sakarcin da sukeyi take so itama ta koya kenan kome? Kamar yanda ta zauna Anty Saratu take baza sharafinta a cikin gidansu da sunan ita ga Amarya haka take so kenan itama ta zuba ido tana zaune Khalil ya kawo mata wata su rabashi tare kenan ai kuwa hakan baze yuwu ba, dole ta tashi tsaye duk kuma yanda zatayi seta hana faruwar hakan. Horn ta ringa fafarawa a qofar gidan Safina kusan minti goma kafin aka bude qofar. Mijinta ne da kansa suka gaisa bayan ta ajiye motar ta shiga ciki har Bedroom din Safina ta tarar da ita tana kwance daidai akan Gado tana shan fruit salad ga waya a hannunta tana chatting. "Yanzu tsabar rashin mutunchi kina jina ina ta horn amma baki saka an bude mun qofa ba" ta fada tana cire Hijabin jikinta dan ya dameta se Safina ta miqr zaune tana cewa "Yi haquri qawata, na aiki Ado Baban Maya nace yazo ya bude miki na manta kuma yana soya mun Irishi inaga shi ya tsaya kwashewa kafin yazo ya bude". Seta saki baki tana kallon Safina jin abinda take fada. Baban Maya da soya dankali daman tasha Mamakin bude mata Get da yayi mutumin da a izza irin tasa ko shine ya dawo gidan me gadi baya nan sedai Safinan ta fito ta bude masa amma yau shiya budewa baquwarta qofa. Kwankwasa qofar akayi Safina ta bada umarnin shigowa se gashi dauke da Try ya doro Irish din daya siya ga kuma butar shayi da kwanon sugar. Hijabinta taja ta rufa ya ajiye kayan ya tsaya yanda kasan dan aiki yana tambayar Safinan ko da abinda take da buqata ne ta wani yamutsa fuska tana cewa "Babu komai daman Toilet dina nake so a adauraye amma ka barshi idan na tashi ko zuqa Anjima na wanke". Jikinsa na rawa yace bari ya wanke, Umaimah ta zabga tagumi tana kallon ikon Allah ya shige kuwa ya hau wankin toilet din ita dai yau ta fito a Sa'a daga ganin abin Takaici sena Mamaki wani na bin wani. Seda Alhaji Lawal ya wanke Toilet tas kafin safina ta sallameshi ya fita, Umaimah ta rakashi da kallo Maganar Safinan ta maidota hankalinta tana cewa "Qawata me kike kallo ne haka ina magana har bakya jina?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Hmm abin mamaki na gani wai dagske Baban Maya ne haka ko kuma wani dan aiki kika samu me kama dashi?" Dariyar shaqiyanci Safinan ta kwashe da ita kafin tace "Shine nan Lawal dai da kika sani daman ai na gaya miki duk Wanda yaci tuwo dani miya yasha, kuma jada baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne. Lakwa lakwa na musu daga shi har yan uwan nasa da suke zugashi na shirya a nutse, gashi dana farka na taso musu gaba daya nayi maganin yan iska yanzu Lawal da Ahalinsa kafin da suka isa dashi kara idan na ajiye basu isa su tsallake ba wallahi se yanda nace haka za'ayi ai Allah ya jiqan Malam na kan tudu badan ya mutu ba haqurin nan dai da yake ta cewa na qara zanci riba a gaba gashi na gani, na ci wuyar jira amma da aiki ya kammalu yanzu dadinsa kawai na kwasa". Tagumin da tayi ta janye tana kallon Safinan dan sam ba gane kan surutanta takeyi ba tace "Kinga ba wannan ya kawoni ba qata wutar ce take shirin kunnomun Khalil neman aure yakeyi har kuma yana iqirarin babu abinda ze hanashi. Bana son nayi tashin hankalin da ze sake saka ran Mama ya baci shiyasa kika ga nazo da yamman nan ki bani mafita, me zanyi na watsa al'amarin tun kafin yayi girma dan wlh wannan karon da gaske yake a gabana ya shirya ya tafi zance gurin yarinyar babu wata shakka ko tsoron bacin raina da yakeyi a baya ya kalleni yana gaya mun gurin wata zeje Khalil fa Safinah Khalil dina ke iqirarin ze auro wata ya kawo cikin gidan da nake" seta dafe kai ta fashe da kuka tana cewa "Wallahi ji nakeyi kamar zan haukace, na je gidan Maman Asad na kai mata kukana na tarar da baqin cikin daya fi wnada na baro kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ido Safina ta saka mata har ta kai qarshr kafin ta kwashe da dariya harda kwanciya tana cewa "Kice abin yazo inji me tsoron wanka". Dakatawa tayi da kukan ta kalli safina a fusace tace "In gaya miki damuwata ki maidashi abin dariya saboda wukaqanci? Koda yake laifi nane dana zo na fada miki" tana gama fada ta miqe ta shiga kici kici da Hijabinta zata saka. "Haba qawata daga wasa kuma se ki maida abun zafi" Safina ta fada tana riqe hannunta, Umaimah ta fizge dan taji haushin abinda ta matan Safina na qunshe dariya ta samu ta zauna tana ce mata "Toh kiyi haquri" Banza ta mata tana jan hanci, Safina ta gyara zama tace "Yanzu kinyarda da abinda nake gaya miki da nace miki Maza duk sunansu Maza karki taba bugar qirji akan Namiji kice bazeyi abu kaza ba sedai idan lokacin yin beyi ba. Gashi nan kina kwance ze tattago miki tashin hankali, lokacin da nace ki tashi a tsaye ki kamashi ta yanda babu wani motsi da ze iya se da yardarki me kikace ke kinsan Mijinki kin yarda babu macen da zata burgeshi bayan ke toh ai yanzu da kikaji daga bakinsa na tabbatar ba qarya ya miki ba Allah nema ya soki da rahma kikaji da sedai azo ana ki matsar da kaya za'a zuba na Amarya qila". "Kinga Safina ni ba cewa nayi ki qaramun damuwa ba, mafita na nema idan baki da ita ki barni na tafi" "Mafita kam a kwaita sedai ke dince nasan zaki iya cewa ba haka ba, amma idan kin shirya ganauce dai ke ba jiyau ba kinga yanda na samu kan Lawal idan kina son haka koma abinda be kai haka ba mintina kadan ne kn samu biyan buqatarki" "Kinga ni wannan abin ba burgeni yayi ba ta yaya zaki maida Mijinki Bawa ni aurene bana so yayi shi nake so a fasa ta sigar da baza'a ga laifina ba, badan Mama ba wallahi da yanzu na gano gidansu koma wace shegiya ce naje na qare musu tanadi ta yanda bazasuyi gigin bashi auran yarsu ba. Kawai yanzu ki gayamin idan da wata hanyar me sauqi da zanbi" Umaimah ta fada cikin qaguwa se Safina tayi fari da ido tana kallonta tace "Yo wannan ai yafi shan ruwa wahala bama se kinje da kanki ba, a waya kawai zan kira Malam yanzu kiga aiki da cikawa sedai ki aika masa da abin sadaka ta Account kawai" "Banda Harkar Malamai kinsan bana so" Umaimah ta fada, se Safina ta watsa hannu tace "To nidai a bangarena taimakon da zan iya yi miki kenan na hadaki da wanda ze miki aiki bayan nan banida wata Mafita Sayyada Umaimah". Shiru tayi tana kallon Safinan, itafa bata yarda da wasu Malamai ba gani takeyi cinye musu kudi kawai suke suna musu qarairayi kuma ace abu sedai kayi tayi ita ba zata iya ba, tafi gane ta dauki mataki da kanta kawai a wuce gurin "Wallahi aikinsa yasha banban dana sauran Malamai da kika sani, aiki yake sadidan gashi kamar yankan wuqa musamman irin nakin nan me sauqi farraqu kawai za'ayi masa da duk wasu yammata su dena burgeshi ke kuma a qara miki tasiri a zuciyarsa ta yanda baze ga wata mace da qima ba idan bake ba kuma ki mallakeshi shikenan fa ba wani abu me yawa za'ayi ba" Muryar Safina ta katse mata tunani seta saki ajiyar zuciya ta na kallonta tace "Safina babu wata hanya dole se wannan?" "Babu Umaimah wai ma meye ne ke da zaki ce ba zaki gidan Malam ba? Duk fa macen da kikga ta isa a gidanta yanzu tana yanda taga dama to tana da Malamin daya tsaya mata. Allah na tuba mu ina muka leqa ma hamshaqan mata da suke bin Bokaye fa wasu Niger ma da su chadi suke fita dan neman biyan buqata ai ki saki ranki kawai in har kina so Ki samu khalil ke kadai wallahi se kinyi abinda akeyi ita wadda ze kawo din kika san nawa ta kashe kafin ta samu kansa balle ace ta shigo gidan ai se kin zama sorry Umaimah". "Bari naje Safina kaina sarawa yake yo zamuyi magana" ta fada tana miqewa dan bata ga mafita a zancen Safinan ba. Har Get ta rakata tana sake jaddada mata da tazo suke gurin Malam zata sha mamakin yanda abubuwa zasu tafi tace mata toh se tayi shawara. Tana tafe a mota tunani barkatai sun cika mata kai ta rasa ina zata kama, idan ta tuna Khalil ne da bakinsa ya gaya mata maganar nan se taji kamar ta kurma ihu. Abu daya da ta sani dashi ko a cikin wasa baya mata qarya dan haka yanzu ta tabbatar da abinda ya fada gaskiya ne kenan sannan abinda Hajiyarsa tayi mata ya sake tabbatar mata da hadin bakinta ake komai. Hannu ta saka ta share hawayen da ya zubo mata kafin ta gangara gefen titi tayi parking. Ita yanzu gurin wa zataje? Yan gidansu duk bakinsu daya haquri za'a bata kai bama taso su sani dan tsafgoya masa baya zasuyi ba zasu hana ba ga Safinan da take zaton zata sama mata mafita tana kawo mata wani zancen shirme. Wayarta ta dakko ta shiga numbobi tana dubawa, akan lambar Rufaida ta tsaya, tafi minti goma tana tunanin ta kirata ko yaya kafin daga qarshe ta runtse ido ta kira "Allah ka nuna Annabi, yau Umaimah da kanki kike kirana" Rufaidan ta fada cike da murnar ganin kiran tsohuwar Aminiyar tata. "Rufaida kina gida ne?" Ta tanbayeta ba tareda ta tsaya wata doguwar magana ba se Rufaida tace "Wallahi bana gida, muna garinsu Habibi Mahaifinsa ne ya rasu yau akayi sadakar bakwai se zuwa jibi zamu taho lafiya dai wani abun ne ya faru?" "Babu komai, Allah ya jiqansa dan Allah idan kin dawo ki gaya mun ina so mu hadu ne" "Babu damuwa da mun dawo zanzo gidan in sha Allah, amma lafiya naji muryarki da damuwa haka idan abun sauri ne muyi magana a waya mana?" "Uhm, ki bari kawai idan kin dawo mayi maganar" ta fada daga nan ta kashe wayar. Gida ta koma, babu wanda ta kula harda yaran dake ta mata sannu da zuwa da suka bita daki ma fafarosu tayi ta korosu waje. Ranar kwanan zaune tayi tana saqe saqen mafita, ba zata iya jira har se Rufaida ta dawo ba kuma bata jin zata dauki shawarar Safina dole ta nemawa kanta mafita kota wanne hali. Cikin dare ta kasa bacci, juyi kawai takeyi gaba daya ta kasa tunanin ma, a hankali ta miqe ta fita daga dakin, cikin sanda ta haye saman, a jikin qofar dakinsa ta jingina tana jiyo shi yana magana da alama waya yakeyi "Nayi maka Alqawari Mansur zan kula da yarinyar nan babu kuma abinda ze sameta, ina sonta ni kaina bansan yanda akayi ta shiga zuciyata har haka ba kuma bana zaton akwai abinda ze ciremun wannan son nata daga zuciyata kadai san yanda nake akan abinda nake so toh dan Allah ka ajiye komai da duk wata magana a gefe kayi mana Addu'a in sha Allahu nida Humaira auranmu har Aljanna". Guri ta samu ta zauna tana jera numfashi, wato Mansur ne, seda ya tabbatar da abinda yake fada na cewar se an mata kishiya ko kuma Humaira idan zata tuna daidai yarinyar da Mamansu Mansur din take ruqo ce. Daman haka nan taji jininta be hadu da yarinyar ba tun a karon farko data fara ganinta saboda Kyan yarinyar yayi yawa gata da wata siffa me daukar hankali da dik in ka ganta se ka sake kallonta. Daman zuwan da yakeyi gidan yace saqon Mansur ze kai abinda yake zuwa kenan ko gara da Allah yasa taji komai ashe ma ta gida ce toh wlh zataje har gidan, se tayiwa Hajiya Hauwa Tijarar da ko me suna Khalil ya sake zuwa neman auran yarinyar bazata bari ta kula shi ba. Haka ta qarasa daren cikin shirya irin rashin mutunchin da zataje tayi a gidansu Mansur kafin daga bisani ta dawo kan uban gayyar dan ba raga masa zatayi ba. Washe gari fuska a washe ta farka abinda ya matuqar daurewa Khalil kai ganin da kanta ta shirya masa abin kari kai bazaka ce wani abu ya faru jiya ba. Kallon abincin ya ringayi ya kasa ci, kwanaki yaji an ce wata ta sakawa mijinta maganin bera a abinci sabida ze mata kishiya wannan tunanin ya hanashi taba duk abinda ta ajiye din har seda ta zauna ta zuba nata ta zubawa yara suka fara ci kafin ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga shima. "An jima zamu fita, yau zumunchi nake ji zamuje mu gaida Hajiyar su Mansur wlh na manta rabon da naje gidan tun jiya kawai take fado mun a rai" ya ji maganarta a tsakiyar kansa ai be san sanda ya kware ba ya shiga tari baji ba gani Umaimah na tsaye kansa harya lafa zagi ta dura masa su a zuciyarta sunfi kala dubu, ya dago ya kalleta da idonsa da sukayi ja saboda kwarewar da yayi yace "Gidansu Mansur kuma yau? Sau nawa nake ce miki kije ki gaishetan kike qi se yau zakije zakije?" "Toh dai qorafi ya qare yanzu dai yau zanje kuma daga yanzu in sha Allah zan ringa leqawa ina gaidata ai Mama nada kirki nice ma da naqi Sakin jiki da ita" ta bashi amsa tana komawa gurin zamanta. Shiru yayi, yasan dai baze yuwu ace tasan wadda yake nema ba amma kuma baze so taje gidan ba saboda gujewa sammatsi yanzu idan ya hanata nan na ya saka kansa a matsa dole tabi ba'asin dalilin hanawar to shi yaya zeyi yanzu? Haka ya qarasa tuttura dankalin data zuba masa ya fita tareda yara da ze sauke a makaranta bayan ya bata kudi akan ta bawa Maman idan taje. Ko Awa daya beyi da fita ba itama ta fice bata kuma zame ko ina ba se gidan su Mansur. Mama na zaune A tsakar gida ta kunna Radion ta tana ji Humaira na kitchen tana hada musu abin karyawa Umaiman ta fada musu kamar dirar Kirsimeti. "Subhanallahi waye haka?" Mama da yanda a bugo qofa ya tsoratat ta fada tana miqewa, ganin Umaimah tsaye yasa ta saki ajiyar zuciya tace "Au kece tafe da safiyar nan qaraso ciki mana kika kafe a bakin qofa". "Ba zama ya kawo ni ba baqar Annamimiya mara tsoron Allah, wato saboda tsabar son zuciya da kwadayi dan kinga Allah ya horewa Mijina abin duniya shi yasa kike so ki laqaba masa wata shegiya da ba'asan Asalinta ba ko ku dandali arziqi? Bautar da Ubansa yayi muku da wadda shima yayi da Danki duk bata isheki ba se kin hadashi aure da yarki? To bari kiji Hauwa na rantse da wanda yake busa mun numfashi babu wanda ya isa yayi wannan hadin, idan kuma kince se anyi to ki tabbata kin hado ta da Likkafani da duka sauran kayan jana'iza dan kuwa daren da aka kaita cikin gidan Khalil a kabari zata qarasa shi". Qarar kwanuka da suka zube ta saka Mama da Umaiman waiwayawa suka kalli Humaira dake tsaye qofar kitchen ta zubar da kwanukan data fito dasu saboda tsorata da ganin yanayin Umaimah da kuma maganganun da take fada jikinta se rawa yake kamar wadda Sanyi yake kadawa. Wani banzan kallo Umaimah ta bita dashi sama da qasa kafin ta tabe baki tace "Da alama wannan kazar kike shirin liqawa Mijina? To ki bar murna aikin Bokanki yaci dan nasan idan ba Asiri ba babu abinda ze burge Khalil a jikin wannan abar me kama da Muciya a tsaye ina tabbatar miki da duk abinda kikayi sena warwareshi, ke kuma idan kina son kanki da lafiya wallahi ko a mafarki karki qara tunanin Mijina dan idan ba haka ba ni nan se na zama Ajalinki, sena lalata na balbalta rayuwarki ta yanda har ki mutu kina danasanin sanin Khalil a duniya kiji da kunnenki ni nan Umaimah na isheki" tana kaiwa nan taja wani matsiyacin tsaki ta juya zata fita Mama ta tareta da cewa "Mungode kwarai da ziyara, amma ina so ki sani shi aure lamarin ubangiji ne duk kuma wanda yace ze dakatar da faruwarsa rabo yana iya kashe shi ayi ko bayan ransa, ke yarinya ce har yanzu baki gama sani inda yake miki ciwo ba a rayuwa dan haka kibi a sannu" tana gama fadar haka ta kalli Humaira da Hawaye su ke mata zarya a fuska tace "Wuce muje ciki" nan suka bar Umaimah tsaye kamar wadda aka dasa kafin taja qwafa ta sake ficewa fuuu tana shan alwashi kala kala akan Maman da Yarinyar, abun da yazo mata a rai shine fuskarta ta rudeshi dan haka dole ta dauki matakin lalatata ta haka ne zata sake kareshi daga dukkan wasu Mata ko Iyayen yara masu kawo masa tallan Yayansu. A cikin gidan kuwa suna shiga palour Mama ta kalli Humaira dake kuka tana yarfe hannaye tace "Yi mun shiru sakarya, idan wannan dan kurarin nata ya firgitaki ta ya zaki iya zama da ita a matsayin kishita kuma a cikin gida daya? Dole ki bude baki ki kuma cire duk wani tsoro da sokonci daga ranki ki kwatarwa kanki yanci dan daga sanda tasan kina tsoronta ta samu hanyar Azabtar dake". "Ni wlh Mama bazan aure shi ba daman na gaya miki kece kika dage akan sena na amsa masa kin gani yanzu tun ma ba'ayi auran ba tazo tana cewa zata kasheni idan kuma aka kaini can daga ni se ita fa baki san abinda zata mun ba sedai kawai a kiraki ace kizo ki dauki gawata" Humaira ta fada tana sake rushewa da kukan tashin hankali. Tsaki Maman taja ta zauna akan kujera tayi shiru tana tunani, tabbas seta koyawa Umaimah hankali kuma zata tabbatar bata zageta a banza ba, setayi mata bazatan da zata girgiza har ta kusa rasa hankalinta. Ganin Humairan nata kuka yasa ta janyota jikinta ta shiga lallashinta. "Kiyi shiru kinji auta karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki kishi ne yake damunta amma babu abinda zatayi mki. Kuma ma ai ba gida daya ze ajiye ku ba na sani kinga babu ruwan kowa da yar uwarta balle har wani abu ya hadaku ma kedai kawai kici gaba da Addu'a Allah ya tabbatar miki da Alkhairi tunda kina sonsa yana sonki ai magana ta qare babu ruwanki da wata matarsa" Maman ta fada tana shafa kanta seta dago da guntun Hawaye tace "Nidai Mama na haqura ni daman ba wani sonsa nake ba gara na auri Noor dina na zauna ni kadai babu me daga mun hankali" "Humaira kenan, shikenan tunda kince haka amma kina da tabbacin idan kin auri Noor din shima wata rana baze qaro miki wata irinta ba? Koma bashi ba duk Wanda kika aura dayan biyu ne ko ki tarar ko tazo ta tarar dake kuma baki sna Mijin ba ko ya zamana matar ce takr juyashi kinga wahala zaki sha. Wannan kuwa kin sanshi kin san komai nasa na tabbatar baze taba bari ta cutar dake ba kefa da kanki kike bani labarin Yanda Ibrahim yake riritaki da alqawarin da yake miki idan kunyi aure" Saurin rufe ido tayi alamar kunya, duk hirar da sukayi seta bawa Maman labari dan haka ta koya mata ta dauke ta kamar qawa tana hira da ita a haka take sanin duk abinsa take ciki na daidai ta qara dorata akai na kuskure ta gyara mata. "Toh kin gani shine kuma kike so ki bar mata ita kadai ta shanye duk soyayyar nan da akayi miki alqawariz ita kanta kishin da takeyi kenan bata so kizo kiji dadin da takeji a gidan shiyasa fa take wannan kururuwar ba wani abu ba so take ta tsorata ki ki bar mata mijinta ita kadai kuma duk mata haka sukeyi amma da anyi auran zaki ga ta saduda ta haqura tunda babu yanda zatayi". Haka taci gaba da lallabata tana bata baki tareda qara mata qarfin guiwa tana bata misalai akan wasu mutanen sannan taja mata kunne akan koda wasa karta gayawa Khalil zancen zuwan Umaiman gidan. Sefmda ta saki ranta kafin ta fita ta gyara barin da tayi ta shiga hada musu wani sabon abin karin amma fa can qasan ranta cike yake fal da tsoron Umaiman. Bata son Hayaniya a rayuwarta ita bata iya fada ba sannan ace za'a hadata kishi da wannan matar da take cewa zata kasheta gaskiya bazata yarda ba kawai tayi shiru ne bata musawa Maman ba amma dole daga baya a san abinyi tana son rayuwarta bazata kai kanta Mahallaka tana sane ba. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 62 HUMAIRAH Duk yanda taso ta gujewa Khalil din da auransa ya gagara saboda wata irin sabuwar kulawa da tattali da yakeyi mata suka rufe mata ido take jinbazata iya rabuwa dashi ba. Soyayya yake gwada mata irin wadda take mafarkin samu a gurin Noor dinta, kuma kamar yanda takejin ana fada idanka auri Yaro kafi samun soyayya sabanin babba da ze ringa ganin kamar bata lokaci ne sedai a yanzu da ta hadu da Khalil ta qaryata hakan. Kamar yanda Mama ta kwabeta da karta gaya masa zancen zuwan Umaimah gidan haka kuwa akayi bata gaya masa ba, shi ya ringa insisting akan ta yardar masa yaje can Jalingo ya gaida Dangin Mahaifinta dana Mahaifiyarta amma taqi saboda ita duk lissafinta fa babu maganar aure a yanzu, so take su ci gaba da soyayya kawai yana lallabata yana sangartata har zuwa ta shiga Jami'a ta gama Kafin sannan Noor dinta shima ya samu abinyi se suyi auransu dan fa bajin zata auri Mijin Umaimah ta kasheta a banza tayiwa Iyayrnta a sarar meyi musu Addu'a bayan ita kadai suka haifa. Ranar da yamma suna zaune da Mama a tsakar gida suna shan iska saboda garin ya dauri da zafi gashi babu wuta, a kishingidr take suna chat da Khalil da ya tafi Anambra yana tsokanarta wai zeyo mata tsabar garin kwaki da kwakwar manja tana dariya Mama ta kalleta tace "Wai ni dariyar me kikeyine tun dazu kamar wata tababbiya kina danna waya?' Seda ta bashi amsa kafin ta tashi zaune sosai tana kallon Maman fuskarta da murmushi tace "Nida Yah Khalil ne Mama, wai tsarabar Garin kwaki zeyi mun shine nace bana so". "Kiji sokuwa aikensa kikayi da zece ze kawo miki abu kice bakyaso in banda rashin wayo aiko qasar garin tax and qullo a leda ya kawo miki godiya zaki masa ba kushewa ba. Ni da ace ma magana tayi qarfi ai inaga gidan Unaizatu zaki tafi ki zauna can tayi miki karatun aure da zama da kishiya dan da wannan salubancin naki kam wuya zakije kisha Mijin ma baki san yanda zaki tarairayeshi ki kula dashi ba balle azo ga batun kishiya" Mama ta fada tana kallonta, seta tura baki tace "Nifa Mama ki dena mun fatan zama da wata kishiya, shiyasa ma da Yah Khalil din yake ta wani cewa zeje Jalingo nace masa ba yanzu ba, haka kawai ni jira nake Noor ya samu aiki kawai muyi auranmu bazan iya ba taje ta zauna da Mijinta ita kadai". Kallonta Maman take harta kai qarshe kafin ta girgiza kai tayi kwafa kawai bata ce mata komai ba. Noor din da tun ran da wancan abun ya faru be sake zuwa gidan ba tana lura da ita kuma kullum ta kirashi baya dauka har takadda ta bawa Amir yaron maqontansu ya kai masa jiya tana zaune Humairan ta fita Islamiyya ya dawo da ita wai yaqi karba shine take lissafi akansa ko to zataci qaniyarta kuwa tunda ita ta hana Khalil din zuwa to da kanta ita zata bashi umarnin yaje ya nemi auran kawai dan ta qudurcr seta nunawa Umaimah ba ita kadai bace yar banza, kuma ita shirme takeyi da hauka aure da yardar ubangiji se anyi shi se dai in ta hadiyi zuciya ta mutu. Washe garin ranar kuwa da dare sega Khalil yak gurin Humairan, da Maman suka fara gaisawa ba kuma tayi qasa a guiwa ba ta bude masa magana akan idan da gaske yakeyi tofa ya kamata manya su shiga ciki harta qara masa da cewar a can garin nasu akwai Yayan dangi da ake so ayi musu hadin zumunta da Humairan dan haka idan ya tsaya sanya ze iya rasawa da wannan maganar ya bar gidan yana fita ya shiga kiran Mansur da tunda maganar sa da Humairan ta fita ya shiga gaba dashi. Takanas ya kirashi ya gaya masa magana akan ya kyale musu qanwa baze aureta ba tun kuma daga wannan wayar idan ya kirashi ma baya dagawa dan ya gaya masa in dai ba ya janye ba tofa zasu samu matsala dan baze zuba ido a hada yarinya da Umaimah ta lahanta ta ba. Gida ya wuce, dukda dare yayi dan goma ta wuce amma ya shiga bangaren Hajiyarsa. Habiba ya tarar a palour da Halima me aikinsu suna kallo ga Mu'ayyad na bacci a qasan carpet suka gashe shi gaba daya ya amsa yana tambayarta Hajiya fa tace tana daki jin haka yayi tunanin tayi bacci seya juya Habiba ta tareshi tana cewa "Ba bacci take ba Yaya yanzu na kai mata shayi zata bawa Bibi idonsu biyu". Juyawa yayi ya hau saman. A dakin ya samu Hajiyar ta gama bawa Bibi shayin harta kwanta ita kuma tana ninke kayan data cire da alama itama kwanciyar zatayi. A kan one sitter dake dakin ya zauna yana sake gaisheta ta ajiye kayan hannunta ta zauna tana cewa "Babana baka kwanta ba, da alama ma yanzu ka shigo gidan?" Kansa ya shafa yace "Eh wlh Hajiya naje gurin Humaira ne daga can kuma na tsaya wani guri s yanzu na shigo" "Toh ya suke? Ya Hajiya Hauwan? Kaga inata zuci zucin na kirata tun ranar nan da mukayi magana Allah beyi ba ni da naji shiru daga bangarenka dana Matarka ma.na zata kun daidaita maganar ta wuce ne ashe kana kan bakanka" Hajiya ta fada seya dagao ya kalleta yace "Wace magana kenan Hajiya?" "Maganar auran naka mana tun waccan ranar bata sake tada maganar ba kuma naga ta shiga sabgoginta kamar babu abinda ya faru" "Toh nima dai haka na gani kuma bata sake mun magana ba, dukda dai gaskiya nima tun waccen ranar ban sake tada mata da maganar ba yanzu ne dai nake so nayi mata saboda dazun da naje Mama tace mun ya kamata Nayi magana idan da gaske nake aje a samu iyayen Humairan abinda ya kawoni yanzu ma kenan na gaya miki saboda ki sanarwa dasu Baba Abu se su saka ranar da zasuje ayi shirye shirye kinga tafiyar da nisa". Kallonsa Hajiya ta ringayi har ya kai qarshe kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Babana dagask dai kake da maganar aurannan, ni da zaka bi ta tawa da ka haqura da matarka ita kadai yanzu kuna zamanku lafiya so kakeyi ka dakko wata da zata zo ta jawo maka tashin hankali da damuwa...." "Hajiya" ya kira sunanta cikin marairaicewa abinda yasa ta dakata da maganar da takeyi kafin yaci gaba da cewa "Dan Allah Hajiya na roqeki da ko saka albarka a abun nan ki dena yi mun fatan tashin hankali ko damuwa. Hajiya ni nake zaune da Umaimah ni nasan dadinta ko akasin haka tunda har nazo miki da buqatar ina son qari ki barni dan Allah". "Shikenan Allah ubangiji ya tabbatar da Alkhairi yasa ayi a sa'a, amma ina so kafin a kai ga yin magana ka fara sanar da matarka tukunna, idan ta karbi abun ta fuskar limana shikenan idan kuma ba haka ba dole a qara lokaci zuwa sanda abubuwa zasu qara sauqaqa kaga ita ma kafin nan yarinyar ta qara girma se ayi komai cikin dadin rai da kwanciyar hankali" Hajiyan ta sak fada, ajiyar zuciya yayi yana kallon qasa yace mata "In sha Allahu babu abinda zero faru is Alkhairi, yanzu dai ki sanarwa da Baba Abun duk abunda suka yanke shikenan" ya sak jaddada mata dan gaba daya kalaman na Hajiya yau jinsu yakeyi akwai son kai a ciki, yanda kasan Umaimah ta haifa ba shi ba yanzu tana nufin kenan seda Amincewar Umaimah zeyi aure idan ba haka ba sedai a fasa kenan. Sallama yayi mata ya wuce bangarensu, a falon qasan ya tarar da Umaimah tana kwance a qasa tana danna waya. Ba yabo ba fallasa ta amsa sallamarsa tareda yi masa sannu da zuwa, daga kwancen ta nuna masa Dining inda abincinsa yake ya wuce ya zauna yana duba abinda suka dafa. Gurasa ce da gasashshan nama se kunun Aya ga Qaramin flask na Tea dinsa an ajiye ya zuba abinda ze iya ci yayi bismillah ya fara lokaci lokaci yana kallon Umaiman dake kwance har sannan a zuciyarsa yana ayyana ta yanda ze sanar mata da zancen auran har ya gama ya tashi daga gurin. Kusada ita ya koma ya zauan ya dauki remote ya chanza tasha zuwa labarai ya tsurawa Tv ido badan yana fuskantar abinda ake cewa a ciki ba yana nan zaune se ji yayi tana masa sallama zata shige daki, miqewa tsaye yayi shima gaba daya bakinsa ya masa nauyi yana nan tunanin me zece mata harta shige ta kullo qofarta seya sauke ajiyar zuciya ya kashe Tv ya haye sama shima dan tuni Ruqayya ta kwashe kayan abincin daya gama. A daren kasa bacci yayi, kwana yayi yana saqa da warwarar yanda ze gayawa Umaimah zancen auran nasa daga qarshe ya yanke shawarar komawa ya sake samun Hajiya ya lallabata ita ta gaya mata dan gaskiya yana shakkar kallon idonta yazo mata da wannan zance be san a yanda zata dauki al'amarin ba yasan idan Hajiyar ce zata fi fahimtarta akansa. UMAIMAH Tun bayan da taje tayi tijara a gidansu Humairah ta kwantar da hankalinta dan gani takeyi barazanar da tayi musu ta isa ta saka a fasa auran musamman da Khalil beyi mata maganar ba kenan sunji tsoro basu gaya masa ba qila dai an rusa maganar to koma dai menene ita dai tayi abinda tayi cansu gane ba matsalarta bace koda Rufaida ta dawo kamar yanda tayi alqawari taje gidan se kawai tace mata babu komai, daman abu ne ya taso mata kuma ta rigada tayi daman bata sake bi takan Safinah ba dan ita shawararta a gunta ba mafita bace. Lafiya lau take ci gaba da zuba mulkinta, yanda Khalil din yake ta tata yana tarairayarta ya sake tabbatar mata da cewar babu waccen magana ta rusata dan haka ta saki ranta take sabgoginta. Hajiya ce dai ta dauke mata wuta ba kamar yanda suke a da ba tunda ta fahimci da hadin bakinta aka so ayi mata qullalliya shikenan ta qullaceta shigar da takeyi part dinta ta dena sau daya take leqawa ta gaisheta ba kuma ta zama suyi hira kamar yanda suka saba zata koma bangarenta su kansu yaran yanzu janye su takeyi da sun dawo daga makaranta suka shiga bazata barsu su koma part din Hajiyar ba se kwanciya bacci shima din saboda ba zata iya zirga zirgar tashi sakasu fitsari ba ne amma ta qudurce a ranta data haihu zata tattaro yaranta gaba daya su dawo gurinta tunda itama fuska biyu ce da Hajiyan toh su zuba su gani. A bangaren Hajiya ma kwana tayi tana juya maganganun Khalil din, har ga Allah ita dai bata son qarin auran nan daya dakko ba kuma dan komai ba se dan gudun tashin hankalin da ze iya faruwa a gidan. Iya abubuwan da suka faru a baya sun isa ishara a sannan ma hasashene ya saka Umaiman aikata abinda tayi ballantana a yanzu da zancen auran na gaske ke shirin qulluwa, ita duk ba wannan ba yarinyar daya dakko yake son auran kanta abar tausayice bata yi kwarin da za'a hadata kishi da mace kamar Umaimah ba banda ma abu irin na Namiji idan auran yake so meze hana yaj ya nemo babbar Mace amma ya dage se wannanyar yarinyar. Haka ta ringa juye tana saqa yanda abubuwan zasu kasance, a yanda ya bude baki har yake mata magana ta tabbatar da har zuci yake son auran nan kuma idan tace zatayi amfani da qarfinta na Uwa ta tauye shi batayi masa Adalci ba dan haka dole ta haqura ta barshi yayi, amma badai ya auri wanann yarinyar ba sedai yaje can ya samo wadda zata iya gogawa da Umaiman dan idan ta bari akayi wannan hadin tamkar daukar Alhaki ne. Ita kanta Hajiya Hauwan tayi mamaki data yarda da wannan hadi amma zuwa da safe zata kiraya suyi magana ta fahimta ta yanda su da kansu zasu fasa bashi auran ta haka komai zero warware ba tareda yayi zargin ita ta hana ba. Da wannan shawara tayi Na'am ta kiran Hajiya Hauwa amma kafin nan zata tara sauran yaranta mata dan taji shawarar su akan wannan al'amari kafin ta yanke hukunci. Washe gari kuwa da safe ta kira Amina ta shaida mata tana son ganinsu gaba daya yau, babu bata lokaci kuwa Aminan ta kira Jamila da Jalilah ta gaya musu daman Habiba na gida dan haka kafin qarfe tara na safe gaba daya sun hallara a gidan saboda amsa kiran Hajiyar kowacce zuciyarta cike da son jin ba'asin wannan kiran gaggawa haka. A taqaice Hajiyar tayi musu bayanin dalilin kiran nasu da tayi, Jalilah taja kabbara harda daga hannaye tace "Alhamdulillahi Allah na gode maka daka nuna mun wannan rana da raina ban mutu ba, ai wallahi na dade da wannan qudurin kuma koda ace Khalil be nemo aure ba ni da kaina zan nemo masa to gashi yayiwa kansa tunani me kyau kai wallahi naji dadi, Allah ya tabbatar da Alkhairi ya nuna mana lokaci" Jamila da tayi tagumi ce ta janye tana cewa "Toni abin ne na rasa me zanyi, murna ce ko kuma fargaba? Yin auran abu ne me kyau amma ni tashin hankalin da matarsa zatayi shi nake tsoro wallahi" "Kamar kin shiga raina Jamila ni kaina abinda kawai nake hasasowa kenan, gashi Hajiua tace yarinya ce qarama idan da ace ma wata babbace da zasu iya gogawa da sauqi amma yanzu ya auro yarinyar mutane tayita azabtar da ita ai anyi ba ayi ba kenan" Anty Amina ta goyi da bayan Jamilan, Hajiya na shirin magana Jalilah ta taresu da cewa "Oh saboda ana gudun Jidalinta shikenan shikenan se yayita zama yana tauye kansa shi bazeji dadin aure ba to ko jaririya ya nemo haka ze aurota kuma babu abinda ta isa tayi mata da ikon Allah taci zamaninta yanzu kuwa sedai ta zama yar kallo a gidan Khalil. Ni bari na kirashi ma yazo muji yanda za'ayi da batun hada lefe gara ayi komai da wuri bana son bata lokaci". Duk ta yanda suka so kawo suka akan lamarin auran seda tabi ta kanainaye musamman da Khalifa ya shigo shima ya mara mata baya seda suka san yanda suka ja ra'ayin Jamila da Aminan suka Aminta da zancen auran dukda daman su bawai basa so yayin bane, Aa Jidalin Umaimah suke tunani da kuma tausayin ita wadda akace yana so ze aura din suna ganin tayi qanqanta a hadata kishi da Umaimah. Hajiya da tunda suka fara bata ce musu komai ba tayi ajiyar numfashi tace "Yanzu meye matsayarku akan maganar nan? Nidai har ga zuciyata bawai bana son auran nan ba Aa tunanin abinda zeje ya dawo nakeyi, bana son tashin hankali musamman a matsayin da yarinyar nan take ciki gata da taohon ciki kuma daman tun samuwar cikin ake ta turka turka daga wannan se wannan bana son abinda ze zo ya taba lafiyarta ko ta abinda yake cikinta amma kuma bazan so na zama me son kai ba shima Babana na tauyeshi, dan haka mecece shawararku ta qarshe akan abinda ya kamata muyi?" Anty Amina ce tayi magana tace "Nidai Hajiya ina ganin tunda har Khalil ya furta yana so yayi aure ki barshi yayi ki kuma bishi da Addu'a Allah yasa hakan ya zama Alkhairi ya kuma bashi ikon yin Adalci a tsakaninsu. Amma yanzu yayi haquri ya dakata da maganar auran har zuwa Umaimah ta haihu saboda kowa yasan halinta, bazata dubi halin da take ciki ba tsaf zata illata kanta ta illata abinda ke cikinta a banza saboda haukan kishi dan haka yaci gaba da naman auransa a hankali har zuwa sanda Allah ze tabbatar". Jalilah da Jamila sunyi Na'am da maganarta amma seda Jalilan ta qara da cewa "Amma kamar yanda yace iyayenta sunce ya tura idan da gaske yake to ya kamata ayi hakan kinga shine shaidar yana nema manya su shiga cikin magana, daga nan za'a iya jan lokaci ta fara makaranta ma zuwa sannan ta qara wayo da sanin yanda duniya take kafin azo ga batun aure ko ba haka ba?" Da wannan suka rufe zaman, kuma basu tashi ba seda Hajiyan ta kira Baba Abu ta sanar masa kuma shima yayi na'am da al'amarin har yana cewa "Ai Hajiya Ibrahim me haquri ne wallahi saboda tunda naji halayyar yarinyar nan a bakin iyayenta na tabbatar da ba qaramin haquri yake dashi ba da aka dauki wannan lokaci babu wanda yaji kansu kinga kuwa yanzu tunda ya nuna yana da buqatar qari babu me hanashi, zan samu Alhaji Garba da Alhaji Shehu se muji ta bakin Ibrahim din inda za'aje masa neman auran, Allah ya tabbatar da Alkairi yasa zamu gani". Guraren sha daya da rabi Jamia ta miqe zata tafi dan tana da duty a Asibiti sha biyu zata karba, tare suka fita da Anty Amina datace itama zata koma gida dan babu abinda tayi kafin ta fito nan suka bar Jalilah da zata wuni tana sake jaddada musu kowa ta hado gudummawarta su fara hada lefe Jamila na mata tsiyar ita da yar dakin nata yau kuma itace ja gaba a kan qaro mata abokiyar zama suka fita suna dariya. Turus sukayi a compound gurin da Khalil yake ajiye motoci, cikin kaduwa Anty Amina ta shiga kwalawa Sammani kira se gashi nan kamar an jefoshi ya fado gurin. KHALIL Tun qarfe bakwai ya shirya saboda zeje Qunchi, suna aikin gina makarantar kwaleji ya manta shaf be sanar mata da fitar safe zeyi ba dan haka bayan ya gama shirinsa dakansa ya tafasa ruwan zafi ya hada shayi yasha da sauran Gurasar jiya da sukayi ya dumamata. Yana cikin karyawar Ruqayya ta shiga kitchen din, cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa yana tambayarta ko Umaiman ta tashi tace masa Eh yanzun ma ita zata damawa Kunun Gyada dan haka ya fita daga kitchen din ya wuce dakinta na qasa. Tana zaune akan gadon ta jingine bayanta da Allon gadon tana danna waya ya shiga ta dago ta kalle shi tareda amsa sallamar da yayi kafin ta mayar da kai tana ci gaba da danna wayar. A gaban mudubi ya tsaya yana kallonta, gani yayi ta kumbura tun daga fuskarta har zuwa yatsun qafarta dan haka ya matsa kan gadon ya danna qafarta da yatsun hannunsa ta janye qafar tana ya mutsa fuska kafin ta gaidashi a hankali. Be amsa ba ya zauna gefenta yana cewa "Meya sameki haka, kinga yanda kika kumbura gaba daya kuwa? Amma jiya da dare naga ba haka kike ba". Baki ta dan tabe kafin tace "Nima haka na tashi na ganni ai" "Kuma shine kike zaune ba zaki kirani muje Asibiti ba, ina ne yake miki ciwo?" Ya fada yana miqewa tsaye seta kalle shi tace "Nifa lafiya ta qalau inda ina jin wani ciwo ai da na tafi Asibitin da kaina, kuma kumburi daman in ciki ya tsufa ai mutum yana yi ba wani sabon abu bane" "Amma ba irin wannan ba, duk cikin da kikayi baki taba kumbura haka ba ki tashi kawai muje Asibiti su duba ki idan sun tabbatar da babu wata matsala sannan zan yarda" ya sake fada yana janyo Hijabinta da tayi sallah ta bari akan Sallayar. Baki ta zumbura tana zaune bata da niyyar tashi kuma bata ce masa komai ba se ya ja tsaki yana kallonta cikin bacin rai yace "Kina da matsala, lafiyar jikinki ma baki damu da ita ba komai se kin saka shirme da shiririta a cikinsa ki tashi nace tun ban bata miki rai ba saboda kin san ni bama wasa da duk abinda ya shafi lafiya". Dole ta miqe badan taso ba, dakyar taken daga qafa saboda yanda jikinta yayi nauyi, ita kanta tasan kumburin ya zarce na yanda ta saba amma saboda bataji wani ciwo ba kuma da rashin daukar abu da muhimmanci kamar yanda yace din yasa tayi zamanta. A hanya yana ta faman yi mata mita ita kuwa ta doni baki gaba kamar zata tabo glass din motar, daidai zasu shiga Gate din Asibitin watarsa dake ajiye tayi qara, yanda kasan ita aka kira ta kalli wayar da sauri 'Shatunah' sunan data gani yana yawo kenan akan screen din wayar ta kalli Khalil wanda shima kallo daya yayiwa wayar ya dauke kai tamkar bashi ake kira ba a haka ya nemi guri yayi parking motar ya kashe kafin ya dauki wayar tasa da Wallet kuma har sannan yaqi yarda su hada ido da Umaimah data kafa masa nata idanun kamar wata sabuwar Mayya. Seda ya kusa shiga Reception din Asibitin ya lura da bata biyo shi ba, yawu ya hadiye kafin ya qara hade fuska ya juya gurin Motar, tana ciki hat sannan ta hada uban zuba kamar me naquda se numfarfashi takeyi yanda kasan ana tsira mata allura zata fashe saboda fushi. "Ki fito muje" ya fada cikin tsare gida kamar tana jiransa kuwa tace "Bazan fito ba, idan kuma ka isa kazo ka fiddani ta qarfi". Kallonta yayi ganin yanda fuskarta tayi ya tabbatar da ba abinda ya mata zafi yanzu zata tara masa mutane ta zubar masa da mutunchi a gurin dan haka ya bude sit dinsa ya shiga seda ya kulle motar kafin ya kalleta babu yabo babu fallasa yace "Ki yi haquri muje a dubaki bayan nan koma menene idan muka koma gida se muyi magana akai". "Ashe kasan akwai abinda zamuyi magana akai kenan, to jikina ne kuma lafiyata ko nace bazan shiga ba, ko ka gaya mun wace yar iska ce ta kiraka da har kake dangantata da taka ko kuma wallahi yanzu a nan gurin nayi maka Tijarar da baka zata ba" Umaiman ta fada tana kallonsa Khalil dayaji ransa ya baci nan da nan saboda yar iska data kira Humairansa da shi yasaka shima cikin fushi yace mata "Kin dade bakiyi Tijara ba ko kuwa an gaya miki ina tsoron haukanki ne? Jiki kuma kamar yanda kika fada nakine lafiyarki ce duk abinda ya sameki ke kadai ya shafa bani ba dan nan bada dadewa ba zan dakko wata dake ko babu ke rayuwata zanyi bani da Asara" yana gama fadar haka ya tada motar a tsiyace ya fizgeta ya fice daga Asibitin Umaimah da tayi suman zaune saboda jin abubuwan da yake fada fizgar da yayiwa motar ce ta tabbatar mata da cewar a Raye take kuma gaske ne ba mafarki ba Khalil ne yake fada mata wadannan maganganun. "Dake ko babu ke zanyi rayuwata bani da Asara" maganar ta caki zuciyarta kamar shigar mashi, cikin azamar da bata san tana da ita ba ta kaiwa Sitiyarin cafka suka shiga kokawa yana qoqarin riqe kan motar tana fizgewa, abin yazo masa a bazata gashi sun rigada sun hau titi cikin taimakon Allah ya hankadeta ya samu ya riqe kan motar daya kwace masa saura qiris su afkawa murhun wata me qosai ga mutane a gurin sun baibayeta dan har seda ya ture mutum biyu Allah ya rufa asiri basu ji ciwo ba suka miqe da sauri suka matsa daga gurin. Motar na tsayawa ya kasheta gaba daya ya zare muqullin kafin ya juya ya zabga mata wani lafiyayyen mari da seda jinta da ganinta suka dauke na wani lokaci kafin ta fasa qara saboda gigitaccen zafin daya ziyarci kwakwalwarta. "Ke wace irin mahaukaciya ce Umaimah, me kike shirin yi? Kashe mu kike so kiyi kome akan Titi zaki gwada wannan haukar?" Ya fada cikin fushi yana kallonta tuni idanunsa sunyi jaa saboda bacin rai haka jijiyar kansa sun tashi rudu rudu alamun ya kai qololuwar bacin rai kenan. Umaimah ko bata iya bashi amsa ba kururuwa kawai takeyi saboda radadin Azabar marin daya kwasa mata, yaja tsaki kamar ze tsinke harshensa kafin ya balle murfin motar ya fita. Be bi takan masu motocin da suka tsatstsaya wasu na zaginsa wasu na neman jin ba'asin abinda ya faru ba ya wuce Gurin mutanen daya afkawa sunyi cirko cirko suna kallon motar tsabar bacin rai ya kasa bude baki yayi musu magana se hade hannayensa biyu yayi alamar ban haquri, wani dan dattijo da yazo siyan qosan ya matsa kusa dashi, ya daga kafadarsa. Akan idonsa ta kama Sitiyarin dan yana daya tsallaken lokacin cikin tausasa murya yace "Kayi haquri kaji Dana, su Mata wani lokacin ka kan rasa inda hankali da tunaninsu yake tafiya, dukda bansan meya hadaku ba amma tayi wauta. Ka jaku a hankali ku tafi gida koma menene ku warware ka kuma kula karka bari ta sake samun damar maimaita abinda tayi yanzu domin ba daban Allah ya taqaita ba qila da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba Allah kadai yasan Adadin mutanen da hatsarin nan ze ritsa dasu". Dakya ya iya cewa mutumin "Nagode Baba" kafin ya juya ya shiga motar, Umaimah dake kuka kamar wadda ake zarewa rai ta dago ta kalleshi, ya kunna motar yana fara tafiya ta sake yunqura zata kama sitiyarin be bata lokaci ba ya riqe motar da hannu daya ya sake zabga mata wani marin da daya hannun "Na rantse da Allah kika sake kwata mun hauka sena nuna miki na fiki rashin hankali, budeki zanyi ki fada kan Titin mota tabi ta kanki kowa ya huta tunda abinda kike nema kenan" ya fada cikin bacin rai ba tareda ya kalleta ba. Cikin kukan radadin Azabar Marin data sha tace "Ai wallahi sedai mu mutu tare dan na grantse da Allah babu wata mace data isa ka hadani da ita, duk kuma wadda tayi gigin shigowa rayuwarmu ka tabbata cikin biyu se daya ta faru, ko dai ita ta mutu ko kai ka mutu idan yaso gaba dayan mu muyi Asara" taci gaba da kuka wiwi dan jin fuskarta takeyi kamar ya watsa mata tafasashshen ruwan zafi. Khalil kuwa dariya ma maganar tata ta bashi dan haka ya dara kadan kafin ya kalleta yace "To kuwa seki shirya saboda nan bada dadewa ba wadda tafiki cancanta data zamo matata zata karbe gurbinta, idan kinga dama ki nutsu ku zauna lafiya idan ba baki ga dama ba kiyi duk abinda zuciyarki take ayyana miki da kiyin aurene babu fashi se nayi idan yaso ki kasheni ko ki kasheta kamar yanda kike fada se mu gani ke idan zaki zauna kiyi gadin duniya ne" daga nan yaja bakinsa yayi shiru duk irin ihu da kururuwar da takeyi tana zaginsa da iyayensa harda Mahaifinsa dake kwance a kabari bata manta dashi ba seda ta zaga yayi mata shiru be tanka mata ba, tafasa kawai zuciyarsa takeyi ya tabbata idan ya biyewa abinda zuciyarsa takr saqa masa to fa sedai ya maida gawarta gida dan se yayi mata dukan mutuwa a motar kafin su isa amma haka ya daure har suka je gida. A bakin get ya tsaya ya kalleta da idanunsa da sukayi jajir ita kanta duk rashin mutunchin da taken zazzaga masa suna hada ido seda ta dauke wuta ta matsa can jikin qofar motar, cikin wani irin Amo yace ta sauka, bude bako tayi da niyyar gaya masa magana ya daka mata tsawar da har seda abinda yake cikinta ya wuntsila, babu shiri ta balle murfin ta fice tana haki, a bakin get din ta tsaya tabi motarsa daya fizga da gudu ya bar layin da kallo nan ta shiga tunanin me zatayi masa. Ta rantse da abinda ze kasheta Khalil yayi kadan dashi da duk ma wanda suke goya masa baya akan yayi auran za kuma ta tabbatar musu da ita Umaimah warkice daidai da qugun kowanne dan iska. Haka taja qafa ta shiga compound din, idonta ya sauka akan sabuwar motarsa Marsandi daya siya ko cikakken wata biyu batayi ba gaba daya zata iya qirga sau nawa ya hauta dan ita kanta sau biyu ta shigeta daga randa aka kawota se da zasu bikin wata qanwar qawarsu ita da Safina ta uzzura mata seta ari motar ta dauka a sace ba tareda ya saniba. A qalla kudin motar ya haura naira Miliyan Goma sha biyar dan sanda ya siyeta ba qaramin fada Hajiya tayi masa ba a cewarta almubazzaranci ne. Ba tareda tunanin komai ba ta matsa gefe inda aka saka musu rumfar shan iska da kujeru, duwatsu ne a gurin ta sunkuya ta tsinci manya da take ganin zasuyi mata aikin da take so tayi ta kwashe su da dama kafin ta durfafi motar. Seda ta cire rigar da aka rufeta da ita kafin taja da baya ta tsaya. Tunani tayi duwatsun bazasu mata aikin da take so ba ta zubar dasu a gurin, cikin gidan ta wuce kai tsaye ta shiga kitchen ta dakko qatuwar tabaryata dawo gurin motar babu tunanin komai ta fara takan glass din baya da yafi kowanne tsada, seda tayiwa gilasan motar rugurugu ta hada harda jikin qarfen motar ta lotsa inda zata iya kafin ta haqura ta yarda tabaryar a gurin tana haki kamar kamar wadda aka saka dole. Ciki ta koma ta dakko muqullin tata motar ta fice daga gidan, kai tsaye gidan safina ta nufa tana da buqatar ta ba zata iya ita kadai ba dan ta tabbatar babu qarya a kalaman Khalil ita kuma tayi alqawarin bazasu tabbata ba. CIKIN GIDA Umaimah na barin Gidan Anty Amina da Jamila suka fito da shirin tafiya. A gigice Anty Aminan ta shiga kwalawa Sammani me gadi kira ya shigo compound din hankali tashe sedai abinda ya gani yasa ya gane dalilin kiran nan da nan ya tsure har ya fisu shiga rudani, Jamila ce tayi qarfin halin tambayarsa wayayi wannan aika aikar Sammani ya watsa hannaye sama yana rantsuwa yace "Na rantse da kwarankwatsa Hajiya bam sani ba, tunda Alhaji ze fita ya aikeni can bayan layi gidan da akayi rasuwa ya bamu Buhun shinkafa da kudi yace mu kai musu, ina dawowa kuma na zauna a bakin qofa ko ciki ban shigo ba se yanzu". Hannu kawai ta daga masa alamar yaje, Anty Aminan ta janyo waya zata kira Khalil Jamila ta hanata tace su koma gurin Hajiya. A falo suka tarar da ita tana waya suka zauna kowacce ranta a dagule har Hajiyan ta gama wayar, tana shirin yin magana Jalilah ta fito daga kitchen da farantin Indomin da ta saka Habiba ta dafa mata, kallonsu tayi ganin yanda sukayi wani sanyi se kace wanda aka fadawa Rasuwa ta ajiye farantin tana cewa "Aa, ku kuma fa ya haka kun fita da fara'a kun dawo kamar Wanda akayiwa mutuwa?" Anty Amina ce ta kalli Hajiya tace "Hajiya, yanzu muna fita muka tarar da motar anyi anyi kwash kwatsa da gilasanta, na tambayi sammani yace besan wanene yayi ba" "Wace motar?" Jalilah ta tambaya tana dafe qirji Jamila ta bata amsa da cewa "Mercedes dinsa" "Babu shakka labari yakai kunnen Umaimah, to wallahi Allah duk wata asara da tayi masa tamkar ta qara zugi ne da qara matso da lokacin auran nan, tunda ta riga taji kuma babu abinda za'a jira Hajiya ki kira su Baba Abu suje su nemo auran nan kuma ko yanzu ta kama a daurashi kawai idan yaso ta hadiye zuciya ta mutu qarewar fasa masa mota, kuma duk abinda ta lalata seta biya bazamu sake daukar Asara bisa ganganci ba" Jalilah ta fada tana huci yanda kasan motarta akace an lalata. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 63 UMAIMAH Bayan fitarta gida kai tsaye gidan Safina ta wuce dan tana da buqatar abokin shawara akan ta inda zata bullowa lamarin. tana tafe a hanya kuka takeyi wiwi kamar wadda aka aikowa uwarta ta mutu, kalaman Khalil na mata yawo akai tana jinsu kamar wasu Allurai ne ake caka mata su a kwakwalwa a haka ta qarasa gidan tana shiga ta zube a falon Safina tana ci gaba da Kuka, Safina dake kwance kan kujera tana kallo ta miqe da sauri ta nufeta hankali tashe tana tambayarta lafiya amma Umaiman ta kasa ce mata komai se ihu take kamar wata zautacciya. Sda tayi me isarta ta samu sauqin abinda takeji kafin ta bude baki dakyar tace "Safina na shiga uku na lalace dagaske Khalil aure zeyi har yana gaya mun rayuwata bata da muhimmanci a gurinsa yanzu dani ko babu baze chanza komai ba, ki taimakeni Safina zuciyata zata fashe" ta qarasa tana rushewa da wani sabon kukan. Tsaki Safinan taja tareda komawa inda ta tashi tana kallon Umaimah dake kuka tamkar Mama ta mutu tace "Amma wallahi kedai anyi banza yanzu daman saboda Namiji da wata kishiya da bata rigada ta shigo bama kikazo zaki saka jinina ya hau na zata ma wata mutuwar akayi miki, to uban me kike so yanzu ni nayi miki? Ina cewa kikayi zaki samarwa kanki mafita to yanzu basirar taki ce ta yanke da zaki sake dawomun kin wani kuka wiwi akan wani Khalil se kace da Gold akayi shi? Ki tafi inda za'a saka miki shi a kwalba se yanda kika yi dashi kin zauna kina batawa kanki lokaci kina zubar da mutunchinki a gari kowa yana miki kallon Mahaukaciya ina dalili, ni kinga bazan iya na ki dena zuwa kina raba baqin cikin ki dani bayan ga hanyar magancewa kin zauna taurin kai ke bazaki je ba". "Ni na gaya miki ki bani wata shawarar banda ta zuwa gurin Malami dan ni bazan iya yawo kullum ina kaiwa qaton banza kudina yana cinyewa ba qila ma duk qarya ze ringa hadamun nazo nayi biyu babu" Umaiman ta fada tana goge fuskarta se Safina ta sake galla mata harara tace "Ai idan baki kaiwa qaton banza yaci ba kyayita yawon Police station da kwanan Cell ko? Kinga nifa ban kiraki ba, shawara dai kike nema a gurina na baki kuma kince batayi miki ba dan haka kiyiwa Allah ki qyaleni nidai kiyi sabgarki ke kadai dan bana son abinda zesa kije kiyi wani cin kan sunana ya fito a ciki banji ba ban gani ba a zo a daureni. Duk ranar da kika shirya kika kuma yarda kizo na kaiki inda ko sunan Mace indai bake ba Khalil baze ambata a bakinsa ba. A kama miki shi a hannunki ba wani mugun abu zakiyi masa ba Kishiya ce bakya so shikenan a cire masa tunanin duk wata mace daga ransa se ke kadai ba shikenan ba meye wani abun zafi anan? Idan ma qyashin bada abin Sadakar kikeji muje ni zan biya miki kodan ki qylaleni na huta haka dan Allah". Dukda bata so amma haka ta yarda da zuwa gurin Malam Sha yanzu magani yanzu saboda hujjojin da Safinan ta bata tana ganin zata iya amfani da hakan a matsayin matakin gaggawa na daqile abinda yake shirin faruwa kafin ta tsara gagarumin shirin a gaba, dan ita ba zata qarar da lokacinta da abinda ta tara a gurin Malamai ba. Babu bata lokaci Safinan ta shirya suka fita bayan ta kira Malamin nata ta sanar masa da zuwansu. Can wata unguwa sukaje a wajen gari. Irin motocin da ta gani a qofar gidan Malamin ya bata Mamaki, haka a dakin da ake karbar lambar ganin Malam din Matane da Maza manya da kana ganinsu kasan sun kama qasa duk suke zazzaune suna jiran layi yazo kansu suga Malam din. Safina ce taje gurin wanda take bada lambar sukayi magana ta dawo inda take tace mata suje, wani daki qarami na daban suka shiga suka zauna ta kalli Safinan kafin tayi magana tace mata "Kin san ni VIP ce tun kafin malam yayi suna a sanshi a duniya muke tare dashi. Asali malamin Kakarmune gashi anzo kaina nima ina cin gajiyarsa". "Ikon Allah" Umaimah ta fada a ranta wato su Ahalinsu gaba daya sun maida bin malamai sana'a kenan tunda gashi har gado sukeyi toh Allah ya kyau. Suna nan zaune mamakin jama'ar data gani yasa ta manta ma da abinda ya fito da ita. Wato dagaske Safina take da tace duk macen data cika ta tumbatsa tana da Malami ko Bokan daya tsaya mata yanzu lalacewar harta wuce kan Mata harda Maza a yawo gidan Malamai to ita dai ba zata iya ba. Tunawa tayi da maganar da Khalil ya gaya mata dazu da safen take zuciyarta ta dauki zafi hawaye ya kawo idonta, har ace an kai matsayin da Khalil zece koda ita ko babu ze iya rayuwa saboda ya samu wata? Wannan dalilin ne kadai yasa ta yarda da tayin safina kuma a shirye take data sabauta koma wacece take shirin kwace mata Miji, Khalil dinta dai bata da buqatar yin wani aiki akansa dan natane, ta sani itama me shirin shigar mata Hancin da Asiri ta neme shi dan haka zata kwato abinta kota halin qaqa kuma tana buqatar tayi hakan da sauri. Kallon Safinah dake faman danna waya tayi tace "Nifa Safina zuciyata bata aminta da wannan abin ba kuma na tabbata koda anyi aikin baze yuwu ba tunda daman shi Asiri ai seka yarda dashi yake ci kuma ni kin san uzurina na sauri ne, kawai kinga ma fasa mu tafi zanje nayi duk me yuwuwa na samarwa kaina mafita iya wannan jiran banzan da mukeyi ya tabbatar mun bazan samu abinda nake buqata ba" Umaimah ta fada tana kallon Safina, murmushi Safina tayi tareda dafata tace "Dadina dake Umaimah garaje wai me kike ci na baka na zuba ne? Wai bakiji sunan Malam bane? In kiyarsa fa sha yanzu magani yanzu ke dakanki ya kamata ki bada shaidar hakan tunda yayi mun kuma kin gani, duka dan jiran da zamuyi na minti nawa ne ko kuwa ke kinfi gane kje kiyi hauka ayita yawo dake a duniya ana surutu ki qarawa kanki baqin jini a gurin wanda kikeyi saboda shi din? Ke yanzu baki ma tunanin abubuwan da kikayi a baya ne suka tunzurashi ga yin auran yanzu toh wallahi kika kuskura kika sake gwada wani shirmen na tabbatar ya sakeki ba wani abin wahala ze zamar masa ba tunda da bakinsa ya gaya miki yanzu bakya gabansa dake ko babu ke babu abinda ze fasayi to gara ki taimaki kanki kibi komai a sannu, ta qarqashin qasa ake yaqi yanzu ki koma gefe kisha kallo kina zaune zakiji zuwan da dawowar kuma babu wanda ze zargeki balle a sakaki a bakin duniya". Janye hannunta da Safinan ta riqe tayi zatayi magana wani saurayi ya shigo dakin da suke zaune yace "Hajiya Malam yace ku shiga bangaren Amarya ku jirashi daya sallami wadda take ciki ze shigo yanzu" yana gama fadar haka ya juya se Safina ta miqe ganin haka itama ta miqe tabi bayanta dukda zuciyarta cike take da wasi wasi. Cikin gidan Malam din suka shiga, part uku ne qerarru a ciki, kallo Umaimah tabi gidan dashi, Safina taja ta tana cewa "Kinga badda kama ba?" Ita dai tabita da "Uhm" a ranta tana sake qaryata aikin Malamin dan quru quru yanzu ta samu hujjar cewar dan damfarane. Yana can yana tatike masu dakon Asara ya danqara gida na gani na fada da kudin su yana shata musu qarairayi. A falon Amaryar Malam din suka zauna, Umaimah dai se bin gurin take da kallo yanda ya gaji da haduwa abubuwan more rayuwa kuwa babu wanda babu a ciki. Seda me aikinta ta kawo musu ruwa da Lemo kafin ta fito, fara kyakykyawar yarinya da bazata haura shekara Ashirin ba da fara'arta suka gaisa da Safina wadda alamu ya nuna akwai sabo sosai a tsakaninsu kafin ta gaida Umaimah dake binta da kallo. Tashi tayi tace tana zuwa ta shige kitchen, Safina tayi qasa da murya tace "Kin ganta yar qawar Hajiyarmu ce in gaya miki daga zuwa karban taimako wai Aljanu na damunta se ji mukayi wai Malam take so shi zata aura harfa an kawo mata kudin aure wani yaro dan masu kudi a gurinsa fa aka ringa aikin har suka shawo kan yaron ya fito za'ayi aure se gashi yarinyar nan ta dage se shi seda akayi auran nan yanzu watanta biyar kenan aiko uwar saboda Haushi tace ko cokali bazata siya mata ba yace babu komai saboda auran nata fa ya rushe gidan gaba daya ya tada wannan ginin kiga Aljannar duniyar daya zuba mata" "Aikuwa taga taimako kinga an yi daidai kudin ku da kuke kawo masa dashi ya hada yayi mata kayan dakin da duk baku saka irinsu ba ma ai" Umaimah ta fada cikin gatsali. Sallamar Malam ta hana Safina bata amsa, Matashin Magidanci da baze wuce shekaru Arba'in da motsi ba ya shigo yasha Babbar Riga ta Shadda Getzner se maiqo take ga uban rawani ya kafa da zabgegen carbinsa a hannu. Ya washe baki yana yi musu sannu da zuwa Safina ke amsa masa Umaimah dai tunda ta gaidashi sau daya ta sake fuska dan ganinsa ya sake saka ta qin yarda da lamarin Na Safina. Wannan ne Malamin da take zuzutawa ta tabbata dai dan 419 ne shima yake kwasar rabonsa kawai. "Hajiya Safina idonki kenan, ai nace tunda kin samu kan Yallabai an dena jinki" Malamin ya fada se Safina tayi dariya tace "Ba haka bane Malam, kwana biyun ne ban fiya zama ba wlh amma ina nan zanyi zuwa na musamman, yanzu ma qawata na rako, abu ne ya taso mata Urgent shine nace bari na rakota inda za'a share mata hawaye". "To to menene matsalar? Ko da yake ina zuwa" Malam ya fada kafin ya miqe ya shiga wani daki dake cikin falon. Amarya ta dawo me aiki na biye da ita da Qaton Try da ta doro kulolin abinci ta ajiye musu Safina tayi mata sannu ita dai Umaimah binta kawai take da kallo harta wuce ta koma dakinta. Minti kusan biyar Malam ya dawo da wata qaramar Jaka ya shimfida buzu a qasa ya zauna ya bude jakar ya ciro qaramin carbi da wasu kwalaben turare. Seda ya gama shafe carbin da turaren yana mammotsa baki kafinya kalli Umaimah yace "Bismillah" Kallon Safina tayi da rashin fahimta se tace mata "Ki matsa kusa yake nufi". Muskutawa tayi gefe tana sake kallon bakin Malamin dake ta motsi seya miqo mata carbin hannunsa yace ta zabi guda uku ta zaba seda suka maimaita sau uku kafin yaci gaba da jan carbin yana muimui da baki. Shiru gurin ya dauka Malam nata juya carbi yana girgiza kai daga qarshe ya ajiye yana kallon Umaimah da Safina da suka zura masa iso suna kallonsa yace "Maganar gaskiya akwai Matsala babba". A tare suka gwale ido suna kallonsa, Safina data dafe qirji tace "Matsala wace iri malam?" Seya karkace ya gyara zama yace "Mijinki ya fada soyayya da wata yarinya kuma munga akwai qauna a zuciyarsa hakan yana nufin aure kenan" "Toh Malam ai munsan da wannan dalilin daya kawo mu kenan muke so a dakatar da auran" Safina ta fada seya sake jan carbi ya hau irga kusan minti biyar kafin ya sake kallon Umaimah yace "Maganar Gaskiya Hajiya naga aure sedai lokacin yinsa ne ban sani ba, sannan akwai mutuwa kuma akwai mutuwar aure duka gaba daya amma zamu iya shawo kan matsalar gaba daya in Allah yaso" "Kaga Malam ka tafi kai tsaye ka gaya mana abinda ka gani ba wani magana a duqunqune ba, nifa daman shi yasa na gaya miki bazanzo ba, akan me mutum be gama da tashin hankalin da yake ciki ba za'a qara kawo masa wani? Mutuwa daman dole ka ganta dan koma wacece take shirin shiga sabgar Mijina Ajalinta ta siya mutuwar aure kuma ka ganta a gidanka. Ni kinga tafiyata da nasan batamun lokaci zaki saka ayi wlh da ban biyo ki ba" Umaimah ta fada a fusace tana miqewa tsaye, riqeta Safina da hankalinta yafi na Umaiman tashi tayi tana kallonta tace "Umaimah ki nutsu ki fahimci abinda yake fada, kin rigada kinji matsala s ki jira kiji yanda za'a maganceta" "Karki rainamun hankali mana Safina, Mutuwar ze hana faruwarta ko auran wanne yake da ikon dakatarwa a ciki? Kinga karki qara batamun rai ki barni na tafi naje nayi wadda zata fishsheni kedai da kikaga zaki iya seki zauna yayi ta karanta miki qanzon kurege" ta fada tana fincikewa se Safina ta sake riqeta, miqewa Malam yayi yana kallonsu yace "Bari naje, idan ta shirya kya yimun magana na bar mutane suna jirana a waje" "Aa kayi haquri dan Allah Malam, wallahi damuwar da take ciki ce tayi mata yawa har ta fara taba tunaninta amma tana da buqatar taimakonka matuqa wallahi. Ka taimaka mana duk abinda ya dace ayi dan hana faruwar auran nan kayi shi kawai Malam" Safina ta fada se Malam yace "Toh Hajiya naga wadda take da damuwar nan tace bata da buqatar aiki ke menene naki a ciki ne ki barta kawai taje, nidai na gaya miki akwai aure, akwai mutuwar aure sanann akwai mutuwa duk kuma inda zakije kije nasan bazakiji sabanin wannan binciken ba". Yanda kasan wanda aka zarewa Laka haka Umaimah ta bishi da kallo ta kasa motsawa ta tafi daga gurin kamar yanda tayi niyya. "zauna" Safina ta fada tana kama hannunta seta zauna kuwa babu musu zuciyarta tana wani irin bugu na tsoro data rasa tsoron menene. "Yanzu Malam ya za'ayi a shawo kan matsalar nan" Safina ta fada bayan da Malam din shima ya koma ya zauna yana wani munafikin murmushi da suka rasa na menene. Carbinsa ya sake dauka yaci gaba da motsa baki Umaimah ta zura masa ido kamar me son gane abinda yake fada ya gama surutunsa ya watsa carbin yace ta dauka jiki babu laka ta dauka ta miqa masa ya karba yaci gaba da ja zuwa can ya kalleta yace "Da akwai aikin da zamuyi wanda ze iya dakatar da auran amma fa se kin bada hadin kai tukunna" Shiru tayi bata ce komai ba dan haka yaci gaba da cewa "Kusan ke zakiyi aikin ma da kanki nawa kawai tallafine na makamai da zasu taimaka miki amma fa kibi a sannu". Nan ma shirun tayi se Safina ce tace "Zatayi duk yanda aka ce Malam babu matsala in sha Allahu". Miqewa yayi ya sake shiga dakin dazu ya gama buruntunsa ya fito da wani kwando a hannunsa. Gurin da yake zaune ya koma ya shiga ciwo fararen robobi qanana yana ware kowanne da yan uwansa seda ya gama tsaf kafin ya bude jakar dazu ya ciro wata takadda. Sticker ce a jiki ko waccean rubuta yanda ake amfani da maganin ya ringa daukar roba daddaya yana mannawa yana tarasu a gefe seda ya gama ya sake tashi ya mayarda ragowar kayan ya dawo da Allo da tawada ya zauna ya fara rubutu, befi layi biyu ba yayi ya dago yana kallonta yace "Ya sunanki?" "Umaimah" ta bashi amsa kamar me ciwon baki ya rubuta ya sake tambayarta sunan Mijinta ta gaya masa, seda ya gama tsaf kafin ya kwalawa Amaryarsa kira ta fito jikinta na rawa tayi musu sannu ta durqusa a gabansa, ruwa yace ta kawo a kwano bayan ta kawo ya miqawa Umaimah Allon yace ta wanke, kamar wadda yake controlling haka ta karba ta wanke ya karbi kwanon a ciki wata yar jarka ya dure rubutun ya hada cikin sauran kayan daya ware kafin ya zauna yana kallonta ya shiga daga robobin yana cewa "Wannan ko wanne da yanda zakiyi amfani dashi a jiki ki kula, kada a samu kuskure, sannan na wannan" ya ciro wani qulli daga Aljihunsa ya miqa mata yace "Turarene a tsakar gida ake yinsa duk kuma wanda ya shaqi hayaqin bakinsa zai rufe ruf daga fadar abinda bakyaso. Ki turarashi a inda duk wani me fada aji akan al'amarin auran yake shikenan kin gama dasu, sannan wannan" ya sake zaro wani qulli a farar leda sabanin na farko da yake a baqa ya miqa mata yana cewa "Ki samu kan Tinkiya, Tinkiya Mace ba Rago ba kiyi farfesun sa ki zuba wannan garin maganin a ciki, duk wanda yaci zaman lafiya tsakanin keda shi har abada babu wani sabani da ze saka shiga tsakani, duk wasu dangin Miji da suka saka gaba ki dafa ki basu suci an gama magana". Ita dai Umaimah juya abubuwan takeyi a hannunta kawai amma tunaninta yayi nisa da inda suke, 'akwai aure,akwai mutuwa ga kuma mutuwar aure duk akan wa?' Abinda take ta tunani kenan, tana ji Safina na zabga masa godiya ta bude jakarta ta ciro kudaden da sun haura dubu dari ta ajiye masa ya miqe yana ce musu suci abinci kafin su wuce sannan ya juya ya fice daga falon bayan ya sake kallon Umaiman. Ita dai bata iya shan koda ruwa ba Safina ce ta tsakuri Abincin saboda Azalzalar Umaiman suka tafi. A hanya suna tafiya Safina na sake jaddada mata da tayi amfani da Abubuwan nan kamar yanda yace "Ki kwantar hankalinki qawata kinsan fa binciken nan nasu sau da yawa basa ganin daidai se kiji zancen wani ya shiga na wani ta yuwu can wata yayiwa Istaharar tun dazu se a akanki Labarin ya fito" Safina ta fada ganin Umaimah ta zurawa hanya ido bata magana tunda suka fito. Ita kanta ta tsorata da jin zancen mutuwa daya kawo, a iya sani ta da Malam Sha yanzu kuwa be taba fadar abu be tabbata ba (wa'iyazubillah) toh babban abin fargabar shine waye ze mutu? Sanin wannan kuma se Allah. Haka suka qarasa gidan Safinan, Umaimah ta dauki motarta dan data Safina suka fita, bata zauna ba ta wuce gida faran faran babu sallar Azahar balle La'asar duk a yawon gidan Malam ta riske su. Sanda ta isa gida Khalil be dawo ba. Dakinta ta wuce ta adana kayan data shigo dasu kafin ta shiga bandaki tayi wanla hade da alwala har zuwa sannan kuzarin jikinta be dawo ba. Sedata rama sallolin sannan ta kulle qofar dakin da muqulli ta dauko jakarta ta zazzage kayan a kan gado. Daya bayan daya ta shiga duba su, wani a abinci wani abin sha harda na dafa shayi se nata na amfani wasu a ruwan wanka gana tsarki da hayaqi duk dai gasu nan kala kala. Zuciyarta ta kasu biyu akan amfani da kayan ko akasin haka kuma kowanne bangare ya kasa rinjayar dan uwansa dan haka ta hade kayan ta maidasu jakar gaba daya. Kallon robar rubutun daya ce ta zuba masa a ruwan sha tayi, seta dauka ta riqeta a hannunta, dakyar ta haye saman saboda nauyin da jikinta yayi kai tsaye ta wuce inda Dispenser take ta kalli ruwan da yake ciki ya wuce rabi dan haka beyi mata wahalar dagawa ba ta cire shi, rubutun ta juye a ciki, tana so ta dandana taji ko ya canza taste amma bata san na menene ba, haka ta mayar da robar kai kafin ta wuce dakin Khalil din ta shiga gyarawa. "Shi Aikin Asiri da kike gani se kin hada da kissa yake ci da wuri" abinda Safina ta gaya mata dazu da suna hanya kenan ta kuma jaddada mata data taushi zuciyarta ta nuna komai ba komai ba kawai ta zura ido taga ikon Allah. Tsaf ta gyara masa dakin daman falon a gyare yake ta kwalawa Ruqayya kira akan ta kawo mata garwashi. Seda ta turare dakin da hayaqin da Malam din ya bata kafin ta shiga bandaki ta kashe wutar tayi flushing gawayin da ragowar maganin kamar yanda ya fada kuwa hayaqin bashida wari ko qamshin komai, yanda kasan bata saka komai ba se dan qaurin wuta dan haka ta zuba turare a bunner ta kunna bayan ta fesa Room freshener sanna ta koma qasa. Kunun da bata sha da safe ba ta sha yanzun dukda kwata kwata bataji yunwa badamur da take ciki ta cushe mata ciki, Ruqayya na kitchen tana hada abincin dare, Tuwo takeyi da Miyar Kuka kamar yanda yake a Time Table din abinda zasu dafa. Daki ta koma ta kwanta lamo, tsoro takeji haka nan zuciyarta taqi aminta data cutar da Khalil dinta amma ya zatayi? Bata da wata mafita idan ba wannan ba da bakinsa ya tabbaatar mata da aure zeyi ya hadata da wata a cikin zuciyarsa ya kuma raba musu kansa a shimfida abinda ba zata taba lamunta ba ko bayan ranta bata fatan Khalil ya sake auran wata mace, so takeyi ya dawwa babu aure har ya tarar da ita su sake ci gaba da zama tare a Aljanna. Wannan tunanin ya saka ta miqe, Robar abinda yace ta zuba masa a Miya ta dauka dana shayi. Suna da banbancin kala dan haka ta cire takaddar jiki ta miqe ta tafi Kitchen din. A bakin qofa suka hadu da Ruqayya da ta dakko Fulasandata zuba abincin Khalil zata kai kan Dining, Ciki Umaiman ta wuce, kaitsaye ta bude butar shayin da Ruqayyanta dora ba tareda tunanin komai ba ta zuba abinda zata zuba ta mayar ta rufe haka ta zuba na miyar shima bayan Ruwayyan ta ajiye, har zata shiga daki ta tsaya ta kwalawa Ruqayyan kira ta fito daga Kitchen din da sauri "Gobe idan Allah ya kaimu zan aikeki Abbatuwa da Safe, karki manta da kin tashi koda ni na manta ki tunamin" ta fada mata Ruqayya ta amsa da "Toh Hajiya" kafin ta juya ta koma Kitchen din a ranta tana tunanin me yake faruwa kuma dan tunda Umaiman ta shigo taga yanayinta ba yanda take ba. Kwanciya tayi a dakin sanyin jikinta ya ninka na dazu, sosai take zargin kanta da rashin kyautawa amma kacokan ta dora laifin akan Khalil, shiya ja duk abinda ya sameshi shine Sila. KHALIL Cikin matuqar bacin rai ya kama hanyar Qunchi dan har ya manta da Anwar zasu tafi seda yaci rabin hanya sannan ya kirashi yana tambayar be fito bane har yanzu yana ta zaman jiransa. Haquri ya bawa Anwar din kan cewar yayi gaba ya taho kawai, yana ganin Kiran Humaira amma ya qi dagawa, baya so ya sauke fushin da ba nata ba akanta shiyasa kawai ya tura mata saqo cewar yana tuqi idan ya tsaya ze kirata. Gaba daya ransa babu dadi yayi aikin daya kaishi, se yamma Lis suka gama suka kamo hanyar Kano. Anwar ne yake tuqi shi kuma yana zaune a kujerar gefe ya jinginarda kansa baya yayi shiru yana tunani. Tunani barkatai suke yawo a kansa wai har se zuwa yaushe Umaimah zatayi hankali? Ya tambayi kansa. A kullum girma suke warawa shekaru na dada yawa amma ita tamkar baya takeyi kaifin tunani da hangen nesanta yana dada raguwa Kishi ai ba hauka bane da har ze saka tayi wasa da rayuwarsu, yanzu abinda tayi dazun da ace yazo da tsautsayi ko basu mutu ba ai zasu wahala musamman ita da tak da qarin wani nauyin a jikinta amma sam ita kamar mara tunani abinda yazo mata a zuciya kadai takeyi bata hangen abinda hakan ze iya haifarwa. "Mutumina ka rage tunanin nan haka, kowa yana da damuwa idan mukace zamu saka a rai muyi ta tunawa qila kama tafe a hanya sedai kaga mutane kawai suna ta faduwa damuwarsu ta kashe su" Anwar daya gaji dayi masa magana ta yaba shi yana fada. Ajiyar numfashi yayi kafin ya tashi zaune da kyau yana cewa "Damuwar ma kala kala ce Anwar, kai dai ka godewa Allah kawai da be jarabceka ta fannin aure ba, kaga duk wani jin dadin rayuwa to Macece cikonsa idan kuma har ka rasa nutsuwa a gurinta wlh ko kafi qaruna wadata da iko seka tawaya ta bangaren nutsuwar zuciya Allah dai kawai yasa mu dace". Wayarsa ya zaro a Aljihunsa ya kunna dan yana isa ya kasheta saboda baya son Humaira tayi ta kira shi kuma baze iya magana da ita a cikin fushi ba. Tana gama kunnuwa kuwa saqonta ya shigo, qorafi takeyi akan yace ze kirata idan ya isa kuma ta sake kira wayar a kashe "Ka kirani da ka kunna wayar idan ba haka ba babu ruwana da kai, I love you Yayana" ta rufe saqon dashi. Be san sanda ya saki murmushi ba babu bata lokaci kuwa ya danna mata kiran kamar tana jira ringing daya ta daga wayar da sallama kafin ta dasa masa kukan shagwaba. Seda ya kwashi wasu mintina yana aikin rarrashi tareda kare kansa akan dalilin daya saka be kiratan ba kafin ya samu ta haqura bayan ta kafa masa sharadin daya shiga Kano seya je gurinta shine hukuncin hanata magana da shi da yayi wuni guda. "An gama my Boss lady, amma idan nazo me zaki bani kinga dai na gaji da yawa ki taimaka ko dan hug ne da kiss na samu mana" ya fada cikin sigar tsokana kafin ya kai qarshe kuwa har ta kashe wayar ya zareta daga kunnensa yana sakin dariyar dabe shirya mata ba. Kunyar ta tana burgeshi duk sanda yake son ya tsokaneta da yayi mata irin wannan maganar zata dauki fushi ita ala dole ya kauce hanya. Be gama dariyar ba kuwa saqonta ya shigo tana cewa "Na fasa karkazo, kuma kayi iatigfari tunda aini ba matarja bace kake gaya mun wannan maganar". Sake tuntsurewa yayi da dariya har yana dukan gaban motar, Anwar ya kalleshi da murmushi yace "Gida biyu maganin gobara mutumina" "Fadi ka qara Abokina musamman ace ka samu danyan jini duk wata damuwarka ta yaye wlh" ya bawa Anwar din amsa yana sake kiranta amma taqi dagawa. Haqura yayi dan daman baya so yaje din ne shi yasa yayi mata haka se ya kunna Datarsa ya shiga WhatsApp, hotuna ya gani Jalilah ta tura masa ya bude yana ganin abinda yake ciki ya zaro ido tareda dafe bakinsa saboda mamakin abinda ya gani. Motarsa akayiwa haka? Bashida buqatar tambayar wa yayi dan yasan yar dabar daya ajiye a matsayin mata shi kansa zata iya masa haka ba motarsa ba se ya kashe Datar kawai ya fita daga WhatsApp din yana qoqarin hana bacin ran sake dawo masa. Daya isa gidan ma kallo daya yayiwa motar ya hadiye wani abu me daci ya wuce, da Hajiya tayi masa maganar ma kai tsaye ce mata yayi "Kiyi mun Addu'a Allah ya maidamun da mafiyinta" yayi shiru. "Amma Babana haka zaka zuba mata ido ta ringa barnatar maka da dukiya babu gaira babu dalili?" Hajiyar ta sake fada seya miqe yana murmushi yace "Wancan karon fa Hajiya ke kikayi mun fada akan me zanyi fushi saboda na rasa wani qyale qyalen duniya, wannan ma ba rabo bace shi yasa hakan ya faru da ita. Gobe kawai zan kora company suzo su dauka su bani abinda ya samu dan banida kudin da zan iya gyarata gara kawai na siyar yanzu dai ni ya maganar da mukayi jiya kin kira Baba Abu din?" Ya canza maganar da wata. Seta sauke numfashi tana kallonsa. A idonsa ta karanci bacin ransa amma ya danne ya nuna komai ba komai ba. Numfasawa tayi tace "Na kirashi yace babu damuwa ze samu sauran kawun nanka suyi magana se suji sanda ya kamata suje din kuma gurin wa zasuje" "Kuyi magana da Maman kawai Hajiya ita zata gaya miki duk ma inda zasuje, sannan dan Allah ina roqon Alfarma idan sunje karsu bari a saka lokaci me tsaho Hajiya, duk abinda za'ayi karya wuce wata biyu" ya fada kansa a qasa kafin ya miqe hahiyar tace "In sha Allahu, Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi sannan kayi haquri da abinda ya faru Babana taci Albarkacin zuri'a". Murmushi yayi mata ya fice daga part din ya wuce nasu. Yana shiga dakinsa yaji kansa ya sara, ya dafe kan yana kiran sunan Allah ya zauna a gefen gado yana jin bugun zuciyarsa yana qaruwa, a hankali ya tashi ya fita palour, ruwa ya tsiyaya yasha dan ya fi ta'allaqa bugawar kan da gajiyar da yayi ga bacin ran da yake ciki Allah yasa ma ba jininsa ne ya hau ba. Seda yayi wanka yayi sallar Magriba kafin ya zauna cin Abinci. Kallon tuwon yana jin yunwa amma gaba daya abinci ya fita a ransa bacin rai ya cika masa ciki taf kuma bayaso ya fitar dashi anyi masa ne da gayya dan yayi magana shi kuma ya qudurce baze ce mata komai ba ze tarata yana kuma dab da ramawa. A hankali yayi bismillah ya fara cin tuwon, kadan yaci ya ture ya tsiyaya shayi a cup ya koma cikin falon ya zauna. Yana fara sha aka kira sallar Isha seya ajiye ya fita, Umaimah dake tsaye bakin qofarta tun zaman Khalil din tana ganin fitarsa ta fito daga dakin. Cup din shayin ta dauke ta wuce kan Dining ta maidashi cikin butar shayin kafin ta dauka ta kai kitchen. A sink ta korashi, ragowar wanda bata saka komai ciki ba ta dumama ta maida masa dan tasan be gama sha ba ta sake dakko flask din miyar shima ta zubarda ta ciki ta maida wata ranta duk a dagule. A falon tayi sallah ta zauna a gurin harya shigo, kallo daya yayi mata ya wuce gurin Dining din ya tsaya yana kallon kayan dake gurin. Yana da tsananin lura da abu, ko takadda ya ajiye aka canza mata mazauni yana ganewa dan haka nan take ya fahimci da an canzawa kayan yanayi. Butar shayin ya bude dan ya tabbatar da zarginsa ilai kuwa yaga yawan wanda yake ciki ya zarta wanda ya bari kamar ma be taba ba. Kallon Umaimah dake h Jan carbi yayi ya girgiza kai a ransa yace "Idan ma kasheni kike so kiyi nayi shahada ke kuma kiji da dakon haqqina" ya maida murfin ya rufa ya haye sama yana jin wani iri a jikinsa. Gaba daya ji yayi ya kasa nutsuwa se kawai ya dauki muqullin motarsa ya fita. Ya fahimci Umaimah tayi nisa ba yanda ya santa bace a baya, wannan Umaiman ta yanzu zata iya aikata komai akan cikar muradinta. Asibiti ya wuce, be samu nutsuwa ba seda akayi masa gwaji aka tabbatar masa da babu wani abu me kama da guba a jikinsa kafin ya sauke a jiyar zuciya a ransa yana zargin kansa da yi mata rashin Adalci. Me yasa ze zargeta akan abinda bashi da tabbaci? Ta yuwu an maida wanda ya zuba ya fara sha ne ciki shi yasa yaga shayin ya qara yawa sannan an kwashe plate din daya bata dole zata gyara zaman kwanukan. Yasan ma Ruqayya ce tayi amma zuciyarsa ta tafi ga zargin Umaimah tayi masa wani mugun abu. Hakannan yakeji be kyauta mata ba, can qasan ransa wata soyayyarta ta qara motso masa yana tafe a hanya yana tunani Ya sani Umaimah tana sonsa kuma tabbas se ana son mutum ake kishinsa kenan soyayyarsa ce ya janyo take aikata duk wadan nan abubuwan idan har ya karbeta a yanda take zasu zauna lafiya ya yarda ya kuma karbi laifin akan cewar shi yake tsokanota a koda yaushe har take sauka daga layi tayi abinda kowa yake ganin bata kyautawar. Wasu tunani barkatai suka shiga gewaya masa kwakwalwa, yanda kasan wanda Iska suka shiga haka ya kama hanyar gida jikinsa na rawa dan so kawai yakeyi yaje ya bata haquri ya kuma gaya mata duk abinda ya fada mata dazun wasa yakeyi tayi haquri su zauna lafiya. Daya isa gidan ta koma daki ya murda qofar yajiya a kulle, a hankali ya shiga bugawa, kusan minti biyu yana bugu bata bude ba jikin qofar ya tsaya ya shiga kiran sunanta nan ma shiru haka ya haqura ya wuce sama ransa duk babu dadi. Raba dare yayi yana tunanin halin da take ciki, daga qarshe dayaga ya kasa bacci ya miqe yayiwo Alwala, yana tayar da sallar dakyar ya kai raka'a biyu yana sallamewa bacci me nauyi ya kwashe shi a gurin. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 64 Hasken ranar daya galle masa ido ne ya farkar dashi ba tareda ya shirya ba. Dakyar ya iya bude idanunsa da sukayi nauyi yanda kasan wanda ya kwana be runtsa ba, yabi dakin da kallo, hasken daya gani ya tabbatar masa da cewar safiya ta rigada tayi cikin hanzari ya miqe yana istigfari wayarsa dake kan mudubi ya janyo ya duba lokaci qarfe bakwai harda minti Arba'in seya ajiyeta ya shige bandaki da sauri a ransa yana mamakin meya shiga kansa haka? Da wayonsa baze tuna ranar daya rasa sallar Asuba ba, koda ace ya makara be samu yinta a cikin Jam'i ba tofa kafin gari ya gama haske yayi amma yau shine har takwas saura yana baccin da besan lokacin daya kwashe shi ba. Saboda yanda jikinsa yake a mace seda ya watsa ruwan sanyi kafin yayi alwalar ya fito. Ya dade yana istigfari bayan ya idar kafin yayi Azkar dinsa ya gama komai ya sake komawa bandakin. Wanka yayi sosai ya fito dan takwas ta wuce idan beyi da gaske ba ze makara fita aiki. Yana shiryawa ta fado masa a rai, seya ajiye body spray din da yake fesawa ya zura kayansa da sauri ya fita daga dakin. A bakin qofarta suka hadu da Ruqayya ta fito da Tray a hannunta da alama abinci ta kai mata tana ganinsa ta rusuna har qasa ta gaidashi ya amsa yana shiga ciki da sallama. A tsaye ya tarar da ita tana saka hula akanta, kallo daya Umaiman tayi masa ta dauke kanta tareda qarasawa kan carpet ta zauna inda Ruqayya ta ajiye mata kayan abincin. Jikinsa har rawa yakeyi ya qara sa inda take ya durqusa a gabanta hannu biyu ya saka ya kamo hannayenta da yatsun suka kumbure yana kallon fuskarta yace "Har yanzu kumburin be sace ba?" Banza tayi masa ta kwace hannunta ta shiga zuba Kununta a Cup. "Jiya nazo nayita bugawa kuma nasan idonki biyu dan baki dade da shigowa ba sannan amma kikaqi ki bude mun me yasa?" Ya sake jefa mata wata tambayar, yanda yayi maganar a sanyaye cikin kulawa yasa ta kalleshita mayar da kanta taci gaba da abinda takeyi, se kuma me ta tuna ta kalleshi tace "Banji ba, nayi bacci lokaci, ina kwana?" Ta fada cikin sanyin murya,seya zauna dakyau yana amsa gaisuwar tata kafin yaci gaba da cewa "Ki shirya idan kin gama se mu koma Asibitin" "Ni bazanje ba, ba jiya kagama cewa rayuwata bata gabanka ba kona mutu ko na rayu duk matsalata ce kai baka da Asara wata zaka auro" ta fada cikin qunquni tana kallon cikin idonsa. Kansa yaji ya sara masa har seda ya dafe kan kafin ya kalleta shima yace "Kiyi haquri bana nufin duk abinda na fada miki jiya ba har zuciyata bane kawai raina ne ya baci kinji kiyi haquri". Baki ta sako galala tana kallonsa mamaki da Al'ajabi ya cikata da jin abinda yake fada, dagaske yakeyi jiyan ba har zuci yayi maganar ba ko kuwa aikin Malamin ne yaci a dare daya har Khalil din ya dawo qarqashin ikonta? Ta tambayi kanta, bata sake tsinkewa da Mamaki ba seda ya miqe yana ce mata "Kici abincin ina jiranki muje Asibitin yanzu dan bana son wani abu da ze taba lafiyarki kin sani" ya sumbaci hannunta tareda furta mata kalmar "I love you" da rabon da tajita a bakinsa tun randa ta rusa mata Kwangila. Haka ta takashi da ido kamar somuwa har ya fice daga dakin kafin ta miqe da dauri ta dauki wayarta ta shiga kiran layin Safina. "Umaimah jarabarki bata qarewa yanzu meya faru da safiyar nan zaki fara doko mun kira?" Safinan ta fada cikin muryar bacci da alama kiran Umaiman ne ya tasheta. "Ke dallah sauraramun malama kira nayi ki in baki feedback, ni ban gane ba daman aikin Malam din nan take yake ci ne ko kuwa naga daga farawa jiya har yanzu yazo yana bani haquri akan abinda ya faru" "Aa to ke da me kika dauka? Sha yanzu magani yanzu ake gaya miki aikin Malam tamkar yankan wuqa ne ga kuma lasting da ba kin tsaya kina ta wani kokonton banza ba yanzu ai gashi a qasa da awa ashirin da hudu kin tabbatar da abinda nake gaya miki, seki turo mun da kudadena Malama kuma harda qari akai tunda aiki yaci" Safina ta fada. Umaimah na niyyar sake magana aka kwankwaso qofar dakin dan haka tace mata "Bari zan kiraki anjima dai" tana fadar haka ta kashe. Ruqayya ce ta shigo da dumamen tuwon da tace ta kawo mata ta ajiye har zata juya ta tsaida ita. Jakarta tace ta miqo mata, dubu goma ta qirga ta bata bayan ta sake jaddada mata ta siyo mata kan Tinkiya ba Rago ba kuma kar a fasashi kamar dai yanda Malam ya gaya mata ta karbi kudin ta fita a ranta tana mamakin me Umaiman zatayi da Kan Tinkiya ita da ba cin naman kai takeyi ba ko dafawa sukayi qarqari tasha romon amma abun me ciki ta yuwu kwadayinsa ne ya taso mata kuma bata son wanda suke dashi a gidan se Sabo ita dai ta wuce ta qarasa soya Dankali da kwai ta shiryawa Khalil akan Dining kafin ta tafi aiken Umaiman da zummar idan ta dawo ta karya. Khalil kuwa yana komawa sama a falo ya zauna saboda wani ciwon kai dayaji ya taso masa wanda ya kasa gane na menene. Gaba daya jikinsa ya mutu haka yayi masa nauyi, yana zaunen ji yake kamar bacci ze daukeshi seda yayi da gaske yana karanto Addu'oi kafin ya iya miqewa ya shiga dakinsa ya qarasa shiryawa. Wayarsa dake kan mudubi ya dauka ya bude,Missed call daya ya gani na Humaira se saqon barka da safiya da take tura masa kullum tareda qorafin beje ba jiya kuma be kirata ba. Danna kiran layin nata yayi gabansa ya yanke ya fadi yanda kasan wanda yayi karo da wani mugun abu haka zuciyarsa ta shiga bugawa harta daga ya yanke kiran ya zauna yana jera ajiyar zuciya se kace wanda yayi tsere, yana kallo ta biyo kiran amma ya kasa dagawa, gaba daya ya gaza fuskantar abinda yake ji a jikinsa da ruhinsa gaba daya, ya kasa ma yin wani tunani me amfani Umaimah kadai ke fado masa a rai duk sanda yayi niyyar raya wani abu a zuciyar tasa. Yana nan zaune Humairan tayi masa kira uku amma ya gaza dagawa, dakyar ya iya daukar wayar ya tura mata saqo akan ze kirata yana wani abu, yana tafiya kuwa ya goge saqon ya saka wayar a Silent ya jefata a aljihu sannan ya fita daga dakin kamar wani mara gaskiya ya sauka qasan. Kadan ya ci Dankalin ya shanye shayin daya hada ya miqe ya tafi dakinta. Tana kwance akan gado tana danna waya ya shiga, a gefen kanta ya tsaya yana cewa "Ya naga kin kwanta kuma?" "Ni kayi tafiyarka kawai lafiyata qalau na gaya maka yanayi ne kawai kuma ma naje Asibitin da kaina jiya sunce babu komai" ta fada tana yamutsa fuska, kallonta yayi kamar meson tabbatar da abinda take fada kafin ya matsa yana cewa "Shikenan, ni bari naje amma idan kinji wani abu fa ki kirani". Da "Toh" ta amsashi taci gaba da danna wayarta, a gefen qafarta ya ajiye mata kudi da batasan ko nawa bane amma suna da yawa yace "Gashi nan ko da abinda zaku siya, kiyi list zuwa gobe na abinda kike da buqata na haihuwa inaga ai watan ya shiga ko?" Tashi zaune tayi tana kallonsa da mamaki kafin cikin izgilanci tace "Ai na zata baka san da cikin ba da har zuwa yanzu baka ce komai akan tanadin zuwansa ba" "Se na dawo" ya fada tareda juyawa ya bar mata dakin ba tareda ya maida hankali akan abinda ta fada ba. Shidai haka nan yau ya tashi dason kyautata mata dan haka baze tsaya sa'insa da ita ba balle har ta kaisu ga bacin rai. Motarsa ya hau ya fice bayan Sammani ya bude masa Get ko bangaren Hajiya be tuna shiga ba abinda be taba tsallewa ba tunda suka dawo zama gida daya da ita. Duk Asubar duniya idan ya dawo daga Masallaci bangarenta yake fara shiga ya gaisheta sannan idan ze fita aiki se ya shiga ya mata sallama tayi masa Addu'a da fatan Alkhairi haka idan ya dawo seya fara shiga ya sanar mata daya dawo kafin ya shiga gidansa duk ranar da haka bata faruba kuwa dayan biyu sedai idan ba'a gidan ya kwana ba ko kuma ita Hajiyar ce bata nan to wannan ze kirata a waya su gaisa se gashi yau ya rasa tunanin daya dauke masa hankali har ya kasa shiga ya gaida mahaifiyarsa. Daya isa office dinma kai tsaye ayyuka ya shiga dan jiya kwatakwata be samu ya shiga ba. Seda suka tafi sallar Azahar yaga Missed call din Hajiya ta kirashi sau biyu da na Humaira daya, ya dafe kai yana salati shi kam yau meya same shi haka ne kamar wanda ya gamu da cutar mantau. Kiran Hajiyar yayi suka gaisa tana cewa "Babana lafiya yau banganka ba ina fatan dai ba damuwar jiya ka saka a ranka harta haifar maka da ciwo ba ko?" "Aa Hajiya lafiya qalau wlh yau makara nayi ban fita sallar Asuba ba shiyasa kika ga ban shigo ba kuma na tashi na fita a gaggauce munyi baqi suna jirana se yanzu muka sallame su shine naga Kiranki ma" ya shatowa Hajiyar qarya dan be san me zece mata daya hanashi shiga ya gaidata ba. "Toh ai shikenan dan har hankalina ya tashi danaga har goma babu motsinka kuma yara sun shiga sunyita bugu ba'a bude ba se yanzu Ruqayyan ta shigo take cewa Maman tasu bacci takeyi kai kuma ka fita tun safe sannan hankalina ya kwanta daman ita kwana biyu ta dena shigo mana ballantana yanzu da ka sake shafa mana baqin fenti a gurinta amma babu damuwa kayi aikinka Allah ya taimaka idan ka taso se muyi magana dan dazu Kawunku yazo kuma daga nan yace zeje can gidan Hajiya Hauwa ne saboda ta hadasu da Maza da zasuyi magana dasu ba'ayita magana da Mace ba" Hajiya ta fada, seya shafa kansa kamar yana gabanta yace "Toh Hajiya duk yanda kukayi ai daidai ne, ita kuma batajin dadi ne. Bakiga yanda duk ta kumbura ba kuma nayi nayi da ita muje Asibiti taqi wai lafiyarta qalau" "Toh subhanallahi Allah ya bata lafiya amma dai ya kamata ta daure kuje din dan kumburin idan yayi yawa bashi da dadi gara a gane koma menene sikarsa tunda wuri a magance. Shi yasa nace ka ringa binta a sannu da maganar auran nan saboda yanayin da take ciki Allah dai ya raba lafiya" Hajiya ta sake fada aga nan sukayi sallama ya kashe wayar. Zancen Hajiya Hauwa da tayi yasa ya tuna da Humairan ma dan shaf kamar an shafe masa ita daga tunaninsa gaba daya. Office dinsa ya koma ya zauna, a maimakon ya kira Humairan seya danna number Umaimah. Seda wayar ta katse ya sake kira shima kiran na dab da katsewa kafin ta daga murya can qasa kamar me bacci. "Bacci kikeyi na tasheki ko?" Ya tambayeta a sanyaye, cike da Izza kamar wata basarakiya tace masa "Bacci nakeyi, kuma dakyar na samu ya daukeni gashi yanzu ka tadani". "Allah ya baki haquri ki kwanta kiyi baccinki, idan kuma yaqi sake daukanki ki kirani se nazo na lallabaki kiyi kinji" ya fada jikinsa har yana rawar daya rasa dalilinta. Qaramin tsaji taja kafin tace "Nidai ka katse mun baccina haka kawai me zanyi maka toh?" "Babu komai kawai so nakeyi naji ya kike, sannan Yara sun shigo qofa a kulle idan kin tashi se ki kirawo su ko na zatama kin shiga kun gaisa da Hajiya ai" yanda yake maganar kamar wani me tsoronta ko tsoron fadar wani abu daze bata mata rai, baki ta tabe kamar yana ganinta tace "Idan na tashi naji daidai zan shiga ai kasan bana jin dadi dai" se yayi saurin cewa "Na sani, to kiyi kwanciyarki ki huta idan na dawo se mu shiga tare kawai ba se kinje ba". Sallama sukayi ya ajiye wayar yana sauke numfashi, shi dakansa yasan abinda yakeji is unusual, wata muguwar shakkar Umaiman yakeji da ya rasa ta mecece. Humaira ce ta fado masa a rai seya dauki wayar ya kirata dukda yanda zuciyarsa ke qoqarin hanshi tana nuna masa ran Umaimah fa ze baci idan ta gano yayi waya da wata. Seda wayar ta kusa tsinkewa kafin ta daga wayar da sallama ya amsa se tayi shiru "Fushi kikayi" ya fada a sanyaye, shiru tayi batace masa komai ba seya gyara zamansa yana sake yin qasa da murya yace "Haba qanwata yanzu fushi kikeyi da yayan naki ba zakiyi mun uzuri ba bayan kinsan aiki nakeyi tuquru saboda in tara kudin auranki?" Bata amsa shi ba dan haka ya sake cewa "Haba mana Umaimah ta kiyimun magana naji muryarki ko zuciyata zatayi sanyi kinji Autar Mata" kamar tana jira se ji yayi ta fashe masa da kuka harda shashsheqa,a rikice ya miqe daga kujerar da yake zaune ya shiga zaga office din yana salati tareda tambayarta abinda ya faru me ya sakata kuka. "Ni daman nasan ba sona kakeyi ba shiyasa ma tun jiya kake tayi mun wulaqanci na kiraka kaqi dauka duk message din dana tura maka babu reply sannan yanzu saboda ka nunamun ka fi son matarka bana gabanka harma manta sunana kayi kake kirana da nata" Humairan ta fada dakyar tana kuka. Dafe bakinsa yayi jin abinda ta fada, yaushe akayi haka ya kirata da Umaimah shi wallahi be sani ba bema yarda ya fada ba amma yasan idan yace ze tsaya kare kansa rigimar ba qarewa zatayi ba dan Huamira yar daruce itama idan ta murde dan haka cikin rarrashi yace mata "Kiyi haquri wallahi idan ma na fada banyi dan na bata miki rai ba, yanzu muka gama magana da ita a waya inaga shiyasa sunan yazo bakina ban sani ba kiyi haquri kinji Shatuna ki yafewa Yayanki kuma ni ba ina sane duk naqi daukar wayarki ba akasi aka samu amma kiyi haquri". A maimakon tayi shiru sema qarawa kukanta amo tayi tana cewa "Oh daman da ita kake waya nayita kiranka kanaji baka amsa ba ai dai ko second biyar ne seka dauka a gunta kace mun zaka kirani aidai zansan ka damu dani ba kayita share mun waya ba tunda dai naga nima din matarka zan zama" "Humairah kishi, toh kiyi haquri bazan sake ba daga yau koda qa nake qaya indai ba Hajiya bace zan dauki excuse na amsa wayarki shikenan?" ya fada cikin lallashi da mamakin yanda take magana yau, rage kukan tayi nan ya shiga aikin rarrashi, besan adadin lokacin daya kwashe ba seda Anwar ya shigo office din yana gaya masa lokacin shigarsu Meeting yayi sannan ya ankare da a qalla sunfi awa daya suna waya. Sallama sukayi bayan da yayi mata Alqawarin daya tashi ze biya ya ganta saboda ya qara wanke laifinsa sannan ta haqura ya kashe wayar. "Kai Subhanallahi" ya fada yana dafe kansa, shikenan idan wannan ta garo shi ta nan se waccen ta bugo shi ta nan kenan to Allah ya bashi wuyan dauka. UMAIMAH Suna gama waya da Khalil ta miqe daga kan gadon ganin daya ta gota, seda tayi sallah kafin ta fita zuwa kitchen. A Freezer taga saqon da aka siyo mata gashi nan kan guda ba'a fada ba ta ciro ta ajiye shi cikin sink tana toshe hanci saboda qarnin da ya fara hawar mata kai. Safina ta kira ta sake tambayarta yanda zata dafashi ta gaya mata seta wuce dakinda Ruqayya take ta sameta ta idar da Sallah tana lazumi. "Idan kin gama ki sake wanke kan can ki dora ki hadashi duk yanda kikeyi idan ya kusa dafuwa se ki gaya mun amma fa kar a fasashi na gaya miki" "Toh Hajiya sedai sun zazzage kwakwalwar a can ban sani ba ko anyi laifi?" Ruqayyan ta fada se tayi gaba tana cewa "Babu damuwa ki hadashi yanda nace. Haka kuwa akayi tsaf Ruqayyan ta hada Kan a qatuwar tukunya tana yi tana mitar meye dalilin da za'a dafa kai sukutum se kace na tsafi danma pressure pot din tasu nada girma ta dauke shi, seda ya dakko dafuwa kamar yanda ta buqata taje ta sanar mata. "Ki wanke mun bandaki amma kar ki saka Hypo bana son warinsa" ta fada tana miqewa Ruqayya ta bita da kallo, ta rasa gane alqiblar uwar dakin nata. Dazu data gyara dakin ita tace ta bar bandakin karta wanke yanzu kuma tanaso a wanke kai wannan yarinya dai kamar me juju haka ta shiga aikin tana mita ita kuma ta wuce kitchen din. Tsaf ta barbade naman da garin maganin da Malam ya bata, ta debi romon ta dandana seda ta hadiye kuma ta zaro ido "Kema zaki iya ci" kalaman malam suka dawo mata se sannan ta samu nutsuwa harta hadiye yawun data fara tattarowa dukda romon ya rigada ya shiga cikinta. Mayar da murfin tayi ta rufe ta koma palour ta zauna. Saboda ita ta saka kanta zama tayi har naman yayi laushi sosai lokacin Ruqayya ta gama tace ta farfasashi a raba a zubawa kowa nasa harda su Hajiya da Sammani. Ba sabon abu bane dan haka Ruqayyan bata kawo komai a ranta ba tayi yanda tace ta zubawa kowa. Umaiman da kanta ta dauki na Hajiya ta saka Hijabi ta fita dashi, Ruqayya kuwa Buredi ta dauka ta zauna taci abunta tana dangwalar romo, ta huta da tunanin me zataci da rana kafin a dora girkin dare dukda ba wani abu zatayi da daren bama doya kawai zata soyawa Oga yaci da Romon kan tunda an ajiye masa. Da sallama ta shiga falon Hajiyar, seda tayi qoqari ta daidaita fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna akan kujera Khalifa dake aiki a Laptop dinsa ya gaidata ta amsa tana tambayarsa Hajiya yace tana kitchen sega Hajiyar ta fito Umaiman ta zame qasa ta shiga gaidata ba tareda ta bari sun hada ido da Hajiyar ba. "Sannu Umaimah" Hajiya ta fada tana zama kafin taci gaba da cewa "Dazu yake gayamun bakya jin dadi ai ban dauka kumburin yakai haka ba kuma kike zaune ba zakuje Asibiti ba haka ai be kamata ba gaskiya idan ya dawo kuje kiga likita asan abinda yake damunki". "Munafuka se kace ta damu dani" Umaiman ta fada a zuciyarta a fili kuwa ta qara rausayar da kai tace "Ai jiya naje Hajiya sun dubani sunce babu komai kawai na ringa motsa jiki sosai" seta tura mata Flask din Naman tana cewa "Gashi Hajiya sha'awar Naman kai nayi shine na dafa daku". Hajiya taja flask ta bude qamshi ya cika falon tace "Madallah mun gode Allah yayi Albarka, aida baki wahalar da kanki ba kinyo waya ko Khalifa se yazo ya karba tunda Habiba basa nan sun fita da yaran wai zata kaisu Shoprite" "Ba komai ai na motsa qafata nima" Umaimah ta fada tana dan murmushi. Hira suka shigayi jefi jefi, Hajiya naso ta kawo mata zancen auran Khalil tana tsoron abinda hakan ze iya janyowa dan haka ta kama tsufanta tayi shiru ita kuwa Umaimah jira kawai takeyi Hajiya taci naman ta kama gabanta dan ba dadin hirar takeji ba, a zuciyarta ko banda antaya mata zagi babu abinda takeyi. Me aikin Hajiya ce ta fito da Fulasan abinci data gama Hajiya tace "Kinga zubomun farar shinkafar naci da Romon nan, kaima Khalifa idan zakaci gashi nan" "Aa nikam Alhamdulillah" Khalifan da be saka musu baki ba tun dazu ya fada, Umaimah ta galla masa harara a fakaice ita dai Hajiya aka kawo mata shinkafarta ta zuba abunta ta fara ci tana cewa "Ka huta ai, na ajiyewa su Auta sauran idan sun dawo suci". Baya bar gurin Hajiya ha seda Jalilah ta shiga da sallama Sammani na biye da ita da uwayen ledoji niqi niqi kamar wadda ta siyo kasuwa gaba daya. Tana shigowa Umaimah ta miqe, kallon banza suka jefi junansu dashi ta wuce fuuu Jalilah taja tsaki tana qarasawa cikin falon Hajiya ta kalleta tace "Meye haka Jalilah ya zaki shigo ki harari yarinya har ki bita da tsaki? Wani ni se yaushe zaki dena wannan halin da kika samu duk kinbi kin kwarzabeta na tabbata yanzu ma shigowarki ta sakata fita ba wani abu ba". Ita dai bata ce komai ba ta samu guri ta zauna tana zare dankwalin kanta ta gaida Hajiyar ta amsa mata a cukule. Me aiki tacewa ta kawo mata abinci taja Flask din gaban Hajiya tana cewa "Naman kai kuka samu haka duk ya cika falon da qamshi" ta fada tana kaiwa bakinta, Khalifa ya dago yace "Mutuniyarki ce ta kawowa Hajiya" "Wa?" Ta tambaya tana tauna na bakinta se ya ce "Anty Umaimah mana" ai be qarasa fadar sunan ba Jalilah ta tofo naman daga bakinta kafin ta miqe da gudu ta shige kitchen. Gaban sink ta tsaya ta ringa kakarin amai seda ta janyoshi ta amayar da duk abinda yake cikinta kafin hankalinta ya kwanta ta dawo falon tana mayar da numfashi. Cikin fada Hajiya ta kalleta tace "Wane irin iskanci ne haka Jalilah zaki dawowa da mutane abincin baki kina kakari se kace wadda taci mushe a rashin sani?" "Toh ai wallahi Hajiya gara ace Mushen naci ban sani ba Allah baze kamani da laifi ba akan naci abinda ya fito daga hannunta. Yanzu Hajiya ana wannan gabar zata dafo nama ta kawo miki kici hankali kwance babu abinda ya dameki?" Harararta Hajiya tayi tace "To se akayi yaya idanta bani nama naci zata bani abin cutarwa ne ko yaya?" "Toh Allah ya rufa Asiri, koda yakr daman ai ta dade da gamawa daku ta daga ta baku kun cinye dake da Khalil din shiyasa bazaku taba ganin laifinta ba, to mudai munfi qarfinta in sha Allahu duk wani tsubbunta bazeyi tasiri akanmu ba kuma muna muku addu'a Allahya kwato ku" "Toh Amin dai amma Anty Hajiya da Yah Khalil ai sunyi nisa. Jiya fa ta rotsa masa mota a gidan nan ace yau ta zo salin alin ta kawowa Hajiya abu taci shiyasa da aka mun tayi nace na qoshi to waya aikeni? Daman an ce Asirin da aka ci a abinci yafi tasiri kuma yafi wahalar magani" Khalifa ya fada yana tattara kayansa se Hajiya tayi shiru ta kuma kasa ci gaba da cin naman data qara. Me aiki Jalilah ta kwalawa kira tace tazo ta dauke sauran ta zubar. "Saura kici nasan ku da shegen son zuciya zubarwa akace kiyi ki kai canbolar qofar gida ki zubar karnuka su samu" ta fada mata ta tattara harda na farantin Hajiya ta fita dashi Umaimah dake labe najin tahowarta tayi saurin barin gurin a ranta tana cewa "Daga baya kenan wadda nayi dan ita taci kuma baki isa kisa ta amayo shi ba kema ina tafe kanki senayi maganinki wlh. Basira me aiki kuwa tana fita Sammani ya tareta ganinta da kwano yana tambayarta ina zata, tana fada masa abinda zatayi ya karbe yana cewa "Amma baki da hankali naman zaki zubar a bola maganin bera aka saka a ciki kome?" "Nima ban sani ba, Anty ce tace a zubar" ta bashi amsa seya bude kwanon da aka kawo masa nasa da har yaci rabi ya juye a ciki yana cewa "Ke dallah rabu da wannan matar tafi kowa fitina a yaran gidan nan na rasa meyw hadata da Hajiya Umaimah da bata sonta shine zata saka a zubar da abincin data dafa saboda mugun to mu zamu ci abin mu mayar da kwanon kice kin zubar kawai" "Toh dan sammun wlh tunda aka kai yawuna ya tsinke" Basira ta fada seya dan yafita mata kadan a kwanon yana cewa "Kinga wannan sake rabashi biyu zanyi naci rabi da dare rabi seda safe zan dumama abuna, Allah yasa ma Alhaji yayi wo mana tsabar balangu na hafa yau na kashe dadi abuna. Daga yanzu duk randa aka ce ki zubar da abinci ki ringa kawo mun nan kinji ko" ya dauke kwanonsa ya shige dakinsa. A cikin gida kuwa Jalilah bayan ta zubo abinci ta zauna tana ci ta cewa Khalifa ya fito da kayayyakin da suke ledojin data zo dasu nan ya shiga zazzagewa a qasa kayane iya ganinka Atamfofi, Laces, Material sunfi Kala Hamsin ga Mayafai nan da gani sunfi Dozen biyu suma da sauran tarkacen mata na kwalliya. Da mamaki Hajiya ta kalleta tace "Ke kuma Kanti zaki bude ko yaya wannan uban kaya haka da kika rakito?" "Wane kanti Hajiya? Siyayyar Hussaini ce, wata qawata ce tayi sales shine naga an samu ragi sosai na kwaso su, dudduba ki gani manyan Atamfa Super kadai ya rage za'a qara ko guda biyar haka dan nan akwai su Holand da sauransu Chiganvy ce qarama a ciki Laces din kuwa sun isa guda Goma sha biyar ne ga Material biyar Voile biyar, nasa a kawo Lafaya Lace biyar ai sun isa ko?" Ta fada tana kallon Hajiya data saki baki kawai tana jin lissafi. "To duk na menene haka kafinna gama jin abinda ya rage a ciki din" Hajiya ta fada seta miqe ta tafi gurin Fridge tana cewa "Bakiji ba nace na Usainina ne kayan lefe na fara hadowa Khalil, ai yau bazan bar gidan nan ba se yazo munyi lissafi tas mun ga abinda ya rage a siya, se kuma inji batun inda ze ajiye Amaryar, daman ni Saman nan da babu kowa nayi mata tanadi ita wannan ta tattaro gaba daya ta dawo qasa daman nan aka san uwar gida ta bar Amarya a sama kusa dashi yanda zasu wataya da kyau babu me saka musu ido" "Sannu Jalilah da iya tarar Aradu da Ka" Hajiua ta fada tana kallonta. KHALIL Qarfe biyar ya tashi aiki, seda ya tsaya yayi mata tsarabar chocolate da Ice cream kafin ya kama hanyar gidan. Maman kadai ya tarar a gida wai Humairan ta tafi Islamiyya. "In banda shaqiyanci irin nata da tasan zakazo ai zeta haqura yau daya dai da Makarantar" Mama data kawo masa ruwa ta fada se yayi murmushi yace "Ba laifinta bane Mama, jiya nace mata zanzo banzo ba inaga shiyasa ta dauka yau dinma bada gaske nake ba, daman daga office nake na biyo na kawo mata wannan" ya ajiye mata ledar siyayyar da yiwo seta dauka tana cewa "To an gode Allah saka da Alkhairi a kuma ci gaba da haquri da mutuniyar kasan akwai quruciya akanta. Dazun Alhaji Abubakar yazo da safe ai to har ma na bashi number Babban Yayanmu zasuyi magana dashi can se abinda suka zartar Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi yasa yin na Allah ne". Kasa tantance yanayin da zuciyarsa take ciki yayi, farin ciki zeyi na kasancewar Manya sun shiga maganat auran sa ko kuwa Akasin haka? Ya Umaimah zata karbi Al'amarin abinda yake ta tuani a zuciyarsa kenan. Haka ya kama hanyar gida dukda Maman tace ya zauna ta aika a kira Humairan yace Aa ta barta kawai in ya samu dama da daddare ze dawo. Yana fitowa a qofar gidan suka ci karo ta taho da sauri kamar wadda aka biyo zata shiga gidan ganinsa yasa ta dakata se kuma tayi sauri ta rabe shi ta shige jin Noor daya biyota yana koran sunanta. Kallonsu Khalil yayi ganin Noor din shima yana neman shiga cikin gidan har yana riqo mata Hijabi Khalil din yayi saurin riqeshi yana cewa "Kai lafiyar ka qalau kuwa? Baka da hankali zaka kama mata hijab?" "Malam kai kuma wanene? Dallah sakeni kafin na nuna maka danyan kai a nan gurin" Noor din ya fada yana zare ido tareda qoqarin kwace hannunsa da Khalil ya riqe. Mamakin tsaurin idonsa yayi yaron da befi sa'an Khalifa ba shine yake gaya masa haka take ya sake riqe hannun dakyau ya murde har seda Noor din ya saki qara kafin ya sake shi ya nuna shi yana cewa "Idan ka kuskura koda wasa hannunka ya sake taba suturarta sena karya ka, wuce ka fita ka bawa mutane guri". "Wallahi se kayi dana sanin abinda kayi mun, kw kuma ko bajima ko ba dade sena dauki fansa akan abinda kikayi mun zaki san ni kika yaudara" Noor din ya fada cikin wani irin fushi kafin ya juya fuuu ya fita daga gidan Mama da Hayaniyarsu ta fito da ita ta bishi tana cewa "Babu abinda zata gani se Alkhairi Insha Allah mutumin banza kawai, kema shegen taurin kanki da nace ki fita a sabgarsa bakiji ba kenan". Kuka Humairan ta saka tana cewa "Ni Mama babu abinda na masa, haka kawai mun taho a hanya ya tareni wai dole se na tsaya munyi magana ni kuma nace bazan tsaya ba sedai ya zo gida idan maganar yake so muyi shinrme fa yake ta zagina ya biyo ni wai Macuciya mayaudariya zan auri wani bashi ba" ta qarasa tana sake rushewa da Kuka. Kallonta Khalil yakeyi wani mugun kishi na cinsa se kawai ya juya ya fice yana cewa Mama seda safe. Jiki a sanyaye taja Humairan suka shiga ciki ta ringa lallabata seda tayi shiru kafin tace ta kira Khalil ta bashi haquri. Ransa babu dadi ya shiga gida. Yanasaka qafarsa a falon kansa ya sara kamar jiya, Umaimah na zaune a falon suna kallo da su Mu'ayyad suka tafi da gudu suna masa Oyoyo ya daga su sama daddaya kafin ya kama hannunsu suka shiga ciki. Idonta akan Tv tayi masa sannu da zuwa ya amsa yana zama a kusa da ita Ruqayya ta kawo masa ruwa ya fara sha kenan Wayarsa dake hannun Mu'ayyad ta shiga qara, be kawo ita bace dan haka Mu'ayyad din na miqo masa ya rigada ya daga dan haka ya danna speaker kawai yaci gaba shan ruwan bayan yayi sallama. "Dan Allah kayi haquri Habibi, wallahi bani nace ya biyoni ba kawai ganina yayi a hanyar Islamiyya ya tsayar dani kuma ni bansan zakazo ba ma da na shiga gidan Anty Habi kawai saboda karka ganshi ranka ya baci" Humairan ta fada cikin muryar shagwaba. Kallon wayar yayi ya kalli Umaimah data zura masa ido kamar farin shigar maita ya rasa abinda zece se kawai ya dannan ya kashe wayar, Mu'ayyad da Bibi ya kalla yace "Kuje gurin Hajiya nima gani nan shigowa" suka kwasa da gudu suka fita seya juya yana kallonta zuciyarsa na wani irin tsalle yanda kasan wanda ya tsaya gaban Alqali yace "Umaimah wallahi..." "Ka riqe rantsuwarka munafiki karka kuskura ka gaya mun wata magana anan, abu daya nake so yanzu ka kira koma wace yar iska ce a gabana ka gaya mata daga yanzu koda wasa karta sake kuskuren kira layinka, idan kuwa ta sake ka gaya mata da bakinka seka lalata rayuwarta". Zare ido ya shiga yi yana kallonta amma ya kasa bude baki yayi magana, ta yaya ma ze iya haka ya kira Humaira ya gaya mata wadannan maganganu gaskiya abun da wahala. Yawu ya hadiye yana qoqarin kama hannunta ta fizge yace "Dan Allah base na kirata ba, zanyi blocking number kawai yanda bazata qara samu na ba" "Kayi abinda nace Khalil idan kana buqatar kwanciyar hankali idan ba haka wallahi" Umaiman ta fada cikin daga murya se ya janyo wayar ya shiga kiran layin Humairah saboda yanda tayi maganar ji yayi akmar saukar aradu akansa. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 65 A fusace ta fizge wayar daga hannunsa ganin ya tsaya yana mata magiyar banza da wofi, seda ta fara ringing taji an daga kafin ta saka wayar a speaker ta cilla masa tana cewa "Maza gashi nana ka gaya mata da bakinka idan ba haka ba wallahi ba zaka so abinda zanyi ba, ai ka sanni tsaf bana shakkar kowa idan nayi niyyar rashin mutunchi babu wanda ya isa ya dakatar dani" "Haba Umaimah haba Umaimah yanzu ina hadaki da Allah amma kamar ba musulma ba aba zaki haqura ba? Dan Allah ki bari nayi miki alqawari ni da kaina zance gurinta amma kar kisakani yin abinda be kamata ba, ko wani naji yayiwa Humaira haka se inda qarfina ya qare guri kwatar mata haqqinta balle ace ni da kaina zan wulaqantata karki manta jinin Mansur ce" Khalil ya fada cikin rawar murya, wata gundumemiyar Ashar ta mulmulo ta watsa masa tana jifansa da wani matsiyacin kallo tace "Ni kake gayawa haka Khalil? To karkayi abinda nace kaji har ka iya kallona kana gayamun dole ka kare darajar wata banza shashasha a waje amma ni kana wulaqanta tawa darajar ko? To karkayi, wlh se kayi nadamar qin yin abinda nace. Sena balbaltata na lalata darajar tata da kake iqirarin karewa" "Babu abinda ze sameta da yardar Allah sannan kibi duniya a sannu Umaimah in har kina so ki mutu ki taradda ubangiji cikin salama to kiyi gaggawar tuba ki koma ga Allah in ba haka ba wlh ina tausayawa qarshen ki, sannan aure dai babu fashi da yardar Allah gara ma ki saka a ranki dan dazun ma munyi magana da Hajiya Aisha kuma a cikin satin nan masu zuwa nema zasuje can Jalingo" sukaji Muryar Mama daga cikin wayar, a firgice ya kai hannu ze dauki wayar dan shaf ya manta da cewar tayi kira suke ta wannan taqaddamar amma ta rigashi dauka ta miqe da sauri tana ja da baya tace "Idan kutumar ubanki ne yake rabon Aljannar karya bani ko kuma idan nazo shiga ku hanani tsohuwar banza kawai" "Ke Umaimah baki da hankali" Khalil daya yunquro ya figze wayar ya fada haryana tureta ta fada kan kujera se ta taso yanda kasan babu wani nauyi a jikinta, Ashar ta shiga dura masa ta uwa ta uba tana jifansa da duk kalaman da sukazo bakinta. Waiwayawa yayi ya kalli falon seya sauke ajiyar zuciya ganin Ruqayya da da take jera abinci a Dining bata gurin, yaran daman ya kada su da yanzu a gabansu zatayi masa tijarar kenan. "Wallahi Tallahi Khalil se nayi Ajalinka in har kace ba zaka janye qudurinka ba, sannan kuma na kashe duk yar abu ta kazan da tace zata shigo gidan nan, ni zaka munafunta ka mayar sakarya to wallahi dakai da duk wanda suke daure maka gindin yin abinda kake shiri daidai nake daku se kun gane kurenku". Kururuwa take tana surutai shidai tuni ya haye sama ya kullo qofar nan bakin qofar ya durqusa ya dafe kansa dake neman rabewa biyu saboda tashin hankalin daya riske shi. Yana jiyo yanda yake ihu daga qasan tana zaginsa shi da iyayensa kafin daga bisani ta fashe da kuka se kuma qarar fashe fashen abubuwa daya fara jiyowa da alama kayan falon take farfasawa seya miqe dakyar ya shige daki, bandaki ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi yafi minto talatin a tsaye har aka kira sallar Magriba kafin ya dauraye jikinsa ya fito zuciyarsa tana bugawa da qarfi. Jallabiyya ya jura a jikinsa ya dauki wayarsa da muqullin mota, cikin takatsantsan ya bar gidan bayan daya tabbatar da bata falon. A bakin qofar sata raba bangarensu dana Hajiya ya tsaya saboda jiyo hargaginta da yayi tana cewa "Haka kikace? Toh na rantse da girman Allah sedai kowa ya rasa, se nayi sana din Khalil dani da ku sedai kowa ya rasa" kafin ya gama tantance abunda take nufi aka bude qofar Umaiman ta fito buzu buzu yanda kasan farin shigan hauka gashin kanta a tsaitsaye fuskar nan tamkar Hadari banda kumburi da idonta yayi kamar an doketa a gurin. Wani kallo ta watsa masa da se da yaji hantar cikinsa ta kada taja tsaki ta wuce cikin gida ta barshi a tsayr daidai nan Hajiya ta fito itama tana kiran sunan Umaiman Jalilah na biye da ita a baya tana cewa Haba Hajiya yanzu har zaki bita saboda son ki qarasa zubar mana da mutunchi a idonta, saboda ita ba mutuniyar kirki bace vata dubi ko darajat shekarunki ba idan ma bata kalli matsayinki a gurinta ba ta iya takowa har gabanki ta zageki to idan duk kun makance ta gama da ke da Khalil din wallahi mu ba zamu zuba ido qata yar iska ta taka uwarmu ba, kuma idan ta cika mara kunya ta dawo ta sake miki ko kallon Banza na rantse sa Allah sena karyata idan yaso a kaini inda bazan fito ba". 'Ki rufe mun baki Jalilah kima wuce ki dau gyalen ki kibar gidan nan tunkafin na saba miki, haka kawai muna zaune lafiya zaki janyo mana jidali ina ruwanki keta zaga ko kuwa? In ma haka ne ai abin zagin aka mata gara ita an ga kalar nata kishinke wayasan abinda zakiyi idan naki Mijin yace ze qara aure?" Hajiyar fada a fusace tana kallon Jalilah se tayi saurin tare Hajiyar da cewa "Allah ya tsareni ya tsari zuri'ata da hauka irin na Umaimah dan wannanba kishi bane zallar jahilci hauka da son rai take gwadawa. Ita har tana da bakin crwa ba zata zauna da kishiya ba bayan data tashi gidan ubanta ma ina mata biyu ta tarar? Da haka tata uwar take ai da bata zauna a gidan ba harta haifeta shine mu zata zo nan ta daga mana hankali to karta fasa, aurene kamar anyian gama da izinin Allah sedai baqin ciki ya kasheta Khalil kuwa nan gani nan bari wlh tana kallo ze dauko santaleliyar Matarsa su more soyayya ita yana can Kishi ya haukatata an kaita Dawanau" "Idan baki bar gidan nan ba se na bata miki Jalilah" Hajiyan ta sake fada, se Jalilah ta koma ciki tana qunquni, jakarta da gyalenta ta dauko ta fito tana Kallon Khalil dake nan kamar gunki tace "Har daki ta tarar da uwarka ta zaga tace kuma idanka haifu kayi mata kishiya ta gani, to ina jira na gani nima ka haifu cikin Bayero ko kuwa a Asibiti aka qarawa Hajiya kai bayan ta haifeni" dukan da Hajiya ta kai mata yasa ta matsa da sauri ta fice daga gidan Hajiya ta kalli Khalil tace "Babana ya isa haka tun ba'aje ko ina ba kaga abinda ka kira mana to ka janye maganar nan kawai ka haqura kayita addu'a Allah ya daidai ta maka zamanka da matarka kawai dan ni bazan iya tashin hankali ba" ta juya ta koma cikin gida. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daga qafarsa da kyar ya fice daga gidan, seda yayi sallar isha kafin ya dawo, a compound din tsakiyar ya zauna ganin Khalifa a gurin shima is muzurai yakeyi Khalil din na zama yace "Gaskiya Yaya ya kamata kayiwa gidanka garambawul, ace har rashin mutunchin Anty Umaimah ya kai taje har gaban Hajiya ta kirata da munafuka? Wallahi tun wuri kayiwa tufkar hanci dan idan ba haka na gaba bamu san abinda zatayi ba kuma muma ba zamu zauna mu zuba ido tanayiwa mahaifiyar mu duk cin kashin dataga dama ba" "Munafuka?" Ya maimaita kalmar cikin mamaki, Umaimah ta kira Hajiya da Munafukan akan me? "Kuma itama Hajiya da laifinta fa Yaya, saboda Anty Jalilah ta mareta bakaga yanda Hajiyar ta taso mata ba kamar zata rama mata marin kuma wai ta shiga lallashinta tana bata haquri ai wlh naji dadi dan antyn ta gaggaya mata magana ta kuma jaddada mata aurenka babu fashi sedai ta mutu da yake mahaukaciyace se cewa tayi se tayi Ajalinka ni kuwa nayi recording wlh kuma ko kwarzane ya sameka se mun hadu da ita a Kotu akanta zan fara practicing profession dina" Khalifa yaci gaba da magana Khalil dai kallonsa kawai yakeyi shi maganar zata kashe ma bata bashi mamaki ba dan ba yau ya faraji ba tun kafin ya aureta take jaddada masa wannan kuma ta gwada ya gani Munafuka data kira Hajiya dashi ne ya daure masa kai sosai ya bashi mamaki dan be dauka rashin darajarta harya kai haka ba, ya zata dai shi da yake marainin wayonta take zaginsa sanda taso abun akansa ya tsaya ashe ya tsallake ya isa har kan uwar data haifeshi. Can qasan ransa sosai yake jin fushi da bacin ran abinda tayin yana kuma ayyana abubuwan da zeyi mata na daukar fansa amma kuma cikin zuciyarsa ko kusa ya kasa hasaso laifin da tayi balle ya samu kwarin guiwar hukuntata, dafe kansa yayi yana karanta hasbunallahu wani'imal wakeel a fili seda ya samu yar nutsuwa daga abinda yakeji kafin ya miqe a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ya wuce cikin gidan Khalifa ya bishi da kallo. UMAIMAH Dan kanta ta gaji da zage zagen ganin ya haye sama ya barta nan se kuma ta juya kan kayan dake cikin falon ta shiga jifa dasu tana kuka kamar wadda kanta ya tabu, kan kujera ta zube taci gaba da kukan, kamar wadda aka tsikara ta miqe tunawa da maganar Mama Hauwa da tace sunyi magana da Hajiya dazu kuma ta gaya mata a satin nan za'ajewa Khalil neman aure wato ma Hajiya ce ta shirya komai, qila ma ita ta turashi yaga Humairan ita take so ta hada auran me yasa tun farko batayi tunanin bama. Fita tayi ta wuce bangaren Hajiyar, tun daga kan barander ta jiyo muryar Jalilah na cewa "Nifa bazan tafi ba Hajiya se Hussaini yazo mun qarasa lissafin nan, da za'a bi tatawa ma a hada komai har lefen su tafi dashi kawai a huta da jeka ka dawo kinga gari da nisa ga yanayin hanya an huta tunda daman Mazan ne dai zasu koma su kai" "Toh uwar Azarbabi duk saurinki dai ai se kin jira sunje sun tambaya ance an basu kafin kice akai lefe ko?" Hajiya ta mayar mata cikin raha kafin Jalilan ta sake cewa wani abu Umaimah ta banka qofar falon ta shiga duk suka kalleta a tsorace saboda bazatan da tayi musu. "Lafiya Umaimah ko jikin ne?" Hajiya ta fada seta watsawa Hajiyar wani kallo tace "Dole ki tambayeni ko lafiya Qasurgumar munafuka. Ni daman na sani babu yanda za'ayi wata uwar Miji ta qaunaceka tsakani da Allah har ta fifitaka sama da yayan data haifa ashe jira kike na saki jiki dake kafin ki nuna mun Halinku na rashin Amana to wallahi bari kiji ni kadai kika haifawa Khalil ba kuma ki isa ki sake soko wata mace cikin rayuwarsa ba bayan ni duk wani munafunchi da kutunguilar ku ya qare akanku amma Khalil nan gani nan bari idan bakiyi wasa bama kedashi sedai gani daga nesa dan se nayi...." Marin da Jalilah ta dauketa dashi ne ya sakata yin shirun dole ba tareda ta shirya ha ta dafe idonta da taji kamar an watsa mata barkono a ciki. Nunata Jalilan tayi tana cewa "Ke qaramar mahaukaciya ki iya bakinki ki kuma san a inda kike, tsakaninki da Khalil canku gane dan da saninsa ya kwasowa kansa Annoba dan haka duk wani haukanki da dabbanci ya tsaya akansa na rantse da girman Allah koda wasa kika sake takowa nan kika ce zaki harari uwarmu balle har ta kai ga ki zageta sena zubar miki da haqora na karyaki na watsar da abin banza ko yanzu darajar abinda yake jikinki kikaci bazan dakeki na yi dakon rai na amma dana banbance miki tsakanin aya da tsakuwa yanzun mara kunyar qarya" "Ya isa haka Jalilah, wani irin sakarci ne wanann bakiga a halin da take ciki bane zaki mareta?" Hajiya ta daka mata tsawa se Jalilan ta kalli Hajiya fuska dauke da mamaki tace "Hajiya naga halin da take ciki Halin hauka ba ta samu zaucewar tunani dan shine ze saka ta aikata abinda tayi yanzu to ko Dawanau ce a kanta qarewarta ita ya shafa nidai na fada" seta juya kan Umaimah dake dafe da ido tace "Sannan kuma maganar hadin aure da kikeyi ta isa ne shiyasa ta hada, wace uwace ma har zata dauke ido danta ya zauna da shaidaniya irin tsahon shekarun nan bata saka ya kadaki inda ya kwasoki ba? Yazu kuwa aure take so tayi masa da yarinyar kirki data san mutunchin mutane ba irinki ba kuma ko zaki mutu se anyi auran nan in Allah ya yarda". Cikin qunar rai Umaiman ta kalleta tace "Haka kikace? To na rantse da Allah se nayi sanadin Khalil sedai kowa ya rasa nida ku duk se dai muyi Asara" tana fadar haka ta juya fuu Hajiya ta bita tana kiran Sunanta Jalilah ma bin bayansu tana cewa "Ai idan Khalil ya mutu Umaimah se kinfi kowa shiga uku wlh mu sedai muyi jimami na rashin dan uwa ke kuwa Allah dai ya taqaita amma inaga idan baki bishi ba se kin haukace". Sanda ta koma bangarenta zama tayi a qasa cikin kayan data farfasa ta sake fashewa da kukan dayafi ma dazu, Ruqayya ta tsaya tsuru daga gefe tsoron kulata takeyi karta huce akanta amma haka ta ja numfashi ta matsa kadan tana ce mata "Hajiya kiyi haquri ki dena kukan nan kodan halin da kike ciki, kishiya ai ba ciwon Ajali bace ba kuma kanki aka fara ba dan Allah ki tattara hankalinki guri daya ki nutsu, addu'a ya kamata ki tashi tsaye kiyi akan duk ma wadda zata shigo Allah ya tsare ki daga sharrinta ya hadaki da Alkhairinta". "Ruqayya idan kika sake yimun magana se naci abu ta kaza kazan ubanki" Umaiman ta fada tana kallonta da jajayen kumburarrun idanunta da suke tsiyayar sa hawaye kafin ta juya taci gaba da kukan kamar yarinya se kuma ta ta miqe ta shige dakinta, wayarta ta dauka ta shiga kiraj Safinah tana dagawa tace "Safina duk inda kike duk abinda kikeyi ki bari ki maido mun da kudina da kuka damfareni keda dan abu ta kaza kazan Malaminki, kuma daga yau ko hanya karki bari mu hadu idan ba haka ba sena huce haushin bata mun lokaci da kika kaini akayi kuka yaudareni na dauka aikinsa yayi ashe zagon qasa yayi mun ya daka rusa komai" ta qarasa tana rushewa da kuka. Safina dake zaune a falo tayi baqi qannen Mijinta ta miqe ta shige daki tana ce musu tana zuwa. Seda ta shiga bandaki ta kullo qofar dan kar wani ya shigo yaji abinda take fada kafin tace "Haba Umaimah kiyi shiru kiyimun bayani me ya faru kuma? Ina dazu da safe kike ce mun har aiki ya fara ci me kuma ya faru yanzu har ya kawo wannan maganar?" "Babu ruwanki sa abinda ya faru kwai kiyi abinda nace idan ba haka ba kin san halina wallahi se nazo na farke miki laya, yanda banyi nasara ba kema se Alqadarinki ya karye wlh" Umaiman ta sake fada a fusace se Safina tayi saurin mayar mata itama cikin fushi tace "Kinga bafa tsoronki nake ji ba da zaki ringa gaya mun magana ina wani lallashinki, aiki na rakaki akayi miki da yardar kuma ba daukarki nayi akai na ballantana kice ke uwar garaje da jaraba an ce miki kibi komai a sannu amma ba haka ba na tabbata yanzun ma wani haukan kika tafka ya warware komai zakizo kina dora laifi akaina. Daman ai na gaya miki ko kinyi Asiri dole ki hada da kissa idan kina so kiga daidai amma ke kamar wadda ake girki a zuciyarta dan qaramin abu kin dau zafi bazaki ringa tankwara zuciyarki kina dauke kai ba ai ita rayuwa bata yuwuwa haka idan kana so kaci riba ai seka yi haquri kayi juriya". Shiru Umaimah tayi tana rusa mata kuka, Safina ta sake jan tsaki dan harga Allah ita kanta Umaiman ta isheta inaga Khalil kuma ai wallahi yana bala'in qoqari, sake ce mata tayi "Kinga kuka baya maganin komai gara ki bude baki ki gayamun abinda ya faru najin idan da akwai ta inda zan taimaka miki in kuma Malam zan kira na gaya masa toh se musan abinyi" "Ni karki sake sakomun wani malam a magana kuma ba haqura nayi ba se kin biyani kudina, bayan yace mun maganar aure zata watse kuma se yanda nayi dasu gashi nan ba inda aka je ni banga komai ba. A gaban Hajiyar yar uwarta take jaddadamun aure babu fashi kuma bata hana ba bayan har naman kan na dafa kuma taci sannan shi kansa na bashi umarnin ya kira yarinyar ya gaya mata ta fita a sabgarsa yaqi qarshe ma se munafukar uwar ruqon nata ce ta daga wayar har takr yaba mun magana tana gayamin wani satin za'aje tambaya, wallahi Safina ji nake kamar na dau wuqa na cakawa kaina kawai na mutu na huta da baqin ciki" ta sake rushewa da Kuka wiwi. "Yanzu akan dan wannan abun kike kuka kamar wadda akazo daukar ranta wallahi Umaimah Jidalinki na banza da wofi ne. In banda ke banma san me zan kiraki ba shi aikin ce miki akayi ana yi take yanke yake ci daman se kace wani tsafi? To ai ko tsafi Malama se Aljanun sun samu zama a Jikin mutum kafin su fara aikinsu kuma wannan dinma ai kya jira duk abinda kikayi yabi jikinsu kafin kice zaki fara gwada iko nidai nayi mamaki da a dare daya kika ce aiki har yaci koda yake hayaqin da ya baki na Jinnil Ashiq ne da kwarjini to su babu Mamaki idan kince sun miki aiki amma rufin baki dai se a hankali ai bawai nan take ne zasu kasa musa miki ba. Kawai yanzu ki share hawaye ki dena wannan kukan idan kin samu dama gobe ki fito mu koma gun Malam in kuma ba zaki iya ba zan kirashi ko aikene se yayiwo miki a samu a daidaita a shashantar da maganar auran". Haka ta ringa lallabata tana sake tabbatar mata da ta kwantar da hankalinta tasan aikin Malam zeci kawai haquri zata koya da danne zuciya nadan lokaci kafin Ludayinta ya hau kan Dawo seda taga ta dan nutsu kafin sukayi sallama akan gobe ita Safinan zataje gurin Malam taji koda abinda ze qara bata tunda ita Umaimah ta kafe bazata koma ba kuma se an biyata kudinta. A nan inda suka gama waya da Safina baccin wahala yayi gaba da ita, bata farka ba se uku da motsi na dare shima wata Azababbiyar Yunwa ce ta tada ta se a sannan tayi sallar Magriba da Ishar da batayi ba. KHALIL Tunda ya samu ya haye Sama ba tareda sun sake haduwa da Umaimah ba be sakko ba, yana so yaje gurin Hajiya amma besan me zece mata ba. Matarsa ta zageta ta kirata munafuka amma ya kasa yin komai to da wanne ido ze kalli Hajiyar? Haka ya kwana saqa da warwara akan abinda ya kamata yayi, wani sashe na zuciyarsa yana ganin beyiwa Humaira Adalci ba da yake shirin janyota cikin wannan rayuwar da yake a ciki inda wani bangare yake tabbatar masa da ita ce warakarsa, za kuma ta fiddashi daga duk wani qunci da damuwa da yake ciki ta maye masa da tarin farinciki da ya dade yana mafarkin samu idan Umaimah ta barsu kenan. Tunanin raba musu gida ya fado masa yana ganin hakan shine ze kawo masa sauqin da kuma kwanciyar hankali idan ya zamana kowacce tana muhallinta na daban ba kamar yanda Su Jalilah suke fadin ya ajiye Humaira a nan separate part dinsa na Sama da Umaimah ta hanashi amfani dashi hasashenta ya tabbata kenan daman da tace dan wata ya gina gaskiya baya zaton haka zata yuwuwu gara ya gyara tsohon gidansu da suka taso ya ajiye Humairan a can yafi musu kwanciyar hankali daga shi har ita. Yana gama tunanin ya miqe ya dakko Laptop dinsa, seda ya duba lokaci sha biyu ta gota kafin ya bude ya shiga binciko proposal design din dayayi ze maida ginin dan da yayi niyyar ya gyara shi ne ya siyar amma yanzu zeyi masa amfani. Zanen ya duba ya dakko takadda da biro ya shiga lissafin abinda yake ganin ze kashe da tsahon lokacin da ze dauka kafin ya kammalu, a nasa lissafin idan yayi sauri yana ganin ze gama a wata uku in kuma yaja lokaci wata biyar zuwa shida, akan wata shidan ya bari ze gayawa su Baba Abu idan sunje neman auran su saka rana wata shidan zuwa sannan yasan hatta ita Umaiman tayi duk abinda zatayi ta saduda shikenan. Washe gari bakwai bata qarasa ba ya bar gidan, a waya ya kira Hajiya yayi mata qaryar ya tafi Rano, yanda batayi masa maganar jiya ha shima beyi ba illah ce masa da tayi Jalilah ta kawo kaya jiya idan ya dawo ya shiga ya gani yace mata toh gaba daya beji dadi ba saboda yanda yaji muryarta yasan abinda Umaiman tayi mata ya doketa sosai kawai dai ta shanye ne bata nuna ba. Seda ya kira Habiba ta tabbatar masa Hajiyar na lafiya kawai dai magana ce bata cikayi ba tun jiyan se ta zauna tayi shiru yace mata ta zauna da ita karta ringa bari tana tunanin saboda jininta idan ya dawo ze shigo, haka ya tafi office ya zauna aikin ma ya gagara yi kansa ciwo ya ke masa, shafa ya manta ma jiyan beci abinci ba seda Anwar yazo yake ce masa ko karyawa beyi ba ya fito saboda ya ce masa yana office sannan suka fita tare sukaje cin abinci. Suna dabda komawa Kiran Baba Abu ya shiga wayarsa, seda gabansa ya fadi ya daga da sallama kamar yanda yayi tunani kuwa ko amsa masa beyi ba ya dira fada ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba fadi yake "Ibrahim wace irin shaidaniya kake zaune da ita a matsayin Matane yanzu ace rashin tarbiyyar yarinyar nan har ya kai ta kalli idon uwarka ta kirata munafuka saboda ta shahara a rashin mutunchi? Wallahi badan dattijantaka irin ta uban ta ba da nace ka sakar musu ita kowa ya huta amma iyayenta mutanen kirki ne, Jarabawa ce da kowanne bawa baya rabo da kalar tasa Allah ya basu wannan yarinya amma dukda haka ba zamu zuba mata ido ta tinga iskanci yanda taga dama a rasa me taka mata burki ba, ina dai akan kiahiya take wannan diban Albarkar ko to kuwa aure babu fashi, da na cewa Hajiyar se qarshen wata zamuje toh na fasa, yanzu zan kira Alhaji Garba da Sabi'u da Imrana tunda dasu zamuje na gaya musu duk su shirya Juma'ar nan mu tafi mu kwana a can Asabar mu juyo, seka shirya dan tare zamuje dakai gu ganka ko ka gaida surukan naka amma wannan mata taka dole ka tashi tsaye ka dauki mataki a kanta, idan ta kama kasa ayita sauke mata qur'ani in makarai ne a kanta masu son tada husuma duk ayi maganinta". Shidai har Baba Abu ya gama banbaminsa bece komai ba seda yayi shiru kafin yace masa toh, Allah ya kaimu Juma'ar kwanaki uku harda ranar masu zuwa kenan dan suna Talata. Yana gama wayar Anwar da yaji kusan rabin maganar ya kalleshi fuska a sake yace "Ango kace uwargida tayi bore ta sakw ballowa kanta ruwa to Allah ya fitar da ita" "Hmm" kawai Khalil yace masa ya wuce Office dinsa zuciyarsa duk babu dadi. Ana cikin wannan halin wane Jalingo zasu tafi kuma itama Jalilah tana da matsala wani lojacin akan me zataje ta gayawa Baba Abu yanzu daya gayawa Hajiya Mansura Matarsa ya tabbata yanzu dangi duk se sunji labari su qara sakata a gaba. Bayan sun fito sallar Azahar ya duba wayarsa yaga Humaira ta tura masa da saqon ban haquri, murmushi yayi ya kirata tana dagawa ta fasa masa kuka, Khalil ya dafe kansa da daman a cike yake da damuwar Umaimah yace "Me kuma ya faru?" "Ba kaine kake fushi dani ba" "Ni ba fushi nakeyi dake ba tun jiyan nima bana jin dadi shiyasa ban kiraki ba ki dena kukan". Seda yayi aikin rarrashi kafin ta haqura, Humaira akwai shagwaba ya fahimci ma da gayya take masa dan ya rarrasheta shi kuma baya gajiya da lallashin nata dan abin nata burgeshi yakeyi. "Kina ina naji surutan yara?" Ya tambayeta jin yara na hayaniya a kusa da ita se tace masa "Ina gidan Anty Unaiza, jiya da daddare da taje Mama tace na bita wai na koma gidan da zama yanzu" ta bashi amsa, se ya bude ido yace "Toh, me yasa?" "Nima ban sani ba amma inaga saboda Noor ne dan jiya bayan ka tafi yazo yanata Hayaniya har seda ma sukayi fada da Yaya Habibu, ni tausayi ma ya bani wlh kamar nayi kuka kuma be samu Army dinma bafa wannan karon shiyasa abun yayi masa yawa". Gimtse fuska Khalil yayi kamar yana gabanta yace "Oh to tunda ya baki tausayi ai da se kicewa maman ta aura miki shi kawai a haka ko bashida abinyi zaki zauna dashi ko" "Auw" Humaira ta fada tana riqe baki, Unaizatu data tarar da katobarar da takeyi ta dana mata duka a cinya ta shiga sosawa tana cewa "Nifa ba haka nake nufi ba, bayan kazo kayi mun Asiri ka rabani da saurayina tun ina yar yarinya" tayi maganar tana zumbura baki se Khalil ya saki murmushin da be shirya ba yace "Oh Asiri ma nayi miki lallai yarinyar nan wai yaushe bakinki ya bude kika fara magana haka?" "Oho nima ban sani ba" ta bashi amsa cikin qunquni se ya saki qaramar dariya yace "Idan na tashi zanzo na ganki, har yanzu a Gandu Unaizatu take ko sun chanza gida?" "Eh sun chanza amma duk a unguwar ne amma ta layin bayan wancan gidan suka koma" "Asalin gidan iyayen Mijinta kenan ko? Idan zan tuna sanda ta haifi Danta na farko a can ta zauna Mama tana aiken mu mu kai mata saqo" "Eh nan" ta fada cikin tabbatarwa se yace mata "Toh shikenan, zan zo idan nazo layin sena kiraki dan qila an chanzawa gidan fasali bazan gane ba" "Toh shikenab se kazo" "Alright babe" ya fada tareda yin shiru amma be kashe wayar ba, kamar daga sama yaji tace "I love you take care" ko numfashi be aje ba ta kashe wayar shi kadai ya fashe da dariya a ransa ko yanda kasan ta wanke shi da Hypo, wayaga yaushe rabon duniya da Ayyaraye ace masa I Love you tun farkon tarewarsu a sabon gida. Har Allah Allah ya ringayi lokacin tashi yayi ya tafi gurinya, yanayin sallar La'asar kuwa ya fita, seda ya tsaya yayiwa yaran Unaizatu tsarabar chocolate itama ya siya mata kalar wanda ya saba kai mata kafin ya kama hanya. Har cikin falo tayi masa iso wanda aka gyara tsaf ko ina se qamshi yakeyi, yaranta biyar duk suka shiga suka gaidashi ya basu tsarabar daya tafi da ita kafin Unaizan ta shiga itama. Har qasa ta tsugunna ta gaidashi ya amsa mata cikin kulawa a ransa yana mamakin yanda ta zama wata big madam kamar ba Unaiza Lilo sunan da suke tsokanarta dashi lokacin suna yara, ita take bin Mansur dan haka basa shiri a sanann Khalil ne abokinta komai da Yah Khalil ake qullashi danshi Mansur ya fiya tsokana shine ma ya saka mata sunan Lilon kuma har a makaranta haka yake kiranta kuma ya bita tayita kuka harta haqura take amsawa. "Ikon Allah Unaiza, ashe zakiyi qiba" Khalil daya kasa shiru ya fada se ta fashe da dariya ita kanta abin mamaki yake bata tace "Wlh Yah Khalil gashi kuwa kuma qibar ta lokaci daya abin mamaki" "Shine nima na gani ai, yaushe na ganki na qarshe ai baki kai haka ba yanzu nasan ko Sumayya ai seta buda miki" "Kai rabani da kamo Sumayya qiba Yah Khalil wannan Mata kamar Bijimar Sa kuma a qaryarta Najib din ne yake son qibar shi yasa taqi ta rage" Unaizan ta fada tana riqe baki, hirar baya suka dakko ana tuna yanda kowa yake da yanda ya zama yanzu Humaira ta shigo da Try data doro kayan ciye ciye Khalil ya kalleta yace "Kice wannan ma wata rana zata zama giwa kenan" seta waiwaya ta kalleta tana yar dariya tace "Wannan kuma kiwonka ne ze tabbatar" daga haka ta miqe ta basu guri. Beyi niyyar jimawa ba amma hirarta me cike da quruciya da labarai da basa qarewa yasa ya shantake se ji sukayi ana magriba. Seda yayi salla a masallacin layin kafin ya koma yayi mata sallama, sun fito ta rakoshi yake sanar mata da zancen zuwansu Jalingo ranar Juma'a se tayi shiru tana juya zoben hannunta. "Ya naga kinyi shiru, ko bakiyi farin ciki da magana bane?" Ya fada yana kallonta, ba tareda ta dago kanta ba tace "Amma Yaya cewa kayi fa se na fara makaranta" "Maganar makaranta Humaira ni nayi miki Alqawari indai karatune zakiyi harse kince kin gaji, nida zaki zama business partner ta, idan na ginawa mutane gida ke kuma kiyi musu furnishing da kayayyaki na yan gayu ko kin fasa bude Interior design company din?" Ya fada cikin lallashi, nan sabuwar hira ta balle, burinta kenan ita a ringa bata kwangilar gidaje tana saka kaya a ciki ta zabi fenti da duk kalar abinda ze dace da gida. "Karki damu ni zan fara employing naki da na gama miki gidanki zan baki dama ki shiryashi mu gani, kinga idan yayi kyau daga nan zan fara recommending ma abokan kasuwanci na ke amma tare zamu ringa raba ribar fa kin yarda" Khalil ya fada ganin Isha na neman yi suna tsaye seta daga masa kai alamar ta yarda tana murmushi daga nan ya shiga mota yana ce mata "Karki manta ki gayawa Mama dukda nasan zasuyi magana da Hajiya amma dai ki gaya mata dan ta san da yardarki za'aje" daga haka yaja mota tana daga masa hannu ya bar gurin. Ciki ta koma tana shiga ta gayaqa Unaizatu yanda sukayi dashi. "Wallahi Humaira kinyi dacen Miji matsala daya ce matarsa amma itan ma Allah ya fita in sha Allahu zakuyi auranku ku zauna lafiya" Unaiza ta fada, Humaira ta rafka tagumi tace "Nima wlh Anty ita nake tsoro, kinsan fa ranar nan tazo gida, nan ta bata labarin zuwan Umaimah Unaiza ta bude baki tana jinta harta gama tana cewa "Amma fa karki gayawa kowa dan Mama tace karna fada koshi Yayan be sani ba. Kuma kinga Yaya Mansur ma baya so, kwanaki kirana yayi yana tamun fada akan nacewa Mama banason Yah Khalil ita kuma ta kirashi tayi masa fada shine fa har yanzu yake fushi dani shima Yah Khalil din yace koya kirashi baya dauka to kinga ai shi yasan halin matar abokinsa toh ita Mama taqi ganewa" "Toh ke kina son Khalil din?" Unaiza ta tambayeta tana kallonta, seta rufe fuska da hannunta tace "Kai Anty baki san Yah Khalil bane indai kuka fara magana dole ka fara sonsa baka sani ba" 'Toh ai shikenan se kiyita addu'a in sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi. Yanzu dai ki ajiye shirme ki maida hankali dan kinsan abinda ya kawoki gidan nan, gobe zaki fara zuwa gidan Maman Ayman inaga sau hudu tace a sati zaku ringa Classes din, nasan kin iya girki se ki qara maida hankali ki gane dabarunda zata qara miki sannan akwai saqon da za'a kawo gobe suma ki fara amfanj dasu, bari ma kiga na tashi na hada Miki TULA-TULA ki fara sha wannan qirjin dake nan kamar na yara a samu su taso dan matarsa idan kikaji ana Figure 8 toh itace gara kema kidan qara auki yawwa". Dariya ta shiga kyalkyalawa jij wani suna wai TULA-TULA, Unaiza ta dawo Salalan ta ajiye mata da madara ta dauka tana cewa "Wai Anty shine TULA TULAN? ina jira naga wata balloon ni ashe ma kunu ne" "Ba zaki gane ba yarinya kedai dauki kisha a jikinki zakiga tula tulan da ake magana nan duk da kika ganmu shi yake taimakar mu gamun mun haihu nawa amma Qirji na nan a cike" se ta rufe fuska kuma wai kunya Unaizatu tace "Kyaji da munafuncinki Malam ni maza ki shanye ki bani kofina. (Domin mallakar naki ki tuntubi Maman Ilham mai Tula Tula akan 08135613021 tana Kaduna tana aikawa da kaya ko ina a fadin Nigeria). *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 66 UMAIMAH Kasa zama tayi ta jira Safina ta gwammace ita ta tafi gidanta, a Get suka hadu da Jalilah zata shigo ita kuma zata fita suka jefi juna da kallon Banza motar Jalilah na shiga ta Anty Amina ta biyo baya dole Umaimah ta jira suka shige dan a jere suke se hararar su take tamkar idanunta zasu fado. Jalilah ce ta kwalawa Sammani kira ya bar bakin Get da gudu ya shiga cuki, ta bude masa boot ya dakko wani kwali da Umaimah ke da tabbacin na akwati ne gasu nan guda biyu ya dauki daya ya shige bangaren Hajiya ita kuma Jalilan ta fara fito da kayayyaki daga back sit dinta Haka ma Anty Amina cikinsu babu wanda ya sakw kallon koda inda motarta take. Kwafa taja kafin ta taka motar da qarfi ta bar gidan, a falon Safina ta baje bayan ta soya musu kwai da dankali sunci Wanda turawa kawai Umaimah take amma komai daci yake mata a baki. "Qawata ki kwantar da hankalinki na kira Malam tun jiya kuma yace kwana zeyi yana aikinki, yace in tambayeki hayaqin daya baki yace kiyi a tsakar gida kinyi kuwa?" Safina ta fada se Umaiman ta tabe baki tace "Ni hayaqi daya na gani wanda yace na ringayi a dakinsa kuma nayi" "Sun dauke abinsu kenan" Safinan ta fada kafin taci gaba da cewa "Haka fa suke wlh se Malam ya baka abu me ci subi dare su dauke abinsu, bari toh na gaya masa ya sake hado miki dashi se kiyi Azama da an kawo ki turara dan alamu sun nuna Faka faka ne" haka tayi ta subadadi ita dai Umaimah jinta takeyi har aka kira Safinan a waya ta fita se gata tareda wnai saurayi se bayan ya zauna Umaimah ta ganeshi Almajirin Malam din da sukaje gurinsa ne. Wasu sababbin tarkace ya kawo mata harda layu ya bata wasu qananu da yace a abinci zata sakawa Khalil din ta tabbatar da ya hafiye se wata lafceciya da zata tsaga pillow ta saka a ciki, se Rubutu irin na farko yace ta qara ruwa ta bashi dana Abincin shima harda qarin na Nama kamar yaji yake amma shi da gasashshen nama za'aci yaron ya miqa mata yana cewa "Dandanonsa kamar yaji yake amma fa ki kula koke karki dandana kuma kar ki bashi yaci sama da sau dan qarfi ne dashi wlh, yace wancan turarenya qare amma idan an hada wani za'a kawo miki kuma wai ki ringa haquri kina danne zuciyarki dan kinada saurin fushi da hasala ga qawa zuci shi yasa aikinki baze ci da sauri ba". Daze tafi wasu uban nin kudin Safina ta debo ta bashiya kaiwa Malam sannan ta bashi na mota ya wuce yana musu godiya. "Nifa bazanyi amfani dasu ba ingaya miki wanda ya banin ma me suka mun balle na qara wasu, tashi zanyi ma na tafi yanzu naje naci kutumar ubansu gaba daya dan nasam sun hadu a gidanda zan fito yar iskar Jalilan nan da Amina sunzo nasan Jamilan ma tana tafe duk zan hada naci uwarsu la'ada waje" Umaimah ta fada Safina dake hade mata kan tarkacenta tace "Umaimah ikon Allah, na roqeki sau daya a rayuwa ki gwada juriya ki dauke kai ki bawa aikin nan sati daya kedai ki tabbata kinyi komai yanda Malam yace se ki koma gefe ki zubawa sarautar Allah ido wlh na tabbata se kin sha Mamaki" "Uhm, kanki ake ji" Umaiman ta fada tana tura qeya Safina tayi dariya tace "Ohni Allah Kiga yanda kishi ya fitar dake daga hayyacinki a dan lokaci Allah dai ya kiyaye bacin rana amma in aka samu kuskure auran nan ya yuwu kice zaucewa kawai zakiyi dukda ma bame yuwu ba bane in sha Allahu" Safina ta sake fada, Umaimah tayi mata banza tana danna waya Safina ta sake cewa "Nifa idan nice Mijina yake sona kamar ke din nan wlh ko zeyi auran ba wani damuwa zanyi ba, kwantar da hankali zanyi tazo na mayar da shegiya yar aiki se yanda nayi da ita kuma Miji nawane, koni da kikaga ina tsoron amun ai saboda a dofane nake gurin Mijin Uwarsa da danginsa kaf ba sona suke ba da banida Malam Sha yanzu ai bansan ya rayuwata zata kasance ba wlh". Ita dai Umaimah bata kulata ba haka ta gaji tayi shiru, bayan Azahar tace zata tafi, Safina ta rakata har gurin Mota tana sake jaddada mata da dan Allah ta dauke kai kome za'ayi karta kula su. "Ke ni ban tambayeki ba ya kukayi zancen mota ne?" Safina ta fada se Umaimah ta juya tace "Bece komai ba, to ya mayi maganar na rotsa masa kai shima ai yasanhaukata shi yasa baya tanka mun in ina sama" "Toh Allah ya sakko dake amma fa kinyi ganganci kuma ko dan gaba ki ringa sanin abinda zakiyi. Banda shirmen ki da haquri kikayi idan ya tashi ma kice ita kike so a matsayin kayan fadar kishiya tunda zaman lafiya yake nema mu samu ta yawo muyita zaga gari muna hura hanci amma kika mata rotse ke shi be mora ba ke baki mora ba wannan ai mugunta ce" Motarta taja ta fice Safina ta koma ciki tana mita. Sanda ta isa gida cike ta tarar da Compound din da motoci kamar ana wani biki a gidan dan motarta ma a waje ta ajiyeta, har ta niyyaci ta shiga bangaren Hajiyar tayi tijara tace se fita da motocin zata aje tata kuma ta fasa, bata san su waye a ciki ba karta taroqa kanta abinda ba zata iya ba. Ruqayya ta gyara falon tas ta kwashe duk abinda ta lalata jiya ta kai store, tana aje mayafinta taji sallamar Nuratu a bakin qofar tana kwankwasawa seta koma ta bude Nuratunta shigo tana cewa "Inata kiran sunanki kamar wadda ta toshe kunne bakiji ba". Zama Umaiman tayi tana cewa "Banji ba wlh, kamar tare muke nima shigowata kenan gyalena kawai na ajiye naji knocking" "Ai taren ma muke ina ta binki a baya tun daga babban Titi" "Au wai kece daman kinsan na kusa tsayawa naji waye yake bina haka kamar jela sedai na fasa mota kika canza kenan?" Umaimah ta sake fada, se Nuratu ta gyara zama tana cewa "Ba tawa bane, ta Yah Hajiyayye ce Baban Asad ya gwangwajeta da dalleliyar mota cikin kayan fadar kishiya". Wayar da Umaimah ke dannawa ce ta subuce daga hannunta ta fadi qasa kafin ta zubawa Nuratu ido yanda kasanbata fahimci yaren da tayi mata ba ita kuwa ko a jikinta taci gaba da cewe "Kinga danqareren gidan dayake gina musu? Ko ita bata sani ba se a satin nan Qanwarsa ta fesa mata gulmar bangaren Maman Asad hawa biyu ya mata yace ta sakata ta wala ita da yayanta Amaryar kuma yayi mata hawa daya sannan a bangaren kowacce yana da nasa part din kinga babu abinda ze hadasu se idan su suka so haduwar kuma ma Allah ya taimaketa yanda take babu ruwanta haka Allah ya dubi zuciyarta ya sakashi nemo yarinyar itama an shedeta bata da matsala sedai fatan su zauna lafiya idan an hadu". Har Nuratu ta gama surutu Umaimah ba zatace ta fahimci wani abu ba tun bayan zancen kayan fadar kishiya da taji, Bandaki ta wuce ta bar Nuratu na gaisawa da Ruqayya data kawowa Nuratun ruwa da snacks zuciyarta ta ringa bugawa yanda kasan ita aka ce an kaiwa kayan fadar kishiyar wato da gaske kenan yarinyar data gani gidan Maman Asad din budurwar Mijinta ce amma kuwa Hajiyayye ta cika Jakar mata mara zuciya (in ji Umaimah fa). doguwar rigar Atamfar jikinta ta cire ta watsa ruwa kafin ta dauro Towel ta fito, Nuratu ta kalleta ta zaro ido tace "Kai Umaimah kin ganki kuwa anya cikin nan be wuce lokacin sa ba kuwa yaushe suka ce miki EDD?" "Ai ke bazaki taba ganin abu kiyi shiru ba se kinyi magana tunda dai bake kike dubani ba se ki saka ido in lokacin haifarsa yayi ai ze fito" ta fada cike da fitsara tana kallon Nuratun se ta maida mata da cewa "Ke ai baki gama sanin ciwon kanki ba daman har yanzu shi yasa, ni ba zuwa nayi muyi rigima ba, zuwa nayi na gaya miki gaskiya a matsayina na yar uwarki tunda mun zura miki ido gaba daya munga ke baki san zuru ba. Naje gida yanzu duk na tarar dasu har Yah Naziyya tazo tun shekaran jiya tana Kano ke kadai ce babu kuma daman wannan bashi ne karo na farko da za'ayi wani taro a gida kike qin zuwa ba shiyasa yanzun ma sukace bazasu gaya miki ba kowa a cike yake dake. Yanzu Umaimah tsakaninki da Allah yaushe rabon da ki daga waya ki kira wata daga cikinmu da sunan ayi zumunchi ballantana ki taka kije gidajenmu? Ni daman na cire kaina a lissafi amma ko Maman Asad ban zata harda ita kika watsar ba duba da kunfi shiri da ita duk a cikinmu. Yanzu Naziyya da ba'a gari take ba waya yar mecece da bazaki daga ki kirata ba ashe har tayi rashin lafiya ta kwanta a Asibiti baki dubata ba kuma Mama ta gaya miki kika share. Su kansu can gidan ba zuwa kike ba se idan taki ce ta kaiki anya kuwa Umaimah rayuwa zata yuwu a haka? Ke idan kin nemi mutum to matsala ce amma in kina zaune lafiya babu ruwanki da kowa se yawon bin gidajen qawayen ba babu abinda kike amfana dasu duk qawayenki na kirki wanda kuka tashi tare kin watsar dasu saboda suna gaya miki gaskiya kuma suna hanaki abinda be kamata kin gwammace kiyita bin irinki babu meyiwa wani fadan be kyauta ba a cikinku. Yanzu wace qawa kika samu a unguwar su Anty Hafsa da kullum kina hanyar gidanta kuma saboda tsabar baki da mutunchi wani lokacin ma ta qofar godanta kike wucewa sedai Yayanta su ganki suce mata kin wuce se kace ba Yarki uwa daya uba daya ba anya Umaimah akwai hankali a lamuranki?" "Toh sannu uwata Malika, yanzu a taqaice kiyi saving duk wadannan surutan ki fadi abinda ya kawoki kawai. Da zakice bana neman ku ku me yasa da ban kiraku ba ko banje inda kuke ba ku nemeni ko dole se nice zan nemeku? Kuma su duk basu da bakin qorafi se ke uwar iya zaki kwaso qafafu na zata ma wani abun arziqin ne ya kawoki ashe can kin gama hado Bomb dinki shine zaki wani taho kega yar uwata kinzo kiyi mun fada to sannu kinyi abin kirki, amma in gaskiya za'a bi ai Babba shi ya kamata ya ringa duba qarami yaga ya yake kuma da zakice bana zuwa gida wannan kuma sedai a qi Allah ayiwa mutum sharri tunda daman ba sonsa akeyi ba naga har cewa suke na ishe su na rage zuwa kuma naja baya an zagaye ana wasu maganganu wlh ku canza Halo kowa da abinda ya dameshi amma se Umaimah zaku saka a baki kuyita caccaka" Umaiman ta hayayyaqowa Nuratu kamar zata daketa. Kallonta kawai ta ringayi hartayi shiru saboda tsabar yanda ranta ya sosu bata iya cewa Umaiman komai ba ta miqe ta dauki jakarta ta juya zata fita, se kuma Umaimah tayi saurin binta tana cewa "Toh kuma muna magana kin wani suri jaka ina zakije? Ba fada kika zo ki mun ba se ki zauna kiyi ai in ma kina buqatar bulala in dakko miki ai kin Isa" ta qarasa tana kamo hannun Nuratun seta fizge a fusace ta juya ta kalleta tace "Baki gama ci mana mutunchin bane ko ya akayi? Koda yake ba laifinki bane, laifina ne nida na tako nazo inda kike amma kiyi haquri bazan sake ba" tana gama fadar haka ta fice daga dakin Umaimah ta bita tana kiran sunanta taqi tsayawa. A bakin qofar falon ta tsaya saboda Towel ne kadai a Jikinta ta kwalawa Ruqayya kira akan ta dakko mata Hijabi lokacin har Nuratu ta fice ta kusa kaiwa ina ta ajiye mota Umaiman tabi bayanta. Magiya ta shigayi mata tana bata haquri da rantsuwar ita ba abinda ta fada har zuciyarta bane kawai rantane a bace shiyasa ta fadi hakan amma tayi haquri. "Saboda ranki yana bace se ki kasa lankwasa harshenki, idan kuwa haka ne wata rana se kin furta abinda ze kaiki ya baroki, kuma ni bazan koma cikin gidanki ba garama ki adana ban haqurinki baki mun komai ba, iya abinda zance miki shine kiyiwa kanki Hisabi, in har kinga cewar layin da kike akai daidai ne kici gaba, idan kuma keda kanko kin hango kuskuren abinda kike aikatawa tun wuri ki gyara kafin lokaci ya qure miki, ni na tafi yan uwana suna can suna jirana" Daga haka ta shige mota ta kunna, Umaimah ta riqr murfin tana cewa "Toh ki jirani na shirya mu tafi tare ai dai kema kinsan ba'a fadamun za'ayi wani taro ba kuma taron menene ma akeyi?" "Kiyi zamanki mun gama abinda zamuyi tun kafin na fito, daman magana ce akan Yayan Yah Aminu Anty Mami ta samu Miji zatayi aure shine ta ce zata dauki yaran Mijin yace ze riqe Mata" "Agolanci? Allah ya rufa asiri yayan mu suyi Agolanci suje wani gida cin Arziqi a ringayi musu gani gani ana musu gori, taje can tayi auranta tsabar jaraba ko shekara biyu beyi da mutuwa ba zatace zata wani yi aure kamar daman jira takeyi ya mutun" Umaimah ta shiga kumfar baki, tsaki Nuratu taja ta taka mota tana ce mata "Idan kinga dama ki kirasu ki basu haquri ki kuma gyara alaqarki da kowa dan ranar Naka dole se Naka, duk tarin qawayen da kike ganin sun fiye miki mu akwai gabat da za'azo da dole mudin dai mu zamu miki rana" daga haka ta daga Sammani ya bude mata Get ta fice daga gidan a fuska zaka dauka babu abinda ua faru amma cikin ranta kalaman Umaimah na nan suna nuqurqusarta. Umaimah kuwa Nuratu na fita ta juya har ta kai bakin qofa kuma ta fasa shiga ta dawo nan Compound din taja kujera ta zauna bayan ta cewa Ruqayya ta kawo mata wayarta. Tafi qarfin awa daya a gurin a zaune, jira takeyi taga jama'ar da suka taru a bangaren Hajiyar sun fara fitowa amma shiru gashi tana tsoron ta shiga dan bata san su nawa bane a gurin haka ta gaji da zaman jira ta koma ciki suka ci gaba da Chatting da Safina dakw sake tausarta akan ta danne zuciyarta ta jira taga aikin Malam. Seda tayi sallar Magriba kafin tayi wanka ta saka Ruqayya ta shirya yara suka tafi gidansu. Yanda Mama ta karbeta ya sa ta sake shan jinin jikin damanga Yah Naziyya na gidan itama gaisawa kadai sukayi ta fita a sabgarta, bata wani jima sosai ba suka tafi bayan Abba ya dawo sun gaisa shidai faran faran ya tarbeta yana tambayarta Khalil yaja jikokinsa yana musu wasa da zasu tafi ya basu kudi ita kuma ya sake nanata mata karatun da kullum suka hadu se yayi mata na ta nutsu ta zauna da Mijinta lafiya ya rufe da saka mata Albarka. Duk setaji babu dadi yanda Maman tayi mata, ita bata ga fushin me takeyi ba kawai sunje sun taru an hado da abunda tayi da wanda ba tayi ba sun gayawa Maman ita kuma ta hau ta zauna suda Allah ita basu san abinda yake a gabanta ba za'a qara mata wata damuwar. KHALIL Tun yana office Jalilah ta kirashi akan ta qarasa duk siyayar kayayyaki shi kawai take jira yazo ya gani, be samu ya shigo da wuri ba dan bayan ya bar gurin Humairah seda ya sake biyawa wani gurin dan haka be tarar da Jalilan ba se ubannin akwatuna na garari daya tarar a bangaren Hajiya guda goma sha biyu da sunan kayan lefen Humaira. Buda baki yayi kawai yana kallon kayan, Hajiya tace "Ai Rigimar Jalilah babu me iya mata, nan fa kudaden jama'a babu a gun wanda bata karba ba ta harhada ta siyo kayan nan, ina jinsu dazu lissafin bashin Miliyan kusan uku suke maka wai harda Sarqa zasu siya a saka a ciki nace musu sun baka ajiyar kudin ne ko Yaya? Ga Lafayu can guda biyar Hajiya yagana ta aiko dasu magana kamar wutar daji labari ya watsu dangi wai zakayi aure ai da da wuri ka dawo gidan nan babu masaka tsinke yanda kasan yau ake bikin, nidai addu'a na ringayi su tafi salin alin ba tareda matarka tayi wani abun ba kuma Allah ya amsa mun har suka watse babu abinda akayi kuma tana gidan, ni yanzu da safe ma zuwa zasuyi su kwashe kayan nan kafin wani tsautsayin ya afka musu tun baka biya kudin ba". Kansa na qasa yake sauraron Hajiyar dan ya kasa hada ido da ita. Kunyarta yake ji ace matarsa ta zageta amma ya gagara daukar mataki akai, a hankali ya daga kansa ya kalli gefe yace "Daman itama tace zata dawo ta kwashe goben, munyi magana da Baba Abu Dazu yace ranar Juma'a zamu tafi can Jalingon, to ban sani ba ko ze yuwu ace an tafi da kayan ko kuma se daga baya dai wannan se kunyi magana dashi kun yanke yanda za'ayi" "Eh nima ya kirani da yamma, da na gaya masa ga Lefe ma har an hada yace babu damuwa ze tuntubesu yaji, idan cam za'a kai gara a hada ayi tafiya daya idan kuma nan gidan Hauwa za'a kai kaga za'a iya bari se lokaci ya matso tukunna. Nadai yi musu zancen kayan ita Umaiman Jalilah tayi tsalle tace ba za'ayi ba to ni babu ruwana ba kuma zan goyi bayan rashin Adalci ba, idan kudi zaka bata ta siyi abinda take so to idan kuma kayan zaka mata toh gasu nan ka duba abubuwan da suke ciki ka siya mata itama" Hajiyan ta sake fada se ya daga kai ya kalleta ganin itama shi take kallo yasa ya mayar da kansa qasa cikin taushin murya yace "Hajiya, kiyi haquri da abinda ya faru jiya dan Allah" "Haqurin me kake bani Babana ni baka yimun komai ba, idan ma dan abinda Matarka tayi ne ni ya wuce a gurina na kuma yafe mata kaima kuma ina so kaci gaba da haquri dan daman ai kasan abinda ka dakko dole ka shirya karbar duk wani sakamako daya biyo ba. Kawai kaci gaba da Addu'a ka kuma ci gaba da lallabata". Shiru yayi yana sauraron Hajiyar, idan ya tuna zagin da Umaiman tayi mata zuciyarsa bugawa takeyi amma ya gagara daukar mataki me yasa? Abinci ya buqaci Habiba ta kawo masa yaga Taliya ce yace ta mayar se ya miqe yayiwa Hajiya sallama ya fita. Kai tsaye ya wuce bangarensu, tunda ya shigo bega motarta ba daman yasan bata nan, seda yayi wanka ya canza kaya kafin ya sakko qasan lokacin har Ruqayya ta jera Abinci, Sakwara tayi musu da Miyar Agushi, se farfesun naman rago yana bude kwanon maganar Jalilah ta fado masa da tace jiya Umaimah ta dafa nama da magani ta bawa Hajiya taci se ya maida kwanon gefe ya zuba Sakwarar yayi bismillah tafi qafa dari kafin yayi shahada ya faraci. A falon Umaimah ta tarar dashi yana cin abinci, shaf ta manta da saqon da ta taho dasu dazu da bazata fita ba har se an gama abincin ta zuba masa amma akwai gobe. Da ido ya bita ganin ta dauke kai ta kalli wani guri daban yaran kuma gurin sa suka tafi da gudu. Khalil ya sauke ajiyar zuciya yaci gaba da cin Abincinsa tareda yaran. Seda suka qare Mu'ayyad ya zaro kudin da Abba ya basu ya bawa Khalil din yace ya ajiye musu, se sannan ya san daga inda suke, yana nan zauneda yaran suna kallo har qarfe tara kafin yace suje su kwanta. Dakin da Umaimah take ya shiga da sallama bayan da yayi knocking ta bada Umarnin a shiga. Tana zaune gaban mudubi tana shafa mai da alama wanka tayi gashinta data wanke ya manne a fatar wuyanta zuwa bayanta, kallo daya yayi mata tsigar jikinsa ta tashi wani abu daya dade beji akan mace ba ya taso masa seya qarasa bayanta a hankali ya dora hannayensa kan kafadarta yana matsawa. Umaimah, yanda yayi matan seda yasa tsikar jikinta itama suka zuba amma a fili bata nuna ta karbi saqon nasa ba sema qara tamke fuska da tayi ta ture hannun nasa daga jikinta ba tareda tayi magana ba ta miqe, rigar baccinta data ajiye ta dauka ta saka fuskar nan kamar Kunu ta haye gado ba tareda ta kalli inda yake tsaye yana binta da kallo ba. Seda ta kwanta taja bargo ta rufe qafarta zuwa cikinta kafin yabita shima ya shiga qoqarin kwanciya a bayanta. "Meye haka Malam zaka shigowa mutane daki harda hawar musu gado?" Ta fada a fusace tana tashi zaune, da yasan yanda take ji a zuciyarta da be kuskura yaje kusa da ita ba dan tsaf idan da makamo kusa zata iya qaddamar masa yanzu. Khalil kuwa dan murmushi yayi jin abinda ta fada seya sauke qafafunsa qasa, taja wani dogon tsaki kafin ta sake kwanciya ta juya masa baya tana qunquni. "Umaimah" ya kira sunanta, bata amsa ba shima be saka ran zata amsa din ba dan haka yaci gaba da cewa "Ina so duk abinda zakiyi ya tsaya iya kaina nida ke karki sake sako Mahaifiyata a ciki ballantana har ki iya bude baki ki zageta, ban taba zaton ko kallon banza kika ga wani yayiwa Hajiya zaki yi shiru ba se gashu keda kanki baki ji nauyin komai ba kika zageta" "Khalil, nace Hajiya munafuka ce qarya nayi ko batayi munafuncin ba? Ta nunamun tana sona ta jani a jiki har ta fifitani akanka sata haifa she duk na yaudara ne rana daya ta nemo maka auran yar Qawarta idan ban kirata da Munafuka ba Annamimiya kake so nace mata kome?" Umaimah data tashi zaune ta fada tana kallonsa ido cikin ido babu tsoro ko shakkar komai a fuskarta. Wani yawu me daci ya hadiye ya rufe idonsa da lokaci daya ya rikida yayi ja saboda bacin ran da kalamanta suka dira masa, yana jinta taci gaba da cewa "Ai na gaya maka kaida zaman lafiya har abada a gidan nan Khalil ba dai aure kace zakayi ba toh mu zuba mu gani" taja wani tsaki kamar zata katse harshenta kafin ta yunqura ta shige bandaki ta barshi a gurin. Bibbiyu yake gani da haka ya ringa dafa bango har ya haye sama a nan kan carpet ya kwanta yana dafe da kansa daya sara masa yana hawa saman. Ya rasa abinda yasa a kwanakin yake jin haka kwana yakeyi da ciwon kai ga wano baccin Asara daya sameshi daya rasa kona magani da menene baya sanin sanda yake daukarsa duk kuma yanda yayi ya yakice shi kasawa yake yi balle har ya samu damar tashi yayi Nafila cikin dare Sallar Asuba kanta kwana ukun nan a makare yakeyi amma ya ta'allaqa hakan da rashin kwnanciyar hankali da yake ciki a kwanakin. Da hannu biyu ya dafe kansa, wancan fada masa akayi yanzu kuma ta maimaita masa harda qarin wasu kalaman da suka fi na farko muni duk akan Hajiyarsa anya idan yaci gaba da zama da Umaimah kuwa ya cika dan Halas? Macenda zata kalli cikin idonsa ta zagi uwar data haifeshi zagi mafi muni ta cancanci yaci gaba da zama qarqashin inuwar aure da ita kuwa? Be ga ta inda ya kamata ace yayiwa Umaimah uzuri ba bayan wannan abun da tayi masa, idan zata zageshi ya shanye baya tsammanin ze jure cin mutunchin mahaifiyarsa kuma dole ya nuna mata cewar yana martaba Hajiyarsa kuma be hadata da kowa da komai a duniyar nan ba. Dakyar ya iya miqewa ya bude jakar Office dinsa dake ajiye a falon ya dauki biro da takadda ya zauna amma ya kasa rubuta abinda zuviyarsa take ayyana masa. Ya gwada rubutun yafi sau goma amma ya kasa yanda kasan an daure masa yatsu haka yakeji ga wata faduwar gaba tamkar zuciyarsa zata tsaga qirjinsa ta fito haka yake ji se yayi jifa da takaddar da bironya miqe tana layi ya isa gurin Dispenser ya tsiyayi ruwa me sanyi ya ringa sha har seda yaji kamar zeyi amai kafin ya haqura, a nan gurin ya tsugunna ya dafe kansa da hannu biyu, wani irin abu yake ji a cikin jikinsa, ikon Allah ne ya bashi qarfin bude baki ya shiga karanto duk addu'ar da tazo bakinsa be san tsahon lokacin daya dauka a halin da yake ciki ba sejin qarar wayarsa yayi ya bude ido dakyar yana kallon inda yake, anan gana Dispenser yayi bacci, ya yunqura dakyar ya tashi zaune nauyin da kansa yayi masa ya ragu wayarsa ta sake daukar qara ya shiga lalubenta ya dakko, qarfe biyar da minti Ashirin ya gani Alarm din daya saita ne tun qarfe biyar ze yanzu Allah ya bashi ikon ji. Bayan yayi wanka ya shirya ya fita masallaci, a sahun baya yayi sallah sabanin da da kullum yana sahun farko. Bayan an idar da sallah be tashi ba yana zaune a gurin yana jan carbi, Malam Hashim Dattijo ne baban daya daga cikin Maqotansu ne ya dakko shi daga garinsu bashida lafiya, kullum a sahu daya suke SallarAsuba da Khalil din, haka Magriba da Isha indai a gida yayi su kwanakinya lura da Khalil din baya zuwa sallah masallacin se yau ya ganshi yana shigowa a yanayin da be saba ganinsa ba. Kusada Khalil ya zauna yana kallonsa yanda yayi zuru yana jan carbi ya saka wa guri daya ido bashi da tabbacin yasan abinda yake karantawa m seya kai hannu ya dafashi Khalil yayi firgigit ya kalli Dattijon kafin ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga gaishe shi. "Ibrahimu kwana biyu baka zuwa Masallaci har na tambayi wannan yaron ko kayi tafiya ne yace Aa yana ganin gilmawarka, lafiya dai naga dukka rame ka fita a hayyacinka haka?" Dattijon ya fada har sannan hannunsa na kan kafadar Khalil din se ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Tsohon yace "Ina nan Baba, kwana biyun banajin dadi shi yasa bana iya fitowa amma yanzu Alhamdulillah na samu sauqi" "Toh Allahya qara rufa Asiri, amma kaganka kuwa wane ciwo ne yake damunka haka daya saka duk ka firgice?" Tsohon ya sake fada yana qare masa kallo se Khalil ya sunkuyar da kansa qasa dan be san me zece masa yana damunsa ba. Shi kansa in banda ciwon kai babu abinda zece gashi yana damunsa dan haka ya bude baki a hankali yace "Ciwon kai nakeyi Baba, aiki ne yake mun yawa kwana biyu yake saukar mun da ciwon kai" "Ko naji kasan shi ciwon kai yafi saurin gigita mutum gaba daya kaga ya fitar da mutum daga hayyacinsa, amma bayan ciwon kan babu abinda yake damunka kuma" Baba ya sake fada se Khalil ya daga masa kai alamar Eh Tsohon yaci gaba da cewa "Bari idan na shiga gida zan duba maka wani magani da na taho dashi daga gida, kwanaki da wannan yaron shima yayi fama da ciwon kan harda jiri yayi ta yawon Asibiti suna cewa jininsa ne ya hau ana bashi magani, tunda ya shaqa maganin nan sau daya kan ya sauka, da yake shi hade hade ne duka da maganin miyagu da makaru na sihiri kuda kuke harka ta mutane daman dole se kun nemi tsari dan baku san zuciyar wadanda kuke tare dasu ba. Sannu bari na shiga gidan yanzu zan dakko maka na bawa takwarana ya kawo maka Allah ya qara afuwa ya ci gaba da doraku akan maqiya". Da Amin ya amsa danya gaji da surutun tsohon, sun saba sosai kullum se sunyi hira amma yanzu da kansa yake masa kamar ana daka baya buqatar wani dogon surutu, tare suka fita Baban ya wuce gidan dansa shi kuma ya shiga gida. Badan akwai ayyukan da yake so ya qarasa ba saboda tafiyar da zasuyi da yau baze fita aiki ba. Be ko saurari abin karin da Ruqayya ke hadawa na ya wuce bangaren Hajiya a can ya tarar da qullin maganin Musa yaron maqocinsa ya kai mata ta ajiye masa. Bayanya gaya mata yanda sukayi da Dattijon tace masa "Ka gwada toh gashi nan kuwa dare daya ka rame dan jiya ba haka ka shigo ba duk idonka sun fada idan ka fita ka biya Asibiti a sake dubaka, na gaya maka ka cire komai daga zuciyarka kaqi bafa a fara ba Babana idan ka karaya tun yanzu ta yaya zaka tafiyar da zaman naku? In har kana ganin ba zaka iya jurwwa na lokaci be qure ba ka janye zama lafiya aka ce yafi zama dan sarki meye amfanin abinda za'ayi a maimakon ka samu nutsuwa da farin ciki ka sake gayyatowa kanki wata damuwar?" "A can tsohon gidana nake so na ajiyeta, gyaransa kuma a qalla ze iya daukana wata shida Hajiya, idan kun sake yin magana da Baba Abu ki gaya masa se kuma maganar abinda za'a kai shima idan ya yanke se ki gaya mun na tura masa" ya bagarar da maganar da takeyi ya canza mata da wata, se taja numfashi tace "Yace Alhaji Garba ya bada dubu dari biyu dukiyar aure shi kuma ze bada Dari Sadaki se kaji da biyan bashin da Hasanar ka ta tattago maka su" "Allah ya saka musu da Alkairi" ya fada kafin ya kwance maganin yana kallonsa Hajiya tace "Musa yace baya komai suma idan suna ciwon kai Kakan shi yake shaqa muba se ma daya gwadamun yanda akeyi bari ka gani" ta debi garin kadanta shaqa Khalil na kallonta haka ya diba shima ya shaqa da dan yawa ya qulle ledar. Zama yayi yana jiran Habiba da take soya doya, kamar qura ta taso haka yaji kansa yayi dummm kafin kace me ya shiga jera Atishawa babu qaqqautawa. Tun Hajiya na daukar abun da sauqi harta tsorata ganin yanda yake yinta ya kasa zama akan kujera ya sauka qasa yana ci gaba da jera ta da qarfin gaske idonsa ya tara hawaye. Habiba ta kwalawa kira ta fito a rikice itama dan tana jiyo Atishawar tasa data zarce hankali. "Kiyi maza ki shiga gidan Officer kice wa Musa yazo" Hajiya ta fada tana riqe Khalil dake Atishawa kamar wanda ya sauka daga iska, fitar Habiba babu dadewa se gata sun dawo tareda Baba Musa, Hajiya ta kalleta tace "Musa qarami nake nufi ba kai ba Alhaji" "Wannan kiran ai nawane Hajiya bana Takwara ba, ta gaya mun halin da ake ciki ne nace bari nazo da kaina na gani sannu Ibrahimu kaji Allah ya qara taqaitawa ai mantawa nayi daman ban gaya maka ba, idan da Sihiri ko sammu indai shaqarsa yayi da izinin Allah seya fitar da duk ma abinda ya shige masa kai wannan Atishawar da kika gani shaidanun da suka samu guri akan sa suke haddasa masa ciwon ne suka fita sannu kaji, da za'a samu tazargade se a sake turara masa babu komai in Allah ya yarda sannu" ya sake fada yana dafa Khalil dake zaune a qasa yana maida numfashi dan Atishawar ta lafa masa, kuma wani ikon Allah duk wannan nauyin da yake jin kansa ya masa ya sauka sakayau yake jinsa kamar wanda yayi sabon Aski. A tarkace Hajiya ta binciko Tazargadenta dade da wata Qanwarta ta kawo mata tace ta ringa turarawa itama amma ko sau daya bata taba gwadawa ba nan Habiba ta kunna coal ta zuba, ba iya Khalil ba duka gidan suka bi suka turare Hajiya na cewa "Ni Aishatu Babana a ina ka shaqo wannan jaraba kuma koma ina ne dai an auna arziqi tunda mun samu makarin abun da wuri kai Allah kayi mana maganin abinda ya dame mu" "Nifa Hajiya ban yarda da wani Asiri ko menene ba kawai ciwon kaine kuma stress ya kawo shi, me nayiwa wani da zeyimun Asiri nida hayaqi in ba akan titi ba na motoci a ina nake ganinsa ma ko turaren wuta za'a saka a gidan nan kin sani kafin nadawo an saka dan bana son na ringa shaqar qaurin" Khalil ya fada se Hajiya tace "Ai shikenan, Allah yaci gaba da karewa ka tashi kaci abincin idan babu hali ka haqura da zuwa aikin ma kawai yau daya dai ka huta" . Hakan kuwa akayi Anwar ya kira ya bashi uzurin bashi da lafiya yayi duk abinda ya kamata, a nan bangaren Hajiya ya wuni daman Itama Umaimah tara bata cika ba ta bar gidan. Sanda Jalilah tazo haka ta sakashi gaba seda suka bude kayan, ya ringa mamakin yanda ta zabo kaya haka kuma Undies da dogayen riguna duk yana tunanin zasuyiwa Humairan se ya kalleta yace "Wai ya akayi kika san size din yarinyar ne?" "Kai dai ka zauna anan ai wlh tunda na saka raina akan se kayi auran nan babu abinda bazanyi akai ba, ni yanzu muyi maganar kudi itace a gabana na samu na sallami masu kaya" "Ai tunda kika siyo bakiyi shawara dani ba se kiyita Addu'a har sanda zan samu kudi na biyaki dan ni banyi lissafin wani lefe a yanzu ba. Se bayan Isha Umaimah ta dawo gidan yana zaune a compound yana waya da Humaira ta wuce shi ba tareda tayi masa kallo biyu ba. Seda ya gama wayarsa tsaf sannan ya shiga gidan, haka nan yake ji shakkarta ta ragu a zuciyarsa tana zaune a falo tana waya ya haye sama warin Tazargaden da Jalilah ta saka masa duk ya cika gurin dole ya sake bude windows ya kunna Ac. Tunda Hajiya ta labar ta mata abinda ya faru da safen tayi tsalle ta dire akan Umaimah ce "Toh Hajiya a ina zeje ya shaqo wani abu in ba a gidan sa ba wannan matar tasa fa ta zarce duk yanda kike tunaninta a banza zata dauke wuta haka kema kinsan canza salo tayi ta koma yaqin ta qarqashin qasa kuma ta Allah ba tata ba, ina kowa zan gayawa Abban Sadiq ya hada masa magungunan karya sammu dana tsarin jiki daman ya fara hada naki in Allah ya yarda duk mugun abunta sedai ya koma kanta" haka ta kwashi tazargaden taje ta turara Hajiya na hanata amma taqi ji sa'a daya Umaiman bata nan da Allah kadai yasan yanda za'a kwashe. Seda ya feffesa freshener kafin ya sake sauka qasan, bata falon ya zauna dan yasan zata fito so yakeyi ya gaya mata zancen tafiyarsa jibi yana nan zauna ta fito tana tura ciki se yamutsa fuska takeyi bata ko kalli inda yake ba ta zauna a qasa tana kiran Ruqayya. "Idan Allah ya kaimu ranar Friday zamuyi tafiya dasu Baba Abu zamu iya dawowa Saturday ko Sunday ya danganta da yanda muka gama abinda ya kaimu" ya fada a sanyaye qirjinsa na bugawa. Be zata zata kula shi ba se kuma yaji tace "Ina zaku je?" "Jalingo" ya bata amsa zuciyarsa kamar ana kodan kwarya dan seda ya fada yayi dana sanin fadar idan kuma tasan garinsu Humairan fa ya sake kunno wata wutar da ze kasa kashewa. Zaman jiran yaji ko zata sake magana yayi amma har Ruqayya ta kawo mata abinci ta shiga cin abinta bata kulashi ba se ya miqe yana sauke ajiyar zuciya yace "Zan tura miki da saqo ta account" kamar da dutse yake magana haka ta masa banza, ya wuce sama yana sauke Ajiyar zuciya, Umaimah ta bishi da wani matsiyacin kallo kafin taja tsaki a fili tace "Se inga da qafar da zakaje Jalingon ai Mtsw" ta sake jan tsaki taci gaba da cin abincinta. Seda ta gama tsaf kafin ta koma dakin ta dakko yar robar da Malam ya sake aiko mata da ita bayan ya kira shida kansa ya sanarwa da Safina zancen tafiya neman auran dasu Khalik din zasuyi. A corridor ta tsaya inda yake ajiye takalmin da yake zuwa sallar asuba dashi ta saka leda a hannunta ta debi man dake cikin robar zuciyarta ta rigada ta qeqashe biyan buqata kawai take nema babu bata lokaci ta shafe duka takalman qafa biyu da yake zuwa salla dasu tunda bata san wanda ze saka ba. A sharar waje taje ta yarda ledar da robar maganin ta wanke hannunta tasa kafin ta koma daki ta kwanta, seda ta turawa da Safina saqo a WhatsApp cewar tayi seta maido mata da cewa "Yawwa qawata, kedai ki ci gaba da jurewa ranar biyan buqata ai rai ba a bakin komai yake ba in Allah ya yarda mune da nasara. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 67 KHALIL Cikin ikon Allah a daren yayi bacci me dadi wanda har ya iya tashi yayi sallah raka'a hudu kamar yanda ya sabayi a kowanne dare, da yake dab da Asuba ya farka bayan ya idar da sallar be koma bacci ba, Lazumi ya ci gaba dayi har akayi kiran farko kafin ya tashi ya shiga wanka yayi shirin masallaci bayan ya cire kayan da ze saka da sauran abinda zeyi amfani dasu saboda da wuri yake so ya fita, jiya beje office ba kuma akwai abubuwan daya kamata ace yayi dukda Anwar yana nan. A masallaci Baba Musa daya ganshi yake cewa "Madallah kace jiki yayi kyau gashi yau ka fito da wuri yanda ka saba, toh Allah ya qara kikayewa. Ka nemi ganyan magarya masu kyau ka zuba a ruwa ka tofa Ayoyin nan na karya sihiri kayita sha kana shafe jinka sannan koda yaushe bakinka karya yi shiru daga ambaton Allah duk abinda kake yi ka ringa Istigfari kana hailala kaga Istigfari waraka ne daga duk wata damuwa sannan karka ringa rabo da Karanta Lahaula, ka kuma ringa tofata qafa dari a ruwa kullum kaida Yayanka da Iyalinka kusha ku shafe jikinku duk abin maqiyi sedai yayi amma baze same ku ba da yardar Allah". Godiya yayiwa Baban suka rabu bayan an idar da sallah ya shiga gida. Yana tsaye yana saka kaya haka kawai yaji qafarsa ta sage kamar wanda ya taka qanqara, zama yayi akan gado yana duba qafar, shidai baya tunanin yaji ciwo ko ya buge da wani abu a kwanakin nan kuma ko dogon tuqi beyi ba qarqarinsa daga gida ne yaje office idan ma zasu fita site yawanci Anwar ne yake tuqasu. Haka ya qarasa shirin ya fito, dakyar ya iya sauka daga benen ya zauna a falon qasan yana maida numfashi. Takalmin daya saka ya cire hada da safar yana sake duba qafar. Yafi minti goma a zaunen, jin an bude qofa ya sakashi daga kai ya kalli gurin, Umaimah ce tayi masa kallo daya ta nufi hanyar kitchen bata dade ba ta fito da cup a hannunta ta sake wuce shi ta shiga daki. Haka ya ringa takawa dakyar ya fice daga gidan ya shiga bangaren Hajiya. "Babana lafiya kake dogara qafa kamar me karaya?" Hajiya ta fada tana kallonsa ganin yanda yake tafiya kamar wani Saqago. Seda ya zauna yana cije baki saboda yanda yake jin qafafun nasa kafin ya shiga gaisheta ta amsa tana cewa "Me kuma ya samu qafar?" "Nima ban sani ba Hajiya, ina dawowa daga Masallaci naji ta riqe mun kuma abin qaruwa yakeyi, ba ciwo take mun kawai qashin ya riqe tun daga guiwata har zuwa tafin qafar" ya bawa Hajiyar amsa seta matsa kusa dashi tana duba qafar tace "Ikon Allah sanyi ne toh, shiyasa nake yawan maka maganar Ac da baka rabo da ita gida da Office irin wannan sanyin qashin nake gudar maka wani baya tashi tambayarka se girma yazo musamman ku da daman kuna da Gadonsa kana kallo Mahaifinku harya rasu yana yana fama da ciwon qafa toh Allah ya taqaita, bari na dakko man zafi na shafa maka ko zata saki in yaso kaje Asibiti su baka magani daga baya". Sama ta wuce ta dawo da qananan robobi na Man Mainasara da kuma kwalbar Aboniki, da kanta ta shafe masa qafafun tun daga guiwar har tafin qafa. Seda ya karya a bangaren Hajiyar kafin ya fita zuwa sannan qafar ta saki dukda ba gaba daya ba haka ya wuce office. A can dinma aikin yana yi yana hutawa saboda yanda qafar take riqewa se kuma ta saki. Rigima Humaira ta saka masa akan tanason ta ganshi kamar ba jiya yaje gurinta ba, babu yanda ya iya haka ya biya Gidan Unaizatu bayan ya tashi aiki. Be shiga ciki ba a qofar gida suka tsaya. Cikin kulawa Humaira ta kalleshi ganin yanda yake cije baki yana canza tsayuwa tace "Yah Khalil meya sami qafarka naga ka kasa tsayuwa da kyau?" "Babu komai dan ciwo takeyi mun amma yanzu idan na tafi daga nan zan biya naga Likita inaga nayi over working kaina ne shi yasa nake ta jin babu dadi a jikina" ya bata amsa seta sake narke fuska kamar zatayi masa kuka tace "Wayyo sannu Allah ya baka lafiya, ciwon qafa babu dadin ina gani idanya tasarwa Mama ko bacci bata iyayi amma idan na tofa mata Fatiha se kaga ta dan samu sauqin ciwon kaima idan kaje gida kacewa Anty Umaimah ta tofa maka". Kallon ta yakeyi har ta kai qarshe yayi dan murmushi yace "Ashe kin san sunan matata amma shine kullum kika tashi magana sedai naji kince Matarka?" Tura baki tayi ta kalli gefe ba tareda ta tanka masa ba ya sakeyin murmushin qarfin hali dan sosai qafar ta matsa masa ya ce mata "Bari naje Baby, zamuyi waya idan na isa gida kinji" seta daga masa kai tace "Toh, Allah ya qara sauqi yanzu a haka kuma gobe zakayi doguwar tafiya?" Shaf ya manta ma da wai gobe zasuyi tafiya, se ya sake yi mata murmushi yace "Eh mana ko bakya so naje?" "Aa kaga fa qafarka na ciwo ka bari kawai se next week se kuje saboda zaman mota fa da wahala ko baka ciwon qafa daga nan zuwa Jalingo se kaji jiki ballantana kuma kana fama da qafa" Bude ido yayi yana kallonta yace "Dan Allah fa? Kinsan ni ban taba zuwa Taraba ba nadai je Yola shima a jirgi so ban san nisan tafiyar ba" "Aiko da nisa ga hanya bashi da kyau shine ma abinda yake qarawa tafiyar nisa" ta bashi amsa. Se ya bude motar ya shiga, Carton din Madarar waken suya ta kwalba daya tsaya ya siya a hanya ya miqa mata yana cewa "Gashi, kwanaki naga Anwar ya siyawa Matarsa wai yana saka qiba ki gwada sha mu gani ko ze karbeki kinsan Matata qatuwa ce kar kuzo dakuwa tafi qarfinki". Kallonsa ta tsayayi se kuma ta zumburi baki ta harareshi qasa qasa tace "Allah ya sauwaqe nayi dambe da Kishiya" "Me kika ce?" Ya fada yana kallonta seta dauki Carton din ba tareda ta bashi amsa ba ta wuce seda taje Get ta waiwayo ta murguda masa baki irin yanda yara sukeyi tace "Da zakace matarka qatuwa zata dakeni ai abun ba a qarfin jiki bane kuma ai a qauye ne ake kishin hauka ana doke doke" tayi saurin shigewa ciki Khalil daya saki baki yana kallonta yace "Ikon Allah" lallai ya yarda da Jamila da tace ba'a raina mace komai qanqantarta gashi kuwa ya gani, in har zata iya maida masa da Magana to Umaiman me? Tashin motar yayi ya wuce, yanda yake jin qafarsa dole ya wuce Asibiti tun kafin ya isa ya kira Dr Al'amin likitan da Umaimah take gani a yanda ya fada masa yayi sa'a Physiotherapists dinsu is on Sit dan haka zeyi masa booking kafin ya qaraso. Sanda yaje be jima ba ya samu ganin likitan, bayan duk bincike da tambayoyin daya kamata yayi masa akan musabbabin ciwon qafar tasa ya rubuta masa magani nasha dana shafawa da zasu rage masa Ciwon qafar sannan ya gaya masa ya daure dukda yanda yakeji ya ringa motsa qafafun kafin ya bashi X-ray dan su duba da kyau suga ko wata matsala ce ta ciki dukda Khalil din ya tabbatar masa da wayonsa be taba faduwa ko wata buguwa da zata janyo ciwon ya tasar masa yanzu ba kamar yanda Likitan yake tunani. Seda ya koma gurin Dr Al'amin ya gaya masa yanda sukayi ya karbi takaddar X-ray din yace masa ya dawo da safe sannan yayi masa fatan samun lafiya. Har Khalil ya kai bakin qofa Dr Al'amin ya tsayar dashi yana cewa "Yauwa kaga na sha'afa, Madam bata zo Antinatal ba jiya ina taso na kiraka wlh aiki ya dauke mun hankali. Daman tun last week na gaya mata ban sani ba ko kunyi maganae idan har ta wuce satinnan bata haihu ba to gaskiya sedai Muyi mata CS kawai a cire abinda yake cikinta dan tun farko data bamu hadinkai ma da yanzu anyi amma ta nuna bata so ita amma kai ina so ka fahimci halin da take ciki da complications din da cikin nan ya samu CS din is the best option dan haka ka lallasheta, if possible within the weekend kuzo kawai a cire Babyn". Ajiyar zuciya Khalil dake sauraronsa yayi kafin ya tabbatar masa idan ya koma zeyi magana da ita duk kuma yanda sukayi ze kira Dr a waya ya gaya masa, suka sakeyin Musabaha ya fita yana tafiya a hankali saboda duk in ya motsa qafar shi kadai yasan abinda yakeji. Dakyar ya iya kai kansa gida saboda mommotsa qafar da akayi tamkar an qaro masa ciwon da takeyi ne, seda ya dafa Khalifa sannan suka iya shiga gida. Saboda yanda yake be iya hawa Sama ba anan falon qasa yace ya ajiye shi kafin ta lafa masa se ya hau saman, Khalifa ya ringa kallonsa da tausayawa se yake tuna Lokacin da Mahaifinsu ya ringa fama da qafa dukda yana qarami a sannan amma be manta ba kamar haka wata rana idan ta tasar masa sedai Khalil din da Me Gadinsu su kama shi su shigo dashi cikin gida gashi yanzu Yah Khalil ma yayi Gado. Shi yaje ya gayawa Hajiya a yanda Khalil din yake, yana zaune kan carpet bayan ya samu dakyar yayi alwala a bandakin dake falon yayi sallar Magriba data riskeshi a hanya a zaune yana Azkar Hajiyar ta shiga da sallama ta zauna kan kujerar da yake jingine tanacewa "Babana qafar ce yanzu Khalifa yake gaya mun se shi ya kamak kuka shigo kaje Asibitin kuwa daka fita" "Naje Hajiya sun bani magani na sha dana shafawa sannan gobe zan koma ayi hoto" ya bata amsa yana nuna mata ledar magungunan dake kusa da ita. Miqewa tayi ta Kashe Ac da aka kunna a Falon ta sama data qasa ta sake zama tana cewa "Ko wannan uban sanyin da kuke babalawa kanku ya isa ya sakar maka da ciwon qafa ai, ina Matar gidan da zata samu ruwan Zafi ta dan gargasa maka qafar ka shafa maganin in Allah ya yarda zatayi sauqi kafin goben tayi ayi hoton ko?" "Ciwon ma ya lafa Hajiya yanzu zan tashi naje nayi wanka sena gasa da kaina" ya bata amsa yana yunqurawa cike da qarfin Hali dan ji yake kamar an qara dora masa duwatsu an danne qafar. Hajiya ta miqe tana cewa "Zaka iya hawa bene kuwa Ka shiga can dakin ba nan Umaiman itama take yanzu ba?" "Babu komai Hajiya zan iya kuma likita yace karna zauna na ringa motsa qafar sosai, bari nayi wankan kafin a kira Sallah zan shigo idan na dawo daga Masallaci" "Shikenan Allah ya qara afuwa je kayi wankan" cewar Hajiya, Khalil ya fara takawa cikin qarfin hali amma kana kallonsa kasan yana jinjiki, ya fara hawa stairs din kenan aka bude qofar falo shida Hajiya dake tsaye har sannan tana jiran ya haye saman suka kalli me shigowar, Umaimah ce ta shigo da qaramar sallama ganin Hajiya tsaye yasa ta danyi turus se kuma ta kalli Khalo daya tsaya shima yana kallonta. "Ashe bakya nan, to wannan jikin naki ma keda shi din ai duk masu neman taimako ne da se nace kije ki kamashi ya hau saman amma bari na turo masa Khalifa" tana gama fadar haka ta rabe Umaimah dake tsaye tana kallon Khalil ta fita. Ajiyar zuciya Umaiman ta sauke a sanyaye tana ci gaba da kallonsa ganinya juta yaci gaba da qoqarin daga qafar yana hawa saman Khalifa ya shigo ya qarasa da sauri ya kamashi da yake shima jikin nasa irin na Khalil ne kusan daga shi ya ringayi se gashi ya haye dashi saman seda ya rakashi har bakin qofar bandakinsa ya shiga ze fita Khalil din yace ya jirashi ya nemi kan kujerar dake dakin ya zauna zuciyarsa fal cike da tausayin yayan nasa. Umaimah kuwa gaba daya jikinta ne yayi sanyi yanda taga Khalil din na tafiya ya bala'in taba zuciyarta yanzu fa ita ce sila me yasa ba tayi tunani ba ta aikata yanzu idan ya rasa qafarsa gaba daya fa ya zatayi? Dakinta ta wuce ta kullo qofa da muqulli, watsar da jakarta tayi dake cike da tarkacen abubuwandata karbo a gidan wani sabon Malami da Safinan ta sake kaita yau, a cewarta gara ayiwa aikin rubdugu dan a samu biyan buqata da gaggawa. Wayarta ta dauka ta shiga kiran Safinan, tana dagawa tace "Safina na shiga uku karfa Malamin na ya gurgunta mun Miji kinga yanda Khalil ya koma kuwa a dare daya sefa an kama shi yake iya tafiya" Tsaki Safina tayi tace "Ban taba ganin mutum me garaje a duniya ba irinki Umaimah tukunna ma bake kika ce ayi masa abinda ze saka ya fasa tafiyar da yayi niyya ba? Da kinsan ma da zeyi tafiyar ne ba Malam din ne ya gano miki ba kuma dazu kike tabbatar mun da bayan kin koma jiya ya gaya miki da bakinsa zeyi tafiyar meye to abin tayar da hankali a ciki? Malam ya gaya miki aikin ko ba'a karya baqar qarinsa kwana uku ze karye da kansa amma in so kike ya dakatar bari na turo Miki lambarsa kawai ki kirashi da kanko kawai ki gaya masa dukka ayyukan ma da yayi miki ya karya kowa ya huta na gaji da shegun qorafinki da basa qarewa". "Ba haka bane Safina wlh dan baki ganshi bane daman tunda aka fara ayyukan nan wlh ya fita a hayyacinsa sam bashi da nutsuwa kamar ba Khalil dina ba nifa gaskiya indai haka za'a ci gaba to gara a bari dan ba so nake Mijina ya zauce ba ana zaune lafiya ni aure nace a hanashi yi amma gaba daya ya samu se damalmala masa rayuwa yakeyi" Umaiman ta sake fada se Safina taja tsakin da yafi na farko tace "Kanki ake ji, in kinga dama ki aikata saqonnin da muka karbo yanzu in kuma baki gani ba ki bari, sannan wannan na Gasashshen naman na gaya miki kiyi dan nayi jiya kuma naga Aikinsa amma in kinga har yanzu zuciyarki na kokonto to ki saki ki dauki qaddara kawai ki zauna da kishiya" "Allah ya isa tsakanina dake kuma kishiya sedai ki ganta a gidanki banza muguwa kawai" Umaiman ta fada kafinta kashe wayarta ranta ya harzuqa da maganar Safinan ta qarshe. Idan zuciyarta ta karaya taga rashin kyautawa akan abinda takeyi seta tuna da cewar Khalil din shi ya jawa kansa koma menene daya ce zeyi mata kishiya. Wanka ta shiga har sannan jikinta a sanyaye da yanayin Khalil din tana fitowa tayi sallah, kitchen ta wuce ta cire Kaza da tun da safe ta saka Ruqayya tayi mata Marinating dinta kafin ta tafi gida wai Mamanta aka kira akan bata da lafiya. Hadata tayi irin hadin da Khalil din yafi so ta saka a Oven sannan ta dora masa ruwan shayi, seda ta juye ruwan a flask ta koma falo tayi Sallar Isha. Har kazar ta gasu ta fito da ita ta jera masa komai akan Dining. Ragowar tuwo ta dumama abinta taci ta sake neman guri a falon ta zauna tana jiran Khalil dinya dawo daga Masallaci amma har kusan qarfe goma be shigo ba zuciyarta ta kumbura iya wuya, tasan yana can gurin Hajiya suna qulla qulle amma duk suyi su gama ta tabbatar da ita ke da Nasara akan su. Ciccibawa tayi ta miqe tana shirin shigewa daki Khalil din ya shigo yana takawa a hankali kamar Wanda ya warke daga Paralysis. KHALIL Wanka yayi ya gasa qafar sosai da ruwan zafi ya sake Alwala kafin ya fito yana dafe bango Khalifa na ganinsa ya tashi da sauri ya taimaka masa ya zauna a gefen gado, Khalifan ya nunawa duk abinda yake da buqata ya dakko masa yanayi a zuciyarsa yana zagin Umaimah, yanzu a ace tana cikin gidan Mijinta na a halin buqatar taimako amma ko a jikinta, a ringa cewa bata da lafiya amma ai hakan be hanata tsinannen yawo ba tunda kullum seta fita kuma ita takr jan mota da kanta. Tare suka sake sauka qasan, motsin da yaji a Kitchen ya tabbatar masa itace haka suka fita zuciyarsa babu dadi, yanda tayi data shigo kamar bataga Hajiya ba balle ta gaidata dukda Hajiyar tayi mata magana abin ya qona masa rai daman shi yasan ba zata kulashi ba. A masallacinma a zaune yayi sallah, Hankalin Baba Musa yayi bala'in tashi dayaga Khalil din fadi yakeyi "Ibrahimu anya al'amarinka da lafiya kuwa ya za'ayi daga ciwon kai kuma se qafa ta riqe gaskiya ya kamata ka tashi a tsaye ka nemi magani wannan daga gani maqiya sun shammaceka sun maka bugun kwaf daya bari goben nan in Allah ya kaimu zan kira qanina a can qauye in gaya masa komai ya hado maka magani ya bayar a kawo dan aikinsa kenan karya sammu wannan maganin ciwon kan ma shi yake bani shi, yanzu baka ga wannan Yaron ba da da kuke zaune kai da kanka kana mun qorafin yanda yake tafiyar da Al'amuransa amna da muka dage da roqon Allah ba gashi komai ya daidaita ba? Mutanene babu Allah a ransu yanzu kyashi da hassada yayi yawa a zuciyar jama'a". Shidai Khalil murmushi kawai yayi dan baze taba yarda da cewar wai Asiri wani yayi masa ba to meya hadashi da wanin da har zeyi masa Asiri ana zaune lafiya?. Daga masallacin bangaren Hajiya ya wuce, a can yaci abinci yasha maganin dan ya shafa na shafaqar tunda yayi wanka. Bayan ya gama Hajiya ta kalle shi tace "Yanzu tafiya ba zata yuwu ba kenan Babana ga ciwo ya sako kai kuma bana zaton ka kira kawun naku ka sanar masa ko ka barsu suna ta shiri sun katse abubuwan da suke a gabansu" tana rufe baki wayar Khalil dake ajiye ta dauki qara ya dauka yana cewa "Kinga Baba Abun ne yake kira" se ya daga ya saka a kunnensa da sallama. Fada Baba Abu ya shigayi masa bayan daya amsa sallamar ya shiga cewa "Yanzu Ibrahim zamu yi doguwar tafiya gobe kasan kuma Asubanci zamuyi amma baka zo mun tattauna yanda za'a tsara tafiyar ba ko kuwa mu kake so mu biyoka tunda mu zaka je tambayowa auran" "Aa ba haka bane Baba kayi haquri, yau din na fita da wuri ne na qarasa wasu ayyuka saboda jiya ban samu fita ba sannan kuma na dawo bana jin dadi daman yanzu muke maganar da Hajiya nace zan kiraka muji yanda za'ayi". Sassauta fadan Baba Abu yayi saboda ko daga muryar Khalil din ya fahimci dagaske bashida lafiya yace "Toh me kuma ya same ka?" "Ciwon qafa ne Baba dakyar nake taka qafar wlh" ya bashi amsa se Baba Abu yace "Subhanallahi badai ciwon nan namu na gado bane ya sarqafeka tundaga yanzu? Toh Allah ya taqaita ya rangwanta maka kaga kenan tafiya bazata yuwu dakai ba kenan" "Toh da tunani nakeyi ma Baba ko zamu daga tafiyar zuwa idanna dan samu sauqi koda wani satin ne kona sama se muje" Khalil dinya fada se Baba Abu yayi saurin katse shi da cewa "Toh kuwa sedai ka tafi ka nemowa kanka auran da kanka, seda duk muka dakatar da abubuwan da suke a gabanmu saboda kai baka daukar komai da muhimmanci zaka ce a daga wani satin Aa wata shekarar za'a daga ba sati ba, Malam ka turo mana da kudin Mai kawai tunda Alhaji Garba yace a motarsa za'ayi tafiyar dan cin banzar baze yi maka yawa ba mu biya maka sadaki sannan muyiwa kanmu kudin motar zuwa nema maka aure" "Allah ya qara girma Baba zan tura yanzu harda wanda zaku sha ruwa a hanya ma duka" Khalil din ya fada yana murmushin rikicin Baba Abu, Hajiya dake sauraronsu dan a Speaker yasa wayar ta karba tana cewa "Rabu dashi Abubakar banda ma kace zaku tafi taren ai daman ku kadai za kuje, badan abun yazo a qurarren lokaci ba daman ai kamata yayi ya fara zuwa ya gaida su kafin yace ze tura iyaye, amma tunda sun yarda da hakan ma babu laifi Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya ya kuma saka a qulla Alkhairi. Ga kayan Lefe nan uwar Azarbabi Jalilah ta gama hadawa idan zaku hada dashi ku tafi toh suna can gidanta yanzu se ta kai gidan Alhaji Garban a zuba a Mota kawai gobe ku dauki hanya" "Aa wannan ta gaya mun ai har munyi magana da waliyyan yarinyar suka ce su basa karban wani lefe ya ajiye idan taje gidansa se ya bata to na gayawa Jalilan ai se ku barshi in dangin uwarta sunzo Biki a kai musu nan gidan Hajiua Hauwan ko tunda abune da akeyi ba ace a barshi ba, shi kuma ya samu man Tafarnuwa ya ringa shafawa qafar yana maganin sanyi se kuma ya rage zama cikin Ac nan tasu ta fama" "In sha Allahu, Allah ya qara girma, Allah kuma ya tsare hanya ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" Hajiya ta sake fada kafin Khalil ya karbi wayar suka sakeyin magana, so yakeyi ya gaya masa zancen wata shida da yake so a saka amma yasan Baban yanzu ze sake birkicewa amma haka ya daure yace masa "Baba nace idan sun tambayi lokaci asaka kamar wata shida haka" "Idan kuma basu tambaya ba fa? Kaga ka fita a idona in bamu fasa zuwa ba kace ba Abubakar nake ba" Baba Abun ya fada ze Khalil ya fashe da dariya yace "Allah ya huci zuciyar Babana" "Yauwa naji Alert yanzun nan inba haka babu inda zamuje sedai kayi ta zama da matarka me motsi akai" Baba Abu ya sake fada daga nan sukayi sallama. Dubu dari biyu ya turawa da Baba Abun daman yayi niyyar badawa kudin auran to sun biya masa dan haka ya maida musu sa sha Man dashi duk da yasan rigimar Baba Abu ce kuma daga qarshe dai in one way or the other se kudinsa sun sake dawowa. Hira sukaci gaba dayida Hajiya har qarfe goma kafin yayi mata sallama kamar karya tafi ya wuce bangarensu yana tafiya a hankali danya danji dadin Qafar bayandaya sha ya shafa maganin. Seda gabansa ya fadi daya tararda ita a falon shi yanzu baya son abinda ze saka su zauna guri daya da Umaimah balle har magana ta hadosu, tunda ya kalleta sau daya ya yi qasa da kansa yaci gaba da tafiya a hankali, muryarta yaji abazata tana ce masa "Yaya qafar?" Seya dakata a inda yake ya kalleta itama shi take kallo fuskarta babu yabo babu fallasa. Qasa qasa yace mata "Da sauqi" yaci gaba da tafiyarsa se ya sake ji tace "Ga abinci nan, Ruqayya bata nan Mamanta bata da lafiya taje gida Kaza na gasa mana se Tea". Kallon Mamaki ya sake yi mata a zuciyarsa yana qoqarin gano shin wannan shiri ne takeyi na wani abun ko kuwa har zuciyarta da gaske take be gama Mamakin ba yaji tana cewa "Nasan abubuwan da suka faru ban kyauta ba kayi haquri kuma da Safe zanje na bawa Hajiya Haquri itama sharrin shaidan ne". Ikon Allah wai na kwance ya fadi to meya samu Umaimah haka amma daya tuna jiya taje gidansu seya ta'allaqa hakan da cewar Tirsasata Mama tayi data basu haqurin. Ajiyar zuciya ya sauke kafinya juya akalar tafiyar sa zuwa kan Dining din ya zauna dukda baya jin yunwa amma ze cine saboda samun daidaito a tsakaninsu, tunda har aka ci Sa'a aka tan kwarata kuma ta biyu ta bashi haquri harda yi masa girki yana saka ran komai zezo da sauqi in Allah ya yarda koda ace maganar aurance ta taso zebi ta hannun Maman ne kawai ita ta sanar mata yasan zata fi shi sanin ta hanyar da zata lallashi Umaimah. Kwanon Kazar ya bude yaga ta yanki kusan rabi ragowar ta bar masa seya miqe ya wanke hannunsa a Sink ya zauna da bismillah ya fara cin Kazar bayan daya Hada Tea. Umaimah dake zaune tana kallonsa daga cikin Falon a fili tayi magana yanda baze jita ba tace "Zaka gane kurenka Khalil tunda har ka shiga gonata". Yana cin Naman wayarsa tayi qara ya daga ganin Anwar ke kiransa, speaker ya saka yana ci gaba da cin abincin dan ya saba yawanci a speaker yake amsa qaya shi bayan sun gaisa Anwar ya tambayeshi ya qafa kafin yace "Na manta har muka rabu bamuyi maganar zuwa Jalingo gobe ba koda yake ga qafa kuma anya zata yuwu?" Seda ya kalli bangaren da Umaimah take yaga hankalinta nakan Tv besan kunnuwanta na nan ta bazasu tana jiran taji dawa yake waya ba kafin yace "Tafiyar nan an fasa babu ita Anwar se wani lokacin idan Allah ya kaimu" "Toh, amma dai shikenan, Allah ya nuna mana lokacin yasa hakan shine mafi Alkhairi" Anwar da yayi niyyar yin magana ya fasa saboda tunawa da yayi da dabi'ar Khalil din kuma yaji maganar na dawo masa kar yaje ya kunno wutar da ba zata kasu ba. Sallama sukayi akan se gobe sa hadu a office idan yaji dadin qafarsa yaci gaba da cin Naman yana satar Kallonta be wani ci da yawa ba ya rufe ya wanke hannunsa ya koma cikin falon. "Har ka cinye" ta fada tana kallonsa seya zauna yana cewa "Aa kadan naci na rigada naci abinci gurin Hajiya, ko ajiye mun ragowar da safe se na qarasa". Shiru sukayi na dan lokaci ya canza tashar labarai yana kallo yaji ta sake cewa "Ka fasa tafiya goben kenan" "Eh wlh saboda ciwon qafar nan bazan iya dogon zama a mota ba, daman wani aiki muka samu zamuje dubawa amma na basu uzuri idan naji sauqi se muje ko kuma Anwar da su Patrick suje kawai" ya bata amsa yana duba wayarsa da yaji saqo ya shigo, Humaira ce ta aiko masa da wani zazzafan Text na soyayya ya karanta ya sake karantawa ya tabbatar wannan aikin Unaizatu ne seya maida mata da martanin "I love you, karkiyi bacci zan kiraki seki fadamun kalaman nan da bakinki bana son su a rubuce" "Ni kashe wayat zanyi ma yanzu, i love you more Gud nyt" ta maida masa itama yana karantawa kuwa ya shiga kiranta amma a kashe kamar yanda yace din ya daga kai yana murmushi ze dauki remote karaf suka hada ido da Umaimah da tun fara dannan wayar tasa take kallonsa. Duburburcewa yayi dan gaba daya ya manta da tana zaune a gun, ya saba zama a falonsa shi kadai shiyasa yanzu ma yaji kamar a can yake se ya shiga borin kunya dason kare kansa daga balahirar ta yace "Wani abu na gani a Twitter ya bani dariya" "Uhm" tace masa tana maida kanta kan tata wayar da suke chat da Safina tana gaya mata yaci naman, daman Yajin Maganin barbade kazar tayi dashi dan karma a samu akasi yace baze dan gwala da yaji ba dan haka yake wani lokacin. Khalil kuwa satar kallonta ya ringayi ganin bata kulashi ba yasa ya shiga WhatsApp, saqon Anwar ya gani yana tambayarsa da gaske an fasa zuwa nan yayi masa bayanin Su Baba Abu zasuje "I thought that bana so nayi subutar baki ko Sarautar tana kusa na tada Bomb shiyasa nayi shiru" Anwar ya tsokanesa, seya kalli Umaimah data dukufa tana danna waya kafin ya maida masa da cewa "Aiko da sedai na taho gidanka na kwana dan tana kusa kuma yai kaga abin Allah har girki tayi mun alamun ta fara sakkowa kenan kafin azo ayi fadan qarshe" Emojin dariya Anwar ya turo masa da cewar "Ai ko fadan qarshe a kashe Boss, Ni'ima na nan tunda na gaya mata zaka qara aure wai jira kawai take ranar tazo ta qagu taji ana bada labarin Abinda Umaimah tayi ta ringa cewa ai ta santa matar Abokin Mijinta ce" "Ni'imar nan taka is Sick Anwar, ka gaya mata babu abinda ze faru se Alkhairi jikina yana bani hakan" "I pray so Bro, ka ci gaba da Addu'a Allah ya kawo komai cikin sauqi, bari naje na lallaba Baby na tayi bacci Bye" Anwar ya maido masa da Amsa. Murmushi Khalil yayi ya kashe Datansa ya kalli inda Umaimah take yaga bata nan ta shiga daki kenan. Dakyar yaja qafarsa yana cije baki zaman da yayi yasa ta qara yi masa nauyi ya isa qofar dakin nata ya kwankwasa. "Come in" ta bashi amsa ya tura qofar da Sallama, tana kwance har taja bargo ta rufe jikinta saboda uban Ac data warewa dakin seya qarasa ya zauna gefen gadon yana cewa "Idan bazan takura miki ba zan kwanta a nan qafata ta matsa mun bazan iya hawa sama ba" "Mutum da gidansa se ya nemi izinin inda ze kwanta" ta bashi amsa tana gyra kwanciyarta, baya ta juya masa yayi murmushi kawai yana kallonta seya miqe dakyar ya wuce bandaki, alwala ya dauro ya dawo dakin, seda ya rage qarfin Ac kafin ya kwanta a gefenta yana sauke numfashi gaba daya qamshin turaren data saka ya dameshi ya nemi saka shi a wani hali. Kanta zuwa Bayanta ya shiga shafawa a hankali Umaimah dake jinsa tayi laqwam kamar me bacci, a hankali ya juyo da fuskarta, ta bude idonta cikin nasa da sukayi laushi, be bari tayi magana ba ya hade bakinsu ya shiga aika mata Kiss me zare lakar jiki. Yafi minti goma yana kissing nata tareda kai hannunsa jikinta yana ya mutsata, yayi mamakin yanda ta saki jiki sosai tana maida masa da martani da alama itama tayi missing dinsa, mantawa yayi da wani ciwo da qafarsa takeyi suka gurji junansu kamar babu gobe seda komai ya lafa munafukar ta juya baya tana wani muzurai. Haushin kanta ya kamata wai ya akayi ma ta wani sakar masa fuska har haka shi kuwa Khalil kallonta kawai yake yana murmushin rigimar Umaimah darunta se Allah. Haka ya doddogara yayi wanka yana jin yanda riqewar qafar ta sake haurawa har kusan qugunsa daya fito daga wankan kasa kwanciya yayi haka ya zauna yana shafa qafar, Umaimah data fito daga wanka itama ta kalle shi ganin yanda yake cije baki tace masa "Sannu, ko na dakko Aboniki na shafa maka?" "Da zaki iya akwai magani a dakina na shafawa ki dakko mun". Seda ta saka kaya ta tafi Saman ta dakko masa maganin ta bude hanci tana shaqar wani qauri da bata san kona menene ba kamar dai na magani. Baki ta tabe ta dauki abinda ya kaita ta kashe fitilun daya bari a kunne ta sauka qasan. Da kanta ta shafa masa, sun dade a zaune seda yace mata ta kwanta kafin ta kwanta dukda na bacci takeyi ba tana ta kallon yanda yake juya kai yana cije baki sosai tausayinsa ya kamata duk ita ta janyo masa wannan Azabar ai kuwa gobe dole Safina ta kira Malam ya karya abin nan ba zata jure har kwana uku tana kallonsa cikin wannan Azabar ba. Washe gari babu yabo babu fallasa ta ringa ayyukanta, ita ta shirya musu abin karyawa, ragowar Kazar ta sake dumama masa ta dafa shayi ta gasa masa buredi ita kuma ta dumama tuwo ta dama Koko dan yanzu su take jin dadin kari dashi. Falon qasan ma Sammani ta kira ya shiga ya share ya goge dan ba zata iya ba, tana ganin ma sedai ta nemo wata me aikin kawai tunda bata san sanda Ruqayya zata dawo ba. A gida Khalil ya wuni, tunda ya fita sallar Asuba ya dan tsaya bangaren Hajiya suka tattauna bayan sunyi waya dasu Baba Abu da suka dauko hanya se gurin bakwai ya koma bangarensu tun sannan kuma be sake fita ba seda zasu tafi Masallaci da Khalifa. Yaji dadin qafarsa harma ya manta da batun komawa Asibiti daya dawo daga Masallcin ma kuma gida ya sake zama saboda yau har yar hira sukeyi jifa jifa data kwanta bacci ne ya koma bangaren Hajiya se kusan qarfe biyar na Yamma su Baba Abu suka sauka Jalingo, sun yi waya dasu Khalil din ya sanar masa sun basu masauki yanzu sunce su huta, se zuwa dare zasu zauna da Waliyyan Humairan suyi abinda ya kawo su washe gari kuma suyi Asubanci su juyo Kano. Qarfe takwas bayan ya dawo daga Sallar Isha suna zaune a falon Hajiya shida Jalilah data zo gidan babu dadewa wai tazo jin yanda akayi a Jalingo Hajiya natayi mata fadan ta cika Azarbabi idan bata fita daga sabgar maganar auran nan ba ranta ze baci ita dai tayi shiru bata ce komai ba. Wayar Khalil dake ajiye kusa da ita ce ta dauki qara ta miqa masa tana cewa "Mansur na kira" ta bashi wayar seta miqe jin Hajiya na kiranta daga daki Khalil dake cin tuwo ya miqa mata hannu bayan yace ta daga masa, ya kara wayar a kunnensa yana cewa "Allah ya taimaki babban Yaya yau ka sauka daga fushin da kakeyi damu kenan ka kirani?" "Malam ba surutu na kira muyi ba number Matarka zaka tura mun yanzu dukda I'm not in support of abinda ya faru amma Alqawari nayi kuma ina so na sauke dan na gaya maka in Allah ya yarda duk randa ka qara aure ni zan fara breaking ma Umaimah labarin nan maza ka turo mun kafin wani ya rigani" Dariya Khalil yayi yace "Toh ai duk mugun halinka ka bari lokacin auran yazo ba ka kunnamun wuta tun yanzu ba daman cikinta nake na samu Allah ya kashe zaka sake tadota, har sun gama maganar kenan wata nawa aka saka Yayanmu?" "Wata ubanka aka saka dan iska kawai badai ka rantse seka saka qanwata a tashin hankali ba to kafin ta shigo kai zaka fara tarbar rabonka ni dallah turo mun number na kirata na gaya mata tun maganar da zafinta in yaso ta mutu aure dai an rigada an daura" Mansur ya sake fada se Khalil yace "Aiko bazan baka number ta na kuma san babu inda zaka samu dan ta canza layi ba kowa yake dashi ba, auran wa kuma aka dauka naji kana magana?" Tsaki Mansur yayi yace "Ko ban gaya mata ba zata ji ai nasan kuma ni zan fara fado mata a rai ko haka aka tsaya burina ya cika kai kuma Allah baka ikon yin Adalci dan idan kuka cutar mun qanwar kaida ita duk se naci ubanku" yana gama fada be jira Khalil yayi magana ba ya kashe wayar dan daman a fusace yake. Guda yaji an rangada saman kansa ya dago yana toshe kunnen Jalilah dake tsaye ta sake rangada wata gudar tana cewa "Alqawarin Allah ya cika aure kuma ya dauru yan baqin ciki sedai su mutu Humairah da Khalil Allah yayi mun nema kuma an bamu" yanda kasan wata maroqiya haka take maganar. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 68 JALINGO Ana kiran Sallar Magriba su Baba Abu suka isa gidan Alhaji Muhammad Jibril wanda yake matsayin yaya ga Mahaifin Humaira Marigayi Malam Nura Jibril kuma qani ga Mama Hauwa. Sun rigada sun san da zuwansu dan haka sun tanadesu, a matuqar gajiye dattijan suka zauna a katafaren falonsa inda aka ajiye musu kayan abinci nau'ika kala kala, ruwa kadai suka sha suka fita zuwa Masallacin dake qofar gidan a can sukayi sallah kuma a sannan suka fahimci Ahalin gaba daya suna zaune a unguwa daya ne dan tun a Masallin Alhaji Muhammad ya fara gabatar musu da yan uwansa wanda kamannin da suke kadai ya isa ya gaya maka alaqarsu mutane masu karamci. Cikin gidan suka koma bayan sunyi Sallah, Basa tare da yunwa sedai gajiya dan haka suka zauna a falon aka shiga sake gaggaisawa. Bayan gabatar da juna Alhaji Musa wanda shine babba a gidansu Maman gaba daya ya fara magana da cewa "Hauwa ta rigada tayi mana bayani akan shi manemin Aisha da kuma zuwanku, bamu da buqatar sake yin wani bincike akansa saboda a duniya mu zamu fara bada shaidar irin tarin qaunar da Hauwa takeyiwa Aisha tun mun kuma san ba zata taba yi mata zabin Mijin da bana gari ba, amma dukda haka domin mu sauke haqqin da Allah dora mana mun sake bincika wanene Ibrahim is aka sake yin wani katari ashe na gida ne domin Abokin aikin dan uwan mune gashi nan" ya Nuna Alhaji Muhammad se Alhaji Muhammad din yaci gaba da magana yana murmushi yace "Tabbas Khalil Abokina ne kuma qanina nafi shekaru biyar da saninsa mun hadu a qasar Africa ta Kudu lokacin da wani aiki ya kaimu daga nan alaqa me qarfi ta qullu tsakaninmu saboda kasantuwar harkar neman abincinmu daya, munyi kwangiloli da yawa tare kuma ya kasance mutum me Amana da kyakykyawar mu'amala shi yasa nayi matuqar farin ciki a lokacin dana fahimci shine manemin auran Yar dan uwana". "Toh masha Allah haqiqa munji dadi kwarai da wannan shaida da kuka bayar akan Dan mu ina kuma me qara baku tabbacin yarku ba zatayi dana sanin auran Khalil ba domin mutumin kirki ne ku da kanku da sanin nesa kukayi masa kun shaida hakan, sedai muyi fatan Allah yasa su zama abokan arziqi na har abada Allah kuma ya hada kawunansu" Alhaji Garba ya fada kafin yaci gaba da cewa "Ina ganin idan har babu damuwa zamu iya gabatar da abinda ya kawo mu saboda yanayin jiki da akwai gajiya tattare damu mu samu mu tafi masauki mu huta saboda Asubanci muke so gobe mu qarayi mu juya Kano, Alhaji Abubakar Bismillah". Baba Abu ya zura hannu a Aljihu ya ciro kudi badir yan dubu guda uku ya ajiye gaban Alhaji Musa yana cewa "A matsayina na waliyyin Ibrahim Khalil ina nema masa auran yarku Aisha wannan kudi Dubu Dari biyu kudin gaisuwar Iyayene dana na gani ina so, se wannan dubu dari kuma Sadaki ce kamar yanda waliyyinta Alhaji Muhammad ya yanka mana" "Amma Alhaji mun rigada munyi magana da kai cewar mu a qa'idar gidan mu bama karban wani dukiyar aure Sadaki ne kawai kuma mun yanka muku" Alhaji Muhammad ya katse Baba Abu se Baba Imrana yayi saurin cewa "Mun sani Alhaji amma muna neman alfarma tunda mun kawo ayi haquri a karba, Ya fa zaku bamu ina ganin ko Duk abinda muka mallaka muka kawo be kai mu biyaku karamcin da kukayi mana ba". Bayan Alhaji Muhammad ya karbi kudin ne Alhaji Musa ya sakeyin gyaran murya yace "Ba karambani ba duba da yanayin tazara dake tsakanin garuruwanmu da rashin tsaro da ake fama dashi ga kuma damar da tazo a kan gaba yasa nake tunanin tunda har mun samu daidaito kuma yarjejeniyar aure ta qullu a tsakani, me ze hana mu taqaita komai domin mu hutashshe ku dawainiya da sake dawowa harma da yin gayyar mutane zuwa daurin aure. Yanzu da yardar Allah idan an idar da Sallar Isha'i da akwai auren yar dan uwanmu da za'a maida a nan masallacin, ina ganin idan har babu damuwa daga gurinku dan mu a shirye muke in kun Amince a hada gaba daya ina nufin a daura auran ita Aisha da Ibrahim kaga mun sallameku Yarinya ta zama taku se ku koma can Kano ku yi shirinku duk sanda kuka so ku dauki Amaryarku a hannun Hauwa, muma daga nan sabga ta mata idan an tashi tariya suje suga mazauninta shi kenan ba se munyi rakiyar Kura ba kunzo kun koma ku sake dawowa sannan muma mu biku, zamu baku guri ku tattauna a tsakaninku yanda kukayi se muji". Shiru sukayi ganin waliyyan Humairan na shirin miqewa Alhaji Garba ya numfasa yace "Idan akayi hakan Alhaji zamu fi kowa murna to sedai wani hanzari ba gudu ba, bamu san shirin ma'aurin ba ina nufin ta bangaren gurin zaman ita yarinyar da sauran abubuwan buqata bamu da tabbacin ya tanade su amma hakan baze zama wata damuwa ba da yardar Allah, Abubakar seka kirashi ka sanar dashi halin da ake ciki Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" gaba daya suka Amsa da Amin. "Ai maganar muhallima nasan wannan ba matsala bace Lefe kuwa ya gama danma sunce kar azo dashi ne kaga babu wani abu da yayi masa saura inaga se zuwan Amarya kawai" Baba Abu ya fada cikin raha kafin ya shiga kira wayar Khalil sau biyu be dauka ba, jin fara kiran Sallah yasa suka fita. Masallacin ya cika danqam ciki da waje ba kamar yanda sukayi sallar Magriba ba Baba Abu ya kalli Angon da za'a maidawa aure da zugar abokansa ya cewa Baba Imrana "Kaga shirin Allah, qila da munzo dashi yayi mana taurin kai shiyasa can qafarsa ta riqe muka zo babu shi, Allah ya sanya Alkhairi yasa mutuwa zata raba. Bayan an daura auren suka niyyatu wucewa Hotel inda zasu kwana amma iyayen Humairan suka hanasu dan tuni an tanadar musu makwanci Abincin da basu ci bama can aka kai musu, duk wani abu da zasu buqata an tanada bayan sun dan sake taba hira suka barsu saboda su huta se a sannan Baba Abu ya kira Hajiya ya shaida mata, kasa magana tayi seda ya sake cewa "Hajiya ko bakya Ji nane" kafin ta aje numfashi saboda kaduwar da tayi da zancen daurin auran tace "Ina jinka Abubakar labarin ne yazo mun a bazata har na rasa abinda zance akai" "Me kuwa zakice muma duk haka abinya shammace mu kuma su da zasu bamu suka yanke haka kinga babu damar muce Aa se ya zama kamar ba dagaske muke neman ba fatanmu dai Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi kawai amma yanzu kuyi shiru da maganar karta fasu a Dangi tukunna har se mun dawo" "Toh ubangiji yasa hakan ya zama Alkhairi Allah ya basu zaman lafiya kuma yasa matarsa ce har gidan Aljanna" Hajiya ta fada daga nan sukayi sallama. Gaba daya rasa ta inda zata fara tunani ma tayi, an daura auran Khalil daga zuwa tambaya ta ina zasu fara fitar da wannan Labari har ya isa kunnen Matarsa a wane matsayi zata karbi abun? Jalilah ta kwalawa kira dan tanada buqatar wanda zasu shawarta tunda wuri, seda ta sauke tagumin data rafka saboda Jimami Umaimah kawai take tunowa a duk cikin al'amarin dalilin daya hanata yin murna da daurin auran gaba daya kenan. Bude baki tayi da kyar ta gayawa Jalilan yanda sukayi da Baba Abu, sak tayi da farko kamar bata gane abinda Hajiyar take fada ba kafin ta saki Kabbara ta waiwaya gabas ta tsugunna tareda kai goshinta qasa tayi Sujudushshukur seta miqe tana kallon Hajiyar bakinta kamar ze tsage tace "Kin gani ko Hajiya Allah kadai yasan sirrin daya boye cikin wannan auran Allah yasa silar fitar Khalil daga qangin rayuwar da yake ciki kenan" seta juya da sauri ta koma falo, a kan Khalil ta tsaya ta rangada masa guda tayi ta qarayi yanda kasan wadda ta kawo Amarya. KHALIL Kallon bakin Jalilah kawai yakeyi yana so ya tantance abinda take fada, wai shi Khalil take nufi an daura masa aure kowa? Maganar da sukayi da Mansur ta fado masa take ya hadasu da maganganun Jalilar lissafin ya bashi daidai da gaske kenan aurensa aka daura amma ya akayi hakan ta faru? Wayarsa ce ta sake daukar qara ya daga ganin Baba Abu ne kafinma yayi magana yace masa "Kai ina ka shige ina ta kiranka baka dauki waya ba ina fatan da kaji abinda ya faru ko? Toh daman kira nayi in ja kunnenka ko zaka fadawa matarka ka bari seda safe dan wlh babu ruwana ga Hajiya nan ka tambayeta sanda Nayiwa Zinatu Kishiya lokacin kana Ingila seda nayi sati daya a gidanku Hajiya ta bani Maboya kafin su Alhajin Gabas Allah yajiqan rai suka shiga suka sasantamu dan haka kabi a hankali" A hankali yace "Toh Kawu, nagode kwarai Allah ya qara girma Allah kuma ya dawo daku lafiya" "Ai dole ka gode mun mana dan qusa irin wannan cin bagas da kayi koda yake cikin iyayen yarinyar akwai Abokinka MJ yace sunan daka sanshi dashi seda safe ka dai ji abinda na gaya maka idan kuma kaudi ya kaika ka gaya mata shikenan". Mamakin MJ da Baba Abu ya kira ya kamashi tabbas MJ constructions dan Jalingo ne ashe sirikinsa nema be sani ba. Komawa yayi cikin kujera ya kwanta yana jin karadin Jalilah dake buge bugen waya lokaci daya yaji zuciyarsa ta washe wani farin ciki ya lullubeta, a fili ya yi Hamdala har sau uku seya sake daukar wayarsa daya ajiye ya shiga kiran layin Humaira amma harta katse bata dauka ba, ya sake kira karo na biyu bata dauka ba seya shiga rubuta mata saqo kamar haka "Nayi alqawarin zama mutum na farko da zanyi miki albishir din kin zamo tawa, dukda nasan kin rigani ji saboda abun ya shammacemu duka nida ke bazan haqura ba ina farin cikin sanar dake cewa kin zama matar Khalil, tun sanda nafara ganinki naji a jikina kedin Alkhairi ce a rayuwata. Ina roqon Allah daya sanya Alkhairi da Albarka a cikin tarayyata dake ina Alfahari da kasancewarki Mata a gare ni Humairata I love you moreee" ya hada da Emojis na heart da kiss ya aika mata. "Babana" Muryar Hajiya ta fito dashi daga shauqin daya tafi, jinsa yakeyi kamar bashi da sauran wata damuwa a duniya. Hasaso kansa kawai yake rungume da yar babyn tasa da ta zama halaliyarsa a sanda be taba zato ba duda yasan ze sha daru qarshema kacokan ta dora masa laifin cewar shiya saka a daura musu aure amma wannan duk me sauqi ne, burinsa shine auranta kuma Allah ya cika maaa sedai yayi fatan ta zamo Alkhairi a rayuwarsa. "Babana kaji lamarin ubangiji ko? ashe auran a kurkusa yake irin wannan rabon ne fa idan kayi ja'inja dashi se ayi babu kai? Hajiya ta sake fada se ya shiga shafa kansa ya kasa ma hada ido da ita wata kunyarta taji ta kamasa yanda kasan wanda ya kwana dakin Amarya kansa na qasa yace "Wlh Hajiya har yanzu mamaki nakeyi abin kamar wasa, Mansur ne ya fara kirana duk banma gane abinda yake cewa ba ashe ma Baba Abun ya kirani se yanzu muka sake yin waya dashi" "Haka yace toh ubangiji ya sanya Albarka Allah kuma ya kade fitina sedai ni yanzu babban tashin hankalina yanzu Khalil matarka ce ta yaya zata fahimci wannan al'amari?" Hajiya ta qarasa maganar cikin muryar damuwa. Kallonta Khalil yayi, tunda ya darsa qarin aure a zuciyarsa yana yawan Hasaso a yanda irin wannan rana zata riskeshi da kuma yanda Umaimah zata karbi Al'amari, kuma bisa mamaki se yaji sam hankalinsa be tashi ba farin cikin da yake ciki ya saka yake jin komai ma da zezo me sauqi ne, Allahn da ya qaddara faruwar auran shi ze wanzar da zaman lafiya ya kuma sanya mata dangana, yana fata yana kuma addu'ar Umaimah ta karbi abun da kyakykyawan tauhidi ta yarda cewar Allah ne meyi babu kuma wanda ya isa ya qetara masa iyaka. Ajiyar zuciya yayi ya kalli Hajiyar yace "Duk ma wani abu yanzu Hajiya ai daga baya ne aure dai an rigada an daura nasan zatayi tashin zatayi rigima zatayi duk abinda zuciyarta ta ingizata tayi amma na lokaci ne dole da kanta zatayi ta gaji ta kuma haqura tunda babu yanda zamuyi da abinda Allah ya qaddaro". "Hakane to Allah ya shiga cikin al'amarin ya kawo faruwar komai cikin sauqi, Abubakar dai yace kar a gayawa kowa to ita waccen uwar karambanin gata can ta gama gayawa yan uwanta dukda dai na tsawatar mata akanta gaya musu maganar ta tsaya iya mu cikin gidan nan, se kaje kayi tunanin ta hanyar da zaka fada mata wannan maganar amma ka bari ba yanzu ba mu jira har zuwa Allah ya rabata da cikin jikinta lafiya tukunna se ayi wacce za'ayi" Hajiyar ta sake fada. Shiru sukayi kowa da tunanin da yakeyi a zuciyarsa. Jalilah ta fito cikin shirin tafiya ta kalle shi tace "Ango kasha qamshi irin wannan murmushi tunanin me kakeyi?" Kallonsa Hajiya tayi yayi sauri gyara zamansa dakyau yana daure fuska tareda hararar Jalilan shi kansa besan murmushin da yakeyi a zuciyarsa ya fito fili ba ita kuma da bata gani tayi shiru shine se tayi magana "Da dai kin wuce kin tafi gida kina gani har goma saura" Hajiya ta fada swta yafa Mayafinta tace "Ai tafiyar zanyi Hajiya ni wlh tsabar murna ma ji nakeyi kamar nayi kwanciyata a nan nasan ko naje gidan ma ba iya bacci zanyi ba wlh Allah Allah nake gobe tayi in dawo" "Daman karki kuskura naga qafarki a gidan gobe bama gobe ba sati biyu nan gaba bama gayyarki kuma kin daiji abinda nace nasan Jamila da Amina basuda dan banzan surutu da neman magana irin naki, Habiba da Khalifa basu sani ba dan haka in har naji maganar nan a wani guri kece kuma se ranki ya baci" Hajiya ta fada seta zumbura baki ciki ciki tayi musu sallama ta fita, Jalilah na fita Hajiya ta kalli Khalil tace "Bi bayanta, Jalilah ba gudun magana take ba yanzu se kaji wani abun" Ilai kuwa yana fita a qofar shiga bangarensu ya tarar da ita tana kwankwasawa dan dazu daya fita ya saki Jamlock din "Me zakiyi a nan kuma?" Ya fada yana qarasawa seta kalleshi tana murmushi tace "Sallama zanyiwa Uwar gida yau duk bamu hadu ba tunda nazo" ya bude baki da niyyar bata amsa aka bude qofar Umaimah ta leqo ta saka dogon Hijabi qamshin turarebta ya bigi hancinsu. Qara washe baki Jalilah tayi tana kallonta tace "Uwargida sarautar mata ina wuni, ya jiki jiki? toh Allah raba lafiya". Tsaki Umaiman taja ganin itace ta juya ba tareda ta amsa mata ba Khalil ya ballawa Jalilah harara yace "Toh neman maganar taki be samu guri ba ki tafi dan Allah seda safe" "Korata kakeyi daga gidanka ko Khalil ai shikenan nida na sake taka qofar nan se randa na kawo Amarya daga nan se naga uban daya isa yamun iyaka da shiga gidan dan uwana "Allah ya bamu Alkhairi" ya sake fada yana jan hannunta kamar yar yarinya, seda ta shiga motarta Sammani ya bude mata Get ta leqo cikin shaqiyanci tace masa "Amma dai zakaje kadan ji dumin yar shilarka ko tunda Allah ya ceceka kaima dai yau ka canza ka rungumi sabon jini" "Allah ya shiga lamarinki Jalilah" ya fada yana dariyar dabe shirya ba, Jalilah shaqiyya ce ta gaske neman rigimarta kuwa besan a inda ta samo shi ba dan Babansu har yafi Hajiya sanyin Hali nesa ba kusa ba. Be koma bangaren Hajiya ba kai tsaye ya wuce nasu bangaren, be tarar da Umaimah a falo ba se Tv da take aiki ya shiga kitchen ya dakko ruwa ya fito kenan itama ta fito daga daki ta cire Hijabin, wata Bubu gown ce a jikinta pure cotton ta kwanta a cikinta sosai ya kalleta se yaga kamar cikin a karkace yake indai ba idonsa ne be gani da kyau ba. Fuska ta sake hadewa ta zauna a qasa sgi kuma ya hau kujera duk wata nutsuwa da yake da ita ya tattaro ya aza wa kansa dan baya so yayi abinda ze tunzurota balle har ta fahimci wani abu saboda Umaimah shu'umace, kamar me aiki da Aljannu yanzun nan tana iya karanto masa abinda yake cikin zuciyarsa. "Ka ja mata kunne wlh idan ta sake shiga sabgata ba zatayi mana da kyau ba daman bawai na haqura da abinda tayi mun bane danbata mari banza ba lokaci kawai nake jira da zan rama" Umaimah tayi magana seda ya gama sauraronta kafin cikin sanyin Murya yace "Allah ya baki haquri ba kuma zata sake ba Mari kuma da kaina zan rama miki karki damu" "Qaryar banza kawai, kumada take cewa zata rako Amarya duk yar abu takzan uban da tsautsayi yasa ta shigo gidan nan da ita da masu rakotan sedai a fita da gawayinsu danma mutum ya sani qonasu zanyi qurmus babu abinda ya shafeni" ta sake fada shidai shan ruwa yake kamar an sakashi dole ya sake ce mata "Ai kinci gida naki ne kiyi yanda kike si babu wadda zata shigo miki". Banza tayi masa ganin ta maida hankali kan Tv yasa ya miqe yana ce mata "Babu dan wano snack a gidan ne?" "Babu" ta bashi amsa kai tsaye ba tareda ta kalleshi ba, se yayi hanyar Bene yana cewa "Bari na duba Sama kwadayi nakeji nasan bazan rasa ragowar Biscuit din Bibi ba oh that's reminds me yaushe zasu dawo gobe fa akwai Tahfiz" "Na taba tambayar sanda zasu dawo idan sukaje gidan yan uwanka? Kasan dai ba cinye su za'ayi ba se ka jira goben tayi kaga ba'a dawo maka dasu ba kafin kayi magana uban yan son yaya" Umaimah ta fada a hasale tana kallonsa. Jiya da safe Maman Asad ta mata text a WhatsApp akan jiyan Birthday din UmmulKhairi Salman yazo ya dauke su da yake ana hutun makaranta shine kwana daya ze wani fara cigiyarsu se kace taga shi nasa yan uwan wata ranaana makarantar boko ma Jalilah daukarsu takeyi sedai su ringa zuwa daga can. Khalil kuwa sama ya wuce ba tareda ya tanka mata ba, seda ya kulle qofa da muqulli kafinya wuce Bedroom dinsa ya cire jallabiyyar jikinsa ya kwanta akan gado ya shiga sake kiran Humaira, daman babu wani biscuit da ze dauko yanda yaga yau har yar kwalliya tayi masa yasan yan mutunchin na kusa shi kuwa Muryar Amaryarsa kadai yake so yaji shi yasa ya nemi hanyar da ze samu space. A kashe yaji wayar tata, ya cije yatsa danba haka yaso ba, wata tsumammiyar soyayya yakeji yau din kuma so yake ya fara dora mata hadda da wuri dan baya so ta shigo gidansa da sauran ruwan yarinta a kwakwalqarta, so yake ta goge tas ta yanda zasu tsinki furen soyayya da allura, rayuwar auransa is just a fantasy which he wants to brought into reality yanzu yake so ya san yayi aure duk nutsuwar daya rasa a baya so yakeyi ya sameta shiyasa baze taba hada Humaira da Umaimah gida daya ba dan yanda bata kwantar da hankalinta ba babu yanda za'ayi ta bar nasu ya kwanta. Kwanaki biyu da suka biyo bayan daurin auren sosai alaqarsu da Umaimah ta sake gyaruwa, ta sakko sosai ta fara dawowa Umaimanta dan jiya Lahadi har Hajiya ta shiga ta gaida dukda bata jima ba Ita bata sake ba Hajiya kuwa jinin jikinta ne ya daskare har seda Umaiman ta fita kafin ta iya aje numfashi me kyau. Amarya Humaira kuwa wasan yar buya sukeyi dashi, washe gari Asabar daya gaji da kiranta bata dagawa ya tafi gidan Unaiza amma qememe taqi fitowa suyi magana har dakin da take ya shiga amma ta shige Toilet ta kulle kanta a bakin Unaizatun yaji kalar drama da sukasha jiya kuka da birgima ta ringayi wai an daura Mata aure da abinya ishi Unaizatu ta kira Mamaa speaker ta saka mata ita Mama cikin fushi tace mata "Toh tunda bakya sonsa bari yanzu na kira Baban naki ai daman yan uwannasa basu juyo ba kawai a warware auran shikenansu duba cikin yaransu a sake daurawa da wata kowa ya huta tunda ke bakya sonsa" se kuma rigima ta dawo sabuwa akan me Mama zatace Khalil ya saketa a aura masa wata a Jalingo, da dai sukaga lamarinnata yarinta neda shirme suka qyaleta tasha kukanta ta gode Allah ta haqura amma fa taqi amsa wayarsa saqon ma daya turo tana karantawa tana murguda baki kamar Khalil din ne da kansa tana gamawa kuma ta kashe wayar har washe garin yana zuwa gidan tana kwance da taji muryarsa da alamun ze shiga dakin ta runtuma Toilet ta kullo qofa taqi fitowa. Rarrashi babu wanda beyi mata ba amma taqi budewa daya gaji yace mata "Shikenan tunda ba zaki bude ba bari na tafi na koma gurin matata da take sona, nima fa auran ba wai ina wani sonsa bane da ace ma sun nemi shawarata kafin a daura zance musu Aa ba yanzu ba amma kin kasa fahimta se wani fushi kikeyi kina qin daga wayata na tafi kuma bazan sake dawowa ba". Taku yayi ya bude qofar ya rufe yayi saurin labewa a bayan Wardrobe a ransa yana addu'ar Allah sa plan din nasa yayi aiki aikuwa se gata babu shiri ta banko qofar bandakin ta fito tana waige waige, fita tayi daga dakin da sauri yaron Unaizatu ta gani a corridor ta tambayeshi Khalil shi da besan ma Khalil din ya shiga dakinta ba yace mata ai ya tafi ta kusa fashe da kuka harda shashsheqa ta juya dakin Khalil ya fito daga maboyarsa ya tsaya a bakin qofar tana shiga ya saka mata qafa gaba dayanta ta tafi zata fadi amma ya tareta ya fada jikinsa ya rungumeta irin rungumar da akeyiwa jariri sabon haibuwa. A kunnenta ya rada mata "Zan iya jure komai amma banda ki hanani jin muryarki da ganin fuskarki, I so much love you my little wife". Lamo tayi a jikinsa banda rawa babu abinda nata jikin yakeyi haka zuciyarta se bugawa takeyi da qarfi saboda tsintar kanta a sabon yanayin da bata taba shiga ba, hannunsa daya daya zagayeta dashi ya cire ya tallafo fuskarta amma taqi bari su hada ido sema ta kulle idanun nata ganin ya dage dole seta kalleshi, idonta a rufe ba tayi tsammani ba se jin saukar Cold lips dinsa tayi akan nata babu shiri ta bude idonta tareda zaresu Khalil dake kallonta da nasa ldon da sukayi laushi ya saki murmushi har sanna Lips dinsu na hade seya lumshe nasa idon ya shiga aika mata da wani passionate kiss me tafiya bisa umarnin zuciya be barta ba seda yaji numfashinta na barazanar barin jikinta, rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta yana sakin ajiyar zuciya a jere a jere dan dan wannan abun da yayi ba qaramin tayar masa da kwadayi yayi ba kuma dole ya hadiye abinsa kafin ya qarasa tsorata Amaryar tasa dan yanzunma se jan numfashi take tana qoqarin ture shi amma ta kasa. "Relax mana Aisha" ya fada a hankali kamar me magagin bacci seta dena tureshin da takeyi, zuciyarta fal cike da tsoron abinda Khalil din yayi mata ga wata kunyarsa da tayi mata rubdugu bata zaton daga wannan abun zata qara bari su hada ido dashi ita fa badan Anty Mariya matar da take zuwa gurinta gyaran jiki ta gaya mata ana wadannan abubuwan ba daman da cewa zatayi kawai Dan iska ne Khalil. "Idonki yana kyau idan kika tsorata" ya fada yana kissing saman idonta,Humaira dai taga abinda yafi qarfin qaramar Kwakwalwarta bata iya cewa komai se ido take wulgawa tana neman hanyar da zata tsere daga wannan tashin hankali daya sameta. Tafiya ya farayi da ita still a jikinsa ya zauna gefen gadon dakin tareda zaunar da ita akan cinyarsa, ta zabura saboda jinta akan wani abu da bata san menene ba "Me yasa kike fushi dani?" Ya fada yana sake zaunar da ita a jikinsa mutsu mutsu taci gaba dayi tana qifta ido tana so ta fashe masa da kuka seya jata jikinsa ya rungumeta yana cewa "Cry cry baby kinga abinda Allah yayi ko? Ba kuka zakiyi ba addu'a ya kamata kiyi mana Allah yasa hakan ya zamo mana Alkhairi sannan Allah ya bani ikon kulawa dake nayi miki Adalci. In sha Allahu ba zaki dana sanin aurena ba". Lamo tayi a jikinsa saboda duk maganar da yayi a cikin kunnenta ne kuma cikin wani sauti da ya saka gaba daya tsigar jikinta ta miqe, peck ya sakar mata a gefen kunnenta ta zille da sauri ta sauka daga jikinsa ta durqushe akan gadon seya miqe shima yana kallon yanda take rawar jiki kamar wadda zazzabi ya rufe a zuciyarsa yace "Akwai aiki". Bandakin data fito ya shiga, Humaira ta bishi da kallo kamar munafuka be jima a ciki ba ya fito yana goge fuskarsa suna hada ido tayi saurin juya masa baya ya qarasa inda take yana cewa "Zan tafi ki kunna wayarki". Shiru tayi bata amsa ba yayi taku biyu da niyyar riqeta ta duqe qasa tana yarfe hannu seya fasa ya juya yana murmushi dan idan ya biye mata za'ayi abin kunya. Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah ana maganar kwanaki biyar kenan da auran Khalil da Humaira wanda har zuwa yanzu Uwargida Umaimah bata san da wannan Al'amari ba. Sharafinta kawai takeyi saboda ta samu duniya yanda take da buqata Khalil ya dawo tafin hannunta juya shi takeyi son ranta haka zancen auran daya taso dashi ya mutu murus, koda wasa bata sake jin wani ya tayar da maganar ba haka nan shima tana biye da sawunsa kuma bata ga wata alama da take numa cewar yana tare da wata Mace ba. Abinda bata sani ba shine tsabar iya taku ne ya saka Khalil din ya koma mata yanda yake dukda ta wanni bangare tayi nasarar Samunsa amma fa ba kamar yanda take gani a zahiri ba irin biyayyar da yake mata da riritata da yakeyi damkar Jaririya duk yana yin hakan ne domin gujewa abinda ze kawo fasuwar sirrin da yake ta ririta yanda ze bayyana shi. Sabuwar waya ya siya da sabon layi kuma da ita yake amfani gurin kira ko chat da Amaryarsa wadda tun tana bore tana noqewa a yan kwanakin nan ya bude mata ido da soyayyarsa wanda tun kafin ta kai ga sanin inihin Khalil din bala'in kishinsa takeyi, idan suna tare dan kullu yaumin ne se yaje ya ganta idan yace mata ze tafi ta ringa fushi kenan tana tura baki tunaninta gaba daya tafiya yakeyi yanzu haka zeje yayi ta Hugging Anty Umaimah yana gaya mata kalamai masu dadi irin wanda yake mata haka zatayi ta baqin rai tana fushi Unaizatu dai sedai ta kalleta tayi murmushi a ranta tace "Yarinya dan ma baki san ainihin abinda ake yiwa Kishin ba kenan" ita dai ta dage tana gyara Humairan tareda koya mata duk wasu dabarun zaman aure da idanhar ta riqe su zata zauna lafiya da kowa". Tun zuwan da Khalil yayi ya kai mata madarar waken suya da akace tana qara qiba Unaizatun ta fahimci yana so Humairan ta murmure tafi yanda take batayi qasa a guiwa ba gurin Siyo mata ZUMAR QIBA A GURIN KHADYS EMPIRE ( 08147832793). Zuma ce gangariya da take ciko da jiki ya murmure ba qiba me yawa wadda zata saka muni ba tayi amfani da ita taji dadinta shiyasa saboda ta tabbatar da ingancinta sannan babu kwaya a cikin hadin zumarta kuma ta karbi Humairan nan da nan jikinta ya fara murjewa ta ciko ta qara haske saboda Hadaddun Mayuka da Sabulan da take amfani dasu ga qamshi duk inda ta gifta seta barshi tuni ta lura da Khali ya dena bari su kebe su biyu idan yazo a falo suke zama suyi hira a ranta tayi ta dariya tana cewa "Su Yah Khalil ana gudun abun kunya". Ranar da aka cika sati guda da daurin auran ta kama Juma'a, kamar yanda ya saba yana ya tashi daga Masallaci ko office be koma ba ya wuce gurin Humaira. Yunwa yake ji sunyi waya ya gaya mata dan haka tace zata hada masa Lunch, a cikin satin nan har wata yar qiba yayi ta kwanciyar hankali har tunani yakeyi shib baze yuwu ba aci gaba da tafiya a haka ba tareda Umaimah tasan da batun auransa ba? Shi a nasa bangaren bashi da Matsala tsaf ze iya dauke Humairan ya ajiyeta inda koda wasa Umaimah ba zata tana sanin da zamanta ba haka kuma ze iya takunsa kamar yanda yakeyi a yanzu ba tareda ta gano ko ta zargi wani abu ba amma matsalar yasan babu me bashi goyon baya akan hakan. Jiya seda Hajiya tayi masa magana akan ya kamata zuwa yanzu yasan matsaya akan maganar auran saboda sunyi waya da Mama Hauwa kuma a cikin hira ta kawo mata zancen son sanin inda ze ajiye Humairan saboda su san shirin da zasuyi nayi mata kayan daki. Rasa abinda ze cewa Hajiyar yayi a zuciyarsa so yakeyi yace mata ita da kanta ta sanarwa da Umaimah maganar auran idan wannan qurar ta lafa daga baya se azo ayi ta zancen inda ze ajiye amarya amma ya kasa. Jalilah tayi masifar tayi bala'in lusari ko ta kirashi yafi sau cikin kwando akan ya tsaya tsoron mace ya kasa tabuka komai, badan iyakar da Haiya tayi mata shiga sabgar gidansa ba da tuni ta fasan kwan kowa yaji amma ko yanzun lokaci ta basu idan taga sun gaza zatayi musu aikin dan babu yanda za'ayi a bar yarinyar mutane da aure yana zagayawa yana lalubeta ya kasa yin jarumtar da ze kawota cikin gidansa a cewarta kenan. A falo tayi masa masauki kamar koda yaushe, irin kwalliyar da tayi dole ya kasa riqe kansa a gaban Unaizatu ya rungumeta kunya kamar qasa ta bude ta shige ita kanta Unaizatun babu shiri ta basu guri ya zauna akan kujera kafin ya dorata akan cinyarsa yana kallon fuskarta da tasha light make up. Dinkin doguwar riga ne a jikinta na wani Burn orage din Lace ya karbi farar fatarta ya mata kyau mara misaltuwa ga qamshibta da yake gigitashi kullum suka rabu se yayi wankan turare a mota gudun kar yaje gida Umaimah taji wani qamshi na daban tsiya ta balle. A baki yau ta ringa ciyar dashi saboda gataz Khalil ya lalace a gurin yana kallonta kawai kamar wani soko, Allah ya sani dauriya yake ba yar kadan ba amma da tuni ya dade da daukarta sunje wani gurin ya kashe qishinta daya addabeshi amma bazeyi hakan ba, yafi so ta samu kulawa kamarta kowacce Mace me gata ya kwanta da ita a cikin gidansu kan Gadon auransu dalilin daya saka ya rage aikin daya dakko kenan a gidan da yake so ya ajiyeta, Bene yaso ya dora amma ze ja masa lokaci dan haka ya barshi a flat din da yake amma ya canza masa fasali kuma yana saka ran aikin ze kammala a qasa da watanni biyu in Allah ya yarda. "Wannan kallon fa haka kamar zaka cinyeni" Humaira ta fada cikin salon kissar da Anty Mariya da Unaizatu suke koya mata, seda ya gyara zama saboda yanda muryar ta shige shi kafin yace mata "Kyau kikayi mun ji nakeyi kamar na daukeki mu tafi kawai" "Mu tafi ina?" Ta tambayeshi tana bude ido seyaja hancinta yace "Gidana mana ko ba zaki bini ba?" "Aini banga alamar kanaso na kasance a gidanka ba dan babu wani shiri da naga kanayi" ta fada tana kallon gefe. Mamakin maganarta yayi se ya janyo wayarsa yana cewa "Waya gaya miki haka? Kin san yanda abubuwa suka faru so fast ban taba tunanin za'ayi haka ba amma kalla ki gani tuni har anyi nisa a gyaran gidanki ke baki san na fiki qaguwa da ki tare bako kawai dan kince ke ba zaka zauna da matata bane da kawai bangarena zan bar miki kiyi zamanki a sama" ya miqa mata wayar bayan daya kunna mata video aikin gidan da akeyi. Baki ta tabe bayan data gama gani ta sake cewa "Wancan ai gidan matarka ne kaima da kank kana fada kuma ni bana raba abu da wani na fison nawa ni kadai" "Gashi kuwa kin yiwa wata kwacen Miji" ya bata amsa cikin zolaya seta gimtse fuska tayi masa shiru wato abun ya motsa. "Haba mana karki bata ranki hak kawai muje ki dan rakani wani guri mana" ya fada yana jan kumatunta seta miqe ta shiga tattara kwanukan da yaci abincin. Bayan dogon gargadi da jan kunne data sha a gurin Unaizatu suka fita taren, gidan Jalilah yakaita data kwarzabeshi akan seya kawo mata ita zasuje a aunata ayi mata dinkunan fitar biki. A gidan ya barta saboda Anwar daya kirashi suna da wani emergency daga qarshe se Khalifa ya saka yaje ya mayar da ita saboda Magriba tayi kuma har sannan be gama abinda yakeyi ba. Yana komawa gida ya tarar da saqon Baba Abu da yaje be same shi ba, kamar yanda ya barwa Hajiya saqo cewar sunyi waya daga can Jalingo Alhaji Musa ya kirashi yana tanbayarsa gurin zama zasu siyawa yarsu Gado sun kuma tambayi Mama Hauwa ta sanar musu Basu rigada sun nuna guri ba dan haka ya kirashi da kansa dan yaji. Baba Abun ya bar masa sallahu bayan da Hajiya ta gaya masa shirin Khalil din na raba gida yana kuma kan aikin gyaran inda ze saka Amaryar ne. Baba Abu ya ringa fada yana cewa "Wane irin gurin zama kuma yana nufin duk girman gidan nan babu daki fmda ze sakata a ciki ina a can sama ma a kwai bangare guda nasa ko kuwa ita uwar gidan duk ta baza kaya a ciki? To idan ma ta baza se ya gaya mata ta kwashe dan ba zan dauki wannan sakarcin ba a bar yarinya qarama da aure wannan ai ba girma bane duk karamcin da iyayenta suka mana bayannaje na gama cika baki akan a shirye yake shine ze zo da wani sabon shaqiyancu? Ni wlh ban zata za'a ci kwana uku ma be san abinyi ba gashi har sun gaji sun magantu to yazo ya share mata daki a nan a basu suyiwa yarsu jere yawwa". Mamaki be kashe shi ba seda yaji cewar har a sannan matar gidan bata san da halin da ake ciki ba seya miqe yana cewa." Wannan kuma ya rage nasa da yasan be isa ba ya dakko abin Isassu? To ki gaya masa tun wuri idan ze ari Jarumta ya sanar mata yayi idan ba haka ba ni nan zanzo da kaina na shigo mata da Amaryar se muga qaryar boye boye, ki gaya masa na bashi daga nan zuwa rana irin ta yau Takwararki ta tare a dakinta idan ba haka ba kuma ze gamu dani". Da wannan maganar ya kwana a ransa, idan ta qure dole ya ajiye Humaira da Umaimah a gida daya na wani lokaci amma ta yaya yanzu ze sanarwa da Umaimah wannan al'amari? Shine babban tashin hankalinsa da tunanin yake kwana yake tashi a kullum kuma ya tabbata dole komai dadewa maganar zata fito idan be gaya mata da kansa ba Baba Abu ya shammaceshi kamar yanda ya fada ya kuma san ze aikata kai qaramin abu ne daga ayyukansa ma. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 69 Yanda yaga rana haka yaga dare washe gari kuwa qarfe shida ya fita daga gida bayan ya shiga bangaren Hajiyarsa ya sakeyi mata magiya akan ta kira Umaimah da kanta ta gaya masa maganar auran. "Babana kaida kake Mijinta ka kasa gaya mata se ni kake so na debi baqin jini bayan wanda na rigada nayi? Idan ba zaka iyaba ka kira Jalilah nasan da murna zatayi maka wannan aikin amma ni kagan ni nan idan ka shirya gaya mata ma ka sanarmun dan na bar gidan ranar kar tsautsayi ya rutsa dani" amsar da Hajiyar ta bashi kenan se kawai ya zabi daya bar gidanya tafi can wani gurin ya samu damar yin tunani da kyau. Can kan hanya ya samu inda babu hayaniya ya faka motar ya lula cikin tunani. Duk Abokanansa daya nemi shawara amsa daya suke bashi akan wai ya sameta suyi magana ta fahinta ya nuna mata qaddara da muhimmancin yarda da ita sannan ya nuna mata cewar beyi aure danya wulaqantata ba ta qaddara cewar Allah ne ya hukunta faruwar hakan kuma ba zaka tsallake ba to idan banda abinsu a yaushe a kuma wanne lokaci zata samu nutsuwar fahimtarsa? Ya tabbatar daga inda ya faro mata wannan nasihar tasan inda ya dosa ba duk kuma abinda ze biyo baya ya tabbatar da be me kyau bane. Allah sarki Yaya Aminu, da ace yana raye kai tsaye gurinsa ze tafi ya kai kukansa kuma ya share masa yau gashi baya nan a lokacin da yake tsananin buqatarsa ya kuma kasa zama Jarumin da har a maganarsu ta qarshe seda ya goranta masa. Shi dai indai a gurin Umaimah ne baya zaton ze taba zamowa wannan Jarumin yanzu bayan Yaya Aminu se waye fada mata taji kuma tayi babu ja'in ja? Mama Malika ce ta fado masa a rai, sosai kuma yayi na'am da shawarar zuciyarsa dukda wani bangaren yana so ya hanashi dalilin nauyi da kunyarta da yake nema ya kamashi. Yana ganin rashin kyautawar ba iya Umaimah yayiwa ba ita kanta Maman abin ya shafeta amma dukda haka uwa uwa ce yasan kuma a karamci irin nata ita kadai ce zata fahimce shi kuma ita take da kalaman Ladabtarwa da zatayi amfani dasu gurin kwantar masa da hankalin Umaimah. Tayar da motar yayi kai tsaye ya kama hanyar gidansu Umaiman, be damu da lokaci ba da kuma kasancewar ranar Asabar qila mutanen gidan basu tashi ba haka yayi musu tsinke yaci sa'ar tarar da Salman a qofar gidan ze fita makaranta yana da Test, shi ya koma yayi masa iso ciki bayan sun gaisa Mama dake tsakar gida tana aikace aikace ta tsaya a gurin gabanta na faduwa jin wai Khalil ne yazo da safiyar nan daman daren jiya tayi mafarki da Umaimah, yanzu niyyarta idan ta gama abinda takeyi tabi Abban idan ze fita ya sauketa gidan Umaiman ta dubata dukda se kuma ga Khalil da farar safiya, Allah yasa lafiya. Har qasa ya durqusa ya gaisheta ta amsa masa cikin dattako, yanayin da ta ganshi a nutse beyi kama da wanda wani mugun abu ya faru a gidansa ba ya sa hankalinta ya dan kwanta. Falonta ta bude masa suka shiga, yabi gurin da kallo dakin Dattijuwa kenan ko ina qal qal anyi shara an goge ga qamshin turare yana tashi ita kanta Maman dukda Dogon Hijabi ne a jikinta amma yanayinta ya nuna tayi wanka shiyasa be taba alaqanta qazantar Umaimah da kowa ba, Ya shaida Mamanta me tsaftace, haka duk yan uwanta babu wadda ya taba zuwa gidanta ya tarar da abinda ba haka ba. They are super neat gashi sun iya girki ita kadai ta fita zakka dalilin dan banzan son jiki data dorawa kanta da waya data aura, ita take hanata komai ta wuni tana Chatting da mutanen banzan da babu abinda suka qareta dashi se qara jefata cikin Jidali. Fita Maman tayi bayan ya zauna bata dade ba ta dawo dakin ta Flask din ruwan zafi Sharifa na biye da ita da Try da aka dora kuloli qanana guda biyu da kofi da cokali ta ajiye gaban Khalil din tana gaishe shi Mama ta qarasa ciki ta dauko container Sugar sannan ta zauna tana cewa "Kunun gyada ne ga qosai ga doya nan se ka saka wanda zaka ci, yau da muri mukayi abin karin saboda yara masu zuwa Tahfiz" "Nagode" ya mayar mata kansa a qasa yana ayyana ta yanda ze fara gaya mata abinda ya kawo shi, se Mama ta miqe da niyyar ta bashi guri tace "Bari na duba Abban naku naga ko ya tashi se ka shiga ku gaisa" tana gama fadar haka tayi waje tasan magana ce ta kawo shi koma wace iri ce tana fatan ta zama ta Alkhairi. Sanda ta isa bangaren Abban ta taraddashi a falo yana duba wani Littafi da yake rubuce rubucen Cinikayyarsa ta zauna a kan Kujera, seda ya qarasa kwafar abinda yake nema a takadda kafin ya rufe ya kalleta cikin raha yace "Hajiya Malika irin qamshi haka tun daga waje na jiyo shi nace Sarauniya ce tafe" Murmushi tayi masa tace "Yau kuma da zolaya ka farka kenan" "Ba zolaya bace kema ai kinsan gaskiya ne azo a sammin turaren nima an jima zanje Daurin aure, ya maganar fitar taki kuwa tana nan? Koda yake ya kamata kije ki dubota dai gaskiya mu fita da wuri saboda nima na dan tsaya mu gaisa kafin na wuce daurin auran" Abban ya sake fada se Mama ta gyara zama tace "Ai yanzu ma abinda nazo na gaya maka ga Mijinta can yazo dukda dai banga wani alamun tashin hankali a tare dashi ba na tabbatar dai zuwan bana haka kawai bane idan kayi duba da lokace, takwas ma bata cika ba ace Khalil yazo gidan nan kuma shi kadai ai da magana" "Tohh Allah yasa lafiya, kije kiji abinda yake tafe dashi idan kuma ya shafeni toh se kuzo nan din nima naji" Seta miqe tana cewa "Wane irin idan ya shafeka kai ko abu ya shafa dumu dumu dan kasan babu abinda ze kawoshi gidan nan se maganar Umaimah kaga kenan kai keda ruwa sa tsaki a ciki". Sanda ta koma Dakinta ta tarar da Anty suna gaisawa da Khalil din, bata shiga ba ta tsaya daga bakin qofar tana kallon kayan abincin da be taba ba tace "Ka qaraso Alhajin ya tashi" seya miqe kamar daman jiran umarninta yakeyi ta matsa masa yayi hanyar dakin Abba ita kuma ta tsaya amsa Anty dake tambayarta lafiya dai ko "Lafiyar kenan" ta bata amsa kai tsaye tana bin bayan Khalil din. A mutunce ya gaida Abba ya amsa masa yana tambayarsa su Hajiya se sukayi shiru gaba daya kafin Abban ya sake cewa "Malam Khalil lafiya dai ko muka ganka da safiya ko mutuniyar ce tayi bore?" Khalil dake zaune a qasa ya sosa kansa idanunsa na kallon qasa dan sosai yake jin nauyin abinda ya kawo shi amma bashi da wata mafita idan basu din ba, maganar Abba ce ta katse masa tunani da yake cewa "Ka saki jikinka kayi magana Khalil kar kace zakaji nauyi ko wani abu" se Mama ta amshe da cewa "Nasan dai baze wuce wani shedancin ta sake yi maka ba to ka bude baki kayi magana idan kuma kana jin nauyi ka kasa fada yanzu daman da niyyar zuwa gidan naku na tashi yau zanje na titsiyeta ita ta fadamun da bakinta me tayi tunda dai ita kunnen qashi gareta idan kuma aka jita shiru to wata tsiyar take qullawa" "Aa Mama wannan karon ni nayiwa Umaimah laifi ba ita ce tayi mun ba shiyasa ma nazo gabanku da qoqon bara dan ku shiga cikin Al'amarin ku tayani shawo kanta tayi haquri" Khalil ya fada a sanyaye ba tareda ya daga kai ya kalle su ba, shiru sukayi gaba daya ya tabbatar a zukatansu mamaki sukeyi suna kuma ayyana wani laifi yayiwa Umaimah da har yake neman su shiga ciki. "Ikon Allah, wane laifi kayi mata haka da har se mun shiga ciki zata haqura? Koda yake a kafiya da dan banzan rashinji na Umaimah na tabbata qaramin abu ta dauka ta maida babba saboda ta hanaka nutsuwa irin yanda ta saba to zata ci gidansu kuwa zanje gidan" Mama ta sake fada se Khalil yayi qundum bala cikin karyayyar murya yace "Aa Mama dagaske a wannan karon nine mara gaskiya kuma ni nayi mata laifi, laifi babba da na cancanci ko wanne irin hukunci daga gurinta amma wlh nima ba laifina bane tsarine daga ubangiji wanda babu yanda na iya akai" se Mama da Abba suka kalli juna kafin suka sake kallon Khalil daya ci gaba da cewa "Ban sani ba Mama ko ta gaya miki zancen ina neman aure tun kwanaki dan a sannan mun dan samu matsaloli da ita ta kuma nuna rashin amincewarta a lokacin har Hajiya ta goyi bayanta akan na haqura da batun auran tunda bata so to wlh Mama nima bansan yanda akayi ba, kawai na dauki duk abubuwan da suka faru a matsayin qudurace daga ubangiji wanda yake aiwatar da abinda yake so a kuma sanda yaso" tiryan tiryan ya labarta musu abinda ya faru dama matsayin da ake ciki a yanzun ya qarasa yana cewa "Wlh Mama bani da wata masaniya akan haka ze faru kuma da ace sun sanar mun kafin su kai ga daura auran zan dakatar dasu saboda ban shirya ba amma Ubangiji ya rigada yayi nasa tsarin ba kuma ni da wani abu daya bi bayan na karbi abinda aka rubutamun". Kallon Khalil sukeyi gaba daya harya kai qarshen dogon bayanin daya dakko, Mama dai tsam tayi a inda take kalmar aure tana mata yawo a kwakwalwa yana nufin yayiwa Umaimah kishiya kenan, Abba kuwa gyaran murya yayi kafin yace "To Alhamdulillahi Khalil ina tayaka murna bisa wannan abun Alkhairi daya sameka Ubangiji ya Albarkace ku gaba daya ya kuma baka ikon yin Adalci a tsakaninsu, yanzu abinda ban fahimta ba anan shine laifin menene kake iqirarin kayi mata da har taqi haqura?" Sake sunkuyar da kansa qasa yayi yana ajiyar zuciya saboda fitar da abunda ya tokare masa maqoshi ya hanashi nutsuwa da yayi se ya bude baki a hankali yace "Nayi aure ba tareda saninta ba kuma wlh Abba nima..." "Kai da Allah wannan rantse rantsen ya isa haka, kamar yaya kayi aure bada saninta ba? Ita zata nemo maka auran ko kuma ita zata baka muhalli da abinda zaka ciyar da matar da dole se ta san abinda kake ciki? Sannan yanzu kake cewa tasan zakayi aure har kunyi rigingimu Mahaifiyarka tace ka haqura to Ubangijin daya halasta maka yin qarin ya nufa se kayi se akayi Yaya kuma Umaimah ta isa taja da hukuncin Allah ne, aure an daura Mata ta tare a gidanka to kuma duk tashin hankalin na menene yanzu?" Abba ya katse Khalil ita dai Mama kallonsu kawai takeyi tana kuma jinsu amma ta gaza ce musu komai. Harga Allah a wanann gabar tausayin Umaiman seda ya kamata a matsayinta na mace ta saka kanta a matsayin ita akayiwa haka dole abin da ciwo musamman a gurin wadda take tsananin Adawa da tsarin zama da wata kamar Umaimah, tabbas dole Khalil ya rude ya kuma tsorata akan rashin sanin yanda zata karbi Al'amarin. "Aa Abba Amaryar bata tare ba kuma a yanzu maganar da mukeyi ita Umaimah bata san da zancen auran ba na rasa ta yanda zan gaya mata saboda bansan a yanda zata dauki al'amarin ba Allah ya sani ina sonta kuma ina gudun bacin ranta musamman a wannan Halin da take ciki bata buqatar jin wata magana da zata tayar mata da hankali shiyasa naso ace har se zuwa bayan ta haihu sannan zan gaya mata amma jiya Baba Abu yazo akan iyayen yarinyar sunyi magana akan a nuna musu inda zata zauna, yayi ta fada ya kuma jaddadamun idan banyi wani abu kafin cikar sati daya ba to shi da kansa ze dakko Amaryar ya kaiwa Umaimah". "Zancen banza ma kenan yanzu kana nufin yarinyar tana gidan iyayenta kenan saboda kana tsoro ka gayawa matarka tayi tashin hankali ka gwammace ka fara nuna rashin Adalci a tsakaninsu tun gabanin su zauna tare ko? Dan ubanta ita ba'a aure ka aureta kake kuma zaune da ita duk mugun halinta shine har zaka gwammace ka cutar da wata saboda kar ran Umaimah ya sosu to yanzu da menene shirinka? Idan iyayenta basuyi magana ba kenan haka zaka bar musu ya tayi ta zama da aure akanta ko?" Girgiza kai yayi kawai saboda jin yanda Abban yake magana cikin fusata se yaci gaba da cewa "Saboda Allah Khalil se yaushe zaka zama namiji a cikin gidanka? Kayi aure haka Allah yaso kaima ba tsarinka bane se kuma meya faru da bazaka iya zaunar da ita ka gaya mata ba har se kazo kana rara gefe kana neman wanda ze tayaka gaya mata ita ba musulma bace ai tasa san lamarin aure abune da babu me shiryashi haka babu me hana faruwarsa idan Allah ya kawo shi shi se anyi babu makawa ni gaba daya ma kai ka bata mun rai yanda kake wani karya murya kana fadar kayi mata laifi cika umarnin ubangiji ne laifin da kayi mata kome? To ko Abubakar be dauki Amarya ya kai mata ba ni ubanta zanje da kaina na dakko yarinyar na kai cikin gidan domin duk muna da Yaya idan kuma wani ya aure su ya jingine mana su haka ba zamu ji dadi ba dan haka babu ta yanda za'ayi mu bada goyon baya ayiwa yar wasu haka. Ka tashi ka tafi duk ma yanda zakayi a yau ka sanarwa da Umaimah kayi aure kuma idan har iyayen Amaryar a shirye suke a gobe su kai yarsu dakinta babu abinda za'a jira zan kira Abubakar din yanzu ina gaya masa" Abban ya qarasa maganar a fusace se Khalil ya daga kai ya kalleshi yana zare ido jin wani zazzafan hukunci daya zarce na Baba Abu. Shida ya rugo gurinsu da fatan samun Agajin gaggawa amma shine za'a sake yi masa turin jeka ka mutu da wane qarfin guiwar ze doshi Umaimah kai da Alama Abba ya manta akan wa ake magana gaskiya. Maganar Mama Malika ce ta cece shi da taja numfashi ta ajiye tace "Alhaji da akalama baka fahimci abinda yake nufi ba, aure fa aka daura masa yau sati daya Matarsa bata da labari, kamar ka manta wadda ake magana akai kake cewa gobe zaka saka akai yarinyar mutane gidan haba Alhaji kadai tsaya ka duba wannan abu dakyau tabbas qarin aure ba laifi bane amma yanda al'amarin ya afku kowa cece hakan ta fada akanta dole taji babu dadi kuma zata buqaci a bata lokaci ta samu nutsuwar zuciya" Wani Kallo Abban dake danna waya yana neman number Baba Abu ya watsa mata kafin yace "Tunda batun kishiya akayi ai dole yau ki rikida kibi bayan yarki, duk iya shegen da ta ringa tata masa ina keda bakinki kinsha ce masa yayi auran ashe duk maganar ba taje zuci ba kenan iya fatar baki kike yinta yanzu kuma da ubangiji ya zartar da hukuncinsa zaki ce wani ba'a kyau ba saboda ku mata akan kishiya duk bakinku daya toh aure dai an daura amarya kuma zata tare a gidan Mijinta kuma dole tayi haquri ta karbi qaddara a yanda tazo mata yawwa" yana gama fadar haka ya miqe yana sake jaddadawa Khalil akan ze kira Abubakar. Dakinsa ya shige ya bar Mama da Khalil daya zabga tagumi dana sanin zuwa gidan ya kamashi tunda gashi ya zama sanadin da Mata da Miji auran sama da Shekara Arba'in suna Musayar yawu a dalilinsa. Kallonsa Mama tayi cikin sanyi tace "Kace bata san da kayi aure bako?" "Bata sani ba Mama kuma wlh ni ban boye mata da wata manufa ba tsoron yanda zata karbi abun ya saka har yanzu ban gaya mata ba, kuma auran a yanda ya faru nima babu sanina a ciki Allah ne yayi" Khalil ya fada cikin yanayina karaya se Mama ta daga masa hannu tace "Na sani Khalil kuma koda kayi hakan da niyya ba kayi laifi ba, Umaimah tayi maka abubuwa da yawa da ta cancanci hukunci amma ka haqura ka jure, yanzu da ubangiji ya saukar da qudurarsa yayi mata sakamako da abinda take qi wanda shine silar duk abubuwan da ta aikata hausawa sukace gudun qaddara guzurin taradda ita ai ba yinka bane yin Allah ne kuma bata isa taja da hukuncinsa ba dan haka duk abinda zatayi dole tayi ta haqura, babu damuwa yanzu kaje gida kamar yanda Alhaji ya gaya maka ka sameta kayi mata magana ta yanda zata fahimta, nasan abin da wahala amma ciwon da zataji idan ta tsinci maganar a bakin wani ze ninka wanda idan kaine da bakinka ka gaya mata in sha Allahu kuma ina fatan ta karbi qaddararta da kyakykyawan yaqini, yanzu kaje gidan jimawa kadan idan Allah ya yarda zanzo". Kallon Mama yake da idanunsa da suka bayyana tsoro qarara kamar ba Namiji ba yace "Wlh Mama bazaniya ba, ranar dana gaya mata ina neman aure a mota muna tafiya ta fizgi kan sitiyari badan muna da sauran kwana a gaba yanzu da wata maganar akeyi, kiyi haquri Mama bana nufin cin fuska a gareki amma Umaimah bata da tunani akan Halin kishinta idanunta rufewa sukeyi a shirye kuma take da tayi fito na fito da kowa da komai haka duk matsayin mutum bata tunawa a sanda zuciyarta ta qeqashe, ta rantse mun yafi sau nawa akan seta kashe duk wadda tayi gangancin aurena. Ni kaina tasha maimaita mun cewar zata kasheni kuma ta kashe kanta ina tsoro Mama ina tsoron kar wani abu ya sameta a yanzu bazan yafewa kainaba saboda nine sila" ya qarasa maganar kamar ze fashe mata da kuka Mama kuwa tsabar kidima kasa ce maaa komai tayi se dafe qirji tayi da hannu biyu tana kallonsa. Tabbas a halin da Umaimah take ciki bata buqatar tashin hankali ballan tana taji baqin labari akan abinda idan aka ajiye mata zabin mutuwa ko kishiya tabbas zata iya zabar ta mutu da dai ta hada Miji da wata yanzu yaya zatayi ta fahimtar da ita ta kuma samu ta sassauta zuciyarta ta karbi abun da kyakykyawar zuciya? Numfasawa tayi ta kalli Khalil dake zabga zufa tace "Babu abinda ze faru da yardar ubangiji kaje gida zanzo din" "Toh Mama" ya fada yana yunqurawa, yanda kasan kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya ringa tafiya ji yakeyi gaba daya ma kamar ya sake dagula komai. Khalil na fita Mama ta miqe cikin sanyin jiki ta iske Abban a daki yana waya data tabbatar da Baba Abu qanin Mahaifin Khalil ne bayan ya kashe wayar ya kalleta fuska a daure yace "Ya akayi?" Seda ta zauna a gefen gadon kafin tace "Alhaji ina ganin kamar yanda yaron nan ya fada da za'ayi haquri zuwa ta sauka saboda kaga ba'a so me ciki ta ringa fuskantar tashin hankali. Sannan idan ka kalli Ita Umaimah a karan kanta ba abune me sauqi a gurinta ba aje mata da maganar kishiya, a baya kasan duk abubuwan da suka faru, a wai wai take jin Mijinta yana kulasu kaga irin tijara da diban Albarka babu wanda bata yiwa yaran mutane ba haka shima Khalil din be tsira ba, yanzu haka yace tace zata kashe duk wadda ta aure shi, ban yarda zata aikata ba amma zuciya sharrinta yana da yawa musamman idan ta hadu da fushi, gudun kar azo ana abun da be kamata ba kuyi haquri a barshi ya raba musu gida kamar yanda ya tsara wata biyun kamar yau ne hakan ze rage kaifin duk wata fitina da zata taso sannan ita kanta yarinyar se tafi samun nutsuwa dashi" "Yaushe kika zama me son kai Malika? Yanzu a duniya har akwai abinda Yaron nan zeyiwa Umaimah da zakiga rashin kyautawarsa? Nawa tayi masa kafin wannan kuma idan kika kalli abun nan meye ma laifinsa a ciki? Daman ita jarabawar ubangiji babu ta inda bata zuwar wa mutum, Allah yakan jarabceka da abinda kake so kamar yanda shi ta zamar masa jarabawa haka nan idan yaga dama ya jarabceka da abinda kake qi ga Misali nan akan ita Umaiman dukka idan skayi haquri kayi tawakkali se kiga ka dace da rabauta a duniya da lahira kawai abinda ya rage miki a matsayinki na uwarta ki nuna mata muhimmancin haquri da tawakkalo sannan ta maida lamarinta ga Allah duk wani tashin hankali da zatayi babu abinda ze canza, babu wanda yasan Abinda Allah ya boye game da wannan auran idan ta matsa rabo yayi Ajalinta ai shikenan". Yanda Abban yake magana tamkar babu abinda ya dameshi, ganin baze fahimce ta ba yasa ta fita ta bashi guri jiki a matuqar sabule ta qarasa ayyukan da zatayi duk yanda Anty take ta rara gefe da son jin meya faru tayi mata banza, karyawar da bata iya yi ba kenan ta zauna jiran ya qarasa abinda yakeyi su fita fatanta Ubangiji ya sanyaya Zuciyar Umaimah ya bata haquri da juriya akan wannan al'amari daya fado mata. Ita kadai ta fita saboda Abba wasu maqotansu da sukazo gurin Abba dan su tafi daurin auran tare da yake bikin Yaron wani maqocinsu ne ada dukda ya tashi daga layin amma har yanzu suna zumunchi sosai musamman shi Abba da yake kasuwarsu daya dan haka yana gaya mata uzurin nasa yace ko zata jira ya dawo tace Aa haka kuwa akayi da wuri ta fita dan ta rigashi barin gidan. Kai tsaye gidan Qanwarta Laure data daura aure babu jimawa satinta uku da tarewa kenan ta nufa. Sama sama suka gaisa da Angon Anty Lauren daya bude mata qofa,ta kalli qanwar Tata data ci uwar kwalliya da qananan kaya yanda kasan wata Titin Lagos ita a dole ga Amarya wani sabon takaici ya qumeta taja tsaki ta zauna akan kujera kawai ta rafka tagumi, data Sani Hafsa ta kira ko Hajiyayye sukaje tare. Anty Laure ta kawo mata ruwa da Lemo ta zauna tana cewa "Bari na soya miki Kwai akwai ragowar Dankali yanzu muka gama karyawa amma Yaya irin wannan zuwa da safe babu sanarwa lafiya dai ko?" "Ba lafiya na Laure, yanzu dai tashi ki cire wadan nan abun dan Allah ki saka suturar arziqi rakani gidan Umaimah zakiyi" "Kin san dazu nake zancen yar banzar yarinyar nan a raina rabona da ita tun ranar daurin aure kowa yazo yaga gida ya mun murna banda ita halan ta haihu wannan ciki dai ko na Aljanu ne ya isa a haifeshi haka dai" Anty Laure ta fada se Mama ta miqe tana cewa "Laure ki tashi idan kuma ba zaki samu zuwa ba in tafi ni kadai" "Wai Yaya lafiya kuwa?" Anty Lauren ta sake fada ganin Maman na shirin tafiya ta wuce daki tana cewa "Yi haquri bari na shirya, da dai Yallabai yace bacci zamu koma amma wata kusan ai tafi wata". Tsaki Mama taja abin takaicin Laure yawa ne dashi, wani abu take yanda kasan ba ta taba aure ba ita idan ta kallesu daga ita har Mijin nata ma haushi suke bata. A motar Mijin Anty Laure suka fita, a taqaice Mama tayi mata bayani a hanya Anty Laure data kusan sakin sitiyari ta gangara gefen Titi tana salati tace "Yaya kice Khalil ya taro mana yaqin duniya na uku ni Lauratu naga abinda ya isheni wannan wace kalar jaraba Khalil ya janyo mana yaje yayi aure bata sani ba dan ubansa a ina aka taba haka? Nidai wlh da kin gaya mun tun a gida daman bazab biyo ki ba, nifa nasan Tijarar Umaimah sarai kawai dan Yata ce yasa nake take gaskiya nake bin bayanta amma mara mutunchi ta qarshe yarinyar nan toh Allah kaga zuciyata dan zumunchi zan rakaki Allah kasa na fito da raina da lafiyata kar tayiwa Angona Asarar wani abun a jikina". Tsabar baqin ciki har sukaje gidan Mama bata sake ce mata komai ba. A waje ta ajiye motar a cewarta kar wani tsautsayi ya afkaqa motar Mijinta ta shiga uku. Bangaren Hajiya suka fara shiga sun tarar da falon cike da yan uwan Hajiyar da yayayensu ga Akwatuna saiti uku masu hurhudu a bude kaya maqil a ciki iya kallonka da alama su suke dubawa. A mutunce suka gaisa da jama'ar falon wasu sun santa irinsu Jalilah wasu kuma kamanninta da Umaimah yasa suka fahimci ko wacece, Falon Sama Hajiya ta kaisu, seda ta saka Habiba da me aikinta suka cika musu gaba da kayan sha dana ciye ciye kafin ta zauna suka sake gaisawa. Maganar dai guda daya ce aka maimaita, Hajiya ta kalli Mama cikin Jimami tace "Wlh Hajiya tun da abin nan ya faru na rasa sukuni nan kullum yake zuwa ya tasani gaba akan se ni in sameta na gaya mata na ce masa bazan iya ba akan me ni zan kwashi baqin jini shida aure nida fadar bakin saqo daman yaushe aka gama rikicin tasowar maganar ma se gashi daga zuwa tambaya kawai suka daura aure kayan can da kuka gani yan uwan ne suka hada wai yau zasu kai Lefen saboda Qanin Babansu yayi rantsuwa se Yarinyar ta tare a cikin satin nan tun jiya abin duniya ya isheni Hajiya ko baccin kirki na gagarayi saboda tsakani da Allah na sani bamu kyautawa yarinyar nan ba, kuma da ace na san zasu tada maganar tariyar da wuri da tun sanda aka daura auran nan za'a gaya mata, amma gaba daya lissafinmu wata uku ne nan gaba saboda gurin da ze ajiyeta ma be kammala ba yanzu Kawun nasu yace sedai su zauna nan gaba daya idanma daga baya ze canza mata gida yayi haka amma yanzu ya rigada ya sanarwa da Iyayenta a satin nan zata tare". Numfashi Mama taja tace "Babu komai Hajiya haka Allah ya tsara kuma in sha Allah hakan ze zamo musu Alkhairi baki daya Mahaifinta ma dayaji fada ya ringayi akan me yasa Amaryar bata tare ba har yanzun ai tunda an rigada an daura aure duk kuma wani abu daga bayane, zan sameta yanzu zan kuma yi mata bayani ta yanda zata fahimta in Allah ya yarda ba za'a samu ko wacce matsala ba zata karbi al'amarin da sauqi nasan Umaimah nada rigima amma idan aka tafida ita ta yanda ya kamata da izinin ubangiji komai zezo da sauqi" "Toh Allah ya yarda Hajiya Allah ya yarda" Hajiya ta fada tana gyada kai Anty Laure dai daman bata ce musu komai ba saboda wani mugun haushi daya turnuqeta, gani tayi abin nasu ma rainin wayo ne ita yanzu bata ma yarda da cewar wani babu shiri aka daura auran ba da ma sun shiryi abinsu idan ba haka ba duk a cikin sati dayan ne suka hada wannan uban lefen sannan yanda suke raha suna jin dadinsu kana gani kasan daman abin shiryayye ne kawai so suke su raina musu hankali to abiyar kowa ta bishi kuma idan anyi dan a wulaqanta yar Yar uwarta ne mugun nufinsu ya koma musu kuma dukkansu Mata ne suma kuma sun haifa in har sunyi dan su Musguna mata Allah yasa su gani a kwaryarsu. Tsaki taja a fili Hajiya da Mama suka kalleta seta miqe tana kallon Mama tace "Ki tashi muje Yaya, aure dai sunrigada sun masa duk wani jaje da za'a zauna anayi da taraddadin meze faru daga bayane, in har zuciya da gaske an ga rashin kyautawar abinda akayi me yasa tun gabanin ya afku ba'a dauki mataki ba? Kawai anyi abinda akayi bisa son rai kuma in Allah ya yarda tozartar da ake so tayi ba za'a ganta a kanta ba ehe". Basu da buqatar ta fadi dawa take dan maganace tayi ta a fili tana kuma gama fada ta fice ta sauka qasan tana mita ko yayar tata bata tsaya jira ba, a falon qasan tana sauka taji wata zaqaqura tana cewa "Ai ni live zanyi, bazan ma iya tsayawa wani recording sannan nayi posting daga baya ba tun yanzu ma nayi sanarwa qarfe hudu zanyi Live kowa ya shirya kallon Tambelen Kishi dan wlh yau se an fasa kwan nan a tsakar gida kowa yaji warin sa" suka kwashe da dariya. Da daddaya Anty Laure ta kalle au fuskar nan tata kirtif yanda kasanita akayiwa kishiyar ma ba Umaimah ba ta nuna Lubna da tayi maganar tace "Ko banza akan Mijinta zatayi tambelen kishin ke kuwa banida buqatar a gaya mun a kwalta kike an rasa me, ku kuma da kuka zauna kuna tayata duk a gidajen aure kuke kuma yanda kishiyar batayi sallama da zata diro gidan taba haka kuma kowa ta jirayi tata tana tafe". Qugu Lubna ta riqe zatayi mata fitsara Jamila ta riqe hannunta tana girgiza mata kai Anty Laure ta ce "Da kin barta in nadawa yar iska duka inga abinda za'ayi aikin banza kawai" fuuu tayi waje ta buga musu qofa duk suka bita da kallo. "Tab kice abin nasu Gado ne" wata daga ciki ta fada daidai nan Hajiya da Mama suka sakko Hajiya dai bakinta ya kasa dena bada haquri, bugun da Anty Laure tayiwa qofar yasa ta cije taqi buduwa dan haka Hajiya tace suje ta qofar kitchen, seda Maman ta fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma ciki ta tarar dasu suna hayaniya akan abinda Anty Laure tayi ita dai sama ta wuce dan jininta ya rigada yayi sama tun ma kafin me afkuwar ta afku. UMAIMAH Qarfe tara na safe ta farka daga baccin data koma dalilin kiran da Safina tayi mata akan zatazo, seda tayi wanka ta shirya sannan ta fito Ruqayya dake goge kayan kallo ta kalleta da fara'a ta gaisheta ta amsa tana yamutsa fuska saboda yunwar da takeyi kai gaba daya ma bata jin dadi ita bata taba ji cikin jikinta ya dameta irin yau ba dan haka ma ta tashi da niyyar da dare zataje Asibiti ita ko Inducing ne su mata ta haihu amma banda CS tunda naqudar taqi tazo. Tuwonta taci da Koko da already Ruqayyan ta hada mata su, a bakinta taji cewar da wurwuri Khalil ya fita a falon ta zauna bayan ta cewa Ruqayya ta hada abin karyawa zatayi baquwa yanzu tana hanya. Wuraren goma da yan mintina Safina ta isa gidan Afujajan da ita kamar wadda ta dawo daga qauye, Umaimah ta kalleta ganinta da qatuwar jaka tace "Ke kuma daga ina haka ga wata qwanqwamemeiyar jaka kamar wadda zakiyi tafiya?" Safina ta zauna tana sauke numfashi tace "Daga gidan Malam nake fitar ce tazo mun babu shiri tun Asuba n fita kai mun jakar ciki toh saboda tsaro me kuka rage a gidan?" "Kamar na sani nace a hada miki abinci bari ta kawo" Umaimah ta fada kafin ta shiga kiran Ruqayya. A daki suka qule seda Safina taci tayi nak kafin ta fara fiddo da kayan cikin jakar tana kallon Umaimah tace "In gaya miki jiya naga Suleiman namun wani gani gani na sakashi abu ya qiyi shine fa yau babu shiri na bazama ina zan zauna kallon ruwa kwado yayi mun qafa? Kedai ai duniya ta samu hankalinki ya kwanta Khalil ya dawo hannunki se yanda kikayi dashi, to kema ga saqonki inji Malam wannan turaren ne kuma yace na jaddada miki ki kula dashi karki kuma nemansa ki rasa" Safina ta fada tana bata wani dan qullin baqar leda. Drawer gefen gadonta taja ta saka a ciki daga nan suka ci gaba dayi, Mu'ayyadya shiga dakin da Sallama yana tafiya a hankali, seda ya gaida Safina kafin ya qarasa jikin Umaimah ya jingina ta dagoshi jin jikinsa da zafi tace "Zazzabin ne ya dawo?" Kai ya daga mata kafin ta sake cewa "Toh me yasa baka kwanta a gurin Hajiya ba ka fito?" "Hayaniya akeyi Momy duk su Momyn Sharada ne sukazo harda su Maman Kaduna ma su da yawa" ya bata amsa yana kwanciya akan gadon. Mamaki ya kamata jin yace mutane a bangaren Hajiya, su Jalilah ba baqi bane daman kullum suna tafe amma Maman Kaduna Maman su Lubna kenan dayace sunzo da yawa su kuma me ya kawosu? "Kaga tashi kaje dakinku ka kwanta kaga nan ma hira mukeyi karmu dameka" ta fada ganin yana shirin yin bacci se Safina tayi saurin tareta tace "Ki barshi mana mu se mu koma falo ai na gama bude kayan duk da ba zama zanyi bama gara inje in aikata abinda ya kamata" ta fada tana miqewa tsaye. Falon suka koma, suna zama tayi qasa da murya tana kallon Umaimah tace "Kinga ga dama kin samu duk suna gidan dangi na kusa dana nesa yanzu ki tashi kiyi turaren nan kowa ta shaqa shikenan fa kin gama dasu tsakaninki da dangin Khalil se yanda kikace haka za'ayi" "Kuma fa hakane, bari to ina tashi" Umaimah tayi na'am da zancen babu bata lokaci ta shiga kitchen ta kunna coal ta saka a kasko ta fito falon, seda ta dakko maganin ta kwance zata zuba Safina tayi saurin tareta tana cewa "Ke uwar hankali waya ce miki haka zakiyi? Ai se kin je can kin ajiye kaskon a inda kika san idan kin zuba duk zasu shaqi hayaqin sannan ki zuba ki bar gurin. Ki samu kamar bayan windown falon ki saka a can zefi samunsu kuma ki tabbata babu wanda yaga sanda kika zuba maganin haka qa'idar aikin take". Harararta Umaimah tayi kafin ta dauki kaskon ta fita, harta zagaya ta bayan falon babu wanda ta hadu dashi, tana jiyo hayaniya da shewarsu daga ciki dukda bata tantance abinda suke cewa ta tabe baki a ranta tana tunanin ko taron uban me sukeyi haka se Allah. Seda ta samu guri me kyau ta ajiye kaskonta ta kwance qullin ta debi turaren bayan ta dauke numfashi ta zuba, murmushi ta saki ganin yanda iska take kadawa ta bangaren da haqin yake bi kai tsaye tana sake ingizashi zuwa cikin falon "Me kikeyi haka Umaimah" taji Muryar Mama kamar a mafarki a bayanta. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 70 "Meye wannan kika zuba?" Maman ta sake fada tana matsawa kusa da ita Umaimah ta saki ragowar qullin hannu ta a qasa saboda kidima cikin rawar baki tace "Mammma yaushe kika zo ya kika biyo ta nan?" "Ba wannan na tambayeki ba me kika zuba a cikin kaskon nan nace?" Maman ta sake fada tana qarasawa kusa da ita ta kalli kaskon dake bulbula uban hayaqi mara dadi ta kalli Umaimah da alamun rashin gaskiya suka gama bayyana a jikinta cikin in ina tace "Am Mama maganin Miyagu ne aka bani" "Kuma maganin se akace kibi gida gaba daya ki saka musu kuma a boye?" Maman ta sake tambayarta tana tsareta da ido se Umaimaha ta zumbura baki tana kallon gefe tace "Toh ai Mama haka me maganin yace Mayun na gida ne kuma idan suka sani ba zasu bari na saka ba dan kwanaki ma da aka bani daukewa sukayi na neme shi na rasa" "Dauki kaskon muje" Maman ta sake fada tana girgiza kai Mamakin Umaiman yana kamata dan ta yarda da gaske maganin Miyagun ne mamakinta kawai yanda tace wai Mayun na gida ne kenan Mijinta ma Mayen ne da Yayanta tunda dai a Barayin uwarsa take kunna maganin itace mayyar kenan. Umaimah kuwa babu yanda ta iya haka ta dauki kasko gudun kar Maman ta zargi wani abu, addu'arta daya Allah yasa bataga sanda ta zuba maganin ba inda bata gani ba toh ai magana ta qare hayaqin ya shiga kuma ko yaya ne ya gauraya da iskar gidan duk sun shaqa. A bakin qofa suka ci karo da Safina da uwar jakarta ta rungumo,ta gaida Mama data bita da kallo tana cewa Umaimah zasuyi waya, suka shiga ciki tana gaba Maman na binta a baya. Anty Laure na zaune kan kujera tana girgiza qafa kana ganinta kasan bala'i nacinta Umaimah dai ta wuce Kitchen ta juye garwashin a sink ta kashe kafin ta koma falon gabanta na faduwa wannan zuwan na Mama babu sanarwa tasan ba Alkhairi bane, qila wani sharrin aka qullo mata shine maman ta taddota har gida kenan zata ci mata mutunchi. A qasa ta zauna ta gaishe su, Anty alaure bata amsa ba Mama dai ta amsa a sanyaye tana kallon Umaiman tunanin yanda zata isar mata da wannan saqo me nauyi take yi. Ruqayya ta fito daga kitchen da Babban Try ta doro Ruwa da Lemo ta ajiye ta gaida Mama cikin girmamawa ta sake komawa ta dakko Babban Bowl data zubo dambun nama, jiya Khalil ya shiga dashi ko Umaiman ma ta manta bata gayawa na se yanzu ta tuna dashi. Seda ta ajiye musu duk wani kalar kayan dadi da suke dashi a gidan kafin ta koka kitchen ta shiga shirin dora abincin rana na Alfarma duk saboda zuwan Hajiya Mama. Duk kayan da Ruqayya ta ajiye musu babu abinda suka taba, Mama ta kalli Umaimah da duk ta fita a kamanninta tace "Umaimah haka ciki ya mayar dake? Yaushe ne lokacin haihuwar taki wai?" "Nima ban sani ba Mama amma sunce na kusa" ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba se Mama ta sauke ajiyar zuciya kafin ta sake cewa "Khalil yana gidan ne?" "Ya fita tun safe amma nasan qila yana hanyar dawowa saboda yau be cika fita bama indai ba da wani babban dalili ba" "Toh yayi Allah ya dawo dashi lafiya" Maman ta sake fada se sukayi shiru gaba daya kusan minti biyar Umaimah ta kalli Anty Laure tace "Anty ya Babanmu ina ta cewa zanzo gashi kin rigani zuwa" "Kiyi ta kanki yarinya ahto kiji da abinda yake a gabanki ba gulma" Anty Laure ta fada, shirun suka sakeyi, gaba daya Umaimah ta tsargu da yanayin Mama. Da ace laifi tayi fada zata fara mata amma yanda ta ganta a sanyaye gashi se kallon ta takeyi yasa hankalinta ya fara tashi, kodai wani abu ne ya faru a gida? Amma idan haka ne ai ba Mama ce zatazo da kanta ba wani za'a turo to ko qararta Khalil yakai shi kuma me tayi masa kai babu ma wata qara da ze kai da can ma baya kai qararta gida balle yanzu da ya sake zamar mata Mijin tace qila dai wani abun ne na daban ya kawo Maman. Maganar Mama ce ta katse mata tunani jin tana cewa Cike da qarfin Hali Mama tace "Ni kam ya maganar qarin auran Mijin ko?" Tamkar saukar aradu haka taji maganar, seta muskuta tana kallon Maman tace "Toh ya gaya miki kenan, to ni ina ruwana na hanashi yayi aurene da zeje ya hadani dake? Yayi auransa mana ai ba akaina matar zata zauna ba". Yanda tayi maganar seka rantse da Allah har ranta kamar yanda ta fada abin be dameta ba, cike da samun kwarin guiwa Mama tace "Haka ne kam ba akanki zata zauna ba kuma na godewa Allah da kika fahimci hakan in har da gaske kikeyi kenan" Mama ta fada seta gyara zama sosai kafin ta kira sunan Umaiman cikin muryar dake nuna muhimmancin maganar da take so tayi mata. "A matsayinki na Musulma kinsan cewar Imaninki baze cika ba har se kin yarda da Qaddara me kyau ko Mara kyau haka ne ko ba haka ba?" A hankali Umaimah ta bude baki tace "Hakane Mama" "Toh ina so ki bude kunnenki da kyau ki saurari abinda zan gaya miki sannan ina so kiyiwa maganata kyakykyawar fahimta" Maman ta sake fada Umaimah dai kallonta kawai takeyi tana jin gabanta yana faduwa. A hankali kuma cikin hikima Mama ta fara mata Nasiha irin wadda duk taurin zuciyar mutum seta raunana tayi laushi, seda ta tabbatar da jikin Umaiman yayi sanyi qalau ta yanda ko motsi ta gagarayi daga zaunen da take kafin ta sake gyara zama tana dauke idonta daga kallonta. Cikin nutsuwa ta warware mata zare da abawar abinda yake faruwa ta rufe da cewa "Kiyita maimaita Hasbunallahu wani'imal wakeel har se kin samu gamsashshiyar nutsuwa, karki yarda ki bawa Shaidan damar shiga zuciyarki yayi wasa, ubangiji ne yayi hukuncinsa kar kice zakiyi fito na fito da umarnin ubangiji Umaimah kiyi addu'a Allah yasa hakan ya zamo muku Alkhairi baki daya, Mijinki yana sonki na tabbatar kuma babu abinda ze canza hakan daga zuciyarsa. Haqurin da zakiyi da juriya su zasu qara girmama soyayyarki da martabarki a zuciyarsa". Shiru falon ya dauka kamar babu abu me rai a ciki kafin Umaimah da tayi mutuwar zaune ta ja numfashinta daya bar jikinta na wani lokaci, babu yabo babu fallasa ta kalli Maman tace "Toh Mama nagode da Nasiha ina kuma addu'ar kar Allah ya tabbatar da wannan mafarkin naki" "Mafarki Umaimah, duk maganganun da na gama yi miki a mafarki kika daukesu?" Mama ta fada cikin mamaki se Umaimah ta miqe tsaye tana kallon Maman tace "To idan ba mafarki bane Mama tatsuniya ce ko kuma makuwar tunani kima samu da har kikayi irin wannan hasashen?" A hasale Anty Laure tace mata "Ke shagga idan zaki hada hankalinki guri daya tun wuri kiyi ki fuskanci abinda yake a gabanki, munafunci ne an rigada anyi ruwanki ki maida musu da aniyarsu ruwanki kiyi hauka su samu yanda suke so suyita yawo dake a duniya suna yadaki zabi ya rage naki yanzu ita dai Kishiya kafin ta shigo ne kake yin barazana ko hakan ze sa a fasa idan kuma ta rigada ta shigo sedai kayi yaqin tsira da mutunchi dan ko kin koreta a banza ta rigada ta kafa tarihi ko magana aka tashi se an jinginaki da ita ace tsohuwar Kishiyarki to gara ki rungumi qaddararki kawai ki zauna lafiya ki kuma bawa munafukai kunya dan gasu can sun cika gida suna jiran suga yanda zakiyi". Wata dariya Umaimah tayi tana girgiza kai tace "Toh inaga ba Mama kadai ta rikice ba harda ke Anty Laure shiyasa she na ganku wani iri kamar an muku mutuwa to gaskiya ya kamata ku nemi magani tunda wuri kar abin ya zarce haka. Idan ba rashin lafiya ba taya ma tunaninku ze fara baku wai Khalil yayi aure kuma ace ban sani ba? Ai wlh ko na mutu ina cikin kabari na tabbata idan Khalil zeyi aure se yaje kan kabarina ya fada mun saboda kar na tashi na ringa yi musu fatalwa ballantana ace da raina ina zaune cikin gidan nan yaje yayi aure hhhhhh" ta sake yin wata dariya duk se suka saki baki suna kallonta Anty Laure tace "Eh lallai babu shakka Umaimah kai tsaye kice hauka mukeyi kawai meye wani sakayawa kice bamu da lafiya? Toh karma ki kidina kanki a banza kiyi kamar baki san me muke fada ba, Khalil dai yayi aure bakuma yanda kika iya" bata tsaya qarasa jin abinda Anty Lauren take fada ba ta shige dakinta da sauri ta kullo qofar dan karma su bita cikin. Wayarta ta dauka bayan data zauna gefen gado ko kusa taqi ta bawa kwakwalwarta damar daukar abinda suka fada ballan tana har tayi tunani akai. Kwanciyarta tayi kusada Mu'ayyad tana jin ana buga qofar dakin tayi banza dasu har suka gaji suka bari daga wajen tana jiyo Anty Laure na qunduma mata zagi ko a jikinta sema ta rufe ido babu dadewa kuwa bacci ya kwasheta bata farka ba se bayan Azahar shima dalilin bugun qofarta da ake tayi babu qaqqautawa. MAMA Da ido tabi Umaimah harta shige daki ta bugo musu qofa. Anty Laure ta kwashi salati tana tafa hannu tace "Yaya kina kallon abinda yar iskar yarinyar nan tayi mana? Mu ta kira da mahaukata sannan ta shige daki ta barmu a zaune kamar wasu gantalallu to dan kanta kuma ni wlh yanzu naji dadin kishiyar da akayi mata yar banza me baqin hali da bamu san a inda ta gado ba" "Laure ni duk ba wannan ya dameni ba, yarinyar nan fa bata yarda da abunda muke fada ba. Ina tsoron abinda ze biyo baya idan ta farga" "Toh ba ita ta sani ba Yaya ina cewa tayi bamu da lafiya ita da take lafiyayyar ai shikenan idan taji ana ta matsa za'a shigo da Amarya ai a sannan zata sha jinin jikinta wawiyar yarinya da babu abinda ta sani se hauka da rashin hankali nidai tafiya zanyi idan zaki tafi muje idan kuma se kin zauna kin fahimtar da ita Allah ya bamu Alkhairi ni nayi nan" Anty Laure ta fada tana figar jakarta zata fita se Mama ta miqe a sanyaye itama tabi bayanta. Gidan Maman suka wuce a can suka tarar da Maman Asad tun kafin ma ta tambayi ba'asi akan ganin yanayin Maman Anty Laure ta kwaza mata zance, Anty na tsakar gida tana aikace aikace da yake cikin daga murya Anty Laure take maganar dan haka taji komai a kidime ta saki tsintsiyar hannunta ta dafe qirji babu shiri ta afka dakin. Maman Asad kuwa sunan zaune tayi, seda ta kwashi wasu mintoci kafin ta iya bude baki tace "Tashin hankali da ba'a saka masa rana toh yanzu Anty Laure ya zamuyi?" "Ya zamuyi Hajiyayye ko ya zatayi? Meye namu a ciki ya wuce mu koma gefe musha kallo ba cewa tayi bamu da lafiya ba se mu jira muga yanda tata rashin lafiyar zata bayyana aure dai an rigada an daura" "Amma tsakani da Allah babu Adalci a cikin wannan abun, yama za'ayi ace Khalil yayi aure ba tareda Umaimah ta sani ba kawai saboda ya jazawa mutane da wanda yaji da wanda beji ba duk jidalinta ya shafe su gaskiya ba'a kyauta ba" Anty ta fada kamar zatayi kuka, ita dai Mama tayi shiru tana jinsu kawai kafin ta nisa ta kalli Maman Asad tace "Hajiyayye ki kira Nuratu da Hafsa qila ku fimu dabarar da zaku fahimtar da ita ta gane bana son azo ana tashin hankali daga baya gara yanzu duk abinda zatayi ta gama kafin tarewar Amaryar. Bari na shiga ciki na kwanta kaina yana mun ciwo". Ita dai Maman Asad ta rasa abin cewa se Anty Laure keta bala'i Anty Saratu kuma ta rafka tagumi tana wasiqar jaki. Hasashen abinda ze faru daga sanda Umaimah ta fahimci dagaske Khalil yayi aure. UMAIMAH Bacci tasha da gaske dan bata farka ba se kusan qarfe uku na rana dalilin buga mata qofa da akayi. Seda ta wanko fuskarta da bakinta tukunna ta bude qofar jin me bugun har sannan be haqura ba. Fuska a hade ta bude qofar tayi tozali da Lubna, rabonda su hadu ido da ido tun haihuwar Mu'ayyad da sukazo suna. Wani kallon banza suka aikawa junansu Umaimah ta harde hannu a qirji tana qarewa Lubna Kallo kamar yanda itama take kallonta kafin Lubnan taja tsaki cike da mugun kishin da yake nuqurqusarta na rasa Khalil a karo na biyu tace "An fito da kaya za'a tafi kaiwa nace be kamata ace uwar gida bata gani ba dan haka ki fito ki saka albarka amma se kin daure fa dan nasan lokacinki baki samu kamarsu ba" Gajeran murmushi Umaiman tayi kafin ta turo qofar tana cewa "Kece baquwar saka sutura da har Lefe zeyi intimidating naki, koda yake ba'a taba kawo miki ba shiyasa" tana gama fadar haka ta maido qofarta ta rufe, Lubna ta ciji yatsa cikeda takaici ta daga murya tace "A banza dai wlh kuma ki shirya duk wano Alqadarinko Allah ya kawo mi karyashi sati i war haka kin zama bora a gidan nan kina ji kina gani Khalil ze ringa ririta yar babynsa sedai bakin ciki ya qumeki kiyi bunga". Haka suka kwashi Akwatunan suka fita dasu daga gidan ba tareda Umaimah tasan me akeyi bama, da Magriba Bibi take mata surutun biki za'ayi taga Akwati da yawa kuma an ce na Dady ne ko kusa bata maida hankali na, bama wannan ba hatta da zuwan Mama ma ta manta da anyi seda Ruqayya take tambayarta me zata ci, ta gaya mata akwai abincin data hadawa su Hajiya dazu kuma suka tafi basuci ba se a sannan ma ta tuna da zuwan nasu da abinda Maman ta gaya mata. "Uhm Mama da Mafarkanta mara sa kan gado wanna karon kumai kaina suka fada" ta fada qasa qasa tana taunar Chewing gum. Kiran wayar Safina ya shigo mata, suka gaisa Safina na tambayarta yaya dazun kuwa ta saka "To wama ya sani ne na dai saka ban sani ba ko Mama ta gani dan jin muryarta kawai akaina, zan dai sake turara ragowar gobe inma sun shaqa su qara" Umaimah ta fada se Safina ta kwashe da dariyar shaqiyanci tana cewa "Ke matar nan gara dai ki jira ki gani karki qara guma musu su susuce gaba daya" "To meya ruwana ciki in ma zaucewa zasuyi su ta shafa gonata suka shiga kuma dole na hukuntasu ko dan su kiyaye faruwar hakan a gaba. Ke ni ba wannan bama kinsan wai Mama zuwan da tayi wai gaya mun takeyi Khalil yayi aure ko zeyi aurene ma ni ban gane kan abin ba" "Halan Mama nada hawan jini ko kin san idan yayi yawa yana saka mutum ya ringa tunanin abubuwa ba daidai ba, se su ringa tunanin abu suna gani kamar a gaske ya faru Illusion ake kiran abun ko to inaga shi Mama takeyi" Safina ta fada cike da shaqiyanci se Umaimah tace "Kema kya fada, ni gudun kar abun ya bata mun rai ma daki na shige na barsu" "Ke kuma ya haka gaskiya baki kyauta ba Maman zaki tashi ki bari a zaune tana miki magana matsala ta dake Qawata kanki akwai ruwa wani lokaci ai duk iskanci a dagawa Mama qafa dai" Safina ta fada se Umaimah ta yanutsa fuska tace "Ai tashin nawa yafi zaman Alkhairi saboda kalar zancen data zo dashi badan ita bace bama da sena zagi uwar wanda ya fada wlh kafin in gurje masa baki" "Toh Allah yayi mana tsari da mugun ji da mugun gani, yanzu dai ki turamun da ragowar kudadena dana ranta akayi miki aiki tunda dai aiki yaci ina da buqatar kudi gobe ma Qaraye zanje Sailuba ta hadani da wani sabon Teacher kinsan fa shi aikin Suleiman idan ba rubdugu akayi masa ba baci yake ba dan Uwarsa a tsaye take akansa imata in gaya miki sau da yawa ma da nata aikin nake basaja na cusa nawa idan ta kawo Masa Rubutu dasu hayaqi sena canza na ajiye masa nawa yayi tayi to yanzu ta dena bashi sedai kullum yaje gidanta yayi koma menene shiyasa nake so ayi mun kwaf daya kawai, farraqu nake so ayi masa da uwar ta yanda ko inda take baze ringa zuwa ba balle ta ringa lalata mun aiki" "Toh Allah ya tsare ni kam bazan iya aikin shuka dusa ba" Umaimah ta fada mata cikin izgili se Safina tace "Na nawa kuma ai kin shuka sedai kiyita aikin ban ruwa kuma qaryar banza da wofi kawai" Safina ta fada a hasale Umaimah na shirin bata amsa Khalil ya turo qofar da sallama qasa qasa kamar wanda akayi qara a Kotun qoli ganinsa yasa Umaimah ta fasa fadar abinda tayi niyya tace mata "Zan kiraki anjima" daga nan ta kashe wayar tana kallon Khalil daya qwamo wani baqin Glass cikin dare kamar sabon Makaho ya kuna kasa daga kai ya kalli inda take. "Khalil ciwon ido kakeyi?" Ta fada tana miqewa tsaye seya daga mata kai still be kalleta ba yace "I think Apolo ne ya kamani daman Anwar yana yi may be gurinsa na dauka" "Kai Allah ya sauwaqe gara ma daka saka Glass kar mu dauka muma musammani da idona yake kwalamamme kar na tashi dashi gobe" ta fada tana ja baya kamar wanda yace mata ya gamu da cutar kuturta shidai Sama ya nufa yana riqe da numfashinsa dan ba qaramar qundumbala yayi kafin ya shigo gidan ba. Babban abinda ya bashi qarfin guiwar dawowa tabbacin da Jamila ta bashi akan Lafiya lau gidan yake babu abinda ya faru har suka tafi kai Lefe, kuma ta tabbatar masa da cewar Mama tazo, to meya faru dayaga Umaiman cikin nutsuwa tamkar babu abinda yake wakana wane irin abu Mama tayi amfani dashi da har tayi nasarar shawo kanta haka ta karbi Al'amarin da Salama? Koma dai menene baze tona ba, tunda Allah ya dube shi ya amsa addu'arsa ya tausasa Zuciyar Umaiman shikam ba abinda zeyi sedai ya qara Godewa Allah. Seda yayi wanka ya gasa jikinsa dan wunin ranar bega ruwa ba tunda ya fita daga gidansu Umaimah office ya wuce babu kowa yau se Masu gadi saboda ba ranar aiki bace ya bude office dinsa kawai ya shiga yana jiran tsammanin jin gidansa ya kama da wuta amma har yamma beji wani labari ba, tunanin ko dai kowa na gidan ya mutu ne yasakashi kiran Jamila ta tabbatar masa da yanzu suka baro gidan Mama Hauwa sun kai Lefe ita ta wuce gida ta tabbatar masa da lafiya lau suka fito kuma gama wayarsu kenan da Hajiya ma da wani abu ya faru bayan fitar su zata gaya musu. Yunwar da yake ji ta sakashi sake sauka qasan dole, har ya kusa kaiwa qasa ya koma ya dakko Glass dinsa ya saka tubda ya laqawa kansa qaryar ciwon Ido ya ya iya? Umaimah na zaune tana kallo ya samu kujera daga can gefe ya zauna cikin dar dar kar yaje gadar zare ta shirya masa, Ruqayya ya kwalawa kiraz ta fito ta durqusa daga nesa cikin ladabi ya tambayeta abinci ta wuce Kitchen, a kan Center table ta ajiye masa dan yace baze iya hawa Dining ba. Ua zuba abincin ya fara ci kenan Umaimah ta kalleshi tace "Dazu Mama tazo ita da Anty Laure" Shinkafar da yake taunawa ta sarqesgi ya shiga tari babu ji babu gani Umaimah ta matsa ta zuba masa ruwa ya karba yasha kadan ya ajiye idonsa sukayi ja sosai yana maida numfashi, seda taga ya dena tarin kafin taci gaba da maganarta dan ita bata ma lura wai abinda ta fada ne ya kwarar dashi ba. "To dai tazo tana ta wasu maganganu kayi aure wanene wanene nace ni meye nawa a ciki kaina matar zata zauna ko ni zan ringa ciyar maka da ita ai kanka ka qarowa wahala ko ba haka ba?" Ta qarasa tana kallonsa. Yanda kasan gunko haka Khalil ya zama a gurin, Umaimah taci gaba da cewa "Ni dana gaji daji ma na shige daki nayi bacci gaba daya bansan me aka daukeni ba wai zata akeyi tsoron kishiya nakeji ne ko Yaya ni yanzu ba mace daya ba ko uku zaka cike an gaya maka hankalina ze tashine nasan duk tsiya badai ka auro wadda ta fini ba kuma koma wacece zatazo a bayana take dan haka Allah ya kawota lafiya ta shigo gata ga gidan ai". Da yana shaye shaye tabbas ze gasgata abinda ta fada amma ko a magagin mutuwa yake yasan wannan maganar ba gaskiya bace sedai idan ita Umaiman ce ta fara shaye shaye ba kuma ya raba daya biyu akwai wani abun data taka shiyasa tayi wannan ladab din. "Toh yaushe Amaryar taka zata tare kuma?" Ta sake jefa masa wata maganar seya fara in ina dukda besan ma sanda ya budr baki yayi magana ba yace "Uhm eh kin gane Umaimah nasan dai Mama tayi miki duk wani bayani ni yanzu bani da bakin da zan kare kaina Allah kuma shine shaidata baniyi komai da niyyar na musguna miki ba, al'amari ne yazo daga Allah babu kuma wanda ya isa ya hana faruwar hakan" Tsam tayi tana kallonsa har ya kai qarshe seta dauke kanta gefe tana cewa "Idan ka gama cin abincin Inada Panadol Night zan dakko maka kasha kayi bacci" daga haka ta maida kai kan Tv abinta ba tareda ta bawa maganganunsa muhimmanci ba. Babu shakka shima kan babu dadi ko kuma wani wasan kwaikwayo Mama ta shirya musu to can su gane, kai wannan abun ma babu qanshin gaskiya a ciki, babu yanda za'ayi Khalil yayi aure kamar yanda ake iqirari sannan ya iya zama a gabanta haka ai ba mahaukaci bane shi tsaf yasan abinda zata aikata masa. Duk yanda yaso yayi mata magana ta hade girar sama da qasa taqi bashi dama haka ya tashi ya koma sama abincin da beci ba kenan dan tunda ya kware ya haqura dashi daman, kwana yayi yana juyi da Jimami, ranar litinin za'a zo yiwa Humaira Jere kamar yanda Baba Abu ya yanke cewar ranar Laraba zata tare, da yamman nan se kashe wayarsa yayi saboda Rigimar data dira masa akan ita ba haka sukayi dashi ba se ya kira Iyayenta yace musu a qara masa lokaci danita ba zasu saurareta ba shiko a sannan yana jiran jin yanda ta qare da Gimbiyarsa bema tsaya wani sauraronta ba yace zasuyi waya daga haka ya kashe wayarsa gashi yanzu Alamu sun Nuna kwakwalwar Umaimah ta qi karbar saqon da ake aika mata, shi kuwa bega abinda ze saka Humaira ta tare a gidansa Alhalin besan makomarsa a hannun Umaimah ba. Washe gari da safe bayan ya dawo daga Sallar Asuba ya taddota a daki ta idar da Sallah itama tana zaune a qasa, suka gaisa ta kalleshi fuska dauke da Murmushi tace "Ango Ango" Gabansa ya yanke ya fadi seya juya ya fasa zaman da yayi niyya Umaimah ta fashe da dariya ganin ya fita kafin ta miqe ta koma kan Gado ta kwanta abinta kafin gari ya qara wayewa tasan abinda zata saka Ruqayya ta shiryawa su Maman Asad da sukace zasu zo yau. Khalil kuwa bangaren Hajiya ya tafi a daki ya sameta tana sallah dan ta makara tashi yau seda ta idar ta shafa addu'a kafin ya gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin yanda duk yayi zuru zuru tace "Jiya na manta ince maka Hajiya Malika ta zo, wlh banji dadin ganinta ba gaba daya kunya ta dabaibayeni amma naji dadi data fahimci abun kuma Alhamdulillahi gashi ta fahimtar da Umaiman ta karbi qaddara kaga fa yarinyar nan Lubna ashe saboda son tada zaune tsaye da zasu tafi kai kaya har qofa ta kwankwasa mata wai tazo ta gani cikin ikon Allah ta tura mata aniyarta bata kula su ba kaga kuwa ai addu'a tayi tasiri sedai aci gaba da roqon Allah ya sake kore shaidan daga zuciyarta danshi yake ingizata take yin komai amma ba halinta bane". Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Hajiya ni na kasa fahimtar ta ne gaba daya ma, yanda take magana kamar bata yarda da abinda aka fada bane Kwata kwata fa Hajiya babu alamar damuwa ko wani abu a tattare da ita yanzu fa har tsokanata tayi wai Ango ni wlh Hajiya tsoron ta nake ji saboda Umaimah bata shiru komai qanqantar abu idan akayi mata se tayi magana idan kuwa kikaga tayi shirun to abinda zata aikata se an gwammaci sau dubu ta fitar da abinda yake cikinta wai fa cewa takeyi ina ruwanta idan ma mata uku zan aura ai ba akanta zasu zauna ba Sannan ace lafiya kuwa Hajiya" "To in banda abunka Babana Mahaifiyarta ce fa tazo da kanta gidan nan kuma dai ka sani a duniya ita kadai take sakata kota hanata abu tayi babu musu yanzun kasan irin abinda ta gaya mata da jan kunnen da tayi mata ka ringa kyautata mata zato mana kuma ma ai wani lokacin idan zuciyar mutum ta qeqashe haqura ma yakeyi da komai. Saboda Allah me kake so tayi kuma aure ne ka rigada kayi to kuma ta wahalar da kanta a wane dalili ai gara ta sallama ta miqa lamarinta ga Allah kawai. Nidai ina da kyakykyawan yaqinin har ranta kamar yanda ta fada babu komai babu din, ka rabu da ita karka ce zaka takurata dole akan seta fitar da fushinta idan ka tunzurota bamu san iya inda rigimar zata tsaya ba dan haka ka barta tunda Allah ya tsayar mana da kansa". Shidai ko kusa be gamsu da zancen Hajiyar ba amma babu yanda ya iya baze zauna suyi ta ja inja da ita ba amma lashakka yasan babu wata magana da za'a ce wai Umaimah tayi tawakkali farat daya akan maganar auran nan abu biyu ne kuma ciki dole daya ya tabbata, kodai dagaske ta toshe tunaninta taqi fahimtar abinda ake gaya mata saboda tana ganin hakan baze taba yuwuba ko kuma tanada wani tanadi na daban akan al'amarin a cikin biyu babu wanda yake so ya zama gaskiya saboda dukka sakamakonsu baze kasance me kyau ba. Yinin ranar shima beyi shi a gidan ba, kafin ya fita seda ya faki idonta, tana Kitchen tareda Ruqayya ya Ya dakko spare keys din gidan da suke a dakinta ya ciri wadanda yake da buqata. Seda ya bude Part din daya ginawa kansa amma jarabarta tasa ya haqura da amfani dashi gashi yanzu tayiwa kanta baki kuma ya kamata. Sammani ya kira da wani Yaro Ahmad dake gadin maqotansu, cikin taka tsantsan ya shigar dasu, seda suka share gurin tas suka goge dukda ba qurace kawai babu wani datti a gurin ya duba komai lafiyarsa qalau sannan ya sallame su ya koma dakinsa yayi wanka ya shirya ya fita, gidan Unaizatu ya fara zuwa ya kai musu Key kamar yanda suka buqata, Be samu Humaira ba daman sunyi waya ta sanar masa zataje can gidan Mama da akwai qannen Mahaifiyarta guda biyu da suka zo daga Gashaka jiyan Mama tace taje saboda sunce akwai abubuwan da suka zo mata dasu gashi babu isashshan lokaci dan haka kome zasuyi ya kamata ayi da wuri. UMAIMAH Lafiya lau taci gaba da sabgoginta, guraren sha daya suka gama shiryawa su Maman Asad kayan maqulashe wanda Ruqayya tayi ita kuma tana bata Umarni, ta fito daga wanka tana shiryawa suka iso Maman Asad, Nuratu se Anty Hafsa kowacce ta samu kujera ta zauna jugunjugun kamar gidan Mutuwa dan tun jiya da labarin ya riske su kowacce ta rasa kuzari. Hajiya Umaimah ta sako Bubunta ta fesa turare ta fito tana daga qafa dakyar, fuska a washe ta tari yan uwan nata kowacce ta amsa mata da murmushin yaqe, ita dai Ruqayya nata aikin kawo abinci a ranta tana mamakin wannan ziyara da yan gidan nasu Umaimah suke kawowa daga jiya zuwa yau kuma kowanne yazo jiki babu kuzari ta gama ajiye musu abinda zata aje ta wuce dakinta a ranta tana fatan koma menene Allah yasa ya zama Alkhairi. Ruwa kadai suka iya sha shima bisa tursasawar Umaimah, Anty Hafsa ta dake ta sake nanata abinda Mama tazo dashi jiya ta akai Aya Maman Asad ta dora da nata lallashin tana sake nusar da Umaiman muhimmancin haquri da yarda da qaddara a duk yanda tazo maka. Seda tayi Shiru Umaimah ta kalli Nuratu da bata ce komai ba tace "Ke kin rafka tagumi baki da abin cewa ne halan?" "To me zance Umaimah ai sun rigada sun gama magana nidai fatana kiji ki kumayi amfani da abinda suka fada na tabbata zaki ga ribar hakan a gaba" Nuratu ta qara da nata se Umaimah ta gyara zama tana kallonsu su ukun tace "Toh duk naji ku amma ina so ku sani cewar badan ina ganin mutunchin ku ba da wlh se na muku rashin mutunchi a cikin gidan nan. Ai na gayawa Maman tun jiya kawai dan ita ce shi yasa har nayi shiru bance mata komai ba amma yanzu ku da kuka kwaso qafafu kun yarda da abinda ta gaya muku ku gaku zakuyi mun nasiha ko to iya abinda zance muku Allah yasa kuga irin wannan kishiyar a gidajenku, Ke daman Maman Asad taki tana tafe banga laifinki ba tunda kin karbi rabonki kowa ma ya samu ba damuwar ki bace ke kuma Anty Hafsa me mata uku zaki aura in sha Allahu sannan ke Hajiya Likita kina Asibiti kin tafi Duty zaki dawo gida ki tarar da kishiya keda Naziyya dukda bata nan nasan bakinku daya kuma shawararku daya dan haka tun ina ganin sauran mutunchinku ku tashi kowa ta kama qafarta tayi gidanta kuje can kuci gaba da jaye jayen masifarku kuma ta qare muku akanku". Yan uwan Humaira basu samu zuwa yin jere ba ranar litinin kamar yanda suka tsara saboda qaryar da Khalil yayi musu akan ana sake fentin gurin dan haka suka bari se ranar Laraba ranar da Amarya zata tare suyi gaba daya saboda talata Mama zatayi wunin biki. A bangaren Khalil kuwa babu wani fenti da ze sake ya dakatar dasu ne kawai saboda har sannan be samu gamsuwar da yake da buqata daga Umaimah ba ta tabbacin ta karbi auran, hankalinsa be qara tashi ba seda sukayi waya da Nuratu ta gaya masa abinda Umaiman tayi musu daya samu Hajiya da Maganar Jalilah Amara na zaune nan take ta fitittike ta hana hajiya cewa komai, fadi takeyi duk Umaiman ta gama haukan qarya da nuna bata san abinda akeyi ba aure dai an daura Amarya kuma zata tare babu kuma abinda ta isa tayi dan suma ba zuba mata ido zasu hakanan tayi yanda take so ba. Ita ya zame ta sake kiran Baba Abu ta gaya masa Khalil ya hana azo ayiwa Amarya jere ya kuwa kirashi yayi masa tatas yana sake jaddada masa muddin be bari an kawo Amarya ta lallami ba to kuwa za'a kawota ta tsiya dan haka washe gari Talata tun safe yacewa Umaimah ta shirya zasuje Asibiti, ya gama tsara ze kaita kawai su kwantar da ita. Idan ma da akwai Allurar da za'ayi mata a qalla tayi sati tana hutawa bayan anyi Mata CS din ayi kawai shidai su rufa masa Asiri ta rabu da cikin jikinta kafin duk wani tashin hankali ya biyo baya. Qarfe tara suka bar gidan, suna fita motar masu kayan gado da Kujera ta kunno kai dan danan yasan da suna tafe, shirita Umaiman ta tsayayi har suka kai wannan lokacin basu fita daga gidab ba. Suna hanya Jalila ta kirashi akan ya tura mata da kudin kwalliyar Amarya dan gaba daya ita ta karbe bikin daidai da kayan da Amaryar zata saka yau din na yinin ita ta zabar mata ta kai dinki haka gurin da zasuyi Yinin da kudinta ta kama dan da A gida Mama tace zatayi dukda Khalil ya sallami Amaryarsa ya bata kudi kamar yanda akeyiwa kowa amma ya gaya mata baze samu damar halartar duk wani abu da zatayi ba dan haka Maman tace suyi a gida kawai a huta amma Jalila ta kafe akanba haka ba,shi kanshi Khalil seda suka haura kafi ta sarara masa danda cewa tayi se yaje koda yake ko yaje ko kar yaje duk abu daya ne hakan kuma baze chanza duk tsarinsu ba. Bayan sun isa Asibitin, duk su biyu Dr Al'amin ya ringa surfawa bala'i damanita Umaimah ya cire ta a layi saboda a cewarsa ya dade bega mutumin ba besanciwon kansa ba kamarta to Khalil dinma yabi sahunta, ciwon qafar da yaje yana yi ma daga cewa ya dawo washe gari ayi X-ray se yau ya sake ganinsa haka yayi tayi musu fada kafin ya bashi form ya cike ya biya duk wasu kudi da ake buqata suka bata daki bayan akan washe gari qarfe goma na Safe za'ayi mata aikin. A office ya tarar da Dr bayan ya raka Umaimah dakinda aka bata wanda a VIP section ma ya biya mata saboda ta fi samun nutsuwa da kulawa sosai. Dr Al'amin ya kalli Khalil bayan ya gama sauraron duk abinda yake fada na ya girgiza kai kawai yace "Kasan me, tsakanin kaida matarka na rasa wayafi wani cin kai. Dan Allah Malam kaje ka hado mata abubuwan da zata buqata tunda naga shirin zuwa dubiya kukayo sannan ka taho da wadda zata zauba da ita idan kuma kana buqata muna da Nurses da zasuyi maka aikin se kaje a baka Bill ka biya, ina da abinda zanyi idan shikenan maganar ka zaka iya tafiya" ya nuna masa qofa. A sabule ya fita koda yake hakan ma wani achievement ne ze sake ninka qoqari ta wata hanyar dan tabbatar da komai ya tafi kamar yanda yake fata. Yana tare da ita har akayi Azahar kafin yace mata zeje yayi sallah daga nan ze biya ya gayawa Mama se ya koma gida ya debo mata kayayyakin amfani. Umaimah daketa mitar ita bata ga dalilin da za'a kwantar da ita tun safe ba, ina laifin ace su dawo da dare? Ita ya bari su tafi tare ta hado kayanta da kanta kawai dan be zama lallai ya dakko mata abubuwan da take buqata ba shidai Khalil ya lallabata ya tafi. Ko minti goma beyi da barin Asibitin ba itama ta fita ba tareda ma ta bari Nurse din dake kula da ita ta sani ba bare ta hanata. Adaidaita ta tara ta tafi gidan, a hanya sukayi waya da Safina take gaya mata gobe za'ayi mata CS din yanzu ta gudo gida se dare zata koma idan ta hada kayanta. Da akwai wasu kayan Baby data siya gurin maqociyar Safinan bata karba ba ta roqeta ta kawo mata su gida yanzu dan akwai wanda zatayi amfani dasu sannan sukayi sallama. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 71 Tun daga compound take mamakin kwalayen data gani wanda take da tabbacin na kayan gado ne saboda gashi nan a rubuce seta tabe baki irin ina ruwanta din nan saboda tunanin daya zo mata Hajiya ake sakewa gado, ita fa can su gane yanda suka dena sakata a sabgar su ba bazata saka kanta ba, tasan dai duk wannan shirin baze wuce na auran Khalifa ba daman yaron ba mutunchi ne dashi ba shiyasa tun da ma ake zancen auran nasa bata taba saka baki ba kuma dalilin daya sa taqi fita taga lefen kenan sanann sisinta bazata bayar ba da sunan gudummawa tunda dai ba'a sakota a ciki ba (A lissafin Umaimah kenan lefe na Khalifa ne saboda ta san da zancen yayi budurwa abinda bata sani ba babu wata kwakwkwarar magana ma tsakaninsu balle har aje ga batun kai lefe) Kanta tsaye ta wuce cikin gida sedai mutanen data gani zaune a falonta sunyi daidai suna cin abinci yasa ta tsaya turus ta kasa gaba da kasa baya tana kallonsu kamar yanda suma suka zubo mata ido suna kallonta. Cikin daga murya ta shiga kiran Ruqayya, ta fito daga kitchen da sauri jikinta na rawa dan tun zuwan Matan da batun da sukazo dashi daman ta firgice. A gaban Umaimah ta tsaya kanta a qasa tace "Gani Hajiya" Cikeda bala'i tace "Su waye wadannan da kika barsu suka shigo mun falo kamar nasu saboda tsabar rashin mutunchi ji yanda suka zubar mun da abinci akan carpet?" Kafin Ruqayya ta bata amsa wata qatuwa daga cikinsu tace "Aa karki ga laifinta mune mukayi kuskure mun dauka falon na masu gidan ne gaba daya ashe naki ne ke kadai da bamu zauna ba to Allah huci zuciyarki mu kam mun gama abinda ya kawo mu ma wucewa zamuyi". Kallonta Umaimah tayi na wani lokaci tana qoqarin ta tuna a ina ta san fuskarta amma ta kasa "Kinga Sumayya mun ma gama bari mu tattare mata gurin mu Alkhairin ne ya kawo mu ba tashin hankali ba" daya daga cikin masu cin abincin ta fada tana miqewa ragowar suka shiga tsince wanda ya zube a qasan, Umaimah data gama tunano inda ta san wadda aka kira da Sumayya qanwar Mansur ce to uban me ya kawo su gidan kuma koma mene duk fadin gurin Hajiyar be ishe su ha se an kawo mata mutane falo kuma ba'a gaya mata ba lallai mutanen nan sun raina mata wayo. Gani tayi Sumayyan ta juya ta haye sama abunta yanda kasan dakinta ya saka Umaimah dakatar da ita da sauri tana cewa "Ke ina zaki, kinyi hauka ne da zaki haye mun sama se kace gidanki?" "Nan fa daya, falo dai da kikace naki ne mun bar miki amma baki da ikon hanamu hawa Sama tunda ba mallakinki ne ke kadai ba, da dakin yar uwarmu a gun kinga kuwa babu wnada ya isa ya bamu dokar sanda zamu shiga ko ya hanamu" Sumayya ta fada kafin ta juya taci gaba da hawa saman. Wata mulmulalliyar Ashar Umaimah ta kora kafin cikin Azama tabi bayanta. Rabon data hau saman harta manta amma yanzu saboda bala'i nacin ranta tsaf ta haye har suna bangazar juna da Sumayyan kai bakace da wani kaya a jikinta ba. Qofar part din Khalil data gani a bude kuma nan Sumayyan ta shiga babu bata lokaci ta mara mata baya, sosai ta bude ido tana kallon Falon da aka qawata yayi kyau harya gaji da haduwa, daga kan Kujeru Zuwa labulale kayan kallo da sauran kayan kwalliyar falo babu abinda ba'a saka ba masu kyau da tsari. Wasu Samari biyu suka fito daga dakin da yake matsayin Master bedroom suka kalli Sumayya suna gaya mata sun gama. Daman suna shiga da Umaiman kitchen ta wuce abinta ta dakko kaskon da suka kunna garwashi dan haka tayi musu sannu tace su sauka qasa su karbi Abinci gasu nan fitowa yanzu zasu wuce. Showglass din turaren wuta ta bude ta debi wanda zata zuba nan da nan qamshi ya fara tashi a gurin, bata ko nuna alamar tasan da tsayuwarta ba ta shige dakin da Samarin suka fito se Umaimah ta bita kamar Jani Talo, Sumayya ta ajiye Kasko ta wuce tana gyara zaman labule kafin ta kashe fitilar dakin ta dakko kaskonta ganin Umaimah tsaye a bakin qofa kamar wadda ta samu mantuwar tunani yasa cikin gatsali tace mata "Malama ki fita zan kulle tunda nan ba dakinki bane" "Ke da izinin ubanwa kuka shigo mun gida sannan wadannan kayan na wanene?" Umaimah data rasa tunanin da zatayi ta fada se Sumayya ta watsa mata wani banzan kallo kafin tace "Da izinin uban wanda ya isa, kaya kuma ki tambayi Mijinki ze fiyi miki bayani kalar wanda qaramar qwaqwalwarki zata dauka ni da Allah Malama ki fita na kulle muna da abinda zamuyi inke baki dashi" ta janyo qofar garam ta rufe har tana buge Umaimah ba tayi wata wata ba kuwa ta finciko Sumayyan duk qibarta da yake a bazata abin yaje mata se gata wanwar a qasa Kaskon hannunta ya fadi qasa ya fashe wuta ta zube a qasan. Da sauri ta matsa tana dafe qugunta daya bugu, wata Qanwar Maman Humaira da ta bi bayansu saboda tsoron abinda ka iya faruwa tayi saurin kama Sumayya ta miqe tana mata sannu. "Kan uban nan ni kika kayar wallahi sena nuna miki na fiki hauka a gidan nan" Sumayyan ta fada tana qoqarin fincike hannunta Umaimah ta kalleta cikin ido tace "Tun kafin raina ya gama baci ku tattara tsiyarku ku fitar da ita daga gurin nan" "Saboda gidan ki ne ko yaya? Ke ki qaddara ma gidanko ne tunda Mijinta yace nan ze ajiyeta baki isa ki hana ba kuma kaya sun shigo kenan kamar yanda me su take tafe gobe da yardar Allah gara ma ki Adana haukarki qila tayi miki amfani a gaba" Sumayya ta mayar mata se Umaimah ta sake zabura tayi kanta tana cewa "Zan nuna miki hauka kuwa ganin idonki karku kwashe ku jira na dawo duk se kun gane kurenku" fuuuu ta fice daga falon ta sauka qasa, bangaren Hajiya ta nufa a fusace so takeyi taje taji da izin wa za'a ajiye wata a gidanta bama zata kira Khalil ba dan tasu daban seya gane kurensa wlh. Hajiya na zaune da wasu Aminanta da suka zo mata Allah sanya Alkhairi ana ta maida zancen yanda abu ya faru Umaimah ta diro musu kamar Kirsimeti ta cake a tsakiyar falon tana haki qirjin Hajiya ya buga dum kafin kace me zufa ta fara keto mata a ranta fadi take ta faru ta qare wai anyiwa me dami daya sata. "Hajiya bana buqatar sanin koma su waye wadancan kwanciyar hanka kowa na gidan nan su fitar mun daga gida da duk tsiyar da suka shiga da ita idanba haka ba na rantse da Allah se rankowa ya baci a gidan nan, saboda tsabar neman bala'i me ya hana ke ki sauko daga naki saman ki bashi ya saka matar seni ana mun hassada na sakata na wala a cikin gidana za'a kawo faccala a ajiye mun to wlh qaryane kuma har gaban abada na ci gida gara ma ku cire idonku daga kai". Yanda kasan sakarkaru haka qawayen hajiya suka bude baki da hanci suna kallonta, Hajiya Uwani guda daga ciki tayi qarfin halin cewa "Amma dai ke wannan yarinya duk inda kika fito ba yar arziqi bace ke, uwar data Haifi Mijinki kika iya tsayawa a gabanta kina gaya mata kausasan kalamai haka saboda baki da tarbiyya? Koda yake ma sakarya ce ke baki san abinda kike fada ba naga alamar Kishi ya taba miki kwakwalwa har baki gane abinda kikeyi to ki fita daga nan tun kafin na harzuqa nayi miki dukan tsiya a nan mara kunyar banza da wofi". Tun kafin ta idar Umaimah taja uban Tsaki tana kallonta tace "Idan ban kasa da mutum ba karya dauka" kafin ta sake kallon Hajiya da gaba daya ta muzanta tace "Hajiya ki tashi ki fitar dasu tun kafin nayi abinda kowa ze zo yana nadama a cikin gidan nan" "Kinga Umaimah ki nutsu, ni Babana ba yace kina Asibiti an kwantar dake ba?" Hajiya ta fada tana nufarta se Umaimah taja da baya tana cewa "Saboda yasan munafuncin da kuka shirya ai shiyasa ya daukeni ya kaini Asibiti zanyi maganinku gaba daya yanzu" ta juya sukayi karo da Lubna wayar dake hannun Lubnan ta fadi qasa Umaimah ta bita da kallo saboda ganin wani hoto akai kamar na Khalil akan wayar Lubna ta tsugunna ta dauka har tayi gaba kuma ganin Umaiman ta tsaya ta dawo baya tana murmushi tace "Aa ya na ganki haka baki shirya ba ko ke ba zakije ki taya Habibin naki murna ba bayan shi gashi can saboda zumudi ya kasa zama seda yabi Amarya gurin kwalliya, kalle su ki gani dan Allah basu dace ba" Lubnan ta qarasa tana nuna mata screen din wayarta. Video Khalil ne yake tafiya rungume da wannan yarinyar ta gidan su Mansur, dukda kwalliyar data sha irin ta Amare bata kasa ganeta ba saboda irin tsanar da tayi mata a zuciyarta, Khalil din ya riqeta a jikinsa yana dariya ita kuma tana boye fuskarta a jikinsa alamar Kunya bata san sanda ta fizge wayar daga hannun Lubna ba ta dawo da video daya qare farko, yanda ta kwale ido tana kallon wayar ka rantse kwalli tayi da Attaruhu take neman iska ta shiga ta fifita mata. Ta maida video baya bayan ya qare yafi sau nawa duk a qoqarinta nason ganin abinda take ya canza daga Khalil dinta zuwa wani mutum amma hakan ta gagara, ta ko ina Video ya tabbatar da cewar Khalil ne dan video daukar kusa ne tar fuskokinsu suka fito kamar ma magana sukeyi cire sautin akayi ga kayan da suke jikinsa dasu ya barta a Asibiti yanzu wayasa da Key din mota dake riqe a hannunsa duk ta shaidasu se kuma meya rage da zata tabbatar da cewar Khalil ne? "Kawo na nuna miki sauran naga kina ta maidashi baya" taji muryar Lubna a tsakiyar kanta, cikin Azama ta dago a abinda be wuci second daya ba ta rotsa wayar da qasa kafin ta saukewa Lubna kyakykyawan tukuicin Mari taci kwalarta cikin wata murya tace "Idan kina so ki tsira da ranki da lafiyarki ki bani amsa kawai, Ina Khalil kuma wacece wannan dana gansu tare?" Lubna kuwa Mari da shaqar da tayi mata a lokaci data sun shigeta, lokaci daya ta firgice da ganin yana yin Umaiman ba tareda bata lokaci ba kuwa ta bude baki dakyar saboda shaqar data sha tace "Yana gurin Kwalliya yaje dauko Amaryarsa daga can ze kaita gurin da zasuyi Yinin biki" "Amaryarsa? Yinin biki?" Ta shiga maimaitawa a fili abinda yasa ta sassauta riqon da tayiwa Lubna kenan har Qawayen Hajiya da suka kawo mata dauki suka samu nasarar karbarta daga hannun Umaimah nan ta durqushe kuwa ta shiga tari dan ta dandana mata qamshin mutuwa, matsa tayi mata bata wasa ba hakan ya tuna mata da dukan data taba lakada mata shekarun baya randa suka fara zuwa gidan da Yayarta. A sannu kuma cikin nutsuwa Umaimah taja qafafunta ta qarasa inda Hajiya take zaune kamar dutse tun shigowar Umaiman ta dauke wuta, ta bude baki yafi sau goma amma ta gagara furta abinda take so ta fada saboda yanda kalmar tayi mata nauyi a qirji, a hankali ta lumshe idonta ta hadiye wani abu kafin ta budr ta sake kallon Hajiyar cikin wani irin sauti tace "Hajiya nasan kina jina mu me Lubna take nufi da maganarta?" Dagowa Hajiya tayi a sanyaye ta kalleta tace "Umaimah kiyi haquri ki koma Asibitin kinji" "Hajiya tambayarki nayi kawai ki bani amsa babu ruwanki da dukma inda zani daga nan nidai kawai buqatata ki qara mun bayani akan abinda kunnuwana sukaji" ta sake fada tana dagawa Hajiyar hannu se daya daga cikin Qawayen Hajiyar ta yunqura da niyyar Magana Hajiya tayi saurin dakatar da ita tana miqewa tsaye ta nufi Umaimah tace "Muje ciki nayi miki bayani toh" "Babu inda zanje daga nan gurin harse kin gaya mun abinda nake son naji" Umaiman ta fada cikin daga murya tamkar me yi da yar cikinta daidai nan aka sake bude qofar falon Jalilah da Jamila suka shigo cikin shiga ta alfarma sunyi anko na Lace haka fuskokinsu sunsha make-up. "Meye haka? Ke wace fitsarar kikeyiwa mutane da ake jiyo muryarki tundaga tsakar gida?" Jalila ta fada tana kallon Umaimah swta juya a fusace ta kalleta tace "Bada ke nake ba da uwar data haifeki nake dan haka ki sararamun" ta sake jutawa kan Hajiya da jikinta ya dauki rawar tsoro saboda hango kamar Iskokan Rashin mutunchin Umaiman zasu tashi da tayi cikin rawar baki tun kafin ta sake yi mata magana tace "Kinga Umaimah kiyiwa Allah mu shiga ciki bari na kira Khalil din duk inda yake yazo yanzu se kiji komai a bakinsa ma" "Wai Hajiya menene haka saboda Allah wannan mara mutunchin yarinyar kike bawa haquri me aka mata ba dole ma ta sake rainaki ta ringa miki duk cin kashin data ga dama ba, dallah Malama zo ki fita daga nan bakiji kashedin da nayi miki ba kenan akan Hajiya to wlh ko kishiga hankalinki ko yanzu jikinki ya gaya miki" Jalila ta fada a fusace "Idan baki dakeni ba Aisha da Usman shegenki sukayi Jalilah, ni zaku rainawa hankali ni zaku yaudara? Ashe daman abinda Mama da yan uwana suka fada mun gaskiya ne ni zaku yiwa rufa rufa a cikin gidan nan ku cuceni ku daurawa Mijina aure da wata ba tare da na sani ba?" Umaimah ta fada cikin wani sauti jikinta ya dauki rawa take idanunta suka rine zuwa Jaaa kamar jini ya kwanta, da hannu ta shiga nunasu tana jan nufashi maganar ma ta gagara fitowa daga bakinta se ta juya kawai ta fice daga falon Jamila tabi bayanta Ita kanta Jalilah da take a hasale nan take jikinta yayi sanyi saboda ganin yanayin Umaiman Hajiya kuwa hannu ta dora a kai tana kiran "Shikenan kun gani ko Jalilah kinga abinda nake gudu Allah gamu gareka ka karemu daga sharrin zuciyar wannan yarinyar". "Hajiya Aisha Allahya sanya Alkhairi ya kuma rufa asiri nidai bari naje" Hajiya Uwani ta dauki jakarta ta maqala gaba daya sauran suka mara mata baya sunayiwa Hajiya sallama ganin wannan tashin hankali dake shirin ballewa a gidan kowacce ta fita da tambayar daman Uwargidan Khalil din bata san yayi aure ba kenan? Umaimah kuwa tana fita a compound din daya raba bangaren nasu taci burki tabi motar yan jere da kallo Sammani ya bude Musu Get suka fice. Gurin da Sammani yake zama ta kalla, wata ajiyar zuciya ta sauke saboda hango zungureriyar Kokarar da yake ajiyewa a kusa saboda barayi, bata kulashi ba da yake tambayar me take buqata ta zari qaton sandan tayi cikin gida, Jalilah data biyota taja da baya a zatonta ita zata lodawa Umaimah kuwa ko kallonta batayi ba ta shige falonta kai tsaye ta haye sama ta murda qofar falon Amarya cikin Sa'a ta jishi a bude ta tuta qofar ta shiga, bata tsaya bata lokaci ba ta shiga dukan duk abinda hannunta ya kai kansa. Sedata rugurguza mata kayan kallo tas da su Centre table, Showglass, frames, flower vase da duk wani abu da ze iya fashewa kafib ta wuce da niyyar shiga bedroom din nan qofar a kulle bata haqura ba ta ringa dukan handle din qofar a qoqarinta nason ta lalata shi ta samu ta bude qofar daidai nan Su Jalilah suka hawo saman gaba daya saka saka salati ganin irin barnar da tayi cikin Tashin hankali Hajiya take cewa "Haba Umaimah ba se kinyi haka ba kiyi haquri a warware komai cikin nutsuwa wallahi muma ba'a son ranmu ba Allah ne ya qaddara faruwar hakan amma..." "Kiyi mun shiru tsohuwar munafuka har kina da bakin cemun wani abu bayan duk abunda kika shirya yanzu zakice mun ba'a son ranku ba a son ran kutumar ubanki ne kenan kika aura masa yar qawarki sannan kice mun ba'a son ranki ba to idan kin cika ki qaraso nan ki gani na rantse da Allah sena rotsa miki kai ki mutu kowa ya huta na rage mugub irin Azzalumai macuta" "Ke Umaimah baki da hankali ne Hajiyar kike gayawa haka?" Jalilah ta harzuqo zata qarasa inda take Hajiya ta riqeta tana girgiza mata kai tace "Aa Jalilah karkije ba a hayyacinta take ba maza ki kira Khalil, Jamila dakko wayata ki duba lambar Hajiya Malika ki kirata dan Allah su taima suzo" "Amma Hajiya.." "Kiyi abinda kawai na sakaki Jalilah" Hajiya ta dakatar da ita, wani mugun kallo ta watsawa Umaimah data tsaya taja jiran wani cikinsu ya qarasa ta sauke masa kafada tayi kafin ta juya ta sauka qasa suka bar Hajiya tsaye dan tuni Jamila ta tafi dakko wayar Hajiyar itama. "Ki bisu idan kina son ranki da lafiyarki" Umaimah ta fada mata cikin hargagi se Hajiyan ta juya da sauri ta bar saman, Umaimah kuwa dukan qofa taci gaba dayi so kawai takeyi ta bude ta qarasa aikin data fara kafin ta ragargaza Angon ta kumaje ta ragargaza Amaryar kamar yanda tayi mata alqawari, seda ta gaji da dukan qofar amma taqi buduwa ta haqura ta sauka, bazata iya misalta abinda take ji ba a taqaice ma zata iya cewa bata tantance komai ita dai tasan tana da rai kuma tana numfashi sauran abunda takeyi umarnin zuciyarta kawai take bi badan tasan abinda take aikatawa ba. Abu daya take ji a kunnenta kuma take gani Lokacin da Mama take gaya mata Khalil yayi aure se kuma hotonsa da waccen yarinyar da yake mata yawo a ido. Qofar part dinsu ta dawo ta tsaya, Hajiya da yayanta na tsaye daga tasu qofar da alama jiran masu kawo dauki sukeyi akayi horn Sammani ya bude Get da gudu motar Khalil ta danno cikin gidan, kamar walqiya haka ta miqe tadurfafi motar da gudu, Khalil dabe lura da tahowarta ba dan waya yakeyi da Amaryarsa daya baro yanzu zuwan da yayi gidan kaya yazo ya canza danta kafa rigimar ko bazeje gurin Kamu ba to yazo suyi hotuna dan haka yazo ya saka babbar riga,duk uban kiran da Jalilah ta ringa masa be daga ba saboda zatonsa maganar Bikin zata masa yana qoqarinfaka mota se ganin mata yayi kamar an jefota Allah ya taimaka ya riqe motar yana salati kafin ya qarasa gane abinda yake faruwa qarar fashewar glass din gefen da yake zaune ta cika gurin cikin Azama ya durqusa dukda haka seda wani ya yanke shi a gefen fuska, ya balle murfin motar da bala'in sauri ya fice ganin ta sunkuya daukar kokarar data yi masa aika aikar da ita ta fadi. Qoqari yakeyi ya gane me yake faruwa a gidan dan shi bema gane Umaimah bace so yake yaga wace mahaukaciya Sammani ya bari ta shigo musu saukar dutse yaji a goshinsa se a sannan kuma idonsa ya gane masa Umaimah datayi biji biji kamar wadda ta tsumu a cikin hauka ta sauke masa Kokarar a qeyarsa Dafe be ko tsaya takan Zugin Azabar daya ziyarceshi ba yayi baya ganin ta sake durfafoshi ido rufe, baya buqatar wani qarin bayani abin boyene ya fito fili qila se yanzu kwakwalwarta ta gama fassara mata duk maganganun da ake gaya mata ko kuma yanzu ne ta samu gamsashshiyar hujja data saka ta yarda da, amma ita daya baro a Asibiti meya kawota gida? Ganin tana qoqarin qara loda masa itace a duk inda Allah ya bata sa'a ya saka qarfi ya murde hannunta ya kwace Kokarar ya jefata gefe Sammani yabi da gudu ya dauke, Umaimah kuwa ganin ya rabata da makamin ta cakumi kwalarsa ta shiga kai masa duka kota ita da hannayenta se a sannan ta fashe da matsanancin Kuka tana cewa "Allah ya isa tsakanina dakai Khalil Dan iska macuci maci Amana Azzalumi mayaudari ma ha'inci wallahi Allah baze barka ba yanda ka cuceni ka yaudareni se Allah ya bimun haqqina akan ka kaida munafukar uwarka data tayaka kuka yaudareni wallahi se kunga sakayya akan abinda kukayi mun". "Relax Umaimah relax" ya iya fada yana qoqarin riqe hannayenta amma ina qarfin data samu yau din ya zarce misali gashi shi kuma dukan datayi masa a qeya ba qaramin shigarsa yayi ba dan daga tsayen da yake jiri yake ji kamar ze kadashi, ya waiwaya ya kalli su Hajiya da sukayi cirko cirko aka rasa me kai masa agaji a cikinsu kowa ka kalla fuskarsa ta nuna zallar tashin hankali, kome ta tuna a sukwane Umaimahn ta saki kwalarsa tayi part dinsu tana ci gaba da kuka kamar ranta ze fita Khalil ya bita a baya yana kiran sunanta, a duniya bayan ranar da ze mutu wannan ce rana ta biyu da tun faruwar al'amarin yake taraddadin zuwanta domin be san a yanda zata zo masa ba. A tsakiyar falon yaci birki ganin ta fito daga kitchen da sharbebiyar wuqa a hannu ta se kyalli takeyi ya bude ido dakyau yana kallonta ganin shi ta durfafa da wuqar ai tuni ya manta da wani jiri da zafin da qeyar sa takeyi ya kwasa a dari da sittin ya fita waje Umaimah ta mara masa baya tana kuka tana fadin "Na gaya maka duk ranar daka kuskura ka hada soyayyata data wata sena kashe ka na kasheta sannan na kashe kaina baka ji ba yau zan nuna maka da gaske nakeyi wallahi Khalil sena kashe ka da dai ka hadani da wata mace gara na rasaka har abada" ta fada tana binsa da wuqa tsirara hankalin su Hajiya ya qara tashi gaba daya suka rude suna kiran sunanta amma ina bata ji se bin Khalil take tana kuka shi kuma yana gudu hankali tashe dan babu yanda za'ayi ya tsaya be san me zata aikata masa ba. Get ya nufa da gudu ta bishi, yana qoqarin bude qofar aka turo ya saki ajiyar zuciya ganin Mama cikin tashin hankali Salman na bayanta da AbdulBasit dan Yayanta jikinsa sanye da Uniform dinsa na police da alama daga gurin aiki yake, ko a jikin Umaimah babu abinda ta fasa saboda ganinsu kai tsaye ta sake durfafar Khalil daya maqale jikin Get yana raba ido dake da qeya, Qafa AbdulBasit din ya saka mata ta tafi kamar zata fadi kafinta kai qasa ta tareta wuqar hannunta ta fadi Salman ya dauki yayi waje da sauri. "Ka sakeni, ku bani wuqata in kashe shi wlh sena kashe shi ai na gaya masa amma beji ba ku rabu dani" Umaimah ta fada tamkar me maye lokaci daya numfashinta yana sarqewa idanunta suka qaqqafe kafin suyi wani yunquri jikinta ya saki gaba daya Abdilbasit ya gyara ruqon da yayi mata yana cewa Khalil "Kama munita mu sakata a mota akaita Asibiti ta suma" se Khalil din yayi gaba ya dawo baya saboda yanda gaba daya tunaninsa ya rimice ga wani mugun ciwo da kansa yake masa sakamon dukan datayiwa qeyarsa. Su Hajiya suka qarasa bakin Get din Jamila ce tayi qarfin Halin matsawa ta kama masa Umaiman tana cewa "Baze iya ba, shima ba a hayyacinsa yake ba abu ta buga masa akai" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha" Mama ta fada gaba daya ta rikice ta rasa abinyi, haka suka taru suka ciccibata aka sakata a motar dasu Maman suka zo su kuma suka shiga motar Khalil banda Jalila da tace babu inda zataje, Asibiti suka nufa. Emergency aka karbi Umaiman, suna dorata akan Gado ta farka da wani mugun qarfi ta zabura zata sauka Nurses uku suka hadu suka danneta, tana bige bige tana zaginsu maganganu takeyi marasa kan gado da su basu fahimci abinda take magana akai ba abu daya suke iya fahimta kalmar seta kashe da take ta nanawata a haka Likitan yayi mata allurar bacci wadda seda akayi da gaske kafin ta dauketa. A can reception kuwa gaba daya sukayi cirko cirko banda Khalil daya zauna a qasa ya dafe kansa da yake ji kamar ana girki a ciki tsabar zafin da yayi masa, Abba da Mama ta kira tun suna hanya ya qaraso Asibitin tareda Anty hankalinsu a mutuqar tashe, a taqaice suka gaya masa abinda ya faru suna nan tsaye suna jajantawa Wata Nurse ta fito da gudu daga ward din da aka kwantar da Umaimah tana kiran Dr, "Wannan patient din da aka kawo Dr inaga tana da tabin hankali gata can ko 29 mins ba'ayi dayi mata allura ba ta farka tana ta buga kanta a bango tana kuka mun rasa ya zamuyi da ita" Nurse ta fada jikinta na rawa dan tunda take a Asibiti bata taba cin karo da psychiatric patient ba se yau kuma shahararre da haukansa yayi nisa irin na Umaimah. A fusace Abba yabi bayan Dr zuwa dakin, Umaimah na tsaye tana zugawa Nurses din zagi na tsamar nama akan su bude mata qofa ta fita sunqi Dr ya bude ta waje suka shiga tana ganinsa ta yunqura da niyyar fita Abba dake bayanaa ya zabga mata marin daya sa tayi gefe ta tsaya babu shiri "Ki nutsu ki shiga hankalinki wlh tun kafin kija nayi miki abinda zanzo ina nadama daga baya. Ke wace irin kafaffiyar yarinya ce da baki san Annabi ya faku ba? A rayuwarki baki san komai se tashin hankali da bala'i ke baki zauna lafiya ba mu baki barmu munsamu nutsuwa ba kashe mu kike so kiyi kome Umaimah?" "Ni babu ruwanku dani Abba babu wanda nace ya shiga sabgata baku ga abinda akayi mun ba Aure fa Khalil yayi Abba ya munafunceni ban sani ba se yau sannan kuma ku hanani hukuntashi wannan ai ba adalci bane nidai tunda babu me qaunata duk ba zaku iya kwatarmun haqqina ba se ku barni daman nasan ba sona kuke yi ba na sani ma da hadin bakinku yayi shi yasa Mma dasu Anty Hafsa suka ringa zuwa suna fadamun maganganu ashe kunsan abinda kuka shirya nidai Allah ya isa kuma an cuceni Allah yana kallo bazan yafe ba duk wanda yake sa hadin baki a maganar nan Allah ya bi mun haqqina" Umaiman ta fada cikin matsanancin kuka Abba da baqin ciki ya qumeshi ya sake niyyar kai mata Mari ta goce yayi taga taga ze fadi saboda jirin daya taho masa Likita ya riqeshi yana cewa "Yi a hankali Alhaji karka fadi kayi haquri ka kwantar da hankalinka". Cikin bacin rai ya kalli Umaimah da har sannan take kuka yace "Kaiconki Umaimah kaicon zuciya irin taki, ashe ke ba zaki taba yarda da cewar duk abinda ya samu bawa daga Allah bane? Ba zaki iya haquri da duk jarabawar data sameki a rayuwa ba? Iya wannan auran idan kinada hankali ya isheki ishara amma a maimakon ki dauki darashi ki nutsu sema sake bude babin hauka kikayi ko to kiji da kunnenki karki fasa duk abinda kika yi niyya zan kuma sake jaddada miki Khalil yayi aure babu kuma abinda ya isa ya tada wannan aure se ikon Allah kuma ko kinso ko baki so ba a yau ba se gobe ba ze tare da Matarsa a cikin gidanki a dakinki tunda kin Lalata abinda iyayenta suka saka mata idan yaso baqin ciki yasa ko hadiyi zuciya ki mutu kowa ya huta yar banza me zuciya irinta kafiranfarko" yana gama fadar haka ya sa kai ya fice daga dakin zuciyarsa na wani irin tuquqi, badan karya butulcewa Allah ba daya yi nadamar kasancewar Umaimah jininsa. Cak ta tsaya da kukan kalamansa sukayi mata dirar Mikiya wai Abba ne yake gaya mata Khalil ze tare da wata mace yau a dakinta akan Gadonta? Seta miqe da wani irin sauri a take kuma kamar wadda aka mayar ta fadi yaraf a gurin kamar me farfadiya tana jijjiga Likitan yayi kanta da sauri Nurses suka rufa masa baya, seda suka mayar da ita kan gadon kafin suka shiga bata taimakon gaggawa sun kwashe sama da minti talatin akanta kafin jijjigar ta tsaya jikinta ya saki gaba daya numfashinta kansa se a hankali dole suka saka mata oxygen bayan Likitan ya mata duk abinda ya kamata yayi suka fita daga dakin aka barta da Nurse guda daya. Reception din ya koma yana dafe kansa da jarabar Umaimah tasa ya fara maaa ciwo, suna zaune kamar ana zaman makoki sabanin da yanzu su Nuratu sun qaru da wasu daga bangaren Hajiyar dan tuni Lubna ta dake maqale a daki tunda tasha matsa ta kai labari Family group dinsu. Suna ganin Likitan Hajiya da Anty sukamiqe da sauri suna tambayarsa jikinta cikeda qosawa yace musu "Da sauqi amma kuyi haquri yanzu ku barta kar wanda ya shiga inda take saboda tana da buqatar hutu sosai" "Toh likita cikin jikinta fa, daman ba kunce gobe zaku mata aiki ba meze hana ayi yanzu saboda gudun kar wani abu ya same shi" Hajiya ta fada se likitan ya girgiza kai yace "Baze yuwu ba Hajiya, maganar gaskiya a yanzu haka ta sake Suma sannan jininta ya hau har ya wuce qa'ida baze yuwu muyi mata Allurar Anesthesia ba saboda idan abun yazo da tsautsayi zata iya zarcewa dole se mun jira ta farka sannan jininta ya daidaita kafin koma menene ya biyo baya, nidai roqon da zanyi muku ku barta ta huta dan Allah zuciyarta da kwakwalwarta su samu hutu sosai, Ina Mijinta ya biyo ni ina son magana dashi" daga haka ya wuce office ya barsu nan a tsaye. Khalil ya fito daga wani office dayaga likita shima ya auna BP sa ya rubuta masa magani yace yasha ya samu yayi bacci ciwon kan nasa ze sauka, seda yaje gurin likitan daya duba Umaimah ya sake masa bayanin daya musu kafin ya fito yaje pharmacy ya siyi maganin da aka rubuta masa a gurin ya sha ya sake dawowa reception din ya tarar dasu, Abbane ya kirashi suka fita tare. Duk su biyun idan ka kallesu kasan babu me nutsuwa a cikinsu, can gurin wata bishiya suka tsaya Abban ya kalli Khalil da shi kuma yake kallon qasa yace "Ibrahim kayi haquri ka qara akan wanda kakeyi dukda dai Allah ya sani ban rufeka ba tun kafin na baka auran Umaimah seda na zaunar dakai na gaya maka wacece ita kuma a hakan kace kaji ka gani kana sonta na tabbata a sannan baka san cewar Jidalinta ya kai har haka ba, bamu tara sani da ikon Allah kuma ita qaddarar mutum baya kauce mata badan da qila yanzu kana gudanar da rayuwarka cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. A taqaice abinda nake so na gaya maka shine karka dauki wannan abun da tayi a matsayin wani abu da ze tsorata ka kota dakatar dakai daga yin duk abinda kayi niyya. Naji ance ta lalatawa Amarya dakinta kuma gobe ya kamata ta tare ko?" Khalil ya gyada kai kawai se Abban yaci gaba da cewa "Shikenan amma hakan baze canza komai ba, ka dauki dakinta da take ciki da komai ka bawa Amaryar ita kuma idan ta warke ta shere inda ta lalata ta koma ciki ban kuma yarda naji ka ce ba haka na Umarni na baka idan har ka daukeni a matsayin Uba sannan kamar yanda aka tsara tarewar Amarya a gobe idan Allah ya kaimu zan kira Kawunka nida shi zamu dakko Maka Amaryarka mu kawo maka ita idan Allah ya yarda". Kallon Abban yayi yana so yayi magana amma ya sake katse shi da cewa "Bana so naji komai sannan maganar nan ta tsaya tsakanin nida kai ko Mahaifiyarka karka fada mata nida kaina zanyi mata bayani babu abi da za'a jira kuma yarinya zata tare a dakinta ita kuma Allah ya kaimu ta tashi zanyi maganinta in Allah ya yarda. Se Magriba suka watse daga Asibitin aka bar Mama da Anty Hafsa har sannan kuma Umaimah bata kuma farkawa ba sedai likita yana shiga ya dubata ya kuma tabbatar musu babu damuwa zuwa dare zata farka suna fatan kuma kafin sannan komai ya daidaita. Guraren goma Khalil ya koma Asibitin dan tun bayan da suka gama magana da Abba ya wuce gida Adaidaita ma ya hau ya kaishi be zata ze iya bacci ba nan da sati daya ma se gashi da taimakon maganin daya sha yayi bacci sosai har bayan Isha sannan ya tashi bayan yayi wanka ya rama salloli ya leqa Dakin Humaira yaga barnar da Umaimah tayi, gaba daya gidan Qamshin Humarar da suka malale a qasa yakeyi ya maida qofar ya rufe yana tunanin abinyi ya wuce bangaren Hajiya a canya tarar da Jalilah ta kafa daba sun dawo daga gidan biki dan duk wannan tashin hankalin da aka sha seda taje da mutanenta Jamila ce kadai bata je ba suna Asibiti tare dasu Hajiya sunje sun sha bidirinsu dan basu gaya musu abinda ya faru ba suma kuma yan jeren da yake ba masu surutu bane basu fadi abinda akayi ba Mama kadai Sumayyan ta gayawa ita kuwa da dama tasan za'a rina batayi mamaki ba. A daki suka qule da Hajiya take gaya masa zancen kawo Amarya gobe da Baban Umaimah yayi, "Babana ina jin tsoro, nayi nayi Alhaji ya fahimceni amma yaqi ya kum samu goyon bayan Baban ku Abubakar sun kafe akan gobe zasu dakko Amarya dan har ma sunyi magana da Kawun nanta su kuma sun sanar da Hajiya Hauwan dazu ta kirani take ce mun babu komai hakan ma yayi ai suma iyayenta ne daga baya duk me son zuwa yaga daki se yazo, nidai ban gaya mata halin da ake ciki ba gaskiya dan bansan ta inda zan fara mata bayani ba" Hajiya tayi maganar cikin jimami, se Khalil yace "In sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi Hajiya" "Toh Allah yasa" daga nan yayi mata sallama ya koma Asibitin. A canma dai maganar suka sakeyi da Mama da Anty Amina suna sake qarfafa masa guiwa, har gurin sha biyu yana can kafin yayi musu sallama ya tafi har sannan kuma Umaiman bata farka ba. Kamar yanda Abba da Baba Abu sukayi Alqawari washe gari aka kawowa Khalil Amaryarsa, sedai basu je da kansu ba kamar yanda suka tsara daga baya suka canza shawara dan haka Aka wakilta Mata guda uku daya daga bangaren Mahaifinsa daya qanwar Hajiya se Aminiyarta daya suka dakko masa Amarya ta iso da rakiyar nata iyayen guda hudu suma. A bangaren Hajiya aka tarbesu kuma anan suka barta suka wuce suna yi musu fatan zaman lafiya. Khalil na Asibiti aka kawo Amaryar dan wunin ranar gaba daya acan yayi shi kuma tun jiya da rana da suka rabu akan zeje ya canza kaya ya koma suyi hoto basu sake yin waya ba wayar tasa ma a motar ya barta be dauka ba har sannan, a bakin Sammani da sukaje kai abincin dare yaji cewar Ankawo Amaryar. Seda Mama ta matsa masa kafin ya bisu gida suka koma tareda Khalifa da Sammani. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 72 Ko minti goma Khalil beyi da fita Abba da Anty suka isa Asibitin. Abban ya tsaya akanta yana kallo ta kafin juya yana tambayar Mama har yanzu bata farka ba Maman ta sauke numfashi tace "Bata farka na Alhaji amma sunce da vi gaba tunda gashi numfashinta ya daidaita sun cire mata Oxygen bacci takeyi kowanne lokaci kuma zata iya farkawa" "Toh Allah ya tashi kafadunta ya kuma sanyaya mata zuciyarta ta karbi qaddara a yanda tazo mata tunda me afkuwa ta rigada ta afku yanzu haka yarinyar ma tana cikin gidan, ni ina ganin koda ace an sallameta daga nanzamu wuce da ita can gidane zuwa wani lokaci seta koma, Allah dai ya qara rufa Asiri". Haka suka ci gaba da zama a Asibitin basu ankare da lokaci ba se gani sukayi sha biyu tayi, Abba da Anty suka tafi gida suka bar Mama da take kwana da ita kafin ya tafi seda ya sake magana da Likita ya tabbatar masa da komai lafiya sannan idan bata farka zuwa Safiya ba zasu farkar da ita da kansu. A hankali ta sauke dogon numfashin data riqe tun zuwan su Abban ta farka daga baccin wahalar da take tayi tun jiya tana farkawa kuma duk abinda ua faru ya dawo mata a kwakwalwa tamkar a lokacin yake faruwa. Hirar da Abba da Maman sukayi kaf a kunnenta, sanda taji yana gaya mata Amarya ta tare seda tayi da gaske kafin ta hana kanta fasa Ihun da ze sa susan idonta biyu, taci gaba da kwanciya tana saqe saqen abinda ya kamata tayi a zuciyarta, a haka Nurse did da take dybata ta shiga ta sake mayar mata da ruwan da ta cire mata dazu ba tareda tayi aune ba bacci ya sake awon gaba da ita. KHALIL Cikin mutuwar jiki ya shiga bangarensu, Dakin Humaira ya fara shiga an guara shi tsaf dan tunda safe ya saka su Sammani suka gyara aka kwashe duk abinda ya lalace a ciki kijerunta kadai ta tsira dasu baya ga haka babu wani abu da ze moru a kayan falon sedai ko Carpet idan an wanke shi. Seda ya gama duba gurin kafin ya kulle ya wuce Dakinsa. Wanka ya shiga, ya dade yana wankan shikansa bazece ga dalilin wannan wankan da ya zauna ya ringa dirje jiki kamar wanda ya shekara beyi ba. Kansa ya kalla a Mudubi yaso ace yayi Aski jiya se kuma wannan tashin hankalin ya bullo. Haka ya fito ya shafa mai da turaruka a jikinsa gaba daya a sanyaye yakeyin komai. A gurin zabar kayan da ze saka ma seda ya bata lokaci, Sky blue sabuwa ce be taba sakata ba ya zura kayan sun zauna masa a jikinsa irin dinkunan da Umaimah take so Abuja style Riga Jumper me gajeran hannu kayan sunyi matuqar yi masa kyau kamar a jikinsa aka dinka su. Seda ya sake feshe Jikinsa da turaruka ya dakko Hular data dace da kayan ya kafa ya daura Agogo, harya zura takalmi ze fita se kuma ya dawo da baya. Wardrobe ya bude ya dakko sabon Bedsheet babba dan Turkey, Umaimah ce ta siya masa da kudi bata taba shimfida musu ba ya cire wanda yake kan gadon ya mayar da sabon, seda ya sake bin dakin ya kawar da duk wani abu da ba'a muhallinsa yake ba dukda babu tarkace a dakin saboda shi baya ajiye kaya a ko ina duk abinda yayi amfani dashi ya gama ze mayar dashi gurin zamansa, ya jona Bunner ya zuba turaren wuta sannanya saisaita sanyin Ac daya kunna kafinya kashe fitila ya fice daga dakin. Missed calls din Hajiya ya gani a wayarsa dana Anty Amina, qarfe goma da minti biyar ya ringa mamakin lokacin daya bata dan haka cikin hanzari ya tafi bangaren Hajiyar dan yaji kiran da take masa. A bakin qofa suka hadu da yan uwansa da alama tafiya zasuyi. Jalilah ta dauke kai tayi gaba Anty Amina ma fuska babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwar da yayi musu kafin tace "Ai mun zata can zaka kwana tun dazu ake kiranka ga yarinyar mutane can ka barta ita kadai". Kansa ya sosa ba tareda yace mata komai ba Jamila ce ta dan saki fuska tace "Zaka sha rarrashi yau dan Amaryar nan taka da gani rigimammiya ce tana can ko ruwa taqi sha tunda aka kawota, na aiki Khalifa dai ya siyo muku dan abinda zaku buqata dan nasan dakyar in kayi tunanin nemo mata abinda zataci" "Backs yar uwata you are the best" ya fada yana rungumeta ta gefe Jamila ta tureshi tana dariya tace "Toh Allah bamu Alkhairi", a fusace Jalilah da har tayi nisa ta dawo tana kallon tace "Idan ba zaki tafi bane muyi gaba kin zauna kina bata wa mutane lokaci da wanda basu san darajar kansu ba, be tanka mata ba kamar yanda itama Jamilan binta kawai tayi yasan jarabar Jalilah yanzu se a shekara tana wannan fushin to shi dan Allah meye laifin sa a nan? Idan bata tausaya masa ba ai be kamata ta qullaceshi ba. Da sallama ya shiga falon Hajiyar suna zaune ita da qanwarta Hajiya Maimuna Mamansu Lubna suka amsa masa a tare ya samu guri a qasa ya zauna yana gaishe su suka amsa gaba daya tareda tambayarsa yame jiki se ga Khalifa ya shigo da manyan Ledoji guda biyu ya kalli Khalil yace "Yaya gashi Anty Jamila tace na siyo" Ba tareda ya kalli Khalifan ba yace "Ka shiga dasu can gurin" se Khalifan ya juya ya fita. Bayan yar gajeriyar Nasiha da Hajiya da yar uwarta suka sakeyi masa Hajiya Maimuna ta miqe tana cewa "Yaya bari naje dare na qarayi" "Mama ina kuma zakije a daren nan?" Khalil ya fada yana kallonta seta yafa mayafinta tace "Gidan Alqasin zanje na gaji da ciwon bakin da yake muk akan duk sanda nazo Kano ina kwana gidan kowa banda nasa yau can zan kwana gobe in Allahya kaimu muyi Asubanci mu koma gida kuma mu huta haka" "To bari nazo na kaiki" ya fada yana miqewa se tayo saurin dakatar dashi ta riqe baki tace "Waya isa ya fitar da Ango a daren nan? Kaga tafi ka rarraso Amaryarka tana ciki tana kuka kaga ni Khalifa na can waje yana jirana shi ze saukeni daman su Lubna sunyi gaba tun dazu" daga haka tayi gaba Hajiya ta miqe danta rakata. Har Hajiya ta dawo daga rakiyar yar uwarta Khalil na zaune inda yake, so yakeyi yaje yaga Humaira hankalinsa gaba daya ya koma kanta tun jiya rabon dayaji saga gareta gashi yanzu ance Kuka takeyi. "Babana kana zaune ka tashi ka hau Saman ka sameta mana tana nan a dakina" Hajiya data dawo ta fada seya miqe yana sunkuyar da kai kamar wanda yake gaban surukai ya haye saman. A hankali ya tura qofar dakin Hajiya ya tsaya yana kallonta tana zaune a qasa ta sunkuyar da kai Habiba na tsugunne gabanta da Kofi fuskarta ta nuna damuwa yana jinta tana ce mata "Dan Allah ki dena kukan haka kisha ko madarar nan ce tunda kinqi cin Abinci, kona kira miki Yaya?" Qarasa shiga cikin dakin yayi da sallama qasa qasa Habiba ta amsa da sauri tana cewa "Yawwa ga Yayan ma yazo" ta miqe tsaye tana gaishe shi ya amsa mata idanunsa akan Humaira data sake curewa guri daya saboda shigowar tasa. Habiba ta sake shagwabe fuska tace "Yaya taqi cin abinci tunda aka kawota take kuka duk su Anty sunyi sunyi taqi haquri kuma komai aka bata taqi taci" "Jeki abinki zataci" ya fada yana qarasawa inda take se Habiban ta ajiye kofin hannunta akan Bedside drawer ta fita daga dakin ta kulle musu qofa. Seda yaga fitar Habiban kafin ya qarasa a hankali ya durqusa a gabant, a sanyaye ya kira sunanta bata dago ba haka bata fasa kukan da takeyi ba sema qara masa qarfi da tayi. Khalil ya saki murmushi kafin ya janyota gaba daya ta fada jikinsa yana cewa "Na sani nayi laifi amma ayi mun afuwa kiyi shiru yanzu i promise an jima zan rarrasheki har se kince kin haqura kinji". Banza ta masa tana ci gaba da shashsheqar kukanta, ya janye mayafin data rufe fuskarta dashi kyakykyawar farar fuskarta me cike da quruciya ta bayyana, se yaga ta qara masa kyau ya saka hannu yana share mata hawaye yace "Kin gani har idonki sun kumbura ki bari haka mana kuma kar kanki yazo yana ciwo". Rarrashinta ya ringayi ganin bata da alamar barin kukan dan idan tayi shiru kome take tunawa se ta sake fashewa da kukan dan haka ya miqe bayan ya maida ita kan Gadon Hajiya ta zauna yace yana zuwa. A qaramin falon dake sama ya samu Hajiya a zaune ta zabga tagumi, ta kalleshi tace "Ya dai Babana" "Hajiya taqi dena kukan" ya fada a hankali kamar shima zeyi kukan abin nasa ma ya bawa Hajiya dariya har seda ta murmusa kafin tace "Toh ai se ka dauketa ku tafi can kayita rarrashi aiki ya sameka, Amina tace an gyara gurin nata ko dazu sun shiga se kayi qoqari a maida mata da abubuwan da suka baci kafin yan uwanta su fara zuwa ganin guri dukda dai dazu dasu Maimuna sukaje dakkota sun sanarwa da Hauwan komai kuma Alhamdulillahi ta fahimta daman kuma nasan ba za'a samu matsala da ita ba, ina fatan kuma Allah ya tsayar da rigimar haka. Allah yayi muku Albarka ya baku zaman lafiya kai kuma ina sakeyi maka addu'a Allah ya qara maka juriya ya kuma baka ikon yin Adalci a tsakaninsu, kuje ta samu ta huta nima magani na zansha na kwanta kaina yana ciwo" "Hajiya ki cire duk wata damuwa daga ranki kodan saboda lafiyarki in sha Allahu babu abinda ze sake faruwa" Khalil ya fada a sanyaye se Hajiya ta sakeyi murmushi tace "In sha Allah, ka kira ku tafi kar kazar tata tayi sanyi" sosa kansa yayi shima yana murmushi ya juya ya koma dakin. Tana nan inda ya barta ta dai yi shiru tana jan ajiyar zuciya ya qarasa ya kamo hannunta yana cewa "Let's go wife" "Ina?" Ta tambayeshi cikin muryar kuka seya miqar da ita tsaye yana cewa "Gidanmu mana ko a nan kike so ki zauna?" "Ni gidan Mama zan koma" ta sake fada tana shirin fashe masa da kuka yayi saurin cewa "Muje na mayar dake shikenan" ta daga masa kai. Hannunsa cikin nata suka fita, a falon qasa suka tarar da Hajiya da Habiba harda Khalifa daya dawo daga kai Hajiya Maimuna dan babu nisa sosai. Har qasa Humairan ta tsugunna tana yiwa Hajiya sallama ta dagota jikinta tana saka mata albarka tareda sake maimaita mata tayi haquri, Habiba ta rakasu har bakin qofar shigowa part din tana cewa Khalil "Yaya bata ci abinci bafa" "Kin fada mun Habiba zataci kinji" ya mayar mata yana murmushi itama tayi murmushi, sosai Humairan ta shiga ranta dukda ta dan girmeta amma ta samu qawa. Humaira dai binsa takeyi ganin suna shirin shiga wani gidan a maimakon mota ta tirje ya juya ya kalleta ta fara qifta ido alamar zata ci gaba da kukan tana cewa "Kace gida zaka mayar dani kuma naga zamu shiga wani gurin" "To ai key din mota zan dakko ko a qafa kike so muje?" Ya bata amsa seta girgiza masa kai yace "Good girl" kafin ya bude musu qofar falon suka shiga. Daga bakin qofar ta tsaya tana zare ido, Khalil ya kalleta yanda takeyi ya bashi dariya kamar wadda aka sato, ciki yayi ya barta tana rarraba ido se gani tayi hasken falonya dauke ba shiri ta fasa ihu tayi ciki da gudu inda taga yabi, Khalil daya kashe hasken yayi saurin kunna fitilar wayarsa yabi bayanta gudun karta bige da wani abun ta fadi tana ganinsa ta rungumeshi jikinta na rawa tace "An dauke wuta" "Anya kodai bulb din ne suka mutu kinga waje can da haske" wajen ta kalla kafin ta kalleshi ya saketa yana cewa "Jirani Bari na dakko key din" bata ko kulashi ba yana daga qafa ta bishi, a tare suka hau saman tana riqe da hannunsa data qi saki suna shiga ya mayar da qofar falon Saman ya kulle ya murza key kafin ya zare ya jefa a aljihunsa seta saki hannunsa da sauri ta shiga buga qafa tana yarfe hannu, Khalil kuwa kasa riqe dariya yayi ganin abinda takeyi din ya wuce daki yana cewa "Yarinya keda gidab Mama ai se dai idan gaisheta kika je yi". Kuka riris ta zauna tanayi Khalil daya fito ya bude baki yana kallonta a ransa yace "Ikon Allah" a fili kuwa ya qarasa kusada ita ya zauna tareda cire hularsa ya dagata cak ya dorata akan cinyarsa, qoqarin sauka ta shigayi ya saka hannu daya ya riqe fuskarta ta gane me yake sonyi dan haka tayi saurin damtse bakinta amma ina seda ya samu nasarar shigar da harshen sa cikin bakinta ya shiga nanata mata karatun data rigada ta haddace dan tun ranar da aka daura musu aure yake biya mata. Seda tayi laqwas daman tuni Kuka ya kama gabansa kafin ya saketa yana sauke numfashi a hankali kamar yanda ta lafe a jikinsa itama taana sauke numfashin. Wayar sa tayi qara ya janyota ganin Khalifa ne yake kira ya amsa, da "ok" ya amsa abinda ya ce masa kafin ya maida wayar ya ajiye ya kalleta fuskarsa dauke murmushi yace "Bari na dakko Miki Akwatinki a qasa se nazo na baki Abinci sabuwar qawarki nata nanata mun baki ci komai ba" ya sauketa ya miqe se itama ta miqe jikinta duk yayi sanyi tabi bayansa suka sauka qasan tare. Akwatunanta saiti daya ya gani a nan cikin falon ya dauki babbar ta kama qaramar ciki zata dauka yayi saurin tareta yana cewa "Aa ban sakaki ba karki wahalar mun da jikinki" ya wuce sama ita kuma ta tsaya tana qarewa falon kallo yayi mata kyau sosai a ranta tana tunanin falon waye nan na sane kenan ko. Seda ya gama hawa da akwatunan kafin ya shiga kitchen ya dakko Abubuwan da zasuyi amfani dashi ta karbi wasu ta riqe masa suka hau Saman. Cikin tattali da kulawa ya ringa ciyar da ita wani hadadden dankali da Khalifan ya siyo bayan ya dumama mata a microwave dake nan saman kazar kadan taci, seda ya tabbatar ta qoshi kafin ya cika mata Cup da tatacciyar madara me sanyi yace tasha sannan ya fara ciyar da nasa cikin seda ya qoshi shima kafin suka tattara komai suka sake sauka qasa dashi a sannan ta shiga kitchen din tabi ko ina da kallo dukda komai a tsaftace yake amma ta gane ba nata bane tunda beyi kala da sabo ba kenan nan kitchen din matarsa ne gabata ya yanke ya fadi data tuna Umaimah da kashedinta se ta matsa kusa dashi qasa qasa muryar ta na nuna alamun tsorata tace "Tana ina?" "Wa?" Ya waiwaya ya kalleta se tayi farfar da ido tace "Matarka mana" "Yanzu saboda matar tawa duk kika firgice haka kina shirin yin kuka toh tana dakinta yanzu zamu shiga ku gaisa". Gwalo ido tayi Khalil ya fashe da dariya kafin yaja hancinta yace "Matsoraciya kwantar da hankalinki bata nan tana Asibiti CS za'ayi mata gobe" "Wayyo daman ciki ne da ita Allah ya raba lafiya toh" ta fada cikin jimami a ranta tana mamakinsa, yanzu matarsa na Asibiti zata haihu amma shi yana gida da wata matar lallai Namiji. Seda ya kashe fitulun kitchen din dana falon gaba daya kafin suka haye saman tana sake ce masa "Ita a qasa take zama kenan?" "Eh duka qasa da nan saman nata ne, ke ga bangarenki can" ya nuna mata qofarta tana cewa "Key din ne ya fadi se gobe da safe zan saka a yanko wani". Seda suka shiga falon ya lura da yanda tayi kicin kicin da fuska kamar zata fasa ihu ya janyota jikinsa yana cewa "Meya faru kuma?" Se hawaye sha ta shiga cewa "Shine zaka kawoni dakin matarka da kasan ka yarda key din da ba seka bari se gobe idan an bude qofar a kawoni ba kawai dan ka nuna mun iyakata zaka kawoni dakin wata" "Haba mana Baby meye abun nuna iyaka anan? Kema kinsan bazan iya qara wani kwana ba tareda ke ba you have no idea irin wahalar dana sha daga sanda nasan kin zama mallakina kullum na kwanta se nayi mafarkinki kuma ai dazu key din ya fadi fa bayan ma an kawoki ne inaga and nan ai daman falona ne ga Master Bedroom nan wancan ne dakinta kema ga extra room nan seki dauka shikenan kowa tana da daki a bangarena ko" Khalil ya fada yana goge mata hawayen seta saka kanta a qirjinsa tana cewa "Ni bana so ai kai kace duka saman nan nata ne kuma ni gaskiya a fitar mun da staircase ta wani gurin yanda ba se na ringa shigo mata falo ba idan zan hau sama" "An gama ranki ya dade ai bama dadewa zakiyi a nan ba da an gama gyara miki gidanki zaki koma can ki zuba iko son ranki Madam Kishi" Khalil ya fada yana jan hancinta, qara boye fuskarta tayi tana murmushi, tafiya ya shigayi da ita a jikinsa har suka shiga MasterBedroom din, qamshi da sanyin dakin suka sakata sakin Ajiyar zuciya kafin ta daga kanta tana kallon dakin, da zuciya daya tace "Gidan nan yana da kyau and komai na ciki ya dace dashi" "Nasan naki se yafi wannan ma haduwa" ya bata amsa yana sakinta daga jikinsa. Agogonsa yaje ya cire akan mirrow ya kalleta yace "Kije kiyi wanka ki kwanta dare yayi fa it's almost twelve" yana gama fada ya wuce cikin closet dinsa ya bude wata drawer ya ciro sabon towel fari ya miqa mata ta karbi kafin ta wuce inda ya aje mata akwatunanta ta dauki qaramar ciki ta kwantar da ita akan gadon ta bude. Ita kadai tasan yanda qirjinta yake lugude daurwa kawai takeyi saboda hudubar su Anty Unaiza da suka ce ta daure duk abinda zezo mata dashi kartaqi, a irin wannan ranar mace take qara kafa kanta azuciyar Mijinta haka idan tayi wani abu akasin kyautata masa nan ma baze taba mantawa ba. Shower Gel dinta ta dauka da soso da duk abinda zatayi amfani dasu ta wuce bandakin, tayi wankanta tsaf ta tsane jikinta kafin ta daura towel kayan wankanta ta jere su inda taga nasa taga wasu products dinna mata ta hararesu tasan na matasa ne harda matsar mata gefe ta ajiye nata duk ta gama shiriritarta kafin ta sako zumbulelen Hijabin data shiga dashi ta fito a hankali tana keqa dakin ganin baya nan ta fito gaba daya. Seda tabi duk ilahirin jikinta lungu da saqo ta shafa Lotion din Miski, ta ware gashin kanta ta taje tsaf ta daure da qaramin Ribbon kafin ta ware rigar baccin data dauka ta tura baki ganinta yar qarama wannan ai babu abinda zata rufe mata amma tunda da Hijabi zata kwana babu matsala. Bayan ta saka rigar ta qara shafa sauran turarukan tanaji kamar sannan Anty Sumayya take mata takarar wanka da saka qamshi idan zataje turaka, tsaf ta mayar da komai ta dauki Towel din da ta cire ta koma ta shanyashi a Bandakin daidai nan Khalil ya shigo dakin ta kalleshi ganin ya canza kayan jikinsa zuwa na bacci shima tace "A ina kayi wanka?" "A dakin matata" ya bata amsa yana dage mata gira ta harareshi ba tareda tasan tayi ba Khalil ya zaro ido ya matsa ze riqeta yana cewa "Seriously ni kike harara bayan kin shigar mun nawa Bandakin kuma dare yana yi ina so nayi wanka idan kuma nace muyi tare ba yarda zakiyi ba" Kunya kamat ta nutse wai suyi wanka tare ta tura baki tana kare fuskarta a jikinsa ya sake cewa "Kinyi Alwalane?" "Kai ta daga masa ya ssketa yace "Bari muyi nafila toh its getting late" ya janyo qaramin carpet na sallah ya shimfida musu. Cikin nutsuwa ya jasu sallah raka'a biyu kamar yanda Manzon Allah ya koyar, ya dade sosai yana musu Addu'a har seda yaga ta fara hamma alamar bacci kafin suka shafa ya miqe ya fita ita kuma ta ninke Carpet din. Sanda ya dawo dakin harta kwanta ta qudunduna da Hijabinta, ya ajiye robobin ruwa daya shiga dasu ya zauna gefen kanta yana kiran sunanta ta tashi zaune tana yamutsa fuska. Paracetamol ya bata guda biyu yace tasha, shima ya sha tareda Maganin ciwon kan da aka bashi jiya, seda ta koma ta kwanta kafinya miqe ya cire rigar jikinsa danshi komai sanyi ko zafi baya kwana da Riga dogon wando ne kawai ko gajere depending on the weather. Fitulun dakin ya kashe gaba daya ya bar Bedside lamp ta bangaren da ze kwanta, seda ya miqe bayansa akan Gadon ya kalleta zuciyarsa ta raya masa "Yau gashi da wata macen da ba Umaimah ba akan Gado Allah kenan. Bashida niyyar tabata a yanzu duk zumudin da ya ringayi a baya gaba daya karsashin ya barshi saboda halin da yake ciki, kallonta ya sakeyi ganin yanda ta qudundune da Hijabi yasa ya matsa kusa da ita dan ya cire mata saboda tsaro kar ya shaqeta cikin dare Humaira da tayi lamo zuciyarta na bugawa sama da qa'ida saboda tsoron karya ce ze mata wani abu, jin yana ja Hijabinta yasa ta zabura ta miqe zaune har seda ta bashi tsoro yace "Relax Hijabin zan cire miki karya shaqe miki wuya" "Ni ka barmun abuna sanyi nake ji" ta fada kamar zatayi kuka seya kalli lallausan duvet din dake kan gadon yace "Ga duvet nan seki rufa idan ma ya miki kadan akwai wani se ki qara amma ba zaki kwanta da Hijabi ba" "Toni kaina babu dankwali ai" ta sake fada ganinya dage Hijabin fararen qafafunta zuwa cinya sun bayyana dan rigar tata rabin cinya ce, kwanciyar kuma da tayi tasa harta dage ta koma kusan qugu to idanya cire mata Hijabina haka yake so ya ganta kenan. Yanda take kokawar riqe Hijabin ya bashi dariya ya kuma San abinda takeyiwa dan haka yace "Ki kwantar da hankalinki I'm not going to touch you, not today not tomorrow until you are all ready" "You promised?" Ta tambayeshi tana kallon idonsa da suka fara canza kala alamar bacci ya daga mata kai alamar he mean what he said seta saki Hijabin ta rufe idonta saboda kunya, Khalil kuwa numfashinsa ne ya tsaya na wani lokaci saboda arba da Surarta da yayi muraran dan baze kira rigarta a matsayin sutura ba danita ce ta manne a jikinta ta sake fito masa da ainihin zanen jikinta. Ya hadiyi yawu dakyar ya jefar da Hijabin qasa, hannunsa har rawa yake ya janyo duvet dinya rufa mata har gurin wuyanta yana sauke ajiyar zuciya, daya sanin kallonta ya rufeshi saboda wani abu dayaji ya taso masa lokaci daya se ya juya mata baya ya kwanta amma ina ya rasa nutsuwar yin hakan. Yujawa yayi ya janyota jikinsa ta baya, ta sake zabura zata tashi ta riqeta a kunnenta ya rada mata "Bacci zamuyi i just want to feel your warmth" ya fada yana cusa hancinsa cikin gashin kanta da qamshin da yakeyi ya sake hargitsa masa kwakwalwa. Be san ya akayi ba se gani yayi ya juyo da ita suna fuskantar juna, qamshin turarenta ya cika masa hanci gashi kamar wani magana disu jansa yakeyi kawai so yakeyi ya ji daga inda qamshin yake tasowa haka. Shinshinarta ya shigayi kamar wano tsohon Maye hannunsa na bin jikinta yana shafawa nan da nan ta qarasa rikicewa jikinta ya dauki rawa, qoqari takeyi tayi masa magana ta tuna masa da alqawarin da yayi mata yanzu yanzu amma ya hanata damar saboda bakinta daya kama ya shiga tsotsa kamar ya Samu sweet. Kuka ta fasa masa ganin yanda ya birkice lokaci daya ya shiga sarrafata son ransa, wani kalar romance yake mata wanda ya zarce qaramar kwakwalwarta, ashe duk abubuwan da yake mata da wasa ne yanzu ne take ganin asalin abu. Khalil ya daga rinannun idanunsa da basa ko buduwa da kyau ya kalli Humairan dake kuka kamar wadda ya tsare da wuqa cikin muryarsa da tayi can qasa yace mata "I'm sorry babe i lost control, kiyi haquri ki bani dama let me make you mine for ever. Allow me to show you how much love i have for you amma idan baki yarda ba zan kyaleki kinji but please wife i promised a hankali zanyi". Jinsa kawai takeyi tasan kota yarda ko bata yarda ba seya cimma muradinsa batun kuma ze wani yi a hankali tatsuniya ce se abinda ta gani kawai tasan. Janye jikinta tayi daga riqonda yayi mata tana ci gaba da kuka ya sake maidata jikinsa yace "please wife nayi?" Bata da zabi ta daga masa kai danbataga hujjar da zata hana masa kanta a daren farko ta fara kwasar tsinuwar mala'iku ba, wahala dai ta shirya karba kuma yanda babu wadda ta taba mutuwa tasan baza'a fara akanta amma dai ta saddaqar ita da moruwa kuma se bayan wani lokaci dan bata ga alamar sassuci a idanun wannan bawan Allahn ba. "Thank you Babe i will be gentle da gaske" ya fada cikin mayen abinda yakeyi kafin ya shiga kissing tundaga wuyanta har zuwa qirjinta ya zarce cikinta. Wani kiss ya sakar mata a daidai cibiyarta ta saki numfashi babu shiri ya dago suka hada ido yayi mata wani murmushi yace "Ki saki jikinki you will enjoy it though i will enjoy the most" Wani kalar hot romance ya sakeyi mata dukda tsoron da take ciki da fargaba seda jikinta ya karbi saqonsa, seda ya tabbatar da ta tafi duniyar da bata sanda akwwaita ba kafin ya shammaceta ya shiga cikinta dakyar bayandaya karanta Addu'ar saduwa da iyali daya baya taba manceta komai qoluwar nishadin da yake ciki. Humaira bata gane kuskurenta ba seda Khalil ya gama samun hanyar shiga jikinta dakyau, ya shiga gurzarta son ransa da alama ma ya manta dawa yake tare. Tayi kuka tayi magiya yan gida dansu da nasa babu wanda bata kira neman ceto ba amma bawan Allah besan tanayi ba ya rigada ya lula a duniyar da in ya jeta baya ji baya gani se yayi abinda ya kaishi ya dawo sannan be sarar mata ba seda ya samu cikakkiyar gamsuwar da yake buqata sannan ya rungumeta tsam a jikinsa yana saka mata Albarka ita kuma tana kuka wiwi. A ransa yake ayyana shi kam dan gata ne dan Matansa sun kasance zababbu da ya tabbata ba duk mata ba dana dandano daya da ya mata ya samu gamsuwar da yake buqata kuma irin wadda yake samu a gurin Umaimar sa wannan harda qarin tukuicin sabunta da kuma quruciya. Sake rungumeta yayi a jikinsa yana rarrashi, badan ba daya qara amma a yanzu haka yasan da wuya idan beyi barna ba danshi da kansa yasan ya so kansa da yawa. ASIBITI Qarfe biyu ta gota Umaimah ta sake farkawa, a hankali ta bude idonta ta kalli Mama ta cikin dan hasken dake dakin tana zaune akan kujera bacci ya dauketa motsin da tayi ya farkarda Mamanta bude idoda sauri tana kallonta kafin tayi Hamdala tace "Kin farka Umaimah" "Na farka Mamq" ta fada a hankali tana yunqurawa zata tashi zaune Maman tayi saurin kamata ta zauna. "Bari na kira Nurse na gaya mata kin farka kuma fa bata jima da zuwa dubaki ba bari naje" Mama ta fada tana miqewa Umaimah ta bita da kallo harta fita kafin ta dafe kanta da yake sara mata a hankali. Tare Mama suka dawo da Nurse din, seda ta sake gwada jininta ta tambayeta ko akwai inda yake mata ciwo tace Aa "Yunwa nake ji kuma ina so nayi fitsari" Umaiman ta fada. Mama da Nurse din ne suka kamata har bandakin tayi fitsarin ta wanke bakinta tareda Alwala suka maidata kan gadon gaba daya jikinta ya mata nauyi ji takeyi kamar an dora mata dutse. "Mama ki bata dan wani abu taci Mara nayi kuma karya zama da gishiri sosai a ciki bari naje Allah ya qara lafiya idan da akwai wani abu se ki kirani" ta ajiye file ta fita. Shayi Mamanta hada mata me kauri ta zuba mata farfesun Naman rago da Anty ta kawo musu dazu, saboda yunwa kawai ta ringa tura shayin bataci Naman ba ta gama tsaf tasha ruwa Mama na zaune tana kallon ta ta gyara kwanciya tana cewa "Wani baccin nakeji Mama" "To ki kwanta kiyi ni bana jinma zan iya komawa bacci yanzu bari kiga nayi alwala nayi Nafila da zaman banza maza ki koma baccinki Allah ya qara lafiya" tana gama fada ta miqe, seda ta gyara mata abin rufa taga ta rufe ido kafinta juya ta shige bandakin Umaimah ta sake binta da kallo. Kalaman Abbana cewar Amaryar Khalil ta tare suka dawo mata, Khalil ya tare da wata Mace daban, yanzu haka suna can suna abinda ita kadai take da lasisin yinsa dashi, wlh ba zata sabu ba, da ranta tana gani Khalil ya zauna da wata mace bayan ita ba zata iya haqurin Khalil ya hada shimfida da wata ba dole ta taka masa birki idan kuwa harya cimma hakan hukunci ya tabbata akansa da duk wadda ta keta mata gonarta ta shiga alfarmarta. Seda ta tabbatar da Mama ta shiga bandakin tajiyo qarar ruwa alamar ta fara uzurin daya shigar da ita kafin ta sauke qafafunta qasa dakyar saboda yanda gaba daya jikinta yayi mata nauyi. A yanda take bazaka taba zaton zata iya motsawa ba amma da yake ita ta saka kanta se gashi cikin abinda be wuce minti biyu ba cikin sanda ta fice daga dakin ta taki sa'a kuwa harta salallaba ta bar ward din bata hadu da kowa ba saboda dare ya rigada ya tsala Asuba ma ta fara kawo kai daga Marasa lafiyar har ma'aikatan da yawa sun samu bacci se masu jiran kiran kota kwana acan dakin su. Qarfin hali kawai take tana daga qafa har ta fice daga get din Asibitin, zuciyarta ta qeqashe babu alamar tsoro ko fargabar wani abu musamman a irin yanayin da ake ciki na rashin tsaro da garkuwa da mutane haka Umaimah ta ringa tafiya a cikin daren nan a matuqar galabaice ga tsohon ciki seda ta kwashe kusan minti Arba'in kafin ta kai layin gidan nata zuwa sannan ikon Allah ne kawai yake tafiya da ita dan tamkar zata mutu haka ta zube a bakin Get din layin tana bugawa. Masu gadi ne suka taso da dalleliyar fitilar su suna tambayar waye, Sammani me gadin Gidan su ya gane ta, da sauri ya bude mata Get din yana mata sannu qasan zuciyarsa fal mamakin ya akayi ta taho daga Asibiti a wannan yanayin? Dazu fa da sukaje ko motsi batayi kai shi tunda uwarsa ta haifeshi be taba ganin mace tamkar Aljana irin Hajia Umaimah ba, haka ya ringa binta da sannu har ya rakata cikin gidan, daga bakin qofar palour ya tsaya ta shige ya jawo qofar, a ransa yana Addu'ar Allah yasa a kwashe lafiya. Kai me ma ya kaishi barinta ta shiga gidan be fara sanar da Alhajin ko ya kira Hajia Babba ba? Tunanin abinda kaje ka dawo ya sakashi runtumawa da gudu ya nufi bangaren Hajia Babba beyi la'akari da cewa dare bane ya ringa buga musu qofa jikinsa har rawa yakeyi dan se a sannan ya gane qatuwar wautar daya tafka kuma duk abinda ya faru yanzu shi za'a fara ganin laifi. Ganin yana ta bugu ba'a bude ba ya sakashi zagayawa ta baya inda window dakin Khalifa yake ya zuge Net ya shiga kwala masa kira yana cewa "Khalifa, Halifa ka tashi ga Hajia Umaimah can ta dawo ka tashi dan Allah kar ayi kisan kai a gidan nan ace da sa hannuna". khalifa daya farka da niyyar qundumawa duk uban da yake buga qofa Ashar da sauri ya wantsalo daga gado yana raba ido, Anty Umaimah kuma matar da suka baro a Asibiti bata hayyacinta waya dawo da ita gida toh? Da gudu ya fice daga dakin ya nufi Sama gurin Hajiya, a matattakala suka hadu tana shirin saukowa Habiba na biye da ita a baya kana ganinsu kasan hankalin su a tashe yake. "Yawwa Khalifa kaima kaji bugun kenan, muje mu duba wanene a wannan lokacin Allah dai yasa lafiya" ta fada tana qarasa sakkowa. "Hajiya Sammani ne wai Anty Umaimah ce ta dawo gata can ta shiga gida" Khalifa ya fada yana yin gaba se Hajia ta dafe qirji tana cewa "Umaimah? Umaimah kuma yaushe ta dawo ita da bata da lafiya waya dawo da ita gida? Kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wannan bala'in har ina Umaimah bazaki kashe ni da raina ba" da wannan surutan suka dunguma bangaren Khalil sedai suna zuwa suka tarar da qofar palour a datse. Sammani ya saka muqullin hannunsa amma yaqi buduwa alamar an rufe qofar ta ciki kenan. Khalifa ne ya koma cikin gida da gudu ya dakko wayarsa ya shiga kiran Yayan nasa, Hajiya na tsaye ta kasa cewa komai, Addua kawai takeyi Allah ya tsare mata Dan nata da Marainiyar Alah. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 73 A bangarensu Khalil kuwa Humairah tana kwance lamo akan gado idan ka kalleta zaka dauka bacci take yi amma idonta biyu, ita kadai na san abinda take ji a jikinta bisa sabon al'amarin daya sameta. Sam Yaya Khalil be tausaya mata ko ya dubi qarancin shekarunta ba seda ya gurjeta son ransa tamkar me biyan bashi kafin ta samu kanta a hannunsa. Yanzun haka da tana da qarfin tashi da barin masa dakin za tayi dan bata san abinda ze biyo baya ba idan ya fito daga wankan da yakeyi, bata tunanin ze barta ta huta duba da yanda dakyar da sidin goshi ya barta ta fito daga bandakin kafin ya shiga yin nasa wankan. Idanuwanta da sukayi laushi tubus suka qanqance saboda kuka ta lumshe tana jin wani bacci bacci yana fizgarta amma bata so tayi tunda asuba ta kawo kai gara idan sukayi sallah se tayi baccin amma in Yaya Khalil ya bata dama kenan. Juyawa tayi daga rufda cikin da take zuwa rigingine wanda yayi daidai da bugun da akayiwa qofar dakin da take cikin wani irin tashin hankali kamar za'a balla qofar idan ba kunnenta bama harda kururuwa take jiyowa daga wajen. A firgice ta yunqura tana cije baki ta miqe zaune, jitayi bugun yana qara qarfi, ta waiwaya ta kalli qofar bandakin a daidai sanda Khalil ya fito daure da babban towel fari a qugunsa yana goge fuskarsa da wani qarami yana cewa "Badai bacci kikayi ba yarinya dan yanzu ma aka fara..." se maganar sa ta maqale saboda bugun daya jiyo anayi tareda hargagin daya tabbatar na Umaimah ne ba shiri ya wurgar da towel din hannunsa ya nufi Humaira data dora hannu biyu aka tuni hawaye suka balle mata, zatayi magana ya dora hannunsa a kan lebe alamar tayi shiru seta shiga girgiza masa kai. Seda yaja numfashi ya ajiye zuciyarsa na tsalle saboda tsoro kafin ya nufi bakin qofar ba shiri Humaira ta kwasa da gudu ta shige gurin walk in closet dinsa ta fara neman gurin buya. Ita dai tana ga ajali ne yasa ta auri Yaya Khalil dan dai bata ga alamar tana da rabon komai a cikin zama dashi ba sena wahala. Ta tabbata ko Umaimah bata kashe ta da hannunta ba kamar yanda ta dade tan iqirari to kuwa tabbas fargaba da tsoratarwar da take mata zasu saka zuciyarta tayi bindiga. Khalil kuwa seda ya gyara muryar sa kafin a shaqe kamar wanda ya tashi daga bacci ya ce "Waye wannan yake bugamun qofa a daren nan Sammani wane irin rashin hankali ne me ya faru zakazo kana mun bugu yanzu?" "Kutumar bura ubanka ce ta faru Khalil, ka bude mun qofar idan ba haka ba wallahi har kaje lahira kana dana sanin abinda zan aikata maka Maci amana Macuci" Umaimah ta fada cikin hargagi. An rigada an kai gabar da bayajin komai dan Umaimah ta zageshi, a yanzu tashin hankalin sa daya ne, idan ya bude qofar ta shigo taga Humaira besan me zata aikata ba haka idan yaqi budewar nan ma besan me zata yi ba waima ta yaya akayi ta farka har aka sallameta daga Asibiti tsakar daren nan wannan wane irin bala'i ne haka. "Khalil bazaka bude bako? Shikenan ka zauna a ciki kaida Yar iskar Karuwar da ka dakko amma ka jirani na dawo zakaga abinda zanyi" Umaimah ta sake fada kafin ta juya dakyar take daqa qafa ta sauka qasa. Tana jin ana buga qofar kuma ta tabbatar da Sammani ne ze taso yan cikin gidan amma bata kukasu ba ta wuce. Kitchen ta nufa, zuciyarta ta rigada ta gama qeqashewa abinda ta ayyana mata tayi kawai shi zatayi kota mutu ko ta rayu wannan duk ba damuwarta bace amma dole ta koyawa Khalil hankali na cin Amarta da yayi. ASIBITI A nutse Mama ta fito daga bandaki bayan data dauro alwala taja qofar ta rufe a hankali gudun karta tashi Umaimah. Kai tsaye idonta ya sauka akan gadon da Umaimah take kwance se taga babu kowa, da mamaki ta qarasa Gurin ta daga bargon dai dagaske bata nan. Hijabin ta ta zura ta leqa waje ta tambayo ko Ma'aikatan ne suka dauki Umaiman tunda daman sunce akwai gwajin da za'a mata amma ta dauka ai seda safe. Bacci sosai ta tarar da Nurses din sunayi abinsu, seta qarasa kusada wadda take kula da Umaimah ta shiga tashin ta, Nurse Halima ta farka bakinta dauke da salati ganin Mama a tsaye yasakata wartsakewa tana cewa "Aa Mama badai jikin Umaiman bane? Muje na dubata mu gani se a taso likita" "Ba ku kuka dauketa ba ne Nurse? Na shiga alwala na fito yanzu banganta a dakin ba" Mama ta fada cikin firgicin jin maganar Nurse, to ina Umaimah zata tafi a daren nan ita da ba lafiya ba? Kafin kace me Asibiti ya hargitse ana neman Umaimah daki daki, da yake Asibitin  ba wani girma ne dashi ba cikin dan lokaci suka bincike ko ina amma babu Umaimah babu me kamar ta har Get an tambayi masu gadi sukace basuga fitar kowa ba zuwa sannan tuni Mama ta fara kuka, wayarta ta dakko ta shiga kiran Abba ta gaya masa halin da ake ciki seda ta kira sau biyar kafin ya daga wayar. GIDANSU UMAIMAH A daidai sanda Mama take kira Anty Saratu ta farka yin fitsari, da yake wayar a vibration take bata ji ba, seda ta yiwo fitsarin ta dawo, dakyar take bude ido saboda bala'in baccin da take ji to kusan kwana biyar kenan a jere baccin su ragagge ne ko yau din se gurin qarfe daya suka dawo gida daga Asibitin kafin ta kwanta biyu tayi. Hasken data hango wayar Abba tayi ya saka ta miqa hannu tana hamma ta jawota dan tasan qila Alarm din nasa na fama ne ze fara kadawa ya hana mutane bacci, sunan Maman Yara da ta gani ya saka fara tashin Abban ya yi juyi yana cewa "Ohni Saratu wai me kuma kike so dan Allah ki barni na huta mana idan dai ba so kuke ku qarasani na mutu kawai ba" "Alhaji Maman ce take kiran ka a waya, ina ga jikin Umaimah ne fa" ta fada tana miqa masa wayar, seya karba da sauri ya saka a kunne, Mama ta fashe da kuka tana cewa "Alhaji An sace Umaimah, daga na shiga Bandaki nayi Alwala na fito babu ita a dakin gashi mun duba ko ina amma ba'a ganta ba". "Kamar yaya ba'aga Umaimah ba? Ita Umaiman Allura ce ko me da za'ace ta bata wannan ma ai zancen banza ne, jira gani nan zuwa" Alhaji Sabo ya fada yana miqewa tsaye, jiri ne ya jashi ya koma dabas ya zauna da sauri Anty Saratu ta taro shi tana cewa "yi a hankali Alhaji kasan kaima fa ba lafiyar ce dakai ba" "Ba'a ga Umaimah ba Saratu, wannan abu har ina daga wannan tashin hankali se wannan kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miqomun riga ta muje Asibitin mu gani". "Ba'a ganta ba kodai wani gurin ta shiga taya za'a ce baa ga mutum ba a Asibiti Ahaji sudai duba dakyau ko bayan gida ta zaga" Anty Saratu ta fada tana miqa masa jallabiyya se ya karba ya hau kici kicin sakawa amma ya gagara saboda yanda jikinsa yake rawa. "Saratu bane babbar riga ki gani na dora zata fi mun sauqi" ya fada yana zama a bakin gadon ya dafe kansa da hanna ye biyu, al'amarin Umaimah nema take yi ta kashe su kawai ta huta dan ya tabbatar yanzun da kanta ta tashi daga Asibitin wannan kadan ne daga aikin ta. Tareda Salman suka fito daga gidan, Salmanun ne yake jan motar. Seda suka hau titi ya kalli Abban yana cewa "Abba ya kamata a sanar da Yaya Khalil fa yasan halin da ake ciki?" "A kyake shi kawai Salmanu muje mu gani idan ba'a sameta ba sannan se mu sanar musu" Abba ya fada yana rufe baki wayar Salmanu da take gefensa ta fara qara, seya cirota yana duba. "Lah Abba kaga Yaya Khalil din nema qila toh yasan abinda yake faruwa" Salmanu ya fada yana daga wayar ya sakata a speaker. "Salman ku taimaka mana, ga Umaimah nan tazo ban san me zatayi ba tace na bude qofar dakin da muke ciki idan ba haka ba se tayi abinda har naje lahira ina dana sani. Tsoro nake ji karna bude tayi mana wani abun kuma idan ban bude din ba bansan me zata aikata ba" Khalil ya fada cikin rawar murya dan da gaske ya gama karaya da lamarin Umaimah. Ya shaida yar daba ce ta gaske, a HALIN KISHI irin nata za ta iya aikata masa duk abinda zuciyarta ta raya mata tunda ai ba yau ta fara ba. "Muje gidan, bari na kira Maman ku na gaya mata, yanzu ita wannan yarinyar bazata bar rayukan mutane su huta ba ko? Ai Shikenan" Abba ya fada yana latsa waya. Sanda suka isa sun tarar dasu Hajiar su Khalil a tsaye har sannan Sammani da Halifa na qoqarin buge qofar amma abu ya gagara saboda qofar ba ta wasa bace, Cikinsu Salmanu ya shiga suka ci gaba da kici kicin, Abba na kusada Hajiya da ta kasa cewa komai ya na bata baki. Kamar an ce Habiba ta waiwaya ta hango haske ta gurin qofar Kitchen ta baya, hannun Hajiya ta janyo da qarfi ta nuna mata suka yunqura zasu tafi gurin Abba ya dakatar dasu da yi musu alamar kar suyi motsi ya fara sanda a hankali har ya isa gurin da Umaimah take kiciniyar kunna cylinder Gas saboda duk dare suna kashe ta ne daga wajen idan zasu kwanta gudun tsautsayi, ko wani abun zasuyi sedai suyi amfani da electric.Abba na zuwa kuwa ya shammaceta beyi wata wata ba ya dauke ta da marin da seda taga taurari a idonta Halifa dake bayansa yayi azamar kashe Gas din data kunna dan sosai suka jiyo qarar fitar sa daga Kitchen din alamar ta zare pipe din ne yana fita kaitsaye. "Me kike yi Umaimah" Abba ya fada ciki matuqar bacin rai yana dubanta. "Igiyar Gas na cire daga jiki, zan sake shi ya cika gidan sannan na kunna mana wuta dani dasu dukka mu qone dan wallahi da nayi zaman KISHI da wata mace akan Khalil gara mu mutu, kuma yanzun ma ba fasawa nayi ba, ko ba yau ba wallahi se na kashe ta, na kashe Khalil sannan na kashe kaina" Umaimah ta fada babu alamar wani tsoro ko nadama a fuskarta. Duka Abba ya sake kai mata a zuciye kafin ya angizata suka shige cikin gidan Hajia ta tare tana cewa "Kayi Haquri Alhaji kodan halin da take ciki, Umaimah me yasa kike haka me yasa bazaki bar mu mu huta ba ki dauki haquri da dangana dan Allah?" "Karki sake taba ni munafuka Annamimiya, idan da kina so na haqura ai tun farko seki hana danki yin auran tunda yana jin maganar ki amma saboda baqin munafunci kika mara masa baya yanzu kuma kizo kina bani haquri se kace ke har naki mijin ya mutu kin bari anyi miki Kishiyar. To wallahi bazan fasa abinda nayi niyya ba kuma duk wanda yayi yunqurin hanani se ta shafe shi Idan yaso kowa ma ya mutu a huta" Umaimah ta fada tana fizgewa daga ruqotan da Hajia tayi, ta sake yunqurawa kafin su ankare har ta kai matattakalar benen kai bazakace ciki wata tara ne a jikinta ba a yanda take tafiya. A daidai lokacin Khalil ya fito tareda Humairah dake sharbar kuka a bayansa ta tsorata sosai ta gama saddaqarwa yau kwananta kawai ya qare a gidan, Umaimah na hangota ta kai mata wata muguwar cakuma ta goce, mantawa tayi da duk wani ciwo da take ji a jikinta ta ware qafa uku uku ta hada matakalar ta diro qasa tana ganin mutane da mugun gudu tayi bayana Hajia tana sauke numfashi. "Ka fito ko to kuwa ka shirya baquntar lahira yanzu Khalil sena kashe ka" Umaimah ta fada tana daukar Abin flower da yake akan benen ta nufi Khalil da yayi mutuwar tsaye gadan gadan, tana dagawa marata ta katsa mata ba shiri ta wullar da abin hannunta ta dafe ciki tareda durqushe wa Khalil yayi kanta kafin ya qarasa taja baya tana cewa "Karka taba ni munafuki karka kuskura qazamin hannunka ya tabani kuma ba barinka nayi ba se naga bayanka da duk wata mace da kace zaka hadani da ita" "Kai Khalil wuto daga nan ka rabu da ita" Abba ya daka masa tsawa kafin da kansa ya hau benen ya kamo hannunta, tana tirjewa da komai seda ya direta a tsakiyar palour sannan ya qyaleta. Idanunta da suka rigada suka qeqashe ta daga tana binsu daddaya da kallo kamar yanda suma suke kallonta ko wanne da kalar tunanin da yakeyi akanta. A saitin Khalil ta tsayar da idonta se kawai ta fashe da kuka tana cewa "Kasan ina kishinka Khalil me yasa? Me yasa zaka hadani da wata Mace dame na rageka da zakayi mun kishiya Khalil me nayi maka" ta qarasa cikin daga murya tana sake rushewa da kuka. Halifa ne ya matsa kusada Hajiya qasa qasa yace "Anya Hajia Anty Umaimah bata da motsi a kwakwalwarta nidai ina ga akaita gurin likitan kwakwalwa dan abinda takeyi ya fi kama da na masu motsi a kai" "Uwarka Aisha gata nan a kusa da kai itace take da motsin kwakwalwa, se kaje ka tono ubanka Ummaru a kabari yazo yayi mata magani" Umaimah ta fada idonta cikin na Halifa babu ko dar da tunanin matsayin uwar tasa da ta zaga a gurinta. "Umaimah ashe baki da mutunchi har haka? Hajiya Aishar kika ambata kika zaga harda Mijinta da yake kabari saboda ke baki da mutunchi kin kuma zubar da tarbiyyar da muka baki a titi ko kin kyauta nace kin kyauta, ki tashi ki wuce mu koma Asibiti ga motar Ambulance nan sunzo da ita zasu dauke ki" Mama da shigowarta kenan ta fada cikin tsananin fushi tana qarasawa inda take ta kama hannunta. Seta fizge tana cewa "Wallahi babu inda zani, indai kuma ana son zaman lafiya se dai Khalil ya saki yarinyar nan. Ba'a halicce shi dan kowacce mace ba bayan ni dan haka bazan taba raba shi da wata ba". "Ke a wa? Yanzu har kin isa mace da zaki tsaya kice baza'ayi miki kishiya ba ko kuwa kenan har wata macece data san ciwon kanta balle tayi kishin mijinta? To bari kiji kishi ba hauka bane idan zaki dawo hankalin ki tun wuri ki dawo saboda kinga ana lallabaki ya saka kike botsarewa ko to daga yau zanga uban da ze sake lallabakin, ki tashi ki wuce muje aure kuma Khalil da Humaira har mutuwa idan yaso baqin ciki ya kashe ki shasha sha mara tunani" Mama ta sake fada a mugun fusace. Se Umaimah ta miqe tana cewa "ai ko baki fada ba nasan kina baqin ciki da zama na ni kadai a gidan mijina ina yin yanda naga dama bayan ke kina da kishiya dole kiyi murna tunda anyi mun, to wallahi daga ke har ita Hajiyar baku isa ba, naga itama ba ayi mata kishiyar ba shine ni zaku taru ku hada baki ayi mun ko to sedai ya zaba koni ko ita, Idan kuma ita ya zaba to se na kashe shi in yaso kowa ya rasa" Mari Mama takai mata kafin ta rufeta da duka tana cewa "Kaiconki Umaimah kaiconki, wallahi da ba'a gida na haife ki ba tabbas zance ke ba yata bace ba jinina bace dan kaf ahalina dana Ubanki babu me mugun hali wanda be dauki kalmar kisa a bakin komai ba irin ki, kafin ki kashe shi ni gara na miki dukan daze lahantaki Muguwa me baqar zuciya" "Aa Hajiya ki bari ki dena jifanta da wadannan kalaman yawun uwa kaifi ne dashi akan Da, Ke kuma Umaimah kiyi haquri mu bar komai zuwa safiya in Allah ya kaimu" Hajiya Aisha ta fada tana qoqarin janye Umaiman ai kuw ata hankada ta da yake a bazata abin yazo mata se gata tim a qasa ta bugu da qugunta sosai har seda tayi qara. "Karki sake tabani munafuka tun farko ai komai yana hannunki da kinso ki gyara da ba'a zo haka ba se yanzu ne zaki ce na bari da safe toh an qi a bari din" Umaimah ta fada tana zarewa Hajiya data zuba mata ido kawai tana kallonta ido. Khalil kuwa runtse idonsa yayi, Allah kadai yasan irin daci da qunar da zuciyarsa takeyi masa a duk sanda Umaimah ta zagi mahaifiyarsa amma yana danne zuciyarsa ne ya hanata aikata mata abinda take raya masa saboda yana mata uzurin me rangwamen hankali, kishi ya taba mata kwakwalwa qari kuma da cikin da take dauke dashi. Yasan Umaimah nada kishi amma be zata zata bari hankalinta ya gushe ta ringa abu irin na mahaukata ba akan abinda ita ce silar faruwarsa, meye lefinsa dan yayi aure bayan ita ta bashi qofar na yaje yayin sannan yanzu zatazo tana tambele da rashin hankali har tana iqirarin zata kashe shi? Hadiye wani abu daya tsaya masa yayi ya bude baki dakyar yana nufar ta yace "Duk abinda zakiyi Umaimah ni zakiyi wa ni nayi miki laifi karki sake zagin Mahaifiyata ko wani akan wannan abun ina kuma yi miki uzurine kawai saboda halin da kike ciki a yanzu" "Ni kake yiwa uzuri Khalil? Idan ka sakeyi mun uzuri kai ba dan halak bane, idan baka dauki mataki akaina ba to Aisha da Ummaru shegenka sukayi kai ba dan halak bane Sannan kace karna sake zaginta ko? (Seta waiwaya ta kalli Hajiya datayi suman zaune tun dazu kawai tana kallon Umaimahn) tace "Aisha kinci uwarki, Khalil ka tsireni na zageta kayi abinda zakayi" A mugun fusace Halifa yayi kanta amma se Hajiyar tayi saurin riqe shi tana cewa "Barta Halifa wannan ba Umaimah bace, na tabbatar idan ba shafar Aljanu ba to ta samu tabin kwakwalwa amma wannan ba Umaimar da muka sani bace" "Uwarki ce mahaukaciya bani ba" Umaimah ta sake fada kafin ta rufe baki Abba ya kai mata wata mahangurba ba shiri ta durqushe a gurin ko ihu ta kasayi saboda yanda duka ya shigeta . "Khalil kana tsaye, mace ta zagi uwarka a gabanka kana tsaye baka dauki mataki ba Hajiya ko dai bake kika haifi Khalil ba?" Mama ta fada cikin kidima tana tafa hannaye, Khalil da idanunsa suka rine zuwa ja jijiyoyin kansa gaba daya sun tashi ya kalli Mama yace "Mama dagaske wannan ba Umaimah bace, ko dai kwakwalwarta ta tabu ko kuma mugayan Aljanu ne suka shafeta amma kema Mama kinsan wannan ba Umaimah bace, kowa ya sani ina son Umaimah itama tana sona na tabbatar ba a hayyacinta take wadannan abubuwan ba". "Allah ya wadaran soyayya irin taka Khalil Allah kuma ya wadaran zuciyarka zuciyar da kana tsaye matar aurenka zata zagi uwar data haifeka ka saka mata ido ba tareda ka chanza mata kamanni a bugu daya ba, Umaimah ko dai kin siyar da Imaninki kin bi bokaye ne ban sani ba dan dai wannan yafi kama da zuciyar wanda aka tsafance Dodo ya cinyeta dan Ubanki me kika aikata masa? Ko da yake ba banza ba, tun tuni ya kamata na fahimci cewar Umaimah kin bar turbar Allah da Annabi amma ban gane, taron qawayen da kullum nake harqilon rabaki dasu inda ya kaiki kenan wayyo Allah na ni Malika ubangiji ka yafe mun ka sassauta mun wannan jarabta da kayi mun da kangararriyar yarinya da take neman kaini kabari" Mama ta fada tana fashe wa da kuka, se ta sake kallon Khalil tace "Saketa mara zuciya, ka saki Umaimah yanzun nan Khalil" "Mama mu fara mayar da ita Asibiti a bincika kwakwalwarta, idan basu ga komai ba se mu tafi gurin Malam Ishaq qila a can a dace amma nasan ba yin kan Umaimah bane dole akwai abinda yake zungurinta" Khalil ya fada cikin rawar Murya kamar yanda jikinsa ya dauki rawa lokaci daya. "Wallahi seka saketa Allah yasa Dawanau ce ita ko kuma kukar bulukiya, kai ko kashin awaki na haife ku yau Khalil seka rabu da Umaimah idan kai baka san darajar kanka ba to ni bazan zuba ido yata ta wulaqanta uwar mijinta ba nima na haifa, na kuma san zafin abinda takeyi idan ni akayiwa bayan saki wallahi se na saka an hada mata dan bura uban duka ta yanda ko akuya bazata sake yiwa tsawa ba bare ta zagi bil'adama" Mama ta sake fada cikin hargagi. "Ai wallahi ko be saketa ba a yau se Alqali ya kashe auran nan, ni kaina da zan iya canzaki daga cikin Ahalina da a take a yanzu zanyi dan banyiwa iyayena haka ba ban san dalilin da yasa Allah ya jarabce mu da ya irinki ba amma muna roqonsa ya kawo mana dauki" Abba ya fada cikin qololuwar bacin rai. "Abba Mama dan Allah kuyi haquri, ku bari muga safiyar nayi alqawarin idan har aka tabbatar lafiyar Umaimah qalau a take zan rubuta mata takaddar sakinta" Khalil ya fada yana kallon Hajiyarsu da sigar roqo, Hajiya da kwallar baqin ciki ta zuraro mata ta kauda kai, ta bakin na Mama ne itama ta fara zargin shikansa Khalil din ba kansa daya ba, duk yanda akayi da gaske an bawa Dodo zuciyarsa ya cinye in ba haka ba wannan abu har ina? Kai da Fata Mama da Abba suka dage se Khalil ya saki Umaimah da tunda tasha marin Abba ta durqushe bata sake dagowa ba saboda wani Azababben ciwon mara da kai da suka dirar mata lokaci daya. "Shikenan, taje na saketa saki daya" Khalil ya fada kamar wanda ze fashe da kuka. "Uku zaka mata ka yanke duk wata alaqa da take tsakanin ku yanzun nan" Mama ta sake fada, "Hajiya dayan ma yayi ba se ya qara ba" Hajiyar su Khalil da tunda ta fadi bata sake magana ba ta fada "Wallahi se ya qara Hajiya ko beyi uku ba se ya mata biyu" Mama ta sake kafewa dole Khalil ya sake qarawa Umaimah da tayi mutuwar zaune jin wannan Drama da ake tsarawa. "Durun uwar nan, ka sake ni Khalil a maimakon ka saki wannan Yar iskar daka auro? To wallahi dani da kai da ita sedai duk ayi biyu babu" Umaimah ta fada tana miqewa, dukda azabar da take ji a jikinta da a kwayar idonta ma kana iya karantar halin da take ciki haka ta yunqura, kafin kowa ya ankara ta finciki wani flower vase da yake kusa da ita babu bata lokaci ta saukewa Khalil a daidai Mazantakarsa, ihu daya ya kwalla ya fadi wanwar a gurin. "Shikenan ta kashe shi, Ta kashe Khalil dama ta fada gashi kuwa ta cika ku riqeta Salman Na rantse da Allah yanda kika salwantar da ransa Umaimah da hannuna zan miqawa Hukuma ke" Abba ya fada cikin tashin hankali yana Kallon yanda Salman da Khalifa suka rufu kan Khalil daya ke nan babu alamar rai a tattare dashi. "Baya numfashi Abba" Salman daya kama tsinyiyar hannun Khalil ya duba a matsayinsa na Dalibin litanci ya fada, Mama ta fashe da kuka tana cewa "Allah ya wadaran haihuwa irin taki Umaimah Allah ya wadaran zuciya gafalalliya irin taki ki shirya karbar hukunci daidai da abinda kika aikata dan wlh idan har kinyi sanadin ransa sekin biya diyyar sa da naki Alhaji ku kamashi muje Asibiti in Allah ya yardada sauran shan ruwansa a gaba. Qoqarin Kamashi suka shigayi, Hajiya da Numfashinta ya tsaya na wasu daqiqu ta gagara yin komai kamar ma bata cikin duniyar gaba daya, kukan Humaira dake cikin tsananin tashin hankali kadai ake ji a falon, babu wanda ya lura da Umaimah da tun da Khalil ya fadi ta qame tamkar ruhinta ya bar gangar jikinta. Kunnuwanta sunyi mata Dummm, kwata kwata bata jin abinda suke cewa ma a gurin abu daya data ji shine Khalil ya mutu da suka fada, a hankali ta motsa bakinta da niyyar magana kamar jikinta na jira lokaci daya wani Azababben ciwo da zata iya alaqantashi da ciwon mutuwa ya dirar mata kafin kace me Jini ya balle mata ta tafi zata kifa Humaira datafi kusa da ita ta tareta suka sake tafiya gaba daya Kujera tayi musu birki, cikin kuka Umaiman ta kalli Mama tuni su Abba sunyi waje da Khalil Hajiya kuwa na nan inda take zaune ba uhm ba uhm "Mama jini take zubarwa kinga kamar itama ta suma" Humairan ta fada tana kallon Umaimah da idanunta suke lumshewa suke budewa, tsananin azabar da takeji bazata misaltu ba ta gama saddaqarwa wannan shine radadin zarar rai da ake fadin baze misaltu ba, ta kalli Mama kamar yanda itama take kallonta da wani irin expression da baze fadu ba, hawaye masu tsananin quna suka ziraro mata, Humaira ta sake kai hannu zata riqeta ganin nauyinta ya tura kujerar tana nemanta fadi amma dukda halin da take ciki seda ta yunqura ta bige hannun Hunairan "Ki rabu da ita ta mutu idan Allahya sota tayi shahada se ya zame mata kankarar zunuban data diba a rayuwarta Mama ta fada tana wani irin kuka kafin ta matsa inda Hajiya take tana cewa "Tashi muje Hajiya Allah yana kallo baze dauke miki shi yanzu ba Alfarmar Annabi da alqur'ani" "Subhanallahi Jini kuma" Abba daya dawo kiran su dan su tafi Asibitin ya fada tuni Salman da Khalifa sunyi gaba da Khalil, ya tabbatar daga Hajiyar Har Mama da shi kansa suna buqatar ganin likita shiyasa ya tsaya. Dukda zafinta da yakeji a sannan rashin imaninsa be kai yaga Mace a yanayin da take ciki ya kauda kai ba balle yarda ya haifa a cikinsa koda baya son halinta yana qaunarta a matsayin jininsa "Na kashe Khalil Abba nima mutuwa zanyi" Umaimah ta fada kamar wadda take a gangara daidai Abban ya kamata, be kulata ba ya kalli Mama dake riqe da Hajiya yace "Zo ki kamata mu tafi" "Bazan iya tabaya ba Alhaji kar kuma ka sakani dole" Maman ta fada kafin ta juya ta fice daga falon tana kuka. A yanda takeji da da abinda ze kankare zamowar Umaimah yarta a yau da tayi. Humairan dai da bata so ita ta kamawa Abba ita dakyar suka sakata a mota jikinsu yayi face face da jini baki dayansu. Ikon Allah ne kawai ya kaisu Asibitin dan Abban tuqi kawai yakeyiba danyasan abinda yake ba, suna isa aka karbeta kai tsaye suka shiga da ita Theatre Dr Al'amin kuwa kamar ze ari baki saboda Masifa babu Wanda ya tankashi to wama yake da lokacinsa a cikinsu kowa ta ishe shi, Hajiya ma gado suka bata, Mama dai Kukanta yaqi tsayawa Abban kansa kujera ya samu ya zauna saboda yanda yakeji ya tabbata idan yaci gaba da tsayuwa faduwa zeyi faduwar da baya zaton ze tashi da sassan jikinsa gaba daya. Istigfari kawai yake a zuciyarsa, suna zaune kusan awa daya kafin Dr Tahir likitan daya karbi Khalil ya fito daga dakin da suka kwantar dashi Salman da Khalifa suka nufeshi da sauri cikin nutsuwa data bayyana har a muryarsa yace "Alhamdulillahi yana raye kuma numfashinsa da bugun zuciyarsa sun daidaita, for now zamu kula dashi zuwa safiya whenhe is fully awake sannan zamuyi masa gwaje gwajendaya kamata, ku kwantar da hankalinku in Allahya yarda babu wata matsala". A tare gaba dayansu suka saki ajiyar zuciya, Humaira dake can labe kamar mara galihu tana ta kuka ta kalli Khalifa daya dawo ya zauna tace "Yaya Khalifa ka tambayeshi za'a iya ganinsa" "Zaki iya Yata tashi kije ki ganshi Allah ya tashi kafadunsa" Abba ya fada dakyar yana kallonta seta miqe tabi bayan Khalifa da shima ya miqe suka shiga dakin tana ganinsa ta sake fashewa da wani kukan Nurse din dake tsaye kansa tana nazarin na'urar da suka jona masa tace "Aa ya haka kuma baiwar Allah ki fita idan kin shigo ne ki qara masa hayani" "Kiyi shiru ze samu lafiya in sha Allah" Khalifa ya sake nanata mata. Ta hadiye kukan tana share hawaye ta Kalli Khalil dake kwance marabarsa da Matacce numfashi, tunanin abubuwan da suka wakana a tsakaninsu dazu ta shigayi yanzu idan mutuwarce ma haka zata daukeshi da ace bata yarda dashi ba da harta mutu ba zata dena dana sani ba "Allah karka sa ya mutu dan Allah" ta fada cike da yarinta tana fashewa da wani kukan Nurse din ta kalleta ba tareda ta shirya na ta fashe da dariya jin wannan addu'a ta humaira seta kalleta tace "Da alama kina ji da Yayan nan naki, ki kwantar da hankali babu abinda ze same shi in Allah ya yarda" "Ba qanwarsa bace Matar sa ce yau ta tare a gidansa" Khalifa ya bata amsa seta riqe baki cike da mamaki lokaci daya ta hada kan lissafi bata san sanda tace "Kai kar dai kuce mun daya matarsa ce ta masa wannan aika aikar?" Basu bata amsa ba amma kallon da suka mata ya tabbatar mata da hakane, tsabar saurinta fita ta watsa gulma nan ta bar Takaddar Checkup din da Likita yace ta kai ta fice daga dakin, kiran sallar da akayi yasaka Khalifa shima tashi yana cewa Humaira zeje ya duba Hajiya daga nan yaje Masallaci. Yana fitowa Dr Al'aminda suka shiga da Umaimah Theatre ya zo gurin shima. Ya kalle su ransa a hade yace "Mun samu nasarar ciro baby girl but she is in the PICU saboda long term da tayi a ciki ga kuma abubuwan data fuskanta ya saka she is critically ill i just hope she survives, ita kuma zamu kaita dakin hutu dan Allah kar Wanda ya shiga inda take har seta farka munga state din lafiyarta" yana gama fada ya juya abinsa. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 74 Guraren qarfe tara na safe Khalil ya farka cikin wani matsanancin ciwo da duk wanda yake gurin seda ya tausaya masa yanda ya dafe mararsa yana juyi akan gadon tareda nishi meqarfi wanda yake tsananin azabar da yake ji amma dauriya irin tasa ta hanashi ya kurma ihu, Humaira dake zaune dashi a dakin tayi kuka har hawayenta sun qafe. Tun wayewar gari Mama da Abba suka tafi gida saboda gaba daya su biyun suna buqatar nutsuwa badan sunqi ba gado likitan yaso ya basu kamar yanda Hajiya take kwance tun Asubar itama tana bacci taimkon Allurar da akayi mata. Har kuma sannan Umaimah bata farka ba bayan tafiyar su Mama Anty Hafsa da Nuratu sukazo amma Nuratun bata jima ba saboda zata wuce gurin aikinta ta tafi cike da Alhinin abinda ya faru se Anty Hafsa ta zauna a gurin Umaiman. Da taimkon Allah da taimakon wani Likitan da ya karanci bangaren matsalolin Al'aura ta maza wanda Asibitin suka gayyato Khalil ya samu sauqin Azabar da yake ciki. Allura yayi masa wadda ta kawo masa sassaucin azabar da yake ji dukda ciwon Marar be tafi gabadaya ba amma ya samu rangwame sosai, basu da Na'urar da zeyi amfani da ita gurin binciko ainihin inda matsalar Khalil din take dan haka sukayi referring nasa zuwa Asibitin Malam, babu bata lokaci suka dashi tareda Khalifa dakyar Jalilah ta lallabi Humaira suka koma gida bayan an wuce da Khalil din dan ta samu itama tayi wanka ta huta saboda yanda gaba daya ta fita a hayyacinta. Tafiyar su da kadan Hajiya ta farka Qanwarta Hajiya Maimuna da Anty Amina dake zaune da ita sukayi kanta da sauri suna mata sannu. "Ina Khalil, anyi jana'izar shi ko?" Shine abinda ta fara fada Hajiya Maimuna ta girgiza mata kai tana cewa "Baba yana raye an dai tafi dashi Asibitin Malam yanzu akwai gwajin da zasuyi masa ki kwantar da hankalinki babu abinda ya same shi" Ajiyar zuciya ta sauke me qarfi kafin ta koma ta kwanta Amina ta fita kiran Likita Hajiya Maimuna taci gaba da tausar yar uwarta tana bata tabbacin Khalil ze tashi, da Asuba suka wayi gari da mugun labari dole tafiyarsu ta tashi ta taho Asibitin babu shiri tsinuwa dai baza'a iyakance wadda Umaimah tasha ko ince take kan sha ba saboda tuni labari ya watsu kamar wutar Jeji a dangin Khalil babu wanda be samu labarin ta'asar data aikata ba tun sassafe suka fara tururuwar zuwa Asibitin suka dakatar dasu se iya makusantansu aka bari suka zauna dasu. A can gidansu Umaimah kuwa suna isa kowanne ya wuce dakinsa, cikin wani yanayi me ban tausayi Mama ta zube a tsakiyar falonta ta sake rushewa da Kukan daya tokare mata maqoshi, bata damu da kashedin da akayi mata yanzu a asibiti ba akan ta daure ta cire damuwa jininta ya hau sosai to ta ina ma hankalinta ze kwanta duk duniya babu wanda ze fahimci irin zafi da qunar zuciya da takeji se ko Abba wanda suka da matsayi daya dashi a gurin Umaiman. Yau a wayi gari a ce dan da ka haifa a cikinka ne ya zama taqadiri Umaimah bata kyauta wa kanta ba bata kyauta musu ba. Kuka takeyi tamkar ranta ze fita, tunani takeyi idanhar Khalil ya rasa ransa Umaimah ce sila daman ta dade tana fadar zata kashe shi basu taba yardar da gaske takeyi ba se yanzu domin irin dukan datayi masa a makasa ya nuna daman ta shirya yin hakan. Maman Asad ce ta shiga falon da sallama tayi saurin wullar da jakarta ta isa gurin Maman cikin kukan itama ta dagota tana cewa "Kiyi haquri Mama dan Allah ki dena kuka kodan saboda lafiyarki idan wani abu ya sameki mu ta shafa ita bata da Asara dan bata dauki kowa cikin Ahalinta da muhimmanciwani.ldan Allah Mama karki bari bacin ranta ya shafi lafiyarki ki barta kiy mata Addu'a Allah ya shiryeta idan tana da rabon shiriyar" suka hada kai suna kuka riris babu merarrashin wani Anty ta shigo fuskarta itama jiqe da Hawaye ta zauna tana cewa "Hajiyayye keda zaki rarrasheta kuma se ki tayata kuyi dan Allah Kiyi haquri qaddara ce a rayuwa kowa da kalar tasa ina fatan kuma abun ya tsaya iya haka sannan hakan ya zame mata izina a rayuwa" Seda sukayi me isarsu kafin kowa ya bawa zuciyarsa haquri yayi shiru. Dakyar Hajiyayye ta lallaba Maman tayi wanka tasha ruwan shayi da maganinta ta kwanta Anty Ma gurin Abba ta koma dan seda yayi wankan yasha shayi da magungunansa bacci ya dauke shi daman kafin ta fito gurin Maman. Mamaki ya kamasu ganin yanda yan uwa da maqofta suka ringa shigo musu Jaje, Maman Asad ta tambayi Anty Zee cousin dinsu da tazo tana ta kuka itama a bakinta taji wai a WhatsApp ta gani an tura da hoton Umaimah da Khalil din harda na Amaryar wai Uwargida ta kashe Ango saboda kishi a daren Angwancinsa. A can Asibitin Malam kuwa bayan kammaluwar duk wasu gwaje gwaje daya kamata ayiwa Khalil din suka sake mayar dashi Asibitin Dr Al'amin zuwa sannan ya dan samu nutsuwarsa dukda dai baya magana kallon Likitocin kawai yakeyi da Khalifa da suketa kai kawo akansa har aka mayar dashi Asibitin bayan likitan ya fita ya kalli Khalifa dake zaune gefensa yace "Ina Hajiya?" "Tana nan an bata gado itama tun jiyan" Khalifa ya bashi amsa seya gyada kai kawai kafin a hankali ya sake cewa "Humaira fa? Ina fatan babu abinda ya sameta" "Lafiyanta qalau dan tana tareda kai se da zamu tafi AKTH ne bata bimu ba, bari naje gurinsu Hajiya na gaya musu mun dawo probably tana tare dasu" daga haka Khalifan ya miqe ya fita Khalil ya bishi da kallo a zuciyarsa yana hakaito abubuwan da suka faru a daren jiyan. Ajiyar zuciya yayi ya gyara kwanciyarsa gaba daya ji yakeyi daga qugunsa zuwa qafafunsa kamar ba a jikinsa suke ba, Umaimah ta cutar dashi ta nakasa masa rayuwa A iya saninsa babu komai tsakaninsu se Alkhairi me yayi mata daya cancanci wannan danyan hukuncin daga gareta? Ko ba'a fada masa ba yasan bashida sauran amfani a matsayin Da namiji ta kassarashi. Tausayin Humaira me girma ya lullubeshi, idan da yasan jarabawar da zata afka masa kenan dabe tabata ba, dabe rabata da burcinta ya dora mata iddarsa ba haka kawai domin yasan dole ze haqura da ita ko yana so ko baya so baze cutar da ita ba ta hanyar zama da ita alhalin bashida ikon sauke mata haqqin da shi ya banbanta Matar aure da Marar aure. Zuviyarsa ta tambayeshi Waya ce masa ya nakasa da har yake tunanin baze qara amfanuwa ba? Take ya bawa kansa amsa da tabbacin hakanne ba kuma ya buqatar wani ya gaya masa shi kansa a Jikinsa ya sani ya rasa lafiyarsa. Wasu hawaye masu dumi suka ziraro masa yayi saurin daukesu saboda qofar da aka bude. Hakiya ta shigo sauran yaranta da Yar uwarta biye da ita a baya tana ganinsa ta fashe da kuka ta qarasa gaban gadon ta kama hannunsa ta kasa cewa komai se Kuka takeyi abinda ya karyar da zuciyar sauran gaba daya suka saka kukan suma Khalil ne yayi qarfin halin cewa "To kuma kukan me kukeyi bayan ba mutuwa nayi ba ai murna ya kamata kuyi tunda dai gani a gabanku a raye" "Allah ya isa tsakaninmu da wannan shaidaniyar yarinyar, ranka ta nema da Allah yasa da sauran shan ruwanka a gaba gashi ka tsallake kuma in sha Allahu se taga sakayyar abinda ta aikata maka tun a duniya ba se taje lahira ba. Duk wahalar da kasha ta sanadinka da baqin cikin data qunsa mana se taga ninkinsu a kanta da yardar ubangiji seta qare rayuwarta cikin nadama mara amfani" Hajjya Maimuna ta fada cikin matsanan ci kuka se Khalil yayi saurin dakatar da ita yace "Haba Mama ki dena magana haka ko babu komai Umaimah uwar yayana ce duk wata muguwar Addu'a da kikayi akanta zata iya shafarsu, ki nema mata shiriya a gurin Allah shi kadai ne abinda take da buqata" "Ai Allah ba Azzalumin sarki bane babu ta inda zaluncin Umaimah ze shafi Ahalinmu sedai ma haqqin ubansu data dauka dasu kansu ya bibiyi rayuwarta. Allah dai ya kwashewa Umaimah Albarka kaikuma Allah ya baka lafiya abinda take baqin cikin wata ta mora sedai ta mutu dan tana Kallo zaka samu lafiya kaci gaba da Sasakar matarka tana zazzago maka Yaya" Hajiya Maimuna ta sake fada tana kuka dukda halin da suka ciki seda maganarta ta qarshe ta basu kunya Khalil ya sunkuyar da kansa qasa, ransa ya rasame yake ji akan abinda Umaimah tayi masa, ko kadan beji ya tsaneta ba amma abu daya ya sani koda ace ita kadai ta rage mace a rayuwa ya haqura da ita kuma har abada ze dawwa ma yana nema mata shiriya a gurin Allah domin ya yarda tana da lalura da kowa ya gagara ganewa. UMAIMAH Bayan Azahar ta farka, surutai da ta ringa yi cikin fitar hayyaci ya saka dole suka sakeyi mata wata allurar data dauketa har zuwa bayan Isha'i kafin ta sake farkawa a lokacin Anty da sauran yayyanta duk suna Asibitin. Daga yanda suke mu'amalantarta zaka tabbatar sunayi mata ne kawai Albarkacin zumunchi idan sukace zasu bi ta halinta babu wanda ze taka qafarsa yaje Asibtin gurinta. Iyakar bacin sunan data ja musu ya isa, a iya yau mutanen da suka je gidansu qafa da qafa da wanda suka kira a waya bazasu irgu ba duk akan Abinda Umaiman ta aikata. Labari nata yawo a gari anqara masa gishiri da maggi babu ta sigar da ba'a chanza zancen ba, wasu sunce ma har ana kamata tana hannun Yan sanda, wasu kuma suka ce yan uwan Mijin ne suka mata dukan mutuwa tana Asibiti a kwance masu son tabbatar da yanda akayi ne suka ringa binsu gida su dai babu wanda suka bude baki da sunan yiwa bayani daga gaisuwa shikenan idan mutum ya gaji da zaman gulmarsa ya tashi ya tafi. Daga Mama har Abba kuwa yini sukayi a dakunansu suna jinyar jiki data zuciya. Ruwan shayi kadai suka ringa iya kurba bisa tirsasawar Yayansu har kuma suka fita zuwa Asibitin a cikin Mama da Abban babu wanda ya sake tayar da maganar. Jikinta yayi mata nauyin da ko bakinta ta gagara budewa tayi magana se binsu takeyi da kallo kawai, so takeyi ta tambayesu ina Khalil, ta tabbatar da yana raye ko kuwa da gaske ya mutu? Idan har ya zama Khalil ya mutu kuwa tasanbata da sauran amfani a duniya binsa zatayi. Seda Likita yazo ya sake duddubata ya tabbatar da komai normal kafin ya fita yana sake jaddada musuda su barta ta huta kar su sakata magana ko yin wani dogon yunquri Likitan na fita gaba dayansu suka miqe da niyyar tafiya. Babu wadda ta kula Umaiman a cikinsu haka itama ta rakasu da ido suka bar dakin Anty Hafsa ta rakasu a hanyarta ta dawowa suka hadu da Jalilah da Humaira sun dawo Asibitin suka gaisa babu yabo babu fallasa ta tambayesu jikin Khalil kafin ta juya jiki a sanyaye ta koma dakin da Umaiman take. Kujera ta samu ta zauna ba taredata kulata ba itama, Umaimah tayi qarfin halin bude baki ta kira sunanta tayi mata banza seda ta sake maimaitawa kafin a hasale Anty Hafsan tace "Karki kuskura kice zaki matsawa rayuwata saboda kin ganni anan, banda ina tsoron Allah ya kamani da laifin watsar da zumunchi da wlh Umaimah baki isa na sake kallon koda inuwarki ba, kiyi ta kanki kawai ni bana zauna bane saboda nayi hira dake ko wani Ahto". Kallon Anty Hafsan ta ringayi harta gama sababinta kafin a hankali idonta ya ciko da kwalla tace "Idan kin kwantarda hankalinki ma Anty hafsa ni nasan tawa ta qare a duniyar dan idanhar Khalil ya mutu da gaske nima mutuwa zanyi" "Dallah rufe mun baki maqaryaciyar banza, Idan Khalil ya mutu zaki mutu sannan har ki nemi ransa da hannunki saboda kin rainawa kanki hankali to idanso kikeyi ki tabbatar da qudurinki to bakici nasara be mutu ba yana nan da ransa Allahya kubutar dashi daga sharrinki ya kuma raba shi da Uqubar auranki. Kaiconki Umaimah, tunda kika yiwa kanki sanadin rabuwa da nagartaccen Mutum kamar Khalil har ki mutu ba zaki maida makwafinsa ba idan kuma baki tubarwa Allah ba haqqinsa baze taba barinki ki zauna lafiya ba" Anty Hafsa ta sake hayayyaqo mata cikin daga murya da har seda wata Nurse ta shigo tana cewa "Haba baiwar Allah ya zaki ringa yi mata ihu akai bayan an gaya miki tana da buqatar hutu da kwanciyar hankali a yanzu? Idan ba zaki iya kulawa da ita ba ki tafi wata tazo amma ba zakizo kina ma patient dinmu ihu akai ba" Banza tayiwa Nurse din data matsa gurin Umaimah dake kuka a hankali tana rarrashinta da abin ya isheta ta fita ta bar musu dakin badan Mama cetace ta zauna ba bataga abinda ze saka tayi jinyar Umaimah ba. Umaimah kuwa dakyar Nurse ta lallabata tayi shiru, ta kalli Nurse dinda idonta da yayi jage jage da hawaye tace "Nurse Dan Allah ki taimakmun ki kaini naga halinda Mijina yake ciki shine kadai abinda ze saka hankalina kwanciya dan Allah" "Kiyi haquri kinga yanzu kika farka jikinki na buqatar hutu ko magana da kikeyi yanzu da yawa be kamata ba ki yi haquri zuwa gobe idan kika ji qarfin jikinki se a kaiki ki ganshi" Nurse dinta fada mata cikin lallashi. Washe gari da Safe ta kwarzabi Nurse akan seta kaita taga Khalil, jijjiga gadon da take kai ta shigayi saboda tsabar takaici daman Anty Hafsa fita ta sakeyi ta bar musu dakin Nurse din ganin Umaiman na neman ta janyo musu sabon Aiki bisa tilas ta kirawo Dr, jijjigar qarya ta shigayi babu shiri ya basu Umarnin su turata akan Wheel chair su kaita dakin da Khalil yake, haka Nurses din suka fita da ita cike da zumudin ganinshi take, kwata kwata bata tuna wani abu makamancin saki ya gifta tsakaninsu Allah Allah take ta ganshi taga lafiyarsa a haka suka shiga dakin da aka kwantar da Khalil din a bangaren VVIP. Yana zaune akan Gadon ya jingina bayansa da Pillow da aka saka masa dan ya bashi support Humaira na zaune a gabansa da bowl me dauke da Quaker oat tana bashi a hankali wani kalar tsadadden murmushi ne akan fuskarsa yake jifanta dashi a wannan yanayin Umaimah ta riske su wani abu me kama da saukar Aradu ya dirar mata a zuciya take komai ya tsaya mata wani tuquqin baqin ciki ya tokare mata maqoshi ta kasa cewa komai nan da nan hawaye suka balle mata. Khalil daya ga shigowarsu lokaci daya murmushin dake kan fuskarsa ya disashe. Ya zuba mata ido yana kallonta wani abu me kama da tsanarta yana mamaye tarin soyayyar da yake mata a baya. Ganinya zubawa bakin qofa ido ya saka Humaira kallon gurin itama a tsorace ta saki Bowl din hannunta a qasa abinda yake ciki ya zube Jikinta ya dauki rawa saboda ganin Umaimah hannu biyu Khalil ya saka ya kama kafadunta yajata ta fada jikinsa ya lumshe idanunsa da suka fara canza kala saboda bacin ran ganin Umaimah. "Ku fita da ita" ya fada a hankali ba tareda ya bude idonsa ba Nurses din da suka zama hoto suka shiga tura Umaiman dake kuka kamar ana zare mata rai, baqin cikin abinda Khalil din yayi a gabanta kamar ya kasheta da ace zata iya tashi tsaye kan qafafunta da babu abunda ze hana ta janyo yarinyar nan daga jikinsa tayi mata dukan mutuwa. Wai me yasama ba ita ta kwalawa abun akai ba ta mutu kowa ya huta? Da wannan tunanin suka maida ta dakin da take, Anty Hafsa taja tsaki ba tareda tace musu komai ba. Nurse nagama maidawa Umaimah drip Jalilah ta shigo dakin kamar an korota ta nuna Umaiman da yatsa tace "Ki kama sauran mutunchin daya rage miki karki kuskura ki sake rabar dan uwana. Aurene ya hadaku kuma ya sawwaqe miki Ubangiji ya sake gajarta tarayyarku ya yanke Miki iddarsa kinga babu sauran Kare bin damo idan kuma ba so kikeyi ki hasalamu mu dauki matakin daya kamata a akanki ba ki fita daga rayuwarmu Umaimah, iya daukar Alhakinmu da kikayi Allah yabi mana haqqinmu amma bama buqatar ki sake rabarmu har abada" tana gama fadar haka ta juya ta fita Umaimah ta bita da kallo cikin kaduwa da kalamanta. Tabbas bata manta Khalil ya saketa ba amma bata yarda cewar aure ya qare a tsakaninsu ba. Ta sani Khalil yana sonta itama tana sonsa duk abinda ya faru tursasashi akayi amma badan ra'ayinsa ya saketa ba kuma tasan baze taba haqura da ita ba duk ma a yaya ze dawo su ci gaba da rayuwarsu. Ranar wuni tayi zuciyarta babu dadi, idanta tuna wai babu igiyar auran Khalil akanta se taji kamar tayita kurma ihu. Ita dai Anty Hafsa tafi ki mutu batace mata, idan kaji tayi magana yan dubiya ne sukazo wanda da yawa tsurku ne yake kawo su saboda irin labarun da suke ta yawo a gari. Randa suka cika kwana uku a kwance ranar Abba da Mama suka sake komawa duba Khalil, Hajiyarsa ma an sallameta tun washegarin ranar ta koma gida shida Umaimah ne a kwanceda jaririyarsu da itama a ranar aka fito da ita dan Alhamdulillah jikinta ya murmure ta samu sauqi. Jalilah ce ta karbota kai tsaye ta wuce da ita dakinda aka kwantar da Khalil din yana zaune bayan Humaira ta gama bashi abinci sun tafi gidada Jamila saboda ita ta kwana dashi ranar Khalifa ya tafi wani aiki ta shiga da Babyn ta miqa masa ya karbeta yana kallon kyakykyawar fuskarta sak Umaimah. "Kamar uwarta tayi kaki suna bani ita nayi addu'a na tofa Mata Allah yasa ta tsaya a iya kamannin karta kwaso baqin hali irin na uwarta" Jalilan ta fada Khalil dai kallon yarinyar yakeyi wata irin qaunarta me zafi tana shigarsa. Sallamarsu Abban ce ta katsewa Jalilah Mitar da takeyi, cikin girmamawa ta gaishesu dan duk abinta ba zata zargi Iyayen Umaimah da saka hannu a cikin abinda yarsu take aikatawa ba. Dattijai ne gaske da suka nuna hakan a cikin al'amuransu. Iyakacin jajaircewar da sukayi gurin tabbatar da samuwar yancin Khalil ya isa ya qara siya musu qima da mutunchi a idon kowa. Ta karbi Babyn daga hannunsa ta bawa Mama ta karbeta tana kallonta itama tausayin yarinyar ya kamata ta fado a yanayi mara dadiz tazo a ranar da Uwa da Ubanta suka raba hanya. "Masha Allahu Allah yasa ko dakko Haliyyar kwarai ta mahaifinki tunda kinyi karar dakko fuskar mahaifiyarki" Abba ya fada har zuciyarsa bayan da Mama ta miqa masa yarinyar ya sake kallon Khalil bayan yayi masa ya jiki yace "Wane suna kukayi mata huduba dashi" "Daman sunan Mama za'a saka mata ba'a rigada dai anyi hudubar ba" Khalil ya fada a sanyaye se Abba ya dagata yana cewa "Allah ya raya yayi akbarka yasa ki gaji me sunanki gurin haquri" Jalila da Khalil suka amsa da Amin. Sun jima sosai a dakin suna sake tattaunawa har zuwa sanda wasu Abonana Khalil suka zo dubashi kafin suka fita har sannan yarinyar na hannun Abba. Bisa tursasawarsa Mama ta bishi dakinda Umaimah take, tana kwance kan gado ta zubawa Bango ido dan ta mayar da kanta kurmar qarfi da yaji, jinyar zuciyarta kawai takeyi ta daga kai ta kalli Mama da Abban da suka shigo da Sallama Nuratu da Anty Hafsa suka amsa tareda basu gurin zama suka shiga gaishe su. Seda Umaimah ta dauke hawayen daya zubo mata kafin cikin rawar murya ta shiga gaida iyayen nata. Abba ya amsa a gajarce Mama kuwa daman ko kallon inda take batayi baya miqawa Nuratu yarinyar yana cewa "Ga ta Mahaifiyarku yayiwa takwara" "Ni bana so sanda na ce ya saka mun ai be saka ba ya je ya canza mata suna infact ni bazan riqe masa yarsa badai ya sakeni ba yaje ya kaiwa Hajiyar ita ko matarsa su riqe masa amma wlh bazan shayar masa da Ya ba" Umaimah da basu saka ta cikin maganarsu ba tayi tsugul ta amshe tana gama fada ta rushe da kuka me sauti kamar daman jiran dalilin yinsa takeyi. Kallonta sukayi gaba daya, Abba ya sauke ajiyar zuciya Mama kuwa sake maida kai tayi tana kallon qofar fita badan tana kokawa da shaidan dake mata hububar tsiya ba da qila tsinewa Umaimah zatayi tabi duniya kawai kowa ya huta. Ganin tana neman caza musu kwakwalwa babu gaira babu dalili gaba daya suka fice suka barta a dakin tana kuka tamkar ranta zefita. Turo qofar akayi ta daga kai bazato suka hada ido da Safina data shigo dakin a kidime kamar an jefota. Gajiya tayi da kiran Umaimah a waya bata samu yau taje gidan Sammani ya shaida mata Umaiman tana Asibiti bata da lafiya hankali tashe ta nufo wajenta ta taki sa'a Umaimah na neman wanda zata kwance sauran haukan daya rage mata a kwakwalwa. Fadar irin tashin hankalin da sukayi da Safina bata baki ne, ta manta da zancen wani dinki da yake a jikinta da qarfin da kowa yayi mamakin inda ta samoshi saboda ganin tunda ta farka bata iya wani motsa jikinta dakyau se gashi ta kama Safina ta sakata a kwana ta ringa kilarta aka rasa me kwatarta saboda kowa yana tsoron ya shiga ta hada dashi. Ta zagi Safina da kafatanin danginta ta kuma tsinewa Malaman Safina da Ahalin su gaba daya ta kuma jaddada mata da ta nemo mata duk kudadenta data san ta karba ta kaiwa Malamai idan ba haka ba se tayi mata abinda harta mutu baza'a sake hada baki da ita a yaudari wani ba. Dakanta ta ringa shelanta irin abubuwan Safinan ta kaita tasa akayi mata ashe duk yaudara ce tunda gashi nan har Khalil din yayi aure bata sani ba qarshe ta karbi tukuicin Saki sanadin wannan uwar sabada da akaci seda dinkin jikinta ya bude aka sake maida mata da wani jiki ya dawo danye sati daya ya kamata a sallameta amma seda ta shafe sati biyu a Asibitin cikin wani mawuyacin hali kafin suka sallamesu gaba daya ta koma gida da Babynta Malika wadda ta karbeta bisa tirsasawar Abba da yayi rantsuwa akan in har bata karbi yarba kamar yanda take iqirari sedai ta nemi wani gidan uban badai nasa ba. Ta karbeta dukda seda suka qulla yarjejeniya akan Idan Malikan ta cika shekara daya Khal ze karbi yarsa, kuma yace ya dauki Alhakin samar musu da duk abun buqata har zuwa wannan wa'adin, zaman Asibitin da tayi kaf shiya biya kudin sannan yan uwansa basuyi qyashin siyan duk wani abu da Jaririyar zata buqata ba sun kai gidansu Umaimah, dukda zafinta da sukeji be shafi yarsu ba. Sun yi mata ragon suna da duk wani abu da akeyi lokaci kawai suke jira shekarar da aka diba ta cika daga nansu karbi yarsu su hada da Sauran saboda koda ace Umaimah ce ta buqaci su bar mata yaran babu yanda za'ayi su yarda ballantana da har ta budi baki tace bata qaunar ganinsu, yanda Ubansu ya fitar da ita daga rayuwarsa itama ta bar masa dunda daman bada su taje ba. Mamakin da lamarinta yake bawa mutane kadan ne, daman sunsan dacewar zata iya aikata abinda yafi haka ma amma da yawa sunyi zaton rabuwarsu da Khalil din da yanda abubuwa suka wakana zasu ladabtar da ita ta koma cikin saiti sedai ko kusa a lissafin Umaimah ba haka bane, ta qulla a ranta duk aje a dawo Khalil baze taba rayuwa babu ita ba kuma tana zaune ze dawo gareta a lokacin zata jashi aqasa ta rama duk wani wulaqanci data fuskanta a dalilinsa shi yasa sam hankalinta beyi wani qololuwar tashi ba dukda idanta tuna yana tare da wata macen ba ita ba se taji kamar ta hadiye zuciya ta mutu amma tasan na dan lokaci ne matsawar da zatayi daga kusa dashi kuma ze qara bata damar tsara ta yanda zata magance komai a lokaci daya. KHALIL A bangaren Khalil kuwa Sakamakon gwajin da akayi masa ya fito kuma ya tabbatar da ya samu Nakasa a al'aurarsa a gurin sa abun be zo masa a bazata ba domin ya rigada ya sakawa ransa faruwar hakan tashin hankalin da kadai ya fuskanta shine rashin iya controlling fitsari da yakeyi, daman tun bayan da aka kaishi suka saka masa robar Fitsari shika dai ne fargabarsa ace ze dawwama yana amfani dashi bayaga haka duk wani qalubale da ze bibiyeshi me sauqi ne yana kuma roqon Allah daya bashi ikon Jurewa kuma cikin ikon Allah randa ya cika sati daya suka cire masa robar kuma be fuskanci wata matsala ba, abunda kadai ya rage masa ciwon mara da yake fama dashi lokaci zuwa lokaci wanda likitan yace yaci gaba da shan magani da yardar Allah ze rabu dashi maganar samun daidaituwar lafiyarsa ce wannan ya fawwalawa Allah domin shine meyin yanda yaso, kai tsaye baze ce masa ya samu tawaya ta har Abada ba domin babu yanda Allah baya iya juya lamarinsa amma mawuyacin abune koda ace ya warke lafiyarsa bazata dawo gaba daya ba haka suka sallameshi ya koma gida sedai ya ringa zuwa check up lokaci lokaci. Ya koma gida ya cigaba da Jinya cike da zullumi da tausayin Humaira da ko kadan bata gajiya da kulawa dashi tun ya na gadon Asibiti har zuwa sanda aka sallamo shi haka yan uwanta sun nuna masa karamci, su suke qara qarfafa mata guiwa tareda sake nuna mata dumbin ladan dake tattare da aikin jinyarsa da takeyi. Idan ya kalleta tausayinta da soyyarta suna qara nunkuwa a zuciyarsa amma ya qudurwa ransa baze taba bari son zuciyarsa ya sa ya cutar da ita ba, ze yi mata adalci ya kuma yiwa kansa Adalci shekarunta sunyi qanqantar da ze tauyeta ta zauna dashi da lalurar sa baze yarda ya zama me son zuciya ba ze sallameta taje ta auri wani tayi rayuwarta shi kuma ya rungumi qaddarar sa a yanda tazo masa. Dangane da Umaimah kuwa da abinda tayi masa ya fawwalawa Allah komai ya kuma dauki abinda ya same shi a matsayin qaddararsa yana kuma roqa mata sassauci a gurin Allah sannan yana mata fatan Alkhairi akan duk rayuwar da zata fuskanta a gaba. Baze qullace ta ba kuma yayi mata uzuri saboda yasan duk abinda ta aikata Soyayyarsa ce sila, haka ya fawwalawa Allah komai be sare ba dan haka ya shiga neman Asibitoci a qasashen qetare da suke da kwararru akan matsalarsa zeje ya gani saboda shi magani baka san inda zaka dace. UMAIMAH Umaimah ta sake koma gidansu amma wannan karon a Matsayin Bazawara, dakinsu na yammatanci ta gyara ta shiga kimanin watanni uku da rabuwarsu da Khalil kenan amma gani takeyi kamar ba gaskiya bane, dauka takeyi ireiren sabanin da suka saba samune ta taho gida bayan wani lokaci ze huce ya dawo ya maida ta dakinta Musamman irin yanayin da take ciki na cewar babu abinda ta nema ta rasa se kulawarsa data yan uwanta. Tunda ta dawo gidan bata qara samun wayarsa ba kai ba shikadai ba hatta Hajiya idan ta gwada kiranta wayar bata shiga harta gaji ta dena bayan dawowarta gida dai Khalilfa yaje sau daya ya kai musu saqo dukda be shiga gidan ba a waje ya tsaya ya bawa yara tulin uban siyya duk wani kayan amfani daga kan naci zuwa na tsafta seda ya siya ya aika mata dashi kamar yanda yayi alqawari sannan ya dora mata da dubu Ashirin a kan kayan. Sanda yara suka shiga dashi Mama na zaune a tsakar gidan ta tambayesu daga ina suka ce mata wani Khalifa ne yace a kawo. Bata sake ce musu komai ba suka gama ajiyewa suka fita dan da Umaimah da duk wani abu daya shafeta ta dade da jingine su a gefe. Tsakaninta da ita ido idan sun hadu kenan tayi mata iyaka da shigar mata daki kuma bisa dukkan alamu abun be dameta ba dan bata nuna ba sabgoginta kawai takeyi wuni guda tana daki ta kwanta nan ta tashi can tunda hidimar yar ma Anty ce take yi mata ita dai a zuciyarta tana yi mata fatan shiriya idan tana da rabo dan babi wanda ze so yaga nasa ya halaka rana gobe qiyama. Haka rayuwa taci gaba da gungurawa sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da shudewa Umaimah na nan zaune gidansu ita da me zaman kanta marabarsu qalilan ce domin kuwa babu me sakata haka babu me hanata domin kwata kwata idan ka cire Anty a gidan ma babu me shiga shirginta se Yasir da lokaci lokaci takan aikeshi ya siyo mata kayan kwadayi duk ranar da aka girka abinda beyi mata ba tunda tana da uwar kudinta gashi duk watan duniya bayan kayan abinci Khalil din zo doro mata dubu Ashirin yasa take sharafinta son ranta kuka babu wanda ya daga kai ya kalleta kamar yanda Abba yace Duniya tafi bagaruwa iya jima tayi yanda take so ba ranar kuka tana gaba. Tunda tayi tayi ta samu Khalil a waya abin ya faskara ta haqura ta watsar dashi, abu daya ta ajiye a ranta ze dawo gareta dan baze iya rayuwa babu ita ba. Maganar Humaira ko a ranta ma gani takeyi basa tare domin ta tabbatar ba zata zauna da Khalil din da lalurar data sameshi ba ko bata nemi rabuwa dashi ba yan uwanta ba zasu barta taci gaba da zaman ba shiyasa ta kwantar da hankalinta sosai kamar babu wani abu tana jiran lokaci kawai da Khalil din ze kawo kansa a sannan zatayi masa wankin babban bargo ta qarasa tashin hankalin da batayi a baya ba. KHALIL Sannu a hankali rayuwarsa ta daidaita bashida wata matsala da ze iya cewa gata idan bata lalular data sameshi ba. A bangaren zamansu da Humaira kuwa babu abinda ze ce sedai ya godewa Allah kamar yanda a koda yaushe bakinsa baya gajiyawa gurin godewa ni'imar da yayi masa. A cikin watanni shida da auransu ya samu nutsuwar da besan da ita ba a tsayin shekaru Bakwai daya shafe da Umaimah. A yanzu ne ya san yayi aure ya kuma san dadin aure, irin kulawar da Humairan tak bashi tana saka ya manta da duk wata damuwar duniya idan yana tareda ita baya tuna komai da kowa se ita dashi ta shayar dashi zallar madarar soyayyar da ya dade yana mafarkin samu shi yasa be tauye kansa ba ya ware ya ajiye komai ya rungumi Matarsa suke zuba qauna domin tayi masa halacci ita da iyayenta da har ya koma ga Allah baze biyasu ba. Tun bayan fitowarsa daga Asibiti ya fito da qudurin cewar zamansa da ita bame yuwuwa bane domin ko a shari'an ce akwai cutarwa tunda har yasan bashida lafiyar da zero ci gaba da biya mata buqatarta dole ya sallamata ta auri wani tayi rayuwarta shi kuma ze rungumi qaddara ya cigaba da rayuwarsa harzuwa iyakar abinda Allah ya hukunta masa. Bayan komawarsa gida irin yanda take kula dashi take ririta shi ya karyar masa da zuciya, idan ya kalleta tausayin ta yakan narkar dashi ko kadan bata taba nuna alamar gajiyawa ko wata damuwa da abinda ya sameshi ba. A duk sanda taga yayi shiru ko yana tunani se tayi duk iya qoqarinta na ganin ta kore masa damuwa tareda qarfafa masa guiwa. Watansa biyu cikin wannan yanayin ya warke garas a zahiri tunda dama ba lalura bace da za'a gani a jikinsa har ya ci gaba da fita ayyukansa amma a cikin zuciyarsa rauninda Umaiman ta rigada tayi masa ya gaza warkewa. Duk sanda ya kalli dakinta se yaji wani abu ya dake shi ya kan zargeta da son rai da ace tayi haquri ta fawwalawa Allah lamuranta da yanzu suna zaune tare yaransu kullum cikin tambayarsa ina Momy take suke tun yana samun abin da ze gaya musu har suka haqura suka dena tambayarsa musamman saboda yanda Humairan take iya qoqarinta akan su, jansu takeyi kamar qannenta har wasan goyo da guje guje sukeyi abinda yake dauke musu kewa kenan har suka fara dena damuwa da neman uwarsu se lokaci lokaci. Dukda irin kwanciyar hankali fa nutsuwar da yake samu tattareda ita zuciyarsa taqi nutsuwa akan yaci gaba da zama da ita a yanda yake, baya so Allah ya kama shi da haqqinta Humaira yarinya ce qarama da bata gama sanin menene auren bama tukunna. A yanzu yasanbe zama lallai ta damuda halinda yake ciki ba amma ana tafe dole za'a kai lokacin da zata fara buqatuwa da Namiji shi kuma bashi da lafiyar da ze biya mata wannan buqatar daga nan fitina zata iya bullowa wadda baya fata, domin gujewa hakan tilas ya samar musu maslaha ta hanyar rabuwa da ita koda ace hakan zeyi sanadiyyar da shi ze qare rayuwarsa cikin qunci kamar yanda Umaiman take fata. Yanke shawara yayi akan fara samun Hajiya da maganar kafin ya aiwatar dan haka ranar bayan ya dawo daga aiki kai tsaye ya wuce gurin Hajiyar. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 75 A falo ya tarar da Humairan da Habiba suna hira, yabita da wani malalacin kallo saboda yanda kwalliyarta ta dauke masa hankali yaji gaba daya ya rasa kwarin guiwar daya shigo da ita. Seda ta waiwaya ta kalli Bene kafin ta taso da sauri ta rungumeshi ya dagata sama dan tsahonta be kai kafadarsa ba yayi pecking lips dinta da suka sha Red lipstick kafin ya ajiyeta ya kalli inda Habiba take ya ga ta bar gurin kawai ya saki murmushi. Wannan yar babyn tana sakashi yin abin kunya a gaban Qannensa ta kama hannunsa tana murmushi tace "Yau ka dawo da wuri, yanzu nan fa na shigo nace na rage lokaci kafin lokacin dawowarka yayi ka shiga can bana nan shiyasa ka taho nan?" Hancinta ya dan ja yana qare mata kallo ta qara qiba da haske tayi kyau sosai ya zauna akan kujera ta zauna a gefensa yana ce mata "Missing dinki nake tayi shiyasa na taho gida da wuri, ina Hajiya na ganku ku kadai?" "Yanzun ta hau sama bari na gaya mata ka dawo" ta miqe sega hajiyar ta fito ta sakko qasan tana masa sannu da zuwa zame daga kan kujerar ya gaisheta ta amsa itama tana tambayarsa ya akayi yau ya dawo da wuri yace mata aikinr babu sosai. A kitchen din Hajiya ta dakko ruwa da Lemo ta kawo masa ya karba qasa qasa ya furta mata "I love you" tayi qasa da kanta tana zuba masa ruwan Hajiya dake kallonsu tayi murmushi a ranta wani dadi yana qara mamayeta. Idan ta kalli Khalil da Humairan tana tsintar kanta cikin matsanancin farin ciki harta ce inama tun farko ita ya aura ba Umaimah ba? Ita ce irin matar data dade tana yiwa Khalil dinta addu'ar Samu a rayuwarsa se gashi al'amari mara dadi ya biyo bayan Gamuwarsu tana fatan hakanya zama wani Alkhairi a gabada basuyi tsammani ba. Yana gama shan ruwan ya miqe yana cewa Hajiya bari yaje anjima ze shigo akwai maganar da zasuyi, suka fita tare ta daukar masa jakar sa. A bakin qofar ya fizge jakar ya ajiye ya dauketa kamar yar tsana ya haye sama da ita tana fizgewa da shagwabar ita ya sauketa be direta ba se akan Gadon dakinsa ya bita ya danneta ya sakar mata nauyi yanda yaga tana kokawa da numfashi ya sakashi saurin dagata yana cewa "Yarinyar nan bakya motsa jikinki gashi nan qiba ta fara miki yawa har kina haki daga an dan wujijjigaki". Baki ta tura masa tana qunquni ya kuma kama bakin nata ya shiga kissing nata passionately badan yana jin komai ba. Seda yayi sosai kafin ya cire bakinsa daga naya ya kalli fuskarta ganin ta rufe idonta yanayinta ya nuna tana jin dadin abinda yayi mata, a hankali ya saketa ya shiga qoqarin miqewa still idonta a rufe ta sake shigewa jikinsa be gama mamakin abinda tayi ba se ji yayi ta sake maida bakinta cikin nasa tana biya masa haddar abinda ya koya mata. Kasa yin komai yayi kawai ya bude ido ya kallon yanda takeyi cike da mamakinta. Har sannan idonta a kulle ta kama Hannunsa ta ta dora akan qirjinta da suka qara cika gabansa ya yanke ya fadi abinda yake gudu har yazo kenan, seda ya hadiye wani yawu kafin ya tattaro duka nutsuwarsa ya shiga yi mata abubuwan da yasan zasu bata nutsuwa dukda bayajin komai a tattare da abinda sukeyi din. Tausayinta ya kama shi ganin yanda jakinta yake rawa, yayi iya yinsa gurin ganin ya gamsar da ita ta hanyar amfani da hannayensa da kuma bakinsa har seda ta samu gamsashshiyar nutsuwa se kuma ta kife a jikinsa ta fasa masa kukan da kana jinsa kasan na zallar shagwaba ne yayi yayi ta dagashi taqi ita a dole kunyar sa takeji abinma ya bashi dariya dakyar ya rabata da jikinsa ya shige bandaki jin ana kiran sallar Magriba. Seda yayi wanka tareda Alwala zuciyarsa cike da zullumin abinda ya faru. Qirjinsa ya ringa bugawa duk yanda yake da jaraba ace yau gashi ga mace a cikin irin yanayin da yake so amma ace beji komai a kanta ba. Hawaye ya digo masa me zafi daga ido daya ya share yana jin wata tsanar Umaimah da be taba zaton zeyi mata irinta ba ta taso masa ita ce sila ita ta janyo masa ya zama mara amfani dashi da dutse yanzu marabarsu kadance tabbas Umaimah ta zalunce shi kuma ta zalunci Humaira yanzu ta yaya zama ze yuwu a tsakaninsu bama ita ba da duk wata lafiyayyar mace da ze aura ko ita kanta Umaiman a yanzu yasan babu abinda zatayida shi tunda ta rigada ta kassara abinda takewa wasu baqin cikin samu a gurinsa. Qofar da Humairan ta buga masa ta sakashi qarasa wankan ya fito fuska babu walwala ya wuceta ta bishi da kallo jiki a sanyaye kafin ta shiga wankan itama tana mamakin meya bata masa rai? Haka tayi wankanta ta fito tana shafa mai tana tuna abubuwan da yayi mata. Da hannu biyu ta rufe fuskarta saboda kunyar yanda ta sako jiki harda fa wani kuka ta ringayi ita wlh bata ma san meya shiga kanta ba da har ta shishshige masa. "Amma fa akwai dadi na yau daman ya iya irin haka shine yayi mun na mugunta kwanaki?" Ta fada a fili kamar me magana da wani. Tana saka kaya tana tunanin ya warke kenan ma tunda takamaimai fa ita daman ba wai ta san meye ciwon da yake damunsa bane qarancin shekarunta be barta ta fahimci illar da ake iqirarin Umaiman tayi masa ba ita dai tasan ta buga masa abu a ciki shikenan. Tsaf ta shirya cikin qananan kaya ta kalli kanta ita kanta ta lura da qibar data yi sosai fa abin ya mata dadi tunda daman ai shi so yakeyi tayi qibar seda ta gama shiryawa kafin ta zura dogon Hijab akan kayanta tayi sallah. A gurin ta zauna har akayi isha tayi tareda shafa'i da wutri kafin ta cire Hijabin ta sake gyara jikinta ta wuce bangarenta ta dakko Baqar Abaya ta dora akan kayan jikinta kafin ta sauka qasa. Ta rigada tayi girki tun tuni, qara gyara kwanukan tayi ta ciro Jug din Zobon data hada daga Fridge da ruwa ta ajiye komai ta koma cikin falon ta zauna tana kallon Tv a ranta tana tunanin to se yaushe kenan Umaimah zata kwashe kayanta tunda an saketa gashi kusan wata nawa har yanzu kuma ba' acire komai ba. Khalil kuwa seda yayi sallar isha'i kafinya koma bangaren Hajiya, tayi masa tayin abinci ya girgiza kai yana sosa qeya, Hajiya tayi murmushi ba tareda tace komai ba. Qara gyara zama yayi fuskarsa na qara bayyanar da damuwar da yake ciki yace "Hajiya daman maganar da nace zamuyi akan Humaira ne" "Toh me kuma ya sameta?" Hajiyar ta fada tana gyara zama se yayi qasa da kansa saboda nauyin maganar da ze fada din kafin ya fara magana cikin sanyin murya yace "Hajiya nayi la'akari ne da halin da nake ciki ina ganin kamar akwai cutarwa a zaman mu da ita tunda bani da lafiya ita kuma dole tana da buqatun da bazan iya biya masa su ba. Tun ina Asibiti nayi tunanin na sawwaqe mata kamar hakan zefi mana sauqi dani da ita sedai kuma banyi hakan ba. Hajiya kullum qara sonta nakeyi harta kai yanzu ina jin bazan iya rayuwa babu ita ba amma kuma bana so Allah ya kamani da haqqinta shiyasa nake so nayi yaqi da zuciyata na rabu da ita taje ta auri wani me lafiya ni kuma naci gaba da rayuwata a yanda Ubangiji yaso ya ganni" ya qarasa maganar cikin rawar murya saboda abu biyu da suka shaqe masa zuciya, baqin cikin abinda Umaima tayi masa ga kuma fargabar rabuwa da Humaira da yake jinta har cikin jini da tsokarsa. Jin Hajiyar tayi shiru bata ce komai ba ya dago ya kalleta, a rikice ya sauka daga kan kujerar da yake ya durqusa a gabanta yana cewa "Kiyi mun afuwa Hajiya idan a cikin maganata da akwai wadda ta bata miki rai har tasa kike zubar da hawayenki ki yafe mun zubar kwallar ki ba Alkhairi bace a gareni". Ganin yanda ya rikice din jikinsa har yana rawa ya saka Hajiya qoqarin tsaida hawayen nata tana cewa "Bakayi mun komai ba Babana ba kuma kaine silar zubar kwallata ba. Ina tuna irin Halaccin da mukayiwa yarinyar nan a rayuwa amma ka dubi da abinda ta saka mana. Umaimah ta cutar damu sedai mu barta da Allah ya bi mana haqqin abinda tayi mana" Hajiyar ta fada tana sake rushewa da kukan daya fi na farko, dakyar Khalil ya lallabata tayi shiru cikin yanayi na rashin dadi tace "Maganarka gaskiya ce Babana tabbas zamanka da Humaira a halin da ake ciki da akwai cutarwa amma ai bama fatan ka dawwama a haka, ba zama zamuyi ba zaka ci gaba da neman magani har Allah yasa a dace saboda bazan so ace ka rasa nagartacciyar yarinya kamar Humaira ba ka rabu da waccen alaqaqai sharrinta be rabu damu ba yana nema ya sake rabaka da Alkhairin da a kullum nake roqa maka gurin Allah nayi imani da cewar Allah ze karbamin ya maida maka da madadin Alkhairi. Kar kayi gaggawar yanke hukunci ka fara tuntubarta kuyi magana duk abinda ta zaba se muyi fatan ya zama mafi Alkhairi dukda in har rabuwar ku ce ta kasance wadda bana fatan toh tabbas bazan yarda nayi Asarar suruka kamarta ba, zan umarci Khalifa ya nemi auranta qila abinda Allah ya...." "Haba Hajiya wace irin magana kikeyi haka a gabana kike kiran Khalifa ya auri matar dana tara da ita da raina ban mutu ba haba Hajiya" Khalil ya katseta cikin wani irin sauti da ya sakata yin shiru babu shiri sannan ta fuskanci katobarar da tayi. Idanunsa suka kada sukayi jajir ya sunkuyar da kansa qasa a hankali ya sake cewa "Kiyi haquri na daga miki murya amma Hajiya dan Allah karki qara kawo wannan tunanin bazan jure ba zuciya zata iya yin bundiga na mutu kawai kowa ya huta" ya fada tamkar ze rushe mata da kuka. "In sha Allahu ba zaka mutu yanzu ba Babana yanda ka fara dandana rayuwar farin ciki da Izinin Allah haka zaka qare rayuwarka cikin farin ciki da annushuwa. Kaje ka samu matarka kuyi magana ta fahimta nima zan samu Mariqiyarta domin babu abinda zamu boye musu sannan muci gaba da addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkhairi" "Amin Hajiya" ya amsa se ya miqe da shirin tafiya maganarta ta dakatar dashi ya kasa gaba ya kasa baya jin tace "Babana naji kace ka tara da ita kana nufin ka dora mata iddarka kenan?" Dakyar ya iya daga mata kai saboda bala'in kunyar daya lullube shi Hajiya ta zabga tagumi tace "Allah ina roqonka kasa da dogon zama tsakanin wadannan yara, Babana bansan da idon da zamu kalli iyayen yarinyar nan ba idan rabuwa ta gifta tsakaninku bayan ka maida musu da yarinya bazawara, ashe hasashena ba qarya bane da nake ganin kamar tana da Shigar ciki" Wani quum yaji a kansa kamar ta buga masa guduma Jin wai kamar Humaira nada ciki, a hankali ya furta 'Hasbunallahu wani'imal wakeel' idan kuwa har ya zamo gaskiya Umaimah ta cutar dasu da abinda Humaira zata haifa tayi sanadiyyar da ze rayu ba a tsakanin iyayensa ba kamar yanda ta janyo wa nata yaran. Haka ya fita daga bangaren Hajiya a salube kamar mara lafiya ita kanta Humaira ganin yanayinsa ya jefata a damuwa ta shiga tambayarsa ko bashi da lafiya ne amma yace mata qalau yake. Abincin ma kadan yaci yace suje su kwanta ta kalli agogo tara ma sannan tayi hakan ya qara tabbatar mata da tabbas bashida lafiya to ko abinda tasa yayi dazu ne ya tayar masa da ciwon sa gashi ita kuma ji takeyi kafin su kwanta ma da ze qara da taji dadi haka ta bishi suka kwanta ya sakata a jikinsa sosai ya rungumeta gaba daya ya rasa ta ina ze fara tambayarta tana so taci gaba da zama dashi ko yaya, idan kuma ya tuna furucin Hajiya na cewar zata nemawa Khalifa auranta se yaji kamar ya hadici zuciya ya mutu wata zuciya ta hakaito masa kenan abinda Umaimah take ji game dashi kenan? tabbas Abune me matuqar nauyi a zuciya amma be kai ta aikata abubuwanda tayi ba inda tana da Iklasi a zuciyarta. A haka bacci ya fara fizgarsa yana ta tunane tunane ya kasa yi mata maganar, qirjinsa da yaji tana shafawa ya sakashi bude ido ya kalleta base ta gaya masa abinda take buqata ba yanayinta kadai ya fahimtar dashi gabansa ya fadi to me yake faruwa kuma, wace jarabawar ce ta sake tun karo shi? Wata uku kenan yanzu duk idanba shi ya jata jikinsa ba kunya da tsoron ya tabata takeji har seda ta tabbatar da ba abinda take wa tsoron zeyi mata ba kafin ta sake dashi sosai amma a yau tazo da wani sabon Al'amari da yake rikitashi, babu yanda ya iya haka ya sake yamutsata kamar na dazun har seda ta samu nutsuwa kafin tayi wanka suka kwanta zuciyarsa fal cike da tunanin mafita. Tabbas idan har yanayinta ya fara canzawa zuwa ga yawan buqata rabuwarsu ita ce maslaha duk kuwa surutun da za'ayi gara ayi akan ya cutar da ita kota fada wata halakar da baya fata a dalilinsa baze yafewa kansa ba. Dakyar bacci ya daukeshi saboda tunanin da yake ta famanyi. A bangaren Hajiya ma haka ta kasance da ita ta kasa bacci tana saka da warwara daga qarshe ta yanke shawarar takawa qafa da qafa taje ta samu Mama Hauwa washe gari, hakan kuwa akayi qarfe Goma na safe a gidan tayi mata Mama Hauwa ta tareta da murya a ranta kuma tana mamakin zuwan Hajiyar dan haka kawai bata taba zuwa gidan ba seda kwakwkwaran dalili, ita ce take leqata lokaci lokaci tun ma a zamanin baya daga baya itama ta watsar suka zamana se idan abu ya farun sannan za'a hadu sudai yaransu da Allah ya qulla Aminta a tsakaninsu kullum suna tafe gidajen junansu. Bayan ta ajiye mata Kunun gyada da Alala me kyau da tayi na karyawa gamawarta kenan tayi wanka tana shirin zama ta karya Hajiyar ta shiga. "A qoshe nake Hajiya kedai ki karya se muyi maganar data kawoni dan zanfi so kici ki qoshi tukunna" Hajiya ta fada se Mama Hauwa tayi sak kafin ta saukeajiyar zuciya taja kwanukan ta shiga cin abincin a ranta tana addu'ar duk ma abinda Hajiyan tazo dashi Allah yasa Alkhairi ne. Seda taci ta qoshin kuwa ta kwashe komai kafin ta zauna tana cewa "Ina jinki Hajiya, Hajiya ta janye tagumin data rafka kafin cikin nutsuwa ta shiga zayyanawa Hajiya Hauwa komai game da matsalar Khalil da kuma hukuncin da yake shirin yankewa. Mama Hauwa tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta zuciyarta na bugawa da qarfi tausayin Khalil din ya rufeta kwari ainun, dukda sun san da maganar kwada masa abu da tayi amma basu zata munin abun ya kai haka ba kuma harda Mansur sunyi maganar se yanzu ta fahimci irin jimamin da yaketayi ku ya da nauyi ya hana ya fayyace mata ainihin abinda yake faruwa amma wannan yarinya Umaimah lamarinta se Allah. Numfashi ta ajiye tana kallon Hajiya tace "Abun babu dadi Hajiya amma duk abinda kaga ya samu bawa da sanin Allah kuma in sha Allahu shi ze warware komai wata rana se kiga komai ya zama labari tamkar ba ayi ba. Sannan Hajiya wannan al'amari a hannunsu yake su zasu yanke wa kansu shawarar abinda ya kamata suyi su da suke yan zamani duk dabarun jiyar da kai dadi wanne ne basu sani ba? amma ina ganin rabuwa ba ita bace Maslaha su zauna suyi magana shi yafi idan anyi haquri da sannu se kiga Allah ya bashi lafiya sunci gaba da zamansu qalau" Hajiya tayi qasa da kai irin maganar Maman ta bata kunya ita kuwa ko a jikinta taci gaba da cewa "Allah kuwa Hajiya me ake nema ne dama dai ba wancan abun ake tunani ba dan dai kawai za'ace ita yarinya ce baya ga haka Allah na tuba masu lafiyar ma nawa ke zaune basa samu wasu sun manta ma ana wannan a cikin aure sannan ni ashe ido na ne be gani daidai ba zuwan da sukayi na qarshe ma gani nayi kamar tana da shigar ciki ashe ba haka bane to idan ma Haihuwa ce shi rabo ai lokaci ne in a nesa yake se kiga anja lokacin har lafiyar ta samu a zo a hayayyafa" se sannan Hajiya ta iya cewa "Nima haka na gani kuma jiya munyi magana dashi a yanda na fahimta dai qila da akwai cikin dan be musa ba dana fada" Mama taja Kabbara tace "Kin gani ko? Allah kadai yasan abinda ya boye cikin auran nan dan haka ayi haquri a bi komai a sannu shi kuma Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne zan saka Sumayya ko Unaizatu suje gidan suyi magana da ita idan ma akwai wata damuwa wadda nake fatan babu zasuji Allah ya shige mana gaba" "Amin Hajiya mun gode Allah ya saka da Alkhairi na sani abubuwan da suka faru daga fara neman auran nan zuwa yanzu yanzu da a waje Khalil yaje da ba'ayi shi ba koda anyi da yanzu gari kaf ya gama jin abinda ake ciki Mungode" Hajiya ta sake fada Se Mama Hauwa tace "Haba dai Hajiya mu daku ai daya ne dan ni yanda Mansur yake a gurina haka na dauki Khalil shi yasa banji ko dar ba na bashi auran Humaira domin nasan ze kula da ita kuma Alhamdulillahi bana nadamar hada auransu ba" "Allah ya jishshemu Alkhairi Hajiya, bari naje se na sake zagayowa" daga haka sukayi sallama ta tafi. Hajiya na tafiya Mama Hauwa ta kira Unaizatu, sunfi fahimta da Humairan dan haka ita zata saka tayi mata wannan aikin. Washe garin ranar kuwa Unaizatu tayiwa gidan Humairan tsinke da sassafe dan ba qaramin kaduwa tayi da jin Al'amarin ba taya ma za'a yi yarinya qarama kamar Humaira da bata san komai a cikin rayuwa ba ace tayi irin wannan zaman? Gangan kenan. Bata nunawa Mama komai ba tace mata dai goben zata je a ranta ta qudure niyyar baiwa yar uwarta shawarar data kamata dan ba zata zuba ido a saka yarinya qara ma a tasku ba. Sanda taje ta tarar da Khalil a gidan be fita ba saboda Humaira data tashi bata jin dadi suka gaisa cikin mutuntawa shi ya kawo mata Ruwa da lemo da abin tabawa dan basu rigada sun dauki me aiki ba tunda Ruqayya ta tafi seda ya ajiye mata komai kafin ya shiga ya kirawo Humairan data dan kwanta ta huta. Tana ganin Unaizatun ta fasa ihun murna ta fada jikinta Khalil ya bude ido yace "Kiyi a hankali fa karki jima kanki ciwo, seya juya dakin yana cewa "Tunda kin samu abokiyar hira bari naje Anwar yana jirana bazan jima ba zan dawo" be jima ba ya fito a shirye yayi musu sallama ya fita bayan ya cewa Unaizatun karta tafi ta jirashi jintana cewa ba dadewa zatayi ba ya fita ya barsu. Humaira kuwa rasa inda zata saka ranta don murna tayi, Anty Unaizan bata taba zuwa gidan ba tayi nacin harta gaji se yau gata bagatatan tazo mata. "Muje ku gaisa da Hajiya Anty se na girka miki duk abinda kike so" ta fada tana kama Hannunta Unaiza tayi dariya tace "To yar Hajiya ai can na fara shiga kafin nazo nan ya jikin tace baki ji dadi ba" "Ni ai na warke kawai bana so ya fita ne daman shiyasa na langwabe" Hunaira ta fada tana tura baki se Unaizatu ta kama haba tace "Lallai yarinyar nan to idan be fita ba so kike ya zauna kuci soyayya kenan?" "Eh mana Anty ni bana so yana fita yana barina ni kadai gara ya zauna inyiyi masa shagwaba yana lallashina" "Ikon Allah" Unaizatu ta fada jin abin bana wasa bane, seta miqe tana cewa "Muje dakinki to magana nazo muyi" Humaira ta miqe tayi gaba Unaizatun na biye da ita a baya suka shiga falonta. A Bedroom suka qule kan Gado Unaizatu se qare mata kallo take ganin yanda ta canza gaba daya ta cika kamar ba ita ba ga wani haske data qara masha Allah kamar seka wanke hannu ka taba. A nutse kuma cikin dabara take bugar cikinta dan taji koda wata matsala daga bakinta amma bataji komai ba hakan yasa ta gyara zamanta dakyau tana kallonta tace "Kinsan abinda ya kawoni maganar rashin lafiyar Mijinki ce jiya Hajiya taje gurin Mama tayi mata bayanin komai akan abinda ya same shi dalili daya sa tace mu tambayeki kenan kar kiji kunya ko nauyi ki fadi tsakaninki da Allah idan kina son zama dashi" "Bangane ba Anty wani abu ya samu Yaya Khalil ne daga baya ko daman be warke bane?" Humairan ta fada cikin rashin fahimta se Unaizatu ta gyara zama tana kallonta tace "Yace miki ya warke ne ko ke kinga alamar hakan?" "Toh Anty tunda aka sallaameshi daga Asibiti ya warke kenan shekaran jiya nema dai daya dawo naga kamar bashida lafiya kuma yace qalau yake gashi nan ma kin ganshi ai yanzu" Humairan ta sake fada innocently se Unaizatu taja tsaki tace "Bana son sakarci ki nutsu ki gaya mun gaskiya tun bayan da kika tare wata Mu'amalar aure ta shiga tsakaninku ne?" Kafin ma ta rufe baki Humairan ta juya baya ta rufe fuska wai kunya Unaizatu ta dana mata duka a baya ta gantsare tareda yin ihu dan dukanya shgeta bata barta ba a fusace tace "Dan ubanki ki juyo ki bude baki kiyi mun magana kunyar uwar me zakiji ana neman yanda za'a kwatar miki yanci kin zauna kinawa mutane yarinta da shirme nace kun taba kwanciyar aure da Khalil bayan kin tare a gidan ko yaya?" Baki ta tura kamar zatayi kuka tana soshe soshe ba tareda ta bari sunhada ido ba tace "Sau daya ne ranar da aka kawoni da daddare" "Bayan nan fa? Tunda aka sallamo shi daga Asibiti ya nemeki?" Ta sake jefa mata wata tambayar zuciyarta na bugawa da jin ya kwanta da Humairan, sam bata so haka ba, taso ko rabuwar zasuyi ta fita a yanda tazo amma aikin gama ya gama. Baki Humairan ta sake tunzurawa tace "No shike nan sau dayane to wai tambayar mecece ma haka bayan bake kikace karna ringa yin hira da kowa ba koda kece ko Anty Sumayya kuma yanzu kin zo kina ta tambayata" A hasale Unaizatu tace "Dole kimun rashin kunya mana tunda yanzu mun zama kai daya kema kin san Namiji, to bari kiji tunda naga har yanzu yarinya na damunki baki ma san abinda yake faruwa ba Rashin lafiyar da Mijinki yayi kayan aikin sa ne ya samu matsala, a taqaice dai ina nufin dake dashi yanzu marabar ku kadance dan baze iya miki abinda sauran Maza sukeyi ba. Daman zuwan da nayi Mama ce ta turo ni akan na tambayeki kina son Mijinki zaki ci gaba da zama dashi da lalurar sa ko kuwa ba haka ba? Sannan in miki dalla dalla zama dashi da lalura yana nufin babu haihuwa tunda ba harka yawwa dan nasan kanki ba ja yake da kyau ba". Tayi fakare tana kallon Unaizatu danharga Allah kam bata gane me take nufi ba, maganar haihuwa kadai ta tsinta wannan kuma in ta fassara daidai tana nufin Khalil baya haihuwa to Mu'ayyad da Bibi yayan waye? "Kin tsaya kina kallona kamar wawiya ko baki gane me nake nufi ba?" Unaizatu ta sake fada ganin irin kallon da take mata seta daga mata kai alamar haka ne bata gane ba, takaici ya qume Unaizatu, bayan yarintar Humaira harda rashin wayewa saboda gaba daya rayuwarta ta tashi ne tsakanin Makaranta se Mama, qawayenta kuma duk yara ne kamarta lissafinsu da tunaninsu be san wadannan abubuwanba a da suna jin dadin rashin wayewar kannata domin hakan ma wani mataki ne na kariya daga fitina amma yanzu titsiyen nanda tayi mata na seta fadi komai gatsal gatsal yasa taji haushin rashin iliminta ko yaya ne a wannan bangaren. Cikin dakewa tace "Ai kin san Manhood a biology ko?" Seta sake daga kai alamar ta sani ta zaburo mata tace "Ki bude baki kika sake daga mun kai kamar qadangaruwa sena mareki kin sani ko baki sani ba?" "Na sani" Humairan ta fada tana sunkuyar da kai a ranta tana hakaito na Khalil daya kusa kasheta dashi. "Yawwa to shi wannan abin nake nufi tsohuwar kishiyarki data kwada masa abu akai hakan yasa ya samu matsala baze iya kwanciya da Mace ba kinga kenan baze iya baki ciki ba" Unaizatu ta fada tana basarwa saboda kar Humairanta kawo mata raini ita kuwa dafe qirji tayi ta gwalalo ido tana kallonta jin abinda tace kafin bakinta na rawa tace "Daman a nan ta buga masa? Innalillahi shi yasa Yaya Khalil ya ringa ciwon ciki kamar ze mutu koda yake ai ance nan ne makasar Maza daman kenan kashi taso tayi?' "Oho dai koma menene kinji abinda ake ciki, kuma dai kinsan shi aure badan aci abinci kawai ayi kashi ake yinsa ba akwai biyan buqata ta sha'awa, wannan abinda kike cewa kina ji a jikinki idan kin sha magunguna lokacin to shi ake nufi da Sha'awa koda yake ai kin ma san komai rainamun hankali kikeyi tunda kina zuwa Islamiyya an karanta muku komai" Inji Unaiza, Ita dai Humaira na cike da Jimamin abinda taji dan har idonta ya tara hawaye tausayin Khalil ya kamata ta tuna wani dan Ajinsu a makaranta suna Ball aka buga masa ita a gurin ya Suma dalilin cire shi kenan ita bata masan ya rayu ko ya mutu ba anan ne ma taji Mazan Ajinsu na fadar nan ne Makasar Maza yanzu ashe abinda ya samu Yaya Khalil kenan gaskiya Allah ya saka masa Maman Mu'ayyad muguwa ce. "Toh yanzu dai seki zauna kiyiwa kanki tunani ki gani zaki iya zama dashi a haka ko kuwa saboda ke yarinya ce baki san komai ba a yanzu amma dukda haka babu me miki dole ke zaki zabarwa kanki abinda kike ganin shinr mafita a rayuwarki" "Wai yanzu Anty kina nufinna bar Yaya Khalil saboda ya samu lalaura? Kin manta a dalilina hakan ya same shi nasan badan ya aureni ba babu abinda ze saka tayi fushi haka harta kwada masa abunda ze janyo masa matsala kuma ko ba wannan abun ya rasa ba ko qafa da Hannu Yaya Khalil ya rasa zan zauna dashi saboda shi nake so ba wani abu nasa ba" Humairan ta fada kanta tsaye tana kallon Unaizatu da tayi suman zaune tsabar mamakinta, damanta iya magana haka babu shirme babu shiririta a ciki? Tabbas gaskiya ta fada ta dalilinta Khalil ya samu lalura amma a ganinta wannan ba hujja bace da zata saka Humairan ta tauye kanta ta zauna dashi, maganar data ci gaba dayi ta tsayar mata da tunanin da takeyi jin tana cewa "Kuma ma Anty ni daman ko kadan banji dadin abinda yayi mun bama banda wahala babu abinda nasha duk yaji mun ciwo rashin lafiyarsa sa ce fa tasa na warke babu shiri ni banma san ya akayi na denajin zafin da nake ji ba danma ranar Anty Jalilah ta taimamun sosai ta ringa sakani a ruwan zafi ta bani magani amma daman na rantse bazan ma sake yarda ayi ba se Allah ya dubeni ma gaba daya abin ya dena aiki shikenan a dadina iya wanda mukeyi ma ya wadatar yafi dadi wlh". Ajiyar zuciya Unaizatu ta sauke haka duk yanda taso ta fahimtar da Humairan abinda yake da akwai ta ce ita fa ba haka ba, soyayyar da yake gwada mata ta isheta duniya da lahira harda cewa "Anty dan baki ji abinda yake mun bane shiyasa kike cewa haka" "Indai kalar nasa ne bana fatan naji Humaira shikenan Ubangiji yasa hakan ne yafi Alkhairi Allah kuma ya bashi lafiya idan da rabo" daga haka ta miqe zata tafi Humairan ta ringa naci da magiyar ta zauna amma taqi haka ta tafi ta barta tana hawaye. Khalil be jima ba ya koma gidan ya tarar da ita tana kuka ya ringa rarrashinta kukan yasa zafin jikin data kwana dashi ya dawo dole ya dauketa suka wuce Asibiti, gwajin farko ya nuna tana da shigar ciki, dukda yaji qila wa qalan hakan a bakin Hajiya amma yayi matuqar Mamaki ya kuma godewa Allah domin ko iya haka ya tsayar masa da rabonsa sun ishe shi, ya kuma haihu da Humaira. Magunguna suka rubuta mata kafin suka kama hanyar gida, yanda yake tuqi a hankali kamar baya so bini bini ya kalleta ya tambayeta ya dai kamar ba'a taba daukar ciki a gidansa ba se wannan koda yake wannan din na daban ne dan haka dole ya ririta shi. Da suka koma gida da kansa ya ringa lelenta ya dafa mata doya da sauce da tace tana so ya bata a baki yayi mata wanka tsaf tayi sallar La'asar tana so tayi bacci amma ya hanata saboda rashin alfanun baccin bayan la'asar musamman ga me ciki. Tana kwance a jikinsa yana shafa kanta tana zuba masa shagwabar da tasa yake qara narkewa a sonta, so yakeyi yaje gurin Hajiya tun jiyan be samu sun zauna yaji yanda sukayi da Mama Hauwa ba ga kuma wani Al'amarin ya bullo wanda yake ganin dalilinsa kadai baze iya rabuwa da Humaira ba, ze je ko ina ne a fadin duniya ya nemi magani saboda yaci gaba da zama da ita "Yah Khalil" ta kira sunansa a shagwabe seya kalleta yace "Yau kuma Yah Khalil na dawo?" "To yi haquri Heartthrob, dazun da Anty Unaizatu tazo take gaya mun abinda ya sameka me yasa baka gaya mun ba nifa duk bansanme ya faru ba, shine wai Anty take tambayata idan zanci gaba da zama dakai a haka" ta sake fada kamar zata fasa masa kuka seya dagota suna fuskantar juna zuciyarsa na bugawa amma ya dake saboda besan abinda zata ce masa ba, daman yasan zuwan Unaizatun nada nasaba da maganar da Hajiya tajewa Mama yana fatan koma menene yazo masa da sauqi "I'm sorry Babe, ban san taya zaki karbi al'amarin ba, bana so kice zaki rabu dani zan qarasa mutuwa ne kawai dan na rasa komai nawa, amma kiyi haquri tunda yanzu kin sani" Hannunsa ta saka ta saqalo wuyansa tace "Ni na gaya mata ina nan tareda Mijina ko qafa da hannu da ido ya rasa ballantana wannan mugun abun me jiwa mutane ciwo" ta qarasa tana rufe fuskarta da wuyansa. Wani farin ciki ya dirar masa fargabar da yake ciki ta bace, kalmar mugun abu da yake jiwa mutane ciwo ta bashi dariya matuqa harya kasa riqeta daman be samu damar ya tsokaneta akan abubuwan da ta ringayi a daren farkon nasu ba, tashin hankalin daya riskeshi ya saka duk be tuna wannan ba se ya shiga qoqarin cireta daga jikinsa yana cewa "Thank you wife, ki kalleni ina so ki kalli idona dan kifi jin abinda zan gaya miki" "Nidai Aa ka fada ai kunne ne yake ji" ta fada tana sake maqalqale shi seya birkitota gaba daya a dole ta saki wuyansa ta kulle idonta gam tana dariya dan kunyar abinda ta fada ce take cinta Khalil yace "Kinyi mun hallaci da yawa Humaira ina fatan ubangiji ya ara mun damar da zan maida miki, Nagode da kika yarda zaki zauna dani a yanayin da ba kowacce Mace ce zata iya haquri dashi ba sannanna miki Alqawari zanje ko inane a fadin duniya na nemi lafiyata, idan har Allah ya lamunce mun na warke zan miki biyan bashinda ke da kanki zaki goge sunan Mugubta da kika laqaba mata ki canza mata da sunan Abin dadi" ya qarasa maganar a kunnenta yana dora hannunta a jikinsa. Ta zabura ta fasa ihu kamar wadda ya saka wa wuta Khalil ya riqeta da kyau yana dariya yace "Ki rufa mun Asiri karki jirkita mun Baby na" seta shiga kai masa duka yana karewa harta gaji ta fada jikinsa tana kukan shagwaba, Bayyanar cikin yasa ya fahimci nata laulayin itama irin na Umaimah ne me qara mata buqata zeyi iyakar qoqarinsa gurin ganin be gaza ba, godiyar da yayiwa Allahdaya sa bata rigada ta san dadin abin ba ballantana rashinsa ya dameta iyakar abubuwan da yake mata ya tabbatar zasu wadatar da ita. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 76 Tun daga wannan rana ya daura aniyar riritata tamkar kwai kamar yanda take riritashi take jiyar dashi dadin da besan akwaishi a duniyar aure ba. A yanzu ne ya sake gasgata Nutsuwa ita ce Aure abinda yake dauka a matsayin jin dadin auran a baya ake wulaqanta shi akansa gashi yanzu baya ko jin sha'awar sa koda ace Mace zata tube a gabansa baya jin komai game da ita amma irin dadi da nutsuwar da yakeji har cikin ransa ba zata Misaltu ba, idan ze fita har ya shiga Mota tana binsa da dadadan Addu'oin fatan nasara, wuni guda ta ringa binsa da Text messages din da harya dawo yana murmushi da dokin son ya dawo ya tarar da ita sannan idan yazo gida ya tarar da ita tayi kwalliyar da take kusan zauta tunaninsa ga girki me tsinka harshe tsabar dadi ga Shagwaba idan ta fara masa manta kansa yakeyi gaba daya yakance me yasa ba'a haifeki tuntuni kin girma munyi aure ba idan ya fadi haka sedai tayi dariya kawai tuni ta mantar dashi Umaimah da duk abinda ya shafeta. Idan ba yaga wani abu nata a cikin gidan ba ko yaran sun ambaci Momynsu baya tunata a haka ya shirya musu Tafiya India bayan Mansur ya hadashi da wani likita daya kware a bangaren Matsalarsa. Watansu daya a can duk kuma wani bincike da ya kamata sunyi masa suka canza masa magani akan wanda yake sha a Nan kamar dai yanda Likitocin nan din suka gaya masa suma haka suka maimaita masa, ba zasu ce masa ya nakasa gaba daya ba haka ba zasu bashi tabbacin samun lafiya ba ko kuma ga lokacin da hakan ze samu kawai yaci gaba da Shan magani yana addu'a haka suka koma gida bayan sun biya Dubai sunyi sati daya a can da yar babynsa da cikinsu dake cikin watanni na biyar a sannan. Haka rayuwa taci gaba da gurgurawa, bayan zuwansu India ya sake zuwa Egypt ganin Likita duk kuma dai Amsa daya yake samu a gurin su, qarfafawar guiwar da yake samu a gurin Humairan yasa ya haqura kamar yanda suka ce ya zubawa saurautar Allah ido yana fatanya kawo masa sauqi a sanda yafiye masa Alkhairi a cikin haka har cikin Humairan ya isa haihuwa ta haifi Danta daya dakko farinta kamar balarabe amma kamarshi daya da Khalil kamar sauran yan uwansa. Fadar irin murnar da Familyn biyu sukayi bata bakine da yawa kuma abin yazo musu a bazata dan ba kowa ne yasan tana da cikin ba se Haihuwa sukaji daga sama da yawa fadi sukeyi rabo ne da ace Umaimah ta matsanta da yawa qila da se ta mutu kuma ayi auran Allah ya taqaita mata ya tsaya a mutuwar aurenta. Se bayan da akayi suna yaro yaci sunan Mahaifin Humairan Auwal suna kiransa da Aryaan, Gida ta koma tayi sahihin wanka Maman ta kula da ita sosai kuma taji dadi yanda a zaman Kwana Arba'in din dukta yanda zatayi ta bigi cikinta taji ko tanada wata matsala akan zaman da takeyi ta nuna babu, dukda tana so ace Humairan tayi Yaya da yawa saboda ita kadai iyayenta suka haifa amma ko iya haka ta qarasa rayuwarta da Khalil ta bar baya ba lallai se ta qara wata haihuwar ba zasu ci gaba da lallaba rayuwarsu a haka. Seda suka kwana hamsin kafin ta koma dan har Taraba seda sukaje yawon Arba'in, kiran da Khalil ya ringayi da zaryar da yakewa Maman tasa ta tattara masa matasa suka koma dan be qara sanin tasirinta a rayuwarsa ba seda ta tafi wankan gidan, jin sa ya ringayi kamar wani Maraya Hajiya kanta seda ta ringa tsokanarsa idan taga ya zauna ya rafka tagumi tace ya tashi ya tafi gidan Hajiya Hauwa mana sedai yayi dariya ya sunkuyar da kai dan shi kadai yasan me yake ji akan rashin matarsa kusa dashi. Kwanci tashi akace asarar me rai se gashi Shekara ta cika, watanni goma sha biyu da Khalil ya nemi Alfarmar Umaimah ta shayar masa da Malika da suke kira da Iman sun cika. Zullumi ya shiga akan karbo yarinyar, tausayinta yake ji sosai saboda za'a rabata da mahaifiyarta tun bata san kanta ba amma hakan ya zama dole, yasan kafiya da Nacin Umaimah, tunda ta fada da kanta ba zata riqeta ba gara ya karbi yarsa cikin girma da Arziqi ya hadata da sauran yan uwanta shi kansa yana kewarta dan rabon da ya sakata a idonsa tun tana kwanaki a duniya. Ba'a taba kawota ba kamar yanda suma basu taba kai musu su Mu'ayyad ba tun bayan rabuwarsu kowanne bangate sun kama kansu sun zauna inda Allah ya ajiye su. A gurin Khalifa yake ganin hotunanta duk sanda yaje kaiwa Umaimah kayan abinci qarshen wata ze dauki yarinyar yayi mata hotuna ya nunawa Hajiya a nan shima yake samu ya ganta ta girka tayi wayo sosai kamanninta da Mahaifiyarta sun sake fita sedai kamar yanda kowa yake fada baya fatan Allah yasa ta kwaso zuciya irin ta Umaimah wadda sam babu salama a cikinta. Yana kwance kan Gadonsa yayi nisa cikin tunani Humaira ta shiga dakin, qamshinta ne ya fara sanar masa da ita ce, ya bude ido ya kalleta tayi kyau harta gaji cikin doguwar rigar Atamfar data saka ga daurin nan ta kawo gaban goshi Umaimah ta fado masa, Humaira da Umaimah suna kamanceceniya ta wasu halayen kamar bangaren kwalliya da tarairaya idan fa yan mutunchinta suna kusa kenan sabanin Humaira da a kullum haka take cikin kyautata masa dayin duk abinda tasan ze faranta masa rai badan tana buqatar wani abu daga gurinsa ba. Ta qarasa ta zauna gefen Gadon tana murmushi tace "Wai kana kwance har yanzu? Ka tashi kayi wanka ga abinci nan yana jiranka" Mirginawa yayi kusada ita ya jata ta fada jikinsa yana kallon idon ta yace "Kinyi kyau". Yanda tayi farr da ido kamar Umaimah a duk sanda yayi complimenting nata seya miqe yana cewa "Bari nayi wankan ki kawo mun abincin nan qyuyar fita nake ji" "An gama ranka ya dade" ta fada tana miqewa ya rakata da ido yana murmushi seda ta kulle qofar sannan ya wuce ya shiga wanka yana yi yana tunanin karbo Malika, Hajiya bazata iya da hidimar yaran ba saboda shekaru da yanayin lafiya da tayi mata qaranci daman Habiba ce qarfin Kula dasu to yanzu ana maganar saura watanni biyu Bikinta data bar gidan kulawar yaransa zata koma kacokan hannun me aiki kenan dan baze iya bawa Jalilah ita ba kamar yanda take haqon in an dakko yarinyar ita zata karbeta, indai zeyi haka to gara ya barta a hannun Mahaifiyarta shi kuwa yana so ya hada kan Yaransa su tashi tare a gabansa. Duk wannan abun uwarsu taja musu da tayi haquri da yanzu suna tare bashi da tunanin ya zeyi dasu, shawarar daya yanke ita ce ze kira Nuratu tunda ita ta kawo musu Ruqayya ta dawo taci gaba da Aikinta ya yaba da Qoqarinta yasan kuma bazata cutar masa da yara ba saboda ko a lokacin baya duk sanda suke a nan bangaren ita take musu duk wata hidima sun saba da ita. Tsaf ya shirya, yana fesa turare Humaira ta shigo da qaton Try yayi saurin ajiyewa ya kama mata yana cewa "Bakya tsoronsu zube kika hado kaya haka?" "Ba gashi na kawo ba ai ba zasu zube ba" ta fada tana sauke kwanukan qasa ya koma yaci gaba da taje Sajensa ita kuma ta bude Warmer ta shiga zuba masa hadadden Dambun cous cous din da tayi. Ta mudubi ya kalli abimcin yawunsa ya tsinke ga wani qamshi na musamman daya karade dakin take yunwar da yake ji ta qara qarfi ya ajiye Comb dinya dawo kan Carpet din inda ta zuba abincinya tankwashe qafa yana cewa "Gaskiya a bani a baki bazan iya ci da kaina ba" "Da ze yuwu ma base ka tauna da bakinka ba kawai sedai kaji cikin ka ya qoshi amma babu komai Allah ya kaimu Aljanna" ta fada tana kai masa abincin baki. Haka ta ringa feeding nasa kamar wani qaramin yaro yana ci yana sakin murmushin da shikansa be san na menene ba kawai dai yasan dadi har ya masa yawa. Seda ya qoshi sannan ta barshi ta kwashe komai ta fita dasu kafin ta sake dawowa ta tarar dashi yana saka hula ta qarasa gyara masa zamanta tana cewa "Kayi kyau da yawa Allah sa kar wata mace ta kalleka sau biyu idan ka fita" seya ja dogon hancinta yace "Babu wadda zata kallar miki ni, muje ki rakani nasan Anwar na can yana jirana". Haka suka fita ta rakashi har gaban motarsa tana masa Addu'a, se bayanya fita ya tuna da yanaso yayi mata maganar dauko Malikan dukda ta sani amma ya kamata ya sake tuna mata kar ta ganshi da yarinya kawai. Da dare suna kwance yake mata maganar nan tace tare zasuje, daman su Mu'ayyad nata cewa suna so suje gurin Momynsu, bata son masa maganar ne saboda taga duk sanda suka tambayeshi da kansu se ya nuna bacin rai dan haka yayi haquri ya tafi tareda su su ganta "Yaya baze yuwu kace zaka rabasu da Mahaifiyarsu ba Alhalin tana raye, koni dana rasa tawa hat abada wani lokacin nakanji dama ta dawo badan na rasa komai ba sedai kawai dan ita uwa batada madadi" Humairan ta fada a hankali seya sake janta jikinsa sosai ya rungumeta ba tareda yace mata komai ba. Ranar kuwa da tayi daidai da cikar Iman shekara daya bayanya dawo daga Masallaci yace mata su shirya ita da yara zasuje dakko Iman, irin Ihu da murnar da yaran suka ringayi ya sanyaya masa jiki matuqa saboda kiran yau zasuga Momy kawai suke suna tsalle. Tsaf Humairan ta shirya su cikin kyakykyawar shiga Mu'ayyad ya saka shadda irin ta Mahaifinsa ita kuma Bibi ta saka mata Gown kalar Lace din da ta saka a jikinta se suka fito kamar wasu furen fulawa da baza'a iya dauke kai daga kallonsu ba. Seda sukayiwa Hajiya sallama kafin suka kama hanya, kamar yanda ya saba duk lokacin da zeje gidan su Umaiman a wani super Market ya tsaya yayi musu siyayya sosai kafin suka dauki hanya yaran nata surutu suna gayawa Humaira wadanda zata tarar a gidan idan sunje a haka suka qarasa gidan su Umaimah. UMAIMAH Tana kwance a dakinta tana sana'ar ta ta danna waya dan bata aikin fari balle na baqi illa taci tayi wanka ta kwanta tana latsa waya. Tana nan kwance Anty ta shigo tana tambayarta rigunan sanyin Iman da Naziyya ta aiko mata dasu ta nunaww Antyn inda ta ajiyesu ta wuce ta dauka Umaiman ta bita da kallo dan tun jiya taga Anty nata kai komon har hada kayayyakin Iman, ko a jikinta bata nemi jin ba'asin dalilin hada kayan ba dan kusan wata biyu kenan data yaye yarinyar gaba daya ta sallamawa Antyn koda yake daman tsakaninta da ita shan Nono ne wanda shima se taga dama tsakanin Anty da sauran yaran gidan take gararanba har zuwa kan Mama da daga baya ta sauke fushin daya shafi harda Iman din ta rungumi yarinyar ganin cewar Uwarta tayi nisa a lamarin Duniya, duk abinda Anty zatayi mata kuwa karace ita din ce a haqqu datayi mata dan haka taja ta a jikinta sosai ya zamana sun raba hidimarta ita da Anty. Tunda satin ya kama daman Hajiyar Khalil da sukanyo waya jefi jefi da Maman ta kira akan ranar Juma'a ne cikar Malikan shekara daya kuma kamar yanda suka Alqawarta zasu karbeta su hada da sauran yan uwanta a lokacin taji kamar ta cewa Hajiyar suyi haquri su bar musu yarinyar domin tana jinta a ranta ta maye mata gurin Uwarta data rigada ta sallama sedai nauyi da kunyar Hajiyar ya hanata furta hakan suka rabu akan zata sanarda Mahaifinsu Umaimah a ranar kuwa bayan Abban ya dawo ta gaya masa ta ce "Amma da zaka roqar mana Alfarmu su Alhaji su bar mana yarinyar nan kaga mun saba da ita" "Karma ki saka wannan a ranki Malika zasu karbi yarsu su hadata da sauran yan uwanta abu daya dai zan kira Hajiyar da kaina na roqi sassaucin janye mana ragowar yaran da sukayi, badan uwarsu ba kodan kasancewar su din jininmu ne su barsu su ringa zuwa muna ganinsu koda ace ba da kwana ba dan Kwanaki da akayi hutu Nuratu ta sanar mun ta kira Khalil din akan tana so ta dauki yaran suje gurinta yace Aa to sassaucin kadai da zan iya nema kenan ita kuma daman lokaci nake jira na zuba mata ido ne naga ko zata hankaltu tayi nadamar abinda ta aikata ta kuma dauki abinda ya sameta a matsayin darasi amma naga sam babu alamar hakan a tattare da ita, zan dauki mataki me tsauri akanta" Abbaya fada se Maman tayi shiru dan harga Allah ta shaqu da Iman din kuma zata so a bar yarinyar amma ya ta iya haka ta sanarwa da Anty nan suka shiga tattara mata duk wani abu da yake nata a gidan, kafin ranar Juma'ar sun hada mata komai tsaf yaran gidan duk sun shiga Alhinin tafiyar Iman din banda Uwarta da bata san dawar garin ba hidimarta kawai takeyi ba kuma ta damu da tambayar hada kayan da akeyi na menene ba. Misalin qarfe hudu na yamma suka karbi baquncin Khalil da Humaira tareda yaransu. Cikin yanayin jin nauyi, kunya da kuma murnar ganinsu Anty da Maman suka tarbesu a falon Maman dan ko kusa basu kawo cewar da kansa ze zo karbar Iman din ba. Mama ta ringa satar kallon Khalil da yayi wata canzawa da Mamaki. Yayi kyau ya qara cika da girma Alamun nutsuwa da Jin dadi sun bayyana tare dashi kana kallon sa kasan bashida wata damuwa tsayin shekara daya kenan rabon da ta saka shi a idonta tun yana Asibiti dan gara Abba yakan je lokaci lokacin har gidan ya duba shi amma ita ta gaza yin hakan ta kance kunyar Hajiya Aisha ba zata barta iya sake hada ido da ita ba. Anty ta kasa zama har seda ta cika musu gaba da duk nau'in kayan ciye ciye da suke dasu a gidan danma basu san da zuwansu ba. Cikin girma da mutuntawar daya saba yi musu ya gaida Mama da Antyn, Humaira dake zaune a qasa itama ta gaida su Babu yanda basuyi da ita ba akan ta hau kan kujera ta zauna taqi, Mama dai se kallon Dan Baby dake hannunta take yi gashi nan tamkar Balarabe saboda haske tamkar Uwarsa da itama ta canza ta zama babbar Mace. Anty ta miqa hannu ta karbi Aryaan tana cewa "Kawo megidan na gani anya kuwa bazan saki na qarfen ba daman ba awo ba cefane wannan kuwa ko babu komai na kalli farar fata naji dadi". Mu'ayyad ya tura bakin shagwaba dan shi take cewa na qarfen yana kuma jin dadin sunan se ya zura hannu a Aljihu ya ciro dari biyun da Khalil ya bashi kudin Juma'a ya miqawa Antyn yana cewa "To gashi kiyi cefanen". Dariya suka saka gaba daya ganin abinda yayin, Anty ta ci gaba da juya yaron tana yaba girma da wayonsa kamar ba dan wata uku ba Mama dai da Khalil surukuta sukeyi ita dai se murmushi take tana kallon rabon daya rabo Umaimah daga gidan Khalil a hannun Antyn shi kuma nauyinta ne ya hanashi sakewa se yanzu yake jin yayi kuskuren zuwa da kansa, daya sani Khalifa ya turo irin yanayin daya ganta ya tabbatar da har yanzu tana cikin radadin zafin abinda ya faru. Dakyar ya iya tambayar Abba suka sanar masa be dawo daga Kasuwa ba amma duk inda yake yana hanya dan ranar Juma'ar da wuri yake dawowa. Sun zauna kusan Minti sha biyar Anty nata jan Humaira da hira ita dai se murmushi takeyi Khalil kuwa wayarsa yake dannawa Mama kuma tayi shiru tana ta tunani yaran dama sun fice gurin su Momynsu ganin bata dakinta yasa sukayi waje nan suka ci karo da Yasir Autan Anty da yana shigowa ya gansu ya buga tsallen murna ya kwashe su sukayi waje gurin Abokanan sa. "Amma dai a nan zaku bar mana su suyi week end ko? Munata zuba ido anyi hutu kusan sau nawa ba'a kawo su ba" Anty ta sake katse musu zaman shirun da sukayi se yayi yaqe yace "Za'a kawo su in sha Allah yanzun dai basu taho da kaya ba" "Toh ai shikenan Allah ya kaimu toh, Amarya zo muje can kafin a dawo da yar taki wai kitso Sharifa ta tafi kaita tun dazu kinji su shiru" Anty ta sake fada tana miqewa dan su bawa Mama da Khalil din guri tasan ba zasu rasa abinda zasu tattauna ba Humaira tabi bayanta suka fita. A tsakar gida suka ci karo da Umaimah Anty ta kalleta ganin da Hijab a jikinta tace "Ke kuma se ina"? "Kati zan karbo gurin Ilu" ta bata amsa tana kallon Humaira da fuskarta tayi mata kamar ta santa a wani guri amma ta manta ina ne dan haka ta juya ta fice karbo katin. Wata mota ta gani me kyan gaske a qofar gidan, ta matsa jikinta tana kallonta seta bude hanci saboda qamshin da taji yana fitowa daga ciki amkar na Khalil, tsaki tayi ta matsa a ranta tana cewa "Hasashe ne kawai me ze kawo Khalil nan kuma idan yazo ai ita ze nema" ta qarasa Shagon Ilu dake jikin gidan da yake kallon nasu ta karbi katin, fasa komawa gida tayi ta shige gidan Maman Nana. Babu inda take zuwa kullum tana gida idanta samuta fito siyan kati nema take leqawa gidan Maman Nana dukda babu wanda yace karta fita koda yake wa yake ta sabgarta ma balle ya sakata ko ya hanata? A canta shantake suka shiga hirar duniya, ganin biyar tayi yasa ta miqr tana mata sallama dan tasan Abbana dab da dawowa gida yanzu tana fitowa daga gidan Maman Nanan idonta yayi kyakykyawan gani. Khalil ta gani wanda badan sanin da tayi masa ha zata iya cewa me kama dashi ne saboda yanda ya canza yayi qiba, yana tsaye ya budewa yarinyar data gani tareda Anty yanzu qofar mota ta shiga ya ranqwafa ciki yana mata magana tana iya hango tsadaddan murmushin da yake kan fuskarsa. KHALIL Bayan fitar su Anty a hankali Mama ta bude baki tana kallonsa tace "Khalil ina qara baka haquri akan abunda ya faru.." "Haba Mama ni ya kamata na baku haquri na kuma nemi yafiyarku bisa cin fuskar danayi muku na saki yarku a gabanku amma Allah ya sani ba'a son raina ba amma haka Allah ya tsara, ina fatan hakan ya zame mana Alkhairi a rayuwar mu gaba daya" Khalil yayi saurin Katse Maman, kasa sake ce masa komai tayi a ranta tana sake takaicin rasa Miji Kamar Khalil da Umaimah tayi amma tana nan ko a jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta suna gaya mata qaryar ze dawo gareta wanda a yanzu ko Makaho ya shafashi yasan ya samu canjin rayuwa ya samu nutsuwa babu yanda za'ayi yana sane ya sake maida kansa cikin ramin daya fito dakyar. Zaman shirun suka ci gaba dayi, shigowar Sharifa da sauran yaran ya katse musu shirun ta miqa Masa Iman dake ta yiwa yan uwanta dariya tamkar ta sansu. Fuskarta data sha kitso ya tsurawa ido yana sake ganin ainihin kamanninta da Umaimah tamkar an tsaga kara, besan irin kallon da yake mata ba seda yaji Mama tana cewa "Kana mamakin kamanninta da Umaimah ko? Kowa ya ganta se yace kamar har tayi yawa" tana gama fada ta miqe tana sake cewa "Bari nayiwa Saratu magana tasa a fitar da kayan nata ko zaku jira Abban naku ya dawo kafin ku wuce?" Kansa ya shafa yace "Zan samu lokaci in sha Allah na dawo na gaishe shi" "Shikenan to bari nayi mata magana" ta fada ta fice ta barshi da Iman dan sauran yaran suna rakota daman suka juya sabgarsu. Rungume yarinyar yayi a jikinsa yana jin wani yanayi na taso masa. Salman ne ya shiga da Sallama, ya bashi hannu suka gaisa yana tambayarsa karatu da suke gangara dan Jarabawar qarshe sukeyi. Muqullin motar sa ya bashi saboda yace za'a saka kayan Iman ya gaya masa ya fito da kayan Booth din ya shigo dasu sey miqe da yarinyar a Jikinsa ya fito tsakar gidan, yana tsaye yaran suka fita da Akwatunan Iman harda Mota da Kekenta da sauran tarkacen kayan wasan da yake siya ana kawo mata seda suka gama saka kayan tsaf kafin Salmanya dawo masa da Key din, shiya shiga dakin Anty ya kira Humaira suka fito tareda Anty da seda ta sakata ta sake dan dole sukayi hira. Dakin Mama ta koma tayi mata sallama ta bata Leda Babba tana cewa "Gashi babu yawa bamu samu munzo barka ba Allah ya raya yayi Albarka sannan ina fatan zaki qara haquri akan wanda kikeyi sabgar yara se an kai zuciya nesa musamman yanzu kin samu qarin wata Allah ya taya miki ya baki lada" "Amin Mama babu komai in sha Allahu Da ai na kowa ne in sha Allah zanyi iyakar iya wata kuma ina fatan idan da rabon daidaito Allah ya shiga tsakani Mamansu ta dawo muci gaba da zaman mu" Humairan ta fada se Maman ta kasa amsa mata haka ta rakota har inda Khalil din yake jiranta da sauran yaran. 50k ya bawa Mama da Antyn yabi sauran yaran gida da 2k kowanne suka ringa saka masa Albarka suna tsaye tsakar gidan Anty na sake jaddadamasa zancen kawo yaran har ya hada kan iyalansa suka fice sauran yaran suka rakasu. A baya Mu'ayyad da Bibi suka zauna kafin ya zaunar da Iman itama dan se hanqoron shiga takeyi ganin su a ciki kamar ta sansu, da kansa ya budewa Humaira qofar gaba ta shiga ta zauna sannan ya karbi Aryaan daga hannun Salman suka sakeyin Musabaha ya miqa mata shi sannan ya sunkuya yana gyara mata mayafinta daya fito waje yana tsokanarta da cewa "Qannenki sun qara yawa daga hudu kun zama ku biyar" ita kuma ta mayar masa da cewa "Eh naji dai qannen nawa ne kai kuma Babanmu" ya saki murmushi saboda yanda tayi maganar, seda ya kulle mata qofar kafin ya juya zuwa bangarensa kamar ance ya kalli gefe karaf idonsa suka shiga cikin na Umaimah data qame a bakin qofar wani gida tana zare ido kamar wadda ta taka jelar Maciji. Kallonta yayi na second biyu kafin ya dauke idonsa ya shiga motar zuciyarsa na bugawa, Tabbas So ba qarya ba, seda ya kwashi minti biyu yana qoqarin daidaita nutsuwarsa kafin ya iya kunna motar shima dalilin tambayarsa da Humaira takeyi lafiya taga yanayinsa ya canza lokaci daya seya dafa kansa ya kalleta yana yamutsa fuska yace "Kaina ne ya sara" "Sannu kona karbi Driving din?" Ta fada cikin nuna damuwa seya taka motar yana cewa "Dadai ni dake ne kadai amma yanzu na debo gaba dayan Ahalina kice zaki jamu a Babban Titi Nooo" yayi maganar cikin zolaya seta zumburi baki tana cewa "Allah yasa wata rana ka sake cewa ka gaji bazan kuma tuqaka ba" shidai yaci gaba da tuqinsa amma hoton ganin da yayiwa Umaimah ya gaza barin kwakwalwarsa. Kenan bata damu da rabuwarsu ba dan babu alamar hakan a tattare da ita gani yayi ta qara kyau tayi qiba dukda Hijabi ne a jikinta ya tantance hakan koda yake me yasa zeyi tunanin zata damu dan ta rabu dashi ita da taso ta rabashi da duniyar ma gaba daya? Haka suka qarasa gida yayi qoqarin ganin ya kawar da komai daga ransa gudun kar wani ya zargi wani Abu, Humaira kuwa kallonsa kawai takeyi dan taga fitowar Umaiman kuma taga sanda Khalil din ya tsaya yana kallonta dan haka tasan damuwar daya shiga nada nasaba da ganin ta da yayi kuma bata ga laifinsa ha Matarsa ce da suka rayu tsahon shekara bakwai kuma yana sonta Qaddara ta rabasu dole zeji wani abu idan ya sake ganinta. Da suka isa gida ma ganin yana buqatar fili yasa ta barshi ta shiga hidimar yaranta a Daren ta ware kayan Iman din tsaf ta shirya mata su a dakinsu na nan bangaren ta ware wasu ta kaiwa Hajiya aka saka mata a dakinsu na can tunda suma sauran haka kayansu suke, Ruqayya ta dawo dan haka bata samu wani qalubale ba ita take taimaka mata da hidimar Iman din ta bata abinci tayi mata wanka da shirin bacci ta goyata babu bata lokaci kuwa tayi bacci abinta daman Anty ta gaya mata bata farkawar dare indai taci ta qoshi haka kuwa sukayi baccinsu lafiya lau dan a dakinta ta kwana da ita da Aryaan ganin Khalil ya dage akan kan sa na ciwo yasa ta tafi dakinsa ta barshi yayi jinyar famin ciwon da ganin Umaimah yayi masa, washe gari kuwa da kansa ya bita ya lallabata bata ja magana ba dan daman ba fushi tayi ba suka ci gaba da rayuwarsu, Duk yanda ta tsara zata kula da yaran data haifa a cikinta haka take tafiyar da yaran a kullum kuma tana addu'ar ubangiji ya taya mata ya bata ikon kulawa dasu tsakani da Allah ba tareda ta cutar dasu cikin sani ko akasin haka ba. UMAIMAH Seda motar Khalil ta qurewa ganinta kafin ta farka daga suman tsayen da tayi, dakyar take jan numfashi saboda yanda zuciyarta tayi mata nauyi a hankali ta ringa tafiya tana dafa bango gudun karta fadi dan bata gani da kyau harta shiga gida, Mama da Anty na zaune tsakar gidan suna bude ledojin tsarabar da Khalil ya kai musu ta shigo Anty ta miqe ganin tana shirin fadowa kansu ta tareta tana tambayar lafiya? Cikin muryarta data shaqe saboda abinda take ji tace mata "Khalil na gani shida wata mata ya bude mata mota har ya sun kunya yana mata dariya" "Eh Matarsa ce daga nan suka fita ai yazo ya dauki yarsa" Mama ta fada cikin yanayin ko a jikinta se Umaimah ta bita da kallo kamar bata gane meta fada ba aranta tana maimaita kalmar Mataraa data fada, kenan tana Nufin Humaira ce wannan data gansu tare? Kuma ai itace ta gani da Anty se yanzu ta fahimci kallon sanin da tayi mata ashe ita ce. Wasu hawaye masu tsananin zafi suka shiga tsere a fuskarta se kawai ta juya ta shige daki Anty ta saki baki ta bita da kallo tana cewa "Toh kukan me takeyi kuma?" "Na jin dadi mana" Mama ta bata amsa tana miqewa ta shige dakinta. Umaimah kuwa zama tayi kan Gadon dakin tana hawayen da bata san dalilin yinsu ba. Wani radadi zuciyarta take mata kamar ana gasata idonta ya kasa dena ganin Khalil yanayiwa Humaira tsadadden murmushin da ita kadai take samunsa yanda yake kallonta kadai ya isa ya tabbatar maka da cewar soyayyarta ta huda Qashi da tsokarsa babu wata alama a tattare dashi da take nuna damuwa ko wani abu kenan ya manta da ita sannan yana nufin yayanta ma ya rabata dasu kenan duka ya mallakawa Matarsa ya dena sonta ya haqura da ita zeci gaba da rayuwa batareda ba? Tambayoyi ta jefawa kanta da bata da amsarsu haka bata da me bata amsar a kusa da ita A sannu a hankali kwakwalwarta ta fara yarda da tabbacin cewar Khalil yana raye tareda wata Mace bayan ita ta kuma gasgata cewar a yanzun babu igiyar aure a tsakaninsu mafi munin abun ta haihu iddarta ta kammala tuntuni koda ace zasu sake komawa qarqashin inuwar aure dashi se bayan an sake daura musu aure wanda bata zaton iyayenta da a yanzu basu da abinda suka tsana sama da ita zasu yarda da hakan balle aje ga nasa yan uwan da bata matsayinta a gurinsu ba. Dagaske ta rasa Khalil ya zama mallakin wata daban ba ita ba. Zamewa tayi ta kwanta akan Gadon saboda ji da tayi dakin yana juya mata gaba daya a maimakon ta nemi taimakon Allah ya sauqaqa mata abinda take ji a ruhi da gangar jikinta se kawai ta bude baki ta ringa zunduma ihu tamkar ba diyar musulmi ba babu kiran Allah se maimaita Kalmar ta shiga uku ta lalace takeyi. Anty dake tsakar gida tana cigada ayyukanta dan ita ce da girki tana shirin dora abincin dare ta zabura tayi dakin dan ganin abinda ya saka Umaiman irin wannan ihun. Abba ya shigo gidan da Sallama dawowarsa kenan daga Kasuwa yaci burki a bakin qofa yana jiyo ihun Umaiman da muryar Anty dake qoqarin kwantar mata da hankali da nuna mata cewar Addu'a ya kamata ta ringayi ba iface iface ba. Zuciyarsa tayi baqi ta kawo masa wuya, tun bayan Dawowarta gida be yarda sun hadu ido da ido ba saboda gujewa baqin cikin da yake tsintar kansa a ciki duk sanda ya tunata balle ace ya ganta a cikin gidansa. Tun sanda ya fahimci Anty da Maman ne suke hidimar Malika ransa ya qara baci wato Umaimah bataji maganarsa ba amma ya qyaleta kawai domin lokaci yake jira da duniya da kanta zatayi mata karatun da tilas ta fahimceshi yayi niyyar ya zuba mata ido ne yaga iyakar Hankalinta amma Ihun da take masa yanzu a cikin gida ya bata masa rai matuqa ya tunzura zuciyarsa, kasa dauke kai yayi dole ya koma waje, wani saurayi dan maqotansu ya kira yasa ya tsinko masa Bishiyar Dogon Yaro dake qofar gidan ya zuge masa guda uku Saurayin yanata mamakin abinda Abban zeyi dasu ya diba ya koma cikin gidan har sannan Umaimah bata bar ihun da takeyi ba abin baqin ciki daya shiga dakin a qasa ya tarar da ita tana birgima da ihu kamar wadda ta gamu da ciwon hauka, ba tareda bata lokaci ba ya shiga dukanta tamkar an aikoshi Anty batayi gigin shiga tsakani ba tayi gefe da sauri gudun kar ya hada da ita dan irin bacin ran data gani a idonsa tasan ya kai maqura yau kam. Jikinta ya dauki rawa saboda ganin irin dukan da yakeyiwa Umaiman da gushewar tunanin dan lokaci ta sameta saboda yanda dukan ya zo mata a bazata ta dena birgimar ta tsaya kawai kwakwalwarta na qoqarin gane abinda yake faruwa. Wani gigitaccen ihu na gaske ta fasa sanda zafin dukan ya ratsa kwakwalwarta ta shiga neman ceto Abban kuwa be bata dama ba, a kwana ya sakata ya ringayi dukanta iya qarfinsa tamkar ya samu Jaka, tun tana ihu da guje gujen neman taimako harta haqura ta zauna guri daya ya ringa lafta mata bulalu seda duka ukun suka karye a jikinta kafin ya jefar da sauran yana haki ya kalli Anty da ta gama tsurewa a gefe ta gagara ko motsawa agurin da take saboda firgici yace "Ki kawo mun ruwan zafi" ya fice fuu har yana shirin hardewa da babbar rigarsa. Duk budurin da akayi Mama na zaune a falonta ko gezau batayi, ba qaramin dadin abinda Abban yayi taji ba dan ita kanta ta kusa tashi taje ta kwada mata mari seya fansheta yayiwa Umaiman dukan cire raini. Tana ganin wuce warsa ta tashi tabi bayansa da ruwa me sanyin gaske harda Zobo ta dora a Try ta kai masa dan tasan yanada buqatar abinda ze sanyaya masa zuciya yanzu. Da kanta ta tsiyaya masa bayan tayi masa sannu da zuwa, be iya amsawa da baki ba se hannu ya daga mata ta miqa masa Cup cike da ruwa tana cewa "Karbi kasha Alhaji akan me zaka bata ranka a banza akan wadda bata san ciwon kanta ba, Umaimah cefa haukarta ce ta tashi saboda Khalil yazo tareda matarsa ta ganshi cikin nutsuwarsa ba kamar yanda tayi fatan jefa rayuwarsa a cikin garari ba, ai daman duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba tasa ko dumi ba zatayi ba". Tasya shanye ruwanta sake qara masa yasha sannanya shiga sauke ajiyar zuciya a jere a jere tsahon lokaci kafinya bude baki yace "Ina tsoron fushin zuciya ya saka na furtawa Yarinyar nan kalmar da ba zata zama Alkhairi a gareta ba". Cikin kulawa Maman tace "Ka ci gaba da haquri Alhaji, shiyasa kaga nake nesanta kaina daga duk shirginta, banga abinda takeyi ballantana raina ya baci a banza tunda ita bata san daidai, kullum addu'ata Allah ya duba mata yasa ta gane abinda takeyi ba daidai bane tun tana da sauran damar gyarawa". Jigum sukayi suna zaune aka kawo Nepa cikin dashewar murya yace ta kunna masa heater bandaki, ta shiga ta kunna tana fitowa Anty ta shigo da qaton Flask din ruwan zafi da ka ganta kasan a rikice take. Ita ta shiga ta hada masa ruwan kafin ta fito Maman ta koma dakinta Abba ya shiga wanka ita kuma ta koma kan aikinta tanayi har sannan zuciyarta bata bar tsinkewa ba. Ita dai wannan jaraba ta Umaimah daga tayi sauqi se wata ta bullo tana Addu'a Allah ya fito mata da Miji nan kusa ta daga su samu sa'ida dan idan taci gaba da zama itama seta dora mata hawan Jinin data sakawa uwarta da ubanta sunyi Anko, ina dalili wai gashi ita kamar Afi bata iya dauke kai taga abu ya samu Umaimar, sonta takeyi tsakani da Allah gashi babu abinda son yake tsinana mata se wahala. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 77 UMAIMAH Daren Ranar bata iya bacci ba seda Anty ta kira wani me Chemist ya dubata yayi mata allurar rage zugi tasha magani sannan, washe gari da safe ta tashi da wani sabon tashin hankalin. Qarfe goma gaba daya yan gidan manya da yara suka hallara bisa umarnin kiran da Abban yayi musu tun daren jiya. Bata san kiran me ya musu ba tadai ga sun shige can bangarensa kuma sun dade suna magana dan har se gurin sha biyu sannan Salman yazo yayi kiranta. Dakyar take tafiya saboda yanda jikinta yayi tsami, badan kar ta sake yin wani laifin ba daman da bazataje kiran ba. Irin yanda gaba daya suka dauke kai tamkar babu wanda yasan da tsiron halittarta a gurin ya mata ciwo daman tunda ta dawo gidan in ka cire Anty babu me shiga sabgarta Mama kuwa in zasu hadu sau dubu ta gaidata bazata amsa ba daman tun randa tadawo tayi mata iyaka da shiga dakinta tace bata buqatar ganinta a ciki. Tana zama kamar wata Mujiya a cikinsu suka fara darewa daya da daya duk suka fice daga dakin kowanne yazo giftata seya bugamata tsaki sannan su harareta, seda suka fice gaba daya kafin Mama ta kalleta rai babu dadi tace "Matso ciki". Gaba kadan ta muskuta amma bata yarda tayi kusa dasu da yawa ba cikin rawar Murya ta shiga gaishe su ta kalli Abba dake Kishingide da gani bashida lafiya, babu wanda ya amsa gaisuwar Tata har Antyn yau tana daga gefe idonta yayi jajir alamar Kuka tayi se Umaimah ta sunkuyar da kanta qasa, muryar Abban taji cikin dakiya yana cewa "Ina so ku zama shaida tsakanina da Umaimah zan kafa mata sharudda da har idan tana neman zaman lafiya a cikin gidan nan dole ta bisu. Ban yarda Umaimah ta taka ko nan da qofar gida ba tareda izinina ba haka zalika banyarda wani yazo gidannan gurinta ba, sannan zata bani wayarta" Abban ya fada yana kallon Umaimah data sunkuyar da kanta qasa tana hawaye, takaicin yanda gaba daya kowa ya tsaneta ya kamata, babu wanda ya dubi halin da ta tsinci kanta a ciki ita ta rasa Khalil a maimakon su tausaya mata suyi qoqarin kwato mata haqqinta se suka bige da tsanarta kamar ta aikata musu wani mugun laifi. Tana jin Abban ya gama maganarsa, zancen ba zata fita ba ko ba za'a zo gunta ba be dameta ba kamar na karbe mata waya. Idan ya rabata da wayarta ta ina zata samu damar magana da Khalil harsu daidaita ta koma dakinta? Tsawar da Mama ta daka mata ceta sakata miqewa da sauri dan dakko wayar, tana hawaye kamar yarinya ta bashi wayar tata ya karba a gabanta ya zare layin ya ballashi biyu kafin ya sake kallonta yace "Abu na gaba daga yau duk wani aiki na cikin gidan nan ya dawo hannunki, ina nufin daga kan shara girki wanke wanke da duk wasu sauran ayyukan tsakar gida ke zaki cigaba da yinsu har wankin kayanku idan kuna da buqata ku bata tayi muku dan ba zan ringa ciyar da ke a banza ba tunda kinqi zaman aure kiyi na Farilla ki samu lada zakiyi Mustahabi anan. Idan har na kamaki da laifin saba daya daga cikin sharuddan nan ina me tabbatar miki da cewar sekin gane kuskurenki tabbas". Da sauri ta daga kai ta kalli Abban bakinta na rawa alamar son yin magana amma mugun kallon da Mama ta aika mata dashi yasa ta kasa cewa komai ta maida kanta qasa hawaye suka sake balle mata kamar famfo. "Rayuwar da kika zabarwa kanki kenan zaman gida ba gaki ga gidannan se kici uwar da kika ajiye a ciki. Kinsan dai ba zamu zauna muna goga kafada dake a cikin gidan nan ba mu dafa mu baki kici ki ajiye kwano mu share guri ki zauna na iya lokacin da aka miki ma Allah ya bamu lada dan haka dolenki kiyi aiki in har kina son zaman lafiya damu koda yake ma bata bakina nakeyi saboda na manta da kin rigada kin zama yar kanki kiyi duk yanda yayi miki Umaimah babu wanda zesake tilasta ki akan kiyi daidai amma kin sani matuqar kika qi ji ba zaki qi gani ba kuma kinji abinda Mahaifinki duk ya fada se ki zaba zama lafiya kibi abinda yace ko ki fara neman wani gidan uban da zakije kici gaba da yanda kika ga dama" Mama ta fada cikin fushi ita dai Umaimah kanta na qasa in banda hawaye babu abinda takeyi. Shiru sukayi na kusan Minti goma babu wanda ya sake cewa komai se Abban ya yunqura ze tashi Mama da Antyn suka miqe a tare suma dan taimaka masa ganin Anty tafi kusa dashi yasa Maman ta tsaya ita kuma ta kamashi suka shige cikin dakin "Idan baqin cikin ki ya kashe shi se ki zuba ruwa a qasa kisha" Mama ta sake cewa kafin ta juya ta fice daga falon ta barta tana kuka da tunanin ita me tayi kuma da za'ace baqin cikinta ze kashe Abba? Haka taja qafafunta da suka sake yin tsami saboda zama ta fita daga, a bakin qofa sukaci karo da Sharifa zata shiga da Flask qarami a hannunta ta kalli Umaiman tayi tsaki qasa qasa tace "Wlh mutum ya kashe mana Uba ba yarda zamuyi ba se munyi shari'a dashi" tayi gaba a hasale Umaiman ta fincikota baya tareda watsa mata maridukda ba wai taji abinda ta fada bane saboda ta sauke fushin su da take cike dashi tace "Dan uwarki ni sa'arkice da zaki mun qunquni?" Kuka Sharifan ta fasa, Nuratu data taho da Kwanuka tayi saurin direwa a qasa ta fincike hannun Umaiman data shaqe Sharifan tana cewa "Karki sake gigin taba lafiyar wani daga cikinsu" "Ke kuma ina ruwanki ai ban saka ki a ciki ba balle ki shiga" ta sake zaburowa Nuratun seta daga mata hannu tace "Karki kuskura kice zaki zageni dan nima kinsan ba sa'arki bace ba, kuma iskancin da kika sabayi a baya muna daga miki qafa yanzu kinyi kadan wlh duk wanda kika nemi ki taka se ya mayar miki da raddi dan haka ki kama tsumman rayuwarki kija sauran mutunchin daya rage miki, mtsww" taja tsaki ta dauki kwanon data ajiye tayi cikin falon Sharifa ta faki idon Umaimah tayi mata gwalo kafin tabi bayan Nuratu da sauri. Kamar yar yarinya haka ta wuce dakin Mama tana kuka da hawaye shabe shabe zata shiga ta tuna da Gargadin data mata dan haka ta coge daga bakin qofa cikin kuka ta kalli Maman da suke magana da Anty Hafsa da Maman Asad tace "Wlh Mama kiyi mun tsakani da Nuratu karta sake shiga shirgina akan me yarinya zata mun rashin kunya na hukuntata sannan tazo ta bada ni a gabanta ta gaya mun magana wlh karta sake idan ba haka ba..." "Idan ba haka ba me Umaimah?" Mama ta dakatar da ita kafin taci gaba da cewa "Ke har kina da kunya ma da zakiji haushi dan wani ya miki fitsara? Yanzu maganar da kika zo kina mun a sama kamar yarki ki ai ladabi da Biyayya ne ya jawo haka ko to kici gaba karki fasa" Seta juya tayi dakinta tana ci gaba da kuka haushin kanta ya kamata data kaiwa Mama qarar ma bayan tasan ba goyon bayanta zatayi ba. Yanzu zaman nan da taga sunyi ma Allah kadai yasan abinda suke fada akanta ita dai Allah na kallo duk Wanda yaci namanta ta barshi dashi. Kwanciya tayi tana ci gaba kuka baqin cikin ganin da tayiwa Khalil jiya naci gaba sa nuqurqusarta gashi Abba ya kwace mata waya abinda ta qudura yau zata bawa Yasir kudi ya siyo mata sabon Layi tunda yayi blocking wanda yasanta dashi gashi yanzu babu wayar ba ta san yanda zatayi ba kuma tasan a cikin gidan babu me bata tashi wayar. Tana tsaka da Tunanin Sharifa ta daga labule ba tareda ta shiga ba baki a tunzure tace mata "Kizo inji Mama kuma tace karki bata mata lokaci" "Wlh se naci uwarki idan na riqeki zaki san ni kikewa fitsara shegiya sa a haihuwar Kaji nayi Jika dake ko Salman wanki na biyu na girmeshi ballantana ke qaramar mara mutunchi" Umaiman ta fada tana miqewa ita dai tayi gaba abinta saboda son ta qara bata rai harda daga murya tana waqa "Ruwa yaci garin maqiya ashe dai mune da guri na kwana se inga tsiya". Kwafa Umaimah tayi a ranta tana ayyana zasu gamu ne. Seda ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da tayi luhu luhu gefen idonta da dukan jiya ya sama ya tashi dukda maganin da me chemist ya bata ta shafa. A qofar Kitchen ta tarar da Maman ta qarasa gurin ta tsaya Maman ta nuna mata Kayan Miya dake ajiye a qasa tace "Gashi nan ki debi wanda ze isa ragowar kisaka a Fridzer akwai Nama a ciki ki dauki qulli uku Jollop din shinkafa zakiyi lokaci ya qure bare ayi me Miya". Galala ta saki baki tana kallon Maman da kuma kayan Miyar da ta nuna mata ita kuwa bata ma sake kallonta ba tana gama fada mata abubuwan da zatayi ta juya ta bar gurin ta koma dakinta suka ci gaba da tattauna abinda ya dame su ita da yayanta. Umaimah kuwa tafi qarfin minti goma a tsaye tana ayyana wai da gaske ake ita zata ringa girki a gidan? Girkin da ko zamanin yammatanci idan da abinda ta tsana ace tayi shine girki balle yanzu data qara sanin dadin jikinta komai tana daga kwance ake mata shine za'a ce ta dora tukunyar Abincin kusan mutum Ashirin gaskiya ba zata iya ba. Ganin tsayuwar da takeyi ba zata bata mafita ba yasa taja qafafunta ta wuce dakin Anty danta gaya mata ita fa ba zata iya ba gara ma a san me dafa abincin tun wuri. Tareda Fatima qanwarta ta tarar dasu bata san sanda tazo ba, qerere tayi musu akai ba tareda ta gaida Fatiman ba saboda a ganinta Sa'ar Nuratu ce ba wani girmarta tayi da yawa ba da zata gaisheta. Anty ta daga kai ta kalleta ranta babu dadi tace "Ya akayi?" "Mama ce tace wai naje na dora girki ni kuma gaskiya banida lafiya bazan iya ba" ta bata amsa kafin Antyn tayi magana qanwarta ta rigata tace "Ai se kije ki gayawa Maman data sakaki ko dan saboda itace marainiyar wayonki zakizo ki fada mata?" "Ya haka Fatima?" Anty ta tareta kafin ta kalli Umaimah cikin yanayin qosawa da Halinta tace "Ba girki na bane kinga bani da damar cewa karkiyi, kije ki gayawa Maman baki da lafiya zuwa kiji sauqi seki karbi aikin" bata ko tsaya taji me zata kuma fada ba taja fuu tayi waje tana jin Fatiman na cewa "Wlh Anty ke kika bawa yar iskar yarinyar nan dama take taka ki a gidan nan, kin gama shan wahalarta tun tana yar mitsitsiya ta tafi yanzu ta kuma dawowa zata ci gaba da Addaba miki tun wuri idan zaki tashi ki kwatarwa kanki yanci kiyi" bataji Me Antyn tace ba tayi kwafa a fili tace "Shegiya me suffar munafukai shiyasa aka sakoki saboda halinki ai" "Ina fata da kanki kike" taji muryar Nuratu a bayanta ta galla mata harara amma batace komai ba. Kitchen din ta koma dan dai ko hauka take bata isa tajewa Mama da raini a wannan gabar da suke ba. Ta shiga ta duba Gas ta kunna taga da akwai tayi hamdala a ranta, tsabar dorawa kai Jidali ga Gas Allah ya rufa musu Asiri be hanasu kudin Refilling ba amma a ringa kunna itace a gidan. Store ta shiga ta dakko Industrial Gas dinsu ta hada dan tukunyar ba zata hau kan wancan ba Haka ta debi kayan miyar diban wulaqanci ba tareda ta wanke sauran ba ta zuba a Freezer yanda Maman tace ta barsu a gun ta hau aikinta. Ita kanta data gama dafa abincin seda gabanta ya fadi kan tunanin abinda ze biyo baya amma haka ta daure ta juye shinkafar a babbar kular da ake zuba abinci fara tas da ita tun a ido idan ka kalleta babu sha'awa ta debi tata a Qaramin Flask ta qara mai a ciki dan bata saka yanda ze wadata ba ta samu leda ta kwashe musu rabin Yajin dake cikin Roba ta qulle tayi dakinta ko zuwa tace musu ta gama batayi ba. Kukan yunwar da qananan yaransu Nuratun suka fara ya sakata zuwa ta duba abincin, ta kalli Kitchen din da yayi kaca kaca kamar anyi gasar girki a ciki, kwanukan data bata duk ta barsu a nan ga ledar Maggi ta watsar hatta da ledar data cire Nama nan cikin kitchen din ta yar dasu, kada kai Nuratu tayi taqarasa kan kular ta bude "Kan bala'i" ta fada a fili tana bin shinkafar da kallo se kace a gidan prison ga qamshin kayan Miya alamar basu soyuwa yana tashi seta dakko cokali ta debi kadan ta kai bakinta bata iya taunawa ba ta furzar da ita saboda Azababben Yajin daya ratsa bakinta wato duk fato faton Jajjagen data gani a ciki zallar Attaruhu ne kenan da alama kwano dayan ta juye duka. Plate ta dauka bayan data sha ruwa ta zuba shinkafar ta fita, a gaban Mama dake kan Sallaya tunda ta idar da Sallar Azahar ta ajiye ta kalli abincinta kalleta se tace "Abincin ne ta gama". Shiru Mama tayi tana bin shinkafar da kallo ranta na baci, na farko Umaiman ta sani basa saka jajjage a abinci indai Abba zeci sedai a markada kayan miyan dakyau ko babu wuta se an kai Inji sannan wannan fari fat din da shinkafar tayi ina laifinta zuba Kori tunda bataji zata saka wadataccen kayan hadi da ze canza mata kala ba" "To me zanyi da ita da kika ajiye mun se ku zuba kuci Abbanku dai nasan ba zeci wannan abun ba bari naje na tafasa masa ko Taliya ce tunda inada sauran Miya" Mamanta fada tana miqewa, tsakaninta da Umaimah dai sedai tace Allah ya shiryeta dan ba zata mata baki ba iya bacin ran da take sakata ma Allah ya yafe mata. "Mama mi dandana kiji ban sani ba ko bakina ne beji daidai ba" Nuratun ta sake fada se Maman ta dakata ta debi lokaci daya ta kai bakinta, dakyar ta tauna ta hadiye lokaci daya idonta yayi jajir saboda bacin rai ta kalli Nuratu tace "Dakko mun Kular Abincin". Salman daya shigo ta cewa ya kama mata suka kaiwa Maman ta bude ta kalli uwar Shinkafar data dafa ta zarce awon Abincin da suke sakawa koda ace duk yaran gidan da iyalansu suna nan ga girkin babu kai bare qafa, Babu mai a ciki yaji kamar yayi magana sannan bata tsammanin ta saka Maggi salam yanda kasan girkin Asibiti na masu Hawan Jini ko ciwon Sugar. "Kirawo mun ita" Mamanta fada cikin tsananin bacin rai, se Anty Amina tayi saurin cewa "Dan girman Allah Mama ki kyaleta, ta rigada tayi abinda take so zuwan ta nan babu abinda ze canza illah ya qara miki bacin rai da damuwa shiyasa nace ki bari muyi girkin amma yanzun ma Kiyi haquri bari na tashi na dora ko Taliya ce aci ki barta dan Allah". Badan Maman taso ba ta barsu suka fita su ukun suka fara kiciniyar dora sabon girki, Nuratu ta gyaro Kitchen din ta fito da kwanuka ta taresu gurin wanke wanke su kuma suka hura wuta suka dora Sanwa suna aikinsu suna yan hirarraki dan basu bari Abinda Umaimah tayi ya bata musu rai ba, nan da nan suka gama tsaf suka raba kowa aka saka masa Nasa, Maman Asadta kaiwa Anty nata daki suka gaisa cikin mutuntawa da Fatiman dake ta zubawa yar uwarta qorafi akan Umaimah suka sallami duk sauran yaran kafin suka saka nasu a babban Try sukaci. Bayan sun gama Nuratu ta hado kan ragowar kwanukan zata wanke Mama ta dakatar da ita. Da kanta ta wuce dakin Umaimah, tana kwance daidai a Gado cikinta na juya mata saboda yajin data nada gana abinci ga wanda ta qara dan ta samu abincin ya ciwu mata Mama ta shiga da Sallama ta tsaya akanta tace "Tashi kije ki wanke kwanukan da aka bata". Bata musa ba ta biyo bayan Maman ta kalli uban tulin kwanukan a bakin famfo ga wata babbar tukunya bayan wadda tayi girki da ita ta tabe baki ta zauna tana shafa kwanukan kamar me wasa, tun ana dab da kiran La'asar ta fara ba ita ta gama wanke wanken ba se ana Haramar shiga Magrba shima ganin Laqai laqai din nata na mafita bace yasa ta ware ta shigayi tana hawaye tsabar wulaqanci tanayi ana qaro mata wasu seda ta Zagi Salman daya shigo da kwanuka daga dakinsa wasu ma da gani sunfi Sati ba'a wanke ba dan har wari suke ko a jikinsa ya ajiye mata aiko ta ware su gefe ta rantse ba zata wanke ba. Duk tana zaune yayyenta kowacce tayi Harama ta tafi gidanta. Bayan ta gama dakyar ta tashi daga gurin ta bar kwanukan. Seda ta watsa ruwan Zafi ta gasa jikinta dan an kawo wuta kafin ta iya yin Sallar La'asar da Magriba tana shirin aje haqarqarinta ta huce gajiyar girki da Wanke wanke Sharifa ta sake shiga fuskarta a washe da alama tana jin dadin aiken zuwa kiran Umaiman tace "Mama tace ki fito ki dora Tuwan dare" "Na rantse da Allah se naci kutumar ubanki idan na riqeki" ta fada cikin tsananin fushi tana tashi zaune muryar Abba ta jiyo daga waje yana cewa "Gani a kusa fito kici uban nata kuma karki fito kiyi abinda tace kinji". Kuka daya riga ya zema mata jiki ta fasa amma bame qara irin na jiya ba, jikinta kamar ana sarata haka take ji bata warke daga jinyar dukan data ci jiyan ba ga Azabar aiki an tasota a gaba. Harta sauke tuwon tana kuka, Miyar dai yanzu ta saka musu maggi dukda bata dan dana taji yanda yayi ba gurin kadin ne daman ita hannunta baya yauqi dan haka kubewar ta tsinke kamar Romo, ta Jibge Tuwon a Kula gaba daya ba tareda ta Malmala ba danma na Semovita ne amma dukda haka jikinta ya gaya mata gurin tuqin tana gamawa ta tsallake komai a inda yake ta wuce daki harda kwanukan data wanke tun dazun bata kau dasu ba. Seda ta shiga dakin Mama dake lura da duk abinda takeyi ta fito. Ta bude tukunyar Miyar ta dandana, kai kawai ta girgiza ta maidata kan wuta ta qara abinda ya kamata ta kuma daureta sannan ta sauke ta shiga rabon tuwon dan Goma ake nema a lokacin daman badan Abba daya ce setayi girkin ba batayi niyar sake jira ta kwashi takaicin Umaimah ba da tuni ta gama girkinta. Guraren sha daya tuni tayi nisa a bacci dan tana shiga dakin ta kife tana kukan takaici a haka baccin ya kwasheta kiran sunanta taji anayi tareda bubbuga qafarta ta bude ido dakyar dan bata da Nauyin bacci taga Ummu-Salma tsaye, seda ta tashi zaune da kyar kafin Ummu-Salman tace "Anty Umaimah kije inji Abba" "Inje kuma Me zanyi masa?" Umaiman ta fada tamkar zata fasa kuka wannan wane kalar bala'ine? Ita dai Ummu-Salma na tsaye a gefe, bata dade da shigowa gidan ba ta taho daga makaranta Dutse take FUD tana Final Semester dinta Motarsu ta lalace se goma ta iso tana shirin kwanciya Abban ya ce ta kirawo masa Umaiman. Seda ta gama qunquninta da qananun hawaye kafin ta miqe tana layi ta fita, tsoronta karya sake mata irin dukan jiya da babu inda zata wlh haka ta isa falon Abban suna zaune tareda Mama da Anty ga Kular abincin ranar da tayi a gabansa tana kallon fuskarsa gabanta ya fadi saboda fushin data gani akanta wai shi da Bashi da lafiya dan Allah baze sararawa zuciyarsa haka ya dena fushi ba? Qasa ta samu ta rabe idonta har sannan yana yajin bacci Abban ya fara magana cikin fada yana cewa "Wato saboda ki nuna ke bakya ji duk kuma abinda aka ce kiyi sekin bata wa mutane rai shiyasa kikayi haka ko? To bari kiji daga yau kamar yanda na fada miki zan sake jaddadawa aikin gidan nan kaf ya rataya a wuyanki kuma Tilas kiyishi akan lokaci sannan a mutunce yanda kikaga iyayenki sunayi. Karki kuskura qarfe bakwai tayi baki gama abin karyawa ba a ranakun makaranta sannan duk rintse karki wuce biyu ba tareda kin sauke na rana ba haka na dare kin sani kafin na dawo daga Sallar Isha'i an ajiye mun abinci. Sannan maganar wanke wanke da shara bana so na sake maimaita miki daga yanzu kinsan yanda akeyinsu Kwanukan da kika ajiye tun Yamma kuma suna nan suna jiranki ki gyara su yau kin samu yan uwanki sun rage miki aiki gobe basa nan ke zakiyi komai kuma ki yarda kiyi wani abu da ba haka ya kamata ba zamu gauraya a cikin gidan nan maganar wannan abincin kuma( ya nuna kular gabansa yace) daga yau har zuwa sanda ze qare shine abincinki a cikin gidan nan Umaimah koda ace zeyi tsutsa Wallahi se ya qare zan ci gaba da baki abinci a cikin gidan nan idan kuma kika ci wani abu nawa ba tareda umarnina ba Allah ya isa" A firgice suka kalleshi gaba dayansu Anty tayi saurin cewa "Haba Alhaji me yayi zafi zakayi mata Allah ya isa akan Abinci?" "Sharadi na bata idan kuma idan har ta qi bi na maimaita Ban yafe ba" ya sake fada cikin tabbatarwa se aka rasa wadda zata sake magana a cikinsu se Umaimah data rushe da sabon kukan tashin hankali dan lamarin kam ya girmama ya zarce tunaninsu, Abba kuwa ko a jikinsa yaci gaba da cewa "Sannan komai ruwa komai Iska da Itace zakiyi girki ban yarda ki sake kunna mun Gas a gida ba tunda bada kudinki na siya ba wanda kikayi amfani dashi yauma se kin biyani". Anty da Mama dai sun rasa ta cewa Umaimah ko kallonsu takeyi a qoqarinta nason su roqa mata sassauci akan wannan lamari ina zata kai wannan shinkafa da ta ranar ma dakyar ta iyaci muguntarta ta qare akanta kenan ai wlh gara yace ta biyashi kudin shinkafar kawai da wannan tsatstsauran hukunci ita zancen karta kuma ci masa abinci ma be dameta ba tana da yan kudadenta zata iya ciyar da kanta na tsahon lokacin da yace amma zancen tayi ta cin shinkafa ai bema taso ba. Ganin Abban ya miqe Alamar zeje ya kwanta kuma har sannan Anty da Mama basu roqa mata sassauci ba yasa ta zabura cikin kuka me tsanani tace "Dan girman Allah Abba kayi haquri wlh bazan iya ci ba na yarda ayi lissafi zan biyq duk kudin amma ka barni na fita dashi na bawa Almajirai" s Abban ya dakata ya juya ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Wato saboda su basu da uwa da uba a kusa shine zaki basu abinda kika kasa ci ko? To ban yarda ba kuma ban janye maganata ba" daga haka ya shige cikin dakinsa ya barsu. Anty tayi tsaki qasa qasa ta miqe ta fice daga falon Mama ta bita da kallo a ranta tana ayyana idan ba'ayi wasa ba Umaimah na shirin rusa zaman lafiyar da sukeyi a cikin gidan dab tun a daren jiya ta lura da Anty ta kai maqura da Al'amuran Umaiman dan a daren jiya da Abban ya yanke jiki ya fadi bayan ya fito daga wanka Allah ya rufa Asiri Antyn na tsaye ta kai masa ruwan shayi ita ta tareshi tana kuka take cewa Maman "Gaskiya kija mata kunne ta dena dagawa Alhaji hankali haka dan idan ya mutu bata da Asara ke kanki kukanki kadan ne dan duka yayanki kin aurar kuma suna da Madafa nice me qananan yara" tun a daren Jiyan maganar take nuqurqusarta amma ta shanye ko su Nuratu bata gayawa ba ta kuma tabbatar dalilin da ya saka dazu har Sharifa take sake maimaitawa Umaiman cewar karta kashe musu uba kenan qila ita Antyn tayi zancen da yayanta. Gajiya da kukan da Umaiman takeyi ya saka Maman miqewa ita ma se ta zabura ta bita har suka je bakin qofar Maman bata dena gunjin kukan ba ganin tana shirin shigewa daki ta barta yasa cikin kuka tace "Dan Allah Mama dan darajar Manzon Allah kisa baki Abba ya haqura na bawa Almajirai abincin wlh bazan iya ci ba ni na yarda kar a bani abinci har tsahon lokacin daya kamata na cinye wannan din". Yanda take kukan da magiya abin Da da Mahaifi se zuciyar Maman ta kamu da tausayinta dan haka cikin sanyi tace mata "Ki samu Robobi ki juye ki saka a Freezer idan ta kitchen din bata dauke ba ki kawo nan ki saka a Fridge dare yayi yanzu da Safe maga yanda za'ayi" daga haka ta shige daki ta barta babu yanda ta iya ta koma ta dakko Kular abincin tayi yanda Maman tace dan tasan idan ma ta barshi ya lalace qarin laifi ne a gurinta. Seda ta gama Adana abincin tas ta kwashe kwanukan wanke wanken data bari bakin famfo ta shigar dasu kitchen kafin ta koma daki tana ci gaba da kuka, daren bata iya runtsawa ba tunanin yanda zata cinye shinkafar nan safe rana dare harta qare takeyi idan Abban be haqura ba seda Asuba ta gabato bacci ya fara fizgarta, motsin shigowar Abba dasu Salman daga Masallaci ya farkar da ita kamar wadda aka koro fit ta fice daga dakin ta tsaya gaban Abban tana muzurai so takeyi ta sake kafa masa magiya amma yanda taga fuskarsa a daure ya hanata iya bude baki tace masa komai se hawaye suka fara mata tsere Abba kuwa yayi wucewarsa ciki ba tareda yabi ta kanta ba indai juninta rashin ji yana da hanyoyin dafata cikin ruwan sanyi har tayi laushi kuwa. Ciki ta koma tana sharar kwalla tayi Alwala tayi sallah, harta kishingida tana ci gaba da share Hawayen ta tuna da zancen girke seta fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa musamman data tuna itace zata hura kai wannan bala'i da me yayi kama? Sanda tana gidanta iyanzu tana kan Royal Bed cikin Turkish Duvet ga sanyin Ac da qamshin freshner suna ratsata, tana kwance Ruqayya zata shigo mata da abin kari har kan gado ta shiga Jacuzzi tayo wanka taci a yangance ta sake kwanciya amma yanzu Murhune yake jiranta da Itace kai Allah ka kawo mata dauki. Kuka tasha bana wasa ba kafin ta lallabi kanta ta fita dan zaman ba amfani ze mata ba bandama ta sake ja wa kanta wata shiga ukun. A qofar falon Mama ta durqusa ta gaisheta ta daga mata kai kawai a hakan ma taji dadi dan tunda ta dawo Maman bata taba amsa gaisuwarta ba, murya na rawa tace "Me za'a dafa Mama?" "Kunun tsamiya da Alala, wake yana nan an jiqa seki wanki ki bawa Yasir ya kai markade shima qullin kunun yana nan a Kitchen idan kinga dama ki bata ke zakiyi taci harsu qare" Maman ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba harta miqe kuma ta koma murya na rawa tace "Mama kinsan idan na dama kunu tsinkewa yakeyi, sedai na dafa Abba kuma baya so a dafa". Shiru Maman tayi kamar ba zata ce mata komai ba se kuma ta numfasa tace "Idan ruwan ya tafasa kizo ki gaya ki debi kwai ki dafa a saka a cikin Alalan" daga haka taci gaba da jan carbinta Umaimah ta ja qafafunta ta wuce Kitchen din. Waken ta fara dubawa ta sauke ajiyar zuciya ganin gyararrene har ya juqu ma dan haka ta wanke shi ta dubo Attaruhu da Albasa ta zuba cikin takatsan tsan, sedata hada markadan tsaf kafin ta wuce qofar dakin Anty ta kwankwasa dan babu wanda ya fito a yaran Lahadi ce kuma an musu hutun Tahfiz ga garin yanayin sanyi ya fara shigowa tasan suna nade a bargo se ita da uwarta bata sonta ce take gararanba a tsakar gida da farar safiya. Tafi Minti biyar tana bugu kafin Antyn ta bude fuska babu yabo babu fallasa tana kallonta, kamar karta gaisheta saboda qin roqar mata da Abba da batayi ba jiya amma ta dake tace mata ina kwana. "Mama ce tace Yasir yazo ya kai markaden Alala" ta fada a cukule itama Antyn murya babu walwala tace "Yasir ya tashi da Zazzabi sedai ko Sharifa dan Firdausi ma tabi Fatima jiya". Jin cewar se Sharifa yasa ta juya ba tareda ta cewa Antyn komai ba dan indai yar iskar yarinyar nan ce qarshe seta jawo mata wani laifin ace bata gama da wuri ba sawunta a likafa ta wuce ta kunna wuta danma itacen busashshene tana yi tana hawaye wai ita Umaimah ce ta sake dawowa girkin itace? Seda ta hada wutar ta dora ruwan kunu kafin ta leqa waje ta samo Almajiri ya kai mata markaden a ranta tana Mamakin duk Almajiran da suke musu hidima a gidan suna ina tunda satin ya kama ta dena ganinsu ko saboda an shirya maida ita boyi boyi yasa aka sallamesu. Ta kalli tsakar gidan ta tabbatar kuma ita din ce dai me sharewa duk dan saboda a jance zancen cin shinkafa ta tattara kwanukan da aka fito dasu na wanke wanke a gefe ta hau shara, kafin ta gama bayanta ya riqe dakyar ta iya miqewa saboda Azabar ciwon daya dauka ta wuce dakin Mama tana kuka kamar yarinya dan ruwan ya tafasa Mama ta kalleta kawai bata ce komai ba, ganin Almajirin ya kawo markaden ta kama hada Alalan tana yi tana diga musu Hawayen daya kasa tsayar mata a ciki Mama dai ta dama kununta tafi ki mutu bata ce mata ba se sanann Anty ta fito suka gaisa ta kawo Flask din da ake saka musu Kunun Maman ta zubawa kowa nasa ta koma dakinta. Umaimah na zaune tana jiran Alalal ta dafu tana aikin kuka kamar matar Mamaci har yayi ta kwashe ta hada kwanukan ta hau wanke wanke. Tana kallo kowa ya debi abin karinsa yaci kamar kwayar idonta zata fita saboda kuka yanzu duk ta gama wahalar nan ba zataci ba kenan ake nufi haka ta wuce daki ta kwanta dakyar saboda ciwon jiki tana kuka data ci shinkafar nan ta gwammace yunwa ta kasheta kawai kowa ma ya huta tunda an tsaneta. Sha biyun rana Mama ta kwala mata kira, ta yunqura dakyar ta fita jikinta kamar wadda ta fado daga kan bishiya saboda ciwo ta tsaya tana kallon Zogalen dake jibge a qasa ba'a tsinke shi ba ta kalli Mama dake cewa "Gashi nan Dambu zakiyi tsakin kwano biyu zaki auna dan za'a kai nan baya gidan Malam Bala anyi Rasuwa dazu ga Madambaci nan nasa a aro na gidan su Harira shi babbane sosai in kika hada da wannan zaki fi sauri". "Dambu" ta maimaita tamkar bata san kalmar ba, ta waiwaya jin Yaro yayi sallama da wani uban rafkeken madambaci ya ajiye take ta tuno da zuwansu gidan Qawarta Abu Maman Nihal a irinsa suka tarar da ita tana dambu shikenan ta shiga ukun ta ta lalace. Cikin kuka tace "Wlh yunwa nakeji Mama bazan iya aikin dambu yanzu ba" "Ga shinkafarki can ai ki diba ki dumama kici kuma ki hanzarta ki dora da wuri dan Abbanku yana gida kin san kuma Azahar nayi ze nemi Abinci" Maman ta bata amsa cikin ko in kula kafin ta zura Hijabin dake hannunta tana cewa "Idan kin gama bamu dawowa ba ga Kwano nan(ta nuna mata wata fanteka) indai kinyi awon daidai ragowar ze cika wannan bayan ki debar mana na gida se bawa Ko Salman ne ya miqa gidan rasuwar se Mundawo" tana gama fada tayi gaba sega Anty ta fito da fitsararriyar yarta inji Umaimah a bayanta da alama tare zasu tafi suka rankaya suka barta a tsaye ta rasa abinyi se hawaye takeyi.*HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 77 UMAIMAH Daren Ranar bata iya bacci ba seda Anty ta kira wani me Chemist ya dubata yayi mata allurar rage zugi tasha magani sannan, washe gari da safe ta tashi da wani sabon tashin hankalin. Qarfe goma gaba daya yan gidan manya da yara suka hallara bisa umarnin kiran da Abban yayi musu tun daren jiya. Bata san kiran me ya musu ba tadai ga sun shige can bangarensa kuma sun dade suna magana dan har se gurin sha biyu sannan Salman yazo yayi kiranta. Dakyar take tafiya saboda yanda jikinta yayi tsami, badan kar ta sake yin wani laifin ba daman da bazataje kiran ba. Irin yanda gaba daya suka dauke kai tamkar babu wanda yasan da tsiron halittarta a gurin ya mata ciwo daman tunda ta dawo gidan in ka cire Anty babu me shiga sabgarta Mama kuwa in zasu hadu sau dubu ta gaidata bazata amsa ba daman tun randa tadawo tayi mata iyaka da shiga dakinta tace bata buqatar ganinta a ciki. Tana zama kamar wata Mujiya a cikinsu suka fara darewa daya da daya duk suka fice daga dakin kowanne yazo giftata seya bugamata tsaki sannan su harareta, seda suka fice gaba daya kafin Mama ta kalleta rai babu dadi tace "Matso ciki". Gaba kadan ta muskuta amma bata yarda tayi kusa dasu da yawa ba cikin rawar Murya ta shiga gaishe su ta kalli Abba dake Kishingide da gani bashida lafiya, babu wanda ya amsa gaisuwar Tata har Antyn yau tana daga gefe idonta yayi jajir alamar Kuka tayi se Umaimah ta sunkuyar da kanta qasa, muryar Abban taji cikin dakiya yana cewa "Ina so ku zama shaida tsakanina da Umaimah zan kafa mata sharudda da har idan tana neman zaman lafiya a cikin gidan nan dole ta bisu. Ban yarda Umaimah ta taka ko nan da qofar gida ba tareda izinina ba haka zalika banyarda wani yazo gidannan gurinta ba, sannan zata bani wayarta" Abban ya fada yana kallon Umaimah data sunkuyar da kanta qasa tana hawaye, takaicin yanda gaba daya kowa ya tsaneta ya kamata, babu wanda ya dubi halin da ta tsinci kanta a ciki ita ta rasa Khalil a maimakon su tausaya mata suyi qoqarin kwato mata haqqinta se suka bige da tsanarta kamar ta aikata musu wani mugun laifi. Tana jin Abban ya gama maganarsa, zancen ba zata fita ba ko ba za'a zo gunta ba be dameta ba kamar na karbe mata waya. Idan ya rabata da wayarta ta ina zata samu damar magana da Khalil harsu daidaita ta koma dakinta? Tsawar da Mama ta daka mata ceta sakata miqewa da sauri dan dakko wayar, tana hawaye kamar yarinya ta bashi wayar tata ya karba a gabanta ya zare layin ya ballashi biyu kafin ya sake kallonta yace "Abu na gaba daga yau duk wani aiki na cikin gidan nan ya dawo hannunki, ina nufin daga kan shara girki wanke wanke da duk wasu sauran ayyukan tsakar gida ke zaki cigaba da yinsu har wankin kayanku idan kuna da buqata ku bata tayi muku dan ba zan ringa ciyar da ke a banza ba tunda kinqi zaman aure kiyi na Farilla ki samu lada zakiyi Mustahabi anan. Idan har na kamaki da laifin saba daya daga cikin sharuddan nan ina me tabbatar miki da cewar sekin gane kuskurenki tabbas". Da sauri ta daga kai ta kalli Abban bakinta na rawa alamar son yin magana amma mugun kallon da Mama ta aika mata dashi yasa ta kasa cewa komai ta maida kanta qasa hawaye suka sake balle mata kamar famfo. "Rayuwar da kika zabarwa kanki kenan zaman gida ba gaki ga gidannan se kici uwar da kika ajiye a ciki. Kinsan dai ba zamu zauna muna goga kafada dake a cikin gidan nan ba mu dafa mu baki kici ki ajiye kwano mu share guri ki zauna na iya lokacin da aka miki ma Allah ya bamu lada dan haka dolenki kiyi aiki in har kina son zaman lafiya damu koda yake ma bata bakina nakeyi saboda na manta da kin rigada kin zama yar kanki kiyi duk yanda yayi miki Umaimah babu wanda zesake tilasta ki akan kiyi daidai amma kin sani matuqar kika qi ji ba zaki qi gani ba kuma kinji abinda Mahaifinki duk ya fada se ki zaba zama lafiya kibi abinda yace ko ki fara neman wani gidan uban da zakije kici gaba da yanda kika ga dama" Mama ta fada cikin fushi ita dai Umaimah kanta na qasa in banda hawaye babu abinda takeyi. Shiru sukayi na kusan Minti goma babu wanda ya sake cewa komai se Abban ya yunqura ze tashi Mama da Antyn suka miqe a tare suma dan taimaka masa ganin Anty tafi kusa dashi yasa Maman ta tsaya ita kuma ta kamashi suka shige cikin dakin "Idan baqin cikin ki ya kashe shi se ki zuba ruwa a qasa kisha" Mama ta sake cewa kafin ta juya ta fice daga falon ta barta tana kuka da tunanin ita me tayi kuma da za'ace baqin cikinta ze kashe Abba? Haka taja qafafunta da suka sake yin tsami saboda zama ta fita daga, a bakin qofa sukaci karo da Sharifa zata shiga da Flask qarami a hannunta ta kalli Umaiman tayi tsaki qasa qasa tace "Wlh mutum ya kashe mana Uba ba yarda zamuyi ba se munyi shari'a dashi" tayi gaba a hasale Umaiman ta fincikota baya tareda watsa mata maridukda ba wai taji abinda ta fada bane saboda ta sauke fushin su da take cike dashi tace "Dan uwarki ni sa'arkice da zaki mun qunquni?" Kuka Sharifan ta fasa, Nuratu data taho da Kwanuka tayi saurin direwa a qasa ta fincike hannun Umaiman data shaqe Sharifan tana cewa "Karki sake gigin taba lafiyar wani daga cikinsu" "Ke kuma ina ruwanki ai ban saka ki a ciki ba balle ki shiga" ta sake zaburowa Nuratun seta daga mata hannu tace "Karki kuskura kice zaki zageni dan nima kinsan ba sa'arki bace ba, kuma iskancin da kika sabayi a baya muna daga miki qafa yanzu kinyi kadan wlh duk wanda kika nemi ki taka se ya mayar miki da raddi dan haka ki kama tsumman rayuwarki kija sauran mutunchin daya rage miki, mtsww" taja tsaki ta dauki kwanon data ajiye tayi cikin falon Sharifa ta faki idon Umaimah tayi mata gwalo kafin tabi bayan Nuratu da sauri. Kamar yar yarinya haka ta wuce dakin Mama tana kuka da hawaye shabe shabe zata shiga ta tuna da Gargadin data mata dan haka ta coge daga bakin qofa cikin kuka ta kalli Maman da suke magana da Anty Hafsa da Maman Asad tace "Wlh Mama kiyi mun tsakani da Nuratu karta sake shiga shirgina akan me yarinya zata mun rashin kunya na hukuntata sannan tazo ta bada ni a gabanta ta gaya mun magana wlh karta sake idan ba haka ba..." "Idan ba haka ba me Umaimah?" Mama ta dakatar da ita kafin taci gaba da cewa "Ke har kina da kunya ma da zakiji haushi dan wani ya miki fitsara? Yanzu maganar da kika zo kina mun a sama kamar yarki ki ai ladabi da Biyayya ne ya jawo haka ko to kici gaba karki fasa" Seta juya tayi dakinta tana ci gaba da kuka haushin kanta ya kamata data kaiwa Mama qarar ma bayan tasan ba goyon bayanta zatayi ba. Yanzu zaman nan da taga sunyi ma Allah kadai yasan abinda suke fada akanta ita dai Allah na kallo duk Wanda yaci namanta ta barshi dashi. Kwanciya tayi tana ci gaba kuka baqin cikin ganin da tayiwa Khalil jiya naci gaba sa nuqurqusarta gashi Abba ya kwace mata waya abinda ta qudura yau zata bawa Yasir kudi ya siyo mata sabon Layi tunda yayi blocking wanda yasanta dashi gashi yanzu babu wayar ba ta san yanda zatayi ba kuma tasan a cikin gidan babu me bata tashi wayar. Tana tsaka da Tunanin Sharifa ta daga labule ba tareda ta shiga ba baki a tunzure tace mata "Kizo inji Mama kuma tace karki bata mata lokaci" "Wlh se naci uwarki idan na riqeki zaki san ni kikewa fitsara shegiya sa a haihuwar Kaji nayi Jika dake ko Salman wanki na biyu na girmeshi ballantana ke qaramar mara mutunchi" Umaiman ta fada tana miqewa ita dai tayi gaba abinta saboda son ta qara bata rai harda daga murya tana waqa "Ruwa yaci garin maqiya ashe dai mune da guri na kwana se inga tsiya". Kwafa Umaimah tayi a ranta tana ayyana zasu gamu ne. Seda ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da tayi luhu luhu gefen idonta da dukan jiya ya sama ya tashi dukda maganin da me chemist ya bata ta shafa. A qofar Kitchen ta tarar da Maman ta qarasa gurin ta tsaya Maman ta nuna mata Kayan Miya dake ajiye a qasa tace "Gashi nan ki debi wanda ze isa ragowar kisaka a Fridzer akwai Nama a ciki ki dauki qulli uku Jollop din shinkafa zakiyi lokaci ya qure bare ayi me Miya". Galala ta saki baki tana kallon Maman da kuma kayan Miyar da ta nuna mata ita kuwa bata ma sake kallonta ba tana gama fada mata abubuwan da zatayi ta juya ta bar gurin ta koma dakinta suka ci gaba da tattauna abinda ya dame su ita da yayanta. Umaimah kuwa tafi qarfin minti goma a tsaye tana ayyana wai da gaske ake ita zata ringa girki a gidan? Girkin da ko zamanin yammatanci idan da abinda ta tsana ace tayi shine girki balle yanzu data qara sanin dadin jikinta komai tana daga kwance ake mata shine za'a ce ta dora tukunyar Abincin kusan mutum Ashirin gaskiya ba zata iya ba. Ganin tsayuwar da takeyi ba zata bata mafita ba yasa taja qafafunta ta wuce dakin Anty danta gaya mata ita fa ba zata iya ba gara ma a san me dafa abincin tun wuri. Tareda Fatima qanwarta ta tarar dasu bata san sanda tazo ba, qerere tayi musu akai ba tareda ta gaida Fatiman ba saboda a ganinta Sa'ar Nuratu ce ba wani girmarta tayi da yawa ba da zata gaisheta. Anty ta daga kai ta kalleta ranta babu dadi tace "Ya akayi?" "Mama ce tace wai naje na dora girki ni kuma gaskiya banida lafiya bazan iya ba" ta bata amsa kafin Antyn tayi magana qanwarta ta rigata tace "Ai se kije ki gayawa Maman data sakaki ko dan saboda itace marainiyar wayonki zakizo ki fada mata?" "Ya haka Fatima?" Anty ta tareta kafin ta kalli Umaimah cikin yanayin qosawa da Halinta tace "Ba girki na bane kinga bani da damar cewa karkiyi, kije ki gayawa Maman baki da lafiya zuwa kiji sauqi seki karbi aikin" bata ko tsaya taji me zata kuma fada ba taja fuu tayi waje tana jin Fatiman na cewa "Wlh Anty ke kika bawa yar iskar yarinyar nan dama take taka ki a gidan nan, kin gama shan wahalarta tun tana yar mitsitsiya ta tafi yanzu ta kuma dawowa zata ci gaba da Addaba miki tun wuri idan zaki tashi ki kwatarwa kanki yanci kiyi" bataji Me Antyn tace ba tayi kwafa a fili tace "Shegiya me suffar munafukai shiyasa aka sakoki saboda halinki ai" "Ina fata da kanki kike" taji muryar Nuratu a bayanta ta galla mata harara amma batace komai ba. Kitchen din ta koma dan dai ko hauka take bata isa tajewa Mama da raini a wannan gabar da suke ba. Ta shiga ta duba Gas ta kunna taga da akwai tayi hamdala a ranta, tsabar dorawa kai Jidali ga Gas Allah ya rufa musu Asiri be hanasu kudin Refilling ba amma a ringa kunna itace a gidan. Store ta shiga ta dakko Industrial Gas dinsu ta hada dan tukunyar ba zata hau kan wancan ba Haka ta debi kayan miyar diban wulaqanci ba tareda ta wanke sauran ba ta zuba a Freezer yanda Maman tace ta barsu a gun ta hau aikinta. Ita kanta data gama dafa abincin seda gabanta ya fadi kan tunanin abinda ze biyo baya amma haka ta daure ta juye shinkafar a babbar kular da ake zuba abinci fara tas da ita tun a ido idan ka kalleta babu sha'awa ta debi tata a Qaramin Flask ta qara mai a ciki dan bata saka yanda ze wadata ba ta samu leda ta kwashe musu rabin Yajin dake cikin Roba ta qulle tayi dakinta ko zuwa tace musu ta gama batayi ba. Kukan yunwar da qananan yaransu Nuratun suka fara ya sakata zuwa ta duba abincin, ta kalli Kitchen din da yayi kaca kaca kamar anyi gasar girki a ciki, kwanukan data bata duk ta barsu a nan ga ledar Maggi ta watsar hatta da ledar data cire Nama nan cikin kitchen din ta yar dasu, kada kai Nuratu tayi taqarasa kan kular ta bude "Kan bala'i" ta fada a fili tana bin shinkafar da kallo se kace a gidan prison ga qamshin kayan Miya alamar basu soyuwa yana tashi seta dakko cokali ta debi kadan ta kai bakinta bata iya taunawa ba ta furzar da ita saboda Azababben Yajin daya ratsa bakinta wato duk fato faton Jajjagen data gani a ciki zallar Attaruhu ne kenan da alama kwano dayan ta juye duka. Plate ta dauka bayan data sha ruwa ta zuba shinkafar ta fita, a gaban Mama dake kan Sallaya tunda ta idar da Sallar Azahar ta ajiye ta kalli abincinta kalleta se tace "Abincin ne ta gama". Shiru Mama tayi tana bin shinkafar da kallo ranta na baci, na farko Umaiman ta sani basa saka jajjage a abinci indai Abba zeci sedai a markada kayan miyan dakyau ko babu wuta se an kai Inji sannan wannan fari fat din da shinkafar tayi ina laifinta zuba Kori tunda bataji zata saka wadataccen kayan hadi da ze canza mata kala ba" "To me zanyi da ita da kika ajiye mun se ku zuba kuci Abbanku dai nasan ba zeci wannan abun ba bari naje na tafasa masa ko Taliya ce tunda inada sauran Miya" Mamanta fada tana miqewa, tsakaninta da Umaimah dai sedai tace Allah ya shiryeta dan ba zata mata baki ba iya bacin ran da take sakata ma Allah ya yafe mata. "Mama mi dandana kiji ban sani ba ko bakina ne beji daidai ba" Nuratun ta sake fada se Maman ta dakata ta debi lokaci daya ta kai bakinta, dakyar ta tauna ta hadiye lokaci daya idonta yayi jajir saboda bacin rai ta kalli Nuratu tace "Dakko mun Kular Abincin". Salman daya shigo ta cewa ya kama mata suka kaiwa Maman ta bude ta kalli uwar Shinkafar data dafa ta zarce awon Abincin da suke sakawa koda ace duk yaran gidan da iyalansu suna nan ga girkin babu kai bare qafa, Babu mai a ciki yaji kamar yayi magana sannan bata tsammanin ta saka Maggi salam yanda kasan girkin Asibiti na masu Hawan Jini ko ciwon Sugar. "Kirawo mun ita" Mamanta fada cikin tsananin bacin rai, se Anty Amina tayi saurin cewa "Dan girman Allah Mama ki kyaleta, ta rigada tayi abinda take so zuwan ta nan babu abinda ze canza illah ya qara miki bacin rai da damuwa shiyasa nace ki bari muyi girkin amma yanzun ma Kiyi haquri bari na tashi na dora ko Taliya ce aci ki barta dan Allah". Badan Maman taso ba ta barsu suka fita su ukun suka fara kiciniyar dora sabon girki, Nuratu ta gyaro Kitchen din ta fito da kwanuka ta taresu gurin wanke wanke su kuma suka hura wuta suka dora Sanwa suna aikinsu suna yan hirarraki dan basu bari Abinda Umaimah tayi ya bata musu rai ba, nan da nan suka gama tsaf suka raba kowa aka saka masa Nasa, Maman Asadta kaiwa Anty nata daki suka gaisa cikin mutuntawa da Fatiman dake ta zubawa yar uwarta qorafi akan Umaimah suka sallami duk sauran yaran kafin suka saka nasu a babban Try sukaci. Bayan sun gama Nuratu ta hado kan ragowar kwanukan zata wanke Mama ta dakatar da ita. Da kanta ta wuce dakin Umaimah, tana kwance daidai a Gado cikinta na juya mata saboda yajin data nada gana abinci ga wanda ta qara dan ta samu abincin ya ciwu mata Mama ta shiga da Sallama ta tsaya akanta tace "Tashi kije ki wanke kwanukan da aka bata". Bata musa ba ta biyo bayan Maman ta kalli uban tulin kwanukan a bakin famfo ga wata babbar tukunya bayan wadda tayi girki da ita ta tabe baki ta zauna tana shafa kwanukan kamar me wasa, tun ana dab da kiran La'asar ta fara ba ita ta gama wanke wanken ba se ana Haramar shiga Magrba shima ganin Laqai laqai din nata na mafita bace yasa ta ware ta shigayi tana hawaye tsabar wulaqanci tanayi ana qaro mata wasu seda ta Zagi Salman daya shigo da kwanuka daga dakinsa wasu ma da gani sunfi Sati ba'a wanke ba dan har wari suke ko a jikinsa ya ajiye mata aiko ta ware su gefe ta rantse ba zata wanke ba. Duk tana zaune yayyenta kowacce tayi Harama ta tafi gidanta. Bayan ta gama dakyar ta tashi daga gurin ta bar kwanukan. Seda ta watsa ruwan Zafi ta gasa jikinta dan an kawo wuta kafin ta iya yin Sallar La'asar da Magriba tana shirin aje haqarqarinta ta huce gajiyar girki da Wanke wanke Sharifa ta sake shiga fuskarta a washe da alama tana jin dadin aiken zuwa kiran Umaiman tace "Mama tace ki fito ki dora Tuwan dare" "Na rantse da Allah se naci kutumar ubanki idan na riqeki" ta fada cikin tsananin fushi tana tashi zaune muryar Abba ta jiyo daga waje yana cewa "Gani a kusa fito kici uban nata kuma karki fito kiyi abinda tace kinji". Kuka daya riga ya zema mata jiki ta fasa amma bame qara irin na jiya ba, jikinta kamar ana sarata haka take ji bata warke daga jinyar dukan data ci jiyan ba ga Azabar aiki an tasota a gaba. Harta sauke tuwon tana kuka, Miyar dai yanzu ta saka musu maggi dukda bata dan dana taji yanda yayi ba gurin kadin ne daman ita hannunta baya yauqi dan haka kubewar ta tsinke kamar Romo, ta Jibge Tuwon a Kula gaba daya ba tareda ta Malmala ba danma na Semovita ne amma dukda haka jikinta ya gaya mata gurin tuqin tana gamawa ta tsallake komai a inda yake ta wuce daki harda kwanukan data wanke tun dazun bata kau dasu ba. Seda ta shiga dakin Mama dake lura da duk abinda takeyi ta fito. Ta bude tukunyar Miyar ta dandana, kai kawai ta girgiza ta maidata kan wuta ta qara abinda ya kamata ta kuma daureta sannan ta sauke ta shiga rabon tuwon dan Goma ake nema a lokacin daman badan Abba daya ce setayi girkin ba batayi niyar sake jira ta kwashi takaicin Umaimah ba da tuni ta gama girkinta. Guraren sha daya tuni tayi nisa a bacci dan tana shiga dakin ta kife tana kukan takaici a haka baccin ya kwasheta kiran sunanta taji anayi tareda bubbuga qafarta ta bude ido dakyar dan bata da Nauyin bacci taga Ummu-Salma tsaye, seda ta tashi zaune da kyar kafin Ummu-Salman tace "Anty Umaimah kije inji Abba" "Inje kuma Me zanyi masa?" Umaiman ta fada tamkar zata fasa kuka wannan wane kalar bala'ine? Ita dai Ummu-Salma na tsaye a gefe, bata dade da shigowa gidan ba ta taho daga makaranta Dutse take FUD tana Final Semester dinta Motarsu ta lalace se goma ta iso tana shirin kwanciya Abban ya ce ta kirawo masa Umaiman. Seda ta gama qunquninta da qananun hawaye kafin ta miqe tana layi ta fita, tsoronta karya sake mata irin dukan jiya da babu inda zata wlh haka ta isa falon Abban suna zaune tareda Mama da Anty ga Kular abincin ranar da tayi a gabansa tana kallon fuskarsa gabanta ya fadi saboda fushin data gani akanta wai shi da Bashi da lafiya dan Allah baze sararawa zuciyarsa haka ya dena fushi ba? Qasa ta samu ta rabe idonta har sannan yana yajin bacci Abban ya fara magana cikin fada yana cewa "Wato saboda ki nuna ke bakya ji duk kuma abinda aka ce kiyi sekin bata wa mutane rai shiyasa kikayi haka ko? To bari kiji daga yau kamar yanda na fada miki zan sake jaddadawa aikin gidan nan kaf ya rataya a wuyanki kuma Tilas kiyishi akan lokaci sannan a mutunce yanda kikaga iyayenki sunayi. Karki kuskura qarfe bakwai tayi baki gama abin karyawa ba a ranakun makaranta sannan duk rintse karki wuce biyu ba tareda kin sauke na rana ba haka na dare kin sani kafin na dawo daga Sallar Isha'i an ajiye mun abinci. Sannan maganar wanke wanke da shara bana so na sake maimaita miki daga yanzu kinsan yanda akeyinsu Kwanukan da kika ajiye tun Yamma kuma suna nan suna jiranki ki gyara su yau kin samu yan uwanki sun rage miki aiki gobe basa nan ke zakiyi komai kuma ki yarda kiyi wani abu da ba haka ya kamata ba zamu gauraya a cikin gidan nan maganar wannan abincin kuma( ya nuna kular gabansa yace) daga yau har zuwa sanda ze qare shine abincinki a cikin gidan nan Umaimah koda ace zeyi tsutsa Wallahi se ya qare zan ci gaba da baki abinci a cikin gidan nan idan kuma kika ci wani abu nawa ba tareda umarnina ba Allah ya isa" A firgice suka kalleshi gaba dayansu Anty tayi saurin cewa "Haba Alhaji me yayi zafi zakayi mata Allah ya isa akan Abinci?" "Sharadi na bata idan kuma idan har ta qi bi na maimaita Ban yafe ba" ya sake fada cikin tabbatarwa se aka rasa wadda zata sake magana a cikinsu se Umaimah data rushe da sabon kukan tashin hankali dan lamarin kam ya girmama ya zarce tunaninsu, Abba kuwa ko a jikinsa yaci gaba da cewa "Sannan komai ruwa komai Iska da Itace zakiyi girki ban yarda ki sake kunna mun Gas a gida ba tunda bada kudinki na siya ba wanda kikayi amfani dashi yauma se kin biyani". Anty da Mama dai sun rasa ta cewa Umaimah ko kallonsu takeyi a qoqarinta nason su roqa mata sassauci akan wannan lamari ina zata kai wannan shinkafa da ta ranar ma dakyar ta iyaci muguntarta ta qare akanta kenan ai wlh gara yace ta biyashi kudin shinkafar kawai da wannan tsatstsauran hukunci ita zancen karta kuma ci masa abinci ma be dameta ba tana da yan kudadenta zata iya ciyar da kanta na tsahon lokacin da yace amma zancen tayi ta cin shinkafa ai bema taso ba. Ganin Abban ya miqe Alamar zeje ya kwanta kuma har sannan Anty da Mama basu roqa mata sassauci ba yasa ta zabura cikin kuka me tsanani tace "Dan girman Allah Abba kayi haquri wlh bazan iya ci ba na yarda ayi lissafi zan biyq duk kudin amma ka barni na fita dashi na bawa Almajirai" s Abban ya dakata ya juya ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace "Wato saboda su basu da uwa da uba a kusa shine zaki basu abinda kika kasa ci ko? To ban yarda ba kuma ban janye maganata ba" daga haka ya shige cikin dakinsa ya barsu. Anty tayi tsaki qasa qasa ta miqe ta fice daga falon Mama ta bita da kallo a ranta tana ayyana idan ba'ayi wasa ba Umaimah na shirin rusa zaman lafiyar da sukeyi a cikin gidan dab tun a daren jiya ta lura da Anty ta kai maqura da Al'amuran Umaiman dan a daren jiya da Abban ya yanke jiki ya fadi bayan ya fito daga wanka Allah ya rufa Asiri Antyn na tsaye ta kai masa ruwan shayi ita ta tareshi tana kuka take cewa Maman "Gaskiya kija mata kunne ta dena dagawa Alhaji hankali haka dan idan ya mutu bata da Asara ke kanki kukanki kadan ne dan duka yayanki kin aurar kuma suna da Madafa nice me qananan yara" tun a daren Jiyan maganar take nuqurqusarta amma ta shanye ko su Nuratu bata gayawa ba ta kuma tabbatar dalilin da ya saka dazu har Sharifa take sake maimaitawa Umaiman cewar karta kashe musu uba kenan qila ita Antyn tayi zancen da yayanta. Gajiya da kukan da Umaiman takeyi ya saka Maman miqewa ita ma se ta zabura ta bita har suka je bakin qofar Maman bata dena gunjin kukan ba ganin tana shirin shigewa daki ta barta yasa cikin kuka tace "Dan Allah Mama dan darajar Manzon Allah kisa baki Abba ya haqura na bawa Almajirai abincin wlh bazan iya ci ba ni na yarda kar a bani abinci har tsahon lokacin daya kamata na cinye wannan din". Yanda take kukan da magiya abin Da da Mahaifi se zuciyar Maman ta kamu da tausayinta dan haka cikin sanyi tace mata "Ki samu Robobi ki juye ki saka a Freezer idan ta kitchen din bata dauke ba ki kawo nan ki saka a Fridge dare yayi yanzu da Safe maga yanda za'ayi" daga haka ta shige daki ta barta babu yanda ta iya ta koma ta dakko Kular abincin tayi yanda Maman tace dan tasan idan ma ta barshi ya lalace qarin laifi ne a gurinta. Seda ta gama Adana abincin tas ta kwashe kwanukan wanke wanken data bari bakin famfo ta shigar dasu kitchen kafin ta koma daki tana ci gaba da kuka, daren bata iya runtsawa ba tunanin yanda zata cinye shinkafar nan safe rana dare harta qare takeyi idan Abban be haqura ba seda Asuba ta gabato bacci ya fara fizgarta, motsin shigowar Abba dasu Salman daga Masallaci ya farkar da ita kamar wadda aka koro fit ta fice daga dakin ta tsaya gaban Abban tana muzurai so takeyi ta sake kafa masa magiya amma yanda taga fuskarsa a daure ya hanata iya bude baki tace masa komai se hawaye suka fara mata tsere Abba kuwa yayi wucewarsa ciki ba tareda yabi ta kanta ba indai juninta rashin ji yana da hanyoyin dafata cikin ruwan sanyi har tayi laushi kuwa. Ciki ta koma tana sharar kwalla tayi Alwala tayi sallah, harta kishingida tana ci gaba da share Hawayen ta tuna da zancen girke seta fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa musamman data tuna itace zata hura kai wannan bala'i da me yayi kama? Sanda tana gidanta iyanzu tana kan Royal Bed cikin Turkish Duvet ga sanyin Ac da qamshin freshner suna ratsata, tana kwance Ruqayya zata shigo mata da abin kari har kan gado ta shiga Jacuzzi tayo wanka taci a yangance ta sake kwanciya amma yanzu Murhune yake jiranta da Itace kai Allah ka kawo mata dauki. Kuka tasha bana wasa ba kafin ta lallabi kanta ta fita dan zaman ba amfani ze mata ba bandama ta sake ja wa kanta wata shiga ukun. A qofar falon Mama ta durqusa ta gaisheta ta daga mata kai kawai a hakan ma taji dadi dan tunda ta dawo Maman bata taba amsa gaisuwarta ba, murya na rawa tace "Me za'a dafa Mama?" "Kunun tsamiya da Alala, wake yana nan an jiqa seki wanki ki bawa Yasir ya kai markade shima qullin kunun yana nan a Kitchen idan kinga dama ki bata ke zakiyi taci harsu qare" Maman ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba harta miqe kuma ta koma murya na rawa tace "Mama kinsan idan na dama kunu tsinkewa yakeyi, sedai na dafa Abba kuma baya so a dafa". Shiru Maman tayi kamar ba zata ce mata komai ba se kuma ta numfasa tace "Idan ruwan ya tafasa kizo ki gaya ki debi kwai ki dafa a saka a cikin Alalan" daga haka taci gaba da jan carbinta Umaimah ta ja qafafunta ta wuce Kitchen din. Waken ta fara dubawa ta sauke ajiyar zuciya ganin gyararrene har ya juqu ma dan haka ta wanke shi ta dubo Attaruhu da Albasa ta zuba cikin takatsan tsan, sedata hada markadan tsaf kafin ta wuce qofar dakin Anty ta kwankwasa dan babu wanda ya fito a yaran Lahadi ce kuma an musu hutun Tahfiz ga garin yanayin sanyi ya fara shigowa tasan suna nade a bargo se ita da uwarta bata sonta ce take gararanba a tsakar gida da farar safiya. Tafi Minti biyar tana bugu kafin Antyn ta bude fuska babu yabo babu fallasa tana kallonta, kamar karta gaisheta saboda qin roqar mata da Abba da batayi ba jiya amma ta dake tace mata ina kwana. "Mama ce tace Yasir yazo ya kai markaden Alala" ta fada a cukule itama Antyn murya babu walwala tace "Yasir ya tashi da Zazzabi sedai ko Sharifa dan Firdausi ma tabi Fatima jiya". Jin cewar se Sharifa yasa ta juya ba tareda ta cewa Antyn komai ba dan indai yar iskar yarinyar nan ce qarshe seta jawo mata wani laifin ace bata gama da wuri ba sawunta a likafa ta wuce ta kunna wuta danma itacen busashshene tana yi tana hawaye wai ita Umaimah ce ta sake dawowa girkin itace? Seda ta hada wutar ta dora ruwan kunu kafin ta leqa waje ta samo Almajiri ya kai mata markaden a ranta tana Mamakin duk Almajiran da suke musu hidima a gidan suna ina tunda satin ya kama ta dena ganinsu ko saboda an shirya maida ita boyi boyi yasa aka sallamesu. Ta kalli tsakar gidan ta tabbatar kuma ita din ce dai me sharewa duk dan saboda a jance zancen cin shinkafa ta tattara kwanukan da aka fito dasu na wanke wanke a gefe ta hau shara, kafin ta gama bayanta ya riqe dakyar ta iya miqewa saboda Azabar ciwon daya dauka ta wuce dakin Mama tana kuka kamar yarinya dan ruwan ya tafasa Mama ta kalleta kawai bata ce komai ba, ganin Almajirin ya kawo markaden ta kama hada Alalan tana yi tana diga musu Hawayen daya kasa tsayar mata a ciki Mama dai ta dama kununta tafi ki mutu bata ce mata ba se sanann Anty ta fito suka gaisa ta kawo Flask din da ake saka musu Kunun Maman ta zubawa kowa nasa ta koma dakinta. Umaimah na zaune tana jiran Alalal ta dafu tana aikin kuka kamar matar Mamaci har yayi ta kwashe ta hada kwanukan ta hau wanke wanke. Tana kallo kowa ya debi abin karinsa yaci kamar kwayar idonta zata fita saboda kuka yanzu duk ta gama wahalar nan ba zataci ba kenan ake nufi haka ta wuce daki ta kwanta dakyar saboda ciwon jiki tana kuka data ci shinkafar nan ta gwammace yunwa ta kasheta kawai kowa ma ya huta tunda an tsaneta. Sha biyun rana Mama ta kwala mata kira, ta yunqura dakyar ta fita jikinta kamar wadda ta fado daga kan bishiya saboda ciwo ta tsaya tana kallon Zogalen dake jibge a qasa ba'a tsinke shi ba ta kalli Mama dake cewa "Gashi nan Dambu zakiyi tsakin kwano biyu zaki auna dan za'a kai nan baya gidan Malam Bala anyi Rasuwa dazu ga Madambaci nan nasa a aro na gidan su Harira shi babbane sosai in kika hada da wannan zaki fi sauri". "Dambu" ta maimaita tamkar bata san kalmar ba, ta waiwaya jin Yaro yayi sallama da wani uban rafkeken madambaci ya ajiye take ta tuno da zuwansu gidan Qawarta Abu Maman Nihal a irinsa suka tarar da ita tana dambu shikenan ta shiga ukun ta ta lalace. Cikin kuka tace "Wlh yunwa nakeji Mama bazan iya aikin dambu yanzu ba" "Ga shinkafarki can ai ki diba ki dumama kici kuma ki hanzarta ki dora da wuri dan Abbanku yana gida kin san kuma Azahar nayi ze nemi Abinci" Maman ta bata amsa cikin ko in kula kafin ta zura Hijabin dake hannunta tana cewa "Idan kin gama bamu dawowa ba ga Kwano nan(ta nuna mata wata fanteka) indai kinyi awon daidai ragowar ze cika wannan bayan ki debar mana na gida se bawa Ko Salman ne ya miqa gidan rasuwar se Mundawo" tana gama fada tayi gaba sega Anty ta fito da fitsararriyar yarta inji Umaimah a bayanta da alama tare zasu tafi suka rankaya suka barta a tsaye ta rasa abinyi se hawaye takeyi. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 78 Zama tayi gaban zogalen tana kukan daya aureta, Abba ya fito daga bangarensa yayi mata kallo daya ya wuce abinsa ko amsa Adawo lafiyar datayi masa a shaqe beyi ba yana fita Ummu-Salma dake labe ta fito daga dakinsu. Tausayin Umaiman ya cikata, tun jiya da dare Sharifa ta bata labarin ance ita zata ringa aikin komai ta tausaya mata dan abin yayi mata yawa musamman da bata sababa ko sharar gidan aka bar mutum da ita aiki ce balle ga wanke wanke Ina laifin ace ta ringayin iya girki? A hankali ta qarasa kusada ita tace "Kiyi haquri Anty Umaimah nasan Abba ze huce ya sassauta miki yanzu dame zan kama miki kinga lokaci yana tafiya?". Fuska shabe shabe kamar wata yar Yaye ta kalli Ummu-Salma tace "Yunwa nake ji bazan ma iya aikin ba idan banci Abinci ba" "To bari na dakko Miki akwai ragoqar Kunu da Alala a dakin mu se kici" Salma ta fada harta miqe Umaimah ta tuna da maganar Abba ta dakatar da ita tace ta bari. Shinkafar dai da bata so ta debo, Ummu-Salma ta karba nan da nan ta hada jajjagen zallar tumatir da Albasa tayi mata Sauce ta dumama mata shinkafar tana nan zaune gefe kamar me shirin gangarawa ta kai mata Abincin harda Baqin Shayi kafin kace me kuwa ta tadashi ko tuna rashin dadin shinkafar batayi ba ta cinye ta tsaf tasha ruwa sa'annan ta fara gani daidai dan yunwar ta mata karo, Da rana jiyan bata wani ci dayawa ba kuma haka ta kwanta bata ci tuwon ba ga safiya tayi har sha biyu sannan ta sakawa cikinta Abinci. Tareda Ummu-Salman sukayi aikin Dambun nan da nan suka gama ta rabashi kamar yanda Maman tace, seda suka gyara tsakar gidan tas suka wanke kwanuka kafin ta shige daki jikinta na nuqurqusa. Ba daban Salma ba da yau bata san yanda zatayi da ranta ba ta shige bandaki tana qunar rai, Dambun yayi kyau duk kuma wahalar data sha babu rabonta a ciki se hawaye haka tayi wanka ta fito tana ci gaba da tsane hawayen. Tayi sallah saboda baqin ciki a gurin ta kwanta cikin Sa'a bacci yayi awon gaba da ita bata farka ba se ana idar da Sallar La'asar. Fuska a kumbure dalilin kuka da bacci ga gajiyar dake tare da ita ta fita tsakar gidan bayan tayi sallah, babu kowa se tashin murya da take jiyowa daga falon Mama seta nufi can, Anty Laure ce da Anty Uwani. Daga bakin qofar ta durqusa ta gaishesu Anty Uwanin ta amsa Anty Laure kuwa sama ta dage kanta, Mama ta kalleta tace "Ya akayi?" "Dama tambaya zanyi me za'a dafa!" Ta fada muryarta na rawa se Maman ta nuna mata wani farin bokiti me dan girma tace "Ga Awara nan ita za'a soya se ki damawa Abbanku Kunun gyada shikenan". Da 'toh' ta amsa ta shiga falon a darare ta Kinkimi bokitin zata fita Anty Laure tace "Wai ni Umaimah takaba kikeyi ko qaqa? Tun dawowarki gidan nan kike fama da wadannan shegun rigunan bana jin sun kai goma Zawarci hauka ne ko kuwa Qazantar ce har yau baki dena ba duk ina uban jibgin suturunki da bazaki ringa sakawa?" Seta rasa amsar da zata bata ta kalli Mama kawai dan dai tun dawowarta gidan kayan datayi amfani dasu zaman Asibiti ne taketa dirza basu fi goman ba ta bakin Anty Laure ita kuma ganin ba inda taken zuwa yasa bata damu da bin ba'asin kayanta ba, Mama ce ta nunawa Anty Laure Dayan dakin dake cikin Falon ta tace "Suna ciki Akwati sun kusa Ashirin ni har Mamakin uban suturun da suka debo da sunan nata na ringayi dan da tana gidan nasa ma ba sawa takeyi ba. Tun tana Gadon Asibiti su Nuratu suka debo mata kayan katako ne Alhaji yace a barsu tunda daman shi yayi" "Aa shi kuma Yaya wace irin magana ce haka kamar yaya shi yayi? Ai ba haka nan aka kaita babu komai ba babu abinda ba'a sai mata ba na aure canji ya mata kuma ko bataje da komai ba wadannan da ya matan sun zama nata ai kyutace saboda baqin hali shine kuma da akace ya barsu ya riqe din" Anty Laure ta fada se Mama ta muskuta tace "Aa fa ba laifinsu bane babu yanda basuyi ba akan a diba Alhaji yace Aa yace ya tattara ya siyar ya rage Asarorin data masa dan ashe har Mota me tsada yarinyar nan ta fasa masa bamu sani ba se daga baya" "Kuma haka ne fa ai shikenan kinga kinyi zaman shekara bakwai a banza baki tsira da komai ba randa kika tashi yin aure kina ruwa dan mun rigada mun miki na fari ke ba sana'a ba ke ba aiki ba toh Allah ya rufa Asiri". Ita dai Umaimah tuni ta fice daga tsakar gida take jiyo sababin Anty laure, ta rafka tagumi wato duk lokacin nan an debo mata kayanta amma babu Wanda yace mata gasu ta tambaya kuma cibi ya zama qari saboda tsabar an tsaneta kayan dakin ma bar masa akayi ai shikenan. Haka ta shiga yanka Awara ta gama ta jere duk kayan da zatayi Amfani dasu cikinta se kiran ciroma yake amma ta qudurce ko zata yi me ba zata sake cin shinkafar ba, ta dazu ma yunwa ce babu yanda zatayi ga yar kwaskwarimar da Ummu-Salma tayi mata toh yanzu saboda mugunta suna dawowa Anty ta aiketa wai gidan Yayarta tasan kuma dan karta tayata aikine ai Allahya kaimu gobe da yake girkin Antyn sedai ta fito tayi abinta dan bayi zatayi ba. Tana shirin Hura wuta Yasir ya shigo da barkono da alama aikensa Akayi ya siyo ya ajiye mata harda kayan Maggi ta kalle shi ta kalli barkonon, ko zamanin yarinta bata daka dan da tayi hannu ta zeyi kanti seta dade tana jinyarsa kafin ya warke ko tuqin tuwo tayi me yawa hala yake mata shine yanzu za'a kawo mata wani yaji kusan kwano guda ta daka me za'ayi dashi? Yasir kuwa yana aje mata ya wuce dakin Mama ya fito da ledar citta da Tafarnuwa ya ajiye mata yana cewa "Mama tace ko raba barkonon biyu kuma kar ki saka farin Maggi iya dunqule da gishiri za'a saka". Seta wai waya ta kalli dakunan kafin tayi qasa da murya tace "Kana ji ka dauka ka kaiwa Maman Nana kace nace ta bayar a daka yanzu ka kawo mun in ka dawo zan baka dari biyar maza ka boye kar ka bari wani ya gani" jin zata bashi cin hanci ya tattari kayan ya fice dasu Umaimah kuma ta shiga qoqarin kunna wuta a ranta tana ayyana kota kunna Gas tunda Abban baya nan sega Yasir ya dawo da barkono ya dire mata yana cewa "Abba yace a dawo dashi". Bata iya amsashi ba saboda takaici, kenan Abban na waje. Seta miqe da sauri ganin An kawo wuta, a Blander ta hada ta warwatsa musu yajin tana kuma sane da Abban yafi son dakan hannu dan Maman Asad na siyar da su Spices da Yaji idan ta kawo niqan Inji baya ci sedai a daka masa a turmi. Ba yanda ta iya ta shiga suyar Awara, tana cikin tsame kaskon farko Salman da Abokansa biyu suka shigo gidan da sallama. Ahmad daya daga cikinsu irin mutanen nan ne nan masu shegiyar zolaya ya kalli Umaimah harda bude baki irin na mamakin nan yace "Kai Salman dama Yah Umaimah na siyar da Awara shine baka gaya mana munzo mun yi mata cikini ki ba? Dan Allah kalli yankan manya manya ba irin na Rabin bakin layi ba Yah Umaimah a samun ta dari a kyauta mun saboda naje majalisa nayi miki tallah" tsabar wulaqanci Salman da dayan yaron suka kalleta suka tuntsure da dariya harda duqawa qasa saboda yanda bilhaqqi tayi kama da me siyar da Awarar gasken. Zuciya ta zowa Umaiman wuya kamar zata yi Amanta ta kalleshi tace "Uwarka ce me suyar Awara bani ba shege dan masu..." "Akul dinki da yi mana zagi a cikin gidannan idan ba haka ba sena gurje bakinki, aida Awarar kike soyawa ma da kin samu abinyi" Abba daya shigo ya dakatar da ita, seta fashe da kuka babu shiri tana cewa "Haba Abba ku kumin sannan wasu su shigo sumin ku goya musu baya wannan wane irin abu ne?" "Halinki yaja miki da ace kin zauna inda Allah ya ajiyeki da babu wanda ze ganki ya zageki amma tsarin da kika dauka kenan ai shikenan" ya fada yana wucewa ciki dan ana shirin shiga sallar Magriba ne. Salman da Abokansa kuwa jiki a sanyaye suka fice daga gidan Umaimah ta ringa kuka tana suyar Awara, wlh da Ace yaron nanya matso kusada ita seta dulmiya kansa a kaskon dan ubansa sedai duk yanda za'ayi ayi. Haka ta gama suyar wata danya danya wata ko harta qoneta ta bar musu a gaban kaskon ta shige daki tana ci gana da gursheqan kuka. Waiita me tayi data cancanci wannan qasqanci haka? Idan laifinta suke gani ai ba ita ta kashe auranta ba su suka ce a sakota akan me kuma za'a kafa mata qahon zuqa idan ba'a dubi cin Amanar da Khalil din yayi mata ba kuma ai ba a qullaceta ba inma taqamarsu abinda ta masa ba gashi nan ya warke ba yana yawonsa ita fa illar daya mata ai harta mutu ba zata warke daga ciwon cin Amanar daya mata ba. Yayi aure a bayan idonta sannan ya bita da tukuicin saki. Haka ta sake kwanciya bata ci komai ba dan tunda ta shiga dakin bata sake fitowa ba kuma babu Wanda yabi ta kanta da safe kuwa dakyar ta ke zama saboda yanda jikinta yake rawa dalilin Yunwa. Yanda ta fito tana bin bango ga fuskarta data jeme a dare daya ya sa Mama kama aikin abin kari saboda yan makaranta da Abbazeyi fada shima daya ga Umaiman yayi shiru duk sun san yunwa ce take rarakarta, ta gama bin bango kamar qadangaruwa Mama ta daga Ruwan shayi dan tun dare an siyo biredi suka hada da ragowar Awarar kowa ya kama inda zashi ganin babu sarki se Allah yunwa na neman halakata yasa ta farwa shinkafarta da qanqararta da komai ta hau ci. Seda taci taci se Amai kuma ta tafi bakin famfo ta ringayi gaba daya jikinta yayi laushi dakyar ta iya kuskure baki ta tashi ta koma qofar dakinta ta zauna jikinta na kaf kaf kamar zazzabi na shirin rufeta. Duk yanda Mama taso ta dauke kai seta kasa ta tafi dakin Abban ya zaune yana karyawa ta zauna a kujerar dake kusa dashi a sanyaye tace "Alhaji kayiwa Allah ka sassautawa yarinyar nan akan batun Abinci kar yunwa ta illa tata" "To se me? Mu illoli nawa tayi mana?" Abba ya fada ba tareda ya kalleta ba Se Maman ta shiga share hawaye tana cewa "Na sani amma Alhaji kamata yayi mu bar komai a hannu Allah muci gaba da nema mata shiriya dan ni na fara yarda kwakwalwar Umaimah ba'a saiti take ba mutum me cikakken hankali baze ringa abubuwan da takeyi ba" "Oh kema tayi nasarar yaudarar zuciyarki kenan to bari kiji lafiyarta qalau tana kuma sane da duk abinda takeyi. Saboda tasan ta sabayi tana sha shiyasa bata shayin yin komai amma ki sani ni tsakanina da ita babu duka babu zagi ba kuma zan mata mugun kalami ba sedai yanda take zuba iskancinta haka nima zan hukuntata cikin ruwan sanyi har seta ladabtu. Har yanzu Umaimah bata san da tayi ba daidai ba balle ta nuna nadamarta kina Jin inkarin da takeyi na mun tsaneta a zatonta tsana ce tasa ake mata abubuwan da ake matan amma kwakwalwarta bata bata lissafin me tayi ko me takeyi da ya saka a tsane tan ba? Tsayin shekara guda tana zaune a cikin gidan nan ko gaisuwarta ba ma amsawa bansani ba ko ke amma nidai rana daya yarinyar nan bata tareni ta bani haquri akan qin amsa gaisuwarta ba saboda abin be dameta ba a maimakon haka ma seta dena gaba daya se yanzu data ke neman sassauci ne ta dawo da gaisheni kinga ashe da hankalinta tunda tasan idan tana da buqata ta kwantar da kai to muci gaba da tafiya a haka daga nan har ran da qasa zata rufe idon daya daga cikin mu muddin bata hankalta tasan tayi badai dai ba ta nemi afuwa akan hakan bazan rangwanta mata ba dan ba ita kadaibace yar banza in fact a gurina ta gaji kafiyar tata kinga bata fini iyawa ba" Abbaya fada daga haka ya dauki ruwan shayinsa yaci gaba da kurba. Kasa ce masa komai Maman tayi se hawaye da take sharewa lokaci lokaci, ita ba wai tana nemawa Umaimah sassauci akan wani abu bane amma maganar abinci takeyi be kamata ace za'a horata da Yunwa ba ai ko ayyukan gidan idan bata qoshi ba ba zata iya ba sannan wani ciwon ze iya kamata. Yana lura da hawayen da takeyi kuma abin ya dameshi amma baya so ta bari rauninta ya rinjaye ta su kasa Nunawa Umaiman kuskurenta. Cikin yanayin rashin jin dadi yace "To yanzu da kike wannan hawayen na menene me kike so ayi?" "Nidai ka janye Allah ya isan da kayi mata akan abinci ka bari taci gaba da cin komai kamar sauran yan uwanta" Maman ta fata cikin kuka kamar wata yarinya se abin nata ma ya bashi dariya ya murmusa yace "To yanzu so kike na dauki asarar abincin data mun kenan a zubar dashi a shara wannan ai Almubazzaranci ne" "Ni ba haka nake nufi ba yanzun ma ai tana ci jiya shi taci yanzu ma gashi can taci tana amai ai kaga taji maganarka koda ace zata ci gaba da ci harya qare amma kayi mata lamuni idan ta dafa wani abun taci ba iyakar wancan ba" Maman ta sake fada se ya nisa yace "Shikenan taci darajarki amma seta biyani kudin shinkafata dan ba zan dauki Asaraba in yaso tayi duk yanda zatayi da ita kirawo mun ita" seta miqe ta fita, Umaimah na nan zaune a qasa tana numfarfashi tunani takeyi yanzu da tana gidanta abinci dai se wanda ranta ya raya zataci ko basu da abu duk inda yake Khalil ze tafi ya nemo mata danye ko dafaffe muddin tace tana so amma yanzu a cikin gidan ubanta yunwa na neman ta halakata. Dakya ta iya tashi tabi bayan Maman, tayi tsuru tana sauraron Abban da yake cewa "Mamarki ta nema miki afuwa akan abinci naji kuma nayi amma akan sharadi se kin biyani kudin abinda kika lalata sannan karki kuskura ki zubar ki san dai yanda zakiyi dashi" "Na yarda wlh Abba zan biyaka" ta fada cikin rawar murya se yayi murmushi kawai yaci gaba da cewa "Sannan abubuwan da kikeyi na ganin dama inaso kisan cewar dolenki ne kiyi bawai kamar yanda kike dauka ba karki kuskura na sake maimaita miki maganar nan a cikin gidan nan" ya zaro dubu biyu ya miqa mata yace "Ki bayar a siyo miki Cefane Miyar Taushe zakiyi da dare idan na fita zan aiko da Qashi a qara da Nama" seta tsaya ta kasa karba ya watsa mata kudin baki na rawa tace "Abba ai yau girkin Anty ne bana Mama ba" "Dana tashi baki Umarni kinji nace girkin uwarki kadai zaki ringayi? In kinga dama kiyi idan kuma kinga akasin haka karkiyi ita Saratun ma bata nan Uwarki da sauran yan uwanki su zauna da yunwar dan ban yarda wani ya girka abinci cikin gidan nan ba idanba ita ba kuma ki hado lissafin kudina ki kawo mun yanzu ina jiranki" Abban ya fada a fusace kan ta na qasa tana Hawaye ta tabbata dai ta zama boyi boyi kawai a gidan bata da hutu daga girki se shara da wanke wanke. Cikin kuka ta kalleshi tace "Toh dan girman Allah Abba bada itace ba wlh har cikin kwakwalwata nake jin hayaqinga idona duk ciwo sukeyi ka barni na ringa Amfani da Gas din" "Ban yarda ba sedai idanda kudinki zaki ringa zuba Gas din" ya bata amsa kai tsaye har tana zabura kuwa tace "Na yarda sannan Abba Shara ma zan samo Almajirai zan ringa biyansu sunayi " "Ai shikenan kiyi duk yanda yayi miki" ya sake fada yana wani murmushi tareda girgiza kai, su zubasu gani ai duniya tafi bagaruwa iya jima daga haka ya sallameta ta fita tana jinta sakayau ko babu komai an rabata da wahala tunda ya yarda ta samu mataya. Indomie ta debo a store ta samo Almajiri ya siyo mata sardine ta dafa abarta taci tayi nak har wani sabon qarfi takeji saboda sassaucin data samu a wautarta. Ta dumama Dafadukanta tsaf ta bawa Almajirin tace ya fita da ita ya rabar sannan ta ce masa ya ringa zuwa kullum safe da yamma ze ringayin shara da wanke wanke suka tsadance yanda zata ringa biyansa ya zama girki kadai ne aikinta. Cike da kuzari ranar ta ringa aikinta tayi musu Dafaduka da rana amma ba irin waccen ba tana saukewa ta mayar da Ruwan Tuwo haka ta tuqa musu shi sama sama duk dan kar hannunta yayi kanta danma shinkafar me laushi ce kuma tasha ruwa zata kwashe a kula Mama tace mata karta kuskura, dole ta dakko Leda ta malmala shi yanda akeyi ita dai Maman kallonta kawai takeyi dan gaba daya rayuwar Umaiman tausayi take bata. A maimakon ta roqi Mahaifinta ta bashi haquri yayi mata afuwa saboda shedan na mata kururuwa tana ganin ta tara Abin duniya ai shikenan yau da gobe dai tafi qarfin wasa ko nawa take ganin tana dasu wata rana zasu qare. Haka rayuwa taci gaba da gangarawa Umaimah, Yasir tasa ya kira mata Me POS din qofar gidansu tunda an hanata Fita ta bashi ATM dinta ya duba mata balance tunda babu waya, dubu dari uku da Hamsin da biyar take dasu a cikin account dinta na UBA, dayan first bank dinta bata da ATM tunda yayi expire bata sake wani ba ta san ma kuma ba wasu kudine a ciki ba sunyi yawa sukai dubu Hamsin dan a nan take Saving kudi kuma su ta tattara ta biyewa Safina suka ringa rabawa Malaman qarya gashi yanzu bata ga tsuntsu bata ga tarko. Tas tace ya cire kudin ya bata ta ajiye su, ta debo akwatunanta na dakin Mama a cikin kayan ma ta samu kudade irin wadanda take ajiye wa cikin drawer kaf suka hado mata komai nata Mayukan shafawarta da yawa se zubar dasu tayi dan sun lalace ta debi abubuwan da zatayi amfani dasu yauda kullum ragowar ta hadesu ta rufe tunda ba fita takeyi ba. Kwanci tashi Asarar me rai se gashi tun ba'aje ko ina ba Al'amura sun fara yi mata tsanani, kudin da take gani a hannunta suka sa ta sake miqe qafa tana yanda taso suka tasamma qarewa dan a cikinsu take hidimar komai da wadda ta zamar mata dole da wanda ta dorawa kanta ta siyan Gas da biyan Almajirin da yake mata wanke wanke da shara ga ciye ciyen banza da wofi baki ya saba da dadi kullum tana hanyar aiken Yasir siyan shawarma da Icream ko Kaza gashin Inji wadda ta sabaci a gidan Khalil a zahiri idan ka ganta zaka dauka bata da wata damuwa amma a badini ba haka bane, a sannu rashin Khalil yake dukanta kullum cikin zuba idon ganinsa takeyi yazo da niyyar maidata se gashi babu wata alama da take nuna faruwar hakan dan daga shi har yayanta babu wanda ya sake tako qafarsa gidan har gara takan ji a bakin Nuratu ko Maman Asad an kai musu yaran Musamman Nuratu da take nacin su abin ya qara bata mata rai wato ana kaisu gidan yan uwanta se ita da take uwarsu ce ba za'a kai mata su ba duk tsiya dai ba'a isa a canzawa Tuwo suna ba suna nan a matsayin yayanta kuma ko bajima ko ba dade zasu nemeta idan ba'a kawo su ba. Ba'a cika wata shida data kama ayyukan gida ba kudi suka qare Almajiri ya gudu saboda daman ba abinci ake bashi ba kudi take biyansa yaci wata biyu bata biyashi ba sedai ta hadashi kanzon tukunya tace yayi haquri in ta samu zata biyashi daya gaji ya fece shikenanta sake shiga ukun data fi tada dan yanzu ga aiki ya mata karo ga qangin talauci dan kudin da zata siyi sabulun wanka ma Wahala yake mata a da kuwa duk wata Khalil yana sako mata Shower gel din da take amfani dasu tunda Iman ta bar hannunta kuwa ya janye tallafi a farko bata damu ba dan gani take kamar tana da abinda ze ci gaba da riqeta se yanzu ta gane karin maganar da Hausawa suke cewa Zara bata barin dami tunda gashi sake dawowa square zero. Rayuwa tayi mata gwatson kenwa, idan kaga yanda Umaimah ta koma a shekara daya da fara Zawarcin gaske se ka tausaya mata kuma ka sake gasgata Al'amarin Ubangiji dakan sauya abu a sanda yaso. Ta yi wata irin rama da baqi babu rashin Abinci amma ta fita a hayyacinta kana kallonta kasan bata da nutsuwar zahiri data zuciya a koda yaushe idan ba aiki takeyi ba zaka sameta ta zauna tayi shiru tana tunani, a yanzu kam ta gama yarda da cewar Khalil ya barta tunda har ze iya daukar tsayin shekaru biyu cif ba tareda ya waiwayeta ba tabbas ya zareta daga rayuwarsa. A kullum dare kwana takeyi cikin kuka da juyayi, nadama mara amfani ta dirar mata akan abinda ta aikata har yayi sanadiyyar barinta da Khalil. Me yasa batayi haquri ba? Me yasa bata karbi qaddara a yanda tazo mataba ta gaza fuskantar duk wanda ze tausheta a baya ya nuna mata tayi haquri me yasa basu fito sun bayyana mata makamanciyar wannan rayuwar da take fuskanta a matsayin abinda zata tarar sakamakon butulcewa? Ta biyewa kururuwar shaidan da zigar qawayen banzan da tsayin lokacin nan babu wadda ta waiwayeta balle harta san halin da take ciki koda yake duk tarin qawayen nata da daman ita take bauta musu ita suke mora babu wadda ta bi sahun sanin inda take tsayin shekara guda da rasa wayarta. Tayi mamaki kwarai da ace Rufaida bata nemeta ba, daman batayi tsammanin Safina ba kodan kalar rabuwar da sukayi a Asibiti amma Rufaida fa a baya baya dabda Al'amura zasu rikice mata ta dawo sun qara dinkewa amma ace tajita shiru bata zo inda take ba tunda dai tasan gidansu ai ya kamata ta tun tuba taji tana da rai ko ta mutu. Babbar damuwarta irin yanda Iyayenta da yan uwanta gaba daya suka banzatar da ita, irin yanda suke mu'amalantarta na mata ciwo amma ba laifinsu bane a yanzu ta fahimci tarin wautarta a baya da abubuwan da tayi ta kuma ji irin zafin da sukaji a lokacin data banzatar dasu itama ta daukaki wasun su suka zame mata komai yau gashi a sanda ta shiga halin da take buqatar dan uwan da zata jingina dashi tayi kuka ta rasa badan bata dasu ba sedan kunya da nauyin abinda ta aikata musu a baya baze barta ta iya tun karar su ba. Tana kallo su Nuratu zasu zo gidan su qule da Mama a daki suna hira cikin nishadi da jin dadi ita tana rabe a tsakar gida ko tana aiki tsakaninta da Maman umarnine na yin abu idan ta sakata aiki dan a tsahon lokacin nan bata taba ce mata Umaimah karkiyi ba, ta rasa damar shiga dakin Mamanta tayi hira da Ita Antyn ma da take ta tata tun wancan lokacin ta watsar da ita ta dawo tsakaninsu ga Yayanta da suka mayar da ita tamkar Tabarma Yanda Sharifa da Firdausi suke tata mata rashin mutunchi a gidan kuma bata isa tayi magana ba dan akwai ranar data Mari Firdausin Abba da kansa yayi mata kaca kaca har yana fadin idan tana da kunya har taji Haushin wani dan ya mata rashin kunya kota manta sanda taringa kallon Idon Sa'ar Uwarta kuma Matar data tsugunna ta haifa mata Miji ta ambato iyayenta ta zaga har akwai rashin kunyar da za'ayi mata taji haushi? A ranar tayi kuka tamkar hawayenta ze qare ta shiga rudu da Dana sani kuma se a ranar hankalinta ya dawo jikinta ta shiga tariyo zamanta da Khalil da irin mugayen ta'adundata ringa aikatawa. Ta ringa hakaito tarin qaunar da Khalil da yan uwansa suka nuna mata domin babu wanda zata cire a ciki duk sun sota, mugayen halayanta suka sanya su yi mata tawaye kuma duk da haka Khalil da Hajiyar sa basu barta ba, tana iya tunawa har a daren da Khalil ze saketa dukda hauka da Tijarar da takeyi Hajiya bata fasa yi mata uzuri ba ta shafawa idonta toka ta manta Alkhairan matar a gareta tayi mata zagin da idan da ita ta kirki ce ko wani taji ya kwatanta yiwa Hajiyar se inda qarfinta ya qare amma a gaban Danta da iyayen da suka haifeta bata dubi Alfarmarsu tayi musu kara kodan Haifarta da sukayi suka bata tarbiyya ba ta watsar tayi abinda taga dama toh waima banda son zuciya irin tata ta ina Khalil ze sake waiwayarta bayan duk abinda tayi masa hatta ubansa dake kwance cikin kabari besan an aureta na seda ta ambato ta zaga to ya dawo gareta kuma a wanne matsayi idan dai da kunya ai itama ba zata yarda ta sake hada ido da wani daga cikin Ahalin Khalil ba dan bata da kwarin guiwar da zata kalle su ba kuma tasan da irin Kalaman da zatayi amfani gurin wanke kanta ba. A hankali ta yada duk wasu makaman da take taqama dasu ta fuskanci rayuwa da abinda take tafe dashi ta kuma yarda da cewar lokacin girbar abinda ta shuka a baya ne ya zo mata. Duk wanda ya santa a shekara uku baya idan ya ganta a yanzu baze ganeta ba saboda yanda ta koma. Bayaga aikin bauta da takeyi domin a yanzu Umaimah da bawan da aka siya banbancinsu kadan ne, a rana bata samun hutu na cikakkun awanni hudu, tun Asuba idan ta farka ta fara gyaran gida da dora abincin safe data gama aka karya zata yi wanke wanke ta maida na rana duk a qoqarinta na kiyaye duk wani abu da ze qara mata laifi a gurin Abba da Mama da yanzu take neman hanyar wanke kanta a guri su sannan duk inda Qarfe shida take ta sauke abincin dare. Da itacen data qi jini take aikin tunda bata da Asi yanzu kuma komai ruwa ko iska haka zatayi aikinta ita da Gas dinsu sedai Kallo dan sau da yawa idan aka samo danyan itace Mama takance ta dora a Gas dinse tace Aa, muddin ba Abba ne ya bata umarnin taba masa abu ba ba zatayi ba. Sosai take shan wahalar rayuwa ta jeme ta fige idan ka kalle ta se ido kawai babu wannan gayun bare ta samu damar zuga iskancin data saba to dame zatayi gayun ma suturu dai gasu nan tana dasu bila Adadin amma babu damar sakawa dan kayayyakinta gaba daya yanzu sun mata yawa saboda rama. Man shafawarta Vaseline ne Habiba se Sabulun Give da Abban yake bata dubu daya duk wata wai ta siyi sabulun wanka, wanki da man shafawa kamar wata yar tsana babu zancen tutare daman Alumun take gogawa a hammatarta kayanta kuwa qaurinitace ya isheta ba seta qara dawani turare ba koda yake a hakan ma ya mata bata tsammaci zata samu ba tunda Mama da take zaton zata fishi laushi abinda bata so bata bata a haka take jalauta rayuwarta duk buqatu a cikin dubun nan zatayi wanda ya zama dole, hatta da Pad data ga cewar tana cinye mata fiye da rabin dubun a hakanma kuma leda dayar na wadatarta takeyi ba seta yankewa kanta amfani da ita, ta samu wani zani a kayanta ta yayyankashi tayi qunzugu wadatattu. A ranar data fara amfani dashi tayi kuka tamkar ranta ze fita da tana wankewa, ta tuna a gidanta drawer guda take da ita ta pad hatta baqo idan tayi buqatarta ta kamashi Pack haka take kyatarta kuma yar waje me kyau ma ba made in Nigeria ba take amfani dasu amma wai yau itace take amfani da qunzugun Atanfa a gidansu tabbas a tsoraci rayuwa. Cikin wannan qangi da matsatsi taci shekara uku babu kuma wani sauyi ko sassauci kullum tana cikin gida tana aiki zata iya cewa ma ta manta da kalar qofar gidansu ita abu daya da zata iya cewar na jin dadi daya sameta shine fara kawo Yaranta gidansu da akayi tun shekara daya data wuce dukda zuwan nasu wuni ne basu taba kwana ba sannan su kansu yanda suke Mu'amalantarta abin na matuqar duk zuciyarta ranar da suka fara zuwa batayi tsammanin tayi kewarsu har haka ba se a lokacin tana tsakar gida tana shara suka shigo su ukun cikin kyakykyawar shiga Bibi da Iman sunyi Anko da gudu suka wuceta suna kiran sunayen yan gidan da alama suma cike suke da murnar zuwa gidan kakannin nasu. Sakin tsintiyar tayi ta bisu da kallo, shekara uku kenan rabon da ta saka Mu'ayyad da Bibi a ido sunyi wani irin kyau da girma Musamman Mu'ayyad din ya zama sauriyi ga Iman ma da take shekara uku kenan yanzu tayi wayo sosai tana bin yayyenta tana maimaita sunayen da suke fada tunda ita dai bazata tuna yan gidan ba. Dakin Mama suka fada gaba dayansu, tana jiyo muryar Maman daga inda take cikin tsananin murna tana tambayarsu daga ina waya kawo su seta kasa ci gaba da sharar ta tsaya a gurin wasu hawayen tausayin kanta suna zubo mata wata qila sun manta da ita shiyasa babu wanda ya nemeta a cikinsu se su Yasir suke cigiya. Dakinta ta wuce ta fada kan gado ta fashe da kuka a hankali amma irin me cin ran nan, me tayiwa rayuwarta haka? Wace riba taci? Da ranta bata mutu ba yayan data haifa sun haqura da ita basa tunawa da ita anya idan mutu ba ta gyara alaqarta ba kuwa zata samu wanda ze ringa tunawa da ita kuwa yana mata addu'a? "Momy" taji an kira ta se tayi saurin saka hannu ta share hawayen fuskarta ta juya Bibi na tsaye a bakin qofar ta tafi da gudu ta fada jikin Umaimah ga mamakinta se kawai yarinyar ta fashe da kuka tana cewa "Momy dama kina nan gidan kullum na tambayi Dady ina kike se yace mun kinyi tafiya zaki dawo". Rungume yarinyar tayi a jikinta wani irin kewarsu na sake shigarta a hankali tana shafa kanta tace "To kukan menene kuma ba gani yanzu kin ganni ba" se yarinyar ta dago tana shafa fuskar Umaiman tace "Momy kin rame baki da lafiya?" Se tayi saurin janye fuskarta saboda wani kuka daya sake taho mata dai dai nan mu'ayyad da Iman suka shiga shima da gudu ya fada jikinta yana cewa "I miss you Momy ina kika tafi kika barmu kullum se Dady yace mana kinyi tafiya kinqi ki dawo?" Ta kalli Iman data tsaya a bakin qofa wata sahihiyar qaunarta da bata tsaya ta tantance ba sanda ta haifeta ta shiga zuciyarta, seta miqa mata hannu alamar itana ta taho yar gasken ta maqe kafada ba zataje ba, Mu'ayyad ya tashi ya janyota yana cewa "Kizo gurin Momy" kai tsaye ta fizge hannunta cikin muryarta da bata gama iya magana ba tace "Ni ba Momy na bace, Mamah na tana gida da Aryaan". Yanda kasan dukan guduma haka taji maganar har ranta, ta zubawa yarinyar ido yanda ta dauke kai ta cuna baki a dole ba zataje gurinta ba zuciyarta ta qara karaya, babu tantama haqqin banzatar da ita da tayi ne ya fara bibiyarta Mamanta da tace tana gida ta tabbata Matar Khalil take nufi tunda ita ta bude ido ta gani a matsayin mahaifiyarta batayi laifi dan tace ita ba Momynta bace. Wunin ranar sir da yaranta tayi shi wani irin dadi mara misaltuwa ta ringaji suka ringa bata labarai na Hajiya Dadynsu, Mamah da Aryaan da ta kas gane wanene shi kp wata daga cikin su Jalilah ta sake haihuwa ne? A bakinsu taji cewar Habiba tayi aure harta haihu tun tuni sunanr Yarinyar Hajar. Har Magriba suna gidan suna kuma maqale da Momynsu dan da Abba ya dawo ma sukaje gurinsa basu dade ba suka gudo gurinta, Mu'ayyad da Bibi na lafe a jikinta Iman ce take ja baya da alama dan yan uwanta na gurin Umaiman nema yasa ta zauna da bazata tsaya ba su kuwa kewarta ce tasa suka kasa barin inda take dukda motsi kadan se sun tambayeta bata da lafiya ta rame se tace musu eh kawai se kuma suka kafa tambayar yaushe zata koma gidansu haka kawai taji bakinta ya furta "Ku tambayi Dady, duk sanda yace na dawo zan dawo". *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)* *WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* *A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼 Page 79 Seda akayi sallar Magriba akazo daukarsu dan daman sun fada musu ba kwana zasuyi ba. Wata Farar mace kyakykyawa ajin farko tayi sallama riqe da yaro kalarta Umaiman na tsaye bakin qofar shigowa tana jiran yaron data aika ya siyowa Mu'ayyad Awara wai zeci matar ta shigo qamshinta me sanyi da Aji ya kai mata ziyara ta shaqa tana ware ido akanta saboda akwai hasken nefa a gurin ta ga fuskarta tar seta zuba mata ido tana so ta gano inda ta santa. Humaira ta fadada murmushin ta cikin ladabin data ke gaida duk wanda ya girmeta ta dan rankwafawa Umaiman tana cewa "Ina wuni" "Lafiya lau" ta amsa ba tareda ta gano inda ta santa din ba seta raya qila baquwar Anty ce dan da ta bangarensu ce zata santa. Qara gyara tsayuwa Humaira tayi tana kallon Umaiman tace "Mama fa tana ciki?" Seta nuna mata qofar Maman kawai ba tareda ta sake cewa komai ba dan haka siddan taji tsanar matar ta dirar mata dukda bata da tabbacin wani abu ya taba hada, murmushi ta sakeyi mata kafin ta shige cikin gidan Umaimah ta bita da wani siririn tsaki daidai nan yaron data aika ya dawo ta karba ta wuce dakinta inda yaran suke jiranta. A plate ta juye musu sun fara ci kenan ta Mama ta kwala mata kira seta miqe bayan ta mayar da Hijabinta ta fita. Tare ta tarar dasu da matar dazun tana zaune a qasa yaronta na kan cinyar Mama se wani sunne kai takeyi Umaimah ta tabe baki qila cikin surukanta ne yaran yan uwanta tunda anyi bukunkuna da yawa a shekarun duk bata je ba tana zaune kamar Prisoner Mama ta nuna mata Humaira tana cewa "Mamansu ce tazo daukarsu" set kalli Maman kafin tace "Maman suwa?" "Su Malika, su fito su tafi kar su bata mata lokaci dare yanayi" Maman ta bata amsa tana harararta Umaimah kuwa daskarewa tayi a inda take kamar wadda ta samu cutar mantau kusan minti biyar kafin ta dawo hayyacinta sanadin tsawar da Maman tayi mata akan ta wuce ta turo yaran ta tsaya musu aka kamar wata kurma seta juya jiki a matuqar sabule tana jefa qafafunta kawai badan tasan ina ta nufa ba, a qofar dakin ta kifa kanta ta fashe da kukan data kasa riqewa wanda ta rasa ma na menene, ta tabbata dai waccen Matar ana nufinitace Matar da Khalil ya aura wadda tayi sanadin barinta dakinta ta rabata da yaranta har Iman take fadin ita ba Mamanta bace to idan haka ne shi kuma yaron hannu ta na waye dandai tafi kowa sanin cewar Khalil ya rasa lafiyar da ze iya yiwa Mace ciki ta haihu? Kuka takr haiqan, Mu'ayyad daya fito da plate ya ganta yayi saurin ajiyewa ya matsa kusa da ita fusakarsa ta nuna damuwa yace "Momy me akayi miki kike kuka?" Se a sannan ta tuna a inda take tayi saurin daga kanta ta shiga share hawayen amma sun gagara tsayawa se ta juya tana tafiya tace masa "Anzo daukarku kira qannenka ku tafi" tayi can hanyar tsofaffin dakunan su na baya da se ana wani sha'ani ake amfani dasu. Guri ta samu ta cigada da rera kukanta da takeyi tundaga can qasan zuciyarta. Kishin matar da ke amsa sunan ta Khalil a yanzu ya cikata, yanzu duk wata soyayya da tarairaya da yakeyi mata ita take samunta kenan, Khalil ya iya mallakawa wata mace bayanta kansa abinda bata taba tsammatar ze iya faruwa ba. A zatonta irin tarin qaunar da Khalil yake mata ko a Aljanna da da hali ze iya haqura da Kyautar Hurul ayni ya zauna da ita kadai suci gaba da cin soyayyarsu amma se gashi tun a duniya tana raye ya manta da ita ya juya mata baya ya sadaukarwa da wata kansa ba tareda ya dubi halin da take ciki ba wanda shine sila shiya jefata shiya janyo ta aikata koma menene Soyayyar sa ce sila. Tana nan zaune tana kukan suka fito Mama ta rakosu har bakin qofa tana musu Addu'a ga qatuwar leda a hannun Mu'ayyad da bata san ko menene a ciki ba haka suka fice daga gidan tana jin Bibi na cewa "Ina momy? Bamuyi sallama da ita ba fa" tayi maganar cikin son fasa musu kukan rigima ta jiyo tashin muryar Humairan dukda bata ji abinda take fada ba amma tasan lallashin tayi suka tafi seta sske kecewa da wani kukan dana sani da nadamar ayyukanta suka ringa taso mata, me yasa ta biyewa zuciya ta gazayin aiki da kwakwalwarta? Me yasa bata saurari yanuwa da abokan arziqi da suka ringa qoqarin nusar da ita ha ya ta kwarai ba a lokacin bata yi tunanin makomarta ba ta biyewa hudubar shaidar da son zuciyarta kawai gashi Khalil din da tayi danshi ya barta harya samu lafiyarsa yaci gaba da mu'amalantar watanta tubda ga shaida ta gani da idonta wanda kadai ya isa ya tabbatar mata da cewar yayi gaba a rayuwarsa ba kuma zai waiwayeta ba. Bata san lokacin data bata a gurin tana kuka da dana sani mara amfani ba kafin daga qarshe ta haqura ta tashi daga gurin tana jin kanta tamkar ya tsage saboda ciwo. Ragowar awarar da suka bari taci ta kwanta kawai amma bacci ya qauracewa idonta, duk inta motsa Khalil take gani a idonta da Humairan yana gwada mata kalar soyayyarsa me tsayawa a zuciya ta dora pillow akanta ta fasa qara kamar zata tsaga dakin, a fusace Mama ta shiga ta saiti bayanta ta watsa mata Carbin dake hannunta Umaiman ta zabura ta sake zuba mata shi yanda ta bude baki ta fara kuka me hade da ihu ya sake tunzura Maman ta ringa caula mata carbi ta ko ina seda ya tsinke kafin ta rabu da ita tana haki tace "Ke dan ubanki baki san ki ambaci Allah ba a duk sanda kike cikin tsanani se ihu da kwaroroto kamar diyar Arna? Ihun ne ze miki maganin damuwarki ko me, se yaushe zakiyi hankali Umaimah ki maida Al'amuranki zuwa ga Allah sannan ki ringa neman agajinsa akan duk abinda ya dameki? Kullum cikin yi miki tunatarwa nake akan duk a abinda ya sameki ki nemi taimakon Allah ki lazumci karanta Hasbunallahu wani'imal wakeel da sannu Allah ze kawo miki rangwame da salama cikin lamuranki, sannan ki riqe 'La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin' duk tsanani da yardar Allah zaki samu mafita amma inase ihu da kururuwa kadai kika sani babu Istigfari babu hailala babu salatin Annabi babu karatun Alqur'ani se Kuka da tagumi kika qulla aure dasu tayaya zakiga daidai a sha'ani ki Umaimah? Tun lokaci be qure miki ba ki gyara badan wani ba sedan ke a karan kanki kodan kiji dadin sauran rayuwar data rage miki Umaimah ki kama Allah" daga haka ta juya ta bar mata dakin Umaimah da tayi luqus jikinta gaba daya radadin dukan carbin data sha yakeyi amma maganganun Maman tabbas sun shigeta matuqa. Gaskiya Mama ta fada a duk lokacin da taji wani al'amari me nauyi ya taso mata a zuciya a maimakon ta miqa komai ga Allah seta zabi tayi ta zunduma ihu irin yanda take karantawa a littattafan turawa da gani a finafinan su idan abu ya samesu sukayi irin wannan ihun me qarfi kamar yana tafiya ne da dukkan damuwarsu ta dauki hakan kuma ta gwada taga yayi mata tun daga nan ta mayar dashi dabi'a da wata damuwa ta sameta zata taqarqare tayi ta zunduma ihu har ada suke tunanin tana da shafar Jinnu bata mantawa kullum Maman cikin nuna mata falalar addu'a takeyi amma ta gagara riqewa, ko Malamin da aka taba kaita ruqiyya gurinsa seda ya jaddada mata yin addu'a a duk sanda zuciya ta bijiro mata da abinda yake harqitsa mata tunani. Haka a islamiyya Ya sayyadin su kullum seya karanta musu falalar Hasbunallahu da sauran lazumai da suke sanya nutsuwar zuciya kuma idan yanayi yawanci ita yake kallo alamar in directly da ita yake dan ita ce majanuniyar ajin tayi shura kaf makara tar babu Wanda besan Tijararta ba, Headmaster idan aka fita sallar la'asar takanas yake sakawa a kirata bayan yayi alwala ya bata butar yace tasha ragowar ruwan ciki akan wannan abun har dena zuwa Islamiyyar tayi wai ya raina mata hankali yana sakata shan ruwan buta idan suka tafi gaba daya se ta zame tayi wani wajen tayi zamantahar se an tashi sannan zata biyosu su dawo gida seda Mama taci Ubanta bayan da su Nuratu suka ce basa ganinta idan anfito sallah tunda kowa ajinsa daban se an tashi suke haduwa a get sannan fa ta nutsu ta koma zuwa Islamiyyar amma bata yarda ta sake shan ragowar ruwan Alwalar Uztaz Muslim ba. Ta muskuta ta gyara kwanciyarta ta sake fadawa kogin tunani, ita da kanta ta yarda da cewar rayuwarta akwai dazgado a cikinta. Tana salloli biyar na farilla tana Azumin Ramadana baya ga haka babu wata Ibadah ta neman lada da takeyi ta bari sharholiyar duniya da abinda yake cikinta yayi tasiri a zuciyarta. Idan da ace mutum yana haifar Da ya haifi halinsa tabbas data kasance daga cikin mutane masu kyawawan dabi'u da ake misali dasu domin ba fariya ba Mahaifiyarta maceceta gari me matuqar kirki da riqo da Addini kuma tayi iyakar qoqarinta gurin basu tarbiyya kuma duk cikinsu kowanne yana kamantawa daidai misali banda ita data fita zakkah. Ta tashi a gidansu taga Mahaifiyarta ta kasance me yawan ibadah tasha ji a bakin Abba yana fada yana nanatawa Maman ita ta koya masa tsayuwar dare da Azumin litinin da Alhamis kuma tunda ya kamasu yake ganin haske a Kasuwancinsa da rayuwarsa gaba daya shiyasa a kullum yake qara godewa ubangiji akan hadin da yayi musu domin Malika ta zama haske a rayuwarsa. Tun suna qanana sanda suke kwana a dakinta tasan tana tashi kullum dare tayi sallah koda raka'a biyu ce haka nan koda ace tana fashin sallah wannan abin ya zame mata jiki seta tashi tayi addu'a tayi musu idan suna bacci haka zata shiga dakinsu ta tsaya akansu ta ringa tofa musu addu'oi yawanci tanayin hakan akan idonta saboda bata da nauyin bacci koya akayi motsi seta farka amma bata mori wannan baiwa da Allah yayi mata ba gurin ringa tashi tana bauta masa cikin dare sanda sauran jama'a suke bacci tana kallo su Nuratu zasu tashi subi Maman suyi sallar koda ba kullum sukeyi ba amma banda ita tun suna ganin yarintarta su barta har ya zamana suna tashinta wani lokacin tayi wani lokacin ta tsaya daga bayansu suna sallah tayi kwanciyarta bawai sallar dare ba har lokutan Azumi idan anje Tarawi haka takeyi tasha baccinta ta dawo gida ayi fadan a daka duk a banza har suka haqura suka zubamata ido randa Allah yaci da ita tanada rabon samun ladan tayi randabata dashi taqiyia haka ta tashi ta girma ta auri Khalil ta same shi shima me tsayuwar darene a farko farko tana binsa suyi daga baya ta saki tana kallo ze tashi yayi sallolinsa ita ko ta shanya baki tana bacci wani lokacinma idonta biyu sedai ta dauki waya tayi ta danne dannenda bazasu amfaneta da komai ba idan ya matsa mata tace da wanne zata ji gajiyar daya tara mata ko kuwa ya barta tayi baccinta tunda ba farilla ta tsallake ba bare yace ta sabawa Allah seya rabu da ita kawai taci gaba da rayuwarta a yanda ta zabar ma kanta babu Allah a ciki waddaga sakamakonta ta fara girba tun BA's ko ina ba duniyar ta nuna mata cewa ita ba koman kowa bace ba a dan qaramin lokaci ta zama abar tausayi. Daren ranar kwana tayi cikin jimami da tunanin neman mafita da hanyar da zata bi ta gyara kura kurenta, tana da buqatar wanda ze saurareta ya kuma nuna mata hanya domin kwakwalwarta ta rufe ruf bata tunanin gaba baya kawai take hasko mata tana tariyo irin mugayen abubuwan data aikata a rayuwarta da tun a nan duniya sun fara farautarta sun hana mata nutsuwa. KHALIL Kallon qofar gidan ya ringayi abubuwa da yawa suna bijiro masa tun daga farkon fara zuwansa gidan har kawo yau din nan dayazo daukar yaran. Jiya suka hadu da Abba a wajen wani daurin aure, ba qaramin kunyarsa yaji ba harya kasa hada ido dashi shi kuwa Abban ko a jikinsa suka gaisa ya tambayeshi iyali har yake ce masa "Malam Khalil mun tuba kar laifin Umaimah ya shafe mu a taimaka a ringa kawo mana yara muna ganinsu ko da a wuni ne, kaga Amaren nan nawa biyu ba qaramar kewarsu nake yi ba a dubamun na dan samu na gansu ko naji sanyi a raina" Abban ya fada cikin raha abinda ya sake jefa Khalil cikin matsananciyar kunya kenan dan haka da yamma yana komawa gida yace musu washe gari da sun taso daga Boko zasuje unguwa dama kuma Alhamis ce babu islamiyya ya sanarwa da Sabon Driver daya daukar musu saboda makaranta da sun taso ya jira su shirya ze kaisu wani guri. Seda sukaje kwanciya yake gayawa Humairan gobe za'a kaisu gurin Mamansu tayi masa murmushi me kyau tana lafe a qirjinsa tace "Ko kaifa Habibi amma ace tsahon lokaci ka raba yara da mahaifiyarsu Alhalin tana raye kasan kuwa zafin rashin uwa?" "Shiiii" ya dakatar da ita ganin tana so ta tado da wani abu kuma kafin yaci gana da cewa "Basu rasa uwa ba tunda suna dake kuma ai gashi nace gobe zasuje wajenta shikenan se ki dena yi mun mita" "Toh kwana nawa zasuyi? Kaga daman gobe da Monday babu makaranta se su zauna kawai zuwa Sunday se a dakko su ko ba haka ba?" Ta sake fada seya zuba mata ido kawai ba tareda yace komai ba. A tsahon shekara ukun nan babu abinda ta rageshi dashi da yaransa, ta karbesu da hidimarsu gaba daya a hannunta take tamkar yadda uwa zata tarbiyyantar da yaranta haka take musu babu mugunta bare qyashi ko hassada ya gamsu da cewar tsakani da Allah take riqe masa yara amma dukda hakan a kullum cikin haqurtar dashi take akan ya bari su ringa zuwa gurin Mahaifiyarsu ko Yayane. "Ita kadai ce Alfarmar da zaka mata idan ka rabata da yaranta baka san irin taskun da zata shiga ba Yah Khalil ka ture komai kayi mata wannan Alfamar ko ba dan ita ba saboda su kansu yaran nasan duk yanda zan kula dasu tunda har sunsan mahaifiyarsu tana raye dole zasuyi qulafucinta kaga kullum cikin tambayar ina take suke ina tsoron su qara girma suyi wayo su zargeni da laifin raba su da ita Alhalin tana raye" abinda kullum take nanata masa kenan shi kuma hujjar daya riqe itace Umaiman bata damu da yaran ba tunda har ta iya dawo Masa da Iman kamar yanda ta fada sannan ko a waya tun bayan rabuwarsu bata sake waiwayarsa ba wannan abun yana masa ciwo ya kuma tabbatar da Gaske ta dena sonsa koya mutu koya rayu a gurinta dayane ballan tana ta nemi yaranta yan uwanta da suke son ganinsu ai suna zuwa su gansu in ta damu dasu itama ai zata neme sun ko yanzu kunyar idon Abba da har ya karya bille ya roqi akai su tasa ya yarda kuma ba kwana zasuyi ba, suje su wuni su dawo baze sake barwa Umaimah dansa ko daya ya kwana a gurinta ba. Washe garin kuwa yasa akakaisu, Magriba nayi yace tashirya zasuje dakko su dan baya so ma ya tura wani balle har a hanashi daukarsu yana dawowa daga Masallaci kuwa suka kama hanya Humairan nata mitar se kace za'a gutsiresu ai se su Mama suga rashin kyautawarsa ma sama da shekara biyu rabon da yaran su taka qafarsu a gidan kuma suje yanzu ko cikakkun Awa shida basuyi ba ace zasu tafi ai babu dadi. "Aisha, idan kin fara gajiyawa da Hidimar yaran nan ki gayamun kai tsaye, zanyi miki uzuri domin nasan daman nauyin yayi miki yawa kuma ke kika dage zakiyi dan haka babu laifi yanzu idan kin gaza zan qaro musu me aiki taci gaba da kamawa Ruqayya kulawa dasu" ya fada mata fuskarsa babu alamun danuwa ko bacin rai seta kasa ce masa komai danda tasan tunanin da zeyi kenan da bata saka bakinta a maganar ya kaiwa Umaimah yaranta ba. Akan me ma ze kawo wannan tunanin a zuciyarsa ya za'ayi ta gajiya da hidimar Yayansa bayan ko a zuciyarta bata taba banbantasu da Aryaan data haifa ba kallon abu daya take musu kamar yanda suma suka mata kallon Uwa ba matar uba ba. Yanda tayi kinini da fuska bacin ran abinda ya gaya matan ya bayyana har akan fuskarta ya saka shi gangarawa bakin hanya yayi parking ya kama hannunta cikin nasa ta fizge seya janyo ta jikinsa gaba daya ta kuwa fasa masa kuka Aryaan dake baya yana wasansa ya saki da sauri ya matso jin Mamansa tana kuka "Kin gani ko kar kisa ya dauka wani abun nayi miki" ya fada a hankali yana shafa bayanta seta bude baki cikin kuka tace "To akan me zaka ce na gaji dasu ba Yaya na bane ko daman uwa tana gajiyawa da hidimar yayanta ne?" "Kiyi haquri subutar baki nayi kuma na janye amma kema ki dena takuramun da maganar Umaimah bana so, akwai lokacin da ko ba'a kaisu ha da qafarsu zasuje" ya fada mata cikin rarrashi seta dago tana kallonsa tace "A lokacin kuma zasu tsaneni dominzasuga nice silar da basu yi rayuwar quruciyarsu tareda mahaifiyarsu ba" se ya maida kanta qirjinsa yana cewa "Ko kadan bazasu taba tsanarki ba ni nasan zasu soki saboda ke sukeyiwa kallon uwa ita sedai kawai ta amsa sunan Mahaifiyarsu amma ba Uwa ba. Tun kafin kizo Habiba suke yiwa kallon Uwa ita tasha wahalarsu ita tasan me sukeso da wanda basa so, ta rigada ta rasa wannan damar a gurinsu saboda ta sakarwa wasu al'amuransu da Uwa ce ya kamata ace ta dauka ke kuwa yanzu kin karba kinga kuwa har duniya ta nade suna miki kallon uwa a gare su, sannan ita take da abunda idan suka sani zasu tsaneta akansa kinsan da haka ko ita ce silar tashinsu ba tareda ita ba dan haka karki sake zargar kanki da laifinda ba ke kika aikata ba". Seda ya lallasheta kafin suka ci gaba da tafiyar duk ransa babu dadi, baya qaunar abinda ze tuna masa da Umaimah saboda seya tuno da rayuwarsu gaba daya tun daga gabar daya ji dadinta har zuwa yanzu da yake dandana dacinta domin kuwa ta bar masa babban tabo a rayuwa, ya rasa lafiyarsa tsayin shekara uku a dalilinta sau da yawa yakanyi fatan dama ace ba Umaiman ce ta zama silar halin da yake ciki ba, dama ace accident yayi ya gamu da wannan matsalae da abin yazo masa da sauqi amma a duk sanda ya kalli kansa yaga abinda ta ja masa tsanarta da beyi niyya bace take qara shigarsa duk yanda yake qoqarin yayi mata uzuri abin ya faskara da wannan tunanin a ransa suka qarasa gidan. Har powder seda yasaka Humairan ta sake gogawa kafin ya bari ta fita daga motar tana dariyar lamarin nasa yana nan zaune suka fito tun daga nesa ya hango Bibi da hawaye a fuskarta yayi saurin bude motar ya fita ya tarota tana zuwa kuwa ta fada jikinsa tareda fashewa da kukan shagwaba me daga hankali. "Me ya sameki Mamana me akayi miki?" Ya fada a rikice yana duba fuskarta ita kuwa qara kukan take harda tirza qafa, Humaira dai ta bude mota ta shiga daman tuni Mu'ayyad ya shige da Iman da Aryaan suka bar uba da yarsa a waje suna nanaye seda ya rarrasheta badan ta fada masa abinda yake damunta ba kafin suka shiga motar, saboda tsabar tabara a kan cinyarsa ya dorata, Humaira ta kallesu ta sheqe da dariya tana cewa "Yanzu saboda Allah ko kunya bakiji ba ga Iman ga Aryaan ko dane cinyar Dady to dake kike so yayi tuqin ko yaya?" "Baki ta cuna irin na uwarta ta dauke kai gefe Khalil yayi qaramin murmushi, Bibi da Hajiya take kama amma halinta tas na uwarta ne babu abinda ta manto a ciki shiyasa be taba dora goshinsa a qasa ya tashi ba tareda ya roqa mata shiriya a gurin Allah ba da gudun zuciya irinta uwarta, Allah ya tsayar da ita ga gadon iyakar halayyarta ta kirkin ta zubar dana banzan amma tun yanzu fitsara a cikin Bibin se wanda ta manta. "Koma cinyar Mamah kinji Bibina yanzu zan tsaya a hanya na siya miki Icecream ai kina so ko?" Ya fada cikin lallashi se Iman ta leqo tace "Nima dady" "Ki tambayi Yaya idan tace a siya miki toh" se kuwa ta noqe kafada kamar itace qaramar tana tura baki tace "Baza'a siya mata ba ai jiya Mamah ta basu ni ta hanani kuma harda Burger zaka siyamun da Suya ko Dady?" "Yes Dadys Girl, maza koma cinyar Mama kinga dare nayi mu tafi" ya sake fada yana dagata ze dorawa Humaira ita ta tare tana cewa "Ba zaki hau mun cinya ba sedai Dadyn yayi tuqin dake" "Haba mana Mamah ai kinsan bazaniya ba da dai kece se nayi dake" ya fada yana kashe mata ido se tayi saurin gyarawa ta dauki Bibin dake wani basarwa ta babu gaira babu dalili ta dan harareshi da wasa tace "Kai kam baka jin kunya wlh a gaban yara" "Kinga idan basu gane abinda na fada ba yanzu ke seka qara musu bayani" ya mayar mata daga haka taja bakinta tayi shiru. Tafiya sukayi motar shiru se Mu'ayyad da Iman da Aryaan dake baya suna buga game a Tab dinsa Bibi ta hade rai ta kalli window Humaira ko wayarta take dannawa shi kuma yana tuqi ya tsaya wani gurin siyar da kayan kwadayi ya fita Bibin ta balle murfin motar da gudu tabi bayansa se Humaira ta girgiza kai kawai a ranta tana ayyana rigimar yarinyar da taji Hajiya tana fadin Halin uwarta tayo aikuwa in hakane Mamansu ba qaramar fitinanniya bace dan Halin Bibin se a hankali wata irin yarinya ce me wuyar sha'ani da badan tana da haquri tana kuma dauke kai ba da tuni anji kansu da ita musamman akan shegiyar barbarta kamar Buranya wani sa'in idan tayi abu setaga kamar harda mugunta ma dan bata lalata abunta se na wani. Basu jima baya fito da ledoji guda hudu a hannunsa Bibin na riqe da daya tana faman tura baki da alama ba'ayi mata yanda take so ba. A baya ya aje ledojin ya shiga suka dauki hanyar gida, tun a motar ta bude Ice cream dinta ta fara sha tana yi tana batawa Humairan jiki amma bata ce mata komai ba ganin kamar ma tana sane take zuba mata, titi ya hau suka dauki hanyar gida motar tayi shiru se ji sukayi Bibin tace "Dady munga Momy ta dawo, kuma fa bata da lafiya dukta rame nace mata yaushe zata dawo gidanmu tace mu tambayeka, Dady yaushe zaka dakko Momy ta dawo gidanmu?" Tayi maganar tana tsare Khalil da ido kamar yanda shima yake kallonta tunda ta fara maganar ganin yana neman bugawa na gabansu yasa Humaira saurin kai hannu ta juya sitiyarin motar dukda yanda qirjinta yake bugawa da magabar Bibin yayi firgigit ya kama kan motar seda ya daidaita a titi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya sake kallon yarinyar data zuba masa ido tana jiran amsa ya kalli Humaira data dauke wuta itama a hankali yace "Seta warke tukunna tunda kince bata da lafiya" "Toh ai ta warke Dady ta dawo kawai ta qarasa warkewa a gidanmu" tayi saurin sake fada seya maida hankalinsa kan titi ba tareda ya sake ce mata komai ba itama taci gaba da shan Icream dinta da rabi take zubawa a jikin Humairan. Yanda yaga tana abubuwa a salube bayan sun isa gida ta shirya yaran bayan sun gama ciye ciyensu suka kwanta kafin ta wuce dakinta itama tayi wanka ta shirya a can ta kwanta dan gaba daya jinta takeyi se a hankali ta kuma rasa abinda ya janyo mata hakan. Gajiya yayi da jiranta ya bita dakin ya tarar harta kashe fitila seya kunna yana kallon yanda ta qudundune a bargo dukda dakin babu wani shahararren sanyi ya matsa kusada ita ya zauna yana cewa "Ya kika zo kika kwanta baki ci abinci ba?" "Naqoshi" ta bashi amsa kaitsaye ba tareda ta kalleshi ba se yaji wani iri yanda tayi masa maganar seya saka hannu ya dagota gaba daya zuwa jikinsa ya cusa fuskarsa a wuyanta yana cewa "Fushin me Humairata takeyi?" "Ni ba fushi nakeyi ba kawai bana jin dadi ne bacci nake so nayi" ta fada tana qoqarin zame masa saboda yanda yayi matan yasa ta fara jin wani yanayi a jikinta da bata so ya tsananta dan a yanzu abubuwa sun fara rikice mata, wasannin da yake mata suke bata nutsuwa tana jin kamar sun fara mata kadan jikinta yana buqatar sama da haka tunda kuma ba samu zatayi ba shiyasa take nesa nesa da duk abinda ze motsata. Ganin tana tutture shi yasa ya tallafo fuskarta ya shiga kissing nata a hankali cikin kwarewa nan da nan kuwa tayi laqawas tana amsar saqon tareda maida masa da martani seda suka bata lokaci sodai dan shima yaji dadin yanayin bata fuskar sha'awa ba a'a kawai yana jin dadin tsotsar bakinta a kullum yana addu'ar ubangiji ya qare shi da lafiyar da jiyar da ita dadin data rasa ya sani tayi haquri tana kuma kanyi musamman a yanzu da ta qara girma jikinta ya bude yana lura da duk wasu sauye sauye tare da ita ya tabbatar tana buqatar sama da abinda yake mata shiyasa ya qara miqewa da gaske gurin neman magani dukda shekara uku kenan be zauna ba, duk inda yaji wani me maganin matsalarsa se yaje ya yarda warakar daga Allah take kuma idan yana da rabo ze samu. A hankali ya zame bakinsa daga nata ya kalli idonta da suka rikice alamar tana kusa yace "Toh idan ba fushi kikeyi ba muje ni ki bani abincin tunda kin qoshi". Seda ta nitsa kafin ta miqe jikinta a sanyaye ta fita yabi bayanta. Tea yace ta hada masa yasha da Cake ita kuma ta kwanta akan kujera ta hade jikinta lokaci lokaci tana juya kwanciyar saboda abinda take ji yana qara mata qarfi ya gama shan Tea din ya miqe, seda ya kashe fitilu kafin yazo ya dagata kamar yar Baby suka hau sama, a gadonsa ya kwantar da ita ya shiga bandaki be jima ba ya fito da alamar brush yayi ya fesa turare kafin ya isa kusa da ita ya kwanta ya jata jikinsa yama cewa "Na ganoki yarinyar nan wato kishi ne ya ke nuqurqusarki daga jin Maman Bibi tana biko" ai be rufe baki ba ta sakar masa kuka dan harga Allah maganar data saka ta qunci kenan dan take Maganar Anty Unaizatu ta dawo mata sanda take mata qorafin Khalil baya bari akai yaran gurin Mamansutace mata "Kwanciyar hankalinki kenan Humaira dan muddin suka fara zuwa ba baki na miki ba se kinga abinda ba zaki so ba dan ba haqura tayi dashi ba kuma nasan zata so ta dawo dakinta yaran kuma su zasu zamar mata makami sanin hakan qila shiyasa shima yake hanasu zuwan dan a sannu zata iya cin galaba akansa ta dalilinsu" gashi kuwa daga zuwa daya abu ya tabbata harta kitsa musu su tambayeshi yaushe zata dawo. "To saboda Allah kuma menene abin kuka anan daga magana?" Ya fada cikin damuwa yana dagota seta fizge tana cewa "Ni ina ruwana toh idan kana soka dawo da matarka meye nawa a ciki ce maka akayi kishi nakeyi" seya sake ruqota yana cewa "Toh yi haquri naji ba kishi kikeyi ba shikenan kinga bani da matsala dake ashe idan nace zan kawo wata?" Seta kalleshi zuciyarta na bugawa da qarfi jin abinda yace, cikin sanyin murya tace "Kenan dagaske zaka dawo da itan kenan?" "Bansan zan rabu da ita ba daga Allah komai yazo dan haka bani da amsarki abu daya da zan fada miki ki saki ranki indai wannan ne damuwarki ni ina nake da lafiyar da zan ajiye mata biyu ma ko kin manta kedin ma zaman haquri kikeyi dani?" Se tayi qasa da kanta saboda ganin idonaa ya fara kadawa irin yanayin da yake shiga duk sanda yayi zancen lafiyarsa, a hankali tace "Waya ce maka zaman haquri nakeyi, kaifa sadauki ne a hakan nan zaka iya ajiye mata huduma ba biyu ba" tayi maganar dan ta kwantar masa da hankali, Jin shiru be bata amsa ba yasa ta maida kanta jikinsa ta kwanta tana shafa gashin dake kwance a qirjinsa, yasan me take da buqata dan haka ya hadiye duk wani bacin ran da tunanin Umaimah ya taso masa dashi ya shiga qoqarin bata nutsuwa, hankali yake tafi da ita yana taba duk inda yasa zataji dadi a jikinta, wata irin miqa tayi saboda ziyarar daya kaiwa qasanta da bakibsa, qirjinta dake a cike kuma a tsaye tamkar bata shayar da yaro ba suka girgiza take yaji wani abu ya taso masa tun daga tsakiyar kansa ya dire a tafin qafarsa yanda kasan an watsa masa ruwan sanyi jikinsa ya hau karkarwa lokaci daya kuma mararsa ta murda yaji wani abu me kama da Sha'awa yana bin jikinsa seya saketa da sauri ya dago suka fuskanci juna, yanda gashin kanta ya bazu da idanunta da suka jirkice suka qarawa abinda yakeji a jikinsa kaifi da saurin gaske ya kaiwa bakinta cafka ya shiga aika mata saquna masu nauyi har abin nasa ma ya bata tsoro dan bata fahimci yanayin daya shiga ba, qoqarin shigarta taji yanayi da zafi zafi Mamaki da Al'ajabi tareda tsoro suka dirar mata lokaci daya data tuno da karonsu na farko sannan mamakinta yaushe har haka ta faru? Tsayin shekara uku tun karonsu na farko be sake hada jikinsa da nata ba duk abinda zeyi mata iyakar tayi amfani da hannunsa ko bakinsa amma yau gashi dagaske taga yana qoqarin shigarta seta takure jikinta ta shiga tureshi duk wutar feeling din data taso mata tuni ta mutu ta shiga zare ido tana nema ceto dan riqon daya mata bana wasa bane "Ki tsaya dan Allah ki tsaya mu gwada" ya fada cikin wata rawar murya kamar me kuka yana qara dannan kansa jikinsa wata azaba ta ratsata saboda samun damar fara shigarta da yayi se kuma taji ya mata wata irin matsa ya saki ihun da kana jinsa kasan bana jin dadi bane sedai wahala kafin jikinsa ya dauki rawa fiye da farko se kuma taji wani abu kamar ruwa yana mamala a jikinta take kuma ya saketa ya kwanta kan gadon ya shiga juyayi yana sakin nishi me hade da gurnanin Azabar da yake ji a marar sa. Tuni ta dire itama ta take qafa dukda radadin da takeji yana ratsata ta zagaya bangaren da yake da sauri ta riqeshi ganin ya danne mararsa da hannu yana malele kuwa me ruwa a kusa tuni ta fara hawaye shikanshi qarfin hali yakeyi amma abinda yake ji da zeyi kukan da ba haka ba cikin kidima tace "Ko naj na kira Hajiya?" Yayi sauri daga mata hannu alamar Aa seta sake cewa "To mu tafi Asibiti?" Nan ma hannun ya daga mata kafin ya bude baki dakyar yace "Ki dakko mun magungunana na manta yau ban sha ba". Da gudu ta diba shaf ta manta da babu kaya a jikinta saboda rudewa ya bita da kallo yanda bayanta yake juyawa take wani abu ya qara taso masa daya fahimci shi yake sake ta'azzara ciwon da yake ji a Marar tasa kamar an kunna masa wuta dan haka ya daga murya dakyar yace "Zo ki saka kaya" seta sake juyo masa gaban ya runtse ido da qarfi yana kiran sunayen Allah. Dakyar da taimakon ubangiji ciwon ya lafa masa bayan yasa magungunan sukayi jugum jugum musamman Humaira da gaba daya ta tsure a ranta tunani takeyi yanzu kuma meya sameshi? Se kace abu ace duk sanda ze kusanceta se wani mummunan abu ya faru dashi ita kam ta barankadi. Murmushi yayi mata ya miqa mata hannu ta iso gare shi yana kallon idonta da duk ya hargitse yace "Menene duk kika tsure? Ina ganin kamar fa na fara samun lafiya dan yau naji wani abu dana kalli jikinki kuma kinga nan ma harta motsa" yayi maganar yana dora hannunta akan jikinsa da har sannan bata gama daidaita ba daman kuma duk sanda ciwon ya motsa masa yana fuskantar haka Gabansa ya tashi amma bana jin dadi ba na zallar Azaba da ciwo. Saurin janye hannun tayi cikin kunya ta kwanta a jikinsa tana cewa "Nidai babu ruwana daman gari na wayewa zamu tafi Asibiti a dubaka dan hankalina ya tashi da yanayinka, ko sanda kana Asibiti banga kayi murqusus irin haka ba" "Yes baby ai ko baki fada ba dole naje Asibiti dan na samu tabbacin abinda nake yaqini in sha Allahu na samu lafiya Baby" ya qarasa yana qanqameta da haka bacci ya daukeshi, irin baccin da rabonda yayi shi tun kafin a daura auransa da Humaira. UMAIMAH *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 80 UMAIMAH Washe garin ranar ta tashi da sanyin jiki fiye dana ko yaushe, yau kam ko arziqin daga hannun bata samu a gurin Mama ba data gaisheta da alama fushi takeyi da ita dagaske, hannu ta saka ta share guntun Hawayen daya zubo mata a ranta tana ayyana me yasa Maman take mata haka? Batayi fushi da ita bama ya ta qare? haka ta ringa ayyukan gidan da suka zame mata jiki tun tana jin wahalarsu harta saddaqar ta haqura dan ruwa da iska babu abinda yake hana tayi gashi wata qudura ta ubangiji a tsahon kama aikin nata batayi wani shahararran ciwo da ze saka a daga mata a qafa harta samu damar fita akaita Asibiti taga waje ba, ita kam ta manta ma yanda unguwarsu take yanzu shekararta Uku da watanni a kulle cikin gida kamar wadda ta kashe mutum. Tana cikin share tsakar gidan Bayan La'asar saboda ruwan sama da akayi yazo da qura ta gama sharar ta tattarata guri daya ta fita Gareji inda babban Dustbin dinsu yake ta juye akayi sallama cike da mamakin wadda take gani a gabanta ta saki abin sharar tana kallonta lokaci daya wata irin kunya ta lullubeta. Rumasa'u ce tsaye gabanta da qaton cikin da zata iya juye shi a ko yaushe tayi qiba tayi kyau badan sanin data mata bana wasa bane tsaf zata iya cewa kamace, tambayar da takeyiwa kanta yaushe Ruma tayi aure har gata da ciki amma bata da labari? Kamar yanda Umaimah ke kallon Ruman itama haka ta zuba mata ido tana so ta tantance itan ce ko kuwa a hankali ta kira sunanta Umaiman ta dago ta kalleta kadan ta sake sunkuyar da kai lokaci daya kuka ya kwacewa Ruman ta matsa kusa da uta babu bata lokaci suka rungume juna suka shiga kuka kamar an aiko musu da mutuwa "Wane irin abu ne haka zaku zo kan hanya kunawa mutane koke koke ke daga zuwanki bakiga halin da take ciki ba zaki daga mata hankali? To saketa juya ga megidan naki can a tsaye daman be wuce ba" Abba daya shigo ya fada cikin fada fada se Ruma tayi qarfin halin sakin Umaimah ta kama hannunta suka shige ciki Abban na tsaye yana sababin akan me daga zuwa zata sakata kuka da tsohon ciki salon wani abu ya sameta. Su Umaimah kuwa dakin da take suka shige suka sake rungume juna suna garsheqar kuka, seda sukayi me isarsu, irin wannan damar Umaimah ta dade tana nema ta samu abokin kuka daze fuskancin dacin da takeji, dakyar Ruma ta daidaita nutsuwarta ta miqe tana cewa "Bari naje mu gaisa da Mama na kuma sallami Barr dan ziyarar tawa ta canza akala" seta fice tana jan qafa da alama cikin nata yayi nauyi dab take da saukewa. Mama kanta tayi mamakin ganin Ruman dukda tasan tayi aure kuma bata ga laifinta na qin sanar dasu na saboda ta dade da sanin Umaiman ta watsar da ita kamar yanda ta watsar da duk sauran qawayenta na kirki ta cicciba ta fita, Mijinta Barr na tsaye jikin motarsa yana jiranta dan ta sanar masa ba zama zatayi ba tun kafin suzo Kano dan a Sokoto take aure take nanata masa idan sunje zataje gidansu Umaiman da ya haddace sunanta saboda yanda take yawanyin hirarta, ta rasa number ta kuma tambayo duk qawayensu bata samu ba dan haka jiya suka zo yau tayiwa gidan tsinke danta gaida Mamanta kuma karbi number Umaimah se gashi taci karo da sabon Al'amari. "Har kin fito?" Barr ya fada yana qoqarin bude mata mota seta yi qasa da kai saboda kar yaga idonta da sauran hawayen dake ciki tace "Kaje kawai Barr zuwa bayan Magriba se ka dawo la daukeni na ma tarar da Umaiman tana ciki". "Are you ok? Yanaga kamar ma kuka kikayi?" Ya fada yana matsawa kusa da ita tareda nazarin fuskarta setayi saurin juyawa dan tasan yanzu inya fara jera mata tambayoyi ba sauqi tace "Kaje kawai idan mun koma gidan zan gaya maka koma menene" ta shige gidanta barshi yana binta da kallo tareda hasashen meya samu qawar tata tunda tace tana ciki ko duk kewar ta ce ta sakata kuka haka yaja motarsa ya tafi kafin Magribar tayi ya dawo ya dauketa. Ruma kuwa dakin Umaimah ta sake komawa, tana nan inda ta barta ta zubawa bango ido alamar tayi nisa cikin tunanin da takeyi hawaye suka sake kawowa a idon Ruman data qarewa Umaimah kallo, ko a hasashe bata taba tunanin akwai taskun da ze sameta ta dawo haka ba, ta tabbata akwai wani babban Al'amari daya faru wanda bata da masaniya seta zauna a hankali ta dafa kafadar Umaiman tayi firgigit ta kalleta a tare kowacce ta sake fashewa da kukan da take riqewa suka rungume junansu kuka Umaimah takeyi me nuna raunin ta da irin halin da zuciyarta take ciki wanda tafe yake da tarin nadama da dana sani tareda neman mafita. Tun Ruma na kukan itama har tayi shiru ta shiga rarrashin Umaiman da dakyar ta iya hadiye kukanta badan ta gama gaba daya ba sedai kawai ta samu sauqin nauyin abinda ya danne mata qirji. "Umaimah ki fada mun meya sameki, ki fitar dani daga rudanin da ganin yanayinki ya jefani meya faru?" Ruman ta fada cikin qoqarin son hana kanta sake fashewa da kuka dan yanayin Umaimah ya raunata mata zuciya da yawa. Seda Umaiman taja numfashi tana riqe da hannayen Ruma biyu kafin ta bude baki cikin muryar kuka tace "Komai ma ya faru Ruma ni yanzu abinda kadai ya ragemun ganin ranar da zan koma ga Allah dan a duniya na rigada na rasa kowa da komai nawa" "Kiyi mun magana a bude Umaimah kiyi mun bayani yanda zan fahimta, kamar yaya kin rasa kowa? Ga Mama da Abba na gani da Ransu basu mutu ba Yanayin dana ganki na san cewa akwai wani al'amari mara dadi a tareda ke Umaimah kin ganki kuwa kinga yanda kika koma?" Ruma ta fada tana kallon Umaiman tareda dauke kwallar dake qoqarin sake dawo mata. Umaimah ta dauke kanta gefe tana goge nata hawayen nauyi da kunyar Ruman ya rufeta idan ta tuna wukaqancin data mata a baya se taji bata cancanci ta sake hada ido da ita ba, Ta banzatar da ita a matsayinta na Aminiyarta tunta yarinta da take saita ta a hanyar kwarai take kuma gaya mata gaskiya. Rabonta da Ruman tun Haihuwar Bibi, qarfi da yaji ta yakiceta daga rayuwarta saboda tana gaya mata gaskiya itama kuma tayi zuciya ta fita daga sabgoginta kamar yanda ta fada Umaiman bata da Aljanna ballantana taci gaba da binta tana wulaqantata tun daga nan suka yanke alaqa bata sake ganinta ba se yau da kwatsam ta fado gidansu kamar jifa a yanayin da tayi mamaki kwarai. Matsa hannunta Ruman tayi cikinsigar lallashi tace "Ki tuna a baya babu abinda muke boyewa juna, Rumanki ce fa idan baki sanar dani damuwarki ba wa zaki gayawa?" A hankali Umaiman ta bude baki muryarta na rawa tace "Ruma rayuwata ta gamu da qalubale kala kala a halin yanzu ina cike da Nadamar abubuwan dana aikata a rayuwata na godewa Allah daya kawo mun ke a daidai lokacin danake buqatar taimako wlh Ruma a yanda nake ji na tabbata wata rana za'a iya wayar gari a tarar da gawata zuciyata ta buga na mutu saboda irin baqin cikin da nake kwana dashi nake tashi" Ki dena fadar haka Umaimah duk abinda kikaga ya samu bawa a rayuwarsa da sanin Ubangiji" "Haka Ruma kuma duk abinda ya sameni ni na hawa kaiba, halina ya jefani a yanayin danake ciki kuma nasan da cewar haqqin Khalil ne ya fara bibiyata tun yanzu, Ruma banida nutsuwa bana iya bacci har na rasa me nake tunani kaina da qirjina tamkar zasu fashe haka nake jinsu gashi a cikin gidan nan babu me saurarata kowa haushina yakeji basa kulani sun gazayi mun uzuri su karbi cewar tawa kalar qaddarar ce a haka" Umaimah ta sake fada tana fashewa da kukan daya fi nada rauni ita dai Rumana riqe da hannu ta tana matsawa alamar rarrashi tana kuma qoqarin gano inda bakin zaren maganar Umaiman yake a hankali ta Sake ce mata "Qawata me yayi zafi har haka, me kika aikata da har su Mama sukayi fushi dake? Yanzu yan uwanki da har kwatance akeyi daku saboda yanda kowa ya shaida qaunar dake a tsakaninku suka banzatar dake me kika aikata Umaimah?" Shiru Umaiman tayi kafin ta nisa a nutse ta shiga warware mata iya abinda take ganin ya kamata ta sani. Ruma ta ringa kiran sunayen Allah saboda rudanin da labarin Umaimah ya jefata, a sanyaye tace "Umaimah kinyi kuskure kin kuma shafawa kanki baqin fentin da gogeshi zeyi wuya domin kin taba martabar da ba kowa zaka keta masa ya dauke kai ba, na tabbata yau da ace rigimarki ta tsaya iya kan Khalil da tuni kowa dade da mantawa saboda tsakanin Mata da Miji daman ana sabawa kuma a koma a zauna kamar ba'ayi ba amma Uwa fa Umaimah kin keta alfarmar Mahaifiyar sa koda ace Allah ya qaddara da sauran zama a tsakaninku a duk sanda ya kalleki se wannan abun ya dawo masa sannan mafi muni shi a karan kansa kin bar masa tabon da har abada baze manta dake ba a kullum ina gaya miki ki dena biyewa zuciyarki ki ringa amfani da kwakwalwarki yanzu kin gane abinda nake nufi? Ita zuciya a koda yaushe tana qawata mana son ranmu duk kyau ko munin abu yayinda kwakwalwa takanyi lissafi ta tantance abinda ya kamata da wanda be kamata ba. Na tabbata a lokacin da kin yi amfani da Tunaninki ba son zuciya ba da yanzu haka bata faru ba amma duk da haka lokaci ne qure miki ba kina da damar ko tubarwa Allah ki kuma nemi gafarar duk wadanda kika batawa amma a farko se ke a karan kanki kin yarda da cewar kinyi ba daidai ba" "Na nawa kuma Ruma na rigada na yarda da cewar na aikata kuskure nayi dana sanin komai daya faru rashin mafitar yanda zanyi na gyara shine abinda ya dameni yake cin zuciyata duk dare da wannan baqin cikin nake kwana nake tashi. Iyayena muna zaune gida daya dasu Ruma na rasa alfarmar da zasu amsa koda gaisuwata yan uwana kaf babu meyi mun magana na zama kamar wata mujiya a cikinsu yau tsayin shekara uku da watanni kenan Ruma ban sake saka qafata a qofar gidan nan ba tunda aka sallamoni daga Asibiti Abba ya kafa mun dokar babu fita kullum ina zaune nike aikin komai a cikin gidan nan amma dukda haka be sa sun rangwanta mun ba a kullum qara kyarata da hantarata akeyi a cikin gidannan a ganina ko Mutum na kashe ai iyakar abinda zasuyi mun kenan" Umaimah ta fada muryarta na rawa se Ruma tayi qaramin murmushi tace "Umaimah kenan iyayenki da yan uwanki suna yi miki haka ne saboda ki gane kuskurenki kuma koda ace kinyi nadama ke a karan kanki bana zaton kin nuna musu hakan kinga kuwa dole zasu ci gaba da nuna miki halin ko in kula tunda baki nuna musu kema kin gane kuskurenki kuma kin shirya gyarawa ba". "Toh ya zanyi, ta yaya zan nuna musu na karbi kuskurena Ruma?" Umaiman ta katseta se Ruma tace "Tun da al'amarin nan ya faru wa kika taba samu a cikin su ke dashi kika bashi haquri kika nuna musu cewar kinyi nadama kuma kin karbi kuskurenki?" Ruma ta fada tana tsareta da ido a sanyaye tace "Babu" "Dama na tabbatar da amsar Babu ce danna sanki farin sani tun ba yanzu ba baki san kiyi laifi ki bada haquri ba nayi tsammanin aure yasa kin canza ashe har yanzu kina nan da baqar kafiyarki da da babu abinda take ja miki kullum se wahala. Har ki iya zama tsayin shekara uku Mahaifanki suna fushi dake ku kwana gida daya ku tashi bama kya tsoron ki mutu a wannan halin me zaki gayawa Allah meye hujjarki ta kasa neman yardarsu?" "Wlh Ruma nayi, Abba cewa yayi karna qara gaisheshi Mama ta hanani shiga dakinta itama idan na gaidata ba amsawa takeyi ba ya zanyi?" "Ya zakiyi kike tambayata, saboda sunce karki sake gaidasu se kiji ki dena gaishe shin saboda tsabar rashin tunani irin naki ai a lokacin nema ya kamata ki daura dambar gaidasun da duk wata kyautatawa da kika san zata saka zuciyoyinsu yin sanyi su sauka da fushin da sukeyi da ke amma se kika zauna kina jira su gaji da fushin su sakko su su nemi kushirya kome ashe ma ke kika haife su basu suka haifeki ba" Ruma ta fada fusace se Umaimah tayo saurin cewa "Ba haka bane wlh..." "Na sanki Umaimah babu abinda zaki gayamun wanda ba gaskiya ba na yarda idan na rantse bazanyi kaffara ba muguwar zuciyarki har a yanzu tana ayyana miki cewar abinda kikayi daidaine shiyasa kika qi Sasantawa da Mahaifanki ki nemi gafarar su to tun wuri idan kin shirya gamawa da duniya lafiya Umaimah ki san abinda kikeyi ki kuma maida Al'amuranki ga Allah shine kadai Mafita a gareki yanzu". Maganganu masu shiga jiki Ruman ta ringayi mata ta fito mata da laifukanta ta kuma bata hanyoyin da zata gyara har wata nutsuwa Umaiman taji tana sakko mata saboda ta samu ta amayar da abinda yake cinta kuma an bata mafita in sha Allahu kuma zatayi amfano da duk abinda Ruman ta fada mata. Nisawa Ruma tayi ta gyara zamanta tace "Toh yanzu ina yaranki, suna tare dake ko ya riqesu?" "Suna gurinsa, tunda muka rabu ma se jiya aka taba kawo su kuma basu dade ba matarsa tazo ta daukesu" Umaimah data rafka tagumi ta bata amsa se Ruma tayi wani murmushi me ciwo tace "Kayya kin gani ko? Duk haukanki da tashin hankalinki babu abinda ya hana gashi nan tana zaune dashi ke kuma kina gida cikin qunci da takura meye ribar abinda kikayi? Ai wlh Umaimah da ace kinsan me kikeyi tundaga sanda aka ce miki an rigada an daura aure ya kamatavki zubda makamanki saboda kinsan cewar yaqin ya wuce kan Khalil Ubangiji yayi ikonsa idan kika matsa abinda bazaki so ba ze faru gashi kuwa" "Harta haihufa Ruma" Umaiman ta sake fada kamar zatayi kuka wani mugun kishin Khalil din yana taso mata amma tayi qoqari ta hadiye is Ruma ta tafa hannu tace "Kinji ba, to qila da baki bar gidan bama ki mutu tunda baki yarda da qaddara ba Rabon sa na jikinta da a titi kike so ya haifi dan" se kuma ta kama baki tace "Ikon Allah bashi da haqqinki nakasar da kika so ja masa Allah beyi ba". Yanda kasan ta cakawa Umaiman Mashi a qirji haka taji, Khalil ya samu lafiya kenan yanawa yarinyar nan kalar abinda yake mata shiyasa harta kasa ganeta tayi qiba tayi fresh jiki duk madara kawai ta fashe da kuka ba tareda ta shirya ba tunanin Khalil na Mu'amala da Humaira kamar ze zautata "Tab toh Allah ya kawo miki dauki Umaimah gashi can ana kiran sallah bari mu tashi nasan da an idar Barr ze dawo" Ruma ta fada tana yunqurawa Umaimah ta rage qarfin kukanta tana cewa "Baki fada mun yanda naki al'amuran suka kasance ba se kawai ganinki nayi da ciki bayan tsahon lokaci" "Wannan labarin wata rana ne Umaimah se hankali ya kwanta kedai kiyi hanzarin gyara alaqarki kafin lokaci ya qure miki" daga haka ta shige bandaki ta barta tana jan Majina. A dakin sukayi sallah har bayan sun idar seda Ruma ta sake yi mata tunatarwa akan yawan ibadah, "Ki daure Umaimah cikin dare idan kin juya ko raka'a biyu ce kiyi ki kaiwa Allah kukanki yafi kwanciyar da kikeyi alhalin ba bacci kike ba bakinki karya zauna shiru daga ambaton Allah kiyawaita yin tasbihi da istigfari sannanki rage damuwa dan babu abinda zata miki sedai ta haifar miki da ciwo ta lalata miki jiki ko a yanzu baki ga yanda kika koma ba kamar me ciwo duk ina gayunki Umaimah kalli fatarki yanda ta yamushe kamar ta tsohuwa" "Uhm Ruma kenan har wani maganar gayu kikeyi keda kike cikin nutsuwar zuciyata data jiki ke kike buqatar kwalliya wa zanwa" Umaimah ta fada tana janye tagumi kafin Ruman ta bata amsa wayarta ta shiga qara ta daga ganin Mijinta ne yake kira ya sanar mata yana waje seta miqe bayan ta kashe wayar tana gyara gyalenta Umaiman ta kalleta tace "Badai tafiya zakiyi ba?" "Tafiya zanyi mana zamuyi waya idan kuma na samu dama gobe ko jibi zan dawo" ta bata amsa se Umaiman ta miqe tsaye itama tana cewa "Na fada miki banida waya yanzu, dan Allah ki dawo Ruma wlh bakiji yanda naji dadin zuwan ki ba da zan samu ace kullum kizo dana rage kewa" Dariya Ruma tayi tana cewa "Lallai ko kiyi qoqari ki gyara kura kurenki zakiji dadin rayuwarki Umaimah dan rabuwarki da Khalil bashine yake nufin rayuwarki tazo qarshe ba kici gaba da Addu'a in sha Allahu zaki samu madadinsa a gaba" daga haka tayi waje Umaiman ta bita a baya kamar kazar da kwai ya fashewa gaba daya bata ji dadin kalaman Ruman na qarshe ba yanda ta nuna bata da sha'awar ta koma gidan Khalil kenan. A tsakar gidan suka tarar da Mama tana qarasa girki dare Anty na zaune daga bakin qofarta suna hira se sannan Ruma ta gaida Anty ta amsa da fara'a Mama tace "Kin fito Ruma?" "Na fito Mama ya dawo zamu wuce ne" ta bata amsa tana sunkuyarda kai, taso a daki suka tarar da Maman tayi mata magana amma babu komai zata dawo daga haka ta yi musu sallama Umaimah ta rakata bakin qofar shigowa kamar karta barta ta tafi yau din jinta tayi kamar sallah ta samu abokin hira. Seda taji Ruman ta saki Get kafin ta dawo, gurin Mama ta wuce kanta a qasa tace ta kawo ta qarasa girkin "Jeki abinki na gama kwashewa kawai zanyi" Maman ta fada jin haka seta wuce ta fito da kular da ake zubawa Maman ta sauke tukunyar Tuwon taja gabanta ta shiga kwashewa a leda ganin haka yasa Maman ta sakar mata ta wuce dakin Abba dan ta gyara Umaimah taci gaba da kwasar tuwon maganganun Ruma na dawo mata sedata gama ta tattara tukunyar da sauran kayan gurin kafin ta koma daki dan an kira sallar Isha. Tana nan zaune taji shigowar Abba ta miqe a hankali ta fita kamar munafuka ta rabe daga bakin qofa tayi masa sannu da zuwa worn nta na bugawa da tsoron meze biyo baya amma ga mamakin ta se ji tayi ya amsa fuska a sake har yana tambayarta gida kafin ya shige ciki abinsa. Ta sauke ajiyar zuciye me nauyi ta koma ciki a ranta tana ayyana komai zezo da sauqi da yardar Allah. Washe gari da wuri ta kama ayyukanta kamar yanda ya zame mata jiki qarfe bakwai ta gama komai saboda ranar makaranta ce ta shirya abin Karin Abba a Try yanda akeyi ta ajiye a bakin qofarsa dan kullum haka takeyi idan ya gama ma a nan za'a aje kwanukan ta dauko. Daki ta koma ganin Mama bata fito ba tayi wanka ta zura rigarta ba tareda ta shafa mai ba dan ya qare kuma wata beyi qarshe ba balle ta samu ta siya a pocket money ta. Seda taji motsin Mama suna gaisawa da Anty kafin ta fita, ta gaida Antyn da take mata wani gani gani yanzu a tata fahimtar tunda ta aurar da Ummu-Salma ta samu gidan daula ta ke wani buda hanci itama ta aurar da ya a ganin Umaimah fa. Seda ta jira Mama ta shiga falonta kafin ta bita jiki babu kwari a bakin qofa ta dakatar da ita ganin tana shirin shiga tace "Lafiya?" Seta diririce, dakyar ta iya cewa "Aa daman gaisheki zanyi" se maganar tata ma ta bawa Maman dariya ta murmusa tace "Toh yau kuma ina a tsakar gida muka saba gaisawa yau ta musamman ce da se kin biyoni har daki?" Raurau tayi da ido hawaye na shirin kwace mata daman tasan fushin Abba me sauqi ne na Maman tafi tsoro, durqusawa tayi daga bakin qofar da take murya na rawa tace "Dan girman Allah Mama kiyafe mun ki barni na ringa shigowa dakinki ina gaisheki" ta qarasa kuka na kwace mata Mama ta juya ciki abinta tana cewa "Kekam idanunki basa ciwo kullum kuka kamar matar Mamaci? Gaki ga dakin ai bismillah ki shigo" ta wuce cikin daki ta barta a qofar falon tana kuka, ita kam tana rasa ajin da zata saka Umaimah lokuta da yawa ta rasa wauta ce ko gabunta suke damunta se Allah amma Al'amarinta bayan Iskanci na qashin kai harda rashin cikakken wayo ma duk ta hada. Umaimah kuwa ta gama kukanta ta tashi ta koma daki ta dora, to ita tayaya zata nuna musu ta gane kurenta bayan babu fuska? Ai ya kamata koda sau daya ne su saurareta duk wanda ya kalleta ko bata fada ba ai yasan tana cike sa nadama da dana sanin abubuwan data aikata. Da zata gaida Abbanma dai kasa shiga falonsa tayi ta durqusa daga bakin qofa ya amsa mata faran faran kai ba zaka ce akwai wani grudges tsakaninsu ba. Haka ta wuni tana bare bare da Maman ta yunqura zatayi abu zata karba koda baya cikin ayyukan da take musu a gidan so takeyi tayi mata magana ta roqeta amma tsoron yanda zata karbeta takeji ita kuwa Maman tana ankare da ita tsaf sedai tayi murmushi a ranta da zahiri ko a kullum cikin nema mata shiriya a gurin ubangiji takeyi dan ta yarda fushi bazeyi mata magani ba. A haka suka sake kwashe sati biyu kuma Ruma bata sake zuwa ba damuwa ta sake mata rubdugu ta kasa sakin jiki kamar yanda Ruman ta gaya mata dukda tayi Namijin qoqarin ranar Juma'a dasu Nuratu sukaje gidan kamar yanda suka saba har bakin qofar Mama taje ta durqusa ta gaishe su ai kam seda sukayi Suman zaune na sakanni kafin suka hada baki gurin amsa mata kowacce cike da Mamakinta, yanda ta sunkuyar da kai tana hawaye kamar wadda tazo Maula ya taba su amma suka dake, jin daga gaisuwar bata qara cewa komai ba suma basu ce mata ba ta gaji da durquson ta tashi Anty Hafsa tace "Allah ya yayewa yarinyar nan abinda yake damunta" Mama ta amsa da Amin kafin tace "Haka take kullum zatazo bakin qofar nan tayi ta zubar da hawaye ni kuwa kanzil bana ce mata daga nan har randa qiyama zata tsaya muddin bata budi baki tayi magana ba mu zuba mu gani itace a wahale". A haka rayuwa taci gaba da gara mata kullum kuma maimakon ta samu sauqin Al'amura qara tsananta sukeyi a cikin wannan yanayi Ummu-Salma diyar Anty da akayi aure wata goma kenan tadawo gida haihuwa. Nan dakin da take Abba yace Ummu-Salman ta zauna dake ita bata da Matsala kamar qanwarta lafiya lau suke zaune zuwan nata ma seya zamo mata wata sa'ida tubda ko babu komai ta samu abokiyar hira musamman da yanzu itama tayi aure ta fara sanin rayuwa da yanda take cikin hikima take nunarwa da Umaiman kurakuren daya kamata tasha kansu tamkar dai maganganun da Ruma ta gaya mata sedai tsoro yasa har sannan ta kasa tunkarar Maman ko Abban kai tsaye da magana se rara gefe takeyi da suke nuna tamkar basu san me take ciki ba. Satin Salma daya da dawowa gida ta haihu, Umaimah ce ta zama yar saka ruwan wanka bisa Umarnin Abba ga damuna a lokacin wata rana haka take zama kamar zata zauce saboda hayaqi gana girki ga na ruwan wanka safe da yamma shikansa girkin ya qaru saboda yan zuwa barka haka yan uwan Anty zasuyita yada mata magana wasu a fakaice wasu kai tsaye yanda ta ringa musu a baya wai ta baro daula ta dawo Boyi boyi da zaman dabaro, ana gobe suna wata yar Yayar Anty da suke sa'anni zamanin yammatanci tare sukayi tana yawan zuwa gidan haka Umaimah zatayi ta gwaba mata magana wai tazo cin arziqi saboda gidansu Babu kullum tana tafe yawon kwadayi abun na bala'in yiwa Nabilan ciwo amma lokacin se Anty ta hanata mayar mata da martani. Ana gobe suna tazo barkar Ummu Salman itama da tsohon cikinta sukayi kicibus da Umaimah na kwashe ruwan wanka tayi yarkace yarkace dan ba qaramar wuya taci ba kafin itacen ya kama Nabilan ta kalleta cikin izgilanci ta kalli wadda suka shigo tare tace "Kinga ma shikenan ina zancen neman me zaman dabaro ga wata bari mu shiga na tambayi Anty inda suka samota dan da gani zatayi aiki sosai sannu baiqar Allah" yanda tayi maganar seka rantse bata gane Umaiman ba nan kiwa tsabar wulaqanci ne daman Allah Allah take tazo ta ganewa idonta yanda akace Umaiman ta koma lokacin biki basu wani ganta ba daki ta ringa shiga tana kulle kanta har aka gama yanzu kuwa bbau dama tunda an dora mata Alhakin dora garwar wanka ya ta iya da ranta. Maganar Nabilan ta mata ciwo kwarai har seda ta zagaya bayan gida tayi kuka ta more ta yarda duk abinda ta gani ba komai bane akan irin tsiyatakun data shuka a baya. Washe gari ranar suna sega yaranta babu zato an Kawo su suka wuni tareda sauran cousins dinsu duk inda suka gifta se anyi maganarsu ta haka kuma za'a zageta wasu a fakaice wasu kai tsaye kamar yanda suke fada ai ba tsoronta sukeji ba, Mijin da take taqamar ya tsaya mata yanzu babu ita da banza duk daya suka a gurinsu da Magriba aka zo daukar yaran seda aka sha daga da Bibi kafin ymta yarda ta bisu tana kuka sosai Driver su daya kaisu ya dauke su haka rayuwa taci gaba yau baqi gobe tsumma. GIDAN KHALIL Washe gari hankalinsu be kwanta ba daga shi har Humaira seda sukaje Asibiti. Dr Mahmud likitan da yake dubashi ya kalleshi da murmushi bayan ya gama examining nashi ya kuma hada da bayanan da yayi masa akan abinda yaji a daren jiyaj fuskarsa dauke da murmushi yace "Kaga abinda muka gaya maka ko? Dama na gaya maka bazamuce ka rasa lafiyarka gaba daya ba haka nan ba zamu baka tabbacin zaka warke ko kuma lokacin faruwar hakan ba amma gashi yanzu cikin yardar Allah alamun nasara sun fara bayyana. Abinda nake so dakai shine kayi qoqarin kiyayewa kar kace zaka takura kanka kamar yanda al'amarin jiya ya faru ba tareda ka shirya masa ba muna fatan hakan taci gaba da faruwa amma kayi haquri karkace zakayi gaggawa kabi komai a sannu ciwon kuma da kaji wannan dolene idan kayi la'akari da cewar ka kwashi shekaru ba tareda irin saqon nan yaje kwakwalwarka ba jijiyoyin da suke da alhakin hakan duk sun kwanta dole yanzu da aka motsa su za'a dan sha wahala kafin su daidaita su koma aiki yanda ya kamata shiyasa nace se kabi a sannu banda Garaje in Allah yayarda a dan lokaci komai ze daidaita dan Alamun nasarar da qafinsu sukazo tinda har kace kaji alamar kayi releasing sannan koda ace lafiyarka ta dawo zaka fuskanci wannan matsalar ta saurin Inzali amma kar hakan ya dameka da sannu komai ze daidaita". Khalil dai baki kamar gonar auduga inda Humaira ta sunkuyar da kai qasa a ranta tana cewa wannan likitan bashi da kunya me makon yace ta fita. Seda ya canza masa magunguba kafin suka miqe zasu fita sukayi Musabaha da Khalil ya kalleta tana masa se anjima yace "Madallah Amarya ina sakw tayaki murna, se a lallabamun patient dai kar ayi masa garaje". Da kusan gudu ta fice daga office din suka rakata da dariya kafin Khalil yabi bayanta, a mota ma tasa ta yayi da tsokana ita dai ta kanne taqi kulashi, a gida Hajiya ta ringa tambayarsa meya faru saboda farincikin dake kan fuskarsa ya kasa boyuwa amma rashin kunyar tasa bata kai ya iya mata bayani ba balle Humaira se ta barsu akan kawai dadin zama ne domin ita shaida ce irin zaman da sukeyi me tsafta da girmama juna. A haka yaci gaba da lelen lafiyarsa kamar yanda likitan ya fada kuma beyi garaje ba dan be sake attempting tabata ba sedai suyi abinda suka sabayi wanda shima yanzu baya iya jurewa da yawa saboda jikinsa ya fara komawa daidai daya fara tabata zeji yana son kasancewa da ita sedai wani lokacin kafin yakai ga jikinta ma zeyi releasing daga nan komai ze sakeshi wannan al'amarin ya dameshi har yaso yafi sanda ya tabbatar da basho da lafiyar gaba daya shiga tashin hankali saboda a yanzu baya iyayi mata abubuwan daya saba a baya hakan kuma na damunta wanda ya fara fahimtar hakan a tareda ita. Walwalarta ta ragu, duk sanda ya jagwalgwalata ba tareda ta samu nutsuwa ba ranar wuni zasuyi babu dadi ita dai bata taba bude baki ta masa qorafi ba amma yasan abun yana damunta. Shi kuma ciwon da yake damunsa da mutuwar jikin da yake fuskanta da zarar ya fitar da abinda ya dameshi ne suke hanashi samar mata da nutsuwar, gashi daya fara tabata yanzu jikinsa ze amsa har ya fara jin dama ya zauna a yanda yake yafi samun kwanciyar hankali da iyalinsa dan yanzu wannan sabon Al'amarin na neman ya dagula musu lissafi. Tilas babu shiri ya sake tafiya India ganin likita, suka gama masa duk gwaje gwajen daya kamata suka qara masa magunguna tareda kalaman ban haquri akan komai zeyi daidai with time haka ya tattaro ya dawo cike da fargabar yanda zamansu zeci gaba da kasancewa sedai be yanke qauna ba Allahn daya farfado dashi shi ze bashi isashshiyar lafiyar daze cigaba da kulawa da ita. Wata uku cikin wannan yanayi Humaira ta fara zazzabi me zafi da Amai suna zuwa Asibiti gwajin farko aka tabbatar masa da tana da shigar ciki bayan an mata scanning suka sanar masa da watannin cikin uku da kwanaki. Seda numfashinaa ya tsaya na wani lokaci kafin ya dawo hayyacinsa ya rasa gane yanayin da yake ciki, tambayar kansa ya ringayi tayaya hakan zata kasance Humaira da ciki to yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da ita har da zata iya daukar ciki? Salati kawai ya ringayi a zuciyarsa da a'uziyya bisa ga tunanin da shaidan yake so ya darsa masa wanda ko kusa baya so ya samu gurbi a ransa yana kyautata mata zato kuma koda gaya masa akayi baze yarda ba dan haka baze taba bari tunanin yayi tasiri a ransa ba. Ita kanta bayan data farka daga bacci saboda ruwa da aka sakata sosai ta tsorata dajin wai ciki ne da ita, yanayin yanda ta firgice din ya sake darsa masa wani abu a ransa seya sulale ya fice daga dakin ba tareda yace mata komai ba zuciyarsa ta ringa bugawa kamar zata fito daga qirjinsa wani bangare kuma yana qoqarin kareta ta hanyar nuna masa ba laifinta bane, shiya kasance me son zuciya daya tilasta mata zama dashi alhalin bashida Lafiya tsayin shekara kusan hudu da yarinytarta tabbas dole cutarwa ta shigo ciki. Can ya samu waje ya zauna ya rasa kalar tunanin daya kamata yayi, yana zaune a gurin yaji an dafashi ya daga kai suka hada ido da Dr Mahmud daya dade tun daga nesa ya hangoshi ya ringa masa magana amma be amsa ba dalilin daya sa ya qarasa kusa dashi kenan. Cikin kulawa da tausayawa yake kallonsa dan a zatonsa matsalar dake damunsa ce ta sakashi zama haka ko gurinsa yazo baya nan tunda shigowarsa kenan shi dan haka yace masa suje office. "Khalil na sani akwai damuwa ga mutum lafiyayye ya gamu da ibtila'i irin wannan dole abin ze dameka sosai amma abinda nake so ka gane yawan damuwar kansa matsala ne domin yana iya kawo cikas gurin samun abinda ake buqata" Dr Mahmud ya fada bayanda suka zauna a office din se Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Dr samba wannan ne ya dameni baai tun farko na gaya maka na karbi qaddarata a yanda tazo mun, wannan wani al'amari me me daure kai ya sameni daban, yanzu haka maganar da nakeyi maka Matata tana cikin Asibitin nan munzo bata da lafiya kuma an tabbatar mana tana da shigar ciki har wata uku na kasa gane yanda hakan zata yuwu Dr nida bani da lafiya tsahon shekara uku da wani abu yanzu". *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 81 "Calm down Khalil calm down" Dr Mahmud ya fada kafin yaci gaba da cewa "kar ka bari shaidan ya jefa maka mummunan zato a zuciya shin baka yarda da matarka ba?" ya fada yana kallonsa cikin nutsuwa, se Khalil ya gyara zama yace "Dr na yarda da ita ba kuma na kawo tunanin cewar Humaira zata ci Amana ta ba amma yanda abun ya zo nake tunani taya ya haka zata faru Dr?" Se Dr Mahmud ya janyo system din gabansa ya kunna, File din Khalil ya binciko yayi shiru yana dubawa zuwa wani lokaci kafin ya daga kai yana kallonsa yace "Idan zan iya tunawa, ranar da kace kaji wani abu akan matarka kamar kace har releasing kayi ko?" Shiru Khalil yayi kafin a sanyaye yace "Hakane Dr amma bana tunanin wannan ya isa ace an samu ciki, na gaya maka duka faruwar abun ne wuce minti daya ba, ban samimu dama na shiga jikinta ba and before i know komai ya faru ya tsaya kuma bayan hakan ma ya sake faruwa kuma ko yaushe dai kamar yanda na maka complain wani lokacin sena fara qoqarin yi wani ma kafin nayi attempting nakejin ya fita daga nan kuma zanyi loosing interest da strength dina bana ko iya satisfying nata da romance din yanzu" yanda yayi maganar zaka karanci tsantsar damuwa da fargabar da yake ciki Dr Mahmud ya fadada murmushinsa yana cewa "To ina so ka yarda abinda ya faru a wancan lokacin dalilin samuwar wannan rabon ne har Allah ya baka qarfin yin abinda kayi. Kuma shi sperm da kake gani yana da matuqar sauri, inhar ya samu hanyar shiga jikin mace ko yaya take shikenan kuma kaga se akayi sa'a ita matar a lokacin a shirye kwanta yake koda yake daman Allah ya shirya faruwar hakan kaga wannan yana maka nuni da kaida Amarya duka sharp shooters ne, kaga Dayan Babyn ma kace sau daya akayi aka dace to ga wani ma idan lafiya ta samu se anyi taka tsan tsan idan ba haka ba Amarya zatayi ta jera babys ne duk shekara" ya qarasa maganar cikin zolaya kuma yayi nasarar saka Khalil din murmushi ya dauke kansa gefe Dr yaci gaba da cewa "Ka kwantar da hankalinka in sha Allahu waraka zata samu baby kuma naka ne karka kuskura shaidan yasa kayi kokonto akansa kaji ko?" Seya daga masa kai alamar yaji ya kuma samu nutsuwa a zuciyarsa dukda cewar daman baya zarginta da cin Amana amma abin ne yazo masa da rudani sannan kukan da takeyi sanda ya gaya mata tana da cikin ya qara dagula masa lissafi to kenan meye dalilin kukanta ita? Abinda ya kamata ya sani yanzu kenan. Sallama yayi wa Dr Mahmud ya fita, dakin da take ya koma ya tarar da it har sannan tana kukan seya nemi guri kusada ita ya zauna cikin nutsuwa yajata jikinsa yana cewa "Wai kukan me kikeyi haka ne kuma?" Lafe masa tayi ta rage kukan tana cewa "Habibi ciki fa, ni wlh tsoro nakeji baka san wahalar dana sha a haihuwar Aryaan ba ko shekara uku beyi ba na sake haihuwa" ta sake fashewa da wani kukan. Ajiyar zuciya me qarfi ya sauke jin dalilin kukan nata daya fi kama da shirme yana shafa bayanta yace "Shine kike kuka haka baki san haihuwa baiwa bace ba mutane da yawa nema sukeyi basu samu ba fa Humaira" "Amma da wahala baka san yanda ake jiba" tayi saurin katseshi se yace mata "Na sani da wahala amma karki butulcewa Allah ki kalli fa a yanayin da muke ciki amma dukda haka yayi ikonsa ya azurtamu da wannan cikin ai murna ya kamata kiyi ba kuka ba". Shiru tayi tana qoqarin rage kukanta a zuciyarta tunani takeyi shikenan kawai se a ganta da ciki bayan ita ba wani abu tayi ba wai to shi daman cikin daga sama ake samun sa ko yaya tunda dai na Aryaan tasan sunyi abinda ake samu wannan fa? "Ki share hawayenki kinji kiyi Addu'a Allah ya raya mana in sha Allahu kuma cikin salama zakiyi rainon cikin ki haifeshi ba tareda wahala ba. Ina son yara da yawa fa Humaira ina da burin na tara zuri'a kamar yara Goma sha haka duk nawa amma daga biyu kin karaya to wa kike so ya tara mun su?" Ya fada yana jan hancinta ta janye daga jikinsa tana cewa "Nidai uku zanyi tunda Maman Bibi tayi uku ai six sun isheka" "Ina dozen zakiyi in aka hada da nata ukun kinga 15 kenan s nayi Manaji" ya tsokaneta aiko ta zaro ido tana cewa "Tabdi qarya da ciwo wlh ba zan iya ba kawai ka haqura da abinda Allah ya baka shikenan banda ma kai biyar din ma ai Allah yasa musu Albarka ko?" "Haba mana nida nake zaton in kika fara haihuwa har sena ce ki bari kodan kasancewar ke kadai aka haifa a gidanku shine daga biyu zaki ce ba haka ba?" Seta miqe tana sake ce masa "To ai da dabansan ya cikin yake ba nima goma nace zan haifa idan na girma amma yanzu na fasa" ta shige Toilet ya bita da kallo yana mamakin yanda bakinta ya bude sosai yanzu ta rage shirmen yarintar da takeyi da koda yake tana shekaru Ashirin ne fa yanzu tabbas hankali ya ratsata tasan me take so da wanda bata so a yanzu. Yana zaune ta fito sega Nurse ta shigo dakin itama ta sake dubata ganin zafin jikin ya sauka ta bashi takaddar magungunan da aka rubuta musu da next appointment dinta ta basu. A mota suna tafe babu me cewa komai lokaci lokaci yake kallonta yanda tayi shiru alamar tayi nisa a tunani seya kama hannunta ta daga kai ta kalleshi ya sakar mata murmushi yana cewa "Komai zeyi daidai da yardar Allah kinji ki qara haquri" Murmushi ta maida masa kafin ta kwantar da kanta jikin kujera tana cigaba da tunanin da takeyi a ranta. Da suka isa gidan seda ya rakata ta kwanta kafin ya wuce gurin Hajiya dan da wuri suka fita be samu ya shiga ba bayan sun gaisa take tambayarsa jikin Humairan yace da sauqi yana shafa kai dan be santa yanda ze fadawa Hajiya maganar cikin ba, bari kawai yayi akan idan lokaci yayi da kanta zata gani be jima ba ya wuce office dan ya rigada ya makara ma. Guraren qarfe biyu Driver su Bibi ya kirashi, bayan ya daga yake ce masa "Alhaji, me sunan Hajiya ce gata nan tana ta kuka harda birgima a qasa nayi nayi ta shiga mota mu tafi taqi hatta da Malam sunyi banbaki amma ta kafe ba zata shiga ba" Khalil ya dafa kansa yana jinjina rigimar Bibi dan haka yace ya bata wayar tana karba kuwa ta fasa masa kuka me hade da ihu taqi cewa komai "Me akayi miki kike kuka har kina birgima a qasa?" Ya tambayeta seta tsagaita kukan dukda haka murya na sarqewa tace masa "Tun jiya na tambayeka yau zamuje gurin Momy kace toh na gaya masa shine yace shi baka gaya masa baze kaimu ba ni kuma in dai ba gurin Momy ze kaimu ba bazan hau motar ba" ta qarasa tana sake fashewa da wani ihun da seda ya janye wayar daga kunnensa. Lallashinta ya shigayi akan ta bari su fara zuwa gida idan yaso sukayi wanka se a kaisu amma taqi daga qarshe ma ta yarda wayar dan yana jin tsawar da wani ya mata yana cewa "Akan me zaki jefar masa da waya idanta fashe fa?" Manniru Driver ya dauki wayarsa a qasa cikin qunar rai ganin Khalil din be kashe ba ya sakashi cewa "Ranka ya dade jefar da wayar tayi" "Ka kaisu Manniru amma ba ajiyesu zakayi ba ka jira su shiga su fito idan kun kusa qarasawa ka kirani a waya zan musu magana" Khalil ya fada a hankali daga nan ya kashe wayar zuciyarsa duk babu dadi, sam baya son damuwar yaransa amma fitinar Bibi kullum qara yawa takeyi tunda aka fara kaisu gidansu Umaimah yanzu basa sati biyu bata saka rigimar se sunje ba dukda basa kwana sedai au yini su dawo dan wani lokacin ma ita kadai ake kaiwa Mu'ayyad ya kance ai munje ranar nan Iman kuwa daman ko a jikinta saboda yan uwan take zuwa amma ita tana da bala'in qulafucin uwar ga dan banzan naci idanta fara roqon akaisu harse ya yarda zata barshi ya sarara ko jiyan nacin ta ringa masa ya amsa mata badan da gaske yake ba dan basuyi cikakken sati da zuwa ba ashe ita ta riqe shine taje tana creating scene a makaranta ze koma gida zasu hadu ne. UMAIMAH Kuka takeyi haiqan kamar ranta ze fita Abba ya zuba mata ido yana sauraronta ba tareda yace mata komai ba, seda ta haqurtar da kanta ta tsagaita kukan kafin taci gaba da cewa "Na sani na tafka babban kuskure a rayuwata kuma kunada duk wani dalili na daukar ko wanne mataki a kaina. Na biyewa zuciya da zugar mugayen mutane na watsa muku qasa a ido na zubar muku da mutunchi a idon duniya Allah shine shaidata nayi nadamar abinda na aikata kuma a shirye nake dana gyara kuskurena hakan kuma baze yuwu ba har se na fita daga fushinku, Abba dan girman Allah dan Darajar Ma'aikin Allah ku dubi rauni na ku yake mun laifin dana aikata muku. Ku sassauta fushin ku akaina ko na samu ubangiji ya dubeni ya yafemun sauran laifukan dana aikata tsakani na dashi. Wallahi nayi nadama nayi dana sani biyewa son rai" ta sake rushewa da wani kukan daya fi na farko ganin Abban na zaune still ko gezau a kallonta kawai yakeyi kamar wata talabijin. Sunkwashe kusan minti goma sha biyar a haka tana kukan kafin Abban ya nisa yace "Toh ni abinda ban gane ba ni menene nawa a ciki Umaimah da kikazo kina bani haquri sannan duk tsahon lokacin nan se yanzu ne kikaga mun isa da ki bamu haquri ko me me kike buqata?" Se tayi saurin tsayar da kukan tana cewa "Wlh Abba badan baku isa bane a kullum nauyi da kunyar yanda zan tunkareku bayan duk abubuwan dana aikata a bayane ya hanani gurfana gabanku na nemi yafiyarku amma yanzu na gane bani da wata mafita domin fushinku a kullum qara dagulamun lissafi yakeyi. Abba kuyi haquri ku yafe wlh nayi nadama kuma in sha Allahu zan gyara kuskurena". "Toh Alhamdulillahi dama abinda ake so da mumini idan yayi kuskure ya gane ya tuba ya kuma guji sake maimaita kuskuren a gaba idan har dagske kikeyi kinyi sahihin tuba ina fatan Allah ya shiga Al'amuranki Umaimah ya duba miki ya rabaki da duk wani abu dayake ingizaki ga sabon Allah ya rangwanta miki zafin zuciyarki dake kaiki ga aikin dana sani. A bangarena na dade da yafe miki, domin da banyi miki afuwa ba da baki samu yancin zama a cikin gidan nan ba zan sallawa duniya kene kamar yanda kika dade da sallama mata kanki amma bamyi hakan ba mun rungumeki a kullum kuma muna miki fatan shiriya Sannan maganar Yafiya da akwai wadanda yafi kamata da ki nemi yafiyarsu bayan mu, idan har dagske kinyi nadama ki nemi yafiyar ubangiji a farko kan sabawar da kika masa sannanki nemi yafiyar wadanda kika zalunta domin kinsan ubangiji baya yafe haqqin bawa da dan uwansa bawa ya dauka dan haka in har kina so kiga daidai Umaimah dole sekin sauke haqqin wadanda kika dauka" Abba yayi maganar cikin nutsuwa. Umaimah taja majina kafin tace "Nagode Abba kuma in sha Allahu bazan sake komawa ga abinda na aikata a baya ba ku tayani da addu'a" "Allah yayi miki Albarka ya shiga cikin lamuranki, shikenan zan iya tafiya?" Abban ya sake fada dan yana shirin fita tayi masa dirar mikiya tana shiga kuma ta fasa masa kuka, saurin girgiza kai Umaimah tayi kafin tace "Aa Abba bashi kenan ba dan Allah Abba zaka tayani roqan Mama" "Ni yanzu waya tayaki roqona?" Ya fada yana kallonta seta marairaice tace "Abba kai da sauqi amma Mama fushinta ya zarce naka wlh na rasa ta yanda zan tunkareta Abba ko dakinta bata bari na shiga duk yanda kuma naso nayi mata maganar seta nunamun ita ban mata komai ha kaga kenan ta qullaceni da yawa". Shiru Abban yayi kafin yace "Shikenan kiyi ta qoqarin kyautata mata kuma karki dena bata haqurin har se sanda ta sakko ta saurareki abinda kika aikata Umaimah dole badan mu muka haifeki ba babu yanda zamuyi dake da tuni wata maganar akeyi yanzu dan kinyi mana cin fuskar da badan zuciyar musulunci ha da sanin tasirin da bakinmu da fushinmu zeyi akanki dole muka taushi zukatanmu amma ya wuce tunda har kin gene kuskurenki kin nemi afuwa nayi miki itama kuma nasan zata sakko a hankali in sha Allahu" "Nagode Abba Allah ya saka da Alkhairi ya qara girma" ta fada cikin murnar samun daidaito da Mahaifinta ya amsa mata da "Amin, Allah yayi muku Albarka keda sauran yan uwanku Ubangiji ya dubeku ya tsare ku daga dukkan sharri" ya fada yana dafa kanta. Tare suka fito daga dakin, Mama da Anty na tsakar gidan a tare suka musu kallo daya suka dauke kai Abba ya yi murmushi yana kallonsu yace "Zan fita" suka hada baki gurin yi masa a dawo lafiya Umaimah ma tayi masa bakinta yaqi rufuwa saboda farin cikin da take ciki seda Abban ya fita kafin ta matsa inda Mama take ta durqusa gabanta tace "Mamame za'a dafa da rana?" "Girkin Antyn kune ai banawa ba" Maman ta bata amsa seta juya ta kalli Anty data dauke kai ta hade fuska tun fitowarsu da Abban kafinma tayi mata magana tace "Ki barshi zanyi da kaina ai naga kun shirya da Abban naki". Yanda tayi maganar seta bawa Mama da Umaiman mamaki har seda Mama ta kasa daurewa tace "Kamar yaya zakiyi da kanki saratu ba doka Alhaji ya kafa cewar ita zatayi aikin gidan nan ba ko kunyi dashi yace miki ya janye ki karbi aikinki?" Seta kalli Maman bayan data miqe tsaye tace "Aa kawai dai zan karbi aikina tunda har sun fara shiga daki su fito suna dariya kinga alama tana nuna gwamnatinta ta dawo kenan gara na karbi aikina da kaina kafin a maidomun tunda daman bani nace a karba ba" ta shige dakinta Mama ta bita da kallo dan sam bata fahimci abinda Antyn take nufi ba mema ya bata mata rai yanzu yanzu bayan hira sukeyi cikin nishadi daga fitowar Alhaji da Umaimah seta canza fuska me yake faruwane? Ita dai Umaimah na zaune ta sunkuyar da kai Mama ta kalleta tace "Kinji abinda tace ai se ki wuce inda wani abinda zakiyi kiyi" "Babu abinda zanyi yanzu sedai ko in akwai Aikin da zanyi miki" Umaiman ta fada cikin ladabi, Mama ta girgiza mata kai alamar babu seta narke fuska kalar tausayi tace "Jiya naga an kawo miki kayan wanki tunda akwai wuta sena goge miki". Bata zata Maman zata amsa ba taji tace "Toh, amma kiyi a hankali karki qona mun kaya nasanki ba iya guga kikayi ba" seta miqe cike da murna tana cewa "Bazan qona ba In sha Allah" ta shige dakin Maman. Tsalle ta buga kamar yarinya ta fada kan gadon Maman da rabon data ganshi a ido bare ta hau tun dana da yanci tayi juyi akai se kuma tayi saurin sauka tana dariya kamar wata fagal, kayan ta diba ta fita falo ta jona Iron ta fara gugar Mama ta shigo ta zauna haka ta ringa gugar dukda ba magana sukeyi ba amma taji dadin yau gashi sun zauna inuwa daya da Maman ga kuma Abba sun shirya. Ta bude baki yafi sau nawa da niyyar yiwa Maman magana seta kasa duk kuma tana ankare da ita har aka kira sallar Azahar ta ajiye Gugar ta fita ta dauro alwala Anty na hidimar girki tayi mata sannu bata tsammanin ta amsa a ranta tace "Kyaji dashi idan ma baqin ciki kikeyi na shirya da ubana sedai ki mutu" ta wuce falon Maman a can tayi sallah Mama ta ringa Mamaki ganin yau Umaimah ce take sallar Nafila bayan ta idar da Azahar din tayi Raka'a biyu sannan ta zauna tana lazumi Umaimanda Farillar ma yinta take kawai dan ta zama dole idan ta idar kuwa bata tsammanin tana Addu'a dan minti biyu yayi yawa ta tashi daga gurin se gashi yau bayan ta idar tafi minti talatin zaune tana lazumi kafin ta daga hannu tana addu'a nan ma ta dade kafin ta shafa sannan taci gaba da gugar bata dade da ci gaba ba suka jiyo karadin Bibi se gata ta fado falon ta watsar da jakar ta a bakin qofa da gudu ta fada kan Umaimah da tayi saurin janye Iron din ganinta nufota "Ke kuma ya haka daga ina kike harda uniform kin fadowa mutane daki babu sallama haka akeyi?" Mama ta fada kafin ta bata amsa Mu'ayyad da Iman suka shigo da sallama, seda suka cire takalmansu kafin suka shiga ya durqusa a gaban Maman ya gaisheta ganin haka itama Iman tayi yanda yayi Maman ta amsa cikin kulawa sannan ya juya ya gaida Umaimah dake ta kallonsu "Tashi ki fita ki cire takalmin nan a waje da zaki gama tako dattin makaranta dana gari kike taka mun daki babu sallama bare gaisuwa qanwarki ma ta fiki hankali". Baki Bibin ta zumbura tana qara maqalqale Umaimah Mama ta zare mata ido tana daga maficin dake gefenta tace "Sena zaneki da wannan idan baki tashi ba futsararriya kawai me irin halin uwarta" seta miqe tana bubbuga qafa irin na tabararrun yara ta fita tana zuwa saitinta kuwa ta kwada mata maficin a baya da qarfi ta kwalla qara kuwa kafin ta kwanta a gurin zata fara birgima ganin Maman ta fizgo wayar caja daga jikin socket yasa ta take da gudu ta fice daga dakin "Ja'ira daki tsaya dana cire miki iyashegen da yake damunki" "Yanzun nan ta gama birgima a school Mama saboda Driver yace baze kawo mu nan gidan ba seda ya kira Dady har wurgar masa da waya tayi a qasa" Mu'ayyad yayi maganar cikin nutsuwa tamkar Mahaifinsa se Mama ta riqe baki tace "Eh ba shakka ai daman barewa ba zatayi gudu danta yayi rarrafe ba to kuwa uwarki zakici bamu gama da wata bama balle ki tashi ki fitine mu, yanzu Ina Dtiver yana waje ko ajiye ku yayi ya tafi?" "Ina ga ya tafi naji tace masa se anjima ze dawo ya dauke mu" Mu'ayyad din ya sake fada se Mama tace "Dabdi itace ma me gaya masa abinda zeyi kenan?" "To ai Mama shima Dady se abinda take so yakeyi ba shiyasa take yin haka ba ta ringa mun rashin kunya a school a gaban friends dina kuma idan na doketa ta gayawa Dady ni yayi mun fada kuma a gida ma ko Mamah ce tayi mata fada Dady baya so" yanda yayi maganar zaka gane jin haushin abun har ransa "Ai kuwa ya dakko hanyar da bazata bille ba kuma tilas ya gyara wadda bata tashi a sangarce bama ta fitini mutane balle wadda tun tana qarama babu kwaba ai kuwa ba'a taki gaskiya ba". Umaimah dai kanta na qasa ta gagara cewa komai kan wannan magana da Mama take yaba mata ita da yarta seta shiga tattara kayan gugar data gama ta shige mata dasu daki ta ajiye akan gado se anjima idan ta yarda zata shirya mata su a wardrobe. Dakinta ta wuce can ta tarar da Bibin kan gadonta a kwance tana ganin Umaiman ta tashi da sauri ta rungumeta tana cewa "Momy nayi missing dinki da yawa" "Kai Bibi se kace ba last week kuka zo ba me yasa zaki ce se an kawo ku yau daga makaranta bayan akwai islamiyya yau?" Baki ta tura tana cewa "Ni Momy so nakeyi na ganki kuma indai baki dawo gidanmu ba kullum haka zan ringa cewa se an kawo ni kefa kika ce zaki dawo gashi an yi wata da yawa baki dawo ha Dady ma idan na tambayeshi yaushe zaki dawo baya cemun komai Momy kodai kema irin na Mamansu Halima Dady ya sakeki ba zaki dawo gidan mu ba?" Rasa abinda zata gayawa yarinyar tayi dan haka ta wuce bakin gadon ta zauna Bibin ta sake binta tana maimaita mata tambayar still tayi shiru seta zauna tana cewa "Daman na sani Dady ya sakeki yanzu Mamah ce matarsa kenan muma step Mom ce kawai damu zata ringa maltreating namu yanda akeyiwa su Halima?" "Me yasa kika fiya surutu Bibi Wacece Halima kuma me Steo Mom din tasu take yi musu?" Umaimah tayi qargfin halin fada se Bibin ta riqe hannunta tana cewa "Momy Step mom dinsu Halima muguwa ce daman kuma mun karanta wani story book na wicked step mom, dan Allah Momy ki dawo kinji ni bazan iya zama a gidan bakya nan ba". Kallonta ta ringayi yanda take maganganun da suka zarce wayonta to ita yanzu wane bayani zatayi mata da zata fahimta ba tareda ta sake kawo wata maganar ba? "Ko saboda Dady ya auri Mamah ne ya sakeki ba zaki koma ba?" Bibin ta sake jefa mata wata tambayar kafin ta bata amsa tace "Zan gayawa Dady ya saki Mamah kawai ki dawo ni daman bana sonta takura mun takeyi kullum tayi ta mun fada idan nayi abu kuma ba haka takeyiwa su Mu'ayyad ba". Murmushi yayi ya kalli Mama data rafka tagumi tun zamanta kuma batace komai ba yace mata "Toh kinji kiyi magana ta tabbatar kin haqura indai ba kuma da sauran wani abu a ranki ba" seta janye tagumin tana cewa "Toni me zance Alhaji ai ba yanzu ya kamata muyi maganar ba tuntuni ya kamata ace anyita tunda se yanzu tayi lokacinmu to ni banda lokacinta seta jira se randa nayi" KHALIL Ayyukansa yaci gaba dayi, wuraren qarfe hudu ya tashi kai tsaye gida ya wuce yayi mamaki dabe tarar da motar yaran a ajiye ba dan haka yayi tunanin ko Humaira ta aiki Mannirun ne, seda ya fara shiga gurin Hajiya ya kai mata Fruits din daya shigo dasu kafin ya wuce bangarensu, falon shiru se motsin Ruqayya da ya jiyo daga kitchen seya wuce sama qilan suna can. A falo ya tarar da Aryaan yana bacci da alama wasa yayi ya gaji baccin ya daukeshi ba tareda ya sani ba ya gyara masa kwanciya ya wuce dakinta yana tunanin toh ina sauran yaran suka shige tunda be gansu a bangaren Hajiya bama. Humaira na zaune akan kujerar dake dakin tana shan Baqin lipton dan tun da suka dawo daga Asibin take kwance sallah kadai ke tada ita gaba daya kasala ta mata rubdugu se yanzu ta samu tayi wanka tasha ruwan Tea saboda cikinta da ya daure dalilin bata ci komai ba. A sanyaye tayi masa sannu da zuwa ya amsa yana qarasawa kusa da ita ya rungumeta ta gefe yana cewa "Ya jikin?" "Da sauqi, yau ka dawo da wuri" ta bashi amsa seya saketa yana cewa "Yah kwana biyu ayyuka sun mana sauqi so far kusan duk wasu constructions da mukeyi mun kammala se ragowa shiyasa bana kewayen Site" "Toh Allah ya taimaka ya kawo wasu ayyukan na Alkhairi" ta sake fada se ya amsa mata da "Amin Baby" yana murmushi yana bala'in jin dadin yanda take masa addu'a a koda yaushe kuma yana ganin hasken hakan. "Ina yaran naki naji gidan shiru ne?" Ya tambayeta seta ajiye kofin hannunta tana cewa "Ban sani ba koda suka dawo sun shigo ina bacci dan ban dade da farkawa ba qila sun wuce islamiyya" "Ok" ya fada kafin ya fita daga dakin zuwa nasa. Seda yayi wanka ya canza kaya ya fito sannan itama ta fito falon Saman ya kalleta tana zaune a spot dinda Umaimah take yawan zama sanda tana gidan, dukda ya canza kujerun falom saman dana qasa amma dukda haka wani lokacin idan ya kalli guraren da take yawan zama se yaga kamar ze ganta a gun. Kusada Humairan ya zauna ya kalli Aryaan dake baccinsa yace "Ba za'a tashe shi ba kuwa baccin la'asar karya kasa na dare" "Ai kasan shi da kafiya seda na hanshi baccin a daki ashe daya fito kwanciya yayi anan na tashe shi yanzun ma yaqi farkawa se nauyin bacci kamar wani babba" Humaira ta fada tana sake tada yaron amma ko gezau data dago shi ze janye ya koma da alama baccin ne a kansa sosai. "Ai dashi da Bibi bansan inda sula samo kafiyar nan ba har gara itama, dazu fa a makaranta da Manniru yaje daukarsu" (nan ya bata labarin yanda sukayi) se ta kama baki tana cewa "Gaskiya kafa dena abinda kakeyi ba yanzu ake ji ba gaba ce abin dubawa wai tayaya za'ayi ace komai Bibi take so shi za'ayi a gidan nan?" "Baki san sunan Hajiya ne da ita ba kuma gata matata ai dole nayi abinda tace" ya fada da sigar tsokana seta hade fuska tana cewa "Ba wasa nakeyi ba Yaya Khalil maganar Allah itace tun yana danye ake tankwarashi. Yanzu abinda kayi mun shekaran jiya shiru kawai nayi amma naji haushi sosai wlh ya za'ayi tayi laifi ina mata fada a gabanta ka nuna abinda tayi be kai nayi fada ba har kace mata ta tafi ta kwanta kuma ko a jikinka? Shekara takwas ai ba wata takwas bace da zata ringa yiwa mutane barna kuma baza'a tsawatar mata ba gaskiya karka sake yi mun haka ko a gaba idan yaro yayi ba daidai ba in ba zaka taya muyi musu fada ba karka sa mun baki kuma yanzu banda wulaqanci a makaranta zata je tana ihu da birgima akan abu kuma kayi mata gobe ma kace ta maimaita kenan". Kallonta ya ringayi yanda take kumfar baki a kan abinda be kai ya kawo ha a ganinsa kenan amma duk tabi ta haqiqance seya kama hannunta yana cewa "Yanzu meye abun fushi a maganar shekaran jiya da har kika riqe a ranki Bottle water ne fa ta dauka tayi Alwala shine abintada jiniyar wuya kika ringa fada kamar wadda tayi alwalar da Mangyada ko Madara sannan maganar yau ni na amsa mata jiya kan za'a kaisu kinga ai bazan saba mata alqawari ba" "Ai shikenan" ta bashi amsa dan zuciyarta ta qulu da maganar tasa tunda bega rashin dacewar abinda yakeyi ba seya ci gaba ita dai ba zata fasa tsawatarwa duk wanda yayi ba daidai ba a cikinsu sedai yaji haushi tunda idan sun lalace qarshe ita za'a zaga ace ta musu mugunta tunda ba ita ta haifesu ba. Ganin da yayi ta hada rai yasa ya ringa rara gefe amma tayi masa shiru bata cewa komai suna nan zaune har aka kira Magriba ya tashi yayo alwala ita ma ta shiga daki da Aryaan daya farka daga bacci, yanda ya shigo a firgice bayan an idar da sallah ya bata tsoro. Ta kalle shi tace "Lafiya?" "Ina fa lafiya, har yanzu yaran nan basu dawo daga Islamiyyar ba, kuma na tambayi Sammani ina Manniru yake dan motarsu bata nan yace tunda ya tafi dakko su daga Boko be dawo ba which mean basu je islamiyyar ba kenan ma ashe gashi ina ta kiran wayarsa bata shiga" Khalil dinya fada a kidime take itama hankalinta ya tashi ta miqe tsaye tana cewa "Number sa bata shiga kuma Sammanin bashi da wani layin nasa da za'a kira?" "Number sa daya ce babu wata" ya bata amsa yana zagaye dakin, tunanin inda yaransa suka shiga yakeyi kar fa wani abu ya same su. "Toh ba kace ya kaisu gurin Mamansu ba ka kira can mana kaji" Humairan ta fada cikin damuwa se yayi saurin zaro wayarsa dan ya manta da can din ma. Number Mama ya kira a kashe, baya tsammanin Abba na gida dan haka kai tsaye zuciyarsa ta bashi ya kira Umaiman. Da ka ya zuba numberta dake haddace, sunan da yayi saving ya fito 'WIFE' da Emojin Heart guda biyu daga shi har Humairan dake kallon wayar wani abu ya daki zukatansu sedai kowanne da kalar nasa, tabbacin da aka bashi na wayar a kashe take itama yasa shi jan tsaki ya juya yana cewa "Bari naje gidan na gani" kafinta ce masa wani abu ya fice daga dakin da saurin gaske har yana hada hanya seta bishi da ido wani abu me daci yana taso mata, number wayarta da Sweetheart yayi saving amma shine ita da basa tare hau yau be canza mata suna a wayarsa ba. Khalil kuwa cikin qanqanin lokaci ya isa gidansu Umaimah saboda gudun da ya ringa shararawa a hanya idan wani abu ya samu yaransa be san yanda zeyi ba. Layin babu kowa saboda an shiga sallar isha, ya kasa haqurin jira se kawai ta kutsa kansa gidan bakinsa dauke da Sallama tareda taraddadin samunsu ko akasin haka dan rashin ganin Motarsu a waje ya qara daga masa hankali seda yayi sallama uku kafin ya shiga ainihin tsakar gidan daidai nan Umaimah ta fito daga daki jin kamar ana sallama sukayi ido hudu dashi yana tsaye daga bakin qofa yana jiran ganin giftawar wani. Cikin qasa da seconds biyar ya qare mata kallo kafin ya dauke kansa sama saboda yanda zuciyarsa ta shiga wani bugu kamar zata fito, Umaimah kuwa ido ta zuba masa kamar farin shigar Maita, ta kasa gasgata Khalil ne da gaske ko kuma Mafarkan data sabayi ne amma kuma qamshin turarensa dake busata yasa ta ke son gasgata shi din ne da gaske ba mafarki ba "Naji kamar ana sallama ko ba a nan bane?" Mama data leqo ta fada ganin Khalil a tsaye yasa ta fadada murmushinta tana cewa "Au kaine? Shigo ciki mana ka tsaya a qofa kamar wani baqo". Cikin takunsa me cike da nutsuwa ya giftata tamkar bega mutum a gurin ba qamshinsa ya cika mata hunhu ji ta ringayi kamar tana shaqar sabon numfashi seta rufe idonta ta bude ta sake rakashi da kallo harya shige falon Mama jikintavna wani irin sanyi kamar wadda ake daskararwa. Yanda Khalil din ya debeta ya watsar bema nuna alamar yaga mutum a tsakar gidan ba lallai abin Azimun ne. A sanyaye taja qafafunta ta matsa jikin bango zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, takai kusan minti biyar a tsaye kafin ta jiyo qamshin turaren sa yana sake tun karota, tayi saurin bude idanunta jin takunsa kusa da ita muryarta na rawa ta kira sunansa ya tsaya cak a inda yake ba tareda ya juyo ba tamkar kuma wanda aka tsikara yaci gaba da tafi da sauri ba kamar yanda ya fito daga dakin Maman yana tafiya a hankali ba. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 82 Seda ya dauki kusan minti goma zaune a cikin motar kafin ya kunnata wayarsa dake ajiye kan kujera ta yi haske ya janyota ganin Sweetheart ke kiransa kafin ya daga ta katse se sannan ya lura da tarin missed calls din data yi masa da alama tun fitowarsa daga gidan take kira. Cikin mutuwar jikin da ganinta ya haifar masa ya sake kashe motar kafin yabi bayan kiran Humairan "Habibi ina ka shiga tunda ka fita nake kira gasu sun dawo qila ma kun hadu a hanya dan motarka na fita tasu ta shigo" Humairanta fada cikin damuwa seya sauke ajiyar zuciya murya can qasa yace mata "Sorry wayar a silent take bangani ba se yanzu gani nan zuwa gidan nima" "Amma lafiya naji muryarka haka? Nagaya maka fa gasu sun dawo babu abinda ya samesu tun ranan suna gurin Mamansu shi kuma cajinsa ne wai ya qare shiyasa kaji wayar a kashe" ta sake fada saboda jin muryarsa da tayi wani iri seda yayi qoqarin saita kansa kafin yace "Babu komai fa nazo gidan nima suka ce sun tafi gani nan ina hanyar dawowa" daga haka sukayi sallama. Yana tuqi amma gaba daya hankalinsa baya kan Titin, wani irin mix emotions ke damun sa. Ganin Umaiman ya haddasa masa abubuwa da yawa ta tuna masa da wancan daren daya zama baqin dare a rayuwarsu gaba daya abubuwan da suka faru suka ringa dawo masa kamar a sannan suke faruwa a bangare daya kuma daga can qasan zuciyarsa yana jin wani abu na motsa masa akanta. Allah shine shaidarsa yana son Umaimah irin son da be taba yiwa wata Halitta shi ba. Yana jinta har cikin jini da jijiyarsa amma ta barar da damarta tayi masa abinda idan harda gaske shi dan Halal ne kamar yanda take fada koda ace ita kadai ta rage mace a doron duniya ze zabi ya qare rayuwarsa babu aure domin ta keta alfarmar wadanda baya hada komai dasu. Tabbas idan da ace iyakar abinda tayi masa ne tabbas ze iya yafe mata ya rungumeta suci gaba da zama Albarkacin son da yake mata da zuri'ar dake tsakaninsu amma a yanzu baya zaton akwai wani uzuri da ze iya yi mata daze kankare tarin laifukanta a zuciyarta data sauran Ahalainsa. Maganar da Mama tayi masa bayan shigarsa akan Bibi ta tsaya masa a rai, ya gagara ganin abinda yakeyi mata da kowa yake cewa yana lalata ta shin laifine dan ya samarwa da yarsa abinda take so Alhali yana da halin hakan? Shi haka kawai duk cikin yaran tafi shiga zuciyarsa hakan kuma ya samo Asali da suna da kuma kammanin Hajiyarsa data dauka kuma shi baya nuna banbanci tsakaninta da yan uwanta kamar yanda ake cewa yanayi kawai ita tafi sakewa dashi kuma tafi tambayarsa yayi mata abu shiyasa amma suma duk wanda ya nemi abu a gurinsa ai yanayi masa ba wai ita kadai ba yana wadannan tunane tunanen ya isa gida. Yaran har sunyi wanka suna cin abinci ya shiga falon sukayi masa sannu da zuqa gaba daya ya amsa ba tareda ya kalle su ba ya haye sama. Har suka kwanta Humaira na lura da yanayinsa dukda yanda yake ta qoqarin kawar da komai amma seda ta fahimci wani abu tayi kwanciyarta ta barshi a zaune yana danne dannen laptop data tabbatar babu abinda yakeyi kawai dan ya dauke hankalinta ta zata aiki yakeyi ne dan haka tayi baccinta ta barshi. Khalil kuwa tambaya ce baya so tayi masa dan besan amsar da ze bata ba gaba daya ganin Umaiman ya haifar masa da wani yanayi mara dadi, juyi yayi tayi akan Gadon tunani kala kala suna yawo a kwakwalwarsa daya gaji gashi ya kasa bacci ya tashi ya dauro Alwala ya fara sallah har seda yaji ya fara jin bacci kafin ya sallame yayi addu'a ya kwanta. Abinda be tabayi ba tsahon lokacin rabuwarsu se gashi daren yayi mafarki da ita cikin wani yanayi me firgitarwa dan tana daure da sarqoqi wani mutum yana janta tana miqa masa hannu tana kuka akan yazo ya ceceta yayi yunqurin miqa mata nasa hannu wani haske me tsananin kaifi ya kashe masa ido har ya hanashi sake hangota se amsa kuwwar Kukanta yake ji a kunnensa tana fadin "Khalil ka taimakamun ka gaya musu ban aikata ba". A gigice ya farka daga baccin yana salati ya kalli Humaira data miqe zaune itama tana kallon cikin wani yanayi, tana bacci taji ya kama hannunta da matuqar qarfi yana kiran Umaimah da har seda ta farka sedai yanayin data ganshi ta tabbatar koda mafarkin Umaiman yayi tofa bame dadi bane. Addu'a ta ringa tofa masa kamar yanda shima yake tayi zufa na keto masa kamar babu Sanyin Ac a dakin ga jikinsa na rawa yanda kasanwanda aka rutsa da wuqa a mafarkin. Seda suka kwashi wasu mintuna a haka kafin ya daidaita nutsuwarsa ya koma ya kwanta tareda janta jikinsa ta zame be takura mata ba ya saketa dan har sannan bawai jikinsa ya gama daidaita bane Humaira ko tsaki taja a zuciyarta ta juya masa baya babu bata lokaci kuwa bacci yayi awon gaba da ita shi kuwa haka ya ringa juyi ya gagara komawa baccin har aka kira sallar Asuba kafin ya tashi yayi wanka ya fita masallaci. Kwanaki biyu da suka biyo baya duk haka yayi su sukuku shi kansa bazece ga abinda yake damunsa ba amma jikinsa gaba daya babu qarfi, da Hajiya ta matsa masa da tambayar me yake damunsa ne dole ya qarfafa jikinsa ya koma sabgoginsa daman Humaira koda wasa bata ma nuna masa ma tasan abinda yakeyi ba, daya ware dinma shareshi ta ringayo seda yayi ta rara gefe yana lallashinta kafin ta sakko suka koma daidai amma qasan ranta danuwa ce fal akan abubuwan da taga suna faruwa. Haka rayuwa taci gaba da gangarawa, seda cikinta ya shiga wata shida kafin mutane suka farga dashi. Ranar da Hajiya ta gama tabbatar da cewar cikine har kuka tayi tasa aka dafa abinci me yawa aka fita dashi akayi sadaka, Khalil kp kasa hada ido yayi da ita a dole kunya yake ji ita kuwa ko a jikinta ta ringa bige bigen waya tana shaidawa yan uwanta da abokanan Arziqi matar Khalil nada ciki yanda kasan be taba haihuwa ba sedai duk wanda ta gayawa yasan me take nufi, shaida musu takeyi Khalil din ya samu lafiya sun kuwa taya su murna tareda fatan Alkhairi kafin tofin Alatsine ya biyo baya akan Umaimah datayi masa sanin wannan tonon silili. Hajiya Hauwa kanta barka suka ringayiwa Juna ita da Hajiyan, tace mata 'Kinsan ta da zurfin ciki, tun kwanaki nale hasashen cikin amma tace na haka ba to tunda kasan ga yanda abu yake kinga ba zaka matsanta ba ashe iyashege ne kawai irin nata yanzu da baze boyu ba ai kowa ya sani Allah ya inganta shi kuma ya bashi lafiya me dorewa". Jalilah kuwa ta samu abin yi, daga shi har Humairan bata bari ba dukda yanda take bala'in jin kunyarta amma idan ta tasata a gaba da tsokana seta kusa kuka take qylaeta, saboda ta samu iya shege ma cewa tayi ta haqura ita ce Hussaina yanzu shi ya zama Hassan din dan haka yanzu a qanwar Miji take dole ta tsonaketa "Haba nidai nace ashe su Khalil anji garau an shiyasa ko gidan nan aka zo ba'a jinku kunyi muqus a daki ana biyan bashi, dan Allah tun yaushe ka koma duty?" A gaban Hajiya tayi masa tambayar yanda kasan qasa ta tsage ya shige cikinta Hajiyar kanta seda ta dafa kai tana jinjina hali irin na Jalilah, bata haqura ba taci gaba da zaro zance dayaga babu sarki se Allah dole ya shafawa idonsa toka ya mata ta yan barikin shima yace mata "Kedai ki bari shekara uku ai ba nan bace nida ita duk munji jiki yanzu kuwa da lafiya ta samu ai dole mu biya bashi " Hajiya dai se tashi tayi ta barsu dan ba zata iya da wannan fitsara ta tagwayen nata ba. BAYAN WANI LOKACI Misalin qarfe goma na safe suka fito shida Humairan da ze sauke a Asibiti zataje Awo, dakyar take daga qafarta saboda yanda cikin me watanni takwas a sannan yayi girma sosai dan yafi na Aryaan, fuskarta a hade ta shiga motar haka shima tashi dukda shi yana qoqarin hadiye bacin ransa dayi mata uzuri akan abinda take masa. Tagiya sukeyi babu me tanka dan uwansa ta juyar da fuska tana kallon waje lokaci lokaci yake waiwayawa ya kalleta Ya rasa abinda yake damun Humairan kusan wata biyu kenan ta canza gaba daya daga yanda ya santa a kullum cikin takalar rigimarsa takeyi abu kadan kuma zeyi mata ta hau fushi da koke koke ya rasa inda ze tsoma ransa ta kasa yi masa uzuri akan abinda shi kansa yana damunsa, a yanzu data rigada tasan dadin jikinta a kullum cikin zuwar masa da buqata takeyi wadda yake gaza biya mata, ya lura ta raina qoqarinsa dukda cewar Abubuwa sun qara daidaitar masa dan a yanzu yana iya takarta amma bayayin dogon zango, abinda ya lura dashi ita kuma halittarta me zurfi ce tana daukan lokaci kafin ta samu gamsuwa duk kuma yanda ya sabayi mata yanzun baya wadatarta tafi so yayi mu'amala ta gaske da ita duk kuma da qoqarin da yakeyi dan lokaci da yawa bayan sun gama hala zeyi ta murqususun ciwon Mara a maimakon ta yaba masa sedai tayi ta bata rai yinin ranar kuwa zir haka zasuyi cikin qunci daga shi har ita dan baya taba iya walwala idan batayi ba. Sau da yawa yakan zaunar da ita yayi qoqarin fahimtar da ita amma setaqi qarshe ko tasa masa kuka ko tayi shiru har ya gaji da magana yayi shiru, be san me take tunani ba gani takeyi shine baya so yayi mata yanda take ko yaya sam shi be fahimta ba yanzu da safen ma rigimar da suka tashi da ita kenan, har yayi wanka yana shiryawa ta shige masa jiki, yasan me take so a lokacin kuma bashi da sha'awar hakan a tattare dashi amma gudun shiga haqqi dole yayi mata yanda take so, haka kawai yama jikinta ta tureshi, cikin fushi take ce masa "Daman an fada idan Namiji baya son mace ko burgeshi batayi, inda wacce kake so ce ba rashin lafiya ba koma menene zakayi mata yanda take so ai" ta shige bandaki ta barshi cikin tsananin mamakinta. Ransa ya ringa baci zuciya tana harzuqo masa, ba yau din ta fara fada masa haka ba duk ranar da Yara suka ambaci Mamansu taga wani sauyin yanayi a tattare dashi ta ringa yada masa da magana kenan akan saboda an tuna masa da wadda yake so zeyita daure fuska yana fushi a gidanamma be taba daga kai ya kalleta ba shine yau zata kafa hujja akan abinda ba haka yake ba shi yaushe rabonsa da ko a tunani ya tuna da wata Umaimah? Idan ba Bibi ta tada rigimar zata gurinta ba wlh shi mantawa yakeyi da ita amma ota Humairan ya fahimci ta tsaya mata a zuciya tana yawan son kawo zancenta ya kuma zaunar da ita ya nuna mata baya so amma ya lura duk in tana so ta bata masa rai ne take ambato Umaiman. Haka yayi wanka suka fito, yana yai mata uzuri ne da cikin jikinta shi kansa yana iya qara mata fitina da neman rigimar da takeyi yana kuma fatan idan Allah ya sauketa lafiya ta canza karta ce zasu ci gaba da rayuwa hakan dan zaman baze musu dadi ba idan har zata cigaba da quntata zuciyarta tana quntata shi. Tun farkon daya gamu da ibtila'in irin abubuwan daya ringa hangowa kenan har yayi tunanin sawwaqe mata amma tace taji ta gani zata zauna dashi se yanzu kuma data gama mamaye zuciyarsa sannan zata tsiro da wasu baqin halaye na daban gaskiya baze dauka ba. Seda ya jirata ta gama abinda zatayi a Asibitin saboda ya Driver yara ya tafi kai Hajiya Gaya gaisuwar rasuwa, sun fito daga office din Dr Al'amin suka wuce pharmacy zasu karbi magungunan Awo, yana gaban me bada maganin tana daga can bayansa ya juya da niyyar ya tambayeta idan tana da sauran Paracetamol ko a hada musu dashi idonsa yayi kyakykyawan ganinta da wani Dogon saurayi fari suna dariya. Kallon saurayin ya ringayi yana qoqarin tuna inda ya sanshi take ya gano wanene wani kalar tashin hankali ya rufto masa daga inda yake yana jin muryarta tana fadin "Nuru kaine ka zama haka?" Ta sake fada cikin madaukakin farin ciki tamkar yanda Noor din dake tsaye gabanta da rigar Lab coat shima fuskar sa ta nuna farin cikin ganinta. "Nine, Ashanty, oh my God look at you kin zama wata big Mama dake, but wait ya naganki heavenly pregnant While naji ance Mijinki ya zama mace? Ina ta neman contact dinki nayi miki jaje duk wanda na tambaya seya hanani bayan kuma dai ai ko babu SO yanzu tsakaninmu akwai zumunchi dukda ni har abada bazab dena sonki ba" Noor ya sake fada yana qarashewa da wata kalar dariyar shaqiyanci take murmushin kan fuskarta ya dauke ta kalli bangaren da Khalil yake tsaye suka hada ido ya saki ledar magungunan hannunsa saboda yanda qirjinsa ya shiga bugawa da qarfi cikin dabarbarcewa ta kalli Noor din tace "Uhm Nuru se anjima Habibi muje idan ka gama" "Oh ashe tare kuke?" Noor din ya sake fada fuskarsa dauke da murmushi ya miqawa Khalil dake tsaye tamkar an dasashi hannu da niyyar Musabaha seya kalleshi ya kalli hannun kafin ya dauke kai, be ko bi takan magungunan dake qasa ba ya bar gurin cikin takunsa na nutsuwa. Dakyar ta iya daga qafa tabi bayansa tana jin Noor din ya biyota da wayarsa yana cewa ta saka masa numberta amma taqi koda kallonsa, zuciyarta ta tsinke da tsoro bazata manta kashedin sa ba tun a zamanin baya akan Noor din ballantana a yanzu da take matsayin mallakinsa lah shakka kuma tasan yaji maganar su ita bata ma san yanda zata wanke kanta ba dukda ai ba wani tayi ba da be kamata ba. Kamar munafuka haka ta bude murfin motar ta shiga, ta saci kallonsa ya riqe haba da hannu daya dayan kuma ya dafe sitiyarin motar sedata maida murfin ta kulle kafin ya tayar da motar ba tareda tace masa komai ba. "Wlh Habibi kawai ganinsa nayi a gurin" ta fada cikin rarrabewar murya, shiru ya mata kusan minti biyar suna ta tafiya kuma ba hanyar gida suka nufa ba ta cire ran baze kulata ba kamar daga sama taji yace "Wanene shi?" Da sauri tace masa "Nuru ne" "Nuru?" Ya maimaita da sigar tambaya seta dafe bakinta yanda kasan zata rusa kuka tace "Noor ne, wannan dan makwaftan nan namu Abokin Yah Habib" "Dan maqwaftanku ko tsohon saurayinki? Shine har kike jaddadamun sunan soyayyar da kike kiransa dashi wato NURU ko a gaban mutane kina washe masa baki kina dariya saboda kinga abinda zuciyarki take so ai shikenan" Khalil yayi maganar a fusace. Kuka ne ya kwace mata ta fara rantse rantse ya dakatar da ita da cewa "Karki qara harzuqani, idan dai dai kikayi kanki Allah dai yana kallo kuma har yamadidi wato kukeyi dani na zama mace bana amfana miki komai tsohon saurayinki yaci zarafina kina tsaye kina murmushi nagode, tunda naga yanzu ya nutsu ya samu abinyi idan kinada buqata sena sawwaqe miki kije ki aureshi shida yake Namiji yake da abinda ze baki ni kuma naci gaba da rayuwata a yanda Allah yaso ya ganni" Khalil din ya sake fada daidai sanda ya faka mota a qofar gidan Mama Hauwa. Ta daga kai ta kalli gidan a firgice ta sake kece masa da kuka tana cewa "Wlh Yah Khalil ba haka bane ni ban san a ina yaji maganar nan ba rabona dana ganshi tun ranar daka koreshi daga gidan sama da shekara hudu ban sanke ganinsa ba. Kaga gidansu can ma Tunda Hajiyarsu Tayi aure an raba musu gado babu kowa a ciki sunma siyar da gidan a ina zan ganshi me zanyi dashi kuma sannan daka kawo ni gida yanzu me zanyi?" "Ki fitar mun a mota" ya sake fada a fusace, wani irin mugun kishi ne yake cinsa, saqe saqe kawai zuciyarsa takeyi masa idan bata matsa daga kusa dashi ba ze iya rufeta da duka a yanda yake ji" "Ba zaki fita ba" ya sake daka mata tsawa ganin taqi fita sema kai data hade da guiwa tana rizgar kuka seya ja wani dogon tsaki saboda yanda kukan nata kuma yasa yaji ba dadi, tada motar yayi suka bar layin shi bema sanme yasa ya kawo ta gidan ba tsabar yanda ransa ya baci ne yasa ya rasa ina ya kamata ya kaita ma kai tsaye Kamfani ya wuce da, a office dinsa ya barta ya shiga meeting tasha kuka ta gode Allah haka siddan tana lallaba rayuwarta Nuru ze jangwalo mata tashin hankali. Ita wlh ta manta dashi, koda a yanzu ba zaman dadi takeyi da Khalil ba amma rashin wani abu be taba sa ta tunano wano Namiji ba balle Noor da tun data auri Khalil ya zama tarihi a zuciyarta tamkar an goge mata tunaninsa haka taji se yanzu kwatsa ze dawo ya haddasa mata fitina da Mijinta shida Allah. A nan tayi sallar Azahar Sakatariyarsa ta kawo mata lafiyayyen abinci da nama fal dan wannan cikin ya mayar da ita kamar Kura. Ranta ya danyi sanyi tunda har ya tuna da akawo mata abinci irin wanda take so tasan ya huce ko ba duka ba. Tana zaune a qasan carpet din Office din bayan ta gama cin abinci tana maida numfashi ya shigo ya mata kallo daya ya dauke kai dukda fuskarsa babu fushi irin na dazu. Kalar tausayi tayi tana masa sannu da zuwa ya amsa a ciki kafin ya shiga hada kan takaddu yana cewa "Ki tashi akai ki gida" "Ni zan zauna idan ka tashi se mu tafi tare" ta fada cikin muryar shagwaba, seya waiwaya ya kalleta kafin yaci gaba da abinda yakeyi kawai yaji ta fasa masa kuka. A fusace ya sake juyawa yana cewa "Saboda kinga na kulaki bayan haushinki nakeji shine zaki zo kina mun kukan banza to ki tashi ki tafi idan ba haka ba kuma ki kwana a nan dan ni fita zanyi kuma daga inda zani zan wuce gida". Cikin kukan ta shiga cewa "To ai gara na kwanan da dai na koma gida kana wannan fushin dani bayan kuma Allah na gani ni ba laifina bane hanya ce ya hadamu kuma indai ba zargina kake da wani alkaba'i ba menene zesa ka dauki fushi daga kawai na gaisa da Noor, kai da kake zuwa gidansu tsohuwar matarka har mafarkinta kakeyi me na taba ce maka akai seni daga gaisuwa se cibi ya zama qari". Jikinsa ne yayi sanyi ya zuba mata ido kawai yana kallonta dan kalamanta sun taba shi amma ai shi da ita ba daya ba. Shi namiji ne Allah ya yardar masa ya kula Mace sama daya amma ita ai Macece kuma matar aure bata da wata hujja da zata kula wani Namiji kuma ma tsohon saurayi babu ta inda alaqa ta kamatu a tsakaninsu tunda dai har So ya taba giftawa kodan gudun shigar shaidan be kamata ace an ci gaba da wata mu'amala data zarce ta dolen dole ba idan ta kama. Dukda haka seya gyara tsayuwa yace "To ai ni namji ne kuma tsohuwar matata kikace kinga idan naga dama zan iya maido da ita kona auro wasunta na ajiye cikin gidana ke kuwa sedai ki zaba ko ni ko shi" "To na zabe ka ni babu abinda zanyi dashi ko a da dinma yarinta ce tasa na kulashi amma yanzu dan Allah so kakeyi na wulaqanta shi daga ya gaishe ni ai kaima ba zakaji dadi ba kaifa kake gaya mun babu kyau wulaqanta dan Adam abinda ya fada nima beyi mun dadi ba, kuna badan ina gudun karna kulashi ka sake fusata ba ai da zan mayar masa da martani da yace maka Mace Aryaan da wannan kuma a ruwa na sha su kenan" tayi maganar tana nuna cikin jikinta, seya dan sassauta fushin yana cewa "Kodan gaba bana so, karna sake ganinko dashi balle magana ta hadaku" "In sha Allahu, yau dinma ai hanya ce ta hadamu" ta sake fada seya daga mata hannu yana cewa "Kawai ki amsa mun da Toh, ko a dakin Mama kuka hadu banyarda ki amsa gaisuwarsa ba haka ko kallonsa baya ga na rashin sani banyarda ki qarayi ba. Asibitin ma canzawa zamuyi indai na tabbatar a gurin yake aiki" "An gama ranka ya dade hasken zuciyata" ta fada tana isa gareshi ya riqe hannunta yana cewa "Bana so ki kirani da komai banda Haske dan sunansa ne haka kuma kike kiransa. Baki san yanda zuciyata tayi baqi ba sanda naji kin ambace shi da NURU wlh ba qaramindauriya nayi ba na iya danne zuciyata da dake dashi zan hada na muku dukan tsiya a Asibitin yanda gaba baze qara gigin kula matar wani ba kema ba zaki sake kallon Wani da bani ba" dariya tayi tace "Kayi haquri, kuskure nayi kuma bazan sake ba in sha Allah yanzu ka dena fushin zaka bari na jiraka idan ka tashi se mu tafi gida?" "Na haqura yanzu ma zamu tafi ai amma kafin nan muje kiji wani abu" ya jata kan Kujerar dake gefe gane nufinsa ya sa tayi saurin janye jikinta cikin dabara tana cewa "Naqi wayon ni dai mu tafi gidan kawai na gaji ma bacci nake so nayi". "A sanyaya ya zauna ya janyo ta itama dole ta zauna yana kallon fuskarta yace "Humaira, kar kiji nauyin komai ki fada mun damuwarki bana so Allah ya kamani da haqqinki ko kuma na zama silar da zaki cutu". Kanta na kallon gefe ta qi yarda su hada ido, kwana uku da suka wuce seda sukayi Magana da Anty Sumayya dataje mata ita ta fara takalarta da maganar wai taga bata da walwala menene matsalarta da yake tafi Anty Unaizatu iya bugun ciki da jan mutum a jiki se gashi ta bude baki ta fada mata abinda yake damunta dan gane da rashin samun gamsashishiyar nutsuwa a gurin Khalil. Ta gaya mata qunci da damuwa basu zasu bata mafita ba ta bude baki ta gaya masa sannan dole se tayi haquri akan wani abun tunda tasan ga abinda ya sameshi ko baya ga haka masu lafiyar ma da yawa haquri akeyi dasu dan haka suyi magana ta fahimta dashi to ita me zata ce masa bayan duk irin dabarun da Anty Sumayyan tace anayi yana mata fiye dasu amma a yanzu bata jin suna mata ita dai kawai wancan abun da da bata so shi take qulafuci har mafarkinsa takeyi. "Humaira" ya fada yana girgizata ganin tayi nisa a tunani, ta kalleshi idonta ya kawo kwalla seta sunkuyar dakai yajata jikinsa ya rungumeta yana cewa "Karki bari shaidan ya lalata zamanmu, karki yarda magauta su mana dariya ki daure ki gayamun menene damuwarki me kike so" "Kaji rainib wayo bayan yasan menene damuwar tawa kuma zezo yana wani tambayata" ta fada a zuciyarta a fili kuma taja Majina kafin tace "Ni babu komai". Rungumeta yayi a ransa yana jin babu dadi, iyakar qoqari yanayi gurin nemawa kansa lafiya a kullum kuma cikin addu'ar Allah ya tsare masa iyalinaa yakeyi shi yasa hankalinsa ya tashi sosai da ganin da yayi mata da wancan yaron, baya zarginta ba kuma ya tunanin zata iya aikata wani abu makamancin wanda shaidan yake yawan kawo masa amma kuma hakan baze sa ya nade hannu ba tareda ya miqe da Addu'a ba da kuma kulawa da lamuranta. Sau da yawa irin wadannan matsalolin da maza sukeyin shakukatun bangaro dasu akan matansu su suke jefasu a halakar da daga baya kowa zezo yana tofin Ala tsine dasu bayan kuma Mijin shi ya bada qofar da barakar ta shigo gidansa. Sun dade a zaune yana rungume da ita kafin ya saketa saboda bugun qofar da akeyi ya bada izinin shigowa Anwar ya shigo da takaddu. Cikin mutuntaka suka gaisa yana tambayarta yara "Yan China nan ne suka zo fa yanzu nan kawai Jacob yake gaya mun suna conference room ya musu iso" Anqar din ya fada yana miqa masa takaddu ya karba ya duba yana cewa "Amma gobe sukace" "Yau ko gobe dai, sun dai fi qarfafa zuwan goben so kuma tafiya ta kama shugaban kamfanin nasu yau da dare ze tafi shiyasa ya turo su yau dan a gama abinda za'ayi kafin ya tafi dan ze jima" Anwar ya sake fada seya ja kujerar gaban system dinsa ya zauna yana cewa "Allah yasa na gama hada takaddun bari na tura maka ta Mail dan ban fito da system dina ba tana gida seka projecting mana". Seda ya gama tura takaddun ya kalleta yace "Na bar miki ita a kunne akwai Korean movies a ciki wannan ne ya saka" ya nuna Anwar,Anwar din yayi dariya yace "Saboda irin haka kinga bakya zauna boring ba zaki samu abin kallo tunda nasan ku mata daman daga India se Korea kuke kallo". Khalil ya tashi suka fita yana ce mata "If you need anything ki kira Secretary se ki gaya mata ba zamu jima ba in sha Allah da mun gama se mu wuce ko?" "Allah ya bada sa'a yasa a qulla Alkhairi" ta fada suka amsa mata da Amin gaba daya dan Anwar kansa yaji dadin Addu'ar, abinda ya rasa kenan matarsa ta ko ina bata da makusa seta bangaren yi masa addu'a idan ze fita ko godiya idan ya mata abu, qarqarinta tace "Nagode, A dawo lafiya" shikenan. Kan kujerar daya tashi ta koma ta shiga Media, a maimakon ta bude movies din seta wuce gurin hotuna wata folder guda taga an rubuta 'LIFE' ta bude. Hotuna sun wuce ta irgasu kala kala shida Maman Bibi, wani irin abu ya ringa taso mata zuciya ta ringa tunzurata har ta kasa haquri kai tsaye ta dannawa folder gaba daya delete saboda bacin rai ma ta kashe system din gaba daya ta sauka qara ta dirar ma ragowar naman da bata cinye ba tana huce fushinta a kansa. Bayan sun koma gida da daddare ma seda ya sake sabon Rarrashi dan yaga abinda tayi daya kunna system din be ce mata komai ba kuma ya bi recycle bin ya maido folder tana ta kumbure kumbure shidai be kulataba har suka je gida seda dare yayi yaga tana neman ta tada sabuwar fitina yasa ya lallabata ta haqura suka kwanta a ransa yana ayya su Mata gaba daya haka suke da Kishi, na Umaimah ne kawai ya fito fili. UMAIMAH A sannu a hankali nutsuwa ta fara saukar mata domin nauyin daya danne mata qirji fiye da kaso saba'in cikin dari ya sauka. Tsakaninta da Mama da Abba sun samu daidaito domin ta nemi afuwarsu kuma sunyi mata haka kullum cikin Istigfari take domin tun lokacin da Mama tayi mata tunatarwa akan babban laifin biyewa Safina da tayi ta kaita gidan yan tsubbo hankalinta ya qara tashi. Dare da rana cikin roqon gafarar ubangiji take haka ta rage bacci duk dare seta tashi tayi sallolin Nafila cike da yaqinin ubangiji ya yafe mata tarin laifukanta a garesgi. Ta rasa sallolinta babu adadi sakamakon yawon gidan Malamn tsubbu da suka ringayi da Safina, gaba daya hankalinta yayi nisan da bata taba hango illar abubuwan da ta aikata a baya ba se yanzu. Lokacin da Maman take sake tuna mata da cewar muddin tana so al'amuranta su daidaita seta nemi yafiyar mutanen data musgunawa a rayuwa domin Allah ze iya gafarta mata laifukan da tayi tsakaninta dashi muddin tayi kyakykyawan tuba ta kuma roqeshi amma babu sassauci a cikin haqqoqin data daukarwa kanta na mutane dan haka tilas ta daura damarar neman yafiyarsu amma babban tashin hankalinta ta inda zata fara? A ina zata nemo su? Tijararta tun tana qanqanuwa takeyinta, bakin Manya da yara babu wanda bata dibarwa kanta ba banda tarin Allah ya isan yaran da take cin zali a Boko da Islamiyya yanzu ta ina zata nemosu ta nemi yafiya wasu ma sun mutu wasu sun bar inda take wasu bata ma sansu ba wannan tunanin ne yake qara dagula mata lissafi ta rasa inda zata tsoma ranta. Cikin manyan kurakuren data tafka a rayuwarta bayan tarwatsa rayuwar auranta da tayi A yanzu ne ta gane girman Al'amarin daya faru tsakaninta da Hadiza. Tana cike da nadama da dana sanin abinda tayi mata ta tabbatar da cewar iyakar haqqin Hadiza ya isa ya hanata nutsuwa a rayuwarta, a yanzu ita komawa gidan Khalil bashine burinta ba, buqatarta ya yafe mata, Hajiyarsa ta yafe mata irin tozarcin da tayi mata haka yan uwansa duk suyi mata afuwa daga baya idan Allah ya qaddara da sauran zama a tsakaninsu zata so ta koma masa idan kuma babu ta haqura ta karbi qaddara a yanda tazo mata sedai hakan yana nufin zata qare rayuwarta babu aure dan babu sauran matsuguni da wani Namiji ze samu a zuciyarta domin ta Khalil ce kuma har abada ba zata dena Sonsa ba. Tana tsaka da wanke sauran kwanukan da akaci abincin rana dan har a yanzu babu abinda ya canza daga ayyukan da takeyi a cikin gidan, hatta Anty data ce ta karbi girkinta Abba yace ya hana ya kuma tambayeta dalilin da ya saka ta take umarninsa ta tabbatar masa da babu komai. A gaban Mama da ita Umaiman yayi mata tambayar dan Maman tana yawan yi masa tanbihi akan wasu sauye sauye datake gani daga Antyn, tana tsoron zamansu na shekaru ya canza salo a gargara dan ta tabbatar da mawuyacin abu ne su maimaita shekarun da sukayi a baya tare sedai wani iko na Allah. Anty ta dage akan ita babu komai Yayin da Abba ya dage akan seta fada masa dalilinta, cikin wani yanayi tace "Allah ya sani Alhaji babu wani abu a zuciyata akan Mama ko yaranta. Kuma ni idan ma akwai wani abu dana kasa jurewa be wuce yanda tsayin lokacin nan tun dawoqar Umaimah gidan nan ka rasa walwalarka ba. Baka da isashshen lokacina hira me dadi yanzu bana samunta dakai Alhaji a koda yaushe idan ina tare dakai idan ba tunani kake ba to kana Sallah ko lazumi kuma se naga idan kana tareda Maman Yara kana walwala koda yaushe kana cikin tarairayarta da kwantar mata da hankali wannan abun ne yake damuna kuma zuciya bata da qashi se na ringa ganin kamar ka fifita buqatunta akaina bayan ni bani cw silar bacin ranka ba" Gana daya sukayi shiru suna sauraronta jin tayi shiru itama Abban ya nisa yace "Ina jinki Saratu se me kuma?" Seta ci gaba da cewa "Idan nayi zancen da Qawayena ko yan uwana maganganun da suke gaya mun su suke qara sakani a damuwa amma koma menene yanzu ya wuce tunda kaima fara dawowa Alhajin dana sani shikenan" "Oh Saratu kenan Saratu iyayen soyayya wato ke kulawar Mijinki da kika rasa itace tasa kika fara Kishi da yarki kina ganin ita ta dagula miki lissafi ko? To kiyi haquri, maganar kuma nafi tattali da bawa Malika kulawa ba abinda kia dauka bane ko Mutane marasa son a zauna lafiya suke gaya miki. Tabbas mun tsinci kanmu a cikin Jarabawa wadda dagani har Malika muna buqatar wanda ze lallashe mu ya jamu a jiki domin halin da muka tsinci kanmu ba qarami bane dole na shanye duk tawa damuwar na qarfafa mata guiwa amma baya ga haka babu wani banbanci ko bangaranci danake nunawa a tsakaninku kuskuren tunani ne kuma nagodewa Allah da beyi nisan da har wata baraka ta shigo tsakanin Iyalaina ba dan haka idan har a tsahon lokacin nan Saratu kina ganin cewar mun cutar dake muna neman afuwarki dani da Malika da kike ganin mun shiga haqqinki ke kuma ga Antynki nan ki nemi afuwarta akan muzguna mata da kikayi kika hanata samun sukuni da Mijinta" Abban ya sake fada gaba dayansu seda suka murmusa da jin maganar tasa se Anty tayi saurin sake cewa "Haba Alhaji wlh babu komai yafiya kuma tuni ta nema dukda bata mun komai ba ni na yafe mata dama ai Umaimah tawa ce ita take qina kuma komai ya wuce a gurina daman nasan shedan ne kawai da maganganun mutane suka nemi suyi tasiri akaina kuma nima ina neman afuwarku idan akwai abinda nayi na rashin kyautawa ku yafe mun" "Allah ya yafe mana gaba daya" Abban ya fada daga nan suka tashi kowa ya koma sabgogin gabansa. Sallamar Maman Asad ce ta katse mata tunanin da takeyi, ta dauraye hannunta ta miqe tana mata sannu da zuwa tareda karbar ledar data shigo da ita. Seda ta rakata har dakin Mama kafin ta fito ta shiga kitchen ta debo Zobo da Kunun Aya na roba data farayi na siyarwa bisa shawarar Nuratu, itace ma ta bata Jarin Dubu biyar ta fara kuma Alhamdulillahi tana samun na kashewa tunda daman sana'ar Anty ce ta saki ta dena. Seda ta ajiye mata su ta dauka tana cewa "Karfa mu karya Jarin" "Haba dai, ina su Khairi kikazo ke kadai" Umaimah ta fada tana miqewa harta Juya Hajiyayyen ta tsayar da ita tana cewa "Ni Umaimah wai baki da kaya ne se wadannan tsummokaran?" *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 83 "Ina dasu Mana amma gaba daya sunyi mun yawa. Wadanda kika ga ina sakawa su kadaine suke zama a jikina shiyasa" Umaiman ta bata amsa hawaye na neman balle mata, abu kadan ke sakata kuka yanzu yanda kasan matar mamaci. Mama data fito daga dakinta tace "Kema da sonbata bakinki kike daman tunda kike da ita kinga tana saka suturun arziqi ne? Ga dai kaya nan kamar su kasheta bata saka ba bata kyautar ba shekara da shekaru a haka duk zasu ratattake su mutu bata mora ba" se kuwa hawayen da take riqewa ya balle dukda Mama tace ta yafe mata abubuwan data aikata amma sauda yawa irin yanda take mu'amalantarta se taga kamar har sannan da sauran fushinta a ranta. Babu ranar banza da bazata fada mata maganar da zata sosa mata zuciya ba, idan bata goran ta mata cewar sa'anninta nacan a gidan aure suna aikin lada ba seta mata shaguben koda ace zatayi aure a gaba inta samu ma'aurin kenan abinda take gudu gidan me mata zata shiga, ta kaso auranta akan wata kuma zata auri Mijin wata me kenan tayi da sauran maganganu masu sosa rai kuma ko a jikinta zata yaba mata kuskure kadan zatayi ta rufeta da fada tasani Mama na da duk wata dama ta jin haushinta domin tayi abinda dole koma waye ya washsheta amma a kullum tana addu'a Allah yasa su yarda da nadamarta, su yarda da cewar tayi dana sanin duk abubuwan da suka faru a baya sannan a shirye take data gyara kurenta idan ta samu damar hakan. Jiki a salube ta koma taci gaba da ayyukanta tanayi tana goge hawaye sosai zuciyarta take mata zafi, idan da ace tana da yanda zatayi ta goge baqin febtin da tayiwa kanta da tayi kota samu sauqin abubuwan data ke fuskanta a rayuwarta a yanzu. Ta tabbatar badan tasirin addu'a ba data zauce, ta kuma yarda abinda ta rasa kenan a baya rayuwarta ta ringa walagigi ta ringa ayyuka cikin rashin nutsuwa da tunani babu neman zabin Allah a cikin lamuranta abinda zuciyarta ta darsa mata kawai shine daidai a gurinta da ace tun a sannan ta karbi gyaran da masu sonta suka ringa yi mata da bata tsinci kanta cikin Halin nadama mara amfani ba. Harta gama wanke wanken ta wuce daki da tayi niyyar ta koma falon Maman suyi hira da Maman Asad amma ba zata iya ba ta lura yau Mama da uta ta tashi a ranta gara taja jiki ta koma gefe. Tana kwance Maman Asad ta shiga da jakarta alamar tafiya zatayi daman ba zama tazo yi ba, ta tashi zaune tana kallonta itama ta nemi guri ta zauna tana cewa "Kwanciya kikayi?" "Eh wlh so nake na dan huta kafin anjima" ta bata amsa seta gyara zama tana cewa "Dan Allah ki ringa gyara jikinki Umaimah tsafta ai tana cikin Imani amma ki ringa yawo a gida yarkace yarkace dake duk wanda ya shigo ya fita se yayi dake meye amfanin hakan bayan kina da suturun sakawa ba baki dasu ba. Sannan wannan uban baqin da kikayi da rama bafa sune zasu nuna cewar kinyi nadama ta gaske ba, wannan tsakaninki da Allah ne da kuma ta hanyar ayyukanki za'a fuskanci hakan amma quntatawa ranki da kikayi babu abinda ze qareki dashi sedai ya haifar miki da ciwon damuwa dan haka ki saki ranki, qaddara dai kowa da kalar tasa ke kinga taki Jarabawar a rayuwa se kiyi qoqarin cinyeta amma damuwa kuka tunani duk ba zasu baki mafita ba Addu'ar dai ita zaki cigaba dayi ki nace da roqon gafarar ubangiji in sha Allahu komai ze daidaitar miki, komai ze wuce ki gani tamkar be faru ba". Kanta na qasa har Maman Asad tayi shiru kafin ta dago fuska shabe shabe da hawaye tana cewa " Yah Hajiyayye kenan ai wanda yake da nutsuwar zuciya shiyake kwalliya nikam a matsayin da nake in har kaya zasu suturtani sannan babu wata qazanta a jiki da zata kawowa Ibadah ta tangarda bani da matsala. Wanka ma idanta qure harda Klin inayi mai kuwa sedai ka shafa dan kar qaiqayi ya dameni amma badan wai fatata tayi kyai ko wani ba ba. Maman Asad, Allah kadai yasan halin da nake ciki irin zafin da nakeji a zuciyata baze misaltu ba. Nasan na tafka babban kuskuren da babu wanda zeyi mun uzuri amma ina fatan ubangijin daya ce idan munyi kuskure mu tuba saboda shi ze yafe mana ya dubi nadamata. Allah ya sani ina cike da nadama me tsanani da dana sanin ayyukana na baya, da ace ina da iko dana sauya rayuwata Yah Hajiyayye, da ace zan samu dama a karo na biyu danayi qoqarin wanke kaina a zukatan duk wadanda na batawa amma bana zaton zan zamu wannan damar, abu daya nake da buri a yanzu kafin na koma ga mahalicci na na samu damar neman gafarar duk wanda na zalunta a baya su yafe min shi kadai ne abinda ze samar mun da nutsuwa a rayuwata". Hajiyayye tayi shiru, tausayin yar uwarta ya cikata ita shaidace da cewar Umaiman tayi laushi ta kuma gasgata Nadamarta ta gaske ce bawai wuya ce ta sakata saduda ba kamar yanda Mama take fada. A taurin kai irin na Umaimah ta tabbatar da ba aikin wahala ba ko kasheta za'a yi babu abinda ze canza mata ra'ayinta haka inda ace bata zubda makamanta ba bazata taba kulluwa tsayin shekara hudu da ranta da lafiya ba tareda ta fita ba koda ace hakan na nufin ta bar gidan kenan na har abada a Umaiman dasuka sani a baya zata iya zabar hakan tunda kuwa harta jure komai tsayin lokacin nan ta yarda da gaske takeyi sedai kamar yanda ta fada zeyi wahala mutane su yarda da ita har suyi mata uzuri amma yardar Allah ita Umaimah tafi buqata a yanzu domin idan harta gyara tsakaninta da Mahaliccinta komai zezo mata da sauqi sedai kamar yanda ta fada haqqin wadanda ta cutar baze barta ta samu nutsuwa ba harse ta saukeshi. "Dan Allah Maman Asad zan roqeki Alfarma, karkice ba zaki mun ba. Banida hanyar da zan hadu da Khalil ko wani cikin Ahalinsa kinga bana fita sannan bani da waya kuma koda ma ace na gansu bani da kwarin guiwar da zan iya kallonsu. Kiyi mun wannan alfarmar koda ace shine abu na qarshe da zaki mun saboda Allah ki nema mun afuwa a gurin Khalil da Hajiyarsa a matsayinki na Jinina. Ina so na roqi Mama ko Abba suyi mun wannan alfarmar amma nauyi da kunyarsu baze barni ba, sun roqeni dana kwantar da hankalina a baya na toshe kunne na nayi abinda nayi a yanzu da komai ya rincabemun bazan iya roqarsu da su nema mun sassauci a gurin wadanda na batawa ba iyakar alfarmar da sukayi mun ta yafe mun muzgunawar da nayi musu ta isheni". Shiru Maman Asad din tayi tana kallonta saboda abinda ta roqetan yayi mata girma ba kuma tajin ita kanta tana da qarfin guiwar da zata je nemawa Umaimah yafiya a gurin Khalil ko Hajiya. Iyakar murje idon da sukayi suke neman Yaran ya isa ba zata so ta tado da abinda ya shude ba ballantana radadin abun ya waiwayesu har a qarasa gutsire yar guntuwar alaqar da ake riritawa a tsakani. Umaimah ta kama hannunta idonta na zubda hawaye tace "Nasan abin da wahala amma idan na mutu da haqqinsu nasan Allah baze dubeni ba Yah Hajiyayye. Na cutar da Khalil matuqa na sani kuma ba lallai ya yafemun ba amma dukda haka ina so ki gwada nema mun wannan alfarmar su yafe mun nauyin da nake ji nasu akaina ya ragu ko zan samu nutsuwar da kuke buqata ku ganni a ciki". Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kalli Umaiman tace "Ban daukar miki alqawari ba amma zanyi bakin iyawata dukda ni kaina inajin nauyi da kunyar abubuwan da suka faru. Tun gabanin haduwarki da Khalil na zauna da Hajiya ta kuna daukeni kamar yarta irin yanda ta riqeni yasa har tayi sha'awar hada jini damu ta dage har seda ta tabbatar da qulluwar aure a tsakaninki da gudan jininta. Duk abubuwan da kika aikata Hajiya bata taba kware miki baya ba. A gabanta kin zageta amma tayi miki uzuri har Mama ta umarci Khalil ya rabu dake Hajiya bata so haka ba a yanzu da nake miki magana tunda muke turawa a daukar Mana Yayanki ko a fuska Hajiya bata taba nuna wani abu ba tayaya kike so naje gurinta Umaimah na sake tado mata da abinda ya wuce wanda na tabbatar da ba mantawa tayi ba tsabar dattako da karamci irin nata ne yasa ta mayar da komai ba komai ba. Zanso ki bar komai a yanda yake kici gaba da addu'a da neman yardar ubangiji muma muna tayaki in sha Allahu komai ze daidaita Umaimah kinji" "Kina nufin ba zaki iya ba kenan?" Umaimah ta fada cikin kuka domin Maman Asad dince kadai dogaronta da zata iya nema mata gafara a gurin Khalil da Hajiya a madadinta, se Maman Asad ta kama hannunta tana cewa "Ba haka nake nufi ba Umaimah. Kece mafi cancanta da ki nemi yafiyarsu abinda nale nufi kici gaba da addu'a har zuwa sanda komai ze daidaita ki samu damar neman yafiyarsu da kanki" seta sassauta kukan tana kallon Hajiyayyen tace "Kina ganin zasu yafe mun?" "Meze hana, a rayuwata ban taba ganin mutane masu karamci kamarsu ba Umaimah na tabbatar ko a yanzu sun yi miki afuwa tunda har suka bar Yaranki suke zuwa gurinki hakan yana nuna fushin da sukeyi dake ya ragu, kici gaba da addu'a yanadaga cikin tasirinta" Maman Asad ta fada kafinta miqe tana cewa "Bari naje saqo na kawowa Mama daman se ranar Juma'a in Allah ya kaimu duk zamu zo Naziyya ma tana tafe ranar Alhamis kuma idan tazo karki kuskura ta sake barin garin nan baku warware gabar dake tsakaninku ba" "Toh ai ba laifina bane, cewa tayi bata yafe ba idan na sake yi mata magana babu ita babu ni ni kuma naga haqqoqin da suke kaina da yawa balle na sake daukar wani shi yasa na rabu da ita amma Allah ya gani ni ba gaba nakeyi da ita ba maslaharta na duba" Umaiman ta fada tana miqewa tsaye itama seta juya ta fita tana cewa "Nidai na gaya miki kuma ki fitar da kayayyakinki wanda suka miki yawanki bayar akai gidan Mama Nana ta rage miki ki dena yawo kamar wata Yar gudun Hijira" "Kiyi haquri amma bazan kai kayana gidanta ba, ita ta ringa yawo dani a unguwar nan tana fadar abinda ya faru da Wanda ma be faru ba dayawanmasu shigowa siyan zobo fa badan Allah suke zuwa ba se dan kawai suga yanda na koma. Baki ga tururuwar da aka ringayi ba sanda Salman ya fita dashi yace an dawo yin Zobo a gidan nan, harda Maza A gulma Maman Asad ba kunya suke shigowa da girmansu wai siyan zobo ni wlh har fargabar ranar da zan sake fita daga gidan nan nakeyi nasan gaba daya labarina ya karade ko ina qila har Film da Novel anyi a kaina ko? Inaga bazan sake fita daga gidan nan ba gara nayi zamana nayita istigfari ina hailala har ranar da ubangiji ze dauki raina kawai bazaniya fita ba ina tsoron tozarcin da zan fuskanta idanna fita waje" Umaimah ta fada tana shirin sake fashewa da kuka se Maman Asad taja tsaki tana cewa "Ai sekiyi, duk me cikakken Imani ya yarda da qaddara me kyau ko mara kyau dan haka idan ya ganta akan dan uwansa ba dariya zeyi masa ba sedai ya nema masa sauqi gurin Allah ya kuma nemi kariya daga afkawa irinta ki nemi yardar Allah kawai shine mafita a gareki ni bari naje yara sun kusa tasowa" daga haka ta fice ta barta. Komawa tayi ta kwanta tana cigaba da tunanin da ya zame mata jiki yake kuma neman zauta mata tunani. Ranar Juma'a su kazo kamar yanda ta gaya mata, Naziyya tazo tun Alhamis amma kamar yanda suka saba tun bayan dawowarta gida ta shata mata layin babu ita babu ita wannan karon ma haka akayi. Ranar Juma'ar da suka takura mata akan tayi haquri ta janye gabar ko babu komai ita babbace tayiwa qanwarta uzuri Kuka ta fasa musu kai tsaye tace "Babu uzurin da zan mata ai da hankalinta ba mahaukaci bace ita kuma tana sane ta aikata duk abinda tayi ba tareda tayiwa kowa uzuri ba. Ni nasan girma da darajar Iyayena dan haka bazan taba shiri da wanda ya wukaqanta su ba, Yanda ta saka su cikin tasku ta jefe su da maganganu har tayi sanadiyyar zubar hawayensu bazan taba yafe mata ba kuma zata gani, itama ta haifa da ranta dan cikinta seya gwada mata abinda tayi koma wanda ya fishi, haqqin Khalil dana sauran mutanen da kika dauka Umaimah baze taba bari ki zauna lafiya ba". Gaba dayansu suka dauki salati Cikin tsananin tashin hankali Umaimah ta rushe musu da kuka, Mama ta sallame sallar La'asar da takeyi babu bata lokaci ta dauke Naziyyan da mari tana cewa "Wace irin zuciya gareki Naziyya dagani har mahaifinku bamu kasance masu taurin kai da kafaffiyar zuciya ba a ina kuka samo taku? taskun da yar uwarki take ciki be isheki ba se kin bita da mugun baki akan me? muda tayiwa laifin munce mun yafe se kece zaki qullaceta ki ja mata mugun Alkaba'i to ahiri dinki kuma idan na isa dake ki janye kalamanki kuma ki shirya da yar uwarki. Iyakar bakin data dibarwa kanta ya isheta base kin bita da naki ba Allah ka shiga lamarin Zuri'ar mu karka saukar da rabuwar kai a tsakaninsu" Maman ta qarasa tana fashewa da kuka itama. Tashin hankalin Umaimah ya qaru, yanda falon ya rikice da kuka kuma ita ce sila. Ta ringa wani irin kuka danta gagara cewa komai, nadamar rayuwarta ta sake daureta, tun usuli itace matsalarsu, itace kukansu duk wani jaye jayen rigima itace bata taba barin zukatansu su huta gashi yanzu tana neman zama silar rugujewar zumunchinsu Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Dakyar take tafiya saboda yanda idonta ya rufe bata gani ta samu ta fada kan gadon dakin da take, Nuratu data bi bayanta tana kuka itama ta dagota tana cewa "Ki kwantar da hankalinki, karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki" "Gaskiya ta fada Nuratu nima kuma na sani, duk abinda yake faruwa a yanzu na tabbata ba komai bane domin tsiyar dana shuka ta zarci na fuskanci iyakar wannan matsin a matsayin sakayya na sani dole haqqi seya bibiyeni amma dan Allah ku tayani roqon Allah kar Yarana su kangare, bana so laifina ya shafesu bana fatan su tashi da mummunar dabi'a irin tawa" ta qarasa tana fashewa da kukan dayafi na farko rauni ta fada jikin Nuratu suka rungume juna suna kukan tare, yanda jikin Umaiman yake rawa ya sakat tsayar da nata kukan dole ta ringa bata baki, dakyar ta dena kukan itama tace mata ta kwanta bata musa ba ta kwanta maganganun Naziyya na mata yawo akai yar uwarta ta jini kenan to inaga wani bare? Wane irin maganganu mutane suke fada akanta? Wace irin tarba zata samu idan ta sake fita duniyar mutane? Nuratu data fita ce ta koma dakin da ruwa da kwayar magani guda biyu ahannu ta bata, bata musa ba tasha dukda bata san kona menene ba amma tana da buqatar abinda zegusar mata da hankali a yanzu koda bacci ne ta samu tayi kafin zuciyarta ta ida tarwatsewa, kanta sara mata yakeyi kamar ze rabe biyu ga bugun da zuciyarta takeyi ya wuce qa'ida jikinta kansa rawa yakeyi. Tana sha ta mayar da idonta ta kulle bata dauki minti biyar ba bacci me nauyin gaske yayi gaba da ita se sannan Nuratu ta sauke ajiyar zuciya ta fita. A falon Mama ko kukan da takeyi ya daga musu hankali Matuqa har Anty da hayaniyarsu taja hankalinta ta shiga tayasu kukan, ta kalli Naziyya dake kuka itama tamkar tace "Kinga ai kun zama daya keda ita har gara ita dan yanzu tana qoqarin goge duk laifukanta ta hanyar farantawa Mahaifiyarku amma ke yanzu me kikayi? Kinyi sanadiyyar zubar hawayenta kin baqanta mata zuciya a zatonki abinda kikeyiwa yar uwarki dadi zataji ko kuwa kin dauka ta dena sonta ne kamar ku? A yanzu babu abinda ze faranta mata illah taga hadin kanku amma a maimakon hakan kina nema ki haifar da sabon tashin hankali a cikin gidan nan iya wanda muka gani a baya ya isa ina roqonku dan girman Allah ku sararawa rayukanku ku rungumi yar uwarku da qaddarar data afka mata dan bata da kowa sama daku. Idan Umaimah nada laifi kuma kuna dashi saboda baku da wata hujja da zaku kafa data saka kuka barwa Duniya ita kuka zame hannunku daga al'amuranta qarqari kuce bata jin shawararku shiyasa kuka wofantar da ita, da ace kun cigaba da naci da cusa kanku cikin lamuranta da ko baku san komai ba dole zaku san da yawa daga abubuwan da suke faruwa da ita amma kuka barta a hannun qawayen banza da suka kaita suka baro a yanzu babu wanda ze zage su kudin dai ku za'a zaga akan idonku qanwarku ta lalace take abubuwa tamkar bata da kowa a duniya da ze nuna mata daidai. Ke kanki Mama yau zan fada miki kina da naki laifi domin ke kika fara bada qofar da Umaimah ta samu damar yin duk abubuwan da takeyi. Tunda kika san Umaimah zuma ce seda wuta be kamata kiyi mata sako sakon da har zata ringa aiwatar da abubuwa yanda taga dama ba. Dukkan mu nan shaida ne duk sanda kika murde kika nuna mata fin qarfi tana lankwasuwa tayi abinda kikeso koda ace ba'a dadin rai ba amma zatayi idan kuma kika bata umarni bata qetarewa koda kuwa ranta be so ba, da ace kinci gaba da bibiyar rayuwarta kamar yanda kikeyi da farko da abubuwa da yawa basu faru ba amma se kema kikayi fushin zuciya kika zuba mata ido Alhalin kin san Umaimah tana cikin zubin Halittar da ubangiji yayi basu da tunanin kansu suna amfani da duk abinda suka gani ko sukaji kuma yayi daidai da qawa zucinsu basu duba kyautuwa ko rashin dacewar abu muddin yayi daidai da ra'ayinsu shikenan kinga kenan kamata yayi ace kinci gaba da zama tunaninta kamar yanda kika fara tun farko kina tursasata tabi ra'ayinki koda bata so da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Nida nake janta a jiki tana wulaqantani ai ba zuciya ce bani da ita ba data sa na shanye naci gaba jibantar lamuranta nayi hakan ne saboda karta rasa kowa cikin rayuwarta. Muna yiwa Ubangiji laifi ya yafe mana wani ma ba tareda mun roqi afuwarsa ba me yasa bazamuyi koyi da haka ba muma mu zama masuyin uzuri ga junanmu? Mu rungumeta mu tayata fuskantar duk wani qalubale daze taradda ita bawai muci gaba da tunzurata ba harta sare nutsuwar data saukar mata ta barta ta koma ruwa abinda zata aikata se sunfi na baya muni sannan duniya taci gaba dayi mana tofin ala tsine saboda baza'a zagi Umaimah ita kadai ba tilas duk wanda labarinta ya riske shi seya hada da ahalinta". Kalaman Anty suka kashe musu jiki muqus suka kasa yin ko wani kwakwkwaran motsi a gurin se jan majina da ajiyar zuciya sukeyi. Tabbas Anty batayi qarya ba suna da hannu cikin tabarbarewar Umaimah kuskurensu kuwa shine fushin zuciya da sukeyi akan lamuranta da kuma qin tsanantawa da cusa kai yanda bata daukarsu da muhimmanci suma suka saketa ta hadu da masu tunani irin nata suka qara dulmiyata ruwa gashi yanzu suna raba bacin randa ita dan duk inda suka shiga a shekarun baya se anyi zundensu wasu ma suna fadin da saka hannunsu tayi abinda tayin, a lokacin Maman Asad Mijinta fasa auran dayayi niyya yayi saboda ya tsorata da abinda Umaimah ta aikata. dukda be taba ce mata komai akan maganar ba itace dataji zancen fasa auran tayi masa magana kai tsaye kuma yace mata "Daman bawai na matsu danayi auran bane kuma na haqura tunda ina sonki kar nayi biyu babu" maganarsa ta daure mata kai sosai kuka bata fahimce shi ba seda yan uwansa suka tasata a gaba suka ringa yada mata da magana sannan ta fuskanci tsoratar da yayi, har kuka seda tayi tana ce masa ko a tunani bata taba kawo cewar ta cutar dashi saboda zeyi abinda Allah ne ya halasta masa ba shi kuwa yace mata babu wannan maganar, daman rashin nuna damuwar da tayi ya bashi mamaki to maganin kar ayi kar a fara aure dai ya haqura har gaban Abada na bar maganar qara aure Hajiyayye ta ishe shi shikenan maganar ta mutu. Ranar dai haka sukayi wunin jigum jigum Abba ya dawo Anty ta kwashe yanda akayi ta mayar masa ya ringa fada kamar ze ari baki ga baccin da Umaimah take tayi ya sake rufe Nuratu da bala'in me ta bata har yana rantsuwar idan suka kashe masa Ya duk se yayi qararsu ai badan basa son ta bane laifi tayi suke nuna mata kuskurenta ba kuma hakan ne yake nuna basa qaunarta ba. Nuratu ta ringa rantse rantae akanita maganin bacvi kawaita bata saboda damuwar data shiga komai ze iya faruwa da jininta ko zuciyarta amma idan ta samu bacci zata huta kuma hankalinta ya kwanta, be barta ta fita daga gidan ba se qarfe goma bayan Umaimah ta farka kuma Mijinta Dr Sagir yazo ya qara tabbatar masa da maganindata bata bashi da illah, wai ranar har Abba ne yakecewa shi be gama yarda da sahihancin Likitancin ta ba, ya manta da cewar ita take kula dashi, kaf jinyar hawan jinin da Umaimah ta sababamas aita ce take lura dashi amma yau da yake antabo tsomar zuciyarsa ya fitittike, daman abinda take amfani dashi kenan ta karanci sunfi sonta shiyasa take wahal dasu, kuma daman a rubuce take, duk abinda mutum ya kwallafa rai a kansa se an jarabce su dashi, babu wata soyayya data cancanci dukkan zuciya data wuci ta Allah da Manzonsa. Wannan dambaruwa ta ninka damuwar Umaimah, duk yanda suka yi qoqarin nuna mata komai ya wuce hatta da Naziyya da kanta ta bata haquri ta kuma nemi afuwarta ta akan abinda ta fada ta gagara samun nutsuwa. Kalaman Naziyyar sunyi matuqar yi mata tasiri kuma sun qara tsoratata tareda maido mata da abubuwan da suka wuce tana hasaso ta inda haqqindata fada ze fara bibiyarta, a kullum ta daga hannu sama takance "Allah ka bani ikon neman yafiyar wadanda na zalunta tun ina da sauran numfashi, ubangiji na roqeka karka karbi raina na dawo gareka da nauyin wani akaina Allah ka dubeni ka karbi tubana ka kawo mun dauki a cikin al'amurana", a haka rayuwa taci gaba da tafiya, duk yanda take tunanin samun sauqi abun ya faskara, damuwa ta mata yawa, hatta da zobon data fara ta saki dan masu siyan zobon da yawa da biyu suke mata cinikin izgili da wulaqanci yake sakasu siyan zobon dan hatta gidansu an canza masa suna zuwa gidansu Umaimah me zobo irin abubuwan da ake mata idan an shigo siyan zobo na izgili da wulanci ya saka Abba ya hanatayi, ta roqeshi akan ya barta taci gaba amma zata samu Almajiri ya ringa fita dashi waje a dena shigowa cikin gida siya dan har sannan dubi dayan nan yake bata zobo kuwa ba qaramin rufin Asiri yake kawo mata ba sannan suma yan gidan susha, na musamman takeyiwa Abban saboda yana da Sugar kullum kuma yasha ze saka mata albarka ko babu komai zata tasiranci bacin ran data sakasu a baya shiyasa ta nace akan ya barta taci gaba, sedai sau biyu tayi ta bari gaba daya dan ranar farko na dubu biyu tayi bama kamar yanda ta sabayi a cikin gida ba zubin Hamsin da Dari takeyi seta yi na dubu biyar ya qare tas har ana nema se gashi a na dubu biyun dakyar akayi dari bakwai, dari biyar ma Almajirin ya kai mata wai sauran bashi aka karba Jikokin gidan suka shanye dan ranar suna nan washe gari yanda aka fita dashi haka aka dawo mata dashi dan taja masa kunne akan karya bada bashi yace kuma duk wanda yaje wai se yace bashi shiyasa ya dawo mata dashi shikenan sana'ar zobo ta gurgunce ta tasa dan abinda ta tara a gaba da buqatu suka qare ta sake komawa yar gidan jiya amma duk wannanbe wani dameta sosai ba domin tasan kowanne tsanani yana tareda sauqi kuma wata rana komai ze zama tarihi. Babban tashin hankalinta a yanzu fitinar Bibi da a kullum qara bunqasa takeyi, a yanzu bata kwana uku bataje gidanba haka zata tasata a gaba da kuka akan ta dawo gidansu idan tayiwa Dady magana se yace ta tambayeta shi babu ruwansa itace taqi dawowa, idan ta saka mata wannan darun seta ce mata "Idan kinyi sallah kullum ki ringa mana addu'a idan da Alkhairi tsakanina da Dadynku Allah ya daidaita mu". Bibin bama gane hausar takeyi ba, data gaji da nacin tambayar Umaiman ta ranar ta tambayi Mama yaushe Momynsu zata koma, kai tsaye tace mata "Momynki da Dadynki sun rabu ya saketa ba zata sake komawa gidanku ba ga sabuwar Momy nan ya samo muku kuma tana sonku tana kula daku keda kanki kina fadamun koba haka ba? Dan haka itace matar Dadynku yanzu Momynku kuma gata nan anan gidan kina zuaa kina ganinta karki sake damun wani da tambayar yaushe zata koma gidanku dan ba zata koma ba". Umaimah tayi tsam dan kalaman Maman basu mata dadi ba sannan gani takeyi ai sunyiwa Bibi girma ba zata fahimci abinda take nufi ba, ga mamakinsu gaba daya se ji sukayi yarinyar tace "Dama Halima ta gaya mun indai Mamah tana gidan mu Momy ba zata taba komawa ba dan haka zan gayawa Dady sedai ya zaba ko Momy ko Mamah" Umaimah ta riqe baki, Mama ta fizgota tana cewa "Dan ubanki wacece wannan Halimar da kika samu da duk wani abu na diban albarka idan kinayi zakice Halima ce takeyi ko ita ta fada? Tun yanzu kema kin fara tara qawayen banza masu gurbata tunani ko to kuwa baze sabu ba da kaina zan kira uban naki sedai ya canza miki makaranta ya rabaki da koma wacece da take nema dasa miki mummunar dabi'ar qin matar ubanki" ta sata a hammata ta kileta, tana kuka take cewa "Wlh sena gaya masa kuma ai yana sona nasan zeyi abinda nace" ta ringa birgima tana tijara, Mama ta dakko wata dorinar Yasir da yake zane yara a Islamiyya wai shi prefect ta ringa caula mata ba shiri ta miqe ta bita seda tayi mata lilis kafin ta watso mata hijabinta da wata yar Berbi bag tace "Wuce ki tafi, daman zanzo har gidan naku Allah yasa naji wani labari mara dadi zaki gane kurenki yar banza me kunne kamar Area", ita dai bata ko debi takalmanta ba tayi waje seta dawo da gudu tana kuka tace wa Maman "Kuma Hajiya tace na gaya miki Mamah ta haihu amma bazan fada ba tunda kika dokeni kuma dan kiji Babyn qato fari irin Aryaan sunansa ma Mukhtar Dady yace" tana gama fada ta diba da gudu ta fice, daman ita kadai aka kawo Manniru ya dauketa suka wuce gida tun kuma daga wannan zuwan seda aka kwashi tsahon lokaci basu je ba. Wani irin Duum, kunnen Umaimah yayi mata, ta kalli Mama data bi Bibin da dariyar yarintarta tana cewa "Ja'ira to ai kin fadi saqon Masha Allahu Allah ya dayyaba wannan karon ko zamuje barka in Allah ya yarda bari Alhaji ya dawo na gaya masa gashi ma Takwara ya samu, Allah ya rayashi yayi masa Albarka" har Mama tagama addu'arta ta juya tana zaune inda take wani irin abu ya shiga bijiro mata seta dafe zuciyarta a fili ta shiga maimaita Innalillahi, Mama ta kalleta ta gyada kai tana cewa "Iska na wahal dame kayan kara, to ke yanzu Kishi za'ace yana damunki ko kuwa baqin cikin kinji matarsa ta haihu lahanin da kika masa beyi tasiri ba se kije ki dauki ruwan sanyi kisha kiyi maimaita Hasbunallahu ko kya samu ciwon naki ya lafa" taja tsaki ta shige daki hali irin na Umaimah dai Allah ya canzawa masu shi. Ita kuwa daki ta cige ta kife akan Gado ta shiga kukan da bata san dalilinsa ba, Khalil dai rayuwarsa yake yi ya manta da ita da alama ita ce take ta dakon soyayyarsa da yaqinin wata rana ze iya sake dubanta amma daga alamun da take gani bata da wannan sauran damar. GIDAN KHALIL *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 84 GIDAN KHALIL Rayuwa taci gaba da tafiyarwa da ma'auratan cikin aminci da yarda da Juna, cikin Humaira ya shiga watan haihuwa, da kyar da lallami Khalil ya janye qudurinsa na canza mata Asibiti tunda ya tabbatar da cewar a nan Asibitin da suke zuwa Noor tsohon saurayinta yake aiki. Tun ganinsu dashi na farko hankalinsa ya kasa kwanaciya, haka kawai gabansa ya ringa faduwa idan ya tuna irin farin cikin daya gani akan fuskarta a dalilin ganin Noor din daya tabbatar shita fara so kafin shi. Da sati ya zagayo zata koma Asibiti tare sukaje dukda tarin ayyukan da suke kansa haka ya share ya tare ya tsare har seda ta gama komai ya maida ita gida kafin ya wuce office, seda suka jera sati biyu yana kaita kullum sukaje kuma se yaga Noor din amma baya taba bari su hadu da Humairan. Haka kawai ta tashi da rigima a cewarsa kenan wai bata jin dadi ita Asibiti zataje, takaici ya qumeshi, daman kwana sukayi suna rikicinta da bashida qarshe yanzu da cikin ya tsufa lamarin ta qara tabarbarewa yakeyi kullum cikin nemansa da magana take tana sane tun dare ya gaya mata zeje Katsina duba wani aiki amma safiya nayi ta shiga riqe qafa wai ciwo take mata bata iya tafiya dole yace ta shirya su tafi Asibitin. Har sun fito ze kaita Jamila ta kirashi Danta ya fado daga Bene kansa ya fashe gashi babu kowa a gidan Babansu baya nan ita kuma bata iya mota ba daman ta roqeshi akan ya tura mata Khalifa idan yana gida ta kira bata same shi ba.. Khalifan baya gari yana Dutse inda yake aiki a CBN dinsu dole ya bar Humairan ta tafi da Driver shi kuma ya wuce gidan Jamilan ya daukesu ita da yaron da yake ta kuka saboda yanda yaji jiki, seda sukaje Asibiti aka fada musu bayan fashewar kan ya samu karaya a Hannunsa na hagu da Targade a yatsun qafa. Suna Asibitin amma hankalinsa yana kan Humaira, ya kira wayarta ta ringa qara bata dauka ba ya sake kira nan ma haka seya maida akalar kiran ga Manniru inda ya sanar dashi har sannan suna Asibitin basu fito ba. Ganin da yayi anyi stabilizing Amir, duk sun liqe masa ciwu kan har an bashi gado yasa shi cewa Jamilan zeje ya dawo "Ai bama seka dawo ba kawai ka tafi aikinka tunda komai ya daidaita munyi waya da Babansu yana hanya ze zo shima nagod kwarai Allah ya qara zumunchi" Jamilan ta fada seya fita bayan ya sake yiwa Amir din fatan samun sauqi. Zuciyarsa cike da wasiwasin abinda ze hanata daukar wayarsa, ya saqa wancan ya kwance shaidan na son kawo masa wasi wasi yana kaucewa shi a haka ya qarasa Asibitin. Kai tsaye office din likitan da take gani ya wuce ta sanar masa da ta turata Lab ayi mata test ita dinma zaman jiran ta kawo mata result takeyi dan ta gama sallamar kowa ita kadai ta rage seya wuce Lab din zuciyarsa na bugawa da qarfi, daga inda yake tsaye yana kallonsu ta cikin Glass Noor din riqe da hannun Humaira ya daure sangalalen da farar roba yana shafa inda jijiyoyinta suke fuskarsa dauke da wani murmushi da Khalil ya fassara daban ita kuma ta shagwabe fuska harda kwalla a idonta irinta me tsoron Allura. Daga wajen ya tsaya saboda yanda qafarsa tayi masa nauyi amma zuciya ta harziqo masa har wani rawa jikinsa ya dauka cikin zafin nama ya tura qofar Lab din ba tareda ya bi dokar hana mutane shiga dake rubuce a jikin qofar ba yana shiga beyi wata wata ba ya make hannun Noor dake shirin sokawa jijiyar daya nemo Allura dan ya debi jini da qarfin da Allah ya bashi, Allurar ta fadi qasa shi kuma ya miqe a razane dan jiyayi kamar ya kwada masa rodi a hannun saboda zafi ya ware ido yana kallon Khalil kamar yanda shima yake kallonsa tsoron yanayinsa ya shigeshi da kuma gargadin da Dr Al'amin mamallakin Asibitin ya kirashi takanas yayi masa akan Matar mutumin daya kira Khalil. Ya kalli Humairan ya kalli Noor gaba daya sunyi tsilli tsilli kamar ace musu ket su fece da gudu, shi fargabar rasa aikinsa ceta cikashi wanda dashi yake riqeda mahaifiyarsa da qanwarsa dan tun bayan da aka raba musu gado Yayyensu da suke uba daya suka dena yi musu komai Mijin data aura kuwa daman dashi gara babu dole yayi nutsuwar dole ya koma makaranta ya saki Aikin Sojan daya kwallafa rai akai da rayuwar shaye shayen daya fara dalilin rasa Humairan ganin Rayuwar Mahaifiyarsa na nema shiga garari na rashin mataimaki, yana kuma gama karatun ya samu aiki a wannan Asibitin da taimakon wani Malaminsu da suke shiri sosai kuma abokin Dr Al'amin ne, ko sanda ya kirashi yayi masa kashedin kula Humaira seda ya kira Malamin ya zamar musu shaida yanzu idan labari ya komawa Director yasan korarsa kawai zeyi wannan tunanin ya sakashi kai guiwoyinsa qasa ya dage hannaye yana cewa "Dan girman Allah kayi haquri kayi mun rai gasu nan ka tambaye su muna zaune ta shigo Lab din nan kuma duk sunyi sun kasa samun jijiyarta shiyasa ma karba wlh bada wata manufa nayi ba karka ce zaka hadani da Dr ni bani na gayyato ta ba da kanta tazo". Wani matsiyacin kallo Khalil din ya jefa masa ya sake kallonta ta sunkuyar da kai qasa ta kasa koda motsi a gurin seya ja tsaki ya juya kamar iska ya fice. Badan karya zubda mutunchinsa ba kuma duk inda akaje doka zata bashi rashin gaskiya dase ya nadawa yaron dukan tsiya a gurin. Da sauri kamar zata fadi tabi bayansa ganin ya nufi hanyar fita, ita kam yau ta shiga dari ma ba uku ba tsautsayine ya sakata zuwa Asibitin data sani ta daure ciwonta tayi zamanta kota bari seda daddare kamar yanda yace mata tun farko yanzu ta tabbata fassara daban zeyiwa Al'amarin saboda yanda yake tafiyar cikin fushi kafin ta fito harabar Asibitin fuce da motarsa babu bata lokaci ta shige itama Manniru yajata. Text ya shigo wayarsa ta bude hannunta na rawa tana ganin abinda yake ciki ta fashe da kuka kawia tana cewa Manniru Sharada ze kaita. Hankalin Mama Hauwa ya tashi da ganin Humairan dan a safiyar ma sunyi waya kuma bata ce mata zatazo ba sannan gata ta shigo tana kuka ta ringa tambayarta meya faru ta kasa bata amsa se Kuka dan bata san me zata ce ba, tana gudun suyi mata gurguwar fahimta kamar yanda Khalil din yayi ganin taqi shiru kuma taqi magana Mama ta dauki waya tana cewa "Bari na kira Hajiyar naji ko wani abun ne ya faru a gidan tunda kin kasa magan" se tayi saurin riqeta tana cikin kuka tace "Aa Mama karki kirata zece nakai qararsa, sabani muka samu da Yah Khalil yace na taho gida Hajiyan ma bata sani ba". Salati Mama ta dauka bayandata ajiye wayar tana kallonta tace "Yace ki taho gida? Me kika masa Humaira? Daman Sumayya ta gayamun kin saka jaraba a ranki gana daya kin kwarzabi rayuwarki kikayi haquri a sanda ma babu se yanzu rashin qoshi ze saka ki tayar da hankali to auran kike so ki kaso ki dawo gida kome?" "Ni wlh Mama ba wannan bane, laifi na masa daban yayi fushi amma nasan yana hucewa ze zo ya daukeni" ta fada tana kauda fuska tareda tura baki gaba. Daman ita Anty Sumayya matsalarta kenan Hansfiri ba'a maganar sirri da ita Anty Unaizatu kuwa kunya tasa ta kasa buda mata sirrin tasan lafiya lau da babu Wanda zeji amma yanzu ace har kunnen Mama ba zatayi mamaki ha idan Yah Habib ya sani ma. "Kyaci ubanki sakarya da bata da wayo, idan kikayi sagegeduwar da auran ya mutu ke kika sani kin ga kinyi tutar babu, kuma abinda kike rainawa wata idan ta samu godiya zatayi banda mafitina kina fama da kanki kina jaye jayen magana yanzu daya koroki ai shikenan" Maman ta sake fada kafin ta shige daki tana mita. Tunda Sumayya ta mata zancen har tace zata kira Humairan ta hanata a ganinta sunyi maganar sirri idan ta saka baki gana ba zata sake gaya masa cikinta ba. Humaira kuwa dakinta nada ta shige itama ta kwanta kukan da tayi yasa kanta yake mata ciwo ta kira layinsa duka biyu a kashe ta tabbata kuma kashewa yayi alamar fushin nasa me yawane amma ai ya kamata ya bata dama ta kare kanta ba wai kawai ya yanke hukunci daga abinda ya gani ba. Har Magriba tana gidan cike da zullumi dan har sannan wayar Khalil a kashe take sannan nabu wanda ya biyo sahunta. Ruqayya ta kirata tun da yamma akan Aryaan da Imaan sun dawo makaranta sunata rigimar nemanta tace ta rarrashe su tana gidan Mama idan Dadynsu ya tashi ze biyo ya dauketa se ce mata tayi ai ga Dadyn a gida tun gurin sha biyu ya dawo gabamta ya fadi kenan daga Asibitin gidan ya wuce lallai abun Azimun ne ita take daukarsa wasa. A sanyaye tayiwa Ruqayyan Sallama akan zata kirashi yanzu. Mama dake tsaye a bakin qofa da Hijabin data idar da sallah ta qarasa ciki tana kallonta tace "Laifin me kika masa idan na sasanci ne ayi tun wuri ki tattara ki komadan bazaki kwanar mun a gida ba idanba haka ba kuma sedai ki tafi gidan Unaiza tunda tun Asali daman ita take zugaki ko kashe auranki, se kace ba gara nako Mijin ma da nata ba". Ta sunkuyar da kai qasa wai ita Mama ba zata bar wannan maganar ba se tonata takeyi sannan ita ba zata iya fada mata abinda ya hadasu ba, ai ta tababta seta gwammace fushin Khalil akan Mama taji wannan labari. "Shikenan bari na kira Hajiya Aishar na gaya mata, ai baya koroki gida da tsohon ciki ba kuma tana gidan koma menene ai da gabanta ya kamata ku fara zuwa" Maman ta sake fada tana miqewa se Humaira ta marairaice mata danba zata manta ba yana yawan jaddada mata duk abinda ze hadasu komenene ta tunkareshi kai tsaye ta gaya masa, baya so takai qararsa gurin kowa musamman Hajiyarsa idanbata fada mata Alkhairinsa ba toh karta kuskura tayi masa lamba a gurinta dan shima baya kai qarar Mace gidansu danta masa abu, a ranta take ayyana qila Maman Mu'ayyad haka ta ringa masa shiyasa yake ja mata kashedi. "Ayya Mama dan Allah kiyi haquri karki kira Hajiya, na gaya miki zezo daya huce wlh koba yau ha gobe da safe zaki ganshi inma kiran kike so to shi ki kirashi ai shiya koroni ba Hajiya ba" Ta fada tana riqe hannun Maman, seta maka mata harara tace "Naqi na kirashin ita zan kira tu da ba zaki gaya mun abinda kika masa ba ai kinga seki fada a gabanta" "Dan Allah Mama karki kiraya wlh fushi ze qarayi ya gaya mun baya so ina kao qarar sa gurin kowa shima baze kai tawa ba" "Idan bekai qararki ba ai gashi ya koroki gida qarewar qara kenan ni raina ya baci ni kadai ko to sedai mu raba da uwarsa daga nan a tantance koma wacece me laifi a bashi yawwa" Mama ta fada tana ficewa daga dakin. Tsaf ta tsarawa Hajiya zuwan Humairan da kuma yanda sukayi da ita, Hajiya ta ringa salallami tana cewa "Shiyasa yau najita shiru kuma yanaji inata jajenta amma yayi muqus ya shigo tun Azahar yace mun baya jin dadi ko aiki be fita ba a bakin yara ma naji bata nan itana da suka dawo daga makaranta, dan Allah Hajita kiyi haquri yanzu kuma zan taso shi yazo ya maidota ai na gaya masa nice uwarta duk abinda tayi amsa kafin ya kaiwa kowa kukanta ya gaya mun shine ze turata gida saboda ya nuna mun ban isa ba zamu gamu duk baqin ran da yake ji dashi kwana biyu ina sane dashi zan kumayi maganinsa" "Aa Hajiya ba'ayi haka ba be kamata ayi masa dole ba tunda bamu san me ta masa ba har ya turota gidan danita ma da kike ganinta ja'ira ce ta gaske kawai dai na sanar dake ne dan kisan abinda ake ciki tsakaninau kuma mu zuba ido harsu daidaita dan kansu ba shikenan ba" Mama Hauwa ta fada, Hajita ta dage se yazo Mama Hauwa ta dage akan kar a taso Khalil ta barshi dakansa idan yayi niyya zeje sannan ta qara da cewa "Kuma dan Allah karkice zaki masa fada Hajiya tunda taqi fadar abinda ya hadasu na tabbata ita ce bata da gaskiya" daga haka sukayi sallama. Jalilah dake maqale a gefen Hajiya tana jin abinda suke cewa ta tafa hannaye tana cewa "Ahaf, ai wlh nasan se an rina. Wannan shige da ficen da yara suke tsakanin gidannan da nasu ni nasan swta qullo abinda ta saba ta aiko su dashi to kuwa tayi kadan dataga bayan Khalil da matarsa duk mugun abun da tayi ya koma mata wlh". Hajiya tayi sakato tana kallonta tace "Ke kuma dawa?" "Tsohuwar matarsa mana, ko kaffara bazanyi ba idan na rantse cewar ita ta saka musu hannu. Daman bana gaya miki ba ashe turo yarta takeyi ta sashi gabada tambayar wai yaushe ze maidata daman an tura masa yar azuciya kina kallo duk abinda ta fada ya zauna haka zeyi mata to wlh bata isa ba yanda ta bar gidan nan ta bar shi har abada alfarmar Annabi da Alqur'aniduk kuma wani qulumbotonta sedai ya koma mata" Jalilan ta fada tana hura hanci Hajiya ta saka ido tana kallonta kafin tace "Kardai ki daukarwa kanki nauyin da ba zaki iya saukewa ba haka kawai zakiyi mata Qaharu kina da shaidar da zaki bayar akan ita tayi musu wani abu? Ko a baya da kike babatun zancenki idan ance ki bada shaida baki da ita zatone kawai kuma babu kyau dan haka bana so karna kuma sake jin kinyi magana makamanciyar haka, abinda ya rigada ya faru Allah ya tsara faruwarsa tilas seya kasance hakanan rabuwar Babana da Umaimah daga Allah ce yanda tazo ba a dadin rai ba kawai shine abinda ba'aji dadi ba". Hangame baki Jalilan tayi itama tana kallon Hajiya kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu Hajiya duk bayan abinda tayi miki tayi masa shima har zaki iya kare ta idan an fadi aibunta? Umaimah ce fa Hajiya kin manta tarin haqqoqin mutane da ita ta diba har kike cewa karna dauki haqqinta?" "Ita dinfa Umaimah ina sane, bari kiji Jalilah har gaban Ubangiji na yafewa mata duk abinda tayi mun kuma ina mata fatan abinda ya faru ya zama darasi a rayuwarta ta gaba, meya ragu a jikina bayan abinda ya faru? Sannan shi dan uwan naki ya fasa rayuwa ne ko kuwa wata nakasa ta sameshi? Duk abinda ya faru babu laifin kowa qaddararmu ce a haka kuma mun karbeta bamu da ja akan hakan" Hajiyan ta sake fada se Jalilah ta miqe tana cewa "Babu shakka Asirin data miki har yau he sake ki ba ko kuna an sake ninninkashi, to wlh ko da buzun baqin Jaki take tsafi tayi kasan a wannan karon kuma mu bamu yafe Tozarta mana Mahaifiya da lahantana mana Dan uwa da tayi ba Allah ya isan mu kuna se Munyi shari'a da ita a gaban Allah sannan wlh muddin wani abu ya sami auransa seta gane kurenta" tana gama fada ta fice daga falon a fusace Hajiya ta bita da kallo tana cewa "Allah ya shiryaki Jalilah, Allah ya sanyaya miki zuciyarki ya azurtaki da yafiya ya yaye miki qullaci". Jalilah kuwa na fita bangaren Khalil ta wuce suka ci karo a hanya yana fitowa ran nan a hade saboda tunda ya dawo da rana abinda ya gani yake damunsa. Gaba daya zuciyarsa ayyana masa takeyi da gangan ta fita saboda tana so su hadu dashi dukda be kawo wata Alfasha a tsakaninsu ba amma zuwan da tayi yayi bala'in yi masa ciwo akan me? Me take nufi da take so lallai seta ringa haduwa dashi? Tunda tasan baya so kuma tayi masa alqawari akan me zata bari harya kama hannunta yana shafawa har wani murmushin jin dadi yakeyi Allah kadai yasan abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. Jalilah ta girgizashi ganin ya zuba mata idonsa da suka kada sukayi jaa saboda tunanin daya tafi tana cewa "Nema take ta zautar dakai ma kenan to wlh tayi kadan, idan tana taqama da Boka mu da Allah muka dogara kuma se munga qarshenta". Rintse idonsa yayi saboda yabda take maganar a sama kansa kuma yana sara masa, da muryarsa dake nuna bacin ran da yake ciki yace "Ke kuma hayagagar me kikeyi haka keda nakya rabo da abin magana?" "Zakace haka mana tunda ina shiga Al'amuranka muna murna mun rabu da kaska ashe tana can tana jiqo mana aiki, sake kayi da addu'a shiyasa har ta taradda kai kenan ka bari abin yayi tasiri a ranka ka kori matarka to wlh tayi kadan duk kuma shirinta nata dawo baze tabbata ba in zaka miqe da addy'a ka miqe dan wadda muke maka ba isa zatayi ba naga alamar hatsabibancin ta gaba ya sakeyi ba baya ba tunda har ka fara tafiya kana tunani ba tareda kana ganin hanya ba". Tsaf ya fahimci inda maganarta ta dosa sharrin da kullum takewa Umaimah ne na cewar Asiri take masa shi kuma yace mata idan Umaimah batayi asiri ba ita ta tafi lahira da tulin laifin Qazafin da take mata ai. Yanzun ma Tsaki yaja me qarfi ya rabeta yana cewa "Ki bar mutum yaji da abinda ya dameshi dan Allah ba wata Umaimah ba, ke take a gabanki shiyasa har kika kasa mantawa dacita shekara hudu kullum se kinyi zancenta" tayi sakare tana kallonsa harya shige part din Hajiya kafin ta juya tana cewa "Maganina kenan danake shiga sabgar wanda besan mutunchin kansa ba, su Maza daman macen da zata tijara su taci musu mutunchi ita sukewa naci, me biyayya da kwantar da kai itace shararsu ai shikenan idan ta dawo ta qarasa abinda ta fara randa ka farka ka ganka a kabari ka kiyayi Umaimah" ta ringa sababi harta fita saga gidan Sammani na mata Allah ya tsare bata ma jishi ba. Khalil kuwa yana shiga falon Hajiya ta rufeshi da fada, "Saboda ban isa ba Khalil ina cikin gidan nan ka tura matarka gida se uwarta ce ta kira take gaya mun ko? To ka kyauta kuma yanzu zaka tashi kaje yanda ka turata ka dawo da ita dan ni ba butulu bace bana manta Alkhairi. Yanda Yarinyar nan da iyayenta sukayi mana Halacci bana tsammanin ko Dukanka takeyi zaka ce ta tafi gida ballantana akan abinda na tabbata bekai ya kawo ba". Ransa yayi bala'in baci, wato Qararsa ta kawo gurin Hajiya bayan yasha jaddada mata baya so. Irin halin Umaimah zata dauka kenan, su guma masa sannan su hadashi da mahaifiyarsa tayi masa fada toh kuwa zata gane kurenta, ya dena shiru cutar da kansa da ya ringayi lokacin Umaimah yanzu ya gane kuskurensa kuma baze maimaita ba duk wadda ta masa abu seya fada idan yaso ran kowa ya baci. A fusace abinda tayi masa yana sake tunzurashi yace "Hajiya baki san meta mun ba, turata gidan kawai shine maslaha idan na huce zan dawo da ita" "Toh yanzu nace kaje ka dawo da itan sedai kuma in ban isa ba seka gaya mun, meta maka? Duk abinda zata maka dai nasan baze kai na wacce ta tsaya a gabanka ta zageni ba toh tunda muka yafe mata banga laifin da za'a mana ya gagara yafuwa ba dan haka ka tashi kaje ka dawo da matarka banda tsabar rashin tunani Yarinyar data rufa maka Asiri ta zauna dakai a halin lalura yanzu daka samu lafiya shine zaka fara gwada mata halinku na Maza ko kuda baku san abin arziqi ba daman" "Toh saboda ina da lalura shine zata ringa kula wasu Mazan a waje?" Maganar ta subuto daga bakinsa ba tareda ya shirya ba take kuwa Hajiya tayi tsit saga bambamin da takeyi qirjinta ya shiga dokawa ta kalli Khalil da shima yayi tsilli tsilli saboda subul da bakan da yayi, a sanyaye tace "Babana me kace? Wane mqza take kulawa a waje?" "Am ni ba haka nace ba, kawai dai ki bar maganar dan Allah Hajiya ta kwana gobe da safe ta dawo shikenan" ya fada yana qoqarin miqewa seta daka masa tsawa tana cewa "Bana son rashin arziqi, ka dakko magana irin wannan sannan ka tashi kana neman bagarar da ita kasan me kake cewa kuwa? Maza fa naji kayi zancen tana kulawa a waje, koma ka Zauna Khalil ka gaya mun gaskiya ka samu lafiya da gaske kuwa? kuma wane irin zama kukeyi? tun yaushe hakan take faruwa?" Zaman yayi gaba daya ya rasa me zece mata ganin ta rikice ya tabbata fassarar datayi wa maganar daban da abinda Yakima nufi dole ya tattaro nutsuwarsa jin tana cewa "Cikin jikinta kuma fa a ina aka sameshi" se yayi saurin cewa "Haba Hajiya abin be kai nan ba, bafa irin kula Mazan da kike tunani bane nine ban daka miki maganar a yanda zaki fahimta ba daman wannan yaron saurayinta ne yake aiki a Asibitin Al'amin, tun randa muka fara ganinsa naja mata kashedi akan sa amma bataji ba shine yau.." Tiryan tiryan ya labarta mata komai ya qara da cewa "Ni daman nasan ba wata rashin lafiya kawai ta shirya zuwa ta ganshi ne, na gaya mata ta zaba koni koshi, idanta zabeshi wlh data haihu zan sawwaqe mata taje suyi aure bazan tauyeta ba dan nasan zaman haquri takeyi dani bawai samun yanda take so takeyi ba" yayi maganar kansa a qasa saboda nauyinta. Hajiya ta sauke numfashi saboda jin abin beyi girman data zata ba amma dukda haka hankalinta be kwanta ba dan ita fitina tana qarama idan ba'a maganceta ba girma takeyi. A hankali tace "Bata kyauta ba amma kaima kayi saurin yanke hukunci wannan ai abinda za'azo gida a sasantane ba wai seka turata gidansu ba. Sannan shedan ne kawai yake tunzuraka yana qara rura maka wutar kishi amma babu wani abu, aikinsa yakeyi ita kuma kace likita ta turata yin test kaga baze yuwu ai tace ba ze dauki Jininta ba tunda shine a gurin" "Amma ai bashi kadai bane a gurin Hajiya, data san tsakaninsu akan me zata bashi jikinta har ya wani riqeta yana shafata yana murmushi? Daman ai ya fada mun se ya zama fitina a rayiwarmu to gara kafin muga fitina taje can ta aureshi su qarata ni na haqura" ya sake fada idonsa nayin Jaa dan abin ya bala'in qona masa rai se Hajiya tayi saurin cewa "Ashsha ka dena cewa haka Mana Babana shaidan ne kawai ya haska maka haka babu tabbacin ma murmushin yakeyi sannan waccen magana daya fada na tabbata a lokacin cikin fushi ne shima bazamuga fitina ba da yardar Allah amma koma yayane kayi haquri tayi kuskure kuma ba za'a sake ba ka daure dan ni badan halin taba ka daukota ta dawo gida karka ja mana abin fada, kana ji har yar uwarka ta fara jifan tsohuwar matarka da cewar Asiri tayi muku to lallaba ka dawo da matarka kafin kasa can itama a fara jefa mata wani zargin, Mace da tsohon ciki haihuwa kowanne lokaci a turata gida ai abin a tambayi ba'asine, zan gayawa Hauwa na tabbata zatayiwa tufkar hanci ba za'a sake yin hakan ba kaji" Hajiya ta shiga lallabashi dole badan yaso na ya tafi ya daukota, harta kwanta Mama ta tasheta akan Khalil yazo ta zare ido tana shirin yin kuka ita dai data barta ta kwana gobe koma me za'ayi ayi amma ya ta iya haka suka kama hanya har sukaje gida be kulata ba. Sum sum ta shige bangarenta shima yayi nasa, yara duk sunyi bacci dan haka itama ta kwanta washe gari kuwa qarfe tara Mama ta dira a gidan dan Hajiya kasa bacci tayi saboda zullumi seda ta kirata ta gaya mata komai. Irin labaran da take yawan ji akan Tsohon saurayi da budurwa yasa ta kasa samun nutsuwa, bata zargin Humairan da wani banzan hali amma shaidan abin tsoro ne musamman su da suke da baraka yana iya amfani da wannan damar ya kaisu ga abinda ba za'a so ba ga kuma maganar shi yaron da Khalil yace mata ya taba gaya masa tuna shekarun baya na cewar ya jira ya gani, seya zama fitina a rayuwarsu idan har qullin na nan a ransa har yanzu gara ayiwa tufkar hanci da wuri kafin azo ana kukan da an sani. Tana shiga kafin takai qasa Mama Hauwa ta dauketa da Marin daya gigitata, Khalil dake bayabta ya tareta dan tafiya tayi zata fadi ta kuwa fashe da kuka dan hannun Mama badai zafi ba kamar na maza haka yake. Ta shiga surfa mata bala'i tana zaginta, duk yanda Hajiya taso ta tausheta taqiyin shiru seda tayi mata tatas tana cewa "Saboda bakida hankali baki saninda yake miki ciwo ba, ke ko a hanya kika ga Nura ya kamata kibi inda yabi yaron daya sha Alwashin lalata rayuwarki shine kike bibiya wato ki bashi damar aiwatar da shirinsa a sauqaqe kenan to ki jini da kyau idan kika kashe auranki sedai ki san inda zaki nufa badai gidana ba tunda ke baki san abin arziqi ba". "Haba Hajiya abinfa bekai haka ba, na sanar dake ne kawai saboda ya kamata ace kin sani amma badan ki dau abinda zafi ki ringa maganganu haka ba, naga kinada alaqa da uwar yaron zaki iya mata magana taja masa kunne ya fita a sabgarta shikenan ba se anje ga wannan tone tonen ba" Hajiya ta fada, Khalil dai yana riqe da Humaira dake gunsheqar kuka idonsa ya kada yayi jaa shima kamar yayi kukan daya sani be sanarwa da Hajiya ba, beyi tsammanin zata fadawa Mama maganar ba gashi yanzun abin nema yake ya qara girmama. "Ki barni da mutuniyar banza Hajiya wannan yarinyar da kike gani kunnen qashi ne da ita ai, banda ma abu irin na yaran zamani ina ke ina kula wani tsohon saurayi da auranki duk ba daga nan fitinu suke bullowa ba wai se suce mutunchi mutunchin yaci uwarsa da ubansa ai tunda soyayya ta gifta Shaidan na iya shiga ya taka rawa son ransa yayi abinda yaga dama dan haka kowa ya zauna a iyakarsa babu wani mutunchi da tsohon masoyi ai da ka sani tun jiyan ka fada mun da bazata dawo ba seta zauna a gidan idan yaso ka saketa ta gani idan Nuran ze aureta in ma abind akije saqawa a ranki kenan to sedai ya lalata miki rayuwar kamar yanda yace ya kashe miki aure kuma shi ba auranki zeyi ba dan daman kafin su bar unguwar ya dade yana fadar maganganu akan seya fito dake kuma na auranki zeyi ba sakarya shine har zaki taka kije inda yake. Daga nan shima gidansu zani na samu Hajiya Asaben" Mama ta fada tana miqewa tsaye ta kalli Khalil tace "Kar kaji komai Khalil in kaga ba zaka iya ba ka sakota duk inada labarin diban Albarkar da take maka ai ta dawo gidan taga idan zawarcin da take sha'awa wasane, abinda take rainawar se naga a gidan ubanda zata same shi". Kamar qasa ta tsage su shige shida Hunairan, wannan tonon silili da yawa yake dai Mama ta fice Hajiya ta bita rai babu dadi datasan haka zata dauki abin da bata gaya mata ba. Seda ta rakata ta dawo ta sake hadasu su biyun tayi musu fada da Nasiha kafin suka koma bangarensu, fita yayi niyyar yi amma ya haqura ya zauna ta ringa kuka tana bashi haquri da rantsuwar ba abinda yake tsammani bane. "Wlh bansan a Lab yake ba, kuma danaje duk Matan sunyi sun kasa dubo jijiyar ne" ta miqa masa hannu ta se sannan yaga kumburin da yayi taci gaba da cewa "Sun kasa ganin jijiyar se caka mun Allura sukeyi shiyasa ya karba yace zeyi amma wlh dana shiga koda na gaishe shima dauke kai yayi be amsa ba" "To murmushin da yakeyi yana shafa hannunki fa?" Khalil ya sake tambaya dan abin nan ya tsaya masa a rai seta cigaba da kuka tana cewa "Wlh badani yake ba kuma ba shafawa yakeyi ba jijiya yake dannanwa hirar su sukeyi suna labarin wani abokin aikinsu aida ka kalle su duka dariya sukeyi ba shi kadai bane" se kuma yaji wani iri dan da gaske take dukkansu dariyar sukeyi amma a lokacin dauka yayi su sukewa Dariyar ganin yanda tayi da fuska shi kuma yana mata murmushi, be nuna mata nadamar zaton daya qulla ba ya miqe yana cewa "To se ki dena kukan haka kuma Test dinna menene gashi ba'ayi ba?" "Nima ban sani ba na Fitsari dai ta bani dana jini kamar protein dai naji tace" Humairan ta bashi amsa seya fita yana ce mata "Bari na kira Dr Al'amin in yaso da yamma se muje idan ya zauna. Asibitin ma canza shi zamuyi bazan iya jurewa kuna haduwa dashi na zuciyata zata iya tarwatsewa" ya fice daga dakin. Seda ya kira Dr Al'amin din, be gaya masa abinda ya faru ba dan dukda baya qaunar Noor baze so ya zama sanadin rasa aikinsa ba dan Dr Al'amin ya masa bayanin nauyin da yake kansa, da ace babu yar tsama a tsakaninsu ma tsab shi me iya taimaka masa ne. Dr ne ya masa bayanin Dr Huriya wadda Humairan ta gani jiya ta sanar masa da sunzo amma sun tafi basu kai mata Test result ba, yana taso ya kirashi ya shafa'a yace masa "Da daddare kuzo Khalil ayi gwajin ina ga ma in zaka yarda ayi mata CS kawai a cire babyn yafi sauqi" "CS kuma Dr, da akwai wata matsala ne?" Khalil ya tambaya hankalinsa na tashi daya tuna cikin Imaan da shima yace sedai ayiwa Umaimah CS" cikin son kwantar masa sa hankali Dr Al'amin yace "Aa fa babu wani Abu Khalil kawai dai babyn ne nake ganin yanada girma, zata iya haifarsa amma zata dan ji jiki kaga idan akayi mata aikin za'a sauqaqa amma shawara ce idan ka yarda itama ta yarda shikenan". Hankalin sa ya dan kwanta sukayi sallama, da daddaren kuwa ya kaita ya kasa ya tsare a Lab din har akayi test din Noor bama ya nan shi ya tashi tuntuni. Dr ya dan rubuta mata magunguna da zasu rage mata ciwon kan da tace tana yana damunta basu bar Asibitin ba seda aka basu appointment na CS din da tace ta yarda ayi mata dan tunda yace mata Babyn yayi girma zata dan sha wahala ta tsorata, Aryaan ma data haifa 2.8kg taji jiki balle wannan da yake cewa ze iya kaiwa 4kg ina zata iya gara a cire kawai Allah ya raba su lafiya. Sati daya ya basu satin na zagayowa kuwa sukaje ko Hajiya be sanarwa da za'ayi aikin ba se bayan da aka ciro mata Qaton Babynta fari tas dashi shima aka kaita dakin Hutu kafin ya kira Hajiya ya gaya mata. Ta ringa fada kamar zata aro baki Mama dai da taji tace ai auna arziqi tunda anyi aikin lafiya an gama. Haka tayi kwana uku cikin kyakykyawar kulawa kafin aka sallameta ta wuce gidan Mama kamar yanda Hajiya tace. Sau daya suka hadu da Noor yaje karbar Sample a ward din da take kansa a qasa ya kasa ko kallon qofar dakin nasu da yake a bude sosai Mama taje tayi musu Tijara a gida Ummansa har kuka tayi tana roqon ya fita a sabgar Humaira ya barsu su zauna lafiya ya ringa rantse mata akan shi wlh babu wani abu tsakaninsu tun tuni ya cire komai, ko a baya hankali be gama masa jiki bane shiyasa yake wasu tunanuka amma yanzu babu komai game da ita a ransa illah mutunchi tunda dai shiya hadasu ba rashin mutunchi ba. Yanda yake sunkuyar dakai Maman da kanta ta kirashi ya shiga dakin, ta bashi dan da biyu tana cewa "Ga danku kaga na farin can" ta nuna masa Aryaan dake cinyar Jamila yana shan Yoghurt tace "Kana ganinsu kasan namijin gaske ya haifesu" shidai yayi yaqe ya musu Addu'ar Allah ya raya ya kama gabansa, to shi ko qaddara ta fito da Humaira ai yasan ba sa'ar auransa bace dan bashida abinda ze riqeta dashi ta saba da rayuwar jin dadi me zatayi dashi da har yanzu neman madafa yakeyi babu abinda ya ajiye. Ranar Suna yaro yaci sunan Mukhtar sunan Mahaifin Mansur Amininsa kuma Mijin Mama mariqiyar Humaira kenan. Har kuka Maman tayi da wannan kara daya musu, kullum burin Mansur kenan a haifar masa Namiji ya saka sunan Mahaifinsa yayansa biyar yanzu duk mata Khalil be gaya musu sunan yaron ba har se ranar sunan da Safe dan data dameshi da tambaya cewa yayi kawai ta samar masa Laqabi se ranar suna zataji, aiko Yayan Mama sunji dadin wannan kara a gidan Hajiya kuwa ana fadar sunan Jalilah tayi tsallen Arbarka tace qarya yake, sunan Abban Umaimah ya saka. Hajiya ta riqe baki tana cewa "Jalilah jidalinki yawa ne dashi, yanzu sunan ma se kin janyo magana akai" "To idan qarya nakeyi Hajiya ya fada mana, babu wani sunan Baba me Mota daya saka (haka suke kiransa da suna yara) sunan tsohon sirikinsa ya saka ze wani fake da haka" "Toh Jalilah ko sunan Abba na saka ai babu aibu a ciki dan Abba uba nane kuma ya isa da nayi masa takwara, karki tunzurani idan ta sake haihuwa na sake maimaita Mukhtar" ya fada mata kaitsaye ta tafa hannaye tana cewa "Eh lallai Allah ya tsamoka Khalil a kwale kwalen Asiri kake yawo babu kuma wani ka sake sakawa daman shi ka saka kuma sena zuga Humairan akan me za'a saka mata sunan uban kishiya, kishiyar ma yar iska mara mutunchi" "Kiyita rage mata zunubi kina jibgawa kanki" ya fada yana ficewa dan inya zauna se sun haura sauran yan uwan kuwa dariya suke musu kawai dramar tagwayen bata qarewa su basu ganin sun girma sun haura Arba'in inji Jamila amma kullum kamar wasu yan sha takwas, mita ta dira akan me za'a saka sunanda Hajiya ta gaji tace "Ke dai in baki sararawa kanki ba ciwon damuwa ne ze kasheki kafin lokacinki yayi, ni banga dalilin dorawa kai damuwar wani ba taka ba. Umaimar nan fa baki isa ki kankareta daga cikinmu ba, yaya uku ta haifawa dan uwanki gasu nan duk inda akaje aka dawo fa an hadu babu yanda za'ayi a rabu kuma Alhaji Sabo Dattijo ne kuma in ma shiya saka banga laifinsa ba dan ya masa abinda uba yakewa Dansa haba ki rage wannan zazzafar qiyayyar taki Yayanta suna girmamaki karki bari su fahimci qin da kikewa uwarsu ba zasuji dadi ba kuma kema zasu iya qinki a dalilin haka dan duk yanda uwa take Yayanta suna sonta. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 85 Sha tara ta arqizi iyalan gidan Alhaji Sabo suka hada na kayan barka bisa karamchin da suka ce an musu na maida sunan mahaifinsu. Mama da Anty suka shirya Khalifa ya kaisu gidan Hajiya, Mama ta ringa kallon gidan abubuwan da suka faru a ranar data saka qafarta na qarshe na dawo mata shekaru kusan biyar kenan kota layin bata sake biyowa ba se yau din nan tunanin yanda zata sake kallon idon Hajiya takeyi a haka akayi musu iso cikin falon Hajiyar daya sake qawatuwa fiye da da. Hajiya rasa inda zata sakasu tayi saboda murna, tasa aka ringa kawo musu abubuwan motsa baki yanda take haba haba dasu duk yasa kunya ta sake dabaibayesu jikinsu ya qarara sanyaya da lamarin karamchi irin nata. Tabbas Umaimah tayi asarar Sirikar kirki da samun irinta keda matuqar wahala a wannan zamani. Seda ta gama cika musu gaba da abubuwan ciye ciye kafin ta zauna suka shiga gaisawa. Da suka tado zancen baya ma hade fuska tayi ta nuna musu ita a gurinta komai ya wyce, ashe qullatarsu sukayi shiyasa suka yanke zumunchi dasu Mama da Anty suka hau rantse rantsen ba haka bane yanda suka rude yasa tayi dariya tace "Komai ya wuce wlh kuma kamar yanda nasha fada miki nayiwa Umaimaha uzuri ba halinta bane kuskure aka samu tareda zugar shaidan data mugayen qawaye amma komai ya wuce sedai muyi fatan hakan ya zama Alkhairi a rayuwarsu gaba daya, Allah kuma ya fito mata da wani Mijin idan kuma da rabon daidaitawa se kiga an koma". Daga Anty har Maman kasa amsa mata maganar qarshen sukayi dan basu da tabbacin har zuci tayita seta sako musu wata hirar tun suna dararewa har suka saki jiki akayi ta labarin duniya. Duk abinda aka ajiye musu Mama dai Lemo kadai tasha se Dubulan Anty kuwa ta zage taci abinda ya mata dan daman ita bata iya fulako ba. Sun jima kafin Hajiya ta shirya tace suje can gidan su Humairan suga Baby tunda bata dawo ba, a compound suka hadu da Khalil daya dawo daga Abuja saukarsa kenan ya shigo gidan suka hadu ya ringa sunkuyar da kai qasa kamar ze kwanta musu saboda ladabi ya gaida su Maman, ta amsa tana murmushi Anty ce tadan jashi da wasan data saba yi masa kafin suka masa barka suka tafi. A mota Mama ta yiwa Hajiya zancen Bibi daya tsaya mata a rai danma suna makaranta shiyasa zancenya kwanta mata tun suna zaune se a motar ta tuna. "Wlh Hajiya muna iyakar qoqarinmu, tabarar takwarata ai da ba'a kwabarta da abin seyafi haka dukda laifin Ubanne kuma shima ina tsawatar masa akan abinda yakeyi sam be kamata ba dan har yan uwan sun fara nuna rashin jin dadinsu dan idan abu ya hadosu tofa ko itace mara gaskiya ze shigar mata seda naci mutumchinsa akan haka na kuma gaya masa ze raba kan yayansa ne sa kansa. Ga wata yar banzar qawa da take da ita a makaranta da take qara dora mata karatun iyashege duk wani abun rashin kirki da kika ga tayi zakiji a gurinta ta koyo ga magana kamar Goyon tsohuwa, nidai na gayawa Uban ya canza mata makaranta tunda daman Idan sun gama Jarabawar zangon nan yace Sakandire zata shiga to ya kaita wata makarantar dan barin yaranka da irin qawar nan tata hadarine, kana tarbiyya suna warware maka kullum cikin tura mata mugayen aqidun qin matar ubanta da Yan dan uwanta takeyi, karkiso kiga yanda take hantarar yaron nan Auwalu da duka tun uwar tana kawaici har takai ta fara magana to yanzu dai abin yayi sauqi tunda Hasanar uban ta zaneta kwanaki da cewa ma tayi zata dauketa yaqi to nima ban matsa ba dan Azabar Jalilah tayi yawa, nata yayanma suka samu suka ballo bason koma mata suke ba dan ta fiya jaraba amma iya qoqari munayi Hajiya sedai mu qara". Haka sukayi ta jajanta maganar har suka isa gidan Mama Hauwa ita dinma kamar ta goya Mama da Anty, yanda kasan akwai wata sanayya ta sosai tsakaninsu haka ta tarbesu basu jima sosai ba anan suka sube musu kayan barkar da Hajiya tace a tafi dasu can, Mama ta ringa godiya kamar me, a gidansuka bar Hajiya dan Salman ne ya kaisu ita zata jira Driver ya maidata gida suka tafi da santin kirkin Maman harda yayanta da suka tarar a gidan. Da suka koma gidama wuni sukayi hirar fitar tasu, Umaimah nata zirga zirgarta tsakanin daki da tsakar gidan tana aiki duk abinda suke fada a kunnuwanta, idan tace batajin zafi duk sanda aka ambaci Matar Khalil tayi qarya amma babu yanda ta iya, Khalil ya zama tarihi a rayuwarta wanda ita tayiwa kanta silar rasashi ta sani kuma zata qare rayuqarta cikin nadamar abinda ta aikata ma kanta. Wata uku da suka biyo baya yayi dadai da cikar Umaimah shekara biyar cif a cikin gidan ba tareda ta leqa koda qofar gidansu ba. Ita badan taji suna fada bama ta manta ba kuma ta damu data fitan ba to ina ma zataje? Wa take dashi da zata gurinsa yan uwanta ne kuma suna haduwa a gida a kaf qawayen nata data daukaka sama da komai babu wadda ta waiwayeta, har gara kwanaki Nuratu take ce mata ta hadu da Rufaida taje dubiya Asibinsu harta tambayeta, a lokacin murmushi kawai tayi duniya tayi mata karatu da yawa shiyasa sam bata damu ba da watsar da itan da sukayi ba, daman Mu'amalar da ba'a qullata domin Allah ai ba zata dore ba. Tana kwance a dakinta sakamakon ciwon Mara data tashi dashi ranar saboda shirin zuwan baqonta aikin gidan ma Abin kari kadai ta iya hadawa Abba dakansa yace ta bari saboda yanda fuskarta ta nuna bata jin dadin. Tana kwancen ta jiyo sallamar Anty Hafsa da Maman Asad, bata iya tashi ba saboda yanda mararta ta daure mata tana jiyo hirarrakinsu a tsakar gida kafin suka shiga bangaren Abba dan yana gida. Sun jima acan dan har bacci ya fara daukarta taji muryar Maman Asad akanta bayan ta dana mata dukan daya farkar da ita tana cewa "Yau halin ya motsa kenan, kina jinmu kika lafe a daki to se ki tashi dan wake nake sha'awa yau ga gari nazo dashi ki jefamun idan nayi da kaina bazan iya ci ba". Ta tashi tana yatsina fuska saboda yanda Cikinta yake karta mata Anty Hafsa kuwa cari ta shigayiwa Hajiyayyen tana cewa "Ni ba cewa kikayi kinyi auta ba Hajiyayye? Asad fa Ya shiga Jami'a ki rufa masa asiri haka karku zo kuna jera Jego da matarsa" Hajiyayye ta zauna gefen katifar Umaimah tana cewa "Kai Yaya toh nawa ma Asad din yake Ashirin da daya fa, kuma wlh ni nayi niyya daga Afifa nayi auta Babansu yace ban isa ba tunda na hanashi qara aure sena haifo wanda yayi niyyar samun qari, ai shi yanzu hudu yake jira na qaro su zama goma nace wannan dinma Astagfirullah tsautsayine ina haifeshi ca zanyi su juya mahaifar Allah sa musu Albarka" suka saka dariya ita da Anty Hafsan Umaimah dai tana ta faman yatsina da gyara zama Anty Hafsa ta kalleta tace "Qalau kiketa yatsina ke kadai, seta yunqura saboda jin kamar abu na zubo mata tace "Marara ke ciwo" "Aiko gashi nan kin bata jikinki, dan iskanci da a haka kike zaune kina period babu pad?" Maman Asad ta fada ita dai ta tattare rigarta ta wuce gaban Sif ta dauki Zani da panta kafin ta janyo qaramar Jakar da take zuba Yankunan da take amfani dasu saboda gudun datti ko qura ya tabasu ta dauki wanda zatayi amfani ta mayar ta rufe ta shige bandaki duk akan idon Maman Asad da Anty Hafsa. Jikinsu yayi sanyi qalau, Anty Hafsa ta tashi ta dauko jakar ta bude taga Tsummokaran da yawa ta kalli Hajiyayye tana cewa "Yanzu da tsumma take amfani saboda Allah a gidan nan?" Maman Asad ta sauke ajiyar zuciya ta miqe ta fice daga dakin itama ta maida mata da jakar tabi bayanta, a falo suka tarar da Mama na duba wasu Atamfofi da zata fitar duk suka zauna a sanyaye ta kallesu tana cewa "Lafiya dai?" "Babu komai" Maman Asa tayi saurin fada seta miqe ta dauki jakarta tana cewa "Ina zuwa bari na karbo abu a bakin titi" ta fice. Bata jima ba ta dawo da Babbar Leda ta shiga dakin Umaiman lokaci har tayi wanka ta shirya tana shan ruwan zafi, ta ajiye mata ledar tana cewa "Gashi nan". Umaimah ta kalli ledar ta kalli Maman Asad din seta ajiye kofin hannunta ta karba tana cewa "Nagode, Allah saka da Alkhairi ya bar zumunchi" "Amin" ta amsa mata kafin ta juya tavar dakin tausayin qanwar tata yana kamata. Akan gado ta zazzage kayan, saitin man shafawa da sabulu ta gani Wanda ko ba'a fada ba masu tsada ne sanann zasu gyara fata, ga turaruka bodyspray, bodysplas da perfume harda oil Shampoo da condioner, Sabulan wanki da Omo Powder lip gloss, Harda su Eyeliner da Mascara ga Pad ta Virony me 32 guda hudu. Hawaye taji ya zubo mata data rasa na menene, ta sharesu kafin ta tattara kayan ta mayar cikin ledar ta zari Pad daya ta wuce bandaki, sedata gyara jikinta kafin ta dan fesa turare ta dauki ledar ta fita dakin Mama. A gabanta ta ajiye mata ledar tana cewa "Maman Asad ce ta siyo mun" "Allah ya saka mata da Alkhairi ya qara muku zumunchi" Maman ta fada ba tareda ta bude ledar ba, Anty Hafsa ta bude jakarta ta zaro dubu uku ta miqa mata tana cewa "Wata yayi nisa idan munyi Albashi zan miki aike" ta karba tana godiya kafin ta miqe ta mayar da kayan. Danwaken ta dora mata dan taji dama dama tayishi da dan yawa ko wani zeyi sha'awa aiko har Abba da ze fita sallar La'asar yaga tanayi yace zeci dan haka ta zuba masa ta kai masa bayan ya dawo. Se Magriba su Hajiyayye suka bar gidan, suna zaune da Mama bayan sallar isha suna kallo take ce mata "Baki gaji da zaman gidan nan ba haka Umaimah? Ya kamata ki ringa fita kina ganin gari zaki rage wannan damuwar datake tsomareki ai". Shiru tayi dan bata san me zata cewa Maman ba, ta fita kuma da izinin wa? Kuma ma ina zataje ita gaba daya ma bata sha'awar fitar, haka nan jikinta yake bata zamanta a gidan ya fiye mata Alkhairi yanzu tasan da yawa sun manta da ita duk ranar data fita aka fara ganinta kuwa labari ne ze dawo sabo, wanda bema san anyi ba yanzun ze sani. Ganin tayi shiru yasa itama Maman bata sake ce mata komai ba, seda aka yi sati biyu a tsakani ranar Asabar bayan sun taso daga Islamiyyar da suke zuwa ita da Anty Umaimah na girki take ce mata "An fara siyar da form na daukar sababbin dalibai, kiyiwa Abbanku magana a karbo miki ki ringa zuwa tunda wannan baqin ya fara washewa zaman ya isa haka" Kallon kanta tayi, dagaskiyar Maman tunda ta fara wanka da Sabulu me kyau ta shafa mai me kyau ta washe, wannan uban baqin da tayi fatarta ta bushe har waskane tayi duk ya goge dukda bata koma Asalin kalarta na amma ta fara dawowa hayyacinta. Cikin In ina take cewa Maman "Mama nayi masa magana kuma? Kin manta yace karna fita idan na gaya masa ze barni?" "Ki tambaye shi mana idan ya hana srki haqura ki zauna kici gaba da girka tukunya" Maman ta bata amsa. Ta ringa juya maganar a ranta, ita kanta zata so ta koma Islamiyyar to amma bata so ta lalata shirin da suka fara da Abban in so samu ne zata cigaba da zama harse randa shi da kansa yace ta fita tunda ai yana sane bawai ya manta bane. Se washe gari Lahadi da Mama ta sake mata maganar cikin fushi tana cewa "Dama ba karatun Addinin kikie so ba bayan harda rashin ratsa miki jiki da beyi ha yasa kika ringa tambele kina hauka a baya to se ki zauna ki qare rayuwarki babu wan babu qanin, keba aure ba keba neman ilimi ba bazan sake miki magana ba tunda baji kikeyi ba, dama na manta ne ai hali zanen dutse". A daren ta samu Abba da zancen son shiga Islamiyyar, jikinta na rawa ga maganganun Mama ga tsoron yanda ze karbi maganar tata, ta sauke ajiyar zuciya ganin ya zaro dubu uku ya bata yana cewa "Gashi nan ki bawa Antyn ku kamar haka tace mun kudin Hijabi da suka dinka kwanaki, idan na fita anjima zan karbo miki form din a Masallacin gurin Malam Babba, sauran Litattafai kuma seki duba anan duk ina dasu suna a nan suka samu". Ta ringa jera masa godiya kamar zatayi kuka kafin ta tashi har takai bakin qofa ya tsayar da ita, dakinsa ya fito ya miqa mata Wayarta da har ta manta da kalarta ma ita wlh. "Gata nan, se ki siyi layi ki dora dan wancan qila sun siyar da number ko kinyi Welcome back bazeyi aiki ba". Hannunta na rawa ta karbi wayar cike da Mamaki ta wuce falon Mama, seda ta fada mata yanda sukayi ta nuna mata wayar da kudin kafin ta wuce ta bawa Anty kudin Hijabin sannan ta shige dakinta tana juya wayar. Rasa ta inda zata fara amfani da ita tayi gaba daya se kawai ta ajiye, shekara biyar ba wasa ba, ta dai ganta da chaji full a ranta ta ringa mamaki tsahon lokacin kuma wayar batayi komai ba. Seda yamma bayan Salman ya shigo gidan ta bashi yana murmushi yace "Ni ya tambaya fa ya za'ayiwa waya karta lalace ai kuwa duk kwana biyu se Abba ya chaja wayar nan ba qaramin aiki kika bashi ba, ba yanda banyi dashi ba ya bani ita a lokacin ma in kin tashi amfani da ita na siya miki wata yaqi gashi ke kin manta ma yanda ake operating nata, kyanki Rakani kashi yanzu" ya fada yana gwada mata yanda zata yi amfani da wayar nan da nan ta tuno tunda daman ta sani mantawa tayi. Shiya siyo mata layi yayi mata register sa dan da yace suje tare qi tayi, haka kawai take tsoron fita waje, bayan ta dora layi a wayar ta shiga duba numbobin kai duk sunanan babu abinda ya goge ta tsayar da idonta kan number Khalil qirjinta yana bugawa da qarfi tanajin kamar ta danna kira wani sashi na zuciyarta kuma yana hanatayin hakan, dakyar ta yaqi zuciyarta ta haqura da kiran, seta kashe wayar gaba daya ta ajiye ranta babu dadi abubuwan datayi qoqarin bunnewa suka fara dawo mata dalilin wayar nan, haka datazo bacci ta sake kunnata ta shiga hotuna ta ringa kallo lokaci daya hawaye ya shiga zubo mata data gaji da kallon hotunan ta ajiye wayar tasha kuka taqoshi kafin bacci yayi awon gaba da ita me cike da mafarkai kala kala. Kamar yanda Abba yayi Alqawari ya karbo mata form din amma ba kamar su Mama da suke zuwa sati sau biyu ba ita sau hudu ne litinin zuwa Alhamis qarfe goma zuwa daya na rana. Ta ringa saqa da warwara akan yanda zata fara fita makarantar, to *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 86 Ta ringa saqa da warwara akan yanda zata fara fita makarantar, da ranar tazo kuwa tun Asuba haka ta tashi da faduwar gaba, a sanyaye ta ringa ayyukanta. Tunanin yanda zata fuskanci mutanen unguwarsu kawai takeyi ta tabbatar ganinta seya maido da labarin baya amma ya zatayi? Ba zata cigaba da zama haka ba, dole ta fuskanci komai ta girbe shukar da ta dade tana yi. Qarfe tara da Rabi ta shirya tsaf cikin Hijabin Makarantar Ruwan Madara me haske, ta leqa Dakin Mama tana zaune a falo tace "Har kin shirya?" "Eh na shirya Mama" ta fada tana zama. Maman ta tura mata litattafan data ware mata wanda aka rubuto na Ajin da aka dauketa tana cewa "Gasu nan toh, amma da kin jira Firdausi na aiketa ta siyo mun kati seta rakaki dan ba a inda kika sani ake makarantar yanzu ba" Seta gyara zamanta ta zuba litattafan a jakar data sako Alqur'aninta, Firdausin ta shigo da aiken Mama ta karba tana gaya mata ta raka Umaiman makaranta tace toh. Harta miqe Mama ta tsayar da ita, dakinta ta shiga ta fito da baqar safa da niqab ta bata ta karba tana sakin boyayyar ajiyar zuciya. Tuntuni take shawarar neman niqab din amma tsoron kar Maman tace wani abu yasa ta haqura zata fita a haka. Dalilin Niqab din yasa ta ringa taka qafarta da kwarin guiwa har suka fita daga gidan. Seda ta tsaya tana kallon layin nasu kamar sabuwar baqauyiya. Kwalta har qofar gidansi dukda daman Hanya ce babba motoci nabi amma babu kwalta yanzu kuwa harda fitulun solar aka saka musu. Unguwar ta sake habaka sosai, shagunan data sani qanana duk sun bunqasa gidajen kansu wasu bata ma gane su ba saboda gyare gyaren da suka sha. Haka suka ringa tafiya tana kalle kalle kamar farin shiga birni, suka wuce tsohuwar Islamiyyar su wadda take hade da babban Masallacin unguwar suka qara tafiya kadan kafin suka isa sabon ginin makarantar qato hawa uku ga Ajujuqa birjik da ofisoshi. Har gurin shugaban makarantar ta rakata, Umaimah ta daga Niqab din tana gaishe shi, kalolin iya shegen data ringa tsula masa na dawo mata a shekarun baya Yah Sheikh din ya zama babban mutum yanzu gemunsa duk furfura dukda be kai shekarun su Abba ba amma girman daya hau kansa ya qara masa kwarjini da haiba ake masa kallon Babban mutum sosai. Fuskar sa da walwala ya amsa gaisuwarta kafin ya kira wani Malami da baze wuce sa'an Salmab ba yace masa ga sabuwar dalibar Ajinsa. Ta kalli Malamin daman tun Asali abinda ya ringa hadata da makarantar kenan, Yah Sheikh baya dauko Malamai manya sedai ya debo qananan yara da acewarta basufi sa'anninsu ba suzo suna zare musu ido ku suce zasu dake su shiyasa ta raina Malam a wancan lokacin amma a yanzu cikin tsantsar ladabi ta gaida Malamin da aka ce na Ajin nasu. Yayi gaba yana cewa ta biyo shi, harta yunqura ta koma ta zauna, wannan dama ce ta samu da zata fara rage tarin haqqoqin Jama'a dake kanta. Muryarta na rawa ta shiga roqon Yah Sheikh din gafara akan abubuwan data yi masa a baya, ya ajiye Takaddun da yake dubawa har sannan yana murmushi ya kalleta yace "Haba Umaimah wace yafiya kuma kike nema a gurina ni ai bakiyi mun komai ba. Ko a baya nayi miki uzurin yarinta a duk abubuwan da kikeyi bani kadai ba duk sauran Malamaina bana zaton akwai wanda ya taba qullatar abinda kikayi masa a baya har yanzu duk kusan muna tare, a cikin Malaman ku Malam Sa'adu ne kadai Allah yayiwa rasuwa se Malam Lawi daya bar qasar yana Jami'atul Madina yanzu saura koda bama aiki tare suna yawan kawo mana ziyara har su bada darussa a wasu ranakun nasan wata rana zaki gansu. Ki saki ranki kinji kiyi abinda ya kawoki yawancin karatun Tishi ne akan abinda aka koya muku a baya kuma duk kin iya da an tuna miki zaki tashi se kiyi qoqari a wannan karon ba wai kiyi karatu kawai ba Aa ki maida hankali gurin fahimtar abinda kika koya tare da aiki dashi, Allah ya wuce gaba". Jikinta a sanyaye ta fita bayan ta maida Niqab dinta. A waje ta taradda Malam Najib kamar yanda taji ya kirashi yana jiranta ya wuce gaba har Aji biyu inda aka sakata suka shiga tare ya nuna mata gurin zama cikin sauran Dalibai da sukayi shiru saboda shigowarsa. A sanyaye ta nemi guri ta zauna, murya babu Amo tayiwa wadanda ke kusa da ita sallama suka amsa suna kallonta. Malam Najib ya zauna a teburinsa ya dauko Register, seda ya kira suna kowa ta amsa wanda basu zoba ya saka musu kafin yayi gyaran murya yace "Sabuwar Daliba menene sunanki?" Gabanta ya fadi, dukda da Niqab a fuskarta seda ta zaro ido ta waiwaya kamar me ciwon wuya ta kalli Yan Ajin da suka zuro mata ido suna jiran amsarta a haka dai bataga fuskar sani ba duk cikinsu dukda dai ba wani kallonsu tayi dakyau ba. Seda ya sake maimaitawa kafin ta bude baki a hankali tace "Umaimah Sabo" "Masha Allah Malama Umaimah muna miki barka da zuwa" ya nuna wadda take kusa da ita yace "Wannan Malama Aisha kenan itace Monitar ku, duk wani abu daya shige miki duhu ki tuntubeta, Daliban Ajin nan Dalibai ne masu hazaqa ina fatan kema zaki bamu taki gudummar gurin tabbatar da kambun mu". Kai da gyada masa kawai dan ta kasa magana. Ya bude Drawersa ya ciro Littafin UmdatulAhkam tuni daman sauran yan Ajin kowa ta fito da nata suka shiga bitar inda suka tsaya kafin ya dora musu sabon Karatu. Yana gamawa wani Malamin ya sake shiga a haka har qarfe daya basu samu hutun ko minti biyar ba dan da wani ya fita wani ze shiga duk kuma wanda ya shigo seya tambayeta sunanta Malamin qarshe dayake da surutu yace ta dage Niqab din tasha iska dan kusan duk yan Ajin suna saka Niqab din amma kowacce ta daga nata se zasufita suke saukeshi, shima dai kai ta girgiza masa Alamar Aa. Da yake bema tambayeta sunanta ba yace "Tohz, kurma ce kenan", maganar ta bata haushi amma ta dake da lokacin baya ne seta maida masa da martani in ma bata ce uwarsa ce kurmar ba amma yanzu kura tayi lafiya. Da aka tashi tareda monita suka fito tana ta janta da hira har suka fita saga makarantar tareda wasu yan Ajin. Masu Motoci suka ragewa wanda suka saba tafiya tare hanya masu hawa na haya suka tafi su kuma na kusa suka daba a qasa. Kusan su bakwai suka jera acikin yan Ajin nasu, Malama Aisha take ce mata "Kema gidanki nan kusa ne Ashe" "Eh" ta bata amsa, layi daya tsakanin gidansu suka rabu Malama Aishan ta shiga gidanta dake bakin hanya, Umaimah tasan Matar gidan dan tana Amarya sun dan yi hulda suna haduwa a gidan Maman Nana kafin tayi aure ta bar unguwar kenan kishiya aka mata. A cikin layinsu suka rabu da sauran mutum biyu da suka taho tare ta shiga gida tana Mamakin ganin daya ta shiga gidansu Maman Nana dayar kuma ta miqe. Sallar Azahar kawai tayi ta karbi aikin Abincin da Anty ta fara tana cewa ta barshi ita data kwaso gajiyar makaranta amma ta dage setayi. Seda ta sauke na dare tayi wanka taci abinci kafinta zauna bitar karatun da akayi musun. Ranar da wuri ta kwanta tunda tasan yanzu hidima ta qarun mata akwai zuwa makaranta a haka lokaci yaci gaba da tafiya harta share sati biyu a makarantar kuma Alhamdulillahi tanajin dadin karatun sosai har sannan kuma babu wanda ya taba ganin fuskarta a ajin, tsakaninta da kowa sallama ce bata magana dan ko Malama Aisha da suke zama benci daya gajiya tayi da janta da zance ta haqura, idan ba Umaiman ce ta tambayeta abu ba itama seta kama kanta. Tana jin yan ajin na gulmar wai tacika girman kai bata kula kowa. Zance har sauran Ajujuwa cewar an kawo wata sabuwar Daliba kullum fuska a rufe kuma bata magana da kowa. Ita dai ba abunda ya shafeta dasu musamman data godewa Allah babu yan unguwarsu da yawa a Bangaren Safen nasu, yara ta yamma sukeyi saurab Matan unguwar kuwa yawanci ta Asabar da Lahadi suke irin tasu Mama. Wannan Matar data ga ta shiga gidansu Maman Nana mabata sake ganinta ba tun zuwan farko, a bakin Malama Aisha taji cewar Bari tayi bata da lafiya shiyasa bata zuwa dan har yan Ajin sunyi qungiya anje dubata da tace mata ko zataje tace Aa kawai se daga baya ta sake jin maganar a bakin Anty ashe Amaryarsu ce, da yake itama Maman Nanan sun babe tuni tun farkon dawowarta gida ita ta ringa qarawa wutar gulmarta fetur a unguwa har tana fadar ita bata taba dauka ma airan Umaiman ze jima har haka ba'a sakota ba saboda halinta, ta ringa cewa yarinyar da take da fuska biyi, a gidanta take zuwa tayi shigar banzarta idan zata fita yawon barbada inta dawo taje can ta canza labari yayita yawo a unguwa data san Umaiman taji tun daga nan ta dena shiga gidansu kwata kwata ta dauke qafarta shiyasa ma Umaimah bata san an cika she mata kishiya ta uku ba kenan sun zama su hudu. Anty ta aiki Firdausi takaiwa Maman Nana wata Riga ta gyara mata Zip, Maman Nana na chanza zip din ta shiga tambayar Yarinyar wai Umaimah tana nan kuwa tace mata eh, Samira Amaryar su na daga qofar Kitchen tana duba girkin data dora, sunan Umaiman ya tuna mata da sabuwar yar Ajinsu, bata taba jin sunan ba se a kanta ranar se yanzu da taji Maman Nana ta ambata. cike da son Gulma bayan Firdausin ta fita ta matsa gurin Keken Maman Nana dukda ba shiri suke ba take ce mata "Niko sunan da nJi kin fada kamar na santa" Maman Nana ta galla mata harara dan tafi jin zafinta duk cikin kishiyoyin da aka mata. Seda yaga mamorarta ta kusa qarewa yaje ya dauko musu yarinya me shegen kadifiri Sa'ar Nanarta rana daya ya aurar da Nanan ya qaro Amarya shi kuma gashi yanda yake lelenta baya ko jin kunyar idonsu itama ta samu guri tayita zuba musu iskanci a gida shiyasa basa zama inuwa daya. Tsaki Maman Nanan tayi tace "Kika santa a ina? Matar da tun kan ki isa aure take kulle a gida babu inda take zuwa". Samirah tayi murmushi tace "Wlh Maman Nana, wannan data fita ba yar gidan Saratun Alhaji Sabo bace? To itama waccen haka naji sunanta Umaimah Sabo, ajin mu daya a Islamiyya wata doguwa siririya ko zuwana na qarshe tare muka jero kuma gidan naga ta shiga har na ringa tunanin ko Amarya aka musu saboda nasan Yammata biyu ne a gidan ko?" Maman Nana ta aje Almakashi saboda jin gulma harda gyara zama tana cewa "Doguwa Siririya? Kai Umaimah ba siririya bace amma qila rama tayi dan na fi shekara uku banganta ba tun ina shiga gidan amma bari na tambayo Nafisa dan ko shekaran jiya ta shiga ta karbo Atamfofi gurin babarsu" ta miqe jiki na rawa ta shige dakin ta biyun su, bata jima ba ta fito tana tafa hannu tace "Aiko itace, dan Nafisa tace data shiga ta ganta da Hijabin makaranta ta dawo ikom Allah an gama kulletan kenan ta fara fita? Yo ko ta fita ko karta fita dai tambari ta rigada tayiwa kanta wlh, Allah dai ya wadaran dai naka ya lalace". Samira ta sauke tunkunya ta dawo tana cewa "Me tayi da ake boyeta? Badai wani ta kashe ba? Dani daman yanda take ta fama da Hijabi nata yafi na kowa tsaho kofa qafarta ba'a gani ga Niqab har aka tashi bata daga shi ba har wani Malami seda ya mata magana duk a wani darare take ina lura da ita kamar mara gaskiya ashe da walakin dan Allah wata kashe Maman Nana?" "Mijinta ta kashe mana" Maman Nana ta fada, Samira ta saki Ludayin miya ta dafe qirji, Haulatu ta ukunsu dake daki tayi saurin fitowa jin abinda Maman Nanan ta fada tace "Ke Maman Nana kiji tsoron Allah ta kashe Mijinta a ina?" "Yo abinda ta masa menene marabarsa da kisa Haulatu? Ta kashe masa kayan aiki meyayi saura bari fa kiji" ta juya kan Samira ta shiga labarta mata qarya da gaskiyar yanda akayi. Samira ta ringa tsuma jikinta na rawa, Allah Allah take litinin tayi taje makarantar da ta kusa wata bataje ba tunda tayi Bari ta fake dashi taqi komawa dan daman Mijin ne ya sakata dole ba so take ba musamman da sauran ta Asabar da Lahadi suke zuwa ita kuma cikin sati. Watanta daya Umaimah tana zuwa Islamiyya cikin lumana Kishiyar Maman Nana na komawa labari ya canza dan randa ta koma a ranar ta bajewa yan Ajinsu labarin wacece Umaimah wanda ta tattaro daga bakin Kishiyoyta. Daga yanayin kallon da yan Ajin suka ringa mata daya banbanta dana kullum tasha Jinin jikinta, ta zauna a sit dinsu Aisha bata zo ba danta bashida lafiya haka ta gama darasin ranar a takure tana yin yanda maganganu suke tashi qasa qasa gaba daya seta tsargu dukda babu wanda ya kira sunanta ko ya saka da ita amma ta kasa nutsuwa. A haka ta rarrafa aka tashi ta kama hanyar gida tunda abokiyar tafiyar tata bata zo ba. Washe gari kuwa ba iya kar yan Ajinsu kadai ta ga suna binta da kallon qurillah ba harda sauran mutante, abin yayi gaba, gani kawai ta ringayi ana shigowa Ajin kamar wani gidan Zoo duk kuma wadda ta shigo saitinta zata kalla ta kama baki ta juya. Wani rukuni da suka shigo a qarshe kafin Malamin da zone musu darashi ya shiga har kanta suka qarasa, wata daga ciki datafi kowa zaqewa taja tsaki tana cewa "Ai dole mutum ya ringa saka Niqab yana rufe fuska tunda bashi da gaskiya, to se kuyi hankali kudai yan Aji kar abinya motsa ayi muku aika aika a cuceku kun san da tsofaffin yan daba aAjin" ta sake jan tsaki wadanda suke ta qananan maganganu a Ajin suka fashe da dariya. Suka hada ido da Matar gidansu Maman Nana take gabanta ya fadi saboda irin murmushin da tayi mata ta tabbatar da cewar ita ta kawo gulmarta da har tasa ta zama abin kallo kenan. Ranar bata iya fahimtar abinda aka koya musu ba, Allah Allah tayi a tashi ta tafi gida, sun fito a hanya wasu Mata uku yan Ajinsu suka tareta. Kai tsaye daya ta kama Niqab din fuskarta ta fizge Daya daga ciki tace "Ke kuwa Barira ya haka? Ya zaki cire mata abu haka kawai?" "So nake naga fuskar munafuka, nifa tunda na fara ganin matar nan daman jikina ya bani Bata da gaskiya ashe kuwa qasurgumar yar Ta'addace tayi badda kama take rufe fuska to Asirinki ya tonu kaf makarantar nan babu wanda be san aika aikar da kikayi ba kika saukewa Mijinki kayan aiki tir da halin ki wlh" wadda aka kora da Barira ta fada har tana tofar da yawu qasa. Dake cikin hargagi take maganar se gashi hankalin masu wucewa yakai kansu suka fara tsayawa ana tambayar meya faru take kuwa suka shigar fadar abinda suka sani akan Umaiman. Mata suka zagayeta, wadanda suka santa suka shiga Mamakin jin itace dan da yawa dauka sukayi ko garin ta bari tsahon lokaci tubda ta denaZobo babu Wanda ya san ya take ciki. Abin mata,a maimakon su tsawatar da tozarcin da ake shirin yi mata se suka hadu sukayi mata caaa da yawa so suke suga fuskarta tunda sunji labarin so suke suga idanunta kawai yanzu. Umaimah ta riqe Niqab dinda qamqam tana durqushe a qasa saboda yanda takeji kukan ma ya kasa zuwar mata. Zuwan Malam Najib Malamin Ajinsu ya ceceta, shi ya watsa taron dandazon Matan yace ta tashi se sannan hawaye ya balle mata ta shiga kuka tamkar ranta ze fita ba kuma taga laifin kowa ba sai kanta ita tayi abinda ya janyo har aka tireta haka. Haka ta koma gida tana kuka kamar me, Mama bata bi takanta ba Anty ce ta ringa lallashinta da tambayar meya faru amma ta kasa ce mata komai. Washe gari bata tashi da niyyar fita makaranta ba amma Mama tace babu fashi setaje. Ta fasa mata kuka amma tayi mirsisi. "Duk abinda kika gani kekika jawa kanki dan haka seki nemi jarumtar tarar kome zaki gani" Maman ta fada mata tayi ficewarta daga dakin haka ta shirya ba yanda ta iya ta tafi, a Ajin ranar ma seda suka sake tireta suka ringa jifanta da maganganu marasa dadi ta kwantar da kanta a Desk har sukaci suka cinye bata tankawa kowa ba. Kamar yanda Mama ta fada ita ta jawa kanta dole ta nemi qarfin guiwar tarar abinda ze sameta. Haka ta ringa rayuwa a makarantar cikin tsangwama da takurar dalibai, duk kashedin da shugaban makaranta yayi akan abinda aka matan basuji ba danhar suspending Barira da qawayenta akayi amma hakan besa Matan makarantar sun sarara mata ba. Kadan ne suke tausayinta irinsu Malam Aisha da ta tsaya ta zama bakin Umaiman, duk wadda ta fada mata maganar banza ita take maida musu da yake me bakice kuma ta iya tijara se gashi tayi maganin da yawa saga ciki musamman yan Ajin da suka addabi rayuwar Umaiman. Abin ya munana ya zarce makaranta dan labari sabo ya koma a unguwa data fita an ringa nunata ana tuno ai ga abinda tayi. Majalissun Samarin unguqarsu suka samu nayi, sun kuma dana mata tarko jira kawai sukeyi lokacin da zata afka ciki yayi. Wannan sabon yanayin ya saka damuwar da take ciki qara nunka tada saboda a baya iya damuwar yan gidansu ce yanzu kuwa tsangwama take fuskanta sosai daga gurin mutane tayi kuka akan haka harta haqura, ta saki zuciyar ta dole ta tunkari koma menene ba zata cigaba da buya tana gujewa Laifukanta ba Niqab dinma ta dena sakawa. Wannan kwarin guiwar data bata kanta da kuma tasirin addu'ar da takeyi babu dare babu rana yasa ta samu sauqin Al'amura. Taci gaba da zuwa Islamiyyarta masu gulma da zundenta har sun gaji babu dai me kulata in ka cire Malama Aisha da tsirarun yan Ajinsu wannan be dameta ba karatunta takeyi dan shine a gabanta ba kuma neman qawa takeyi ba dan ta shata ta warke. An samu dogon hutun yammakaranta, babu tsammani sega su Mu'ayyad an kawosu da Jakar kayansu abinda ba'a tabayi ba ko na kwana daya tunda ta bar gidan Ubansu. Zuwan yaran ya sake rage mata kewa da gaske dukda ta wani bangaren zuwan nasu Fami ya zamar mata na abinda take qoqarin shafewa daga rayuwarta. Tunda Bibi ta qyalla ido taga wayarta data sake ajiyewa dan ba abinda take da ita. Ba me kiranta babu wanda take kira social media kuwa bata gabanta ma yanzu kullum sedai kawai tayi mata chaji ta ajiye amma tunda su Bibin suka zo ta samu wayar shikenan ta banu ta mayar da ita kamar tata. Kullum seta kira Dadynsu idan suna wayar sedai Umaimah ta tashi ta fita saboda abinda takeji. Iya kallon Mu'ayyad ya isheta tashin hankali, a shekaru sha biyun da yake gaba daya ya rikida ya zama Khalil, kamanninsa, tafiyarsa, maganar da komai nasa na Khalil ne. Idan yana cin abinci zama take ta zuba masa ido dan hatta yanda yake riqe cokali da tauna abincin sak Khalil, lokaci da yawa seta juya gefe ta share hawaye, babu abinda ya ragu daga ranta na daga soyayyar Khalil sedai ma abinda ya qaru son zuciyarta ya rabata dashi gashi suna raye cikin duniya daya amma yafi qarfinta. Idan suna waya da yaran se taji kamar ta kwace taji muryarsa, haka wani sa'in kasa riqe kanta takeyi ta kirashi amma kafin ya dauka seta kashe shi dan bata san me zata ce masa ba. Tana so suyi magana, ta roqi yafiyarsa amma ta gagara hada wannan jarumtar, a haka hutu ya qare yara suka koma gidansu. Ranar da zasu tafin da kansa yazo daukarsu tareda Humaira data qara zama wata hamshaqiyar Mace. Tana cikin irin matan da shayarwa take karba suyi kyau su cika ga jin dadi da zaman cikin raba ya qarawa farar fatarta kyau da sheqi duk inda ta wulga daukar ido takeyi. Yanda ta ringa fara'a tana gaida Umaiman ya soketa ta ringaji da biyu take mata haka, ta gama hade musu kayansu tana jiyo tashin hirarsu a falon Mama Bibi ta shigo tana tura baki ta fada jikinta, murmushi tayi kawai tun safe take rigimar ita ba zata tafi ba anan zata zauna seda Mama ta binciko Dorina ta ajiye kafin ta shiga taitayinta. Iman ta shigo tareda Aryaan Umaimah ya kalleshi fari tas kamar ka tabashi jini ya fito a haka zaka dauka da Mamansa yake kama amma ita tana kallonsa ta hango kamanninsa da Khalil sedai banbancin launin fata ya boye wasu. Tayi masa murmushi kamar yanda shima yakeyi Iman na kallon Bibi tace "Dady yace kizo mu tafi" "Ni bazan tafi ba" ta fada a tsiwace Umaimah ta daki bayanta ta zabura dan taji zafi ta kalleta tace "Wuce ku tafi, daman karki fasa halinki kinji ko" hawaye ya zubowa yarinyar se kuma Jikin Umaiman yayi sanyi, duk cikinsu ita ce me qulafucinta sauran basu wani damu da rashinta a gidan ba ko sun damu basa nunawa ita kadai take damuwa da son ta koma gidansu. Hijabinta ta zura dogo jin sun fito daga dakin Maman. Mu'ayyad ya shiga ya fara daukar musu kayansu yana fita dasu ta fito masa da ragowar qofar dakin ta tsaya. Kanta na qasa tana jin suna sallama da Mama, bata so ta dago balle taga abinda ze sosa mata rai, dariya da kuma muryar Khalil dataji dab da ita ta sakata dagowa ba tareda ta shirya ba. Yana riqe da Abid yanayiwa Humairan magana fuskarsa a washe ita kuma tana dariya wani abu ya dirar mata a zuciya amma tayi qoqari ta hadiye jin Humairan nayi mata sallama ta amsa yanda be kulata ba haka itama ta dauke kanta har suka fice daga gidan kafin ta koma daki tayi shiru. Wunin ranar haka tayi shi babu dadi, ga kewar yaranta ga tasowar tsohon tsumi, duk yanda taso tayi baccin a daren ya gagareta. Ta tashi tayo Alwala tayi salloli, qarfe uku da wasu mintina haka kawai ta dauki wayarta ji takeyi tamkar idan bata kirashi ba zata iya madewa hannunta na rawa qirjinta na bugawa ta dannan kiran muryar matar kamfanin Mtn ta shaida mata da cewar layin a kashe yake, seta sauke ajiyar zuciya me nauyi ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta hawaye suka shiga yi mara tsere. Ta dade tana kukan daga qarshe ta lallabi kanta tayi haquri. Babu zato Abba ya bata offer aiki a qarqashin Ma'aikatar sadarwa ta Jaha. Ranar rasa abin cewa tayi se kuka da godiya kawai dan abin yazo mata a bazata, bata san da zancen neman aiki ba bata ma taba zaton za'abarta tayi aiki ba se gashi Abban da kansa ya nema mata seda komai ya kammala kafin ya sanar dasu. Inda gizo yake saqar rashin sanin ta inda zata fara, se take ganin kamar ba zata iya ba amma da Abban ya zaunar da ita ya sake yi mata nasiha tareda gargadi seta samu nutsuwa a ranta. Kafin ta fara zuwa aikin seda Salman ya sake koya mata abubuwan computer dan tace ta manta komai abin Mamaki kuna daya fada mata zata tuna yanda akeyi kodan tana buqatar aikin ne yasa kwakwalwarta tayi qoqarin tuna duk abinda ta sani a baya cikin qaramin lokaci oho, a haka ta fara fita aiki wanda hakan ba qaramin taimakonta yayi ba dan a dan lokaci Walwalarta ta fara dawowa, yanayin aikin da mutanen da take mu'amala dasu suka taimaka mata matuqa gurin fuskantar gaba ta dena tuna bayanta. Qarfe tara take fita ta taso hudu dan haka zatayi Breakfast, an cire mata shara da wanke wanke se kuna girkin dare idan ta dawo wata rana ma yin abinsu sukeyi basa jiranta musamman Anty takance ta gaji taje ta huta kawai tayi abinta. Albashin da ake bata ya matuqar taimaka mata, bata da matsalar suturu dan yanzu datake fita nema take saka kaya dan haka ta dinka dogayen Hijabai har qasa kaloli masu kyau dasu take zuwa aiki yanda ta kame kanta bata shiga sabgar komai da bata aiki haka magana ma ba kasafai takeyinta ba se abinda ya zama dole hakan yasa kowa a gurin yake mutuntata. Da sallama ta shiga office din Hajiya Huda zata kai mata wasu takaddu data buqata, Cike da tsananin mamaki take kallon matar data kira sunanta tana zaune akankujera tana zabga mata murmushi. Umaiman ta gyara tsayuwarta tana sake kallon matar. A jikinta tana jin tabbas ta santa a wani guri amma ta kasa tuna ina ne. Hadiza ta qara fadada murmushinta tana cewa "Baki gane ni ba ko Umaimah? Hadiza ce, shekarun da yawa kin ganni na zama qatuwa duk wanda ya dade be ganni ba se yayi da gaske yake ganeni" Qirjin Umaimah ya buga da qarfin gaske da jin sunan matar, Numfashinta ya tsaya na wani lokaci har bata san sanda ta saki takaddun hannunta ba kafin ta shiga jansa da qarfi jin sunan Hadizan kadai ya haifar mata da wani yanayi tareda shigar da ita rudani na gaske, lura da hakan ya saka Hadiza miqewa ta kama hannunta tana cewa "Lafiya dai ya naga kamar bakiyi murna da gani na ba?" Idon Umaimah yayi rau hawaye suka shiga sakko mata, so take ta bude baki amma ta kasa cewa komai se kawai ta fashe da kuka, Hadiza ta sake kallon Umaiman cikin yanayin nuna rashin jin dadi tace "Kiyi haquri, ban dauka ganina ze bata miki rai ba, tunda na shigo na ganki kafin nayi miki magana kika shiga wani office na bari se zan fita se mu gaisase kuma gaki anan amma kiyi haquri, da nasan bazakiji dadi ba da ban miki magana ba" ta sake hannun Umaimah tana yunqurin tashi se Umaiman ta damqe hannunta lokaci daya ta durqushe a gaban Hadizan cikin tsananin kuka tace "Dan girman Allah ki yafe mun, nayi nadamar abinda na aikata miki a kullum cikin Addu" a nake Allah ya hadani dake ya bani ikon neman yafiyarki gashi yau ya amsa mun Addu'ata ki yafe mun" ta qarasa tana riqe qafar Hadizan dake qoqarin dagota amma ta kafe taqi tashi. "Dan Allah ki tashi kar wani ya ganki haka, Anty Huda kiyi mata magana ni zumunchi kawai nazo muyi ba tayar miki da hankali ba ki tashi koma wace magana ce se muyi a zaune dan Allah" Hadizan ta sake fada, dakyar ta samu Umaima ta zauna a kan kujera har sannan hannunta riqe dana Hadiza tana kuka kamar me ta sake cewa "Haqqinki ne yake bibiyata, na rasa aurena, uwa uba na rasa mutunchina Khalil din da nayi hauka akansa na rasashi ina Ji ina gani ya zama mallakin wata bani ba. Dan Allah ki yafemun Hadiza ko zan samu sauqin rayuwar da nake ciki". Jikin Hadiza yayi sanyi da jin maganar Umaiman, sun rabu da Khalil kenan take nufi meya faru?" "Ki yafe mun Hadiza" Umaiman ta sake fada cikin tsananin kuka. Hajiya Huda da tayi shiru tana kallon Dramar tasu ta sauke numfashi tace "Ya isa Umaimah ki dena kukan haka, Hadiza meya hadaki da ita haka da take kuka tana neman gafararki?" Se Umaimah ta sunkuyar da kai ba tareda ta dena kukan ba wata irin kunya da nauyi sukayi mata rubdugu. Idan Hajiya Huda taji labarinta tabbas duk wani girma da mutuntawa da ake mata a ma'aikatar ya qare daga yau zasu ringa mata kallon mara mutunchi da bata tsoron Allah amma hakan ya fiye mata idanhar Hadiza zata yafe mata a shirye take data sake yin Video ta roqi yafiyarta kamar na wancan karon. Hadiza kuwa murmushi tayi tana kallon Yar uwar Mijin nata tace "Babu komai Anty Huda, can an dade mun taba samun sabani da ita amma ya wuce a gurina kuma tun a lokacin mantawa tayi amma na fada mata na yafe har gaban Allah babu komai a raina" seta koma kan Umaimah tana cewa "Wallahi na dade da yafe muku Umaimah tun a wancan lokacin banida wani abu dana riqe akanki amma naji kince kin rasa Khalil, kardai Rasuwa yayi ban sani ba?" "Khalil be rasu ba Hadiza amma bama tare kusan shekara shida kenan ya sakeni" Umaimah ta bata amsa tana sunkuyar da kai qasa se office din yayi shiru na wani lokaci kafin Hadiza ta sauke numfashi tace "Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi a rayuwarku gaba daya". Umaimah dake kuka har sannan ta daga kai ta kalleta tace "Harda haqqinki da yake bibiyata ki yafe mun dan Allah" "Umaimah, na gaya miki nifa ban riqeki da komai ba amma dai tunda so kike na sake fada kiji na Yafe miki Umaimah na yafe miki abinda kikayi mun Allah ya yafe mana gaba daya". Ajiyar zuciya me qarfi ta sauke tana jin nauyin zuciyarta na raguwa. Hajiya Huda ta miqe da kanta ta dakko ruwa me sanyi ta miqa mata a sanyaye tana cewa "Kisha seki shiga ki wanke fuskarki tunda tace ta yafe kukan ya isa haka". Ta karbi ruwan tasha kamar yanda tace ta shiga bandakin dake cikin office din, Hajiya Huda ta kalli Hadiza data sunkuyar dakai, maganar rabuwar Umaimah da Khalil din ta tabata seta dafa kafadarta tana cewa "Madallah da kyakykyawar zuciya irin taki Hadiza, Ubangiji yana son masu yafiya Allah ya yafe miki kurakurenki kema kamar yanda kika saka sharri da Alkhairi, ubangiji yaci gaba da dabaibayeki da Ahalinki da Albarka mara yankewa, dan uwana yayi sa'ar mata" Hadiza tayi murmushi daidai nan Umaimah ta fito ta wanke fuskar amma har sannan bata dena hawayeba tana jan majina, Hajiya Huda ta nuna mata kujera tana cewa "Zauna a nan har se kin dena kukan zaki fita, ba zaki ja a fara tuhumar me akayi miki ba ina tace ta yafe to kukan ai ya isa haka ko" kamar tace ta qara kuwa ta sake fashewa da wani kukan. Auna qirman laifin da tayiwa Hadizan takeyi a zuciyarta wai duk ina tunaninta yake tafiya a baya idan zata aikata mugun Abu? Khausar da Rufaida sun cuceta, su sukayi mata ingiza me kantu akan Hadizan, wannan be zamar mata darasi ba ta sake janyo Safina rayuwarta gashi yanzu ta tarwatsa komai ya lalace ta rasa komai da take taqama dashi. A ranar se Hajiya Hudace ta maidata gida dakanta saboda irin kukan data ringayi harya haifar mata da ciwon kai me tsanani. Seda ta kwana biyu tana jinya kafin ta koma aiki ta kuma yi maruqar qoqari gurin danne duk wata damuwa ta cigaba da walwalarta. KHALIL *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 87 BAYAN SHEKARA DAYA A hankali kamar wadda akayiwa kiran yan zawarawa suka fara kawo mata caffa. Idan ta fita bata dawowa gida ba tareda wani ya taya ba saboda yanzun Alhamdulillahi ta murmure, jikinta ya fara dawowa dukda bata maida cikarta irin tada ba amma tayi kyau fatarta ta goge musamman da yanzu take daukar Albashi tana kula da kanta ta siyi mayuka masu kyau dan har Supplement Maman Asad ta sakata dole ta siya masu gyara fata bana qarin wata halitta ta jiki ba ya kuwa karbeta ya bude mata ciki ta ringa cin abinci sosai kuma me gina jiki nan da nan se gata ta dawo hayyacinta tayi tas shiyasa duk idan ta gifta Mazan basa iya dauke kai akanta amma a bangarenta ta shata musu layi, babu Wanda ta bawa dama duk irin yanda Yan uwanta suke mata magana akan bafa zata zauna haka ba, gara ta sako ranta ta bawa wani dama su daidaita dan mutunchin Mace gidan auranta. Anty Hafsa ma da take zaune tayi aure tuni, daman ita tace saboda Yaranta Mata take zaune duk manemanta idan ta kawo musu zancen da yaranta zata zauna se su zame ita kuma tace ba zata barsu hannun dangin Mahaifinsu ba dan basu nuna musu zumunchi ba, tunda ya rasu aka rana gado suka karbi rabonsu kowa ya zame ya barta da wahalar Yayan nata hudu da suke duk Mata. Tashi daya Allah ya aurar mata da uku, babbar ta gama Jami'a, me binta tana level 3 se ta ukun ta shiga kenan duk suka samu Miji Mama tace babu abinda za'a jira haka aka hada da Sharifan Anty da itama ta gama makarantar tuntuni se sannan ta samu Mijin aka sha biki. Auran yaran da wata uku ita ma ta daura nata da wani tsohon Abokin Baban yaran shima matarsa ta mutu shikenan ta tare da sauran yarta data rage ta hada da nasa ta riqe masa. Auran Anty Hafsa yasa suka taso Umaiman itama a gaba. Dole badan tana ra'ayi ba ta fara barin maneman nata suzo gida saboda Mitar Mama ma kadai ta isheta sedai kuma wata sabuwar jarabawa data bullo mata duk wanda yayi zuwa daya gidan baya dawowa sedai su shiga yi mata wasa da hankali a waya da son cewar su hadu a wani gurin, wasu ma daga haka se zancen banza ya shigo ciki duk wanda kuwa ya kawo mata zancen banza zagewa take tayi masa tijara dan ba wai tayi sanyi ne gaba daya ba daman rayuwa ce kawai ta bida ita. Mama ta sakota a gaba da cewar ita take korarsu da baqin halinta. Sassauci da rahamar data samu a gurinta ta fara ja baya suka koma yar gidan jiya fada kyara da hantara kullum ta dira mata mitar taqi fitar da Miji tunda ba maneman ne bata dasu ba korarsu takeyi. "Nasan me kikeyiwa qulafucin komawa gidan Khalil kikeyi to tun wuri Idan zaki cire ranki akan sa ma ki cire dan baze maidake ba, ke idan kina da kunya ma in aka ce ki koma se ki yarda? Ki kalli Hajiya Aisha da wane idon bayan dibar Albarkar da kikayi mata? To idan ma zaki fiddashi a ranki tun wuri dan rigada ya miki nisa, tazarar ku tamkar ta sama da qasa ne. Yana can yana rayuwarsa cikin jindadi da kwanciyar hankali tareda matarsa da take sonsa take girmama mahaifiyarsa shekara bakwai kenan kina zaune idan da ze waiwayeki da tuni ya nuna alamu dan haka gara tun wuri ki samu wani ya rufa miki asiri ya aureki dan ke kam a yanzu sedai kiyi auran rufin asiri" haka Maman take yaba mata magana duk kuwa sanda ta fada mata haka ranar wuni zatayi tana kuka. Amma ta yarda da ita datace Khalil baze waiwayeta ba. Yaranta suna yawan kiranta da wayarsa musamman Bibi, sau da yawa suna tare dashi tana jin muryarsa yana hira cike da nishadi amma koda wasa be taba gaisawa da ita ba ita ma kuma tayi namijin qoqari gurin riqe kanta bata tambayar yaran shi haka indai ba su suka kira ba bata kiran layin nasa, daga bayane ma da zuciyarta ta gaza, tana ganin idanhar bata nemi yafiyarsa ba bazata qarasa samun cikakkiyar nutsuwa ba se ta ringa tura masa da Text message na ban haquri amma ko sau daya be taba maida mata da amsa ba haka ko ya kawo yara sun hadu be taba yi mata kallon wata halitta da zaman aure ya taba hadasu ba balle har tasa ran ganin soyayyarta a kwayar idonsa. Idan ta gwada kiran layinsa ma baya shiga sedai idan yaran ne suka kira da kansu tasan kuma shiya saka lambar tata a wani tsarin ta yanda bazata same shin ba, seta koma canza layuka dukda hakan batayi nasara ba dan baya dauka, daman tun Asali ta sani da wuya ya amsa baquwar number in dai ba me ita yayi masa saqo ya fadi wanene shi ba, dan haka kota kira baya dagawa. Daga baya ma har wayar Mama take dauka ta kirashi, tayi haka kusan sau uku duk be daga ba sedai daga baya ko da daddare zataji suna waya da Maman alamar se sannan ya samu sukunin kira kenan akan hakan Mama tayi mata tatas data gane ita ce take kiransa da wayar, ta ringa mata gori da Tijara kai ba zakace ita ta haifeta ba, irin wadannan abubuwan kadai sun isa su sanar mata da matsayinta a gurin Khalil yanzu dan haka dole taja jikinta ta kuma karbi qaddara a yanda tazo mata koma meya faru itace sila, ita ta siya da kudinta. Data haqura ta zauna dashi kamar yanda yasha fada mata ta sani babu wata Mace da zata zo ta zarce ta matsayi a gurinsa seta biyewa kururuwar shaidan ya kaita ya baro gashi ta qare a nadama da dana sani mara amfani. Tun daga nan ta sake janye jikinta akan lamarin Khalil amma bata fasa tura masa da saqonnin ban haquri ba dan wannan ya zame mata dole, tana buqatar Afuwarsa data sauran Ahalinsa amma Khalil din ya shareta funfurus kamar baya ganin saqonnin Alhalin kullum ta turo seya duba ya karanta sannanya goge. A haka taci gaba da aikinta, Al'amarin zawarawa kuwa abin tun baya damunta har ya fara bata tsoro. A lissafe cikin qasa da wata biyu tayi Zawarawa sun kai Goma amma babu guda daya daya tsaya daga zuwa dayan nan basa dawowa. Dama duk wanda taga take taken ze zo mata da wata maganar blocking dinsa kawai takeyi ta dena biye musu tayi masifa tunda ta fahimci Al'amarin Mazan yanzu ya qazanta sedai kawai ace innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Fasadi yayi yawa a doron qasa, babu kunya babu tsoron Allah mutane sun maida zina Ado musamman ga Mazan aure da matan auran ma dan abin ya zarce yammata yanzu masifar ta girmama kuma babu tsoron Allahn daya halicci mutum qiri qiri suke zuwar mata da buqatarsu, ita dai batayi kalar yar iska ba haka nan bata shiga da take bayuynar da jikinta Hijabine kullum take bulalawa har qasa dan da yawan zawarawan seda suka mata qorafin shogar tata wai tana rage mata kyau sannan bata da sakin fuska ko sakin baki da ze saka suga lakwa lakwan da zasu zo mata da maganar banza amma a hakan dai bata tsira ba. Da Hadiza kadai ta iya tattauna maganar wadda yanzu sun dinke sun zama Qawaye har gidansu take zuwa itace dai sau daya ta taka gidan Hadizan tana kuma bala'in jin dadin tarayyarsu saboda yanda take qaruwa da ita ta fuskoki da dama. Kasancewar Hadizan Lawyer gomnati Umaiman najin labarin kesa kesai a gurinta da suke qara sakata tsoron Allah ta kuma tsoraci duniya. Idan taji wani abun se taga ashe ita a iskancin ma ba abinda ta iya manyanta na gaba ta kuma godewa Allag daya bata ikon gano kuskurenta ta kuma gyara tun gabanin lokaci ne qure mata ba. Sanda take yiwa Hadiza zancen matsalarda take damunta game da rashin tsayawar Maneman nata sa kuma irin abubuwan da suke bijiro mata dasu dariya kawai tayi take ce mata "Ki godewa Allah ki kuma cigaba da neman taimakonsa dan a dukkan al'amuranki, ba wayo bane ba dabara ba Umaimah muna cikin wani zamani da ubangiji ne kadai ze shige mana gaba. Karki sakawa ranki damuwa duk wanda kikaga yazo ya tafi ba mijinki bane babu kuma Alkhairi a tare dashi, in sha Allahu da sannu zaki rabauta da tanadin da ubangiji yayiwa bayinsa da sukayi kuskure kuma sukayi tuba na haqiqa karkiyi sauri a rayuwa labari na kadai ya isheki Misali, kina kallon abubuwan dana fuskanta a rayuwa qila badaban faruwarsu ba bazan dace da irin Mijin da kalar rayuwar dana samu a yanzu ba". Jikin Umaimah yayi sanyi laqwas da kalaman Hadizan, koda ba da wata manufa ta fada ba amma maganar ta shafeta saboda duk idan za'a bada tarihin Hadiza da gwagwarmayar data sha tabbas seta fito a shafin mummunar qaddadararta. Data sakeyiwa Rumasa'u Farar Aminiya maganar itama dai kamar Hadizan ce mata tayi ta share komai taci gaba da Addu'a in sha Allahu Alkhairi yana gaba da wannan tadan samu nutsuwa amma kwarzabar Mama tasa dan kumarin data farayi ya nemi guduwa, data dawo gidan zata kafa mata mitar wance ta haihu wance tayi kaza, tun ba da Hajiya ta kira Maman take gaya mata wai Bibi ta fara Al'ada ba ranar kam taga abu, Mama harda cewa seta jira su jera ita da Bibin suyi aure rana daya tunda taqi tsayar da Miji to ga yarta nan ta girma ko yanzu za'a iya kaita daki. Akayi katari ranar wani ya aiko sallama da ita ta fatattaki Yasir dayazo fada mata saqon Mama ta qara samun nayi seda Abba ya saka baki kafin ta barta ta shaqi iska me dadi a gidan. Kodan abinda Mama take mata da zata samu Miji ko wanene zatayi aure amma ta rasa, abinda bata sani ba duk wanda yazo da yan Majalisar qofar gidansu sun qyalla ido sun ganshi zasu bi baya su lalata komai ta hanyar bashi labarin qarya da gaskiya daya faru su kuwa daga nan su gudu se su zagayo mata da zancen iskanci. Ire iren wadannan abubuwan suke qara jefata cikin damuwa idan ta tuna zamanta da Khalil a lokutan data ringa wukaqantashi da gayya tana hankadawa Matan waje shi. Me yasa bata taba yin wannan dogon tsinkayen ba, mata na waje suna farautar Maza wasu ma basuji ba basu gani ba matan ke jansu tana kallo irin haka na faruwa a gurin aikinsu ballantana irinsa a lokacin da yake cikin buqata badan tsarewar ubangiji ba ai da tuni Khalil yayi tambari a neman Mata amma ya kame kansa duk saboda ita magana me tsaho bayayi da mata hatta wanda suke ciki daya a gaban idonta se yayi mata wannan Alkunyar dan kar ranta ya baci duk irin halaccin nan da yayi mata amma ta kasa yi masa uzuri akan abinda ba haramci ba to da ace Khalil Matan banza yabi da qila idan ta gano take zuciyarta zatayi bindiga ta mutu dan ba zata iya hasaso irin tashin hankalin da zata shiga ba. Tayi Adawa da matar sunnah wadda suke da matsayi daya da ita har a gurin Allah ita kam wai ina hankali da tunaninta suka tafi sanda tana gidan Khalil? Soyayya da Kishin karya hadata da kowa ya rufe mata ido yasa bata tunanin komai se son zuciyarta. KHALIL A kullum cikin godewa ubangiji yake bisa ni'imar da yayi masa. Tabbas ya yarda da cewar sakamakon haquri Alkhairi ne mara iyaka. Soyayyar Umaimah, Auranta da rayuwarsu ya dauke su a matsayin jarabawa daga ubangiji haka haqurin da yayi da ita ba sakalci bane kamar yanda da yawa suke dauka dan a yanzu gashi yana dandanar romon dutsen daya dafa. A baya ya kanyi tunanin yanda rayuwarsa zata kasance ba tareda matar da yake tsananin qauna ba se gashi yanzu ya rayu babu ita na tsayin shekaru kuma babu abinda ya canza a rayuwarsa sema tarin alkhairai da suka dabaibaye shi. Dukda dai lamarin zuciya da abinda take so amma bashida zabi illah yaci gaba da bata Matsayin uwar yayansa bawai Masoyiya ba. Samun Humaira da yanda Al'amura suka daidaita tsakaninsu ya sakeyin tasiri matuqa gurin mantar dashi kewarta da tunaninta dukda a wasu lokutan su kan motsa masa. Kewar Umaiman tana damunsa idan ya tuna wasu abubuwan dadi da suka wanzu tsakaninsu se ya ringajin tamkar yaje gareta musamman idan yaji suna hira da yaransa yanda tayi sanyi qalau da mu'amalarta na matuwar dukan zuciyarsa tana kuma bashi tausayi, idan yaje gidan ya ganta sanyi qalau se yaji wani iri kamar ya tsokaneta tayi buyaginta tafi kyau a haka amma yanzu ta zama wata Umaimah ta daban da ko yatsa aka saka mata ya tabbatar ba zata gatsa ba. Duk sanda yaso shagala a irin shauqin nan daya ya tuno da wasu al'amura da suka gabata tilas yake danne komai yaci gaba da shafa mata fentin da ganinsa tareda ita ne kadai ze hana zuciyarsa karaya ta koma mata a karo na biyu. Allah ya sani yana qaunar Umaimah Al'amarin da yakeji a kanta baze misaltu ha ba kuma ya tsammanin ze jishi tareda wata mace amma ya haqura da ita tunda ya haifu dan Halal ne shi ba shege ba yanda tayi iqirari. Qofar bandaki aka bude Humaira ta fito daure da Towel babba ta yafa wani qarami akanta, Khalil dake kwance daidai ya lula duniyar tunani qarar qofar ta farkar dashi ya kalleta, a tare suka saki murmushi kowanne da ma'anar nasa a ransa ya miqa mata hannu ta noqe kafada seya fashe da dariya sosai ita kuma ta shagwabe fuska kamar zata fasa kuka tana cewa "Dole kayi mun dariya mana tunda ka kusa jawomun aiki, ni wlh bazan yarda bama se munje an duba ance babu komai sannan zan yarda mutum babu tausayi daga yin Arba'in dina baka ko duba ni yar yarinya ce kayita cin zalina ai Mala'ikun Allah suna kallonka" Dariyar ya qarayi har yana shirin kwarewa ya tashi zaune yana cewa "Ji wata magana fa yarinyar nan, Fushi zumbura baki da qunquni babu irin wanda ban gani ba a gidan nan ke kin rainani sannan yanzu tun ba'aje ko ina ba kin karaya dama ai na gaya miki yatinya lafiyata ta miki yawa baki yarda ba amma yanzu gashi kin fara gani a shekara biyu kinyi yan uku, to ki shirya wasu biyun suna tafe nan da wata tara dan aikin dana sha jiya ba a banza ba nasan nayi babbar Ajiya". Pillows da suka watso qasa ta shiga diba tana jefa masa tana kukan shagwaba, tunda ta dawo daga wankan Abid abubuwa suka qarasa warwarewa Khalil din ya dawo garau kamar wanda aka canzawa inji, tun tan jin dadin abin seda ta fara kuka tana neman mafaka dan kamar me biyan bashi haka ya ri ga gurzarta kullum babu daga qafa kamar abinci seda ta fara rama kafin ya tattara hankalinsa guri guda ya fara saurara mata, shikansa ya ringa mamakin inda ya samo wannan qarfin da Lafiyar amma ya danganta hakan harda tsoron rasata daya fara tunda har ta nuna qiri qiri ta gajiya da halin da yake ciki tofa shikenan rayuwa ta qara armashi, Humairan riritashi take kamar Gwal shi kuma yana kasheta da kalolin soyayyarsa masu tsayawa a rai. Sunyi kyau dasu da yayansu gidansu na cike da walwala a kullum cikin godewa Allah yake bisa ni'imar da yayi masa. Watan Abid din goma sha takwas ta haife yan biyu Mace da Namiji wanda basu san da cikinsu bama seda yayi wata kusan uku sannan, yasha daru da ita, dukda bata ce bata so ba amma kullum cikin kukan danta jariri ne ko yayeshi batayi ba ace ciki haka ya ringa lallabata da aka ce musu biyu ne nan ta sake rigimewa qarshe se Mama ce ta dauke mata Abid dinda cikin yayi wata bakwai saboda ta samu sauqin abubuwa haka kuwa akayo ta turawa har Allah ya rabasu lafiya aka cire mata Hauwa (Jiddah) da Takwaran da yayiwa kansa suna ce masa Adil. Yau din kwananta shida da dawowa daga wanka dan wannan karon ma gidan Mama ta koma bisa umarnin Hajiya Khalil kuwa ya ringa bala'i kamar ze ari baki saboda masifa akan me za'ace haihuwa ta uku ta tafi gida Hajiya tayi masa banza a cewarta lafiyar Humairan tafi komai ga aiki ga rainon yan biyu idan ta zauna a gidan fitinarsa kadai ba zata barta ta warke ba gara taje gida haka kuwa ya haqura qarshe ma ya qirqiri tafiyar dole ya bar qasar seda ya rage saura kwana uku ta dawo sannan shima ya dawo, tunda ta dawo din kuwa yake murzarta son ransa da sunan hukuncin yarda ta tafi gida da tayi, ita kuwa tadawo da shirin tarairayar mijinta dakyau, zata jurewa yanayinsa a kowanne hali ba zata gajiya ba. Seda yayi dogon rarrashi kafin ya barta ya shiga wanka saboda buga qofa da akayi yan biyu na kuka. Ta shirya shi kuma ya shiga wanka, seda ya fito ya lura da lokacin daya bata qarfe goma yake so ya fita gashi har goman tayi da kusan minti ashirin. A gurguje ya shirya ko karyawa be tsaya ba ya fita saboda akwai baqin da zeyi kuma sha daya zasuzo shiyasa yaso fita tun goma ya sake duba takaddun da zeyi amfani dasu. Qarfe sha dayan daidai baqin suka iso, kai tsaye Conference room dinsu Anwar ya kaisu. Seda ya hada duk abinda zeyi amfani dashi kafin ya shiga, fuskarsa a washe ya shiga yi musu maraba yana kuma basu haqurin jiran da sukayi ya zauna akan kujerarsa idonsa ya sauka akan Umaimah data sunkuyar da kai da alama wani abu takeyi a wayarta take zuciyarsa ta buga har seda wayarsa ta subuce Anwar yayi saurin taro masa ita yana duba abinda Khalil din yake kallo da har yasa ya saki wayar be sani ba. Seda yayi qoqarin tattara nutsuwarsa kafin ya zauna yana qoqarin kore abinda ya taso masa. Umaimah data gama turawa da sabon Bazawarin da tayi me suna Abdulwahab saqo danya kirata ne ta katse ta sanar masa sun fita wani uzuri idanta gama zata kira ta ajiye wayar bayan ta sakata a Silent kafin ta dago ganin dakin ya danyi duhu an kunna projecter karaf suka hada ido da Khalil da duk yanda yaso ya hana kansa kallonta ya kasa. Jikinta ya dauki rawa zuciyarta ta ringa bugawa da sauri da sauri seta hade hannayenta biyu ta runtse idonta ji takeyi kamar ta tashi ta fice daga gurin, mamakin yanda ganinsa ya rudata haka ma ya kamata dan ba yau ne karon farko data ganshi ba bayan sun rabu, sun sha haduwa a gida a kusa kusa ma ba kamar yanzu da suke da tazarar gurin zama ba dukta ringaji mema yasa ta rako Hajiya Hudan. Aikin sabunta ginin Ma'aikatarsu za'ayi sun rubuta gwamnati ta sahale musu Hajiya Huda ce ta nemo musu Falcon Bridge construction company din a matsayin wadanda zasuyi musu aikin dan haka yau din tace tazo suje tareda wanda suke kula da bangaren kudi dan au qarasa qulla yarjejeniyar. Har akaci aka cinye ba zatace ta gane abu daya da sukayi a gurin ba, muryar Anwar dake ta zuba bayani kawai takeji dan Khalil din shiya bawa takaddun ganin kamar Khalil din baya cikin nutsuwarsa yakashi karba kawai ba tareda yace wani abu ba ya jagoranci yarjejeniyar har aka gama suka saka hannu a takaddu Umaimah na ganin Hajiya Huda ta miqe itama ta miqe dan jinta takeyi kamar akan qaya, karo sukaci da Khalil da shima yake shirin fita tayi baya zata fadi ya tarota kafin ya saketa da sauri ya fice kamar wanda ya tuna wani abu. A mota da Hajiya Huda ta tambayeta meya sameta ta birkice haka take ta fashe mata da kukan da take ta riqewa. Idan za'a saka mata wuqa ba zatace ga dalilin kukan ba, duk ta rikitasu, Aminu Sani daya daga cikin ma'aikatan da suka tafi tare, irin mutanen nan ne masu dan banzan surutu da saka ido, seya kalli Hajiyar yana gyara zama ya ce "Hajiya kamar da sanayya tsakaninta da Shugaban kamfanin nan dan naga suna hada ido gaba dayansu suka rikice, shima bakiga a yanda ya fita ba? Hajiya Umaimah ko tsohon masoyi ne kun fitar da ran sake haduwa yau kuka gamu?" Daga Umaiman har Hajiya Huda babu Wanda ya kulashi, ita tana cigaba da kuka qasa qasa ita kuma Hajiyar tunanin maganganunsa takeyi a zuciyarta tana tunanin to ko shine tsohon Mijin nata? Tabbas ta lura da yanda ya rasa nutsuwarsa ba kamar yanda ya shigo da farko ba kafin ya lura da Umaiman, irin kallon da ya ringayi mata duk tana ankare har ta ringa ayyana Allah sa tsuntsun soyayya ne ya dirar musu da kuwa Umaiman tayi Miji to amma yanzu ta gasgata maganar Aminu duk yanda akayi shine Mijinta da suka rabu inko hakane dole tayi kuka domin ya kai Mijin da wani ma ze maka takaicin rabuwa dashi balle ita da ta zauna tare dashi dan tasan shi sosai, Abokin qaninta ne tana jin labarin kirkinsa a gurinsa dan har akwai wata qanwarsu da qanin nata ya ringa cusa masa lokacin Khalil din yaqi yace shi yana son matarsa baze mata kishiya ba. Da suka koma office din jiki a sabule ta dauki kayanta data bari bayan ta dauraye fuskarta ta gyara dukda haka idan ka kalleta seka san tayi kuka. Abdulwahab daya isheta da waya ya iso ze dauketa, Kyakykyawan Farin bafulatani Matashi ne da zasuyi sa'anni da Khalil ko ya dan girme shi da kadan. Ma'aikaci ne a hukumar yaqi da cin hanci da rashawa (EFCC) kusan Hadiza ce ta hadasu dan a office dinta suka fara haduwa yaje gurin itama Umaiman ranar taje suka gaisa har sukayi yar hira a gurin kafin suka rabu kwana biyu a tsakani Hadizan ta kirata tana sanar mata da cewar ya nemi number ta kuma ta bashi. "Mutumin kirki ne Umaimah, na sanshi tunda dadewa munyi aiki tare yana da mata daya Khadija da yara hudu kuma ya tabbatar mun dagaske yakeyi idan kun daidaita kafin Azumi ma yake so ayi aure nan da wata hudu kenan. Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki bashi dama, nasan harda rashin bude zuciyarki da bakiyi ba yasa duk cikin wadanda suke zuwa kika rasa wanda yayi miki amma nasan in kika bawa Abdul dama zaki ce na gaya miku, halayensa suna kamanceceniya dana Khalil zaki so shi a hankali kuma ki tsananta addu'a" Hadizan ta gaya mata. Badan taso ba kuna dan karta ga tayi rashin kyautawa dan ita bama tason farin Namini amma a haka ta fara kula Abdulwahab. Se gashi cikin qasa da sati daya sabo ya fara shiga tsakaninsu kamar yanda Hadizan ta fada halayensa suna kamanceceniya dana Khalil, yana da matuqar kirki da sanyin hali ga shi ya iya kula da tarirayar mace. A sati dayan kullum se sunyi waya ya kuma sanar mata da duk wani abu daya kamat ace ta sani akansa hatta da hoton matarsa da yaransa ya tura mata, ya gaya mata Hadiza ta gaya masa komai akanta kuma ya gamsu dan haka shi da gaske yakeyi auranta yake so yayi kuma daya dawo Kano dan a Abuja yake aiki zezo kuma da yayi zuwa daya yana so na biyu ya zama iyayensa ne zasuje nema masa auranta. Gaban Umaimah ya ringa dukan dari dari da cewa da yayi Hadiza ta gaya masa komai akanta. Tana so ta tambayeshi yasan komai harda mugun HALIN KISHInta amma ta gagara, tsoro takeyi karta tono abinda zesa shima ya gudu dan zuciyarta ta fara amincewa dashi amma ba zataso ace su qulla magana akan qarya ko kuskuren tunani ba. Zata so ace yasan komai akanta kamar yanda tasani akanshi sannan ya yarda ze zauna da ita a hakan tana tsoron kar yaji wani abu daga baya yasaka shi canza ra'ayi dan haka ta qudure duk in suka hadu ita da bakinta zata fayyace masa komai. Kafin yaji a bakin yan unguwar da suke kore mata maneman gara yaji gaskiya daga bakinta akan wannan shawarar ta tsaya. Da kanta ta gayawa Maman Asad haduwarta da Abdulwahab din, ta ringa murna ita ta gayawa sauran da Mama gaba daya suka tsaya akan shawarar kar Umaiman ta kaishi gida kai tsaye. Ta kaishi gidan Baba Abdullahi, shawarar Maman Asad din take Nuratu tace babu wannan maganar dan ta tabbata kawunda kansa ze fara watsa gayyar dan yayi rantsuwa duk wanda yazo neman auranta seya gaya masa komai dan baza'a hada baki dashi a cuci mutum ba haka kawai taje ta illatashi. Nuratu tace mata ta kaishi gidan Maman Asad din, suyi zancen su a can idan sun daidaita sun gama shirya komai sannan se yaje ya gaida Abba da yan uwansa base an gansu tare ba bare aje a lalata maganar tun kafin taje ko ina. Da wannan maganar sukayi Na'am, zuwansa na farko ta kaishi gidan a can sukayi zancensu tayi matuqar qoqari gurin sake bayyana masa wacece ita da Mugun HALIN KISHInta da yayi sanadiyyar mutuwar auranta amma seta gagara fada masa aika aikar da tayiwa Khalil da irin diban Albarka da tayiwa surukarta, ai Allah ma bayason wanda yake aikata laifi sannan ya ringa fada cikin Alfahari. Abdulwahab yace yaji ya gani ya kuma yarda tunda har ta iya fada da kanta to dagaske take da cewar ta canza,ya sake jadda mata da cewar yana tsananin sonta kuma yasan bazata samu matsala da matarsa ba dan tana da haquri da kawaici ya tabbatar daga bangaren ta dai ba za'a taba samun wata matsala ba sannan kuma ba gida daya ma ze ajiye su ba, ita Umaiman ze tafi Abuja da ita saboda ita Hauwa tace tafi son zaman Kano yana daga babban dalilin daya saka yake son qara aure dan ya gaji da zama haka a can kuma zaman nasa yafi yawa a Abujan akan Kano ba kuma yaso ya shiga haqqinta yayi mata dolen komawa can shiyasa ze auri wadda zata yarda ta bishi a karan kanta. Daga nan soyayya ta falle a tsakaninsu, dukda bawai tana Jinsa har cikin zuciyarta bane amma ta karbeshi kuma zata aureshi a rashin wanda zuciyartata take da muradi. Zuwan da yayi yau din kamar yanda suka tsara zeje ya gaida su Abba sannan qarshen sati iyayensa zasuje nema masa auranta, duk wasu shirye shirye sunyi nisa hatta da matarsa ya hadasu a waya sun gaisa haka Mamansa da qanwarsa guda daya ita kam tuni suka qulla zumunchi tana yawan kiran Umaiman itace dai bata shige mata. Suna tafe yana janta da hirarsa ta barkwanci kamar yanda ya saba amma gaba daya yaga yanayinta ba kamar kullum ba dan haka yayi shiru ya qara musu sautin kidan dake tashi a radion motar, dama tunda ta fito yaga idonta ya tambayeta meya sameta tace masa zazzabi takeyi shiyasa fuskarta da idonta suka kumbura, yace su je Asibiti taqi, a cewarta taje an bata magunguna suna gida. Haka suka qarasa gidan, ta rigada ta sanar dasu zuwansa dan haka sun shirya. A falon Abba aka saukeshi, suka gaisa a mutunce Anty ta gabatar masa da abinda aka tanadar masa, tambaya daya biyu Abba ya gano Mahaifinsa Alhaji Sale sun zauna a kasuwa tare Rumfuna uku ne tsakaninsu, baban nasa ya gamu da paralysis kusan shekara goma yanzu abinda yasa suka bayar da hayar rumfar kenan dan babu me kula da gurin yaron shagunan nasa suka ringa Almundahana su kuma duka yayansa aikin gwamnati sukeyi babu wanda ya maida hankali a kasuwa dan haka ya bada hayarta kawai sukayi gwanjon kayan ciki. Hira sosai suka sha da Abban, shiya kwatanta masa wani Alhaji Zakari da yake nan qasan layinsu shima dai tate suke a Kasuwar kuma Aminin Alhaji Salen ne sosai Abdulwahab din yace tabbas ai ko jiya ma Alhaji Zakarin yaje duba Alhajin nasu, komai yazo da sauqi ma tunda abin na gida ne. Be bar gidan ba seda sukayi sallar Magriba, ya cikasu da Alkhairi Umaimah na kwance ya kirata a waya akan ze tafi. Seda ta rakashi har bakin motarsa ya tafi kafin ta koma ciki tana kallon Samarin da suka maida musu da qofar gida Majalisa duk saboda suka giftawarta ko wani yazo gurinta suyi rige rigen bata ta. Komeye ribarsu a soke aure oho. Zuwan Abdulwahab da kwana biyu waliyyansa sukayi waya akan zasu tambaya tunda har Abba sunyi waya da Alhajin nasu an qara tantanto juna. A daren ya kira Umaimah yake ce mata ta kira Abdulwahab suje suyi duk wasu gwaje gwaje daya kamata ace anyi tun kafin magana tayi qarfi base abu yazo ba kuka ba fata ba a samu wata matsala da zata iya hana auran saboda ita AS ce. Tana barin gurinsa ta kira Abdul din, abin dariya abin haushi wai shi a shekarunsa bema san Genotype dinsa ba, koda za'a daukeshi aiki kawai zuwa yayi aka masa medical report din ba tareda an gwadashi ba ta ringa masa masifa kamar wani danta, sune suke yaqi da cin hanci da Rashawa amma suna aikatawa ya ringa dariya kawai, washe gari kuwa da sassafe yazo suka tafi Asibitin dan jirgin yamma zebi ya tafi Abuja. Seda gabanta ya fadi da taga Asibitin da sukaje, Asibitin Dr Al'amin inda suke zuwa a gidan Khalil. Seda ya biya kudin duka gwaje gwajen da za'ayi musu, tana jinsa yana waya da wani likita da yace Abokinsa ne ya sanar masa baya Asibitin amma kafin su gama ze shigo. A office din Abokin nasa suka zauna bayan an dauki Jininsu, Abokin ya ringa kallonta, ita dai ba ta sanshi ba dan ko lokacin da take zuwa ba zaton suntaba haduwa gaba daya ma tunda sukaje Wata Nurse daya ta gani data sani a gurin duk sun canza ma'aikata amma shi wannan se wani kallon qurilla yake mata ya tambayi sunanta kuwa yayi sau uku harda wani gayyato wani Likita wai su gaisa da Abokinsa da Amaryarsu shima ya tasata a gaba yana kallo har seda ta tsargu ta ringa duba jikinta ko akwai abinda ta saka da ya ja suke kallo ta amma taga babu, Hijab ne dogo har qasa ta dora akan doguwar Rigar Atamfar data saka qafarta ta saka safa fuskarta da hannunta ne kadai a bude to me suke kallo a jikinta? A haka dai aka kawo musu sakamakon Gwajin komai yayi daidai sukayi sallama da Dr da daya Abokin gulmar da ya kirawo suka kama hanyar gida. Seda suka tsaya yayi mata siyayya sosai dukda tace bata so ya barshi amma ya kafe har yana cewa ai yanzu ta zama responsibility dinsa dole yayi mata. Be zauna ba yana sauketa ya tafi saboda be qarasa shirin tafiya ha kuma sun bata lokaci a Asibitin, ta shiga gida da tulin siyayyar da yayi mata da kuma sakamakon gwajin da sukayi, ta rigada ta makara itama dole ta haqura da fita aiki dan haka ta shige daki ta kwanta dan ta dan yi bacci kafin lokacin dora Abinci yayi. Abdulwahab ya isa gidansa ya tarar da matarsa Khadija cikin damuwar da tunda ta dawo daga gidansu jiya ya ganta a ciki. Dare yayi sanda ya dakkota dan haka be tsaya ya fahinci maganar da tazo masa da itan ba. Tana zaune akam gado inda ya fita ya barta ya sake tarar da ita da alama ma kuka tayi ya matsa kusa da ita yana taba wuyanta yace "Wai Dija baki da lafiya ne? Tun Jiya na lura dake gaba daya baki da walwala tunda kika dawo daga Sallari ko wani abun ne ya faru acan?" *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 88 A maimakon ta bashi amsa seta fashe masa da kuka tana cewa "Nidai Abban Fahimah maganar auranka, ban hanaka ba amma dan Allah banda ita ka auri koma wacecena yarda amma banda wannan Umaiman". Sakinta yayi ya miqe yana mata wani kallo kafin ya dauke kansa yana cewa "Kar muyi haka dake Dija, karki lalata mana farincikin mu muna zaman lafiya kin karbi maganar nan seda abu yazo gab zaki tayar da hankali, duk wanda ma ya zigaki yace kizo ki tayar mun da hankali I'm sorry to say ke zasu cuta dan ni babu abinda ze saka na canza ra'ayi tunda tuntuni munti ta da wajewa babu yanda za'ayi yanzu kuma kizo mun da wata magana gara ma ki sanyaya zuciyarki, gobe za'a kai kudi na gaya miki kuma sati takwas za'a saka" yana gama fada ya shiga zuba kayansa a akwati ganin bata hada masa ba dan ita take shirya masa kayan. Kuka ta ringayi duk yanda tayi qoqarin fahimtar dashi akan wacece Umaiman yayi biris yaqi fahimtarta, data ishe shi da cewar Kishine na bala'i da Umaiman yace mata ya sani, babu abinda ta boye masa kuma a hakan yaji ya gani ze aureta ya kwashi kayansa ya bar mata dakin dan gani yakeyi kawai taje gidansu ne sun zugota zata zo ta fara masa wani koke kokeb banza bayan komai da saninta kuma da yardarta yakeyi, daman yasan babu yanda za'ayi salin alin ayiwa mace kishiya ba tareda tayi tashin hankali ba. Saboda kukan nata da wuri ya bar mata gidan bayan ya jaddada mata aure babu fashi gara ma ta saki ranta taci gaba da sabgoginta kishiyar da ba gari daya ma zasu zauna ba to me ze dameta. Ita kuwa Khadija tashin hankalin data shiga bayan jiya taje gida yayarta Ummia dake zaman gida take sake tambayarta wadda Abban Fahiman ze aura dan tunda ta gaya mata sunan Yarinyar take tunanin kamar ta santa bata haqura ba kuwa seda ta binciko inda tasan Umaiman. Ta nunawa Khadijan hotonta tace tabbas itace. A tsakar gida ta zauna ta ringa basu labarin Umaimah da tijararta tun suna poly ta santa dan sun taba hada saurayi ma a lokacin da ta gano ta hada ita da saurayin tayi musu Tijara a Lecture hall ta dire tana basu labarin Upgraded haukan Umaimah da irin ta'asar da tayi aka sakota shekara bakwai kenan tana zawarci. Hankalin Khadija ya tashi matuqa dan ita irin mutanen nan ce da basa son damuwa, tun a daren taso Mijin nata ya saurareta amma yaqi, gashi yanzun ma yayi tafiyarsa har yana cewa yasan komai. Bata yarda da wannan ba dan a sanin da ta masa ko a social media ya jiyo labarin irin mata masu bala'in kishin nan sunyi abu ya ringa jimami kenan yana cewa ai babu dole a auransu baze dakko matar da zata zamar masa fitina kota lahantashi ba ta tabbatar yanda yake jida Injinsa idan yaji ta lahanta na wani babu abinda ze saka ya yarda ya aureta. Tunanin wanda zata gayawa maganar nan ya fahimceta ta shigayi qarshe ta yanke shawarar zuwa gidan Yayarsa ta gaya mata, ita ba ta kanta take ba Jihadi zatayo ta tabbata ko masifar ta tashi sakkowa kansa zata fara ruftawa kafin ita tunda shi ya kwasota can zata kashe shi a Abuja ta cuceta ta barta da marayun Yaya. Abdulwahab din na fita itama tayi wanka ta tafi gidan Yaya Suwaiba babbar Yayarsu Abdul din. Tana kuka ta gama zayyana mata komai dataji, Yaya Suwaiba tayi shiru tana jinta seda ta kai qarshe kafin ta sauke ajiyar zuciya tace "Yanzu ke Khadija ina kika jiyo wannan maganar kuma kin tabbatar da sahihancinta?" "A gurin Yaya Ummi, ta santa tare sukayi makaranta kuma shima dana fada masa cewa yayi yasan komai kuma a hakan ze aureta" Khadijan ta sake fada tana share hawaye se Yaya Suwaiba ta gyara zama tace "Toh nidai abinda zan fara ce miki shine kiyi haquri ki kuma bi komai a sannu. Kinsan namiji idan zeyi aure bayaji baya gani ke kuma duk abinda zaki fada yanzu za'a dauke shi a matsayin kishi kawai kuma tunda kince yasan komai kenan ba'a rufeshi ba kuma a hakan yaji ya gani ze aureta ke meye naki a ciki to tunda ma ba gari daya zaku zauna ba duk abinta ai iyakar kansa can zata tsaya ko?" "Wlh Aa Yaya Suwaiba dan bakiji labarinta bane shiyasa kike fadar haka. Ni ba kishi nakeyi ba hasalima da yardata ze qara aure amma ni ita wannan dince kawai bana so ya nemo wata ya aura amma banda ita" Khadija ta fada tana kuka, rarrashinta Yaya Suwaiban tayi tareda yi mata alqawarin zata kira Abdulwahab tayi masa magana sannan tace mata itama tayi haquri taci gaba da addu'a idan da Alkhairi a abin Allah ya zaunar dasu lafiya in anyi idan kuma babu Allah ya watsa al'amarin salin alin ba tareda bacin rai ba. Haka ta koma gida hankalinta ya gaza kwanciya. Harga Allah ita auransa be dameta ba wadda ze auro matan ce tashin hankalinta dan ta tsorata da labarin Umaimah dataji ita bata son damuwa a rayuwarta tana zaune lafiya baza'a dakko mata wadda zata tayar mata da hankali ba. Yaya Suwaiba kuwa kamar yanda ta mata alqawari ta kira qaninta ta gaya masa yanda sukayi da Khadijan, kai tsaye yace mata "Yaya ki rabu da ita bafa ita zata zauna mun da mata ba bare ta zabar mun wadda zan aura. Kawai halinku ne Mata da daman bakwa rasa qirqiro tashin hankali da zarar ance za'a kawo muku wata cikin gida na tabbatar ko ba Umaimah ba duk wadda ma na ce zan aura seta san abinda zata bullo dashi dan na fasa to plan dinta beyi aiki ba dan kafin tasan wacece Umaiman na rigata sani aure kuma babu fashi dan yanzu haka ma nasan su kawu na hanyar dawowa gida dan tun dazu sukaje kai sadaki" Yaya Suwaiba ta rasa abin ce masa, ta wani fannin yana da gaskiya ko Khadija bata fito ta nuna ba kowa yasan dole tana kishin Mijinta kuma zata iya riqar duk hujjar data samu dan ta kauda maganar auran amma kuma itama zancenta abin dubawa ne a irin yanda tace ta jiyo labarin Amaryar da abinda ya kashe mata aure to amma tunda ma'auri yaji ya gani su meye nasu ciki banda suyi fatan Alkhairi. Da taje gidansu ma tayiwa Hajiyarsu magana tana farawa ta katseta bata ma saurara taji qarshen bayanin ba tace babu ruwanta. Duk iyakar bincike Alhaji yayi yasan uban yarinyar nan basuda wani abin Ashasha tsatsonsu tsatsone me kyau da kowq zeso hada zuri'a dasu kuma magana ma ta qare tunda har an kai Sadaki an tsayar da ranar aure dan haka ta gayawa Khadijan idan zata kwantar da hankalinta ma tun wuri gara ta kwantar dan kishiya da kudinta ta siyota tunda tace ba zata bishi inda yake aiki ba ko bata da hurumi cikin maganar auransa daga haka zance ya mutu. A bangaren Amarya kuwa shiri sukeyi babu kama qafar yaro, dukda ita a sanyaye take komai. Gani takeyi kamar bada gaske ba wai zatayi aure ta rayu da wani Namiji daban ba Khalil ba se taga abin kamar mafarki da zata iya farkawa a kowanne lokaci taga ba gaskiya bane. Miliyan daya ya bata kudin lefe, Maman Asad tace ya turawa daman suka hada da tanadinta da kudin auran suka fara shirinsu dan bata da ko cokali na kaiwa daki kuma Abba bece musu komai ba haka Mama dan haka suka fara siyan abinda ya samu tunda bikin da saura kusan sati bakwai kafin nan dai dolr zasu magantu tunda dai ai ba zasu kaita babu kayan daki ba. Wani weekend su Bibi sukaje a nan suka samu labarin auran da Momyn nasu zatayi, Bibi ta fasa kuka, Mu'ayyad kansa da ba zatace ga alqibilarsa akan rabuqarta da Mahaifinsu ba ranar seda idonsa da jikinsa suka nuna rashin Jin dadin Al'amarin. Yayi shiru yana kallon Bibi dake rusa kuka kamar ance mata an saka ranar sarewa Umaiman kaine, a hankali cikin nutsuwarsa irin ta mahaifibsa ya kallu Umaiman yace "Momy bazaki haqura ki dawo gidanmu ba?" Ta zura masa ido na wani lokaci, shekarunsa goma sha hudu yana shirin cika ta sha biyar. Yana da nutsuwa da kaifin tunani da basira ta tabbatar da cewar koda ace sanda ta rabu da Khalil akwai yarinta a tattare dashi amma zuwa yanzu kwakwalwarsa ta gane komai daya faru dan haka boye masa ko bagarar da zancen babu abinda ya canza. Seta gyara zama ta kalli Bibi dake gamsheqar kuka tace "Ko kiyi shiru ko ki fita ki bamu guri". kukan ta rage dan yanzu ta fara kintsuwa tana jin magana shagwaba dai da sangarta wannan sedai idan bata samu dama ba dan yanda uban yake lelenta daukar kanta takeyi kamar wata Jiddah jaririyar wanwarsu. Umaimah ta kalli Mu'ayyad daya sunkuyar dakai qasa tun bayan da yayi mata magana tace "Mu'ayyad bani zanyi haquri ba, Dadynku nayiwa laifi shiya kamata yayi haquri ya yafemun ko badan na dawo gidanku naci gaba da zama ba Aa ina buqatar ya yafemun duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninmu. Ina so na bashi haquri amma na rasa ta hanyar da zanbi ya saurareni, idan na kirashi a waya bata shiga kullum sena tura masa da Text na ban haquri sama da shekara amma be taba maidamun da martani ba. Bana so na sakaku a ciki na qarawa kaina laifi a gurinsa amma inaga ta hakan ne kadai zan samu afuwa da sassauci a gurinsa. Idan ka koma gida yau ka tayani roqonsa kace masa ko minti daya ne ya bani dama na nemi yafiyarsa kota wayane ko bazece mun komai ba ya amsa wayata kawai hakan ma ya isheni". Shiru yayi yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "Idan ya haqura zaki dawo toh?" Bibi ta fada cikin kuka har sannan seta jata jikinta tana cewa "Ban sani ba Bibi, duk abinda Allah ya tsara mana ina fatan ya zama mana Alkhairi gaba daya a rayuwarmu. Koda ace na auri wani babu abinda ze canza zaku cigaba da rayuwa cikin walwala kamar yanda kukeyi yanzu kuma zaku cigaba da zuwa gurina ko?" "Nidai Momy kawai ki dawo gidanmu, shikenan mu se mu tashi Mamanmu da Babanmu basa tare nidai wlh kawai ki dawo" Bibin ta sake fashewa da kuka se Umaimah tayi murmushi tana janyeta daga jikinta tace "Ke ai matsalar kina girma amma tunaninki na nan kamar na yar baby, to idan kuma mutuwa nayi fa gana daya ya zakuyi?" "Toh Momy mutuwa ai daban munsan ba zaki dawo ba yanzu kuwa kina da rai. Wlh Dady yana sonki, ko jiya seda naga yana kallon hotonki ni nasan daman kece bakyaso ki koma gidanmu. Momy indai saboda Mamah ne bata da matsala, tana da kirki zaku zauna lafiya da ita dan Allah indai Dady yace ki dawo ki yarda kawai kinji" Mu'ayyad ya sake fada kamar shima ze saka mata kukan. Qirjinta ya ringa bugawa da qarfi jin da tayi yace wai Khalil yana sonta har yana kallon hotonta koda yake ba abin mamaki bane ta sani Khalil na sonta kamar yanda itama take Sonsa amma babu yanda suka iya da qaddara haka Allah ya nufa a tsakaninsu kuma itace sila. Be sake cewa komai ba itama tayi shiru, haka suka qarasa wunin ranar babu dadi. Zancen auran nata ya cirewa yaran karsashi ita kuma maganganunsu suka sake jefata a dimuwa suka qara sanyaya mata jiki matuqa. Suma gani sukeyi itace bata son zaman lafiya kuma taqi komawa gidansu ne saboda matar Babansu. Abinda ya qara sanyaya mata jiki qalau yanda Iman ko a qafarta zancen auran be shafeta ba uzurin gabata kawai ta ringayi. Daman haka take ita, babu wata shaquwa a tsakaninsu yanda take mu'amalantarta babu alamar ta dauketa matsayin uwa mahaifiya maganarta kullum Mamah kaza Mamah tayi kaza. Da akazo daukarsu kafin su tafi seda ta sake jaddadawa Mu'ayyad kan ya hadata da Dadyn nasu, tana matuqar son magana da Khalil din, bata so ta shiga sabuwar rayuwa da dakon haqqinsa ita ta sani ba zata samu nutsuwar da take fata ba. A daren ranar suna komawa gida Bibi bata iya jiran Khalil ya dawo gida ba ta dauki wayar Humaira ta kirashi dan tasan be zama lallai Yayannata ya fada masa saqon Momy ba. KHALIL Yana office yana qarasa wasu ayyuka besan magriba tayi ba seda kiran wayar ya shiga ya daga yaga lokaci, cikin muryar gajiya yayi sallama tare da ce mata "Afuwan Love, aikine ya riqeni amma gani nan tahowa yanzu in Allah ya yarda duk kewar tawace tasa kika kasa haqurin jira?" "Dady nice" muryar Bibi ta katseshi, seya dafe kansa, Allah yaso ba qata baranbaramar yayi ba. Cire wayar yayi da kunnensa yana qarasa hade takaddun gabansa dan yasan wayar Bibi ba qarewa take ba baze wuce qorafi bane an mata wani abun ba zata iya jiransa ya dawo ba zata kira a waya dan haka yace mata "Meya faru sweetheart har kun dawo daga gurin Momyn taku ne?" Kamar tana jira kawai tasa masa kuka,da sauri ya aje takaddun hannunsa ya dauki wayar ya mayar kunnensa, yanda take kukan harda shashsheqa ya bala'in daga masa hankali take ya fara hasashe hasashen meya faru? "Kiyi shiru gani nan zuwa gidan ok" yana gama fada ya kashe wayar ya zirata a Aljihu ya dauki abinda yake buqata badan ya gama aikin gabansa ba ya tafi gidan. A waje ma ya ajiye motar ya taka da qafa yana shiga ya tarar da Mu'ayyad zaune bakin qofar shiga falonsu ya rafka tagumi a fuskarsa zaka karanci damuwa sosai gabansa ya sake yankewa ya fadi, to meya faru ne? Mu'ayyad dinna ganinsa ya miqe tsaye amma ya kasa yin magana Khalil ya matsa kusa dashi ya kama hannunsa yana cewa "Wai meya same ku? wani abu akayi a can gidan ne?" "Dady.." Mu'ayyad din ya kira sunansa se kuma ya sunkuyar da kansa qasa ya kasa cigaba da magana Khalil ya zuba masa ido yana karantarsa, Mu'ayyad yarone me shiru shiru sosai sam bashida hayaniya ko kadan halinsa sak na takwaransa Mahaifinsu yana kuma da qoqarin shanye damuwa da wuya kaga ya furta fushi ko ya nuna a fuskarsa dan haka yasan yanzun dole da akwai wani abun daya faru. "Ina Bibi?" Ya tambayeshi swya bude baki kamar baya so yace "Tana ciki, kuka takeyi tun dazu taqi tayi shiru". "Me akayi mata take kuka kai kuma meya bata maka rai?" Khalil din ya sake jefa masa wata tambayar aeya kuma sunkuyar da kansa kafin ya dago kamar an fizgo maganar daga bakinsa yace "Momy ce zatayi aure, saura 4 weeks". Yanda kasan wanda ya harba da bindiga haka yaji har seda ya saka hannu ya dafe qirjinsa da yaji tamkar ze fado saboda razana da zancen Mu'ayyad din. "Aure" ya maimaita kalmar a fili Mu'ayyad ya daga masa kai kafin ya qara da cewa "Tace na roqeka ka amsa wayarta ko minti daya ne ka bata tana so kuyi magana". Tabbas yaji abinda yaron yake cewa amma kwakwalwarsa bata iya fassara masa ba, se kawai ya tura qofar ya shiga yana tafiya kamar wanda ya fito daga sahara saboda yanda wata irin kasala take bin qabobinsa tana riqe su. Humaira na tsaye gaban Dining tana gyara kwanuka yanda ya bude qofar yasa ta waiwaya ta kalleshi, daman tasan duk inda yake dole yana hanya tunda an taba yar gwal. Yanda taga fuskarsa da yanayin sanyin jikinsa yasa ta ajiye abinda takeyi ta nufeshi tana cewa "Lafiya kuwa?" Tayi saurin tareshi saboda tuntuben da yayi da jirgin Adil ya tafi kamar ze kifa qara yunqurawa yayi yana yin taku biyu ya sakeyin baya kamar wanda Jiri yake diba seta riqeshi a jikinta, yanda taji zuciyarsa na bugawa da qarfi ya saka ta ce masa "Ka zauna Dady bari na dakko Mayafina mu tafi Asibiti baka da lafiya" swya girgiza mata kai dan harshensa ya masa nauyi Mu'ayyad dai na tsaye a bayansu ya harde hannaye a qirji ya miqa masa hannu ya matso dakyar ya iya cewa "Ku kamani muje sama Jiri kawai nakeji nayi stressing kaina da yawa da nayi bacci zan dawo daidai". Badan ta yarda ba kawai dan ya kafe akan lafiyarsa qalau din suka kamshi zuwa saman saboda yanda jikinsa ya saki ba zata iya riqeshi ita kadai ba. Har kan Gado suka kaishi ya zauna ta fita da sauri ta dakko masa ruwa tana fita Bibi ta shiga da kukanta tana cewa "Dady wai Momy au...." "Shut up and get out" ya buga mata razananniyar tsawar data saka Humaira sakin Bottle din hannunta babu shiri ta toshe kunne, Bibin da yayiwa tsawar kuwa rikicewa tayi ta durqushe a gurin kukan data shigo dashi ya bace bat se rawa da jikinta ya dauka kamar mazari saboda tsoro. Kallonsu yayi gaba daya se kuma yaji wani iri a hankali yace "I'm sorry, banyi niyyar na tsorata ku ba. Ina buqatar hutu yanzu ku fita kawai kar wanda ya sake shigowa idan bani na buqata ba". Yana rufe baki Bibi ta fice da gudu har sannan jikinta rawa yakeyi dan tunda take Dadyn be taba daga mata murya balle yayi mata tsaya irin haka, Humaira ma fita tayi jiki a sanyaye a ranta tana tunanin to meya faru ne me ya saka Khalil din birkicewa haka? Kallon Mu'ayyad yayi dake tsaye ko gezau beyi ba har sannan hannayensa harde yana kallon Khalil din shima, wani abu me daci ya hadiye kafin ya bude baki da kyar yana kallonsa yace "Wa zata aura?" "Nima ban sani ba, tace ka kirata nasan zata gaya maka" ya bashi amsa seya daga masa kai kawai dan maganar qara harzuqo masa zuciya takeyi. Ya ringa juyi akan gado yama rasa tunanin me zeyi, aure? Umaimah? Abubuwan da suka ringa masa yawo a kwakwalwa kenan. Har gurin qarfe goma ya gagara qulla komai, kamar ya kirata yanda ta buqata to me zece mata ko me zata ce masa ma idan ya kiratan? Badai aure zatayi ba taje tayi shi meye nasa a ciki? Yana kwance yana malelekuwa, tunawa da yayi da ko sallar Magriba beyi ba gashi har anyi Isha tuni ya sakashi miqewa dole yana dafa bango saboda ciwon da kansa yake masa ga jiri ya shiga bandaki. Seda ya watsa ruwa kafin ya rama sallolinsa, yana zaune ya janyo wayarsa dake kan gado dan tun yana sallah take kawo haske saboda a silent take, missed calls din Humaira ya gani seya miqe jikinsa a matuqar sanyaya ya fita daga dakin. Tana zaune a falo gaba daya ta firgice itama baya zaton ko abinci taci ya qarasa kusa da ita ya zauna murya babu amo yace "Ina yaran?" "Sunyi bacci" ta bashi amsa tana kallonsa seya kallo agogon dake jikin bango, goma harta gota ashe ba qaramin lokaci ya bata a kwance ba. Janta yayi jikinsa yana cewa "Kuyi haquri dazu na tsorata ku raina ne a bace ita kuma tazo tana yi mun kuka" "Amma ka tsoratata sosai, dakyar tayi bacci tana ta kuka ni kaina kukan ne kawai yaqi zuwar mun amma tunzu nake so nayi, waye ya bata maka rai " da yaja ka huce akan mu?" Humaira ta fada tana dora kanta a qirjinsa, yanda zyciyarsa take bugawa ya sakata dagowa ta kalleshi ta sake cewa "Kaji bugun zuciyarka kuwa? Dan Allah ka gaya mun meya sameka?" Murmushi yayi yana maida kanta qirjinsa yace "Babu abinda ya sameni, wani abu ne dai yake damuna amma na roqi Allah nasan ze yaye mun" "Tunda kace Allah ka gama komai, amma idan ba zakaje Asibiti ba ka kira azo gida a dubaka dan wannan bugun zuciyar ya wuce normal ga jikinka ma yayi zafi" "Humaira, na gaya miki lafiyata qalau da nayi bacci koma menene ze dena, ki dena damun kanki" ya fada a tausashe dole tayi masa shiru kusan minti biyar ta miqe ya kalleta yana tambayar ina zataje tace Abinci zata kawo masa "Naqoshi, bazan iya ci ba" ya bata amsa kai tsaye, seta dauki dankwalinta dake ajiye tana cewa "Gara naje na gayawa Hajiya kawai qila ita idan ta maka magana zakaji ya zakace mun lafiyarka qalau bayan gashi nan jikinka duk ya nuna baka da lafiya" "Saboda kawai nace bazanci abinci ba shine zaki gayawa Hajiya? To ki kawo mun Tea, cikina ya cushe bazan iya cin wani abu me nauyi ba" ya fada yana kwanciya. Ta kawo masa Tea din da cake harda maganin ciwon kai dayace yana damunsa yana sha ya koma daki ya kwanta, damuwar data shiga ta sakashi dole ya saisaita kansa amma abin yafi qarfinsa, kafin safiya zazzabin gaske ya rufeshi da ciwon kai me tsanani sannan bugun zuciyarsa ya qaru sosai har qirjinsa yana dagawa. Duk yanda Humaira tayi dashi akan su tafi Asibiti yaqi, yasha paracetamol kawai yaci gaba da kwanciya a cewarsa stress ne daya samu hutu ze warware nan kusa qasan ransa Allah kadai yasan irin jinyar da yakeyi. Idan ya tuna wai Umaimah zatayi aure zata zama mallakin wani bashi ba se yaji kamar yayita kwala ihu. Hajiya da taji shi shiru tun dare be shiga ba ga safiya tayi har gurin goma nan ba babu labarinsa ta taka dakyar saboda jiki daya motsa mata itama kwana biyu taje bangaren nasu dan ta duba ko lafiya ta saba yaran ma kafin su fita makaranta duk zasu shiga yau kuwa babu wanda ya leqata. A Kitchen ta tarar da Hunaira na hada masa faten dankali dan yaqi cin komai da sukayi na kari yace shi yake so, ta gaida Hajiyar, yanda ta ganta sukuku ya sakata tambayar lafiya take idon Humairan ya kawo ruwa tana gaya mata Khalil bashida lafiya tun jiya kuma yaqi yaje Asibiti. Hajiya ta ringa masa fada yanda taga jikin nasa dole ya tashi badan yaso ba suka tafi Asibitin ruwa aka fara daura masa kafin sauran gwaje gwaje ya biyo baya Likita yace musu da Malaria yar kadan se damuwa itace ta haddasa masa bugawar qirji da ciwon kan. Ranar a Asibiti suka wuni, Hajiya ta sakashi gaba da tambayar meyake damunsa da har yake neman ya kwantar dashi ciwo amma ya kafe akan babu komai shi ba damuwa bace ayyukane da suka masa yawa kwana biyu dan Anwar baya nan shine kawai gajiyace, badan ta yarda ba ta rabu dashi sedan likitan yace kar su ringa matsa masa su barshi ya samu wadataccen hutu tukunna. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* Page 89 A gida da suka koma yanda taga yaran na dararewa musamman Bibi yar gaban goshinsa amma ta kasa ko zuwa kusa dashi ta maqale jikin kujera yasa Hajiyan ta sake shan jinin jikinta ta kuma gasgata zarginta dan taji qishin qishin din zancen auran Umaimah ta tabbata maganar tazo kunnensa kenan tunda jiya sunje kenan shine dalilin ciwon nasa. Bata ce masa komai ba ta daiyi masa gargadin rage tunani da kuma shan magani yadaiji abinda likita yace. Seda yayi sati a kwance dukda yaji sauqi amma jinyar zuciyarsa bata warke ba irin damuwar da gidansa gaba daya ta shiga ya sakashi qarfafa kansa dole ya koma walwalarsa amma duk sanda ya tuna zancen Umaimah zatayi aure se qirjinsa ya buga idan a tsaye yake seya zauna da addu'a da komai ya samu nutsuwarsa ta daidaita, yana so ya kirata, yana so yayi magana da ita amma yana tsoron abinda hakan ze haifar. Baya so rauninsa yayi yawa harya kasa daurewa, ya rigada yayiwa kansa alqawarin rabuwa da ita ta har abada ya tabbata kuma a yanda take ji a zuciyarsa muddin ya hadu da ita komai ze kwance masa yasan baze iya tsallakewa tarkon Sonta ba. Haka yaci gaba da lissafin kwanakin da suka rage ta zama matar waninsa, a tsayin lokaci yayi rama da kana ganinsa zaka fahimta amma ya fake da cewar aiki ne, waya ya siyawa Bibi da qaton Makeup kit da tace tana so zata koya tuntuni a matsayin ban haqurin tsawar da ya mata data saka take gudunsa tun lokacin, yanda ne tada zancen Momynsu ba suma sunyi hankali babu Wanda ya kuma masa maganar amma fa kana kallonsu suma kasan basuda walwala kamar baya tun Humaira na damuwa harta zuba musa ido kawai dan ta kasa gane menene musabbabin damuwarsu gaba daya, tsakaninta dasu Addu'a akan koma menene Allah ya shiga ciki ya yaye musu. UMAIMAH Tun tana saka ran kiran Khalil harta cire taci gaba da kaiwa Allah kukanta kawai tana cigaba da roqon gafararsa. A bangaren shirye shiryen biki tuni sunyi nisa, wannan karon ma Anty ta dage dayi mata jiqe jiqe da tsume tsume, ita kam ta rasa yanda zata misalta karamci irin na Antyn, idan da ace ta kasance me dogon tsinkaye ada da bata kyamaci kishiya har haka ba, ya kamata ace Antyn ta zame mata kyakykyawan misali da zesa ta saki zuciyarta akan dukma wadda zatazo ta tarar da ita amma ta gagara yin hakan sema ya zamana ita ta ringa jin zafin kishin Antyn a maimakon Mama da suka hada Miji daya da ita. Sati hudu suka shude wanda ya rage saura sati hudu cif auransu da Abdulwahab kamar yanda aka saka rana. Lafiya lau suke waya tareda duk wasu shirye shiryensu dan hatta gidan da zata zauna a Abujan ana can anata aikin gyara da fenti, ya gaya mata kuma yana da kusan komai na amfani dan haka kartace zata yi wasu kayan daki idan taje duk abinda babu ko taga beyi mata ba daga baya s su canzadata gayawa Maman Asad tace babu damuwa dukda haka akwai abubuwan da ya kamata ta siya kamar kayan Kitchen dasu Bedsheets da sauran kayan qyaleqyale na gida amma dai zasu jira saura sati daya biki dayace za'aje a ga gurin in yaso daga nan se su qarasa shawarar abinda ya kamata suyi. Da suka gayawa Mama cewa tayi duk yanda sukayi daidai ne dan bikinsu ne se Anty da take tayasu shirye shiryen. Sunyi waya da Abdul din ranar Alhamis ya sanar mata Juma'a ze shigo Kano, tun tafiyarsa bezo ba irin yana kuma yana daga dalilan da suka shi qara aure saboda zamansa yafi yawa acan ita kuma Khadija ta kafe akan ba zata iya zaman Abujan ba daya rasa dalilinta na hakan. Shiri sosai Umaimah ta ringayi na tarbarsa. Maman Asad bata gari Qanwar Mijinta ta haihu ta tafi suna Jigawa kuma se Lahadi zata dawo dan haka a nan gidansu zata tarbeshi. Yanda ta kasa zaune tana ta hidimar hada masa abubuwan motsa baki tun ana gobe ze dawo din yasa Anty sakata gaba da tsokana, Mama dai nata ido idan Anty ta sakota a maganar sedai tayi murmushi tace sunfi kusa a zuciyarta kuwa kullum cikin godewa Allah takeyi da Al'amuran suke zuwa a sauqaqe, taji matuqar dadin yanda Umaiman ta ajiye komai ta karbi zabin da Allah yayi mata. Auran nan da zatayi ba qaramin faranta mata yayi ba sannan ga Mijin data samu yaron kirki a kullum addu'arta kenan kar Allah ya jarabci Umaiman da abubuwan data aikata a baya gashi Addu'arta ta karbu tana kuma fatan kar ta basu kunya ta zauna lafiya da Mijinta karya zamana tuban muzuru tayi idan taje tajo dadi halinta na baya ya dawo dukda tana mata kyakykyawan zaton tuba tayi na gaske. Ranar Juma'ar da Abdulwahab ze dawo bata fita aiki tun safe ta shiga qarasa shirye shiryen da batayi ba. Ya sanar mata jirgin safe ze biyo kuma a unguwarsu ma zeyi sallar Juma'a dan yayi missing dinta sosai yana so yazo ya ganta shiyasa ta dage qarfe daya ta gama komai Yasir tasa ya gyara mata falon baqin Abba tun safe bayan tayi wanka ta dauki garwashi ta zuba turaren wuta daga wanda akayi mata na auren takai falon wani abu ya ringa taso mata data tuna shekarun baya sanda Khalil yake zuwa wajenta. Ta saka turaren ta qara gyara gurin kafin ta kulle ta koma daki. Seda tayi sallar Azahar kafinta shiga rangada masa kwalliya, tunda suka fara haduwa da Hijab yake ganinta da safa dan haka ta qudurce yau zatayi masa kwalliya saboda kamar yanda Hausawa sukace wai ka gaida me gaisheka, Abdul din ya cancanci duk wata kulawa da tarairaya daga gareta saboda yanda yake ji da ita zaka rantse be taba son wata Mace ba se a kanta. Ta shirya tsaf ta haye gado tana zaman jiran wayarsa yace mata gashi a waje dan an sakko daga masallacin unguwar tuni batayi aune ba se ji tayi ana kiran sallar data tabbatar da La'asarce, agogo ta kalla uku da rabi da minti takwas mamakin ma dadewarta a zaune haka tayi seta miqe jiki a sabule tana tunanin to ina ya tsaya kuma be kirata ya gaya mata ba. Wayarsa ta shiga kira sedai aka matar Mtn ta sanar mata a kashe take, mamaki ya qara kamata, sunyi waya gurin sha daya yana sake jaddada mata da cewar a unguwarsu fa zeyi sallar juma'a to kardai wani abun ne ya faru dashi? Da wannan zulumin tayi sallar La'asar ta fito Mama na gyara zogalen da zatayi miyar dare Anty na daka mata gyada a turmi suka kalleta Mama tace "Har baqon naki ya tafi ne?" "Ai bana jin yazo ma ko dan ga Zobon da aka masa can a Fridge din dakina bata dauka ba fasa zuwa da ranar yayi?" Anty ta fada seta ja kujera ta zauna kawai zuciyarta na tsinkewa ta rasa me zatace musu ma. "Kinga ana magana tayi wa mutane banza kamar bataji" Mama ta sake fada seta dago idonta ya fara tara hawaye tace "Befazo ba Mama kuma na kira wayarsa a kashe" se Mama ta harareta tace "Toh shine zakiyi kuka? Daman banda son zuciya ma mutum ya dawo daga wani gurin tsahon lokaci baze zauna da iyalinsa ba seya kwaso qafa ya taho gurin gaibu ita ta gidan ce miki tayi bata iya girki da tarairayar miji ba kenan da zata sako shi ya taho daga dawowarsa" Anty tayi dariya tana cewa "Toh Allah dai yasa lafiya amma ko dazu ina ji yana jaddada mata a unguwar nan zeyi salla keep nga ko indai ya fito din da doke zezo kuma dai ai ba zata hanshi fita sallar Juma'a bako sedai idan wani gurin yayi kiyita gwada wayar tasa dai dan wannan dabge gaskiya baya wuce shi ba" "Idan kuma rabon mune ai shikenan" Mama ta sake fada yana miqewa Umaimah dai ta zabga tagumi tana sake gwada kiran Abdulwahab se ta shiga amma har wayar ta qaraci ringin be daga ba tana katsewa ya turo mata da saqo akan ze kirata. "Kinga ta shiga Anty amma be daga ba ya turo mun text wai ze kirani" ta fada tana nunawa Anty wayar ta kalla tana cewa "Yawwa to ai haka yafi qila wani abun yakeyi ze kirakin inya gama. Shiru shiru be kirata ba har aka kira magriba lokacin ta gama cire rai da zuwansa dan qila dai ta bakin Mama ko Matarsa ce ta hanshi fita ya kashe waya wannan tunanin ya bata mata rai, kumallon mata ya motsa ta idar da sallar ta jiyo Yasir a tsakar gida da Abokinsa ta kwala masa kira yana shiga tace yaje ya kwaso kayan Abincin data ajiye a sitting room, Nuratu data zo gidan ta taso daga aiki tace "Kice rabo na ne ya rantse da kamar karna biyo" Umaimah tayi mata banza ta nemi plastic robobi ta debi komai tace ta huta girki idan ta koma daman daga ita se Dr yaran na gidan Kakanninsu duk Umaimah najin su suna buduri da abincin da tun jiya take wahalar shiryawa bata ko fito daga dakin ba bare ta kulasu. Wasa wasa har gari ya waye be kirata ba kamar yanda yace kuma idan ta kirashi wayar zatayita ringing harta katse baze dauka ba tun tana daukar abin a matsayin wulaqanci har ya koma bata tsoro, to meya faru kuma? Ita tayi masa wani abun ko kuma daga bangarensa ne wani abu ya faru daya saka baya amsa kiran nata kuma shi be kirata ba? Weekend ya qare dakyar ta iya fita aiki saboda yanda damuwar Abdulwahab take neman kwantar da ita. An cinye sati guda cur be kirata ba kuma idan ta kira ita baya dauka Alhalin tana ganin sa online yanayin status idan ta masa magana ze bude amma baya bata amsa abinya dameta qibar data farayi duk ta zube a satin saboda ko abincin kirki bata iyaci, lissafin saura sati uku biki akeyi amma Ango ya shareta to meya faru? Tana da buqatar qarin bayani a gurinsa idan ma wani abun tayi masa kamata yayi ya fada mata bawai ta hanyar wannan horon ba. Mama kanta ta shiga damuwa tunda ta shaida mata bata samunsa a waya idan ta kira baya dagawa har seda ta yiwa Abba maganar a cewarta ko ze tuntubi Alhaji Zakari yaji lafiya kar aje wani abun ne ya sameshi basu sani ba yace mata babu komai, ya tabbatar idan da wata damuwa kafin ma su tuntuba zasu sanar dasu su zuba ido koma menene Allah ya shiga ciki kawai. Ranar Juma'ar data kama sati daya cif daya kamata yazo din da daddare tana kwance a daki Abba ya kirata a waya yace taje falonsa ta sameshi ta zura Hijabinta ta tafi tana shiga gabanta ya fadi saboda yanda ta taraddasu jigum jigum ta samu gefe ta zauna tana gaishe da Baba Abdullahi da Baba Liman. Baba Liman din ne yayi magana cikin sanyi yace mata "Yanzu waliyyan Abdulwahabu suka tashi daga nan kuma sunzo bamu haquri ne akan cewar Dansu ya janye daga neman auranki bisa wasu dalilai sannan sunce mu baki haquri a madadinsa yace yana jin nauyinki dalilin dayasa ya gaza daukar wayarki kenan dan haka kiyi haquri ki kuma yi addu'a Allah yasa hakan ya zame miki Alkhairi daman Allah yayi ba mijinki bane shidin kinga babu yanda za'ayi" "Yo haqurin me zaka bata kuma ai daman duk wanda ya siyi rariya yasan zata zubda ruwan mugun halinta da abinda ta aikata a baya sune suka koma kunnensu har yasa suka hana dansu auranta ba wani abu ba daman kuma ai za'a rina, a zamanin nan ka shuka Alkhairi ma yaka qare ballantana kayiwa kanka mugun tabo? Ai keda aure dai yanzu sedai ki samu Dattijo irinmu wanda bashida me sakashi ko ya hanshi amma badai Matashi me jini a jika ba dan babu dan da uwarsa take raye da zataji abinda kikayiwa Halilu da uwarsa ta bari a auro ki cikin Ahalinsu" Baba Abdullahi ya amshe, kanta na qasa wani qululu daya taso mata tunda Baba Liman ya fara magana ya tokare mata wuya, sam ita maganganun Baba Abdullahi basu bata mata rai ba dan tuni ta haddacesu sedai idan basu haduba cinmutunchi se wanda ya manta ne baya mata. Abba ne ya dakatar dashi jin ze cigaba da tijarar tasa yace mata "Kije, karki saka damuwa a zuciyarki kinji kullum muna yi muku Addu'a da fatan Alkhairi a rayuwa komai ya faru da sanin Allah kinji" "Toh Abba" ta fada muryarta na rawa kafin ta miqe ta fita daga falon. Bata tsammaci zataji ciwon fasa auranta da Abdulwahab yayi har haka ba, ita bata ma san tana sonsa ba se yanzu da wannan abun ya faru ranar kwana tayi tana sallah tana Addu'a tana kuka gwanin tausayi. Meyasa Abdulwahab zeyi mata haka? Dayasan ba auranta zeyi ba meyasa ze bata mata lokaci har ya bari ta sakashi a ranta meye ribarsa yanzu akan abinda yayi mata kenan ya bata lokacin sa da dukiyarsa a banza alhalin ba auranta zeyi ba duk a na me? Hankalinta be qara tashi ba seda magana ta shiga yawo a unguwa, batayi mamakin yanda akayi zancen auranta da fasuwarsa ya bazu ba tunda da Alhaji Zakari akayi komai tasan kuma ko a bakin matansa maganar zata fita amma abinda aka ringa yawo dashi ana jifanta dashi yayi mugun tabata da har seda ta kwanta jinyar data qarawa magauta hujjar yamadidi da ita a gari cewa akeyi tayi cikin shege abinda yasa Abdulwahab ya fasa auranta kenan, yanke jiki tayi ta fadi lokacin da Yasir ya shigo yana maida musu da abinda yaji a Unguwa ana fada, da yammane, Masu zaman banzan unguwa sun kafa majalissu aka fita da ita Asibiti ranga ranga tuni labari ya chanza salo cewar gata can tasha maganin zubar da cikin an tafi Asibiti da ita harda masu cewar Jini har qofar gida sun ma gani da idonsu kai maganganu dai kala kala masu fadar dama sun sani kullum da motar da take zuwa gurinta aikin da akace tana zuwa ma duk qaryace kawai fakewa take da yawon ta zubar ba wani abu ba. Bata taba zaton haka sharri yake da ciwo ba se daya fado kanta, tayi kuka babu iyaka har idanunta suka soye zuciyarta ta qeqashe, ta ringa tuna Hadiza ita da ba iya unguwa ba Nigeria gaba daya babu inda hoton batancinta be zaga ba har yau bata fitar da ran hotonta na kan yanar gizo da batancin da tayi mata ashe haka taji? Tabbas irin Hadiza basu da yawa a duniya, ta yafe mata abinda tayi mata gashi Allah ya saka mata cikin ruwan sanyi ya jarabceta da abinda ta jefeta dashi, idanta kalli irin quncin da Abba da Mama suka shiga akan wannan sabon Al'amari hankalinta na matuqar tashi batayi musu Adalci ba. A kullum burinsu su faranta mata sannan tayi musu sakayya da bacin rai. Ita ta fita zakka a yayan da suka haifa Maza da mata babu wanda za'a daga a kawo wani aibunsa se take kullm cikin janyo musu magana take. A wannan karon seda akayi dagaske kafin nutsuwarta ta daidaita, ciwon damuwa ya nemi kamata ta dena fita dan duk inda tayi nunata akeyi ana cewa tayi cikin shege ba ita ba Mama kanta seda ta dena zuwa taro a unguwar saboda yanda ake zundenta duk inda ta shiga saboda Umaiman, ance tana zaune shekara bakwai Ashe karuwancinta kawai takeyi se yanzu da ta samu Miji Asirinta ya tonu, Addu'a da tawakkali yasa suka cinye wannan jarabawar har masu surutu sukayi suka gaji rayuwa taci gaba da tafiya a yanda take. Yanda Abdulwahab be nemeta ba itama bata sake nemansa dan taji dalilinsa na fasa auranta ba, tasan dai koma menene yana da alaqa da rayuwarta ta baya haka ta sake fawwalawa Allah komai taci gaba da aikinta zancen aure ya sake fice mata daga rai saboda duk wanda zezo badan Allah bane se kuma Dattijai irin su Baba Abdullahin masu mata uku da yaya bila Adadin. Maman da take matsa mata da zancen auran ma ta haqura tana mata addu'a dan haka ta aje komai ta rungumi aikinta da sana'ar siyar da turaran wuta data fara dalilin na auran Abdulwahab da tayi, suna da yawan gaske sunfi qarfin tace zata ajiye ta ringa amfani dasu ita ba Gida ba ba Miji ba Maman Asad ce ta bata shawarar siyo container ta zuba su gwada tallatawa dan Turaruka ne masu kyau da Inganci tayi ai kuwa Allah ya saka mata albarka a sana'ar sosai take samun Alkhairi a ciki. Rabuwarsu da Abdulwahab da kusan wata shida kamar daga sama Allah ya sake hadata da Alhaji Kabir taje kasuwar Sabon gari siyo Mai da sabulun wanka suka hadu a shagonsa tayi siyayyar babban dan kasuwane dan shagunan sa sun kai biyar a cikin kasuwar yana ganin Umaiman ya rikice nan duniya yace shi yaga mata, daya daga cikin yaransa yace ai ya santa unguwarsu daya, shi ya bashi labarin abinda ya sani game da Umaiman Alhaji Kabir yace yaji ya gani dan irinta yaie ta nemi tuntuni abinda ya hanshi qara aure kenan. Shiya kaishi gurin Umaiman, Matarsa daya da yara biyu babban dansa Sa'an Iman ne. Shekarun sa talatin da takwas ya bata shekara uku kenan Nasibin rayuwa daya samu da kuma kamala ta yan kasuwa yasa ake ganinsa kamar wani babba ita kuwa tunda ya sanar mata da shekarunsa ta rainashi, gurinta shekaru uku sunyi kadan tsakananinta da Mijin da zata aura musamman a matsayin da take yanzu. BTa bashi fuska ba dan tun a zuwan farko ta nuna masa cewar yayi haquri ita ba aurene a gabanta ba amma ya nace. Kiran waya kamar maye haka idan bezo yau ba gobe zezo tun tana shareshi harta haqura ta fara kulashi musamman da kowa yake ce mata tunda tana addu'a ta saurareshi ta yuwu Alkhairin da kowa yake roqar mata ne yazo. Abba da kansa yayi mata magana saboda nacin Alhaji kabir din yayi yawa kuma a yanayinsa mutumin kirki ne ga ladabi idan ya bazo babbar rigar nan tasa har Yasir girma yake bashi autan gidan gaba daya wadannan abubuwan suka saka dole ta fara sakar masa fuska tana qoqarin ganin sun fahimci juna a sannu har maganar aure tayi qarfi a tsakaninsu a wannan karon bata maimaita kuskuren da tayi lokacin Abdulwahab ba. Da kanta ta bashi labarin duk abinda ya faru a baya cikin tsantsar nadama da dana sanin da fuskarta ta gaza boyewa, Mamaki ta kusa kasheta sanda yake ce mata yaji komai hatta da sharrin ciki da aka mata ya sani kuma shi wadannan dalilai ma suka qara masa sonta har yake son auran nata a maimakon taji dadi se abin ya shiga bata tsoro. Ya za'ayi yace shi komai da tayi burgeshi yayi hakan nema yasa ze aureta anya qalau yake kuwa? Ko ita a karan kanta tasan halintavna baya bame kyau bane kuma idan da ace wata ce take da wannan Halin wanda ta sani ze aureta zata hana. Addu'a ta sake tsanantawa a kan lamarin, babu wani shiri da tayi wannan karon dan gani ta ringayi kamar shima auran bame yuwuwa bane yan uwansa zasu hana kamar yanda daga baya ta samu labari a bakin Hadiza cewar Hajiyarsu Abdulwahab dince ta hanashi auranta bayan uwargidan Alhaji Zakari taje qafa da qafa ta bata labarin gaskiya da qarya daya faru itace kuma ta kafa masa sharadin ko sake waiwayar Umaiman yayi bata yafe masa ba, wata biyu kenan daya auri diyar Alhaji Zakarin yanzu ita bata ma san shi ta aura ba seda Hadizan take gaya mata shiyasa take taka tsan tsan da Kabir kar shima iyayensa suji wani abu daga baya suce zasu hanashi auranta sedai kamar yanda akace Al'amarin aure da Mutuwa daya suke idan lokaci yayi babu fashi se gashi cikin hukuncin ubangiji ranar wata Juma'a aka daura auran Umaiman da Kabir auran da yazowa mutane da yawa a bazata irinsu Khalil dan ba'asan da labarinsa yinsa ba. Al'amarin ya dakeshi matuqa da har ya kasa jurewa seda kwanta Asibiti magashiyyan kowa ya gane halin da yake ciki. Beji neman auran ba kamar na wancan karon da daga baya yaji ance an fasa se kawai ji yayi wai ta daura aure badan a bakin Hajiya yaji ba da tabbas qaryatawa zeyi. Ya dinga rama a tsaye abinci se an masa dole zeci ya dena fita aiki na kusan sati biyu tun Humaira na fushi tana ganin abun kamar cin fuska harta ajiye komai ta fahimci yana da buqatar tallafi, ita shaidace akan son da yakewa Umaimah amma tambayar da takewa kanta me ya hanashi dawo da ita duk tsahon lokacin nan se yanzu da tayi aure ze nemi kashe kansa a tsaye da tunani? Hajiya kanta ta shiga damuwa, ta ringa ce masa "Me yasa Babana, kasan kana son dawo da matarka duk tsahon lokacin nan meyasa baka maido ta ba?" "Hajiya ni bani da ra'ayin dawo da ita" ya bata amsa cike da dacin zuciya, Jalilah datazo dubashi tayi caraf tace "Qarya kakeyi kuma sedai so ya kashe ka wlh badai ka sake zama da Umaimahba mara zuciya kawai wato kai nan da lambu lambu kayi kana jira lokaci ya qara turawa ka maidota ko to ko bayan ran Hajiya baka isa ba balle yanzu da take a raye" "Kiyi mun shiru Jalilah ni na gaya miki haka?" Hajiyar ta daka mata tsawa kafinta juya kan Khalil daya rintse ido saboda yanda kansa yake sarawa idan ana magana da qarfi tace "Kayi qwauran baki Babana da kuma ni bana adawa da dawowar Matarka, idanhar dan abinda tayi mun ne wlh na dade da yafe mata tuntuni idan da ka nuna mun kana ra'ayin dawo da ita tuni dana shige maka gaba kuma ko yanzu zanci gaba dayi maka addu'a idan har da Alkhairi a zamanku Allah ya kawo dalilin da zata dawo gareka" A ransa ya amsa da "Amin" Jalila kuwa a fili ta furta "In sha Allahu babu, ba zata sake dawowa zuri'armu ba data samu ta auru dakyar taje can ta qarata muda ita sedai dan zuri'ar dake tsakani amma da babu abinda ze sake hadamu". Sati biyu aka saka tariyar Umaiman, ana saura kwana hudu ta tare yaje gidansu cikin matuqar qarfin hali. Ba Umaimah ba hatta su Mama sunyi matuqar mamakin ganin Khalil din da kuma yanayinsa daya nuna baya jin dadi har seda Mama ta tambayeshi yayi murmushi kawai yace mata rashin lafiya yayi ya kasa dauke idonsa daga kan Umaimah data sha gyaran Amarare tayi bulbul tana sheqi daya tuna matar wani ce a yanzu seya sadda kansa qasa wani abu me daci da maiqo yana taso masa. Shirun da Khalil din yayi ya saka Mama tashi ta basu guri, da alama zuwannata ne bayan tsayin shekaru yau ya waiwayi Umaiman kenan qila daman irin wannan lokacin yake jira. *HALIN KISHI* *NA MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *FIKRA WRITERS ASSOCIATON* *(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)* *DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH SWT DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI, INA FATAN ALLAH YASA MU'AMFANA DA DARUSSAN DA SUKE CIKI, INDA MUKA KUSKURE UBANGIJI KA YAFE MU DARAJAR ANNABI DA ALQU'ANI* 🤲🏼🤲🏼 *AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GAREKU MASOYAN RUBUTUN UMMU-MAHEER, UBANGIJI YA SOKU, YA JIBANCI LAMURANKU, NAGODE DA TARIN QAUNAR DA KUKA NUNAMUN KUNE QARFIN GUIWATA KUNA DOMINKU NAKEYI. WANDA NA BATAWA A TSAYIN LOKACIN DA NAKE RUBUTUN NAN INA NEMAN AFUWARSU, A BANGARENA NA YAFE DUK WADDA TA ZAGENI NA YAFE MATA 🥲🥲 ALLAH YA YAFE MANA BAKI DAYA SE MUN SAKE HADUWA A SABON LITTAFI NA DA ZEZO IDAN ALLAH YA YARDA* *MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER* *Last page* Bayan Mama ta fita sun kwashi kusan minti biyar kafin ya nisa a hankali ya kira sunanta, tsigar jikinta suka zuba dalilin saukar muryarsa da lafazin da yayi amfani dashi gurin kiran sunanta se ta shiga a'uziyya a zuciyarta tana kiran sunayen Allah. Cikin sanyi ya shiga ce mata "Umaimah, da farko zan fara da tayaki murna bisa auran da kika daura, Allah ya sanya Alkhairi ya kuma kade duk wata fitina da abin qi a gidan aurenki ya sanya Albarka da farin ciki a rayuwarku sannan se abu na biyu ina roqon a tsayin zaman mu idan nayi miki wani abu na kuskure ki yafe mun" kuka ta fashe dashi jin abinda ya fada, idan ba dai son ya qara mata laifi ba wace magana ce kuma wai ta yafe masa ita me yayi mata sedai idan so yake yace baze yafe mata ba kawai yafi ya fito kai tsaye akan wannan alayenda yakeyi. "Ki dena kuka dan Allah, ko ba zaki iya yafe mun ba?" Ya fada muryarsa a karye seta dago da sauri ta kalleshi, idanunta sun gaza boye tarin qaunarsa da kewarsa dake cinta ya kauda nasa idon daga kallonta yana tunatar da kansa matar wani ce cikin kukan tace "Bakayi mun komai ba Khalil, Allah ne shaida ka kasance Mijin kwarai kuma uba na gari gurin Yayansa, ni na zalunceka kuma naga sakayyar hakan akaina haqqinka yana ta dawainiya dani, ka tausayamun ka yafe mun ko zan samu nutsuwa a sabuwar rayuwar da zan shiga" ta fada cikin tsananin kuka. Yaqe yayi yadan kalleta yace "Na dade da yafe miki Umaimah, abinda kikayi mun tsakanina dake ban riqeki ba, daga randa Hajiya ta furta ta yafe duk abinda kikayi mata nima na yafe fushin tabata da kikayi" "Hajiya ta yafe mun?" Ta tambayeshi cikin tsananin mamaki seya daga mata kai cike da tabbatarwa yace "Ta yafe miki tuni, Hajiya bata kwanciya bacci da fushin kowa a ranta kuma muma akan haka ta horemu mu ringa yafiya akan duk abinda aka mana. Babu abinda riqon wani a zuciyarka ze qareka dashi a rayuwa sabanin haka idan ka yafe se kaima Allah ya dubeka ya yafe maka naka kurakuren da suke tsakaninka dashi". Qirjinta ya ringa bugawa, wani sabon nauyi da kunyarsu ya sake lullubeta a ranta ta ringa godewa Allah da bebi ta halinta ba ya zabarwa Yayanta tsatso na kwarai, sukam sunada karamci gashi su rabauta da zuciyar da ba kowa Allah yayiwa Arziqin irinta ba ta yafiya. A hankali cikin rarrabewar harshe tace "Toh toh me yasa duk tsahon lokacin nan tunda ka yafe mun amma ka kasa waiwayata?" se yayi murmushi kawai ba tareda yace mata komai ba har ta fitar da ran samun amsarsa taji yace "Kina so kisan meya hanani waiwayarki tsahon lokacin nan?" Ya fada yana kallon idonta seta girgiza masa kai alamar Eh ta sauke kanta qasa "Saboda ina sonki, bana iya riqe kaina idan ina tare dake. Zuciyata bata taba fushi dake idan har nazo inda kike tabbas nasan zan karaya na kasa cika alqawarin dana daukarwa kaina na haqura dake har Abada Umaimah". Zabura tayi ta dago ta kalleshi saboda abinda ya fada, hawayen da ta samu suka tsaya suka sake balle mata cikin tsananin kuka tace masa "Saboda baka yafemun bako?" "Na yafe miki amma bazan miki qarya ba duk sanda na kalleki nasan zan ringa tuna sanda kika tsaya gabana kika zagi Hajiyata" ya fada idanunsa suna sake canza kala da alamar abinda ya fada din ya sosa masa rai. Umaimah ta duqar da kanta qasa, da tana da damar maido da baya data canza abubuwa da dama cikin rayuwarta, Khalil yaci gaba da cewa "bana so mu sake komawa rayuwar aure tare son da nake miki yakai girman da zan iya jure komai da zakiyi mun naji tsoron kar soyayyata ta halakar damu gaba daya kar kawaicina ya kaimu wuta saboda Allah babu ruwansa shiyasa na zabi haqura da son zuciyata na barki badan bana sonki ba ko na dena sonki ba kuma dan bana son ci gaba da zaman aure dake ba sedan kawai hakan shine maslaha a rayuwarmu gaba daya kullum nayi sallah sena roqi ubangiji ya zaba mun mafi Alkhairi a cikin komai na rayuwata duk abinda na rasa kuma ina fatan yasa nayi tawakkali ya bani dangana kuma Alhamdulillah, ina cikin farin ciki tattare da musanyar da yayi mun kullum cikin gode masa nake kema ina miki fatan ki samu farin ciki sama da wanda nake ciki a yanzu zanci gaba da Addu'a yanda na rasaki a duniya, Allah ubangiji ya hadamu qarqashin inuwa daya a Aljanna ya dawo mun dake a matsayin MATATA a inda babu DAMUWA babu BAQIN CIKI babu KISHI babu SAKI babu MUTUWA balle SAKIN AURE". Kuka take tamkar ranta ze fita shikansa dauriya ce kawai irin tasa amma da zeyi kukan yasan ze samu sauqin radadin da yake ciki. Ya ajiye mata wata Leda fara mara girma sosai sannan ya ciro wata Envelope daga Aljihunsa ya dora akai yana cewa "Kiyi haquri da wannan akwai ayyukan da nakeyi duk na zuba kudade kuma abin yazo babu shiri, Naji Hajiya tace zatazo gobe may be su taho tareda yara dukda yanzun ma nacewa Mu'ayyad yazo ya rakoni yaqi da alama kishi yake sosai fa" ya fada yana dan murmushi da bekai zuciya ba, bata dago ba kuma bata bar kukan ba, ya sake cewa "Ki dena kukan nan haka kar Angonki yaci tarata yace na saka masa kuka Amarya, yawwa sannan dan Allah banda tsaki banda muguda baki mazan yanzu saurin hannune dasu be zama lallai yana da haquri iri na ba kar azo ana daddoke mana ke" dukda kukan da take seda tayi dariya dan yanda yayi maganar tasa yace mata "Ko kefa, bari na tashi naje dan ban gayawa Babyna inda zanje ba kar ta jini shiru" ya miqe itama ta miqe tabi bayansa maganar Babynsa na sukar zuciyarta. Sauri Mama tayi ta bar bakin qofar da take tsaye, badan bata yarda dasu ba sedai shedan baya raina qofa ko yaya take. khalil da Umaiman masoya ne da ko Makaho ya shafa yasan suna qaunar Junansu kuma shedan na matuqar son irin lokutan nan na rauni dan ya shigar da lamarinsa. Har qasa ya durqusa yayiwa Mama sallama yana sake yi mata Allah ya sanya Alkhairi tace baze jira Abinci ba yace Aa, Anty suna gidan Amarya yin jere yayi musu sallama ya tafi Umaimah daki ta wuce ta kife a gado taci gaba da Gamsheqar kuka, Mama ta duba Envelope din daya bari, Daloline a ciki bata san ko nawa bane dan ba sanin kansu tayi ba amma suna da yawa ta rufe envelope din ta zazzage kayan cikin ledar, wani dan Akwati ta gani me kyau ta bude shi Zobuna manya ta gani guda biyu da Awarwaro suma guda biyu na gold se sauran takracen fashion Dan kunnaye, zobe Agogo, Ribbon turaruka wasu yan qanana na Mai kusan guda biyar ba'a budeau bama se Hijabi guda daya dogo da carbi ta ringa mamakin wadannan kuma daga ina? Wata farar takadda ta gani ta dauka yayi rubutu kamar haka "Kayanki da suka rage a dakina, kudi kuma na kayan furnitures dinki ne da Abba ya hana a diba" ina miki fatan Alkhairi". Jikin Maman yayi sanyi laqwas, duk yana ajiye da kayanta tsahon lokaci kenan ita kam bata san wane kalar So Khalil yakewa Umaimah ba, komai idan ya faru tabbas akwai hikima me yawa tattare da faruwarsa ta tabbatar a irin wannan zazzafar soyayyar zasu iya halaka gaba daya ma. Da Abba ya dawo ta dauki kayan gaba daya ta kai masa ya ringa juya kai yana cewa "Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi a tsakaninsu, haqurin da sukayi Allah yasa ya zame musu kaffara. Se bayan Isha yan jere suka dawo jiki a sabule, Umaimah na daki har sannan tasha kuka ta haqura tana ta jan carbi Naziyya ta shiga ta sameta tana cewa "Tab wannan gida naku Umaimah se ace Allah ya zaunar lafiya, kinga kishiyar taki kuwa? Aba kamar Kazar mayu amma masifar dake cikinta tafi girman giwa. Hana mu shiga gidan tayi fa tasa aka kulle get, seda megidan yazo da kansa ashe shima ba kwallo bane tantirin dan Tijarane in gaya miki suka ringa rashin mutunchi a tsakar gida ya zageta ta zageshi mudai kamar mu juyo Mama Asiya tace ai ba zancen juyowa haka muka shiga muka jera abinda ya sawwaqa. Keda meya hana kice ya kama miki gida tunda kinsan yanda tsarin gidan nasa yake?" Kallon Naziyyan ta ringayi dan sam ta gagara gane inda kalamanta suka dosa, zancen matarsa be dameta na amma shidin da take cewa sunyi zage zage a tsakar gida a gabansu ya daure mata kai matuqa hartace "Kabir din?" "Shifa, ai bakiga abin mamaki ba, tube kaya yayi daga shi se vest da gajeran wando yace su daku har yana ce mata kar dan ta ganmu ta dauka ze raga mata mu ba baqin da zeji kunya bane kai ai yau nikan naga abinda ya isheni. Ba wannan bama, Daki biyu ne fa ya baki daya sama daya qasa, falonku daya haka kitchen, kujeru dai daman ba'a rigada an dakko ba da su Fridge da cooker suna inda aka siya mukace a barsu idan kun daidaita kin samu gurin ajiyesu seki dakko, an dai saka gadaje ragowar duk abinda be shiga ba su Kayan kitchen da sauran tarkace suna gidan Hajiyayye tun muna can da muka kira Mama tace ayi abinda ya samu wanda be samu guri ba mu kai can mu ajiye". Jikin Umaimah ya ninka da sanyaya zuciyarta ta ringa bugawa da jin sabon Al'amari, duk zancen gida da wani waye be dameta ba kamar abinda Kabir din yayi kenan kurane da fatar akuya yazo mata da suffar Kamala ashe kwankwararran Dan tasha ne tunda Namijin da ze tube a gaban dangin matar da bata rigada ta tare a gidansa bama yace zeyi dambe da matarsa ta gida ai ko ya isa Executive Dan tasha. Tsabar rudewar da tayi bata ko iya fitowa daga daki ba tana jin su a tsajar gida suna ta maida zance, Kabir din ya ringa kiranta amma taqi daga wayar, to me zata ce masa ko me zece masa ita kam wannan aure ma bata ga yuwuwarsa ba gaskiya ba abinda ta shiryawa ba kenan aure take so tayi na Ibada ko babu jin dadi tana buqatar kwanciyar hankali. Da Asuba tana idar da sallah ta tafi qofar dakin Abba ta tsaya jiransa dan daren jiyan har mafarki ta ringayi wai ana kaita sun hadu shida matar sun mata dukan tsiya. Abba ya gama saurarar qorafin data zo dashi kafin yayi murmushi yace "Tun jiya Antynku ta gaya mun komai kuma nayi takaici matuqa da jin abinda ya faru amma ya muka iya da hukuncin ubangiji? Kiyi haquri bawa baya gujewa qaddararsa abinda zan gaya miki kawai kiji tsoron Allah ki saka a ranki kinyi aure dan ibadah dama kowanne aure da kalar qalubalensa a yanzu ne zakiyi zaman aure na haqiqa dan a baya kinyi rayuwa ne irin wadda ke kika tsarawa kanki dan haka kiyi haquri" ta ringa kuka, kenan Abba yana nufin a haka zataje ta tare gidan Kabir din kome? Allah ma ya sani ba zata iya ba, ita daman ba wani sonsa take ba lallantana ace taje tayi haquri ta tafi falon Mama ta dasa mata kukan dukda Al'amarin itama ya shammaceta amma haka ta dake ta maida mata magana tamkar ta Abban tana gaya mata qaddararta ce dan haka tayi haquri se taga qila sanadiyyarta ya shiryu su dena Tijarar da akace sunayi daga shi har Matar. Ranar ko gyaran jikin da take bata iya zuwa ba ba, cike take da zullumi, wato dukda ta samu afuwar wadanda ta zalunta a baya haqqin aure data wulaqanta na nan yana bibiyarta. "Allah karka jarabceni da gidan aurena na tuba nayi nadama ubangiji ka karbi tubana ka sassautamun" ta fada tana tsananin kuka. A karo na bar katai Kabir ya sake kiran wayarta bata dauka ba tana tsaka da kukan sejin sallamatsa tayi a tsakar gida ta zabura ta leqa danta tabbatar shidinne kuwa yau ko Shaddar da yake sakowa babu T-shirt ce da wandon Jins ya tsuke abinda kamar wani qaramin yaro takaici ya kawo mata wuya, haskensa da da take gani ya dusashe cike da takaici ta kalleshi se wani doka mata murmushi yake yana cewa "Na kasa samun nutsuwa tun jiya nake kiran wayarki bakya dauka lafiya? Me yasami idonki haka suka kumbura?" A maimakon ta bashi amsa se ta sake fashewa da wani kukan takaicin kawai ta juya daki, yayi kamar ze biya suka hada ido da Mama da tun sallamarsa ta fito itama seya sosa kai itama cike da takaici tace masa "Shiga mana" ta juya daki abinta tuququn baqin ciki na taso mata. Da tayi haquri a inda Allah ya ajiyeta ai da bahakaba, tana zaune cikin rufin Asiri da wadata ta raina ni'imar da ubangiji yayi mata daman idan baka gode masa ba zaka godewa Azabarsa. Umaimah kuwa tana shiga daki Kabir ya bita duk ya rikice yana tambayarta me akayi mata "Dan Allah ki gaya mun in ba so kike nima na miki kukan ba" ya fada yana matsawa kusa da ita tayi saurin direwa daga gadon tana jifanta da wani mugun kallo tace "Karka kuskura ka tabani, gara da Allah yasa na gane wanene kai tun kafin na shiga gidanka dan haka yanzu base anjima ba saki na zakayi dan bazan iya zama da Tantiri mara nutsuwa irinka ba" "Ikon Allah" Kabir din ya fada yana gyara zama kafin ya tuntsure da wata dariya kamar sabon shigan hauka yana cewa "Tantiri na tantiriya" yasake kwashewa da dariya seta tsaya kawai tana kallonsa yayi me isarsa kafin yasha kunu yana jifanta da wani kallon raini yace "Sa'arki daya a cikin gidanku nake da wlh sena gurje miki baki akan zagina da kikayi kuma bari na fada miki tun a nan ni ba lusari bane irin sakaran Mijinki na baya da kike zagi kamar Almajirinki ya shanye kallon da bae gamsheni ba idan kika mun casaki zanyi ahto na san jiya yan gidanku sun gaya miki yanda naci uwar Abida to basuga komai ba dan haka duk wani gigi da rashin mutunchinki ki haqa rami a nan ki binneshi karki ce zaki gidana dashi. Ke banda ma ina neman wadda zata ringa cimun uwar Abida dan itama ba kyalle bace kina zaton zan aureki ne bayan duk labaranki da nake dasu? Bafa wani sonki nake can can ba ni inaga ma Asiri kika mun wlh amma babu komai ai na taimaka miki na rufa miki asiri dan wlh badan niba sedai ki qare rayuwarki a gidan nan babu me tsautsayin da ze kwasheki dan haka tun wuri ki shiga hankalinki jibi qarfe hudun yamma za'a kaiki ki shirya in ma kika bata mun rai ba zaki tare ba anan zan barki kiyi ta zama kuma wlh na sake kira baki daga mun waya ba se na miki rashin mutunchi". Kamar mutum mutumi haka ta zama har ya gama Tijararsa ya fita ya bar mata dakin, ta zube akan guiwoyinta hannu akai a fili ta furta "Na shiga uku ni Umaimah" tana sake fashewa da sabon kuka, da wannan zata zauna wato pretending ya qare ya fito mata a zahirinsa kenan shikenan rayuwarta ta shiga lahaula ita kam. Da yammacin ranar Hajiya tazo kamar yanda Khalil ya gaya mata Umaimah ta kasa daga kai ta kalleta ita kuwa ko a jikinta ta ringa mata addu'a da saka albarka tareda nasihohin da seda suka saka Mama ta zubda hawaye. Cikin dattako ta ringa tariyo mata kuskurenta na baya tana fada mata yanda zata kaucewa sake maimaita su, tsadaddun Food flask ta kawo mata saiti biyu da Jug shima me shegen kyau se wasu kaya a Leda da tace Habiba ce tace akawo mata taso ta biyo Hajiyar, "Kin san abokiyar takun saqarki na gidan ita ta hanata zuwa amma tace na karbo mata number ki zatazo miki har gida idan kin tare" Dan Allah Hajiya ku yafemun, ki roqar mun suma su yafe mun abinda nayi musu" Umaiman tayi magana a karon farko dan tunda ta gaida Hajiyar take kuka, Hajiya ta jata jikinta tana cewa "Sau nawa zan maimaita miki Umaimah mukam baki mana komai ha idan ma da akwai mun yafe, Allah ya rigada ya qaddaro duk abubuwan da suka faru bamu da yanda zamuyi kuma na godewa Allah da hakan yasa kika gane kuskurenki kuma kika gyara daman haka ake son mumini na kwarai idan yayi kuskure ya gane ya tuba ya nemi yafiyar ubangiji sannan ya guji sake maimaita abun a gaba, Allah yayi muku Albarka ya cigaba da yi muku jagora a rayuwa in sha Allahu zanzo idan kin tare naga dakinki kinji" haka ta ringa lallaba Umaiman har tayi shiru ta bar kukan, ta jima sosai a gida har seda tayi sallar Magriba Abba ya dawo suka gaisa kafin Driver daya kawota yake jiranta ya dauketa suka tafi. Washe gari haka aka tattarata aka kai gidan KB da take ji kamar kurkuku aka kaita. Basu tarar da matar gidan ba dan muqullin qofa ma yaronsa ya bawo ya kawo musu daga Kasuwa se bayan sun shiga sannan wasu Mata suka zo a matsayin yan uwansa suna ta bada haqurin rashin zuwa dauko Amarya wai wadanda aka saka su kaisu ne basu je da wuri ba sun tafi kuma ya kirasu yace ai har an kawo Amarya ma. Ita dai tana lafe akan gado ta kasa yin koda kwakwkwaran motsi tunin wannan sabuqar rayuwa data shigo kawai takeyi seda yan rakiyar tata sukayi Magriba kafin kowacce ta kama gabanta aka barta ita kadai tsuru kamar mayya a gida. Ta gaji da zaman daki ta fito tana leqa falon, qato ne ya kuma tsaru dakyau dakuna uku ne a ciki da a zaton ta daya na matar gidan daya kuma qila na yara ga qofar kitchen nan da take hango ciki saboda qofar irin ta glass ce batayi gigin shiga ba ta koma daki taci gaba da jan carbi har akayi Isha babu Ango babu matar gida tana zaune har ta fara gyangyadi sannan taji motsin ana taba Get ta zabura ta miqe, Windon dakinta a cikin compound din yake dan haka ta leqa, motar Kb ta gani ya fito yaci uwar babbar riga kamar gaske ya ringa kwaso ledoji yana shiga dasu falo harya gama kafin ya shiga dakin lokacin ta koma bakin gado ta zauna. Bakinsa a washe kamar wani soko ya nufeta yana cewa "Sorry Amaryata mun barki ke kadai, go slow aka samu yau a hanyar Kasuwa na fito tun kafin Magriba amma babu hanya kuma na tsaya na siyo miki kazar Amarci" ya qarasa yana wani kashe mata ido daya. Takaici kamar ta kwada masa mari seta juya fuska tareda jan tsaki ya tsaya cak a inda yake murmushin fuskarsa yana bacewa yace "Na miki uzurin yau kadai amma ki sake mun tsaki ki gani, dallah malama tashi an ma fasa tarairayar taki zanje nayi wanka kafin na fito ki shirya mun Abinci a Dining kuma ki dumama komai kafin k ajiye". "Wato auran yaro dai beyi ba" ta fada a zuciyarta kafin ta miqe tabi bayansa dan ta tabbata bayan Tijara ga danyan kai a tattare dashi shiyasa har yake gwada yar qashi da matarsa to ita dai na zata bashi wannan qofar ba, umarni dai in ya bata zatabi tunda qinyin kamar ta sabawa Allah ne baya ga haka ita ba zama ya kawota gidansa ba gara ta koma taci gaba da zaman gidansu ya fiye mata alkhairi akan wannan rayuwar takurar da ake neman jefata. Seda ta dumama komai kamar yanda yace ta shirya masa akan Dining din nama ne sunfi kala biyar harda wani farfesu, shi ta bari a microwave din ta koma daki kafin ya sakko, tana shiga taji yana kwala mata kira kamar ze tashi gidan ta koma yana tsaye daga kan Matakalar bene Matar gidan da bata san sanda ta dawo ba na tsaye daga bakin qofarta ita kuma wata busashishiyar mace fara tas kamar Aljana ta harde hannaye tana kallon Mijin shi kuma ya kalli Umaimah data fito ta tsaya tana kallonsu gaba daya "Kin gama Baby" ya fada yana mata wannan murmushin nasa data tsana a yanzu seta daga masa kai ta fara tafiya hanyar kitchen din tana cewa "Saura pepper soup din bari na dakko" "Kan kutumar uban nan Kabiru, kitchen dina kace ta shiga tayi maka girki ko Yaya" Abida ta fada har sannan tana tsaye a bakin qofarta, Umaimah ta waiwaya ta kalleta sau daya ta qarasa shigewa kitchen din, shi kuwa kan Dining ya wuce abinsa ya zauna yana duba abubuwan data ajiye ta fito ta bowl gadan gadan Abida tayi kanta ta kauce mata saboda abinda ke hannunta da zafi bata ma zata da niyya tayi kan nata ba seda taga ta sake durfafota babu bata lokaci ta dauke Umaiman da mari abinda ya sakata sakin kwanon naman ya fadi qasa ya fashe ya watsar musu a qafafu musammab Abidan dan a kan qafarta ma ya fadi ta fasa ihu tana cewa "Kika qona ni, wlh bazan yarda ba se kin gane kurenki yau a gidan nan" Marin da Kb ya kwasheta dashi ya sakat sakin Umaimah babu shiri se kuma ta juya kansa ta shiga zaginsa kamar bama gujiya Abu kamar wasa se gani tayi ya tube jallabiyya damben da taji labarin sunyi se gashi akan idonta kici kici suka kama kokawa ya sameta ya ringa tamola da ita yana bugawa da qasa amma saboda qarfin zuciya irin nata bakinta be mutu ba ta ringa zaginsa, ita dai taja gefe tana kallon ikon Allah, ya gama casa Abida ta bakinsa da fada kafin ya kalleta a fusace yace "Ku gyara gurin, kuma wlh se anyi lissafi kun biyani kudina ai ke kinsan ban gaji Asara ba daga kudin namana harna plate din tunda bada kudin uban wata a cikin ku na siya ba" ya wuce fuu ya dirarwa Namansa ya hau ci Umaimah kam taga abinda ya girmi tunaninta yau, wannan bala'i har ina ko awa biyar cikakkiya batayi a gidan ba. Duk dukan dayawa matar nan ga mamakinta haka ta tashi ta dakko tsintsiya se ita kuna ta hado ruwan mopping suka gyara gurin kamar yanda yace Abidan na kuka tace "Wlh se kin san kin qona ni kuma kinsa ya dakeni" ta shige dakinta seya kalli Umaimah data rakata da kallo yana cewa "Zo nan sweetheart bar yar abu ta kazan uba yanda kika san Jaka in ba'a daketa ba bata gane komai, zo kici kazarki da Allah karta bata mana daren Amarcin mu dan na fara chaji kinsan hadi me kyau aka mun saboda na gurji Amarci son raina". Badan kar itama ta karbi rabon dukan ba ta qarasa amam ta gagara cin komai se madara kofi daya itana dan ya matsa mata ne, yana tsaye ta wanke komai daya bata ta adana sauran abubuwan kafin ta shiga dakinta nan ma ya kafa ya tsare wai ta shirya su hau sama. Yanda tsarin qasan yake haka saman shima yake harda kitchen da komai dagani daman tsarin mata biyu akayi tunma daga yanda Matakalar take acan gefe za'a iya yin katanga a cireta daga falon a fasa qofa ta waje amma saboda baqar mugunta beji ze iya yin hakan ba. Ya bude mata dakinta na saman suka shiga, gadon da aka saka harya fi na Qasan kyau, babu batun sallah balle aje ka wata soyayya ko tarairayar dayace daman ya fasayi ya afka mata, ta ringa kuka kamar zata hadiyi zuciya ta mutu, shekara takwas rabonta da abun gashi a yanayin da yazo mata shiyasa taji jiki matuqa shi kuwa sambatu harda na banza fadi yake babu Asararre irin Mijin daya sakota shi kam idan da wannan dadin ko uwarsa zata kashe ai ya yafe mata baqin cikin maganganun nasa suka qara qume mata zuciya, be barymta tayi bacci ba sannan tsabar bala'i tun Asuba ya tasheta wai taje ta hada masa abin kari da wuri ze fita ta rasa me zata ce masa tafiya kanta dakyar takeyi kamar wata yarinya haka ta sakko qasan ta zauna a kitchen din ta ringa kuka na rashin mafita. Ta dumama masa Ragowar Namansa ta dafa Tea harta gama komai ta ajiye bataji motsin matar gidan ba jikinta yayi rau da zazzabi tana gama ajewa ta shige daki ta kwanta se ganin mutum tayi akanta wai ze qara na safe ba yanda ta iya haka yayi mata yanda yaga dama ya tashi ya fita, ta tuna zamanin da ana tarairayarta ana mata soyayya me kashe zuciya amma seta ga dama take yarda dashi se gashi daha daren jiya zuwa yau ta dandana kudarta a gun wanda ta tabbata idan ta masa gardama se an hada da tiyata za'a gyarata dan a haka ma ji take kamar ta samu matsala. Daze fita ya leqa daki ya ajiye mata dubu biyu kudin cefane, ta rasa abin cewa jin yana fada mata abinda zata dafa kuma za'a kai masa kasuwa qarfe dayan rana ake zuwa daukar Abincin ita dai ta amsa masa da toh tana addu'a a ranta Allah ya kawo mata dauki yana fita baccin wahala ya yi awon gaba da ita. Saukar sanyi kamar na ruwa ruwa taji a jikinta cikin baccin, tayi juyi tana tunanin ko mafarki ne dan a zahiri babu abinda ze kawo ruwa dakin saboda na farko ba lokacin damuna bane kuma ko hakanne a qasa take ba sama ba balle ace Silin ne yake yoyo dukda ma POP ne dasu, jin fa da gaske ruwan yake zubowa dan gaba daya jikinta ya jiqe yasa ta miqe da sauri tana dube dube, hancinta ya shaqo mata warin wani abu kamar fetur, bata qarasa tunanin ba ta miqe da qarfin gaske ta bude qofa saboda hango Abida da tayi tsaye a jikin window da Ashana a hannunta tana qoqarin qyastawa tana fita daga dakin kuwa ta cilla Ashanar taje wuta ta kama dakin balbal ko ina. Yanda kasan wadda aka jonawa lantarki haka jikinta ya ringa rawa ta fice daga falon sukaci karo da Abidar na shigowa ita kuma "Au baki qone ba? Yanzu kuwa zan qarasa ki wlh dan nayi alqawarin sena kasheki sannan shima ya dawo nabi dare na qona shi" ta fada tana qoqarin kama Umaimah ta maida ita dakin, qarfin da bata san ina ta samoshi ba ta tattara ta hankadeta gefe babu batun mayafi balle aje ga takalmi ta fita daga gidan da gudun tsiya tana kuka. Tundaga daga cikin Darmanawa seda taje round about din cout road a qasa kafin ta shiga tare Adaidaita dakyar ta samu wani ya dauketa dan dallon mahaukaciya suka ringa mata ganin yanayin data fito. Su Mama na tsakar gida ana tattara kayan Gara da za'a kai mata da yamma ta fada musu kamar jifa suka miqe gaba daya a rikice suna tambayarta lafiya? Kuka ta fasa ta gagara cewa komai, yanayinta da rawar da jikinta yake ya saka Mama cewa au rabu da ita tukunna, Anty tace "Nifa warin fetur nakeji ku duba ko inji ne yake zuba" Cikin kuka tace "Nice nake warin fetur, matarsa ce zata qonani, tana can ta kunnawa dakin ma wuta" ta sake rushewa da kuka, yau kam taga masifa qarara harda bala'i. To ashe ita qaramar yar jagaliya ce manyanta na inda suka. Bayan Isha Kabir yaje gidan saboda kiran da Abba ya masa, dama yana kasuwa maqocinsa ya kirashi akan gidansa ya kama da wuta ya taho hankali a tashe Allah yasa an kashe wutar kuma da yake gini zamani ne iya dakin ta ci babu abinda aka fitar a ciki komai ya zama toka. A bakin yan unguwar yaji sunga fitar Umaimah da gudu Abida kuma ta fita a mota daga baya ya ringa sauke ajiyar zuciya tunda Allah yasa babu kowa a cikinsu amma tabbas ko sama da qass zata hade babu abinda ze hanashi cin kan uwar Abida dan ya tabbatar ita ta kunna masa wuta. Abba beja doguwar magana ba yace masa ayi haquri kawai da auran nan ya sawwaqe mata tunda ga yanda Al'amira suka fara kasancewa, kamar yanda ta fada badan Allah ya farkar da ita ba da yanzu qata magana ake ta daban dan haka kafin azo ana batacciya kowa ya haqura kawai. Tsabar iya makirci harda kuka yana durqusawa a qasa akan shi yana sonta baze iya sakinta ba Abida kuma ze dauki mataki akanta bazata qara kwatanta abinda tayi ba Abba yace shi duk wannan be shafeshi ba ya sakar masa yarsa kawai, aka kada aka raya yace shifa besan zance ba daga qarshe ma ya tashi ya bar musu gidan yana jaddada wlh baze sake taba zama da ita yanzu ya fara dan ta masa yanda yake so. Haka taci gaba da zama a gida cikin tsammanin ze aiko mata da takardarta dan har iyayensa Abba ya samu sukace su basu da ta cewa shine ma'auri tunda yana son matarsa ayi haquri kawai a koma tunda yace zeyiwa tufkar hanci. Watanta daya a gidan daga zazzabi, ciwon kai se Amai ana zuwa Asibiti ciki, hankalin Umaimah idan yayi dubu ya tashi ta ringa kuka tana tumami Mama kanta batayi farin ciki da wannan ciki ba a halin da ake nema a yakice ubansa Abba ko ya ringa ce musu kun gani ko duk abinda kaga ya faru da dalili yanzu ina za'a kai wannan rabon. Da kansa ya kira Kabir din ya gaya masa ya ringa murna a ranar se gashi a gidan, Umaimah na kwance tasha kuka ta godewa Allah se ganinsa tayi kawai a dakin ta tashi dakyar ya ringa mata murmushi yana cewa "Sannu Baby, kinga yanda kika rame kuwa da kina gidana da tare zamuyi rainon cikin nan ai" ya ringa mata soki burutsu har ya gaji ya tafi, shikenan ya maida gidan kullum se yaje baya kunyar kowa yake zuba musu iskanci son ransa shi yakeyi Umaimah kejin takaici a haka Abba yace ta haqura ta koma kawai kodan wannan rabon bayan sun zauna anyi yarjejeniya ya kuma yarda ze raba musu mahalli ita zata koma sama gaba daya kamar yanda daman tsarin gidan yake. Wannan yasa ta samu yar nutsuwa amma ba gaba daya ba tunda dai Abida na gidan bayan ubanta ya biya kudin Asarar da tayi masa dan hatta gadon daya qone seda suka biya yace shi be gaji Asara ba kuma baze sake taba itama bata nemi sakin ba dan son abinta take a hakan suke zaune kamar auran Bariki ana doke doke da zage zage. Umaimah ta koma gidan Kabir taci gaba da rainon ciki ga bala'in sa da kullum cikin neman sauqi a gurin Allah take. Dan Kutumar uban data dade tana laqawa Khalil ta aura kuma tana ganinta ganin idonta. Ya hanata aiki, kasuwancin ma badai a shigo gidansa a siya ba dan baqi ko yan uwanta ne zasu zo se an sanar masa idan ba haka ba ranar babu zaman lafiya haka itama ba zata fita ba seda kwakwkwaran dalili kuma shi ze kaita ko ya hadata da Driver, kudi kuwa idan ya bata seya bi diddigin komai yaji yanda akayi dasu kuma kamar yanda ya fada be gaji asara ba ko abinci kika dafa yayi yawa se kinsan yanda zakiyi dashi kika bata masa abu kuw abiya zakiyi babu abinda ya shalleshi, bala'in Kabir da Jarabar Matarsa da bata da buri sena ayi tashin hankali suka hadu suka tasota a gaba ga ciki me dan banzan laulayi a wata shida da auran idan ka ganta se ta baka tausayi. Dole ta haqura ta saki ranta da irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki ta nemi hanyoyin samar wa kanta farin ciki da nutsuwa ta hanyar lazumtar Karatun Alqur'ani, istigfari da kallon shirye shirye da zasu ringa debe mata kewa wani lokacin takan taba karatun littattafan hausa Wanda bayan farawarta ta samu darussa sosai a ciki, ta samu hanyoyin warware matsaloli da yawa tsakanin ta da Kabir dan ta karanta blabaran hutsayen mutane irinsa da yanda ake tafiyar dasu kuma Alhamdulillah idan ta gwada dabarun tana ganin ci gaba dukda me hali baya fasawa amma darajar son da yake mata da kulawar da take qoqarin bashi tasa abubuwa da yawa sun sauqaqa tana iyakar qoqari gurin kiyaye duk abinda ze kawo sabani har yayi mata tijarar tasa musamman daman abinda yafi hado su batun Yammatansa da yake waya dasu cikin gidan duk sanda yaga dama tana ganin ai cin fuska ne idan tayi magana ranar ko cin mutunci se wanda ya manta dole ta tattara shi ta watsar ta fuskanci rayuwar ta, duk abinda yafi qarfinta kuma seta barwa Allah taci gaba da kai masa kokenta. Seda ta haihu sannan yaranta sukaje gidan ta samu Muhammad Sabir kayan barka Tuli Humaira da sukaje tare ta kai mata da kudi kuma wai inaji Dadynsu ta ringa kallon Humairan da baka buqatar a gaya maka irin kwanciyar hankali da walwalar da take ciki wanda ribar haquri ya kawo mata. Bata san Khalil ne ya kawo su ba seda zasu tafi ta rako su har qasa, Humairan na Murmushi tace mata "Ko nayi masa magana ya leqo ku gaisa tunda kin sakko?" Gabanta ya fadi, amma ta daure tace mata toh. Ta fita babu jimawa suka shiga tare da Khalil daya qara zama wani Hamshaqi dashi suka gaisa ya sakeyi mata barka bata ga wani abu bayan qaunar matarsa dake gabansa a tattare dashi ba. Har a ranta taji dadi kuma tayi masa fatan Alkhairi, ta tabbata da ita dashi kowa ya samu kalar sakamakon daya dace da rayuwarsa. Kwananta Arba'in da biyar da haihuwar Sabir Allah yayiwa Abbansu rasuwa cikin dare sugar sa ya tashi da hawan jini duk lokaci daya, kafin ma su isa Asibiti a mota rai yayi halinsa. Fadar kalar tashin hankalin da suka tsinci kansu a ciki bata baki ne, abinda kawai take tunawa kwana uku kenan dataje gidan yawon arba'in, irin hirar da sukayi da maganganun daya ringa gaya mata se da akace ya rasu ta gane wasiyyace yake mata. Ya ringa jaddada mata cewar tayi haquri da rayuwa a duk yanda ta zo mata a sannan yake ce mata "Kinga ko yanzu na mutu zan kwanta lafiya saboda nasan cewar babu wata fitina da tayi saura a cikin ahalina Alhamdulillahi ko ba yanda aka so ba amma kowannen ku ya samu rayuwa me kyau daidai da yanda Allah ya nufa ze samu. Kinga Kabir din nan idan kika yi haquri kika jure wata rana zakiyi farin ciki da auransa koda yake ma gashi har kin fara tunda yau mun zauna kusan minti nawa baki ce Kabir yayi ko Kabir yace ba" "Kawai haquri nakeyi Abba amma ko yanzu da zamu fito seda muka haura" ta fada tana yar dariya shima yayi dariyar yace mata "To kici gaba da haqurin kinji ki riqe auranki karki bari shaidan ya sake samun damar da zeyi rawa cikin al'amuranki kici gaba da Addu'a ita ce babban makami in sha Allahu komai ze daidaitar miki wata rana ko cewa akayi yayi miki fada ma bazeyi ba". Suka ringa hira yana tuno mata da abubuwan baya, harda hotunanta na yarinta ya debo mata ya bata da yake ta ajiye dasu Mama na tayi masa tsiya wai soyayyar ce ta motsa kenan da yar gaban goshi yace mata Eh se Bayan Sallar Isha Kabir ya dauketa bayan Abba ya sake hadasu yayi musu nasiha tare suka tafi gida ashe ganin qarshe tayi masa. Haka rayuwa taci gaba da garawa rasuwar Abba tasa suka qara hada kansu dukda daman a hade suke amma suka qara dunqulewa ya zamana komai zasuyi se sun shawarci juna ba duk abinda ya shige mata duhu su zata nema su warware mata, har yanzun kuma Kabir be barta aiki ba seta qara qarfafa kasuwancinta na turaren wuta daga baya ma da kansa yace ta ringa kaiwa Kasuwa ana zuba mata a shagunansa se gashi kuwa sun karbu kasuwa ta qara bude mata kuna babu mugunta ze bata kudinta daidai idan an siyar ta sake hada wasu ta kai shiyasa rashin sake mata hannu da wani tsantseninsa baya damunta tunda tana samun na kanta ba kuma ta da wata hidima akanta dan tun Sabir bata sake haihuwa ba su Mu'ayyda kuwa sedai tayi musu abu kawai a matsayinta na mahifiyarsu badan suna da buqata ba, tsakaninta da Ahalin Khalil kuwa abin se sambarka. Yaran su na zuwar mata dukda basa kwana sukanzo su wuni tareda sauran qannensu wani lokacin Humaira da kanta take kai su wani lokacin Driver ita dai batada qarfin guiwar da zata iya sake taka qafarta a cikin gidansu. Bata sakeyin qawa ba a yanzu idan ka cire Rumasa'u ita kadai ce qawarta se Hadiza. Ta samu labarin Safina wai ta tafi Libiya neman kudi bayan da itama auranta ya mutu watanni kadan bayan na Umaimahn kusan shekararta biyar acan se gata an dawo da ita babu yanda take ciwo an rasa kalarsa suka hadu da Mshaifiyarta da itama take jinya duk an rasa kan abinda yake damunsu ita dai data ji labarin tayi mata addu'ar samun sauqi a gurin ubangiji dan bata fatan ko a lahira Allah ya sake hada fuskokinsu. QARSHE